16/11/2021, 17:28 - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 16/11/2021, 17:31 - 🀐🀐🀐: SARKA FADI KA RIKICE ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI. GODIYA YA TABBATA GA ALLAH MAI KOMAI MAI KOWA DAYA BAMU IKON GANIN WANAN LOKACIN MAI DARAJA DA ALFARMA GA MUMINI WANDA YASAN KANSHI DA IMANI DA ALLAH DA ANNABIN RAHAMA S A W. ZAI RIKE ABINDA MUKA KARU DASHI A CIKIN WANAN WATAN NA RAMADAN MAI DARAJA DA DAUKAKA GA MUSULMI INA MIKA TUNINA GUN YAN UWA MUSULMAI DA MU RIKE IMANI DA TUBANB DA MUKA ROKO GUN ALLAH ALOKACIN IBADUN NA WATAN RAMADAN DA FATAN TSORON ALLAH DA KOYI DA SUNNA ZAI TABBATA A ZUKATAN MU HAR ABADA UBANGIJI KABA MU IKON RIKE IMANI A ZUKATAN DAYI MAKA BAUTA TSARKAKKE A RAYUWAN MU ALLAH KA BAMU CIKAWA DA IMANI. YAN UWA ALLAH YASA IBADIN MU KARBABBE NE A GARE KA AMIN YA ALLLAHU. Mama Maimuna wace akafi sani yanzu da suna mamu don canza mata suna da yaran ta sukayi daga maimuna zuwa mamu. Tana duke tana sharan dakin ta don al,adanta ne tunda safe zata gyara daki da zaran ta gama ibadan ta na safe kafin tayi komai zata gyaro daki har zuwa wajen part din ta. Duk da masu aiki dake gida bata amince da gyaran su ba kasancewan ta mai kishiyoyin da ba a zaman lafiya a gidan don kishi irin na mata da muke rikewa kamar ba gobe a rayuwan mu. Sai dai duk aikin nan da take hankalin ta yana gun yar ta dake cikin wani hali a can garin da yanzun zaman shi ya zama mata tari a rayuwanta. Kasancewa auren ta na farko mijin ya rasu ya barta da yarta a lokacin yar shekara goma a duniya wanan mutuwan ne ya kawo sanadin rabuwan hjy maimuna da yarta tillo da suke so a rayuwan su ita da marigayin mijin nata. Wanda hakan yayi sanadiyar kara auren ta a yanzun wanda sanadin mutuwan ya jawo mata auren gidan da ta guda tun farko a rayuwan ta. Sallaman hadiye ne ya katse mata tunane da aikin da takeyi a yanzu, hadiye ita ma kamar yar uwa take a gun maimuna wace itama auren ta ya mutu tana zaune a gidan dan uwan ta a yanzu tare da yaran ta biyu yan mata. Hadiye ta karaso cikin dakin tana murmushi tare da fadin kai sarkin tsabta gari ya waye ke nan kin shiga hada hadan gyaran guri duk da ba wani dattin a zo a gani a shiyan naki. Wanan tsabtan naki yake saka a kullun hankalin yayana yana gare ki don tsaban tsabta da iya kwaliyan dake boye maki shekarun ki a kullun kina komawa kamar wata yarinya can. Murmushi hjy maimuna tayi a lokacin da take aje tsimyan hannun ta tare da zama zaman lazy chair din dake gefen ta a dakin. Kai Anty hadiye harda ke gurin wanan sherin kuma da ake min a gidan nan ko gaisuwa babu zaki tare da zolaya tunda farar safiyan nan haka ? To ina kwana ya dare ya kuma yarana suka kwana tana tambayan hadiyen don kawar da wanan maganan a lokacin. Lafiya kalau muka tashi kin sai dai kin san Allah dama nace wa umma yanzun haka kin tashi kina nan kina wanan aikin naki na gyare gyare tun da safen nan. Kin san fitina irin na gwagwan ki tun sallamay sallah take fadin wai inzo in dubaki tunda yau ba a turaka kika kwana ba sai kizo ki shafa mata maganin ta. Murmushi hjy maimuna ta sake a fuskanta tare da fadin ai da kun kirani a waya don tun dazun nake falke ai kin san ban iya komawa barci idan na tashi sai kuma wani daren idan Allah ya kai mu. Tare suka fito zuwa sasshen Amma tshowar gidan wace gwagoce gun hjy maimuna din kuma mahaufiyar mai gidan nasu ke nan. Kallon saura part din dake rufe Hadiye tayi tare da fadin su wa yan nan basu ma san Allah yai dare gari ya waye ba sai ta hantse masu zasu tashi daga su har yaran nasu ba wanda ke tuna Allah. Da sauri hjy tace kai tun da safen nan zaki daukarwa kanki nauyi da bai shafe ki ba a cikin su ai babu yaro a yanzu ko ? Basu da abin yi may zai fitar dasu da wanan sanyin hakan waje , hadiyen tace rashin sanin ciwon kai dai . Daga hakan ba wanda ya kara tofa wani zance kuma a cikin su don inda sabo sun saba da galin hjy don bata yarda ai maganan kishiryata da ita ko kadan da wuya kaji bakin ta akan abokan zaman ta. Duk da su a nasu bangaren da zancen ta suke kwana suke tashi a gidan sun kawo karar tsanan duniya sun dora mata akan auren dan uwan nata da tayi. Wanda ita in har a so ranta ne ba zatayi shi ba sai dai fin karfin ta da iyayye sukayine aka yanke mata wanan hukuncin ba auren shi din. Har yanzu Allah ya azurta su da yara uku mace daya da tagwaye maza biyu data yaye duk hakan bai sa sun daina kishin ta ba. Farkon da ta haifi mace dashi tasha gori da zunde a guri kishiiyoyin nata wai an kawo wace zata cika masu gida da diya mata. Daga baya kuma da Allah ya azurta ta da diya maza biyu lokaci daya sai kishin su ya tsanan ta a kanta wai zata cika masu gida da diyan baya don su sun gama haihuwan su. Wanan surutan kamar bata san sunayi ba don bata kula zancen su zaman ibadan ta take da mijin ta hankali kwance bata shiga tabgan kowa a gidan sai abinda ya shafe ta. Basu da suke kishiyoyin ta ba abin ya tsaya har yaran gidan sun kwashi mugun akidan iyayyen nasu suna gwada mata ita ba uwa bace a gare su . Gwagon ma da suke kiranta dashi yayin zawarcinta a gidan yanzu sun soke sun koma kiran ta da hajiya mamu ko mamu kamar yarda yarta Fatima ke kiranta da tazo masu hutun sati biyu. Wanda a lokacin wanan hutun daga hajiyan har yar tata sunga tsangwama na wullakanci a gurin mutanen gidan sai agun mai gidan take samun sauki a haka dai tayi hutun ta ta koma gurin kakanta dake rikon ta can Azare. Tun wanan karon bata sake dawowa kano hutu wurin mahaifiyar tata ba sai dai dan abinda ta samu ta aika mata dashi can. To gashi yanzu kakan nata dake rikon ta ba lafiya zaman ta ya koma gidan babban danta dake misau da zama wanda tarbiyan gidan bai kwantawa hajiyan a rai ba sam. Da wanan tunanen take kwana take wuni a ranta tun da labarin hakan yazo mata hankalinta yaki kwanciya da zaman yar tata a can don kada a lalata mata yarinyar. Amma ce zaune a inda ta gabarta da sallah safe ta mike kafuwan dake mata ciwo tana dan tabasu a hankali don taunar da kafan ke mata suka shigo suka samay ta a hakan. Sallaman hjy maimu yasa Amma dago kai ta kalli kofa shigowa sashen nata tare da fadin yar albarka yanzu nake zancen ki a raina wallahi. Na dauka ai wanan maigardaman kamar mutanen farko bata je kiran ki ba in dogara in samay ki da kaina. Hjy tana murmushi tace haba gwago hadiyen ce kamar mutanen farko aiko hadiye bata da gardama ko mussu ta tafi mun dai tsaya gaisawa ne da ita. Yo na sani tunda ciwon ba a jikin ta yake ba suna gani kamar wasa ne kece kadai a gidan nan kike tausaya min kan kafan nan nawa. Shiyasa ban yarda kowa ya taba min kafan idan bake ba don har da gayya suke min tausa kinga jiya da kikai min da dare da maganin nan da kika dafa min na samu barci sosai. Kasa hajiya maimu takai ta fara gaida gwagon nata tare da tambayan lafiyan kafan nata tana kokarin kai hannun ta saman kafan da tsohuwar ta mike tare da fadin . Gwago sai nake ganin kamar hauwan da kafan yayi ne yake sauka a hankali , sai da ta sake ajiyan zuciya tace nima hakan nake gani yar nan. Don yau da kaina na je ban daki ba tare da na rike komai ba kin ga ke nan sauki na samuwa gare ni ai. Allah yasa saukin yafi haka gwago hjy tace tana zama a kasan tare da mayar da hankalin ta kan kafan tsohuwar tana bi da kallo a hankali. Hadiye ce tace tunda ga maimu tazo barin tafi in watsa ruwa in dawo tana fadin haka ta fice dakin ta barsu su biyu. Addu,a take ma kafar kamar yadda ta sabayi duk safe hakama da dare kafin su kwanta take bin kafar tsohuwar da addu,a wanda hakan ke ma tsohuwar dadi sosai don sanin addini irin na yar dan uwan nata tilo da ke a hannun ta tun bayan rabuwa da mahaifiyar da mahaifinta yayi. A wana lokaci ne ya dauko ta ya danka hanun yar uwanshi wace yake ganin zata rike mashi ita amana wanda har gimanta zuwa yanzu take a karkashin gwagon nata. Wanda gwagon nata take ji da ita a matsayinta na yar dan uwanta a firin ta tun farko bata so auren ta da mijin ta na farko ba taso cikin yaranta maza uku da take dasu ta sai hakan bai faru ba don fitowan wani can dake son yar tun bata karasa mallakan hankalinta ba . Dole ba don taso ba ta yarda da auren ta a wani ashe zaman ba nai dorewa bane Allah yayi ikon shi a kansu. Suma a can azare sun so rike maimuna kada ta fita gidan don kyawawan halin ta sai dai hakan bai samu ba don gwagon nata da ta sa yar nata a gaba tazo da ita kano ta karasa rakanan ta a gabanta don hankalin ta yafi kwanciya. Bayan gama wankan hjy maimuna ne taje karo ilimi a makarantan FCE don ta kawar da kadaicin dake damun ta inda wanan lokacin ne gwagon nata ta fitar da kudirin ta nason hada yar tata da wani daga cikin diyan ta. Inda karamin nasu ya nuna shi matar shi ta ishe shi tun a wurin sai shi Alhaji sani ne ya nuna sha,awan hakan a kanta ya kawar wa yan uwan nasa da gardama ya nuna shi zai aure ta tun farko yaso hakan Allah ne bainufa ba. Amma taji dadi wanan zancen sosai don abinda takewa yar tata kwadayin samu ta samu do yafi sauran kwaciy hankali da samu sosai. Tasan wahalan yar tata ya yanke do haka zata kwantarwa yar tata da hankali don su zauna lafiya duk da tasan akwai badakala a tsakanin zama da abokan zaman don gidan nasa ba kwanciyan hankali kowa jin kanta takeyi. Wanan ne ma yasa yake so ya kara aure sai ga wanan zancen yazo mai a saukake ya yayi saurin yin na,am da zancen mahaifiyar su ya karbi auren yar uwar ta shi don maimuna mace ce da kowani namiji zaiso zama da ita. Duk da yasan akwai aiki a gidan shi don rashin hadin kan matan shi da babu shi a lokacin bai hana shi kwadayin saka yar uwan nasa cikin iyalin nasa ba duk da yasan akwai matsala a yin hakan. Daga hjy maimuna har Alhaji Sani sun fuskanci matsaloli da dama a wurin iyalin shi farkon auren su sai da ya jajirce masu suka samu lafiya ta hanyan tura kowace gidan su ta kwana biyu a can aka zauna lafiya. Wanan zuwan gidan da sukayi yasa kowace ta shiga hankalinta don sun san komai zai iya faruwa idan sun matsa fitina akan kishin yar uwan tasa. Ba shi da hajiya maimuna suka fuskanci wanan matsalan ba har Amma da take tsohuwar gidan ta fuskanci matsaloli da dama a wurin sarakkan nata wanda dama tasan da hakan. Ada can baya Amma a gidan ta wanda mijin ta ya bar mata take zaune sai daga baya da jikin tsufa ya fara tsanan ta mata Alhaji Sani ya dawo da ita a cikin iyalin shi. Farkon dawowan ta gidan sun nuna rashin amincewan haka don a ganin su Amma tana nuna masu wariyan akan yar tata . Wanda sune suka ja hakan don haketan da sukayi a cewan su itace ummul,abasin kulla auren mijin su da yar uwan tashi. Inda ita kuma hajiya maimuna ke nuna mata kulawan zumunci da nuna halin tarbiya a gareta wanda hakan yana kara tunzura zukantan yan uwan zaman nata. Don yadda take matukar kulawa da tsohuwan yana ma mijin nasu dadi sosai har bai iya boye hakan ko a gaban kowa wanda hakan ya kara ma hjy maimunan daraja a idon kowa. Amma dake kallon ta na dan lokaci ta nisa tare da fadin wai may kike tunane haka ne yar nan tun dazun nake magana dake kinyi nisa ga tunane. Kkari kakaro murmushi hjy tayi a fuskanta tana gyara zaman ta tare da fadi babu komai gwago tana so kawar da tambayan da tsohuwar tai mata. A, a kinga yar nan tun jiya nake ganin ki a wani hali kina kokarin boye min babu komai idan baki fada min abinda ke damun ki ba wazaki fadawa. In dai halin abokan zaman nan naki ne ai yaci ace yanzu kin saba da halin su dai ko ko kuma shi sanin ne yake maki wanin abin ban sani ba ? Saurin girgiza kai hjy tayi tare da fadin a, a gwago halin su ai inda sabo yanzu na saba da shi a gidan nan shi kuma yaya tsakanin mu dashi sai godiya da sam barka don bai rage mu da komai na rayuwaba a gidan nan. Cikin jin dadi Amma tace to ai shi na gani yo Allah na tuba kishiya idan ba taga ka fadi ka mutu ba ai kiyayya ba zai kare ba a tsakanin ku. Gama ke da suke ganin ki shigo daga baya ciki su kin na kokarin fin su da komai a gidan nan ai dole su sakaki a gaba haka. Gwago ba komai wallahi dama zancen yarinyar nan dai ne ya tsaya min a raina hankalina yaki kwanciya da zaman ta a gidan yaya da sukeyi a misau yanzu. Don babu tarbiya sam a gidan nan ko wani yaro gaban kan shi yake babu mai kwaba mashi ki ga dole hankalina ya tashi don yanzun ne lokacin da ya dace ta samu tarbiyan kwarai a rayuwan ta. Zancen dai A ruwa ne ke ban kikaki sake ranki dashi yar nan ina zaune take da kakanta a gidan kina ganin zata saka mata ido tayi halin yaran gidan ke nan. Gwago ba zaku gane abinda nake nufi bane yarsu ce ai komai zasuyi mata daidai ne a gurin su to amma ni abinda zaije ya dawo nakewa gudu ba wani abu ba can. Haba yar nan ana baki kina roko addua ya dace mu bita dashi a duk inda take mutuwa ce mai yake kauna ta raba ku da ita. Da mahaifinta yana raye ai da duk wanan bai taso ba yanzu to rabo yana kashewa yana rayawa rabon yaran nan ne ya kashe mata nata uban. Sallaman Alh sani da ya shigo dakin gaida mahaifiyar shi da kwana ya samay su a hakan kallo daya yai masu ya gane suna wani magana ne mai muhinmanci a tsakanin su. Sai da ya zauna ya fara gaida mahaifitar tasa tare da tambayan lafiyan jikin ta yana mai mayar da hankakin shi a kafanta dake mike. Muryan hjy maimu ne ke gaida dashi da kwana inda ya dago yana amsa mata a cikin kulawa tare da tambayan lafiyan yaran shi. Ta amsa da Alhamdullahi lafiya muka kwana suna barci kodana fito yace dama ai ke ke nan kullun kiwa mutane wayau ki kwashe ladan farko a wurin hajiya. Murmusawa tayi don jin abinda ya fada mata din kafin tai magana Amma ta karbe da fadin yar albarka tafiku kaunane shiyasa. A cikin raha da jin dadi yace to yau dai gaskiya tayi halin ta tunda hajiya ta fadi gaskiya dama mun sani kin karbe muna ita ai. Suka sa dariya ga baki dayab su a dakin inda yace da alama dai wani magana mai muhinmanci kuke tunda safen na haka dai ? Baki Amma ta tabe tare da fadi ba wani magana bane sai zancen yar nan dai A ruwa da taki kwantar da hankalin ta akan shi tu lokacin da taji suna Misau ita da kakarta taki kwantar da hankalin ta kan zama su can din. Sai da ya mayar da kallon shi gun hjy a cikin kulawa yace da ita, Why maimu, ina gun iyayye ta take a can din may zai sa ki tayar da hankali ki kuma ina mun gama wanan maganan dake tun ranan ? Kanta dake kasa ta dago tana kokarin mayar da hawayen dake barazanan fitowa daga idanuwan ta tana fadin ba hakana bane yaya. Kwata kwata hankaliba bai kwanta da zaman yarinyar a gidan bane amma ni ba naki bane da zaman nata a gurin su ai su din iyayyen tane na jini. To kin san da hakan may zai tayar maki da hankali kuma yanzun kan wanan maganan sai dai idan kina boye muna wani abinda bamu sani bane a can. Da sauri hjy maimu tace cikin girgiza kanta a, a yaya wallahi ko daya don kawai tarbiyan da yarinyar zata taso a cikin sane nake jawa nan gaba. Dan murmushi ya sauke a fuskan shi irin ta manyan da suka gama sanin duniya tare da fadin yanzun dai na fahinci yar ki hajiya. Ta fi bukatan rikon yarta ya dawo hannun ta ke nan hakan zaifi kwantar mata da hankali nake gani. A sanyaye ta amsa da fadin hakan nake nufi sai dai kuma ina tunanen inda zata zauna isan na dauko tane don nasan ba zasu hani ita ba idan har na bukaci hakan din, Wanan wani irin magana ne kikeyi ke a ina kike zaune yanzu koda baki gidan nan ai Fatima mai zama a gidana ne balle gaki a gidan baki daya. Amma ta karbe da fadin yar nan tana da gaskiyar ta ubana hutu kawai yarinyar nan tazo ba a kwshe lafiya da matan ka ba ina ga tazo da zama baki daya a gidan yanzu ? Haba hajiya yaya kuke wanan magana haka ne kamar ba gidana ba yata ce fa ta cikina Fatima ko ban hada alaka ta jini da uwarta ba ai na hada na aurataya da uwar ta yanzun ko ? Kafi wani yai magana a dakin sallama hajiya Jumai uwar gidan Alh sani ne ta shigo dakin gaida Amma da kwana. Wanda hakan doka ne daga maigidan da ya kafa wa kowa a gidan babba da yaro duk safe dole kowa yazo dakin mahaifiyar tashi ya gaida ita da kwana kamar yadda ya tsara masu a gidan. Amsa mata sallaman sukayi lokaci guda inda ta karaso tana watsawa mijin nata da hjy maimu data samu suna wani maganan wanda bata san ko na may ye ba a dakin. Ciki kishi daya motsa mata irin na mata ta gaida mahaifiyar tashi da kwana babu tambayan komai ta juya zata bar dakin sai Amma ce ke tambayanta kwanan yaran ta don ta gama fahintar halin da ta shiga lokacin. A dakile ta amsa da suna lafiya har ta juya hjy maimu ta fara gaida ita da fadin yaya ina kwana kamar ba zata amsa ba ta dai amsa a cikin saurewa da lafiya kawai ta juya ta fita. Kai Alh sani ya girgiza bayan fitan ta tare da mikewa do barin dakin yana fadin ni zan fita hajiya ina mu kare wanan maganan ke nan ko ? Kallon hjy maimu Amma tayi tare da fadin ai ga tanan idan ta gamsu da maganan ka sai a saka lokacin da za a dauko yarinyar ko ? Sai lokacin ta dan murmusa tun fara maganan yarinyar da sukayi tare da fadin a,a magana yana hannu uban yar dai gwago ni na isa in saka rana da kai inyi rashin kunya kuma ? Ko ya manta a gaban mahaifiyar shi yake ya dan kalle ta cikin kulawa tare da fadi see you kamar ba ita bace ta burkicewa mutane yanzu kan yar tata. Ranshin kunya ai kin riga da kin gama ko tunda kin nuna muna kin fimu son yar har hakan yana dariya ya fice daga dakin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 17:31 - 🀐🀐🀐: πŸͺ’SARKA FADI KI RIKICEπŸͺ’ ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU A KULLUN INA GODEWA UBANGIJI ALLAH SUBBAHANAHU WA TA, ALLAH DA YA BAN DAMAN FADAKAR DA DUKU TA HANYAN RUBUTUNA . DANI DAKU, DUKA UBANGIJI ALLAH YA SHIRYA MU YASA MUFI KATFIN ZUKATAN MU. LITTAFINA, NA KUDINE MAI SO ZATA IYA TURO DARI UKU TA ACCOUNT DINA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL DON KIRA ZAKI NEMAY NI A WANAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257 DON ALLAH KI DAURE KI BIYA KI FITA SHIGA HAKKIN WANI KI TUNA DA NAUYIN HAKKI WANI A GARE KI YAR UWA KULLA SABODA ALLAH. 2️⃣ Tafiya take kamar zata tashi sama sai maganan zuciya take ita kadai wanda ba wani abu bane sai zafin kishin dake cinta a lokacin. Ba komai take rayawa ba azuciyar ta sai yadda mu,amulan kishiyan ta da mijin ta kullun yake karawa karuwa a zukatan su yanzu ma ganin da tai masu a daki Amma. Yasa zuciyar ta zargin su akan suna fakewa a dakin ne suna ha,intar su ta hanyar tsohuwar gidan wace take gani da sanin ta ake masu komai na cin fuska a gidan. A,a giwan bukkan daji kedawa da safen nan kuma ke da ya kamata ace kin tashi da irin annashuwa din nan sai gaki kuma a haka. Da gani dai wani ya tabaki da safen nan wanda bai san da ba,a taba giwan gida a zauna lafiya ba. Hajiya maryam ce ke wana maganan mata tabiyu a gida;take magana cikin iri;zolaya da takewa uwar gidan nasu a kullun tana kara izata don ta tunzurata a gidan. Duk da tasan zolayan ta take bai hana ta tsaya da ita ba cikin dan ja tsuki tana fadin barni da wanan zolayan naki na kullun. Wanan yar rainin wayau ne mana da Alhaji sai su fake a dakin wanan tsohuwar suna zuba soyayya sun mayar damu wasu bi nan a gidan nan wanda basu san komai ba damu. Dan dariya hjy maryam ta sake mai sauti tare da fadin hjy kina ban dariya ke sai yanzun kika gane hakan wai ? Kamar ya sai yanzu na dauka abin nasu mai karewa ne sai gani nake abu sai gaba kawai yake a gare su. Wallahi ya zama dole in takawa wanan makiran yarinuyar burki a gidan nan don ba zan iya lamuntan wanan cin fuskan da suke muna ba. Wai ita shu,uma tu da safe zata dauki wanka ta shige wirin wanan tsohuwar da sunan gaida ita ta yadda tasan maigidan da ya shigo da ita zai fara tozali. Wallahi hjy maganan ki wani zubin sai ya ba mutum dariya makircine fa irin namu na mata ke sa tana zuwa sashen tsohuwar don ta kara kafa gawunatin ta a gurin Alhaji da sauran yan uwanshi. Amma ai hana wanan abu mai sauki ne a wurin mu nuna masu kawai zamuyi muma mun iya itama dake nata a fili ne zamu rasa ganeta . Fitowan Ahj sani daga sashen Amma da alama sauri yake a lokacin sai dai ganin su yasa shi dan rage saurin da yake yi din. A,a yaya na ganku haka kuma lafiya dai ko ya tambaya cikin nuna kulawan shi gare su baki dayan su. Hjy jummai dake cika tana batsewa har lokacin ta aika mai da wani irin kallo na tuhuma da sauri hjy maryam ta tare da fadin . Magana dai muke akan jikin hjy wai don jiya ta kwanta tana mitan kafan yana damun ta sosai cikin jin dadi da nuna kulawa ga abinda ta fada yace. Ai ta samu sauki sosai da safen nan don yanzun ma zaune na samayta tana hutawa tare da yar ta au ashe yarta daya ne a gidan nan gara dai daka fada da bakin ka inji hjy jummai da sai lokacin ta saka masu baki a zancen su. To hjy ko na fada ko ban fada ai ko diyan cikin hajiya musan maimuna yarta ce ko fadin hakan kuma yanzu laifi ne ? Ya fadi yana mai tsure ta da idanuwan shi ta wani juya tare da jan tsuki tana kokarin barin wurin. Kai mata dai baku ranuwa da zancen kishi yanzun kuma may ye a cikin wanan maganan na fushi. Alh baka fahinci maman salma bane irin yadda kake nuna maimuna ita kadai ce ya gun hjy shine yake bakanta mata rai. Yanzun dai ba wanan ba naga kamar fita zakayi ko da sauri yace eh fita nake son yi dom ana jirana a kasuwa yanzun haka kaya sun iso gare mu Saida ta dan rausaya kafin tace da zancen tafiyana gurin maganin nan ne naso in tuna ma don gobe ne tafiyan nawa. Da sauri ya juya tare da fadin aiko nima ina da abinda zanyi a bauchi kin ga ke nan sai mu shirya tafiyan tare don maimuna zata tafi don yarta dake can. Wata maimuna kuma kaga Alh kada kama kawo wanan zancen don hanyar jirgi daban ta mota daban ina zan kwashi kishi zuwa tsabagata ta lafiya kuma ? Don Allah kadama ka hada muna tafiyan mu don ba zani ba sai dai a fasa a fasa fa kika ce ke nan lafiyan taki bata damay ki ba. Kaga Alh indai har da maimina zamuyi wanan tafiyan saidai a fasa haka kawai kallon mamaki Alh ya bita dashi yana mamakin irin wanan kishin nasu bai iya furta komai ba yasa kai ya fita don idan ya tsaya zata bata mai lokaci. Shikuma ba zai so hakan ba don abindake gaban shi a lokacin kishin su a kullu kan maimuna ba mai karewa bane. Ga wani kokarin hadin kai da sukewa junan su yanzu tsakanin ta da hjy jummai wanda yasa ba na Allah bane. Inda ya barta tsaye da mamakin maganan shi tabi shi da kallon takaici a ranta kallon shiyan hjy tayi kamar ta fasa shiga don maimunan dake ciki sai kuma ta tuna da yin hakan wani laifi ne a gurin ta kuma. Haka dai ta daure ta fada sasshen tsohuwan abinda ta guda shine ta sama do hjy ce zaune tana bare goron dags cikin ledan data dauko wanda ke cike da fararen goro manya kursa kursa dasu. Sai hjy maimuna dake zaune a gefen ta tana dan motsa mata kunun da ake dama mata tun da safe ta karya dashi wanan al,adan tsohuwar ne a hakan. Ga fuskunan su a washe alaman nuna farin ciki a gare su ke na take zuciyar ta ta raya mata wani zargi akan mijin nasu da ya fice daga sasshen yanzu. Wanda shi ke halaka rayuwan mata da dama watau zargi zargin ma harda mahaifiyar miji za a hada a cuta mai idan ba rashin tunanen mu na mata ba. Abinda zuciyar ta, ta nasa mata shine wasu kudi suka bukata a wurin alhajin don maimuna din ta kaiwa yarta shi kuma ya yarde masu zuciya ke nan uwar nashe nashe. Kamar yadda hjy jummai ta gaida Amma ita wanan ta daure takai zaune a dakin cikin nuna kulawanta take tambayan lafiyan hjyn. Maimu da tun shigowan ta dakin kanta yake duke ta dago tana gaida ita da kwana kamar bata ji ta ba haka ta share maimu din taci gaba da tambayan hjyn halin da take ciki ? Tana dan bata fuska take fadin kafa da sauki sosai don yana samun kulawan daya dace don yar nan na tsaye a kaina dare da rana wuri ganin na samu lafiya. Hjy ke nan aiki godewa Allah don shinr mai bada lafiya ba wani ba , lafin takai ayya hjyn ta karbe da fadin godiya kan kullun munawa Allah shi yar nan amma yabon gwani ya zama dole ai. Yau da babu yar nan a kusa dani ai da ban san yadda zan karata ba mikewa hjy maryam tayi tana fadin. Kai hjy maganan gizo dai bata wuce na koki ai ko ba ki fada ba munsan zaman ta a kusa dake yana da manufa sosai a girin ku ni zan tafi Allah ya sauwaka. Har takai kofa ta ce a dai rage fakewa ga sabara a harbi barewa don a idon mujiya ake komai. Allah ya sauwaka maimuna dake zaune ta fadi cikin rashin kulawa da maganan kishiryar tata don idan da sabo ai ta saba don basu haduwa basu sake mata irin wanan maganan ba na kishi wanda ranta yakan baci sai dai bata yarda ta nuna masu gazawan ta a kullun. Bata dade a part din ba ta mike tana fadin gwago ni zan tafi don yaran nan nan san yanzu sun falka ban kusa dasu. Hakane inji Amma yanzun ko zaki iya ganin su a nan don ba karamin aikin uwata bane hakan ta fado muna da korafin kin fito kin barsu kamar wata wace za a kama. Yarinya haka bata da yarda da kowa a gidan nan sai kace bakuwa a gidan nan. Gwago yanan gidan ne yasa ta tashi da hakan don in ba nan gurin ki ba babu mai kulasa ni shine matsalan dake damuna a gidan nan . Ace kishi harda yara ake hadawa don rashin tunane an hana yara zumunta a tsakanin su saboda wani akidar banza can . Daga haka ta bar dakin tsohuwan data barta a zaune ta bita da kallon tausayi don tasan gaskiya yar tata ta fada yanayin gidan yana nuna kowa dan shi ya sani. Hakama yaran gidan kowa dan dakin su ya sani baisan wani ba duk wanan abin yasamo asaline daga gun hjy jummai dake zama da yaranta a daki tana tura masu mugun akida akan kowa na gidan makiyin su ne. Dan garama yanzu da akwai dan shirin yaran nasu sukan dan kula juna a tsakani su wanda ya zama dole dama don alaka ta jinin dake akwai. Sai dai diyan maimunanen basu yarda dasu ba a cikin su wanda hakan na bata ran uwar yaran shine abinda take tunane ga dauko yar tata tazo ta zauna a gidan tare dasu . Yaran dama ta haifa a kidan an kisu balle yarda ba a gidan ta haife ta ba duk da maigidan yana iya kokarin shi wurin kawar da wanan akidar a gidan. Yakan tara yaran nasa wani lokaci wuri daya yana nazarin halaiyar kowa a cikin su akan dan uwan shi. Inda ya kula dacewa suna ware yan kannen nasu tare da nuna masu cewa yaran daban suke a cikin su wanda yakan yi amfani da wanan daman wurin nuna masu yaran nasa kanana ma yan uwar su ne na jini. Ba laifi wasun su suna rage wanan akidar a cikin su suna dan kokarin kwatantawa akan yaran wanda wasu kuma hakan bai shiga zuciyar su ba don sun riga da sun samu huduban hakan daga gun iyayyen su tun farko. A ko wani gida akan samu tsageran yara a ko wani daki hakan ne yake faruwa a gidan Alh sanin don yaran hjy jummai da koda yaushe ita akidan tane zama da yaranta tana nuna masu rashin yarda da kowa daga bangaren yan uwan su. Abin ma bai tsaya a nan ba har yakai kowa suna mashi wanan kallon na maha,inci a gare na yarda basu da marmari a gun kowa da ya san su. Sai mutane ke masu kallon masu ji da kansu ko marasa marmari a gun jamma,a din sai ba mai son wani mu,amula dasu sosai yana da wuya su yi saurin amincewa mutum wanan ke nan. Rai bace hjy maryam ta karasa part din ta inda ta samu mai aiki na mata gyaran part din wayan ta dauka tayi waya da wata yar uwarta da zasuyi tafiya tare. Inda take sheda mata yadda sukayi da maigidan nasu akan tafiyan da zasuyi a washe gari da wani irin mamaki aminiyar tata ke fadin . A, a lallai wanan matar samun wurinta ya na son wuce wuri a gidan ku yanzun tafiyan neman maganin ki ma harda ita za,a tafi don son kure mutane ko may ? Barni da Alh wanan karon za,a jimu sosai idan yace har da ita zamuyi wanan tafiyan don ba zan kyale su ba. Sin dan dade suna tauna maganan inda yar uwar tata ba hakkuri take bata ba sai nausar da ita hanyar bata irin na matan da basu da fahinta. A bangaren hjy maimuna ta samu yaran ta na barci har lokacin kasancewa ba school a lokacin yaran suna hutu makaranta a lokacin . Bata barsu ba kokarin tayar da yaran tayi tana koya masu yin sallah a cikin lokaci duk da sun makara amma hakan take kokarin koya ma yaran sallah safe. Suna gama sallah tayi masu wanka inda ta shirya su suka fito falo don karyawa duk da gaba daya ake abin karyawa a gida kowa yakai kayan shi dana yaran shi a zuba mai abincin sa a ciki. Duk da tana kai nata kulan don karban rabonta amma hakan bashi ke sa suci wanan abincin ba don rashin yarda da masu aikin da batayi ba tun ranan da aka saka masu magani a cikin nasu abincin. Allah ya taimakesu basu ci ba ta gani tun wanan ranan bata kara yarda da wanan abincin na taro da ake kawo mata daga cikin gida. Har sai idan itace da girki ta shiga kitchen da kanta ta dafa kamar yadda takeyi a kullun idan tana da girki ita zata je kitchen ta girka abincin da kowa zaici a gidan tare da ya aikin gidan dake masu abinci su biyu . Da farko ta samu korafin yin hakan daga gun kishiyoyin nata sai dai ta fannin maigidan wanda hakan yai masa dadi yasa maganan tai shiru a gidan. Bata fadawa kowa zancen ganin maganin da tayi ba a cikin abincin su sai dai daukan matakin da tayi na rashin cin abincin daga ita har yaran nata da bata yarda ta rasa abinda zata basu a part din nata ko suje gun su hadiye ko Amma suci wanda ba surkule a cikin sa. Yau ma tea ta hada masu da safe suke karyawa dashi ita da yaran nata sallama taji daga kofan shigowa dakin ta karba. Lami ce mai aikin su ta shigo mata da abin karyawan su ta gaida ita da aiki duk da bata yarda da lami din do ta hannun daman uwargidan nasu ce tu farko a tare suke da ita. Gashi hjy jummai din ta hana bada daman kowa ya dauki mai mashi aiki duk da suna da halin yin hakan a gidan idan bukatan hakan ya taso masu. Saidai ido kowa ya saka duk da wani lokaci hjy maryam takan turza akan matsalan Lami mai aiki idan tayi mata ba daidai ba a gidan ko ta batawa yaran ta rai. Irin dai wanan matsalolin da ba, a rasa ba a gidan yawa irin nasu mai mace fiye da daya haka yake faruwa a kullun sai dai ita hjy maimunan takan shanye nata a ranta. Wanan yasa ko da yaushe take a takure ita da yaran nata basu da wani walwala sosai a gidan don yawan matsalolin da ake yawan samu a kullun. Hjy Jummai mace ce mai so mulki a gidan miji ta wanda ta rike damanta na uwargida bata yarda ta bari wata ta kwance mata wanan daman nata ba. Shine yakesa data ga wani abinda yake son shige mata gaba bata yarda dashi yanzun zata dauki mataki akanshi ta rufe wanan abin ya zamo tarihi. Yaranta shidda da Alh Sani maza uku mata uku shimkafa da wake inji hausawa inda take kokarin ganin rayuwan yaranta ya inganta tako wani hanya. Hjy jummai auren saurayi da budurwa sukayi da Alh sani aure na nagani ina so a tsakanin su don haka suna zaman su na jin dadi da kuma gadara da hakan akoda yaushe tana alfahari da uwargidancin ta a gidan. A wurin hjy jummai gani take tankar duk wata mace da Alh sani ya auro daga baya dole ne su bita subi umurnin ta a gidan. Hakama yayan da suke haihuwa take ganin gasunan daine a gidan yayan tane masu cikakken yanci a cikin gidan fiye da kowa. Wanan ra,ayin natane ya sa ba zaman lafiya a tsakaninta da hjy maryam da farko da take ganin ta shigo mata gidan mijin nata don ta hana mata jin dadin ta da mijin ta da yaranta da take ganin su kadaine keda mijin nata da farko. Sai ga hjy maryam da rana tsaka ta shigo rayuwan su duk da wayen kan hjy maryam din haka hjy jummai ta kasa ta tsare komai sukai ta samun matsala har hajiya maryam din ta haifi nata diyan kwara hudu a gidan mata biyu maza biyu itama a gidan. Sin sha faman kishi akan hakan inda hjy maryam din bata yarda da akidar uwargidan tasu ba ko kadan suna cikin wanan rikicin ne kwatsam sai ga zancen auren yar uwarshi yazo masu wanda basu taba zaton hakan zai taba faruwa dasu ba. Wanan mulkin da ikon nata taso nunawa lokacin da zancen auren yazo kunnen su ga maigidan nasu inda a cikin gadara ta nuna mai hakan ba mai yuyuwa bane a gare shi. Sun sha rikici sosai da Alh sani kan auren nasa da zai kara kuma wai yar uwarshi ta jini da ta san komai nasu na gidan zai dauko ya saka a cikin su. Bata tsaya gare shi ba har yan uwanshi sun sha gori a wurin hjy jummai a lokacin inda takance . Ni da Alh aure ne na saurayi da budurwa mukayi don haka ko gaba dayan ku za,a daura mashi mace dai a bayana take don ba wani abinda ban sani ba wanda ya shafi Alh har ku. Na aure shi tun bai kai hakan ba arzikina da nasa ne yazo daya har ake kwadayin jefo dangin shi a cikin mu tun yana da mashin har muka kai ga mota yanzun anga samu ake son kowa ya shigo yaci arziki ko ? Babu wata macen da zata shigo ta girgizani nida gidana don ana hangen samu a wurin shi yanzu. Sukan maida ita wace zafin kishi ke ci a lokacin don haka basu biyewa babatun ta a lokacin sai ma wasu tsageri kan bata amsa da sai dai maimuna ta shigo gidan Alh kun zauna tare. Muma aci arzikin nan da kike kurin kun samu tare dashi damu mu samu mai tarbon na arziki idan munzo gidan nan. Takan basu amsa da fadin ta shigo ai jummaice zata zo ta samay ni kujera nake daidai da duwawun ko wace mace. Wa yan nan kalaman nata duk suna komawa kunnen yan uwa wanda hakan yake matukar tayar da hankalin maimuna a lokacin . Sai dai ba yadda ta iya don don auren nan ba gudu ba jada baya a wurin ta don shine farin cikin gwagon nata marikiyar ta a lokacin. Da hjy jummai taga auren ba fashi sai anyi shi sai ta koma fadin a shigo mana ko wace ke gidan zaune dani may ta gane gun mijin . Arzikin dai ake kodayi ba za a gane komai ba duk wace tayi gigin shigowa rayuwata don hangen arzikin mijina zata zone zaman hakkuri dani a gidan nan . Iya gaskiyarta take furta kalaman ta da wasu suke dauka da izgili take yin shi ko shakiyanci don a fasa zancen auren da ake shirin yi din tsakanin shi da yar uwar tashi. Alh sani dai yakan yi murmushi idan tana haukanta na kishi don inda sabo ya saba da wanan tun akan auren martam da yayi a baya wanda hakan suka kwasa da ita. Shi Alh sani mutum ne da bai faye magana ba hakan yasa take samun dama sosai a wurin shi take abinda ta fa dama a gidan. Don kawai a zauna lafiya wanda ita take ganin so ne da fin karfi hakan don a kullun takawo ra,yin ta zai iya sakin nasa ya dauki nata a zauna lafiya. A bangaren hjy maryam taso tayar da hankalinta akan wanan auren sai da yan uwar ta suka lurar da ita kuskuren da take shirin tabkawa ta dawo cikin hankalin ta. Amma da makirci da zolaya saida hjy Jummai taja ra, ayinta suka hadewa maimuna kai da ta shigo gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:35 - 🀐🀐🀐: SARKA MAI, , , , , , , , , 3️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA GODIYA YA TABBATA GA ALLAH SARKIN KOMAI DA KOWA DA YA NUNA MUNA WANAN RANAN TA JUMMA,A UBANGIJI KA TAIMAKI MUSULUNCIN AKAN KAFIRCI KAYI MUNA DA YAN UWAN MU MUSULMI DAUKI A KO INIA MUSULMI YAKE A DUNIYAN NAN . JUMMA, AT MUBARAK YAN UWA UBANGIJI YA BAMU ALBARKAN DAKE CIKIN WANAN RANAN MAI ALBARKA AMIN. WANAN LITTAFIN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A NATSE YAR UWA BATARE DA SHIGA HAKKIN KOWA BA NAGODE, , , , , DOMIN SAMUN WANAN NOVEL ZAKI IYA KIRAN WANAN LAYIN 08036959257 KO KI TURA KATIN DARI UKU TA WANAN LAYIN 225428015 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL NA GODE, , , , Da sauri take tafiya don zuwa kai gulma wurin uwar gijiyan nata da ke dan mata ihisani kan orin wanan halin ko da yake sabone kawai don kowan su na mata abin arziki daga cikin su. Da sallama ta isa dakin hjy jummai wace ke zaune tana kwasan girkin abin karyawan safen da aka kawo mata wanda sai da aka yaye mata wurin abin miyan kafin a zubawa sauran busashe akai masu. Ganin yadda ta shigo yasa hjy Jummai sanin da magana a bakin ta ta shigo dakin nata a lokacin haka yasa ta mayar da hankalinta gurin lami din. Cikin irin yanayin munafukai lami ke magana hjy ashe abinci kike ci barin bari ki gama saina dawo in fada maki abinda ke nan. Haba yi magana ki mana Lami tunda kin zo ai ba zai hanani cin abincina hjy Jummai dake zaune take fadin hakan. Hjy dama ba wani abu bane sai zancen wanan amaryan taku ne yanzun naje nakai mata abincin safen ta na samu ta hada nata suna karyawa da yaranta. Hjy da kanta yake duke ta dago da sauri tana tambayan may kika samu ta dafa a can din, hjy ta tambaye ta da sauri ? Lami ta gyara zama tana fadin ruwan shayi ne mai kauri sai kwai suke ci a plate . Da sauri hjy tace Lami kardai ince kwan da aka ajewa Alh na amfanin shi ne ta diba ta dafa da yaranta ? Lami tace ai shine nazo na fada maki kar aga ya kare a tuhumay mu muda ke aiki ko yaushe a cikin kitchen din . Kwarai kuwa don kune a kitchen din ko yaushe dama nasan a rina wanan shiga kitchen din din da takeyi ba banza bane a gidan da akwai zanban da take shukawa. To yau ya kare don asirin ta ya tono a gidan nan gaskiya idan ankai mata abincin suke kin tabawa sai dai ta dawo muna dashi kitchen. Abincin da hjy Jummai bata karasa ci ba ke nan dama tana da takaicin hjy maimunan a ranta yanzun kuma an kara dada mata wani sai taji duk abincin ya fita ranta ga baki daya. Da kyat ta yaki zuciyar ta har maigidan ya dawo ansan wace ake don ba zai yuyu maimuna ta dinga nuna masu tsageranci hakaba a ckin gidan. Ita wacece da bazata ci wanda aka girka wa kowa ba sai tayi nasu ita da yaranta akoda yaushe lami tana ganin ta hada wanan ta mike zuwa aikin ta don tasan yau ko ba komai ta gyarawa uwar dagin nata rai da wanan maganan. A bangaren hjy jummai kuma bayan sun gama karyawa ne ta tasa yaranta gaba don suje su gaida kakar su Amma tare da daukan kulan data sakawa hadiye dan abinda ta soya din. Da sallama suka shiga dakin Amma inda ta samu hadiye a dakin suna hira da mahaifiyar ta da murna Amma ta tari yan jikokin nata inda hjy maimuna ke fadin. Ashema kina nan tana fadin haka ne lokacin da take mika mara kulan data riko masu din. Hadiye sai cewa tayi mai muka samu kuma a nan tana kaiwa zaune take fadin dan sauran kwanda yaya mustapha ya bamu ne ranan na gidan gonar shi na soya. Kin san yaran kin ga har yau basu iya cin wanan abincin safen da ake girkawa a gidan nan yau ai kinga basu zo shan kunun gwago ba. Cikin tabe baki Amma tace na rasa may ake da wanan uban kayan girkin da ake shigowa dashi gidan nan sai ga an shigo da kayan girki mai yawa. Amma karshe haka za a kawo abincin nan ko almajiri kaba almajiran nan na yanzu ba zasu karba ba. Hjy ke nan ana ko amfani dashi sosai don da yanzu zaki sashen yar mulkin gidan kiga abincin ta ita da yaranta sai kice ba guri daya aka girka da wanan din da ake kawo muna ba. Hadiye ce ke fadin wanan magana ta karasa da fadin ni yanzun haka ko budeshi yaran nan basuyi ba don ba zasu iyaci ba ma ko sun bude din. Nina rasa wanan akidar ace gida kamar wanan wai sai gaba daya za ai girkin da za a ci ranan dana shiga na samay ta tana ci nayi mata magana sai cewa tayi babban goro ai sai budin karfe dole itace za a fara zubawa don hakane na ga nata a hakan. Tsuki Amma taje tana fadin wanan yarinyar tana daukarwa kanta nauyi da yawa ina zata da wanan alhakin haka a kanta. Nina rasa hali irin na jummai a ce mutum baida abinyi a rayuwa sai kokarin danne hakkin wasu abin nan ana bayarwa ba ba a kawowa bane amma don kawai ta cutawa yan uwan zama ta kawo wanan akidar banzan haka. Hjy ni indai zata barmu mu zauna lafiya duk wani akidar ta baya damuna kamar rashin kwanciyar hankalin nan da babu a gidan nan a kullun. Hjy maimuna ce take wanan maganar cikin nuna damuwan ta da yanayin gidan nasu. Kasancewar bata da girki yasa takai har sha biyu da wani abu tare da hadiye suna hira kafin ta koma part din ta da yaranta. Wanda hakan ba karamin bata ran saura natan gidan yakeyi ba don a zaton su zaman zagin su akeyi gurin hadiye din. Basu san abin ba haka bane kokarin kulla alakan business suke a tsakanin su shine yawan zuwa part din juna da sukeyi. Bata fito ba tunda ta shige tana cikin sashe nata wanda haka ne komai a ciki duke da yaranta idan ba maigida ya dawo ya nemi yara a gurin shi ba sam bata yarda su fita daga sashen nasu. Don da farko tana bari har i yaran suki fita ta tillasata masu wai don su saba da yan uwan nasu take yarda su fita da farko. Sai daga baya ta gane fitan nasu cuta masu akeyi idan sun fita cikin tan uwan nasu don duk sun fisu girma a gidan da yawa kuma. Shine dalilin da bata yarda su fita ko ina hakan kuma yana ma yaran dadi sosai na rashin fita inda za,a duke su da zagi iri iri. Karfe biyar duk wani wanda ke gidan yasan lokacin dawowan maigidan gidane hakan ke sa kowa na gidan yake natsuwa. Matan gidan kuma kowa takan dauki kwalliya don burge mai gida sukan shiga daya bayan daya wani lokaci ida yana da magana zai tsayar dasu yayi masi shi a cikin jam,i. Idan ko ba wani magana sai a bar wace ke girki ita kadai tare da maigidan ta dauke mai sauran dawainiya kafin ya fita sallah mafariba. Irin bada abinci miko min yi min wancan sai idan yana da baki suka dan samu su sarara. Inda shi kuma yakan zauna da yara shi kanana suna hira kafin su fice masallaci dashi da yaran nasa. Yauma irin hakan ya kasance a wurin hjy maimuna din inda take saye cikin atamfar code, voi,re dinkin zanin da riga half gun sai yaran da ke saye da yar katin su uku ta tasa su a gaba. Ta makara zuwa gaida maigidan nasu a yadda ta saba zuwa idan ya dawo hakan ya samu dalili ne na tsayar da ita da yan biyun ta sukayi na yin kashi bayan ta shirya su kinsan abu ga mai kananan yara. Da sallama ta shigo fallon kallon yanauin su kawai tayi tasan da akwai matsala don haka tana gaida shi da ta juya zata bar fallon. Muryan mijin nasu taji yana fadin dakata maimu samu wuri ki zauna inda ya kalli yaran mm nata yace kuje ku jira maman ku ta dawo ko . Yaran suka juya don bin umurnin mahaifin nasu yayi da yar mulkin ke zaune a gefen shi tana harare hararen yaran da suka saba da irin kallon da take masu a gidan. Dan shiru ya biyo a falon sai can Alh ya kira sunan ta inda ta karba da fadin na,am yaya don haushi hjy jummai ta wani kawar da fuska tana mayde bakin ta. Maimuna wani magana nale jin yanzu wanda banji dadin jin shi daga gare ki in ma har haka kike so ai sai ki gabatar da zancen a gabana in san abinyi ko ? Hjy jummai bata so haka ba sai haushi ya kamata sosai na yadda yake mata magana a cikin tsigar lalashi itako a cikin sanyin murya tace wani abin akace nayi kuma tunda ba, a raina abin laifi a gidan nan. Alh baikai ga magana ba yar mulkin ta karbe da fadin kina nufin kake akai maki ko may wa kikafi a gidan nan da bazaki ci abincin da kowa yaci ba sai kin fake ga satan kayan gida kin shige daki kin dafa da yaran ki kuci. Salati hjy maimu ta saka tare da fadin yau kuma sherin yakai a laka min satan abinci a gidan nan ? Ji munafuka waisheri cikin tsawa da daga hannu Alh ya dakatar da ita da fadin ke Jummai banson irin haka don Allah ki bari muji dalilin ta na yin hakan saboda Allah. Falon ya danyi shiru kafin ya nisa yace hajiya babba da hakuri fa aka sanshi kila tana da wani hujjan yin hakan kamar yadda na fada da farko. Hjy ta sake fadi may ye kuwa hujjanta illar son nuna gadara da isa ita a dole fata matar gida a yanzu za ta iyayin komai a gaba gadi. Yace wai ba zaki shiru muji ta bakin ta bane ko may ko ke zaki daukarwa kanki mataki in kyale ku da ita. Ai idan ya kama sai mu dauka don batafi karfin kowa a gidan nan ba ke nan ita gata yar gida muko bare ke ba zakici abinda aka girka kowa yaci ba ke nan sai ki fito da naki fi, ilin. Don kina takama da hjy na cikin gidan da zance ya tashi abi bayan ki to ko hjy ba zata yarda da wanan halin da kika dauko yiba. Irin maganganun da take fadi dole suka saka mata ido har ta kai aya don bata jin taro a lokacin kishin ya motsa sosai kan dan abinda baikai ya kawo ba. Sai fadi take ai ba akanki na fara zama da kishiya ba a gidan nan balle kizo ki min aikin gaba gadi ke gaki yar gatan dangi . To ki sani nan din dai gidana do a ciki kika samay ni balle kice zaki zo ki kafa min wani iyayi can a gida . Wallahi tunda na gane abin naki tsiyane yanzu zamu saka kafa wando daya dake a gidan nan gobe ko ance ki raina ma wani hankali ba zaki sake ba. Abinci ne yadda na tsara ayi dole haka zakici dake da yara ki don ba fin mu kukayi ba a gidan don shi ko wan mu ke ci har yaran mu. A fusace hjy maimuna da ta gaji daji abinda hjy jummai ke fada mata kamar ita ta ajeta a gidan yayi yawa bata san lokacin da ta bude baki ta fara bata amsa ba. Ke hjy jummai zancen ya isa hakan koda nayi balle van san da nayi wani abu a gidan nan makamancin hakan ba don ni kinfi kowa sani kayan gidan nan basu taba tsone min ido ba ko kadan. Kuma ki sani idan kin bada doka a dafa muna abunda kike so ai ba zaki shiga dakin Alh ki bashi dokan ga yadda zaiyi dani a gado ba ko ? Yau wanan bakin halin naki na gadara da nuna isa yasa dan sauran mutuncin ki da nake gani a gidan nan ya zube wallahi. Shi yaya din kika raina da ita wanan ta nuna hjy maryam dake zaune tana kada kafa wai itama ta hasala da zancen ke nan. Dokan ki na banza tunda ba dokar Allah da annabi bane ra,ayine hakan idan mutum ya ga zai iya yabi do a zauna lafiya idan ba ka iyawa ba dole bane tunda takardana ba a hannun ki yake ba. A fusace hjy Jummai tace haka kika ce zan ko nuna maki wata abu nake a gidan nan don kina ji kina gani sai zaman gidan nan ya gagare ki zama da duk wani wanda ya daure maki gindi, a gidan nan. Ta Allah ba taki ba idan kin saba batar da mutane ni maimuna nafi karfin ki wallahi zaman gidan nan gare ni mutu ka raba tunda nariga da na shigo. Da dai ace ban shigo bane sai barazanan ki ya dan tsoratani sakariyan banza kawai wace bata amfani da ahekaruta uwargidancin naki na zalunci har kike gadara dashi. Ba hjy jummai ba har hjy maryam da Alh ranan sunyi mamakin hjy maimu din yadda ta tsaya tana fadin magana ga yadda kowa ya santa mace mai hakkuri da kawar da kai ga komai na gidan. Tashin muryan su ya dawo da hankalin mutanen gidan gare su cikin sauri Hadiye da Amma suke rige rigen zuwa inda suke a garden suke maganan. Tu daga nisa Amma ke tambayan abunda ke faruwa a tsakani shi da kyar aka samu sukai shiru Alh sani ya fara bayani abinda hjy jummai ta samay shi dashi daga dawowan shi. Salati hadiye ta saka tare da fadin hakika Allah yayi gaskiya da ya ce zato zunubi ne koda yazama gaskiya. Kwanan da muka samo gidan yaya mustapha da muka samu an debo a gonan shi shine ya dibarwa su yan biyu mai yawa muna zuwa gida ta raba ta aikawa kowa da nasa sauran da take dafawa yaran ne yau ta soya masu shine kuka gani kuke wanan magana. Hadiye dakin kyalesu ai har ina naga kwan gidan da zan diba bayan makuli store din yana gurin ta ko gishiri kake so sai da umurnin ta za a baka. Alh sani yace to ke kinji da kike ta wanan irin tayar da jijiyoyin wuyan akan abinda baikai ya kawo ba tun dazun na fada maki abi maganan nan sannu don a gane gaskiyar maganar kin kiya. Yanzu ga gaskiyar maganan ya fito may gari ya waya da hakan da kukayi shiyasa ake son bincike kafin yanke hukunci. Amma da dakyar ta kawo kanta ta samu wuri ta zauna tana fadin to ai yanzu shike nan gara da Allah yasa haka ya faru yau din nan. Abinda nake so dakai daga yau aiwa kowa cefanen ta a bata ita da yaranta mace ta dafa abinda ranta dana yaranta ke so suci. Wanan bakar akidar ba dai don baka dashi bane ake hakan don shiga hakkin wasu ne kawai wanan maganan kuma umurni na baka ba son jin ra,ayin ka nake nema ba kan magana ta. Gaba dayan su sunyi mamakin jin fyrucin tsohuwar da bata faye sa baki a cikin zancen da ke wakana a gidan dan nata ba don kawaici. Sai gashi yau da rana tsaka tana bada umurnin kawar da dokan da hjy jummai ta kafa take ganin ba mai iya ta da wanan dokan a gidan. Tsohuwar ta kawar akan dalilin fadan ta da yar ta kuma amaryam su sai take gani anyi hakane don dama a kuntata mata a gidan. Har taso tayiwa tsohuwar rashin kunya nan Alh sani ya falfalle ta a gaban kowa abinda take ganin gazawa ne hakan da yai mata din. Tun daga wanan ranan suka kulla da hjy maimu a gidan wanda zaman lafiya ya kara kawuwa a tsakanin su. Ta dauki kiyayyan duniya ta dora akan hjy maimuna da yaranta bata kaunar abinda ya shafesu ko kadan ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:35 - 🀐🀐🀐: SARKA MAI , , , , , , , , , 4️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA SAKON GAISUWA DA FATAN ALHERI HAR KULLUN GARE KU MASOYANA DA BAKU LISSAFUWA A GARENI DA MA WA YANDA BAN SAN DA SU BA NAGODE NAGODE UBANGIJI I A SADAMU DA RAHAMOMIN SA AMIN ALLAH YA BIYA MUNA BUKATUN MU NA ALHERI. MASU FADON ZAINAB NADA NAKASA DA GIRMAN KAI RASHIN SANI NE YASA KUKE DAUKANA HAKAN AMMA INA MAI BAKU HAKKURI GA DAUKAN DA KUKAI MIN DIN. YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A NATSE BA TARE DA DAUKAN NAUYI A KANKI BA MALAMAI SIN SUN CE NAUYIN AMMA KADAN SAI YA HANAWA MUTUM NASARAN SHI ALLAH YASA MU DACE. DARI UKU NE KACAL KATI KO TA BANK ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 2254380105 ALLAH YA BADA IKON BIYA AMIN Idan nace maku masu jin dadin wanan tsari da tsohuwar gidan ta kafa yau sunfi wacce akai case din domi ta sun fi yawa a gidan don hjy maryam tafi kowa farin ciki da wanan tsarin da akayi masu. Hjy maimuna bata so wanan hukuncin ya fado a sanadin ta ba don sanin halin waye hjy jummai da riko a ranta sai dai batai wani damuwa ba iya kokarin watsar da zancen da tayi a ranta taci gaba da harkokinta. Bayan kwana biyu da yin wanan maganan mota dake kawo masu kayan masarufi ya tsaya a kofan gidan tare da yaron shagon Alh sani babban yaron shi dake kula da al,amuran komai na Alhajin daya shafi shago da gida da duk wani al,amuran daya shafi rayuwan Alh din. Ahmed yaro ne mai rikon ammana da sanin ya kamata sosai shi din ba wani hadi tsakanin shi da Alh sani haduwa ce ta irin gamon jinin nan ya hadasu tun yana yaro yana yawon almajiranci suka hade da Alhaji a kofan gidan shi. Yayo bara bai samu ba ya dawo kofan gidan Alh sani ya kwanta ga hadari ya gama gari a lokacin ruwa na barazanar saukowa a ko wani lokaci a garin . Hakan yai daidai da dawowan Alh sani daga kasuwa don ganin hadarin da yayi suka rufe shago don sun san idan ruwa ya gwauce wanan hadarin sai yadda hali yayi a lokacin . Yana sauri zai shiga gidane ya ankara da yaron a waje kamar ya shige ya kyale shi sai kuma yanayin yaron ya bashi tausayi sosai ya dawo baya yana tambayan shi komay yake a nan ? A ciki yanayi damuwa yaron ke fada mai yayi bara bai samu bane ga hadari ya dawo nan ya fake tausayi shi ya kara shiga ran Alh sani kaaancewan shi mutum mai tausayawa na kasa dashi. Sai yaji ba zai iya barin yaron a yanayin wanan hadarin da ya gama hade gari bai dace ya bar wanan yaron a waje haka ba sai ya umurce shi da ya biyo bayan shi zuwa ciki. Hjy jummai na ganin shi shigowa da yaro a bayan shi ga yaron bagidaje dashi kana ganin shi kasan almajirine don yana dauke da dan kwanon baran shi. Nan ta hau fada don ko tariyan arziki ranan Alh bai samu ba a gurin ta sai fadan ina ya kwaso wanan yaron dake binshi a baya haka. Dan murmushi Alh sani ya sauke a fuskan shi tare da fadin yanzun dai bashi abinci kafin ki fara tambayana zan shiga in fito sai in fada maki komai akan yaron. Yana fadin haka ya shige ya barta da yaron a wurin tana binshi da harara mai nuna kiyayya a gare shi inda yaron ya sha jinin jikin shi da kallon da take aika mai din. Cikin tsawa ta dubi yaron tare da fadin bace min da gani ni banda wani abincin baka daga ganin ka irin almajiran nan ne munafukai ka fake ka marairaicr mai kamar na kwarai ashe mayau dari. Da wanan kazantar naka zai wani kwaso min kai har cikin falona haka kana wani irin bashi da tsami kazo ka kakkaba min keyan kuna almajirai iyayyen ku ma sin gaji daku a can suke turo ku cikin duniya da sunan almajiran ci. Haba jummai wai mai yasa ke baki da tunane ne wai idan idon ki ya rufe ai ba yaron zakiwa fada ba nida na kwaso shi ya kamata kima fada yanzu. Alh sani ne daya fito daga daki yake wanan maganan rai bace inda bai tsaya jin amsata ba ya tambayi abincin sa ta mike tana cika tana batsewa ta tafi dauko mai abincin nasa. Zo nan yace wa yaron tare da tambyan sunan shi yaron ce dashi Amadu yace kace Ahmed kake mai babban suna samu wuri ka zauna kaci abinci idan ruwa ya tsaya sai ka wuce makaranta kaji. Nan yaron ya samu wuri daga nesa ya dan tsugun na yana ma Alh sani godiya irin wanda almajirai kewa wanda ya kyautata masu sukaji dadi. Lokacin ta fito dauke da tire din abincin data shiryawa maigidan ta nufo inda yake sai dai ganin shi tare da yaron yasa ta bata ranta sosai. Sai da ta aje abincin ta samu wuri ta zauna tana kallon ikon Allah a cikin plate din da ta dora mai saman kayan don cin abincin shi ya fara zubawa da yawa ga mamakin hjy sai taga ya mikawa yaron abincin a cikin plate din. Haba kaiko a cikin plate dinka ma zaka bashi gaskiya ya kawo kwanon shi a zuba mai kuma da ka kwashe abincin ka zuba mai kai wani zakaci yace . Jummai ke na ai cin wanan yaro yafiye ma cin dani zanyi albarka baki sa wanda ya taimaki iri yara nan ba ga Allah shike da lada ciyarwa Ko banza fa yaro na kowa ne don baka san abinda Allah zai mai dashi watarana ba kaima har ka more shi. Yana ci yana mashi tambayoyi akan garin su yaron yana fada mai komai nasa har izon da yake sai da Alh sani ya tambayi yaro a karshe dai ya juya wuri hjy jummai yana mata nasiha aka taimako, Bayan a gama ruwa ne yaro yace zai tafi sai godiya yake zabga masu akan taimako shi da sukayi din Alh sani bai barshi haka ba yasa hannun a aljihun shi ya ciro sabuwar naira dari yabawa yaron yare da fadi ya dinga zuwa kullun ana bashi abinci ba sai yaje bara ba. Ran hjy jummai ya kara baci sosai da wanan sabon yaye yayen da miji ta ke kokarin mata don ita a rayuwanta bata iya daukan dawainiyar dan kowa. Ai da iyayyen shi na son sa da ba zasu sako shi cikin duniya da niyar yin bara ba tunda akwai tsangaya a kowani gari ana karatu kuma. Taso ta musa ya murtuke fuska tare da fadin umurni na baki na yin hakan har yaron ya gwauta ya sake kiran shi tare da fadin da karfe biyar nake dawowa gida. Kullun zaka zo da safe kafin karfe tara ka karbi abin karyawan ka a nan gidan kaji Allah ya tsara muna ku a duk inda kuke ya karasa fadawa yaron. Na gode Alh Allah ya biyaka da gidan Aljanna sarki da akaiwa ya sani Allah ya daukaka a cikin duniya dakai da zuri,an ka baki daya Allah ya kara maku soyayya dakai da matar ka. Inda hjy Jummai take tsaye Alh sani ya kalla tare da fadj kinji cikin dan sake rai da adduan da yaro yayi masu tace ai yawan adduan kai yaiwa bani ba. Alh sani yace in banda abinki idan addunan ta kamani aikema ya shafe ki don Allah jummai ina rokon ki arziki ki dinga sawa yaron nan abinci fisabillilah. Sai da ta nisa tace naji amma kuma nima ya zama dole in har zan bashi abinci gidan nan sai yai min dan aiki shima a gidan nan. Jummai wani irin aiki kuma wanan dan yaron zai iya maki kamar wanan in ba hali na wasu iyayye ba ai baici ace an barshi ya shigo duniya ba haka. Don Allah ki jaye wanan zancen aikin ki bashi abinci saboda Allah kamar yadda na bukata kiyi din ba don ni ba sai saboda Allah. Tace naji cikin wani irin murya dake nuna rashin jin dadi ta ga maganan mijin nata idan ba do son da takewa mijin nata ba da babu abinda zai sa ta dinga wahala da dan wata can. Sai dai maganan bai wani shigeta ba don sai da ta dinga ba yaron aiki irin wanke wanke da shara tun yanayi tana maida shi ya sake har yazo ya gwane da aikin sosai daga nan kuma ta buge da bashi aikin wankin kayan ta da na yaran ta. Amadu dan dogon yarone siriri dashi baki baida kauri sosai kana ganin shi kai kasan daga kauye ya fito sosai yazo kano almajiranci. Don hakane aiki da hjy Jummai ke bashi a lokacin bai taba bata ran yaron tunda ya saba da aikin wahala tun a gida kuma shi yana samun abincin da zaici koda yaushe haka yasa ya fara murjewa jikin sa na kyau ya fara wayewa. Tun bai san hanyar kasuwa shagon Alh sani ba har ya sani da ya fara wayo hjy tana aiken shi gurin Alh karbo wani abin indan tana bukata. A ciki yan shekaru Amadu ya murje yayi gwanin ba sha,awa dashi saboda kula da yake samu a gidan Alh sani din. Duk da yawan aikin da hajiya jummai ke bashi bai hana jikin shi ya nuna samun hutu a gare shi ba ga gorin da take mai wai yana da bakin cin tsiya ko yaya ta cika mai kwano da abinci zai cinyeshi tas idan an bashi sudi kuma jikina rawa yake karba. Mahakurci mawadaci don hakkurin Ahmed bai baci ga banza ba lokacin da ya sauka iyayyen shi suka zo daukan shi ya gabatar dasu ga uwayen gidan nasa da yayi a nan kano. Inda Alh sani yai murnan haduwa dasu har ya bukaci da su bar mai yaron a hannun shi yana son ya sakashi makarantar boko don ya samu karatun zamani. Ganin yadda yaro nasu ke samun kulane a gidan yasa suka yarda da bukatan Alhaji sani di amma da sharadin zasu kaishi gida yaga iyayye shi mata daga baya zasu dawo dashi. Har Alh sani ya debe rai ga dawowan Ahmed gare shi rana kwatsam sai gasu dashi da mahaifin shi da zasu zo har da dan tsaraban su na kauye suka zo mashi dasu. Inda mahaifin nasa ya danka amanan dan nasa a hannun Alhaji sani din suka tafi bai barshi a gidan shi ba can gidan hjy Amma ya aje yaron don sanin halin maidakin nasa. Inda Amma ta rike shi tsakani da Allah har yake jin sune yan uwansa na jini a jikin shi ya samu karatu gwargwado sannu a hankali ya fara harkan kasuwanci da Alhjin shi inda ya fara zama dan hannu ya murje yai kyau dashi ya zama dan gari. Sai dai suna shan artabu da hjy jummai don ya kasance shi din mai hakkuri ne kamar uban gidan nasa yasa har ya cin ma bukatar shi a duniya. Lokacin da ta farga da sanin Alh sani ya dora shi ga harkan kasuwancin sa ta nuna rashin yardanta ga hakan sosai sai dai ba yadda zatayine dole ta kawo ido tasa amma duk da hakan takan so bashi umurni wani lokaci yabi wani sa,in ya nuna mata hakan ba mai yuyuwa bane a gare shi. Wanan ne dalilin da yasa har gobe take tsanan yaron da take ganin baida galihin da za a kaishi ga matayin da aka kaishi a yanzun a gidan yasa suke yar tsama dashi akoda yaushe. Wana ke nan yana tsaye aka sauke komai da yazo dashi gidan inda ya kasa komai hudu kamar yadda suka tsara da ubangidan nasa tun a kasuwa in yazo za a yi da kayan a gidan. Bayan ya gama rabawa ne ya shiga ciki ya kira dukka matan gidan harda hadiye dake part din su ta fito kowa da mamaki akan may ake neman su a farfajiyan gidan. Hjy Jummai bata taso ba sai da dole ya sheda mata abinci aka kawo gashi can a farfajiya ya zube. Da sauri hjy ta taso jin abinda ya ce mata din sai dai tana tunkaro wurin ta hango yadda aka kasa kayan abincin sai ranta ya baci taja tayi turus ga kuma kowa na fitowa daga part din shi bayan kiran su suma da akayi. Wanda da can baya idan an kawo kaya ita kadaice mai bayar da ikon yadda za a yi da kayan a gidan tana karasowa ciki fada tace kai Amadu ya naga haka kuma ? Don har yanzu da Amadun shi, da yazo gidan take kiranshi ita da yaranta ba kamae yadda maigidan ya mayar dashi Ahmed kowa ke kiranshi dashi ba yanzu Cikin wani murya tace kai Amadu ya nags haka kuma yace hjy may kika gani kuma abinci ne aka kawo Alh yace in mikawa kowa nata a hannu ta idan na kawo ba wani abu bane ai. Kaba kowa nasa kamar yaya ta bukaci kari bayani daga guri Ahmed din daya mayar da hankalin shi wiri kayan. Yace eh Alh ne yace indan nazo inyi hakan da kikaga nayi din shine dalilin kiran kowa don ta kwashe nata a idon ta. Eh lalai wuyar ka ya isa yanka Amadu a gidan nan idan gaskiya ya shuka shi Alhjin yazo da kansa ya bamu din amma da yake yasan bai shuka gaskiya ba shine kai issashe ya turoka kai wana rabon. To ka koma ka fada mai wana rabin baiyi ba a gurina babu wanda zai raba muna kan gida saboda a gyarawa wata rai taji dadi a cikin mu akai hakan ko ? Don samu wuri to ba za a raba muna girki ba don kawai wata can a gidan nan sai ka hade shi kamar yadda ka kawo shi ka koma ka fada mai nace ba za, a raba ba. A, a hajiya Jummai ke wa ga yadda mai gida yace ayi mai da abinsa zaki wani ce ba za ayi hakan ba to mukan namu kwasa zamuyi duk wanda zai tsaya bin dokan ki sai ya tsaya ya biki mukan mun bar bin dokan wata mace gidan nan kuma tunda ba ke kika ajemu ba. Hadiye ce data iso gurin yanzu take wanan maganan ga hjy jumman ta kara da fadin Ahmed wanine namu daga ciki mu dauka. Salati hjy jummai ta saka tare da fadin yau ni jummai naga abin al,ajabi abin mamaki ke Hadiya kin kasa zaman gidan mijin ki kinzo nan zaki bata muna namu zaman. Duk da maganan ya batawa hadiye rai bai sa ta tsaya mayar da martani ba alokacin sai ma umurtan mazan dake tsaye a gurin da tayi akan su dauki buhuhunan su shiga muna dasu sassan mu takare da fadin idan baki da niyar daukan naki kya iya barin shi a gurin. Tana tsaye tana kallo hadiye ta umurci kattan nan su saka muna kayan abinci a part din mu dole muka bar wurin ba shiri don mu nuna ma mazan wurin da zasu aje muna kayan abincin don akwai store da kitchen a part din kowa dama. Fin karfi ne yasa dole ake girki gaba daya a gidan na kowa da kowa don ra,ayin uwargidan namu ran gida. Sai da Ahmed ya tabbatar da an shigar wa kowa da nasa bayan ya mika masu kudin cefane yabar gidan zukatan kowa cike da farin cikin samun yancin kai a gidan ranan. Ranan ba karamin jidali suka sake yi da Alh sani da hjy jummai ba don ta nuna bata yarda da wanan tsarin raba tukunya a gidan ba. Inda shi kuma ya dage akan hakan za a yi tunda yana da halin yi kuma mahaifiyar shi ta umurta da ai hakan a gidan dole ne kuma kowa yabi dokanta har shi. Ranan dai fadan hjy jummai bai tsaya ga mijin ta kadai ba har tsohuwar gidan ta hada ta fada mata abinda ke mata zafi gamay da ita akan zaman ta gisan dasu. Har tayi ta gama babu wanda ya lekota daga sashen Amma don Amma din ta hana hadiye ta tanka mata tace a barta da zafi abinda ya samay ta ya fi komai ciwo a zuciyar ta. Sai Alh sani ne da yaga abin nason ya wuce wuri akan mahaifiyar tashi ya fito da kanshi ya tsawata mata. Ganin ba wasa ga maganan daya furta akan idan ta kara tankawa a gurin zai dauki mumunan mataki a kanta a lokacin. Tuni ta bar wurin ta koma dakin ta tare da kamay bakinta tayi shiru don tasan zai iya yin abinda yace din wanda tasan akan mahaifiyar shi zai iya yin komai. Yar ta ta uku ce ta fito daga daki a natse don tunda aka fara maganan tana ji bata fito ba sai da taji shigowar uwar tata ta leko falon nata ta samu guri ta zauna daga gefen uwar tare da kura mata ido. Jin uwar taja tsuki yasa ta kara dago kai ta kalli uwar tasu kafin ta soma yi mata magana a cikin natsuwa tana fadin. Mama maiye acikin yin hakan da har kike tayar da hankali ki kan dan wanan abi tunda baba ya zabi a raba ai shike nan ko shi yaga zai iya tunda ba kudi ki bane. Ni ina ganin ai sai ki kya,, , , , , , , , tsawan da uwar ta daka matane yasa bata karasa abinda tai niyar fadi ba a lokacin inda mahaifiyar taci gaba da fadin wallahi salma ki fita idona a gidan nan. Idan kema son samay ki kamar yadda suka samu ubanki suna juyawa ni ba su samay ni ba kuma ba zasu taba samuna ba. Yarinya kamar ba nace ba baki san kishin uwarki ba ko kadan ki sa may yin haka ke nufi kuwa a gare ni a gidan nan hakan na nufin durkushewa na ne ga idon kowa yau ace har an samu macen da akanta za a rushe abinda na dade ina kafawa a cikin gidan don wata can mace yar uwata. Mama ki kwantar da hankalin ki ba wai haka nake nufi ba nima kaina wanan matar sam batai min ba wallahi don bata kaunar ki nima ba zan taba kaunar ta ba a raina. Kin san da hakan zakice in kyale saboda ita ai min yadda aka ga dama a gidan nan wallahi bai wanan matar ba a duniyan nan. Mama ni naga idan kina irin haka sai su dauka abin yaci maki rai ne sosai har kike wanan magana tunda gaba na da yawa mamaki faketa har gaba ai zaku hadune da ita in tana ganin sunyi maki haka yanzu sunji dadi. Nan gaba zaki kama su a hannun ki amma fa sai idan kin kwatar da hankalin ki har wanan munafukan maman su Rashida ni sam ban yarda da ita ba a gidan nan . Don da tana bayan ki ai da zata baki hadin kai ku hada kai kar hakan ya faru amma sai kika jita shiru batai magana ba sai komai ya lafa zaki ganta nan tana maki dadin bakin data saba. Sannu a hankali maganar yar tata ke shiganta wanda yasa a hankali ta fara saukowa daga zafin da zuciyar ta ke mata a lokacin. Kafin suyi magana wayan uwar yai kara inda ta kasa duba mai kiranta a lokacin sai yar tata ne ta iya yunkurawa ta dauki wayan tare da fadin yaya Abbsa ne ke kiran ki mama. Ki dauka uwar tace mata don yadda take ji ba zata iya daukan wayan kowa ba a lokacin salman ne ta dauki wayan yayan nata. Bayan sun gaisa yake tambayan maman nasu tace gata zaune tare damu bata wayan man yace wa kanwar tasa bro ka kira anjima don yanzun bata iya daukan wayan kowa. What yace cikin wani irin murya tare da fadin may ke faruwa da mahaifiyar tasu ce sai salman tace kawai dan matsala aka samu a gida yau da ita. Kinga fito fili ki fada min abinda ke faruwa cikin tabe baki tace akan dai wanan matar ta baba ce wai Amma ta tsaya mata akan su raba girki a gidan kowa ya dinga yin nasa a part din shi. And so what ya furta sai may idan anyi hakan ai an hutar da mamane da wani abu salma tace shi nake fada mata ai yanzun mamane bata ganewa. Yace common bata wayan muyi magana ta karawa uwar wayan a kunne taji dan na fadin mama akan dan wanan maganan kike tayar da hankalin ki a gidan. Bayan kin san kina damu gani ga yaya Habbib ga su salma da Abba karami akan may hankalinki zai tashi haka kin san dai zamu iya tsare maki komai a gidan yanzu. Abbas ba zaku gane abinda ke tayar min da hankali bane ku yarane har yanzu No no no mama kibar fadi hakan don Allah. Yanzun dai ki kwatar da hankalin ki don Allah wanan maganan kada ya tayar maki da hankali zanyi magana da yaya habbib asan abinda za a yi kan maganan . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:37 - 🀐🀐🀐: ALLAH SARKI YAU YAZO YA TAFI KE NAN UBANGIJI YASA MUN AIKATA ALHERI A CIKIN WANAN RANAN ALLAH YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA YA GAFARTA MUNA KURA KUREN MU GA BAKI DAYA AMIN. Mai karatu zaki dauka zancen yaran hjy Jummai zai kwantar mata da hankali ne don da farko har ta dauki maganan yaran da muhinmanci a ranta. Ta sakar da maganan duk da ranta yana matukar sosowa da zancen don ya tsaya mata a rai tana ganin hakan komawa baya ne a gurin ta. Shigowan hjy maryam part din yasa maganan yarta Salma yazo mata a rai dama tayi tsamanin hakan da farko kallon ta tayi ta watsar sai da hjy maryam din da yake makirace ta in ma bakinta tace. Giwan gida kada ki dauki wanan maganan da zafi haka don ni tun ranan da aka kitsa hakan na sanda zancen sai dai banyi magana bane sai na gano abinda ake kitsawa din. Don ina ranan da kika fito gaida tsohuwar nan kina fada kan suna labewa da Alh suna hira a can ba ranan girkin ta ba. Tun wanan ranan aka kulla hakan a gidan sun riga da sun kulla abinsu dama aiwatar wa ne da tsohuwar taga baiyi ba yasa ta fadi a fili. Dama ni a tayadda na samay su ranan nasan akwai wani babban al,amarin da zai faru a gidan nan don samun su nayi suna raha suna zaune kamar wasu kawayen junna. Zancen tafiyana kuma da nayi wa Alh sai cewa yayi sai dai idan da maimuna zanyi tafiyan don itama tana da abinyi a bauchin. Nuna masa rashin yardana da hakan da banyi ba shine mfarin rashin zuwana har yau da banyi ba tunds naki yarda inyi tafiya da yar gwal din gidan shi. Jin hakan ya sasauta zuciyar hjy jummai tace ke kuwa gaki wace bata san abinda takeyi ba mana ba dole ki tafiya da ita ba tunda kowa na tsoronta kamar yadda ya take juya shi. Ita wanan da taki zaman aure ta kaso tazo ta zaunawa mutand gida har da yara biyu dama abinda suke so ke nan su samu dukiya suyi yadda suke so dashi ta samu yanzu ji abinda ta fada a wurin. Ni wallahi na dai bari an kai min nawa ne don kada ace mutum ya karya dokan maigida a sashi ga baki. Ji munafuka bayan ta gama dariyan mugunta a daki yazo tazo nan tana dadin baki don kishiyar tata ta kara tunzura. Nan ko mai zafin kishi ta hau ta fara fada tare da fadin dama nasan da manufa akai mi hakan don kawai aga bayana a gidan nan . Anzo a taru a wawashe dukiyar banza a watse daga baya a koma ana fadin bai da komai yanzun don haka suke so wallahi zanyi maganin kowa a gidan nan har hadiyen dake zaman kama mata su ga yan uwa ko ? Ni da naga tasbaha a gurin zumunta banji tsoro ba shida kafin ka gama da dan uwa daya ya biyo hannun ka. Sun dauki lokaci suna zancr daya a dakin tana kara iza ta akan itama zata dauki mataki kan abinda ake masu a gidan cewar hjy maryam din. Ya kasance yau ranan girkin hjy jummai ce a ranan ta kudirci yin magana da maigidan ba wani abin kirki tayi ba don kamar kullun yan aikin gidan tasa suka shirya mai abinci kamar na kullun. Sai da ta gama abinda take ta tun kari part din maigidan da harta samu yana shirin kwanciya a lokacin ta shigo da sallaman ta dakin. Ya dago tare da amsa mata sallaman a takaice don yasan har yanzun fushi take da shi kan abinda ya faru dan kwana biyu a gidan don babu walwala a tare da ita tun lokacin. Don hakane shima bai yarda ya bata kafan da zafa kawo mai zancen ba don Ahmed ya fada mai duk yadda ya faru a gidan ranan. Muryan tane bayan ta samu wuri ta zauna tace Alh magana nazo muyi ni dakai ba tare da ya daina abinda yakeyi din ba yace umhumm ina sauraren ki ai. Gaskiya Alh bangane abinda kake nufi damu a gidan nan ba kokarin zama shima yake tare da fadin kamar ya dake da wa kuma ? Tace dani da kowa na gidan nan da wanan maganar ta shafa kana tsamanin ban san abinda kukeyi ba a gidan ko ake shiryawa don dai kawai aga an kuntata ma rayuwan mu. Wai kina fadin ana kuntata maki dake dawa kifito fili ki yi maganan da zakiyi kin tsaya kwana kwana. Hakan ma zakace tunda ka na kokarin fifita wata akan mu yau ka fada min da abinda maimuna tafi mu dashi a gidan nan da tun shigowan ta kake kokarin muzanta muna haka akanta Kai Alh ya girgiza lokacin da tayi wanan maganan tare da fadin nikan Jummai da zaki bi shawarata da sai ince kifita harkan yarinyar maimuna tun tana ganin ki da daraja a gidan nan. Wallahi Alh yau dai ayita ta kare don sai ka fada muna abinda ta fimu dashi don ban gane may kake nufi ba da bin ra,ayinta Mtss yaja tsakin takaici yace ke a tunanen ki haka ake daukan girma idan Allah yaba mutum don zaki zubawa da kanki da kima a idon kowa ne. Kefa babbace ba sai na tsaya maki bayanin daukan girna a cikin lumana akeyin sa . Indan fa kin matsa a kanta komai na iya faruwa na iya faruwa tazo bata girmamaki a cikin gidan nan wanda ni kaina ba zanso hakan ya faru ba a gidan nan kodon yarana dake kallon ku. Don kina dai gani tun bata iya baki amsa har gashi yanzu ta fara budan baki tana magana a gaban kowa ba komai bane fa halin yau da gobe ne ya fara isarta. Ita may yasa kuun bata kawo zancen kunyi mata abu koda kuwa din kunyi sai dai kune a kullun tayi maku wani abin mussanman ma ke jummai why ba zaki tayani gyara gidan nan ba kamar yadda naso sai kokarin bata min gida. Da kike maganan ina kuntata maku ai ita maryam nan tazo tayi min godiya kan abinda hjy ta bada umurni ayi nakumayi sai ke ne da baki gudun halakana zaki zo ki sakani a gaba kina wanan babatu haka ina ilimin ki da hankalin ki yaje ne wai. Abin nan fa sauke nauyi ne a gare mu duka akayi idan kin gane ko da basu magana amma kema kin san ana cuta masu dai a gidan nan ta wani famni ko ? Ya kamata ki dinga nazari idan kinga na aiwatar da abu ba wai ki dauka nayi hakan don ra,ayin wata bace a gidan . Tunda ya fara magana har ya ambaci sunan hajiya maryam jikin ta yayi sanyi akan maganan nasa da yaga yanayin nadama a gurin ta yaci gaba da fadin. Ni da zaki bi ta nawa ki kwantar da hankalin ki don bada ke ya kamata kullun a rika ji bakin a gidan nan da maimuna ba tunda dai kece babba. Shi kuma auren maimuna da nayi ba haramun bane yinsa sai karin zumunci idan kin matsa na saki maimuna ma wata zan kawo gidan nan tunda yanzu na gane auren mace fiye da biyu kuma. Wani kallo ta watsa mai daya fadi hakan tare da fadin watau ma ba zancen zama da mace daya kakeyi ba ke nan ? Kwarai kuwa ban maki wanan alkawarin ai tun farko kinga idan kun fitar da maimuna wace zan kwaso kila tafi maimuna fitsara da kuke fadin tana maku ko yaushe tazo ta gyara min zaman ku a gidan nan tunda ita maimunan tana bin ku a hankali bai maku dadi ba. Mu maza ba ai muna haka ku bar mu da abinda muka gani muna so on haka gara maimun kin santa tun farko kin san halinta . Gaba daya jikin ta yai sanyi da jin maganan ta hankalinta yafi tashi dajin yace ko maimuna ta fita wata zai kwaso masu take natsuwa ya kamata har take fadin. Ai sai mu zauna muci kan mu nidai dama raini ne ban son a gidan nan don haka sai a kiyayye don gaba. Yace ba wanda zai rainaki a kidan nan muddin ina raye don haka ki barni nasan abinda nakeyi ranan hjy jummai da tunanen maganan shi ta kwana a ranta. BAUCHIN YAKUBU, , , , , , A cikin garin misau gidan malam sale ba wani babban gida bane na azo a gani gidane irin ginan kwatas din nan da ake sayarwa na gwauni aima ma,aikata gwajon shi su saye. Gidane na mata biyu sai falo a tsakiya da ban daki sai kitchen wanda kowa yake sharing a gidan Yaran malam sale tsohon malamin asibiti ne a primary health care aiki ya kawo shi misau daga azare har ya zauna misau din saboda dadewan shi garin da kuma auren yar garin misau din da yayi. Yaransa goma wanda mata biyun suka haifa mai sai dai yanzu wasun su sun girma do haka ba zaman gida sukeyi sosai ba. Gidan malam sale gidane da mata ke iko a cikin shi hakan ya jawo lalacewan tarbiyar yaran gidan kamar yadda wasu dake gane masu suke hango hakan a gare su. Don uwar yaro zata iya saka shi yin abu yaro ya kafe akan ba zaiyi wanan abin ba ko a hana shi yace sai yayi . Hakan ya samo asali kan rashin zaman gidan da malam sale din bai faye yi ba din da zaran ya dawo daga gurin aiki zai wuce chemest di shi da yake dan sayar da magani a kasan uguwar su. Malam sale wane ga marigayi Abubakar mijin hjy maimuna na farko da Allah yayiwa rasuwa shekaru biyar da ya wuce inda ta dawo kano da zama a lokacin ta bar yarta can a hannun kakanta mahaifiyar marigayi din. Sai lalura ya kama tsohuwar zaman su yanzun ya dawo misau din gidan danta wa ga marigayin danta. Kamar yadda kowa yasan mutan misau da karatun addini dana boko suna noma da kiyo kamar yadda yake al,adane hakan ga kasan hausa sai wani dan sana,an daba,a rasa ba. Sai dai gidan malam sale abin yasha bambam don yaran gidan gasu da son hutu sun ki tsaya su dage ga karatun boko ko na addini wanda hakan yana cikin matsalan da hjy maimuna take hangowa yarta akan zaman gidan. Wanan yasa da zaman su fatima yar gurin hjyn ta dawo nan karatun nata ya fara rawa aje yau gobe ba a zuwa har ma a debi lokaci ba a je ba. Gashi ba wani kula a gidan zakaga yaro ya shigo da ledan idomie yana dafawa ya bad abincin gida bai ci ba duk da malam salen yana iya kokati shi gurin ganin ya kawo abinda za a sarafa aci a gidan wanda shine ya jawo mashi wanan bakin wahalan bayan yayi ritaya. Ko dan makarantar da take zuwa sai da taimakon gwagon ta kanwar mahaifin ta Adda ta samu take zuwa makarantar jefi jefi don ba,a sata da zaman su ya dawo garin ba. Da kyar yaran gidan suke kare secondary school di wanda dags nan sun kare karatu ke nan sai zaman bin gari da yawon buki. Wanda duk wanan abubuwan yana cikin abinda ya tayar da hankalin hjy maimuna da zama ta gidan ba wanda ke kula lamatin wani kowa kansa ya sani a gidan daga manyar har kananan. Dan abinda kakan ke samu take tallafawa rayuwan yar jikan nata dashi idan kuma bata dashi sai dai su hakkura ke nan. Hakan baisa yarinyar ta dan canza ga tarbiyan da take dashi ba sai dai akwai inda take da dan rauni wanda zaman gidan yasa ta koyi rashin kunya sosai don hakan taga anayi a gidan itama ta koya ta iya. Ga yawo bin makwata saboda gudun aiki da aike tula mata a gida don sun ganta da zafin nama aiki baya sha mata kai ko kadan Kamar yadda kowa ya sani mutanen azare gauraye ne sai dai akwai fulani da yawa a cikkn su hakan zuri,an su fatima ma fulani usuline don har yanzun kakar tata bafa jin hausa a baki ta sosai sai ta hada da fulanci. Itace komai na kakan tata da farkon zuwan su babu mai taimaka ma lalurar kaka sai da Adda tazo gidan tayiwa mata gidan yankar kauna kafin su fara dan taimakawa dattijuwar. Yau ma zaune take a gaba kakar nata tana ci dan abincin da ka saka masu wanda wani lokaci dole kaka ke hakkura ta barwa jika nata tacinye sai dai tausayi kakar nata wani lokaci bai barin yarinyar taci abinci sai tace ai taci a gidan su kawar ta Rahama gidan da ke makwabtaka dasu inda duk yawon ta idan ka nemay ta ana zaka samay ta. Dan kadan ta taba shinkafa da waken da take ci tace da kakar tata ta koshi don kakar ta samu itama ta taba bawai don ta koshi tace hakan ba. Sai da yarinyar mai tausayi ta tabbatar da kakan ta koshi ta debo ruwa ta kawo mata ta wanke hannu ta kawar da kayan ta dawo ta dan zauna a dakin nasu wanda ke ta wajen gidan da aka gina aka kewaye da kwano ya shigo ta cikin gidan. Ganin kaka nata ta dan kishingida yasa ta mikewa don tasa yanzun za a kwala mata kiran aike ko wani aiki na gidan wanda ya kamata ace yan matan gidan sunyi gasu zagada zagada dasu amma basu kawar da kara a gidan nasu. Na fito ke nan daga dan dakin mu da aka ware muna a gidan ina sanda don kada wani a gidan ya ganni ya aike ni ko yace in mashi wani aikin. Ta kai daidai kofan fita tajiyo muryan mama saude tana kiran ke ke ke Fatima ina ji hakan tuni ba baza da gudu na bar gidan ina jin tana fadin ai zaki dawo ko yaushe kika gama gantalin ki kika dawo wanke wanke yana nan yana jiran ki a gida nan. Jin hakan ya falkar da kakan nata da bata san fitar yarinyar daga dakin su ba sai murya taji ana kwala mata kira daga waje kuma tasan bata dawo ba tunda taji kalamin saude din kan yarinyar. Da kyar ta samu ta mke ta dan dogara kafan ta zuwa waje ta samun sauden a zaune tana wanki tana sauraron wankan yan wasan hausa tana bi. Sai murya dattijuwar saude taji a kanta tana fadin haba saude yar nan ita kadaice a gidan nan ina ga yaranan birjit a gidan nan su ba yayan moriya bane sai wanan yar marainiyar Allah kwaya daya tilo a gidan nan da ba uba uwa kuma tayi mata nisa ita kadai ce ko yaushe tsaye a gidan nan. Yarinya babu daman ta motsa kowa dai fatima fatima don Allah ku bar yar nan ta huta hakana mana, ko kwatanta a kan ku idan haka ya samay ku ko yayan ku. Tsohuwar bata kai ga ci gaba da maganan ta ba tajiyo muryan Tj bayan ta daya daga cikin jikokin ta na gidan yana fadin dallah ji wanan tsohuwar. Yomar idan ba a saka ta aiki ba wani moriya take dashi a gidan nan bayan dan aikin da takeyi mafarin ki lalata yarinya kawai. Shiyasa ai yanzun bata tsoron kowa a gidan nan wata jikan nata da taji ana maganan ta fito daga daki tana daura dankwali a kanta zata fita yamma yayi zata ta zubar din da suka saba . Take fadin kema wai manjo ina ruwanki kiyi fama da kanki mana kina wani fada kan wata fatima can kamar ita kadaine jikan ki a gidan nan. Da anyi magana kice yeyeyeye, , , , wai yar marainiyar Allah ce ita kada a taba ta ubanta ya mutu waye waye da sauran su. Ikon Allah yanzun ni kike kwakwayo yar nan komai abinku dai nice na haifi uban ku sai yaro farko yace yo ai shi kika haifa bamu ba sai kije ki ta haihuwar su can. Badai zaji taba haihuwan mu ba mu tace wa ni Allah ya tsari gatari da saran dutse da in haifi irin ku ai gara in zauna ba haihu yafi mun jika ji shigan ka kamar ba dan musulmai ba ji kanwar ka a haka zata fita uwayen ku na ganin su. Shine bakin cikin ki inji yarinyar da ke murza janbaki a bakinta ta gyaran fuskanta ko inzo in shaga mak ne dallah ban wuri gantalaliyar da bata san ciwon kanta ba . Diba uwarki ne nan zaune take wankin kayanta da kanta baki san ki kama mata ba aini yarinyar nan Fatima tafi mun ke sau dubu wallahi a gidan nan. Ke tafiwa ba muba inji namijin kai rufe mun baki mai sufar arnakun farko jika ji wanan shigan a haka kake bin gari kamar wullakantace. Haba babba zagin yayi yawa hakana ai shigan zamanin nan ne haka ba wai ra,ayi bane Saude dakan ki kike fadan haka a gaban yaran nan. May ye a ciki babba yanzun akan yar jikan ki da kike so kike wanan tada jijiyan wuyan haka yaron ya matsa kamar zai mangare yar tsohuwar. Salati ta saka tana fadin yau naga yaron kawai Allah ya ban lafiya in bar gidan nan da kafana. Aike ne dai da aiki fatima ba zatayi ba yau a gidan na soke wanan a gare ta caraf uwargidan malam sale ta fito daga dakin ta tana fadin. Babba kibar wanan zancen don Allah kada yarinyar nan taji dadin kara finjiraiwa a gidan nan hinjira kan ai ga hinjirarun nan a gaban ku su da ba a iya aike ko nan da can. Aikine daga yau idan fatima bata yi shi ba bazata kara cin ko loma a gidan nan kunji na fada maku. Manjo dake kallon ta a ciki mamaki ta kasa magana sai cewa tayi Allah ka kawowa yar nan dauki a gidan nan ta huta ganin wanan warin a gidan wan ubanta. Ta juya da kyar zuwa dakin ta na faman mita akan abinda akewa yarinyar a cikin gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:37 - 🀐🀐🀐: YA ALLAH KA GAFARTA MUNA KURA KUREN MUN WANDA MUKA SANI DA WANDA BAMU SANI BA UBANGIJI KAJI KAN MU KA GAFARTA MU. KASA MUNA YSORON KA DA IMANI A CIKIN ZUKATAN MU YA ALLAH KA BA MU IKON BAUTA MAKA BAUTA TSARKAKKE A SAURAN RAYUWAN MU AMEEN YA ALLAHU, , , , , , , Lokacin da nafito dan gidan baffan nawa bayan na gama jin umma saude tana kwala min kira wanda nasan kiran na dayan biyu ne ko aiki ko aike da bai kare min a gidan muddin ina cikin gidan sai idan Manjo ta hanani zuwa ko fita na ke samun sauki. Shiyasa na kwammace zuwa gidan Atika ita kadaice kawata a garin tunda nazo tsiwa da fada bai bari muyi nisa da sauran kawayen da suke sona da kanwance a garin. Amma ita Atika banda matsala da ita yanzun zamuyi fada mu koma mu shirya hakama mahaifiyar Atikan takan nuna min kulawan ta sosai kasancewa ta marainiya a gidan da ban samun kulawan da ya dace. Da sallama na shiga gidan wanda doka ne hakan ko kana dan gida zaka shigo dole sai kayi sallama kafi shiga idan ba haka ba sai ka koma baya ka kara sallama zasu barka ka shiga. Ba iri gida Baffa na ba da kirikiri kana sallama suna ji ka za, a kyale ka wasu ma suce ka damay su da sanaben yin sallama idan zaka shigo ka shigo kai tsaye. Atika ce zaune tana tsifan kai a yar kujerar mata ina ganin hakan na bata rai don nasan za ai dayan biyu ko in taya ta ko mahaifiyar ta malle tace nima in sance nawa kan ai muna kitso a tare. Wanda ban son hakan ko kadan naki jinin abinda zai taba min lafiyan kaina a rayuwana sai kitso yai min wata daya akai har tsagan kitso ya fara bacewa akaina ban sance shi sai wani yaji tausayina yasani sance kan dole zan kwance kan. Atika tana ganina bayan karba min sallama da tayi tace yauwa kamar kin san yanzu malle ta gama maganan ki kizo mu kwamce kai mu tafi kitso yau. Harara na watsa mata tare da fadin ki dai tafi kitso ni har yaushe kaina ya tsufa da zan sance kai tace lah yanzun wana kan da nayi kitso uku bayan wanan zaki fadi haka. Fuska na bata ina zama tare da fadin kin san Allah Atika bana son abinda zai taba min lafiyan kan nan nawa ko kadan . Tace rashin sabo da yi a koda yaushe ne yasa baki saba da taba kan ba har yanzu amma mutucin mace ai shine gyara kitso kuma na cikin gyaran mace don da zaran wani yaga kanki a haka sai yai maki kallon kazama. Na harare ta tare da fadin kina nifin ke nan ni kazamace ko haka ma ranan ya sadi ya kirani da kazama wai na daga karyayi ball dani gurin da yake cin abinci. Sai kuma naja tsuki tare da fadin koda yake wa yan nan ma ko may nayi haka zasu ce min don babu mai kaunar zamana a gidan don ciwon Malle kawai muke zaune a gidan nan. Yanzun mu guduwa nayi ina jin umma saude na kwala min kira nasan wani aikin zata sani ga jaka sun samu a gidan ke nan ko ? Atika tace ko basu son ki tunda Baffa shi yana son ki da Malle ai shike nan dama don Baffa di kuke zaune a gidan ai. Nace matsalan ai shi Baffa baya zama agida kullun yana wurin tsaron shagon shi Malle kuma kinga ba maganan ta suke ji ba tunda sunga yanzun bata da kafa da zata mike ta daki mutum. Mikewa nayi ina fadin kowa kibiyar in kama maki tace ke ba zaki kwance naki kan ke nan ba raina kara batawa ina fadin idan baki so na zauna. Ta miko min kibiyan na shiga kwance mata kan muna hira wanda hiran duk zagin yan gidan mu nake muna fadin halin kowa a gidan. Muryan Malle mukaji a kan mu tana fadin yau naga ikon Allah Fatima bana ce idan kin shigo ta fada maki ki sance wanan kan daya komar dake kamar mahaukaciya ba. Ba dama in magana saboda nauyi da kunyan marar da nake ji a raina yasa na sakewa Atika kanta na samu guri na zauna. Daki ta koma sai gata ta fito da wani kibiyan ta miko min nan na fara kwance kan nawa na dole ba don na so ba. Saboda wanan kitson da muka tsayayi yasa na kai dare ban dawo gida ba abinda ya kara tunzura ran yan gidan mu ke nan fiye da yadda nayi tsamanin zasuyi min dama idan na koma gidan. Ga laifin da nayiwa umma saude ga kuma wani na kara a samsn shi nasan kuma Manjo na can cikin damuwan rashin dawowana gida da wuri don duk dadewa na a gidan su Atika ban kai magariba ban shigo gida ba. Ban yarda na shiga gidan ba kai tsaye sai da na dan leka ko babu kowa a waje ganin basu kusa yasa nayi wuf zan shige dan dakin mu wurin Manjo. Naji an kai min duka a kai kumb tare da fadin shegiyar yarinya dazun da ake maki magana kika gudu gidan uba kika je har wanan lokacin ? Yakara kai min wani duka ban san lokacin dana sake wani ihu mai kara ba da ya karkato da hankalin kowa gare mu. Yar iska ba kina ganin Manjo na kama maki ba agidan nan yasa kike abinda kikaga dama yanzun. Cikin kuka da jin zafin rikon da yai min nace may nayi ma da zaka mare ni don anga banda uwa a gidan nan kowa ke dukana haka ? Shegiya an duke ki din kira uwar ki ta rama maki ihun dana sake yasa kowa na gidan fitowa a lokacin dama dukkan su hake suke dani. Karawa yar iska marajin magana yarinyar nan yanzu ta fitsare a gidan nan da kike fadan haka wani ya kori uwar taki a gidan nan halan ? Ummatu ne ke wanan maganan uwar gidan Baffa wani ihun na sake sakewa mai karfi don Manjo taji tazo ta cece ni don naga su ba hakkuri zasu bada ba sai ma zugashi yai min tsinanen duk yadda yake murdai murdai din nan. Aikuwa manjo najin kuka na tun ihuna na farko ashe tana can tana kokarin tasowa daga daki ne sai muryan ta mukaji tana salati a bayan mu. Tana fadin yau naga abinda yafi karfin ganina a gidan nan yanzu sadi kashe yar marainiyar Allahn nan kake son yi ko may ? Wanan irin duka da kake mata har a dakina ina jin kara tana karasowa gurin take magana tana zuwa ta sa hannu zata kwace ni daga hannun shi ya kare rike gam don kada ta kwace yana min ketan daya saba. Tana jan hannu na tana fadin shikata dan banza mara hankali da tunane yar nan kwara daya ta tsone maku ido a gidan nan . Ina ga kannen ka nan baka tsawata masu su daina yawon banza ba sai wanan da aka san inda take ina nan gidan makwabta take shiga duk iya yawon nata. Da taga yaki saki hannu nawa takai mai duka a baya tim yace wai wai wai manjo akan wanan yar kika dukeni haka yau ko sai na balla ta a gidan nan inga iya fitinan ki. Baka isa ba dan banza uban ka ma yayi kadan ya balla ta balle kai yaron kawai sauran mutanen gidan sai abin ya koma basu dariya. Don shi a zolaya yake mata magana inda manjo iya bakin gaskiyar ta take fada dashi zata kara kaimai duka ya sake ni da karfi na fada jikin ta da kadan mun fadi kasa Allah ya kare bamu kai kasan ba. Tace dan kawai na gane so kake ka karasani bawai a yar abin naka ya tsaya ba yace in karasa ki in gane may manjo ki dai ji da kafan nan naki tukun. Na dai gane zaman mu a nan ne baku so zan koma azare inda na fito da yardan Allah goben nan zamu bar maku gidan tunda na gane nufin ku. Haba yar nan ita kadai ce a gidan nan kowa ya tashi dai A ruwa dau a ruwa yace ai da na kamata yau yadda nake so data zama a wuta. Tace kai tafi can dan kawai kai kan bakayi hali mahaifan ka ba sam wallahi daka biyo su daka dace. Yace halin ki na kwaso ai bakiga muna kama dake ba ta kara sukewa da yaron tana fadin ke kuma shige mu tafi kar ya karasa min ke don ba mutunci ne da su ba. Har mun dan gwauta muryan ummatu mukaji tana fadin gaskiya babba ki dinga barin suna hukunta wanan yar. Yanzu gashi akanta kike zagin wanan yaron haka kina wufinta shi akan yar da kika fi so a gidan koma dai yayane su duk ai jikokin ki ne kaf a gidan nan. Saude zaki fita idona ko sai na bata maki don banyi tsufan da har sarakuwa zata wufintar dani a gidan nan daga can gefe nace Manjo kyalesu mu tafi ina jan hannun ta. Bayan mun shiga dakine ta juya gare ni tare da fadin ke ma kingane ki bakya jin magana . Kinfi son ko da yaushe su dinga dukan ki kamar sun samu jaka ko ? Haka kike yi da muna gida ina kike fita yanzun kinzo nan kin koyi halin yaran banzan nan da uwayen su basa son ai masu magana. Yanzun akan na hana yaron nan sadi dukan ki yasa saude ke son fada min maganan banza goben nan idan Allah ya tashe mu lafiya zan bar masu gidan nan indai akan nasa ido haka suna ci muna fuska ne. Na bata rai tare da fadin nifa manjo ba da gangan naki dawowa gida da wuri ba kin ga kaina dole malle ta kwance min kai aikai min kitso an gama kuma tace sai nayi wanka naci abinci zan dawo gida saboda tasan halin gidan nan. Tunda na dade haka ba lalai bane su bani abinci don ba bakin, ta suke ba gun sanin halin su malle tace to kin gani har makwabta sun san da bakin halin su. Ki kama kan ki cikin yan uwan nan naki na kula ba son ki suke a cikin su ba don hakane nima bana raga masu ko kadan. Wallahi Manjo dukan da yai min ai banso ki masa kadan ba tace rufe min baki iya karafina ke nan da dukan bai maki ba ai sai ki ramawa kan ki. Ni dai abinda nake so dake ki koyi natsuwa ki kama mutuncin kan ki kodan mahaifin ki dake kasa kwance. Ina jin haka bace manjo yanzun banda natsuwa ne ko may ina fadin haka na koma daga karshen dakin na zauna na bata baya alaman nayi fushi ke nan. Kyale ni tayi na dan lokaci nasan ba zata juri ganin fushina ba da ita sai naji can tana fadin ga abincin naki dauka ki kara don nasan ma basu saka maki ba kada ma ki tambaye su don ba baki zasu yi ba. Kyaleta nayi kamar banji ta ba sai can tace ke dadina dake baki da fahinta da wayau ni ina nufin ba baki da natsuwa bane ina nufin ki kara kama mutuncin ki da kowa mutuncin mace kimar ta. Nagane may take nufi wanan maganan dashi na bude kunnuwa na a gurin ta kullun nasihan manjo ke nan a gare ni tun ban fahinci mai take nufi da hakan ba har na gane . Mikewa nayi ba tare da nai magana ba na dauki kofi nayi hanyar waje tace ina kuma zaki bazaki zauna kici abincin ba nace ruwa zan debo a famfo. Da na debo ruwan na dawo na dire a gabanta tare da dauko mata abincin data ce inci don nasan tun dan abincin rana data dan taba bata ci komai har wanan lokacin da take kokarin sadaukar da yuwanta ta bani rabon ta inci. Dago kai tayi ta kalle ni tare da fadin yaya kuma kika aje a gabana nace Manjo kici ni a koshe nake wallahi na fada maki naci biski a gidan malle sai dana koshi . Kai ta gyada tare da saka min albarka kamar nice na girka abincin ko na sayo aka girka nace baffa ya kamata ki sakawa albarka shida ya kawo aka dafa. Bude abincin tayi ta ja tsuki don can yake manne a kwano har yayi sanyi kalau sosai tana shirin magana mukaji sallaman Atika a kofa. Tana tafe da kullan abinci ta shigo ta dire a gaban manjo tare da gaishe ta tace manjo biski ne malle tace a kawo maki tasan kya so. Manjo na washe baki tace usse, usse, malle ko ta kyauta min yau tayi min abinda naji dadi sosai ga abinci ga yar nan ta koma goshi na mata kyalli saboda gyara. Atika tace Manjo don ma Fatima bata so gyara aida tasha gyara gun malle to ita fatiman ne idan an mata gyara sai an dauki lokaci bata kara ba. Malama ban fa son kushe kin fini gyara ne ko may na fadi ina hararan Atikan sama da kasa da sauri tace , a,a ni na kai can. Dallah rufe mana baki ke badon Allah yayi ki fara ba ai da bamu san iyaka ba kin gode kin kwaso iyayyen ki duka a gurin fari har makin so ki fisu da kina gyaran jikin ki aida kyaun ki badai nan ba. Bude kulan da Atika ta shigo dashi nayi sai kamshi ya tashi a daki yana daukan ido nace kinga Atika manjo fa bataci komai ba tun kan na fita gidan nan dazun har yanzu don Allah bari ta danci wani abu kada ta fadi muna. Nan na tursasa manjo taci abincin taci abinci ni kuma na hau ba Atika labarin yadda muka kwashe da yaya sadi lokacin dana dawo gidan ina sanda. AMERICA Yana zaune ya mayar da hankalin shi ga computer shi yana aiki so yake ya gama aiki dake gaban shi wani aiki ne daya kawo shi kasan daga england duk da ya kusa kammala aikin kuma akwai sauran kwana uku da yake son karawa garin kafin ya wuce. Wayan shice tayi kara har tana batu tsukewa bai daga ba sai can ya daga wayan ya duba sunan kanin shi ya gani rubuce a fuskan wayan. Receive ya danna kada wayan ya katse tare da fadin habbib ya kayi ne cikin muryan shi dake nuna gajiya da natsuwa. Habbib din yacd haba bros ka shige kwana biyu ko labarin ka ba aji wanan ai sai hankalin mu ya tashi. Yanzun ma hajjaju ne ta kirani tana fada wai kwana biyu ta nemi layinka bata samu ba shine hankalin ta ya tashi. Sai da ya shafa goshin shi ba don zufa ba sai dai don gajiya da aikin da yasa a gaban shi yace wallahi habbib na danyi tafiya ina America sati biyu ke nan nazo wani aiki ne daga ma,aikatar mu. Bros shine babu sanarwa kasa hankalin mum ya tashi kasan fa halin mum a kan mu yace wallahi zan kirata I will call her leter. Gaskiya ya kama don hankalinta ya tashi sosai wallahi kasan kuma ga matsalan gidan nan yanzu dad ya birkice mata sai korafi take min ko yaushe ta rasa gane kan dad a kwanakin nan. For what reson may ke faruwa a gidan ne wani abu ya hada su yana tambaya cikin nuna damuwa. Wai fa akan wanan matar daya aura ne fa yake kokarin juyawa hajiya baya kaji mun dad fa duk yadda suke da mum yanzu akan wata zai juya mata baya. Nasan duk wanan abin ba sherin kowa bane sai , , , , kai habbib mind you togue ka daina shiga zancen mata da miji don Allah. Duk abin dad nasan ba zai taba juyawa hajiya baya ba akan wata matar diba ga yadda shakuwan su yake kai ma wai baka san halin mata bane idan an masu kishiya. Ka daina shiga irin wanan maganan kai na miji ne idan kaji ka bata hakkuri ka kwantar mata da hankali shi yafi. Yace ni wallahi shi yasa ban son wanan auren da dad ya kara ba tun farko don , , , , Kai ni ba wanan ba na fada ma ka daina shiga harkan mata don Allah zan turo maka da kudi ka tura masi gobe ita da dad din kodaya yake ma barshi dai zan turawa dad nasa da kaina . Daga haka ya kashe wayan yana girgiza kai alaman kai mata halin su daya a gurin kishi ba yara ba ba manya ba indai har kan kishine. Shi yama manta da kamanin wanan matar da ake cewa yar uwan su ce dad din nasu ya aura sai kuma ya ja tsuki don bai son abinda zai dagawa mahaifiyar tasu hankali ko kadan don yadda take son su haka suma suke son mahaifiyar tasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:37 - 🀐🀐🀐: YA ALLAH MUNA ROKON KA KA AZA MU HANYAR TSIRA KABAMU IKON TSARKAKE IMANI DA BAUTA A GARE KA TSARKAKKE YA ALLAH MUNA ROKON CIKAWA DA IMANIN KA A LOKACIN KOMAWAN MU GARE KA AMIN YA HAYYU YA KAIYUMU. Alh sani yana kishingide yana kallon labaran NTA na kasa gefen shi hjy maimuna ce a zaune wacce hankalin ta baya kan tv ita. Jin tsukin da yaja ne yasa ta daina latsan wayan hannjn ta da take yi ta kallo shi tare da fadin lafiya ko ? A rayuwana na kijinin hurda da arnakun nan sai dai yanzun boko da wayenwan kai yasa komai zakayi a duniyan nan sai tare da su muddin kabar kasan hausan nan to ka rabu da akidar hausawa ke nan . Shiyasa nake fadawa hajiya yaron nan ya dawo gida hakana tunda ya gama abinda ya kai shi can yau shekara nawa da kare karatun shi. Zaman da yake can kwata kwata bai kwanta min a rai ba na fi son su dawo gida kusa dani idan ma aiki ne akwai ire iren aiyukan su a nan gida nigeria ai. Umm,humm yaya sai nake ganin yanzu umar ba yaro bane ai don akwai sa,annin shi da sukai aure da iyali , kaga wanda ya kai munzalin rikon iyali ai ba za,a ce zaiyi wani abin asha ba yanzu. Kai dai kawai ka bisu da addua a duk inda suke ubangiji ya tsare muna su tare da sauran yan uwa musulmai. Ko banza indai umar ba ya canza bane kaf yaran gidan nan yafi su natsuwa da sanin ya kamata a iya sanin da nai masa a baya. Murmushi jin dadin yabon danshi da tayi yayi tare da fadin Umar kan akwai natsuwa da tausayi wanan haka yake ba karya kika fada ba ga halin sa. Jin shigowan mutum kamar daga sama falon yasa suka daga fuskokin su dauke da murmushi kan maganan da sukeyi na dan Alh din. Kallo daya kowan su yai mata ya hango fitinan kishi a tare da ita gama ga yadda ta samay su a zaune din. Kusan hjy maimuna rabin jikin ta na ga jikin mijin nasu wanda take kokarin bawa juice din shi na zalla diyan icce da yake sha duk dare kafin ya kwanta a matsayin abincin daren shi. Da zaran ya dawo da yamma ya ci abinci ba zai kara cin wani abin ba sai yayan icen don tsaron lafiyan shi da yake yi din wanda har ya saba da hankan yanzu. Sai da hjy jummai ta samu wuri ta zauna kafin ta fara magana da miji nata gani haka yasa hjy maimuna azaman fita daga falon mijin nasu. Ina kuma zaki baki gama dani ba cewan Alh sanin yana mai kallon hjy maimun duk da yasan shigowan uwar gidan nasu yasa zata basu wuri su gana. Kamar ba shi yai magana ba sai kuma ya juya inda hjy jummai take zaune yana fadin kin gan munan yanzu haka maganan umar muke kika samay mu. Uumm, tace dashi ba tare da ta fadi komai sai dai a can cikin ranta fada take da maigidan nasu akan may zai zauna yana maganan danta da wata mace a gidan nan mafarin ya sake masu siri ke nan kuma ko. Juyowa tayi inda suke da hjy maimuna yana fadin baida sanyi dai sosai ko cewa da juice din data kara daukowa zata zuba mashi din. May umar din yayi kuma har kake maganan shi da wata a yanzu irin haka ai kamar wani abin ne ko ? Wani abu kuma hjy ba zanyi maganan dana duk lokacin dana so ba sai dake ke nan, wai may yasa ku mata kuke da karamin tunane ko wani lokaci. Kai tsaye tace maganan da na ni da kai ya shafa bada wani ba a gidan nan ko cikin yan uwa bada wani bare ba can daban. Maimunan ce bare Jummai ? Ta dago kanta da sauri don jin kiran da yai mata ta dan kalle shi jin sunan ta da ya kira ba sakaye don haka tasan ranshi ya baci ke nan. Yaci gaba da fadin idan ma kina tamtamane to ki bari don maimuna ta wuce bare a gurin diyana kin fi kowa da sanin hakan kuma. Ban san da hakan vmba sai dai idan yanzu kike kokarin raba hakan a tsakanin diyan ki da yan uwana. To sanun sarkin yan uwa dadin abin dai kowa nada nasa yan uwan a duniya balle ai min gorin yan uwa a gidan nidai nace al,amarin diyana ni ya shafa a gidan ni kadai. Yace haka kika dai fadi sai dai ni kuma ban lamunce da hakan ba don ba ke kadai kika haifi yaran ba. Ummummm ashe manufar ki ke nan da kike kokarin nisanta yaran ki da kowa to bari kiji kowa yasan ni yasan ni mutum ne mai son raya zumunci. Ganin zasu rikice a falo yasa hjy maimuna bari falon ba tare da Alh sani ya farga da fitanta ba nan dai ta barsu suna kwama rikici a tsakanin su. Part din ta koma ta gyara yaran ta zuwa wurin gwagon su hadiya dake zaune tare dasu a gidan don idan tana da girki tun zuwan hadiye gidan a gurin su take kai yaran su kwana ita kuma taji da dawainiya da maigidan. Yanzun ma data shigo ta samu har yaran sunyi barci a falo inda ta barsu suna cin abinci kafin ta fita zuwa sashen maigidan don gabatar da hidimomin shi na yau da kullun da suke may kafin shiga barcin shi. Gyara yaran tayi kamar yadda ta saba yi kullun sai ta shirya su tsab tare da kayan bukatan su takan goya daya a bayan ta ta rugumay dayan ita kuma mama ta rike mata hannu zuwa part din hadiye dake hade da gwagon ta sarakuwan su ke nan. Suna zaune a falon su suna hira ta shigo da sallama suka amsa mata Amma dake taunan goro kafin shiga kwana tace yanzun nake maganan ku a raina banga an kawo min mazaje na tun dazun nace ko basuyi barci bane. Kamar kullun sai da tayi halin nata watau murmushi a fuskanta tace ina gwago aikin san hali su basu kai tara basuyi barci ba. Yabzu ma na san shiga hadama baban su shan shine na dawo na samu wai har sunyi barci a inda na barsu suna ci abinci. Ba magana yara kamar kasa a gurin barci hadiye kama mata na hannun nata mana taji dadin sauke na bayan ta wa yan nan manyan diya haka tubarkallah dasu kamar su kadai ubansu yake ciyarwa a gidan nan. Amma ta tabe baki tare da fadin ke kama bakin ki kar kisa a saka masu ido kuma a lalata min kimar yara ba,a fada ba sun tsone ido inaga an fada din kuma. Hadiye dake shimfide yaron saman kujera tace yaya ko zasuyi dasu sai gani sai hangeb don Allah ya riga da yayi ikom shi. Da jummai tasan yadda zata kawar dasu tun suna jarire aida ta kawar dasu a gidan nan don wanan matar kishin ta sai ita. Maimuna tace yanzun ma ita tasa na fito suna can suna kwasa da yaya a falon shi daga magana ta hau fadar bakaken magana don kawai Alh yace yanzun ko maganan Umar muke yi dashi shike nan ta hau fada don may zaiyi maganan diyan ta da bare. Da sauri Amma dake ta ya tsunan fuska tace waye bare a gidan nan banda ita da maryama kaji min mata da fada karya rikicin Jummai wani lokacin kamar mai motsi a kai. Tayi ta gama don yanzu na kula shima yayan hali nata ya fara fita kanshi don ya fara gane halin ta ko kuma abinda akai may ne ya fita kan shi ba. Amma ta karasa fadi cikin kunan rai da halin rikici iri na hjy jummai wanda ba gaira ba dalili takeyin shi a kan dan abinda bai kai ya kawo ba a gidan. Sun dan zauna sun taba hira a part din sai lokacin da ta kwatanci hjy jummmai ta bar gurin Alh ta mike tana fadin barin leka wurin maigidan ko sun gama badakalar su. Jummai mai rikicin gangan fada ba naki ba ya zama naki ni har mamaki halin mulkin ta ke bani ko ance mata samun wuri haukane ? Ita dai hjy maimuna bata kara tsunkawa ba don bata faye son maganan kishiyoyin nata ba a gurin kowa, takan ce daukan nauyi ne hakan. Har ta gama shirin ta ta rufo part din ta zuwa sashen maigidan hankalin ta yana ga maganan hjy jummai da tace mata wai ita din bare ne gun yayan mijin su da yake wa a gurin ta. Ba abinda ta tsana kamar mutum ya ci mata fuska irin haka don muzantawa ne ba kadan ba. Ta koma ta samay shi har ya gama abinda yake ya kwanta ta shigo dakin sai da ta tsaya ta kashe kayan wutan dake aiki a falon ta karasa uwar dakin shi. Zaune yake saman sallaya da alama shafa,i da wutiri ya gabatar a lokacin yake addu,a ta shigo dan dago kai yayi ya kalle ta tare da fadin kin rufe kofa da wutan falon ta bashi amsa da eh tunda ban gan ka ba a falo na san ka shige ke nan . Ai tun fitan wanan mara hankalin na shigo daki, mata kamar wata mai kwankwamai a kai ban gane ma Jummai ba a gidan nan tunda na auri maryam halin jummai ya sake baki daya a gidan nan. Yaya laifi fa kayi mata kuna zaman ku na dadi rai daga kai sai ita da yan yaran ku, ka karo mata iyali a gidan don may ba zatai fitina ba da kai ? Ku mata shine matsalan ku ai kada dai na miji yace daku zai kara aure yanzun komai dadin ku da mutum za a jiku da shi. Yau na wuni da murna da farin ciki a gidan mu ba don komai ba sai don jin Baffana yace Addah mu zata zo ganin mu daga malammadori. Fita nayi zuwa gidan su Atika don in sheda mata zun gwagon mu garin misau yau in Allah ya yarda. Na fito da murna na daga gida naji ance ke ina zagi haka kike shirin buge mutane baki ganine ko tsaban rashin kunyar takine ya tashi kuma. Ganin babu mai cetona a gurin yasa nace a tsorace ba gidan su Atika zan shiga ba in fada mata zuwan Addan mu yau na bashi amsa ina dan ja da baya. Uban wa yace ki yi yawon shelan sirin gidan mu a makwabta don kina munafuka ko ashe kece mai kwasan sirin gidan mu kina badawa a gari ? Cikin inda inda nace wa ni wallahi a a ban taba kai maganan kowa na gidan nan wani guri ba ni may na sani da zan fada. Mumushi ya dan sake na keta ganin yau ya sami gamina a waje yadda manjo ba zata jimu ba ya gasa ni yadda yake so. Sai dai kuma yadda yaso inyi din ba hakan nayi ba don ban tsaya mashi tsiwa ba ashe dama iskancin naki a gaban manjo kike yin shi don kinga tana kama maki iya shegen ki a gidan nan ko ? Ban tanka shi ba don Allah Allah dai nake ya matsa in samu in shige tun bai min wani muguntan daya saba min ba. Kina ji ko duk naji kin fadawa wani zuwan Adda sai na balbalaki a gidan nan ko wa yai maki tsaye yau da sauri nace to kawai na dan gwauta shi na wuce. Tun rikon da yai min nake ranan nake matukar tsoron yaya sadin don na dade manjo na shafa min robb a gurin don ciwon da hannun ya dinga yi min. Ina shiga gidan na manta da gargadin da yaya sadi yai min saboda doki na fara ba Atika labarin zuwan Addah da dadin da nake ji wurin ta idan tazo don ita kadai ke nuna min kulawan ta sosai. Mahaifiya ta yanzu ba zan iya tuna dadin ta ba tunda tun ina karama aka rabamu ko hutun danaje gurin ta banji dadin shi ba ga rashin sabo ga kuma matsin mutanen gidan su. Kullun muna part dinta zaune sai kuma idan munje gidan Amma wanda ba kullun ake zuwa ba da kyar nayi satin biyu na dawo Azare. Ashe tafiyan safe adda tayi ina can gidan su atika ashe har ta iso ban sani sai da aka aiko kirana daga gidan mu koda naje ba samu Adda mu ta iso ko. Da murna na , na tare ta hanyar kankamy mata jiki ina fadin oyo yo addana ta rike ni tana fadin kai kai kai Fatima kece kikai wanan girma haka kamar na shekara ban ganki ba. A,a tubarkallah masha Allah yarinya ba inda ta rago mahaifin ta wurin kama wanan ai kamar photo copy din marigayi ne sai dai da yake ke mace ce kindan dara shi kyau gaskiya. Nace Adda yaushe zaki koma halan ? Kaji min ya daga shigowan ki sai tambaya ina dai yanzu ta iso ba kya, barta ta huta ba dai. Manjo na matsu mubar garin nan ne wallahi mu koma azare sai dai don Atika ce ban son barin garin . Na juya gurin Manjo dake kallona ina magana nace Manjo kinga mugun nan ko dazun ya tashi kara masgana Allah kadai ya kwace ni a hannun shi. Da yau sai dai kiga an kawo ni karara a gidan nan manjo tace kina nufin yaron nan Sadi bai fita hanyar ki ba har yanzu. Adda ta kura muna ido tana sauraren zancen mu da manjo tace badai dukan yar nan yaran nan ke yi ba manjo ina fatima ina wanan yaron har da zancen duka a ciki. Kema kya fada dai ni yanzun kullun addu,a nake Allah ya kawo muna mafita a gidan nan mu tattara mu bar masu gidan su. Manjo yanzun ma zancen Fatima ne ya kawo ni gari nan don munyi waya da mahaifiyar Fatima akan tana son zaman Fatima ya koma guri ta. Baki na turo gaba ina fadin ni ba inda zan tafi in bar manjo na ni gaskiya a bar wanan magana Addan mu. Idan kin so ki kama bakin ki kawai ba wanda ya isa ya rabani dake A ruwa sai Allah daga manjo sai Amma ke kirana da Aruwa a duniya kancewa an haifeni lokacin malka sosai ranan da aka haife ni tun asuba ake ruwa har yamma. Wanan dalilin yasa tsufin ke kirana da aruwan da suke ce min ita da Amma yar birni kamar yadda na laka mata saboda abubuwan more rayuwan da na gani a gidan ta lokacin danaje masu hutu. Manjo taci gaba da fadi cikin hawaye yar ita kadai nake gani in tuna da Abubakar a duniya tana debe min kewar ubanta dana rasa sosai a rayuwana. Barin jikin Addah nayi na koma wurin manjo na make a jikin ta kamar a lokacin za a rabani da ita nake ji. Na masan fadi ne kawai manjo ba zata taba bari a rabamu duniya don haka na sake ajiyan zuciya. Don jin manjo nake a raina kamar ita ta haife ni a duniya banda wani wanda na shaku dashi irin manjo na . Don haka nake daukanta komai nawa itace uwa da ubana dana sani kamar yadda kowa yasan dadin mahaifan shi. Jin abinda manjo tace yasa Addah taja bakinta tayi shiru sai dauko wani hiran tayi don dai kawai ta kwantar muna da hankalin mu a lokacin tayi hakan. Don ta manta ina dakin ta kawo wanan magana don a gaskiya yanzun tafi bukatan mahaifiya ta ta dauke ni ko don bayanin da tai mata akan rayuwa na a nan gaba. Ni dai tun wanan lokacin banji an kara ta da zancen ba ban kuma tayar masu ba tunda na nuna ban son zama da mahaifiyata din. Zaman da Addah tayi damu na dan kwanaki zamane na jin dadi a gare mu don da kanta zata girka muna abinci muci sai mun koshi haka yasa na rage shiga gidan su Atikan da nakeyi yanzu. Wanda dama ashe yunwa ne ke kaini gidan ban sani ga gyaran da nake samu ko ban wa Allah wanka biyun nan yanzu dole in yi shi. Don sai dai tace min ga ruwa can a ban daki in tashi inje inyi wanka tu ina ki har nazo na saba da hakan. Lokacin da naga ta fara shirin komawa garin da take aure sai kuma hankalina ya tashi sosai nake ji kamar in bita mu tafi tare saidai kuma ba zan iya barin Manjona ba a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:38 - 🀐🀐🀐: YA ALLAH MUNA NEMAN KARIYAN KA GA DUK WANI ABIN KI DAGA GARE KA , ALLAH KA TSARE MU DAGA HALAKA KA SADA MU DA RAHAMOMIN KA AMIN YA ALLAH, , , , , Amma na zaune saman sallayan data kare sallahn la, asar bata daga a wurin ban tun bayan idar da sallah nata Alh sani da ya dawo kasuwa a lokacin ya nufo part din nata. Jin muryan shi yasa ta dago kai cike da farin ciki tana mai amsa mashi sallaman shi a cikin fara, a da sakin fuskan irin na da da maaifiyar shi. Yayin da har saida ya samu guri taga ya zauna hankalinta na a kansu tana duban su shi da yaran biyu da ya riko ma hannu cikin so da kauna kamar kullun . Hannu ta mikawa yaran su zo inda take sai yaran suka noke alaman basu zuwa gurin ta a lokacin tace . Lalai yau don kunga uban ku shine zakuyi min butulci irin haka har da kai hussaini da nake ganin kafi dama a gurin kyuya ? Shi wanan dama zubin wan sa ne sak yz kwaso wurin miskilamci bai ragewa umar komai ga hali gashi suna da zube dashi sosai da umar yai aure sai ace yaran nan nasa ne wallahi. Alh sani yayi dariya don jin abinda ta fada yana shafa kan yaran yace a she bani kadai ke ganin hakan gare su ba hajiya idan sunyi wani abin sai su tuna min da umar lokacin da yake karami. To abin ne bai faduwa a gidan nan sai ya zama karamin magana tunda uwar su umar din na fadin yaran ta kaman su daban sun fi kowa zubin kyau a gidan nan. Cikin dan tsuke fuska cike da damuwa yace Hajiya ko bata son a danganta ta da yaran nan yaya zatayi tunda Allah ya nufa zasu fito a tsatso daya. Halin jummai yanzu ya canza ga baki daya sai addu,a amma ni ban taba ganin kishi irin nata ba a duniya mace sai kace bata tunanen makomar ta. Babu garin Allah da zai waye yanzu Jummai bata tayar min da hankali ba a gidan nan don kawai na karo mata abokan zama kamar da can da zan aure ta nayi mata alkawarin ban kara aure ne. Ki duba yanzu yaron nan dake can yayi zaman shi yaki ya dawo gida tunda ya kare abinda yaje nema a kasan ai ya kamata ace ya dawo gida yanzu dai. Amma ita Jummai taki gane abinda nake nufi da dawowan nasa gida a kan lokaci yanzu shekara biyar ke nan fa da ya gama karatun sa wai sin bashi aiki a can england din. Duk wani aiki da zaiyi can yanzu akwai makamancin shi a na kasan amma ita ta ki ta gane hakan sun hada kai dashi duk lokacin da zan mai maganar gida sai ya kai karana a gurin ta nasan kuma ba komai bane sai dan abinda take ganin yana dan turo mana nan ne yake tsone mata ido kawai. Tun da ya fara magana ido kawai ta tsura mai tana sauraren shi har lokacin da taji yayi shiru ga maganan shi ta sauke ajiyan zuciya tana fadin. Nima dai wanan zaman da yaron nan ke yi kasan masu jajayen kunnuwan nan bai kwanta min a rai ba sam duk da na gari ai gida aka sanshi ka gama abinda ya kai ka sai kuma ka dawo gida a san ka gama amma may ye amfanin zaman shi a can shi ba iyali ya ajeba. Balle a ce don su yake can zaune wani kasan kuma da hakan ne ma ai hankalin kowa zai fi kwanci dashi koda yana can din. Sai dai ina ganin ita uwar bata tunanen hakan gare su don dan abinda suke aiko mata din dashi nan tana famkama wa mutane ita ta iya haihuwa. Kamar tasan abinda Allah zai mayar da sauran yaran nan gaba idan Allah ya raya muna su ai shi mutum ba a gama hallitan sa sai ranan da ya mutu. Zaman su gida shine kimar mu da cikar kamalan a garin nan don ba abin alfahari bane ace danka ya tsabbari ya koma wata kasan na uwan duniya ba tare da iyali ba. Alh sani ya sunkuyar da kanshi kasa yana nazarin maganan tsohuwar daya girgiza mashi zuciya ya kasa furta komai ga hakan . Sai dai a zuciyar sa yana nasawa dole ne yaran nasa su dawo gida yanzun don gaskiya mahaifiyar tasu ta fada yanzun don haka zai dauki mataki a kan komai. Da haka ya tashi yai mata sallama tare da yaran ya nufi hanyar fita daga part din cikin sanyin jiki bayan yai wa mahaifiyar tasu sallama. Yana aiki a shago kira ya shigo mai bai dakatar da abinda yakeyi ba don kada lissafin ya kubce mashi sai da wayan ya tsinke inda ba lokaci wani sabon kira ya kara shigowa again. Don haka ne ya dakatar da aikin ya rarumi wayan nasa a ciki fushi sai dai ganin wanda ke kiran shi ne yasa ya katse fushin yana mata sallama. Tare da fadin Allah ya barmin min antyna ta kaina ya gida ya waje su inna kuma ? Tace Amadu lafiya ba lau ba da sauri ya tare ta yana fadin anty may ke faruwa a gidan ? Tace wallahi jikin baba ne yaki dadi yau kwana uku ke nan yau ma dai jikin nasa yafi tsanani gaskiya. Cikin kidima ya furta subbahanallahi anty shine ba wanda ya kirani ya fada mi ko jiya fa munyi waya da Abu bai fada min komai ba. Tace baban ke fadin kada a fada ma a tayar ma da hankalinka zai samu lafiya da ikon Allah sai dai kuma har yanzun jikin ba dama gaskiya. Yace yanzun dare yayi anty amma gobe da yardan Allah da safe zan shigo garin sai a zauna da shiri idan nazo zamu wuto asibiti dashine don wanan karon ba zan yarda da zancen a barshi a gida ba. Asibiti zamu zo dashi gobe a duba shi tace Allah ya kaimu Amado gaskiya yanzun kan dare yayi sosai sukai sallama ya kashe wayan lissafin da bai tsaya ya karasa ba ke nan ya nufi gidan uban gidan shi wanda yanzu ya zamay mai kamar mahaifi a gare shi. Bai samu kowa a farfajiyan gidan ba don haka ya nufi hanyar shiga gidan kai tsaye Ahmed da yanzu ya goge ya zama dan birni sosai ga ilimin bokon daya samu har master sai da yayi ga na arabiya. Don hakane yake aiki da ilimin shi duka biyu wurin gogayya da al,amuramshi na kasuwanci har kasan waje yake fita ya odo masu kaya irin wanda suke bukata a kasuwancin su. Daga kofa ya tsaya yana kwala sallama bai yarda ya shiga ba kai tsaye duk da yasan baida shamaki yanzun a gidan. Sallama biyu gana uku yaji zazzakan muryan salma na amsa mashi sallaman nasa ko ita yayi dace ne ta fito sashen Amma a lokacin wanda ba kasafai take zuwa ba sai idan taga dama takan dan je suyu barkwanci da tsohuwar. Salma na farin cikin da zuwan Ahmed gidan su kodai da take kokarin boye hakan a zuciyar ta bata son wani ya fahinci hakan musaman ma hajiyar su data dauki karan tsana ta sakawa yaron. Ahmed yayi aure farko a nan kano inda ya hadu da wata yarinya Alh sani ya tsaya mai har akai auren shida su Amma, gurin haihuwar farko matar tasa Allah yai mata rasuwa ta bar yaron da ta haifa har wanan lokacin bai kara wani aure ba. Ita salma da farko bata dauka son Ahmed takeyi ba sai daga baya ta fahinci ta fada son Almajirin gidan nasu kamar yadda hjyn su take kiran shi idan ya bata mata rai. Ya fahince ta sarai sai dai bai yarda ya bata fuska ba ko kadan sanin halin mahaifiyar ta da yayi ba mutunci ne da ita ba ko kadan . Don hakane yake kara kaucewa duk wani abinda zai hada shi a gida Alh sani da ita balle kuma salma ba irin choce din shi bace don yana son mace mai addini da tarbiya ba wace zata iya yiwa babba rashin mutumci ba kamar uwar ta. A cikin dakewa yace ke Alh yana kusa ba tare da ya bari magana komai ya shiga tsakani su a gurin tace yana falon shi a sanyaye. Ya wuce baiko kara waigo ta ba yabarta a tsaye tana kare mai kallo murya mahaifiyar tane take fadi salma yaya haka kuma ? Salma tayi saurin fadin ni da dan rainin wayau nan ne daga zuwa yana tambaya wai Alh na ciki ne kamar ya aje ni a nan. Wanan yaron ai gani yake wuyan shi yayi kauri yanzun shiyasa yake ganin kamar daidai yake da kowa a gidan nan. Salman tayi kwafa ta wuce ba tare da ta tsaya jin sauran maganan uwar nata ba don zata iya jin abin haushi a wurin wanda zuciyar ta ba zai so ba. Ahmed ya tsaya daga falo yana ma Alh salma sai yaron wurin hjy maryam ya leko don ganin maima Abban su salma a lokacin. Yana ganin Ahmed yaron ya washe baki yana fadin kazo min da keke na Ahmed yace bako gaisuwa boy don haka suke kiran yaron dashi. Yaron yace ina wuni yana dariya sai daga ciki Alh yai magana yana fadin ba zaka bashi wuri ya shigo ba ka tsare shi da magana. Yaron yana kokarin juyawa Ahmed din ya kama mai hannu suka shiga falon tare inda baya salman da ya kara yi ne ya shigo falon. Gaida dattijon yayi da wuni wanda ke mashi kallon mamaki don ganin shi gidan a wanan lokacin do basu dade da rabuwa ba. Wuri ya samu a kasan kafet din ya zauna kamar yadda ya saba yi idan ya shigo falo ya fara gaida Alh dake mai kallo mamaki har wana lokacin a fuska shi Baya gama gaisuwan su ne Alh ke tambayan shi ko lafiya yace Alh da sauki yana gyara zaman shi a daidai lokacin da Alh ke tambayan shi may ke faruwa hjy jummai ta shigo falon tana cika tana batsewa. Ahmed yace yanzu nayi waya gida suke fada min mahaifina baida lafiya sosai shine nake son gobe idan Allah ya kaimu in yi asubancin zuwa gidan in dubushi. Sai Alh sani yace ka duba shi kodai azo asibiti dashi ai asibiti yakamata kaje ka dauko shi kuzo zai fi. Yace haka nake so idan Allah ya kai mu din idan naje yace subbanallahi ubangiji ya bashi lafiya Allah yasa kafarane hakan Ahmed yace amin. Hajiya jummai dake zaune kanzil bata ce dasu har addu,an da Alh sani yayi bata karba ba sai wani kada kafa da takeyi a saman kujera inda take zaune. Alh sani ya juya wurin ta yana fadin Ahmed ne yazo yanzu ashe mahaifi shi ba lafiya kuma yanzu fa muka rabu ance baya baida kadan? Tace Umm,wummm Allah ya sauwaka taci gaba da kada kafan ta da takeyi su kuma suka fita batun ta suna magana akan ciwon tsoho. Addah ta koma ta barmu da kewan ta bayan tayi muna sati biyu tana duban mahaifiyar ta kamar yadda take muna tun lokacin da mukazo misau din. Tun tafiyan ta sai gidan ya koma muna babu dadi zaman dai ga munan ne a cikin sa haka yasa na dan fara shiga gidan su Atika don in debe damuwa a raina na rashin Addah. Tun ina kunyan su na kaurace masun da nayi na kwana biyu don zuwan Adda din har yakai na sake jikina mun koma kamar yadda muke a baya don banga wani alaman sauyin fuska ba a gare su kaf gidan. Sai dai yanzu ina zuwa makarata ban yarda in daga kafa da zuwa school din tunda Addah tayi min nasiha akan hakan. Irin nasihohin da taimin ne ya ratsa min jikina na daina fashin zuwa karatu har da islamiyan da Atika ke zuwa yanzu a tare muke zuwa kullun. Haka yasa wani irin natsuwa ya fara shigana a hankali wanda ban san inayi ba sai dai nakanji mutane na fadin zuwan Addah ya canza ni kwanan nan. Nidai sai murmushi nake masu a dole ina son fita daban da yaran gidan baffa da Addah tace tana son inyi ga kuma manjo kamar zuwan Adda tazo mata da maganine don ta samu lafiya yanzu sosai ba kaman can baya da take a rabke ba. Don Addah taja min kunne sosai kan in kula da Manjo don kada in rasata don in manjo ta halaka ni zanfi kowa shiga damuwa. Banso abinda zai taba manjo har yakai ga halakata don haka na daure ko bayan wucewan Addah ina kula da kakata yadda ya kamata kamar yadda na Adda tana mafa data zo. Sai ga tsohuwa tana samun sauki sosai ashe dama damuwa da kuma yunwa ne yake batun halaka yar tsohuwar a gidan. Ko baffa Adda bata kyaleshi ba akan kula da mahaifiyar tasu haka yasa yanzu duk dare sai ya dan sawo mata dan abin kwadai ya miko muna da yake dakin mu ba a cikin part din matan shi yake ba mu muna daga waje farkon shigowa gidan. Wani lokaci dan kunshin nama ko burodi da kayan shayi ba tare da iyalin shi sun san yana hakan ba don idan sun sani ba zasu bari ba. Ranan da baida zarahi kuma yakanzo yai tabata hakkuri kamar wanda zaiyi kuka a ranan hakan ba karamin fahintar dani darajan iyayye a guri da yayi ba. Kamar yadda na canza hakane yake sa ko na dan shifa gidan su Atika ban dadewa koda yaushe kazo gida zaka samay ni a dakin mu ko ina wani aiki wa kakata. Sai dai haka bai hanani aikin wahala ba a gidan Baffa din inda hakan ke bata ran manjo tayi fadan haka din har ta gaji basu daina ba. Don haka na taso aikin wahala baya damuna ko kadan sai dai abinda ban sani ba a gamay dani ashe kafin tafiyan Addah sun zauna sunyi magana a kaina. Inda Adda ta zaunar da manjo cikin hikima da dabara ta fahintar da ita illan barina in tashi a gidan baffa da suka hango min itada mahaifiya ta. Wanda hakan yasa jikin manjo yayi sanyi don jin ance zan iya lalacewa ko samarin gidan Baffa su lalatani yasa tsohuwan saurin yarda da shawaran su din wanda bata fatan haka a gare ni . Ni da take gani yanzu farin cikin rayuwanta kamar don ni ni kadai Allah ya bar muna ita tace ba wani gardama duk sanda mahaifiyata ta shirya tazo ta dauke ni. Ta Amincr da zamana a gurin ta muddin rayuwana zai inganta a can kano din da wanan maganan suka tsaya har ta tafi. Yadda Ahmed yaje gida ya samu mahaufin shi hankalin shi ya tashi sosai inda ba bata lokaci ya dauko shi zuwa kano ko ina bai tsaya dasu ba sai asibiti Hjy maimuna bata sanda zancen ciwon mahaifin Ahmed ba sai washe gari takd ji a gurin gwagon ta da maigidan su ne ya fada ma mahaifiyar shi zancen. Batai kasa a gwiwa ba wurin kiran Ahmed din tana tambayan shi jikin mahaifin nasa lokacin suna hanyar kano daga katsina. Ya dauki wayan bayan sun gaisa take fadin Ahmed ashe abinda ke faruwa ke na yanzun nake jin wanan maganan a gurin gwago. Yace hakanane hjy yanzun haka muna nan hanyar kano zan shigo dashi asibiti tace subbahanallahi ashe jikin sosai ne Allah yabashi lafiya ya kawo ku lafiya ta kashe wayan. Ajiyan zuciya ya sauke yana mai jin dadin kiran da taimai din don ta kula da abinda ya shafe shi sabanin hjy Jummai da agabanta ya fada ma maigidan nasa amma ba wani damuwa data nuna akai. Sai dai shi Alh sanin yana ta kiran su koda yakai can ma sai da sukai waya da majincin kan shine yace azo dashi asibiti a duba shi. San nan tsohon ya yarda zaizo don yana ganin zai dorawa mutane lalura ne kaishi can din da Ahmed yace zaiyi. Shine Ahmed din ya kira Alh sani don yaiwa tsohon magana ko zai yarda su zo dashi asibitin. Suna zuwa ba,a tsaya wani abuba gado aka basu inda aka daura mai drip aka fara gwaje gwaje akanshi. Ana haka hankalin Ahmed a tashe saiga hjy maimuna sunzo ita da hadiye da Amma niki niki da kayan abinci da sauran abubuwan bukata har Alh sani kanshi yana asibitin akan tsohon don kafin su kawo kano ya gala baita sosai. Sai zuwan su ne ma ya tuna da abinci da bai sawowa sauran mutanen da suke tare ba a lokacin yaji dsdin hakan inda ya kara ganin mutunci da kimar hajiya maimuna di sosai a idon shi. Haka sukai ta zirga zirga akan tsohon kafin agane abinda ke damun tsohon wanda sai an mashi aiki dole akace . Hjy maimuna bata gaji ba wurin hada masu abinci kullun sau uku a rana Ahmed din ke zuwa ya dauko ko ita da hadiye su kai masu asibitin. Inda take shan zagi sosai a wurin kishoyin nata sai dai hjy maryam takan dan leka asibitin wani lokaci ta gaida su sai dai su basu sani ba. Hakan ba karamin Alheri ya jawowa hjy maimuna a wurin maigidan nasu don bayan kimar da tayi har da alheri take samu wurin yin hakan ga maigidan nasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:38 - 🀐🀐🀐: YA ALLAH KA SAKAWA IYAYYEN MU DA GIDAN ALJANNA, KASA MUTUWA TA ZAMO HUTU A GARE SU ALLAH KA RAYAWA KO WATA UWA DAN TA TAFARKIN ADDIN MUSULUCI KAYIWA ZURI,A ALBAKA ALBARKAN ANNABIN RAHAMA AMIN INA TAYA KOWACE UWA FATAN ALHERI GA ZURI,ANTA HAPPY CHILDREN DAY,, , , , , , , , , , Ina kwance dakin mu barci ya soma daukata hayaniyar dake tashi daga tsakar gidan mu ne ya falkar dani dagaz barcin dana soma din a lokacin. Dagani har Manjo saurara abinda ke faruwa daga wajen gidan mukayi wanda hayaniyar ba iya cikin gidan mu kawai ya tsaya ba har wajen gidan muke jin hayaniyar yana tashi. Hankali tashe muka fito daga dan dakin mu don ganin abinda ke faruwa a wajen kada a rutsa damu a ciki. Mun isa wurin daidai lokacin da wani mutum ke fadin ku dai bakuyi halin mahaifin ku ba mutumin kirki duk unguwar nan kowa yasan mutumin arziki ne. Don ba abinda ya taba hadashi da wani a cikin unguwar nan na assha amma ku, kun addabe mu kun hana mu zaman lafiya. Kuna nema ku gurbata muna tarbiyan yaran mu a cikin unguwa yanzu may ye amfanin irin wanan ki dinga jawo muna mazan banza a unguwa suna zuwa suna tayar muna da hankali a cikin unguwa. Yanzu may ye amfani irin wanan abinda ya faru daidai lokaci muna guri yake ta rabtako bayanin shi a hasale. Manjo ke tambayan na kusa da ita abinda ke faruwa duk da matar bata sheda manjo sai fadi take . Wallahi fa wanan fitsarar yarinyan gidan nan ne saliha tana tare da wani a mota suna iskanci ashe kuma ta gyayaci wani shi fada ya kaure a tsakanin su har da fashe fashen kai . Salati Manjo da muke rike da hannu juna sarke da juna ta saka tare da fadin kai wanan yarinyar batai gadon arziki ba nasan fitsaran yaran nan zai kaisu ga hakan. Da sauri ta tasa keya na muka koma daga ciki don kada mu karasa jin abin takaici yau ace jininta ne akewa wanan shedar haka ba dadi ji a bainar jamma,a. Duk da naso in tsaya inji kan maganan don ban fahinci komai da matar nan ta fada muna ba sai dai ba yarda zanyi dole in bi manjo mu koma ciki tunda haka take bukata din. Shigar mu gidan ba daki muka shiga ba daga waje tsakar gidan muka tsayawa tayi waje anan tsakar gidan tana surfa masifa tare da nuna yaran halin iyayyen su mata suka biyu ba jinin ta ba. Har tayi ta gama basu kulata ba da kyat na jata zuwa dakin mu ranan dai ina ganin batayi barcin kirki ba saboda bacin ran abin kunyar da jikanta ta jawo mata a gari. Washe gari da safe kamar yadda baffa ya saba zuwa ya gaida manjo kafin ya fita yauma haka ya shigo daga kofan dakin mu inda muna ciki kwance don sanyin da akeyi. Mukaji muryan shi a sanyaye ba kamar kullun ba shima dai ko ba a fada ba nasan da bakin cikin abinda saliha tayi jiya ya kwana dashi. Ciki ciki manjo ta amsa mashi jin hakan ya bani haushe don lokacin wayau na bai kai ba don haka banga laifin baffana a cikin maganan ba sai laifin iyayyen su mata da basu son aiwa diyan su fada naji. Don haka na amsa mai da karfi yadda zai fahinci ba barci mukeyi ba a dakin hakan yasa ya cire takalman shi ya shigo dakin da ganin yanayin sa yana a cikin damuwa sosai. Ya samu wuri ya fara gaida mahaifiyar tashi ya samu ta karba mai da kyat tana cika tana basarwa sai dan shiru ya biyo a dakin ganin haka yasa na fara gaida shi da kwana. Sai lokacin ya dan sake fuska yana fadin fatima kun tashi lafiya yaya daren kuma na amsa da Alhamdullahi ina kokarin tashi don in fice a dakin don ba zan so manjo tai mashi magana ba a gabana. Ya dan dade a dakin kafin ya fito ranshi bace ya fice daga gidan duk da iyalin nasa duk suna waje bai samu wanda yai mashi a dawo lafiya ba daga cikin su. Sai ni dake tattara kwanukan da akai amfani dasu a daren jiya don in wanke nake fadin Baffa a dawo lafiya yace dabi tare juyowa Amin yar albarka. Wanan kalman yana mun dadi idan yana fada min hakan bayan fitan shi baiko gama ficewa ba naji muryan mama saude na fadin wa yanda ba,a sawa albarkan ba ace su mutu. Ina jin ta ban dago ba sai danaji muryan yaya hashimu yana fadin ai wanan shegiyar yatinyar iyayi ne da ita da sanabe ya fita baicewa kowa komai ba sai itane mai mashi a dawo lafiya. Haushin maganan shi naji nace babu ruwan kowa dai dani tunda ba mutum nacewa hakan ba dama yafi kowa zama dan iska a gidan. Don sai yayi kwanaki bai leko gida ba yana can gurin shaye shayen shi ko dabanci da yakeyi aiko ban san ya taso ba yana bayana sai jin gau gau ya sharara min mari har biyu a kumatu na. Wani irin kara na sake daya ruda gidan wanda yasa manjo yin tsale daya sai gata waje daga dakin mu tana fadin kai kai may ye hakan may taima ka doke ta ? Yace ko zaki rama mata ne kin wani fitowa kina tambaya a tsawace tace nace may taimaka ka doke ta da safen nan haka ? Bai ankara ba yaji duka a jikin shi dim dim sake baki yayi yana mata kallon mamaki ta juya tare da ja min hannu tana fadin bar dan banza wanke wanke ma ba zakiyi ba su da suka bata su wanke abinsu ba baiwa na kawo maku ba ai a gida. Muna shiga dakin daki tace garin nan zaki bari maganar Addan ku ya soma zama gaskiya zaman ki a gidan nan ba zai yuyu ba don yaran nan suna iya illanta ki wata rana. Cikj turo baki nace ba nace maki mu koma misau ba kin ki tace bana ki bane A ruwa lafiyata nake nema a nan idan bashi ba may zai kaini zama wannan gidan ina ganin bakin ciki tunda baffan naki bai iya tsayawa ga iyalin shi. Nace manjo may ye laifin baffana a nan dole fa ya fita ya samo abinda za a ci tace nasan da hakan. Matan kirki ne dai bai aurowa diyan shi ba tun farko ai wanan halin daga gun uwayen su suka kwaso shi nidai yanzu so nake yar nan tazo ta tafi dake kano wurin ta hankalina zaifi kwanci gaskiya idan kin daga daga gidan nan. Da sauri na dago kai tare da fadin kano kuma manjo ni dai gaskiya ban zuwa kano ki mayar dani misau mukoma can ko gurin Addah. Kano gidan da basu son bako gidan da ba,a fita kullun ana daki gidan da suke fada kullun ni gaskiya ban son kano din nan manjo ko kadan. Bata tankani ba sai dai shirun da tayi tana tunanen tunda nace ban zuwa kano sai dai ta hakkura ta koma misau inda muka fito duk da gidan namu yanzu duk ya lalace yana son gyara yana daya daga cikin abinda ke kara maga gwiwa da komawa misau fin don gidan ya tsufa sosai. Da taji na matsa da mita akan kanon sai tace to ai shike nan tunda bakya son can din sai muyi hakkuri mu zauna a nan din kafin Allah yayi muna mafita. Rayuwan gidan Alh sanj haka yake gudana a cikin iko da nuna isa a gurin hjy jummai don takaman da take itace mai gida ko banza yaranta sun kawo jiki. Hjy maimuna bata biyewa duk wani barazanar su da suke son janta da tashin hankali don ganin sun hanata jin dadin gidan mijinta. Ranan wani laraba tsotsayi yakai tagwayen hjy maimuna wurin motar da yaron hjy jummai ya aiko mata dashi a cewan ta data fada ma yayan nata wai mota daya Alh ya aje mata ita da kishiyoyin ta duk wace zata fita sai a ciki zata fita ita kuma bata son hakan da akeyi tunda yana da karfin da zai sayawa kowa motar hawa . Jin haka dan nata yace kada ta damu indai don mota hawa ce ba matsala zai saya mata mota har ta mance da sunyi hakan kwatsam sai ga mota ranan ta iso wace ta dauke hankalin kowa a gari. Shine yau yaran suna wasa sukaje gurin motar ba tare da sanin kowa ba suka shafa farin kala wa motar da sukai rubutu. Ai kuwa da yar ta ta fito ta gani ta koma ta fada mata ga yaran can a gurin motar ta suna rubutu ta mike a sukwane salma na kiranta amma bata tsaya ba ta fice. Kallon yarinyar salma tayi tare da fadin may yasa kika fada mata bayan kin dan halin hjy da rashin hakkuri. Hjy maimuna da sauran mutanen gidan suka jiyo ihu yaran cikin tashin hankali suna tafe tana bi tana shadi da zagin su. Uwar su suka zo suka rungumay a gigice hakan baisa ta barsu ba sai fada take tana kokati dukan su a gaban uwar. Muryan Amma ne ke fadin amma wanan matar baki da tausayi wanan duka hakan ga wa yan nan yara kananu ko mutuwa na tsoron idon mahaifa. Maganan tsohuwar bai sa ta daina abinda take shirin yi ba ga kowa tsaye cirko cirko yana kallon su ta sake daga hannu da niyar takai masu duka a jikkn uwar . Lokacin ne hjy maimuna tace kada ki soma ki kara taba min yaya don abin naki da biyu kike dukan su . Turus tayi tana kallon ta da mamaki don jin kalamin nata tace ni zaki gwadawa haihuwan yaya a gidan nan tunda kafin kizo na haifi yayan da ake cin moriyan su. Don wa yan nan yaya naki yayan baya taka kushewa har yayane a gidan nan tun kan kizo duniya nasan haihuwa nasan da hakan ai hjy sai dai yanzu ai kowa ya sani ko ? Ke ko don maganan wanan tsohuwar ai ke barsu haka komay sukai maki tunda ta haifa maki mijin da kike kurin kin haifi yayan naki dasu. Maimuna ni kike fadawa hakan kan wa yan nan yayan naki to bari kiji ko kadan ni din nan a cikin gidan nan dake da yayan da kike ganin kin kutso kin haifa ba abakin komai kuke gare mu ba . Kuma ki kiyaye rashin kunyanki gare ni, don ba zai haifar maki da alheri ba nan gaba shiga tsabgata fitanane gare ku dake da diyan ki. Don haka doso ni ba abinda zai haifar maku sai karin bakin jini da kiyayya a gidan nan ba ruwana da yayan ki don dake har su baku a gabana don baku tsare min komai ba a rayuwa ta don haka duk ranan da suka kara shiga tsabgata dukan dayafi wanan zan masu. Tabe baki hjy maimuna tayi tare da fadin a baki ke nan ba amma kowa nan yasan da mun tsone maki ido a gidan nan duk da suna diyan taka kushewa. Don da kin san da zuwan su a baya da baki bari sun fito duniya ba da kina da ikon yin hakan tana fasin haka taja hannun yaranta zuwa part din ta don ta yi masu wanka saboda kukan da sukayi duk sun yi zufa ga majinan wahala yana tsiyayo masu a hancin su. Sai bayan shigewan hjy maimuna ne Amma ta matsa da tambayan abinda yaran sukayi take fadi yara kanana sun san hassada da kishi idan ba turasu akayi ba may ya kai su wurin motata su zane min ita da rubutu. Amma tace yanzu akan mota yar nan kikaiwa yaran nan dukan a kawo ruwa haka waye baisan halin yaro ba tunda duk nan mun haifa mun sani. Idan kuna magana ku dinga sanin abinda kuke fadi kada zafin zuciya ya sa ku aikata abinda ba daidai ba tace yanzu hjy kada in hukunta su ke nan gobe ma su koma ko ? Wanan irin hukunci naki yayi tsauri da yawa yaran nan har guda nawa suke su ina suka san wani abu ai tsawatawan yafi wanan duka don in yaro ne gobe ma komawa zasuyi wurin. Salma ne ta fito tana fadin haba hjy tunda kin dauki mataki ki bari hakana mana tana jan hannun ta don su bar gurin. Amma tayi kwafa bayan tafiyanta tace aidaiyi hasara a nan babba bai san girman shi ba haka nina taba ganin hakan. Alh sani daya dawo sai baiga yaran shi sunzo taron shi ba yake tambayan ina yan biyu sai dan gurin hjy maryam yace mama ta dukesu tun dazu suna barci. Duka kuma mai sukai mata ta duki su kuma ya tambayi yaron da mamaki yaron yafara fadin don sun rubuta A ga motar ta. Kuma akai fada da mamu da Amma da mama akai tafada daddy wani iri yaji a ranshi ya kama hannu yaron suka shige. Bai leka ba sai lokaci da ya gama abinda yake ya shiga part din hjy maimuna din yaran suna kwance har lokacin suna barcin wahala don ba,a taba dukan su irin haka ba tunda suka zo duniya. Hjy maimuna dake zaune a gefen su tana duban wayan ta ta dago kai tana amsa mashi sallaman shi tare da mashi sannu da dawo wa ya amsa yana fadin yanzu samir ke fada min wani magana yana kai hannun shi ga jikin yaran yana dan tabawa a hankali zafin da yaji jikin yaran yayi ga kuma shartin bulalan a jikin su yasa yace wai yanzu a kan mota tayi masu wann dukan ? Hjy maimuna tace akan mota tayi masu duka ashe ni ba ko tsayaji abida sukai mata tunda da biyu ta doke su tunda tana da manufa akansu ta fadi kowa yaji. Murmushi irin na manya yayi tare da fadin amma jikin yaron nan ya kamata a kaishi asibiti don jikin yayi zafi sosai gaskiya amma ina zuwa. Sai ya daga waya y kira Ahmed daya dauka Ahmed din na gai da shi bai tsaya amsawa ba yace kana ina ya bashi amsa da gani nan hanyar gidana . Yace in ba damuwa don Allh ka biyo nan ka dauke ni mukai yaran asibiti basu da lafiya Ahmed da sauri yace subbahanallahi gani nan zuwa Alh. Ba fi yan mintina ba ya bugo ma Alh waya gashi a kofar gida yace ya shigo ya kama mai yaro guda zuwa waje sai gashi ya shigo yana gaida hjy maimuna tare da mata jajen ciwon yaran. Lokacin da zasu fita da yaran yar guri hjy jummai ta gansu itace taje tana fadawa uwar tace su dai suka sani duk abinda zaiyi ya dade bai yi ba. A asibiti sun duba yaran inda suke son bayanin abinda ya samay su bai boye ba yace dukan su akayi likitan yace ayyah yara kanana haka da duka irin wanann yana kara duba jikin tare da tausaya masu. Sai baya an gama basu treatment ne sun fito Ahmed ke fadin Alh wa yai masu wana dukan haka kamaf ba tausayi dan murmushi Alh ya sake a fuskan shi tare da girgiza kai yace Jummai ce da wana haukan don sun taba mata mota wai . Innalilahi Ahmed ya furta shima yana girgiza kai tare da fadin dukan yayi yawa wallahi Allah ya sauwaka ranshi ya baci sosai da hakan daya ji yana mai tausayawa hjy maimuna da yaran ta kan matsin da suke gani a gidan. Basu dawo gida ba sai da suka biya da yaran ya sai masu abubuwa suka juyo zuwa gida suna lafe jikin mahaifin su don wahala. Shigowan su bai kai su gurin uwar su ba dakin Amma suka wuce da yaran nan ya samu Amma da tunda abin ya faru take cikin bacin rai ganin shigowan su da mahaifin su take fadin gaku kamar fita kukayi man ? Yace daga asibiti muke da yaran jikin nasu ne ya dau zafi sosai yana kokarin zama yake kuma ciro wayan shi daga aljihunn shi. Wayan matan ya kira daya bayxn daya su samay shi a part don mahaifiyar shi zan iya cewa kowa yasan kiran da ake masu din don haka ko wace tazo da shirin ko ta kwana a cikin su. Hjy maryam yar sari ka noke ta fara shigowa sai hjy maimuna hjy jummai itace tazo karshe tans cika tana batsewa. Yana zaune da yaran sun lafe a jikin shi don basu da walwala shi mara lafiyan har yayi barci a lokacin rike da goran yought da aka saya masu. Wuri ko wace ta samu ta zauna akan kushin sai maimuna dake kasa can gefe daga kofan shiga kuryan dakin Amma. Kallon inda take zaune yayi yace kira min hadiya ba tare da ta amsa ba ta mike daga dakin zuwa kiran hadiye dayace tayi. Sai gasu tare da hadiyen sun shigo falon kowa ya samu wuri ya zauna kamar yadda sauran sukayi. Dan gyaran murya yayi tare da fadin Amma na dawo gida dazun banga yan biyu na tambaya sai Samir ke fada min wai hjy ta doke su yau. Shine ban gane kan dukan ba hjy nake son karin bayani ga abinda ya faru don ban fahinci maganan yaron ba sai kuma gashi naje parr din ita maimuna na samu yaran akwance ba lafiya yanzu haka daga asibiti muke dasu shine kikaga mun shigo nan . Hjy takatse shida fadin nina duke so kan barnan da sukai min a motata kuma uwar su ta nuna min niba kowa bace a gidan nan tunda na daki yayan ta. Akan mota kika dake su haka jummai kashe su kike son yi komai don dukan yayi yawa ko ni na taba kama wani yaro a gidan nan nai mashi makamancin dukan nan. Nan aka fara cacan baki da ita don cewa tayi kan dan dukan danai masu kake kokarin kare su ko ? Ko banda halin da zan dauki mataki akan yaro a gidan nan ne in sani don ban gane manufarka na tara mu a nan ba in wani abu ne muyi shi daga ni sai kai mana don in akwai abinda taki jini shine fada gaban wani. Don suba yayan mai ke nan bari kazo nan ka turke ni ko tunda ta zama yar gwal ita da yaran shine hjy maimuna ta saka baki suka fara musayar kalamai a tsakanin su. Tsawa ya daka masu tare da yima jummai kwakwaran kashedi akan duka irin haka yace ya kafa hujja ne a gaban mahaifiyar shi. Wanan fadan yana daga cikin abinda ya kara saka bakin cikin maimuna da yaranta gurin hjy jummai da duk wani nata. ZAINABU IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:38 - 🀐🀐🀐: JUMM,AT MUBARAK YAN YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA SADAMU DA ALHEREN DAKE CIKIN WANAN RANAN MAI ALBARKA YA KARE MU DAGA SHERIN DA KE BAYAN SA AMIN, , , , , , , , Yau an tashi da yanayin sanyin da yawa a garin haka ya hana mutane fitowa wurin aiyukan su na yau da kullun a gari saboda sanyin da ke barazana ga fatar jikin su. Sai dai hakan bai hana tsirarin mutane fitowa neman abinda zasu rufawa kansu asiri ba duk ko da sanyin da yai yawa a garin. Sallaman driver Alh sani ne a kofa gidan wanda yazo daukan motar da za ai tafiya dashi kamar yadda ubangidan nasa ya umurce shi da safe yazo ya dauki motar akai service din ta. Ganin ba kowa a farfajiyan gida har maigadin gidan ya shige daga ciki saboda yanayin da aka tashi dashi a rana na sanyi. Waya ya dauko ya kira ubangidan nasa dake tare da hjy maryam a lokacin sukai magana ya zura sillifas a kafan shi ya fito waje inda yake ya samay shi. Bayan sun gama maganan da zasuyi ne Ya dawo inda ya samay ta sai rawan kai take yau ranan girkinta ne miji bai fita ba yana tare da ita bayan kowa ya kama ai ma hakan za a yine. Ranan haka zata wuni tana rawan kai a gidan ita a dole sun kai wani lokaci da miji daki basu fito ke nan miji ya daukakata akan sauran matan nasa. Kamar yadda ta sani wanan irin yanayin yakan bata ran uwargidan nasu har ita ma din idan ba da ita yake ba a daki takan dan dauki fushi da wace yanayin ya rutsa da ita. Don Alh sani mutum ne mai taka tsam tsam da yanayin sanyi don bai bashi lafiya a jikin shi wanan yasa idan anyi sanyi yakan dan tsagaita fita har zuwa rana. Kamar yadda tasan hjy jummai tana can kule da rashin fitowan su akan lokaci a dakin hakan ne ko yake faruwa a part din ta din don kadan kadan taja tsuki tana zage zage ita kadai. Tana fadin wai mutane sun girma basu san su girma ace mutum kamar Alh ya shige daki da mace har wana lokacin ko may yake da mace har haka oho ? Sai kuma ta juya gurin hjy maryam tana fadin ita kuma wanan munafukar yau rawan kai da jin kai zai tashi a gidan nan ke nan wai ita miji ya kula ta yau. Dakin hjy maimuna ma cewa tayi akaiwa yaran hjy Jummai abin karyawa kafin uwar ta fito don su karya don shiyasa bata damuwa da yanayin yaran don tasan hjy maimuna na kula mata dasu. Amma kishi da munafucin baisa taga halarcin hakan a gare ta kullun cikin tsangwaman ta suke don kada dai ta wala ita da miji a gidan. Sai da ya gama shirin shi tsab ya fito zuwa part din Amma wace sanyin bai hana ta zama da yaranta a lokacin suna hira ba da hadiye da maimuna a part din suna debewa mahaifiyar su kewa. Sai yaran su dake nasu harkan duk a cikin falo inda jefi jefi suke kula yaran wurin tsawata masu ga kijin da sukeyi a falon. Sallaman shi da gyaran muryan shi ne ya sanar dasu zuwan shi a wanan lokacin don haka kowa ya shiga gyarawa banda hjy maimuna dake zaune a yadda take takure saman kujera ta kudundune a cikin hijabi sky colour don sanyin da take ji a jikin ta. Amsa mai sallaman sukayi tare da gaida shi da kwana yana amsa masu ya zube kasa don gaida mahaifiyar shi shima. Bayan sun gaisa ne sameer da salim suka haye jikin mahaifin nasu suna gaida shi yake tambayan su lafiyan su sai kuma ya juya gurin mahaifiyar tasa dake fadin yau antashi da yanayi a garin dama nasan ba zaka fita maza ba yau. Yace wallahi hajiya hakana ne ina tsoron sanyin nan kada ya taba lafiyata in kwanta shiyasa na dan sahirta mashi kadan ya rage. Hakan yafi ai riga kafi yafi magani yanzu ba gaka zaka fita ba sai ya juya inda hajiya maimuna take zaune ta mayar da hankalinta ga wayan ta tun shigowan nashi bayan sun gaisa ya fara gaida mahaifiyar shi ta mayar da hankalin ta ga wayan ta. Ke ki shirya gobe zan shiga bauchi sai mu karasa katagum din zancen yarinyar nan yake ce wa hjy maimuna din da kanta yake duke. Jin zancen katagum yasa ta dago kai tana kallon shi tare da fadin ai ina ganin iya misau zamu tsaya don can suke yanzu karfin maganar kuma hannun yaya sale yake dama. Madallah inji Amma zancen dawowan Aruwa gidan nan ya taso ke nan ashe ina da babban bakuwa tafe ke nan ? Hadiye ta amsa da fadin a, a Fatima zata dawo gidan nan da zamane ashe banko sani ba sai yanzu. Amma tace kin san halin uwarta da zurfin ciki ai bata son wanan zancen a fili sai dai tabar abu ga zuciyar ta yayi ta cin ta a rai. Murmushi Alh sani yayi tare da kallon su yana fadin shi zai fita ke nan sanin ita zata karbi girki kuma bai sallamay ta ba yasa ta mike tabi bayan shi do sirantawa suka fita a tare. Sun dan taba tafiya yaja ya tsaya yana kallon ta kai ta sada kasa yace yaya naga jinkin ki yayi sanyi ne kuma ko an fasa dauko yarinyar ne tace. To Amma yaya, sai kuma tayi shiru kallon ta yake har lokacin ya rasa gane may take son fada mashi kuma akan tafiyan sai yace amma kuma may ? Gani nayi dai ya kamata in san da tafiyan da wurin don indan tanadar masu dan tsaraba da zan tafi dashi na tafi masu hannu rabbana hakana ? Dan murmushi ya sake tare da fadin wanan ba matsala bane don na gama shirin komai a bangare na. Nagode ta furta tare da dan tsayawa batare da tayi magana ba kuma hannu ya tura cikkn aljihun shi ya ciro kudin da baisan ko nawa bane ya mika mata tare da fadin sauran kyayi amfani dashi ga tafiyan idan da abinda zaki kara a wajen ki . Godiya ta sake mai lokacin har ya fara tafiya tayi mai Allah ya tsare a dawo lafiya ya amsa da Amin ya fice daga part din sai dai ashe yar gurin hjy na shigowa komai akan idon ta akayi. Wani kallo mai fassara yarinyar tayi masu ba tare da ta tsaya gaida maimunan ba tana kokarin shiga wurin amma dan gara ta hangota tana rusunnin gayu tana gaida mahaifin nata. Yau saboda sanyin muma a nan ba wasu mutane a wajen don kowa ya rufawa kan sa asiri an she gida muna dan dakin mu da yafi ko wani sanyi a gidan saboda rufin shi babu silin kwano ne zalla a sama kawai. Daga can cikin gida muke jin muryan umma na kwalla min kira ke fatima fatima fa, ko sai nace a ruwa zaki gane dake nake yi inda ta karaso har kofan dakin mu. Zubur na amsa daga barcin daya dan dauke ni na safe wanda ban dade da farashi ba donndan hiran da mukayi da manjo lokacin da na gama sallah. Ga manjo na fadin tana barci amma umma sai kwala min kira take kamar da gaiya. Fitowa nayi don jin kiran kamar ba na lafiya bane sai fadin take da na leko kifito rana yayi baki wanke muna kwanonin abinci ba ko kin aje wanine da zai wanke su. Nace umma sanyin nan nake jira ya rage in fito sanyi nake ji sosai yau tace zaki shige ki dauraye kwanonin nan ko sai na bata maki ranki. Umma nifa ko abincin daren jiya ba a bamu ba don an ga na dafa taliya da yamma tace eyyeh ke nan ba zaki wanke ba tunda bakici abincin ba ?. Na turo baki ba tare da nayi magana ba sai dai kuma ban gusa ba ta sake fadin zaki gusa ko sai na falla maki mari na sake fadin umma ai zan wanke bance ba zan wanke ba. Ban kai ga karasa magana ba naji saukan mari a fuskana halin nawa nayi na ihu Manjo tayo waje a gigice tana gyara daurin dan kwalin kanta. Tana fadin may yar nan tai maki da safen nan kika duke ta haka safiya sunan da take kiran ta dashi ke nan. Muryan yaya dan tantirin gidan mukaji yana fadin dallah ji wanan tsohuwar kamar an wani duke ta sosai umma saude da ta leko tace dama ai don ta fito tai wanan ihun. Kai kuji tsoron Allah may wanan yar marainiyar Allah ta tsare maku a gidan nan ne wai yarinya bata da daman magana sai duka ina nan diyan ku ke maku abinda suka ga dama wana na taba ganin kun duka a cikin su. Sai kuka nake wi wi wi wanda ke kara zuga zuciyar manjo tana sababi dasu yace ke dallah ki ruwa mutane baki karna zo wirin nan in lalatsaki yanzu. Manjo tace in ka iso zo ka lalatsata din dan banza mara kunya kawai yace idan batayi shiru ba yanzun nan kuwa zan mata dukan banza idan yaso tayi kukan da tushe . Jin abinda yake fada baisa na daina kuka ba don manjo na gurin nasan ba zata bari ya duke ni ba sai dai da biyu nake kukan don kar nayi wanke wanken kwanonin da sasfe safen nan. Ganin nama kara volume din kukan ne bata san lokacin da ya zagayo inda nake ba ya fara kai min duka ta ko ina ya samu a jikina har sai da uwayen nasa suka tsorata sukai mai magana. Manjo tayo kanshi da icen girki dats gani a wuta ta dinga kwala mai a jiki iya karfin da Allah ya bata shima sai da yaji jiki ranan haka manjo ta haukace masu a cikin gidan ranan sai da a ka kira baffa ya dawo gida kafin ta lafa. Baffa yaga irin ta,a san da yaya hashimu yai min yayi fada sosai shima ya kafa dokan kada wanda ya kara duka na ko harara manjo tace har aiki. Lokacin umma safiya tasa baki tace wanan kan bata isa ba muddin zamu dafa mu bata taci sai tayi muna wanke wanke da shara. Manjo tace ai sauran yaran basayi ba kunya umma safiya tace ai itace karaman su a gidan yanzu dole ita zata dinga yin wanan. Baffa sale na tsaye sororo bai iya tsawata mata komai ba a lokacin manjo ta juya gare shi tana fafin kana tsaye matar ka ke ci mun mutunci a gidan nan baka iya daukan mataki ba a kai. Sai lokacin yace ke safiya ya isa hakan kin dai ji abinda nace yana kokarin juyawa ya fita daga inda manjo take ta sake kuka wi wi wi. Abinda ya kashe mashi jiki ke nan ya kasa fitan da yai niyar yi da farko ya juya zuwa wurin ta yakai kasa tsugun ne yana bata hakkuri. Nan su umma suka hau zagina suna fadin na kai ga yadda na keso ai yanzu mukan zaman ki a gidan bai haifa muna alheri ba. Gidan wan mahaifinta ne sai dai ku ku fita ku barta a nan amma ba inda zata tafi daya fi nan din dama abinda mahaifiyar ta tagani ke nan ta barta anan kada ta kashe mata auren ta a can. Ai babu uwar da zata bar ya kamanki ko waige ta batayi dake ta kwaraice da tuni ta dauke gurin ta ai. Amma da tasan abinda ke nan tazo ta watsar dake ko waiwaye babu an kwaso jangwan gwan aka kawo muna gida da rana tsaka . Duk wahalan da muke dake ba a gani a gidan nan don kina makira uban naki ai da yake da rai kan shi ya sani da uwarki sai ke wa yake taimakawa da yanzu wallah zai ganmu ? Salati manjo ta kara sakewa ta aza hannu a kai tana masu kururuwa a cikin gida daya kara tayar da hankalin baffa don baffa shiru shirun shi har yasa iyalin shi kaf sun raina shi. Da kyat wanan fitinan ya mutu suka shige part din su baya fitan baffa suna surfa min zagi da aibanta ni iri iri da mugun fata a kaina. Zagi dai iya zagi na sha shi ranan a gurin su sai dai Allah ya kyauta kawai don kiri kiri suke goyon bayan diyan su suna nuna min banbanci a gidan. Ta shirya tsab ta dauki yaran zuwa part din Amma don ba bazata tafi da yaro ko daya ba tunda ranan zasu dawo garin. Bayan ta rufo kofan ta ne ta juya tare da yaran suka nufi can a daidai lokacin da maigidan su ya fito daga part din shi ya nufi part din hjy jummai don su gaisa. Hjy maryam da ta fito gaida Amma ce suka hade tun daga nisa take kare mata kallo irin shigar da tayi alama ya nuna mata fita zatayi a lokacin. Dan murmushi ta sake mata don samun fuska taji inda zata tafi suna hadewa hjy maimuna tace ina kwana anty maryam. Lafiya kalau maman biyu yau sai ina haka kuma ta dan sake murmushi itama tare da fadin zamu shiga wurin gwago ne ta saka ta a kwana itama tace to a fito lafiya. Alh na shiga part din jummai dake hake dashi kan kudin da yarta ta fada mata jiya taga yana ba hjy maimuna a kofan Amma. Bayan sun gaisa sama sama da sune yake fadin zanyi tafiya yau tare da maimuna zamu tafi bauchi gurin yarta. Kamar bata ji shi ba tace dama ina son ka shigo ka bada kudin yaran nan su samu su tafi duba takardun su. Kallon mamaki yai mata tare da fadin shi duban takardun har sai da kudi akeyin shi yanzu kuma in kuma na trasport kike magana ina dai diver ne zai kaisu. Amma kaima kasan dole sai sun rika wani abu dai ko don ba za a sake su haka su kama hanya ba wani abu a hannun su ba ? Yace to ki basu yau dai kan ban yi niya ba ni tace eh ai ba abin mamaki bane don ka hana su kudi yanzu amma kana iya ba wa yanda ka mayar mutane a gidan dul sanda suka bukata su. Wani kallon mamaki yayi mata tare da girgiza kan shi ya juya zai fita ta kara fadin duk dai abinda mutum keyi Allah na ganin sa ai. Idan na cuce ki sai ki barni da Allah yana fadin haka ya sa kai ya fita ranshi bace da al,amarin ta yanzu ko wurin hjy maryam da ya shiga itama basu kwashe da dadi ba da ita. Don duk wace yacewa da hjy maimuna zasuyi tafiya wurin yar ta sai ran maishi ya baci itama hjy maryam din korafin tayi mai wai kiri kiri ita ya hanata karbo maganin ta da takeyi amma gashi zai tafi da maimuna da kanshi wurin yar ta ai. Cewa yayi mata da bake zuwa dake da farko amsan magani sani akayi ko wani ya gune maki a gidan nan koda maimuna muke zuwa na hana din in kin isa sai ki tafi mu gani. Ita ko hjy maimuna bata fito ba sai da ta bisu daya bayan daya tayi masu sallama duk da ba wani Allah ya tsare janya mai kyau data samu a wurin illa sai kun dawo. A haka suka kama hanya sai bauchin yakubu sammakon da sukayi ga kuma lafiyar yayyar mota suka isa da wuri. Ta san gidan don haka ne basu wani sha wahala ba gurin neman gida sun iso da karfe daya saura garin misau din lokacin na gama kukan wahala ina barci jikina duk yayi min tsami sosai ga zazzabi na son kamani Allah ya taimaka baffa ya aiko min da magani in sha. Mutanen gidan suna zaune suja dinga jin sallama daga kofa sai wani yarone ya fito daga falon su inda suke yawan zama babu komai a cikin falon sai kwamatsen su da kayan dauda da suke tarawa a ciki don dakuna sun masu kanana yan matan kuma a falon suma suke kwana amma hakan baisa sun gyarashi ba. Yana amsa sallaman ya juta don fadawa iyayyen don bai san ta ba sai umma saude ta leko da farko bata gane ta ba sai da tace yaya baki gane ni bane maimuna ce fa daga kano. Tace Lah maimuna kece hakan ban sheda ki ba sa;un ku da zuwa yanzun kuke tafe ne sai ta hau kamay kamy da sabarin baki. Saude ke da wacece a gurin wai umma safiya ke tambaya tace wallahi yaya kinga maimuna ce uwar fatima a garin namu yau. Wace fatiman kuma tana fitowa take tambaya ganin maimuna a tsaye cikin shiga ta alfarma babu inda zaka ganta ka kushe mata ta waye ta zama babban mace sosai kamanin ta na asali ya kara fitowa fili. Turus tayi tana fadin maimunan Abubakar ce haka ta zama wata yar gayu da ita ikon Allah lalai duniya mai canza kama. Iso sukai mata da ta shigo falon nasu mai kama da dakin mahaukaciya don ko tsohuwa ba zata bar guri ta haka ba. Bayan sun gaisa da ita ne suna dan kamay kamay take fadin babba fa ko sun koma azare ne ? Babba na nan suna shiyan su bara a kai ki saude tace tana mikewa bata zaci a gidan part din yake ba sai da taga an nufi dan dakin da take zaton ko akulkine da ita a ranta tace ikon Allah tare da rashin jin dadi cikin zuciyar ta. Daga kofa suke sallama sau uki suna yi can manjo ta karba masu sallaman tare da fadin iso daga ciki suka daga labulen tsohon zanin manjo da muka sa a kofan suka shiga. Babba maimuna ce a garin namu yau ta zo tace wace maimuna fake nan tana tambaya hjyn ta kutso kai cikin dakin. Suna arba da manjo sai tsohuwar ta sa kuka dan gurin ta samu daga gefen da nake kwance ta kai zaune itama tana share nata hawayen . Maimuna ashe kina tafe manjo tace bayan gama kukan ta datayi tana kara dan gyara mata wurin da take zaune sai saude ne tace wanan barci take ne ? Yomar ai dole tayi barcin wahala tasha duka haka da sauri saude dake jin tsohuwar na shirin masu tonon sila ta juya tare da fadin bara na kawo maki ruwa dai . Hjy ta kalli tsohuwar tace tare da maigida na muke yana waje ko za, a kai mai abin zama a wajen . Sauden tace barin tura yaro yanzun ya kira shi a shago don kada a barshi shi kadai a waje nan ta bar hjy da manjo. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:39 - 🀐🀐🀐: ALHAMDULLAHI ALAH QULLI HALIM MUNA KARA GODIYA DA TAWASSALI GA ALLAH MAI KOMAI MAI KOWA FATAN CIKAWA DA IMANI GA DUKKAN MUSULUMI AMIN, , , , , , , , , Kallon inda nake tayi tana fadin wanan barci ne haka idon ta a kaina tana mamakin irin girman da nayi a cikin dan lokacin da ta dauka bata ganni ba. Idanuwan ta still a kaina tana tausaya ma itin rayuwan da muke ciki a can kasan zuciyar ta tunanen mijin ta marigayi ya fado mata a rai irin daulan da ya dauko basu dasu da mahaifiyar shi da yan uwan shi saida kash Allah yayi ikon shi akan sa. Da yana raye da yanzun yana cikin masu fada aji a wanan nahiyar don kwazon shi ga aiki gashi mutum ne shi mai kokarin yiwa zumunci hidama. Manjo dake gefen ta zaune tana share kwalla itama irin abinda take rayawa a ranta ke nan a lokacin daidai ganuwan su na jin dadi rayuwa Allah ya yanke masu shi ta hanyan dauke wanda suke sa ran hakan a gare shi. Murya a raunane tace yar nan kin gan mu nan yadda Allah yake nasa ikon a duk lokacin da yaso yau nice haka Allah ya dawo damu nan. Ta kara share hawaye hjy maimuna da itama hawayen takeyi tace Allah shiya san dalilin dauke muna dear a cikin mu babba a daidai lokacin da duk kan mu muke buakatan shi gare mu. Manjo tace ki duba wai yau safiya ce mai goranta wa yar nan mahaifin ta bai tsinanawa kowa komai ba a rayuwan shi kiji mi butulun mata har ta manta da lokacin da mijin ta ke dirka mata cikin yayan nan ya dauki nauyin komai a kansa duk wanan agare ta ashe ba taimako bane. Yar wanan marainiyar Allah daya bari ya daya tillo a duniya itace kuma don rashin tausayi suka saka a gaba cikin gidan nan bayan sun gama kwashe ganiman komai da mahaifinta ya bar mata yanzu sun dawo suna goranta mata da duka. Wani miyau mai daci hjy maimuna ta hade a makoshin ta tare da fadin babba ai wanan ba komai bane dukan dai shine mai munin ciki. Manjo tace kwarai kuwa yar nan ina wanan yar ina kattin diyan su kowa ya tashi dan magana kadan ya kai mata hannu. Yar ina cikin bakin ciki yau irin dukan da dan banzan dan nan yaiwa yarinyar nan a gidan nan kan wanke wanke kawai alhali baci ko loman abincin ba sun hana muna. Wani irin sosai hjy maimuna taji a cikin ranta ta tuna lokacin da mijin ta ke raye takanas zai sawo zabbi ko kaji ko naman rago yace aiwa babba girki aikai mata don ta na sayo shi don taci taji dadi yau itace kuma sarakai ke wa rowan abinci. Naji dadin zuwan nan naki ko yar nan ta zama abinda ubanta bai kai ga cinmawa a rayuwa ba da farko da Asiya tazon min da maganan naso naki ne amma da ta lurar dani alfanun hakan sai na yarda don zaman A ruwa anan ba zai amfane mu da komai ba nan gaba sai dinbin dana sani idan na hana ta tafiya dake a yanzu. Nasan zan shiga wani hali kamar yadda yarinyar zata shiga sai dai na dan lokacine ni nawa mai saukine dama may yarage min a rayuwa. Hjy maimuna tace babba kada kice hakan ai mairai baya debe tsamani ga rayuwa kin sani ko sai kinga jikokin yar a duniya. Sai lokacin manjo ta dan sake murmushin takaici a fuskan ta tana fadin kaiyya abin da kamar wuya yar nan. Ji magana sama sama a dakin yasa na motsa sai kuma idona yai min nauyi budawa a lokacin don yanayi jikin nawa sai dai kuma maganganu nasu ya hanani komawa barci na. Gani ina motsi alama ba barci nakeyi ba manjo tace ki tace A ruwa ga mahaifiyar ki tazo gare mu yau. Zubur na mike daga kwancen da nake ban gara ko second guda ba ina wiki wiki da idanuwana a kan hjy dake zaune a gefe na wace kamshin turaren ta ya cika mi hanci tun ina kwance. Bazaki min sannu da zuwa ba tace a dan hasale kin wani zuba mi manyan idanuwan kin ga sai dana turo baki gaba nace to sannu da zuwa ya gida ? Kai ta girgiza tare da hango tarin matsaloli da take hangonwa yarinyar tu ba a kai ko ina ba a rayuwa ta ga rashin tarbiya ta fara hango mata tun yanzu Kokarin mikewa nakeyi a lokacin don in fita daga dakin a lokacin ba ko ina nake so zuwa sai gida su Atika don in shakawa mahaifiyar su zancen zuwa hjy gidan . Ina kuma zaki manjo ta fada tana kallona lokacin dana kai kofa na daga labule nace bako ina zan dan kewaya ne kawai. Sai dai ina fita ban tsaya ko ina ba na nufi hanyar waje ina mai sauri har ina hada kafa wurin sauri a lokacin. Turus naja na tsaya do ganin dirkekiyar motar dake fake a kofan gidan mu na gane Alh sani amma sai nayi kamar ban sheda shi ba saboda miskilanci. Zan dan gwauta shi i wuce yana tsaye yana waya a waje motar driver na cikin mota zaune naji yace wa nake gani kamar fatima a nan ? Kamar ban ji shi ina tafiya na nufi hanyar zuwa gidan su Atika kai tsaye ya sake fadin ke A ruwa baki ga baffan ki bane ? Daga inda nake na tsaya cak don jin suna na daya kira kai tsaye tare da in kiyar sunan gaba daya don shi wani lokaci yana kirana da sayadi. A hankali nake takawa zuwa inda yake har na iso na kai kasa ina gaida shi baiyi fushi ba ka abinda nai masa din sai ma fara,an ganina da yake sakewa a fuskan shi a lokacin. Baffa ina wuni nace ina tsungune a gaban shi ya kura min ido sai kallon shartin dukan dake fuskana gefen idanuna daya kumbura sosai da gefen baki na dukan da yaya hashimu yayi min yau da safe. Ba tare da ya amsa min gaisuwn ba have Sayadi may nake gani haka kamar duka a fuskan ki sai kuma ya kasa magana sai furta innalillahi ashe maimuna tana da gaskiya da taki kwantar da hankalin ta a kan ki yan kwanakin nan. Muryanane ina fadin baffa kunzo lafiya ya hanya dasu Amma sai daya nisa yace Alhamdullahi suna lafiya. Ina zuwa haka har lokacin yanayin fuskanshi na tausayine a kaina yana dan girgiza kai cikin mamaki. Wancan gidan zan shiga na bashi amsa a takaice ina kokarin dagowa daga duken da nake din. Baice dani komai ba na wuce shi da zumudi na shiga gida su Atika din a waje na samay su har yayun ta da mahajfiyar su ina kokarin gaida mahaifiyar tasu ce yaya yusuf yace dani. Ke fatima wasu bakine suka zo gidan ku da tsadaden mota haka ashe malam salle nada yan uwa masu kudi hakan nan. A sanyaye kai duke na ce dasu mahaifiya ta ce da mijin ta suka zo umma shine nazo in fada maki hjy tazo yau. Umma na fadi kai yasuf wanan wani iri tambayan kwakwaf ne haka basu da yan uwa masu kudi sai ku. Sai taji ina fadin mahaifiyatace da maigidan ta ai sai ta zaro ido tace Allah fatima yau mahaifiyar ki ce a garin nan nace wallahi amma Atika tace shine kika fito kika barsu ? Nace nazo fada ma ummane kuma ni fa kunyar tama nake ji sosai wallahi shiyasa na fito na zo nan na barsu da manjo a daki. Amma anyi yar kawai wurin nan kunyar mahaifiyar take hala sarakuwa ki ce ita da shirmay nan naki na banza kullun. Ina kokarin zama ne tace tashi zakiyi ki koma yanzu kuwa mata tazo ta gane ki sai ki wani gudo ki barta a can zaune yanzu bata fi bukatan ganin ki akan kowa a gidan ba. Anty murjane ta gidan mu da kanta ta fado gidan tana fadin kin wani zo nan kin zauna ana can ana neman ki a gida. To ki taso baffa na kiran ki yanzun nan umma dake rike da hijjab a hannu tace yanzun nan ai zan tasata gaba mu shiga tazo min albishir din zuwa mahaifiyar tace. A can cikin gida kuwa da suka farga da fita nayi hjy dai batace komai ba sai fitowa da tayi don ganin halin da mijin ta yake a waje. Alh sani yace yanzun nan na ga sayadi ashe ta girma ne sosai hakan sai dai kuma na fara fahintar dalilin ki na so ta dawo gare ki da zama tun yanzu. Don yanayin da nagani a tare da ita gaskiya banji dadi gani hakan ba don alama ya nuna sayadi na zama hakkuri ne a wanan gidan . Maimako tayi magana a lokacin sai cewa tayi kin ko iya shan ruwan da aka kawo muku din? Yace bar zancen ruwan nan don Allah muyi abinda ya kawo mu nan daidai lokacin Baffa ya iso daga kiran gagawan da saude ta aika mai cewa yana da baki a gida. Shima bai sheda su ba sai da Alh yayi mai bayanin bayan sun gaisa yake fadin maimuna ce tazo daga kano lokacin yace a a a maimuna hjy kune tafe ? Sannun ku da zuwa yaya hanyar duk ya rude ya rasa ina zai saka su a wani gindin bishiya mai yawan innuwa baffa yasa akai masu shimfida suka zauna . Sai sabon gaisuwa ya biyu baya lokacin Alh sani ya saka driver ya fitar da tsaraban akaiwa hjy maimuna a cikin gida turamay zannu da bandarin shaddo dana yadi sai kayan masarufi dai sauran abubuwa iri tsaraba ne shake a bayan jef din nasu. Akai ta shiga dasu gida ana labtawa a kofan manjo don nan hjy maimuna din take zaune tare da manjo suna hiran yaushe rabo. Mutan gidan Baffa sai leken kayan suke suna gulma abubuwan da suka ga ana shigowa dasu gidan wai duk tsaraba ne. Daga can ciki umma safiya ta tabe baki tana fadin dama ashe duniya ta samu haka tayi watsi da yar gun wana tsohuwar. Kai umma kin taba gani uwar da taki yar ta a duniya ko yaya yar take balle fatima ai babu uwar da ba zataki taja ta ajiki ba daurowa ne haka kawai inji yaya sadi dake zaune. Yana gugan wandon da zai saka a jikin shi rana wani kallo ta watsa mai tare da fadin kai fa naga kwanan nan ko maganan Fatima ake sai kai wani tattare mata may kake nufin da hakan. Sai murja dake zaune a gefe tace kila yar gida yaks son ayi dashi baki ga kwanan nan yana wani gayu ba. Yace ashe kin gane yar gari gaskiya kinci dari a wurina yau tunda kikai saurin dago ni dariya suka saka a falon gaba dayan su banda mahaifiyar shi. Maganan gaskiya ne don na samu sassauci a gurin shi sosai indai yana gida ba wanda ya isa ya harare ni ko maganan banza yanzu. Sai dai ni ban gane manufan shi ba ko kadan don wayau na da kuma tunane basu kai can da zan gane wani soyayya ba ni. Mun shigo da umman su Atika tana ta gaishe su amma suna hayaniya basu ji ba don haka muka wuto kai tsaye dakin manjo dukan mu ukku din Atika na Allah Allah taga mahaifiyata yau. Mun shiga da sallama manjo tace dama nasan tana gidan ku ai tunda na nemay ta ban ganta ba gidan nan . Umma ta amsa da tana can babba taje fada muna hjyn ta zo yau garin sukai ma hjy sannun da zuwa umma na fadin lallai kuwa ga kama nan na zahiri ba sai an tambayaba. Hjy tayi saurin fadin a, a ke ko anty yar ba inda ta kwaso ai ita gidan su duk ta biyu banki ba dai kice ido da hanncin tane kawai nawa. Sin gaisa cikin raha da jin dadin ganin juna inda manjo ke gabatar da umma akan wace ke min kokarin komai tun zuwan mu garin sanadiyar shakuwar da yarta danayi. Hjy tayi mata godiya sosai tare da fadin sai dai fa yau zamuyi maku laifi anty don yar naki zata barku ke nan da mamaki umma tace. Ai da ita zaku tafi ke nan in sha Allahu hjy tace sai manjo ta karbe da fadin ai gara su tafi yar nan gidan nan ba wurin zaman A ruwa bane. Kina gani yau ba son Allah ya gyara ba da dan banzan dan nan hashimu ya illanta mun ita gara kawai ta dauki abinta Allah ya taya ta rikon amanan da akabar muna duniya tare. Jin haka nace ni kan ba inda zan tafi in bar manjo nan dan na fara kananan maganganu ciki ciki Atika tana tsunkula wai in daina tare da rada min wai zanji dadi a can fa fiye da nan. A cikin bude murya nace ba wani dadi ninafi jin dadi a wurin manjo na gaskiya ba inda zan tafi umma tace to ai tunda baki zuwa ai shike nan ba mai maki dole kinji yata. Shigowan su baffa dakin ne yasa muka fito gidan su umma muka koma tace kin ga Fatima maza debi ruwa ki watsa ma jikin ke baki ganin iyayyen ki a garin kika zauna haka. Ina fitowa wanka ta bani sabon kaya daga cikin kayan Atika masu kyau dasu tace in saka na fito fes dani gwanin ban sha,awa. Sai bayan la,asar aka aiko kirana har lokacin ina gidan su Atika kuma ba a nemay ni ba badon komai nayi haka ba sai nauyin mutanen da kunyan su, da nake ji a raina. Muna shiga na samu a rabon kayan da suka zo dashi ana fadin wai ga na baffa gana matan shi da yara sai nayi carf nace dama kada a basu wallahi dan dama aba yaya hashimu da saude kai ko sauden ma kada a bata. Murmushi hju tayi tace ke banda abinki wake hana alheri balle wanda akayi don ki ai sinci albarkacin ki ke nan sun san uwarki bata watsar dake ba. Nace to a basu din ina wani daure fuska baffane ya shigo yana fadin Alh yace ta fito ina ta murnan zasu wuce sai naga yan kayana da Manjo ta bata ta hada guri daya wanda takardu ne kawai sai abinda ba a rasa ba ta dauka nawa komai tace manjo ta bayar ga mai so a nan. Hankalina bai tashi ba sai da naji manjo tace to yar nan Ubangiji yasa da rabon zamu gana a gaba ki kula da kanki a duk inda kike ki kwantarwa mahaifiyar ki da hankalin ta idan na samu lokaci zanzo nagane ki a nan kano din sai kuma ta kasa karasa maganan ta fashe da kuka. Nima ban san lokacin da wani kuka yazo min ba nan na fara ihu ina turje turjen ba zan bi hjyn ba baffa ya shigo ya tsawa ta min amma banki barin kukan ba. Sunyi sai da hjy tayi min jan ido na shiga mota ga yan gidan mu sun min rakiya gaba daya da makwabtan arziki sai fatan alheri kowa ke mun a zaman kano da zanyi. Mutane da yaiwa namin sam barka da barin gidan Baffa danayi tun ban hinjire kamar sauran yaran gidan nasa ba nima. A haka dai muka dauki hanya ina faman rusa kuka kowa na jina har mukai nisa da garin misau kuka nake bil,haki ba kakautawa. Muryan Alh sani ne da jikin shi ya mutu akan yadda muka rabu da manjo dole mutun ya tausya muna yayi gyaran murya ya kirayi sunana a hankali yace Sayyadi . Ban karba sai kuka da nake rusawa ya kara kiran sunana yace fatima dake nake fa ki saurare ni . Hjy ta daka min wani irin tsawa a motan yace a a a barta tai kukan ta kin fi kowa sanin shakuwan dake tsakanin ta da kakarta a duniyan nan. Fatima kina jina ina son ki kwantar da hankalin ki ki daurare ni ba wai mun raba ki da kakan ki bane har abada a a mun dauko kine don mu inganta maki rayuwan ki ta yadda zaki taimaka wa kakan ki nan gaba . Ko baki son ki zama likita kizo ki dauketa daga gidan baffan ki ki taimaka mata da magani ita da amma nima nan ki taimaka min da ciwarwutan nan na zamani dake damuna har hjy gata idan kin zama likita zaki iya taimaka mata watarana ya kare da fadin ko baki son hakan gare ki. A lokacin na dan tsagaita kukana ina sauraren shi ya sake fadin idan mun barki a gidan baffan ki kina ganin wahalan ku dake da kakan ki zai kare maku ne na girgiza mai kai a hankali. Yace da kyau Sayyadi da kika fahince ni kin ga idan kin zauna gurin kakan ki wanan mafalkin naki ba zai taba faruwa ba gare ku. Amma kinga kinzo kano kin mayar da hankali ga karatu kin natsu ki cin ma burin ki mahaifin ki dake kwance a cikin kasa yasan yabar ya tagari mai tausayi da taimakon yan uwan shi a duniya. Ajiyan zuciya na sauke yadda dukkan su a motar zasu iya jina a lokacin yace da kyau yar kawu haka ake son da mai tarbiya ya saurari nasihan manya idan suna mai maza share hawayen ki kinga mun kusa kaiwa kano kada Amma ta ganki da hawayen nan ta dinga maki sheri akan sa. Hannu nasa ina share fuskan nawa kamar yadda ya bukata sai lokacin hjy ta sauke ajiyan zuciya a fili ya juya gurinta yana fadin kin san yaro dan lalashi ne fada bai yiwa yaron yanzu don Allah ki kula Allah ya bamu rikon amanan nan da aka bamu baki daya . A sanyaye tace Amin ni dama ai ba tsanani nayi mata ba kukan nan ne naga yayi yawa wallahi yarinya kamar zamu sayar da ita. Bamu shiga kano ba don munayi muna tsayawa a hanya yana sanyen abubuwa don haka sai bayan magariba muka ga sanyin da akeyi garin yasa ba wasu mutane sosai a titin sai kwan fitulun da suka haska garin sukai mata kawa kamar taurari a sama. A gidan ma kowa na part din shi don haka koda muka shigo muka nufi part din hjy kai tsaye driver yana kwaso tsaraban hanya yana shigowa dashi cikin part din ta. Kallona inda bake tsaye daga kofa rakube tayi tace ki shiga mana ki tsaya a nan sai bin gidan da kallo nake yadda ya tsaru da komai. Ko da nashiga na ma kallo na tsaya yi naji muryan ta tana fadin ai ba zama zamuyi ba don lokacin sallah ya shige tun dazun don haka zo muje na nuna maki daki ki ke da kannen ki a ban zaki zauna . Har ta fara tafiya ta juyo tace ko kin fison ki zauna ke kadai da sauri na girgiza kai har muka kai kofan dakin ta bude tare da nuna komai yadda zanyi amfani dashi. Bayan fitan ta daga dakin zama nayi ban shiga wankan ba ina karewa dakin kallo wanda gado ne a ciki sai mirrow gadon da wardrop babba a dakin sai tv dake a kashe a lokacin. Ina karewa dakin kallo na sauke ajiyan zuciya a hankali sai kuma manjo ta fado min a raina na sake sabon kuka ni kadai a dakin ina fadin an rabani ds kakata mai sona mai kaunata da tausayina yanzu dz ban nan yaya manjo zatayi a gidan nan ina nan ma yaya ta kare balle bani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:39 - 🀐🀐🀐: ALLAH ABIN GODIYA NE GASHI YA BANI IKON KARA MAKU WANI PAGES A YAU DON HAKA NAKE KARA GODEWA ALLAH YA KARE NI DAGA RUBUTA MA KU HARAMTACIYAR KAMAL DAGA ALKALAMI AMIN, , , , , , , , , , , , Har taje ta dawo dakin ina zaune a takure yadda ta barni kallo na tayi da mamaki tana fadin ashe ba zamu shirya dake ba ke nan idan baki daukan maganata da muhinmanci. Oya maza taso mu koma dakina kiyi wankan a gaba mu gani dole na tashi ina jin haushinta har kasan zuciyata na rabamu da manjon da tayi . Muna shiga dakin wani kamshi ne ya daki hanci na mai dadi dakin kamar shagone a saman mirrow don tab yake da kayan shafe shafe da turararruka masu kwalabe masu kyau da dauka ido saman mirrow din ina tsaka ga kallon naji muryan ta tana fadin ga bandaki nan maza ki shiga ki wanka ki fito. Kallon ta nayi nasan ta gane may nake nufi ta miko min wani tawul hakan na nufi hnyar bandakin data nuna min. Ina shiga na tsaya kallo nan ma ban yi wankan ba kamar yadda ta bukata da sauri sai dana kare kalle kalle na kwabe kayan jikina na fara wanka. Da tunane fal a raina don ba gidan su dana sani bane wanan, ke nan sun canza gida yanzu kuma. Ashe su umma safiya basuyi karya ba ina can ina bakar wahala da manjona tana nan a cikin daula ita ta manta dani cikin duniya iba shan bakar wahla ba karya sukayi da sukace ta watsar dani tana jin dadin ta tabarwa mutane taulalina. Da na fito bata dakin sai ganin zani da hijab data aje min a bakin gado da alama ni ta ajewa su don haka ban tsaya yin shakku ba na dauka na daura a jikina na tayar da sallah. Na jima a wurin zaune sai gata ta shigo ta kalleni tace har kin idar da sallah ke nan ki dinga kwantar da hankali kina sallah mai kyau fa bari ma dai zamu kai ga wanan nan gaba yanzu ki tashi ga abinci nan ki ci kafin ki kwanta. Na koshi na bata amsa ciki ciki tace oya maza ki tashi kici abinci ni ba babba bace da zan maki magana ki musa min. Ina hawaye na mike nazo gaban abincin na zuba mai ido duk da haduwan abincin a idona hakan baisa naji sha,awanci ba don damuwan da nake dashi lokacin. Ina nan zaune naji ta daka min tsawa dole na kai hannu ga abincin na fara ci da dan sauri sai dai kuma bakina ba test da alaman zazzabin jikina bai gama fita mun ba ke nan har lokacin. Ina hawaye ina cusa abincin a bakina har nayi loma kamar biyar na dago kai inda take tsaye ta tsatdare ni da ido nace cikin rawan murya na koshi hajiya. Murmushi ta dan sake a fuskanta tare da fadin Sayyadi yau nice hjy kike kirana da bakin ki ke nan har yanzu baki dauke ni a mahaifiyar ki ba. Kaina girgiza don tsoron ta da na fara yi tace ki dan kara barin dauko maki magani ki sha kada zazzabin ki ya dawo again. Tana wuce take maganan lokaci ne wasu hawaye suka zo min kamar an bude famfo kuma idan akwa abinda naki jini shine fada shine asalin abinda ke hadani fada da mutanen gidan mu don ban son fada shiyasa nake shan gwauran banza a wurin su. Ta dawo dauke da kayan barci na wasu yadi mai taushi a hannun ta tana fafin ungo wanan ki saka sai ki hau gadon nan ki kwanta a nan yau don sauran yaran suna sashen Amma. Ina gama sakawa na kashe sai dai barci bai daukeni ba naji shigowan ta dakin sai da ta kewaya ta kare duk abinda take yi lokacin har barci ya fara zo min naga ta kashe wuta ta hau gadon da nake kwancen ta kwanta daura dani. Dan shiru ya biyo baya a dakin na wani lokaci ashe addua take don naji tofawan ta tare da ajiyan zuciya a lokaci guda. Juyawa nayi daga fuskantar junan da mukeyi haka yasa ta kara gaskanta ba barci yarinyar ke yi ba a lokacin. Sayyadi nasan kin kullace ni a zuciyar ki ko shiyasa har yanzu kike wanan fushin dani haka ke a zaton ki akwai uwar da zata watsar da diyar ta kamar ki zuciyar ta ya zauna lafiya ? Sayyadi mutuwa ce mai yake kauna tayi muna hijabi a tsakanin mu a daidai lokacin da ya kamata ace kin san dadin mu mun san naki. Ina son ki sani a karkashin iko iyayyena nake dana mijin da nake aure a yanzu bawai zaman kaina nakeyi ba daidai da rana daya da ina da ikon kaina da ban barki kin ba koda na second guda a rayuwana. Sai dai ba yadda zanyi da abinda yafi karfi sai addu,a a tsakanin da yake Allah maji rokon bawa ne sai gashi a cikin ruwan sanyi na nuna bukatan son dawowan ki a kusa dani ban samu wani matsala suka yarde mun da hakan. Sai dai ina son ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada maki ka zaman gidan nan da zakiyi kada ki shiga harka kowa a gidan nan kamar yadda nasan suma ba zasu shiga harkan ki ba. Haka kuma ki koyi kama bakin ki akan duk wani abinda bai shafeki ba ko ni ko yan uwan ki cikin gidan nan . Ina son ki zamo yarinya ta gari da za, a dinga kwatance da ita ako wani irin magana ya taso kai ba gida ba har ma wajen gidan nan kaf garin nan. Kin zo gidan da kowa kansa ya sani da nasa gidan da nuna bambamci a gare su basu dauke shi komai ba a wurin su. Don haka ki koyi halin da kikaga ina yi a cikin gidan nan ke ma watau hakkuri kada ki damu da maganan kowa a kanki kiyi harkan dake gaban ki kawai a yanzu shine karatu kamar yadda kikai wa kawun ki alkawarin yi. Don nasa Alh ba zai taba gazawa da karatun ki ba har sai in kece kika nuna masa da kin gaji din ina son ki rike shi tankar mahaifin ki da baya duniya ko banza shi din mai rikon kine ko bani gidan sa . Ina fatan kin dan gamsu da maganata kaina gyada mata na manta da cewa a cikin duhu muke a lokacin sai da ta ce ko kinyi barci ne nace na gamsu. Don har lokacin haushi nake balle da tace min nazo gidan danger to don may ta dauko ni zuwa gidan danja din tasan abinda ke ciki. Kamar tasan tunanen da nake naji tace sayyadi ina kaunar ki ina son ki kamar yadda ko wata uwa take son diyan ta asalima yarana kaf nafi sa rai a gare ki ban sani ba ko don baki kusa danine hankalina yafi karkata a gare ki. Ni dai da irin wanan maganganun har barci mai nauyi ya dauke ni ban sani ba sai can cikin dare na falka ina jin kamar ana magana a dakin tsoro ya kamani don na manta shaf a inda nake sai dana saurara da kyau na tuno kuma da inda nake nike jiyo abinda ake fadi a cikin kuka a kunne na. Ya Allah nakai kuka na gare ka ka kare min zuri,ata daga fadawa halaka ya Allah yadda na dauko amanan wanan yarinyar ubangiji ka shige min gaba ka tayani diban yar matainiyar Allah ka tsare min su daga duk wani abinki. Ya Allah ka inganta rayuwa yar mairainiyar Allah yadda kowa nata zai wadata a karshin innuwan ta tana kaiwa nan sai kuma ta fashe da kuka tana fadin Allah kai kasan dalilin daukan mahaifin ta a daidai lokacin da muke cikin bukatan ka gare mu. Dagowa nayi daga inda nake kwance ban san cewa nima hawayen nakeyi ba a lokacin duk da taji na motsa bai sa ta daina abinda takeyi din ba sai data gama ta shafa ta juyo tare da fadin yaya . Mai kike so ne kika tashi nace fitsari zanyi ta nuna min ban dakin da hannu na shiga na yi kwarari na fito ta wurin dana barta ni dai har na koma barci ban san lokacin da ta kwanta ba kuma. Washe gari ban iya tashi ba duk da ina jin hayaniyar yan kanne a dakin tunda ta tayar dani nayi sallah asuba na koma na kwanta sai zazzabi mai karfi ne ya rufeni kuma. Ina jin tana fadin kada ku tayar da anty ku mana sameer duk da hankan na kasa bude ido inga yan kannen nawa a duniya da nake dasu. Alh ne ya shigo yana fadin ko asibiti za a kaini ne alokacin tace tana jiran in tashi ne in karya in kara shan magani ko jikin zai sake min a lokacin. Naji yace kin san Allah ba karamin danne zuciyata nayi ba a garin nan jiya don ji nake kamar inyi kara mutanen nan ga hukuma. Tausayi mahaifin nasu naji a lokacin dana ganshi ya hana in dauki mataki a kansu kamar wanan yarinyar zasu bari kato kaman wanan yana dukan ta. Tun jiya sai gode ma Allah dake nakeyi a raina da kika matsa akan a dauko maki yarinyar nan ta dawo wurin ki aida bamu dauko ta ba muka barta a can Alhakin ta zai iya tauye mu bamu sani ba. Yanzu ba don Allah ya kaimu a jiyan ba da haka zatai ta wahala jinya daga ita sai kakanta a daki su kadai ga kakan tana fama da kanta itama. Dattajuwar ta bani tausayi matuka na rasa ta inda zan taimaka mata wallahi sai dai idan hankali ya kwanta sai a dauko ta nan ta kwana biyu wurin amma daga nan sai a kaita asibiti a dubata sin bar mata tana wahala haka a daki ba wani kulawan da take samu. Hjy maimuna tace nima abinda na kwana tunane ke nan gashi mai taimaka mata din mun dauko ta ga shi yayan ba wani zarahi ke gare shi ba manejin rayuwane kawai yake yi. Dama marigayi din ne mai dan hali a cikin su Allah kuma ya karbi abinshi abindai gashi nan wallahi sai godiya ga Allah. Alh yace zan zauna da hajiya muyi maganan akai sai ayi yadda ya dace ni zan fita idan ta falka ki fada mata na shigo tana barci. Har yakai kofa yace a raba wanan kayan abawa kowa nasa don Allah ta amsa da to dama na tsaya sallaman yan makarantan nan ne yanzu zan raba ai. Ya fice naji wani irin dadi a raina don maganan Manjo da naji sunyi a lokacin tunda ya furta yana da niyar taimakawa ke nan . Sannu a hankali na sauko saman gadon na taka zuwa falon ds nake jin muryoyin su a ciki inda na samu hjy tana faman raba tsaraban da suka sayo na bauchi a hanya. Inda naga ta kasa gida hudu daidai daidai tana ganina tace a, a kin falka ke nan yanzu ko Alh ya fita yazo duba jikin ki ta kara da tambaya yaya zazzabin yanzu ya sauka ko yana nan ? Na dan ya mutsa fuskana tare da fadin naji sauki ina kokarin samun wuri in zauna tace kada ki zauna ki tashi ki wanke bakin ki wanka kizo ki karya kisha magani. Na amsa da to tace kije dakin ki kiyi wanka idan kin fito kaya na nan cikin wardrobe dana dan fara tanadar maki kafin kizo inga tsayin ki dama. Da to na amsa na fice a falon zuwa dayan dakin da ta kira da nawa ban shiga wanka ba sai dana bude wardrobe din sai naja nayi turus don kayan da nagani a ciki a jere. Kaya nabi da kallo ina tunanen yaushe har taimi kaya iri haka ne da yawa tun banzo ina yan matan gidan mu masu dinka roba suna mi yanga dashi yau suzo suga inda kaya ke karya. Ina dakin sai dana gama shirina wasu material da suka dauke min hankali na jawo naga ashe dogon riga akayi dashi . A raina nace wanan kaya mai kyau aka bata a dogon riga kuma hakana dai na saka don kayan sun shiga raina sosai. Ban tsaya yin makeup ba a lokacin don ban ma iya ba na fito falon inda take tana zaune da kayan data raba tana waya. Ban kai ga zama ba sai ga wata tayi sallama ta shigo da kaso daga cikin kayan tana fadin wai hjy tace a maida maki sun gode. Tace to ikon Allah a je a nan ki tafi sai da ta dan kalle ni kafin ta fita a dakin ashe lami mai aikin hjy ce don yanzu ita kadai takewa aiki a gidan tun lokacin da aka raba girki kowa ya dauki nasa. Tana fita tace kin soma ganin matsalan gidan mu ke nan wanan ai ba komai bane daga cikin halin hjyn gidan nam. Bance komai ba don ban fahinci maganan ta ba don haka ban wani kula da abinda take fadi din ba a lokacin. LAMI tana komawa take fada ma hjy cewa hjy naga wata yar matashiyar yarinya mai kamada hjy maimuna sak a sashen ta. Hajiya tace yarinya kuma wace yarinya ce wanan a ina ta kwaso ta kuma ko yar aiki ta dauko ba sani ba don shegen kishi ne da ita. Kinga lami ki saka mi ido kiji daga ina yarinyar ta fito kuma ni ba zance yar uwan ta bace tunda nasa yan uwan ta kaf sai dai ida daga gutin mahaifiyar ta tafito amma kuma ina zata gansu matar da bama a kasan nan suke ba. Au hjy ashe wanan batai kama da yar aiki ba fa wa itane fa yarjnyar sak sai dai idan yar wani nata ne tazo. Da wanan maganan suka tsaya kan Lami zata gano mata ko wacece tazo dakin maimuna din don bata kawo cewa nice nazo ba don irin yadda suka nuna min zuwa na na farko ina karama a gidan. Hjy maryam ta karbi kayan da aka kai mata sai dai bata wani yaba don ko godiya balle kin dawo lafiya. Bayan ta kammala abinda take ina zaune na kurawa tv dake aiki ido tafito daga daki tana fadin taso in kaiki wurin gwago. Don tun safe take mintan baki tashi ba har yanzu ta ganki don haka taso muje tunda jikin naki ya yi sauki. A hanyar na zuwa ne muka hade da hjy maryam take fadin sai ga sako mun gani tace eh wallahi. Har zata wuce tace wanan fa sai hjy maimuna ta danyi murmushi tace Sayyadi ce fa a, a tare kuka zo ne ta tambaya cikin mamaki. Muka wuce ta tana tsaye tana mamaki mu har muka shige shiyan Amma tsuhuwar gidan mai sona kamar manjona . Muna sallama a falon tana zaune da ledan goro a hannun ta tana dagowa taga tare mu da hjyn tace a a a wane kagani haka kamar kawallina yau a garin inji maki bako ? Ina dan fara,a a fuskana nace ina wuni hjy tace har an wuni ne kwana dai ko na gyara tare da fadin ina kwana Amma tace kinga barni da ita fatan wunin take muna ai . La le lale lale marhabin yar nan ashe kina nan na da bauchi kun shige kunyi shiru haka ? Ta miko hannu alaman inzo gurin ta na dago daga inda nake zuwa wurin tsohuwar dake mika min hannun. Ta rungumay ni zuwa jikin ta tana fadin A ruwa kece kikai girma haka ikon Allah kamar jiya ne fa rabon mu dake. Na dade tare da tsohuwar don hjy fita tayi ta barni a dakin muna dan taba hira da Amma wanda hiran namu duk kan kakatace sai zaman misau da mukeyi. Nakai wani lokaci a dakin nata don gidan ya koma tsit yara suna makaranta a lokaci sai gidan ya koma ba wani hayaniya a lokaci haka ya bani daman yin barcin gajiya sosai sai da lokaci ban falka sai da akai kiran sallah na tashi nayi sallah tare da Amma a wurin ta. Yaro aka aiko wai inzo inji mamu yaro ya fada ashe yana nufin hjyn mu don ni yanzu har na manta da ana kiranta da mamu don hju ya karbe sunan a gurin tun lokacin da mukaji taje makka. Amma tace muna shiri cin abinci ne bata dade da tashi daga barci ba har na mike a lokacin don zuwa amsa kiran mahaifiyata. Inawa Amma din sai anjima tace bazaki dawo ba ke nan nace zan dawo idan nagama da haka na fice a part din zuwa sashen hjy na. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:42 - 🀐🀐🀐: ALHAMDULLAHI ALLAH KA SADA MU DA ALHERORIN DA KE CIKIN WANAN RANAN NA LAHADI ALLAH KA KARE MU DAGA SHERIN DUK WANI SHEDANIN ABU MUTUM KO ALJAN KO DABBA KO KWARO DA DUK WANI NAU,IN MASHERANCIN ABU, , , , , , , , , A ranan dai na san yan kanne na wanda muka fito ciki daya uba kowa da nasa ni dasu inda yaran ke daridari dani sun ki sake jikin su dani kamar yadda ni ma basu gabana a lokacin. Don tunanen manjo dake addaban zuciyata har wanan lokacin ba,a taba raba mu haka ba ina da wayau na sai wanan karon. Abincin da mamu kamar yadda naji yaran na kiranta dashi ta aje min haka nasaka shi a gaba ina kallo ko tabawa banyi ba balle in san dandanon shi. Sai tv dake aiki a falon nakan dan kalla jefi jefi bawai don nasan may suke yi ba a lokacin. Fitowan mamu daga dakin ta taja tayi turs tana kallona don ganin ban taba abincin ba ko kadan. Takowa tayi zuwa inda nake ta samu wuri ta zauna hakan yasa na mayar da hankalina a kanta kai ta dangirgiza tare da fadin . Watau sayadi ba zaki kwantar da hankalinki ki kama jiki har burin kakan ki damu ya cika akanki a hakan har zaki cin ma manufan iyayyen naki ? Kin saka damuwa da tunane a gaba kinayi ko abincin da na kawo maki baki kalla ba wanan ai sai ki sa mutanen gidan nan suyi min dariya tunda dama ba son zaman ki a nan sukeyi ba din. Idona ne ya kawo ruwa bulbul tace indai haka zakiyi na tabbatar da ba zaku shirya da Alh na gashi ya dauki son duniya ya dora a kanki tun baki zo ba . Kinzo din kuma kina son watsa nai kasa a idanu ga idon jamma,a inda kin kwatar da hankalin ki gidan nan ina mai tabbatar maki duk wani dake gidan sai kin fishi jin dadi . Amma fa sai ki kwantar da hankalin ki hakan zai faru, idan kuma kin ce ba zaki kwantar da hankalin ki ba haka zaki ci gaba dayi to ki sani ke keda wahala kuma ba komawa zaki ba don ki sani. Jin da nayi tace komai zanyi ba zan koma wurin manjo ba yasa ni fashewa da wani kuka mai karfi tace ikon Allah ai sai kiyi tayi yarinya tunda baki san lalashi ba. Yan kanne da suka ga ina wanan kukan sai tsoro ya kama su ina kallo suna shigewa jikin mamu suna lafewa inda ta koma kansu ta fita batu na sai haushi ya kara kamani lokaci. Ina jin suna fadin mamu kuka takeyi ita macen ke tambayan ta tace she is not well. Sai naga yarinyar ta bata fuska suna Zaune sunyi sai ni suke kallo yadda nake kukan yarinyar ta mike ta fita daga falon can sai gata da goran ruwa ta kawo min tana bani tare da fadin sorry anty ki sha ruwa. Ban karbi ruwan ba na mike zuwa dakin da ta nuna min a matsayin nawa na fada saman gado naci gaba da kukan ni kadai a dakin. Sallama tayi ta shigo falon kamar yadda tayi tsamani haka din ne ya faru don hjy Jummai na zaune suna cin abinci da yaran da dawowan su ke nan daga school. Salma ce sai kannen ta biyu mace da namiji ta saba da irin karba sallaman su wanan kuma yanzu ya bar damun ta ko kadan. Yaran ta fara magana don tasan shi kawai zatayi ta samu kafan yin abinda ya shigo da ita shiyan tace a, a yan makaranta sai yanzu kuke cin abinci ne. Hjy jummai ta dan ya mutsa tace kin san su da shiriri ta ai ko cin ma ai sai na matsa masu suke zama har da wanan babban banzan. Babu wanda ya dago kai daga cikin yaran ya kalle ta tace hjy ashe kuma mun samu bakuwa ne a gidan jiya ? Bakuwa daga ina kuma ina take a, a yarinyar nan mana wa take da suna yar wurin maimuna da ta haifa can bauchi mana ashe jiya tare da ita suka zo. Wani irin kibiya ya soki zuciyar hju jummai ta dago da mamaki tana fadin ke nan an kawo muna agola a cikin gidan nan ke nan ? Masuyi iya magana sukace wai sani in fika ba wai agola da rabon gida lallai kan tana nan tazo kin ga yadda yarinyar ta girma kuwa ? Ba zaki ce , , , , , don Alh hjy maryam rabani da wanan zancen kazantan wai may ke damuwan Alh ne haka yanzu ? Lalai kan a bincike shi don abin ba lafiya ba wanan ma na gidan ya muka kare dasu balle an dauko agola an jefa a cikin namu kuma . Hmmm, cabdijam ashe ko akwaita a gidan nan ke nan don ba zata sabu ba bindiga a ruwa samun wurin na maimuna har yakai ta dauko yar ta ta kado muna ita gidan nan . Hjy maryam tace sai dai inda sunan hutu tazo nan amma kuma ai yanzu karatu akeyi ko ina shi yasa abin ya bani mamaki . Ke yaba mamaki ko ni maryam zamu gani idan zai fada muna ko zaiyi shiru inko har yai gigin fada min zai ko ji amsa a wurina wallahi. Hjy maryam da ta samu abinda take so ta hau zuga hjyn har da fadin wana karon akan maganan yar nan ba kyale shi zamiyu ba bore zamuyi masa wallahi. Ko bakiyi ba aini zanyi don ni ake cutata fiye da kowa ni mai yaya da yawa a gidan nan abin bai tsaya ga wa yan nan shegun data tara muna ba har ya kai a dauko wata a dada muna kuma. Duk da kalamin ya bata wa hjy maryam rai sai ta shaye da yake munafunci ne tace. Duk fa abinda akeyi da sanin wanan tsohuwar mai glass tana zaune take bada umurni komai nina dade dagano su ai hjy maryam ke fadin haka. Ta san komai mana, idan ma ance maki da shirin ta ne wanan ba za a yj musu ba don kuma kawai ta kuntata muna tayi haka amma maimuna bata farawa tace yar ta tazo ta zauna damu wane ita. Wai a gidan an ake nufin yarinyar ta zauna sallama da tun shigowan hjy maryam ta hade rai sai yanzu tayi magana . Maryam tace niyar su ke nan Allah, salma kun samu karuwa don wallahi yar ta kusa kama kafan ki wurin tsayi da komai nagani. Kai haba maryam ko da na haifi salma ai fatima bata koyi aure ba sannan kuma da tai auren ta dade Allah bai bata yar ba sosai. Hjy maryam ta nisa tana mikewa tare da fadin tana nan naganta dazun zasu sashen hajiya da cewa Amma tace munafuka ke nan inji hjy jummai. Haba mama stop saying that to her ko banza she is Dad mum kinga bai dace and beside idan maganan ya fita ace kece mara kunya kina zaginta. Hjy maryam ta gane nufin yarinyar saboda shayin uwar yar da takeyi ya hana tayi mata magana a lokacin. Batai wani dadewa ba ta fito daga part din da zuman itama idan Alh ya dawo zasuyi mai maganan basu yarda da zaman yarinyar a gidan ba dukkan su. Tana fita salma taja tsuki tare da fadin amaybo olo popo ita wanan aikin ta ke nan ta gani ta kwaso ta fada Allah mama yaci ki gane wanan matar haka. Laifi tayi don taga abinda bai dace a gidan ba ta fada min idan an kyale wataran sai abin yafi haka girma take bani yanzun da take ban girman watau baki sun hakan kuma ? Tabe baki tayi salis ya shigo yana fadin mama dad ya kara sayen motane naga mota har biyu sabbi a waje . Da sauri tace wajen gidan nan ko ko dai kafin yaron ya bata amsa wayan ta yai kara ta dauka habbib ne a layin da sauri ta daga wayan ta kara a kunnen ta tare da yin sallama. Sama sama suka gaisa da dan nata yace mama kin san da zancen motar da Dad yasa ya umar ya sayawa matan shi kuwa. Cikin wani murya tace what tare da dagowa daga kujeran tana fadin umar ko na da hankali yaya akayi hakan ya faru ? Ta mikw tana fadin hold on barin leka inga abinda ke gudana yace ai har motocin sun karaso gidan ko yanzu umar din ya kirani yake fada min wai ai ma Ahmed magana ya yi masu takardu. Kai habbib yaushe umar ya canza hakane yace wallahi bai camza ba mama yana nan dai umar din da ko koka san shi miskili sai ma abinda ya karu. Wai kana nufin matan nan za a ba motar yace kwarai kuwa nima yanzu yake fada min ashe tun lokacin da aka saya maki naki Dad yai mashi maganan nasu. Ashe akwai bura uba a gidan nan don ba zai yuyu ba lokacin da nayj wahala daku su ina da yanzu zasu ce komai alai min sai an masu shi a gidan nan. Mama wani abin ba amma ina zasu hada kanki dasu da dai kin kyale kowa ai don ki akayi hakan sun ci albarkacin ki. Kin san shi bros wani bahagon mutum ne shiyasa ban masa magana a kan hakan ba sai ya nuna min nafishi sanin abinda zaiyi ne. Kwai dai ki saka masu ido nasan ai Dad din zai maki bayanin ko ma may nene so ki basar kawai mama. Ai bai fufe baki ba ta kashe wayan tare da mikewa zuwa hanyar wajen gidan inda ake aje motocin gida wuri ne mai girman gaske ko wacen su zata aje nata dana mai gidan guda biyu. Turus taja ta tsaya tana karewa motocin kallo duk da nata ya na gaba sosai ga wa yan nan amma sai kyashi ya tartsu a zuciyar ta a lokaci daya take ganin nasu ya cunawa nata. Ranan ina wuta ta jefa kanta idan da tasan ba zai kone ta ba ranta yayi bala,in baci da wani zataji a gidan da zancen dauko masu agola a gida ko kuwa zancen motocin da aka tillastawa dan ta ya saya wa kishiyoyin ta Salma ne da kanwar ta suke tausan uwar tabi a hankali har ta gane komai don kila Alhajin ne ya bada kudi a saya mashi aiko a hasale ta juyo gare su tana fadin idan ya bada kudi sai akace an fitar dani a ciki ko ? Ranan sai dare Alh sani ya dawo gida don haka bata samu zaunawa dashi ba don ko dan kewaya sun da yakeyi ranan bai samu yayi masu ba. Sai washe gari suka samu ganawa da maidan wanda ta samu yana shirin shi na fita kasuwa a lokacin . Tana shigowa dakin tace fita zakayi ne yace yau har na makara don jiya na gaji da yawa sai ta samu wuri ta zauna a bakin gado tare da fadin. Dama nazo magana akan motocin da aka shigo dasu jiya ne gidan nan don banji kayi bayanin komai ba akansu. Wani irin mamakin ta ne ya kama shi lokaci daya tare da takaicin ta ba ko gaisuwa zata fito mai da wanan zancen gatsau. Sai kuma tace gaba da fadin bayan nan sai zancen yar wirin maimuna da hjy maryam tace min ta gani a gidan nan jiya da safe wani abin tazo yi garin nan halan ? Lalai yau yasan Jummai sakariyace girman kawai Allah ya bata a gidan mutum mai yara irin jummai zai zauna yana kishin ba gaira ba dalili haka. Jin yayi shiru yaci gaba da saka tufafin shi ta sake fadin Alh bayani fa nazo kai min kana jina kuma kayi shiru. Wani irin kallo ya watsa mata daga inda yake kafin ya hade abinda ya taso mai azuciyar shi yace. Jummai nike auren ki ko ke ke aure na dani dake wa ya,aje wani a gidan nan ne, jummai wai wanan wani irin rayuwa kike neman jefa kanki a cikine wai ? Kada fa ki manta a karshina kike gidan nan dake da duk wani wanda ke zaune a gidan nan kada fa ki mata kamar yadda na auro ki haka na auro kowace ku a gidan nan. Ina son ki sani na auro kune a gidan nan baki dayan ku kamar yadda kowan ku keda hakkoki a kaina. Amma ke kin kasa tuna wanan hakin da nauyin da ya rataya a kanki kina kokarin shigo min da wanj akida na daban a gidana. Aje ni kikayi da zaki zo min da wanan maganan ba ko gaisuwa ko wani da, a gaba daya kina kokarin cusa min wani ra,ayi naki a cikin gidana. Kafin ki zo nan duk yan uwan ki sun shigo mun gaisa dasu da kwana amma banji wata wace ta tambayeni komai ba. Amma ke kin taso zakal zakal don kin raina ni zaki sani a gaba kina tambayana kamar kin aje ni. Zancen yarinya ai uwarta na gidan sai ki tura wace tace ta ganta taje ta tambayo maki abinda tazo yi maku gida. Mota kuma ki manta ki tambayi wanda ya kawo su ya aje kafin ya tafi yai maki bayani kada fa ki manta ke matar aure ce kamar kowa a gidan nan. Abinda ya kamata ace kin tsaya kin yi kin koyar bashine a gaban ki ba sai shirmay banza kin watsar da cina da sha na balle gyaran muhalina uwa uba hakkina don wani dalili naki na banza. Yarana da iyalina a kullun sai kokarin watsa min tarbiyan su kikeyi don baki da tunane da lissafi zaki taso ki sani a gaba kina tambayana yar wurin maimuna Shin kin mata da nima ya tace tana da daman zuwa gidan nan duk lokacin da taso koda kuwa ba maimuna a gidan nan.. ZAINAN IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:42 - 🀐🀐🀐: RABBANA ATINA FIDDINIYE HASSANATAN WA FIL A FIRANTAN HASSANATAN WA, KIN,NA AZZABAN NAR Wani kallo take mai ba don taso ba ta kyale shi don ya fito mata a namijin sak ranan babu hanyar ko daman da zata fada mai wani magana kuma akan wanda ya fada mata don duk abinda ya fada tasan gaskiya ne. Lalai tana da rauni a zamantakewan su to amma ai duk da yan aiki keyi komai kamar yadda yace bata gaza wurin basu umurnin komai ba. Ganin bai kulata ba sai harkan gaban shi yakeyi ya barta zaune a dakin kamar ba mutum wurin yasa ta tashi fu fu fu ta fice zuciyar ta cike da bacin ran shi. Tana gani bai mata adalcin ba akan komai kokarin yake ya fifita wasu yanzu a kanta abinda ko ba zata taba bari ya yuyu ba ke nan a gidan. A hanyar ta na fita ne suka hade da hjy maryam zata shigo ko kallon arziki bata samu ba a wurin ta, ta wuce ta fuuuu ta dan kalleta tare da sauke murmushin keta a gefen fuskanta. Da sallama ta shigo dakin ya dago ya bita da kallo ranshi a bace har lokacin ta dan dade a tsaye bai dago kai ya kalle ta ba sai da tayi gyaran murya ya juyo a fusace yana fadin. Kin zo hada wani sheri ne a nan kuma ke may yasa baki barin halin ki na sarika noke ne a gidan nan nasha sanin kina wanan halin ina zuba maki ido ko zaki canza sai dai abin naki ya fara kureni a yanzu. A marairaice tace may kuma nayi kake fada min haka Alh da shigowana ban san matsalan ku da matar ka ba zaka aza min laifi irin haka na zargi ? Ba zargin ki nakeyi ba don Jummai ta fada min kece kika kai mata tsegumin yarinyar nan Fatima yar wirin maimuna. Wiki wiki tayi da ido tana dukar da kai kasa tana cewa ni bada wani manufa na fada mata ba don dai naga yarinyar ta girma ne shine nake magana amma in hakan ya bata ma rai kayi hakkuri. Yace wanan abin ya isheni kun dauki tsana kun sakawa yar mutane may ye laifin maimunaa wurin ku har make ita jummai din wa ta bari a cikin ku tunda tun akan auro kine bamu da kwanciyar hankali da ita a gidan nan. Abinda baku sani ba shine hadin kan ku yanzu na dauko hanyar gyaran shi tunda ba na Allah da Annabi bane sai kuje can ku hade kan ku ni kuma zan hade maimuna din mu gani. Yarinya kuma tazo ke nan da zama a gidan nan babu idan zata sai ku dafata kuci idan kuna iyawa ku zauna lafiya Yana fadin haka ya juya yana kokarin saka babban rigarsa nan ya barta ya fita batunta tana tsaye kanta a sunkuye ta kasa koda furta wani abin kuma balle ko ta motsa don bata taba tunanen mijin nasu yasan sari ka noken da takeyi tsakanin shi da matar shi ba uwargidan su. Sai gashi yau daga sama yana fada mata halayen ta a natse gashi ta kasa fadin abinda ya kawo ta dakin don nauyi da kunyar abinda ya gama fada mata. Yana gamawa zai fita ya kara fadin ku baku ko tunanen kaddara da mutuwa ya kawo maimu da yar ta cikin mu yanzu kun manta kaddara tana iya fadawa a kan kowanen ku don Allah babu inda baya ikon shi a duk lokacin da yaso. Wani irin yanayin nadama yazowa hjy maryam sai dai kafin tayi magana ya gwauta ta yai ficewan shi daga dakin ya barta tsaye tana sauke ajiyan zuciya. Ina zaune a falo babu kowa sai tv dake ta faman aiki shi kadai babu abinda nake sai faman tunanen makoma a gidan Alh sani da akace zama a yanzu ya dawo nan din din din. Hjy maimuna ta fito daga daki ta tsurawa diyar nata ido na wani lokaci haka yasa ta fahinci yarinyar tayi nisa a tunane wanda tasan ba na komai bane sai na kakarta. Ke sayadi shiru sai data fada sau biyu firgigit Fatima ta dawo cikin hankalin ta tare da dago kai tana kallon mahaifiyar nata sai kuma tayi kasa da kan ta don kawar da idonuwan ta da suka tara hawaye a lokacin. Take tausayi da soyayya yar ya tarsu a zuciyan ta wuri ta samu gefen yar nata takai zaune sai data sauke ajiyan zuciya kafin tace. Kiyi hakkuri sayadi ki dauka wanan wani abu ne kaddarare ya hau kan mu dani dake duka nasan akwai zafi a yanzu raba ki da kakar ki danayi a lokacin da kuke bukatan junan ku. Amma ba yadda zanyi ne yin hakan ya zama dole a gare ni don samun ci gaban ku baki daya nan gaba . Munyi maki alkawarin duk hutu idan kina son zuwa wurin ta za a kaiki ko ita tazo nan tunda naji Alh na maganan taimaka muna ma ta hanyar dauko zuwa asibiti nan. Kin san kuma don ke ce zaiyi hakan daba haka ba sai dai a barta can ta halaka kina ji kina gani tunda babu abinda zakiyi. Tun zaman ta data fara magana sai yanzu naji sanyi ya ratsa min zuciyata jin za a dauko min manjo kusa dani da gaskiya. Tace amma fa hakan bai faruwa har sai kin sake ranki a gudan nan ya gani haka zai sa yaji karfin dauko manjo din kusa dake. A hankali nasa hannu na share hawayen da ya bata min fuska da farko na sauke ajiyan zuciya tare da dago kaina na kalle ta a karo na farko data zauna a gurin . Tace kwarai amma fa sai kin daina wanan tunanen yaga kina walwala a cikin mu kin sake jiki da kowa a gida nan kin rugumi yan kannen ki kin saka su a jikin ki. Kin mayar da hankali a wurin karatun ki na boko dana mahamdiya hakan zai sa ya ji dadin tallafa muna amma idan kina cikin wanan halin karshen shi ma yace a mayar dake can din kin ga ke nan ke kika cuci kakan ki mai neman taimako a yanzu da kanki. Da sauri na kara kallon ta tace eh ke kika cuce ta mana tunda kin ki ki kwantar da hankalin ki mukai ga manufan na son ya taimaka maku tunda ba halin in fito baro baro ince ga yadda nake son aiwa mahaifiyar tsohon mijina daya mutu. Da kyat na bude bakina da yai min nauyi nace mamu na daina insha Allah zanyi kamar yadda kika ce inyi insha Allahu. Tace da kin kyautawa kanki tana mikewa take fadin hakan daga haka ta fice a dakin ta barni ci gaba nayi da tunane can dai na dan gano abinda take kokarin fahintar dani din da sauri na mike na tsiri gyaran falon dole har zuwa dakunan kwanan mu duk dako a gyare suke a lokacin. Ta dan dauki lokaci sai gata ta shigo tsayawa tayi tana bin falon da kallon aikin danayi har zuwa bedroom din ta sai dai bata tarar dani a falon ba lokacin na shiga wanka. Na fito daidai lokacin ta leko dakin nawa tana fadin yanzu Alh ya bugo min wai gobe za a kaiki makaranta ai maki inter view. Sai dai ina ganin kamar makaranta daya zaku dinga zuwa da sauran yaran gidan nan don haka nake son ki koyi kawar da ido a kansu domin su din ma kamar sunfi iyayyen su kishi dani a gidan nan. A Cikin rashin kuzari na amsa mata da to kawai babu abinda zancen bayan wanan amsan don yanzu ba zance ga diyan gidan ba tunda ban san ko dayan su ba har lokacin. Takai kofa ta juyo tana fadin kina iya yin sallah yanzu don azahar ya yi nake gani idan kin idar sai kije gun Gwago tana tambayan ki wai kwana biyu baki shiga ba gurin ta ba. Duk a sanyaye nake jarbawa do har lokacin ban gama walwalewa daga damuwn da nake ciki ba. Ban gama shiryawa da wuri ba don haka na bata lokaci zuwa sashe Amma din har lojacin da kanne na suka dawo gida daga school. Wanka nayi masu ba tare da umurtan mamu ba don gani dama na kawai cikin kokarin ganin na sake kamar yadda mamu ta bukaci inyi. Sai dana shiryasu muka zauna cin abinci wanda na gani ga fuskan mamu hakan yai mata dadi ba kadan ba saidai bata fito fili ta fada min hakan ba. Mun samu amma zaune da yan matan mama hadiye da suka dawo makaranta basu ko cire uniform din jikin su ba suna zaune dashi muka shigo part din da sallaman mu. Amma tace wa nike gani nan kamar yar bauchi wai nikan aruwa uwarki rowan ki takewa mutane ne a gidan nan. Ace muna gida daya tun shekaran jiya rabon da in saki a idona ko da yake takawo min uzurin baki da lafiya ne. A raina nace Allah sarki uwa ke nan ta boye halin da nake ciki ashe bata fada masu gaskiyan abinda nake mata a part din ba don in na shige ban fitowa ina ciki zaune ko kwance ga matsin da nakewa yaranta koda yaushe. Har kasa nakai ina gaida ita yayin da yan matan biyu dake zaune ban ko ishesu kallo ba a gurin tana min ba,a tace ke ni kawar ki ce ki daina tsugunna min. Ga kujera can ki zauna yarinyar albarka kin samu tarbiya irin wanda ya dace diya mace tayi ba irin wa yan nan marasa hankalin yaran gidan nan ba tana magana tana nuna jikokin nata dake zaune. Sai kuma ta sake juyawa wurin su tana fadin ga yar uwarku nan nasan baku santa ba diyar maimuna nane tadawo nan gurin mu da zama ke nan ita ma. Kara sako min idanuwa sukayi suna kallona dayan tace a nan gidan itama zata zauna ke nan ? Amma tace gashiko kin ji na fada maku dama ai itama yar gidan nan ce ba bare ba a binda yayiku shiyayi ta itama don haka ina son a zauna lafiya a tsakanin ku. Suna wani ya mutsan baki tare da fadin mu may ye namu a ciki sai dai idan wa yancan dake kurin gidan su ne kullun. Amma tace rabani da zancen su daku dai nan nake magana idan kanku yana hade wane su su kawo maku wanan iskancin. Dayan ta koma ta kwanta ba tare da ta furta komai ba sai mu ke fira da Amman jefi jefi wanda ba wani hira bace ita dai ce mai tambayana labarin kakata ina dan bara amsa daya dace. Mun dan dauki lokaci a gurin ta na kado kan yaran muka dawo part din mamu inda muka samay ta tana girki. Ban zauna ba na nufi kitchen din gurin ta tare da tambayanta abinda zan kama mata dan murmushi tayi tare da fadin. Koma ki zauna na kusa kammala ba abinda zaki iya min yanzu kan nace nafa iya girki don nike girka muna abinci a dakin mu kuma manjo na cewa yayi dadi. Tace eh lalai manjo kan tace yayi dadi tunda girkin mu ba iri daya bane ki bari sai nan gaba kyayi ai ban dai fita ba na kama dauraye kayan da nagani tayi aiki dasu kafin in fito kitchen din. Ban yi wani hiran dare ba tunda ban saba kai wani lokaci a falke ba da anyi magariba nake shigewa barci don hakane muna gama cin abinci nayi masu sai da safe. Washe gari tunda na tashi ban kwanta ba a zatona tare da yaran zamu fita amma sai naga har sun fice batace min komai ba. Haka yasa na kara shigewa na kwanta ban sani ba ashe barci ta dauke ni a can cikin barci na nake jin ana tasheni a hankali na bude idona mamu tana tsaye a kaina tace ki tashi ki shirya ga mai kaiki school nan zuwa . Tana fadin haka ta fita ta barni a dakin na shirya wani dogon rigar na saka na tamfa sai hijjab dina dana dauko. Na dawo falo na zauna ita kadaice duk yaran sun wuce makaranta a lokacin don haka dags ni sai ita a lokacin muryanta na tsinkayo tana fadin. Don Allah ki natsu idan kunje don a san ajin da zasu ajeki a nan din don karatun na yasha bamban dana can sosai nna gyada mata kai kawai bata kai ga ci gaba da maganan ta ba mukaji sallama daga kofan part din ta. Ta amsa tare da fadin Ahmed shigo mana ka tsaya kuma can ya shigo yana dan gyara natsuwan shi a natse suna gaisa wa ta kalloni tana fadin ga yayan ku na nan nace ina kwana ya amsa a dan sake da lafiya. Anzo lafiya ko yaya mutanen gida ? Nace suna lafiya ba tare da ya karasa shigowa ba yace idan kin shirya sai ki fito mu tafi don Alh najirana zamu fita dashi. Hjy tace a shirya take zuwan ka take jira kawai a dauki hijjab dina dake gefe ina kokatin sakawa a jikina tace ubangiji Allah ya bada sa,a na amsa da amin tare da fadin sai mun dawo. Ta kara fadi Allah ya tsare ya bada sa, a muka fice mun fito daga part din tane naga hjy Jummai a karon farko tun shigowa na gidan mace ce kamar basamudiya ga tsawo ga kiba sai dai bakace sosai amma tana da dan kyau fuska gaskiya. Kallo daya tai muna ta kawar da kanta gare mu daga itama fita zatayi a lokacin don makulin motar da take kadawa a hannun ta ya nuna alama. Kamar yadda naji ya gaida ita nima haka na gaishe ta sai dai banji alaman ta amsa mako dayan mu ba. Muka fice itama ta fito a daidai lokacin ta shiga nata motan tare da wata mata daga cikin motar mu ina kallonta sun zuba muna ido musanman mani din suna magana. Tunda muka fara tafiya ya kunna kira,a a motan na shek Abdullahi Abba zaria a hankali nima nake dan kama inda na iya a cikin karatun. Mun danyi nisa da tafiya naji yace fatima kike ko na amsa a sanyaye da eh amma wasu suna kirana da sayadi wasu kuma suce min A ruwa, sai dai kakanina kawai ke kirana da a ruwan nan. Yace Fatiman dai yafi dashi zamuyi maki amfani a school din ke nan na gyada mai kai yakara cewa, kina zuwa islamiya a can nace eh sai dai ba ko yaushe ba don ni ban iya karya ba. Subbahanallahi naji yace har sai dana firgita ina kallon titi ko wani abu ya gani ya firgita shi ashe wai magana tace yake wa tasbihi. Don may baki zuwa kullun yace baki san shine zai cece kiba gobe kiyama wanan ai yafi na bokon da kikaga an mayar da hankali gare shi ma,ana sosai. Ko baki san da haka ba ya kara tambayana yana mai juya tare da dan kallo na nace naji ana fadin hakan . Sai naga ta dan saki murmushi kadan tare da fadin ji ma kikayi baki tabbatar ba nace hakana ne gaskiya yace to kin gane ina son kiyi min alkawari daya don Allah daga nan idan mun fito zan biya islamiya dake kusa da layin ku in maki register a nan. Don Allah ki mayar da hankali sosai ga karatun duka biyu wataran zasu amfane ki sosai jin nayi shiru yace kinji ? Nace eh cikin gyada mashi kai kawai yace alkawari fa kika dauka zakiyi tsakani da Allah kada in kai ki kwana biyu kuma kice kin daina. Nace a sanyaye zanyi don ko mamu naji tana maganan islamiya din gare ni yace dakyau shiyasa nake kara son halin hjy maimuna wallahi akwai sanin Allah ga al,amarinta . To yanzu kin gani tunda itama tana so kinga hakan zai mata dadi ni kuma nayi maku alkawarin zuwa in kaiku kullun kuma in dauko ku kin yarda da hakan ? Nace na yarda, banji kince in sha Allahu ba yace cikin dan kallo na nace insha Allahu din. Dan dariya yayi mai sauti yace bari mu gama da nan din sai mu wuce can ganin yana shiga wani gida mai kyau yasa na mayar da hankalina ina tunanen ina zai kaini kuma ? Sai da muka shiga naga ashe babban makaranta ne haddade mai kyau ga yan makaranta nan birjit dasu maza da matan su kowa harkan gaban shi yakeyi a gurin. Wani wuri muka tsaya da motar yace bissimilah muje na fito bayan ya bude min motar don ban iya budewa ba. Office din shugaban makarantar muka nufa namiji mutumin sai dai ba wani mai shekaru ba sosai muna zuwa suka gaisa da alama sun san juna sosai dashi don sai da suka dan taba hiran yaushe rabo dashi kafin su dawo zance na. Niko ina zaune sai raraba idanuwa nake a office din sai can naji yace wanan ne yarinyar yace eh itace kanwar tawa. Ya juyo gareni yana fadin maye sunan ki nayi saurin Fatima Abubakar Azare kallon Ahmed din yayi yana fadin na dauka ai yar garin ku ce ? Yace a, a diyar Alh nane a azare ake tayar da ita yace masha Allah fatima wani aji kike a can nace to a can ina jss 3 muyi exam din zuwa ss1 ne . Yace kai ya akayi karama dake karatun ki yai sauri haka amma ba matsala bari mu gwada ki mu gani. Waya ya daga ya kira wani layi ba a dade ba sai ga wata malama ta shigo suka gaisa ya nuno mata ni yace ina son ki gwada min wanan yarinyar ko zata iya wucewa ss. Tace yes sir tashi muje ko ta fada tana kallona na mike na bita ashe da ace ina zuwa makaranta dani gifted ce har ga Allah don Allah ya taimaka na amsa duka tambayan da tai min sai wurin lissafine na fadi daya. Muka dawo fuskanta dauke da murmushi har suna hada baki wurin tambayan ta to yaya tayi making ? Tace ba matsalan komai wallahi nan gaba ma zamuyi alfahari da samun ta a school din nan in Allah ya yarda. Ahmed yaji dadi tare da washe baki mutumin yace ta biyo ka ke nan wurin kokari unlike sauran yaran da ka kawo muna gaskiya sai a hankali lamarin su. Bamu fito ba sai da yabiya kudin komai da aka bukata har uniform sai da aka bani kafin mu bar wurin zuwa islamiyan nan ma sai da akai min gwaji akasan ajin da za a ajeni suma har uniform suka bani kafin mu dawo gida. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:42 - 🀐🀐🀐: HASBUNALLAHU WANI,IMAL WAKEEL, , , , , , , Ke mai kikai mata salma ta tambaya cikin wani murya ba tare da na juyo daga inda nake zaune ba nace ai gata nan ki tambaye ta . Cikin kuka take magana tana fadin wallahi dukana tayi fa anty sallama tace what ke kika duke ta fa ?? Ashe akwai tsiya yau a cikin motar nan nace ayi tsiyan mana wake jin tsoron ku wallahi kaf din ku ina iyawa daku na fada ina zare idanuwana gare su. Ganin hakan yasa Aisha ta dan duka tana mata magana a kunne ashe fadi take kinga yarinyar nan salma akwai abinda ta taka tunda kikaji tana fadin hakan. A cikin daga murya tace may ko ta taka a rayuwan ta Aisha yau sai na koyawa yarinyar nan hankali gobe ba zaki kara rashin kunya ba haka. Driver daga inda yake yana tsawata muna amma baisa mun bari ba idan sun fada mi in fada masu mai zafin da yafi nawa daci. Har motar ya tsaya muka fito tana kaimin dangwara a kaina a zikin zafi na rike hannun na murde ta ba tashin mu daya ba dasu suda sukai tashin gata daga falo sai mota ba wani abincin kwarai ake ci ba kuma. Sai gata tana batun faduwa nan sauran yan uwan sukayo kaina da duka nima na haukace masu ina kai masu duka iya karfina sai duk suka dare. Wani malami da abin ya faru a gaban shi ne ya kiramu mun fara mai bayani sai ya gane rikicin gidane muka kawo har school don haka ya kwashe mu sai wurin pc. Sai da ya gama sauraren bayanin kowa yace mahaifin ku zan kira don wanan abin ba za a kawo muna shi nan ba ku lalata muna sauran dalibai da rigima. Nan wurin ya daga waya bayan ya nemi layin Alh a addimition book ya kirashi sun gaisa ya fara mai bayanin komai yace ya bari gasu nan zuwa. Ba,afi awa daya ba muna rusunne a cikin rana duka yan gidan sai ga Alh tare da Ahmed sun iso hankali tashe yake kallon mu. Nan pc yayi mai bayanin komai ranshi ya bace ya juya wurin salma yace salma yaya akayi haka ya faru da girman ki bayan kece babba a cikin ku. Salma a ina kika koyi wanan halin banzan na rashin tausayi da zage zage a bakin da har kike iya budan baki ki zaki uwar mutum a gaban shi. Yana fadin a cikin yanayin bacin rai a fuskan shi karara kukan da salma keyi ne ya taba min zuciya naji ba dadi a raina nace don Alh a yafe muna mun yi kuskure Salma kiyi hakkuri. Jin hakan yasa kowa na office din kallo na da mamaki har abokan fadan nawa saida na basu mamaki. Nan dai akai muna fada sosai kada mu kara irin hakan nace a fada masu su bar zagan min uwa a gabana don ko gobe aka zagi uwata ba zan kyale ba Abba. Yace ba ma za a sake ba sayadi insha Allahu na amsa da to Abba nan dai muka shige zuwa azuzuwan mu har munyi nisa na cin ma salma da sauri nace kiyi hakkuri sherin shedan ne . Batayi magana ba sai kallona da tayi kasa da sama ta wuce abinta sai dai kafin mu bar school din har labari fadan ya karade school din ko. Inda yan ajin su salma da yake siniors ne su suna gaba damu da shekara biyu don tana matakin karshe ne ita inda su Aisha su uku muke classmate class din mu daya da Aisha. Haka seniors sukai ta shigowa suna ba punishement iri iri ranan sai dai duk ban dauke shi wahala ba a gurina nida na saba da wahalan samarin gidan baffa na . Don duka da zagi ba wanda basu koya min wahalan shi wasu senior har zagina suke wai don ina da kyau nake son daukan kai wa mutane. Nan dai yan matan ss suka kewayeni kowa na fadin albarkancin bakin shi a kaina wai ni da nazo gidan su salma cin arziki nake son in kawo masu rainin wayau wai sai inba salma hakkuri a gabanta in durkusa in taba takalman ta. Muna cikin haka sai can naji wani na fadin kai ga dan rainin wayau nan ya tunkaro ajin nan kila wani dan gulma ya kai mai tsegumin muna nan. Da sauri suka juya don ganin wa take fadi ganin mai zuwa tare da tawagan shi ajin sai naga sun fara natsuwa ni na dauka wani malami zangani sai naga ashe dan makaranta ne shima wanda ke sasu natsuwan. Yana gaba makaraban shi suna biye a bayan shi su biyar har yan class din naga sun shiga natsuwa a lokacin. Tsayawa yayi daga kofa yana kare masu kallo a raina nace shi kuma waye wanan din daya shigo suka wani kamay lokaci daya. Idon shi ya sauke a kaina lokaci daya tare dan tsura min ido sai kuma ya juya gare su yana fadin may tayi maku haka ? Da sauri wata ta juya tana fadin zagin Salma sani tayi don tana ta, , , , ke tashi don Allah yace dani sai dana tsaya kamar ba zan tashi ba ya sake fadin baki ji bane ya sauke min kallon shi dake girgiza yanmata a kaina. A hankali na mike ina karkarde buje daya dan kwashi kuran wurin a hankali daga haka ya juya mutanen shi suka mara mai baya da sauri naga yan matan suna ficewa class din. Suna fita yan aji sukayo kaina suna fadin ke kan kina da sa,a don yau sai sun dandana kudan su suma a wurin shi. Ko a mota da zamu dawo gida inajin suna magana ta kasa kasa banda salma da har lokacin tana a cikin fushi sosai da kowa. A ka,ida idan mun dawo da mun gaida mamu sai in kwabewa kanne na kayan school muje bayi in masu wanka daga nan sai in wanke uniform din mu. A daidai lokacin ne Nafisa take fadawa hjy jummai abinda ya faru ai yarinyar bata karasa ba uwar ta mike tsaye zubur tace wace Fatima kuke magana dai ? Wanan dai yar ta mamu data zo zataci gaba da bata labarin yadda abin ya faru uwar ta daka mata tsawa da fadin dallah rufa min baki . Ta juya ta fita sai part din mamu ta shigo babu ko sallama mamu na zaune tana sakawa yara tufafi a jikin su sai ganin ta tayi ta shigo tana huci. Da sauri take fadin hjy lafiya nagan ki a hakan shiya kawo hakan don yar agolan ki ta dakar min yarinya don tsaban rainin wayau. Ashe dama da biyu da uku kika dauko ta gidan nan don tazo ta tayaki kishi akan yayan mu . Hjy wanan wani irin magana zaki shigo min dashi haka ban san hawa ba ban san sauka ba asali ma wanan yarinyar tunda ta shigo bata fada min wani abu ya faru a tsakanin su ba yau. A daidai lokacin na fito zanje inshanya kayan dana wake a kofan baya wanda ake bi ta kitchen din su a fita a lokacin na tsinkayi abinda hjy jummai ke fadi. Tana gani na tace ehhe gata ma ke may ya hada ki da yaran gidan nan har kika iya daga hannun ki kika mari Nafisa. Mari hjy har abin yayi muni haka dama bashi kika sata tayi ba zaki wani nuna baki san komai ba yanzu akai. Ta sake juyowa inda nake tsaye tace tambayan ki nake samun aurin yar angola har yakai ta daki yaran gida kina tunanen ki zauna lafiya. Nace cikin dan tsiwa uwa ta take zagi niko nasan zafin uwata shine na kwabe ta na bata amsa da hakan. Eyye ke gaki mai uwa ko to an zagi uwartaki ko ita tai abin zagi ai zaginta za a yi balle ke agolan gida. Hjy wanan maganan bai kamata yana fitowa a bakin ki haka ba naga dai yar nan kema dai yar ki ce idan ga kara ko. Kin bari an kara maki ne da kika shigo da fankama da isa a cikin mu suna cikin hakane sai ga hjy maryam dan gara ita ta shigo da sallama falon saida ta bimu da kallo tace. Yanzu ran nan ke fada min abinda ya faru dazu da safe ai naje can ban samay ki ba sukace min kina nan. Ai dole inzo gutin wanan gitsaran yarinyar da aka jajibo muna a gida da sunan agola dama nasan shigowan yarinyar nan cikin zurian mu ba alheri bane gare mu gidan nan. Hjy maryam tace nima abin ya bani mamaki wallahi wai ace kamar wanan yarinyar ta daga hannu ta mari nafisa habadai. Yo ba zata mare ta ba an sakata rashin mutunci don tana yar ido to bari kiji idan ma daurin gindi kika samu nayin hakan zamu zuba a gidan nan muda ke a gani. Wanan marin sai ya zamo maki fitina da bala,i a cikin gidan nan don ba kyale ki zanyi ba ki daki banza . Hjy wanan maganan ga yarinyar nan bai dace ba gare ki don fadan yara babba bai shigan sa don kunya zaiji daga baya don haka a tsawata mazu dukkan su kada su kara nan gaba. Kyace haka mana tunda kin kawo muna jangwagwan a gida idan dai har sayadi jangwagwan ne a gidan nan ke nan sauran yaran suma sun zama jangwagwan a gare ku data mareta may yasa bata rama ba. Kinga da abin wata kila baikai haka ba a ranki tunda kinji zafin marin da akai mata amma bakiji zafin zahin datayi ba. Ranan dai sunyi nasifa sosai akan maganan inda da kyat mama hadiye da Amma suka shiga tsakanin su. Kowa abu daya yake fada mata akan fadan yara bai kamata kuna shiga ba haka inji mama hadiye. Kiran fatima da agola kuma fatima ta wuce a kirata da agola a cikkn gidan nan yanzu don itama gida tazo ba agolanci tazo yi ba a nan koda kuwa maimuna baga gidan nan fatima mai zuwa ne ta zauna daku. Mama hadiye bata kai kafshen maganan ta ba tayo cikin ta tana fadin dama nasan ku da daurewa karya gindi sai dai dadin abin sunan ta dai agolan gidan nan . Har mai gidan ya dawo gida daga kasuwa ya samu ana fitina a gidan tu a get maigadi ke fada mai yau gidan ba lafiya tunda rana ake abu daya a cikin gidan. Wucewa yayi ba tare da yayi magana ba yana jin muryan matan ya shige part din shi don rage kayan jikin shi ranan su salma basu leka islamiya ba suna daki suna zuga uwar su wai mahaufin nasu ya goyi bayana a school daya je. Sai bayan isha,i ya bukaci kowa ya hallara a part din shi ko wace ta shigo tana takama yana aiki shi bai kula da su ba sai bayan wani lokaci ya dago yana gyaran murya Yace hjy mai ke faruwa a gidan nan har na dawo ina jin muryoyin ku abinda naki jini da gani a gidana abin bakin ciki ace gidana ake wanan abin. Shiru falon yayi sai daya kara maimaita tambayan shi gare su ne hjy jummai tace Alh a gaskiya bakai muna adalci ba daga mu har yaranka yau. Yace ni din nan danayi maku mai kuma Alh yanzu ace daidai ne ka goyi bayan yar nan yar gurin maimuna don kawai tazo agolanci sai ta taka muna yara kuma ka dauki laifi ka basu. Jummai kin san abinda kike fadi kuwa ? Tace ai dama yanzu kullun magana ta ba daidai bane gare ka a daki mutum kuma a hana shi kuka. Yace su yaran suka fada maki hakan naje school din su kan fitinan da sukayi yau na basu laifi tace kwarai kuwa a to ka basu laifi mana tunda su kaiwa fada. Mikewa yayi zuwa waje ko anan ma daya barsu sai da suka dan taba don wanan karon hjy maimuna bakin ta bai mutu ba gare su. Karshe tace ko an sake ni na bar auren Alh dole dai ku gan mu cikin gidan nan don ba inda zamu tafi daga ni har su. Hjy tacr ina ko zaku tafi tunda ba a iya komawa gidan tsohu aci tuwo da kuka yanzu. Saukin abindai anan mata ta samay ni ba kuka kuma gidan kowa ana cin shi don ba abin raina wabane inji hjy maimuna din. Kada ki sake kice zaki zagan min iyayyena ban iya wanan ba don nasan darajan mahaifana sai ga Alh ya shigo damu falon buuuu a bayan shi. Wuri ya nuna muna mu zauna kowa ta nemi guri ta natsu ya fara tambayan karaman yar gurin hjy maryam ta koro magana tiryan tifyan ta fada mashi. Kallon gurin da take yayj yana fafin ki fada min goyon bayan da nayi a nan don Allah ta wani tabd baki tana fadin koma maynene aikai kaja muna shidai a gidan nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:43 - 🀐🀐🀐: SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI, SUBBAHANALLAHI AZEEMUN, , , , , , , Mamu tayi murnan ganin har islamiya akai mun register da kuma yabona da yayi kan an gwadani na samu nasaran wucewa gaba. Tayi farin ciki sosai da har ta kasa boye mai hakan a fili sai godiya take zuba mai tare da fatan alheri gare shi. Bai jima ba yana gama mata bayani tare da kara ja min kunne ya bar gidan namu a daidai lokacin da nake kokarin shigewa dakin mu don rage kayan dake jikina don ban saba da hakan ba sosai mamu kanta duke tana karanta takardan da aka ban admision a makarantar . Nakai kofa naji muryan ta tana fadin ashe makaranta daya kuke da sauran yaran gidan nan har kananin duk a can suke karatun su ai . Banji komai ba ga zancen ta illa faman tunanen yadda zan saka dan kayan da naga yan makarantar dashi a jikin su wanda dan buje ne sai guntun hijjabin da baikai ko ina ba a kawunan su. Har takalma da sock duk an bani a scchool din da littatafai masu yawa na karatu dans rubutu school bag kawai za a saya min a gida. Ina tsaka da cire tufafi jikina Mamu ta shigo dakin tana fadin idan kin gama sai ki fito na kwance maki wanan kan a gyara su nan kin san duk sati ake kitso a school din su. Wani iri naji gabana ya bada ace duk sati yanzu sai an taba lafiyan kaina ashe ko da magana ke nan a gurina don ba zan yarda ko wani sati ina cikin sance kaina ba aiko zaman kitson da sancewar aiki ne babba gaskiya nace a raina. Ita da kanta rana ta sance min kai ta wanke min shi da kayan kamshi na gyaran kai sai faman fada takeyi dani yadda akayi na bar kaina a hakan dankare ina mace dani. Shiru nayi ban bata amsa ba sai faman noke kai da nakeyi kawai a lokacin ranan dai na kara zama bakauya don abubuwan da take wa kan nawa. Sai ya kasance a karshe banjin zafin dana nake ji sosai bata barni ba sai da tayi min kitso shuku manya a kaina sai ga fuskana ya fito wani fau dashi ni kaina sai da naji sha,awan kaina a lokacin don kyauna da ya fara fitowa duk yinin ranan ban leka wurin Amma ba ina sashen mu a zaune. Da wuri na kwanta ina idar da sallah don dokin ganin gari ya waye na saka uniform din da aka ban a jikina. Ranan tare mukayi aikin break fast da Mamu sabanin da kwana hudun da nayi a gidan idan tana aikin ina dakin kwance abini ina kallon komai da take hadawa a lokacin. Sai da muka hada komai tace in je inyi wanka dana fito na zauna shiri ta leko tana fadin kiyi sauri don kada yan rigiman gidan nan su rigaki fitowa sina iya sa driver ya wuce ya barku ba karamin aikin su bane hakan. Jin abinda ta fada yasa na kara sauri kagin wani lokaci na shirya inda tasa mu a gaba mu hudu muka fito tana gaba muna biye da ita har wani part da ban san ko na waye ba a gidan ashe part din mijin sune takaimu mu gaisa dashi. A falon shi muka zauna inda na zube a kasa kafin ta fito daga dakin da ta shiga gurin shi can sai gasu sun fito a tare da maigidan ganina a kasa yace a, a Sayadi maynene haka zaki bata uniform din naki tun baki isa school ba ? Ina kwana nayi mai daidai lokacin da yake magana inda kuma maganan nashi baisa na tashi daga inda nake zaune din ba har lokacin. Yace kinga halin da baku koyawa yaran ku ba a gidan nan babba na saman kujera suma suna zaune a saman daidai lokacin da tagwayen suka ga na zube a kasa suma sukayi kamar yadda nayi iyayyen na masu dariya. A daidai wanan lokacin hjy maryam ta shigo da nata yaran duka hudu a falon ko ba a fada ba nasan zasu girmay mun ga shekaru. Mamakin yadda naga suna gaida mahaifin nasu nayi a tsaye ba tare da girmamawa ba a lokacin kuma mamu ke fadin ku tashi muje ko na yunkura da sauri bayan na gaida hjy maryam din da kwana tun shigowan ta yayin da sauran yan matan basuyi min magana ba sai kallo suke kare min tun shigowan su falon. Muryan Alh ne ke fadin ina kuma zata ban gama magana da ita ba koda yake ku tafi idan Allah ya kaimu anji mayi maganan a tsanake. Hakan yasa muka juya muka fara tafiya don barin shi da sauran iyalin nasa da suka shigo. Lokacin naji dayan yarinyar na fadin Daddy who is she ? Na ganta tare da mamu a gidan nan take ne kafin su bata amsa har mun fice daga falon bamu ji amsan da aka basu ga tambayan nasu ba . Part din Mamu ta nufa damu inda a gurguje muka gaida su tare da fitowa da yan matan shiyan duk da ba wani maganan kirki mukayi dasu ba bayan gausuwa sama sama. Wurin wata doguwar mota muka nufa data nuna muna shi da hannu tace muje ga motar kai yara makaranta can. Sai dai suna tsaye waje basu riga da sun shiga motar ba ina tafe tare da yan kanne na har muja kawo gurin motan. Kokarin tura kanne na nake a motar ba tare da nayiwa kowan su magana ba sai kokarin nemawa yaran inda zasu zauna nakeyi. Suna kallo na suna magana kasa kasa suna dariya bakun ta nake masu a lokacin don haka ban kula da abinda sukeyi ba a lokacin. Sai bayan mun zauna ne na hango wasu kuma tafe mutum uku suna tafiyan takama lokacin da suka kawo wurin motar naji babban nasu tace wace yar isan ce ta shiga motar ta zauna. Watace muma dai bamu san da ita ba gata nan dai a ciki daya daga cikin yaran hjy maryam ke fadi don su ganin su dazun da mahaifiyar su danayi yasa na sheda su. A cikin wani murya mai kama da tsawa tace min ke ki fito dan Allah kin zo kin wani shege mota kamar dashi kikazo daga gidan ku. Kamar ban san dani takeyi ba lokacin na basar da ita ta kara fadi da karfi sai naji yar wurin mama hadiye tace ki bita sannu mana kin san ita bakuwa ce a gidan nan bata san yadda tsarin yake ba. Bakuwa wurin mu tazo dallah malama fito kasa manya su fara zama koda yake ba saban ba na kauye yaga mota sai duk na kasan suka kwashe da dariya. Yar wurin mamu ce fa ita kuma ma ai bauchi ta fito zakuce ta kauye ce inji yar wurin mama hadiye dai ta kara fadin tare kara wai may yasa kuke haka wa bako ne don Allah. Mamu ko mamu tazo nan ai dole ta fito matan nan tunda ba don ta dady ya sai motar ba ehhe, sai yar wurin mama hadiye din ta leko cikin motan tana fadin ummm wanan fito daga ciki har su shiga sai su nuna maki inda zaki zauna ko ? Nace ok ina kokarin dagawa daga inda nake zaune naji karamar ta kara fadin su ok manya wanan kowa ya sanshi harda yan kauye. Ni dai bance dasu komai ba na fito daga motar lokacin naga tana jera yan gidan kaf din su yayan Alh daya haifa mu muna kasa zube da yaran mama hadiye. Sai can ta nuna muna bayan motar ta hanyar dan kallona a kyamace tace ke shiga can baya karshe sai ku, ku zauna daga bakin nan ta farko wani kallo na watsa mata bayan na daure na fito daga motar. Sai da kowa ya shiga tace oyo ki shiga cikin daurewa hakan na shiga sai dai a hanya a wani school muka sauke yaran mama hadiye. Dama ina mamakin kayan mu ba iri daya bane don su nasu wando ne da riga da hijabin su fari . Har muka kai school din raina yana bace da abinda tayi min ina jin suna shakiyancin su a mota ban kula su ba don rashin ambatan sunana da basuyi ba kuma mamu taja min kunne dama tun a gida. Wurin pc din na koma kamar yadda yace idan nazo inzo wurin shi ina zuwa ya kira wata malama ya gabatar dani a matsayin sabuwar daliban ajin ta ss1A. Ban samu matsala ba don bakowa na sani ba yasa na mayar da hankali gin darasin da ake koya muna. Kamar yadda mukaje haka muka dawo ban ma kowa magana a cikin su ina zaune a bayan motan a inda ta aje ni din da safe cewa shine kujerana can bayan kuma karshe. Mun dawo gida da murna da farin ciki a fuskan mahaifiyar mu tana tambayana ko na gane karatun da akeyi nace ina ganewa sosai don ni banga banga bambancin shi da namu ba ai . Dan dariya tayi tana fadin ki dai mai da hankali nace zan mayar insha Allahu mamu abinci mukaci kafin muyi sallah tace in shirya don karfe uku zamu tafi islamiyan yau don haka time table din ya nuna. Tace amma inje in gaida mamu da wuni na kwashi kanne na muka je part din tsohuwar mun samu su Aisha da bilkisu sun labartawa Amma abinda ya faru a wurin shiga motan. Dan murmushi nayi da Amma ke fada tana fadin duk bakin halin uwarta yar nan ta kwaso shi har salma ne zata zauna tana bada doka haka a gidan nan. A raina naji kwaein gwiwan yin abinda na shirya masu a gidan don na biyo uwata dake auren mahaifin su ai bace nazo bauta bane ? Mikewa nayi ina fadin zamu tafi islamiya sai mun dawo tace masha Allah hakan na da kyau wallahi kinfi wa yan nan da jahilci yaiwa yawa a rai. Tana magana tare da nuna su Aisha dake kwance mike saman dogon kujera bilkisu na dayan two seater. Nidai na fice na barsu suna badakala a dakin da Amma irin na jika da kaka sai suka tuna min da manjo na wace nake kwana da ita ina tashi a raina da duk motsina. Kamar yadda yace yazo ya bugo wa Mamu waya yana tambayanta idan na mun shirya don tun jiya tace tana son a hada da sauran yaran a tafi. Muka fito lokacin babu kowa a wajea mota muka samay shi zaune yana jiran fitowan mu gaida shi na fara bai karba yace sallama ya kamata ki fara yi mun. Sai kunya ya kamani nace na manta ne to sallamu alaikun na fada a kunyace ya amsa fuskan shi a washe. Ya bude muna motan muka shiga baya dukan mu motar yai shiru duk yaran suma sun natsu a motan. Sai ya kama dan jan twis da hira har suka dan sake jiki dashi duk da rashin sabon da diyan gidan basu dashi ga mutane duk zuwa gidan da yake yin bai sa yaran sun saba dashi ba. Sai da aka gwada ni sosai Allah ya taimakeni dan karatun dana fara a azare da kuma muka dawo misau ina dan bin Atika jefi jefi ashe karatun yana mu amfani ba sani ba. Naji dadin kasancewa na busy don yana debe min damuwan dake tare dani sosai dan kwana biyun dana fara karatu sai gashi ina warwarewa a hankali. Zan zauna a part din mu muyi hira da kanne na ko in koya masu assigment din da aka basu hakan yasa ba ma yawan fita idan ma mun fito bai wuce mamu bace ta matsa muna muje gurin Amma. Lokacin da sauran mutanen gidan su ka farga da ina canzawa a yan kwanamin da nayi a gidan wanda a lokacin kirana na asali dake samun gyara yanzu akai akai yana dada fitowa fili ga abincin lafiyayye har ina zaben abinda zanci a yanzu. Yasa aka fara gulma wai dama wahala da yunwa nazo dashi ashe hallitana na asali yake boye. Abinku da mata sai ga hassada da kyashi ya fara shiga fiye da da a tsakani da yayan Alh na cikin sa sosai duk da babu wani maganan atziki dake hadamu a ko inane. Lokacin da Alh sani ya samu labarin muna zuwa islamiya mu kaidai ranan yayiwa yaran shi fada sosai akan haka nan ya tillasta masu zuwa suma dole. Haka yasa sukai ta jinini akan wai iya yina yasa Abba ya tillasta masu sai sunje islamiya ai da a gida ake nemo malamin da zai koya masu. Amma yanzu nazo da iya yina na saka an tillasata masu zuwa cikin yara dole ban damu da zancen su ba idan sunayi don kallon mai saman ruwa nake masu. Satina biyu a gidan har lokacin ba wani abin arzikin dake hadani da kowa a gidan wanda hakan yasa na lura da hakan ma mahaifiyata take zaune dasu a gidan. Yau kamar kullun mun shirya zuwa school ranan kuma Alh zai fita da wuri mun riga kowa fitowa kamar kullun muna tsaye muna jiran su fito mu tafi don dokan Salma ne ba wanda zai shiga mota idan bata fito ba. Sai Alh yace ku shiga mana ku zauna kafin su fito akwai sanyi a waje don jan magana sai na kamay a wurin zaman salma din. Can sai gasu sun fito tana ganina ta daure fuska lokacin uban yana waya tana karasowa gurin tace ke fito daga nan waya baki izinin ki zauna a nan yau. Na nuna mata mahaifin nata nace gashi a tsaye sai ta dan juya don ganin wa nake nufi gaba dayan su suka juya sai mahaifin su suka gani a tsaye wurin da na nuna din. Waro ido tayi tace wai Daddy kike nufi nace shi mana ko kina da magana ne shiko Alh ganin yaran cirko cirko a tsaye basu da niyar shiga ga lokaci na wucewa yace. Cikin tsawa ba zaku shiga ku tafi bane may kuke a tsaye suka ce wanan yarinyar ce ta zauna ma anty salma wuri . Yace motar ba daya bace maza ku shiga ku tafi don Allah kafin in saba ma wanan zancen banzan naku. Dole ba yadda suka iya suka shige motar da sauri kowa ya zauna wurin zaman shi sai gurin da tace shine mazaunina dole ta zaunaTaTana cika tana batsewa muna barin wanjen suka taru a kaina da farko na kyale su amma da naga zagin yana son kaiwa ga mahaifiyata na saka masj waigi ta hanyar fadin kai fa malamai ku sani shiru shiru ba tsoro bane. Duk wace tace zata fadi magana mara dadi ga uwata yanzun zan nuna mata koni wacece don kar nake kallon ku, idan yarinya ta isa kuma ta kara:. Nafisa ce a kusa dani yar gurin hjy Jummi maibiwa sallama ra buds bKk zatayi magan ke nan sai ji tayi na kaiwa bakin ta naushi kut . Ta yanka wani irin ihu nace kadan ke nan kika gani wallahi idan kin ce mamu zaki zaga a gaba baki ba dai idan ban gurin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:43 - 🀐🀐🀐: JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA YASA MUNA CIKIN YAN, TATTATUN BAYIN SA ALLAH KA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , , Falom yayi tsit babu mai magana kowa ya natsu don ganin yadda Alh ke magana rai bace ga kowa dake falin a lokacin . Inda ya jaddawa matan shi idan sun kara fada zai dauki mataki akan ko wace mace data kawo masa fitina a gida. Sai kuma ya juyo kan yaran gidan inda yake fada sosai akan dole ne mu hade kai bai son nuna bambaci kuma ya zama dole na baya ya girmama na gaban shi. Haka ku ya zama dole ga babba ya tausayawa na kasa dashi bai yarda da akidar nuna banbanci ba a gidan shi. Ranan dai yayi fada sosai akarshe ya sallami kowa daga falon yace a bashi wuri yana son ya huta. Mu yara muka fara fita sai ga manyan mun hango suna firowa suma haka ya nuna yana son ya kadaice ne a lokacin. Muna shiga part din mu ina kokarin shigewa dakin mu muryan mamu ya dakatar dani daga shiga dakin da zanyi. Sayadi mai ya kaiki dukan Nafisa don Allah har yaushe kika zo gidan nan da kika fara fada dasu ? Mamu zagin ki fa tayi a gabana ni kuma ba mare ta dan murmushi naga ta sauke a fuskanta ni kuma naci gaba da fadin kuma tun ranan da na fara zuwa school suke min rainin wayau a gidan nan kullun hakuri nake dasu. Kai ke kan da ace zagi yana tsiro a jikin mutum ai da ban saura da fata a jikina ba don zagi kullun a cikin sa nake gidan tunda na auri mijin su. Baki na dan turo gaba ina magana ciki ciki tace don Allah ki daina biyewa shirmay su kuna zama daidai dasu a gidan nan in munyi hakkuri watarana wucewa zaiyi. Duniyar har guda nawa take ma da mutum zai biyewa rudin ta shedan ya ribance shi. Kinga neman magana dama suke a kan mu don zaman ki gidan nan bai masu dadi ba ba dai yadda zasuyi damune don Allah ki bar biye masu kuna wanan jidalin haka. Nace na bari mamu tace kin kyauta Allah yayi maku albarka ki kula da kannen ki dakyau duk lokacin da kuka fita don haka idona yake a kansu zuwan ki ne ma har suka daina shiga tsangwama sosai. Bayan mun gama na shiga nayi wanka ranan dai zukatan kowa ba dadi a gidan don su a nasu bangare duk da adalcin da Alh yayi hakan bai masu ba. Sai suke ganin ai ya goyi bayan mu nida mamu ne don baiyi masu yadda suke so ba haka yasa hjy ta daga waya tana kiran yayanta tana labarta masu abinda ya faru. Sai dai ta canza maganan inda ta fada masu abinda ba shi ba rayukan su ya baci sosai kan irin abinda mahaifi su kewa hjy akan sauran matan shi yanzu Washe gari ko da muka tafi school har muka dawo gida ba wanda yai mi magana a ciki su nasan sun hade min kaine don su matseni a gidan. Sai dai mun dawo mun samu farin ciki a gidan don a ranan Alh ya gabatarwa matan shi da kyautan motocin da dan shi ya turo masu. Haka yasa mamu zuwa part din hjy jummai tayi godiya akan alherin da danta ya aiko masu don yaba kyauta ai tukwaici ne. Sai dai tayi da ta sanin zuwa duk da dai ta debe mata hakki zama a tsakanin su dan ta yayi masu alheri kuma ta gode. Don hjy cewa tayi bani ya kamata kiwa godiya ba ai tunda bada miyau bakina aka sai maku motar ba aima baku iya ba da kuke son gasa dani ai da sai diyan da kuka haifa su sai maku ba dana a tillasata mashi ya saya maku ba don kawai ana son yin gasa dani a gidan. Mamu dai godiyan ta dada yi mata ta fito ta barta tana mita akan zancen danta ya saya masu mota wai a munafuce ta . An tillata mashi dole don ya sai mota mota suma sai ya saya masu mamu na fita daga part din ta takasa hakkuri ta nufi part din Amma a fusace. Muna falon lokacin muna dan hira da Amma sai su Aisha da bilki dake kitso a gefe daya ganin ta haka Amma tasan ba lafiya ba wanan shigowan da tai mata a part. Wanda yanayi ta ya kara tabbatarwa Amman da hakan don bata shigo idan ta zo da safe sun gaisa sai kuma wani washegarin idan ta shigo gaida ita. Gaida ita mukayi nice ta karshe bata karba muna gaisuwan namu ba sai makarin hawa fushi da tayi. Tun daga tsaye take fadin hajiya gurin ki nazo Amma tana fadin ai gani nayi but na mike ina fadin yan kanne suzo muje. A daidai lokacin ta juyo inda muke tana fadin ku bamu guri zamuyi nagana sai tayi rashin sa,a don ni har na daga zan bar wurin ko. Amma tace ai ita wana tasan ta ido do harta mike kafin ki kora su ko idanuwan ta sun kada sunyi ja saboda fitina. Sai da taga ficewan mu a falon ta kara kallon Amma tace hajiya gurin ki nazo Amma ta dago kai ta kura ma yanayin da take ciki na tashin hankali ido kafin tace. Samu wuri ki zauna ki natsu jimmai naga ranki kamar abace yake a yanayin da kika shigo wuri ta samu ta zauna kafinta fara fadin. Hajiya Alh bai son zaman lafiya a kidan nan asalima shike kawo rikicin komai a cikin gidan nan yanzu hajiya ya dace ace Alh ya turasawa yaran don sun min abu yacd sai sunyiwa sauran matan shi . Babu haufi babu ko jin nauyi da dogon turanci Amma tace kwarai don ko shi ya haife su kamar yadda kika haife su matuka suna son albarkan mahaifi ya bibiye su. Sai dai ban tari numfashin ki ba na kai ga baki amsan maganan ki bansani ba ko yayi haka ta hanyar da sharia ta hanane kinga anan kuma maganan ki gaskiya ce. Kallon Amma takeyi kamar ta kurma ihu a lokacin saidai jin maganan ta na karshe ya bata kwarin gwiwan cigaba da maganan ta. Tace hajiya kin san komai a gidan nan yanzu ya dace don kawai yaran nan sun saya min mota Alh ya tursasa su akan sai sin sai ma sauran matan shi dole. Shi sanin ya akaita hakan idan ko hakane bai kyauta ba Amma ta fadi tana gyara daurin dan kwalin ta. Hakan ne ma hajiya don ban sani ba sai da motocin suka zo dana yi magana yace min ban isa ba Amma ta katse ta da fadin. Shi umarun ya fada maki da bakin shi an tursasa shi ya sai masu mota ko wani ya fada maki haka ? Hajiya kin san halin yaron nan ba zai fito fili ya fada min kai tsaye ba da binkice nane na gano hakan ya faru. Amma ta girgiza kai tana fadin hasashen ki da binciken ki ya fada maki karya jimmai idan ma gaskiya ne haka ne ina abin farin cikine ya samay ki a gidan nan. Yau har Allah ya nuna maki ranan da dan da kika haifa zaiyi alheri irin haka kinga ke nan ko a nan kin nuna kina sama dasu ke nan tunda har danki yana iya aiko masu da alheri irin haka. Kinga Allah ya nuna masu ke har kullun kina gaba dasu ke nan don har dan ki bake ba zai iya kyautata masu da abinda basu dashi. A lokacin hjy jummai ta sauke wani ajiyan zuciya Amma taci gaba da fadin kin ga kuma maganan nan Allah yasa a gabana akayi shi. Zaki tuna da ranan da kika daki tagwayen nan har zazzabi ya kama su aka kaisu asibiti bayan sun dawo uban ya shigo dasu nan ya zauna ke nan sai ga umar din ya bugo wa mahaifin nasa waya. Suna gausawa yaji kukan yaron da murya na ina fadin yaron yayi shiru uban yayi waya shine umar din ke tambayan ina kusa ne yaji murya na a gurina uban yake yace eh. Shine yakd fadin a bani wayan mu gaisa bayan na karbi wayan yakd fadin ke dawa ke fada nake cewa nida kanin ka mai irin zubin ka ke muna kukan banza don raki. Nan dai nake fada mai abinda ya faru a lokacin ne yace damu suyi hakkuri zai saya masu mota maman su taita shiga dasu. Jimmai kinji yadda zancen sayan motan nan yazo don haka ba wanda kike tunane bane ya tilasata wa danki sayen motan nan. Ta lumshe ido a hankali tana mai jin zafin tsohuwar kan maganan dafa fadi mata lokacin 16/11/2021, 22:43 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM TAWAKKALTU ILLA, LAH, LAUHAULA WULLA KUWATI, INNA BILLAHI ALIYAL AZEEM, , , , , , , , Ina zaune a class fuskana yana ga littafin lissafi da aka gama koya muna don kawai in gane nake da naci ga karatu idan an koya muna malami ya fita ban tsayawa surutu kamar yadda da yawan mu ke samun sakewa idan ba kowa a cikin ajin mu. Jin shiru da ajin yayi sai kuma kanshin da yadaki hancina yasa ni dago kaina da sauri a zatona wani malamin ne ya shigo muna. Sai dai ina dago kai na gansu a gabana seniors din makarantan ne wanan da ranan su salma suka gudu don shi yana tsakiyan su mutum biyu biyu a gefen shi su biyar sun shi a tsakiya. Gabana ne ya fadi na juya da sauri naga duk yan ajin a mike suke sai ni kadai da kaina yake duke lokacin da suka shigo ajin ban sani ba haka yasa nayi yunkurin mikewa a lokacin. Kamar yadda naga kowa yayi masu a ajin sai ya nuna min hannu ba tare da yai magana ba alaman in koma in zauna. Dam kara juyawa nayi in ga ko da wani yake magana sai naga akasin hakan gare shi ba da kowa yake magana ba kuma yaki budan baki yayi magana. A hankali na koma kamar yadda nake da farko ina gyara littafina da ke saman table a bude ya juya ba ba tare da ya tafi ba sai wani yace min. Ke may ye sunan ki na dago a hankali nace wa ni ina nuna kaina gare shi yace dake nake may ye sunan ki akace. Fatima Abubukar azare na basu amsa a takaice ina fadin haka ya fara tafiya sauran suka bi bayan shi suma. Har lokacin ajin na tsit ba wanda ke magana a cikin students sai da suka fice ajin da kamar minti biyar dan kus,kus ya fara a ajin sai ga su sadiya sani sun zo table dina sukace ke may kikai wa su gentle yau ? Waye kuma gentle na tambaye su a cikin tsiwa don ban son abinda zai hada ni hurda dasu don na lura yin kawa babu abinda ke cikin sa sai munafunci da saka wasa yasa nake jaye kaina ga kowa. Don ina ganin yadda kullun ake turke a cikin ajin ba mazan ba ba matan ajin ba sai kuma wasan banza a tsakanin yan mazan da mata da zaran babu malami a jin. Ganin haka ke sa da zara babu malami zan dauko littafina in dinga bita da sannu har in gane abinda aka koyar damu may yake nu. Da mamaki suke kallo na har suna hada baki wurin fadin ke baki san Gentle ba duk zaman ki school din nan ga yan mata na rushing a kasa duk yawancin seniors din son shi sukeyi. Yana masu yanga da han aji kuma mahaifin shi a garin nan last done ne na kudi shi din ma ai ba a nan ya tashi ba daga baya ne suka dawo nan kasan. Bansan shi ba kuma bani son sani don ba abinda nazo yi ke nan ba don Allah ku ban wuri abu nake anan yanzu. Ina fadin haka na dukar da kaina naci gaba da karatun da nake ba tare da nasa abinda nake karantawa ba a lokacin. Don haushi da takaici daya lulube lokaci daya karshe ma rufe littafin na kifa kaina a table ina tunanen da ban samu amsan shi ba don ban san dalilin tambayan sunana da seniors din sukayi ba. Bayan mun tashi daga school har lokacin ban sake ba can na hangi kanne tafe yana dangyashi alaman yaji ciwo a kafa shi da sauri sauri na karasa gurin yaron. Ina tambayan shi samir ke cewa wai wani moniter din su ne ta duke shi har ta fadi a hasale na dago daga duken da nake ina tambayan shi waye monitor din ajin nasu ya nuna mi wata bakar jeep dake gefen mu. Ba tsaya wani abu ba na nufi motar a hssale rike da hannu kanina lokacin driver yana kokarin rufe kofan motar yara sun gama shiga ciki. A tsiwace nace malam kada ka rufe kofa zanga yaro dake cikin motar nan dan Allah ya juyo da mamaki yana kallona duk da kakin dana gani a jikin shi bai sa naji tsoron shi ba. A ckiin harshen turanci ya kara tambayana na fada mai sai yayi kokatin rufe kofan ashe ma bashi bane driver driver yana gaban mota yana jiranshi. Rike kofan motar yayi kokari yi sai nasa karfina na tare kofan daga ciki motar naji ana bashi umurni da ya bude. Ya sara kafin ya bude motar wanan ne da suke kira da gentle zaune a bayan motar tare da wani karamin yaro da yarinya dukkan su saye da uniform din school din. Juyawa nayi wurin salim dake yamotse fuska nace kai waya tabe ka a cikin su yaron a hankali ya dago hannun shi yana nuna min cikin motar cikin tsawa nace bazakai magana ba ka tsaya kana nuni da hannu. Yace a hankali wanan ne ya nuna min yaron gaba dayan su sun tsare da ido har security din nasu nace. Kai may yai maka kajin masa wanan rauni haka a kafa halan a gidan ku ba,a koyama tausayin na kasa dakai bane? Haiy haiy make faruwa ne wai wanan gentle din ya dakatar dani daga magana ta yaci gaba da fadin may ya faru ne da kafan tashi yana magana da karamin yaron a cikin yanayin kallon shi. Banji may yaron yake fada mai ba sai dai karshe da yace nikuma na dake shi, nace don ka fishi girma ko may ? Ke dakata su fada muna yace kamar baison magana shiru nayi ina murguda vaki har ya gama tambayan yaran ba,asin maganan su. Ok ka bashi hakkuri yace bayan ya gama sauraren yaran akan abinda ya hada su tare da fadin John ina son mu kai yaron nan asibiti a duba kafan shi. Nace ku barshi tunda ya bashi hakkuri ai maje gida a duba mai lokaci ya kure a yanzu ina fadin haka na juya zuwa wurin motar mu. Wanda sai lokacin ns kula ashe hankalin mutane duk akan mu yake ban kula da hakan ba illa jan kanne zuwa wurin motar mu daya riga ya faka ko. Muna zuwa na dinga tura yaran a mota sai da naga sun shiga sun zauna na yun kura nima na shiga wurin zamana dake can baya inda salma ta bani tun ranan farkon zuwana school din. Sai dai ina zama naga wanan Gentle din yazo har bakin motar mu ya zura hannu ya dauki yaron ya juya zuwa wurin motar su. Kkarin fita nake daga inda nake zaune sai dai kafin na iso har motar tasu ta daga daga wurin ko tana kokarin barin makarantar. Na shiga uku ba furta ina kokarin bin motar da gudu sai dai ina motar har ta halba saman titin ko tana kokarin bace min da gani. Ba sanin garin nayi ba don haka ban san inda suka dosa da yaron ba a lokacin iba kokari tsala ihu baji salma na fadin. Kai wana masifan da daddy ya kwaso muna da may yai kama don Allah yarinya kamar yar mahakaciya gata nan kina shiga mota ko mu wuce mu barki a gurin nan yanzu. Sai Adawiya tace don Allah kyale ta da haukanta anty salma akace mata bata zaiyi ne a wurin su waye bai san yan gidan general ba a garin nan ? Koma sace shi sukayi ai sun rage muna fitina a gidan mu ne tunda ba su kadai bane yara Nafisa ke fadin wanan maganan . Na kalleta shekeke tare da fadin dama kowa yasan fatan ku ke nan a garin nan kuna bakin cikin buda ido ku ganmu a gidan ku. Sai dai kun makara don jini ya riga da ya gauraye da ruwa mun zamay maku ciwon ido ko sai kallo ko tsiyayyan hawaye. Zama salma tayi a mota tare da ba driver umurnin da su tafi ina kallo sukaja mota suka barni gurin tsaye. Sannu a hankali ake watsewa a haraban makarantar har aka dauki yaran karshe. Ya rage saini sai security makaranta kowa har malamai sun watse a school din na hada kai da gwiwa ina kuka a hankali mara sauti ba abinda zuciyata keyi sai tunanen halin da dan uwana yake ciki. Ko su din su waye da har zasuyi min gaba gadi haka da dan uwana jin karan motan da nayi baisa na dago kaina daga yanayin da nake ciki ba. Muryan nan mai kama dana izza nasa ya karade min kunne yana fadin ke tashi kuje gida time na shigewa kada a ga kun dade. Da sauri na dago kaina ina kallon su na sauke ga kanina dake rike a hannun shi an daure kafan da bandage. Cikin wani kuzari na mike tsaye ina fadin samir ina suka kai min kai may sukai maka samir. Maikon yai magana sai kawai ya jingina kansa a jikina yana lumshe ido kamshi na shafa a hankali ina ma yaron sannu samir. Ina kokarin rike hannun yaron muka fara tafiya ba tare da nasan inda zamu dosa ba don a mota muke zuwa kullun sai gashi yau zamu a kafa tunanen da nakeyi ke nan a raina . Horn din mota mukaji a bayan mu na juyo sune na kawar da kaina da sauri daga kallon su muryan shi naji yana fadin ku shigo mu sauke ku gida. Kamar in ce a,a sai na tuna ban san hanya ba don haka banyi gardaman shiga ba wani irin kamshi da sanyi naji ya doki hancina da gangan jikina a lokaci daya. Duk sai na raina kaina a karo na farko a gaban wani na zauna a takure wuri daya can nisa dashi kadan kannen shi da samir suna tsakiya mu haka yasa nagane basu je gida ba suma har lokacin. Hanya kawai nake iya nuna masu ban san sunan unguwa ba lokacin da muka kai kwanan unguwan na nuna a cikin sauri da fadin wanan ne unguwar mu. Da kwatance na nuna gidan muna tsayawa mamu da Alh tare daAhmed suna kokarin shiga mota muka karaso a gaban su muka sauka daga motar fuskokin su da alaman damuwa karara. Ina kallon ajiyan zuciyar da mamu tayi da mukai arba da ita na fito da sauri ina fadin mamu wallahi ba da gangan na tsaya ba samir ne yayi targade a kafan shi shine, , , , , Muryan Gentle ne ya katse ni da yake gaidasu Alh a cikin ladabi tare dayi masu bayanin abinda ya faru tsakanin yaran a class. Ya kara da fadin shine muka dauki yaron zuwa asibitin mu don a duba kafan idan baiji ciwo sosai Alhamdullahi mun samu dan targade yayi a kafan shine aka daure tare da bashi wanan maganin yana miko masu ledan magani. Nasan zamu samu wanan a school don yarda muka barta hankalin ta ya tashi muna komawa muka samay ta can shine muka kawo su gida yanzu. Ya kare da fadin don Allah ayi hakkuri ga abinda ya faru kuskure aka samu Alh yace babu komai dan albarka mungode hakika hankalin mu ya tashi. Da yan uwansu suka dawo ba tare da su ba sai dai da suke fadin wai da yan gidan kune suke rikici yasa ban wani daga hankalina ba. Don nasan gidan ku ba batacen gida bane a garin nan ayi hakkuri dai nagode da fahintana da kukayi mu zamu tafi ke nan. Godiya Alh dake rike da hannun Samir ya kara yi mai suka wuce sai lokacin Ahmed dake kallon yaron tunda ya fara magana ya yi magana. Ya akayi yan uwanki suka dawo ba tare dake ba nace da zasu tafi da yaron ban san inda zasu kaishi ba na fito daga motar shine salma tace su wuce su barni. Nafisa kuma tace wai ina cika su da ihu in ma samir ya bata ai sun rage mugun iri a gidan su ido suka zubo min ina rabbata masu yadda akayi . Muryan Amma ne bayan mu ta fito cikin tashin hankali tana fadin yaran sun dawo ne ko angansu ne ? Mamuce tace yanzu aka sauke su ashe asibiti aka kai samir din shine ita kuma ta tsaya tana masu ihu yan uwa suka wuto suka barta a can. A man tanada gaskiyar ta ina zata dawo tabar dan uwanta a can bata san halin da yake ciki ba su da dauke shi bai abin bai damay su ba ai kinga sun dawo ko ? Hajiya wa yan nan yara ban san ya akayi haka ya shige su akan yan uwan su ba ga Alh na iya kokarin shi wurin hada kan su guri daya Ahmeda ke fadi cikin bacin rai. Kaiyya kamar baka san tsatson da suka fito ba ai wa kumbo wa kayan cikin sa mugun akidar da ake cusa masu ne a zukatan su tun suna kanana shine ke aiki. Hajiya mu shiga daga ciki Alh ya ce da ranshi ke mashi suya kan abinda yaran shi suka aikata amma sun zo gida sun fadi abinda ba shi ba da farko. Ganin kafan ya farawa yaron tsami yasa na sunkuya na dauke shi na barsu a gurin suna karasa magana don Amma bilhaki take fada yadda wanda duk ke ciki zai iya jinta. Kasuwan da Alh bai koma ba ke nan ranan ya zauna a gida gashi girkin mamu ne haka ya kara tunzura ran matan shi kunsan mata basu raina abin kishi sai suke ganin hakan da yayi yayi ne don ya gyarawa mamu ranta damu yayan ta. Bai yi maganan ba sai dai washe gari da muka shirya zamu school naji mamu tace min mu dakance ta itace zata dinga sauke mu school daga ranan. Hakan yai min dadi a raina sosai don zan huta da shaguben yayan gidan da suke min idan zamu school dasu gara da rana wurin zuwa islamiya don Ahmed ke yawan kai mu kamar yadda yayi alkawarin kaimu din kullun sai dai wani lokaci idan aiki yai masa yawa driver ya kaimu. Idan kuma yarinya bata fito da sauri ba ko taki zuwa zai dauki matakin haka da kanshi don har kofan uwarta zai tafi ya ci mata mutunci a can sai ta fito ko an fada mai dalilin rashin zuwanta. Hakan yana bakanta ran iyayyen sosai ba yadda zasuyi don maigidan ya bashi go ahead din haka dole ko subi umurnin shi. Mun rigasu ficewa gidan don a zaton su bamu fito ba mun makara ne yasa sukaja motar su suka tafi ba tare da sun jiramu ba duk da su Aisha sun ce a dan dakanci fitowan mu mana. Sai suka yayyako su da masifa dole sukai shiru suka kyale su hakana suna kallo aka tafi badamu ba . Samir bai samu fita ba ranan saboda kafan shi da yai masa tsami ga zazzabi na barazana akanshi yasa mamu tace ya zauna gida. Kai rayuwan gidan yawa da gidan da ake da zafin kishi sai a hankali duk wanan abinda ya samu yaron bai sa wani daga cikin matan gidan ta jajantawa mahaifiyar mu ba. Don banga wanda ya leko part din namu ba da sunan zuwa duban yaron da ake fadin wasu sun tafi dashi a mota ni kuma an barni a school ina ihu. Hakan yasa na kara fahintar zaman da mahaifiyar mu takeyi a gidan da abokan zaman ta abin duk da nake yarinya a lokacin ya ban haushi da mamaki a raina sai dai babu galin magana a gare ni don mamu ta kwabeni ga hakan. A school kuma tun bayan gama assemble ina class din mu zaune sai dai ban sani ba ashe maganan ya karde school wai nayiwa headboy rashin mutunci jiya a gaban kowa har yasa security din sa suka zane ni. Wasu kuma suce ba haka bane kanina ne yayi rashin kunya wa head boy din da kowa ke tsoro ya sa aka hukunta yaron karya dai iri iri gashi nan irin na students ranan yana yawo a school. Haka yasa yan matan dake rawan kai gare shi sukaji zafi suka shirya daukan mataki a kaina duk ina classa ban san anayi ba ciki kuwa harda salma don itama senior ce a lokacin. Bayan breakfast sai gashi wata ta zo kirana wai in samay su a bayan shop din school ban faye fita ba during break sai idan zan duba kannena ne nakan dan fita. Na tattara kayana na nufi inda suke nema din na samay su sun kai su goma sha a wurin ko wace ta murtuke fuska ga wani dogon bulala a hannun wace ta fisu tsaruwa da girma a hannun ta. Cikin rashin ko in kula na isa gurin tunda nasan ban masu komai ba asalim ko yan ajin mi ni ba abinda ke hadani da kowa. Ina zuwa nace ance kuna nema na anan ko gaba dayan su suka hayyayako min lokaci guda wai may na taka da bazan rusuna ba zan zo masu a hakan. Wata tace inda ba ke din yar wata da wani ne wace ke labe a gidan mutane take agolanci zakiwa mutane daukan kai. Raina ya baci da kalaman ta nace dadin abindai ba shegiya akace maku nake ba mutuwa ce inda ubana yaje uban kowa zai iya zuwa can. Daga kirana sai ku kama zagina may ya hadani daku ba ruwana da kowa a school din nan abinda iyayyena suka kawo ni yi nakeyi. Taaaa naji saukan wanan bulalan a jikina sai da na murde a wuri daya kafin in rike bulalan da tayi niyar kara zabga min a jikina again. Sake yar iska ko na illanta ki yau a school din nan inga uban da kike takama dashi da zai tsaya maki a garin nan. Ke har kin isa kiwa gentle rashi kunya na rasa may ye dalilin shi na rashin daukan mataki ga wanan yar iskan mara kunya. Banda kowa sai Allah kamar yadda aka fada maku ina zaman angolanci ne a wurin mijin uwata kuma kawuna. Allah ne gatana shine gatana a garin nan ke da ubanki zai zauna gadin duniya sai ya zauna na karasa fadi ina mikewa tsaye tare da kokarin tattara bujena don na shirya masu bala,in dana boye a ranan. Wata tace ji yar iska har mikewa tayi bayan ana fadi tana fadin da takeyi nace ke uwata ce da zanji tsoron ki komay na san dai ban maku komai ba a kan gaskiyana nake don haka wace ta isa ta kara buguna ta gani. Salma tace ba na fada maku yar iska bace bata da kunya dama yanzu ai zaku gani da idon ku nace salma rufe bakin ki naki bala,in yana zuwa don nasan kece da hadin wanan sherin. Sai wata tace kunga ku kyale wanan yarinyar ta tafi kunga dai wanan abin ba zai haifa muna da mai ido ba tunda tafimu gaskiya bata san komai ba tace. Sukai cikin ta da sababi dole tayi shiru a wurin ta koma gefe tana kallon ikon Allah ga bulala na rike a hannu na da shirin bala,i gare su sauran yan makaranta har sun fara zagaye wurin don mutane basu raina abin kallo balle sun samu ana rike tsakanin prefect da jinior din school. Kokarin kwace bulalan tayi sai ko na hanata nan kokawa ta kaure muna da tasan inda na fito da ita tashin falo tuntube da remote bata gwada hakan gare ni ba ranan. Na iya kokawa da yan matan gidan baffa shiyasa na samu lafiya ga matan sai mazan kan jibgeni son ransu. Batai aune ba sai gata a kasa na kashe ta nan sukayo kaina da duka nace in bakayi bani guri suna kai min duka ina ramawa na haukace masu gaba daya sai wuru ya dauki ihu baki daya hankali ya dawo gare mu. Muryan maza ne suke fadin amma ko kunji kunya wanan yar ficiciyar yarinyar ne kuke haka da ita ta gagare ku wata ta kawo min duka na kustsa cikin taro suna ja da baya sai dana cin mata muka kaure da ita. Sai da malamai suka zo suka raba da kan su aka kwashe mu zuwa staff room inda da farko aka ban laifi sai na fashe da kuka ina fadi don anga ubana ya mutum zai sa su zageni. Ina zaune na ban san hawa ba ban san sauka ba suka aika in fito suna nema na ina zuwa suka hauni da zagi da duka wai nayiwa wani gentle rashin mutunci wanda nima ban san hakan ya faru ba don tunda safe nake aji zaune ban fito ba. Will you keep quiety malamin ya fada da karfi sai wata malama tace amma malam sadiq kabi maganan nan yarinya ka fahinci abinda take fadi. Nan jikin shi yai sanyi ya fara bin ba,asin maganan dalla dallah har suka fahinci abinda ke faruwa aka gane duk salmace mai hadin a kaina. Har mansur din da suke kira da gentle aka kira a wurin yayi masu bayanin abinda ya faru tsakanin mu jiya bai rage komai ba nan malamai mata sukai kansu. Zane su akayi akai muna assemblen kan mu ranan ni hukuncin yin ruduness ga senior na aka kamani dashi inda aka hukunta ni wanan yasa aka san da ni a school din. Bayan mun dawo gida ban fadawa mamu abinda ya faru dani ba sai yamma ta tsinto maganan a dakin Amma ida su Aisha sukaji a wurin su ikilima yaran hjy maryam suke zancen. Ran mamu ya baci sosai tace zata canza min makaranta tunda abin yaki ya kare a tsakanin mu sai da Amma tace ta bari Daddy ya dawo zasuyi magana akai. Ta dawo part din ta ta samay ni ina wa kanne na assigment din su take tambayana may ya hadani dasu salma a school har mukai fada haka ? Nan dai na kwash komai na fada mata sai naga ta tsura min ido kawai lokacin da nake mata bayanin har na gama sai naji tace ke kan baki biyoni da hakkuri ba hakama mahaifin ki. Dago kai nayi na kalle ta don jin kalamin ta gare ni tace kwarai da ki barsu ga Allah idan ma sun zageki din ai kansu suka zaga din . Ita salma tana maki hakane don haddasa wani bala,i a tsakanin mu don su kawo rigiman da Alh zaiji ya tsaneki a gidan nan don su a kullun karshen mu suke son gani a gidan nan. Daga yau ban son in karaji kinyi fada da wani kan ko may nene ballae wanan dan zagin da hakan yana kan kowa ai kema bada son ranki kike zaune a gidan nasu ba da sunyi hakkuri kwana nawa ne ke mace ce fa kin kara gaba kin bar masu gidan su. Sannu a hankali mamu ke fahintar dani manufar su salma a kaina wanda ina fahintar ta saida a lokacin kurciya da wauta yasa ba zan gane komai ba don banji zan iya kyalesu suna zagan min iyayye ba a banza su tashi free. ZAINAB IDRIS MAKAWA AYI HAKKURI DON ALLAH NA RASHIN JINA KWANA BIYU YAN UWA. 16/11/2021, 22:45 - 🀐🀐🀐: YA SUBBAHANALLAH, KARIMUN, RAHIMUN, YA HAIYYU YA KAIYUMUN, , , , A dakin Amma muke zaune dasu Aisha dan na fara dan sakewa dasu yanzu su kadai ne zan dan raba inji dan sanyi a gidan. Kitso nazo suyi min sai dai har lokacin ban kwance kan ba su suka taimaka min na don haka nafi son zuwa wurin su duk sati suyi min kitson duk da mamu ta iya sosai. An kusa gama kitson ne mama hadiye ta shigo falon tana fadin hajiya ashe mutumin ki zai zo kasan nan ne dashi da yan uwanshi. Da mamaki Amma ke fadin wani mutumin nawa a ciki tace umar dai mana dan gaban goshin ki na gidan nan. Da sauri Amma tace ina kika samo wanan labarin kuma yau ake wanan zancen daurin gindin uwarsu suka samu yo waya sani ko sin kai ga tara iyali ma a can tunda ba wanda yasan wainar da suke toyawa a can yanzu. Haba hajiya da hankalin su zasu aikata hakan a kan su aiko wani da dangin shi yake kuri haka dai tasu rayuwa yake ba tunanen abinda kaje ya dawo gare su. Amma ta tabe baki tana fadin idan ma zasu zo Allah dai ta kawo su lafiya idan muna da rayuwa ma gansu . Lokacin azumi ya gabato saura yan kwanaki a tashi da azumi a fadin duniya don haka ake ta faman shirye shiryen taron watan mai alfarma a ko ina na fadin duniya. Hiran su bai shafe mu ba har mama hadiya ta gama ta fita zuwa unguwa kasancewa ranan weekend ne bata fita gurin aiki ranan. Sai da ta fita Aisha ke fadin wai Amma duk hjyan su salma ta haife su su ukun duka. Amma tace wai kina nufin baku san yannen naku ba da kike tambaya koda yake ba yau yaran nan suka tafi ba har shi wanan da ya tafi daga baya din sai lokacin Aisha tace ya kamal ko shi wanan na sanshi mana yana zuwa gidan mu lokacin da muke gidan Abban mu. Shi dai zaki iya shedawa su wa yan nan ai sin dade da barin kasan yanzu sun tasan ma shekara goma sha fa da tafi sai nayi karaf nace ashe tsufi ne ba yaraba. Dariya sosai Amma tayi wa magana ta tace inda ba tsofi ko yar nan karatu suka tafi yi can waje shine shiru basu dawo ba kin san ita jummai tana da son komai nata ace ya fita daban dana mutane. Yanzu gashi alama ya nuna yaran basu son kasan su ta haihuwa balle yan uwan su na jini kai Allah dai ya kyauta da hali irin na jummai wallahi. Ban faye sa baki ba idan ina part din Amma ana hiran yan gidan kawu din don horona da hakan da mamu keyi ko yaushe sai wanan halin ya fara bi min jiki. Koda naga sin buge da hiran sosai yasa na mike ina fadin barin leka mamu in taya ta aiki kafin yamma yayi sai Amma tace zaki gudu ke nan yarinya da radhin son shiga jamma,a haka. Ina dariya na fita na barsu suna zancen su kodana shiga wurin mu na samu tana sallah bata fara aiki ba nima dakin mu na shiga nayi sallah kafin in fito in fara gyaran ko ina na part din namu don shi nakan fara yi idan zamu yi aiki ko ina gida. ENGLAND, , , , , Suna zaune da merry a falo wayan shi yayi kara itace ta duba ta tabe baki tana fadin is from Nigeria da sauri ya karbi wayan a hannun ta yana duba mai kiran nasa . Mama ya gani a rubuce saman screen din wayan sai daya dan daga daga yadda suke zaune da Merry din ya gyara muryan shi. Ya dauki wayan da salma daidai lokacin yana kokarin gaida mahaifiyar tasu ta amsa mai a cikin jin dadi da annashuwa. Bayan gama gaisuwan su take fadin ranan wanan mondya mai zuwa ne tafiyan ku ko a cikin mamaki yace mama zuwa ina. Gaban hjy jummai ne ya fadi tace kamar ya zuwa ina kuma ina dan uwanka ya kirani yake sheda min zuwan ku ranan. Cikin murya mai taushi yace hakane mama saida nada ni bane zuwa ranan sai nan gaba kuma idan Allah ya kaimu zan sa lokacin zuwa don akwai aikin a gabana da zai, , , , , Jinan babawo umurni ne ba tambaya ba duk abinda kakeyi kayi haraman zuwa gida a cikin satin nan mai zuwa don nagaji wallahi. Na gaji da korafin mahaifin ku a kaina ko yaushe ya debo zugan shi a kan ku wurina yake sauke haushin shi. May kake son ka zamane babawo kana ko da tausayin mu a zuciyar ka, baza kayi kokarin sauke hakkin mu dake wuyan ka ba sai bayan mun mutu ko may ? Subbahanallahi mama may yai zafi haka harda wanan maganan in sha Allahu cikin wanan shekaran zan zo gida da yardan Allah kamar yadda na fada maki da farko. Ka dai ji abindana fada ma kuma gaskiyar magana ta kenan na fada ma yaya kake son inyi da surutun mutane a kanku ne ? Ko jiya jiyan nan sai da muka kwasa da Alh kan zancen ku har yake fadin don kana takaman kana turo muna da abin duniya kake ganin ka fita hakkin mu ko may ? Har yake fadin da goyon bayana kake komai don nice na daure ma gindi kake haka may ye a cikin zuwa gida ka gane mu idan kai baka son ganin mu. Mu iyayyen kane muna son ganin ka a rayuwan mu tunda muna raye bamu mutuba idan kuma dayan mu ya mutu sai kazo gausuwa idan ka samu lokacin hakan . Jikin shi yayi sanyi yake fadin Allah ya huci zuciyar ki mama insha Allahu zanzo kamar yadda na fada a dai dan kara hakkuri don Allah sai yaji kit ta kashe wayan. Hakan ya tabbatar mai da ta katse layin ke nan kuma tana cikin fushi dashi abinda bata faye yi dasu ba ke nan indai ta fara yai mata alkawarin makudan kudi yanzu zata aje zancen da take fitina akai. Sai dai yau an samu akasin hakan don ya lura mahaifiyar tasu ta hau sosai dashi duk maganan da yake merry ta tsura mai ido daga inda take zaune. Don fahintar da tayi yana cikin wani yanayi kan maganan da yake a wayan saboda yanayinsa daya canza a lokaci daya. Idan akwai abinda taki ninin ji shine taji ya ambaci zuwa gida yanzu hankalinta zai tashi su dinga rikici har sai taga ya janye tafiyan da yayi niyar yi din. Duk da itama kasanta ne na haihuwa amma bata son abinda ta danganta ta da Nigetia a yanzu saboda son mijin ta da takeyi . Don tasan ba abu kadan zai iya faruwa a tsakanin su ba idan har ya taka mahaifan shi yaje kano tasan sai yadda Allah yayi da al,amarin su ita kam. Don kafinta samu kanshi ta aure ba karamin yaki tasha kan haka ya faruba sai data hada da gargajiyan su nan ta samu ta ciwo kanshi ya yarda ya aure ta. Wanda tasan ba wani ahalin shi da yasan da zaman shi da ita don aure da sukayi snyi shine a can daga su sai abokan arzikin su. Ba damuwanta bane sai wani nasa yasan da ita ita dai burin ta ta samu kan mijin ta akoda yaushe ta kuma samu yadda take so din. Ko ita ta shiga tashin hankali lokacin da iyayyen ta suka samu labarin auren ta da dan kabilan hausawa kuma musulmi wanda abin gori ne da kyama a gurin su balle shi da tasan addinin su bai yarde masu da hakan ba kasafai. Wanan dalili ne yasa bata kaunan abinda zai sa yace zai je gida don tana ganin zuwan shi wurin iyayyen shi komai zai iya faruwa da auren su din. Kasancewan ta itama yar kasan Nigeria kuma daga yakin jos mahaifinta ya fito mahaifiyar ta ce yar kudu ko zo in kashe ka bata ji da hausa haka ma ita merry bata jin hausa sai dan gaisuwa da sauran kalama mai saukin haddacewa. Dan dama mahaifinta yana danji koshi ba sosai ba yafi bada amanna ga yaren da yafito daga ciki bai yi rayuwan shi a gida nigeria ba. Duk rayuwan su a kasan turai sukayi shi acan ya hadu da mahaifiyar merry din sukai aure wanda wanan dalilin yasa da merry ta hadu da Umar tana jin daga Nigeria ya fito suka kulla abotan daya zama aure a gare su. Yanzun haka da ake maganan nan tana dauke da cikin umar din wanda suke expecting din haihuwan ta ban da wata shidda masu zuwa. Kallon shi da yaga tananyi ne yace da ita is my mum tana magana akan rashin zuwana gida da banyi duk dadewan nan. And kin san gaskiya ke ma don kin kusa zama uwa very soon kin san irin feeling din dake tsakanin da da uwarshi a yanzu. Tunda ya fara magana ta kura mai ido babu ko kiftawa har ya gama sai lokacin tace may kake nufi da maganan ka Omar ? Yace kin sani zan tafi inga mahaifa very soon don nima rashin zuwana gare su yana damuna sometimes ina jin kewan su ina son ganin su. Ina son inga Family dina da, , , hannu ta daga mai tana fadin is eenough Omar ma,ana dai kana nufin gida zaka ka barni nan ke nan ? Yace yes haka nake nufi zanje gida in duba su in kwana biyu a tare dasu su gane ni nima in gansu in yaso daga baya munyi settle da mahaifina zan dawo gare ki da baby mu. Mikewa tayi tana fadin wanan ba zai taba yuyuwa ba Omar banki ba in kace mu tafi tare wanan zan dan yarda dashi. Da kuma sharadin idan munje zamu sauka a gurin iyayyena ba a garin ku ba har sai idan iyayyen ka sunyi acepting dina a matsayin daughter inlaw din su. Wani kallo ya watsa mata kafin shima ya fara magana a hasale yana fadin kada ki manta da alkawrin mu kafin muyi aure na fada maki koni waye kika yarda. Don haka idan kina son muci gaba da zama a cikin salama dake ki bari in fuskanci iyayyena ta ruwan sanyi bada garaje ba kamar yadda kike nufi din yanzu a kaina. Ganin da gaske yake idan akwai abinda ta ki a wayi gari su rabu da umar din ta don haka dole ta kyale shi a lokacin don tasan muhinmancin alkawari sosai. Ya juya ya barta wurin sha waran da kawai ya yanke shine zai tafi Nigeria cikin hakan kuma zai sanar dasu zancen auren nasa inyaso ayi wace za, ayi tsakanin shi da mahaifan nasa. Da wanan tunane ya kwana a ransa na yadda zai kalli ifon mahaifin shi da wanan laifin dayayi masu yasan cewa mahaifin shi mutum ne mai ra,ayi akan addinin sa sosai. Uwa uba irin tarbiyan daya basu tunda farko bai sako yaro wani kasa sai ja haddace alkurni da dan taba wasu litttafan addini. Shikan shi yakanyi mamakin yadda ta samu kansa dumu dumu da auren Merry koda kuwa ace itama din yar addinin shi ce ya kamata ace iyayyen shi sun san da auren su tun farko. Sai dai kaddara ta riga fata don Merry ta zama wani bangare na rayuwan shi yanzu zama suke a tsakanin su na so da kaunan junan su sosai. Yasan merry ba yarinya bace ko zai girmay mata da kadan ne a wurin shekaru sai dai hakan ba illa bane idan akwai so da kaunan juna. Auren shi da merry yanzu shekara hudu ke nan sai bana tayi ra,ayin haihuwa don a ganin ta ya kamata su zama iyayye a lokacin. A karshe dai daya gaji da tunanen sa sai yaga bai kyautawa merry sa ba a yadda suke akwai fahinta mai karfi a tsakanin su sai dai bai san dalilin ta na rashin son zuwa gidan shi ba. Gashi ita tana zuwa wurin nata iyayyen sun shirya da sukaga bata sake akidar taba na christanci dama su shine damuwan su. Haka dai yai ta sake sake a zuciyar shi har barci barawo ya sace shi ranan washe gari bayan ya gama abinda yake yaga har lokacin baiga merry ba yasan fushi take akan maganan su ke nan. Ya shiga daya dakin da take a ciki don idan tayi fushi haka sukeyi ko shi idan yayi fushi da ita. Tana kwance fuskan ta yana kallon daken din dakin ya shigo har inda take a kwace din yana fadin kin dai san condition din da kike a ciki da kikai wanan kwanciyan yanzu. Ta dago ido tana kallon shi yana tsaye ya harde hannayen shi a saman kirjin shi yace ko ba zaki gyara bane in gyara maki. Sai lokacin ta gyara tana fuskantar shi ya samu wuri ya zauna a gefeb gadon yana fadin ban san may yasa kike son yanke alakata da iyayyena da yan uwana ba. Ke baki tunanen lokaci yayi da zan fuskace su akan matsalan auren mu da basu san nayi ba don unborn baby din mu dake zuwa ? Ko kina son baby mu yazo ya samay mu a wanan halin na rashin wani nasa daga bangaren mahaifan shi ne ? Kai ta girgiza don jin abinda ya fada wanda tasan gaskiya ya fada ta bude baki da kyar tace a a ba haka nake nufi ba dear. Ina dai tunanen kamar in ka tafi ba zaka dawo gare mu bane kuma idan suka san da zaman mu a wani matsayi zasu karbe mu can. Yayi murmushi yace ina son ki gane idan naje gida nasan zamu sasanta da iyayyena akan abinda muka dade muna boyewa gare su nasan surely zasu fahince ni. Don aure nayi ba zaman banza nake dake ba and nasan halin iyayyena duk abinda nake so suma zasu so abin nan. So zama haka a cikin duhu ba zai yuyu akan mu ba, idan naje nasan babu wani dogon matsalan da zamu samu a gare su matukar na zauna nayi masu magana ta fahinta akanki. Sai lokacin mery ta danji sanyi a ranta taga zuwan nashi yana da amfani gare su matuka ta tace yanzu na gane na fahince ka amma kabi sannu kada kazo kaje a samu wani matsala kuma ya biyo baya. Yace kada ki damu da wanan ni nasan yadda zan fito masu da zancen ba tare da an samu matsalan komai ba. Da haka dai ya ciwo kan merry din har take ta faman taya shi shirin tafiya gida da zaiyi ba tare da an samu matsalan komai ba a tsakanin su don kawai unborn baby din su ya samu saki a wirin dangin mahaifan shi shima. Ni dai ina ganin yan part din hjy jummai sai shirye shirye sukeyi gashi an bude dayan bangaren da babu kowa a cikin sa sai dai lokaci lokaci akan bude wurin a gyara shi. Ko idan anyi baki a sauke su a gurin sai naga duk wanan kwanakin ana ta yan gyare gyare a wurin hakan dana gani baisa na mayar da hankalina in san abinda akeyi ba a gidan harkan gabana kawai nakeyi. Mun dawo daga islamiya ban shiga part din mu ba na bi ta baya don in kwashe shanyin uniform din mu danayi a baya sai nake jin murysn hjy jummai a wanan part din. Nayi abinda zanyi har na bar gurin bata fito ba bayan na shigo ne na samu mamu a zaune tana waya don haka na shige ba tare da na gaishe ta ba bayan sallama. Ina kokarin shiga bayi don in dauro alwalan magariba idan nayi sallah in zaman gugan kayan makarantar namu naji mamu ta kwala min kira. Da sauri na fito daga dakina ina amsawa na fito falon na samay ta har lokacin tana rike da waya a hannun ta. Nuna min wurin da yaran da suka dawo suka bata tayi da hannu nasan bata son kazanta don haka na gane may take nufi na juya zuwa dauko tsintsiya da packer don in dan tattara wurin. A lokacin naji abinda take fadi a wayan tana fadin ko sun dawo gidan nan ina ruwa na dasu hajara ? Idan mutum yace yanayi dani in yi idan kuma naga su maza sun dauki akidar uwarsu sai in share su tunda ba zaman su nake a gidan ba. Banji may na cikin wayan ke fadi ba sai naji tace gobe fa gobe goben nan idan dai ba sun fasa bane baki ga yadda mahaifan ke ta rawan kafa ba mu dai iyakan mu ido ai. Suwa zasu zo gobe naji mamu na magana na rambayi kaina da kaina da yake ba abinda ya shafeni bane na kwashe na fita daga falon. Ina zaune ima zaune ina guga bayan magariba mamu ta fito daga daki na san ta sallamay sallah ne a lokacin don tana saye da hijjab din sallah ta har lokacin tace. Sayadi kije part din gwagona ki karbo min kankara idan suna dashi nace to ina kokarin dagawa daga wurin gugan take fadin don Allah kada ki tsays hira dasu Aisha ki barni ina jiran ki. Nace ba ma zan tsaya ba mamu fon ban gama gugana ba gashi dare yayi na fito ne naga ana shiga da wasu kaya part din har Alh kanshi yana gurin a lokacin . Ko da na dawo still suna cikin part din fon daga can part din mu mutum zai iys hango abinda akeyi na raya a raina idan na shiga zan tambayi mamu . Sai dai ina shiga na samu ta kara tayar da sallah haka yasa ban samu tambayan ta ba komai. Washegari Jumma a ce tunda muka dawo nake kwance ina barci don ranan ba islamiya ga gajiya na kwaso yass na kwanta in huta. Can cikin barcina naji gida ya rude da hayaniya sosai sama sama nake tsinkayo muryoyin mutanen gidan har da Amma. Gyara kwanciya na nayi don nasan bai wuce wani fitina suka samu a gidan don su basu raina abin fitina gidan nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:48 - 🀐🀐🀐: YA, HAYYU YA , KAIYYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS, , , , , , , , , Daga manyan gidan har zuwa yaran gidan gaba dayan su murnan zuwan bakin su sukeyi har Amma kanta saida ta fito lokacin da ake fadin gasu nan sun iso gasu nan. Wanan hayaniyar ya hanani komawa barci na mike na fito falon mu babu kowa a cikin sa na nufi hanyar fita waje. A daidai lokacin da Amma ke fadin banga angona a cikin ku ba don shi na fito taro saboda shine yasan da zama na yakan kirani jefi jefi mu gaisa dashi. Kallo juna sukayi sai habbib ya daure fuska shi kuma dayan yace kai wanan tsohuwar da rigima kike dama muma ai bake muka zo gani ba dama. Ta dan tabe baki tana fadin daga fadin gaskiya sai bakar magana ka dawo ke nan baka ko huta ba ka shiga halin naka. Yace ai amsa na baki don ba wanda ya gyato ki nan maman mu da daddy muka zo gani sai yan kannen mu gasu nan sun tare mu. Aikin banza tace tana tabe baki ta juya wurin habbib tana fadin kai kuma abinda ka kara koyowa ke nan a kasan rashin fara, a, ? Ya dan gyara tsayi tare da fadin ohh wanan tsohuwar halin ki dai yana nan ashe ? Dan murmushi ta sake tare da fadin kai da alaman zamu shirya wanan karon don da gani kafi wanan mai askin arnan da shiryuwa. Kai Amma ki bar wurin nan ki bari mu gaisa da iyayyen mu don Allah tace ai yanzu ko ba sai ka kore ni ba marata ido. Ba dai naga saukan ku lafiya ba yace wanda dai kika zo taro bai zo ba sai ki shirya ki samay shi can idan kin so ganin sa. Hjy jummai dake ta bata fuska kan ba,an da suka tsaya yi da tsohuwan ta mayar da kallon ta gun habbib cikin nuna kulawa tare da fadin . Ku shiga daga ciki ku zauna kafin ku isa sassanku sai lokacin su mamu suka shiga gaida su da zuwa wanda sun sha jinin su tun kalamin Aliyu din dayace mahaifan su suka zo gani ba wani va sai yan uwansu. Ke nan su basu damu da tsayin su a gurin ba ke nan sai iyayyen su duk da haka abinka ga kawaici sai basu nuna jin zafin hakan ba a fuskan su. Sai lokaci su mamu suka samu gaisawa dasu inda suka amsa ba yabo ba fallasa a fuskan su ko wani kula da su, su nuna su din matan mahaifinsu ne kuma uwayen kannen su basuyi ba. Ni dai ganin Amma ta juya zata wuce nayi sauri kafin ta ganni ta sa inyi gaisuwan dole na bar wurin inda na samu kanne na a falon mu. Hjy jummai ta kalli yayan nata cikin so da kauna ta nuna ma su mamu kuma itafa ce da gida tace ai sai ku shige daga ciki ku huta. Daga baya ku gaisa da daddy da kyau ba mussu yaran suka fara shiga part din ta a can ta fara gabatar masu da lafiyayyen abincin dana sha wanda ba karamin kudi ta karba a wurin Alh ba don shirya ma zuwan yayan nata. Abinci da abin sha har sun rasa wanda zasu fara dashi a falon suka dan tsukura ana fira sama sama dasu da mahaifiyar su. Can tace watau dai ya tabbata shi babawo ba zai zo gida ba ke nan zaman can ya fiye mashi dawowa gida cikin yan uwan shi. Aliyu dake goge bakin shi da tisue yace ba wai hakana bane mama kin san yanayin aikin sa baima da lokacin kansa balle na tafiya . Ko yaushe shi a cikin aiki yake shiyasa ma ba,a faye samun sa sosai ba ai daiyi hakkuri don muyi waya dashi kafin mu taso na samu layin shi yace zai shigo da yardan Allah. Sai lokacin habbib da yake shiru shiru yace mama sai kun yi hakkuri da yanayin bros don wallahi aiki yayi mass yawa sosai kin san in mutum ya zama haziki haka kowa ke son aiki dashi. To amma habbib ace mutum ya shige cikin duniya haka ya manta da kowa nasa kamar bamu a raye ashe idan bamu raye ma shike nan sai ya manta da gida a rayuwan sa tunda shine agogo sarkin aiki. Yanzu fa akalla babawo yakai shekara goma sha da zuwa kasan nan shike nan shi bama zancen aure yakeyi ba a rayuwan sa sai neman duniya. Aliyu yace mama ke nan yanzu bros in dai duniya yake nema ai ya samu don ya wuce yadda kuke tsammanin sa gaskiya. Yanayin sa ne haka tun farko kun sani ko anan din da yake ai kin san irin halin sa na kin shiga jamma,a sosai. Amma ai zai zo fon ya tabbatar min da zuwan nasa tace yama zauna can idan mun mutu sai yazo gaisuwa . Haba mama hakkuri dai za a yi yana tafe in sha Allahu don su kawar da zancen dan uwan nasu saboda sunga ran mahaifiyar su ya baci yasa habbib din mikewa yana fadin zai shiga ya dan watsa ruwa ya mike don akwai gajiya a tare da shi. Nikan ina shiga wurin mu na gyara ko ina na saka kamshi na dawo falo muna kallon catton da kanne na muna dan hira a haka mamu ta shigo ta samay mu. Bin yanayin fallon tayi da kallo tana zama take fadin yau baki ne a gidan namu yan wirin hjy suka dawo daga kasan waje. Nace ai ihun murnan zuwan su ya tayar dani daga barci sai mamu duka maman su anty salma ce ta haife su ? Ashe kin gansu ke nan ta tambaya tana kallona nasan abinda take nufi bangaida su ba nace ni mamu yadda naga suna sakin magana wa Amma ne bai mun dadi ba kamar ba jikokin ta na jini bane su. Jikokinta ne kuwa don dukkan su uku hjy ta haife su babban nasu ina ganin bai samu zuwa bane kuma shi tun ina gidan mahaifin ki ya tafi. Da yana dan shigowa lokaci lokaci daga bayane kuma ya daina zuwa don ance yanzu aiki yake ma kasan england da wasu kasashe. Amma da ganin su zaman turai ya canza su ji don Allah yadda suke rungumar su salma da girman su tace ke dai don baki da yaya na miji ne kike ganin haka. Ni kan har kwanan su uku da dawowa ban saka ko dayan su a idona ba na shiga part din Amma karban abu na samu suna maganan akan tsaraba da aka raba a gidan wanda suka zo dashi. Sai nake jin Aisha na fadin kilama ko Fatima itama bata samu komai ba a cikin rabon nan hankalin su ya dawo kaina suna son ji ko an bani wani abu a cikin tsaraban nace . Ban ma san da su ba balle tsaraban su don ni bada abin wani na dogara ba Amma ina kayan abinci in dauka mamu tace in karbo mata. Tace shiga ciki yar nan ki duba kitchen sunanan a wanke na shiga kitchen din na fito Amma na fadin halin wanan matar sai ita duk irin kayan da yaran nan suka jibgo abawa yan uwa ta rike sai ita da yayanta ke shiga da fice a ciki. Ni ban tsaya jin abin haushi ba ba wuce tunda ba magana na bane muna raba abunci da mamu nake fadin yanzu su Amma ke tambayana wai an ban tsaraba bakin gidan nan ? Wani tsaraba kuma kai gwago ma dai da wani magana take komu da yaya aka bamu wanan tsaraban nasu ina sai da Alh yayi magana a kai ta dan yafuto muna Allah dai ya ba kowa nasa. Ni kinga irin abubuwan nan ba damuna suke yi ba a rayuwa idan ta bayar ya kare idan bata bayar ba wataran ma ya kare don haka ba wani abin damuwa bane hakan. Balle ma may ye a cikin tsaraban da suke magana wasu riguna ne sai atamfar holand guda daya yana nan saman gado na aje. Don basu wani gamshe ni ba dama ake na ajewa su idan kina so a dinka maki su nace da sauri a,a mamu ki dinka abinki kayan da kikai min sun wadatar dani nikan. Da dare ina zaune naga mamu ta kwashi kayan zuwa part din su amma ta dade a can sai gata ta dawo da su hade da wasu kayan ta zube saman kujera. Ta fita da abincin maigidan dana gama blending bada dadewa ba ganin bata dawo ba yasa na dauki yan kanne na da sukai barci nakaisu dakin barcin mu. Na dawo na kwashe kayan na shiga mata dashi ciki na jawo kofan mu na haye dogon kujera na kwanta a falon . Har barci ya dauke ni sai gata ta shigo na bude idona inga ko waye ya shigo falon tace dama nasan kunyi barci ina can na samay shi da yaran shi suna hirane kin san halin sa yace in zauna in jira fitan su. Jin banyi magana ba tace ina kayan dana aje wurin nan nace suna ciki na kwase dazu tace dama gwago ce tace akawo maki naki tsaraban kuma in tabbatar da kin dinka su kin saka. Nace ni ba zan saka ba tunda bani aka bawa ba mamu tace na fada mata tace ai tunda bata baki ba sai ta ganki dashi a jikin ki . Kai ita Amma akwai son rigima wani lokaci da kawai ta kyaleta tunda ba a tsirara nake tafiya ba. Wai yar nan ashe da gaskiya akace tashin kaka manyan magana ke ga bakin su ke wai har kin san wanan zancen da kike fada. Dan dariya nayi nace mamu wallahi har kin sa naji kewan manjo na ko a wani hali take yanzu bari dai in duba lamban Atika ko zanga inda na taba rubutawa a littafina da dadewa. Ba wanan ba don babba lafiya kalau take don munyi waya da Addah ki kwanan baya take fada min hakan. Sai dai abinda nake so dake yanzu a gidan nan ki kara kama kanki da zuwan yayan hjy gidan nan don ba mutunci ne dasu ba ko ni da nake mahaifiyar ki. Ban ishe su kallon arziki ba a yanzu bayan a baya can tare muka taso dasu cikin wanan family din ko don yanzu suna ganin su din wata tsiyace ko kuma zugan uwar sune a kaina ban sani ba. Nace mamu may zai hadani dasu niko a gidan nan yaushe ma na zauna a gidan ina gurin neman abinda zan zama in tallafawa manjona. Kallon tausayi tayi min don dama tasan jajircewa a kan karatu da karfin gwiwan maganan manjo datayi min nake yin sa. Sai dai a fili tace min nasan ki da tsiwa da rashin kunyawa na gaba wanan halin bai min dadi a raina ko yaya ne idan mutum ya girmay ka ya girmay kane. Ban san irin tsonewa mutane ido da kikeyi ba sayadi duk da nasan kin rage wanan tsiwan naki amma kullun laifin gidan nan bai wuce kanki saboda haka ki natsu sosai da komai da kowa. Wanan maganan da mamu tayi duk da bata fito fili ta gaya min dalilin ta ba na fagince ta a raina. Watau tunda gida mahaifin su nazo inbi a hankali saboda a zauna lafiya don ita ba mai son hayaniya bace a rayuwan ta ko kuma tsoron su take ban sani ba. Don haka naji a raina na tsani hjy jummai da dukka yaranta a raina matar da bata kaunan ganin kwanciyan hankalin mahaifiyata a rayuwan ta akan may zaga mutuncin ta nikuma. Kamar yadda mamu taja min kunne haka ma Amma da yaya Ahmed don shi cewa yayi bai yarda kwata kwata da tarbiyan su ba . Kamar sati daya da dawowan su garin ranan ina duke ina shara Aisha tazo shiyan mu tana daga kofa muna magana sai naji tana fadin ina wuni yaya Aliyu. Ya karba mata a takaice da lafiya yana fadin wanan na ciki wai cewa da mamu yake nufi naso in share shi sai dai na dago ina fadin ina wuni kamar yadda ya amsa mata nima hakan ya karba min don jin zazzakan muryan da nake gaishe shi dashi. Da sauri ya ware ido ya sake kallo na daga dauke kanshi da yayi da farko da kyar ya kara buda baki yace mai shiyan tana ciki ne ? Na daure a yatsune nace tafita kawai ba tare da na sake dagowa na kalli inda yake tsaye ba naci gaba da aikina. Ganin bai tafi ba ya tsaya yana danne dannen wayan hannun shi yasa na aje tsintiyar hannuna na shige part din mu. Ya bi bayana da kallo har zan shige naji yana fadin idan ta dawo ku fada mata na shigo ban samay ta ba Aisha ce ta karba mai da to yaya Aliyu nan nasan shine Aliyun gidan. Alhamdullahi ko ina a fadin duniya an dauki azumin watan ramadana har ya fara nisa ana neman rufe goman farko ba wasa a wanan lokacin . Da safe haka zamu tafi tafsiri da Mamu da yan kanne na idan mun dawo ba wani hutu zan dan gyara gida inyi duk wasu aiyukan daya dace . Don lokacin muna hutu dana gama zan tafi daukan karatu islamiya don ba kowane ke zuwa a wanan lokacin ba sai yan tsiraru daga cikin mu. Idan na dawo da nayi sallah azahar zan fara aikin abinda zamu ci a part din mu sai part din su Amma da muke sakawa abinci koba watan azumi bane wannan ka,ida ne sai mun saka masu nasu daga tukunyar mamu. Sai zamana a gurin mamu ya zamay mara alheri yanzu don dan lokacin ta samu saukin abubuwa a gidan sosai don yanzu na gwane sosai ga komai ba sai ta shiga kitchen ba idan ina gida. Ga wani girma dana kara makerin yan matanci na ya zauna ya kerani gwanin ban sha,awa duk wani sura da akeso ga ya mace ya fito min fili. Wanda hakan yake kara mun bakin jini gurin yan matan gidan don sai mutane su dauka nice ma yar gidan basu ba haka ke basu haushi har basu son abinda zai fitar damu tare dasu. ENGLAND Damuwa ne karara a fuskan ta ba sai an fada ma mutum tana cikin tanayin bacin rai da damuwa ba a lokacin. Merry ce tana zaune ta hade kai da kujera tana faman tunanen tafiyan mijin nata wanda zuwa lokacin ya gama duk wani shirin da yake son yi don tafiya gida gurin iyayyen shi ko. A hankali ya tako zuwa inda take zaune har ya zauna bata iya dago kai ta kalle shi ba sai daya dan dafa mata kafada ta dago jajayen idanuwanta ta sauke mashi. Merry wanan abin da kikeyi na fada maki ba shine mafita a gare mu ba ina tafiyan nan da yardan ki na shirya yin sa. Instead ki bani kwarin gwiwan yin sa don mu samawa kanmu da yayan mu mafita yanzu kuma zaki sare min gwiwa da wanan yanayin naki. Ajiyan zuciya ta sauke tare da dora kanta saman kafadan shi tana fadin Omar jikina yana bani idan ka tafi gurin iyayyen ka ba zasu barka ka dawo gare mu ba. Nasan irin rikicin dake a kanmu yanzu wanda dama na dade ina fargaban zuwan wanan lokacin a tsakanin mu nasan halin mutanen mu akan akidar su ta addini. Abune mai wuya gare mu su yarda ka dawo gare mu idan ka tafi ka barni yaya zanyi da baby mu da sonka dake cikin jinina a yanzu. Wani irin tausayin ta yaji a ranshi yasan maganan ta gaskiya ne abune mawuyaci mahaifanshi su yarda da zancen auren su kai tsaye. Sai dai gaskiya ba zai iya barin merry da dancikin ta ko may kuwa zai faru dashi a gidan idan ya tafi wanan ya bashi karfin gwiwan karfafawa merry din zuciya akan zai dawo gareta ba dadewa ba don su tari abinda zasu haifa a tare . Dadadan kalaman dayayi ta jera mata yasa ta kara yarda da mijin nata dari bisa dari har taji tafiyan nashi yana da muhinmanci sosai a gare su baki daya don ko ba komai yanzu lokaci yayi da zasu daina boye boye wa ahalin shi a san da ita da abinda zata haifa a zurian shi nan gaba. Tun da safe ita da kanta ta kashi airport inda zai shiga jirgi zuwa gida na Nigeria tare da tarin abin arzikin daya kullo daga can wa iyayyeb shi da yan uwa da abokan arziki na kusa dashi. Haka suka rabu cikin so da kaunan da suke wa junan su bayan sun dade manne da juna har sai da sukaji ana sanar da pasingers da su hallara a kofan shiga screning. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 16/11/2021, 22:48 - 🀐🀐🀐: WALLAHU GALIBUN ALAH AM,RIHIMM, , , , , , , Bakin Nigeria, jirgin su ya sauka a lagos sannu a hankali yake saukowa daga matakalan jirgin da zai sada shi da kasa. Yanayi yana kokarin gyara nicktie din dake wuyan shi yana mai sauka a hankali iskan canjin yanayi ne ya ke barazanan tunkarar sa. A hankali ya lumshe idon shi yana mai sauke numfashin shi saboda shakan iskan yanayin gida da ya dade bai ji shi ba. Ko kadan bazai taba mance wanan yanayin ba kasan shi na haihuwa ba da ya jima baya cikin sa ya samu kamar yadda ya gama tsara komai akan zuwan nasa komai ya kammalu masa. Motocin da ke dakon zuwan shi sun iso ko ba bata lokaci suka bar filin jirgin don yana son sai ya huta a lagos zai shiga jahar su. Duk da yana son hutu a lokacin sai dai hakan bai samu gare shiba don masu dakon zuwan shi kasan nan Allah yai yawa dasu lokacin kowa yana kokarin yin bucking dinsa ne ta hanyar PA din shi na nan kasan. Hakan yasa kwana biyun da yayi a lagos bai samu wani hutu sosai ba don haka yayi haraman tafiya gida don ganin iyayyen shi sai dai bazata yake son yiwa iyayyen nasa da zuwan sa. Gida kano kasancewa azumi ne sai ya kasance ba kowa ne ke fita da safe ba sai idan rana ya dan buda mutane sun gama barcin safen su zakaga an fara zirga zirga a garin. Tun daga layin namu har titi mutane jefi jefi zaka gani a waje da sanyin safiyan daidai wanan lokacin na gama shirina don ranan ba zuwa tafsiri makarantar safe zan shi don in tula karatuna wanda bamu samun yin shi sosai yanzu a cikin waran azumin. Sun dade tsaye a kofan gidan dake rufe suna jiran fitowan wani su aika ayi masu iso ciki don ko ya kira waya a wanan lokacin yasan ba dauka zasuyi ba don basu da sabon layi shi na Nigeria. Karan bude get din gidan ya nuna masu alaman wani zai fito daga cikin gidan a lokacin haka yasa suka mayar da hankalin su sosai a kofan. Ina fitowa wasu irin bakaken motocin manya nagani guda uku tsaye a kofan sun faka tsoro naji da farko kamar in juya in koma ciki lokacin ganin yadda layin namu yayi wani tsit kamar abin hadin baki ga mutanen unguwar ranan. Sai da na dan tsaya tsaye rike da kofan get din gidan naga na cikin motar yana kokarin bude motar yafio na juya da sauri zan koma ciki. Wata murya naji tana fadin don Allah tsaya ki muna iso wurin mutanen gidan na dan juyo da mamaki ina kallon mai shi din . Ya na gyara tsayuwa yake fadin nasan baki sanni ba ko ? Kai kawai na iya daga mai lokacin alaman ehh, . Ya sake fadin a gidan kike ko kin zo ne nace kaga malam ba shi na fito yi ba balle ka tsare ni da tambaya idan ma aikin jarida ka fito yi sai ka bari har diyan gidan su fito ka binciki sirin su a wajen su ni kaga tafiya ta. Ido kawai ya tsura min da mamakin irin karfin halina yar ficiciya dani nake wanan zancen ga fuskana a boye da duk wani surana a cikin hijjabi. Haka a raina kuma ina tasbihi akan irin baiwan da Allah yayiwa wanan mutumin dake tsaye a gabana. Tsayi, hasken fata kamar balarabe dashi kyau fuska, ga uwa uba wayewa da na hango karara a fuskan mutumin. Don Allah ki taimaka ki shiga ki fadawa hjy jummai cewa Umar ne danta a waje yake masu sallama ya fadi a takaice yana gyaran tsayuwan shi. A hankali na maimaita sunan nace Umar Umar din da nake jin Amma na yawan maganan sa ko da yaushe ? A she Umar din bature ne ma sai na dan ja tsuki ina fadin ni yanzu makaranta zan tafi dadai zaka samu wani ka aika da zaifi don ina ganin ma ba wanda ya tashi a gidan yanzu. Ko ni don zan tafi islamiya ne yau muna da tulawa yasa ka ganni nan yanzu, ido kawai ya tsura min yadda nake zuba ba gajiya da magana. Ki taimaka don Allah ki sanar masu nace wai kai ba kace gidan ku bane to ka shiga mana ni ban san abinda zai hada ni da part din nan na su a raina ma mutum wayau da safen nan. Ganin kamar ma baiji abinda nake fadi ya mayar da hankalin shi ga wayan shi yasa na juya ina gunguni zuwa cikin gidan har kofan hjy jummai na je sai da na tsaya nayi shawara na fara nokin din kofan da karfi don nasan ko na tsaya bugawa a hankali ba bude kofan zasuyi ba shiyasa nayi masu na mahaukata . Da zagi a bakin Nafisa ta fito tana fadin wani dan rainin wayau ne haka ke dukan kofa kamar gari zai tashi da safen nan ? Arba mukayi ta galla min harara nima na mayar mata take fadin ke lafiya kika zo muna haka da sassafen nan kina dukan muna kofa. Idan kin gama ki fadawa maman ku wani yana mata sallama a waje yace wai ace Umar ne danta yazo ina fadin haka na juya don in wuce. Ta riko hannu na tana fadin ke hjy sa,ar kice da zaki mata wanan wasan da sassafe haka nace akan may zan mata wasa haka ? Nace na saba wasa da kene abinda yace in fada ke nan na fada maki tare da galla mata harara ina fadin, ni sakeni in tafi don Allah . Idan baki fada ki bari sai bayan na fisge hannu na daga rikon da tayi min na fara tafiya naji ta sake wani ihu. Karan Ihun da ta sake ne ya sa na dan juyo ina kallon ta na tabe baki na bar gurin da sauri ina fadin kamar wani basarake yazo gidan. Tun ban karasa fita ba naji gida ya rude ihun yan part din hjy jummai suka nufo waje da gudun su hjy jummai jikin ta har rawa yake don daukin ganin dan nata. Yana ganin na fito yana tsaye kamar yadda na barshi saidai wanan karon ya dan jingina da motar daya fito daga ciki. Na kalle shi sau daya na dauke kaina ba tare da fadi komai ba na nufi hanyar islamiyan mu da kafa sai dai ban yi nisa ba yaya Ahmed ya tsaya a gabana da mota. Yace ba nace ki daina fitowa ke kadai da wanan safiya haka ba baki tsoron a sace ki wani kallo nayi mai daga cikin nikaf dina a raina ina fadin kamata za a sace ? Ya bude min motar na shiga ya tayar muka dauki hanya sai lokacin nake gaida shi da kwana ya amsa min tare da fadin ina sauran suke nace suna gida sai dai ban sa zasu samu zuwa ba yau dan sunyi bako a gidan wani ne wai Umar yazo yanzu. Cikin dan zaro ido yace Umar kika ce nace haka yace sunan shi daya turani in masu sallama. Umar dai dan Alh yazo garin nan bayan su habbib da suka zo nace eh haka yace sai dai ina ganin kamar wanan din ko bature ne ko balarabe. Yace kiji nace dan hajiyane da Alhaji zaki wani ce bature ne shi ki dai iya kanki dasu don ba mutunci ne da su ba koga kannen su. Sai dai muna zuwa na samu ana dawowa daga islamiyan wai malam ba zai samu fitowa ranan ba haka yasa muka juya muka nufo gida. Basu shiga ciki ba har lokacin da Ahmed din ya sauke ni suna farfajiyan gidan ana murnan zuwan bakon su . Ahmed din bai tafi ba shima daya sauke ni ya shigo su gaisa dashi nikan nazo na raba su har su Amma da mamu da Alh kai kowa na gidan yana waje a lokacin har bakin da suka zo din. Shiko bakon sai dadi yake ji na ganin sa a cikin dangin shi suna nuna mai so da kaunan juna a lokacin. Haka nayi kokarin raba su zan wuce sai muryan Amma naji tana kwala min kira A ruwa ke Aruwa na juyo inda nake jin muryan nata. Da hannu tayi min dakuwa tana fadin kinci gidan ku baki ganmu bane ga yayan ku daya dade da bata yau ya gane hanyar gida yazo. Kai na daga na kalli bakon sau daya nace Amma nafa riga kowa ganin sa gidan nan don nice ma ya aika in fadi zuwan shi. Na juya da tafiyana da suke kira na yauki da yanga zan wuce abina da mamaki gaba daya suka bini da kallo. Don kin masa iso sai ba zaki gaida shi da zuwa ba kamar yadda kowa ya fito taron sa a gidan . Naji kamar in fasa ihu don tsohuwar na son ta takura min kan gaida shi nace kai Amma duk wanan taron da kukayi a kansa bai isa ba sai na cika zai sani ? Ke kan anyi yarinyar kawai a nan gaisuwan zai rage kiko kara ki idan kinyi yarinya sai gardama kamar arnan farko . Muryan Alh ne yake fadin Hajiya kyale ta ko banza kada ya shamce ta kisa ta gaida tobashin ta akan dole balle tace sun gaisa da yazo. Bai kai ga rufe baki ba muryan hjy jummai ya tare shi tana fadin hajiya data gaida shi da karta yi ai duka daya ne. Ki duba nan duk yan uwa ne suka baibaye shi ta ko ina kika diba a gidan nan don haka barta kawai ta rike gaisuwan ta. A daidai lokacin da takuran Amma yayi min yawa har na isa dan kusa dashi inda suke saye da yan uwan shi da suka baibaye shi. Fari sol dashi sai yanzu zaka gane hakan da yake a tsakiyan kannen shi duk da suma di farare ne sol dasu. Yana cikin suith bakake masu taushi da tsada agogon hannun shi baki sai sheki yakeyi a tsintsiyar hannun shi daya dan fito waje daga saman kot din jikin shi. Ga bakin gashin kansa dana dan sajen daya bari a fuskan shi ya kwanta lub a jikin shi yana sheki daganin sa ba sai an fada ma ba duniya tana yayin sa a lokaci . Duk da fuskokin su yana dauke da fara,a banda nasa dake a daure wanda babu alaman sauki a cikin sa ba sai an fada ba kansan irin mutanen ne da babu wasa ga al,amarin su dagani dai zaiyi wuyan sha,ani duk wanda yasan jan aji da isa yasan ya zauna ga wannan bakon dan Alhajin da yazo . Sai na kasa bambamta shi da kanin nasa habibbi wayafi wani jin kai a cikin su don dan dama dama shi wanan Aliyu kamar ya fisu saukin kai a cikin su. Ina mamaki yadda yan uwa zasu baibaye mutum ya kasa fara,a gare su haka zai kai shekara talatin ga haihuwa ko kasa da hakan . Yana da tsayi sosai don zan iya cewa mahaifiyar su ya kwaso wurin tsawo sai ya zarta ta yana da dan lange langen jiki ba sosai ba wanda ke nuna ya jiku da ilimi ya goge sosai da duniya. Cikin yar murya da sai ka saurara zaka jini nace sannu da zuwa ya hanya ? Na fadi ina kallon amma cikin jin haushin takura min da tayi din a lokacin na wuce abina fuuu cikin gida ba tare da na tsaya bin ta kowa ba a lokacin don haka banji amsan shi ba ga gaisuwan da nayi mai din. Ina jin Aliyu na fadin big bros haka unexpected ka diro muna kasan nan dai na shige su na nufi hanyar part din mu ba tare da naji sauran maganan su ba. Su salma dake gefe suka tabe baki tare da fadin wanan da itace yar gidan nan bamu san inda tsiyanta zai tsaya ba . Uwar ta amsa da fadin tsiyar abin tsiwanta ya tsaya ga agolacin gidan ku don dole ko tabi mutane. Ni yanzu banda takaici a rayuwana, dama ita din ba mace bace ta dubi rufin asirin da Allah yai min naku don duk cikin ku babu na yardawa. Ga ilimi da rufin asiri Allah ya bani ta ko ina haukan yar ficiciyar yarinya da uwarta ke ingizo ta tai muna rashin kunya ba zai taba damuna ba. A cikin wani kasalalen murya yake fadin mu shiga daga ciki ko ku huta nima da gajiya a jikina yanzu haka. Sai lokacin ya tuna da drivovin daya bari a kofan gida inda yace wa Aliyu yasa a sauke mai kayan shi akai sashen Amma don shi bakon Amma ne a gidan. Ran hjy jummai baiso haka ba ga kuma kowa a wurin haka ya sakata dariyan wayayya aka wasance da fadin aiko ka kyauta babawo don ka wankewa hajiya laifinta wurin Aliyu ke nan don dafa isowan shi garin nan suka fara fada kanka inji mama hadiye dake fadi cikin dariyan fara,a. Yace ai gwago ni na hannun daman Amma ce tun asali bana iya mantawa da Amma cikin rayuwana har abada don ta ban gatan da ban iya mantawa da ita. Nan dai aka wasance hjy na ganin irin ganimar da danta ya shigo dashi akan idon kowa kattan mutanen nan sukai ta jida suna kaiwa part din Amma. Sai wasu ne yake cewa a wuce dasu part din mahaifiyar tasu ba yadda ta iya dole ta sa ido tana kawaici ba don ranta ya so hakan ba. Ni dai har na kwanta in dan huta can naji muryan mamu na fadin ina anty ku take suka ce ina ciki na kwanta sai gata dakin ta shigo. Sayadi barci kike ko may a lokacin na dago ina fadin na kwanta ne in huta mamu munje islamiya ance malam tafiya ya kamashi yau ba karatu. Tace Allah ya dawo dashi lafiya sai dai sayadi duk wanan nasihan da nake maki kamar baya aiki a kunnen ki. Yanzu ace kin shigo gidan nan kin gama a cikin yanayin farin ciki ki iya kada kanki zaki tafi ba tare da tsayawa ba badon gwago tayi maki magana ki gaida yayan ku ba ashe ba zaki gaisheshi ke nan ba. Nace mamu sai da na gaishe shi fa nice ma ya fara gani daya iso a kofan gida na fadawa su part din su gashi a waje. Mamu ta daga min hannu tana fadin idan zaki gyara wanan halin naki ki gyara don ni kike jawa zagi a gidan nan. Ace kaida dan uwanka ba zaka gaisa dashi ba sai an tilasta maka gaisuwa da yake da lada a wurin Allah. Amma ke ko yaushe sai abinda za a zageni akanki kikeyi gaskiya bazan kyaleki a kan wullakaci ba ta juya ta fita daga dakin ranta a bace. Muryan Alh naji a falon mu lokacin yana tambayan ta dawa take fada haka take hasala tace ni da yarinyar nan ne sayadi wallahi wanan halin nata na nakasa ban son shi Yaya. Yace haba may ye a ciki ina ko kannen nasa kinga ai basu san shi ba balle ita da tazo gidan nan kamar yau. Zata daina idan ta saba dasu wanan ai na bakinci take masu don bata saba dasu ba hakan ma nada kyau ai ki godewa Allah da halin ta yake haka kinga baki da fargaban komai da ita. Ina jin shi bai fita ba sai da yaga ya kwantar mata da hankali a kaina ta sauko har suna yan dararakun su na ma,aurata yabar part din. Niko ina daki raina a bace da haushin Amma ranan don itace taja min wanan fadan da batayi magana ba da kowa bai farga dani a wurin ba. Ko banza yaya nake a cikin gidan wurin bangaren tsana da tsangwama da nake fuskanta a wurin mutanen gidan Sai mama hadiye da yaran su da Amma nake dan raba inji sauki sai ko bangaren mahaifiyata da kowa ke ji dani. A ranan dai murna wurin hjy jummai ba a magana sai dai a wani bangare tana cike da jin haushin yadda yasa akai masa tarkacen shi dakin Amma. Bayan sun gama hiran su na yaushe rabo da mahaifiyar shi da kannen shi ya nufi wurin mahaifin shi tare da yan uwan nasa. Daga can suka nufi part din su da aka gyara masu a gidan inda ya tarar da wurin kamar yadda yake bukatan shi haka yasa bai nuna masu komai ba a lokacin. Don komai na bangaren a gyare ya samay shi tsaba sai kamshi ke tashi a ciki haka yasa ya kwanta ya huta don dama da gajiya a jikin shi sosai. Tun shigan shi ya sauya kayan jikin shi zuwa kananan kaya ya bi lafiyan gadon dake dakin don samun natsuwa ga azumin dake a bakin shi. Sai bayan la, asar ya tashi yayi alwala ya nufi masalcin unguwar don yin sallah bai shigo ba sai gab da shan ruwa ya shigo gidan. Kai tsaye part din Amma yace kanin shi Aliyu ya rakashi su sha ruwa a can inda suka samu Amma a zaune tana jiran lokaci. Yace tsohuwa mai ran karfe gani nazo musha ruwa yau a tare dake ta kalleshi cikin fara, a da jin dadi tace. Wanan aiki sai Umar sanda mazan fama wanan hatsabibin tun da yazo sau daya ya shigo dakin nan nawa balle ace maka wanan miskilin kanin naka guda shi ko sau daya ma bai lekoni ba. Don haka ne nima bai a cikin lissafi na Aliyu yace ga dai miskilin zaune a gaban ki ai don kin samu kuna dasawa ne dashi bai samu zagin ba da tafi kowa zaguwa a gare ki gidan nan. Lumshe idanuwan shi yayi a hankali tare da fadin ka san ita Amma ta daban ce a wurina don har yau banji akwai mai fadana a gurin ta ba. Dan karamin kanin su dake tare dasu a lokacin yayi caraf yace akwai yaya don wanan A ruwa din kamar ta fika fada yanzu a gidan nan don ko kuda ya taba A ruwa zakaji Amma na fadin marainiya ce ai. Amma tace ja,iri so kake ka hadamu fada yo in ban tausayawa yar marainiyar dake cikin mu ba ai da abin baiyi dadi ba gare ku. Don gidan nan kaf kan ku kuka sani baku son bare a cikin ku don haka ne nake tausayin yarinyar da zaman kaddara ya kawo ta cikin ku. Daga Aliyu har umar din ba wanda yai magana sai data kare Aliyu ke fadin Amma haka mukaji abubuwa suna faruwa a gidan nan kan zaman yarinyar nan cikin ku. Amma tace kasan ance idan baka mutu ba ba,a kare hallitan ka ba rabon dai yayan nan ne a cikin ku da maimuna ta haifa da mahaifin ku ya kashe ma yar nan nata uban. Sai dai kishi ya haba iyayyen ku mata su gane hakan a zauna lafiya sun dauki tsanan duniya sun dora kan maimuna da yarta. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:48 - 🀐🀐🀐: YA HAYYU YA KAIYYUMU ALLAH KA KAWO MUNA DAUKI BA DON HALIN MU BA SAI DON DIBA GA MUMUNEI A CIKIN MU. ALLAH KA GANI KA SANI DUNIYA TANA CIKIN WANI HALI NA NEMAN AGAJI A GARE KA YA ALLAH Jack TAUSAYA MUNA KA YAFE MUNA KURAKUREN MU, , , , , , , Shakuwa da so da kauna irin na tsakanin jika da kaka ne a tsakanin Amma da wanan bakon gidan daya zo daga baya. Anan zai ci abincin sa ya zauna yana faman latse latsen wayan shi ko ya juya harshe da turancin yana hiran sa da matar shi a waya. Don bai faye zama a wurin mahaifiyar tasa ba sai gurin tsohuwar kakan nasa dake nuna mai so da kauna fiye da kowa a cikin ahalin ta. Nima tun ranan nake fushi da Amma don bata kara sakani a idon ta ba har yau ko mamu ta ban abinci in kai mata sai in kira kanne na muje tare zan labe daga kofa su mika mata mu dawo oart din mu. Yau ma suna gama sallah isha,i ya shigo gidan don cin abincin buda bakin a wurin ysohuwar nan ya rutsani labe ina jiran fitowan kanwata dana ba abinci ta kaiwa Amman nina labe daga kofa. Girshi na ganshi a gaba lokacin kaina yana duke a kasa don haka banga zuwan shi ba sai ganin sa danayi a kusa dani. Bai mun magana ba ya shige abinshi kawai falon haka yasa na sauke ajiyan zuciya a hankali ina mai bin bayan sa da kallo. Kamshin turaren sa da ya bari a gurin yasa na dan lumshe idanuwana a hankali ina kara shakan kamahin a hanci na. A raina nace sai gyara kamar wata karuwa komai nasan tsab yake kai dukan su ma dai hakan suke da shegen tsabatan tsiya wai su sun waye. Ina jin muryan Amma tana taron shi daga ciki a cikin fara a tana fadin dan halas, yanzu nake zancen ka a raina don naga ka dade baka shigo ba. Yace da nai may Amma yana zama yake tambayan ta tayi yar dariya tana fadin ai baka laifin dan gidan Amma zance dai nake na dabi,un ka dabai canza ba a rayuwan ka. Gaka kana ibandan ka yadda ya dace ko wani dan musulmi yayi dama shine fargaban mu akan dadewan nan dakayi a cikin masu jajjayen kunuwan nan. Ya dora hannun shi saman cinyar ta yana zama a kasa kusa da ita yana fadin haba Amma idan nayi haka ai ba kaina kawai na cuta ba har daku da kuka bani tarbiya a baya. Ganin Fauziya a tsaye tsakan falon yace wanan fa kafin Amma tayi magana yana tambayan fauziya da bai sani ba a gidan. Amma tace kanwar kace yar gidan maimuna da suka fara samu da mahaifin ka a gidan nan yace ikon Allah har ta girma haka ? Ai auren nasu ya dade kai ko don dai baka gidane kake ganin saurin sa kasan yar tata babba tana nan gidan nasa an dauko ta don barin marainiya haka yanzu abin tsorone tunda ita kadai ta samu a can. Ko ita ce na gani labe a kofa yanzu da zan shigo tace ja,ira wai fushi take dani bata shigowa inda nake tunda nayi mata fadan bata gaida kai ba. Fauziya ta karbi kulan abincin asuba a hannun Aisha da ta juye ta fice tana fadin Amma zan wuce sai Amma tace yar nan yanzu banda abin baki sai idan kin dawo anjima don ta saba da bamu dan wani abu idan mun kai mata abinci. Tana fitowa nayi saurin jan hannun ta muka wuce a hanya muka hade da mutum biyu din suma zasu shiga part din Amma din wanda nasan zuwan dan uwan nasu nan ne ke sa suna shiga. Suna shigowa daidai lokacin da Amma ke miko ma Umar fura mai sanyi da take saka mai a fridge, Aliyu yayi saurin mika hannun shi ya amshe furan tayi saurin fadin kada ka karasa gawan da ba naka ba dan nan. Ya kwashe da yar dariya mara sauti yace Amma ai idan naga mai karasa ki sai inda karfina ya kare gara muna ganin kin nan muna wanan fadan dake da murasaki a yanzu sai kin goya yayan mu a bayan nan naki. Yana fadin haka ya zauna gap da ita yana sake mata nautin shi tace kaga ja,iri kai da ka zama wani jibgegen kato dakai dibeka don Allah kana sakar min nauyin ka. Duk suka kwashe da dariya habbib da sai lokacin yagama miskilancin shi yai magana yace ni fa na dauka wanan tsohuwar ta daya tun tuni ai. Hararan shi Umar yayi yana fadin idan ta daya aiko kai ba zakaji dadi ba ina yanzu wanan ya gama fadin sai taga yayan mu ta goya su. Harara Amma ta aika mai tana fadin kaji min dan banza zaka fadi haka mana tunda ni ba uwarka bace da kace uwayen ka na Dalla su mutu. Suka fashe da dariya jin abinda ta fada habbib ya sake fadin kaji tsiyan tsofin nan da anyi maganan mutuwa sai su kama zage zage. Yo ai ko na mutu yanzu na ci gari don na mutu nabar baya a duniya da za, a gani a tuna dani kai ko fa insha Allahu yanzu akwai sa,annin ka dake da diya biyar hudu a duniya. Da sauri umar yace kai ban fura na in sha kunzo kun cika mutane da surutu muna shirin buda bakin mu mai dadi. Dama shi ya shigo dasu zancen mutuwa suka kara fashewa da dariya gaba dayan su tace barin karo ma wa yan nan yan kwara kan sun bar abincin suna turawa can sashen uwar su sunzo nan zasu sauke muna rani. Da sauri habbib yace bar abinki indai nine furan nan bai damay ni ba sai Aliyu yace shikan zai sha ta shekaran jiya tayi mai dadi sosai daya sha. Tace dama ban taya maka ba miskilin banza kawai idan anyi magana kace an matsaka wallahi kuyi wa kanku fada kuyi aure haka na idan ba kuna son mutuwa a haka bane. Bata rai sukayi suna fadin da anyi dan magana ku matsawa mutane suyi har nawa muke yanzu da zaku dinga muna zancen aure. Ido Amma ta ware waje tana fadin kai dan nan kace nawa kuke idan da a kasan nan kake da yanzu bamu dade da shan bukin ku ba har ma matayen ku sun haihu kila. A hankali yake shan furan shi bai kula da zancen su ba kamar ma bai wurin a lokacin sai da tace har kai nawa gaskiya ina dokin ganin auren ka a rayuwana. Dan murmushi ya sake a gefen fuskan shi kafin yace Amma kwantar da hankalin ki kamar kinga aurena ne ai do yanzu ni kusan magidanci nake a idon ki. Tace da kyau dan albarka shiyasa nake kara son ka a raina ba kamar wa yan nan ja,irai kake ba yanzu gashi naji magana mai dadi a gurin ka. Ya kamata ace kun mayar da hankali rayuwan nan yanzu tsada take da shi sai kaga an dauki yaro karami an bar mu mu tsofi. Amma bari dai in huta akwai maganan mai muhinmancin da nake so muyi dake a natse idan na samu lokaci. Shigowan mamu falon gaida Amma da shan ruwa yasa sukai shiru gaba dayan su don tun zuwan su ba wani gaisuwan kirki a tsakanin su ko yanzu da tasan sunan ba zata shigo ba. Ta shigo da sallama ta kai kasa tana gaida gwagon nata kafin ta juyo wurin su tace barkan ku da shan ruwa ya gajiyan tafiya ? Suka amsa ba yabo ba fallasa a fuskokin su Amma da taga yanayin su tace haka ikon Allah yake yau ga maimuna ta zama cikin iyalin mahaifin ku. Abin Allah bai karewa a duniya wanan rubutace ne daga Allah akwai rabo a tsakanin su idan rabo ya rantse sai mai shi. Zanso kada ku biyewa iyayyen ku ku maza ne kunsan abinda Allah ya halasta kanku ko ku din nan haka yana iya faruwa a kanku don ba wanda ya wuce kaddaran sa cikin ku. To baki kike muna muma muyi auren cin amana nan gaba habbib yayi gatsal ya fadi yana kallon Amma da ta tsaya tana kallon shi sarara. Umar yace what noses talk kakeyi waye a ciki dan cin amanan mahaifinka ko ita da take zaman kanwar mahaifin namu kuma macen aure a wurin shi yanzu. Ban son kuna saka kanku ciki shimay gin don ku maza ne ba mafa ba ya juya gurin mamu yana fadin maimuna kiyi hakkuri da abubuwan da suke faruwa a gidan nan. Sai dai ba za mu so jin kuna yawan tashin hankali da mahaifiyar mu ba don kwanciyar hankalin ta yanzu shine namu. Sai da ta murmusa tace , Haba Umar ko wanda zai tayar wa hajiya hankali na gani kasan ni mai tarewa ce ko banza don kishi ya hada mu yanzu kuma sai idona ya rufe . Sauran dai tunda wan yayi magana su basuga abin magana ba don da ta nasu cema da bai tankawa maimuna din ba yadda suke jin zafin ta a ransu, kan ta hana uwar su shakat a gidan ta. Salama tayi masu ta fita daga shiyan don ba zata iya zama ba suna gurin har takai kofa amma tace watau mutumiya ta fushi take dani dai kan nayi mata fadan gyara kayan ka sai kuma ta dauki fushi dani. Gwago ba tazo ko dazun kawo maku abinci ba tace bata shigo ba yar nan karama taba ta shigo min dashi. Kyale ta kurciyane wataran zata gane gaskiya na fada mata ai mamu tace haba gwago a kyaleta kamar ya karama da ita tasan fushi da babba haka. Tace na dai ce ki kyale ta sanda zamu shirya kina ina ai fushin mu bai kai ko ina da ita ina zaune zata samay ni nan nasan ko yanzu ta gaji katfin hali dai ne irin nata. Bayan wuce wanan mamu part din nasiha ta kara masu wanda yasa suka dan rage jin zafinta a ransu kan auren mahaifin su da tayi tana zaman kishi da uwar su inda Amma ta lurar dasu fa,idan abin. Ina kwance saman two seater na dunkule a wuri daya ga goran ruwan sanyi a gefena haka nake da zaran ansha ruwa banda katabus a jikina duk sai jikina ya mutu sai ruwa da zanta sha a cikina idan nayi azumi. Mamu ta shigo tana fadin kin kuwa je kingaida mutanen gidan nan da shan ruwa sayadi ? Na dago kaina da kyat ina fadin ban tafi mamu so nake in dan huta tace sayadi may yasa magana daya bai huda kunnen ki ne ke ? May ye a cikin gaisauwa idan kin je ba sai ki dawo ki kwanta ba har na mike zaune ina bata fuska don ni banga wanda ke shigowa part din mu gaida ita ba yaro da manya na gidan. Amma ni sai ta matsa min kan sai naje na gaida su wanda zuwan bai amfanani da komai sai bacin rai wata ma son karta karba haka zata kyale ni a tsaye kamar basu ganka ba. Naji tana fadin watau ke ba ai maki magana kiji a gidan nan yanzu ashe fushi kike da gwagona don kawai. Ita Amma ta faye surutu shi yasa na kama kaina da ita a gidan nan haka kawai zata sani gaida mutanen da basu ganin ki da daraja ko kadan kowa fa yasan zafin uwarsa mamu. Hannu ta miko min da dakuwa tana fadin sannu mai uwa ai ban san kin san zafina ba don banga kina bin magana ta ba ke ma. Na mike ina fadin ke mamu ai duk abinda mutum yayi kanki bakya gani ni dai gani zan je gaida su tace fauziya tabini ida banje gurin Amma ta fada mata idan mun dawo. Da shiyan hjy maryam muka fara shida ke kusa damu inda na samay ta tana uwar daka sai yaranta neva falo ina shirin fita ta fito tana fadin A ruwa ce an shigo gaidamu ko anzo ganin abinda ke nan . Nace abinda ke nan hjy ai akwaishi a gurin mu kila ma na aurin mu yafi na nan don yawan ku yafi namu a can. Ina fadin haka na juya ina jin yar ta na fadin tau rasa kunya yau mommy mu zakiwa rashin kunyar naki ? Uwar tace kyaleta tayi aiko ta dama akayi ta fada min magana tunda itace bata data ido ni dai na wuce ban kula ta ba. Shiyan hjy jummai tun bamu shiga ba nake jiyo dararakun su da yaran ta haka yasa nasan suna cikin shiya na shigo da sallama ta ban san wa ya karba a cikin mazan ba. Daga kofa na tsaya ina fadin hjy ina wuni banji ta amsa ba na sake fadin ina wunin ku ansha ruwa lafiya sun baje a kasa gaba dayan su suna buda baki ? Lafiya aka sake amsa min daya daga cikin mazan da ba zan tantance muryan ko waye a lokacin ba cikin su na juya abina na fita. Part din Ammace karshe da muka shiga da sallama muna shiga sai mama hadiye ke fadin kai yar nan kina gidan nan ban saki a ido ba kwana biyu ? Kya ganta kwana biyu tana fushi dani tun ranan da saudaki ya sauka a garin nan a, a hajiya kems kya mata magana haka a cikin mutane bayan kin san yadda take mutanen nan ? Yo ko basu so dai ina sai sun ganta a gidan nan kamar yadda dan kowa yake cikin gidan nan in banda lalacewan zamani A ruwa ne wai abin kishi gin yan gidan nan ? Na kai zaune ina fadin mama ansha ruwa lafiya ya ibada ? Tace ibada Alhamdullahi faima ki bar fushi da hajiya don kada ta shammace ki kinji. Naji mama har karana takai gun mamu wai ina fushi da ita ban shigowa wurin ta don hadin fada kin san mamu da tsohuwar nan haka yanzu ta hauni da fada. Salati Amma ta saka tare da fadin yanzu yar nan ashe sai da tayi maki fadan dana hana ta nace ai na kare da fadin ni dai bani fura insha in an jima. Kinkoyi rashin sa, a don yanzu samari nan suka shaye furan sai dai idan wanda suka rage gashi ba yawa ki dauka. Nace kai amma dai Amman nan ni zan sha ragowan wasu katai can da sauri ta tareni tana fadin yanzu ragowan yayyen naki ne ba zaki sha ba yar nan ? Bafa zan sha ba amma nace ina mikewa ta kara fadin ga na jiya nan baiyi komai ba ni sai in sha wanan din. Amma in dai shima ragowar su ne ba zan sha ba gaskiya tace wai da gaske kike baki shan bakunan su sai ta kyalkyale da dariya da ban san ma,anan shi nidai na shiga kitchen wurin fridge na dauki furan a cikin gora nayi masu sai da safe na fito. Mun samu mamu tana cin anbinci take fafin fauziya ta shiga ko tace eh mamu sai na daga mata goran furan dana karbo a wurin ta. Nan dai ta kara yi min nasiha akan hakkuri tana cin abinci muna dan hira sai fauziya tace mamu ki bar tura anty gaida hjyn su anty ikilima tana zagin antu idan munje . Ita kuma hjyn su anty Nafisa sai ta kama hararan mu bata karba muna gaisuwan mu kullun. Kallon inda muke tayi tare da fadin wai abinda take fadi gaskiyane sayafi nace gashi ko fauziya ta fada kullun haka muke dasu wai leken asirin abinda sukaci kike turani yi. Kai ta gyada tana fadin karki damu da wanan mu dai muyi kokarin sauke hakkin mu na zama a tare dasu da Allah ya shari,an tawa musulmi nace insha Allahu mamu. Don ban son zancen yayi gaba nace mamu kunyi waya da Addah na yaya manjo take ciki ina son jin muryan ta. Ta dan tabe baki tace wallahi kwana biyu ban samun wayan ta ko da nackirata lambar baya shiga. Mikewa nayi tsab ba tare da magana ba na shiga daki wurin tsofin litatafaina na nuna na kama bincika sai ga abinda nake nema na gani can kasan kayana. Da sauri na fito zuwa falo inda nabar mamu a zaune ina zuwa na dauki wayanta na shiga loda nomban mahaifiyar Atika a ciki ya fara ringing can aka dauka. Da sallama nima na amsa masu mamu ido kawai ta tsura min lokacin bayan mun gama gaisawa ne nace Umma Fatima ce. Wata fatima sai na rasa abinda zance mata don kunya tunda nazo ban taba kiran su sai yau din dana kira layin don ina bukatan jin muryan kakata. Wace fatima nace da sauri nace ta kano yar wurin manjo makwaciyar ku da sauri tace fatima kai amma yar nan yar kin tabbata yar halasa da yamman nan mukai maganin ki fa. Fatima shiru haka tun tafiyan ki ba kira ni ina dauka baki da layin mu ne yasa baki kiramu ba gashi kuma ranan nayi rashin azanci in karbi layin mahaifiyar ki. Umma kuyi hakkuri ba waya a gurina ne yanzu ma ina tone tone naga lambanki da na taba rubutawa ranan shine na kira ko zai shiga. Aiko muna lafiya sai naji kunyar tambayanta wurin manjo sai ita din tace min kakarki ko ba lafiya sosai don har Addah ki ta shigo dubata. Da karfi nace umma manjo ba lafiya may ya samay ta tace daga kafan nan nata daine sai ga abin kuma yana ci gaba . Ban iya sauraren abinda take fadi ba na fara hawaye sai naji mamu ta karbe wayan a hannuna tana fadin hajiya ashe yar nan nada layin ku ? Nan suka shiga gaisawa a tsakanin su inda mamu ke fadin ashe jikin babba kuma ya motsa banjin abinda take fadi a lokacin sai mannewan da nayi a jikin mamu don inji may suke fadi a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:50 - 🀐🀐🀐: :BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHHIM AU,ZU BIKKALAMAT, TAMMA,AT MIN SHHARIN MA, HALAQ, , , , , , Tun wanan maganan hankalina ya tashi sosai da jin zancen da nayi na ciwon kakata manjo ranan ko abinci ban iya ci ba dan dama ruwan da nake sha. Da asuba ban fito yin sahur ba kuma ba barci nakeyi ba raina ke min sake sake a kan ciwon manjo ganin ban fito ba yasa mamu shigowa dakin. A kwance ta samay ni na lafe sai dai tasan ba barci nakeyi ba lokacin mamu tace haba sayadi sai kace ba musulma ba in banda abinki ai ciwo ba mutuwa bane. Kuma kowa dole ya tausayawa hin da babba take ciki a garin nan ida ma mutuwa tayi wani ba zai iya tarewa wani mutuwa ba ai. Don Allah ki tashi kina tayar min da hankali nima da wanan halin da kikeyi kukan ki kara sakani cikin wani hali yake banda natsuwa da zan nemawa babba mafita. Abinda zuwa islamiya naki ya koya maki ke nan idan bawa ya shiga wani hali maimakon addu,a aita mashi kuka. Ki tashi kije ga abinci can a falo kici kada lokaci ya kure ki fara wanke bakin ki kafin ki fito kai kawai na iya gyada mata na tashi jiki ba kwari zuwa bayi don ita har ta fita dakin ko ta koma falo. Dana fito kasa cin abincin nayi na tasa shi a gaba ina kallo sai daga can mamu ta farga da bancin abincin tace bazaki ci abinci ba sai lokaci ya shige ko. Cikin muryan kuka nace mamu Allah ban iya cin komai a yanzu na koshi wani irin kallo ta watso min wanda nasan kallon warning ne gareni . Da sauri na mika hannu na dauki spoon din na fara dan cakulan abincin a hankali cibi daya da kyat na kaisa a bakina ina ji kamar guba ta bani don halin da nake ciki a lokacin. Dubana mamu tayi tace ashe ba zaki wa kakarki addua ba idan da mutuwa tayi ko kin rasa wani daga cikin mu sai kuka. Da kyat na iya bude baki da muryan kuka don a lokacin ji nake dai Manjo ta mutu ko don yadda naji maman Atika nawa mamu dogon bayanin da banji ba. Mamu ban iya ci na koshi sai ta miko min kofin tea mai zafi danaga ta hads tun zamana ta aje gefen ta na karba babu mussu na kafa kai na zuka kadan na aje kofin. Don banga amfanin cin wani abuba a lokacin masoyiya ta tana can cikin wani halin ciwo da ban san iyakar shi ba. Maimakon inyi magana sai na fada jikin mamu ina kuka gwaunin ban tausayi ina fadin mamu banda kowa daga Allah sai ku bayan ke da manjo na . Kai ki daina fadar haka sayadi ina kika baro Alh da Amma da suke nuna maki kauna na sahihi in Allah ya yarda ba abinda zai samu babba ina jiran gari ya waye ne in samu su gwago da maganan inji yadda za a yi. Wanan kuka haka kina sare min gwiwa da shine sanan Alh ba zaiji dadin wanan kalamin naki ba bayan kokarin shi da yakeyi a kanki yana gwadawa duniya ke yarshi ce ta cikin shi. Nayi alkwari muddin ina raye sayi ba zan taba barin kiyi maraicin mahaifi ba zan baki duk wani kulawan daya dace duk wata uwa ta gari ta baiwa yarta. Ina rokan Allah ya haskaki a idon zurin an ku baki daya amma fa sak idan kin taimaka min haka zai samu gareki. Duk da nasan kina da tarbiya sai dai ki kara kula yanzu da da ba daya bane a gare ki saboda haka ki kawar da idon ki aurin kula samari don nasan ko baki kulasu ba su zasu kula ki Ki fita batun duk wani da namiji ki mayar da hankalin ki wurin karatun ki sosai don da kin gama ki samu gurbin shiga jami, a. Don Allah ki kiyaye ki kare mutuncin ki ga kowa da idon shi ke a kan mu aga yadda zamu kwashe nan gaba da rayuwan mu a gaban ki yaya take fadin haukanta a kan yaran ta . Ta manta Allah ke yi ba mutum mu tasan abinda gobe zai haifa ga namu yayan ba don haka fatima kiwa Allah ki natsu akan tarbiyan dana doraku akai. Dagowa nayi da sauri na kalleta da mamaki don jin kiran sunana da tayi a karo na farko ke nan da naji ta ambaci sunana na yanka a bakinta . Insha Allahu wataran sai labari da yardan Allah sai kin zama abin kwatance a idon jamma,a koda kuwa bana raye . Allah yai maku albarka ya kare min ku daga duk wani abin ki, ya azurta min ku da ilimi mai amfani ya baku mazajen aure masu albarka da sanin ya kamata. Da kyat ta kai maganan don muryan ta da ya juye zuwa na kuka Allah kadai yasan abinda mamu ke ji a zuciyar ta akan mu. Gashi ba wasu dangin mahaifiya ke gare ta ba tun da mahaifiyar ta suka rabo da mahaifinta ta koma kasan su basu kara jin labarin ta ba har yau. Nasiha mai ratsa jiki mamu tayi min wanda ya kara min karfin gwiwa da sanin matsayina yanzu a duniya wanda ya zama dole inyi taushi ko don kwanciyar hankalin mahaifiyata mai son ganin farin cikina itama a duniya. Ban kwanta ba sai da nayi sallah na samu batci mai nauyi ya dauke ni can cikin barci na nake jin muryan kawo na mijin mamu yana fadin ina ita sayadi din. Tana ciki tana barci nasan sai yanzu ta samu barci a yadda ta kwanta a jiya yace tayar min da ita . Itama matar da ta fadi wanan bata kyauta ba bata ganin fatima yarinya ce kamar da zata sanar mata da wanan magana sanin yadda suka shaku da kakan nata. Barcin data samu ne yanzu don nasan ta kwana tana kuka jiya yace kin gani ba wanan ai ba sakon yaro bane wasu haka suke basu da tunane. Mamu ta shigo ta tayar dani na samay shi tsaye a falo yana jiran fitowa na daga daki na fito na dan rusuna ina fadin kawu ina kwana ? Ya amsa min fuskanshi ba yabo ba fallasa yace har yanzu kukan kike yi fatima ? Haba fatima ai ciwo ba mutuwa bane daina damuwa insha Allahu zata samu lafiya abubuwa ne sukai min yawa yasa na shagala da zancen kakanki a raina. Murya Amma ne ke shigowa part din mu wanda zance duk zuwa na gidan baifi sau biyu ba data shigo part din sai kuma wanan karon. Tana shigowa tace ashe kana nan yanzu maimuna ke fada min yar nan she kakanata jikin ya motsa kuma a can. Ta juya wurina tana fadin haba A ruwa kiyi hakkuri ki daina kuka ciwo bawai an rabo bane gaba daya daurowa yake idan Allah ya saka ma bawa lalura sai addua yanzu. Hawaye masu zafi suka zubo min wanda ban iya bambance na maynene ba ko na ciwon manjo ko kuma na irin so da kaunan da ake nuna min a gidan kawuna tsakan shi da mamu da Amma. Wanda ada ba debe tsamanin samun irin wanan kulan na mahaifa a gareni sai wurin mahaifiyar uba da take kulani ita kadai wanda kesa nake ganin banda kowa a duniya sai ita. Tashi ki shiga ki kwanta abinki tunda akwai barci a idon ki kawu ke fadi na mike tsam na nufi dakin kwanan namu. Barin wurin keda wuya baji mamu na magana kasa kasa sun dan dade a wurin suna tataunawa wanda ban sa may suke magana a kai ba lokacin can dai har na daina jin su ko don barcin daya dauke nine lokacin. Amma da ta fito daga part din mu tana komawa ta samu Aliyu da umar a falon ta sun shigo gaida ita basu samay ta ba. Tana shiga ta gansu a zaune kowa hankalin shi yana ga wayan shi ba maima wani magana a cikin su. Da sallama a bakinta ta shigo part din kamar yadda tsofi keyi a duk inda zasu shiga wuri koba kowa sai sunyi sallama a guri. Dago kai sukayi suna amsa mata sallaman ga baki dayan su Aliyu yace ji wanan tsohuwar ke da baki da kafa ina kika je da safen nan haka ? Tace bari kaidai yar nan A ruwa ce aka bugo wanan wayan wai kakarta mahaifiyar ubanta bata da lafiya. Waye kuma keda wanan sunan banzan wai a ruwa ke yanzu har kina da kafan shiga makwabta a hakan. Kaji ja,iri sai ana maganan kwarai ya jefo shirmay yar nan mana yar gurin maimuna na dake gidan nan. Ba wanda ya amsa masu daga ciki ita kan taci gaba da fadin wallahi abin akwai tausayi yar kaka wace take gani taji sanyi yanzu kuma ance kafa ba lafiya gara ni ai tashine aiki a wurina yanzu. Haba Amma ko gausawa bamuyi ba kin damay mu da zance wata wace bamu da hadi da ita a wurin mu. Dan nan kana da imani a ranka kuwa Amma ta tambaya cikin mamaki da bata fuskanta. Yanzun kai ko tausaya mata bakayi a matsayinta na tsohuwa balle ace yarta jinku ce ita aiko don yar uwanku ka tausaya mata da addinin ka. Ke kowa fa ba irin ki bane sarkin tausayi haka kawai kina kokarin lika muna yarinya a jiki don kawai wani alaka can. Haba please kasan may kake fadi aiko don zamanta a gidan nan ko yar aiki ce zamu tausaya mata balle yar maimuna ce fa yarinyar. Ku daina irin wanan maganan please ya karasa yana maida fuskan shi a wayan shi sai Amma tace. Fada mashi dai dan albarka shiya nake kara son ka saudaki don ka biyo ni sak wurin fadin gaskiya da tausayin mai bukatan a tausaya mai. Ni da banda tausayi sai kisa a rufeni ki daina ganina a duniyar nan ga baki daya . Wai ba abinda habbib ya karato ke nan ba Amma matar tana ina ne sai ya duba ta ido Aliyu ya zaro waje da sauri yana fadin wani habbib din zaije aikin kalar dangi. Dakuwa ta nuna mashi da hannu tana fadin kaci gidan ku yaro ana baka kana roko idan baiyi ba abu na kudi sai wasu suyi. Ke ma dai kinsan habbib bai wanan aikin don bai fara duba kowa ba a kasan nan balle ya fara da tarkacen ki. Wai wanan dan may ka dauki duniya ne kadai bi duniya a sannu don Allah bani fatan haka a cikin zurian dana haifa. Rashin imani da tausayin mabukaci ba wanda yana cikin abinda ke kai mutum Aljanna idan an dace anyj wurin daya dace din. Amma don Allah dai ki barshi zanyi magana da habib din ansan abin daya dace a kai tace sannu dan albarka yadda kake da zuciyar nan ubangiji ya tausaya maka ya jibanci al,amuran daka sa a gaba duniya da lahira yasa maka albarka ga zurian ka ya baka mata tagari mai irin zuciyar ka. Yace Amin amma na gode Aliyu zaiyi magana ya daga mai hannu yana fadin please please ka barta hakana kana sa kaina yana ciwo wallahi . Yana fadin haka ya gyara ishishirewa saman kujera yana dafe kanshi da hannun shi daya mikewa Aliyu yayi yana fadin ke dama ba a zuwa maki abin arziki ni kinga tafiyana . Lokacin ya cire hannu a goshin shi yana fadin jinan kada ka fara ka tari habib da wanan magana yace naji bros ya fice. Ban san yaya akayi ba sai kawai naji ranan mamu na magana wai za a dauko manjo a dubata a nan kano ranan murna a wurina ba,a magana ina Allah Allah gari ya waye in bude ido inga manjo don ance Addah ce zata zo da ita. Washe gari basu iso ba sai bayan la,asar Ahmed aka tura ya dauko su tasha daga shagon su ko gida baizo da ita ba don yanayin daya ganta ya wuce asibitin da akai bucking da ita daga can . Sai zuwa yayi yake fadin abinda ya faru a can mamu ta samay su bata fada min halin da ake ciki ba don kar hankalina ya tashi. Azumi yana damuna gashi na gama girkina mamu ta fita ban san inda taje ba sai shirun yayi min yawa na yanke shawaran muje part din Amma kafin lokacin shan ruwa yayi. Muna shiga ban kula da mutum a falon ba na nufi inda Amma take ina zhwa na kwanta saman jikin ta ina fadin Amma zumi ga mamu ta fita tundzun bata dawo ba. Idan ta dawo wani abin zatai maki na gyara kwanciya saman jikinta nace wallahi Amma yau akwai azumi sosai. Ta dan turani tana fadin ke dallah ja can raguwar banza da kike hawan jikina an fada maki ni ban azumin ne halan ? Muryan namiji naji a hankali kamar yana rada nayi saurin juyawa wurin yana zaune yana waya jikin shi saye da yadin shadda mai laushi da maiko brown color saj walkiya takeyi. Tun ganin da nake mai da yazo wanan karon na ganshi a cikin kayan mu na gargajiya sai na rasa da kayan mu dana turawan da yake sakawa wani yafi mashi kyau a lokacin. A hankali na mayar da kaina baya ban kara kallln shi ba abinda naji yana fadi da harshen turancine ya dan girgizani. Mace mai suna merry yake waya da ita sai dai wayan nasa kalaman rarashine ne yake mata inda yake fadin tayi hakkuri ya karasa abinda yazo yi. Sai kuma ya tsaya dan saurarenta can naji ya fadi a dan tsawace kada ta soma ta biyo shi nan ko ranta ya baci saurin juyowa nayi na dan kalle shi yadda yake magana a hasale kamar mai fada da dan shi. Nace a raina shegu sun gama watsewan su a turai sai da suka gaji suka dawo gida kilama abokiyar shashancin shi ce ta matsu ta kirashi yanzu. Bankai karashen tunane ba naji muryan shi yana fadin Amma zan je masallaci lokacin sallah ya kusa tace a dawo lafiya dan albarka. Yana fita naja tsuki ina fadin kamar na Allah da sauri amma ta juyo tana fadin wa nace wanan jikan naki mana Amma. Yanzu fa ya gama waya da mace a gaban ki kuma baki masa fadan haka ba tace lah ha,ila ha, illah yanzu yar nan ki rasa wanda zakiwa sheri sai dan nan ? Sherin may kuma amma inji abu da kunne na kice min sheri da wata merry arniya fa yake waya a gaban ki dan gwara takai min a kai tana fadin lalai yar nan kin iya sheri. Na mike ina fadin don na fada maki gaskiya shine zaki dangware ni bari ki gani idan na sake zuwa wurin ki duk abinda kikaga dama ki mun. Na mike tana kirana naki koda juyowa yan kanne dake a takure rashin sanin inda mahaifiyad mu ta tafi suka biyo ni a baya. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:50 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, LA, ILLAHA ILLA, ANTA SUBBAHANAK INNI KUNTUM MINAL ZALUMIN, , , , , , , , , , Mamu bata shigo ba sai bayan shan ruwa koda ta shigo bata wani tsaya ba sallah tayi tare da umurtana in biyo ta kitchen. Sai nake mamakin mai kuma zamu hadda da daren nan bayan mun kammala abincin ranan da zamuci har asuba. Kuloli ta jawa ta miko min in wanke bayan na wanke ne naga tana ta faman zuba abinci a cikin kulan tare da fadin in zuba ruwan zafi a flask. Muna gama hadawa Ahmed ya sallama mata tare da shigowa falon namu ina zaune takure saman one seater na dunkule kafafuna a saman kujeran na takure a wuri daya kaman mai jin sanyi. Shigowan shi bai sa na canza zaman da nayi ba kamar wace ke a cikin damuwa ina ganin shi daga inda nake zaune na gaida shi. Naji mamu na fadin ka iso ashe yace banje nisa nan muka sha ruwa da Alh a falon shi don kada mu makara. Bata wani tsaya ba ta kallo inda nake zaune tana fadin ku tufe part din nan idan nafita in na dawo zan buga maku. Na amsa da to kawai suka fita ya karbi kayan abincin ina mamaki a raina ko may suka samu kuma ? Ni dai ko da ta dawo na dubi lokaci naga sha daya da rabi na dare na shige na barta a falo zaune. Washe gari ne tunda safe zanfita na fito tunkan in karasa naji mutum yana waya daga kofan shigowa gidan haka yasa ban bude get din gidan ba na dan saurara inji ko waye. Daidai lokacin kunne na jiyo yana fadin merry giwa kika sha da cikina a jikin ki kina haukane ko may ban fada maki shan giyan nan zai rabamu. Gabana ya fadi ina sauri inga ko waye a cikin su yake wanan maganan bansan lokacin dana taba kofan ya bada kara kiiiiiii, Ya juyo yana duban kofan yaga mai fitowa wanan lokacin da sasafe haka ina kuma mai shi zai tafi ? Karaf muka hada ido dashi daga cikin nikaf din da fuskana ke rufe ido ya dan dauke gareni tare da ci gaba da wayan shi Umar faruq ne dai wanda yammacin jiya naji yana wayan shedanci da mace. Yau kuma da safiya na kara jiyo kalamin da ya girgiza min zuciyana daga bakin shi wai cikin shi a wata mace bayan Amma tana fadin baiyi auren fari ba to a ina ya samo mace mai ciki kuma. Na sakar mai harara bayan na kware dan nikaf din fuskana don ma ya shedani da kyau kuma na jishi. Da ace a cikin su zanji wani yayi irin wanan magana a kanshi zan iya karyata mai shi a lokacin don shine yafi kowa shiru shiru da dan kirki zaka gaishe shi ya amsa kuma gashi ibada bai wuce shi. Ke da wata murya a kausashe ya kirani kamar kada in tsaya sai kuma na juya ina dan magana da baiji nace ba sunana ke ba malam. Ashe yaji abinda na fada yace idan ba sunan ki ke ba waye sunan ki ko da yake sunan ki da sanin shi da rashin sanin shi a gare ni duk daya ne. Ina zaki fita da wanan safen haka kin wani bat da kama kamar wata ninja dake dan baki na murguda nace ba dai yawan banza zan tafi ba kaga abinda ke hannuna ai . Juyawa yayi ba tare da yayi magana ba bayan ya sauke idon shi akan litattafan dana rika a lokacin. Na dauke kai nima na fara tafiya yace kin iya labe kina sauraren mutun ko kamar kada in jiyo sai kuma na tsinci kaina da juyowa ina fadin. Laben mai zanyi ko inji may inji aikin da kake aikatawa kana fuska biyu a gidan ku ? Kallon mamaki yake min karamar yarinya da irin wanan maganan a gare shi har yaushe raini ya shiga a tsakanin mu haka ? Fuska biyu har na wuce yana maimaita magana ta a ran shi koda ya dago kai nayi nisa da tafiya ko haka yasa ya kyaleni bai sake magana ba. Nikan har nakai makaranta ban daina zagin shi a raina ba ina tsine masu gashi Ahmed ya hana ni fita yau ma ganin ya dade baizo ba yasa na fito sai naga na iso school din a cikin lokaci., Muna tashi na dawo gida da sauri don zuwa tafsiri da mukeyi da mamu har lokacin ina mamakin rashin zuwan Ahmed ranan. Sai dai koda na shigo ban samu mamu ba ta fita na tsaya ina mamakin mai mamu ta samu ne ina take zuwa haka don ban santa da yawo ba yawan zuwa unguwa don ba wasu kawayene gare ta ba sosai. Wanka nayi bayan na na fito na shirya na hada ma kanne na abinda zasu karya dashi sanan na kara kwanciya ina jiran dawowan mamu anan barci mai nauyi ya dauke ni na barsu suna kallon katun a falo. Bani na falka ba sai daya na rana koshi fitsari ne ya damay ni a lokacin yasa na tashi bayan na fito daga falo ne na samu mamu ta dawo lokacin . Tana zaune a falo da yara tana waya sai dai tana ganina tace bari ai zan dawo yanzu dama wanka nazo inyi a gida. Ta dago bayan ta kashe wayan tana kallona nace mamu fita zaki kara yine kuma ? Tace eh yanzu ma nake fadin in tayar dake ai don tun da na shigo kike barci a gidan nan kinga sai karfe hudu zaki dora girki idan ban dawo ba ta fada min abinda zanyi, Bata dade ba ta fita na cewa yan uwana mu leka Amma mu gaishe ta muka dunguma zuwa sashen Amma din a zaune muka samay ta tana gyagyadi ita kadai. Dan sanda nayi zuwa gaban ta nace agudu ta mike zubur tana waige waige tace ja,ira ubanki sani kika tsorota. Na turo baki nace ke Amma daga dan magana sai ki kama zagin mutum dakuwa ta kara min tace gidan ku ki fita idona yar nan . Ni zaki ba tsoro a dakina nace ke halin ki ke nan da anzo wurin ki sai kin batawa mutum rai tace yanzuma waya kiraki ko kinga sakona gare ki ? Ina jiya nan kikai fushi dani aina dauka zuciyar naki zakiyi a yanzu ma nace da yake kin iya hadi ba inyi fushi ki hadani da mamu ko kiji dadi. Baki da kirki wani lokaci A ruwa yanzu ki rasa wanda zakiwa sheri sai sadauki yaro natsatse mai hankali da sanin ya kamata . A wurin ki ba nikan ai a tafin hannu na yake Amma don nasan abinda baki sani ba wanan mai fuska biyun zaki wani ce wai natsatse dashi. Wani kallon haushi ta aika min nace ai in an kawo maki goyon dan shege kuma na kafira zaki bayani . A take annurin fuskanta ya kara gushewa gaba daya tace a cikin wani murya da ban taba jinshi gare ta ba. A ruwa sherin naki har yakai ki kalli tsaban idona ki fada mi wanan maganan lallai da akace da wasa da yaro gara kwana da yunwa na yarda yau. Ganin ran tsohuwar ya baci sai jikina yayi sanyi nace Amma don Allah kiyi hakkuri naga tobashina ne ban zaci ranki zaikai ga baci haka ba. Sai naji ta sauke ajiyan zuciya tana tana girgiza kai tace badon kece kikai min wanan wasan ba da yau anjimu a gidan nan. Shiru nayi kafin in kara fadin yi hakkuri Amma don Allah tace ai ya wuce amma kayiwa dan uwanka fatan alheri shine kyau. May ye laifin yaron nan da yai tsaye sai da yaga an dauko kakarki an kawo ta garin ya tsaya tsayin daka sai dan uwanshi ya dubata. Da sauri na dago kai nace Amma ban fahince ki ba wai wa kike magana akai tace barshi kawai idan baki sani ba sai lokacin ta tuna da basu son in sani don kada in daga hankalina a yadda take. Ganin tayi shiru yasa na kasa kwantar da hankalina kafin in magana sai tayi kokarin mikewa tana fadin lokacin sallah yayi kinzo kin tsatsare ni da wanan surutun banzan naki ni kinga tafiyata zuwa alwala. Ta barni ina binta da kallon mamaki da sauri wani tunane yazo min nace a raina kodai shi yasa nake ganin mamu bata zama tana busy tun jiya. Zubur na mike ina kokarin tattara yan kanne dake wasa a falon suka karbe key din suka sheka da gudu. Ina tafe jiki ba karfi hankalina ya tafi ga tunane banyi aune ba mukai karo da mutum da sauri na dafe goshina da naji zafi ina dago kai don ganin waye. Habbib ne sun fito zasu mosque da dan uwan shi yace a hasale ke wata irin balagazan yarinya ce mara tarbiya ke mahaukaciyar inace ? Ka barta yace daga baya shin inji yayan nasu kila iskacin nata zai kawo gare mune da nine ball zanyi da yar iska a wurin nan. Tsuki yaja yana fadin may yasa baku da tunane wanan yarinyar haka take da rawan kai ku kyale ta kada mu rasa sallah. Daya bayan daya suka wuce ni suna magana akai a hankali nake bin su da kallo har suka fice gidan. Naja kafana da kyar ban dade da shiga ba sai ga kiran sallah anayi haka yasa na shige bayi na dauro alwala. Amma na zaune a inda ta idar da sallah a falon ta tana jan tasbaha ya shigo falon yayi sa, a babu kowa a falon ita kadai ce zaune. Ta dago kai fuskanta cike da farin cikin ganin shi a lokacin ya tako ya zauna gab da ita yana tankwashe kafa tayi sauri ta shafa adduan da take ta dube shi tace. Dan nan ina kake shiga kwanan nan baka zama ga azumi ga zafin rana kana cikin sa ya dan canza yanayin fuskan shi zuwa na damuwa yace. Wallahi Amma wasu aiyuka masu muhinmanci nake yi suka dauke min hankali sai dai yanzu na gama kammala su sai dai damuwa ta daya ce. Tace Saudaki maye damuwan ka kuma bayan gamu a raye muna gaban ka har wani abu zai damay ka. Yayi wata sanyayar ajiyan zuciya tare da tsure ta da idon shi yace Amma ai barin ki da Allah yayi har wanan lokacin ina ganin kamar don nine gaskiya. Gabadaya hankalinta ta mayar gare shi tana mai kallon a cikin rashin fahintar inda maganan shi ya dosa sai da ya gama tace kai ko may ke damun ka dakake tunane haka ? Yayi shiru sai wani gumi ke feso mai a goshi ya kasa magana Amma ko sai tsura mai ido tayi a cikin gigita hankalin ta ya tashi ganin dan lelen nata a cikin tashin hankali. Can tace sadauki kayi magana karka daga min hankali nima kan abinda ban sani ba tukun ka tayar min da hankali sosai. Wani ajiyan zuciya ya kara saukewa yace Amma nasan ke kadai ce mutum na farko da zata fara fahintana a gidan nan. Amma nasan duk irin abinda na dauko ba zaki taba guje min ba idan ma kowa yaki abin nasan kina tare dani domin fahintar ki. Kayi maganan ka kai tsaye Umaru don in fahinci inda ka dosa ka tsaya kana min kwanaye kwanaye. Yace cikin dukar da kanshi kasa Amma ina da aure har da rabo sai dai matar tawa a yanzu bata haihu ba shiyasa, , , , Sadauki, Umaru kace kana da aure harda rabo yace kwarai Amma sai tayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi ta dukar da kai kasa tana tunane. Can ta dago tana fadin sadauki haka kai muna ina daukan ka mai hankali ashe abin ba haka yake ba ? Umar ya sunkuyar da kanshi ya kasa dago kai ya kalle sai ya ji wani nauyi da kunyar kakar tashi a karo na farko a rayuwan shi. Cikin dakewa yace wallahi Amma kin san mai rai bai wuce kaddaran shi a zane yake nifa damuwa ta daya ne yanzu yadda su baba su amice mata a gidan nan. Don ita din ba musulma bace ina dai kokarin ganun na musultar da ita ta zama musulma din nan gaba. Jikin Amma ne ya fara bari tana tafa hannu alaman mamakin jikan nata da take gani mai hankali a cikin su tace ni Amamata na shiga uku yau ni jinina ya daukowa kafira a gidana. Allah mayyasa ka barni inga wanan bakin ranan a gareni baka daukeni daidai lokacin da ka dauki mijina Attahiru ba a duniya. Nan hankalin umar ya kara tashi kololuwa yake ji kamar ya hadiye ranshi a lokacin don zafin kalamin tsohuwar shi bai ga laifin a cikin auren da yayi ba da ake wanan tayar da jijiyoyin wuyar haka ? Haka Amma ta barshi a zaune ba magana kamar bata san dashi a wurin ba lokacin sai faman salalami takeyi. Can yaji muryan ta a cikin wani yanayi tana fadin idan ka gama zaman naka zaka iya tafiya tunda ka isar ma kanka ai. Dan murmushi ya sakar a fuskanshi na karfin hali tare da fadin haba Amma a gurin ki nake kyautata zaton samun sauki a kan komai dana aikata ba tare da sanin ku ba don ke din ba jahila bace kinsan kaddaran rayuwan bawa. Sai kuma yanzu na fahinci kuskuren tunanen hakan a yadda kika sanni kika san tarbiyar da kuka bani bai kamata ki mani fahintar da bashi ba Amma. Umar ta ambaci sunan shi yace yau ta baci mai sau biyu ke nan Amma tana ambatar sunan shi da bata kira don yana sunan surikin ta. Tace bawai ban fahince ka bane na yarda da nasan kaddara sai dai abinda baka gane ba shine niba auren ka na jahilta ba auren kafira arniya na jahilta a zuria ta. Idon shi ya runtse lokaci guda yana jin zafin zagin da Amma ke surfawa matar shi merry har cikin ranshi. Amma tace shike nan abinda mahaifin ku ke nunar da Jummai ya tabbata a kanka umar mahaifin ku a kullun fargaban shi ke nan da tsoron kada haka ya faru da dayan ku tun lokacin da ta sa fitinan sai kuje kasan waje karatu ita duk diyan kawayen ta suna waje . Amma, Amma kin san ba laifi bane hakan ga addini ina sane da abinda nayi ita kanta yarinyar mace ce ta samu irin wanan kalubalin a gurin iyayyenta amma ta nace sai ni . Ta bar komai nata da kowa nata tazo ta aure ni Amma don may nina miji ba zan iya hakkuri in rungumi kaddara ba tunda Allah bai hanani ba. Wani irin nisawa Amma tayi tare da fadin Uhhmmm zamani yau Allah ya kawo ni kallon zamanin Annabi shaho da rayuwa a cikin zuria ta. To ai sai ka je ka fadawa iyayyen naka abinda ka aikato masu can da bakinka ka fada masu tsaraban da kazo masu dashi. Haba Amma ban taba tsamanin haka daga bangaren ki ba a duk iyaa tunane na dauka wallahi ke mai fahintar rayuwata ce ai. Ki yarda dani Amma ba zan taba barin addini na ba don wata ko don wani abu ince na fita ga musilunci na sai ma abinda ya karu min a zuciyata. Ai naga alama dan zamani tunda har kake iya kallon idona kana wanan maganan haka kan kafira data lasa ma zumar ta kaji dadi. Dan murmshi ya sake tare da mika hannun shi ga nata ya dafa yake fadin Amma a gafarce ni nasan nayi kuskure amma a yafe mun. Nan tayi saurin son jaye hannun ta yana fafin don Allah Amma ki gafarce ni kuskure na riga da na tafkashi idan kikayi fushi dani yau ban san inda zan jefa rayuwa ta ba a garin nan. Saukowan ki shine kwanciyar hankalina Amma ki yafe min Umar din ki ya tafka kuskure mai girma a wurin ki amma don Allah kada kice kema zakiyi fushi dani a gidan nan ya kare yana hada hannayen shi guri daya. Wani iri Amma taji a ranta yadda ta hango tashin hankali a tare da yaron lokaci guda sai tausayin shi ya kamata sosai sai dai a fili tace dashi. Sai ka sanarwa iyayyen naka ai don ni wanan zancen yafi karfin fada a bakina gidan nan kasan komai kayi sai suce nice mai goya ma baya. Ya kara fadin don yaga saukowa gareta ko yanzu kece dai mai sanar masu da halin da ake ciki don jiya Daddy ya fara min maganan aure. Ai dole yai maka don hankalin mu ba akwance yake ba kunkai munzalin aje iyali ace baka motsa ba balle kannen ka su motsa. Ashe mu bamu sani ba kai da iyalin ka a hannu mune ka mayar wasu bi nan can kana kallon mu wawaye. Da sauri yace nina isa haba Amma kuna iyayyena zan ayyana haka gare ku lalacewan nawa bai kai can ba ai ya kare magana a cikin ladabi da kulawa a gareta. Haka ya kara sa jikin Amma sanyi jikan nata ya bata tausayin kaddaran data samay shi gaskiya ya fada don kaddara na kan kowa amma dole ta nuna mai bacin ransu a fili don gaba. Zaka iya tafiya ta bashi amsa sai yai shiru ta sake fadin bakaji bane ya dago a sanyayaye yace Amma fushi kike dani ke nan ? Tace Umar ka barni in huta saboda Allah kasan a rike muke muna cikin lokaci ya fahinci mai take nufi ya mike a sanyaye ya bar falon nata zuciyar shi ba dadi a lokacin. Bin shi tayi da kallo a ranta take fadin ban so haka gare kaba dan nan kaddara ta riga fata kai daya dace ace ka samu mace natsatsiya kamila mai rikon addini a cikin dangi kai ka aikata haka a kan ka. Tirr da wani wayewan idan yai yawa bai haifar da alheri ta yaya yaro karami kamar sadauki zai yankewa kanahi hukunci a rayuwan shi. Shiko umar yana fita ya sauke ajiyan zuciya tare da fadi a ranshi ashe akwai aiki Amma ke nan da yake gani da saukin samu tayi mashi haka ina ga iyayyen shi kuma ? Tafiya yake kamar wanda kwai ya fashewa a ciki jiki ba kuzari can ya hango Ahmed da mamu sun shigo da kayan da suka dawo dashi daga asibiti kallo daya yai masu ya kawar da kanshi gare su. Idan da sabo ta saba da halin yaran mijin nata wurin nuna ita ba kowa bane gare su don haka ne abin bai damuwan ta gashi dai tana son mai godiya sai dai ba fuskan hakan a wurin shi tun a dakin Amma dataji shiyasa a dauko manjo tana son mashi godiya ya daga mata hannu alaman bai son hakan gare ta ta kyaleshi. Hakama Ahmed da shima yake nuna bai damu dasu ba don akwai tsana karara a idanuwan su indan sun hade dashi saidai da yake maza ne basa fitarwa fili. Mamu ta shigo da sallama tana aje flask din data dauko a gefen kujera ina daga kitchen naji muryan ta, na fito ina mata sannu da dawowa. Bayan ta amsa take tambayana ya aiki nace na kammala gyara wurin nakeyi naji muryan ki tace sannu da aiki sai dai da zan samu a dan sa min ruwan zafi kadan tuwo nake son tukawa yanzu . Nace tuwo kuma mamu may zakiyi da tuwo na tsare ta da ido ina tambaya tace asibiti zan tafi dashi nace asibiti kuma wa naki ke asibiti ? Sai da ta mike tsaye take fadin wasu ne baki san su ba amma dai da sauki jikin maishi yanzu. Mamu da gaskiyane Manjo ke asibiti garin nan kika boye min na karasa fadi kamar zanyi kuka. Ta kalleni da mamaki tace a ina kikaji haka itace a asibiti ? Ammace tayi subul da baka ta fada dazun tunda naji ko ta fada tunda tana boyewa nasan da gaske ne don zuciyana taki natsuwa da maganan. Ta mike tsaye tana fadin eh itace don baki da natsuwa komai kuka yasa na boye maki don kada ki tayar muna da hankali. Sai na dora hannu a kai na fashe da kuka ta daka min wani tsawa da sauri na shaye kukan dana fara tace wawiyar banza ai kinga irin haukan naki ba. Ke yanzu dadin kine a yadda akazo da babba garin nan wani ya sani a samu abin goranta maki nan gaba kul naji zancen nan ya fita sai na saba maki a gidan nan wallahi. Da sauri na ja bakina na rufi na bita da kallo har ta shige dakin ta na sudada na koma kicin ina aiki ina kuka a raina ina fadin kila ma mutuwa manjo xatayi yasa basu fada min ba tunane kala kala nayi shi a gurin ni kadai. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:50 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, LA, ILLAH HA,ILAH, LA HAULA WALLA QUWATI ILLA BILLAHI ALLIYAL AZEEM Don kada inga fuska mamu ta kara daure fuska gare ni ina kallo bayan ansha ruwa ta fice zuwa asibiti ita daya a cikin motar ta. Sai dai sa,a na daya ta manta da wayan ta a falo yana caji ina zaune ina faman sake saken a raina can idona ya killo min wayan ta a caji. Take wata dabara ta fado min a rai na dauki wayan na kira layin ya Ahmed nace yazo mamu tace in kirashi yazo ya kaini asibiti in kai mata waya. Da mamaki yace anya Fatima maman yan biyu zata ce hakan tasan zan shiga massalici yasa tace in huta abina. Nace itace tace haka da zata fita yace to shike nan gani nan zuwa ya bani amsa yana kashe wayan . Zubur na mike tsaye nacewa yan kanne na suzo i kai su part di Amma su jirani a can yanzu zan dawo. Ko dana shiga har lokaci ran Amma yana bace karewa ma abinda ban taba gani ba na sama tana kwance wai bata da lafiya tun kan asha ruwa. Nayi mata sannu na fito bayan nayi wa su Aisha bayani ina fitowa Ahmed yana zuwa yace muje nace to yana gaba ina binshi baya har wurin motar shi muka dauki hanyar asibiti. Har mun kusa ya rage gudu yace ke Fatima da gaskiya maman ku tace kizo asibitin nan kodai shirin ki ne ? Nayi kasa da kai ba magana ya ja wani dogon tsaki yace dama nasan karya kike don karyan ki baya kai ko ina tunda baki iya ba zan sauke ki kiga abinda kike son gani a can. Amma ki sani idan kika kuskura kika ce nina kawo ki kika mayar dani mutumin banza ga mutanen da nake jin nauyin su da kunya wallahi kema ranki zai baci fiye da nawa. Baki san halina ba yasa kika sakani cikin shirmay ki fita min daga mota mara hankali kamar wani ubana har jikina yana cire na balle motar na fita da sauri. Sai bayan ba fita na fara kalle kallen wurin da nake tsaye ga duhu ga hasken kwan lantarki a lokaci daya sai lokacin tsoro ya kamani. Na juya naga yana kokarin ribas da motar shi nayi saurin kaucewa wurin na rasa inda zan nufa a cikin gurin . Har na fara surfawa Ahmes zagi a raina sai naji muryan shi a bayana yana fadin wuce in kaiki dakin da suke. Sai dai karki manta kika kuskura kika fada masu nina kawo ki asibitin nan sai ranki ya baci dani. Har kofan dakin da suke ya nuna min ya juya da sauri ya bar asibitin saida na tsaya yin shawara kafin in tura kofan da sallama na shiga. Idona akan manjo wace ke kwance kamar gawa sai na,urorin dake zagaye da ita a ko ina bata san wanda ke akanta ba a lokacin. Dea sauri na karasa wurin gadon ban farga da wace ke sallah ba a dakin lokacin sai muryan Addah na naji tana fadin wacece wanan ? Na juyo da sauri zuwa gareta na fada jikin ta sai kuka mai karfi ya zo min da sauri mamu data kagu ta sallamay sallah ta sallama. Tace ke ke waya kawo ki nan may kika zo nema ko kinzo ki tayar mata da hankali ne kuma ? Maza ki fice daga dakin nan tun ban saba maki rai ba yanzun nan maza ki fice ki bamu wuri tace a cikin wata murya mai karfi ba shiri na bar dakin dafe da bakina daya cika da sautin kuka. Sai bayan na fita Addah ke fafin maimuna may yasa kika koreta haba dai kin san fa irin kaunar dake tsakanin su da babba. Yanzu da kika koreta ina zata tafi mamu tace damay tazo dama ta nan ban san wanda ya kawo min ita nan ba wallahi shegen naci ne da ita. Ina fitowa a tsorace hankalina tashe ban san inda zan dosa ba a lokacin na dade tsaye bakin get din ina sake sake a raina kafin in yanke shawaran bin kafa in koma inda na fito. Do zan iya gane hanya don yanzu na dan san garin sai dai akwai tazara da gidan kadan da asibitin. Ga garin sai walkiya ake alamun hadari zai taso a garin banyi nisa da tafiya ba aka fara iska a hankali na kara sauri don kada ruwa ya fado. Tafiya nake don da kyat nake ganin gabana don iskan dake mayar dani baya duk kura ya cika min ido sai dai hakan bai hanani rike wayan mamu a hannu na ba gam. Tasowan hadarin yasa abin hawa suka rage gudu a titin sai jefi jefi suke gilmawa . Haka nake dan hadawa da gudu don in isa gida da wuri ina cikin tafiya mai kama da sarsarfa har ban san na hau titi ba a lokacin. Karan taka burki danaji da karfi gaf dani yasa na rufe idanuna sai na jini a kasa tim na cikin motar ya leko daga tagan motar daidai lokacin da nake kokarin tashi tsaye yace ke wata irun mahaukaciya ce kamar dabba baki kallon hanya zaki wani hayewa mutane tsakiyan titi kamar na gidan ku. Muryan yayi min kama da na yan gidan mu ina dan dangesawa na mike don jayewa a saman hanyan. Ya sake fadin kauce dan Allah kina bata min lokaci har ruwa ya sauko ko na latse ki a wurin in take banza ke har da watan azumin kike fita yawon banza ki ? Da sauri na matsa daga wurin da sauri ina kaucewa saman titi ina kallo ya ja motar shi ya barni a gurin sai lokacin naji kafana yayi min tsami na fara tunane naji ciwo a kafan. Sai kuma na fara tunanen waye a cikin su da sauri na tuna shine habbib a cikin su nace lalai wanan yakai mara imani da rashin tausayi . Ka buge ni kuma bai tsaya bani hakkuri ba ya hauni da fada da zagi lalai ba karya yaran hjy jummai basu da imani a zukatan su ko kadan. Nasan duk ya gane ni amma ya nuna kamar bai san daga inda na fito ba har yake zargina da yawon banza haka dan iska kaci arzikin manjo yau don ba fada ne a gabana ba yanzu lafiyan kakata na damu dashi yanzu. Da tunane kala kala har na karaso gida lokacin an fara dan ruwa da karfi ina zuwa na tura get naji a rufe na shiga duka. Abin mamaki mamu na gani a tsaye ta kauce a hanya na shiga ba tare da tai min magana ba har muka shiga part din mu ina dan dangyasawa. Mamu bata nuna min tausayawa ba ga abinda ya samay ni sai dai ko ba a fada na hango damuwa a fuskanta karara. Ruwan sama mai karfi akayi ranan tun shigewa na daki nake jin dan zazzabi na son kamani ajikina wasa wasa kafin asuba sai ya rufe ni lif. Gani ban fito ba yasa mamu duba dakina a cikin fada sai ta ganni dunkule a cikin bargo tundaga kaina har kafa. Abinda yasa ta karaso inda nake ke nan tana fadin ai kinga na wanda baijin maganan iyayyen shi yanzu hankalin ki ya kwanta kin gano ma idon ki tashin hankali. Dama kwancin kike son yi ke ma saj kije asibitin ku kwanta da kakar taki tunda haka yafi maki yarinya bajin magana . Ta fita daga dakin can abin da da mahaifi sai gata ta dawo dauke da cup da magani a hannun ta tace oya tashi ki sha magani mara jin magana. Banda wani katabus a jikina kamar ma na zautu a ranan komai sai ido nake bi dashi kawai ban iya yin maganan komai da kowa. Ina kubawa naji tea ne mai zafi ashe na dan hade maganin ina miko mata kofin tace cikin tsawa kurbe shi maza ki shanye. Haka na daure na sha fiye da rabi nayi kokarin aje kofi zan sauko daga kan gado tace ina zaki kuma nace zan shiga ban daki ne mamu. Ta kauce tana bina da kallo sai lokacin ta kula ban tafiya daidai tace da sauri ke may ya samu kafan ki kuma ? Nace mota ta buge ni a hanya ta tsura min ido kamar mai nazari kafin tace kin tabbatar nace wallahi mamu ina tafiya ban san na hau titi ba ashe mota na tafe ban sani ba. Tace a ina ta buge ki na dan daga rigan dake jikina ina nuna mata wurin abinka ga farar mace wurin yayi wani irin ja da sauri mamu tace amma yar nan kikaki fadan wanan rauni irin haka ? Nan dai na barta a tsaye na ja kafana a hankali zuwa bayin da kyat na iya dukawa da kafan na gabatar da uzurina lokacin. Har na fito na samu mamu a dakin sai na nufi hanyar falo tace ina kuma zaki nace ruwa zan sha mamu. Dawo ki zauna in dauko maki tana fadin haka ta juya ta fita sai gata da goran ruwa mai dan sanyi kadan ta miko min na karba ba kurba kadan na mika mata ta fita. Sai gata ta dawo da man tiger tace in bude wurin ta shafa min tana tsaye na koma na kwanta ta sake fita. Ban falkaba sai takwasa ranan na iya mikewa zuwa sallah fada ma Amma abinda ya faru dani mamu tayi sai gata ta shigo gaida ni tana ta faman tsinewa wanda ya kade ni da mota. Nan dai na daure cikin karfin hali nace mamu dan gidan nan ne fa ya kadeni da mota kuma ya zageni da yar iska mahaukaciya wai na fito yawon banza. Nan ta saka salati tana fadin yaran nan ko suna da imani wani irin bakin ciki suke son sauke muna a gidan nan ne wai. Dama wanda yabar akidar shi ba wani imani ne da shiba ance yaren ka addinin ka kowa yabar gida gada ta barshi babu alherin da yarab nan suka koyo ga wanan tafiyan nasu sai bakin ciki da takaici idan kwai ya tashi fashewa a gidan nan tsiyan abin ba kan uwarsu zai tsaya kadai ba bakin cikin har mu zai shafa duka. Mamu bata gane may Amma ke nufi da zancen ta ba sai tace ai basu dawo da wani matsala ba sai dai daukan kai da rashin ganin darajan mutane. Uhhummm kawai Amma tace tare da fadin Allah dai ya kyauta yar nan ta juyo gareni tana fadin wanne daga cikin su yai maki wanan karen aikin haka ? Gwago da ki barsu ai itama bata jin magana saj da na cewa yarinyar nan kada ta fita ban san yadda akayi yarinyar nan tasan vurin nan ba don bakin bin kwakwafin ta na tsiya ai sune maganin ta. Amma gwago don Allah a bar zancen sai gaba idan sun kara don irin kawaicin da dan uwansu yayi muna kan kakarta kinga ina ganin har yanzu mahaifiyar tasu bata da wanan labarin. Amma tace toh shike nan daba don haka ba wallahi da yau mai shi ya jini a gidan nan wanan an kashe ta yaso yin don haushin ta da suke ji. Ta dade tana fada a kaina har zuwa lokacin da suka fita daga part din lokacin zazzabin ya kara taso min na kwata barci mm ai nauyi a dunkule. Ban garen Umar yana jiran yaji kiran mahaifin su kan maganan su da Amma kamar yadda yai tsammani kira daga gare su tun bayan maganan su da Amma. Sai dai har gashi ana ta faman shirin sallah har lokacin baiji wani abu ya taso akan zancen ba ko canjin fuska a gurin iyayyen shi. Sai Amma din daya rasa gane ma inda ta dosa tun ranan da sukai maganan ta canza mashi kwata kwata bata bashi fuska yanzu ko kadan. Yanzu ma yana son zuwa ya gaida ita sai dai yanayi daure fuskan da take mashine baya so ko kadan haka dai zai daure yaje su gaisa din. Don Amma din wani babban makami ne a gare shi nan gaba a abubuwan dake shirin tasowa tsakanin shi da iyayyen shi nan gaba. Da sallama a bakin shi ya shigo falon tana zaune tayi tagumi ta zuba ma wuri daya ido jin sallaman shi yasa ta dago tana kallon shi. A sanyaye ta amsa mai sallaman ya shigo yana fadin dazun zan shigo naga ficewan ki nan sai na fasa shigowan . Tace cikin dan bata rai wallahi naje duba wanan yar ne kuma yace wata ya ke kullu sai kin tafi duban ta ne kuna shagabata tana kara narkewa. Kai ma ba haka nai maka duk cikin jikokina kaf ku fi tsaya min a rai ku biyun ban don naku yafi zuwa daya da nawa ko yanzun ma wani mara imani ya kade da mota a cikin gidan nan jiya da dare. Amma mota fa kika ce tace zan ma wasa ne kafa yana nan ya hau sosai kuma uwarta da kawaici ta hana a fadawa mahaifin ku don gudun fita da halarcin da kai masu. Amma Amma wanan aiba abin kyalewa bane don ba karamin magana bane idan tsotsayi ya kaishi ga kashe ta fa ? Ganan min hanya kadai dan nan nima abinda na hango ke nan zan bincika in san ko waye don gaba tace shine daidai don bai kamata a kyale zancen ba don wani dalili can rayuwa ne fa . Can dan shiru ya biyu baya saj Amma take fadin dama ina neman ka akan zancen kayan nan gasu aje har yau baka ce komai ba kuma har gobe jajibur. Kaya Amma ya kallo ta yana tambaya yana rike da haban shi da hannu daya yayin da kafan shi daya ke tankwafe saman kujeran da yake zaune a kai. Tace kayan da kasa aka shigo dasu nan mana tayi mai bayani yadda zai gane may take nufi da maganan ta. Yace kai Amma suna aje ashe naki tsaraban ke nan ai da zaki rabawa mutane su dan jikan ki ya dawo kibawa yan uwa gaba daya mama ma na bata na bangare su ai ita da yan uwanta. Kai dan nan Allah yayi maka albarka ai ban san manufarka ba ke nan ya mike yana fadin zai fita nan Amma ta shiga kasafa kayan ita da mama hadiye mukan yan gaban goshi ne na samu tsaraba masu yawa sosai wanan lokacin don ammace mai rabon. Wanan labarin yaje kunnen hjy jummai ta kulu da danta sosai sai dai saukin abin akwai da shakku da shayi tsakanin ta da dan don shi kaifi daya ne idan ya furta abu. Tayi ta dakon shigowan shi bai shigo ba sai kuma ga su Aliyu sun shigo lokacin shan ruwa suna fushi yayi masu fada kan buge ni da mota da habbib ya tashi yi. Suna shigowa uwar ta tare su tana fadin yaya na ganku haka Aliyu yana zama yace dan matsala suka samu da big bros a waje. A gigice take fadin matsala kuma akan may kuka samu matsala kai da dan uwanka har haka sai Aliyu ne dai ke iya bata amsa da fadin. Don kawai ya buge wanan yarinyar shine yake masa fada akan ya kula kin san hahbib shine yaso taso mashi ya dakatar dashi a cikin fada. Kallon habbib tayi ranta na mata kuna tace wace yar ka tashi duka yace ba duka fa ba da mota ya kade ta lokacin da iskan nan ya taso jiya. Habbib yace wallahi mama abinda bros keyi wani lokaci haka ya tursasa ni akan sai nayiwa wata tsohuwa can da Amma tayi magana aiki ashe kakan shegiyar yatinyar nan ne ma wa kuke kiranta yar agolan gidan nan taku. Dam dam zuciyar hjy jummai ya harba take ranta ya fara baci idon ta ya rufe ta mike tsaye ta fara fada. Lalai munafincin gidan nan yakai dama nasan yaron nan ba a banza aka barshi ba har abin yakai a hada min diyana fada a gidan nan. Aliyu yace bafa fada sukayi ba mama ki kwantar da hankalin ki don Allah shi bros din ne yayi ma habbib fada a kan ya daina kada tsautsayi da kadara yasa ya kashe ta kinga ko gaskiya ne ai ya fada mai. Suna tare uwaf amma ina tayi gaba ta fara da wurin mu na samu na dan tashi ina buda baki don mamu saboda ciwo na yau sau daya ta leka asibiti wurin manjo. Daga sama mukaji sababin ta tana fada da tonon asiri kala kala wanda hakan ne ya jawo hhankalin sauran mutanen gidan suka fara fitowa daga part din su don gane ma idon su abinda ke faruwa dasu. Alh sani shima ya fito hankali tashe yana tambayan mai ya faru a hasale ta juya inda yake tana fadin munafuncin gidan ga mana. Diyana basu taba fada a tsakanin su ba sai a kan wanan bakar annoban yarinyar A ruwa ta kai muna ko ina a cikin gidan nan saboda samun wuri. A ruwa fatima ke nan kike nufi munafuncin may akai maki keda diyan naki ? Hjy jummai tace a munafunci mana tunda har aka iya boyen min abinda aka tursasa shi yayi wa dan uwanshi abinda rashin bai so ba. Ke nifa ban fahince ki ba ki fito fili kiyi magana kin tsaya muna kwana kwana. Sai ta boye zancen kade ni da mota ta fito da zancan asibitin kawai muryan Aliyu ne da tun dazu ne ya shigo ya tsaya yana sauraren ba tare da sunsan yana nan ba. Yace mama yanzu fadan da nayi mai kan ya kula da kada tsautsayi ya gitta ya kashe ta iyakan fadan da nayj mai ke nan . Mahaifin su yace wai shin wa aka kade Amma dake fitowa tace A ruwa ya kade ta fito asibiti duba kakarra jiya da dare. Ranan sun ji nacin ran mahaifin su ya nuna ma uwar har diyan bacin ranshi akan abinda suke nuna min gidan yace shi amana ya dauko ni yana riko ba agola ba kamar yadda suke fadi. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:52 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMAIN RAHIM , ALHAMDULLILAHI RABBIL ALLAMIN, , , , Ranan haka mukai buda baki babu dadi a gidan kawuna mijin uwata wanda hjy jummai fadan ta duk akan taimakon da danta yayiwa kakanane take fadan. Rayuka sun baci a ranan don kowa yana wurin har mamu ta kasa hakkuri take fadin ban taba zaton don Umar ya taimake ni a gidan zai zama laifi ba don ko yaya dai su din diyan dan uwana ne ko ba aure a tsakanin mu. Tace alfaharin ki ke nan dake da ma su zuga ki to ban haifarwa duniya da ba idan kina so ki jira naki su aimaka maki daidai lokacin Umar ya juya yabar gurin don zai iya cewa bai taba zaton haka daga mahaifiyar su ba. Ganin ya fita suma sauran suka juya suka nufi hanyar fita waje suna mai mara mai baya sai dai kafin su fito ya riga da ya shiga mota yabar unguwan gaba daya. Zuciyar shi cike da kunan rai ga halin da mahaifiyar tasu ta nuna a gaban su ranan ya fahinci wani abu sosai a zama gidan da take yawan korafi akai. Tsaye sukayi cirko cirko a kofan gidan mai karatu abinda kika sani ne a wanan zamanin mai hali koda shine karami shike juya kowa. Balle shi da yake babban su a gidan kuma suna sane da abinda iyayyensu ba su sani ba a gamay dashi jiran dan wani lokaci yake kafin ya baiyana kanshi gare su. Har goman dare bai shigo gidan ba wanda hakan mahaifiyar tashi bata ji dadin yin hakan ba don tasan a ranan ran kowa a bace yake a gidan. Sai dai bata damu ba abinda ya damayta shine rashin walwalan diyan nata da tagani a tare dasu gaba dayan su sun kasa sake jiki har lokacin da suka dawo gidan. Shiko yana barin gida wani katafaren hotel yaje ya kama a nan ya kwana tare da kashe wayoyin shi. Haka yasa uwar ta kara shiga damuwa don kashe wayoyin da yayi a lokacin dan haka tun da safe ta samu mijin su da zancen . Nan kuma sabon rikici ya kara barkewa a tsakanin su tun sunayi a daki har abin ya kaisu ga zancen ta bar mashi gida hakan ya jawo hankalin kowa a gidan. Haka akayi jajibirin ranan rayuka a bace a gun kowa babba da yaro don hajiya ta hanawa mutane zaman lafiya dadin takaicin ts shine rabon tsaraban da Amma tayi na danta . Halin da ake ciki bai hana tayi fadan haka ba sai da maigidan yace duk ta kara tankawa ranan sai ya sake ta ganin da gaske yake yi yasa ta ja bakinta tayi shiru akan maganan. Ita ko Amma kamar da gaiya dan duk wa yanda batai tsamani ba sai da Amma ta tsakura mata tsaraban ana sa albarka sai bugo waya mutand keyi suna godiya gurin hjy jummai din. Nikan ina fama da kafana daya hanani shakat a rayuwana don ko wajen ban iya lekawa ba tun dawowana dana shige sai dai ina samun kyakyawan kulawa don Alh yasa an duba min kafan an ban magani. Sai na ke samun sauki sosai ga kafan washe garin sallah haka na tashi sumul kafan ya huce sai dai alaman a aurin don jan da yayi bai bace ba har wanan lokacin. Rigan da Amma ta bani cikin tsaraba mai kwaliya sosai na duwatsu na saka tare da rolling din dan kwalin shi a kaina zuwa kafada na. Ranan har kwalliya nayi sosai a fuskana tsurana ya fito tsab na mace yar matashiyar balaga. Sai dai duk abin da nake a cikin dauriya nake yin sa don hankalina yana gurin manjo dake kwance sharkaf a asibiti. Ina dakewa ne don in nunawa mamu yadda take so dani don hankalina ya daga akan korar da tayi min a saibiti ranan har na hadu da kaddara macuci ya buge ni da mota a hanya. Badon komai nake dakewan da dauriya ba sai don mamu taga nayi hankali ta barni in je in duba kakata dake cikin wani haki lokacin. Mun gama duk wani abinda zamuyi har abinci na danci tare da fauziya don dai mamu taga na sake kamar yadda take so din. Ganin muna zaune sai kallo nace ma fauziya ta tashi mu leka Amma muyi mata barka da sallah a part din ta. Muka fito zuwa wurin ta a daidai lokacin duk yan matan gidan suna waje suna daukan photo tare da yannen su. Gaba dayan su kallon su ya dawo gare mu kowa da abinda ke a cikin zuciyar shi ba kamar Umar da yagano rigan da ya sayawa mahaifiyar shi a jikina abinda yasa shi kura min ido ke nan lokacin da muka tun karo wurin da suke don shiga wurin Amma din. Bazai mata da rigan ba don kudi ya bayar mai yawa yace a zaba mai riga ta kece raini a cikin mata. Mai shagon ya zabo mai to yaya akayi wana rigan yazo hannun wanan yarinyar sai ya tuna da marrry yabawa ta saka mai a cikin kayan hjy jummai ke nan surin Amma na samay shi ke nan. A lokacin Aisha kece min dana karaso gurin da suke A ruwa zo kema mu dauki photo da su bros yau take sallah a tuna baya wata rana. Ke Aisha wace A ruwa kuma can don kema kin samu an laba ki ciki shine zski muna kalar dangi a nan sai Ikilima yar wurin hjy maryam tace wanan namu yan gidane bada yan ci rani ba gaskiya iya mu jikokin Amma zamu dauka. Ke mayar da yukan ki kube, don ni ina da tarbiya don ba zanyi photo da mazan da ba Ahalina ba nasan mutuncin kaina ku da kuke ganin hakan wayewa sai ku mayar da hinma ai na wuce abina zuwa cikin part din. Na fadi haka ne a daidai lokacin da hankalin mazan yake gurin da suke kallon wani a waya suna dariya hankalin su baya gare mu. Ashe duk sun jini wani kallo suka jefeni dashi a lokaci daya na mamakin abinda na fada Aliyu ne yace ke wanan yarinyar may take daukan kanta. Kada kaga laifin ta don su suka fara takalan ta da basu fada mata irin maganan nan ba da bata basu amsa daidai da su ba Aisha ke fadi. Ni har mamakin yariyar nan nake ji wai tana ganin kamar tafi kowane ko may Habbib ya tare shi da fadin haka. Nan dai aka shiga aibantani inda umar yana jin su yayi shiru kamar baijin abinda ke faruwa a wurin tsakanin yaran ya mayar da hankalin shi ga wayan shi. Sai lokacin ya dago kai yana fadin na lura kuna cikin bada gudun mawan tashin hankali a gidan nan yanzu da yarinyar nan ta biyo nan wa tayiwa magana a cikin ku ? Sai kowan su yayi shiru ganin yadda ya ke magana don da kyat duka fsayar dashi ayi photo bukin sallah yaci gaba da fadin. Yarinyar nan kun sata a gaba ku kwantata ku gani idan kune a matsayin ta yaya zakuji idan ana maku hakan dan magana kadan kunsan zai iya zama babba a gidan nan. Yana fadin haka ya juya yabar wurin sauran ma basu dade ba suka shigevwurin mahaifiyar su photon da aka fasa dauka ke nan dasu. Ina shiga dakin Amma tana zaune an kewayeta da kwanonin abinci a gaban ta tana fisgan nama a bakin ta mukai sallama muka shigo. Tana hadewa take kokarin magana ashe kafa yayi sauki har kin samu fitowa yau nace ina zama dana sani da ban fito a yanzu ba ai. A jaka fada idan kayi magana ace baka da gaskiya da ke da waye yanzu kuma ta tambaya tana maida dubanta gare ni. Ban bata amsa ba sai kokarin hayewa kujeran da nakeyi don in mike kafana dana dan tako yake min zugi a lokacin tunda ba wani fita nakeyi ba sosai. Kafin muci gaba da magana sai ga Aisha ta shigo tana fadin kai mutumiyar wanan shiga haka kamar wata balaraba dake wallahi bakiga yadda kika tafi da imanin mu ba a gurin lalai hajiyan ki tana ji da budurwan nan nata. Ido naga Amma ta kyat min sai kawai nayi dan murmushi na gane may take nufi na basar da maganan da Aisha take min ta zauna a kusa dani tana fadin . Amma dai ba a kasan nan aka sai maki wanan rigan ba wallahi duk kin fimu mu haduwa baki ga yadda sallama ta tsuke fuska ba da tana muna sallo a cikin nata sai gashi sun ga naki ya cunawa nasu din. Ranan hira mukayi da Amma da Aisha sosai do ban fito ba saboda nauyin da kafan ke mun yasa na dade a zaune a gurin. Da yamma lis na fito don komawa part din mu a daidai lokacin Ahmed ke fitowa daga wurin Alh da yazo gaida shi da sallah. A yadda na hango kofan falon da takalman maza da yawa ya nuna cewa Alh yana da baki a lokacin. Tun daga nisa Ahmed dake kokarin saka takalma yake min murmushi abinda bai taba yi mun ba sakin fuska. Haka yasa nima na mayar mai da martanin murmushi a fuskana na tunkari inda yake ina fadin Ya Ahmed barka da sallah. Yana kallona a wani yana da ban iya fassarashi yace yau kanwatace haka a cikin kwaliya kamar wata yar sarkin larabawa ? Wai ya Ahmed kayan sunyi min kyau ne kowa sai yabon kwalliyata yakeyi yau dama ai kaida mamu kuke hanani kwalliyan ai dama na iya abina tun a gida. Yanzu dai barin nuna maki kyaun da kikayi gyara in dauke ku photo dake da fauziya ku gani nan yayi ta daukan mu photo muna dariya. Sai ganin mutane na fitowa fallon wanda yaran gidan ne su uku sai wasu biyu da van sani ba a bayan su naji daga cikin bakin na fadin . A a Ahmed ashe baka tafi ba ya dan yi dariya so guilty yana fadin wallahi wanan kanwar tawa ne ta tsayar dani da shiririn tan ta. Nan ya tafi ya barmu da wayan shi muna kallo a cikin sa sai da muka gama naba fauziya ta kaimai inda nake hangen su. Kwana biyun ranakun sallah mun sha gasan kwalliya a gidan wanda akeyi kamar ko wani gida da ke da yan mata duk da ban kai su shekaru ba ina tsone masu ido. Har na bar fita ranan na uku ga sallah da safe sai ga mamu a dakina ta tsaya daga kofa tana fadin ki shirya idan mun gama girki muje wurin babba asibiti yau. Wani irin tsale nayi ina murna da sauri nabi bayan ta ina tambayan ta may za a girka don in dora da wuri mu gama. Tace tuwo don kin san shi tafi so don yanzu tana cin abinci har da yunwa yaso yai mata illa saboda rashin kulan da bata samu sosai a can. Haka na zage nayi aiki mamu tana duba min har na gama muka shirya gaba dayan mu zuwa asibitin . Mun fito ne daidai lokacin da baki ke zuwa gidan na sheda su kannen kawu ne su kawu bala da kawu suleiman muka tsaya muna gaisawa dasu a wurin . An dan taba yar magana tsakanin su da mamu wanda ni ina bakin motar ta banji abinda suke magana akai ba tazo ta shiga muka tafi. Ashe mun bar baya da kura a gidan don Amma ce ta aika suzo gaba dayan su tana son ganin su wanda dama suna da niyar zuwa sai dai ba a lokaci daya sukan zo ba don haka ta nemay su a wanan lokacin. Duk da kiran bai daga masu hankali ba don takan nemay a haka idan wani magana mai muhinmanci ya taso gare ta daya shafi kowan su . Sai da suka shiga wurin dan uwan su suka taba hira dashi suka fito zuwa jin kiran da tsohuwar ke masu a lokacin. Su shiga sun samay ta zaune da diyan ta mata su biyu a lokacin suna dan maganan su ba mata shigowan su aka fara gaisuwa a tsakanin su. Bayan gaisuwa da yar hiran lokaci kawu bala ya fara magana akan neman da mahaifiyar tasu take mashi a lokacin. Sai kowan su ya natsu yana sauraren dalilin kiran a cikin ladabi gaba dayan su suna kasa zaune har matan sun sauka ka kujeran sun zube a kasa kamar yadda yayyu su sukayi. Dan kallon gefen Alh sani tayi tana fadin zanso kafin in fara magana a kira min matan ka gaba dayan su do suma maganar ta shafe su. Alh sani yaji wani iri don yana zaton irin iya shegen da iyalin ke yawan yi ne a lokacin wani abu ya shafi tsohuwar har zatai magana. Don Amma bata da yawan magana kan sarakanta ga duk wani abinda suke mata tana kokarin kawar da kai don kada suga takurawan ta gare su. Kawu sulaiman yace maimuna ko bata gidan nan don muna shigowa naga fitan ta tace asibiti zasu gaida kakar yarta da aka kwantar tun kan ayi sallah ko ? A kira min ita ta dawo don wanan maganan ya shafi kowa na ahalin nan shiya saka na kiraku yanzun ma. Wayan shi ya ciro daga cikin Aljihun shi ya fara neman layin mamu din a daidai lokacin da muna zaune na makale manjo muna yaushe rabo da ita. Sai ga kiran mijin ta ya shigo mata yana fadin ta dawo gida yanzu hajiya tana neman ta da gagawa haka kuma bayan ya gama waya da mamu ya kira sauran matan nashi a waya. Mamu bata kara lokaci ba ta mike tana fadin mu je gida tana ganin wanj abi ne ya taso a fida don Alh ya kirata cewa gwago tana neman ta. Ta juya gurin da nake tana fadin ko kinyi wani abin ne da wani ban sani ba da sauri nace ni ko part din Amma ban shiga ba yau. Haka muka fito ba don naso ba muna nufi hanyar gida tayiwa manjo alkawarin dawowa dani wani lokacin i wuni a gurin ta. Ko da ta dawo har Alh yayi mata kira biyu da cewa ita fa ake jira tana fadin gata gida a na karshen kiran. Bahan ta shigo ta gaida su ta samu wuri ta zauna kamar yadda kowa yake zaune a falon kafin Amma ta fara magana tace. Dalilin kiran ku anan ba wani abu bane sai dalili kamar biyu don haka na bukaci kowa yazo don zancen ya shafi kowan ku nan wanan dalilin yasa na kira harda matan ka kai yaro don haka take kiran shi kasancewar shi dan farko a gare ta. Ta sake fadin kun san dalilin wanan kiran yanzu gaba dayan su falon suka amsa da a, a banda hajiya jummai dake cika tana batsewa ta dauka maganan ta za a yi da farko. Tace zancen nasan wasun ku zasu jishi kamar almara kamar kuma tatsiniyar sai dai gaskiyar magana zan fada maku. Sai da ta dan nisa kafin tace yaron nan Umar ne ya samay ni da wata maganan da ban taba kawo rai gare shi ba kwanakin baya. Kafin ayi sallah na daure ne na hade maganan don ku sha ruwa lafiya zuciyar ku da sanyi ta kara da fadin sai dai ina son ko wanin ku bayan kunji ni ku yarda da kaddara kamar yadda nayi tunane a baya. Jummai da tun ambatan Umar ta tsurawa hajiyan ido tana kallon ta da son jin may zata fada gamay da danta data tara su haka wuri daya koma mainene tasan magana ce mai tsauri. Amma taci gaba da fadin ya samay ni wata rana yake fada min wai yana da aure a can har matan tana da ciki yanzun haka maganan nan da nake maku. Ba hjy jummai da ke mahaifiyar shi ba gaba daya sun kadu a falin don ji abinda tsohuwar ke fadi tace ba iya zancen ke nan ba lokacin da taji kawu bala yana fadin shi umar din dai hajiya. Tace aban haushi abin takaici da yaron nan ya dauko muna wai matar tashi arniyace don bata sallah kuma a haka yake son abinshi. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:52 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHUMA INNI AS, ALUKAL HUDA WAL TUKA WAL FAFA WAL LUDAIINA, , , , , , Gaba dayan su ba mai iya furta komai sai innalillahi wa inna alahim raji, un bamunan su ke iya ambatawa. Da kyat hjy jummai ta iya furta hajiya wanan maganan ina ya fito haka wani sabon sherin kuma ake son kulla wa diya don kawai anga sun dawo kasan nan lafiya cikin wadata. Ke dakata don Allah a nan wa kike fanin zai kullah wa umar sheri a cikin mu ko hajiyar ce zata kulla mai wanan sai Amma tayi murmushi tace in banda abin jummai sunan kin haifi yaron nan saudaki ne kawai amma baki fini son shi da shakuwa da shi ba. Ina nan zaune yaron nan ya samay ni fuskan shi da yanayin sa a cikin damuwa kwana biyu na shiga damuwa sosai sai daga baya yake labarta min damuwan shj dana damay shi da tambaya. Farkon wljin wanan maganan vun yar kakabun nan na fara ji A ruwa take min wanka da jurwaye da zancen. Da sauri mamu tace Sayadi kuma gwago ina ta jiyo wanan maganan itako babban magana irin haka ? Allah masani ke dai yar nan anan ta samay ni cikin damuwan rashin walwalan shi kwana biyu kin san itace abokiyar firan nawa wani lokaci ina magana shine take fadin wai kai sai kuma ta kasa fadin abinda na fada mata ranan don ganin idanun da sukai mata yawa lokacin. Ehh lalai wanan yarinyar takai shu,uma har sherin yakai gun yarana haka a hasale kawu bala yace ke jummai ki bari mu fuskanci matsalan da ya kunnu muna kai ki daina muna wanan shirmay. Ko ta fada yanzu ai ba abin mamaki bane don kila a wani wurin ta samu labarin don yanzu maganan duniya ba boye yake ba mama Altine yayan mama hadiye ke fadin haka. Yanzu naji inda wanan sherin ya tafito a gidan nan dama ko ba,a fada ba kowa yasan a rina har bakin cikin yakai haka ban sani ba. Ke jummai na fada maki ki daina muna wanan shiman may ye na bakin ciki da diyan ki ina abinda yai yaran ki shiyayi yar nan da kike son zargawa magana. May ye abin zargi a cikin maganan nan Bala sadauki da kansa yazo ya samay ni da zancen yana son in roka mashi gafaran ku. Tun fara maganan Alh sani bai iya furta komai ba sai zufa yake yayin da kanshi yake duke zuviyar shi tana batun bugawa a lokacin. Sai mama hadiye ta katse mai tunane da fadin yanzu may ake ciki da wanan zancen mai daure kai yaya. Sai lokacin Alh sani ya dago kai yana fadin may ko ake ciki hadiye illar yaje ya nemi wasu iyayyen tunda ya nuna yana dasu cikin duniya . Ni dai na zamay hannu ga duk wani alamari Faruq a gidan nan yaje ya nemi iyayyen shi can duniya ce fadi gare ta ke kuma jummai kin kai ga yadda kike so Allah ya isar min a gare ki yana fadin haka ya mike yana sharan hawayen dake barazanan zubo mashi a idanuwan shi. Ba hajiya jummai duk wani wanda ke falon a lokacin ya tausayawa Alh sani da kuma firgita da kalamin Alh sani daya furtawa hjy jummai. A hankali hawayen bakin ciki ya fara zo mata na nadama tana fadi a cikin kuka yanzu may ye nawa a cikin wanan zancen don Allah. Yaron yanzu ne ka haife shi baka haifi halin shi baka shedan dan yau har kina kokarin dora laifi kan yar mutane sai Amma tace . Balle zancen yar nan dutse ne don zaman su da arna take magana na kwabe ta ashe bamu tsira da zancen ba. Yaya yanzu mainene abin yi don Alh ya tashi a cikin fushi bai tsaya an samo ma maganan mafita ba. Tunda ya riga ya aikata har an kai ga rabo ai sai a san yadda za a gyaro maganan yanzu kuma mama Altine ke magana don su din yayyun mahaifiyatace yasa nake kiran su da mama sabanin yaran gidan da suke kiran su da gwago. Ni banga wani abin bata lokaci ba ai gaskiyan Yaya din daya ce duniya da fadi yaje tunda dangin matar shi sun fi mai da zaiyi abu gaba gadi babu sanarwa. Amma ta dan girgiza kai tace zanso muji ta bakin umar din don ya fada muna dalilin shi na yin haka ba tare da sanin mu ba saboda kada mu yanke mai hukunci a cikin duhu . Yanzu sai mu bari har wani lokaci idan mun kara tataunawa akan zance sai mu sake zama sai maganar gaskiya wanan yaton bai kyauta muna ba wallahi. Hjy Jummai kamar ruwa ya cita a gurin don zaune take tun bayan da zance ya tabbata gaskiya shi yazo da wanan maganan mai kama da tatsuniya a wurin su. Da dadaya suke ficewa a falon kowa ranshi a bace da wanan zancen da yazo masu na bacin rai inda hjy jummai ta bi bayan su kawu Bala ta fice a cikin wani yanayi. Duk ido matan dake falon suka bita dashi lokaci daya kowa yasan irin halin tashin hankalin da take ciki a lokacin don duk wata uwan da tasan zafin dan ta bata kaunan wanan abu ya faru dashi. Bayan kamar yan dakiko mama Altine ta fara magana tana fadin irin abinda akewa gudu ke nan wallahi. An sosa wa hjy maryam rai don zuciyar ta fari yake kal kan wanan zancen don tasan komai na iya faruwa tsakanin hjy jummai da maigidan su a yanzu. Tace dama idan kace baka son ran yaro ya baci kai naka sai yafi dubu bace don yaya bata son afadi laifin yayan ta ko kadan. Don haka ne ko kaga yaro yana abu a gidan nan kaidai iyakan ka ido yau ina alfaharin da ake muna yaranta sune gida su suka iya, , , , Haba anty maryam wanan magana bai dace ba don wanan abu ya shafi kowan mu a nan sannan duk mu nan iyayye ne idan daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kukuture barka don babu bare a nan yanzu cikin mu. Mama hadiye ta amsa da wanan haka yake gaskiya indai baka tausaya ba bakace kuma gwai ba ai ba. Tace ba haka nake nufi ba kowa a nan yasan halin yaya akan rashin son a fadi gaskiya akan diyan ta shine nufi na. Sun dauki lokaci ana magana a wurin kafin su watse kusan lokaci daya mamu da hjy maryam suka fito daga part din. Hjy maryam bata daddara ba tace maimuna baki gane nufi na ba zakice baki jin zafin yawan gorin da alfaharin da ake muna gidan nan ne. Don kawai mu an maishe banza a gidan nan damu da yaran mu ana daukan mu damu da babu duk daya ne a gidan nan. Kai duniya amma wanan maganan naki baiyi ba wallahi Allah ya kyauta tana fadin haka ta shige ta barta tana hadiyan kili bibin dake cin ta lokacin don ita kan a wurin ta hakan yai mata dadi taga kurin zuwa turan yaran da ake mata ga tsaraba turai ta samu dan ta ya jajibo mata arniya a matsayin sarakuwa a gida da gari duka. Hajiya Jummai a har gitse ta shiga shiyan ta dama kiris take jira ta fashe da kuka don ba karamin daurewa tayi ba na controling din hawayen kada su zubo a gaban makiyan ta. Jin sheshekan kukanta yasa su salma saurin fito da sauri a rude suke suna tambayan abinda ke faruwa sai dai ba baki kuka kawai take rusawa zaune. Wanan ya tayar da hankalin salma ta daga waya tana kiran yayyun ta tana fadi suzo gida babu lafiya hjy ce daga an kirata part din Amma ta dawo masu tana kuka cikin tashin hankali take maganan. Umar din data kirashi tana fada mai yace shi yana lagos tun da safe baya gari a cikin zuciyar shi cewa yake am fasa kwan ke nan shike nan Amma ta fasa kwai a gidan. A rude su Aliyu suka shigo gidan kowa ya gansu yasan hankalin su a tashe yake dan sun dauka wani rikici ne ya faru a gidan sun shiya cin mutunci yau ga ko waye don basu iya jure ganin mahaifiyar su a kullun cikin bacin rai hakana. Mama may ke faruwa ne haka may ya faru dake kuma mama ta kasa basu amsa daidai lokacin sisters din ta suka iso suma. Tambaya daya suke mata suma ta kasa basu amsa saida suka matsa mata da kyar ta iya bude baki tace yau ni Alh ke jawa Allah ya isa akan babawo. Salati suka saka lokaci daya suna fadin may yai zafi haka kuma har yakai ga furta hakan gareki kuma ? Wai ashe babawo yayi auren arniya a can ban sani har tana dauke da cikin shi yanzu haka yaron nan bai fada min ba asan mafita sai a bakin kakarshi nake ji. Salati suka saka tare da fadin aure arniya kafira mara sallah kuma a can ko a nan ne ai ya jawo muna abin kunya gare mu. Yanzu ina babawon yake ne dayan yar uwar nata ta tambaya Salma tace bros yana lagos tunda safe. Ta juya tana fadin kinji ba nasan duk wanan abin ba a banza bane mahasda sunyi muna yawa a tattare damu. Haba mama may ya kawo zancen hassada ga wanan zancen da ya shafi bros a can kawai yayi aure sai kuyi mai fatan alheri ciki ai yanzu bros shiba yaro bane zai iya yin abinda yake so. Habbib ne da ya fara gajiya da irin halin mahaifiyar su yake fadin haka yace ni banga abinda zai sa ki wani tayar da hankalin ki haka ba sai dai in akan kalamin daddy ne ? Shi daddy may zaisa ya furta hakan don kawai ke kika haifi bros ko may yana da incin da zai auri wace yake so yanzu ai. Balle auren yau fa kusan shekara hudu kenan da yayi shi komai kuma bai faru ba gare shi so ni banga wani abin tayar da hankali ba a nan ? Kallon shi sukayi suna fadin kun san da wanan zancen baku fadawa mahaifiyar ku ba amma ko kunyi kuskuren boye mata dai . Mama may ye a ciki don yayi auren shi a can ba a can yake zaune bane zai zo nan yayi aure ne kuma idan matan nan basuyi mashi ba fa. Sai lokacin tace ni ba abin bakin ciki gare ni duk da naji haushi wanan zancen amma wai yadda aka tara kowa ake fadin wanan maganan kamar kaina aka fara hakan gaban maryam da maimuna fa Alh ya kirani suke fada min. Amma ai mashi auren gata a cikin dangi kamar kowa a mutunce ai zaifi yaya arniya kafira zata shigo cikin mu da sunan sarakuta ?. 16/11/2021, 22:55 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANI RAHIM YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTA GIS, , , , , Yinin ranan ya kasa bude wayogin shi tun lokaci da salma ta kirashi tana fada mai halin da mahaifiyar su take ciki yace bai gari ya kashe wayoyin nasa. Can ya mike ya fito ya nufi mota ba inda zai tafi haka yasa ya nufi beach don ya sha iska a can tafiya yake a bakin beach din hannayen shi duka biyu a cikin aljihun wandan shi sai dan kafan wandon daya tankwashe su kada ruwa ya bata mai. Kusan awa daya ya dauka a haka bai kaiga samo ma kanshi mafita ba a lokacin can yaja ya tsaya a guri daya yana fadin. Imposible imposible yana girgiza kanshi a hankali, nan ya fara tunane baiga dalilin hana shi abinda ranshi ke so a yanzu ba saboda wani akida can da bai sabawa addinin shi ba. Shidai yasan ba zai iya auren wata yar hausawa ba yanzu a yadda yake ganin su lulube ko yaushe a cikin hijjab gani abin rufe fuska da suke wani amfani dashi suna rufe fuska wanda bai san dalili su na yin hakan ba ? Kai ya girgiza daya tuna harda wanan yar ficiciyar yar maimunan wai rufe fuska take wa mutane ko may take boyo oho ? Sai kuma yaja guntun tsuki lokacin daya tuna yadda na fito babu wanan abin rufe fuskan gaba daya sun yi mamakin ganin irin surar da Allah yai min. Ko shi yasa Alh ke ji dani a cikin yayan gidan kamar yadda mama ke yawan korafin yana mun tsuki ya kara ja yana fadin how comes maimuna ta samu ya haka kamar halfcase wai ? Ita kanta maimuna inya tuna lokacin data tashi ai haka take da zuben kyau how he wish shima yasamu yara kyawawa haka a rayuwan shi kamar yadda diyan maimuna suke biyo ta da kyawo. Maimuna maimuna ya furta maimuna you deceved all this care wurin Alh don ya tuna suna secondary maimu din tana da hali mai kyau wanda tun a lokacin maza ke rushing a kanta. Mama why baki hakkuri don yarinyar nan tafiku da komai da maza ke so a wurin mace don idan ba don wanan alakan auren ta da mahaufin shi ba daya sa yanzu bai sakar mata fuska da can mutumiyar shi ce sosai a baya don kusan tashin su daya tare sukai karatu. Idon shi ya dan kara runtsewa iskan teku na bugun shi tare da guguwan ruwan dake fesowa har inda yake yana saukar mai da wani yanayi mai dadi dake kwantar mai da hankali. Zubur ya budo idanuwan shi tunawa da mahaifiyar su na iya shiga wani hali akan maganan da bata san mafarin shi ba. Tafiya ya dan fara yi a cikin sauri ya nufi inda ya aje motar shi a can nesa da bakin ruwan ya shiga. Hotel din daya sauka ya nufa ya Sarafa yana sanar mai ya karkare proces din da suke zai tafi kano a lokacin yayi dai dai jirgin marance na shirin tashi a lokacin. A kano yayi sallah isha,i bai shiga gidan su ba sai da ya dan samu abinda ya cima cikin shi don rabon shi da wani abu ya shiga cikin shi tun safe da ya dan sha ruwan coffee. Sai dai yayi rashin sa,a don abinda yake gudu ne ya faru dashi a gidan yana shiga suka hade da mahaifin shi da ya fito part din Amma. Kamar yadda suka saba gaida shi haka ya duka yana gaida mahaifin nashi da sukai haduwan bazata dashi dai dai sabanin yadda suka saba gaisuwa a da can da babu matsala suka hade din nan zai tsaya su dan taba hira kamar wasu abokai. Sai dai wanan karon yana gaida mahaifin nasa a cikjn tafiya ya karba mai kamar bai san inda ya fito ba a lokacin ya barshi a gurin tsugune yana mashi kallon mamaki. Faruq ka kyaleshi har ya sauko sai ku fuskaci juna dashi da yardan Allah komai zai zo da sauki kasan yanzu yana cikin fushin abin ne da kai. Muryan mamu ne da tafito sashen Amma gaida ita, shine ta biyo bayan mijin nasu don bashi abin shan sa da maganin shi don baida lafiya duk wanan lokacin. Sannu a hankali ya mike yana fuskantar inda muryan nata ke fitowa daga bayan shi duk da a yanzu ba wani mu,amula a tsakanin su tunda ya dawo kasan ya samay ta a matsayin matar mahaifin su. Saidai yaji dadin nuna kulawata a lokacin gare shi don ko ba komai ta fada mai gaskiya haka yasa ya kakaro murmushin dole a fuskan shi. Yana fadin ba komai na gode ya yaran karo farko ke nan wani maganan arziki ya shiga tsakanin su tun bayan dawowan nasa tace suna lafiya. Kadawo ke nan ashe, ya hanya yanzu nake ji a gurin gwago wai kayi tafiyane ashe ? Yace eh na tafi dan wani aikine a lagosa tun shekaran jiya ina can na gods daga haka bai kara furta komai ba ya wuce kai tsaye wurin Amma. A kofa ya tsaya yana sallama kamar kulun idan zai shiga sashen don yasan ba ita kadai bace a part din don haka yake tsayawa daga kofa yayi sallama. Yana saye cikin wani yadi mai laushi fari na maza mara nauyi zaka iya hango farin singlet dake cikin jikin shi gashin kanshi ya kwanta a kanshi sai sheki yake kamar ya shafa mai, maia cikin muryan shi dake ruda matan dake binshi yayi sallaman. Yayi sa, a daga ita sai mama hadiya da suka gama hira da mamu ta fita ta barsu zaune da Amma suna hiran raman da Alh sani yayi a cikin kwana biyun da zancen nan ya bullo. Mama hadiye ce tace a a mutan legas an dawo ke nan a ranshi yace ikon Allah ba halin mutum ya motsa sai kowa yaji halin da yake ciki sabanin can da ko daga wurin aiki tafiya ya kamashi zai iya tafiyan shi babu wanda ya sani . Amma sai gashi nan duk da bai fadi zaiyi tafiyan ba dan fadawa salma dayayi yana lagos duk ya karade kunnuwan mutanen gidan ko. A, a ashe ya sallamai kine da kike taron shi yayi dan murmushi yana gaida mama hadiye dake kokarin mikewa a wurin da take zaune. Yana dan shafan keyan shi yace Amma ba a fa shiga tsakanin da da mahaifi ke gaki kina kokarin hadani da gwagona fada yanzu. Fada kan ai ba,a farashi gare ka don kowa a jirace yake dakai a gidan nan wallahi yanzu dai na gane sadauki baka da kirki sam ? Tafiya irin wanan har ikko ka kasa fadawa kowa dan rashin daukan mutane da muhinmanci da bakayi ko may ? Ya dan kara sake murmushi yana zama yace tunda kin gama hadin fada ai zakice haka amma tafiya kuma ayi hakkuri daurowa yayi hakan nima bada niyar tafiya na fita ba a raina aikine ya taso min can na gagawa. Sai Amma tayi wani hade rai tana fadin ku dai san abinda kukeyi yaran nan ku dinga daukan iyayye da muhinmanci a rayuwa . Amma ban dauki wanan a laifi ba amma za a gyara da yardan Allah shike nan ko ya fadi yana kallon Amma din sai mama hadiye data kai kofa tace shike nan matar na tuba bata laifi tunda yace ayk hakkuri fada ya kare hajiya. Ya saki ajiyan zuciya bayan mama hadiye ta shiga yace Amma ya bayan rabo kuma ? Tace har lokacin cikin rashin walwala sai alheri sai dai mahaifan ka dake cikin tashin hankalin sakon daka bani in basu har yanzu. Cikin zakuwa yace tashin hankali kuma Amma may nayi aure ne fa nayi ba wani alfasha na aikata ba ? Kan Amma ya daure da maganan shi tace ban fahinci ba fadin ba wani laifi kayi mai tsauri ba don kayi aure ? Auren da kake tunkaho kayi a cikin tsarin addinin mu kayi shi ko yaya kai yanzu ka kwatanta a kanka idan diyan cika sukai maka haka zakaji dadi a rayuwan ka ? Ya saki wani wawan ajiyan zuciya a lalace yace may ye a ciki idan yaro yace ga abinda yake so yi amma sai in mashi fatan alheri final. Galala Amma ta tsaya tana kallon shi don ta fahinci idan ba sunyi da gaske ba ga yaran sun fara nisa ga barin al,adan su na gargajiya. Allah ya kyauta ta furta tare da fadin kaga ka samu iyayyen ka ku sulhunta a tsakanin ku yanzun mahaufin ka yabar nan . Na rasa gane ma jikin shi tun ranan da ya samu wanan labarin ga ba zaman lafiya tsakanin shi da mahaifiyar ka tun faruwan maganan. Ya gyara zama yana fadin yaya zan tun kari Daddy da wanan zancen a yanzu Amma yanzun nan ma din ai mun hadu ina gaida shi bai karba min ba. Nasan yana cikin fushi da nine har yanzu ina son in bashi lokaci har ya sauko mu fuskaci juna dashi sannan ni banga abinda zai sa Daddy yaga laifin mama a cikin wanan zancen ba. Don itama bata da labarin komai so a daina zargin ta a cikin wana magana don Allah Amma . Kai sadauki in fada maka gaskiya kayi kokarin gyarawa da iyayyen ka don suna cikin fushi da kai sosai ko ni nan don nakai zuciyana nesa ne nasan baka shaku da kowa a gidan nan ba sama dani yasa nake dan sasauta maka. Ya lumshe ido yana nazarin zancen tsohuwar kafin ya budd idanuwan nasa yace Amma ban taba zaton wanan abin zai kai haka ba wallahi. Domin irin macen da nake sha,awan samu ne na aure kuma ni zan zauna da abata ba wani ba kuma muna zamun lafiya da ita yarinyar. Kai rufa min baki mara hankali kai auren fari har kasan abinda ya dace da kaine in ba zamani ba daya kawo mu irin haka. Ya dan yi dariya cikin dauriya yace Amma ke nan kin san shekara nawa nake nema a yanzu ki duba inda yar maimuna takai fa ga girma da ace nima macd ce da yanzu kin san na haifi sa,anta ko ? Kai rufa min baki don Allah shekarun ka na banza da bai amfana maka da komai ba sai shiriri ta ina kai ina kwaso muna kafira cikin zuri,ata ? Haka dai shigowan nasa ya kasance tsakanin shi da Amma don ya fuskaci har tsohuwar take kufule dashi a lokacin duk kan dalilin auren nasa dai. Mikewa yayi yana shirin fita sai ta kalle shi tace zaka fita bakaci komai a cikin ka ba ba yanzu ka dawo daga tafiya ba ? Sai da ya mike da kyau yana gyara rigar sa data danyi sequzin yace bana jin yunwa zan fita akwai inda zanje idan na fito wurin mama don ban shiga mun gaisa ba ko dasu. Allah ya tsare tace a daidai lokacin da ya fara tafiya do barin part din yana jin cikin ranshi babu dadi a lokacin. Ta rakashi da kallon tausayi don tasan duk abinda yakeyi a cikin dauriya yake yin shi a daidai lokacin hjy maryam ta sawo kai zuwa part din Amma din . Nan suka hade hanya da shi sama sama suka gaisa da ita ba tare da ta furta mai komai ba ya wuce abin shi. A falon hjy jummai ya samay su zaune da yan uwanshi dake cin abinci suna ganin shi suka tare shi da murnan ganin ya dawo lafiya. Hjy jummai dai tana zaune kamad bata ganshi ba ya shigo su salma dake dakin su sukaji muryan shi sai gasu sun fito da murna suna taron shi. Wani tsawa ta bugawa yaran a take suka sha jinin jikin su a aurin da suke bata bari sin karasa surin shi ba. A hankali ya daga yana kallon mahaifiyar tasu dmamaki don sanin halinta dayayi akansu sai yau yaga sabanin hakan gare shi. Haka yasan ba karamin kuskure ya tafka a rayuwan shi ba na rashin sanar masu da zancen tun farkon faruwan almarin ya kamata ace ko bai fadawa kowa ba ya sanar da mahaifiyar tashi gaskiyar alamarin. Habbin ne ya aje spoom din hannun shi a hankali yana fadin why mama zaki hanasu zuwa gare shi ? Idan kin mashi haka da wani zai ji da fushin ko dana daddy da Amma ko da namu da kike kokarin hana mu zuwa gare shi ? Habbib ni kake son yiwa nasiha akan wanda ya maidani ba kowa ba a wurin shi har sanadiyar laifin shi yana barazana da aure na da yafi shekara nawa da kulluwa da Alh hakan bai taba faruwa a tsakanin ba sai akan wanan maganan. Kasa ci gaba tayi da maganan da takeyi saboda kukan dayazo mata a lokacin yaci karfin zuciyar ta. Bata taba tunanen irin ranan nan agaresu ba dukkan su gani haka a sanyaye ya mike yana fadin mamakiyi hakkuri idan wanan abin ya bata maki rai don Allah ? Habbib ne ya mike yana magana a cikin harshen turanci yake fadin bros mu tafi har ta huce don wanan hawayen indan tana ganin ka bai daina fita yanzu. Bai ki ta kanin nasa ba suka fice daga falon sun danyi magana da habbib din ya fita daga gidan sai ga habbib din ya dawo shi kadai yana fadin Aliyu ya taso su fita. Ba bata lokaci ya biyo yayan nasa don shima a rude yake ganin mahaifiyar su tana kuka akan dan uwan nasu. Sun samay shi har ya tayar da mota zai fita suka dakatar dashi komai na rayuwa yayi masa kunci a lokacin. Hakan da suka samay shi ya sun kara tausayawa dan uwan nasu motar suka bude suka shiga suma sai habbib ya kira sunan yayan nasu bros. Umar ya dago kai yana kallon su yace ina ganin wanan case din ya kamata mu hada da baba Nuhu muje muyi masa bayanin komai yadda zai iya fahintar mu. Don yanzu baba Nuhu shi kadai ya ragewa su daddy a matsayin uba da suke jin nauyin shi a garin nan shi kadai zai iya kawo karshen fushin nan da sukeyi haka dakai. Aliyu yace kwarai hakan yayi daidai don tsohon nan kadai zai iya saukar da Daddy a garin nan kaf don suna jin maganan shi sosai. Don ko su baba Bala suna hake dakai da wanan maganan don jiya na samay su da hjy maryam suna magana tana kara zugashi. Suna gani na ita ta bat zancen shiko baba bala yana fada yana fafin su zaka mayar kananan mutane a garin nan ka kwaso masu wata arniya a cikin zuria su ba zasu yarda da wanan shashancin ba. Habbib yace kai ina tsoron wanan matar wallahi a cikin matan daddy kaf don munafukace ta karshe baka lura da irin munafunci da take kawowa mama na maimuna . Sai dai sunyi rashin sa, a koda suka isa gidan kofan gidan a kargamay yake a lokacin har tsohon ya rufe gidan shi ya shige ko. Haka yasa suka juya zuwa gida sai dai umar yana sauke su ya juya don baijin zai iya kwana a gidan mahaifan shi suna cikin fushi dashi haka. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:55 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM RABBANA ATINA FIDDINIYE HASSANATA WA, KINNA AZBAN NAR, , , , , , Ko da na koma part din mu mamu tana kitchen tana hada breakfast don fita nayi zuwa wurin Aisha sai muka tsaya shiririta a can har kaddara rabon mari ya hau kaina. Jin motsina da tayi ta leko daga kitchen tana fadin kina can kin samu gwago kin shagala da zancen abinci ko ? A sanyaye a cikin murya na daya dan danlashe don kukan da nayi nace Amma ce ta tsayar dani can. Tsaye take a gurin frige tana daukan abu jin muryana da tayi hakana yasa ta saurin juyowa tana kallona ganin ta zuba min ido kamar tana nazarina yasa nayi saurin dukar da kaina kasa. Kallon shatin yatsun habbib da ya kwanta a kunci na da suka feto ras a binka da farar fata sai wajen yayi jajir dashi alaman taruwan kwancin jini da shafin hannun shi a kumatun nawa. Sayadi waye mare ki haka har wuri ya nuna tana tambayana fuskanta karara da mamaki ? Na sunkuyar da kaina hawaye na gangarowa a fuskana ban iya buda baki na bata amsa ba haka yasa ta aje kwalban data dauko a fridge a hankali ta tako zuwa wurina. Ta sake tambayana a hasale nace wayayi maki wanan mari haka da sanyin safiyan nan kin kyale ni ? Mamu wanan dayan yayan su salman ne ya mare ni na fada ina karashewa da kuka sosai tace da kikai masa may ya mare ki haka sayadi ? Nayi shiru ina sheshekan kuka a cikin bacin rai ta fara magana wanan wani irin cin fuska ne haka wani irin laifi kika aikata masu mai zafi haka akai maki wanan marin haka har shedan yatsu ya tsaya a fuskanki ? Wallahi wanan karon ba zan yarda ba abinda ma ba zai yuyu ke nan ba ban taba dan kowa a gidan ko harara ba ba zan zauna ana saka min diya a gaba ba. Ta kara tambayana nace may ya hadaki dasu a cikin kuka nake fadin ban san suna tafe ba naci karo da babban su shine gudan ya mareni. Hannuna taja fuuu muka fito daga part din hanyar part din Amma muka nufa sai ga kawu ya fito ranshi a bace daga part din. Yana hango mu yayi saurin karasowa gare mu yana fadin ina zaki da ita ku koma a gabanta ai nayi magana ko baki fada mata bane ya juya saitina yana tambayana niko sai kuka nakeyi sharba. Yanzu Yaya ya dace hakan da sukai mata diba fa shafin hannun shi a jikin ta yadda ya kwanta a fuskanta tana nuna mai don idon ta ya rufe bai taba gani ta haka ba akan diyan ta. Ya dai samu ya lalasheta ta koma dani a ciki tana cika do yasan idan ya barta ba zai ai mai dadi ba ranan. Waye a cikin su ya mareki haka ta tambaye ni nace wanan dayan ne wanda baya dariya a cikin su tace habbib ke nan ko shine mai bakin ran tsiya. Gaskiya ba zan laminci hakan ba dole na kwata don wahalan dana kwana biyu ban shiga ba. Wanan abin yaiwa mamu zafi sosai sai da ta samu Amma sukai magana ta kara bata hakkuri. A kasuwa Alh ke fadawa Ahmed abinda habbib yayi min tare da abinda umar ya aikato a can ya jajanta wa Alh kan hakan. Sai dai hankalin shi yana gun maganan marin da akai min din wanda yake jin zafi a ranshi haka ya samu daman sulalowa daga kasuwa zuwa gidan kawun nawa. Ya iso gidan namu direct part din mu ya nufo ya tsaya daga kofa yana sallama kani yazo yana dubawa sai ya dane mai jiki. Tura yaron yayi, yayi mai iso gurin mamu yaron ya juya da gudu sai a wurin Ahmed kawai suke jin dan sanyi a gidan idan ya shigo. Mamu tace dashi ya shigo falon lokacin tana kokarin saka hijjab din ta a jikin ta ya karaso yana zama yake gaida ita ta amsa har lokacin yanayin ta ba dadi kallo daya zakai mata kagane hakan. Bayan sun gama gaisawa yake fadin hajiya ashe abinda ya faru ke nan dazun Alh ke fada min a kasuwa maynene ya hadasu haka dasu har ya iya marin ta ? Malam Ahmed ke nan a gidan nan ai ba sai munyi wani abuba zasuyi iya muna haka tunda so suke su rabamu da gidan ko ta halin kaka. Idan ba haka ba daga bangaza kawai sai wanan irin marin Ahmed yace shike ban mamaki ai Don ran Alh ya baci sosai yau shike fada min abin ya taba mai zuciya sosai wallahi. A to ni dai na fada mai abin ya isheni wallahi dan magana kadan sai a kama min yara da duka sai sun kwata ciwo don ha,inci. Yace ina fatiman take ne ta nuna da hannu tana fadin tana nan daki tun da ta shiga ta kwanta kila barci takeyi. Kai shima dai yasan bai kyauta ba tunda yarinyar nan dai batayi mai komai ba idan dai ba dama suna hake da ita bace din don hjy bata da dama yanzu haka wani abin ta fada masu wanda zai sa suki yarinyar nan a ransu don halinta ne na sani. Mamu tace idan ma ta fada masu ai kansu zai kare sheri dai kare ne maishi yaka bi tsakanina da kowa a gidan nan sai fatan alheri. Gidan dai take son mu bar mata kota halin kaka shine take kokarin daga min hankali dana yayana. Dan dariya mara sauti yayi yace yanzu kan ai sai dai ita tabar gidan idan batayi hankali ba don kiris ya rage tsakaninta da Alh yanzu. Itako abinda Umar ya aikata bai isheta tunane ba gaba dayan su basu da tunane nake gani mamu tace abinda nake son ka gane ke nan. Ace kishi har da yara a ciki yaran ma maza da suka san ciwon kansu haka ai ko kaga akwai aiki a gaba ke nan. Ta kalli fauziya tana fadin jeki kira masa anty ku kice ga yayan ku nan Ahmed ya zo dubata. Fauziya ta mike da sauri zuwa dakin mu ta samu ina barci ta shiga tayar dani daga barcin na bude ido take fada min anty yaya Ahmed yazo gaida ke wai inji mamu. Sai da nan danyi mintu a kwance na dago da kyat daga saman gadon na sauko kasa na dauki dan gyalena dake gefe na yafa a kaina. Na fito falon yana zaune yana fuskantar dakin dana ke fitowa daga ciki a ranshi ya ke fadin tsarki ya tabbata ga mahaliccin mu Allah daya halita wanan yarinyar. Yaga na kara cika nayi mai kyau a fuskan shi na kara cika nayi bul bul dani fatan jikina ya goge yanzu yayi kyau sosai ba kamar yadda nazo gatin ba. Na koma kamar a tabani jini ya fito saboda gogewan da fatana yayi ga zanen lalen da akai min na sallah wanda ya kara kawata kafana da hannuwa ya fito radau dashi. Ina dago kai muka hada ido dashi nayi saurin kwantar da kaina kasa na karaso kujeran da mamu ke zaune na tsaya daga bayan ta ina gaida shi. Gaba daya yaga na sauya mai a yadda ya sanni dana zo tunanen shi yana neman kwancewa a cikin dan kankanin lokaci. Da kyat ya iya saita kanshi ya karba min gaisuwan da nake mashi yace Fatima yanzu Alh ke fada min kasuwa abinda ya faru dazun. Ba ina fada maku tunda suka zo gatin nan kuyi taka tsamtsan dasu ba na dan bata fuskana nace ban san suna tafe bani Aisha ce ta biyo ni da gudu sai naci karo dashi. Yace barsu da Allah ai suma suna da kanne mata ko ina dai bai maki ciwo yanzu ko nace kaina dai ke ciwo sai fuskata dayayi min nauyi dazun yanzun kuma naji ya rage dana tashi. Duk abinda muke mamu tana zaune tana jin mu sai can tace banace kisha magani ba kafin ki kwanta. Na sha na bata amsa a takaice a daidai lokacin da Ahmed ke dagawa yana fadin zan koma hjy Allah ya tsare gaba adaiyi hakkuri don Allah watarana sai labari insha Allahu. Tace nagode Ahmed sannu da kokari yace haba ba komai wallahi danaji ne nace ai barin zo in duba ta idan ba matsala. Yana fadin haka ya fita har yakai kofa ya kira fauziya yana fadin kuzo in baku goron sallah ku ko ban samu shigowa na baku ba yaran suka bishi sai gasu sun dawo da kudi zaikai dubu goma a hannun su suna murna ya bamu don yace su raba har dani. Sunyi sa, a sun sami tsohon a gida bayan karfe biyar da suka koma gidan akai masu sallama dashi jin sune yace su shigo falon shi da yake zaune. Ya tare su da fadin ko dai kunyi batan hanya ne don naji kuna garin nan tun kan ayi sallah sai yau kuka tuna da dan tsoho. A cikin jin kunyar abinda tsohon ya fadi suka karasa shigowa suna neman wuri a nan take ya umurci wani jikanshi da ya shiga ya kawo masu abin motsa baki a cikin gida. Bayan sun gaisa ne yake tambayan su bayan rabo suka dai dan taba hira sai dai basuci komai daga abinda aka kawo masu din ba. Can Umar yace cikin girmamawa malam wurin ka muka zo neman taimakon ka don Allah ka shiga cikin wanan maganan don kai kadai ne yanzu muke ganin zaka iya shawo muna kan mahaifin daga fushin da yake yi dani . Subbahanallahi may ya faru yake fushi dakai kuma daga dawowan ka kasan nan shi ba abin alfahari bane ganin haka. Bakuji irin dadin da naji ba lokacin da kuka shigo falon nan yanzu kun zamay muna abin alfahari a cikin zuria . Aliyu yace haka ne malam sai dai yayan mu yayi kuskuren yin aure a can ba tare da sanin iyayyen mu ba shine tashin hankalin dake tsakanin su da Abban mu yanzu. Nan dai Aliyu din ya kora ma tsohon duk bayanin komai da yadda maganan ta fara har fushin da mahaifan su keyi dashi umar din. Subbahanallahi tsohon yace yana girgiza kai tare da fadin innalillahi yaya hakan ya faru kaiko abokina da ilimin ka da tarbiyan ka zaka aikata muna hakan. A sanyaye Umar yace kaddarace malam kasan mutum duka bai wuce kaddaran shi a rayuwan shi. Malam Nuhu ya jinjina ganshi kafin ya fara karanto masu ayan Allah yana fassara masu ayoyin alkur,ani mai girma wanda yake magana akan hakkin iyayye da sharian aure. Bayan ya gama masu bayani yaga yadda jikin su yayi laushi sai ya fara nuna ma Umar kuskuren shi na rashin daukan iyayye da muhinmanci dayayi . Yace yanzu barin ji inda mahaifin naku yake sai dai ita Amamatan wani mataki ta dauka akan wanan magana sai umar yace . Itama dai ta dauki zafi da farko amma yanzu naga ta sauko sosai ba kamar farko ba kawu ya dauki wayan suka gaisa yake tambayan shi yana ina ne ? Yace yana kasuwa yanzu zai koma gida yamma tayi yace a dawo lafiya yace dasu barin shiga ciki in fito mu tafi gidan naku ayishi ya kare can. Sun yi daidai da kawu ya dawo daga kasuwa ya shiga part din mahaifiyar shi suna gaisawa da ita sai ya tura a kira hjy jummai ta samay su a part din Amma don da ita za ai maganan Suna zaune sai ganin su sukayi sun shigo gaba dayan su har da kanin mahaifin su kawu din malam nuhu. A cikin girmamawa Amma na fadin ina kafito da wayan nan gardawan a bayan ka yace to gasu nan dai waya sani ko satoni sukayi. Aka sa dariya banda su a falon su umar suka zube suna gaida mahaufin nasu yayi kamar bai jisu ba. Ganin haka malam Nuhu yace bakaji yaran na gaida kai bane Sani ashe abinda naji gaskiyane ba karya ba. Amma kina cikin gidan nan kika bari abubuwa suna gudana haka aure ne dai yaron na ya rigada ya aikata son ranshi sai ayi hakkuri. Na fada masa ya aikata babban kuskure to amma abin lura a nan shifa yaron nan dan Adam ne shima kuma kowan ku nan yasan dan adam ajizine bai wuce yin kuskure a rayuwa. Sai lonacin kawu yai magana yace baba indai maganan yaron nan ne na sallama da zancen shi a raina. Yaje yayi duk abinda yaga dama a duniya tunda har yake ganin shi ya isa mu bamu isa dashi ba sai dai ya sani duniya ta isa da kowa. Malam Nuhu yayi murmshi gami da gyara zaman shi yace a daiyi hakkuri tunda ya gane kuskuren shi yanzu. Ubangijin daya hallice mu ma muna masa laifi idan mun rokeshi ya yafe muna don kai zakace ka yafe shi ma, ana yaje yabi duniya ko ? Kawu Yace baba haka naga ya zabawa ranshi kamar umar yace ni zai tozarta a garin nan a idon jamma,a. Aure ne fa sani ba wani aikin shedan ya aikata ba a can sai dai matsalan yarinyar a hallul kitabice ita ko shine zafin ku dashi. Amma duk da haka idan kukai duba da ubangiji bai hana hakan ba sai a sasauto mashi hakana amma kai ka hau mahaifiyar shi ta hau har ke Amamatan kin hau dashi da sauran iyayyen su. Yaya kuke ganin karshe zaiyi ai sai ya koma can wurin matar tashi da yan uwanta su karbe shi tunda dama haka suke so. Nan dai tsohon yaci gaba da lurar dasu duka bangaren biyu kuskuren su ya kare da yiwa iyayyen nasu nasihan suyi hakkri an san ya tabaka kuskure sosai. Bai kyauta ba inda ya tare su yin magana ya umurci umar da ya kara neman yafiyan iyayyen shi . Idanu shi suna zubar da hawaye ya mike zuwa wurin ko wanen su yana neman yafiyan su. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:55 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR, RAHHAMANIN RAHIM, , , , , Haka ranan suka kwana rayukan su babu dadi a cikin sa tun dai na uban aikin umar wanda shine ya dauko maganan. Washe gari haka suka daka sakko zuwa gidan tsoho inda a nan ma suka samu yayi sammako zuwa daurin aure garin zaria. Haka suka dawo da haushi a zukatan su na rashin samun tsohon a gidan rayukan su har lokacin babu dadi a cikin ta gashi suma hjy jummai duk ta hade dasu tana fushi. A guje na fito daga part din Amma inda muka gama gardaman littafi da Aisha ta biyo ni aguje ina dariyan kwace littafin a hannun ta. Ban san da mutane ba tafe mukaci wani uban karo dana gaban sai da ya dan tangaleni danayi baya zan fadi ga zafin da naji kamar zan kare. Wani tsawa Habbib dake bayan shi ya buga min don shi ko isar shi kallo ban yi ba yana kamani banje kasa ba ya jaye daga gurin. Cikin wani irin tsawa habbib din ya ke fadin ke wace irin makaciya ce a daidai lokacin da hannun shi ya sauka a fuskana. Yaci gaba da fadin ke makauniyace baki ganin mutane a tafe ne da zaki fito haka kamar gidan ub, , , , , Kai kai kai haba habbib why da zaka mare ta haka da safen nan kan dan wanan abin haba hakan bai dace ba kana saurin dukan kannen ka mata. Aisha da ta sandare wuri daya don jin zafin marin kamar itace aka mara ta juya da sauri ciki tana fadawa Amma sai ga Amma a fusace ta fito a daidai lokacin da yayan nasa ke masa fada. Kai mara mutunci mai wanan yar marainiyar Allah tai maka ka mare ta haka da safen nan don radgin imani da tausayi ? A hasalen ta juya gurina tana fadin mai kikai masa ya mare ki haka A ruwa cikin rawan murya da idanuwa da suka kawo hawaye nace ban san suna tafe ba na bangaji wanan yayan nasu shine ya mare ni. Amma habibu ka cika mara imani da tausayi wai ma kai ta bangaza ko shiyan kane nan in sani tana tambayan shi cikin tsatsare shi da idanuwa irin na tsofin da ransu ya gama baci sosai. Yace a a ke ta bangaza ita bata ganine da zata fito a guje ko tsaban rashin kunya da samun wuri ne haka ? A gidan ka ta samu wuri mara ta ido nace ko nan din gidan ka ne yau zaka san ka mare ta a gidan nan kuwa yace oho ko zaki rama mata ne don dama ance kece ke daure mata gindi tanawa mutane iskancin dataga dama a gida. Umar da ya gaji da zancen su yace haba ya isa haka Amma ke kuma ki kula idan kina tafiya da yanzu kin fadi kinji ciwo fa ? Amma na fadin a a haa wanda dai ya isa dakai zan sa ya rama mata tunda kai kana ganin kafi karfin mu sai jin muryan Alh mukayi yana fadin hajiya lafiya kike fada haka da safen nan ? Gaba daya suka juya wurin da sukaji muryan suna zubewa don gaishe shi Amma na fadin wallahi wanan mai zubin arna ne ya wanke yarinyar nan da mari tunda safen nan. Subbahanallahi mari kuma yana yi yana kallona da mamaki karara a fuskan shi ya sake mai mai ta mari akan wani dalili ka mari yar mutane haka ? Ga shafin hannun ka nan radau a fuskan ta har lokacin hawaye yana zubo min a fuskana iskancin naku da kuka koyo har yakai ku dakan min diya a gidana ? Fada mashi dai don ni ya tsaya yana min iya shegen daya koya a can don shi bai ganin kowa da ta ido a gidan nan sai daukan kan tsiya da girman kai karshe dai nasan wata yarniyar kai ma zaka kwaso dan wanan halin naka sai su. Haba Amma kin cika mutane da rigima don Allah baki jin daddy yana masa magana ne wai Aliyu yace haka a hasale ta mika mai dakuwa da yatsun hannun ta tana fadin kaci gidan ku a zulunci yarinya ka hana ayi magana. Don Allah daddy ayi hakkuri nayi masa fada ai, , , , hannu ya daga wa umar din kafin ya fara fadin nayi nadaman tura ku waje karatu a rayuwata don baku koyo alheri ba can. Na dan gega kawu dake tsaye zan wuce na kalli umar ina fadin ya umar kayi hakkuri don Allah ban san kuna tafe ba ba da gagan na buge ka ba . Na wuce naji Amma tana fadin kaji ba nace ko kaji yar arziki ka doketa ta baku hakkuri yanzu bakaji kunyar kanka ba don Allah. Kamar ka ka mari wanan yarinyar aiko baka san inda ta fito ba taci ragowan matsayin ta na ya mace a gurin ka da badon naji dan uwanka na ma fada ba da sai na rama ma wanan yarinyar marin ta wurun nan. Ya dago jajjayen idon shi yana kallon ta yace ki rama mana udan kin isa ganin daddy ya kallo shi yasa yayi saurin sauke kanshi da sauri Alh yace ina yanzu idan kuna da hankali kun banbance tarbiyan kasan nan da wanda kuka koyo a can to ba agida za ai wanan shashancin ba. Uwar yarinyar nan bata kasa daku har yau akan zancen wanan babu irin magiyar da batayi min in yi hakkuri ina facale ta gefe. Amma ku idon ku ya rufe wurin bakin kishi da uwar ku ta cusa maku a zukatan ku kuna maza nasan idan nayi kukan safe akan ku itako na marance zatayi don Allah ba azzalumin kowa bane. Amma da taga fadan yai yawa yana so wuce wuri tace ya isa haka ai ya koyi darasi ita ya zalinta amma ta basu hakkuri ko wanan ya ishe su nadama . Banga abinda yar nan ta tsare maku a gidan nan ba ko bamu san A ruwa ba yau ai mu masu taimakawa rayuwan tane ko tunda tana bukatan taimako. Hajiya bance wani ya taimaka min cikin rikon yar nan ba tsakani da Allah na dauko ta hannun iyayyen ta don in tallafawa rayuwan ta don haka ba zan lamunci wani iya shege a gidana ba akan kowa. Yana fadin haka ya kai kasa daga inda yake yana fadin hajiya mun tashi lafiya duk sai sukaji wani iri matsayin mahaifi su da shekarun shi bai hana shi neman albarka a wurin mahaifiyar shi da Allah ya bar masa raye ba. Duk sai sukaji sun muzanta a gabab mahaifin nasu duk da dai suna iya kokari su wurin ganin sun kwatata abinda suke gani ga iyayyen nasu wurin girmamawa. Hakan bai isa shesu mamaki sai jin yadda uwar kewa danta fatan alheri da gamawa da duniya lafiya sabanun nasu uwar da suna gaishe ta tana masu zancen su bata wani abin. Nan mahaifin su ya juya ya wuce bai kara bi ta kan su ba bayan sun gama gaisawa da mahaifiyar shi din ta juya wurin su tana fadin kun gani. Har yanzu mahaifin ku fushi yake da dan uwan ku kai kuma kazo ka kara dada wani zancen dukan yarinya a kai. Aliyu yace a dai ba daddy hakkuri Amma don in kiyi mai magana zai ji amma wanan fushin da sukeyi da bros yayi yawa wallahi. Kai rufe min baki mara kunya da zai aikata hakan ya manta yana da magabata a gida ko may ko shi yanzu da ya mari yar mutane wani ya turo shi ya duke ta haka. Ko yaushe kuna kokarin tozarta yar mutane don kawai Allah yayi zaman ta a gidan ku komay idan wani na waje yai mata haka ashe dadi zakaji. Kuyi hakkuri Amma don Allah umar yace ni kaina banji dadin marin da yaiwa yarinyar ba ai kinji ina masa fadan. A a aini ya wuce a wurina sai dai ku kula don ku maza ne ba a san diya maza da shiga kishin mata ba balle ku da ilimin ku da shekarun mai zaisa ku kama amfani da abinda baku gani ba da idanun ku. Idan ma an fada maku wani hali nata na daban ne ai sai ku natsu ku kwantar da hankalin ku ku karanci halin ta ko ? Yanzu kuko wanan abin da tayi maku ai ya isheku nadama kai ka mare ta ita kuma ta baku hakkuri da hawayen ta. Duk shiru sukayi suna sauraren zancen da Amma ke kora masu din wanda duk gaskiyane zalla a cikin sa ta fada don dai ba zasuce ga rashin kunyar da yarinyar tayiwa dayan su ba. Daga umar har habbib ido suka kurawa Amma dake magana sai dai a ransu tunane sukeyi basu taba ganin an saka su gaba irin wanan lokacin ba a rayuwan su. Don Amma bata da zafi iri hakasin san ran tsohuwar a bace yake dasu sosai sai suks kalman da zasu bata hakkuri dashi. Wayan shi dake cikin aljihun sa ya dauki ruri a lokaci daya haka yasa hannu yana lalaban wayan don ganin kiran nasa. My wife ganin haka yasa ya juya da sauri dan nesa da wurin da suke yana daukan wayan tare da fadin. Hy merry how are you dear ? Omar ka tafi ka barmu baka kulamu all this days why Omar ta karasa cikin muryan kuka tana fadin dama abinda nake gudu ke nan gashi tun yanzu alama ya nuna ka daina son mu. Cikin karfin hali ya hade wani miyau mai daci daya taru a bakin shi yace . Why zan daina son ku merry ba wai na daina son ku bane kwana biyun nan muna case da parents dina ne akan matsalan mu. Kema kin san kina makale a zuciyata ko wani lokaci lokacin zama ne ban samu ga aiyukan da nake a nan yanzu aikin yake tafiya da na shigo kasan. Merry ta saki ajiyan zuciya tace na dauka ko iyayyen ka sunyi nasaran raba tsakanin mu ne ai yace saboda may zasuyi muna haka ai suna da understand sosai. Ya kawar da maganan don baison dongon zance saboda yanayin da yake ciki na bacin rai yace ya baby mu ? Ta dan shafa ciki tana fadin yana lafiya dear yaushene zaka dawo gare mu muna cikin kewan ka daga ni har baby din mu. Yace very soon zatayi magana ya katse ta yana fadin dama ina son in kiraki don jin inda maganan mu ya kwana dake ? Tace maganar may ke nan fa dear ta tambaya da son ji maganar don ta manta da zancen wani magana da sukayi dashi. Yace ya mukayi dake akan karban musuluncin ki don baby mu ya taso a cikin addini daya da iyayyen shi kada mu raba mai hankali. Tace Oh i remember wanan zancen bata waya bace kabari zan shigo Nageria nima sai muyi maganan a tsanake. Yace cikin murmushin kasaita merry you think iam jork wanan karon da gaskiya nake zance tace ai kasan ina son ka zan iya yin komai saboda kai. Mu dai ka kula muna da kanka don kasan kaine rayuwar mu ba zan iya rayuwa idan babu kai a tare dani ba. Wanan karon murmushin ya kara sakewa a tausashe yana fadin kada ki damu kin san ai you are The best baki da damuwa da Omar dinki. Wani irin son shi taji ya kara tsaya mata a zuciya tana lumshe tare da tunanen ita kan tayi sa, an miji shiyasa take kokarin jaye shi daga yan uwan shi baki daya su zauna su ka dai sai yayan su idan sun tara nan gaba. Idan da son samu a kokarinta na juyeshi ya koma akidar ta yana nan mata daram a cikin zuciyan ta ita da iyayyen ta suka san shirin da suke yi akanshi. A bangaren Umar kuma ya gane manufanta sarai na son dauke mai hankali ga komai suna gama wayan ya kagu dama ta katse layin. Bai koma wurin da yan uwanshi suke ba ya nufi hanyar part din mahaifiyar su kai tsaye suna ganin haka suka mara mai baya dama sun gaji da badakalar da sukeyi da tsohuwar a nan. Kusan a tare suka shiga falon hjy jummai tana zaune tayi tagumi da hannu daya tana tunane suka shigo. Gaba dayan su suka tsurawa mahaifiyar tasu ido do basu saba ganin ta a cikin wanan yanayi ba a baya tana da kokarin jajircewa abu idan yazo mata. A cikin kwantar da murya Umar ya fara mata magana yace mama ki kwantar da hankalin ki kada wanan abin ya tayar maki da hankali haka don Allah. Mama nine fa kin sanni kin san halina akan abinda zai iya da wanda ba zan iya ba fushin ki gare ni wani komawa baya ne a gurina yanzu. Kanta ta daga sama sai ga hawaye na zuba daga fuskanta tana kallon sama kamar wace ke tunane. A hankali ya bar gurin da yake ya tako zuwa gare ta ya zauna daf da kafanta yana fadin na tuba mamaki yafe min don Allah . Mama idan kinyi fushi dani haka ina zan saka kaina ga daddy shima ya dauki zafi dani na rasa abinda ke mun dadi a garin nan. Sai lokacin hjy jummai taja wani irin ajiyan zuciya tace fushi babawo dole muyi dakai yanzu ina kake son nakai wanan abin kunyan da komawa bayan daka ja min a garin nan ? Idan maganan nan ta fashe da wani ido zan kalli mutane dashi a matsayina na mahaifiyar ka ke nsn bamu baka ingantattacen tarbiyan daya dace da kaiba ke nan. Mama nagane kuskure na yanzu don Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru tace hakkurina daya ne babawo. Gara tun wuri kayi hakkuri da wanan yarniyar ka cire ta a ranka kafitar da zancen kun taba zama a zuciyar ka. Ya dago kai a raunane yana kallon ta tare da fadin mama idan nayiwa merry haka ban kyauta mata ba tana fa dauke da cikina yanzu haka. Babawo idan kana son kanka da lafiya karabu da ita tun kan Alh ya yanke hukucin mai tsauri a kan mu baki daya don babban aiki ka daukowa kan ka nan gaba. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:57 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA HAIYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS ALLAH πŸ‘ Kawu ya maida duban shi ga baban nasa yace shike nan baba na yafe masa tunda kazo da kanka sai dai nima ina da uzurina akan hakan daya aikata bada sanina ba. Gaba daya kowa ya kallo kawu da kyau a falon ana sauraren irin hukuncin da zai yankewa umar din. Malam Nuhu yace kana da daman yin ko maynene a kansa matukar dai zaka yafe masa har cikin ranka idan kuma naka uxurin bai sabawa shari,a ba. Kawu ya dan girgiza kai yace har yanzu akan koyi da addinin da kuka tarbiyarta dani nake baba. Sai tsohon ya kada kai alaman gamsuwa da maganan dan nasa yace kai muke saurare dana. Kawu yace ina son duk wanda ke falon nan ya sheda kai balarabe da sulaiman ku sani ko bayan raina idan na, idan ba ayi abinda na bada umurni ba ban yafe maku ba. Gaba daya sukace subbahanallahi har abin yakai can yaya wanan wani irin hukunci ne mai tsauri kake shirin yankewa akan yaron nan ? Kawu ya dan yi murmushi yace bashi kadai ba baba dukkan su ne abin ya shafa tunda haka suke so gareni. Hakan kuma naga yafi dacewa ga wanda bai dauki iyayyen shi da zumunci da muhinmanci ba a rayuwan shi. Jin yace dukkan su yasa gaba dayan su har mahaifiyar su suka kara mayar da hankalinsu wurin shi sosai. Yace ke kuma jummai kafin in fadi hukuncin nawa ina son kowa nan ya sheda cewa duk kika kawo min wani izgili a cikin magana ta zai iya kaimu ga sakin auren ki wallahi. Gaba daya zufa ya gama jikasu a inda suke zaune don fargaba da rikicin da suke fuskanta daga mahaifin nasu ga tsatsauran kalamin dayayi akan mahaifiyar su kuma. Bai damuba da abinda sauran yan uwan shi ke fadi sai takardan da ya ciro daga Aljihun shi yayi rubuto a cikin sa kamar haka. Rukkaiya, Aisha, fatima a ruwa. Ya dun kule su wuri daya ya watsa a tsakiyan falon tare da duban yayan nada yace kowan ku ya zabi daya duk wanda mutum ya dauka shine zabinsa a gurin Allah . Allah kuma ya albarkaci auren har zurian mutum yasa masa albarka da gamawa da duniya lafiya ga baki dayan ku yana fadin haka ya juya yana gyara zaman shi a hankali. Duk falon akai tsit ba wanda ya iya motsawa a cikin su sai gumin dake fetso masu a lokacin duk sun fita a cikin hayacin su ga baki dayan su. Kallon kallo aka fara a tsakanin su kowa nawa dan uwa alaman ya fara dauka sai dai dukan su sun kasa. Hjy jummai da ta kusa fashewa a zaune tace baba nima ina da magana don bashi kadai ke da hakki akan yara nan ba nima ina da hakkina don lokacin da nayi goyon abina nashi damu idone kawai. Subbahanallahi jummai wanan wani irin magana ne kike sakewa haka da girman ki da shekarun ki kawu dai murmushi yayi yana kallon ta. Tace dole inyi magana don nima ina da hakki sosai a kansu ya manta lokacin da nake wahala da abina lokacin da kowa ya saka min ido dasu sai yanzu ne zai kawo min wanan sharadin nasa. Mama please umar yace yana hade hannuwan sa alaman yana rokonta tayi shiru don Allah sai kawu yace nina gama yanke hukunci na akan su don yayana ne idan kuma suna da wani uban bani ba yau ta fada min. Ku bar wanan zancen don Allah ayi abinda ke gaban mu mama hadiye dake gefe ta fadi cikin damuwa da abinda ke wakana a falon. Habbib ne ne cikin zafin rai ya mika hannu ya dauki takardan daya ya rike a hannun shi ganin haka shima Aliyu ya dauki nasa ya rike a hannun shi shima sai Umar din daya dauki na karshe a kasalance shima ya jinke yana runtse idanuwan shi a hankali. Baba Nuhu yace bissimillan ku ku bude mana muji abinda kowa ya dauka a cikin ku wanan hukuncin na mahaifin ku yana da kyau matuka don nasa Sani bai aikata abinda bashi ba. A sanyaye kowan su ya fara bude takardan a hankali suna dago kai ga abinda idanuwan su ya gane masu cikin takardan lokaci daya. Banda umar da tunda ya duka bai dago ido ya kalli kowa ba bai ma san a inda yake zaune ba alokacin. Amma dai tayi mutuwar zaune a inda take bata sanda wanan irin hukuncin da dan nata zai dauka ga diyan shi ba da ta dauki mataki tun farko kada ya soma sai dai yanzu bakin alkalami ya bushe ko don ya zantar da abinda yake gani shine mafita a gare shi. Da kyar Amma ta iya budan baki tace sai ku fada muna abinda ke ciki don mu bamu sanda wanan hukuncin nasa ba don baiyi shawara da kowa ba kafin ya yanke. Kawu yace hajiya ki gafarce ni don suma ba shawara suke damu ba idan zasu aikata abinda sukai niyar yi. Tace baka ganin su akwai kurciya a tare dasune yace shiyasa nayi aikin basira a kan su hajiyan mu nima. Kallon umar da kansa ke sunkuye tayi don shine damuwanta tace sadauki may ke a cikin takardan naka kai ? Maimakon ya bata amsa sai ya kara dunkule takardan a hannun shi yana kakaro murmushin dole a fuskanshi kawai. Habbibulah fada muna naka don kai naga namijin gaske ne dama soja kaje da wanan zuciyar taka mara imani kawai. Ya harare ta kawai yana sauke ajiyan zuciya da karfi baba bala yace may ke a takardan naka dana ? Yace wai Rukkaiya balarabe aka rubuta kawai a cikin karfin hali da dakewa yake maganan shi yana kallon kawu bala kai tsaye . Kawu bala ya juya gurin sauran Aliyu shima cikin karfin hali a kasalance yace Aishan hadiye na gani rubuce. Kai fa baba na malam Nuhu ya tambaye shi kai ya dago a hankali ya kalli tsohon tare da nuna mai takardan hannun shi ba tare daya furta komai ba. Sai Aliyu dake kusa dashi ne ya yi saurin karba yana fadin Fatima A ruwa. Ba umar ba duk wanda ke falon Amma a lokacin sai da ya kalli inda kawu yake zaune da sauri yayin da hjy jummai ta mike tana fadin wallahi ban yarda da wanan hadin in har zan yarda dana kowa banda wanan hadin. Ina sam wallahi ba acikin jini ba wallahi kowa ido ya zuba mata da gani kasan bata a cikin hayacin ta sai malam Nuhu ne ke kokarin fadin haba hjy ki kwantar da hankalin ki kina sane da irin hukucin da Sani ya dora maki a wanan maganan . Da sauri Umar yace mama please ki bar zancen nan a haka Allah yasa haka yafi muna alheri nasan nayi kuskure ina mai kara rokon ku ku yafe min don Allah don ni na jawo maku wanan rigima don Allah ku yafe mun. Yana fadin haka ya mike zai fita malam Nuhu yace dashi dawo ka zauna babana bamu gama da ku ba ai don bai gama bayanin shi akan takardun da kuka dauka. A sanyaye ya dawo ya zauna inda ya tashi da farko ya dukar da kanshi kasa bai san inda yake ba a lokacin sai tunanen da yake a cikin ranshi. Yana raya waye fatima a ruwa waye ita da har daddy ya yanke wanan hukuncin da ita gashi yaji mama na fadin ko ta yarda da na kowa bata yarda da nasa hadin ba. Aruwa ya maimaita sunan a zuciyar shi da sauri ya dago kai yana dan duban kowa a falon don tuna mai sunan da yayi cikin gidan. Babana yaya naga kamar kuma kana da magana a bakin ka da sauri ya dan dukar da kanshi kasa tare da fadin ba komai. Alh sani malam Nuhu ya dan kalla yace da sauran bayani ke nan ko ka gama hukuncin naka ? Kawu ya dan duka a cikin ladabi ga tsohon yace baba sauran bayani shine sai mun zauna da yan uwana mun tsayar da magana yaushe ya kamata a daura auren ? A lokacin kuma na samu iyayyen ita fatima nayi masu magana zuwa lokacin da yaran zasu kare karatun su sai ai bukin gaba daya. Idan kuma ta Allah ta kasance a gare ni ga yan uwana nan su sheda ko bayan raina idan ba , ayi abinda nabar wasiya ba ban yafe ma duk wanda ya daga zance na ba ni shine bayani na yanzu. Malam Nuhu yace alhamdullahi duk kowa nan yaji bayanin dan uwan ku akan yayan ku sai dai kafin in tashi zanso nima inji yaran daga inda suke. Kawu yace ba wasu yara bane na waje dukkan su yaran gidane babu bare a cikin su fadin haka da kawu yayi yasa hjy da yaran ta kallo shi a lokaci daya. Yace ta wajen shi habbib yar wurin balarabe ne gashi nan sai yar gurin hadiya gata da Aliyu ya dauka dayan kuma wanan yarinyar ne da nake riko yar wurin Maimuna yar mutanen bauchi dake nan gidan. Kai daga malam Nuhu har kawu balarabe suka girgiza don jin irin danyen hukuncin da ya yake ga kuma sharadin daya kidanya masu akai. Amma dake zaune wani irin farin ciki take jin ya lulube gaba daya don wanan abin yai mata dadi sosai a ranta. Malam Nuhu yace Alhamdullahi yanzun abinda ya rage ina son tsakanin ku da maidakin ka ku sulhunta junan ku ku yafe ma juna a zauna lafiya a tsakanin ku. Don kwanciyan hankalin ku a yanzu shine fatin cikin yayan ku da gaba daya family mu. Kawu Sani yace ni ban rike ta ba muddin ana son a zauna lafiya kada wanda ya sabawa maganata don haka a kiyayye gaba. Zuciyar hjy jummai data kawo iya wuya tace baba ni sam ban yarda da zancen hada zuria da maimuna ba da Alh yayi mun . Yarinyat nan fa yar agolan gidan nan ce marasa asali da rashin tarbiyan tazo muna sai lokacin Amma ta kara magana a wurin tace. Haba Jummai idan hakali ya bace hankali ke nemo shi don haka kada kiwa yar nan sheri ki masu fatan alheri ga abin nan da aka hada. Ta kai iya kololowa wurin sukuwa nan ta botse tana fadin ita saman kawu bai mata adaLci a nan. Taro dai ya watse da addua bayan sun samu sun lalabata tabar gurin hankali a tashe kowa ya kama gaban shi bayan fitan yaran suka kara tautaunawa akan matsalan za a bar zancen iyasu yasu yasun su har lokaci yakai na buki. Daga uwar har yaran nata da suka biyo ta daki banda umar da kai tsaye fita yayi daga gidan baki daya don yana son ya kadaice a lokacin. Suna shiga haka suka koma kamar mahaukata shi habbib nashi ya kaiwa kujaran da yake tsaye a gaban shi. Aliyu ko tunda ya zauna ya dafe kai bai dago ba har tsawon wani lokaci hjy tun da take daga ita har su basu taba shiga irin wanan halin ba. Kuma hakan ya faru ne sakamakon irin hukuncin da kawu din ya yankewa yaran nashi suna ganin ha,incin akai masu. Ganin habbib zaiwa kansa illa tace ya zauna su neme mafita su dan bata time tasan abinda zatayi nan gaba kan maganan. Hanyar fita daga falon habbib ya nufa uwar ta kalloshi da sauri tana fadin ina zaka kuma ka zauna mana muyi magana ina shi yayan naku ya tafi ? Hannu habbib ya iya daga mata kawai ya fice ta bishi da kallon tausayi tana kada kai cikin takaici. Tasan lalai yau ran yan mazan nata ya baci ga ba dayan su su uku ta rasa wanda zata fara dashi don ita duk zabin da akai masu din bai gamshe ta ba ga baki dayan su. Can suna zaune shiru ta sake dago kai ta dan kalli Aliyu tana fadin ina yayan ku ya tafi ? Kasa bata amsa yayi da magana sai inkiyan da yai mata da hannun shi na yana waje. Can shima ya mike yana fadin wallahi mama imposible ina imposible yana mai girgiza kanshi hadi da fara tafiya zai bar falon shi ma. Ganin yaran zasu salwance mata yasa ta daga waya ta kira sisters din ta da suke uwa daya uba daya su biyu tana fadin suzo gidan ta akwai matsala babba dasu. Tana zaune zurun ita daya a shiyanta don su salma sun fita zuwa islamiya tun four na yamma. Shigowan yan uwan nata a gigice yasa ta dan jin sanyi dukkan su suna a rude suke tambayan may ke faruwa ne wai ta kirasu haka don har magariba yayi a lokacin. Dama na fada maku akwai asiri yanzu tsakanina da Alh har diyana asiri ya shafe su a gidan nan. Wai yaran nan Alh zai yankewa tukwaici don kawai laifin babawo gare shi har ya yanke hukuncin hada su auren gida gaba dayan su. Da sauri cikin mamaki suke hada baki auren gida dawa yau akewa da namiji wani auren hadi yanzu ? Dama abinda nakewa gudu ke nan da dawowan yaran nan kasan nan ke nan yanzun an sihirce shi kan mu gaba daya. Wai kamar yaran nan Alh zai dauko diyan yan uwan shi yace a dole su zasu aura wai dan rainin wayau da son kai irin nasu har da yar agolan nan yar wurin maimuna yasaka. Gaba daya sukace ina wanan tsarin ya fitowa Alh haka kuma yanzu wa ya saura yin wanan akidan hadin irin aure gida din nan ? Wanan abin baiyi ba gaskiya da sake a cikin maganan nan dole a zauna a duba wai ma yaya hakan har ya faru ne wai ? Hjy tayi dan murmushin takaici ta girgiza kanta tare da fadin don kawai wanan auren da yaron nan yayi a can bada sanin mu ba duk ya kawo hakan. Yaran da suka waye idan su ya bude yan mata tsalatsala kyawawa son kowa kin wanda ya rasa suke rubibin su wai zai dauko wasu kwailan diyan su ya hada su dasu. Yanzun Anty ba wanan ba kamata yayi ace an samu mafita tun wuri kafin wana magana yai nisa ya lalace a dauki matakin hana wanan abu faruwa. Tace waini abin haushi a gare ni idan ma aure yake son suyi a nan ya basu dama da zasu diba yan mata da kansu da suke ke suka waye na gwadawa duniya mana. Kallon ta juna sukayi a fakaice don a zaton su zatace a cikin yayan su don ko wacen su tana da yan mata tsala tsala dasu ke son yan uwan nasu tun dawowan su kasan da suka gansu suke damun iyayyen su da zancen su. Sun kai wani lokaci suna kulawa suna kwancewa a tsakanin har karshe suka aje maganan zasu zauna da kawu akan maganan wanan hadin a canza lale. Dukkan su ranan basu kwana a gidan mahaifin nasu ba kowa hotel ya kama ya kwana a can don shi umar yana barin gidan kai tsaye motar shi daya ke amfani da ita a kano da tunkan yazo yasa a bokin shi ya saya mai mota uku daya a kano daya lagos da Abuja don yayi zirga zirga dasu idan ya zo. Ya koma hotel din daya kama na kwanaki ya shige dakin shi ya kulle kanshi don ya kawar da tunane wayan merry ya kira yaji lafiyan ta dana baby su. Tana dauka ta fara mai kuka ita ba zata iya jure rashin su a kusa dasu ba don haka zata shigo Nigeria ne idan ma yana tunanen komawa can ne da zama ta yarda su zauna nan tare yanzu a inda take ganin sa kulun. Ciki tsigan lalashi ya samu ya lalashe ta akan ta saurara masa karshen wata yana tafe insha Allahu da haka ya samu ya rarashe ta bar kukan da take mai. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 22:57 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA YAHHYU YA KAIYUMU BIN RAHAMATIKA YA ASTAGIS, , , , , , Kasance yau zamu koma makaranta ranan farko na wanan time din yasa bamuyi wani sakkon fitowa da safe ba kwarai sai dai duk da hakan sai da muka tsaya jiran su salma da kannin ta a bakin motar. Don yau driver zai sauke mu gaba dayan mu don mun dade bamu je makaranta tare dasu ba mamu ce ke kaimu ganin haka sai hjy maryam itama take kai yaran ta hakan ya rage muna fitina a tsakanin mu yanzu. Sai dai ko mun hadu ba wani shiri ake ko gaisawa ba sai dai kowa ya wuce ba tare da ya kula dan uwan shi ba. Yau ma tana ganin mu ta wani bata rai sosai sai da kowa ya shiga ta zauna taja tsuki tare da fadin in dai da kwadai da wullakanci ai . Nafisa ta karbe da fadin rashin zuciya ko kare bai jan mai shi haka kawai don anga haske a cusa kai a inda ba kwar jini. Salma tace komai matar mutum kwalelen shi dai don bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane. Wai ke salma wa kike jefawa wanan arashin haka ke baki so dai a zauna lafiya yanzu kuma may akai maku don Allah kuke sake wanan maganan haka ? Dallah malama rufe mun baki da wanda ya tsargu dashi mukeyi idan kin tsargu dake muke Aisha . Aisha tace wani aiko kunyi wa banza indai nice don ban san kunayi ba ni indan da sabo na saba da wanan halin naki ai. Kamar ban cikin motar don yanzu ni abinsu ma dariya da haushi yake ban ko kallo basu isheni ba idan suna haukan su rabona da tanka su tun ranan da sukai min gori da agola gaban yannen su da sallah wani abu bai kara shiga tsakanina dasu ba. Yau ma na sha alwashin har mu dawo ba zan kula su ba saboda hudubar da mamu take min ko yaushe a gidan a kansu. Har muka sauke su Aisha da zata fita tace Allah ya hadaki da daidai dake ta fita suka bita da zagi da kushewa hallitanta sai dai ni banga wani abin kushewa ba a gurin ta da suke zagi. Nasan don in tankane Nafisa tace mu za a gwadawa fari mutum kamar zabaya fari ma ai idan yayi yawa cutane ake wani zuzuta mutum har ana wani hadawa da kalar dangi. Mota na tsayawa taki fitowa sai data batawa mutane lokaci ta sauka muka samu muka fito mu dake baya. A nan na barsu suna yan dararakun su naja hannun kanne na muka nufi hanyar ajin su. Tun ranan da akai case din nan kowan su ke yar boya tsakanin su da kawu su a dole suna fushi da kawu din don yai masu ba daidai ba don da kyat mahaifiyar su da yan uwanta suka shawo kan su don sunce su zasu koma ne abinsu inda suka fito. Shikan umar ma tun ranan baizo gidan ba sai yau yake niyar zuwa gidan don mahaifiyar su dake nacin kiranshi a waya. Bakin wandon jeas ne a jikin shi sai wata bakar riga mai guntun hannu da anineiya har kasan riga rigan ba wani sauka sosai tayi masa ba a jikin shi. Ya fito fes dashi a cikin kayan kana ganin sa kaga wayayyen namiji tashin turai wanda boko ya gama ratsa ko ina nasa sosai. A waje ya parker motar shi sai dai kafin ya fito sai daga motar ya kara gwada layin merry wace tun safe yake neman layin ta bai samu ba zai iya cewa rabon shi da suyi magana kwana uku zuwa hudu ke nan lokacin. A kan idon shi motar kawu ta dawo ta shiga gidan yana mamakin mai ya dawo da kawu gida wanan lokacin haka. Ganin layin nata yaki shiga ya fito daga motar ya tunkari cikin gidan nasu inda ya samu kawu a tsaye bakin mota shida Ahmed yana duba wani takarda. Sai da yazo dab da mahaifin nasa ya tsuguna yana gaida shi a cikin ladabi kawu ya dan dago kai ya amsa ba yabo ba fallasa ya mayar da hankalin shi ga abinda yakeyi. Sun gaisa da Ahmed sama sama kamar yadda suka saba gaisu ba wani sabo saidai sanayya kawai daga haka ya shige part din mahaifiyar shi direct inda ya samu su habbib a zaune. Fuskan shi babu annuri ko kadan a cikin sa ya samu wuri ya zauna yan uwan na gaida shi sama sama don damuwan da suke ciki. Ya juya wurin mahaifiyar su yana gaida ita da wuni saboda lokacin anyi azahar ko ta amsa tana kallon shi tace babawo fushi kake da kowa ke nan a gidan nan daki shigowa tun ranan da akai zaman nan da mahaifin ku. Don may zaka daura muna laifin da muma ya shafemu yanzu duk a dalilin ka. Ya dafe kai yana sauraren ta ya kulu matuka ji yake kamar ya hadiye ranshi don kawai ya yi aure zaisa daddy ya yanke masu wanan iron hukuncin. Ai koma auren ne sai a barsu su zaba a nan gida tunda akwai yan mata da zasu dace dasu amma sai kawai daddy ya yanke hukuncin da shi yake gani daidai ne a gurin. Da kyat ya iya buda baki bayan ya hadiye wani miyau mai daci daya tsaya mai a bako yace . Mama ya dace ace daddy yayi shawara damu ko ke kafin ya yankr muna wanan hukunci. Habbib yace ni tuni dana bar kasan nan ko badon mama da suka tsayar dani ba kamata za ayiwa auren hadi na gida why daddy zai muna haka kamar bai san darajan mu ba. Duk naku bai ban haushi ba kamar na babawo don may zai hada zuria ta dana wanan makiran yarinyar da bata kaunan cigabana a gidan nan ko kadan. Tana bakin ciki da hassada da komai nawa kuma yau yarta ce Alh ke kokarin jefawa a cikin zuriata a gidan nan duk yakan kauna ai bayan wanan hadin dayayi ne. Mama ki daina fada haka akan maimuna mu fuskaci matsalan dake gaban mu yanzu don ni a iya nazarina banga wani rashin da a da take maku a gidan nan ba. Ni matsalata yar maimuna za ace waini na aura yau dan dama dama ace Aliyu ne ko shi habbib din daya daga cikin sune ya zabi yarinyar mama ina zanje da yar cikina sai dai idan rainon ta zanyi . Babawo ka ban mamaki da wanan maganar taka yanzu kai baka damu da koma bayan da yarinyar nan take jawo muna ba a gidan nan kilama fa da hadin bakin ta a ka kitsa komai da Alh ya zartan don kawai taga ta kuntatamin. Yasa tace ya jefa yarta a gunka dama da gaiya ya aikata hakan yana sane ya jefa ma takardan wurin ka don ka dauka. Mama ba hakana nake nufi ba ke yadda kike nufin mu dauki wani mataki a kanta maimuna mu bata nuna muna wani hali na rashin dacewa a gare mu ko a gareki. Gaskiya ya fada mama inji Aliyu dake kallon su ni yanzu sam ban ganin laifin ta kamar wana hjy maryam din dake da fuska biyu wa mutane. Yanzun mama ina kuka aje magana da daddy don naji shi bros har yana wani magana wai dama mune da nasa zaben, ma,ana ya yarda shi da hukuncin daddy din akan mu. Habbib kasan abinda rashin biyayan mu ga daddy zai haifar akan mahaifiyar mu kana dai jin abinda daddy ya fada ranan kan mama. So kaga maganan wai bama so ma bai taso ba agaremu ya zama dole muyi biyayya a furin daddy tunda mahaifin mu ne shi yana da ikon komai a kan mu. Kai ka rufe mun baki kai ya zama na dole kai masa biyayya ba dai ni ba akan maganan da wata mace tasashi ya aikata har kake tunkaho akan hakan. Bari kaji muddin ina raye wanan auren naka da yarinyar nan ba zai taba yuyuwa ba a tsakanin ku. Mama kibar fadin haka kinji irin abinda daddy ya fada a kanki gaskiyar bros ne zamuyi biyayya ga daddy kodo farin cikin ki a gidan nan Aliyu ke magana. Kai rufe mun baki ku may kuka sani a zaman kishi idan doni zayi wanan auren ban yarde masa yayi shi ba. Idan kuma har Alh yaci galaba a kaina ya matsa akai wanan hadin a tsakanin ku ban yafe ka kula wanan yar mara asalin kwarai ba. May akayi akai maimuna mutumiyar banza munafuka mara asali da ita may ke ga maimuna balle yarta a duniya irin tsiya da minafunci. Kiyi hakkuri mama ya zama dole muyi biyayya a gare ku batace masa komai ba tabarshi yana a tsaka mai wuya a lokacin. Wayan shi dake hannun sa tayi kara ya dauka yana duba bamuwar nomba layin mtn na Nigeria yaga bakuwar nomba yana mamaki har wayan ya katse bai dauka ba. Ba a jima ba aka sake kiran shi ya daga da tsuki yana who is on the line ? Omar i am in Nigeria right now in kano inside your family compound where are you ? What ya fada a razane yana dagawa har saida kowa ya zabura a falon a tare suke hada baki may ke faruwa bros hankalinsu a gare shi. Akasale ya kalle su ya fara tafiya yana fadin wai merry ce tazo. Gaba daya suka mike tsaye suna mara mai baya zuwa waje inda tace take sai dai ganin Alh sani tare da Ahmed tsaye a waje ya dakatar dasu daga saurin da sukeyi su fito din. Kawu da Ahmed kewa bayanin sakon daya tura mai na kudi sukayi aune da wasu mata biyu suna shigowa gidan. Ko wace tana saye da dan karamin buje iya cinya ganin yanayin su kawai basai ka tambaya daga wani akida suke ba. Don kamannin su ya gama nuna daga inda suka fito saidai yanayin jikin su ya nuna jindadi da kulawa a gare su sosai. Dayance tace wa kawu hyy a cikin dan dags hannu kawu dake masu kallon mamakin abinda ya kawo su gidan shi don shi baida wani alaka da irun su ya kasa amsa mata don bai iya kallon su kamar a tsirara suke yake ganin su. Ahmed ne ya karba yace are you looking for someone here ? Yeah we looking for Omar dis his wife merry tana nuna mai merry din dake tsaye tana dan murmushin tana kokarin gaida kawu din. Umar da yan uwanshi suka karaso wurin da sauri yana fadin merry how dear you come here ? What bout you here ? Suna ganin shi dayan ta miko mai hannu tana fadin O Omar so you are around nice to meet you ta miko mai hannu ya rike suka dan rugumay juna ya dan bubuga mata baya kadan ya sake ta ya juya wurin merry din ya rike mata hannu sukai kamar yadda sukayi dana farkon sai dai ita bata sakeshi ba sai ta makale a jikin shi. Kawu dake tsaye ya daskare a wuri daya ga wani irin malolon bakin ciki yana taso mashi. Sai can umar din ya tuna da daddy su na gurin ya saketa bayan sun gama tabaran su ya gama shafan cikin jiki ta a gaban daddy ya juyo yana fadin. Kawu wanan ce matana da na aura a can merry ya juya wurin ta yana fadin merry meet my Dad dan my brothers. Tace wanderfull daddy nice to meet you tana dan rusunawa kadan da sauri kawu ya kawar da kanshi gare su ba tare da ya amsa ba Hjy ta fito ya nuna ma merry mahaifiyar shi a cikin yanayin rashin jin dadin abinda dady yayiwa merry din na nuna mata kyama a gaban ta. Hjy kan ta dan washe karan kada ham tana karewa merry din kallon mamakin abinda yaja danta a ga wanan bakar arniyar dake gaban su yanzu. Ganin su a tsaye waje yasa hjy cewa ku shigo daga ciki da sauri kawu ya juyo yana fadin kada ki soma ki shiga min gida. Ya fadi a tsawace gaba dayan su dake wurin sai da suka razana don irin tsawan daya daka a lokacin. Ran hjy jummai ya baci itama tace don may zaka hana ta shiga gidan bayan kasan bamuwar danka ce gata dauke da jinin ka a jiki. Wanan hayaniyae da suke yi ya jawo hankalin sauran mutanen gidan gare su suka fito waje da gudu. Jini na fa kikace jummai a ina badai a jikin wanan kafirar data shigo min gida haka tsiraci waje ba tir da wanan rayuwan da danki ya zabawa kanshi. Yaya gaskiya hjy ta fada idan baka raga mata don komai ba zaka raga mata ko don cikin jinin mu dake kike jikin ta ai balle ba a kore bako don da dalili tazo nan din da bata da dalili saita wuce ko kallon gidan nan ba zatayi ba ai. Ke ke maimuna ni kike son koyawa ilimi ko may a gidan nan har ke kin isa in kafa doka kice zaki min nasiha. Tun lokacin dana fito daga aji na dauko yan kanne na zuwa wurin da zamu shiga mota na hango taron students da alama wani rikici suka samu akeyi. Ban damu ba sai dana tsaya nasaiwa fauziya ruwan leda da tace kishin ruwa take ji suka sha na riko su zuwa inda zamu shiga mota. Tun daga nesa nake jin muryan yan ss3 suna fadin gobema ki kara yiwa wani iskanci ki gani a school din nan. Fuskokin yan gidan mu na kalla naga yanayin su ba dadi a lokacin na kara ina dan lekawa inga abinda ke faruwa a wurin salmace wanan ya zaga wanan ta dangwara. Kallin su ikilima nayi ina fadi ido rufe ku mai kuke jira baku shigar mata ba a hankali tace ke sinours ne fa ke fada kuma ai mu bari a nuna mata darasi. Wani kallo nayi mata na kama ture mutane ina kutsawa cikin taron wallahi kada wace ta kara dangwaran ta . Nace daga bayan su dayan tace idan aka dagware ta may zakiyi nace may tayi maku da zakuyi mata wana abin. Wanan yar iskan agolan gida ce mai rashin kunyar tsiya ko idan ta isa ta tanka ki gani a nan. Nace anty salma tanka masu don Allah muga tsiya salma na tsaye kimkam taki ko motsawa wata tace idan bata tanka ba bari mu, mu tanka mata ki gani. Tana kai hannun ta saman jikin salma ina kai mata doka ta baya daga inda nake sai fada ya kaure tsakanina dasu Nafisa na ganin haka itama ta fara kai masu duka salma ma ta fara sosai na nuna masu tashin kauye daban yake dana birni. Fada mukayi sosai sai da sauran malam dabasu wuce ba suka raba tare da daukan sunaye mu suka tsaya saida kowa ya watse a wurin. Sai ga motar mu tazo daukan mu muka shiga ranan ba zancen da mukeyi sai na fadan har muka dauki su Aisha mukaje gida. Muna zuwa muka samu tashin hankali a gidan wanda yafi namu na shirmay da muka baro a school. Don daga Amma zuwa kowa na gidan suna waje cirko cirko dasu a cikin tashin hankali muka samay su. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:02 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALHAMDU,LLAHI RABBIL ALAMIN, , , , , , , Tun muna daga get muke jin hayaniya muryan Amma dana kawu sai na hajiya jummai dayafi na kowa tashi a gidan. Abinda sukewa fitinan basu sani mamu ta kaita shiyan ta don kada su bar abin fadi wa dan su a baya. Har ta fara gabatar mata da abin sha sai dai merry da taki kwantar da hankalin ta ga abinda taga sarakain nata sunayi wanda tasan saboda dalilin zuwanta ne gidan da tayi Sai dai a lokacin mamu na iya kokarin ta wurin ganin ta kwantar da hankalin merry din a lokacin a part din mamu din. Lokaci daya suka juyo suna mamakin rashin ganin su merry a gurin da suka barsu a tsaye lokacin da rikici ya kaure tsakanin Alh da hjy jummai akan kada merry ta shiga mai gida hjy kuma tace sai merry din ta shiga . Ba inda zata da lalura a jikinta tunda don dan su tazo gidan sai dai in gaba daya zai hada ya kori merry da dan nasu. Shine ya haukace yace sai Umar ya bar maigidan shi yau din nan ya kwashe takarcen matan shi yasan inda zai kaita shi dai kan ba dai gidan shi ba. Mamu ta sulala ta kira Amma da mama hadiye suka fito shine har ta samu ta shige da merry part din ta. Anyi daidai da zuwan mu umar ya jawo yar troler din kayan sa kannin shi na binshi a baya ya tsaya a sasanta zancen yana fadin kada su damu zai san yadda yayi indai wanan zai kara kawo rikici a tsakanin iyayyen nasa. Ido rufe Alh ya juyo yana fadin ina kafiran ta shiga min a cikin gidana hjy maryam da bata san idon su Aliyu yana kanta ba ta nuna part din mamu da hannu. Rai bace ya nufi gurin kofan ga su salma da basu san dalilin kukan uwar su ba suma suna kuka don ganin mahaifiyar su na magana a cikin kuka. Haka yasani saurin zubewa a gaban kawu ina wani irin kuka mai ban tausayi ganin ya tunkari kofan mahaifiya na da tuzajara a fuskan shi kawu kayiwa Allah da manzon sa kayi hakkuri kada kaje kofan mamuna don Allah ka barta kawu. Cak yaja ya tsaya wuri daya don jin kalamina na sake fadin kawu kayi hakkuri don darajan Allah da annabi kawu. Suma su salma yadda nayi suka zube a gaban shi don dun dan fahinci abinda akewa rikici a gidan yanzu. Nikan ban san komai ba na dai dauka fadan harda mamu ne yasa zai shiga yai mata rashin mutunci a part din ta lokaci. Hannaye a hade ina rokon shi suma su salma suna a yadda nake har kannen mu muna kuka a cikin tashin hankali. Amma tace ka duba yanzu ko abinda yaran nan sukayi bai isheka ishara ba kan dan abinda za a sulhunta ka tsaya kuna tashin hankali da mata. Yace hajiya akan may zanyi magana su nuna min ban isa ba dasu karan bude part din Amma din yasa duk muka waiga wurin ta fito tana fadin. Gwago tana part dina na sauke su a can don abinda ake a gaban su bai dace ba kodon cikin nan da halin da boyar Allah nan take ciki bai kamata ai mata yadda yaya yake nufi ba. Kada ka manta jinin kafa ta biyo nan bata san kowa a garin nan bayan shi da Allah yau in abinda ta haifa ya girma ta bashi labarin abinda akai mata ranshi ba zaiyi dadi ba. Kamar fa koran kare ake shirin mata a gidan nan fa alhalin da aure danka a kanta shiru kowa yayi a wurin lokacin da mamu take maganan Maimuna may ke kanki kike son jifa kanki da abinda bai shafe ki ba a gidan nan ya shafe ni yaya tunda ya shafi jinin ka kamar nima ya shafe ni ne yau . Duk abinda mutum baison aiwa nasa watarana ba zaiso shi ga dan uwan shi ba Ahmed dake gefe yana kallon rikicin gidan mai kama da sarka mai rikicin gangan yace. Alh gaskiya hjy take fadi namu fa matar nan ta biyu yau ashe itama tana cikin ahalin ka ke nan don idan wani abu zai samay ta a garin nan kamar ya samu kowa na tare dakai ne ai. Sani wai kanka daya kuwa idan hankali ya bace ko rai ya baci hankali fa ke nemo shi maimuna ki rike ta a wurin ki wanan umurni nane tana fadin haka ta juya rai bace ta bar gurin. Kallon inda muke muna kuka yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya wuce part din shi ya bar mu wurin tsugune muna kuka. Kallin mu mamu tayi tana fadin ku tashi kuje ku cire wanan kayan don Allah ta wuce zuwa wurin bakin ta. Daga hjy jummai har yaranta a wurin muka barsu a sandare suna mamakin abubuwan dake faruwa matar da yanzu suke maganan a kanta ta zamay masu bango yau. Har mamu takai kofa ta juyo ta kara komawa wurin su tace don Allah hjy ki ja yaran nan ku bar wurin nan kada mutanen su kai ga fahintar halin da ake ciki a gidan nan. Kuyi hakkuri da halin Alh har da girma a cikin al,amarin shi yanzu sai hakkuri da tsoho don Allah ku shiga daga ciki wanan tsayin baida amfani anan. Kamar umurnin ta suke jira habbib ya karbi troler hannun yayan nasu ya nufi part din su da kayan hjy jummai ta daga kafanta da kyar ta juya zuwa part din ta. Yana shiga yace mama zan wuce tace ina kuma zaka yanzu a wanan halin yace zan dan fita in dawo akwai abinda zanyi yanzu. Tace samu wuri ka zauna ba inda zaka yanzu sai ka huce idan ka fita ai yarinyar ba zataji dadi ba. Aliyu yace ki barshi ya fita tunda daddy ya rufe idon shi yace bai son ta zauna mai a gida may zata zauna yi kuma. Ku baku san komai ba maganan maimuna data fada koda a munafunci tayi shi gaskiya ta fada barin yarinyar nan gidan nan yanzu ba zai haifa muna da mai ido ba a gurin ka nan gaba sai taga kamar an kyamace tane hakan. Habbib dake shigo ya kalli yayan nasu dake tsaye ya dafa kushin yace yau nasan ko waye hjy maryam a gidan nan matar nan ita fa ta nuna ma daddy inda merry ta shiga dayake tambaya. Na gani nima Aliyu ya fada a sanyaye yace ni na dade da karanta matar nan don yaranta ma idan kun lura ai basu ba daddy hakkuri ba kamar yadda yar wurin maimuna tayi. Don itace ta sare mai jiki da kalamab data hadashi dashi yasa jikin daddy yayi sanyi hjy da ke jinsu tace wanan ai neman kindin zamane kawai har uwar duk abinda take badon Allah takeyin shi ba. Nafisa dake rakube da salma tayi caraf tace a, a mama ba wanan ba dubi fuskan anty salma wallahi yau ba don A ruwa ba da sai kinje kin kwaso anty salma a school don taro yan ajinsu sukai mata ita daya su iklima na kallo basu shiga ba nima saida naga ana danbe da A ruwa na shiga akayi dani. Abin da ya basu dariya ke nan dukan su a falon banda umar da uwar da shi murmushi yayi kawai don jin abinda kanwar shi ta fada ita kuma hjy haushi taji har cikin ranta. Ta kalli salma tace amma anyi yar kawai yanzu may wanan yar kwalar zata shigar maki fada a wurin nan kafin uwar ta rufe baki Nafisa tace kwala mama bakiga yadda take daga katai bane tana kai kasa wallahi karfi gare ta sosai kamar mai aljannu. Rufa min baki da maganan takaici kun bani kunya wallahi kun badani salma salma dai batace komai ba sai turo bakin da tayi gaba kawai tana dan magana ciki ciki . Aliyu yace salma yaya akayi haka ya faru kuma tace wallahi yaya ban iyasu ne sun tarar min ni daya zuwan A ruwa ne na samu karfin fada nima kada naji kunya. Daidai lokacin na shigo falon da sallama na gaida su ina fadin mamu tace wai yaya umar yazo bakuwar shi tana kiranshi. Ina fadi na juya don zanine da katon hijab a jikina kawai a lokacin na tube uniform ke nan zanyi wanka mamu ta kirani ta aike ni. Har na juya naji muryan Aliyu na fadin ke A ruwa a she ke shagoce a wurin danbe ance yau kin kada mata a fage ko ? Dan dariyan gefen fuska nayi kawai na fita a daidai lokacin uwar ke fadin kada ka soma cewa zakayi wasa da wanan yar na fada maku. Mama yanzu ai ya zama dole tunda tana shirin zama matar dan uwan mu yaya zamuyi da ikon Allah tace kadai ji na fada ma kada ka kawo min maganan banza a nan. Ina shiga suna zaune sun wani isheshire kafa a falon namu mamu tana gefe dinining din mu tana zubawa yara abinci na shigo ina fadin mamu na fada mai. Har na wuce naji dayan mai ciki tana fadin beauty sister what is your name na dan juyo nace mata fatima a takaice zan wuce. Tace a cikin turanci yaya akayi nafi mijin ta kyau tana miko min hannu wai mu gaisa kallon inda mamu take na danyi naga ta kada min kai don yana daga cikin huduban da take min kan kada in yarda in hada jiki ko da mace yar uwata ce bata yarda da hakan ba gare ni. Hannun na mika mata ta dan kama yaba hallitana ni dai duk a tsarge nake da matan don basu kwanta min a rai ba a yadda naga shigan su sai naji kyaman su a raina. Duk sai na matsu da ta dauke hannun ta a nawa nace nima a cikin turanci ina son inyi wankane sai da ta danyi murmushi kafin ta sakeni tana fadin haka na da kyau. Na shiga naji mamu na fadin idan na fito in samay su a part din Amma in bar bakin su huta a nan na dan dauki lokaci na fito da shirin zuwa islamiya daga can na nufo falo ina sauri. Sai dai abinda na samu a falon ya ban mamaki don a makale na samay tsaye yana shafan cikin dake jikin ta wanda ni sai a lokacin ma na kula da mai ciki ce matar. Yi nayi kamar ban gansu ba zan shige sai matar tayi magana tana fadin wanan sister din naja tafi ka kyau sosai how comes na dauka a gidan ku ba wanda ya kaika kyau ai. Yayi dan murmushin da baikai ciki ba yace merry ke nan tace kada ka damu ina son ka hakan kayi mun fiye da ita ta fada tana dariya tana rogumoshi a jikin ta. Ni dai na fice da sauri har kafana yana hardewa wurin sauri ina fada da mamu a raina data barsu suka shigo mata shiya suna iskanci haka do ban taba ganin mace dana miji a haka ba sai a film din tura idan muna kallo. A part din Amma na samay su suna magana ina shigowa take fadin kin dauko abincin na zauna ina bata rai nace mamu wa yan nan mutanen suna nan fa harda wanan yayan su salma din da kika ce in kira masu yana ciki suna maki iskanci a falo. Iskanci yar nan mutun da matar shi ki kira masu iskanci kallon mamaki nake wa Amma dake magana nace. Amma wanan arniyar ce matar sa gashin doki da wani dan buje ta sa a jikin ta fa na fada a cikin mamaki. Amma tace sai ki koyi zama da su don hakan dabi,an su yake ke dai kada ki koyi halin nasaran nan danagani yau a gidan nan. Nace da sauri Amma a nan zasu zaune tare damu a aurin mamu na tambaya ina kallon ta tace yanzu wa sanar masu ni abin duk ya daure min kai ai. Sallaman Umar ne a kofan falon suna bayan shi wani haushi naji don na dauki abinci ke nan zanci suka shigo dakin yana gaba suna bayan shi. Ya samu wuri ya zauna yana nuna masu wuri a gefeb da mamu take zaune da sauri na kalli mamu sai naga ta dan mike tana fadin ku zauna ga wuri nan ta koma gefen Amma ta zauna. Yace Amma ga merry nan nakawo ta ta gaida ke da kaina Amma tace uhmm naga mari sai dai ba haka akaso ba wai kanin miji yafi miji kyau. Amma zaki fara ko yanzu kuma may tai maki ya fada yana dariya yace m hjy maimuna wanan itace merry matata ita ma yar nan kasan ce sai dai ba a nan aka haife ta ba haka yasa bata jin hausa ya kalli merry a cikkn kulawa da so da kauna yana gabatar mata dasu mamu da amma da matsayin su gare shi. Ya mike yana fadin zan kaita ta gaida mama sai mu wuce inda zan sauke su don wanan ne zuwan ta na farko kano. To,to to wani wurin zaka kaisu su sauka ko ai hakan yana da kyau don tafi sakewa a can gata da juna biyu ga tafiya da suka sha a hanya. Ta fada tana dariyan yake a fuskanta wanda baikai ciki ba da gani kakaroshi take kawai a zauna lafiya. Mamu tace abincin dana basu nasan basu ci ba yace No kada ki damu na gode yana mikewa yace nagode da kulawan ki gare mu sosai . Mamu tace ai hakan yiwa kaine bakin ka ai nawane Umar sai dai idan baka dauka haka ba shidai baiyi magana ba ya kalli arnan nasa yace su tashi suje gun mummy shi su gaisa. Suna fita Amma tace wai da ranka kasha kallo a duniya wanan may ya gani a wurin wanan mai kama da iccen . Dariya muka kwashe dashi a falon mamu tace gwago kin san goban wani zuman wani shi abinda yai mashi ne ya zabawa kansa. Amma ta tabe baki tana fadin a hakan kamar anyiwa icce kwalliya mace ba gaba ko wani fasali in banda abin maza may ya gani anan har yake fuskantar wanan tasgin hankalin. Sai dai hakkuri tunda ya riga da yayi yanzu Allah dai yasa ta gane yayi jihadi Amma ta wani kallo mamu tace ki bari don Allah yar nan. A hakan kinga ruwan musulunta a gurin nan mace zata zo gidan sarakanta da wanan matsiyacin shigar na banza. Sun samu hjy jummai ba yabo ba fallasa ta karbe su sun gaisa tare da mata ya gida duk a cikin harshen turanci suke maganan da ita. Taji dadin samun yan gidan suna jin harshen ta haka ya nuna mata su din wayayyu ne ba jahilai ba a yadda tayi tsammanin samun su. Don haka take ganin komai zai zo mata da sauki sai dai daddy sune bata fahinci fadan dataga yana yi ba dazun din. Hotel ya kai su inda yake ya kara kama daki daya ya don aminiyar ta linda data rako ta tasauka a ciki shi kuma suka zauna dayan dakin da yake din. Sai dai ranan da za a tona aga abinda ke ranshi da mutum zaiyi mamakin wayayyan da yakeyi a lokacin don baiyi farin cikin zuwan merry din Nigeria ba don duk plan din shi merry ta rusa mashi su yaso ko zata biyo shi nan sai ya kammala abubuwan daya sa a gaba shi da bai fadawa kowa ba har lokacin. Don mamaki yake son ba kowa nasa sai gata tazo saura kiris ya rage mai ga abinda yake hadawan sai gata ta fado masu kasan. Don shi mutum ne mai zurifin ciki mutum bai iya gane cikin sa ko inda ya dosa gashi rashin maganan shi yayi yawa hakan ya kara mai zurfin cikin nasa. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:02 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM . Yau asabar bamu shiga school tunda na dawo islamiya goma na safe nayi wanka na dawo falon mu na kwanta saman dogon kujera inda kanne na suke kallon katon don sin saba da kallo shi sosai tun ban sha,awa har yanzu ina dan binsu nima. Ban san sun fita ba sun bi mamu part din Amma inda take kwashe ma Amma kai takan mata soro hudu a kai duk sati biyu biyu. Shi ke gaba tana bayan shi Umar da tun daga nesa ya hangoni kwance kyakayawa sura kafana suna waje a baiyane sun fito daga kasan bujen dake jikina na atamfa. Subbahanallahi ya ambata a zuciyar shi yana saurin kawar da idon shi inda nake kwance na shaga da kallon katun din yaki ana guje guje. Saboda gaba daya sharaba na duk a waje yake sunyi lub lub dasu tankar bana taba kasa dasu. A hankali ya karasa shigowa cikin falon yana mai kara salma ta yadda zan iya jin su da sauri na dago kai sai lokacin na lura da yaran duka sun fita a falon. Shigo sukayi yana nuna mata wurin zama tare da tambayana ina maimuna take ? Haushin tambayan naji sai nake ganin yayi rashin kunya wa uwata ko dan saya sunan babu zaice wani maimuna haka gatsau dashi. Ina kokarin tashi ba tare da na bashi amsa ba illa daure fuska danayi a lokacin ban kalle su don shigar ta tayau ma dai buje ne da riga iya cinya sai bakin coth din mata data dora saman farar rigan ciki. Ya kara maimaita nace ina maimuna na turo baki gaba nace tafita naji ya furzo da iska daga bakin shi ya sake kallona yace ke baki iya gaisuwa bane halan ? Ba yanzu kuka shigo ba kana tambayata mamata yaushe zan gaishe ka hakana kuma ya kalle ni kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya wurin matar nasa yana fadin. Ta zauna zai shiga ciki ya dan fito sai su je gun maman shi haka ya juya ya fita ya barni da arniyar zaune tana wani faman tatara bujen ta don zama dakyau. Tace a cikin raha common baby i forgot your name nace Fatima tace oh sorry fatima who are you today nace mata lafiya ina juyawa gurin tv abina. Sai naji tace how old are you now Fatema ? Ina mikewa nace fifteen years daga haka na wuce zuwa kitchen in hado mata abin sha don in mamu ta samu ban aje mata komai na motsa baki a gabanta ba fada zansha gurin ta. Ruwa da cup na fara kawo mata na koma na hado mata fruit din da nagani a cikin fridgen din na kawo mata ina kokarin zama ya shigo tare da kallon abinda ke gaban ta din yace ok nasan kina son lemo barin bare maki ko ? Ya zauna gap da ita yana bare mata lemon yayin da idanuwan ta ke a kaina tana kalle min halittana tsab. Zan fita daga part din naji tace i like dis dress can you saw it for me yace why not if you like it. Ya bini da idanuwa yana kallon kayan dake jikin nawa da take magana a kansu bujene da riga na atamfar hausa sai dan kwalin shi dana daura a kaina. Murmushi naga ya sakar mata mai laushi yana fadin zai so ya ganta cikin su ai ko wani lokaci ni dai naja guntun tsuki ta yadda ba zasu jini ba ina kokarin fita falon . Wani kallo ya jefa min tare da fadin ke wakikewa tsuki nace ni daku nake halan daga haka na fice abina na barsu nan falon mamu zaune. Can na samay ta suna soron karshe ganin na shigo ta dago tana kallona na san fada zatayi min na bar mata part babu kowa ba tare da na rufo mata ba. Nace wanan yayan ne yazo da arniyar nan suna falon zaune shine na fito na basu wuri da sauri tace Umar sun shigo ne shine kike kokarin zama baki fada min ba. Ina dai ai yanzu ta shigo ko kada ki koya mata jin tsoron yaron nan nan gaba tasha wuyan su don banga laifin ta fito ta basu guri ba da wanan tabaran nasu ai. Amma gwago yayanta ne fa koma ince kawunta tunda dai ai umar zai haifi sa,anta ko ? Daga baya ke nan ko zai haifa bai haifa din ba ai kuma ba A ruwa ya haifa ba don haka kada ki matsa mata a kansu don Allah. Shiru mamu tayi don ba wurin magana bane don mamu bata san komai ba akan alkawarin da kawu yayi damu ga iyalinshi. Da sauri ta kai tsoron ta lakabe jiki ta fita ta barni nan a wurin Amma ina ganin ta fita nace Amma ni bansan abinda yasa mamu ke jan arniyar nan a jiki ba haka wani karni fa matar naji tanayi. Aisha dake zaune kusa dani ta kwashe da dariya tana fadin matar big bros din ke karni Fatima bari yajiki yayi maganin ki a gidan nan. Amma tace yo karya ta fada ranan daya shigo min da ita nan na dade ina kyamar falon nan nawa musanman wurin nan data zauna. Da sauri na kalli wurin anan nake zaune nai azaman tashi Aisha ta rike ni tana dariyan keta tana fadin dallah ja can da suke koya maki a school fa ? Nace ai ban zuwa kusa dasu ko a can nisa da nisa mukeyi nida su gata da son tambayan tsiya wallahi. Haka dai muka zage ta tas amma tana tayamu zagi sai gasu tare sun shigo shiyan sai kuma Amma ta ban mamaki kamar ba itace ke zagin arniyar yanzu ba. Sai gata tana haba haba da ita kuma ita dai merry idon ta yana kaina duk abinda ake a falon Aisha ta mike ta dauko mata ruwa sai tace wai ita dai dress dina take so yafi daukana sosai bisa ga na Aisha data daura zani. Amma ke tambayan may take fadi yana mayar wa Amma din tare da tambayana yana kallon inda nake yace a ina ake maku wanan dinkin ne ? Ban sani ba mamu ke kawai na bashi amsa kamar ban son maganan ina kawar da kaina gefe daga kallon su. Bai kara kula ni ba sai cewa da yayi Amma ina son taje su gaisa da daddy ta matsa min tana son zuwa wurin daddy su gaisa. Amma tace eh hakan yana da kyau sosai sai dai mahaifin naku ne dake nuna mata kyama karara a fuskan shi bai iya kokarin boyewa kamar yadda kowa ke boye nasa. Yace Amma har kema kyaman merry kike ke nan ko mai sai Amma ta dan tabe baki yayin da ni da Aisha muka tsura mata ido muji abinda zata ce muna dariya kasa kasa. Tace yoni waye da ba zanyi kishin addinina ba sadauki ai ba komai saya kaga muna haka ba sai horo da addinin mu daya haramta tsakanin mu dasu. Shiru yayi ya dafe kanshi ba tare da ya iya magana ba itako dabata san abinda ake fadi ba tace Fatema can teach my ausa i want lean it. Dan dariyan yake nayi don jin yadda ta kira hausan da wani gurbatacen kira nace nima koyo nake ban iya ba sosai. Ido ta waro waje tana fadin bata yarda ba don gashi ina yi da grandma taji Omar ma yai min na basa amsa. Hankalin shi kamar ba a wurin mu yake ba alhalin yana saurareb mu sarai sai dakalan wayar shi yakeyi kamar baijin mu da ganin sa abin duniya yayi masa yawa a rai lokacin. Itama Amma fita batun shi tayi don ta fahinci amsan data bashi ne yai masa zafi ya ja yana fushi gefe daya. Daga inda nake na mike don barin falon tace ina zanje nace zan koma wurin mom dinane part din mu. Sai naga ta mike tana fadin zata koma can ne ita ma ta kwanta kamar in sa hannu a kaina nace na fasa sai dai babu halin hakan sai Aisha dake min dariyan keta na dan buge ta ya dago kai a cikin takaici yana kallon mu don ya gane abinda mukeyi sarai yace a cikin tsawa kai may kukeyi haka yana fito da ido waje. Mu dai muka fice har Aishan da zata bini gulma part din mu muka barshi zaune da Amma. Baya fitan mu yace Amma abinda yaran nan sukaga ana nuna min suke kokarin nuna wa ga matana da sauri Amma ta katse shi da fadin. Kaga kada ka tsargi yaran nan suna nasu zaka dora masu zancen daba shi ba may suka gani gare ta da zasu tsarge ta . Ya mike yana fadin zan leka mama daga can zan wuce zan barta a wurin maimuna. Yana fadin haka ya fita ba tare da ya tsaya jin abinda Amma zata fadi ba sai daya shiga wurin mama ya hjy jummai dake zaune a falon ta tana waya taga ya shigo. Sallama tayi da mai wayan tana kallin dan nata da ya dan fada kadan yana zaune ya dafe kai ya rufe idon shi ruf yana tunanen halin da ake nuna ma matan shi a gidansu. Sabanin gidan su merry din da kan nuna mashi kauna da nuna shi na gidane gare su idan yaje ziyaran su. Hjy jummai ta dan kura mai ido na wani lokaci sam shi bai san tanayi ba saida ta kira sunan shi da babawo may ke damun ka kuma ? Ya bude idon shi da sauri yana sauke hannun shi daya dafe kai yana gaishe ta kwana ta amsa har lokacin fuskanta yana garshi. Tace mai ya faru nagan ka kamar da wani damuwa a tare dakai kuma ko baka da lafiyane kuma ta tambaya tana tsure shi da idanuwanta kanana. Ya dan dago kanshi yana fadin mama lafiyata lau wallahi may kika gani mama ? Tace naga ka fada ka shiga tunane da zaman ka yanzun haka kila ko abinci bakaci ba kana tunanen banza . Umar ya danyi murmushi tace kana son wani ciwo ya kamakane a hakan kan wani tunanen banza indai akan wanan auren ne da ake son lakaka maku ba zai yuyu ba na fada maku. Yace mama ni wanan baya damuna matsalata a yanzu kan zuwan merry kasan nan ne kawai. Tace wani abin kuma aka karayi bayan wancan yace ba ai komai ba mama sai dai yadda ake karbanta ne a gidan nan bai mun dadi. Hakkuri zaka kara dama kasan halin mutanen mu ai ga kuma yadda suke ganin tazo din a cikin kananan kaya shi dai ne abinda zasuyiwa tsegumi ko? Zata gyara ai mama nima nasan da hakan don yanzu itama ganin shigar yaran nan tace tana so zan ba maimuna tayo mata wanda zatai amfani dashi kafin ta koma. Hjy jummai ta wurgawa dan nata harara tare da fadin wace maimuna kuma ? Kai baka rabuwa da zancen yatinyar nan naga kamar kana zurfafa kanka gareta fa don kawai kaga tana irin kissan nata gun matar ka. Wana wani makircine namu na mata ni kar nake kallonta don daidai nake da kowa a gidan nan don na riga da nafi karfin su ko na shiga gaban kowa a gidan nan. Umar da kanshi yake kasa yana jin kalamin mahaifiyar nasa ba dadi har cikin ranshi don shi maimuna ta gama masa komai tunda baiga wani kyamatar merry a gurin ta ba ko kadan. Shi dai bai ga abinda wanan baiwar Allah takeyi ba da mama take kiranta da wa yan nan kalaman nata haka. Haka dai ya gama jin ta da zai tafi tace ya kawo kudin kayan ta sa a dinka ya sa hannu a aljihu ya miko mata ta karba tana duban kudin kamar basuyi mata ba Ya dawo part din mu yana fadin zai shaga gari sai yamma zai dawo su tafi. Mamu ta dan kauce ta basu wuri don du gana yadan dade gurin da ita kafin ya kira mamu yana fadin ina son don Allah a dinka mata sutura irin na nan koda kala biyar ne ta matsa min kan kayan da taga yaran nan sun saka. Ya fito da kudi masu yawa yana mikawa mamun sai mamu tace indon wanan ne ka barshi zan saka ai mata yau zuwa gobe insha Allah. Zanso nima idan ta saka sai in kaita wurin Alh su gaisa don nasan yana daga cikin abinda yake kyamatar ta a yanzu don shigan nan nata haka daya gani. Dan murmushi ya sakar mata a karon farko yana fadin na sani maimuna nasan abinda daddy ke gudu da sannu komai zai zo karshe. Ya sa hannu a aljihun shi ya ciro dubu dari yana mika mata kallon kudin mamu tayi tana fadin nace ka bar kudin ka za a dinka mata insha Allahu. Ba kalman godiya ya kada kai ya fita ta juya wurin merry dake kwance saman dogon kujera take fadin ta tashi ta shiga ciki ta kwanta da kyau. Dama a gajiye take abinka da mai ciki bata ki ba ta bi mamu zuwa kuryan dakin ta a can ta haye gado ta kwanta sai barci. Zai fita ya hadu da mahaifinsu a waje yaje su gaisa dashi sun gaisa kamar kullun har lokacin akwai dan sauran fushi a fuskan mahaifin nasa har lokacin. Ya dan dubi mahaifin da ke tsaye yana fadin daddy nazo tun dazin akace kafita yace eh yanzu ma dawowa nayi in sha maganina dana manta ban sha ba kafin in fita. Daddy mai zai hana aje asibiti sai nake ganin zaifi da shan magani haka a gida ko yaushe sai kawu yadanyi murmushi kadan yace. Asibiti ai munje su suka dorani akan maganin kasan yanzu idan girma ya fara kama mutum sai a hankali. Yana fadin haka ya juya yana kokatin barin wurin don tafiya yace to daddy Allah ya sauwa sai ka dawo ke nan ya gyada kai yana kokarin shiga mota yace Amin Umar fuskan shi a matse ya ja mota ya wuce ya barshi a gurin har ya fita get din gidan yana tsaye yana kallin mahaifin nasa. A hankali ya rufe idanun shi yana tunanen sauyawan daddy nasu gare su kamar ba sune suke kamar abokai dashi ba. Can ya bude idon ya sauke numfashi ya fara takawa zuwa inda ya aje motar shi ya shiga ya fara tokawa a hankali. Lokacin zuwa islamiya yayi na fito na fara kiran kanne na don mu wuce don Ahmed yayi tafiya kwana biyun nan da kafa muke zuwa islamiyan. Ban tsayawa jiran kowa yanzu don bata muna lokaci suke idan mun makara kuma a duke mu ni nawa bai damuna sai na kanne na da ake tsala suna kuka yasa nake saurin zuwa islamiyan kada mu makara. A hanya mun dan taka kadan da gida a wurin wani gida da ake aikin sa ba dare ba rana dan nisa kadan da gidan kawu naga wani a tsaye ya bada baya kamar ya umar. Faduwan da kanina yayi yasani dakatawa da tafiyan da nake ina gulma na tsaya ina fada dashi ya daga yana kuka. Jin muryan mu dayayi yasa juyowa inda muke yana fadin ba zaki daga shi ba kin tsaya kina fada wawiya kawai. Yana takowa zuwa inda muke ya karbi yaron dake kuka a hannu na ya jashi haka yasa dole muka tsaya yana tambayan shi ina zamu tafi haka da wanan ranan lokacin uku da wani abu na rana hudu batayi ba ko. Yaron yace yana bata fuska islamiya zamu baiyi magana ba yaja hannun yaron zuwa wurin motar shi kawai sai da yasa shi a motar ya juyo inda muke yana fadin kuzo in sauke ku inane islamiyan naku yake ? Ganina a tsaye ya kara fadin ke ba zaki zo ki nuna min gurin ba kin tsaya kina shagen kallon tsiya da sauri na daga kafata zuwa inda suke ya bude mota muka shiga da kwatance na nuna mai wurin . Zan iya cewa ban taba shiga mota mai kyau da haduwa ba irin wanan ga kamshi da sanyin AC dake tashi a ciki sa. Tunda muka shiga baiwa kowan mu magana ba har ya sauke mu nima ban samu bakin masa godiya ba yaja motar shi ya tafi. A gajiye na shigo gida don yunwar da nakeji wanda rashin tsayawa inci abinci rana da zan fita ya haifa min jin wanan yunwan da nakeji. Nayi sallama na shiga falin namu suna zaune a falo yana bata fruit a baki na fado falon. Sai kuma na dan ja na tsaya daga kofan a juyo yana kallo na tare da fadin may kika tsayawa mutane akai kina kallo tsaban gulma kuma. A hankali na taka zuwa ciki ina fadin ni nasan kuna ciki ne har yanzu kawai anzo an takurawa mutane na karasa fadi ciki ciki dakin mu na nufa ina cire hijjab din jikina da nikaf . Ban kara fitowa ba duk da uban yunwan da nakeji sai da na daidaici sun bar gidan na fito lokacin har sallah isha,i nayi a cikin don kada in fito in samay su a falon. Na samu kanne na suna cin abinci suna ba mamu labarin kaimu islamiyan dayayi dazun sai dai mamu bata gane wa suke nufi ba a cikin su. Na gaida mamu tun kan in zauna ta amsa da fadin badai sai yanzu kika tashi ba nace har nayi sallah ko mamu tace kin kyauta. Tace yaran nan ke fada min wai yayan ku dazun ya sauke ku islamiya wanne daga cikin su ta tambaya tana kallin fuskana. Wanan daya shigo nan dazun ne ya kaimu na bata amsa tare da fadin mamu akwai abincin rana kuwa don dazun ban tsaya naci ba. Tace ban ma girka wani ba don da yawa nayi dama don bakina sai kuma ta kasa cin abincin sosai nasan bata saba da irin shi bane. Mamu may yasa bata zuwa part din maman su nafisa take zama muna a nan ko yaushe wallahi mamu ni ban son zamanta anan sam. Ke ki rufa min baki anya Sayadi kina da tausayi kuwa yanzu ko ban jata a jiki ba ke ba mai min fada bane injawota a jiki yadda ake mata a gidan nan. Ko haka kika koya ga karatun naki da kike fita dare da rana daukan darasi rashin tausayi ga wani. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:02 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA ALLAHU YA KAIYUMMU, , , , Ranan lahadi da yammaci kawu suna zaune da mamu a falon shi tana hada mashi abincin sa da idan yadawo yake ci sai kuma dare idan zai kwanta yasha yayan itacen da akullun baya katsewa gun matan shi don sun san shine abincin shi. Umar da merry ne suka shigo gidan tun a waje ya san daddy su na gida don motan daddy daya gani a waje. Don haka kai tsaye part din daddy ya nufa da matar nasa dake cikin atamafa buje da riga sai dai kanta babu dan kwali ko hula balle hijjab sai dan kwalin kayan ta dan dora a saman kafadan ta daga gefe. Daga kofan falon ya tsaya yana sallama aka amsa mashi kawu da ya sheda muryan dn nasa tunkan su shigo ya kalli kofan yana kokarin kawar da kanshi gefe daya. Yana gaba tana bin shi a baya suks shigo falon mamu dake gefe zaune tana ganin tare da merry suke ta dan sake murmushi a fuskanta tana tashi a inda take zaune kusa da kawu din tana fadin. A cikin murna yau inlaw dina ce haka ban sheda ta ba kin fito yar African ki tsab wallahi suka dara gaba dayan su banda kawu daya kara tsuke fuskanshi a lokacin. Ta kamo hannun ta tana dan rada mata tayi yadda taga mijin ta yayiwa mahaifin nasa ta amsa da thank you ma. Cike da fargaban abinda zai biyo bayan shigowan nasu umar yake, don bai san irin karban da daddy zai masu ba a lokacin . Sai dai samun mamu dayayi a gurin yasa ya danji sanyi a rashi don yasan komai zai faru kasancewar mamu gurin abin zai zo mai da sauki. Ya karaso har inda kawu yake zaune ya zube bisa gwiwoyin shi tare da dukar da kanshi yace daddy barka da wuni an dawo lafiya ya kasuwa ? Merry da takai kasa da kyat don bujen jikin ta da nauyin ciki tace good afternoon dad. Umar da kirjin sai bugawa yake a lokacin don sauraron amsa kawu din zuwa gare su. Kawu ya dan dago kai yana kallon umar din yace cikin dakiya Alhamdullahi umaru kasuwa ma masha Allahu. Mamu dake gefe ke fadin marry ta zauna da kyau don taji dadin zama mana sai tace a a hakan ma yayi tana son daddy bless on her. Lokacin kawu ya dago ya dan kalle ta yace thank you iam fine fuskan ahi ba yabo ba fallasa gare ta. Dan shiru ya biyo baya falon kafin ya juya wurin mamu ya ce a shiga da ita wai kunu take son sha yanzu. Mamu dai tace to bari aje a dama mata yanzu Allah sarki abu ga mai ciki ita yanzu kunun kawai ya biyo mata a rai ? Dan juyawa yayi gurin ta ya danyi magana da ita ta mike ta bi bayan mamu zuwa part din suka barshi nan tare da mahaifin nasu a falon. Shiru ne ya dan kara wanzuwa a falon sai karan na,uran dake aiki a falon lokacin umar ya rasa ta inda zai fara bayani wa mahaifin nasa don yana tsoron ya sake wani laifi a gurin shi. Kawu ya kula umar magana yake son yi dashi lokacin sai dai da alama yana jin nautin fadin maganan da yazo mai dashi ne. Kawu ya dan kai kishin gide yana fadin umar may ke tafe da kaine don da alama wani magana ya kawo ku gare ni yanzu. Umar din yayi murmushin karfin hali yana gyara nade kafan shi yace eh daddy sai dai ba wani magana bane ina dai son in kara baka hakkuri bisa ga laifin dana aikata maka don Allah ka yafe min. Kai kawu ya girgiza yace yaro ke nan umar idan banyi hakkuri ba kashe ka zanyi aini na hakkuri muddin dai kabi sharadin dana kindaya maka akai ba tare da kuntatawa marainiyar Allah da na zaba maka ba ni ya wuce a gareni ai. Umar ya dan sosa keyan shi yace in sha Allahu daddy zaka samay ni da maka biyayya kamar yadda Allah yace a cikin natsuwa yai maganan shi. Kawu yace daya fima alheri umar yanzu ina dadin wani koda dan uwana yau yazo gidan nan ace wai wanan arniyar ce uwar yayan ka. Ka kwatanta a kanka yanzu zakaji dadin hakan a rayuwan ka wace irin uwa ka nemawa zurin,an ka da zasuzo duniya nan gaba ? Umar yaya kake son mu,amulan mu da iyalin ka ya kasance a gidan nan nan gaba ? Umar a cikin yayana kaf kai nake sa ran rike min zuriata koda bayana ne don hankalina gare ka yafi karkata da hakan sai dai kash ashe ban yi tunane mai zurfi ba da nake wanan shawaran a raina. Maganar kawu ya saka hankalin umar a wani hali sosai a lokacin don shi sam baiyi tunanen wanan ba a gaba shidai ya biya bukatan kanshi kawai don jin dadin sa. Sai yanzu da mahaifin nasa ke fadakar dashi yake tuna hakan hankalin shi idan yayi dubu ya tashi da zancen kawuna da yake mai yanzu. Saboda hakan na yanke shawara akan ku akan abinda ku kuka kasa hangowa nan gaba uwar ku kuma tana goya maku baya kan shirmay da kuke yi din. Lalai kawu yayi ya tuno mashi abinda shi ya kasa tunowa gaba ake duba ba kusa ba don maganan kawu gaskiyane umar yace a ranshi. Kawu ya kare da fadin saboda haka ko bayana idan kuka saba alkawarina ban yafe maku ba umar. Da sauri yace in Allah ya yarda daddy zaka samay ni mai biyayya a gare ka don Allah daddy ka yafe min nayi kuskuren da ba zan sake irin sa ba a rayuwana. Dan shiru ya kara biyo a falon sai kawu yace akwai wani abin ne bayan wanan don ni kaji magana ta na dade da yafe maka don duk mairai bai wuce kaddaran shi sai dai taka kaddaran tazo muna a kyamace don haka nake maka fatan shirguwan wanan yarinyar nan gaba. Yace insha Allahu daddy ina kokari a kai yace kamatsa da hakan don yana da kyau gaba akewa gudu ai. Nagane nufin ka yanzu daddy a gare mu in sha Allahu haka ba zai sake faruwa ba gareni. Ya gyara zama tare da fadin daddy dama tun dana dawo bamu samu zama da kai munyi magana sosai ba don ina son fadama irin ci gaban dana samu a gun aikina a can. Ina jinka kawu yace tare da fadin uwarku tana kokarin nisanta ku dani kan wani dalili nata na banza ta yaya zan iya sanin halin da kuke ciki a yanzu. Yace No daddy ba hakana bane zama ne ban samu yi ba amma ta yaya mama zatace ta nisanta mu da kai. A can bayan kare karatu mataki na biyu na samu aiki da wani company daga nan na wuce karo ilimi ina aikin kuma da na kamala sai gwaunatin kasan ta dauke ni aiki a ma,aikatansu nacan. Ganin irin riban da hakan ke dashi yasa na yarda zanyi aiki dasu na dan wani lokaci idan adadin danake ganin Kawu ya girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin dan nashi yace yaro ke nan sai dai ina son ka sani rayuwan mu yau ba a hannun mu yake ba umaru. Don ko yayane kasanka tafi bukatanka a yanzu don haka ban lamunce ma zaman ka acan ba dindindin kaji na fada maka. Ya amsa da insha Allahu daddy don nima ba zanso yarana su taso da wani akidan da baishafi al,adana ba a yanzu. Kayi tunane mai kyau Allah yayi maka albarka yasa a gama da duniya lafiya yace Amin daddy na gode. Kawu yace zanso ka bani dama in gana da ita matar taka idan ba damuwa don ta fahinci irin gidan da ta shigo. Cikin dauriya da faduwan gaba yace ba matsala ai daddy sai dai kuma ka gafarce ni don nayi wani karanbanin ba ban shawarce kuba daddy don nasai gida tun ina can a nan unguwar aka rusheshi akai min tsarin da nake so gare shi. Kawu ya jima shiru ba tare da yai magana ba yana tunanen halin rayuwan dan nasa na zurfin ciki. Yaya har akai ya sai gida akai masa gina duk basu da labarin hakan sai yanzu yake fada mai ga wanan bakin aure da yayi ace duk yara matan musulmai dake cikin kasan nan da garin kano basuyi mai ba ya jajibo masu kafira a matsayin suruka don yawan zurinfin cikin su bai sanar dasu ba sai da abu yayi nisa haka harda rabo. Sai dai babu yadda zai da dan nasa tunda ya fahinci halin sane hakan ba wai yin kasa bane illar nisan ta su da kowa da mahaifiyar su tayi tun farko duk yajawo hakan. Allah ya kyauta yasa albarka ka more kai da iyalin ka lafiya da yawancin rai. Wani irin dadi ya ziyarci zuciyar umar da wanan adduan da mahaifin shi ke masa a yammacin nnan haka ya bashi daman ci gaba da fadin akwai wasu dana saya a lagos da Abuja sai kanfanin da muke son hadawa ni da wani abokin aikina bayerabe a can kudu. Umar duk wanan lissafin da kake min a ina ka samu kudin yin su cikin wanan dan shekarun da kayi kana aikin ka ? Dan murmushi umar yayi tare da fadin daddy ka yarda dani ba abinda kake nufi din nan bane don idan ka duba can kasan ba irin nan bane da ake tauye ma,aikaci shiyasa mutanen mu yanzu basu son yin aiki a kasan nan. Don albashin can ya nunka na nan nikin baninkin idan kuma kayi duba gani international referner ne na hadin kasa da kasan turai zaka fahinci ta yadda kudi suke zo min a yanzu. Shiru kawu yayi na dan wani lokaci yana nazarin maganan dan nasa kafin yace Allah ya kyauta a dai riki gaskiya ga duk abinda akasa a gaba. Ya dora da fadin a dinga kyautatawa yan uwa da mabukata dake a kwai kasa damu don muna da yan uwa a birni da kauye wa yanda ke bukatan kulawan mu. In Allah ya yarda daddy za a kula zan yi kokarin zagawa a cikin dangi mu kai ziyara kawu yace Allah ya bada iko ya amsa cikin jin dadi da Amin. Kawu yace kaje kazo min da matar taka kafin lokacin sallah ya gaba to in fita ya amsa da to daddy yana yunkurawa ya tashi. Ba karamin dadi umar yaji ba na fahintar juna da sukayi da mahaufin wanda ya samay shi a cikin saukin kai a yadda bai zata ba. A falon mamu ya samay mu zaune ana dariyan merry dake shan kunu tana santin shi don hadin da mamu tayiwa garin kunnun tsamiyan kafin ta dama dama yana aje a ckin fridge din ta don ba kullun ake damawa ba. Muna ganin shigowan shi kowan mu ya natsu muna gaida shi da shigowa gidan ya dan kalli mamu yana fadin daddy yana son su gana da ita. Tace masha Allahu hakkuri bai bar komai ba umar dama nasan in anbi Alh zai sauko a sannu a cikin muryan shi kamar mai rowa yace hakan ne nagode maimuna. Wani kallo na watsa mai da mamakin yadda yake kiran sunan mahaifiyata haka gatsau sai naji ya kara zube min a idona. Ita ko mamu hakan ko a jikin ta bata damu da yadda nasha toka ba na bata raina sosai sai ji nayi tace sayadi dauko mata dan karamin hijab din nan naki na zaman gida ta saka kada taje masa haka nasan shike kara hadasu da yaya. Ba tare dana kallo inda suke ba nace yayifa dauda mamu tace daya ne halan dan Allah shiga ki dauko mata kinji ta fada a cikin zafin rai. Haka yasa na mike na shiga na dauko mata bakin dan just to cover na fito dashi na mika mata tabi da kallo tana dan dariya tare da tambayan yaya zata saka ? Ya juyo inda nake zaune yana fadin taimaka mata ta saka mu tafi dole na taso na gyara mata ta dinga wani rawa ba kunya a gaba shi tana wani juyawa shiko gogan yana lushe ido yana binta da kallo cikin sha,awa. Ya rike mata hannu suka jera a tare suka fita daga falon suna dan magana yana kallonta yana murmushi. Suna shiga falon ta kara gaida daddy a cikin gurbatacen hausan data koya a lokacin kawu dai ya karba mata. Bayan sun natsu kawu yace may sunan ta yana kallin dan nasa yake tambaya yace merry da sauri. Kawu ce merry take to mu nan zamu kirata da maryam ya fada mata cikin harshen turanci ta danyi dariya tace that's my name. Kawu yace maryam ina fatan kin san wanda kika aura ma,ana addinin sa da yaren sa da al,adun mu ? Da sauri ta amsa da yes uncle yace good sai dan zan kara fada maki idan ma shi bai fada maki da kyau ba ki sani mu ga addinin mu mata basu shiga irin wanda kika shigo gidan nan dashi. Kai ta sunkuyar kasa don nauyin maganan kawu din gare ta don ko shi umar din yayi mata korafin hakan. Sai na biyu kin dai san umar musulmine tun kan ki aure shi kika yarda kika aure shi a hakan ta gyada kanta alaman ta sani. Kawu yace good masha Allah yace adfinin mu bai hana mu aure ku ba matukar ba zaku sauya mijin da kuka aura i zuwa naku addinin ba. Sai dai mu Allah ya haramta ma yayan mu ta auren yan naku addinin ga baki daya addinin bai yarda da hakan ba. Da sauri ta dago kai tana kallon Umar din da kanshi yake sade yana sauraren maganan mahaifin nasa. Kawu yace don haka ne nake horon ki da ki bar min yarona yayi nasa addinin tunda mu bamu kyamaci addinin ki ba. Sai dai idan kikai kokarin yin hakan ki sani ni mahaifin shi ne zan iya raba auren ku a duk lokacin da na fahinci haka a gare ki. Tace cikin sauri i will never try that uncle and beside Omar is riligious somebody he will never accept that. Kawu yace again kin ga family din mu babba ne ga al,adan mu shi babba a gida kamar uba yake a gun kowa na wanan family din kada naji wani yaje gurin shi an samu matsala dake. Ita kan may yai zafi haka wanan tsohon yake ta kidanya mata sharuda haka dama haka auren musulmi yake ko nasu al,adan ne haka merry ki rayawa a ranta. Ita dai burin ta shine suyi accepting din ta as a daughter inlaw din su idan ma sun barta a hakan ya wadatar da ita may ya shafe ta da wani al,adun su kuma su da suke can uwan duniya mai nisa in ba ma shi da ya matsa zaizo gida ba yaushe zasu gansu ma. Kawu yace kin san addinin mu ya bamu daman auren mace da daya don duk lokacin da umar yaso kara aure a cikin kabilan shi yana da daman yin hakan. Da sauri ta daga ta kalli tsohon inda yake zaune ta sake juyowa ta kalli umar din kafin ta sada kai ganin umar ya girgiza mata kai alaman ta yarda kawai. Kawu yace sai na karshe dole ne dana ya ding zuwa nan dubamu duk bayan wasu watanni akala sau uku a cikin shekara ko biyu idan kuma zamuyi sallah ya kasance yana gida tare damu a matsayin na babban da a gidan nan . Idan wanan yayi maki a tsarina baki da matsala komai damu muna maku fatan alheri da samun zuri,a masu albarka. A sanyayr merry ta dago kai tana fadin taji tagode kwarai yace ba matsala cikin daga masu hannu yana kokarin mikewa tsaye don zuwa maslaci don sallatan magariba. A daidai lokacin kuma hjy jummai tana shiyan ta tana bala,i jin cewa su umar na gidan tun dazun shiyan hjy maimuna ta dinga surfa ji dali da sauran yaranta. Tana fadin ita bata yarda da wanan tsarin ba watau maimuna mamircin data kulla ke nan na janye mata suruka a wurinta don ta jata a jiki saboda taga wurin ci ko ? Tana cikin wanan masifan ne Umar din ya shigo da merry don su gaisa fuskanta babu annuri take karba masu gaisuwan su. Tare da tambayan shi ance tun dazun kake gidan nan kana wurin maimun da wanan yarinyar makitcin da maimuna zatayi min ke nan tanan take ganin zata bullo min taci galaba na. Ido merry ta tsura mata duk da bata jin abinda ake fadi tana iya gano fada matar keyi da Umar din sai dai bata sa ko a kan may bane ? Umar daya tsaya sauraren maganan mahaifiyat tashi jin tayi shiru yace haba mama tace haba din may babawo yanzu har kai kokarin hada wani alaka kakeyi da matar nan. Nifa daga ita har kakar taku da kake wani soye mata ban yarda dasu ba dukkan su makasa nane idan sun samu wuri don haka ban yarda da hakan idan kunzo gidan nan ku shigo nan kai tsaye daga yau. Yace mama ba haka na bane tun dazun a gurin Alh muke muna magana dashi fa har yaushe muka zauna a gurin maimuna din. Tace Alh may kuma ya kiraku yake fada maku shi bai son a zauna lafiya ina ganin sai na fito masa ta hanyar bayan gida a zauna lafiya don kawai an cusa mai ra,ayi a kanku na kiyayya shine har yanzu abu yakici yaki karewa a tsakanin ku. Innalillahi mama nine fa nakai merry din su gaisa saboda ta damay ni tana son su gaisa da shi na kaita yau dana yana gida sai muka tsaya ya danyi muna nasiha. Daga nan nake fada mai irin plan din dana shiryo a can kafin in dawo and kuma daddy yayi muna magana ta fahinta sosai wallahi. Sai lokaci ta dan sauko tana fadin oho ai dai na dauka wani abi ne kuma yake sharada maku don shi bai gajiya da tsincen mata. Haba mama tun dazun kina ta fada haka a gaban surukan ki mun fada maki ba komai bane kinki ki gane ai shi brother yana da wayau shi . Salma wallahi ki fita a idona tun ban saba maki rai ba yanzun nan a gutin nan abinda nasani zaki tsaya kina mussamin akan shi. Hannu ya dagawa salma din tare da fadin is ok mama don Allah ba haka zancen yake ba zan tafi sallah idan na dawo zamu wuce a nan zan barta. Ya juya yana fadawa merry shi zai tafi masallaci ta zauna a part din mum din shi har ya dawo mikewa merry tayi tana fadin No ba zan tsaya a nan ba nafi jin dadin wacan part din don muna hira dasu a can sosai. Dan tsayawa yayi yana rarashin ta fafir merry tace ba zata tsaya a nan ba don ta karanci hjy dan zuwan ta matar bata da marmari sam tana da dan fada da jin kai. Daidai lokacin har ta fara tafiya ta nufi hanyar fita daga falon sai hjy tace ba masalaci kace zaka ba ita kuma ina zata ? Yace a cin cool voice tace gun maimuna zata tafi tafi sabawa da ita can ai kaga matsalan tun ba,aje ko ina ba abinda nake fadi ke nan ya fara fitowa. Mata da kinibibin tsiya harda wanan da zuwan ta ta sace mata zuciyar ta wai a haka ake son i hada zuria da ita ina wallahi ba zai yuyu ba sam. Merry ka har ta kai kofan mamu can taga fitowan shi hannu kawai suka dagawa junan su ya fice daga gidan zuwa wurin sallah. Haka yaje sallah ya dawo ya samay su a falo da mamu suna dan hira hefi jefi ba wani hira bane sai labarin irin al,adan hausawa da sukeyi. Haka ya shigo ya samay tayi da daya a falon ta sake jiki ga plete din ferfusun kayan ciki a gaban ta tana sha a hankali. Yaji dadin hakan da mamu ke nunawa matar tasa wanda har kasan zuciyar shi ya yaba da hakan sosai don baiga wani kissa da mahaifiyar shi ke fadin mamu tanayi ba shi kam. Don mamu sai kokarin farantawa merry take don kawai ta ingata darajan shi a gare ta wanda ko na munafunci tayi mai dai ya gode da hakan. Yace maimuna zamu tafi dare ya soma da sauri mamu tace dashi km kaci abinci ne Umar da fa abunci nan na zuba maka kai da matarka. Yace banda lokacin cin abincin nan yanzu maimuna ta taso mu tafi kawai in kaita ta huta akwai maganin da zata sha karfe tara. And ina son mu shiga mu duba Amma kuma lokaci ya kure sai dai idan mun sake dawowa kuma. Mamu tace sai ku tafi da abincin don daku na girka dama ta mike tana kokarin zuwa kitchen don dauko basket ta saka masu a ciki. Ina daki ina jin duk yadda sukayi a tsakanin su don tunda na shiga sallah da gangan naki fitowa falon do takaicin mijin da mata saboda tabaran su a gaban kowa babu kunya a tare dasu ko kadan. Mamu ta fito tana kwala min kira na fito na kai masu abincin bakin motar su yace No ki barta zan dauka dare yayi yanzu ba kowa a wajen gidan nan. Sun fito bayan sun mata sallama ne suka hade da hjy maryam data dawo daga unguwa tace a, a umar ashe ku shigo gidan namu ? Yace eh yanzu muke shirin komawa bata damu da kallon ta da yakeyi ba gulma ya cita tana karewa merry kallon kurlla tsab tana kada kai ya wuce merry da bata san tana yi ba tabi bayan shi zuwa inda ya aje motar shi a waje. Da gulma a bakin ta fam ta nufi part din ta cike da tsegumin merry wa yayan ta lokacin nan suka zauna suna dariyan shakiyanci wa halitan merry din suna dariya. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:03 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH SADAMU DA ALHERUN SA AMIN πŸ‘ Hjy jummai dake zaune har lokacin tana fada dakin ta yaran ta kowa na harkan gaban shi don dun gaji da bata hakkuri taki yin shiru suka fita batun ta. Kawu da shigowan shi daga masalaci ke nan ya na dan zagawa dakunan matan nasa ya fara da sashenta don itace babba a gidan idan ya gama sai yaje gun Amma itace karshe su dan taba hira ya dawo part din shi mai girki ta samay shi a can wanan zagayawan da yake a lokacin yakan ji korafin diyan shi da damuwan su. Tun da ya tunkaro sashen yake jin muryan hjy tana masifa ya karasa shiga da sauri don ganewa idon shi da wanda take fadan. Sai dai ga mamakin shi babu kowa a cikin yaran ta da alama ya nuna dashi take fada a lokacin wurin da take zaune ya diba yana fadin ke dawa ke fada haka muryan ki har waje ? Yi tayi kamar bata ganshi ba a wurin taci gaba da fadan ta saida ya tambaye ta a tsawace tace. Alh ina son ka tsawatawa maimuna ta fita harkata don ban shiga nata ba da zatai min kakagida don neman waje da sarakuwa na ta jira zuwan nata sarakan nan gaba. Ya gyara tsayuwa yana fadin haba jummai wai ke may yasa baki hankaline klun yanzu may ya kawo wanan irin maganan don Allah ? Yanzu ace wanan yarinyar sam bata son ma shigowa wurina sai dai taje gurin maimuna inba tasan abinda tayi ta rabani da ita bane. A kan wanan kike wanan fadan haka don kawai an maki kara an karama sarakuwar ki sarakuwa ma kafira har kike wanan jidalin haka ba kunya a idon ki ? Eh banyi mamaki don ka fadi hakan dama kai ba zaka taba hango illar hakan ai do ko mai maimuna tayi daidaine a gidan nan. Ya girgiza kai yana fadin kaji matsalan ki ai indon wanan ne zanwa maimuna magana tafita harkan kafiran sararkuwar ki ina shike nan. Duk da tasan ya gasa mata magana hakan bai hanata cewa daya fi ba haka kawai don munafunci ki shishigewa yarinya ke kinga wurin ci. Fitowa Nafisa tana fadin daddy sannu da dawowa ya hana shi yin wani magana a cikin sakin fuska yace Nafisa an wuni lafiya ya karatu ? Salma ma da lastborn suka fito suka gaida shi ya amsa tare da danyi raha da yaran ya fita zuwa part din hjy maryam dake zaune suna cin abinci da yaranta ga waya a hannunta tanayi. Sun gaisa nan ma yadanyi hira dasu ikilima yai masu saida safe har yakai kofa yaji muryan hjy jummai tana fadin nikan Alh wai maina kashewa Umar ne har yau fa bai shigo nan ba balle ya kawo min matar shi mu gaisa. Amma zai iya kaita wurin maimuna ko ni da wata manufa yake daukana a gidan nan ne. Yace don wanan maganan kika tsayar dani maryam ki tambaye sa mana idan ya shigo tunda kina son shigowan su nan din ne. Yasa kai ya fita yana jin zafin maganganun su duk akan abu daya wanda ba komai bane sai zalla kishi akan yar uwan zaman su din. Zaune muke a kasa saman carpet muna cin abinci sai fauziya dake gefe daya tana fitina kan dan uwanta wai ya sha mata ruwa. Yin sallaman shi yasa duk muka shiga cikin natsuwan mu tunkan ya karasa shigowa muma shiga gaida shi yana amsa muna hankalin shi yana kan fauziya dake kuka. Yace mai akai mata take wanan kuka haka fitina kawai take ji mamu ta bashi amsa yace mutum na fitina babu dalili ina dan dariya nace kawu da ita da samir ne ke fada wai ya sha mata ruwa sai ya debo mata wani ruwan. Yace fauziya baki son kuyi zumunci da dan uwan ki ko baki son ki bashi abinki idan kin girma shima ya baki nasa. Kada kiyi rowa fauziya ke ba antyn shi bane ki kara ruwan yadda kowa zaisha ki kwashe ladan aikin ki ko baki son ladane ? Ya tambaye ta yana kallon fuskanta mamu tace fitina da gangan takeyin shi don kawai ta azawa mutane tashin hankali niko yanzu dan banzan duka zan mata idan bata rabamu ba da kukan banzan nan. Kawu ya duka ya rike hannun ta yana fadin a, a akan may zaki doketa gadon uwar ta jummai tayi mai rikicin gangan don jummai sarkace ko ba dalili sai tayi fada. Aiko tayo mugun gado inji mamu tana dan ya mutse fuska yanzu na samay ta tana jidali tun ina waje nake jin harshen ta na shiga ina tambaya wai dake take fada. Mamu tace subbahanallahi dani kuma may nayi mata ni dake nan yau zan iya cewa tun safe ma bamu hadu ba a gida nan da ita. Yanzu dai tace in maki magana ki fita harkan sarakuwanta ki jira taki sarakuwan in su hussaini sunyi aure. Wani irin gulolon bakin ciki ne ya ziyarci zuciyata lokaci guda tare da yiwa mamu gwai a raina da taba kafira fuska ga goron data samu a baya. Itako mamu cewa tayi ikon Allah ni na dauka hakan karane a gare ta amma ba matsala zan kiyaye in Allah ya yarda . Dayafi maki alheri don jummai bata san ya kamata ba ita sai abinda zuciyar ta ya anyana mata. Allah yasa mufi karfin zuciyar mu mamu ta fada yace Amin ya juya gurina yana fadin yau fatima may aka karanto a islamiyan ne kafin in bashi amsa mamu tace yau basu shiga ba wai malam suna wani taro. Nace kawu kayan islamiyan mu sun dake muna ranan har an dukemu kan hakan wai hijjab dina baikai kasa ba sosai. Yace shine baki fada min ba yana kallon mamu tace da rigima take banace zan yanko masu yadi a dinka wani ba mantawa nakeyi wallahi. Yace gobe insha Allahu za a kawo maku idan na fita yai muna saida safe ya bar part din wurin Amma ya nufa. Sun dan dade da Amma suna hira ya koma part din shi inda mamu ta samay shi bayan ta tabbatar da na rufe part din. Ammace zaune a falon ta tana taunan goro daya zama mata jaraban rayuwa idan tana ita kadai ta kama tauna ke nan har sai ta samu abokin hira ta dan tsagaita. Nayi sallama na shigo ta dago tana kallo na yanayin ta kawai na duba nasan tana cikin dan damuwa ina kawai kwance nace kedawa da safen nan haka kuma Amma ? Ni da dan uwanki ne mana yaro ka shige cikin gari kayi shiru haka ni tun zuwan wanan matar tashi ban gane kanshi ba. Wani kallo nayi mata daga inda nake kwance nace kai Amma dai Amma din nan mutum da matar shi ya manta dake ne mana tunda matar shi tazo. A dan hasale tace au haka zakiyi idan kinyi aure ki rike min majin nawa kada yazo inda nake. Nace nikan mijina ma a ina zaki ganshi Amma balle ki dinga damun shi da mita baizo inda kike ba nifa Amma kilama dake zan tafi don kallon danaga tayi min na gyara magana ta da sauri. Kamar an jefoshi dakin ni kaina saida nayi mamakin ganin shi a wanan lokacin da safe haka . Amma tace ikon Allah kai kuma daga ina haka da safen nan muna maganan ka sai gaka kamar an jefo ka daga sama. Sai lokacin ya kalli inda nake da sauri nace banice ke magana ba itakeyi ita kadai wallahi na fada a dan tsorace. Dama an ce dake ake yanzu dai nake fada maki damuwa na kan rashin ganin shi kwana biyu. Yace wallahi abubuwa ne sukai min yawa Amma yanzu ma na sauke merry church ne daga can na biyo nan mu gaisa. Na mike don in basu wuri Amma ta kalleni tana fadin ina kuma zaki keda kika shigo yanzu shi gudu zaiyi kinji yace daga coci yake . Allah da ka taro min wanan dan wai jininane yau da zuwa coci ni Amamatan da kaina ta karasa fadi a cikin takaici ban fasa yunkurin fitan da nake son yi naji tace zo ki mika mai abin karyawa don nasan bai karya ba yanzu haka. Yace wallahi kuwa Amma kamar kin sani sai dai taje gin maimuna ta tambayo ta idan akwai kunu merry ke son ta sha. Yi nayi kamar ban ji shi ba don kiran maimuna da yayi gatsau ba sakayawa ko kadan Amma tace baki ji ba wai ki je gun uwar ki ki samo masu kunu kin san ya zama mijin tace yanzu. Dan baki na turo tare da fafin ai bansan ita yake nufi ba don naji yace maimuna kaji min ya da fitina A ruwa haka kike fa kamar tsohuwar mace. Shi dai yana dakilan wayar shi bai dago kai ya kallemu ba balle yace yasan abinda mukeyi a falon. Ina fita tace dashi haka ba kyau ka duba yar nan tayi fushi ga yadda kuke kiran uwarta gatsau ba ko sayawa ga bakin ku kamar ba wayayyu ba daku. May zan kirata ya dago kai yana kallon Amma din da mamaki ? Ta dai ci daraja biyu a wurin ka ko uku na farko matar ubankane na biyu sarakuwan ka nan gaba sai na uku ko kunki ko kunso kaunar ubanka ne . Kai Amma ke da wani magana kike wallahi ni wanan duk bai a gabana yanzu abinda ya damay ni ya damay ni. May kuma ya damay ka kaiko yace merry ta matsa sai mu koma gashi ban gama abinda ya kawo ni nan kasar ba ni ban san ya zanyi da ita ba , , , Kai tafi can hular mata har yaushe mace zata saka abinda baka tashi yi ba tare kukazo da zata matsama ko zata hanaka ganawa da yan uwan kane ?. Kai da zaka dinga bata umurni zaka zauna tana baka umurni ko may ka zama namiji a cikin iyalin ka shine cikar kamalan magidanci a idon jama,a ba ya zauna mace na dorashi a hanya ba wanan akidar nasarane. Lalai zama da tsoho wani lokaci babban ilimi ne yanzun dan zaman da yayi Amma ta bashi haske biyu da bai daukeshi komai ba a da. Gaskiyar daddy da yace yana son ya dinga shigowa akalla sau uku ko biyu a shekara don shi yanzu yadda yake jin dadin kasancewa a kasar shi yana ganin abubuwan da ya kamata ayi naci gaba da irin tsarin rayuwan su daya baro a baya. Na shigo da sallama dauke da flask a hannu na na aje a gaban shi tare da fadin wai tace tana lafiya, ? Yace kamar baison bada amsa lafiya take na juya abina nafita daga falon Amma din. Amma tace maimuna ke nan jiyan nan uwarku ta kama hauka wai maimuna tana son raba tsakanin ta da sarakuwar ta don haka yaron nan yai mata iyaka da ku. Yace subbahanallahi may yasa mama take hakane Amma ni abin yana damuna wallahi irin yadda mama bata daukan girman ta ko kadan. Yanzu fa nasan ko na aika mata ba samun kunnun nan zamuyi ba gashi tunda maimunan ta koya mata shan kunun ta zage da sha yanzu haka wanan ya isheta sha har gobe. To ita ai bata duban hakan don kanta kawai ta sani gani take kamar wani abin kukewa maimuna din na alheri. Yace ni har kunyar matar nake wallahi har dinkuna tayi wa merry taki karban kudi amma ita sai da na bata kudi har yau ba a kawo din kunan ba datace. Sai hakkuri uwarkace kadai kiyayye yanzu dama nacewa maimuna ta bari zan maka magana idan kazo ku dinga zama a wurin mahaifiyar taku tunda haka takeso. Ran umar ya baci sosai da jin wanan maganan don baiga abin laifi a gurin tarbon da mamu tayi masu in banda abin mama matar dake kokari danaka ai mai son kane. Ina fita komawa nayi part din mu na kwata cike da mamakin halin irin ya umar ba kunya yake fadin wai yakai matarsa coco a gaban Amma. Har barci ya fara daukana naji murya shi kamar daga sama a part din mu ya shigo suka gaisa mamu ta tambaye shi merry yace ta tafi coci kai tsaye. Tace Allah sarki Allah ya fitar da ita daga wanan akidan Allah yasa tana da rabon gane haske a rayuwan ta. Yace a sayaye Amin nagode yanzu daga gurin Amma nake take fada min yadda kukayi da mama shine na shigo in baki hakkuri kan hakan. Mamu tace babu komai don Allah nake komai gare ku ba kamar yadda hjy take tsamani ba duk wanda ya taimaki wani kanshi ya taimaka. Gani nayi merry tana bukatan a jata a jiki don ta sake jiki damu yasa nake mata abinda zataji dadin zama damu. Don merry bakuwa ce a cikin mu al,adan mu ba daya bane da nata sai ta samu wanda yake lurar da ita wasu abubuwan don tana da saukin kai sosai. Yace nasan wanan maimuna kuma nasan manufarki akan ta sosai shine nake kara baki hakuri kar hakan yasa kice zako janye daga gareta don hakan nima ba zai min dadi ba. Kamar daga sama sukaji muryan hjy a kofa tana fadin yau zanji zan gani wai an birne tsohuwa da ranta. Mata kamar manya idan ba kina da wani manufa ba yanzu abin har yakai ki tura babawo a daki kina mashi hudubar tsiya da zai kini wai a haka ake son lalaka mashi jinin ki mu kaita ina tin yanzu kina kokarin raba shi damu ace ya shigo gidan nan bai zamay ko ina ba sai gurin ki. Muryan hjy maryam ne ke fadin kokarin ta ke nan da manufarta wanan halin ai sai addua yanzu kan don ta rigada ta tura masu mugun akida ko. Dama ita yasan ta ganshi da zai shigo yana rike da flask din kunun da mamu ta aika mai dashj suka hade gaisheta kawai yayi ya shige part din mamu shine taji haushin hakan taje ta tseguntawa mahaifiyar su. Shiru mamu tayi don abin ya daure mata kai bata da abin cewa ga kuma umar a wurin bai dace tayi wani magana mai zafi ba gare su a lokacin don ana barin halas don kunya badon tsoro ba. Umar ya fito ranshi bace yace haba mama wanan bai dace ba matar nan tana kokari duk saboda mu amma ke ban san abinda yasa baki ganin hakan ba. Oh kai baka san halin mata ba ko to ina zaka sani kafan ka na rawa kana son a lakaka ma wanan yar mai zubin aljannu duk shine makircin da maimuna keyi ba komai ba. Haba mama yanzu ma merry ce tace in karbo mata kunu a wurin ta shine nazo fa. Eh lalai shike nan ni nawa ya samay ni abinda nakewa gudu ya soma faruwa babawo kazo gidan nan ko kallon shiyana bakayi ba kazo nan tun yanzu ke nan kafara hakan. Ina ga ka auri yarta hajiya maryam tace lalai fada masa yaya domin wanan dai ba abin hadawa bane duk hakan takewa take take . Jikin umar yayi sanyi sosai takaci ya ishe shi kamar ya buge hjy maryam yake ji a lokacin don itace taje ta hasalo mahaifiyar tasu da alama ma daga barcin safe take ta tayar da ita. Jikin shi babu kuzari ya juya yana fadin mama Allah ya baki hakkuri nidai nasan maimuna taimakon mu take kan hakan amma tunda baki so ai shike nan . Har ya juya muryan mamu data kasa hakkuri ne ta fito tana fadin kaji yaya da wani magana wace yar kike tunanen zan hada da umar wai Sayadi kike nufi ko wa ? Kema yaya da rikici gangan kike kina bi ta wanan hadasanan tana saki abinda bai dace ba sayadi kan ai ba kayan umar bace har nawa sayadi take da aka fara mata wanan hasashen. Umar ai kamar matsayin uba yake a gurin ta don ya wuce ace mashi wa a gurin wanan yar don Allah a dinga tauna magana kafin a furta koda rai ya baci. Ni don zama tare da zumunci nake abinda nake ko kun mata da umar dan dan uwane wai don haka abinda duk ya shafi diyan ku ya shafeni. Kaji munafuka karya kike munafuka ko kin dauka bamu san komai da kike shiryawa bane a gidan nan . Bai tsaya jin karshen fadan su ya juya ya shaki wani iska takaici ya fesar ya fara takawa a fusace ya nufi hanyar fita yana zuwa ya tayar da motar shi ya bar unguwar rai bace. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:04 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, RAFANAHUM MAN KANA ALIYAN, , , , , , Koda Alhaji ya fito inda yake jin yayan bakin natsu ya tsawata tare da tambayan ba,asin maganan a daidai lokacin Amma da mama hadiye suma suka karaso gurin. Kowa ya kasa magana suna tsaye cirko cirko kowa na hadiyan zuciya ya kara maimaita tambayan shi gare su a dan fusace yana kallon su. Mamu tace akan dai maganan diyan ta ne da tayi min iyaka dasu yanzu ina zaune sai ga umar ya aiko yace matar tana son shan koko shine na dama na aika mai a gurin gwaggo. Ina zaune sai gashi ya shigo yayi min godiya sai muryan su mukaji a kofa tana auna min zagi wai harda fadin ina son in cusa mai wanan yar sayadi ne zan kammale ta kan diya da asiri Alh may ya kawo fadin haka udan yaya ta san kanta. Har take hada sayadi da umar wanda yake matsayin uba da wa a gareta. Wanda za a iya zuwa gutin shi neman auren yarnan watarana amma saboda, , , , Muryan Alh ya katse ta da fadin idan ya aure ta laifi ne ko sharia bai yarda da hakan bane ke kika haife shi ke kadai da zaki hanashi hurda da mutane na. Maimuna kanwatace kuma matana kinga yana da daman zuwa neman taimakon ta ta ko ina ke kuma da kike zancen Sayadi ya juya gurin mama har kina fadin wai kanwarsace ko yarshi addini ya hana ya aure ta a hakan ne ? Ko addini ya yarda ni ba zan taba yarda da wanan bakin hadin ba muddin ina raye ai da gurin kwarai mutum kewa nasa fata ba jeka ka dawo ba. Daga hjy har mijin basu taba tsamanin wanan kalamin daga bakin mamu ba uwa ke nan kowa yana son nasa zata iya taka kowa akan danta in dai uwace. Amma tace ai bakin alkalami ya bushe don aure a tsakanin su ba fashi ko da bamu raye kuwa . Wanan wani irin hauka kuke muna a gida na safe daban na rana daban haka da dare yanzu da kuke fadan nan ina shi wanda kuke fadan a kanshi yake. Ke jummai har kullun wai baki hankaline da sanin ya kama may yasa idon ki yakan rufe akan diyan ki ne ? Ina kara ne hakan da babu mai kulasu a gidan nan irin haka rayuwan ki zai maki dadi ne a mayar maki da diya bola dasu da babusu duk daya a gida. Ai mai son ka tsakani da Allah a yara kake ganewa ni wanan jidalin naku ya isheni wallahi kawu yace hajiya ki barsu zanyi maganin su ga badaya tunda kowa ya koyi rashin hakkuri ga dan uwan shi. Mama hadiye dake tsaye takaci ya hanata magana tace ina yanzu ya baro wurin kakanshi yace zai je ya gaida maman su yazo basu bude part ba shine yazo gutin hajiya su gaisa ya shiga gurin maimuna ne ashe ? Nima ina kwace maryam ta samay ni da zancen yaya raina ba zai baci ba ace kana gida danka ya dinga nuna ma halin ko in kula sai kishiyar ka. To kin gani wata kila ya kara samun wurin a rufe ne ya nufi gurin maimuna din maryam kin zama hadasana a gidan nan. Kawu yace sunan take ne wallahi halin maryam.ya isheni hajiya mai ake da munafuki a wuri duk wani fitina da zakiji maryam ce ta hada shi a gidan nan. Ke nan nice munafuka kake daukana hjy jummai tace kece kan don ke kika zo kika samay ni dazancen don ban san ya shigo ba. Amma nima aikin samay da zancen may yasa nake basu fuska kada ta lalata min tarbiyan yara na nace maki idan mun ma Umar hakana bamu kyauta mashi ba bukatan taimakon mu yake so kan matar shi yanzu. Wiki wiki maryam tayi da ido tana fadin kai maimuna ashe ke munafukace haka ke rufamin baki munafukar banza da wofi kin hada wanan kinji dadi ki kara gaba ki gani idan zan kyale ki kawu yace. Sai dai koda suka bar wurin sai maganan da akaiwa mamu ta baibai ya tsaya mata a rai duk aunin tana faman tunane nikan ina ta sharan barci na don ba inda zan tafi ranan. Sai biyu idan nayi sallah nake son zuwa kitso don hakane ban tashi da wuri ba a can dan gaba damu akwai mai mun kitso idan kuma ina jin kiuya in tsaya Aisha ta jagwalgwala min kaina hakana duk da mamu ta iya bata tsayawa yi min kitso sai naci sa,a take kwashe min kan wai na faye tsawon gashi ga yawa ita bata da lokaci takan ce min. Har lokacin dana yi sallah nashirya don zuwa aurin kitson na fito na samay ta zaune a falo tana dunkulawa Fauziya kai nace mamu nima inzauna ki min tace banjin dadin jikina Sayadi kije wurin kitso zaifi maki. Na dan turo baki gaba alaman fushi ina dan kunkuni na nufi hanyar fita waje a cikin tsawa tace min kyauta zasuyi maki kitson a can. Na juyo ina fadin gun Aisha zanje tayi min tace a tsawace zaki zo ki karbi kudi kije inda za a kwashe maki dakyau ko sai na bata maki rai yanzu da wanan dunkulan da Aisha kan maki a kai ba kyau gani. Ina Aisha zata iya kama maki wanan kan naki haka da kyau tana magana tana watsa min harara nace mamu a can sai nabi layi dole fa. Ta kara daka min tsawa daya razanani na makale gefen labule ina kallon ta a raina ina fadin lalai yau mamu ba lafiya kan. Bada ke nake ba ko taurin kai kika koya ban sani ba nace da sauri a, a mamu naga rana yayi ne dama ba zan , , , , . Ke karbi nan ban nemi jin komai ba ki wuce kije shagon linda tayi maki kitso yanzu na iso da sauri na karbi kudin ina fadin na gode na fice da sauri ina mamamin maike faru da mamu haka take a hasale ? Haka na fito kamar ina tsoron takawa da karfi ina tunanen halin da naga mahaifiyata a ciki na bacin rai kodai dazu da barci ya fara daukana haniyar da naji sun fara ne ? Part din Amma na nufa a lokacin ko Aisha zata tafi mu tafi tare a zaune na samay su suna cin abincin rana nace Aisha zakije shagon linda wurin kitso ? Tace yau kuma kin tuna da linda ne zaki wurun ta ? Nace ban san may ya samu mamun mu ba yau na tashi na ganta a cikin bacin rai da nace tayi min koke ki min sai ta hauni da fada wai inje can ta kwashe min kai. Amma dake zaune tana jin mu ta tabe baki tace mai ko ya samay ta banda halin nasu sukayi yau muna nan naji fada ya kaure a gidan. Ashe munafukan nan ce maryam ta samu jummai da tsegumin taga sadauki zai shiga gurin maimuna. Ita ko da bata da tunane sai ta taso da fada tunda bata girma hankali bai zo mata na tunanen may ya kaishi can ba. Aisha tace kai maman su ikilima ita ko kunyan munafunci batayi may ye a cikin wanan halin don Allah ? Nace ita mamu bata rabuwa mata da diya a zauna lafiya tunda tana da yaranta itama Ammace ta katse ni da fadin. Don may zata rabu da dan dan uwanta akan wani dalili mara tushe can idan ta rabasu yanzu zata rabasu nan gaba ne da yake shirin zama surikin ta ? Aisha tace suriki kuma Amma tace wayan gobe banda Allah abu suke basu tunanen gaba dan tsaban kishin tsiya. Ni dai ban damu da zancen Amma ba don raina a bace yake ga halin da na ji ya batawa mamu rai har take son sauke haushi a kaina ga banza. Hjy jummai ne a falonta tana zuwa tana dawowa ranta a bace kallo daya zakai mata ka fahinci halinda take ciki na bacin ran. Su Aliyu dake zaune suna karyawa a lokacin don da dare sosao suka iso kano daga Abuja sunje can cika wasu takardu nasu ya dan kalli uwar yana fadin mama yau ko lafiya ? Ta juyo gare shi fuska daure tace kira min yayan ku. Yace to ya dauko wayan shi dake gefe ya shiga neman layin yayan nasu kira biyu ya dauka yana fadin Aliya ya akayi ne ? Bros mamace ke son magana da kai yace lafiya wani abu ya farune kuma ? Ta karbe wayan a hannin Aliyu a lokacin tace sai wani abu ya faru ke nan zan kiraka ko ? Kiyi hakkuri mama ba haka nake nufi ba . Ta dan gyara tsuke fuska tace duk inda kake kazo gida yanzu ko a ina kake ina son ganin ka yanzun nan. Mama gashi yanzu ina, , , , , Ban tambayeka inda kake ba umurtan ka nayi da kazo yanzun nan ina jiran ka tana fadin haka ta katse layin tare da mikawa Aliyu wayan shi. Aliyu daya gama karanta bacin rai a fuskan uwar tasu yace mama kila yana wani gunne kin san yanzu aiki yayiwa bros yawa. Ta katse shi cikin daga mai hannu tana fadin Aliyu ka fita idona tun kan na saba maka rai a wurin nan. Habbib dai yana zaune sai cin abincin shi yakeyi bai tsinka mata ba kamar bai gurin a lokacin. Haka suka zauna zurun zurun zaman jiran zuwan dan uwan nasu don suji abinda ke damun mahaifiyar tasu haka tayi mashi kiran gagawa hakan. Da sallama a bakin shi fuskan nan a daure da baka ganin fara,an shi ya shigo part din yana bin su da kallo a yadda ya samay su zaune din tare da fadin lafiya dai ko ? Sai Aliyu ne ya nuna mashi mahaifiyar tasu da hannu yana fadin muma dai haka mukaji kiran bamu san dalili ba bros. Hjy ta dago rai bace da idanun ta da sukayi ja jajir tayi mai kallon ni ka raina tace babawo ashe ban isa da kai ba a gidan nan ? Ni zaka mayar mutumiyar banza a idon mutanen gidan nan kana kokarin ka nuna masu ni ba kowa bace a gare ka yanzu. Haba mama mai yayi zafi haka har kike wanan irin magana yanzu tace daga yau nayi maka iyaka da duk wata mace a gidan nan. Ba maimuna ba kawai kowa nake nufi da hakan idan kuma kace bazaka ji magana ta ba you will see my worse a kan ka mara tunane kawai. Akan wata yarniyar matarka can kake son take magana ta don kawai ka dadada mata rai niko nawa ya baci suna shigewa suna maka kulle kullen sheri kai baka sani ba wake yarda da mace idan ba kuba sakarkaru. Ka shiga hankalin ka dani a kan maimuna da wani tarkace nata if i see you near her again i will show you my true clour. Haba mama bros namiji ne fa ba mace ba Aliyu ya ce wani wawan mari ta yarfa mai da bai zata ba a lokacin sai da kowa na falon ya dago yana kallon ta. Aliyu ya dafe gun don marin ya shige shi sosai har cikin ranshi ya jishi idanun shi suka juye a lokaci daya sukai kwamcin jini ya mike tsaye tare da mata kallon ni kika mara ? Daga haka ya fice a falon rai bace dakin su ya nufa ya fara harhada kayan shi a ckin fushi. Yana fita ta juya gurin Umar dake kiran Aliyu din tace kai kuma ka kiyayyeni don ina kyale ku kuna abinda kuka ga dama kada ku dauka tsoron ku nake ji hakan. Kai har ka isa ka turo dokan dana sa a kanka kake gani yanzu daga yau ina son ku sani ban magana yaro ya ketare min zance na a gidan nan. Amma mama kan wanan maganan kika mari Aliyu haka a gaban kowa mu har da kannen sa ta daga hannu zata mare shi habbib yace kada ki soma mama is enough don Allah mama may ke damun ki yau marin bros wani fitina ne babba a gare mu. Waye shi da ba za mare shi ba ko a gaban kowa da zaice zai fada min abinda ya dace dani mama wanan kuskure kike a rayuwan ki. Kan maganan ku na kishi bai kamata ace kina sakamu a cikin shi ba ko salma da take mace ai bai dace su shiga zancen ku ba balle mu. Irin haka ke sa muna nisa dake wallahi ni badon Aliyu daya matsa muna kan lalai sai mu dawo gida ba babu abinda zan dawo inyi a nan yanzu din nasan abinda zamu dawo mu tarar a gidan. Haba mama yanzu ai mun wuce wanan hukuncin haka a gare ku idan kina muna haka ta yaya na bayan mu zasuga girman mu tunda a gaban su kike muna komai ni wanan zuwa gidan Allah ya gani banji dadin shi ba wallahi . Dama nasan kai fitsarare ne sai ka zo ka rama mashi marin tunda kaji zafi abinda nai mai da bakazo ba kaga sakona ne. Zai kara magana Umar dage gefe kanshi a sunkuye sai idanuwan shi da ke fitar da kwala ya daga mai hannu yace habbib mamace ka kyale ta tana da iko da daman yi muna duk hukuncin data ga ya dace damu idan mun kauce hanya. Ya juya wurin ta yace Allah ya huci zuciyar ki mama shike nan ina iya tafiya ya fada murya a sanyaye. Tace kadai ji abinda nace yace na gode ya juta ya marawa habbib baya daya riga da ya fita kafin shi yana kiran sunan habbib din. Kafin ya kai Aliyu ne ke fitowa jaye da jakar kayan shi ranshi a bace ya nufi hanyar fita gidan da sauri suka nufi gurin shi . Daidai da fitowan mu da Aisha zuwa gurin kitso ke nan muka tsaya muna kallon su don dagani ba lafiya ba dai kowa ranshi a bace. Ban san lokacin da Aisha ta sulale ta kira Amma ba saboda kallon yadda suke faman rike dan uwan nasu da sukeyi yana fisgewa sai jin muryan Amma nayi tana salati tare da mama hadiye Amma na fadin yau may zan gani haka a gidan nan ? Haka yasa na juya da sauri inda nake jin sautin muryan nata ina kallon ta tana sauri ta karasa gurin su. Mama hadiye sai kokarin kiran kawu a waya takeyi a lokacin may haka kusan yaki may ya hada ka da yan uwanka da alama kokarin barin gidan kake gadanga kusan yaki. Da kyat habbib ya buda baki yace bada mu yake fada ba tsohuwa da maman mu ne ya dau zafi. May kuma ya hada shi da uwar taku tana kokatin kama hannun shi da umar ya rike suna kallon juna sai dai ya kasa magana a lokacin don zafin ran da yake ji. Ina jummai din mai tayi mai haka naga kamar kwancin jini a idanuwan shi dukan ka tayi komay haka ? Umar ne ya yi karfin halin bata amsa yace dan matsala aka samu amma shine ranshi ya baci yake shirin tafiya wai. Ta kara rikeshi da kyau tana fadin ji nan gadanga ba, a fushi da iyayye fa daga yau ka daina hakan kayi fushi da uwar ka har kace zaka bar gida. Ka nuna mata abinda tayi ma yai maka zafi ke nan ko may laifi ne idan iyayye suka tsawata wa diyan su baku gani ga mahaufin ku har gobe bai wuce fada a gurin mu ba ai. Ina yake shirin zuwa muryan kawu ya na tambaya a hasale yana kallon Aliyu din a lokacin kam kowa na gidan yana waje har Ahmed da suka shigo da kawu din. Kawu ya kalle shi yace maida kayan ka ciki kafin muyi magana ba musu ya juya da kayan zuwa part din su daga haka bai fito ba ya samu wuri ya zauna. Kawu ya juya gurin umar yace umar faruq kaine babba kayi kokarin koyar da yan uwanka hakkuri . Kana kallo yana irin wanan tabargazan haka a gaban kannen shi da kowa ba kunya wai gida zai bari. Daddy kuyi hakkuri abinda muke lurar dashi ke nan kuka iso nan yanzu yayi kuskure ba zai sake ba insha Allahu. Ku tafi bayan sallah magariba ina neman ku dukkan ku har iyayyen naku kawu yace yana wuce wa abin sa suka amsa da Allah ya kaimu daddy. Daga hakan kowa ya watse cikin shi cike da gulma don ba wanda yasan mafarin maganan sai su yasu yasun su yan part din. Umar kan fita yayi gidan yayin da habbib ya samu Aliyu a dakin shi yana kara bashi hakkuri kan kuskuren da yake son tafkawa. Hjy jummai tana part din ta bata fito ba bakin ciki nadama damuwa da tashin hankali sun ishe ta a lokaci daya ta rasa inda zata dafa taji sanyi a ranta lokacin. Don tana ganin yaran suna son sufi karfinta a lokacin don irin yadda take ganin take taken su a lokacin. Amma kan dasu mamu da mamaki a ransu kowa ya shiga part din shi suna mamakin abinda yai zafi haka har ya jawo wanan matsalan. Mun bar gidan tun kan su bar gurin muna hanya umar yazo ya wuce mu da motar shi lafiyayya mai daukan ido. Aisha tace sukan masu kudi nan najin dadin su kiji wanan motar kamar a baka ka lashe don kyau na kalle ta nace ke motar yayan su salma ne fa baki ganta a kofan gidan mu ba aje da zamu fito. Tace bata kula da motar ba ai yanzu shine a wanan hadadan motar nace sai dai babu matar sakawa a motar ba . Kin kashe masa mata ne Aisha ta tambaye ni cikin kallona nace wanan arniyar zai nuna a matsayin matar shi idan ba don baida kunya ba. Tace A ruwa kin san abinda ya daure min kai naso fa inji abinda ya hada yaya Aliyu da maman su har sukai fada haka wanan matar mai son diya kamar ta mutu balle tana ganin su sun zama taurari. Nace wallahi niko haushin su Amma naji da suka hanashi wucewa don dai kawai ranta ya kara baci kamar yadda tasa Mamun mu bacin rai yau. Ke muguwace Aruwa idan tsiyan ki ya tashi idan an barshi ya tafi wa yasan halin da zai shiga a can kilama ya wuce inda ya fito a daina jin labarin sa. Nace to wa ya damu dasu dama mutanen da basu taimakawa iyayyen mu uwar su kawai suka sani ni kin san karin takaicina dasu tace a, a sai kin fada. Nace yadda suke kiran mamu da sunan ta gatsau hakana kai tsaye ai ko banza taci hjy ko gwaggo a wurin su dai. Tace ba mamaki fa hjy ce ta hana su kirata aiko su salma haka suke ce mata wani lokaci yanzu dai ne naji suna dan cewa maman fauziya din. Wallahi duk ranan da suka kira sunan mamu a gabana sai naje gaban uwarsu ince ke jummai kaza sai ta kai min duka a kafada tace zaki iya shi shago ina son ki wurin jidali ai. Haka mukai ta shakitanci a kansu har muka isa saloon din bamu dawo ba sai gab da magariba muka shigo gidan yana tsit kowa na dakin sa nasa ya damay shi a rai. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:04 - 🀐🀐🀐: ONCES MORE AGAIN ASSALAMU ALAIKUN YAN UWA MUSULMAI YAYA RUWA YA LOKACI ALLAH YASA MU FI KARFIN ZUKATAN MU AMIN, , , , , Na idar da sallah har isha,i na fito falon inda su mamu suke ta dago kai ta kalle ni tace koke fa gaki da gashi sai ki tsaya ana dunkula maki shi wani iri gashin ki na wullakancewa nan gaba idan ya zube ai kya nemay sa. Nace mamu ni idan zai zube duka ma ina so in huta wanan wahalan kitson har shawan kai askake ne idan na gani. Tace shike nan kin zama irin su meery yayan ku Faruq nace da sauri arniya fa ke nan mamu ? Tace to ba haka kike so ai yana daga cikin bambamcin mu dasu don Allah ya halasta muna aje gashi mu gyara shi yana daga cikin bambamcin da maza sai kumshi a kafa gashi ke duk bakya son yi. Nace mamu harda kushin tace kwarai musaman irin namu na asali yana bada sha,awa da lafiya da kariyan mace daga tarkon aljannu. Koda a hannu ne ko yan tsun ki ya kasance kina saka lale dai nace tsiyan abin makaranta basa barin aiyi kumshi. Tace ba jakkadun shedan bane su ta yaya zasu bari muyi abinda Annabin mu ya umurce mu muyi wayan ta ne yayi kara ta dauka sunan mijin su ta gani take fadin Alh ne ko lafiya yake kirana yanzu ? Nace ina zama zan fara zuba shinkafa da salad din da suke ci mamu kin manta da yace bayan magariba yana neman ku falon shi ne ? Ba ruwa na da rikicin yayan hjy sayadi wanan matar bata sona da alheri na gama karanta ta har wayan ya katse bata daga ba ina kallon ta can ya sake kira ta daga yace kin manta da ina neman ku ne a sashe na bayan sallah. Tace naga maganan bata shafe ni ba Alh tunda tayi min iyaka da yayan ta don Allah ka fitar dani cikin wanan zancen ban iya jidali kullun kan dan kankanin abu a gaban diyan mu. Yace haka kikace ya kashe wayan ko mai mamu ta gani ta tashi tana kunkumi ta fita daga dakin naci gaba da cin abincina muna kallo da kanne na kafin barci ya dauke su. Daya bayan daya suke shigowa falon da sallaman su kowa nayi wa kansa wurin zama a gefe daya samu inda yaran suka ware kansu a gefe daya. Kowa na maganan zuci a ransa banda hjy da ta tasha mur wa kowa har diyan nata abin alfaharin ta a duniya. Har Amma yau a falon dan nata tazo don amsa kiran gagawan da yai masu a zauna da yaran shi ba wanda yasan manufan yin hakan. Wai Alh zaman may muke a nan haka ina kowa ya halar ai a kan mutum guda zamu tsaya mu bata lokacin mu haka ? Ido kawu ya zuba mata cikr da zafi da takaicin ta yace lalai jummai baki da ta ido mutum dayan ita bata da hakkin jin tsarin gidana ne kokuwa ? Yadda kike da hakki da ke da diyan ki haka take da hakki da ita da diyanta a gidan nan don haka ki kama bakin ki sai ga mamu tayi sallama a falin cikin zubulelen hijab din ta wanda ya rufe mata ko ina sabanin sauran dake zaune kimkan a falon don dan gara jummai atamfane a jikin ta. Bayan kowan su ya zaunane kawu ya bude masu da addua kamar kullun ya dan ja lokaci kafin yace yau ina kasuwa aka kirani hankali tashe a gidan nan. Wanda banji dadin abin danazo na sama a gidan nan ba don hakan ya nuna munyi sakaci da tarbiyan yaran gidan tunda har yakai da yana iya fushi da iyayyen shi kadan karamin matsala yace zai shiga duniya. Amma ta karbe da fadin hakan baiyi dadi ba sai dai kasan aikin kurciya yadda yake kuma fa Aliyu ne mazan fama. Ya juya gurin yaran tare da fadin irin tarbiyan da muka baku ke nan ko irin tarbiyan da zaku ba diyan ku ke nan nan gaba ? Kowa na shiru sai hjy jummai dake aikawa mamu harara tana dauka itace ta kira Alh ga waya don sheri. Alh ya kula da hakan tun lokacin dayai magana sai taji yace yau idan badon hadiye data kirani ba da tafiya ke nan zakayi ko don ba wanda ya isa dakai. Ran maza ne ya baci yau ai ban san wanan Aliyun nawa da zuciya ba Amma ke fadi tana dan kallon shi. Fada sosai yayi wa yaran kafin yasa ya ba uwar tasu hakkuri ya juya gurin hjyn su yana fadin mamakiyi hakkuri a sanyaye. Alh ya dubi hjy yace ke kuma ki yafe masa tace aini ban dauka da zafi ba dama fada ne dole in masa don bata zaci Alh zaiso jin fadan ba a lokacin. Sai muryan shi taji yana fadin ai zanzo ga na dan zan so naji abinda ya kawo wanan fadan haka ? Ya juya gurin Aliyu tare da kafe shi da ido yana fadin ubana may yayi zafi haka ka fada min gaskiya al, amarin. Da sauri hjy tace ai ba dole bane duk abinda mukayi da yarana a daki sai anji shi a waje don kowa na siri da diyan shi a daki. Bai kulata ba yace kai nake saurare don wanan yazama dole in ji shi don ba karamin magana bane a gurina ifan kina daukan shi da wasa ke ya fada tare da juyewa zuwa namijin zaki lokaci guda. Ganin haka Aliyu ya fara fadin No daddy kawai dai don nace ta bar brother yayi gaban kanshi yanzu shi ba yaro bane don kawai tace bata son shi da hurda da maimuna shine nace bai dace tana samu a harkan su na mata ba shine tayi min wanan marin. Ikon Allah kan dan wanan maganan don kawai ya fadi gaskiya jummai zaki hana Umar hurda da maimuna ne ko ta halin kaka. Eh to ban dai sani ba ko a yanzu zaki iya kiyi nasara amma a lokacin da ya zama surikin ta na gaskiya nasan ba zaki iya ba sai wahal da zuciyar ki da zakiyi kawai. A hasale tace dama burin ku kenan ku kwace min dana daga gare ni na gano shirin ku shiysa nake sin yiwa hakan ruwa tu yanzu. Ke nan kina iya ja da ikon Allah na fada maki aure a tsakanin yarinyar nan Fatima da umar ba fashi haka tsakanin Aisha hadiye da Aliyu habbib da Rukkaiyan balarabe. Ihun hjy jummai saida ya firgita kowa a falon tana fadin wallahi karya kasha Alh wanan ba zai taba yuyuwa ba sam. Don an maishe ni mara iko zaka tsara son ranku don kawai an zuga ka kan hakan bazan taba yarda a hada jina dana maimuna ba kai duka ma ban yarda a aura masu matan da hankalina bai kwanta ba ai nima ina da yayan yan uwana da suka dace dasu. Kawu yace kiyi duk abin da zakiyi wanan magana ba fashi a cikin sa muryan mamu ne take fadin haba yaya kadai gyara zancen ka kam badai sayadi zaka hada da wani a cikin yayan hjy ba. Don wallahi wanan abin ba zai taba yuyuwa ba ni dai su basuyi min komai ba a rayuwana ita dai ce ba zan hada iri da ita ba don kowa nason ma dan shi kwanciyan hankaline. Shima ai Alh da gangan yayi wanan hadin don yasan ba abinda zai yuyu bane ya hada inji hjy maryam mara zuciya. Mama hadiye ta karbe ta da fadin don may ba zai yuyu ba kanwa ke aikin ki kenan maryam baki gyara sai bata zance to idan ya yuyu ki hana. Maryam kyale hadiye duk munafukai ne don da ita akai wanan shirin don kawai su cusa diyan su ga yayana anga wurin ci watau ko za a zo aci banza. Sauikin abin dai ba kanki aka fara diya da arxiki ba don in kinga nawani a garin nan baki ko motsi mama hadiye ke magana ta kare da fadin babu yar dake da mugun kama a cikin diyan mu. Wata kilama idan yaya ya barsu baiyi wanan hadin ba su dauko muna wanda sai kinyi mamakin sa mu bamu tayar da umurnin dan uwan mu don musan muhinmancin da a gare mu. Koma dai may nene ni ba a wanan hadin dani mamu tace don kowana ma dan shi fatan shiga gidan arzikine ba wurin tashin hankali ba . Kai haba haba maimuna yaushe kika zama haka har kike fada akan yar ki yar farin ki ban so jin haka daga bakin ki ba Amma tace. Gwaggo in dai in zauna wanan tana gasa min magana kullun ne abin ya fara isata nima banyi maraba da wanan hadin ba kije ki jika diyan naki kisha. Kawu ya dubi Amma da zatai magana yace hjy ki kyale kowan su yayi haukan shi don ba sauraransu zanyi ba na gama maganata ya dubi diyan nasa maza yana fadin zaku iya tafiya abin ku a kara da hakkuri. Kowan su ya mike jiki ba kwari suna fadin sun gode suka fice daga falon zuciyar su babu dadi ga uwayen nasu. Amma tace dama idan tura yakai bango haka ke kasancewa don bai kyau wanan halin tun kuna yin shi a bayan idon yaran nan yau har gashi kunyi a gaban su. Aure ne ba wani abin haramun ba zai hada kowan ku ke wanan bakin rantse rantsen haka hajiya aiki barsu in ga iyakar su akan zance watau ke maimuna kina son nuna min ban isa da yarki ba ke nan. Don ita ta dade da nuna min ni ban isa da yayana ba a gidana yanzu gashi kema kin nuna min hakan a gabana maimakon mamu taci gaba da magana sai ta fashe masu da kuka tana fadin yaya ba ai mi adalci bane wanan yar itake nan ubanta ya bari a duniya. Sai ace za a hadata da jinin hjy jummai don kawai a kuntatawa rayuwan mu ko may da sauri kawu ya kalle ta tace maimuna da bakinki kike fadar wanan maganan haka a kaina yau din kawai nayi bugun gaba da fatima ? Tace ba haka bane yaya a cikin kuka ni kowa zaka bata ka bata amma dai ba cikin yayan jummai ba kan matar da ta fito fili ta nuna bata yarda da hakan ba zaka hada yar nan da diyan ta. Ya gyada kai tare da kada kafan shi Amma ta kalli mamu tana fadin kin ga maimuna tashi ki bar falon nan tun ban kai ga saba maki ba mara kunya kawai. Mamu ta tashi ta fice daga dakin tana kuka gwanin ban tausayi a yadda naga ta shigo dakin ina zaune ina karatu da kallo rabi da rabi na mike da sauri ina fadin mamu mutuwa akayi ne ? Bata tankani ba sai rufo part din da tayi ta juyo gare ni tana fadin ki kashe kayan kallon nan kije ki kwata hakana. Na mike nayi abinda ta ce min daga haka na kwanta zuciyana cike da tunane kala kala ina faman sake sake a raina. Washe gari mun shirya tsab a cikin uniform muka nufi hanyar part din kawu don mu gaida shi don lokacin da muke tafiya school bai fito ba wani sa,in shiyasa muke samun sa a falon shi mu gaidashi da kwana. Kawu yana zaune saman kafet din sallah dake falo daga shi sai babban riga a jiki sa yana duke yana karatun kur,ani kawu mutum ne dogo ba sosai ba mai dan jiki ya kwaso jikin su Amma da haske shima wanda wasu daga cikin yaran shi suka debo a guri shi. Kawu mitum ne mai dattako da sanin ya kamata a zamana gidan sa ban taba ganin bambamci a fuskanshi ba gare ni. Ga ilimin addini dana boko daya ratsa shi don ranan danaji yana turanci sai dana sake baki ina kallon sa haka idan yana larabci da malaman islamiyan mu sai kace a saudiya aka haife shi. Sai da Kawu yakai ayyah ya juyo gare mu yana fadi a cikin fara, a kamar komai bai faru ba a daren jiya fatima har an shirya zuwa makarantar yana kallon agogon falon shi yake magana. Nace kawu ina kwana don tun ranan da su salma sukai min gorin ba ubana bane shi Amma tace in ba ubanki bane ai kawun ki ne don haka kema yarsa ce ta cikin shi Allah dai ne bai nufa shi zai haufe ki ba tun ranan na fara kiran shi da kawu a bakina a gaban kowa kuma. Fatima zaku fita ke nan uwar ku zata kaiku ko motan gida zaku bi nace motar gida zamubi yau tace bata jin dadin jikinta yau. Yace to ku kula da kanku ki kula da kannen ki kiji Allah yayi maku albarka nace amin cikin dan siririyar murya ya daga gefen kapet din da yake zaune ya ciro sabbin yan dari biyu guda hudu ya miko min yace to ga kudin taran ku nan na yau. Na karba ina godiya muna shirin dagawa yace banda fada dai a schoool din kunji ko nace insha Allahu kawu a daidai lokacin su Salma suka shigo falon suma Nafisa tace ashe har kun shirya. Kuma kinga A ruwa na manta banyi assignment din maths dina ba fa nace ni tun a school nayi abina ranan. Mun fice mun barsu da kawu suma yana gaisawa dasu muka fito daga falon muka barsu a ciki basu wani dade ba suka fito su ikilima suka shiga ba group din dake yarda su shiga da yan uwan su ganin haka nima na koya a gidan. Mun dawo har lokacin mamu tana a yanayin da na barta a cikin hakan mun samu tayi muna abincin da zamuci idan mun dawo nina bawa yan kanne na don ita tana daki dunkule har lokacin. Muna zaune muna cin abinci mama kubura tayi sallama a kofan falon mu muka tare ta da murna tace ke fatima idon ki ke ga ke baki zuwa wurin kowa garin nan sai idan anzo gidan nan ake ganin ki. Nace mama ba inda muke zuwa ne sai makaranta tace harda in anyi hutu ba a zumunci ke nan ko nace islamiya muke zuwa mama. Rufa min baki ai baki da laifi anty maimuna ce mai laifin tace ina antyn take ne da hannu na nuna mata kofan dakin mamu. Mama kubura kanwar mamu ce da suka hada uba duk cikin yan uban su tafi shiri da mamu sosai mamu na zuwa itama tana zuwa gurin ta sosai akai akai basu yada zumuncin su ba don sauran ukun maza ne su. Ta shiga sun dade banjin hanayin su sai can na kama jin kamar kuka a dakin haka yasa na kashe kunne na ina sauraren su. Muryan mamu nake ji tana kuka abinda ya kara samin natsuwa da sauraren su ke nan a dakin daga falo inda nake. Yaya yaya zai mun haka kuma gwaggo ta goyi bayan shi idan nayi magana ace banyi daidai ba ya rasa wanda zai hada da zuriata sai diyan hjy jummai ina ma laifin Ahmed da yake nuna mata so a fili haka kodai da bai baiyana ba. Yafi mun don ya halin shi yafi kwanta min a rai sau dubu da wanan hadin da yayake son yi matar da ta nuna a fili ba a boye ba bata so bata kaunar mai kaunana a duniya. Zan yarda a kaita akai mun ya inda za a salwantar mata da rayuwan ta ita kadai nake gani a duniya mu tuna da mahaifinta. Mama kubura tace nima dai abin ne da daure kai wallahi wanan hadin fitina kawai za a yi a gidan nan karshe rayuka suzo su baci. Yanzu dai dole samu gwaggo zamuyi ansan yadda aka gyaro zancen a samu a shawo kan yaya sani ya janye wanan maganan. Jin zasu fito yasa na bar falon da sauri na shige daki na ba a dade ba naji muryan su suna zasu fita mamu na fadin ina nake daga dakin mu na amsa da gani nan ina shirin islamiya. Tace kijirani mu dawo zamu shiga wurin gwaggon mu ne na amsa da to ina tunanen wai maganan wa akeyi haka don kurciya ya hani fahintar may suke magana a kai. Sun samu Amma a falon ta aka gaisa ta dago sau daya ta kalli Mamu ta kawar da kai gare ta alaman fushi take da ita har lokacin ita ma. Bayan dan shiru mama kubura tace gwaggo munzo wurin kine akan wanan maganan daya fito jiya daga bakin yaya na hada fatima aure da dan wurin hjy gidan nan. Gwaggo sai nake ganin kamar in anyi hakan kamar anyi ganganci sanin halin jummai da kowa yayi a gidan don ba zata barsu su zauna lafiya ba karshe ma yarinyar ita zata sha wuya tunda itace mace. Maimakon Amma tayi magana sai ma ballan goron ta da tayi tana tana kaiwa bakin ta. Mamu tace ni abinda yafi kona min rai wai fa bako Aliyu ba sai umar dake da mata ga uwar shi azzababiya da wani yar nan zataji. Sai lokacin Amma ta dago kai ta watsa masu wani irin azzababen kallon daya sa suka shiga hankalin su a lokaci daya kowa yaja bakin shi yai shiru. Sai can tace yanzu dai tunda kunfi dan uwan naku sanin ya kamata sai kuje kuyi abinda yafi zama daidai ko baki haka ba ai kin nuna muna kekeda yar ki bamu ba don haka ku tashi ku ban wuri da maganan banza. Ke maimuna in kina da kunya har zaki kalli idona ki fada min abinda dan uwan ki ya zartan akan yar ki yau bai maki dadi ba don tsaban raina mutane da kikayi . Maimuna kin ban kunya wallahi yau idan wani ya fada mi zaki iya aikata haka zan ma maishi musune sai gashi a gabana kika nuna min mu ba kowa bane a gare ki. Gaki ga yar taki sai ki zaba mata wanda kike gani daidai ne a gare ki ke da wata ce aiko yadda jumnai take haukan nan bazaki watsawa dan uwanki kasa a ido ba. Ke kuma kubura dayake kema sha shace iri ta shine kika kasa lurar da ita wanan haukan da takeyi kika wanko kafa kikazo gani gwaggon banza anzo a sani abin da ban tashi ba. Yau kun nuna min cewa akwai bambamci a tsakanun jinina dana musa ke nan don gashi kun nuna min karara babu sakaye. Da sauri su mamu suka zube a gaba ta suna fadin gwaggo ba nufin mu ke nan ba mu saba maki baki dai fahinci manufar mu bane gwaggo. Tace shi al,amari in yazo addua ake son bawa yayi idan mai yuyuwa ne ba hani sai anyi wanan aure haka idan babu alheri a cikin sa idan Allah yaga dama sai ya karba adduan bawan sa amma kunzo min na goyawa karya baya ko may ? Haka dau suka samu suka fita daga part din bayan tai masu tas suna bata hakkuri. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:04 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMAN RAHIM HASBUNALHI WANI,IMAL WAKIL SUBAHUL HAIRI YA JAMA,ATUL MUSULMIN, , , , , , , Ba Amma kadai tayi mamakin mamu kowa da akai case din a gaban shi ya kwana da mamakin mamu a ranshi ranan. Mu saman hjy jummai data dauko ta shirya wullakanta mamu sai gashi taga mamu ta gasa mata magana a bainan jamma,a kan itama batai na,am da wanan hafin da nata zuri,an ba . Wanan abin ba karamin kona ra hjy jummai yayi ba sosai har mamu da take ganin fakiriyace bata da komai zata bude baki cikin jamma,a tace bata kaunan hada jini da ita may wanan yarinyar take takama dashi ne a gidan ? Shi kanshi kawu ya kwana da wanan rufa idon da maimuna tayi a bainan kowa ta nuna bai isa ba da yarta sai dai ya danganta abin da zafin kishi irin nasu na mata. Don yasa gatan da zaiwa marai niyar yarta ke nan ya gama da ita sai kash maimunan bata gano manufar shi ba kan hakan da yayi. Dayake shi namiji ne sai ya shaye maganan a ranshi ta yadda babu mai iya fahintar shi ko kadan. Bangaren yaran hjy sun hade a gidan dan uwan su suna kallon irin aikin da yayi a asirce ba tare da sanin kowan su ba har iyayyen su. Aliyu ne yace wace mai sa,an mace ce aka shiryawa wanan gidan haka bros ya dan kai ma Aliyun duka yana fadin ina ka kai merry da ranta ita ke da wanan gidan. Habbib yace merry kam bata zama a garin nan kuma kun sani sai dai wanan yar kwalar da daddy ke shirin lakaka mai har uwarta na jan aji. Kai haba nasan fa halin bros kwanton yayiwa su daddy tunda kaga yayi shiru bai tankawa kowa ba kan wanan zancen rana daya zasu memashi su rasa ya ware abinsa. Umar dake dan taba wani guri da yake ganin kamar aikin gurin baiyi ba ya juyo yana fadin habbib kaga laifin maimuna ko. Aliyu yai saurin fadin ni dai ban gani ba don babu uwar da zata so hada sarakuta da mama a yanzu don maganan maimuna ne yar zata zo zaman bauta ne da masifa. Kai komai zaka iya fada yanzu akan mama tunda kun bata da ita amma aikoma may nene bai kamata ta fadi wanan maganan a gaban mu ba. Kamar wata ya can wace takai mace ko wani aji take dashi da har take iya budan baki a gaban kowa ta nuna bata son hadin daddy. Habbib ya fada ba tare daya kalle shi ba yace zaka so ka aurar da yar ka inda bata da daraja ka kwantata a kanka halin da maimuna ke ciki a gidan mu ka gani. Matar nan ko a munafuce take muna abinda take taci a dan yabe ta sai dai kuma babu wanan gun mama mutumin daya tarbi naka yasa a jiki har kuma shine zai zama makiyin ka a yau. A da nadawo da niyar ciwa duk wani wanda ke taka mama a kasan mutunci sai kuma nazo na samu abin ashe ba haka yake ba. Idan baku sani ba ku sani yau mama da bakinta take kiran matana da arniya wanda ya dace idan wani ya fadi haka ran mama ya baci. Amma sai ya kasance a gabana mama ke furta hakan kaya wanan da merry ke son irin namu na hausa sai da mama ta karbi kudi shi a hannu na kuma har yau ba a dinka kayan ba. Wanan maimuna din danabata kudi ayi cewa tayi nabar shi kawai ayi yakai maimuna ita ta shigar da merry da karfi da yaji a gidan nan wurin kowa. So yau don maimuna ta fadi haka ni sam baga laifin ta ada ina zargin da hadin bakinta kamar yadda mama tace aikai komai sai yanzu na gane bata ma san da wanan zancen ba ashe. Don a gaban ku ta nuna reaction din ta kan zancen yaya mama take son mu zauna da mutane yau tace tayi muna iyaka da wanan gobe tace wanan kawai ta yarda muyi hurda dashi shin har yanzu mu yarane ? Kiri kiri tun muna yara mama ta hana zaman lafiya a tsakanin mu da yan uwan mahaifin tun bamu so har yakai wanan halin yanzu yabi jikin mu. Tun shigowan mu gatin nan akwai wanda ya leka wurin dan uwan daddy ba tare da wani dalili ba ? Sai nake ganin daddy yana kula da hakan shiyasa yai amfani da nashi karfin ikon akan mu duka ya nuna ma mama iyakarta na mace a gare shi kuma ya kawo hujja mai tsauri ya kidanya a kan maganan. Kaga daga mama har mu ya daure kowan mu da jijiyoyin shi ke nan kin wanan maganan ta daddy a wurin mu yana nufin baraza ga auren mahaifiyar mu. Sai dai kash ita mama a yanzu bata gane illar abin saboda idon ta dake rufe kan kishin su na mata dawani dalilai nata. Idan muyi mata biyayya mun ba mahaifin mu baya akan maganan shi hukuncin saki zai hau mama wanda sai daga baya gaba dayan mu zamuzo muyi damun sani akan hakan. A karshe duniya ba zata zagi mama sai mu za,a dauka marasa tarbiya da rashin biyayyan mahaifa sai laifin ya dawo gare mu. Gaba datan su ido suka tsurawa dan uwan nasu jikin kowanin su yayi sanyi lokaci guda suna sauraren shi. Ya dafa habbib yana fadin yin biyayya ga mahaifin mu yana nufin ceto rayuwan auren su da mama ne da mukazo duniya muka samay su a tare. Wanda kuma yin hakan gun daddy rata zumuncin sane da yake ganin a bayan sa zai watse kun san daddy yana sane da rashin kaiwa yan uwansa ziyaran da ba wanda yayi a ckin mu. Fuska habbib ya bata yace yes munyi maganan dashi a ranan da nake fada mai zancen wanan gidan nawa sai naga baiyi murna ba kamar yadda na alkawarata mashi zamu ziyarci yan uwan shi da yardan Allah. Abinda nake son ku gane akwai aiki a gare mu babba daga ko wani bangare namu ga mama da shi kanshi daddy din don cikan farin cikin su dukan su. A yanzu mama zata ga cewa mun goyi bayan daddy ne ga nashi kudirin amma a gaba zata gane yin hakan shine farin cikin ta da namu baki daya. Don haka ni a shirye nake badon naso ba in karbi kaddaran auren yarinyar nan da hannu biyu kamar yadda daddy ya umurce ni dayi. Duk da nasan abinda zan fuskanta a gaba yafi wanan matsala a gare ni yanzu don haka kowan ki yaje yayi shawara ya zabawa kanshi farin ciki. Shiru sukayi gaba dayan su kowa yana nazarin maganan nasa Aliyu ne ya nisa tare da fadin bros ai shawaran ka shine final decition kowan mu ya hakkura da kaddara ya fada a cikin rashin damuwa. Habbib daya gama cika a lokacin yace kai ina yaya za ayi in auri yarinyar da ban sani ba ban san kalar ta ba hakama ba zai yuyu bane. I will live dis country by all means ba sai sun ganni zasu daura min ita ba kawai mutum na early age din shi za a dauko wani wahalan aure a lakaka mai a kai . Duk mama ce ta jawo muna wanan fushin a wurin daddy data tsaya sun fahinci juna ga yadda yake so da abin bakai haka ba. Dan murmushi umar ya sauke a fuskan shi kada kaga laifin mama duk nine na jawo maku wanan matsalan da ace banbi son zuciya na yarda na auri merry da yanzu abin abin ahankali don ran daddy ba zai baci haka ba. Bros ni bani ganin laifin ka dama abin haka yake muna rubuce a littafin so kaga mutum bai wuce kaddaransa ke nan. Mamu ce bayan fitan mu zuwa makaranta ta shirya tafiya zuwa wurin mahaifin ta don ta sanar dashi halin da take ciki. Ta samay a farfajiyan gidan shi yana shan iska tare da sauraren redio a gefen shi ya dan jingina jikin shi da filo. Sun gaisa yake tambayan ta yara tace suna makaranta baba sai uku suke dawowa daga nan nake son in biya idan na fita na kwaso su. Baba magana mazo wurin ka dashi yace to maimuna injin dai lafiya ta sada kai kasa tana fadin lafiya baba sai dai wani abu ne ya tasa a gidan akaina da kuma yarinyar nan. Yace subbahanallahi Allah yasa abinda zan iya maganin sa ne baifi karfina ba tace in sha Allahu baba zaka iya. Ya nisa tare da fadin kada inyi rashin hankali ina ita gwaggon naki da baki fada mata matsalan ki har kika zo nan wuri na anya yin hakan ba zataga mun juya mata baya. Baba itama gwaggon nawa mun zauna da ita a kan matsalan tasan da zancen yace to shike nan don kada muyi abu a cikin rashin sani yace ina sauraren ki. Ta fara rabbatabo mai duk yadda sukayi da mijin ta da kuma gwaggon nasa bata boye mashi komai ba. Bata kai karshe ba yacewa ayyah maimunatu kina cikin hankalin ki kuwa ? Yau sani ne kike son ki watsawa kasa a ido haka yayi bugun gaba da yar ki don baki da kunya har zaki wanko kafa kizo wurina kina fada min maganan banza ga tsohon banza kin samu ko ? Idan ke mai hankalice maimunatu ai godiya ya kamata ki masa don ba karamin gata yai maku daga ke har yar taki da kike fada a kanta yanzu. Yanzu kin kwaso kafa kinzo gurinane in bude baki ince ni musa ban yarda Sani ya aurawa dan shi jikata ba komai ? Yanzu yace zai bada yarki ga dan sa kince bai isa ba yanzu wa kike ganin ya isa ga yar taki tunda kin iya rufe ido kinwa sani haka. Maimunatu samun wurin naki har yakai ki fara yiwa dan uwan ki wullakacin kin manta da gatan da yai maki ya rike maki yar tankar shi ya haifi abinsa. Shin samun mutum mai hakkuri irin Sani ya jawo har kin fara mai iya shege to ki sani ba sani kika watsawa kasa a ido ba gwaggon ki Ammatan kika watsawa kasa a ido don ita kika wullakanta yau ace kina fada akan jikanta jinin ta don baki da kunya daga ke har kubura ku iya duban idon ta kije mata da wanan zancen. Dama jiran ku nake dayan ku ya tunkare ni da wanan zancen don tuni yaya ta kirani tana fada min iya shegen da kikayi masu. Kin nuna masu cewa basu suka haifar maki yar ba banta sanin ke sakariya bane shasha in banda sakarci yauko dan baro sani yace zai aurawa diyar ki ke har kinada bakin musa mashi. To ko ni nan yaya tana da iko dani a yanzun haka don tana gaba dani kuma ita kadai ta rage min a duniya. Shi al,amarin aure in yazo ai sai addu,a ga yaro don ya wuce duk yadda ake tunane abinda yakama ace kinyi baki tsaya kinyiwa yarki ba. Mamu ta buda baki tace a cikin kukan da yaci karfinta baba ni ba maganan yaya na raina ba cewa nayi ya bata kowaye amma dai dan jummai ba. Wani kallo mahaifin yai mata kafin yace Jimmai din ita keda dan ko sani zai fita yai tunkaho da jummai ne a waje ? Nan taci kukanta saida ta gaji ta tashi tayi mai sallama bai ko amsa mata ba ta fita da kunan rai a tare da ita. Bata tafi dauko mu ba kamar yadda ta tsara don tabar gidan kafin lokacin tashin mu yayi don haka ta nufi gidan babba lami da rake dauka takar mahaifiyar ta. Don matar aminiyar mahaifiyar tane a unguwar da suka taso har izuwa yanzu bata daina mata biyayya ba. Saida babba lami ta gama sauraren ta tace assh maimuna baki kyauta ba yau ko baki gidan Alh ai shi mai bugun gaba da yarkice yaba duk wanda yake so. Ai yanzu sai yaga kamar baki daukeshi uba ba gareta don bashi ya haifar maki itaba da tun farko kika zo nan da ban yarda kin aikata hakan ba. Ai wanan abin bake aikawa ba ita akaiwa ita da ta nuna ko gidan bata kaunar ganin ki a cikin sa yanzu karewa yarki kuma zata auri danta. Kinga ko anan kin nuna mata rinjaye don ba ita ke yiba Allah ke ikonsa a inda yaso tafadi ta mutu. Yarki fa mace ce ke ke ganin ta yarinya yanzu babu yara babu manya a gidan aure sai kiga yarinya kankanuwa ta baki mamaki. Don haka ko yanzu kin gara zuciyar ta ki barta da tabon bakin cikin da kika samata ya isheta kaya. Ki san yadda zaki gyara da mijin ki kadana karajin kin daga wanan zancen kuma sai dai kada ki kuskura ki zake a fili har ta dauka kina dokin auren dan nata da yarki ne ta samu daman gasa maki magana nuna mata kema hakan baki so a tafi a hakana. Tai mata godiya tare da jin dadin shawaran ta ko ba komai ta samu hanyar da zata cusawa hjy jummai bakin ciki ke nan itama taji idan da dadi. Ta biya school din mu dauko mu ta samu mun biyo motar su salma duk da a lokacin ina ganin sun dan daure min wanda ni ban san dalili ba amma haka na daure muka biyosu muka dawo gida. Motan ta ya tsaya a daidai lokacin data su umar da merry suka shigo gidan da ganin yanayin mamu basai an fada ba tana tare da damuwa a lokacin. Yana tsaye bakin motar shi har mamu ta fito daga nata motar har ta karaso inda suke don dole sai tabi ta inda suke da ta canza hanya don nauyin shi daya kamata a lokacin ta tsunci kanta da dan jin nauyin shi yau. Ta karaso a daidai inda suke ya dago yana fadin barka da iso ya hanya ashe bakya gidan ma ? Na dan fitane ne ta basu amsa a cikin murmushi itama kamar yadda shima din bai wani daure mata ba can. Tadan juya inda merry take tana fadin yau jikin ya sake kenan kin samu fitowa ? Merry tace nayi missing din ku kwana biyu nasa yau ya shigo dani in ganku tace my dear help me to carry that load. Ya juya ya bude mota ba kunya ko jin nauyi ya dauko manyan ledoji daga bayan motan tasu ba tare dajin komai ya dauko ledojin. Ganin haka yasa mamu ta fara tafiya ta barsu a gurin har ta bude part din zata shiga ta yadda take iya jiyo hayaniyar mu a ciki yace am dama naso in ganki mu danyi magana akan abinda ya faru ranan. Dou ban samu shigowa sai yau don Allah ki kara hakkuri wanan tashin hankalin kuna kara sa daddy a cikin wani matsala ne a gidan nan. So ranan naga ranki ya baci sosai shine na baki time ki dan huce gashi kuma naga har yanzu kamar kina a cikin damu up to now. Mamu tace ba komai wallahi komai ya wuce gare ni don ni bani rikon magana a raina abinne ya ishe ni wallahi shine ranan idona ya rufe har nakai ga bata amsa. Yace ba komai ga wanan merry ta saya maku a hanya tace a nan zata kai dare yau. A, a umar kakaita part din mahaifiyar ku kamar yadda ta bukaci ku dinga zuwa can wurin ta ai yanzu merry ta zama yar gida a gare mu kaga idan kaje sai ku bata wanan tsaraban zataji dadin hakan sosai a ranta. Kallon mamu yayi yace ba ita muka rikowa ba don da sunan ku ta saya sanan kuma ina daddy ai ya kashe wanan maganan ko ? Bin umurnin ta yana da kyau gare ka zanwa merry magana yadda zata fahinci ne dan bamu dama tana tafe yanzu. Na gode yace ya fara tafiya suka danyi magana da merry ya nufi part din hjyr su sai dai yana tun kara yake jin muryan su kamar fada ita da hjy maryam. Wani irin takaici yaji a ranshi da sauri ya taka ya karasa shiyan fada sosai sukeyi wanda bai tsaya sauraran abindaya hada fadan ba yace haba mama haba dai. Rai bace yake maganan tare da ba hjy maryam hakkuri batare daya damu da abinda ya hada fadan ba. Gumi ya dinga karyo mai na bacin rai kadan ya rage hawaye ya zubo mai a lokacin don takaici ganin hakan yasa jikin su yai sanyi suka bar tankiyar da sukeyi din. Merry ce a tsaye kofan dakin tana kallon abinda bata saba ganin wanan halin na sarakuwar nata ba. A ranta take fadin wai wanan matar itako ta haifi my dear ko dai mum din shi bata nan ne amma kuma yanzu step mum din shi taga fada min inzo dakin mahaifiyar shi mu gaisa ma. Itace dai mahaifiyar nasa don suna kama da kanin sa habbib sosai dan juyowa hjy tayi taga merry tsaye daga kofa tana kallon su. Dan wani malalacin kallo hju jummai tayiwa merry tana fadin au ashe tare kuke tafe kace ta shigo mana ta tsaya tana kallon mutane wani iri. Da hannu ya kira merry ta karaso zuwa inda yake sai data zauna ta fara gaida su bayan sun amsa ne hjy maryam ta juya tana fadin yaya ni kingana tafi tunda kinyi baki. Wani kallo tayiwa maryam din tare da fadin babawo din ne kuma baki ke fa sai ana zaune kalau kike takalan mutum. Yaro ne dakan dazo ya zubar da sharan da ake tarawa a kowani part yayi sallama da ledoji a hannun shi yace gashi hjyan shiyan can tace in shigo dashi. Merry tana ganin ledan ta dan dago tace no retuning to her is her own tana bata fuska hjy sukayi tsaye suna kallon ta kasa hakkuri tayi tace wanan kuma kayan waye. Bai dago ba yace na maimuna ne tazo mata dashi ba wani abu bane a ciki sai tsaraban yarane da sauri hjy tace kai ilu kawo ladan ka wuce. Cikin harshen turanci merry tace no ma is not you on is for other hjy tana fadi tana dan buga hannun ta guri daya cikin bata rai. Hjy tace look merry exchange words with you ki bar wanan kayan a nan daga haka ta juya wurin umar tana fadin ka fara ganin abinda nake fada maka ko ? Mama ki bar wana zancen hakan bai dace ba wallahi irin dawainiyar maimuna gareta yasa ta sayowa yaranta chuculet. Nan babu yara na datun farko damu ra saba zata san wata maimuna ne can ? Mikewa meery tayi duk suka kalleta lokaci guda yana tambayanta ina zuwa tace the other part daga haka ta fice daga part din. Ehyeh wanan kafirar dani take wasa zan sasaba mata a gidan nan ita wacece da har zatai bugun gaban kanta ka fada mata ta dawo nan yanzu ko in saba mata tasan halina. Yacw haba mama hakan bai dace ba gaskiya bakuwace fa kuma su ba al,adan su bane hakan suna zamane da wanda zuciyan su ya kwanta ne. Babawo kana son mu gama dakai lafiya to ka kiyayyeni a gidan nan wallahi. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:05 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, WA DADAKA A, ILAN FAHADDE, , , , , Mamu na zaune tana waya yayin da mu muna zaune mun fara cinn dan waken fulawa da dan wake kadan a ciki da mamu ta shirya muna as a lunch. Ko wanan mu na son wanan cimar haka yasa muka bazu a falon mu mun mai dashi abin marmari don haka wasu mu naci da tsinke wasu suna ci da fork. Sai ganin merry mukayi ta fado falon ranta a bace tana fadin i told you I don't want to go there that woman hate me at all she fight with out resing. Mumu tai dan murmushi tace don't mind her is her habit, she can't talk polityly. You have to bear it she is you mother inlaw so nerver mind with her habit. Dan zaku dawo ku zama daya wata rana idan kun saba yanzu abin yana sabo ne a gare ki ta dan mede baki alaman abin ya ishe ta. Dan wake mamu ta zuba mata a plate tana mika mata saida ta dan kalla ta girgiza kai don bata taba fani shi ba kuma bai burgeta ba. Mamu tace test it will enjoy it , is made with bean and flower tadai karba a ya tsune tana dan kokarin dauka a kyamace daga inda nake zaune haushe da takaicin yadda mamu ke lalashin ta taci ya cika ni. Yaji na dauko ina karawa nawa da mai ta bini da ido tana kallona sai gashi ta hade wanda ta saka a baki tana kara daukan wani takai baki. Sai ga merry na batun tashi da plate din abincin gaba daya da aka zuba mata ko magana bata yi sai ruwa da mamu ta zuba mata mara sanyi don ta kula bata shan ruwa mai sanyi sosai. Muna gab da gamawa ne ya fado falon da sallaman shi ya dan tsaya daga kofa yana fadin sorry nayi distubing din ku a yanzu. Mamu tace ba komai dan wanke muke ci da mai da yaji dan murmushi ya kirkiro a fuskan shi yana fadin ta iyaci don an tsanmanin ta taba cin sa ba? Aiko gashi sai ci take babu kakautawa mumu ta fada da dan murmushi ya danyi kamar zai zauna sai kuma ya ja ya tsaya yana fadin na gode kwarai maimuna da wanan karramawan sa kike mata sai dai ina ganin zuwa wani sati zamu koma don shirin haihuwan ta don ina ga ta kusa haihuwa yanzu ga lissafin mu. Mamu tace da sauri haka zaku koma ai na dauka a nan zaku tsaya sai ta haihu kan ku tafi ? Ya dan sosa kai yana fadin zanso hakan nima sai dai hakan ba mai yuyuwa bane don ba zata so hakan ba ita ga kuma wanan yawan fitinan datake fuskanta wanda ba sabawa da hakan tayi ba ita. Kayi hakkuri umar wanan ba zai sa ku wuce a yanzu ba da zaku dan daure ku kara lokaci zaiyi kyau har ga iyayyen ku yanzu sai suga ai ba wani dadewa kukayi a kasan nan ba zaka koma kuma. Kaga sai su dora laifin ga ita merry din datazo daga baya ya dan ja iska ya furzar tare da fadin nasan zasuyi wanan tunanen a ransu amma ba yadda zanyi ne don tun yanzu merry ta fara fuskantar matsala da hjy wanda ba zan so hakan ya faru ba gaskiya. Hakkuri zakuyi don iyayye dama zama dasu sai hakkuri don kullun a yara suke kallon ku kadai ga yadda yake kasancewa ko ga mahaifan mu ai. Dazun da ka ganni daga wurin baba nake yau min tas daga naje mai da shawara sai yake ganin na raina su. Dan tsohon nan ai bashi da fada ko sosai sai dai yanzu da tsufa ya fara zomai dole ne ya fara fada kan dan magana kadan. Muryan merry ne take fadin ta koshi da yawa bata dauka zataci sosai haka ba yace ta tashi su tafi wani kallo tayi mai tana fadin so soon ai na dauka kace sai dare zaka dawo ka dauke ni yace haka naso amma yanzu na fasa. Tayi kokarin mikewa sai ta koma ta zauna dan murmushi yayi ya duka yana kokarin dagata da kanshi da sauri na kawar da kaina ina kokarin kara yaji sosai do ya dauke mi hankali daga kallon su. Wai ke may ye haka kina ta zubuda yaji ga abincin ki tun dazu kina sane da bai baki lafiya kuma. Mamu ina son sa da yaji ne na dan fada a shagwabe ina bata fuska lokacin har ya mikar da ita tsaye suka tsaya suna kallon plate din abincin nawa. Prity ko zaki bimu zuwa masaukin mu yau ki debe muna kewa na dan lokaci kadan ina son zama dake mu danyi hiran yanayin ku na nan. Merry ta fada tana kallo na da sauri na girgiza kai ina fadin No no no is time for my qur,anin school and want to miss it. Ganin suna magana da mamu tana mata bayanin abinda nake nufin nayi saurin shigewa dakin mu na fara shirin barin gidan suna nan na fito a cikin zubulelen hijjab dina ina fadin fauziya ku dauko hijjab mu rafi kada mu makara. Ranan da mamu ta karbi girki hakana ta daure zuciyar ta ba dadi har lokacin ta shirya zuwa sashen mai gidan don gabatar da hakkin shi daya rataya a kanta. Kawu ya debe rai da zuwan mamu part din shi do har ya fara gabatarwa kanshi wasu al,amuran da sukeyi masa idan sun shigo. Sai ga ta ta shigo fuskanta ya kalla wanda har lokacin ba walwala a tare da ita , sallaman da tayi ya karba ta aje abinda ta shigo dashi a hannun ta. Sai da takai zaune ta fara gaida shi da dawowa shima ya karba kamar yadda ta gaida shi din a sanyaye, Dan shiru ya biyo falon kafin kawu ya kawar da shirun da falon yayi da fadin kinki ki tuna min zancen kayan yaran nan don ni na manta da zancen shaf a raina.. Sai da na hadu da Fatima dazun suna dawowa na tuna dan kunya ne ya kama mamu tace abubuwan ne da yawa itama dai fitina ne da ita wallahi. Yace kin san halin malaman da saka yara a gaba suna takura masu in bashi ba ai wanan da take amfani dashi ba laifi yana da tsawo nagani. Ai ka santa da shegen son uztazanci dan maganan da akayi bai saukaba ya daga mata hankali. Wanan ai yana da kyau yaran nan kaf din su ina hankalce ta fisu son addini shiyasa nake son zancen fatima akwaita da kokari wurin wurin riko da addini sosai. Kai yaya sayadin da saida nayi da gaske take wanan halin yace to ai kinji tunda har zaki iya sakata abu tayi shi. Jikin mamu ya kara sanyi tayi shiru sai can race shekaran jiya naje gida gun baba . Ya katse ta da fadin kinje kai karan mu ni da hajiyan mu ko ba haka bane yaya ta fada a dan kunyace tare da fadin kun dai ki fahintana ne kan wanan zancen. Amma ta yaya zanki umar da sayadi tunda ban san abinda kayi tunani kai wanan hadin ba ni abinda nake jawa yadda tun yanzu hjy ta nuna bata son hada komai dani a fili yasa nima na, , , Kema sai haukan kishin ya kwashe ki kuka kara bakanta min rai ko kawu ya karasa fadi kafin ta furta nata. Kin ban mamaki maimuna da har kikayi zaton zan kai fatima gurin da zata sha wahala ko wani abu makamancin hakan nafasan abinda nake maimuna. Yaya kayi hakkuri banayi hakan don in bata maka bane abinda nake hange cikin wanan auren duk kun kasa hangen shi ku a yanzu. Matar da ta nuna wa bare ma halinta balle yar nan da tun yanzu ta nuna bata kaunan ta don may ni zan nuna ina kaunan wanan hadin kenan nida yar mun zama kwadayayo ke nan a wurin ta tana hattaran mu muna biye don kwadai wanan ba zaiyuyu ba. A takaice dai baki yarda da hukunci na ba ke nan har yanzun ? Tayi kasa da kai tana magana kasa kasa a cikin ladabi tace ni bance na ban yarda ba kai tsaye ai kadaiji hujjan da nake dashi. Girki dai haka akayi shi ba wani dadin rai gare su dukkan su duk da mamu tayi kokarin danne zuciyar ta ga zancen kamar yadda shima kawu bai kara tayar da zancen ba a fili sai dai ba gudu ba ja da baya ga abinda ya zartan. A cikin satin ne kuma kowa na gidan yasan da zancen gidan da umar ya gina dama wasu harkoki da yakeyi. Hakan bai hana mumu wanke kafa taje har falin hjy jummai tai mata murna ba lokacin suna zaune da yaran ta ana hiran haduwan gidan daya gina din. Tayi addua tare da fatan alheri daga haka ta juya ta fita ta barsu tana fita hjy jummai tace munafukan banza munafukan wofi. Ta wanko kafa tazo don wani simi simi da ita tana fadin wai Allah sa kaza Allah sa kaza kamar yakai ciki munafuka watau a yarda da yar ta ko mai. Mama ai tayi kokari don tazo habbib ya fada cikin rashin kulawa shiko Aliyu mikewa yayi yana fadin bros yanzun zaka fitane ? Binsu tayi da kallo suna ficewa daga dakin Aliyu yace mama bata son zancen gaskiya may ye laifin matan nan datazo mata murna ko yan uwanta ai ta riga su zuwa. Gidan umar sukaje sun samay shi a waje da wani abokin shi suna magana haka yasa basu tsaya ba suka shige ciki. Merry dake kwance ta karde falon da kidan coci tana bi daga inda take kwance din ta dago ta kalle su ayatsune tana fadin wanan shigowa haka kamar wasu yan aike fa. Sai da kowan su ya samu wuri ya zauna suke fadin gunki aka aiko mu inji Aliyu habbib ne ya kalle ta tace ba zaki bamu ko ruwa mu sha ba ai ki tare mu da wani zance. Tace ruwa nine zan debo maka ruwa kasha ko wa tana fadi tana gyara kwanciyar ta amma kin san mu haka akidar mu yake maigida shi zai tari bako da abin sha ai . Tace to hell with your culture at all no any respect in that culture baku san ku yadda ake girmama bakon ku ba ko kadan. Sunyi galala suna kallon ta haka yasa habbib ya fara mikewa yana fadin kai mu tafi ta tabe baki tana kallon su a wullakace tace akan ku zan fara rama wullakancin da ake mun. Umar dake shigowa falon yace har zaku tafi ke nan yanzu fa kuka zo bako zauna ba halan. No bari mu tafi zamu dawo wani lokacin habbib yace yana tafiya Aliyu ya mara mashi baya. Ciki ya shiga ya samu merry a yadda suka barta yace kinga su brothers sin shigo ko zama ina basuyi ba kuma sun wuce. Tace eh da sanina suka wuce don raini suke son kawo min wai na basu ruwa su sha wani kallo yake mata kafin yace merry kin san mai kike fada ke kika kore su ke nan ko ? Tace idan zasu zo su kawo min raini zan masu abinda yafi wanan ma a gidana don ba zasu zo suna takura mi ba. Alamarin merry ya fara ba umar tsoro ga matsin da take mai kan tagaji da zaman Nigeria ita dai sai su koma taki yarda kuma ta koma ita kadai. Ya dai samu ya dan rarashe ta kan ta yarda ya karasa abinda yasa a gaban shi ita babba damuwan merry shine ta samu ta raba umar da mahaifan shi da take ganin tsana daga idanuwan su. Tunda ya samu ya rarashe ta tadan yarda zasu kara lokaci sai kuma dokokin data na ba zata sake zuwa guri mum din shi ba koda kuwa ta shiga gidan. Gashi kuma zuwa lokacin ita hjy ta dan sauko ta fara nunawa merry ta fuska da baikai ciki ba tana son jan ta a jiki. Hjy da kanta tayiwa merry korafin rashin zuwanta gidan su kwana biyu merry ta kama mata yawo da hankalin cewa ai suna tafe. Sai dai har lokacin bata ga duriyan ta ba a gidan sai kuma ta fara zargin ko mamuce ta zuga merry din a kanta kada ta yarda da ita ko kuma ta zuwa gidan ita a boye. Haka yasa hjy ta kasa hakkura ta tun kari dan da zancen a ciki waya yace yana lagos idan ya dawo zasu shigo ai . Har kwana biyu bata ganshi ba ta kara kiranshi a waya yace insha Allahu yana tafe a gobe zasu dawo. Washe gari da yamma sai gashi ya tun karo gidan lokacin baiko karasa gidan shi ba ya nufo gidan su don yawan kiran mahaifiyar tasu da take mai yake daukan wani abune ya faru. Yayi sallama ya shigo gidan ranan saye yake da wando da rigan bakaken kayada farar riga a cikin kayan suit din. Wuyan shi yana daure da nicktie sai kamshi turaren sa ke tashi mai dadi da kan gauraye wuri idan yana gurin. Kayan suyi mashi matukar kyau a jikin shi kai kace don shi aka hada kayan ya karasa shigowa yana fadin mama na dawo don naga kamar kina bukatan gani na sosai. Tace ai dole babawo kana kasan nan matar ka tana kokarin rabaka damu ina ga kun koma can yanzu dai maimuna takai ga bukatan ta fafir wanan yarinyar takini a kasan nan.. Haba mama merry har ta isa ta rabani daku kawai dai daurowane hakan tace wana dalili;yasa bana son ka auri wanan yarinyar yar gurin maimuna. Kai mama har yanzu kina ga wanan zancen na dauka ai an bar wanan maganan tunda itama ta nuna bata son hadin . Karya ne munafukane balle yanzu da take ganin ka samu ci gaba haka ai yanzu take da kwadan hakan sosai wai ranan don bata da kunya sai gata tazo min murna har nan part din. Mama ni sam ban dauki wanan wani munafunci ba tunda kuna wuri daya tare haka kema watarana alheri zai samay ta kizo mata murna ina har hjy maryam duk sun zo. Wani kallo tayi mai tace maryam ne zata zo min murna nan ta dai zo min gulman wai taji hajiya na fadin gidan ya tsaru ke nan suna zuwa gidan naku ke nan. Kai mama ku dai baku rabuwa da wani zance zan karasa gida don ko gida ban samu zuwa ba na wuto nan mu gaisa do ki ganni. Dadin haka hjy taji tamike ita ma tana fadin yaran nan sun min magana wai suna son su koma hakana sai dai nasan ba abune mai sauki ba Alh ya yarda da zancen komawan naku kuma. Tsaye suke aharaban gida suke wanan maganan sankarewa yayi a tsaye tankar ruwa ya ci shi dama yasan wanan abin zai faru gun mahaifin nasu. Motar da tashigo na mamu data kwaso su manjo da Adda daga tasha ne ya dauke mata hankali har bata san shock din da dan nata ya shiga ba a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:05 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM HASBUNALLAHI WANI, IMAL WAKEEL, , , , Kallon mamaki take yi masu ba don komai ba sai ganin bakin kamar da shirin kwana sukazo gidan abin yake bata mamaki a ranta. Lalai maimuna ta kafu har wasu baki ta gaiyyato masu a gida gaba gadi wasu irin kauyawa can dasu . Abinka da yan karkara ganin su a waje su Addah da basu san kan gidan ba suka dakata suna jefa masu gaisuwa hakan yaba mamu daman nufansu itama tana gaisawa dasu don ganin umar a tare da ita da tayi. Bayan sun gaisa ta kalli hjy tana fadin kakar sayadi ce tazo da yarta yar marigayi din daya rasu tana nuna Addah. Ummumm hjy jummai tace ba tare da furta komai ba a gare su sai umar din ne ya daure yace sannun ku da zuwa ya hanya? Wani kallo hjy ta jefa mai da yasa ya dan kwantar da kan shi kasa ba tare da ya shirya ba sukan suka juya suka tafi. A dakin mu ta sauke su basu zauna ba don gabatar da sallah dake a kansu sai da sukai sallah ta gabatar masu da abinci. Suna zaune suna cin a bincin mukai sallama dawowan mu ke nan daga islamiya lokacin. Na dan tsaya waje iba magana da Aisha kafin in tunkari part din namu kai tsaye tun a kofan na fahinci akwai baki a part din don takalman roban da na gani aje a kofan shiga part din. Ban damu ba don na dauka ire iren yan uwan su ne dakan dan leko lokaci lokaci wurin mamu din. Murya naji kamar na Addah tana fadin kun dawo ya makarantar ina ita A ruwa din tubarkallah masha Allah yara sai dada girma suke yi . Da sauri na nufi dakin da nake jin muryan nata na daga labulen dakin da sauri wani ihu na yanka da mukai arba dasu ina fadin wayo ni manjo na. Na nufeta da gudu na fada mata a jiki sai kuma na fashe da kuka a lokaci daya manjo sai fadi take ni daga min kada ki karasani kin wani girma haka kamar ke kadai ake kiwo a gidan nan. May kuma kikewa kuka yanzu kuma na kasa magana sai kuka nake na makaleta sai manjon itama ta kama kukan . Muryan mamu daga kofa take fadin yau ka tsiya zaki dagata ki fice nan wanan shegan takar banzan da kikeyi fa ? Barta suyi Addah ta bata amsa tana fadin kin san tsakanin fatima da babba sai Allah. To kuma sai akace tazo ta tasa ta a gaba tanawa mutane kukan banza haka ? Wanan ai sai ki tayar mata da ciwon ta dan Allah daga ki ba mutane guri mara ta ido kawai cikin dan share hawaye manjo tace mata. Maimuna barta tayi abinta Allah ya nufa ta kara sani a ido ne dana tafi dana barta da dawainiyar dakon kewata a zuciyar ta. Kai babba ba gaki yanzu tana gani ba zata cikamu da kukan banza haka kawai ? Da kyat na banbare a jikin manjo naje wajen kiran da mamu ta kwala min a kitchen na samay ta tana dora ruwan abinci tace in kin gama shagwaban naki sai ki zo mu hada masu abinci. Ina dan goge fuskana nace may zanyi mamu tace ki debo kayan miya ki fara jajagawa a turmi miyar kubewa zanyi. Haka na daure na kama aiki hankali yana daki wurin manjo na matsu in gama inje in samay su a dakin muyi hira. Umar yana tsayawa kofan gidan shi wayan shi yana kara ya dauka ganin sunan mama yasa ya furta mama kuma da mamaki karara a fuskan shi don yaga yanzun suka rabu da ita ai. Ya dauka yana fadin mama lafiya dai ko ? Tace na kiraka ne in fada maka ba ruwan ka da wa yan nan yan kauyen bakin na maimuna kada inji kada in gani ka barta da mutanen ta don zuciyata ta kasa natsuwa a yadda naga kana wani gaidasu. Yace mama kada ki manta bakin gidan mu ne fa dole muyi gaisuwa irin ta musulunci ga bakin mu ai. To ubana fada min yadda akeyi kasan ban sani ba sai ka koya min yanzu yace mama Allah huci zuciyar ki nima ina zasu ganni kuma. Ta sauke ajiyan zuciya tace yanzu naji magana don nasan wanan makiran tunda ta fara fadin wai kakar yarta ce wai tsigar makirncin ta kulla kuma. Na gode mama ya fada a gagauce don hango merry da yayi a garden tana murnan dawowan shi. Ya fito motan da sauri ya nufi girin ta tare da ware hannayen shi alaman tazo gare shi a lokacin cikin so da shaukin ta sosai. A haka suka shige ciki suna makale da junan su kamar zasu cinye juna a lokacin zaka dauka yayi wata barkatai ne bai garin. Mamu bata bari nabar kitchen din ba sai da muka kammala aikin mu gaba daya daidai ana kiran sallah na fito don inje inyi sallah . Bayan na idar na fada dakin na samu manjo ta idar tana jan tasbaha a hannun ta hakan bai hanani zuwa i rabeta ba lokacin. Ta shafa tana fadin ja,ira har yanzu kina nan da shegen son jikin nan naki haka ? Adda ta dago tana fadin ke dagata kada ki tumurmushe ta don Allah kin ganki kuwa yanzu yadda kika koma cikkkan mace dake makerin halittan ki ya gama keraki tsab. Na mike daga jikin manjo ina dan dariya tare da fadin kai Addah ni wani girma na kara a hakan ina kamo hannun manjo . Nace cikin yanayin damuwa anya manjo kina ko cin abinci a can nasan mugayen ban ba wani kulaki zasuyi ba ai. Adda ta kalleni tare da dan harara tace a, a da yunwa take kwana tun bayan zuwan ki nan . Na danyi dariya nace ba haka bane Addah wallahi manjo duk ta zube min a idona wai ina Atika da umman ta na kawar da zancen don gudun maranbarama. Addah tace ai kuwa har kofan yaya suke da zamu taso Atika kamar ta biyo mi take ji tazo ta ganki sai mahaifin tane dai ba lafiya sosai shima tunda yai wanan hatsarin motar bai kara samun lafiya ba. Duk sai naji ba dadi a raina don ban manta da irin halarcin da mutanen suka nuna min ba dan zama a azare danayi. Ina like da su muna ta hira sai ga mamu ta shigo dakin a cikin hijjab din ta tana fadin watau sayadi ba zaki barsu su hutaba kin cika su da surtun tsiya tun dazun. Ki barsu su huta har zuwa gobe tunda ba yanzu zasu koma ba sai babba ta gama ganin likita. Manjo da ta koma min shiru shiru yanzu bata son yawan hayaniya tace ki rabu da ita tayi kewan mu ne yar nan. Ki tashi ki kaiwa gwaggo abincin ta kin barshi a kitchen tun dazun yana sanyi manjo tace watau dai kin kore muna ita da wayau ko ? Ina shiga part din Amma na samay ta zaune tana jan tasbaha itama na kai abincin inda muke ajewa zan wuce tace dawo yan nema yau kinga kakan ki zumudi ya hana ki tsayawa to ba inda zaki sai na more ki a nan nima. Kinga dauko min ledan can dake aje dazun maigidana ya shigo min dashi wai ya dawo ikko haka yake tafiyan shi ba salma shi sai dai idan ya dawo mutum yaji. Ina daukowa nace Amma wani maigidan ki ya kawo maki ko mijin ki ya dawo ne ? Tace ja,ira kin taba ganin inda aka mutu aka dawo duniya yayan ku dai umaru ne wai ya je ikko ya kawo min tsaraba . Na bude ledan kaya ne irin na kurmi a ciki kwakwa abarba ayaba da sauran tarkacen kurmi shake da ledan baco mai girma. Tace ki dabarwa uwar ki don nasan ko yakawo masu nasu ba deban masu jummai zatayi ba sai dai ta aje idan ya rube ta zubar. Nace kinga ko Amma dama duk manjo ta rame sosai da gani basu bata kulawan daya dace a can . Amma tace yar nan ke nan azamanin nan ai diya mace kadai tasan zafin uwarta wanan sarakan zamanin babu abinda suka sani banda su mayar da uwar miji banza. Nace bandani Amma nikan yadda naga su umma saude nawa manjo bani fatan inyi wanan rayuwan da sarakuwata. Anya A ruwa zaki ko samu hakan gurin sarakuwar ki don babu alaman hakan zai samu sai dai gyaran Allah. Nace ji Amma kamar kin san wanda zan aura har ki san halin uwarshi kina mun mugun fata haka ? Tace cikin dariya kai yaro man kaza yo ni ai har na hango sarakuwar taki ko a idona idan baki sani ba san nan ke din nan da nake gani kayya a dai bar zancen don Allah. Nace Amma Allah dai ya bar muna ke kiga auren namu nan da shekara goma mai zuwa kilama da dan hayi don ni nan kawu yace min sai na zama babban likita a gidan nan. Kinga kuwa ai ba zancen yanzu akeyi ba ke nan tace hakane fa kinga dauki kayan ki kaiwa uwar ki kafin wa yan nan sarakunan kwadan su fito su saka maki ido. Nace to sai da safe Amma tunda dau naga yau baki son hiran tamu dake ke tafi can tace min wa zakiwa tako hankalin ki na gun kakar ki sarai. Na fice ina dariya da kayan a hannu na ina sauri in koma part din mu in fara ba manjo ta sha lemo da ayaba. Na samu mamu ta gyara masu guri da zasu kwanta inda manjo tace ita a kasa zata kwanta bata hawa gadon da aka gyara masu din. Haka yasa aka kayar mata da katifa a kasa ta kwanta a nan sai gani na shigo sai dana nunawa mamu tace in kai kitchen in aje har da safe mm ace barin dibawa manjo lemon ta dan sha. Washe gari nayi sa,a ba zuwa school ranan a na public holiday sai aka hada muna meettime break din mu don haka zamu zauna gida na kwana biyu ke nan. Ga mamu tayiwa merry alkawarin zamu shigo muga gidan su idan Allah ya yarda ranan ko dana tashi tun safe ban zauna ba ina aiki a part din. Na gama abinci ne mamu ke fadin nace su Aisha su shirya don nayiwa matar yayan ku alkawarin yau zaku shigo wurin ta don ta matsa da maganan baku je ba. Take na daure fuskana don ban son zuwa gidan ni dai har ga Allah kyaman su ma nake ji daga matar har mijin saboda arnarcin su sai nakw ganin kamar shima arne ne . Tunda irin kayan da yake yawan sakawa irin na kafirai nake ganin kamar shi shiyasa ranan da naga yana alwala a wajen gidan mu zaije masallaci saboda gulma har tuntube nake ina waigen shi ko ya iya alwalan. Ko ba zaki je bane kin tsaya kina wani tunane banza naki kuma kada inji ance ga abinda kikayi na rashin mutuncin a gidan nan. Mamu ni ina ruwana dasu muje kawai mu gaida su mu fito har zan tsaya wani rashin ji kuma mamu ni yanzu na bar rawan kai fa tunda na girma. Sai da na dan zauna wurin su manjo muka dan taba hira na shiga wanka yadi da ya kawo wa Amma tsaraba ta dinka ta vani shina saka a jikina. Don ban taba saka shi a jikina ba sai yau na dauko na saka saboda kawai in kara burge su Addah na saka su san rikon arzikin da ake min a gidan kawu din. Dinkin da yadin ya kara fito min da surana karara a fili ni kaina dai sai da nasan yau nayi matukar kyau sosai ba kadan ba. Na kama jelar gashina nayi gawo dashi na nade guri daya na cushe shi san nan na daura dan kwali a kai. Sai dana gama kallon kaina tsab na dauko sabon hijjab dina na aza saman kayan ya sauko min har kasa sosai ya rufe min kwalliyan dana bata lokaci inayin sa. Muryan su Aisha ne a falin mu suka shigo na fito kallo na sukayi gaba dayan su Aisha tace kai amma dai fatiman nan. Wallahi ni ban taba ganin wace ta auri hijjab kamar ki ba a duniya yanzu wanan fitan da zamuyi shine kika dauko wanan jibgegen hijab din kika saka kamar mai zuwa islamiya. Ke kullun gaki sai kace rainon kauye dake ke kullu banga ranan da zaki waye ba wallahi kamar ba a cikin kano kike ba. Naja na tsaya ina kallon ta a raine kafin in ce ke ba zaki gane ba Aisha may zanwa kwalliya yanzu tunda ba saurayi nake nema ba a waje. Ki bari lokacin kwaliyana yana zuwa idan na gama neman illimina lokacin zan faso duniya ta san dani kinga lokacin masunsunina zaizo. Kinga ko yaga surata a lokacin babu komai domin a yanzu bayyana sura bashi zaisa ka samu kasuwa ba ni dai fatana Allah ya ban na gari . Yanzu dai ke kadai ne zakka a cikin mu zaki bimu da wanan zunbulelen hijjab din haka kamar matar uztazu. Baki na tabe lokacin mamu na fitowa tana jin zancen mu dasu tace idan kunbi ta wanan sai ku shekara a nan tana cin ku da wanan baki nata. Kunga ku kula idan kunje banda sai da hali don Allah kada naji anyi wani abin asha a can. Daga haka muka fita na rike hannun fauziya don da ita zamu tafi su samir sun fita da kawu tunda safe. Tare da Amma muka fita don ta samu wanda zai sauke mu a can tunda muka fito yaran hjy maryam suka ganmu suka tsura muna ido. Murja tace kada ku fada masu inda zamu yanzu zasu fadawa uwar su zancen muna fita sai ga Aliyu zai fita mamu ta tsayar dashi tayi mai magana bamuji mai tace mai ba sai yace muzo mu tafi. Har zamu zauna a baya sai naji mamu tace ke Aisha ki dawo gaba ki zauna sai su su zauna baya. Haka mukai zaman motar sai faman kalle kalle muke na kauyanci a motar ga sanyi ga kamahin turare a ciki. Shiru motar yayi kowan mu na gudun yayi wani dogon motsi da ba daidai ba sai can yace ke wanan hijjab din haka kamar matan malam fa ? Haka kikaga yan uwan ki ke kullun kamar mai zuwa tafsiri dake nayi dan murmshi don na fahinci dani yake saboda ni kadaice mai hijjab a cikin mu. Duk rawan kaina ina dan shayin yaran hjy jummai kaf din su musanman tu lokacin da naji sun taimawa mamu nake ganin mutuncin su a idona saidai ba ruwana dasu ne sai gaisuwa. Ya dab bugi sitiyarin motar yana fadi yarinya duk zaki bar wanan ne nan gaba sai lokacin na bashi amsa da fadin ai ban fatan in bari yaya don shine tsaron mutunci na. Ganin hakan yasa da ya sauke mu nayi mai godiya kamar yadda kowa yai masa zuciyana fam da mamakin sakar min fuskan da yayi yau ko dai don ba a gida muke bane ? Ban ankara da inda muke ba sai da na fito daga motar tsarin gidan ya tafi da imanina sai naji kamar a mafalki nake ganin kaina a ciki. Bani kadai ba har dasu wayayon sai da gidan ya tafi da imanin su tun a waje suka fara santin gidan dan baya naja kadan ina fadin ku ku tsaya .. Ni dai wallahi naji tsoro ace wanan katafaren gidan wai na dan kawu ne to a ina ya samu kudin dayayi wanan gidan haka ? Kunga kuzo mu koma mucewa mamu bamu samay su a gida ba zaifi muna alheri don ni wallahi na tsorace da wanan gidan tun bamu shiga ba gabana wallahi faduwa yake yi sosai. Ke dan Allah mu shiga may ye na wani tsoro kamar sai damu za ayi akace maki yau sai mun ga kwam wallahi. Aisha ke maganan tana fadi ta jawo hannun fauziya dole nima nabi bayan su inda ya Aliyu ya nuna muna hanyar shiga gidan. Cirko cirko mukayi a wajen kofan kowa na tunane nace yanzu sallama zamuyi ko may kun dai san ba gidan musulmai mukazo ba. Ke kika mai dashi kafiri ko jiya daya shigo Amma tayi mai tayin fura cewa yayi yana azumin thursday ne. Nace kika sani ko nasu na kafirai yakeyi kin san suma fa suna azumin su akace . Wai ke aka ce maki yaya din shima kafirine kamar matar shi nace in ba kafiri bane yaya ya zauna da wace bata sallah da sunan aure. Ni kinga kallo daya da matar shi nake masu fa shiyasa ki yazo part din mu yana sallama ban karbawa don ance baida kyau ka karbawa kafiri. Gashi da girman kai da jiji da kai ko kana gaidashi sai yayi kamar bai sanka ba kullun ba sakin fuska dashi da dan uwan nan nasa guda kusan halin su daya nake gani. Ke ni ko kannesa su salma bance yana sake masu ba balle mu naja wani tsuki nace ni ban san may yasa mamu ke son hurda dasu ba in anyi magana tace dan uwan tane may ne may ne. Aisha ta ja tsuki tace ke don Allah muna neman hanya kin dami mutane da surutu nace maganin yan gulma ke nan sai kun shiga an baku giya yau zaku gane baku da wayau ai. Aisha ta wurga mi harara tace dkn Allah A ruwa raba mu da wanan zancen banzan naki nace a, a ba aruwa ba a wuta ko amma zan kashe masu wanan sunan banzan ne a bakin su. Zaune yake yana kallon duk abinda mukeyi tsab ganin bamu da niyar nocking mun tsaya muna budan ido yasa shi ya taso ya bude kofan fuskan shi a daure tamau. Yana fadin kai wai su waye hakane kunzo kun cika mutane da surutun tsiya tun dazun. Mu mm mune yaya Aisha ta fada tana dan inda inda tare da fadin ina wuni yaya ? Bai amsa ba sai juyawan da yayi ya bar muna kofan a bude ga wani sanyi daga ciki yana bugun fuskan mu daga waje. Ni kan dariyan keta ne ya kamani lokacin ban san har nakai wurin da sai an taka step ba sai jina nayi zan fadi kasa murja ta rikoni ta baya. Ku zauna tana ciki yace ba tare da ya juyo inda muke ba ya shige ciki yana shiga mukabi falon da kallon gulma ido gulma hanci gulma ko ina mun baza shi sai kallon kallo mukewa junan mu. Shiru muna zaune kamar ba wanda ya kula da zuwan mu har na fara hasala a raina sai jin muryan merry mukayi tana fadin. Wawoo yau prity ce a gidan namu sun fito rike da hannun junan su yana saye da three quarter da farar riga a jikin shi ita kuma wani dan riga iya cinya armless ne saye a jikin ta sai cikin jikin ta dayai tsini ya dago rigan. Tana zuwa ta sake hannun shi ta rugume ni ta sake ta rugume su Aisha kamar yadda tayi min din ta juya wurin shi tana fadin yau kaga su sisters a gidan mu sun kawo muna ziyara. Ya danyi dariyan yake yana juyawa zai bar gurin tace idan ya shiga ya turo mata mai aiki daya ta bamu abin sha. Satan kallon Aisha na danyi kadan ina mata alaman kada mu sha komai a gidan ban don ni na gama tsorata da su gaba daya sai sake sake nake a raina. Ina kuma mamakinwai matace ke aiken miji haka a gaban mu ko kunya baiji to ina zaji kunya nace fitowan ma nan da falon saida ya rakota. Shigowa yar aikin mai guntun buje itama ya katse min tunane na ta shigo tana gaida mu cikindan rusunni. Kallon kwalban nayi ban gane kwalban lemun ba shiba fanta ba ba kuma cock ba da wani leda an rufe saman shi da gani dai kaga abin maye. Tace mu sha mana sai muka kama kallon juna suna tuna zance na kafin mu shigo gashi ko ya zama gaskiya. Hira sosai muke kwasa da ita tana bamu labarin kasar su har dai muka dan sake jiki da ita tace ita fa tana son rawa don haka kowan mu sai yayi mata rawa tagani. Kida ta saka duk ya gauraye gidan sai nake mamakin yadda mijin bai damu ba ya kyale take wanan tabaran haka da alama dai yau taji dadin zuwan namu din sai take jin mu kamar wasu kawayen ta can. Su kuma Aisha uwayen rawan kai sai suke ganin zatace basu waye ba yasa suke biye mata suna ta hauka. Suna rawan sai gashi ya fito saye da wasu tufafin ya sauya kayan sun mashi kyau sosai sun fitar mai da kurciyar shi fili ta mika mai hannu wai yazo suyi rawan ko mai ya rada mata sai tayi dari ta sunbance shi yana dan dariya ya juya ya fita sukaci gaba da rawan su nan. Ganin ya fita gida nima na mike nace haka ake rawan sai tace sai fa na cire hijjab a jikina za a ga rawana. Naki nan suka kamani da kokawa sai da suka cire min hijjab din wai in taka hakana ina cire hijjab din nan kuma suka shagala da dada kyau danayi wai ina boye kaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:07 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM HASBUNALLAHU WANI,IMAL WAKEEL, , , , Yana tsaye daga kofan falon da waya a hannun shi yanayi ya tsura muna ido da mamaki yake kallon rawan da mukeyi din duk mun shagala mun buge da rawa bamun ya dawo ciki ba a lokacin. Merry sai tafa muna take da hannayen ta duka biyu a hankali ya tako zuwa wurin remote din ya dauka ya kashe kidan. Gaba daya muka mike muna mamakin abinda ya tsayar da kidan kuma juyowan nan da zamuyi mukai arba dashi ya daure fuska tamau kamar bai taba dariya ba a rayuwan shi. Merry ta tako zuwa gare shi tana fadin why dear zaka kashe muna redio muna enjoyed din kan mu zuwan yaran nan gidan nan yasani yau na shiga nishadin da tun zuwa mm a kasan nan ban taba shigar shi ba tana magana tana kokarin kwanci saman kafadan shi. Dan ture merry yayi ya yana fadin why merry why kin san hakan mu ba al,adan mu bane zaki saka yaran nan rawa kija muna hatering gun iyayyena. Rawan kawai na nishadi da suke tayani yi diya bafa gun fati naje dasu ba da kake wanan maganan haka ya kara daga mata hannun yatare da fadin please, . Daga haka ya shige ciki ya barmu zaune tsuru tsuru muna boye fuska ni dai kasa wani mosti nayi tunda na samu na saka hijjab dina a jikina na dunkule bayan Aisha. Ina ganin merry ta bishi nace ku tashi mu fice don Allah kun jawa mutane abin kunya Aisha duk jece kika jawo min haka wallahi na fada a dan hasale. Merry ta fito da dan murmushi a fuskanta tana fadin mu saki jikin mu nan fa gidan dan uwan mu ne taga mun tsorace dashi ta kai zaune tana fadin shi haka yake baison abin jin dadi a rayuwan shi sai idan shi yaso. Can sai gashi ya fito bai ko kalli inda muke ba har yakai kofa ya dan juyo yana fadin ku fito in sauke ku gida idan kun tashi. D way yadda yai maganan umurni yake bamu kowan mu ta mike da sauri muna shirin tafiya merry mamaki ya kamata ta take fadin don may zaka kore min abokan nishadina kuma kai ba zama zakayi a gidan ba. Bai kulata ba sai ficewa yayi daga gidan mukan har mun daga kowa na kokatin daukan jakkan shi nidai hannun fauziya na riko muka fito tana biye damu da tikeken cikin ta a baya tana fada dashi. Yana cikin motar dake rufe lif a lokacin muka karaso wurin motar muka tsaya ya sauke glass din motar yana fadin kanwata zagayo ki shigo nan gaba wurina da cewan fauziya don ita yake kallo yana magana. Ban san lokacin da bakina yace zamu iya karasawa gida ai ba nisa don islamiyan mu ma yana gaba da nan. Shoutup ban tambaye ki ra,ayin ku ba yace da sauri na rufe bakina muka fada bayan motar da tsoro da mamakin shi ashe yana iyawa matar shi haka yadda nake ganin su a soye kullun. Maimakon ya mike damu hanyar gida sai ya dauki hanyar da zai fitar damu daga unguwar gaba daya. Kallon kallo muka fara yi kasa kasa na radawa Aisha da ido ina kuma zai tafi damu haka ? Sai muryan shi mukaji yana fadin sayar daku zanyi kin san ni dan yankan kaine ai ko baki sani ba yace ba tare daya juyo ya kalle mu ba. Sai ya ja tsuki yaci gaba da tukin motar shi shiru na wani dan lokaci yace idan ni ba kafiri bane aike da kika buge da rawa yanzu kin dauki hanyar zama kafiran sallon kuje gida ku fada kunyi rawa a gidana ace zata koya maku kafirci. Duk wanda naji wanan maganan a bakin shi sai na bata maku rai dukan ku baku san halina ba ko ? Kina wani boyewa a cikin wanan abin kullun ashe shedaniya ce ke ko bai fada ba nasan dani yake fada nidake cikin hijab din ya kama ina rawan shakiyanci. Ya furzo da iska daga bakin shi ta yadda muke iya jin sa bai kara magana ba sai daya tsaya a bakin wani katafaren shago da akaiwa manyan haruffa rubutu. Ina dan kallo wurin naji yacewa fauziya barin maku tsaraba kuje dashi gida ko yana kallonta tare da fadin wa yan nan yan shagalan sun kwaso ki sun barki zaune. Ya fita ya zagayo ya budewa yarinyar nata bangaren ya rike mata hannun suka fara tafiya a nan ya barmu zaune tsuru tsuru a cikin motar. Murja ta fara magana tace ashe gaskiyar fatima da ki kace bahagon mutum ne sosai gashi ko ya nuna muna yau din. Ni wallahi da nasan yana nan da banyi rawa ba har ya zargemu wai muna karya da uztazanci a fili. Shiru nayi ban iya furta komai ba sai lokacin da naji Aisha ta fadi hakan na dago kai daga kallon wajen da nakeyi nace bafa daku yake ba dani agolan gidan su yake kukan ai kannen sa ne bai maku fada . Ba yazo ya samay ku da farko kuna rawan ba baiyi fadan ba sai Aisha tace ke kila fa don yaga yadda mumun ku da hjy su suke yasa yayi gudun fitina. Muna nan ciki zaune sai ga wani yazo da uniform din wurin yana fadin wai ance ku fito ku shiga daga ciki yana fadi ya juya abin shi. Bin mutumin nayi da kallo sai kuma na juyo nace ku shiga ni ba inda zanje Allah. Kallona sukayi kawai kafin suce mukan zamu shiga mu dibi rabon mu suna fita zuciyana ta bani in bisu muga gudun shi. Da sauri na samay su har sun tura kofan sun shiga nima nabisu yana rike da hannun fauziya yace kowa ta dauki duk abinda take so. Tsayawa mukayi muna shawara a tsakanin mu kunga mu dauki biscuit da sweet kawai koda bibiyu ne kada yaga haukan mu ko muyi kauyanci nace enyyeh kawai. Ban tsaya ko inaba danaga sun nufi sashen kayan zaki nikan na nufi sashen wasu kaya dana hango. Dogayen riguna mai tsaron wurin yana ganina ya taso yana fadin hjy a tayaki dubawa ne nace eh kawai nan ya shiga zakalo dogayen riguna masu tsadan gaske har guda biyar. Nace sun isa na nufi gurin turamay nace ya zaba min ya dauko masu tsada gaske ni dai ban hana ba guda hudu na zaba nace ya saka a basket din ya bini da kallon mamaki na fuske sosai. Sai na koma wurin turare da man shafi ina dubawa nan ma mai tsaro yace bari na zaba maki daidai da jikin ki ya zabar min turare masu tsadan gaske da kamshi na juya kowa sai kallona yake yana mamaki. Daga haka na nufi gurin mai lissafi nan na samay su harshi suna jirana Aisha da murja suna ganina ido waje sun bude baki suna kallona da mamaki na iso inda suke tsaye. Kallon kayan Aisha tayi tace A ruwa nace A wuta dan Allah niki kyale ni kin ji tace cewa fa yayi abinda muke so nace ai shine na dauko wanda nake so din tunda raina yana so. Yana jin mu baiko kalli inda muke ba sai mai lissafin yace oya hajiya ina naki na tura mai basket din na ja baya sai da acounter din ya dago kai ya kalle ni ya girgiza kai yana dariya. Ni dai na fuske ya buga tare da dago kai ya kalleshi yace 2,2500 a cikin rashin damuwa da komai ya mika mai dan kati naga sun cire ana saka kayan a leda. Nace kai an saye duka ne ya dago kai yace har an biya ai hajiya sai kuma tsoro ya kamani dan ni ba haka na shirya a raina ba. Naso yace don may na dauko wanan kayan kamar mara hankali ince bakai kace in dauki abinda nake so ba sai kuma aka samu akasin hakan ni yanzu may zance a gida idan mun koma. Amma wallahi A ruwa ke yar iskace wai yaya akayi kikai wanan tunanen haka , ? Nace ganin iyaka najeyi na fada a ciki akaga nawa ni mai zance akan kayan nan gida yanzu ya juyo a fusace yana fadin ba zaku shiga mota ba kun tsaya kuna gulma a nan. Da sauri muka shige motar yadda mukazi haka muka koma ya sauke mu a kofan gida bai shiga ba yaja motar shi ya wuce. Cirko cirko mukayiba kofan gidan ance ko lahira mai kaya shike wahala yanzu a nan sai aka barni da tarin ledoji a gaba ganin sun fara shiga sai dariya suke min yasa nabi baya su da sauri da tarin ledojina a hannu. Muka shiga part din Amma sai dariyan keta suke min na zauna ina kumbura baki . Amma da ta fito wanka tana saka riga a jikin ta ta kalle mu tace lafiya kuke wanan dariya haka ? Nuna mata ni sukayi tare da kayan dana tara a gabana tace wanan kayan na may ye kuma ? Aisha tace bari ke dai Amma ta fada maki da bakin ta yau tarko ne yakama mai shi a wurin nan. A ruwa bata labari da bakin ki taji na kalle ta da harara bace A wuta dai wallahi Aisha ku daina kirana da A ruwa din nan na juya gurin Amma nace. Amma ai duk keda manjo ne kuke kirana da wanan sunan har suka samu. Baki son sunan ne yar nan ai wanda aka haifa ana ruwa akecewa A ruwa ko damana shi kuma namji ace mai Ana ruwa. Ni har suna nawa za a saka min a barni da fatima na zai fi mun dadi wallahi amma wai wani a ruwa can babu dadin ji haka ? Na karasa ina bata rai ledan na taka da kafana na tuna dashi a gurin itama Amma ledan ta kalla tana fadin wanan kayan fa na maynene a ciki ? Sai suka kama dariya babu kakautawa har hakan yasa mama hadiye data dawo daga gurin aiki ta fito daga dakin ta tana fadin gaku kamar mahaukata mana ? Nace a marairaice mama wani sukewa dariya don kawai wanan mijin kafirar da mukaje gidan ta ya kaimu shago yace kowa ya dauki abinda yake so nikan na kwaso wa yan na rigunan na daukowa Amma da manjo da mamu da Addah zannuwa shine suke min dariya. Murja tace mama ba hakana bane taso yace ta mayar tai mai halinta sai gashi ya biya kudin babu tambaya. Maimakon inga mama tayi fadi wani magana sai itama ta kwashe da dariya a gurin na kalli kayan cikin marairaice murya nace mama yaya zanyi da wanan kayan haka yanzu shiyasa ma nayo nan gurin Amma in samu mafita da kayan. Mama ta dan tsagaita dariya tace aisai ki saka abinki wanda kika daukowa su hajiya kuma ki basu abinsu. Da sauri Aisha tace wallahi sai dai mu raba Amma tace ta hanaku daukowa ne shifa ya bada bakin duk abinda mutum ke so ya dauka ku ina abinda kuka dauko a shagon ? Sai lokacin suka dan shiga natsuwa suna fadin wallahi Amma a ruwan nan shegen wayau ne da ita mu san bamuyi tunanen haka. Da mun sani ai muma jidan kayan zamuyi kamar haka mu biscuit kawai da sweet muka dauko daya daya . Allah ko ya shirye ku da bakin kwadai yau kunga illar kwadai gare ku, sakarkarun banza kawai . Jin haka murja ta kara fadin to mu munsan da hakane in bada mukaga ya biya wanda ta dauka ba mama hadiye tace ai kune abin dariya ba ita ba. Yar albarka shiyasa nake sonki kamar yadda kike sona watau ko a ina kike ina ranki ke nan yar nan da har kika kasa mantawa dani. Nan tayi ta samin albarka tana yabawa sai hankalina ya dan kwanta don nasan ko ba komai zata tare min fadan da nake tsoro na mamu. Cewan da Amma tayi cikin maganan ta ashe Sani nada gaskiya wanan hadin da alama zatai kyau kyakayawan jumma,a tun daga alhamis ake ganewa. Na shagwabe fuska ina fadin Amma yanzu ke zakiwa mamu magana ko tace maganan may zanyi abin yiwa kai idan yayi maki dawainiya ai kansa yaiwa ba wani ba. Jin shiru da mamu tayi ashe ban sani ba fauziya har ta fice zuwa part din mu mamu suna tambaya akace da ita ina nan shine ta biyu ni don bata gane zancen da fauziya ke mata ba na gulman an saya muna kaya masu yawa wai nace ban so. Hankali tashe mamu tayi sallama a falon tana fadin yanzu fauziya take fada min wai kun dawo kina nan kinawa gwaggo rikici. Ke ba wani rikici da tayi tsaraban fitan su ne wai take tayar da hankali a kai kada kice tayi rashin hankali. Kallon kayan da mama hadiye ke budewa a gaban ta tayi da ido tana fadin kayan may ye hakan ? Nayi tsuru tsuru da ido sai mama tace Umar ne da zasu dawo gida ya biya dasu shago yace kowa ya zabi abinda yake so su wa yan nan sakarkarun wai sai biscuit suka dauko. Ita ko diyana sarkin wayau kinga sai ta zabo wanan kayan haka shine fa take nan wai tsoro fadan ki takeyi. Inda nake ta kalla take fuskan ta ya sauya tana fadin sayadi wanan rashin hankalin fa haka ? Kin fi yan uwan ki ne da suka tsaya iya matsayin su sai kece zarara kika kwaso wanan kaya haka kamar hauka. Muryan mama hadiye ke fadin ke tayani ganin abin mamaki wai fa super ne atamfar nan ? Sai mamu tace wanan hauka daga ina hakan nan Aisha tace wallahi mama A ruwa bata san zai saya ba kai tsaye kin santa do tsokana don yace kowa ya dauki abinda yake so shine ta dauko su haka . Idan yayi magana ta rama haushin fadan da yai muna a mota tayi wani rashin hankalin ne kuma ko ? Bayan wanan shima umar zai biyewa karamar yarinya haka ai wanan abin magana ne gidan nan idan hjy ta sani sai ta gaskanta abinda take fada a kan mu. Ikon Allah yanzu don umar yaiwa wanan yarinyar hidima haka shine abin tsayawa bata baki don zamani ya canza ko aimu da garemu wanan abin alfahari ne gare mu. Don an baka toshi gwaggo wanan fa ba toshi bane rashin hankaline irin nata kawai sai amma tace yanzun dai na fahince ki sosai watau dai kin raba daya biyu a tsakanin yaran nan dai. Jikin mamu ne yayi sanyi tace ba haka bane gwaggo wallahi abin ne naga kamar yayi yawa duk irin nasihan da naiwa yarinyar nan sai da ta zubar da kimanta a idon su. Abu haka kamar wata zararariya har ina yar nan tasan ta zabo kaya haka masu kyau da tsadada sauri nace bafa ni na zabo ba yan wurin nace su tayani zaba. Tace ina kinji rashin hankalin gwaggo tana kallon Amma data kawar da kanta daga kallon mamu din tana jawo ledan goron ta. Ta juyo tana fadin ki fita daga idona maimuna tunda ke baki san abin arziki ba dai kayane kuma nace yar nan sai ta saka su a gidan nan kowa ya gani. Mai mutuwa yaje ya mutu da bakin ciki ganin ran Amma ya baci sai mamu tace ban hanata sakawa ba ai amma ta bar wanan halin don watarana. Kuma ta raba da yan uwan ta suma su samu da sauri Amma tace la,la,la haramiya wallahi ba wanda zata ba su a yanzu gaba daya ita zatai amfani da abinta tunda tana so waya hanasu su zaba cuncan ai dama ya basu Allah ya cisheta daga gare shi. Dole mamu taja bakin ta tayi shiru tunda ta fahinci Amma ta daure min gindin abin dole ta kyale badon taso ba. Mamu ta juya zata bar shiyan tana fadin ki kwaso kulolin abinci idan zaki dawo Amma tace yaki nan maimuna. Sai mamu ta dawo dan shiru Amma tayi tana kallon ta kamar yadda kowa na fali yai shiru yana sauraren ta tace kada inji kada in gani kin yiwa yarinyar nan magana a bayana don zan saba maki sosai. Ki godewa Allah kin samu yarinya mai tunane da har samun ta bai wuce muba tun yanzu don turamay nan da kike gani ra dauko da gaiya da sunana dana kakarta da yar uban ta saike ta dauko su tun can. Wanan abun datayi ashe ba zai zama abin alfahari gare ki ba su wa yan nan sakarkarun ai kinga kayab shirmay da suka kwaso a can . Sai magana na biyu wanan magana a barshi a nan inda akayi shi a tsakanin mu duk wanda ya fitar da zancen nan waje ban yafe mai ba bandai ki shi mijin naki ba zaki iya fada mai don ko baki fada ba ninan zan fada mai komai. Don haka shine maganata dana kiraki sai mamu ta sauke ajiyan zuciya jin an hanata ta yi min fada da tasha alwashin yau sai naji a jikina sosai a gurin ta . Mamu tace gwaggo ni ba nice uwarta ba ga anty hadiye nan ita ya kamata ta dauki na uwar bani ba. Aiko da sauri Amma tace haram ai na fada maki ko kyale ba za a tabawa yarinyar nan ba yadda ta tsaro abinta haka za a yi. Su gobe du kara idan haka uwar su tayi masu tarbiya da abin kwadai maza kwashe kayan nan ki tafi dasu kibi uwarki idan kuma kika bata shi ban sani ba ban yafe maku ba. Kai hajiya ai abin bai kaican ba may ye na abin Allah ya isa a cikin maganan mama hadiye ta fada adan hasale tana barin falon. Ni dai na kwashi kayan nabi mamu dasu a baya tare da dauko kulolin abincin Amma din na mara mata baya da kaya nikiniki a hannu na. Sai dai muna fita mukai arba da hjy maryam da yaran ta a barandan part din ta zaune wai suna shan iska duk da wutan nepar da akedashi. Dagani har mamu babu wanda ya kalli inda suke yayin da gaba dayan su suka tsuro muna idanuwan su a kan mu. Ikilima ce tace A ruwa ina kuka je yau baki shiga islamiya ba nace inda kika aike ni sai uwar daga inda take tace magani ki ke nan da tambaya ina ruwan ki da ita aikin samu amsan bakar magana yanzu. Mu dai muka shige muka kyale su a nan ina ta dari dari da mamu kada tayi min fada don naga ranta ya baci.. Sai dai muna shiga ganin manjo zaune a falon yasani matawa da fadan mamu na zube kayan ledan a gaban ta na kai kayan dana kwaso na abinci kitchen na dawo ina cire hijjab dina. Yar nan ina kika shige haka duk yinin yau baku yini damu ba kafin in bada amsa Addah tace an fada maki sunje gaida matar yayan su na nan gidan ne ita da yan uwanta tace to to ai na manta wallahi. Muna nan zaune da manjo muna hira da yake ina fashin sallah yasa na ban rama sallolina ba da akayi muna waje. Kiran sallah ne ya tayar damu a gurin sai da muka fito bayan kawu ya shigo ya gaidasu manjo ya fitane na dauko ledan ina fito da turamay zannuwan daga cikin leda. Wanda duk na dauko da sunan kowa na mika mai don na barwa Amma nata tunda zan dauko kayan a part din ta. Turmin suke bi da kallon mamaki har na gama mika masu wanan fa na maynene Addah take tambaya ? Nace wanda mukaje gidan sa ne ya saya muna su ni dama da sunan ku na zabo do yace kowa ya zabi abinda yake so. Nan dai na sake na basu labarin komai da ya faru lokacin fitan namu manjo ta kalle ni tace A ruwa duk wanan kayan haka mai yawa ya saya maki a lokaci guda haka ? Ko dai da wata a kasa ne yana toshi ba sani ba nace kai kaji manjo kuma sufa masu kudine ana fadin kudin kayan ya mika kati aka zare kudin. Manjo yau naga gida wallahi wai fa duk nasa ne bana kawu ba wanan ma ai ina yafi kawuna kudi nake gani. Ikon Allah kuma kawun ki ne ya haife shi nace shine babba dan sa ina gani ni dai ban sani ba son yawa ke gare su kuma fa uwar su daya dukan su. Shigowan mamu yasa naja baki na ba tsuke don kada tace min na cika zuba kallon kaya tayi tana zama sai Addah tace gamunan muna sauraron ikon Allah wai fatima ce tayi muna tsarabab kaya haka. Anty Addah wanan yarinyar ni ban san irin ta ba yau ai gwaggoce ta kwace ta a hannuna don tace kada in fara in mata fada zata saba mun in banda hauka irin na yar nan daga ance ku zabi abinda kowa ke so sai kiyi diban hauka haka. Kurciyace wataran zataji kunyar yin hakan shine wanda kuka gani jiya da kuka iso suna magana da uwarsu a waje babban dan maugidan nan ne a kasan waje yake zaune da italin shi ta fada a takaice. Amma tana fada muna yanzu wai gidansa abin tsoro ne kamar gidan dan yankan kai. Da sauri mamu ta kallo inda nake zaune tana hararana tace wanan yar da sheri take wallahi umar din ne dan yankar kai ? Bakinki kanin kafan ki duk na sake jin wanan magana zan saba maki sosai wallahi nan dau ta shiga fada masu irin aikin da yakeyi a can nima na bade kunne na ina sauraren sirin da ban sani ba. Ya shigo gidan ya nufi gurin hjyn su sun gaisa ba wani damuwa ya dan taba hira da ita take mai maganan bukin yar uwanta da take son su halarta ranan asabar yace mama ai tunda muna gari zamuje daurin auren insha Allahu. Ya mike yana fadin zan leka wurin Amma kwana biyu bamu hadu ba sai hjy ta tabe baki tana fadin ai kunfi kusa da ita kadaiyi takan tsantsan don kasan kansu a hade yake da wanan. Yi yayi kamar bai fahinci may take nufi ba yace babu komai mama insha Allahu ina kiyayewa ai taji dadin samun kansa yadda take so a ranta. Ya shigo da sallaman shi tana zaune saman kujera three seater inda ta mayar kamar shine wurin zamanta. Shidai da zai samu sai yace Amma ta koma gidan sa da zama har matar shi ta haihu sai dai yasan hakan ba zai samu ba. A yadda yasan Amma tana taushe zuciyar tane kan shi da matar shi don kawai, kawai a gare shi don haka ne ya kasa fadar manufan shi ga hakan tunda yana ganin wata kila merry ta haihu a kasan nan kafin su koma. Tunda aikin daya dauka wasa abin ya wuce nan saboda wasu abubuwan sai a waje ake sayosu can. Wanan matsalan ya kawo mai cikas ga komawan nasa inda da kyat ya samu ya shawo kan merry ta yarda ta zauna na dan lokaci ga kuma can iyayyenta ba faman kiran waya ta dawo kada haihuwa ya rutsa da ita a nan din. Zama yayi a gefen Amma saman kujeran da taks zaune a kai tace nikan ban gane wanan auren ba yanzu tun zuwan matar ka sai ka share fiye da sati baka shigo gidan nan ba. Ya dan kalleta yana fadin dama nasan da haka ina zuwa sai dai a kuraren lokaci nakan shigo gaida mama wani lokaci ma ban samun dady a gida idan nazo. Eh lalai kuwa yanzu na fahince ka watau har ka shigo gidan nan ka fice sadauki baka damu da ka leko nan inda nake ba ? Yana dan dariya yace tuba nake tsohuwa mai ran karfe kaina a kasa kin san ni ban iya karya ba a rayuwana ko nayima kamani akeyi. Turmin zanin da ke shan kallo a gurin Amma tu lokacin dana bata ya gani aje a gefe yace wai ke Amma har yanzy kina dinki da kanki ne haka ya mika hannu ya dauki turmin yana juyawa tare da fadin zanin nan ko yana da kyau sosai. Amma ta dan kalle shi tana murmushi tare da fadib kaima dai ka fada din daga masu kaunana zani yafito yasa yake da kyau sosai haka kowa na fadin kyawon zanin ai. Su waye masu kokarin kife min gwaunati a furin ki har kike murna haka Amma a sanina dai nine dan gaban goshi naki tace har gobe kuwa. Don wanan zanin daka gani daga gurin ka ya fito ya fada hannuna saboda so da kauna. Da sauri ya kalleta yace ni kuma Amma yaushe akai hakan tace gashi nan dai ka tuna idan zaka iya. Ya dan girgiza kanshi yace ban tuna ba gaskiya tace to ba wani ya bani ba sai amaryan ka cikin wanda ka saya mata dama wamu ta zaboshi ko dakin uwar ta batakai ba ta kawo min nan. Da sauri ya aje zanin saman kujera yana tsuke fuska Amma tace ni wanan hadin naku yafi min dadi dana sauran . Ta dago kai tana kallon shi ganin yadda ya bata rai tace ya kuma naga kamar bakai murna ba da hakan ko ita kaso ta daura zanin kagani a jikinta ? Kai Amma da wani zance kike ni ban ma san abinda ta dauka ba a shagon don hankalina baya gare su. Dan murmushi Amma ta sauke a fuskan ta tare da fadin sadauki ina fatan ba uwarka taci galaba bane a kan ka yadda na dauko maganan yarinyar nan ka bata ranka haka. Yace No ai idan nace zanyi abu zanyi ne tunda kikaji na amsa zanyi din ne da ba zanyi ba tun farko zan bijire maku kan zance sai dai ina son farin cikin daddy mu nima tunda hakane burin shi. Shiru Amma tayi tana dan nazarin maganan shi a ranta kafin tace sadauki shin tsakani da Allah ko zaka auri yarinyar nan don kada azo ai abinda za a dawo daga baya ana da an sani a cikin sa. Yace watau Amma har yanzun dai baki gama fahinta ta ba ke nan tace ina zan fahince ka dan nan da wanan maganan taka. Yace ba wani abu bane Amma sai rawan kan yarinyar dayai yawa dole daddy ya bamu time har zuwa lokacin da zatayi wayau. Ikon Allah A ruwa din ce yarinya dan nan yarinyar data dade da zama mace mu lokacin da akai muna aure aiko faduwa bamuyi don a dakin mijina na fara al,adata ganni nan ko har yanzu ba abinda ya samay ni. Amma maganan da kikeyi ba na yanzu ba zanso ace anbar zancen nan har nan da shekaru masu zuwa nan gaba daidai lokacin ta kara karatu sosai tasan komay. Kaima sadauki da wani zance kake ai indai ina raye yaran nan ba zasu kara shekara ba a gidan nan nan gaba. Yace amma Amma tace hakan ne buri na gare ku sadauki kaji na fada maka. Shiru yayi yana tunane a ranshi kafin ya mike ba tare daya kara furta komai ba yana fadin ni zan tafi Amma sai wani lokacin. Tace ka gaida iyalin naka idan ka isa gida maganata dai babu fashi a cikin sa baice komai ba ya nufi hanyar fita tace wai ko kasan kakan yarinyar nan tazo tana garin nan kaje ku gaisa. Ya kulu matuka ji yake a lokacin kamar ya hadiye ranshi don haushin maganan tsohuwar shi da yazo da niyar su danyi hira ta dauko mashi magansn wanan fitsarararan yarinyar kuma. In ko banda biyayyan mahaifa kamar shi za ace wai za aiwa irin auren nan na hadi haka kai tsaye. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:07 - 🀐🀐🀐: YA ALLAHU YA RAHAMAN YA ZUL,JILLALI, WAL,IKIRAM ALLAH, Kawu ya dawo a gajiye yau girkin hjy jummai ce yasan ba wani kulawan da ya dace zai samu a wuri ta ba. Ga mamaki shi hajiya ce ta shigo dakin dauke da kayan abinci yau bata turo yar aiki ta kawo mai ba kafin ya dawo a jera mai sai dai ya dawo gidan ya samu an aje . Zama tayi bayan ta aje abincin tana mashi sannu da zuwa ya amsa mata a cikin sakin fuska don yaga yau tazo gare shi da shiri. Sai dai yasan ba zuwan Allah da Annabi bane dole akwai wani shiri da tayi a kasa da take son gabatar don ya gama sanin halinta kamar yunwar cikin shi. Remote ta dauka tana rage karan tv don karan yai mata yawa shidai bai tanka ta ba yana kallon ta sai da ta rage take fadin . Yau ka jima a waje mana tana kallon shi yace eh abubuwa ne suka tsayar dani don kayan da Ahmed yaje daukowa suna gap da shigowa kasan nan. Sai ta dan nisa tare da yin shiru kafin tace amma ina ganin lokaci yayi da Ahmed zai daina wanan tafiyan a samu wani daga cikin naka su fara wanan hidiman da kan su. Dan murmushi ya sauke irin na manyan a fuskan shi yace jummai ke nan a cikin yaran nan yanzu wa kike ganin zan dorawa wanan nauyin mai wahala a kansa ya iya dauka . Ko kin dauka aikin wasa yake fita yi can din kawai tace koma may nene shi ya iya balle naka humm kawai yace ba tare da yai mata magana ba. Sai can yace zuba min fruit din nan in sha kafin a fara labaran kasa ya fadi ba tare daya kalleta ba yake magana. Ta mike da kyat tinkis tinkis zuwa wurin data aje ta fara zuba mai ta kawo mai gaban shi ta aje tana zama ne tace wai ni wasu irin bakine haka suka zo muna gidan nan. Da sauri ya dago kai yana fadin baki a ina suke don shi ya manta shaf da su manjo na gidan lokacin . Tace wa yan nan bakin mana da suke dakin maimuna kasan fa muna da yara kankanu a gidan nan irin tsofin nan data kwaso ba abin yarda bane a yanzu da duniya ta lalace din nan. Sai da ya kurba fruit din yace ai kin gama maganan ki da kika ce duniya ta lalace ko ba baki sai a samu mugai a cikin gidan nan ba a bin mamaki bane. Tace Alh ke nan ai na gida an saba da halin su wlh gaskiya nake fadi a magana ta kasan tun farko ni ba son wasu suzo su zauna muna haka a gida nake so ba don tsaron lafiyan mu. Yanzun may kike nufi da wanan maganan naki bakin nan fa ba wasu baki bane can na waje kakan yarinyar nan ne fatima tazo checkup da yarta su kike kira da baki ? Tace baki ne kan tunda ba zuriam kowan mu bane banga dalilin da dan wanan halakan zaisa suzo su zauna muna a gida haka ba. Don ni ban yarda da zubin mutanen nan ba kamar wasu muna fukai dasu kullun a daki kumshe. Kai jummai kin san abinda kike fada idan ma hankalin ki bai kawo ba ki tuna mutanen nan nan gaba halaka zamu hada su mai karfi a tsakanin mu ba gida na ba har gidan dan ki watarana zasu iya ziyarta. Wani kallo tayi mashi kafin tace gidan dana fa kace Alh wani dan nawa kake tunanen zasu ziyarta a cikin yaran nan , ? Yanzu dai na fahinci abinda ya kawo ki dakin nan kinzo ne kawai ki tayar min da hankali na dawo da gajiyan kasuwa a jikina haka ? Wanan kuma sai in kaso fadin hakan ni dai akan wa yan nan mutanen yanzu nayi ma magana ba fitina nazo nema da kai ba. Yace bakina ne tunda bakin matatace don haka ki barsu nan inda kika gansu tunda ba a kanki suke zaune ba. Mutanen da ko waje ban tsanmani suna fitowa zaki zo da wanan maganan ke yanzu ba abin farin ciki bane a gare ki yau bakin sun sauka a gidan nan zamu samu ladan da Aah ya kwadaita muna ga wanda ya ciyar da bakon sa. Hjy data gama hasala da zancen shi don ba haka taso ya dauki maganan ba tace dama nasan abinda zaka fada ke nan akan may maimuna zata gaiyato muna su a gida haka ? Wai maiye matsalan ki da mutanen nan kilan ma tun da matan suka zo baki sauke hakkin ki kun gaisa dasu ba to don may zaki zo ki sakani a gaba da zancen su yanzu. Gidan nan gidanane fa gidan mata hudu kuma saboda ke sai in tauyewa sauran iyalina hakkin su ko haka kikayi a baya kan yan uwan maryam dake zuwa gidan nan kai da kai sai da kika samu fitinan da kika dora mutanen nan suka dauke kafan su da gidan nan. Ta kalle shi tana fadin sheri zakai mun kuma yanzu akan maryam yace meye abin sheri a ciki tunda anyi hakan nasani. Daga haka ya mika hannu ya dauki remote din shi ya kara ya barta nan tana cicika do ba haka taso ya dauki maganan nata ba. Sauri nake na fito daga part din mu zan shiga wurin Amma dake kirana hjy jummai ce tsaye da wasu hamshakan mata a waje. Tunda na gansu nasha jinin jikina dasu hakan kuma bai hanani saurin da nakeyi din ba nazo daidai inda suke naji hjy tana fadin kungama ga yarinyar nan da Alh ke son lalakawa yaron nan. Gaba dayan su suka jiyo suna kallo na a raina nace kiyi ki gama ni ba ruwana da lamarin ki iyaka dai ki nunani kice nice agolan gidan ku ga kowa don na dauka shi take fada masu din. Dayar matar dake da haske a cikin su tace tuburkallah ai Alh baiyi hadin banza ba a nan kina ganin ta nan idan ta samu wuri bajewa zatayi sosai yanzu akwai sauran kurciya a tare da ita. Dayan mai tsayi kamar hjy tace eh da alama kan zai more auren sa sai dai matsalan abin ne ai yar kishiyar tace fa aka fada maki shine babban matsalan ai. Ni ai ban hango wanan hadin ba don zancen banza naji kunayi a nan kamar baku tayani bakin cikin wanan abin ma ? Har nakai Part din ina mamakin maganan su don duk abinda suke fada a kunne na yake ina jin su. Ina shiga nace Amma ji min wanan matan tace wacece kuma na kai zaune ina fadin hjyn su salma mana yanzu na wuce ta da kawayen ta a waje suna gulman wata har da fadin wai ita ba zata yarda dan ta ya auri yar kishiyar ta ba sai fa da ta ganni take wanan maganan Amma ? Ko an fada mata diyan ta suna burgemu ne oho indama ba yaran nata arna suke auro mata ba a matsayin sarakai. Ni kan indan na tashi don taji haushi uztazu zan dauko gidan nan yazo yai ta maku wa,azi taji haushi. Amma tace kaiya yar nan ai kaddara ta riga fata koda yake mijin naki ba laifi a wani wajen yana da gwargodon ilimin shi sosai. Ji Amma don Allah ke kin san wanda zan aura din ne da kike wanan magana keda kuun kina a falo zaune murmushi tayi tana kallo na tare da fadin idan na sakaki a lale zaki bayani. Fauziya ce ke fadin wai inzo mamu na kirana dama guduwa nayi kawai in tsokali Amma zamu tafi islamiya ne lokacin. Hakan yasa na mike da sauri ina fadin bari in mun dawo sai inzo ki fada min mijin da kike min hasashen. Bayan fitar mu islamiya mamu na tuka tuwon dona dora kafin in fita hjy maryam ta yi sallama a falon part din mamu din. Daga ciki mamu ta karba tana fitowa falon don ta sheda muryan nata ko ta fito tace a, a hjy kece ashe da dan murmushi a fuskanta. Wlh nice nace bari idan leko in gaida baki ashe baki kikayi haka gurin hjy nake ji da take fada akai. Mamu taja ta tsaya tana fadin ikon Allah fada akan may kuma ko wani abu ya faru ne tace kawai dai kin san halinta ita kanta kawai ta sani ai. Ta fada maki zancen bukin da sukeyi ne sai mamu tace hjy ke nan ina zanji tana da buki Allah dai yasawa auren albarka. Ta tabe baki ba tare da fadin amin ba take fadin ai ko yaya ne dai zaka sanarwa wayanda kuke tare dan uwan ka na buki ko addua aikayi masu. Idan da sabo aini na saba da halinku a gidan nan tun ban iyaba har na iya yanzu Allah dai ya huci zuciyar ku ya bamu hakkurin zama da juna tunda zama ya hada. Dan dariyan yake tayi tana fadin kai maimuna akwaki da wani zance aiko ni ba zaki fada min haka ba a kanki. Ida ban damu dake ba ai ba zan shigo yanzu in kula da bakin ki ba dama dai ai itace mai nuna bata son mu,amulan kowa a hade. Allah ya kyauta mamu ta kara fada tana kwantawa sama ha;u kujeran da take tsaye kusa dashi. Tace zama tare ne ya kawo hakan sai hakkuri da junan mu sai hjy maryam itama ta dafa kijeran kamar yadda mamu diin tayi tana fadin aiko kan maganan hadin auren nan bakiji abinda take fadi ba. Mamu tace komai zata fada nafita baki ciki da wanan hadin don ni diyata na sani kamar yadda tasan danta. Itama ta kyamace mu balle mu da za a tauyewa yarinya yancin ta na budurci a hada da mutum kamar umar ni ainafita jin zafi da kyamatan hadin wake son hada zuri, a da ita idan ba dole ba. Anty bari kiji nifa badon gwaggo da Alh da suka roke ni in yarda da hadin nan ba babu abinda zai sa in yarda da wanan bakin hadin. Mumu tasan zancen ta a kunnen hajiya yake yasa take bada sako a kai mata don tasan da dawowan ta sakon ta zai isa gare ta ta tsaya ta fadi magana iya son ranta kafin hjy maryam din ta fita. Muna islamiya fauziya tazo min da kuka dan wurin hjy maryam ya duketa don suna fada da kanin su karamin. Ina zuwa ban tsaya tambaya na rama mata dukan naja hannun ta muka tafi har mu fara hanya ikilima ta samay tana fada wai don may zan doki kanin su. Nace na doke shi ki tambaye shi shi may yayiwa fauziya na rama mata shike nan don wani yafi wani karfi sai ya duke shi daga dan magana kawai. Kamar zatai magana sai kuma tayi shiru na juya na fara tafiya naji muryan ta tana fadin wai ita A ruwa din nan don kawai taji ance zata auri yaya umar ne takewa mutane wanan rawan kan dama ba cusa mashi ke akayi ya aura dole ba balle kiwa mutane sallo. Na juyo da sauri ina fadin wani ya umar din tace ai duk kin sani bari kiji idan ma cusa mashi ke akayi ba ya aura bai so shida hjyn su. Balle ki dinga yiwa mutane rawan kai a gida kina kutin ke zaki auri mai kudi har asirin da akayi don hakan ya faru muna da labarin komai. Ikilima shirin naku na gado har ya kawo gare ni dama kulle kullen da kukeyi ke nan daku da uwar ku don kawai ku bata muna suna. Yau Allah ya matsi bakin ki ki fada da kanki kowa yaji sai dai ki sani ni har yanzun ma ban gama sanin sunayen diyan hjy ba a kaina balle in san ko waye umar a cikin su. Nace kukan kunyi hasaran rayuwa uwa gulma diya gulma sai ko ta kai min duka nan fada ya kaure a tsakanin mu Allah yaban sa an ta na kaita kasa na haye na murji bakin ta sosai ban daga ba sai da naga hancin ta da bakin ta yana fitar da jini su Aisha dasu salma suka banbareni a kanta. Har muka kawo gida ana cacan bakin maganan ida nake ji kamar dukan danayi mata bai isa hakana ba. Dan tsayawan da mukayi a hanya fada yasa muka bata lokacin mu sosai a hanyar dawowan mu gida. Muna shiga gida wani sabon fadan ya kaure don ban kai ga shiga gida ba su ikilima suka rigamu shiga gidan har sun fadawa uwar su tana ganin jini ranta ya baci ta fito da jidali. Sunana uku da ake kirana dashi ta kirani dasu a jere tana fadin an aiko kine ki masu wanan dukan haka don jin haushi da takaicin su da kike ji ko may ? Saratu kanwan ikilima tace wai fa don kawai tace kanta yana rawa don taga za a aura mata yaya umar ta daketa. Hjy maryam tace dama ba asirin da rokon shi akayi akan ya aure ki ba din ba har uwar ki na wani cika bakin banza ga mutane. Munsan komai wa zaku dagawa hanci nan idan ba asiri bane mai zai kai Alh yin wanan hadin haka tunda kowa yasan ba ajin ki bane shi. Uhumm dama abinda kakeyi shi kake dauka kowa shiya keyi ai hjy maryam ke kika san zuwa wurin boka da malam ni ban gaji wanan ba a rayuwana. Auren Umar da ya tsone maku ido ki wanko yarki ko wata naki ki bashi ki gani in ya taba ran maimuna ko wani nawa. Fada ne na yara amma ke babban kanki kin fito kina wanan baran bakin a gaban yara haka. Allah waddan wanan halin naki maryam ke da diyan ki yanzu don baki da kunya ke, ke fadan haka a bainan jamma,a waye baisan har gatin nan kike bari zuwa bin bokayen ki ba. Mama hadiye ke magana a fusace tana kallon hjy maryam din wanan maganan da aka barshi iya mu manya gidan nan muka san da zancen nan ashe har kin feasawa yaran ki shi. Fada sosai da musayar harshe ne tsakanin mama hadiye da hjy maryam da har yakai su Alh dawo gida suka samu suna wanan rikicin tsakani su da fadan ya koma tsakanin ta da mama din. Wai may ke faruwa ne haka tun bakin get nake jin muryoyin ku haka cirko cirko akayi a gurin gaba daya saida ya kara tambaya mama ta juyo tana fadin. Zancen yaran na fa sun dawo islamiya ashe sunyi fada a can tau shine sai abindai ya zama musu rikici har yakai ita ikilima tayiwa Fatima gori wai sunbi boka da malam ita da uwar ta don a aura mata umar. Wani kallo ya watsawa su hjy maryam har yaranta kafin yace ita ikilima a ina taji wanan zancen ? Shiru ikilima tayi ya daka mata tsawa sai data kada tana rawan baki tace dama daddy na sani zaki fada min yau ko hukuncina ya hau kanki. Kuka ta fara ya sake fadin wallahi ko ki fada ko yau gidan yayi maki tsami da sauri yaron da ya jawo maganan muke fada akan shi yace. Daddy ranan da kukai maganan ne maman mu tace taje ta labe taji mai kuke ma taro har da baba na dawanau. Innalillahi ya fara ambatawa a bakin shi yanawa hjy maryam kallon tsana a fili kafin yace maryam abin naki har yakai can don kawai zan gana da yan uwana har ki tura min yara suyi muna labe ke a dole sai kinji kinga komai a rayuwan ki ? Tir da wanan rayuwan da kika koyawa yara nan ya juya gurin ikilima da idon shi yana cewa ke kuma nasan maganin ku kafin ku karasa gurbacewa a gurin uwar ku ai. Kai ranan dai sarka tayi halinta a gidan kawu don gidan ya rikice a baki daya don sarka gidan ta fadi kasa kowa ranshi babu dadi a ranan. Don hjy maryam ta fadi har maganan da sukayi da mamu ranan cikin fadanta haka yasa hjy jummai hawa sosai. Sai fada take da mamu wanda mamu na tsaye tun amsan farko da ta bayar Amma ta kada mata kai tayi shiru taja bakin ta gum tana sauraron ta. Ganin hakan tana cin mutunci a gaban kowa duk abinda yazo bakinta na aibanci gareni ko mamu fadi take ba jin nauyin kowa a wurin. Kawu da har ya shiga part din shi ya fito yana fadin kowa ya koma gurin shi a barta taita haukan ta aure dai ne ba fashi har salma da ikilima in Allah ya yarda rana daya zan wanke su gaba dayan su gidan nan. Dama shi mutum in yayi ilimin iya shege idan ya rika sai ya koma yiwa kansa ai gaskiyar maimuna da tace albarkacin mu danki ya samu a gurin ta ta yarda da auren don haka na gode tunda har naci albarka gurin ta nida mahaifiya don mun fada taji. Sai ga hjy na kuka da hawayen ta abinda yasa jikin duk wanda ke gurin sanyi ke nan itama hjy maryam din kuka ta aza wai har ikilima nawa take da zaice zai aurar da ita. A cikin part din mu tunda kawu yai furucin sa na tabbatar da gaskiyar maganan ashe ba kake ikilima tayi min ba haka zancen yake na yanka wani uba ihu a gurin mamu ta bugeni a baki na shige dakin da sauri ina mai ci gaba da kuka ni kadai. Mamu na shigowa falon ina takure a kasa gefen kujera nace mamu wai da gaske kawu keyi zai mun aure da ya umar don su Aisha a hanyar dawowan mu sun fada min ko waye ya umar din cikin yaran hjy. Mamu ki fadawa kawu ban son shi don Allah a mayar dani gidan baffa na misau da ai min wanan aure. Wani irin tsawa ta daka min saida na firgita na manne da kujeran dake kusa dani tace ke har kinsan wani so can yanzu. Halan shima an fada maki yana son nakine ba biyayya yakewa mahaifin shi ba dake zaki kasayin abinda yayi ko butulci zakiwa kawun naki ne yanzu bayan ya gama inganta maki rayuwan ki na baya har kike fadi yanzu da bakin ki wai a mayar dake misau gidan baffan ki. Kaina dake dunkule na sake dagowa ina fadin don Allah mamu ki taimake ni ke kadai nake da a garin nan ki hana aimin wanan auren don Allah mamu na karasa cikin kuka mai ban tausayi da marairaice muryana. Au sayadi har kawun ki zai saki abu ki iya watsa mai kasa a ido ke nan ban sani ba ashe shi yana ganin yayi bugun gaba dake ya nuna ma duniya shiya isa dake kike son bashi kunya to ki matsa har ya sani baki da biyayya kamar yadda ya zata zaki mai. Tana fadin haka ta shige uwar dakin ta itama kukan take a daki data shiga abin duniya ya taru yai mata yawa dama tasan za a rina duk ranan dana tsunci zancen. Jin shiru mamu bata fito ba naci kukana ya isheni a gurin sai yan kanne na da suka zagaye ni kowa yai tagumi saman kujera sun zuba min ido suna kallo na kawai. Na mike da kyat na nufi part din Amma a cikin kuka da yai min yawa har ya fara sakar min da ciwon kai lokacin. Ina shiga na samay ta saman sallaya tana sallah isha,i lokacin ban ma san lokaci yayi haka ba sai dana fito zan shiga wurin ta naga ko ina yayi duhun dare. Ban damu da wai tana sallah ba haka na zube a gabanta ina kuka Allah yasa ashe tahiyan karshe takeyi zaune. Cikin kuka ina fadin wayo Amma ki ceci rayuwana ki taimakeni su kawu da mamu zasu ci amanan yar marainiyar Allah da suka dauko. Sun rabani da yan uwana da sunan karatu Amma sunzo nan zasu min auren dole kuma yanzu Amma an tsaneni gidan ga dama ba a sona ban dauka har da kawu da manu basu sona ba sai yanzu Amma. Amma son Allah kisa a mayar dani gidan mu inda aka dauko ni kar ai min auren nan wayo ni amma na shiga uku na lalace agarin mutane. Ban dauka takai adduan da takeyi ba ta shafa ta dago cikin damuwa da kulawa a gareni tana fadin haba A ruwa ba tsana bane wanan so ne kin taba ganin iyayyen da zasu haifi da su tsane shi. Yanzun ke ba abin alfahari bane wanan hadin a gurin ki yaron da yafi kowa kwazo da sanin yakamata Allah ya zabar maki. Kwazo Amma wanan mugun da bai sallah cikakke ne zanyi alfahari dashi Amma kin fa sani matarshi kafirane kuma wayo ni Amma su kawu sun tsane ni dana sani inbi su manjo mu koma tare jiya. Tunda nan ba,a sona an kini har ana sadaka dani Amma sai na fashe da kuka sosai na kasa ci gaba da maganan sai kuka nake sosai. Su Aisha da sukaji kukana wurin Amma daga dakin su suka fito suma kukan sukeyi daga inda suke tsaye sun kasa furta komai a wurin. Naci gaba da fadin Amma kin san fa bai sallah ko shigar shi kika kala bana musulmai yakeyi ba bai mu,amula da kowa a cikin yan uwan shi sai kannen sa ranan fa har giya mukaga matar sa nasha a gidan sy kuma ya gani baiyi magana ba. Amma wanan mugun ai ko kasheni zai iya yadda uwarsu bata son mamu damu din nan a fili suke nuna muna tsana fa. Ran Amma ya dan tabu da aibanta mata jika da nakeyi da wasu maganganu da nake fadi ba a cikin hayacina ba. Sai data daure tace yakashe ki hauka yakeyi komai lalacewan shi ai ba zai fara ya baki wani mugun abu ba a gidan sa. Ke zama aure fa zaki dole sai kin sauke wanan tsiwa naki da kaifin bakin nan na tsiya idan ba haka ba ki sha bakar wahala inkinje masa da rashin kunya haka don kin san su umar bakar zuciya ne dasu shima wanan yana da zuciyan yasa kikaga bai faye mu,amula da mutane ba sosai. Na kalli Amma da idanuwa da sukai ja don kuka nace Amma kema kin yarda da maganan kawu ke nan yanzu a aurani ga wanan mugun? A ruwa zan hana abinda Allah yace ayi ne aurene fa sunnan ma,aiki don may ba zan zamo cikin masu so ba nikuwa. Kaina jijiga nace yanzu na gane Amma yanzun na gane komai wallahina gane dalilin rabani da kakata mai sona da kaunana tsakani da Allah. Wayo babana wayo daddy na ka dawo ina bukatan ka a yau kusa dani banda kowa sai Allah sai manjo na Addah kuma an rabani dasu anzo nan za a cuce ni. Amma bata iya cewa komai ba gaba tasani tana kallona kamar yadda kowa yake kallona cikin mutuwan jiki suna sauraron kalamina. Mamu ce ta shigo falon tana fadin ashe nan tayo wurin ki gwoggo da shirmay ta tazo zata daga maki hankali da daren nan ko ? Kamar kada inga mamu na fara kuka da karfi ina fadin wayo daddy na ka dawo ka dauke ni mu tafi tare na kwanmace ma in mutu in bika da a zarga min wahala a kaina daddy basu sona basu kaunana sun rabani da manjo na sunzo nan zasu cuceni. Kayau kayau mari har biyu mamu ta sauke min a fuska sai da nayi mutuwar wacin gadi lokaci guda kafin in tashi in ruga da gudu sai mukaci karo da kawu ya riko ni yana fadin yaya hakane may akai mata kuma ? Ya sake tambaya a hasale yana fadin nace may akai matane haka fuskanta ya hau cikin takaici Amma tace dukan ta tayi wallahi a gabana . Ya juya wurin mamu yana fadin wanan ai cin zalin ne maimakon abi yarinya da lalama sai kuma ki hada mata da duka haka. Ko kene da girman naki za ai maki haka ai ba zaki ji dadi ba lokaci daya wanan wani irin haline haka maimuna ? Mamu tace yaya don may yarinyar nan zata daga muna hankali haka tazo ta saka gwaggo a gaba tana fadin wai mahaifin ta ya dawo ya dauketa hannun makiyanta. Kawu yaja tsuki yana fadin banji dadin haka ba wallahi ba abakin yara yan uwanta ya kamata yarinyar na taji magana nan ba taji kuma sai a hanata shiga wani hali. Zaki samu yarinya da duka kamar jaka dawani kike son taji dukan ko wanan magana kawu yayi fada sosai kafin ja hannu zuwa wurin kujera ya zaunar dani a kusa dashi yana kiran sunana da Fatima. Share hawayen ki kinji ki saurare ni mu nan da kike gani kaf ba makiyan ki bane mu illar masayon ki kina ganin ni zan cuce ki ko mahaifiyar ki koko hajiya zata hada baki damu ta cuce ki na girgiza kaina alaman a, a gare shi. Fatima kin taba ganin inda uba yaki yarsa yayi abinda zai halakata ko baki dauke ni mahaifi bane a gare ki cikin kuka nace kawu na dauka Amma don Allah kada ka hadani aure da mijin arniyar nan koma waye ka bani ba wanan da bai sallah ba yana auren kafira. Kawu yadan runtse ido yace naji to ki kwantar da hankalin ki yanzu zamu san abunyi amma fa sai kin kwantar da hankalin ki haka zai faru ko kina son gani bacin raina ne dana mahaifiyar ki. Na girgiza mai kai ya kama min magana a cikin nasiha da lalashi har ya samu na rage kukan da nakeyi din sai kuma ya lura da rawan darin dana soma a lokaci guda haka yasa yakai hannu shi a goshina yaji jikina ya gashe gaba daya. Da sauri ya mike yana fadin ina zuwa ya fita daga dakin sai can gashi ya dawo da goran ruwa da serchers din panadol a hannun shi ya bare ya bani biyu yace in sha. Nasha yace in samu wuri in kwanta na mike ya tambaya ina zani nace part din mu yace dawo ki zauna nan guri hajiya ban yarda ki koma wurinta tunda bata san ta rarashe ki ba. Ban zauna ba nace a wahalce sallah zanyi ya gyada min kai na shige dakin Amma na barsu a falon suna ma mamu fada a kaina. Na dade a ban dakin ina kuka kafin mama hadiye ta kwala min kira na fitoda kumburarun idanuna ina neman hijab. Aisha mama ta kwalawa kira tazo tace kawo ma Fatima hijab ta saka sallah zatayi ta koma da sauri ta shigo dakin Amma ta kawo min . Rana dai a dakin Amma na kwana har dare barci yaki zuwa min sai tunanen banza nake barkatai a raina ina jin Amma ta tashi zata je alwala tana magana ita kadai. Wanan rayuwan damay yai kama ace ta ko ina babu dadi duk jummai ta rikita min rayuwan gida wanda ma bakayi zaton zai iya abu ba halinta ya koya mashi. Mata kamar ibilishiya kun hana min farin ciki a rayuwana dana iyalina baki daya wanan yaron dake kokarin ganin ya gyara tarbiyan gidan shine kuma yazamo makiyin su a yanzu. Taja wani uba tsuki ta dan dade a ban dakin koda ta fito ta samay ni a zaune bakin gado ta kalleni tana fadin tashi kikayi nace banyi barci ba dama Amma. Ido ta zaro waje tana kallona yar nan ai gara ki ba kanki lafiya ki runtsa shima wanda ake rikicin kanshi nacen bai san abinda akeyi ba yanzu. Wuce ta nayi ba tare danayi magana ba na shige ban dakin nima alwala na dora na fito na tayar da sallah koda na sallamay na dade a gurin zaune na hade kaina da gwiwana ina hawaye. Ban san lokacin da kukan nawa ya tsananta ba har ya fito fili daga inda Amma take tace Allah buwayi gagara musali yar nan har yanzu kukan nan bai kare ba. Ina kunyi magana da kawun ki yace zai duba a kai kodai makiyin ki za a daura maki ai kyaba kanki hakkuri ko ? Nace cikin kuka Amma ki taimakeni ki ceci rayuwa ta kada ki bari a aurani ga wanan mutumin don Allah wallahi Amma tsoron sa na nake ji wallahi. Ki kwantar da hankalin ki yar nan ai tunda na fahinci bakya so ba maiyi maki dole idan kuma sun matsa sai anyi ni da kaina zan warware auren idan naga yana maki ba daidai ba. Nace Amma baki faga iskancin da sukeyi da matar sa ba ko a gaban kowa ne baida kunyar rungumar ta Amma haka Allah yace ayi don Allah? Tace ina fa yar nan nima yanzu ai na gano ki sosai ba so hadin nake son ayi ba amma fa kinga sai idan kin kwatar da hankalin ki. Don kada su dauka kece baki da tarbiya tunda shi namiji yayi shiru ke mace mai zai hana kema kiyi kamar yadda yayi . Kin san mutane a ruwa sai a dauka baki da kunya da har kika tsaya kina fito na fito da iyayyen ki a kan auren ki gashi kinji har kawun ki ya fara fadin ko baki daukeshi a matsayin mahaifi ba. Wanda hakan nasan ranshi ya baci sosai ne ga irin abinda yaga kina nunawa akan dan cikin sa kamar kin nuna shi bai haifiki ba ke nan tunda shi yayi biyayya ga mahaifin shi bai musa masa ba tunda ya tunkare shi da zancen. Jin haka da sauri nace Amma nima in sha Allahu zan dauki shawaran naki kamar yadda kikace. Tace to kiyi shiru duk abinda sukace kice masu to kamar yadda suke so kinji ko nace to Amma na gode. Tace nasan manufar mahaifin ku kan wanan hadin shine yaga rayuwan ki dama ya inganta ne kamar yadda yake tausayin ki ke kadaice gun mahaifin ki kuma gashi ba wani mai karfi a gidan ku . Haka yasa yai wanan hikimar ki samu suma yan uwanki su samu ta karkashin ki suci arzikin da Allah yai maki. Shiru nayi ina sauraron ta tace ai da farko itama uwar taki tayi wanan haukan sai dana zauna muka fahintar da ita manufan yin hakan ta kafin ta sauko ta yarda da auren . Don ba wanda ya zaci haka daga gurin ki tunda ai kina da ilimin ki yanzu kin san abinda ya dace mai kyau da marakyau ashe abin ba haka yake ba ke a gurin ki. Jikina ya fara sanyi don tulamin kasan da Amma keyi don dai kawai taga hankalina ya kwanta a lokacin. Na nisa kafin ince Amma nifa duk wanda kawu zai ban ya bani amma dai ba wanan dan hjy ba tunda ta nuna bata so na shima nasan ba zaisoni ba Amma. Tace kwantar dai da hankalin ki yanzu abinda nake so dake shine ki samu iyayyen ki da safe ki basu hakkuri akan abunda kikai masu su yafe maki. Sanan da kike fadan wau ba zai soki ba ai halin su ba daya ba da mahaifiyar sa kuma ke mace ce A ruwa zaki iya jan hankalin duk wani da namiji komai shekarun shi ko mukamin sa balle umar da yake mai saukin kai wani lokaci. A hannun mu fa yake har yanzu ko da kike wanan maganan da uwarsa zata iya raba sa da abinda yake so da nine mutum na farko da jummai zata rabashi dani a duniya. Sai dai ba yadda zatayi jinina ne shi din ko taki ko taso dole ne diyan ta su bini don nice dai kakar tasu balle ke da zaki zama matar shi nan gaba tasan lokacin da zaki kama abinki ga hannu ne. Kai na dago na kalli Amma don jin furicin ta na karshe a gare ni sai dai ban iya furta komai ba don yadda nake jin bakina yayi nauyi ga magana yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:07 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI, , , , , Saida akai sallah mun dade zaune kafin nakai kwace a gurin in faras barci barci mai nauyi ya dan dauke ni har Amma ta fita daga uwar dakin nata zuwa office din ta inda a nan zata wuni har dare watau falon ta. Bai fi minti talatin ba na tashi zubur ina dube dube a dakin sai kuma na mike na nufo falo inda na samu Amma ita kadai tana dube dube cikin kayan ta tana ganina tace da sauri badai har kin falka ba yar nan nace Amma zanje wurin mamu ne. Tace ki bari gari ya iddasa wayewa mana na dan tsaya kamar mai tunane nace Amma barin je kawai na nufi part din mamu din yayin da Amma ta bini da kallon tausayi tana gyada kai kawai. Na samu part din a rufe haka yasa saida na tsaya na kwankwasa kafin ta bude tare da tambayan waye ? Da muryana da bai fita nace sayadice ta bude tare da jayewa hanya na kutsa kai ciki ina shiga falon naja na tsaya guri daya yayin da ta mayar da kofan falon ta rufe kamar yadda na samay shi. Ta tako a hankali zata shige dakinta nayi saurin kaiwa kasa cikin sheshekan kuka ina fadin mamu ki yafe min don Allah sai kuma kuka yaci karfina a lokacin. Kamar zata wuce sai kuma taja ta tsaya guri daya ba tare da tayi magana ba ita kuma bata wuce ba. Samun wuri naga tayi ta kai zaune kafin ta fara magana sayadi kiyi hakkuri da hukuncin da yaya ya yake akanki dani dake duk a karkashin ikon sa muke. Haka Allah ya kaddara a kanmu sayadi kin san idan ta nawa ce bazan taba yarda da wanan auren ba don kamar yadda hjyn umar bata son auren nan kusan nina fita rashin son shi a raina sai dai ba yadda zanyi ne tunda ina karkashi ikon iyayyena da mijina. Don haka kamar yadda nayi iyawa yina wurin ganin na hana yiyuwan wanan aure bai samu hannuwa ba na barwa Allah zabin sa haka kema nake son kiyi hakkuri kada ki yarda ki rsgin kunyan da za a tsane ki gidan nan har ai Allah waddai da halin ki. Addua bai bar komai ga dan adam adduan mumumini bai taba faduwa kasa banza kin sani don haka don Allah sayadi ina rokon ki Allah kiyiwa Allah ki sakawa zuciyar ki salama kamar yadda na sakawa nawa na barwa Allah alamarin shi. Ki koma ga Allah kamar yadda muka saba mika alamari a gare shi idan babu alheri cikin auren nan ubangiji ya wargaza shi tun kan a yishi. Ki nunawa mara kunya cewa ke din diyace mai tarbiya da biyayya ga iyayyen ki kamar yadda shima yake kokarin nuna biiyayya gun mahaifin shi din. Kema ina son ki taushi zuciyar ki duk abinda zakiji ko ki gani sayadi ki toshe kunnuwan ki da idanun ki a gidan nan. Sai yanzu na fara gane manufan yaya akan wanan hadin da yayi wanan bin kuma bake kadai yaiwa shi ba dake da Aisha ce da Rukaiyyan gida yaya balarabe. Babu wanda ya nuna tshin hankali daga bangaren su don haka sayadi mu may zaisa mu kasa hakkurin haka mu nunawa mutum mai adalci da mutunci a gare mu gazawan mu a cikin jinin shi. Kukana ne ya yawaita alokacin ta yadda ba zan iya tsayar da shiba itama mamun kukanne ya kwace mata lokaci guda sai da mukayi mai isar mu ba mai ba wani hakkuri a cikin mu. Itace ta fara tashi tabar falon na dade a wurin bata fito ba sai can gata tafito ta shiga kitchen bata wani jima a ciki ba tafito dauke da cup cike da tea a cikin sa yana tururi ta miko min tare da fadin ki karba ki sha. Nasan rabon ki da abinci tun jiya da rana kafin kuje islamiya ko na dago kaina da idanuwana da suka kadai sukai jajir kamar gauta don kukan dana kwana inayi har fuskana ya dan kunbura. Zama tayi gefena bayan na karba tana fadi a cikin wani murya mai nuna rauni a zuciyar tace sayadi ba zaki daina kukan nan haka ba. Sayadi ya kike son in yi nima fa al,amarin nan yafi karfin tunanena yanzu sai naga kamar dama haka Allah ya tsara abinsa a kanki. Don dolene ni kaina nabi umarnin iyayyena don su manyane sun fimu hagen nesa nasan idan da babu alheri gwaggo ba zata taba yarda da wanan hadin ba sam. Sayadi kiyi hakkuri badon bana son ki bane kikaga na kyale a, a sai don ban san abinda Allah ya shiryawa al,amarin ba . Ba don wanan tunanen danayi a raina ba wallahi yadda kika nuna din nan baki so zan iya tsayin daka inga cewa an fasa wanan auren sai dai duk abinda zai faru ya faru. To amma idan nayi hakan kamar nayiwa Allah shishigine ga al,amarin shi yanzu idan nace zan hana. Sayadi baki san halin da nake ciki ba a yanzu don a halin nan badon nakai zuciyata nisa ba ko auren nan zan iya kashewa na huta idan hakan zai maki dadi a rayuwan ki. Da sauri na dago kai ina kallon ta don mamakin furcin ta nace a razane mamu kada ki kashe auren ki sabodani kodon su fauziya mamu kina gidan nan ma yaya yaran nan suke fama a gidan nan. Mamu ta daga kai ta kalleni naga idanuwanta sun canza alaman itama tasha kuka a daren jiyan sosai ke nan yanzu kuma ga furcin da tayi min koda nake yarinya ba zanso ace auren uwana ya mutu a sanadin aurena ba . Haka yasa naji wani tausayin uwata ya kamani na karfafa hakuri da juriya akan komai gamay da auren nan har in ya tabbata a zuciyana. Tea data miko min na fara kurba a hankali don hankalinta ya kwanta dani sai naji ta sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi tana mikewa ta shige daki. Haka na daure nayi ta kurba tea din a hankali har ya saura kadan na mike nakai cup din kitchen ban fito ba don ganin yanayin kitchen din danayi alaman tun jiya rabon shi da samun gyara haka na daure na wanke kayan ciki na sharo na goge ko ina. Falo na dawo na gyara na kakkabe kujerun na fara moping sai ga ta tafito don jin motsina da takeyi tace aiki kuma kika kama yi nace a kunyace eh mamu. Na gama na shiga nayi wanka tun wurin shafa mai naji wani irin zazzabi mai karfi ya rufe ni a dadafe na karasa na zura digon riga kawai a jikina na haye gado na kwanta ranan dai a takaice ban shiga school ba. Ban dade da kwantawa ba zazzabi mai karfi ya kara rufeni ni kadai a daki ina makyartan sanyi jikina ya gashe sosai saboda zafin jiki. Shirun da mamu taji ta dauka ina part din Amma ne sai ta shiga kitchen ta dora girki har lokacin zuciyar ta ba dadi gareta. Kayan yara da suka cire ta shiga daukowa sai hangoni tayi saman gado dunkule a cikin bargo ina kaduwa. Mamaki ya cikata ta nufo inda nake tana yaye bargon irin yanayin da nake ciki ne ya bata tsoro da sauri takai hannunta saman jikina tana tabawa hakan ya sani bude iddanuwa na ina kallon ta cikin wahala. Sai kuma na lumshe idon ina hawaye tare da kokarin fadin mamu banda lafiya ne a kidimay take fadin may ke damun ki ne sayadi nace nima ban sani ba. Innalillahi tace tana kokarin fita daga dakin namu jima kadan sai ga su tare da Amma sun shigo Amma na fadin. Dama abinda nakewa gudun ya faru ke nan, amma yan banzan yaran nan masu gadon uwarsu suka fadawa yarinyar nan maganan nan yanzu. Takai hannun ta saman jikina da sauri tacire hannun tana fadin wanan sai asibiti kiramun sani yanzun nan akai yarinyar nan asibiti. Ta juya gare ni tana fadin sannu uwata sannu kinji da jiki yaran nan basu kyauta muna ba gaskiya har uwar su naso koda zakiji zancen nan sai nan gaba. Waya mamu ta dauko tana kiran layin kawu kira biyu ya daga kiran yana fadin maimuna yaya akayi tace yaya barka da kasuwa dama jikin yarinyar nan ne yayi zafi gwaggo tace a kiraka a sheda maka. Yace subbahanallahi ga Ahmed nan zan turo ya kaita asibiti yanzun nan ni ina nan nazo unguwa ne daga haka ya kashe wayan. An dan jima sai ga Ahmed ya iso gidan kofan mamu yaje yana sallama aka amsa mashi kamar kullun daga kofa ya tsaya suna gaisawa sai ga Amma ta fito daga dakin tana fadin ka iso ba dan albarka. Fito muna da ita mu tafi takecewa mamu tana fada tare da Amma muka tafi asibitin Ahmed tun fitowana yake faman yi min sannu yadda nake tafiya ban ganin wuri yaji kamar ya kamani a cikin ransa sai dai ba halin yin hakan gare shi. Privet Asibitin da suke zuwa gidan mukaje inda ya fara shiga ya samu hanyar ganin likita da sauri ya dawo ya taimakawa Amma ta kamani zuwa ciki. Likita ya dubani yace zai ban gado in dan kwata tare da allurai a gani zuwa yamma yadda jikin zai sauka min. A take Ahmed ya sawo maganin dayace basu dashi a lokacin sauran treatment za a saka a bill din Alh. Bayan ya dawo ne Amma ta gaida shi da kokari ta fara korafin fadin ban taba ganin yan banza yara irin yaran nan ba ace kada wanda ya fadawa yarinyar nan zancen auren nan a yanzu amma don bakin tsegumi irin nasu sai da suka fada taji. Da sauri Ahmed yace zancen wani aure tana gyara zama take fadin auren ta da yaron nan umar mana sanin bai fada ma bane. Ai hadin gida yake son yi da yaran wurin su uku yabawa yaranan dasuka dawo da wasu dabi,un kasan turawa sai yanzu yake fadin har sauran ya bada su a tare rana daya zai wanke su duka. Da Amma ta daga kai taga yanayin da Ahmed ke ciki a lokacin da bata karasa zancen ta ba gaba daya hankalin shi ya tashi da jin wanan zancen da tsohuwar ke rabtaba mashi. Taja tsuki tana fadin ko ma ina umarun yake yanzu yasan halin da yarinyar nan take ciki oho ta dago kai tana kallon Ahmed din da bai san inda yake ba lokacin. Ina kake ne tace tambayan ka nake layin wayan umaru idan kana dashi mu kira in sheda mai halin da ake ciki. Ahmed da gaba daya hankali shi bai tare dashi yaji maganan ta kamar daga sama ta sake maimaita abinda tace din . Ya sauke ajiyan zuciya yake fadin banda layin kowa a cikin su hajiya daga haka ya fara kokarin ficewa dakin zuciyar shi cukushe da bakin ciki yana fadin . Shike nan nauyin bakina ya jamin hasaran abindana dade ina mararin sa a raina yanzu shike nan yarinyar nan ta subuce min ke nan mafalkina a kanta ba zai zamo gaskiya ba. Wuri motar shi ya nufa ya shiga yai mata key ba tare da sanin ina ya dosa ba a lokacin hankalin shi gaba daya ya tashi da zancen tsohuwar da yasan bata karya. Innalillahi ya ambata yana shafo kanshi tare da fadi a fili shike na an min sakiyar daba ruwa fatima ta subbace mani kenan . Ashe yarinyar nan ba rabona bace sai kuma yace kai yana bugun sitiyarin motar da hannun shi mema ya hana in fito tun wuri in nuna ra,ayina gurin Alh nasa dana fadi da baiyi wanan shawaran ba gidan shi ya yanke shawaran zuwa a karshe. Gaba daya lokaci guda ya fita hayacin sa ga zufa na karyo mai duk ilahirin jiki shi zama yayi a falon shi yana nanata innalillahi a fili kafin yaji dan natsuwa nazo mai a hankali. Daga haka yakai kwance ya dafe kanshi dake sarawa da hannu shi daya yana sauke numfashi a hankali har barcin natsuwa yazo mai bai sani ba. Mamu da taji shiru bamu dawo ba kuma ba wanda ya kirata tasan halin da ake ciki ta daga waya ta kira maigidan su hankali tashe tana tambayan shi halin da muke ciki. Yace suna tare da Ahmed na shigo gona in zagaya ni tare da malam mudi amma barin kirasu inji halin da ake ciki. Kiran Ahmed yai tayi wayan na rigin ba a dauka ba sai hankalin Alh ya kara tashi asibitin ya nufa daga gona shida malam mudi. Yazo ya samu ina barci ga Amma a zaune ko abin sallah da abinci ba a kawo mata ba da mamaki yake tambayan Amma yaya akai haka inashi Ahmed din Amma tace tun dazun ya fita ina magana dashi naga ya juya ya fita daga dakin. Kawu yace to lafiya don na kirasa wayan na shiga bai dauka ba ya sake gwada layin sa har ya katse ba a daga ba. Yace to yaya haka don dai Ahmed bai taba yi min haka ba gaskiya gida ya nufa sai gasu sun dawo tare da mamu da mama hadiye. Tare da abinci da duk wani abinda za a bukata a zaman asibiti har lokacin hankalin kawu bai kwanta ba na rashin daukan wayan Ahmed din. Shiko Ahmed da kyat ya tashi yai sallah daga gurin da yake ya jawo wayan shi ganin misscalled ratata a wayan yayi saurin dubawa Alh ne da wasu yaran shagon su ke kiran shi kamar hadin baki sai ga Alh ya sake jefo mai kira da sauri ya daga yana sallama da kyat Alh yace lafiya kake kuwa Ahmed waya nata ringin baka daga ba haka kana ina ne yanzu. Ahmed yace Alh banjin dadin jikinane ina gidana kwance da sauri Alh yace subbahanallahi gida kana may dabaka zo asibiti ba ? Yace ciwon ba sosai bane Alh nasha magani ai na kwata ne yasa banga kiranka ba. Allah ya sauwaka indai ciwon ya matsa ma kayi maza ka kawo kanka asibiti kaji ko yace naji Alh ya kashe wayan . Su mamu dake jin yana subbahanallahi suke tambaya yace wai ashe baida lafiya ne yasa bai daga wayan ba. Amma tace ikon Allah lafiya fa ya kawo mu asibitin nan ya danyi zirga zairga ya shigo har ina fada mai abinda ya jawowa yarnan ciwon ta nace dashi ya kira min layi umar din tun lokacin ashe baida lafiya shima dan mutum ba a bakin komai yake ba wallahi. Ai ikon Allah yafi da nan ko mutuwa akace yayi aiba abin mamaki bane ga ubangiji yanzu suka ce hakane. Amma ta juyo tana fadin a kira shi umarun yasan da zancen ciwon yar nan don kada muyi abu a cikin duhun kai tunda yanzu yana da hakkin sanin hakan . Ba bata lokaci kawu ya sake ciro wayan shi ya kira umar din sai da wayan ya kusa tsukewa ya daga yana gaida mahaifin nasa tare da bashi hakkurin rashin zuwa kwana biyu. Kawu yace ba matsala Allah ya tsare muna ku a duk inda kuke ya amsa da amin sai kawu yace dama na kirakane in sheda maka zancen ciwon yatinyar nan . Da sauri Umar din yace wace yarinya ke nan daddy a cikin damuwa ya tambaya ? Fatima yar gurin maimuna da zaka aura muna asibiti da ita tun dazun da safe aka kwantar da ita ba lafiya . A cikin wani irin murya ya cewa kawu daddy Allah ya bata lafiya ina porthacourt yanzu zuwa safe zan dare zamu sauka insha Allahu. Daga haka suka kashe wayan lokacin dakin yayi tsit kowa na sauraren abinda zai bada amsa a wayan. Umar ko yana aje kiran daddy ya sauke ajiyan zuciya a hankali don hjyn su bata dade da kiranshi ba tana fada wai akan auren nan idan daddy su matsa sai anyi zasu iya samun matsala dashi. Hakkuri ya ba mahaifiyar tasu yana fadin mama ki kwatar da hnkalin ki na fada maki nasan abinda nakeyi fa kwanan ma zamu koma America don haihuwan merry ya kusa insha Allahu mahaifan ta sun matsa mu dawo can. Babawo yanzu da bakin ka kake fada min mahaifan matar ka sun matsa ma akan ku dawo can mai kake nufi da hakan a can kake nufi zata haihu ba nan ba ? Ke nan mu nan bamu da wani darajan da matar ka zata haihu a gaban mu sai ka dauketa ka mayar can wata kasa. Yaya kake son inyi da mutanen arzikina a nan auren ka ban samu yin wani shagali ba ga haihuwan kuma ka dauko wanan zancen ka aza to ban yarda da wanan shawaran ba. Ya samu ya bata hakkuri tana bambami har katse layin abu goma da goma sun taru sun mashi yawa a kai ga mahaifin merry koda safe ya kirashi ya kara jaddada mashi akan ya kawo masa yarshi kada ya bari ta haihu a Nageria. Ga kuma abinda mahaifiyar su ta fada yanzu ga kuma daddy da nasa matsalan ya kunnu kai hakan yasa ya dafe goshin shi bai karasa jin meeting din da sukeyi da abokan harkan shi na can. Yana fitowa kai tsaye airport suka nufa don jirgin da zai taso zuwa Abuja na yamma zasu bi dama ya fito da shirin sa gaba daya. Sai misalin bakwai saura ya iso kano gidan shi ya nufa kai tssye sallah ya tsaya waje yabi jam,i kamar yadda yake idan yana cikin unguwan. Sai da aka fito ya shiga gida inda ya samu merry zaune ga kida na tashi tana dan ciye ciyen ta tana bin wakan wani iri yaji a ranshi ba dadi gaskiyan daddy da yake kyamatan merry a daidai lokacin daya dace bawa ya kusanta kanshi da ubangiji yakai kukan sa gare shi. Ita a wanan lokacin ne take zaune tana bin rudin shedan yana kara zuga ta itako merry tana ganin shi taso yunkurawa ta tashi zuwa gare shi saidai nauyin da tayi ya hanata tashin. Bai nufo inda take ba sai gurin speaker dake sake sautin ya kashe ya juyo zuwa gurin ta tare da dan dukawa ya rankwafo ya sunbace ta tare da fadin wanan kidan yayi yawa merry baki ganin is time for prayer's now. I send my pray to god of heaven since morning wani addu,a kuma kake son inyi a wanan lokacin sai kuma idan zan kwanta idan na samu time sai inyi. Kai ya girgiza yana fadin merry you have to fear god at dis situation you are yace weat Omar what d you mean with dis word ? Don a zauna lafiya yace nothing ya fara balle maballen rigan sa yana kokarin shigewa dakin su da suke a kasa don saboda condition din merry hawa saman yana mata wuya yanzu. Bin bayan shi tayi da kallon tare da fadin weat woo what dis man mean with me now ? Shabi he want me to pray like him, d holl day no rest for humanbeing at all. Yeeeeee sai ta ja tsuki tana ci gaba da gunguni a fili ita daya tare da kwalawa mai aikinta na kitchen kira. Tazo da sauri da dan bujen ta tana fadin madam kina nemane tace eh ki kawowa maigidana abinci ya dawo. Ta amsa da fafin yes ma ta juya zuwa kitchen din da sauri ta tana rawan jikin bin umurnin madam din gidan. Ta dawo tana jera abincin sai gashi ya fito a cikin wasu kaya sai kamshin turare yakeyi yana gyara hannun rigan shi yace zan fita i will right back in thirty mins . Tace how about your food is ready yana saman table kallon gurin yayi tare da aikawa mai aikin kallo yayi saurin kawar dakai gurin. Ya fara tafiya take tambayan shi ina zaka haka ne kake sauri ? Yace kai tsaye asibiti a dan firgice ta sake tambayan shi wirin wa yace yarinyar nan daughter din step mum take asibiti don shi baya karya kai tsaye yake maganan shi idan ya tashi. Weat for me zan je in duba ta yarinyar da uwar ta suna da kirki gaskiya ba zan iya mantawa dasu a rayuwana ba. Dole ya ja ya tsaya yana jiranta sun iso subitin a daidai lokacin su mamu sun dawo da kawu kawo min abinci na tashi suna rarashina inci abincin yayi sallama a kofan dakin bayan sunyi waya kawu ya gaya mai dakin da muke. Da fara,a fuskan Amma tana fadin lale marhabin da maigidana babban giwa har an da, , , , Ganin merry tafe a bayan shi yasa ta gimtse maganan da ta kasa karasa a bakin ta tana kawar da kanta gare shi. Yi yayi kamar bai gane may Amma ke nufi ba dayin hakan ya karkata gurinta yana kai mata ruguma ta dan duki bayan shi tana fadin kana son haka kazo da aanan jelar taka nan . Ai da kazo kai daya dakaga runguma mamu dake duke tana gyara min kwanci don nace na gaji da kwanciya ta gefe daya. Ta dago da sauri tana masu sannu da zuwa oh sister inlaw may ke faruwa ne haka tana nufowa gurin da nake kwance take wanan maganan. Idanuna na lumshe a daidai lokacin data karaso inda nake ina jin wani irin ba dadi a raina koba komai merry na nuna min kulawan matsayi na kanwar mijin ta . Ni yanzu da wani ido zan kali matar nan da wanan hadin da kawu ke son min da mijin ta wasa da dariyan da muka dinga yi a gidan su ranan da muka kai masu ziyara ne ya fado min. Ban san lokacin da wasu hayeb tausayin kaina ne kona merry wani hali zata shiga idan taji za a hadani da mijin ta ? Saukan hannun ta naji saman jikina tana dan tabawa tare da fadin eyyah sorry my dear ban sani ba sai yanzu da dear ya dawo yake fada min. Ganin ina hawaye yasa merry kai hannun ta saman fuskana tana share min hawayen a hankali tare da min sannu da jiki. Ta juya gurin mamu tana tambaya may ke damuna ne haka muma ta bata amsa da fever ne ya kama ban dade kwance ba ai. A daidai lokacin ya juyo yana gaida kawu kafin ya juya wurin mamu yana fadin ina wuni ta amsa da kadawo lafiya. Ya hanya ce Alhamdullahi ya mai jikin fa ashe bata jin dadi haka har asibiti ? Wallahi tun daren jiya zazzabin ya fara har gashi sai da aka hada da asibiti ya dan tsura min ido can yace sannu ko idana suna a lumshe sai marry dake bakin gadon da nake zaune ta dafani tana fadin brother din ki na gaishe ki. Kai kawai na gyada ba tare dana bude idona ba ya juya gurin Amma yana fadin yanzu may likita yace ? Amma ta tabe baki tana fadin ciwo haka ba cin abinci ba dadin jinya gare shi ba don nasan harda yunwa na damun yar nan ace mutum tun jiya baici abinci ba a cikin sa sai ruwan leda kawai ake dura mai a jiki. Dan shiru dakin yayi kafin ya furta zamu koma don akwai gajiya a jikina yanzu na dawo daga tafiya kiran daddy dazun yasa na nace barin inzo in duba ku ? O to ai da ka sani baka zo ba tunda bamu da albatkacin da zaka zo nan don mu yanzu. Kallon Amma ya danyi ya girgiza kai kafin ya juya yana fadin merry ta tashi su tafi ta yunkura ta tashi da kyat tana fadin get well sson my dear takai mi dunbata a hannu. Ina jin shiru yasa na dan bude ido naga daga ni sai Amma a dakin mamu bata cikin dakin haka yasa na gane ta dan rakasu ne don kawu ya fice tun shigowan shi nasan ba komai ya fitar dashi daga dakin ba sai ganin merry a kusan tsirara take da shiganta don dan rigace armless ba hannu rigan ta saya mata iya cinyar ta. Nayi mamakin yadda yaya umar ya ke iya fita da ita haka a cikin mahaifan shi ba tare da yaji nauyin hakan ba. Sai da mamu taga wucewan su ta juyo zuwa dakin tana fadin gwoggo bai dace kina wa Umar haka ba sai matar tasa ta tsargu da rashin kulatan da bakuyi alhalin tasan matsayin ku gare ta. Yo yayi haushin mana idan yai fushi yabar zuwa muna da ita gida man idan akwai abinda baki a duniyan nan ingsnshi tare da kafiran yarinyar nan bai son muyi fushi dashi ya kwaso muna ita. Shiko umar suna shiga mota merry ta fara korafin wai may grandmother din shi take nufi da ita ? Ko haka halinta yake ne kamar na mum din shi bata son mutane itama shiyasa fa take son wanan step mum din nasa don tana da friendly lokaci daya. Iska ya furzu jinta kawai yake zuciyar tana faman da sake sake a kan yadda zasu kwashe da merry idan wanan zancen ya fito fili don yaga son da takewa mutanen bana wasa bane saboda duk halin da take tana arba da mamu koni zata washe. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:08 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , , Tun dasowan shi gida zuciyar shi take cike da tunanen wanan al,amarin bai taba gaskata yarintana a fili ba sai yau din da yai min kallon tsaba. Tsuki yaja yana gyara kwanciyar shi tare da lumshe idanuwan shi ya rasa gane dalilin nacin daddy akan sai ya auri wanan yarinyar wanan ai wahala kawai daddy yake son dora min. Yarinyar da ma kila yanzu take shirin fara period din ta ko ta fara ma ai wanan bada wani dadewa ba can. Juyi ya kara yi sai jin hannun merry yayi a saman jikin shi tana sauke numfashi tare da fadin mey yasa bakai barci ba dear ? A hankali ya sauke numfashi yana kai hannun shi saman cikin ta ya dan shafawa sake tambayan shi tayi may ke damun zuciyar ka haka ? Yace nothing kai tsaye tare da dan sunsunan wuyar ta yana lumshe idanuwan shi a hankali. Sai dai ba wanda yai magana itama merry kamar yadda ya makaleta haka ta manne a jikin shi a haka barci ya dauke su. Washe gari ma akwai damuwa a tare dashi sai dai yayi kokarin boyewa merry din abinda ke damun shi a wanan dan takin yan cikin halin damu iri iri. Ga na tafiyan merry da suka sashi gaba ita da mahaifanta ga hjy shi tace ba zancen tafiyan merry din a gurin ta da kuma umurnin bijirewa mahaifin shi data umurceshi yayi ga mahaifin su dake son yayi mai nasa biyayyan kuma. Wanan abin ne ya taru yai masa yawa a zuciya ya kasa samun natsuwa a tare dashi a cikin dan yanayin da ake. A gagauce yayi breakfast ya fito don merry na ciki kwance bata tashi ba tun barcin daren jiya din akidar tace bata tashi sai kusan sha biyu ko sha daya da wani abu na safe. Duk da yasan ba wani itin hurdan nan a tsakanin shi da Nasir abokin shi amma sai yau yaji yana bukatan shawaran Nasir din don shi yafi kwanta mai a rai duk cikin wa yanda yake mu,amula dasu yanzu Yana fita gidan ya kira layin Nasir sai da Nasir yayi mamakin ganin nomban Umar din dake kiran shi yau yasan tun suna yara suke tare dashi. Zuwanshi kasan waje ne yayi sanadin raba karfin abotan su sosai suka dan rage yawan hurda da juna da farko Nasir kayi kokari ya neme shi a layin sai ya kasance ba kasafai yake daukan wayan shi ba. Hakan ne yasa Nasir din ya fita batun shi shima ya hakkura da lamarin umar din a tafi a hakan ko wanan dawowan da Umar yayi kasan bai wuce sau biyu da suka hadu ba dashi. Shi yasa yanzu da yaga kiran umar din yake mamakin kiran nasa a yanzu din don hakada mamaki ya dauki wayan nasa yana sallama gare shi. Umar da zuciyar shi ke cike da kunci da takaici daya taro mashi a zuciya sai tunane barkatai a yanzun yana ganin ta hanyar Nasir kadai ya rage mai ya samu mafita da tashi shawaran don shi a bangaren shi abubuwa sun taru sun masa yawa. Ta yadda ya kasa lalubo don bai son yai wa kowa daga cikin mutanen nan uku butulci a rayuwan shi. Sallaman Nasir ne ya katse shi a lokacin yaji yana amsa wayan tasa daga bangaren shi amsa sallaman yayi tare da fadin Nasir kana ina ne ya bashi amsa da ina gidana umar lafiya ko ? Yace kajirani ina hanya yanzu gani tafe gidan daga haka ya kashe wayan yana ci gaba da tukin motar. Da lalube da tambaya ya samu ya isa gidan Nasir ya isa ya tsayar da motar a kofan gidan ya fito sai da ya dan tsaya yayi tunanen abinda zai fadawa Nasir din ya danna remote din motar tashi motar ta rufe. Kallon gidan yayi gidsn na a rufe haka yasa ya dubi wayan shi na laluban layin Nasir din yana ganin kamar ya fita dayaga bai zo ba. Nasir kana inane gani na iso kofan gidan naka a samu get a rufe . Nasir ya bashi amsa da ina ciki ai tunda kace kana tafe ban fita ba ina jiran ka gani nan fitowa yanzu. Cikin yan seconds sai yaji ana budan kofan gidan Nasir ne ya fito daga ciki yana washe baki da ganin umar din yana mamaki. Umar din dake tsaye a cikin wata shada gizna mai kalar ruwan kasa dinkin rigan mai dan karamin hannu din kin bai sauka kasa sosai ba sai gaban rigan da akaiwa dan karamin ado da aninaya kalar shaddan. Hulan dake kanshi kalan kayan ne yar karama da gani daga waje yazo dasu sai takalama bakake masu daukan ido ga kamshin turaren sa da yakeyi. Ganin Nasir din da fara,a shima ya yana dan fara,a a fuskan shi wanda bai hana dinbin damuwan nasa ya boyo a fuskan shi ba. Nasir ya kalle shi yana mika mai hannu tare da fadin abokina yanayin ka ya nuna min akwai damuwa a tare dakai mana yau. Dan murmyshin da baikai ciki ba ya kara kakarowa a fuskan tashi yana rike da hannun Nasir din yake fadin gani dai Nasir yau garin babu dadi a gurina. Nasir ya sake hannun nasa yana fadin subbahanallahi mu shiga daga ciki mana mu tsaya nan waje muna magana don naga maganan mai muhinmanci ne sosai ke rafe dakai. Umar yace kasan yanzu kai magidanci ne ba zan so shiga gidan ka kai tsaye haka ba Nasir. Nasir dai yayi murmushi yana fadin ka wuce hakan a wurina umar har abada ko da ka yar da Friendship din mu ni ban yar ba a guna don haka ka shigo kawai ciki malam nan kamar gidan ka ne ai in ga zumunci. A tare suka shiga falon Nasir din wanda umar din kalamin Nasir yasa yaji ba dadi a ransa don gaskiya ya sake abokin shi na kwarai mai kaunar shi tun farko. Suna shiga Umar ya fada a saman kujeran farko na shiga falon yana lumshe idanuwan shi a hankali kallo daya zakai mai kasan yana cikin tashin hankali. Nasir ya tsura mai ido ya kasace masa komai har tsayin dan lokacin kafin ya dago ya dawo kujeran dake fuskantan na umar din. Yau yanayin abokin nasa ya bashi tsoro don yasan halin sa idan abu ya damay shi sosai yake ganin sa hakan . Da kyat nasir ya bude baki yace mai wai lafiya mayke faruwa ne haka abokina don yanayin naka ya fars rikitani gaskiya. Maimakon Umar din ya bashi amsa sai ya koma kwantar da kanshi saman kujera ya daga kai sama tankar wanda ke tunane. Naris daya kura mai ido yakai hannun shi saman kafadan shi yana fadin be a man abikina ka fada min abinda ya faru ko zamu samo mafita. Saida umar ya sauke ajiyan zuciya ya dago kai yana kallin nasir din tare da fadin Nasir ina cikin tsaka mai wuya akan mutun uku daddy da mama da kuma matana dana fadama na aura tana nan ta biyo ni da tsohon ciki tun bayan tahowana. Nan dai Umar din ya labarta mai komai dake faruwa dashi wanda ya rasa shawo kan matsalan da kan shi. Nasir ya jinjina kanshi yana fadin lalai abokina kana cikin matsala sosai sai dai idan mun kwantar da hankali mukabi maganan a sannu ko wani zamu samu mafita akansa da yardan Allah. Jin hakan ya sa umar din yadan fara samun natsuwa yace na rasa yadda zanyi ne Nasir don mama tana kan bakanta auren sauran yan uwana bai daga mata hankali ba kamar nawa. Nasir ya murmusa yana fadin tana da nata dalilin in kayi la,akari da halin su na mata akan kishi don kaga ba wani shiri bane sosai a tsakanin diba ga yadda ita maimuna din ta auri daddy yanzu. Umar wanan bai isa ya tayar ma da hannkaliba haka har yanayin ka ya nuna kamar wani abin tashin hankaline ya samu haka. Umar yace maganan ka gadkiyace don yadda da farko mama ta matsa muna mu dawo kasan nan mu kwatar mata inci a gurin daddy da kishiyoyin kai har Amma abinda take fada muna a kanta muna can babu dadi in gajarce maka. Sai bayan mun zo ne din muka samu abin ba haka yake ba don da farko har ina mamakin sauyawan ita maimuna din ga yadda mama ke fada muna maganan ta muna can. Sai gashi mun samu maimunan tana binta sauda kafa saidai ita mamadin bata bukatan hakan don tana ganin wai don a kuntata mata ne maimunan ta shigo gidan. Tsuki Nasir yaja yana fadin wanan ku maza ba damuwanku bane ai akan wanan bamu da matsala nake gani yiwa daddy biyayya gare ka ya zama dole amma fa sai ta hanyar yiwa mama hikima ka nuna mata kana bayan ta a yanzu dari bisa dari ka yarda da maganan ta . Ta haka ne har a sannu ka cikawa daddy nasa burin a boye ta hanyar yiwa daddy bayanin gaskiya. Sai maganan matar ka da zamu fahintar da mama kada wani matsala yazo ya faru da meery din a nan a kuka da ita har daddy kai masa wanan bayanin tunda ita mama ai dole ta yarda shawaran da daddy ya yanke a gidan sa. Umar da yai kasake yana sauraren Nasir din ya nisa sannu a hankali tare da kada kanahi alaman gamsuwa da maganan Nasir din. Sai da yaji Nasir yace ina dai fatan ba zaka ha,inci daddy ba ga wanan manufan nasa zaka rike mai amanan yarinyar kamar yadda yake rikonta shi a gidan sa? Murmushin karfin hali Umar yayi a fuskanshi yana fadin don wanan kada ka damu nasan ta yadda zanyi in farautawa daddy din rai a kan ta idan na inganta rayuwanta kamar yadda nasan shi daddy ke hasashe a gare mu. Ya marauraice murya yana fadin yarinyar fa karamace sosai Nasir ina zan kaita yanzu ina jiyewa kaina ranan da merry zata fahinci hakan Nasir a raina. Nasir da yai shiru yana sauraron abokin nasa da yake fadin zaiyi auren yarinyar ne a bisa umurnin mahaifin shi shima kawai. Can Nasir ya nisa yana fadin Nasir naji maganan ka a yanzu kan yarinyar sai dai ni shawaran da zan baka shine ka rike amana aure yafi gaban wasa wallahi. Dole ka ba yarinyar nan hakkinta daya rataya a wuyanka koda kuwa ranka ba zai so hakan ba sai ka cire son zuviya a ranka komai zai zo maka daidai. A fusace ya juyo yana fadin bani da ra,ayin yin mata biyu a raina nasir kafi kowa sanin wanan tsarin nawa tun muna yara banda ra,ayin yin hakan a rayuwata. Nasir yayi murmushi yana fadin a dai bi wanan a sannu yanzu domi aure wani babban sha,ani ne sosai. Waya Umar da yai kara ya hanashi magana da nasir din ya bi wayan dake aje a gefen shi da kallo yaga merry ce ke kiranshi lokacin ta tashi bata gamshi a gida ba. Bai san lokacin da ya saki guntun tsuki ba ya bar wayan bai dauka ba har ya tsunke. Nasir ya kalle shi yana fadin kayi hakkuri a bokina mu hwada wanan mu gani ko zai fishemu ga wanan maganan kaga daga baya sai mu san yadda za a bullowa sauran magana yanzu a samu ita merry din ta bar kasan nan tukun. Saboda hakan ne ake son auren yar kasanka don wani tsari na al,adan mu nan kaga a wani fannin mama tana da gaskiyanta . Don ka riga da kayi kuskure tun farko na auro bare baren kuma yar a halul kitabi da bata sallah kamar mu sai dai shi kaddaran mutum bai wuce shi. Da safe aka sallamoni daga asibitin don sunga zazzabin ya sauka sosai yasa suka ban sallama muka dawo gida a daidai lokacin da mamu ke shirin zuwa dubani. Sai gamu mun dawo gidan hakan shi ya hana mata fita a lokacin sashen Amma muka nufa har ni . A can ma shigewa dakin Amma nayi na kwanta bayan nayi wanka sai wani barci mai nauyi ya kara daukana kuma. Amma tajini shuru ta leko dakin ta samay ni ina barci itama wanka tayi ta wanke warin asibitin da take korafin ya bi mata jiki tun safe take maganan. Har ta fito ta dawo falo tana mita a cikin ranta na rashin zuwan kowa na gidan kawu ya dubani ba tun tana mita har mamu da ta shigo kawo mata abincin rana ta samay ta a damuwa sai Amma ke fadin. Ni wanan zama da jummai ta juye min gida dashi yana damuna yar nan a raina ace tunda yarinyar nan ta kwanta ciwo ko karen su bai leko mu ba. Murmushi mai kama da dole mamu tayi tana fadin babu komai ai gwaggo wanan idan da sabo na saba a cikin sa ni wanan bai taba damuna ba don nasan manufar su dayin hakan. To Amma a ce yar nan har da ciwo za a hada a kishi haka ? Ina ciwo ya kauda komai a rayuwa sai yanzu nake tausayawa yar nan nima don irin rayuwan da zata tarba a gidan yaron nan don jummai ba zata bar yan nan su zauna lafiya ba. Gwaggo duk abinda zatayi Allah yafita don shi yasan dalilin wanan hadin a da can kan na tayar da hankalina don haka. Sai dai a yanzu banjin komai a cikin wanan barazanan nasu don kamar taki suke zubawa zuciyata nake ji hakan na kara sani fahintar wasu abubuwa da dama dasu. Don haka gwaggo ki kwantar da hankalin ki kada wanan abin ya dami zuciyar ki ko kadan. Amma ta nisa tana fadin ki kara hakkuri yar nan don wanan zama sai hakkuri da addua a cikin sa komai yai farko yana da karshe. Ban falka ba sai wurare n karfe hudu da rabi sallah nayi na dawo falo gurin Amma na kwanta a saman doguwar kujeran falon na kwanta. Abinci fa Aruwa ki bar cikin ki yana zama da tunwa haka ina yanzu an samu mafita ga wanan maganan taku tunda uban naku ya fahinci dai bakya son hadin. Dago kai nayi ina fadi Amma da gaske kawu ya hakkura ba a cikin fushi ba tace to yaya zaiyi yar amanan sa tana ciwo haka kan. Kaina na mayar na kwanta ba tare da nayi mata magana ba ina tunane a raina. Nan su Aisha suka dawo suka samay ni kwance sukai min yaya jikin na amsa da kyat da sauki. Basu jima a gurin ba suka shige ciki don cire tufafin su don daga islamiya suke mikewa nayi zan shiga ciki Amma tace ina zuwa nace ban daki. Ban fito ba sai da alwala na fito na dan zauna bakin gadon dakin na Amma ina karewa dakin kallo yadda yake cike da kaya fam dakin ashe gaske idan daki ya faye tarkace ake cewa kamar dakin tsohuwa. Murja ta shigo dakin da sallama sai dai da yake nayi zurfi a tunane banji ta ba. Ta samu wuri ta zauna a kusa dani tana dafani tare da fadin A ruwa tunanen fa yai maki yawa baki ganin wanan hadin bake kadai akawa shi ba ki duba fa Aisha ita murna ma take da hadin nata tun jiya dataji. A jiyan zuciya na sauke na dago kai ina kallon ta da idanuwa da suke shirin zubar da hawaye don banjin zan iya yin abinda tace Aisha nayi a nata hadin. Ta kada kai tana fadin kai A ruwa kinfa san kawu ba zai maki abinda zai cice ki ba inkiyi duba ga wanan hadin kinfi kowa fa dace a cikin sa. Kallon ta na sakeyi tare da fadin uhumm murja ke nan don bake bace a matsayin da nake yasa kike fadin wanan zancen haka. Ni badon kawu da zai ga nayi masa rashin hankali ba babu abinda zai sa ban nunawa kowa koni wacece a gidan nan ba. Dariya ta bushe dashi tana fadin yarinya kin maji dadi zaki fada cikin daula har kike yanga ? Wani kallo nayi mata tare da fadin daula ko wahala murja gun hjyn tasu zaga daulan ko a gunshi. Ki duba fa yana da mata fa kuma matar tasa ma kafira ce fa wace bata sallah murja kike fadin nafi kowa dace a cikin mu? ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:08 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM YA JULLALI WAL, IKRAM, , , , , , Nace murja ki gyara kalamin ki kice nafi kowa fadawa halaka murja ku kiran da marigayi tun yanzu shiya fi sauki a gare ni. Ke kanki kin sani babu wani karuwa ga auren ya umar a gareni murja mutanen da basu kaunar majaifiyata da yan uwana da suka fito tsatso daya. Haba A ruwa kada kice hakan don Allah karki manta sanaditan fauziya ranan yaya ya kaimu shago ya saiwa kowa abinda ranshi ke so fa ya kuma nuna kulawan shi sosai ga yarinyar a gurin. Dan dariyan yake nayi mata ina daukan hijjab don ana kiran sallah a lokacin na juyo nace murja son da ba,a iya nuna masu a fili ai raggage ne. Ina gani da zanje gidan sa a matsayin makiyar su tunda shima dole akai mashi a kaina kamar yadda akai min dole yanzu. Ina fadin haka na fara kokarin tayar da sallah bina tayi da kallo tana fadin Allah ya kyauta ki dai yi abinda ba za,aga laifin ki ba shine shawarana na kada kizo ki jawa kanki matsalan da bai gyaruwa nan gaba. Mamu ta leko dakin tace mufito muyi sallah sai ta samu har na tayar da sallah don haka ta hau murja da fada ta fice dakin itama. Ban fito ba sai kusan takwas bayan nayi sallah isha,i na fito daga dakin ina sayi da hijjab a jikina nan falon na zube Amma ta shafa tana juyowa gare ni tace ina zuwa kuma yanzu nace zanje gun mamu ne in gaida ita. Tace zauna muci abinci itama yanzu ta kawo min abinci ta fita ba dama in musawa Amma saidai kuma na zauna din babu alaman cin abinci a gare ni. Ina gurin kawu ya shigo wurin Amma gaishe ta da sauri ba mike daga inda bake don girmamaqa gare shi ina bashi guri tare da mashi barka da dawowa daga kasuwa. Ya kalleni yana fadin Fatima ya jikin yazun na shiga wurun ku gaishe ki ashe kina nan wurin hajiya ? Amma tace tunda muka dawo ai tana nan wurina jikin nake son yayi kwari kafin ta koma can din sai dai kagane ta bata son cin abinci ta yaya za a gane tayi lafiya yanzu tun abincin safe da kakai muna har yanzu bata ci komai ba. Subbahanallahi yace ya juyo gareni yana fadin Fatima kina son ki kashe kanki ne ko yaya ? Kafin in bashi amsa mamu tayi sallama falon ta kalli inda nake tsaye da sauri na kai rusunne tana fadin tayi halin rashin hankalin nata ko ? Amma tace wani rashin hankali kuma yarinya bata da lafiya kuma zaki hauta da fada abincin da bata ci muke magana don ban tamtama tun abincin shekaran jiya ne a cikin yar nan sai ruwan shayin da take dan kurba. To a barta mana cikin wanine ai nata ne idan tace tayrin kan tsiya ke gare ta shima namiji bai muna wanan boren ba sai ke har kin san wani abu auren dole ? Kawun ki kike son ki watsawa kasa a ido a idon jamma kuma baki isa ba walla, , , Hannu kawu ya dagawa mamu yana fadin maimuna idan ba zaki bi yarinyar nan a sannu ba to ki fitar da bakin ki cikin maganan nan ya fada ranshi a bace. Cikin kuka nace mamu bazan taba ba kawu kunya ba a rayuwa na don kawu mahaifina ne saboda ban taso nasan mahaifina ba sai kawu. Duk abinda kawu yace inyi duniyan nan zanyi indai ina raye a duniyan nan koda kuwa abin nan mai cuta min ne a rayuwata. Kaji diya da hikima da hangen nesa a rayuwa Amma ta fada tana washe bakin ta gare su kawu ko cewa yayi . To Alhamdullahi ina godiya ga Allah daya bani diya masu albarka dama ni nasan Fatima ba zata taba watsa min kasa a ido ba yadda ake tsamani . Yasa nayi wanan abun da nake ganin haske mai tarin yawa a cikin sa nan gaba ki kwantar da hankalin ki ki taimaki rayuwan dan uwan ki Fatima wanda yake gab da fadawa ga halaka . Rokona Allah a kullun in ga rayuwan ya dauro a ta farkin addinin musulunci sai gashi umar yana gab da rushe min wanan mafalkin nawa a kanku. Kada tsoro ko razanan matar shi ya kamaki a zuciyar ki zaki shiga da haske irin na salama ki shiga da akidarki da addinin ki ya koyar dake fatima. Ina tsaye gare ki ga duk wani al,amuran rayuwan ki fatima dashima kanshi umar din duk cikin yayana umar yafi kowa zafi dakuma saukin kai wayewan shi bai kashi ga barin muna biyayya ba har gobe hakan yasa nake alfahari dashi a cikin yayana sai kuma ke yanzu dana buga gaba dake baki watsa min kasa a idanuna ba Fatima. Ubangiji ya albakaci auren ku dashi abinda muke hasashe a kanku ya zamo mai albarka a garemu baki daya. Ina son kada kiji komai akan mahaifiyar shi hjy duk wani barazana da zasu kawo maki ko mahaifiyar ki kada ki dauki wanan wani abu komai zaizo karshe da ikon Allah. Kukana ya yawaita wanda hakan ya tunzura mamu tace shi kuma wanan kukan na maye kawu yace maimuna ki fita falon nan don Allah ta danyi murmushi tare da mikewa ta bar falon ba tare da fadin komai ba. Kawu bai fita ba sai da yasa na zuba abinci naci yana ta kara kwantar min da hankali yayi da Amma kuma ke masa korafin gidan shi yace zai dayki mataki ga kowa yana sane da komai dake faruwa a gidan. Sai da yaga na dan cinye shikafan dana zuba a plate yayi muna sai da safe ya fita daga part din. Da safe ma da muka tashi nace zanje school Amma kin yarda tayi wai jikina bai gama warwarewa ba in bari wani sati in shiga kawai tunda gobe jumma,a dole na yarda da hakan ba don naso haka ba. Hakana na wuni a kwamce lalace daga tunane sai barci har lokacin babu dan gidan dake shigowa wurin Amma kamar hadin baki har yar gaisuwan safen da suke mata ma ni banga sun shigo yi mata shi ba haka yasa na yarda hadin baki ne kuma sun hani diyan su da raban kakar tasu yanzu. Washe gari safiya jumma,a kawu bai faye shiga kasuwa ba ranan jumma,a yana wuni ne tare da iyalin shi a gida sai dai idan wani abu maimuhinmaci ya fitar dashi lokacin zuwa kasuwa. Wayan Ahmed da bai gani ba tun ranan da ya kaini asibiti ya kara kira yayi sa,a Ahamed din ya daga kira don kawu har gidan yake ya samu gidan nashi a rufe kuma wayan shi bata shiga hakan ne ya kara daga hankalin kawu. Ahmed may ke faruwa da kaine kwana biyun nan kai baka zo ba naje gida a rufe kuma wayan ka baya shiga ? Yace Alh na danzo gidane gani hanyar dawowa kano kana jin maganan sa kasan baida lafiya ko damuwa na damun sa sosai. Amma da kasan zakai tafiya ai sai ka sanar dani ko ka barmu nan hankali a tashe yace Alh ayi hakkuri nima tafiya ya dauro min ne ba shiri. Allah ya kawo ka lafiya kawu yace yana kashe wayan dake hannun shi din mamu sake gefeb shi tace ka samay shi ke nan yace eh wai garin su ya tafi tafiya ta kama shi can . Allah ya sauwaka mamu tace tana tatara kayan abinci dake gefen shi na faten waken da yasha da don karyawa safe gare shi. A daidai lokacin ne Umar yayi sallama ya shigo falon sai da suka gaisa da mamu tare da tambayan shi merry ta fita. Gaisawa sukayi da mahaifi nasa da ya lura dan nasa ya fada sosai a idon shi ya kalle shi yana fadin dattijon gida may ke faruwa da kaine kwana biyu kai wanan fadawan haka ne ? Umar ya dan shafi kanshi yana fadin daddy al,amurorin yau da kullun ne kawai sai kuma zancen merry da muke muhahawara da mama a kanta. Hannu ya mika yana dauko tooth pick saman table din dake gaban shi yace wani abin kuma matar naka tayi mata kuma ? Yace a a daddy akan dai maganan komawan merry din can gaban iyayyen ta ta haihu ne mama ta nuna bata yarda ba da hakan. Kawu yace akan wani dalili nata zatace bata yarda ba tunda kai ka yarda da hakan ita ke auran maka itane ? Idan ma ta rike ta a nan wani abin zatai mata yaushe jummai ta tsaya taba kanta kulawan daya dace balle ta ba wani can ? In ma dai din zata bata zata iya da al,adan sune ko tasan yadda al,adun su yake ne a nan *wanan* maganan banza ne yaushe ne ka shirya tafiyan nata ne ? Ya tambaye shi yana kallon shi a fuska yace daddy naso next week mu tafi ne sai daga baya idan ta haihu zan dawo in karasa aiyukana a nan din. Ita matar taka na nan may kake nufi da ita idan ka tafi ya dago kai da mamaki yana kallon mahaifin nasa tare da saurin dukar da kai kasa yana fadin. Daddy naga kamar ai karatu take yanzu tukun ko ? Karatun a yanzu ba zai hanani fitar dasu gidan nan ba kamar yadda nayi niya a raina karshen shekaran nan nake son gaba dayan su a wanke su. Idan kana da bukatan taci gaba zata karsa a gidan ka idan taje idan baka da ra,ayin hakan sai ka barta a gida kamar yadda uwayen ku suke suna bautan aure. Sai dai saboda bambamcin zamani kaga ita zata iya karasa nata karatun har ma ta dora ga hakan idan da halin yin hakan a wurin ka. Zama ya gyara zuba na karyo mai a goshi don baiyi tsamanin har wuri haka kawu yake nufin yin auren ba. Kawu ya kalle shi yace ko kana da magana ne naga kayi shiru ? Daddy banda magana sai dai ta fanin mama ne ban san yadda zan fahintar da ita ta gane ba har yanzu. Indon wanan ka barni da ita zan mata magana sai dai abinda nake so dakai shine ka kula da addinin ka a duk inda kake umar don shine haske da jagoran ka gobe kiyama kada ka bari rudin shedan ya rude ka don Allah. Daddy insha Allahu zan kula na gode Allah ya saka da alherin sa yace tare da yin shiru gaba daya ya dukar da kai. Ya fito ya shiga part din mahaifiyar shi ya gaida ita ya dan dade a gurinta suna hiran zancen aikin da habbib zai fara nan kasan. Kafin yai mata sallama yana fadin zai tafi ga mamakin shi har ya bar gurin ta bata tambaye shi merry wace ke dauke da cikin shi a jikin ta ba. Yana tafiya part din Amma zuciyar shi fam da tunane irin halin hjyr su har ya fada tunanen kodai shine hjyn ta daina so kwata kwata tace bata son wanan choice din daddy haka kuma har yanzu ta kasa na,am da merry a matsayin sarakuwar ta. To may hakan ke nufi a gare shi ne wai babu yadda zaiyi don mahaifiya ce sai ya basar da zancen kada ya fara zargin mahaifiyar cikin sa haka. Ni da Amma ne a falon tana zaune nikuma ina kwace a falon ta fuskana yana kallon inda take zaune sai dai a zahiri ba ita din nake kallo ba. Ya shigo da sallama ya tsaya daga gefen kujera haka kawai ganin sa ya sanya kirjina bugawa nayi kokarin mikewa yayin da Amma ke masa sannu da zuwa ya tsaya a mangali kujera yana amsawa ba tare da ya zauna ba. Sai dana daga na juyo ina fadin ina wuni Amma tace ke kuma ina zaki muna hiran mu zaki gudu kuma ? A takaice nace mata daki zan shiga. Tace wanan ba mai zama bane ai tunda ya zama magidanci yake guduna yanzu. Nidai ban tsaya ba ya dan kalli bayana ina tafiyan ya dan basar yana zama saman kujera Amma ke fadin. Kai kuma gaka duk ka ramay mana may ke damuwan ka haka angon karni don nasan matar ka bata nisa da haihuwa yanzu. Maimakon ya bata amsa sai cewa yayi ita wanan bataji sauki bane har yanzun komai Amma tace gata nan dai kasan yaran nan yan banzan yarane su suka tayar mata da hankalinta. Yace wasu yara ke nan Amma tace kannen ka mana marasa ta ido da suka koyi mugun abu a gurin iyayyen su. Kai Amma muke nan gaba daya fa kike nufi tunda kinyi jam,i haka ? Kaji nace dakai tace tana tsure shi da idanuwan ta tare da fadin na tambaye ka kaki ban amsa ko har haihuwan boyansa kuke yi kamar na auren ? Murmushi yayi yace ko auren ai ban boye maku ba Amma nisa ne kawai ya hana kuji ai. Wani sati nike son mu koma insha Allahu don iyayyen ta sun matsa ta dawo hakana gaban su. Allah dai ya raka taki gona umma ta gaida Assha duk sai yaji ba dadi irin yadda ahalinsa ke nunawa akan merry din yayi kasa da kansa kafin yace . Nina dauka dake zamu tafi ki kwana biyu muna a can tace in ka ganni lahira maza suka kaini kaidai da ka saba dasu ka karata can. Yace a a Amma kada muyi haka dake ina kullun addua kike Allah yasa ki goya yayana yau kuma zaki dare haka kiki zuwa don kinji maganan barin kasa zaki inda baki samun fura ko. Tace ja,iri koma dai maynene ban zuwa idan ka gannin gidan ka naje reno sai in A ruwa ta haihu wanan kan komai nidan duniyan da kuke zan taka idan muna da rai da lafiya. Ahogon dake daure a hannun shi ya kalla tukun ya mike tsaye yana fadin Amma ni zan tafi kin san yau jumma,a lokacin kurarene. Zaka gudu ke nan don kaji na dauko ma zancen da baka so ko haba Amma may zaisa in gudu dama ba dadewa nazo inyi ba nazo ganin daddy ne don nasan yau yana gida bai fita. To ka gada ita mai dakin naka a sauka lafiya sai ka sake shigo ya amsa da nagode Amma yana fita. Ina jin su daga kuryan Amma inda nake kwance har ficewan shi wasu zafafan hawaye ne suka gangaro min a idanuwana ina tausayin kaina da kaina. Hjy wace ta shigo falon don amsa kiran maigidan nasa bayan sun dan gaisa ne yake fadin wai umar ko yayi maki zancen komawan su can England ? Tace komawa kuma kamar ya Alh shida yace zai iya kai wata shidda zuwa takwas a nan kawu yace da farko ke nan ko don yanzu dai kinsan matar sa ta biyo shi nan ai. Gata da tsohon ciki kina nufin a nan zamu bar yar mutane ta haihu muna bayan mu bamu san irin al,adun su ba can. Alh sai naga itama dai ai yar kasan nance gaba da bayanta har wani al,ada suke dashi daban da namu koma suna da wani yanzu tunda ta auri dan mu ai dole tabi al,adun mu kuma. Ke jummai ki dinga cizawa kina hura abu kafin ki tauna ke baki gudun wani abu yazo ya samu yar mutane a nan wurin mu. Da ganin yarinyar fa kasan irin sagartattun yaran nan ne da iyayye suka sagarta tun farko saboda haka ki barshi ya maida ita inda ya daukota shine umurnina . Maganan daya dauko min na auren ta ya isheni a barni dashi kada ku dauko min wani ina zaune kalau. Koko so kike su dira garin nan suzo su barmu da abin kunya nan gaba bayan wanan dayayi don haka su tattara su koma inda suka fito. Tace to amma Alh naga, , , Hannu ya daga mata alaman shine umurnin shi hjy ta cika fam ta dade zaune batayi magana ba sai can ta mike zata fita tana fadin shike nan ita mace bata datace da danta sai abinda aka tsara mata. Shidai baiyi magana ba ya basar da ita haka ta fita tana jinini da korafin tauyewa ne hakan a gare ta don ba karamin shiri taiwa kanta ba kan haihuwan. Yanzu shike nan duk Alh ya rusa mata plan din ta kan wani dalili nasa can sai kuma ta koma zargin shi umar din ko shi yakai karanta wurin Alh. Neman dan nata tayi tana fadin tana neman sa bayan ta fito wurin maigidan nasu rai bace. Yadda yaji muryan ta ya fahinci tana cikin bacin rai sosai bai samu zuwa gidan ba sai da yamma ya shigo. Tun shigowan shi ya farga da tana cikin fushi sosai har lokacin sai ya soma zargin kansa. Tun bai zauna ba yake fadin mama lafiya ko naga kamar ranki a bace wani abin kuma ya faru ne ? Hjy ta dago kai tana masa wani kallon daya kara shan jinin jikin shi sosai da ita. Babawo yanzu har kakai in kiraka kaki zuwa a lokacin dana bukace kazo gurina da sauri yace haba mama nina isa koda kika kirani a lokacin ma muna jigawa nida Nasir. Ta kara kallon shi a shesheke tace yanzu babawo karana kakai gun mahaifin ku na hanaka tafiya da matarka ? Subbahanallahi mama shi daddy yace na kawo karanki akan may zanyi karan ki gun daddy kuma mama ? Da kyat ta samu ta daidaita natsuwanta kafin tace nasan zaka iya tunda na hanaka tafiya da ita ? Mama ina mun gama wanan magana dake ko akan may kuma zan tayar da maganan yanzu kuma ? Kara kallo shi tayi irin duba na tuhuma duk sai yabi ya tsargu don bai san abinda zai biyo baya ba kuma yanzu yadda yaga ta hau din nan. Tace bawai ya fada min kakai karana bane tuhumar hakan dai nakeyi dama babawo wai may yasa baku gudun bacin zuciyana ne ? Yace mama idan ni na fadawa daddy ai zan fada maki gaskiya ko cewa nina fada mai din. Tayi shiru bata tanka ba na dan wani lokaci kafin tace yanzu dai burin ka ya cika amma ka tabbatar da sanin duk wani abin al,ada da akeyi idan mace ta haihu zaka barmuna muma nan ayi kamar yadda al,ada yake. Dago kai yayi ya dan kalle ta tace eh haka nace babawo don ba zaka maishe mu dakarkarun iyayye ba. Naka tsarin kaje can ka kashewa kafiran banza kudade munan ko oho kenan mun haifar masu da daga sama. Ayi hakkuri mama insha Allahu za ayi yadda kikace din sai a lissafo min duk wani abinda zaku bukata a nan din ayi yadda aka saba din. Tace dama hakan za ayi don ba zan haifawa wata da ba saida lokacin cin moriyan ku yazo wata can daman ta amshe min ku. Ga mata nan kasan yan asali amma duk basuyi maka ba saida ka tsalaka kaje inda zaka jawo min abin gori ga jamma,a. Tana fadan haka ta mike zata shiga dakin ta ya bude baki da kyat yana fadin mama don Allah kiyi hakkuri idan ranki ya baci ne ? Sai ta juyo jin yadda yai maganan kuma sai ya bata matukar tausayi sai dai babu yadda ta iya don hakan da takeyi tana son dasa masu tsorontane a zukatan su. Ta maida kanta ta juya ta shige umar yaji kamar ya dora hannu akai ya kurma ihu dan tsaban takaici saidai koba komai daddy ya kwatoshi daga tafiyan tunda alama ya nuna ta yarda. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:08 - 🀐🀐🀐: BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHEEM Ban shiga school ba sai ranan monday kamar yadda Amma tace mun kuma har lokacin a gurin ta nake kwana sai dai danaji sauki ina dan zuwa part din mu in kai wani lokaci a can. Haka sai yasa Amma bata son inyi nisa da gurin ta ko kadan ko yaushe idan ina gida ina wurin ta zaune idan kuma nazo part din mu zakaji ta aiko wai in zo. Koda nazo din kuma ba wai wani abin zan mata ba zakaji tace kin je can kin zauna ta dinga matsa maki kawai. Kawu ko da ya dawo da dan tsaraban Amma kullun wanda muke taruwa dani dasu Aisha mu cinye abin mu sai yan kanne na dakan biyo ni nan part din ta din su zauna tare dani saboda sabon da mukayi. Wanda hakan yana a kunnuwan mutanen gidan da suke ganin kamar an kaini can gun Amma ne don wani abinda muke kullawa tsakanin mu. Salma ne ta shigo muna tare da Amma a falon wanda a yanzu zamana a cikin sa yana samun gyara sosai kai da kai ina tsabtace shi. Wuri ta samu ta zauna ba tare da taiwa kowa magana ba sai Amma ta kalleta tana fadin gaki kamar a jefo ki kinzo kin zaunawa mutane kimkam a kai ? Cikin wani murya na shagwaba tace yanzu Amma don na shigo gurin ki shine kuma zakiwani ce min na zauna maku kimkam a kai ? Amma tace kinga sakona nane kizo naki dai ya kawo ki dama ta mike zuwa wurin fridge din Amma tana fadin akwai fura a fridge din ko baki dama ba ? Aiko ina dashi bazan baki ba son ba don ki nake ajewa ba ta juyo tana fadin Amma ai kin ba A ruwa tasha ko ? A ruwa ai bake bace don A ruwa ta fiku sanin zafi na da darajana a gidan nan yaushe rabon da na sakaki a idona gidan nan ? Dama ai hakane sai bare ya zo ya fika daraja kai da gidan uban ka ko baki furta ba mu san da hakan a wuri ki Amma. Amma tace A ruwa tafi karfin zama bakuwa a gidan nan ko bare don duk daya kuke a gurina tunda suka fara magana ban kulata ba tun shigowanta falon sai yanzu da tayi wanan maganan. Dadin abindai da ubana ba shegiya aka haifeni ba gida kuma gidan kawuna nazo salma ko anty salman da tasa muke kiranta ban kira ba lokacin. Tace dama wani yace baki da ubane ko kinji na fadi hakan sallon kuma ki koma kice ga abinda nai maki yanzu daddy ya samay ni da fada. Allah sarki ai bagware ba bobawa bane kowa yayi jifa a kasuwa yasan wanda ya jefe balle ma kin fito fili kin kira sunana kai tsaye abinda kuke dauka ba shi nake a nan ba. Kada ki soma ki fada min maganan banza a gidan nan don kina ganin wuyan ki ya isa yanka ke a gidan nan kowa zaki iya fadawa magana kai tsaye. Cikin bacin rai Amma tace salma ki fice mun daga shiya tunda ba alheri ya kawo ki nan ba yarinyar nan ko lafiya bata da amma saboda bakin halin ku kuda iyayyen ku ba wanda ya iya budan baki ya tambayi jikin ta. Yanzu kuma kinzo zaki tayar mata da hankali haka muna zaunen mu kalau a nan wanan wani bakin hali ne shin inda uban yar nan yaje ko yau ko gobe iyayyen ku kuma tafe suke sai ko idan zasu tsaya gadin duniya ne in sani. Mutane a kullun baku da magana sai gori a kan mutuwa to iyayyen naku da suka dauki duniya da fadi su zauna jiran duniya. Juyawa tayi tana fadin shigowa nan yasa har za a fada min magana kan iyayyena saboda wanan yae sadakan da ake neman likawa mutane. Kikai kuwa nace mata dama a kwance nake ina magana na mike zaune ina fadin duk mune yan sadakan idan sadaka illace ashe . Gara wake da kowan wake don a sarafa waken a nau,i nau,i wani ko a kowan yake tsayawa tace may kike nufi nace kije wanda ya turo ki yai maki bayani ni yar sadakace . Daga hakan ta wuce fuuu ta bar falon nan tabar Amma na sababi da ita bayan fitan ta na dauka zasu dawo da hjyn ta sai naji shiru kuma. Sai washe gari kawu ya shigo yana tambayan Amma abinda ya faru Amma ke fada mai yadda akayi ta kare da fadin wa yan nan mutane ba mutanen arziki bane. Ni ba don ka rigada kayi wanan alkawarin ba da an fasa wanan hadin abu tun yanzu yakici yaki karewa haka tun ba,aje ko ina ba. Hajiya dama ai shine bukatan jummai ta dagawa mutane hankali ba gaira ba dalili ni amsan da fatima ta ba salma yai min dadi. Da yake basu da tsoron Allah ni ba haka uwarta ta mayar min ba don cewa tayi Fatima tana zaginta ta hanyar diyar tane. Lalai wa yan nan mutane basu tsoron Allah a rayuwa su yar nan ta shigo muna kamar an jefo ta tazo muna da tashin hankali haka ? Hajiya nasan halin kowa a gidan nan fa ba sai kin tsaya kina bata ranki ba a kansu ina daga ciki ina jin su ban fito falon ba tunda baji ya dauko zancen namu da salma. Ya fice tare da yi mata sallama saida takai kofa yake tambayana tace ina ciki na kwanta ne tun dazun yai mata saida safe ya fice . Umar da merry wace yanzu cikin ta yayi girma sosai suka shigo gidan don yin sallama da iyayyen nasa wanda daga sama sauran mutanen gidan sukaji tafiyan nasu. Sun dan jima gurin kawu kafin su fito su shiga dakin mahaifiyar shi a nan ma sun jima a dakin merry data kagu su tafi tace zata fara shiga wurin mamu kagin ya iso ta mike da kyat zuwa gun mamun. Zaki gane kuren ki idan kin san sheri da macuciyar suke kulla maki sai kare ya fiki daraja gidan nan ta fada kasa kasa ba tare da daga murya ba. Sai kuma ta juya gurin dan nata tana fadin ka sai dai ban yarde maka zuwa gurin maimuna ba yace na sani mama. Daga haka yai shiru yana latsa wayan shi dake hannun shi ba tare daya sake magana ba sai can dataji shirun nasa yai yawa tace ke nan goben zaku wuce kai sai yaushe zaka dawo idan kun tafi ? Ina ganin sai ta haihu zan shigo kasan nan ya bata amsa tace aikin dakake a nan fa tunda kace baka kare ba. Na barshi a hannun wa yanda ke aikin ya bata amsa mata a yanayin rashin son magana don yadda yake ji din a lokacin. Kasan zaka bar komai da za ayi a nan kamar yadda na fadama ina son ayi ta sake fadi ya dago kai yace amma mama cewa kikayi ai sai idan ta haihu zan turo maku ko ? Ban yarda da hakan ba yanzu na canza shara kabar komai daya dace a gurina yadda zai ishe mu yace ba matsala mama. Yana mikewa tace zaka tafi ke nan tunda matar ka ta kasa zama nan din ko ? Yace gurin Amma zan shiga muyi sallama da ita yana kallon fuskanta yaji may zatace mai sai tayi wani iri da fuska kawai ba tare da tayi magana ba. Yana ganin haka ya fita kiran layin merry yayi don baida halin shiga part din mamu a yanzu saboda bin umurnin uwarshi. Merry ta fito suka shiga gurin Amma don yi mata sallama sun dan zauna bayan gaisawa yace Amma mun zo mu sallame kine gobe zamu koma England insha Allahu. Ta kalle shi tana fadin goben nan dan nan ni na dauka wasa kake min ai da ka fada min ranan hankalin shi yana ga wayan hannun shi da yake tura sako yace. Ina fatan kin shirya tafiyan ta dan tabe baki tana fadin rabani da shirmay yanzu in ka tafi sai yaushe zaka dawo ke nan ? Yace gaskiya Amma ba maza ba don zan dan dauki lokaci a can sosai kafin inzo kasan nan. Amma tace idan ka tafi zancen yarinyar nan fa da sauri ya dago kai yana fadin wace yarinya ke nan Amma ? A ruwa nake nufi don naji mahaifin ku na fadin karshen shekaran nan zai aurar dasu duka. Ya dauri fuska kafin yace Amma yaran nan kanana ne fa may daddy kewa sauri ga auren su haka yanzu da wuri ? Ka tambayi uban nakama shida yake son hakan yarinya ko kallon arziki bata samu gare ka yaushe ka tsaya ma kai mata kallon tsab, Amma may yasa kika damu zancen auren nan ne haka wanan yarinyar ma fa bata kai wani shekarun aure ba. Nifa Amma kin sani auren biyayya ne zan maku don haka duk lokacin da kaga ya dacd sai a fada min. Kallon kai a suwa Amma tayi mai taja tsuki tare da fadin banga laifin ka ba tunda idon ka ya bude yanzu da masu dan bujen nan. Ban san da su a falon ba dawowa na ke nan daga unguwa nida su Aisha ina saye da les dinkin buje da riga yau anyi sa,a na saka mayafi a jikina . Sai kitson da ke kaina daya dan fito don daurin dan kwalin danayi sai kamshin da jikina ke fitarwa don daga wurin bukin kawar Aisha muke don tare suka kare karatun su dasu salma akai mata aure. Yana hangoni yaji gaban shi yayi mumunan faduwa saboda saboda shigata ra yau ya fitar min da surana na asali a fili. A hankali ya lumshe ido daga inda yake zaune merry ko tana ganin mu ta shiga washe baki gare mu tana fara,a tace dama tana tunanen ta tambaye mu kada ta tafi bamu gana ba. Kallon inda yake sukayi suna fadin yaya ina wuni kunzo lafiya ? Ya amsa ba tare daya dago kai ba da lafiya nikan wurin Amma na nufa ina fadin Amma yau duk na gaji wallahi a cikin muryan da ban san inayi ba wanda mai saurare zan dauka shagwane. Merry ta tace in zo kusa da ita tana son muyi sallama gobe zata koma kasar england maiyuyuwa ba zata dawo kasan nan maza ba idan ta haihu. Jin haka na yasa Aisha ta ce ba zaki tsaya ki haihu a nan ba mu dauki baby tayi murmushi tace gaskiya ba zata iya zama nan kasa ta haihu ba . Ban san ya akayi bakina ya furta amma uban babyn naki ai a nan aka haife shi kuma kema ai yar kasan nan ce. Ba tasan may nake fadi ba sai kallona ina magana tayi tana fadin nayi fushi da kika zo gun grany kika nufa bayan kin gani a falon. Dan rage murya nayi ina fadin ban kula ku bane a falon sai yanzu. Idanuwan shi da suka sani saurin dukar dakaina ya dago ya watso min na jin nace ban farga sune a falin ba. Nayi saurin dukar da kaina kasa tare da juya gurin Amma ina fadin Amma yunwa nake ji wallahi. Ke yar nan yanzu kika dawo gidan buki zaki kira min yunwa a nan yanzun kuma? Amma kin san Fatima kamar tsoron mutane take yi taki sake jiki taci komai da aka bamu a gurin . Shine filancin ta nuna maku asalinta na kwarai ne ai macen kwarai bata zubar da mutuncin ta a duk inda take. Amma mu zamu tafi sai kuma idan Allah ya kara sadamu da alheri don jirgin mu da safe zai bar kano zuwa lagos insha Allahu. Yaya tafiya zakuyi ne da gaske Aisha ta tambaya bai bata amsa ba sai mikewan da yayi tsaye daga zaune. Amma tace miskilin zai koma inda yafi wayau nan kunsan cizon shi akeyi komai tsiyan ka dai daga kauye kakani ka suke. Ya dan murmusa yana fadin gara sai da kika tsaya akan kakanina da sai ince wani uban nawa kika gani ba kauye ? Nikan dadi naji har cikin raina sosai jin zasu bar kasan gaba daya ina Allah yasa ma kun tafi ke nan namamajon kawai. Jin kamshin shi kusa dani yasa na dago kaina shine kuwa ya matso kusa da Amma yana mika mata kudi tare da fadin ga wanan kiyi hakkuri sai idan na yo maki sako kuma. Ya dan lakuci kumatun ta yana fadin Amma ki kula muna da kanki kin san muna ji dake sosai daga haka ya juya ya fara tafiya merry ma ta mike tana fadin zasu tafi tana kallon Amma din. Hannu amma ta daga mata tana mata na bebaye alaman a sauka lafiya. Wanan tafiyan nasu ni ji nayi kamar an min albushir da aljanna don ina ganin ya samu ya kurce masu ke nan ba zai dawo ba kuma nan maza. Don ko hjy maryam sai daga baya take jin wai sun tafi basuyi sallama dasu ba dan gara ma mamu don shigan merry ta san zasu koma amma batai tsanmanin zai tafi bai sallame su ba ai. Bata dauki wanan komai ba a gurin ta don ba bakon abu bane haka a wurin ta sai bayan sun tafi ne sai ga Aliyu da sako a boye ya kawo masu yana mai basu hakkurin rashin yin sallama dasu da bai sami daman yi ba. Hjy maryam.tace ita kan ko ba sallaman baki ai ya gama mata komai ko Allah dai ya kaisu lafiya dashi da arniyar shi. Sai dai mamu bata ji dadin hakan ba don taso suyi magana dashi a kan merry sai gashi kawai tafiyan shi taji daga sama babu sallama . Ayi manege yau ban samu natsuwan typing ba yan uwa sai kun jini kuma zuwa gobe insha Allahu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:09 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM YA FATTAHU YA SALAM, , , Sun isa lafiya inda ya samu abokan arzikin shi suna kewan shi sunyi missing din shi sosai musanman a gurin aikin shi mutane da yawa sunyi missing din shi gurin. Tunda suka kaishi gida suka dire ya shige sallah ya gabatar da ake binshi yana gamawa yadan ci abinci don shigan dare sukayi . Ya kwanta bai fito daga dakin ba saida hayaniyan su merry da akazo yiwa adduan kore mata evils sprit din da ta kwaso a Nigeria ita da baby ta da maigidan. Pastor mahaifinta ya dauko masu dungurun gun don yin addua gare su don ma a ciki dare suka sauka da abin yafi nan don da church za a kaita ai mata wanan adduan. Saukowa yayi yana saye da wando three quarter a jikin shi sai riga fara daya saka a jikin shidon shan iska. Tunda yake saukowa yake kallon merry da take tsugun ne ta rufe ido hannaye ta na sama alaman roko take yi kenan. Pastor da mahaifin merry sukai mai alama da yazo gurin adduan shi ma ya kalle su da mamaki ya kara tsare gida a fuskan shi don haka yake masu idan zasu tursasa shi yin wani abu na addinin su . Pastor din yace ya kamata kaima kazo a kore maka evils din da suka biyo ku a tafiyan ku yace cikin kada kai banda matsala ni yana tafiya yake fadin hakan ys nufi hanyan fita daga wajen gidan wurin wani dan shan iska na gidan ya tsaya yana karewa dogayen gine gine garin kallo daga inda yake ya sauke ajiyan zuciya a hankali. Dafa dan karfen dake gaban shi yayi yana lumshe idon shi a hankali babu abinda ke zuciyar shi sai tunanen abubuwan da suka faru zuwan shi nigeria suke dawo mai a rai. Ya sauke ajiyan zuciya yana kara lumshe ido tare da dan damke karfe da karfi yana hadiyan zuciya. Daidai lokacin mahafin merry ya fito yana bin kusurwan gidan yana wasu sambatu irin nasu na kiristoci da sukeyi wai ana koran shedanu a gidan . Bai kula shi ba don idan da sabo ya saba amma shi ko a jikin shi duk wana abubuwan da sukayi yakan nuna takar bai san dunayi ba. Inda har yakan basu mamaki irin taurin kan shi akan riko da addinin shi don basu san zai iya riko haka da addinin shi ba sai zuwan nan da sukayi nigeria ne merry ta tabbatar da idan tushen rikon addinin shi duk yan gidan su tana ganin kamar malamai ne don irin shigar su da suke . Ita babu abinda ke bata mamaki kamar yadda har da kananun yara suke saka zunbulelen hijab da nikaf a fuskan shi tunda wanan yar ta step mum din don tun a waya ta labarta wa iyayyen ta wanan akidan na yan gidan. Muryan maman merry ne ta zo inda yake tana fadin my inlaw ya hanya ya mutanen ka can ya dan lumshe ido cikin rasgin son nagana yace suna lafiya ta sake fadin . Munzo kana kwance tu safe don yiwa merry addua ta samu kariya daga evils ayes ta haihu lafiya ita da baby ta su samu kariya. Yana da kyau ya bata amsa da fadan hakan yana juyawa don barin gurin matar tana kokarin ganin ta jawo shi a jiki kamar yadda suke da dan cikin su. Wanda daga hakan zasu yi amfani da daman wurin samun jawo ra,ayin shi gare shi na addinin su sai dai kuma yaron tauri ne dashi da rashin sabo sam baida yarda da kowa ko sakin jiki wanan halin yana matukar damun su a rai. Tsoron su shine kada watarana yaja ra,ayin yarsu tace zata juye ta koma tasa a kidar wanda wanan babban kalubali ne gare su don su din suna da wani mataki a cikin church din su na shugabanci. Haka zai zama abin kunya sosai a wurin su shine dalilin su na kin yin fushi da halayan yaron garesu na rashin yarda da amincewa dasu da baiyi ko wani lokaci. NIGERIA Tafiyan ya umar da sati aiyukan yan uwan uwanshi ya fito yana daya daga cikin wanda sukai hanya aka samu aikin don mahaifin su yayi iya kokarin shi a samun aikin abu ya faskara . Gashi bai son zancen komawan su waje yanzu koshi umar din akwai dalilan da yasa ya barshi ya koma din don ya koma ya karasa. Habbib yafi kowa korafin wanan tsayar dasu da akayi din wanda ba haka yaso ba yaso ya koma kamar yanda yayan nasu ya koma can. Kawune ya fadawa sauran mutanen gidan inda suka dinga layi zuwa yin murna wa hjy jummai yar mulkin tana amsawa da kyat don bata so haka ba ita a nata ganin ai sirin su ne hakan ba dole sai kowa yasan da maganan ba a saka masu baki. Itako abinda bata so ke nan kowa ya kama fada ana nanata magana ta dauki hakan da yawan saka ido ga mutum. Wata rana kuma sai gashi umar ya bugo waya yana sheda masu haihuwan merry din wace ta haifi diya mace wai har anyi sati uku a lokacin da ya bugo wayan yace ya radawa diya sunan mahaifiyar su Aminatu. Gida sunyi mamaki kwarai da jin hakan kowa na tofa albarkacin bakin sa ga irin halin umar din wanda shi bai damu ya fadawa yan uwa wani abin shi ba idan ba yaso hakan ba sai dai daga baya suji. Hjy su tayi fada sosai kan rashin fada mata da baiyi ba da wuri lokacin da aka haihu din yace mama ni dai a nawa bangaren nayi wa yarinya huduba da sauran abin da ya dace ayiwa yaro idan an haife shi. Amma ta bangaren merry ita har yanzu basuyi nasu bukin sunan ba tukun tace yau ga hauka ? Kace sati uku da haihuwa zakace basuyi bukin suna ba har yanzu yace eh mama ga nasu al,adan ai yarinya zata iya kaiwa har wajen shekara ba ai bukin suna ba sai idan an shirya akeyi. Tsuki hjy taja tare da fadin wanan bakin kwashe kwashen naka babawa mukan bai karamu da komai ba sai dadin ta kaici ni a ina na taba jin wanan shirmay haka ?. Yace haka sukeyi ga al,adan yahudawa da suke koyo yasa na barta da akidar su hakana idan sun tashi sai suyi sai hjy tace sai dai kuyi ku tafi church ke nan har kai ana faman raye raye ko a can ? Shi dai yai dariya kawai ba tare da ya furta komai ba sai ta kara fadin to kaga kamar yadda nace ma idan ta haihu zamuyi namu hidima a nan ya zama dole yanzu ka aiko da wasu kudi ayi don wancen da ka bayar nayi amfani dasu bayan wucewar ku. Yace ai da kawai ku bari tunda ba mai jegon ma nan itama batai komai ba aiko kamar jiran take ta fadi hakan ta haushi da sababi sai daya koma bata hakkuri da baki tare da alkawarin zai aiko mata da kudin kamar yadda ta bukata. Sai take fadin saura naji wanan zancen bakin mahaifin ku don yanzu na kula ko wanka kayi baka bushewa sai ka fada mashi ya sani. Dariya yayi yana fadin kai haba mama ni di kuma kike wa wanan shedan haka ya dai samu har uwan ta sauka daga fushin data dauka dashi da farko. Daga shi sai Aliyu suka iya bi da ita a cikin yayan ta idan ka ganshi miskili zaka dauka ta ko ina baida dadin sha,ani. Sai dai abin ba haka ba don fanin mahaifiyar shi yana kokarin kare mata hakkinta sosai yana gudun bacin ran mahaifan sa fiye da komai a duniya. Ba laifi hjy ta dan shirya dan kwarya kwaryan walima a gidan wai matar danta ta haihu yan uwa da kawayen ta aka taru a gidan tun safe ana shagalin suna. Bata gaiyaci kowa na fannin kawu ba har matanshi sai dai hakan bai hana hjy maryam shiga cikin tsabgan ba don ganin kwam. Mamu kan ficewa tayi abinta unguwa bata tsaya ganin takaici ba gidan sai data daidaici lokacin dawowan mu school yayi ta dawo gidan saboda yara. Ni kan ban san da zancen ba mun dai dawo na samu gidan dankare da manyar motoci tun daga wajen gidan dole haka muka raba muka shiga ganin part din mu a rufe yasa naja kanne ba muka nufi gurin Amma. Tafe nake amma tunane ya addabeni a rai na may ke faruwa a part din hjy yau naga ana ta shagali haka ? Da sallama muka shiga na zube saman kujera ina cire safan kafana dana kanne na Amma ta fito daga daki jin motsin mu. Tana fadin har kun dawo ashe agogon falon ta na daga kai na duba nace Amma yanzu kusan hudu fa don munyi jiran mamu bata zo daukan mu dole motar haya muka biyo. Tace nima bansan ina taje ba tun dazun nasan dai fitan ta bai rasa nasaba da wanan taro da taga anyi yau gidan nan. Da sauri nace wai Amma taron may akeyi ne haka a gidan nan yau naga motoci har wajen gida ga mata zaune gungu gungu a wajen gidan. Sai da ta tabe baki kafin tace wai yau suna ake muna a gidan haka tana fadi tana juyawa da kai da gani abin bai gamshe ta ba. Da sauri nace suna Amma wa ya haihu kuma tace wai matar dan uwan ku kafiran nan mana matar saudaki. Kallon mamaki nayi mata ina fadin tau a gidan nan ake bukin ko suna kasan nan ne ? Tace ina fa daukarwa kaine kawai irin na jummai data iya abin kwarai batayi sai abin banza. Kai Amma ba danta take tayawa murnan samun karuwa ba taja wani irun tsuki tare da fadin Allah kadai yasan irin riban data samu aurin wanan bukin. An fada maki jummai tana abu don Allah ne ita barta nan inda kika ganta da halin ta sai kurum kawai. Abinci na tashi na dibanwa kanne ba tare da basu ruwa sun zauna suna ci ne mamu ta dawo part din Amma ta nufo don ta diba idan mun dawo. Bayan ta ganmu ne sun gaisa da Amma sai Amma take tambayan ta ina ta fito sai data kai zaune take fadin ina gidan kawu cewa mahaifin ta don haka take ce mai kamar yadda yayan Amma ke kiranshi. Gwaggo yau gidan bai zaunuwa ne yasa na dan fita zuwa gaida shi dama na kwana biyu banje can din ba. Sai dai idan kina da jiyar fita dama kan wanan shirmay da ake zaisa ki bar gida nan don kawai guje masu. Nikan mikewa nayi na shige dakin Amma don akwai kayana a nan wanka nayi na dauki bakar riga na saka tare da dauko wani dan gyale daura a kaina na fito na samu har mamu ta tafi part din ta. Wani flat takalmana dake nan kofan Amma na saka ina fadin Amma zanje inwa su fauziya wanka in dawo tace kada ki dade ki dawo nace tau Amma. Kidane yau yake tashi a gidan ga mata nan gungu gungu zaune saman fararen kujeru da akayo hayan su sai dai duk cikin taro banga yan bangaren kawu ba. Wasu yan mata ne naga sun zubo mi ido har na kawo kusa dasu naji daya na fadin ai wanan ce yarinyar dama ? Ashe ma ba wata babba ce haka dama gaskiya dai wanan sai dai in an kwan biyu kan auren su ni dai yi nayi kamar banji su ba sai daya tace uwar ta fa ta cusawa daddy su ra,ayin ta amma wanan ina zai kaita shida yake dan gayu yadda ya waye din nan. Allah ya sauwake ai hanyar jirgi saban data mota sai suka kwashe da dariya dayan ta kare da fadin a to kwarya tabi kwarya dan uwanta badai a cikin dangin mu ba don su mama sunce ba zai taba yuyuwa ba wanan zancen. Dan murmushi na sake a fuskana nace a raina kuna da gaskiyan ku komai akai muna baku da laifi don dole yanzu na zama mujiya a idon jama,a ke nan . Ban kula da wata mace dake zuwa ba sai ji nayi na buge da mutum na dawo daga tunanen da nakeyi da sauri ina bata hakkuri. Don maganganu yan matan yasa hankalina dagawa har na shiga tunane ban san matar tana tafe ba lokacin. Matar na fadin ba komai sai jin muryan hjy maryam mukayi daga bayan mu tana fadin ke A ruwa kanki daya kuwa zaki bangaji babban mace kamar wanan. Ban san tana tafe bane maman ikilima kuma na bata hakkuri ai, ta watsa min harara tare da fadin dallah rufewa mutane baki marasa tarbiya kawai har da baki ma sai kin nuna masu halin ki sun sani. Cike da mamakin kalamin ta na waro ido ina kallonta matar ta sake fadin haba hankalinta ne baiya a hanyan ai bata san ina tafe bane itama asali nima waya nake ban san da zuw ba goan ta ba. Wanan ma aiko ta sani hakan zatayi don rashin kunya da take takama dashi da jiji da kai kin dai ga inda abin arziki yake don haka a daina kwadayin shiga manya mutane don ba kamun kai. Sai duk wa yanda ke wajen suka sako muna idanuwan su suna sauraren ta kamar daga sama mukaji muryan hjy tana fadin maryam may kuma ke faruwa ne nan ? Yanzu Asma,u ta samay ni ciki take fada min magana mara dadi wai matar DG wanan yarinyar ta bangaza don kawai tana takama da rashin kunya har na waje su sani. A tausashe nace maman ikilima ba bangazan ta nayi ba karo mukayi da ita kuma na bata hakkuri . Acikin tsawa suna hada baki in masu shiru da rashin kunya suna magana ina fadi don banda kunya ta tara taron arziki don bakin ciki zan wargaza mata taro. Watace da ganin ta malama ce suna zaune a gefe ta daga nikaf din kanta sama tace haba ku dinga kyakyawan bincike kafin ku yada magana mu nan muna kallon abinda ya faru asalima ai matar dg itace ta buge yarinyar ba yarinyar ta zo ta bugeta ba. Amma duk da haka hjy lami bata iya tausasa harshe ga manya ita ta bada hakkuri zata tsaya muna haka a kai kimkam. Matar dai ta sake fadin yo ai wanan yarinyar nada kirki tunda tana bugeta ita tashiga bata hakkuri dazun akwai wata yar bakar yarinya data fito wancan part din kunsan mata kadani tayi a gidan nan cewa part din hjy maryam take nunawa. Hjy jummai tace yaran banza ne kawai an tara muna su a gida babu tarbiya suna abun da sukaga dama wa mutane. Kin fito kamar wata bakuwar buzuwa dake kina baza ido don gulma wa gaiyace ku gaiyan tsiya. Na daga ido na kalli hjy dake ta muzantani a gaban bakin ta uffan ban furta mata ba har sai da matar mai kama da malama tace min ke wuce ki tafi inda zaki. Jummai idan ta samu fada bata jin assh na juya nacewa matar nagode hjy tace kinji kilibibin ko ? Wa yar da kike gani ta koyi kilibibi har ta gaji a gidan nan haka kawai zaki zo min cikin tarona kamar bakuwar shedan. Dariya yan matan nan suka kwashe dashi har suna tabawa tare da fadin wuuuu. Mama hadiye dake tsaye tace amma dai kunji kunya wallahi don kunyiwa a ruwa haka a cikin taro shi zai zama may ? Tunda duniya ta wanke ta ga gaskiya ana fada kin fito da abinda ke cikin ki a fili a bainan jamma, a hakan ne zai hanata shiga gidan danki don kin muzantata ko may ? Hjy ko tace bakikai labari ta hau mama hadiye da fada sai kallon ya dawo gare su nikan har na shige part din mamu ina jiyo hayaniyar su wajen. A take zazzabi ya sauka min na karasa falon mamu da kyar na haye kujera na kwanta ina tunanen wanan wani irin kiyayya ne hakan tsakanin mu da matan nan. Ina nan zube saman kujeran idanuwana a lumshe naji mamu tafito daga daki tana ganina sai tayi turus a wurin tana kallo na. May ke faruwa ne waje sayadi naji kamar muryan maman ku hadiye da hjyn su salma ? Nace sune mamu fadan dani ake mama ta shiga wai na bangaji wata mata alhali matar ta fada masu ban bangajeta ba itace ta bugeni bata gani ba. Sayadi mai ya kaiki guri su don Allah mamu ta fada a cikin wani murya na bacin rai nace wallahi mamu banje gurin su ba na fito inzo inyiwa su fauziya wankane muka hade da matar a hanya na karasa idona yana kawo hawaye. Sayadi banson abin fitina sam wallahi shiyasa kikaga na bar masu gidan tun safe ashe ban tsira ba daga sherin su. Mamu ta ban tausayi yadda tayi maganan ya nuna ta gaji da wanan rayuwan na gidan su itama tana dai hakkuri ne kawai. Kwana biyu bayan taro ranan asabar da dare ina falon mamu zaune da littafi ina karatu don jerabawan da zamu fara. Kawu ya shigo part din namu yana sallama a ladace na zamo saman kujeran ina gaida shi ya amsa ya samu wuri ya zauna. Mamu dake zaune kasa ta gaida shi da dawowa ya amsa ya dago kai ya dan kalle ni kamar mai nazarina yace. Fatima kin ramay haka da yawa ko har yanzu zazzabin ne a jikin ki kuma ko damuwa dai kika sawa kanki haka ? A ladabce nace a, a kawu naji sauki jerabawa dai zamu fara nake karatu. Murmushi yayi yace shine kike matsawa kanki haka akan jerabawa ai nasa an saka sunayen ku cikin masu fita bana . Na dago na dan kalle shi sai kuma na sada kaina kasa a hankali murna zanyi ko bakin cikin hakan ? Mamu ne tace zata iya kuwa naga karatun nasu yanzu sai a hankali yace sai da nasa akai min bincike a kanta sosai zata iya insha Allahu. Ya juya gurin mamu yace ina ganin idan akai haka zata tafi da kwalinta can kinga da taje sai kawai ta fada jami,a baki daya dama kin san tace likita zata zama ko kin fasa ne fatima yana kallon fuskana. Ban san lokacin danace ban fasa ba kawu ina nan da kudirina har yanzu sai kuma naji kunya ya kamani daga baya na noke kai. Ai fa ka tabo mata inda ke mata kaikayi yau da zancen zama likita sai dai itama gata da tsoron allura nagani sosai amma tana sha,awan tayiwa mutane ita. Mikewa nayi zan fice kawu yace dawo ki zauna abinki nace zan je in kwanta ne kawu na fice tare dayiwa mamu saida safe. Cike da farin ciki na shiga gurin Amma da dan guduna na rugumay ta na kama hannunta ina fadin Amma kawu yace bana zan fita school sai in shiga jami,a. Tayi murmyshi tace aure yazo ke nan kusa tunda har zai katse maki karatun ki yanzu. Da sauri na girgiza kai nace a, a Amma yace karatuna zan dora sai kuma nayi shiru tuna yadda yai maganan. Dan jimm nayi sai na mike tsaye tace aure sha kan yaro sai gida umaru sanda babuga yarinya a can zaki digree ke nan ko ? Fuskana bata na koma saman kujera na zauna na shiga tunane can kuma na mike na shiga ciki don in kwanta ita kuma amma tafi kwanciya a falo tana nafilfilin ta ba dare wanda yanzu zama da ita yasa ina koyo. Can kusan barci ya fara daukana cikin tunane na naji muryan kawu gurin Amma suna hira tana fadin tana ciki nasan ta kwantane. Yanzu tazo min da murna zaka katse mata karatu don nace aure yazo tayi fushi ta shige dakin. Ai hakan yayi daidai don a wuce wurin kowa ya shiga hankalin shi zaifi fitina jummai yayi yawa haka kawai ki tozarta yarinya a bainan jamma,a don wata manufa taki kawai na banza. Hajiya kin hana in mata magana ne danayi mata tsiya wanan karon haba a bainan jamma,a haka ki muzanta yarinya kankanuwa kamar fatima ? Zubur nayi na mike daga inda nake kwance ina sauraren su naji Amma tace yanzu ai tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa ka doka don dai ta kara kawo nesa kusa ne ai. Toshe bakina nayi don kukan da yazo min a lokacin har kawu ya fita ina jin su suna magana ne duk a kaina da matsalan gidan shi. Ranan dai barci rabi da rabi nayi shi da asuba koda na idar da sallah na jima ina rokon Allah yasa a fasa wanan auren ga baki daya. Ya kuma kareni daga ko wani sheri duniya da lahira ga baki daya na dade a dakin kwance don naji ban bukatan fitowa saboda gani nake Amma tana cikin masu zuga kawu akan yin auren namu. Har kusan goma ina kwance kuma ba barci nakeyi ba Amma ta shigo tana fadin yau ko barcin lafiya kike yar nan ? A sanyaye na dago kaina na kalle ta da idanuwana da sukai luf luf dasu nace ba barci nakeyi ba ai. Kallona tayi fuskanta ba yabo ba fallasa ta zauna bakin gadon da kyar tace banyi tsamanin kina da taurin kai irin hakaba yar nan ? Ina maganan nan kunyi shi da kawu ki kin amince yanzu kuma zaki shiga wanan halin haka ki dami zuciyar ki. Maimakon in bata amsa sai na barke da kuka ina fadin Amma kin dai ji abinda hjyn su take min wullakanci har a bainar jama, a. Mikewa tayi ta fita daga dakin zuwa falon ta ba adadeba kamar daga sama naga mamu a kaina lokacin na kifa ciki ina kuka ban san shigowan ta ba dakin. Jin kamshin turaren ta yasa na dago kai na na kallo bayana ta tsaye ta kura min ido tana min kallo tuhuma. Tace sayadi nace na,am murya a dakushe . Bata kara cewa komai ba sai tayi shiru kamar mai tunanen wani abu sau can tace ashe ba an gama maganan nan dake ba wai ? Wani irin tsoro ne ya lullubeni na mike zaune tukun na dukar da kaina kasa ga barin kallon ta. Karo na biyu ta koma kirana tace kina jina ai ina magana yau dai ayita ta kare kada ki boye mi komai na yarda in kashe nawa auren da in jefaki cikin damuwa ke. Wani irin kaduwa naji dajin furcin ta da sauri nace mamu ni may nace yanzu kuma kan maganan ? Tace gashi tun jiya kin tada hankalin ki dana tsohuwar nan dake kokari dake har ta fara yanke shawaran fadawa kawun ki a raba wanan auren da yake son hadawa tunda hankalin ki bai kwanta ba. Nace a marairaice wallahi mamu ni bancewa Amma komai bai tunda dai nayi sallah ne na koma barci kawai. Murmushi tayi tace ba gaskiya bane ko kina tunanen gwaggo zatai maki karya akan abinda bakiyi bane. Da sauri na girgiza kaina nace na bari mamu ni ba kuka nake ba gani dai nayi kamar ba za a barni naci gaba da karatuna bane shine damuwa na ayanzu. Wa yace ba zakici gaba da karatun ki ba indin abinda kikaji ya fadi ne jiya ai hakan yana nufin taimakon ki yayi da hakan. Nan dai ta nuna min bacin ranta tare kuma da dan min nasiha na share hawayena karshe nayi wanka na fice zuwa part din mu don har lokacin ina fushi da Amma. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:11 - 🀐🀐🀐: .BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM, , , Akwana a tashi ba wuya a wurin Allah abubuwa sun faru da dama a cikin gidan kawuna wasu na jin dadi wasu ko na tashin hankalin zamantakewa rayuwan mutanen gidan. Izuwa wasu watanin da suka shude har hjy ta gaji ta debe tsammani akan auren don irin shige da ficen da taitayi na ganin hakan bai faru tsakanina da danta ba. Sai dai bata sani ba a maimakon abin yayi tasiri kamar yadda take son ayi sai Allah ya juye lamarin ya sako ma dan nata rashin son gida gaba daya. Don kamar yadda take tunanen ba wanda yasan takon ta a gidan bata san a idon makwarwa take shuka ba. Ba hjy maryam kadai ba har shi kanshi maigidan da baya barci yana raya daren shi a tsaye gurin mika kukan shi ga Allah yasan da abinda ta bizzine a gidan kan yayan ta. Wanda a da can bai dauki abin komai ba yafi danganta lamarin da sherin mafalkine kawai ke rudin shi. Sai daga baya ya farga da zaran ya gama nafilolinshi ne yana zikiri wanan abin kanzo mai a mafalki. Inda yake yawan ganin hjy din tasa danta gudu kullun da bai san may yakewa gudun haka ba. Har dai ya gaji inda yakai koken yawan mafalkin nasa akan danshi da take yawan yi idan barci ya fisgeshi. Kwanaki malam ya bashi akan zai dawo yaji abayanin daga baya sukai sallama sai bayan sati biyu ne kamar yadda aka diban mai ya koma gidan malamin don son jin ba,asin maganan mafalkin. Nan malam yayi mai bayani yadda zai iya fahintar shi kamar haka, da farko dai kana da yara maza da mata a gidan ka sai dai dukkan su suna da ma bambanta iyayye a gidan a yadda nake gani. Sai dai wanan mai dan tsayin da kauri itace matsalan gidan ka don matsalan daga gurinta yake don tafi sauran hasala a cikin su. Nan dai malam ya koro mai duk abinda ke nan har yadda hjy tayi aiki kan danta sai dai an samu akasin aikin don aikin ya juyene ranshi ya bar gida gaba daya yanzu. Shiyasa kake ganin sa a halin gudu da kake ganin shi yanayi ba kakautawa a mafarkin ka . Kafin malam ya gama bayani har Alh sani yayi zufa sosai a goshin shi lokaci daya sai maimaita innalillahi yake a ranshi hankalin shi tashe. Bai bar gurin ba sai da malam ya bashi addu,oin da zai dingayi don samun masallaha a al,amarin. Alhamdullahi shi ya rike kuma yana ganin hasken adduan a lokacin don bai cika sati daya ba sai ga kiran Umar ranan a wayan shi. Mamakine ya cika kawu dayaga dan nasa na kiranshi a waya ya dauka da addua a bakin shi tare da sallama. Jin kamar ba zai amsa ba sai can ya amsa yana fadin daddy i am very sorry na rashin kiranka tsawon lokaci. A cikin hikima da nuna ba komai ya katseshi ta hanyar fadi umaru sanda mazan fama ga aiki ga ban tsoro. Dan murmushi ya sauke tare da ajiyan zuciya ya kara fadin sorry daddy aiyukane sukai min yawa a nan . Kawu yace umar na sani ai in kaji shiru lafiya ne yaya wurin ita matar taka da amarya na dan gajeren murmushi yayi yana fadin suna lafiya koda yake na kwana biyu ban tare dasu ina nan mun zo aiki a kasan italy. Kawu yace haka na da kyau amma a kula da hakkin iyali a dinga sauke masu hakkin su kada a raja,a ga aiki kullun . Nagode daddy yace tare da danyin shiru na wani lokaci Alh ya kawar da shirun ta hanyan fadin kun gaisa da mahaifyar taka ko ? Yace daddy idan mun gama yanzu zan kirata itama sun dan dauki lokaci yana janshi da hira mai kama da nasiha, kamar babu abinda ke damun shi a rai. Kafin suyi sallama umar din yana mamaki da babu abinda mahaifin nasa ya nuna mai na rashin zuwa gidan da baiyi kuma baya kiransu. Don shi haka kawai yaji gaba daya kasan ya fice mai a rai ko aikin daya fara ya dakatar da yin sa gashi saura kiris ya rage komai ya kammala gare shi. Yayi mamakin jin daddy baimai fada ba kamar yadda yayi tsamani sai gashi karshe sun kwashe da wasa da dariya da mahaifin nasa. Yana mamakin hali irin na kawu da ko abu ya bata mai rai bai faye fitowa fili yai ma mutum magana a kansa ba sai in abin yakai intaha zakaji yai dan fada dasu. Ko case din merry yasan ya batawa daddy rai ne sosai yasa yai mashi hakan sai lokacin ya tuno da alkawarin auren dake kanshi wanda ya manta da zancen sam a cikin ranshi. Gaban shi ne ya fadi har ya furta oh shit to amma kuma yaya akayi yanzu daddy bai jefo min zancen nan ba a hiran mu. Wayan maman shi ya kira kamar zai tsuke ba,a dauka ba sai kuma can aka dauka tana fadin hello a kausashe. Yayi sallama tare da fadin hjy mama an wuni lafiya tace yau kaga dama ka tuna damu ? Ya danyi murmushi yana fadin mama tuba nake don Allah wallahi aiyukane sukai min yawa nan. Rufa min baki aiyuka ko matarka ta dauke maka hankali gare mu har ka fara mantawa damu. Babawo ka lissafa yau wata nawa rabonka daka kirani mu gaisa koda a waya ne ? Yace mama ayi hakkuri abubuwa ne sukai min ya, , , , Kada ka mayar dani mutumiyar banza babawo ka tuna ban daga cikin irin uwayen da yaro zai min son ranshi ba zan gama wahala daku ba yanzu hutu yazo kace zaka manta damu don ka samu wata mace. Shiru yayi yana sauraren yadda mahaifiyar nasa ke kwasan fada dashi tace watau abinda nake guje maka ga auren yar wurin maimuna shine kuma zaka gwada min ga wanan mai guntun bujen naka ? To idan ma dan abinda kake turo muna ne ta hana ka sani yanzu ba kai kadai bane mai bani don bakai daya na haifa ba. Wani irin yaji a ranshi ba dadi hakan yasa ya shiga bata hakkuri yana kokarin kare merry akan ba laifinta bane sai dai uwar bata bashi daman korafi ba. Suna gama waya ya cika mata account dinta da kudi masu yawa haka yasa ta daina jin zafin shi da take ji da farko. Ranan ma ya kira Amma sun dan taba hira take tambayan shi ko lafiya taji shi shiru haka kwana biyu ya dinga tuna gida da iyayyen shi shiru haka sai hankalin mutane ya tashi ai. Yace Amma za a gyara da yardan Allah komai zaizo da sauki insha Allahu sukai sallama. Daga wanan karon kuma saida ya dauki lokaci bai kira wani ba duk dai kawu yana kan addua ga yayan nasa har lokacin. Mun samu mun kammala karatun mu lafiya yanzu gidan wa yanda suka rage sai kanana mai dan girman cikin su itace yar gurin hjy maryam kanwar ilkilima a cikin masu zuwa school. Har lokacin ba wani jittuwa a tsakanin mu sai dai ba yawa fada tunda bamu shan innuwa daya dasu balle mu hade ayi fada ko islamiyan da muke zuwa kowa tasa yake zuwa. Mun gama da kamar wata daya ranan kawu ya shigo wurin Amma ina falon ya kalle ni yace Fatima tunda an kare karatu yanzu sai ki shirya muje bauchi ko ki gaida su. Wani dadi naji a raina har bansan lokacin dana saki ihun murna ba suka kwashe da da dariya shida Amma. Nan na bar kawu wurin Amma na nufi part din mu ina murna na samu mamu ina fada mata kawu yace in shirya zai kaini bauchi wurin su manjo in dubasu. Tace yanzu yake fada min saidai yace ai ba zaki dade can ba na bata rai tare da fadin ni dai a barni can inyi koda wata uku ne mamu wallahi ina kewan su sosai. Tace da wuya saidai ai tsakanin ki da kawun ki ne kila idan kin lalasheshi zai yarda. Don zumudi tun ranan na fars shiri ina daukan kayan da zanyi tafiya dasu ina jefawa a yar jekkana da wanda zanyi kyauta dashi idan naje can. Har kwana biyu banji kawu yace min komai ba nikuma ban fasa shirina ba har lokacin ba karamin kaya na kwasa ba , wai duk kyauta zanyi dasu a can idan naje. Da dare ranan bayan kamar kwana uku da maganan ran daren jumma,a sai ga kawu ya shigo yana fadin mu shirya da safe zamu wuce. Haba murna wurina ba a magana na matsu gari ya waye Ingani a garin misau gaban manjo da Atika inga yaya Atika ta koma itama. Da safe muka fito a cikkn shirin mu wanan karon duk yaran zamuyi tafiyan dasu wanda hakan yai min dadi sosai a raina. Mun sallami kowa a gidan don sai da mamu ta turani nayi sallama dasu ba don naso ba ssi da muka fito shiga motane naga ashe ba mu kadai zamuyi tafiyan ba har da wasu abokan kawu sai dai mu tamu motar dabance. Sai na dauka kila dama wani abu kawu zaije yi can bauchi din yaga ta dace ya kaini gida. Su Aisha har wurin motan mu suke sun min rakiya sai da muka tashi suka bar gurin sai kuma naji ba dadi a raina. Sako mai yawa Amma ta bayar akaiwa manjo ina ta godiya kamar nice manjo din da akaba sakon. Mun isa musalin daya da wani abu na raba wai dukda mun daka sakko da safe muka taso amma sai kusan azahar muka isa garin. Gida yana nan kamar yadda na barshi saima kara lalacewan da yayi lokacin a idona ko don na saba da gidan kawune yanzu nake ganin hakan. Wani dadi naji a raina na kalli gidan su Atika shima yana nan kamar yadda na barshi bayan motar ta tsaya ne na fito da zumudi mamu ta kalleni tace ki natsu mana kin san yanzu kowa idon shi zai koma kanki ne. Hakan yasani na gyara da kyau duk da hakan banyi yunkurin yin wani sallo ba can sai dai ban san komai nawa ya canza ba a yanzu don su ganin gaba daya na sake masu ne don gani ga yayan Atika mai koramu karatu bai gane ni ba nima ban masa magana ba. Na hango wasu gungun maza matasa zaune a darbejiyan dake duban tsohon shagon isah mai shegwo har yanzu shagon na gurin sai dai ba kamar da can baya ba da yake cike har baki muna zuwa sayen abu a gurin shi kusan duk unguwan anan ake sayen abu. Yanzu ko shagon ya watse ba wanan kayan irin na dacan baya a shagon don har cikin shagon zaka iya hangowa daga inda muke . Mazan ne naga sun zubo muna ido suna magana ban tsaya bin ta nasu ba na nufi hanyar shiga gidan. Da sallama na shiga gidan mama saude ne zaune tsakar gida da daura gaba tana tsifan kai. Jin sallaman mu ne yasa ta dago kai tana kallin mu gurun ta na nufa ina rike da yan kanne su biyu fauziya tana rike da mamu suna bin gidan da kallon mamaki. Nace mama ina wuni tace wa nake gani nan kamar fatu nace nice mama ina murmushi a fuskana. Tace ku fito yau ga fatu a gidan nan tana fadi da yar fara,anta sai gasu sunyo waje ruuuu daga cikin tsohon falo namu. Fati ce nan fatin manjo fa sai ga umma ta leko itama da daura gaba a jikin ta tana fadin fatin manjo ina kuma ta fito nan ko tayi halin natane can suma sun koro, , , , Ganin yanayi ga kuma mamu a bayana yasa ta katse maganan datayi niyar fada gare ni ta washe baki tana fadin ashe tare kuke tafe da maimu. Itama na gaida ita kamar yadda na gaida mama saude din da farko sai fadi mama saude take ina zasu shiga ne yaya ? Mun barsu a waje tsaye mama tace a, a dakin tsohuwa zasu kin sani nan na juya na nufi dakin kwanon manjo da nai rayuwa a ciki a baya ya kara lalacewa har an tare shi da su leda da ragga dai sauran tarkace nasan don ruwan sama ne. Manjo na zaune a sama tsumakara wai katifa sai ganina tayi kamar a mafalki ina fadin manjona na fada saman jikin ta. Salati ta fara sai kuma ta fashe da kuka tace wallahi tunanen ki nake a raina yar nan nace manjo ai gani nazo tunane ya kare. Sallaman mamu kofan dakin ya katse muna tace ashe tare kuke da uwar taki sannun ku da zuwa tana kokarin tashi na hanata don rabin jikina a jikinta yake. Tace daga jn tashi in gyarawa uwarki wurin zama mana nace ki zauna manjo in gyara mata tace tsintsiya yana daga waje ki dauko. Dakin ne ba mai gyaraw sai ni idan na dan ji daman jikin nakan dan kora in samu wurin sallah. Na fito daukan tsintsiya naji yaya hamshin ya shigo yana fadin wai wa nake gani kamar fatin manjo gidan nan ya nade kafan wandon shi daya da ganin shigar shi kasan har yanzu sai a hankali. Nayi murmushi ina fadin sannu da zuwa yaya hashimu sake baki yayi yana kallon ikon Allah kafin yace wai da gaske kece fati kika koma haka ? Nayi far da udanuwana nace nice yaya mun samay ku lafiya ? Sai mamakin canzawa yake ya kasa amsa min niko banga abinda sukewa mamaki a jikjna ba yace fati kin koma kamar wata baturiya haka dake ?. Dan dariya nayi ina fadin kai yaya hashim kuma har da zolaya yace ba zolaya ko daya kin canza fati kin koma yar birni dake kamar bake bace fatin manjon dana sani. Muryan manjo ne take fadin wai ina kike ne kin bar mutane a tsaye nace gani nan na barshi na wuce tsaye a gurin yana mamaki na. Suma can dai ciki gulman sukeyi kan canzawan danayi cikin shekara biyu da rabin danayi rabona dasu. Saida na share dakin na fito da shera nake fafin ai ina su anty kubura ne ban gansu iba tambayan mama saude tace sadiya tana ciki kubura ina jin ta fita. Bayan an gama gaisawa Mamu tace ai mata magana da baffa don zasu komane su yau aka tura a kira baffa din yazo. Bai dade da zuwa ba suka fice wajen harda mamu nan suka barni na fara gyaran abinda zan iya a dakin na kusa karasawa ne sai jin murya Atika nayi tana fafin ina Fatin take ne ? Na yarda tsintsiyan hannu na na fito muka rungumay juna da ita a wurin mun dan jima muna hira ta tayani gyara dakin kafin su shigo sai fadi Atika keyi kin ganki kuwa fati kin canza fa ga baki daya wallahi ni dai murmushi kawai nake mata ina kallonta. Da gani yanzu duniya ta dan basu baya ganin yanayinta kawai yasa na gane hakan koko din girshi ta fito ne ban sani ba. An dauki lokaci a wajan don har na fara tsarguwa sai ga mamu ta shigo yara suna biye da kayana a bayan su tana fadin kije kuyi sallama da kawun ki kafin mu fito. Atika ce ta rakani wurin shi na samu wuri na tsugun na yace Fatima kinga gida kin shige kin manta da mutane ko ? Nayi murmushi ina fadin kawu mamu tace yanzu zaku tafi yace eh kinsan hanyan sai a hankali gara mu bishi da wuri ido na ganin ido zaifi tunda mun ga baban naki. Nan dai yadan ja min kunne akan in natsu kwana biyar zanyi driver zaizo ya dauke ni mu koma nace kamar in kuka don ba haka naso ba ni tunda na gama karatu ai da a barni na kwana biyu nace a raina. Hannu yasa a aljihun shi ya ciro kudi masu yawa ya bani yace ki rike wanan na karba ina godiya yacewa Atika itama ga nata ya sake kirgo wani yace i bawa mutanen gidan idan na shiga . Muna wurin sai ga su mamu sun fito har da yan gida kawu din da sukai mata rakiya don ta jikasu da alheri dumus. Nabar gurin kawu Atika tana biye dani na kwanta a kafadan mamu ina fadin mamu har nafara ji kewan ku fa. Tace yau ga tsiya ni dagani mu wuce zaki ga sako acikkn hand bag dinki na saka maki kidai kula da kanki don Allah. Uwa dadi kamar ince na fasa tsayin kuma nake ji yanzu a raina na nuna mata kudin da kawu ya bani tace kuma yabada wani fa da farko kuma a baki nace to ko in baki wanan ki tafi dasune mamu ? Tace bar abiki yadda naga gidan nan sai a hankali ki tabbatar da kuna cin abinci mai kysu kada ku zauna da yunwa nace to mamu ina shafa kan samir daya makale mun nikuma ina jikin mamu kamar zan koma ciki. Sai muka ba mutanen dake kallin sha,awa yadda muke abu kamar wasu ya da kanwacan haka sai ina kallo suka tafi ina daga masu hannu. Nace mu shiga in gyara kayana kafin mu shiga wurin umma nasa ba zan fito maza ba idan naga umma yau. Mun shiga na gyara wuri komai tsab na fito tare da Atika da kallona bai isheta ba har lokacin don har ga Allah ba Atika kawai ke mun kallon kurulla ba kowa na gidan ne. Haka muka fito zuwa gida su Atika ban fita ba saboda sabawan da nayi yanzu sai danaje na fadawa su mama saude zan shiga gidan su Atika in gaida umma. Bayan na wuce ne aka sa topic dina a gidan mama saude tace ai na fada maki ba dawo da ita sukayi ba baki ganin yadda iyayyen keyi da ita kamar zasu mai data ciki. Koma dai maynene ai dai bata canza uba in kuma tasa tsiya in hana malam ya barta ta koma muga tsiya. A gidan su Atika na shiga da murna ina kiran umma tace har nayi fushi tun dazun muna nan muna saka idon ganin ki sai ji mukayi shiru. Na rungumay umma ina fadin umma na tsaya sallaman su mamu ne amma kina raina wallahi ranan dai mun sha hira kamar babu gobe sai dare na koma gida bayan yayan su Atika ya sawo wa mamu nama mai yawa da abin sha mai zafi nakai mata na samu ta idar da sallah har ta fara barcin wahala ba abinci. Bayan su kawu sun dawo gida da washe gari da safe yayi waya da yaran sa maza a kan komai sukeyi su bari su hadu gida ranan talata mai zuwa. Allah ya taimaka daga cikin su ba wanda ya fadawa hjy su don su a zaton su tasan ko may yasa yake nema su din . Dan dama Aliyu da suna waya yake tambayan ta baba lafiya yake kuwa tace may ka gani yana nan lafiyan shi kalau, Daga haka ya basar sai bai dauki abinda muhinmanci ba ranan sai ga Aliyu da habibbi sun iso da rana yan part din su sukai ta murnan zuwan su. Sun shiga gurin Amma sun gaisa sai dai har yanzu babu halin shiga sauran part din gidan don basu saba ba ma dasu din. Sai cikin dare umar ya sauka garin don haka gida shi ya nufa sai da safe ya shigo gidan nasu a natse. Yana saye cikin bakar suith ya kara haske sosai ya goge don yanzu kusan shekara da rabi rabon shi da kasan. Aisha ce ta fara ganin shi ta fito daga gurin mamu sai ganin mutum tayi tace yaya umar sannu da zuwa ya amsa mata a dakile kamar wanda bai gane ta ba. Har lokacin yana jin ba dadi a ranshi don zuwan dole dole yayi ya shigo ne da niyar kwana biyu kawai ya koma don akwai aiki mai tarin yawa a gaban shi sosai. Aisha da kamar dole har ya wuce ya nufi sashen mahaifiyar shi tace ya su anty merry da ummi karama ya amsa ba tare daya juyo ba da suna lafiya. Suna zaune falon Amma sai gata da murna tana fadin mutanen nan abinsu kamar hadin baki jiya su yaya habbib dunzo yau kuma ga yaya umar yashigo shima. Cikin fara, a Amma tace ikon Allah duk gaba dayan su sunzo a lokaci daya. Allah yasa lafiya dai don uwarsu bata rasa abin tsegumi a gaban ta ko yaushe wata kila kuma wani abin suka zoyi sai dai ni bakin cikina da sadauki zuwa ds wanan kafiran haka tsirara a gidan nan. Dariya suka kwashe dashi suna fadin kai ji amma fa irin ku ne yan sa ido kan mutane. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:11 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM, , , , A can garin misau kuma bayan mun dawo wurin manjo na tayar da ita tare da gabatar mata da abinda aka sawo mata yar tsohuwar ta mike jikinta har rawa yake da ganin kayan dake zube a gaban ta. Gabana ta sai da naga taci sosai sai ta dago kai tana fadin nifa nace banjin yunwa sosai don naci abinci gidan su Atika. Tace ba zai yuyuba A ruwa yau naji kunya a gidan nan yadda iyayyen ki suka zo ko ruwan gidan nan basu sha ba haka suka juya suka tafi. Sai ta fashe da kuka tana fadin kai duniya abin tsoro ne A ruwa lokacin da kakanku yana raye muna zaune ne garin ikko dashi. Sai idan munzo ganin gida muke zuwa nan nahiyar a lokacin mulkin shagari kakan mai kudine sosai yana kasuwanci bayan aikin gwaunati da yakeyi. Idan zamu zo zaki ce wani sarki ne zai sauka a garin don yawan jamma,a motoci ko tun a wacan lokacin sai mun shigo da guda uku garin nan daya yana dauke damu iyalin shi dayan kuma na makaraban shi sai ta kaya da yake rabawa itace babban mota. Yan uwa na nisa dana kusa haka zasu dinga tururuwa a gidan mu ana zuwa gaida mu nidashi muna raba alheri gare su. Saidai kaya mutuwa bata barin wani don wani yaji dadi tun lokacin da kasa ya rufe idon kakan ku sanadiyan hatsarin mota kamar yadda mahaifin ki shima ta wanan sanadin ya tafi haka ma kakan ku don sai gawan su kawai aka kawo muna a gida. Kuka ne yaci karfin ta ta kasa magana juice din dake gaban ta na dauka na tsiyaya mata a kofi na mika mata sai dai ta kasa amsa tasha. Da kyat na iya budan bakina da yai min nauyi nima nace manjo ki sha kin san baki da lafiya kada ciwon ki ya tashi don Allah. Bata karbi cup din danake mika mata ba sai dai ta tsagaita kukan nata tana dan share hawaye ta dan ja jikin ta zuwa dan langa langan dake a matsayin bango a dakin ta jingina jikin ta dashi. Nima zuciyana babu dadi yadda ta ban dan labarin na dan lokaci kafin taci gaba da fadin watau a ruwa duniya babu gaskiya tunda can haka take don mutum abin tsoro ne. Kinga bayan mutuwan kakan ku tun lokacin na fara fuskantar rayuwa mai tsanani gashi a lokacin mahaifan ku ba wani girma sukayi ba sosai. Kafin kice haka abokan kasueanci dama yan uwan shi duk sun wawashe dukiyan daya bar muna haka muka tataro muka dawo sai motar daya mallaka min da gidan daya gina a nan azare muka dawo ciki. Ashe tsugune bai kare muna ba don nan ma yan uwa sai cewa sukayi suma gidan da muke ciki ya zama na gado duk dasu don gonan su na gado ne mahaifin ku ya noma ya samu aiki a karshe ma ya sayar ya tafi ikko yayi dukiya don haka yanzu rabawa za a yi abinda muka samu shine rabon mu. Haka ina ji ina gani aka sa gidan nan kasuwa aka saida shi dan kudin da suka bamu dashi na sai wani fili dashi da niyar mu gina idan na samu sarari. Cikin ikon Allah sai ga amin mahaifin su na nan misau AD Rufa,i ya aiko min da wasu kudi dake tsakanin su da maigidan nawa ban bari kowa ya sani ba na dauki kudin nan na sai muna gidan dashi shine wanan gidan da muke zaune a azare dakika sani. Da sukaga haka sai kuma suka fara zargina kan na boye wani dukiya dama na hanasu ne don kada a raba tare dasu abu har kotu sai can ne nayiwa alkali bayanin komai. A ruwa nasha wahalan rayuwa wanda har yau a cikin sa nake tun rasuwan kakan ku zance na dan ji dadi lokacin da mahaifin ki ya taso ya fara aiki a wanan lokacin gaskiya wahala ya kawu. Saidai ashe shima rayuwan ba mai tsawo bane kwatsam sai ga labatin rasuwan shi a hanyar shi ta komawa wurin aiki munyi sallama dadi dadi dashi sai kuma labarin rasuwam shi ya girshe mu. Badon nakai zuciya nesa ba da sai nayi shari,a da kanin mahaifin su don a ranan sun samu matsala dashi don Abubakar yazo mai da maganan filin su na mahaifin su daya rage mutumin nan ya murje ido yai mai rashin mutunci har gida a gabana ya furta mai sai ya gani gobe bai kara tuntuban zancen filin su. A ranan mahaifinki bai kwana duniya ba Aruwa innalillahi nace a fili tare da fadin manjo dama su baffa suna da yan uwane a Azare ? Murmushin takaici tayi tare da fadin ras kuwa Aruwa ba ko adadi amma duk sun share mu sun fita batun mu nima hakan yasa na share kowa daga mazan har matan su kuwa. Babban takaicina shine baffan ki Amadu yanzu tun lokacin da yazo min da zancen auren lami ban so abin nan ba don ba gidan kwarai lami ta fito ba. Abinda nake gudu ga auren lami shine ya faru don sanin halin baffan ki ba mai yawan son magana bane. Wanan tabarbarewan yaran Amadu yana ci mun rai sosai a ruwa ace yara babu daya na gari da zai zama mutum yau a dube shi har shima ya duba nasa iyayyen . Yau naji dadi a yadda na ganki kin koma din nan ina godiya ga Allah da bai kashe ni ba har naga ingantar rayuwan ki A ruwa ta sanadiyar mahaifiyar ki mutumiyar kirki mai sanin ya kamata wace bata manta alheri. Kasake nayi ina sauraren ta na kasa furta komai a gare ta sai kallon tausayi nakewa kakan nawa lokacin don ba abu mai sauki bane ace yau ka wayi gari ka tsunci kanka cikin wanan halin da manjo ke cikin sa. Jin shirun danayi ta dauka ko barci nakeyi tace ko zaki je gidan su Atika ki kwana can ne kinga ninan sai a hankali wurin nawa. Da sauri na girgiza mata kai tare da fadin manjo kema kika iya zama nan ni mai zaisa ba zan iyaba ba wurin su Atika nazo ba gunki nazo don haka ko wani hali kike a nan zan zauna. Tace to ki hau wanan kayan ki kwanta ni sai i kwanta nan inda nake sallah ko nace tare dai zamu kwanta dake manjo ki gama cin abincin ki sai in gyara wurin idan kin tashi. Tace nagama ke nan don naman ya fita min rai ko ai naci rabona ubangiji ya saka maku da alheri dama rabona da nama tun a gidan kawin ki da mukaje kano din nan banci nama haka ba sai yau din nan ta sanadiyar ki. Nace naki nefa manjo dan ke na sayo shi haka kici sai kin koshi in kai masu sauran waje. Da sauri manjo tace ba zaki basu ba wa yan nan marasa tausayin da rashin imani a ruwa mutanen nan barsu nan inda kika gansu har yanzu halin nasu yana nan basu canza ba kamar yadda kika san su. Dazu ma ai bayan fitan ki saida naciwa lami mutunci a kanki gidan nan wai kilama sun dawo dake ne kin ishe su a can. Nace ta taba ganin inda uwa taki dan dan ta to ba dawowa dake akayi ba kinzo ne ki gane mu ki koma. Mutane ba abinda suka aje a ransu sai bakin sheri da gulman tsiya du kuma tsuliyan su tab da kashi. Wan yar gurin lami har ciki tayo na banza ban san ya sukayi suka barar dashi ba a gidan nan bayan ciki ya girma kowa ya gama gani ta dashi a gari. Tasha wahala kamar zata mutu Allah dai yayi da sauran shan ruwan ta bayan taji sauki sai gashi kuma ta koma harkan banzan yanzu ai baki ga tun shigowan ki garin nan bata gidan nan ba. Wani irin ba dadi naji har cikin raina dan dan uwanka dai dan uwankane ko yaya wani abu mara kyau ya samay shi dole kaji daci. Mikewa nayi ina daukan ledan naman zan fita manjo tace ina kuma zaki dashi nace su umma saude zankaiwa kada ya lalace tace ban abina nan gobe ke dumama min inci ko ki muna miyan shi. Manjo ki bari a basu don Allah goben sai a sayo maki maikyau in maki miya da akwai kudi sosai a wurina ai. Ba dan taso ba haka ta kyale ni na fita tana mita kansu naje kofan dakin najiyo muryan saratu din ta dawo tana fadin a ruwa fa mama saude. Tace ita kuwa saratu girman dan mutum baida wuya wallahi kinga yadda yarinya ta goge ta zama wata yar birni da ita haka ? Tayi kyau kamar a waje take zaune ba a cikin kasan nan ba ni canzawa yarinyar ya ban mamaki sosai. Umma lami tace kai saude tun dazun fa kike dada yarinyar nan wa yasan tsiyan da take shukawa a can. Sallama na yasa su dakatawa da maganan na shigo falon sai wani warin da gahi ya doki hanci na nace ina mikawa mama saude leda ga wanan manjo na sayowa ta kasa ci kada ya lalace. Da sauri ta karba tana fafin a, a kuma dai babba yanzu sai a hankali muryan saratu ne ke fadin wai a ruwa kece nan da gaske ? Murmushi nayi nace nice anty saratu mun samay ku lafiya ai tun dazun nake tambayan ki akace bakya nan. Ina kokarin juyawa tace don Allah tsaya in kara ganin ki wai kece a ruwa haka ? Murmushi nayi tare da fadin anty saratu bari da safe ma hade zan gyarawa manjo wurun kwanci ne. Ina fita naji mama na fadin may ye a cikin wanan leda din ta bude tace may nama ne mai tarin yawa fa. Ai gaba daya sukayo ruuu wa nan nan aka fara gardaman yadda zasu raba ba tare da saura diyan sun gani ba daga ciki anty kubuta tace ina jinku wallahi a rabashi kowa ya samu ehee. Tare muka kwanta da manjo saman katifan nata na ragga sai dai nayi dabaran gyara wuri ta bakin katifan idan tayi barci in sulale in koma sama hakan akayi. Don ina jin tayi barci na dawo kasa ina ta tunanen labatin da manjo ta bani yau wanda ban taba sanin shi ba. Washe gari kiran sallah masalacin unguwar ne ya tayar damu tunda nayi sallah na zauna ina karatun kur,ani na wajen do yanzu na sauka sai dai tulawan da nakeyi din. Sai da rana ya dan haska na mike na fito gidan babu motsin kowa don ba zance sun tashi suyi sallah ba ma lokacin daga dakin manjo na fara na share ko ina. Sai na fito tsakar gidan shima na gyara ko ina jin motsina yasa mama saude fitowa tana fadin fatu har kin tashi a raina nace ni yasu nikan naci suna kala kala a duniya. Amma a fili dan dariyan yake na sakar mata tare da rusunnawa ina gaida ita da kwana ta amsa a washe tana fadin baki gaji da gajiyan hanya ba kika hau aiki da wanan safiyan haka ? Mama wurin ne yai min ba dadin gani shine nake gyarawa na bata amsa tace kin san gidan namu ne ai sai a hankali. Bayan na gama na shiga hura wuta ruwa wanka na fara kaiwa manjo kafin in dawo na dora na shayi don nayi niyar yau a gidan sai kowa yasan nazo garin. Bayan na dora na fita na sayo bread mai yawa leda biyu yadda zai ishi kowa da kayan tea ban samu a shagon isah ba kamar yadda nayi tunane sai dana dan taka zuwa gaba na samo abinda nake son saya. Na dawo na samu manjo ta fito ina shiga take tambayana ina naje nace na sayo abin karyawa ne waje. Tace da kin bar naman jiya da bamu karya dashi din ba dariya nayi mata nace manjo kefa kikace ya isheki naba masu ci yanzun kuma zancen naman bai fita ranki ba har yanzu ?. Ba kunya ranan har fada suke wurin rabon bread din dana kai masu da ruwan shayin dana hada mai yawa kowa yasha. Na dawo na zauna na mulke jikin manjo da mai tun tana fadan hakan har ta kyale ni nace ko may yasa ku tsufin nan baku son mai haka nake fama da Amma idan tafito wanka sai na mulke ta da mai itama . Sai lokacin na tuna da zancen tsaraban da Amma ta ban in kawowa manjo mikewa nayi na dauko da kyat ina mamakjn may ye a cikin kayan haka mai nauyi ajewa nayi gabanta ina fadin wanan sako ne daga Amma tace a kawo maki. Kallon kayan tayi kafin tace ikon Allah wanan duk may ye a cikin sa haka ? Ban sani ba na bata amsa tare da fadin ga dai abin da nauyi sosai tace bude muga abin arziki nikan wa yan nan mutane suna kashe ni da farin ciki a duniya. Bayan na bude na fara zaro kayan a hankali abune a cikin leda baka an nade sai wani buhu wanda na bude semo ne ciki irin na leda leda din nan su tumatur da galon din mai sai shimkafa irin wanda diyanta ke kawo mata ko wani lokaci bata ci sai mama hadiye da yaran ta ke amfani dashi. Shine ta bayar a kawo wa manjo din yanzu ikon Allah wanan matar ta kashe ni da kunya na zauna ina bude ledan turmin zani ne a ciki guda biyu suma dai irin da ake bata din nan ne kyauta ta hadowa manjo dasu. Naja kayan gefe na dauko nawa tsaraban na fara fitarwa ina nuna mata harda abinda ban sani ba mamu ta hado min irin sabulu dasu omo clean man shafi masu yawa don rabo. Manjo tace yar nan wanan uban tsaraban haka mai yawa mutanen nan basu gajiya haka da dawainiya. Duniya ke nan baka san inda zakaci arzikin wani ba rabonki yasa muna ci daga tsagon wanan mutumin yanzu a ruwa. Allah baibar maki mahaifin ki duniya ba gashi ya baki uban goyon da ko mahaifin ki na raye sai hakan gare ki. Manjo ke nan nace ina zama don bude jakkar da na shako da kaya wanda duk rabi na kyautane a cikin su ga wani ghana most go dana shake daban don ni ko yaushe cikin yi min kaya mamu take shiyasa na iya kwaliya kamar may yanzu. Duk wanan kayan da kike fitarwa na maynene manjo ta tambaye ni nace bayarwa zanyi amma sai Atika tazo ta zaba ikon Allah yau A ruwa kece mai ba da kaya hakan ga wasu. Ta kara jijiga kai tana fadin abin Allah wuya gare shi yau ina lami mai maki gori da sallah ta fito taga ikon Allah tunda farar safiyan nan haka ? Nace kai haba manjo ki barsu kawai Allah yafi su akaina ko yanzu ai hakan dadin kine manjo koba haka ba na fadi ina kallonta don kawai in hanata wani katobara don nasan abu nacin ran tsohuwar sosai. Atika ta shigo na baje mata kayan ta zabi wanda ranta yake so a ciki don ba zan manta halarcin su a gare ni ba ni da kaina na tayata zabe na kwashi kayan nakai wasu kubura sauran. Ban samay su wurin ba sai na bawa mama saude dake aiki kamar jaka a tsakar gidan ita kadai na basu nasu tsaraban danazo masu dashi. Fita mukayi da Atika zuwa gidan su acan na aika akayo mun chafane na dawo na hadawa manjo abinci mairai da lafiya har da ganye na hada mata. Naba kowa na gidan rana har da godiya akai min hakan da umma lami taga inayi sai hassada ya shiga cikin zuciyar ta da yamma sai gata ta yafa wai zata unguwa. Ta dan jima da fita na sharo dakinn na fito ina share waje mama saude ta dan fita ta leka waje sai gata ta dawo naji tace nikan fatu ina son yin wata magana dake idan zaki rufani. Da sauri nace mama may ke faruwa ne kuma tace tau zan dai fada maki gaskiya kiyi hankali da yaya a gidan nan don ta fito fili ta fadi tana bakin ciki dake fatu. Yanzu ma wanan fitan nasan wani sheri za,a tafi kulla maki don ki aka fita tace sai ta danbalaki kin koma kowa na kyamarki duniya. Innalillahi nace tare da fadin may nayi mata mama saude na fada cikin tsshin hankali tayi saurin fadin rufa min asiti fatu kada babba taji zancen nan don Allah. Kin san idan baba taji yau akwai tashin hankali a gidan nan sai a dauke ni munafaka kuma. Nayi maki alkawarin fada maki duk wani mugun nufin da yaya ke yi a kanki ko ba yau ba don har nima bata barni ba. Yanzu dai don ki yarda dani har in indan ta amsa wani sheri zakiga ta baki abin dadi tace wake kawai ta dafawa shi kada ki yarda kici wanan abin idan ma son samu ne kawai ki kiyayyeta ki saka mata ido na kwana biyu ki fahinci komai a kanta. Nace mama na gode tace don Allah kada ki bari babba taji wanan zancen din ba zata iya rikeshi a ranta ba. Naji mama na gode nace na juya na tafi zuciyata cike da fargaba zancen sai tunanen abinda naiwa umma lami nake a raina sai dai na rasa kamo amsa. 16/11/2021, 23:11 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM Haba yar uwa mayye ribanki cikin daukan alhaki ki saida imanin ki don kawai ki gyawa wasu rai bada abinda zan hada ki dashi sai daran Allah dana Annabin rahama sai darajan iyayyen ki. Uhumm wai duk baki dubaba saboda son zuciya da da hassada kin gwammace mu abiki hakki gobe kiyama baki san ko kwayan zarra sai an futarwa mutum hakkinsa ba kina ganin kamar a nan duniya zamu tabbata ne. To ki sani yanzu Allah baiba mutum bashi tun duniya zaka girbi abinka wallahi na biki hakki dake da kika fitar da wanda kika turawa ya yada Allah ya bi mu hakkina. Ranan dai idan nace nayi barcin kirki a gidan nan karya nayi maku don tunane ya cika min zuciya na da firgice saboda na rasa gane mai nayiwa umma lami har take son ta illantani duniya. Washe gari kamar kullu ina tashi bayan na idar da sallah karatun kur,ani nayi sai da gari ya haska na mike dan gyara wuri da wuri nayi ma manjo abinci nace unguwa zamu da Atika don haka nai mata abincin da zai isheta har wani lokaci. Bayan na gama ne na dibar masu nasu kashi biyu na mikawa kowa nasa hikimar yin hankan gare ni umma lami ne da yaranta zasu cinye su kadai. Ruwa na debo a bakin famfo na surka na shiga wanka na dade a zaune ina shiri duk da ba kwaliya nake yi ba amma ranan na bata lokaci ina kwalliya. Wani yello less na saka a jikina mai dan flawer da zare bulle a jikin shi sai duwatsun dake shana shi idan ka gitta. Takalama da jakka blue na dauka sai dan oud dana shafe jikina ya dauki kamshi don mamu ta saba min da shafa turare mai mai na arab a jikina ko tufafina banda hammata da chest dina kawai ban shafawa don gujewa cancer. Manjo na tambaya ko tana son wani abu sai cewa tayi bana son komai yar nan dan dama wanan lemon kwalban mai sanyi. Murmushi nayi ina fadin wann bakin dai naki manjo na gane kwadai yake so a cikin sa fita nayi zuwa waje inda shago yake na sayo mata multina da fanta guda hudu na kawo mata . Yayin da idanuwan su kubara dake kwaliya a kofan shiga wurin su yayo caaa a kaina har saida na tsargu da kalln da suke min din. Ban dade da manjo nayi mata sallama bayan na aje mata komai a kusa da zata bukata a wuni hatta ruwan sha na sayo mata mai sanyi nayi mata dibara sakawa a wani tsohon kulan dake dakin tana fadin kin ga maganin ajiyan tsofi gwaggon duk zuwa sai ta min korafin in yarda shi naki. Ina fitowa duk suna waje nasan gulmana wa yanda ke waje suka kai harda umma sai da nagani a wurin na taka kamar tarwada zuwa wurin su tun kan inyi magana mama saude tace yau kan yar gidan babba ina za a haka da wannan kwaliyar ? Muushi nayi ina fadin zamu nan gidan samirace yar ajin mu da tai aure na juya ina fadin umma zamu ziyar ne yau zan tafi. Ba zaki dade ba ke nan ko ta tambaye ni cikin kallon fuskana kada plan din ta ya baci nasan nace zuwa sha daya insha Allahu zamu dawo. Tace to a dawo lafiya ina bada baya taja tsuki tana fadin sai na kasaraki ai yanda ko kare bai sunsun naki don bakin jini mu za,a kawowa barkado a gida ? Ke a dole uwarki ta fifitaki akan yayan mu wallahi karya ne baku isa ba daga ke har uwartaki da kike kuri da ita. Haba umma ni ban son irin haka wallahi fatima fa yar uwan mu ne umma idan kin kasarata ai mun kara yawa ke nan muku a gida ? Kubura wallahi ki fita min a idona tun ban saba maki ba wawiya daba tasan inda ke mata ciwo ba kinfi bukatan ta dinga kwaso tsumakara tana kawo maku kwance kuna jin dadi sakawa ba ku hakan zaima ku dadi ko hakazaifi maku dadi ? Nidai don Allah da kin barta har sau nawa fati kr zuwa garin nan da zamu ganta harara ta watsa wa yar nata sai ta kasa karasa maganan don kallon da uwar tai mata. Hjy jummai tayi mamakin ganin yayan nata data gani kamar daga sama washe gari ne suna zaune Umar ya shigo falon kamar an jefo masu shi sai mamakin ta ya karu sosai. Abinci aka gabatar mai bayan yan gaishe gaishe tana fadin ku lafiya wanan tafiyan haka babu sanarwa zuwa ai maku tanadi. Daddy bai fada maki komai bane mama Aliyu ke tambayanta hakan cikin tsure ta da idanuwan shi. Alh kuma ni bai ce min komai ba ta fada slowly a cikin muryan mamaki da tunane a ranta. Ko ma dai mainene ai zai fada muna tunda ya kiramu kuma gamu munzo inji habbib ya fada a miskile shiko umar baiko ta kansu don ko abin karyawan da aka aje mai bai taba ba. Kodai wani abinne ya taso yake neman mu hakan cikin zolaya Aliyu yace zancen auren ku ba kila wani kallo habbib ya watsa mai tare da fadin kainan daban ne idan ma auren ne ? Wani aure kuma hjy tace tana mere bakin ta tace aure kai ai yabi ruwa kowa yaje gaba ya neme nasa badai diyana da wanan gamin gambizan ba. Mama ni fa har yau ban ko san yarinyar da daddy ya lika min ba don koda yace inje mu gana wani zuwa danayi banje ba har na wuce. Ai gara ma yar wurin bros wancan zuwa naga ta girma sosai tayi clean gaba daya lokaci guda kodan ban ganta da katon hijjab din nan bane oho ? Umar ya dago kai daga abinda yake a cikjn waya ya watsa mai wani kallo ya kama dariyan mumuke . Yace Allah bros da abin mai yuyuwa ne akwai iri mai kyau fa gurin don ko ina zaka shiga da ita nan gaba. Kai karabani da zancen haushi a gabana habbib ke wanan irin magana ko da itace autar mata ba zata taba shigowa ahali na ba mudfin ina raye. Kyau dan maciji ko kunama may ake da irin da ko asalin su basu gama sani ba maimuna fa har yau bata san uwar ta ba a duniya. Kai wai mama da gaske ne wanan zancen ni tun tasowana nake jin ana wanan maganan fa ashe gaskiya ne ? Yo ina tasan ta dama irin yan cin ranin nan ne ai ubanta ya gani ya aura da iyayyen ta zasu koma kasar suna sudan suka matsa saida ya sakae masu ya suka tafi da abinsu har yau basu kara waiwayan ta ba. Shegiya dama ta tafi da wanan annoban amma hajiya ta hana a wanan lokacin dole ta tafi tabar yar a nan ashe annoba zata zomowa mutane nan gaba. Umar ya dago kai ya kalleta don jin zagin da ta aikawa mamu din tace na zagi kanwar uwar ka ko miskilin banza. Maimunan nan kamar tayi ma wani asiri a kanta tun kuna yara nake rabaka da ita kuna leke da juna. Dan murmyshi yayi yace kai mama zagin dai ne ba dadi maimuna kuma tare muka taso a gidan nan muna yara shine shakuwana da ita ba wani abu ba. Koma dai may na hana wana hurdan a tsakanin kai baka ko kishina da alama mai kina kake shigewa jiki. Shidai bai daga kai ya kalleta ba sai dakilan wayan hannun sa yakeyi can dai ya mike ta kalle shi tana fadin ina kuma zaka yanzu. Zan leka Amma ne a wurin ta nasan yanzu tasan nazo don akwai yarinyar data ganni gidan nan nasan zata fada mata nazo. Ko dai yar tsanarkace ta ganta hjy ta kalle shi tana tsuki tace wanan yar banzan yarinyar bana wai ta tafi garin su ganin gida nima jiya maryam ke fada min tafiyan su. Shidai yasa kai ya fita ya barsu a gurin yana ficewa tace wata kila wani abin ne ya bata mashi rai da zuwan shi haka ? Yana tunane iyalin shi daya barone ba shiri kila don kiran gagawan da akai mai ba shiri yazo. Arniyar matar nan zan waiwayeta don har yanzu bata kwanta min a raiba na tsani ganin ta a rayuwana. Babu wanda ke son ta a gidan nan idan ka dibe shi daya kwasota gidan nan kaf in maka na mahaukaci kyamarta suke. Ba wani abin kyama halin merry dai na rashin son yayi hurda da yan uwanshi shine matsala ranan fa munje gidan ta hana muna ruwa common ruwan sha fa mama. Ta gyara zama tana fadin ita din da kanta lale arniyar nan ta samu guri da yawa zafin ran babawo na banza ne. Shiyasa nake kara kyamatan wanan bakin hadin da Alh ke son yi maku don maimuna na iya kwace min da da kilibibin nan nata. Shiru sukayi suna sauraren ta ba tare da sun furata komai ba ga kalaman ta da takeyi akan maimuna din. Sallama yayi kofan falon tace lale marhabin da mutanen turai sadauki kaine yau ka leko mu kasan nan ai ka kyauta duk da dai kadade baka zo din ba ko yar nan da aka haifama bamu santa ba. Zaku santa Amma idan sunzo don zuwan merry kasan nan ba yanzu ba don yarta sai kila idan ta girma zamu shigo dasu wani lokacin yana zama yake wana magana wa Amma din da take tambayan shi. Sadauki irin dadewan nan haka ba a leko gida ba baida dadi wallahi an san aiki yana yawa amma mutum ya share gida har wani lokaci. Ai hakkuri Amma nima hakan bada son raina nake dadewa ba don aikina ne da yaimin yawa ko wani lokaci. Ina mai dakin naka take da yarta ina suna lafiya ya kuma jama,an wurin naku suke ? Dan bata rai yayi yana fadin suna lafiya Amma baki san dalilin kiran mu da daddy yayi ba haka a cikin gagawa ? Shiya kiraku kasa nan ashe tayi mai tambayan malam bahaushe mai ban haushi. Mayar da kanshi yayi saman kujeran da yake zaune a kai ba tare daya iya bata amsa ba ga nata tambayan. Itace tace wata kila dai akan wani maganan siri ne ya aika kuzo haka sai dai ni bai sanar dani komai ba gaskiya. Shidai baiyi magana ba sai faman tunane yakeyi a ranshi ko dai maganan mama gaskiya ne idan haka ne mai zaisa daddy ya lakantani da zancen dukiyan shi bayan yasan ina da nikin baninkin din su a hannu na koma dai may nene zamu ji ai yace. Ta shiga ta fito daki hankalin ta a tashe tana jan tsuki tana magana ita kadai kamar mahaukaciya mama saude ne da abin ya dama tace wai yaya lafiya yau kuwa ? Tace uhumm bari saude abubuwa ne suke son yi min yawa a kaina yau ta fadi tare da shigewa dakin mama saude ta bita da kada kai tana fadi a ranta mugun nufi yabi mai shi. Daga gidan su samira mun shiga wurin gida biyar muka dawo gidan su Atika muka yada dandali bayan karfe hudu. Hankalina yana gida wurin manjo saidai kamar an kashe min jiki da zuwa gidan bayan muyi sallah na kwanta a gurin ina dakilan wayan Atika shiya dauke min hankali na manta da komai dake gabana a lokacin. Bayan sallah magariba dana isha, kuma na dasa wani kallo ina kallon ci gaban shi hakan ya jani har goma da rabi ban shiga gida ba. Saida umma ta leko dakin tana fadin nikan yau a gidan nan zaki kwanane dare fa ya somayi sosai take fada min na zabura da sauri ina kallon lokaci a wayan na mike ina fadin yau nasan zan sha fada wurin manjo kan don nace ba zan dade ba da zan fita. Har cikin gidan mu Atika ta rakoni muka shiga dakin manjo da muka samu har ta kwanta a lokacin sai dai batayi barci ba. Tana ji mu ta daga tana fadin yaran nan ina kuka shiga haka tun safe kuka fita nace wallahi manjo ina nan gida su Atika muna kallo ne ya dauke mi hankali. Jin hayaniyar mu ne ya sanarwa umma mun dawo sai gata kofan tana fadin yau ina kuka shige haka yarnan tun safe ? Umma muna gidan su Atika kallo mukeyi ya dauke muna hankali umma ayi hakkuri don Allah tace hankalinane ya tashi rashin dawowan ku gida har wanan lokacin. Daga haka ta juya ta fita Atikama tace zata wuce sai manjo ke fadin ni yau bansan wani imani yazowa lami ba don tunda rana take neman ki gidan nan fa. Kallon juna mukayi da Atika muka bar dakin har muka kai waje ba wanda yai magana sai da muka bar gidan kadan Atika tace yanzu yaya za a yi fatima. Wanan matar fa da gaske take da nufin ta a kanki nace yaya kuwa Atika addua dai nake ko yaushe Allah ya tsare ni a duk inda na samu kaina. Mun dan jima muna hira na koma ciki na samu wai miyar kaza umma tayi ta debo min bana nan taba manjo ta aje min. Ina shigowa manjo tace wanan zuwa kan kinci da fari ga miya nan ummar ku ta kawo maki wai dazun tayi shi tace kinga ni dake gidan ko kashi bata ban ba. Nace miya kuma tace eh wai kaza aka yanka mata yau shine ta zubo maki ki daure kici kafin ki kwanta. Na bata rai duk dagabana dake faduwa da Naman nace na koshi bancin abinci da dare kuma ai na fada maki nama bai damay ni ba yanzu. Kokarin mikewa naga tanayi tare da fadin bari indan taba kada tace ba a ci tayi maki abin arziki tana kokarin jawo kwanon silver dake gabanta. Da sauri nace manjo kada kici naman na do Allah na fada ciki daure fuskana gare ta. Wani kallo tayi mun na tuhuma nace manjo barta da halinta kawai tana dauka ban san komai bane da take shiri mun. Wani abu ke nan kike nufi nace ba dai zakici naman nan ba wallahi naja kwano zuwa baki kofan mu na aje. Sai kallon mamaki manjo ke mun na share ta ina shitin kwanciya abina ba tare dana kulata ba har na gyara wuri na haye kusa da ita tana zaune tana kallona da mamaki a fuskanta. Bata iya ce mun komai ba don ba fuska a guna da zatayi min tambaya a lokacin sai da na tabbatar da manjo tayi barci baffa ma har ya shigo naji rufewa part din su na fito a cikin sanda na kai nama waje na zubar dashi can nesa na dawo gidan na kwanta. Washe gari tunda asuba saiga umma dan dakin kwanon namu ta leko tana fadin babba an tashi lafiya ya dare ? Lafiya kalau muka tashi manjo ta bata amsa da hakan tace fatima fa yar gidan babba an tashi lafiya ya gajiyan unguwan dai. Umma ina kwana nace bayan na shafa addu,a a fuskana da jikina na waigo ina gaida ita idon ta na yawo tana neman kwanon naman ta. Nace umma jiya na dawo na samu miya na gode shi naci na kwanta da guntun bread din daya rage bari in fito in wanke kwanon in kawo maki. Tace ba sai kin wanke ba indan kinci ai shike nan bukatar maje hajji sallah dama ta duka ta dauki kwanon ta fita. Kallo mamaki manjo ke mun har lokacin kafin tace A ruwa kaddai ince wanan lami din neman rayuwan ki take yi. Kusan haka nake hasashe na bata amsa koma may ye ai ya kare a kanta shiru tayi kamar tana nazari na dan wani lokaci . Wunin ranan sai ban fita ba ko girkin da nake muna sayowa na kira Atika akai muna umma ko taje ta dawo wata kila bokan nata ya fada mata wani abu zai samay ni ne ranan takewa wanan zawaron daga part din su zuwa namu tana dubawa. Sauran kwanakin daya rage mun kuma sai naga umma ta canza min fuska ba kamar lokacin da take tarkona ba. Shirin komawa na fara yi tunda akace min kwana hudu zanyi a nan don a yanzu na gaji do akwai tsoro da fargaban tarkon umma a kaina yanzu. Na bar gidan kawuna ina murna zanzo gidan mu inda yan uwana jini zasu kaunace ni sai gashi nazo naga gidan kawun nawa ma ya fiye min nan kwanciyan hankali a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:12 - 🀐🀐🀐: BISSIMILAHI RAMANIN RAHEEM HAS BUNALLAHU WA,NIMAL WAKEEL, , , , , , Da kyat na yarda zuwa wurin kumshin da kitson da Atika tace zata kaini don kada na koma hakana gida ban so ba sai dai ba yadda zanyi don ummata da ta saka baki tana fadin kinzo haka ba kumshi kice kuma haka zaki koma. An min kitso da kumshi wanda hakan ya kara haskani sosai na fito wata shar dani ranan, na koma gwanin ban sha,awa dani. Ni kaina nasan da nayi kyau matuka a gidan su Atika umma tasa aka wanke mun kaya na almarin su ya gogemun su koda muka dawo mun samu an kawo kayan wurin manjo. Sai da na dan dade gidan su Atika muna hiran ban kwana nadawo gidn lafiya na shigo gidan Amma ina shiga kaina ya dan fara min ciwon da bansan dalilin sa ba. Sai dai na dauka duk gajiyan kitsone don banson abinda zai taba min lafiyan kaina ko kadan shiyasa idan muna hutu nayi ba kwana da kitso ke nan sai mun koma school kuma. Ganin ciwon kan nason ya kaini kwance ne manjo ta fita ta sayo min magani nasha kafin ta dawo ne a dakin ina kwance kawai akaji na yanka wani uban ihu ni kadai. A cikin razana duk wanda ke gidan baffa a lokacin saida ya fito waje don karan ihun dana yaka din. Suna tsaye cirko cirko suna son gano mai nakewa ihu haka don su basu masan manjo bata gidan ba a lokacin. Wani ihun na kara karde hidan dashi da kubura saratu da mama saude suka nufo dakin da gudu don ganin abinda ke wakana da ni a cikin dakin. Ni dayace a dakin an wani murdeni a lankwsa ni kamar ruboce jikina idanuwana sun wani firfito ga baki daya a lokaci guda. Innalillahi mama saude ke fadi tare da tambayan ina tsohuwa ta fita ne ko mai ina babba ta shiga ko tana bandaki ne ? Tana tambaya a kidime hankali tashe babu mai bata amsa don duk su kubura sun dare daga kofan dakin . Ta juya zuwa bandakin manjo bata ciki haka yasa ta fita a gigice zuwa hanyan kofar gida hankali tashe sukaci karo da manjo da ta dawo dauke da leda maganin da aka hado mata chemist. Ganin mama saude a kidime yasa manjo tambayan ta ko lafiya mama saude tace babba ba lafiya tafi ce a cikin wani yanayi a daki. Wani itin rikicewa manjo tayi habkali a tashe suka shigo gidan tare kamar ba itace mai jan kafa ba na ciwo lokacin. Ga su kubura da saratu cirko cirko da sauran yaran gidan nesa da kofa manjo din dun tsaya. A ruwa, ke Aruwa lafiya ta fada dakin ganin yanayin da nake ciki yasata kara rikicewa tace ayi maza a kira mata baffana don Allah kada yar mutane ta mutu mata a daki ba a san sanadi ba. Ganin kamar baffa zai dade baizo ba tace mama saude ta kira mata umma Atika da sauri a gidan su ta tafi don hankalin kowa ya tashi gidan . Sai umma lami da bata gida itace bata san abinda akeyi ba gida tare da umma da Atika da wata bakuwa da sukayi suka shigo cikin tashin hankalin labarin da mama saude taje masu dashi din nawa. Wanan karon ina wani abu ne kamar na kutare abar bankare ni din sai kuma abin kutare nake zaka rantse da Allah wata tsohuwar kuturawa ce ni. Can kuma na juya ina wani marmar da idanuwa kamar wata yar bariki ina wani kwalliya da sauran su bakuwar tace wanan iskace gare ta haka dama ? Iska kuma yaushe ta samay shi hakan ban sani ba don dai uwarta bata fada min ba gaskiya manjo ke fadi. Matar tace kuban tsaba idan akwai mama saude tace babu tsaba agidan gaskiya sai umman Atika tace Atika tai maza ta debo gyaro a gidan su. Bata jima ba sai gata ta dawo da gyaron matar ta fara surkule tana fadin kuke ganin mu bamu ganin ku kuyi hakkuri ku tausaya wa wanan boyar Allah ta huta hakana don Allah. Abindata saka a baki ta tauna shita furza min a kai har sau uku ta juya tana fadin kunyi ajiyan komai da ruwan ka ko hantiti gidan nan ? Mama saude tace sai dai babba itace mai yawan sayen sa don kafanta manjo ba baki sai da hannu ta nuna inda yake imani ya kashe ta. Dauko mu shaka mata da yardan Allah zasu sauka daga kanta insha Allah wanan iskan baya zuwa haka babu dalili dole akwai dai wata a kasa don manyan iska ne a kanta gaskiya. Kaina ta daga ta shaka min hantitin a cikin hancina wani irin atishawa na sauke lokaci daya tana shaka min komai da ruka din a hanci na. Sau uku ina sauke atishawa mai karfi kowa ya fara fadin alhamdullahi sun sauka wai sannu fatima ikon Allah wai dama yar nan tana da wa yan nan mutanen a kantane haka ko dai yanzu ta samay su ? Umman Atika ce ke tambaya manjo da tayi mutuwan zaune bata iya bata amsa a da baki ba sai kai ta kada mata don imani ya kashe ta lokaci guda. Suka fara jera min sannu ban amsa ba sai can kuma na fashe da wani irun kuka mai cin rai da ban tausayi . Sunyi kira sunyi kira ban amsa ba sai matar tace wani ne yazo kuma nake gani basu gama takawa a kanta ba ke nan . Matar tace idan da alheri kuka zo muna maraba daku don Allah kuyi magana musan abinda kuke so ? Babu amsa har lokacin sai da ta kara fadin fatima kila sun sauka ne wani murya kamar na kato yace ba fatima bace mune . Ba fatima bace kaine wa sai na ci gaba da kukan tana ta roko maishi yayi magana sai can akace ina ina wanan baiyuyuwa. Muna kallo a cutawa jinjiran mu daga zuwa zumunci sai kuce zaku cuta mata yau akwai kaniya a gidan nan kaniya kaniya. Subbahanallahi don Allah kuyi hakkuri ku fadi may kuke so ai maku ku tafi sukace bamu tafiya don tabamu akayi mun dade akan jinjiran mu bamu cuta bamu cutarwa amma ake son halaka muna jinjiran mu. Ikon Allah manjo tace kun dade kuna tare da ita ya kada kai yana fadin duk inda take muna biye da godiyar mu mu ba masu fitina bane amma yau an taba mu an taba mu. Haka kawai sai bakina ya dauke kuma dip ba magana ko kadan sai na fara abin kuramay salati umma Atika ta saka tana fadin kurma ke nan yazo kuma ? A daidai lokacin ne bafa ya shigo a cikin tashin hankali ya samu abinda ke faruwa salati ya fara tambaya yaushe na samu wanan laluran haka ? Yau dai muka ga wanan laluran gare ta manjo ta bashi amsa sai bayani nakewa matar nan tana bada amsa don da gani ita tasan halin iska can dama. Ta juya tana masu bayani tana fadin abin da kurma ke fadin yau suna da fada a gidan nan don an daukowa jinjiran su mugun abu. Matar tana fassara masu abinda kurman ke fadi tana fassara masu abinda yake fadi din hankali tashe. Manjo tace ni hauwa,u wake bin yar marainiyar Allah nan da mugun nufi haka a rayuwan ta ? May wanan yarinyar tamai wani har ta tsune masa ido sallaman umma lami data dawo zufa zufa gidan daga unguwa ganin yamma yayi ta dawo kafin ta laga na dare ta fita. Kamar an tsikare ni na mike zubur na nufi waje ina tafiya kamar gurguwa sai wurin umma nako shake ta take diyan ta su hashim da su kubura suka hau bambarana har baffa sai dai sun kasa kwatar ta daga shakan da nayi mata din. Gida ya rude da ihu da kuruwan neman agaji da kyat da boni ta samu kanta tana hakin ceton numfashin ta. Har lokacin ba baki a gare ni sai kwatance a gareni kawai nake iya masu ina nuna ledan baka mai kauri data shigo gidan dashi a hannun ta. Nan hayaniya ya tashi wasu na fadin tunda na dage ina nuna ledan dole akwai abinda ke cikin ledan ke nan ga umma duk shakan data sha taki sake ledan hannun nata. Sai da kyat aka kwaci ledan tana wiki wiki da idanuwanta tare da fadin sheri zaki mun daga dswowana ban san hawa ban san sauka ba ki kulla min sheri ? Sai da naga ana bude ledan na kuta sai gani kasa suuuu na fadi a cikin kasa kwalliyan da nayi duk ya baci wurin turmuzan dana sha. Da sauri du umman Atika sukayo kaina hankali tashe yayin da baffa da manjo suka tsare ledan da ake budewa da kallon babu komai ciki sai wani abu da aka soke da allura da sauran tarkace itin na surukulle. Fatima fatima umman su Atika ke kiran sunana na amsa a wahalce kin ganeni umma tace na gyada mata kai to wacece ni na sake kallon ta nace ummace tace sannu. Na amsa mata suna fadin sun sauka sai sukaji na fashe da wani ihun kuma na tashin hankali nan kuma akayo kaina cikin tashin hankali. Kamar bebiya nake fadin ba zamu yarda ba sai mun dauki famsa kan macutan godiyan mu kuyi hakkuri tunda kun baiyana komai don Allah ku sauka haka ku bar godiyan ku ta huta. Ranan dai na sha wahala sosai kafin su sauka nayi barci sosai ban falkaba sai dare mutanen unguwa dama gari sun ji labarin komai daya faru gashi washe gari zan koma idan Allah ya kaimu. Washe gari haka na tashi jikina ko ina yayi min tsami babu dadi ga kayana ko karasa shiryasu ban yi ba. Ban iya tashi inyi komai sai manjo ne da Atika suke dan hada mun kayan ina kwance har suka karasa baffa bai fita ba don hankalin shi bai kwanta ba. Ya shigo dakin ganin shi na yunkura zan tashi yace kwanta abinki gurin babba nazo muyi magana jin haka sai Atika tayi saurin ficewa a dakin. Daga kofa ya samu wuri ya tsugunna ya sake duban inda nake yana fadin Fatima yaya jikin naki nace da sauki baffa yace zaki ko iya tafiya yau din kamar yadda sukace za a zo a daukeki ? Zata iya idan ma ba zata iyaba sai mu tafi tare mu ratse mu dauki Adda mu kaita gida muyi masu bayani don ba zamu saketa haka a cikin wanan yanayin ta tafi ita kadai ba. Ganin Atika ta fita dakin na mike da kyat nabi bayan ta a waje na samay ta zaune na zauna a gurin muna dan hira. Baffa yace Nima hakan na gani babba tunda dama ga wanan zancen da bamu san ya ake ciki ba ranan jumma,a nima zan shigo kamar yadda nayi masu alkawari zamu zo din nidasu sha,ibu da sauran yan uwa. Ina ga in zai yuyu da sai ku tafi koda lami ne ko kukai ku uku ke nan kunga a nata bangaren dai anga yan uwa aiko . Da naso bayan tafiyan tunda yabar kudin motar zuwan ku din a dauki mota wasu mata suje ranan. Yanzu ma wanan abin zai faru ga wanan al,amarin dayazowa yarinyar nan haka kuma zai yuyu mana wanan ba lalura bane babba taba su akayi shiyasa suka tashi da waya santa dashi. Amma dai kuma sai naga idan kun bita da yawa kamar zaku bata masu shirin su don ba hakan aka tsara ba da farko. Amma dai sai yadda kika gani babba tace maganan ka gaskiya ne kawai mu barta ta tafi din Allah zai kare a duk inda take ai manjo tace. Karshe dai suka aje shawaran abinda zaifi zuwa rana ko sai ga driver yazo har lokacin bamuyi arba da umma lami ba . Dana shirya zan tafi na shigo har part din su na sallamay su da kyat ta leko mukai sallama ta koma. Na samu rakiyan yan uguwa da sauran mutane haka motar ya daga raina babu dadi na rabuwa da yan uwa da nayi ko kadan. Bamu shiga kano ba sai gab da za a fara magariba ina takure a bayan mota ni kadai daga misau zuwa kano ina fada da zazzabi mai karfi a jikina. Haka muka iso gida babu kowa waje har ya shiga min da kayana part din mu mamu na zaune a falo cikin damuwan rashin isowan mu taga na shigo. Sai dai yanayi na bata babu lafiya don yadda na shigo falin ina gaida ita cikin makyarkyata na samu dogon kujera na haye na dunkule a wuri daya. Ikon Allah ba lafiya ne kuma a hanya zazzabi ya kamaki ko tun can ne ban iya magana ba tace bari zo sai wayan ta yai kara tana dauka naji tana fadin sun iso yanzu sai dai gata tadowa ba lafiya kuma. Nasan da kawu take wayan yana tambaya ko mun dawo a lokacin shine ta fada mai mun dawo din. Sai bayan an sallamay sallah kawu ya shigo part din kai tsaye yana fadin fatima ba lafiya kuma kika biyo hanya hakana ai da sun barki har kiji sauki. Mamu tace ina ganin dai a hanya ta kamu da masasaran kila don ba zasu barta ta taso haka ba ki shirya zan turo wani ku tafi asibiti. Da sauri na dago kai nace kawu a bani magani kawai naji sauki murmushi yayi mamu tace kasanta da tsoron asibiti ruwan ki aike ke wahala a jikin ki ba wani ba. Bamu dai je asibitin ba tasamun ruwa masu zafi nayi wanka asha tea mai zafi da magani sai na kwanta. Koda su Amma suka shigo dubana duk nayi barci mai nauyi a lokacin ban san shigowan su dakin ba ma. Washegari na tashi jikin nawa da dama ya rage min ciwon da nake ji ina son fadawa mamu abinda ya samay ni ina jin tsoron fadamata. Don ban san halin da zata shiga ba idan taji yasa na kyale na bar maganan a cikina ban fadawa ko Amma da take abokiyar hirana ba. Na dan daure naje part di Amma don na rage yawan tunanen da nakeyi din a raina muna falon duk dasu Aisha sai hira sukeyi ban saka baki na. Ga hiran su Aisha tace lalai wata tana kewan gida dan murmushi nayi ban kullata ba sai murja tace wai baki san yadda muka matsu kidawo bane halan . Yi nayi kamar ban jita ba saida ta dan zungure ni Amma tace kyaleta ai tana jinki tunda ta dawo take da wanan miskilancin haka ko kuma ciwon ne ya sakata haka oho ? Kamar daga sama naga mutum yayi sallama falon Amma din ya shigo duk sai na tsargu don ban san da zuwan shi ba sai ganin sa nayi yanzu ya shigo. Gaishe mukeyi kamar bai son amsawa ya dan tsaya hakan yasa muka mike don barin falin mu barshi da Amma. Hanyar fita na nufa Amma tace tafiya zakiyi kuma bayan baki dade da shigowa ba nace a shagwabe Amma zanje in kwanta ne kaina naji ya fara min ciwo yanzu na juya na suce ba tare dana jira inji abinda zatace ba. Kasan gida akwai dadi tun jiya data dawo mun rasa gane kanta a gidan nan har yanzu yi yayi kamar bai jita ba tace sadauki anya kuwa zaka iya rike wanan Amanan kuwa ? Ya dago kai yace Amma kina magana ne tayi mai dakuwa da hannu tana fadin miskilin banza ai kunyi daidai da ita don yanzu tagamauna miskilanci wuri nan Kuyi hakkuri wallahi duk kwanakin nan banajin dadin jikinane ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:12 - 🀐🀐🀐: DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI GODIYA DA YABO YA TABBATA GA ALLAH SARKIN BAIWA DA RAHAMAN SA UBANGIJI MUNA ROKON KA KA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN GOMAN JUL, HAJJIN AMIN πŸ‘ Kawu ne zaune a falon shi tare da yaran shi a daren jumma,a kallo daya zakaiwa kowansu kagane halin tashin hankalin da suke ciki lokacin. Kowa yakasa magana baya sj fahinci dalili kiran da mahaifin nasu yayi masu sai zufa ke ketowa ko wani su a lokacin . Umar ne yayi karfin halin yin magana a cikin su yace to daddy don wanan ai kowan mu yasan da zancen nan cikin mu. Dama ka fada muna tun can a waya da sai a turowa mama da kudi ayi duk wani abinda ya kamata ayi . Cikin farin ciki kawu ya kalli dan nasa yace Allah yayi maku albarka dama nasan ba zaku taba kinyatani a duniya ba . Gaban habbib ya yafadi dake shirin fadln daddy nifa ban shirya ba sai yaji umar ya ari baki su yaba mahaifin su aamsa da fadin sun amince yana saka masu albarka da godiya tare da yaba masu. Idan ranshi yayi dubu ya baci a lokacin hakan yasa ya kasa daurewa a ranshi ya dago fuskan shi daya gama nuna tashin hankali a ciki yana masu wani irin kallo. Kawu yace yaya habbibu ko baka shirya hakan bane kai a wurin ka yace cikin sunkuyar da kai a,a daddy gani nayi dai baka sanar damu zancen da wuri ba sai yanzu muke ji. Alh yace na isar maku ne yasa hakan sanan kuma daura aure a yanzu ba yana nufin tarewan su bane ranan sai nan da zuwa satin sama mai zuwa kaga zuwa lokacin aika gama wani shirin da duk zakayi. Umar da takaici ya gama cikawa babu halin nunawa yace sai dai daddy ina ga ni ba zan kai wanan lokacin ba a kasan nan don ina da aikin da zamuyi a hong kong idan na koma. Alh yace ai shike nan tunda an daura aure zaka iya tafiya da matar ka dama shine wajibin aure ai wanan ba wani matsala bane mai girma. Takaici da badaman fadin haka ya rufe mai zuciya yace a fili shike nan daddy yadda kace haka za ayi. Sai Alh yace saidai ina kara rokon wani alfarma a gurin ku don Allah don gujewa rigimar uwar ku kan hakan ina son ku rufe wanan maganan don Allah ba dan niba sai an daura zataji idan zai yuyu. Kowan su tunane yake a ranshi ta yaya zasu iya boyewa mahaifiyar su wanan maganan mai muhinmanci a garesu haka duk da sun san idan taji ma daga bayan ba,a hutaba. Sun dan gama tataunawan yace zasu iya tafiya Allah ya kaimu gobe bayan ya mika masu kaya a cikin ledoji dinkaku da zasu saka a ranan. Haka suka mike suka fice daga falon jikin kowan su babu karfi sai tarin bakin ciki da takaicin dake cin ransu lokacin. Har sun nufi hanyar part din mahaifiyar su umar ya dakatar dasu yana fadin ina son ku sani yiwa mahaifin mu biyayya ya zama wajibi a gare mu . Mudin muna son haske a rayuwan mu ya kamata kowan mu yabi umurnin mahaifin namu don mu gama lafiya dashi kamar yadda yake so har ya nuna muna jin dadin shi a fili haka kan yardan namu. Don haka zuwa gurin mama a wanan lokacin yana nufin rushe farin cikin mahaifin mu ne don babu yadda za yi mu shiga wurin mama yanzu bata fahinci komai ba gare mu. Don haka ina shawartan ku da ku daure mu kyale mama har sai komai ya kammala kamar yadda daddy ke so damu daga baya koma may zai faru sai ya faru mundai nuna ma daddy mu masu biyayya ne a gare shi . Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke da tun fara maganan ya kasa furta komai sai lokacin yace nima hakan nake gani don ba komai yasa zan hakkura da hakan da daddy ke so sai do goben mu don muma zamu so diyan mu suyi muna biyayya a gare mu wata rana don tarihi yakan maimaita kanshi akan mutum. Kayi tunane Aliyu abinda na dade ina faman tunane ke nan a raina yasa nake nuna yarda na, babu gardama ga mahaifin mu don mu rabu lafiya dashi. Ya dafa kafadan habbib dake cika yana batsewa tsaye gefe daya hannayen shi daye cikin aljihun wandan shi yace be cool bros komai zai zama sauki da yardan Allah. Kai kawai habbib ya iya kada mai ya juya zuwa hanyar fita gidan hankali a tashe daga haka sukai sallama kowan su ya bar gidan. Hjy jummai ta aje masu abinci tana jiran shigowan su har goma na dare bataga shigowan su ba yasa ta kira layin Aliyu don shi keda saukin samu a cikin su sai dai waysn tasa a kashe take haka yasa ta gwada na habbib shima hakan. Tayi tunanen kiran umar sai dai tasan tunda yakai wanan lokacin bai shigo ba tasan ba zai shigo din bane don baikai karfe tara ma a gidan shi. Haka taita gwada layukan nasu baya shiga dole ta hakkura da rashin samun su din ta kwata da tunanen ina suka shiga haka basu fada mata ba don tasan komai under control din ta sukeyin shi. Ba zasu iya yin wani abu kai tsaye ba indan suna garin kai koma basu garin hakan kamar ya zamo masu jiki sai sun sanar da ita dan dama umar da ya fara girma ya fara yarda wanan akidar tasu na yan dakin nata. Don haka ne wanan damuwan nata a ranan yai yawa rashin jin yaran nata ko washe gari haka ta aje abinci ba wanda ya shigo daga cikin su dan dama Aliyu ya dan leko a gurguje daukan abu salma ta ganshi yace tace yana zuwa suna wani aiki ne yasa bai samu lokacin shigowa ba. Taje ta fadawa uwar tasu kafin ta fito ya fita yabar gidan bata samu ganin shi ba ya wuce ko da saurin shi. Karfe biyu daidai A massalacin dake unguwan an tashi daga sallah jumma,a aka sanar da daurin auren wanda ranan mafi yawan bakine suka halarci masalacin daga cikin su harda su baffa da sukazo daga misau a ciki da sauran abokan daddy da suka samu labari a kuraren lokaci. Wanda hakan yaba mutane mamaki da dama hjy jummai da bata san abinda akeyi ba tana can tana sheka barcin ta a dakin ta ta saka wayan ta a silent don tana son ta huta haka yasa kira da yawa na masu son cinta tara yai ta shigo mata bata sani ba. Hjy maryam data tsuncin labarin daga sama shiganta uku wurinta tana samun tana barci ga tsegumin haka yana cinta dole ta hakkura har ta tashi taji kwam. Sai bayan anci an sude kanen ta da suka zo a fusace don jin yaya harkan ya faru basu da labari su bayan ko jiya da yamma suna tare da ita bata fada masu ba. Ta daiyi masu korafin ya kira yara ba tare da ya sanar da ita zasu zo ba bata kuma san dalilinn shi nayin hakan ba ya kyale yaran a cikin damuwa . Cikin barci taji bugun kofa a tashin hankali ta farka a razane tana kallon kofan tare da fadin wai waye ne don Allah ke damuna. Turo kofan sukayi suka shigo kallon yanayin fuskan su kawai ya nuna ba lafiya ba a rude take tambayan su lafiya ta gansu haka hankali tashe ? Kallon juna sukayi tare da samun wuri suka zauna ba wanda ya iya magana a cikin su kara tambaya ta maimaita masu may ke faruwane wai na ganku haka kamar a rude ? Anty Alh yayi maki bayani ko a rikice tace wani Alh bayani akan mau kuma don Allah ku fada min abinda ke faruwa kun barni a duhu ? Kara kallon juna sukayi sai babba daga cikin su tace bai maki bayanin kan auren yaran nan da aka daura yau ba bayan sallah jumma,a harda na salma aciki ? A rude take fadi tana nuna kanta tana fadin yarana harda salma wace salma wai kuke magana ne ? Salma dai nake dasu babawo yau an daura masu aure yanzun nan ma har gida ya fara cika da jamma,a. Ta sake nuna kanta tana fadin ni ni Amina ni din nan Alh zaiwa sheri a idon, , , bata iya karasawa ba sai ta tafisu ta fadi a sumay. Ihu suka saka suna kiran sunan ta ina bataji tayi suman gaskiya a lokacin don bata san wanda ke kanta ba. Hjy maryam dake jiran taji kwam sai ganin yan uwanta tayi maza suna shigowa wurin ta da kwandunan goro da minti dasu chewing gun. Tana kallon su da mamaki ta karaso falon tana fadin yaya kune tafe ashe ai wanan kwandunan ba a nan za a kawo suba don na yan shiyan hajiyace kayan . Yayan su babba yace wanan na nan shiyan ne don kayan daurin auren ikilima ne da sadakinta yanzu aka bamu don karramawa mu shigo maki dasu nan. Ikilima kuma yaya ta tambaya da sauri cikin tsure su da ido tana kallon su eh yanzu aka daura masu aure harda ita ciki ai. Yau da safen nan yaje ya fada muna muma haka mukaji zancen daga sama wallahi shiyasa bamu tsaya neman ki ba don ba lokaci kamar yadda yai muna bayani din. Ni ni Alh zaiwa haka ya tozartani a idon duniya maina aje yanzu na auren ikilima har nawa ikilima take ne wai da zai daura mata aure ban sani ba. Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi a lokaci guda suka shiga bata hakkuri a wurin. Sallah na idar naji ina bukatan kwanciya a kasan don yanayin jikina dake min ciwo a lokacin yasa na dan kwanta in huta. Na soma barci naji murya kamar na baffa na suna gaisawa da mamu zubur na mike zaune ina kokarin tashi naji mamu na fadin yaya ashe kun iso ko ? Yace eh maimuna mun shigo makare yasa muka wuce wurin daura auren baki daya don mota ya dan bamu matsala a hanya ne . An daura yanzu alhamdullahi Alh yayi kokari har yara goma maza biyar mata biyar sai addua ake masa a gurin taron. Tsaye nake na kasa karasowa gurin don jin maganan da sukeyi sai dai gaba ya fara faduwa ganin har da baban Atika a cikin falon da sauran fuskokin da ban iya shedawa a lokacin. Baffa yana fadin banda abinda zancewa Alh sai godiya don har surukin namu an kirashi mun gaisa yanzu yaron kirki kamili mai mutunci baban su Atika ke fadi. Huce na ke wanda ban san daga in yake zo min ba kafin na fara kuka in kai kasa a wurin jin faduwa na ya jawo hankalin su a inda nake suna fadin subahanallahi ku kamata. Da sauri mamu ta isa gurin da mama suwaiba da ban san zuwan ta gidan ba suna fadin yaya haka kuma wani irin mika nayi na sake ihu mai karfi daya gigita kowa a falon take gurin ya rude. Baffa yace subbahanallahi wanan matsalan ya taso ke nan na yatinyar nan wai dama haka abubuwan nan suke damun fatima ne yanzu ? Wasu abubuwa kuma yaya mamu data gigice take tambaya tare da fadin bata da matsalan komai dama yau dai ne na fara ganin haka a gare ta ai. Wanan matsalan ko a misau ya taso mata haka akasha fama da ita ranan har dare ana abu daya da yarinyar nan a gurin. Mamu tace tau walllahi bata taba yin haka a nan ba gaskiya tunda tazo garin nan sai yau din nan na fara ganin haka gare ta. Murde ni ake ana wani irin lankwasa ni da juyani guri daya sai mai kallona ya dauka bazan iya more jikina ba kuma a rayuna. Fita tayi da sauri zuwa part din Amma suna zazaune ana mayarda yadda abubuwa suka tafi kamar yadda kawu da yan uwan shi suka tsara komai sai ganin mamu hankali tashe sukayi tana fadin gwaggo kizo ki duba sayadi halin da take ciki. Gaba daya su mama hadiye suka mike suna tambaya ta kasa fada masu komai don hankalin ta dake tashe a lokacin. Suna shiga falon mamu kowa ya tsaya da mamakin yana kallon ikon Allah abinda ke faruwa a falon lokacin salati Amma ta fara tana tafa hannayen ta a cikkn mamaki tana fadin. Yar nan dama tana tare da mutantanin nan ne haka ba a sani ba sai yau ranan auren ta suka taka haka a kanta ? Kowa na tsaye yana kallon ikon Allah shigowan kawu sani ya ce kawu balarabe ya kai su baffa masauki suci abinci kafin su juya. Waya ya dauko yayi kiran wani layi baifi mintina ba wani mutum ya shigo saye da jallabiya fara a jikin shi . Tunda ya tun karo inda nake wa yan nan abubuwan ya kura min ido har lokacin daya tsugunna daidai inda nake din kwance yace assalamu alaikum idan musulmine su amsa min muyi magana. Sai shiru ba magana kusan biyu suka zagayo suna nasu sallon sai can akaiwa malam din sallama kamar ba muryana ba. Ya amsa tare da fadin may ke tafe daku mai zaisa kuzo mata yau ranan farin ciki a gare ta kuma zumunci ya kawo yaran mu wurin ta don su nuna mata farin ciki. Yace amma ai ba haka ya kamata ku nuna farin cikin ku ba gare ta ko yace kasan yaran zamani ba jin magana sukeyi ba sai dai nima nazo ne don in fadakar daku akan wanan baiwar Allah. Tana tare da makiya a ko ina mun dade a tare da ita bama yarda wani ya cutawa rayuwan ta da can munsata rashin ji sosai da wasu abubuwa na yarinta. Sai dai yanzu zan fada maku duk lokacin da kuka ganmu ku sani wani abin cutarwa ne yake harinta zamu taka duk wanda ya nufeta da sheri komai kankantan shi. Dan murmushi malamin yayi yace Allah ne kadai ya isa ya kare bawan shi ga komai sai yayi dariyan manya tare da fadin ka manta Allah na sanadin sa ta ko ina a cikin wanan sanadin muna daga ckin kaddaran ta . To idan ku musulmine don Allah ku bar boyar Allah nan ta zauna lafiya kunga yanzu tana gap da shiga sabon rayuwa ne . Ya tare malam da fadin saboda hakan ne muke yawan biyanta wanan lokacin domin sihirin da ake kokarin aikowa gare ta . Da kyat dai bayan sun gama kwasa da malam tare da jin abubuwa daga bakin su suka fita kaina tun lokacin na kwanta wani barci mai nauyi ban kara sanin inda kaina yake ba saida Amma har mamu suna kaina ranan. Zan iya cewa ranan mama hadiye da yaranta ne suka kwana cikin farin ciki a gidan bayan su ko wani part a ciki tashin hankali suke. Part din hjy jummai ke asibiti da ita inda yaranta gaba dayan su suna asibitin sun zagaye ta cikin tashin hankali fuskan kowan su babu walwala a cikin sa ranan. Sai shaga da fice suke a dakin zuwa office din likita uwa ke nan mai yafi uwa dadi a duniya. Alh sani ma da yan uwan shi da farko sun dauki abin kamar wasa sai da sukaje suka iske halin da take ciki ne suka gaskanta girman maganan nata. Zagi da diban albarka ga auren an shashi ga bakin yan uwan hjy jummai ranan duk wanda yazo da irin abinda ake fada saida wani baba a gare su da kawun su suka tsawata masu aka koma yi a boye. Kawun yace may kuke nufi da zagin bawan Allah nan da kukeyi dashi da yayan shi zaku hanashi yin iko da abinsa ne ? Wani irin mulki da nuna isa ne jummai batayi a gidan Alh sani ba har mutane na ganin ta koma miji shi ya koma mata sai yau da yafito ya nunawa duniya ya isa da gidan sa yanzu shine zaku zageshi. A lokacin da yar uwarku take nata mulkin da nuna isa may yasa baku zage ta ba sai shi dayayi abinsa bisa kan ka,ida zaku saka shi gaba da zagi haka ? May ye laifin Alh sani cikin yiwa yaran sa gata dayayi wanda ku duk nan baku sanda hakan ba sai gaba. Ya fiku hange da tunanen nesa don yasan abinda yakeyi lokacin da dan ku ya dauko maku maidan buje may ye nan baku fada ba ga hakan ? Sai yanzu da yake son nunawa duniya shidin mutum ne wanda ya isa da iyalin shi kuke kokarin hurewa yar uwan ku kunne ? Shiru sukayi har su Aliyun su uku dake tsaye daga gefen gadon suna jin batacin da sukewa mahaifin su da sunan son yar uwarsu gare su. Ya juya wurin su Aliyu yana fadin kunyi daidai don ku ba mata bane ubangiji Allah yai maku albarka ya kawo haske ga lamarin ku yaba abinda zaku kula da iyalan ku ta hanyar halal ya baku zuria dayyaba masu albarka. Idon ko wanin su yayi ja don tashin hankali da fitina tsohon yace kunyi daidai kun nunawa duniya iyayye suna gaba da komai wayewan ido ba shine sanin duniya ba bin iyayye shine alheri. Sannan ku idan kun san ba zaku taushe yar uwarku ba na rokeku Allah ku bar kysantan ta a wanan halin sai idan komai ya lafa. Yana mai hade hannaye shi guri daya yake wanan maganan tare da bin kowa dake dakin da ido cikin bacin rai da kunan zuciya. Ban garen hjy maryam ma yan uwa sai da suka taru suka taushe ta da kyat aka ciwo kanta ta hakkura tabar kukan da takeyi. Ikilima ma kusan halin da nake ciki itama ta kwana ranan don su ko mijin ma ba wanda ya sani don koda suka tambaya akace masu sunan mijin dai nata Abubakar . Ba wanda yasan wani Abubakar ne don Alh baya cikin hankalin shi ranan ba wanda yaga fuskan shi balle a zauna maganan. A ranan su baffa suka koma bayan sun kara ganawa da Alh ya sanar dasu ba zamu kai lokacin daya diba na shagalin bukin da mata zasuyi ba don mijina yace yana da aikin yi can zai koma da wuri. Don haka masu zuwa zasu iya zuwa gobe ko jibi za ai yinin bukin gaba daya a huta tunda komai da za a tanada dama an gama shiryawa. Da wanan bayanin suka koma gida bayan ya kara bin su da alherin dayace angone da kansa yace a basu su kara namai a motar su. Kowansu ya koma misau ciki da farin ciki da al,ajabin karamcin irin na Alh sani a zukatan su har suka kai suna hiran irin hayan wanan mutumin. Mamu da su mama hadiye sunje asibiti duba hjy a cikin daren ta barmu da Amma dake zaune damu a part din yayin da ni ban san inda kaina yake ba saboda narcin da nakeyi. Ba wani tarbon arzikin da suka samu don yan uwan hjy ne maza da mata tab a dakin gaida ita sukayi inda bayan hakan ba wanda ya kara bi ta kansu kuma. Sun dan tsaya sukayi masu Allah ya sauwaka suka fito daga dakin a haraban asubiti suka hadu da yaran sun fito sallah isha,i suka tsaya suna masu yaya jiki. Sukan sun amsa masu a cikin kulawa da nuna su nasune tare da tambayan ya akaji da taron jamma, a kuma dan dama habbib wanda tunda ya gaisa dasu ya koma daga baya kadan ya tsaya yana dakilan wayan shi. A hankali kamar baya sauraren su har suka gama gaisawa suka tafi Aliyu ne ya fara magana gaskiya maimunan nan tafi mun hjy maryam mamace dai kawai bata son a fada. Diba yanzu duk irin halin da ake ciki saida matar nan ta tako kafanta asibitin nan kai ma da ganin ta kasa akwai damuwa a tare da ita wallahi. Humm ka manta mutumiyar mama ne sosai har dinki mama take muna tare da muna yara takance batayiwa bros kaya ba tare da hussainar shi ba. Sai lokacin ya dan saki murmushi a gefen fuskan shi yana fadin daddy da mama sun raba wanan tagwaicin yanzu maimuna sarakuwanace can you imagine wai yau nine da auren yar maimuna ta cikin ta fa ? Wata kanwar hjy ce ta katse masu dan hiran rahan da sukeyi ta fito tana fadin wai a kawowa hjy ruwa masu zafi daga gida yanzu. Likita yace idan ruwan hannunta sun kare ta dan watsa ruwa ko jiki zai kara sake mata dan haka ne su Aliyu da habbib suka nufi hanyar gidan a wurin packing din motocine suka samu su mamu da motar mama hadiye yaki tashi suna fama da ita dole suka tsaya suka duba masu motar kusan a tare suka iso gidan. Sai a lokacin suka tuna da babu kowa a part din sai kuma suka rasa yadda zasuyi dole gurin mamu suka nufa ta samasu shi da sauri tare da bada babban ktele din ta akai don bukata haka suka wuce suna zancen a mota. Koda suka dawo sun samu hjy a zaune ana jiran dawowan su suna zuwa aka juye mata ta watsa sai data fito ne tana zaune ana zancen dora wani ruwan zafin ta kyala idon ta ga kytele din mamu tayi saurin gane shi don sunyi sababin don may aka sayo mata shi lokacin haihuwan twis da tayi a asibiti tace don may Alh zai saiwa maimuna electric ita kadai a lokacin. Sai ga shi yanzu ktelee din yai mata rana itama bata damu da halin da take ciki ba ta lailayo ashar tana fadi ubanwa ya kawo wanan electric din nan, nan ? Wani electric kike magana wanan ai su Aliyu suka zo dashi da aka bukaci ruwan zafi fada take sosai kannen ta suna bata hakkuri a daidai lokacin suka shigo dakin tako hausu da sababi tana fadin don may suka dauko mata kayan makiyiyar ta. Tsayawa sukayi suna kallon ta da mamaki don basu san aka abinda takewa fadan ba haka sai daga baya suka fahinci abinda takewa fadan . Bayani sukai mata tace da ba kowa a gidan ba sai kuje wani gun ba ku karbo min Ammani ko kayan maryam ba zanyi amfani dashi ba balle na maimuna. Haba mama matan nan fa har rawan jiki take da sauri ta sa ruwa na don a kawo maki kuma har asibitin nan take wurin gaida ke. A zabure tace makira algunguma tazo ganin halin da nake ciki ko don ta gani ko na kusa mutuwa ko yaya ance mata na fadi kasa warwas shine ta kwaso kafa tazo gani. Aiko do wanan yarinyar bazan mutu yanzu ba don kawai inga bayan ta gobe dole ne babawo ya sake mata shegiyar yarta don duk bala,in da za ayi dole ne auren salma dana babawo ya mutu a goben nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:12 - 🀐🀐🀐: YAHHAYU YA KAIYUMU BI RAHAMATILLAHI YA ASTAGIS Dakin yai shiru ana sauraren ta kafin ta dago kai tace dawani sakaran mara hankali ya samu yaba salma shi don sai mara hankali zaiyarda da aure yata ba tare da sanina ba wanan wani dan iskan nemawai ? Kowa ya kasa fada mata sai habbib ne yaja dogon numfashi kafin yace ba wani bane fa mama Ahmad ne yaron daddy. Tayi saurin fadin wa iye tare da sakin wani uwar ashar kafin tace Ahmad, Ahmad dai almajirin mu kowa ? Yace almajiri kuma mama Ahmad ai ya wuce a kirasa almajiri kuma yanzu. Mikewa tayi tsaye lokaci daya tana fadin yanzu na gane kuskurena na auren Alh don wallahi Alh ya nuna baya kaunana ko kadan. Amma zai gane kuren shi nayin hakan gare ni na fahinci nema yake ya tozartani a idon duniya kai yama gama tozartani din yanzu. Saidai wallahi yayi karya don wanan auren basu dauro ba kamar an warware shi angama a wurina. Haba mama ki kwantar da hankalin ki don Allah har ki samu lafiya mu yanzu lafiyan ki shine a gaban mu umar da tun shigowa shi kamar baya dakin yai magana cikin zafin rai ga mahaifiyar tasu a laron farko tunda ta tashi tana haukanta yana zaune yana dakilan wayan shi. Cikin wani tsawa tace rufa min baki don na fuskanci baka son laifin mahaifin ku a fakaice idan ayi magana ka wani nuna damuwanka a kanshi duk zaku gane kuren ku na yarda da wanan bakin hadin da kuka bari akai maku. Zaiyi magana habbib ya daga mai hannu tare da fadin bros mu tafi idan yin biyayyan data koya muna muyiwa mahaifin mu ya zama laifi a gare mu yanzu. Yana fadin haka ya juya yabar dakin cikin zafin rai Aliyu bai tsayaba ya mara masa baya umar suka bari zaune ranshi inyai dubu ranan duk a bace suke mai. Katashi kabi su kaima don banga abinda kake muna a nan ba tunda bakin ku daya da mahaifin ku na sani. Umar ya sake dago kai ya dan kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya mike ya kalli yan uwanta dake tsaye cirko cirko suna kallon yace mama zan tafi sai da safen ku ya juya wuri ta yace Allah ya baki lafiya mama daga haka ya fice dakin shima. Yana fita ta fashe da wani irin kuka Asma,u ta kalleta tace haba yaya bai kamata ki fito masu ta wanan hanyan ba gaskiya. Ki tuna yaran nan suna maki matukar biyayya duk inda kika dorasu basu ketare wurin yanzu suwa mahaifin su bore a fili kike so may ye laifin yaran nan cikin maganan nan don Allah ? Asma,u barni naji da abinda ke damuna Alh rayuwata yake nema tace koma dai may ye anty munsan irin halinda kike ciki don dukkan mu nan muna jin zafi amma yaran nan yadda kikai masu ne bai dace ba. Tun dafa aka kawo ki nan bansa wanin su yasha ko ruwa da dadi ba yaya kike son suyi da ransu bafa don Allah ya dora mu akansu yace muyi masu yadda mukaga dama da rayuwan su ba. Sai ki bisu a sannu tunda suma baki san kudiri su ba gagawa fa motar shedan ne anty. Ta jefawa Asmau wani harara tare da fadin ke kika damu da hakan yanzu ban tausayin su tunda da sukazo nuna min sukayi basu san komai ba ai. Asmau na jin hakan ta mike tana kallon agogon wayan ta tana fadin dare yayi anty mu zamu gida saidai da safe mu sake shigowa Allah ya baki lafiya. Babu wanda ya tankata cikin su uku dake dakin ta mike ta fita abinta tana fita dayan tace ita asamau dama haka take a kan yara bata son ran daya baci. Mikewa hjy jummai tayi tana fadin ni yanzu zaman may nake a nan yashe ga aiki nan ja a gabana ai banga zaman asibiti ba tunda naji sauki. Ki dai bari zuwa safe sai a kara ganin yadda bp din naki yake kinga sai a neme sallama wirin likita zaifi. Da kyat ta yarda da shawaran su sai zuwa safe zataga likita ya sallamay ta takoma gida da safe tunkan likita ya bata sallama ta salami kanta tana idar da sallah din. Ita ta buga gida maigadi maigadi da bai dade da dawowa daga masalci ba ya bude masu kofa ta shigo da jidalin ta tana fadin. Ina munafukan banza da wofin gidan nan ban mutu ba na taso do a hada baki aga bayana maiganin bayana sai Allah. Yanzun za,a fara wasan tsakanina daku tunda haka kuke so duk wani tsohon banzan gidan nan da baiba da shawaran alheri na daina shayin maishi daga yau din nan. Jin hakan da mama hadiye tayi yasa ta bude kofan part din su ta fito tana fadin tsofin banza na gwale kin barsu Amina . Indai wanan ne ba a son ki ba a son ki din Amma dake zaune a kaina tun kare sallah na tana ban baki taji muryan mama hadiye tafito tace. Hadiya idan nina haife ki ban yafe ki kara tankawa duk haukan da jummai zatayi a gidan nan ba. Haka yasa mama hadiye komawa badon taso ba don ta shirya su cashe juna ranan da hjyn a gidan. Kawu da bai dade dawowa daga masalaci ba yana dakin shi sama sallaya yana karatu yaji wanan hayaniyar nata zai fito ne yaji abinda Amma tacewa mama hadiye haka yasa ya koma bai fito ba. Nan aka barta tana ta zage zage ita da yan uwanta a tsakar gida ba wanda ma ya bude part din shi ya kula da abinda takeyi kowa nasa ya ishe shi a gidan. Ta kare da fadin duk uban daya daura aure diyan ta shi zai koma ya warware shi don ba wanda ya haifa mata diyan balle yai masu auren dole don an raina ta. Alh dake daki ranshi ya gama baci yana son fitowa kalamin mahaifiyar shi ya hana ya fito sai mamakin irin kalamin da take sake mai shida yan uwanshi harda mahaifiyar su. Hakana ya daure ya kyale ta saida ta shiga part din ta ita da yan uwanta ya tashi yai wanka ya shirya ya fara shiga wurin hjy maryam dake tare da yaran ta da wasu tsofi gudu biyu yan uwanta da suka kwana suna tausanta. Sun gaisa dashi a ciki mutunci inda hjy maryam dataci kuka har ta gode tana zaune a kasan kafet ta dukar da kai. Zai fita yace babba gobe idan Allah ya kaimu ne yaran nan zasu tare a dakunan nasu da naso sai satin sama ayi buki amma yanzu saboda wasu dalili an fasa haka gobe ne tarewan nasu. Wani kuka hjy maryam ta sake maicin rai tana fadin ita bata aje komai ba bataba wani ajiya ba zai sa mata buki bata shirya yinsa ba. Ya kalleta yai murmushi tare da fadin ina dai nine mahaifin wanan yaran ni kuma nasa bukina to ku barni da dabarana ku gani. Tsohuwa guda tace Alh mu damuwan mu shine yarinyar nan tace bata san wanda aka daura ma yar nan aure dashi ba shine damuwan nata. Yace babba wanan ba matsala bane don ni nasan wanda na zabawa diyana da kaina kuma haka tsarina yake idan an kaita zaku sanshi ai. Allah ya kyauta matar tace yace amin ya fice abinshi ya barsu ta sake barkewa da wani kuka daga ita har ikilima din. Part din mamu ya shiga ya samaysu falo zaune tare da Amma ya dan sake fuska saidai hakan bai boye mashi damuwan dake tare dashi ba har lokacin. Kasa ya zube yana gaida mahaifiyar tasa ta amsa itama cikin yanayin damuwa a tare da ita take tambayan shi yaya gajiyan jamma,a yace Alhamdullahi. Ya dago yana fadin hajiya gobe in Allah ya kaimu yaran nan zasu tare a dakunan su don na gama shirin komai saboda umar yace yana son zaikoma nan da jibi bakin aikinsa. Haka yasa na mayar da tarewan nasu gobe idan Allah ya kaimu don haka nake son idan da wani shiri a bangaren mata sai ai min lissafi na bada komai ayi yadda ya dace din. Tace gobe goben nan aiko dai kamar yayi kusa yace baiyi ba hjy idan kinyi la,akari da haukan da jummai ke nunawa gara ayi a kare komai kowa ya huta hakana. Allah yasa hakan shi yafi alheri mamu da taji maganan kamar daga samane ta fashe da kuka da bata iya cewa na maynene ? Kallon ta sukayi yana fadin ke kuma may ye abin kuka anan zaki sarewa yarinyar nan zuciya ne ko may kukanki yake nufi yanzu ? Cikin karfin hali tace yaya naga komai fa bamu shirya ba kan tarewan nasu a bangaren mu yanzun kuma za,a ce wai gobe gobe ? Wani shiri ne zakuyi ina ita fatima ba ko garin nan zasu zauna ba tafiya zasuyi don gudun hakane gaba dayan su nace su tare ga goben ai. Nagaji da wanan tashin hankalin naku da kowa ke mun abinda taga dama a cikin gida kuna son daukana mutumin banza. Ammace ta bashi hakkuri har ya bar part di mamu bata daina kukan da takeyi ba saida ya fita Amma tace gaskitan yayanku ne ai kukan ki yana nufin kina sarewa yarnan gwiwa ne. Ki bata kwarin gwiwa da hikimomi muna mata da zai amfane ta don yanzu ba abinda ya rage tunda an daura aure ko. Gwaggo har nawa sayadi take da za a dauke ta a wanan hali zuwa wani kasa mutumin nan bafa so yarinyar nan yake yi ba wani fuskan tausayi bai taba shiga tsakani su ba har yau. Ahir din ki maimuna nace ahir din ki da furta wanan kalami ga yarki na karajin wanan a bakin ki nida kaina zan saba maki a gidan nan . Ganin irin fushin da Amma tayi yasa ta fara bata hakkuri kan kuskuren datayi din nan dai amma ta kara sata a hanya daga haka ta mike tana fadin zama ba namu bane yanzu tunda tafiya ta canza sallo. Sam basuyi tsamanin shigowan shi ba a lokacin sun zube a falo sai cacakanshi sukeyi ga salma sai kuka take rusa ana mata huduban shedan. Ganin shi tsaye yana sauraren su yasa aka hau kalon kalon a tsakanin su ashe duk fitsaran hajiya jummai da sauran shakkan shi a zuciyar ta. Kallon salma yayi yace salma tashi ki shige daga ciki hjy zatai magana ya daga mata tsawa yace nace ki tashi ki shiga daga ciki. Amma dai Alh kasan wanan abinda ka, , , , hannu ya dagawa hjy rabi data soma magana wace kebiwa hjy jummai gurin haihuwa. Yace ban yi dake ba rabi ko kina cikin iyalina ne in sani tace banciki amma dalili ya kawo haka ai. Yace to wanan dalilin ya tsaya iya ku da yar uwan ku banson ina magana da iyalina wani bare na saka min baki ki kiyayye hakan. Wallahi ba zai yuyu ba hajiya jumai tace tana mikewa an tabamune dolemuyi magana wanan bakin auren wallahi yadda ka daura shi haka zakasa a warware shi yace dakyau. Ya nuna mata kofan fita tare da fadin magana na yana nan har yanzu ina bisa bakana niko ko ki bar wanan zancen ko ki fice min daga gidan nan. Hjy rabi tayi caraf tace don gidan ka zata bar maka gidan ka amma ka sani kaida kanka zaka nemay ta ai hjy ce kasan ta . Suka mike lokaci guda suna fadin don an bar maka gidan sai may dama ai ba a gidan aka haifeta ba diya kuma bada su tazo ba. Yace ashe kun san da hakan kuke son nuna min yadda zanyi da abina tace ko zan tafi da salma zan tafi bazan barta a nan ba kai mata dole. Yace kiko tabbatar da idan kin tafi da ita ta tafi ke nan sai dai ki nema mata wani uban bani ba tunda kinfi gareta. Salma dake saurare daga daki tayi saurin daukan waya ta kira yannen ta tana kuka cikin kashe murya take labarta masu abindake faruwa a gidan. Kawu ya fice ya barsu a falon hjy rakiya tace lalai anty mutumin nan a shirye yake da ko wani irin mataki zaki dauka akan zancen nan don haka muyi hakkuri ku barshi a yadda yake so daga baya musan shirin da zamuyiwa zancen. Hjy rabi tace gara mu nuna mashi muma muna da right din mu aiba shi kadai ya haifi yaran ba da yakewa mutane iko dasu. Ke salma fito muje yayi abinda zaiyi din anty bata kara minti goma cikin gidan nan gidan shi din banza may ya aje a gidan banda tarin matan banza ko a hakan da yake ganin ya gama da ita akwai mai sonta wanda yafishi. Shi inba ma aure mu kaddari ba har ya isa yace zai auri anty ne bakauyen banza dashi ma. Ta kara kwalawa salma kira salma taki fitowa har lokacin hjy tace idan baki fito muka wuce ba sai na balbala ki a dakin nan idan na samay ki ciki. Jin haka da sauri nafisa ta taso ta datse kofan dakin tana fadin kada ki bisu wallahi ba inda zaki tunda su basu ba mama sharawaran alheri. Ranan salma tasha zagi duka fice suna bambami a kofan gida suka hadu dasu Aliyu da sauri ya fito mota yana fadin mama lafiya don Allah kada ki tafi ki koma daga ciki muyi magana. Ba inda zan koma ai yunda Alh da bakin sa ya iya fadin in bar maigida yau ko gidan shi ya saura a duniya na barshi ke nan. Har wanan yar iskan salma wai nace tafito taki fitowa din uban ta yace mama yi hakkuri mu koma amma fir hjy taki bin shawaran dan nata. Tasa kai suka wuce da yan uwan ta a gaban Aliyu dake masu magiya basu ji ba haka yasa Aliyu din ya kira yan uwanshi yana fadin akwai matsala. Shi umar har lokacin bai fito ba yana cikin dakin sa na gidan sa kwance ga dan aikin su ya gama abinci kari yana jiran shi har lokacin bai fito ba. Sai dai ba barci yakeyi ba don basu dade da gama waya da merry ba da take mai korafin yaushe zai dawo ne har yana batun kai one week a wanan kasan mai zafi da sauro. Shidai murmushi yayi mata yana fadin ai itama saukin abin asalinta ke nan daga kasan take gaba da bayanta . Yace shifa yana ganin ma karshen ta Nigeria zai dawo da zama baki daya don ya gaji da zaman turai da yakeyi can tace saidai ya koma shi kadai ita kan bada ita ba. Yana cikin tunanen hiran nasu ne kiran Aliyu ya shigo yana dauka ko gaisawa basuyi ba Aliyu ke fadin bros babu lafiya fa gida don hjy ta tafi. A razane yace ta tafi ina kuma ? Sun samu matsala da daddy ne ta bar gidan itada su Anty rabi innalallahi ya fada a zabure yace yanzu ina suka nufa ? Ban san inda suka nufa ba a yanzu sun dai tafi yanzun nan yace shi daddy fa yana gidane ? Ban shiga ciki ba Aliyu ya bashi amsa yace gani tafe idan nayi wanka habbib fa yana inane ? Yana hotel na barshi yana barci salmace ta kirani tana fada min shine nayi saurin zuwa in hanata tafiya barin zo gidan kajirani a nan ka bugawa habbib waya mu hadu a gidan. Mikewa yayi ya shiga wanka bai dade ba kamar kullun ya fito a gurguje ya shirya yafito ya samu an hada mai abin karyawa ruwan tea kawai ya iya sha ya fito. Ya samay su a part din sun jima suna zancen da yan uwan shi inda yanuna bacin ranshi kan yadda yan uwanta basu bata shawaran kwarai kuma mahaifiyar tasu tana dauka. Sun tabbatar da daddy su baya gidan haka yasa ya mike ya dan leka Amma don shi maganan ma da yan uwan nasa keyi kara bata mai rai yakeyi. Ya shiga a yadda Amma ta ganshi yasata tambayan shi ko azumi yake ya zauna yana fadin may kika gani Amma tace au baka azumi zancen auren ne yasa ka ramay haka ? Ko tsoron fadawa matarka an aura maka yar uwarka kakeyi yace tsoro kuma Amma akan may zanji tsoron wace nina ajeta ba ita ta ajeni ba. Tace haka nake son ji namijin duniya kaida har yanzun kana da daman da zaka kara biyu nan gaba yace kai haba Amma ? Kamar dai wani injin can may zanyi da mata har hudu haka please ni Amma ba wanan ba tace sai may ? Kace tafiya zakayi da matar ka dan anajiran ka wurin aiki saudaki don Allah ka rike amanan yar marainiyar nan da aka baka a yanzu baka sanin dadin hakan sai nan gaba dadin hakan yana tafe da yardan Allah. Naji Amma yace a gagauce yace yanzu Amma abinda su daddy sukeyi da girman nan nasu yayi daidai ke nan ace mama bata taba fita ba gidan nan tunda kurciyar ta sai yanzu da girma ya kama su. Saudaki ina kake tunanen Amina zata a wanan shekarun nata wace keda kaman ku haka sakwa sakwa wani abu kuma ya rage masu banda hakkuri da junan su. Amma mama fa bata gidan nan tunda safe wai daddy yace subar mashi gidan shi shine yan uwanta suka zugata suka fice din. Kaga laifin yan uwan nata da ita dasu waye a gaban haihuwa ya kamata ace jummai tayi watsi da kishi ta kama gidan ta a hannun ta. Yau da safen nan su suka tayar damu da tankiyar su ba irin zagin da batai muna ba yau ni na hana kowa ya tanka masu a gidan nan. Kada mu zama daya dasu mu raba abin kunya wa jamma, a kaga koku ba zakuji dadin hakan ba idan mun biye masu. Wallahi in ba yanzu da kazo kana wanan maganan ba ban san bata gidan nan ba sam don tunda na baro yar nan dana kwana da ita ba lafiya ban lekawaje tinda na dawo shiyan nan. Bata nan Amma ya fadi cikin wani murya mara dadi yace ni nafi ganin laifin su mama rabi da suka kara zugata basu bata hakkuri ba ta zauna dakin ta. Basu da laifin don jummai ai babban kantane yanzu wanda ya aje kaman ku mai ya rage mai ba hakkuri ba . Bai jima ba ya mike yace zai fita tace ance jibi zaku tafi ko yace haka nake so Amma da yardan Allah indai an gama takardun yarinyar nan da wuri don nace Aliyu ya kaita ai mata idan wanda akai masu na umura ba zai fita ba. Ke nan kai ba zaka tasa matar ka gaba kaje kuyi ba wanan wani haline kamar mutumin da ? Yace idan kuma nai hakan kuce nayi rashin kunya ko Amma hakan kuma danayi yanzu ma ban tsira ba. Yana fadin haka ya fita dama maganan ya ishe shi sun aje dasu Aliyu idan sun san inda mahaifiyar su take zasu je in ya dawo. Ina nan kwance rijib sai ga Nafisa ta shigo part din mu tana wani daure fuska tace maman Fauziya wai Fatima ta shiya ta fito yaya Aliyu yana jiran ta a waje. Ina zasu ta wani ya tsune baki tare da fadin ban sani ba yadaice in fada mata hakan, daki mamu ta shigo ina barci saman gadon ta taba jikina taji yayi sanyi. Jin an tabani cikin barci na bude idanuna a hankali mamu nagani a tsaye kaina tace zaki iya tashi ga Nafisa nan wai Aliyu yana jiran ki a waje. Nace a shagwabe mamu banda lafiya tace daure ki fita kiji may ke tafe dashi don ban son Nafisa ta gane komai. Tana fadin haka tasa kai ta fita daga dakin ashe fadawa Nafisa tayi ina zuwa. Ta dawo dakin dauke kaya a hannun ta tashi ki shiga ki gyara jikin ki da kyau ki kula ko yaushe banda zama babu kamahi sayadi kada ki bari wani yaji wari a jikin ki duk da nasan kinayi yanzu ya zama dole ki kara don kinga yanzu kina da miji. Ina cije baki na tashi da kyat don bin umurnin mahaifiyata dake tsaye a kaina tace banda sanyin jiki ko yaushe ki kwanta wai ke baki da lafiya ko kina ciwo idan ba yakai intaha ba ki daure kinawa mijin ki aiyukan daya dace kiyi. Ni dai ban tsaya ba na shiga bandaki naji muryanta tana fadin akwai humran wanka yana nan ida kin fito ki murza tundaga can ko ina a jikin kuma kiyi sauri kada ki saba da barin namiji yana jiran ki idan zaku fita. Ni dai ban kula abinda take fadi ba na shiga nayi yadda tace ban dade ba na fito tana zaune tana mun kallon tausayi zuciyan ta ba dadi har na shirya ita da kanta ta rakoni daga kofan falon ta tsaya shi kuma yana cikin motar Umar zaune ina tafiya ina layi alaman dai banda lafiya har na karaso wajen motan na tsaya nisa kadan dashi. Ya sauke glass din motan yana fadin ba saceki zanyi ba amarya angon ki ne yace a kaiki wurin pasphot yanzu. A raina nace don pasphot aka tayar dani daga barci paspho din may kuma may zaiyi da pasphot dina ? Bude min gefen shi yayi na shiga na zauna ina gaida shi ya amsa tare da tayar da mota muka fice daga gidan. Ina jin shi na kifa kaina ga hannu na na hago fuskana na kallon window din motan yana canza kira,an dake cikin motan nasan neman waka yake ko wani abu. Can yayi tsuki yana fadin mijin ki fa kamar ustazu yake shi bai damu da kida ba ko kadan tun farko haka rayuwan shi take. Ajiyan zuciya na sauke na dan kalle shi ta gefe bance komai ba yace kinyi dace da miji mai hakkuri a rayuwan ki mudin zaki bi umurnin shi babu mai jin ku a duniyan nan. Bros yafimu hakkuri sosai duk dakin mu yafi kowa saukin kai da hakkuri da mama don haka ina baki shawaran da ki bi mijin ki ki watsar da duk wani fitina da akayi a nan zakiji dadin shi sosai. Shi mutum ne mai saukin kai maiba na tare dashi hakkin shi baida rowa sam sai dai matsalan shi shi bai son yawan surutu. Zan baki shawara duk yadda ya nuna yana son zaman ku ki daure ki bishi a hakana don Allah zaki ji dadin hakan a gaba. Ba ruwan ki da merry idan bai fada mata matsayin ki ba kada ki yarda ki fadawa merry komai a gamay dake har zuwa lokacin da zata gane. Jin yayi shiru yana fakin yasa nace nagode yaya Aliyu yace ba komai ake kanwar muce ba zamu so muga wani abu ya samay ki ba kuma ki bashi girman shi sosai duk abinda ya hana ki kada ki yarda ki maimaita abin nan. Daga haka ya bude mota yana fadi fito mu shiga ciki har lokacin ina tunanen a raina ashe haka yake in hakane itama Aisha ta dace da miji ke nan kamar yadda shima yake yabon dan uwan shi. Office ne wurin kala kala ba zuwan mu na farko ke nan bax don mun gama school muje da daddy yace zamu raka Amma umurah kuma Allah bai nufa tafiyan yayi ba. Yanzun kuma sai gashi na sake dawowa ke nan dai ina da rabon shiga jirgin ke nan harwa yau. Anyi mun komai yadda ya dace muka fito muna shiga mota wayan shi na ringing ya dauka naji yana fadin gamu mun fito an gama komai sunce in dawo zuwa gobe da rana. Yana aje wayan ya kecewa mijin kine yaga mun dade kila sai kuma yace yaya nagan ki haka kuma ko baki da lafiya ne ? Banda lafiyane yaya na bashi amsa ina dora kaina a window mota har lokacin yace subbahanallahi may ke damun ki ko kema irin na mamane kan auren kike ciwon ? Dan murmushi maganan shi ya sakani nayi murmushi kawai ba tare da nayi magana ba. Maimako muje gida sai baga ya dauki hanyar gidan yaya umar din dan juyowa nayi ina kallon shi yace kada ki damu kanwata nasan abinda nake ai ba kaiki zanyi ba dauko shi zamuyi fita zamuyi tare. Idan mun tsaya sai ki koma bay ina fatan bamu takura maki ba dai nace babu komai yaya nagode ya dan juyo yana fadin da may kuma ? Ban iya bashi amsa ba har ya fita daga motar ya shiga gidan nikuma na fito na koma baya na zauna. Ina nan zaune na hango su sun fito suna magana kamar kullun yau ma yana saye da kananan kaya a jikin shi bakar rigace da anini daidai damtsen hannun sai farin wando daga ksa da bakaken takalma. Kodai ban sanshi ba da sosai zan iya cewa naga ya fada sosai ya danyi duhu kaina na kawar daga kallo su har suka karaso bakin motar. Tun daga nesa ya ya kalli Aliyu yace yaya haka kuma baka kaita gida bane ko yaya yace na ratsene mu dauke ka sai mu wuce idan mun sauke ta. Daga haka baiyi magana ba muna karya kwanan gidan muka hango motar daddy a wajen gidan. Daddy ya dawo gida ke nan yace a waje Aliyu ya tsaya da mota na fito na barsu ciki bayan fitana Aliyu yace yarinyar nan bata da lafiya fa. Yana magana ya balle mota ya fito ba tare da yayi magana ba sai daya dira kasa yace fito mu shiga muga daddy kafin mu wuce. Koda nashiga su hajita maryam nagani ta rako wasu kawayen ta zasu tafi suka tsuro min idanuwan su na shige ba tare da na gaidasu ba don nasan gulmana akeyi. Shigowa su ne ya hana suyi maganana kallon ya koma gare su ikon Allah shi wanan ma badamu ba uwarshi na can tana ciwo don auren shi . Shi yana nan yana yawo da amaryan shi a gari lalai zamani kuwa maganan uwarshi ne an gama dashi sannu kawai sukace masu suka shige kai folon mahaifin su kai tsaye. Sun samay shi yana shirin fita kuma yana ganin su suka tsayar dashi dole ya zauna suma suka samu wuri suka zauna a kasa. Dan shiru ne kafin umar din yace daddy munji abinda ya faru tsakanin ka da mama da safe ya sai ya kara sunkuyar da kai cikin ladabi yace don Allah daddy kayi hakkuri mama ta dawo dakin ta. Ya dubeshi da mamaki yace umar ai ban koreta ba zabi na bata kuma taga hakan yafi mata don haka ko jummai zata dawo gidan nan sai ta gane kuren ta tayi nadama. Ku kankuma sai kunyi min alkawarin amincewa da zabina gare ku ba zaku watsa min kasa a idon duniya ba. Zaku riki matayen ku bisa amana ba zaku wullakanta diyan mutane ba kamar yadda suma iyayyen su sukaga mutuncina suka bada su Amana. Umar yace daddy ai kasan bamu taba maka musu ba ga duk abindaka umurcemu muyi yace na sani umar sai dai mahaifiyar ku tasha alwashin sai ta raba wanan auren danaku dana salma ga baki daya. Har tana ikirari salma tafito su tafi da ita na nuna idan salma tabisu bani ba ita a duniyan nan. Aliyu yai saurin fadin daddy abin baikai can ba ai su salma sun mayar muna da yadda akayi adaiyi hakkuri daddy don Allah. Sun dan kara bashi hakkuri yace sai yayi shawara nan yake fada masu zancen tarewan matan su gobe don ba za a tsaya jiran komai ba. Sun mai godiyan dole kafin su fito zuwa gidan da mahaifiyar su take itama su bata hakkuri kamar yadda suka ba mahaifin su din. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:13 - 🀐🀐🀐: YA AR-RAMANIN AR RAHIM YA HAYYU YA KAIYUMUN, , , , , , , Ina shiga part din mu na samu baki a part din mama saude da umman su Atika sai Atika da manjo da Addahna da wasu mutum biyu dana sani a azare. Ina ganin su na fashe da kuka maimakon farin ciki jikin umman Atika na fada na darji kuka na wanda duk wanda ke falon sai da yai hawaye. Daya daga cikin kannen manjo da suka zo tare tace ki share hawayen ki yar nan aure ba mutuwa bane abin farin cikine tunda kikaga har munzo murnan haka. Ya kamata ace farin cikin ganin mu kikayi sai kuma ki aza muna kuka haka maza ki share hawaye ki daina wanan kukan haka. Yadda tace hakan nayi don yadda take magana umurnine take bani a lokacin haka yasa nayi saurin dakatar da kukan da nakeyi din. Umma ta dan bugi bayana tana fadin ai saiki saka mu jin ba dadin zuwan mu nan nidakewa Atika fatan samun nasara irin haka har yaushe zaki tsaya kina kuka. Duk wata uwa yana cikin farin cikin zuciyar ta yau ace ka kai yarka aure haka cikin lumana aike ba karamin sa,an aure kikayi ba yar nan. Tashi ku shiga ciki da Atika kuci abinci nasan ke take jira ta kasa cin komai tun da muka iso. Mikewa nayi muka shiga daki nida Atika nan saida mukai kukan mu muka share hawaye muryan Aisha ne ta shigo tana fadin yanzu mai kumshi tazo zamuyi dama ai nace naki yana nan kamar yau akai maki shi. Saida ta kalli Atika ta dan rage tsawo tana fadin ance kun fita tare da ya Aliyu dazun dana shigo nace gurin photo ya kaini nayi. Photo kuma wani irin photo ke nan ko kuma harda photo zakuyi ne na amarya da ango wai ? Ango da uwargida zamuyi ba photo na harareta ina fadi tare da ya Aliyu muka fita ashe haka yake da saukin kai sosai . Wani dadi taji tana kaiwa zaune tare da fadin don Allah da gaske kikeyi A ruwa ? Harara na kara aika mata nace a,a a wuta don Allah tafi nama fasa baki labarin ta rungumoni tana fadin haba yar kanwata fada min don Allah yadda kukayi dashi mana. Yayi maki magana na don Allah ta fada tana tsurenu da idanuwan ta tana son jin amsa daga bakina. Kai na girgiza mata nace ko daya bai mun maganan ki ba wallahi ya dai bani shawara sosai kuma naji dadin hakan da yai min don ya kwantar min da hankalina kadan. Rarashi na take wai in dan fada mata abinda yace mun nace ki bari kema zai fada maki ai idan kun hadu. Hannuna ta kama tana fafin haba yar kanwata kin san fa bamu haka dake a gidan nan keta hannun damanane aru wai fatima. Na kara hararanta nace ba zaki daina kirana da sunan nan ba ko ? Bakina ya saba hakan saboda Amma dake yawan kiran sunan kulun nace ni rabu dani don Allah na kashe wanan sunan dai tace naji matar yaya. Ashe baki son kiji komai ke nan gara ma bakin ki ya saba da kirana da kanwar yaya din zaifi maki sauki. Ni ba wani abu yace min ba magana kawai yai min akan inda zanje shine ya ban shawara kawai. Ina fadin haka nakai kwance tace waike ko kina shirin wankin amare da za ayi muna gobe ? Yi nayi kamar ban jita ba na kyale ina kallon gefen da nake kwance ina tunane a raina. Suna zaune a dan karamin falin gidan yayan su gidan da hjy su take zaune duk kansu su uku ne a zaune suna fuskantan mahaifiyar tasu da suke zaune ita sisters din ta duka uku. Tace kundai ji abinda mahaifin ku yai mun ko saboda ku har wanan yar banzan salma zance tafito mu bashi gidan shi taki fitowa. Ba wanda ya iya magana daga cikin su sai habbib da yakai iya kuluwa da zancen yace. Amma mama kema kina da laifi gaskiya yau kuke da daddy bai taba cewa ki barmasa gidan shi ba sai kan wanan zancen . Mun fada maki ki kwantar da hankalin ki tun farko tun abin nan bai kaiga haka ba kinki kwantar da hankalin ki. Abi abin a sannu cikin hikima da muke shirya kin dai san ba son abin nan muke ba dukan mu muna hakane saboda farin cikin ki. Amma mama kikaki bin shawaran mu har abin yakai ga muni haka garemu dake don daddy ya hau fiya da yadda kike tsanmani gaskiya. Yayi ta hawa mana shine may don ya koreta gidan shi akace nufanshin ta aka katse ko may ? Look mama rabi wanan magana ne tsajanin mu da mahaifiyar mu don ba zamu so wanan abinda ya faru yayi tsauri ba don Allah ina rokon ku idan ba zaku tayamu kwantarwa mahaifiyar da rai akan zancen nan ba kuyi shiru. Babawo ni zaka fadawa haka ko kin fimu son tane zaka nuna min yau ka tuna uwa daya uba daya suka haifemu don haka ba zaka nuna min son ta ba yanzu. Kuna son ta aka hada kai daku akai mata waban cin fuskan da yankan kauna wai har kanwarku ne za a dauka a hada da almajirin gidan ku don rainin wayau ? Please mama ciki hade hannayen shi habbib ne ke magana na rokeki kamar yadda dan uwana ya rokeku ku fitar da bakin ku ga wanan zancen don Allah. Ba zasu fitar ba ai bansan kunzo nan kuyi muna rasgin kunya bane da kuka koyo a kasan turai. Karya tafada ba gaskiya bane bakin ku hade da mahaifin naku don a tozartani haba mama ya kamata ki fahince mu yanzu mafa mun zauna da daddy akan maganan nan ya kidaya muna sharudan shi akan in har kince ba zamubi zabin shi ba gare mu a bakin auren ki. Mama yaya kike son muyi da zuciyar mu wanan abin fa don farin cikin ki muka yarda mukayi shi ba wai son ran mu bane Aliyu ya fada shima rai bace. Tace haka yace yace kwarai kuwa don mun zauna dashi da baba balarabe ya kara jaddada muna hakan da yamman nan. Kallon juna sukayi sai hjy rakiya tace ya kamata Alh yai muna uzuri tunda muma muna hakki a kan ku ai. Musanman salma da akaiwa wanan bakin hadin dakai babawo di yan matar shi cefa yayiwa gata amma mu namu ya bata mata asali. Habbib ya kalle ta yace kada kuce haka mama don salma tana son mijin ta munyi magana da ita tana son mijin ta. Kabar wanan zancen wai salma nason mijin ta uwar tace kabar wanan kazamin zancen habbib . Yace wallahi mama da bakinta ta fada muna da muka zauna da ita bawai mun tursasa mata ta fadi ba. Kallon juna sukayi kafin uwar tace zanko halaka yar iska idan tace wanan dan almajirin take kauna mutum da naki jinin shi a duniyan nan. Haba anty ki bar fadin haka don Allah tunda yanzu ya zama surikin ki nifa naga ku bar Alh kawai yayi iko da iyalin shi yadda yake son yi shine saukin mu. Ki samu ki koma dakin ki don zaman nan ba zai fishe ki ba tun mutane basu farga da hakan ba. Bazata koma ko ina ba Asmau idan bamu samu sabani dake akan wanan zancen ba a wurin nan may nake ? An gaya maki kowa irin kine da namiji ke takawa kina kurun don ruwan cikin tsiya nina rasa inda kika kwaso halin nan kamar ba Auta ta haifeki ba. Ku tashi muje umar daya mike yace da sauran ku tafi mana mai bakin zuciyar tsiya dama nasan bayan ubanka kake ai. To bari kaji muddin ina raye yar iskan yarinyar nan ba zata shigo min cikin zuri,ana ba . Amma anty da kin kyale kamar yadda sukace suna bin mahaifin nasu a hankali ne ba a san manufan su ba ai. Su kan sun fice sun barsu a nan ba wanda yaiwa dan uwa magana daga cikin su har suka shiga motan da suka zo a ciki. Saida safe hjy keji wai ranan ne tarewan amare don Alh ya aiko ma kawun su da yayan su yace a fada masu yau salma zata tare gidan mijin ta tare da sauran Amare. Don haka yake sanar dasu idan akwai mutum biyu daga bangaren su da zasuzo da dare akai salma dakin ta. Yayan nasu ya kare masu bayani hjy tace yasha karya wallahi babu inda salma zata gidan wanan mijin da zuciyar ta bai amince dashi ba. Yayan nasu yace kinga jummai tashin hankali yanzu ba naki bane zan tafi in samu kawo a gyara zancen nan naku ki koma dakin ki ki kai yarki aure kikuma tari sarakan ki da zasu shigo hannun diyan ki. Maimakon ta saduda sai kawai tace amma yaya in kun min haka baku min adalci ba sam yadda yake tunanen banda amfani a gidan yanzu ya koreni sai idan yazo da kafan shi zan koma don nasan barazana yakeyi bazai kai mu aure bani gida ba. Hjy Rabi tace ni dama nasani wanan kamay kamay da yakeyi don dai ta dawone barazane kawai yakeyi . Nan dai suka kananaye shi da dasin bakin mata har yaji ya gamsu da maganan shi bai neme kawun nasu da sukejin maganan shi ba. Ina kwamce dakin mamu inda na mayar gurin zamana a yanzu sai ga mamu ta shigo ta bude wardrobe din ta tana fito da kaya a ciki sabbi an dinka su ta zube saman gado a gefena . Atika ta tashi ku shiya tana nuna kayan da zan saka a lokacin tare da mata bayanin sauran kayan lokacin da zanyi amfani dasu. Sannu a hankali gida ya fara cika da mata yan wunin buki ko wani bangare yan uwan iyayyen mu mata ne suka cika shi idan an debe part din hjy da ba wani nata wanda yazo daga mata har mazan su. Kawu tun safe ya maida salma part din Amma inda dukkan mu muka taru a can nayi mamakin ganin har sunyi karfin hslin gaiyato abokan su sunzo ashe. Bangare na daga ni sai Atika da Allah ya rufa min asiri tazo muke dan kus kus din mu mu biyu. Yan uwan kawu birni da kauye sun cika gidan fam sai faman kuskus ake na zancen hjy da bata gidan lokacin. Karfe biyu akayi mothers daya da wankin amare sai lokacin ne mukaga yan uwan mazajen salma da ikilimi ashe sadiq din shagon kawu ne shima sun dade tare tun yana karami sai dai baikai Ahmed bunkasa ba a wurin. Amma shima yana da rufin asirin shi gwargwadon hali don sun ginu daga Alh sosai shida Ahmed din yanzu. Hjy maryam tayi kuka tayi korafi saidai fin karfin yan uwa da iyayye ya hanata motsawa ta saida hali. Karfe hudu sai ga su mama hadiye sjn shigo suna fadin maza mu shirya kawu yana neman mu a falon shi. Kusan a tare muka shiga falon bisa jagorancinn Amma mama hadiye mama Atine da matan kawu balarabe sai hjy maryam da mamu Addah da gwaggon Aisha daya. Kowa ya samu wuri ya zauna yayin da nake manne gurin Amma gwaunin ban tausayi dani kawunan mu suna a duke. Kawu ya dan dauki lokaci yana rubutu saman fararen envelop guda biyar sai kawu balarabe da kawu mustapha zaune a gefen shi. Can ya dago kai yana fadin hajiya kunyi hakkuri ina rubutu koda kuka shigo ya fara gaisawa da mutanen wirin kafin ya dora da godiya ga Adda da gwaggon Aisha a karshe. Ya kira sunan salma da rakiya sai Aisha da ikilima nice ta karshen kira nace na,am kawu ina wuni cikin dakusasshen muryan da ya gaji da kuka lokacin. Ya amsa da kyat yana kallona tausayi yakeun don dai tausayin nake bashi sai dai ba yadda zaiyi ne don hakan ne mafita a gare mu baki daya. Yace diyata har yanzu kukan bai kare bane kiyi hakkuri haka musulunci ya gadar damu mu raya sunna a tsakanin mu karfafa zumunta a tsakanin yan uwa musulmai. Ya kare da kiyi hakkuri kinji na gyada kai kawai ba bakin magana gare ni shashekan kuka nake saukewa a hankali daga inda nake zaune. Dago kai yayi ya kallemu dukan mu yace da farko zan fara da godiya da Allah ya nuna muna wanan ranan mai albarka ranan da ya nufa a cikin kudin tarihin ku zamu kaiku gidan mazajen ku lafiya. Nasiha yayi muna mai kashe jikin bawa a gurin yayin da falon yayi tsit ga baki daya na dan wani lokaci ana sauraren shi. Ya kare yana saka muna albarka tare da fatan zaman lafiya a tsakanin mu da mazajen namu yace a tsarin su ba zancen saki ko yaji a gidan nan din haka kowa yaje ya zauna lafiya da mijin shi. Salma ya kalla yana miko mata envelop dake dauke da sunnanta tare da fadin wanan sadakin ki ne hannkin ki ne don haka muka yanke shawaran bawa kowan ku ga hannun ta don sadaki ba abin wasa bane. Haka yai ta kiran mu daya bayan daya yana mika muna envelop din dake tare a gaban shi wanda muka samu yana rubutu a kai. Bayan ya gama bamu ne yace yanzu sai ku shiya ga balarabe ga mustapha da gwaggonin ku zamu kaiku dakunan ku kfin yamma ya karayi. Ke fatima ina ganin gobe zaku bar kasan nan ko zuwa jibi da fatan zakiyi amfani da tarbiyan da muka doraku akai. Kada kikaga bamu kusa ki dauki wani tarbiyan daba namu ba ki dorawa kanki a can. Shigan ki gidan dan uwanki yana nufin wani haskene a rayuwan shi daya manta a baya ke zakiyi kokarin dawo muna da akidun mu da al,adun mu a acikin zurian shi. Don haka ashe aikine babba ja a gaban ki aka doraki kiyi ba kamar sauran da su mazajen su basu cunkushe da wasu al,adun a gidajen su ba. Kawu balarabe ya karbe da fadin kindai san wanan kafiran matar tashi sai kin ture wasu al,adu nata kada ki yarda al,adunta yayi tasiri a gare ku ko kadan kiyi kokarin kafa naki akidan addin nin a zukatan duk na tare daku. Kibi mijin ki sauda kafa yinayi bari na bari sai a zauna lafiya a tsakanin ku kuka mai tsuma rai nakara fashewa dashi a wurin saida naba kowa dake gurin tausayi Amma ma kukan ta fara tana fadin ko zaku barta gida ta kwana biyu alabashin daga baya idan yazo sai su tafi. Kunga ko yanzu ba lafiyane a jikin ta ba a hakan kuke tunanen kaita cikin wanan halin ? Dan murmushi kawu Alh ya sake yayi da kawu balarabe yace haba babba mai zaisa a barta gida bayan mijin ta yana gari ? Daga haka kowa na falon ya shiga yi muna nasiha kawu yace mu tashi mu shiga muyi bankwana da iyayyen mu su bamu mintuna talatin a fito. Kowa ya tashi a guri mamu na zaune kanta a duke tana zubar da hawaye a fuskan ta kawu mustapha yace kiyi hakkuri maimuna tashi kije kuyi sallama da yar ki ko ina take Allah ya tsare muna ita. Kuka nake darza sosai a part din mamu saman jikin manjo mamjo din tana tayani . Haka mamu ta shigo ta samay mu da bata kukan ana bata hakkuri sosai takardan hannuna na miko mata wanda kawu ya bamu tace dashi zaki sayadi hakkin kine a cikin sa. Kaina gyada nace mamu ki aje a wurin ki tunda va abinda dashi a can ki karba Addah tace don kada ya salwance a wurin ta . Basu tsaya jiran komai ba ko kebewa bamu samu yi da mamu ba haka su mama hadiye suka shigo suna fadin wai in fito kowa na waje ni ake jira. Kukan da nakeyi naba kowa tausayi mota na samu a bude kawu balarabe ne maija kawu Alh yana zaune a gefen shi. Amaren na zaune baya jeep din dukkan su sai kuka sukeyi kawu mustapha yana jan dayan motan dasu gwaggo Addah ke ciki harda su mamu da Hjy maryam su kawu sunce sufito su rakamu dakunan mu. Aka dauki hanya damu zuwa gidanjen mazan mu sai fatan alheri a gare mu ga sauran mutanen da aka bari basu je ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:13 - 🀐🀐🀐: EID MUBARAK YAN UWA ALLAH YA MAIMAITA MUNA NA BADIN BADADA AMIN, , , , , , Allah sarki rayuwa aure yakin mata gishinkin rayuwan mace muna kallo abinda bamu taba kawowa a ran mu ba yau ya faru damu wai gidan aure za,a kaimu wanan fitan da mukayi gida. Gidan salma aka fara zuwa nan muka samu gidan a cike da yan uwan Ahmed da sukazo daga garin su can jahar katsina. Daga gidan salma sai gidan Rakiya gidan yana rufe babu kowa daga bangaren hjy ko Alh do bukin ba tsari akayi shi duk yan uwa nacan gidan kawu Alh. Itama dai an mata nasiha sosai muka fito zuwa gidan Ikilima yan uwan sadiq sundan cika gidan daga jahar sokoto dama abokan arzikin shi. Sai gidan Aisha inda muka samu yana gida da wasu abokan shi mutum uku bamu fita ba hjy Asmau tazo da kawayen ta da matan kawun su suna bada hakkuri . Mun fito tare dasu ana raha sukace zasu riga isa gidan umar kada acisu tara hakan akayi don sun rigamu isa gidan. Su suka tare mu ina jin mota ya tsaya na kara makalewa a jikin Addah ina rusa kuka haka Addah ta rikeni muka fito daga cikin motan. Ta dan tsaya dani tana rada min a kunnena abinda zan karanto bissimilah kafa goma sha uku sai falaki da nasi da kulhuwallahu uku uku kowa harsu kawu aka tsaya daga kofa. Muna shiga ina jin mutane na fadin masha Allah gida yayi kyau kusan duk gidajen sun fadi hakan bawai a nawa kawai suke fada ba. Kawu ya riko hannu na yana fadin ina part din yata din yake aka nuna mai har dakin suka kaini su uku dashi sai kawu balarabe da Addah. Ya zaunar dani saman gado tare da dafa kaina yana jero min addu,oi suna amsawa da amin yakare ya dan bubuga min baya yana fadin inyi shiru insha Allahu wanan auren zai zamo min alheri a rayuwana. Zai wuce na riko hannun shi ina kuka tare da fadin kawu kada kutafi ku barni don Allah kawu yaya umar ba sona yakw ba dukana zasu dinga yi don Allah kawu kada ku wuce ku barni a gidan nan da kyat ya iya bambare hannun shi daga nawa yana share hawaye shima. Nace wayo Addah na Addah kada ki tafi ki barni kema Addah mutuwa zanyi wallahi idan kin tafi kin barni. Itama kukan ta fito tanayi kamar yadda kawu ya fito yana sharan kwalla a gaban jamma,a itama haka tafito hakan yasa masu saurin kuka yin kuka a lokacin. Suka fice suka barni sai su hjy Asmau da yan uwansu da kawayen ta a gidan. Ankaisu fa kukace hjy rabi tace wallahi anty yanzu yaya yazo yana fada muna wai harsu asma,u sunje taron amare kawu ya turasu suka tafi. Ni Alh zaiwa haka ni ni jummai zai tozar, , , sai ta kasa karasawa ta fashe da wani irin kuka lokaci guda. Abinda bata taba tunane ba a rayuwan ta shine ya faru da ita ayau suma sin tsorace da ganin tana kuka don ba abu kadan ne zai girgiza ta ba a rayuwan ta har ta sake hawayen idon ta ya sauko kasa. Da kyat suka shawo kanta tayi shiru duk shawaran da sukeyi tana jin su ta kasa furta ko a alokacin. Sai mikewa tayi tana fadi ku tashi mu tafi . Ina zamu tafi anty ? Hjy rabi ta tambayeta cikin son jin inda zasu tafi din don kallon bata cikin hayacinta suke mata. Wani tsawa ta daga masu tana fadin idan ba zaku tafi ba ku ban makulin motata in tafi ni kadai idan baku zuwa dole suka mike suna mara mata baya. Sai dai suna zuwa wurin motar ta kawo masu cikas taki tashi kuma lafiya lau aka aje motan don cikinta suka zo gidan. Wanan ya kawo masu cikas aka tsaya duba masu motar tana ji kamar tabi motar haya ta tafi inda tayi niya din. Kawu sai hankalin shi bai kwanta yayi sa,a umar yazo gidan ya samu basanan zaifita sai gasu suka jera a tare zuwa falon shi . Ya zauna shima ya samu wuri ya zauna tare da kura mai ido na san lokaci kafin yace Umar faruq dama ina son ganin ka a yau din nan. Ga Amana yata nan na baka koda bana raye ban yarda kaci amanan yarinyar nan ba ban yafe wani kalman saki ya shiga tsakani ku ba ko wani mugun hali amana na danka maka kamar nima yadda aka ban amanan ta naga ya dace in ba wani ahalina wanan amanan . Alhamdullahi kai ka zaba nayi farin cikin wanan zaben naka fiye dana kowa a cikin ku don dama kaine hope dina kanta. Nasan zaka rike mun ita amana kamar yadda nake rikonta a nan zaka tayani cike mata gurbin da girma bai bari in cika mata shi a yanzu. Umae faruq kai namiji ne nasan zaka kai hankali a inda na nufa a yanzu don nasan kasan girman amana sosai a wurin ka. Sabanin yadda iyayyen ku mata suke hangen abin da wani manufa a zuciyar su sai suka fassara abinda kishi a nasu manufan . Idan ka lura yar nan marainiyace a ckin mu dole mu riketa kamar yadda Annabin rahama yace mu kula da maraye . Don Allah umar ga amana nan na baka nauyin komai nata yanzu ya rataya a kan ka kazama mata kaine uwarta kaine ubanta data rasa a kusa dakai. Kan ahi na kasa idanuwan shi sun kade sunyi mai ja da wanan kalaman daurewan da mahaifin shi kemai a lokacin. Daidai lokacin da kawu yake fadin fatima tana son karatun likita a ratuwan ta saidai ban san naka ra,ayin ba a yanzu ko zaka bari tayi wanan fannin ko kuma kana da naka ra,ayin ne na daban ban sani ba ? Lokacin ya dago kai ya bude baki da kyat yace daddy karatu sai idan ita da bakinta tace ta gaji dhi insha Allahu. Kawu yace nagode nagode ubangiji Allah yai maka albarka ya haskaka maka samun ka duniya da lahira nagode kwarai umar da wanan halarcin da kukai min kun nuna min ku diyane nagari a duniya ina alfahari da samun ku a duniyan nan. Sai kuma ya fashe da kuka saida yayi mai isanshi shima umar din kukan yakeyi kawu ya tsagaita yace mahaifiyan ku takasa fahintana umaru. Maina rage jummai dashi a duniyan nan duk abinda jummai keso shi takeyi amma kan wanan burin nawa nason raya zumuncin ku da yan uwana ko bayan bana raye ta kasa cika min shi. Daddy kayi hakkuri don Allah zata gane abinda kake nufi da hakan daga baya ayi hakkuri don Allah mama ta dawo dakin ta. Ko yanzu ka nuna mata kai namiji ne sama da ita ayi hakkuri don Allah bamujin daddin haka na faruwa a tsakanin ku. Ai zanyi amma ina son jummai ta gane kuskuren ta ne na yin hakan agare ni ko don watan watarana. Mama hadiye ne ta shigo falon tana fadin kai tsufin nan da rikici suke ganin umar falon zaune a yanayin da suke da mahaifin nasa yasa tayin turus tace ashe kana nan ma ? Ai gara dana samay ka wanan tsohuwar ne kakan Fatima take kuka wai a barta taje tayi sallama da jikanta don Allah. Kawu yace ku barta tatafi mana ku kaisu can don Allah ai zasu iya kwana a wurin ta don yau kawai ku kaita don Allah dai. Gashi ina gidan zaka yanzu sai ku tafi ka saukesu dayani yace ba matsala daddy idan sun shirya sai su fito. Gidan salma ta fara zuwa sun samu an fara watsewa a gidan sai gasu mamakin ganinta mutane keyi a gidan. Ana taron su da zuwa ba wanda ya amsa daga cikin su sai kokarin shiga tana tambaya ina dakin da salma take ? Aka nuna mata ta nufi kofan gadan gadan Nafisa ne ta fara lekowa don jin muryan su da tayi tace salma ga mama nan. Wani irin zabura salma tayi tace da gaske wallahi ko nafisa ta fadi da sauri suka nufi ban daki suka rufo dukka su biyu sai kawayen su suka bari zaune a dakin suna mamakin su. Suna shiga tun falon takebin wurin da kallon mamaki tace ma kawaye ina salma take da yake suna da wayo sun dan san halin da ake ciki sukace ta fita an kirata. Bata fita ba tana dakin nan hjy rabi tace tana kallon kofan bandakin da idanunta. Tana cikin bandaki ta rufe ko tace a hasale nan suka hau aika mata da zagi sai ta fito su wuce yau bata kwana wanan matsiyacin gidan wallahi. Hayaniyan da matan sukaji yasa su shigowa dakin nan suka shiga bata hakkuri tace su suka haifa mata yar da zasu bata hakkuri ? Ganin haka yasa wasu kiran Ahmed hankali tashe suna fada mashi ranshi ya baci ya kira kawu yana sheda mai. Umar na shirin barin wuri mahaifin shi kiran ya shigo mai yake fada masu abinda ke faruwa a gidan nasu. Jummai ko nada hankali kawu ya ambata hankali tashe haka yasa umar dake sa takalman shi tsaya daga kofan falon ya dawo ciki yana fadin daddy wani abin tayi ne kuma cikin sanyin murya yake magana ? Wai gidan salma suke yanzu ala dole sai sun fito da salma gidan ta jimmai ko nada hankali ? Barinje gidan daddy a kwatanta mun gida yace a, a kada kaje ai kaima tana tafe gidan ka kaje ka kwashi matan ku tafi ku barni da ita. Badon yaso ba haka ya bar gidan ranshi a bace sun hadu dasu mama hadiye da saurin su zasu shiga wurin kawu din. Yasan shine ya kirasu a kan maganan hakana dai ya wuce ya dan jira su manjo suka zo tunda suka shiga motan suke kwarara mai addu,a har yakai gidan baiyi magana ba. Suna sauka yaja motan ya fita wuri ya samu ya faka ya kira layin habbib yana fada mai halin da ake ciki dashi da Aliyu. Wai may yasa mama take biyewa su mama rabi ne tana bar muna abin kunya nafara gajiya da halin nan na mama habbib yace. Yanzu ba wanan ba yaya za ayi shine na kiraku muji Aliyu yace ba daddy yace a barta dashi ba mu bari muji matakin da yake son dauka Aliyu yace. Ina tsoron kada daddy yai fushi ya hadata da hukuma umar ya fada rai bace yace ba zai kaita ga hukuma ba nasani inji habbib. Can kuma su mama hadiye na shiga suka samu suna cacan baki da Ahmed yana fadin kema kin san ba don ki na yarda da wanan hadin ba . Kamar yadda kike kyamana numa haka nake kyaman halayan ki a rayuwana ban taba ganin uwarda bata san ciwon kanta irin ki ba hjy. Amma jummai kinji kunya idan kin santa ai gasjkiya surikin ki ya fada yau yay da kawo yarinya ki gidan mijin ta kizo masu da tashin hankali haka ? Sarka mai rikicin gangan yau kan sarka ta rikice a gidan Alh sani har bata iya haduwa don rikicewa. Sun gwada mata suma yan zamani ne sosai don sun barda abin fadi kafin su bar gidan zuwan kawu mustapha gidan ya tsayar dasu. Don dole badon taso ta bar gidan don taga abinda batayi tsamani ba gare su dan hakkin daka raina sukai mata. Tana sababi a cikin motan tace dauki hanyan gidan babawo inje in fitar da yar iskan nan itama kafin in je gidan sauran yau yadda suka hana zuciyana sanyi suma nasu ba zai taba sanyi ba garin nan. Ina takure a dakin sai ga su Atika da murja sun shigo shigowan su ya dan sani sakin dan jiki na tsagaita kuka da tunanen ba,a sona da nakeyi. A haka su manjo mama saude da umma su Atika da sauran suka shigo suna sallama gidan ne da shegen gima haka ya hanamu jin sallaman nasu lokacin. Da tayake Addah tasan dakin ita ta kawo su inda nake ina ganin su na bata rai na bada baya waini nayi fushi muna cikin har akai sallah da isha,i muna ta hira manjo ke fada min ai nan zasu kwana tare dani. Naji dadi hakan yasa na saki raina muna tsaka da hirane hjy ta fado dakin daidai an kawo muna abinci suna ci ina rabe gefen Manjo dake cin abinci da kyat. Eyyah lalai har kunga gidancin abinci ko to ba mamaki andade ba a hadu an samu banza ai dole aci yanzu kamar mayunwata. Hjy rabi ta karbe to keko anga gidan ci ba dole baje anacin dadi ba dole a baje talauci ba a nan ana kwasan banza. To ba wanan ba kune matsiyatan yan uwan yarinyar nan ko wa kike da suna koma dai wa kike ke ya shafa. Yadda kuka shigo gidan nan ku tatara kayan tsiyan ku, ku kwashi munafukan yar ku kubar gidan nan tun muna sheda juna daku a wurin nan. Amma hajiya wanan kamar ba mutuncin ki bane a baka kuautan dan mutum baki gode muna ba sai ki zo da zancen Allah waddai. Umman Atika ke fadin hakana daga inda ta kare sallah ke kuma a wa kike idan ma baku sani ba ku sani ni dai na haifi maigidan nan da cikina. Don haka nace ba zai auri yarku ba indai nono na yasha a duniya aure da ita ya haramta gare shi. Banga laifin Alh ba daya gargadaki ya nuna maki shi namiji ne aikai sha,anin nan salin alin ba zamu bar gidan nan sai idan shi mijin nata yazo ya koremu da yar tamu zamu fita ko minti daya ba zamu kara ba zamu fice maki gidan dan ki. Addah ke bata amsa tace aiko zan nuna maki bana magana biyu yau ba sai dana yazo ba zaku kwashi tsiyan ku kubar gidan nan. Nan suka fara cire gyalen su suna shiri fada kamar an jefo part din yace cikin tsawa haba mama wanan bai dace ba gaskiya. Tsayawa tayi tana kallo shi kafin tace gara da Allah ya kawo ka yanzu maza ka saki yar kauyen yarinyar nan tun kan na saba maka . Mama ku fito muje waje muyi magana do Allah tace ba ida zan tafi sai ka sakar masu yarnan yau yau ta koma masu gida. Ya dukar da kai kafin yace ba zan iya ba mama amana take a gurina kamar yadda nayiwa daddy alkawari tun farko. Ta juya da sauri wurin ya uwanta tana fadin may na fada maku dama na fada maku maimuna ta shanye shi tun farko. To kaji da kyau ko ubanta ya baka amana saika saki yar nan yanzu ba ko sai na gusa daga nan ba . Mama kiyi hakkuri don Allah ba zanyi hakan da kike so ba don wani dalilina . Babawo kai da bakin ka kake fadawa uwarka hakan a kan wanan matsiyacin yarinyar da aka kwaso aka daura ma wahala. Mama rabi wanan abinda kukeyi bai da kyau kuna zuga mama tana abinda bai dace ba don Allah kuyi hakkuri ku fita daga waje mayi magana. Baza a fita nace babawo koni ko ita yau a gidan nan ka zabi daya a wurin nan. Ba zai zabi kowa ba kawu balarabe ne yake fadin haka daga kofa kawu mustapha yace amma dai jimmai kinji kunya dakin santa. Kin gama da gidan yarki kinzo nan suma zaki tayar masu da hankali don baki san ciwon kanki ba. Mama rabi zatai maganaz ya daga mata hannu yana fasin malama ba dake muke magana ba don Allah. Ku fice gidan nan in ba hala ba yanzu hukuma ta futar muna daku gidan. Hukuma ai nafi son kuje ga hukuma ayita ta kare ba aamuje ko ina ba dole ki fita kibar gidan nan yanzu in ba haka ba zakiga ba daidai ba yanzu kin dai sanni ki san halina. Sanin waye kawu balarabe tace kuzo mu tafi ai zamu hadu ku rubuta ku aje sai yar na tabar gidan nan. Kamar yadda mutuwan auren ta yake daidai da mutuwan naki auren ba ke baki da wayau wallahi suka fita suna cacan baki. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:13 - 🀐🀐🀐: ALHAMDULLAHI ALA QULLI HALIM, , , , Jirgin da nake mafalkin shiga yau gani cikin sa saidai bada dadin rai ba don da kunci da takura nake zaune a jirgin. Kujeran mu daya dashi sai dai tun shigan mu jirgin danaji yayi ajiyan zuciya bai waigo inda nake zaune ba a hankali ina tunane da kewan gida bansan lokacin da barci ya dauke ni ba. Barci nake sosai har bansan lokacin da na rankwafo kaina gare shi ba barin abinda yakeyi yayi ya waigo kadan yana kallo mm a gani yayi barci nake kaina a saman kafadan shi. Baison ya tayar dani yasa ya aje wayan hannun shi ya barni ina barcin tare da sauraren saukan numfashi a cikin kunne shi a hankali. Idanuwan shi ya lumshe a hankali tunanen abubuwan da suka faru a gida suna dawo mashi a rai daya baya daya. Ido ya bude tare da danke hannunshi guri daya ba komai yasa shi haka ba sai tuna kalamin kowa a kansa kowa zaiyi magana sai ya furta umar ka rike amanan yar marainiyar Allah. Ido ya kara runtsewa a ranshi yace may yasa suke daureni akan wanan yarinyar hakane ? Shi wani amana a yanzu zai iya rikewa na wani yaro wanan ai wani sabo aiki daddy ya hadashi dashi ga yarinya karama haka under etheety. Wani aure zaizo nan yayi da ita kawai daddy yace rainon ta ya bashi yau daba don daddy bane ba wani mahalukin daya isa ya dora mai wanan nauyin haka a kansa shida ko yarsa mimi bai tsaya ya kula da ita ba yaushe ne zai tsaya duba wata babba can. Shi dai zaiyi kokari yaga ko yaya ya inganta rayuwan yarinyar kamar yadda daddy su ke son yayi din don alkawari ya daukanwa daddy. Dan tabanin da naji anayine yasa na bude idona da sauri dan bansan na dauki awani haka ina barci ba lokacin. Ba tare daya kalleni ba yace ki tashi mun kawo idan zamu sauka sai mun huta zamuci gaba da sauri nayi yunkurin tashi sai lokacin na farga a yadda muke. Ganin ya tashi ya dauki yar jakkarshi yasa nima tashi nabi bayan shi muka sauko daga jirgin binshi kawai nake a baya don ya fini sauri banda lakkan da zan iya jerawama dashi lokacin. Tsuki naji yayi lokacin da yake jan yar jakka na da mamu ta lodamin kayan amfanina a ciki wanda a lokacin ban san may ye acikin jakka bama. Wani guri muka shiga bayan mun fito daga cikin haraban wurin inda naga dakuna a jere ya bude wani daki yace in shiga dakine mai nuna wurin hutawa gado da yan abubuwan bukatan daki. Na zauna a bakin gadon tare da bin dakin da kallo aje jakkana yayi ya fice daga dakin har yakai kofa ya juyo yana fadin zaki iya watsa ruwa idan kina so ki dan huta. Bayan fitan shi na mike tare da duban lokaci nayi ganin lokacin sallah yayi na shiga duk da bansan lokacin da kasan ke sallah ba. Na dai gabatar da sallah azahar bayan na watsa ruwa a jikina sai dai ban sauya kayan jikina ba a daidai lokacin naji ana nocking din kofan dakin wani farin bature na gani tsaya yana dauke da abinci yace miss fatema na gyada mai kai ya shigo da abincin . Bayan fitan shi na kalli abincin ba wani abincin dana sani bane saidai shinkaface kadan sai yawan ganye da tarkace a cikin sa wanda ban taba ganin irin su ba. Kyaman ci naji da kyat na daure nakai cibi daya a bakina babu test din irin abincin mu na gida haka yasa na ture abincin gefe nasha lemo kawai na dan kwanta har lokacin banjin dadin jikina. Wani barcin na danyi sai zuwa yamma muka bar kasan lokacin dare ya soma haka yasa na gyara kwanciyana a jirginn har ban san lokacin da aka tsaya ba. Wani farar fatan mutum ne yazo taron mu da fara,a a fuskokin su suka shaking din hannu tare da dan ruguman hannun baya sun gama gaisawa da ya umar din sai mutumin ya juyo inda nake yana murmushi ya miko min hannun wai mu gaisa. Hannun nasa nabi da kallo kafin in dago ina girgiza mashi kai nabi ya umar da dan kallo naji yayi saurin fadin oh Alex meet my sister fatema . Yace kasa mu a al,adan mu bamu gaisawa haka da fata haramun ne yin hakan gare mu. Juyawa nayi ina fadin kaga min dan iskan mutum kawai nayima kama da yan iska ne da zaka miko min hannu. In kin gama kunkunin kizo mu bar wurin nan yace dani wanan mutumin ya saka kayana a mota don shi dagashi sai yar jakkar dake rataye a kafadan shi yake. Bayan mun shiga motan ne yace dani a harshen hausa zaki nunawa kowa ke kanwatace a nan don su nan basu san matsayin mata biyu ba a wuri su. Ina fatan kin fahinci magana har merry a matsayin kanwata zaki zo mata don a haka tasanki da farko. Ina fatan kin fahince ni cikin dan basarwa nace naji ba tare dana kalli inda yake zaune ba na bashi amsa a takaice nima. Jefi jefi suke kira da mutumin inda hankalina baya gurin su ina can ina kallon gine ginen da bantaba ganiba na ban mamaki. Cikin wani unguwa motar ta dosa da kusan ginan gurin iri dayane ba zaka iya banbantasu sin tsaru wurin kyau kamar ba hannu ya kera ginan ba. Ga furannin da suka kara kawata ginan duk wurin kamar babu kasa titine da grass carpet ko ina sai dogayen itatuwa masu tsawo da suka kara kawata gurin kamar kurmi. Kofan wani gina motar ta tsaya nan naga suna kokarin fita daga motan haka yasani mayar da hankalina garesu daga kallon da nakeyi, Kofan da nake gefen shi ya bude hakan yasa ni dauko dan handbag dina na fito daga cikin motar nima. Kofan gidan naga ya nufa ya danna bell bayan dan wani lokaci sai ga wata mata ta bude kofan dan dukawa tayi cikin girmamawa tana gaishe shi ya amsa mata a daure yadda yake. Ya dan taka ya juyo yana fadin oh sorry Greco meet my sister fatema zata zauna damu na dan wani lokaci a nan. Wace ya kira da Greco ta juyo tana kallona tare dan fara, a a fuskan ta tana min sannu da zuwa . A cikin girmamawa na amsa mata ta karbi kaya a hannun Alex ta fara ja muryan merry ce dake saukowa take mashi sannu da zuwa. What sister in law in this house ta fada a cikkn mamaki bayan munyi arba da juna da dan saurin ta ta karaso gareni tana rungumay ni. Nima rungumay ta nayi yayin da ta sake ni ta juya gare shi tana fadin wani abin mamaki kai mun hakan a bazata. A daidai lokacin ta sake ni naji tace let me guest you name tana tunane sai can tace fatem yeah fatema am i right ? Tana dan dariya yayin da naga ta mikawa Alex hannu kamar yadda ya bukata dani da farko suka gaisa. Yace cikin dakewa she is here for schooling wow sister inlaw will stay here with us ? Bai bata amsa ba ya wuce naga ya nufi hanyan hawa sama ina tsaye ina binsu da kallo mutumin nan ne yace kinsan Omar suna da kyau family su sosai ganin sister din shi na gane hakan dariya tayi naji ta kwalawa wanan matan na farko kira sai gata ta fito da sauri wani hanya tace take her to her room . Matar ta juyo gare ni tana murmushi tace muje ta nuna min dakin da zan zauna . Hjy maryam motar mu na dagawa ta koma part din ta a cikin kunan rai zubewa tayi saman kujera tana haki kafin ta furta shi ke nan. Yanzu ana nufin yarinyar nan taci gaba ke nan ko may yanzu yaran mu da suke diyan gata an zube muna su nan a wullakance sun kare ga auren yaran shago yar agolan gida ta aure umar. Alh bai muna adalci ba a rayuwan mu Allah ya cuta ma rayuwan yaran nan da sauri dayan matan tace ki bar fadin hakan ina hanin ki da furta kalami mara kyau ga auren yar ki. Kinsan abinda gobe zai iya haifarwa gare su shifa ya haifi diyan shi yasan abinda yakeyi ko kin taba ganin inda mutum zai mayar da danshi baya a duniya ya fifita dan wani. Shiru tayi badon ta yarda da zancen yar nata ba taci gaba da kada kafa Allah kadai yasan irin tunanen da takeyi a ranta. Wayan ta dake gefe ne yayi kara ta kasa kallon wayan balle ta daga sai sadiyace tace mama wayan ki na kira fa ta juya ta kalli wayan a lalace tana duban sunan dake kiran wayan. Gani hjy babba a screen din wayan ta fisgi wayan da sauri hannun sadiya tana receiving. Tana dauka hjy jummai tace maryam kin ban mamaki koda yake ba abin mamaki bane don kishiya tayi farin cikin barin kishiya gidan miji. Ace wai maryam baki kirani ba tun da nazo nan ke nan kins farin ciki da barina gidan kema dama nasan zakuyi murna na matsa na baku wuri kuyi yadda kuke so a gidan. Haba yaya wanan abin fa bulalan hanyane fyadi yaro fyedi babba Alh yai muna bake kadai ke cikin wanan hali ba don kowa a gidan nan an fyede shi. Haka dai nake ji daga baya wai har Ikilima ashe a cikin auren ita kuma wani dan kaddaran ya ba ita don duk wanda ya karbi auren yaran mu akan ganganci ne sai ya sako muna diyan mu. Daga kai tayi ta kalli yarta dake tsaye suna kallon ta tace uhumm sadiq dai na shagon kware da kika sani. Hjy tace sadiq sadiq dai wanan miskilin yaron da bai damu da mutane wanan yaron dan jin kai da fadi rai ? Wallahi shi kuwa yaya shi ya hadata dashi yayi son ranshi ga yaran mu kamar bashi ya haifi abinshi ba. Amma ita yar son agolan shi ya hadata da danshi inda yasan zata huta yanzun haka mun dawo daga rakiyan sune sun tafi kin san yau suka bar kasan ai. Wa ya bar kasan kike nufi tace su umar da yar nake nufi mana . Wai kina nufin dai babawo nawa kowa hjy maryam tace wai baki san da tafiyan su bane ko may cab ai sukan yanzu hakama jirgin su ya daga yabar kasan nan watakila. Dif taji ta kashe waya bata kara kallon wayan ba ta wurga gefen kujera tana cewa yannen ta ashe uwar ma bata san da tafiyan su yau ba ke nan ? Ni dai ina horon ki da kikama bakin ki mijin ku kin san yayi kokarin kan yaran nan don ba duka maza zasu tsare maka haka ba maryam. In kinyi duba mutumin nan fa gata yayiwa yaran shi a fakaice a yanzu baku gane hakan gare ku sai nan gaba halin dattakone iri na mutanen da kega maigidan ku wanda mutanen yanzu ke ganin shi wani abu na daban. Uba ko ince iyayye sukeda hakkin zabawa diyan su abokan rayuwa na gari amma boko da zamani ya sauya muna al,adan hakan. Inda ada can baya ne ko kaka yana iyayiwa jikokin shi hakan ko wani daga cikin yan uwan shi yai bugun gaba ya aiwatar da hakan kuma a zauna lafiya babu mai korafi kan hakan. Amma yanzu shida abinshi kuna son nuna mai ba isa da kayan shi ba shi kuma ya nuna maku ya isa da gidan shi. Kuma yayi dacen samun diya na gari daga mazan har matan ba wanda ya musa mai kan hakan. Har ita agolan nashi da kuke ganin yaiwa gata kunsan yanayin da uwarta take ji ne kan hakan babu wata uwa a zamanin nan da za ai mata haka da yarta taso a ranta. Amma da yake tanada wayau bata nuna hakan yai mata zafi ba ta dake ta daure rabar abin a ranta kinga kenan darajanta saiya hauhafa a gare shi. Shine kema nake nuna maki hakan don ba karamin daraja zakuyi a idon shi ba ya sakaku kun bi umurnin shi. Yanzu ita hjy data bijire masa mai hakan ya haifar gareta gashi anyi din kuma bata gidan ita da kanta ta dabama cikin ta yuka duniya sukaji ta. Da tabishi a sannu sai ayi abin salin alim ba wanda yasan abinda dake gudana a tsakanin su amma yanzu mai hakan ya haifar a gareta ? Danka har yabar kasa da matarshi ke uwa baki da labarin hakan yanzu ai duk inda take wanan labarin tafiyan da taji tana can hankali a tashe. Don haka ki natsu kiwa kanki fada tun baki barar da darajan ki da yake gani a idon shi ba har wani dadi kikaji wurinta da zata wani neme shiri dake don kawai ta dinga jin sirin gidan a bakin ki. Idan magana ya fito kiji kunya ya dauka kina ha,intar shine da iyalin shi kece ke kawo rashin zaman lafiya gidan tunda keke tsegunta mata komai. Sauran sukace wallahi hakan ne zai faru shiru tayi tana nazarin maganan da suke fada mata. Hjy jummai tana jin abinda hjy maryam tace ta kashe wayan zabura tayi zuwa falo suka hadu da yayan ta yake fadin lafiya dai maryam tace yaya ni yaran nan zasuyiwa haka ? Sai ta fashe da kuka ta kasa magana hakan yayi daidai da shigowan su hjy rabi a lokacin don nasu iya zama a gidajen su saboda abinda suke kullawa a tsakanin su na ala dole sai sin raba aurarakin nan don manufan su ya cika. Da mamaki suka karaso falon suna tambayan abinda ke faruwa ta kasa fada sai kuka take tana aikawa umar zagi da kyat ta iya buda baki tana labarta masu abindake faruwa. Murya sukaji daga bayan su ana fadin kwarai nine nan na tursasa ma yaron wucewa a yau don wanan irin shiririta naki da hauka da kikeyi. In banda lalace da maida kai baya kin taba jin wanan haukan da kukayi jiya uwa ta dauki kafanta zuwa gidan auren yayanta tace wai sai an sakar mata diyanta ko sarakuwanta ? Jummai na rasa inda hankalin ki da wayauki ya shiga a yanzu yara suna iya kokarin su suga kun zauna lafiya da mahaifin su amma ke kina kokarin kara bata abu. Yaran nan don farin cikin ki a gidan uban su suke wanan abin don sharudan da mahaifin su ya kindaya maki. Amma ke tunanen ki da hankalin ki ya kasa gano hakan jiya suna gidana da dare ni nan da yayan ki gashi nan muka tilas ta mai ya dauki matarshi su bar kasan nan suje nesa dake inda ba zakiji duriyan su ba har zuwa lokacin da hankalin ki zai dawo gareki. Umar dane na gari don a daren jiya yayi niyar sakin yar nan idan haka kike so shiya saba da ubansh. Mu muka hana su yin hakan don barin su aikata hakan abinda zai haifar yafi wanan haukan da kikeyi yanzu karshenta ma ku rasa Alh ga baki daya kinga waya kashe shi bakin cikin ki dake da yaran ki ya kashe masu uba. Kina ganin yaya zasu daukeki daga baya idan haka ya faru dasu bafa zasu yafe maki ba jummai don diya ma suna da hakki akan iyayyen su suma. Don haka nina tilasta mai dole a yau ya bar kasan nan tunda dama komai na yarinyar a kammale yake mahaifin shi ya gama shirin tafiyan su kafin ya aiwatar da komai. Don haka ina rokon ki jummai ki bi abin nan a sannu kada rabo ya kashe ki idan ya rantse don idan kin matsa da wanan fitinan Allah na iya daukanki cikin wanan halin kowa ya huta. Dago kai tayi ta kalle shi tun lokacin daya fara magana a falon yace kwarai kuwa rabo yana kashewa yana rayawa idan ya ratse. Allah ana mashi dolene kamar fa kina jayaya da hukuncin ubangiji ne hakan da kikeyi. Kince baza ayi ba anyi din da ranki da lafiyan ki kin gani kuma ba yadda zakiyi. Kawu tana da yadda zatayi kan tunda ita ta haifi diyan ta ba shi kadai keda iko da su ba ai hjy rabi tace mai. Rufa min baki mara kunya dama zan dawo gareku ai duk wanan abin dake faruwa da jummai da zugin ku takeyin shi. Yar uwarku na cikin wani hali mara kyau maimakon ku bata shawaran kwarai a zauna lafiya sai ku buge da zugata ta bar dakinta ku kuna zaune naku dakunan kalau. Ashe wanan zumuncin munafuncin zamu samay shi a cikin zurianmu kawu kamar yaya munafunci ya dakatar da ita cikin daka mata tsawa yana fadin ke rabi ki fice min daga ido har yanzu ina nan ga Adon da kika sannin a baya. In ba munafunci ba da wani manufa naki zakiga yar uwarki na aikata ba daidai ba ki kara zugata yanzu da tazo ta zauna nan gidan dan uwanku shima so kuke ku kashe mashi nashi auran. Tun wuri jummai kiwa kanki fada ki koma dakin ki kibar biyewa rabi da wanan mai kamar sunlobiya suna kara rikitaki don kyashi da hassada da ta dora a zuciyar ta. Don haka yau din nan zamu je mu zauna da Alh sani yayi hakkuri ki koma dakin ki zuwa dare kuma kada naji kin muda mashi kan wanan zancen kuma. Yaran ki sun san abinda sukeyi kuma suna da biyayya kwarai don sun zabi farin cikin ki sama da nasu ke kinfi kowa sani badon sharadin Alh ba gareki ba babu yadda za,ayi su karbi auren da basu shirya ba. Yayan musa yace kwarai kuwa kawu don kawai suga iyayyen su a tare kowan su ya hakkure ya rugumi kadda ke kanki kin sa da ba haka ba umar da habbin ba akai masu can ba don taurin kan su ke baki la,akari da hakan. Shine har zaki zauna kina shirin yiwa diyan ki baki akan sun zabi farin cikin ki a zauna lafiya su da mahaifi su ? Kiyiwa kanki adalci da yaran ki idan kin masu baki suka lalace kanki kika zalunta jummai ba wani ba don kowa albarka yake sakawa nasa kullun da fatan gamawa da duniya lafiya. Kawu yace fada mata dai dan albarka yayan yace ku kuma kada kuce ko bamu gane manufan ku bane kallon ku mukeyi sarai. Munki magana ne muna kallon ko zaki gano manufarsu a kan diyan ki ki barsu sai dai kassh baki da niyar gano hakan har yanzu. Nikan yaya kun tsaneni akan zancen nan wani manufa nake dashi akan antyn mu yace ki cusa yarki ga umar ko habbib dasu basu san kina yi ba har uwarsu din. Kukan munafunci ta fashe dashi tana fadin an mata kage indai haka suke dauka tabar zancen koma tayi hakan ai ba laifin bane ta karasa fadi tana mikewa tabar falon. Kawun yayi murmushi yace kingani rabi bata da gaskiya harke Rakiya kin san komai amma kika kasa haskawa yar uwarki hanya. Shin in kun rabata da dakinta ko iyalinta ta zauna muna haka a gida riban mai zakuci in yar ku ta kaso auren ta da girmanta ta dawo gida ta zauna muna. Hjy rakiya tace kawu ba haka bane ni naga ai duk gidane wa zanki wazan bari a cikin su amma Rakiya baku kyauta min ba hjy tace. Ku barni inji da abinda ke damuna mana yake gabana mana na fada maku hakan bamai yuyuwa bane tun farko da kuka nuna min hakan ai. Yanzu dai kyawa kanki fada Asma,u karamace a cikin ku amma ta fiku wayau da sanin ya kamata. Don da ita muke komai a tsanake tun tasowan wanan magana itace tsaye ta bangaren ki ita taje ta zauna da yaran nan a madadin ki gidan. Hawaye ta soma tana fadin da wani zanji yanzu da yaran da na kasa fahintar su ko da Alh da ya nuna min dani da babu duk dayane a gidan sa ko da abinda ku yan uwana kukai min ? Yanzun dai a bar wanan zancen mu samu ki koma dakin ki ki zauna cikin iyalin ki shine mafita a garemu yanzu. Ita gurin ta yanzu bai wuce taga ta koma dakin ta ba kamar yadda kawun nasu ya fada in yaso daga baya sai ta san inda ta bulowa zancen. Don har yanzu bawai ta yarda da auren umar da salma bane a cikin ranta don ba zata yarda ta hada zuri,a da fakirai ba tana ji tana gani. In ma auren zaiwa salma ai bata rasa masu sonta ba da aure amma ace wai yau almajirin su shine a matsayin surukin ta haba dai damay duniya yai kama ? Hakama ba zata taba yarda da saka fatima a cikin dakinta ba nan gaba ta zamo mata annoba kamar yadda uwarta ta zamo masu yanzu. Yadda kawun nasu yace haka ya faru sun samu Alh da sun bashi hakkuri yace shi baida matsala fa indai ta amince da bukatan shi a zauna lafiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:13 - 🀐🀐🀐: INA WA YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI MURNA SALLAH UBANGIJI YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA ALLAH YASA MU DACE AMIN HAPPY EID MUBARAK TO ALL MUSLIMS UMMAH πŸ‘πŸ‘πŸ‘ Tun fitan su hjy ban daina kukan da nakeyi ba sai manjo itama ta dauka tana fadin yau yar marainiyar Allah akewa haka ? Idan sun san ba zasu rike muna ita amana ba su bamu ita mu tafi da abin mu don mu bamu gazawa da ita. Su umma suna bata hakkuri ganin haka yasa Addah yi mun fada na daina wanan kukan da nake kada injawa kaina ciwo kokuma so nake manjo ciwon ta ya tashi ne ? Sai kuma ta koma fadin kina wanan kukan haka anya kuwa fatima zaki iya kwatarwa kanki yanci a gidan miji da wanan shegen kukan da kike yi haka. Rarashina suka dinga yi har na lafe na daina kuka suka koma hiran hjy da yan uwanta da suka zo suka kare haukan su sai da suka gaji. Mama saude tace godiya ga Allah yau da bada yaya akazo garin nan ba da munji zance a gurin ta yadda take hassada kan wanan zancen. Umma tace saidai ta mutu don da yardan Allah fatima taci gaba ke nan a rayuwan ta manjo tace Allah yasa, Allah yasa umman Atika. Daga nesa ya tsaya ya kira Murja dax muke tare don itada Atika sune a wurina bata ko leka gidan Aisha ba tunda aka kaimu. A falo ta samay shi tsaye yana jiran fitowan ta, yace kira mun wanan yarinyar da wani babba nata tace fatima yace mata eh a dake kice ina jiran su a falo ya fada fuska a daure. Gabana ya fadi dam da murja ta shigo tana fadin sakon nan dai Addah ta shiruani muka fito tare daga dakin. Yana zaune ya hade hanayen shi guri daya ya dora saman cinyoyin shi tare da dan zakudowa gaban kujeran kadan . Da ganin sa kasan yana cikin damuwan a rayuwan shi ba sai ka tambaya ba ya fada sosao don tashin hankali da yake fuskanta. Yana ganin yace mama sannun ku da kokari ku zauna magana nake son yi daku nace a kiraku samun wuri mukayi muka zauna ina a takure naji yana gaida Addah a mutunce yace bayan sun gama gaisawa. Mama dama nace ai mun magana daku ne don ina son zuwa gobe karfe takwas na safe zamu bar garin nan don gujewa fitutunun da suke tasowa a tsakankanin iyayyen mu. Zan koma bakin aiki na a can inda nake zamu tafi a gobe idan Allah ya yarda don haka a hada mata duk wani abinda take bukata a tare da ita musanman takardun ta na karatu. Sai dai bayan shi ba zamu tafi da komai ba duk a nan zamu barshi idan akwai abinda take bukata za a iya aje mata nan gidan idan watarana mu shigo tayi amfani dashi. Addah tace amma dai za a hada mata tufafinta ko yace har su mama idan munje can zan saya mata wasu sai dai tana iya diban kadan ta tafi dasu din . Gobe karfe takwasa na safe jirgin mu zai daga daga kano zuwa can don haka sai ayi duk wani abinda ya dace don Allah da wuri. Sai in akwai wani abinda kuke bukata a yanzu sai a sanar min a sawo don amfanin ku ko ya fada karshe. Da sauri Addah tace wallahi babu komai sam barka mun gode kwarai a dai rike muna yar marainiyar Allah amana idan kuje can ita kadai muke gani mu tuna da mahaifin ta a yanzu. Insha Allahu kada kuji komai kudai yi muna addu,a don shi muke bukata a gare ku tace insha Allahu. Ya kara mata godiya yana mikewa ya fita a nan ya barmu saida ya fice daga falon muka koma daki mun samu suna jiran dawowan mu suji abinda ke faruwa don hankalin kowa a tashe yake da farko. Bayan mun zauna ne take labarta masu yadda sukayi sai murja tace wai ana nufin har kayan ki a nan zaki barsu ba zakije da komai ba ? Addah tace harsu yace a diba kadan don Allah kada a dauki masu yawa idan sunje can zasu saya sai umma Atika tace a dai saka mata hijjab da zani don sallah a can . A cikin daren nan suka kira mamu suna sheda mata don haka ta shirya mun duk wani abinda zan bukata na tafiya a cikin daren nan. Mamu ta nuna bata san da zancen ba sai dai batayi sanyi a gwiwa ba wurin daukan duk abin da tasa zan bukata a can ta cusa mun su a dan karamin jakkan trolley . Karfe hudu suka tashi kafin a tayar da sallah duk anyi wanka an shirya yana fitowa sallah sukace ya kaimu cikin gida don inyi sallama da mahaifiyana. Wani yasa ya kaimu sai ganin mu akayi mun shigo ashe mamu bata fadawa kowa ba nan dai muka samu kebewa da mamu tace to sayadi zaki shiga sabon rayuwan mai kama da incin kai kamar kuma bauta. Kiji tsoron Allah a duk inda kika samu kanki ki sani aure bautane na ubangiji don Allah sayadi kibi mijin ki sauda kafa ki girmamashi ki bashi hakkin ki daya rataya a kanki a duk lokacin daya bukaci hakan. Ki kula da ibada kada ki sakaci da rikon ibandan ki komai ritsi komai wahala ki rike ibadan ki kada naji wani abu akasin haka daga gare ki . Sauran magana zamuyi a waya idan kun isa don nasan ba zai barki ki zauna haka ba waya ba ubangiji Allah yai maki albarka ya baki zuria masu albarka. Kuka na fashe dashi duk da muryana daya dakushe don kukan dana sha kaina kamar zai tsage gida biyu Addah ce ta shigo dakin ta samay mu har mamu kuka mukeyi tace haba maimuna maimakon ki bata karfin gwiwa sai kuma kema ki zauna kinawa yarinya kuka haka ? Nan ta tsaya tana fadin ai da alama yaron arziki ne don jiya yadda ya nunawa mahaifiyar shi cewa amana yar nan take wirin shi ya isa a gamsu dashi mu dai fatan mu Allah yasa muce gwamma da akayi . Yanzu taje ta sallami wanan tsohuwar idan ta dawo taci wani abu kada tabar gida bataci komai ba ita ta riko hannu na zuwa part din Amma da mamaki muke kallon shi don ba wanda yasan yazo gidan . Kasa na zube kamar bani ba gaban Amma ina hawaye tau A ruwa Allah yayi yau umar zai rabamu dake. Kije kiyi hakkuri kinji a zauna lafiya yi nayi bari na bari manya sukace dashi ake kama miji kada inji ko in gani kin canza ga tarbiyan da muka sanki dashi. Shi dai yana zaune yana shan tea din dake hannu shi ta juya gurin shi tana fadin sadsuki Allah ya baka ikon rikon Amana kaji . A kwatanta adalci ya mike ba tare da yati magana ba yana aje cup din tea din data hada mai a gaban ta yace zamuje mu sallami daddy lokaci yana kurewa. Ya fara fita ya barni a gaban Amma saida Amma taga fitan shi tace ke ki zage kada ki zama raguwa komai ya saki kiyi yadda ya dace idan ya haneki da abu kada ki yarda kiyi shi . Idan kinyi haka kin gama samun kan mijin ki sadauki mutum ne mai saukin kai ga wanda ya fahince shi. Ta miko mi cup din tea din da take sha tace karbi nan ki kurbe duka ki bani kofin shima haka nai masa yanzu don da haka yayi niyar tafiya baici komai ba kada ki yarda kina barin sa da yunwa kinji ko ? Karban cup din nayi na sha ruwan tea din na mika mata kofin ta karrba mikewa tati muka fito tare a kofan falon muka hangoshi yana jiran isowan mu. Tare dashi muka shiga yana gaba ina binsa a baya kawu yana ganin mu ya fadada fara,an shi yana fadin. Har kun fito na gode ma Allah daya nuna min wanan ranan ko yanzu burina ya cika a kanku sadauki ka rike amana kamar yadda kaimun alkawarin rikewa. Yace insha Allahu daddy zan rike ta dauki takardun ta kawu ya tambaya ? Kallona ya danyi nace cikin muryan daya dushe mamu ta hada min duka to Allah yaba da sa,a yasa a dace mukace amin sai ga waya an kirashi ya dauka yana fadin gani tafe Nasir. Nan muka fito sai Amma tace mu sallami hjy maryam haka yasa muka je kofan nata ni kadai na shiga suna zaune da wasu mata da basu tafi ba da gani a nan suka kwana matan. Tana ganina tace fatima lafiya na ganki da sassafen nan haka tare da kashe ni da idanuwan ta duka.. Cikin wani irin murya nace nazo muyi sallama ne maman ikilima zamu tafi tace ina cikin kara fito da idanuwan ta waje don mamaki. Zamu tafi tare da yaya can inda yake aiki gabanta ne yai wani mugun faduwa tace england Fatima kina nufin dake zai tafi ko mai ? Muryan Amma ne daga kofa tana fadin ki fito yarnan jiransa akeyi da kyat hjy maryam ta iya controling din kanta ta fito daga part din ta sai ganin mutane tayi sun cika an rakomu dole ta wayance a furin har bakin mota aka raka mu ina kallo muka shiga baya har kawu yana wurin da kowa na gidan. Ban san Aliyu yana cikin motan ba sai muryan shi naji yana fadin kai amarya kukan ya isa haka mana kamar mun dauko amaryan kwace. Kada tayi shiru mana tayi tayi ta gaji ta kyale a can wa zatayiwa kukan munafunci a nan habbib ne yake fadin haka daga gaban mota inda yake ja. A,a a bros kana jin shi fa ya fara fada maka da mata tun yanzu ? Dan murmushi naji ya sauke tare da dora hannayen shi saman nawa yana fadin ina jin shi ka kyale shi na bashi bashin na yau. A hankali yake murza yan yatsuna alaman yana rarashina ke nan sai dai miskilanci bai barshi yayi magana ba. Wani itin yarrr nake ji har cikin raina yaushe rabo da wani namji ya rikeni haka tun ina yawo da dan buje a cikin unguwa a misau. Mun so makara muna zuwa bami tsaya jiran komai ba a gurguje mukai sallama dasu inda yaya Aliyu yake ce min zanganshi bada dadewa ba zai shigo haka yasa na danji sanyi a raina. Salma bata samu ganin mijin ta ba sai washe gari da baki suka watse a gidan, gidan ya rage sai ita da kawayen ta biyu da suka shigo mata su suka tayata gyara ko ina na gidan bayan tafiyan bakin . Har suka tafi Ahmed bai shigo gidan ba sai wajajen sha biyu saura na dare tana zaune a dakin ta taji motsin shi ya dawo yana rufe gida. Dakin shi ya nufa saida ya watsa ruwa ya fito ya dade a falo tana jin motsin shi sai can ya nufo dakin nata. Kamar yadda yai tsamani zai samay ta hakan ya samay ta kwance a takure a guti daya ya tsaya daga kofa ya karewa yadda take kwance kallo. Har zai juya ya fita daga dakin ganin tayi motsi yasa shi dan dakatawa yana fadin baki barci ba ke nan ki tashi ina falo ki samay ni. Ya dan jima da fitowa sai gata ta fito tasha uban kwaliya sosai kallon ta yayi ya kawar da kanshi gefe daya. Karsowa tayi cikin falon ta dan tsaya nisa dashi kadan ya nuna mata kujera da hannu shi alaman ta zauna. A takure ta zauna din ya dan dauki lokaci kafin yace salma kike ko don ni kin san ba sanin sunan ku nayi ba sosai musaman yaran dakiku din. Dago kai tayi tana kallon shi da mamaki yau ita Ahmed zaice bai sani ba mutum da kusan ko wani sati yana gidan su do yin wani abinda ya shafi gidan. Yace kina mamaki na ko kada kiyi mamakin hakan don ba abin mamaki bane. Tun lokacin da hjyn ku ta nuna bata sona tare da Alh na tsani duk wani dan dakin naku. Din na lura kuma baku son kowa ya rabi Alh don wani tunane naku can na daban yanzu dai va wanan ba don kinci albarkacin mai albarka a wurin na. Ina fatan kin san gidan wanda kika shigo ma,ana kin san ko waye Ahmed dan almajiri kamar yadda hjyn ku take fada ko yaushe. Kamar yadda kika sani sunana dai Ahmed din idan kinga dama zaki iya kirana da Ado Almajiri kamar yadda kuka saba da shi bai taba damuwana ko kadan. Don Almajiri ma mutum ne mafi daraja a wurin mutanen da suka san hakan irin su Alh namu don yasan daraja da mutuncin amajiti kai ba almajiri kawai ba Alh yasan darajan dan adam da ace yaran shi zaku kwaso halayen shi da gidan ku ya zama gidan kwatance a gurin tausayi. Naso ace fatima na aura kamar yadda naso ta tun farkon ganina da ita a gidan Alh badon saboda komai ba don halin mahaifiyar ta dana sani kyawawa. Hjy maimuna mutum ce da tasan yakamata da badon nasan kan gidan Alh ba sai ince uwa daya uba daya ya haifesu ita da Alh din. Dago kai tayi ta kalle shi a karo na biyu yace yes nasan zakiji zafin magana na sai dai yana da nasaba da abinda yasa na zaunar dake nan yanzu. Da farko naso yi watsi da zance auren ki dayazo min a bazata lokacin da nake jinyan rashin fatima a gare ni sai zancen auren ki yazo min kwatsam da rana tsaka banda labarin hakan. Da ace wurin da zan iya gardama ne da na hutar da hjyn ku da tazo gida tana min cin mutumci data san abinda ke raina da batazo ba a lokacin. Hawaye ta fara don tasan komay ya fada mata taci hakan agare shi don ita kanta kafin hankali yazo mata hjy tasha turata tai mashi rashin mutunci. Dan murmushi ya sauke dayaga tana hawaye yace a yanzu kan zaki iya fidda hawaye son ranki sai dai ki kwatar da hankalinki don Ahmed ba maci amana bane ko maimanta alheri don kinci albarkacin Alh da darajan shi a gurina. Ba zan taba kallo ki da ido cin amana ba saudai ina fada maki abindake zuciyana ne a yanzu don ki fake sharudan da zan fada maki. Dan sanyi salma taji a ranta don jin kalamshi yace na karshe yace ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada maki idan kin kiyaye mu zauna lafiya idan baki kiyayye ba mu saka kafan.wando daya dake don dai kin san auren mu babu zancen saki a aure mu. Ns farko dole ne gare ki ki tsabatace gidan nan tunda safe idan gari ya waye haka kuma zaki hada mana abin karyawa kafin in fita karfe tara na safe. A ka,idan gidana ban daukan yar aiki matata itace zatayi mun komai daya shafi rayuwan mu don ta dorawa yarana tarbiyan daya dace. Fuska ta bata don antabota soai yayin da tabi fadin gidan da kallo yace yes haka ra,ayina yake don kinsan ni da kauye ne.. Haka kuma ya zama wajibi gareki ki kare min mutuncin ki yayin da zaki fita ko wani bakon namiji zai shigo a gidan nan ko wanene kuwa. Yasan halinta na rashin son saka sutura masu rufe tsiraici yace wana ke nan ki sani ba a fita ba tare da izinina ba ko nan da kofan gidane. Ki tabbatar da bakin da bn aminta dasu ba kada in gansu a gidan nan don ban zama mutumin banza a gari. Ban son barnan abinci zaki iya dafa duk abinda zuciyar ki ke so a gidan nan muci haka kuma idan kina da ra,ayin wani abu zaki iya fada min kafin lokacin fitana ban son sai abu ya kare ace za a fada min. Ban yarda da yada sirin gidana a gurin wani na wajeba ko waye sirin mu sirin mune iyamu duk ranan da naji wani zance gidan nan a waje ki kuka da kanki don banda dadi idan an taka min doka. Idan kinbi tsarina mu zauna lafiya dake a gidan nan zaki iya zuwa ki kwata don dare yayi yanzu Allah ya bamu alheri ya mike yana kokarin kashe kayan wutan dake falon. Gidan ikilima yan uwa da abokan arziki sun watse kamar yadda al,adan buki ya tanada gida ya rage saura ita da kanwar ta. Ana sallamay isha,i abokan nan shi suka rako shi gidan sun samay su a falo suna hira don ba wani wayewa sukayi dashi ba sosai. Daki suka koma da sukaji hayaniyar su tafe shida kanshi ya shiga ya kira su don suyi sallama da abokan shi dake son ganin ta. Ba laifi don ta dauki dan haske kawu sun dan masu nasiha da shawarwari yadda ya dace da zasu tafi suka aje mata alherin da sukazo mata dashi. Mikewa sadiya tayi tace itama zata tafi yace su sauke ta a gidan su ya dan jima bai shigo ba sai can ya shigo ya rufe gidan. Ledadojin daya shigo dasu ya mika mata fuskanshi a daure tamau don shi mutumne da baida fara,a ko kadan baida yawan surutu. Yana mika mata ya fice dakin tun lokacin bata kara ganin sa ba sai safe da zai tafi masalaci ya tayar da ita ta hanyar bubuga mata kofa. Ya wuce bai shiga gidan ba sai dai har ya dawo baiga alaman ta tashi tayi sallah ba balle ta fito gyara gidan . Har karfe takwas saura ya nufi dakin ya buga ta taso da kyar tana ya mutsa fuska ta bude kofan shi ta gani tsaye ciki hade fuska yace ke kinyi sallah kuwa ? Bansan gari ya waye haka ba ta bashi amsa cikin rashin damuwa da abinda ta fada yace a dan hasale ke wata irin mara hankali ne ? Sallah asuba kice baki san lokacin yinsa yayi ba bari kiji ban daukan wanan shashan a gidan nan ya zama maki na karshe duk lokacin sallah yayi bakiyi sa a lokaci ba sai na saba maki. Ki shige kije kiyi sallah tun kan na saba maki ya juya yana tunane a ranshi lalai mahaifinsu ya fadi gaskiya suna da aiki sosai a gare su gamay da amaren nasu. Bai yarda ya sake mata fuska ba ko kadan hakan yasa ta shiga tsoron shi don umurni yake bata gashi gidan shiru ita data saba da yawan surutu a part din su suna hayaniya da uwarsu da yan uwanta ko yaushe. Wanan zaman shiru din ya fara damuwan ta da zaran ya shigo zata fito daga dakinta tazo ta zauna falon saidai suyi zama kaman kuramay ita dashi bai mata maganan komai har sai ta gaji tayi magana ya basar da ita ba amsa don haka halin shi yake shi a rayuwan shi. Gida;rakiya da habbib an gama komai kamar yadda ya dace gidan ya koma shiru dama shi bawai yasan rakiya bane don da dare suka taba haduwa da daddy ya matsa masu sai sunje sun gana din. Ko yanzu a gajiye ya shigo gidan ga haushin da takaicin abubuwan dake faruwa a tsakanin iyayyen nasu a lokacin tare da tunanen wai yau shine da aje macen da baiso a gidan shi. Ya shigo ba tare da sallama ba don gidan ba kowa ita kadaice a zaune a falo tana kallo cike da tsoro don babu alaman motsin kowa a gidan. Ganin shi tayi murtun da fuska haka ta daure tare da dan mikewa tsaye tana fadin sannu da zuwa yaya tana dan dariyan yake . A dakile ya kalle ta sai dai bai taba tsamanin haka rakiyan take ba a fili yadda ya ganta yanzu tasha kwalliya kyawon ta na diya mace ya fito sosai a fili. Duk da haka yayi kokarin hade mamakin shi wurin amsa mata ciki ciki ya nufi hanyar daki shi ta bishi da dan kallo tana murmushi kasa kasa don tasan abinda suka shirya da mahaifiyar ta. Ya jima a dakin shi tana zaune bata shiga daga ciki ba sai can gashi ya fito da alama wanka yayi duk dadewan da yayi a dakin. Yana saye da three quater wanda da yar riga armless yayi mamakin ganin ta a inda ya barta zaune har lokacin. Yana fitowa ta sake fadin barka da fitowa yaya ya gajiyan taro wanan karon da mamaki ya amsa mata rashin zuciya irin nata. Zama sukayi gaba daya falon ba wanda yai magana a cikin su sai habbib da yazaro wayan shi yana kiran dan uwan shi yaji ko sun sauka lafiya ? Sai dai layin bai shiga ba a lokacin haka yasa shi jan guntun tsuki yana wani layin ya kira saidai wanan karon mace ce yakira da wayan nasa. A yadda take jin suna magana cikin tausassa murya ta fahinci akwai soyayya duk da da harshen turanci suke magana. Rakiya dake zaune duk da taji haushin cin fuskan dayai mata din bata yarda ta nuna hakan ba gare shi. Tasan dama don ya musguna matane yake waya da wata mace a gabanta don taji haushi kuma gurin shi ya cika taji haushin saidai ta yi kokarin shanyewa. Sai da ta bari ya gama ya dauki remote yana chanza chanel ta kalle shi ta mike tana fadin sai da safe yaya . Ya kalle ta cike da gadara yace ke a gidan ku ba a koya maki tarbiyan ba miji ko ruwa bane ? Ta dan murmusa tana gyara gyalen ta kamar bata damu ba tace kayi hakkuri yaya na dauka ai ba zaka sha ruwa yanzu da dare bane ?. Cikin takama yace kinga inba zaki debo min ba kada ki cikani da surutun tsiya don Allah doluwa kawai dakikiya . Allah ya baka hakkuri tace ta nufi gurin da fridge din yake ta dauko goran ruwan da yayi raba har ya gaji don sanyi tare cup a saman fridge din ta kawo mashi. Kallon cup din yayi yace ashe ke sokuwace kasheni kike so yi tun yanzu ba zaki dauraye kofin kafin ki bani ba don cuta zaki bani shi a haka da datti ? Dauka tayi ta nufi kitchen ta dauraye saida ya tsane ta fito ta kawo mashi ya dauka yana wani juya cup din a yatsune ya tsiyaya dan ruwa kadan ya kurba ya aje da gani dama ba shan ruwan zaiyi ba. Dauka tayi zata mayar bayan ya gama habbib ya kalleta cikin kallon tsana yace wama sunan ki kamar wata tsohuwa da suna mutanen da can. Tace sunan kakan mu aka saka min amaryan Amma ance bata taba haihuwa ba har ta rasu ban tabaye ki jin tarihi ba. Idan ina son ji ba kece zaki fada min ba don Amma na da ranta a gurin ta zan iya jin komai ya fada yana mata kallon mugunta. Kina son zama dani a gidan nan ya fada cikin tsare ta da idanuwan shi masu bata tsoro ta bude baki da kyat tace. Yaya kaman yaya ina son zama dakai bayan kuma kaga gani gidan a yanzu tunda , , , Ke ki bani amsa tambayan ki nayi kin amince da wanan hadin da akai muna na aurena dake ? Ta danyi murmushi kafin tace mai zai hana yaya tunda kana dan uwana kuma musulmi kuma iyayyen mu sukai wanan hadin don cikan wani burin su . Tunda ba mu kadai akaiwa wanan hadin ba kowa kuma ya hakkura sai mune zamu nuna masu gazawan su. Ya kura mata ido yana kallon yadda take fitar da lafuza a bakinta karamar yarinya da ita ta iya kinibibi yace a ranshi. Amma a fili sai data gama magana yace good yana kallon ta tare da kasheta da ido saida ta dukar da kanta kasa. To tunda hakane ina son ki sani kin shigo gidan da sai kinyi hakkuri da zaki zauna a gidan nan tare dani don kin taro wa kanki kunci da bakin ciki a rayuwan ki yarinya habbib ba mijin mace bakauya irin ki bane . Yana fadin haka ya mike ta bishi da kallon mamaki ta juya ta mayar da ruwan ta shige dakin ta take ta kira uwarta ta labarta mata abinda ya faru a tsakanin su. Uwar tayi dariya tace haka yace tace wallahi mama tace ki barshi baisan shi karamin dan iska bane sai ya shigo hannu zai gane kuren sa. Shiko daki ya koma yana cika yana batsewa har ya kwanta yana tunanen irin ukuban da zai gana mata a gidan. Aisha da Aliyu basu samu wani matsala sosai ba don da ya dawo gida dakinta ya nufa ya samayta a kwance ganin tana barci ya jawo mata kofan bayan ya gyara mata rufa ya koma dakin shi. Washe gari koda suka tashi ta samu har ya dora masu girki abinda zasu karya dashi a gidan da mamaki take kallon shi tare da rabewa kofan falon tana fadin yaya ina kwana ya amsa a sake yana fadin yan mata kin tashi. Ya dare ya gajiyan buki na shigo jiya na samu kinyi barci harda mafalki kikeyi kina harbin iska. Dan kunya taji ta noke kai cikin hijjabinta tace a shagwabe yaya shine ka fara aiki baka tashe ni ba yace ke rufa min asiri kada su gwaggo su zo suganki da safen nan kina aiki su zarge ni don haka su zaman su yazo da rashin akasi. ZAINAB IDRiS MAKAWA 16/11/2021, 23:14 - 🀐🀐🀐: JUMMA,AT MUBARAK YA UMMAH MUSLIMIN Dakin yana da dan girma sosai sanyin garin kawai ya wadatar da mutum balle na dakin kuma haka yasa ni takurewa a wuri daya. Tunawa nayi da sallah nayi zubur na mike da lalube na gano bandakin kallon tsaruwan shi na dan tsayayi kafin in karanbanin taba wani wuri da nike zaton nan ne makunnin ruwan sai ga ruwa ya zubu daga dan wayan dake makale a wurin. Wanka na fara tare da dorawa da alwala na fito ban san satin gabas ba dan tunane na tsayayi sai na tuno na fara ina cikin sallah merry ta shigo dakin ganin yanayin da nake yasa ta juyawa ta koma zuciyar ta cike da tunanen irin akidar mu. Sai lokacin na bude kayan troller dina na dauko wani bakin dogon riga mai shap na saka tare da hijjab dina fari na tayar da sallah. Na dade zaune a gutin ba zance banjin barci ba don nayi a jirgi haka kuma bai hanani jin wani barcin ba. Mikewa nayi zuwa gadon na kwanta banjima ba barci ya daukeni kuma na jima ina barci ban falkaba sai sha dayan rana jin motsin mutum kusa dani yasani bude idanuwana. Merry ne zaune a bakin gadon tana sake murmushi a fuskanta haka yasa na yunkura na tashi zaune ina gaida ita. Tace kinsha barci tashi kici abinci rana yayi a hankali na yunkura ina kokarin saukowa saman gadon. Kusan a tare muka fita falon tun fitowan mu na hangoshi zaune yana cin abincin shi hankali kwance. Yana saye da yar rigan da kamar yana dasu da yawane don kala kala yakan saka wani lokaci. Yauma sin saye yake da bakarta a jikin shi sai wando milk color a kasan shi ya zauna yana cin abinci a hankali. Saida na karaso inda yake na kai rusunne nace yaya ina kwana ya amsa min ba tare daya juyo inda nake ba yaci gaba da cin abincin shi. Wuri ta nuna min in zauna itama ta jawo kujera ta zauna tanacewa yarta oya come and pray before eat. Sai yarinyar dake wurin mahaifin nata tana mashi gwalanci umm kawai yake amsa mata dashi da alaman ko cikin iyalin nasa haka yake bai da sakewa. Uwar tace oya close your eyes sai yarinyar ta rufe idanuwan ta uwar nata gwalanci adduan su yarinyar nacewa Ameen kamar yadda uwar tace ta amsa. Sun gama ina zaune ina kallon su tace fatema eat now dan murmushi nayi na kai hannuna ina diban abincin a hankali sai dai na kasacin don kawai abincin ban ma taba ganin irin shi ba. Da dai ta matsa min dole na dan kai abakina ina taunawa a hankali kamar ansani ci dole. Shi ya fara mikewa har ya dan taka ya juyo yana fadi da hausa idan kin hda takardun ki kiba merry a san inda za,a saki. Ya juya wurin merry yana mata bayani ina dan tsuntan abinda suke fadi saboda turancin su jin shi nakeyi kamar na turawan gaskiya dan kwaraiwan da sukayi dashi. Ina gamawa na mike don merry tana waya a lokacin yar tasu ta kura min ido hannu na mika mata alaman tazo sai ta noke jikin uwarta. Juyawa nayi na fara tafiya ta katse wayan tana fadin Ina zanje nace zuwa zanyi in dauko takardun nawa . Ki dawo ki zauna wanan barcin gajiyan yayi yawa haka nayi dan murmushi na juya zuwa kujerun falon na zauna saman daya. Ta taso itama zuwa wurin kujerun tana fadin ina that your grandma da step mother nace sunce a gaida ke. Tace ki sake jikin ki yayan ki ya fada min baki so zuwa ba shiyasa na ganki haka ki kwantar da hankalin ki you should feel free here nan ba mai takurawa wani ko kadan irin can. Kowa yana da incin kansa a nan zaki iya yin duk abinda ranki ke so kiyi babu takura zaki san duniya idon ki zai bude sosai. Dan murmushin yake na karayi don jin abinda take fadi din haka hiran namu dai sama sama mukayi shi don ita ba hausa take jiba ni kuma ba wani turanci sosai nake ji din ba. Abincin rana ba wani abinci bane don da safe sai dare sukafi ba abinci muhinmanci koda ta dire min snack da tarkacen kwalama a gabana . Kallon abincin nayi ina bata rai tare da kai bayaba a saman makarin kujeran da nake zaune. Curious tace may ke damun ki gajiya ko yunwa tana kallona tace you can cook any delicious you want. Da mamaki na dago kai ina kallon ta ta daga min gira ta daga min tana fadin kin san ku yan nigeria kun saba da cin abinci sosai. Ban san lokacin da murmushi ya subuce mun ba a fuskana don ji abinda ta fadi din. Tace yes haka kuke cin abinci matan ku na zama manya da sun fara shekaru mana may kuke kiran sunan wanan abincin da step mum ta ke yawa muna ? Na gaji da zama na mike zuwa ciki sallah nayi dan da lokaci nake amfani don ba kiran sallah ba komai a garin . Gashi tun safiyan zuwan mu ban sake saka shi a idona ba sai da merry ke waya nake jin wai ashe yayi tafiyane bai garin. Duk zaman garin babu dadi duk son sanin wanan kasan da nakeyi yanzu da nake cikin shi sai naji duk garin ya isheni shiru ba abokin hira ba wani motsa jiki ko kadan. Yau tun safe dana tashi naji ina son zagaya gidan har girkin abinda zanci nake son yi a ranan. Bayan na gama shiryawa na fito a hankali nake dan takawa ina bin ko ina na gidan da kallo sai dai inda nagani a rufe ban gigin shiga gurin. Hankalina ya dauku ga kallon wasu gumakan dake zubo ruwa a tsakiyan gidan jin muryoyin su ya dawo da hankalina daga kallon da nakeyi. Merry ce ke magana kamar a fada yana tafiya tana fadin don may zaka kaita wanan school din na fadama wanda na zaba mata yafi dacewa da ita. Ka tuna yarinyar tana da kamar baiwa a tare da ita ya kamata ace baka damu da akida ba ko wani abu tunda karatu ne ya kawota nan dama ai wanan rashin adalci ne ta karasa fadi. Why merry why zance ga abinda za ayi kina kawo naki ra,ayin akai yarinyar nan fa yar uwatace ina da right din zaba mata abinda nake so daidai da ita. Tace ok yanzu na fahince ka ra,ayin ka kake so kai bana wani ba ka nuna min cewa yar uwankace kai kadai. Merry stay away from my family issue nina san mutanen mu nasan halin su fiye da sanin ki. Tace a fusace Am i not your wife Omar don haka ina da right din shiga maganan yan uwan ka idan ya taso. Merry why are you disturbing me about dis isue na fada maki ra,ayina Muslim college na zaba mata final ya fada da karfi cikin anger yana wucewa. Binshi tayi da kallo da jajayen idanuwan ta da suka rikide mata ta takowa nayi zuwa inda take tsaye sai lokacin ta ganni tayi kokarin saita kanta lokacin. Fatema kina waje ashe kinji mu muna rigima da yayan ki kan ya kaiki makarantar da zaki waye ki san duniya. Ban san may yasa ku musulmai kuke da akidan son addinin ku ba har cikin zuciyar ku baku duban goben ku sai abinda addini yace daku. Wani kallo nake mata dan na kasa mata magana saboda ban san abinda zance da itaba wanan lokacin. Ta kama hannun yarta tana fadin fita zamuyi nima zan koma bakin aiki na don kin san ba a nan nake aiki zuwa nakeyi in danyi kwanaki a nan. Shima naji yana fadin ba a gidan nan zaki zauna ba zaki koma can central London don yafi maki kusa da school. Daga haka tayi man sallama ta fice kitchen din su na nufa nan na samu masu masu abinci maza guda biyu na gaida su da aiki. Suka amsa mi tare da tambayana idan ina son wani abune nace abincin gargajiya irin namu nazo dubawa idan akwai shi. Da sauri bakan fatan yace min akwai su bari a duba maki idan basuyi expearing ba don su ka,idan su ne sai an duba abinci kafin amfani dashi. Nayi mamakin ganin ledojin abincin dake can sako an ajesu dagani ba a amfani dasu ko yaushe. Dubawa nayi daya bayan daya ina karantawa garin doya na dauka don sai naji sha,awan cin sakwara ranan duk daba cimana bane a gida. Sosai na tsaya nayi aiki shi don naga yadda mamu take tukawa kawu idan yace yana son ci sai dai tasu baikai wanan laudi ba da haske. Miyan ganye nayi don na samu ganye a cikin fridge din su nama daine sai dana tambaya wanan dan aikin bakar fata ya nuna min wanda ogo yake ci nan na gane naman halal ne naman tunda har ya ware na amfanin shi. Kamshin girkin mu daban yake haka yasa gidan ya dauki kamshi na gama a daidai yamma yayi masu gidan sun dawo. Sai da suka dauki lokaci kafin su fito nima wanka nayi nai sallah na dan saka wani riga mara nauyi tare da daura gyalen shi saman kaina. Na fito da zuman cin abincin dana girka sai na samay shi zaune yana yankan loma hankalinshi kwance. Da dan mamaki nake kallon shi kamar baisan ina tafe ba don baiko dago kai ba don jin tafiyan da yayi shawaran juyawa nayi in koma har ya gama don gaba daya ya juye min kamar ba ya umar din dana sani bane a yanzu tun zuwan mu kasan. Muryan shi naji yana fadin ke zo nan na juya na dan kalli bayana koda wani yake magana ganin babu kowa a kusa yasani matsawa kusa dashi kadan. Sannu da dawowa nayi mai yace ba tare da ya amsa gaisuwa naba merry ta gaya maki zuwa jibi zaki wuce makaranta. Kamar ince bata fada min ba don ba ita ya dace ta fada min ba sai dai a yanzu tsoron shi nakeji sosai. Kaina girgiza mai yace bakiji bane ana magana kin kyale mutane nace a cikin wani murya bata fada min ba kamar a shagwabe. Yace zaki wuce an gama komai na tafiyan ki kamar yadda daddy ya bukata ai maki don haka har gidan da zaki zauna na tanadar maki shi a can da komai yadda ya dace. Idan kinga wani abinda bai maki ba zaki iya magana a kawo maki daga baya do haka ki fara shirin tafiya ke nan. Nagode Allah ya saka da alheri nace ya dan dago kai ya kalleni ya kawar da sauri yana fadin ki mayar da hankalin ki ki kuma tuna da matsayin ki a can saidai bai fadi wani matsayi zan kula dashi ba . Shin matsayina na musulma ko matsayin matar aure dana zo dashi kasan zan kula ko may oho ? Na kara yunkurin juyawa zan wuce yace ba abinci zakici ba zauna kici abinki nina gama cin nawa. Ya mike tare da daukan tissue yana goge bakin shi ya bar wurin cikin tafiyan shi na izza da kamar sallo. Ajiyan zuciya na sauke ina rayawa a raina wani lokaci kagan shi kamar mutumin kirki amma a zuciya baude yake ko iyalin shi bai raga masu ba ni yanzu ba zance ga halin shi na gaskiya ba. Don wata rana nakan ji sanyi wata rana kuma ya juye min kamar mara imani haka yasa na kasa fahintar yaya halinsa yake na gaskiya. Zama nayi na zuba abincin ina ci sai ga merry ta fito daga dakin su tun daga nesa na fahinci yanayin ta yau ba dadi. Samu wuri tayi ta zauna tana kallo abincin da nake ci din take tambaya waya hada abincin nan haka ? Nace nice na girka da kaina nunani tayi da baki tana fadin you will become mumu very soon. Tana gwada yadda zan koma da hannayen ta abinda ya dan sani murmushi sosai ke nan. Kara kallon abincin tayi tare da fadin naga alaman kinji dasin wanan abincin sosai yadda naga kina cinsa yau da yawa. Kai na gyada ma ta fara bude kulan abincin su sai taga ba,a taba ba da mamaki a fuskanta take tambayana brother din ki baici abinci bane ? Nace yaci sai ta kalli abincin nawa da ido ta kuma maida hankali ga plate din da yaci nasa tace i understand now wanan da kika girka yaci ke nan. Nan suka fara adduan su na gwalanci ido rufe ita da yar ta danaji tana kira da paith. Bayan sun gama ne ta fara diba zata ba yar sai yarinyar ta girgiza kai why paith ta tambayi yarinyar ? Mum i dont want to eat dis ta nuna nawa da hannun ta tace wawoo you means wancan zakici ko may ? Ba tare da nayi magana ba na jawo plate na dan zuba kadan na tura mata gaban su yarinyar ta fara murna tana nuna abincin da hannun ta. Ina tsakuran abincin ina kallon yadda yarinyar ke amsan abinci a hannun uwarta tana ci. Can merry ta dago kai tace brother din ki yace tafiyan ki next tomorrow ne zaki zauna a centeral London. Naso ace ya barki gida tunda zaki iya zuwa daga nan kullun duk da dai wurin yana da nisa da nan inda muke. Anyway hakan ma da yayi yana da kyau don zakifi maida hankalin ki ga karatun ki saidai banso wanan school daya zaba maki ba don komai su a addinence suke abinsu. Naso ya kaiki inda kanki zai bude ki waye sosai ki koyi mu,amula da mutane kala kala a duniya . Zakiji dadin rayuwan ki idan kin je gurin saidai shi har yanzu yana da wanan kishi na islama a zuciyar shi. Ba laifi ko can zaki waye din don zaki koyi abubuwa da dama dangane da addin ku saidai ni ba hakan naso dake ba. Yadda kike Queen din nan ya kamata ace idon ki yafi nan budewa sosai koda zaki koma gida suga kin canza daga yadda suka sanki a baya. Dan murmushi na sakar mata kafin ince ko wanan ma nagode don yaga ya dace danine ya kaini can ban faye son abin wayewa ba kwarai tace see you. Tunda naji zancen tafiyan na fara shirin a tsanake don dama har lokacin kayana suna a yadda mamu ta saka min su ban taba ba. Ina kewan gida sosai a raina saidai ba yadda zanyi don ni nawa kaddaran auren a haka yazo min zama kadaici yana min yawa saidai in fita dan wani hili dake bayan tagana daga dakin zaka iya tsayawa kana kallon ko ina na garin. Ina kwance a dakin da dare sai gasu sun shigo ita dashi ina ganin su nayi yunkurin mikewa zaune. Gaida su nayi merry ta amsa min da kyat itama wani kati ya miko min nasa hannu na karba yace wanan Oyster din ki ne don saukin tafiya guraren da kike so zuwa katine na shiga jirgin kasa ta wanan kasan. Duk wani sauran abinda zaki bukata yanzu akwaishi a gidan zakiyi registration idan kinje Aaliya Arnall ki maida hankalin ki kiyi abinda ya kawo ki nan ban son wasa ko hurda da abokan da basu dace ba ki tsare . Kudi ba matsalan ki bane don a kwai komai da zaki bukata a wanan katin ya sake miko min wani karamin katin na kudi. Gobe merry zata kaiki idan ta dawo zata wuce itama gidan zai koma ba kowa ke nan sai masu aiki. Har ya juya na furta nagode Allah ya rufa asiri nasan dama ba zan samu amsa ba na dai fada ne saboda sabo da hakan. Mikewa merry tayi ta bi bayan shi ba tare da taimin magana ba suna fita na sauke ajiyan zuciya ina bin katin da kallo tare da fadi a fili wai wanan kudine don Allah. Alam din agogon dakin ya tayar dani daga barci hakan na nuna min asuba yayi ke nan tashi nayi na fada ban daki nayi wanka tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah gari dip ba wani alaman lokacin sallah yayi saidai mutum ya ksatanta kawai. Nockin din da naji anayine yasa na mike a raina na dauka merry ce koda na bude shine a tsaye da sauri nace dashi ina kwana yaya ? Lafiya yace tare da fadi a lokaci daya kin shirya ko nace eh yace ga usman nan zai shigo ya daukar maki kayan ki ya fadi yana daure fuskan shi. Juyawa nayi cikin dakin na karewa dakin kallo ba abinda na bari mallakina a dakin saidai nasu ban taba komai daga cikin abinda na samu a gidan ba. Shiya ja motan kai tsaye zuwa unguwar dayace din tafiya ne mai nisa sosai a tsakani na yarda central London muke bayan nan kuma wai a acition town gidan yake (lahore). Gidane mai bene daya kamar sauran yawancin gidaje unguwar dauke da dan get da garden da garge gidan nada dan girma dakuna hudu ne sai kitchen da dan hilin shan iska a waje da falo mai dan girma irin dai gidajen su na can komai na gidan neat. Bayan ya gama nuna min komai mun fito daga gidan sai makaranta don yin registration ba wani nisa da gidan don koda kafa zan iya zuwa kuma in dawo. Sai da yaga komai ya kammala ya dawo dani gidan tare da tambaya ko akwai wani matsala kuma ? Cikin nuna alaman ya gaji shima da zirga zirgan da mukayi din lokacin . Nayi raurau da idanu na fadi a sanyaye ba komai saidai yaya ni kadai zan zauna a wanan gidan kuma ? Kina tsorone ya tsareni da idanuwa yana son jin amsa ban iya bashi amsa ba nayi kasa da kaina kawai. Gyara tsayuwan shi yayi yana fadin ki saki ranki kiyi karatu yadda ya dace daddy ya fada min likita kike son zama. Koba haka bane na gyada mai kai alaman eh yace to baga shi kin samu ba har zaki fara karatun ki . Zan dinga zuwa ina dubaki idan ina gari abinda nake so dake kawai ki maida hankali ta yadda daddy da maimuna da sauran iyayyen ki zasuyi alfahari dake nan gaba. Kinji ko wanan unguwa yana da tsaro sosai fiye da ko ina a cikin garin nan don kuna kusa da birnin sarauniyan kasan . Ina kallo ya ja motar shi ya bar gurin har ya bace min da gani ajiyan zuciya na sauke nabi gidan da kallo ina mamaki a raina wai ni kadai zan zauna a cikin sa. Tsoro yasa na rufo get din gidan a hankali naja kafana zuwa cikin falon kamar wace za a kama har nakai tsakiyan falon naja na tsaya wuri daya ina bin ko ina da kallo. Komai akwai na more rayuwan dan adam a falon takawa nayi zuwa kitchen din daya nuna min din. Fridge din kitchen din na nufa na bude ko zan samu wani abin sanyi koda ruwa ne in sha a cikin sa. Tab yake da kayan shaye shaye da sauran tarkace na girki lemon gwangwani dana gani nakai hannuna dauka tare da rufe fridge din na fito. Falo na dawo na zauna na bude lemun ina kurbawa a hankali cikina ya fara karan wahalan yunwa don samun dan wani abu daya shiga mai yanzu. Ina gamawa na tuna banyi sallah ba ko a zahar ga la,asar ya nuna lokaci dakin daya nuna min shine matsayin bed room dina na nufa a hankali na haura saman nan ma na tsaya ina bin ko ina da kallo. Alwala nayi na fito na tayar da sallah bayan na idar na dade zaune ina rokon Allah kariya daga duk wani masheran cin abun da zanyi karo dashi a cikin wanan kasan. Bayan na idar na mike don gyara kayana cikin wardrobe din dana gani a dakin ina budewa sai da gabana ya fadi. Tufafine ciki a jere wanda babu kalan da babu daga dogon rigar abaya zuwa english wear da pakistan komai a natse tsab. Zaune nakai bakin gadon ina kallon kayan cikin mamaki da firgici a raina sai lokacin na kula da saman mirrow din dakin kuma, Mayuyuka shafine da su turare da sauran kayan kwaliya irin na mata a saman table din mirrow din. Mikewa nayi daga inda nake zaune da sauri na karasa wurin ina duban kayan a hankali. Hatta su pad da duk wani abinda zan bukata an ajiye a gidan don bukatan mutum komai ke nan saida ya tanadar min shi kafin inzo. Fitowa falon gidan nayi na zauna shiru ina faman tunane can dai na mike don samawa kaina mafita kitchen din na koma ina bude bude naga abubuwan bukata na abincin nodles na dauko irin hadin mu nayi na gama na zauna naci saida na koshi. Wanka nayi tare da sallah na haye gado na kwanta don banson makara da safe don farkon zuwa nane ga dokin da nake faman yi a raina. Ranan wednesday na fara shiga school kowa ya ganni yasan bakuwa nake farkon zuwa na ke nan don irin yarda nake nesa da mutane. Sosai na mayar da hankalina ga karatu Alhamdullahi kuma ina fahinta da kyau shida saura na iso gida don takowa nayi da kafa don inkara garin da kyau duk da ashe akwai dan jawa kadan tsakanin mu dasu. Tun ban saba ba har na saba da safe zan tafi a mota don gudun makara idan zan dawo kuma nakan tako da kafa don in dan motsa jikina. Ranan da ba karatu kuma haka zan wuni da kewa gida a raina idan zama da tunane ya isheni nakan fito ina zagawa cikin unguwan don debe kewa. Ban manta da karatuna na addini ba don nakan dan taba idan ban komai kuma makarantar suna da kula wajen koyar da ibada. Saiko kallo dana koyi yi yanzu saboda zaman kadaicin da yake min yawa ni dai gani nan zaune a kasan mutane ba wanda na sani sai Allah sai ma,aikin sa. Tun ranan daya kawo ni wanan gidan daga shi har merry ban kara jin durinyan kowa daga cikin su ba, har tsawon sati uku ni kadai ke rayuwa na tun ban saba ba har yakai na saba da hakan yanzu. Zama ni kadai baya damuna sai dai rashin waya a tare dani yanzu ne nasan matsalace rashin waya a tare da mutum. Gashi dai gidan babu abindana nema na rasa na rayuwa zan ci mai kyau in saka mai kyau in kwana wuri mai kyau. Amma kadaici ya hanani jin dadin hakan sosai sai yazama har na fara yar rama saboda damuwan dana jefa kaina a ciki. Yau ina shawan saka irin tufafin mu na hausa don haka na dauro zani da riga da sai hijab dina dana dora saman kayan. Abin kallo na koma a wurin mutane wasu har waige na sukanyi idan na wuce su niko hakan bai damay ni ba don ban ma san sunayi ba. Gurin sallah na fito ina sauri in koma lectures karshe da zamuyi ranan naji ance Am i dreaming ko gaskiya ne ? Jin ana magana da hausa yasani dago kai inga ko waye nayi mamakin ganin wanan the guy din na makarantar dana kare a kano. Rabo dana kara ganin sa tun suka kare karatu dasu salma ban kara jin duriyan shi ba sai wanan ganin danayi mashi. I can,t believe that faiting girl in my former school wai kece ko dai kamace ya sake tambaya ? Dan murmushi kadan nayi mai tare da fadin an wuni lafiya ashe kana nan kaima ? Yana kokarin takowa inda nake ya kara girma kyawon sa ya kara fitowa ya goge sosai yanzu Ya matso yana fadin yaushe kika shigo don ban taba ganin ki ba sai yau bai kamata ki min haka ba ai a kalla zaki nemi yan uwan ki yan nigeria da kika shigo. Nace bai zama dole hakan gareni ba don ni matar aurece a yanzuban son yawan shiga mutane don kare kaina daga zargi. Ya lumshe ido kafin ya bude yana nunani da yatsan hannun shi sai kuma ya bushe da dariya yace wa zakiwa karya kamar ki zakice wai wani ke mai aure ce a yanzu. Nace wani kama ke gareni ni ba mace bace wallahi ina da aure shiya kawoni kasan nan ma. Sai naga yaja numfashin shi ya dan natsu yana min kallon mamaki kafin yace. Na yarda tunda kince wallahi kuma naga canji sosai da ya nuna hakan tare dake ki yarda dani ni musulmi ne kuma dan kasan ku don haka zamu zama kamar yan uwa anan yanzu. Naja numfashi gami da saukewa nace kana ganin hakan zai yuyu bayan kai ba muharamina bane ? Kasan anything can happen idan an fahincin hakan tare damu yace ki yarda dani babu abinda zai faru believe me zai koma magana . Nace nagode zan shiga lactures yanzu zamu hadu wani lokaci yace anyway ba matsala ki kula da kanki nan na wuce na barsu tsaye a gurin . ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:14 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , , , Wasa wasa na share kusan sati shidda banji duriyan kowa daga wani bangare ba gashi banda lamban kowa ko waya babu a hannu na na koma kamar marainiya a ari mutanen da banda uwa banda uba balle wasu yan uwa najini a tare dani. Yau na dawo a daidai lokacin da nake shigowa gidan sai dai abinda ya ban mamaki tun daga waje shine ganin sayun shigan mota a gidan. Da mamaki na karasa ciki sai dai gidan yana a kulle kamar yadda na barshi sai mamakina bai kare ba lokacin da nayi arba da wasu takardu a saman table din falon . Ban bi ta kan takardun ba ciki na shiga da sauri in duba ko an min sata a gidan na samu kayana tsab ba abinda aka taba min. Sai na sauke numfashi na aje jakkan dake hannuna saman gado na numfi bandaki don in kewaya. Alaman wanka naga anyi a bandakin ruwa a ko ina bai gama bushewa ba gurin a tsorace nayi abinda zanyi na fito ina mamakin waya shigo gidan bana nan ? Wake da key din gidan bayan ni haka na kwana tsorace ga yunwa ga tunane saida safe na dan dafa shayi nasha na fita zuwa school. Inda yanzu na fara fahintar komai banda matsalan karatu komai na zama min a kaina idan na dauka. Duk da rayuwan London yana cike da abubuwan mamaki da debe kewa na zamani da debe kewa sai dai duk basu a gabana a wanan lokacin. Na zama kamar kanwar the guy wanda yanzu anfi sanin shi da Yusuf bin Abdoulah shi kadai nake gani inga kamar naga wani na gida nawa. A hutun farko da muka samu bayan share watani uku muna daukan kararu mukaje hutun karshen zago. Sai lokacin na shiga damuwa sosai ni kadai a gidan ba fita ko ina daga inyi wanka inci abinci inbi lafiyan gado in kwanta ko in kunna kallo ko kuma indan fito wajen gidan ina kallo abubuwan ban mamaki. Ina zaune a falo bayan na gaji da barci na fito don in samu abinda naci jin kara bude daya kofan dakin yasa da sauri na dago kai na kalli kofan. Ya umar nagani ya fito yana saye da yan kananan kaya waya a hannun shi yanayi ya nufo falon gidan a inda nake a zaune. Ido na zuba mai da mamaki har ya karaso falon ya zauna da hannu yai min alaman in kawo mai ruwa har lokacin bai bar wayan da yakeyi ba din. A cikkn sayin jiki na mike zuwa kitchen don na dauko mai goran ruwa na fito daga kitchen din duk da ina gida ni kadai ne hakan bai hanani dan saka kaya mara kyau a jikina ba don ma dai din banda shi a gidan ko banza duk kayan dake gareni na kwarai ne tun zuwana garin. Ya zuba min ido yana wayan kamar mai kallon style din jikin rigan dake jikina din tunda na sanyo kai falon gaba daya ya tsura min idanuwan shi har saida na tsargu da kallon da yake min din. Nazo gaban shi na aje goran ruwa da cup saman table din na juya zan bar wurun sai lokacin naji yai magana a cikin wani yanayi daba zan iya fassarawa ba lokacin tsawa ne ko lalama oho ? Wa zai zuba min ruwa da kika aje min haka ya fadi yayin da yaci gaba da wayan shi hankali kwance. Hakan yasa nazo gaban shi na dan duka na tsiyaya mai ruwan cikin cup na aje a gaban shi ina zubawa na mike na bar wurin. Kai ya dago ya bini da kallon mamaki tankar wani wanda yaga abin mamaki a tare dani kitchen na nufa dama yunwa ya fito dani falin na zauna kuma ina tunane ? Ina cikin tunanen abinda zan dan dafa inci naji muryan shi daga kofan kitchen din yana fadin watau haka kike zama da yunwa don lalaci ba zaki dafa abinda zakici ba ? Sallon daddy yace na kawo ki garin mutane na bar mashi ke da yunwa ko ? Idon daya kashe ni dashi lokacin yasani saurin dukar da kaina kasa har lokacin ban iya koda gaida shi ba. Ganin banda niyar magana ya juya ya fita na dauka ya tafi ke nan don ni fanin shi bayan mamaki sai tsoran shi ya kamani don ina mamaki yaya yashigo min gida bada masaniyata ba haka ? Na dora ruwa ina kokarin ciro nodles in bare sai naji shigowan shi gidan again leda ya aje min tare da fadin ki fito ki zuba min nawa don yunwa nake ji kada ki bata min lokaci. Nazo a hankali na dauki ledan na koma kitchen dashi na bude bread din alkama ne irin wanda ake ci da source a kasan. Na dan dade tsaye ina kallon bread din don ban taba kokarin cinshi ba asalima nafi bukatan in dafa da kaina inci saboda tsaron addini na kada inzo inci abinda ba halal ba. Na dauko plate masu kyau na shirya masa nasa na nufo falon dashi yana zaune hankalin shi a sytem din shi kamar wani mayen na,ura. Naso in share shi in aje kawai in wuce sai dai dana aje na dan tsugunna daga gefe nace ya sannu da zuwa ina kwana. Da kai kawai ya amsa min da uhumm na juya zan shige inda na fito naji muryan shi yana fadin wani yaro ne kike yawan tsayawa dashi a school din ku wani lokaci ? Cikin mamaki na dago kai da sauri na dan kalleshi ganin niya tsurawa ido yasa na dukar da kaina da sauri ba tare dana bashi amsa ba. Ya sake fadin bakiji bane na tambaye ki sai da na tsaya nadan yi dan tunane don ni na manta da zancen yusuf a raina sam. Ya fadi a tsawace nace wani yaro ne wanan ya zubo min idanu sai kace wani tsohon zaki can dashi. Nace ni ban san wani wanda nake kulawa ba a school din mu sai dai idan sheri za ai min yace sheri cikin mamaki sheri fa ? Wa zai maki sheri ni ko wa zai maki sheri zaki fada mi ko sai na bata maki rai a gurin nan ? Innalillahi nace a fili wallahi yaya ban san wanda kake magana a kanshi ba asalima niko kawa mace banda ita a makarantan balle wani na miji can . Wa ya baki coffee da kika fito sallah ranan gabana yai mugun faduwa na dago kai da sauri nace yusuf ne . Dan makarantar mu ne tun a Nigeria shine muka hadu dashi a nan yana daukana tankar kanwar ce a nan ko magana bama yi dashi. Asalima ranan na samu sun sayane sai gani ya miko min sai nayi shiru yace da yake ke mabukaciyace lalaci ya hanaki ki girka a gida kika fita da yunwa ko ? Nace a cikin laushin murya idan hakan ya bata ma rai kayi hakkuri ba zan sake ba in sha Allahu. Kasa magana yayi duk wani fadan daya kulla zai mun sai kuma na bashi tausayi don bai tsamaci karaya haka da sauri a gurina ba a yadda ya sanni fitsarariya. Bread din da baici ba ke nan ya mike cikin fushi ya bar falon ina jin tayar da motar shi ya bar gidan ban damu ba tunda nasan banyi komai da yake zargina ba akai. Zama nayi inda ya tashi na fara cin bread da source din daya bari gurin rana banci abinci ba sai ruwa danayi ta sha ranan sai yamma na girka abinci naci. Tun wanan ranan na gane wanan bread na alkama ban yarda in rabu dashi a gidan dama na gane masuyi din musulmai ne yan pakistan sai na kara mayar da hankali gutin cin sa sosai sai ya kosar dani har yamma. Ranan na dauka zai dawo sai dai ban sake sa shi a ido ba nima hakan bai damay ni ba ko kadan. Kwance yake mike saman dogon kujeran dake karamin falon su yana nazarin wasu jirage da suke so gyarawa a kasan Dubai. Sai dai yanayin kwanciyar nasa yana nuna akwai damuwa sosai a tare dashi ya mika hannu ya dauki wayan shi dake gefe a je ya sake dialing din nomban merry din karo na barkatai ke nan tun dawowan shi london din. Kamar yadda computer ta saba mai babatu wanan karon ma itace ta soma zancen cikin sanar dashi layin baya shiga. Karan kararawan shigowa falon kamar ba zai dago kai ya duba ba yadan share don ya dauka cikin yan aikin gidan nasa ne ke masa sallama. Merry tace ta shigo falon cikin shigar wani dogon riga da cinyan shi yake bude har kasa rigar mai hannu kamar dan shimin mata sai yarta dake dauke hannun mai aikin su ta daukota tana barci. Dan peck takai mai daga inda yake kwance din hakan yasa shi mikewa zaune tare da rike mata hannun yana fadin yanzu ya gama trying din layinta yana rufe. Merry bata amsa ba illa amsar yarta datayi a hannun mai aikin tana kokarin kwatar da ita saman kujeran daya tashi akai. Itama taka zaune tana kokarin cire takalman kafanta masu tsinin gaske kafin ta juyo gurin shi tana sauke ajiyan zuciya. Mai aikin cikin gidan su ce ta shigo dauke da abinsha tana kokatin ajewa a gaban ta kallon kayan yayi yace Greco na hana a kawo min wanan abin a gidana kin sani. Yaya akayi ya shigo min gida ya fada tare da hade fuskan shi a lokaci guda yana kalli merry din rai bace kamar bashi bane ya gama fara,a yanzu ba. Tace commo dear cikin dan marairaice murya tana fadin iam testing let me have some please you know we are in long joining. Ya kalleta da idanuwan shi da suka kada sukai ja a lokaci guda sun sauya kala ya nunawa Greco hanyar fita da kayan da sauri ta dauke kwalban giyan zuwa waje. Hakan yasa merry din tashi ta barshi a gurin tana fada a fili ya bita da kallo mai kama da harara kafin ya juyo ya mayar da kallon shi zuwa ga yarsu dake barci hankali kwance. Wani irin tausayin yarinyar yaji ya darsu mashi a ranshi ya kai zaune a hankali yana dan shafan kan yarinyar tare da runtse idanuwan shi. Lalai duk abinda babba ya hango yaro baya hango shi don sai yanzu bayan auren su ne yake sanin wasu munanan halaya na merry data boye mai a baya daya dauka ba dabi,un ta bane. Ta boye mashi wasu abubuwa da dama daga cikin dabiun nata da sai yanzu ne yake gano hakan bayan haihuwan yarsu mm a farko ta fitar fili. Wani irin ajiyan zuciya ya sauke tsoro da nadama auren merry ya darsu mashi a zuciyar shi. Tsoron ingancin addinin shi da abinda addini ya shari,anta yana zo mai a rai take tsoron kada Allah ya kamashi da laifin daba nasa ba yazo mai a rai. Take tunanen yar mutane da ya kawo kasan ya rabota da kowa nata ya darsu a zuciyar shi lokaci guda. Idan wani abu ya samu yar mutane a inda ya watsar da ita da sunan karatu mai zace ma iyayyen su a gida ya samay ta ko basu tambaya ba ai Allah yana ganin shi. Shine mafarin zuwa ranan ya dubani dayayi bayan ya saka wanda zai dinga kulla da duk wani movement dina a school din ba tare dana sani ba ya fara zuwa guri shi ya tambaye shi yace mai ina nan lafiya sai dai yana ganin ina yawan tsayawa da wani yaro dan Africa ne shima. Tun wanan ranan idan ya dauki fushi da merrey yake zuwa nan ya huta ba tare da na sani ba idan ya gama abinda yakeyi ya wuce abinshi tunda dai yasan ina lafiya. Ranan bayan ya bar gidana ya koma gida ya samu itama bata kwana a gida ba sai yarsu kawai ya samu a wurin Greco tana rainon ta . Bayan ya gama duba yar ya shige dakin kwanan su a hankali yake bin dakin da kallo ido ya lumshe take mahaifin shi ya fado mai a rai lokaci guda. A hankali ya kai kwance saman gadon dakin ya rasa abinda ke mai dadi a rayuwan shi wanan wani al,amarine da bai taba zaton zai iya faruwa dashi ba yake cin ranshi. Duk wani tunane nasa yau ya dunkule a wuri daya yana hango zancen daddy su a lokaci guda tun farkom ganin shi da merry da daddy ke fadin su din basu da tabbas domin munafukai ne. Bai taba tunane merry zata iya sauyawa daga irin sharudan da suka sakawa junan su tun kafin suyi aure da yake gani a nasa tunanen ta rike don son da take mashi din bayi zaton zata iya karya alkawari ba hakan Can a cikin barcin gajiyan da yakeyi don idan ya dawo aiki yakan zauna a gida ya sauke gajiyan shi na yan kwanaki kafin a nemay su kuma . Jin dararakun nasu harda kamar maza a cikin su yasa shi saukowa kasa bai shiya ba a hankali yake takowa daga steps din tsayawa yayi yana kare masu kallo su hudu ne mata uku sai namiji daya dake ta shafan macen guda a falon. Wani tsawa ya daka masu tun daga saman inda yake tsaye duk suka juyo a firgice suna kallon shi da mamaki. Ya tako inda suke ba tare da yayi magana ba ya nuna masu hanyar fita daga gidanshi kallon mamaki suke mai har lokacin rai bace yace merry may kike so mayar mun da gidane wai ? Tace no no bamuyi haka dakai ba dear kada ka fara korar min abokai a gidan nan don ni ban kori naka ko daya ba. Wani kallo yai mata ya juya ya shiga daki sai gashi ya fito rike da key di motar shi ya wuce su ya bar gidan. Ina gidan zaune a cikin kadaicin da yanzu ya zama min jiki saye a cikin doguwar rigar kirar Oman baka a jikina naji ana lwankwasa kofa da farko naji tsoron hakan sai daga baya na daure ina tambayan waye ? Yace ki bude nine gabana ya fadi na bude a hankali naja baya don in bashi hanya. Ya shigo rike da ledodi da da jakkar laptop din shi a hannu bai tsaya min magana ba ya haye saman benen na bishi da kallo kafin in rufo kofan. Tun da ya shige dayan dakin ya rufo ban kara jin duriyan shi ba har safe na dauka ko baya gidan ma don har lokacin muna hutu ban fita ko ina. Har na gaji da kwanci na taso in sama ma cikina abinda zanci a lokacin naji karan budan kofan shi. Daga kofan kitchen din ya tsaya yana fadin daddy ina kusa da ita yanzun hakan ko a bata ku gaisa ne. Da sauri na juyo don jin abinda ya fadi ina kallon shi miko min wayan yayi da sauri na karaso inda yake na karbi wayan . Sai dana share hawayen daya gangaro min a fuska a lokacin na iya cewa naam kawu yace hasbunallahu wani,imal wakeel yata nake ji haka radau a waya ? Sai da na hade wani abu daya tokaro min zuciya na amsa mai da lafiya lau muke kawu yaya su Amma da mamu da sauran mutanen gida? Yana tsaye ya tsare ni da ido yana sauraren yadda muke wayan da kawu a lokacin hakan ya hanani yin wani motsi mai karfi. Bayan min gama gaisawa ya miko min hannu ya karbi wayan shi ya fara tafiya ina jin yana fadin tana karatu sosai daddy. Lokaci guda hankalina ya tashi a wurin daya barni na rushe da wani itin kuka mai tsuma rai sosai bai kara shigowa gidan ba haka ya barni cikin kewan gida don jin muryan kawu danayi ranan. Kuyi manaji dashi don Allah da kyat na iya rubuta makushi wallahi ban ma san abinda nake rubutawa ba karshe. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:16 - 🀐🀐🀐: DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAIIII, A gida Nigeria kawu yana gama waya da dan shi cikin murmushi ya dago kai ya kalli Amma data matsa sai an kiramu anji lafiyan mu. Za ace yara tun tafiyan su ba,a kirasu anji lafiyan su ba ai hakan bai dace ba. Itama Amman murmushi ta sauke cikin jin dadi da kwanciyan hankali tana sauke ajiyan zuciya don ko ba komau yanzu hankalin su zai kara kwantawa tunda sun tabbatar da muna lafiya. Karewama gashi ana tambayana ya mika min waya mu gaisa lalai hakan ya nina muna zaune lafiya ke nan. Nan Amma ta shiga bada labari ga duk wanda yazo ta bangaren ta tana fadin ita kan wanan hadin yayi mata dadi sosai umar ya rike amana yar marainiyar Allah da aka dora mai a kai. Sai dai ni a nawa ban garen ranan ban yi barcin kirki ba ina tuno mutanen gida da kewan su a rains harma da wa yanda ban shiri dasu ranan naji kewan su sosai a raina. Ance inda kake nan aka sanka gani a garin mutane ba fada ba girma da arziki da kowa a garin ba zancen wance na sona wance bata sona duka dai gashi na rasa hakan yanzu a tare dani. Na juya ina mamakin irin karyan da yaya umar yayi a gabana kan wai muna tare ko wani lokaci su barima ya bani waya mu gaisa ai. Tabe baki nayi na sake juyawa tunanen mamu da hjy jummai na fara ina anyana ko wani hali suke ciki bayan mu barsu a can ? Ko yanzu hjy su yaya umar ta saduda tabar zancen raba auren da tace muddin tana raye sai taga bayan wanan bakin auren namu. Da za acema zataci nasaran rabawan a yanzu da sai nafi kowa farin cikin hakan matsala ta daya shine karatuna da zai iya samun cikas. Wani shawara ne yazo min in jure in kara hakkuri akan wanda nake na zaman kadaici ni kadai a katon gidan nan har lokacin da burina dana iyayyena zai cika gareni na kammala karatuna. Don yanzu komai ina fahinta ga kayan koyan komai a wadace banda matsala ta ko ina indai kan karatuna ne. Tausayin mahaifiya ta dana baro a cikin wani hali duk da bata nunawa tana kokarin boyewa nasan wanan abin ba karamin taba mata rayuwa yayi ba. Don na fahinci mamu na tausaya min tana matukan son ganin rayuwana ya inganta a duniyan nan. Ban san yadda akayi ba ana saura sati mu koma karatun mu ne ranan ya shigo gidan kamar an jefo shi ina zaune ina kallon wani shiri na musulunci a tv mai suna women in hijjab. Kafana suna mike saman dan center table ina tauna dan porncorn din daya zama min dabi,an ci koda yaushe. Ganin shigowan shi yasa na dan rude na mike tsaye ina mashi sannu da zuwa ya amsa min kamar dai kullun ya nufi hanyar sama har ya fara hawa ya juyo yana fadin ki shirya nan da minti talatin kafin in fito. Haka kawai ya fadi yasa kai ya haye saman abinshi binshi nayi da kallo ina tnane wani irin shiri yake magana ke nan ? Hakana na mike na shiga daki sai kuma na rasa wani irin shiri zanyi a dakin lokacin ba wasu kaya sai dogayen riguna dole daya na zaba har kasa wani mai adon ja da bakin jan maron colour da adon baki gaban rigan gyalen da zai shiga da kayan na yafa na rufe daga kaina zuwa wuya duk da haka ina jin kaina kamar a tsirara ne duk da rigan ya rufe min ko ina. Wai baki gama shitin bane ya fada a dan hasale da sauri na dauko dan jakkana na fito daga daki ina fadin na gama. Kallona yayi daga samana har kasa ya kawar da kai ga kallona tare da fara tafiys na biyo bayan shi daga can cikin motan yace wa zai kulle maki gidan ? Jikina na rawa na koma na dauko key inda nake ajewa nazo na kulle gidan na nufo wurin motan don tsoron shi da nake ji na takure a wuri daya zan shiga bayan motan. Wani harara da tsawa yai min sai ganina nayi a gaban motan zaune ya bar gidan sosai yake gudu da motan . Ni dai ban san inda muka nufa ba don ba garin na sani ba kaina a duke don nagaji da kalle kallen abin mamaki a idona ga tafiyan mai nisa sosai da alama. Don tun da rana har wani lokaci muka isa gurin Jin hayaniyan mutane yasani dago kai a hankali wani signboard na gani anyi rubutu manya a cikin style welcome to CUMBRIA PICNICK LAKE WINDERMERRE, , , , Bayan motar ya bude ya miko min wani bakin coat na mata kallon rigan nayi yace ki saka in ba haka ba sanyi ya illanta ki a nan. Da sauri na karba na saka sai ga rigan yazo min har iya gwiwa na sai dogon rigan dake jikina ya koma kamar buje . Waya yayi banji may akace ba naji yace muje don Allah bin bayan shi nayi ina fadin mutum haka komai a hasale yakeyin shi ? Zaune suke duk da duhun dake gurin sun saka wuta a tsakiya wasu na kwallo wasuna shaye shaye wasu a kwance . Hi Omar we are here muryan merry naji sun sauka a kunnuwa na lokaci guda da sauri na dan kalli wurin na karasa ta hanyan bin bayan shi zuwa inda suke zaune a cikin yashin teko da wasu mutanen da kusan rabin jikin su duk tsirara ne. Unbelieveble wa nake gani nan kamar fatema ta fada tana kokarin tasowa daga inda take zaune din . Haka yasa wa yanda suke tare a zaune suka juyo suna kallon mu tasowa tayi sukai dan wani musayan gaisuwa na gefen mumuke. Nidai ina tsaye ina kallon ikon Allah ta barshi zuwa wurina taimin irin wanan gaisuwa hannunta yana rike a cikin nawa take tambayana yaya karatu ? Nace da ita Alhamdullahi dan bubuga min baya tayi tare da jan hannu na zuwa wurin mutanen da ke zaune tare da ita tana fadin. Meet Omar sister Fatema tana karatu ne a nan kasa tazo daga nigeria ne itama suka kara kallona suna fadin she is so beutiful. Tare da tambayan merry din yaushe nazo basu sani ba tana fada masune hankalina yaje gurin yaya umar dake rungumay da yarshi zaune a cikin kasa suna hira cikin kwantar da murya yana rungumar yarinyar . Cewan da merry tayi ga abokanta mu gaisa ya dawo da hankalina inda suke hannu suke kokarin miko min nayi saurin masu jam,i ga baki daya na gaida su. Don nasan ko mazan zasuyi kokarin miko min hannunnsu hakan gareni wanda nasan sai dai in ba merry din kunya don bazan karba masu ba. Merry tayi saurin cewa halan ba al,adan mu bane mun rike addinin mu sama ga komai don haka mijin ta yake shima. Sai suka sa dariya a tare lokaci guda kamar yasan may sukeyi yace kezo nan zakace badani yake magana ba. Ganin ni kadai ke jin hausa a gurin nasan dani yake magana na juya a hankali zuwa inda suke dashi da yar shi din ya rungumay ta wanan karon. Ki zauna yace dani da yana nuna min wurin zama da hannun shi haka yasa da sauri nayi abinda yace din . Na kai zaune saman yashin a kusa dasu na zauna tare da dan takurewa a guri daya. Fuskokin mu yana facing din ruwan sake iska keta kadawa a lokacin mutane wuri ba adadi kowa da abinda yakeyi a furin ba wanda ya damu da wani. Ina can ina kalle kalle naji muryan shi yana fadin ke yar nan nake son ki rike min kada ki bari tana bin wa yancan ya nuna su ba tare daya daga hannu ko kai ba. Da dan mamaki na dan kalle shi yace eh nasan yarinyar tana da sabo zata saba dake idan kin nuna mata kulawa daya dace. Yana fadin hakan ya mike ya barmu da yarinyar zaune tare dan hannu na mika mata sai ko tazo gurina yayin da hankalina yake gare shi ina kallon inda zai tafi. Muryan yar yarinyar ya dawo da hankalina gare ta kallonta nayi naga ta bata rai tana fadin i want to sleep now. Yanayin maganan ta ya ban sha,awa ganin tayi karanta sosai da zuwa irin gurararen nan haka. Fuskana take kallo take maganan na dan sakar mata murmushi kadan ce tazo ta kwanta a jikina bata ki ba sai ta matsa inda nake zaune. Zaune muke kafafuwan mu a cikin ruwan lake din na rugumay ta sai lokaxin tunanen kanne na yadda nakeyi dasu a hankali nakai hannuna saman kanta dake da kitso hudu na kalaba yaji dauri da ribon masu kyau. Ina dan bin zanen kitson da hannuna naji yadda take sauke ajiyan zuciya a hankali alama barci na zuwa mata a lokacin. Tace my mum sing for me idan ina jin barci duk dare na dan kalle ta ikin kamilaliyan fuska nace ban iya irin wankan da maman ki ke yi ba ni ai. Tace kiyi ko wani iri kika iya na dan yi tunane kadan sai na fara karanto mata fatiha har zuwa karshen shi. Nakai aya nayi shiru don na dauka tayi barci saboda yadda ta lafe a jikin nawa lokacin sai kawai naga ta dago kai ta kalle ni tana fadin may yasa na bari kuma taji dadin wankan sosai ci gaba nayi da maimaita mata karatun ina dan taba mata kai a hankali. Yanayin da nake ciki yasa na zarce da karatuna a cikin zazzakan murya ba tare da nasan ina daga murya sosai ba a lokacin. Sannu a hankali suke taruwa suna kallon yadda nake karatun su basu raina abin kallo a wurin su hakan ya jawo hankalin su merry gare mu ta tako har zuwa inda muke zaune din . Hannu ta mika tana fadin tana baki wahala ko fatema a daidai lokacin da take mika hannu don daukan yarinyar a jikina tana fadin ina Dad din ta ne ya barki da ita haka ? Abin mamaki ga yarunyar da tayi nisa a barci sama jikina uwar na tabata da niyar ta dauke ta saman jikina di don ta fahinci abinda nake karantawa yarinyar nata a lokacin. Uwar na daga yarinyar sai ta zabura ta kankamay min a jiki tana girgiza kai tare da fadin no no zan tsaya a wurin wanan aunti din . Daga bayan ta taji muryan mijin yana fadin ki kyale su tare ko kin manta da alakana da yarinyar ne ? Yana gama fadin haka yarinyar tace thank you dad ta mayar da kanta saman jikina kamar ta koma barci lokacin. Ina mamaki a raina don kalman godiyan da ta jefawa uban tana a lokacin yana nuna taji dadin hukuncin daya yanke a kanta ke nan na hana uwar ta dauketa wurina. Can na dauka tayi barci ne saboda irin lafewan datayi saman jikina din lokacin sai naji muryanta tana fadin. Whats your name please ta fada tana dago kai tare da duban fuskana dake manne a jikin ta lokacin. Kallon ta nadan yi nace fatima sai naga ta girgiza kanta tana fadin okey i will called you anty fatima na danyi shiru ina mamakin wayau karaman yarinyar haka. Na kalle ta nace ba kince kina jin barci ba da farko kiyi barcin ki tunda daddy yace a barki a nan gurina. Ajiyan zuciya naji ta sauke tana sone kanta da kyau saman kirjina a hankali. Merry dake rungumay da hannayen ta tana tsaye da kawayen da duk bakaken fatane suna tambayan ta yaya muke da mijin nata. Sai da ta sauke ajiyan zuciya tace kaunar shi ce wata ta jefo mata tambaya da fadin uwa daya uba daya ? Tace yar step mum din shine mahaifi suka hada dashi kawai tace tana kokarin tafiya wurin mijin ta . Amma kyan yarinyar yayi yawa ya nuna kamae ba jinin su daya ba wani fannin sai dai kama na fari da suke dashi kawai don wanan tana da zubin yan arab sosai. Bata juyo ba ta dai wuce shi yana tsaye yana kallon ruwa babu komai a ranshi sai tunane karfin hali kawai yake da tsayuwa a wurun taron nasu. Yayi kokatin mata kara ne kawai dan taya ta bukin da zasuyi na Esther da ya gabato ko wani shekara wanan dalilin yasa ya dauko ni don manufa biyu. Na farko nazo don yar shi sai na biyu yasan zan danji dadin zuwa cikin mutane dana kwana biyu a zaune a gida ban fita ko ina. Karatun da yaji ina wa yarshi ne ya kara daga mai hankali abinda ya dace ace shiya fara tunanen koya mata hakan sai gashi yaji ya gani da idon shi nayi hikimar koyawa yatinyar karatun addinin mu lokaci guda. Hakan yayi mai dadi sosai a zuciyar shi har ya saka shi tunanen wani abinda yasan ba zai yuyu ba ga yar nashi sai a cikin hikima da basira. Jin hannun merry dayayi saman jikin shi tana kokarin rungumay shi ne yasa shi sauke ajiyan zuciya a hankali. Ya juyo da ita zuwa gaban shi goshinta ya hada da nasa kafin ya hade da jikjnta ya rugumay ta yana dan sakin murmushi wanda hakan ne halin shi idan yana cikin yanayin jin dadi. Daga inda nake zaune na mike da yarinyar a saman jikina da kyar ina dube duben inda zanga iyayyen nata don sallah dana tuna banyi ba a lokacin ina son samun kebeben wuri da zan gabatar da sallah din. Hango su nayi a inda suke tsaye rungumay da junan su wurin su na nufa a hankali ina fadin lokacin sallah yayi zan shimfide ta inyi sallah ne. Don har azahar ban samu yi ba a lokacin ba tare da ya sake merry a jikin shi ba kuma baiyi magana ya bani amsa ba ya juya ya fara tafiya . Nidai na gyara yarinyar da nauyin ta ya cika min hannu sosai a lokacin nabi bayan su muka jera har zuwa gurin motar su dake can aje dan nisa kadan da inda muke din. Bude motar yayi ya juyo ya karbi yarinya tare da fadin sannu da kokari kamar ba dani yake magana ba zakace. Nima ban amsa ba amsan yarinyar yayi ya ahimfide ta a bayan motan dan hakan na juya zuwa bakin ruwan dake ta feso muna ina kokarin tattare hannun rigana don yin alwala . Na fara naga shima yazo yana alwalan a can dan nesa da inda nake ina idarwa na hango ya shimfida muna abin sallah gurin motar shi kusan tare mukai sallolin da ake bin mu din don shi ya jamu sallah lokacin. Sai bayan mun idar ne naga merry tana fito da kayan abinci a bayan motan tashi yayi ya taimaka mata suka jera kayan a gurin . Shi yati min basimilla nace a koshe nake bana jin yunwa dan kallona yayi a dake yana fadin may kikaci fun dazun muka bar gida don haka ki zoba abinda ranki ke so a nan kici. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:16 - 🀐🀐🀐: ALLAH ABIN GODIYA JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI, , , , , Ina cikin mota zaune nake barci cike da dinbin mamakin wanan sabuwan rayuwan wahalan dana gani yau a rayuwata. Wai abin mamaki dan adam ya hana kanshi barci yana rayuwan sharholiya saboda jin dadin duniya da yai mai yawa. Zakace wurin kasuwa ne har tsofi akwai wurin da yara kanana na goye an hanasu barci suji dadin dare saboda wanan shirmay banza sai ciye ciye kungiya kungiya suke faman yi. Barci na samu ya dauke ni cikin mamakin ya umar wanda yayi watsi da addinin shi da dabi,un aladanshi akan mace. Alam din agogona da na saita don jin lokacin sallah karan shi ya tayar dani daga dan barcin dana samuyi. Da mamakin dana kwanta dashi na falka don sai ince wurin yafi lokacin dana kwanta barci cika. Tsofine da yara har na goye gasu nan kungiya kungiya sai masha,a da raha akeyi a wurin babu zancen tunanen Allah. Mamaki kan yau na sha shi wurin kallon abin al,ajabi da mamaki ace mutum mau ilimi irun ya umar ya biyewa wani ikidan banza na mace don dai kawai taji dadin hakan a ranta. Gashi yazo ya maida kanshi wani kototon katon jahili cikin addinin shi saboda kawai ya dadadawa macen da yake so rai. Na dade zaune cikin motan ina sake saken zuci ni kadai ina hango su daga inda suke zaune din. To waini ma a wani matsayi nake a wurun nan don ban fahinci dalilun su na kawo ni wanan wurun haka ba. Ko wanan ne wayewan da merry take kiran tana son ya kaini makarabtar da ta zaba inyi. Ko madai ma maynene nabar abin a raina kamar yadda shima din ya barni a rufe nidai burina in samu in kammala karatuna in koma gida wurin a halina. Saidai nasha alwashi a raina cewa da zaran mun koma gida zan fadawa kawu da Amma irin zaman tanbadan da sukeyi da arniyar matar shi a turai. Kallon yarinyar dake barci a jikina nayi na dab daga ta a hankali cikin sanyin jiki na bude motar a hankali nafito. Kara kallon su nayi da wani irin kyama da tsana don sun cutar dani na zuwa wanan wuri dani haka ina zaune kalau abina. Cikin sanyin jiki da kasala na fara tafiya a hankali zuwa nesa da inda ba mutane sosai na dan tatara hannun rugan sanyun dake jikina a hankali na fara gabatar da alwala don asuba ya gabato sosai a lokacin. Na kusa kai karshe naji murya a bayana ana fadin hy babbe idan ba damuwa zanso kasancewa dake. Ko kina tare da wani ne a gurun nan ban dago ba sai kokarin alwala nakeyi har na idar na daga yatsana sama ina hailala ga ubangijina Allah. Yace Wa, woo, so you are muslims girl baby kinzo da wasu ne ko ke kadaine a gurin nan zaso mu dan kasance tare dake na dan wani lokaci. Naso yimai rashin mutunci sai ba tuna nan ba Nigeria bane kada yazo ya turani cikin teku ruwa ya wuce da banza ba a san na mutu ba wanan wurin. Ke idan kin gama abinda kikeyi kizo ki wuce ya umar ne ke magana a bayan mu da sauri na shafa na raba baturen zuciyana yana min kuna da maganganun da ya rabbatamin din. Wurin motar na nufa ina kokarin tayar da sallah yayin da na barsu can tare da baturen komay yake fada mai oho. Ganin zanyi sallah ya kyaleni ina kallo shi shima can gefe daya yana sallah a cikin yashin teku. Ke idan kin idar ki tashi muje yace ni wanan ke din da yaya ke fada min waidai ko baisan sunana bane wai na tambayi kaina ? Mota muka shiga muna baya da yarsu har lokacin tana barcin ta sai gyara kwanciyan da tayi saman jikina tana dunkulewa a wuri daya. Ba kan garin na sani ba don haka ban san titin dayake bi damu ba a lokacin nidai tun muna tafiyan arziki har yakai nagaji ina dan jan tsukin dana dauka a zuciya na nakeyi. Merry ce ta fara juyowa inda nake zaune tana fadin kingaji ko sorry fatema kin tayani zuwa eather da abokaina da yanuwa da abokan arzikina naji dadin hakan da kukai min ke da dan uwan ki. Magana take tana murmushi cikin nuna fari ciki irin na wanda yaji dadin abu yayin da idanuwanta ke kaina a kafe. Da murmushin yake na kakaro a fuskana ina jin ta dan juya ta kalli mijin tana fadin taji dadin wanan kasancewan da yayi dasu harda sister din shi. Mun iso gidan sai lokacin na fahinci inda mukazo shiya zagayo ya dauki yarinyar a wurina ya sabata zuwa ciki, A falon mukaya da zango kallona yayi yana fadin zaki iya shiga wanan dakin da kika taba zama yana nan babu kowa a cikin sa. Jin haka yasa na mike da sauri don duk a matse nake a gurin damaina shiga nayi ban daki na hada ruwan dumi masu zafi na gasa jikina dashi. Alwala na dauro na fito cike da tunanen a raina na kayan da zan saka inyi sallah sai ina ganin zuwa wurin yasa tufafi na basu da tsarki yanzu kuma. Naji mamakin ganin kaya saman gadon an aje min na dan tsaya ina karewa kayan kallo kafin in karasa zuwa wurin da sauri hannun kayan na fara dubawa idan ba yar shimi bane. Dogon rigane irin na matan turai yana da yan hannuwa ba wani dogo sosai ba da ganin kayan zai bi jikin mutum ya lafe mai a jiki. Dayan kuma kamar abayane sai dai yana da shape shima ba irn na matan larabawa bane ganin idan na gama ramuwan barci zanyi yasa na saka na farkon a jikina. Dan gyale na dauko ina takaicin barin hijab dina danayi gida banzo da shiba don sallah to mutum kawai yace ka shirya ba tare da fada ma komai ba ina zan tsaya shirin kwarai lokacin. Allah ya isa nayi ta ja a raina zuwa nan inda suka kwasoni ba don na sani ba wurin wullakanta kai da kiman mutum. Tun inda na idar da sallah na fara gyangyadi na mike da kyat zuwa bakin gadon nan nahaye na yada kaina sama sai barci. Barci sosai nake a kife a dakin sai dai ya umar da ya fito ya shigo yana dubani yakai sau uku har lokacin yana samuna ina barci. Har mamaki yayi wanan wani irin barcine haka don yasan cikina akwai yunwa ban ci wani abin kirki ba tun jiya din koma dai yaya ne yasan yunwa zai tayar dani ai. A razane na mike kan gadon gami da salati a zato har lokacin rana ne ban jima ina barci ba. Duban lokaci nayi nayi na lumshe ido da sauri ina mamaki na zabura nayi bandakin na wanko bakina gami da alwala na fito na tayar da sallah don har isha,i ya wuce lokacin. Banji nauyi ko kunya ba yadda nake jin cikina a lokacin firowa nayi neman abinda zanci tunda dai gidan ba bakona bane yanzu. Ganin abinci a saman dining din na nufi can saida na bubude naga abinda zan iya ci na zuba nayi dik na kora ruwa nayi hamdala. Sai lokacin na kula da irin kwalliyan da akaiwa gidan irin nasu na chirstoci idan suna shagalin su ba buki. Ikon Allah na fadi a fili ina mamaki tare da tunanen ko dai ya umar din ya canza shekane basaja yake wa mutane. Wata zuciya tace min ko da asubah baki ganshi yana sallah bane da zaki masa sheri to amma abun yai yawa mana nace a raina. Banji fitowa shi ba sai dai ganin mutum nayi a gabana haka kawai naji gabana yana faduwa . Cikin dan i,iniya na fara gaida shi kamar yadda ya saba amsawa a dake hakan ya amsa min gaisuwan wanan karon ma. Wanan kallon wullakancin nasa ya jefo min yana fadin kin ga dama kin tashi kin wani kwanta kamar wace tayi wani aikin dake ? Yana waso min idanuwan shi masu kama dana mayau dari da naki jini tun a gida kamar yana jin tsoron kallon mata yakeyi. A takaice na bashi amsa da dama aikin nayi ai zaifi min wanan zaman. Ni kaina amsan yazo min a bakine don bansan lokacin dana fadi ba don takaicin shi da nake ji din. Kallona yayi ya girgiza kai cikin mamakina kamar zaiyi magana sai kuma ya wace ga yar shi data fito tana kiran daddy daddy. Mikewa nayi zan tashi in bar wurin naji muryan shi yana fadin ina son ki kula min da yata don yau muna da baki a gidan. Cikin kunkuni nace ni ina ruwa da baki ku da zaka mayar dani yar raino na juya naji yarinyar na fadi cikin turanci daddy na manta da sunan ta ya dago ya dan kalleni yace mata fatima. Sai ta girgiza kai yace oh sorry aunt fatima tace yes that's her name ta juyo tana fadin tana wani kada idon kinibibi zaki wasa dani ? Na nuna kaina nace wasa ta langabe kai tace mummy bata da time dina iam lone now ta kuma bata rai kamar wata babba. Yayin da shi kuma ya wani kasheni da ido kamar yana son jin amsan da zan ba yarinyar. Jin nayi ahiru yasa ta kara maimaita maganan a dan shagwabe na riko hannunta ina fadun dare yayi yanzu lokacun barci ne ai. Tace No no tana dan bubuga kafanta irin na shagwaba tare da fadin mummy tace zamuje wurin prayers ne yanzu and I don't want to go with her. Jin hakan yasa na kama hannunta muka nufi dakin da nake muka barshi tsaye yana bin mu da kallo har muka shige ciki. Muna shiga dakin ta fada saman gado tare da fadin ina wayana muyi game dan jin nayi sai can nace mata ai banda waya ni. Mikewa naga tayi ta fita da sauri ashe zuwa tayi wurin baban ta tace ya bamu waya zamuyi game dani da ita nace banda wayani. Can sai gata tadawo da gudu tana dan ihu tana fadin daddy give us his phone tana hawowa gadon. Kallon ta nayi naga da gaske wayan ya ba yar tashi kuwa ta zauna tana dan danne danne a cikin wayan jin nayi shiru. Ta dan juyo tana fadin sunayen game din dake wayan hankalina baya wurinta a lokacin. Aunt may samayki kike tunane tace tana hawowa inda nake kwance a ringigine din. Ajiyan zuciya na sauke nasa hannu na rugumay ta zuwa jikina nace mata ina tuna mamace dake gida da yan uwana. Fuska ta bata tace kema kina da mama ne ? Na shafa mata kai nace baby girl kin taba ganin wanda baida mama a duniya ? Ta dan rage sautin muryan ta tace harda daddy ta yana da mama ta dago kai tana kallona taji abinda zan fada mata din. Mamaki yarinyar tabani don tayi kankanta da wanan tambayan idanun ta har lokacin suna a kaina tana jiran amsa taji. Shiru na sake yi na dan lokaci can a hankali nace yes yana da mama da baba har da grany tace har da brothers ? Tana watso min idanuwanta masu girma kamar na ubanta gasu dal kamar hasken kwan lantarki. Rugumay ni tayi tana shige min jiki ta marairaice murya tana fadin can you take me to them ? I want to see them aunt ta fadi a dan maraice take naji wani tausayin yarinyar da sonta yana kamani lokaci daya. Murya ta ne take fadin tasan uncle joshua tasan anty linda da grandmun da dad ashe tana da wasu yan uwa kuma na daddy su. Shiru dukkan mu mukayi da hakan har barci ya dauke mu bamu sani ba muna lake da junan mu don har uwar tazo daukan ta don zasu can church sai dare sosai zasu dawo. Samun yanayin data gamu yasa taji bata son tayar da diyar nata a lokacin ta fito rana fada mai ta samu munyi barci dukkan mu don haka zata tafi ita kadai. Sai cikin dare na falka naga yadda muke kwance ta yarda wayan can gefe daya ta make a jikina gyara mata kwanciya nayi da kyau na kashe wutan dakin. Washe gari ma tunda asuba ina sallah uwar ne ta shigo dakin a uzurce ta samu na tashi ina saman salaya take fadin tazo daukan faith ne zasu tafi wurin ibada yau special day ne na addua a gare su. Haka ta kinkimi yarinyar tana barci suka fice a dakin kallon tausayi nabi yarinyar dashi har suka bace min na sauke ajiyan zuciya a hankali naci gaba da abinda nakeyi Nikan tunda nayi sallah ban fito ba kuma banyi barci ba sai faman tunanen da nake a cikin dakin yayin da kamshi ke ziyartan hancina ta ko ina na girgi. Fitowa shi ke nan daga daki da tunda ya dawo motsa jiki yayi wanka ya kwanta bai fito ba shima wanan zaman gidan ya damay shi a lokacin don dai kawai ya bama iyalin shi lokaci yake zaune gida tare dasu din ana shagalin esther dashi. Yanayin data zo mai yasa ya gane tans dauke da magana a bakinta a lokacin. Wuri ta samu takai zaune tana fadin your sister want to creat a sin to us why zata fadawa faith about your parents. Alhalin tasan bata san da zancen su ba zata dauko muna wahala kasan halin faith da rigima fa yanzu gashi ta damay ni tana son tasan su ita. Murmushin takaici ya sake yace Okey ke kuma baki son ta san dasu ko ya fada yana duban fuskanta . Yarinyar ne ta zo ta rabe a jikin shi yadan rungumo ta yana fadin Queen what's your problem tell me about it. Ta bata rai kafin tace is aunt thinking about her parents na tambaye ta tace min akwai dad da mum da grany da ban sani ba. Yace Oh realy tace aunt tana tunanen gida sosai daddy nima ina son sanin mutanen da take tunane din. Merry tace you see na fada ma zata kawo muna matsala fa idan tana irin wanan maganan. Kare mata kallo yayi da kyau kafin yace may wanan maganan naki yake nufi merry kina nufin yata ba zataje gurin iyayyena ba komay ? Nan suka fara musayan baki tana fadi a hasale yarta va zataje inda ake kyaman su ba ko ita yaya ta kare balle yarta dasu. Wanan maganan ya kawo muna matsala da merry ta fara canza mi fuska tana dadaure mun fuska ban gane zaman gidan ba ga baki daya ga wanda ya kawo ni ma ba kula nake samu ba gurin shi. Na fara ganewa ta hanyar hana yarta ta kusance ni da zaran taga tazo inda nake yanzu zata zo ta cajata idan kuma na fito tana waje sai ta tashi ta shige ciki. Ranan kawai tun safe na shiya suna barci na bar gidan don dama nagaji da zaman gidan sosai Allah ya taimakeni katina na shiga jirgin kasa yana cikin yar jakkar dana dauko. Na sulale na tafi abina don nasan yadda ake shiga jirgin kasa din zuwa lokacin cikin ikon Allah na kawo kaina gidana. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:16 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM YA JAMA,TUL MUSLIMIN, , , , Na samu na isa gidan raina a bace duk da naji saukin bacin ran a lokacin don gani nake kamar na dawo gidane na ainihi. Ina bude gidan na shiga na kunna nauran gidan ya gauraye da haske gami da dan fara sake sanyi. Zama nayi saman dogon kujera ina bin gidan da kallo kamar yau na fara ganin shi a rayuwana. Ajiyan zuciya na sauke a daidai lokacin dana mike zubur kamar an tsakareni sama na hau zuwa dakin kwana na wanka nayi tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah. Ina idarwa na zauna ina addua sai kuma tunane yazo min a raina anya ranan da merry ta san maysayina a gurin ya umar za ayi abu mai dadi kuwa ? Shin dawa sakamako zata karbe ni, anya zan iya kallon ta da idanuna kuwa wasu hawaye masu zafi suka sulalo min tausayin kaina ne ya kamani nace ni nawa kaddaran aure a haka ya fara zuwa min . Nayi kuka har na gaji kafin in mike zuwa nemawa cikina abinda zanci don na fara jin yunwa. Kitchen na shiga na bude fridge dina dake lode da komai na bukata bread din dana gani ya rage wanda yanzu na maryar dashi abinci na a saukake. Shina dauko na bude ovon na gasa tare da dumama source din danayi don wata bukatana na dauko tare da kifin gwangwani na dawo falo ina ci a hankali . Bayan na gama na kwashe kayan na nufi daki tare da kashe komai na gidan a lokacin nabi lafiyan gado na kwanta abina. Zaune yake kadan kadan tun bayan dawowan shi gidan daya dan shiga ya fito ya zauna falo yana aiki a laptop din shi yake dago kai yana kallon kofan dakin da nake ciki. Don ya fahinci lokacin da nakan fito inci abincin tun zuwana gidan saidai yau baisan dalilin da ya hanani fitowa ba inci. Zuwan queen din shi tana tambayan shi kamar mai rada cikin kashe murya da daddy ina wanan anty take yau ne ? Mummy ta hanani zuwa wurin ta tace kada na yarda da ita zata koya min wani hali. Daddy i want to see her, where is she now ? She is in her room ya bata amsa a takaice tare da nazarin yawan surutun yarinyar nashi da wayau ta . Sai kuma mamakin merry daya lura harshi tana dari dari da kasancewan shi da yarinyar tashi. Wai ma may ya hana wanan yarinyar fitowa ne yau ya fadi yana mikewa don sanin babu mai alhakin kula dani in bashi ba ya kuma gane a takure nake zaune gidan dasu wanan zuwan. Mikewa yayi tare da rike hannun yar shi suka nufi dakin da nake din yana rike da ita ya tura kofan dakin . Babu kowa a ciki ga gadon a gyare don ban tafi ba saida na mayar da komai tsab kamar yadda na samay shi da farko. Ya dauka ina ban daki ne haka yasa shi juyawa yana shirin komawa inda ya fito sai kuma yaja ya tsaya wuri daya da yai wani tunane . Da sauri ya kara komawa dakin ya shiga ciki da kyau yana dan kalle kalle a dakin ya taka a hankali ya kwankwasa kofan dakin . Shiru ya fara kira sunana nan ma yaji shiru ba amsa haka yasa ya tura bandakin da sauri wurin a bushe yake babu alaman anyi amfani dashi wanan lokacin. Juyawa yayi ya kara fitowa yana dan dube dube cikin dakin ya daga filon yaji kamshin turaren da nake amfani dashi ya daki hancin shi sai kuma yaji gaban shi ya dan fadi. Aje filon yayi da sauri ya juya ya fita don ita queen ta dade da fita tunda bata ganni ba a dakin da farko. Fita yayi yana tambayan yan aikin gidan ko wani yaga fitana ko ina wani wuri na gidan kowa yace bai ganni ba sai Greco ce tace taga fitana da rana tun lokacin bata kara gani na ba kuma. Hankalin shi yadan tashi gashi ba waya a hannuna balle ya kirani yaji ina ina a wanan lokacin don yamma yayi sosai a kasan. Merry ce ta fito tasha kwaliya sosai tana waya suka hade dashi a falon cikin damuwa yace merry. Where is dat girl ? Wani kallo tayi mai tana katse wayan doba zaton ta ta dauka yarsu yake tambayan ta. Tace faith tana cikin gidan nan mana na dauka tana nan gurin ka ne ai ta fara dan dube dube can tace may be tana gurin GRECO. Yace not queen iam talking fatima nake nufi sister na ta dan tabe baki tace may be she is in her room ta fara tafiya. Look merry ina tambayan ki ina yar mutane ta tafi kina tafiya bata dakin ta na duba ko ina a gidan nan bata gidan. Tace is she a small girl ina zataje ai yanzu tasan gari yace ina ta sani banda gidan nan dan haka ina zata je kuma bayan nan. Bata tsaya sauraren shi ba tajuya ta zuce dama fita zatayi takai kofa ta juyo tana fadin take care of our daughter shaaa. Har takai kofa ta juyo kuma ko tayi mantuwane a lokacin tana sauri zuwa cikin gidan . Yamma yayi sosai yasan ba karamin tafiya bane daga unguwan su zuwa central London inda nake. Haka ya kwana yana juyi merry dake ta shagalin bukin su bata church bata gidan abokai da iyayyenta da suka zo mata easther a nan. Bai maga hankalinta ba balle ta san yar akuyan shi ta bace a gari sai ranan yayi dana sanin barina da yayi babu waya a hannu na yafi sau dubu. Sai faman juyi yake saman gado yana tunane yanzu in wani abu ya samu diyar mutane may zan fada a gida. May zancewa daddy ya samay ta gaskiya yayi sakaci da duk wani al,amuran nauyi da hakkin yarinyar nan karama daya rataya a wuyan shi. Ya juya a karo na barkatai yana tsuki merry ce ta mike zaune a cikin fada tana fadin may yake damun ka ka kasa barci tun dazun . Yace will you keep quety merry ke har kin san damuwana yarinya tazo gidan nan ta bace ki nuna min rashin damuwan ki kan haka don ba yar uwarki bace ita komay ? Tace amma dai kasan wanan yarinyar tunda tazo nayi kokari a kanta ko so yanzu na gane an turota nan ne tazo yin wani mition daga bangaren iyayyen ka don haka ba zan saka mata ido tana jefawq diya wasu akidu na daban ba. I even ask faith how thet stat the coversition with her faith ta fada min komai daya faru a cikin hikima. Though nasan ba wai yin kan ita fatema din bane amma duk da hakan zamuyi nisa da ita don kada ta raba min hankali yata. Wani kallo yai mata tare da fadin good yanzun dai na gane cewa kece kika kori wanan yarinyar gidan nan ashe to ki sani idan wani abu ya faru da yar uwata a garin nan kece don bata san ko inaba a cikin garin na. Tace ban kore ta da baki ba nadai kore ta da hali kamar yadda kaima iyayyen ka suka nuna min a can Nigeria. Ok yace ya koma ya kwanta yana dana sanin yin watsi da yar uwan shi zabin iyayyen shi ga merry ta nuna mashi akwai matsala a gaba ke nan tun yanzu. Kan yarsu yasan zasu kwasa da ita gashi yayi ta dauke hankalin ta kasancewan ta macen aure a yanzi har da ya ta daina wasu dabi,un da bai dace ba na akidun su na black American taki. Yasan wanan ba shawaran ta bane daga abokanta wanan shawaran ya fito don da farko data barsu yana iya juya ta yadda yake so sai dai tana haihuwa dashi taga ai ta gama kamashi ga wautan ta. Hakan yasa take mai duk wani abinda taga daman yi a yanzu don tasan ta gama dashi ko ta ko ina. Sai dai merry ta manta da sanin halin dan Nigeria ganin irin halin data fara mai sannu a hankali yake tura komai da yake samu yanzu gida Nigeria da wasu kasashe ba tare da sanin yana hakan ba. Yayi mata kifi na kallon maijan koma bata sani ba tana haukan cewa komai da yake nema da shi kan shi din yanzu mallakanta ne ita da yarta. Ranan dai tunane kala kala yayi shi a gurin asuban fara tana barci ya bargidan ya kamo hanyan zuwa gidana kai tsaye cikin tashin hankali. Merry bata san barin gidan nasa ba a lokacin tana kwance tana sharan barcin ta a lokacin hankali kwance ya barta don hankalin shi dayaki kwantawa yana ganin ban san gari kada wani abu yaje ya samay ni can. Barci nake sosai don nima sai kusan asuba na samu barci ya dauke ni ina karatu daga nan na tashi nayi sallah na dade ina addua kafin in kwata. Jin bell din gidan ana ta dannawa ba adadi yasani bude idanuwana da kyat na sauko dan shimin barci da wandon shi ne kawai a jikina don rudewa wakw min sallama da wanan safiyan haka. Saboda ban taba dauka daga can zai iya zuwa nan ba a wanan lokacin haka yasa na fito a firgice zuwa kofan inga mai sallaman. Ina budewa mukai ido biyu dashi sai lokacin na tuna da yanayin da nake ciki daga ni sai shimi a jikina da dogon wando kawai. Haka yasa nayi saurin juyawa zan koma ciki a fusace naji yayi magana cikin daga murya yana fadin ke don may kika wuto nan baki fadawa mutane ba ? Ban tsaya sauraron shi ba na juya don ni na farko ina son zuwa na rufe jikinane na biyu kuma yanzu duk wani tsoron shi ya fara fice min a rai yadda naga ya zama kamar bawan mace a nan don ban saba ganin hakan a gida ba wurin mazajen mu tun tasowa na. Bin bayana yayi da kallon mamaki har na shige hijjab dina na dauko da sauri na saka nafito daga dakin baki daya. Yana tsaye a tsakar falon bai zauna ba gani yaya nace mai ya dan juyo ya kalleni ya sake fadin ubanwa ya dawo dake nan nace. Sai da na danyi jin kadan kafin nace uban wa yaya bakai ka kawoni gidan nan ba tun farko ? Umar jin zancen nawa yayi da mamaki yace amma da yake dan duniyan namiji ne sai ya boye mamakin nasa yace nace waya dawo dake gidan nan jiya ? Nace rai bace ni na dawo da kaina don ba zan zauna inda ake nuna min kyama ba alhalin su din ne abin kyama ai. Ina fadin haka na juya na bar falon nan na barshi tsaye da mamakin irin kalaman dana fada mai kai tsaye yau ba tare dana ji shakkun shi ku tsoro ba yadda na saba. Harshen shi ya sanya ya lashi leben shi na sama dayake jin ya bushe mai cike da takaicin kan shi. Zaune yakai yana mamakin yadda na iya bashi amsa haka kai tsaye yau don kalaman sun firgitashi jin ina fada mai magana yau haka kai tsaye. Idanuwan shi ya lumahe a hankali yana tunane wani irin hukunci zai daukan min wata zuciya tace mai hukuncin may zaka dauka kuwa tafika gaskiya. Ban san yana falon ba har lokacin ganin gari ya haska yasa na fito zuwa neman abinda zan saka a cikina. Ban ankara dashi ba zaune saida na kusa saukowa kan benen na tsinkaye shi zaune ya dafe kai yana kada kafa. A firgice naso juyawa saidai nayi rashin sa,a shima jin takona ya dago jajayen idanuwan shi yana watso min kallo mai kama dana takaici. Ina zaki koma ai gara ki sauko ki nuna min kin isa har ke kin isa ki kalli idona fatima ki zagi iyalina a gabana haka ? Da sauri na dubeshi nace zagifa kace yaya ni ban zage su ba halin su kawai na fada ni may sukai min da zan zagesu ? Ya gyara zama yana kallona kafin yace ke may kika fadawa Queen gamay da iyayyena wanda uwarta bata kaunan ta sani. Nuna kaina nayi da mamaki nace ni din nan wanan yar har guda nawa take da zan fada mata wani magana da zai tayar mata da hankali. Sai can na tuna nace ko zancen hiran iyayyen mu data tambaye ni na bata labarin kana da baba da mama har da gyany. Yaya ko baka son yarinyar ta san da zancen iyayyen mu ne na fada mata a rashin sani na fada da mamaki ina kallon shi. Yace sosai don lokacin fada mata baiyi ba a gare mu ban san may yasa na kaiki wanan gidan ba ma don kawai ina zaton kaiki can zai dan sakaki walwala na kwana biyu. Ka cuceni yaya da kakaini wurin dabi,un kafirai nace babu tsoro a idanuna ko kadan lokacin. A fusace ya mike tako biyu na ganshi a gabana yace ke wacece mara kunyar banza ina fada kina fada zaki rushe min plain dina. Ganin yadda ya taso kamar zai makeni yasa na duka jin shiru bai kai min dukan dana zata ba yasa na dago kai. Naga duk yanayin shi ya sauya a lokaci guda idanuwan shi duk sun kankance sai kuma naga ya juya kawai ya fita ma gidan ga baki daya. Ajiyan zuciya na sauke jin bai tabi lafiyan jikina ba a yadda naga ya fusata din lokacin. Karasa saukowa nayi zuwa kitchen din na dora abinda zanci ina ciki kuma naji shigowan shi sai abin ya ban mamaki sosai don a zatona ya tafi ke nan. Ban fito ba sai dana karasa aikin da nakeyi na aje falon sama na hau tare da kulle daki don inyi wanka. Na sako dogon riga na mai ruwan kwai da adon duwatsu a gaban rigan na fito don yunwa nake ji sosai. Wanan karon a dan kwance yake yayi filo da hannayen shi kamar mai tunane banji komai ba a raina na nufi wurin abincin na. Na zauna na fara cin abincin nayi kamar cibi uku naji muryan shi yana fadin ina nawa a bincin yake ? Ban san zakaci ba na bashi amsa ya dubeni fuskan shi dauke da mamaki da kuma alaman magana nima ison na tsura mai don jin abinda zaice min din. Da kyat ya iya bude baki shi cikin hadiyan bakin ciki yace kada ki zaton don ance an daura min aure dake raini ya shiga tsakanin mu dake haka. Ina fada kina fada baki tsorana nace ba zan taba raina ka ba yaya ko dan zamanin da kukayi da mahaifiyata. Na fadi ina kada idanuwana tare da rausaya kaina kan abincin da nake ci din har na soma ci naga rashin dacewan hakan kada na biye mashi ina dauki alhakin shi shida abincin shi. Na mike na nufi kitchen abincin na hado mai nakai mai saman dining na aje da ruwa da komai na dauki nawa dana fara ci na koma saman kujera saidana zauna nace . Ga abincin nan na shirya ma ban dauka zaici ba yadda ya share ni sai can naga ya mike ya tashi dauko wani leda yayi a gefen shi ya miko min ya wuce zuwa table din. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:17 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA BAMU WUNI DA DARE MAI AMFANI GARE MU AMIN YA ALLAH πŸ‘ Ban bude ledan ba har ya zauna ya fara cin abincin sai dai nayi mamakin yadda ya ci abincin nawa sosai duk da ba wani hadi nayi maiba kamar yadda a girka abinci special a gidan shi don ina ganin merry nada mai girkin ta shima yana da nasa. Yana gama cin abincin baice dani uffan ba ya mike ya fita a binshi sai bayan ya fitane na ja ledan na bude wayace dallele a cikin kwalin da sim da komai ya saka min a ciki. Idona lumshe tare da jin haushin kaina da ban duba wayan ba tun kan ya fita gidan gashi ban samu yi mashi godiya ba har ya fice don naji tada motar shi. Na dade zaune a gurin kafin in mike na fara gyaran gidan sako da lungu don sanin cewa yan kwanaki suka rage min in koma school hutun mu ya kare. Wanan dakin da nake ganin nasa ne na nufa na tura nayi mamakin ganin dakin a bude ban tsaya wani tunane ba na kutsa kai cikin dakin. Tsayawa nayi ina bin dakin da kallo tare da mamaki a raina nace lalle ya umar jarumi ne a cikin mazaje. Mai tsananin kwazo don abinshi ya ban tsoro yadda komai nasa a waye da tsada yake don wancan gidan nasu ba abinda zai nunawa gidana na jin dadi sai girma da jama,a dake cikin sa. Yadda yaya yake matashi mai tasowa a lasan wasu ya mallaki wanan daulan haka kara matsawa nayi na shiga dakin da kyau. Bin dakin naci gaba dayi da kallo can na hango yadda aka tsara wanan dakin da shimfido masu kyau ga gefe da yake ibada shima an kawatar da wurin gwanin ban sha,awa. An aje kur,anai manya da kanana ga casbaha har da turare a gurin da mamaki nake kallon dakin wani irin tausayin shine ya tsargu a raina. Watau mutum duk inda yake baya mantawa da ibadan sa dai ko wani irin akida yake bi kenan maganan kawu ne ya fado min a raina. Da yace Fatima nauyi ne babba a kanki a cikin wanan auren kece muka ba wuka da naman jawo hankalin mijin ki ga addinin shi. Na miji bai kammaluwa namiji sai da taimakon iyalin shi ki natsu ki gane ida yake da rauni a cikin addini dama wani hali da bai ahafi addini ba don in kin duba rayuwan mu na hausawa duk a addinece yake tafiya sai dai wasu gurare akan saka al,ada da yawa ya zarce sunna. Idona lumshe tunowa da su kawu danayi yatin dana bude su kuma a hankali don sai yanzu na fara fahintan inda maganan kawu din ya dosa don a lokacin ban fahinci mai maganan yake nufi ba. Ban dakin na nufa komai nan ma a natse yake na wanke mai shi tas duk da ba zama yake nan din ba sosai na fito na gyara ko ina a dakin sai dai nayi mamakin ganin takardun shi na komai dake gidan a cikin wardrobe din da gani masu muhinmancine sosai don yadda ya ajesu din a daure. Ban fito dakin ba sai da nayi sallolina a gurin nan daya kawatu don ibada sai naji na samu natsu sosai da kusantuwa da Allah . Addu,a nayi sosai tare da addua ga iyayyan mu dashi kanshi ya umar din na zauna nayi mai addua sosai ranan don ni a ganina merry tana gab data janyeshi zuwa nata a kidan ne yadda naga sunayi dashi a cikin yan uwanta din wurin picnic . Bayan na gama na fito na samu ruwa na watsa ma jikina har lokacin bai shigo ba hakan yasa na rufe gidana da wuri. Sam na manta akwai waya yanzu a hannu na karan wayan dake ringing a gefena ya dan razanani don ban saba da rike waya ba ko a gida. Dauka nayi Allah ya taimakeni na iya komai na waya da wayan mamu danakan dan jagula a gida. Salama nayi naji yace ba tare da tsayawa amsa min ba gobe ki shiga schools din ku kiyi komai don kafin a koma ake komai. Kudi na nan na aje a wardrobe dakina nasan zasu isheki idan basu isa ba ki bugo min ta wanan layin nawa. Jin yana sgurin kashe wayan shi yasa nayi saurin fadin yaya nagode Allah ya kara budi na alheri. Uhumm yace kamar zai kashe wayan sai kuma yace ki dai kula da kanki kin san garin nan sai mutum ya kula sosai ninayi tafiya ban ma kasan a yanzu haka. Mamaki abin ya bani nace Allah ya dawo dakai lafiya yaya amin yace ya kashe wayan. Kallon wayan dake hannuna nayi na sauke a jiyan zuciya tare da fadin a shirye nake kawu dana fara auwatarma da aikin daka bani tsakani da Allah. Shiko ya umar yana kashe wayan ya sauke ajiyan zuciya da kyat ya iya daga kafan shi ya fara tafiya cikin filin jirgin da yake. Sai faman tunane yake yarinyar dabi,un ta da sauyawan ta suna kashe mata jiki ji dan wanan abinda ya fada yadda yarinyar take zuba mai godiya. Motan da tazo daukan shi ya bude ya shiga zuwa hotel din da yake sauka idan ya shigo kasan da yar jakkar da yake rataye a bayan shi da komai ya fada saman gadon yana sauke numfashi. Yana kwance ya zubawa kwaliyan dakin ido cikin kankanin lokaci ya umar ya tsinci kanshi a cikin tashin hankali mara musaltuwa don irin rigiman da suka kwasa da merry kafin ya bar gida. Take kwakwalwan shi ta dinga hasko mai maganan mahaifin shi yake jin muryan kawu kamar a lokacin ne yake masa maganan. Tabbas ya yarda komai shekarun ka manya sun fika hangen nesa yayi huci yana dafe kanshi. Yau ya sani yayi babban kuskuren bin son zuciyar shi na yarda da yaudara irin na mata da har ya yarda da dadin bakin merry ya aure ta. Bayan irin alkawarin da sukayiwa juna na zama a cikin amana da junan su har karshen rayuwan su . Sai gashi wai yau merry ce ta fito baro baro take fada mai ba zata yarda yarsu tabi akidan shi ba don haka bata yarda kowa nasa ya mami yarsu a yanzu ba don kada a juye mata zuciyar yarinya. Ya kare huci yana mirginawa tabbas ba zai daina dora laifin hakan a kanshi ba don tun yana karami yasan manzon rahama ya fada mazaje su zabawa yayayen su uwaye na gari. Gashi yau sanadin abinda yar kankanuwan yarinyar nan fatima taga merry tana masa har yakai tsoro da shakkun sa sun fara fita idon yarinyar. Dolene mana ta nuna min hakan yace na biyewa son zuciya don kawai matata taji dadi na take gaskiya da gangan. Idanuwan shi ya rufe yana fadin gara da daddy ya dawo dani a hanya da nasihohin shi masu kama da wa,azi yana godiya ga Allah da baiyiwa daddy din butulci ba da abinda zai gani sai yafi hakan. Zai iya jure komai da merry zasuyi mai da yan uwan shi amma ba zai yarda yarshi ta taso da akidan kiristanci ba a rayuwan ta. Yana tsoron may zai je ya fada a gaban ubangijin shi akan yarinyar.. Bangaren merry kuwa tun bayan yadda suka kwashe dashi a gidan ya fito bai ce mata komai ba ta gane tafiya zaiyi hankalin ta ya tashi. Don ita tsoron kada ya gudu ya koma kasan shi take ji don saida ta daure taci masa mutunci kamar yadda aka dorata tayi din. Haka yasa take ta kokarin gwada layukan shi ko zai shiga sai dai amsan daya ne har lokacin wayab shi a kashe take. Zuciyan ta ya kasa samun natsuwa kan maganganun daya rufe ido ya fada mata lokacin shine ya tsaya mata a rai. Don cewa da yayi addinin shi ya bashi daman kara mata da yaya ko yaushe ta tuna wanan yana cikin alkawarin su a baya tunkan suyi auren. Ta gyara zama tana fadin anya kuwa shawaran kawayen ta da iyayyen ta idan tabi har ta hana yarta koyi da addinin mahaifin nata da yake son koya mata zata samu mafita. Greco ce ta dan zo inda take tana tambayan idan wani abu take so a lokacin ? Kai merry ta girgiza mata gami da cewa bana bukatan komai hutu nake so yanzu kawai jin hakan yasa ta bar gurin da sauri. Kamar yadda yaya yace inje school hakan yasa da safe na shirya zuwa clearance din takarduna. Saida na shiga na fita ban samu matsalan komai ba sai mutum daya nake jira in kammala na samu wuri ina hutawa inda va mutane sosai a wurin. Hankalina yana gun wayan da a lokacin banda layin kowa a cikin ta sai game da nake yawan yi dama shine aikina idan na dauki waya. Dan dago kai nayi tare da duban lokaci ina jan tsuki tare da fadi cikin hausa na tsani jira wallahi. Da sauri matar da ke kusa dani ta juyo tana kallona tace sister ke bahausa ce ? Kaina kada mata kawai ban iya bata amsa ba lokacin na kara jan tsuki ina kokatlrin mikewa don gajiya da zaman danayi wurin. Matar data manyace ni sosai ta sake fadin gaki da alama dai kina a cikin damuwa da ganin ki. Dan murmushi na kakaro a fuskana tare da fadin ba komai nagode nace mata ina kokarin mikewa. Hannun ta takai saman kafadan ta dafa tana fadin kinga kanwata ban yarda baki cikin damuwa ba don duk wani mahaluki mamanlakin hankali ya dubi fuskanki a haka yasan kina a cikin damuwa yar uwa. Sai dai idan boye min zakiyi and kinsan abinda yasa nayi saurin fahintar hakan kanwata na sake girgiza mata kai alaman a a. Tace na dauka idan yan kasa daya suka hade a wani kaaa suna daukan janunan su tankar yan uwane don kamar sunga wani na jikin sune, . Amma ke sabanin hakan na gani a gareki ya kamata at list ace kinyi farin ciki da ganin yar kasar ku yau koba komai a zamu dinga zumun ci ko ? Gaki da gani ke yarinyace baki da aure niko kinga macen aurece sai mu zama kamar yada kanwa dake nan ni suna Farida Aliyu daga kano nake tace tana kallona da dan murmushi a fuskanta. Murmushin dole na kakaro a nawa fuskan nima nace anty farida ke nan ni kuma fatima Abubakar nake nima daga kanon nake a old GRA. Tace kice dai dukan mu yan gari dayane ashe kinga surutuna da naci bai zama banza ba don kin samu yar uwa a nan ke nan. Murmushin na sake sakewa a karo na barkatai tace kina tare da iyayyen ki ne ko yayan ki ke nan ko ke dai kika zo karatunan ? Nace ina tare da yayana ne sai dai gidan shi yana can wani unguwa ni kadai ke zaune a gidana sai lokaci lokaci nake zuwa ganin su. Hakan yana da kyau sosai don kinga mu bamu da nisa sosai mijinane ya samu aiki a nan ya kwaso mu shine nayi amfani da wanan daman nake karatu kada inyi zaman banza ai kinga gaba idan zama ya mayar damu gida zai amfane mu. Gama can yadda karatu yake da wahalan nan hakan yasa na kuke saida maigidana ya nema min addimition nan na fara karatu. Ta nisa tare da fadin well fatima ko kada in cikaki da surutu naga kamar baki da yawan hayani sai dai idan mun kara haduwa ko ? Nace a ciki murmushi ayya ba matsala wallahi ai na gode ta mike tana gyara gyalen abayan ta ta fara tafiya sai kuma ta tsaya tana fadin ko zaki ban layin ki don muji saukin kara haduwa. Nace a cikin sakin fuska ayyah kiga kuwa ban hadece layina ba saidai idan zaki saka min naki saina kira ki samu layina din. Tana fadi ina dauka na danna kiran sai ya shiga a wayan ta tace yashigo sai anjima mukayi da ita ta wuce. Ranan dai ban samu karasa abinda naje yi ba don haka na koma gida a gajiye saida na dan huta na mike zuwa ciki na watsa ruwa don banda niyar dafa komai ranan kifin gwagwani da bread zanci. Saman kujera mai zaman mutum uku nake zaune ina kallo ni kadai a gida kamar manya na manta da zancen waya sam don ban saba dashi ba. Karan wayan ya dan firgitani na zabura daga inda nake zaune na dauko da sauri nayi recieven call. Sister yaya kike kin dawo gida lafiya ko sai lokacin na tuna da zancen ta mun gaisa har yaran ta biyu taba waya mukai gaisuwa dasu mukai sallama ta kashe. Ban kai ga aje wayan ba wani kiran yana shigo min a daidai lokacin na dauka. Ke wata irin dakikiyace wai may ye amfanin wayan dake hannun ki da baza ki kira mutum kiji lafiyan shi ba. Wai ma da wa kike waya ne tundazu ina kira ana fadin kina busy ? Wai waye wanan daga kira sai fada min maganan banza kaika ajeni ko may ko a kanka nake na azama nauyi ? Ina jin yana sake wani irin murmushi mai dauke da takaicin kalaman da na fada mai na nuna ban gane mai magana ba. Yace yanzu na san ke din ba karamar shedaniya bace ni kike fadawa haka don samun wuri ni zakice wai baki sheda muryana ba komai don shedan ci. Nace to ni nasan wanda ya kirani ne da kake kirana da shedaniya ka fada min ko waye mana kai tsaye. Yayi huci tare da dafe kanshi ya kuta ya kashe wayan gaba daya dan tsuki naja ina aje wayan tare da fadin miskilin banza kawai gobe ka kirani ka zageni idan halin kane . A bangaren shi tun yana mamakina har abin kuma ya bashi dariya yasan da gangan nayi haka don haka bai kara kirana ba nima ban kirashi ba din. A fili ya furta zan hadu dake yar iskan yarinya mara kunya yaci gaba da aikin shi tun wanan lokacin ya fita batuna. Haduwa da anty farida yai min dadi don ashe dan kasa kadan suke da layin mu mukan tako da kafa muna hira zuwa gida. A cikin sati daya sabo sosai ya shiga tsakanin mu da ita sai naji zuciyata ya kara kwantawa sosai na sake banda sauran damuwa ko kadan a tare dani. Wasa wasa saida yaya ya share sati uku bai leko ba nima ban kira layin shi gashi duk zaman mu da anty Farida ban taba fada mata cewa ni matar aure bace. Don haka take daukana a matsayin budurwa har take fadin zatayiwa kanin ta kamay idan mun koma nigeria ta hadamu. Ni dai nakan mata murmushi kawai nakanyi ban bata amsa maganan ta don ban yarda da ta san sirina ba ko kadan dukda ita ta mayar dani tankar wata yar uwanta can ta jini. Yau ma da zamu dawo mun dade dade tsaye a waje tana ban labarin wani tafiya da sukayi dan duban lokaci nayi nace zan shige gida wai ina gidan naki yake ta tambaya na nuna mata da hannu tace wancan babban gidan wai kike nufi. Aiko maigidana ya fada min kamar gidan wani dan Nigeria ne na katseta da fadin yayanane ai tace au a cikin mamaki. Munyi sallama ta tafi na nufo gidan don nagaji saboda na fahinci ita mai yawan dumine sosai bata gajiya. Na tura gidan na shiga sai naga kofan a bude gabana ne ya wani irin faduwa take laifin da nayi mai yazo min a rai. Haka na daure na karasa shiga gidan duk da banga motar shi a gidan ba lokacin. Na shigo falon dake gauraye da sayin AC ga kamshi yana tashi a falon TV kuma yana a kunne lokacin. Sallama nayi danaga haka na shigo sai dai shiru da babu kowa a folon ko wani motsi bayan na tv da ke aiki a falon lokacin. Saboda hakan na ratsa ta bayan kujerun falon zan nufi dakin baccina sai dai zuciyata a cikin tsoro take lokacin . Har na fara taka step din na hangoshi zaune kasa zaune kasa saman rogh carpet din falon ya jingina bayan shi ga kujera daya na falon. Ya kuma sanya duks hannayen shi guda biyu ya dafe kanshi ta baya ya tsurawa wuri daya idanu kamar mai tunane. Dan dawowa baya nayi zuwa wurin shi ina fadin a sanyaye sannu da zuwa yaya na hada da gaishe shi. Da kyat ya iya dago kai ya amsa min cikin dauri ya kawar da kai ta hanyan mayar da kanshi saman kujeran. Ban tsaya ba na ja kafa da kyat zuwa sama ina tunanen ko may ya samay shi haka ban sani ba. Sanin yana gida ga kuma yamma yayi na fito a gurguje na dora muna girki don kada kuma inyi laifi a gurin shi. Cikin dan kankanin lokaci nagama na nufo falon samu nayi baya nan falon lokacin dakina na koma har nayi wanka tare da sallah na fito har lokacin bai fito falo ba. Har nufo falo sai kuma wata zuciya tace in lekashi dakin batcin shi a kofana tsaya na kwankwasa. Sai naga kofan dakin ya bude sallama na kara yi yanzun ma a zaune yake a gurin nan da nagani ya tanada don sallah. Wanan karon godin shine ya dafe da hannun daya shi kadai yasan irin halin da yake ciki . Gaishe shi na kara yi a sanyaye ya amsa min cikin gyada kai nace yaya na gama abincin yana dining. Cikin dauriya yace min zan fito amma sai anjima yanzu na gama shan magani mura yana damuna sosai . Nace Allah ya sauwaka na juya na fita a karon nan naji dan tausayin shi a raina cikin zuciyana ina kuma tunane anya muran ne kawai ke damun shi haka ? ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:17 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH, , , , , A sanyaye ba bar part din zuwa kasa ina tunanen abinda ya samay shi haka na ganshi a cikin wanan damuwan haka ? Zama nayi na fara juya abincin cibi biyu sai na kasa ci naji abincin ya fice mun a rai na dade zaune ina tunane har na kaiga yadda kaina saman tablen din na dan kwanta. Ban san nayi barci a wurin ba gwanin ban tausayi dani idan kin ganni jin ana dan bubuga table din tare da kiran sunana ke fatima. May nene haka kuma ki rasa inda zaki barci sai a nan kin saka abinci a gaba da alama ma baki ci abincin ba ? Firgigit na bude idanuna yana tsaye a kaina ya harde hannaye shi guri daya idanuwan shi akaina baya ko kyaftasu. Ina ganin shi nayi saurin tashi tsaye ina dan matsawa baya tare da fadin sannu yaya jikin yayi sauki ke nan ga abincin nan naka aje. Ba tare da yace min komai ba ya juya zuwa wurin kujeran dake fuskantan wanda na tashi akai. Abincin ya bude nau,in abincin mu na gidane nayi don akwai garin semo da miyar ganye don shi ke gareni. Ganin ya zauna yana kokarin zubawa yasa na juya zan bar gurin ya dago kai ya dubeni tare da fadin ina kuma zaki bakici abincin ba. A cikin dan murya kamar shagwabe nace na koshi ne yaya daga haka na juya na tafi na barshi a gurin ba tare da ko waigowa ba. Ajiyan zuciya ya sauke bayan ya gama bina da kallo ina hawa sama tausayi na bashi don ya fahinci yanayin dana ganshi a cikin ne yasa na koma hakan lokaci guda. Ina shiga daki na rufo ban tsaya yin komai ba nabi lafiyan gadona na kwanta sai barci. Washegari na tashi kamar kullun ban tsaya komai ba nahau gyaran gida da giriki don nasan dole a nan zaici abinci kafin bakwai da rabi na kammala a gurguje nayi wanka na shirya. Na fito banji motsin shi a falon ba kamar in fita don ba hurimi na bane shiga mashi daki don a matsayin dayace in dauke shi nake daukan shi. Wata zuciya tace min ba daidai bane in fita ban lekashi ba bayan nasan ya zo baida lafiya gidan. Da kwankwasa kofan nayi tare da sallama daga kofan dakin ciki ciki ya amsa min da shigo na dan shigo tare da hangoshi nade a cikin bargo yana kwance. Ya ina kwana ya karfin jikin naka nace daga inda na dan rage tsawo ina gaida shi a matsayin shi na magabaci a gareni yadda aka koya muna a gida. Amsawa yayi ciki ciki tare da fadin taimaka ki hada min dan ruwan zafi don Allah a bandaki ya ban tausayi sosai don haka kai tsaye na wuce gabatar mai da ruwan kamar yadda yace. Wayana dake cikin jakkar da zan fitane ya dauki ringing a lokacin ina fitowa naji na dauko wayan da sauri naga mai kirana din ? Anty Farida ce ina dauka tana fadin kina ina ne sister baki fito ba har yanzu don mun saba duk safe sai mun gaisa kafin mu wuce department din mu sai kuma idan an tashi zamu hade. Anty yau yayana ne yazo gidan kuma baida lafiya da sauri tace yana gidan ki ne ? Nace eh yana nan gida jiya ya dawo daga gurin tafiya da ciwon tace kinga zauna gida kawai ki kula dashi. Idan kin fito wa zai kula dashi kuma zan tafi department din naku inyi complain tace a karshe. A sanyaye na amsa mata da nagode anty muka kashe wayan bayan sallama. Na juya inda yake ina fadin yaya na hada ruwan kada ya huce shiru naji na koma kiranshi da yaya ga ruwan a bayi na hada. Yayi firgigit ya dawo cikin hayacin sa tare da juyowa yana kallona yana fadin naji. Fita nayi daga dakin zuwa dakina na aje jakkata dana dauka da niyar fita makaranta anty ta hanani. Dan kwanciya nayi da niyar idan ya fito in shiga in gyara mai dakin shi ina game a waya har ya fito yayi breakfast ban sani ba. Ya gama ya fita daga gidan zuwa sayo magani daga can ya wuce wurin wani abokin arkallan shi wata unguwa. Bayan la,asar ina falona zaune cikin dan walwala don yanzu samun waya a hannuna yakan debe min kewan komai tare dani. Wayana ne yayi kara na duba anty farida dai ne still take kiran layin don ita kadai keda layina a lokacin bayan ita banda wani layin waya bayan nata kuma. Ina dauka take fadin sister gani a layin ku ki mun kwatancen gidan ki gabana ne ya fadi don sanin yaya yayi mun kashedin yin abokai barkatai tun farko. Haka dai na daure nayi mata kwantancen gidan ba,a dauki wani lokaci ba sai naji bell din gidan yana ringing. Dama ina falon na mike zuwa duba kowaye a wajen da anty farida mukai arba tana min murmushi ta shigo tare da bin gidan da kallo. Muka samu wuri muka zauna har lokacin tana bin gidan da kallo ko mamaki hakan take a ranta oho. Bayan mun gaisa ne take tambayana yaya mai jikin nace da sauki take fadin Allah ya sauwaka . Take min bayanin ta daukan min excuse na one day a school an yarda nayi mata godiya muna cikin hiran school din ne ya dawo. Gabanane ya fadi don tsoron matakin da zai daukar min idan ya ganni da bakuwa a gidan don dai a yanzu banson in masa laifin da zai jawo min matsala ga karatuna yanzu. Sannu da zuwa nayi mai ina mai rakubewa gefen kofan tare da dukar da kaina kasa. Yana ganin ta yaja yayi turus tare da kallonta da mamaki sai kuma ya fara tafiya itace ta fara gaidashi tana mashi ya jikin shi a cikin harshen hausa. Lafiya ya amsa ba tare da ya tsaya falin ba ya wuce zuwa ciki kai tsaye ta bishi da dan kallo. Bayan ya shige ta dan kalleni tana fadin shine yayan naki da baida lafiya na amsa mata da eh kawai. Na dawo na zauna acikin dan tsarguwa da wasancewa ina fadin yaji sauki ai don tun dazun ya fita sai yanzu ya dawo. Ke fatima yace daga saman inda yake tsaye hakan yasa na amsa da sauri ina mikewa a daidai lokacin kuma anty ke fadin nima zan tafi ke nan don ko gida ban karasa ba nabiyo inga jikin nasa. Zan rakata tace da sauri a,a je gurin shi kawai ni zan tafi godiya nayi mata tare da dan rakata kofan fita falon taso ta dan bugi cikina taji shine yayan nawa kuwa kodai wani ne shi . Naki sanar da ita komai don tsoron tonawa kanmu asiri da kuma warning dina dayayi tun farkon zuwana kasan. Da sauri na juya zuwa guri shi ina isa na dan rakube ina fadin gani yaya. Shiru yayi min yana tsaye a tsakiyan dakin ya dunkule hannayen shi a guri daya ina a rakube a guri daya na sake fadin gani yaya. Ya juyo tare da tsareni da ido yace wanan wace matace na gani a gidan nan ita din wacece a ina kuma kika santa har tazo gidan nan. Kaina na dukar kasa kafin ince anty faridace a makarantar mu take nan na santa a school din mu itama take karatu. Yau ban shiga school ba shine take tambayana nace kaine baka da lafiya banzo ba shine tazo ta gaida kai. Yaune farkon zuwanta gidan nan ya dago mi hannu yana fadin ya isa don Allah kin kama jero min magana kamar redio haka. A raina nace kaida ka jefo min tambaya babu iyaka har na rasa wanda zan amsa ma ba laifi ba saini dana ba da amsa. Muryan shi ya dawo dani yana fadin kenan kin fada mata alakan dake tsakanina dake ko ? Dago kainayi na kalle shi nace eh na fada mata kafin in karasa ya dago kai da sauri yana kallona cikin zare mun ido nace na fada mata cewa kai yayanane kaine ma ka kawo ni karatu a kasan nan. Yayi saurin kawar da kanshi daga kallo ya juya sai yace ban fada maki banson hurdan ki da kowa ba a kasan nan ? Naga ita din ma yar kasan muce kuma a gari daya muka fito da ita kuma itace ta, , , , hannu ya daga min . Yace bari kiji duk ranan da kika kuskura kika fadawa wani alakan dake tsakanin mu dake sai na batar dake a garin nan kowa ya huta Na dago kaina kalleshi cike da mamaki da tsoron abinda ya fada sai ranan na tabbatar da baya kaunana har abada a rayuwan shi . Hakan yasa nayi shiru ban karasa fadin abinda zan fadi a lokacin ba nayi shiru. Ganin zai shiga bandaki yasa nayi saurin fita daga dakin zuwa kasa na kyale shi a dakin nashi na dawo na zauna ina mamakin wanan irin al,amarin nasa na boye matsayina a gurin shi. Har washe gari bamu kara haduwa dashi ba har na gama abinda zanyi na wuce zuwa schoool daukan darasi. Bamu samu haduwa da antyna ba sai da muka hade a school mosque wurin sallah azahar. Daga can muka wuce zuwa wurin cin abinci sai dai na zauna ina kallon abincin ban taba ba yadda aka kawo min shi. Anty farida tana hankalce dani saida tayi nisa da cin abincin ta kalleni tayi murmushi tare da fadin sister . Hakan yasa na dago kai na dan kalleta abincin ta nuna min da idanun ta ma,ana inci abinci mana. Hakan yasa na dan murmusa na dauki spoon din ina dan cakula abincin a hankali. Amma dai yayan nan naki sai naga baku da kama na jini tare dashi wuri daya ko biyune kuke da kama shine hasken fata da tsayi kawai. Nace ko anty ? Ta sake fadin saidai sam sister bakuyi kamar wa da kanwarshi ba gaskiya. Da sauri na kalle ta nace anty don may kikace tayi murmushi tare da fadi kanwata kunfi kama da miji da mata fa anya ba kina boye min gaskiyan wanan al,amarin bane kuwa ? Dan murmushi nayi tare da fadin kai haba anty yayanane fa na fada maki tun farko ai. Tace aina sani saidai kin san akwai aure a tsakanin wani wa da kanwa din wani lokaci kodai hakan ne kanwata ta tambayeni tana dariya. Hannuna dake saman abin cin abincin ta dafa tare da fadin ina son ki sanu ciwon diya mace na ya macene yar uwanta. Koda bamu zama kamar yan uwa na jini daya a nan ba matsayina na diya mace zaki iya fada min matsalan ki in magance maki shi. A matsayina na wace ta girmay maki sosai ga haihuwa don haka idan har kin daukeni kamar yar uwanki na jini ina son ki fada min damuwan ki sister. A hankali na dago kaina na kalleta da idanuwana da suka fara zubar da hawaye a lokacin nace anty yaya yayanane kuma mijinane. Wani kallo tayi min tana murmushi kafintace ai na dade da fahintar hakan ban kara gaskanta zargina ba sai da naje gidan naga gidan ki da mijin ki. Dan kankanin lokaci na fahinci cewa akwai matsala a zaman auren ku gaskiya alama ya nuna min akwai tauyewan rayuwa sosai a zaman ku don yawan tsorin mijin ki da kikeyi. Nace hakane anty tiryan tiryan na fara bata labarin komai tun daga farko har zuwan mu gidan merry da tun lokacin yake dan kula dani da komai nawa. Anty Farida ta cika da mamakin a zuciyar tbata labarin dana bata wanan wani irin mugun mutum ne ka dauko yarinya karama amana. Kazo ka dinga muzguna mata duk da tana yar uwanshi kuma amana iyayyen su suka bashi don taimakon kanshi da kanshi nan gaba. Wanan rashin imanin da mai yai kama ranan bata iya fada min komai ba sai hakkurin data bani muka mike zuwa gida daga nan. A gida kuwa ya umar ya danji sauki ya mike da kyat baiji motsina ba ranan haka ya daure ya mike ya shiga bayi ya watsa ma jikin shi ruwa. Saida ya fito daga bayin ya kalli lokaci yaga rana tayi sosai har kusan fast twelve na rana. Ya fito rai bace da zuman yi min fada don sam ya manta da ina zuwa makaranta a lokacin . Abincin shi ya fara arba dashi a dining din ya duba har kitchen din gidan na gyara komai neat kamar ba gidan karamar yarinya ba. Tunane kala kala ya dingayi a ranshi sai can ya tuna da ranan akwai school abincin ya zauna yadan taba kadan ya fita. Na shiga na watsa ruwa na dan huta na fito na dora girkin abincin dare duk da ban san ko yana gidan ba ko yatafine. Kafin in gama ya dawo gidan lokacin duhu yadan fara ina rike da blender ina juye kayan miyan dana markada. A bakin kofa yaja ya tsaya kamshin girkin na dukan hancin shi sai lokacin naji alaman mutum.a bayana na juyo na ganshi gabana ne ya fadi. Nayi saurin yin dan kasa ina fadin sannu da zuwa yaya cikin rawan murya bai amsa ba sai fadin dayayi may kika tsaya yi har dare yayi maki ga girki , ? Nace na dawo da wuri girkin daine ban dora da wuri ba don ban san ko ka koma gida ba. Ya kara hade rai tare da fadin wanan bakin mai yawan surutun tsiya kan ya ja tsuki ya juya ya tafi naci gaba da aikina har na karasa komai na gyara gurin kamar banyi girki ba ciki. Baya falon koda na fito na shiga daki wanka nayi nai sallah saida har isha,i na idar sannan na fito falon don cin abinci. Turus nayi don ganin shi kwance saman dogon kujeran falon yana kallon labaran aljazzera jikin shi yana saye da kananan kaya lokacin. Daga nesa kadan dashi na dan tsaya ina fadin na gama abincin. Ya juyo ya dan kalleni baice komai ba ya mike zuwa dining din yans bude kulan abincin yaja kujera ya zauna ya fara kokarin zubawa. Cikina ne ya fara min kugi a lokacin sai lokavin na tuna na kasa cin komai saboda kalaman shi na jiya gareni. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:17 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , , Gida Nigeria kano ta dabo tunbin giwa gidan kawu sani yau tun da safe sun tashi da tashin hankali a gidan don ciwon kawu daya motsa mai tun yana dan yi a tsatsaye har ya kaishi kwance. A cikin dare ranan dai basuyi barci ba don jikin kawu daya motsa mai da asuban fari mamu ta kira ya Ahmed a waya tana sheda mai halin da kawu yake ciki. Yana idar da sallah a kofan gidan kawu gari ya dan haska mai don dan tazaran dake tsakanin gidan su dana kawu din. Ya shigo kai tsaye gidan inda ya tun kari turakan kawu kai tsaye duk ahalin gidan har Amma suna cikin part din nashi lokacin. Shigowan shi falon da sallama ya nufi inda Alh yake kwance matan shi dun kewaye shi gabaki daya da mahaufiyan har mama hadiye. Ya dan dade tsaye yana kallon shikafin ya ciro wayan shi yana kiran layin Abubakar . Ya amsa da gani kofan gidan na iso ba,a jima ba Sadiq din ya shigo falon shima ganin yanayin da surukin shi maigidan su yake ciki. Ahmed bai tsaya jiran komai ba yace kamashi mukaishi mota ya fadawa sadiq kai tsaye yana kokarin dago Alh daga inda yake kwance. Shima sadiq din yayi yun kurin dago dayan gefen da yake tsaye duk kawu bai san sunayi ba lokacin don jikin da yake ji din. Mata da yara sai kuka sukeyi don halin da maigidan nasu ke ciki a lokacin hankali tashe da taimakon Allah suka samu suka saka tsohun a mota an rasa mai karfin halin shiga cikin su don a zaton su hjy ce ya dace ta shiga motan lokacin. Saidai gane abinda suke nufi yasa mama hadiye fadawa motar a baya tare da Ahmed sadiq yaja motar tasu. Asibiti suka nufa kai tsaye dashi cikin dan lokaci sun isa Ahmed ya fita ya kira akazo da gado daukan marasa lafiya aka dauki Alh . Bayan wuce wansu ne Amma tace yau dai kun fara ganin manufar yaron nan da wanan hadin dayayi ga yaran nan . Yau da yaran nan ba na jikin shi bane, ko suna rakan mu baza muyi bugun gaba dasu haka ba lokaci guda. Kallon juna hjy da hjy maryam sukayi kafin su fara barin gutin daya bayan daya suna shiga daga ciki mamu tace gwaggo barin shiga in shirya in fito in bisu muga halin da suke ciki a can. Ba abinda ya batawa hjy jummai rai kamar yadda Ahmed bai tsaya gaida su ba yana kokatin ceton ran surukin nasa a lokacin. Wanda tun bayan badakalan da sukayi dashi lokacin buki bata kara ganin shi ba sai wanan ranan kuma. Tana cika tana batsewa ga halin da take ciki na tashin hankali mijin su daya daga mata hankali kuma. Kamar yadda ko wani gidan da ba hadin kai yake nan ma hakan ne ya faru don basu hada kafa wurin zuwa asibitin ba daya bayan daya suka isa gurin kusan lokaci guda. Sun samu har an saka mai ruwa ana kara mashi har lokacin bai farfado daga yanayin da yake din ba har lokacin. Suna zaune daga waje a cikin damuwa saidai babu mai ma dan uwan shi magana ko ta tsiya asalima ko gaisuwa hjy jummai ta yake duk wani alaka tsakanin ta da mamu a yanzu tun bayan faruwan auren yayan su. Ahmed ne da sadiq suka nufo wurin dauke da lrdojin magani a hannun su wanda likita ya bukata su kawo. Ganin su yasa sukaja suka tsaya sai lokacin suke gaida su ba tare da wani sakin fuska ba ko walwala a lokacin. Suna gama gaidasu Ahmed yasa kai ya shige shima sadiq ya mara masa baya. Bayan shigan sune hjy jummai dake ta hare hare taja wani dogon tsuki tana kau da kanta gare su. Tare da dan maganganu ciki ciki wanda ita kadai tasan abinda take fadi a lokacin don ba wanda ke jin ta. Daga nan kowa dai ta juya ba maiwa wani magana har lokacin kowa da abinda ke ranshi a lokacin. Can hjy jummai ta mike ta nufi kofan dakin ta shiga sai lokacin hjy maryam ta iya kallon mamu da zuman munafunci sai mamu ta kauda kai gare ta don mamu ta gane nufin ta. Ahmed ne ya leko yana fadin hjy ku shigo daga ciki ku ga halin da yake ciki numfashin yanzu ya sauko daidai. A lokaci daya suka mike don shiga dakin inda suka samu hjy jummai tsaye a kanshi tana kallon yanayin da yake ciki din. Tsayawa sukayi sun kura mai ido kafin mamu ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya sauwaka yasa ciwo kafarra ne. Mazan da hjy maryam da mama hadiye suka amsa mata da Amin lokaci guda hjy dai tankar bata san dasu a dakin ba ta nuna. London a nan hakurina kullun karuwa yake duk abinda yaya zai mun ina kokari shanyewa a raina ban fasa yi masa biyayyan da nake masa a kulun gashi yanzu duk kwana biyu yakan kasance a gidan tare dani duk da ba wani mu,amula a tsakanin mu hakan yasa na dan samu sakewa sosai yanzu. Mun shiga weekend hakan yasa washe gari ban fita zuwa ko ina ba gyaran gida nayi kamar yadda na saba yi din idan weekend yazo. Sam ban sa rai da zuwan shi gidaba a ranan don ban ma saka shi a ido ba tsawon kwanaki ke nan. Kwatsam ya fado min gidan kallon yanayin shi kawai da nayi nasan baya cikin hayacin shi a lokacin saidai halin sa sai ka fahunce shi zaka gane hakan. Ina mai sannu da zuwa ya amsa da yawa yana zama saman kujera dan nisa dani kadan ya samu yakai zaune. Kamar yadda anty ta fada min idan ya share ni in kula shi tunda halin sa ne kusan hakan. Mikewa nayi na dauko mai abin sha na kawo mai gaban shi na aje na koma inda na tashi ina dan satan kallon shi. Kallon inda yake zaune nayi na dan kura mai idanu cikin daurewa karo na farko zan gwada shawaran anty farida a fili nace. Yaya me yake faruwa da kaine ne na ganka a cikin wani yanayi na damuwa yau din ? Yayi firgigit ya dawo cikin yanayin shi tare da dago kai ya dan kalleni kafin ya dauki lemon da na aje mai yana tsiyayawa kadan. Haka ina kallon shi ya dan kurba kadan jiki babu kwari ya aje cup din saman table ya maida kanshi saman kujera tare da lumshe idanuwan shi gami da dafe goshin. Na mike kamar yadda tace in daina jin tsoron shi in dinga fuskantar shi kai tsaye kada in nuna darin shi ko tsoro idan zanyi magana dashi nace. Yaya ka fada min may ya samay ka ko da wani taimakon da zan iyayi sai inyi maka don Allah yaya kada kace zaka boye min damuwan ka ni kamar yar kace ko kanwaka ta jini a nan. Hannun shi daya dafe goshin shi ya cire daga jikin shi yana kallona sai kawai naga ya dan zamo yana dan kallona a cikin mamakin kalamina. Sai da ya kaea dubana da kyau sai ya tsunci kanshi da bani amsa kai tsaye a lokacin don ba wanda zai amayarwa zuciyan shi yadda yake ji din. Fatima ina cikin tashin hankali sosai tun jiya da aka bugo min waya daddy baida lafiya kwana uku ke nan bai farfado ba. Gaba daya na mayar da kallona gare shi cikin damuwa da tashin hankalin abindaya furta a lokacin. Nace ya umar wai kawuna kake nufin baida lafiya har hakan yace tun jiya Aliyu ya bugo min waya yana sheda min nayi kokarin yau din nan in wuce zuwa Nigeria sai dai hakan bai samu ba gareni. Bai farga da halin da nake ciki ba a lokacin sai daga baya ya kula da yanayin dana shiga a rude ya tashi zuwa kujeran danake zaune ya fara jijigani a hankali. A rude yake kiran sunana yana son tabani yana jin shakku yi hakan gareni. Ba yadda ya iya ya dagoni dole badon yaso ba ya fara jijigani a hankali kafin ya juya inda ruwa dana aje mai ya dan debo yana yayafa min. A jiya zuciya na sauke a hankali tare da kokarin bude idanuwana a hankali na sauke a gare shi. Yace ke fatima da dan karfi nace yaya idan kawu ya mutu na shiga uku a duniyan nan kawu da mamu sai Ammane kadai masu sosai a kano sai ko kakata data haifi mahaifina manjo da take misau zaune a yanzu cikin halin rashin lafiya ko yaushe. Ido ya zuba min yadda nake magana kamar wata wacce bata cikin hankalin ta zama yayi gefen kujeran da nake zaune a kai yakai hannun shi a hankali ya rike hannayena yana fadin. Waya fada maki kawun ki zai mutu a yanzu attack kawai ya samu karancin kayan aiki na kasan mu shine dalilin da yasa nake son zuwa a san yadda za ayi muzo dashi nan a dubashi. Din haka ki kwantar da hankalin ki kefa kika ce in fada maki zaki iya taimaka min baki taimaka mi din ba kuma kina kokarin ki kara sakani cikin wani tashin hankali yanzu bayan wanda ke gaba a yanzu ? Yaya kayi hakkuri na daina daga ma hankali don Allah ka samowa kawuna lafiya ban son wani abu ya samu kawu a duniyan nan na fada gwanin ban tausayi. Kafadana ya dafa a hankali yana mikewa tare da fadun insha Allahu kawun ki zai samu lafiya very soon ya fada ya fara tafiya a kasalance. Yaya yaushe zakaje can din nima in shirya mu tafi na fada kamar wata yar karamar yarinyar da bata da wayau. Dan juyowa yayi ya kalleni da mamaki kamar na isheshi a lokacin da surutu yace karatun naki yaya zakiyi dashi . Bayan hakan ai nan zamu dawo tare dashi a duba lafiyan jikin shi idan mun tafi dake wa zai tare mu a nan ya fada yana tsureni da ido. Sai kuma ya juya ya fara tafiya bayan yaga na dukar da kaina a kasa kamar ina tunane lokacin. Har ya shiga dakin shi yana tunanen wani itin so da shakuwane haka tsakanin mu da daddy su don yanzu ya fahinci yadda shima daddy yake ji da al,amarin nawa a ranshi duk da yana boyewa don sauran iyalin shi. Shiga yayi ya zauna a bakin gadon shi tare da hade hannayen shi guri daya ya sauke kanshi kasa yana tunane. A gaskiya yayi kuskuren rike wanan yarinyar da kowa ke nanata mai ya rike amana marainiyar Allah a kasan mutane. Yasan dole yayi hakan don kare mutuncin shi da lafiyan shi saidai kuma yasan rabuwa da fatima kamar yadda ya shirya zaiyi . Hakan zaiyi matukar yin nadaman hakan mara adadi a rayuwan shi dolene yayi hakkuri da zabin mahaifin shi a gareshi. Don a yadda ya fahinci yarinyar tana da saukin kai gara yabita a sannu yana kwantar mata da hankali tunda tana mashi biyayya yadda yake so. Amma sai ya biyewa zugan shedan wanda haksn ke nufin bijerawa mahaifin shi a rayuwa yayi ke nan. A yanzu zai yaki zuciyar shi akan zama da wanan yarinyar ko a hakan da yake mata sai dai zai rage daure mata fuska da takuran da yakeyi din ya bata freedom din ta a matsayin tana yar adam dayasan yana tauye mata. Sai dai merry ce matsalan shi yanzu don sanin dokar kasan nan daman shi ma da yake suna zaune a central London inda kowa ke iya yin al,adun shi a nan kai tsaye don da dama sosai sama da American. Yasan zasu kwasa da merry duk ranan da ta fahinci fatima matar shi ce ta aure matar da iyayyen shi suka zaba mashi ya aura a rayuwan shi. Kwance yakai yana sauke ajiyan zuciya a hankali yana ci gaba da tunane tare da shirya abubuwa da dama a ranshi. Wayan shine yai kara ya dauka Steven ne abokin shi yake fada mai an gama komai na tafiyan shi a cikin daren nan zasu tashi. Bayan gama wayan ne ya mike ya shiga bandaki ruwa ya watsa a jikin shi tare da dauro alwala ya fito ya tayar da sallah ya jima a gurin yanawa mahaifin shi addua kafin ya mike ya shirya duk abinda zaiyi tafiya dashi don merry bata kasan tana can American ya barta a can gurin aikin ta. Sai yamma lis ya fito ya samu har na hada abinci nayi mamakin ganin shi yau yana magana dani tun kan ya sauko kasa yace yar gidan kawu har yanzu tunanen kawun kike ko ? Ina zaune nayi tagumi da hannayena kafauwana suna saman kujeran na takure a wurin daya tare da zubawa kasan falon ido. Yace shike nan yau dai nayi maki Aprilfull don na ga yadda kike son kawun ki da mamaki a fuskana na dago kai ina kallo shi yadda yake magana kamar bashi ba yau. A dan maraice nace yaya dama wasa kake min don Allah kasani a wani hali da ban taba shiga ba a rayuwata ? Yaya bana son in rasa kawu yanzu kamar yadda na rasa mahaifina a baya tun ina karama bai more min ba shine nake tunanen yanzu idan na rasa kawu fa ? Ba zaki rasa kawun ki ba Fatima ya fada yana jawo kujera ya zauna naso ma in kira maki shi sai dai nasan zaki iya fada mai gwada kin da nayi yai min fadan hakan. Ba zan fadawa kowa tsakanina da kaiba yaya ka yarda dani mamu ta haneni da yayin hakan tace in zama mai boye sirin tsakanin mu. Kallin wata yar karamar baby yake min mara wayau ga yadda nake fadin magana abincin ya fara budewa yayin da nake sake ajiyan zuciya daga inda nake zaune din. Bai kara magana ba ya gama ya fita ina zaune mamaki ya cika min ciki wai yau ni yaya kewa April full a gidan nan in dai hakane yako kamani da kyau sosai don na shiga wani hali a lokacin. Ya dan jima bai shigo ba da zai dawo ne sai gashi da kayayakin abinci dans sha kala kala ana shigo min dasu gidan ina dakina lokacin don haka har yagama jida ya kai min store dina ban san hakan ba. Bayan isha,i ya leko dakina yana fadin in rufe gida zai tafi can gidan ya kwana yana da aikin da zaiyi a can din sai da safe nayi mai ya tafi ya barni da mamakin sauyawan shi a raina. Ashe Steven yazo ya dauke shi tafiyan ke nan Nageria yayi ban sani ba nikan yana fita na rufo gidan tare da kashe komai na kwanta sai safe. Da safe koda na tashi ban tsaya komai ba shirin fita nayi do har lokacin ina ji zuciyata babu dadi daga wasan ciwo kawn da yayi min din . Duk da ya kamata inji dadi hakan ganin sakin fuska harda wasa irin na al,adan nasara da yai min a karo na farko do har lokacin kaina bai kawo wuta ba in gane cewa watan April ya wuce ai tun lokacin bukin su merry . ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:18 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM WARAMATULLAH, , , , , , Washe gari bayan na gama komai har nayi wanka na shirya banji duriyan ya umar ba gidan. Har nakai kofa zan fita na dawo don in sallamay shi kamar yadda anty farida ta fada min in dingayi idan yana gida. Na tura kofan a rufe yake sai mamakin hakan ya kamani don bai faye rufe kofan shi ba idan yana gidan. Juyowa nayi da niyar in wuce takardan dana hango ne saman dining table aje yasa na sauko da sauri na isa gurin na dauka ina dubawa. Fatima nayi tafiya ban sani ba ko in dauki lokaci ban dawo ba komai da zaki bukata na amfanin gida na tanadar maki shi a store da fatan zaki kula da kan ki daga yayan ki umar. Kamar ba school zanje ba a lokacin sai naga nz kai zaune ina faman tunane a raina gabin zan batawa kaina lokaci yasa na mike na rufo gidan na tafi. Da kyat na samu mota don bus sun dan wuwuce saboda sakkon da mutane keyi zuwa wurin aiyukan su na yau da kullun. Na kusa makara don ina shiga mai koya muna na shigowa lokacin haka akai lecture rabin hankalina yana ga tunanen ina yaya ya tafi. Karfe daya saura muka fito daga daukan darasi don yin break da sallah a ka,idan makarantan kamar kullun duk wanda zaka hadu dashi a irin wanan gurin muke haduwa din girman makarantar ya baci department ne kala kala gasunan sai inda idon ka ya tsaya. As usual mun san inda muke zama mu hadu a kullun a gurin na samu anty farida tana waya samun wuri nayi na zauna ina dakon ta mu gaisa jin da hausa take wayan ya fahintar dani a gida Nigeria take yin wayan lokacin . Tun ina sauraren ta har na fara tunane sai can naji muryan ta kamar a mafalki tana fadin waiko yau lafiya kike yar gidan ya umar kamar yadda nake kiran shi a gaban ta idan wani magana ya taso itama haka ta fada min. Na dawo cikin hayacina ina dan murmushi nace anty mun wuni lafiya yaya jama,an gidan ki cikin kako murmushin dole nake maganan. Ta amsa da duk suna lafiya sai dai yau yanayin ki ya nuna kamar kina cikin tunane da damuwa sister ? Bakomai bane anty na fada ina bude jakkata da nake amfani dashi a school din na dauko wayana dake cikin zip din ciki. Ta kara fadin ko yau da kewan yaya ki kika tashi ne hakan na dan dago kai ina dariya tare da fadin kai anty yau yaya din ai a gidana ya kwana sai dai da safen nan ne naga takarda daya bar min wai tafiya ya kamashi ya tafi bai tasheni ba . Amma dai wana yayan naki da yawan tafiya yake fatima kamar agogo ko yaushe yana saman hanya shi ? Ai dama nasan kina kewan shi ne tunda mutum kike ba dabba ba duk mace mai lafiya da jini a jika ai zatayi kewan mijin ta na sunna ko ? Haba anty har wani sabawa nayi da yaya umar ni na fada ina kokarin hade abinda nake ji a raina. Tace da sannu zaku saba ai ki barshi kawai ya gama iskancin shi da iya shegen su na maza shi da kansa zai kawo kanshi inda kike sister. Nace jiya yazo min da wata magana sai daga karshe yake fada min wai April full yayi min da sauri tace wani irin April full kuma ana April full sau biyu ne a shekara ? Da sauri na dago nace na shiga uku anty watau yaya wayau ke nan yayi min ashe da gaske yake zancen ciwon kawu ganin hankalina ya tashi yasa yace mi wai april full yayi min. Take idanuwana suka fara tsiyayan ruwa hankalinta ne ya tashi a rude take fadin maynene haka sister zaki jawo hankalin mutane gare mu kuma ? Cikin dan rage sautin muryana nake fadin watau da gaske yaya keyi kawuna baida lafiya ganin hankalina ya tashi shine yace min wai wasa ne. Kinga ki kwatar da hankalun ki kimin bayani yadda zan fahince ki mu san mafita tace dani. Da kyat na hade kuka nayi mata bayanin komai tana saurarena sai dana gama tace banda abinki sister ai ciwo na Allahne. Damu dake da lafiyan bamu fishi ga Allah ba sai kiga mai lafiyan ya tafi ya bar masu lafiya a jika shi lamarin Allah idan ya taso addua ake so bawa yayi don yanzu adduan mu yafi bukata ba wanan kukan da kikeyi ba. Mijin ki yayi maki wayau manyane ya wuce ya barki don kada ki daga mai hankali idan kin matsa sai kin bishi can zuwan may zai karaki dashi ? Ai addu,an ki kawai kawun ki yafi bukata gareki ki kwantar da hankalin ki Allah yasa mijin ki yayi farar tafiya ya tad kafadan kawu lafiya. Cikin murya mai kama da rada na amsa mata da amin anty ina kada kaina ina fadin amin anty cikin damuwa. KANO Ba wanda yasan da zuwan shi suna zaune cikin halin damu har lokacin ga fargaban halin ciwon da maigidan ke ciki ga kuma kishin da ba,a daina shiba har lokacin. Sallaman shi yasa su gaba daya dago kai suna amsa mai mai a yanayin yadda ya shigo cikin damuwa ganin su ya kara sa hankalin shi tashi tun bai gamsu ba. Hjy jummai tunda tayi arba da dan nata tayi saurin kawar da kai daga kallon shi. Yanzu idan zata kirga shekara daya da rabi kenan rabon data ganshi tunzuwan da yayi ya samay ta gidan wanta sai wanan ganin da tayi mai. Ga al,adan bahaushe girmamawa gana gaba duk da fadin da malaimai keyi baida kyau malam bshaushe bai yarda ya yar da wanan al,adan na tsugunawa gaida mahaifanshi ba wani lokacin. Shima Umar hakan yayi don bai gaida kowa ba duk da sannu da zuwan da suke mai sai daya samu wuri ya dan rage tsawo ya gaida su a cikin jimmila ga baki daya wanda ke gurin. Su mama hadiye sukace ashe kun samu labari rashin lafiyan yace eh gwaggo Aliyu ya kirani yake gaya min abinda ke faruwa naso tasowa saidai hakan bai samu ba saboda wani dalili. Yau ai jikin nasa da dama sosai don yana dan motsa idanun shi kadan kadan hakan yasa hankalin su ya dan fara kwanci. Yai masu yaya mai jiki duk a cikin jam,i ya mike tare da tambayan wanda ke cikin dakin a lokacin suka bashi amsa kusana tare banda mamu da hjy su da suka kawar da ido daga kalo shi. Dakin ya shiga su kawu balarabe ne da kawu mustapha a cikin dakin zaune sun tsura mashi ido a cikin tashin hankali. Jin an turo kofa yasa suka juyo lokaci daya suna kallon kofan don sin hana kowa shiga saboda rikicin dayaso tashi tsakanin hjy jummai da hjy maryam wurin jinyan. Yasa suka hana kowa shiga a yadda sukaga dama da farko an rabawa kowa lokacin zuwa saidai hjy jummai tace basu isa ba zata zo a duk lokacin da taga damane ita. Yasa suka kasa suka tsare don sanin halinta suna jinyar dan uwan nasu da kansu wanda hakan yasa duk wanda yazo saidai ya tsaya daga waje inda kowa yake sai idan suna bukatan wani abin zasu kira wacce keda duty a lokacin tazo ta taimaka masu da wani abin. Ganin ya umar yasa su sauke a jiyan zuciya suna fadin umar ka taso ke nan ga Alh nan jikin yaki har wanan lokacin. Direct wurin gadon da mahaifin nasa yake ya nufa kai tsaye ya dan tsaya a kansa ya tsura mai idanu . Can ya juyo yana fadin likita yayi bayanin akan matsalan dake damun shi ? Kawu balarabe yace eh to yayi bayanin don sunce akwai hawan jini da sugar sune mu sabbabi matsalan duka. Ya umar yace zanso mu fita dashi waje don zaman shi a hakan ba ba dadi gaskiya tunda an gwada na nan ba aci nasara ba har yanzu. Allah sarki mukan ai munga sauki yanzudon yau ma an samu cigaban samun lafiya sosai don yana bude idanun shi lokaci lokaci. Ajiyan zuciya ya sauke don jin bayani su ya juya yana kurawa mahaifin nasa idanu mai nuna zallan tausayi a gare shi . Ya kara takun shi zuwa wurin gadon ya tsurawa kawu idanu kamar yasan shine a gurin sai ya bude idanun shi a daidai lokacin ya kafe umar din da idanuwa kamar yana kokarin sheda ko waye a gaban shi lokaci. Daddy sannu umar din yace mai sai ya lumshe idanuwan shi a hankali dan dukawa umar din yayi daidai saitin kan mahaifin nasa yana mashi adduan samun sauki daga Allah. Yakai wani lokaci a hakan kafin ya dago daga dukawan da yayi din ya juya zai fita daga daki nmuryan kawu balarabe ne ya tsayar dashi. Zaifi kyau ko zaka fita dashi a bari har ya kara samun lafiya zaifi tau baba Allah ya tada kafa dan shi yaba daddy lafiya suka amsa da amin. Ya fito da sararen gwiwa don yadda yaga daddyn nasu a lokacin rai a hannun Allah. Jin kara bude kofan yasa na wajen juyowa suna kallon mai fitowa daga dakin . Umar ka fito mama hadiye tace dashi yace a wani yanayi na nuna rashin jin dadin shi ga ganin mahaifin nasa. Ya dan samu wuri ya jingina bayan shi ga bango tare da harde kafan shi daya a cikin daya. Ya lumshe idanuwan shi muryan mama hadiye ne ke fadin kaje gida wurin hajiya ka huta don da alama isowan ka ke nan daga airport ka nufo nan. Bude idanuwan nasa yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace Amman tana gidane mama tace eh dazun nan ta koma tazo taga jikin yaya din. Yaya su Fatima dasu Amina sarka sarkin rikici duk suna lafiya ? Ajiyan zuciya ya sauke kafin yace suna lafiya na barta saboda karatun ta da ya fara nisa yanzu, Dago kai hjy jummai tayi ta watsa mashi wani kallon takaici ta kawar da fuska a gurin su. Wasu daga wurin sunga abinda ya faru sai dai basuyi magana ba ya dan busar da iska yana fadin zan dan je naga likitan dake kulla da daddy din . Suka amsa mai ya tafi ko juyowa baiyi inda suke zaune din zuciyan shi cike da damuwa ko kallon yanayin nasa yaje gurin likitan sun dan dade a office din kafin ya fito kai tsaye gidan mahaifin shi ya nufa wurin Amma. Kamar a mafaki tagan shi falon nata sadauki kaine rafe ashe kana da labarin abinda ya faru da mahaifin naku ? Ya kai zaune tana kokarin tashi da kyat yace ina kuma zaki Amma tace wai in kawo ma abun sanyi ka sha ko ta fada tana kallon fuskan shi. Yace barshi kawai Amma ya mike ya nufi wurun fridgen din nata da kanshi ya bude ledan ruwa da sauran tarkace yagani yadai dauko ruwan ya dawo ya zauna a inda ya tashi da farko. Tace tana kallon shi kai kadaine tafe wai banga mutumiyar tawa ba tashigo. Ya kalle ta da idanuwan shi da sukai mai ja yace banzo da ita ba ni kadai nazo sai wani jikon zan shigo da ita wanan tafiyan bana hankali kwance bane. A ikon Allah zan so ganin mutumiyar tawa inga yadda ta koma yanxu. Ya dan tabe baki tare da fadin tana nan yadda kika santa sai karatun ta da yanzu yayi nisa sosai. Mikewa yayi yace zanje in dran, huta na dan wani lokaxi tun yanzu baka ko huta ba ? Yace eh nazo dai kawai in ganki ne yace yana kokarin fita daga falon nata kai tsaye sai dai cikin ran shi yana mamakin halin mahaifiyar su. Don dai irin kallin da rake jifan shi dashi yasare masa gwiwa sosai do yasan tana cike dashi sai dai ba zaice ga laifin da yayi ba lokacin . Sai ba bayan azahar ya falka wanka yayi yafito yayi sallah kai tsaye asibuti ya nufa. Wanan karon iya hjy maryam ya sama a asibitin wurin mahaifin nasu itace keda zaman rana a wurin shi karfe shidda mamu zata karba ita kuma ta koma gida. Tun dawowa na na kasa sukuta komai a rayuwana sai faman tunanen da nakeyi ni kadai zaune a falo ina yawan kallon kofa da wayana na dake gefena aje ina sa ran kiran yaya umar a lokacin. Saidai har dare gashi bai kirani ba balle inji idan Nageria ya tafi a ban wani na gida muyi magana dasu. Saidai bai kira ba har lokacin da nagaji na mike na kashe komai na shuga dakin kwanana na kwanta da kyat na samu barci ya zo mi lokaci. Waahe gari ma haka na daure zuwa daukan karatu don fita zamuuyi yin pratical da malamin mu . Ban yarda mun hadu da anty farida ranan don kada ta gane ina cikin damuwa tai min wani fassara na daban. Gashi har lokacin ya umar baibugo min waya ba ni kuma banda layin kowa na gidan namu. An shigaKwana uku shiru ba wayan ya umar ba dalilin kiran shi hakan ya kara tayar min da hankalina sosai. Haka yasa na fara zargin ko dai wanu a babu ya faru da kawun ne hae ya saka ya umar ya tafi . Gabana ne ya fadi sosai a lokacin take na shuga share kwallan da ya zubu min a idanuwana daka ganni kasan akwai damuwa a tare dani lokacin A rana na biyar ne ina zaune nayi tagumi sai ga wayana yana ringin na dauka ina dubawa ya umar dinne ke kiran layina. Da sauri na dauki wayan ina kokarin karawa a kunne na da sallama ya amsa min da kyat tare da fadin kina nan kin saka kanki cikin damuwa ko ? Nace ya don Allah ka fada min idan wani abu ya faru da kawuna ne in sani yace ba na fada maki baida lafiya bane ? Yaya kayi hakkuri ban son in rasa kawune yanzu ke kina masa fatan mutuwa ne ko may da kike fadin wanan magana ? Kukan dana fara yasa ya kashe wayan gaba daya haushin kaina naji dana kasa controling din kaina a lokacin balle inji halin da kawu ke ciki lokacin. Daga lokacin bai kara kirana a waya ba duk zaman garin ya isheni ban san ko ina ba daga gida sai school saboda sabon da mukayi tun a gida da rashin fita ko ina yasa ko a nan ma wanan halin ya bini hakana. Na ramay na lalace ko wani gyara duk na daina karatuma kamar ya zama min dole nakeyin shi ban san ina son kawuna haka ba saida hakan ya kasance dani yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:19 - 🀐🀐🀐: SALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , , , Wasa wasa saida ya share fiye da wata daya a gida duk da banda wani matsala a bangarena ko na abinci dana wurin karatuna ga baki daya. Tun ina tunane har na gaji na fawwala al,amarin ga Allah ranan da kadaici ya isheni anty ta karbi wayana ta bude min whatsfapp naji dadin hakan sosai don ranan wuni nayi ina kallon yan makarantar mu da nake da layin wayan su. Wani dp na saka inda mukayi da wasu coursemate dina nice a tsakiya sun rugumoni su biyun muna saye da labcoath a jiki mu cikin nishadi. Tsananin hasken fatana na daya karu yanzu yasa mun saje da su dan banbancin dai kadan ne dasu a photon. Son da nakewa photon yasa na saka shi don sune kawayen da nayi na kut da kut da muke karatu dasu. Munyi photon a cikin farin ciki da so da kaunan juna a tsakanin mu don hakane na zabi wanan photon a matsayin dp din wayana. Zaune nake saman dogon kujeran falon na mike kafafuwana ina kallon tv dake aiki sai corn dake hannu na ina ci a hankali ga waya da na mayar da hankali muna hira da anty farida cikin harshen hausa. Nigeria Kano Ya dawo asibiti gurin daddy da yanzu akafara ganin sauki gareshi sosai yasa hankalin iyali ya fara kwantawa . Ya umar ne ya shigo falon shi a lokacin tun safe da ya fita zuwa asibitin yana can gurin daddy shida yan uwan shi sun kewaye mahaifin nasu a nan su salma da mazajen su suka samay su aka cika taro dasu har wani lokaci suna gurun Alh a zaune sai matan ne suka dan fita daga dakin zuwa inda uwayen su mata suke zaune. Karfe hudu ya baro asibitin zuwa gida sai da ya zauna yaci abincin da mai aikin shi ya girka mai yaci don bai tsaya karyawa da safe ba ya fita . Ya gama a wurin yai zaune tare da balance saman kujeran da yake zaune a kai ba gwanin shiga whatsf bane shi amma ranan sai yaga ya shiga don duba sakonne kamar yadda yakeyi idan sun taru. Ya gama komai kamar ance ya duba sunana daya rubutawa kaddara sai yaganni a online da alama ina saman interneat a lokacin da sauri yace kai , tare da dan zabura da mamaki. Da sauri ya tura sako ke may kike a nan ? Waya bude maki wanan abin kike yi ? Jin sako ya shigo min a jere lokaci guda yasa na aje corn din dake hannuna ina kallon waya da mamaki. Baki na mere ni kadai a gida ina jan tsoki tare da fadin dan rainin wayau kawai so kake in mutu a garin mutane saboda bakin halin ka. Ban bashi amsa ba sai ma sauka danayi ga baki daya na mike tare da kashe komai na falon na hau sama na kwanta. Ina tsaka da addu,an shiga barci waya ya dauki rurin kira a lokacin dubawa nayi ya umar ne yake kirana . Kallon wayan nakeyi ba tare da na dauka ba har ya gaji ya katse ban daga ba sai can naji sako ya shigo min again share shi nayi sai can na duba sakon naga ya rubuta ke ki dauki waya nace. Kaci min mutunci daga can ko ka raina min hankali tunda har yanzu na goye kake kallona a idon ka kin dauka nayi na share shi barci yayi gaba dani a gurin. Shiko yana can yana cika yana batsewa har akai magariba yana jin kamar yai tsutsu ya ganshi a London ya makeni. Kallin dp din dayayi zooming a wayan shi yayi mun fito shar damu a photon da kayan gwaji a jikin mu inda nau,in jikin mu ya nuna mabanbantan kasa muka fito gaba dayan mu. Kiran sallah yasa shi mikewa ya nufi ciki alwala ya dauro ya fita daga gidan a gaugauce kada ya rasa jam,in sallah magariba na lokacin. Yana fitowa ya nufi family house din su kai tsaye wurin hjyn su ya nufa duk da hattaran shi da uwar keyi tun zuwan shi kasan . Sai yake nuna baima sam tanayi ba don zai shigo ya zauna dukda nuna mai kin kulawan da take sai yayi zaune yana bata lokaci da waya a hannun shi. Sai idan su Aliyu sun shigo ne suke dan zama suyi hira wani lokaci kuma su kwasa su fice zuwa asibiti. Har yau hjy saboda bakin ciki ta kasa bude baki tayi mai magana ko ta tambayi iyalin shi ga baki daya batayi ba. Yau ya shigo babu kowa a falon sai tv dake aiki yayi sallama ya shiga kai tsaye ya samu wuri ya zauna shi kadai a falon. Nafisa ne ta fito jin sallaman shi tana amsa mashi sallaman nasa tare da fadin ya umar ashe ka shigo. Yace ummm a dakile tace yaya in kawo maka abin karyawa ne duk da tasan ba zaici ba halin sa ne wanan tun lokacin da ya tare a gidan shi bai damu dayaci abinci a gidan ba. Ta samu wuri ta zauna tana fadin ni yaya wai yaya A ruwa ban samu tambayan ka ita ba tunda kazo ? Dan dago kai yayi yakale ta yace tana lafiya karatu ya hana inzo da ita daka koma da ita inda ka dauko ta. Muryan hjy mahaifiyar su ne, dake fitowa take magana tare da hararan shi dan murmushi ya sake yana fadin barka da fitowa mama. Ya dan zamo daga inda yake zaune yana gaida ita da kwana bata amsa mai ba sai cewan da tayi kana zaton na janye maganata akan auren wanan makiran yarinyar da kakeyi. Idan sun mallake ka sun mallake ubanka ni basu mallakeni ba ni ba kuma ba zasu iya mallakeni ba yadda suke so. Har yanzu ina kan bakana sai ka saki wanan yarinyar don ba zan hada iri da irin matsiyata ba a zuri,a ta. Ayi hakkuri hjy lokaci na zuwa da hakan zai faru ina wanan abin ne saboda ke da daddy mu. Sabodani ta fada da dan mamaki tana kallin shi tare da kada kai tace ka dauka zaka iya yaudarata ne babawo ? May ka mayar dani ne wai kana nufin zaka zauna da yarinyar da baka so har tsawon shekara daya da rabi da ita kana kallon ta ? Wani irin dagowa yayi yana kallon mahaifiyar tasu da mamakin kalamin ta gare shi tace kai waliyi ne ko shehi da zaka zurawa mace haka idanu kana kallon ta ? Kiyi hakkuri mama ba hakan nake nufi ba wanan yarinyar karatu take yanzu haka a can sune dalilin da kikaga ban dauki wani mataki akanta ba har zuwa wanan lokacin. Aliyu ne yayi sallama ya shigo kallon yanayin zaman su ya fara sai kuma ya juya wurin mahaifiyar su yana gaida ita da kwana kafin ya juya wurin dan uwan yana fadin bros ashe kana nan gidan ka na fito yanzu daga can nake nayo nan. Yace na shigo ingaida su da kwana don in na tafi asibiti ba zan fito da wuri ba yana nan yana karanta min hauka don ya daukeni mara hankali. May kuma akayi mama yana kallon dan uwan nasa ta tabe baki tana kawar da kai daga kallon shi. Umar da dama yake neman hanyar gudu daga wurinta yayi saurin mikewa tsaye yace barin leko Amma mu gaisa in zo mu wuce. Zaka dawo ka samay ni ai hjy tace tana hararan shi shidai ya fice ya barsu da Aliyu a falon zaune. Ya samu Amma tare da mamu a part din mamu tana ganin shi nauyi da kunya ya kamata lokaci guda ta shiga dan kamay kamay taga surikin ta wai. Gaida su yayi a daidai lokacin da mamu ke mikewa tace gwaggo zan tafi sai dai idan na dawo ke nan kuma. A,a kardai ince yanzu kuma kunyar Sadauki kike ji kuma maimuna ta fada tana kallin mamu din da dan murmushi a fuskanta. Mamu tace kai haba gwaggo kunyanshi kuma tana kokarin fita daga falon yace naso tunda nazo in baki layin wayan ta sai dai bamu samu kebewa da ke b. Jin hakan yasa mamu ta dan tsaya daga tafiyan da takeyi din tace badai tana lafiya ba ? Lafiya take yace yana kokarin ciro wayan shi a cikin aljinhun shi yana duba lamban na. Mamu da za,a bude zuciyar ta a lokacin aga farin cikin da take ciki a lokacin bai musultuwa . Yace saidai ba a samun ta sai weekend ko bayan karfe biyar a daidai lokacin tana gida ke nan don shine lokacin da ake samun ta kawai. Ya karanto mata lamban ta loda a wayan ta cikin farin ciki tare da fadin na gode tana shirin juyawa Amma tace ni ina ta jiran ace muzo gashin cibiya sai naji shiru? Dan kallon Amma yayi ya kawar da kai ba tare daya iya furta komai ba a wurin Amma taci gaba da fadin gashi yan uwanta wasun su suna da ciki yanzu. Amma kin dai san ita karatu takeyi yanzu ko idan tayi ciki yanzu wa zai taimaka mata da raino da sauran su don gudun kada Amma ta gano komai. Tace may ye aikina a nan ko aikin kakarta dake bukatan taimako sai ni in hakkura wanan boyar Allahn ta tafi don matar tana bukatan kulawa sosai. Wata mace kuma kike magana yanzu kuma Amma ko har kin fara rudun tsufan ne hakan yanzu ? Tace a dan maraice wanan mahaifiyar uban yar nan nake zance don tsakanin ta da A ruwa sai Allah . Shiru yayi bai tanka mata ba sai can ya mike ya kalli Amma dake masa hiran da bai saurare yace zai tafi asibiti ya duba mahaifin shi dake can. Amma tace ni kan ban gane wanan abin ba da na dauko maka zancen matar ka sai ka gudu ka barni anya kuwa sadauki kana kula da hakkin yarinyar nan yadda ya dace a can ? Da sauri yaja ya tsaya guri daya yana kallon Amma kafin yace ko kinji wani abune gamay da zamana da ita ? Tace ko daya yo a ina zanji labarin ku a gurin ka ya kamata muji komai gamay da yar nan saidai tun zuwan ka ba wanda kaiwa zancen ta a gidan nan kaf. Hakan yasa nake zargin irin zaman da kukeyi a can da ita don yar nan Amana take a gutin ka kasani. Ki bari in dawo indai zancen ta kike son ji zakiji komai idan na dawo shike nan ko ? Ya fada yana kokatin fita yayin da Amma ta tsare shi dz ido tana zargin shi. Luckyly ranan ina gida ban fita ba sai after two zamuyi pratical don haka na tsaya dan gyare gyaren gidan. Mamu ta kasa hakkutin kirana har yamma gwada lauin daya bata take ta faman bin nombobin da kallo tayi a wayanta sai ko ya shiga. Daga inda nake tsaye naji waya na ruri a raina na dauka anty Farida ce don nasan ba zai kirani ba shi a wanan lokacin. Haka yasa na isa gurin don daukan wayan saidai ganin nomban Nageria yasa na tsaya wasiwasin daukan wayan ina kallon nomban karshen lamban yasa na gane layin mamu ne da don dama sauran nomban na biyun karshe ne ban haddace ba. Da sallama a bakina na daga yayin data karba min ta bangaren ta ihu na saka sai kuma na sa kuka ina fadin mamu kukane yazo min lokaci guda. Dan murmushi naji tayi ba tare da ta ban amsa ba har na saida taji banda niyat tsahaitawa tayi magana. Sayadi don na kiraki kike wanan kukan hakan komay ashe dana sani da ban kira layin ki ba na barki. Da sauri nace mamu ina kewan ku ina kewan kowa a gida nan banda kowa a nan sai Allah sai anty farida dana hadu da ita a school din mi ta zamay min kamar yar uwa. Tace dama aure haka ya gada Sayadi idan kaji shiru lafiyace inji ba haushe muma muna kewan ki sosai kin sani a kullun sai gwaggon ki da kawun ki sunyi maganan ki hakama kannen ki. Nace mamu bandake ke nan ko dan murmushi tayi tana fadin har yanzu dai kina da sauran wauta ashe ? Na zunburo baki kamar tana ganina nace mamu ni yanzu banda wautan komai ni kadai fa nake rayuwana a gidana sai idan ya umar yana gidan nake tare da wani. Dama ai idan ka auri mai mata Sayadi hakan ne ke faruwa don ba kullun yake tare da kaiba sai lokacin ka ai. Duk da ban fahinci may take nufi ba nace mamu da gaskiyane kawu baida lafiya ? Ta katse da fadin amma ya samu lafiya sosai yanzu don mijinki bai nisa da juyowa gare ku ai. Yaya wurin su merry da yar ta suna lafiya nace banda labatin su mamu don ba gida daya muke zaune da su tsakanin akwai dan tazara so sai. Sai dai wani lokaci nakan tafi inda suke amma yanzu na dade banje ba a cikin hikima da basira irin ta manya mamu ke min tambaya ina bata amsa ba tare da komai ba sai dai bata tambayeni irin zaman da nake da yaya umar ba nima ban fada mata ba. Na tambayeta labarin amma da manjo da su Aisha ta dan ban amsa a gurguje akan suna lafiya Aisha nan haihuwa ko yau ko gobe ma . Dan ihu murna nayi jin hakan tace salma da ikilima sun haihu wata biyu daya wuce nace ikon Allah. Tambayan karshe da tayi mun ne yazo min a bazata tace ke yaya labarin haihuwa wurin ki ko har yanzu baki samu komai bane ? Wani iri naji a raina na canza fuskana a lokaci daya tare da fadin mamu kin san ina karatune yanzu fa . Sayadi ke nan karatun ki shi zai hana wani abu kardai kice min kuna wanan planning din banzanne kuma. Ban san may planning ke nufi ba na hau yi mata shirmay sai dai abin yaro da babba a cikin shirmay na ta fahinci akwai matsala a zaman mu mukayi sallama tace idan taje asibiti zata ba kawuna waya mu gaisa. Mukai sallama a cikin so da kauna irin ta uwa da yarta ta barni ina kewan ta ina hawaye ni kadai a gidan ina jin kamar in bude idanu in ganni a gaban mahaifiyata. Umar yana zaune yayi wani irin zabura wani tunane yayi a zuciyan shi nayin gangancin ba mamu layi na kai tsaye ba tare da yayi worning dina ba kada in fada mata komai gamay da zaman mu. Yana zabura ya duba agogon hannun shi da sauri sai ya mike tsaye don yasan lokacin daya ba mamu na kirana yayi don haka tana iya kirana in tona mashi asiri don ba wayau ke gareni ba. Waje ya fita duk da likitana ciki yana duban yanayin daddyn su lokacin sai dai hakan bai hanna shi fita da sauri daga dakin ba . Can dan nesa da mutane ya nufa ya kira layina lokacin ina zaune na saka abincin a gaba ina kallon na kasa ci sai tunane da nakeyi. Wayana dake aje saman table din yayi kara da sauri na kalla a zato mamuce ke kiran layina lokacin. Ya umar na gani wanan karon da sauri na dauki wayan ina mai sallama ya amsa min yadda yake karbawa nice nayi mai ya jikin kawu yace da sauki a takaice. Zan kara magana ya tareni yana fadin ke naba maman ki layin wayan ki nasan zuwa anjima zata kiraki don haka saura ki mata shirmay da kika saba idan ta kira. Don kika kuskura kika fada mata wani abu gamay dani ranki zai baci sosai wallahi idan na dawo garin nan don na kusa dawowa kwanan nan insha Allahu. Shiru nayi ina sauraren shi har sai da naji yayi shiru nace wai mamu kake magana ai ta kirani ko tun rana mukai magana da ita. Da dan karfi a razane yace what ? Nace eh ina mai jin haushin shi a raina cewan da yayi min shirmay nake dashi a raina. Yace makika fada mata data kira ki nace kamar ya magana tsakanina da mahaifiyata kuma saina fada ?. Yace ke ni kike fadawa wanan maganan don rashin kunya ko may nace ni ban maka rashin kunya ba ai na daiga uwatace ta kirani ai. Ke may kika fada mata nace kin tsaya kina min maganan banza da ina kusa dake dana doke wanan bakin mai maganan banza. Ni zaki nunawa maimuna mahaifiyar ki ce ko mai na mayi regret din bata layin ki danayi tun farko don ba hankaline dake ba nasani. Duk naji wani maganan da kika fada wanda bai dace ba a garin nan sai na saba maki sosai idan na dawo . Jin yana magana kamar tababe yasa na kashe wayan da mamakin shi a raina ina tunanen may yake nufin zan fadawa mamu bayan alherin da yake min a nan din ga karatuna iba yi hankali kwance. Matsalata daya shine kewan gida dake addabata ko yaushe bayan wanan wani hali yake zaton zan fada a gida dayake min din. A bangaren shi kuwa yana kashe wayan Aliyu ne ta gani tsaye a bayan shi da alama duk maganan da yake fadamin Aliyun yaji shi lokacin. Yana juyowa sukai arba da Aliyu din wani irin gilty ya kamashi lokaci guda ya daure fuska yana fadin kai kuma maynene hakan kazo ka tsaya mun a kai ina waya. Dan murmushi Aliyu yayi, yana fadin cool down bros likita ne yace a kiraka ciki haka ya wuce dan uwan ba tare da ya amsa mashi ba. Aliyu ya bishi da kallon maki yana girgiza kanshi cikin takaici yabi bayan shi zuwa ciki. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:19 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, , , , , Mamakin kalamin ya umar na kwana dashi a raina duk da kurciya ya hanani gano inda maganan shi ta dosa a lokacin. Amma zuciyata bata hanani hangon ma,anan maganan tasaba sai dai bankai can inda tashi manufan ya dosa ba. Washegari mun shiga karatun mu lafiya ban nemi anty ba don nasa yanzu ita karatun su yayi nisa tana gab da gamawane lokacin. Bayan mun taso sai ga kiranta a wayana tana fada min ta tafi don yaronta da baida lafiya ranan. Nayi mata Allah ya sauwaka muka kashe wayan bayan na dawo gida abinci kawai naci naga ya dace in leka gidan anty farida a karo na farko duk zaman mu tare ban san gidan ta ba ban ma taba zuwa ko layin nasu ba a rayuwana. Shiryawa nayi duk da yamma yayi sosai na fito tare da rufe gidana na nemi taxi ta hanyan fada mai layin duk da ba nisa sai daya dan kalleni. Ban damu da hakan ba duk da nasan manufan dan taxis din lokacin ganin yayi inda zamu a unguwar muke sanin ban san gurin ba ya hanani damuwa a lokacin. Sunan layin da nomban gidan na fada mai sai gashi cikin dan kankanin lokaci ya ajeni a kofan gidan na biyashi kudin shi ya tafi. Tsayawa nayi ina karewa unguwar kallon mamaki a raina duk kusan ginan iri dayane sai dai bai kai wanda nake girma ba da komai nan na gane ba cikin karamin gida nake ba ashe. Na taka a hankali zuwa kofan na danna bell din sallaman dana gani a gidan ringing biyu aka bude kofan wata yar matashiyar budurwa ce a kofan tsaye tana min kallon mamaki. Dan murmushi na sake a fuskana tare da fadin zainab ko don yawan kiran sunan ta da anty keyi kanwar mijin ta da sukazo da ita don kula da yaran su. Itama murmushin ta mayar min a fuskanta tare da fadin kina neman wani ne a cikin harshen turanci tayi magana nace eh da hausa don ta gane nima ba hausace yar uwanta. Juyawa tayi tana fadin anty farida ga wata bahaushiya yar uwan mu tana neman ki a kofa tare da kokarin jaye min daga hanyar shi don taban guri don in shiga . Lah ikon Allah ashe kina hanya baki fada min ba fatima dan juyowa zainab tayi ta kalleni tare da mamaki a fuskan ta tace anty wanan dince fatiman dama ? Anty tace itace Fatiman zainab yau dai kinganta a gidan mu ko ciwon daddy ya jawo muna ita zuwa gidan nan. Zama mukayi muna gaisawa tare da tambayan ta jikin yarin nata da baida lafiya ta nuna min shi kwance saman kujera tare da fadin gashi nan yaji dama sosai na samu Abban su ya kaishi asibiti sun karbo magani. Ban zauna ba na nufi gurin yaron tare da fadin babana ya jikin naka ina kokarin taba lafiyan jikin inji yadda yake. Yaron ya dan dago kai tare da fadin naji sauki a hankali abinda na zo mai dashi na ciro a jaka na mika mai cikin kayan makulashen da yaya ya tara mu a gida wasu ban ma san dadin su ba har lokacin. Yaron yai zubur ya mike tare da fadin nagode ya karbi ledan ya fara budewa a hankali ya dago kai ya kara fadin nagode anty. Zainab ce ta matso inda muke tana fadin yau dai ciwo ya warke ke nan gidan nan tunda ga kayan kwadai an samu tana kokarin karban ledan a hannun yaron ya kabe mata hannu da sauri yana fadawa uwar. Oya zainab dauki diyan ki zuwa ciki anty tace tana kallin zainab din a lokacin har budurwan ta mike tsaye taja hannun yaron zuwa ciki . Sai lokacin nake tambayan ta yarta guda tace tana ciki tana barci ruwan da ke gaba ta kalla tare da fadin baki sha ruwa ba ko a kawo maki abinci ne don an kare ko ? Nace banda yunwa yanzu gaskiya anty sai dai zuwa an jima wata kila zan dan taba na fada mata hankane don ta saki rai dani. Har yanzun dai maigidan ki bai dawo ba kasan nan ba fatima tana kallona take maganan na dan duka ina tsiyaya ruwan dake gabana nace. Bai dawo ba anty sai dau munyi waya ga jiya dashi har da mama ya bata layina ta kirani . Kai amma ko ya kyau ta gaskiya dama abinda nake son tambaya ke nan yanzu ai. Nace sai dai anty kamar an tursasa shi ya bata layina don daga baya ya kira yana min fada nan dai na kwashe yadda mukayi na fada mata komai . Sai dan murmushi naga ta sake a fuskanta tare da girgiza kai tana fadin barazan banza ke nan yasan yana jin tsoron mahaifan sa amma baya jin na Allah dake kallon shi . Amma ai anty yana kula dani tunda ya tsaya min a karatu gashi babu abinda na nema na rasa a rayuwata matsalata daya shine rashin yan uwa a kusa dani. Wanan kuma nasan na dan lokaci kadan ne da zaran na gama kararuna zan koma gare su ne ba shike nan ba anty. Ido ta zuba min tun lokacin dana fara maganata babu ko kyatawa har na kare . Naji rata wani dogon tsuki tana fadin Fatima kin ko san may aure yake nufi a rayuwan ki ? Mijin kine fa na sunan ma,aiki kina zuwa makaranta a gida malaman kun suna koyar daku abinda aure ya kunsa a addinance kin sani ? Shi kansa yana tauyewa kansa hakkine akanki kuma ke kanki yana cutar da rayuwan ki ta fanni daban daban fatima. Ke bari dai in fada maki gaskiya ki sani rashin tararyan da baiyi dake na aura taiyya yana cutar dake sosai fatima sosai. Iyayyen ku bawai sunyi wanan hadin bane a tsakanin ku don kizo nan kiyi karatu kawai ko ya zuba maki ido haka yadda yake kallon ki. Shin fatima ke ba mace bace baliga mai jini a jiki da zaki kwana gida daya da mijin sunan ki baki ji komai a rayuwan ki ba. Ruwa na dauka na sake kurbawa a hankali idona suna a kanta na aje kofin a hankali nace, ko daya anty don ni a matsayin dan uwa na jini nake kallon shi . Ko kadan ban taba mashi kallon miji a gareni ba sains yan uwan taka har matar shi duk basu gabana wallahi . Ni dai burina kawai in ga na hada karatuna na koma gida gurin iyayyena na kai masu kwalin sun gani. Kai amma sai kuma tace wai fatima in tambaye ki man ? Yanzu shekara nawa kile ne nace cikin dariya sha takwasa nake yanzu zan shiga na sha tara koda nazo nan ina da shekara sha bakwai cif anty. Gaskiya wanan dan uwan naki bai dace dake ba wallahi cutar yayi yawa wallahi . Shiru tayi kamar may tunane kafin can tace kina jina shin wai sharan dana baki a baya kina amfani dashi fatima ? Ta tsareni da ido tana son jin amsa daga bakina a lokacin na dan kai bayana ga makarin kujeran da nake zaune a kai nace ina wasu ban wasu gaskiya. Yau she ma na ganshi a gidan har zan tsaya mai wani kwarkwasa ko shagwaba can anty ?. Mutumin da zai shigo gida a takure kamar wanda yazo bakunta a kullun fuska a daure ns dan ja tsuki tare da fadin bari kawai mu tafi a hankan dashi anty. Ba zan bariba Fatima ta fada a tsawace kamar mai maganan bacin rai a lokacin da wani tace kin san kuwa irin cutar kanku da kukeyi daga ke har shi din yanzun haka fatima ? Wallahi da ace nasan ainihin iyayyen ku da nakai karan ku gaba daya gurin su don hakan ne baya son kiyi hurda da kowa a garin nan. Ko ranan danaje gaidashi ai nasan sai daya titsiyeki da tambayan ina kika sanni ko ba ai hakan ba don yadda naji ya kiraki ranan nasan da akwai maganan da yayi maki akaina ? Kawai dai tambayana yayi a ina ba sanki na fada mai shine yace baison yawa kwashe kwashen mutane ya fada min tun farko. You see dama ai na fada a raina don hakane bai son yaga kina hurda da kowa fatima don kads a fahintar dake abinda baki sani ba ki bitkice mai lissafi. Ya kamata ki natsu ki san may aure yake nufi Fatima kema fa mutum ce kuma aure ne ya haife ki ba a aure ayi tararya da namiji aka haife mu mu ? Don hakan ki canza ki nuna mashi ke din kin san abinda kikeyi bawai ina nufin ki bayar da kanki gare shi ba lokaci guda a,a . A cikin hikima da basira zaki fito mai may kika rasa wanda ake nema a jikin mace Fatima ke zaki iya fitowa gasa sarauniyar kyau wallahi kici aduk inda kike. Ya kamata ki canza idan mune yau bamune gobe ba don yanzu haka in ance yan uwan auren ki sun haihu ko suna da ciki ba abin mamaki bane ga al,adan muna hausa. Mun dade gurin tana min maganan jan hankali akan aure na wani in fahinci may take nufi wani kuma ba ganewa nake yi ba sai da mijin ta ya dawo ne muka kalli lokaci muka gane dare yayi ko sallah bamuyi ba a lokacin. Gaidashi nayi ya amsa min a cikin fara,a tare da fadin kardai ince wanan dince fatiman da ake damun mu akanta kuun tace ka canka daidai honny . Yau dadi ya jawo muna ita gidan nan da ba don babanta bane ke ciwo nasan ba zata zo ba wanan mai kama da kifin rijiyan . Dan dariya nayi a cikin kunya nace kai haba anty zanzo mana don rashin sanin gurine dama ya sa ban zuwa. Sai mamakin yadda naga sunayi a gabana babu ko tar din kunya a idon su biyun lokacin wai don ina zaune suji raban idona basuji ba. Mikewa nayi ina fadin zan tafi nikan anty don dare yayi ashe ina nan dan magana naga tayi mai kamar mai rada sai yace ok ba matsala muje a sauke ta. Tare muka fito suna gaba ina bayan motar na fada mai layin gidan da zai sauke ni ba wani tafiya mai nisa bane tsakani sai gamu a gidan . Nace wancan gidan ne ya dan kalli matar da mamaki tare da fadin wanan ai gidan wani dan kano ne ai something sani wudil ko ? Wai kardai kice min wanan kanwan shice ko may ashe yar gidan manyace ita din ya fada da dan mamaki har lokacin a fuskan shi. Yana daya daga cikin ma,aikatan mai da jirage da kasan nan keji dashi sosai ai sai dai miskilin gaske ne shi din shiyasa ba wanda ke kula harkan shi . Koda yake kiyi hakkuri fa ina fadin halin dan uwanki a gaban ki hakan ko ya fada yana kallon matar shi. Tace yaushe kuma baya ka gama honny ? No gaskiya nake fada matar shi ma yar Nigeria ce sai dai wata arniya yake aure ai nake gani tsayawan da motar tayi ne yasa ina kokarin bude motar tare da fadin na gode fa zan fita. Ya danna gurin bude motar tayi dan kara na bude sai lokacin anty tace dani tau Fatima mun gode da wanan ziyaran sai mun hadu school monday ke nan Allah ya kaimu nace tare da kara mata godiya sai da naga dagawan su na juya zuwa ciki. Ranan ban yi barci sosai ba ina ta juya maganganun mu a raina har lokacin ban samu mafita ba ga zancen anty din nace idan ma cutarwa ne yake min kanshi ya cuta bani ba ai. KANO A hankali Aliyu ke jan motar kamar bai son tukin yayin da dan uwan ke zaune gefen su ya dafe goshin shi da hannun shi daya hankalin shi na akan wayan shi. Niko bros zanso muyi magana idan kana da lokacina yanzu Aliyu ya fada tare dan kallon yayan nasa. Ina jin ka yace ba tare daya dago kanshi yana kallon shi ba a lokacin jin hakan dan uwan shi ya girgiza kai yana fadin. Gaskiya bros kan wayan danaji kanayi shekaran jiyane sai naga kamar har yanzu zaman ku bai saitu ba yadda iyayyen mu suke zaton hakan . A ganina hakan ba girmaka bane ba kuma mutuncin ka bane bros don ranan da iyayen mu zasu fahinci hakan gaskiya girman ka zai fa, , , Dakata Aliyu ya isheka hakan ni zaka kalla ka fada min wanan maganan don raini ko may ? Kayi hakkuri idan ranka ya bacine bros gani nayi duk duniya babu mai fada maka gaskiya kan hakan kamar mu. Kaga ko Habbib daya fi kowa a cikin mu danyen kai ranan danaje gidan su Abuja sai da nasha mamaki . Akwai cutarwa sosai da danne hakki a cikin zaman ku da yarinyar nan ba zanso wani daga cikin family din mu ya fahinci hakan ba bros. Naji kana fadin wai mai ta fadawa mama twices data kirata idan ma bata fada mata komai a yanzu ba na gaba zata fahinci hakan daga hiran su. Sake juyowa yayi ya kalli dan uwan nasa rai bace yace ke nan kai zaka koya min abinda zanyi da iyalina ko ? Dan murmushi Aliyu yayi ya girgiza kanshi tare da fadin ko daya bros gaskiyane ko daddy yayi ba daidai ba za,a fada mai gaskiya balle mu yayan daya haifa. Well zaka iya fadin komai don ba laifin ka bane yace yana kawar da kanshi daga cikin motar yana kallon titin da suke tafiyan. Kaini gida yace kai tsaye ba tare daya kalle shi ba Aliyun yace gidan daddy zamu yace a hasale gidana nace ka kaini malam ban son yawan maganan nan don Allah. Mun fasa zuwa gidan gonan ke nan bai iya bashi amsa ba don ya gaji da surutun shi a lokacin. Kwana ya karya ya dauki hanyar gidan shi dashi ba tare daya kara cewa da dan uwan nasa komai ba suna shiga get din gidan yace tsayanan in sauka. Baibi ta nasaba saida ya kaishi gab da kofan shiga cikin gidan ya tsaya yana cewa in dawo anjima mu tafine ya bude motan ba tare daya kula shiba ya fice motan. Kai Aliyu ya girgiza yace a fili ka yi kuskure bros ba aiwa mace hakan da kake nufin yi nan gaba zamu sha kallon idan muna raye. Shiko sarkin tsabtan yana shiga gida dakin shi ya nufa kai tsaye ya fara cire kayan jikin shi ya fada wanka duk da zai fita yai wankan. Saida ya saka kaya ya fito falon kujera ya hau ya kwanta ya rintse idanuwan shi a zuciyar shi yake tunanen shi yaya zaiyi da matsalan yarinyar nan a rayuwan shi. Ko Amma duk yaje gurin ta da sunan gaisheta sai ta bulomai da maganan wata a ruwa can kafin ya tashi gurin. Shi ke nan shi baida wani damuwa ko matsala a yanzu sai na mace macen kuma karamar yarinyar da bata gama mai. Ga kuma hjy su data matsa mai lamba kan yarinyar lalai sai ya saketa ko su samu matsala dashi. Ga marry da yanzu ta sauya sosai da halayanta ga zamantakewan su ta dauko sabon akida ta dora a rayuwan ta. Shi da wani zaiji cikin wanan shifa idan ba dole ba gaba dayan su sai ya sahile masu da wanan auren. Don hakane ma yake rage yawan shiga gidan nasu ko wurin daddy da yanzu yana gane kowa yana magana kada watarana ya tambaye shi wanan yarinyar wani amsa zai ba daddy din . Ga Aliyu kuma yaji wayan shi da yarinyar nan har ya fahinci halin da suke zama kadafa yaje gurin surutu ya fadawa wani wanan maganan ko da kuwa matar shice. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:19 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH, , , , , Ranan monday karfe bakwai na safe kamar yadda na saba fita daga gidan na isa bakin titi don tare taxi din da zai saukeni school. Jikina saye da dogon riga da coat doguwa har gwiwa sai half sunna hijjab din daya rufe min wuyana da saman kai banda tafin hannuna da fuskana baka iya ganin komai a jikina lokacin. Wanan shigar yana daukan hankalin mutane da dama don shedace mai nuna ni din musulmace a duk inda aka ganni. Wanan shigar kusan ko yaushe hakan nake yin shi idan zan fita don london kasa ce mai bawa kowa daman yin akidar shi dayazo dashi kasan. Idan ka ganni kasan ina da dan damuwa a tare dani ranan don ban irin dan walwalan da nake a cikin kawaye idan mun hadu. Gurina samu inda babu kowa na zauna ni kadai tare da harde hannayena saman kirjina na kurawa guri daya idanu. Har aka zauna kusa dani sai lokacin nayi ajiyan zuciya tare da juyowa inga ko waye ya zauna kusa dani lokacin. The guy na gani yana min dan murmushin shi mai tsada duk da akwai dan tazara tsakanin mu hakan bai hanani kara matsawa ba kadan daga inda nake ? Yace yan mata waya bata maki rai hakan ya hanaki walwala yau don da ganin ki ba sai an tambaya ba kina cikin damuwa hakan. Dan murmushi na sauke a fuskana nace as you say amma ni banda wani damuwa a tare dani sam na fada ina kokarin mikewa tsaye. Yace no kada kice zaki gudu don ni zarah ki zauna ki huta abinki saidai ban son ganin ki a cikin wanan yanayin haka ko mijin ki ne yayi maki ba daidai ba tunda kince kina da aure. Wanda ni har yanzu na kasa gaskanta hakan a raina don ban taba ganin alaman hakan ba tare dake. Da mamaki na dago kai ina kallon shi tare da fadin wani alama ke ga masu aure din da ake gane su. Saida ya mike tsaye yake fadin well tare da dan kakabe wandon shi kamar wanda ya kwashi dadti a jikin shi yace . A bangaren ki irin kamun kan masu aure nake gani a gare ki sai dai ba lalai ne in gaskanta hakan gare ki ba gaskiya. Har yau ban ga mijin naki ba kodai bai damu dake bane zarah ya fada yana kallon fuskana kamar may son gano gaskiya a cikin idona. Nace idan baka sanshi ba aishiya sanka don ko wanan tsayin da mukayi yana da labarin komai yanzu. Ido ya zaro waje da dan mamakin maganata yace kice dai yana da security a boye ke nan saidai ba abin mamaki bane maganar ki don mazan kasan mu masu kudi basu kyale mata kyawawa irin ki dama, har mu matasa mu samu. Mikewa nayi gaba daya nace sai an jima ba zan iya sauraren nan zancen ba nidai na fada ma wallahi da aurena a kaina tuntuni na barshi a gurin yana bina da kallon mamaki. Ya sauke ajiyan zuciya tare da shafo kanshi kafin ya girgiza kai tare da kada hannun shi koma waye mijina har in ina dashi zai gano shi indai dan Nigeria ne. Na dawo kamar kullun ina shiga wayata na ruri kira da kyat na zaro shi cikin jakkata ina duba mai kiran nawa mamu na gani . Kin dauka nayi saidaya katse na kirata tare da fadin mamuna nayi missing din ku ina Fauziya dasu yan biyu ya jikin kawuna ? Ya fara fita kasuwa da sauran gurare mamu na jera mata tambaya a jere tace wani zan fara amsa maki a ciki dan dariya nayi nace na kawuna mamu. Tace kawun ki yana jin ki yanzun haka gashima yana dan murmushin jin muryan ki ai. Dan ihu nayi nace Allah nagodema dakaba kawuna lafiya Allah yakara bashi lafiya da sauran mudulmai baki daya naji yace Amin yar kawu. A cikin ladabi na fara gaidashi tare da jera mai sannu yanayin yadda yake magana yasa na gane har lokacin yana jin jikin sa wai a hakan sauki ke nan suke fada yaji. Kawune ya dan katse shirun da tambaya yar kawu Allah yasa inga diyan ku a duniya kafin in tafi shiru nayi na kasa amsa mashi saida yace hello kina jina Fatima ? Ina jin mamu tana fadin kaima kasan ba zata amsa ma wanan addu,an ba ai ta karbi waya tare da fadin bana gida ina nan gurin kawun ki dana ba su fauziya kun gaisa don suna damuna da zancen ki ko yaushe. Tundai da sukaga mijin ki yazo ba dake ba kuma suka shiga tambayan ki yaushe zaki zo ko a kaisu gurin ki. Mamu ya umar bai fada min zaizo ba dana bayar da sako a kawo masu kuma sai ya kirani yana fadin wai may na fada maki ? Wayan ta danyi kara alaman katsewa na dago na kalli wayan ina mamakin jin ya katse dukda nasan akwai chages mai yawa amma kudina bai isa karewa ba a lokacin. Nayi neman layin kuma baya shiga ko kadan don haka najefar da wayan gefena tare da kaiwa kwance saman kujera ina lumshe idanuna. Sai dana dauki lokaci a hakan kafin cikina ya fara kukan neman abinci na tuna banci wani abin kirki ba ranan bayan ruwan tea dana sha kawai. Daga idonayi na kalli agogo karfe takwas na dare saura lokacin don haka na mike ba shiga kitchen don samawa kaina abinda zanci. Ya fito zai shiga mota ke nan wayan shi yai kara ya dauko daga aljihun shi yana duba merry ce lokacin. Yana dauka tace dashi Omar what are doying in that country of to know ko ka manta da kabar mutane a nan ne ? Tambayan ta bashi mamaki matuka don haka shima ya mayar mata da mai zafi lokacin tare da fadin kada ki manta mahaifina ne baida lafiya . Bayan haka ko kin manta Nigeria kasatace ta haihuwa da zan iya zama so raina. Wanan katon sai ta kwantar da murya tana fadin naga kasan Christmas ya kusa zuwa dear amma baka dawo ba har yanzu almost to one month kake nema a can fa yanzu ? Yace shima cikin kwantar da murya kamar yadda tayi din i will come back very soon insha Allah . Ba tare da tambayan jikin mahaifin nasa ba ko wani na gidan nasu tace love you kawai ta kashe wayan ta. Kallo wayan nasa yayi cikin takaici zuciyan shi cike da mamakin halayan merry din da mugun halin nan nata . Ya fara zargin ta a ranshi daman boye mashi halinta na gaskiya tayi don ya sota don haka kawai idan ba halinta bane hakan ba zata iya hakan ba kai tsaye. Don yanzu kanta da yarta kawai ta sani bata damu dashi ba balle wani nasa ta nuna mai kauna ko kulawa. Ko wanan yarinyar daya kai da sunan kanwar shi da cewani bata tambayan shi komai a gamay dani din. Har yakai inda zai tafi ya dauki nasir abokin shi bai kaiga samun mafita ba akan merry din . Horn yayi Nasir din ya fito ya dauke shi suka tafi har lokacin bai sake ba sai Nasir keta zuba a motan shi kadai. Can dai ya juyo yana fadin yaya dai mutumina naga kamar ranka a bace yake kuma yanzu bayan munyi waya dazun dakai lafiya. Dan shafan fuskan shi yayi da hannun shi daya yana fasin kaidai bari mutumina har kan merry ne ke bani mamaki wani lokaci. Kamar ya Nasiri yace dashi sai yace bari kawai mutumina wai ace matar nan fa tun zuwana duba daddy bata taba tambayana ya jiki daddy na yake ba ? Dan murmushi Nasir yayi yana kallon shi kafin yace hausawa sunce kowa yasai lariya yasan zarayi yoyo ai ? Ba mamaki su a wurin su hakan ai ba komai bane so kaga sai kayi hakkuri kawai da halinta tunda kana son matar ka. Kasa ba nasir din amsa yayi do yasan magana yai masa a fakaice muryan Nasir din ne ke fadin ita wanan yar uwan taka fa kuna waya da ita kuwa don ita kan nasan tarbiyan muce ta musulman hausawa gare ta.. Yayi kamar baiji mai Nasir din ya fadi ba lokacin ya share shi ga zancen kawai yana tuki abinsa. Nasir din ya sake fadi wallahi mutumina kaji tsoron Allah ka dauki yarinya karama kaje da ita inda bata san kowa ba kana gana mata boni can. Ya juyo a harzuke yana fadin ubanwa ya fada ma hakan duk kokarin da nake kenan banyi ba ko. Kai Nasir nifa har yanzu kallon kanwata ko yata nakewa wanan yarinyar har yanzu. Amma ko bakai ma kanka adalci ba abokina kana ganin yanzu ita wanan matar taka zatai maka halarci nan gaba. Ya juyo da kyau yana fuskantar shi yace ya kamata umar ka natsu ka fahinci mai mahaifanka ke nufi da hafin auren nan gareka. Umar baka sanin kayi sakaci da daman ka sai nan gaba kadan idan girma ya fara zo maka. Ko kana neman wani mukami a kasan nan a lokacin zakayi dana sanin watsi da wanan daman da mahaifinka ya doraka akai. Ya juyo shima yana fuskantar abokin nasa cikin fadin ban gane mai kake nufi ba Nasir ? Kana tunanen zan shiga siyasa ko wani abu a kasan nan ne nan gaba ko kana tunanen zan daukowa kaina maganan da zai ja min tozarci. Kai Nasir ya girgiza yana fadin baka dai fahinceni ba abokina mu bar zancen nan bawai ina kalubulantar matar ka bace ko daya wallahi gaba nake hango maka kawai yasa na fadi hakan. Huci yayi gami da furzo da iska daga bakin shi yana sauke ajiyan zuciya tare da dan buga sitiyarin motar a hankali alaman jin haushi a ranshi. Baisan lokacin dayace mata mata ba babba ba yaro a cikin su halinsu daya ne abokina in fada ma yanzu haka a cikin takuran hjy mu nake tun zuwana kasan nan . Don har yanzu hjy bata janye maganan ta ba Nasir kan yarinyar nan taya kake ganin zan yaudari daddy in affaka wa yar karamar yarinya saboda in bata mata rayuwan ta a banza Nasir. Duk abinda mutum zaiyi yayi zurfin tunane a cikin sa bazan taba son aiwa yata ta cikina ko kanwata yadda mama tace tana so in mayar da yarinyar nan karamar bazawara. May karamar bazawara ke nufi Nasir in lalata rayuwan yar mutane in sako masu ita a wullakance Nasir ba zan taba yin haka ba a rayuwata yar maimuna kamar jinanane Nasir. Ido Nasir ya zuba mai a cikin mamaki yake kallin abokin nasa can yace idan har hjy ta furta hakan batayi maku adalici ba dakai da mahaifinka abokina. Shawaran da zan baka a nan shine kada ka yarda ka saki yarinyar nan koda daddy baya raye a duniyan nan don wanan yarinyar kamar makamine a rayuwan ka nan gaba. Shiru sukayi gaba dayan su bayan fadin haka da Nasir yayi kowa da irin abinda yake tunane a ransa gama shi umar dake tuna zancen kanin sa Aliyu a ranshi. Ina zaune akan kujeran dining dake falon ina karatu don test din da muke dashi satin nan kafin aje hutun chrismas da duk kasan sai faman shiri sukeyi ko ina kafi shirye shiryen zuwan lokacin sukeyi a kasan. Wayata ta dauki ruri lokaci daya hakan yasa na duba da sauri na furta mamu again ? Da sauri na dana dauka tare da sallama ina gaida ita ta karba min tare da fadin ga su fauziya ku gaisa kamar yadda nayi maki alkawari dazun. Mun gaisa da kanne na dukkan mu muji dadin hakan karshe sai mamu ta karbi wayan a hannun yaran tace sayadi na amsa da naam. Tace dazun nice na kashe wayan don jin abinda kike shirin yi a gaban kawun ki. May nayi mamu na tambaya a maraice tace kina zaton idan kin fadi magana kadan akan zaman ki da mijin ki hakan zai iya kara jefa kawun ki cikin rikicewa. Jin muryan ki dayayi yau bakiga yadda yake faman saka maku albarka ba duk wanda ya shigo bayan kunyi waya yasan Alh yana cikin farin ciki yau. Jikina yayi sanyi sosai lokaci daya na kasa furta komai mamu tace sayadi ina karatun ki da abindana koyar dake idan kana cikin damuwa kayi ? Shin kin mata da irin rayuwan gidan nan da kika barni cikin sa irin makamin da nake fani dashi gare su baki daya shine addu,a. Sayadi kiyu ta addu,a a rayuwan ki komai yayi tsanani maganin sa Allah ni kaina na sha ji a jikina irin zaman da umar keyi dake a can. Saidai kona fada ba yarda za,ayi dani ba don hakan magana baida amfani gare mu maganan ma tonawa kanmu asirine kawai zamuyi. Kiyi hakkuru a tafi a hakan kodon makiya kada su gane halin da ake ciki duk nan an baza kunne da idone aga yadda zaman naku zai kaya. Don haka karnaji karna gani kowa ban yafe ki fadawa wanan zaman ba shima ya iya boyewa shida yake namiji sayadi sai ke mace ce ba zaki iya ba. Yanzun haka ina jin wai wai a gidan nan tun zuwan shi kasan nan uwarshi ta hasa mai wuta kan lalai sai ya rabu dake . A tonanen ta ya riga da ya bata maki rayuwan kurciyar ki don hakan idan ya sakoki bakin ciki da rakaici ne zai cimu har kawun naki. Don haka nake son ki kara jajircewa sosai ki bishi yadda yake son zaman ku kada ki yarda ki nuna mai gazawa a bangaren ki kan hakan. Kina jina ko sayadi ban son inji komai gamay da zaman ku sai dai idan kiyi hakkuri gaba zakiji dadin hakan sosai don hakkuri bai taba faduwa kasa banza . Kina jina ko sayadi na amsa mata da eh mamu tace Allah yai ma rayuwan ki albarka yabaki zuria masu albarka a sanyaye na amsa da amin naji ta kashe wayan baya ki kula da kanki ki tsare mutuncin ki data fada min. Na dade zaune ina kuka ina tunane na duba dare yayi sosai lokacin ga ruwan sama da ake ta tafkawa kamar da bakin kwarya. Mikewa nayi zuwa daki bayan na kashe komai na falon da nake amfani dashi ina shiga dakin na aje waya da sauran abubuwan da na shigo dashi na nufi bandaki. Alwala na dauro na fito na shimfida abin sallah a cikin natsuwa da kulawa na gabatar da sallah na har lokacin tuwa ake sosai a garin . Na idar na dade a gurin zaune ina tunane ga dare yayi sosai barci ya kauracemin a idona sai faman sake sake zuciya da nakeyi. Na fadi a fili a hankali ni yaya zanyi da rayuwata anty farida ta fada min nata shawaran yanzu kuma ga mamu da nata shawaran duk dai akan abu daya ake magana wanda ni hakan ma bai damay ni ba sam. Gara maganan mahaifiyata duk a kan hakkuri ne gareni ba wani zancen bada kai ga miji illar in daure in samawa kaina madogara nan gaba. Kaina na dafe daga yadda nake zaune nace Allah kaimun gata ka bani mafita kan wanan mutumin idonane ya fara zubar da zazzafan hawaye lokaci guda. Bazan kara yarda da in takurawa rayuwata ba ko kadan zan watsar da komai in kama harkan gabata. Kada watarana azo a samu na mutu ni kadai a gida ya zama dole in fara shiga mutane kamar kowa a gari . Tun ranan naba kaina salama ga komai yadda yaya daukeni hakan zan dauke shi nima mu zuba mu gani dashi. Ganin za,a shiga bukin addini a kasan na yanke shawara a raina in fita in sawo abinda raina ke so tunda akwai kudi a hannuna da ban san adadin su ba idan ya ban ajewa kawai nake ban komai dasu sai dan hawa taxi da sauran abubuwa. Mun samu hutun makaranta muna gida don haka na shirya zuwa siyayya abinda raina yake so . Nasan dan kwanaki ya rage manyan shaguna su zasu cika da jama,a don shagalin bukukuwan chrimas da zasuyi kwana biyu kuma su rufe. Na shirya cikin riga da siket yan kanti har kasa sai dan hijjab dina dana saka a saman kaina takalma masu dan tsini ne a kafata jakkata na dauko na rataya na fito na rufe gidan. Iskan garin na shaka mai sayin ke kadawa don ruwan da akayi aka dauke a lokacin takawa nayi zuwa inda zan samu taxi ya kaini gurin shiga jirgin kasa da yake tafiya a saman mono rail. Shi wanan jirgin a sama yake tafiya anyi mai yar siririyar igiyar bi wanda ke cikin jirgin zai iya hango mutane da motoci a kasa . ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:20 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YAN UWA MUSULMAI DA FATAN MUN TASHI LAFIYA UBANGIJI YA BAMU WUNI MAI ALBARKA DA DARE MAFI DARAJA A RAYUWAN MU AMIN, , , , , Mafiyawan muna cikin jirgin a nan zamu sauka ashe gurin ya cika makil da motoci da mutane nau,i daban daban sun fito sayayya don bukin kirisimeti. Sai dana karewa wurin kallo kafin in bi ayarin masu tafiya da kafa muka shiga cikin plazan . Sai ka turmusa wani kati da muka saya kafin kofa ya bude ka shiga ka hau na,ura mai tafiya da kanshi zuwa sama ko kasan ginan wurin. Muna sauka muka shiga cikin plaza din komai nasu a tsare yake gurin wanan ne farkon zuwana gurin don haka na zama ba kauya a gurin. Gurin kayan gwagwani na fara zuwa ina duba na halal kifi da naman gwagwani na kara siyowa sai pad da nafi bukata fiye da komai a lokacin. Na juya wirin saida turare da kayan kwaliya na zabi wanda nake so mai isata kafin in juya gurin kayan sitiru na fara duba masu mutunci na zaba. Ba wasu kaya bane irin namu sai gown da wanduna da su t,shirt haka na garo zuwa wurin biya kudi masu yawa aka chajeni na basu katina suka cire abinsu aka saka min cikin manyan kwalaye mai dauke da tambarin shagon nasu na fito. Wanan karon taxis na nema don komawa gida saboda nauyin kayan dana lodo lokacin har bakin get din gidan mai motar ya tsayar da motar shi. Da taimakon shi ya kaimin kayan har kofan shiga gidan gaba daya na biyashi kudin shi ya tafi sai lokacin na sauke ajiyan zuciya ganin naje lafiya na dawo lafiya ba abinda ya samay ko kadan wurin zuwa da dawowa. Ina tura kofan gabana ne ya fadi jin kofan a bude lokacin hakana na daure ina shiga da kayan da kyat ta ciki. A razane na juyo ina kallon shi jin muryan shi a daidai lokacin da ban zata ba daga saman benen yana fadin daga ina kike haka yanzu da wanan kayan ? Tsare shi nayi da ido kafin in ce na fita sayayyan abinda nake bukatane . Ya sake jefo min tambaya da izinin wa kuma dake da wa kuka fita zuwa sayayyan ? Nace bada izinin kowa ba ni kadai na tafi naga idan sun fara bukin kirisimati komai wuya yake a kasan . Kai tsaye nake magana na batare da jin komai a raina ba gamay dashi sabanin da can da nake magana dashi ina jin shakkun shi. Tsaye yayi sororo yana kallon yadda nake magana ina aikin shigo da kayana zuwa ciki daga kofan gidan. Tsaye yayi sororo tare da kare min kallo cikin yanayin mamaki karara a fuskan shi. Sai da na gama jido komai zuwa ciki na dawo na samu ya shiga dakin sa ya rufe hakan ya ban daman shiga nawa dakin nabar kayan a nan falo daga sunan zuwa fitsari sai na tsaya na dauro alwala nayi sallah ban fito ba saida na sauya kayan jikina na sauko kasa. Kitchen na fada dafuwa mai sauki nayi muna wanda ganye yafi yawa a cikin sa sai dan sauran abubuwa na jera muna a falo. Wanka nayi na daura wani alwalan magariba na fito sallah na gabatar kafin in gyara jikina kwalliyan wando da yar t,shirt nayi a jikina na sauko don cin abinci. Ban san da fitowan shi falon ba yana zaune yayi dadaya da kayan dana sayo na barsu a gurin yana kallo sai gani na fito daga daki. Ja nayi na tsaya ina kallon shi da mamaki sai lokacin na iya tuna daga tafiya ya fito ban samu gaida shi ba na dan raba gefen kujera ina gaidashi tare da mashi yaya kawu da jiki da mutanen gida duk lokaci daya nayi mai tambaya a jere. Dago kai yayi kamar da mamaki yana amsawa a takaice tare da fadin kayan abincin ki sun karene da kika sayo wanan ? Basu kare ba ina dai ra,ayin canzawane kawai yasa na sayo su don kawar da zancen nace dashi ga abinci a dining yaya. Shiru yayi min ba tare da ya amsa ba na dauka ba zaici ba don bai kula da maganata ba sai kanshi daya dafe ya mayar da bayan shi saman kujeran. Tambayan dana jefo mai yasa ya dago kai ina fadin yaya yaya su Amma da mamu suna lafiya ? Su kika sani ke nan ya fada yana mikewa daga inda yake ya nufi gurin abincin ciki ciki nace don nasan su zasu ce a gaidani mana. Ya juyo yace OK to su din ma basu ce ba don ban fadawa kowa zuwana nan ba. Mikewa nayi zuwa bakin dining din na bude abincin da sai tururin zafi ke tashi cikin cooler na fara zuba mai ba tare dana kalle shi ba. Nima na zuba nawa naja kujera na zaune daga gefe na fara ci ba wanda ke magana a cikin mu sai abinci muke ci da sake saken zuciya. Bell yayi kara da alaman akwai wani a waje yana son shigowa gidan da dan mamaki ya kalloni nima kallon shi nayi kafin in mike zuwa kofan cikin raina ina mamaki. Na bude kofan a hankali ina kokarin duba kowaye a kofan wata farar fatace tsaye a kofan dauke da kwalin cake tana murmushi tace min happy chirismas tana miko min kwalin dake hannun ta. Murmushi nima nayi don na sheda ta makwaciya ta ce matar duk da babu ruwana dasu sai wani lokaci mukan dan gaisa sama sama, da safe da ita. Hannu na mika na karbi kwalin da take miko min nace same to you thank you wishi you many many years retune. Matar taji dadin addu,a danayi mata tace saboda ni makwabciyar tace duk da taga ban kula kowa a layin yau dai ta daure ta kawo min kirismas gift har gida. Nace na gode hannun daya mika zai dauki ruwan dana aje mai gefen shi yasa ta farga dashi ta dan juya tana gaidashi ya amsa mata ciki ciki. Tambayana tayi wanan yaya kuke dashi na bata amsa da brother dinane shi tace kuna da kyau family din ku sosai wani ya taba fada min hakan kuwa ? Nace mutane da yawa suna fada min hakan ba ita bace ta farkon fadin hakan ta juya tana fadin zata tafi ta gode da karramawan da nayi mata a gidana. Tana fita na rufe kofan na juyo na samu ya kakafeni da idanu yana min wani irin kallo mai tatare da ma,ana. Ban koma wurin abincin ba sai na nufi wurin kayan da nasayo ya watsar min dasu a falon na tsuguna rai bace na fara tattara kayan a hankali. Muryan shi naji yana fadin har makwatabta kika fara janyo min a gida ashe ke wata irin yarinyace da bata jin magana haka ? Ban iya bashi amsa ba illa shirun da nai masa naci gaba da dauke kayana a kasa ba tare da na juya ba a yadda nake. Wayan shi da aka kira ya rabamu ranan don tunda na shige da kayana ban sake fitowa ba sai washe gari. Ban tabbatar da yana gidan ko bayanan ba nidai na hada breakfast dashi ranan na koma daki nayi wanka na shirya cikin daya daga cikin dogayen rigunan dana sayo jiya rigan jace andan bude gefen shi don hakane ni nasaka dogon wando daga ciki don kada sharabana ya fito fili. Ina matukar son abu kalan ja ko baki da yellow da sky clour saukowa nayi na nufi kitchen fridge na bude na dauko lemo kwalba na fito. Yau haka kawai naji zaman ciki ya isheni don haka ina son shakan fresh air a waje. Dan barandan gidan da mutum zai iya tsayawa yasha iska na bude na fito akwai kujeru biyu wurin da aka tanada don wanda ya tsaya wurin. Saidai ban zauna bani staye nayi ina karwa gidajen makwabta kallon yadda suka kawata gidajen nasu da shaguna don kawai zagayowan wanan bukin nasu da muke hutu a kansa. A yadda nake tsaye gurin daga gani babu tambaya na samu nishadi sosai a lokacin . Saboda yadda nake tsaye ga airpiece makale a kunnena ina shan wankan larabawa mai take Allah Allahu ya baba asalamulaikum ya, , , , Shi nake saure a lokacin ya shagaltar dani saboda dadin wankan da nake ji ina dan kurban lemon dana tsiyayo a cup a hankali idan na kurba in mayar da hankalina ga titi . Tsaye yake yana karewa yanayi da nake cikina nishadi kallo banda damuwa a tare dani yanzu ko kadan. Yana mamakin sauyawana da sakewa a dan lokaci kankani duk yaga komai ya sauya daga bangare na. Wani irin tausayina yaji ya rufe shi lokaci guda yasan yana danne min hakkina da komai amma daidai da rana daya ban taba nuna mashi hakan yana damuna ba ko a fuska. Na dago ido na dan juya don jin kamar mutum a tsaye bayana sai nayi arba dashi tsaye ya saka suith a jikin shi ash clour yana tsaye ya saka hannayen shi a aljihun wandon shi ya zubo min idanuwan shi. Dama naji hakan a jikina ana kallona da sauri nakai kasa ina fadin yaya ina kwana. Mai hali baya barin halinsa kamar bashi bane ya gama tausaya min yanzu dan harara ya galla min tare da fadin . May kike a nan kuma mutane suna kare maki kallo a haka da kika fito ? Yana fadin haka yaja guntu tsuki tare da juyawa yabar gurin ya koma ciki cike da takaicin da bai san dalilin yinsa ba. Bayan shi na galawa harara ina mai takaicin yadda ya tsaya na kare min kallo a fakaice gani kaina babu ko dan kwali lokacin. Ban bar wurin ba saida na kare shan lemona da kallon wasu yara masu tseren keke a gaban gidan mu. Na shiga falon bai ciki gurin labulen gaban gidan naje na daga na hango shi yana kokarin shiga motar shi . Ya hanani tsayawa idanake ganin mutane shi kuma ya fita ya barni kamar manya a gidan ni kadai na fadi a fili. Ni kadai a cikin gida sai faman mita nake kai kace da wani nake zance a cikin gidan wurin tv dake falon na nufa na kunna. Ko wani tasha nasu nakai babu abinda sukeyi sai hasko bukin wasan kirisimeti da sukeyi . Haushi naji ina fadawa saman kujera na kai kwance tare da lumshe idanuwana take zuciyana ta anyana mun shiya dawo da yaya umar kasan nan. Zubur na mike nakai zaune tare da fadi a fili tabbas abinda ya dawo yi ke nan don matar shi waya sani ma ko shima chocin yake zuwa. Kai amma ko idan hakane anyu hasarare a gurin nan ya zama dole inbi kwakwafin takon shi in gane ko yana cika sallah shi. Taya zan gane hakan na tambayi kaina mutumin da kullun yake faman daure min fuska kamar baisan inda na fito ba. Ta yaya kawu zai dauka harni zan iya gyara mai akidun shi bayan baya son kowama ya rabe shi sai wanan kafirar matar tasa. Nasan akwai abinda mijin anty farida ke son fada ranan gamay dashi sai kuma yayi shiru bai fada ba koma may ye shiya sani nidai in samu in karasa karatuna in koma gida kawai don ba zan yarda in zauna kasan da bansan kowa ba inta rayuwan kadaici saboda shi. A ranan nasha mamakin makwabtana don kusan mutum uku suna kwakwasa kofa suna kawo min charismas gift har gida ina godiya ba wani abu bane sai cake da sukayi da sauran irin su sweet da biscuit. Mamakin hakan nayi sosai a raina don tunda nake dasu ni wani gaisuwan kirki bai taba shiga tsakanina dasu ba ma sai gashi duna buga min gida suna kawo min kyauta har gida don kulawa. Shiko yaya tun fitan shi ban kara ganin shi ba yau kwana biyu ke nan sai dai dama na kudurta a raina wanan karon idan yace zan tafi can dayan gidan nasa wurin su merry zaisha mamakina don ba zan tafi ba yin bukin shedanci. Da zaman ya isheni ni kadai a gida na ina jin kamar zan kamu da ciwo don haka na shirya tafiya gidan anty farida in kai masu yawo. Saidai nayi rashin sa,a sunyi tafiya wata makwabciyarsu yar kasar lebonon ke fada min sai lokacin na tuna amfanin waya ashe dama kiranta nayi inji ko tana gida kafin inzo. Dama da kafa nake don in motsa jikina haka na tako da kafa na kamo hanya ba gida na nufa ba dayan hanyan nabi da kafa ina kallon gari. Naji dadin wanan fitan don naga mutane gungu gungu suna wasan ni a layin da kama layin na talakawan garine ko dai wani wurin nishadi. Haka nayi tabin layin ba tare da nasan takamaimai inda zani ba can naci karo da miji da mata suna tafiya a hanya kamar a mafalki naji suna yaren hausa a tsakanin su. Sam basuyi zaton zanjisu ba matar tace iko Allah su kuma a haka wai bukin murnan sallah sukeyi haka wai ? Mijin yace kin san abinda ka yard dashi ko aka haifeka a cikin sa ban san lokacin danace sannun ku da hutawa ba . Gaba daya lokaci guda suka juyo suna kallona dan dattijon yana kare min kallon mamaki saidai yanayin shigata nasan bana banza bane nayi lokacin. Na sake fadin ina wuni ku har lokacin da mamakina karara a fuskan su suka amsa min kusan lokaci guda. Da barka dai yan mata kema kin fito bude ido ke nan ko matar ta tambayeni ? Eh hjy zaman kadaici ya damay ni na fito kawai inga yanayin bukin su na bata amsa tace ayyah akwai kadaici tundai a irin wanan lokacin da suke zaman gida suna shagulgulan su ta wanan shirmay nasu wai bauta. Mijin yace kada ki zake da yawa don ita din baki san ko wacece ba Ramla ya fada yana tsareta da ido. Nace a a ha baba ni din ma musulmace yar uwar ku sunana fatima daga Nigeria nake nazo karatu ne nan kasar tare da yayana gidana yana bayan layin nan kadan. Kai amma ko nayi murna da haduwa dake yan mata zaman kadaici ba dadi ke gareshi ba tundai a irin wanan kasashen na turawa. Nayi murmushi saboda jin kalaman matar ganin kamar mijin bai yarda dani ba yasa nace nagode da dan lokacin da kuka bani zan tafi sai watarana idan Allah ya sake hadamu kuma. Da sauri matar tace haba haba yar uwa tun yanzu aini ina ganin ki kamar naga wata ta gidane wallahi. Muma daga Kasan ghana muke sai dai shi maigidana dan Nigeria ne don yafi zama a can kowa nasa yana Nigeria sai mahaifiyar shi ce yar kasar ghana. Ba zaki tafi ba tunda kina ke daya a gidan ki kizo mu zagaya a tare muyi kallo ikon Allah wai kin san al,adun su na gargajiya abin mamakine sosai. A yadda na fahinta matar tana da son hira sosai da kuma son mutane sai nake tunane duk wanda ke wani kasa haka yake idan yaga dan kasan su wani gari. Ranan naji dadin wanan fitan don na sake jikina sosai mijin matar ya kaimu wurin cin abincin mai kama data kasan mu kowa yaci abinda ranshi ke so. Har gida suka dawo dani sai da sukaga shigata gida suka ja motar su suka tafi sai lokacin naji wani irin ba dadi don kamar kada su tafi su barni naji lokacin. Ina kokarin juyawa mukai ido biyu da yaya umar dake tsaye cikin damuwa a kofan gidan hannayen shi duka biyu suna saye cikin aljihwayan shi na wandon jikin shi. Dan raza nayi kai kace wani abin tsorone a gabana lokacin yana huci yana cika yana batsewa sai lokacin na saita kaina nace sannu da zuwa yaya kamar kullun . Ke dakata daga ina kike wa yan nan mutanen kuma su waye su da suka sauke ki ya tambaya cikin daga muryan shi. Mun fita cikin gari ne na bashi amsa sunan ta anty Ramla mun hadu dasu ne a garin nan. May kike son zamane Zarah kina son ki zama watsartsane a garin nan komai ? Naji zafin kalaman watsartsar daya kiramin don haka bansan lokacin da zafin rai yasa nima na daka mai tsawa ba kamar yadda yai min. Nace kai yaya ya isheka haka nayi maka kama da mara tarbiyane a shiga ko kaga wani abin Allah waddarai a tare dani. Ka sani koda bani gaban iyayyen mu nasan abinda nake don ba tarbiyan banza sukai min ba ban kuma taso naga ana abin asha ba a gidan mu balle inzo nan in koya a garin mutane. Yaya kake son inyi da rayuwata yaya ka daukoni kazo dani kasan mutane ka watsar dani ba kulawa ba komai nima fa mutumce yaya da dole ina bukatan wani a tare dani. Banki duk yadda kace min ba ina kokarin ganin na bi duk wani dokan ka na tsare shi yanzu kuma zakace kada in fita in ga mutanen arziki. Na sani da sunan aure muka bar gida amma kaida bakinka yaya kace kada in sake in nunawa wani a kasan nan akwai aure tsakanina dakai. Duk da nasan hakan ba gaskiya bane ina kokarin nunawa kowa kai yayanane najini karatu ka kawo ni yi kasan nan kamar yadda kake son in nuna din. Ko zanyi iskancin da kake zato inayi din da mata da mijin ta zanyi yaya ? Ido rufe nake magana duk cikin bacin rai yasa bansan ya karaso inda nake ba sai jin saukan mari biyu masu kyau naji a fuskana. Dafe fuskan nayi yayin da nake duke na kasa dagowa sai can na iya dagowa na kalle shi yana tsaye yana huci akaina. A hankali na ja kafana na tura kofan zuwa ciki ban tsaya a falo ba na hausama inda dakunan kwanan mu suke. A hankali na tura kofan na shiga na mayar na kulle nasa sakata gadona fada na nemi farin ciki da nishadi dana dawo dashi na rasa a lokaci daya. Rutse idona nayi a hankali na furta mamu wayyo Amma wayyo ni manjona da wani irin karfi. A daidai lokacin da yake rufo gidan yaji wanan karan dana sake lokaci guda daga kai yayi ya kalli kofan zama yayi saman kujera tare da kokarin sasauta tie din wuyan shi. Ya mayar da kanshi saman kujera tare da runtse idanuwan shi wayyo mamuna don Allah kizo ki kwace ni a hannun wanan azzalumin kafin ya kasheni. Abinda ya shiga kunnen shi ke nan, kai ya girgiza ya ya kara runtse idanuwan shi zancen kanin shi Aliyu ya tuna yaya matse zai iya sa ta dauki matakin da bai dace dakuba. Ba wai ina nufin tursasaka akan iyalin ka bane a a ya kamata ka rage wasu abubuwan da kake mata itama fa yace kamar kowa. Why ba doki wanan yarinyar yaya akayi har nakai hannuna a jikin ta ya dade zaune yana tunane barkatai. Kafin ya mike ya hausama tun a matakalan yake jin sautin kukana a kunnuwa shi wanda yake jin zuciyan shi na kara tabuwa da baci a lokaci daya. Har ya tura kofan shi zai shiga yaji na kara fadin wayyo mamu na zai kasheni zai kasheni a garin mutane sai ya dauka waya nake a lokacin. Fasa Shiga yayi dakin nasa ya nufo nawa dakin ya tura kofan ya jishi a rufe gam. Ya tura ya tura yana rufe juyawa yayi ya koma inda ya fito har lokaci yana jin wani iri a ranshi ba dadi. Da kyat na iya tashi nayi sallah isha,i ban tsaya cire kayan jikina ba ranan haka na fada kan gado tun ina tunane har barci ya dauke ni gurin ban sani ba. Washe garima haka na falka da bakin rai yinin ranan ban fita daga daki ba ina daki ko falo banyi gigin lekawa ba. Komai ban saka a bakina tun safe har ukuna rana ban fito ba bandamu da sanin ko yana gidan ko ya fita ba lokacin tunda zuwan shi ko zaman shi gidan sai yaga dama ko yazo yin wani abin da yake sirine gare shi zai shafe lokaci yana dakin yana aiki da laptop din shi. Kadan kadan yake dago kai ya kalli hanyar benen kamar may kallon wani abu ba komai yake kallo ba sai fitowa a lokacin tun safe yake zaune a falon sallah ne kawai ya tayar dashi yana idarwa ya dawo ya sake zama gurin. Jin shiru ban sauko ba har lokacin yasa shiikewa yahau benen kofa ta ya nufa ya tura har lokacin a rufe kofan yake. Nocking ya fara yi tun yana yi a hankali har ya fara duka da karfi yana kiran sunna na ina jin shi naki budewa. Ko dagawa banyi a inda nake ba ya kara kiran sunana da karfi yana fadin ki bude kofan nan ko in karya in shigo dakin nan in saba maki nan ma ba amsa sai shiru. Hankali shi ne ya tashi sosai yana ganin kamar wani abu ya samay nine don marin da yai min din. Tun yana fadin zarah zarah har ya koma fadin Fatima nace ki bude kofan nan karna karya shi. Jin shiru ba amsa zuciyar shi ta fara kaduwa da fargaba a lokaci daya. Ya koma yin magana cikin marairaice murya yana fadin kiyi hakkuri zarah ki bude kofan ba dukan ki zanyi ba . Ina jin shi na kasa tashi saboda yanayin da nake jin kaina na yunwa da kukan dana sha kaina da jikina gaba daya ina jin su kamar ba nawa ba. Muryan shi na kara ji cikin wata marainiyar murya yana fadin zarah don Allah ki bude kofan nan ko hankalina zai kwanta kinsan amana kike a gareni kasan nan. Nasan nayi maki ba daidai ba don Allah ki bude kofan nan hankalina a tashe yake da rashin fitowan ki daga dakin nan. A hankali jiki ba karfi na dago daga kwance tare da sauko da kafafuwa daga saman gadon da nake kwance. Jikina ba karfi don yunwan daya ci karfina a lokacin ga kaina kamar zai fashe don ciwon da yake min. A hakali na bude kofan tare da murda marikan kofan jin ana kokarin bude kofan har ya juya yana shawara a ranshi yakira security din unguwar suzo su balle kofan sai gashi yaji ana bude kofan. Ya juyo yana kallon kofan da na riga dana bude a lokacin ina kokarin komawa sama gado in kwanta. Turo kofan yayi da karfi tare da fadowa cikin dakin daidai lokacin dana kai saman gadon ina kokarin zama a bakin gadon. Wani irin kallo yakewa yanayin daya riskeni a ciki don na gala baita sosai bakina duk ya bushe tun rigan dake jikina lokacin da abin ya faru shine saye min har wanan lokacin. Ga kaina babu dan kwali gashina dana tufke ya dan barbaje saman kaina har ya zubo saman goshina. Take yaji wani tausayina ya kamashi ya iso inda nake da sauri yana fadin zarah kina son ki kashe kanki ne kija min magana a garin mutane ko may ? Sai kuma ya juya zuwa waje da sauri ya dan dauki lokaci har na kai kwance sai gashi ya dawo dauke da kofi yana tururi da ruwan tea a ciki. Zuwa yayi har kaina ya tsaya yana fadin ki tashi ki sha wanan tea din hanji ya warware. Kamar badani yake magana na kyale shi ya ja tsuki yana fadin idan baki tashi ba zan dura maki shi ta karfin tsiya yanzun nan wallahi. Jin hakan nayi kokarin tashi zaune saidai na kasa da taimakon shi na samu na dan zauna a hankali karban kofin nayi jannuna sai rawa yake na dan kai bakina. Zafi da dacin shayin naji lokaci guda na sauke kofin ba shiri da sauri ki sha mana ya fada cikin tsatsareni da idanuwan shi. Kisha nace ko in kira ai maki allura yanzun nan tunda haka kike so jin hakan yasa na kara daga kofin ina kokarin kaiwa a baki na. Na kama kurbawa da dan sauri don ban son alluran danaji ya ambata min yasa na daure ina dan sha badan ina so ba. Wayar shi ta dauki ruri ya ciro yana kallon wanda ke kiranshi hakan yasa ya dauke kai a gareni ya mayar da hankalin shi gun wayan . Merry naji ya ambata daya daga waya yana fadin Ina nan mana ina zanje ban fada maki ba wani irin amai ne yazo min lokaci guda na sako shi har wandon jikin shi zuwa kafan shi sai daya taba. Haka yasa ya fita zancen wayan yana fadin subbahanallahi kinga zaki halaka kanki ko a banza. Wai wai nake fadi cikin jin ciwon da cikina keyi a bangaren merry tana sauraren abinda ke faruwa sai magana takeyi a wayan shiko hankalin shi yana gare ni. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:20 - 🀐🀐🀐: ALHAMDU-LLILAHI RABIL ALAMIN, , , , , Duk kokarin danayi na dagawa kada aman ya kai gare shi hakan bai samu ba don aman ya rigada ya zubo min daga cikin baki har ya sauka kasa ya taba mai tufafi da takallaman shi. What noses is this zara ya fada cikin daga murya a fusace saidai yana arba da hanlin da nale ciki hankalin shi ya kara tashi sosai. Don yunkurin fitar da wani aman nakeyi a baki saidai kasancewan cikin nawa babu komai yasa nake wahala komai yaki fitowa a lokacin. Gashi ina son mikewa daga yadda nake inje toilet na kasa yunkurawa hakan jikina yana kara sakewa a lokaci daya. Da taimakon shi na samu na mike tsaye da kyau ina fada da kyat zan iya zuwa da kaina yaya. Yace ki bari na karasa dake koda kofane duk a rude yake magana lokacin ganin yadda jikina yake sakewa gaba daya. BakinToilet din ya kaini ya tsayar dani tare dan jigina jikina ga bango ya shiga ya hada min ruwa masu zafi ya fito yace in shiga, Saida yaga ina kokarin tube kayan jikina ya dauka a gabansa zan iya kwabe komai baisan ban karkare fita hayacina ba. Naga yayi saurin fita tare da dan rufo kofan ya tsaya a tsakar dakin yana karewa gurin dana bata kallo. Cikin daurewa ya sauka kasa zuciyar shi yana jin ba dadi ko kadan abin goge wuri yake nema da kyat yaga inda nake ajewa ya dauko kafin in fito ya gyara gurin har ya shimfida wani zanin gadon saman gadon. Duk da halin da nake ciki bai hanani jin mamakin ganin ko ina na dakin a gyare ba lokaci daya. Na samu baya dakin lokacin haka yasa nayi karfin halin saka tufafi a jikina a daidai lokacin daya shigo da room fresh a hannun shi yana feasawa a dakin ni kuma na tayar da sallah cikin karfin hali na gabar da sallolin dake kaina. Wayan shi dake saman side drower din dakina yayi kara ya dauka a hasale merry ke fadin kaidawa ke magana Omar ka fita batuna. Waima da wata yar iskan kake tarene in ji yace mind you tongue meery kanwata Fatima ce bata da lafiya nake bata kulawa. Kashe wayan tayi ba tare data furta komai ba ashe a lokacin tana can ta haukacewa iyayyen ta da suke tare don bata shigo ba sai new year don sunfi ba bukin new year muhinmanci sosai. Jin ta kashe wayan yaja tsuki tare da kallon inda nake yace idan kin idar ki tashi muje asibiti a dubaki. Na shafa adduan da nake na dan juyo gare shi ina fadin murya ciki ciki naji sauki yaya ba sai munje asibiti ba. Yace a hasale common ki tashi muje tun dare bai muna ba don Allah yana mikewa nima yunkuri mikewa nayi lokaci guda na kasa yace in kamaki ne idan ba zaki iyaba ? Zan iya nace dashi cikin daurewa nake magana na samu na mike da kyat yana tsaye yana kallona har na daura karamin hijjab dina sama na kalle shi . Naga ni din yake kallo shima don haka na nufi hanyar fita daga dakin ya mara min baya muka fice daga dakin. Wurin saukama daga stairs din sai dayayi yana jirana har na sauka a hankali muka fito daga gidan yaja gidan ya rufe ganin ban sauri ya sukuce ni zuwa wurin mota ya saka ya juyo da sauri ya shiga yana ganin kamar wani abu zai samay ni ne a sanadin shi. Mun isa asubitin kadan kadan yake juyowa ya kalle ni har muka kai asibitin nan ma bai bari nayi tafiya ba don dauka na yayi tun ina jin nauyin dauka da yake min har na gaji na daure da hakan. Munga likita ya rubuta magani da kwantar dani don ina bukatan hutu da ruwa likitan yace. Nan ya dinga kai da komowa a kaina saida yaga komai ya daidaita har na samu barci saboda maganin da akai mun allura dashi na samun hutu. Bani na falka ba sai washe gari wuraren shadayan safe na bude idanu da kyat don sunyi min nauyi. Shine a zaune dakin ya tsura min idanuwanshi masu ban tsoro da rikitani yana ganin na bude idanuwana yace kin falka zarah ? Nace eh sannu ya na gode yace don't mind ina ke maki ciwo yanzu nace ba ko ina irin hausan mu na yaran yanzu. Mikewa naga yayi ya tako zuwa inda nake sai kawai naga ya fara dan taba min jiki a hankali. Nan daima sai daya kara tambayana idan ba inda ke min ciwo nace naji sauki. Ya juya tare da fadin likita yace idan kin falka a kirasu haka kawai zaki kashe kanki gurin shegen zuciyar banza waike shagwababa. Fuskana hade tare da dan kawar da kaina ina yunkutin mikewa zaune da kyau ya juyo yana fadin ki bari sai sun shigo sun duba ki sai ki tashi . Yana fadin haka ya fita sai gasu tare da nurse da likita mace sun shigo suna magana saida ta gaidani tare da min ya jikin nace da sauki a cikin harshen turanci. Ta tambayeni in akwai inda nake ji nace banjin komai yanzu ta danyi rubutu a takarda ta juya gareshi tana fadin . Zasu bani sallama yanzu sai dai idan naji wani gurin na mun ciwo in dawo su kara teareting dina. Tana bashi takardan suka fita tare yaje ya biya kudin komai ya dawo lokacin har na sauko daga daman gadon ina zaune ina jiran dawowan shi. Ya shigo ya kalleni yana fadin zaki iya tafiya ko in taimaka maki nace zan iya da sauri don kada yace zai kamani. Oya tashi muje yace yana dan ja gefe daya na mike da kyat don har lokacin ina dan jin rashin karfin jikina. Ya rigani fita daga dakin ko ya lura da tsayawan danayi ina jiran ya fara fitane don ban yarda ya sani a gaba yana kare min kallo. Har muka iso gida ba wanda yai magana a cikin mu ni kaina na hade da tagan motan cikin kasala har muka isa gidan ban dago kaina ba. Daidai shigamu gidan wayan shi yayi kara ya dauko yana fadin how far merry banji may tace dashi ba sai dai shi da ya fadi an sallamay mu ai ya dan yi shiru kafin ya miko min wayan. Ina dauka muryan merry ne tana fadin fatema yaya jikin naki rabon da inji muryan ta ko in gane ta tun zuwana gidan data dauko yi mun wullakanci nabar su na dawo gidana sai yau datake son ta tabbatar idan da gaske yake tare dani yake tace ya bani wayan. Nace mata a cikin muryan marasa lafiya naji sauki anty tace min wish you quick recovering nace thank you na mika mai wayan. Jin yana tambayan ta karfe nawa zasu iso yasa nasan merry zata bakunci London din ke nan daga America. Jin sun shagala da waya da matar shi daga inda yake tsaye ta bani baya na mike har na haura da kyat zuwa sama dakina na shiga ban tsaya ba bathroom na shiga na hada ruwa masu zafi na gasa jikina dasu na fito tare da dauro alwala na fito. Shiko yana gama wayan shi ya juyo gareni da zuman ya tambayeni abinda zanci sai yaga wayau bani gurin . Sama yabi da kallo yana mamakin lokacin dana bar gurin baiji ba dakin ya shiga ya samu ina bathroom ina wanka sai ya fito. Sallolin dake kaina na rama ina gamawa na shirya na hau gadon sai barci can cikin barci naji yana kiran sunana in tashi inci wani abu. Idona bude da kyat don har lokacin maganin bai sakeni ba nace bancin komai . Tsawa ya daka min yana fadin ki rashi nace kici wani abu kinji shagwaba da shiririta yayi maki yawa. Baki na turo ina fadin ni banjin yunwane yaya zaki tashi ko sai na saba maki rai ya ce a hasale. Jin hakan yasa na yunkura na sauko daga kwancen da nake na dago kai ina kallon shi yace a kawo maki nan ne ko zaki iya sauka kasan. Nace zanci a nan na dan kalle shi a fakaice inji abinda zaice min sai naga ya juya kawai ya fita sai gashi dauke da kwalin pizza mai zafi ya jawo table ya aje min a gabana tare da aje min ruwan sha gefe daya. Ganin na tasa kwalin gaba ina yamutse fuska ya matso ya bude min da kanshi ya gyara yace kici zai taimakawa dandanon bakin ki wanan. Ganin na fara ci ya fice daga dakin hakan ya bani daman samu ci sosai dukda ba wani ci nayi da yawa ba nasha ruwa na koma na kwanta. Wanan karon banyi barci ba saidai ina tunanen marin da yaya yai min sai gashi kuma ys koma yana jinyata da kanshi kamar bashi bane ya mareni din kan zargi. Nasan banyi gaskiya bs don na fita bada uzinin shi ba lokacin amma ai hakan bai kai har ya mareni ba tunda na fada mai gaskiyan abinda ya fitar dani daga gidan. Idan zaimun adalci abin baikai ga mari ba ai ga marin ya haifar min da kwanciya ciwo har asibiti duk da dai sanadin marin ya jawo muna dan kusanci a tsakanin mu don ban dauka yana da saukin kai irin haka ba. Kamshin da naji ne yasani dago kai shine ya shigo dakin yayi wanka ya sauya kayan jikin shi zuwa yar karamar rigan t,shirt da bakin wando sai takalma bakake a kafan shi. Kallona yake na dan dukar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannu naji yace ni zan fita zan je in dauko su merry airport. Wata kila ba zan dawo gidan nan ba sai zuwa gobe don haka ga maganin ki nan ya nuna min gefen gado. Ai masu sannu da zuwa nace dashi bai amsani ba yace good night ya fita nabishi da kallo har ya bace min. Ajiyan zuciya na sauke ina tabe baki nace ni yafi min nono fari kazo kawai ka wani tare min a gida ka hanani shakat . Ashe bai tafi ba muryan shi naji daga kofa yana fadin ki sauko kasa ki zauna ko jikin zai kara warware maki kwanciyan nan yayi yawa haka. Nan yayi mun tunda ko na fita falon ni kadai zan zauna a can yace baga tv nan ba ko ki tsaya a backkaloy kiyi kallo. Baki na dan turo alaman ya takura min fa da wani lalarashi shi can da bansan dalilin yimun ba ya juya ya fice a hasale. Na dade a zaune gurin kafin inji ina son fita falon har nakai kofa na tuna da wayata da rabona da ita tun ranan dana fita da safe mukai waya da Rita wata course mate dina tana min happy Christmas. Dan dube dube na fara yi a dakin a hankali ina neman wayan da ido banganshi ba. Nan dai na shiga bincike ban ganshi ba dan tunane na fara yi can na tuna yana cikin hand bag dina dana fita dashi ranan na duba da sauri yana ciki har battery's yayi sanyi yana batun mutuwa. Dauka nayi tare da wayan caji zuwa falo na sauko ban zauna ba saida na kunna tv na hau saman dogon kujera na kwanta ina kallo . Ba abinda akeyi sai bukin chrismati a ko wani Chanel nasu na kasan wasu film daya shafi bukin wasu kuma wai wa,azi sukeyi. Tsuki nayi na jawo wayata na kunnanan na hauyin game abina ba tare da namaida hankalina gun tv ba kuma. Sai dare jirgin su merry din ya sauka tunda suja fito take raba ido ta ganshi don a zaton ta ba zai zo tarbon su ba din kamar yadda ta bukata duk da akwai driver da zai iya kwasosu airport din a gidan.. Dan rugumay ta yayi kamar yadda al,adansu nacan yake kafin ya daga queen din shi sama yana subbatanta. Hakan ya dan sasauta ran merry din a lokacin don tsananin son da takewa mijin nata duk bacin ranta dashi da zaran suyi arba komai take ji gamay dashi zai gushe mata a rai. Bayan sun gama dan rugumay rungumay su ne suka nufi mota merry da yarta sai shagwaba suke zuba mai har suka isa gida. Sun samu masu aikin su sun gama abinci har an jera mai kasa cin abincin yayi baisan may yasa yanzu baijin dadin abincin gidan nasa ba ko kadan. Yana mamakin kanshi da yake iya bata lokacin shi gurin cin duk abinda na jagwalgwala a gidana ya zauna yaci hankali kwance. Ga wani sabon akidan dake shigo mai zuciyar shi wanda shi kadai ya sanda hakan a ranshi yanzu sai yake jin kamar yana dan kyamatar merry din a ranshi wanda bai san dalilin hakan ba a ranshi. Ya kanyi tunanen ko don irin akidojin da take tsiro mashi da sune wansa a da can baya ya hanata ta daina yanzu kuma takeyin su. Ji yayi takai mai runguma ta baya tana dan kai mashi kiss sai ya juyo da ita zuwa gaban shi ya zaunar da ita saman cinyan shi. Goran fresh milk data dauko tana dan sha a hankali ta nufi bakin shi dashi kai ya girgiza mata alaman baisha. Tace saboda may yace just kawai yana dan bubuga bayanta a hankali yana lumshe idanun shi. Tace na fahinci tun zuwan mu kamar kana da damuwa a tare dakai ya dan nisa yace haka dai kika gani banda damuwan komai a tare dani. Dan kiss takai mai ya daure yana biye mata muryan yarsuce ya dakatar dasu tana fadin daddy na kasa barci. Hannu ya mikawa yar alaman tazo gurin shi da sauri ta karaso zuwa inda suke zaune din. Nan ya mayar da hankalin shi gareta yana mata tambayoyi tana bashi amsa cikin wayau ta irin na yara. Ganin ya mayar da hankalin shi gurin yar shi merry taja tsuki tace yasan fa tazo da muradin shi a ranta kuma yana biyewa yarsu. Ya kalli lokaci dare ya soma yanzu gashi sakko zasuyi zuwa church da safe dan kallonta yayi yace zaki dai tafi don ba inda queen dina zata tafi ita . Why tace tana kallon shi da mamaki yace na fada maki tun farko ba zan barta tabi addinin ki ba kuma kin yarda da hakan may zaisa yanzu ki tsiro zuwa da ita church haka ? Mikewa tayi saman jikin shi kafin tace wanan shine ba zaiyiyu ba kasani dolene in koya ma yata addinina ala bashin idan ta girma ta zabi addinin da take so a rayuwan ta. Wanan kuma karya kika sha merry a barta idan ta girma ta zaba din mudfin ba zaki barta ta koyi addinina ba. Wasa wasa suka fara fada a tsakanin su har ya kaisu ga zagin junan su ranan dai fada sosai sukayi har yake fada mata ya gane ko yan uwan shi bata so yanzu. Don wanan yarinyar da tazo kararu da gangan ta koreta daga gidan nan don kada yarsu ta koyi wani abu a gurin ta yana sane ya kyaleta ne kawai. Itama ta mayar maida fadin ta gane manufan iyayyen shi na turo yar uwanshi gare su don a daukewa yarra hankali kan addininta ne. Don haka ba zata yarda da kowa nasa ba yanzun a rayuwanta takare da fadin to hell da addinin shi. Fadin haka ya mike ya yana kokarin daukan rigan sanyin shi ya saba ita a zaton ta daki zai shiga ta rigashi shiga ta rufo kofab da karfi. Key di motar shi ya dauka ya bar gidan bata sani ba ya fice abinshi kai tsaye gidana ya nufo bansan da shigowan shi gidan ba nayi nisa da barci na rufe ko ina na gidan. Ko ina duhu ya mamaye a gidan ya kunna wuta yana bin falon da kallo wayana yagani aje saman table sai juice din danasha na bar rabi a gurin. Kashe wutan yayi bayan ya dauki wayan ya haura sama dashi a hannun shi ya nufi dakin shi sai kuma ya yi shawaran mika min wayan . Ina kwance ina barci hankali kwance bansan wainar da ake toyabani har ya shigo ya tsaya yana kare mun kallo yadda na dunkule wurri daya da alaman sanyi ya takura min ga hannuna dana lankwashe zai iya min tsami a hakan. A hankali ya tako zuwa wurin gadon ya dan duka ya aje wayan a gefena ya kai hannun shi da niyar gyara min hannu . Cikin barci na dan gyara hannun da kaina ina fadin Amma akwai sanyi da yawa na kara dunkulewa a guri daya tare da takure kaina. Samun kanshi yayi da tausaya mun tare da tunanen ashe har yanzu ina kewan yan gida haka harda mafalkin Amma nakeyi. Dan jawo bargon yayi ya rufa min a jikina sai yaji na sauke ajiyan zuciya tare da rike bargon da hannun shi ina kara dunkule kaina a takure naci gaba da barcina hankali kwance. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:20 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL,HAMDULLILAHI RABBIL ALLAMIN, , , , , , Kamar a mafalki nake jin kamar numfashi a kusa dani yayin da na sake jina a jikin mutum kuma sannu a hankali na bude idanuna don tabbatar da yanayin da nake jin kaina a cikin wanan daren. Gabana yayi mumunan faduwa saboda tabbatar da cewa bani kadai bane kwance a wurin lokacin. Na zabura da karfi bakina na furta , innalillahi da karfi shima zabura yayi daga barcin daya fara daukan shi a dakin bayan ya gama tunane tunanen shine barci ya dan dauke shi. Yana fadin relax zarah nine na dawo kina barci don in duba jikin ki na samu kin kwanta a takure, shine na zauna dake ajiyan zuciya na dan sake a hankali ina kokarin zare jikina daga nashi. Saidai rikon da yai min ya hana in iya zarewa a lokacin gabana ya sake faduwa ina fadin may hakan ke nufi kuma a raina. Ido ya zuba min yana kallon yadda nake kokarin kwatar kaina daga jikin shi lokacin. Cikin natsuwa yace may kike yi haka kamar wata karamar yarinya dake da sauri nace zan kewayane dama a dan rude. Kina iya tashi ai yace tunda naga alaman kinji sauki yanzu da rawan jiki na tashi saboda gaba daya na tsorata da hakan . Ido ya zuba min na samu na mike da kyat zuwa ban daki na dan dauki lokaci kafin in fito a zato zai bar dakin kafin in fito daga bayin. Na bude kofan kamar mai sanda sai ganin shi nayi yayi kwance rigigine ya dora kanshi saman hannayen shi yana kallon kofan kamar mai tunane. Ba komai yake tunane ba a lokacin sai yadda yar karama dani ya tsinci kanshi da jin dadin dumin jikina don bai taba zaton zai ji wani abu daga gareni ba haka. Na dan zabura da ganin sa dakin har lokacin ya lura da hakan danayi naji yace kizo ki kwanta abinki . Kamar ban jishi ba naci gaba da tsayuwa a wurin kamar mai tunanen wani abu a raina ya sake fadin bakiji bane ina magana ? Nan ma shiru nayi mai tare da ja da baya kamar zan koma bayin naji muryan shi yana fadin idan baki zokin kwanta ba zan iya zuwa in dauke ki tsab ida baki dawo kika kwanta ba. A hankali na tako zuwa bakin gadon nakai zaune a takure ban iya juyawa na kalle shi ba don yana a yadda yake kwance har lokacin. Ki saki jikin ki don ni a matsayin yayan ki nake gare ki ko ba haka na dan gyada mai kai a hankali. Yace idan kin san hakane ina son ki fada min may ye matsalan ki ko da damuwan ki shiru nayi don ban gane inda tambayan tashi ta dosa ba lokacin. Ina tambayan ki kina shiru may yake damun rayuwan ki ne zarah ki saki ranki ki fada min ko maynene ke damun ki a kasan nan ? Na dan juyo kadan na kalleshi kafin ince ni banda damuwan komai tare dani sai dai na rashin kowa a tare dani. Yanzu ni da nake bata lokacina ina kulaki ba kowa bane a kusa dake kike nufi ko may ? Na dago ido tare da dan juyawa ina satan kallon shi a daidai lokacin da hawayen da nake dannenawa a idona suka silalo min a fuskana shar lokaci daya. Nace da zan samu kaima din ka nisanceni da zai fi min sauki zanso kaimun adalci ka barni kamar yadda kace kana bukatan in nunawa kowa a kasan nan da ba wani alaka a tsakanina dakai sai na yan uwantaka. Yace wanan kuma abinda kika san ba zai samu bane a gare mu don ke kin sani nima na sani akwai hakki mai girma da ke kawunan mu. Na tare mai numfashi da fadin amma mu kaidai muka sanda wanan zancen ai a kasan nan kaf. Yace wanan kuma abinda ya shafe mune don bai shafi kowa ba ko ince tsarinane nida zuciya kan a binda zai fisheni nan gaba. Duk da nasan kina kokari wurin bin dokan dana saka maki don nayi maki umurni kin bi abinda na sakaki bada gardama ba. Saidai a guri daya kina kokarin kin bin dokana ta hanyan yin mu,amula da wasu mutanen dabaki sani ba. Har yakai kin janyo fushin zuciyana na mareki wanda hakan har ya janyo maki kwanciya ciwo na dan lokaci . Dago kai nayi tare da dan juyowa gare shi na kalle shi hawayen idonane keta kwaranya a lokacin da kyat na iya bude baki nace . Banayi hakan bane don in bakanta maka rai yaya zaman kadaicine ya isheni har na fita don in mike kafana a can muka hadu dasu Ramla da mijin da suka kawo ni gida ranan. Amma kin san na hanaki yawan mu,amula da wa yanda ban san su ba tun farkon zuwan mu kasan nan dake . Yaya kike zaton ina mijin ki hakan ba zai ban haushi ba inga wasu sun saukeki ba tare da sanin inda kuka fito dasu ba. Na sake fadin to kayi hakkuri yaya bazan sake hakanba in Allah ya yarda yace ai zancen ya wuce a gurina tun lokacin. Yanzu ki kwanta ki ci gaba da barcin ki ni sallah zanyi yanzu yana fadin hakan naga ya mike yabar gadon a zatona dakin shi zai nufa sai naga ya doshi hanyar bayi na. Na ja a hankali nakai kwance na kwanta a takure tare da jan bargo na rufe kaina dashi ina jin ya fito gurin da nake sallah ya dosa ya tayar da sallah ina mamaki shi a raina. Kusan kwana nayi a tsorace saboda ban fahinci sauyawan da na gani a tare dashi ba har lokacin. Don a rayuwata ban taba zaton ganin sauyawa haka a gareshi ba tun ba a kai wani lokaci ba tun ina jin motsin shi yadda yake karatun sallah har yakai barci ya dauke ni ban sani ba. Ban san lokacin da ya kara kwantawa ba saidai na wayi gari na sake ganin shi a kwance gefena ya takure a guri daya . Saida na karewa yadda yake kwance kamar baison inji motsin kwanciyan shi a dakin ya kwanta lokacin a hankali na sauka daga kan gadon na nufi bandaki don dauro alwala. Sai dai ina zuwa na samu fashin sallah yazo min lokacin na dan kimtsa na fito don in dauki pad sai na ganshi a falke ya dafe kanshi kamar yana mai ciwone. Bina yayi da kallo a lokacin da yake shirin tashi zaune har na dauko pad din a boye ina kokarin komawa bandaki in gyara jikina. Naga ya mike ya fice a dakin da sauri na saka komai har rigan da buje dana saka baki don kada a gane abinda nake na koma na kwanta ke nan ya sake shigowa dakin . Ganina a kwance ya tsaya da mamaki yana kallona sai yace sallah fa ko ba zaki iya yi bane nayi na bashi amsa kai tsaye har zaiyi magana sai kuma naga ya nufi drower din gado ashe wayoyin shi ya manta a dakin ya dauka. Yana fita na sake sauke ajiyan zuciya tare da tunanen ko yaya akayi merry ta barshi ya dawo nan ban sani ba. Bansan ya akayi har barci ya dan daukeni ina rike da marana dake dan min ciwo kadan kadan lokacin don ina son gari ya kara haskawa in sauko in nemi abindana karya dashi in sha magani. Ban falka ba sai da rana yayi sosai na tashi naga gari ya dade da wayewa lokacin da sauri na mike duk da jikina baida karfi har lokacin sosai na shiga bayi na kara gyara kaina na fito zuwa kasa. Zaune na hango shi yana aiki a cikin laptop din shi yana duke jin karan bude kofana yasa ya dago kai ya dan kalleni ya mayar da kanshi ga abinda yakeyi. Kin falka ke nan ga abinci can kici kisha maganin ki ya fadi ba tare daya dago kanshi ba a daidai lokacin da nake step din karshe zan sauko. Zuwa nayi har kusa da inda yake nakai kasa ina fadin ina kwana yaya kaina a kasa do ban iya kallin shi gama ga irin yadda muka kwana gado daya tare dashi a daren jiyan duk da ba abinda yai min. Amma sai na tsunci kaina yau da jin nauyin shi haka kawai kici abinci kisha maganin ki tun maran bai matsa maki da ciwo ba. Gabana ya yanke ya fadi don jin abinda ya ambata min ina mamakin ya akayi ya sani a cikin raina. Kin zauna kina tunanen banza a nan ki dubi lokaci rana yayi sosai baki sha maganin ba yace min. Haka na mike da sanyin gwiwa jiki ba kwari na nufi table din haushi da takaici na sanin ina period daya wanda bansan yadda ya gane hakan ba. Na zauna na bude warmer din abincin mamakin inda ya samo wanan abincin nake na dan zuba kadan na zauna ina tsakura don bakina da bai mun dadi danaci abincin sosai don dadin shi yai min a baki saida ban iya ci lokacin. Ban san ya mike a inda yake ba sai gani shi nayi yana miko min magani gabana da sauri na dago kai na dan saci kallon shi. Fuskan shi a daure daure yake lokacin kamar bashi bane mukai magana a cikin dare dashi karbi kisha yace min a daidai lokacin da wayan shi ya dauki rurin kira na karba da sauri yana tsaye bai dauki wayan dake a inda ya tashi yazo bani magani. Ina sha ya juya zuwa gurin wayan da sauri ya dauka sai naga ya aje ya zauna yaci gaba da abinda yakeyi. Zama na danyi zuwa wani lokaci kafin in mike ina dauke kayan abincin daga gurin zuwa kitchen. Na dawo sai ban zauna ba kamar mai shawaran komawa daki naji yace ki samu wuri ki zauna nan kwanciya baya isan kine ke ? May zanyi to yaya na fadi a dan shagwabe ya dago kai ya dan kalleni sai ya nuna min kujeran dake gefen shi in zauna. A hankali na tako zuwa wurin kujeran na zauna shiru dani dashi ba mai magana a hankali na kai kwance ban san ya akayi ba na tsunci kaina ina karatun suratul maryam. Yana jina baice min komai ba saida na dan kage naji ya gyara min dago kai nayi ina mai kallon mamaki na jin ashe shi din mahadacin kur,ani ne sosai. Wayan ta kara daukan kara yaja tsuki yana ignoring din kiran kallon shi dayaga ina yi yasa ya mika hannu ya dauki wayan . Daga inda nake kwance ba nisa sosai dashi yana dauka ina satan kallo shi naji muryan merry kamar cikin fada take magana dashi ya tsaya yana sauraren ta kafin yace. That is my final decison merry live my daughter alone tayi addinin dana zaba mata a rayuwan mu. Naga ya danyi shiru yana sauraren abinda take fada mai ya dade a hakan baiyi magana ba naji yace good mu zuba ni dake merry zakiyi regret din wanan shawaran karshe. Ya kashe wayan ya dan juyo yana kallona nayi kamar ba saurare su nakeyi ba ina karatuna a hankali. Yaushe zaku koma school ne ya tambayeni kanshi a duke sai lokacin dan juyo ina fadin nan da two weeks in Allah ya kaimu. Banji yace komai ba haka yasa na rufe fuskana da hannayena ina tunane ji nayi shiru yace ko zakici wani abin nace na koshi. Ba tare da na dago na kalle shi ba jin muryan shi nayi yaja tsuki yana fadin zaki wahala kuwa idan kince harda abinci bazaki kula da ci ba gidan nan. Don ina auren ki bashi zaisa in maki magana kiki bin umurni ba don ba zaki mai dani dan yaro ba so kike sai ciwo ya kaiki kwance ki ba mutane wahala ko may da rashin cin abincin nan da bakiyi. Shiru nayi ina sauraren shi ba tare da na yarda nayi magana ba don yadda naga yana magana a hasale nasan komai zai iya faruwa a lokacin. Ni dai a raina Allah Allah nakeyi ya bar gidan zuwa wuri matar shi don ban son yace zai kara kwana a gidan nan sai dai banga alaman haka a gare shi ba. Lokacin sallah nayi zai mike yaje yayi dukda ba fada min yake yi banice kawai ke lura da hakan tunda ba kiran sallah akeyi ba nan. Da yamma kwatsam sai gashi ya fito a cikin shirin shi ina tsaye ina dan goge goge a falon ya kalleni yace. Ki shirya zamu gidan can mu kwana biyu tare dasu don suna gari munyi magana da merry dazun tace ki zo nan ko zaki sake jikin ki. Dago kai nayi da sauri na dan kalle shi a cikin mamaki kafi ince yaya nan ma yayi min banson zuwa gidan nan don nan yafi min can. Shiru ya na dan lokaci yana kallona kamar yana nazarina kafi;yace cikin natsu da nan da can duka gidane kin sani. Akwai abinda nake so zuwan naki can kiyi min do merry da yata ciki natsu yake min magana don i fahince shi a lokacin. Hawaye na soma fitarwa daga idona ba tare dana kalleshi ba yana tsaye shiru yana kallona. Niko nasan muddin naje can zan matukar takura ne kawai don a gaban merry ba wani abinda zai iya min. Ya marairaice murya a karon farko ga zaman mu yana min magana a tausashe yace. Kiyi hakkuri ki shirya mu tafi nasan zuwa can kina takura sai dan zan so kiyi min hakan don ni da yata. Zamuji dadin kasancewan ki tare damu a daidai wanan lokacin yin haka garemu kamar ki mutuntamu ne ai. Haka na daure ba don naso ba na shiga ba shirya duk wani abinda tafiyan nawa zai bukata a can na fito na samay shi tsaye yana jiran fitowana. Bamu tsaya jiran komai ba ya rufe komai na gidan banda frezer dake aiki muka tafi. Tafiya mai nisa mukayi saidai shi waya yake da abokin shi Nasir dana fahinci daga Nigeria ya kirashi suke magana kan filayen da aka sai mai naji yana fadin har an dora gina kamar yadda ya umarta. Har muka kusan kaiwa wayan yakeyi sai can suka katse ina mamaki a raina kamar ba kudi suke batawa ba lokacin don da Nasir din ya kirashi yace ya kashe zai kirashi shi. Mun isa gidan lokacin duhu yayi inda ys shiga get ya samu wuri yayi parking mun fito shike gaba ina binshi baya zuwa cikin gidan. Merry na zaune a falo tana waya daga ita sai wani dan rigarta iya cinya sosai ya tsaya mata. Tana ganin shi kafin in shigo gidan ta kalle shi tare da fadin where is she banace kazo nan da ita ba ? Baiyi magana ba ya wuce ta zuwa wuri yarsgi dake kwance a kass tana wasa ya daga ta ta juyo gare shi tana dariya. Niko saida na tsaya nayi adduan neman tsari da kariya ga duk wani sheri da wani abinki na shiga gidan da sallamana a bakina duk da nasan yana da wuya a amsa min a gidan. Tana ganina na shigo ta katse maganan da take mai tace tana min wani irin kallon mamakin ganin sauyawa a tare dani sosai don na kara mata girma na cika sosai a idon ta. Wanda ni kaina nasan na canza a lokacin don ban nemi komai na rasaba banda kewan ya uwana da gida da nake kwana dashi nake tashi dashi a raina kawai. Bata san lokacin da tace mamaki wai kece kika koma haka fatema kodai gizo idona keyi min. Dan murmushi na sake a fuskana ina gaida ita zan iya gane tana cikin wani yanayi na bacin rai ko tashin hankali a lokacin don yanayin ta daya nuna hakan. Dan murmushin dole ta kako tana min tace kin girma kinyi kyau sosai har kin so kifi mijina fa. Zama yayi a daidai lokacin shi ya nuna min kujera in zauna nakai zaune nan ma aikatan gidan ke fitowa daya bayan daya suna mai sannu da zuwa suna gaidani kuma da zuwa. Sun dan juye harshe suna maganan da ba jinsu nake iya yiba a lokacin don akwai dan tazara daga inda nake zaune . Kadan kada merry take satan kallona ina nuna ban san tanayi ba don baczan manta canza min da tayi ba a zuwana karshe gidan ba. Don hakane nima ban yarda na sake jiki da ita ba don na mayar da hankalina ga wayata sai shine ya dago daga tabar gazan da sukeyi a gabana yace a kawo maki abinci ne zarah ? Wanka nake son yi na bashi amsa yace zaki iya shiga dakin ki ai yana nan a gyare ba kowa a ciki sa . Mikewa nayi zuwa dakin ban ko juyo ba har na shige daidai na samu yanzu an canza komai na dakin ga baki daya haka ma komai na gidan an canza zuwa sabbi wani kallan kuma wanka na shiga na gyara jikina na fito ina zaune na gama saka kayan jikins naji an turo mi kofan dakin an shigo. Dago kai nayi ina kallom mai shigowa lokacin da merry mukayi arba tana tsaye a kofan dakin har lokacin wanan shegen rigar daine a jikinta saye. Kawar da kaina nayi daga kallon ta ina rufe man dana gama shafawa lokacin tace tana iya shigowa dakin ? Nace zaki iya kofa a bude yake har lokacin kallon mamakin sauyawana take min lokaci guda, Ta karasa shigowa ta samu wuri ta zauna a bakin gado na juyo ina fuskantan ta kafin tace dani. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:21 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI , , , , Saida ta dan kura min ido na wani lokaci nima kallin ta nayi ido cikin ido kamar yadda take kallon nawa ba tare da yau naji wani shayinta ba ko kadan atare dani. Karfin adduan mudulunci ke nan da hausawa ke fadin addua makami mumuni na gwada a gare ta. Fatema nazo wurin kine da magana don nasan zaki fahinceni fiye da maigidana ta fadi tana kalona ido cikin ido. Nan nace Allah yasa abinda zai yuyune kikazo dashi ta kara kallona karo na barkatai tace ko zaki tuna wancan karon kin tafi ba tare da sanun mu a gidan nan. Kan wani dalili da nake zaton ko kin sanshi ko baki sanda zancen ba wanda ba wani abu bane sai zance yata guda daya tilo da nake da ita. Kallon ta nake a cikin mamaki don ban san may take son fada min ba lokacin sai zuba take. Nasan da biyu kika zo kasan nan kada ki dauka ban san may ya kawo ki kasan nan ba Fatema ? Da sauri ba dago ina kallon ta cikin mamakin jin tasan zancen auren mu da yaya ashe dama nunawa ne batayi ba. Nayi kasa da kaina cikin kunya jin tasan mijin ta na aure na bata nuna min komai ba. Saida naji tace don kawai ku dauke wa yata hankali ga addinin mu aka turoki kasan nan ki zauna damu. Saidai baku san cewa mu din dagani har yata ba a London muke zaune ba don haka nazo da murya mai kaushi don baki warning kan yata. Wanan can karon kin fada mata abinda bata taba sani ba zancen ku yan uwantane kuma tana da grany da aunts da sauran su a Nigeeia. Wanda da kyat na samu ta bar zancen nan a ranta don haka nake son inyi warning din ki wanan zuwan kada ki fara ki shiga harkan yata har ki fada mata wani zance gamay daku can . A jiyan zuciya na sauke da gama adduan bakina na kalleta jin inda ta dosa na dakatar da zancen ta da fadin . Nace wait merry zancen fadin wai ya takice ko wani abu duk bai taso ba don zaki iya fadin haka a yanzu saidai nasan nan gaba fadan hakan zai maki ciwo. Don ko wani dan Adam yana daraja danginshi ne a duniya yana basu girma da sanin kimar su kada ki zalunci yarki don wani manufa naki merry bance ko anty ba wanan karon. Kallona take da mamaki nace yes idan Amina bata nemay muba a yanzu nan gaba zata iya neman mu dole ne wanan sai ya faru. A yanzu zanyi kamar yadda kike so merry don ni ba wanan ne ya kawoni gidan nan ba nazo nan bisa tursasawan dan uwanane kawai. Yar kice Amina saidai ki sani nan gaba ba da yarki kawai yaya zaiyi alfahari ba don zai iya haihuwan wasu da wata mace yan uwa da dangi kaf su sosu a bar taki a gefe yadda kike so. Shin idan anyiwa yarki hakan zakiji dadi a rayuwan ki kuwa naji daga yau na daina kulaki har yarki. Saidai ki sani gida daine gidan dan uwanane ina da right din shigowa kamar yadda kema yan uwan ki suke zuwa duk lokacin da suka ga dama. Maimakon inga bacin rai ga merry dake min wani irin kallon mamakin yadda na tsaya ina fada mata magana haka sai naga murmushi a fuskanta. Tace kinyi kokari wurin fada min wanan magana saidai zan so ku san cewa dani da yata yanzu keda iko da komai a gidan nan na Omar. Don nice matar gidan queen kuma diyar mu ce kowa a kasan nan ya san da hakan so banga wani dalili da Omar daku yan uwanshi kuke kokarin sakamu gaba hakan nan ba ? Dan murmushin karfin hali na sake don maganan ta ya razana nani sosai jin abinda tace dani yanzu saidai ban nuna mata razana na ba kadan lokaci. Komai zaki iya fada a nan merry saidai kada ki manta kin aure hausa man wanda keda addini daban da al,addu daban da naki ki rubuta ki aje komai zai yi faruwa daga baya wanan haka yake. Wani kallo tayi min tare da tafa hannayen ta tace yarinya kinyi kokari kin nuna min aikin ki yana tafiya daidai a yadda wanda ya turo ki ya koya maki karfin halin jajircewa don yanzu idanun ki sun nuna a bude suke sosai. Dama nasan da zaman ki a cikin dangin Omar kina daya daga cikin masu kyamata na tun farko saidai darajan mahaifiyar ki da kimar ta ba zai bari in dauki wani mugun mataki a kanki ba don ni mutum ne da bana mance halarci a rayuwata. Nace realy ta gyada kai alaman kwarai kuwa don steps mother tayi min abinda ba zan taba mantawa ba a rayuwata danaje gidan ku. Kin san da hakan kike kirarin cewa wani aiki aka turoni yi a kanki da yarki in ma wanan kike tunane ki cire a ranki don ba wanda zai tsaya yana wahal da kanshi kan mijin ki ko yar ku don ba shi kadai iyayyen mu suka haifa ba. Kin san mu musulmai wanan ne fa,idan yin aure gare mu fiye da mata daya da kuma yara da yawa don idan wata ko wani ya kika ba zaka rasa wanda zai soka ba. Don haka cewa Umar nakine keda yar ki ina son ki gane cewa kin makaro ga hakan don dai shi din musulmi ne mai alfahari da addinin shi. Kofan a bankado da karfi ya Umar din ne a tsaye yana muna kallon tuhuma dukkan mu gaba daya wurin. Merry may hakan ke nufi ne ya tambaya lokacin da yake karasowa tsakiyan dakin da tarin tambaya da fargaban abinda muke tsutaunawa a tsakanin mu. Don yanayin kowan mu ya nuna ba maganan arziki mukeyi tsakanin muba a lokacin yadda yanayin fuskan kowan mu yake hade. Sake tambayan ta yayi may ya kawo ki wurin ta yanzu bayan ki san ba lafiya ke gare ta ba kece kika matsa tazo nan ko zata samu karfin jikin ta. Wani kallo ta watso min don amsan da bata samu bani ba ya shigo yana cin zuciyar ta. Banga alaman mara lafiya da kake fadi ba a nan don wanan yariyar alama ya nuna min garau take ba abindake damun ta. Yayi mata wani kallo shekeke yace zaki iya fadan hakan don ciwo ba a jikin ki yake ke da yarki ba ko ? Tayi mai wani kallon wullakacin ba tare da yin magana ba ta fice daga dakin tana fita ya juyo yana min kallon tuhuma ? Na kawar da kaina daga kallon shi da sauri yace may kika fada mata yanzu na juyo ina kallon shi nace amsan abinda ta fada min kawai. Kamar zai sake magana sai kuma naga yaja ya fita dakin da sauri ya banko min kofana kafada na daga irin mai nuna ko a jikina. Dakin barcin su ya nufa a nan ya samu merry tana zariyo a tsakar dakin tana ganin shi ya shigo ta tare shi da fadin sister din ka ta fada min magana masu zafi Omar. Yace kamar yadda kema kika je kika fada mata ko wanan ne dalilin da yasa kika yaydareni akan a kawo ta nan zaki kula da ita ? Kashedi nayi mata a kan diyata dani sai na fahinci yanzu yarinyar ta wuce yadda nake tsamanin ta. Don ta fada min abubuwan da tun farko hankalina ya kawo a kanka rashin wayau ya hanani gane hakan da wuri. May ta fada maki ya tsure ta da ido yana tambayan ta kasa bashi amsa tayi sai hannayen ta data dunkule tana dukan juna dasu da gani dai tana cikin wani irin yanayi lokacin na bacin rai. Ya gaji da tsayi don jin bai samu amsan tambaya shi ba gun ko wacen mu ya nufi gadon kwanan su zai zauna tace. Omar muna nan akan alkawarin mu dakai ko ka canza ra,ayin ka garemu yanzu yayi murmushi may kama da yake yana kallon ta yakai zaune yana fadin wani alkawari nayi maki ada da kike tunanen zan canza yanzu. Dole in tambaye ka don abubuwan da nake gani dama wanda yar uwanka ta fadamin yanzu sun sa na shiga halin tunane ? May ta fada maki gamay dani wanda har yasa kike ganina mai karya alkawari gareki ? Kallon shi tayi tai murmushi ta karaso bakin gadon ta zauna ita ma shiru sukayi na dan lokaci yayin da shi yaya yake jiran amsa a gareta na abindana fada mata din. Don a tunanen shi na fada mata abindake tsakanin mu dashi na aure hankalin shi inyai dubu ya tashi maimakon ta bashi amsa sai ma yaji ta buge ga waya da abokanta na nan da zasu zo su fita. Ganin ta kyale shi ga dare yayi lokacin ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakin kamar ya sani ya fito a daidai lokacin da nima na fito rataye da jakkan dana zo dashi da zuman barin gidan. Ke yace a cikin wani irin tsawa daya daka min yana fadin ina zaki yanzu ciki wannan daren haka ? Kina da hankali kuwa waima ko ke kinsan darajan kanki kuwa zarah da bin dare a kasan nan bai zama maki komai ba? Hawaye suka soma zuba min a idanuwana shifa ya daukoni ina gidana zaune cikin rufin asirina zuwa gidan matan shi. Tazo tana fada min maganan banza akan abinda baishafe niba yanzu kuma har yana kirana da ban san darajan kaina ba. Ganin irin hawayen da nake daga inda naja na tsaya yanayin fuskan shi ya dan sauya kadan ya tako zuwa gareni yana fadin . Kiyi hakkuri ke kika daukan min alkawarin zaki taimaka min kan yata sanin haka da merry tayi zuwan ki na iya jan ra,ayin yarta zuwa gare ki yasa tayi wanan zaman dake. Kada kice zaki fushi ki kara barin gidan nan don shine burinta taga kowa nawa bai mamay mu ba da zakibi daren nan yanzu baki tsoron wani abu yaje can ya samay ki a hanya kasan nan fa ba kamar tamu bane Nigeria. Yaya haka ya isheni na fadi a cikin kuka tun yanzu matar ka bata san alakan dake tsakanin mu ba tana nuna min hakan ina ga ranan da tasan cewa ni matar kace ta sunna ? Idan ta sani saimay zara iyaka dai rabuwa zamuyi idan bata iya zama dani dake don ke ba saki a tsakanin mu har abada. Ka daina fadin haka yaya kada ma kasa zama da kaida nakeyi na har abadane tsakanin mu ko ka manta da abinda ke jiran mu a gidane bayan wanan ? May ke jiran mu a gida zarah nace cikin kallon shi da mamaki yaya har ka manta da hjyn ku tana kalubulantar auren mu ne. Dan murmushi yayi yana fadin wanan ba matsalan ki bane tsakanina da mahaifiyatace zarah don haka bai shafeki ba yana matsowa inda nake yake magana. Yace ki duba yadda kike shirin fita a gidan nan wai mako kinsan darajan auren dake a kanki kuwa zarah ? Kina da darajan da babu wani mahalukin da zai ganki a haka bai kara kallon ki ba kallon kaina nayi don sai a lokacin naga yadda nake shirin fita daga gidan dagani sai dan riga irin tasu dake saye a jikina lokacin. Kunya da nauyin hakan ya kamani koshi da yake kare mun kallo haka a lokacin jin motsin merry data fito ta tsaya tana kallon mu bai hana shi riko hannuna ba ya rungumay ni a jikin shi yana dan bubuga min baya alaman rarashi. Jin nayi shiru yasa ya ja hannuna zuwa dakina sai da ya kara ban magana ya fita daga dakin sai bayan fitan shi daga dakin na sauke ajiyan mikewa nayi zuwa kofa na rufe da key na dawo saman gado har lokacub ba komai a cikina da naci tun karyawan safe daya tursasani nayi a gaban shi. Wani tunane yazo min nayi zubur na mike zauna daga kwanciyan ruf da ciki danayi da farko. Na fahinci akwai rikici a tsakanin yaya da matar shi a wanan yan watannin da suka shude duk dai a kan rikicin yarsu ce hakan ke faruwa tsakanin su. Daman kine wanan sayadi damaki ne hakan a ruwa muryan mamu da Amma ne ya ziyarci zuciyana lokaci guda. Ba sai mun koya maki yadda zaki samu kan mijin ki ba kije ilimin ki da kika samu ya fitar dake a matsayin ki na diya mace. Abinda zan kara maki shine juriya da hakkuri da al,amarin rayuwa sayadi sai ladabi da biyayya da zaki kara dashi mamu ke fadin haka lokacinda Addah ta kaini gurinta muyi ban kwana. A ruwa ke mace ce don haka ba sai na koyar dake komai saidai zan kara da hakkuri da kwantar da kai ta haka ake cin ma manufa a saukake A ruwa. Nasan zaki iya kawun ki baima saudauki zaben banza ba don kece kika dace da daidai da rayuwan shi ki kula da addinin ki a duk inda kika riski kanki addua ko takobin mumune Aruwa a kula da yawaita yin addua ko yaushe. Amma ce take fada min hakan wani dare saura kwanaki bukin mu na dawo daga misau ina korafi gareta na banyin aure mai mata kafira. Yo itama kafira ina tasan kissa irin namu na nan a ruwa ko zama gidan nan kadai ya isheki koyon duniya abinida iyayyenku keyi a gidan nan. To ta ina zan fara wai idan ma har na saki jiku dashi na dan lokacine wanan kulawan dayake bani don kawai sun samu matsala da matar shine har nake samun sakin fuska gurin shi kwana biyun nan. Ranan da suka daidaita fa tsakanin su suka koma shiri da ita idan na sake jiki har sabo ya shiga tsakanin kwana biyu kaina abin zai koma tunda ba sona yake ba yadda yake fadi kuma ya nuna. Ke nan nice da mahaifiya ta za a cuta a karshe tunda nice zan yi hasaran kimata da martabata na mace . Ni da wanan zaman ai garama ina gidan mu gaban iyayyena yafi min zama mai kamar ukuba dashi. Kaina gyada ina fadi a fili anya nayiwa kawu adalci idan naki dan shi da yake sa ran gyarauwan komai a dalilina. Ya zama dole dai in bi shawaran mutane in fara wani abu nima a bangarena kodon wanan bakar arniyar mai zagin iyayyen mu a gaba don na kula taki jinin kawuna don dashi take adawan ta. Ranan dai barci rabi da rabi nayi shi gidan wasu na fatan suje kasan waje suji dadin rayuwan su ni kuma da na samu zuwa ga irin ukuban zuciyar da nake ciki tun zuwana. Washe gari kodana tashi na gama yanke shawara a raina wanka nayi tsab na shirya cikin green din kaya duk da ba kala na bane kayan dai sun karbi jikina sosai nayi rolling din kaina na tsaya gaban mirrow ina karewa kaina kallo. Ban fito ba saida na kara shafe jikina da oud dina masu kamshi sosai tun tun karowana falon kamshi turaren jikina ya daki hancin su. Dago kai sukayi suna kallona direct wurin table din abincin na nufa kai tsaye fuskana a washe kamar ba wani abindaya faru daren jiya din. Shina fara gaidawa kafin in juyo ina kokarin zuwa wurin yar su nace anty merry good morning ina zaton ba zata amsa min ba sai naji ta amsa min gyatsire da morning dear taci gaba da cin abincin ta. Dan rugumar yarinyar nayi nakai mata kiss a goshin ta tare da fadan morning my dear ta tabure fuska can ta dago tana fadin . Ina kikaje bana ganin ki ina tambayan Mumm tace kin koma garin ku da zama dan kallon uwar yayi ya kawar da kai nace da yarinyar ina zama yanzu ai gani na dawo gare ku kuma. Tace idan zaki garin ku zakije dani ta fada a marairaice nace why not idan kina son zuwa. Ina kallon yadda merry fuska ba annuru ko kadan yarinyar zata kara magana ta dakatar da ita ta hanyar fadin will you kep quaint dear ? Da sauri ta mike ta fada jikin uban tana fadin daddy mumm tana min shauting ba dalili. Dan rugumay yarinyar yayi yana shafa bayanta a hankali ta lafe saman jikin shi abincin da baici gaba da ciba ke nan ya barshi. Ni dai na gama na mike na koma saman kujaran falon na zauna ina karatu a cikin wayana sam na manta da wani zancen new year sai lokacin da naga merry ta fito cikin shiga ta alfarma tana fadin zasu church wurin addua,a ita da yarta yarinyar tana bata fuska rai bace. Daga sama uban ke jefo masu baki akan idan yarinyar bata zuwa ta barta a gida ta gallamai wani harara ta fisgi hannun yar nata. Kamar zata wuce bata sallamay ni ba komai ta gani tace sister inlaw zamu tafi sai sun dawo nayi mata tare da fadin queen tayi min addu,a idan sunje kila kalami na yaiwa merry dadine tace zasuyi suka fice. Da farko ganin da nakewa yaya haka sai nake daukan shi miskili mai ji dakai kamar yafi kowa marason magana ko wani lokaci a cikin daure fuskan shi yake. Sai dan zama na dasu London din nan nake fahintar koshi waye sannu a hankali don na fahinci baison ganin mutum a cikin damuwa ko kadan bai kula da mutane amma idon shi na akan duk wani na tare dashi. Gashi dai yan kwanakin nan yana nuna min kulawan shi amma ni sai kama jikina nake dashi ban sake mai don kada in wuce iyakata a ranshi. Ina kwance a dakin nayi karatun Allah nayi na boko na gaji nayi barci sai da azahar na mike don inyi sallah bayan na idar na zauna bakin gado ina game a wayana don haka hankalina ya dauke banji shigowan shi dakin ba. Muryan shi naji a kaina yana fadin waike baki gajiya da game a wayane haka ko rashin nayine wanan duk. Ki tashi mu fita zuwa cikin gari tunda ke zama wuri daya yana damun ki nasan nan din ma a takure kike yanzu. Dago kainayi jin yakai aya nace barni na koma da sunana na fatimana gida kada matar ka ta kara zargina kan wani abin tunda bata san koni din wacecen kaba har yanzu. Maimako maganata ya bata mai rai sai naga ya dan kara matsowa har inda nake yana fadin kina tunanen ina tsoron fada matane ko may ? Sai da yayi min wani lalatacen kallo kafin yace ni ba irin mazan nan bane masu tsoron matan su har in tunanen ki yana baki don kada ran merry ya baci ne nake maki hakan. Ciki ciki nace ga abu a baiyane kuwa zaka wani noke yanzu don kaga bata gidan ai kayi dadin, , , Tsawa ya daka min tare da fadin ke kada ki bata min rai don kinga ina kokarin tsare hakkin ki dake kaina. Na dan fadi a fili ina gusawa daga inda nake zaune nace aini bance sai an sauke min wani hakki ba can a barni inyi rayuwata ni kadai mana agani. Zarah ashe rashin kunyan da ake fada naki har ya kawo kaina har kin kai ki kali idona kina fada min magana kai tsaye. Kina nufin dan ance kina matata zaki fada min magana irin haka ki kama kanki yarinyar hakan ba yana nufin wai harki rainani bane don kina kurin ina mijin ki. Duk da jan idon da yake min da nuna min bacin ranshi a fili hakan baisa na rufe bakina ba lokacin sai cewa nayi aini ba matarka bace zaman kanwar kace nakeyi ko dako gida muka koma . Juyawa yayi zai fita daga dakin bayan hararan daya watsamin din sai kuma ya sake juyowa ya kalleni cikin na tsuwa yana fadin. Da na dauka kina da wayau da zaki gane abinda nake nufi da yin haka gareki na dauka ko ban fada bake hakan ba zai damay ki ba. Sai gashi ashe har yanzu wayau naki baikai ki gano hakan ba ba laifi nasan kina mutuntani a wani bangare sai dai kada zancen ki da merry yasa kice zaki rainani yanzu. Na dukar da kaina kasa cikin karamar murya nace ni zancen merry bai shafe ba gareni ta fada min na fada mata don ba zata zagan min iyayyena ko yan uwa in kyaleta ba ko addinina. Yace koma dai may ye ki sani aurena dake ba,ayishi akan so ko wani kauna ba anyi shi ne kawai bisa kaddaran rabon sai anyi don haka yadda kike jin ko maynene a ranki hakan kowama ke jinsa. Don haka ki ban lokaci har in gama tsare tsarena kafin in waiwayo ki mu san mafita yana fadan haka ya juya ya fita baiko sake kallona ba. Yana fita na fashe da wani irin kuka mai cin rai tare da kunan zuciya lokaci guda ke nan nazama matar kushe wace aka auro ta a bisa wani kaddaran. Zuciya mai nashe nashe har ta fara naso min irin rashin mutuncin da zan kula mai idan mun koma gida yayin da wani bangare na zuciyana ke fada min in fito fili in fada matarshi gaskiyan koni wacece a wurin shi. Tunda ya fita ba wanda ya kara leko dakin gama tun zuwana banga Greco a gidan ba ba hurmina bane don haka ban tambaya ba. Ina idar da sallah magariba cikin ikon Allah sai ga wayana yayi kara na dago daga inda nake ina duba mai kiran wayan nawa. Mamu nagani rubuce na dauka da sauri da sallama a cikin dakusashen muryata dana ci kuka dashi yau. Shiru tayi ba tare da ta amsa min sallaman ba sai na fara sheshekan kuka muryan ta naji tana fadin sayadi kina son in daina kiran layin ki ke nan ko ? Na daina mamu nace da sauri don jin abinda ta fada nasan kuma zata iya din ba iya fadi a baki tayi ba. Ko mainene hakkuri da mika kai ga Allah shine maganin sa ai sayadi ba wai kukane mafita ba gare ki harki jawa kanki wani ciwo can. Sayadi ina son ki sani daka cuci abokin zama gara ka barshi shi ya cuce ka kina dai gani na a nan bana yarda in wullakanta aurena sayadi. Idan namiji ya cuceka ke mace ki daure ki zuba mai idanu saboda watarana ko ance yai hakan gareka ba zaiyi ba ai, kuka na somayi sosai don zanyi magana ta hanani. Amma duk da hankan sai dana samu na furta abindake cin raina nace mamu yau yaya fa cewa yayi auren mu nidashi ba aurene naso da kauna ba. Aurene da akayi shi bisa wani kaddara wanda sai dai mu barwa Allah lamarin sa abin mamaki amsar da mamu tabani a likacin shi yaba mamaki matuka don cewa mamu tayi ai ya fadi gaskiya sayadi. Ehma ko ba auren kaddara din kukayi ba keda shi fada min dole sai kowan ku ya yaki zuciyar shi dama ai a zauna lafiya muddin kina son kici riban auren ki. Ko ni da kawun ki an fada maki munyi wani soyayyane kafin auren mu da fada min da saka rana duk baifi kwana biyu ba tsakani. Yanzu fa sayadi wa zai gane hakan akayi sai wanda yasan tushen labarin zai sani. Shi hakkuri ai baibar komai ba da wansn wautan taki da kikeyi garama da Allah yasa ba a gida daya ya barki da kishiyar taki ba don da zuwa yanzu ta gane halikin na rashin hakkuri ta dan kara min nasiha akan in daure in kara hakkuri dai ta kashe wayata ta barni da tarin bakin cikina. Ke nan kowa laifina yake gani akan auren nan shi basu ganin nasa ko kadan har zai fada min hakan mamu tace wai banda hakkuri ko din mahaifina baya rayene yasa kowa baisona a duniyan nan. Barci na samu ya daukeni a hakan bayan naci kukana na gaji can cikin dare ina barci na dinga jin kamar hayaniya a gidan tun ban falko ba hardai na bude idona tar jin hayaniyar yayi yawa yasa na sauko daga saman gadon ina saurare. Muryan yaya nake ji sama sama hakan yasani komawa na kwanta don bai wuce wani abin ne tsakanin shi shida matarshi kuma. Hayaniyan sai dada karuwa yake inda nake jin muryan wasu mutane na daban yana tashi. Kamar in fita gashi barci yaki daukana kuma naga idan na fita na kula dasu kenan don ance tankawama yabawane. Nan kuma wata zuciya ta tuna min da gargadin mamu na kada in sake in bari a gane ina kishi ko wani abu tambayan kaina nayi ni yanzu yayi to fita kawai zakiyi zuciyata ta bani amsa. Gabanane ya fadin ganin harda yan sanda a gidan a hankali na taka zuwa inda dandazon taron yake ina sauraren bayanin dan sandan. Daga inda nake na fahinci merry ce sukayi accident da suka fita ashe bayan zuwan su church da aka taso suka wuce yawon su na bukin new year. A can ne suka hadu da wanan kadaran don tana a cikin maye wai ashe tun fitan shi daga dakina ake wanan rikicin ban sani ba yanzu ma yansanda sunzo tafiya da itane bayan ta gudu daga asibiti inda aka kwantar dasu din. Ga bayanin dansanda dayayi karshe na gane har yarsu queen tana asibiti kwance wanan lokacin. Ga uwar ta gudu ta dawo gida tabar yar can asibiti shine mijin ya kira yan sanda suzo hargida don ba zai yarda yarshi ta salwanta ba yace. Kai wai wanan wani irin aure mutanen nan keyi na tambayi zuciyana hakan ina karewa yadda merry din ke fama. Daga inda yake ya watso min wani irin kallo mai kama da harara har na dauke kaina daga kallon shi sai can na tuna a yanayin dana fito falon sake dan kallo shi nayi har lokacin yana watsa min harara hakan yasa na juya da sauri zuwa dakina na sako hijjab dina. Sai dan ban sake fitowa ba ban kuma san yadda suka karkare ba a can don ban kara jin duriyan su ba kuma a gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:21 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAMANIN RAHIM ALHAMDU,LILLAHI RABIL ALAMIN, , , , , , Nikan dai ranan naga abin mamaki a gidan cike da tunane da fargaban merry na kwana a rayuwata da safe dai fashin sallah nakeyi don haka na tsabtace jikina tare da shirya har tsoron fitowa waje nake daga dakina a yadda nake tsoron dan giya a rayuwata yadda muke kyamatan su nan gida Nigeria. Kwance nake na lafe saman gado ina rub da ciki naji shigowan yaya dakin ban juyo na fuskance shi ba ya kuma san ba barci nake ba a lokacin. Ki tashi muje asibiti mu duba queen sai lokacin na dan juyo na fuskance shi kindai ji abindaya faru dasu don itama merry din tana asibitin sun mayar da ita saboda ta bugu a hannun ta sosai. Har lokacin banyi magana ba shi kuma yana tsaye tsakiyan dakin saida yaga na yunkura zan tashi yabar dakin da sauri nikan kayana gaba daya na hada don a ranan nake son komawa gidana ba zan yarda yar giya ta illantani ga banza ba don harga Allah tsoron merry ya kamani har cikin raina. Ina gama hada komai nawa na fito na samu baya falon dan zaman jiran shi nayi na dan lokaci sai gashi ya fito da alama wanka yayi ya sauya kayan jikin shi sai kamshin da yakeyi lokacin. Ban tsaya jiran yace wani abuba na mike da sauri ya dan kalleni don ganin jakkar kayana dana dauko lokacin. Bai min magana ba illa kitchen danaga ya nufa wurin masu aiki duk na kagu ya fito mu tafi lokacin. Sai gashi ya fito masu aiki na biye dashi da abinci a zato asibitin za aikai abincin sai naga sun nufi dining da abincin. Sai da suka gama jerawa ya nufi wurin ya zauna ya juyo yana kallona tare da fadin ba zaki zauna kici abinci ba. Nace na koshi wani tsareni yayi da idanun shi saida tsorata dashi a hankali na tako zuwa dining din dake da dan tazara daga inda nake tsaye kamar ina jiran umurni. Ina karaso naja kujera zan zauna naji yace may kikaci jiya da dare bayan kina daki kina fushin banza da mutane. Dan kunkuni nayi ban fitar da maganan a fili ba yana kallona na dibi abincin maimakon in zauna sai na daga zan bar wurin. Maza ki zauna nan kici yace kamar ya samu yarshi dama kuma ai yar tashi nake don da uwata suka taso dashima mace ce da yanzu kila yana da sa,ata. Sannu a hankali nake kai abincin bakina duk a kyamace don sai ban yarda da yan aikin ba ga baki dayan su. Zakici abincin ko sai raki ya baci yanzu naji muryan shi yana fada min nayi firgigit na tsakuro abincin zuwa bakina yaci gaba da fadin. Ba zai yuyu kina zama da yunwa ba wani abu yaje can ya samay ki ace gidana akwai yunwa ki bata min suna ga banza. Nace bashi nazo yi bani ga dai may shirin bata ma suna nan tana abinda taga dama har dasu shan giya da auren ka. A natse naga yayi murmushi maimakon yai fushi kan maganan dana fada mai mai zafi sai naji yace ai ba gidan ki bane gidanane kuma matatace a haka nake son zama da abina. Nace da wani yace maka shi matarkace kaje kaita zama da ita ko da zindir zatayi yawo mana. Ban iya fadi kalaman sosai a fili ba sai na dadi ciki ciki ina murguda baki banyi aune ba sai ganin shi nayi gabana ya cafki bakina dana murguda mai yana fadin mara kunyar banza wace bata san rarashi ba . Wai may yasa ku mata baku san ya kamata ba sai anyi tsiya daku ko wani lokaci wai harda ke wanan karamar yarinyar kin iya takon tsiya wa maza ko ? Dan ja nayi baya ina fadin nika sake min bakina mutum da baki shi a hana shi magana na fada ina kwace kaina daga rike baki dayayi min. Yana sake min yayi gaba tare da fadin in kingama ki samay ni waje ban tsayaba na mike tare da mara mai baya kusan a tare muka fita daga gidan dashi. Motar ya bude min na shiga da kayana sai lokacin yake fadin wanan kayan fa ina zaki dasu haka banji komai a rainaba nace gida zan koma yau ni. Wanan ba gida bane shi ko wani ya takurawa rayuwan kine a nan sallon kiji dadin fita yawo kice zaman kadaici ya isheki a can ko ? Ni dai gida zan koma daga asibitin na kara bashi amsa baiyi magana ba ya zagaya ya shiga motar muka dauki hanyar asibiti kai tsaye. Asibitin babba ne sosao mai benaye da abin hawa saida muka shiga lifter ya kaimu sama dakin yar shi muka fara zuwa tana kwance an daure mata kafa har cinya da plaster hakama hannun wata na barin hagu da kafan shima a daure yake an rataye kafan a jikin wani karfe kafan yana lilo. Sannu mukai mata mun samay ta tare da wata dadtijuwar mace matar tana saye da wando da rigan t,shirt kanta babu gashi ko kadan an aske ga makeup tasha a fuskan ta bakar fatace matar wuluk da ita. Bayan mun kare gaida yarinyar na dan rike mata hannun dayan dake da lafiya ta sake tiedy din dake rike a hannun ta ta rike hannun nawa. Matar ce ta tambaya wanan ce kanwar taka dake karatu a nan a cikin daure fuska naji ya bata amsa da eh itace. Wani kallo tayi man kamar wace taga abokin gaban ta saita kawar da kai daga kallona da tayi bani kadai naga wanan kallon ba har shi yaga irin kallon da taimun da idon shi. Oya les pray yace wa yarinyar tare da juyowa gareni yana fadin ki muna addu,a ban samu bashi amsa ba naji yana cewa yar komai taji ya fada itama ta amsa da Amin tace Ameen yace No say Amin Ya juyo ya dan kalleni sai na daburce na rasa abinda zan karanta a lokacin fatiha na fara jerowa kafin in dora da adduan . Sai cewa suke Amin yana hadawa da ya Allah jin yadda yake kiran Allah yasa hankalin dattijuwar matan ya tashi gaba daya har ta kasa boye yananin ta a dakin. Mun gama ya dan zauna yana hira da yar shi ina gefe daya a takure ina kallon su sai matar ta fita ya juyo yana fadin bayan fitanta wanan itace uwar merry. Da mamaki nace wanan din subbahanallahi ke may ye haka yace mun nayi saurin dukar da kai ina ci gaba da mamakin abindana gani. Watau ita merry daga gurin uwarta ta gaji katon kafircinta don da ganin matar katuntumar kafira ce gata ta tsufa amma bata bar kwalliyan iya shege ba nace. Ga abin bada labari ina gani a gidan yaya sai dai babu wanda zan ba labarin sai ni kadai zance ke cina a zuciya. A raina nace wanan da kawu zai ganta a haka nasa babu abinda zai hana shi daukan mataki a kan umar din. Don wanan hada zuri,a dasu ai banar sunane sai natuna da addu,a da sauri nace idan suna da rabon shiryuwa Allah ya shiryesu. Na dago kai naga yadda yakai kwance saman gadon suna duban waya da yarshi cikin kwanciyar hankali abinsu dan tsuki naja da bansan lokacin daya fito min fili ba. May ya faru kuma ya dago yana tambayana na girgiza kai kawai tare da dukar da kaina daga kallon su sai daya dan kara bata lokaci dakin kafin ya mike yana fadin ki kula da kanki ki dinga fadin Allah Allah dana fada maki ta gada kai. Yace bakicewa anty bye bata dan dago min hannu alaman bye take min na karasa wurin ta nace Allah ya bata lafiya. A zatona ba asibiti daya suke da uwarta ba sai na dauka tafiya zamuyi lokacin sai naga ya nufi hanyar wani ward na daban sai da muka kai kofan dakin na fahinci inda muke. A nan gurin da ita da mahaifin merry din ne da gani rayukan su a bace yake jin budan kofan mu ya dawo da hankalin su ga kofan suna kallon mai shigowa dakin. Uban yana ganin mu ya wani hade rai lokaci guda yana hadiyan malolon bakin ciki tare da kawar da kanshi gare mu. Shikan yaya ya fahinci may sukeyi ni daice ban fahincesu ba lokacin sai ma kokatin gaidasu danayi lokaci guda. Na juya wurin merry ina mata yaya jikin ta wani ya mutse fuska kafin ta ban amsa na samu wuri gefe na tsaya abina ina kallon su. Umar ya karasa bakin gadon ya tambayan yadda jikin nata yake yanzu ta amsa mai a gyatsire wai ita ranta ya baci da zancen da uwar tazo masu dashi. Look Omar na fadama ban son wanan akidan addinin ka da kake koyawa Faith rikici sukayi sosai a wurin zaman iyayyen nata a gurin bai hanashi fada mata bakaken maganganu ba har mahaifin yaso yasa baki ta daga mai hannu tace ba maganan shi bane wanan. Bayan ya gama fada mata zataga matakin da zai dauka kan abubuwan da take mai tace she will see nothing in her life dama ku musulmai haka kuke da baki ai. Nikan ganin sun kaure da fada na bar dakin zuwa waje inda naga kujeru na zauna ina dakon fitowan shi daga dakin . Ya fito raibace ya dan kalleni yace mu tafi da sauri na mike muka bar asibitin ya fisgi motar shi bamu bar asibitin da wasu yan mintina ba sai ga abokin shi ya kirashi Deved yana mai korafin merry ta kira shi rai bace tana kuka sun samu sabani Farget about that Lady Deved ya bashi amsa ya kashe wayan shi. Maimakon inga ya dauki hanyar da mukazo sai naga sabanin hakan wani hanya muka bi nidai ido na zuba mai kawai. Mun danyi nisa ya juyo yana fadin may kike saukewa ajiyan zuciya tun dazun ? Ban taba tunanen akwai irin wanan rayuwan haka ba a duniya kuma ga bakar fata wai irin mu gaskiya ni ha zan sake zuwa wani guri ba daga yau. Ya juyo a fusace yace kina nufin niba musulmi bane ko may ko ban san abinda nakeyi ba kike daukana. Ki tuna fa a guri daya aka bamu tarbiya dani dake karki tsamani ko ki daukeni wani jahili Qur,ani da hadisi babu ayan da bazan kawo maki ban fasara shi ba da kai. Rasa kalman da zan fada mai nayi don ya fahinci inda maganata tadosa akan fadan su da merry ne da iyayyen merry din. Ba wanda ya kara magana a motar har ya shiga wani unguwa daban taba sani bama ni a gaban wani gida ya Parker motar shi. Banda niyar fita don ban san inda kuma ya kawo ni ba again fita yayi daga motan ya zagayo ya bude min gefena kallon shi na yi yayi tsaye kimkam ba tare da yayimin magana ba. Ganin ba zan fito ba ya daka min wani uban tsawa dole na sauko daga motar da sauri na. Fara tafiya yayi ya barni a baya ina karewa ginan kallo a raina nace nan kuma ko inane oho ? Bell ya danna dan jimawa kadan sai ga wani bakin mutum ya bude kofan yace a cikin fara,a kace yau nayi babban bako a gudan kenan cikin harshen hausa. Sai daga baya ya kula dani tafe yace kai mutumina kace da bakuwa kake tafe mana ka barni ina zuba surutu haka ? Madam tana ciki ya tambayi mutumin yace tana nan kasan ai hutu ake yanzu ko ina fara gaida mutumin nayi bayan na karaso gaf dasu. A cikin hausa ya amsa min yana amsa ya juya zuwa ciki yana kiran Halima halima fito ga bakuwa munyi. Daga ciki ina jin muryanta tana fadin bakuwa daga ina babban Nasma ? Fito ki ganta yar uwam mu ce bahausa itama matar na fitowa taja tayi turus tana fadin ikon Allah a cikin fara,a wanan bakuwan kan ta gidace daga ganin shigarta ya banbanta dana yan kasan nan. Sannu ki da zuwa tace min na amsa mata cikin fara,a kamar yadda tayi min fara,a itama. Ki zauna ga wuri sannun ku da zuwa tana ta jin dadin zuwan mu gidan nasu sai na samu kaina nima da jin dadi a raina sosai ba kamar yadda naji a gidan merry ba. Sai gasu sun shigo falon shida maigidan matar ta kawo muna abinsha da ci ta aje a gaban mu aka kara sabon gaisuwa tsakani mu dasu . Mijin ne ya kalli matar tashi yace ai sai ku shiga ciki kuyi halin ku na mata ko da kuka saba idan an hadu. Tana dariya ta jani tana fadin taso kanwata mu basu guri sun kore mu da wayau ne kawai dai. Wani dan karamin falo na kara gani ta nuna min kujera tace in zauna a kawo maki abinsha ne naga baki sha wancan dana kai maku ba matar tace. No nagode na bata amsa dashi haba ki saki jikin nan kamar gida kika zo ai ban san dai yaya kuke da enginer ba amma ai aminin maigidanane sosai duk da kasan nan suka hadu amma suna amintaka sosai da junan su. Yayanane na ba amsa dashi tace ikon Allah yayan ki na jini ko may nace eh gidan mu daya dashi karatu nazo yi nan ni. Au wallahi har na fara muna ina zaton ko yayi aure ne ai ya rabu da wanan arniyar matar tasa daya aura nan. In fada maki maigidana baiso auren su ba amma saboda nacewan wanan arniyar saida tasan yadda ta auri dan uwan nan naki. Abu kamar aikin asiri tun wanan lokacin zumuncin su da maigidana yayi rauni suka rage arkalla da juna kamar farko. Don matar bata son kowa ya mami mijinta daga ita sai yan uwan shi Allahne ma ya kwato shi har ya waiwaiyi gida daga bayan nan nasan karfin adduan iyayyene yai aiki a kasa. Murmushi nayi kawai don jin abinda ta fada nace ai mu duk da muka taso bamu san yaya umar ba sai zuwan shi daya yan shekarun da suka wuce muna dai jin labarin sa kawai a gidan mu. Gaskiya ba zaku sanshi ba kan don ina ga ai ko ashrin baki rufe bama ko ta fada tana kallona nidai dariyan kawai nayi mata ban bata amsa ba. Hiran yanayin garin ta dauki min da al,adun su sai kewan gida da mutum kanji farkon zuwan shi idan bai ganin na gida a kusa dashi. Har ta kai ga tambayana a gidan shi nake zaune nace a,a ina wani gidane dake kusa da school din mu don yafi mun kusa. Tace sau daya nasa wancan gidan nasa muntafi ganin amarya a lokacin akace bata nan tana America ne da zama. Naji dadin kasancewa a gidan Yusuf baba yola do matar tana da dadin hira sosai ban dai yarda na buga komai a gidan ba sai dare yaya yace in fito mu tafi. Haka muka rabu da sunan watarana zan sake kawo masu ziyara a gidan da zan tafi taimin kyauta na bajinta da ba zan manta da shi ba don har da kayan abincin mu na gargaji ta bani da turare da sauran tarkace. A waje muka samay su sai maigidan nata ke fadin to amarya munyi murna sosai da wanan auren ubangiji yasa wa aure albarka. Kallon juna mukayi nida halima danace wa shi yayanane da farko tace wai kana nufin matarshi ce ita din yace wallahi ai Umar baya da kirki ashe aure ya kara har kusan shekara biyu ke nan bai fadawa kowa ba. Sai yau yake fada min nima na sani tace amma yanzu take fada min shi din yayantane gidan su daya karatu tazo yi nan London. Mungun yace ta fadi hakan ga kowa daya tambaye ta yaya suke umar ai yakai mugu wallahi. Amma ko dana sani ai daba hakan ba dana baki tsaraban ma,aurata don ni ina samun su koda yaushe ana kawo mun. Nifa ba mijina bane na fada ina daure fuska a matsayin yayana yake kuma kawuna na fada na bata rai. Dariya naga miji da matar sun kwashe dashi tace ba laifi zamu kara haduwa da yardan Allah nan bada dadewa ba tunda har kunzo gidan mu muma muna nan kawo maku ziyara watarana. Mukai sallama suna tsaye har motar mu ya daga ba wanda yai magana daga cikin mu har tsawon wani lokaci. Na cika nayi fam har muka kai gida ba wanda yayi magana a cikin mu ina ganin street din mu na sauke ajiyan zuciya sai lokacin ya dan kalloni kadan ya kawar da kanshi. Ban tsaya ya zagaya ya bude min ba nayi wuf na fito daga motar ina sauke ajiyan zuciya a fili na nufi hanyar shiga gidan sai dai key din gidan yana hannun shi dole na jira ya gama rufe motar ya nufo ya bude gidan zuwa lokacin kankara ya fara sauka a ginin gidaje da motoci yana rufewa . Ban tsaya kallon wanan ba Allah Allah nake ya bude in shiga gidan don zuwa lokacin a matse nake sosai don fashin sallah da nakeyi lokacin. Yana budewa har ina bugeshi wurin shiga na haura sama da sauri tare da bude dakina jakata na wurgar saman gado na nufi bandaki don kintsa kaina . Ruwa na hada masu zafi da zasu isheni na dade a bayin ina gasa jikina kafin in fito rigar barci kawai na saka naje na rufe kofa na haye gadona. Washegarima ban fito da wuriba don ban falka da wuri ba dana tashi kuma sai dana tsaya na kintsa jikina kafin in fito. Abinda ban sani ba shine zuwan mu gidan abokin shi ba ziyara mukakai na Allah da Annabi ba shawara abinda zai fitar shi yaje nema gurin Yusuf yola din kamar yadda yake kiranshi. Bayan sun sallame mu zuwa ciki ya dubi Umar din yace abokina lafiya kuwa na ganka haka ? Umar yace ina cikin matsala abokina Yusuf yace subbahanallahi may ke faruwane haka duk yanayin ka ya nuna kana da matsala. Nan ya kwashe yanayin zaman su da merry sauyawan ta gaba daya da komai yana fada mashi. Yusuf din yace kaga abinda nake hango maka tun farko mutumina wa yan nan mutane ba abin yarda bane sam. Yaya mazon SAW zai magana a kansu maganan ya tashi daga baya tun farko na fada maka auren wanan matar matsalane gare ka kana dan bahaushe musulmin asali kajawa kanka wanan nauyin. Ansan idan mace tayi jahadi tsakani da Allah har ta yarda zata musulunta wanan baida illan komai kasan son tsakani da Allah take maka. Amma ni yadda iyayyenta suka kafa sharudan su kai kuma ka yarda dashi kana ganin zaka iya juyata daga baya ne ? Ba yau irin hakan ya fara faruwa ba muna gani wasu ma da farko zasu yarda su musulunta sai daga baya su koma akidarsu ta kiristanci don yaudara. Wasu ko har bayan rai suna cikin islama ba zasu canza ba irin merry yana da wuya ta canza farat daya idan ka tsaya tun farko kayi nazarin waye ita din. Yana da wuya merry ta iya canza addinin ta farat daya idan kayi la,akari da irin kungiyan su datake bi tun muna karatu. Godiyana ga Allah shine da Allah ya kwato muna kai hankalin ka har ya koma gida tun lokacin nasan kana da rabo mai karfi. Ai yadda ta biyo maka ta baya ta cuce ka haka kaima zakayi ka nuna mata namjin duniya kake na gaske. Fita batun da yar insha Allahu yarinyar tana girma ita da kanta zata neme ka ai ya katse a bokin nashi da fadin Yusuf ina tsoron queen ta taso cikin addinin uwarta mai zurfi. Don tun yanzu duk akidar yarinyar irin dabu,un su ne takeyi don merry bata yarda sam yarinyar ta mamay ni ko wani nawa takima fada mata komai a gamay dani. Umar wai ka manta da rijejeniyar kune danasa ka saka cewa zaka iya kara aure aduk sanda ta sauya wani al,ada daga rijejeniyar ku. Ban manta ba umar din ya bashi amsa sai dai ina tunanen sheri irin nasu do hakane kaga yanzu komai nawa yana zuwa gida ina kokarin ganin komai nawa ya koma gida ga baki daya. Merry tasa da wanan shirin naka ya girgizawa Yusuf din kai yace bata san komai nawa ba tun farko don ban yarda da hakan ba ban shi harka sana,anta itama haka bata shiga nawa. Kayi dabara Yusuf yace, yadan kada kafafuwan shi na dan lokaci yace da umar din da yai shiru yana tunane. Umar ka tuna shekarun ka suna korawa fa a yanzu girma yana dada shigan mu ga al,adan mu da iyayyen mu suka koyar damu iyali shine alfari mutum koda yabar duniyar nan muddin kana da diya masu albarka tankar baka barta bane. Sai nake ganin idan ka tsaya ka dogara da merry da yarta tankar kaida kanka ka dabawa cikin ka yukane ka kashe kanka. Kowa yana alfarin zama waje ne na dan lokaci idan ka gama tara abinda kazo nema sai a koma gida ayi rayuwa cikin yan uwa da abokan arziki. Yau idan haka ya kasance dakai umar damay zakai alfahari baka da mata bakaga yarka ko ta canza ra,ayi zata kara haihuwane yanzu. Umar yace ba alaman hakan a tare da ita don kullun ikirarin ta queen ta ishe mu rayuwa do haihuwa akwai wahala ba zata yarda ta sake ba. You see abinda nake hango maka ke nan tun farko abokina nu sai nake ganin ka kara aure kawai shine mafita gare ka hakan zai sa merry ta shiga hankakin ka in har tana son ka. Aure kan ai na dade da karashi yacewa abikin nasa da sauri Yusuf ya dago kai yana kallon shi yace yes almost to two years ke nan ina da aure Yusuf. Sai dai ban ba auren nawa wani muhinmanci ba sosai don aure da iyayye suka daura a bisa kaddara don karamar yarinyar nan daka gani yanzu matatace ita. Saidai muna zuwa nan na canza akalan zancen ta koma yar uwata yanzu haka karatu takeyi a nan tun bayan zuwan mu na sakata a makaranta. Tunda ya dauko chapter dina Yusuf din ya kura mai idanu yana kallon shi da mamaki sosai a fuskan shi sai da yaji yakai aya yace. How comes Umar bansan wanan zancen ba yace laifinane abokina nan dai ya kwashe duk yadda auren ya kullu har irin zaman da yakeyi dani ya fada mai. Yusuf yace lalai Umar kakai namijin gaske kana sa kamar wanan yarinyar a gida may zakayi da wata merry can data dade da shan ruwa tun baka aure ta ga daya sharrr. Wai dakata umar kai baka tsoron Allah ya kamaka da wanan hakkin yarinya karama da kake tauyewa ? Baka tsoron alhakin mahaifin ka yabika ko da akan yayan ka ko wani kaddaran ka ? Umar ka tuba kaji tsoron Allah wanan alhakin yayi yawa ina zaka dashi shawarata ka rungumi matar ka hannu bibiyu kaida kanka zaka dawo ka bani labari. Yusuf na fada ma matsalan da auren yarinyar nan ya jawo min nida mahaifiyata fa sunna ka raya fa umar ba zina kayo ba. Yarinyar nan watarana abin alfahari ne a gare ka ta bangare da dama ka godewa Allah daya baka mahaifi mai hangen nesa. Shiru umar yayi tun lokacin da yusuf ambaci tauye hakki gare shi don shi tausayina yake ji sai yake ganin ban isa aure va sai zuwa lokacin daya kare tsare tsaren shi kafin yasa mafita dani. Sun dade suna tataunawa da abokin nasa mumuna ciki bamu sam anyi hakan ba muna can muna tamu hiran a ciki. ZAINAB IDRIS MAKAAW 16/11/2021, 23:23 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM WARAHA MATULLAH YAN UWA MUSULMAI, , , , , , Idan nace Allah ya isa in kin karata baki biya ace akan novel ina jan Allah ya isa to yar uwa dake da kika fitar mun da novel da ke da kika karanta baki biya alkalin mu Allah na barki gare shi yar uwa. Kuna raina kalman hada mutun da Allah alhali kun san Allah zai iya yafe maka laifin dake tsakanin ka dashi amma ba zaii yafe na tsakaninka da wani bawan sa ba mai hankali da imani kadai zaigane inda maganata yadosa nagode . Koda na sauko karfe sha daya saura ba rana don haka banyi tsamanin yana gidan ba a lokacin tunda yarshi da matar suna asibiti nasan hankalin shi yana gurin su a nawa tunane ya tafi tunda safe baya gidan. Kallon yadda gidan ya danyi mun kura na kwana biyu da bai samu gyara ba don tun kan in kwanta ciwon marin dana sha wanda yai min rabon da na tsaya na gyara gidan. Na sauko ina bin gidan da kallo aikin gyaran gida na fara saida naga komai yayi yadda nake so na feshe ko ina da kamshi. Sai na koma kitchen nan ma gyara na fara kafin in dora girki sai da na kusa gamawa naji kamshin turaren shi ya daki hancina hakan ya sanar da zuciyana yana gidan. Don in tabbatar da zargina a kanshi na dan juya da zuman lekawa koshi din ne ya fito sai mukai arba dashi tsaye kofan kitchen din. Ina kwana nace mai daga inda nake tsaye lafiya yace ya karaso cikin kitchen din zuwa wurin fridge ya dauki goran ruwa ya fita. Sai a lokacin na dan sake zuciyana can naji shi yana bugun kofa da kankara ya taushe shi ta baya. Ya samu kofan ya bude ya fita lokacin na fito kitchen da abinci na aje a saman dining naga ya kara shigowa bai ko kalli inda nake ba ya dauki wani abu naga ya fita. Ashe kankarane ya rufe motar daga dare zuwa wanan lokaci shine ya dauki abin kawar da kankara da ake fesawa ya fita ya fesawa motar. Zuwa lokacin na fahinci kamar fushi yake dani don haka nima na fita batun shi dama ba shiga nake ba sai idan ya sakani ciki. Ya dan dade a wajen har na karya na koma dakina bai shigo ba naso inga ko harda abinci yake fushin da ban san dalilin shi ba tun barowa gidan Yusuf yola da mukayi. Ko daya shigo ban falon hakan ya bashi daman zama yaci abincin daya gani aje saman dining din sai da yaji ya koshi. Ranan dai motar da bai shiga ba ke nan sai jirgi yabi zuwa wurin queen ya dubata bai shiga wurin merry ba. Ya fito ne a daidai lokacin da wasu kawayen merry suka shigo don duba jikin yarinyar dakuma yi mata addu,a. Yafito ya barsu a dakin a zaton su gurin merry ya nufa saida suka gama da da yarinyar suka nufo dakin da merry take . Bayan sun gama abinda sukeyi ne suke tambayan ina mijin ta tace baishigo ba yau itama shi take jira don likita yana son ya sallamay ta yace sai sunga mijin ta. Da mamaki suke kallon juna su kafin guda yayi karfin halin fadin yanzu yabar dakin da Faith take kwance mun dauka yana nan ne gurin ki muyi maku addua a tare. Fuska ta bata don bataji dadin jin hakan ba daga gare su don suna cikin masu adawan auren ta dashi don dai church din su dayane an kuma taso tare yasa bata rabu dasu ba suma dai black American ne a can aka haifesu sai dai su suna ban addinin su sosai irin sisters din nan ne su. Ya tafi gurin likitane ina gani ta basu amsa da hakan don kawai kada su zargi komai a zuciyar su. Fitan su ta mike zaune don dama taji sauki sallama kawai take jira don sai ya saka hannu za a yarda a sallamay ta saboda case din su har yanzu ba akare ba. Ga iyayyenta basu zo ba don yau sun makara saboda matsalan snow da aka tashi dashi sosai a kasan mutame basu faye wani zirga zirga ba. Amma wa yan nan yan tsaurin addinin haka suke bi cikin wanan yanayin suna wa mutane addua don kada a sake hanya abi wani addini na daban. Karshe dai dole saida merry ta jira zuwan iyayyenta don su sukai komai har saka hannu akan zata kai kanta police station. Sai dai ita Faith har lokacin ba,a bata sallama ba don yarinyar tafi jin rauni a jikin ta saboda koda abin ya faru tana gaban mota ita da uwar a lokacin. Matsala shine don suna a cikin maye sukai tukin ganganci wanda hakan doka ne na kasan London din. Sai dai duk abinda ake ita merry hankalinta yana ga mijin ta da bata san dalilin rashin zuwan ta ba sai dai ko maynene yana da nasaba da dan matsalan da suka samu ranan a asibiti dashi harda iyayyen ta da suka so saka baki a cikin case din lokacin. Wanan abin yayi matukar bata mamaki da haushin yadda ya share su din saidai abin mamakin dataji gun yarsu shine kullun uban na zuwa ya duba yarshi asibiti haduwa ne kawai basuyi dashi. Gashi tayi neman layin shi har ta gaji ance baya shiga duk lokacin da ta kira layin nasa din. Haka yasa ta kulle shi a rai sosai tasan duk zai gama fushin ne ya dawo ya nemay ta ko ya samy ta a can garin da take aikin ta din. A nawa bangaren kuwa zaman doya da manja muke a gidan daga gaisu sai kuma gobe in mun gaisa din sai dai bai fasa cin abincin da nake sakawa dashi ba ko yaushe . Watara sai dare yake fita ban sanin dawowan shi watarana kuma tun safe idan ya fita sai yamma yake dawowa gida. Gashi zaman shi a nan ya bala,in takurawa rayuta sosai don banda halin leka ko waje kamar yadda nayi mai alkawarin yi din kafin in dawo gidan. Har Allah ya nuna mun koma makaranta muna cikin wanan halin dashi hakan ba karamin dadi yai min ba don ina haduwa da abokai a can ina dan rage miyau na. Ranan na dawo na samu takarda saman dining ya aje min cewa zaiyi tafiya sai ya dawo bai fada min inda zai tafi ba nima kuma ban damu da in sani ba. Zaune yake a cikin jirgin da zai kaisu kasan Malaysia a hankali ya runtse idanuwan shi ba abinda ke yawan fado mai a rai sai irin karfin halin wanan yarinyar da yakewa daukan yar kankanuwar yarinyar amma sai wayau da hali irin na manyan mata a tare da ita. Zarah ya furta a hankali shi kadai yake magana kamar zarare ya dan sake murmushi a fili tare da mayar da kanshi saman kujera ya lumshe idanun shi. Taso yin kamanni da uwarta maimuna sai dai ta dara uwar da abubuwa da dama yanzu ko ta halaiyan su yasha bamban. Yasan zarah yarinya ce mai hazaka da kokari don yawan bibiyan karatun na da yakeyi ba tare dana sani ba. Ga komai tanayin shi a bisa gaskiya da koyi da addini da abinda iyayye suka koyar da ita a gida. Ya kula yarinyar batada kyashi ko hassada a rayuwan ta don da watace da yanzu ya fara gani ko ji akan irin zaman da sukeyi zata iya samun shi makale da merry a jikin shi amma bata taba nuna bacin ranta ba. Yasan da ace merry ce da wani fitina ya afku yanzu don da kowa ya gama jinsu ko. Zarah tana da kunya da kamun kai don bai taba ganin wani shiga a wurinta na asha ba tun zuwan su nan ko a gida ya kulatafi saura kula da kama jiki a gidan su. Ya kula yarinyar bata da yawan magana amma akwai bakar magana da manyan magana a bakin ta batare da kiyas tawa ba. Ya lumshe ido tare da fadin yarinya karama da halin manya nisan tunane da sanin ya kamata ga babba saboda irin biyayyan dokan daya sa kuma tabi. Ya kara mayar da kai yana fadi a ranshi yarinyar tana da saukin kai da saurin shiga mutane ko shine yasa take saurin samun sabbin abokai a nan wanda ya hana mata hakan. Tana da saurin shiga zuciya duk wanda ya ganta don ladabin ta ga gaisuwa dole jama,a su so zarah don ita din kyakyawace mai kyawon hali. Ido a lumshe yace zarah kedin kyakyawace kina da duk wani abinda da namiji yake bukata gun mace musanman wanan idanun irin na uwarki har sunfi na uwarki dara dara ga yawan lumshesun da takeyi musanman idan tana cikin hushi hakan yana kara burgeshi da shiga ranshi. Kai ya girgiza yace ke komai kin iya karamar alhaki dake zarah tafiya kamar wace take tsoron kasa a cikin natsuwa komai sauri take takon ta. Raban da bata da lafiya yaga gashin kanta ya dauka kari tayi amma daya fahinci nata ne saida yaji tsoron yawan gashin kan nata saidai baya samun gyara yadda ya dace shiyasa Wanan kuma yasan laifin shine da bsya bata kulawan daya dace ta samu daga guri shi. Astangafurullah ya furta da sauri tare da fadin Umar may kakeyi hakan wani nauyi ka daukanwa kanka haka ? Ka kawo yar mutane nan bisa amana ka watsarda ita tana rayuwa a cikin kunci da kadai duk ta dalilin shi. Saboda tsoron ya lalatawa yarinyar mutane rayuwa ya keyin hakan don kawai shida ita su kaucewa furcin mahaifiyar shi ya dannewa yarinyar mutane hakkin ta haka. Gaskiyan Aliyu dayace dashi ranan da mahaifin su ya fahinci hakan da wani ido zai kalli mahaifin nasu dashi. Zaiji kunya matuka yasani don ko Amma fushi sosai zatayi dashi yan gidan su dama wasu mutanen zasu dauka tsoron matar shi merry ne a zuciyar shi. Wani irin daci da bacin rai ya ziyarci zuciyar shi lokaci guda bai sake bude idanun shi ba sai lokacin da yaji mai sanarwan jirgin na fadin sun iso kasar malasia jirgi zai sauka kowa ya shirya. Washe gari ya kama weekend ban fita ko ina ba sai zagewa sosai danayi na gyara gida na tsabba na wanke kayana da duk wani abindake bukatan wanki a gidan. Har dakin yaya ban barshi hakana ba dukda fushin da yakeyi dani kafi ya tafi tafiyan dayayi. Na gama nayi wanka na dawo falo dauke da littafin kawa,idina ina karantawa. Bell din gidan yayi kara ina mamaki waye zaizo min da wanan ranan anty farida ne da dukkan yan gidan su akofan da murna na tare su ina fadin kushigo babana sannun ku da zuwa. Tace yau dai gaki ga baban naki kullun sai damun yakeyi yaushe zaki zo ko a kaishi gidan wanan anty da takece min babanta. Babana yau gaka a gidan yarka da fatan a nan zaku kai dare a gidan nan anty farida tace muna nan hardare tare dake. Littafin dana aje zainab ta dauka tana kallo kagin tace anty wanan kur,anine haka ? Dan murmushi na sake a fuskana nace wanan litafin idan baki sanshi ba zainab addinin mutum ragage ne malamai sukace. Fuska ta bata tare da fadin yanzu anty ana nufin ko wani musulmi sai ya iya wanan littafin yake musulmi ? Na girgiza mata kai nace ita musulunci addine mai sauki da saukin fahinta zainab kinga wanan ya kumshi babin sallah da ka,idojin wanka da saura su ana son ko wani musulmi yasan wasu abubuwa daga cikin shi ma,anan wanan littafin ke nan. Tace yauwa anty sai kuma ta kalli anty farida tace barshi kawai anty. Anty farida tace kiyi tambayan ki kawai idan kina dashi tace a dan marairaice dama tambaya nake son yi akan wankan tsarki. Kaina girgiza kafin ince kai haba zainab aiba akunya ga addini kowa dan koyo ne ki saki ranki kiyi tambayan da kike so. Ni anty idan zaki mun duka aizanso wallahi nace to shike nan da farko dai ai kin san wanka ya kasu akan abubuwa uku ne malaimai sukace zuwa hudu. Na farko shine wankan shiga musulunci sai na biyu wankan janaba saina haila dana Nifasi sai cikon na biyar shine idan Allah ya karbi ran bawan shi shima akwai wanka na barin duniya da ake masa. Farilan wanka kuwa sune yin niya yayin farawa da gagautawa da cudanyawa da gama jiki ko ina da ruwa. Sunnonin wanka kuwa sune wanke hannaye izuwa tsintsiyar hannu kamar yadda kikasan kina yin alwala nakai mata har karshen shi. Sai kuma mustahaban wanka sune shine farawa da wanke najasa ma,ana wanke gaba inda a nanne zakiyi niyar wankan abinda zakiyi wankan kanshi nan ma nayi mata bayanin komai yadda zata gane. Don nasan tunda tayi tambayan nan tana da bukatan bayani a natsene. Har anty farida ido ta zuba min sai danace zainab da fatan kin fahinci abubuwan dana fada maki yanzu. Anty farida tace ai ba zainab harni kin tuna min wasu abubuwa a nan a gida fa na karanta wanan har karshe amma saboda rshin bita a nan kinga na manta wasu abubuwa daga ciki. Nace anty karatu baison ka manta dashi sai shima ya manta da kai komai ilimin ka kuwa don kinga ni ban yarda na aje karatuna addini ba tunda nazo. Mun kai wani lokaci dasu a gidan munsha hira ranan sosai kafin su tafi mijin ta ya zu da dare ya dauke su ina jin kamar kada mu rabu da juna dan dan zaman a tare ya tuna min da abubuwa da dama gamay da gida Nigeria. Bayan tafiyan su gidan ya koma min ni kadai kamar bashi bane yake da hayaniya dazun dan lumshe idona nayi daga inda nake zaune saman kujera ina tunane sai ga hawaye yana zubowa a idona. A daidai lokacin da ya umar yake can kasan malaysia yana gudanar da aikin daya kai shi can na gyaran matatan su na kasan. Sai safe ya farka ya dan fito haraban masaukin su ya tsaya yana kallon yadda suke zirga zirgan su duk da ya sha yawo kasashen duniya sai dai hakan bai hanashi mamaki mutanen kasa ba. Yana ganin yanayin su da wahalan su kamar yan tashi kasan Nigeria sai dai nan din ya dara Nigeria sosai da abubuwan zamani naci gaba amma akwai tallakawa masu tarin yawa a kasan. Yayi mamaki ikon Allah yadda ubangiji ya tsagosu a wanan nahiyar kuma suna musulmai don kusan fiye da rabin kasan duk musulmai ne. Mata suna saye da siket da rigar wani nau,in yadi irin nasu da dan hijabi iya wuyan su yayin da mazan yawancin su suke daure da zani da hula irin ns kasan su. Ya gama kallo da shan iska ya koma ciki don ya shirya don yau da yamma yake son komawa kasan London din daya baro. Sai ya samu kanshi da sha,awan son yayi tsaraba ga iyalin shi akaro na farko a rayuwan shi don shigan matan mudulman kasan ya burge shi sosai. Kasuwan su ya shiga ya dan zaga ya zabi masu tsada harda hijjaban su dan ya kula da irin hijjab din da nake amfani dashi ne gurin fita iya kafada. Da iri kudin su na kasan daya canza zuwa ringgit da suke amfani dashi ya biya su ya dawo masaukin shi ya shirya bai tsaya wani abuba motar da zata kaishi airport tazo ta dauke shi tare da checks din magudan kudin daya samo a kasan. A wanan daren da nake zaune ina kewan gidane ya iso har ya bude gidan ya shigo ban ji shigowan shi ba saidai gani mutum nayi a gaba ya tsaya yana kallona da mamaki karara a fuskan shi. Ganin gani zaune ina tunane sai hawaye ke zubo min a idanuna yanayin fuskan shi ya dan sauya. Ya tako har inda nake zaune sai lokacin na dago kai na dan fitgita da ganin shi yace zauna abinki kin tsorata da ganina ko ? Ban zauna din ba don sai na daburce na mike tsaye ina masa sannu da zuwa tunda ko banza ai ya sallamayni a takarda. May ya samayki kike kuka haka zarah ke kadai a gida yana tambayana cikin kura min idanuwan shi akaina. Ban iya bashi amsa ba don tsareni da idanuwan shi dayayi a lokacin madu firgitani da tsoro shi wani lokacin. Ganin ba zan bashi amsa ba naga ya juya ya fita daga gidan bai jima ba naga yana shigowa da manyar jakkuna a hannun shi ina tsaye na jingina jikina da kujera. Saida ya gama shigo da komai gidan ya tsaya yin waya daki na shige abina na barshi gurin ban fito ba sai safe na samu yaci abincin dana tuka na semo da mukaci da su anty farida wanda na raga zanci da dare na kasa ci. Gyaran gurin na shiga yi har zuwa gidan na hada muna abin karyawa don satin ukun da yayi baya kasan naji dadi kasancewa ni kadai sosai. Bayan na gama na shiga nayi wanka ina zauna na saka kaya ina dan kara gyara fuskana duk da ba wani yin kwaliya na damu dashi ba dama. Ya shigo dakin ya samay ni ina rufe powder dana shafa a fuskana kallo daya zakai mai ka gane dan fadawan dayayi wanan lokaci. Ga ba walwala a fuskanshi ko kadan tun shigowan shi na kula da hakan gare shi. Ganin shi nayi saurin tashi tsaye ya nuna min indana tashi yana fadin komaki zauna magana nazo muyi dake ai. Ban iya boye mamakina ba nakai zaune sai naga yakai zaune bakin gadona tare da hade hannayen ya tokare haban shi dashi yace. Zarah may ye damuwan ki danazo na samu kina kuka ya tambayeni cikin kara tsureni da idanuwan shi. Ban iya bashi amsa ba kaina kuma yana kasa na kasa dagowa in kalleshi ganin ba zan amsa shi ba ya sake fadin tambayan ki nake zarah ? Na dago kai ina kallon shi nace ba komai yaya idona suna tara hawaye ko ina tauye maki hakkin kine zarah ki fada min ? Jin hakan dayace yasa na dago idanu nadan kallo shi sai na kara dukar da kaina kasa. Gani nayi yanauin fuskan shi ya sauya min sosai da alama yana son jin abindake damuna din lokacin. Kiyi hakkuru zarah nasan ina danne maki hakkin ki nima hakan ba da son raina bane hakan ke faruwa a kanmu. Wani mamakin ne ya kamani a karo nabiyu na sake dago kai ina kallon shi . Hawaye suka soma zubo min naji yana fadin na tambaye ki maynene matalan ki zaki fara min kuka. Jikin shi ya danyi sanyi ya dago a hankali ya mike tsaye tare da takowa zuwa inda nake naga ya miko hannayen shi yana kokarin mikar dani tsaye daga zaunen da nake. Bayan ya mikar dani ya dago fuskana yana son mu fuskanci juna dashi da sauri nace yaya ni banda matsalan komai in ma ina dashi ai kasani. Murmushi naji yayi ya dan rungumoni zuwa jikin shi kokarin kwace kaina nayi ina fadin amma kasan hakan bai dace ba a tsakani mu yaya. Yace cikin mamaki kina a matsayin matata kike furta hakan gareni zarah ido na dago ina kallon shi jikina na rawa nace. Na rokeka yaya ka barni inyi rayuwata a yadda nake kai mana adalci dani dakai tunda kasan a matsayin da auren mu yake . Yace ban san komai ba ga auren mu sai kin fada min yanzu zan sani yana kallona cikin son jin bayani a bakina. Amma kasan hjyn ku abinda ta furta akan mu ko ka manta ne yanzu ya girgiza kai ya sake ni tare da juya bayan shi yace. Wanan kuma abinda ya shafeni ne nida zuciyata ba wani ba don nike auren ki ba hajiyata ba. Amma ai tana iko a kanka ko don uwa ba wasa bace ya juyo ya fuskance ni yana fadin idan muna magana kada ki kara jefo zancen iyayyen mu ciki don ina so mutum mai daraja iyayye. Naka ka sani don banga kana daraja nawa uwar ba don tsaban darajan da bata dashi a gare ku kowan ku kaf yan dakin ku maimuna kuke kiranta dashi babu darajawa. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:23 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH YAN UWA ALLAH YA BAMU WUNI MAI ALBARKA AMIN. Littafina na kudine don darajan Allah da Annabinsa yar uwa kada ki karanta idan baki biya ba kibar shedaniya da nauyin ta wace ta fitar abokan halaka take nema daga cikin ku kada ki bari ta ribbance ki don karatu novel kiji tsoron Allah don akwai ranan tsayuwa gaban ubangiji. Kai da yan uwan ka kuna muna daukan marasa daraja da gata a idon ku kun dauke mu tankar yan cin rani a gidan ku. Duk kokarin da mahaifiyata take da kakan ku da mahaifin ku haka baisa tayi daraja a idon kowa a gidan ku . A gaban kowa mahaifiyar ku tayi ikirarin bazan taba zama cikim ahalin ta ba muddin tana raye a duniyan nan. Yanzu mai zaisa kake kokarin canza shawaran ka a kaina yaya kana son nuna min kana tausayin mu ne ko lalata min rayuwa kake son yi in sake jiki dakai ka jefani wani maraicin karo na biyu bayan na mahaifina dake cina a kullun a zuciyata. Na dago ido na kalle shi tare da hade hannayena a guri daya alaman ina rokon shi hawaye na zobo min a idanuwa kamar an bude famfo. Nace yaya ka barni inyi rayuwa a yadda yazo min ka bari ko da sau dayane ka kuyi muna adalci ta hanyan karatun da ka sakani don Allah. Murmushin kunan zuciya da bacin rai naga ya sake a fuskan shi ya tsaya yana kallona har nakai ayah kafin ya furzo da iska daga bakin shi ya furta. Naki tunanen ke nan zarah a zaton ki yan dakin mu basu son mahaifiyar ki a yanzu don tana kishi da tamu mahaifiyar komay ? Kada ki manta mu mazane ba zamu saka kanmu a cikin zancen mata ba ba zamu fito fili mu nuna ga ra,ayin mu ba. Amma mu maitai muna da zamu kita matar da itama tankar jinin mu take mun taso a tare mun ganta a cikin gidan mu tayi rayuwa damu akan dan wani dalili sai mukita ? Idan kina tunanen hakan kinyi kuskure a rayuwan ki zarah ke yarinyace har yanzu shiyasa kike fadan wanan maganan haka. Nidai nasan anbani auren ki na ruguma da hannu biyu a cikin mutunci tare da mutunta darajan aure na ga idon kowa. Aure yaya aure fa kace auren da akayi shi a bisa kaddara da sabanin hankali auren da babu soyayya a cikin sa aiba aure bane. Dan dariyan yake yayi a fuskan shi tare da fadin ai lokaci ne zai baiyanar da komai zarah. Kada ki daukeni ban san abinda nakeyi ba, komai dake faruwa ina sane dashi ina kuma nawa tsarin akan shi don haka ki fito muci abinci yanzu ina dining ina jiran ki. Yana fadin haka bai tsaya ba ya fice daga dakin bai ko karasa fita ba na sake wani kuka gami da ihu ina fadin wayyo ni Abbana ka tafi ka barni rayuwa tana min zafi. Dan girgiza kanshi yayi daga inda yake zuciyar shi na mashi kuna da kala maina masu cin rai da wanan kokekoken banzan da na tsiri mashi a gida yana tayar mai da hankali. Tsananin sanyin da ake a kasa ya hana kowa walwala a wanan lokacin don hakane ko tafiya yanzu ba ko wani lokaci akeyin sa ba a kasan jerabawa muke a wahalce domin hutu zamu koma kuma wanan zangon baida yawa kamar na baya. Tun dana dawo gidan nasan yana ciki don ba inda yake fita yanzu tun lokacin da sanyin ya tsananta sosai motar shi ma dake waje ta rufe da kankara lif jikinta. Don hakane tun dawowan shi yake min zaune gida kusan kwana biyar bai fita zuwa ko ina ba tunda ya dawo sai na dauka ko don matar shi bata garin ne. Duk da daga gaisuwa ba abinda ke hadamu a gidan hakan bai hana shi fita da yamma zuwa wani resturan zai dawo da snack iri iri ya tursa ni a gaba sai naci ko da kuwa banson ci don ban isa in mashi gardama ba. Soboda ya dasa mun tsoron shi a raina tun farko ina shakkun shi sosai a raina da girmama shi. Yau kan garin ba dama saboda sanyi daya dami mutane ga har wani iska da kankara ke sauka yana batun rufe mutum da ran shi idan dai kana a sarari. Kamar an koroni na banko kofan na fado gidan hankali tashe banyi zaton ma yana gidan ba a zatona yana can gidan shine. Ganin shi nayi tsaye ya kunna wa tsakiyan falin wutan fire wood a dan wani guri da ban dauka da farko wurin amfani bane gurin sai ranan da naga ya fara kunna wuta irin wanan lokacin. Yana tsaye ya ba kofan baya hannayen shi suna mike a gurin wutan kamar yana gasa su sai rigan suwaita irin na saka mai v neck brown a jikin shi da dogon wando fari kafan shi socks ne kawai a saye lokacin. Do muna girmama gidan mu kamar na sauran musulmai don ba ko ina muke takawa ba a gidan da takalma sai dan kereriyan inda muke bi mu fita idan mun sauko daga sama. Dan juyowa yayi kadan ya kalleni jin yadda na banko kofan falon lokacin kamar wani na bina a baya. Easy yace ba tare da ya juyo ya kalleni ba na samu kaina da dan tsayewa ina kallon shi har lokacin bai juyo ba cikin kasaita yace min . Yaya akayi baki saka rigan kwarai ba a sama kin kuma san irin sanyin da akeyi kallon kayan jikina nayi da sauri naga doguwar jallabiyace a jikina nayi rolling din kaina har mazaunana da gyalen rigan . Duk da ina son in tsaya in sha dumi a wajen don sanyin dana kwaso ban samu yin hakan ba don har lokacin yana tsaye ba tare da ya juyo ba gurun wutan kamar mai gasa jikin shi. Dakina fada da sauri na kuna heater dakin gado na fada ina maida numfashi Allah ya taimakeni ina fashin sallah a ranan don haka banda damuwa. Sai dana dan huta hakana a kwance ba barci nakeyi ba can na bude idanuwa na wani leda babba na hango har guda biyu aje daga gefen gadona. Tashi nayi da sauri ina kallon ledan cikin mamaki da sauri na karasa wurin ledan na shiga budewa da sauri. Irin kayan da na gani a cikin ledan sun ban mamaki sosai har kala shida yadin mai kamar atamfa amma sai taushi dinkin su gwanin ban sha,awa sosai. Da sauri na bude dayan hijjabai na fara fitarwa sai plat shoe daida kafana shima da yan jakkuna masu kyau sosai abin yayi matukan ban mamaki. Wai yau yaya ne da sayo min tsaraba ko may don ban san abindama zanyi tunane a kansa ba. Zaunawa nayi gaban kayan ina tunanen yadda zan mashi godiya wata zuciya tace min share shi kawai ai aikinsa ne hakan. No ba dadi ai maka alheri kaki yabawa ba haka addini da iyayyen mu suka koya muna ba na fadi a fili. Wanka nayi don on din da nake ciki nasaka wando da riga a jikina sai rigan sanyin dana dora saman rigan bai dai rufe min mazaunana ba ban damu da hakan ba tunda na saba zama a gida hakan cikin irin shigan. Na sauko kasa na nufo falon wanan karon zaune yake ya bude laptop yana aiki a cikin sa a hankali na tako zuwa inda yake sai dana zauna dan nesa kadan dashi nace. Ya naga kaya na gode Allah ya kara budi da sauri ya dago kai ya dan kalleni kamar wanda zaiyi magana sai kuma ya fasa yaci gaba da aikin shi cikin gyada min kai. Mikewa nayi zan shiga kitchen sai lokacin yai magana tunda na sauko yace kada kiyi wahalan dafa abinci na sayo muna abinda zamuci. Dan juyowa nayi ina mamaki sai na fasa shiga kitchen din lokacin falon na dawo na zauna na dauki remote na kunna tv tare da rage karan shi don kada in damay shi. An dauki tsawon lokaci naji yace daddy ya bugo waya dazun suna gaida ke da sauri na dago kaina na kalleshi don jin ya ambaci sunan kawuna. Ya jikinsa nace dashi yace da sauki a yadda naji muryan shi ya samu sauki sosai. Shiru nayi ina tunane kafin na mike na shiga kitchen na hado tea mai zafi na dawo falo ina kallo ina shan abina hankali kwance. Zamuyi hutu zango ina son zuwa gida in dubasu na fada a cikin rashin damuwa da abinda nace. Ba yanzu ba ya bani amsa ba tare da ya dago kaiba sai yaushe yaya na fada a dan shagwabe don nasan tunda ya fada gaskiya ya fada har cikin ranshi. Sai kin tara masu tsaraba mai yawa zan kaiki yanzu hannu sake zaki tafi masu ai kawun ki ba zaiji dadin ganin ki hannu sake babu komai ba. May nake dashi da zan tara tsaraban da zai tsone masu ido yadda kake fadi haka ni abinda ke gareni zan kai masu bana karya. Ai ba ina nufin ki masu karya ba don haka abinda ke gidan sarki akwai shi gidan bafade saidai kyawo da inganci ya banbanta su amma amfanin su dayane duka. Kaina ya daure sosai don tunda ya fara harde maganan shi ban fahince shi sosai ba bansan inda zancen shi ya dosa ba. Diban lokaci naga yayi sai ya mike da sauri yana fadin maza sallah don har lokaci yaso ya kure ba tare da ya tsaya duba ko na tashi ba ya wuce. Niko nasan ban sallah na zauna abina kafin can in tashi zuwa kitchen na duba abinda ya sayo muna din. Abincin kwali ne wanda zai iya daukan kwanaki bai baci muna ci idan munyi worming dinshi a ovon. Tsada kega wanan tarkacen saidai babu dadi ko kadan kodon ba cimarmu bane bamu san dadin shi ba oho. Da zafin shi don abinda yake ci har lokacun yana da sauran dumin shi sai idan yayi sanyi zaka iya dumamawa kaci. Ina zaune na tasa kwali daya a gaba ina yagan kazar ciki hankali kwance ga dai hadi yaji na komai amma baiji maggi irin namu ba πŸ€ͺ Har na kusa gamawa sai gashi ya fito bai zauna ba ya dauki remote ya canza chenal din tv zuwana labarai. Zama yayi naci gaba da cin abincina hankali kwance na gama na dauki tisue ina goge hannu kafi in mayar da hankalina kan tv ina kallon yadda suke nuna aibun da kankara keyi a kasan ko ina. Ganin banda niyar bashi abinci yace ba za a bani abincin bani nakallo shi da sauri irin yadda ya tsareni da ido yasa na dukar dakaina da sauri na mike zuwa kitchen din. Saidana dan tsaya na hada komai na dauko zuwa falon nakai mai saman dining na aje mai na juyo naga irin kallo da yake min a lokacin. Sai naji wani iri a raina don ba irin kallon daya saba mi ya kawar da kanshi bane yake min. A hankali na tako zuwa kujera na zauna sai lokacin naji ya sauke ajiyan zuciya yamike zuwa dining din. Kallon jikina nayi ko yaga wani abin ne a jikina naga babu komai ina nan tsab a yadda na fito raina ya baci don ban san abinda yasa yake min wanan kallon ba haka. Karshe ma mikewa nayi na barshi gurin a zaune falon na shige ciki ban ko kara juyowa ba dama sanyi akeyi. Saida na kara dauraye jikina na kimtsa dana fito na saka rigan barcina tare da dan kara gudun karfin abin dumama dakin. Nahaye gado na kudundumay a wuri daya har barci ya daukeni ina tunane a dakin ni daya. Cikin dare ina barcina hankali kwance na tashi a gigice saboda bakon yanayin da nake ji yana sauka a jikina. Na bude ido da sauri naga har lokacin fitilun dakin a kashe suke sai numfashin da nakeji a gefena cikin wani irin yanayi na daban da ban saba ji ba. Innalillahi na furta firgice a fili ina shirin kwarma ihu naji an rikeni yana fadin easy baby easy nine fa zarah. Irin rikon da yai mun yasa har lokacin jikina bai daina rawa ba sai tsuma nakeyi. Da kyat na samu na kwaci kaina na koma gefe na mike a furgice saidai ban sauka a gadon ba sai mazurai nakeyi tsorona a fili. Komawa yayi gefe naga ya kunna dim light din dakin ya dan dauki haske ta yadda zan iya ganin sa ko ya ganni da kyau. Cikin rawan murya nace yaya may kakeyi a nan kuma ko kayi batan dakine kana barci ? Nama rasa kalan tambayan da nake masa a lokacin na san dai karshe na hada hannayena guri daya alaman roko ina fadin. Yaya may yasa zakai min hakan kana son ka lalata min rayuwa ne kamar yadda kukai guri yin hakan tun farko. Yana kishin gide saman gadon yayi makari da hannun shi saman filo ya zuba min ido yana kallon yadda nake zuba a firgice. Sai can dayaji nayi shiru ina sheshekan kuka don nama kasa ci gaba da magana ta da nakeyi lokacin. Kai ya girgiza yace menene matsalanki ne Zarah do na zo gareki ke ba matata bace ina da hakki a kanki kamar yadda kema kike da hakki a kaina ? Nayi maza nace mai ni banda hakkin komai a kanka yaya na rokeka ka koma dakin ka don Allah idan ma baka cikin hayacin kane ka shigo. Ni ina dashi zarah kuma shinazo karba a wanan daren ya fadi cikin kura min idanuwan shi mai kama da ruwan madara yana wani lumshe su a hankali kamar maganar tayi mai yawa a lokacin. Na dago idona kalleshi yayin da wasu sabbin hawaye suke zubo min a lokacin don jin abinda ya furta min. Don Allah yaya kayi hakkuri ka fita don bukatan ka ba mai yuyuwa bane gare mu ka daure ka karasa aikin ladan da kakewa kawu na sanyani makaranta in samu in karasa. Bansan wanan zancen da kike ta fada ba zarah all what i know ke din dai matatace don haka ko wani lokaci muna iya kasancewa a tare. Bansan lokacin danace karya kake fada yaya niba matarka bace yadda ka fada a matsayin kanwa ko ya ka daukeni tun farko. Amma ai yanzu da bakina kikaji na ambaci ke di matatace ta sunna don haka ki bani hakkina dake kanki don an biya sadaki kin karba a gaban kowa. Yana fadin hakan ban fargaba sai ji nayi yasa hannu guda ya cafkoni daga inda nake gurfane wani kara na saka yasa hannu ya dafe min baki da sauri. Yace ke kina haukane kin san kuwa darene yanzu wasu zasu iya jiyo muryan ki a waje. Kafin inyi yunkurin mikewa yasa hannun shi daya ya kare matseni yana kokarin lalabo inda bakina yake. Wayyo mamu na Amma kizo ki kwace ni don Allah yaya mugu zai halakani yau wayyo kawuna na Allah ya bashi sa,a ya samu bakin nawa ya hada da nasa lokaci guda na hade maganan da zan fada lokacin. Hannun shi daya yai amfani dashi wurin sarafa gangan jikina inda wani sabon yanayi yake ziyarta na lokaci daya da ban taba jin irin sa ba a rayuwata. Motsitsiri nake na son in kwaci kaina daga shitin halakani da yake shirin yi a daidai lokacin naji saukan hannun shi a saman kirjina yasa karfin shi ya farke gaban rigan har lokacin bakin mu yana hade dana juna. Wanan yanayin na saukan hannun shi saman kirjina yafi ko wani yanayi dagula min lissafi a sannun na bankaro kirjin nawa alaman neman ceto. Shiko a wurin shi yanayin yai mai dadi sosai sai ji nake yana wani irin nishi dana dauka wani abune ke samun shi a lokacin. Gurin fadin kalman dake zuciyan shi yayi gigin cire harshen shi cikin bakina don ya fadi a sarari hakan ya bani daman kwarma wani ihu da karfi a daidai lokacin da hanayen shi ya sauka saman marata lokacin na sake wanan uban ihu sosai gidan ya dauka ga baki daya . Hakan bai hana shi fasa abinda yakeyi ba saima kara kaimin da yayi a lokacin. No no nono ya karasa da dan karfi a raze jin pad dayayi a karkashin pant dina yasa yake fadin hakan sai naga ya dan cusa hannu da kyau yaga tabbas zargin shi gaskiyane. Ji nayi jikin shi yana mutuwa a hankali ya koma samana yai lankwas dashi cikin bacin rai saidai bai daga a saman jikina din ba har lokacin. Can naji ya mirgina ya sauka saman kaina bai kara second a dakin ba ya juya ya fita da sauri har lokacin ban iya dago kai na kalleshi ba saboda yanayin da nake ciki na mutuwan jiki ga baki daya. Wani kuka mai cin zuciya da nadama ya zo min lokaci guda da kyat na iya jan kafata zuwa bandakina bakina na fara kurkurewa tare da yin brosh kafin in cire sauran dan yalalon rigar barcin da ya yaga kusan rabi shiba a jikina. Ruwa masu zafi na hada a cikin daren nan na dan gagasa jikina don inji dadin kwanci na dade a cikin bath din zaune ina kuka gwanin ban tausayi dani. Ranan dai nayi mai Allah ya isa yafi dubu a bakina tare da Allah waddai da halin busuru irin nasa shi baiko ji kunyan zuwa kwakwalata ba shedani kawai. Tunawa dani kofan har yanzu a bude take kada ya dawo min daki don bansan abinda yasa ya fita a lokacin ba. Na mike zubur daga cikin bath din ina sauri na fito na nufi kofan na rufo tare da mashi key . Wani rigan barci na dauko na saka na dade a bakin gadona zaune ina kuka ba wanda zai lalashe ni lokacin. Wayata na tuno dashi da sauri na mike zuwa inda na aje saidai na neme shi kaf dakin ban gani ba mamaki ya kamani don a nan na aje wayan lokacin da zan kwanta.. Da sauri na furta mugu ko mai zaiyi da wayana kuma daya dauka ban sani ba saman gado na fada ina birgima kamar mahaukaci ina zagi. Sai goshin asubahi barci yayi gaba dani a gajiye ban san inda kaina yake ba kuma jikina duk ya mutu a lokacin. Kada ki tura min novel waje idan kin turawa wata ubangiji yabi mun hakkina a kanki yar uwa ma hadu ranan nadama ga bawa. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:24 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MALIK YUMUDEEN, , , , , Har wayewan gari bai sake runtsawa ba don yana barin dakin dakin shi ya koma yayi wankan tsarki ya tada sallah. Ya dade zaune a inda yai sallah yana addua tare da rokon Allah gafara kan kurakuran shi daya tafka a rayuwan shi. Ya dade a gurin yana jero addu,oi sai zuwa can ya mike ya nufi gado don babu abinda yake so a lokacin sai kwanciya ko zai samu natsuwa. Ido rufe ya kwanta sai dai barci yaki daukan shi ya sake bude ido a hankali don surana dake mashi gizo a cikin idon shi a lokacin. A sannu ya kara lumshe ido yana tuna kalamaina a gare shi wanda yake jinsu tankar zuban wuta a zuciyar shi. Anyway zarah kina da gaskiyan ki cin fuska da tozarcin mama a gare ki keda mahaifiyar ki. Dolene su zanci hakan sai dai ba zai danganta hakan da tayi da wani ya zugata tai mashi rashin kunya ba. Don ranan yaji wayan da tayi da mahaifiyar ta kaf a kunnen shi inda uwar bata yarda ta furta komai daga bangaren ta ba, don ta hana yar magana sai huduban da tayi mata kanzaman hakkuri duk yana ji ya gani a cct camera din gidan wanda bai yarda kowa yasan dashi a gidan ba. Yakan tara abinda ya faru a gidan bayanan idan ya dawo cikin dare yake kallon komai dana gudanar a falon da wasu sasana gidan banda dakin kwanana kadai. Dan murmushi yayi a fuskanshi kafin yace da sannu zaki saba da halina zarah. Ada ina tausaya maki da wasu dalilai nawa a yanzu ko na watsar da shakkan komai a raina zan rugumi aurena tsakani da Allah kamar kowa a duniyan nan. Shirun da yaji baiji motsin fitowana ba daga daki ga rana har ya haska a ko ina yasa shi mikewa wanka yayi ya shirya ya sauko ya shiga dakin da yake motsa jikin duk safe rana yayi yau sosai don haka bai wani dade don baiyi komai ba a falo ya yada zango ya dade zaune a gurin kadan kadan yake dago kai ya dubi lokaci. Har lokacin ba dalilin fitowana daga dakin balle in hada muna abin karyawa da zamuyi break dashi. Lazy girl ya fada a fili yana mikewa ya nufi kofan nawa ya samu a rufe sai ya juya ya shiga daki shi gado ya koma ya kwanta zuciyan shi cike da tunanen abinda ya faru a dare jiya tsakani mu. A tsorace na falka daga barcin inda dan hasken rana ya hasko inda nake kwance daga waje da kyat na iya bude idanuwana da sukai min nauyi saboda kukan dana sha daren jiya din. Sannu a hankali abinda ya faru dani yake dawo min a rai idanu na runtse ido sai ga hawaye na silalo min a fuskana. Idon na bude ina bin gadon da yake yamutse da kallo da sauri na daga don tuna irin abinda ya yi din saman gadon dani. A cikin fushi na mike tare da dukawa na sukkuci zanin gaba daya na yaye shi daga saman gadon a fili nake fadi cikin kuka bazan kara amfani da wanan bedsheets din ba a tayuwa ta. Wanka nayi na darje jikina dakyau har lokacin kirji yayi min wani irin tsami sai zafi da suke min na dan gargasu a gurguje na fito bayin. Saida na shirya tsab dani, na gyara gadon dakin dana yaye zanin kai inda nake aje kayan wankina na tara don naso inyi wanki a ranan. Sanin yana gida na fasa fita zuwa lanudry din mu nayi zama a dakin saidai hankalina yana falo ga yunwa ga gyaran gidan dana san yana jirana komai dare. Jin ba motsin sa yasa na mike na sauko daga saman gadon a hankali na bude kofa ina dan lekawa kadan har lokacin gidan tsit take babu motsin kowa. Cikin rashin daga kafa na sauko babu kowa a falon har lokacin kallon falon nayi na gane ya fito da safe kilama ya fitane tun lokacin nace a raina. Dan gyare gyrare na hauyi yayun da na saka abincin jiya a ovon ina dumamawa in karya dashi har lokacin ina yi ina waigen bayana. Saida falon ya koma tsab kamar yadda nake son shi na saka kamshi ko ina na gudan ya amsa na zauna ina cin abincin dana debo. Na kusan kammalawa naji karan budan kofanshi bayan ya gama kallin abinda nake a gidan tun fitowana daga dakina a camera. Duk da naji takon shi gaba na yana faduwa ga kunya da nauyi ya sakani gaba alokacin jin ya matso inda nake yasa na dago kaina a hankali. Na dan dago kaina a firgice ina fadin ina kwana fuska a daure sai yanzu kika fito saboda lalaci daga an dan tabaki kadan matsoraciyar banza da wofi sai bakin tsiya. Ban iya dago kaina na kalleshi ba har ya gama yana fadin ki zubo min abincin in karya kuma ki godewa Allah da jiya kina on da nayi maganin wanan bakin mai bakar magana gidan nan. Sai lokacin na tuna da period dinane yaceceni a gurin shi ashe don kaina bai kawo wutan hakan ba sam. Na mike na bi gefe na wuce kaina kasa har lokacin ban iya bashi sa ba abincin yayi kamar yanzu aka dafa shi sai kamshi ke tashi ko ina ma jera mashi har ruwa na aje mai da zai sha. Ya tako a hankali zuwa dining din ya zauna na juya naba da baya naji yace waike a gida baki koyi bawa miji abinci bane ? Jin kalamin shi yasa na dan jiyo da zuman bakar magana saidai na kasa daga idona in kalleshi har lokacin saboda kunyar da nakeji lokacin nasa. Kizo ki zauna ki zubamin saina gama kuma zaki bar gurin nasu. na dago a hankali don jin sharudan da yake kidanya min lokacin kamar wasu ma,auratan dake da kusanci a tsakanin su. Yadda na kalleshi zaka gane da magana a bakina lokacin saidai ban furta shi a fili ba. Na juya tare da takowa kamar yadda ya umurceni in mai din na bude abincin na fara zuba mai cikin plate din dake gefen shi. Na gama zubawa ya nuna min kujeran dake kusa dashi in zauna saida na dan kalli kujeran kafin injashi baya ina kaiwa zaune zuciyana ciki da tunanen may wanan ke nufi danine sallon wani yaudaran yazo min dashi kuma nake fadi a cikin raina. A hankali ya mika hannun shi fari sol ya kara matso da plate din gaban shi ina jin yana bissimillah kafin yakai abincin ga bakin shi. Cibi biyu yaci ya dago kai ba kunya yace wai kwana nawa kike wanan abin nakune ? Yi nayi kamar banji shi ba na share shi ya kara kai cibi abinci a bakin shi saida ya hade ya kara kallo inda nake yace bakiji bane a tambayan ki ? Ni ban san abinda kake tambaya a kanshi ba ai na fada ina ya mutse fuskana kamar raina a bace yake a lokacin. Ai dole ki fada yarinya don wasan boye ya kare a tsakanin mu yanzu auren mu zamu inganta a gidan mu ta hanyar da zamu kai ga gina rayuwa da samun zuri,a masu albarka a duniya. Jin abinda ya fada yasani na dago na tsare shi da idanuwa na da mamaki waini yau yaya ya zaunar yake min wanan maganan haka. Nace yaya nice fa a gaban ka yarinyar da aikai maka dole a kanta, fatiman da hajiyan ku tace bata kaunar hada zuria da ita don ba, a san asalin uwata ba nice dai din yar agolan gidan ku abin kyamar kowa da, , , , Ke ya isheki haka don Allah wanan wani irin aibanta kanki kikeyi haka da bakin ki kin taba jin wani ya fadi wanan kalman a gaban ki ? Ai ba karya na fadaba don a gabana ansha min gorin hakan don hajiyan su salma ma enough enough zarah. Ya fada cikin tsawa tare da buga table din daning har plate din abincin na rawa kamar zai fado ya fashe. Ita din sa,arkice da kike danganta maganar ta da namu yanzu ko wuyan ki ya isa yankane da har zaki zagan min mahaifiya a gaba ke nan rashin kunyar da ake maki kirari har yakai can ban sani ba ? Ko kina nufin don aurataya ua shiga tsakanin mu har zaki iya kallin tsaban idona kina fadin magana gamay da mahaifiyata. Yaja wani huci kafin ya mike tsaye yana fadin na dauka ai ko ban auren ki zaki iya mutunta iyayyen a ko ina kika tsunci kanki don kema taki mahaifiyar tana da kima a idon mu. Sannan kuma har inkin san darajan aure ba zaki yarda ki fadi wani mugun abu na mahaifiyata a gabana ba don darajan kawin ki da aure da ya shiga tsakanin mu daku. Na dauka wanan kin sanshi tun gida duk wani mutuntawa ga miji shine ka mutunta iyayyen shi ko yan uwan shi. Ko may mama tayi maki a zaman ku tare na dauka zata samu albarkacina ki manta da komai yanzu tunda kina gidan dan ta zaune. Nace ni ba zagin ta nayi ba kuma ba zan taba zagin taba ko bayan idanun ku tun farko kawai dai na tunatar da kaine furcin ta gare mu ai. Do haka ban taba raina hjyn su salma bam kuma fadi wani abu yanzu wanda yake raini a gare ta ba don nima ba zanso a fadawa uwata wani magana mara dadi ba. Baki dauka hakan ba aida ba zaki ta kawo min maganan hajiya a gabana ba ko yaushe magana ya taso tsakanin mu. Idan ma tace bata yarda ta hada zuria dake ba nimai aure naji na gani na yarda in hada mahaifina kuma ya yarda da hakan sai ki barni da ita ai mahaifiyatace ba naki ba ko ? Tunda kin kasa manta abubuwan da suka faru a baya tsakani ku a hakan zamu zauna dake kike tunane a kullu kina kulleda mahaifiyata a ranki ? Ko maimuna da kike fadin muna rainata ita ta taba fada maki akwai raini a tsakanin mu da ita a gidan mu in baki sani bama ki sani yau munfi ganin darajanta bisa ga maman su ikilima a idon mu don har yau bamuji wani abin assha da tayiwa hajiyan mu na rashin mutunci ba a gidan. Na fada maki mu maza zamu iya juyewa a ko wani lokaci daga wani matsayi zuwa wani don haka daga yau bakinki yasan abin fada don ba zan lamunci jin hakan ba a gare ki na fada maki. Yana fadin haka ya ja iska ya fice daga gidan ya barni zaune a inda nake na rike kaina don yau naga bacin rai sosai a idon shi kan maganan dana furta na mahaifiyar shi a gaban shi. Tun ranan sai da muka jera kwanaki kowa harkan gaban shi yakeyi ga matsanancin sanyin da akeyi a kasan kamar zai illanta mutum. Sati daya tsakani ina kitchen ina aikin abinci fitowa na kenan daga daki sai kamshi ke tashi ajikina lokacin ina saye da daya daga cikin tsaraban malasiya daya zo min dashi. Hankalina yana gu abinda nakeyi ban san shigowan shi kitchen din ba a lokacin sai ji nayi an rikeni daga baya an rungumay . Dan firgita nayi don bansan ko waye ba dukda mu kaidaine a gidan dagani saishi daga baya na nasa hakan a raina. Daskarewa nayi a gurin tsaye kamar mutum mutumi ya dan kwanto da kanshi gefen kunnena kamar mai rada yana fadin. Kinyi wankan ke nan kin fara sallah zuwa yanzu yayi magana kamar yana rada kada wani yaji mai yake fadi a lokacin. Shiru nayi ban motsa daga yadda nake ba ban kuma yi magana ba ya kara kwanto da kanshi yana matseni a jikin shi ya kara fadin. Bakiji abindana tambaye ki bane zarah bana son ina magana ana kyaleni hakan zai hadani dake matukar ina magana baki ban amsa. Tambayan ki nayi kinyi wankan hailan ki nace a dan tsorace sai nan gaba har yanzu yana nan bai dauke ba. Dan murmushi naji ya sake kafin ya kara manna jikin shi sosai da nawa kamar zai ballani yace tun bakizo duniya ba nasan wanan babin yarinya . Don haka koya dauke ko bai dauke ba a yau din nan zan karbi hakkina gareki gabanane ya fadi na tsorata da jin kalaman shi da kuma abinda hannayen shi ke mun a jikina. Cikin wani irin murya da tsorata dan hawaye yazo min a lokacin nace don Allah yaya ka barni kabani salama a rayuwata na rokeka. No no no zarah kiyi hakkuri yau ki ban hakkina hakkurina ya kare a kanki zuwa wanan lokaci ki tausaya ki daure in karbi hakkina a gutin ki hakana ? Ina kokarin kwatar kaina daga irin rikon da yai min a lokacin naji yayi murmushi naji ba zan so in tilastaki in maki dole ba . Tunda na rigada na gane baki da niyar bani a cikin sauki kamar yadda nake son bi dake a cikin lumana baki da tauayine zarah a ranki ? Ya tambayeni a lokacin da yake dan dago kanshi daga kafada na da yake kwance kin san ban tare da merry a kasan nan balle ta kawar min da abinda nakeji a yanzu. Kaina na kawar gefe gefe nace idan wane neni banda matsala daku zaka iya binta kasan da take ai ba don ni kake zaune a nan ba dama. Anyway komai zaki iya fada a yanzu do ina neman hakkina a gutin ki yanzu saidai ki sani ba zai yuyu in zuba maki ido hakaba muna zaune a gida daya in takurawa kaina tunda sadakina ya bani hakkin yi hakan a tare dake. Da farko naso mu fahinci juna dani dake ki gane hakan da kanki amma sai naga ke wanan baya gaban ki ko kadan . Don haka zan karbi abina nawane bana wani ba aduk lokacin danaso kuma naga dama a wurin ki in yaso daga baya sai ki dauki wanan akidar da kikasa a zuciyar ki ki yafawa kanki kuma don kina ganin in anyi hakan abubuwa zasu biyo baya a zaton ki . Ganin maganan shi da gaske yakeyi ba gudu baja da baya gaskiyar zuciyar shi yake fadi a lokacin don ya koma min kamar wani zarare dashi nake gani ba kunya ko shayi ko kadan a idon shi namiji ke nan. Ganin da nayi shifa da gaske yake bada wasa bs yasa na sake kokarin yunkurin kwatar kaina daga rikon da yai min a lokacin. Saboda na firgita ainun da abinda yake fadi a lokacin don ba wasa ko kadan a fuskan shi lokacin. Don Allah yaya kayi hakkuri ka barni kada ka rabani da daraja ka wullakantamin rayuwa kazo ka kini daga baya in zama abin dariya a gurin mutane nasan bani kake so ba rashin matar ka yasaka zuwa gareni yanzun din. Ban an kara ba naji ya matseni sosai a jikin shi yana aika mi sakkoni a dukka sasan jikina kuka na fara masa ina magiya ina hadashi da Allah. Amma shi ko a jiki shi lokacin yayi nisa baijin kira saida ya gaji don kansa ya janye daga jikina yana maida numfashi idanuwan shina runtse. Ina jin ya sake ni na fito daga kitchen din da sauri na har ina tuntube da kafet din kofan kitchen din na rugada gudu zuwa dakina. Ina fita ya jingina bayan shi da carvenet din kitchen din yana jin wani irin shauki a tare dashi don bai taba zaton jin gamsuwa a jikin wanan yarinyar yadda yaji ba. Yarinyar daya raina yake mata kallon karamar alhaki sai gashi tun farko taba jikin ta ya shiga wani yanayi daya kasa control din kanshi akanta tun lokacin. Taushi da kamshi jikinta zuwa dukiya kirjin ta ya sa ya raja,a daya kasa kama kanshi akanta yanzu yanzu ya gaskanta maganan Yusuf yola da yake fadin kai kake daukata yarinya. Ita mace bata da kankanta ai yadda ka rainata saita baka mamaki idan kaje gareta sai ka raina kanka. A da yasa a ransa zai daure dukda babu soyayyanta a gare shi zai daure ya sauke nauyin daya rataya akanta shiyasa ya fara tilastawa zuciyar shi zama da ita koda ita din bata da ra,ayin hakan dashi. Da kyat ya iya daga kafa yabar kitchen din cikin dayi jiki ya nufi dakin shi gadon shi ya hau ya kwanta rub da ciki ya rintse idanuwan shi babu abinda yake gani sai suran fatima zarah aruwa sayadin mamu a lokacin. A dakina ina shiga na rufo da zumar murza key a kofan sai dai babu shi babu alamashi gutin haka yasa na rufo kofan da karfi na nufi gado na fada zuciyana cike da tsoro da fargaban yaya da wanan sabon yanayin da yazo min dashi yanzu. Sam ban kawo rashin ganin key dina a lokacin yana da nasaba da yaya ba don ba mutum bane daya kula da shiga min daki babu dalili tun zuwa na gidan key din yana makale a jikin kofan. Na dade kwance a dakin can na tuna da girkin dana dora a gas da sauri na yunkura cikin sanda na nufi kitchen ban ganshi a falon ba na shiga kitchen din na samu ya rage min karfin gas din. Sauri nayi na kammala na gyara gurin don kada ya dawo ya riskeni ciki ranan a dakina naci abinci nayi sallah ina gamawa hutu muke na danyi karatu na shiga nayi wanka don akidanane yin hakan ban iya kwanciya banyi wanka ba tun a gida na saba da wanan wankan daren. Na fito har lokacin jikina bai sake ba a gidan tunda nasan yana gidan lokacin don ba inda zai tafi din yanayin sanyin da kasan ke ciki mutane in ha dole ba basu faye zirga zirga zuwa ko ina ba. Bayan na kammala shirina na kwanta har barci ya fara zo min sai lokacin na tuna da ban rufe kofa ba don gujewa yaya ranan don a da haka nake barin kofan koda baya gidan ma. Tashi nayi na fara tunanen ina key din kofan ya shiga duk iya neman da nayi mai ban iya ganin sa ba a dakin. Haka na koma na kwanta jiki a sabule naja bargo na rufe jikina dashi har kai sannu a hankali barci ya fara daukata. Banji shigowan shi dakin ba don barci ya fara daukana a lokacin ya shigo dakin ya tsaya yana kallon yanayin dana kwanta din a tsorace nake da alama. Fitalan dakin ya kunna haske ya gauraye dakin ga baki daya zubur na bude idona daga barcin daya fara fisgata na bude idona na sauke a kanshi. Yana tsaye ya harde hannayen shi ya zubamin idanu akaina ba wasa ko wani sayina fuskan shi yace ki tashi kiyi alwala sallah zamuyi. Banga fuskan yin musu ba a lokacin na tashi kamar yadda ya umurceni ina tafiya kamar zan fadi don tsoro a lokacin. Sai dana dan bata lokaci zuciyana cike da tsoron abinda zai faru a kaina wanda ban sani ban taba zaton haka zaizo min ba. Har na fito na samay shi a tsaye a tsakar dakin nawa ya kurawa wuri daya ido kamar mai tunanen wani abu a ranshi jin karan budan kofana bai tsaya ba naga ya nufi saman sallayata. Jiki ba kwari na fara neman abin sallahna na saka lokacin naji ya tayar da sallah ko. Raka biyu mukayi saidai don dogon surar da yaja muna a lokacin yasa muka dan dauki lokaci muna sallah. Mun idar ya tsaya addua a baiyyane godiya ga Allah da neman zaman lafiya da zuri, a masu albarka ya shafa nima na shafa. Naji ya ambaci sunana a hankali haka yasa na dago kaina na dan kalleshi kafin yace zarah ki kwantar da hankalin ki ba ha,intarki zanyi ko wani abu ba idan nayi hakan na zalunci kaina na zalunceki riban mai zan samu a yin hakan. Ki tashi mu kwanta ba komai zan maki ba kwanciya kawai nake son muyi tare har zuwa ranan da zaki bukaci ban hakkina da kanki. Kuka na soma yi sosai a lokacin ya dago tare da dafa min kafadana ya kara matsowa gaf dani har ina juyo numfashin shi a lokacin. Kidimaiwa nayi lokaci guda don gaba daya ya juye min daga yaya ya koma min wani abin tsoro yanzu s rayuwana. Ban san lokacin dana kai kaina a kadan shiba ina kuka ya dade zaune yana sauraren kukan nawa bai hanani ba. Harsai da yaji na sau#uta kukan ya mike ya dauke ni sai saman gado tare da kashe fitilan dakin yana sauke numfshi a hankali. ZAINAB IDRIS MAKAWA NOVEL DIN KUDINE DON ALLAH KI KIYAYI SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA 16/11/2021, 23:24 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IYYAKA NA ABBUDDU WA IYYAKA NAS,TA,IN, , , , Tun lokacin daya fahinci barci ya dauki ni yayi ajiyan zuciya tare da kallon yadda nake sauke numfashina a wahalce har lokacin a tsorace nake da abinda ya faru tsakani dashi din a wanan daren. Jin ajiyan zuciyana a cikin barci yasa ya dan rungumay ni zuwa jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a hankali tare da fadi a cikin ranshi. Zarah kin shayar dani mamaki a rayuwata dama hausawa sunce samun abin kwarai wahala gare shi. Wahalan da yasha da zuciyar shi da tashin hankalin mutane da dama daga ahalin shi ma duk akan cikan wanan burine na mahaufin shi. Lalai hausawa sunce abinda babba ya hango yaro yaro ko yahau tsauni ba zai taba hango shi ba tabbas daddy yayi gaskiya wurin dawo da rayuwan shi ta asali. Tabbas ance kowa yabar gida gida ta barshi duk daba wai ya taba wani abin asha ba a rayuwan shi saita hanyar sunna. Zai iya cewa matan hausawa daban suke ashe ko ta jinsin su yau sai yake ganin kamar farkon shiga jikin wata mace ya fara a rayuwan shi don irin ganima da ni,ima da natsuwan daya diba a jikin yarinyar daya raina da farko. A fili ya furta Allah ka yafe min daddy na tuba nayi kuskure ka yafe min daddy naso in yaudari kaina in yaudare ka. Ashe ba zabin banza kai muna ba daddy ka fimu sanin abinda bamu sani ba a rayuwan mu yau da nabi ra,ayin mama na bijirewa daddy da na yaudari kaina ashe. Da kyat ya samu ya dan runtsa idon shi barci ya dan daukeshi kadan da asuba alarm din wayan shi ya tayar dashi don sallah. Firgigi ya falka yana kallona har lokacin barci nake ina sauke ajiyan zuciya saboda kukan dana sha. Ya mike yana tunane a ranshi kodai zalaman shi yasa yajinwa yar mutane ciwo bai sani ba in ma zalaman ne yasan yayi mata haka kanta daren jiya zai iya cewa matsuwan shice ta ja mai yin hakan don a matse yake a yan watannin nan yana bukace da bukatan shi. Har yakai bandakin ya shiga don yin wanka yaga wurin a tsabtace kamar inda ba,a amfani dashi ko yaushe komai na gidan yana nan tsab dashi don tsabta zarah badai tsabta ba . Duk tsaba da kulawan shi saida ya yabawa tsabta irin na zarah a rayuwan shi yarinyace zarah karama amma tarbiya data samu a gida yasa ya fara kwadaituwa da halaiyan ta. Don irin yadda ta iya boye sirin su tsawon shekara biyu da rabi ba wanda yasan alakan auratayan dake tsakanin don dokan daya saka mata kawai. Tasan idan yana gidanta ta ciyar dashi yadda ya kamata sai dan gyaran da yai mata kadan wanan kuma yasan karancin shekarunta ne ya hana ta gane hakan. Har ya fito daga wankan bayan ya hada ruwa masu zafi a ciki har lokacin ina kwance ina batcin wahala. Sallah ya tayar a kada ya makara yana idarwa ya nufo gadon ya ya dan kira sunana a hankali haka yasa na dan motsa ganin da yayi ban da niyar tashi yasa shi sukutana a cikin barcin na danyi kara ina fadin a wahalce don Allah yaya kayi hakkuri na dauka wani abin zai kara yi min kuma. Saida ya tabbatar da na zaunu da kyau a cikin ruwan dumin ya bar ban dakin zuciyar shi cike da tausayina a lokacin don kawai baida zabi ne har hakan ya faru tsakanin mu. Don saboda da shakuwan da mukayi a dan zaman tare sai yake jina wani bangare na zuciyar shi yanzu. Sauka yayi zuwa kitchen ya hada min tea mai zafi da kauri tare da dauko magani a dakin shi ya nufo dakina har lokacin ina zaune na kasa anyanawa kaina komai a bandakin sai kukan da nake wanda ba sauti ciki. Muryan shi naji yana fadin ba zaki fito hakana ba lokacin sallah yana shigewa ko sai nazo nayi maki da kaina. Jin hakan nasan yanzu ba karamin aiki bane gare shi don zai iya yin hakan tunda ya furta hakan a fili. Da sauri na dan cudanya jikina yadda addini ya koyar damuyi ji nayi ba zan iya kara sanya zanin dana kwanta dashi ba na dan leko kai daga ban dakin sai na ganshi a tsaye ya ban baya kafita in dauki zanina don Allah na iya fadi a lokacin. Da sauri ya juyo don jin abindana fada yana fadin a ina zanin yake in miko maki nidai ka fita don Allah in dauka da kaina nace cikin dan muryan da bai fita. Baiyi magana ba sai naji ya juya ya fita da sauri na fito na dauki zani na daura na saka hijjab din sallahta na tayar ina idar a lokacin kuma abinda ya faru tsakanin mu ya dawo min a raina tiryan tiryan wasu hawayene suka ziyarci idanuna bal,bal,bal lokaci guda. Kuka sosai na zauna nayi ni kadai a dakin mai faruwa ya riga daya faru a daren jiyan saura in tsura ido inga sakamakon da zai biyo bayan abinda ya faru din tsakanina da yaya yanzu. Tun da har mahaifiyata ta kasa ban zabin kaina na matakin dana dauka da nake ganin zai fitar damu daga manufan su maganan ta kullun nakira ko takira shine inbi umurnin mijina in mashi biyyaya ma,ana dai in mika kaina a gareshi a fakaice . Nasan yanzu sunana karamar bazawace a gurin shi kai ba wurin shi bama a gutin kowa dana sani don ba yadda za ayi indai ba hjyn su ce ta janye maganan ta akan mu ba ya zauna dani har madi. Tau yau dai na mika saura mamu da kawu dasu amma su saurari hukuncin abinda zai biyo bayan umurnin su yanzu gareni. Haka na zauna ban iya tashi a gurin ba balle duk motsi sai na runtse idanuna don ciwo da nake ji a karkashina har a cikin raina nake jin shi lokacin. Ina zaune ina ta sake sake a raina in kulla wanan in warware ni kadai a dakin na kudundune kaina da gwiwa na. Muryan shi danaji yasani razana da sauri na dago kaina fuska shabe shabe da hawaye ido ya kurawa yanayina ido a hankali ya kai tdugunne a idana nake zaune. Dan rungumoni zuwa jikin shi yana fadin oh sorry zarah don't cry again don wanan abin ya faru tsakanin mu kike zubar da hawaye haka ? Makin ki godewa Allah da ya tsareki ya baki ikon sadaukawa dan uwan ki da wanan abin mafi daraja ga mace. Don't cry again kukan nan naki yana taba min zuciya matuka ba sai kinyi kuka zan gane abinda nai maki bada sin ranki ba and kuma wanan kukan yana nuna min irin kiyayyan da kike mun a filine zarah. Ban iya magana ba ban kuma dago kai na kalleshi ba jin nayi shiru ba amsa ya mike tsaye a hankali ya dagoni daga inda nake zaune a takure. Bakin gadona ya kaini ya zaunar dani a hankali ya mika hannu ya dauko flask din shayin daya hado min ina kallo ya tsiyaya a cup ya miko mi yana fadin karbi kisha sai kisha magani don jikin ya rage maki tsami. Da kyat na iya bude baki nace dashi na koshi cikin muryan kuka kin koshi damay yaci yana kallona . Maza karbi nan ki shanye in baki magani ko kuma ranki yanzu ya baci a dakin nan jin yadda yake magana fuska a daure yasa na mika hannu da sauri na karbi kofin shayin na fara kurba kadan kadan saboda banjin dadin shi ko kadan a bakina. Yana tsaye ya dora hannayen shi saman kunkurun shi ya rike da hannu biyu haka yasa corth din jikin shi fara dan dagawa daga baya ta yadda zaki iya hango zanzaron shi da farar rigar shi ta ciki. May zakiyi yace yana kallo na fuska na yamutse nace nakoshi yace kina wasa da nine zarah ki shaye nace sai ki sha magani fuskan shi a daure. Don dole na mayar da cup din a bakina ina kurban shayin a hankali yana tsaye ya kura mi idanu kadan na rage cikin cup din na aje saida ya kalla yace wanan fa na maiye kika rage. Da kyat na iya budan baki nace mai wanda zan sha maganin dashine sai naga ya juya zuwa inda ya dauko flask din magani ya dauko yana barewa kwara uku buyu iri daya guda daya kalan shi daban ya miko min na amsa ina juya kafin in watsa baki ina bata fuska don dole na hade da kyat. Ko ke fa yarinya da raki haka don't be lazy don mijin ki jarumi ne shi don haka ban son mata ragguwa daga dan tabaki kike wanan rakin haka. Aini ba yar iska bace nace a hankali yace niko dan iskane amma fa da matana don haka saiki shirya koyon iskanci daga yau. Zaki iya kwanta ki huta zan dan fita in samo muna abinda za a ci anjima yace ba tare da ya tsaya jin mai zance ba ya fice daga dakin. Nabi bayan shi da kallo ina maida kaina ga filon dana jawo a kusa dani don ban son yin dogon motsi a lokaci. Bayan ya fitane ya duba motar shi idan tana fita ganin kankaran ma kara rufe motar yayi lokacin yasa ya hakkuri ya tare taxi zuwa inda ya nufa. Barci nayi sosai daga kwanciya na don haka bansan lokacin daya dauka bai gidan ba sai wajajen la,asar ya dawo har lokacin ina barci. Tayar dani yayi inyi sallah lokaci ya kure ban koyi azahar ba haka na daure na tashi na shiga bandaki ruwa masu zafi kwarai na hada na kara shiga sai naji dadin jikin nawa a lokacin na dan dade zaune a ciki kafin in fita in daura alwala na fito naji dadin jikin nawa ba laifi don ya rage min yadda nake jin shi da farko. Yana fita falo ya koma yaci abinci sai kuma ya zauna waya da wata kawar merry data kirashi tana tambayan dalilin daukewa merry da yarta kafa da yayi ? Don merry taki kiranshi don tasan shi da kansa zai nemai ta idan yana da bukatanta duk zai kare fushin shine su dawo daidai don bai iya broke da ita. Bai fada mata komai saicewa da yayi is a family issue don haka ba maganan su bane. Yana gamawa ya aje wayan yana juyawa sai wayan ya dauki wani kiran kuma ya dauka itace sai ya dauko da zuman cewa ta barshi kada ta kara kiran layin shi. Saidai baikai ga hade fushin shi ba mamaki ya kamashi ganin sunan mai kiran shi a fili ya furta mama ya dauki wayan. Gaisawa sukayi a mutumce da farko kafin dan shiru ya biyo baya sai can hjyn ta kawar da shirun ta hanyar tambayan shi yaya iyali ya amsa da suna lafiya mama tace kadai ki kawo min takwarana har wanan lokacin in gane ta. Yace zamu zo mama in Allah ya yarda har lokacin yana mamakin kiran mahaifiyar tasu a yau. Baza kuzo ba don kada na tursasa ma ka saki wanan yar banzan yarinyar daka lakawa kanka na fadama ba zan hada zuria da wanan iri tsiya ba a jinina . Haba mama kiyi hakkuri ki bar wanan maganan haka ki barwa Allah dalilin shi nayin haka a kan mu. Rufa min baki mara kunyar banza duk bare baren da kakeyi na na sani bawai ban sani bane don magana bai biyuwa a gidan nan. Uwarta ta mayar dakai saniyar tatsa yanzu sun samu wurin ci tunda na ubanku ya kare yanzu shi yasa tun farko naki wanan abin don nasan idan sun samu namiji ya zama bawan su. Mama akan mai zanyi wani bare bare matar nan fa yarta na a hannuna akwai nauyi a tsakanin mu yanzu fiye da da can baya tunda ina auren yarta. Yarta na gidana zaman matana ace kuma ko gausuwa ba zamuyi ba da ita ai abinda nauyi mama danne hakkin yayi yawa mama. Babawo kasan mai wanan furcin nake yake sakani yanzu a gaba har zaka iya kiran wanan yar da wai matar ka ? Da kasan yadda naji a yanzu da wanan kalamin naka haka da baka furta min ba har yaushe ta zama matar taka kuma ? Ina kace min ba a gari daya kuke da ita ba ba ruwanka da ita rufa ido kawai kake ma mahaifin ku kadai sanyata karatune kawai. Mama amma ai na baro gida da itane da sunan aure ko in banda ke ai ba wanda na fadawa gaskiyar zancen. At list ko bata karu dani da komai ta karu dani da karatun da takeyi don fushin daddy ya rage a kaina sai ya dauka laifinsu ne. Kai babawo kana jina ka turo masu yarsu gida nake bukata yadda suke bakanta min rai a nan da uwarta da duk wani dangin Alh suma suji a jikin su. Yace mama ai saura dan lokaci kadan ta karasa karatun ta gaba daya kinga sai na tarkatota in turo ta gida zuwa lokacin. Amma yanzu tunda bata kare karatun ta ba ai kinga dawo min da ita za ayi nan kuma zaune bai kare muna ba ke nan kuma. Babawo bakan yadda na tsani wanan yar ba a rayuwata naki jinin wa yan nan mutane wallahi balle har in hada iri dasu kai ni wanan matar takama tafi soyo min a rai bisa ga yarinyar nan Fatima. Mama na gane mai kike nufi ai ki dan ban lokaci kadan ya rage komai yazo daidai ai naji tace cikin isa tare da fasin matsiyata ai ko banza saida suka karu damu da wanan karatun daka sakata yi. Ba komai mama kiyi hakkuri komai zaizo daidai a daidai lokacin ya dago kai mukai arba duk da fitowana ke nan daga dakin bai hana in fahunci da mahaifiyar shi suke magana ba lokacin don jin karashen maganan su. Ya samu ya lalabata ta yadda ba zan iya fahintar komai ba lokacin sai bayan ya kashe waya ya dago yana fadin ki sauko mana kinja kin tsaya kuma nan. Kamar in juya in koma saidai da ya riga da ya ganni a lokacin don haka banda zabi na tako a hankali ina saukowa daga saman benen. Nazo na samu wuri na zauna dan nesa kadan dashi zuciya ta sai fadi nake shike nan ta faru ta kare dama hjyan su ce ta matsa ya lalatani ya sako ni ashe ? Ya jikin naki maganar shi yasani dagowa firgigit daga tunanen da nakeyi a lokacin nace a hankali da sauki . Zaki iya tashi ki zuba abinci ko na zubo maki zan iya nace mai ina kokarin tashi ina cije baki ya bini da kallo kafin yace ko mu tafi asibiti ne a dubaki ? Naji sauki na bashi amsa ba tare da na juyo na kalleshi ba na nufi kitchen din kai tsaye. Abincine lafiyayu masu tsada da bazasu lalace ba kwalaye da yawa kala kala ya sayo ya aje a kitchen din ma,ana zan kwana biyu ban girka muna abunci bake nan. Dan tsankwaro abincin nayi na fito ban nufi dining inda na tashi na zauna ina cakulan abincin a hankali. Ya sake dago kai ya kalleni yana fadin wanan abincine ko shirmay wanan din zai kosar dake ? Kinsan yanzu abincun da zai gina maki jiki mai kyau ya kamata kitche shiyasa naje halal store na sayo maki wa yan nan din don sune daidai kici kwana biyu don ki helling. Ban dai dago kai na kalleshi ba ko in tanka mai naci gaba da cakulan abincin ina kaiwa baki a hankali. Wayana ya dauki ruri na dan kalla ga mamakina mamuce ta kirani naso share wayan sai naga ya dago ya kalleni yana fadi bakiji bane wai ? Wayan na kalla ina ya mutse fuska na dauka tare da sallama ciki ciki babu sauti ina fadin mamu ina wuni yayi saurin dago kai ya kalleni. Sai kuma ya dukar da kai yaci gaba da zanen shi a board ya maigidan naki sayadi ta tambaya nace lafiya. Bata saurareni ba tana fadin yanzun muke kallo aka nuna yadda kankara ke ta,adi a garin ku shine nace bari kiraku inji idan da sauki wurin ku ? Nace ai kuwa kawai da ganin yadda ya dago kamar baiji dadin yadda nake amsawa din ba sai ta tambayeni waiko lafiya kike sayadi ? Lafiya,lau na karasa da kuka da sauri ya dago kai yana fadin mainene haka a hankali ta yadda ba zata jiyoshi ba. Mamu a cikin fada take fadin ki godema Allah, Allah baki miji salihi sayadi don da wanine wanan iya shegen da kikeyi na shagwaba da bai daukan maki shi ba wallahi. Nasan Umar sosai nasan halinsa sayadi Umar mutum ne mai hakkuri da sanin ya kamata mutanen da basu sanshi bane suke ganin shi shu,umi. Kawun ki yasan da hakan kullun yana godiya ga Allah kasancewarki matar umar kibi mijin ki sauda kafa sosai zaki ji dadin shi sayadi. Banda shakkan komai akan auren ki don zuciyata ta yarda da wanda kike aure sayadi don haka ban yafe daki sabawa mijin ki ba ta hanyar aurataiya kinji na fada maki. Sunkuyar da kaina nayi kasa lokacin sai hawayeb dake min ambaliya har yana diga daga cikin idona lokacin don haka ki natsu kiyi biyayyan aure don shi kikaje yi ba wai ki raja,a akan karatu ba kawai. Nasan yaya na jin mu don shirun da falin yayi lokacin koda baiji duka ba yana jin wani abinda take fadi ta kare da fadin ni zan kashe ki gaida mijin naki idan ya shigo ubangiji ya kara albarka kice ina masa godiya don Allah. Kamar in ce tamai mamu saidai babu halin yin hakan a lokacin tayi sallama ta kashe wayan har lokacin hawaye bai daina fito min a idanuna ba don takaici da dacin da nake ji na kowa har mamun dake yabon sa yana ji. Saidai ban san hakan karin daraja uwata bane a idon shi don dana dan dago na saci kallon shi yana zaune ya bar abinda yake idanuwan shi a lumshe da gani yana cikin yanayin tunane mai zurfi a lokacin. A raina nace ji munafuki kamar gaske kai namiji dai muna fukine ashe da gaske yanzu fa na gama jin sunayi dani da mahaifiyar shi. Niko ga nawa uwar tana yabon shi kamar ya biya mata makka shidai yaya tunane zancen su da mahaifiyar shi yake ta yaya mama ke son in wullakanta masu ya ta gama zagin su uwarta kuma ta kira tana yabona da sa yarta ga hanyan daidai. Sam ba zai iyaba yanzu ma ya fara zama da yarinyar nan idan mama bata sani ba yanzu ya fara sanin wacece zarah a shirye yake da ya saudakar da duk wani fitina da zai biyo baya idan an koma gida shi yasan irin shawaran daya yake a zuciyar shi ya kuma barwa cikin shi komai. Bai kulani ba harna gaji nabawa kaina hakkuri don dole sallah ya tayar damu do lokaci yayi dakina shiga nanma sai dana dan gasa gabana don ruwan dumin dake min dadi idan na shiga. Bayan na idar da sallah ban fito ba na haye gadona na kwanta sai faman tunane da nakeyi ni kadai a daki. Kofan ba wani kara yakeyi ba idan an shigo dakin sai idan mutum ya kula sosai zai gane an shigo amma shi da yake shike da gidan sa yasa taba kofan ko wani lokaci aka taba din. Ya dan tsaya tsaye yana kallon yadda na kwanta rub da ciki na lafe saman gadon ya dan yi murmushi yana fadin . Nasan ba barci kikeyi kina jina ki tashi kici abinci mu kwanta tunda barci kike ji yau. Shiru nayi ban dago ba daga yadda nake kwance dake fa nake magana zarah ya fada da dan karfi nace ni koshi ciki ciki to ki tashi mu koma dakina daga yau a can zamu dinga kwana tare don ba zan yarda inada mace a gida mu raba dakiba ba wani dalili mai karfi. Cikin dan marairaicewa nace don Allah yaya ka barni nan yace gardama zaki mun tuno da ban yafe ban da mamu tai min dazu dazun nan yasa da sauri nace a, a yaya. To ki tashi ina jiran ki a dakina ya fadi yana fita tun kan ya karasa fita nace ni kan yau na mutu na lalace a gidan nan. Bai juyo ba saidai ya wuce yana murmushin magana ta a fili don shirmayna dariya ma ya koma bashi yanzu. Na dade a kwance ina sake sake a raina kafi in daga a lalace na koma bandaki nayi tsarki da ruwan zafi tare da dauroyo kaina kamar yadda nake kula da mamu idan zata turaka tanayi don wani lokaci ina zaune muna hira zaitai ta faman lakace lakace da shafe shafe ina kallon ta ashe kallkn zai mun rana watarana ban sani ba. Da kyat naja kafa na nufi dakin ina rabe raben bango na tura kofan a hankali na shiga ban samay shi a dakin ba haka yasa nabi dakin da kallo a hankali duk da dakin ba bakona bane saidai a kwai sauyi sosai ga dan kwana biyun da banshigo ba mamakine ya kamani sosai a lokacin. Dan gyara muryan shi naji daga bayana inda hakan yasani nadan firgita kadan haunun shi dauke da plate da goran ruwa da cup. Na gane nufin shi haka yasa na dan yamutsa fuskana kadan bai min magana saida ya aje abincin saman dan karamin table din gaban miro tare da jawo shi zuwa bakin gado ya aje goran ruwa a gefe daya ya kalkeni yana fadin oyo zauna kici kafin in fito. Ni na koshi ina batarai don damuwa yayi min yawan da ba zan iya boyewa ba a lokacin ashe kina da aiki babba gamay dani. Idan baki sani ba yau ki sani ba aimum mussu ga magana idan na fada final ne idan kuma kin ki bi kisha wahala . Yana fadin haka naga yana kokarin sance igiyar dake daure a rigan shi duk rabin kitjin shi yana waje dama da sauri na kawar dakaina daga kallo abinda yakeyi din. Nakai fuskana ga abinda ta aje min kazace taji hadi tana tururi gunduwa uku saidai manya ne yankan kwarai ko daya ba zan iya cinyewa yadda nakejin dandano bakina ya canza min. Hakana na daure ina dan yaga a hankali ina hadewa da kyat duk so kazan da nake wanan yaimin ba dadi a baki. Ya fito ya dan tsaya gaban mirro yana dan lakace lakace kamar mace kafin ya juyo gurina saida ya kalli plate din ya dago ya kalleni takowa yayi zuwa inda nake ya zauna daf dani kafin ya mika hannu ya dauki fork din ya da yuka ya yanko ya mika min kawar da kaina nayi gefe . Sai naga yama mayar dani karamar yarinya a lokacin fuskan shi a hade yake dole na bude bakina ya sa min yanka na uku na dafe bakin sai hawaye naga ya girgiza kai kawai ya aje fork din da yukan kawai ya mike da kayan zuwa waje saida yakai kofa ya juyo yana fadin ki kwanta kawai. Ban yarda na kwanta ba har lokacin daya dawo gani a yadda ya barni zaune ina dan wasa da yatsun hannu na yace cikin mamaki baki kwanta bake nan ? Dan marauraicewa nayi da kaina da murya ina fadin yaya ka barni in koma dakina don Allah wallahi tsoro nakeji kayi hakkuri don Allah. Shiiiii yasa yatsa saman bakin shi yana min alaman inyi shiru ya nuna min gado da hannun da sauri naja nakai kwance na kudundune a wuri daya idanu a runtse. Ban san may ya tsaya yi ba saida ya dauki dan lokaci ya kashe din light din daya rage yana aiki a dakin naji ya hau gadon ya kwanta na kara runtse idanuna a hankali. Saukan hannun shi saman jikina yasani dan zabura kadan zangudu ya rike ni gam a jikin shi yana sauke numfashin da ban san na maiye ba. NOVEL DIN KUDINE DON ALLAH A KULLA NIDAI NA FITAR MAKU DA HAKKINA NA FADA MAKU. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:24 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IHHIDINAS SIRATAL MUSTAKIN, , , , , , , , Sannu a hankali ya umar ya kowa min shakuwa dashi da sake jiki inyi komai a gaban shi ba tare danaji nauyin shi ba kamar yadda muke da farko dashi. A cikin yan kwanaki wani shiri da kaunan juna muke gwadawa junan mu a gidan duk da shi bagwanin son surutu bane amma haka takan biye min ina bashi labaran gida wani guri yayi dan murmushi wani gun yace baki ko kyauta ba zarah shiya ake cewa baki da kunya din tun ban dawo na ganki ba nake jin labaran ki a nan . Sai dai da na dawo nayi nazarin zaman ku dasu salma na dan fahinci wasu abubuwa game daku a baki daya. Nace yaya mai ka fahinta daka fara ganina yace ai kin san kece na farko dana fara haduwa da ita ranan dana dawo ko ? Dan tunane nayi kafin ince haka ko akayi sai na dan turo baki nace ni ai banga kayi kama da hjyn kun bane yasa na tsayama gardama. Zarah wai kinsan a sanadin ki na bata da hjyna da dacan baya nine dan gaban goshin ta kowa ya sani amma yanzu kin sa komai ya lalace a tsakanin mu da ita. Yanayi na yadan canza lokacin da yake wanan magana sai ya ban tausayi ko wanan zuwan danayi duba daddy na dauka abin zaiyi sauki zuwa lokacin ta hakkura dake amma sai na samu abin ba haka yake ba a gurinta haryanzu. Cikin sanyin jiki nace abinda nakewa gudu tun farko ke nan yaya gashi yanzu shakuwa da , , , sai nayi shiru yace damay fa ki karasa mana kinyi shiru ?. Barshi kawai yaya na fada yace ai baki isaba ba kince baki da kunya ba sai kin fadamin shaku damay ya shiga tsakanin mu yanzu ganin ya tsatsareni da manyan idanuwan shi nan nace sabo dan murmushi naga yayi yana fadin ashe kina da saura ke nan tunda kin kasa fadin abinda kikai niya. Tambayan dana jefo mai yasa ya dago don duk hiran da mukeyi kanshi a laptop din shi yana aiki a ciki nace yanzu yaya ana nufin zaka sakeni ne idan mun koma gida ko may ? Da sauri ya dago kanshi yana fadin wanan banzan tambayan ina ya fito maki haka ni ba namiji bane mai sakin mata hakkuri mama zatayi ta barmu tare. Ke dai abinda nake son ki dashi shine kada ki yarda da duk abinda mama ko yan uwanta ko nawa yan uwan zasuyi maki kimasu rashin kunya don ba zan iya lamuntan hakan ba ga matata ta raina min yan uwa ko iyayye don haka ki kula da wanan . Komai nisa da mama da nakeyi a yanzu nasan wata rana haduwa zamuyi dani dake da ita a lokacin abubuwa da dama nasan zai faru so ba zanso ace wai matana tanawa uwana rashin mutunci ba ko kadan. Shiru nayi kamar mai nazari lalai va karamin so yakewa mahaifiyar shi da yan uwanshi nasha jin Amma na fadin haka akwai shakuwa sosai a tsakanin hjy jummai dayaran ta. Wanda har hakan yasa kowa ya jaye ya barta dasu don ita din bazata bar wani ya fadi laifin diyan ta ko kadan ba a gaban ta. Shiru nayi ina cigaba da nazari a raina nasan akwai aiki babba a gabana kan zama da yaya umar nan gaba ta bangaren mahaifiyar shi da wurin matar shi merry da a yanzu na gama fahintar akwai matsala a tsakanin su do merry din banjin tana kiran shi shima hakan bai kiranta kamar da da mintuna kadan zanji dayan su ya kira daya a waya koda a ganane suna soyewar su. Shin hakan na nufin damata ke nan ta hanyar batawan shi da merry shine silar kulawan da nake samu a wurin shi yanzu. Lalai namiji abin tsorone ga mace gashi dai yanzu yaya ya mayar dani tankar wata sarauniyar ruhinshi zakace bai taba son wata mace ko sanin wani soyyaya da mace a baya sai wanan lokacin . Zanbi a hankali har in gama nazarin in fahinci inda ya dosa dani a rayuwan shi don dole sai nayi taka tsamtsam so kada in fada a tarko daba zan iya fitar da kaina ba akanshi. Ganin ya mike daga inda yake zaune yasa na dago kai a hankali ina kallon shi ki dubi lokaci magariba ya gabato kin zauna kina tunanen banza. Mikewa nayi zuwa dakina inda na gabatar da salloli har da isha,i bayan nafila wanka nayi kafin in sauko kamar yadda ya koyar dani cin abincin dare a tare dashi. Tun ina matakalan benen mai hawa daya ya kura min ido har saida hakan yasa na dan tsargu da kallon da yake min din. Gaida shi nayi ya amsa yana lumshe idanuwan shi na wuce kitchen na hado muna abincin na kawo saida na gama aje komai na juya ina fada mai nagama hada wurin. Mikewa yayi a cikin yanayin shi rashin kuzari ya tako zuwa table din ina duke ina zuba abinci a plate naji yakai hannun shi saman west dina. Dan zabura nayi kadan bai damu da reaction dina ba yaja kujera ya kai zaune abincin ya kurawa idanu har na gama zuba nawa naja kujera na zauna. Sai lokacin na dan dago na kalleshi da alaman lafiya a idona kai ya girgiza min yana fadin ba wanan abincin nake so ba yanzu. Zarah na dauka zaki fahinci halin da nake cikine yau ki lissafa satin mu biyu cif da ki ban hakkina nayi hakkuri ko keda kanki zakiga dacewan hakan ki bani sai dai banga alaman hakan ba agare ki ko yanzu. Tunda ya fara maganan shiru nayi ina dan cakula abincin dake gabana na kasa kaiwa a bakina jin yayi shiru na dan dago kaina kalleshi shi din ni yake kallo a lokacin. Yace na dauka kinsan mu maza bamu da dauriya a wanan famnin gashi ni ban iya neman mata ba balle in nema a gurin wata waje. Da sauri na dago kaina dan kalleshi jin abinda ya fada yanzu hakkuri na ya kare akan ki zarah ke kuma na fahinci raguwace a wanan fannin sosai ya zama dolr ki daure ki ban hakkina akoda yaushe don nima mutum ne mai jini ajika. Ma,ana nidin namijine mai bukanta mace a tare dani yana daya daga ciki abinda yasa har na auri merry a lokacin don in kare kaina daga zina. Ba don naso ba dole ranan saida na sadaukar da kaina a guri shi na hakkura na kyale shi yayi yadda yake so dani. Duk iya daurewana na yishi amma a karshe saida nayi raki don na takura da yawa a lokacin tunda ban saba ba. Banji jikiba kamar na ranan farko danaji wanan yadan bambamta kadan da wancan na farko. Nasha albarka a wutin shi tare da alkawura idan har na daure ina faranta mashi rai kamar yadda yakeso dani. Washegari shiya tayar damu da asuba don na kula ashe mutum ne mai yawan addini sosai shi din don wani lokaci saidai in falko a cikin dare inganshi yana sallah ko karatun alkur,ani maigirma a cikin dare. Wanan shi ake ma karin maganan karka yiwa mutum shari da abinda kagani a fili don baka san zahiri shi ba koshi waye ? Bayan mun idar da sallah na yana zaune yana karatu na nufi dakina na fara kimtsawa kafin in fito in gyara falo har zuwa kitchen da sauran wurare a gidan. Dan tsamin da jikina yayi a lokacin baisa na biyewa haka ba ciki dauriya mayarda gidan tas cikin dan kankani lokaci. Daki na koma nayi wanka na saka daya daga cikin rigunan daya sayo min daga tafiya rigan baida nauyi yana da dadin sawa don rashin nauyin shi soft yadi ne sosai. Ban jima da fitowa daga dakin ba shima ya fito muka zauna mukai break yau sai satan kallona yake ina kawar da idona don kunyanshi nake ji a lokacin. Wayan shi yayi kara a daidai lokacin da muka kammala karyawa ya din ya dauka cikin basarwa muryan yarshi queen ne a wayan ban san ita bace sai lokacin da naji ya ambaci sunan ta din.. Dan dago kai nayi ina kallon shi ban dai ji may take fada mai ba sai murmushin danaga yanayi ne yasa nagane wani abu take mai albishir dashi. Abinda naji yace yasa na mike don bashi guri suyi wayan cewa yayi I soon come to see you queen. Ke nan zai tafi guri matar shi nace a raina ashe haka mata ke jin kishin abinda baikai ya kawo a fannin kishi. Saida naje daki na kwanta ina ta sake sake a raina kafin in tambayi kaina a karshe ke yanzu kishi kike ko mai fatima. Dan murmushi nayi a fili nace ke nan na fara kishin merry ko may a raina matar da nazo na samu da mijin ta har yaushe na fara kishin su a raina . Lafiya kika dawo nan muryan shi naji a kaina nace ba komai ina dai son in hutane na dawo daki na kwanta . Kamar bai yarda da abinda na fadi din ba don irin kallon danaga yana min a lokacin. Zama naga yayi bakin gado nawa yana fadin queen ta kirani yanzu tace suna da buki a makarantar su da zasuyi tana kuma bukatana a wurin. Allah ya kai lafiya nace ban bari yaci gaba da magana ba llokacin naji yace amma ai ba yau ko gobe nace maki zanje ba ko ? Idan zan tafima ai tare zamu dake ko nace a,a yaya ba zan tafi ba gaskiya yace saboda may bani na gaiyace ki ba . Gaskiya ba zan tafi ba don suma suna son kadaicewa dakai a lokacin in nai haka kamar na shiga hakkin su ne ai. Wana kuma wani zance kike son kawowa tare zamu tafi don akwai abinda zanyi can idan muje yaya na katse shi ya juyo yana kallona don jin abinda zan fada. Suma fa suna da hakki a kanka kasani don haka ne ba zanje ba don kada matarka ta zargeni da hana mata mijin ta ya basu kulawa. Sannan kuma ka sani ita merry na kulla bata son kusancina da yarta don wani nata fahintar don haka ina rokon ka da ka barni nan Allah ya kaika lafiya. Ido ya tsura min da nake magana azuciyar shi yana fadin yarinya saikace wata babba da iya jera kalamai haka. Mikewa yayi yana fadin tunda nasaki abu har kin kai ki fara min mussu akai shike nan. Yaya ba hakana bane gani dai nayi zan takura masu iyalin kane fa suna bukatan kulawan ka a yanzu. Fita yayi daga dakin batare daya furta min wani abu ba ajiyan zuciya na sauke ina mai ci gaba da tunane a raina. Na sani zuwana tare dashi zai iya haifar da wani fitinan a tsakani shi da merry duk da dai merry bata san akwai aure a tsakani na dashi ba amma tana zargina don bata boye min ba a ranan da mukai masu ziyara asibiti shine gani na karshe da ita harzuwa yanzu din bamu kara haduwa da ita ba. Don a cikin fadsn su ranan merry ke fadin ta fahinci tu zuwa na kasan abubuwa suka canza a tsakanin su koda nake yarinya ai ya kamata in fahinci mai maganan take nufi dani. Tun ina tunane har barci ya daukeni dama ga gajiya a jikina nan na samu na sauke gajiyana sai azahar na falka don alarm din dake kuka a dakin. Har nayi sallah na idar na dan kara gyara jikina na sauko kasa banji duriyan yaya a gidan ba ashe ya fitane lokacin ina barci ya tafi gidan shi. Don yana yawan zagayawa gidan ya duba ya bata lokaci a gidan yana gudanar da wasu aiyukan shi ban taba zaton ma yana zuwa office ba sai ranan da naji suna waya da wani abokin shi. Tafiyan yaya America yasa na fahinci iri shakuwa da mukayi dashi a yanzu don sai naji gidan ya koma min ba dadi gabaki daya ko saukowa banson yi kasa . Don ba karamin koyamin shakuwa dashi yayi a dan kwanakin da muke zaman gidan dole na kariya daga sanyi shi kuma yana more auren shi. Merry tayi mamaki kwarai a yadda ta ganshi ya murje yayi kyau sosai ba wani alaman damuwan rashi a kusa dashi daya nuna hakan. Abin ya dade yana bata mamaki a ranta inda ta fara zargin shi ko ya fara neman matane da har ya iya shareta haka na tsawon watani. Taso fahintar wani abu tare dashi na yadda ya nuna mata in har zata kawo mai rigima ne zai iya komawa abinshi inda ya fito baizo don ta ba don yarsu yazo. Wanan kalamin nasa ya dagawa merry hankali saidai bata yarda ta nuna mashi a fili ba ta barwa ranta abinda ta shirya yi kawai. Ta samu ta lalabashi do itama tayi missing din shi sosai karfin hali kawai take da rashin su har lokacin dai rikici akidar yarsu yananan a tsakanin don yama samu yar ta kara juyewa ga baki daya irin abubuwan daya tanayi din. Tun lokacin da ya isa kasan ya kirani don yaji lafiyata nace dashi ina nan kalau sai dai gidan babu dadi da baya nan. Dan murmushi naji yayi yana fadi gidan ne babu dadi yanzu ke da kikan matsu na baki gidan ki a da can baya. Nace ni ai ban taba fadin hakan ba ko lokacin yace zarah na amsa da naam yace in tambaye ki mana ina jinka ai yace in nace maki a yanzu sona kika farayi zaki yarda ? Nace nidai ban sani ba naji yayi murmushi kadan yace ki yarda da maganata zarah kin fara sona ne har kike ganin gidan idan bani ba dadi a yanzu. Nace ni dai ban sani ba ban ma san wani abu so bacen a rayuwats yayi murmushi tare da fadin zaki sani a sannu may so yake nufi. Nace ban damu da in sani ba a yanzu tunda ban san yadda akeyin shi ba yace kin sanshi ai ko yanzu ada kin taba sanin aure yafi komai dadi a rayuwan bawa ? Yaya zanyi in san haka yaya bayan ban taba aure ba sai yanzu to ki sani aure yafi komai muhinmaci a rayuwa bawa. Kinsan may yasa nace hakan nace sai kafada min yaya wata kila in fahince ka yanzu. Aure shine cikar kamalan mutum , aure shike haifarda fari ciki da natsuwa a ga uwa uba riban da aure ke haifarwa ta samun zuria,a ma,ana magada. Zarah zanso ace kin cika mun gida da yaya kyawawa kamar ki idan haka ya kasance zanfi kowa alfahari da hakan . Zarah a yau dana zo naga queen a cikin wani yanayi na akidar ahalul kitabi na yi bakin ciki da nadaman samuwar ta ta tsatson merry. Da sauri na ce yaya kabar fadin haka addua bai bar komai a rayuwa wata kila har uwar ts gane hanyar gaskiya nan gaba. Ba alaman hakan ga merry zarah merry iyayyen ta ba zasu barta ta musulunta ba da farko na dauka za iya juyar da merry zuwa akidana. Sai daga baya na fahinci wani abu duk inda tasa kafa iyayyen ta ba biye da ita dkn kada ta sauya ba tare da sanin ta ba. Tau sayi yaya ya bani da yake wanan maganan nayi tunane yaje ya samu wani abin bacin raine a gamay dasu a can tunda har ya zaunar dani yana min wanan magana haka lalai damuwar sa takai inda takai masa din sai ina ganin ban isa ba ban kaiba kuma. Zarah yau idan daddy yaji wanan magana da wani ido zan kalle su yau nine na samar da yar dake bin mutanen littafi a rayuwan ta. Kawu ba zai zarge kaba yaya yasan komai mukaddarine ga bawa don haka kabar wanan tunanen shiru naji yayi kafin muyi sallama ya kashe wayan. A hankali na kai kwance daga inda nake ina tunanen magsnan mu da yaya ta yanzu yau nice da matsayin da har yaya zaiyi sharing din matsalan shi dani Kuyi hakkuri da wanan banda lafiya yau wallahi. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:25 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRRATAL LAZINA AN,ANTAALAIHIM, , , , , , Kewan kan naji shi na rashin yaya a gida lokacin sai na gane sabo yana da dadi ashe don abinda yai ta wahalal dani ke nan farkon zuwana kasan da ban ganin kowa na gida a tare dani. Kaina daya damay da kaikayi yasa na shirya don kaina natafi gurin gyaran kai duk da ban son relaxer saida mai shagon ta sharwace da in saka saboda due din da kan nawa yayi sosai a lokacin. Gyaran jiki akaimun sosai a shagon na biya na dawo gida da yamma sosai don ban fita gida da wuri ba. Na dawo a gajiye sallah na gabatar saida na gama na dan saka wando da riga a jikina na sauko don neman abinda zanci. Na gama ina zaune a falo wayana ya dauki kara mamu ce akan layin na dauka da sallama yau ba laifi don ta amsa min yadda ya dace don kwana biyu da suka wuce kona kirata bata wani amsa min a dadin rai. Sayadi abinda nake fada maki ke nan yanzu ga yaron nan ya turo da kudi akai kakarki makka kinga kadan ke nan daga cikin aikin hakkuri gun mace riban shi yana fita ta inda mutum bai taba zato ba. Mamu ban gane may kike fadi ba fa nace mata cikin zakuwa eh a jiya mijin ki ya turo min abokin shi ta hanyar bashi lamban wayana yai mi bayanin duk yadda umar din ke son abin ya kasance ba tare da kowa ya sani a gidan nan ba. Mamu kawunane ya biya mata da sauri tace shi kadai ne mai zarahin yin hakan to wanda baki zatoba shinake nufi Umar mijin ki shiya biya mata. Mamu kina nufin yaya umar ya biyawa manjo aikin hajji a banan nan tace kwarai kuwa sayadi abinda nake fada maki ke nan ai. Wani ihun dadi nayi a lokacin mamu tace har yanzu kina nan da sakarcin nan naki ashe sayadi ? Mamu dadine yai mun yawa tace bai fada maki ba ke nan nace baya ko kasan ya tafi America wurin matar shi satin biyu a can. Tau kindai ji abin arzikin da yai maki saiki mai godiya nace cikin nuna jindadi na dajin wanan labarin mamu ba sai na barima yadawo ba zan kirashi in mai godiya. Da kin kyauta don wanan ba karamin alheri bane gare ki shiyasa nake fada maki shi zaman aure mai karko ba komai bane ke kawo shi sai bari na bari ka tsaya iya inda mutum ya aje ka kada ki kai kanki ga harkan zaman shi da matar shi don a tare kika samay su tundai kema kina samun iya gwargwadon kulawan ki gare shi. Nace mamu na gode ina kokarta yin abinda kike fada min a kullun kin kyata ubangiji Allah yai maku albarka nace amin cikin kunya. Bayan mun gama wayan ne tunane yazo min wai hakan dama shine so ko kauna da nake ji ana fadi don dai nasan babu ko daya tsakanina da yaya . Don shi da kanshi yasha fada min auren mu aure ne da akayishi a bisa kaddara ko dama zama irin hakan yakan iya rikidewa ya koma kauna. Na gwada kiran layin yaya a lokacin saidai layin baya shiga ake fada min dole nayi hakkuri na dena neman shi har sai lokacin daya kirani kuma. Ina shirin kwanciya sai ga kira sai dai alama ya nuna daga kasan chaina ake kirana lokacin nayi mamaki na dai dauki wayan. Muryan yaya Umar ne naji yana fadin badai har kinyi barci ba ko don dare baiyi sosai ba yanzu na sani. Ina dai shirin kwanciya ke nan yanzu yace to ya kike na sauke ajiyan zuciya nace lafiya kalau yaya ya queen da mamanta. Suna lafiya na barsu tun satin daya wuce ina kasan china yanzu mamakin jin haka yasa nace Chaina kuma yace eh ba kince ba zaki tafi ba. Ba haka bane yaya kaima kasan yin hankan kamar izzigiline a gareni ai ya isa yace min tare da fadin idan banyi hankali ba nan gaba sai kice zaki koya min komai akan addinina. Ni na isa ince zan koyar dakai abinda ka riga ka sani yaya ayi hakkuri idan rashin zuwana ya bata makarai ne. Dan murmushi yayi tare da fadin kin wanke kanki yanzu ki kwanta ki huta sosai ki kula da kanki nace insha Allahu yaya zanyi magana akan abinda yaiwa manjo naji ya kashe wayan shi. Wayan nabi da kallo na girgiza kaina tare da fadin shidai yaya bai mai da tafiya wani abu a rayuwan shi yau kaji yana nan gobe kaji yace can yake. Tunane na yakai kan merry nace har ya gama da iyalan shi ke nan daya bulla wani kasan wani zama har yayi dasu a dan kwanakin daya tafi da har yai tafiya daga can. Koma dai mainene ai sunfi kusa don sun saba da hakan kila tashi nayi na kashe komai na falon na nufi dakina. Alwala na dauro nayi shafa,i da wuturri na dade a wurin zaune ina addu,a kafin in mike zuwa saman gadona. Washe gari bayan na idar da sallah na koma saman godo don sanyi yayi yawa sai idan rana ya dan fito nayi aiyukan na gida. Barci mai dadi ya daukeni lokacin ina tsaka da barciname karan bell din gida ya damay ni da ruri don har dakuna zuwa ko ina akai waring din shi. A firgice na falka inda nake kwance ina wani irin mumanan mafalki da salma jin karan ya kara firgitar dani. Duban lokaci nayi shida da wani abu na safe lokacin karan naji yayi yawa na daure na mike da sauri zuwa kasa ban bude ba saida na dan lekka dan kafan kofan. Ya Umar na gani tsaye yana duban agogon hannun shi wata kila lokacin dana bata ban bude ba yake kallo. Saye yake da wando da rigan jeans sai hulan da ya tare fuskan shi dashi da alama sanyi ya damay shi a lokacin don yadda yake takure kanshi a wajen da yake tsaye. Da sauri na bude kofan mamaki karara a fuskana yana jin na bude kofan ya murza hannayen shi guri daya ya shafi fuskan shi sai kuma ya ware hannayen nasa. A daidai lokacin da nake fadi sannu da zuwa yaya yadda ya ware hannayen nasa nasan nufin sa aladole dai sai yaya ya koya min rashin kunya gaban shi. Nadan rausaya kai na fada kamar yadda ya bukata in mai ya mayar da hannayen ya rufe dani a tsakiya yana fadin I am home dear. Dan sunar da kaina nayi saman kafadan shi ina fadin you're wellcome yaya cikin jin kunyan shi dan dagoni yayi yana ja min hanci kadan na kara sune kawaina saman kirjin shi. Can na dago nace yaya mun fayi waya dakai jiya baka fada min kana tafe ba ai. Ina son in baki mamakine ya fada a lokacin da yake sakeni ya juya wurin kwalayen dake aje a kofa ya fara sukkutan su yana dauka. Da sauri nace a a yaya ka baru ni zan kwashe kaida ka dawo yanzu yace no is my duty yin hakan ko baki sani bane. Duk da ya hannani saida na dauko wasu daga ciki na shiga dasu nakai inda ya aje wanda ya fara daukowan. Baki jin magana yace min nayi sauri fadin gaskiya ba zan iya kallo kana daukan kaya ba ina zaune ni . Zaki saba da hakan ai kwana nawa yarage keda kanki zaki bari din ya fada yana ficewa. Ban tsaya ba sama na hau na bude dakin shi yana a gyare tsab don koda bai gari ina gyarawa tun farko. Ruwan wanka na hada na aje mai komai da zai bukata a wurin ina fitowa daga bayin lokacin ya shigo dakin. Barin hada muna break fast da sauri nace ina fita daga dakin kina nan kina barci baki batun abinda zakici ba ko ? Haka kike zama da yunwa idan bana nan ashe nace ban zama da yunwa don ni ban wasa da abinci kamar yadda kake fadan ban son cin abinci kullun. Ganin yana shirin tube tufafin shi a gabana cikin ko in kula da ina wurin wai nayi saurin kawar da kaina na fita. Dan murmushi ya sake kadan tare da fadin silly girl da sannu zan fitar maki da wanan kunyan tsiya haka. Kitchen na nufa cookerorth na hada muna don shi yafi min sauri a lokacin naga kuma yana son sha ko wani lokaci don wani bai kare ba yake sayo wani tun ban iya sha ba har nazo na iya sha daga baya. Don ko a gida haka kawu yana son shi sosai ana yawan dama mashi shi lokaci lokaci ban iya sha sosao idan mamu ta zuba min har tazo tabar zubawa. Ina aiki ina tunane shidai yaya ya zama mai irin dabi,un turawa koda yaushe akidan shi na daban ne motsin shi naji a bayana a inda nake duke . Kafin in dago ya karaso gareni ya rikeni ta baya ya matse da jikin shi ajiyan zuciya muka sauke a tare kusan lokaci guda. Juyo dani yayi a hankali muna fuskantan juna dani dashi yace may kika girka muna hakane shape shape. Dan murmushi nayi nace abinda naga kana yawan sha da safe na hada ma don kada in bata lokaci. Bude bowl din yayi yace ke a wanan yanayin da nake zaki kara dura min madara in sha kuma ? I hope zaki iya daukan lalurana yau ba raki don idan kika bani wanan ehe yarinya zaki dandana kudan ki gidan nan yau. Sam ban gane abinda yake nufi ba da zancen shi nayi saurin fadi yanzu ka daina shan shine kuma ? Ina sha ya fada a lokacin da yake rabuwa da jikina yana zama yace indai kin shirya mun ai shike nan ko ? Ban bashi amsa ba don har lokacin ba fahintar shi nayi ba wanka nayi na fito kwalliya nayi sosai don farauta mashi rai saboda ina son yi mai godiya kan abinda yaiwa kakata. Ido ya kura min tun shigowan shi yake mamakin sauyawana goshina ya haskaka min fuskana nayi wani irin kyau dani don gyaran da nayi jiyan. Wanan gyaran kan ya matukar karbe ki zarah yaushe kikayi shine na amsa da nagode sannan nace mai jiya ina zama naci gaba da fadin kan ya damay ni da kaikayi shine na tafi aka wanke min. Sai an kwana biyu akwai wata yar ghana zanje tayi min kitso a bayan layin nan suke ita da mijin ta. Gyaran ya karbe ki matuka daga haka bai kara fadan komai ba don na samu ya gama karyawa ko lokacin. Ai gyara shine mace don komai tsabtan ka Amma na fadin idan baki gyara kai kin ragu dan murmushi yayi tare da fadin wanan ai komai kina ji a bakinta ita. Sai lokacin na dan dawo kusa dashi na zauna na fasa nufar wurin karyawan da zani da farko ban kuma iya magana ba sai na dan zamo kasa na rusunna tare da fadin yaya Allah ya kara yawan arziki mai amfani yasa albarka jiya mamu ta kirani tana fada min abin arzikin da kaimuna na kakata. Kallo na yayi da mamaki kafin yace may yasa ta fada maki nace ban son kowa ya sani don gudun fitina a gida nayi saurin fadin itama ta kwabeni da hakan fun farko fada min tayi in maka godiya kada a barni a duhu. Kama kafadana yayi yana tayar dani kafin yace ba irin wanan godiya nike so ba yanzu a gurin ki kije ki karya sai ki dawo ki ban goron albishir din. Na kallo shi da mamaki ina fadin goro kuma yaya a ina ni zan samu goro a wanan kasar kuma naga kai ba gwanin cin goro bane ai. Baki san inda zaki samu goro ki ban ba ga abu ajikin ki aini gorona ba wani abu bane illa jikin ki zan mulka . Kunyar maganan shi naji nayi saurin mikewa tsaye zan bar gurin naji ya riko min hannu daya yana fadin ba wasa nake na zarah nayi missing din ki . Kunya naji sosai da abinda yake fadi lokacin ya dan lumshe ido yana fadin jeki karya ki dawo nan na wuce a sabule dakyat nake iya daga kafana zuwa dinning din na zauna. Tunda na zauna ban juyo inda yake ba har na gama saida na gama na dan saci kallon shi kadan hankalin shi baya gurina yana kan wayan shi haka yasa naso gudu in koma dakina ba tare da ya farga da hakan ba cak naji ya rikoni ya dagani sai dakin shi ya dire ni saman gadi bai tsaya jiran komai abubuwa suka faru a tsakanin mu. Ba zance ban wahala ba ranan a gaskiya naji jiki sosai wurin yaya umar don kanshi ya kyaleni yana fadin bari in barki kada anjima in tabaki kice baki san haka ba. Na samu naja kafana da kyat zuwa dakina na gyara jikina sauko ba tare dana huta ba na nufi kitchen hada muna abincin rana. Sai dai sanu a hankali nake jin marana yana dan murda min a hankali sai na dangata hakan da saduwan da ya gama danine da safe yajawo min ciwon maran lokacin. Saidai ina kewaya na sami period ne yazo min a lokacin na tuna dama zan fara expecting din zuwan shi yau da gobe ko a cikin daren yau ya zo min. Sallah da aka hutar dani ke nan banyi ba na kintsa na haye gado koda ya fito ya duba falo har kitchen ban nan ya koma dakina ya samu ina barci yasan ya wahal dani yau sosai anjima kuma yana da bukatana ya barni in huta. Ban falkaba sai karfe hudu koshi yunwa ya tayar dani don naji cikina a lokacin kamar ban karya da safe ba. Koda na fito bai gida ya fita a lokacin zama nayi nayi naci abinci sosai kamar mayunwaci na kora da ruwa don ni abin zaki bai damay ni ba gasu nan kala kala a gidan ban damu dashiba sai wani lokaci nakan sha idan ya biyo min a rai nakan sha. Bai dawo gifan ba sai cikin dare sosai koda ya dawo ina dakina ina karatu ya shigo yana fadin sorry na fita kina barci dazun kada in tayar dake in lalata maki barcin ki. Na tashi ban ganka ba nasan ka fitane baka gidan kinci abincin ya tambaye a lokacin daya juya yana balle maballan riganshi. Naci tun dazun danaga baka dawo ba da fatan banyi laifin yin hakan ba ina baki laifi ba kinma kyauta min dayin hakan kinsan mijin ki jarumine sosai a cikin mazaje. Dariyana na kumshi don na fara fahintar maganan shi zuwa yanzu da yake mun a dunkule. Wanka yayi ya sauka ya ci abincin ya dan jima lokacin na soma barci ya dawo dakin a hankali yakai hannun shi saman wuyana ya dan shafa. Tare da kiran sunana a hankali kamar akwai wani a gidan da baison ya jishi lokacin da yake tayar dani din. A hankali na bude idana na sauke a kanshi yana tsaye yace yau a nan kike bukatan mu kwanane zarah. Dan fuska na yamutse kafin ince maratane ke min ciwo na kwata ashe barci ya daukeni ban sani ba. Da sauri naji yace maine ? na kara maimaitamai abinda nace sai naka ya kai zaune yana sauke numfashi. Can kuma ya juyo gareni yana fadin amma ai bai zubaba tukun ko nace tun da rana yazo min shiru naga yayi bai iya cewa komai ya mike yabar dakin na bishi da kallo. Dan tabe baki nayi tare da fadin Allah ya rufa min asiri yau wai mutum kamar ba wurin matarshi ya fito ba yake wannan rawan kafa haka ? Dama wai wanan abin ake nufi da aure namiji ko yaushe yana manne dakai yana jagula baiko isar shi. Ban kara jin duriya shi ba bankuma je dakin nasa ranan dakina na kwana don sanin halin yadda period ke mun indan yazo zan dinga kewaya ga ciwon mara dake hanani barci da dadi da dare. Washegari ina hada abin karyawa ya fito daga kofa ya tsaya yana fadin kada ki girka abinci dani fita zanyi. Naji mamakin abinda yace din baima tsaya na fadi komai ba ya kama hanya yana kallin agogon hannun shi yadan yi tako biyu ya juyo yana fadin . Ko akwai abinda kike sone ba komai na bashi amsa ina mayar da kaina ga abinda nakeyi. Allah yasa ban zuba komai ba ruwa kawai na dora a wuta. Rage gudun gas din nayi na juye ruwan tea kawai nasha a wurin wani tunane yazo min a raina. Wai ko yaya yana cikin mazajen da suke kyamar matar su ne a lokacin da suke period din su su kama gudun su. In dai hakane zan mayar da hankalina in kula da wanan hasashen nawa inko haka yake akwai matsala babba ke nan a tsakanin mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:25 - 🀐🀐🀐: BISSIMILAHI RAHAMIN RAHIM GAIRUL, MAGDUBBI ALAIHIM WAL DAALIIN, , , , Kamar yadda na saba kwana kin period dina har na gama yaya bai wani zauna a gidaba lokacin zuciya mai nashe nashe sai ta nasa mun ai kyamar jinin al,ada da nake yakeyi. Wanan abu sai ya tunzurani ni kadai nake fada da kaina ina fadin ai Allah ya hallito mu da abinmu hakana idan ko hakan ne koda jinin ya dauke zai sha mamaki na sosai. Dukda awanan lokacin na gujewa kwana dakin shi don kada inyi mistake yaji karni ko wani abu maka mancin hakan nasan komai na iya faruwa. Amma bai hanashi wani lokaci ya shigo dakina ya dan zauna don har zaman falon a lokacin na gujewa hakan ko da yaushe ina dakina ina karatu. Idan ya tambayeni nakan yi karya da marata ke yawan ciwo yasa ban dogon motsi a gidan ina zaune guri daya. Duk da nasan wanan karon na samu sasauci sosai na ciwon maran da nakanyi idan ina period don sai wani lokaci yakan dan murda min kadan ya bari kuma. KANO NAGERIA , , , , Duk da sanyin su ba nan bane saidai ko a can ana tsula sanyi gwargwadon yadda Allah ya tanadar wa kashen Africa dashi. In zaki tuna na fada maki kawu baya fita sosai a irin wanan lokacin yafi zama a gida cikin iyalin shi balle yanzu da jikin nasa sai a hankali jefi jefi yakan leka kasuwa don ya dan motsa jkin sa da yai mai nauyi. Yau hjy jummai zata fita girki mamu ta karba don girkin gidan a daidai yake tafiya basu hautsana shi ba don dokan hjy jummai ce hakan ko tafiya kayi ka dawo dole sai ka jira idan girka ya zagayo ka karba wanan dokane daga gare ta babu mai tayar dashi kuma a gidan. Abu ga wanda tsufa ya fara hara a kaidan su karfe shidda ne fita gitkin mai girki a ranan sai dai zuwa biyar zaka iya zuwa kayi aikin daya dace a shiyan maigida kada yamma yayi ba,ayi ba. Mamu ta dauki abin shara ta nufi sashen nasa a waje ta samay shi zaune yana shan iska duk da sanyi ya fara saukowa a lokacin kowa na haraman natsa kansa guri daya. Gaida kawu tayi kamar yadda sukanyi idan yana gidan ta wuce zata shiga sashen nasa yace da ita. Maimuna da zan samu ruwan dumi in jefa kafafuwana a ciki da zan so hakan yanzu dan jimm tayi kafin tace ko a dauko maka waya kakira hjy ta baka don ban son abin fitina ko kadan da saura lokacina yayi ka sani. Da mamaki ya kalleta yace ruwan ma shi zai zama abin wani kishi a gare ku yanzu ? Kamar tayi magana sai ta wuce zuwa ciki ta tara ruwan zafi a roban da suka tanadar mai don yin hakan. Tana kawo mai yayi godiya wanan yana daga cikin dabian kawu godiya bai bata lokaci ba ya saka kafan nasa kamar yadda yake so don yana jin dadin hakan wani lokaci. Tun data tunkaro wurin idon ta ya sauka akan roban gasa kafan dake gaban shi lokaci daya kishi ya ziyarci zuciyar ta. Ta karaso a fusace tana fadin ya naga haka kuma waya rigani zuwa karasa min aikina ? Kawu da idanun shi suke a lumshe saboda dadin ruwan da yake ji a lokacin kallon ta kawai yake don ya hango masifa a fuskanta lokacin. Alh tambaya nake waya baka ruwan saurin da nakeyi ke nan yanzu nasan zaka bukaci ruwan a wanan lokaci. Jummai zan zaunane ina jiran sai lokacin da kika fito ki bani ruwan mai yasa ke baki da tausayine a rayuwan ki ko kadan bani ruwan ma yanzu laifine a gurin ki ? Amma kasan dai hakkinane yin hakan a wanan lokaci ko ? Dama abinda take son hadawa ke nan mugun iri marasa asali gaba da baya masu abin kunya tatare a duwawon su. Wai har wanan masu kashin tsiyan don son kai zaka dauko yar ta ka jefa a cikin iyalina don su bata min zuri,a da kashin tsiya irin tasu dasuka gada. Wanan ba wani kike zagiba ni kakazo ki zaga dama, idan har wani yana da kashin tsiya a gidan nan to kece gaban masu shi arkin da kike kurin yaran ki nadashi nakine Jummai ? Da bazarwa sukakai hakan da kike yanga wa mutane maimuna dai da kike zagi ina jininane idan kuma tana da kashin tsiya nima ina dashi ke nan don abu daya ya fitar damu duniya. Ke har kina da bakin magana sananin kankine bantaba rike arzikin dana rike ba a lokacin auren maimuna a duniyan nan. Wanan magana daya fada a karshe shiya harzuka zuciyar hjy ga baki daya tace may kake nufi da wanan magana yace kema kin sani ai. Da can da kika matsamin in kai yaran ki waje ba durkushewa nayi kasa ba ga baki daya sai kama kama muke a gidan nan dan shago gudan dake gareni yana neman subuce muna. Alh ya isheka haka kai bakaji kunyar fadan wanan maganan ba yanzu wanan hayaniyar da suka soma ya jawo hankalin yan gidan a baki dayan su suka fito. A daidai lokacin da hjy ke fadi banda arziki ka dauki yar agolan ka ka jefa a zuria ta don kada ta wullakanta . Kai amma jimmai zuciyar ki na kafiraine Amma ke fadi daga nayan ta wace tsofa ya tasata gaba yanzu tace mutumi na cikin wanan irin halin amma ke kishin ki bai barki kun zauna lafiya ba. Hajiya fitina ya kawo dama ki duba yanzu karfe nawa tasan ina nan batazo ta ban ruwan dumin nan ba sai lokacin data kwatanci yar uwarta tazo ta ban tazo tana fitina sakarai wace bata kama girman ta ko yaushe. Amma ita maman fauziya may ya kaita baka ruwan bayan tasan ba haka mukeyi ba inji hjy maryam ta fadi haka . Wai sai a barshi a zaune da lalura yana jiran sai lokacin dataga dama tazo ta bashi bayan tasan ka,idan yadda kukeyi. Kai ku rika maganan gaskiya don Allah ai kishi ba hauka bane don ma antaimake ta dama ke bugi sa bugi taikine aikinki a gidan ba fadan gaskiya kikeyi ba sai son kai don a yabe ki. Hadiye kada ki fada min magana a nan don kawai na fadi gaskiya ai da gangan tai hakan don tasan yana cikin ka,idar mu yin hakan. A daidai lokacin mamu ta bude kofa ta fito daga dakin dauke da tsitsiya a hannun ta maganan hjy maryam yakai kunnen ta. Kallon kawu tayi tace na fadama wanan abin zai iya jawo matsala gashi ko ya jawo din. Kai ni wanan abu ya isheni wallahi yau dai ku sheda na dakatar da jimmai da maryam girki a gidan nan abar mutum daya yai jinya ta har lokacin da Allah yaban lafiya. Ina wuta su sakashi a lokacin har mamun fada take ita bata yarda ba a lokacin saresarin a sakata gaba da wani kullin ya fadi a tsawace yana mikewa tsaye wanan dokanane haka kuma na yanke a raina da kyat yabi bango zuwa ciki cike da bacin rai a tare dashi. Amma ce tabi kawu ciki ita da mama hadiye mama hadiye na fadin hakanma yafi wallahi mutum a cikin lalura za a ce sai lokacin da akaga dama za a kula dashi wanan wani rashin imanine haka don Allah. Wanan abin zaijawa maimuna bakin jini a gurin su kuma shi nake son ku kula maimuna mutum ce mai ruwan ciki sosai. Hajiya don Allah ku barni dasu idan ba ta baya na fito masu ba nagane so suke su karasani da raina. Tau gidan kane iyalin kane abindaka yanke daidaine amma a sasauta don Allah Amma ta fada tana fita daga dakin. Ranan kan zagin tonon asiri da gori mun shashi sosai ga bangaren biyu kowa ya koma sashen shi zuciyar shi cike da bacin rai abinda ya faru. Hjy maryam da tayi waya tana shedawa yar uwarta abinda ya faru sai yar uwan nata tace daidai ke nan yayi min daidai tunda ana rabaki da shiga sharo ba shanu kinki dainawa ta kashe wayan kawai ta barta dashi a hannu. Ita gaiyyan aikin yaranta ta shiga kira tana labarta masu saidai tayi neman layin umar ta sheda mai halin da ake ciki saidai bata samu layin shi ba ya manta tunda ya dawo ya canza layi saboda busy da yai mai yawa. Amma ce tayi wa mamu magana don da ta bijire akan ba zatayi ba saida daddy yakai karanta ta yarda akan zatayi din. Mun kashi rikici sosai da yaya da farko bai gane abinda nake nufi ba sai daga baya ya fahinci manufata din. Kai ya girgiza tare da fadin baki da wayau yarinya karamace ke shiya har kikai tunanen hakan. Banji kyamar merry da idan ta gama ba wankan tsariki takeyi ba sai ke da nasan kina wanka kina kula dashi yadda addini ya tsara zan kyamata ? Ni lokaci ne banda shi kawai na zama gida saboda course din da mukayo a chaina muke gabatarwa a nan don karuwan na baya mu shiyasa nake kai wani lokaci a waje hakan. Kunya ya rufeni gabadaya don yana fadi ya bar dakin ya tafi dakin shi abinshi. Yanzu mai nayi haka na tambayi kaina waini nasan dadin namiji a kusa dani ko may ke nan nayi din. Tunane nayi sai kawai na danna layin anty Farida a cikin daren nan na kirata kaf na kwashe abinda ya faru na fada mata tare da tambayanta abinda zanyi ? Tace tawa kice min komai yai daidaita ke nan yanzu tsakanin ku har kin fara kishin mijin ki kuma. Ba haka bane anty saukowan shi gareni da kuma matsin mahaifiyata daku yasa na yarda makaman yakina dariya ta tuntsure dashi tana fadin yanzu dai ki tashi ki shirya ki samu mijin ki a daki ki san kinyi gyaran da ba zai iya kawar da idon shi a kanki ba. Godiya nayi mata bayan ta gama min bayanin komai na mike sai bandaki banda wani abin da ta lissafa min inyi don haka na dan zauna a ruwan zafi ina zaune ba a dauki wani lokaci ba naji na kara hadewa kamar ba wanda ya taba shigana. Na zauna nayi komai kamar yadda ta umurce ni in yi manyatacen rigar baci na saka daga cikin wanda ya dawo min dashi da farko har ina zagin rigar dana dagashi naga harahara din shi yayi yawa sosai. Zaune na samay shi a dakin shi ya harde kafa kamar mai tunane a lokacin sallamana yasa ya juyo ya kalleni. Bai iya kawar da fuskan shi gareni ba har na karoso inda yake a hankali na tatare rigan cikin sallo na hauwo gadon jikin shi na dan fada ina fadin yaya har yanzu bakai barci ba ashe ? Dan ajiyan zuciya ya sauke kafin ya kai hannin shi ya rungumoni da kyau yana fadin mamaki maganan ki nakeyi zarah kayi hakkuri nace ina kai kaina saman kafadan shi na kwanta da kyau. Wani iska ya furzo daga bakin shi duk cikin sauke ajiyan zuciya ne hakan yace ban san yaya zan maki bayani ki gamsu dani ba. Hakkuri na sake bashi na hana bayanin da yake son min din a lokacin ta hanyan hura iska a hankali zuwa cikin kunnuwan shi wanan abinda nayi ya jagula muna lissafin komai. Sai da komai ya lafa a tsakanin mu na yunkura da niyar shiga bandaki da sauri naji ya rikeni sai da gaba ya sake faduwa a zatona wani abin zai sake min da wanan katon kan ihu sosai zan masa. Amma sai naji yace dani not now ki bari sai dan anjima ka dan zaki iya kewayawa ba a wanan lokaci ba dan kallon shi nayi sai naga ya kawar da fuskan shi kamar bashi yai magana yanzu ba. Kewayan da banyi ba ke nan sai a cikin dare na falka na samu yayi wanka ya gama sallah yana zaune yana karatu. Nima wanka nayi daga gurin kewayawan na fito sai dai da yake ban zo da shirin sallah ba don haka na sake kwantawa da alwala a jikina kawai. Sai asuba ya tayar dani sallah dakina nanufa na sake wanka tare da dauro alwala na fito na dade zaune ban daga ba ina addu,oi wani barci mai dadi ya dinga fisgana daga inda nake zaune dan kwance nakai a kasa gurin da nake zaune. Shikuma samun kanshi da yayi da rage aiyukan dake gabanshi ya tuno wayan shi akashe yake duk wanan lokacin ya mayar da sim din nashi ya kunna waya. Ya Umar zaman turaine kawai amma bai yarda ya yarda addinin shi da al,adun malam bahaushe ba don idan ya tashi ya tashi kenan sai kuma wani daren zai zauna bayan ya gama addua ya duba sakoni a laptop din na mayarwa ya mayar wanda baida bukatan amsa ya barshi. Ranan baisan ya akayi ba sai barci ya dan fisgeshi har yai mafalkin da hajiyan su ina gudu tana bina da sharbeben yuka ga yara ina ja acikin galabaita. Innalillahi yace lokacin daya mike zaune daga ringinginen da yake kwance din yana mamakin yadda akai barci ya dauke shi da kuma tuna abinda ya gani a mafalkin nasa. Addua yayi kafin ya mike ya shiga yai wanka ya shirya daya fito saukowa yayi sai jini gidan tsit kamar babu kowa a gidan lokacin . Haka yasa ya gane banfitoba kamar yadda na saba fitowa inyi aikina da safe dakina ya juya ya kalla yana rufe ya nufi dakin ya tura a hankali ina kwace ina dan juye juye cikin wahala ina dan magana irin na mai mafalki takawa yayi yana kiran sunana ban amsa ba sai ya saurara da kyau yaji ina fadin salma mai nayi maki zaki kashe ni ? Gaban shi ne ya fadi jin abinda nake fadi da sauri ya bugi filon da kaina ke sama ina kwance a kasa yadda na kwanta a wurin danayi sallah. Mikewa nayi a wahalce na sauke idona a kanshi yana tsugene daidai saitin fuskana kamar yana min addua a lokacin. Ki tashi yace yana mikewa tsaye kwanci a wanan lokacin baida kyau kin sani yana toshewa mutum hanyan alherin sa ne. Dan mika nayi tare da salati ina fadin bansan nayi barci ba a nan saidaya juya yace wanan dabi,ar kine nasani ya kamata ki daina. Ban fito daga dakin ba sai dana shirya na fito yana zaune a falo na gaida shi da kwana zan nufi kitchen naji yace ga abin karyawa nan na amso muna yana nuna min kwalin daya sayo din. Dan jakkan kwalin na dauka na nufi danin dashi ina fitarwa a hankali pakege ne a ciki guda uku plates na dauko a kitchen na juye a ciki ina mamakin ko a ina ya sayo shi da wanan safiyan haka ? Chip's ne sai ganye da sauran tarkace irin abincin su na turawa na juyo ina fadin yaya ga abincin ya mike kamar dama ni yake jira in hada lokacin. Har muka kareci ba wanda yai magana a cikin mu saidai ina kula da yadda yake tura abincin kamar yana da damuwa a ranshi lokacin. Yana gamawa ya mike ya barni a gurin na dan dauki lokaci nima cikin damuwan ko may ya samai shi ya canza haka lokaci guda oho ? Yana zama yaji sako ya shigo mai a waya kamar ya share sai yadai ya dauko wayan yana dubawa Aliyu ne yayo mai text. Bros ina komai lafiya a wajenka mama tana neman layin ka bata samu akwai matsala a gida daya faru sai dai kabi hukuncin ta a sannu don Allah don ta dau zafi dayawa. Iya abinda ya rubuta kenan ya dade yana maimaita sakon bai fahinci komai da sakon ke nufi ba iya abinda dai ya fahinta shine . Akwai abinda ya faru a gidan wanda mahaifiyar su ke son daukan fansa a kaina kila kodai wani abin. To ko shiyasa yayi wanan mafalkin dayayi da safe yasan dai shi ba gwwnin yin mafalki bane sosai hakan. Idon shi a lumshe koda na fito yana tunane a ranshi rabuwa da zarah matsala ne gare shi yanzu kamar yadda mama ke nufi abin ya wuce nan yanzu. Na nufi dayan kujeran zan zauna duk da idon shi suna rufe naji yace zo nan ki zauna yana nuna min gefen shi. Sai lokacin ya bude idanuwan shi yana kallona na mike a hankali zuwa inda ya nuna min cikin kunya don munyi kusanci sosai da inda ya nuna min in zauna din. Ta tako a cikin tafiyana kamar na tarwada na zauna a hankali ajiyan zuciya naji ya sauke lokacin dana zauna din hannun shi ya dora sama kafada ya dan karyo kanshi zuwa wuyana yace zarah fada min mafalkin dana samu kina yi dazun dana shiga dakin ki ? Dagowa nayi na dan kalleshi babu wasa a fuskanshi nace mafalkine kawai dai ba kuma yau ne farkon yin shi duk na kwanta kusan kullun ina wanan mafalkin ko yaushe . Fada min akan mainene kike mafalkin nace sai nayi shiru na kasa magana yace fada min mana ke nake saurare inji ? Dama dama sai na kasa fadi yace umhumm dama anty salma ce dai nakan gani tana son wai kasheni. Tun yaushe kika fara wanan mafalkin ya tambaya kunya naji na kasa magana yace kinga fada min in akwai addu,an da zakiyi sai ki dinga yi don yanayin dama samay ki dazun ya daga min hankali sosai yau. Dama dai ba wani abu bane sherin mafalkine kawai yaya ganin ta nake wai zata kasheni sai kuma wani lokaci zata jefani a rami. Nace tun yaushe kika fara tambayan danayi maki ke nan yanzu ai ko ? Ya fadi yana dagowa daga kafadana tare da tsura min idanuwan shi akaina nace tun lokacin daka fara saduwa dani na karasa a hankali. Sai naga ya koma ya kwanta a makarin kujera ya dora kanshi yana lumshe idanun shi a hankali . Bai faye yarda da mafalki gaskiya bane amma wanan din yana da bambamci tunda shima yayi kusan irin wanda nayi din ai to mai hakan ke nufi ke nan ? Ganin yadda ya kwanta yasa na kai kaina a jikinshi na dan mike kafafuwana ga makaran kujeran ta gefe na lushe idanuwa hannunshi naji ya dora a kaina yana wasa da gashina a hankali. Wayan shi ne ya dauki kara ya dauka muna a hakka yadda muke da kusanci da juna din naji yace mama barka da asuba. Jin hakan yasa na mike da sauri zanbar wurin naji ya rikeni gami da yimin alama in kwanta abina. Barkan mu tace mai yace lafiya mama da safen nan haka kallon lokacin da yake kira safe nayi lokacin sha dayan rana yana batun yi a London. Babawo akwai matsala a gidan nan nayi neman layinka in sanar dakai halin da muke ciki ban samu ba. Naji yace may ke faruwane mama a gidan wai kamanni Alh zaice ya dakatar da girki a gidan nan kan wanan shedaniyar matar kaddaran da ya aura maimuna harda hjy maryam laifin ya shafeta don bai son gaskiya . Abinda nake so dakai yanzu shine ka rubutawa yarta takarda ka turota jirgi ta dawo masu gida tasan munfi karfin ta ta ko ina don hakan kawai za kaimun ka wanke min bakin cikina. Shiru kawai yaya yayi bai tanka ba a lokacin ita kuma mama taci gaba da aibantani da uwana ina jin ta kaf don ina saman jikin shi lokacin komai na shiga kunnena. Can ko taji haushin shirun da yayi mata din ne bai bata amsa ba tace wai kanajina kuwa babawo ina magana kayi shiru ko kana nufin bukatana ba zai yuyu bane na sani. Na fadama ban yarda da karatun da kace in bari ta karasa ba yanzun nake son ayita ta kare ba kare bin damo inhar ta kare karatun ai taci riba damu ke nan daga ita har uwarta din don yarta ta samu madogara ta dalilin mu don haka ina duban hanyar ta zuwa jibi ta kashe wayan don baida niyar bata amsa a lokacin. Yana jin ta kashe wayan ta naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin mamake nan laifin wani ya taba shafuwan wani ne ashe ?. Ya dago daga yadda yake kushingide ya zauna da kyau nima mikewa nayi zaune gaba daya yanayina ya canza ga baki daya lokacin. Sai addua nakeyi a bakina don abin ya firgitani sosai Allah kadai yasan tsawon lokacin da hjy ke binshi akan ya sakoni don maganan ta ya nuna ba yau bane farko. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:25 - 🀐🀐🀐: BISSMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AMINN YA ALLAH, GA MASU BUKATAN LAYINA ZASU IYA KIRA TA WANAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257 DON TURA KUDI KUMA ZAKU IYA SAKA KATIN KIRA KO TA ACC NOBA KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK NAGODE DA KULAWAN KU. Ki sani shi hakki kona haramun ne kamar yadda wasu ke fadi hakki daine, don Allah mu kula yan uwa . Tunda na samu naja kafata zuwa daki da kyat ban kara fitowa falon ba ina kwance ina faman tunane ga ba wanda zan iya fadawa wanan halin da muke ciki. Wani bangare na zuciyana yana bani in sulale kafin sakin ya biyo baya in koma gida da kaina inyaso ya kawo min takardan nawa a gida. Ba irin shawaran da banyi ba a lokacin har rana tayi lokacin sallah yayi nayi sallah ina kwance ina abu daya a da(kina har lokacin bancin ma manufa ba saidai ina ga shawaran in gudu in koma gida har lokacin. Tambayan kaina nayi ta yaya zan iya guduwa bayan banga visa dina ba tun lokacin da muka sauka a kasan ya karba daga hannuna. Sai bayan sallah la,asar ya shigo dakin ina kwance rub da ciki saidai ba barci nakeyi ba a lokacin. A hankali ya karasa shigowa dakin yana kallona don jin shigowan shi dakin baisa na dago daga yadda nake kwamce ba a lokacin. Zarah kinyi sallah kuwa ko kina nan kwance kina tunanen banza tun dazun idona da ya cika da kwalla na dago kai ina kallon shi dasu nace ciki ciki nayi dazun. Zama yayi bakin gadon yana kallona cikin yanayin tausayi daya san maganan da mama zatai mashi ke da yabarni natashi kamar yadda nayi niyaryi da farko da banji abinda zai daga mim hakalina ba yace a zuciyar shi. Ki tashi muje falo kayana da na sayo danaje china sun iso akwai kayan dana sayo maki a ciki ko zasuyi maki kyau ban sani ba. Bandago na kalleshi ba ina daga inda nake kwance a raina nace shike nan ta faru ta kare har ya soma min shirin zuwa gida ke nan ashe ? Ganin ban motsaba yace zarah ke nan badai maganan mama ce ya tayar maki da hankalin ki haka ? Zarah kin fara sona har hakane yanzu baki son kiji ance za a rabamu ko mai da har kika shiga tashin hankali hakan. Da sauri don ya fahince ni nace dole ne yaya ya sake kallona a cikin yanayin tausayawa a gareni yace mama bata sani bane ai komawan ki gida yana daidai da komawan ta nasu gidan itama. Bayan hakan ku zarah sai naga yadan girgiza kai kafin yace idan nace maki yanzu babu mai iya rabani dake zaki gamsu da magana ta kuwa ? Da sauri don in kwantar mai da hankali kamar yadda naga yana kokarin yi shima nace mai zai hana yaya in yarda da kai tunda ban gaka da mugun hali ko kadan a rayuwan ka da zaka iya cutana sai naga yayi dan murmushi ya sake kalloni ya gyada kanshi da alama ya gamsu da maganata. Ke nan zaki daure da duk wani halin da mahaifiyata zata nuna maki na kiyayya nan gaba ? Nace nima ai mama mahaifiyatace koda ban aure ka ba yaya yanzun ma zafin kishin mamune ya shafeni ai har take jin bata sona a tare dakai. Naga ya saki wani laulausan murmushi a fuskanshi yayin da hannayen shi ke dunkule a wuri daya yana dan buga kafan shi daya a kasa. Zarah ke nan kin dai iya magana kamar wata babban mace to wai in tambayeki zarah shin kinsan taba noticing mai kalman aure yake nufi a wurin ma aurata ? A daidai lokacin na mike zaune daga kwancen da nake ina bashi amsan duk wani magana da mukeyi sai da nadan yi murmushi nace . Nace yaya ke na indai zaman auren kowa wace mace zatayi dace da namiji kamar ka to ina ganin kaman mata sun gama dace maza da jin dadin aure. Don baka rageni da komai ba na rayuwa yaya kana ban cida sha ga sutura maikyau sai wanda na zaba zan saka uwa uba ga karatu inayi babu matsala ko kadan a cikin sa babu kyashi ko hattara a zaman mu. Sai nake ganin indai auren namiji ne kamar ka babu wace tafini dace da aure wanan zamanin kaf a duniyan nan. Dadin zancena ya kamashi ya jawoni zuwa jikin shi tare da dan bubuga min baya yana fadin nima ina alfahari dake zarah taso muje falo kiga kayan dana sayo maki idan zasuyi maki in basuyi ba sai in sayo maki wasu a nan don kinsan wani sati zaku fara shiga school. KANO NIGERIA. Murjanatu ce tsaye a bakin famfon waje na kofan part din su tana wanki don ko wani part akwai famfon a kofan wurin do laluran waje. Ganin yadda hjy maryam ke dan waige waige zata shiga part din yasa tasan ba alheri zata kullawa ba a lokacin. Samun kanta tayi da bin bayan ta ta window gefen dakin hjy jummai dake bude ta labe tana sauraren su. A daidai lokacin da hjy jummai ke fadin ai na fada maki yadda suka kona muna mai a gidan nan sai na konawa ko wanin kaf rai agidan nan fiye da nasu. Nayi waya da babawo da safen nace ya sako masu yar iskan diyan su yasata jirgi da takardan ta ya turo ta gida karatun da yake fadi tanayi ban yarda koshi ta karasa ba. Da sauri murja ta dafe kirji tana fadin na shiga uku A ruwa kena za,a sako kowa da sauri tabar wurin jin yadda suke faman aiban tani da mamu. Kayan ta tataro ta nufi part din su Amma da mama hadiye dake zaune suka kalleta bayan ganin ta da himin kayan da ta fita dashi don wankewa ta dawo dashi kuma. Ke dai malalaciyace kin kuma kasa wanke kayan ki dawo dashine hakana sai kinjera kina sawa sun kare, daga baya ki dawo ki damay mu da korafi kuma. Murja batai magana ba sai da ta mayar kayan daki su ta dawo ta zauna jiki ba karfi tayi shiru tana tunane haka yasa uwar ta farga da halin da take ciki a lokacin. Kasa daurewa mama tayi abin da da mahaifi tace wai yana ganki kin dawo haka jiki ba kwari kuma kamar wace tayi gamo kuma data fita. Kallon Amma tayi tana fadin Amma Allah yayi gaskiya daya hana lebe a rayuwan bawan shi don mutum zai iya jiwo kanshi ranan mutuwa shi a bakin wani. Labe kika fara yar nan wallahi amma labe nayi na jiyowa kaina abi tashin hankalin da ban taba jiba yau. Aiko baki kyautawa kanki ba ga maryam nan har girmanta ya zama mata cuta har yaran ta komai mutum yace sai yaji ko sai ya gani ya hana zuciyar shakat dagangan da gangan. Wai ma may ki jiyo kinzo muna hankali a tashe haka kamar wani ya aikeki yin mugun abu ? Wallahi mama ruwan famfon mu nai fita da sauri nace barin tafi shiyan hjy intara sai in kawo inda nake wanki din. Sai ga hjy maryam da saurin ta zata shiga part din hjyn su salma har tana tuntube wurin sauri shine naji zuciyana bata yarda da ita ba lokacin sai na matsa bakin windon ina sauraren su mama kinsan abinda najikuwa ta fada tana kallin mama. Sai kin fada uwar labe mu ina zamu sani tunda bamu aikeki ba kiyi labe. Umhumm mama labena kila yai rana Allah dai ya yafe mun wallahi ji nayi suna fadin wai hjy su salma tasa ya Umar ya sako A ruwa ya turo jirgi da takardan tana saki kada ya hado ta da komai yadda sukaji zafin abinda kawo yai mata suma nan suji shi kamar su. Taci gaba da fada masu sauran maganganun da taji suna fadi a kaina da mahaifiyata a lokacin. Abu ga tsufa hankalin Amma in yai dubu ya tashi nan ta shiga sake salalami sai da mama hadiye ta taushe ta. Kada su bari a san an gane wanan magana zata kira mamu yanzu ta tambaye ta layina nacan akan zasu kirani suji lafiyata daga nan sai suji mai ke gudana a tsakanin mu. Amma kafin nan murja karbi kudi ki sayo mun kati don kiran kasar waje saida kudi mai yawa a layi. Ta cire dubu daya ta mikawa murja ta fice da sauri a daidai lokacin hjy maryam ta fito daga part din hjyn su salma a cikin fara,an ta. Murja tace munafuka mun daiji shirin ku bake kadai kika iya wanan laben ba muguwa kinsani yin abinda Allah ya hana yau. Mamu mama ta kira a waya tana son layina don Allah mamu sai bata turo mata ba kamar yadda tace saida ta gama hadaw yara abincin bayan ta gama na kawu da yake ci ta nufo part din da kanta. A daidai lokacin kuma murja ta dawo daga sayen katin dataje ta samu mai shagon ya rufe ya tafi sallah. Maimakon mamu ta tafi sai ta zauna suna hira da Amma wace bata cikin hayacinta abuga wanda kasan halin sa take tambaya gwaggo wani abu ke damun kine ? Da sauri mama tace mutumiyar dai nata take son jin muryan ta yau da ita ta tashi a rai shine zan kira mata ita ko hankalin ta zai kwanta. Murja ta gama loda kudin a waya ta miko ma mahaifiyar nata wayan ta kira layin nawa akai dace ko kiran ya shiga. A daidai lokacin da muna zaune muna cin abincin daren daya tursasa min cin shi don dole ya kafeni da idanu kuma. Wayan na ringin ban kula in dauka ba yai min alama in dauki wayan da idanu nakai hannu na dauka a hankali. Gani bakuwar nombane na bata fuskana tare da fadin ban san mai lauin nan ba saidai daga nageria ne kiran. Yace dauki mana kiji ko waye kika sani ko daga gidane aka kiraki nayi received din kiran daidai lokacin danaji muryan murja na tambayan ya shiga ? Fatima naji murya mama ta ambata da sauri na amsa da na,am ina wuni tace lafiya kalau sai na danyi shiru tace kin gane dawa kike magana nace a,a bangane ba. Yana zaune ya kuramin ido yana saurarena tace mamanki hadiye ne da sauri nace lah mama kece ashe ? Ina Amma dasu mamu ya murja da sauran mutanen gida tace kowa lafiya yake nan yaushe zamu ganki halan sai na dan kalli inda yaya yake zaune nace yaya yace sai na gama karatuna zanzo gida. Ai hakan nada kyau kinga lokacin da jikokin mu zaki zo muna ke nan na danyi dariya cikin kunya nace kai mama wasu jikoki kuma. Na katse zancen da fadin ina Amma a bata waya don Allah inj muryan ta ina nan na cika da kewan ta ina jin suna dariyata ta mikawa Amma wayan. A ruwa kuna lafiya ko nace Amma zamu bata idan kina kirana da wanan sunan har yanzu fa tace to yar nema kin canza sunane daga wanda muka sani da farko nace kada ki bari mijina ya jiki kina batawa matar shi suna da wani aruwa can ? Tace ja,ira har yanzu dai halin na nan har kike kiran mijin ki a gaba shi sadaukin bai fada maki bayana kuke ba kaf matan nasa . Muryan mujane ke fadin miss you Aruwa nace a wuta dai yar iska ya labarine sai Amma tace ke A ruwa kina jina nace ina jinki Amma. Tace badai lafiya kuke ba nace lafiya kalau amma babu wani matsala a zaman naku dai ko nace babu komai sai alheri Amma. Bansan lokacin da yadago ba sai ji nayi ya karbe wayan a hannu na yana fadin to yar leken asiri muna nan lafiya may kike son ji kuma. Ta danyi dariya naji muryan ta tar a kunnuwa na saida na lumshe idona don kewanta danaji a lokacin naji yayi shiru yana sauraren abinda take fadi. Yanayin fuskanshi ya baci can naji yace Amma wani abu ya faru ne da kike fadin haka shiru nayi ina sauraren su tare da canza yanayin fuskana a lokacin. Saida ya gama yace kashe wayan zan kiraki muyi magana a natse ina wayan ki na nan tace bata da waya yanzu ya lalace kasan kuma mahaufin ku ta kansa yake yanzu kada ki damu za a kawo maki waya yau din nan yace mata ya kashe wayan ban karasa magana dasu ba na dago na kalleshi fuska da mamaki. Ya zauna a hankali ya kalleni kafin yace kin kira wanine kin fada masa wani magana ? Da mamaki nace harga Allah ban kira kowa ba ko mamu da muke waya munkai sati bamuyi waya da ita ba. Yace dole wani yasan umurnin da hjy ta bani a gamay dake maganan Amma yanzu ya danganta da wanan magana sak. Anyway barin kira nasir ya kawo mata waya zan kirata an jima muyi magana sai dai ina son ki da rike sirin mu a tsakanin mu na sake fadin wallah Allah banyi waya da kowa a gida ba ka duba wayata ka gani mana. Karshe ma haushi naji har ya fita ban sake magana ba naga ya dade bai shigo na mike na shige har nayi kamar in kwanta a dakina sai naga in nayi hakan banyi daidai ba duk kokarin shi na ganin ya inganta min rayuwan da yakeyi din ta fanni tunda ba haka mahaifiyar shi ke so ba a nata bangaren. Can cikin barci nake tsinkayo muryan shi yana waya Amma na fada maki ku kwantar da hankalin ku don Allah babu abinda zai samu aurena matata. Wanan kada ya tayat maki da hankalin ki don Allah idona na bude tar ina jin yadda suke maganan karshe dai Amma nata saka mai albarka sukai sallama ya kashe wayan . Ke zarah na amsa ciki ciki yace wai fushin may kike hakane ni banyi hushi ba tunda ni ke zargin ki da rashin addana sirin mu sai ke yanzu amma ta fada min komai jinsu sukayi suna kitsawa da hjy maryam. Ni ai dama ba fushi nakeyi ba na bashi amsa yace may kikeyi in ba fushi ba kina jin na shigo amma kika kyaleni tun dazun ban son irin haka koda kuwa mun samu sabani ne a tsakani mu dake. Gane cewa danayi hankalin kowa yana a kanmu ashe kamar auren mu yafi na kowa rikicewa ne kuma ga yadda shi yake kokarin kwantar wa kowa da hankali yasa nayi danmaran bin mijina sau da kafa a zauna lafiya kamar yadda kowa ke bukatan hakan a tare damu. Wanan ke nan haka yasa shakuwa da kaunar dani dashi duk muke a sabon shiga don ba rayuwan aure irin na malam baushe yasan dashi ba irin wanda mukeyi a yanzu kuma muke fatan kafawa a gidan mu nan gaba in Allah ya nufa muna raye. A wanan lokacin da hjyn su ke zuba ido taga dawowanane gida kuma salma suka samu matsala da Ahmed inda yai mata dukan tsiya ya korota gida a wani safiyan. Wanda hakan ya dagawa hjy jummai hankali sosai don a daidai lokacin da take gani fa,idan auren Ahmed din da salma tayi a lokacin ne kuma aka samu matsala mai karfi a tsakanin su. Don hjy tasha tambayan shi kudi ya turo mata ta account din ta dayaga abin ba zai fishe shi ba ya daina koda sun roke shi din sai ta tura salma na zaran mata idan ya shigo da kudin shago kafin su kai banki. Ganin zata kashi a kunya ranan ya shigo da kudi sunyi dare bai samu kaiwa banki ba sai ta zare dubu hamsin a ciki. Washe gari da ya tursasa ta ta fito da kudin tace ba ita ta dauka ba inda ya matsa mata taki fitarwa ya bata wa,adin kafin ya dawo ta tabbatar da ta aje mai kudin shi a inda ta dauka din. Saida ya fita ta kira uwar tana sheda mata abinda ya faru nan ta hau diyar da fada yaya akayi har ta bari ya gane tana zara . Tace hjy bafa darin da kikace in dauka ba na diba hamsin kawai na diba kuma saida ya gane na taba kudin. Hjy tace kaji dan kawai yo kudin na waye da zai hanaki taba kudin uban ki ina nashi shi wahalan banzane nasa a ciki don dole ya baku dukiyan ku a karshe a raba maku bayan ya gama wahala daku. Hjy amma dai da kibari in mayar mai da kudin shi don yayi fushin haka sosai wallahi tace na fada maki ba za,a mayar ba duk abinda zaiyi yaje yayi. Da Ahmed din ya dawo ya samu bata mayar mai da kudin ba shine yai mata duka ya kuma amshe yarsu dake shan nono a lokacin yace kada tasha nonon sata. Ya turo salma gida da sasafe yace taje gida ta fadi halin da take mashi da bakin ta . Salma ta dawo da kukan ta da yawa na gidan sunga shigan ta a cikin wani yanayi tunda safe haka . Ran hjy jummai ya baci sosai da dukan da yaiwa salma hakan yasa ta samu kawu a falon shi tana fada wai kamar Ahmed don a wullakanta mata ya anbashi zai mata duka irin haka. Har ta gama kawu baice mata komai ba ta gaji da bambami ta fita a lokacin ya kira mamu yace ta kira mai mama da gwaggon ta Amma ke nan. Bayanta dawo ne ya tura dan wajen hjy din autan su yaya Umar ya kira mashi salma a part din su don ko da yaushe yaron yana lake da mahaifin su. Bayan sun zo sun zauna ne ya kalli salma yace uwata sai naji wani labari kuma da banji dadin shi ba duk da nasan halin Ahmed tun farko amma baka shedan mutum yanzu. May ya kawo wanan dukan haka har kuma ya koro ki gida da safen na ya karbe yarshi cikin kwanciyan hankali yake mata tambayan. Salma jin yayi shiru ta dago kai a hankali ta kalli mahaifin nata tace a cikin kuka daddy ka gafarce ni ya Ahmed yana da gaskiya. A daidai lokacinb lokacin hjy ta fado dakin tana fadin ni bansan abinda yasa ba a bani yancina yanzu a gidan nan matsalan kowa zai taso ayi shi asiran ce amma idan yazo kaina sai kowa ya gama sanin komai. Ki fada min nan waye bare a gurin nan yanzu mahaifiyata da ta kawo ni duniya ko yar uwar haihuwata abokiyar shawarata ko bana raye zata kula da abinda na haifa. Kallon inda suke zaune ta danyi ta yatsune fuska kafin tace nidai bana jin dadin hakan don ba haka akewa kowa ba bai kulata ba ya juya wurin salma yana fadin ina jinki uwata . Ganin ma haifiyar ta a zaune yasa ta kasa fadin abinda tayi niyar fada din a lokaci sai kukan da takeyi. Waya ya dauka ya kira Ahmed yace gashi tafe an dan jima sai gashi ya shigo da sallaman shi yana rungumay da yarsu a kafadan shi da alaman yarinyar tasha kuka na rashin uwar tane. Ya gaida su a jam,i ya dago kai ya kalli Alh yace gani Alh yace eh na kiraka ne don naga uwata ta dawo gida ga duka ga ka kuma ka karbe mata ya da wani zataji wanan hukunci yayi tsauri sosai mana mlm Ahmed ? Dan dukar da kai yayi kasa yayin da hjy daga gefe take sake mai magana a fakaice ya dai girgiza kai yace Alh ka gafarce ni dole nayi wa salma wanan danyen hukunci don tana gap da sakani a kunya idan banyi hankali ba Alh. Kunya kan ai kariga da kaji shi tunda har kake iya dukan ta kan abinta don baka da ta ido hjy tace daga gefe. Hannu kawu ya daga mata tare da fadin jummai banson i kara jin maganan ki a nan gurin don ban gaiyato ki ba kin sani. Ya juya wurin Ahmed din yace ins jinka malam Ahmed sai Ahmed din ya dan gyara zama yana gyarawa yarinyar kwanciya ajikin shi mama hadiye tace miko tana aida farko naki karban ta ne don da baifi da ba ni ka linkidawa nawa yar duka zan lalashi naka yace dolene gwaggo in duki salma. Yana mika ma ta yar yake magana a lokacin, muna jinka Amma dake gefe a kule ta fada eh kaka wallahi salma gata nan ba a binda ta nema a gurina ta rasa. Koda banda halin shi a lokacin zanyi kokari inga na saya mata daga baya sai dai tun lokacin da naga suna son jefani a cikin wani rikici ita da hjyn su na fara canza mata a karshe da sukaga na sauya hali sai kuma ta koma zaran kudi shago idan na shigo gidan dashi. Sadiq ya ban shawara in dinga kirgawa tunda ina zargin ana tabawa nakoyi hakan sai gashi na samu ta zare dubu hamsin a ciki daga safiya zuwa washe garin jiya. Innalillahi kawu yace salma yashe kika fara haka a ina kika koyi wanan halin mara kyau dole ko nine ylin karbe ya yata ka kyata min da baka koro muna ita gida ba kawai saida sheda halin da kai mata don nima da ina da karfi da yau na karamata akan wanda kai mata. Ya juya wuri hjy yace jimmai kinga abinda kikaja wa yarki ko har kikazo nan kina fadan karya da gangan dama daji nasan kece da matsalan komai donma mlm Ahmed ya saya wani abin bai fada duka na ke nan. Yes nasan ka saya duk wanda yaji bayanin ka kuma yai nazarin sa zai sanda hakan ka saya maganan don kawaici. Yanzu ga yarki nan ba zan bashi hakkuri don ya mayar da ita dakin ta tunda bansan lokacin da kika koya mata yin hakan ba. Dama ba inda zata koma tunda banda duka har kazafin sata yai mata kuma salma naji haka tasa kuka tana fadin daddy ka bashi hakkuri na daina dama mamace ta dorani a hakan don Allah daddy kada kai fushi dani ina son mijina wallahi na daina daga yau din nan. Ke tafi can albasa batayo halin ruwa ba wallahi akan namiji namijin ma wanda keci a karkashin mahaifin ki har zaki zauna kina wanan kukan haka ? Ke ya isa haka mara kunyar banza kawai dama haka Allah yake sakamakon shi idan kace ruwan wani baya tafasa kai naka ko dumi baiyi. Kinso a sako yar mutane ai mata wullakacin da ba ita keda laifi a kanshi ba sai Allah yaki ta taki aka koro maki yarki gida da mugun sheda. Mai yafi haka zafi da akaiwa yarki jimmai har don baki da kunya kike budan baki kike fadan magana hakan nan ke kan bansan lokacin da hankali zaixo maki ba wallahi. Mutum da riko kamar jikan fir,auna haka a,a hajiya may ye laifina a cikin zancen nan da har kike laka min wani zance da ban sani ba can inma nace a sako wata ai danane ko ba dan wani ba kowa yayi iko da nasa dai. Tana fadi haka ta tashi tafita daga falon kallo Amma kawu yayi yana fadin da alama dai tayi wani abin kuma aka boye min Amma ta mike tana fadin tana fasawa ne ita kasan mai hali baya barin halinsa ai. Ta kalli Ahmed dake zaune tace kaga jikana kayi hakkuri idan tana da hankali wanan ya isheta ishara ai. Babu komai kaka kamar yadda yake kiranta komai ya wuce tunda ta gane laifin ta kawu ya kalleta yace ina kudin da kika daukar mai salma ? A hankali ta dago kai tana fadin naba mama da nazo dama ita tace tana son kudin . Ya girgiza kai tare da fadin kin gani uwarki zata kashe maki auren ki salma naku bai hadaki fada da mijin ki ba gashi ta turaki yin abinda ba daidai ba. Kada ki kara haka na rokeki kiji uwata wanan ba tarbiyan zuri,an mu bace ko kadan sai ya dukar da kanshi kasa don bakin cikin da yake ji a lokacin. Abin gulma ya samu a babban gida irin wanan nan danan maganan ya fara yaduwa a gidan kowa na fadan albarkaci bakin sa. Alh bai kara bin ta kowa ba saida aka kwana biyu har salma ta koma dakin ta a lokacin shi da kanshi ya mayar da ita yaba Ahmed hakkuri kan abinda tayi mai. Ya samu hjy jummai har dakin ta bayan ya dawo daga kaita din suna zaune da Nafisa a falo suna kallo da dan autanta dake kwance saman kujera yana karatu yana kallo. Shigowan mahaifin nasu yasa yara tashi bayan sun gaida shi ya samu wuri ya zauna da kyat hjy dake zaune ta zubamai ido don tsan magana ya shigo dashi wurin ta. Ya danyi shiru yana kada sandar hannun shi kafin yace jimmai guri ki nazo yau sai dai magana nake son yi dake na karshe a kan diyana. Ina sauraren ka tace yace haka na da kyau yanzu kinga abinda nake gudu har yakai ga diyana ko halin da kike min a gidan ina daga maki kafa don ba girman ki bane yin hakan. Yau gashi kin koyawa yarki zatayi magana ya daga mata hannu yace dakata in gama magana ta. Yanzu ke dadin kine mijin salma ya kawo karanta gidan nan karan ma akan sata jimmai satan kuma ma da hannun ki a ciki don salma ta fada muna rana kudi data dauka nasa yana hunnun ki ta baki do ke kika turata ta daukar maki. Ita salma ta fada maku haka ita salman tace ni tabawa kudin kaga Alh idan wani sheri kake nema ka lakamin ka fito fili ka fada zaifi. Ba sheri a ciki maganan nan idan nayi maki sheri in karu damay kina uwar yayana damay zai karani dashi. Kin san dai muyi haka dake a shekarun baya har kika koma gida irin haka tun kan a haifi ita kanta salma di ko kin mantane ya fada yana tsure ta da idanuwan shi da sukai ja tsantsan bacin rai a fuskan shi. Ina kin tuna hakan yanzu yau kuma ga yata zaki koyawa wanan halin jimmai ya fada yana kada kanshi. Yau ko yar rikon gidana akace tana wanan halin ba zan yafe mata balle ace yar cikina ne tayi hakan. Shin kin san abinda yasa na kyale salma ban dauki mataki ba akan maganan nan ? Don zafin ciwon da kike dauka ya yi min illa baikai yadda kike zato ba jimmmai duk kika karbi girki tun kwancina ciwo kada ki dauka don ban taba magana bane dan kudaden da nake ajewa gidan nan da wanda nake samu bana gane kansu sai ranan Allah ya nuna min kina dauka a zaton ki ko nayi barci ne saidai baki san idona biyu ina kallin a safiyan ne kuma da zaki kula nace na dakatar daku girki a gidan nan bado komai ba kada in maki ke daya ayi zaton abu. Duk da ita maryam tana da nata halin a wani bangare bakuji tausayina ba a halin da nake ciki jummai sai yaushe zaku tausaya mi kuma. Yau matar da take da zuria haka irin naki a gidan nan zatai maka haka inaga wata dabaka tara zuria da ita ba. Yau idan diyan ki sukaji wanan jimmai yaya kike son suyi da ranau mai suka kasa maki dashi na rayuwa jimmai ? Ni dai a bangare na ba wanda zaiji wanan zancen sai idan ke da kanki kika dabawa cikin ki wuka kika fito fili kika fada amma ina rokon ki jummai kiyi min addalci kada ki bata min yara da halin banza mu sam man matan nan don wuyan aure zasuyi ga al,umma insha Allah ga mazan ma banda abin da zance dasu sai addu,a a garesu. Sai magana na karshe zancen yaran nan dake kasan waje jimmai ina rokon ki daki bar min yara su zauna lafiya do Allah kin daiji abinda hajiya ta fada a kanki. Yana fadin haka ya mike ya digara sandan dake kara mai karfin tafiya ya bar dakin a jiyan zuciya ta sauke da karfi tabi baya shi da kallo har ya fice. Dama tayi tunanen ranan ya ganta do a yadda yake kwance ba haka ta juyo ta samay shi kwance din ba sai dai ta dauka ya gyara kwanciyane kawai ashe duk yana ganin ta hakkuri irin nasa yasa bai mata magana ba. Jikin ta yayi sanyi sosai tare da na daman sai kuma danta babawo daya ya fado mata a rai tace cikin takaici yanzu dan nan babu halin yin siri dashi tsakani da shi ke nan daga lokacin ta dauki fushi dashi sosai. Bata kirashi ba sai dai shi kan turo mata sakon gaisuwa kullun garin Allah ya waye ko sakon barka da jumma,a sai kaji gidan shiru kwana biyu fitina da tsegumi ya rage sai an samu wani haka babban gidan ya gada dama. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:26 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA HAIYYU YA KAIYUMM, , , , GA MASU BUKATAN LAYIN KIRA ZAKU IYA KIRAN 08036959257 KO 09026931792 . DON TURA KUDI SAYA ZAKI IYA TURAWA TA WANAN ACCOUNT DIN KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN KIRA NA DARI UKKU KACAL NAGODE Bayan watanni sun shude sun bada baya abubuwa sun faru dama a wanan lokacin ciki harda rikici sosai da merry da yaya umar sukayi akan yar shi har wurin hukuma. Inda hukuma taba uwar daman rike yarta akan addinin ta har zuwa lokacin da yar zata kai shekara sha bakwai ko takwas a lokacin tana da daman zaban addinin da take so a rayuwan ta. Wanan matsalan shi ya kara ja baya da alakan su sosai suna haduwa don yarsu saidai ba kamar baya ba da ko yaushe suna like da junan su cikin so da kulawan juna irin na family din dake cikin farin ciki a rayuwan su. Ga Allah yasawa yar son mahaifin ta a ranta ita zata matsa sai uwar ta kira mata uban sunyi waya ko ta tursasa mai yazo tana son ganin shi. Zuwan bai haifar da wani jin dadin rayuwa a gare su don a karshe zasu kare da fadane don uwar bata taba yarda ya ya koyar da yar wani abinda ya shafi addinin shi can. Wanan kan hada su fada sosai har yai fushi ya bar masu gidan ganin ya matsa akan sai yar ta koyi addinin shine yasa yanzu ma ta daina zuwa birnin London din sosai. A rayuwa irin nasu na turawa nacan hakan da farko bai wani damay ta ba don tasan zai gama fushin shi na dan lokaci ne ya dawo gare su don baida wata ya da yake gani a duniya bayan faith din ta. Da wanan tunane ta watsar da zancen shi tana jiran dawowan shi gare su a duk lokacin daya kare fushin shi dasu din . Don iyayyen merry din suna tsaye sosai a kan yarsu don sun tabbatar da basu taba yarda ya ja ra,ayin ta zuwa wani addini haka yasa ko yaushe suna manne da yarsu don kada kewan hakan yaja ra,ayin ta ga mijin ta. Yau Friday bamu dadewa a school kamar sauran ranaku wasu na tasowa da goma wasu zuwa sha biyu a ranan jumma,a din ina cikin wa yanda suka bar school din tun goma da wani abu na safe. A gajiye na dawo ina cikin shigana na musulunci da ban yarda in yarda shi ko kadan don ganin irin rayuwan wasu a can . Duk da makaranta yawanci duk diyan musulmai ne a cikin shi amma muna dan gauraye da wasu addini masu daukan karatu din haka bai hana rayuwan wayewa sosai ga wasu daliban. Wanan bai taba darsuwa a zuciyana ba nidai abinda ya kaini nake yi kawai gashi yanzu nayi nisa sosai ga karatuna saura kiris mu karasa ba wani matsala irin ta kasata da muke samu indai zaka tsaya kai abinda kaje nema a wurin. Tsakanina da yaya yanzu sai abinda ya karu a tsakanin mu na bangaren kula da junan mu a cikin aminci da yarda da juna. Ban taba yarda nayi wanin abinda ya haneni yin shi ba zancen yarshi da matar shi kuma ban sa kaina a cikin zancen su ba ina zamana a inda ya ajeni ne . Tun lokacin da sukai kotu nayi gigin fadin magana ya hayayakoni tun lokacin naje bakina a kansu tare da kawar da idona ga matsalan su mai daki shiya san idan ruwa ke masa yoyo. Na sauka taxi don nauyin cikin dake jikina da yai min yawa yanzu ban iya tafiya mai nisa sosai hakan yasa nake hawa taxi zuwa da dawo daga makarantan. Yana zaune don daren jiya ya dawo daga dubai tsaraba kan na sha su lokacin har irin kayan mu na yan Nigeria na samu a wanan tafiyan. Yace yana son in rika amfani dasu don kada amma tace ya juya matani da wani akida ko kawuna. Yau ma daya daga ciki na dauka na sa don yasan na yaba da kyautan haka nakan yi daya sayo min abu zan saka don ko gobe ya koma wani kasan kara kwaso min kayan su zaiyi irin da matan kasan musulmai ke amfani dashi. Shiyasa zaka ganni da shigar mutanen kasa kasa don mijin daya kasance mai yawan shiga kasashen duniya ko yaushe. Ina bude kofa ya dago ya kalleni tare da kallin lokaci yace may yasa baki kirani in daukoki ba kika dawo da kanki. Kina son ku wahala ne zarah na rabaki da wanan tafiyan haka nidai ina cire takalman kafana don haka muke bamu manta da addinin mu da al,adan mu ba koda muke can sai daga bayan zan dawo in goge takalman in shiga dasu gurin da muke aje takalman mu. Nufoshi nayi na zauna da kyat ta yadda jikin mu yake iya gugan na junan mu a lokacin ina sauke a jiyan zuciya. Dan rugumoni yayi yakai min pick saman goshina yana fadin bakijin magana zarah ban san may yasa kike wanan tafiya ba. Ya mike ya dauko min goran ruwan da baida sanyi gami da cup ya kawo gabana yana tsiyaya min ya miko min na gode dan uwa yace see you yana mikewa. Duk na shanye ruwan na aje cup din a lokacin har yakai zaune shi hijjab din dake kaina nayi kokarin cirewa a hankali. Sai lokaci nace bada kafa na tako ba yaya mota na shigo ai da kafane da yanzun ban kawo gidan nan ba ko. Hanncina yaja yana fadin na sanki da kafiyan tsiya zarah ban san may kike son gani da kafa da kike bin hanya yiba. Ki je ki rage wanan kayan yau fita zamuyi da yamma tare dake da sauri na dan kalleshi don nasan shi da kashin fitan dare gareni yana cikin dokan shi. Yau kuma fita zamuyi yaya na tambaye da mamaki yace eh a kwai wani al,ada da musulman kasan nan keyi a ko wani shekara wurin wanan taro nake son mu tafi. Allah ya kaimu na iya fada ina mamaki a raina wanan wani taro ne kuma haka mai muhinmanci da har ya yarda zamu tafi da yamma kuma ? Ya sani gaba naci abinci a nan falon na kwanta tun muna hira dashi sama sama sai barci ya daukeni yaji shiru. Bini bini yakan dago kai ya kalleni don shi tausayi nake bashi a ganin shi nayi kankanta da daukan ciki haka a lokacin . Don haka ne baiko son tafiya ya kamashi zuwa wani kasa mai nisa yanzu ko a garin yake bai dadewa a waje muddin yasan cewa ina gidan ban fita ba. Don hakane yake bani lokacin shi sosai tun abin na ban kunya har na gane haka rayuwan shi yake shi baida irin dabi,un al,adun mu na hausa fulani komai zai iya yiwa mace shi ba matsala bane gare shi hakan ya zauna sai nayi mai abu da kaina a a don in na kyale shi ina gidan zaice zai muna girki da kanshi. Nakan zauna inyi tunanen ranan da muka koma gida Nigeria yadda rayuwan mu zata kasance a can da hjyn su. Barci sosai na samu nayi nan kasa inda na kwanta a falon tun yana min fadan hakan har ya gajiya ya kyaleni don ko cikin darene sai ya falko ya samu na koma kasa na kwanta shiyasa ya gane ina jin dadin hakan da nakeyi ne. Zarah ki tashi anyi sallah kada ki makara yace dani da kyat na bude idanuwana saidana dan dauki lokaci kafin inyi yunkurin mikewa zaune kamar an nasa min mashe naji wanda hakan da sauri yasa na dan saki kara ina komawa a yadda nake. Sai ganin shi nayi a kaina ya duka yana min sannu tare da dan bude cikin yana kallo a daidai lokacin da cikin ke wani irin motsi har zaka iya gani yadda yake motsawan a lokacin. Ya dade yana kallin cikin yadda yake motsi yayin da idanuwana suke lumshe don wahalan dana sha hannun shi yakai saman cikin ya dan taba yana murmushi tare da fadin sorry my dear sai kuma cikin ya motsa fiye da farko ya shiga yin wani bul bul bul. Shiko yana tsugunne yana murmushi sai can ya lafa ya bar motsi ya kara fadin sorry tare da miko min hannayen wai ya mikar dani na gyada mai kai alaman ya bari. Na samu na mike da kyat ya bini da kallon tausayi na haye sama wanka na fara don inji dadin jikina lokacin na fito na tayar da sallah. La,asar nayi na dora sai lokacin na fara shirin fitan da yace min zamuyi da yamma duk da bai fada min lokacin fitan ba dai. Banyi tsammanin akwai wanda yasan da zancen cikin jikina ba har wanan lokacin don irin gargadin da yai min kada in soma in fadawa ko mamu ta san da zancen ciki a jikina balle wani in bar abin har Allah ya saukeni lafiya. Sai dai na kula tsaye yake kyam da kanshi da karfin Allah wurin yin adduan Allah ya rabani da ciki lafiya ya bamu mai albarka. Ban fada ba shi bai fadaba wa zai sani da yaya Aliyu mace ce da shi zai sanda hakan don shi kadaine na gida daya taba kawo muna ziyara ya kuma ji dadin yadda ya samemu zanzan da juna don lokacin ina cikin laulayin cikin yana sabo baikai wata biyu bama. Yaso ya gane cikine amma sai yaya ya batar mai da tunane ya tsare da cewa haka nakeyi duk karshen wata idan ina Al,ada irin namu na mata. Har yaya Aliyu ya koma bai fahinci komai ba a lokacin ne da zai koma naga irin makudan kudin dayake turawa mahaifan shi don a gabana ya bada su. Nasu mamu dasu Amma da sauran yan uwa ya lissafa mai abinda zaibawa kowa idan yaje ba tare da ya bari mahaifiyar su ta sani ba. Dakin ya shigo ina saman mirro zaune yace na dauka kin koma barcin ne na jiki shiru nace banyi barci ba don kada alwalana ya kare kiyi maza ki shirya kada mu rasa kujeran gaba don ina so mu isa da sauri gurin . Ban tsayaba na tashi na dauko wata bakar jallabiya mai kwalliya kananan duwatsu har kasa da wuyanta an kewaye wuyan rigan da adon duwatsun kamar na gaban da ganin rigan ba sai an fada ma ba kasan an kashe kudi wuri sayen ta sosai gyalen ma nasa biyu ne zaka iya yafawa ko ka dora kamar hulan alkyaba a kai ko ka sake a bayan ka. Yace mi tarone mai kamar buki na musulman kasan da sukeyi yasa nayi wanan shigar haka ba ta inda zakace kaga tsirencina waje sai tafin hannayi da fuskana ko kafana suna cikin sock saboda sanyi da ya fara,a lokacin kadan kadan . Zamu kai safe kilafa a gurin ya fada daga bayana haka yasa na juyo da sauri ina kallon shi nace safe kuma yaya idan lalura ya kama mutum fa ? Yace an fada maki wuri ne na wasa komai sun shirya don bukatan mutanen su sadaka fisabilillah bukatan su kawai idan dai kai musulmine kana kuma wanan kasan zaune ka samu halartan taro don wurin ya cika da jamma,a magoya musullunci. Bandai gamsu da bayanin shi kodana fito falo ya gama shirya min komai a yar jakkar daya daukan min don shi ya tsaya rufe ko ina na gidan. Motar daya canza ne wata irin rantsatsan mota baka ba sai an fada ma motar mai tsada bace ya dauko daga can gidan sa itace muka shiga zuwa wurin taron. Mun bar unguwan mu kadan kiran merry ya shigo wayan shi inajin yadda suke hira na kawar da kai gefe har take gaya mai zasu jamaica a gobe yai masu Allah ya kai lafiya . Bayan sun gama ya dan juyo ya kalleni hankalina yana ga kallon yanayin garin yace wanan unguwan baida nisa da unguwan mu muna kusa da gidan sarauniyar england yanzu. Tirkashi tun dosowan wan mu gurin da ake taron tun daga nisa zaka gane taro ne wanda ya karbi sunan shi ashe. Ban taba sani ko kawowa a raina ba cewa akwai musulmi haka da yawa a kasan America ba saida naga yadda maza da mata da yara suke dandazon zuwa wurin taron. A ka,idance zaka nuna wani kati kafin shiga gurin mai nuna alaman tantance mutum tun farko . An sayar da wanan katin shiga taron ne wata uku da suka shude aka fara sayarwa da sanarwa a lokacin ina fama da kaina sosai don laluran cikin jikina. Ashe ban sani ba harni zan samu halartan wanan wurin taron da aka rubutawa London Muslims Forum Group. Zakace a wata nahiyar labawa kake ko Africa ko Asian kasa dai iri ta musulmai. Ina makale a hannun shi daya yana dauke da dan jakkan da ya dauko muna wanda har lokacin ban gama sanin ko maiye a cikin jakkar ba. Na kula suna matukar mutanta mata masu ciki ga gaisuwa da ka hadu da mutum sai anyi ma sallama ana mutunta junan irin na addini. A dai shigar mune muka hade da wasu mata da miji zakace ga yanayin su ba musulmai bane suna tare da yaran su mace dana miji . Omar matar tace tare da nuna sanaya a gare shi sosai miji ma yazo suka gaisa ya dan shafa kan yaran nasu yana gaidasu yayin da yaran sukai mai sallama irin na addinin musulunci ina jin matar na tambayan shi matar shi yace tana gida. Hakan da yayi ya dan so ya bata min rai yadda yai min din ya nuna ni din ba kowarsa bace a tare dashi. Sai kallon mamaki da matar ta bini dashi har muka bar su shiko gogan nawa ya daure fuska babu halin ta kara mai wani tambaya a game dani. Mukai gaba abin mu mun barsu suna sauwa yaran su abu a baya har lokacin matar tana bin mu da kallon mamaki sosai. Duk saurin zuwa wurin da mukayi layi na ukku muka samu wurin zama saidai hakan ba wani matsala bane ga tsarin wajen ko wanda ke karshe baya kamar yana gabane zaune. Tsaya fadan yadda wurin ya tsaru bata lokacine gare mu ga littafan addini ana rabawa da kashigo kofan shiga dana abubuwan da za a gudanar a wurin. Gaskiya kasan Landon tayi wurin bawa kowa yancin da yadda ya dace dashi sai naji na kara son kasan da mutanen kasan a raina. Malamai da dama na addini suyi wa,azi sunyi bayanai akan addini sosai kafin abawa masu bege su shigo suyi suma ba wani bambancin akida a wurin gabadaya an koma bai dayane. Zanyi barci in falka ga gajiya zai ban abinci in ci mu fita muyi sallah magariba da isha,i ayin addu,oi sosai a gurin yadda ya dace. Naji dadin wanan fitan da mukayi bamu dawo gida ba sai goshin asuba don dai yana son in dawo in dan mike kafana ne yasa muka bar wurin . Duk da barcin da nakeji sai da yasani gaba nayi sallah sannan na kwanta barci banda yunwa don ko a hanya haka yaita miko min tarkacen ban banza da wofi irin nasu na turawa shidai kada ya ganni ina cikin damuwa ko takura ko kadan. Ban falko ba daga barcin da na samu wanda shima ya dan taba barcin sai sallah azahar ya tayar damu. Wanka na shiga na fito na tayar da sallah a lokacin babu abinda nake so sai wanka hakane ke dan sa ina ji sanyi a raina duk da yaya yana fadan haka sosai. Bayan mun gama cin abinci ya dan kalli kafata tare da fadin zarah tun lokacin dana dawo ina kula da kafafuwan nan naki kamar suna hawa idan kin huta anjima sai mu leka asibiti a dubaki. Ba dama inyi gardama dashi bayan la,asar muka tafi ba laifi likitan ta dibani inda ta dan bada shawara in dinga dan yawatawa da kafa. Ba wai dani suke bayani ba shike ganin su bayan sun dubani sukan mai bayanin komai don daukana da yakeyi yarinya har yanzu. Washe gari ya fita dani da safe muka dan taka har zuwa karshen layin mu inda yake bina kamar wata jela can. Bayan mun dawo nayi wanka abinci naci barci ya daukeni don akwai gajiya a jikina har lokacin. Sai yaya ya koma yin danasani da fita zuwa sauraren wa,azin da mukayi har wani lokaci kwana biyun daya wuce. A falo na sameshi shida kanshi ya debo min wani abincin na danci kadan yace in zauna saman kujera yandan matsa min kafata kadan kadan. Na zauna namike kafafuwana yana matsa min wayan shi yai kara a daidai lokacin ya kai zaune a gefena yana sauraren wayan merry ce a kan layin. Omar kana ina ne yace may ye matsalan ki na tambayana kuma tace fuck you tare da banko kofan gidan a daidai lokacin da hannuna ke saman kanshi ina dan mai tausa a hankali. Gaba dayan mu kofan da aka banko muka kalla a lokaci guda mukai arba da merry da yarta da wasu kawayen ta biyu . Da farko gabana ya fadi sosai da ganin ta sai daga baya zuciyata ta dake na bita da irin kallon da take min itama. Kara mayar da kanshi yayi saman cinyana naci gaba da abinda nake mai a lokacin. Mamaki ya hanata tsayawa ta fahinci ma jikina akwai ciki kamar yadda tsegumaman ta tsegunta mata ta ganmu din. May zan gani haka da kaida blood sister din ka umar yace and so ? Ta taba hannayen ta tare da fadin karatun da kake fadin tazo yi ke nan ashe ko yaushe kana wurin wanan yar ficiciyar yarinyar shiya baka damu damu ba ashe. Dayan kawarta tace who is she ? Tana kallona cikin harde hannayen ta itako merry tana takowa zuwa garemu a hankali da sauri yarta ta rigata tana murna tare da fadin daddy daddy. Hannu merry tasa ta tare ta ta hanata karasawa wurin mahaifin nata ganin haka ya mike ya nufi hanyar fita yana nuna masu kofan fita ya fadi cikin kakausan murya su fice mai a gida kafin ransu ya baci ya fara neman layin police din su sun san sun taka doka dole suka koma daga kofa. A gaskiya na tsorata sosai da ganin su tun dai lokacin data nufo inda muke zaune kada ta shakeni da dan cikin jikina. Ina jinta sun musayar zance dashi tana kara tambayan shi ya amsa mata yes is my sister and my wife also . Wani ihu ta fara tana turje turje a wurin yan uwanta na kamata ya mayar da gida ya rufe da karfi garam . 16/11/2021, 23:26 - 🀐🀐🀐: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI TA,ALLA, WABARAKAT, TAHU YA JAMA,ATUL MUSULMIN JUMMA,AT MUBARAKAR, , , , INA MAI MIKA GODIYA GA DUK WANDA SUKAI MIN FATAN SAMUN LAFIYA DA WANDA NA GANI DA WANDA BAN GANI ALLAH YA SAKA DA ALHERIN SA DANI DA DUK WANI WANDA BAIDA LAFIYA UBANGIJI YA BAMU LAFIYA MASU SHI UBANGIJI ALLAH YA KARA MASU LAFIYA AMIN, , , , NAGODE NAGODE KWARAI DA KULAWAN KU GARENI INA ASIBITI KUN KIRA WASU BASU SAMU KIRABA DON LAYINA A KASHE YAKE , , , Zan iya cewa zaune kawai nake a cikin falon illahirin jikina sai rawa yake don ba abinda zan iya yi a lokacin banda addu,a. Shi din kuma nake aikawa daga inda nake zaune don ko ina da lafiya iya abinda zan iya yi ke nan kawai neman tsari a wurin Allah. Ban san ya sukayi ba ya samu ya turasu suka wuce naji tsit a kofan daya cika da hayaniyan su da farko. Shiru shiru bai shigo gidan ba har tsawon wani lokaci haka yasa fargaba yasa na dauki waya na kira mamu a lokacin. Kamar jira take in kirata ta daga wayan hankali a tashe nace mamu ke kadaice a wurin magana nake son yi dake. Tace lafiya kike najiki a wani yanayi haka sake fadi nayi mamu idan ba a part din ki kike ba ki shiga daki muyi magana yanzu. Kwantar da hankalin ki ina kuryan dakina yanzu haka kwance lokacin sallah nake jira inyi sai lokacin na sauke ajiyan zuciya. Sayadi lafiya may ke faruwa dakene wai kin daga mi hankali haka mamu ina cikin tashin hankali a kasan nan yanzu matar yaya tazo gidan nan da tashi hankali don bata taba zuwa gidan nan ba sai yau mamu. Kuma yaya ya fada mata yau cewa ni matarshi ce sun fita suna jidali dashi har yanzu bai shigo ba . Kina nufin duk tsawon shekarun nan sayadi merry bata san alakan dake tsakanin ki da shi ba sai yau din nan mamu ta tambaya cikin mamaki ? Nace hakane mamu a hankali yau ni maimuna naji abin mamaki a rayuwana shin wani irin zaman aure kuke da shine hakane sayadi ? Shiru nayi na kasa bata amsa komai a lokacin don ban san mai zan ce da ita ba jin nayi shiru tace dani yanzu ke may ye naki na daga hankali a cikin wanan zancen sayadi ? Ki kwantar da hankalin ki ki saka masu ido shi yasan yadda zai warware matsalan shi can ai namijine yasan yadda zaiyi da abinsa. Ke nan muke namu hauka a nan ashe wata kila ko taraiyan aure baya yayi dake ke nan duk tsawon wanan lokacin sayadi ? Shiru nayi ban iya furta komai ba sai ki abinda kikaga dama kin dai karanta kin san komai ba sai na tsaya fada kullun kan ki ba mijin ki hakkin ki ba daya dace. Wai ace har tsawon wanan lokacin kina zaune sororo a gidan sa shi kuma daya fiki shirmay ya zauna ya zuba maki ido hakana ko tausayin ki yake ji waya sanar mai zanyi magana naji ta kashe waya a cikin takaici. Wayan nabi da kallo ina mamakin ko yaya akayi ma nakira mamu da wanan haukan nawa ban sani duk tsabab rudewa ne ya kaini ga kiranta ko may oho ? Har na gama abinda nake na rufe gidana na kwanta bai shigo ba har barci yafara daukata sai ga kiran mamu ya kara shigo min. Uwa ke nan ashe hankalinta ya tashi sosai daga baya tana tunanen kada merry ta dauki wani mataki a kaina kuma. Shine ta kirani tana rarashi tare da tambaya ko ya umar ya dawo naji yadda suka kwashe da merry bai dawo ba har lokacin na bata amsa. Tace kin dai rufe gida eh na rufe na bata amsa ta dan shiga rarashina tana fadin kada ki soma sa masu baki a duk iya abinda zasuyi kada ki yarda aji wani zance a gareki kinji ko . Ni dai tun ina amsa ta har barci ya daukeni lokacin jin ina barci ta kashe wayan ta ranan dai mamu ba wanda ya gane kanta bata kuma yarda ta fadawa kowa komai ba har amma ta dai bini da adduan neman tsari da rinjaye garesu. Can cikin dare ya shigo gidan abuna farko daya duba shine ko naci abinci alama ya nuna tun abincin da mukaci dashi da rana ban kara girka komai ba naci. Da sauri ya nufi dakina ya tura kofa a hankali ya samu kofan a bude ya tura ya shiga ina kwance na dunkule a wuri daya ina barci a takure. A hankali ya hawo gadon ya kwanta ya sani tsakiyan shi yakai ma goshina kiss hakan da yayi yasa na bude idanuwana a hankali na sauke gare shi. Dan murmushi na sakarmai cikin karfin hali ya kara rugumoni zuwa jikin shi yana fadin may yasa bakici abinci ba don ban nan , ? Naci burglar na bashi amsa ya kalleni kamar bai gamsu da abinda nace ba naga ya mike ya fita yana fadin ina zuwa fita yayi zuwa kitchen ya dora ruwan zafi. Wanka yayi koda ya sauko har heater ya kashe kanshi ya hado muna tea mai zafi ya nufo dakina dashi har lokacin ban iya komawa barcin dana fara ba . Ya samu na tashi na kewaya na dawo ina zaune bakin gado nayi tagumi da hannu daya wanda ke nuna alaman ina cikin damuwa a lokacin. Tun shigowan shi ya mayar da kofan da kafa ya rufe ya nufoni yana fadin mainene kuma ? May ya same ki naga kinyi tagumi haka kuma gargadin da mamu taimun ne yasa da sauri nace babu komai. Baiyi magana ba saida ya aje min tea din da bread din dayai toisting a gabana ya dawo gefena ya zauna ya dauki cup din ya mika min tare da fadin karba ki sha . Kaina girgiza mai yace No no no kinsan bana son musu ki karba kawai ki sha nace maza bude bakin ki na baki yace ba yadda na iya dole na bude baki ya fara bani a hankali tare da dan guntsura min bread din ina ci har na shanye sai zufa sai lokacin naji yayi ajiyan zuciya ya aje cup din. Ya dauki nasa ya fara sha a hankali ina zaune sai zufa nakeyi ina kallon shi har ya shanye ya aje cup din yana fadin tun dazun ina tunanen ki ina gidan Yusuf nasan dama haka zaki zauna da yunwa kiba kanki wahala kan dan maganan da baikai ya kawo ba. Da mamaki na kalleshi har lokacin warning din mamu yana nan tana min yawo a zuciyata bandai iya furta komai ba sai shi naji yace dani kin tuna da wanan matar abokina da muka hadu da ita ranan wurin shiga taron nan ? Na gyada kai a hankali yace itace ta bugawa merry waya ta ganni da wata sai dai ga haukan merry har yanzu ta kasa kwantar da hankalin ta tayi nazarin yaya alakana dake yake ne wai. Ko da ya juyo yana wanan bayanin sai ya samu ina gyangyadi a wurin murmushi yayi ya sauke a jiyan zuciya tare da tayar dani na gyara kwanciyana. Shikan ranan bai iya barci ba don irin rikicin da sukayi da merry da ya fada mata cewa ni din matarshi ce a yanzu. Kuma har ina shirin haifa mai diya da zai iya juyasu yadda yake so ya sa su hanyar addinin shi sai ta fadi kasa a somay. Sun kwashe ta zuwa asibiti bata yarda ta zauna ba tana farfadowa ta juya zuwa America ranan shine ya tsaya gidan yusuf suka shirya irin nasu don sun san tana kasa tana dabo a tsakanin su yanzu. Washe gari bai tayar min da maganan ba nima haka na shirya zuwa school abina dan ban yarda na saka zancen a raina ba ko kadan. Munyi exam lafiya har lokacin tun ina sauraren zuwan merry naji shiru ranan ina zaune ya dawo yake ce min in shirya zan koma gidan Yusuf in zauna a can zaiyi tafiya har ya dawo. Nadan so yin gardaman hakan sai dai ba fuska da zanyi hakan gurin shi . Matar Yusuf din ita da mijin ta sukazo gidan suka daukan min duk wani abinda zan iya bukata a can dukda ba wani abu suka daukar min ba a gidan nidai na bar mamakin hakan a raina kawai. Don na zargi akwai wani abinda suke boye min daga su har yaya din a lokacin wanda basu so in fahinta niko kwatar min da hankali da mahaifiya tayi dukda bata san halin da nake ciki ba yasa na fitar da komai a raina. A kullun sai nayi in fadawa mamu zancen cikin dake jikina sai inyi tunanen yaya zan fada mata waini ina dauke da ciki a jikina wanan abin akwai kunya gaskiya. Haka yasa naja bakina nayi shiru wanda shima yaya hakan yai mai dadi don har gashi ya kaini inda za a taimaka min in haihu batare da wani tashin hankali ba ko wani yasan da hakan don sun rigada sun gama shirin komai. Nidai ba zance banji dadin zaman gidan yusuf ba ba don ko ba komai banda zaman kadaici ko kadan saidai kewan mijina da yakan damay ni don dan sabon da mukayi dashi a lokacin. Ina sati daya da zuwa gidan ya dawo a wani safiyan nayi murnan dawowan shi kwarai da gaske har ban iya boye hakan a raina. Ramla tana zolayana nidai sai murmushi nake mata kawai zuwa karbe biyu na idar da sallah ta shigo dakin tana fadin in shirya zamu fita inji mazan mu. Ba wani shiri nayi ba dan hijjab dina kawai na dora a kaina karami muka fito baya muka zauna . Tafiya mai dan nisa sosai da gidan mukayi zuwa wani unguwa sai dai unguwar yana da kama dana tallakawa a gaban wani gida yusuf ya tsaya da motar shi. Saida yayi waya muka fito lokaci daya da wata mata da naji Ramla na kira da mummy tana kallona tace a masha Allah wanan ce yar tawa gaskiya sun dace sosai da maigidanta ta kamo hannuna zuwa ciki tana fadin yata sannun ku da zuwa. Hausanta nakeji wani iri a raina nace oh nidai Allah ya kawo ni sun dan dade tare suna hira kafin su barmu gidan da sunan sai sun dawo daukan mu. Hira sosai anty Ramla da dattijuwar matar suke keyi akan haihuwa har zuwa rainon yaya da sauran su ni dai ina sauraren su. Tun ban kula da hiran su ba har yakai na mayar da hankalina gurin su kamar uwace ce ke koyar da yar ta abubuwa na fannin haihuwa. Har ya kai ina masu tambayoyi suna ban amsa a tare cikin natsuwa nake fahintar su sai matar tace in miko hannayena ta gani na mika mata ta rike da hannunta bibiyu ta dade tana tsura masu idanu kafin tayi murmushi tace abubuwa ai zasu zo da sauki insha Allahu ke Ramla. Wanan da kuke gani babu wani harin da zai samayta asalima ko sun jefota ba inda abin ke zuwa do itama ba a banza take ba gaskiya. A kwata da yawan ibada ta fada tana murmushi sanan kuna kinganta nan tana tare da mutanen a kanta sosai. Don haka mijin ta ya kwantar da hankalin shi insha Allahu cikin amincin Allah da yardan shi komai zaizo da sauki wanan mafalkin da sukeyi ba karya bane gaskiya. Saidai duk abinda sukayi Allah bai yarda suyi nasara a kansu don makiya kan a kwaisu dana gida dana waje sai dai ta girgiza kai tace dasun sani dasun daina bata kudin su sukeyi ga banza wanan ta zama kainuwa dashen Allah a cikin zuri,an ta ko. Tun ban fahintar ida maganan ta ya dosa har na gane inda Ramla da mijin ta suka kawo mu wanan dattijuwar matar malamace ko kuma wata mai magani irin namu na hausawa a gida. A,uzubillahi nace har ya fito fili suka kalleni lokacin da nake bin gidan matar da kallo ina kara fahintar wani abu a gamay da ita. Tayi murmushi tare da fadin bana shirka kamar yadda kike zato yar nan saidai Allah yaban mutane a kaina dake zama tare dani har yakai bana iya zama a cikin mutane dole na dawo nan bakin ruwa na zauna a kusa dasu. Ba kowa nakewa haka ba sai wanda zuciyana ya aminta dashi matsalan ku babbane tun a gida yake faruwa har yanzu ba a daina bibiyan ku ba. Da maishi zai gane hakan ya daina da zaifi sauki gareshi don abubuwan dake tare dake manyane sosai basu bari wani sheri ya samay ki. Haka dai tayi ta surutun ta ina kallon su kawai ina murmushi don ni banji komai a raina ba kan abinda take fadi lokacin gamay damu. Fita mukayi shan iska ta bayan ta sai lokacin ma kula da unguwar sosai ashe a bakin ruwa gidajen nasu yake sosai. Tayi girki da wani irin kifi kato dan miya kamar miyar kasar hausa na danyen kifi tare da abinci mukaci. Sai dare sosai suka dawo suka dauke mu bayan sun gama ganawa da ita tazo har inda nake tana min addu,an Allah ya saukeni lafiya. Zuciyana cike da mamakin wanan matar ko maiye makasudin zuwa gidan ta da mukayi ban sani ba nu dai na dauki hakan da ziyara kawai muka kawo mata. A zato na dauka zamu sauke su Ramla ne mu wuce gida sai naga sabanin hakan lokacin don har shi yaya din a gidan Yusuf din muka kwana ranan a dakin da aka ware mun gidan. Sai lokacin da muka kebe ne naga irin raman da yayi sosai ya ramay yayi dan baki a lokacin da ya fito wanka. Ya hawo gado inda nake lokacin ina fushin rashin maidani gidana da baiyi ba ina jin shi na kyaleshi . Zarah na san idon ki biyu fushi kike danine haka komay ? Sai lokacin na dan juya ina magana ciki ciki nace ban son zama a gidan nan da nakeyi yaya ka mayar dani gidana don Allah. Sai naji ya sauke a jiyan zuciya tare da rugumeni a jikin shi kamar karamar yarinya yace nasan bakiso zarah amma hakan shine daidai dake a yanzu. Don barin ki wancan gidan ke kadai hatsarine gare ki idan haihuwa yazo maki bana gidan ko wani yazo maki da tashin hankalin a wanan halin da kike ciki ban kusa kinga ai zaki shiga wani halin da ba a son mace mai ciki ta shiga. Mutanen nan su suka bada shawaran in dawo dake nan kusa dasu don kina gab da haihuwa don sun san ni ba zama nake ko yaushe ba. To ka maidani gida mana nace a dan shagwabe haba zarah in kin min haka baki min adalci ba baki fatan abinda zaki haifa ya taso cikakken dan kasan nan ne ? Ko dai kina samun takurawane a nan din da sauri na girgiza kai alaman a,a kawai dai ni ban saba dasu bane har yanzu. Ki daure ki saba dasu ya ban amsa nasan Ramla tana da hali mai kyau don hakanema na yarda da shawaran in bar ki nan din don hankalina zaifi kwanciya. Shiru nayi ban bashi amsa ba yace da fatan kin daina yawan mafalkin ana binki da gudu yanzu jin tambayan da yai min yasa nayi magana a lokacin. Na daina sai dai yanzu mata uku nake gani suna bina amma bada gudu ba kamar da kafin su cin mun wani abu yake dagani sama. Bai kara magana a haka barci ya dauke mu washe gari tunda ya fita sallah bai shigo ba daga shi har mai gidan wurin matar gidan na samu labarin wai ashe suna case ne da merry matar shi ranan zasu zauna kotu. Asalima wai wanan gidan da nake zaune a cikin sa an rufe sai bayan kare case din mu yanzu ba a san inda nake zaune bane da har dani zamu tafi wurin case din. Basu dawo gida tare ba gashi ina son tambayan shi sai dai ba zan iya hakan ba saboda nauyi da kunya itin namu na matan hausawa. Sai bayan kwana biyu sai gashi ya kara ramewa sosai yayi duhu da ganin sa yana cikin yanayin damuwa. Ina dan karamin falon gidan zaune idanuwa suna lumshe ina faman tunanen yanayin da na tsunci kaina a ciki kamshin shi ya daki hancina na bude idanuwana da sauri na sauke a kan shi. Yana tsaye yayin da corth dinshi yake rike a hannun shi daya, dayan hannun na cikin aljihun wandon shi ya zuba min idanuwa cikin yanayin tausayawa gareni. Kokarin mikewa nayi zaune sai na kasa da sauri ya karaso inda nake zaune yana fadin zauna abinki zarah. Mai ya same kike zaune nan ke kadai kina tunane ko an maki wani abune ko kuma cikin na damun ki ne ya jero min wanan tambayotin kusan lokaci guda a jere. Ban san yadda akayi ba sai ganin hawaye nayi sun soma zubo min a idona tun suna zuba a hankali har na soma a cikin sheshekan kuka. Lokaci daya ya Umar ya rikice yana fadin fada min abinda ke damun ki yanzu ko muje asibiti ne dake ? Ko gidan ne bakya so na rabaki dasu yau ganin ya rude har baisan abinda yake fadi ba yasa na dan rage sautin kukan nawa a hankali na bude baki da kyat nace yaya ka maidani gida don Allah wurin iyayyen mu. Wani irin kallo yai min yace haba zarah baki tausayinane matsalan dake akwai a gida yafi wanan sau dubu a wurina yanzu kin sani. Koda yake ba lalai bane ki san da hakan ke amma ina rokon ki zarah ki daure ki taimakeni ki kwantar da hankalin ki har zuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya ki haihu . Izuwa lokacin komai zai kai karshe insha Allahu koba zaki iya min alkawarin komai ba na rokeki ki min wanan don Allah zarah for d sake of our urborn baby. Na dago kai na kalleshi da sauri ni din yake kallo yana jiran amsan da zan bashi yana ganin na dago kai ya gyada min kai alaman in yarda da bukatan shi. Ban bada amsa zancen ba don ba zan iya cewa eh ko a,a alokacin ba don irin yadda nake jin kaina. Ganin nayi shiru ya mikar dani tsaye yana fadin muje daki in ja maki kafa ki ko zai maki dadi badon naso ba dole na bishi ya zaunar dani saman gadon tare da aje rigar jikin nasagefe daya. Ya shiga matsa min kafan a hankali ina dan lumshe ido don jin dadin hakan da yake min din a lokacin. Sai dai har lokacin ba wani magana don zuciyar kowan mu ba dadi a cikin sa shi yana ganin ya cutamin da yawa ga ciki ga rikicin daya taso tsakanin shi da merry. Allah ya taimakeshi a kasan London suke ba a America ba don haka abin ya danzo mai da sauki ba kamar yadda merry din ta dauko zancen ba. Don sam ta manta da yarjejeniyar su da sukayi kafin aure a rubuce dashi bata taba daukan wanan da muhinmanci ba don kamar da wasa sukayi shi. Sai gashi wanan yar takardan ya rusa mata duk wani plain da alwashin ganin bayan shi tare da yan uwanshi a kan kara wasu hallita a cikin family din ta dashi. Yayi barazanan bar mata dukiyan da take fadi akan zai bata takarda ta tafi har da yar tasu ya yafe mata. Jin hakan har yan uwanta da iyayyen ta sun yarda da hakan daga baya merry din ta tubure masu akan sai tayi shawara da zuciyar ta ita kadai shinr aka kara basu lokaci. Lokacin da suka fito cikin couth din dasshi da Yusuf ko kallon inda take baiyi ba ga Faith na kiran daddy daddy ya wuce ya barta a wurin zuciyar shi na masa kuna. Kowa dake wurin saida yai mamakin hakan har yan uwanta sun fara fadin kinga irin abinda muke fada maki ga wa yan nan mutanen ke nan. Basu da tabbas akan addinin su zasu iyayin komai lokaci guda ki kyaleshi don dole ya dawo ko don yar shi gareku. Ku rufa min baki gaba dayan ku banson jin maganan kowa daga cikin ku idan rayuwan aurena ya samu matsala kune silan hakan gareni da yata. Don kun hanani bin abinda mijina keso dani kun hana mu zauna lafiya dashi ga baki daya kuna ganin zamu iya juyashi a lokaci guda. Omar ya wuce hakan da kuke tunani don yana tsaye ga addinin shi sosai hakama iyayyensa basu zauna a kansa ba. Nan ta barsu ta shiga mota ds yarta tabi bayan shi saidai bata samay su ba taje gidan data san Yusuf a da baya gidan yanzu. Ta juya zuwa gidan da suka samay ni gidan yana rufe kamar yadda hukuma tace a rufe shi har lokacin zama tayi tana karewa gidan kallo. Tana mamakin yadda Omar ya zauna wata mace macen ma yarinya karama kamar fatema da ta sani a matsayin matar auren shi. May zai samu gun wanan yarinyar da bai samu a wurin ta ba har ya iya bin umurnin iyayyen shi kanta. Ido ta runtse sai hawaye taja mota kamar an tsikareta ta nufi gidan su ko yana can sai dai tun a haraban gidan ta gane baya gidan a lokacin. Duk wanan haukan da merry keyi har yan uwanta basu kai ga gane akwai ciki a jikina ba har wanan lokacin ita dai zafin ta shine cewa da yayi ya a zaman matarshi nake nima. Duk wanan abinda suke ciki ni ban sani ba don bai zauna yai min bayani yadda zan gane ba har in fahince shi. Ni dai zan iya cewa wanan hutun baizo min da dadi ba din ga laluran ciki gana wanan halin da muke ciki ina zaune a gidan mutane a takure duk kokarin da sukeyi dani sai ban gani don ina ganin da hadin bakin su komai ke faruwa. Ga Anty Ramla bata kasa dani ba kullun zata shigo wurina mu zauna muyi hira ta kawo min wanan ta kawo wancan haka dai take dawai niya dani a gidan. Ni da kaina na ba kaina shawaran in sake jiki da ita wanan fushin ba zai fishini ba don ba zan iya fahintar komai a haka ba. Ranan tana kitchen da safe tana aiki na fito na samay ta kitchen din ta juyo tana fadin mai ciki kin fito na danyi murmushi zuwa inda take ina kokarin karban wanke plate din da takeyi. Tace rufa min asiri kada mai gidan ki ya samu kina wanan yace zan halaka mar mata kin ko san yana can amma kunnuwan sa na nan zarah. Ban taba zaton akwai wata mace da zatazo tayi tasiri haka a zuciyar umar ba sai gashi har naga abinda yafi ma tunanena. Zarah ki godewa Allah mijin ki yana son ki sosai da ba haka ba duk wanan barazanar da matarsa keyi akanki ne zarah. Kin san umar ya zabi ya sadaukar da dukiyan shi akanta da komai nasa ya zauna dake ? Nace ni kuma anty ? Tace ke kuwa zarah ko cikin nan naki a jikin sa yake ya tsaya hakan yanzu haka duk wani shiri ya kamala duk da wanan halin na barazana ga hukuma da yake ciki amma ya gama shiri akan komai na haihuwan ki da ya dawo daga wanan tafiyan zaki sha mamakin shi kwarai Wanan maganan da mukayi yasa naji kunyan kaina da kaina na rashin kwantar da hankalina garesu bayan nasan suna cikin barazana duk kuma a kaina. Sai na samu kaina da jin kunyan kaina da kaina don haka na yanke a raina yana dawowa kawai in bashi hakkuri sai wata zuciya tace min akan may zan bashi hakkuri din ? ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:29 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALHAMDU,LILLAHI RABIL ALAMIN, , , , , , LITAFIN KUDINE GA MAI BUKATA TA KIRA 08036959257 DON TURA KUDI TA BANK KUMA ZA,A IYA TURA DARI UKU KACAL TA WANAN ACC DIN KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KIBIYA KI KARANTA BA TARE DA DAUKAN NAUYI BA, , , , , , Na dade kwance a dakina ina tunanen hiran mu da anty Ramla da mukayi da safe. A karshe dai na gano a kainane duk wani matsala yake tasowa a yanzu tsakanin yaya da matar shi. Har yake kokarin sadaukar da kaddadarorin shi gareta don dai a zauna lafiya a tsakanin su. To ni har wani mutunci ko halarci nayi mai da ya zabi hakan a kaina yanzu iya sani na ba wani so ko kauna irin na masoya a tsakanin mu. Saidai yanzu abinda zance shine akwai shakuwa irin ta zama tare da mutuntawa irin na yan uwantaka da aurataya kawai a tsakanin mu. Har dadin may yaji a gurina da zai sadaukar da komai a kaina har ina da wanan matsayin yanzu gare shi haka ban sani ba. Idan hakane ya kamata in gyara halin zaman takewan dake tsakanina dashi a yanzu fiye da da can baya da nake daridari da zamana dashi. Ta yaya zan gyara hakan kuma na tambayi kaina shawara da manya akace bai baci duk da nima macece yanzu saidai ilimina da wayo na ai baikai in gano hanyar mafita da kaina ba. Mamu zan nema kowa da sauri nace no ba mamu ba sai wa na tambayi kaina a take amsa ya zo min anty farida ko anty Ramla. To may zancewa anty Ramla din in naje gareta dan dama anty Farida akwai shakuwa sosai a tsakanin mu wanda har zan iya sakewa in nemo mafita a gurin ta. Tunda dama har takan ban dan shawaran yadda zanyi in karkato kanshi zuwa gareni saida taga banda ra,ayin hakan ta daina bani shawara. To amma ai da zan baro gida Amma tace min ni mace ce da kaina zan iya kama zuciyar mijina ba sai an koya min yadda zanyi hakan ba. Sallaman da akayi daga kofan dakin ne ya katse min tunanena Anty Ramla ce dauke da dan madaidaicin ture a hannun ta ta shigo dakin . Na amsa mata sallaman a hankali ina kokarin tashi zaune tare da kakaro murmushi a fuskana. Tace ashe ba barci kikeyi ba, yau kinki fitowa waje ki dan sha iska yanzu maigidan ya dawo yake tambayan ki nace kina daki shine yace a dubaki ko lafiya kike. Shine nace barin dan riko maki dan abinda mai ciki ke so ka zaki sha tana aje tire din a gefena take wanan magana. Kawai dai anty na dan kwantane tace tana kaiwa zaune kodai maganan mu ta dazun ne ya daga maki hankali. Dan dukar da kaina nayi kasa ina fadin bai daga min hankali ba anty sai dai maganan yasa na shiga wani halin tunane . Da sauri tace tunanen may zahra ? Sai danyi shiru sake tambaya tayi tana kallin fuskana tare da fadin wai kina mamakin abinda merry tayi ne ko may ? Kin san ai ba tunane gare su ba dama kila da biyu ta aure shi ai da farko tana ganin zata iya juyashi zuwa akidar su. Ko kuma wata kila don kwazon shi da himma data gani yasa ta leke may Allah kadai yasan niyar ta na auren shi tu farko. Amma kowa yasan merry ai ba matar auren mijin ki ba abune dai kamar na rufa ido kin san halin maza abinda ka raina shi suke dauka da muhinmanci su a gare su. Murmushi nayi tace mutum wanda keda mata haka kamarki danya shataf ga kyau ga kurciya in ba abin maza ba may zaiyi da wata merry arniya ma can. Anty nace sai nayi shiru na kasa magana tace au kin dauka da wasa nake fadi nace ba hakabane anty sai na fara hawaye. Subbahanallahi tace hankalin ta ya tashi a lokaci guda wanan maganan ai ban fadeshi don hankalin ki ya tashi ba zahra. Kai na girgiza mata ta dafani tace ki bar kuka kin san kina cikin wani hali da ba,an son tashin hankali a gare ki yanzu. Anty ba haka bane kawai dai ina kukane don zamana da yaya ban taba kyautata mashi ba a rayuwana a matsayina na matar shi kamar yadda shi yake kokarin kyautatawa rayuwana a kullun. Kada kice hakan don shima maganan shi ke nan a kullun kan bai kyauta maki ba ya cuta maki a zaman ku ya ha,inci iyayyen kuna gida da suka bashi amanan ki ya daukoki daga gida ya kawo ki nan yana cuta maki. Kaina girgiza tare da fadin ko daya anty yaya ya inganta min rayuwata wanda har abada zan amfana dashi koda bamu tare dashi. Anty damuwana daya yanzu shine hanyar da zanbi in gyarawa yaya abubuwan da nayi masa wanda ni kaina nasan ban kyauta ba. Dafa hannuna tayi tana murmushi kafin tace kai zahra akwai da wani magana tsakanin mijin da mata babu wanan abinda kike tunane yanzu. Keda kanki a cikin hikima da basira irin namu na mata zaki gyara kurakuran ki na baya gare shi. Ba sai kin furta mai kalman nadama da kike zaton shi zaki amfani dashi ba gareshi a, a zaki gyara mu,amulan ku ne fiye da da can farko ta hanyan yawan kulawa dashi. Damuwan shi ya zama naki harma ki fishi kulawa ki tsaya iya inda ya tsayar dake gyara tsabatan gida da jiki har na yara ya kasance ba sai ya fada maki kiyi ba. Kizama tankar mage gutin mijin ki kina dai ganin yadda muke a gida nan nida mijina da yaran mu. Kifishi son yan uwan shi na jini koda ya nuna baison abinda suka zo mai da bukata a wurin shi ke ki nuna mai idan bai basu ba wazai ba. Lokacin cin abinci tankar yadda kika san zaki ciyar da yaro na goye abinci haka ya kamata ki ciyar da mijin ki kina kula kina tarairayan abin ki. Idan yai tafiya ko ya fita office kira na zuwa yana dawowa kina masa barka da aiki ko barka da hanya. Ke idan kin rike wanan kawai ina mai maki rantsuwa ga Allah babu wata mace da zata zo ta fiki gareshi koda kuwa tazo da nata sallon nakin nan dai daya saba dashi har lokacin yana da tasiri a zuciyar shi. Ina fada maki ba merry ba koda Allah yasa zai auro maki ba hausa nan gaba yar uwarki ba zata fiki komai ba gareshi. Ajiyan zuciya na sauke ta mike tana fadin bari in barki haka nasan yanzu daddy Amar ya fito daga wanka zanje in dubashi. Ta fice ta barni da tunane ashe abinda mamu keyi kenan wanda su hjy basu gane ba suke ganin ta sace zuciyar mijin su ga baki daya. Don mamu idan tana da girki ba mu gane komai a gidan nan ranan bata da lokacin kowa haka bamu gane kanta sai lokacin da ta fita girki. Tsoho ma ya ji dadin kulawa irin haka may zai hana yaro matashi dan shekara talatin da wani abu son haka kamar yaya ? Ke nan ni nayi sakaci don rashin mai gyara min ko lurar dani hakan shine daidai gaskiya da anty Farida tace min in zama karuwan gida naji haushin ta a lokacin. Akan may zatace in koma karuwa do kawai mijina ya soni kada ya soni in sai nayi kwarkwasa da hilla zai soni. Ashe gaskiya tayi fushi dani wurin ganin wautana kan abinda take lurar dani din ban dauka ba Anty farida tana daga cikin masu kaunana na gaskiya ke nan. Haka na kwana cikin tunane da damuwa washegari anty Ramla ta same ni a daki kwance tace yau dai zamu gyaran kai da jiki dake don yau sati biyu da tafiyan mijin ki nasan yanzu bai nisa da dawowa kasan nan. Murmushi nayi kawai don jin abinda ta fada din don haka kamar yadda tace nima din ina so dama ko banza ban gane ma jikin nawa ba lokacin don ga nauyin ciki ga shi na koma gajal dani. Gyara akai min sosai don shagon kitso da kumshi irin namu na Africa ta kaimu ance wanda ya fika dadewa yafika sanin kan gari. Don ban taba tunanen akwai irin wanan wurin a kasan nan ba sai gashi kamar yadda miji da matan dana taba haduwa dasu ranan suka kaini wurin cin abinci ranan haka naga wurin. Saidai abinda ya ban mamaki bai wuce irin kallon mamakin da mai shagon take bina dashi ba don tazo zata shige office din ta ana gaida ita tana wani shan kamshi . Harta dan shige sai kuma ta juyo don hangoni a jikin mirrow din dake wurin datayi ta dawo baya. Yaren su na yan libiya ta fara min ban san dani take yare ba sai da wace ke min gyara tace dake ake magana cikin harshen turanci na dago kai ina kallon ta. Ta kara min yaren taji ban amsa mata ba sai ta juya da harshen turanci tana tambayana bana jin yaren su na arab ne ? Na girgiza mata kai kawai ta dan tsaya jim tana kallona na dan lokaci kafin tayi yare da mai min kitson ta shige office din ta. Ban kulata ba ban kuma tambayi mai kitson abinda tace ba sai da aka gama min aka fara wanke kafa da akaifa a hankali. Saida aka gama komai naga matar ta shiga office dinta sai gasu sun fito tare da mai shagon wanan karon tana fara,a a fuskanta. Take fadin tana son yin photo dani don ina kama da wata yar uwanta sosai muyi photo kala kala da ita a gurin kafin mu tafi. Bata barmu mun tafi ba saida ta karbi layin wayana ni dai ina mamakin ta a raina bamu kara bi ta kanta ba muka koma gida bayan mun biya munyi dan sayayya abin bukatan mu. A gajiye na dawo nikan wanka nayi naci abinci na samu wuri na kwanta don in huta gaba daya kamanin na sun sauya don gyaran dana samu a ranan. Kwana biyu muna zaune sai kawai ganin yaya mukayi sun shigo gidan shi da oga Yusuf abin ya bamu mamaki don bai sanar damu dawowan shi ranan ba. Baiji kunyan kasancewan Yusuf da matar shi wurin ba ya rugume ni yana wani sauke numfashi kamar wanda ya dade bai ganni ba. Anty Ramla ce tace da fatan dai na iya kiwo ko ince mun iya ajiya nida mijina sai lokacin ya sakeni yana murmushi ya daga mata hannu alaman ta iya gaskiya. A hankali na rada mai yaya Oga Yusuf na wurin fa yace zai hanani in duba ajiyata ne ya fada yana kallon Yusuf din. Yusuf din yace ko daya duba abinka da kyau hakan yana da kyau ai suka kwashe da dariya . Wurin kujera ya jani ya zaunar dani yana tambayana yaya kuke zarah kin canza min ga baki daya may Ramla take baki ne haka ? Da alama taji dadin yaba mata da yadda ya ganni a har lokacin yana rike dani cikin rashin damuwa da wai suna gurin tsaye. Yasa nayi kokatin mikewa in bar falon don kunya dariya suka kwashe dashi kafin Yusuf yace zaka koyawa yar mutane rashin kunya. Dakina koma na zauna bakin gado nayi tagumi ina tunanen irin yadda zan tarbe shi idan ya shigo. Sai gashi ya shigo yana fadin tunanen may kike hakane kuma dan firgita nayi ina fadin ba ba komai zuwan bazata da kayi muna ne kawai yake ban mamaki naga ko dazun munyi waya dakai da safe baka fada min zaka dawo ba. Banson ki shiga damuwa saboda ina hanya ya hana in sanar dake dawowana yanzu ba gani na dawo ba . Da sauri na dago kaina kalleshi a daidai lokacin da yake zama a gefena na kai kaina saman kafadan shi ina sauke numfashi a hankali. Yusuf ya fada min sun kaiki asibiti last week may sukace mamaki da kukaje ya tambayeni yana kokarin kallon fuskana. Nace sun dai min bayani ne kawai kan haihuwa zuwa yaushe sukace zaki haihu nace ba zakai wanka yanzu bane ka kwaso gajiya ? Ya dan yi murmushi tare da fadin baki son zancen ke nan to mu barshi zan tambayi Yusuf yai min bayani ai. Azumi saura kwana daya a cikin dare na tashi da ma tsakaicin ciwon mara mai zafi da zogi a hankali na fara nishi ina dan bugun gado a hankali don kada in tayar dashi daga barcin don bai gama susucewa ba a kaina barci ya dan dauke shi lokacin. A firgice ya tashi yana fadin subbahanallahi zahrah lafiya meya samay ki kuma ? Da kyat na buda baki ina fadin wayyo yaya marata kamar zai fashe min yaya nake ji gaba daya ya rude yana min sannu. Ya sauka daga saman gadon da sauri yana fadin barin kira Yusuf muje asibiti ga gajiyan da ya kwaso don tun daya dawo garin bai zama a gida sai dare yake dawowa tun safe idan ya fita. Hakan ya fita da waya a hannun shi zuwa waje sai ga Anty Ramla hankali tashe tana fadin subbahanallahi zarah ko haihuwan ne yazo ? Banda bakin bata amsa a lokacin don yadda nakeji tunda nake duniya ban taba jin wanan yanayin ba a rayuwana. Da taimakon ta na samu na shirya muka tafi asibiti inda ba bata lokaci suka karbe ni zuwa matenity din su aka fara dubani. Sunyi zaton zan iya haihuwa da kaina don haka suka taimaka min da dan abinda zai rage min pain kawai a lokacin . Saidai kamar basu min komai ba a yadda nakeji lokacin wuya matuka na shashi tun ukun dare har zuwa safiya abu bai lafa mun ba. Yaya da kanshi yaga likitan yace su cire min baby din kawai zaifi don wahalan yayi min yawa. Basuki ta nasa ba don suma suna gab da bashi wanan shawaran don a wurin su suna ganin nayi kankanta da haihuwa shiyasa nake wanan wahalan haka. Lokacin da za a shiga dakin tiyatan hankalin shi idan yai dubu ya tashi yayi tunane kala kala a lokacin gashi bai fadawa kowa zancen cikin jikina ba balle yanzu ya kirasu yace ga halin da nake ciki . Hakana ya fawwala ma Allah yabar komai daga shi sai Yusuf da Anty Ramla ke zirga zurga a wurin babu kowa nawa da zai tsaya mai. Karfe hudu daidai na yamma sukai nasaran fitar da abin cikin nawa wanda hikiman su ya bace basiran su ya shige basu gane diya biyune a cikin nawa ba don tun farko yaya yaki yarda da binciken da suke yi na sanin abindake cikin mace lokacin. Diya biyu ne maza suka fitar daga jikina sai mamaki da farin ciki suke a fili kamar sune akaiwa haihuwan . Mamaki ko fari cikine ya hana yaya ya aiwatar da komai lokacin da nurse din suka fito da murna suna sheda masu . Saida komai ya kammala aka kirasu suga yaran suna da kama sosai da junan su kamar har ya fi na yan biyun mamu. Ban san komai ba don wuyan dana sha sai dana farfado yaya da Ramla suka shigo min da yaran a hannun su. Zahrah ya kira sunana na bude ido da sukai min nauyi da kyat na dan kallesu anty Ramla tace ki bude ido zarah kiga kyautar da Allah yai maku keda mijin ki. Dan murmushi kadan na sake a fuskana a galabaice nace nagode na kara rufe idanuwan nawa har lokacin ban cikin hayacina sosai. Har lokacin hankalin yaya bai kwanta ba yana ganin kamar wani abu zai samu rayuwanane shiyasa ya kasa gane farin ciki yake na samun karuwan ko tashin hankalin rashin lafiyana. A daidai wanan lokacin da suka fito daga dakin da nake kwance ne sun mayar da yaran a dakin da suke wayan shi yai kara ya dauko daga cikin aljihun shi yana dubawa. Mama ya furta a fili yasan bata kiran shi sai idan ya kirata koshi sai idan taga dama take dauka ba wani magana mai dadi kuma zasuyi har su gama wayan. Saidai duk karshen wata wanan ka,idane zai tura mata dari biyun nan bayan haka tana iya mai korafi kafin karshen wata zata iya mai text tana bukatan fiye da hakan ya tura mata. Mama kece a wanan lokacin yace lokacin daya daga wayan . Nice ko na yanke ma jin dadin kane na takurama da kira a wanan lokacin yace haba dai mama jin dadi yafi naji muryan ki a kowani lokaci. Kawai dai gani nayi yanzu ma a wurin ku darene sosai yasa na fadi haka mama da fatan dai kuna lafiya. Ni zaka mayar yarinya babawo ka daukarwa kanka fitinan da kake son yafi karfin mu nan gaba na fada ma ga yadda zakayi kaki kayi . Zaka dauko min fitina ka jefa min cikin zuri,ata daga baya tazo ta buwayemu gidan ga baki daya. Barci nake yanzu nai mafalki da wanan yar banzan yarinyar ta wurinka a yanayin da naganeta tana kokarin ta bunkasa tafi kowa a gidan nan ga baki daya. Cikin natsuwa ya tambayeta tafi kowa kamar yaya mama tace kwarai kuwa don ba zan taba yarda yarinyar ta zo ta zarta yaran mu ba. Yayi maza yace mama wanan kuma ai abune na Allah idan haka Allah ya nufa babu mai hana hakan ya faru ga bawa. Rufa min baki mara hankali wanan shedaniyar yarinyar inayi kamar bana yi sai kudi nake narkawa a kanta amma abu yaki jada baya kasan irin kuskuren da kake shirin muna kuwa. Idan har yarinyar ta gama karatunta ta dawo muna kasan nan kasan yadda diyan mu zasu koma a bayanta nan gaba. Mama ki daina fadin hakan da ita dasu dukka Allah ne yayi su shi kuma yasan rayuwan da ya zanawa kowa a cikin su. Kai wanan kafiran matar taka tafi mun wanan yarinyar a gurina kasani ban kaunar wanan yarinyar da kai har abada inma shirin mayar da ita mata kakeyi kamar yadda ubannin ka suka bukata. Ta kashe wayan ta barshi da mamaki a zuciyar shi yana bin wayan dake hannun shi da kallo. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:29 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR,RAHAMANIN RAHIM, , , , , Mama mama da kin san halinda nake ciki a yanzu da baki fadi haka kan yar mutane ba da kinsan Zahra ta haifa maki jikoki har guda biyu a yau godiya ya kamata ki mata. Wanan wace irin rayuwace da da kiyayya haka mama da har zaki zabi merry fiye da zahra a rayuwan ki. Wani hali mama kike son jefani ciki a yau din nan yarinya tana kwance bata san inda take ba kike furta wanan kalamin haka gare ta. Shi a ganin shi ai kamata yayi duk wani abu da mama keji game da zahra yanzu ace ta aje wanan abin wanan masifa da may yai kama hakane ? Yana zaune ya hade hannayen da gwiwan hannun shi yayi tagumi da hannayen shi biyu a ciki damuwa daidai lokacin Oga Yusuf da Ramla suka karaso inda yake zaune. Man lafiya na ganka a haka ko wani abin ya samu zahra ko yaran ne kuma da sauri Ramla tace ba abinda ya samesu don bamu dade da fitowa gurin su ba. Mai yuyuwa wayan da aka bugo maine daga gida dazun ya sakashi tunane dai. Da kyat ya dago kai ya kalli Yusuf din da idanuwan shi da suka kade sukai mashi ja yadan yi murmushin takaici ya furzo iska. Dan wayancewa yayi ya basar da abinda suke fadi yace ina tausayawa yarinyar nan ne ga halin da take ciki a yanzu. Ya dace ace akwai wani na gida a tare da ita a daidai wanan lokacin da zata gani taji sanyi a rayuwan ta sai dai ban shirya hakan ba tun farko don wasu dalilai na na daban. Ka kwantar da hankalin ka mana muna tare da ku ai ko abinda muke maku bai gamsheka banr kake wanan magana. Dan kallon shi yayi yayi murmushin dole a fuskanshi Ramla ta tare da fadin na fahinci abinda yake tunane haihuwa yafi danan baban Amar. Ko wace mace take cikin wanan halin zata so ace wani nata yana tare da ita a wanan lokacin yarinyar tasha wahala sosai gaskiya idan kunyi duba ga shekarunta a yanzu. Wanan ba komai bane nake gani fatan mu a yanzu Allah ya bata lafiya shine abin roko a wurin Allah ka kwantar da hankalin ka ko wace mace da irin yadda take haihuwan ta. Ya dafa kafadan umar din yana fadin be a man with a strong hart haka maza suke daurewa hakan da kakeyi sai ka sare mata gwiwa kuma. Kallon Yusuf yayi yana girgiza kai a ranshi yana fadin da kasan halin da nake ciki yusuf da baka fadi haka ba a yanzu. Mamu ta tashi hankali a tashe don yawan mafalkin da takeyi dani kwanakin tayi neman layin wayana tun safe layin baya shiga. Tana jin nauyi da kunyan kiran ya Umar ta tambayeshi ni don tana ganin idan tayi haka kamar bata gode mashi bane. Abin yaki fita mata a rai duk yinin ranan tana cikin damuwa saukin ta ba itace da girki ba a ranan don hakane ta bayan yara sun tafi islamiya ta koma wurin Amma. Tun shiganta falon yanayin ta ya nuna tana cikin damuwa don hiran da mama ke masu mamu bata kada bakin ta ba a cikin zancen su. Lafiya kike yau yar gwaggo mama hadiye take tambayan mamu cikin yanayin mayar da kallon ta gareta . Nisawa mamu tayi kafin tace yau dai gani nan dai tun dare nai mafalki da wanan yarinyar hankalina yake tashe. Na kira layin ta yafi a kirga baya shiga haryanzu da sauri Amma tace cikin sauri kinyi sadaka akan mafalkin ?. Yanzu da yara zasu islamiya na basu abin sadaka a rabawa yara idan sunje. Ubangiji Allah ya karba tace suka amsa da Amin mama tace in kaji shuru lafiya ke nan ai da mijin yakira idan da matsala. Shiru mamu tayi batai magana ba har lokacin hankalin ta yana a tashe din tana ganin wani abu yana faruwa dani a yanayin data ganni cikin mafalki. Tashi mama tayi don girki takeyi a lokacin Amma ta kalli mamu tace kwanakin baya nayi irin wanan mumunan mafalkin da su ban fada ba kada hankali ya tashi. Nayi ta yawaita sadaka a garesu har abin yazo ya fita mun a raina na kama harkokina don haka ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu komai sai alheri. Sun dan dade da gwaggon nata suna hira kafin ta koma part din ta yayi daidai da yara sun dawo daga islamiya hakan yasa hankalin ta ya dan dauke garesu. Goma na dare har ta rufe part din ta tana shirin kwaciya wayanta yai kara ta dauka da sauri ganin bakon layi na kasan waje yasa jikkin ta na rawa tai received din called din. Sallamu alaikum ya fada a lokacin ta sheda muryan mai kiran nata da sauri ta karba mai suka fara gaisuwa tare da tambayan shi muna lafiya. Yace to Alhamdullahi saidai da sauki idan babu damu naso muyi maganan siri dake don ina cikin damuwa a nan. Da sauri mamu tace subbahanallahi may ke faruwa dakune yace da fatan ke kadaice a wurin a wanan lokacin tace ni dayace umar ina dakina har mun rufe. Sai yayi ajiyan zuciya sai kuma yai dan shiru kafin yace watau dama naso in sheda maki cewa da farko dai ki gafarce ni na rashin fada maku da banyi ba da wuri. Wani abu ya faru da matar takace ta fada a razane yace eh saidai ba wani abin tashin hankali bane sosai . Ina son ki fahince ni nasan zaki gane may nake nufi ga bayanina watau zarah ta sauka a yammacin jiya din nan. Ciki ke gareta dama bamu sani ba yace eh ban fada bane na kuma hana ta fadawa kowa a gida don tsoron lafiyan ta da kwanciyar hankalin mu ga baki damu daku. Kin dai san komai gamay da maganan auren nan namu wanda tun farko har wanan lokacin ina cikin barazanan kan wanan maganan. Na sani Faruq kamar yadda take kiran shi tun farko Allah yasa hajiya ta gane gaskiya yace Amin. Saidai haihuwan yazo mata da matsala don sai da akai mata CS don tasha wuya sosai kafin ta haihu yara suna nan maza biyu Allah ya bamu. Masha Allahu ubangiji ya raya muna su akan sunna yasa masu albarka yaji dadin wanan addu,an har yana rayawa a ranshi dama ace tashi mahaifiyar ce ke mashi wanan adduan ga zurian shi haka. Yace yanzu ina gida tana asibiti da da zan bata waya ku gaisa sai dai nayi iya tunane nan akan wace zaki samo muna ta zauna da ita a cikin karshin kasa ba tare da kowa ya san da hakan ba ta wurin Nasir abokina zai gudanar da komai gamay da wace za a turo muna din. Zan bincika in gani wace ya dace in turo maku raino sai idan an hada da wace tasan kai Allah ya bata lafiya ya raya muna su. Ya sake fadin amin tare da fadin zai kira yaji shawaran data yanke sai dai yana rokon ta da ta bar zancen kamar yadda ya barshi a rufe har zuwa lokacin da kowa zai sani. Sukai sallama tana mashi godiya yace ba komai ta dai tayamu da addua ya kashe wayan. Iska ya furzar daga bakin shi yana sauke ajiyan zuciya yayin da mamu ta bangaren ta ranan ta kasa barci ta kwana nafila da safe ta aika da sadaka makaratuni da duk inda ya kamata akai sadaka. Duk da Amma tana cikin kwantar wa mamu da hankali saidai bata yarda ta fadawa kowa zancen ba kamar yadda ya roketa kada ta fadi. ENGLAND A hankali na bude udanuwana na sauke akan yaya dake tsaye kaina ya kura min ido cikin wani yanayi na tausaya min. Dan murmushin karfin hali na sake mai ina kokarin yunkurawa da sauri ya kai zaune gefen gadon da nake kwance yana bi sannu baki da lafiya zahra. Banda lafiya yaya na fada cikin murya na marasa lafiya kai ya gyada min alaman eh ya kai hannun shi a hankali saman ciki yana nuna min sai lokacin na tuna da cikin jikina. Aiki akai maki aka cire maki babeis jiya sai yau kika farfado da kyau yaya abin cikin nawa yana da raine na tambaye shi ? Suna raye ya bani amsa har lokacin ban fahinci may yake nufi ba da zancen shi sai na mayar da idanuwana na lumshe a hankali. Hannuna ya rike yana dan matsawa a hankali zuciyar shi cike da kunci a lokacin shi kadai yasan irin yanayin da yake ji a lokacin. Likitace ta shigo tare da wasu nurse a bayan ta shigowan shi yasa ya daga daga yadda yake zaune tare dani. Dubani tayi tare da yan tambayoyi tana rubutu kafin tace dani in mike zaune zan iya ko da sauri yaya yaso magana ta tare shi da hannu. Da taimakon nurse din na samu na daga, daga kwace har lokacin jikin nawa akwai dan tsami kadan tace in sauka daga sama gadon na sauka a hankali. Tare da dan umurtana in taka da tsoro na fara dan takawa sai najini wasai dani ba yadda nake tsanmani ba. Shi kanshi yaya yayi mamakin hakan wanda hakan yasa shi dan murmusawa yayi yana mai jin dadu har cikin ranshi. Likitan tace zasu sallame ni zuwa safe idan sunga yadda jikin nawa ya kara sauki suka fita bayan ta umarceni da in zauna kada in kwanta kuma. Daga inda nake zaune ya koma bakin gadon ya zauna ya tsura min ido a hankali ya kira sunana bayan ya sauke wani nauyayyen ajiyan zuciya yace Zahra. Na dago kai a hankali na kalle shi cikin yanayin ciwo da nauyin jiki yace kin san may kika haifa min ? Kaina girgiza mai a hankali alaman a,a yace cikin daga yan yatsun hannu shi biyu yara biyu maza kika haifa Zahra. A zatona wasa yake min sai na dan murmusa kawai shigowan su Ramla da mijin ta yasa muka katse maganan mu. Da murnan su na gani zaune suka shigo suna muna ba,a yanzu kan hankalin shi zai kwanta tunda yaga na farfado ban mutu ba. Sai dan murmushi yake sakewa kawai a fuskan shi sun dade wurina kafin su fita tare dashi zuwa ganin babeis din. Washe gari aka sallamay ni daga asibitin kamar yadda likitan ta fada a zatona gidan su Ramla zamu nufa sai naga an dauki hanyar wata unguwana daban wanda ke unguwar sarauniyar kasan england. Daga gidajen zaka iya hango gine ginen masarautan daga can nesa kadan gidane wanda ya amsa sunan gida ko a can maigirma gidan yakai abin kallo. An ma gidan kwaliya irin na al,adan turawa da furanni masu launi kalan fari da pink gwanin ban sha,awa. A hankali nake takawa bayan na fito daga cikin motan ina karewa gidan kallo da mamakin nan kuma inane aka kawoni kuma ?. Daidai shiga gidan an yi rubutu da flowers wellcome to new world dan dagowa nayi na kalli yaya dake rike da hannuna zuwa cikin gidan. Mamaki bai gama kasheni ba saida naga photo na dashi sai na yan yaran kamar ayi magana mu fito fili. Wani dadine ya kamani har kasan zuciyana wanda ba zan iya musultashi ba a lokacin da taimakon anty Ramla ne ta kaini har dakin da yake mallakina bin dakin nayi da kallo ina mamaki wanda har ban iya boyewa a lokacin. Rayuwa ke nan Ramla tace min idan baka mutu ba ba,a gama hallitan ka ba mijin ki ba karamin so yake maki ba Zahra. Yanzune lokacin da zaki kara zage damtse ki kara kama mijin ki a hannun ki. Kada ki bari haihuwa ya rageki da komai ga mijin ki son shi dana yaran ki zaki auna ki kara akan komai a rayuwan ki. Tsabta ya ganki yanzu zarah idan da kinayi yanzu ki kara ninkin baninki samada wanda kike dashi a baya. Mun kai wani lokaci tana ban shawara kafin mijin ta yace tafito su wuce zuwa gida nan suka tafi suka barmu daga mu sai mu yaran a gefena na juya na kalle su ina mamakin wai a cikin cikina suka fito dukkan su. Shine ya shigo dakin bayan ya dawo daga masu rakiya daga kofa ya tsaya yana kare muna kallo. Dago kai nayi na dan kalleshi daga inda nake kishingide ya tako zuwa bakin gadon ya zauna a hankali tare da riko hannayena yace zahra may zance dake ne wai. Sai ya dan rugumoni zuwa jikin shi yana fadin kin gama min komai a rayuwana ko haka kika barni da yaran nan biyu na godewa Allah a rayuwana. Zai kara magana nayi saurin rufe mashi baki da hannuna ina fadin please yaya don Allah ka bar wanan zancen don Allah. Ajiyan zuciya ya sauke mun dauki lokaci a hakan kafin dayan yaron ya motsa yayi saurin sake ni ya juya gare shi da sauri yana fadin ko nono yake so ne Zahra. Yana kallona yake magana dan langabe kai nayi nace mai yaya yaya zanyi yanzu ? Kokari bude gaban rigana ya shiga yi ya fitar da nono ya juya ya dauko yaron da kanshi ya kama yaron saida yasha nonon ina runtse idanuwa yaron yana ja. Kulawa sosai dagani har yaran muke samu daga gare shi bai bari in yi komai har yaran shike masu komai da kanshi. Jina shiru an koma school Anty farida ta shiga neman layin wayana tazo gidana yafi a kirga karshe wasu turawa ta samu a ciki suke fada mata munbar gidan. Luckly ta kira layina ya shiga ina zaune ya tasani a gaba ina cin abinci saiga kira ya shigo min na dauka tace Fatima ina kika shige haka tsawon wanan lokaci haka ? Naje gidan ki ban samayki ba sai wasu na samu a gidan sukace basu san ki ba. Nace cikin cool voice anty na mun canza gidane kuma na haihu tace kin haihu ban sani ba fatima yaushe kika haihu nace two weeks ago. Amma baki da kirki fatima ina garin nan baki sanar dani kin haihu ba yanzu kuna inane gani nan zuwa. Kallon yaya nayi yana jin duk abinda muke fada sunan unguwan da kwatancen gidan yai mata bayan ya karbi wayan a hannu na. Zuwanta yai min dadi sosai don itace ta samo min wata bakar fata mace saidai yar ghanace da zata dan zauna tare dani. Hakan ba karamin dadi yai muna ba taban kulawa sosai tankar yar uwatace ta jini da ita da Ramla banda abinda zance dasu. Don sun min karamci sosai a rayuwana wanda bazan iya godiyan baki a garesu ba saidai addu, a. Ban san da zancen zuwan wani daga kwatsam naga Addah na sun shigo gidan tare dashi saida naji wani iri a rayuwana. Don kamar a mafalki naga Addah tana shigowa maimakon inyi murnan ganin ta sai kawai na fashe da kuka yana tsaye yana kallon mu. Tausayi na bashi don yasan kukan da nakeyi bana komai bane saina farin ciki ganin na gids yau a idona. Sosai naji dadin zuwan Addah na don dagani har shi mun kara samun hutu sosai da zuwan ta ga maria mai kula da wasu abubuwa a gidan ga Addah. Haka ya bashi daman fara fita wurin aiki nima hakana na fara zuwa makaranta daukan darasi anyi bukin suna irin namu na nan hausa. Inda duk gaiyan na Ramla ne da Anty Farida mundai dan cika gidan inda yaran sukaci sunaye Abdulrahaman da Abdulsalam. Zabin sunayen da mahaifinsu yai masu ke nan kuma dashi sukazo duk sunan da yaro yaci dashi yazo duniya. Ina jin dadin zama sosai da Addah wace take yar uwa a gurin mahaifina ba karamin karama min dangina naga yayi ba ga hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:31 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHAHIM MALIK YUMMUDEEN, , , , , A cikin amincin Allah yarana suke wani irin girma zakace kamar wani abin girma ake basu lokacin. Kula sosai suke samu daga mahaifinsu da Addah da maria nawa dasu nono kawai idan na dawo in dan basu su sha sai kuma idan zasu kwanta in kara masu. Bazakace wai nice ma na haifesu ba idan ba an fadama ba don uban ya fini kula da yaran don hakane ma sukafi shakuwa dashi fiye dani. Don idan yana gida gaba daya shine mai masu komai ko Addah dake zaune damu lokacin tana hutawane saidai abinda ba,a rasa ba. Na murje na zama kamar wata queen dani wayewa sosai ya zo min duk da haka ban yarda na bar al,aduna ba. Ina bisa umurnin shi da dokan shi karatu yana tafiya a yadda yake so don akwaini da kokari sosai a fanin karatuna. Yarana suna da shekara daya da wata bakwai na fahinci ina dauke da wani cikin duk da yaran suna saman kafarsu har an fara kaisu daycare suna dan daukan darasi. Hankalina ya tashi sosai akan cikin dana gane ina dauke dashi lokacin yaya bai gari yayi tafiya sati uku. Nasha wahalan cikin sosai wanan karon ba kamar cikin farko da aka ban sadakan shi ba wanan amai da kasala da yan ciwarwuka yake sakar min. Har abin yaso ya shafi karatuna ga shi yanzu muna matakin karshe in zama likitan mata da matsalolin su don shi yaya ya zaba min. Haka ya dawo ya sameni a cikin wani hali bai huta ba duk da naje asibitin bai yarda da zuwa naba ya daukeni muka garzaya asibitin. Bayan yan gwaje gwaje aka tabbatar mai da ciki ke jikina na sati bakwai shi kanshi yayi mamakin hakan. Ganin yadda na tayar da hankalina dole ya rufe nasa ya shiga aikin lalashina kan na kwatar da hankalina wanan ba komai bane ai, kuka kan nayishi sosai a lokacin. Dole na hakkura na maida hankalina ga karatuna Addah kuma tana kara min karfin gwiwa da ban musalai iri iri wanda hakan ya kara kwantar min da hankalina. Daga baya na fahinci kamar yaya ya shirya da matar shi don yawan zuwan zuwa America da yakeyi lokacin . Ko kuma yana garin zaice min ba zai kwana a gidan mu ba zai tafi wancan gida nasa ya kwana. Ban taba tambayan shi ko nuna mashi bacin raina ba kan hakan kuma ban taba mashi maganan ko sun shirya da matarshine. Shima kuma tunda nasan ba mutum bane mai yawan magana ko fadar sirin shi da damuwan shi hakan yai masa dadi. Muna waya sosai da mamu da kawu dasu Amma inda wani lokaci sukan tambayeni waiku har yanzu dai shiru saidai kawai in masu dariya in wayece zancen akan karatu nakeyi ai. Amma kanyi fada sosai tace karatu zai hanaku aje iyali idan suna waya da Amma mutum yana kusa zaisha dariya sosai a lokacin. Zuwana England zuwa yaya Nigeria uku bai taba zuwa dani nima ban saka raina ba tunda yace sai na kare karatuna zan tafi gida ban san dalilin shi na fadin hakan ba. Haihuwana na biyu ma CS akai min aka cire yarinyar a cikina wanan karon kusan ince namafi wancan karon na haihuwan yan biyuna wahala. Saukin abin Addah tana tare damu don taso komawa gida saboda kewan gida dakan addabi mutum a can. Da kyat yaya ya lalasheta ta yarda don cikin dake jikina a lokacin da haka har Addah ta zauna damu na sheka biyu da wasu watani a kasan kafin ta dawo gida don hankalin ta ya koma gida ga baki daya lokacin. Haka rayuwa yaita gudana al,umurah mai kyau da mara kyau suna faru suna wucewa kuma har dai lokacin abindana sani ba kauna tsakani da sarakuwana. Don a gaba zasuyi waya zata tambayi merry da yar ta bata taba tambayana ba halin da nake ciki. Shekaran dana kare karatuna a shekaran ne kamar yadda yai min alkawari wata rana kwatsam yaya ya dawo dags tafiya yazo min da maganan zuwa gida. Ba karamin farin cikin jin hakan nayi ba ban kuma kawo fargaban yadda zamu kwashe idan muje ba a raina ko kadan. Tun a ranan daya fada min zancen tafiyan tyn wanan ranan na soma shirin zuwa gida duk na fita naga wani abinda ya ban sha,awa zan sayowa kannena da mamu da sauran mutanen gida. Duk wanan shirin bai san inayin shi ba a bangarena Allah Allah nakeyi watan dayace zamu tafi ya kama kawai in ga kaina a gida cikin yan uwana. Wani tafiya daya dawo muna zaune naji yace zan baki kudi kuyi sayayan abinda kike bukata wanda zamu tafi dashi gida. Na dago ina fadin sai dai idan kara masu zanyi don ni tsaraba ban san yadda ma zan dauke shi ba daga nan don tun ranan daka fada min na fara shirina. Wanan kuma naki ne ki tafi ki sayo wanda nace da kudina azo a hada kayan wuri daya a tura ta ruwa su wuce dashi kafin mu tashi don akwai kayan da nake son za a wuce min dashi a cikin satin nan . Ba halin inyi mussu dashi dole na karbi kudin daya bani na fita da zuman sayo wani abinda zan kara dashi. A wanan fitan ne muka hade da wanan matar mai sallon don nayi zuwa barkatai bamu haduwa da ita wai ashe ta tafi libiya ne duk dadewan nan bata nan. Itace ta shedani don ni ban ganeta ba tunda an dade wanan lokacin ta bukaci in bata address dina da layin wayana kan tana son magana dani wanda bai yuyuwa a nan. Mukai musayan layi da ita mun rabo nayo sayayya sosai kudin daya bani kamar ban taba ba . Kwana biyu da haduwan mu da ita sai gata a gidan mu taro sosai nayi mata na karramata. Bayan mun dan taba hirane take tambayana ko ina da yan uwa dake zaune a libiya nace mata gaskiya ni ban san kowa ba a can. Tace ban taba jin labarin ina da yan uwa a kasan ba na girgiza mata kai da a,a tayi shiru can ta zaro wayan ta daga cikin jakkan hannun ta ta dan taba sai ta miko min na karba. Sak da wace ke cikin hoton kamar mu daya kusan kuma shekarun mu daya da mai shi saidai zata dan girmay mun. Ajiyan zuciya na sauke nace lalai muna da kama sosai tace shiyasa ta matsa min da tambaya tace inje gaba in duba akwai wasu photuna na family din su. Kallo nake cikin nazari sosai don kamannin yan cikin photon da nake gani da mu sosai. Tace a Nigeria kowa naki yake nace eh kowa nawa yana nan kasan tayi shiru can nace saidai mamata nakan ji ana fadin babbarta ba yar Nigeria bace ita kuma tun da ta tafi ta barta a zanin goyo har yau basu kara ganin juna da ita ba. Da sauri tace min ko zaki bani photon maman naki ingani don Allah ? Na neme photo mamu na nuna mata a wayana wanda nayi zoming ta tsurawa photon ido sosai sai ga hawaye yana fita daga idon ta. Kallon mamaki nake mata tace wanan yar yarmu ce data bari a Nigeria ko tantama ba zanyi ba yar uwar muce wanan. Yar uwarku na tambaya ina mamaki tace kwarai wanan kamar haka ba zai tafi a banza ba saida dalilina jini mai karfi Ko zaki iya kira min mahaifiyar taki a waya yanzu muyi magana nace zan gwada in gani ko layin ta zai shiga. Sai akai rashin sa,a layin yaki shiga haka yasa na bata layin mamu akan zata kirata suji idan itace. Ta tafi ta barni cikin halin damuwa da tunane tare da fargaba cike a zuciyata sai bayan tafiyan tane yaya ya dawo gidan nake labarta mai zuwan matar. A ina kika hadu da ita ya tambaye yana kallona a cikin mamaki nace a shagon ta mukaje gyaran kai da anty Ramla ranan tun ina da cikin su Abdulrahaman na bashi amsa. Duk wanan dadewan baku hadu ba sai yanzun kuma na bashi amsa da eh sai shekaran jiya muka hadu a shago wurin sayayyan danaje. Shiru yayi na dan lokaci yana nazari yace gashi kuma jibine tafiyan mu banda lokaci da sai mu ziyarce ta in karajin wani bayani a gurin ta. Yanzu sai idan Allah ya dawo damu lafiya zamu neme ta Allah ya kaimu kawai na iya furta mashi lokacin don yanayi sai ina jin shi wani iri. Komai da zamu tafi dashi ya tura gida ta jirgin ruwa sai wanda mukafi bukata da zamu tafi dashi tare damu. NIGERIA LAGOS, , , Karfe bakwai na safe muka sauka Nigeria ta birnin ikko jirgin mu ya sauka nayi mamakin ganin wai yaya yana da gida a garin. Maria ta biyo don dama kudi taje nema a can kuma ta samu yaya na bata hakkin ta yadda ya kamata. Wanan yasa tace ba zamu barta ba a can dama tana son zuwa taga gida daga nan hakan yasa mukazo tare da ita kan sai munje kano tare taga wuri zata dawo ta tafi gida. Ina jin dadin zama da maria sosai don bata da matsalan komai ta ko ina don hakane zaman namu ya dore sosai da ita. Kwanan mu biyu a lagos wai sai yara sun huta yace kuma yana da abinyi duk da banga yana wani fita ba yana gidan ko wani lokaci makale da yaran shi a jiki. Al,amarin yaya yana ban mamaki wani lokaci duk da na saba yanzu da irin halaiyan shi don dole na koyi wasu daga cikin halaiyan nasa. Bai fadawa kowa zancen zuwan mu gida ba haka kuma ga maganan shi na gane nima baison in fadawa kowa zamu zo din. Jirgin rana mukabi zuwa kano don haka hudu da wani abu muna cikin gidan shi na Kano inda gaba daya fasalin ginan gidan ya canza min ba tsarin farko akayi ba yanzu. Anyi gyare gyare da dama a gidan an canza fasalin gidan da girman gida ya kara fadi da tsawo sosai ya koma wani aljannan duniya. Mun samu ma,aikata maza uku da mata biyu dattijuwa da yar karamar matashiyar yarinya duk daga wurin Nasir abokin shi suka fito. Abinci lafiyaye muka samu sun hada muna a falo muka yadda zango muka dan huta suna gaisawa da Nasir da Aliyu daya dauko mu daga airport wanda mamaki ya cika shi na ganin mu haka tafe babu sani ga iyali mun tara. Yara kyawawa kamar mutun ya sace su don kyawo daga ba sai an fadama ba tashin turai su AC ta ko ina yana tashi a gidan. A karshe na mike na shiga daga ciki don gabatar da sallah dake kan mu maria kuma ta kwashi yara zuwa dakin da Aliyu ya nuna muna nasu. Sai Sultana ce ta makale min don ganin bakon yanayi taki yarda tabi maria tunda ya fita da sunan Sallah basu shigo sai dare dashi da Aliyu suka zauna sukaci abinci naji sun dauko maganan siri na basu wuri. Da safe suke jin yazo a bakin Aliyu saidai daga haka bai kara masu ba sun dai san dan uwan yazo don yace ya aikeshi Yola zai tafi ya dawo a ranan kuma yake son ya dawo kano. Uwar tace au yaushe ya sauka garin yace cikin dare suka zo jiya daga haka ya fita baiko tsaya ba da suka gaisa da mahaifin su kuma gaisa yake fada mai zai tafi yola yayan ya aikeshi. Yana kwance bai fito ba nice dana tashi na fito wurin maria da yaran na duba su daga nan na zauna muka basu abinci. Abdulsalam ne ya damu da tambayan daddy daddy na kaishi dakin da yake shigan yaron wurin shi yasa ya taso suka fito tare ya zauna dasu nan suna masa shirmay har lokacin a kage nake inji yaimin maganan zuwa gida. Sai bayan ya karya ya sullace jiki daga yaran ya tafi yai wanka ya fito zuwa lokacin nima na shiga dakina nayi wanka na fito a cikin wata doguwar riga din kin yan chaina. Rigan har kasa sai gurin hannaye aka budashi hannunwan suka dan sauka shara shara sai gyalen su da nayi rolin din kaina dasu kayan sun kara haskani sosai sun fitar min da shape dina waje. Ina kara gyara fuskana ya shigo yana fadin kin shirya mu shiga gida mu gaida mutanen gida nace a shirye nake zamu iya zuwa yanzu ai . Yaran fa nace nasan maria ta shiryasu tun dazun amma yanzu zan fito in duba su ya fita yana waya daga dakin. Kara duba kaina nayi sosai banda makusa ta ko ina na dauko jakkana na fito tare da jawo kofan dakin na murza key don ban san irin mutanen da zamu zauna dasu ba a lokacin. Da ganin shiga kasan akwai sirki a cikin lamarina yanzu don ba shigan mu na matan hausawa da muka saba nayi ba saboda sabo tun a can. Wurin maria da yaran na leka nake fada mata zamu shiga cikin gidan mu ta kula da gida kafin mu dawo ta amsa da yes ma. Kafin ma in fito na samu har ya fita da yaran suna mota zaune suna jiran fitowa na lokacin tun fitowana ya kura min ido wanda ban san dalilin yin hakan ba nazo na bude motar dake sheki da walkiya baka wuluk na shiga na zauna ya tayar da motar muka dauki hanyar gida sai bin ko ina da kallo nake ina tuna abubuwa da dama duk wuraren da muke bi zuwa islamiya wasu ancanza masu falin gina anyi shaguna wasu kuma an rushe ga baki daya ancaza ginan nasu kano ke nan ta dabo tunbin giwa koda may kazo anfika sukace. Idona na lumshe a hankali cikin yanayintunanen irin karban da fassaran da hjyn su yaya zatai mun idan mun shiga gidan. Da farkon shigan mu babu kowa a haraban gidan namu shine tsakiya Abdulsalam da Abdulrahaman suna daga ko wani gefen shi ya safa Sultana a kafadan shi. Sai ni dake gefen shi tafe da yar hand back dina da nake rataye dashi a kafadana cikin shigata ta alfarma da daukan ido. Daga part din Amma murja ta fito da gani fita zatayi a lokacin ganin mu kawai tayi tafe da farko bata sheda mu ba sai daga baya ta fara gane yaya ta sake waro ido da kyau tace A ruwa ? Sai kuma ta juya da gudu tana ihun kiran Amma da mama ga Aruwa ga Aruwa Amma. Ihun ta ya kara jawo hankalin sauran mutanen gidan lokaci daya hjy maryam ta bude kofa da sauri ta fito kafin kowa ya fito. A,a sai kuma taja tayi turus ta tsaya tana kallon mu da mamaki tace ikon Allah duk wanda ya fito abinda yake fadi ke nan sai a kallemu cikin mamaki. Kowa ya kasa karasowa inda muke sai fitowan Amma data fito tana fadin a, a, a lale lale lale marhabin da mutanen turai. Lokacin na wuce yaya da sarsarfa na isa wurin ta da gudu na rugume ta sai hawaye a lokaci daya suka zobo min. Itama Amma kukan ta fara hjy maryam ta karsa inda yaja ya tsaya yaran suna make mashi a jiki cikin rashin yarda. Ikon Allah tana mika hannu zata karbi Sultana ta kara make mahaifin ta sosai alaman bata zuwa ta mikawa su Abdul suma suka yi kamar yadda yarinyar tayi da farko. Wanan abinda mamaki yake yara har sun kai haka bamu da labari a daidai lokacin da Nafisa ta bude kofan part din su ta fito tana ganin shi da yara taja ta tsaya da mamaki sai kuma ta juya da gudu ta koma ciki tana kiran sunan hjyn su. Aruwa duk yaran kine wa yan nan diyan murja da farin ciki ya kasa boyuwa a fuskanta tana tambayana. Na dago kai ina girgiza mata kai nace yaran ki ne ba nawa ba cikin zolaya tace A ruwa yaushe kika haifi yaran nan haka bamu sani ba ? Amma ta sakeni tana mayar da hankalin ta inda yaya yaja ya tsaya da yaran yana kallon mu yana murmushi. Na dago kai ina kallon part din mamu da har lokacin banga wanda ya fito ba daga part din a daidai lokacin Fauziya ta bude suka fito da gudun su a cikin murna. Nima da sauri na karasa na rugumay su ina murnan ganin su mun dade rungumay da juna dasu. Saudaki kakai miskili sai kuma ta fashe da kuka shidai murmushi yake a fuskan shi yana sauraren ta. Kafin yace may kuma nayi Amma daga zuwana yanzu ban yarinyar in dauka ka make ya ka hana mutane iya shegen ka umar yayi yawa saidai addua kawai. Kin zuwa sultana tayi wurin ta a nan ya fara tafiya da yaran yana fadin bari mu shiga wurin mama mu gaisa. Yaja yaran shi suka nufi hanyar dakin mahaifiyar shi sun rigani shiga don haka ban nan suka fara kwasa dashi. Yana shiga tana zaune a cikin mamaki takaicin labarin da Nafisa tazo mashi dashi yayi sallama ya shigo falon. Yana aje yaran saman kujera tare da fadin mama mun samayku lafiya ? Lafiya ta amsa mai a takaice tare da fadin wa yan nan yaran fa daga ina kazo dasu kuma yaran waye kuma ? A daidai lokacin da ya kara rungume Sultana a jikin su su Abdul suna haye mai jiki cikin nuna shi din mahaifin su ne. Saidai hakan bai hana hjy yi mashi wanan tambayan ba ya dago kai a hankali yana fadin jikokin ki ne mama yaranane. Babawo yaran ka ko may kake fada min haihuwa kayi da wanan yarinyar ko may ? A daidai lokacin muka shigo part din tare da murja da fauziya da sallaman mu don yana wucewa Amma tace jeki ki gaida sarakuwan ki. Shine muka nufi part din ina rike da hannun fauziya a makale dani muka shiga part din. Sallama mukayi yanayin da muka same su a ciki ya nuna muna wani magana sukeyi mai muhinmanci a lokacin. Har kasa na kai irin gaisuwan al,adan malam bahaushe cikin ladabi nake gaishe ta da mama ina wuni mun samay ku lafiya ya gida ? Sai daya dago kai ya kalleta tace lafiya tana basarwa mun anzo lafiya ta fada tana kawar da kai gefe. Lafiya kalau na fada saina koma na zauna a kasa nayi shiru tare da dukar da kai ina wasa da hannun Fauziya. Falon yayi shiru na dan lokaci sai shi ke dan hira da yaran shi yana tambayan su may suke so. Hjy dake mai kallon kasa kasa imani da takaici ya kashe ta a lokaci daya don gaba daya ma bata a cikin hayacin ta a lokacin. Can na dago ina fadin zan shiga in gaida mutanen gida bata tanka mun ba sai shine yace kada ki dade kin san yaran nan ba sake jiki zasuyi ba idan basu ganin ki a kusa. Ka bata yaran ta ta tafi dasu wurin kakannin su mana bazasu tafi bane idan ban tashi ba yacewa uwar . Tayi mai wani irin kallo na kaidin tare da kawar da kanta gefe daya kokatin amsan Sultana nayi daga hannun shi akai sa,a yarinyar bataki ba a lokacin ta biyoni muka fice tare muka barsu nan. Zama yayi har ya gaji batace dashi kalaba karshe ma tayi wani nishi ta fice daga falin zuwa cikin dakin kwanan ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:31 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAMANIN RAHIM IYYAKA NA, ABBUDU WA IYYAKA NASTA, IN, , , , , Muna fita har lokacin a tsaye waje muka samu su Amma mama hadiya hjy maryam da sauran yaran gidan kowa na mamakin ganin mu. Amma har yanzu kina gun bara na gaida mamu nazo mu gaisa maimakon in nufi part din mamu kai tsaye na hjy maryam dake tsaya muka nufa. Ganin haka tabar gurin itama ta nufo mu part din nata muka gaisa har lokacin wani irin kallo na mamakine karara a indon ta ban tsaya ba don irin kallon kurullan da take min din a lokacin. Haka na fito dauke da Sultana murja da Fauziya a ko wani gefena muna tafe muna hira murja tana fadin A ruwa ga baki daya kin sauya kamar ba kece ba kin koma kamar balarabiya dake kunyi masifan kyau daga ku har yayan ku. Wallahi kamar ba kece kika haifi yaran nan ba naku don kamar har yanzu kike budurwa kike. Murmushi kawai nake mata muka shiga wurin Mamu mun sameta zaune a falo tana ba dan karamin yaron data haifa a bayana abinci. Da sarsarfa na isa gurin ta na rungume ta a cikin murnan ganin juna tace kada ki karya mu da wanan nauyin naki haka ? Na daga ina dariya kafin in zauna kasa wurin kafanta ina fadin mun same ku lafiya mamu na dubu yaron da aka haifa a bayana nace mamu wanan yaron naki duk mun fishi kyau dakin nan. Ta dan kalleni tana fadin gashi ko gwaggona ko yaushe cewa take yana kama da mijin ki sosai duk shi ya biyo. Dariya na kwashe dashi ina kokarin aje Sultana data makale min a jiki ina fadin haba mamu wanan ina yakai yaya umar kyau ? Sultana taki zama Fauziya ta dauketa da karfi tana fadin bari a goyata ko zatayi barci anty. Yau sai gamu ga mutanen turai har da tsaraban bakin fuska da karuwa aka samu bamu sani ba haka ? Jin muryan mai magana yasa muka juya muna murmushi hjy maryam ce da imani ya cika ta kara biyoni part din mamu. Ta shigo har cikin falon mamu ta zauna saman kujera muka kara gaisawa tana fadin gaba daya Fatima ta sauya kamar ba ita ba. Murmushi mamu tayi mata kawai sai murja ke fadin abinda nake fada mata ke nan nima ai ba zakace ita ta haifi yaran nan ba kamar budurwa har yanzu. Tace ai abu yayi kyau ai haka ake son aure ka auri namijin da zaka karu yan uwanka su karu shine dadin auren wayayyen namiji. Shiru mukayi ba wanda ya tanka mata tana ta zuba can ta mike tana fadin bari na leka Umar da inga sauran yaran. Ta mike ta fita tana bacewa murja tace munafuka gulma ya cita ta rasa yadda zatayi har da shigowa ta zauna. Na kalli murja ina fadin har yanzu halin nata yana nan ne tace may zata fasa saidai Allah ya gyara tunda sun sawa ransu mugun abu kullun. Yanzu ji abinda take fadi fa watau kin samu wuri yan uwanki zasuci arzikin da kike ci kema ke nan. Mamu dai bata tanka muna ba sai cewa tayi a nan ke nan zaku wuni yau nace banyi tsamanin hakaba don yanzun ya gama fadin akai yaran gida sun ki sake jikin su. Zasu sake ai yanzu basu saba damu bane basu sanmu ba shiyasa basu yarda ita wanan gata sun shige sunyi shiru da uwarta ciki kila tayi barcine ta samu baya. Su mazajen nawa suna gun uwargidan su ta rikesu ke nan mama ai ta bar maki don cewa tayi kece kakarsu a kawosu wurin ki da zamu fito. Sai mamu tayi murmushi tana fadin hjy ke nan har yanzu dai abin na nan kiyi kokari ki shaye duk wani abinda zata fada akan ku don darajan mijiki a wurin ki ita din uwace kuma a wurin ki. Yara kuma ko taki ko taso jini ya riga da ya gauraye da ruwa tun farko sun makara. Mamu kawu fa yana shagone tunda muka shigo naga part din shi a rufe na tambaye ta tace bai dade da fita ba kuka shigo kila baisan da zuwan ku bane ya fita. Kin shiga wurin gwaggo ta tambayeni da cewa Amma nace yanzu dai zamu shiga daga gun su hjy muke. Na mike kenan da zuman zuwa gurin Amma sai gashi yayi sallama ya shigo part din na mamu ta amsa mai a cikin mutunci. Sai daya kai zaune suka fara gaisawa dashi tana mashi yaya hanya da yara ya amsa da lafiya mun samay ku lafiya yaya Addah ta iso kwanaki. Ta amsa da lafiya tazo tana godiya sosai Allah ya kara arziki mikewa nayi a daidai lokacin ya dago kai yana fadin ina kuma zaki. Ban shiga wurin Amma ba na bashi amsa ina kokarin gyara gyalen kaina dake sabulewa a lokacin gashina da ya kwanta lub lub a kaina yana baiyana a fili. Amma kin san yaran nan sun gaji hutu suke so yanzu don haka kizo mu mayar dasu gida su huta hakana. Ya idan ban shiga gurin Amma mun gaisa ba kasan ban kyauta ba yara ai nan ma gidane su zauna mana su huta a nan. No ya fada yana mikewa tsaye yanayin shi yana nuna shima a gajiye yake lokacin ko kuma yana cikin wani yanayi mara dadi a lokacin. Ki shiga ki fito muna mota muna jiran ki Sultana fa ya tambaya tana gun Fauziya ta goyata tayi barci sai yayi shiru ya rigamu fita part din. A gurguje na shiga wurin Amma din muka gaisa take tambayana yaya kuma taga ban zauna ba na bata fuska ina fadin yaya ya matsa in fito tafi yaran sun gaji wai. Shi umarun yace haka yana ina mara kunya wa zaiwa iya shege ne yanzu da rashin kunya shi a ina yayi wayau ba a gidan nan ba ? Yana mota na bata amsa ina hade rai nan na barta na shiga wurin mama hadiye saiga yara sun zo kirana da gudu wai ance in fito mu tafi. Raina kara batawa Amma ta mike tsaye tana fadin wanan wanan sadauki akwai iya shege dashi kabar yarinya mu ganeta saboda diyan ka zaka takura ma yar mutane. Amma na biye dani tana masifa a bayana a gurguje na sallami mamu fauziya ta biyoni da yarinyar a bayanta . Ina sadaukin yakene tana kokarin gyara daurin zanin jikinta dake banyewa a lokacin. Ina ja,irin yaron yake ka hana yarinya zama taga iyayyenta don iya shege ko ? Amma may kuma nayi yayi tambaya cikin natsuwa yana zaune gaban mota ya sakewa yara Ac suna zaune a baya. Yo ka matsawa yar mutane tafito tafito ku tafi daga zuwanta kamar ba gidan su tazo ba . Amma dai Amma kinsan matatace dai ko ko wani lokaci ina iya sata ta fito yaran nan sungaji basu huta ba tun shekaran jiya da muka taso dasu. Kaga ja,iri mara kunyar banza ni kake fadawa matarkace yo ai basai ka fada ba tunda gashi ka nuna muna iko da ita. Ya dan sake murmushin dole fuskan shi ya nuna gajiya a lokacin yana fadin Amma zancen kike so idan kina son zama da mune sai ki shirya inzo in daukeki mu tare can gidan mu huta tare ko ? Da sauri nace daga inda nake wallahi daya fi muna sauki yaya mu zauna muna kallonta ko kuda ba zan yarda ya taba min ke ba Amma. A, a karya kukeyi ja,iran yara ku daukeni ku kaini gidan ku ku wahal dani ina zaune kalau yace min don Allah shiga mu tafi na kalli murja nace murja ku shiga muje keda Fauziya don Allah. Baice muna komai ba suka bude baya suka shiga har lokacin Fauziya tana dauke da Sultana data banye a bayanta. Sallamu Alaikum ta fada daga kofa tare da fadin hjyn salma na dakine tana tambaya Nafisa dake zaune da waya a hannun ta tace tana ciki ta kwanta ne. Ta juya zata koma maryam banyi barcita fada daga kofa kinzo tsegumin ganin abin mamakin da yaran nan sukayi ko ? Wallahi kamar kin sani hjy wai dama ashe sun haihu ni ban taba jin labari ba a gidan nan yadda kika gansu haka na gansu maryam. Maryam dani yaron nan yake wasa harni zai rainawa hankali akan yarinyar idan nayi mai magana yace indan bashi lokaci karatu takeyi idan ta kare zai turota. Da zan ganta sai ganin su nayi da iyalinsu abinda banson akai sai da ya kaimu gare shi ta fada tana hade zuciya. Hjy yarinya ta koma kamar wata sarauniyar mata a gurin gwajin kyau ai shike nan dama burin Alh ke nan ya kuma cika. Shigowan salma ke nan gida da goyon yarta wani kallon mamaki tayi masu lokacin da ta samesu tare suka gaisa take tambayan may ke faruwane mama na ganku haka ? Uhummm salma ke dai bari yayan ku ne suka zo wai ashe har yarinyar nan ta haihu har uku amma ba wanda ya sani. Wai wani yayana kuke magana hjy maryam dake fada mata tace umar mana da yarinyar nan Fatima kinko ga yadda yarinyar nan ta koma kamar haihuwan larabawa. Salma ciki murnanta tace lah ashe sun zo don Allah maman ikilima har sun haihu da yaya kike fadi. Sun haihu wallahi salma sai ma kinga yaran kamar ki sace su don kyau da daukan ido wallahi bazakice yaran kasan nan bane. Na banza inji hjy jummai ta fada cikin kunan rai dani yaron nan yai wasa sai na nuna mashi ni ba sa,arshi bace . Don sai na raba wana tsinanen aure na kuma rabashi har ita da yaran mugata tsiya. A,a mama don Allah don Allah mama ki barshi da matar shi tundai yana son abinshi kinga har da zuria a tsakanin su kuma yanzu. Mama abu batun yau ba kina nuna adawan kin wanan auren gashi yanzu har ankai ga hayayafa haka yara kunce har uku don Allah dai mamaki barshi da iyalin shi dai. Ke rufa min baki marasa kinshin zuciya sakarai da bata taba wayau naki na barsu din aiduk ku dinne barayin na tsunta dake dashi. Salma ta dago kai ta kalli uwar tare da fadin ni gaskiya nake fada maki mama kin dai san rabo yana kashewa yana rayawa kuma. Da yanzu rabon yaran nan su fito ta tsatson fatima da yaya ya kashe ki fa mama idan kwananki suka kare kana jayaya da Allah ne mama ? Lalai salma ke sakaraice karan ma ta karshe a daidai lokacin Nafisa ta dawo falon tana fadin anty salma don baki ga yadda fatima ta koma bane wallahi ko ke da kinji wani iri a ranki. Tace wani iri namay nafisa bayan nasan Allah bai raba daidai ba tun farko kowa rabon shi yake ci ke nafisa wallahi in wanan halin zaki dauki zaki samu matsala a rayuwan ki kuwa. Nan su ukun suka haye salma da fada da zagi karshe ma bata zauna yinin da tace zatayi ba tayi masu sallama zata tafi. Har takai kofa uwar tace wallahi naji wana magana ya fita sai na saba maki fiye da tsanmanin ki bata dai ce komai ba tayi dariya tana fadin ni mama ba sune gabana ba yanzu kowa ya iya gidan shi dai ta fice. Hjy maryam ta dade suna mayar da zance da sarakuwa har da basu labarin irin matsa min da yayi in fito mu koma gida don yara. Shike nan maryam yanzu kin fara fahintar abinda nake hangowa a cikin auren yaran nan ko ? Duk da hjy maryam bata fahince taba sai dai tace kwarai kuwa hjy ai na dade da gano manufarki ba yau . Hjy Jummai tace yadda maimuna ta sakani bakin ciki nata sai yafi nawa don ita ga saki kuma in saka ya karbe yaran muga ta tsiyan cin arziki. Muna shiga gida yaya ya kwalawa maria kira ta fito da sauri daga part din su tana zuwa yace ta ba yara abinci suci tai masu wanka su kwanta. A daidai lokacin muka karaso ciki tare da su murja part din shi naga ya shige bai ko waigomu ba. Nan falo muka zube muna hira da murja sosai inda a wurin ta na ji wasu abubuwan da akayi a bayana wanda take ban labarin su. Ban lekashi shi kuma bai fito ba saida naga lokacin sallah yayi na mike na shiga wurin inda samu bai daki yana bandaki a lokacin. Kara budan kofan shi ya dakatar dani daga juyawan da nayi zan bar dakin na juyo ina fadin na dauka baka tashi bane ai kana kwance. Yanzun kika tuna dani kina can kin samu yan uwanki yau kin manta dani na danyi murmushi ina fadin. Haba yaya yaya zan manta da kai yau dai kawai ina bata lokacinane da yan uwa saboda farin ciki yau gani a gida duk da ka hanani zama da Amma muyi hira yaushe rabo da juna. Sai gyara hannun jallabiyan jikin shi yakeyi yana fadin zaki jamin masifan fadan ta akaina da zagi idan ina cewa kiyi abu gabanta kina mun gardama ya fada lokacin da ya dauki tasbahan shi zai fita. Bayan na fito na samu murja a dakina har tayi alwala nima alwalan na shiga nafito nayi sallah muka dawo falo muka zauna don cin abinci. Lokacin ne ba nemi Fauziya dake can leke da Sultana tun yarinyar na mata kiuya har ta dan fara sakin jiki da ita don daukanta da takeyi da goya ta. Murja ta kira mukaci abinci a tare duk yadda tayi yarinyar taci abinci taki ci saima kukan da tasa a karshe na karbe ta daga hannun fauziya din. Ya shigo ya samu muna leke da Fauziya data bar abincinta ta dawo inda yarinyar take saman jikina sai daya shigo ya karbe ta daga hannu na fauziya ta rabu da yarinyar don bata iya zuwa gurin shi. Ya dan zauna a falon sai dai bai kulamu ba din ya kula su murja sun sha jinin jikin su dashi tun lokacin daya zauna wurin yana rarashin yar shi. Mikewa yayi da yarshi a hannu ya nufi dining ganin hakan na mike daga inda nake zaune ina muna cin namu abincin a kasa saman kafet. Abincin na bude ina tambayan shi abinda zan zuba mai yaci sai da ya lumshe ido kamar baison magana lokacin yace ke may kikaci ? Tuwo naci don shi nave suyi mun ya lumshe ido yace zubamin irun shi kawai yaran fa suna barci har yanzu na bashi amsa ita wanan ma goyon da ta samu wurin fauziya shine taki kwanciya. Ya sake lumshe ido tare da mika hannu ya dauki cup din dake aje yana tsiyaya ruwa kadan ya kurba da bisimilllah yasha. Yaja abincin bayan ya wanke hannu ya fara diba yana kaiwa a bakin shi har lokacin Sultana tana a jikin shi naso in karbe ta ya daga min hannu na barshi da ita. Daga inda nake zaune wayana yai kara na dauka nasan mamu ce don ita kadai keda sabon layina ina dauka take fadin kin tafi min da yarinya bayan kinsan tana zuwa hadda. Mamu a barta yau mana mu wuni a tare da ita don Allah gobe sai ta tafi idan Allah ya kaimu kinsan halin karatu nan ba wasa a cikin sa ki dawo min da ita kafin lokaci tafiya karatu yayi. Murja kinji mamu wai Fauziya ta koma gida barta idan na tashi tare zamu koma anji ai daga inda yaya yake zaune ya miko min murya yana fadin ba tace akaita gida ba ta tashi in sauke ta fita zanyi yanzu idan nagama. Mikewa nayi na shiga dakina na fito da wani babban jakka nace ki kaiwa mamu ki ce zamuyi waya murja ma na mika mata ledan ta nace kafin kayana ya iso ki fara amfani da wanan. Fita yayi suka bishi baya har bakin mota na rakasu suka wuce ya sauke su a daidai get din gidan bai shiga ba yace akwai inda zai tafi yana sauri. Kamar mai jiran tsamani hjy maryam ce zaune da yaranta sun zubawa kofan shigowa get ido suna hira sama babban tabarma idan tana son yin wani gulma haka sukan wuni zaune waje don ganin kwam. Ganin fauziya tafe da babban jakka tana ja saida murja ta bude get ta shigo ta kama mata sukaja zuwa dakin mamu suka aje. Daga inda suke zaune suka zuba masu ido saida suka shige da jakkan mai kamar jirgi part din ga tsawo ga nauyi da alama kayane masu yawa a cikin sa. Wanan abinda ta gani ta tafi ta tseguntawa hjy jummai abinda idon ta ya gani aiko nan hankalin hajiya ya tashi sosai dole ta nemi kannenta tana labarta masu zancen zuwan mu da abinda hjy maryam tazo mata da tsegumin shi da yamma. Ranan kamar hjy zatayi hauka a gidan hankalinta a tashe yake sai yamma kawu ya dawo daga kauyen dayaje dauri aure yazo ya samu labarin zuwan mu daga bakin yaran shi dake tasowa yan samari. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:31 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMIN RAHIM IHDINAS SURATAL MUSTAKIN, , , Mun zo mun gaida kawu da imani da mamaki mu ya cika mai zuciya har ya kasa boye mamakin shi gare mu yana fadin wai kai Umar akidar turawane ka dauka ko ra,ayin kane haka nakin fadan komai wa kowa saida a ganka kwatsam da abu daga sama. Yata harda ke kin koyi wanan akidar tashi kuma yanzu yana kokarin mayar dake haka da irin halinsa ace har zaki haifi yara har uku amma bamu da labari a nan? Ayi hakkuri kawu na bashi amsa a cikin ladabi sai ga su hjy sun shigo falon gaida su na fara tayi kamar bataji ba saida kawu tace baki jin suna gaida ke jimmai . Ta dan juyo tana amsa min ta juya wurin kawu tana fadin dama yaran nan nake son magana dasu a gaban ka na shigo. Da sauri ya umar ya dago kai yana kallon ta da mamaki yana son sani abinda aka kawo mu kara wurin mahaifin shi a kai . Ya akai haka daga zuwan ku har kun batawa mahaifiyar ku rai Umar ya akayi haka ya faru kuma ya fada yana mai kallon fuskan dan nasa cikin yanayin nuna damuwa. Kai yaya Umar ya dukar batare da ya furta komai ba sai da yaji mahaifin nasa ya kara maimaita tambayan shi gareshi ya dago kai yana fadin . Daddy a iya sanina bansan nayiwa mama komai ba tun zuwa asalima tunda nazo bamuyi wani maganan kota arziki a tsakanin mu ba balle ince ga wanin abinda ya hadamu da ita. To ke kinji kawu ya fada yana kallon mama tare sa canza yanayin fuskan shi yana fadin jimmai bana son haka ga yaran nan. Ki bar yaran nan suyi rayuwan su babu tsagwama a ciki haka kwanaki habbib ya kawo min kara ki akan iyalin shi . Wanan dalilin yasa nayi karan wana yanzu gurin ka don ina son a tambayar min shi ko yanzu ya samu wasu iyayyen da suka fimu ne ban sani ? Da har wana yarinyar zata tara iyali haka ban sani ba kuma banko ji labari a gurin wani ba sai kawai in gansu kwatsan da yara sunzo muna don may raina ba zai baci ba Alh ? Kawu yace wanan kina da gaskiya don yanzu haka zancen da mukeyi da su kenan kika shigo falon nan. Sai abinda nake so dake ya kamata yanzu ki fahinci halin Umar don halaiyanshi sai hakkuri don na fahinci haka Allah ya hallice shi yadda yake shiru shiru hakama komai nasa yake tafiya. Ni dai ina daga gefe nayi shiru na kama bakina tunda ba wanda ya ambace ni a cikin zancen nasu. Banga laifin shi ba ai tunda ita wace yake bare baren akanta ta kama uwarta ai shidai ne ake kokarin rabawa yanzu da tashi uwar . Yaya ya dan murmusa tare da fadin bare bare kuma mama akan me zan dinga wani bare bare har in manta dake ? Tace gashi kuwa wai har kaine da shiga dakin maimuna ka kasa shiga dakin maryam ka gaida ita don kawai kana auren yarta ko mai ? A natse ya dago kai yace mama koda na shiga part din ai yanzu ba laifi bane don gaisuwa dai kawai saboda akwai nauyi mai girima a tsakanin mu . Don yarta tana a matsayin matata kinga dole munzo in shiga in gaida ita. Ko mama ta manta a gaban kawu take tace da dan bata babawo a gabana kake kiran wanan yarinyar da matarka ? Jimmai ba matarsa bace ko zaki raba abinda Allah ya hadane gaisuwa a tsakanin su shine abin tashin hankali kuma yanzu? Kin manta har gobe ina zuwa gidan yayaki gaida shi da sauran yan uwan ki girmana sukayi ko haihuwana da nake zuwa gaidasu da girmana. Don haka ban son irin maganan nan kin bar yaran nan yadda sukazo a cikin farin ciki su gama su koma lafiya hakana. Nan mama ta fara fada cikin tashin hankali tana fadin abinda ke cikin ranta a lokacin tana cewa dama abinda aka kulla ke nan don kawai a jaye mata da daga gare ta. Da kawu yaga tashin hankalin yai yawa ga yaran har sun fara rudewa da masifan mama suna kuka suna make muna a jiki. Fatima dauki yaran nan ki tafi dasu idan na gama zan shigo in dauke ku mu tafi nan na dauko yaran muka fito daga part din kawu zuwa wurin su mamu don ban shiga ba da muka shigo. Na shiga muka gaisa har lokacin yaran basu bar kuka ba nima idona da hawaye a rude mama ke tambayana na kasa fada mata komai. Murjace tace ya wuce hjy ce don naji muryan ta a gurin kawu yanzu da zan shigo da sauri mama tace may kuma kukai mata daga zuwan ku. Sai an mata wani abu tunda neman nayi takeyi dama a hankali nace wai don may yaya ya shiga gaida mamu da muka shigo bai shiga wurin maman su ikilma ba. Yau naji kitihi a gidan nan yau kuma har turashi ake ya gaida maryam a gidan nan har ta manta da ita da bakinta tace ba wanda ya haifa mata diyan. Har ya fito muka tafi ban samu shiga wurin mamu ba ranan sau murja naba sako ta fada mata mun tafi. Kwana biyu bamu shiga gidan ba gani ina son zuwa mu zauna da ita in mata bayanin kayan dana tura akai mata kafin inzo har zuwa lokacin ban samu bayani da ita ba. Nafisa da salma suka zo gidan saidai basu samu yayan su a gida ba ya fita tunda safe maria suka samu a falo da yar aikin mu tare da yara suna hira. Ina kwance a daki saiga maria tazo tana fada min anyi baki suna falo a zaune nace gani fitowa yanzu ki basu abin motsa baki tace na umurci su Asiya su basu ko. Na mike da kyat don duk jikina banjin dadin shi yai min nauyi haka kawai ranan koda na fito ina jawo kofana sai nayi arba da Nafisa tana bude bude kofofin gidan ga Salma na mata fada a bayanta ta bari haka baida kyau. Ki shigo gida kina masu bincike sai kace an turo mu muzo mata rashin mutunci sai naji tace wa yar uwar . Halan gidan tane da sai da izinin ta zamu yi komai gidan dan uwan mu ne fa ba nata ba kuma kin dai san dole in duba abinda tazo dashi tunda taki ba kowa tsaraba sai yan dakin su kawai ta aikowa katon jakka maman su ikilima ta gani take fadawa mama ranan. Don haka wanan shegiyar sai mun nuna mata gadara da isa akan dan uwan mu zata shiga hankalin ta. Jin hakan yasa raina ya baci nasan ba zuwan girma da arziki sukai min ba ke nan ina shine bada Nafisa ba da take wanan magana haka . Don haka ina jin abinda ta fada tana shirin bude kofan dakin yaya nace wanan wani irin rashin tarbiyane haka kuma Nafisa ? Gaba daya suka juyo don basu san ina tsaye a wurin ba da suke magana nace ya haka zaki shigo min gida kina bincike kamar an turo ki kiyi min hakan ? Gidan ki fa kikace ta fada tana min wani irin kallo a wullakance nace kwarai kuwa ko gidan ki ne wanan ke na tambaye ta ? Tace magana barnan baki amma dai kin san gidan dan uwan mu ne na jini daya ko don haka zan iya yin komai fiye dake a gudan nan ma tunda ke auren ki kawai yakeyi . Nace mijinane tare muke kwana muke tashi tare a shimfida daya muyi komai tare a gidan nan dani dake yanzu wafi kusanci dashi cikin mu. Au har wani gadara kikeyi dashi na kuna kwana tare kuna tashi tare dashi kwana nawa ya rage maki kuyi tare dashi. Nafisa kinsan abinda kike fadi kuwa kizo gidanta kina fada mata maganan banza haka kamar wata sa,ar yin ki matar yayan mune fa yanzu. Kyale ta anty Salma dama abinda tazo yi mun ke nan dadin abindai itama mace ce kamata gidan wani zata tafi ba zata tabbata a gida wurin mama ba. Sannan da kike fadi kwana nawa ya rage mina gidan nan ko yanzu dai na bar gidan nan na riga da na shamci kowa don ko yanzu aka kashe biri, biri yai barna don tun ba yau ba aka so ya sako ni bai sake ba . Yanzu ko ko ya saka ban saku ba don mun riga da mun zama daya dani dashi yanzu rai uku ba wasa bane Nafisa koma ki fada wa wanda ya turoki da ya makara wallahi yar zakanya ta girma. Nafisa tace da mamaki wanan magana ke nan nace mama ba sa,ar yina bace kin sani kedai da kikazo fada min baki da baki dake nake zance yanzu. Nafisa dama saidana fada maki ki bari yanzu gashi kuna kokarin haddasa tashi wani sabon tashin hankali kuma. Fatima don Allah ku bar wanan zancen haka kada yai maku nisa yakaiku inda ba a so kuma yakai nace Anty salma ya kai mana dama da gaiya tazo gidan nan don ta fada min abinda taga dama a gamay dani. Iya kadai ace yaya ya sake ni ko badai raina zai rabani dashi ba ai kuma rabamu akayi da karfi da yaji bada son ranshi ba kinga ashe ba ni kadai zanyi wahalan ba. Salma tace haba Fatima don Allah ki daina biye mata kuna wanan abin haka bai dace a tsakanin ku ba gaskiya. Nagode anty salma insha Allahu nagode bazan kara tanka mata ba kuzo mu zauna a falo. Anty salma idan kin fito ki samay ni gida tace ta fita tana bakaken maganganu na rakata da harara . Fatima kun zo lafiya ta fada tana kallona sai lokacin na juyo na kalleta da kyau tunda suka shigo ban mata kallon kyau ba. Anty salma mun samay ku lafiya ya gida yaya yara da maigida na tambayeta cikin nuna mata kulawa. Ta danyi murmushi tana fadin kun shige England kuyi shiru abin ku haka har kun tara iyali haka masu yawa ? Nace kai anty salma nice dai ai aka kwara da ban zuwa gida shikan ai ko yaushe kuna ganinsa a kasan nan. Mun zauna munyi hira sosai da ita take ban labarin tayi karatu baya auren mu sai dai takardan ta baiyi kyau ba mijin ta kuma yace ba zai sake barin taci gaba da karatu ba. Mun tashi munyi sallah muna cin abinci saiga yaya ya shigo gidan ranshi a bace ganin salma a gidan bai hanashi ya tambayeni ba a cikin fushi. May ya hadaki da Nafisa kuma don kawai tazo gidan nan zaki mata rashin mutunci har kina mata gori. Ni din nan dai yaya ita baka tambayeta ko mai ya kawo har nayi mata gorin da tace nayi mata din ba. Shiru ya danyi na wani lokaci kamar mai nazarin magana na a lokacin kafin ya bude baki cikin natsuwa da kwantar da murya yana fadin. Na fada maki ki kara da hakkuri ga duk wani abinda za ai maki ki daure ki shanye amma baki dauki magana ta da muhinmanci ba kika biye mata kuka saida hali keda ita. Har mama ta kirani sai abinda ya bace mata a baki yau shine bata fada min ba a kanki. Kayi hakkuri yaya don Allah Nafisa bata da gaskiya don a gabana akai komai wallahi don tare muka shigo gidan nan da Nafisa. Sai kayi hankali dasu yanzu akan matar ka tunda kasan komai basai na fada ma ba. Amma ba hujja bane ace mun shigo gidan nan da gadara don kawai muna takama gidan dan uwan mu ne nan muce zamuyi abu cikin gaba gadi. Mumafa matane muna da yan uwan miji bazamu so suzo suyi muna yadda nafisa tazo tayiwa Fatima gaba gadi ba gaskiya. Salma ita ba zata koyi hakkurin zama da yanayin su ba har lokacin da Allah zai sa wanan abin ya lafa tunda tasan yanzu mama tana da cikin mu a ranta. Wanan abi yasa nake ta gudun zuwan mu gida tuntuni na dauka zuwa yanzu Zarah tayi wayau sanin irin halin da muke ciki na barazanan mama a kan mu. Na gaji dajin maganganun shi nace yanzu yaya mai nayi cikin wanan maganan da kake ganin laifina don Allah ? Yanzu daidaine ace Nafisa ta shigo gidan nan ta dinga shiga wurare har dakin kwanan ka wai tana duban abinda muka zo dashi. Dakina fa kikace ya fada a fusace nace ga anty salma nan tana mata magana tace wai sai taga komai da muka shigo kasan nan dashi. Nan anty salma ta kwashe komai daya faru ta fada mai yace shine daidai nafisa ashe bata da hankali haka ban sani ba ? Jin yana fadin haka na mike na bar su zaune na shige dakina sai da anty salma zata tafi ta aika maria ta kirani na fito nace anty salma zaki wuce ke nan tace eh fatima. Daga nan gidana zan wuce don yanzu nasan hardani mama tana can hake dani idan naje yau ba zan shata da dadi ba. Ledan dana fito dashi na mika mata ina fadin anty salma ga wanan kiyi hakkuri dashi kafin kayan mu yazo don Allah a gaida sauran yaran da maigidan ta amsa da ta gode shima ya ciro kudi mai yawa ya bata yana fadin sai mun shigo wurinta. Bayan tafiyanta na juya na nufi hanyar shiga dakina yace ina zaki baki ban abinci ba ? Ban dauka kana jin yunwa yanzu bane na fada ina kallon shi yanayin fuskanshi ya sauya. Yace kina nufin bazan maki fada ba har kike nuna ban isa ba a gaban mutane da wani kike son inji Zahrah da maganganun su mama koda naki yanzu ? Ni yanzu wani abin kuma na kara yi bayan wanda akace maka nayi kuma ka yarda dashi. Dole in yarda zahra tunda na fada maki tun farko kema kuma kin sani auren mu da zaman mu ba son shi mama da wasu a cikin gidan mu sukeyi ba. Gashi har mama yau tana kirana da wai ina bare bare akanki da yan uwan ki na watsar da nawa yan uwan na kama naki. Don Allah zahra ina kara rokon ki ki kawar da kanki ga duk wani abunda mahaifiyata da yan uwana zasuyi maki ki bari in rabu lafiya dasu kamar yadda ko wani da yake son rabuwa da mahaifiyar shi lafiya. Ta hanyan ki kadai zan iya samun haka wurin kawar da kanki da toshe kunuwan ki ga duk wani fitina ire iren haka da zasu tayar nan gaba don kawai su samu dalilin fakewa ta hanyar tuzuraki bukatan su ya biya. Aurena ya samu tangarda wanda bazan taba son hakan ya faru ba tunda kinsan kece dai ba a son zaman ki dani ko ? Ya kawar da zancen yana fadin ki ban abinci inci banci komai tunda safe na fita gidan nan. Banyi magana ba sai nufar wurun cin abincin danayi ina dubawa kafin ya tako a hankali zuwa wurin ya zauna har lokacin banyi magana ba. Ina son mu koma lagos don zama garin nan naga kamar zai iya jawo muna matsala da mama. Nace in dainice ai ba wani abinda yanzu zatayi wanda ban san manufar yin shi ba don haka ba sai har munkai ga barin garin nan ba ai. Ko yan uwa bamu zagaya ba yaya zakai maganan komawa wani kasa kuma yanzu duka duka har yaushe muka sauka garin nan ko kwana goma bamu cika ba fa. Gobe ina sa ran Amma zata bakunce mu gidan nan kuma idan tazo ba zan barta ta koma ba sai ta kwana biyu damu nan gidan . Aiko wanan zancen yai min dadi sai in hada ita da murja mu zauna kwana biyu nan din in samu ta sake jikin ta da dakyau a gidan nan. Yadda duk kikayi nadai fada maki gobe zanje in dauko ta in Allah ya kaimu da safe. Ranan nasa aka gyara dakin da Amma zata zauna aka kara saka komai da zaiyi daidai da rayuwan ta babu takura sai jiranta kawai muke zuwa washe gari. Sai dai duk abinda nake fadab mu da Nafisa bai fita raina ba ina nazarin maganganun data yaba min a cikin fadan sai da dare na kira mamu ina sheda mata yadda duk mukayi da Nafisan. Sai cewa mamu tayi dama mai kike nufi ai kadan ke nan ma kika gani indai dangi mijine da kanne miji ake farawa kafin akai ga maya gaba daya. Saidai idan ka iya hakkuri kana shanyewa sai abin yazo maka da sauki a rayuwa komai yazo ya wuce kamar ba,ayi ba haka rayuwa take. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:32 - 🀐🀐🀐: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRRATAL, LAZINA AL,ANTA ALAIHIM, , , , , , Washegari bayan ya karya ya fita ya ja gida saida ya shiga suka gaisa da kawu suka dan taba hira duniya dashi ya mike yana fadin zai shiga ya gaida su mama. A falo ya samu mahaifiyar shi tana waya tana ganin shi ya shigo ta katse wayan suka gaisa ya samu wuri ya zauna saman kujera. Dan shiru ne ya biyo baya kafin hjy tace dada jiya dai matar ka ta nuna min ta isa ta samu wuri a gidan nan har da kora min ya tayi daga gidan. Dan murmushi yayi kafin yace mama har zarah ta isa ta kori ko dan aikin gidan nan gida balle Nafisa yar uwata. Gashiko ta kora din an gani ta nuna yanzu suke da kai da komai naka yar uwanka bata da iko da abinka yanzu. Mama Nafisa dai ita ta kori kanta don na samu salma a gidan ta fada min komai daya faru Nafisa itace bataje da gaskiya ba. Ya isa ta daga mai hannu tana fadi rai bace na fahinci ka goyi bayan matar ka kaida salma ke nan . Yanzu basu da ikom zuwa gidan ka suyi abinda ransu ke so saboda ka auro yar gwal ka aje a gidan ko kada ranta ya baci. Mama ayi hakkuri don Allah da Nafisa da Zarah duk yarane dukkan su ya kamata a tsawata masu jiya nayi mata magana ba zata sake wanan halin ba insha Allahu. A,a tamayi ai wurin yi ta samu don haka tana da daman da zatayi duk iya shegen da taso a gidan ka. Dan kasa munafuncin da ka kulla lokacin da nake bugama waya akan ka sako masu ya cewa kake dani kana jiran ta gama karatu da mahaifin ku yace ka sakatane a can idan kunje. Ashe kasan munafuncin daka kulla da kai da mahaifin ka don kawai ku bakanta min rai babawo har ka yarda ka hada zuria da wanan matsiyatan mutanen. Tau yau dai zaman ta da kai ya kare ina son ka sallamar mata yarta ta dawo gun uwar ta suci tsiyan su tare. Mama me tayi da zan sallame ta ya bukaci sanin dalili cikin natsuwa tace tun yanzu tana ganin ta kafu a gidan ka don ta haifa maka wa yan nan yaran masu zubin zabaya yan ruwa biyu take ganin sawun ta ya doke na rakumi a wurin tsayi har zata iya gayawa Nafisa irin maganganun data fadamata kuma wanan sakaran salma na tsaye tana ji bata iya daukan mataki akan komai ba. Haba mama ai diniya sai ta zageki keda Nafisa ace nazo da matana lafiya kan Nafisa na saketa . Ni nafison a bari sai idan tayi wani abinda ya shafeni ko ya shafe ki wanda kowa idan yaji yasan muna da hujja mai karfi ba za,a zargeki ba kan hakan. Amma yanzu idan na saketa kan Nafisa ai mutane ba zasu gamsu da hukincina ba karshe ma in dorawa Nafisa baki jini kan hakan . Ko mai mutane zasu fada su fada bai damay ni ba ba zan taba yarda maimuna da yarta suci galaba a kaina na muddin ina raye koda hakan na nufin komai nawa zai kare akansu kuwa. Da sauri yace mama may wanan maganan naki yake nufi hakan mama don Allah akan wanan dan magana kada ki yarda shedan yai galaba a kanki ki kaucewa Allah. Ya juya wurin da Nafisa take rakube yana fadin ke kuma ki fita harkan Zarah na fada maki ku barmu namu ya hadamu da ita idan ma zan saketa ne a lokacin zan saketa ba wanda zai zargeni akan komai. Amma yadda kuke nufin inyi abu a cikin rashin tunane haka kowan ku nan sai wanan abinda kuke so in aikata yanzu ya shafa gaba dayan mu. A yanayin da yake magana cikin bacin ran da basu taba ganin ya nuna ba sai jikin mahaifiyar tasu da Nafisa yai sanyi lokaci daya. Nafisa ta matsa da sauri lokacin da yake shirin tashi tace yaya kayi hakkuru nima daga baya nasan ban kyauta ba kamar yadda Anty salma ta lurar dani daga baya. Mama kan dago kai tayi tana fadin anya babawo mutanen nan basu gama da kai ba duk da shawaran daka bayar yana da kyau amma ni sai ina hango kamar sun gama da kaine. Ina tsoron yadda uwarta tamayar da mahaifin ku idan ba kaima haka ake son mayar da kai din ba ji yanzu yadda ranka ya baci ka rufe ido kana fadawa kanwarka magana akan yarinyar nan. Mama ni ba wanda ya isa ya gama dani sai Allah dayayini kawai dai raina ya bacine yadda Nafisa taje gidana tana rashin mutunci ko yaya take da zarah ai dai matatace a yanzu ko ? Don haka ba zan zura ido suna wullakanta min aurena ba duk da irin kyautata masu danake don may ni zasu so su muzantani. Hjy ta rasa baki magana kanta ya daure don a lokacin bata son wani yasan abinda Nafisa taje tayi min a gida. Don haka ta rasa yadda zatayi ganun ya tubure mata a karo na farko yana fada a gabanta kan matarshi da ta tsana. Ya sake kuma ya kafa mata wasu hujjoji yaki ya saka wai saida hujja mai karfi bai kara second ba bayan ya gama magana da Nafisa ya bar falon mahaifiyar tasu. Mama bata taba tsinkewa da lamarin danta ba sai wanan ranan don gaba daya ya juye mata ya zama kamar na mijin zaki lokaci daya. Part din Amma ya nufa yana shiga ya samayta zaune tana shafa mai ya zauna ba tare da yayi magana ba bayan sun gaisa tunda tsaye kafin ya kai zaune. Jin shirun yasa Amma ta dago kai tana fadin lafiya kake ko sadauki ya danja tsuki yana fadin ba komai Amma ke nazo dauka muje gidana yau. Yau din nan yace eh ina son kije ki dan lekamu kiga yaya muka sauka ai na gani tunda naga iyalin daka tara da idona a duniya. Yayi murmishi yana fadin ki shirya muje na sa zarah ta shiryawa zuwan ki tun jiya zuwa na dai Amma tace ? To barin tashi tunda naga da gaske kake daukana din kazo yi yace ba matsala muje dai . Haka ta fito ba tare da ta dauki komai ba tabi dukkan matan gidan tana fada masu zata leka gidan mu ta ga saukan mu. Allah ya tsare a fili kowa yai mata saidai na ciki na ciki a zuciyar kowa da yadda yake fassara zuwan nata gidamu din. Tsab na shirya komai na shiga nayi wanka nabar yan aiki da yara suna karasa abinda ba,a rasa ba. Shiya shigo dakin a daidai lokacin da nake kokarin saka riga a jikina ya shigo yace sai ki fito gata nan ta iso yanayi shi kawai na kalla nasan baya cikin dadin rai a lokacin . Juyawa yayi zai fita lokacin nace yaya wani abin ya faru ne kuma yau dan girgiza kai yayi kamar karamin yaro. Tausayi ya ban lokaci guda na karasa wurin shi ina fadin yaya nasan nayi kuskure kan biyewa Nafisa danayi jiya sai dai lamarin zuciyane da bata da kashi yasa har na biye mata don furucin data furta min lokacin. Zarah na dauka zuwa yanzu kinyi hankalin da zaki gane matsalan da nike ciki a kanki da mahaifiyata zaki tayani yakar wanan kudirin nata mu zauna lafiya sai dai ashe nayi kuskuren fahintar hakan gare ki zarah. Hawaye ne suka zubo min a idona lokaci daya nasan banyi daidai ba tun farko ya rokeni da inshaye duk wani abinda suka bijiro min da shi na dauki alkawarin hakan gare shi. Nasan kin hakkuri da duk abubuwan da akeyi da kuma wanda ake nuna maki a zahiri kina gani saidai ina son ki sani saida hadin kanki zan samu burina ya cika akan kudirina. Zarah ya kamata yanzu kisan kina da darajan da za,a iya hasada a kanki har yakai mama tana furta min wai nazo ina bare bare a kanki da mahaifiyar ki. Nasan dole mama tace haka don ke din matatace kuma uwar yayana da nake alfahari dasu yanzu a duniya. To idan banyi bare baren da mama ke fadin inayi daku iyalina ba akan wa zanyi hakan bayan duk rabin samuna akan yan uwanane da mahaifana. Koku iyalina din da suke fadin ina bare bare akanku nasan bakuci ko kwatan kwacin abinda nakeyi yan uwana ba daga cikin abinda na mallaka din yanzu. Don hakane nake son ki natsu ki ban hankali ki wuri daya mu samu mu shawo kan wanan matsalan a cikin ruwan sanyi kamar yadda na shirya a tsarina. Ya kamata ki san darajan ki da kimar ki yanzu ya zatar wace zata tsaya ana kananan maganganu irin wanan kin sani zarah ban son yawan magana a rayuwata. Shiyasa nake komai nawa a dunkule sai bayan nayi wanda duk zaiyi magana daga baya ya furta abindake zuciyar shi gamay dani wanan yafi mun sauki a rayuwata. So ki shirya hajiya tana zaune a falo tana jiran ki da fatan zaki amfani da magana ta nan gaba yana fadin haka yasa kai ya fita ina jin su daidai zan fito Amma na fada dashi wai ina ita yar gwal din naka munafukan banza da wofi har kun manta da lokacin da kuka dagawa mutane hankali a baya kan auren ku damun bi ta naku da yanzu ina zaku kai wanan alhakin yaran naku ? Amma gani wanka ya samu na shiga yanzu don kada kizo ki sameni hakana ki dauka haka nake zama a gidana ta dan harareni a daidai lokacin da nake karasowa ina kokari rungumar ta. Shikani karki karasa ni don Allah yadda kika koma din nan kamar ke kadai mijin naki ke kiyo a gidan . Su maria ne suka fara fitowa da abinci suna mata sannu da zuwa tana amsawa tare da binsu da kallo tana nazarin su. Maria daki zaku kai mata komai zatafi sake jikin ta a can na kamo hannun ta ina fadin taso muje daki ki huta kagin lokacin sallah ya karasa sai mu zauna asha labati yaushe rabo. Nanma yayi min ai har wani daki zan shiga in zauna ina dai wuni kawai zan maku in koma anjima to ai kyaso ki dan kishingida dai ko ? Don na fahinci bai mata bayanin yana son zata dan zauna damu bane na kwana biyu na samu tashiga dakin da aka gyara mata tana sallama tana fadin a, a a ikon Allah. Ta kai zaune saman kujeran dakin tana bin dakin da kallon mamakin irin tsara shin da akayi da haduwan shi. Abincin na fara gabatar mata a gabanta bayan na gama ne na tuna ai murja bata zo ba tare da Amma ina tunane a raina yaya akai hakan kuma bayan ga yadda muka shirya dashi kuma. Don hakane zai kara kwantarwa Amma da hankali saboda shakuwan da sukayi da murja din wanan lokacin da su kadaine a gida tare da ita a gabanta a matsayin jikan da take gani a gaban ta. Waya na dauka na fita lokacin danaga Amma ta fara cin abanicin layin murja na kira nake fada mata ta daukowa Amma duk wanin abinda tasan zata bukata a kusa da ita tazo mata dashi muna son su kwana muna biyu nan ita da Amma. Cikin dan lokaci kadan sai ga murja ta hado mata goron ta tasbaha da wasu kaya kala uku don bukatan ta. Mamaki ya kamata tana fada da murja don may ta hado mata kayanta kamar wace zata kwana a nan tace yaya yace na hado maki na kawo. Zai dawo ya samay ni nan abinda zai mun ke nan yaje ya daukoni ina dakina zaune kalau ya kawoni nan inda ko rana bana gani balle lokacin ibada. Sai dariya nake mata ina fadin muma munada bukatan ki a nan ai yaya bai dawo gidaba har dare har ta kwanta bai shigo ba sai dare sosai ya dawo gidan lokacin har tayi barci ya tayar da ita yace taci nama da abin sanyi daya kwaso mata din. Sun dade daki zaune suna tatauna matsalolin shi wanda yana daga cikin dalilin dauko ta gidan shi da yayi. Da wanan tunanen Amma ta kwana a ranta ranan mamaki da tunanen duniya ya cika mata zuciya. Tana tunanen yadda uwa zata matsama farin cikin danta akan iyalin shi ta matsa sai ta daga mashi hankali. Gasu su ba irin iya shigen da basuyi mata a gidan a gabanta ko bayan ta tana shanyewa don kawai kawar da kai a zauna lafiya suda mijin su take kawar da kanta. Donme hjy zata kasa tunanen haka ga yayanta ta lura akwai kishin diyan ta a cikin zuciyar ta . Hjy saidai addua kawai don ta kula da abinda bahaushe kecewa idan uwa ta faye saka matan diyan ta gaba to walau ta ci fitsarin danta ko ta faye saka son diyan ta a zuciyar ta har yakai tana kishin matan diyan nata. Ta kula da abindake damun ta ke nan a zuciya don ta tuna da yadda aka kwasa da habbib da ita da matar shi har yakai habbib din yayi fushi tun tafiyan shi har lokacin bai kara leko kano ba tun lokacin. Wanan abin na hajiya da mai ya kama ko Aisha matar Aliyu haka suka kwasa lokacin haihuwan ta sai da akai jidali da ita da yan uwan mahaifan Aishan kamar Auren zai mutu a lokacin gashi kuma yanzu Umar yazo mata da wani zance na matsin da take mai kan lalai sai ya sakeni na koma dakin uwata da zama . Washegari ina idar da sallah na fito don in duba Amma da yara sai masu aikin da zasu hada abin karyawa kada suyi wanda bai gamshi Amma ba wurin ci. Na samesu zaune suna hira da murja a dakin hakan yai min dadi sosai don naga murja tasa ta sake jikin ta. Saida na zauna na fara gaida ita da kwana na juya nagaida murja don ko banza murja ta girmay ni ita da nafisa gurin haihuwa. Amma ya dare nace bayan mun gama gaisawa da murja na juya wurinta ina tambayan ta. Yar mijin ki yazo min da wani magana wanda ya tayar min da hankali jiya gyara zama nayi ina fadin wani magana yazo maki dashi kuma ? Zancen ku da uwar shi yarnan jiya banyi barci daren jiya ina tunanen wanan hali na uwar ku yaya zaki turo yar ki da batai aure cin mutunci gidan dan uwanta don kawai kiyayya ta batawa yarta kurciyarta. Dadin da nakeji na salma ke nan yanzu da salma ta kama auren ta ta fita zancen duk wani ingiza mai kantu da uwar zatai mata akan auren ta tun lokacin da sukai wanan takai kan satan data turata taiwa mijin ta kara kama kanta da yake tana son zaman auren nata. Sata kuma amma na tambaya cikin mamaki tace mu bar zancen nan don baki sanshi ba yanzu dai na fahinci dalilin daukoni gidan nan da mijin ki yayi. Fahinci wani abu daga cikin magana nan ki mijin ki yana bukatan kulawan a ciki wanan lokacin yana bukatan wanda zai zauna ya dan fahintar daku wasu abinda ku ba zaku iya ganowa ba a cikin zancen nan. Abinda nake so dake da farko natsuwa mu fahinci inda zamu fara dosowa wanan zancen don ba karamin fitina daga ke har shi kuke ciki ba. Shiru nayi lokacin da amma ke min bayanin kaina ya kulle sosai ga abunda take fada min wanda da farko ban dauke shi wani matsala ba a wurina. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:32 - 🀐🀐🀐: Ranan sai na wuni sukuku ina tunanen zancen mu da Amma wanda bata fito fili ta baiyana min shi a baiyane ba amma daga baya da muka zauna da murja mukai maganan sai na fahinci hjyn su yaya tana farautan rayuwana da rayuwan aurena ne ashe wanda hakan yake yawan haddasa min mafalkin su ko wani lokaci. Saidai magana irin wanan bai taba shiga tsakanina da yaya ba ko kadan sai yanzu da nake jin zancen a bakin Amma. Abinda dai na sani da wuya ayi sati daya banyi wanan mumunan mafalkin ba da ita wanda sai yanzu naba abin ma,ana. Idan hakane ai garama ta raba auren da takeso ta barni da lafiyana zaifi min sauki don duk ranan da nai mafalkin haka zamu kwana rikice da yaya wani lokaci kuma shine maiyin mafalkin bani ba. Dabi,ana ne bana fitowa gajal sai na dan gyara jikina kuma ban wuce takwas na safe banyi wanka har yara mun kitsa jikin mu har yan aikina bazaka zo gudan ka samay mu ba dadin gani ba komai sammako mutum kuwa. Ina shirin fitowa yaya ya shigo dakina da sauri yana fadin zarah fito ga kawun ki yau gidan mu. Kawu na ambata a fili ina mamaki yace harda su baba balarabe ai kin san dole suzo gidan nan tunda na dauko masu tsohuwar su ai. Da sauri na biyo bayan shi zuwa falo inda muke jin hayaniyar su suna dararaku a lokacin. Fitowan mu yasa suka dan tsagaita suka mayar da hankalin su garemu a cikin kunya nakai wurin tare da tsunguna kasa ina gaida su kawu gaba daya su. Kawu balarabe ne ke fadin gamu mun biyo ku tunda ku bakuje gaida mu ba umar baka san gidan mu ba balle iyalin ka yanzun kuma ka dauko muna uwa zuwa gidan ka. Yana dan dariya yace baba ba dauke ta nayi ba muma nan muna da bukatantane na dan lokaci a tare da mu. Ja,iri abinda zai fada maku ke nan ai ya daukoni ya kawoni nan ko tana bana gani sai dadi yake cika min a cikina ba dare ba rana ko nayi barci sai yaron nan ya tayar dani ya bani naci. Dariya suka kwashe dashi kawu mustapha yace Amma ai hajiya kin canza gaba daya wallahi da gani ba sai kin fada ba. Daki na mike na shiga na fito da yaran dukan su na kawo su wurin su kawu har yanzu basu son sake jiki da kowa a ckin dabara suka koma jikin mahaifi su suka kara makaleshi. Allah ya albarkaci zuria kawu balarabe yace yara haka tubarkalla masha Allah yau ina jummai dataga wa yan nan yaran da ina zata kai alhakin hana auren da taso yi nasu. Kai ke nan da kasan wanan kake fadin haka Amma tace don ita har yanzu ba wai ta saduda bane ta bangaren ta. Har yanzu tana kan bakan ta ke nan kawu mustapha ya tambaya da mamaki. Ta nan wallahi yanzu haka halin da ake ciki akan matsen lamba take kan sai yaron nan ya saki yar nan bata barsu hakan ba ta kwashi maganan komai ta fada masu hankalin su ya tashi matuka da jin wanan maganan. A hankali na mike na bar gurin don ba zan iya jin kalamin su na manya akan sarakuwar tawa ga dan ta a gurin ya dukar da kanshi kasa yana nuna yanayin rashin jin dadi ga kalaman da ake mata din lokacin. Kawu sani ma baiyi magana ba a lokacin shiru yayi kamar mai nazari a zuciyar shi. Barina gurin shima ya mike tare da yaran shi zuwa hanyar waje abinsha na umurci mai aikin mu ta kawo masu da dan abin motsa baki duk da safiyane sosai a lokacin. Kwana biyu da zuwan su kawu gidan mu muka shirya zuwa ziyaran yan uwa damu dashine gaba sai sultana dana rike su Abdul suna baya tare da maria da murja sai Amma. Ziyaran yayi kyau sosai don yaya yaiwa dagi alheri sosai a wanan dan ziyaran da mukai masu lokacin kayan mu sun iso na rabawa kowa daya dace a cikin dangi tsaraba har wanda ban zataba saida ya samu alokacin. Ranan da Amma ta cika sati uku muka mayar da ita gida tunda safe kowa sai yaba kyawon da Amma tayi a gidan mu akeyi. A nan ya wuce ya barmu zan wuni sai dare zai dawo ya dauke mu yace a part din Amma muka yada zango kafin in koma wurin mamu in zauna. Tare da maria mukazo don laluran yaran na shiga wurin hjyn su yaya na gaida ita muka dan zauna ta barmu nan zaune falo nida yara da maria ta shige daki daga ita har nafisa. Sai dan autan su yayane ya zauna tare damu yana hira tare da kulawa da yaran karshe dai da zaman ya ishe mu naga hjy bata da niyar bamu lokacin tane na fito na koma wurin Amma daga baya kuma na dawo wurin mamu. Har akai sallah azahar mukaci abinci ashe hakan danayi kuma wai ya batawa hjy rai matar da anan ta barmu zaune taki kulamu ko yan jikokin nata bata kalla ba balleni da maria. Sai bayan la,asar yaya ya shigo gidan direct wurin mahaifiyar shi ya nufa inda ya samu ta cika ta hau tayi fam dani. Yana zama yake tambaya nafisa zarah fa tana inane wai ? Uwar ta kalleshi tace wa zaka tambaya ita a nan tunda ba wurin mu tazo ba tana gurin uwarta mana yaran da kake kira da jikokina ina zata yarda su rabeni tunda a na daukana mai mugun hali. Mugun hali kamar ya mama ko ya kike ai bata isa ta rabaki da yan jikokin ba yanzu ni ba gashi amma yau ji nayi kamar kada ta dawo na ba. Ina ji da kunnuwa yaran nan suna tambayar ta kakasu tace bani bace kakarsu tana can part din ta tana rikesu kada suzo wurina a gaban idona ta nuna min banda hadin komai da yaranta yanzu. A hasale ya mike bai gama sauraren ta tana fadin ina kuma zaka yanzu iyayyenta su taru suce ban kaunar zaman lafiyan ka da matarka. To amma mama daidaine ta shigo gidan nan ta hana yaran nan zama a wurin ki bazan taba lamuntar hakaba gaskiya ko ina hakkuri da komai ba zan iya daukan wanan ba gaskiya. Na daice ka barta harku koma gida kuyi shi can don gaskiya abin bai mun dadi ba nima amma tunda kai kaji ka gani kan zama da ita yaya zanyi da kai. Ya kalli mahaifiyar rai bace kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ba tare da ya furta komai ba ya zauna ya dan jima zaune ya mike yana mata sallama. Kofan part din mamu ya tsaya ya tura dan wurin hjy maryam ya kirani yaron ya shigo ya gayar damu muna zaune ana hira yake fadin ga yayan mu a waje yace ki fito ku tafi. In fito mu tafi shida yace sai dare zamu tafi kuma na taso na leka har ya fara tafiya nace yaya ya waigo kace mu fito kuma eh kawai yace yaci gaba da tafiyan shi. Dan jim nayi ina nazarin shi kafin in koma ciki rai bace nacewa maria ku taso mu tafi yana jiran mu a waje don maria taji dadin zuwan mu gidan ta sake sosai a gidan. A mota muka samay shi zaune yana jiran mu har muka shiga yaran na surutu bai kula su ba nidai naja bakina nayi shiru ban tanka masu ba. Muna isa gidan ganin yanayin da yake yasa ban tsaya falo ba na wuce zuwa cikin dakina don nasan halin shi idan yai fushi baison aimai magana lokacin. Muryashi naji a bayana yana fadin meya hanaki shiga dakin mama ki zauna da yara ? Na juyo da mamaki jin abinda ya fadi nace waya fada ma ban shiga na gaida ita ba ? Wani lalataccen kallo ya jefini dashi kafin yace za, ai maki karyane kike son fada min ko may ? Sai maganan ya bani mamaki kafin kuma ya bata min rai saidai na danne nace hummm wani sabon sheri da munafunci kuma ake kokarin kulla min ko may ? Ai ba munafunci da sheri ya kamata ai min ba kamata yayi ace ban kai karshen magana naba naji ya kwasheni da wani gigitacen mari a fuskana saida na duka don zafi. Kafin yace ke har rashin kunyar taki yakai ki kalli idona ki karyata mama a gabana har kina kokarin zagin ta. Na dago ina dafe da gefen fuskana inda ya mare ni ina watsa mashi kallon tsana karara idona yana fitar da hawaye. Yaci gaba da fadi a daidai lokacin da Abdulsalam dake bayan shi ya yanka wani irin ihu shi kuma yana fadin . Don kawai kina dauka ina auren ki yanzu sai ki zagi mahaifiyata a gabana har kina kokarin karyata karya zatai maki komay ? Jin ihun Abdulsalam ya jawo hankalin sauran gaba daya sukayo kanmu suna kuka lokaci guda sultana ta kankameni tana wani irin ihu. Nace ka maraini yaya ba tare da ka tsaya kayi bincike kan wanan maganan ba na barka da Allah wallahi dakai da duk wanda ya zugoka a kaina. Bai tsaya ko kallon yaran ba ya juya ya barmu a gurin tsaye muna kuka muryan maria naji tana fadin madam mai yayi zafi haka yau tsakanin ki da Oga ? Kallon ta nayi na juya zuwa dakina rike da hannun yarana dake kuka har akai magariba ban fito ba har yaran sai maria dake sintiri don laluran yara a lokacin. Faisal autan su yaya ya shigo yana sallama ga tv na aiki a falon saidai babu kowa a gidan ganin haka ya juya zai wuce sai ga yaya ya fito daga dakin shi zai tafi masallaci ya ganshi. Jin motsin fitowa ya juyo yana gannin yayan nasa ya fara gaida shi tare da fadin anty Fatima fa da su Abdul dazu sunce in sayo masu ball na dawo gida shine na samu ance sun wuce shine na kawo masu yanzu. Kallin yaron da suke da shigen yanayi daya yayi yana fadin suna ciki wurin maman su ina gani daga nan ya tsaya yana kwallawa maria kira ta amsa don tana dakin su dama. Kafin maria tazo faisal da bai san kaiba yaci gaba da fadin tare suka so muje don kada kai fada yasa ban fita dasu ba sai na barsu nace su bari naje na sayo masu ai. Don mun dade falon mama tare dasu suna min hira yau ya juyo ya dubi yaron yace falon wa kace yace falon mu muka zauna dasu da maman su. Mama fa ya tambayi yaron mama kyalesu tayi ita da Nafisa suka shige daki nima banso hakan da mama tayiwa anty Fatiman ba wallahi na bita daki nace sun barsu zaune su kaidai ta koreni. Muje muyi sallah yace wa yaron yayin da cikin rashi yake maimaita innalliallahi a zuciyar shi. Amsan ball din maria tayi tana godiya tare sukai sallah a masallacin unguwan inda yaiwa yaron fada yabar kaiwa dare a waje hakana kafin yace driver shi ya kaishi gida bayan yaba yaron kudi da murna yana godiya ya tafi. Inda na idar da sallah na zauna ina tunane idan har hjy ta fara cin galaba akan danta zata iya fada mai magana ya yarda dashi a yanzu ashe kuwa aiki babba ya ganni a gabana. Shine ya turo kofan ya shigo udon shi ya sauka kan sultana dake kasa yashe tana barci a gurin tayi kukan in dauketa naki na tayar da sallah lokacin sai tayi barci. Daukan yarinyar yayi tsab zuwa kan gadona ya ajeta ya dawo saman kujeran dake gefena ya zauna. Ya dan dauki lokaci kamar ba zaiyi magana ba can ya dago tare da ajiyan zuciya yace cikin natsuwa zarah na fada maki tun bamuzo kasan nan ba . Na rokeki cewa ki mutunta min kowa nawa da yake nawa kamar yadda nima zan mutunta kowa naki kamar yadda ni kike mutuntani da aurena. Sai lokacin na dago kai nace wana taba yiwa rashin mutunci a gidan mu kaf ko bayanzu ba sai wanda yaso raina min wayau ko shi sai yara yan uwana zakace na taba wani tashin hankali dasu. Ya murmusa yace amma dai kin san tun farko inda maganan nan ya fito har zaki tsaya gabana kina kokarin karyata min mahaifiyar data haifeni a gaban idona. Nace yanzu kuma ai ya saura gare ka don ban zama ko yaushe dan magana kadan ya hadamu ka daga hannu ka mareni ko a gaban waye . Ni nagaji wallahi na gaji ba zan iya irin wanan zaman ba wallahi da kaje an fada ma magana baka tsayawa kayi bincike sai kawai ka daga hannu ka mareni . Idan ke kin gaji ni ba zan taba gajiya dake ba raini ne kawai ga kowa ba zan iya dauka ba don gaba ki sani ban raina maki naki mahaifan ba bako zan yarda ki raina min nawa ba. Raini kuma na nawa ne ba aiwa mahaifiyata ba ina ji ina gani tunda muka zo sau nawa ka shiga ka gaida ita. Kumani data haifa kana kokarin hanani zumunci da nawa iyayyen . Yayi murmushi ya mike tare da fadin komai zaki iya fadi yanzu ai saidai dadin abin ita maman taki tasan ban taba rainata ko mata wani abin bacin raiba. Don haka kema nake rokon ki akan ki kara yin taka tsantsan da duk wani abinda zai jawo mama tace maki kinyi mata laifi ko wani abu da har za a iya tunzurani a kanki Don nasha fada maki cewa kimin adalci don ni din na mijine namiji kuma yana nufin zan iya juyawa daga matsayina in koma wani matsayi a gareki don haka nake kara fada maki ki bini a sannu. Ya mike ya fita tare da kallin yaran dake ta barcin su saman gadona hankalin su kwance ya fice daga dakin zuciyar shi tana mashi kuna. Yana fita nakai kallona ga yaran dake kwance suna barci tausayin su ya kamani a lokaci guda ban san lokacin da wasu hawaye masu dumi suka kara sauko min a idanuwana ba. Ina kuka ina tunanen sakani gaban da hjy tasha alwashin yi taga bayan aurena da danta yanzu in haka ya tabbata yaya makomar diyana zai koma don nasan karshe dai karbe yaran za,ayi daga hannuna abawa hjy don babu mai rikesu sai ita. Haka muka zauna kusan kwanaki kowa sai harkan gaban shi yake a cikin mu iyakarshi in ya shigo ko kafin ya fita yaba yaran shi kulawa kamar yadda ya saba basu koda ina zaune bai kulawa da ni kamar yadda nima na dauko share shi din. Ranan da safe ya shigo dakina ina kwace muna waya da Aisha ina ganin shi na cewa Aisha zan kirata anjima na dan juya wurin shi a gyatsire na gaida shi da kwana ya amsa ba yabo ba fallasa tare da fadin zanje lagos yau ina ganin zan kwana biyu a can . Don haka ki kula da gida da yaran nan yasa hannu cikin aljihun riganshi ta ciki ya ciro kudi yana miko min tare da fadin wanan ki rike a hannun ki ko wani abin zai iya tasowa bana gida. Da ka barshi tunda komai muna dashi yace na sani ki dai rike wanan din a wurin ki nace na mika hannu na karba tare da fadin Allah ya tsare. Har yakai kofa nace yaushe zani bauchine ganin su yanzu muna batun share wata daya da wani abu a kasan nan fa. Idan na shirya zan fada maki in lokaci yayi ya fada yana fita daga dakin ganin bai gari yasa na kira murja mu zauna tare da ita don bata son zuwa idan yana nan bansan may yasa haka ba. Da rana muna zaune sai ga salma tazo muka gaisa take tambayan yayan nata nace yai tafiya a ranan. Sai naga bataji dadin hakan ba bata dai fada min komai ba nan muka zauna da ita mukai hira taci abincin rana tare damu. Saida tayi sallah tace zata tafi nace ta bari in kira driver gidan ya mayar da ita gida na tashi na shiga daki dubu hamsin na kidaya daga cikin kudin daya barmuna na hada mata da yan abubuwa na saka a leda . Lokacin dana rakota namika mata kudin da kayan saida naji tayi wani irin ajiyan zuciya tana fadin Fatima nagode yau kin rufa min asiri wallahi don ba karamin dadin wanan kyautar naki naji ba. Saboda may anty salma na tambaye ta tace kinsan halin mazan nan yanzu buki ake dashi can garin su dama na kannesa shine nake son dama indan rike wani abu kada in tafi hakana hannu sake. Yanzu kinga zan dan samu na rikewa saura har in samu indanyi dinki a ciki. Wani irin abu naji ya dira min a zuciyana nace anty salma kina nufin shi yaya Ahmed ba zai maki wa yan nan abubuwan ba ta danyi murmushi tana fadin fatima ke dai Allah ya sauwaka yanzu ko namiji yana maka idan baka dashi ga hannu ai ragagene. Karatun nan fatima yaya ya tsaya muna saida mukayi shi muka gama aiki dai ne yanzu ya zama fitina kuma don shi na gidana ya rantse ba zai barni inyi aikin gwaunati ba. Jin hakan shima mijin ikilima yace itama ba zatayi ba nace anty salma haka yaya Ahmed ya koma kuma. Tace bari kawai Fatima ina da maganganu da yawa danaso mu zauna muyi dake saidai ko wani zuwa nayi bamu samun lokaci. Kada ki damu anty salma zanzo har gidan in samay ki mu tatauna sai dai yanzu barin zo na koma ciki na kara fitowa da wani ledan turama a hannu na kawo mata tana batun yin godiya nayi saurin bude mata motar ta shiga ina fadin ta bari sai munyi waya da ita. Nan ta tafi ta barmu cikin tashin hankali ta barni da tunane kala kala a raina ranan ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:32 - 🀐🀐🀐: Salma ta wuce ta barni cike da tunane haka naja kafa na koma falon na samu murja zaune tana kallon film a falon. Ta juyo tana fadin ta tafi na amsa a wani yanayi ina zama nace ta wuce taci gaba da kallon ta sai kuma can ta juyo tana fadin . Yanzu salma rayuwan ta ya sake gaba daya kamar ba salma ba wallahi ta hadu da mijin daya natsa mata daukan kai da izzan nan nata gaba daya. Gashi tana mutuwan son Ahmed a rayuwan ta da bata son shi da tuni maman su tayi sanadin da ta kashe auren su wallahi. Murja inda Allah ya tsara ma rayuwan ka idan kana da tunane sai kayi hakkuri da hukucin ubangiji ai. Dashi Allah yayi zata zauna tace ai gara salma ma in fada maki don ita ikilima raguwace ta karshe ga aukin haihuwa kamar wata akuya. Haba murja dudu yaran su nawa yanzu ki duba fa diya uku suka haifa fa kike fadin haka . Nima ba gashi diyan nawa uku bane yanzu tace aike Allah ne yai maki kyauta da kari kowa ya sani kedai murja a fada a hankali kada duk shekara ki taramu gidan dan batta suna da cewan wanda zata aura. Tace wa ni baki daiji ba da kyau fatima, waneni da rayuwa irin nasu sun mayar da kansu wani iri kowa na fada dasu kan kama jiki kamar ana kara zugasu ne suyi. Yanzu wa zaice wai salma ta hada takarda don Allah ko karatun saida kawu da mijin ki sukai tsaye suka mayar da hankali ga karatu. Karatun ko baka aiki yana da amfani sosai na bata amsa ba wai da niya suka bar kansu haka ba murja akwai rashin waddata yana damuwan rayuwan su. Don kinga yanzu da zasu fara aiki ko wani sana,a mai karfi suna dan fita ko kuma kudi yana shigo masu zaki ga sun dan walwale cikin dan kankanin lokaci. Tace amma ai kawu yana kokari dasu sosai wallahi ke dai kawai akwai battalanci a cikin harkan su. Tun farko fa kin san komai basa iya yi da kansu yanzu sai abin ya zama masu sabo a wurin su ga lalurar yara da dawaiyarsu duk ya taru a kansu lokaci daya yai masu yawa. Na amsa da fadin kinga ke nan dole a taimaka masu ashe tunda Allah ya hore masu yan uwa masu shi da zasu iya tallafa masu din. Fatima yanzu ke da kanki kike wanan magana har kin mata da irin muzancin da salma da mahaifiyar ta suka dinga maki don kawai kawu ya dauko rikon ki ya kawo gidan har ya aura ki ga dan dakin su. Murja dane wanan yanzu salma yar uwan maigidane kuma yar uwatace nima ta jini idan ba don lalacewan zumuci ba ai ni jinin su ce dama. Ki dai bi a sannu kada kiyi zurfi da yawa don su din ba abin yarda bane da sauri. Nace Allah yasan dalilin sakani a cikin su murja don haka da zuciya daya zan zauna da kowani su. Kusan wanan hiran muka wuni munayi a ranan sai wani lokaci ka dan fito haraban gidan muna shan iska. Yara kuma suna wasannin su a inda aka tanada don su suyi wasa karan budan get din gidan da akayi ya mayar da hankalin mu wurin mai shigowa gidan lokacin. Bamu gane mai shi ba saida motan ya tsaya mukaga mata suna fitowa daga cikin motan data shigo gidan lokacin. Gaba daya mun mayar da hankalin mu gurin su da farko ban gane su ba sai daga baya na gane ashe. Hjyn su yayace tare da yan uwanta suka shigo gidan wallahu galibun ala amrihi na fada lokaci daya don nasan da wuya wanan zuwan idan na lafiyane haka. Tun kan su karaso kusa damu na mike tsaye hakan yasa murja mikewa muna masu sannu da zuwa sai shan kamshi ko wacen su keyi su duka ukun. Murja data gaida ita karshe tace a,a yar gidan hadiya kema kina nan ne ashe tace hjy nazone dazun tace kwarai naga alama ai don yanzu kowa inda yafi maski ake dafewa a lakaci arziki. Dayan yar uwar tace yo indai za,a lakata a barka da danka aida sauki amma ina dadin a rabaka da uban dan a kumayi kokarin rabaka da dan ka don samun wuri. Dan kallon juna mukayi a fakaice nida murja lokacin da dayan ke fadin abindai ma a filin Allah akeyin sa don kawai kwadayi da samun wuri irin na wasu matan . Yaya zaki aure uba kiba yarki kuma dan kishiya don samun wuri na sake fadin sannu ku mama ina dan dukawa. Tace yau fatima nice uwarki ko may ko dan mawa ya tilasta maki da ki kirani da mama ban sani ba. Kamar ban fahinci irin maganan da suke sake min ba a lokacin sai dan murmushi nake a fuska ina nuna masu ban damu ba da abinda sukeyi sai ma na juya wurin maria dake can nesa damu da yara ina fadi cikin harshen turanci kawo su su tari grandma din su maria. Kowa kallon yadda nake turanci zakace ko wata haihuwar America ceni lokacin. Maria ta riko hannun yaran tana fadin oya come great her samun wuri ita wanan din wacece hjy Rakiya ta tambaya. Aidai kin gani da idon ki idan ma ji kikeyi da yanzu ganau kike rainon ma harda maiyin shi akazo tundaga can don samun arzikin banza. Gaba na fara yi na tura kofan falon daketa kamshi yasha gyara kamar ba mutane ke zama a cikin shi ba duk da yawan mu gidan. Suma shigowa sukayi suka suna bin gidan da kallon yadda yasha gyara ga haduwa wai ni yaya zancen dayar matar gidan ne anty kanwar ta tambayi hjy. Yo ina zan san inda yasa gaban sa yanzu an fitar mashi da raiga kowa yanzu ai saidai a tambayi sabbin iyayyen shi kuma. A daidai lokacin na fito kitchen dauke da katon tire a hannuna dake shake da abin sha dana motsa baki nake jin suna wanan zancen. Kallon kayan da na aje a gaban su sukayi tanaci gaba da maganan ta tana fadin ya barta can ke nan yazo nan da yar gwal dinsa ganin gida. Ta sake kallon kayan tana fadin ba wanan ya kawo mu ba mu zuwa mukayi mu duba gidan nan muga inda yar mu zata zauna itama kafin lokaci. Dan murmushi nayi tare da fadin ko zaku dan zaga kuga gidan da kyau har ta baya ga hanya can da zai iya sadaku da ko ina ai. Wanan yar a kwaiki da shiga hanci da yawa barta kawai karyan su da kadarin su ya kusa karewa a gidan nan ai . Amma mama sai ina ganin wanan ba girman ku bane da kimar ku zuwa gidan dan ku kuna sake irin wanan magana haka duk da ita fatiman naga bawai zancen ya shigeta bane. Murja ni kike kokarin fadawa magana komay a,a hjy gani dai nayi hakan bai dace da girman ku ba gaskiya aida sai ku bari idan yaya yana gari sai kuzo ku duba ya nuna maku nata bangaren don mu bai nuna muna ba kafin ya wuce. Murja na fada a cikin wani irin murya na bacin rai ta juyo tana kallona nace ban son rashin kunya ki barsu suyi abinda ya kawo su tunda sunce ba gurin mu sukazo ba . Gidan dan tane tana da ikon yin duk wani abinda take so a gidan nan idan ma yau tace bata kaunar ganina gidan nan ya zaunu don haka ki kyale bakin ki don Allah. Eh lailai anty yanzu na kara tabbatar da komai da idona yar nan kafanta ya tsaya a kasa har take iya fadan magana a gaban idon mu haka. Abu kamar a mafalki haka nake kallonsu suna fadin magana babu girma ko sanin ya kamata a cikin zancen. Kamar kananan yara dasu saida zasu tafi hjy rakiya ta dawo wurin tire din dana aje masu abinsha tana fadin ba,a barin mugu da makami akace. Ke kuma murja uwarki hadiya tayi min kadan balle ke idan aure yana da dadi taje tayi aure mana ai bata wuce aure ba yanzu. Ina zatayi tana nan zaune tana aikin saka ido da gulma tana batawa kanta lokaci a gida sai hana masuyi su zauna lafiya take kokarin yi. Da ace zan bi ta murja ranan da mun masu rashin kunya saidai ni na sani dama bakina suka zo ji don i masu rashin kunya a kafe a nan. Allah ya taimakeni yanzu ba da bane kuma na riga da nayi mai alkawarin ba zan taba mayar da martani ba again koda dukana hjy tayi kuwa. Suna fita murja ke fadin girma dai ya fadi wallahi wai banbarakwai uwa a gidan danta take sake wanan maganan dako mu yara ba zamuyi shi ba. Ki koma gida ki fadawa uwar ki dana baifi karfina yadda ake tunane ba don aure zan mashi da yar uwar haihuwan shi kwanan nan. Gidan nan ba na yar agola bace da zata cika min gidan da da haihuwan yuyuyun diya masu zuben ruwa biyu. Tsit nayi har suka fita don ni abin sai ya koma ban mamaki a waje ma sai nake jin yayan su kamar basu tafi ba. Fatima wai yaushe kika koma hakane don Allah wanan ba abin kyalewa bane hjy fa ta wuce sanin ki yanzu sai kin zare kema. Duk maganan da takeyi ban samu bakin bata amsa ba sai ajiyan zuciya da nakeyi a zaune. Ashe aure yakan canza mutun haka ban sani ba yau nice ake fadawa maganan daya dace in bada amsa amma na share don darajan aure kawai ban bada amsa ba. Ina zaune zuciyata takai matuka wajen baci sai tunane nakeyi mainayi wa hjy haka har take nuna min wanan hali haka a fili. Ban san lokacin da hawaye suka fara bin fuskana ba a lokacin kuka na somayi sosai a lokacin. Ganin haka yasa murja mikewa ta bargidan ba tare dana sani ba sai maria ce tazo tana ban hakkuri. Zuwan murja gidane ya harzuka Amma sosai ashe ban sani ba murja tayi video komai daya faru a gidan takai ta nuna ma Amma. Amma bata zauna ba tasa aka kira mata su kawu dukkan su su uku tace murja ta nuna masu video din. Amma dai anyi hasarariya a nan hjy ko wai tana cikin hankalin ta kuwa ki wanke kafa zuwa gidan matar yar ki da yan uwanki kuyi irin wanan hauka haka ? Kawuna dai yana zaune ya rasa abinda zai fada ranan don idan yace zaiyi magana lokacin ba furci mai dadi zai fada ba. Kyale kowa yayi bai tanka ba har suka gama fadan su yana zaune kurum.baiyi magana ba a wurin. Kwana hudu yaya yayi a can bayan hjyn su ta kirashi ta fada mai cewa sunje gidan nayi masu rashin mutunci ni da murja sai abinda na manta a bakina ranan. Hakkuri ya bata sai ya dawo zai dauki mataki kan maganan don bata san da cikin gida sun san da zancen ba. Kafin ya dawo ya turo motoci guda hudu masu kyau gida kafin yazo tare da Aliyu suka dawo wanan karon Ranan da ya dawo naga alaman bacin rai sosai a tare dashi baiyi min magana ba ni kuma ban nuna mashi na gane yanayi ba. Ban yarda na nuna mashi komai ba duk da na zargi zancen ne hjy kila ta juya mai shi yake ma fushi hakan bai hanani shiga wurin shi ba da dare. Kamar yadda shima bai fasa kulani ba don yana fushi dani saida babu sakewa har lokacin a fuskan shi. Da safe muna karya gaba dayan mu har yara da Aliyu wayan shi yai kara ya dauka jin ya ambaci sunan kawu yana gaida shi yasa na dan dago kai ina kallon shi. Dan shiru yayi yana sauraren kawu din sai naji yace gamu nan zuwa insha Allahu yanzu daddy. Yana aje wayan yace daddy ke neman mu a gida dukkan mu yanzu zamu tafi na tambaye shi. Yanzu yace muje ya bani amsa yana cigaba da cin abincin shi nina fara tashi na koma daki na kara kimtsawa na fito na samu ni suke jira muka dauki yaran zuwa wurin mota. Haka kawai naji gabana na faduwa shike magana da Aliyu jefi jefi naji Aliyu yace ashe madam din namu dai zaman turai ya karbe ta sosai haka wanan tsaleliyar motar haka sai matan manya ai dama. Ya juyo ya dan kalleni na danyi murmushi don yadda shi yakan jani da wasa ni har yanzu ban faye sake jiki in mayar mashi da amsa irin na wasan kannin miji ba. Mun shiga gidan tun daga nisa na hango takalma a kofan dakin daddy wanda hakan yasa na gane akwai mutane a falon nashi lokacin. Muma falon muka nufa direct a lokacin ina shiga yadda na gansu zaune jugun jugun yasa gaba kara faduwa. Gaidasu mukayi muka samu wuri muka zauna dukkan mu kawune ya bude taro da addua aka shafa ya mika hannu gefen shi ya dauko wayan shi. Dan tabe tabe yayi a wayan ya fara mikawa hjy dake zaune ta hakince don bai fadawa kowa dalilin kiran nasa ba lokacin. Tana gama gani tace to shine may dama ai nasan zakuji komai tunda gaban yar leken asirin ku akayi koda ita fatima bata fadi ba ba karya na fadi ba abinda nace aure zan masa wanan ba fashi tunda kayi mai nasa ikon nima yanzu zan masa nawa tunda tare muka haife shi ai. Yace kwarai dankine ba wai ba jimmai ya juyo gareni yace Fatima ga uwarki nan ki tashi ki bita dakin ta ke kuma ga danki nan da yaran sa ki dauki abinki na raba wanan gardaman da jidalin yau kowa ya rike nasa. Da farko nayi wanan hadin ne na dauka zaki fahinci manufana kan hakan tunda har yau Allah baisa kin gane ba a zauna lafiya Allah ya bada zama lafiya ga wace zaki aura mai . Saidai kema ki shirya barin nawa gidan a ranan ko kafin ranan don kafar wace zaki aura mai fitar kafarki a gidan nan ke nan. Ciki kaduwa yaya yace daddy kana nufin raba aurena da fatima zakayi kan laifin da bamu mukayi shi ba. Murmushi kawu yayi yace Umar wanan abin yayi yawa kowa yayi hakkuri ya dauki danshi fitina ya kare hakana. A daidai lokacin na mike don barin falon don ba zan iya kara wasu mintina a gurin ba kuma . Ina fita a daidai lokacin da yake fadin mama menayi maki baki son farin cikina a duniyan nan ? Nazo da merry nayi ba daidai ba kun nuna min kuskurena ta hanyan aura min yar uwata tunda na auri fatima ni kaina nasan Allah ya kubuto dani daga halaka. Fatima bata taba wuce inda na ajeta ba tana min biyayya yadda ya dace mama shin shine baki kauna gani a gare mu ? Tace kai babawo ka shiga hankalin ka ka natsu kasan may kakeyi don ya rabaka da wanan gaiyan tsiyar bawai haka na nufin mata sun kare ba a duniya mamaka Ramatu ta baka yar gurin ta data dade tana jiran ka yanzu haka amincewan ka kawai muke jira don mahaifin ta yace saida amincewan ka za ,ayi. Amincewana mama tace kwarai yafi mun kwanciyan hankali don nasan yar yar uwatace kecin gashin kanta ba yar wasu ba. Mama ban amince ba kamar yadda nasha fada maki Fatima da merry sun isheni a rayuwata ba kuma zan taba amincewa da bukatan ku ba ko may zakuyi min kan hakan . Ya juya wurin mahaifin shi yace daddy kaika hadani da fatima yanzu kuma kake kokarin rabamu ba zanyi wani korafi ba a nan don kai kasan dalilin yanke muna wanan hukuncin nida ita saidai ina son fada maka bazan taba sakin fatima ba sai dai muyi ta zama a hakan dani da ita. Kai sadauki a gaban iyayyen ka ke don haka idan rai ya baci hankali ke nemo shi ka bari mubi maganan nan a sannu. Yace nagode Amma daga fadin haka ya mike tare da kallon Aliyu yana fadin taimaka min mu dauki yaran nan don Allah. Hjy tace ina kuma zaka dasu can tunda uwarsu ta koma wurin uwarta da zama ? Yace gidana ni zai raini abina da hannuna don ni Allah yaba hakkin kula dasu bayan uwarsu tace cikin tsawa kai babawo ni kake fadawa magana haka kan wanan yar banzan yarinyar don sun karbe abinsu shine me yafi nono fari a gurina. Mama duk wani biyayya ina maki shi a duniya saidai wanan karon ba zan yarda da kudirin ki ba akan iyalina me fatima tayi maki matsalanki da daddy ne da mahaifiyar ta banga abinda Fatima tayi maki na son ki rabani da ita ba da karfi da yaji. Ya fice falon yana jan yaran shi kowa na falon yai shiru yana binshi da kallo sai can Amma ta nisa tace yau saiki zuba ruwa kasa kisha jummai Allah ya cika maki guri ki kan yaran nan. Biyan bokaye da malamai sai ya kare ki bar kurwan su ya zauna lafiya Allah ya baki da dake maki biyayya kishi da gajin hakkuri yasa kin kasa hango hakan. Daga kofan mamu ya tsaya ya kira wayana naki dagawa sai gashi ya fado falon ina kwance saman dogon kujeran falon yace. Ke fatima ina son ki kwantar da hankalin ki kada haka yasa ki daga hankalin ki wanan yana daga cikin abinda yasa ban son zuwan mu kasan nan. Nayi murmushi lokacin da nake juyowa gare shi ina fadin nace kawu yayi gaskiya yaya don yanzu ya fahinci ban dace da kai ba don nasaban mu ba daya bane. Dama shi ya daukeni yabaka ni kuma yace yanzu ya fasa kyautar dani gareka dani dakai yanzu sai muyi hakkuri do maganan iyayyen mu shine gaba da namu. Ina maman twices take idan ta shigo kice nace ina rokon ta da ku rike min sultana don yanzu itace kawai matsalana don bata yarda da kowa sai ke sauran maria tana nan kafin ki dawo. Dariya ma ya bani dana kalleshi idanuwan shi sun kade sunyi ja nace kaima kasan wanan ba zai taba yuyuwa ba jinikace sultana don haka jinin mamace sai ka kaiwa mama ita ta rike kada ka kara shafawa mamu wani laifi a gidan nan kuma. Ya juya fita bansan ya akayi ba don ni tun ina tunane cikin bacin rai har barci ya daukeni sai dana tashi naga sultana goye a bayan fauziya. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:34 - 🀐🀐🀐: Falon yayi tsit bayan fitan shi kowa na wurin kamar ruwa yaci shi lokacin sai Amma ta fara fadin wanan abin dame yayi kama don Allah. Kina yar musulma diyan hausawa kike kokarin bata auren ahalin ki ko taysayin wa yan nan yara bazaki gani ba jummai. Duk wani biyayya da ya kamata diya suyiwa mahaifan su Allah ya hore makishi yaran nan suna iya kokarin su akai. Ba a hakkuri da lamarin diya ke aka zauna dake da halin ki har wanan lokaci yanzu bukatan ki ya biya an raba auren sai ki zuba rowa kasa kisha. Hajiya ainayi kokari da bansa ya sake taba fin karfin da aka nuna min a gidan yasa nake son gwadawa kowa nina haifi abina ba wani ya haifa mun su ba. Kwata kwata ni yarinyarce tun farko banso da watace aka bashi kila zan iya hakkuri kamar yadda na hakkura da auren habbib da Aliyu. A,a ko su baki hakkura ba baki da dai yadda zakiyine dasu don su ba irin halin sadauki ke garesu ba yasa bakici galaban su ba. A daidai lokacin mamu ta mike ta kalli kawu tace shike nan zan iya tafiya yace shike nan aina gama magana ta. Allah ya sauwaka tace ta fita suka amsa mata da Amin suna barin falon a daidai lokacin ne ta hadu da murja dauke da sultana dake wani iri kukan tashin hankali irin na yaran da suka rikice. Kamar bata gansu ba zata wuce dukda kukan yarinyar har kasan zuciyata take jin shi a lokacin. Mama yaya yace in rike ta har Amma ta fito gashi kuma tana kuka bata yarda dani kaita gurin hjyn shi tana ciki ta bata amsa tana wucewa kamar bata san inda sultana ta fito ba. Tana shiga falon da yarinyar dake ta wani irin kuka gaba dayan su take tambaya nan murja ke mayar masu yadda yarinyar tazo hannun ta da abinda mamu tace mata a kofa. Aikin banza ke nan bani ita nan da batayi kuka ba lokacin data fito aida bata kai haka ba yanzu tana mikewa zata karbe ta . Kada ki karbi yarinyar nan Amma ta daka mata wani irin tsawa taci gaba da fadin ya ganki yace aban ita idan na fito yasan kina gidan ai. Ba a dai raba anta da jini duk inda akaje aka dawo dole ace jikanane ita mama hadiye tace ashe kin san da hakan ke nan yanzu ? Fita tayi daga falon ba tare da ta tsaya bada amsa ba don tasan halin mama hadiye wurin masifa yanzu zasu rikice akasa rabasu. Mamu ta samay ni a dakinta kwance tace min a nan kika kwanta lokacin barci ya fara daukana nace eh nan ma yayi min ai. Naci gaba da barcina mai kama dana tashin hankali bata kara kulani ba sai dana tashi naga Fauziya goye da sultana dataji kukan yai yawa kowa na lalashi taki shiru ta karbeta ta goya sai barci. Lokacin dana tashi mamu bata falon nake tambayan Fauziya meyasa ta daukota a cikin wani yanayi irin na mamaki ta kalleni. Nace maida ita inda kika daukota yanzun nan lokacin mamu ta fito tana fadin barta harta tashi ta maida ita kukan nan zai iya ja mata wani ciwo kuma. Jin haka yasa na kyale ta da yarinyar a bayan ta kewayawa nayi ban dakin su Fauziya na fito na kara kwanciya a falon a daidai lokacin murja ta shigo falin mamu din. Zama tayi fuskanta ya sauya ta kalleni tana fadin da nasan hukuncin da kawu zai dauka ke nan daban gwadawa Amma abinda ya faruba wallahi. Na dauka idan sun gani tsawatawa hjy kawai za ayi da gidan ki sai gashi kuma matakin da aka dauka yayi muni sosai. Murmushi nayi nace murja koda baki nuna wanan ba ai tunda tace bata sona da danta babu inda zamu hakan da kawu yayi Allah yasa shine mafi alheri garemu baki daya. Ranan dai haka muka kwana kowa ransa abace yake gidan idan ka debe hjy da bansan abinda ke ranta ba a lokacin sai kuma hjy maryam dake sintiri part din ta dana mama a ranan. Sultana ta hana su barci da kyat suga asuba kukanta ya karde gidan gaba daya da asuban farko masifan Amma ne ya tayar da mutanen gidan ga baki daya. Wanan wani irin daukan alhakine haka ku raba yara da uwarsu da karfi da yaji wanan ke nan da muka kwana da ita a nan ina ga su wayancan tagwayen dabamu san yadda suka kwana ba tayi masifa sosai kafin ta fito zuwa part din mamu tana dukan kofan da karfi saida mamu ta taso daga inda take zaune tana lazimi ta bude kofan. Ina yar nan take ta tambaya a hasale tana ciki mamu ta bata amsa ta wuce fuuu zuwa dakin sai mamu tace tana dakina a nan ta kwana. Ina kwance bayan na sallame sallah na kara kwanciya ina jiran ayi asuba ta shigo da sultana tana fadin karbeta nace wanan daukan alhakin yayi yawa wallahi. Amma dai Amma kinji abinda kawu yace kan yaran nan ki kaita wurin hjyshi kawai don Allah bana son kawu yaga na saba mai Amma. Ba kawu ba kawulle nace tana min dakuwa ta kara fadi a hasale ba kawu ba nace maka wuya. Dariya ne ya kubce min nace Amma kawun nawa kike zagan min tunda asuban farko haka an zageshi ko zaki rama mai ne nace wace ni hajjaju Ammalle na rama a fakaice. Tare da mika hannu na karbi yarinyar a hannun ta da sauri sultana dake ta miko min hannu tazo wurina tana sauke ajiyan zuciya har lokacin bata bar kukan da takeyi ba din. Kada naji ko in gani kin kaiwa wanan mara imanin yar nan a gidan nan dani take zance wallahi. Ta fita tana fitina a tsakar gida ita kadai ba wanda ya lekota har taci ta sude ita kadai. Baya nayi sallah nayi wa sultana wanka nima nayi banzo da wasu kaya ba dole na saka dogon rigar mamu a jikina lokacin. Na koma muka kwanta zuciya ba dadi nasan yadda akai fama da sultana ko su Abdul haka zaiyi fama dasu a gidan duk da ga maria gashi suna ganinshi amma nasan sai sun taba rikici sosai a gidan. Da tausayin mu a raina ina muna addu,a sosai don Allah kadai yasan halin da kowan mu ke ciki a ranan har mahaifan mu. Har kawu dayai sanadin auren dashi nasan ranan baiyi barci da dadin raiba shima a nasa bangaren . Kamar yadda kawu ke bin dakuna yauma haka ya shigo part din mamu da dan sandan shi dake karamai karfi yana dogarawa . A falo ya samemu zaune muna karyawa muka shiga gaida shi da kwana ya samu wuri ya zauna yana fadin. Fatima ina son ki saka hakkuri a ranki nasan mun cuta ma rayuwan ki mun bata maki lokacin kurciyan ki banyi hakan da niyar cutawa a gareki ba ko kadan. A hankali na dago kai na dan kalli inda kawuna yake zaune yana magana nace a a ha kawu wallahi ni baka cuce ni ba don uba bai taba cutar da yarsa ai. Yace na gode da wanan fahintar da kikai min Fatima hakan da nayi yanzu shine mafita gareku damu duk a barta ta aura mai wadda take so. Abinda nake so dake ki kara kwantar da hankalin ki ki natsu kina dai da takardan ki ga hannu zan duba inga abinda ya dace ayi nan gaba kan aikin ki. Na gode kawu nace a fili a ciki zuciyata kuwa sai wani irin harba min takeyi ina fadin yanzu shike nan an rabani da aurena ina ji ina gani ko may ? Muryan mamu ya dawo dani ga dan tunanen dana fara tana fadin yanzu yaya yaran nan ba,asa makomarsu ba tunda, , , , , Hannu kawu ya daga mata ya hana ta karasa fadin abinda take son fadi a lokacin mikewa yayi yana fadin hajiya ta sameni kan zancen yar nan ita mace ce kuma karama zaku iya riketa a nan don kada a jawo mata wani matsala kuma. Daga haka ya fita nasan part din mu shine karshen shigan shi a zagayen da yake yi don haka muna gamawa na mike na dauki sultana zuwa part din Amma don in gaida ita. Hjy maryam ce na hadu da ita ta fito part din kawu muka gaisa da ita ta dan make murya tana fadi sai hakkuri fatima iyayye suna gaba da komai ba komai hjy nace mata tare da mata godiya na wuce abina inda zani tabini da kallon munafunci. Na samu Amma a zaune falon su kamar yadda na zata ta tasa abin karyawan ta a gaba tana kallo . Jin sallamana yasa ta dago kai tana kakaro murmushin dole a fuskanta tana fadin yanzu muka gama waya da mijin ki yace zasu yi tafiya shida yaran yau. Gabana ne ya fadi sosai dan jin abinda Amma tace min yanzu ina kuma zasu tafi na tambaya a dan mamaki. Bai fada min ba yadai kirani yana tambayana kwanan ku nace kuna lafiya yace min sai idan yazo zamu magana dashi. Fitowan murja daga dakin su yasa na kalleta nace dama ina son in turaki ki dauko min kaya don ko yanzu na mamu na saka a jikina kina gani. Ta kai zaune tana fadin wa ni ai in kin gani kasuwan maza gulma ya kaini yanzu ban ko son hanya ya hadamu da yaya don sai inyi zaton zaiga nice duk na jawo mai wanan abin. Haba dai yaya zaiyi zaton hakan gare ki tunda yasan baki da laifi shi ba haka yake ba ai kawai dai baki gama fahintar shi bane. Muna tsaka da hirane muke dan jiyo hayaniya a tsakar gidan sama sama shiru mukayi muna sauraren hayaniyar meye kuma akeyi. Muryan hjy ce ke masifa da alama wani ya tabata a lokacin inda take shiga ba nan take fita ba. Wai ashe yayane ya turo Aliyu ya kawo kayan abinci part din mamu shine hjy taji ta fito tana masifa hakana . Saida fauziya ta shigo muke ji a bakin ta wai tana masifa da Aliyu bai kula ba sai kai kayan abincin tare da abin sha da suka jibgo mota dashi yake shiga dasu part din mamu abinshi. Zata ko mutu da bakin cikin akan dan yau, idan tace bakin kishin matan diyan cikinta ta saka a ranta haka wanan abinda mai yai kama kiri kiri ta hana yaran nan zuwa garin nan saboda tashin hankali ana zaune a kasa daya amma ya dauke kafan shi da gidan nan. Nace wanene Amma ta kalloni hasale tana fadin habibu ma da yarinyar nan Rakiya matar sa su ai sun fita iya iskanci indai fulanin dajine suna daidai da uwarta ai. Jin hayaniyar yayi yawa yasa murja da Fauziya har mama hadiye fita da sauri sai Amma dake kokarin mikewa irin na tsofi ta rage a falon tana kiciniyar tashi tsaye. Daga inda nake zaune naji muryan yaya kamar diran mikiya a kunnuwa na yana fadin don may ba zan kawoma matana kayan abinci ba tana matsayin matana har yanzu ? Mama banso mukai haka dake ba a gidan nan na fada maki ba zan yarda ki rabani da matata ba don banga abinda ya shigo da fatima cikin tsabgan ku ba da kukeyi. Ba zan yarda darajan aurena ya tabu ba a garin nan matana da yarana nike da hakkin ciyar dasu a kaina. Don haka ba zan yarda wani ya ciyar min da mata ba alhalin ina dashi zamanta a nan wanan ra,ayin kune keda daddy wanan ni bai shafeni ba all what i know aurena yana bisa kanta. Da hjy tana da kunya ranan data jishi a gidan nan don yadda yaran sukai mata a gaban kowa ta rasa abinda zata fada. Sai Ammane ta amsa mai da fadin wanan kayi gaskiya tunda har yanzu a matsayin matarka take wurin ka. Ya juya yana tambaya ina ina ne ? Da sauri murja tace tana wurin Amma. Ya nufo part din Amma din rai a bace a kwance ya same ni sultana tana saman ruwan cikina tana ramuwan barcin da batayi ba daren jiya. Tsaye yayi yana kallon mu kafin yace ramuwar barci wanan keyi ko don Amma tace jiya bata barsu sunyi barci ba da dare . Na amsa mashi da kai. Ya dan kai zaune gefena yana fadin ke naga kamar zaman gidan yayi maki dadi sosai a ranki. Nace to yaya zanyi wai yaya idan ban zauna ba so kake in binka in butulcewa iyayyen mu ko may ? Dama su suka bakani na fada maka yanzu kuma sunce in dawo gida in zauna ai dole ne in dawo yace good may kuke bukata yanzu don yau zan bar garin nan ni. Ina kuma zaka na tambaye shi saida ya dan furzo da iska a bakin shi yace lagos zan koma in na kwana biyu Abuja may zan zauna inyi garin nan kuma yanzu tunda sun kwace min ke ? Nayi murmushi nace yaran fa da maria yace dasu zan tafi duka yau zamu bi jirgin karfe biyu zuwa Abuja motar ki yana nan kofan gida saidai ban son yawan yawo ki natsu wuri guda don Allah zarah kafin komai ya lafa. Idan ka tafi auren naka fa sai bukin ya tashi zaka dawo ke nan wani kallo yayi min yace kina tsoron auren da ake fadin zanyi ne ? A,a ha kan me zanji tsoro tunda ba a kaina zata zauna ba in tazo hanyar jirgi daban na mota daban kaima ka sani. Mikewa yayi tsaye a lokacin Amma ta shigo dakin nace zancen tafiya na gida fa in duba su ? Wani kallo ya jefa min yana fadin haba zarah muna ciki wanan halin kike wani zancen tafiya gida yanzu ? To may nakeyi a nan din ai gara inje gidan mu asan ina da gida agolaci ba zama shegiya bace yafi yace good kina da gaskiya cikin bacin rai. Wurin Amma ya juya yana fadin Amma zan tafi ba lalai bane in dawo ta nan kafin in tafi yana mika mata kudi tace wai ina zakane yace gani nan dai Amma. Tunda yace hakan na gane baison kowa yasan inda ya dosa a lokacin naja bakina nayi shiru ya sake cewa ga amanan su nan na bari a hannun ki Amma don Allah a kula da su ban son yawo ta sani ita. Babu ma inda zata insha Allahu harka dawo tace nace da sauri a,a Amma kada kice mai hakan idan fita ya kamani fa ? Wani kallo yai min a daidai lokacin ya duka ya shafi kan sultana yana kiran sunan ta yarinyat dake cikin nauyi barci tayi firgigit ta bude ido kuka tasa tana mika mashi hannu ya dauke ta. Dan dagata yayi sama ya sunbance ta sai kuma ya rungumay ta a jikin shi yana sauke ajiyan zuciya a hankali. Abincin ta yana nan nasa an kawo mata don Allah zarah ki ba yarinyar nan kulawan daya dace sosai kallon shi nayi ina mamaki komai da yake kai kasan a cikin karfin hali yake yin shi. Kudi ya ciro ya aje min gefena yace ki rike wanan idan na samu lokaci zan turo maki ki kara rikewa a gurin ki. Yana fadin haka ya mike tare da kallon Amma yana fadin to Amma zanyi niya Aliyu zai kawo yaran nan suyi sallama da maman su kafin mu wuce. Da sauri na furta masu ka barsu karsuzo su damay ni nan daga shi har Amma wani irin kallo sukai min lokaci yace don may kikace hakan nace haka kawai a cikin daure fuskana. Barsu kawai sadauki Allah ya saukeku lafiya ka kula da kanku ka kuma kwatar da hankalin ka komai yayi tsanani maganin shi Allah ne. Hakane Amma yace yana sauke ajiyan zuciya ya juya ya tafi ba tare daya kara min magana ba ko kallon inda muke. Wani iri naji a raina saidai hakan shine saukina duk da nasan ban kyauta ba hanashi kawo min yaran danayi muyi sallama. Bayan na idar da sallah ina zaune wurin da nayi sallah a falon Amma nake tunane duk inda suke yanzu suna shirin dawa su bar gari ke nan. Biyu daidai na kalli agogon falon na sauke ajiyan zuciya a hankali na kai kwance a kasa ina lumshe idanuwana. Muryan Amma ke fadin ni na taba ganin wanan bala,in haka kace kai baka kaunan kowa a rayuwan ka a dole sai ka mayar da kowa bawa a gurinka. Ban dai yi magana ba ina jin ta tana maganganun ta na share abinda ya damu zuciyana a lokacin ya dameni. Ban kira shiba shima ranan bai kirani ba sai washegari sai ga kiran shi a wayana na dauka lokacin muna zaune tare da mamu a falon ta. Dauka nayi da sallama sai ya hauni da fada zahra may kike nufi da hakan da kikeyi ne wai ? May kuma nayi yaya na tambaye shi kamar ban gane mai yake nufi ba ga maganar shi. Yaci gaba da fadin kina ganin don sun daukeki daga gidana hakan na nufin sai ki shareni aiko ba don niba zaki kira kiji lafiyan yaran ki ko ? Saida na dan saci satan kallon gefen mamu naga ta kura min ido don ta gama tambayana na kirasu naji saukan su nace na kira ban samay shi ba nayi mata karya da hakan don nasan zata iya min fada kan hakan. Nace nakira bai shiga bane yaya sai naji ya kashe wayan shi na bata rai ina aje wayan a gefena cikin bacin ran kashe min waya da yayi. Ya kamata ki tausayawa halin da bawan Allah nan yake ciki don dake dashi duk ba yin kan ku bane yana zaman zaman shi aka ja mashi magana. Shi kanshi yaya yasan halin matar shi dalilin da tun farko naki wanan hadin naku ke nan amma sai ba a duba min ba. Yanzu ga abinda ake soncin mawa kara lalacewa yayi bai yuyu ba don haka banga abinda zaisa kiga laifin bawan Allah nan ba duk yadda akeyi yayi muna halarci a rayuwa don ba haka mahaifiyar shi taso da shiba kowa ya sani shi dalilin yin wanan haukan haka da takeyi. Su basu gane irin kiyayyan da hjy ke min da duk wani nawa cikin gidan nan don haka duk wani hanyar da zataga ta kuntata min shi take nema ta gasa min kwakwa a hannu na. Ta manta Allah ne mai yin komai bawai ra,ayin ka ba yanzun da mun dage akan ba za,yi auren ki dashi ba ina rabon yaran nan zai kai mu. Sai Allah ya dauke dayan mu ayi ba dashi ba shi yasa wani lokaci jayaya da hukuncin Allah baida kyau mutum ya rugumi kadara duk dayazo mashi maikyau ko mara kyau ya barwa Allah hukuncin sa nayin hakan. Har yau sam ban taba badaman auren ki da umar ba don yadda duk ake halarci bawan Allah nan yayi muna shi a rayuwa . Yadda yake aikowa uwarshi kudi duk wata haka nima yakan turo min da kudi ta account dina duk wata kuma yace kada in fadi don Allah. Nasan halin umar tun muna kanana ba mutum bane mai son magana haka Allah yayi rayuwan shi shi tun farko. Mamu ni bawai naga laifin shi bane kawai dai ina kaucewa bacin ran kawune don kada yaga yana kokarin min gata ni ina kokarin watsa mai kasa a idanu ga idon jama,a. Zaisan kuyi waya dashi ne ko kuma koda ace rabuwa kukayi ai yanzu kun zama daya don ruwa ya dade da gaurayewa da jini ko. Mamu zan kula insha Allah ni bawai ina ganin laifisa bane ni mai yayi min da zanga laifin shi may ye yaya bai mun ba na ingata rayuwa na da zan manta da hakan. Zuwa yamma na fara jin ba dadi a jikina haka yasa nasha magani na kwanta ranan ban fito ba ga fitinan sultana da takeyi min ga ciwo sannan kuma zuciyana ba dadi lokacin. Washe gari ne na tashi da zazzabi sosai don tun cikin dare nake dan jin jikina sama sama har yakai na fara amai sosai . Ganin haka yasa mamu zuwa fadawa kawu banda lafiya yace subbahanallahi may ke damun ta ga mijin ta ina ganin kamar baya gari tun shekaran jiya rabona dana ganshi gidan nan. Ko uwar shi naji tana tambaya wai munyi waya dashi bai shigo ba harshi har Aliyu tun ranan . Mamu tace ina ganin kamar baya garin nan fa yaran fa suna ina su kawu ya tambaya cikin dagowa yana kallon ta. Duk dai inda yake yana tare dasu ai tunda kaji baiyi magana ba bai kuma kawo su nan gidan ba. Yanzu barin baki kudi kuje asibiti taga likita asan abinda yake damun ta yafi tace dama kabar kudin don tace akwai kudi a wurun ta yayi saurin fadin a, a karba dai ki kaita don nauyina ne yanzu kula da ita. Ina kwance na rufe har kai sai naji muryan mamu tana fadin ki tashi murja ta rakaki asibiti ko maman ki hadiya. Don ni ba zan kaiki ba kada kuma yazama wani abin magana a gidan nan yanzu suna ganin mun fita tare za a dauko wani zance a dora muna kuma. Ina fadin ba sai naje ba zan iya treating din kaina ai tace a, a ku dai je asibiti zaifi a auna ki asan abinda ke damun ki muryan mama hadiye ne a falon mamu tana fadin ina take nai yar gidan gwaggo. Mamu ta amsa mata tana fadin gamu nan dakina ai ta shigo tana fadin fatima ba lafiya haka kuma ? Nayi karfin halin tashi zaune ina fadin mama jikin nawa ne banjin dadin shi yau. Tashi muje asibiti tace min dole na mike ba wani complain na shirya muka fita da motan ta muka fita tare da murja hjy maryam ce ta ganmu take fadin uwa da yarta sai ina kuma haka da safe asibiti ta bata amsa nayi karfin halin gaida ita da kwana ta amsa min tana bina da kallon kurulla. Munje anyi min dan gwaje gwaje result ya nuna ciki ne dani dan sati biyar ma,ana dai a nan gida na samu cikin ke nan zuwan mu. Nike fadin abinda ya dace aban saura nace su bari zan rubuta in sayo idan na koma gida. Maganine kawai ba aimin allura ba muka tsaya muka saye a hanya muka dawo gida a lokacin har hjy maryam taje part din hjy sarakuwana ta fesa mata fitan mu da mama hadiye. Sukace karya muke ba asibiti zamu ba wurun biye biyen bokayen mu zamu tafi tunda yanzu bamu ga zama ba ai sai abinda ya turewa buzu nadi kan dan ta. Allah sarki sha daya da wani abu muka dawo gida itace dai still taga dawowan mu na tsaya ina amai a waje daidai shigowa get din gida. Wani sabon gulma ta kara gundawa a cikin ta lokacin bata samu zuwa ta fesawa sarakuwana ba don kawu ya kirata part din shi. Saida nasha magani na kwanta koda Amma tazo har na samu barci yadan daukeni lokacin din haka bansan shigowan ta ba. Ta dawo shiyanta cikin ikon Allah sai gashi ya kira Amma bayan sun gaisa tayi mai yaya hanya yake tambayan ta ko muna lafiya yakira bai samu wayana ba. Tace yanzu daga wurin ta nake sun dawo asibiti bata da lafiya naje na samu barci ya dauketa ko . Cikin wani irin murya yace da sauri subbahanallahi Amma may ke damuwan ta kuma har asibiti tace wallahi jiya uwar tace daren jiya basuyi barci da dadi ba. Amma idan ta tashi akai mata wayan ki ko ta kunna nata wayan ya fada tare da yi mata sallama ya dan shiga tashin hankali don shi yana tunanen ko damuwane na saka a raina yaja min ciwo. Don maganin dana sha na samu yin barci sosai a lokacin ban falka ba sai uku na rana na danji dadin jikin nawa lokacin saidai nauyin da yaimin ke damuna irin na wanda ya kwanta ciwo. Lokaci daya na danyi fayau dani bayan na sallame sallah ne mamu ta shigo da kofin shayi yana tururi ta aje a gabana tana fadin ki daure ki sha wanan ko hanjin ki zai dan warware maki ki samu kici wani abu mai nauyi anjima. Mamu ba kunu insha shi nake son sha yanzu kawai tace akwai da kamu sai a dama maki yanzu. Barshi idan babu nace mata ina kokarin kaiwa kwance kasa a wurin da nayi sallah. Tace sanyin kasan ba zai maki yawa ba idan kin kwanta a nan nace sanyi sanyin kuma nake so bata ban amsa ta juya ta fita daga dakin . Ba a dauki wani dogon lokaciba sai ga kunun an dama min shina samu na dan kurba sama sama na aje cup din sai ga Amma ta shigo dakin tana fadin sannu yarnan . Jikin ya kiya haka kuma ina dai ba danuwa kika saka a ranki haka ba Aruwa babu mai rabaki da mijin ki kinji muddin ina raye. Shima ja,irin tun dana fada mai baki da lafiya ya hani zaman lafiya a gidan na ya bugo waya yafi a kirga yau yace ki kuna waya ko ki karbi wanan. Kawun ki ya dawo nayi mai magana ya mayar dake dakin ki in ba so yake sadauki ya tare muna a gidan nan ba . Maganan mamu ya katse Amma mama ta koma ina kuma ai gara dai kowa ya rike nasa kuma zaifi saukin wanan fitina na hjy. Maimuna ki fita min a idona tun ranki bai baci ba jin abinda mamu tace yasa na gane nufin ta nace cikin karfin hali Amma bazan koma gidan yaya ba idan kuma kin matsa in koma gidan mu bauchi da zama. Shike nan ku kasheni ku huta zaifi min saukin wanan bakin cikin da kuke sakani a gidan nan kan auren yaran nan. Karan wayan tane ya hanani magana ta miko min wayan na dauka da sallama zahrah me yake damun kine haka Amma ta fada min har asibiti kuke yau. Muna fara magana sai mamu ta mike ta bar dakin zuwa falo kusan tare suka fita ita da Amma a lokaci daya daga dakin. Banjin dadin jikina na bashi amsa a sanyaye ya yace asibiti may sukace nace sun dai dubani sun ban magani. Ko kinsa damuwa a ranki ne haka zahra da sauri nace damuwa akan may kuma yaya kawai dai ciwone sukace dani na bashi amsa. Kina amai ne nace nayi daga dare zuwa safiya har lokacin da muka dawo gida sai lokacin na samu barci. Kinci abinci nace na dai sha koko yanzun dana tashi komai naci baya zama a cikina sai kokon dana sha yanzu banyi amai ba. Yace zahra na amsa anya ba ciki kika samu ba kuwa da sauri nace ni banda ciki dawa kukaje asibitin nace murja da mama hadiye. Ok ina maman twices nace yanzu ta fita falo ita da Amma bata wayan zan yi magana da ita. Da kyat na iya mikewa na kaiwa mamu waya ta karba na dawo dakin na kwanta lamo banji yadda sukayi da mamu ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:34 - 🀐🀐🀐: Washe gari ina barci kamshin turaren yaya Umar ne ya karade min hancina haka yasa na bude idona da sukai nauyi saboda zafin ciwo a hankali. Har bedroom din mamu yake yana zaune saman side drower ya tsura min ido yana taba wayan shi. Ganin na bude idanu na ina dan motsawa ya bar abinda yake da wayan shi ya dawo da kallon shi gareni. Zarah ya jikin naki yace lokacin da yaga ina kallon shi a cikin mamaki na zuba mai idanuna. Naji sauki na bashi amsa dashi ina kokarin tashi zaune tare da fadin ka dawone kuma yaya ? Dole in dawo zahra don hankalina bai kwanta yadda Amma ke fada min kina jin jiki jiya ai naji sauki na bashi amsa a daidai lokacin dana kai zaune ina mamaki kuma a raina shine yau har kuryan dakin mamu haka zaune ? May yasa kika boye min abinda ke damun ki badon na kira gwaggo hadiya ta fada min ba daba zaki fada min ba gaskiya ke nan ba ko may ? Ai ba saina fada ba idan lokacin ka sani yayi yaya sani zakayi do ba,a boyon ciki ai. Don may ba zaki fada min ba in sani nace kawai dai ban son ka raba hankalin ka gida biyu ne nabari sai idan Allah ya dawo dakai lafiya muyi magana. Ajiyan zuciya naji ya sauke tare da dan karkatowa inda nake yana kokarin taba jikina yaji jikin da zafi har lokacin sosai. Yace ba zan barki kasan nan ba zamu koma London dis week insha Allahu muyi rainon cikin nan a can hakan zafi mun kwanciyan hankali. Da sauri na dago kai na kalle shi nace yaya ka matana da kawu ya mayar dani hannun mahaifiyata yanzu itace keda iko dani ko ka manta da kawu yace kowa ya rike danshi ne. Robish wanan wani maganan banza kike kokarin fada min ne haka wai suyi iya yin su a kan mu sun daura muna aure a tsakanin mu yanzu kuma basu da hurumin rabamu don aure a hannu na yake ba,a hannun wani ba. Idan na bika mun koma yaya a wani matsayi zan zauna dakai alhalin mahaifiyar ka ta fito gaban kowa na gidan nan tayi ikirarin bata sona bata kauna zaman ka dani. Kawai ni ina ganin mu hakkura da wanan aure kabi zabin mahaifiyar ka don a zauna lafiya kaida za a aura ma sabuwar amarya ka angonce kwanan nan kake batun barin kasa. Wani kallo yake min wanda na kasa fassarashi a lokacin na tsanana ne ko na tsanar kalman da nake furtawa a lokacin. Sai daya daga yace fine kinyi gaskiya zahra koda yake banyi mamaki ba don yanzu kin fadi hakan dama auren bai damay ki ba tun farko nasan da hakan. Saidai ina son ki sani yace daidai lokacin daya kara ran kwafowa saitin da nake yana fadin babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake a garin nan duk wani abinda zaku kimtsa ku kimtsa shi dakyau ina jiran ku yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin. Saida ya dan jima da fita mamu ta shigo tana fadin sai ga mijin ki mun gani da safen nan kuma. Nace rigima yake son jefani a ciki wai na shirya mu koma London yace haba dai ina haka zai yuyu shiko. Nace ai na fada masa ya manta a hannun ki nake yanzu tunda kawu ya mayar maki dani kamar yadda ya karbe ni a hannuki ya bashi ni da farko. Kyalesu dani duk wani abinda zakiga nayi a gidan nan naki goyon bayane kawai gareni idan ita son danta ya rufe mata ido har tana ganin kowa ba kowa bane sai yayan ta yanzu zan nuna mata kema yace kamar kowa. Nace ni yanzu mamu damuwa wanan cikin dana samu kuma shine zullumina tun jiya da aka fada min ban so yaya yasan da zancen ba wallahi sai gashi mama hadiye ta fadamai komai. Ai dole ya sani sayadi tunda nasane a boye mashi cikin shi ai haka baiyi ba dolene yasan da zancen cikin ai. Mamu so nayi na fitar da cikin may ye amfanin inta haihuwa dashi ina tara diyan da ba,a so har ana kiran su da yuyu a gaban kowa tana kokarin sheganta min yara. Kissa kike son yi sayadi ina wanan shawaran ya fito maki haka a bakin ki kuma kota sheganta su tunda mahaifin su yana son abinshi fiye da tsamani ai zance ya kare. Shigowan murja wurina yasa mamu fita daga dakin murja ta zauna tana fadin ashe yaya ya dawo. Nace yanzu na ganshi nima tace na ganshi ya fito dakin hjyn su sai a bace nasan tayi mai sababin ta data iya kan mayasa yake kulaki. Nace ita tasani ni basu gabana yanzu abinda ya damay ni ya damay ni murja . Tun da yaya ya fita ban kara ganin shi ba sai dai yana bugo waya ya tambayi ya jikina sau uku a rana tare da tambayana idan ina son wani abu ya turo min da kudi na saya. Nakan bashi amsa da ban son komai don akwai komai kuma mamu tana tsaye a kaina . Hakan bai hana inji alert din kudi ya shigo min ko a wayan mamu danace tana tsaye dani a gidan . Da yazo ya fadawa iyayyeb shi zancen cikin dake jikina hjy tace ashe samun wurun nawa yayi yawa har ina gwarne a gidan har yaushe na haifi sultana da zan kara samun ciki. Yace shike da diyan shi koda zan cika gidan da diyane hakan bai damay shi ba a wurin shi hjy tace taga a kaina yana son fara mata rashin kunya tana fada yana fada yace auren shi yake karewa mutunci ba wani abu ba shine fitan da yayi har murja ta ganshi ranshi a bace. Ya samu kawu ya mai bayanin yana son zamu koma tunda zuwa nan yana yana da matsala gare mu. Kawu yace umar nasan abinda nakeyi kasa min ido kaga guduna ka bari jimmai ta aurama auren da tace zatayi ma mugani tukun. Ya dago kai yana fadin daddy may kake nufi da hakan bansan ko wace mama ke shirin aura min ba banda ra,ayin kara wata mace a gidana don ban rabu da merry ba mata biyu sun isheni a rayuwana. Ko merry kurciyane ya cine na aure ta lokacin yanzu haka auren mu yana rawa akan rukicin yar mu da mukeyi da ita kan akidar ta da take son yarinyar ta bi. Kawu yayi murmushi yace yanzu ka fara hango abinda nake hango maka har yasa na dauki yarinyar nan Fatima na baka don ka samu diyan da zakai alfahari dasu nan gaba. A hallul kitabi ba abin yarda bane garemu Annabi yace kada mu yarda dasu domin su din mayaudara ne a garemu. Saidai mahaufiyar ka ta kasa gano hakan gatane a gareka nayi maka ta dauki wani manufa na daban tasa a ranta yana wahal da rayuwan ta. Yan uwanta kuma suna kara ingizata tana hauka babu mai bata shawaran kwarai a cikin su ta kasa gane ba son ta suke da gaskiya kyashi da hassadan ta sukeyi. Daddy ni zan koma duk yadda ya kasance sai a kirani don ba zan dawo garin nan maza ba zan duba duk yadda shawara ya kaya zan kiraka in fada ma ka kara hakkuri dai kawu yace. Ya mike ya fita ranshi ba dadi a lokacin tunda ya sa kai ya tafi yau kusan satin shi shidda ke nan ba wanda ya kara jin duriyan shi har yaran. Bansan may ya hada hjy da mamu ba a falon kawu sai dai jin muryoyin su mukayi suna musayan baki har hjy ke fadin ke har kina da bakin magana wace tunda uwarta ta tafi ta barta cikin zanin goyo bata kara waiwayota ba har yau saboda mugun hali irin naku. Shine zan yarda a hada min zuria da ku ku bata min zuria nan gaba saboda son kai ko may ki rike yarki ko yanzu burina ya cika a kanki maimuna don dana ya sako maki yarki ga yara ga ciki sai a nufi wani wanda kaddara ya fadawa kuma. Ina zaune kasa falon Amma ina sauraren maganan su ina lumshe idanuwa na a hankali. Tunanen da nakeyi ne a lokacin yasa na mike daga inda nake Amma tace ina kuma zaki nace ina zuwa yanzu zan dawo Amma. Kada ki saka baki a cikin zancen su kyalesu suyi abinsu su gama na danyi murmushi tare da fadin ba wurin su zan tafi ba ni. Part din mamu na nufa na dauko wayana dake caji na koma saman kujera ina duba nomba naga nomban da nake nema yana nan a wayana har lokacin. Mamu ta shigo falon tana kuka banyi mata magana ba har saida tayi ya isheta nace mamu kiyi hakkuri din Allah. Komai dake faruwa da bawa yana da karshe a wurin Allah barta tayi abinta yanzu watarana koda ance tayi ba zatayi hakan da take maki ba. Sayadi ni fa ba shegiya bace da ubana aka haifeni amma hjy kullun dan magana ya tashi a gidan nan sai tai ta kokarin shegantani gaban kowa. Don uwata ta tafi ta barni na bar kasan da yan uwanta kawai shi zaisa hakan ya zama min abin gori a wurin ta. Kiyi hakkuri don Allah mamu ki natsu akwai maganan da nake son yi dake dama ban samu natsuwa bane da yardan Allah kwanan nan hjy zatayi kunya a gidan nan insha Allahu. Indai mahaifiyar ki tana raye ko yan uwanki sun kusa zuwa gare ki mamu cikin hukuncin Allah kuwa. Da sauri ta dago kai ta kalleni take min kallon mamaki dan jin abinda na fada a lokacin. Nace mamu akwai wata mata da muka hadu a London da ita matar ta damay ni wai ina kama da yan ahalin su sosai komai nawa irin nasu ne. Da farko nace mata kamane kawai don ni dai nasan banda kowa a sudan lokacin. Amma matsina da bi da matar tayi kan maganan har gidana tazo da photuna yan uwan nata tana nuna min saidai a lokacin duk ban dauki maganan nata da wani muhinmanci ba gaskiya. Amma da yaya ya dawo ina fada masa yaba abin ma,ana sosai saidai lokaci ya kure don baifi kwana uku ba mu zo nan lokacin da matar tazo gidana shine yace mu bari sai mun koma mu neme ta muji komai. Har layin kin nan mun bata ashe an sace wayan ki a lokacin bai shiga ba ban sake tuna maganan ba sai yau danaji wanan zancen a bakin hjy gamay dake. Sayadi shine baki fada min ba duk dadewan nan da kikayi a kasan nan nace wallahi mamu na shafane tun lokacin da zancen sai naga ta fara hawaye masu zafi suna zuba mata a idanun ta. Mamu ki bar kuka nasan har shagon matarnan idan har ban samu layin ta ya shiga ba zamu iya neman ta a can London din. Sayadi tsoro nakeji a raina a yadda gwaggo ke ban labarin mahaifiyata tun lokacin da ta barni tabi iyayyen ta har lokacin basu karajin komai daga bangaren taba. Idan ya kasance wanan matar basu bane yan uwan mahaifiyata zan kara shan zunde a gidan nan ke nan. Wa zai san wanan zancen mamu ko Amma ba zan fadawa ba sai na tabbatar da komai yanzu dai ki tambaya ki san sunan mahaifiyar taki da kasan su mu sani a gurin Amma . Gwaggo bata son ina mata zancen nan ko kadan sai nake gani kamar basuyi rabuwan lafiya da ita bane a lokacin. Idan kin ban baki zan tambaya a cikin hikima muji ko tasan sunan ta kafin in kira matan in samu hujjan da zan bata kan tambayoyin da zasu yi mun a kanki. Idan zaki iya tambayan ta sai ki gwada muji nace shike nan zan gwada in gani ban bar dakin ba saida naga hankalin ta yadan kwanta ina bata labarin komai akan haduwarmu da matar. Bayan la,asar na shiga dakin Amma kamar yadda na mayar da part din ta wurin hirana da shan iska tundai idan in murja tana gidan. Nan muke zubewa muyi hiran mu muna mata shewa tana zagin mu don na kwatar da hankalina ban nuna damuwan rabuwa da yaya yana cin zuciyana ba ko kadan a gidan ba har wani ya gane hakan kamar yadda mamu ta lurar dani. Sai kuma yin hakan ya koma yiwa hjy zafi har bata iya boyewa a ranta din nasa an kara gyarawa mamu part din ta danta ya turo kudi mai yawa an muna gyaran an saka sabbin AC don nace zafi yana damuna. Sam bata ganin mu cikin kunci ko rashin walwala sai kuma ta koma cewa mun asirce mata da da asiri baya kallon kowa yanzu idan bani ba da yayana da uwata. Ammace ita kadai na samu a falo babu kowa a part din don shirun da falon yayi ta kalleni tana fadin ai na dauka kinyi fushi ne da kin tafi. Dawa zanyi fushi Amma na zauna ina fadi tace yo ni na sani yar nan tunda abin gidan nan baya karewa kullun da kalar fitinan da ake tashi dashi a gidan nan. Nace komai yai farko yana da karshe Amma idan Allah yayu mamu zata hadu da dangin mahaifiyar ta koda tsufa sai su hadu idan kuma Allah baiyi haduwan su ba sai a lahira Allah ya hadasu. Ina kaiwa kwance don yanzu sam banda jimirin dadewa zaune ko kada nace waini mamu may ye sunan kakana da ta haifi mamune kuma ita mutumiyar inane wai ? Sai naga Amma ta bata fuska tana fadin siyama naji iyayyen ta na fadi amma mu da halimatu muke kiran ta wurin mu. Zancen mutumiyar inane ba zanje ga garun suba na takamaimai saidai nasan su din jinsin labawane dake makwabtaka da kasashen bakar fata a lokacin. Karatu mahaifinta yazo yi a maiduguri da matar shi har ya fara sana,a anan kakan ki Amadu yana aikin kada a lokaci a nan suka hadu da ita haliman . Anyi rikici sosai kafin su yarda su aura mai ita don yarinyar ta nace sai shi a lokacin bamu da hali nice nayi mai jagora lokacin kakan ku mijina yana raye da taimakon shi komai ya kammala. Basu kai shekara biyu ba da aure kwatsam sai ga yanuwan su sunzo daukan shi ashe shidin wani dan babban gidane fushin zuciya yayi ya bargida ya dawo maiduguri ya zauna. Zuwan yan uwanshi shi ya bata komai don sunce har halima ba zasu bari a nan ba tare zasu tafi saidai mahaifin ki ya rubuta mata takarda. Magana har ta kaimu fadan sarkin barno a lokacin nan dai dole hukuma tace ya bata takardan ta su tafi da yarsu ya samu wata ya aura a nan. Fushin haka lokacin mahaifiyar ki nada shekara daya da haihuwa nace su bamu yarmu muma dana san yin hakan zai jawowa mahaifiyar ki gori nan gaba haka da ban nemi su bamu ita ba A ruwa. Baki tabajin sunan kasan ba a bakin kinta amma tace ni dai tana ce min su din bakaken larabawane ko yaushe ban tsamanin tasan komai ba game da iyayyen ta din. Halimatu sadiya kenan take amma tace iyayyen ta kuma suna kiranta da siyama mudai a wuri mu halima muke kiranta. Itama yanzu nasan tana cikin kewar yarta da mararin rashin ta a kusa da ita saidai nisa zai hanata zuwa don da ba wasa bane. Saidai kuma nakanyi tunanen koda tazo din ma mu mubarcan tun bayan rasuwan kakan ku kawun ki ya dawo dani nan gida kusa dasu. Don haka ba wanda zai fada mata a inda muke yanzu da zama koda tazo din neman mu. Shiru nayi ina nazarin maganganun Amma a cikin raina yayin da ita bata kula da halin da nake ciki ba. Ina nan zaune wurin Amma har bayan isha,i a daidai lokacin da nake shirin tashi na koma part din mahaifiyata ne mukaji ihu a cikin gidan wanda yasa mu fito ga baki dayan mu gidan waje. Nafisa ce suka samu matsala da sauriyin da zai aure ta wanda murja tasha min korafi akan basu dace da juna ba nakan ce ina ruwan ta ba ita ke son shi ba hakana. Sai gasu yau dan magana ya hadusu yayi mata dan karen duka a kofan gidan mahaifin ta kuma ya shigo har ta cikin get ya jefo mata zagi da tonon asiri a tsakanin su. Wanda babu dadin ji kowa na gidan yana waje an kasa wanda zaiyi mai magana a gidan sai saurare akeyi abinda yake fadi din. Kai amma dai baka da mutunci da kima aikai ka fita rashin tarbiya da zakazo har cikin gidan mahaifinta kanawa mutane rashin mutunci haka. Ka koma gida a baka tarbiya zai fi don kai baka san darajan mace ba ko a gidan ku na fada a hasale. Don raina ya baci da rainin wayau daya kawo muna har gida yana ciwa iyayyen mu mutunci. Yace naji banda mutunci din ita tana da shine sau nawa ni kaina ina zubar mata da ciki shine yanzu zata koma bin wani dan iska kuma wai a haka akeson lakaka min ita in aura. Salati aka dauka ga baki daya nace fita gidan nan mara mutunci da sanin yakamata har in kuyi hakan ai tare kuka aikata zunubin ku. Asalima kaine wanda ka lalata har taji bata iya hakkuri dakai ta fara bin wasu mazan kajira kaga naka sakamakon dan iska kawai mara tarbiya. Jin ina fada dashi yasa murja saka baki itama ta shiga tona mai asiri tana fadin kai waye baisan abinda kakeyi ba garin nan. Kana sato kudin mahaifin ka kana rudin yan mata dashi har giya da karuwai kake kwasa kuma mun sani. Yace ni kikewa kazafi babu kazafi a zance na don bakin da bai karya ya fada min daga gidan ku na samu labarin komai ka fita zakka a gidan uban ka kakaiwa mahaifin ka ko ina a duniya. Ya nuna mu yana fadin you see karan ku zanyi don wanan sherin da kai muna Allah ya kaika dan iska kaji tonon asirin da baka taba zato ba na bashi amsa. Ke Fatima ku kyaleshi yayi abinshi ga mara kunyar da ta ja min wanan abin har gidana ya juya wurin hjy data daskare a wuri daya yana fadin kin daiji halin yarki yau da kunnuwan ki. Abinda take aikatawa a gidana sai kuma ya kasa karasa maganan ya juya ya koma part din shi. Daya bayan daya muka dinga watsewa a gurin don maganan ya girmi kunnuwan mu da ji. Dagani har mamu ba wanda yabi ta maganan balle mu zauna muyi zancen a dakin kowa yayi shirin kwanciya ya kwanta abinshi. Washe gari ma da wani sabon rigiman muka tashi don iyayyen yaron ne suka zo gidan tunda safe wai anciwa dansu mutunci sun fasa auren a basu kaya su da suka kawo na aure. Da lissafin kudi mai yawa da wai za a bashi wanda taci nasa tun anayi dasu da hjy a daki har suka fito waje suna cacan baki . Hakan yasa aka fito don jin me kuma ya faru yau din ma daya daga cikin matan ke fadi munzo ne mu karbi kayan da aka kawo na auren dan mu yace ya fasa. Ina tsaye daga kofan mu nace hjy ku koma kuce mai ba za,a bayar ba duk abinda yakeji a shirye muke dashi. Shida bakin shi ai yace sau uku suna zbar da ciki shi shida ita don haka an rike kayan a matsayin kayan jegon ta na diyan da yake fitar mata. Ban taba sanin akwai abinda zai girgiza hjy ba haka matan na fita get sai hjy ta sake wani irin kuka a wurin. Gwanin ban tausayi tana fadin Nafisa kin gama dani kinja mun abin fade a gidan nan kin tozartani a idon jama,a. Amma ta karbe da fadin kada kiga laifin yarki ita kadai kece mai babban laifi a gidan nan kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi baiyi. Jummai kin cuceni kin bata min zuria ta ba zan taba yafe maki ba a rayuwa sai Amma ta fashe da wani irin kuka itama mai ban tausayi. Da sauri su mamu da mama hadiye suka isa wurin ta suka kamata suna fadin tazo ta bar wanan maganan don Allah wanda ta fada ya isa. Nikan kafana naja na koma cikin part din mu ina jin babu dadi a raina don abubuwan da suka faru babu wanda zaiso ace nasa ya sama yau. Ko banza Nafisa yar uwatace kuma kaunar uban diyana bako zanso ace wani abu mai muni irin haka ya faru da ita ba. Mamu ta dawo part din ta tana kitchen sai jin sallaman hjy maryam mukayi tashigo gaida ita nayi ina mamakin shigowan ta shiyan mu don ba kasafai take shigo muna ba sam na shafa da zancen daya faru ne yakawo ta. Mamu ra fito tana fadin a,a hjy ce tace kedai nice maimuna magana ya isheni a zuciya nace bara na dan zo nan in rage. Ke kinji mun yarinya da abin kunya haka ana cewa namu sune lalattu ana muna gori ya tayi goshi kaya har sait uku da sauran tarkace ashe ashe ba alheri suke aikatawa ba da yaron nan shiyasa dare da rana suna makale da junan su. Hjy wanan magana ai ya shafi kowan mu nake gani ko kin mata da cewa Nafisa yar dan uwane ne wai ? Kekuma ai diyar mijin kine idan sunan gidan nan ya baci ba Nafisa kawai za a zarga ba duk ya shafi yayan gidan nan ga baki daya. Hakane kuma ta fada cikin wani yanayi sai kuma tace amma dai idan da dayan mu wanan magana ya shafa da yau munji hjy a gidan nan. Ko itace ya shafe mu ai tasan gaskiya don babu musulmin kwarai da sheri zai samu dan uwan shi har yaji dadi a ranshi. Bata dai gane komai ba haka yasa ta fita bayan ta gama yan surantanta a wurin nikan kamar bana falin zaune a lokacin don ko kallon ta banyi ba. Tana fita nace mamu wanan matar har yanzu halinta yana nan ashe tace Allah dai ya rabata da wana halin yanzu ita har taga abin gulma a nan. Can kuma ta juyo tana fadin wai nikan kunyi maganan da kikace da gwaggo ko bakuyi ba har yanzu. Nace munyi mamu ta fada min komai har auren su duk ta ban labarin komai nace amma ai bata da laifin wucewa ta barki don su Amma su suka hana ta wuce dake a lokacin wanda a yanzu take da ta sanin yin hakan. Haka dama Allah ya nufa damu haka ya tsaro min nawa rayuwan kuma nace hakane kuma. Ina son zan kirata yanzu idan na gama abinda nakeyi sai muji ko za,a sameta muyi magana. Ganin hankalin mamu ba zai kwanta ba yasa na dauko wayan na kira layin nayi sa,a ya shiga sai dai ba dauka ba har ya katse. Kira biyu nayi ba a daga ba na fahinci mai wayan bata kusa da waya a lokacin. Tana zaune ta tasani a gaba har na aje wayan ina fadin idan taga kiran zata kira kila daga baya. Mamu ta sauke ajiyan zuciya tana fadin Allah yasa nace idan bata kiraba zan kara kira kafin dare yayi. Har na aje wayan sai naga ya kamata in kira yaya inji lafiyan shi da yaran don yanzu ban san takamaiman ida suke ba dakai. Kira biyu ya daga da sallama na amsa mai yana fadin yau kin tuna damu ke nan nace ai kullun ina tunawa daku. Allah yasa yace nace baka yarda ba ke nan yace ina zan yarda tunda kina son dagwara min laifin da kinfi kowa sanin banawa bane. Akan me zan dagwara ma laifi yaya Allah yasa hakan shine alheri a gare muna fada sai naji yace hakan kamar yaya ?. Nayi saurin gyara zance na da fadin na zama ba kusa dakuba mana yanzu yace gara da kika gyara lafazin ki. Ina sultana gata a hannun mamu tana jin ka bata wayan yace nace sultana din ko mamu yace sultana dai. Na yunkura na kara ma yarinyar waya a kunnen ta magana yake mata tana dariya ba bakin da zata bashi amsa a lokacin. Na cire wayan a kunnen yarinyar ina fadin bari in barka kayi aikin ka yace aiki yafi jinku a yanzu da nakeyi. Yaushe zaku dawo ne ya tambayeni nace babu rana gaskiya kenan baki tausaya muna zahra dan murmushi nayi nace ina tausayin ku mana. Saidai banda yadda zanyi ne a yanzu ka sani ina dai kwantar mai da hankali kada ya fusata in samu mu rabu lafiya dashi a lokacin. Mun dauki lokaci muna wayan saida na tambaye shi queen fa yaya wajen su suna lafiya ko yace ban koma Europe ba har yanzu muna nan landin labawa tukun . Mukai sallama na kashe wayan na zauna ina tunane a gurin yadda wanan al,amari zai kasance muna nan gaba. ZAINAB IDRIS MAKAWA 16/11/2021, 23:34 - 🀐🀐🀐: Ina zaune a inda nake ina tunane naji muryan mamu tana fadin kina son tayar da hankali kan auren da mijin ki zai kara ko ? Na dago kai nace mamu auren shi bai damay ni ba sai dai nasan auren gaiyya ake son mashi a kaina. Don murja ta gano ko wace yarinyar ce ashe diyar hjy sabuwace da sukai zama lagos ance idanun yarinyar a bude yake sosai zata girmi anty salma na a wurin haihuwa sosai. Sayadi ba zaman lagos ba ko zaman turai tayi karewan bude ido mai zai dameki indai kin rike gaskiyar ki da amanan mijin ki a ranki kina kuma aiki da hankalin ki aiko tsakiyan faransa ta tashi karewan bude ido zata barki ne. A yadda Murja ke fada min taji wai ashe zancen nasu ya dade sosai yarinyar taki da farko da hjy taso ayi hadin sai yanzune suka aminta da ayi suna bin hjy sauda kafa har ta yarda. Mumu tace kamar nasan da zancen nan a baya saidai aikin mantuwa kawai ashe zancen nasu yana nan har yanzu ai da farko na dauka diyar Rakiya ce ko Ramatu dan suma suna son auren shi naji wurin hjy maryam. Ashe yar wurin hjy sabuwa ce kuma yanzu idan wanan ce aiki barsu kawai zai fita a tsakanin su don bata da hakkuri ko kadan kowa yasani. Ba mutunci ne da wanan matar ba su kansu suna tsoron masifan ta shine kuma yana zaune zaman zaman shi zasu dauko yarta su bashi kai hjy bata lissafi kafi ta aikata abu wallahi. Mamu ai duk saboda nine nake gani zasuyi wanan hadin . Tace a wurin hjyn gidan nan ba amma su wurin su aiba hakana bane mijin ki kamilin mutum ne da yasan kansa ga zati da kyau da cikkaken ilimi uwa uba arziki wanda ko wace mace yanzu take gurin samun mijin irin shi. Haka ya tashi da farin jinin mata tun muna yara duk da koda yaushe fuskanshi shi a daure yake bai hana mata suce suna son shi ba harda wa yanda suka girmay shi lokacin. Shiya banyi mamaki ba lokacin da yazo gidan nan da matarsa merry don nasan irin nacin da mata ke gwada mai ta gwada mashi har ya yarda da ita. Ni dai abinda nakewa gudu da tsoro shine asiri tun dawowan hjy sabuwa garin nan da zama gaba daya hjy ta fada harkan bokaye da malamai inma da tanayi dai a boye take abinta amma yanzu a filin Allah take lamarin ta. Saidai ni abinta bai faye damuna ba tunda ina bin dare ina fadawa Allah matsalolina ya kuma amsa min na gani. Mamu nidai idan abin zai zama fitina gara in tsira da rayuwana kowa ya kama gaban sa . Da sauri tace kina ko da hankali sayadi mai yasa kikaji manya na fadi anyi hakkuri da yanayin aure mai dadi ko mara dadi duk a kan yarane fa. Kan yaro sai ke mace ki danne komai naki kiyu hakkuri ki barwa Allah al,amarin sa komai da zai faru da bawa Allah yasani. Don yara wasu mata ke zaune gidan mazajen su suna cin boni gun kishiya da miji don sun kwamace da wata ta ba yaron su tarbiyan banza garasu suba abinsu mafi ingancin tarbiya tun zamaninda da ake da sauran imani balle yanzu da imani yai karanci ga zukatan mutane. Idan kinyi hakkuri komai yazo mai wucene a gurin Allah sai a koma kamar ba,ayi ba daga baya. Mamu amma aini nayi karanta da shanye irin wanan abinda kike lissafo min na fada ina kallon fuskanta. Tace kaiyya sayadi hakkuri ga yaro da babba aka san shi balle ban sa a raina cewa don mijiki ya auri yar wurin hjy sabuwa zai juya maki baya yadda kike tsamanin zaiyi ba duk dako itama yar uwasa ce kuma iyayyen su zasu tsaya sosai a kan auren na sani. Kedai ki kwantar da hankalin ki Allah ya saukeki lafiya ayi a zauna lafiya ba shike nan ballema shida baida ra,ayin aje mata a guri daya irin namun nan may zai damu mutum . Ba zama wuri daya ke sakawa mata kyashi da hassadan junan su ba haka abu yakici yaki karewa ko yaushe. Ranan mun dade da mahaifiyata muna hiran abu daya saida likacin sallah yayi muka tashi mukai sallah da cin abinci na shiga wurin Amma. Washe gari na tashi da niyar zuwa gidan Anty salma da tazo tana min korafin naki zuwa wurin ta dama ina da niyar zuwa wanan matsalan yazo muna na dawo gida. Sai ranan nayi waya da drivern gidan yaya akan ya kawo min motana zan fita dashi kwalliya sosai muka sha dagani har sultana fauziya da murja. Rigan dake jikina basai an fadawa mutum an kashe naira a gurin sayen shi ba dayai wani tafiya Dubai ya sawo min shi ga sultana da ta kwaso farin mu kamar yar turawa kwaliyan dan riga pink da wando dogo har ribon da ta kalman kafatan adon pink ne da fari a jikin ta. Daidai mun fito ke nan daga wurin Amma da muka shiga sallama aka turo get din cikin gida za,a shigo. Ban damu da kula matan da nagani suna shigowa gidan ba a lokacin don hankalina yana ga wayan da nake da Aisha muna dariya ina tafiya salo salo kamar da kamar da gangan nakeyi banko san inayi ba. Wani irin kallon kishi da tsana suke aika min daga inda suke suna kallon yanayin shiga na a cikin rudewa. A hankali tacewa uwar wanan kuma a gidan nan take ne tana magana kasa kasa kamar rada ga uwar. Wata kila bakuwa sukayi wanan motar da muka gani waje muna magana kai amma dai wanan ta hadu wallahi. Taji ina ace haka ta samu haduwa koda rabin nawa ne aida tasan dole mijin da take muradi ya so ta. Ga mace kamar balaraba sak da ganin ta yar wani ne ko matar wani a kasan nan irin yaran nan ne da suka taso a cikin hutu kinga fatarta wani irin luf luf dashi kamar wace bata shiga rana dan cikin jikina daya turo ta kalla tace ciki dai yanawa wasu mata kyau wallahi. Ita kadai take zancen ta a zuciyan ta sai taji duk irin kwalliyan data fito dashi suna yauki daga ita har uwarta duk sun muzanta a gurin. Ganin sun danzo kusa damu yasa na dan barwayan ina fadin sannun ku da zuwa ina wunin ku. Mun saba da gaisuwa irin na tura da zaka hadu da mutum baka san shi ba ku gaisa. Tana mamakin jin muryana daya dan girgizata sosai bamu kara kulasu ba mama hadiye ne ta fito tana fadin Fatima ku biya gidan saratu don Allah ku gaisheta na amsa da to mama da cewa gidan kanwar mama hadiye din. Bari na dan riko abin da zamu kai mata nace ina sake hannun sultana zuwa part din mu da sauri. Ba yar ba har uwan saids gaban ta ya fadi uwar tace kardai nace wanan ce matar yaron nan dama ? Da wanan mamakin suka shiga wurin hjy da sukazo dubawa don tun maganan su Nafisa ta kwanta ciyo. Shine suka zo dubata don yanzu zumuncin su ya taso sosai a tsakanin su idan ba a hadu ba ana makale da waya. Hjy dake zaune tana ta dago tana dan murmushi tana masu sannu da zuwa. Suka amsa da um kedai hjy muna shigowa muka hade da wata mace data dauke muna hankali yanzu gidan nan. Hjy tace a gidan nan kuka ganta Nafisa dake gefen ta zaune tunda tayi masu sannu da zuwa ta kawar da kai gare su tace Fatima ne fa suke fadi yanzu da zan shigo na gansu zasu fita ita da murja. Na,ima tace na shiga uku itace fatiman matar Umar dama anya kuwa kuwa Umar zai soni yana da wanan matar haka ? Da sauri hjy jummai tace inkiji soma ai daya ke nan ai sai yayi maki so da kaunar da bai taba yiwa wata mace irin shi ba indai ina raye. Mu zuba dani dasu zaki sha mamaki ke dai kawai mu samu yanzu mu shawo kanshi a samu ayi wana abin gida bai koshi balle in barwa daji ganima . Iya gudun shi nake kallon nan gaba bausan sanda zai kawo kafan shiba gidan nan da kansa yana rokon gafaran mu. Hjy sabuwa tayi dariya tace tun yaushe wasa yake damu ai don dai kawai ma ya zama namu ana daga masa kafa. Mikewa Nafisa tayi ta bar falon zuwa daki waya ta dauko tana tsegun tawa salma zancen da sukeyi a falo tana jan tsuki. Muna fita gidan muka shiga mota nida murjane a gaba fauziya da yarta suna baya zaune suna dan hiran yara. Wai fatima kin san wa yan nan da suka shigo gida yanzu nace wasu mutane ke nan don ni har na manta dasu a raina. Tace wa yanda kika gaiyar mana da zamu fito nace OK matan nan ai ina ga wurin hjyn su yaya suka zo ko ? Itace fa Na,iman da ake fadi yaya zai aura din ta fada tana kallona wanan din da suka shigo yanzu fa murja na tambaya ina kallon ta. Ita face da uwarta ina fada maki kaina girgiza ina runtse idona duk da ban masu kallon kyauba amma na danyi tunanen kamanin su. Ban taba zaton zanji abinda naji a raina ba lokacin da sauri nace innalillahi ina kallon hanya. Suma bakiga irin kallon kurullan da suke maki bane da suka shigo ba lokacin kila suma sun gane ki ne suke kallon ki. Suka sani na bata amsa ina kallon ta tare da fadin sai fa kin mun kwatance don ban iya kai kaina gidan yanzu gaskiya. Tana mun kwatance muka isa gidan tun a waje na gane salma na cikin wani yanayi don har yanzu gidan na a yadda na san shi a baya ba,a gyara komai ba daga gidan. Nan dai muka shiga bayan nasa Fauziya ta riko abinda muka kawo mata sallama mukayi daga kofan shiga tana ciki ta amsa muna. Tana fito da gani girki takeyi a lokacin mamakin ganin mu tayi wanan lokacin yau a gidan nan nace gidan ki kuwa yau dai gamun zo falo ta kaimu tana kame kame aiki yai yawa bata samu ko gyaran falon ba yau. Muka zauna muna gaisai tana tambaya mu mutanen gida ranan mun sha hira tanayi tana duban girki har yayi ta zubo muna mukaci tare bayan azahar sai ga maigidan ya shigo cin abinci dama tace muna kila ya dawo don ba kullun yakan samu dawowa gida ba. Allah ya taimaka sai gashi ranan ya dawo tundaga waje yake kallon bakon motar daya gani kofan gida haka ya daure ya shigo gida da sallama tare da zullumin wanda zai sama a gidan. Kasa nake zaune na sake jikina muna hira dan kwalina yana saman kaina na rufa ya shigo da sallama. Muka karba tare da mai sannu da dawowa da mamaki yake kallona tare da fadin wa nake gani haka kamar Fatima gidan yau nace nice yaya. Duk cikin mu ni kadai ke masa wanan karan kiran shi da yaya tun farko kuma yana jin dadin hakan har cikin ran shi. Gaisawa ya zauna mukayi sosai yana tambayana yara nace suna lafiya baban su ya tafi dasu suna gurin shi. Kefa may kikeyi a garin nan har yanzu sai nayi mai dariya kawai anty salma tace kamanta na fadama tana gida yace amma na dauka laluran cikine ya tsayar da ita aiko ? Shiru yayi na dan lokaci kafin ya mike yana umurtan ta takai mai abunci a daki tunda muna gurin . Nan ta barmu ta shiga hidiman mijin ta muna dan hira da murja sama sama a gurin na lura da akwai biyayyan aure sosai da salma take mai don yana shigowa gaba daya sai naga ta daburce min . Sai da ya gama na mike ina tambayan ta ya kare cin abinci ne ina son magana dashi taje ta fada mai yace in shigo tashi yayi saman kujeran da yake zaune ya koma bakin gado ya zauna. Na shigo da sallama muka kara gaisawa yace banji dadin jin kina gida haka zaune kuma ban sani ba don yanzu na rage shiga gidan tun bayan auren mu da salma bana shiga kamar yadda nake zuwa dacan. Nace yaya dole na zauna gida abubuwa sunki canzawa ta bangaren hjyn su salma har yanzu dani nan dai na kora mai dan bayanai da suka faru. Yace ni abin yana ban mamaki wanan hali na hajiya har kullun ita bata amfani da girman ta da shekarun ta. Yanzu shi Alh dayace ki zauna gida yana ganin hakan shine mafita ga zancen ku ? Nace yaya ni hakan yafi mun sauki gara kowa ya zauna a matsayin shi zai fi abinda ke daga min hankali shine kullun dan zance kadan tayiwa mamu gori da zagi da cin mutunci. Zuciyata ta fara gajiya da wanan abin yaya don ba zan yarda ina ganin mahaifiya ta ko yaushe a cikin tashin hankali yaya meye laifin mamu a cikin barin ta da mahaifiyar ta tayi ? Yace ni yanzu ba wanan ba don in da sabo ai hjyn ki ta saba da halin wanan matar hakana zaman ki gida shine bangane nufin Alh ba. Nace yaya koma dai maye ni ba zan koma gidan yaya Umar ba taje tayi mashi auren gatan da tace zatayi mai din kowa ya gani ba shike nan ba. Yanzun gida nake son zuwa kwanan nan tunda nazo banje gida na dubasu ba idan na dawo zan fara maganan aiki tunda ina da takarduna zaman nan ba zai fitar dani nan gaba. Yace a,a Fatima kada kiyi haka ki bari a zauna ai magana zan tuntubi Alh da zancen nasan ba zai boye min komai ba daga ciki in yaso sai mu san abinyi daga baya. Yaya ba zanso kai mai magana ba don ni abin yanzu ya fita mun a rai ba zan iya daukan cin fuskan da akewa mahaifiyata ba yaya a kaina. Fatima shi aure da kike gani ta wuce nan ya fada yana murmushi shi umar din ai badashi kike da matsala ba yanzu don mahaifiyar shi sai kice kin hakkura da mijin ki da diyan ki ga baki daya. Zamu zauna da Alh duk abinda ake ciki zan kira hjy muyi magana itama hakkurin data saba shi zatayi. Kin gani nan sai da na nuna mata nima na iya ta barmu muka zauna lafiya da salma gidan nan yazu ta fita batun yar nata wai ta yafe min ita. Yakai inda nake sin zuwa nace kai hjy ho dama yaya zanso muyi magana sai ga sultana ta shigo tana kuka a dakin tana nema na. Saida na lalashe ta tayi shiru yace wayan can yaran su ance mazane kika haifa da farko ko ? Nace mazane yaya kafin ince dama zancen Anty salma nake son zamuyi dakai idan mun samu lokaci don naga yanzu kamar kana saurine ? Yace wani abinne tace nayi kuma haba yaya me zakai ma anty salma harta kawo karanta gareni kawai dai ganin dacewan abin yasa nace tunda dai ni zaman kanwarka nake a gare ka zan ma magana ko za a samar mata aiki ko wani sana,a mai karfi wanda zata rike kanta kamar yadda mata sukeyi a zaman nin ba sai mace ta dogara ga abin namiji ba . Dan murmushi yayi kafin yace Fatima nasan da wana gata nan ki tambaye ta kiji nidai ga tsarina ba zan yarda da aikin gwaunati ba. Ko karatun da tayi mijin ki shi yazo ya rokeni alfarma naji nauyin shi na yarda taje karatu. Salma bata da wayau fatima da kike ganin ta ga kazanta da ace ni mai ra,ayi tara matane da yanzu na dade da kara aure don halin salma. Nace abin ko bai mata kyau ba nayi mata magana dazun da muka shigo kuma ta dauku alkawarin zata gyara. Yanzu dai naji yaya ba zaka barta tayi aiki ba zaka barta tayi sana,a mai kwari koda a cikin gidane don ta huta zaman banza . Da alama zancena yana bashi dariya don murmushin da yake sakewa a fuskan shi idan nayi yasa na gane hakan. Fatima yanzu shahon mu ba kamar da bane can baya kuma ni kin san a karskashin wani nake har yanzu dukiyan mutanene amana a hannu na na fada mata tayi hakkuri har Allah ya bani wani dama in samu dan kudi in bata tasamu abin yi dashi. Na sani yaya ba wai ina nufin kai kaimata a yanzu nasan yanayin da kasan nan ke ciki da halin da kuke ciki dan uwan ta dai ne zai mata idan ka yarda. Fatima kin san halin hjyn su sarai yin wani abu ga yarta yana iya jawo muna matsala daga baya mussanman ma idan abin ya fito daga bangaren su. Nace yaya kada ka dubi wanan yanzu idan ana dubun halin hjy komai ba zaiyi ma yan uwan shi ba ita ta kwammace yai ta bata kudin tana bin wani hanya dasu. Yace Allah dai ya kyauta Fatima halin hajiya sai ita muyi ta hakkuri tunda Allah ya hadamu dasu. Wayan shi da yai kara ya katse muna zance ya tsaya daukan waya a daidai lokacin na mike ina fadin yaya na gode zamu tafi gaba har gidansu mama muke son zuwa yau din nan. Na fito na dauki jakkana na suba kudi a ciki yana fitowa daga dakin naji yana fadin ke barin baki dan wani abu a saya maki biscuit ko yana kokarin lalaben aljihun rigan shi ta gefe. Da sauri nace a,a yaya don Allah ka barshi ni ga wanan dama na riko maka lokacin da muka zo ban samu kawo maka tsaraba kayi hakkuri da wanan ina mika mai kudin daga cikin daki da yake tsaye a kofa. Yace Fatima kamar abin bin bashi ni ko wanan mutuncin da kike min keda mahaifiyar ki kun maidani tankar dan uwan ku na jini ai ya isheni daku . Babu komai yaya don Allah ka karba ina dashine aina baka da bandashi gurin ka ai zanzo nima in samu yaji dadi yana fadin kwarai kuwa fatima yasa hannu ya karba yana min godiya. Sai bayan ya karba yace kai kai kai Fatima kudine fa masu yawa kika miko min nace yaya ka wuce nan a gareni idan inada wanda yafisu sai in baka babu kyashi. Godiya yai min sosai ya fita yana mun sallama sai bayan ya fitane na kalli anty salma da ido nace ko dan rakiya baki mai kiji ko yana da wani maganan da zakuyi tunda gamu a wurin. Mun zauna da ita munyi magana sosai bayan la,asar muka fito gidan zuwa gidan mama saratu da kanwar mamu mama saude duk mun kai masu ziyara ranan kuma sunji dadin zuwan mu. Sai gap da magariba muka dawo gida a gajiye part din mu na wuce direct don nagaji sosai a lokacin tun a falo na fara kokarin cire kayan jikina. Mamu tace kin bar wayan ki a gida ana ta kiran ki na dauka ban gane yaren da matar take min ba yare kuma mamu na tambaya ina kallon ta. Tace ni kan yare naji tanayi mun ai don ban fahinci may ake fadi ba nace koma waye ai zai sake kira idan wayan ya damay ta. Har na juya na fara tafiya wani tunane yazo min a raina na juyo ina fadin mamu kodai wanan matar da muka kirane ta kirani yau. Da sauri tace kuma fa yana yuyuwa gaskiya nace bari na duba na shiga na dauki jakkar da wayan ke ciki ina dubawa daga daki nace wallahi mamu itace kuwa ga sunan tanan da nayi serving. Ikon Allah mumun kira ranan bata daga ba yau kuma ita ta kira har sau uku ba a daga ba may wanan abin yake nufi ne wai haka ? Dare yayi yanzu sosai a can zai kai karfe goman dare ko ya dan fi amma dai barin gwada kiranta mu gani ko zata dauka yanzu. Tace shiyasa mijin ki yace idan zan kira na dinga kiran ki goman safe ko zuwa shaday haka yafi a same ku. Kiran sunan yaya da tayi yasa na tuna da zancen mu da Ahmed nake tunane sai dai ban mata magana ba duk da an fara kiran sallah hakan bai hanani kiranta ba a lokacin. Nayi sa,a aka daga wayan da sallama na karba muka gaisa tace kwana biyu nace eh ban dawo ba ina Nigeria har yanzu. Zancen da mukayi dake ne na kira don nazo ga mahaifiyana na tambaye ta tace min sunan mahaifiyar ta halimatu sadiya amma mahaifan ta suna kiran ta da Siyama a lokacin . Sai naji tayi wani irin kanbbara da karfi tana fadin nasani nasani kamar yayi yawa wallahi itace itace wace muke nema shekara da shekaru bamu gane ba. Da gudu na fito falo zuwa wurin mamu sai na sameta zaune tana kuka da alama taji wayan da nakeyi da matar a lokacin. Ban damu da kukanda takeyi ba na fada mata ina ihu da murna ina rike da waya a hannu na lokacin . Munyi magana sosai da ita na fahinta ta fada muna mu saurare ta zuwa safe zata kirani ta fada min yadda sukayi da mutanen ta. Mamu ki bar kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya karba muna adduan mu a lokacin da mukafi bukatan hakan a tare damu. Sayadi dole in kuka yau ta fadi tana share fuskanta jin zancen nan nake kamar mafalki nakejin sa yau ubangiji Allah ka tabbatar min da wanan abin ya zama gaskiya a gareni. Ba zan kara sati ba a gidan nan zan tafi zuwa neman mahaifiyata tunda na gano a inda take yanzu. Tashi muyi sallah mu godewa Allah lokaci yana shigewa kada muyi wa Allah butulci da halin mu na yan adam a lokacin da ya amsa muna addu,an mu. Mikewa nayi ina tafiya duk jikina ya mutu da maganan mamu da tace sayadi abubuwa suna damun rayuwana da zancen rashin ganin mahaifiyata zanji koda rashin kwanciyar hankalin gidan nan kullun nike nan a cikin gori da takala da habaici iri iri. Yanzu idan mahaifiyar mamu tazo yaya hjy zatayi da take yawan mata gori kan hakan irin tunanen da nakeyi kenan ina alwala a ban dakin. Na fito na tayar da sallah muna idarwa kuma muka dasa maganan ta yadda zamu bullowa maganan don haka zamu yi shiru tukun na sai mun gama tabbatar da komai da gaskene kafin ta tunkari kawu da Amma da zancen. Barci nayi sosai ranan don a gajiye nake sosai kamar nayi wani aiki dan fitan da mukayi ya saukar min da kasala a jikina. Washe gari ne da safe muna karyawa sai ga kira kawu a wayan mamu yace ta turo mashi ni falon shi. Da mamaki a raina na mike zuwa amsa kiran kawuna a falon na samay shi zaune tare da hjyn su yaya tana cika tana batsewa ganun hakan yasa nasan ba lafiya bane wanan kiran. Gaida su nayi na samu wuri na zauna daga kofa a kasa ina fadin gani kawu yace Fatima yanzu uwar ku ta kawo karanki wurina. Kan kin sa drivern mijin ki ya dauko maki mota a gidan mijin ki kin fita dashi jiya alhalin ba a gidan sa kike ba yanzu kin sani. Dan kallin hjy nayi cikin mamaki nace kawu ban taba motar yaya ba motanace dana bari a can nasa driver ya dauko min da zamu tafi gidan Anty salma jiya. To kinji jimmai ya fada yana nuna ta da hannu yace jimmai wai may kike nema da wanan yarinyar ne haka a gidan nan ? Shiyasa ban maki magana sai da tazo don muji dalilin ta na daukan kayan danki bai gari ita kuma a matsayin matar shi. Motar ta ni bai sheda min cewa tana da mota ba da zai tafi don haka dole inyi magana akan kayan dana don ba kayan banza ya ajeba da kowa zai dinga dauka yadda yaga dama ko wani lokaci. Kawu bai dago kaiba hankalin shi naga waya sai daya kira aka dauka yasa handfree yana fadin kana lafiya ya yara. Ya amsa mashi kawu yace yanzun ina zaune mahaifiyar ka ta shigo min da wani magana wai Fatima ta aika gidan ka an kawo mata mota ta fita jiya. Shine na kira fatiman yanzu gata a gaban mu take fadin motar tace ta dauko ba naka ba ita jimmai bata yarda ba shine na kira muji a bakin ka. Innalillahi yace munajin shi yanzu daddy don Fatima ta taba kayana shine abin magana wurin mama motar nan nata ne tun a London na saya mata ba fita take nan ba yasa na turo mata dashi gida. Kai mara kunya inada daman da zanyi magana akan kayan ka idan naga za,a wullakanta maka dukiya tunda ba,asan zafin shi ba. Mama matatace fa ta taba kayana tana da iko da duk wani abinda yake mallakinane a garin nan yanzu don tare muka same shi a nan. Lalai babawo ka nuna min an gama da kai har kake fadin haka a kunnuwana yau komai tsiyar ka sai ka rabu da yarinyar nan na fadama. Mama daga yau nabada baki duk abinda Fatima zatayi da kayan gidana a barta tati natane na mijinta na yaran ta final ya kashe wayan. Kawu yace tashi kije abinki na dago ido na kallesu tare da fadin nagode kawu na fita daga falon zuciyana ba dadi abinda hjy take min yayi yawa sosai yanzu. Tayi min tayiwa uwata duk muna daurewa muna shanyewa anya kuwa zan iya nan gaba da halin hjyn su yaya. Na shigo part din mu mamu ta bini da kallo banyi magana ba son banda niyar fada mata wanan magana. Lafiya yake neman ki nace lafiya mamu ganin ta kuramin ido tana son jin akan may ake kirana din nace wai hjy ce takai karana na dauki mota jiya daga gidan yaya na fita dashi. Matarnan tana da hankali kuwa wanan wani maganane haka babu dadin ji ko yaro ai ba zaiyi wanan abinba. Ta dai daukeni matsiyaci dagani harke tana muna kallon wullakantatu a idon ta. Mamu hassadane da ne da kyashi ke damun hjy rashin kaunar ki da batayi ya kawo haka garemu . Niko nasan da hakan don hjy ko kasheni tayi idan ba ta cire min kai taga bana motsi ba hankalin ta baya kwanci. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:13 - 🀐🀐🀐: Barci nake hankalin kwance don ina jin dadin barci a irin wanan lokacin na ba safiya ba ba rana ba don barci kan min dadi sosai balle yanzu da ga ciki a jikina. A cikin barcin da nakeyi ne nake dan jin murya sama sama wanda hakan yasa har nakai ga bude idona a hankali. Bubu kowa a dakin sai sultana dake barci a dakin saman gado a kwance kusa dani ta makale mun a jikina. A hankali na cire yarinyar a jikina na yunkura na sauka daga gadon na nufi bandaki na kewaya . Falo na fito mamune ta dauki abu a kitchen zata fita da sauri daga part din mamu meke faruwa na kuma na tambaye ganin yadda take a rude. Kawun kine baida lafiya ya rikice muna lokaci guda ta bani amsa tana fita daga dakin. Hankalina naji ya tashi lokaci guda da sauri na bi bayan mamu muka isa falin tare lokacin na sami har Amma tana falin itama. Yana kwance sharkaf gani daga wurin yin lazimine laluran ya same shi koda mamu ta fita bai karkare fita hayacin shi ba zuwa ta dauko abu ne muka samu ya fita cikin hayacin shi ga baki daya. Duk yan gidan suna rude sai kuka suke sun rikice a lokaci daya. Kwatsawa nayi tsakanin su hjy da hjy maryam ina fadin a bani cibi da sauri kada ya datse harshen shi lokacin. Da sauri aka miko min cibin dake saman table na daga kanshi ina kokarin samun sa,an cibin ya tsaya a bakin shi. Da dai an kira likita yazo hjy tace ban kula taba sai aikina nakeyi da sauri na dago ina fadin zan samu dan igiya ko yagwai karami haka ? Wanan ba mafita bane kada aje a jawo mashi matsalan da bashi ba kuma ta kara fadi. Ba dai wanda ya kula ta a lokacin sai hjy maryam ne tace cikin kidimewa hjy ya zamuyi dashi haka tunda an kira wayan likitan ba,a sameshi ba shikuma Ahmed nasa bai shiga ba. Tai makon daya samu a lokacin yasa yai wani irin ajiyan zuciya yana fitar da numfashi a wahale. Zan samu ruwan sanyi da tawul yanzu na fada da sauri hjy maryam ta nufi wurin fridge mamu ta shiga daki ta dauko min tawul ta miko min na dan zuba ruwan ina dan mana mai a goshi da saman zuciya zuwa babban yatsan shi a hankali. A hankali na dago kai ina fadin don Allah ku dan rage murya kadan idan son samune a dan rage zuwa waje. Kafin in riki hannuwan shi ina dan murzawa a hankali a lokacin hjy tace kai a daukeshi aje asibiti yafi wanan shiriritan da ake mashi ai. Hjy wanan halin da yake ciki ina mu mata zamu iya daukan shi haka zuwa waje ai kafin mu fita ya wahala da yawa mamu ke fadi. Can kawu yai wani irin ajiyan zuciya wanda hankan ya dawo da hankalin kowa a gareshi. Yace ku dagani don Allah sai dai maganan nasa baya fita sosai daga inda nake gefe rugume da kanshi nace kawu yi shishiru na dan lokaci hakan zai taimaka maka sosai ya rutse idon shi a hankali. A daidai lokacin na dago kaina wurin mamu ina fadin mamu wayana don Allah. Ta juya da sauri zuwa part din mu sai gata dauke da wayan a cikin sauri ta miko min na karba har lokacin ina nan rike da hannun kawu ina dan murzawa a hankali. Karban wayan nayi na dakatar da abinda nakewa kawu na kira wani layi runging aka dauka nace Auwal kana kusa kazo nan gidan kawu da kai da mai aiki guda don Allah yanzu yanzu. Ya amsa da fadin gamu nan zuwa yanzu hjy na kashe wayan ba a dauki lokaci ba sai ga shiya kirani yana fadin suna kofan gida nace ku shigo gani tafe. Na fita nayi masu bayani sai gasu da sauri suna bina a baya muka shiga dakin da taimakon su suka kama kawu suka fitar muna dashi zuwa wurun mota yana fadin a barshi yaji sauki ai nace kawu bari aje asibiti dai tunda taimakon gagawa na baka kawai dama. Auwal da musa mai kula da duk wani kayan gidan suka zo sune suka shiga dashi mota musa ya zauna tare dashi a bayan motar ya dan rungumay shi a jikin shi hjy ta shiga gaba tare da Auwal driver. Da sauri na shiga dakin mu na saka dogon riga da gyalen shi nacewa mamu ta taso muje tace ai ba sai naje ba tunda ga hjy a can. Mu tafi nace mamu zuwan mu yana da rana a wurin don Allah jakkata na dauka muka rufo kofa takai yara wurin Amma hjy maryam ke tambaya can zamu tafi na bata amsa da eh muka fita tare har mama hadiye. Auwal na kira na tambaye shi inda suke ya fada min da kwatancen su mukai asibiti don ni ke jan motan mamu danaji shi duk ya tsufa sai manejin ashe takeyi hakana. Mun same su a waje ko karban shi ba,ayi ba don akwai mutane damkare a wurin lokacin . Mun samu hjy tana masifa da masijan kofan likitan kan yayi masu alfarma a duba shi. Masijan na fadin dole sai sunbi layi zasu ga likita da kike son ganin shi da wuri me ya hana kuyo sammakon zuwa nan. Ran hjy ya baci ta shiga fada ma masijan bakar magana yana fadin ko dukana zakiyi saidai kiyi amma yau sai kin bi layin nan. Wani likitane yazo shiga office din yaji hayaniyar yayi yawa ya tsaya yana tambayan ba,asi ana mayar mai na karaso ina mai bayanin halin da kawu ke ciki yana buka gagawan kulawa a lokacin yadda nake mai bayani ya tsaya yana kallona da mamaki har na cikin office din suka fito ya shiga yaga likitan bai dade ba sai gashi ya leko yana fadin muzo mu shiga. Auwal ya tura keke ina bayan shi hjy tana fada har lokacin muka shiga office din wanda na gani zaune a matsayin likitan mai duba mutanene ya bani mamaki sosai a lokacin. Shima sunana ya ambata da fadin Fatima Abubakar bauchi yaushe kika dawo kasan nan na kwana biyu na bashi amsa ina fadin kawuna ne baida lafiya yana bukatan kulawan gagawa. Yace gaki babban likita tare dasu ni wani kulawa zan bashi yanzu a nan ya juya wurin likitan da yai muna hanya yana fadin ka ganeta tare mukai karatu a London sai dai ina gaban ta da shekara uku. Haba yadda take min bayani yasa na gane tasan wani abu a ciwon mara lafiyan don sai kuma yai shiru . Bawani bane D Guy ne likitan da muka sama ya mike da kanshi ya taimaka aka dora kawu saman gado lokacin dayan likitan yace mu basu wuri. Take ya jona mashi ruwa a office din da allurai daya dace ayi mai kafin su fara mashi aune aunen daya dace suyi mai. Ga na,uran numfashi da zai taimaka mai wajen dawo mai da numfashin shi daidai. Saida suka gama ya kiramu da hjy muka shiga ya dago kai ya kalleni yace Fatima tun yaushe haka ya same shine ? Hjy tace haka ya kwana yana jin jikin nasa da safen nan ya karkare rikice muna a gida. Hjy shine kuka kyaleshi da ciwo haka a gida ke fatima kin san illan hakan kuka barshi har wanan lokacin ? Idon daya kura min wanda yake min manyattacen kallon da banson nan nasa yana karewa yadda jikina ya kara fresh kowa ya kalleni yassn ina samun hutu lokacin. Ganin na tsargu da irin kallon da yake min a fakaice ya mike ya koma wurin kawu ya kara masa wani allura har lokacin kawu barci yakeyi bai san inda yake ba. Muna zaune shiru a gefe daya nida hjy yaci gaba da duban marasa lafiya dake shigowa yanayi yana dan jana da hira ina bashi amsa da kyat game da aikin mu. Saidai hankalin shi yana gurin kawu yanayi yana dan dago kai lokaci lokaci yana kallon inda kawu yake akwance da ruwa a jikin shi. Nayi zurfi cikin tunane naga ya mike zuwa wurin kawu likacin na dago kai ina kallin shi ruwan ne ya kare ashi yaje ya zare mai a hankali. Tare da cire mai na,uran daya jona mai ga hanci na numfashi ya dawo ya zauna yana fadin he be alright insha Allahu. Amma Fatima kin daddy ki yanzu bukatan hutu da kwanciyan hankali yake so mai yasa kike barin kuna daga mashi hankali hakane ? Dan satan kallon hjy nayi da take zaune kamar na dole a wurin nace kasan mutum mai iyali ai sai sannu dole a yanzu. Yace to amma a stage din da yake yanzu bai kamata kuna barin abu yana bata mashi rai ba ko wani lokaci don zaku iya rashi alokacin da baku zataba. Kawu ne dayayi dan tari ya ja hankalin mu zuwa gareshi ya mike da sauri zuwa bakin gadon yana dan tatabashi a hankali. Salati kawu yayi lokacin da yake kokarin bude idanuwan shi mikewa nayi na nufi wurin gadon ina mashi sanu da jiki ya bude idon gaba daya ya sauke su gareni yana fadin fatima kece ? Kawu nice yace Allah yai maki albarka Fatima kinji nace amin kawu a sanyaye. Muryan hjy ce a bayan mu tana fadin sannu Alh a daidai lokacin da likita take tayar da kawu zaune daga kwancen da yake. Ya zaunar dashi tare da jinginar dashi a jikin bangon da gadon yake na dan fita zuwa wurin su mamu dake waje nace su shigo kawu ya falka. Tare muka shigo dasu office din sai faman sannu suke mashi da godiya ga Allah da likita. Nunani likita yayi yana fadin ga wace ya dace kuyiwa godiya don ita ta bashi kulanwan gagawan daya dace kasancewar ta babban likita data san aikin ta. Da badon ta bashi abinda ya dace ai mashi da faduwan shi ba da abin ya zama babban matsala yanzu. Hjy maryam.tace ko za dan bashi ko tea ya shane don bai karyaba koda abin ya faru dashi. Yace komai zai iyaci a yanzu ba wani matsala ai ta juya tana fadin bari aje gida a dauko kayan tea ke nan. Likita yace No zaku iya zuwa dashi ai gida ba abinda zai faru insha Allahu ai ita aikin tane ta sani yana nunani da hannu. Muryan hjy ne take tamnaya nawa zamu bayar likita sai mu koma gida yace haba dai mama. Kuna iyayyen Fatima kuma zan karbi wani abu a hannun ku kawai dai a daina bata mashi rai dan gujewa irin haka yanzu. Ga wanan maganin su zaku saya ya dinga amfani dashi ya kalleni yace kin dai san doze din da zaki bashi ai. Da dai ka fada muna likita zaifi ya danyi dariya yana fadin hjy sai naga kamar kin raina karatun wanan yar taki dai ? Wanan fa ko a can London babban likitace don bata taba faduwa karatun ta ba har ta gama nayi mamakin da ta dawo kasan nan ta labe a guri daya haka gashi ana neman manyan likitoci irin ku a kasan nan yanzu don matsalin mata da yai yawa. Kyaleshi tayi don da ba don taimakon da yai muna ba da yasha bakar magana a wurin ta lokacin yadda ya bata haushi yana wani yabona gaban kowa haka a samu abin bara,dawa kuma. Kawu da kanshi ya taka yana kara yiwa likitan godiya suka fita na juyo a hankali na kalli likita nace a sanyaye doctor mun gode zamu tafi sai wani lokaci kuma ? No ba godiya tsakani mu ai kin sani nace nagode na juya na zan fita ya bini da kallo har nakai kofa na kama zan bude yace wai ina mijin ki ne Fatima ? Yana nan na bashi amsa yaran ki nawa yanzu naga ga wani ciki a jikin ki kuma uku na bashi amsa a takaice yace mijin nan naki ya faye wayon tsiya ya tare ko wani kafa. Ni dai na juya na fita daga office din da sauri zuwa wurin dasu mamu suke na samu suna jirana don key yana hannu na lokacin . Kafin mu zo har hjy tasa an tayar da mota sun dauki hanya sai motar mamu ya dan bamu matsala wurin tashi da kyat na samu ya tashi ina fadin mamu wanan motar take ai ta tashi aiki sai wata sabuwa kuma ke nan . Kowa sai mamakin yadda kawu ya murmure kamar bashi aka kwasa ruwa ruwa zuwa asibitu ba a lokacin. Falon na kawu suka nufa nikan na shige part din mu don in watsa ruwa a jikina kafin inyi sallah. Sai da nayi sallah na fito na samu abinda naci don ban ko karya ba muka fita daga gidan. Bayan sallah la,asar na shiga wurin kawu in kara gaida shi da jiki a nan na samu matan nasa duka yana zaune kasa ya mike kafa kamar ba kawu bane da safe ya daga muna hankali sosai. Da sallama na shigo falon na samu karshen kujera dake kofa na tsuguna ina gaida shi da jiki yace Fatima jiki da sauki. Aiku keda sannu keda likita hjy maryam tace ai yaron nan yasan aiki shi sosai wallahi jifa Alh kamar bashi ba ni abin ya bani mamaki sosai irin hakane fa kwanaki har ya kwantar da Alh kwana da kwanaki asibiti. Mamu tace bakiji a waje yayi karatun shi ba ga kuma kayan aikin da suka saka asibitin yanzu ai shi yasa mutane yanzu suke tururuwan zuwa asibitin nasu. Wasu dai ke karatu waje su karanto abin kwarai wasu kan insunyi sai dai su rike kwali sunan su likitane ba a san komai ba. Amma a gaban kowa yace fatima tafishi kokari don ita tayi abinda ya dace kafin aje can hjy maryam tace . Kai maryam da wani magana kike wallahi zai fito fili ya fadi gaskiyane a gaba kowa kai hjy komu fa nan munsa yarinyar nan tayi kokari kafin aje can. Tayima kanta ai ba wani ba murmushi kawu yayi yana fadin Fatima yaron wani garine wai nace kawu dan garin nan ne ko dan gidan Alh canji naji akace yake . Au kice dan manyane ya samu karatu yadda ya dace ko can ai inga kudi kudin suna aiki sosai. Kawu yace yanzu ai na samu likita sai dai matsalan kada na takura mashi don farawa da iya yaki karban kudi. Kawu muna mutunci dashi tun a nan dan aji su anty salma ne shi yana gaban mu sosai a makaranta. Ai kaji abin hjy ta sake fada yanzu ina wani mutunci ga macen aure da wani namiji don Allah ai irin abinda akewa gudun ke nan. Na mike ina fadin kawu Allah ya kara sauki ya amsa da amin fatima na gode kinji nace kai haba kawu. Ina fita mamu tace umhumm kai duniya yau aka fara karatu ina dai karatun nan dan kowa yayi shi a gidan nan kowa kuma yasan yadda yanayin karatu yake ai. Maimuna kawu yace ki bar zancen nan don Allah kinji abinda likita ya fada kafin mu dawo gidan nan. Duk wanda yai jifa a kasuwa yasan wanda ya jefa akace don haka tankawa yabawa tunda ita bata girma a rayuwan ta. Tau yau kuma taron dangi za ai mun ne a gidan nan don na tabo ya gwal din ku ai komai zanji kenan a gurin ku ashe ? Ke bari na fada maki jimmai ba tsorin ki nake ji ba gidan nan baki haifeni ba baki kuma girmay ni ba asalima a karkashina kike zaune. To wanan fitinan ya isheni haka ki sakewa yar mutane mara tayi fitsari a rayuwan ta kin hana yarinyar nan zama da danki. Yanzu kuma kina kokarin neman sheri ki lakamata naji karatun banza fatima tayi ashe tayi kokari tunda tayi har ta karbi kwalin ta. Ke aiko secondry naga kin kasa tsayawa ki karbi kwali shi a hannun ki saboda takwallancin tsiya. Kai haba wanan abin naki da me yai kamane haka a duniya kullun mutum bai maka kirki sai kokarin ganin sherin mutum kike nema ki fada. Keko ba mai fadan maki hakan baisa kin gano ida matsalanki yake ba balle ki gyara kowa gidan nan yasan bakin cikin ki da yarki ya kaini kwance bawai ba a sani bane . Ido na saka maki ingani ko zakiyi nadama da abin kunyar da kuka jawo min a garin nan dakuma wurun yan uwana. Yanzu Alh ni kake fadawa wanan maganan haka yace an fada ke wacece da ba za, a fada maki ba jiran yaran ki suzo garin nan nakeyi muyi zaman karshe dasu akan matsalan ki da yarki. Yanzu Alh akan maganan nan danayi kake fada min wanan magana haka dan waye baida matsala a duniyan saukin abin dai a tare muka haifeta tare kuma muka bata tarbiya dakai. Tana kaiwa nan ta mike tabar falon fuuu ta fice acikin fushi taji zafi da nauyin wanan maganan da yayi mata a gaban kishiyoyin duk da tasan sun sani. Saidai bata bada kafan da wata zata samu fada mata shiba a gidan shiyasa ma yanzun din bata yarda taji kunya ita kadai ba . Zama nayi ina tunanen kalaman hjy gareni na dan murmusa don zuwa yanzu na gama fidda rai ka kaunar hjy a gareni kuma. Wayana na kalla dake gefena namika hannu dauka naga ya kamata in kira inji na daukane naga miscall din yaya har biyu. Kiranshi nayi ya dauka bai bari nayi mai sallama ba koshi yayi yace ina kikaje kibar waya na ringing baki daga ba. Mun tafi asibiti ne wallahi subbahanallahi baki da lafiyane komai nace a,a kawune yau jikin nasa yadan rikice masa amma yanzu da sauki mun dawo gida dashi. Innalallahi ya fada kafin yace mai ke damun shi ne har asibiti nace damuwane kawai nake gani don faduwa yayi sume dazu din Allah dai ya kawo sauki wallahi amma abin ba dadi gaskiya. Yana ina yanzu nace yana gida yanzun ma nafito gaidashi ya danyi shiru can yace Allah ya sauwaka. Ina Sultana tana barci na bashi amsa zan kashe in kira daddy yanzu inji yaya yakeji da jikin nasa nace a gaida min da yara zasuji yace yanzu sunyi barci tun dazun. Muna kashewa ya kira daddy sun gaisa yake tambayan shi yaya jikin nasa yace da sauki suka dan taba hira dashi akan jikin kafin ya kashe wayan shi. Anyi haka da kwana biyu sai ga yaya da yan uwan shi sun shigo gari da dare sun dade a falon mahaifin su kafin su fito zuwa part din mahaifiyar su. Basu tsayaba don dare yayi a lokacin don haka ban ganshi ba a ranan sai washe gari da suka shigo ya fara shiga wurin mu suka gaisa da mamu daya samu a falo. Jin muryan shi yasa na yunkura na fito falon ina mashi sannu da zuwa lokacin mamu ta fita daga part din ta barmu. Ya dago kai ya kalleni yana fadin may yasa wanan kunnuwan naki basa jin magana zahra ya fada yana kallona. Cikin mamakin abinda nayi na dago kai ina kallon shi fuska dauke da mamaki shi nace may kuma nayi yanzu yaya ? Kin san nazo gidan nan jiya baki fito kin ga saukan mu balle har in samu darajan samun tarbo daga wurin ki zahra. Ciki shagwaba nace yaya shine nafito fa yanzu in maka danaji muryan ka ka shigo ya miko min hannu na make kafada na alaman ban zuwa. Yace me kike nufi da hakan nace kaima kasan ba daidai bane ai tunda an muna iyaka a tsakani mu. Kema kinbi zancen kenan yanzu nace tun ranan da kawu ya furta hakan na dauki zancen don har yanzu wace kawu ke jiran saukowan ta bata da niyar sauka daga maganan. Illa ma kiyayya a tsakanin ni da hjy a kullun kara karuwa yakeyi a zuciyar ta don haka dai nake ganin ya kamata mu hakkura da junan mu zaifi mu alheri musanman ma kai yaya da maganan a wurun mahaifiyar ka yake. Zahra you are very stupid ni kike fadawa wanan maganan haka a tsakiyan idona . Ki fada min laifina a cikin zancen da kikeso yanke mi hukunci haka banga laifi ki ba don kinga kamar na daga maki kafa da maganan yasa haka yana fadin haka ya tashi ya mike yabar falon . Ya barni zaune ina binshi da kallo nikuma ban damu da fushin shi ba don yin haka shine mafita a wurui mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:13 - 🀐🀐🀐: Na dauka ya fita daga gidan ne ashe suna part din mahaifin su sundan dade dashi suna ganawa kafin su fito su shiga wurin Amma. Ana nan sun dade wurinta shi da yan uwanshi tana magana kan fushin da habbib keyi na rashin zuwa gida daya dauke kafan fashi don dan matsala da suka samu da mahaifiyar su. Amma tace ashe da kaine dan uwan ka yaya ke nan zakayi kiri kiri sun rabashi da matarsa don kawai wani dalili na su can . Jin haka ya umar ya mike tsaye yana fadin ina sauri ne fa suma yan uwan suka mike daga inda suke. Tare suka fita daga gidan ya Umar da yan uwan shi duk da basu inda zasu tafi bi a lokacin ido kawai suka sawa yayan nasu. Lokacin ina gyaran falon mamu da ya sha gyara sai kamshi yake bayan na gama don kannena sun tafi school lokacin. Part din Amma na koma muna hira don ranan murja tana gida bata fita ba zuwa school bata zama yanzu suna final year din su ke nan. Amma ne da tai shiru tana tunane can ta juyo tana fadin hankalina baya kwanci idan ba naji kiran yaron nan akan maganan komawan ki gidan shi ba. Allah yasa dai wanan karon a shirya don kamar karfin maganan wurin hjy yake ai kawu ya zuba mata idone ko zata sauko daga kudirin ta nayi mai auren da tace ai. Sallaman mamu dake rike da hannun Abdulsalm tana fadin ga baki kunyi fa. Mamakine kwarai ya kamani ganin yaran don yaya bai fada muna cewa tare suke tafe da yaran ba dazun daya shigo ya fita yana fushi dani lokacin. Na mance a gaban mamu da Amma nake na rugume yarana a cikin murnan ganin su suma kankameni sukayi suna murna tare da tambayana cikin harshen turanci may yasa na tsaya nan na barsu su kadai ?. Kowa yayi shiru a falon yana kallin mu ashe kuna da aiki idan jiran komawar uwarku kukeyi gidan ku mamu ta fada da hausa tana juya zata fita. Mekike nufi da wanan maganan da kike yawan yi ne maimuna tace gwaggo gani nayi dai mahaifiyar umar bata da niyar saukowa ga kudirin ta har yanzu ai. Kudirin tana banza da wofi ita ba zaune take a gidan mijin ta ba lafiya iya shegen da takeyi a gidan nan idan ba yaron nan bane wazai daukan matashi haka . Juyawa nayi aurin maria muna gaisawa na fita zancen su ina tambayan ta bayan robon mu. Maria ta hade hannayen ta guri daya tana rokona inyi hakkuri mu koma tare wanan karon. Murmushi nayi mata kawai ina dan kwantar da yaran a jikina ina jin wani yanayi mara dadi yana sauka min a zuciyana lokacin. Ido na lumshe ina ci gaba da tunanen halin da rayuwan aurena ya fada cikin matsala saboda uwar mijin da ban mata komai ba a rayuwana. Ranan dai tare da yarana na wuni a gidan sai dare ya aiko aka dauke su hakan kuma shi ya jawo magana wurin hjy. Cewa tayi yara sunzo na hana suje gurin ta na hana su santa a matsayin kakan su na hana mata shakuwa da jikokin ta su saba da ita tun yanzu. Zance yakai har wurin Amma don kawu yanzu ba a son yawan bata mashi rai sosai haka yasa Amma tayi masu iyaka da tayar mai da hankali. Bayan ta gama magana Amma ta juya wurin mamu tana fadin maimuna da yaran sukazo basuje gurin ta bane jiya ? Gwaggo bansan ko an kaisu ba ko ba akaisu don ni jiyan ina hidima da Alh ban zauna ba. Yanzu kunyi min adalci ke na maimuna kina kokarin rabani da yaran nan Ida ba baki kaddaran daya hada dana da yarki ba da babu ta jnda zasu hadu ko ki taba gani inda aka hada tsiya da arziki a wuri daya. . Kada kiga nai wanan maganan kice ko yaran yarki sun dameni ne a raina a, a idan ma kun rike abinku duk dayane don dama wanda bai gajiya arziki ba ko sashi a baitalmali duniya tsula zai fito daga cikin shi. Baki san zafin uwa ba maimuna haka ma yar ki yasa a kullun kuke kokarin kuga kun rabani da dana mafi soyuwa a gareni. Hjy inda kece ke bayar da arziki ba Allah sai ince na debe rai ga wanan arzkin da kike kira kullun har yau ke kuma banga arzikin da kika tarawa kanki ba a gidan nan. Kai da kun bar wanan magana haka hjy maryam tace yara ko anki ko anso yanzu sun zama na mutum biyu ai a gidan nan irin wanan fada kan yaro ko fili sai Allah ya dau ran guda daga cikin ku a zauna lafiya. Maryam ni kike kokarin fadawa magana a fakaice hjy tace don taki jin azo magana hjy maryam ta dan kauce mata yanzu zata nuna mata bacin ranta a gurin. A, a hjy akan me zan fada maki magana kamar ina jirake dake gani dai nayi abin bai kaiga kallo ba. Hjy amma dai da kike fadin wanan magana kin san na shiga dasu su gaida ke kika barmu a falo zaune. Irun wanan ba jiya kika fara yi mun haka ba idan na shiga part din ki sanan ina son ki sani mamu dai ba shegiya bace da uban ta a duniya kuma yana raye. Duk magana ya tashi ke kenan a cikin zagin kaddaran da ya sameta don kawai mahaifiyar ta tana kasan su . A laila ba mamaki yarinya wuyan ki ya isa yanka a gidan nan ni kike kokarin yiwa kashedi akan uwar ki ko mai a gidan nan. Ai ba tafiya zakice kakar taki tayi ba kice tana wurin yawon dandin da suka shigoyi dama a kasan nan. Allah sarki hjy gara da yau kika fadi manufan ki kowa yaji a gidan nan mamu tace sai dai saukin abin asalin kowa a tafin hannun kowa yake yanzu. Amma dai kin san mun san mahaifin ki su suka fara budewa karuwai gidan clubs a garin nan a fili yana yawo da betil da mata da rana suna shan giya suna rawan yawon siyasan NPN duk da tsufan shi ko kin manta da hakan duk da ban sani ba kunne ya girmi kaka ai. Wani irin kukan kura hjy tayi mamu ta mike tsaye nan fitina ya murtuke sosai a tsakanin su tana fadi tana fadi duk suka rikita gida mamu na fadin na gaji kullun ina daga maki kafa baki daukan girman ki. Aliyu ne ya samu wanan fitinan a gidan ya juya ya fita rai bace in auren yarki yayi dubu da babawo ya mutu a gidan nan . Mamu tace sai me don kin kashe auren danki naki nakima ai baki damu da yamutu ba balle na wani hjy wani girma da kimar da nake baki duk ya kare a gidan nan daga yanzu yadda baki kaunana da jinina haka nima ban kaunar ki har cikin raina. Kawu da yaji hayaniyar yayi yawa ya fito basu daina ba yace wace ta kara tankawa a wurin a bakin auren ta fadan malam bashe a gidan shi hakan yasa kowa taja kafanta ta koma part din ta cikin kunan rai. Nikan har cikin raina banji dadin hakan daya faru tsakanin su ba don nasan abu zai kara rikicewa a tsakanin mu ke nan. Saidai kuma naji dadin amsa mamu sosai don ta rama cin fuskan da hjy ke mata tana ganin bata san nata zancen ba na fada. Ashe yaya baya garin anyi haka da kwana biyu ya dawo tun yana can Aliyu ya buga mai waya yana sheda mai cikin bacin rai. Koda ya dawo bai nuna yasan komai a kan zancen ba sai hjy ce ta fito mai da zancen karin auren shi yace ban shirya aure yanzu na fada maki mama. Zaman Fatima a gidan nan da daddy ya zaunar da ita nake son ta koma don ban fahinci may hakan yake nufi ba don. Kai dakata kaji idan itace autar mata babawo ka gama zama da wanan yarinyar diyar marasa tarbiya diyar wa yanda basu da mutunci. Mikewa yayi ya bar part din ba tare da ya tsaya sauraren ta ba sai da dare ya kira mamu a waya. Yace ina son Fatima zata koma dakinta cikin jikin ta yana girma zamu koma tare wanan karon. A,a umar ya kamata ku hakkura hakana da kai da ita kasan mahaifiyar ka har yanzu tana kan bakanta ga zancen nan zaifi don Allah idan haka yafi zama alheri a gare ku Allah ya tabbatar muna da hakan. Nagode yace ya kashe wayan shi ina zaune ina jin yadda sukayi dashi a wayan . Kaina na dukar lokacin da take aje wayan naji tace kai bawan Allah nan shima yana cikin wani hali wallahi. Wanan al,amari yakai min inda yakai wallahi tun farkon wanan hadin abindana guduwa ke nan don halin hjy sai ita. Al,amarin sai addua wallahi naji ta fara jero addua,a tanayi sai kuma tace ni yaran ma suke ban tausayi kullun idan sun shigo nakan shiga wani hali wallahi. Ni idan ma auren zatayi mai tayi masa kowa ya huta tunda ba,a kan ki zata shigo ta zauna ba kowa da halin sa ake zama dashi ai. Washe gari ina barcina sa goma zuwa shadaya dake min dadi a yanzu naji mamu tana tayar dani wai kawu suna neman ta a falo ga yaranan zaune falo. Nafito ina tunane kan me kuma su kawu suke neman mamu fitinan gidan nan dai baya karewa wallahi. Mamu tana zuwa falon Amma ta samu falon a cike yake kawu balarabe yace ina ita Fatiman take tace ina daki tabashi amsa. Ka barta tukun sai idan an fara magana a kirata zai fi kawu yace a dai kirani kusa yanzu zaifi dole mamu ta fita ta kirani muka dawo tare da ita falon Amma din. Lokacin da na shiga nayi mamakin ganin mutanen da aka tara a falon na samu wuri kusa da Amma na zauna na fara gaida su. Wanda naji kawu balarabe ya kira da liman ai muna addu,a kafin mu fara abinda ya kawo mu ko ? Sai mutumin yayi addua ya kara da fadin duk abinda za,a tatauna ya zama alheri a garemu baki daya suka amsa da amin. Kawu balarabe ya kalli yaya yace jiya ina gida Faruq ya sameni da wani zance akan matar shi wanda ni duk dadewan nan basan da wanan zancen ba gaskiya. Yanzu dai gashi muji daga bakin shi don kowa yaji wanan maganan dayazo min dashi shiyasa na taraku a nan gaba dayan mu don samun mafita ga zancen. Yaya dake kasa gefe shida habbib ya gyara zama ya fara da sallama yace akan zancen matanane Fatima da daddy ya aura min har mukai haihuwa uku da ita gana hudu a cikin ta yanzu. Don muna zaune daddy ya kirani ga waya muna zuwa ya bada umurnin itata koma dakin mahaifiyar ta ni kuma mama ta rikeni da yayana tun wanan lokacin ban kara jin wani magana a kan zancen ba. Yanzu ina son matana ta koma dakin ta don ina son mu tafi tare saboda cikin jikinta da ke girma ba zanso barin ta nan ta haihu bana nan ba. Hjy bata bari yakai zancen ba ta bude baki tace karana ke nan kakai wurin iyayyen ka ko ? Hjy kiyi shiru nan ai yanzu ba karan ki ya kawo ba inhar kina da laifi zancen Alh dai muke son jin manufarshi nayin wanan hukuncin daya yanke ? Kawu ya dago kai yana sallama kafin ya fara fadin lalai nayi hakan ne kan a zauna lafiya don banyi wanan abin da wani manufa a raina ba sai don karin zumuncin dake tsakani na da yan uwana koda bayan bana raye ne. Sai kuma wanan yaron da ya dauko muna yar ahalulkitabi a matsayin mata yazo min da ita na duba gaban sa hakan ba zai haifar mashi da alfanu ba a rayuwan shi nan gaba Liman yace haka Allah yace ayi Alh hakkun kayi gaskiya sai kawu yace ashe ni ban sani ba ita hjy yin hakan har wanan lokacin bai mata dadi ba. Kai balarabe da mustapha ga baba nan zaune da ranshi tsohon yana jingine da sandan shi baiyi magana ba har lokaci kai kawai ya kada masu. Ba zabi da baki na basu ba takarda na watsa da sunayen yarana mata da nake da niyar basu a lokacin diyan ya uwana. Koba haka akayi shi a falin nan ba ya sake tambayan su suka amsa da hakane. Yace daga baya jimmai ta tuma ta kafe bata yarda da auren shi umar ba da yarinyar nan tun kafin in basu takarda saida na kafa sharadin idan jummai tayi korafi akan auren nan a bakin auren ta. Subbahanallahi liman ya furta kawu yace kwarai anan falon na fade shi gaban kowa jin haka jimmai ta yarda da hakan ta amince. Saidai ashe bansan da manufa ta amincewa hakan ba azuciyanta na dauka daga ta fahinci abinda na hango nayi wanan hadin daga baya. Saidai ashe ita a wurin ta ta dauki wanan abin gaba tsakanin ta da maimuna gata nan. Yakai bayan yaron nan ya wuce da mayarshi ashe ta kafa mai sharadin banza kan idan yaje ya sako muna yar mutane da akai min alfarma aka dubi mutuncina akabamu. Ita mai diya mace da aka cuta tana karama sosai a lokacin aka ba danta batayi koraglfin haka ba sai jummai ne zata kasa hakkuri ta rugumi kaddara har yakai yaran nan sun haifi diya uku acan batare da sanin mu ba anan . Kullun na kira saidai suce suna lafiya yana zuwa kasan nan ya koma ba tare da ita ba duk bai fada muna sun samu karuwa a tsakanin su ba . Ashe duk gudun mahaifiyar shi taji wanan yakw boye muna hakan koda suka dawo hakkurin hakan kawai ya bamu a lokacin nayi fada sosai dashi daga baya na fahinci abinda yake nufi da hakan. Sun dawo gida fitinan mahaifiyar shi kan yarinyar nan sai karuwa yakeyi bata bar masa mata ta zauna lafiya ba haka kuma bata bar kishiyan ta sun zauna gidan nan lafiya ba. Har takai ta kwashi yan uwan ta zuwa gidan yaran nan tayi tataki kan ta shirya zata aurowa danta mata da take bukatan shi da ita a duniyan nan. Ba wani ya fada mun ba ya ciro wayan shi yana laluben yace kai balarabe shedane tare tsohuwar mu ta kiramu ta nuna muna video nan da yarinyar nan murja ta dauko na cin mutuncin da sukaje sukayi a gidan wai sunzo duban dakin da zasu saka yarsu. Wanan dalilin yasa na kira yaran nace kowa ya dauki dan shi a zauna lafiya duk da na fada mata kafar yarinyar a gidan umar gashi fitan ta gidan nan nawa har abada ke nan. Naga alaman ta amince da hakan kuma a zuciyar ta tunda zaman yarinyar nan gidan nan ba wani sauyi da suka samu kullun fitinane da uwar yar nan. Har yau ban taba kiran su da sunan maimuna takawo min karan jimmai ba gata zaune amma ita a kullun cikin korafi take anmata dai an mata a gidan nan. Kawun hjy ya nisa a lokacin yace jummai amma baki biyo halin mu ba wallahi tir da Allah waddai da wanan halin naki. Keda kanki zaki hana rayuwan danki zaman lafiya don wani kudirin ki na baza can da kika sa azuciyar ki gareki wai farau kishiya jummai ? Kawu da kubar wanan zancen don yarinyar nan ba zata koma gidan umar ba har abada shine abinda na yanke akan maganan nan mamu tace. Kowa na falon ya kallo ta don jin abinda ta fada tace kwarai kawu hakkurina ya kare a kan hjy tunda kan auren nan yakai har hjy ta kira min da mahaifiyata da yar yawon duniya. Subbahanallahi hjy da girman kike wanan furcin ga yar uwan ki ya kasance hakan gaskiya ne ai ba fade yakamata ki mataba illa shiryuwan Allah gareta. Kawu balarabe yace a ina wanan zancen ya fito haka mara dadin ji kuma ? Liman ne ya katse su da fadin salamu alaikum suka amsa masa yace da farko wanan al,amarin baiyi dadin ji ba ace babban gida irin na Alh mutumin da duk unguwan nan yaro da babba ake ganin mutuncin sa yau ace a halin sa ne ke wanan irin rikicin kamar gidan da babu adini a cikin sa. Alh kaima kana da naka laifin a wani bangare a ina ka taba jin iyayyen sun samu ikon kwatar yarsu a hannun mijin ta ? Wanan sai idan shi mai auren ya bude bakinsa yace bayayin auren ya fasa wanan ba sauran abin yi sai a raba auren. Yanzu duk mu bar wanan zancen tunda ga ma,auratan a zaune gaban mu ya juya ya kalli yaya yace Umar Faruq kazo tafiya da matar kane a yanzu ? Cikin ladabi yaya yace abinda nake so ke nan idan hakan zai samu a yanzu. Amma idan zai tafi da ita sai an bani dama ya karbi nawa bukatan auren yar wurin sabuwa da nake son yayi. Da sauri kawunta yace bukatan auren diyar sabuwa jummai kina da hankali kuwa a rayuwan ki son kan ki har yakaiki ki halaka kan ki da kan ki yaro suna zaman lafiya da matar shi zaki dauko zancen yar sabuwa da basu da tarbiya ki jefa a cikin ahali ki ? Kawun nata yai mata tas a wurin yayan ta yana taya shi dole taja bakin ta tayi shiru don babu hanyar yin magana a wurin gareta kuma. Yace ka dauki matarka ka tafi wanan magana ya kare a wurin nan yanzu don haka idan ka shirya daukan matar ka ka dauketa ku tafi. Mamu tace ta bishi kuma a haka kawu ku tuna fa ba daku zata zauna ba dasu ne hjy kuma ba fasa abin nan zatayi ba ga yarinyar nan tana fadin haka ta fashe da kuka. Jikin kowa a falon sanyi yayi a lokacin ganin mamu na kuka nima na fashe da kukan lokaci guda falin yayi tsit ana sauraren sautin kukan namu. Kawun hjy yace kuyi hakkuri ansan an cuta maku ana makan cutarwa din don wanan bata da alaman fasa halinta tunda ta kulla da sabuwa. Yanzu ai ga yarinyar nan a zaune itace ke zaman aure ba wani ba yana da kyau muji ra,ayin ta idan zata bi mijin ta su tafi a yanzu din. Da sauri yaya ya dago kai kalli kawun hjy da idanuwan shi da suka kada sukai ja a cikin natsuwa yana fadin malam kada kuyi haka yanzu a lokacin nan da suke jin zafi da ciwo a zuciyar su don furcin mahaifiyar dataji kuma. Kawun hjy yace umar ka kwantar da hankalin ka ba zabi bane hakan hakkintane itama za a bata don muji ra,ayinta a kanka yanzu. Ya juyo gareni yace Fatima kiyi hakkuri ki daina kukan nan kiyayya a filin Allah da tozarci haka baida dadi ko kadan . Fatima kindai ji hukuncin da muka yanke a gaban ki yanzu shin zaki bi mijin kine ku tafi koko wani shawara kika yanke a zuciyar ki ? Kaina a duke ban dago ba sai hawaye nake yi ina tunane a zuciyana ra,ayin uwata da take kokarin kwato min yancina a gurin hjy zanbi koko tausayin mijina da yayana da suka koma kamar marayu zan bi yanzu. Jin malam ya kara kiran sunana yana fadin Fatima ke muke saurare muji ra,ayin ki yasa na dago kai a hankali na kalli inda malam din yake a daidai wurin kuma yaya Umar din shima yake zaune a kasa. Karab idanuwa na suka sarke a nasa ni yake kallo da jajayen idon sa da suka kade ko kiftasu bayayi a lokacin bashi kadai ba duk wanda ke falon a lokacin ido ya zuba min don jin me zan fada. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:16 - 🀐🀐🀐: Na sake dukar da kaina a kasa ina dan sheshekan kuka kowa a wurin ya zuba min ido suna saurarena a lokacin. Azuciyana sai faman tunane nake ba zan yarda in bi yaya a wanan lokacin ba don kwatar wa uwata martsnbata a gurin hjy dake ganin don abin hannun danta mamu ta zuga kawo ya cusa ni gareshi a nata tunanen ke nan ita. Kowa yasa tsakanina da mahaifiyata akwai shakuwa da yawa wanda har mutane ke ganin bata kawaici a kaina irin da akewa dan fari don shakuwane sosai da aminci a tsakani na da mahaifiya ta. Don shi kanshi yaya idan muna waya wani lokaci da mamu ya kance min shike nan kun koma aminai dake da mahaifiyar ki don na lura a cikin ki babu wanda take so kamar ki. Nakan ce mai kasan banda Amma mamu bata da wani wanda suka shaku a baya yanzu ko Amma girma ya kamata dole wani shawaran dani zatayi shi. Sannan ina tuna da namiji ba dan goyo bane in watsawa uwata kasa a ido yanzu a gaban jama,a yazo uwarshi ta tursasa shi yai auren da take so da wani ido zan kalli mahaifiya ta daga baya. Kai Allah waddan naka ya lalace kan yar nan duk kabi ka susuce kanka a banza kamar itace autar mata a duniya. Na rasa mai kagani a wurin yarinyar nan ka juye a lokaci haka babawo har suna daukan kansu su wata tsiyace yanzu muryan hjy ce kewa yaya fada a wurin lokacin. Wanan ai da gani sun gama da kaine don bayin kai sake bane wanan abin don anga wurin cin banza an mayar da kai shanuwar tatsa. Kawun hjy yace jummai wanan wani irin kalamai ga danki kike furta wanan magana nan haka a gaban kowa babu dadin ji. Kawu bari na fada mai gaskiya don Allah idan ba an gama dashi ba zai zaunar damu a nan haka kan wanan diyar makaskanta har ana son a fada min magana akanta. Don kawai suna kurin sun rabani dashi zaiyi kokarin ya kunyatani a gaban jama, a haka yasa ai min dariya nan gaba kan bijire min da yayi. Tana aje maganan ta lokacin zuciyana ya gama tafasa da kalaman ta mai daci a garemu tana ganin don abinnhannun shi yasa nake zaune tare dashi ke nan ko me ? Nace malam ba zan bishi ba gara kawai mu rabu kowa ya huta da wanan fitinan ba don kuma shi yaya yai min komai a zamun yasa na yanke wanan hukuncin ba don kawai hjy tasan koda dan ta ko babu zan iya rayuwa a duniya . Amma ko yanzu mahaifiyata tace in bishi a shirye nake da in bishi don ni bai taba kasawa dani ba a zaman mu tare ko yanzu ba nayi mashi haka don gazawan shi bane sai dai kawai don kwanciyan hankalin mu gaba daya har shi. Aikin bamza ke nan inji hjy don kin san ba wani kadari zakiyi ba koda kin koma din gare shi. In banda abin dan yau har me yaron nan ya gani ga wanan kodadan yarinyar haka da zaka nace mata kamar autan mata. Kaiyya jummai dadin me kikaji ga hankan yau dan kin raba auren yaran nan da hannun ki saboda mugun halin ki na baza. Da kina da hankali da tunane dan zaman wurin nan da mukayi yanzu ya isheki darasi a rayuwan ki amma babu komai gaki ga dan naki sun bar maki shi kan mugun nufin ki na banza sai ki aura mai wace kikeso ya zauna da ita mu gani. A a kawu meye laifina a ciki zancen nan yanzu sun gama dashi ne tunda sun samu abunda suke so gare shi yanzu baida sauran amfani a gare su. Gaba daya wurin ya hargitse a lokaci guda masu ganin laifin mamu na fadi na hjy kuma sun fi yawa. Na dago ido na saci kallon yaya Umar dake zaune ya kura min ido makwal din wuyan shi yana zuwa yana dawowa saboda bacin rai bai iya furta komai ba a lokacin. Wani iri naji a raina na rashin amincewan da banyi in bishi hakan yana nufin na watsawa yaya kasa a idone a bainan yan uwan mu yanzu . Banda abinda da zanyi don kimar uwata da martabanta a gurin hjy dake ganin abin hannun danta muke so nake zaune dashi da sauri na dukar da kaina kasa ina sauraren kalami kowa a lokacin. Muryan mamu ne ya katse ma kowa maganan shi a wurin da tace Umar ya dago kai ya kalleta ba tare da ya iya amsa mata a fili ba. Yau kake son tafiya da matar ka ko sai ta shirya zuwa gobe ko jibi ku tafi kowa yayi shiru yana sauraren su a falon. Yaya yace idan ta shirya yau din sai mu tafi ba wani matsala bane tace to gata nan na danka maka ita amana a hannun ka. Kayi hakkuri da komai da ya faru ita din mace ce yar uwata tasan irin kuncin da nake fuskanta ga auren ku yasa ta zabi in bada zabi a kan ku yanzu. Insha Allahu nayi maki alkawarin rike ta amana kamar yadda na rike maki ita a baya maman twices. Take falon gaba daya aka dauki kabbara lokaci guda sai lokacin kawu sani yai magana tunda aka zauna kowa na magana baice uffan ba a gurin. Alhamdullahi anzo gurin da nake son akai kawu ya furta kowa ya mayar da kallon shi gare shi yace da farko dai niba umar Fatima a matsayina na kawun ta kuma mijin uwarta. Wanda hakan yana daga cikin rashin zaman lafiyan auren nan ga baki daya sai gashi yanzu a karo na biyu uwarta ta kara mika maka nauyi da amanar yarta da hannun ta kuma ka dauka. Aikin banza inji hjy tace tana jan tsuki kawu yai murmushi kafin yace ba bako a wurin nan da baisan halin ki ba jimmai don haka na baki zabi daga yau ko ki bar yaran nan su zauna a cikin salama ko rayuka su baci a gidan nan. Gashi nan a gaban ki idan baki zaki masa ya lalace a kan auren yar uwanshi da baki so sai ki masa a gaban kowa muji. Shidai daya nuna ma duniya matarshi tafini gare shi zai fada ya yafeni a matsayin uwa a gare shi yau. Yaya ya dago kai a hankali cikin halin shi na natsuwa yace mama ban ki kiba don Fatima kina nan a matsayin uwa a gareni kamar yadda Allah ya halat min fitowa ta tsatson ki. Amma mama wanan halin mu kike barwa abin fada a gari ace duk kan mu gaba daya babu mai jin dadi a gurin ki daga mu har iyalin mu mama ? Yau yaya kike son wanan bawan Allah yayi da rayuwan shi ne a lokacin da muke tunanen samun natsuwa da inganta a tare dashi lokacun ne kuma ke mahaifiyar mu kike kokarin tarwatsa mashi rayuwan shi dana iyalin shi. Ina mama kin sha fada muna don mu kike hakkuri da daddy da zaman gidan nan a yanzu don mama kike kokarin sai wata tabar nata iyalin ta tafi. Shin mama idan anyiwa Salma wanan hukuncin ko Nafisa zaki ji dadin abin nan ace sarakansu suna muzanta maki diya a gaban ki suna aibanta su haka. Nan rikicin Nafisa daya taso munji bawai bamuji ba mama Fatima ita ta kwato maki inci ga wullakancin da dan iskan yaro nan yazo har gida yai maki da iyayyen shi Fatima ita ta hana a dauki kayan a gidan nan tare da basu amsan maganan banzan da suka zo dashi. Mama may kike so damune wai a rayuwan mu mu bamu ji dadin ki ba hakama iyalin mu basuji dadin ki na kasancewa sarakuwa a garesu ba kaf din su babu wace kike so da zuciya daya a cikin su. Shin gatan da daddy yai muna a yau muke jin dadin shi hakan laifine ke a gurin ki mama. Mama na rokeki ki bamu salama da iyalan mu mu zauna lafiya don Allah yarinyar nan fatima iya biyayya tana maki yau har yakai ta fara baki amsa ga maganar ki. Mama ina kara rokon ki kiba bawan Allah nan salama duk a cikin mu yafimu karfi ya fimu kulawa dake yadda ya dace babu a binda Fatima ta isa tasa shi kota hana shi aka abinda yake maki da sauran yan uwan shi don Allah wanan abin ya wuce hakana ki barsu su zauna lafiya na rokeki mama habbib ya kare fadi da hada hannayen shi gurin daya lokaci guda. Wani irin kuka hjy tasa tana fadin Habbib ni zakaiwa rashin kunya tunda kaine isashe marakunya wanda ya isa. Mama ni ban maki rashin kunya ba gaskiya na fada don ni ba zan dauki hakan ba shima dai hakkuri yake yasa kika samu nasaran kokarin rabashi da matar shi. Zatai magana liman ya tareta da fadin watau hjy shi musulunci yazo da sauki ga wanda ya fahince shi. Diya da kike gani amana ne a garemu iyayye haka ma diyan suma rashin biyayya ga iyayye wani babban gibine garesu a wurin Allah. Abindana fahinta a nan shine yaran ki kaf dama abokan zaman ki duk hakkuri suke da ke kenan. Shin hjy baki tunanen mutuwa yana iya riskan bawan shi a kowani lokaci a cikin ko wani irin hali. Hjy me kika tanadarwa zuwan wanan lokacin yanzu ace mutanen da Allah ya halatta zaman ki dasu duk korafin su dayane a kanki babu dadin ji haka ?. Malam liman baka san komai ba a nan kiran ka akayi kazo kayi sulhu a gidan nan don haka kayi abinda ya kawo ka kawuce. Assha magana ya kare jummai Allah ya shiryeki ku tashi mu tafi banga fanin zaman mu wurin nan ba kawu ku barta dantane idan taga dama yau ki tsine masa dan ki daine. Bana wani ba zaki iya duk abinda kikaga dama gareshi saidai ki sani kamar yadda malam Liman ya fada su diya amana a wurin mu. Mu dai mun sheda danki yayi maki biyayya yadda ake so don ga shedun haka ya samu habbib yace kwarai kawu. Don ni shedane duk wata yana bata sama da dari biyar na bukatan ta wanda ni din nan in nayi wuta da kyat zata iya samun dubu hamsin zuwa kasa dashi a wuruna. Lokacin hjy tace ina wuta ta saka habbib don tonon asirun da yai mata a bainar jama,a tana kokarin tsine mai yana fasin babu abinda zai same ni da yardan Allah mama don nafadi gaskiya Allah shi yace mu fadeta komai dacin ta ai. Ina ga yanzu ya dace a bar wanan zancen tunda akai ga manufa shi umar zai dauki matarshi su tafi shike nan magana ta kare a nan. Ke kuma hjy Allah ya huci zuciyar ki inji malam liman ya katse maganan yana tashi zaune. Kuka Amma ta saka tana fadin Jummai ubangiji ya saka min a kanki ba zan taba yafe maki lalata min zuria da kikayi ba. Ya umar yace kai haba Amma abin da da uwa yaji haushin maganan Amma kuma zuwa ga mahaifiyar shi. Dole in fadi haka umar wanan bata da mutunci ko kadan bata san Annabi ya faku ba a zuciyar ta. Umar tashi kuje kawu balarabe yace yana umurtan umar din sai yaya umar din ya juya wurin hjy yana fadin kiyi hakkuri mama da abinda ya faru ki yafe muna. Yana fadin hakana ya mike yana kallona yana fadin tashi muje kaina na dukar kasa idona yana fitar da hawaye. Ya duka inda sultana take barci a jikina ya dauke ta tashi kibi mijin ki Mamu tace min a hankali haka yasa na dago ido ina kallon ta ina hawaye tace jeki ubangiji Allah ya albarkaci auren ku da Albarka aka amsa da amin muka fice daga shiyan Amma. Kuka nake wiwi a kofa muka samu hjy maryam zaune saman dan dakalin shigowa wurin Amma ta zauna. Ki bar kuka Fatima haka yafi maki zaman gida kai kuma sai ka kara hakkuri da mahaifiyar ku kundai saba da halin hjy. Mun gode yace mata muka wuce ta bimu da kallo ita tasan abinda take tunane a zucuyanta lokacin. Part din mamu na nufa yace ina zakije kuma abu zan dauka na bashi amsa yace ki barshi ko menene har gobe zan dawo in daukar maki dare yayi yanzu banson tukin dare garin nan. Wayata zan dauko na bashi amsa a cikin kuka barshi nace maki haka yasa dole na bar wayan muka fice daga gidan. Tun kan mu isa wurin motar yasa remote ya bude motar bude min gaba yayi na zauna ya dora min sultana a jikina ya zagaya ya shiga motar. Har lokacin kuka nakeyi ban bari ba cikin natsuwa naji muryan shi yana fadin ina son ki Fatima kin sani ba zan iya rabuwa dake yadda mama take nufin inyi ba. Ban zabe ki na bar mama don in bata mata rai ba na zabi zama da kene don hakan shine alheri a garemu baki daya har maman da bata gane ba a yanzu. Don na gane zafi da ciwon rashin ki a tare da mu yanzu don nagane rasa ki a tare dani wani matsala zai haifar muna nan gaba dani da yarana. Ban taba zato ko tsanmanin zaki zabi mahaifiyar ki ki barni ba koda yake kinyi hakan a cikin hikima da basira irin naki kike gani hakan kuma da kikayi baisa naji wani abu game da ke bs don ni namiji ne nafiki tunane da hangen nisa saboda nasan haka kawai zan muna in samo muna kwanciyar hankali a tare damu. Don haka ki share hawayen nan na banza da kike zubarwa kada ki shiga min gida da hawaye tunda ba satoki nayi ba wallahi. Jin abinda ya fada yasa na dago kai na dan kalleshi ba tare da ya juyo inda nake ba yace eh abinda na bada ke nan kika ji. Wai kin manta cewa nidin nan namijine da nake dagaro da neman na kaina kuma ina fatan in gama lafiya da iyayyena . Kin san ina son ki Zahra barazanan mama gare mu na kara min wata mata ma kada ya daga maki hankali ko ki rike haka a ranki. Ni nayi maki alkawarin babu wata mace ko wani mutum insha Allahu da zai iya juyani daga gareki. Zahra nasan kin min abinda ba kowace mace zata iya hakkuri da jure irin abinda nayi maki a baya ta iya matashi a lokaci guda. Na raba ki da iyayyen ki da kowa naki alokacin da kikafi bukatan su a tare da ke ban dubi maraicin ki ba lokacin gangan shedan da zugin mama yana min aiki a kaina. Na gwadaki da dama baki san da hakan ba a lokacin na hanaki hurda da mutane kinyi rayuwa ke kadai a haka kika hakkura da hukuncina har yau . Yanzun kuma a shirye nake da in gwadawa duniya ke din mace ce data cancanci a nuna a cikin mata muddin ina raye a duniyan ba wani wanda ya isa ya sha gaban ki a gurina ke kin sani bawai da baki nake fadi ba. Don me mun kai ga mafita zaki nuna min baki bukatana a tare dake don yanzun kin fahinci ina bukatan zama a tare dake da mallakan wanan jikin naki kike son nuna min din ba kya sona a yanzu ko kuma baki bukatan zama dani. Dago kai nayi ina kallin shi a lokacin don jin abinda yake fada min. Azuciyana kawai nake iya bashi amsa da ina amfanin zama da mutumin da mahaifiyar ka bata son ka tare dashi. Ina amfanin zaman mu a tare mahaifiyata tana cikin bakin ciki da gori a wurin taka mahaifiyar a kullun don nasan ba fasawa hjyn su zatayi ba kan abinda takewa mamu. Don may ba zanyi kuka ba na bar mahaifiyata a cikin kunci da bakin ciki babu ko sallaman daya dace a tsakanin mu. Goran ruwan dake gefe ya miko min tare da fadin karbi ruwan nan ki sha ko zakiji sanyi a zuciyar ki. Saiki wanke wanan fuskan naki da kika bata kada ki shiga gida haka ki dagawa yara hankali don nasan idon su biyu yanzu suna jiran isowan mune kawai. Karban ruwan nayi kamar yadda ya umurceni a daidai lokacin da yake horn a bude masa get ya bude mota yana fadin wanke fuskan ki kafin mu shiga. A cikin lalashi yake magana dani a lokacin kamar karamar yarinya ana lalashin ta. Duk yaga maigadin ya bude get bai shiga gidan da mota ba saida yaji na sauke ajiyan zuciya yaja mota muka karasa ciki. Kamar yadda yace mun samu yaran a falo har yan aikina a zaune falon jin horn din mu maria ta fito da sauri tana muna sannu da zuwa. Tana kokarin karban Sultana dake barci a jikina yace ta tafi zai shigo da ita . Mun shiga suna min sannu da zuwa yaran suka taso da gudu suka rugumay ni haka yasa na rage tsawona daidai su na rugumay su a jiki. Saida yai masu magana su barni in je daki suka sake nina mike amma basu yarda sun barni ba tare dasu mukaje dakin nawa. Nan ma basu barni ba don sun baibaye ni sun hanani sukuni da tambayoyin su a lokacin. Da kyat na samu na mike naje yayi alwala kafin na fito na tayar da sallah na dade zaune ina ta addua a wurin yayin da yaran ke wasa su uku saman gadona sai abin ya kara bani tausayin kan mu dana yaran ya kara kamani a wurin . Sallaman da akayi daga kofanane yasa na dago kai ina kallin kofan inga mai shigowa dakin nawa. Tani ce mai abinci tana tafe dauke da katon tire da kuloli a cikin sa sai da ta aje ra gayar dani take fadin hjy barka da zuwa ya mutanen gida. Ga abunci Alh yace a kawo maki nan dakin ki ta fada nace Tani gida lafiya na gode yaya bayan rabo ? Tace hjy munyi kewar ku sosai wallahi kullun sai tambaya nake yaushe zaku dawo ne ashema wai kina garin nan ni ban sani ba aida nazo na gaida ke. Nace ba komai ai nagode ko yanzu shine yayi sallama da alama wanka yayi a lokacin ganin Tani gurfane a gabana ya juya wurin yaran yana magana dasu Tani tayi saurin mikewa ta fita daga dakin. Ki ci abinci ki watsa ruwa ki kwanta ki huta don idan ba kwanciya wa yan sukaga kinyi ba yau ba zasu barki ki hutaba da cewa yaran dake ta murnan dawowana gidan. Ban jin cin abincin don bakina bai min dandano na bashi amsa amma kuma kinsan ba zaki kwanta haka ba dai da yunwa a ciki. Dan ya mutse fuska nayi ina fadin banjin cin komai yanzu ne shiyasa ya kalleni ya gyada kai yace sai ki tashi ki watsa ruwa don kin san dai ba zasu je gun maria ba yau suna ganin kamar zaki iya barin sune ki koma inda kika fito. Na kalleshi cikin natsuwa nace nifa ina ganin bawai hjy ta yarda da dawowa na gidan nan bane ? Yace nasan da hakan nima sai dai meye matsalan ki ke ina yanzu rikicin a tsakanin nida itane kuma. Amma yaya kasan ba zanso ace sabodani ka samu matsala da mahaifiyar ka ba gaskiya don nima ba zanyi fatan diyan nan suyi muna haka ba watarana. Zahra mama uwatace na fiki sanin halin ta ciki da waje kamar yunwar cikina don haka ki kyalemu kawai muyi abin mu babu ruwan ki ya yanzu a maganan mu. Ki tashi kije kiyi wanka ki samu ki huta hakana ya juya ya fita daga dakin na sauke ajiyan zuciya. Ya dan jima da fita kafin in mike na shiga na watsa ma jikina ruwa na fito na shirya cikin dogon rigan barci gyarawa yara kwanciya nayi kafin in hau gadon tsakiyan su na kwanta ina sauke ajiyan zuciya a hankali. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:16 - 🀐🀐🀐: Washe gari ban fito da wuri ba saida rana ya fito ko ina ya haska sosai har ranan ta dan fara zafi don ban san lokacin da maria ta shigo ta kwashi yaran tafi dasu daga dakin ba. Ko yanzun ma yunwa dana tashi dashi a gigice yasa na fito daga dakin zuwa falo don in samu abin da naci. Wurin dining na nufa kai tsaye ban kula da mutanen a falon ba a lokacin na fara bubude kayan abincin dana samu a jera saman dining din. Fersun kifi ne anyi mai yanka mai kyau sai kamshin kayan yaji ke tashi a cikin sa na kara bude kula na biyu wanda ke dauke da irish soyayyen karamin kulan na bude wanda na zata kwaine sai naga source din kabeji ne da anty da za,a ci da soyayyen dankalin sai kayan tea a gefe guda da ruwan sha dana tea a flask. Zaune nakai ina jawo dankalin na dan zuba kadan tare da zuba source din da zanci dashi ruwa na jawo na daureye hannayena. Ina shirin kai abincin a bakina naji muryan Yaya Aliyu yana fadin uwar gida ina kwana a lokacin . Da sauri na juya inda nake jin muryan nasa sai ganin su nayi su uku a tare lokacin guda dan nauyi da kunya ne ya kamani a wurin haka yasa na taso zuwa gare su don in gaida su. Ki koma kici abincin ki tukun ki gama yaya yace min don nasan dama da yunwa zaki tashi tunda jiya bakici komai ba kika kwanta yau kuma kinkai har wanan lokaci kina barci. Ki daina wasa da cin abunci Fatima yaya habbib yake fadin haka ba tare da ya dago kai ya kalli inda nake tsaye ba. Ban yarda na koma na zauna ba saida na karaso inda suke na gaida su a cikin ladabi babu zancen wai kannen miji a wurina har yaya Aliyu da kan dan jani da wasa wani lokacin. Bayan su amsa min ne tare da tambayana yaya gida na amsa da lafiya na daga zan tashi naji yaya habbib na fadin amm, fatima ina son ki kara da hakkuri a zuciyar ki. Kada ki dauki wanan abin da daya faru tsakanin ku da mama wani abinda zaki rike a zuciyar ki . Mama dai uwa take a wajen ki kuma mahaifiya ga mijin ki don haka nake son kada ki dauki wanan kiyayyan da take nuna maki a matsayin wani abu cikin zuciyar ki har ki riketa a rai nan gaba. Da sauri nace yaya ban fatan hakan ya darsu a zuciyana nima don mama uwa take gareni na sani don yau mama tace bata sona bawai hakan yana nufin in fasa mata biyayya a rauwana a matsayin ta na uwa a gareni ba. Zan dai gujewa duk wani abinda zai iya haddasa muna fitina a tsakanin mu nan gaba insha Allahu. Don Allah ku kara hakkuri da taimakon ku zamu samu mu rabu lafiya da iyayyen mu. Don jiya bayan tafiyan ku abin yaso ya baci tsakanin mama da daddy mun Allah ne ya gyara magabatan su suna gurin. Allah ya tsare nace ina kokarin mikewa don barin wurin zuwa wurin abincina dana rigana zuba kada yai sanyi. Zam nayi na basu baya don akwai tazara a tsakanin mu sosai da inda suke zaune din don haka ba lalaine inji abinda suke tataunawa ba akai. Har na gama na shige daki suna wurin a nan na barsu na koma daki ina tunanen maganan da mukayi da yaya habbib din don nasan ba karya ya fada sai mun basu taimako wurin shanye duk wani abin da hjynsu take nuna muna zasu zauna lafiya da ita. Har wani barcin ya kara daukana ban sani ba sai da sultana ta tayar dani daga barcin shigowan ta dakin nawa tana kuka na tashi. Falo muka koma muka zauna da yaran suna kallo nima dan kallon catoon din nakeyi jefi jefi a lokacin sai dai raina yana tunanen ko yaya ya fitane a lokacin. Sallaman Amma ne tare da murja ya dauki hankalin mu zuwa falon tana shigowa da sallama tare da fadin shi daga anbashi matar shi sai kawai ya dauke muna ita ya gudu. Dariya na danyi ina ce mata ya sani ko ki kawo shawaran da bai gamsheshi ba a wurin . Aini jiya yar nan kun barni da mamaki danaji ance ko sashen uwarki bai bari kun shiga ba ya wuce dake. Nace uhumm Amma ni yaya na iya da rigiman yaya ko wayana fa a can na barshi ban dauko ba yace da safe zai sa a kawo min su. Ai ni hakan da yayi naji dadi sosai a ruwa don kafin ai wani magana ace a kiraku har kun tada mota kun bar gidan daba haka ba jiya Allah kadai zai hana auren dayan ku tsakanin keda jummai bai mutu ba sai Allah ya gyara kawai hakan bai faru ba. Da sauri nace subbahanallahi har abin yakai ga haka Amma ta girgiza kai tare da fadin ban taba tunanen akwai mace shu,uma irin jummai ba don dai karshe zage malam Liman da kawun nata tayi suka tashi da kunyar su nina hana yaro nan ya saketa a daren jiya. Allah ya sauwaka mata a gaban kowa take aiban ta maimuna da munanan kalamai na ba gaira ba dalilin ban san a ina ta samu wanan banzan labarin ba haka ? Amma wani gori yana zama alheri ga bawa muddin dai baka rama mai zafi ba irin wanda akaima sai Allah yai ma sakaya da abinda baka zata ba a rayuwan ka. Haka tace tare da fadin ina roko Allah ya baiyana muna uwar yarinyar nan kowa ya huta duk nice naja mata wanan gori da na barta a lokacin tabi uwar ta da hakan yafi sauki gaba daya a gare mu. Amma bar fadin hakan rabon mu nida su fauziya ne ya tsayar da ita kasan nan har aka samay mu insha Allahu indai tana raye Allah zai baiyana muna ita bada dadewan nan ba Amma. Yanzu ina mijin naki yake ta tambaya tana kallon kofan dakin shi da idanu. Nace sun fita tare da yan uwan shi ina barci ban san fitar su ba jiya yaron nan habbibu yaci min goro a rayuwana don tsab ya fadawa uwar gaskiya duk ko da dacin ta. Hjy bata da masu fada mata gaskiya a rayuwan ta duk yan uwanta kara izata sukeyi ba masu lurar da ita hanyan daidai murja ta fada. An gama abinci aka kawo muna nan munci mun sha muna hira akai sallah muka tashi zuwa sallah. Bamu dade da fitowa daga sallah ba yaya ya dawo gidan yana shigowa sukai arba da kakan tashi yace may kikazo yi min gida kuma jiya jiya da dawowa da matana ko kin dawo ku kara dauke min itane kuma ? Ja,iri tunda na gama aikina ko dole kace min hakan daba don dabaran dana koya ma ba aida yanzu matar taka tana dakin uwarta zaune su basu damu da zaman nata ba hakana. Ya kai zaune a saman kujera daya da Amma yana fadin Amma ni abin yana daure mun kai sosai wallahi na rasa gano inda mama ta dosa haka ? Aure take son ka kara sadauki idan ba auren nan ka karaba ba zaku taba zaman lafiya a yanzu da mahaifiyar ka ba. Da sauri na dago kaina na dan saci kallin shi don jin amsan da zai bata a lokacin . Karab idanuwan mu suka hade da juna ya dan sakar min malalacin murmushin shi daba kowa ke iya gane hakan ba sai wanda ya sanshi sosai zai gane hakan . Amma na fada mata matana biyu sun isheni a rayuwana ba zan iya kara aure a yanzu ba bandai sanar ma nan gaba don mai rai baya debe tsamani a rayuwa tunda ni din namijine. Kwarai kuwa Amma ta bashi amsa tare da fadin ita waccan matar taka kafiran dauka take baku da aure da ita yanzu ai. Haka take gani shima ya fada yana mikewa tare da fadin Amma zan dan shiga in watsa ruwa tsohuwar tace har yanzu dai wanan dabi,an yana nan maka sadauki na wanka akai akai. Yana shiga na kalli Amma ina fadin Amma naga kamar kema yanzu kina bashi shawaran ya kara wanan auren ne ko . Abinda uwarshi ke so ke nan A ruwa indai zata barshi ya zauna lafiya aisai yayi nagani. Nace shi zai zauna lafiya kan ammani nasan ina kofan fita ga niyar hajiya yadda take kuma sakawa a ranta. Zata iya amma ni hanka yanzu baya damuna tunda har ba ta iya rabaku a yanzu ba hakan ya nuna ko nan gaba ba zata iya ba. Amma idan ya fito ina son ki mashi zancen zuwa na bauchi kwanan nan don Allah murmushi tayi kafin tace kin masa magana yace ba zaki bane. Amma ko nayi mai ban samun wani amsa mai dadi a gurin shi kullun sai yawo yake min da hankali Amma hankalina yana gun manjo karfin hali kawai nake ban nuna damuwa a kan hakan. Ki gwada mai magana kafin ku tafi idan zai bari saiki tafi don dai ba zaki shigo kasan nan ace harkin koma baki lekasu kinga lafiyan su ba, suma suga yaran nan don basu sansu ba. Bai bar Amma ta koma gida ba saida dare ya mayar dasu gida ita da murja kafin ya dawo nayi wanka na kwanta don ya tsaya gaisawa da mutanen gidan duk da dai ya samu hjyn su a cikin fushi sosai har lokacin dashi da yan uwan shi. Dakin ya shigo ya same mu a kwance tare da yaran suna wasa ya samu bakin gado ya zauna yana fadin yau ma wa yan nan a nan zasu kwana ke nan ko ? Nace ai in sun kwana nan ba laifin sukayi ba tunda suna kewanane yace amma nima kin sa ina da bukatan ki a kusa dani ko ? Ba tare dana dago kai ba na kalleshi nace gara ka saba da hakan tun yanzu ai zaifi ma sauki nan gaba. Wani sabone banyi ba da rashin ki a kusa dani yanzu bayan wata biyun da kikayi ba tare dani ba nace nan gaba idan kayi aure zaka iya yin fiye da hakan ma ba bakon abu bane ai ga maza yin hakan. Yace may kike nufi da hakan nace kaida zaka kara auren yar uwanka ina zamu samu kulawan ka kuma lokacin ? Naki tunanen ke nan kan hakan ban taba tunanen zaki iya wanan tunanen haka ba a kaina. Kai ba namiji bane daba zan tuna haka gareka ba yaya kaifa da bakin ka fadin hakan dazu gaban Amma. Yace shine kika rike a rai har yanzu ai gaskiya na fada ni din namijine kin sani niko na sani don da wanan kalamin kayi winning din anty merry ai. Yace oh realy nace kwarai kuwa don ina da labarin komai ai ashe kinyi nisa ne ban sani ba ya fada yana mikewa tsaye tare da dan ja min kafana sai sultana tace mai daddy tana dariya. Ya kada kai ya wuce yana mata bye bye da hannu tana mayar mai da martani sauran hankalin su yana wurin wayana da suke game dashi. Tsab na shirya bayan yaran sunyi barci na same shi a daki zaune yake saman kujera ya tasa laptop din shi a gaban shi yana aiki dashi nayi sallama daga kofa ina dauke da flask din ruwan zafin dana dauko mashi. Don wanan kullun ne sai ya sha ruwan zafi kafin ya kwanta barci har ina tunanen lokacin da ban tare dasu ko yaya yakeyi da wanan halin nasa na baude gashi har yanzu bai sakewa maria fuska ko kadan. Ranan ba zan iya bayanin gamuwan mu da yaya ba don an dade ba hadu ba mun nunawa junan mu kulawa da kewan juna a tare damu. Ban mashi maganan tafiya ta bauchi ba sai washe gari bayan mun karya ne nake tambayan shi yaushe ne zan tafi inga mutanen gidan mu. Bai ban amsa ba haka ya gama abinda yake har abokin shi Nasir yazo suka fita sai lokacin na samu sukunin kiran mamu a wayata data kwana tana caji lake. Bayan mun gaisa ne take tabayana ba dai wani matsala ko nace ba komai mamu aikin san halin shi ko abu yana damun sa baya fada. Sai dai nasan akwai damuwa sosai a tare dashi don jiya ya dawo naga damuwa a tare dashi sosai. Sa,an mu daya sayadi yana sonki tsakanin shi da Allah har zuciyar shi da kuma yaran nan da kika haifar mashi karin abin ke nan. Mamu idan ma bai ra,ayina ni hakan bai dame ni ba wallahi tunda baka ba namiji amana ga baki daya karshe ke mace ce zaki kwana a ciki. Wanan magana ya fita a bakin ki daga yau kiso mijin ki yadda yake kaunar ki shima hakan zai jawo yarda da amincewa a tsakanin ku. Nan har take ban labarin irin cin mutunci da gorin da hjy tayi mata a gaban bainan jama akan wai don kawai kwadayin arziki aka likewa danta da mahaifin shi. Mamu ina fada maki sai hjy tayi data sanin fadin kalaman ta gareki wata rana in Allah ya yarda. Mun dade muna waya take kara tambayana matar bata kirani ba nace bata kiraba har lokacin . Bayan yaya ya dawone yake fada min akwai aikin da zaiyi a kasan nan wanda hakan zai daukeshi lokaci mai tsawo a kasan nan. Shi kuma ba zaiso ace na haihu a nan ba dole in koma nida yara don yana son zasu fara karatu da mun koma din. Ba damuwa na bashi amsa zan koma don ci gaban yarana nima sai in samu inci gaba da karatuna lokaci. Yace shima yayi min tunanen hakan sai dai bai sani ba ko banda ra,ayin yin hakan yasa ya kyaleni don baiji na masa magana ba. Bayan kamar kwa biyar da dawowana ina kitchen tare damasu aiki don nakan bushi iska in shiga gurin su muyi aiki a tare duk da yaya baison hakan yace meye amfanin mai abuncin daya dauko min wace keda takarda a kan girki. Mace bata cika mace saita hada da aikin gidan ta da kanta amsan da nake bashi ke nan idan yana fada sai yayi shiru. Mummy your phone is ringing Abdul yake fada min yana miko min wayan a lokacin na karba da sauri saidai bakuwar lambace aka kirani dashi a lokacin na wani kasan. Na dauka ina sallama yare naji anayi kafin a amsa min da sallama kuma ana fadin nice Fatima bayan mun gaisa nace eh a cikin harshen turanci ake magana. Nace nice waye a layin zaki magana da mahaifiyar muce aka bani amsa nace ok wani murya naji ana sallama dashi na amsa. Da hausa take fadin an ban layin kine don akwai tambayoyin da nake son zan maki nace Allah yasa na sani na bata amsa. Hausan ya hade da harshen su ba fita yake sosai ba a lokacin saidai ina gane mai take fada da nawa hausan da nima ake fadin wai hausana ya canza yanzu. Menene sunan mahaifiyar ki ta tambayeni kai tsaye na bata amsa da maimuna mahaufin ta fa nace Adamu. Yana da yar uwa mace ta tambayeni nace eh muna ce mata Amma kakarmu ke nan wace ta rike mahaifiyata bayan wucewar mahaifiyar ta don na fara fahintar inda tambayan ya dosa a lokacin. Her realy name please ta fada a cikin harshen turaci nace mata Amamatan sai naji tayi kabbara har sau uku ta kashe wayan idan ba kunnena ya rudeni ba zan iya cewa harda guda irin na larabawa naji kafin kashe wayan. Zaku gama ku kawo kan ku na fada ina aje waya don ba zan yarda mamu ta bisu ba sai dai su su kawo kansu gare ta badan komai nake son haka ba don hjyn su yaya kawai nakeson haka ya kasance din. Ranan haka suka wuni kirana suna min tambayoyi muryoyi daban daban ina basu amsa dake sasu nishadi da alama zancen yana masu dadin ji don kowa nason ya tabbatar da hakan a cikin su. Nayi masu kwatancen komai da yadda zasu iya kawo kansu garemu idan sunzo garin kano din har address din gidan duk na basu. Washe gari na shirya naje gida da dakin hjyn su yaya na fara saidai ban sameta gida ba ta fita a lokacin na fito na shiga na gaida hjy maryam dake son jana da hiran abinda ya faru ranan. Ban yarda na bata wani amsa ba saidai na bata amsa mai kama da sako nace shi mutum ai ba a debe rai gare shi idan ba ya mutu ba don wata rana wanda kake gani banza shine wani abu gare ka. Na barta na fito zuwa wurin Amma mun dade muna hira kafin in shiga wurin mamu don kawu bai gida a lokacin ranan ya fita kasuwa. Mun dan dade muna hira kafin ince mamu gobe zaki kwashe kujerun nan a saka maki sabbi da duk wani abinda baida amfani a part din nan don zakiyi baki cikin kwanan nan ba zanso suzo su samu wurinki a haka ba. Sayadi da gaskiya zasu zo na kwashe duk yadda mukayi dasu na fada mata addua naji tanayi a lokacin kafin in mike ina duban abinda ya dace ace an kawar a lokacin. Na fita tare da murja zuwa wani shagon dake decoration din daki mukayi cinikin wasu set har da gado na gani mai kyau na hada dashi da labulaye masu kyau mukai jinga na biya su yaran shangon suka biyomu da kayan a take har gidan. Lokacin marance yayi saidai hakan bai hanasu aikin su ba kafun dan wani lokaci har sun hada komai don nan na barsu suna aikin don kiran me nake a gida har wanan lokaci da yaya ke min a waya. Washe gari muna barcin safe sai ga kiran hjyn su ya tayar damu daga barci inda na fahinci zancen take mai lokacin da naji yace kaya kuma mama wallahi ban san zancen da kike min ba yana kallona. Tashi nayi na shiga ban daki a lokacin ban fito ba sai da nayi wanka na tsane jikina na fito ina goge ruwan a kaina yana zaune a bakin gado naji yace min. Wani gyara kikaje gida jiya kika sa akawai maman twins a part din ta ne ? Nace ina kallin shi cikin rashin tsoro ko darr din shi gyaran part din kawai nasa ayi mata don zatayi baki kwana nan . Ba zan so azo a samu maxaunin ta a haka ba yasa nayi wanan shawaran na gyara mata part din don yanzu kawu baida karfin hakan garesu ita kuma kasa ba aiki takeyi ba ai. Ya danyi dan shi kafin yace mai yasa baki fada min ba kafin ki aiwatar da hakan don gashi yanzu kin ja min magana wurin mama aida kin fada min sai in saka ai masu gyaran yadda ya dace ga baki dayan su. Kayi hakkuri banyi tunanen yin hakan ba don naga hakan kamar ba komai bane shiyasa. Baiyi magana ba illa idon daya tsura min na dan lokaci kafin ya mike ya shiga bandaki hakan ya bani daman fita daga dakin nashi na kuma nawa part din. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:16 - 🀐🀐🀐: Na koma dakina cike da mamakin hjy a raina ina fadin watau ita dai nata rayuwan ke nan bata son taga dayan su ya karu ta ko ina a gidan sai ita kadai. Har nawa na kashewa mamu wanda ya tsone mata ido haka ta kira danta da wanan safiya haka . Duk daz baiyi magana ba na fahinci baiji dadin hakan danayi ba sai dai kawai ya kyale nine don yawan magana da bai son yi amma ranshi ya baci da hakan. Saida na gama abinda nakeyi na fito falo yana zaune ya saka faran suit a jikin shi farare kal dasu kayan sun makur karban jikin shi sosai. Yana zaune ya harde kafa a cikin dan uwa yana amfani da wayan shi ta hannu wanda hakan ya dauke mai hankalin shi a lokacin. Har na karaso kusa sao lokacin ya dago kai ya kalleni har na karaso inda yake zaune na zauna a hannun kujera da yake zaune akai jikina yana dan gugan jikin shi a lokacin. Bayan na zauna nace mai barka da hutawa ya amsa min ciki ciki na dan yi shiru kafin ince nazo in baka hakkuri akan kuskuren danayi na yiwa mahaifiyata abu batare dana sanar dakai bane yaya. Bai tanka min ba a lokacin nima banyi magana ba har tsawon wani lokaci muna zaune a hakana kafin yace. Ba ina nufin idan zakiwa mahaifiyar ki alheri sai kin fada min ba ko yaushe amma ina son ki sani irin wanan bake mace ya kamata kiyi wanan ba. Don kin san ina nan kuma in kince ga bukatan ki dole zanyi masu gaba dayan su a lokaci guda. Amma ke kinyi bugun gaban kanki kin aiwatar da kudirin ki wanda yin hakan yaja min magana gun tawa mahaifiyar don tasan ba aiki kikeyi wanda kudi suke shigo maki ba abinda ta fada ke nan wanda hakan gaskiyane kuma. Jin shi nakeyi a fili banyi magana ba har lokacin amma kuma ina fadi a raina shike nan dai hjy ta mayar damu fakirai da basuda komai a duniya sai an bamu ko sai anyi muna. A daidai lokacin da yace kinsan dan abu kiris take nema a gareki wanda zata samu mafakan da zata sokeki dashi ga kowa. Nisawa nayi nace kayi hakkuri yaya na fahinta da maganan ka hakan kuma wani damane a gareni yanzu tunda dai mu bamu gaji arzikin da zan tsinanawa kaina ko uwata wani abuba a duniya. Don haka ina rokon ka ka bani dama in fara aiki da kowa zai san inada madogara a yanzu wanda zan iya rike kaina da yan uwana dashi. Dago kai yayi ya kalleni tare da fadin mafalkin ki ke nan kuma a yanzu Zarah aikifa kikace in baki dama kiyi ? Nace ba bako abu bane nagani a wurin ka yaya don matarka tana aiki ai Ok nufin ki kenan don merry na aiki sai in barki kema kiyi aiki dom kina ganin kina da takardu yanzu. Ba nufina ke nan saidai hakan kuma ya shafi magana mu a yanzu don tabbas nasan sai inada madogara zanyi abinda raina ke so don a zauna lafiya da kowa. Don ka barni na fara aikina hakan ba zaisa a zargeka ko aga kasawan ka ba tunda kowa yasan merry ma ma,aikaciyace ai ita. Har na gama magana ta na gaji da zama na mike zuwa dakin su maria bai kara kulani ba nima ban tankashi ba. Don na fahince shi yanzu zamu kwashi rigima nan gaba idan nace aiki zan dinga fita zuwa yi. Wanda maganan shi ta yau yasa naji a dole zan samu abinyi nima ta inda kudi zasu dinga shigo min a hannu na lokaci lokaci. Gaskiya ya fada tabbas mace sai tana da madogara take cika mace duk da nasan bai rageni ta ko ina ba da hakan yana bani idan ina da bukata sai dai kuma meye amfanin bani kudin da yakeyi tunda banda yancin yin abinda naga saboda mahaifiyar shi kuma. Kwana biyu haka mukayi shi sama sama dashi ranan da dare ina zaune bayan ya dawo ya shiga dakin shi ya fito ya dawo ya samemu falon har lokacin. Yara suna zaune suna game yace daga inda yake tsaye zaki shiya kije bauchi cikin satin nan don karshen sati mai zuwa nake sa ran tafiyan mu. Allah ya kaimu nace ba tare da nayi wani nuna doki hakan a gaban shi ba sai dai a kasan zuciyana nayi murna da jin hakan. Shima halan na bashi mamaki ne ya tsaya yana kallo na don rashin nuna farin cikina a fili da banyi ba a lokaci. Ya mayar da hankalin shi wurin abinda yaran keyi a lokacin sai lokacin nace ranan me kenan zamu tafi ? Don in sani in fara shiryawa na dauka ai kin fasa zuwa ne a yanzu ya bani amsa da hakan. Nace ba zan bar kasan nan ba ai ban tafi naga iyayyena da yan uwana ba dama don shekara biyar da wani abu ba wasa bane duk da banda mahaifi ko uwa a can amma ai ina da kakan da take kamar uwa a gareni can din. Kafan shi yaja ya bar falon zuwa wajen gidan a lokacin na mike zuwa daki nayi waya da mamu ina sheda mata yadda mukayi dashi. Tace ai sai ki fara shiri kada sai ranan tafiyan yazo ya sanar dake nace nasan halin sa ai mamu zai iya min hakan don yaga iyakata. Kamar ko na sani washe gari da dare yake ce min da safene tafiyan mu don haka in kwana da shiri nace amma da yaran zan tafi duka ko? Da sauri yace banda su Abdul su zasu zauna a nan tare da maria saidai zaki iya tafiya da sultana ita kadai. Amma yaya idan kaimin haka sai nake ganin ka raina da iyayyena tunda suma zasi so suga abindana haifa ai. Bayi magana ba yaja bargo ya rufa don baison dogon magana yasa ya kyaleni saidai har cikin ranshi hakan yake nufi ashe. Washe gari kuwa na bashi mamaki bayan shirin da nayi ne naga magar gaskiya yake nufin yayi na kira kawu a karo na farko nakai karan shi wurin shi. Kawu yayi fada sosai kan wanan magana yace da yaran zan tafi inda murja da fauziya zasuyi min rakiya can. Ban san yaya sukayi da kawu ba ya shigo yana fada wai don me zan kai karan shi wurin daddy so nake in hada shi dashine ko mai ? Sai dai ki sani a maimakon kwana biyar danayi niyar kiyi acan yanzu uku kawai a can naso yin magana kuma dai na shere shi ban tankashi ba muka dauki hanyar bauchi yana tsaye sai da yaga tashin mu ya tafi inda zashi. Mun isa lafiya na gidan bai bace min ba yadda nayi tsamani don yanzu akwai ci gaba a ko ina saidai kuma muna shiga unguwar gidan su Atika kawai na sheda don namu gidan an canza mai fasalin ginan ya koma na zamani ta gaban gidan. Sai da muka tambaya ashe yaya hashim ne ma a zaune ban gane ba a wurin da muke tambayan yana yar tireda a bakin kofan gidan anyi mai dan shago manne da gidan ya nuna muna hanyar shiga gidan inda zamu bi. Can yace wai dai ko fatima ne haka ban sheda ki ba nace nice yaya nima da farko ban shedaka ba ai naga ka zama wani uztazu a yanzu. Yo Fatima za a girma kuma aci kasa ai hakan baiyi ba rayuwa haka muka shigo gidan muna yar hira dashi har muka kai tsakiyan gidan da komai ya canza min yanzu na fasalin ginan gida. Yace ku fito yau ga A ruwan manjo a gidan naku suna falo suna kallo sai gasu a lokaci daya suna fitowa daga dakunan su da yanzu aka rarabashi basu hade. Wanan karon sosai na samu taron arziki ga kowa sai raba idanuwa nake inga kakata dana dade ban ganta ba a rayuwana. Wani part dake daban naga yaya ya nufa da kayana yana kwalawa manjo kira hakan yasa hankalina ya dan kwanta don har gabana ya fara faduwa da farko. Dakin muka nufa ga badayan mu ana ta shigo muna da kayan mu a ciki murna ba zan iya fada ba duk da akwai canji sosai a gidan dana gani sai dai bai hana inga manjo ta sauya min ba kamar yadda naga sauyawan Amma lokacin da muka zo. Bamuyi wani dadewa da zama ba sai ga baffana ya shigo da murnan shi yana muna sannu da zuwa a cikin fara, a da haba haba duk da dama dai banda matsala dashini. Bayan mun gama gaisawa ne manjo take tambayan ina mijin naki ba tare kuka zo ba dan albarka muna ta ganin sakon alheru sa lokaci lokaci. Dama duniya haka ta gada sai Allah ya turo wani a rayuwan ka da baka sani ba ya taimaka ma ta wani dalilin ka. A nan na fahinci dai duk yadda akayi yaya yana taimakawa iyayyena bai barsu a yadda ko yaushe nake a cikin damuwa da halin wahalan da muke ciki ba. Bayan munci mun shane nake tambayan Atika da iyayyen ta manjo take fadin umman Atika dai tana nan lafiya sai dai mahaifintane ya rigamu gidan gaskiya a bara . Salati nayi tare da mashi addua da fatan dacewa da rahaman ubangiji naji mutuwan bawan Allah nan har kasan raina don ban samu saka mai da alherun da yayi min a baya har Allah ya dauki ranshi. Kamar tsohuwar tasan me nake tunane tace min mijin ki ya tallafa masu sosai lokacin da yake kan jiyar saidai Allah baiyi akwai shi da sauran shan ruwa gaba ba don har yaji sauki ashe na tafiyane sauki. Wani dadi da sanyi naji har cikin raina nan take fada min ai har gaisuwa yazo yayi wanan zuwan naku da kukazo yace ba zaki zo ba sai an gama muna gyaran gidan nan daya saka ayiwa baffan ki. Ga shago shi daya fadada masa yanzu yaran nan su hashimu suma yanzu suna da sana, a har aure sukayi . A hankali na runtse idanuwana ina jin wani iri a raina da tunanen shi yaya wai wani irin bahagon mutum ne ? Daidai da rana daya bai taba yi mun hiran wani daga cikin yan uwan nawa ba ko ya fada min irin alherun da yake masu din. Atika fa nace bayan na sauke ajiyan zuciya tace tana gidan mijin ta zaune sai dai auren ne ita batayi dace ba ashe yaron baida kirki sai bayan aure aka gane hakan . Hakan take zaune tana hakkuri dashi tunda ga zuria an tara kuma yanzu tana cikin min bayani ne mukaji sallaman Umma ta shigo tana fadin maraba da bakin turai. Kullun muna ta saka ido mu gane ku don an fada muna kun shigo har da iyalin ki ta shigo dakin da sallaman ta. Manjo tace yar halas yanzu haka maganan ki mukeyi nan ashe kina tafe ? Nace umma kika taso yanzu nake shirin zuwa in gaida ke tashi nayi na rungumay umma sai kuma na fashe da kuka don ganin yadda umma yanzu ta ya mutse kamar ba umma da take yar gayu a daba da mijin ta yake raye. Ba kuka ya kamata kuyi mashi ai yanzu addua ya kamata mu bishi dashi Fatima Allah ya rasu yana mararin ganin ki Allah bai nufi ganawan ku ba dashi. Na kara jin zafi a raina saida na danyi kuka mai isata suna ban hakkuri kafin ince cikin muryan kuka Umma Atika fa. Tace Atika na nan lafiya Fatima haihuwan ta biyu yanzu don bata dade da haihuwan na biyun ba ma. Naji dadin jin hakan a gaban ta don ban yarda na nuna mata manjo ta fada min komai a game da ita. Ummane da taga ina murna tace kayya Fatima mijin naku ai ba yaron kirki bane yar uwar ki tana hakkuri da auren zamanin nan. Gashi ba wani ilimi mai zurfi tayi ba da za,a sama ta aiki dashi yanzu ma kasan nan ko masu ilimin suna zaune zube babu aikin yi. Haka dai muke hakkuri abindana dan samu nake bata tana ci kardai auren ya mutu ta zauna dakin ta. Nuna damuwa nayi a baiyane don na fahinci inda matsalan ya fara a wurin rashin abinci ne tunane nayi ina yayan ta bashir yake ne ? Na dago kai a hankali nace yaya bashir fa umma tace yana Abuja kin san ya auri wata yar can ne ba yadda ban hanashi ba ya dawo gida yayi auren yarin nan ya kiya yanzu gashi bamu jin duriyan shi sakoma sai yaga dama ya tuna damu. A raina nace wani matsala ke nan kuma sabo da iyayyen mu suke fuskanta mutanen da suna da gaskiya da suke matsawa diyan su auren a gida ashe. Mun dan jima muna hira tana koro min matsalolin da suka fuskanta a bayana wanda na tausayawa hakan sosai. Don ban manta irin alherin da wa yan nan mutanen sukai min ba lokacin da nake bukatan taimako a duniya sun daukeni tankar yar su ta jini a cikin su. Da taimakon su na fara zama mutum a duniya har na fara mayar da hankali ga karatuna both boko da arabiyan dana samu a yanzu. Ta yaya zan manta da wa yan nan mutane a rayuwana kuwa sai dai abinda banda shi don sune yanzu abin taimakawa a gare ni don yaya ya tsare min komai daga bangaren yan uwana da nake tunane a baya gaskiya yanzu basu cikin matsala sosai yadda na zata zanzo in same kamar yadda na barsu a baya. Saida nayi sallah na shiga gaida su mama a part din su har yanzu na hango kiyayyana a idanun mama uwar gidan baffana sai dai tana kokarin dane hakan a fili bata nunawa duk ta hakan sai data baiyana din. Don cewa tayi min wasu mata sun iya shige shige a duniya sai kaga suna samun sa,a wurin malamai kamar kamun yuka. Da farko ban san inda zancen nata ya dosa ba akaci gaba da hira ana dan dararaku a dakin ta kara fadin ai ita maimuna yanzu sune kano. Wace ta kama miji har danshi a hannun ta mezai dame ku a rayuwa dama ance kano haka suke da malamai kamar yankar yuka ga aiki sai dai idan baka da kudi a hannun ka. Shiru dakin yayi lokaci guda kamar babu kowa a cikin sa sai yartane tace mama wanan magana fa kuma babu dadin ji. Tace gaskiya na fada safiya yanzu nawane ban kashewa a garin nan ku samu ko auren farko kuyi hakan bai yuyu ba. Baga yar uwanku ba da uwarta tai mata tsaye kamar yadda itama ta tsayawa kanta rayuwan ta yanzu ya koma abin kwatance a cikin ku. Wa yaki yau ace nasa ne a hakan yake jin dadi yadda fatima keji a yanzu ki duba wa yan nan yaran nata kosu kadai abin alfahari ne ga bawa ai. Mama Lami ke nan dani dasu duk daya muke a gare ki kin san kuma ance duk wanda ya dogara ga Allah baya tabewa a duniyan nan. Uwata dani tun farko ga Allah muka mika al,amarin mu abinda kike tunane ni a sani na mamu bata taba bani wani abu a duniyan nan da sunan mallakan mijina ba. Tace Affa ke me kika ani Fatima ai wanan aikin sai anayi ana tushi bawai dole sai ta sanar dake komai ba da takeyi. A,uzzubillahi mina shaitanin rajin nace kafin ince lala mama babu wanan rayuwan a zuciyar mu gaskiya. Sa,ane dai daga ubangiji da rahama irin na Allah muka samu daga ubangijin mu tare da taimakon kawuna da kakata Amma. Shiru dakin ya karayi a lokaci guda babu wanda ke furta wani abu ko ita mama lami taja bakinta tayi shiru don kwabarta da yarta tayi a fakaice lokacin. Mikewa nayi na fita ina masu saida safe don ba lalai ne in dawo part din ba ranan don mama ta gama bani mamaki yau din. Da mamakin ta na koma dakin Amma inda na samu har murja ta gyara shifida gadon Amma da kasa inda zasu kwanta gadon kuma ta barwa yara dani wai. Nace a, a murja ku hau sama ku kwata ke da Fauziya sai mu mu kwanta a kasa. Rufa min asiri yau kin san fadan da kawu yayi da yaya da hjy ne tunda safe kan yaran nan wai ita sam bata yarda azo dasu ba garin nan. Fauziya na kalla nace Fauziya idan ki kara cin abinci ki hau gado tare da yaran nan ku kwanta dasu ni da murja a kasa sai mu kwanta ko murja ta hau wanan dogon kujeran idan zai mata zaifi. Murja tace nan ma ai zai muna mu kwanta a raina nace dama nasan hjy ce zatace bata yarda azo da yaran nan ba don kawai ta kuntata min ga hakan. Ranan bamuyi barci da wuri ba muna hira da Murja da Manjo har murja tayi barci ta barmu muna hiran yaushe rabo. Inda na fahinci cewa har yanzu kakartawa zaman takura da hakuri takeyi da mutanen gidan namu. Washe gari muka tashi dan gyare gyare mukayi kafin yaro yayi sallama da kulan abinci niki niki wai ummace ta bayar a kawo muna abin karyawa. Manjo sai fada takeyi don me umma zatayi wanan wahalan ita da take fama da kanta ga kawu yayi iya nasa kokarin. Wurin sakawa ai muna abin karyawa lafiyayye don girmamawa wanka nayi na fito na shirya cikin wasu kara redimed daga dubai ya sayo min su sai walkiya suke ko ina. Kai Fatima wanan kayan sun sha jinina gaba daya ke ko wani shiga kikayi sai ya karbi jikin ki. Nace ko tace wallahi ba karya kema kin sani ai basai na fada ba kin ko ga duk wa yan nan kayan yawanci a nan zan barsu ba zan tafi da ko dayan suba kila. Da sauri tace ashe zamu samu nace niyata ke nan dama idan zan tafi in raba maku shi sai kizo ki zaba kafin kowa ya dauka. Saidana shirya na shiga wurin su mama na gaida su da kwana daki daki can ma a dakin mama lami saida ta sake sake min magana na haibaici kafin in fito. Gidan su Atika muka shiga muka gaida umma kafin mu fito ta hadamu da yaro zuwa gidan da Atika ke aure a wani unguwa. Atika tayi murna ta rasa yadda zatiyi saita fashe da kuka lokaci daya nima kukan ne yazo min a lokacin muka hade kai muna kuka gwanin ban tausayi sau bayan mun dan lafane ta fara bani labarin halin da take ciki bata boye min komai ba har abinda umma bata taba sani ba. Muna nan mijin nata ya shigo yana fadin yau baki mukayi ne tun a waje na hango mota a kofan mu. Da ganin shi dan duniyane sosai irin yan karyan nan don gashi fes dashi zakace mutumin kirkine shi din. Hjy Fatima ko yace yana zama yana kallon yadda muka zauna a tare da Atika a lokacin. Dariya mukayi nace malam hafiz ke nan ashe ka iya canka daidai mun dame ku lafiya ko yace lafiya nan muk hiran dashi idan na fahinci shi mutum ne mai son nuna ilimin da yake dashi da yawan son nuna turanci a bakin shi. Nace malam Hafiz aiki fa a ina kake aikine halan sai ya dan canza yanayin shi yace hjy kin san halin kasan nan tamu. Ganin canjin yanayin nasa yasa na fahinci akwai matsala rashin jigo a rayuwan shi. Nan dai muka dan taba hira dashi ya mike yana fadin barin dan fita in dawo anan zaku wuni ko nace muna nan da mutumiyar tawa sai dare yau manjo zata gan mu ai. Saida ya fita ya kira Atika sun dan dade tare suna shawara kafin ta dawo dakin tayi dan tone tone ta fita da abu a dunkule cikin jikin ta. Bayan ta dawo ne take fadin wai ni zaiwa wayau ya burge ku nace ina laifin sa har yana kokarin burge mutanen ki na fahinci Hafiz Atika. Bawai yana maki haka bane da gangan umma tayi gaskiya da bata bari auren ki ya mutu da bawan Allah nan ba. Duk mutumin dayasan ya mutanta maka bakon ka ai idan ya samu nan gaba zai maki alherin daya dace . Muna nan ya dawo da ledoji yana kiranta daga waje ta mike ta fita ta dan jima kafin ta dawo dakin ya leko yana gaishe mu da zama zai fita na ba fauziya abinda na tanada masa in bashi. Yarinyar tana kaimashi sai gashi a dakin ya cire hulan kanshi yana fifita dashi yana fadin hjy Fatima sai kuma ya kasa magana a lokacin ya dukar da kan shi kasa na dan lokaci. Ya dago yana fadin na gode hjy nagode yana dan jujuya kudin dake hannun sa nace ka hada ta kardun ka idan zan tafi na wuce dashi . Shiru yayi na dan lokaci kafin ya fara magana a cikin sanyin rai yana fadin Fatima na gode nagode Atika kinga Abinda kawarki ta bani yau, ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:16 - 🀐🀐🀐: Bamu bar gidan Atika ba sai dare muka koma gida mun dawo mun samu abincin da babbafa ya saka ai muna yana jiran mu a dakin manjo. Mukace mun koshi ba zamuci ba munci abinci a gidan Atika sai yaran gidan, ana fita dashi yaran shi suka zauna sukaci . A daidai lokacin Umma lami ta dawo daga unguwar da ta fita tun da magariba tana arba da yaran zaune suna cin abincin ta doka wani uban salati lokaci daya. Hankalin kowa ya koma gareta suna mamakin ta nan ta fara fada dasu tana fadin abincin dana dafawa Fatima da yaran ta kuka zauna kuna ci shike nan. Umma tace ba zasuci ba kada ya lalace ta fito muna dashi fada take wanda duk mai hankali zai fahinci akwai wani abu a kasa. Jin sababin nata yayi yawa har muka gaji muka fito daga dakin manjo a lokacin. Lami wanan fadan haka halan wani sheri kika karbo kika zubawa wanan yar marainiyar Allah da iyalin ta manjo ke tambayan umma Lami a hasale. Ganin kowa yana kallon ta taci gaba da fadin wanan fada naki duk mai hankali yasan bana lafiya bane . Gabana ne yayi wani irin mugun faduwa tsikan jikina ya tashi don sam wanan tunanen baizo min a raina ba da farko. Tsohuwa wanan wani irin magana kikeyi haka kuma gaskiya na fada ina dai wanan abincin na yarnan ne. Kuma tace akoshe suke yan uwanta su dauka suci kada ya lalace kinzo daga baya kina wanan fada anya lami ba wani sheri kikai niyar yiwa yarinyar nan ba kuwa Allah ya kamaki da hannun ki. Ai dama bana abin kwarai a gidan nan sai a dauko sheri a sakawa mutum don kawai kiyayya. Allah ya kyauta manjo tace tare da duban inda muke a tsaye cirko cirko tana fadin maji ma gani ita dai ramin karya kurarane dama sheri karene mai shi yake bi. Har muka koma dakin mu jikina bai dawo daidai ba sai maganan manjo nake ji a kunnuwana lokacin da take tambayan umma lami kan abinda yasa take fada haka tana kumfan baki don kawai diyan ta sunci abincin data girka muna da rana. Jikin kowa a cikin mu yayi sanyi a lokacin don haka muka nemi wuein kwanciyar mu muka kwanta saidai barci bai daukeni ba a lokacin sai zuwa dare sosai. Don nayi iya tunanena banga laifin da nayiwa wa yan nan mutanen biyu ba a duniya watau umma da hjyn su yaya da suke nuna min kiyayya irin haka. Yanzu da munci abincin wani abu ya samemu ko ya samu yaran mutane yaya zanyi da kakar su da mahaifin su nake nanatawa a raina. Can barci ya dan figeni nake jin motsi sama sama a gidan tunda na bude idanuwana na kasa rufe su tun ana wanan motsin kadan kadan har abin yayi yawa sosai ina jiwo hayaniya. Da kuka manjo ne ta mike tana fadin dama na san za a rina akwai abinda ke faruwa a gidan nan duk yadda akayi. Nace ashe baki barci ba kina jin su manjo tace najisu ai kokarin tashi zaune takeyi tana fadin hakan. Kofa ta nufa tana budewa zuwa waje inda na taso na mara mata baya muka fito tare bayan na saka hijabi a jikina. Dan gidan umma lami ne dan matashi sanusi ke faman wulle wulle a kasa ciwon ciki ya turnike shi lokaci guda. Salatin da manjo ta saka tana fadin dama nasan fadan nan Lami dazun ba a banza kikeyin shi ba. Dama yar nan kika so ki kashe da yan uwanta da yaran ta ko me Baffa yace haba babba wanan wani magana ne haka kuma ? Gatanan tsaye ka tambayeta ta baka amsa nan dai cikin fada fada take mayar mai da abinda ya faru. Mutuwan tsaye babffa yayi a gurin tare da nazari a ranshi yace tabbas akwai kamshin gaskiya a maganan nan naki babba. Ihun da Sanusi ya yanka ne lokaci guda yasa mukayi kanshi a gigice dukawa nayi ina kallon shi kafin in ce da sauri mama akwai manja a gidan nan a bani da sauri. Da sauri mama ta wuce zuwa dauko manja zuwa lokacin har ya fara zubar da wani kumfa a bakin shi mai kauri. Tana kawowa na bude bakin shi na dura mai manjan sosai a ciki kafin in ce madara fa akwai madaran ruwa a gidan nan a bani. Akwashi yana nan cikin kayan shayin dana shigo dashi dazun yake cewa mama ta juya da sauri zuwa dakin shi. Madaran na bashi sai kuma ga amai ya biyo baya nace Alhamdullahi yazo akaishi asibiti insha Allahu ba abinda zai same shi sai dai don Allah duk wanda yaci abincin nan a bashi manja da madara yasha. Ruwa ruwa aka kwashe shi sai asibiti ranan umma tasha tsina da zagi wurin manjo da babffa . Nikan ban bisu asibitin ba daki na koma mukayi zugun ni da murja kowa da abinda yake rayawa a zuciyar shi. Can murja ta nisa tana fadin Fatima kina tare da kariyan Allah wallahi duk sanda wani sheri yake tunkaroki sai ubangiji ya kareki daga gare shi. Yau da badon Allah ya tsare mu ba baza,ayi wanan tunanen ba sai ace kwanan mu ne ya kare a nan ai. Murja kin san plain din wanan matar idan anyi magana sai tace unguwar da muka fitane dai mukaci wani mugun abin don ba za a taba dora mata laifin ba. Kiran sallah ne ya tayar damu daga zaman da mukayi son muna zaune mun kasa komawa mu kwanta barci. Bayan mun idar muka ja kofa muka rufe barci sosai mukayi sai hayaniyar mutane dake shigowa ne ya tayar damu daga barcin. Ban bude kofan dakin manjo ba don kada yarana su fita tsakar gida muna dakin don ban bar kowa a cikin mu ya fito waje ba saboda tsaro duk da nasan Allah yana tare damu. Bugun kofan da akeyi tare da sallamane yasa na mike na bude kofan umman Atikace take buga kofan . Ina budewa tana fadin Fatima barka da arziki ashe wanan matar tana nan a bakan ta akanki har yanzu. Umma na rasa mena tare wa umma take bina da wanan nufin haka ko yaushe idan nazo garin nan. Baki mata komai ba Fatima illa hassada da kyashine irin na dan adam idan bashi ba ya kamata yanzu ace matar nan ta saduda da wanan abun a kanki. Muna tsaka da hira wayana yayi kara na dauka ina dubawa wanan matar daine ta sudan take kirana inda take kara tambayana address din dana basu na kara maimaita mata shi yadda ya dace. Murja na dan kalla ina fadin ina ganin yau zamu koma kano don muna da baki a gida zuwa gobe ko jibi. Da sauri murja tace nima tun dazun naso in sheda maki haka mu koma gida kawai zai fi don wanan abin ya firgitani wallahi. Umma dake zaune tana jin mu tayi saurin cewa a, a kada kuyi haka don Baffan ki bazai ji dadi ba a ransa. Ku bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai kuyi sammako ku tafi abin ku shike nan nace ba tare da nuna wani damuwa to umma. A gidan ta mukai wanka muka shirya don ban yarda yarana su matsa kusa dani ba a nan Atika ta same mu gidan nasu ranan dai wuni mukayi muna magana kan abu daya a gidan. Sai dare sosai muka dawo dakin manjo don mu kwanta tare da shirya kayan mu ba wanda yasan cewa zamu koma a washe gari sai umman Atika da Atika din suka sani. Washe gari tunda nayi sallah na fito dakin babffa na nufa nayi sallama daga bayana ya amsa min yana dawowa daga masalaci. Har kasa nakai ina mashi ina kwana yana amsa min yanayin shi kawai ya nuna yana cikin damuwa sosai a lokacin. Na dan kara kwantar da murya ina fadin baffa yau muke son mu koma din an bugo min waya zamuyi baki daga kasan waje a yau din nan ko gobe . Yace Fatima kada ince wanan abinda ya farune ya daga maki hankali kike son komawa kano yau. Da sauri nace a, a baffa wallahi dalilin ke nan na fadama idan bado baki ba ai kwanakin daya bani zancika a nan. Wuri kawo ya samu ya dan tsuguna yana fadin Fatima bansan irin kalamin da zanyi maki amfani dashi ba wurin baki hakkurin abinda ya faru. Da sauri nace baffa akan me zaka bani hakkuri akan laifin da bakai ka aikata min shi ba ya nisa tare da fadin ba zanso ki rike wanan zancen a ranki har kizo ki gujeni Fatima daga karshe. Idan kin muna haka baki dauki sakkayan da Allah yai maki ba ke nan a zuciyar ki da wanan tunane na kwana a raina Fatima ina tsoron sherin Lami ya rabamu dake nan gaba. Baffa idan banzo wurin ka ba wa nake dasu nan duniya da zan nuna a matsayin yanuwana na jini idan baku ba ko kadan wanan tunanen baizo min a raina ba baffa na bashi amsa. Allsh yai maki albarka Fatima dake da iyalan ki banda abinda zan baki sai addu,a a tsakanina dake Fatima. Saidai ina kara rokon ki da ku boye maganan nan ga mahaifiyarki don idan taji maganan ranta ba zaiyi dadi ba ina kunyar kawun ki Fatima da mijin ki na rasa wani irin hukunci ya dace in daukawa Lami a gidan nan da raina zai min dan sanyi ba. Baffa tunda Allah ya mayar mata da abinta ta gani ka barta da Allah Alhamdulillahi dai tunda ba wanda wanan abin yaiwa sanadi a cikin su. Mun dan dauki lokaci tare da baffa har rana ya hasaka muna wurin tun inatsugune har nakai ga samun wuri na zauna yana koro min irin hakkurin zama da umma lami da yakeyi. Nace a karshe zamu biya wurin Addah mu gaida ita kafin mu koma gida yayi murna da jin hakan. Mun shirya tafiya manjo tana asibiti ita da su yaya hashimu suna jinyar Sanusi bata san da zancen tafiyan mu a ranan ba saida na tura driver ya dauko ta. Tana zuwa ta saka muna kuka wai umma lami ta rabata damu ke nan kan abinda tayi muna. Hakuri na bata tare da kebewa gefe da ita nayi mata bayanin komai yadda zata fahinta dani akan ba saboda wanan maganan zan tafi ba a ranan. Mun rabu kamar kada in rabu da yan uwana a lokacin musanman kaka ta mafi soyuwa a gare ni na tafi ina tausayawa halin rayuwar da na barta a cikin shi. Saida muka biya kauyen da Addah take muka dan dade kafin mu kama hanyar kano sai dare muka isa kano din. Mun samu baya gari ya tafi Abuja a nan muka kwana tare dasu murja gidana sai washe gari nake warning din su kan su boye min sirin gidan mu kan abinda ya faru kada su fadawa kowa wanan zancen. Sai dana dan hada masu tsaraba da zasu kai gida cikin dan abinda muka samo da wanda muka sayo a hanya na kaisu gida a muna sannu da zuwa . Na shiga wurin mamu mun dan dade muna hiran gida da ita kafin in fito in koma gida duk da yamma ya soma ina sallah la,asar na kwanta a wurin. Maria ce ta shigo min da jakkata dana bari a falo da wayana a ciki yana ringing na dauka nomban Baffana ne daya bani ya kirani dashi. Naji nauyi da kunyar rashin kiranshi da banyi har ya kai ga kirana a wanan lokacin. Na dauki wayan da sallama na fara gaida shi yace mun iso lafiya lafiya Alhamdullahi ya jikin sanusi ? Sanusi sai dai muyi hakkuri Allah ya kira abinsa jiya da dare ya kare yanzu ma na kirakine ki kira babba ki mata magana kin san mutumin tane tana nan ta tayar da hankalin ta mun rasa gane kanta. Banji sauran karashin maganan da kawu yake min ba don tashin hankalin dana shiga a lokacin ya wuce musali. Gaisuwa nayiwa Babffa mun dade muna magana kan mutuwan Sanusi inda jikina yayi sanyi sosai wanan maganan dolene in fadawa mamu shi babu zancen boyewa a nan. Gani ni kadai a gidan haka yasa na fito falo muka zauna da su maria ana hira har zuwa lokacin da akai sallah magariba duk bani cikin yanayin dadin rai a lokacin. Sallah nayi na shiga daki nayi ban kara fitowa waje ba waya mukayi da yaya nake sheda mashi dawowan mu. Yace yana hanya shima yanzu haka bai samu jirgi ba mota ya shigo zuwa gida shida Aliyu nayi masu Allah ya kawo su lafiya. Haka yasa danayi sallah isha,i na fito don tanadar mai abinda zaici idan ya isa na koma dakin shi don nice mai gyara na kara gyara ko ina na fito bayan komai ya kammalu na shiga nayi wanka na dan kwanta. Basu shigo garin ba sai goma da wani abu na dare suka iso gida ina kokarin daga sai gashi a dakin nawa hakan bai hanani mikewa ba ina taron shi da zuwa. Ya rungume ni a jikin shi yana fadin wanan kara girma da kikeyi haka kamar kin kara dauko biyu a wanan karon ? Da sauri na daga daga jikin shi ina fadin haba yaya baka tausaya min kake min wanan fatan ina zan kaisu yanzu idan na dauko su. Ina tausayin ki yace yana kallon cikin nawa tare da ci gaba da fadin wanan cikin duk yafi sauran cikin da kikayi a baya girma. Nace kasan yanzu tunbina ya kara budewa abincin can kuma ba mai nauyi bane irin wanda nake ci yanzu a nan don yanzu tuwo shine abincina tunda na samu cikin nan. Tare muka fito zuwa dakin shi saida naga ya shiga wanka na fito zuwa falo lokacin ne maria ke fada min tsaraban da yaya yazo dashi nace ba matsala zan gani da safe idan Allah ya kaimu. Saida yaci abinci nake fada mai zancen rasuwan da akayi a bayan mu baiji dadin jin hakan ba yai min gaisuwa tare da fadin da safe zai kira baffa su gaisa. A lokacin ne kuma nake mai godiyan irin dawainiyar dana samu yayiwa iyayyena a gidan mu hannu ya daga min alaman in bar zancen kawai. Washe gari tunda na tashi da safe na kara kiran Baffa nayi mai gaisuwa nace ina son akaiwa manjo wayan an dan dauki lokaci kafin akai mata waya ta karba tana fadin. A ruwa da nasan Sanusi ba zai rayuba dana biki kin tafi garin ku dani a daidai lokacin yaya ya shigo dakin tana fadin A ruwa ke kin tafi sanusi kuma mai kula dani a madadin ki ya tafi ya barni yanzu. Wa zai kula dani yanzu a gidan nan wanan yaron shine idona shine kafata yanzu kuma bashi. Zama yayi a kusa dani yana sauraren mu tana fadin kizo ki daukeni tun basu karasani ba A ruwa idan baki zo ba zaki dawo ki samu bani. Manjo kiyi hakkuri zanyi magana da mijina musan yadda za ayi da hidimar ki amma ki bar kukan nan tunda kika iya rabuwa ni kikai hakkuri a baya. Bayan munyi sallaman na dago na kalleshi zuciyana ba dadi a lokacin . Ki kwantar da hankalin ki ya kalleni yana fadin rudun tsufane zan saka koda kin tafi can azo maki da ita ta zauna maki idan kin haihu haihu zata dan debe maki kewa. Kana ganin idan mun dauki kakata hakan ba zai zama matsala ba a gurin hjy matsalan me har taje ta dawo tunda ba kasa daya kuke ba ina zata san taje. Mikewa yayi yana fadin muje ki ban abinci fita zanyi yanzu sai na biya gida na gaida su zamu tafi wani unguwa da Nasir. Mikewa nayi zuwa falon na bashi abinci nima na zuba nawa muka karya ya fita daga gidan dan kwantawa nayi a falo ina kallo yara suna min hira sai barci ya dauke ni. Can a cikin barcin wayana yai kara firgigit na falka ina daukan wayan tare da duban mai kirana a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:16 - 🀐🀐🀐: Da sauri na mike tsaye don jin abinda ake fada min a wayan da mamaki nake kallon wayan dake hannuna ina ayyana lalai idan ina duba aikina zaici. Na riga dana nasa hakan dama kuma gashi yanzu hakan ya tabbata hasashena ya zama gaskiya garesu sune din suke fada min gasu a garin kano. Sai dai girma da fadin garin yasa sun rude sun kasa fahintar kwatancen da nayi masu shine nace su jira a airport za a zo a tafi dasu. Dakatar da tunanen danakeyi nayi lokaci daya don tunawa da nayi suna dakon mu a lokacin a daidai lokacin da nake shirin kiran yaya a wayana sai wayan ya sake daukan kara lokaci guda. Take sheda min cewa na bari kawai mijin ta ya kira za,ayi amfani da addres din dana basu a samu gidan nace ba matsala. Murja na kira ta dauka nake fadin kije dakin mamu yanzu ki gyara duk wani abinda bai dace ba dakin cikin awa daya ki tabbatar da kin gama komai nima gani nan zuwa a lokacin. Ban hakkura da kiran yaya ba don kada in fita yazo bai sameni a gida ba don bansan ko ba zasu dade ba inda sukaje. Yana dauka wayan yace zahra yaya akayi ne nace yaya mutanen nan iyayyen mamu sune suka kirani yanzu wai gasu a kano . Yace what nace wallahi yanzun suka kirani suna sheda min shine nike son muje can su samemu a gidan kafin su zo. Ok ku tafi yace kafin inzo da sauri na shirya bayan mun gama wayan daga ni har yan aikina gaba daya muka nufi gidan kawuna. Ban shiga dakin mahaifiyata ba saida na gaida kowa na gidan a gurguje kafin in fito zuwa wurin mamu . Na samu murja ta gyara part din na mamu duk da dai a gyare yake tana zaune suna hira da mamu tare da fauziya nayi sallama. Ban kai ga gaisheta ba take fadin kin dauka ni irin kine zakice wai azo a gyara min daki kuna daukan kowa zaune yake sai an mashi abu mutum da karfin shi ya zauna jira. Dariya kawai nake mata ina zama tare da fadin yau ba ranan fada bane gareki mamu don tukwaici ya kamata ki bani babba kan hakan ba kuma tukuicin komai nake so ba sai fauziya zan tafi da ita idan zan wuce. Wai hauka kikeyi ko me haka Sayadi yau gaba daya kin wani zare min kafin in kai ga bata amsa wayana yayi kara na dauko ina dubawa yaya ne ya sake kirana yana tambaya na su nawa ne sukazo nace ban sani ba yaya don basu karaso ba tukunna. Ok kawai yace ya kashe wayan shi na dago ina kallon mamu data tsareni da ido tana son jin bayanin wanda zasu zo muke magana. Nace a hankali mamu yau dai Allah yayi wanan jumma,an zaki gana da mahaifiyar ki in sha Allahu wace zuwa yanzu suna cikin kasan nan ko sun sauka dazun da safe. Ban rufe baki ba mukaji diran motoci har da jiniya sun tsaya a kofan gidan kawu wanda hakan yayi daidai da fitowan yan gidan kawu gaba daya a daidai lokacin da murja take kwalawa Amma kira ta fito yau ga mahaifiyar mamu tazo. Hjy dake kokarin fitowa daga part din ta a daidai lokacin tace haukan banza ina wanan magana ya fito haka kuma ga yarnan. Har kawu sun fito da sauri shida hjy maryam suka tsinkayi muryan murja dake shela a gidan na zuwan bakin. Kowa mamaki ne ya cika shi a lokaci daya suna tsaye suna kallon juna ba wanda ya iya magana a cikin su a lokacin. Tabbatar da lalai a nan motar ya tsaya yasa kawu kokarin fita waje ya duba ko su waye wajen don ya tabbatar. A lokacin na fito zuwa kofan gidan nima mukai arba da wanan matar mai suna sumaiyya wace ke zaune a London. Ko wacen su na cikin shiga irin na al,adan su nace sai dai ko ba a fada maka ba kasan ko a can din manyan matane sudin. Don zinare na sarka ne zuwa awarwaro ke nuna kanshi a jikin su sun kai su shidda mata sai maza dake da kama mutum hudu. Bayan dan bayani da wanda akasa ya rakosu daga gidan gwaunati yayi wa kawu ya basu daman shiga gidan lokaci guda. A daidai lokacin da Amma ta fito tana fadin da gaskene yau Sadiya ce a garin nan ko kuwa. Ai kuwa arba sukayi da ita tace hjy kece itama amma tana fadin tsarki ya tabbata ga Allah halima ce kuwa da kanta nake gani nan. Sai ta fashe da kuka a lokaci daya wanda hakan yasa matar hamshakiyar da aka kira da maimuna itama ta fashe da kuka tana rungume Amma. Ga yaran maza kamar su dauke uwar don manne mata da suke a jiki lokaci guda. Mamu tana kokarin fita aka turo get din gaba daya da sauri kawu yake kokarin bude kofan na karba nida murja muka wagale get din gidan suka fara shigowa ciki. Sai bin gida da kallo suke suna yaren su har lokacin Amma da matar suna rungume da juna basu sake dan uwa ba. Ji nayi an dafa ni na juya dayan matar wace take yar matashiya a cikin su ne ta dafani na juyo ina kallon ta. Tace min a harshen turanci kece Fatima ko nace eh sai ta rungume ni tana fadin kamarmu daya dake yasa yar uwarmu ta baiyana ta dalilin mu don ni kika kwaso sak . Nace harda mahaifiyata don kamartane na kwaso sosai tace da gaske nace kwarai kuwa zaki ganta da ita kuke kama har na kwaso ku. Muna tafe ake dan fira a tsakanin mu murja dake bayan mu ta rada min Fatima duba hjy kiga ikon Allah yau. Da sauri na dago na kalli hanyar part din ta tana tsaye a cikin imani da al,ajabin abinda idon ta yake gani muka shigo gidan. Gaba daya suka ja suka tsaya don ganin mamu dake masu wani irin kallo lokaci guda da sauri matar ta sake Amma tana mikawa mamu hannu alaman tazo gare ta. Da sauri suka hade lokaci guda har yan mazan dake bayan matar tafe suka rungume mamu suka sakata a tsakiya. Kowa na sharan kwalla a fuskan shi suna yaren su na can daya bayan daya suke rungumar ta suna mata gaisuwan su na larabawa na sumbata. Duk wanda ke wurin sai da yai kuka in ka debe hjy jummai da hjy maryam dake tsaye kamar an dasa su a wurin. A daidai wanan lokacin yaya ya shigo gidan shida Aliyu suna masu sannu da zuwa kafin su dawo inda mahaifin su ke tsaye su tsaya suma. Can yace min nazo na dan zo yake fadin yaya zamu barsu a nan a waje mu shiga daga ciki mana zaifi. Nace kukan ne basu kare ba ai yaya sai faman runguma sukeyi suna yare yace shiga dasu ciki don Allah yana gama magana dani ya daga kai suka hada ido da mahaifiyar shi dake mashi wani kallon tuhuma a lokacin. Don a zaton hjy shine mussababin tono inda mahaifiyar mamu take har suka zo din inda take yanzu. Mun shiga ciki har lokacin suna bin part mamu da kallo ina kokarin dauko masu ruwa saiga murja na sallama da katon din ruwa da drinks tana shigowa dashi ita dasu Fauziya. Abinci abinsha da sauran abin baiwa baki duk sai gashi ana shigowa dashi part din na mamu kamar dama an tanadar masu shine. Banyi mamakin hakan ba dana gani don nasan aikin yaya ne wanan dawainiyar sun sake sosai suna cin abincin ba tare da nuna bakunta ba a gidan ba. Dakin Amma na nufa don can nakai yara da yan aikina dana zo dasu sai maria ne ke part din mamu tana ba baki abinci. Hjy maryam tazo har dakin gaida su da zuwa ta dan zauna na dan wani lokaci kafin ta fito suna gaisawa. Su yaya na fitowa daga gun kawu suka shiga dakin mahaifiyar su don su gaisa sun gaisa din duk da ya fahinci yanayin ta bai hana ya dan zauna tare da ita ba a lokacin. Muryan ta yaji tana fadin Babawo makirci da sallon yaudara har da kai za a hada baki ayishi a gidan nan . Subbahanallahi mama mai kuma akace maki na aikata yanzu kuma tace meye baka aikata ba din don yanzu na gaskanta komai dana gani da idona. An hada baki dakai wurin neman uwar maimuna har wani kasa ka nemota wama yasani ko mai kama da ita kukayo haya a wani kasa. Aliyu yace haba mama wanan zancen ai bai dace ace anjishi a bakin ba wallahi don Allah mama ki rufa muna asiri ki daina wanan halin haka ? Yaya za,a yo hayan mutane haka zuwa nan da sunan karya irin wa yan nan mutane har kike tsammanin za a dauko da sunan haya. Da ganin su kaf yan babban kasa don babu yadda za ayi gwaunati ta turo ayo masu rakiya haka idan basu da mukami a gwaunatin su nacan. Koma menena dai bai shafeni ba ko duniya zasu zo dashi don kaina na sani to mama sai ko ki kyale don Allah wanan abindai kowa ya nuna masu farin cikin shi. Kin san kuma dole shi yaya yayi wani abu akai tunda dai yana auren jikan ta yanzu ko ? To ubana saika tsareni kana min fada tunda kun rainani akan matan ku kun fifita matayen ku yanzu a kaina kowa kuma yasan da hakan. Shiru sukayi gaba dayan su babu wanda ya kara magana a cikin su taci gaba da fadin idan bashi yaje ya nemo masu ita ba ai bata taba tunawa tabar diya a kasan nan ba wullakance. Ko ita maimunan da yarta suna da halin zuwa har wani kasane neman mahaifiyarta watau ka nuna min ka gaji da gorin da nake mata ko ? Mama kiyi hakkuri idan kince na nemo masu ita kamar hakane tunda ni nakai ita fatima kasan waje har suka hade da wace tasan mahaifiyar maman ta a can ta hadasu da ita. Tace bakaji zancen ba ta dalilin ka komai ya faru idan ina magana sai a dinga ganin laifina abinda nake gudu ya faru ke nan yake faruwa dakai an mayar dakai wani binan sai abin da suka tsarama kakeyi a gidan nan. Haba mama koda ace kudi na kashe wurin nemawa maimuna mahaifiyar ta ai ba zai zama laifi ba don na sama masu martaban su ko ? Martaba wani martaba ga matar data tafi ta bar yarta shekara da shekaru a wullakance nan wata kila ma zaman banza takeyi a can don ba abin mamaki bane hakan ya kasance . Innalillahi yace tare da fadin Aliyu tashi muje Nasir yana jirana yana kokarin tashi tace kada inji kada in gani ka saka bakin ka a cikin wanan karyan da za ai muna gidan nan. Basu ce komai ba suka fita cike da kunnan rai suna maijin zafin halaiyar mahaifiyar su da ta kasance halinta a hakan . Mata hudu da mazan muka kwasa muka tafi gidan mu dasu zasu sauka a can don zasu fi sakewa a can inda kakata tace a wurin mamu zata sauka ita da kanwar ta guda. Sun yaba da gidan namu sosai don komai a wadace suke yinsa ko wani daki mutum bibiyu suka sauka a cikin sa. Inda na shiga dawai niya dasu a gidan kamar yadda ake karrama ko wani bako idan yazo maka bakunta a gidan ka. Sai washe gari ne bayan sun huta anty Summaiya take min bayanin su kamar haka. Kakan ki itace babba a gidan mu bayan iyayyen mu sun bar kasan nan da mu muka koma gida a cikin bakin ciki take da kyar aka samu tayi aure a cikin dangin mu. Ta aure dan wan baban mu a lokacin wanda ya dawo karatun likita daga kasan waje lokacin dashi ne ta haifi wa yan nan yaran da kike gani tazo dasu dukan su diyan cikinta ne su biyar maza hudu da macen nan da kukai kama muke kiranta da Binta. Da yake yan gidan mu duk gaba dayan su suna ilimi muma komawan mu can yasa aka sakamu a makarantar mukai karatu mai zurfi har ita yayan namu dake da aure bata zauna ba. Mijin ta shine tsohon minister lafiya na kasan mu da tare dashi zamu zo sai dai aiki yai mai yawa yasa ya hado mu da yan rakiya kawai mukazo. Ni dai kin san a London nake zaune mijina ne ke aiki a can shine nima zamana ya koma London din sai dai muna zuwa gida lokaci lokaci don hakane baki faye ganina a shagona ba kowani lokaci. Binta batai aure ba har yanzu saidai tana da wanda zata aura Family din mu daya dashi kin san mu bama auren bare sai dan gida wanan ka,idan gidan mune hakan. Na tausayawa halin dana samu mahaifiyar ki a ciki dama wanda ta shiga a baya don muna zaune a cikin daula ita tana nan tana zaman hakkuri. Saidai ke Alhamdullahi da gani baki da matsala a rayuwa don jikin ki bai nuna hakan ba a kullun wanan ne damuwan kakan ki a can tana yawan magana kan rayuwan mahaifiyar ki. Kin san tsakanin da da uwa akwai motsi na jini dake yawan halin da dan uwa yake a ciki . Sai dana lumshe idona na fara koro mata matsalolin da muka fuskanta a rayuwan mu nan dama wanda muke a cikin sa yanzu. Har rana yayi sosai bamu sani ba muna zaune muna hira a wurin sai kiran sallah azahar daya karade unguwar muke danji lokacin muka kalli lokaci muka san rana yayi sosai ashe. Sallah mukayi mazan suka fita zuwa masallacin don suyi sallah wanan zuwan da sukayi shi ya dage muna tafiyan mu a satin mun shirya zuwa can gidan kawu wurin su kakan tawa don su gaisa da ita. Da sultana kawai naje nabar sauran a gida wurin maria busy muka samu mamu tana faman dawainiya da bakin nata. Tubewa nayi na karbi aikin nata naci gaba dayi sai mamakina sukeyi wai da cikina tsoho ina aiki haka. Bayan magariba muka samu kebewa da mamu na tambaye ta ko hjyn su yaya tazo gaisawa da bakin ta ? Bata shigo ba ta bani amsa tare da fadin kuma hakan ni bai dameni ba tunda Allah ya karba mi addu,a na wankeni daga sherin da ta dade tana min ga mutane. Da ranan nan tagama fada da Alhaji wai yana rawan kafa saboda uwata tazo inda Allah zaisa naji sai gashi na shiga wurin shi kai mashi tsaraban da suka zo mai dashi. Nan ta kama fadan karya tana wani kame kame don tasan naji abinda suke fadi lokacin. Mamu wanan matar tayi nisa sai dai addua ga lamarinta kawai yanzu don abin yafi karfin kishi sai kiyayya a tsakanin mu da ita. Dazun da kawun ki yazo gaishe su naji suna fada mai suna rokon idan zasu tafi zasu tafi dani inje inga yan uwa yan uwa su ganni. Da sauri nace meyace mamu ta dan bata fuska tare da fadin yace sai ya zauna yayi shawara da gwaggo . Da alama ba zai bari ki bisu ba mamu tace ai ba zan yarda da hakan ba kada kiyi wani magana idan ya hana nace mata. Amma kin san za a tauyeni da yawa idan yai min haka don yasan suna bukatana can ke nan hakan kuma shi zai sa kowa ya fahinci karyan da hjy ke masu na cewa uwata ta gudu ta barni idan har na bisu din. Wanan gaskiya nasan kawu ba zai hanaki ba idan kun fahinci juna sai dai ban son ki tayar da hankalin ki kan wanan magana kada yaga kin manta da halatcin da yai maki a baya shi da Amma. Mamu naso fada maki abinda ya faru lokacin da mukaje misau sai dai hakan bai samu ba nan nake bata rabarin abinda ya faru naga hankalin ta ya tashi sosai tana fadin . Ni maimuna na rasa me muka tare wa wa,yan nan mutane suke neman rayuwan mu haka mu bamu damu da al,amarin kowa ba amma sun sakamu gaba haka ? ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:18 - 🀐🀐🀐: Kwanan bakin mu hudu a kano tare damu wanda yaya umar ke faman dawainiya dasu don fitar damu kunyan su. Dukko da irin hattaran shi da hjyn su takeyi saidai ya nuna mata shi baida ko lokacin su aikin gaban shi ya sha mai kai don ya bar gari shida dan uwan shi. Don kada tace lalai shidin ne kuyin abubuwan da take ganin ana shigowa dashi gidan don su. Sai dai kafin ya tafi ya barwa Nasir abokin shi yin komai don bakin a hannun Nasir wanda yake kawowa ta gidana ni kuma sai inba driver ko in kawo da kaina. Sai kuma ta koma zargin kawu tana fadin shine mai hidima da bakin yake nuna masu shi baida hali yanzu amma gashi saboda zuwan yan uwan mamu yana fitar da kudi yana kashe masu don kawai a yabe shi. Yace idan nayi laifine yin hakan don kafin in masu da naki yan uwan nasha dawainiya a baya kika kuma manta da hakan da nayi maki yanzu. Gori zakai min don kawai na fadi gaskiya yace babu zancen gori a ciki sai amsa daidai da maganar ki kinga kenan baga yan uwan maimuna na fara rawan kafa ba ashe ? Wasa wasa saiga muryan su yana tashi har yakai sauran sassan gidan ana iya jiyo abinda sukeyi wanda hakan baiyiwa kowa dadi ba a gidan. Bamu dade da shigowa gidan ba wanan abin ya faru da dabara na dauke hankalin su ta hanyar kara karan tv dake aiki ina masu bayanin abinda mai wanka yake fadi. Hakan ya dauke hankalin su saidai ita kakantawa dake jin hausa tasan abinda ake fadi sarai a gidan kallon mamu tayi tana tambayan ta tace maigidan ne da uwar gidan mu suke dan hatsaniya . Tace har yanzu ana irin wanan halin a kasan nan da addinin nan daya zaga ko ina ana wa,azi akan hakan mai yai mata haka take wanan daga muryan haka ? Nace wanan halin tane mama kamar yadda naji diyan ta suna kiran ta nan na fara bata labarin irin gorin da hjy take wa mamu ita kuma tanawa yan uwanta bayani har ga zuwa aurena da danta har rikicin da mukeyi da ita zuwa yanzu. Suyi da yaren su suyi da turanci ko da dan hausan da sukeji kadan suna kara bamu shawaran yadda zamu zauna da ita. Kawu ya yarda dasu tafi da mamu don taga yan uwa da wuri koshi sai da Amma tasa baki a maganan ya yarda don yace sai daga baya zai shirya sutafi tare da ita. Amma tace sam ba zai yuyu ba yaushe zai samu lokaci yadda yake fama da jikin nan nasa yanzu. Don haka muka fara shirin tafiyan mamu kasan mahaifiyar ta ta dubosu ba karamin kudi muka kashe ba wurin hada tsaraba irin wanda ya dace suje dashi wanda basu dashi can suna bukatan shi . Da muka fitar da tsaraban ba karamin fada kakan tawa tayi ba damu kudin data bamu yafi kudin da muka kashe yawa . Da farko munki karban kudin data bamu din saida ta nuna bacin ranta ga hakan kafin in yarda na karba tayiwa kowa na gidan alheri na bajinta saida kowa ya girgiza bayan tsaraban da suka zo dashi aka raba inda hjy ba kunya ta karbe komai da akabata tana cewa ta rage zagin dukiyan da danta ya barar masu itama. Mamu zata tafi da su yan biyu da mansur karamin danta nan aka shiga zancen ina fauziya zata zauna mamun tace wueun Amma. Da kaina nayiwa kawu magana zan tafi da fauziya don ta kamamin idan zan haihu a can yaso ya hana saida ya danyi tunane kafin ya barmu mu je da ita. Yau dai mamu sun daga muna tsaye muna kallon har jirgin su ya daga saida ya bace muka dawo gida inda kusan gaba daya yan gidan kawu mukai masu rakiya zuwa airport din inka debe hjyn su yaya . Ta daiyi banjin ta ta rakosu har kofan gidan kawu da zasu wuce saidai kana kallon ta kasan naciki na ciki lokacin. Bayan tafiyan sune muka hau shirin namu tafiyan don komawa London din dan karatun yara dayace lokaci yana kurewa yasa muka bar kasan, sai dai bamu samu tafiya dashi ba don aiyukan dayace yayi mai yawa a nan. Kusan yanzu watana takwas rabona da london saidai komai ban canza min ba sai dan kara kawata kasa da kullun suke cikun yinsa su. Muna komawa akakai yaran makaranta harda yar sultana na sai ya zamanto yanzu fafitikan nemawa Fauziya makarantan da zata shiga nakeyi duk da alkawarin wata uku nayiwa kawuna zatayi don nasan idan na fada mai gaskiya ba zai yarda muzo da ita ba. Yaya ya bugo waya yana sheda min bude ma,aikatar su da akayi a kasan guda lagos guda Abuja na tayashi murna jin komai ya kammalu bayan fafutukar dayasha na shekara da shekaru wurin neman yayunwan abin. Tuni nayi mai akan zancen mijin Atika yace bai manta da zancen shi ba ai tunda takardun shi suna a hannun shi . A cikin hiran namu yake fadin yana son ya samu daddy akan maganan Ahmad don yana son suyi aiki a tare dashi tunda kasuwan nasu yanzu baija sosai kuma sabbin yan kasuwa matasa masu amfani da tecnolagy a yanzu. Sai zancen salma da zai budewa gidan buga ruwan leda na sha ban san lokacin da dadi yasa na sake dan ihun murna ba a lokaci guda don dadin danaji na hakan har kasan raina. Bayan kwana biyu sai ga salma ta bugo min waya tana min godiya wai yaya yazo da kanshi har gidan su da abin alheri gare su. Mun dade muna hira har zamu kashe wayan tace wallahi Fatima yaya har tausayi yake bani hjy ta daga mai hankali akan karin auren shi da ta matsa mai yayi. Ashe su har sun saka rana ba wanda ya sani sai da zancen yaje kunnen daddy akeji a cikin gida koshi saida baban ita yarinyar ya kira daddy don yace baiga kowa har lokacin daga bangaren mu ba kan zancen ga lokaci sai karasowa yakeyi na bukin. Gabana ne ya yanke ya fadi lokaci guda nace kai lalai kuwa hjy takai wallahi itako salma sai zubamin labarin takeyi tana fadin. Kin san halin yaya bai nuna abu ya dameshi saida daddy ya kirashi ne yana tambayan shi yake fada mai yadda mama ta tursasa shi har tana batun yi mai baki idan bai yarda ba. Yace ma daddy yana son a dage bukin har zuwa lokacin da zaki haihu idan kin haihu sai ayi bukin. Da salma tasan yanayin da nake ciki lokacin da bataci gaba da fada min wanan bakin labarin datake tsegunta min ba a lokacin. Duk da ina da kishiya amma sunan ta dai ne nake ji na amfani dashi don nida ita tunda ta samu labari bamu taba ido da ido ba har wanan lokacin. Ban yarda ta fahinci irin halin da nake ciki din ba a lokacin don kada in katse ta da jin labarin idan ba haka ba sai dai inji wanan labarin daga sama. Wai kin san wani abin haushi ba naje gidan mama saude ba sai ga yar iskan nagani wai tana yawon nuna anko ga yan uwa na bukin. A raina nace Allah yasa kada yaya ya aminci muga ta tsiya wani iri nake ji gaba daya jikina ya dauki rawa a lokaci guda har abin cikin cikina saida ya juya lokaci daya. Nace dama ashe zancen yana nan salma amma kinga yaya bai fada min ba don munafuncin maza. Haba dai Fatima na fada maki ai bada son ran yaya ba fa wanan shirin duk daga mama da yan uwata masu zugata yake fita. Ke mama fa kin dai san uwatace wallahi lamarin mama sai addu,a kawai don har tana ikirarin idan kun kama yayane keda maman biyu ita a tsaye take kwana kan danta sai dai idan babu boka ko malam a duniya. Fatima wanan magana ya kamata mama tana fadin shi kan matar danta don Allah duk da take uwata shi gaskiya ai dayace. Yanzu ya kamata ace mama ta mayar da lamarin ta ga Allah tana istigifar din kuraren tana bayane ba wanan shirmen ba da ake zugata akai ni nasan sai mama ta dawo tana dana sanin wanan abin daga baya wallahi don ba mutanen arziki ta debowa kanta ba. Allah dai ya sauwaka nace mata don na kasa furta komai akan maganan don idan nace zan furta din zan iya fadin abinda ba daidai ba ga mahaifiyar nasu dake son ganin tarwatsewan rayuwana a kowani hali. Ita bata ko tausayin halin da nake ciki da tsohun ciki haka a jikina take kiran ai min kishiya jin nayi shiru ban tanka ba tace amma fa tunda nace ban sani ba don Allah in rufata a gurin yaya kada yaji ita ta fada min yayi fushi da ita kuma. Nace baki da matsala kan hakan anty salma indai nice ba zan mai maganan ba sai idan shi yayi min. Ajiyan zuciya na sauke bayan mun gama wayan ina mamaki a raina na wanan halin na hajiyan su . Haka na wuni sukuku saukina ma yaran da basu gida sai hudu suke dawowa har na samu lokacin yin tunanen mafita akan maganan. Koda yaran suka dawo hakana suka sameni cikin rashin walwala a tare dani. Ga wani irin bushewa da makogorona suna faman surtun su haka na zauna kamar mutum mutumi ina kallon su. Gaskiya akace ciwo ya mace sai mace yar uwarta don Fauziya ta fahinci ina cikin wani hali na tashin hankali ita ta dauko ruwa da abinci ta kawo min gabana wai inci. Dago kai nayi na kalleta sai lokacin na dan sake murmushi kada yarinyar ta daga hankalin ta akaina. Ruwan na dauka na dan kwankwada na aje kofin ina lumshe idanuwana tare da bin kujera na kwanta har lokacin na kasa aje magana daya a kan zancen da yau salma take fada min din na tabbacin zancen karin auren yaya din. Bayan kwana biyu ya sauka kasan bai samu zuwa wurin mu sai washe gari da yamma ya shigo gidan hakan kuma ya bani tabbacin gane merry tana kasan ke nan. Ya shigo gidan daidai yaran na gidan sun dawo da murna suka tare shi sultana ta sheko zuwa dakina tanayi min albishir din dawowan daddy nasu nace naji kawai. Ya gama da yaran a falo har lokacin ban fito zuwa taron shi ba ina dakina kwance na lumshe idona. Can naji ya murda kofana ya shigo daga kofa ya tsaya yana kare min kallo ni kuma har lokacin ban dogo kai na kalleshi ba. Sai da naji motsin shi zuwa inda nake kwance na dan bude idanuwana da sauri nace sannu da zuwa a kasalance ya bini da kallon yadda na tare shi yana mamakina a ranshi. Bai amsa min gaisuwan ba yace meya sameki ko baki da lafiyane kuma yana tambayana tare da kokarin taba jikina yaji. Lafiyata kalau na bashi amsa kawai ina kokarin tashi zaune ya hanya na kara fadi. Tambayan ki nake kina kin bani amsa meke damun ki ne na ganki haka kamar mara lafiya ? Lafiyata kalau sai dai idan za a lakaka min ciwon dai a yanzu kallon mamaki ya bini dashi yana fadin wani irin magana ne wanan kuma kike fada min. Ai ba,a damu dani ba tunda ana ganina banda galihu tunda mahaifina baya raye kamar na kowa dole azo nan a yardani kamar banza. You are very stupid da wanan magana da kike min zahra daga dawowana zaki tareni da wani shirmen magana taki mara dadi haka. Ya mike ya fita a fusace ya bar dakin rai bace bai sake shigowa ba nima ban fita ba ina dakina kwance a lokacin ban leko falon ba. Yayi wanka yana cikin shirin shi da alama fita zaiyi a lokacin fuskan shi a daure yace ni zan tafi merry na gari nazo duba kune dama. Ban tanka mashi ba ya juya ya fita abinshi ya bar dakin cikin tafiyan shi mai kama da kasaita sai daya dan jima naji tashin motar shi a lokaci. Haka na kwana ina hadiyan zuciya dagani sai yarana da maria a gidan don ko washe gari bai shigo gidan ba sai da dare lokacin har yara sunyi barci ya shigo gidan. Ban san ma shigowan shi gidan ba don haka na wuni akwance sai maria ne ranan take komai a gidan don a zaton ta banda lafiyane ni. Kofana ya murda yaji ta a rufe ya fara kiran sunana ina jin shi ban amsa mashi ba ya kara cewa dani ki bude kofa nace cikin tsawa jin tsoron shi da nake har yanzu yasa na mike na bude kofan lokacin. Wanan wani hali kuma kika dauko na kule kofa da key banyi magana ba na juya in koma bakin gado naji ya rikeni yana fadin. Wai wanan wani hali kika daukone hakane zahra ban fa gane maki ba zahra tun dawowana garin nan. Ka tambayi yar uwanka da kake boye min auren ta don a yaudareni ne aka turoni nan aka barni da yara ai da ka sani baka turoni nan ba don ba zan tareka da komai ga auren ka ba. Hakan baiyi ba sai da kazo ka watsar damu kamar mu ba mutane bane a nan ka shigo garin nan yaya baka damu ka fara zuwa nan kaga lafiyan mu ba sai ka tsaya wurin merry da yarta. Zama yayi bakin gado yana murmushi yace har an samu wanda ya kwarmata maki wanan zancen tun daga Nigeria har nan duk taka tsam,tsam da nake kada kiji ? Ban tanka shi ba don haushin da nake ji a raina a kwana kin nan yasa na kyaleshi kawai bayi magana ba. Karamin filon dake gefen shi ya jawo ya rugume a jikin shi yai shiru har wani lokaci na bashi baya yana zaune sai ajiyan zuciyana yakeji daga inda yake zaune. Bai taba tunanen ina da zafin kishi haka ba don ban taba nuna mai kwatankwacin halin dana nuna mai ba wanan karon. Sai ya danganta abinda harda laluran cikin dake jikina ya hademin jin zafin don ace zuciya sai mace mai tsohon ciki dama. Baiso inji wanan zancen ba a yanzu sai idan na haihu shi da kansa zaimin bayani yadda zamu fahinci juna don shi kanshi auren biyayya ga mahaifiyar shi zaiyi yanzu bawai don so ko kaunar auren ba. Sai gashi wani da bai sani ba ya bata mashi tsarin shi ya kwaramata min zancen a lokacin dabai so hakaba gareni. Yanzu kallon mayaudari nake mashi wanda ke shirin ha,intana ko cin amana nakenan na dauke shi. Can naji ya gyara kwanciyar shi still dai dakin shiru yayi ba wanda ya iya magana a cikin mu a hankali kuma yaji sheshekan kukan da ya fara zo min a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:18 - 🀐🀐🀐: A hankali na sauka daga kan gadon na wuce bathroom nayi alwala na fito har lokacin bai falka daga dan barcin daya samu ya dauke shi ba don ya kwana da tunane a ranshi. Mata biyu ke nan bai iya da halin su ba inaga kuma ya kara na uku yanzu wace ba bakin arzikin dayaji yabon ta a gurin su. Ya bar gidan merry data zo bukin yar uwanta tun yana Nigeria ta ishe shi da kira saida ya dawo akan dole da fitina da komai sai da yazo wurinta karshe ma kuma suka kare da fitina don yanzu yar tsarguwa ya rigada ya shiga tsakanin su ko. Komai yai mata sai taga rashin kyautawan shi gare ta zatace don ya aure illiterated din yar uwan shi yake kokarin wullakanta ta yanzu. Har ya kai ga fada mata wanan din data raina tafita da komai yanzu gareshi don tasan kimar shi da darajan shi tare dana yan uwan shi. Ran merry ya baci da wanan kalamin nasa sosai tace dama an fada mata su musulmai basu da tabbas ai gashi ko ya fara nuna mata hakan. Saida sukayi tsiya tsiya dashi yabar mata gidan rai a bace ya nufo wanan gidan namu . Sai gashi yazo ya samu wani fitinan dake shirin taso mashi kuma wanda yake ganin zaifi na merry idan bai dauki mataki a kan hakan ba. Ashe gaskiyane da akace mace ba abin yabo bane sai idan an mata kishiya bata tada hankalin ta ba za a yabeta. Ina abin tayar da hankali akan wanan auren da yake shirin yi yanzu yarinyar da sau daya ma ya ganta kuma a duhu don samun su tayi zasu tafi bayan sun gama ganawa da mahaifin ta da mama ta tursasa mai yaje ko ta saba mai . Hakan yasa dole ya shirya shi da Nasir da Aliyu suka tafi akai magana suka bada komai. Allah ya gani zaima mamane biyayyan haihuwa kawai don ya gane auren shine salama a gare shi don a zauna lafiya. Ina za,a hada zahra da sauran matan shi don dai kawai halin mata da basu raina abin kishi har may wanan mai zubin mayunwatar daya gani zata ja da zarah ne ? Koda ya aure ta baiji zai iya zuwa da ita ko ina ba bayan Nigeria shiyasa tun farko ya fadawa mahaifiyar shi wanan magana akan ta sani ba zai fita da yarinyar ko ina ba idan ta yarda zata zauna a Nigeria shike nan . Suka yarda da wanan sharadin nasa don su bukatan su kawai ace anyi wanan auren su shiga cikin rigar arzikin su suma a dama dasu kawai. Nan hjy ta kawo zancen Fauziya da taji mun tafi da ita daga baya tana fadin zakace ba zaka iya kai yar yaruwata inda kake ba. Amma ka iya daukan diyan maimun har biyu don ka inganta masu nasu rayuwan suci gaba wanan ba maganan da zai yuyu bane yadda kakai wanan yar matsiyatan itama ya zama dole ka kai wanan din can . Habibb yace ki gyara zancen k mamai don yanzu sun wuce akirasu ahalin tsiya kamar yadda kuke kira masu a baya. Don kowa yaga arziki yanzu a tare dasu har sun zartamu don shi wanda uwar maman twinces ke aure ake sa ran shugabancin kasan nan gaba. Saida na bincika naji komai nasu a kasan ita kanta uwar wata babban ma,aikaciyace a kasan basu da alfaharine kawai yasa baku san wanan ba yanzu haka idan kin shiga kinyi saching din sunan shi zakiga komai masu in deteils. Arzikin su na banza da wofi tunda danashi suka fara karya a gidan nan kowa kuma ya sani in badon arzikin nasa da sukabi ba ina zata taba ganin uwar nata nan a tauye. Kai barin fadama ba wani abinda zaka fada min wa yan nan mutanen su burgeni a duniyan nan na tsane su kamar yadda na tsani ranan mutuwata. Amma mama uwar diyan shine fa bai dace kina aibanta masa mata da take matsayin uwar garken gidan sa ba haka a gaban shi. Tace ko zaka rama mashine marata ido da bai san inda duniya ya dosa ba uwar garken sheri da ba,ayi hakan tsakani da Allah ba tun farko. Da kyat ya samu barci ya dauke shi lokacin saboda tunanen irin abubuwan da suke faruwa dashi duk sabodani wanda kuma a karshe sai baiga laifin nuna kishi na din ba gareshi don ta haka maza ke gane irin son da mace ke masu ai saidai kishin idan yai yawa cutane wani lokaci don ya gani ga mahaifiyar su wanda zafin kishin ta yasa yanzu bata sanin abinda ya dace da ita na daidai. Shine gabanin asuba ya samu barcin yayi gaba dashi har na tashi nayi sallah bai sani ba yana kwance ya dukule a wuri daya kamar yadda yara ke kwanciya idan suna barshi ya dan dora hannu yayi filo dashi. A hankali na bar dakin har lokacin bai falkaba da alaman bai dade da fara barcin nasa ba don nasan ba kasafai sallah asuba yake wuce shi ba tundai wanan unguwan da musulmai keda yawa har jam,i yake zuwa wani lokaci don akwai mosque da sarauniya ta gina don musulmai. Ban wani dade da fita a dakin ba ya falka a razane yana furta subbahanallahi yaya akai haka ya faru dashi baiji karan alarm ba ya tashi. Kallon inda nake kwance yayi bana dakin a zaton shi ina bayi ne lokacin sai da ya saurara yaji bana cikin bayi tashi yayi ya koma dakin shi bathroom ya nufa don dauro alawa. Maria na samu a kitchen tana aikin hadawa yara abincin tana ganina ta shiga gaidani da kwana na amsa mata cikin sakin fuska tare da tambayan ta mai take girka masu ne ? Tace madam burgur ne nake tosting don ko sunje da abincin basa ci har su dawo dan murmushi nayi don tunawa da baya wai yau nice har rayuwa ya nuna min nawa diyan cikina sun fara daukan darasi a duniya. Maria tace in koma kawai in kwanta zata gama komai a cikin lokaci nace ta barshi in karasa sai in dora abinda zamuyi breakfast dashi. Daki ta nufa don yiwa yara wanka da shiyasu naci gaba da aikina a kitchen din hankali kwance. Saidai aikin nake don ya rage min zafin danake ji a raina baiwai a cikin dadin zuciya nake ba lokacin. Ni kaina nayi mamakin kare aikin abin karyawan danayi da wuri koda na fito falo na samu yaran suna fitowa daya bayan daya dakatar dasu nayi sai sun karya tunda maria tace min basucin abincin da ake dan saka masu a jakka suje dashi naji hankalina bai kwanta da hakan ba sam. A daidai lokacin yaya ya fito a cikin shirin shi na da ya saka kwarjin shi ya kara fitowa sosai yana rike da labcoarth din shi sagale a haban hannun shi. Morning dad yaran ke fadi daya bayan daya daga inda suke zaune saman dining table din ina basu abinci. A hankali na dago kaina dan kalleshi tare da fadin ina kwana yaya kun tashi lafiya ya ban amsa yana shafan kan Abdulsamad dayakai inda yake tsaye. Nice ke fadin suyi sauri su shirya kada su makara bus ya wucesu sai naji yaya na fadin ni zan kaisu yau ina da abinda zanyi can. Suka shirya ya fice dasu gidan bayan ya zauna shima ya karya kummalo a lokacin ya fice da yaran. Na dan dade a zaune wurin da suka barni kafin in mike in shaga daga ciki wanka nayi na shirya na kara kwanciya don nima ban samu barcin kirki a daren jiya din ba. Ina tsaka da barci ya shigo dakin ya dan dade tsaye saman kaina yana kare min kallon yadda na dan koma don na dan fada ga cikin jikina da alama ban nisa sosai da haihuwa yanzu yace a ranshi. Ke zahra yace daga inda yake tsaye yaga ban motsaba haka yasa ya dan bubuga min kafa na bude idanuna dake tattare da barci a lokacin. Kallon shi nayi a cikin dakewa nake mashi sannu da dawowa lokacin na mayar da kaina saman filon da nake kwance. Yayi karfin halin hade fushin shi a kaina yace ki tashi asibiti nake so muje a dubaki, da sauri na bude idona nace a dubani banda lafiya ne halan. Yace ina son a duba ki don nasan bakije asibiti ba tunda kika dawo kasan nan ? Nace ni lafiya ta kalau banjin komai balle inje asibiti wani dube dube yanzu kuma . Kin dai ji abinda nace maki ban son raini hankali ana maki magana kina share mutum kamar wace bata san ciwon kanta ba. Dole na tashi ba don naso ba na shiga bandaki na kewaya na fito na sameshi a falo yana jiran fitowa na. Tunda muka dauki hanya ba wanda yai ma dan uwa magana a cikin mu har muka shiga haraban asibitin . Katina ya bika suka dauko file dina sai can aka kirani wanan karon ma likitan mace ce muka sama asibitin ta karbemu kamar ta san mu da farko. Bayan dan dube dube tana rubutu take fadin in rage yawan tunane kada yai min yawa ya shafi abinda ke cikina in dinga samun isashen barci ina yi sosai lokaci lokaci. Mukai mata sallama ta fada min lokacin haihuwa na muka bar office din don zuwa sayen magani. Muna cikin tafiya kamar yadda mukazo din na ba wanda yai magana a cikin mu sai naji yaja tsuki yana fadin. Haka kawai don sakarci mutum yajawa kansa ciwo a banza kiyiwa mutane hasara kallon shi nayi nace injawa mutane ko in jawa kaina. Tunda yanzu ba batun mu kakeyi ba kana zukin sabuwar amaryan da kake shirin daukowa inma wani abu ya sameni aikaina najawa ba wani ba. Eh ai kinsan lokacin dana aure ki nayi rawan kafa sosai ba dole yanzu itama wanan din in mata rawan kafa kan zan shiga inda ban taba shiga ba. Kashi ga mana yaya meye sabo a wurin da zai dameni ga wace tayi rayuwa lagos kowa ya sani ba abune boyayye ba idon ta ya bude da mazan lagos . Karki soma aiban ta min mata don ba zan lamunci hakan ba ga kowa kowa ya zauna a matsayin sa. Raina ya kara baci da wanan magana bace basai ka fada min yar uwaka bace don nasan dama nice bare a cikin ku ai. Zaki iya fadan komai yanzu lokacine zai nuna kasan idan muna da rayuwa daga haka yai shiru bai kara magana ba nima na juya na bashi baya na bar zancen. Muna shiga gida dakina na wuce ban tsaya falo ba ko gaisuwan da maria ke min sama sama na amsa mata shi. Shigowa yayi dakin dauke da ledan maganin da muka sayo yana miko min amsa nayi ba tare dana yarda na kalleshi ba. Zuwa yanzu ma dariya nake bashi don daukan abinda nakeyi a shirme yake kallon shi niko iyakar gaskiyana nake masa hakan. Ban kara fitowa falon ba sai bayan magariba na fito don yunwan da nake ji a lokacin. Yara na falo suna assingment tare da fauziya nake tambayan ta ko sun biya karatun da take koya masu saboda ban son su rasa karatun addini tare dasu don zaman mu a kasan turai da mukeyi babu daman kaisu samun karatun addini din. Sun biya a gurin yaya dazun da yamma kafin ya fita ta bani amsa daga hakan na wuce zuwa dining don jin ambatan sunan shi da tayi. Ina cin abinci ne sai ga kira a wayana nomban kasan sudan dana gani yasa ni daukan wayan da sauri. Mamuce a layin take kiran mu a lokacin gaisawa mukayi tare da tambayan kowa a bangarena nima na tambaye ta zaman sudan da mutanen su. Tace suna lafiya fauziya fa ta tambayeni nace gata naba yarinyar waya suka gaisa take fadawa mamu ta fara zuwa school a nan london. Bayan ta gama gaisawa da yaran har maria tace su ban wayan na karba ina fadin yaushe zaki koma Nigeria ne mamu ? Ba yanzu ba ta bani amsa sai naji tace Sayadi mai ya hada ki da mijin ki kike neman tayar mai da hankalin shi ? Shiru nayi a lokacin na kasa magana saida naji tace ashe baki da wayau sayadi ban sani ba ? Wani abin yace nayi masa ne mamu kada ki kawo min shegantaka tace min kishi haukane da har kike nema ki zubar da mutuncin ki a idon mijinki. Sayadi mutumi yana faman kokarin shi a kan ki dama mu duka shine zaki daga mai hankali don wani magana can da bai shafeki ba . Har kina kokarin jawa kan ki matsala bayan kin san halin da kike ciki akan kine farau kishiya koke ba wata kika shiga kika samu a gidan ba. Ke mace ina ruwa ki kin san donke za,ayi wanan auren shine don shirmen ki na banza zaki bari har a gane takon ki tun yanzu ? Me zai dameki da auren shi da zai kara koda shi ya gani yace yana so dame ya rageki dashi a zaman ku. Ba,a aure ke aka aureki ina wata kika shiga kika sama ta hana ya baki kulawa idan kika nuna rashin damun ki kece da pawer a wurin shi indai kin iya hakuri da gyara da ba mijin ki da yayan ki kulawa. Namijin bahaushe ana hana shi yawan aure aure ne idan yana da hali yin hakan . Shiru nayi ina sauren ta tace ki kwantar da habkalin ki Allah ya saukeki lafiya shine adduan mu. Tadai ta min nasiha karshe kakata ta karbi wayan itama nasiha tayi min kan in kwatar da hankali ina haihuwa in koma makaranta kamar yadda nace. Idan kin haihu zan ba kakan ki sakon mu na yan nan ta kawo maki ki dinga amfani dashi tace nace na gode grany kamar yadda muke kiran ta dashi. Muna gama wayan nayi shiru kafin in mike naji abincin dana zuba ya fita min arai ba zan iya cinsa ba kuma a lokacin saboda yadda nake jin zuciyana yai min nauyi. Na kalli maria da fauziya ina fadin maria kada su wuce tara basu kwanta ba ni zan shiga daki bana jin dadi jikina yau. Sannu suka fara yin mun ina amsawa da kyat don yanayina daya sake a lokaci guda ina shiga daki na fada saman gado da karfi saida naji dan cikina ya motsa min lokacin . Wani irin kuka na sake zuciyana cike da tsaban tunane kan sarakuwa da irin kiyayyan da take nuna min haka. Ina kwance ina kuka sai gashi ya shigo dakin ya dan tsaya yana kare min kallin yadda nake kwance na kifa cikina kamar babu komai a jikina yadda nake. Zama yayi a gefena yana fadin kin manta kina da mutum a cikin ki ne kika kwanta haka zahra yana magana in a cool voice kamar mai lalashina. Na dago fuskana dake jike da hawaye nace mai nayi maka haka kake son hadani da mahaifiyata yanzu kuma ? Don naga kina son wasa da rayuwan kine na kirata tayi maki fada saboda ni yanzu kin rainani . Don kina ganin muna mu,amula tare ko mai ban sani ba don ban taba tsamanin haka daga gareki ba wallahi. Eh zakace haka ai tunda kasan abinda kuke shiryawa kuyi min don kawai aga bayana a gidan nan. Yanzu hardani kike tunanen za a hada baki aga bayan ki idan naga bayan ki in gane me a cikin yin hakan. Kuka na kara wiwi yaja tsuki yana fadin to meye abin kuka a nan tunda kina ganin zaki kwatowa kanki yanci kuma. Ko zaki iya fadin wani laifin da nayi maki a cikin wanan magana ke kanki kin sani ban sanda wanan zancen ba sai ta sanadin ki na fara sani. Don dai kawai ki tayar min da hankali zaki tsiro da wasu halayen da bansan ki dasu ba a baya. Don wata can da dukkan mu bamu santa ba bamu kuma san halinta ba har yanzu ko tazo mai zata gane a wurin ki yanzu tunda kin gama min da zuciyana ke kadai na sani a matsayin mace ta gari da zanyi alfahari da ita. Shiru nayi ina sauraren shi don jin abinda yake fada yaci gaba da fadin ko mama ta matsa min sai na aureta ba a wuri daya zaku zauna ba don ba zan hada zuria,ana da wace ban gamsu da tarbiyanta ba. Dadin kalaman sa da watan kurciya yasa na yarda da kalamin shi na dan dinga sauke ajiyan zuciya a hankali ina rage sautin kukan da nakeyi din. Hakan ya bashi daman kai hannun shi ya rugumoni yana fadin zaki tayar min da hankali ga banza har yara sun fara maraicin farin cikin ki a cikin gidan nan. Haka dai yayi tayi min dadin bakin su na maza har na manta da komai na sake jiki dashi muna dan hira sama sama har ya samu ya biya bukatan shi. Washe gari ban iya fitowa ba har zuwa goma da wani abu ina daki sai danayi wanka na shirya na sauko kasa na samey su zaune tare da yara suna kallo yana zaune a tsakiyan su. Fauziya da mariya suna kitchen kasancewa yau ranan satine babu aiki ko ina fitowa yaran sukayo kaina suka dugumeni suna gaidani. Kansu na shafa daya bayan daya ina karba masu dan zama nayi muna hira dasu sai ga fauziya ta kawo min abin karyawa a inda nake zaune . Lokacin cikin jikina yayi girma sosai ya turo na kara zama wata mace abun kallo da alfahari ga wanda ya mallakeni. Na jawo abincin na fara ci kenan door bell din mu yayi kara da sauri maria ta mike a inda take ta nufi kofan zata bude . Gaba dayan mu mun mayar da hankalin mu ga kofan don ganin wanda ke shigowa gidan don bamu faye yin baki ba kasafai sai lokaci lokaci mukanyi bakin. Dan tsayawa tayi tana magana da wanda ke wajen haka yasa na mayar da hankalina ga abinda nake sha lokacin. Merry ce da yarta queen sai wata mace da fuskanta kamar na taba ganin ta saidai na manta a inda na san matar. Wanderful merry tace lokacin da ta karaso taja tsaye tana karewa falon namu kallon har yara da kowa lokaci guda. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:18 - 🀐🀐🀐: Yadda take tsaye tana kare muna kallon daya bayan daya nima haka nake kallon ta yayin da yaran suka mike suka nufi wurin shi sai sultana ne tazo inda nake zaune tana kokarin shige min a jikina. Daddy who are those kids ? Queen take tambayan shi tana karasowa gare shi ya dan shafa kan yaran ya kalleta yana fadin they are my kids allso. Wani irin buga kafa ta kama lokaci daya tana fadin No no no dad i am d only kid you have mummy said. She just say it to you she know a have those kids also, meet your twin's brother,s and your sister yana nuna mata sultana dake wurina ta haye min jiki don shigowan su. Da kyat na taushi zuciyana nace masu you're welcome anty have a seat ina nuna masu kujera daga gefen su suna tsaye har lokacin tana karewa yaran kallon mamaki don bata taba sanin yaran sun kai haka ba ashe. No ba zama ya kawo mu bayi na biyo mijina ne da kike kokarin kwace min daga gareni yanzu. Murmushi na dan sauke a fuskana ina nuna mata shi da hannuna cikin ko in kula ina kokarin tashi da kyat tace . What a surprise zan kara gani wani cikin ne kuma a jikin ki again ? Lalai kun kai macuta na kwarai dake da wanan mayaudarin daya cuceni sai kuma ta kasa karasa maganan da takeyi don hawayen da yazo mata a lokaci guda. Murmushi yayi a fuskan shi yace you can call me with any name you like na fada maki dama zan baki mamaki ai lokacin da kika tsiro yi min iskancin kan kin gama haihuwa dani . Fadane sosai ya kaure a tsakanin su lokaci guda ganin haka nayi wa maria data sume a tsaye wuri daya signal da ido ta fahinci mai nake nufi. Yaran ta fara kokarin ja ita da Fauziya zuwa dakin su don abin nasu yayi nisa sosai kada tazo suyi wani abinda ba daidai ba a gaban su. Abu kamar wasa karamar magana yana shirin zama babba don hayani sosai sukeyi tun bai daga murya har yakai yana daga muryan shi fiye da nata sunawa juna tonon asiri. Wani iri nake ji a raina don sai nake ganin hakan kamar rainin wayau ne zata zo har gida tana min wanan haukan haka . Ya kamata nima in nuna mata nima mace ce don haka ina da yanci kamar yadda take da yancin yin hakan har gidana. Nan da nan wani courage yazo min yadda nake jin kululun bakin ciki yana rufe min zuciyata lokaci guda. Look madam merry wanan abinda kika zo dashi ki bari sai idan ya koma can gidan shi kuyi shi can na fadi with full confidence a fuskana. Gaba daya suka juyo har shi suna kallona da mamaki fuskana babu sauki da gaskiya nake magana ina fadin. Merry duk wani girma daya dace in baki ina kokari inga na baki daman ki na wace ke gaba a gareni . Saidai yanzu na gane daga maki kafan da nakeyi yasa har kike kokarin cimun fuska har gidana. Banje gidan ki ba, ban sakaki a rayuwana ba kamar yadda kema baki sakani ba bani kadai banw kuma kishiyar ki a yanzu da zaki matsa min dani da diyana kina tayar muna da hankali haka. Na hade hannayena ina fadin na rokeki ki fita mun a rayuwa kamar yadda na fita a naki tun muna ganin mutuncin juna dani dake anty merry. Ki bincika kiji dagani har shi ga yanan auren mu ba auren son kan mu bane mukayi aurene na hadin iyayyen mu gare mu don haka nake daga maki kafa don nasan mun shiga rayuwan ki a lokacin da bai dace ayi maki haka ba. Kallon da take min ta mayar gareshi lokaci guda tana mamaki tare da fadin you have another woman again Omar ? No no no sai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai lokaci guda ta juya da sauri ta bar falon da sauri queen da dayan matar suka mara mata baya lokaci guda. Yana tsaye ya huci don bacin rai na dan kalleshi kawai na bar wurin zuwa dakina ba tare danayi mai magana a yadda nake jin zuciyana a lokacin. Ina shiga dakina kuka ne yazo min mai taba zuciya sai faman tunane barkatai da nakeyi kan wanan rayuwan da muka tsunci kan mu a ciki. Rayuwane garemu na tsaka mai wuya daga ni har yaya din da yaran mu sai yaushe salama zai samu gare mu wai a hakan. Ga hjy data sani a gaba ga merry da nata kalan matsala duk kaina ita da mijin ta yanzu kuma ana kokarin jefo muna wata ita kuma ban san da wanda zata zo muna ba dashi . Ga mama lami can gidan mu da ban san laifin da nayi mata ba take neman halakani ko wani lokaci ta samu sa,an yin hakan gareni. Da wanan tunanen har barci ya daukeni inda dagani har shi banga laifin mu ba a karshe don rayuwan mu mukeyi ba tare da hassadan kowa a tare damu. To mu me muka tsarewa mutanene suke kin mu haka wai saboda kawai munyi aure da yaya ne kome haka ke faruwa damune wai ? Ban fito daga dakin ba sai bayan sallah la,asar na sauko yana zaune tare da yaran suna tula karatun addini. Mummy you wakeup Abdulsalam yace min dan shafa kan yaron nayi ina fadin karatu kukeyi da daddy ? Zama nayi dan daura dasu ina sauraren abinda sukeyi muryan Fauziyane ya dawo dani daga tunanen dana fara a lokacin. Anty kici abinci tace lokacin da take aje min abinci a gabana na dago kai na kalle ta ina fadin na dai gane fauziya kina son ki batani dan kwanakin nan. Dan dariya tayi tare da fadin naga kamar kina kiuyan zuwa dining kwanan nan kici abincin sai nan yasa nake kawo maki nan din. Nace ashe kin gane fauziya bana jin dadin zama saman kujerun yanzu ban san me yasa hakan ba wallahi. Ta juya zata koma kitchen ya kira sunan ta ta juyo da sauri tana amsawa ta nufo wurin shi. Gani yaya tace tana dan rage tsayin ta don girmamawa Fauziya idan lokacin cin abinci yayi ki dinga kawo mata nata nan . Da tau yaya ta karba tana tashi daga inda ta dan rage tsawon gare shi a lokacin. Bude abincin nayi na fara zubawa a plate kafin inji yace dani zaki iya fita zuwa unguwa mu duba su Ramla kafin su tafi Nigeria bukin kannen Ahmed. Zan iya na bashi amsa ina kai abincin dana diba a bakina don in kawar da komai kamar yadda mamu ta koyar dani nace buki zasu ashe kwanan nan ? Yace eh bukin nasu ya zama na gidane ya kama dole yaje tunda shine babba kamar ni a gidan su. Ashe muma in bukin su Nafisa da murja ya tashi zamuje kenan ko yace gaskiya banyi alkawari ba don ba dole bane sai ku kunje. Dan kallon shi nayi kamar zanyi magana sai kuma na share naci gaba da cin abinci na a hankali mikewa yayi yana fadin zamu dan fita da yaran muje yawo. Allah ya dawo daku lafiya nace mai ina nuna mai ba komai a raina don har lokacin yana cikin dan guiltynes dani kan zuwan merry da yake dauka zanyi magana a kan yadda tazo muna har gida da cin fuska. Bayan fitan sune maria ta fito daga dakin su ita da fauziya da har yanzu itama bata iya sake jiki idan yana gidan. Zaman su a falon ya dan kara sani sakin zuciyana don hira muke sosai dasu don yanzu maria ta zama na jikin mu sosai. Nan nake masu hiran merry da dalilin da yasa nake dan daga mata kafa kan irin halin da take nuna min wani lokaci. Basu dawo gidan ba sai da dare wuraren karfe takwas har sultana tayi barci shine ya shigo dauke da ita a kafada ya shimfideta a falo saman kujera. Ya juya ya fita sai gashi yana shigowa da kaya niki niki a kwalaye da sauri su maria da fauziya suka tashi suna karba a hannun shi suna ajewa. Daga inda nake zaune na idar da sallah nake mai sannu da dawowa ya karba yana fadin wanan bataci komai ba taki sakin jiki a can. Wanan kan sai idan da maman ta aka fita take yarda ai fauziya ke fadi ku bata abinci taci yace yana kokarin hayewa sama zuwa dakin shi. Saida yayi wanka ya fito falon lokacin dagani sai Fauziya a zaune maria taje ta kwantar da yaran a dakin su. Dining ya nufa ya zauna yaci abinci yana gamawa ya mike yana fadin shi zai shege ke nan muka amsa mai da Allah ya bamu alheri ya shige. Ban dade ba na mike inawa maria dake kawar da kayan daya shigo dashi kayan yaran ne sai ciye ciyen yara daya kwaso masu. Wanka nayi na dan dade a dakina kafin in nufi dakin shi na tura na shiga da sallamana yana zaune yana duban computer har lokacin baiyi barci ba ashe. Samun wuri nayi na kwanta ba tare da nayi magana ba saman gadon shima bai tankani ba sai da ya dan dauki lokaci naga ya mike ya kashe laptop din ya nufi ban daki. Ya dan jima ya fito ya danyi abinda ya saba yi kafin ya kwanta kafin ya hawo gadon lokacin har barci ya dan fara daukana ko naji hawan shi saman gadon haka yasa na bude idanuna a hankali. Jinayi yace dani nasan baki barci bako zanso zuwa safe kimin list din abubuwan da kike bukata don zanyi tafiya next week. Maiyuyuwa koda zan dawo lokacin haihuwan ki ya matso ko ko kuma idan kina iya fita sai na baki kudin ki sayo abinda kuke bukata kafin ki kara nauyi. Ina jinsa ban yi magana ba shima bai jira na bashi amsa ba yace zanso ki hada da kayan yarinyar nan fauziya da maria don an dade ba a sai mata kaya ba tun tafiyan mu gida. Sai yanzu na gane nufin shi na fita da yaran da yayi dazun don ya sawo masu suturu ne ya fita dasu kasancewa ranan weekend ne. Zan duba ida na samu lokaci sai mu fita tare dasu na bashi amsa ina gyara kwanciyana. Nasan halin shi baya daga min kafa idan muna tare ranan ma kokarin lalabata yakeyi sai nace banjin dadin jikina tun rana nake jin marata yana min ciwo. Shine samun saukina dashi ranan amma idan ba haka ba komai bacin randa yake ciki bai hana shi sauke laluran shi gareni. Kwana biyu yayi a gidan mu kamar yadda yake a sharia muna zaune bayan karfe biyar sai gashi ya fito yana gyara agogon hannu shi yana fadin zanje wancan gidan. Ko bai fadi ba nagane gidan merry yake nufi zai tafi lokacin Allah bamu alheri na iya fada a fili na kawar da kai. Bai shigo gidan mu ba washe gari ga yaran suna tambayana yayi tafiyane nace masu eh baya garine. Hakan ya dan sa zuciyana kara jin babu dadi da zamana a gida yafi mun wanan zaman nake gani a yanzu da a gida muke zanyi baki koni kaina i fita zuwa unguwa. Ranan daya dawo duk yadda naso in boye bacin raina kan shere mu dayayi kwana biyu yana gari na kasa boye hakan gareshi. Don yana magana da kyat nake iya budan baki ina bashi amsa karshema ya sherini kawai ya kama harkokin gaban shi. Yana zama wayan shi yai kara ya dauka jin ya ambaci mama yasa na dan dago kaina na kalleshi kadan. Bayan sun gaisa naji yayi shiru yana sauraren wayan kafin ya mike yana fadin idan ta haihu din ai zan bugo makune mama wallahi bata haihu ba sai wanan watan da zai tsaya idan Allah ya kaimu. Yana fita falon yake fadin haka zuciyana ya ban don auren yarsu hjy ke tambayan idan na haihu badai don kulawa ba kam. Ya jima bai shigo ciki ba har lokacin dana bar falon zuwa dakina don ban iya kara jimirin zama falin lokacin. Bayan na gama komai na kwanta zuciyana ba dadi gareni sai faman tunane da nakeyi barkatai a raina kan hjy dashi yadda za a kwashe nan gaba ga zaman mu. Ni tsorona shine kada hjy ta aura mashi yar uwanshi ta saka ya fita batuna nida yaran don yarsu. Inzo ina ganin wullakanci don kudirin ta ke nan kawai a kaina yasa ta matsa da sai yayi wanan auren data lakaka mai yanzu. Duk da banda niyar zuwa wirin shi haka bai hanani shafe jikina da lotion ba da kamshi a jikina kamar yadda na saba yi kullun koda baya gari hakan yanzu ya zama min dabi,ata. Jin motsin an shigo dakin yasa na dago kai ina kallin wanda ya shigo min dakin. Shine yana saye da dan three quarter da farar singileti a jikin shi ya nufo bakin gado inda nake kwance yana fadin. Lafiya kike kikai saurin shiga barci yau lafiyata kalau ina dai son kadaicewa ne kawai na bashi amsa. Zama yayi bakin gadon yana fadin zancen haihuwan ki mam ke tambayana kokin haihu ban fada masu ba. Yaya ko ban haihu ba zaku iya yin bukin ku ai tunda sun damu in haihu kuyi bukin . Murmushi ya danyi yana fadin naki tunanen ke nan kuma don ta tambaya ? Kuka na fashe dashi ina fadin laifina guda yanzu wurin hjy don ina auren ka yaya da ban auren ka duk wanan kiyayyan da bai kai haka ba tsakani da ita sai dai ya tsaya iya su da mamu. Zahra me yasa haka kina a wanan halin kike kokarin daga min hanka kan maganan da bashi ba a kullun. Yaya dole hankalina ya daga da duk wani mai kaunata ina a wanan halin kuma ba,a barni na huta ba sai kokarin akeyi aga durkushewana ko yaushe. Idan don auren kane ba hannun hjy a cikin sa hakan bai taba damun rayuwana ko kadan don ba,a kaina zata zauna ba idan ta shigo. Amma kirkiri hjyn ku ke nuna min cewa tafi bukatan zaman ka da yar uwanka dani . Ni dai rokona gare ka shine kada ka wullakanta ni kana rawan kafa yadda akeson kaimin don samu sabon wuri ni yanzu mai tsohon wuri a wullakantani yadda akeso a ga kayi min. Magana ta ba karamin dariya taso bashi ba saidai ya daure kamar bai fahinci mai nake nufi ba ga zance na. Zahra yaushe kika zama hakane wai ban sani ba duk kinbi kin daga hankalin ki a banza kan wani magana da baida tushe can. Wani rawan kafa kikags inayi kan mace da zaki fara tunhumana kan wata can tun bata shigo ba. Ke kinfi kowa sanin wanan auren zanyi shine don cika umurni kawai ba don son raina ki koyi hakkuri kina danne fushin ki tunda har kin san da manufa aka sharada min auren nan. Kuka naci gaba dashi ins sauraren yana fadin wanan halin da kika dauko hakkuri ya kusa karewa a kanshi ina daga maki kafane don halin da kike ciki ba don komai ba. Idan sakarcin ki ya kaiki kika bada wani kafa da za,a sameki wanan kuma ke kika jiyo don't blamed me yana fadin hakan ya tashin ya fita daga dakin. Washe gari ina daki naji sako ya shigo min a wayana ban duba ba sai dana gama abunda nakeyi kudine ya turo min masu yawa na sayayyan da zanyi lokacin. Tambayan kaina nayi ni mai zan saye kuma kayan yarana ma wasu banyi amfani dasu ba. Koda na fito ya fita kai yaran shi makaranta sai maria me ke gyaran gidan lokacin . Mun gaisa da ita take fada min sun fita shida yaran ya kaisu makaranta. Na dauka da yai muna kwana biyu gidan zai koma gidan merry ne kamar yadda yayi a baya sai naga sabanin hakan. Haka yasa na gane merry bata garin kenan ta koma inda ta fito shima kwana biyu yayi tafiyan da yace zaiyi din. Mun fita gaba dayan mu zuwa sayayya mun sayo kaya mai yawa kamar ban taba kudin ba daya ban . Har watan haihuwana ya kama a lokacin ya dawo ya dawo da sati a wani dare na kuda ya kamani muka tafi asibiti abin mamaki sai gashi na kasa haihuwa kuma da kaina. Saida aka kara yi min aiki ake cire min yaro a cikina wanan dana haifa duk yafi sauran yaran kyau da girman jiki. Tuni wanan haihuwan ya mantar damu wani zancen kishiya can da muke badakala akai kowa hankalin shi a tashe sai yake ganin kamar zan mutu ne don wahalan da nasha a wanan haihuwan. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:20 - 🀐🀐🀐: Sai washe gari na dan san a inda nake a hankali na dan bude idanuwana da sukai min nauyi saboda wahala ina karewa dakin da nake kwance a ciki wanda babu motsin komai saina na,uran dakin dake aiki a lokaci. Sannu a hankali na gane a inda nake kwance dakin asibiti ne kokarin daga hannuna nayi ina shafan cikin jikina sai naji wayau. Hakan yasa na gane aikin aka sake min wanan karon ma ke nan shike nan ya tabbata ba zan iya haihuwa da kaina ba kenan ko me ? Turo kofa akayi alaman wani zai shigo dakin ke nan lokacin haka yasa na dan mayar da hankalina ga kofan. Nurse sai yaya dake bayan ta dauke da yaron a cikin showel ya rugume shi a jikin shi. Suna kallona nurse din ke fadin thank god ta tashi ma before time din ya cika da sauri yaya ya matso bakin gadon yana min sannu da jiki na amsa mai da kai kawai. Bayan hakan na dan kara lumshe idanuwa yace bude ido kiga baby din ki zahra namiji kika kara haifo muna wanan karon kuma. Dan murmushi nayi ina bude idon nake kallon su shida yaron daya karkato min shi yadda zan ganshi da kyau daidai fuskana. Zahra kinganshi kece ya biyo sak a kyau da fari ba ta inda wanan ya roki har yafi sultana kwaso kamanin ki sosai. Dan murmushin na sake yi ina rufe idona daga kallon yaron ba tare danayi magana ba. Nurse din ne ke fafin alluran bai gama sake jikina ba har yanzu su barni har nan da zuwa anjima idan na falka. Ban kara sanin kaina ba sai goma na dare lokacin na tashi da wani irin matsakaicin yunwa lokaci guda. Kokarin tashi zaune nakeyi naji muryan maria a kusa dani tana min sannu madam ya jikin nace da sauki maria sannu da kokari ashe kina nan ke nan tace eh oga ya koma gida don yara yace in zauna a nan. Zaune nakai ina fadin maria yunwa nake ji sosai da sauri tace me zakici madam tea kawai zansha na bata amsa. Da sauri maria ta tashi ta hada min tea mai kauri ta miko min a inda nake zaune tana kara yi min sannu har lokacin. Na amsa sai nake fadin ba zan iya sha ba ban wanke bakina ba maria da sauri ta karbi tea din a hannu na ta aje tana kokarin mikar dani tsaya nace ta bari zan iya ai Saida na wanko bakin na dawo na zauna na dan kurbi ruwan tea ban wani sha sosai na miko mata cup din da sauri ta karba ta aje gefe. Ban kwanta ba don na gaji da kwanciyan tace madam kina da sa,an haihuwa yaran ki duka masu kyau kamar ku wanan har yaso yafi twins kyau sosai. Oga yana ta murna sai bugama yan uwan ki waya yakeyi kin haihu murmushi nayi don jin abinda take fadi a raina kuwa cewa nayi wata kila ya gyara halinsa ne yanzu. Ko kuma ya bugane don asan na haihu don su fara shirin bukin su da suke jiran sai idan na haihu din suyi kamar yadda ya roka a bari har na haihu ayi. Tabe baki nayi da wanan tunanen yazo min a rai nace maria yaron yana lafiya ko tace lafiya yake sosai madam kullun sai an kawo shi nan ya dan sha dumin jikin ki. Duk hiran da take min sai dan murmushi kawai nake iya mata a lokacin saboda yanayin jikin da nakeji ba dadi. Kwana daya na kara aka sallameni daga asibitin bayan sunga na samu lafiya muka koma gida a gida duk wani kula da gidan yana kan maria da fauziya. Don ni ko falon bana fitowa ina daki ko wani lokaci don yanayin jikin nawa inda muke samun yan barka jefi jefi yan kasan mu da muke hurda dasu can suna shigowa barkan samun karuwan mu. Ina da sati daya da dawowa asibiti kwatsam saiga Nafisa a garin kamar daga sama don bai fada min zuwan ta ba. Ban yarda na nuna komai garesu daga shi har ita kawai dai na mata taro yadda ya dace aiwa bako idan yazo kamar babu komai a tsakanin mu dama. Zuwan ta yasa nake dan fitowa falo yanzu muna zaune muna hira take fada min aida hjyn su suka so zuwa saidai saboda zancen bukin yaya da za, ayi kwanan yasa basu zo tare ba. Ban yarda na nuna mata ko wani re,action ga maganan ba sai cewa da nayi gaskiya kan dole sai hjy tana kusa zaifi. Ta kara fadin ai mun dauka zaku zo sai yaya ke fadin sai kin kara jin sauki zaku shigo gaba dayan ku. Don shinema hjy tace ai in shirya inzo tunda ita ba zata samu zuwan ba kuma nace kin ko kyauta muna aida kikazo don ba wanda ya taba zuwa wurin mu sai yaya Aliyu koshi sau daya yazo kasan nan. Zaman mu ba wani matsala ina sati biyu cif da haihuwane ranan da dare hjy ta kira yayaa waya tana fadin Nafisa ta iso lafiya ko don naji baka kirani ba sai kuma zancen auren ka yaya najika shiru lokaci yana kara karatowa. Yace da wuri haka mama tace a fusace a wurin kane yake da wuri kada ka mayar dani wata bi can nina haifaka bakai ka haufeni ba umurni na baka dole kazo don karshen satin nan ne daurin aure. Don yanzu haka har an fara sha,anin buki kazo ko kada kazo yanzu ya rage naka kuma aure dai ba fashi na fadamaka. Amma mama har yaushe Zahra ta haihu haihuwan nan kuma fa kinsan aiki akai mata da za, ace na tsira buki yanzu ko suna bamuyi ba na yarin anan suna kawai aka rada mashi. Fatimar tafi wanan da taketa jiran kane bukatan ka kome na fadama wanan karon ba zan daga wanan ranan ba. Tana fadin haka ta kashe wayan ta tana huci shima kanshi ya dafe yana fadin innalillahi a fili. Sharan kiran Amma yayi koda abinda zata taimaka mashi a daga wanan auren har zuwa wani lokaci nan gaba. Amma na daukan wayan sun gaisa yake fadin Amma kinji fitinan da mama ke shirin jefani kuma a ciki yanzu ta kirani wai daurin aurena karshen wanan satin za,a daura. Yanzu mai mama take kokarin yi min a rayuwana ya take inyi da yar mutane da nake jinyar ta a nan ? Amma tace cikin yanayin damuwa muma haka wanan zancen yazo muna dazun nan mahaifin ku yake sheda muna zancen wai ashe bukin ya tashi. Kayi hakkuri tunda haka shine farin cikin uwarka aure in anyishi a tafarkin Allah ai alherine sadauki. Indai da zuciya daya sukai wanan hadin Allah yasa hakan shi yafi zama alheri ga rayuwan ku ga baki daya. Idan kuma bada zuciya daya ake shirin yinsa ba don wani kudiri nasune, Allah ya tarwatsa aniyar su. Ka kwatar da hankalin ka kai mata biyayya yadda sharia ya tanada muna tsaye gareku da addua akoyaushe insha Allahu sai alheri aruyuwan ku kaida iyalin ka. Yace yanzu Amma matsalan ai shine yadda zan tunkari Zahra da wanan zancen tana fama da kanta duk a sanadin haifar min yaro datayi. Kada ka zamo umar din mata mana mai sunan ka da jarumta akasan shi ko a inane kuwa balle kaida matar ka. Yace Amma na gode don dole yau in fada mata saboda kwana biyu kawai ya rage min ke nan in zo Nigerian. Amma tace hakana zaka daure ka fada mata Fatima inba ta canza ba zata fahince ka ai yace Amma na gode Allah ya shige muna gaba tace Amin ya kashe wayan. Saida ya gama duk abinda yakeyi ya shigo dakina ina zaune rugume da Abbana don sunan mahaifina Abubakar ya sakawa yaron. Muna kiran shi da daddy yayi sallama na dago ina amsa mashi ya tako har zuwa inda muke yana lakatan bakin yaron dake zukan nono hankali kwance. Fauziyace ta mike da sauri zata bar dakin yake fadin aida kin zauna abinki ba dadewa zanyi ba bata dai tsaya ba ta fice daga dakin kawai. Zama yayi dab da inda nake zaune yana fadin wanan kamahin fa haka yana kai hannunshi don karban yaron a hannuna. Murmushi nayi kawai banyi magana ba a lokacin yace zan shiga Nageria zuwa jibi zahra don mama ta kirani dazun da magariban nan nadai yake fada min wai zancen bukin shi ya taso zai tafi Nigeria ayi bukin. Allah sanya alheri na fadi ina kokarin dauko abu bakin gadona yadda na bashi amsan kai tsaye ya tsaya yana karemun kallo da mamaki a fuskan shi. Na juyo ina fadin munyi waya da mamu tace zatazo kafin ta koma gida ba wani nuna damuwa a fuskana yadda ya zata nake magana na freely dashi. Yace har yanzu ashe bata koma gida ba nace ko yanzu ina ganin ba maza ba don ko zata koma ina ga ba,a wanan gida na kawu zata zauna ba don tace gidan da zata koma ana gyaran shi a yanzu haka. Kara mayar da hankalin shi yayi wurina sosai yana mamakin abindana fada nace eh iyayyen ta wai sun turo an saya mata gida kano tace unguwa dayane dana kawu a nan cikin old GRA ne gidan yake. Amma ina ganin ko daddy baisan da wanan zance ba balle mama yake tambayana nace wallahi ban sani ba yaya. Yaji dadin yadda yaga ban nuna damuwana da auren shi ba a yanzu tun bayan dawowana asibiti ban kara tayar da wanan zancen ba muna zaman mu dashi lifiya yana kuma bamu kulawan daya dace mu samu a wurin shi. Don haka na tatara zancen na watsar a raina bayan zurfin tunanen da nayi tun zuwan merry gidan mu naji kalaman bakin yaya din naba kaina lafiya. Ya dan jima dakin muna magana kan zuwan Nafisa wanda sai wanan lokacin ne yake fada min yadda akayi tazo din. Don hjy ce ta nace kan dole sai wani nata yana gurin wanan karon don asan shima yana da yan uwa a duniya. Ai hakan yana da kyau na bashi amsa kaga yanzu tasan inda muke zaune ai yace gaskiyane hakan nagode da baki nuna komai akan hakan ba don nasan ba ku wani jittuwa a tsakanin tun gida saboda hakan ina kara baki hakuri ku rabu lafiya har lokacin da zata koma din. In dai nice yaya lafiya zamu rabu don kowa yasan halin kowa a cikin mu don haka zanyi hakkuri da ita insha Allahu. Kamar Nafisa tasan munyi wanan magana a kanta sai gashi ta fara tsiro da wasu halaiyan da zai iya kawo muna matsala a tsakani mu. Da yara ta fara a gidan mussanman ma fauziya da nasu baizo daya ba don kamar yadda basu kaunana harda su da suka fito tsatso daya haka suke nuna masu ko yaushe . Dan abu kadan zatayi yanzu zata hauta da zagi kamar zata duketa ina kokarin kawar da idona kan hakan don na kula da yarinyar har ta fara tsarguwa da hakan yasa idan tana falo sai ince mu koma daki tare da ita idan suna gida. Sai kuma abin nata ya koma ga yarana har dukan su takeyi da sunyi dan abu kadan zata kwashe yaro da bugu ko zagi. Ina iya kokarina wurun tausan zuciyana kan hakan don ba zanso taga wani bacin rai a wurina ba ko kadan don nasan da gaiya take hakan. Ban nuna mata hakan yana min ciwo sai kuma ta tsiro yi min hiran da auren da yaya zai kara kan irin shirye shiryen da gidan Amaryan sukeyi na bukin. Nan ka na bata amsa da fadin ana gabas suna yamma ke nan sai wanan uban shirin daga bangaren Amarya kawai ba ango. Kin sani ko duk shi bada kudin da ake wanan facakan haka nace balle kinsan ai dole ya basu tunda yana dashi. Don ko bai bayar ba hjy saita basu a matsayin shi tunda baza a bari aji kunya ba Allah yasa ya tura masu kudin dai. Haka nake biye mata mu zauna muyi ta hira kan bukin ina nuna mata ni ko a jikina hakan bai dameni ba. Ranan muna zaune take ce min wai ke Fatima ba zakuyiwa yaron nan suna bane kome ? Don naga har yana batun cika sati uku da haihuwa ba suna nace kinsan nan ba wani taron suna akeyi ba ai tunda ya je masalci aka rada ma yaron suna shike nan. Tace cabdi jam ina na taba ganin haka a rayuwa namiji ke nan fa yana can yana bushashan shi da amarya ya fita zancen sunan yaro da aka haifa mai. Balle samira tashin binni ne ita ta waye har ta gaji duk iya bude ido idanun su a bude yake tar. Shiyasa da akace wai a gida daya zaku zauna nace ashe akwai aiki don zama da irin su sai ka shirya don ba barin kishiya ta zauna lafiya da miji sukeyi ba. Nace Nafisa ke nan yaro ai gida yazo itako amarya ai bakuwace yanzu a ciki mu kinga gara dai a fitan kunyan bakin ido ko ? Sanan budewan idonta ai ga iya mijinta zai tsaya shida ya aje ta all what ni wayen ta bai taba damuna ba a yanzu fatana mu zauna lafiya dai. Wai ke fatima wata irin mace ce haka baki ko dan gwada kishi irin na mata ko kadan duk inda aka fito da zancen sai ki tare. Mezanwa kishi Nafisa mijina yana tsaye a kaina da diyana harma da yan uwana idan nayi haka ai na zama butulu ke nan . Sai naga tayi shiru ta bata fuska ta shigo dogon nazari kamar mai tunanen wani har muka bar wurin bata kara wani magana kwakwara ba a ranan. Ta dauka maria bata jin hausa don ban dadewa a falin nake shigewa saboda jegone a jikina don falon ko yaushe a cikin sanyi yake sosai. Waya ta dauko bayan shiga na tana waya da hjy su maria na kitchen tana jin duk abinda suke fadi a falon. Maria ta labarta min duk abinda taji Nafisa na fadawa uwar ta a waya game damu har da irin daulan da yaya ya sakar muna a gidan da yadda mukejin dadin rayuwa a nan. Tace komai tayi min cikin abinda ta kitsa sai inyi kokarin kare yayan da kalamai masu dadi sam ban yarda naga laifin shi ba balle ta samu kafan kulla min shirin su nagaba. Saidai bataji abinda hjyn ke fadi a nata bangare maria tana fada min wanan magana hankali a tashe. Maria kin san Ogan gidan nan zai kara aure gobe shine plain din su na zuwan Nafisa kanwarshi nan don ta tayar min da hankalin da zan samu sabani da mijina. Shine hikimar hjy na turo min nafisa a nan a matsayin ta na yar leken asirin hjy don tazo taga irin rayuwan da muke anan asan hanyar da za,a samu nasara a kaina. In Allah yarda saidai suyi kunya nowarder take muna abinda taga dama da izza a gidan nan wanda koke matar gidan baki min shi. Zataci abinci tabar plate ko cup a wurin kamar ba mace ba zata cire kaya ta barshi sai idan nina shigo dakin na dauke a kasa ko saman gado. Ba karamin dadi najiba da kika raba Fauziya da dakin nan yanzuma yaran nake son kwanan su ya dawo nan wurin ki har lokacin da zata koma. Duk da na kula da hakan nima yana bata min saidai don alkawarin dana dauka a raina harta koma inda tafito. Tunda maria ta fadi hakan nasan akwai abinda takewa yaran wanda bai dace don haka zanbi shawaran maria din a cikin hikima kada ta illanta min yara wurin hakkurina . ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:20 - 🀐🀐🀐: Yadda hjy taso hakan bai samu ashe don yaya bai samu isa ba sai bayan sun gama shagalin bukin su wanda haka yaso jawo matsala a tsakanin su da uwar samira amarya. Hjy ita tai uwa tayi makarbiya ga komai sai yan uwan shi da suka tsaya mai dan dole da yan abokai kamar su Nasir suna tsaye a wurin bukin. Hjy bata samu dawowa gida don can ta tare a gidan namu duk da part din mu na ainihi yana rufe sai wanda aka gyara daga baya don Samiran ta zauna a ciki. Wanda hjy bata so haka don cewanta namu part din yafi kyau da tsaruwa da komai dole a ciki samira zata samu daki itama. An buga da yaya yaki yarda da hakan yace haka ya tsara abinsa babawa anya kana da niyar adalci a tsakanin iyalin ka ? Hjy ta tambaya yace muddin zanwa sauran adalci har suka zauna dani zuwa yanzu itama zan mata ai kamar yadda nakewa kowa saidai idan halinta ya bambamta dana sauran wanan kan ba zata ji dadina ba. Duk wanan a waya sukaita musayan yawu da mahaifiyar nasa hakan yasa ba,a bude wanan part din namu ba. A gajiye ta dawo gida washe gari koshi tana gudun ta kara kwana kawu yai fada don taso sai ya Umar din ya iso gidan taga zaman su zata koma gida. Da hjy maryam suka ci karo tana kwasan shaya a waje tayi mata sannu da zuwa ta amsa tana shan kamshi kamar yadda ta saba a kullun. Tun daga nesa ta hango kofan a datse da katon kwado abin ya bata mamaki sosai na ganin hakan a kofan part din ta. Bata yarda da abinda idon ta yake ganan mata ba sai data karaso kusa ta taba kwadon taji kofan a rufe . Juyawa tayi tana tambayan hjy maryam daga nesa wa ya rufe min kofa haka da wanan kwadon ko Nura ne da cewa dan autan ta. Wallahi ban san an rufe ba sai yanzu da kike magana Nuran baya ciki ke nan hjy maryam. Yana ciki za,a rufe dashi muryan kawune ya katse masu magana yana fadin nine nan na rufe kofana . Sai ki koma can inda kika fito tunda kin cika burin ki na kimin bakin ciki akan taimakon danki da nayi kike dauka da wani manufa nayi mai aure da fatima. Har kika dauka yimai aure ta fanin ki shine zaisa ki fashe zafin abinda nayi maki . Banyi tsamanin zaki manta da alkwarina ba akanki ko har kin mantane nace Amaryan ki na shiga dakin Faruq ke kuma kina fita naki dakin da sunan aurena. Alhamdullahi Allah ya cika maki alkawarin ki nima kuma ya cika min nawa Allah yaba da zaman lafiya yana fadin haka ya dogara sandan da yake bashi kariya ya bar wurin. Kallon mamaki duk wanda ke wirin yake bin kawu dashi ya wuce abinshi cikin halin ko in kula garesu. Wanan mutumin mai yake nufi da yin haka dayan kanwar hjyn da suka kwaso ganiman bukin sunzo dashi su raba take fadin haka. Duk abinda yake nufi a shiye nake da shi tana fadin hakan ta juya ta nufi kofan Amma a hasale. Ta samu Amma na ggugan goro a jikin wani dan kwanko a hannun ta ta shigo da sallama a hasale. Bayan karba mata da Amma tayi tana fadin kun dawo ashe bata bata amsa ba sai cewa tayi na dawo na samu Alh ya rufe min kofan part dina yanzu. Garin yaya kuma ya rufe maki kofa dakin ki takai zaune don yadda take ji kafuwan ta ba zasu dauke taba a lokacin kamar ba ita bace ta dawo da farin ciki yan mintutukan da suka shude. Wanan halin naku da girman ku kuna abinda yara ba zasuyi ba a gidajen su yau lafiya gobe fitina wanan hali naku ya isheni a rayuwa. Tana kokarin yunkurawa take wanan magana tana fadin ina shi yaron nan yana gidan tace yana nan yanzu ya gaya min shi ya rufe kofan don haka yai alkawari. Amma dake shirin fita taja ta tsaya wuri daya tana fadin ke nan alkawarin ku kowa ya ciki kuke nufi. Shiru hjy tayi don bata da amsan da zata ba tsohuwan a lokacin sai kuma Amma taci gaba da tafiya ta nufi waje. Mama hadiye ta biyo ta a baya tare da hjyn part din kawu ta nufa yana ganin ta yana zaune a kasa saman kafet ya hada hannayen shi yana fadin don girman Allah hajiya kiyi hakkuri ki barni da matan nan tunda iyakana take son nunawa duniya. Jin da Amma tayi ya hadata da Allah yasa takai zaune daga inda take tsaye tana fadin wanan rayuwa da kuka dauko dame yai kamane haka a gidan nan. A haka rayuwan yayan ku da iyalin ku kuke son suyi koyi daku kuna wanan halin kullun a cikin tashin hankali irin haka ? A daidai lokacin hjy ta shigo dakin ya kalleta yana fadin me kike ma har yanzu a gidan nan na fada ba zan sake fada ba na yanke igiyan aurena daya a kanki wanan abin ya kare hakana tsakanina dake jimmai. Alh kana dauka idan kaimun haka zan damune yace don nasan baki damuwa na tabbatar maki da hakan yanzu. Hajiya wanan ba yar mutunci bace ki koma part dinki zaifi don bata sam Annabi ya faku ba har yanzu duniya sabuwace a gareta ita. Sam bata tunawa da mutuwa a tare da ita har abada yana fadin haka Amma ta mike tana Allah ya kyauta don bata iya tsayawa wurin kuma. Tun Amma bata karasa fita ba hjy ke fadin yadda ka sakeni akan wanan yarinyat nima haka zan saka dana ya sake yar taku inga ta tsiya. Kawu yace bissimillah karki fasa abinda kikai niya ki gani da ita da danki wanda zai wahala a yanzu. Wanan magana da kawu yayi shi yakara konawa hjy rai sosai tana fita a kunyace tacewa yan uwanta biyu suzo su fice a gidan. A,a anty kada ai haka gara dai kiyi hakkuri ku sasanta zaifi ace kinyi fushin zuciya kin tafi tare damu. Rakiya kina son in zauna inga wullakanci a gidan nan fiye da wanda Alh yaimin a yanzu gaban mahaifiyar shi. Gaban wanan tsohuwar Alh ya furta ya yanke igiya daya a tsakanin mu ni Alh zai furtawa hakan saboda yar agolan gidan shi. Yasakeki sukace cikin mamaki hanyar fita gidan ta tanufa kai tsaye suka mara mata baya hankali tashe duk jikin su yayi sanyi ga abinda ya faru. Suna fita take fada masu yadda yayi alkawari tun farko idan har tasa Umar yayi wanan auren ranan itama zata bargidan. Ajiyan zuciya hjy Rakiya ta sake kafin tace yanzu ina muka dosa daga nan don dai ba zamu nufi gidan yaya ba ko kawu da wanan magana mara dadin ji haka. Don gaba daya laifin mu zasu gani kan hakan a karshe don sai su dauka da zugin mu hakan ya faru yanzu. Nima tunanen da nakeyi ke nan yanzu gidan babawon zamu koma in zauna har ya iso garin nan . Saidai yadda sukai min ko su haka zan saka sadauki yaiwa yar tasu da suke ganin ta kafu a gidan. Sai naga bayan wanan yarinyar ina fada maku dani Alh ke wanan wasa bai karkare sanin halina bane har yanzu. Yan uwan duk abin duniya ya ishe su a rayuwa don basu ji dadin kalman sakin da kawu ya furta mata ba haka kai tsaye. Gidan sukaje kamar yadda tace saida sukai horn yafi a kirga kafin maigadi yazo ya bude masu kofa su shiga. Samira da ke zaune da kawayen ta da yan uwanta sai ganin hjy sukayi sun dawo tayi saurin mikewa tsaye tana tambayan hjy lafiya naga kun dawo kuma ga kaya haka. Bude muna wancan dakin mukulin shi yana cikin keys din dana baki hjy tace kai tsaye. Ba musu samira ta dauko key din tana gwadawa dakin ya bude suka shiga nan suka barta tsaye tana mamaki su kuma. Sace jiki samira tayi zuwa daki ta kira mahaifiyar ta tana fada mata zuwan hjy gidan tana fadin da alama umma a nan take shirin zama tare damu don da gani babu lafiya. Wani ashar hjy sabuwa ta lailayo ma hjy jummai tana fadin jummai fa bata da wayau sai na gyara mata zama idan hakane. Ta kamanta dai gidan dantane ko shiyasa ta kwaso kafa tazo maku gida gotai gotai da ita don bata san kunya ba. Shima shashan dan nata mai daukan kan tsiyan banza me yake jira har yanzu bai shigo kasan ba mu fara dashi. Samira tace nima umma abinda ke damuna ke nan rashin zuwan shi har yanzu kasan . Hjy sabuwa tace zai gama kwanaye kwanayen shi ai yazo hannun mu kwana nawa zamu gama dashi . Karamin kudi na kashe kan wanan auren kafin in samu ya yuyu na uwarshi mai sauki ne ban dauketa wata tsiya ba can. Aiko zargin su ya zama gaskiya don sai gashi hjy ta kwana daya biyu a gidan sai rana na uku yaya ya iso Nigeria a cikin dare . Idan ranshi yayi dubu a bace duk suke saboda labarin abinda ya faru da mahaifiyarsu da Aliyu ya kira yana labarta mashi. Shiko habib cewa yayi gwada Alh ya nuna ma mama hakan don ni banga laifin shi ba tunda ya fada mata tun farko taki ji. Itama hjyn sanin halin habbib din yasa bata kirashi sunyi maganan ba sai Aliyu don tasan ba zataji kalman dadi a bakin shi ba. Don shi a tsatsaye yake tun farko gaskiya komai dacin ta baya gudun fadan shi ko ga waye. Direct part din mu ya nufa yai wanka ya samu wuri ya kwanta bai ko tsaya neman wani abu da zaici a cikin shi ba yana Allah Allah gari ya waye mai ya fito. Samira bata tashi sanin yazo garin ba saida safe yarinyar da suke zaune tare take fada mata taga sabbin motoci a gidan kuma wancan dayan shi a bude yake yau. Da mamaki samira ke kallon ta tace ki koma ki gani ko waye ya bude idan ba wanan yar hawan jinin data zauna muna bane nan. Samira uwarta ta kira take fada mata abinda yarinyar tazo ta fada tace ke me kike jira baki fita kin gani ba. Barin gaya maki kada ki tsaya wanan shegen sanyin jikin naki yanzu har su samu sallon takaki a gidan. Ita wacan jikan bakaken larabawa mai shegen wayau an gaya maki haka takeyi dashi data mallakeshi ko uwarshi bata iya kwabashi akanta. Don idan ba kinyi da gaske ba kinyi da gaske kika mallake kowa tun yanzu ba sai kin zama bora a gidan in fada maki. Gida dai tunda mun samu kin shigo da karfi da yaji don haka saiki dage ke kuma yanzu kiyi duk abubuwan da muka karbo mu samu mu mallake yan baza ga baki daya. Haka dai uwar tayi ta zugata da mugayen shawara har taji wani karfin gwiwa yazo mata lokaci guda . Suna gama waya da uwar ta mike cikin karfin gwiwa ta nufi hanyar fita daga part din ta suka hade da yarinyar data turo din. Da sauri yarinyar ke fadin wallahi anty ins ganin maigidan ne don naga yan aikin gida suna ta shiga gaidashi. Babu abinda nakeyi sai juyi nake a gado tsakiyan yarana dake kwance suna ta barcin su hankali kwance. Kallon fauziya dake kasa kwance nayi don gadon bai isar mu ta kwanta a kasa ita. Itama sai barcin ta takeyi hankalu kwance abinta gyara kwanciya nayi inaci gaba da tunane a raina. Yanzu yaya yana can yana morewa rayuwan shi da amarya ni gani nan da yara ina jinyar jikina. Wasu hawaye ne suka zo min lokaci guda masu zafi sai dan jaririna ya motsa ina jin yana kuka na kasa tashi in kamashi a lokacin . Zubur naga Fauziya ta mike daga batcin da takeyi tana fadin anty yaro yana kuka bakiji bane. A hankali nace ina jin sa Fauziya tashi ne ban iyawa kawai da sauri ta mike takai gareshi lokaci guda ta dauko shi tana dan jijigawa. Yaron yaki shiru ta nufoni dashi tana mika min dole na gyara na karbe shi na fara bashi nono yana ja. Zama Fauziya tayi a bakin gadon tana fadin naso in dauko littafina a daki sai dai ban son komawa dakin don lokacin Anty Nafisa batayi barci ba. Wanan ai na rasa me take nufi daku haka a gidan nan na bata amsa tace dazun naji tana waya da maman su harda kukanta tana fadin mama ya sakeki fa ? Fauziya karde ince kawu ne ya saki hjyn su don dama ya fadi haka idan ta matsa da zancen auren nan . Ke nan hakan ya tabbata ke nan ko dama ai sheri karene maishi yake bi akace idan tayi don ni tun yanzu ta fara girban abinta ai. Saidai duk abinda ya faru zamuji ne muna zaune ai maganan duniya baya boyuwa yanzu. Mun dauki lokaci muna hira sosai da Fauziya yarinya mai wayau tana kwantar min da hankali a matsayina na yar uwanta. Washe garine da safe bayan yara sun tafi makaranta mun karaya na koma dakina don ban son yawan hayani ga Nafisa ta sake volume din tv dake aiki ya karade falon da kara lokacin. Nayi barci na tashi sai ga kiran yaya a wayata banyi saurin daga wayan ba har ya katse ba a jima ba saiga wani kiran ya kara shigowa shine kuma again. Na dauka cikin basarwa ina kokarin nuna mashi ba komai a bangarena nace ina kwana yaya don nasan safiyace can a lokacin. A daidai lokacin da Samira ke shigowa ke nan daga part din ta taji yana fadin Zahra ya kuka tashi ya yaran. Ja tayi ta tsaya tana sauraren shi har lokaci bai dago kai ya kalle ta kamar baisan mutum yana gurin ba a lokacin. Har muka gama waya tana tsaye a kanshi sai zafi takeji a zuciyar ta na yarda taga yana hira dani a cikin dadin rai duk da a waya muke maganan. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:20 - 🀐🀐🀐: Yana gama waya dani ya dago kai a hankali yana duban wanda ke tsaye a kanshi lokaci ganin Samira da take tsayen cikin yanayin damuwa tana sauraren shi ta, sauke ajiyan zuciya tana fadin ashe ka iso garin bamu da labari. Ke haka aka koya maki a gidan ku idan zaki shiga wuri kada kiyi sallama ko gaida mutane ya fadi yana kallon ta ido cikin ido na dan lokaci. Kafin ya mike da zumar barin falon don hankalin shi yana gun nahaifin su tun daren jiya da yasamu labarin abinda ke faruwa tsakanin shi da mahaifiyar su wanda baiji dadin hakan ba. Don yanzu abin kunyane a garesu ace da girmasa iyayyen su zasu kashe auren dake tsakanin su shekara da shekaru suna tare ana hakkuri da juna. Balle yanzu data dalilin shi duk yake ganin wanan abin ya faru haka a tsakanin su don hjy ta kasa yiwa mahaifin shi biyaya kamar yadda akeson ko wace mace ta kasance da yiwa mijin ta biyaya koda ya kasance itace da gaskiya ga magana. Dolene na miji ya kasance shine mai juya gidan sa da iyalin sa ba wai mace daya aje tace sai abinda ranta ke so dole za,ayi ba. Ya rasa mai yasa hakan yake kasancewa a tsakanin iyayyen nasu ko wani lokaci irin hakan baka taba jin fitina tsakanin shi da hjy maryam ko maman twin's irin haka mai karfi saidai a tsakanin iyayyen nasu biyu kawai akeda wanan matsalan a gidan. Ko dai sunayi dashi ba mai karfi irin hakan da yake yawan faruwa a tsakanin mahaifan nasu ba . Dear bansan ka shigo ba sai yanzu shine abin ya bani mamaki har na manta da ban maka sallama ba ashe tana magana tana wani kashe mai idanu irin na goggagun mata yan bariki. Zai bude baki ke nan yayi magana sukaji sallaman hjy daga kofa wace itama sai lokacin ta san da isowan shi garin ashe itama ? Wani irin bacin rai ya saukama Samira a rai lokaci guda tana fadin me kuma ya kawo wanan matar nan yanzu a daidai lokacin da zan fara dana tarkona gunshi ? Cikin kula da ladabi yake fadin mama yanzu nake shirin zuwa inda kike ai don jiya da dare Habbib ya kirani yana fada min matsalan da kuka samu da daddy. Da sauri hjy tace amma shi habbib din ya kasa kirana muyi maganan sai kuma yake iya fadawa wani ko idan ka fito ina jiran ka a waje tace tana juyawa. No mama ki zauna muyi magana wanan ai tasan nan din ba part din ta bane so zata iya fita ta bamu wuri mu gama. A take Samira ta kwabe fuska tana mashi kallon mamaki tare da fadin zaka zo hannu sai ka rena kanka a wurina idan nice. Ta juya da karfi ta bar falon alaman bata so hakan da yai mata a gaban hjyn ba ai wanan sallon har hjyn taga wallentane a gidan. Tana fadi a ranta kaida kanka zaka sameni har dakina mu zuba ni dakai sai lokacin take jin bakin cikin rashin jan ajin da batayiwa kanta ba don ko wace amarya ai angone mai binta har dakin ta. Samira na fita hjyn ta sauke ajiyan zuciyan tana kallon dan nata tare da fadin zanso kabi wanan yarinyar a sannu don Allah. Baiyi magana ba sai cewa yayi mama me yakawo haka har daddy ya rufe maki kofa da girman ki aka tozarta ki a garin nan haka ? Kaima ka sani ai zancen wanan auren naka danayi tsaye akayi shine mafarin zancen da sauri ya dago kai yana fadin aurena kuma mama garin ya har haka ya faru kuma ? Dama ai ya fadi idan har na matsa aikai wanan auren in san da sanin na bar nawa dakin ke nan sai dai idan ka manta hakan daya fada a baya. Mama kin san da wanan maganan kika yarda har akai wannan auren da yarinyar nan ? Kin kwammace ki bar dakin ki saboda ki farauta ran su ko ki batawa wasu rai kawai ? Wanan wani zance kakeyi haka idan badon kana auren yarinyar nan ba har Alh ya isa yace kada ka auri yar sabuwa a gidan nan. Mama ya isa har ya wuce duk abinda kaji daddy yai magana a kasan sa wanan abin abin dubawane ga mutum. Ba wai don ina auren Zahra daddy zaice kada na auri wanan yarinyar ba sai dai don abinda ya hango a auren. Da zaice don ina auren zahra kada in kara matane ai da yace in rabu da merry don bata dace dani da addini na ba . Nafika sanin halin mahaifin ku babawo banda wanan abin baida wani abinda yake da hujja dashi kan auren nan. Tunda sun riga da sun gama dashi ko baida tacewa kan maimuna da diyan ta yanzu ga kowa. Har da maimunan bata kasan nan tana da laifi kan wanan maganan naku ke nan don Allah mama ki daina wasu abubuwa yanzu don girma dada shigan ki yakeyi a kullun . Bamu jin dadin irin wanan abinda ke faruwa a tsakanin ku da daddy ko da yaushe. Zanje wurin daddy mu zauna dashi don girman Allah mama kibi wanan maganan a sannu a samu a sasanta wanan maganan hakana din ba zamu so har mutane sukai ga fahintar hanlin nan da kuke ciki ba keda shi. Na dade da fahintar laifina kuke gani kan matsalan dake faruwa atsakanina da Alh a yanzu. Shiyasa banjin zafi idan wani yaji zafina kan haka tunda ance ita mace ba zata kwaci yancin ta ba don tana mace. Mama kiyi hakkuri ba hakan nake nufi ba nidai rokona shine ki don Allah ki kwanta kibi daddy a samu a sasantaku ki koma dakin ki ya janye sakin daya furta a tsakanin ku. Don kinga ita kanta maman twins da suka samu matsala kan gidan da iyayyen ta suka sai mata zata zauna a ciki yace bai yarda ba. Da sauri tace gida fa kace aka sayawa maimuna koka saya mata dai. Da sauri yace subbahanallahi mama ko banson albarka ai zan so fita kunyan jama,a ban sai maki gida ba zanje sayawa uwar matana saboda neman me zanyi hakan mama ? Na sanan maka din komai zaka iya kan wanan shu,umar yarinyar a yanzu da take ganin ta daure ka gaba daya. Murmushi yayi yana girgiza kanshi a hankali yana fadin haka dai kike gani mama amma ni ban yarda mace ta shige min gaba ba ko kadan. Ban dai yarda in tauye hakkin mutum da yake a kaina matukar ina tare da mace bana tauyeta ko shiga hakkin ta. Hjy tace yanzu yaya zancen gidan ita maimuna ake ciki Alhn ya yarda da zancen ne ko yaya ? Bai yarda ba ita kuma ta kafe akan ba zata yarda ta dawo wanan gidan ba kuma suma iyeyen nata suka biye mata. Shine yar nata ta kirani tana fada min abinda ke faruwa a tsakanin su wallahi mama kira daya nayi masu na basu hakkuri suka amince min da hakan. Yanzu babu zancen gidan ke nan ko yace gida na nan a matsayin nata za,a zuba mata yan haya a bangare daya don su dinga kula mata da gidan. Wani irin bakin ciki da hassada ne a lokaci daya ya rufewa hjy zuciya tana kara jin tsanan mamu har kasan ranta sai anyanawa take a ranta idan ba tayi da gaske ba wanan matar zata bata mamaki nan gaba. Muryan dantane ke fadin don haka mama kamar yadda taga darajana tabi abinda na roketa kema ina rokon ki da duk abinda daddy zai fada kiyi hakkuri dashi a zauna lafiya . Bata samu furta mai komai sai hakkuri yake bata cikin kwantar da hankali da taushin murya yadda zata samu fahintar shi. Zama nayi yau na dauki kwalliya mai daukan hankali don yau ina son kaiwa yan uwan mamu ziyara tunda na haihu ban fita daga gidan ba sai yau duk dako yaya bai hanani fita inda nakeson zuwa. Nafisa na zaune muka fito falon tun ina saman steps take bina da wani irin kallo har na sauko kasan inda suke zaune. Da sauri fauziya dake fitowa daga dakin su ta zo ta karbe Abbati a hannuna tana fadin wai anty yaron nan fa girma yake karawa a kullun. Tana zama a gefena da yaron a hannun ta take fadin hakan lokacin duban yaron Nafisa tayi take fadin na rasa wa yaran nan ke kwasowa da kyau haka kamar diyan larabawa dasu. Kallonta nayi ina fadin Nafisa ke nan gashi kin fada dole suyi kama da su tunda suna da jinin su a gauraye dasu. A daidai lokacin ne maria ta fito da sauran a cikin shirin su tsab suma ta bisu da kallo tana fadin wallahi dole yaya yaji dake har ransa ko don wa yan nan yaran Fatima. Yara haka sai daukan ido a duk inda suke shiyasa nake fadawa shiyasa nake fadawa hjy ta bar yaya da iyalin su a kullun ko wani ahali ba a son rasu sukan rabu ba indan kaddara ta gitta masu. Yanzu gashi ke baku rabu da yaya a yadda take so ba yanzu gashi batayi nasaran rabaku din ba ita da shekarun ta daddy ya hasale mata auren shi a kanta. Na dago kai ina fadin Nafisa kin san abinda kike fadi kuwa yaushe wanan magansn ya faru kike furta hakan yanzu. Wallahi Fatima anty salma ta dade tana min nasiha kan mu bar biyewa halin mama don shi kanshi yayan mu ba zaiji dadin halin da mama take sa muna nuna maku ba tare da laifin komai a garemu ba. Ita dai anty salma ai ta huta da bata tsaya bin halin mama yanzu kinko ga ta zauna a dakinta lafiya ba wani tsangwama a yanzu. Ga yaya ya ttaimakawa rayuwanta yanzu idan nayi magana ko ina son yayi min wani abin sai yace dani inyi aure kamar yadda yan uwana sukayi. Fatima yanzu ta ina zan fara neman wani mijin Manir ne mun bata dashi kin sani tun kuna can ya dawo mu shirya mama tace bata yarda ba don ba zata bari taji kunyan mutane ba tunda har ya iya bata min suna a gaban kowa. Amma har idan kina son shi har yanzu Nafisa mai zai hana ki fadawa yayan ki don nasan yaya zai fahince ki idan kin fahintar dashi gaskiyar maganan. Shine kawai zai iya shawo kan wanan maganan har kowa ya yarda da shawaran shi in Allah ya yarda don yaso ace an hada auren ki dana Murja a lokaci guda. Tun wanan dan hiran da mukayi da Nafisa dana lura abin duniyane ranan ya dameta tana neman abokin shawara har ta dan sake layin hjyn su garebi. Munje gida anty don gaida ita tunda ta dawo daga kasan su bamu samu zuwa ba sai itace ma tazo inda nake dana haihu ta duba jikina. Ina tambayanta yaushe su mamu zasu koma Nigeria ne take fadin suna son sai sunyi aikin hajjin banan nan a tare da ita zasu mayar da ita gida. Nafisa kan sai mamakin irin arzikin su takeyi ga gidan babba ko ina yan aiki ne birjit a gidan kamar suna zaune a kasan su . Ni kaina lokacin dana fara ganin su haka nayi mamakin abinda yasa har ta bude saloon ake mata aiki. Take ce min ai ba a son mace ta zauna ba dan inda kudi yake shigo mata ko yayane ya kamata ace mutum yana da dan sana,an rufin asirin shi don ba komai ne zaka roki namiji ba ka samu kai tsaye. Yini mukayi sosai a gidan mun sake jiki don irin yadda matar gidan take jan mu a jiki gaba dayan mu har Nafisa. Da yamma muka dawo gida bayan mun dan kebe da anty ta van sakon da dama nazo karba wanda kakata ta bayar a kawo min ta hannun su. Baya nayi wanka na kwanta ne sai kuma tunane ya dameni don yau kusan kwana biyu ke nan banji kira daga yaya ba. A take zuciya mai nashe nashe ta nasa min cewa ina zai kiramu yana can yana cin amarci da amaryan shi shike nan ya gama da mu nan ke nan . Naji wani irin kishi ya rufe min zuciyana kamar yadda ko wace mace take jin wanan yayin da mijin ta yai aure. Da kyat na samu na yaki zuciyana kan irin yadda nakeji din a raina na samu har barci ya dauke ni hakana. Haka yasa washe gari na tashi da wani itin bakin rai a zuciyana kin ma fitowa nayi daga dakin ga baki daya ina kwance inata faman tunane a raina. Ina kwance a hakana wayana ya dauki ringing ina kallo yai ringing har ka katse ban dauka kira kusan uku yai min naki daga wayana a lokacin. Sai ga Nafisa na doka sallama a kofan dakin nawa wanda tun zuwan ta ban taba yarda ta shigo min dakin ba sai yau da dan uwanta yace a bani waya muyi magana dashi ta wayan ta tunda ya kira ban dauki wayan ba. Bayan ta shigo da sallama na karba mata take fadin barci kikeyi ne dama nace ma yaya ina zaton hakan ai. Tana magana take miko min waya idanuwan ta kuma yana yawo a kusurwan dakin da take bi da kallon mamaki sosai. Dama tayi zaton hakan don ganin yadda aka tsara dakin yaran dana su maria tasan namu abin kallone shi. Na duba wayan har lokacin yana kunne bai kashe ba nayi sallama a hankali ina sauraren shi. Ina kike ne haka waya yana ta ringing baki daga ba nace ina daki kwance ya dan ja tsuki yana fadin wanan ai halin banzane ka bar waya anata kira baka daga ba. Idan da dane cewa zanyi dashi yayi hakkuri sai dai yau baiji hakan ba don amsawan ma sanyaye nake amsa mashi magana. Yace ya yaran da kowa da kowa a gidan nace lafiya a takaice yana jin hakan ya kashe wayan abin shi na mika ja tsuki don Nafisa tunda muka fara magana tabar dakin. Runtse idanuwana nayi ina anyana yadda yake cikin annashuwa a can da amaryan shi muko muna nan. Sai zuwa yamma na samu sa,ida a raina ina fadin wai me nakeyi haka zan bada kafan da Nafisa zata samu wani abin fadi a tare dani. Mikewa nayi na shiga wanka na fito na shirya a daidai lokacin da yaran suka dawo gida suna zaune a falo suna cin abinci na fito. Da murnan su suke gaidani ina masu sannu da dawowa na zauna a tare dasu muna hira sannu a hankali nake jin dan sauran abinda nake ji yana gushe min a raina har yakai na daina jin komai a yanzu. Banda in ba yarana kullawan daya dace su samu tarbiya ingantattace a gurina na watsar da duk tunanen wata kishiya don tarbiyan yarana yanzu shine a gabana kawai na yanke shawara a raina. Zaman mu da Nafisa a dan kwanakin ba laifi don mun gama fahintar halin ta muna binta dashi saidai ban yarda rainin wayau yana shiga tsakanin mu ba don kada taga kafan yi mu hakan. Sam ban yarda wani rainin wayau yana shiga tsakanin mu ba don ba dogon irin wasan nan a tsakanin. Ko zama wuri daya don bakuntar da tazoyi munane har muke dan dasawa saboda nasan bata da dadi salma ta fita dadin sha,ani. Komai da aka ban ina amfani dashi kamar yadda sukace din nayi amfani dashi haka ya jawo min saukan wani ni,ima da kyau a jikina. Wanda ni kaina na hango hasken sirin abin a yana haskani yana kara min wani irin dau kaka ga duk wanda ya ganni a lokacin. Don ko zama nayi na bar wuri zan barwa wanda zai zauna bayana kamshi da tunanen sirin kamshin. Ga yarana yanzu sai wani irin kula na musanman da suke samu suma sai baiwan su sannu a hankali ya fara haskawa din. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:20 - 🀐🀐🀐: Suna zaune su uku a falon mahaifinsu sai mahaifin nasu dake dan kishingide yana sauraren bayanin kowanin su daya bayan daya tundaga kan Umar har habbib da Aliyu. Baiyi magana ba har zuwa wani lokaci saida ya fahinci sun gama fadin abinda ke zuciyar su yana gyara zama yace. Da fatan dai har zuciyan ku kusan banda laifi a cikin wanan magana don nine na aje jummai a gidan nan ba ita ta ajeni ba kamar yadda take tunane. Na fahinci abinda kowanku yake ji a ransa game da wanan maganan sai dai kule tunanen haka don ita a bangaren ta hakan bawai ya dame ta bane. Yau ankai har jimmai tana tunanen zatayi jayayya dani a gidan nan kan naba dan dana haifa umarni yabi take ganin ban mata daidai a rayuwan ta. Sai yaushe zata gane niba makiyin ta bane wai idan bamu taru mun rufawa kanmu asiri ba a yanzu sai yaushe ake tunanen zamuyi hakan. Sam a yanzu banga laifin jimmai ba don nine da sakacin dan na bata dama har ya wuce yadda ya dace ace an sakewa mace shine ya haifar da illa a tsakanin mu yanzu har jimmai take daukan kanta a matsayin miji nina koma mata. Daddy hakkuri zakayi itama mams tasan bata kyauta ba abinda tayi a yanzu don duk wanda yasan gaskiya yasan babu gaskiya a cikin maganan nan. Daga baya ke nan Aliyu don yanzu bukatan ta ya biya idon ta ya bude ko tunda tayi yadda take so ta nunawa duniya ban isa da danta ba. Allah sarki daddy kada kayi tunanen hakan garemu don mu bamu da wanda ya fika a gare mu sai ita mama. To aikai malam umar abinda take tunane ke nan take ganin ban isa ba gareku ta matan a karshen ikona take zaune. Daddy a daiyi hakkuri a yafe wanan magana tunda har abin ya rigada ya faru sai a hakkura hakana a yafe. Ai habbib idan kaga na janye sakin dake tsakanina da jummai a gidan nan to ta bi umarni ne shine za,a zauna lafiya dani don bata isa tace ni ban isaba ga idon duniya. Shiru gaba dayan su sukayi falon don sun san idan yai irin maganan nan har cikin zuciyar shi yake nufin abinda ya furta. Don kawu mutum ne da zaka dade kana mashi abu bai tanka mutum ba amma ranan daya tanka sai ran kowa ya baci a gidan. Daddy a dai kara hakkuri don Allah wanan abin bamu jin dadin shi wallahi gashi yanzu muma muna da iyalan da zamu koyi da wasu halaiya naku a yanzu. Tabbas hakane habbibu shiyasa ma nake son nuna aini ba lusarin namiji bane kamar yadda ta dauke ni . Har zance ga abinda nake so ga dana yau jimmai ta fito a gaban jamma, a tace ban isa da abin nan ba ai kaga haka ba dadi ko. Kowan su ya kasa magana sai can Umar yace daddy zamu tafi don wanan maganan yana son fin karfin mu ba zamu iya sasanta tsakanin ku ba. Umar meye laifin ku a cikin maganan nan jimmai tasan da sharadi na ta zabi barin dakin ta don ta farauta ran yar uwarta na zumunci. Zumuncin ma daga sama don ba zan matan da lokacin tafiya ku waje ba naje lagos kan mutumin nan ya taimaka min sabuwa da kanta ta hana shi ya taimaka sai barene can daban taba sani ba ya taimake mu. Wai yau wa yan nan mutanen Jimmai ta jawo min cikin a hali har ta zabi farin cikin su da nats nan gaba me kake tunanen za,a yi a gidan nan idan ina lamuntan haka na faruwa tun yanzu. Gaskiyane daddy na fahinci abinda kake ji kuma kake nufi a kan wanan magana zamu zauna da mama mu fahinci juna yana fadin haka ya mike sauran ma mikewa sukayi suna mara mai baya bayan sunyi sallama da mahaifin nasu. Tuki yakeyi hankali a tashe gabaki dayan su cikin motan babu wanda ke iyayiwa wani magana sai faman sake sake suke a ransu. Nauyayyan ajiyan zuciya Habbib ya sauke lokaci guda yana fadin yau danine a matsayin ka bros yarinyar nan ba zata kara kwana min a gida ba. Don ba zan yarda kan auren wata mace na uwana ya mutu ba ga banza ni bansan abinda mama take nema a gurin wa yan nan mutanen marasa mutunci . Don naji ana fadin ko wurin bukin wullakanci suka so yi mata a lokacin salma ne tare da wasu suka taka masu birki. Duk maganan da yan uwan keyi a motar Umar baiyi magana ba har lokacin gaba dayan su sun fahinci baya cikin dadin rai a lokaci. Gidan shi ya nufa inda suka samu mahaifiyar su saidai sunyi rashin sa,a tana da baki yan uwanta sun ziyarce ta a lokacin. Suna jin muryan su da kalaman su har inda suka tsayar da motar su part din mu suka shiga kai tsaye har lokacin ba wanda yake iya yiwa wani magana. Mama Asma,u dake ta wajen kofa tana wayane taga shigowan su gidan har shigan su part din akan idon ta haka ya bata daman sace jiki zuwa wurin su ba tare da yan uwan nata sun sanda haka ba. Ta shiga wurin su suka gaisa ta danyiwa umar din murnan aure da yayi sai kuma ta kare da fadin saidai kuma wanan abin bai kawo kallo ba. Ace sanadin wanan auren yaya tabar nata dakin da tai shekara da shekaru a cikin sa haka bai taba faruwa a tsakanin su da Alh ba sai akan wanan bakin auren haka. Don mu auren baki yake a gurin mu don shine sanadin wanan abinda ya faru saidai yannen nawa basa son gaskiya don basu lurar da ita gaskiya sai kara dulmiyar da ita sukeyi. Mama mun sani shine abinda ke kara daure muna kai ace da girman su mama wanan abin yake faru haka ko yaushe a tsakanin su. Yanzu sun tsameni cikin al,amarin su zasuyi abu ban sani ba don fadin gaskiyana danake masu yasa ake abubuwa bada sanin nawa ba. Ko wanan auren naka ban san dsshi ba sai ji nayi daga sama don ban dauka abune da zai yuyu ba a tsakan zurian mu dasu. Sai gashi ashe har hurdi Alh yayi mata amma yaya ta rufe ido har ta yarda wanan abin ya faru tsakanin su haka. Yau ma din ninaje gidan mahaifin naku dan in mata ban gajiyan buki sai hjy maryam ke dan tsegunta min abinda ke faruwa wanda banji dadin hakan ba. Naso ganin Alh aka ce min bai tashi ba yana kwance har lokacin haka yasa na shiga neman inda yaya din take nazo. Saidai banji dadin zaman ta a inda na sameta ba don tun yanzu an fara samun matsala don yarinyar bata son zaman yaya a nan din. Gidan ubanta ne nan din da bata son hakan habbib ya fada rai bace cool down mana habbib, umar ya fada yana kada kafan shi cikin takaici. Don shi kadai yasan yadda yakeji a lokacin wayan shi daya dauki kara ne ya tsaya dubawa cikin mamaki yayi received din wayan yana mamaki a ranshi na kiran danayi mai na bazata. Haka yasa ya fara tunanen wata kila wani ba lafiya ko wani abin ya taso tasa nake neman shi a layin shi sai ya dauka yana fadin . Zahra ya lafiya ko tambayan nasa ya bata min rai saidai na dake ina fadin lafiya kalau yaya mu kiraka ne kawai muji lafiyan ka gasu Abdul suna son jin muryan ka na fada a kunyace don Nafisa na gurin zaune tare damu ta kura min ido tana sauraren mu. Ya dauki lokaci yana waya da yaran shi hankali kwance yayin da su mama Asmau suke dan tataunawa dasu Aliyu kan zancen da sukeyi da farko. A karshe yace suba maman su waya duk a cikin harshen turanci yake magana dasu nice mai dan kokarin koyawa yaran harshen hausa don kada su taso basu iya ba. Saiko zuwan fauziya yanzu ba karamin taimakona zuwan yarinyar yai min ba lokacin. Na karbi wayan ina sauraren shi yace i miss you Zahra how far ya Abbati na amsa a sanyaye da muna lafiya ya Amaryan ka kuma ? Dan murmushi yayi babu amsa yana tambayana baku dai da matsalan komai ko ko a turo maku kudi zaku sai wani abin ? Babu abinda zamu saya yaya we are ok mun gode yace take care of your self and the children nace in sha Allahu yaya . Kaima ka kula muna da kan ka yana fadan hakan mukai sallama na kashe wayana ina jin zuciyana ba dadi a lokacin. Badon komai bane sai don tunanen shi can yana more rayuwan shi da wata mace can ta daban mu muna nan ya barmu a cikin maraicin shi. Gashi ba lafiya nake dashi ba don ban gama helling a jikina da akai min aikin wurin cire baby har yanzu ban gama warwarewa ba sosai. Da kyat suka samu zama da mahaifiyar su kan hujjan da mahaifin su ya kafa game da komawanta dakin ta. A take hjy ta hau fada inda take shiga ba nan take fita ba karshe ma sai nuna masu tayi ai mamune ta jefo masu bakin asiri daga can har haka ya kasance a tsakanin su. Kai amma dai mama idan wanan halin zaki ci gaba dayi gaskiya akwai matsala babba don kina daukanwa kanki nauyi ne. Ina wanan maganan kin san shi tun kan ayi auren nan da kika matsa ayi din kin amince da hakan ke nan . Yanzun kuma zaki dauko wani zancen daba shi ba mama ki dora kan matar da bata ma san anayin wanan abin ba a nan. Wai kai habbib haihuwana kayine ko me da kake kokarin nuna min kuskurena a kowani lokaci na dauko zancena. Mama kiyi hakkuri abinda kikeyi ne wani lokaci ke kanki kinsan ba daidai bane sai kuma ki yarda shedan ya rudeki a ciki. Don Allah mama ki bar wanan yarinyar ta koma inda ta fito tunda dai itace duk ta jawo wanan matsalan a tsakanin ku da daddy . Inyaso mu lalaba daddy ya hakkura ya mayar dake dakin ki don Allah wanan abin kunyan ya, , , Habbib kabar falon nan tun kan na sabawa rayuwan ka anya kuwa yaron nan baya shaye shaye zaman shi a turai tana magana idon ta yana kan babban nasu umar. Dan murmushi yayi yana dagawa habbib hannu yace bai shan komai mama halin turai dai ya kwaso na fadan gaskiya ga ko waye idan bukatan hakan ya taso ayi. Mama gaskiya yake fadi don a kan auren wata can ba zamu taba yarda ke naki auren ya samu tangarda ba muna kallo. Nan ko ta hau fada tana fadin na gane yan uwanane baku kauna a tare dani don an riga da an zuga ku akansu. Don haka ku barni da yan uwana komai zai faru ya faru ba matsalan ku bane. Ta mike har takai kofa ta juyo tana fadin kai kuma babawo sai ka shirya shiga gurin amaryan ka don ban fahinci manufar ka ba na kin shiga gurin ta. Nan dai shima aka haushi da fada da tashin hankali da kyat ya samu fada mata mama zanyi yadda kikace insha Allahu . Tana fita daga falon ta nufi hanyar shiga part din tun daga nesa ta hango part din a saye har takai ta tura kofan taji shi a rufe. Da mamaki ta dan tsaya tana buga kofan shiga part din har ta gaji ba wanda ya bude kofan mamakine ya cika mata zuciyan ta lokaci guda. Ta rasa yadda zata fassara wanan abin ko dai yarinyar ta fita unguwane bata sani ba. To waima wani unguwa kuma yarinyar da bata wani kwanaki da shigowa gida ba har zata fara fita haka unguwa. Tana tsaye tana wasi wasi a kofan daidai lokacin aka bude kofan dayan part din gaba dayan sune suka fito a part din kamar yadda ta barsu a ciki su uku. Da mamaki suke kallon mahaifiyar nasu wace take tsaye a rakube kofan part din samira din a cikin damuwa. Lafiya mama Aliyu yayi saurin tambaya yana isa gurin da sauri wallahi na fito kawai na samu kofan a rufe yanzu Daga inda umar yake yace kamar ya kofa a rufe mama ya takowa zuwa wurin da take tsaye da mamaki fal a fuskan shi. Yana zuwa ya fara dukan kofan a cikin wani irin hasala can yaji ana kokarin bude kofan habbib kan lokacin har ya kai wurin motar shi don shi haushin hakan bai bari ya tsaya jin meke faruwa ba a wurin. Wata yar bakar yarinya ce ta bude kofan a hasale tana fadin wai waye ke damun mu da dukan kofa hakane don Allah anty tana kwance fa. Tana karasa budewa sukai arba da umar dake tsaye a hasale cikin wani kakausar murya yace ke waya baki umurnin rufe kofa haka gidan nan ? Ta fara dan inda inda tana fadin dama dama anty ce tace in rufe bata son damuwa zata kwanta. Anty waye anty a gidan nan kuma ya tambaya da mamaki karara a fuskanshi da sauri hjy tace samira take kira da anty ai. Yace a hasale common bude kofan nan kada kiyi gigin kara rufe kofa a gidan nan da rana yana fadin haka ya juya rai bace da sauri ya bar gurin. Aliyu dake tsaye ya kalli mahaifiyar tasu yana fadin mama shiga a cikin wani irin sanyin murya yake magana rai bace shima. Sun kama hanya gaba dayan su an rasa wanda zaiyi magana daga cikin su sai Aliyu ne ya iya fadin amma wanan yarinyar bata da kunya mamane ta rufewa kofa ko me ? Ita ta rufewa mana baka san halin zurian hjy sabuwa ba ko wanan ma ai kadan mama ta fara gani wurin su. Ka daina fadan hakan Habbib kamar baka damu da halin da mahaifiyar mu ke ciki ba don Allah. Mama a yanzu idan ka kula dabara na kokarin kubce mata ne don in ka kula duk abinda takeyi ba a cikin hayacinta takeyin sa ba umar ce yana sauke numfashi. Kaike daukan hakan yasa suke kokarin gara ka aiko shi daddy ya dawo daga rakiyan halin su ne yanzu duk wanan damuwa ne ke damun ta don bata taba zaton daddy zai iya mata haka ba gaskiya. Ya juya wurin Umar da kyau yana fadin yanzu kaine zaka kawo karshen wanan matsalan gaba daya nake gani. Hannun shi daya kare fuskan shi dashi ya sauke yana kallon dan uwan tare da fadin as how zan kawo karshen abin ? Kwarai kuwa ya kara fada yana jijiga kai kafin ya fara fadawa dan uwan nasa maganan abinda yake gani shine mafita kan mahaifiyar tasu dasu nan gaba. Gaba dayan su shiru sukayi kowa na nazarin zancen a ranshi can Aliyy yace kana ganin mama zata yarda da wanan hukuncin kada kuma wani abu ya biyo baya a karshe. Nafisa dake zaune ta kurawa tv dake aiki ido tun zaman ta a wurin take faman tunane a ranta. Gaskiya ita yanzu gida take muradin zuwa wanan zaman kadaicin haka ya ishe ta ace mutum ko rana baya gani balle dan adam kana cikin gida a kulle jiddadun alaina baka ganin komai a garin. Tana mamaki na yadda bata ga mun damu da fita ba dagani har maria dake wuni a tsaye tana muna aiki a gida. Na fito daga daki ina daye da wani bakin wando da ya dan zarta wuyan kafana kadan sai dai bai sauka min ba kasa. Sai rigan daya dan sauko min har kysan gwiwa mai umberal sai dai ta kare min kallon yanayin shigana take fadin. Wai ke fatima haka kuke zama wanan garin zugu zugun ba fita ba komai kullun mutum a gida. Har mama wai tana ganin wani daula da jin dadi kuke ciki nan ashe abin ba haka yake ba ma ashe . Yawo kike son fita tace min tun zuwa na garin nan baki fita ya kai sau biyu ba gaskiya idsn mutum ba yazo yaga yadda kuke rayuwa ba dole idan ya ganki yayi zaton duk komai na yaya yana hannun ki ai... ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:20 - 🀐🀐🀐: Sauraren maganan nafisa nakeyi kamar a mafalki don azaton su ashe a cikin daula nake sai abinda naga dama nake a gidan dan uwan su. Ke nan wanan zuwan ya fara wankeni daga zargin da suke min ke nan a baya ni dai nasan su matane dole gidan wani zasu su zauna kamar yadda nake zaune a gidan dan uwan su. Tabbas ko wace mace sai tayi irin wanan rayuwan da yan uwan miji wata rana dan dama ma ni nawa dangin mijin yan uwanane amma basu raga min ba a cikin zaman mu don wani dalili nasu can da suka ratayawa zaman namu. Hakane kuma suma nasan ko wace zata fuskaci irin nata kalubalin daga yan uwan mazajen su kamar yadda suke min suma. Don hakane na nake hakkuri da komai ina danne abinda duk Nafisa take min na takalan bakina don kawai ta samu madogara ga kudirin ta gareni. Kallon ta nayi bayan gama tunanena ina fadin Nafisa ke nan ai kin san dama idan mace tana zaune kalau da mijin ta hakan mutane kanyi zato gare ta. Sai su dauka tana zaune tana juya mijin ne ita son ranta sai abinda taga dama takeyin shi a gidan basu dauka hakkuti da jarircewan wasu matan ne yake kaisu ga hakan. Nafisa idan kinyi wa zaman mu da yaya adalci ni ko shi har yau ba wanda ya taba korafin wani a gidan mu da sunan rashin jin dadin zamantakewa da dan uwan shi. Nafisa ke kin sani ba wai bamu samun sabani bane a tsakanin mu kwarai muna samu saidai hakkurin da Allah ba kowane a cikin mu ya hana har mu bada kafa a fahinci hakan. Ke dai yanzu ganauce kinzo kinga rayuwan da muke a gidan nan daga ni har yaran mu ba wai wani abin duniya da kuke tunane bane yaya yake sakar muna, muna yadda mukaga dama a gidan nan . Rayuwa muke na sese wa sese da zama rufawa junan mu a siri yadda ya dace duk wata macen kwarai ake bukatan samu hakan a wurin ta. Yanzu kinga ke nan zaki koma gida da hujjan kan abunda idon ki ya gane maki a zaman mu gidan nan . Wanda kuke ganin kamar wani daulan duniya nake cikin shi zaune a nan tace da sauri wa kike tunanen zan fadawa hakan ? Bawai ina nufin ki fada kai tsaye bane ai Nafisa kawai na tabbatar da idan magana makamancin haka ya taso a kan mu kina wurin zaki bada shedan abinda kika gani wa idon ki ai. Sai lokacin naga ta danyi murmushi kadan a fuskanta tana fadin kwarai kuwa don ni din dai ganauce don ban zaci hakan ba gaskiya a zaman ku. Duk da dai ba a gane tsakanin miji da mata sai Allah amma dai duk da hakan na fahinci dan wani abin yanzu kan zamantakewa na aure wanda a baya ba haka na dauki abin bani. Mun kai wani lokaci muna jefawa juna magana a dunkule da sunan hiran salma wanda kowan mu ya gane nufin dan uwa. Rashin dawowan yaya har sati hudu yasa na fara shirya yadda zan fara karatuna don dama mun gama magana dashi haihuwana ne ya tsayar dani kan hakan amma na dade da applying anyi komai. Nafisa kan iya gajiya ta gaji da zama wuri daya don bata saba da hakan ba ita ni har mamaki take bani don idon ta yanzu ya matukar budewa kamar ba yar gidan kawu bace ita. Muryan hjy sabuwa ce ya tayar dasu ranan daga barci don kamar a hanya tayi sallah asubahi a yadda tayi sakkon zuwa gidan cikin rashin mutunci. Bada kowa take wana jidalin ba saida hjyn su yaya tana fadin yo jummai ai bansan makira kike ba sai yanzu. Haka kawai kin wanko kafa kin dawo gidan yara cikin ki kin zauna don kawai ki batawa Samira jin dadin auren ta. Ashe kin yarda an hada wanan auren ne don ki yaudaremu ki samu daman da zaki dawo gidan danki ki zauna ki kasa ki tsare don sheri. Budan kofan da akayi yasa ta tsaya ta dan dakata da maganan ta don ganin wanda ke fitowa a part din lokacin. Hjy jummai ce ta bude kofan tana kallon hjy sabuwa da mamaki hakan bai hana hjy sabuwa fasa fada abinda take fadi ba a lokacin. Tana fada ta nufi cikin part din a hasale tare da fadin tabbas kuwa na sheda don ga zahiri nagani yau hjy jummai kinsan kunya kuwa ? Ki rasa inda zaki tare sai a gidan yarinyar dake ganuwan amarci da mijin ta kinzo don rashin ta ido kin zauna masu a gida kin hanasu rawan hantsi a gida don kawai kina takama gidan danki ne nan. Hjy sabuwa irin sakkaiyan da zaki mun ke nan bayan duk abinda ya faru sanin kanki ne a dalilin auren yarki ya faru dani. Ni zakizo ki watsawa kasa haka ga ido tunda farar safiyan nan haka a gidan nan . Naki dai ki daina cewa sanadin samira hakan ya faru dake don Allah kada makiya suji su canfa min yata ga banza. Yo koma hakan ne yanzu ke daidaine ki dawo nan ki tare masu nan ne kawai gurin zama a cikin gidan nan kome ? Wallahi jummai kinban kunya don ban zaci hakan da wuri a gareki ba koma me kika shirya ai kya bada lokaci ko ? Hjy da imani da mamaki ya cika lokacin kasa magana tayi don jin abin take kamar a almara wai duk gwagwalmayan da take sha duk akan auren yar sabuwa irin sakaiyan da zatayi mata ke nan da farar safiyan nan. Samira da bata son auren ta ya balgace ne takewa uwar nata magana kamar a fada haba umma yakamata abi abin nan a tsanake bada tashin hankali haka ba. Ta juya wurin yar tana fadin barni in fada mata gaskiya idan bakanta ya kamatane ? Mama wai me ke faruwa hakane a gidan nan muryan wa nakeji cikin rashin kamun kai zai shigo muna gida da safen nan da masifa haka ? Wanan wata irin bakuwace haka mai kaifin harshe mara tunanen gidan mutane tazo da safen nan take wanan nuna tarbiyan haka gareki. Aliyu ne da sauran yan uwanshi da dawowan su ke nan daga masallaci basu dade da shiga ba suke jin muryan hjy sabuwa komai da take fada a kunnen sune. Allah ya nufa za,ayi wanan abun a gaban su yayan su yace su kwana a nan don da safe zasuyi sammako zuwa gurin wani dan uwan su daddy su a kauye. Gaba dayan su juyowa sukayi a inda suke jin maganan suna kallon su da mamaki. Dan kame kame hjy sabuwa ta farayi don batayi tsamanin gaba dayan su har shi umar din yana gidan ba a lokacin. Au kuna ciki ashe tace ba wanda ya amsats sai shi umar din ne cikin sanyin murya yake fadin mama meya faru ne haka wai da safen nan ? Wanan matar tazo muna da jidali gida babawo sarakuwan kace fa mahaifiyar samira amaryan ka . Wani kallo yaiwa hjy sabuwan don harga Allah matar ta sake mai ga baki daya don ba haka yasanta ba a baya gaba daya yaga ta sauyamai ga gani. Wani kallo yai mata bai iya magana ba ya juya zai bar dakin ba tare da yace da ita uffan ba sai jin muryan ta kowa dake falon yayi tana fadin . Babawo ko ban baka mata ba a matsayin uwarka nake balle na wanke diya na baka do dole alakan mu dakai ya karu a yanzu. Ta fada a gadarance tana kallon shi kamar mai bashi umurni tace ban san matsayin daka dauki yata ba a wurin ka don har yanzu kwanan ka nawa a garin nan tana cikin gidan ka tace ko gaisuwan ka bata samu. Ban san dalilin hakan ba tunda ba mutum mutumi na kawo maka ajiya ba a gida mace ce lafiyaya na dauka na baka aure. Tunda ta baci sunan shi yaja ya tsaya wuri daya yana sauraren maganan da take fada mai ba tare daya juyo inda take ba har zuwa lokacin data tsayar da maganan ta. Sai lokavin ya juyo gareta jin ta tsaya da maganan da take koro mashi ya dan murmusa kafin yace hjy zanso ki gyara kalaman ki kan komai nan gaba ko abin zai zo maku da sauki. Yar ki bata fadi karya ba don har yanzu ban san tana gidan nan ba don bamu je an muna gwaji ba a tsakanun mu a tantance lafiyan ta. Me kake nufi da fadan hakan gwaji gwajin me kake nufi zakuyi tuhumar yar nawa kake dawani cuta ko me kuma ? Eh a ka,idana sai anyi wanan gwaje gwajen an tattance tsakanin mu kafin in tabatar da komai a gare ta. Uwarka jummai gatanan za, a gwada ka kalli tsaban tsakiyan idona babu kunya kake furta min wanan maganan gwajin ko me ? Nasaran da kake koyi dasu sunci abu kazan kazan su wa zaka kawowa wanan bakin akidar naku na nasara a nan sale sale salin ka batawa yata suna ko me kake nufi. Kiyi hakkuri mama haka ka,idana yake ni don haka zan samu lokaci muje a auna mu ta kara fadi a tsawace a aunaku akan me ? Nace cuta gare ka ko ita kake tuhuma da cuta da sai an aunaku zaka fara takata kamar wasu arnaku can da basu yarda da Allah da kaddara ba. Sorry yace ya juya ya fara tafiya yan uwan suka mara mai baya yayin da hjy sabuwa ke fadin wani sabon kullin da kukayi da dan naki kenan hjy don ku tozarta mu kome ? Sabuwa mamakin wanan dabian da kike min a yanzu nakeyi nima yadda kikaji wanan maganan yanzu a nan nake jinshi yanzu don baiyi wanan zancen wani gwajin dani ba. Koma me kuka shirya samira ba zatayi wanan gwajin ba waya sani ko kun shirya da wani likitane ya bata mata suna ga banza. Kuma bari kiji samira ba zata zauna dake gotai gotai haka a part daya ba ga dakuna birjit a gidan nan baki zauna ba sai wurin ta don sheri irin naki kawai. Idan har kika bari auren Samira ya samu tangarda a dalilin ki jummai ina mai sheda maki tabbas auren ki ya tabu kema a gidan nan. Umma ni banji dadin zuwan nan naki ba gaskiya don kin kara bata wanan abin ne hakan da kikayi . Da ki barni in gyara komai da kaina basai kinzo ba saida nace dake kada kizo ki bari zansan yarda nayi amma umma baki ji ba saida kikazo gashi yanzu abinda zuwan naki ya jawo min kuma . Ke rufamin baki ke me kika sani cikin halin wanan matar nida ita kar yasan kar idan tana tunanen zuwane ni a hanya na kwana wurin sheri. Hjy jummai da tun fitan diyanta part din ta kasa zaune ta kasa tsaye a dakin da take har nan din tana iya jiyo murya hjy sabuwa da yarta da suke magana a daki game da ita. Sai lokacin da taji fitan hjy sabuwan wani kukan mai cike da nadaman yarda da dadin bakin da hjy sabuwa ta dinga mata a lokacin da take son wanan hadin yazo mata. Bata san lokacin da hawaye masu zafi suka dinga zubo mata daga idanuwan ta ba yaune rana na farko da ta fara nadama kan abinda take aikatawa ga mijin ta da yaranta da basu gazawa da al,amarinta ta sani wani lokaci tana tauye su da yawa amma saboda son zuciya irin nata tana ganin har yanzu su yarane basu san daidaiba. Yau da a gaban wani ba diyan cikin ta bane sabuwa tayi mata wanan tujaran haka ina zata saka kanta taji dadi a duniyan nan. Do ita abinda taki a rayuwan ta shine taji kunya ko nauyi a gaban wani saboda girman kai irin nata da take dashi. Yau sai gashi sabuwa ta wanko kafa har gidan dan nata tazo taci mata mutunci saboda yarta har tana ikirarin sai taga bayan auren ta idan na yarta ya mutu. Ashe haka mutum yake saida Asma,u kanwarta ta rabata da wanan maganan hadin auren amma ta rufe ido tayiwa kanwar nata tas da gangan. Can falon mu kuma bayan sunyi wanka sun shirya mai girkin shi ya jera masu abin karyawa ne a dining sun fito. Ba wanda ya kalli abincin don rayukan su da suke jin ba dadi a lokacin saboda abinda hjy sabuwa tayiwa mahaifiyar su a gaban su dazun. Shine ya fito karshe yana daura agogo a hannun shi ya nufi wurin abincin kallon yan uwan yayi yana fadin ya baku fara ci ba kun san ni ba wani abu zanci ba ai yanzu. Bros wake zancen abincin nan yanzu wanan matar ta cazawa mutane kai tunda safe haka duk da dai banga laifin wanan matar ba ai don basu da laifin komai a nan kansu sukewa faiting. Wanan maganan kun daukeshi wani zance ne can mai muhinmaci kune baku san halin sabuwa ba har zaku wahal da kanku don ni na rigada na gama shirin komai. Zancen zuwa kauyen ma mun fasa ba inda zamu fita yau zamu zauna gidane akwai abinda nake so mu gane kan shirin wanan auren da suka kulla min. Na fara gane akwai wani manufa cikin wanan hadin wanda ita mama kanta bata fahinci hakan garesu ba. Zuwa gobe zan kawo karshen maganan kowa ya huta idan suna ganin sun kamani a hannu ne yadda suke tunane tun yanzu. Da hjy tana da gaskiya ba zata ce bata yarda aje asibiti da yarta ba wanan kawai ya ishe mutum mai tunane ya gane . Aliyu yace abinda nake faman tunane ke nan tun dazun ai tayi zaman lagos tasan amfanin gwaji kafin aure bawai dole sai ciki ko wani abinda take tunane ba za a iya ganowa a wurin gwajin ba har ma abinda mutum baiyi tunene shi ba sai ya bashi amsa. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:20 - 🀐🀐🀐: Fadan hjy sabuwa ya komawa samira matsala don gaba daya ya fita zancen ta a gidan bata ma ganin dawowan shi ko sanin fitan shi gidan daga ita har hjyn su yanzu. Tafiya yayi duba company shi na farko daya kafa lagos dashi da Aliyu hakane ya kara harzuka ran hjy sabuwa ta addabi hjy jummai da masifa na rana daban na dare daban. Sai shige shige ya tashi abu ga wanda addini bai zaunawa kai ba dama sai fadi take wai ba a banza hakan yake faruwa ba da yar ta. Saidai ta tafi tsirara amma sai taga bayan mai shi a duniyan nan gaba daya da farko sun dauki laifin sun dora min ne . Daga baya kuma suka komawa merry don wayan da Nafisa tayiwa uwar cewa ita bataga wani abin da nake samu na jin dadi ko kulawa daga gareshi wanda zai tsonewa mutane ido . Don ta gama fahintar ko nan ba ganin shi muke yi yadda ake tsamani yana muna ba don ta binciki mai aikina ta fada mata komai a yadda ta fada masu. Don hakane suka juya akalar su zuwa gun merry kuma wace bata san hawa ba bata san sauka ba kan maganan. Shiko a nasa bangaren ya kudurta cewa muddin mahaifiyar shi bata koma dakin ta ba da sunan aure ba zai taba kallon samira da sunan mata a gareshi ba. A cewan habbib bai dauki auren samira wani aure ba can don babu waliyi daga bangaren mahaifin aure ko yana wajabtane daga bangaren ma,aurata biyu. Sin bar hjynsu a cikin dibin tunane don ko ganin su ma su duka ukun batayi balle ta sauke masu sababinta a kansu. Abu ya taru a lokaci daya ya rikicewa hjy wace bata taba zaton hakan ba da farko daga can lagos ya juya ya wuce zuwa united state of America inda ya samu wani kira na gagawa a can kan aikin su. Sai bayan Aliyu yazo kano ne suke jin cewa baya kasan a baki daya lokacin . Samira tana jin haka saida ta kwanta ciwo aka kaita asibiti nan ran mahaifiyar ta ya kara baci sosai tana fada wai zatayi karan Umar da mahaifiyar shi kotu. Mijin ta yace akan may da kukai auren ku kinga kafan shi ko wani nasa gidan nan da sunan aure ? Dama abinda nake fada maku ke nan kuka kasa gane mai nake nufi saida kika san dabaran da kikayi kuka kulla wanan auren yanzu kije kotu ki tonawa kanki asiri ko yar ki. Duniya ta san halin da kuke ciki idan ma baki sani ba ki sani wanan yaron ba zaku iya juyashi ba yadda kuke nufi saidai kuyi ta barnan kudin ku ga banza. Don irin su kansu ya riga da ya waye wani asiri ko jefa da kira ba zai shige shi ba don a tsaye yake a kafan shi. Shi wawane da zai yarda auren mahaifiyar shi ya lalace ya gyara auren yarki bayan yasan furcin mahaifin shi kan wanan auren . Idan zaki natsu ku bi komai a sannu ki tarkato yar ki da kayan ku zuwa gida zaifi don shidai ya nuna ba zaman shi takeyi ba a gidan yanzu haka. Samira wace ke kwance saman gadon asibiti ta sakewa iyayyen nata wani irin kuka lokaci guda. Mahaifin yace dama ai daga kin gaskiya sai bata tun kina da mutuncin ki nake baki shawaran ki natsu ki fitar da mutum daya wanda zaki aura saboda kinga kina da daurin gindin uwarki tana zugaki kika kasa yin haka. Tace daddy ni wallahi in yace ya fasa aurena mutuwa zanyi wallahi ka taimakeni kasa baki a cikin wanan magana don naga umma ta kasa wanan aikin ita kadai. Yace samira yanzu kuma ni din da kuka mayar ba komai ba ke da uwar ki yin abinku kukayi ba ku dauki shawaran dana bayar da muhinmanci ba kun mayar dani wani makiyin ku. Asiri ba a ko ina yake tasiri ba haka asiri yafi aiki kan wanda yake sakaci da adfinin shi yanzu na kara fahintar hakan. Kan irin kudaden da kuke kashewa a kullun kan yuyuwan wanan abin gashi kunyi nasaran abin ya yuyu saidai zama gidan kuma ya gagareku zama yanzu. Kun taba jin anyi wani na banza a duniya ai in kaji wani ba banza ba zai zauna hakane bai shirya kansa ba yana gwagwalmaya a cikin duniya da mutane kala daban daban. Hjy sabuwa taja wani irin tsuki tana fadin yanzu wanan magansn me ya kawo shi idan ba zaka taimaka ba ka saka muna ido kawai nida yar ta dama zan sama muna mafita. Tana fadin haka ta muguda baki kamar karamar yarinya tana juyawa baya. Na shigo gidan a gajiya don ranan dana kwaso a falo na samu Nafisa zaune na samu har yaran sun dawo gida lokacin. Suka shiga yi min sannu da zuwa ina amsawa a lokacin da nake kokarin zama ina tambayan yarona don in bashi nonona da sukai min nauyi a lokacin . Kallon Nafisa nayi wacce tunda na shigo bata dago kai ta kalleni ba har lokacin nasan tsiya take ji ranan don haka na shashantar da ita ina fadin hjy Nafisa ke nan kina jin dadin ki. Sai lokacin ta juyo tana fadin naga kin dawo iyalin ki sun baibaiyi ki da sannu ne ai. Dan dariya nayi ina fadin shine farincikin mace Nafisa ta wayi gari ta ganta takiyan iyalin ta a cikin farin ciki da kwanciyan hankali irin hakan. Ubangiji ya nuna muna kuma kun tara naku iyalin irin haka na gyara zancen don kada in bada kafan da zamu samu wani matsala da ita a wurin don nasan gatse tayi min na mayar mata da amsa na. Zatayi magana taji a karshe na mata addu,a tace Amin Fatima kun huta ku da daddy yai maku auren ku a cikin gata. Yau gaki abinki zaune a dakin ki hankali kwance idan na kalli yaranan na tuna wai duk nakine Fatima sai inga kamar mu ba,ayi muna adalci ba wallahi. Da sauri nace haba dai Nafisa kada ki manta komai mu kaddarine ga bawa tun ran gini ranan zane. Tace hakane ni yanzu ba Mansur ba wallahi duk wanda ya fito idan dai yana da hali kwarai zam bashi bakine fatima. Nace hakan yana da kyau don kinga bawai lalaine ka samu abinda kake so ko wanda kakeso ya soka ba . Tace shina zauna nayi tunane sosai wallahi wai yau ki duba sati uku ke nan idan na kira Mansur bai daga waya karshe ma sai ya jefani block ko mai yake nufi da hakan oho ? Kema kiyi kokari ki nuna mashi baya gaban ki yanzu don Allah nafisa ki nafisa ki natsu yanzu ki samu ubangiji ya turo maki miji na gari daidai ke. Ki daina bin irin yar karyan nan da ba aure ne a zuciyar su ba sai holewa da jin dadi suna zubar wa mata da mutunci a banza. Tace nagode da wanan shawaran da kika bani Fatima dama saida Anty salma ta fada min ke din mutumiyar kirkice ban yarda ba a lokaci. Gashi yanzu ina ganin gaskiyan maganan ta idan da wata ce nasan tun zuwa na ba zamu kwasa da dadi dake ba a gidan nan. Wallahi fatima ku godewa Allah ke da mahaifiyar ki don nasan shawara da tarbiyan mahaifiyar kine yake amfani a gare ki. Da ace kowa haka yake samun mahaifiya irin naki da duk wani matsala mutum bai ganshi ba a rayuwa. Yanzu ki duba Fatima mu din da kullun ake nunawa mune diya mune kuma da gida muna iya taka kowa yadda mukaga dama mu zauna lafiya. Ke kanki kin sani izgilanci babu wanda ban iya iyiwa mutum shi ba saboda ina da daurin gindi a gurin hjyn mu nake hakan. Mun dauki kishiyoyin hjy tankar makiyan mu ko kuma sa,oin mu don saboda tsanar su da hjy ta dasa a ranmu. Murmushi nayi jin abinda take fadi tace Allah fatima ke ma kin san hakan ai ? Tace ni yanzu abinda ya ban tsoro Fatima shine duk irin kudi da kaddaran da hjy suka kashe wurin auren samira da yaya wai ace wanan abin baiyi tasiri ba don ance har yau yaya baisan samira na gidan shi ba. Nace ke da kike nan yaya akayi kika san wanan labarin tace wallahi labarin ne ai ba dadi Fatima . Allah ya kyauta nace ina mikewa don zuwa dakina don ban son hiran yaci gaba daga nan. Na shiga daki cike da tunanen abinda Nafisa ta fada duk da nasan kadan ne daga cikin halin yaya don nima na fuskanci wanan a wurin shi ai . Sai dai ko na fada ba yarda zasuyi ba don ba kowane zai iya hakkurin da halaiyan yaya din ba don shi a baude yake sai idan ka san halin shi zaku zauna daidai. Dole nakara sakawa kaina tanatsu na kara sauke komai daga kaina don dai banda matsala a yanzu dashi wanda hakkurina ne takaini ga hakan yanzu. Munyi maganan da kamar kwana hudu kwatsan sai gashi ya sauka a garin daga sama kamar wanda aka jefo muna shi. Nuna mai babu komai a raina nayi wanda Allah yaiwa fada haka mai zan tsaya yiwa fitina kuma don ko yanzu Allah ya gwada masu iyakarsu ai a kaina idan ma ni akewa don in koma baya. Har dare yana tare da yaran shi sai faman bashi labarai sukeyi yana biye masu Nafisa sai kallon su takeyi kawai. Nice na fara barin falin don ina da test ranan monday wanka nayi kafin in kwanta ina dan karatu. Ban dade da fara karatun ba ya shigo dakin ya zauna a kusa dani injin zaman shi na sauke takardan da nake karatu a fuskana ina kallon shi. Ya gida yace min ina kara sauke takardan nace lafiya ya mutanen gida suna lafiya koda yake ban samu sallama dasu ba na wuto daddy kawai na fadawa tafiya ta ya bani amsa. Nace har hjy da amaryan ka balle Amman mu tsohuwa ko ita baka sallama ba ke nan ashe yaya ? Yace bata ko ganni yakai sau uku ba wansn karon don ban samu zama sosai ba aiki yai min yawa. Akwai aiki kan na bashi amsa nace tundai ga mai sabuwar amarya dal iri ka ina zata ganka ? Yau kuma sheri zaki mun zahra ke da kanki ai na dauka kinfi kowa sanin halina yanzu idan ma sheda ce na dauka kece zaki bada a kaina. Wurin kokarin nuna adalci a tsakanin iyalina duk da kalubalin da nake samu daga ko wace ku na zaman tare don kowa gani take nafi maida hankali a wurin yar uwanta. Sai dai ni hakan bai hanani tsaya inyi adalci yadda ya kamata ba in tauye wata daga cikin ku ba ko wacece.. Sai dai ita bakuwar a cikin mu nake ganin kamar hadin mama ba zabina bane don ba zan yarda in dauko wanda baida tarbiya yanzu in jefa a cikin iyalina . Yana fadin haka ya mike tsaye yayin da nabishi da kallo ina son jin kanun labarin da ya dauko bani a lokacin kuma ya katse. Binshi da kallo nayi har ya fita daga dakin ba tare da ya kara furta min komai ba gashi ina son gulma don samun makami don ko wata kishiya tana son jin dan wani zance game da kishiyar ta don shine makamin bakin mu kamar yadda itama dole tana da dan wani labari data rike game dake. Fauziya ne ta shigo dakin dauke da Abbati a hannun ta karban yaron nayi na bashi nono sai barci zama nayi na shirya yaron tare da aje mai abinci koda zai falka da dare. Na kara shiryawa na nufi dakin nasa a zaune na same shi yasa wasu takardu a gaba yana duba jin shigowa na dakin ya dawo da hankalin shi gareni. Aje abinda na shigo dashi daki nayi na zauna kusa dashi a hankali sannu da aiki yaya nace mai ya aje yana fadin ina yaron yake kuma ? Yana gurin mamanshi na bashi amsa fauziya ke nan ko don nasan wanan sakaran bata iya komai ba sai gulma da cewan nafisa . Nafiss kan ai kasan bata saba da rainon yara ba haka ai zata saba idan tayi nata ai ni wanan yarinyar mama ta bari ta lalace da yawa. Gashi bata son a fadi gaskiya a kanta ko kadan nasan kunsha fama da ita nan a bayana . Da sauri nace lafiya lau muke wallahi ba matsalan komai tun da na san halin ta tun farko yasa mukaci maganin zama da ita ko yanzu don bamu shiga harkan ta. Sai dai hakan ya bani amsa yana kai bayan shi saman gado ina so ta koma satin nan mai zuwa daddy yayi maganan Fauziya sai dai na bashi hakkuri don nasan yana da wuya ki barta ta koma yadda kikaji dadin zama da ita nan. Nace wallahi kuwa yaya ka kyauta daka rokan min kawu ita don yanzu nasan dadin zama da yarinyar sosai nama rasa irin godiyan da zanma wallahi. Ji nayi ya da mirginoni zuwa jiki shi ya rungume ni yana fadin ba godiyan da zaki min banda in ta ganinki ke da yaran a ciki farin ciki ko yaushe kamar yadda na dawo yanzu na same ku a gidan kunayi. Bana jin dadi idan naga kin sa damu kan wani abinda bashi ba can ki saka kan ki a damuwa ga banza. Nace ba hakana bane ai yaya na fadi ina gyara kaina saman kirjin shi nace kasan ni mace ce dole inji haushin kasancewan ka tare da wata can daban. Magana ya dan bashi dariya don sauti murmushin danaji ya sauke lokacin. Sai naji yace yanzun dana je can na dawo gareki kin ga abinda na canza ne daga jikina ko wani halaiya nawa gare ku ? Zahra ki saki ranki don Allah ki kara fitar da wani kishin dake makale a zuciyar ki kin fi kowa sanin har abada ina bayan ki. Nace in sha Allah yaya nakuma gode dani da yaran da irin kulawan da kake bamu ko yaushe nima nasan banyi daidai ba a baya kayi hakkuri da abubuwan danai maka da farko. Yace ni komai ya wuce a wurina muddin zan samu farin ciki a gurin ku ai kun gama min komai zahra. Jin ya fara taba min jikina yasa nace dashi kasan fa haihuwa nayi ko suna har yanzu ba aiwa yarona ba ka tafi gashi kuma da sunan ubana. Nasan dama za a biyoni bashin hakan ai sai dai yanzu ina rokon don Allah ki tsaya ki tayani kwana a nan don nayi kewan wanan laulausan jikin naki da ban gajiya da tabawa. Na danyi murmushi tare da fadin dole ai mu saba da rashin juna yanzu fiye da yadda muka saba don yanzu mu ukune a wuri ka. Ji nayi ya rufe min baki ya fara aika min da sakonni a jikins a hankali a ranshi yans fadin baki san komai ba ke nan yarinya da baki fadi hakan ba ke ma. Haka dai yaita lalabani har ya samu ya samu abinda yake so a gareni ban fito dakin ba sai goshi asuba ko shi saida ya tayar dani don yaji wayana na kuka ya duba yaga fauziya ce a layin haka yasa ya gane yaron ne ya tashi take kirana a waya. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:21 - 🀐🀐🀐: Kudi masu yawa yaban don tsaraban Nafisa tare muka fita zuwa sayayya da ita inda na bata zabin abinda ranta ke so tunda kudin ta ne. Sai dai a lokacin ban yarda na nuna mata komai ba dangane da kudin tana ganin kamar kudin banza nake kashe mata tunda ina dashi. Komai take so mun saya an kumayi mata packed din shi yadda za a iya tafiya dasu har Nigeria. Ana gobe zata wuce muna falo zaune salma ta kirata a waya tun suna magana a gaban mu har yakai ta mike ta shiga dakin kwanan su ta dade a ciki suna waya. Bayan sun kammala wayan tafito tun lokacin naga sauyi a gareta sosai ta koma shiru kamar wani abu yana damun ta. Washe gari take ce min ita fa tana jin kamar ta fasa tafiyan nan har zuwa nan gaba . Nace idan baki tashi ba ai sai kiyi zaman ki nafisa nan ai gidane gare zaki iya zama abinki har lokacin da kike son tafiya. Saidai yaya yana dawowa nakw fada mai abinda tace yace sam ta koma gida don mahaifiyar su zata bukace su a yanzu ita da salma fiye da zaman ta a nan. Nafisa bata so tafiya ba dole haka ta shirya muka rakata airport sai gida Nigeria ita da tsaraban ta na London. Ba yaran ba har maria da fauziya murnan tafiyan Nafisa suke a ranan har yaya ya tsurasu suna zancen yi yayi kamar bai fahince su ba. Sai bayan kwana biyu yake tambayana irin zaman da mukayi da Nafisa da farko ban so fada mai ba saida yayi min jan ido nake fada mashi komai da tayi muna a gidan sai dai ban fada duka ba. Nasan ba zaiyi wani magana ba kyalewa yayi koda zai dauki mataki nasan sai gaba . Karatuna na mayar da hankali sosai gare shi don ina son in fito a matakin na biyu ga likitanci yanzu don haka na mayar da hankalina sosai ga abinda nake koyo. Mamu sun kawo muna ziyar bayan tafiyan Nafisa da sati daya najo dadin hakan sosai saida bata zo da yaran ba daga ita sai mahaifiyar ta da kanneta biyu babban yana makaranta a lokacin basu zo dashi ba. Naso su sauka a wurin mu sai dai ban samu hakan ba ina dai girka abinci in kai masu a masaukin su can. Satin su daya suka juya take fada min data koma zata koma gida insha Allahu don kawu har ya fara fushi da dadewan ta a sudan datayi. Sun tafi sun barmu da cike da kewan su don mun dinga jin kamar kada su koma don kewan juna da muke ji. Banga yaya yana zancen matar shi sabuwa ba nima bandamu da in san komai game da hakan ba. Bansan zamu saudayi ba sai da tafiya yanzo gab yaya yake sanar dani hakan inda nayi murna kwarai da jin hakan. Gaba dayan mu har yaran da maria don kula dasu muka nufi kasan saudiya inda na kara tabbatar da yaya ba karamin mutum bane a lokacin. Komai namu special akeyin sa a can tun saukan mu madina har shigan mu birnin maka komai a tsare yake gare mu kamar wasu manyan mutane sai faman kafa kafa yake da yaran shi dani don tawaga na musan man muke daga kasan London. Mun sauke faralin mu lafiya mun dawo gida a satin da muka dawo ne Allah ya karbi ran mahaifin merry kuma wanda yayi dan karamin jinya ya mutu. Muna gida zaune da yamma yaya ya fita da yaran shi zuwa cikin gari sai gashi sun dawo muna da wanan labarin. Lokacin daya shigo yanayin sa kawai na duba nasan yana cikin tashin hankali a lokacin baiyi magana ba saida ya zauna na dawo kusa dashi na zauna. Yaya lafiya nagan ka a haka bayan ba haka ka fita gidan nan ba nake tambayan shi cike da kulawa a gare shi. Ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin zahra mahaifin merry ne ya mutu dazun ta bugo min waya da kukanta lokacin daya mutum tana sheda min. Cikin kidimay wa nake fadin innalillahi sai naga ya dago ido ya kalleni da sauri na tuna da katobaran da nake shirin yi a lokacin. Nace oo mutumin nan ya mutu yau Allah ya kara nauyin kasa a gare shi baida amsa min da komai ba naji yayi shiru . Mun dade zaune a hakan ba wanda yai magana a cikin mu kafin ince yanzu zaka tafi ke nan don ka samu a kawar dashi a gaban ka ko ? Dan tsuki yaja yana bata fuska tare da fadin an fada maki irin kawar da gawan mu sukeyi da sauri su sai nan da dan wani lokaci mai zuwa idan sun shirya hakan. Sai dai ban jin zasu dauki lokaci mai tsawo don shi member ne na church din su a can suna da shirin hakan gare su ko yaushe sai dai duk da hakan za,a dauki lokaci kafin su kawar dashi din. Zan dai shiga na jajanta masu mutuwan inji shirin da sukeyi kan bizzine shi din Allah ya kyauta na iya fada mai kawai. A wanan ranan na karbi layin merry wurin shi don banda layin ta akan zan kirata in mata gaisuwan rashin da sukayi din . Ba nuna min zaiyi yaji dadin hakan da zanyi ba sai dai wanda ya fahince shine zai gane hakan kawai. Washe gari ya dauki hanyar zuwa wurin merry sai lokacin nima na samu kiranta na kira kira farko bata daga wayan ba . Ba zance taki dagawa bane don tasan layina don bamu taba waya da ita ba duk dadewan nan sai wanan ranan da dole yasa zan kirata din. Karo na biyu yakai ringing uku ta dauka cikin muryan ta da ya dakushe tana fadin hello a sanyaye. Nace anty merry its me Fatima from London na kiraki ne don in maku gaisuwan kan rashin papa da mukayi. May his soul rest in piece ina fadin haka na kashe wayan yayin da merry ta dade tana kallon wayan dake hannun ta tana tunane. Sauke ajiyan zuciya tayi tana kallon uwarta data tsura mata ido tana son taji wanda ya kirata a lokacin. Omar wife ta bata amsa don tasan abinda take son sani a lokacin don irin kallon da take mata. Omar wife uwar ta tambaya cikin mamaki sai kuma ta mede baki tana fadin is her business don,t mind her. Mama stop sayin dis at dis moment please all what we need is to pray now to papa I fucking care who she is now if she can pray to my father. Amma kin san haka suke da yaudara musanman ma matar musulman mu na Africa akwaisu da kissa sosai . Ban damu ba da komai tunda har ta iya kirana kan rashin papa koda tana da wani abu a ranta ita ta sani don ban damu da ita ba. Abinda na damu dashi shine mijina kawai ya dawo gareni da yata basu bane a gabana. Duk da abinda yai maki merry kike mafalkin dawowan shi gareki baki sake kada ki manta da diya hudu ya haifa da ita yanzu fa a cikin dan wanan shekarun kan kani. Mama stop all this rubish now let,s face our problems mun tsaya muna magana kan wanan yarinyar haka. Kamar yadda ya zaci zaikai gurin su da dan safe haka ya isa don tashi asuba yayi zuwa can din. Merry taji dadin hakan daya nuna masu don yakan nuna kulawan shi kan abinda ya shafe ta sosai. Bayan ya jajanta masu ne suna ta faman koke koke ya katse su da tambaya ya suka shirya bizzene mamacin yanzu. Uwar tace bamu da abin fadi sai yadda pastor ya tsara muna ina ganin hakan zai dauki tsawon wata daya kafin a rufe shi. Ya zauna wurin su har sati yana basu kulawan daya dace kafin ya juyo zuwa London ya same mu a kullun muna waya dashi yakan bamu Queen mu gaisa wani lokaci har da yan uwanta. Ban taba nunawa yaya kyamar iyalin shi ba duk da inajin dacin hakan a raina saidai mai kaya ya daure sai mai cirane zaiyi raki. Haka yasa nake danne abin a raina saidai mai karatu kin san hakan yana da zafi sosai ace ana taraiya dakai da wanda bai sallah . Dolena zama tare ya hada tawa kaddaran haka yazo min da hada alaka dasu ba yadda na iya da hakan. Nafisa tana kwance daki lokacin barcine ya fara daukan ta can a cikin barcin nata take jin murya sama sama kamar fada a gidan . Hakan yasa ta bude ido da sauri tana sauren abinda ke faruwa muryan hjy sabuwa ne ya karde gidan tana fada da karfin harshen ta. Wanan ba zai yuyu ba jummai din bake yata ke aure ba wata da watanni ya wuce ya barta a gida tana masa gadin gida. Kin san baki isa ba da danki kika yi min dadin baki akan kin isa dashi wanan abin kunyan dame yai kama hakane wai ? Gaki ba kunya gototo dake kin tare masu a gida wai ke a dole gidan danki yau idan dai kece kika haifi umar ina son ki nunawa duniya kin isa dashi mu gani. Zubur Nafisa ta mike a lokacin daga kwancen da take tana kokarin saukowa daga gadon hjy sabuwa na fadin jummai kin ban kunya kin kuma ba duniya. Ace ka haifi da ka kasa juya shi yadda ranka ke so akan wasu iyalin shi can marasa asali da tushen banza. Arniyar ce ko ita wanan yar filon bauchin mai kama da yanyawa zata fi karfin ki banyi mamaki ba don ko uwarta ta gagare ki kawarwa balle yarta da take juya ahalin ki yanzu. Hjy idan ta gagari mama ai ke bata gagare ki ba sai ki dauki mataki akan yarki idan kina ganin itace matsalan ku. Yarinya tana can bata masan kunayi ba nan don bata ko ta zancen yarki tunda aka aure ta ban taba jin tayi wanan zancen ba har na baro kasan. Yanzu kinzo ki kara zuga mama kan ta tayar da kwanciyar hankalin danta saboda yarki tayi farin ciki mu mu rasa namu farin cikin uwar mu. Hjy jummai ne cikin wani murya take fadin Nafisa kina da hankali kuwa hjyn kike fadawa magana haka kai tsaye babu kunya a idon ki ? Barta ta fada min don ta isa take gani tunda tasan har abinda bamu sani ba mu gun maza idan batayi hakan ba ai bata cika yar bariki take ba yanzu. Allah sarki dadin abin dai ba a kaina aka fara zama yar barikin ba don da yarki aka fara kwatancen hakan a gari anci legas an dawo cin kano don an rasa masunsuni a can saboda, , , , Marin da taji daga bayan ta ne ya hanata karasa abinda tayi niyar fada a lokacin don sai da ta dafe fuskan ta. Juyowa tayi da mamakin ganin wanda ya mareta din lokacin Samira ce tsaye tana nuna tace ke har kin isa mara kunya da zaki tsaya kina fito na fito da uwata. Sai in nuna maki karyan bariki yanzu in fasa maki kai a gidan nan ba,a komai dani. Nunawa yar banza kinci legas da tushe ba a nan kika koya ba Nafisa ta daga hannun ta rama marin ta nan fada ya kaure a tsakanin su lokaci guda. Hjy jummai dake kokarin rabasu batai aune ba taga hjy sabuwa da yarta sun taru a kan Nafisa suna duka da zagi . Amma dai hjy sabuwa ke mutumiyar banzace ashe ban sani ba fadan yara kika shiga haka anayi dake. Samira ta juyo tana fadin a cikin fada kada wanda ya sake zagin uwata wallahi don ban ragawa kowa akan uwata ehhe. Hakan yaba Nafisa samun daman kaiwa samira kwalban data rarama na flawer vese saman table duka dashi ta samu gefen goshin ta. Sai jini samira ta yanka ihu tana fadin kasheni zakiyi yar iska da karfin Allah suka kara taran wa nafisa har yar aikin su wanan karon sukai mata lis a gaban hjy sai fita hjy tayi tana kiran mazan dake aiki a gidan azo a cece yar ta lokacin. Da gudu suka shigo sai dai kowa ya shigo sai ya koma baya saboda yanayin da suke a ciki babu dadin gani ga kuma nafisa kwance a kasa shame shame kamar ta mutu a lokacin. Da sauri dayan mutumin ya nufi get ya rufe don tsaro kuma kada abuncin su ya kare saboda yana gudun karsu hjy sabuwa suzo su gudu su barsu cikin wahala. Mai wanki ne yayi kundun balam shiga yana dago Nafisa data some a lokacin jinta koma sharkaf yace hjy shike nan kun kashe yar mutane har gidan su. Ai hjy jummai tana jin hakan tayi kukan kura ta shake hjy sabuwa da karfin da bata san tana dashi ba a lokacin. Sai fadi take ba zata tafi ita kadai ba sai da dayan ku wallahi gaba daya ta fita cikin hayacin ta sai sambatu takeyi . Samira da tasan ba karfin uwarta daya da hjy bane don hjy sabuwa irin yan firit din mutanen nan ne sai masifan tsiya. Tazo da gudu iya karfin ta ta ture hjy ta baya ta fadi saida kwatolon ta ya amsa hannun ta data tare don kada taje kasa ya amsa yaba da wani irin kara a lokaci guda. Wani kara ta sake mai firgitarwa lokaci daya duk gidan dai da ya amsa ranan yan aikin gidan sunga tashin hankali. Dabara kiran yan sanda driver yayi ba,a jima ba sai ga yan sanda har biyar a gidan maza da mata don shiga gidan. Ya kira Alh yana sheda mai abinda ke faruwa da iyalin nasa jin bai samu wani amsa bane a gurin shi mai dadi yasa ya kira Aliyu wanda yasan shine kan gaban komai na ogan nasu. Aliyu yace a tsare su har yazo kowa yazo kada a bada belin su harsai yazo da kanshi dan sanda yace angama don yaji za a turo mai kudi. Sun kwashe su zuwa asibiti yayin da aka wuce dasu hjy jummai asibiti cikin ambulance din asibitin. Kafin wani lokaci dangi kaf sun ji labatin abinda ke faruwa a gidan umar din sun cika asibitin lokacin da ake neman rayuwan Nafisa din ta dawo. Nan zumunci yaso rabuwa a tsakanin su don ko wani bangare suna goyon bayan dan uwan su a cikin dangi nan wani tonon asiri ya taso a tsakanin su ana fadin kan zumutar su ai ba wani mai karfi bane. Kawu ne ya raba gardama don yace a sake Samira ta koma dakin ta kawai bayan ya kira Aliyu da ya hauda fada akan me zai sa a tsare mata da auren su. Nan kowa ya cika da mamakin adalci irin na Alh aka shiga tsuguri tsoma a kan maganan kowa da abinda yake fada. Muna zaune dashi a falo wayan shi yai kara Aliyu ya ambata yana kallin lokacin agogon wayan nasa. Sun gaisa sama sama Aliyu ya shiga jero mai matsalan da aka samu da hukuncin da kawu ya dauka kan maganan. Yace please Aliyu don Allah kada ka kara kirana kan wanan maganan don ko me sukayi ai hjy ce tajawa kanta tunda kowa ya fada mata gaskiyan halin wa yan nan mutanen . Ina zaune kamar ban sauraren abinda suke fadi a lokacin don na mayar da hankalina gun yarona ina wasa dashi. Saidai hankalina yana ga abinda suke fadi a fakaice naji ya kashe wayan yana jan tsuki tare da fadin sun ma rainawa mutane wayau. Na dago kamar ban fahince shi ba ina fadin su waye kuma dan kallona yayi kamar ba zaiyi magana ba can kuma sai yace wai wanan matar ce . Uwar yarinyar nan Samira tazo gida da fada har abin ya kaisu ga bugaiya har suna kwance asibiti Nafisan da mama . Ita mama ta tabu a bayan ta da hannu ta samu kariya itako Nafisan dai har yanzu bata farfado ba. Innalillahi nace ya akayi hakan ya faru kuma yace maganan ne babu dadin ji ai yana mikewa. Nace yanzu ya ake ciki don bai kamata a kyale wa yan nan mutanen ba gaskiya don rainin wayau nasu yayi yawa wallahi. Kawun ki ai ya kashe magana don yace a sake su su koma gida a dan razane nace an sake su kuma may yasa kawu zaiyi haka kuma ? Yace ko nine shi haka zanyi ai don shine daidai ko kin manta yadda mama ta rufe idon ta akan su taci wa kowa mutunci ido rufe. Don suyi mata haka kema kin san daddy ba zai kyale su ba ai dole ya dauki fansa tunda ta nuna tana son su fiye da kowa. Allah ya kyauta nace ya wuce ciki yana fadin Amin rai bace don nasan ba zai juri zaman da mukeyi ba a lokacin cikin yayan muna hira. Washe garin wanan jidalin ne mamu ta iso gida ta samu wanan labarin mai tayar da hankali. Ta samu kawu ya hana kowa ta bangaren shi zuwa asibitin ga hjy maryam da gulma ya addabeta tana son zuwa kada a bata labari da ba daidai ba. Ga kuma gulman dawowan mamu da abin arziki da canzawan ta daya tayar mata da hankali sosai tana son samun abokin rage mata nauyi wanda zasuyi gulman hakan dashi. Gaba daya mamu dan lokacin da tayi a can ya sauya mata dabi,un ta ta koma wata irin classic lady a idon kowa. Yanayin ta gaba daya ya canza a lokaci guda sai tarin dukiya da aka hadota dashi ita da yara suka dawo Nigeria dashi. Abin sai ya taru yaiwa hjy maryam yawa saidai da yake gulmane haka ta taushe zafin da takeji taje gun mamu tana tsugunta mata abinda ke faruwa bayan tafiyan ta. Mamu dai kallon ta takeyi tana sauraren ta da mamaki a ranta tana fadin hali zanen dutse don har yanzu hjy maryam na nan da halin ta ashe. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:21 - 🀐🀐🀐: Tun shigan shi dakin nake zaune ina nazari a raina irin rikicin da aka kwasa har takai wanan abin ya faru a tsakanin su haka. Na dade yaran suna wasa ina zaune sai jefi nake dan saka masu baki ga harkan su don Allah ya taimakeni. Basu da yawan hayaniya da magana idan kaji kuka ko fitina sai idan sultana ce ta jasu fada kuma ita ke kuka a karshe. Ban tashi ba sai da naga yaran duk suna jin barci a lokacin nasa maria ta kaisu daki don akwai school washe gari. Na dan tsaya da maria dake aikin gyaran falon sai hadawa yaran abinda zasuci da safe don tafiya zuwa school. Kafin in koma dakina inyi wanka lokacin fauziya da Abbati sun dade da yin barci ko haka na samu daman shirina tsab na bar dakin nawa zuwa dakin yaya wanda a zatona nake dauka yayi barci ko a lokacin. Saidai ina tura kofan na samu ganin akasin hakan don yana zaune ya tasa computer a gaba yana aiyukan shi hankali kwance. Sannu da aiki nayi mai tare da samun wuri na kai zaune a gefen shi naji lokacin da ya sauke ajiyan zuciya a fili ya dan dakatar da abinda yakeyi yana kallona. Yaran sunyi barci ke nan ya tambayeni nace tun dazun suka kwanta ai mun tsaya da maria ne a falo. Ba tare da ya dago kan shi ba yake fadin yanzun na kare waya da Ahmed da sauri na dago kai ina fadin mijin salma ya gyada min kai kawai batare da yin magana ba. Ya fara aiki da kune na tambaya ina kallon fuskan shi sun fara ya ban amsa a takaice ba tare da dago kai ba har lokacin hankalin shi yana ga computer shi. Mansur na bashi shawara ya dawo kano da zama don jigila zai mai yawa tsakanin bauchi da kano din sai abin hawa da zasu samu don rage dawainiya gare su. Kallon mamaki nayi mai don ban taba tsamanin Mansur mijin Atika ya samu aiki ba shima a gurin su kamar yadda na roka a sama mashi din. Hamdala nayi ina fadin kai ban ma san irin godiyan da zanma ba yaya wallahi naji dadin wanan maganan sosai yaya . Din Atika ta taimaki rayuwana a lokacin daya dace a taimakeni nima yanzu kuma ka wanke min zuciyana da irin sakaiyan da zan mata a kullun shi nake tunane. Ni nasan ai irin godiyan da zaki mun idan baki sani ba ke ki bari ki gama sai in nuna maki kalan shi. Dan mutmushi nayi ina girgiza kai kamar yadda in yai min irin wasan nan nasan me yake nufi da hakan. Nace basai ka nuna min ba yaya ni da kaina nake son in godema ai amma ka dan ban lokaci nan gaba in gama tunane. Na baki yace yana rufe laptop din tare da juyowa gareni yana fadin idan ban rufe wanan abin ba zaki saka in tura sakon da bai dace ba . Ganin ya rufe laptop din yana fuskantana nace mai barin koma dakina in barka kayi aikin ka hankali kwance. Wanan kuma shine baki isa ba dakin ki dauko me Fauziya tana tare da baba don haka baki da matsala da komawa daki yanzu. Har kwana biyu ban sake jin halin dasu hjy shi ke ciki ba ga gulma kuma ya cika min ciki gashi ya dace ace na kirata in mata ya jikin. Saidai ina gudun jawa kaina wata fitina don nasan halin hjy sarai zata iya yaba min bakar magana mai zafi idan na kirata. Don ba abinda zata so inji bane tunda tsakanun su dasu hjy sabuwane abin ya faru hakan akwai kunya da nauyi gareta. Hankalina kwance nake karatuna dagani har yarana yayin da yaya shi kuma yake faman kujiba kujiban neman haliyan shi ko yaushe. Mutuwan mahaifin merry da wata daya yake fada min zancen bukin rufeshi ya taso don haka zai tafi a cikin sati mai zuwa. Kallin shi nayi nace ai muna zamu tafi don mu nuna mata kulawa tunda abin ya shafe ka ai amma idan hakan ba zai zama matsala ba. Babu wani matsala don kun tafi kawai dai bana son ina danganta lamarin sune daku ya bani amsa. Wanan ai mutuwa ne don haka ya kamata muje a jajanta mata don in ba a yanzu zamu tafi babu lokacin da zamu hadu da ita kuma. A kwai lokaci don ina ganin kina gama karatun nan gaba daya zamu tattara mu koma gidane don na gaji da zaman kasan nan zan koma gida inyiwa kasata aiki haka. Dadin hakan naji har kasan raina a lokacin nace Allah yasa hakan shine alheri a garemu ya amsa da Amin. Washe gari da ya fitane sai gashi yazo muna da kayayyaki da nawa dana yaran dukka bakake wulluk sai dai mu mata namu jallabiyane dogaye yan kasan Jordan. Sai mazan yara dashi daya saya masu suit bakake daidai su masu kyau sosai. Ni dai banyi magana ba duk da naji zafin hakan kenan dole idan munje muyi akidar su ke nan a gurin yake nufi. Ni na dauko zancen tafiyan don haka dole na shanye komai a raina na nuna ba komai a hakan. Shirin shiga US mukeyi wanan satin ga tafiyan yai muna daidai don andan samu break a lokacin daga ni har yaran namu haka yasa zamuyi tafiyan babu takura. Saidai a raina ina tunanen irin taron da zamu samu a wurin merry din idan mun tafi koma dai menene ai kulawa zai kaimu. Bai fada mata komai ba game da zuwan mu sai ganin mu kawai merry tayi a kasan sai dai ba,a gidan muka sauka ba kamar yadda ya tsara. Mun saukane a wani katafaren hotel mai kyau da tsaruwa nayi mamaki a raina ganin a hotel zamu sauka ba a gidan merry din ba. Saida yaga komai yayi yadda yake so damu kafin yai muna sallama zuwa gidan merry din. Rayuwana yaso ya baci da hakan da yai muna sai da wata zuciya ta gargadeni kan hakan don zan bata rawana da tsale idan na nuna hakan. Asalima ai wanke kaina da gyaran kaina a idon mijina nake hakan tunda ban ko san yaya merry din zata karbe mu ba ma. Ban yarda mun fita ko ina ba muna dakin daya kama muna din munci mun sha daga nau,in cimar da suke dashi a cikin hotel din tare da dan taba hira da maria. Na irin yanayin kasa da namu kasashen irin bambamcin kasashen da rayuwan mu a Africa don ko wani lokaci su basu taba rabuwa da ni,ima a turai. Banyi barci da wuri ba na dade ina zaune ina adduoin neman kariya a wanan tafiyan namu daga ni har yarana na gama na shafa tare da nade abin sallah na koma saman kujera na kwanta don in barsu su sake a saman gadon . Can barci ya dan fara dauka na bayan na gama dan tunane tunanen yadda haduwan namu zai kasance a gobe da merry din. Mafalki nayi wai merry tana ganin mu ta haukace a wurin tayo kaina ni da yaran tana fada tana fisge fisge ana riketa sai kawai ta nufo gadam gadam zata caka min yuka. Da sauri na zabura daga barcin ina fadin innallilahi sai zufa nakeyi lokaci guda duk da sanyin dake dakin na AC dana yanayin garin. Kasa komawa barci nayi ina bin dakin daya dan gauraye da duhu da dan haske da muka bari don haska dakin. Wani irin tsorone ya rufeni a lokaci daya sai adduan da duk yazo min a rai nake karatowa don neman kariya ga abinda na gani a cikin mafalkin nawa. Tsoro iya tsoro na jishi a wurin wasa wasa ga barci ya gagareni mikewa nayi zuwa ban dakin na kara dauro alwala na fito nayi sallah neman kariya ga duk wani abin kin da zai tunkaremu a wanan tafiyan. Daidai lokacin da yaya yake can suna kwasan rikici da merry din a gidan ta kan rashin zuwan shi da wuri da baiyi ba duk da kuwa tasan a satin ya dawo yai tafiya zuwa kasan chaina wani aiki a can. Yaya baidai fada mata tare damu yazo ba sai sauraren ta yake har tana fadin gabadaya ya sauya mata daga umar din data sani zuwa wani umar din. Zagi da cin mutunci dagani har shi babu wanda batai muna ba tana fadin dama itace ba a so dashi yasa aka aura mashi yar uwan sa gashi kuwa yana nuna mata hakan a fili. Yana kwance yana jin ta uffan baice da ita ba lokacin don ranshi babu dadi don bayan kudin daya bata don tai hidimar saida bai fito fili yace da ita don bukin ya bata kudin ba. A gaskiya irin kudin da merry take wawura gurin shi ko kwatankwacin rabin shi bamu samu nida yarana . Nasan da hakan amma ban taba nuna bacin raina ba a kan hakan tunda bani na nema masa ba. Sai washegarine ya shiya da safe don duk hankalin shi yana gurin mu a lokacin saboda banda layin kasan a wayana. Dakin ta shigo tana kallon shi cikin mamakin ganin ya shirya a cikin bakaken kaya kamar shigan su don bata tsamaci hakan ba sam a gareshi. Mamakin ganin hakan yaki boyowa a fuskanta daga inda take tsayen tana mai kallin mamakin sai ta fashe da kuka mai kama da kukan murna lokaci guda. Tana karasowa inda yake ta fada jikin shi tana ci gaba da kukan nata a hankali bayan ya rugume tane ya fara dan bubuga mata baya a hankali. Sun dan dade da hakan kafinta zare jikinta daga nasa tana mai dago kanta tare da mashi godiyan yin hakan da zaiyi mata don bata taba zaton zai tafi wurin birne mahaifin nata ba . Don tun bayan rikicin su a kan queen data nuna mai bata yarda da yarinyar ta koyi addinin shi ba wanda hakan ya kawo rashin jittuwa har wanan lokacin a tsakanin su suna sama sama da junan su ne kawai. Bata kaiga karshen mamakin ta ba sai lokacin daya kwaso mu zuwa inda suke bidi,an nasu muka tun karo wurin a cikin shiga daya burge kowa don jallabiyan jikin mu dake daukan ido da nuna martaban mu a gurin. Dan nisa kadan da inda suke muka tsaya muna nuna namu jimamen kan mutuwan mahaifin nata daya mutu ya karawa kasa nauyi. Juyowan da merry zatayine tana magana da wata ta kusa da ita ta hango mu a inda muke tsaye din tare da iyalina . A bazata ta ganmu saida ta kare bude idanuwan ta don ta tabbatar da abinda ta hango din a lokacin. Sai bayan su a halinsa sun dibi kasa sun fara zubawa a ramin sauran jama, a suka dinga diba daya bayan daya suna zubawa sai masu kada flawer a ramin da sauran tarkace. A wurin daida muke nan muke ban yarda mun gusa ba har lokacin da suka kare akidan su aka fara watsewa bayan addu,oi. Yana rike da merry dake ta faman share hawaye a fuskanta sai queen da itama tasha adon bakaken kaya da suka matse jikin ta sun fitar mata da suran ta sosai. Mutane merry suna zuwa daya bayan daya suna dan rungumar ta alaman yi masu sallama da jajanta masu mutuwan . Alama nayiwa maria mu tafi inda motar da mukazo da ita take tun kan a farga damu a wurin. Duk da hakan saida wasu suka dinga kallon mu sun dai san mu musulmai ne tun daga yanayin shigar mu har zuwa tsarin rayuwan mu a gurin. Merry ce suka iso inda muke tsaye a gutin motan muryan ta naji tana fadin Fatema you are welcome for dis funeral. Sai kuma ta fara hawaye don maganan da take son fada ya makale a bakin ta saboda kukan daya zo mata a lokaci guda. Tausayi sosai ta bani a gurin nima hawayen ne yazo min na fara dan sharewa da gefen gyalena dake rufe a kaina nayi rolling. A cikin shakaken muryan tana kuka take fadin a tafi damu gidan su inda za,a hadu ayi last respect ga mamacin a can. Sai da ya dan yi magana da ita kafin yazo ya shiga mota muka dauku hanya zuwa gidan mahaifin merry din . Gidan yana makil da ire iren su saidai akwai musulmai dake da dan alaka dasu a gutin saidai bamufi yan tsiraru ba a gurin. Merry ta bamu lokacin ta sosai a wurin koda tana data ciki dai ta boye muna hakan don duk abinda na zata zatai muna batayi shi ba a gurin. Sai na dangata al,amarin da karfin addua ya kai ga hakan don a yadda merry take jin zafina a ranta. Tana ganin nice na shigo rayuwan su na raba farin cikin dake yabe a tsakanin su ina kokarin raba jin dadin su koma na raba din . Merry sam bata yarda da sharing din miji a tsakanin mataye ba don hakan ne koda ya tafi wurin su suke kwasa rikici kafin su dan daidai ta. Wani zubin haka zaije ya koma ba tare da komai ya wakana a tsakanin su ba wanda hakan har ya fara bin jikin shi ya fara rashin jin dadin mu,amula da merry din ta ko ina a yanzu. Bamu jima ba do mutanen da suka fara fahintar mu su waye ga merry din dan gulma yana tashi ana kus kus tare da zubo muna ido. Wanda mahaifiyar merry din ne tabar bakin cikin dake damun su na rashin mijinta ta dauko kishi ta saka a ranta tana ji kamar tayi poisining din mu dani da yarana a gurin. Ganin yadda uwar ke son muna rashin mutunci ne yasa merry kiranta daki tana ja mata kunne a kanmu kan kada ta yarda ta nuna muna wani halin da bai dace ba. Koma meye a yanzu na gama mata komai tunda har na iya zuwa tayata bakin cikin bizzine mahaifin ta wanda suke daukan hakan da sai masoyin kane zai ma hakan. Ko ruwan su bamu yarda mun sha a gurin ba komai aka bamuba wanda muka kalla a gurin. Indana kara godewa Allah shine yarana basu da daukan ido irin na wasu yara komai bai faye shiga ransu ba a lokaci guda na basu tarbiyan kada su karbi abu a hannun kowa koda ka basu sai su girgiza ma kai alaman basa so. Da haka mukai sallama muka bar gidan zuwa masaukin mu don a ranan zamu koma London zamu bar yaya a nan don mun gama abinda ya kawo mu kasan US. Taka a hankali mama zaki iya insha Allahu Aliyu ne ke wanan maganan yana rike da hannun mama dake kokarin tashi tsaye daga saman gado. Sai dai duk kokarin ta takasa tashi yadda suke so matsalan daga mahadan kashin joint dinta na kafan tane ya gwauce. Komawa tayi ta zauna tana runtse idanuwan ta saboda zafi da radadin da take ji har cikin rayuwan ta a duk lokacin datayi yunkurin tashi tsaye kamar yadda ake son ta mike . Ido a rufe tana sauke ajiyan zuciya tare da tunanen sanadin hakan a gareta ga yarta Nafira da itama tana fama da jikin ta duk sanadin su sabuwa da yarta. Mutanen da ta dauko ta saka a cikin ahalin ta don kawai suma a ci arzikin danta dasu saboda zumunci. Ido ta kara rufewa lokaci guda tana mai kara jin zafin su a ranta gashi Aliyu yazo mata da labarin Samira tana nan gidan dan nata zaune. Hankali kwance har da kokarin kafa dokan ba zata sake zama da hjyn ba a part din ta saidai a bude mata dayan part din ta zauna har in tana son zama a gidan. Kuma daddyn yara ya yarda da hakan da suka bukata a cikin sharadin su tun a wurin yan sanda kafin a sallame su. Jin wanan labarin da dan nata yazo mata dashi ya matukar bakanta ran hjy take jin kamar ta tashi ta samesu a gidan ayi duk abinda za, a yi sai dai ba halin hakan gareta yanzu. Don ko tsaye bata iya mikewa dole sai likita yazo an kara duba lafiyan ta ansan inda matsalan yake a jikinta. Ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki har tsawon sati yasa Aliyu ya kira yan uwanshi ya fada masu halin da mahaifiyar tasu take a ciki. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:21 - 🀐🀐🀐: Mun dawo a gajiye ana labta ruwan sama muka shigo gida a gajiye maria ta gama tanadar muna abinda zamuci a gidan idan mun dawo kafin mu tafi don haka warming din shi kawai tayi taba yaran da su suka zauna ci. Yayinda ni nake dakina ina ramuwar sallah dake kaina wayana da na bari a falone yake ta tsuwa Fauziya ta kawo min dakin. Mamuce a lokacin na dauka muna gaisawa nake fada mata zancen tafiyan mu tace duk da dai hakan yana da kyau saidai makomar shi ga addini ne ban sani ba. Mamu yaya zanyi tunda rayuwana yana surke da nasu yanzu koda banje don wanan ba zan tafi kan wani dalili na daban watan watarana ai. Tace Allah ya sauwaka dama dalilin kiraki shine ki sheda wa mijinki cewa mahaifiyar shi fa tana jin jikin ta dan haka yayi gagawan zuwa dubata don Allah. Yau munje dubata dan da kyat Alh ya barmu muka tafi duk da na fahinci hjy maryam kamar ta riga da ta tafi da farko. Mun samu hjyn tana mai jin jikin ta sosai wallahi don ko matsawa bata iyawa don jikin yayi tsami sosai gaskiya abin gwanin ban tausayi. Ga Alh yayi fushi sosai da wanan lamarin ya hana kowa zuwa dubanta daga bangaren shi haka itama nafisa kan ta ya bugu sosai ya hau yana bata matsala. Innalillahi nace tare da fadin ke nan ba,a dauki wani mataki a kansu bane mamu ? Ban san me suke ciki da zancen su ba don na dawo na samu wansn matsalan daya rigada ya farune nace yayan yana can mun barshi wurin merry nida yara da maria kawai muka dawo. Mun dan jima da mamu muna zancen fadan su hjy din karshe dai mukayi sallama a lokacin ne na fito falo wurin yarana. Har lokacin suna cin abinci basu kare ba zama nayi na dan taba kafin na karasa yaya ya kira layina yaji saukan mu. Bayan mun gaisa dashi ne nake fada mai sakon mamu yace Aliyu ya kirani ya sheda min halin da ake ciki gobe zan dawo nan zuwa dare sai in tafi. Allah ya basu lafiya nace ya amsa da amin cikin yanayin rashin jin dadi a ranshi a lokacin. Sai bayan na gama waya nake ba su fauziya da maria labarin abindake faruwa a gida da hjyn na su. Yaya ya dawo ya dauki wasu takardu ya tafi da yamma zuwa duba mahaifiyar shi inda yaje ya samu abin babu dadi a gare su don hjy tana jin jiki sosai a lokacin. Yana zuwa dole yasa aka sauya mata asibiti don halin daya sameta a ciki na jin jiki sosai. Alhamdulllahi don kudi yasha kashi sosai a gurin aka samu gano inda matsalan yake sosai don haka sai a hankali sauki zai dinga shiga. A gidan shi kuma tunda ya iso samira ta fara farga ban abinda zai faru tsakanin shi don bata san irin matakin da zai dauka ba a kan hakan daya faru tsakanin ta sa mahaifiyar shi har sister din shi Nafisa. Uwar ta kira tana sheda mata zuwan nashi a cikin tashin hankali da damuwa don ita dai tasan korarta zaiyi kawai a gidan. Uwar taja wani dogon tsuki tana fadin wanan shashancin fa haka da kike yi ya kore ki mana idan kora banza ne ai yadda kikaga ubansa yayi shima hakan zaiyi don ba zan kashe kudin banza a nan. Kedai abinda nake so dake yanzu shine ki maida hinma wurin ganin yaci yasha a bubuwan da muka karba da sunan shi. Ta karba da tau umma don samun karfin gwiwan da tayi gun mahaifiyar nata taji wani dakewa yazo mata a lokaci guda. Sai dai duk yadda tayi kokatin ganin yaci ko yasha daga gareta bata samu hakan ba don ko ganin shi ma yai mata wuya a gidan. Don haka ta dauko dabaran barin abincin ga yan aikin shi ita ala dole sai yaci abinda suka hada da sunan shi din don su samu kanshi yadda suke so tunda mahaifiyar shi ta kasa juyashi yadda suka zata Jin shiru yasa ta dauka yaci bincin da take aje mai a lokacin don haka ba wani matsalan da zata samu daga gareshi kamar yadda daddy shi ma bai iya daukan mataki a kansu ba. Umar suna zaune a gaban mahaifin su dukkan su suna tataunawa dangane da matsalan mahaifiyar tasu kan abinda ya faru . Don rayukan su duk a bace take bisa ga halin da suka samu hjyn tasu a cikin na tsananin jin jiki a lokacin. Sai dai kawu din ya nuna masu rashin yadda su dauki wani mataki a wanan lokacin don a cewan shi ba a daukan mataki irin haka a cikin bacin rai. Sai yayin da mutum ya gama nazarin abinda yake son a dauki mataki a kan nasa din ko abokin gaban naka ya gama kwantar da hankalin shi da kai. Wanan maganan na kawu ya dan saka zukatan su sanyi don su da farko sun dauka saboda abinda mama din tayiwa kawune yasa yace samira da uwarta a sake su a police station. Sai yanzu suka gane sanyin raine kawai irin na mahaifin su yasa ya yanke wanan hukuncin gare su. Kulawan da hjy ta samu a yanzu yasa saukin da take samu yana kara wanzuwa a jikin ta har ya kai yanzu tana iya dan mikewa da kanta ba tare da an rike ta ba kamar farko. Duk da hjy na kwance hakan bai hanata aikata wasu daga cikin halaiyan ta ba munana don ranan da Amma ta dan samu karfin zuwa dubata a inda aka mayar da ita ta matsa sai a kaita ta ga hjyn. Suna zuwa basu dawo a cikin dadin rai ba don can ta shiga sake masu habaici wai anso aga bayan ta Allah bai nufa ba gashi diyanta sun mata gata bata kai ga halaka ba. Sai mama Hadiye ne duk da warning din da Amma ke mata da ido da kai ta bata amsa tana fadin banda abinki jummai wa zai tsaya daukan wa kanshi nauyi a kanki kowa tasa ta isheshi yanzu. Faduwan ki ai da abinda ya faru tsakanin ku da sabuwa wanan matsalanki ce ke dasu don mu ba abinda ya shafemu a cikin zancen ku domin kunfi kusa ai keda su. Matar da kika zabi ki farauta ranta dana yarta kika iya barin dakin auren ki da yaran ki don ta don ta baki wanan goron har zamu tsaya bakin ciki kan hakan aimu bamu ga abinda tai maki ba da zaisa muji dadi hakan. Tukun na ai yanzu kuka fara nunawa duniya nau,in taku kallan soyayyawa juna don yanzu aka fara wasan a tsakanin ku. Amma ta gardadi mama hadiye suka bar dakin hjy tana jidali wai dama ai tasan ba gaisuwan Allah da annabi ya kawo su ba gurin ta anzo ne a samu abin fada . Tun wanan lokacin kawu ya hana kowa daga cikin iyalinshi zuwa a kara duba jikin ta sai hakan yai mata zafi kuma, . Salma tazo gidan don ta gana da yan uwanta maza kan zancen komawan mahaifiyar su gida don a yadda suke so daga asibiti hjy ta koma dakin ta a gidan kawu. Sai da ta gama maganan ta habbib yace salma ke nan ina ganin kece kika damu da hakan don ita mama wanan zaman da kuma abinda ya faru tsakanin ta da hjy sabuwa kamar bai dameta ba. Din jiya jiya jiyan nan ta gama ciwa so Amma mutunci kan kawai sun tafi gaida ita asibiti yanzu kuma yau korafi take a kan matan mu babu ko daya dayazo gaida ita wai kamar bata da gata. Duk zancen su umar bai saka baki a ciki ba sai can da yaji sunyi shiru yake fadin ban dauka har yanzu mama zata saduda da halayen ta ba gaskiya . Yadda mama takewa Amma tasan cewa itace mahaifiyar daddy amma take rufe ido tana ci mata mutunci daddy da Amman suna hakkuri hakkuri da hakan. Yau gashi Allah da ikon sa an fara samun wace zata rama hakan daga kuma zabin ta sai yanzu nake kara gane mai daddy ke nufi da rashin daukan mataki a kan wa yan nan mutane ashe. Sanin halin mama ya saka daddy yin hakan da hanani ni kaina daukan wani mataki garesu duk da yasan girman abinda suka aikata a gareni, amma ya tilasta min barin su su zauna min a gida. Aliyu ya karbe da fadin wanan matakin daka dauka yayi daidai a yanzu ba dai gidan bane sai su zauna idan gidan zasu aura. Zasu dauki mataki nan gaba don ba kunyane garesu ba a lokacin ya kamata a basu amsa habbib ya fada . Din haka ke salma ki koma ki kara hakkuri har lokacin da mama zata dawo gida nasan lokacin zasu so sanin matsayin yarsu a gidan nan. Ni dai da nine yanzun da an gama tsakanina dasu koda daddy ya hani daukan mataki a yanzu ya zama dole gareni in dauka koda a boyene. Murmushi umar yayi yana kwantar da kai ga kujera tare da lumshe idon shi yana jin zafin irin yadda yan uwan shi keji game da maganan. Salma ce ta kawar da shirun falon da cewa sai maganan Nafisa don daddy yayi fushi da zaman ta nan gurin mama datayi tun dawowan ta kasan nan sosai. Dole yai fushi don sam basuyi tunane ba daga ita har mama din data barta a nan tunda nura ma daddy bai barshi ya biyo mama nan din ba ai habbib ne ke magana. Eh hakane gaskiya don lokacin dana zo munyi wanan magana da daddy kan zaman ta wurin mama ya nuna min bacin ran shi kan hakan sosai ranan. Yanzu shi Nura a gurin wa yake zaune umar ya tambaya cikin kulawa tare da bude idanuwan shi ga yan uwan nasa a lokacin. Yana gun maman twins tun data dawo da farko a gurin maman su ikilima yake sai fitina ya dinga aukuwa a tsakanin shi da yaran ta a cikin hakan ya koma gun Amma dawowan maman twin's din yace a gurin ta yake yanzu. Idon shi ya lumshe yayin da Aliyu ke fadin you see zaici gaba da magana takon takalman da sukaji shine ya dakatar da shi ga maganan da yai niyar yi a lokacin. Gaba dayan su ido suka sakawa samira da ta shigo cikin wani tako tana rangwada har ta kawo garesu. Kuna nan ashe sannun ku da zuwa sai Aliyu ne da salma suka amsa habbib kan waya ya dauka yana duba a lokacin kamar baisan tazo gurin ba. Akawo maku abin tabawa ne tace tana kallon inda umar din yake zaune idan bako tazo gidan ka sai ka tambaye shi ka bashi ruwa habbib ya bata amsa a gwatsale. Ba hakana bane kawai naga kamar har kunsha a nan ne yasa na tambaya ki barshi duk a koshe muke. Ta dan taka zuwa gefen kujeran da umar din yake zaune da niyar zama a hannun kujeran da sauri ya daga yana fadin. Zamu iya tafiya yanzu salma muje mu sauke ki asibiti daga can mu duba mama kan mu tafi yana fadi a daidai lokacin da samira ta iso gurin . Tsayawa tayi sororo tana mai bin shi da kallo kowa na falon ya fahinci may yasa yai hakan a lokacin. Wani kallon banza habbub ya bita dashi lokacin da yake kwasan wayan shi saman table din. Har suka fice tana binsu da kallo ranta yai bala,in baci da disgatan dayayi a gaban yan uwan shi din. Wayan ta dake hannun ta dauka tana duba lanban mahaifiyar ta takira take fada mata abinda ya faru. Bata kai karshe ba uwar ta hauta da sababi tana fadin ke tafi can samira kina ban mamaki da har yanzu kika kasa juya wanan sokon mijin naki. Har yaushe kamar umar zai tsaya yana wani baki baya kina faman binshi kamar wata sokowa ki saurareni da kyau kiji may zan fada maki yanzu. Ina jin ki umma ke har yanzu laifina kike gani kan hakan umma kwata kwata fa baida lokaci na balle in samu daman juyashi yadda kike nufi din. Rufa min baki ke ba mace kike ba da har namiji zai gagare ki juyawa samira ? May kika rasa a jikin ki wanda maza keso da baki dashi a yadda ya baro wacan matan nashi yanzu ne ya kamata ki nuna mai ke din mace ce. Nan dai ta shiga nuna mata hanyar da zatabi ta samu kanshi tunda asiri ya gagareta aiwatarwa a gareshi sai su juya hanyar kisa da kisisina irin namu na mata. Samira tace na gane umma yau insha Allahu zanyi duk yadda kika fada idan ya shigo tace kada ki manta ki dakatar da duk wani dan aikin gidan daga yi masa komai ki daina wanan kwanciya a dakin har mu samu kanshi. Umma komai fa kikace har girki da komai ke nan fa ta fada a shagwabe katseta uwar tayi ta hanyar kiran sunan ta a kausashe da Samira . Zakiyi abinda nace ko sai kwabar mu yacin ma ruwa zaki gane kuren ki don ina gab da fita bayan ki muddin baki bi abinda nake fada maki ba. Umma zanyi abinda kika fada min daga yau din nan zan fara koke fa uwar nata tace da ita tana kashe wayan bayan ta ce ina sauraren ki zuwa dare. Zaune nake a wajen haraban gidan muna shan iska yaran ke wasannin su yawancin lokaci nakan dan fito dasu idan muna gidan bamu komai don yara saida dan wasa. Juice din dake gefena Abdulrahim ya zubar sai a jikina hakan yasa na kaiwa yaron dan duka a cikin hasala ina mai fada kan rashin ji. A daidai lokacin kuma danake fadan wayana ya dauki kara ina fada nake dauka batare dana kula damai kiran nawa ba. Muryan ya umar naji yana tambayan meya samu yaron yajin yana kuka nace dukan shi nayi don baya ji wallahi. A cikin wani irin murya yake fadin kika dokeshi Zahra har kike fada min ba wanan ba ma me yayi maki kika doke shi ne haka ? Yaya idan sunyi abin fada ba za,a ai masu fada ba yace banda duka ko kin manta naki kurciyar ne zahra kewa ya duke keki ? Mamaki ne ya kamani na kasa magana har ya gaba min fada ya kashe wayan a hasale nan ya barni zaune ina mamakin shi. Tunane yazo min a rai ina fadin wanan ai sakacine gareni ace ba zanwa yara fada ba irin hakan shike kawo matsala a gaba. Yaro ya taso a cikin gata lokacin da mahaifa keson su tankwarashi ba zai takwaru ba a garesu sauda dama nakan kayi hasashen hakan ga yarana yadda yaya yakan hana a tsawata masu wani lokacin idan sunyi abu. Mikewa nayi daga inda nake zaune zuwa cikin gidan dakin kwanan mu na shiga har lokacun ina jin ba dadi don sam ba zan yarda da wanan irin akidar ta yaya ba kan yaran mu. Wanan yasa kwana biyu dagani har shi babu wanda ya kira dan uwa a cikin mu don ina son nuna mai hakan ba zai yuyu a gare mu ba kan yaran mu. Wanan yass yanzu ma daya bar gida don gujewa Samira da sallon da take son nuna mai a gidan na shishige mai a jiki datake kokarin nunawa a yanzu yake jin bacin rai a tare dashi don ya fahinci kamar bata san laifin da tayi ba a gare shi ita da uwarta. Yayi kiran layin mu a lokacin na bar wayan daki muna kasa muna hira da maria. A daidai lokacin ya shigo gidan daga masallaci ya nufo dakin part din mu inda yake yana jin ranshi babu dadin fushin da nake dashi haka. Dakin kwanan shi ya shiga tun a kofa ya fara cire aninin rigan shi baya yabawa kofan dakin don haka bai san da shigowan ta dakin nasa ba. Sai jin an kai mai runguma yaji daga bayan shi wanda yasa ya firgita da sauri ya juyo da mamaki yana fadin subbahanallahi meye hakan kike mun a nan ya tambaya rai bace. Cikin kashe ido tace ni ba matarka bace idan baka neme ni ba ni gani na kawo kaina gareka yau ina neman hakkina gareka don ba zama shan sanyi AC da dadi na baro gidan mu ba ta kare magana tana kokatin kara kai mashi runguma. Rashin tarbiyan naki yakai haka ban sani ba har zaki shigo min daki ba tare da izinina ba . Kina son nuna min barikin da ake cewa kina da digree din shi a tare dake ne ko me ? Don nazo gurin mijina shine bariki to bari kaji yau a dakin nan zan kwana a tare da kai ko ka shirya hakan ko baka shirya ba. Wani irin mari ya kwashe ta dashi lokaci guda yana nuna mata kofan fita rai bace tare da fadin kin dauka kowa irin kine mara mutunci. Da zaki shigo min daki haka babu sani na don kinga ban dauki mataki kan abinda kukayiwa mahaifiyata ba har kika samu daman shigo min dakina kai tsaye. Waye ya baki wanan daman da har zaki tako nan don baki da kunya ki fice min daga nan kafin ranki ya kara baci. Ki koma ki jira wace ta aje ki a gidan nan idan ta dawo daga asibiti tasan yadda zatayi dake don ba zamana kike a nan ba. Kin ga kafata a gidan ku ina aure a inda ya kamata nayi aure a gurin da aka san darajana dana iyayyena . Na barki gidan nan don mahaifiyata data dauko ki hakan bai maku ba saida kuka saka mata da duka daya kaita kwance asibiti a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:22 - 🀐🀐🀐: Mahaifiyar ta ta kira cikin kuka tana fada mata yadda sukayi dashi irin koran wullakancin da yai mata ya hankado ta daga part din. Har ta kare fadi hjy sabuwa bata samu bakin magana ba sai da taji yar nata tayi shiru tace. Amma samira anyi yar banza kikaki yi mai koda karfin tsiya ba namiji bane idan kin masa tsirara ki ka hayesa ai dole ya baki hadin kai ko baiso ba daga nan komai ya kankama a tsakanin ku. Umma baki ga yadda yai min bane kike fadin haka wallahi ya rike mu sosai daga shi har yan uwan shi kan maganan wanan matan mahaifiyar su. Umma shiyasa naso ki bari tun farko mubi wanan abin a sannu har ya sauko amma kika zo da rigima da uwarshi gashi yanzu komai ya kara lalacewa kuma. Rufa min baki danazo da rigima don wa nazo ina don kine don abu ya kwabe yanzu zakina ganin laifina ni kadai. Duk wa yaja wanan abin haka idan bake ba ni yanzu kin fara ban haushi wallahi ace yarinya kamar ba mace ba tana fadin hakan ta kashe waya a cikin haushe. Samira hankali tashe ta kara kiran uwar bata daga wayan ba don takaicin yarinyar da take ji saida tayi mata kira uku gana hudu ta dauka a hasale tana fadin ki ban lokaci mu san abinyi nan gaba. Don wanan ne daman da muke dashi a yanzu kafin ya kubce muna don idan ya koma bamu san ranan dawowan shi kasan nan ba kuma. Ta amsa da don Allah umma ki san abin yi do nima ban son ya kubce min a yanzu ba tare da mun shirya ba. Da wanan sukai sallama ta dan kwantarwa yar nata da hankali hakan yasa tadan ji sanyi a zuciyar ta. Ana cikin hakan Nafisa ta samu sallama don jikin ta yayi sauki habbib yana dauko ta daga asibiti gidan kawu ya nufo da ita. Tana ta turo baki gaba alaman bata son zuwa can tunda taga sun dauki hanyar gidan kawu din. Yana kulla da ita saidai bai bata fuskan da zatai mai korafi ba kan hakan don dole ta kyale ba don taso ba. Koda suka shiga gidan kawu din part din Amma ya nufa da ita bayan sallama suka gaisa ana mata sannu da jiki tana amsawa da kyat ta hanyan nuna hakan bai mata ba a lokacin. Muryan habbib ne ke fadin tsohuwa ga Nafisa nan an sallamota daga asibiti zata zauna a gurin ki nan har abubuwa su koma daidai ta koma part din su. Amma ta dan murmusa tana fadin banda abinka ba don abubuwa suna zuwa haka a gidan nan ba har sai ka kawo Nafisa nan da kan ka ai nan din na kowa ne a gidan nan. Hakane Amma a daita hakkuri damu don Allah ya fada yana mikewa don barin su a lokacin don a ranan yake son komawa abuja. Yana fita Nafisa na inda take a rakube cikin rashin sake jiki don ita bata jin zata iya zama a wanan part din yadda suke nufi ta zauna a wurin Amma din don su a ganin su hakan shine daidai. Fitowan murja a daidai lokacin Amma take fadin yauwa yar albarka kinga dauki kayan yar uwan ki ki shiga mata dashi daga ciki don a nan zata zauna har komai ya daidaita. Duk da suna maganan a dunkule ta gane me suke nufi da hakan wai a nufin su sai lokacin da har komai ya daidaita tsakanin iyayyen su mahaifiyar su ta dawo duk tana zaune a gurin Amma din. Ba yadda ta iya dole haka ta mike tabi bayan Murja kamar yadda Amma ta umurce ta zuwa ciki. Ya kasance hutun da aka samu yana dan tsowo don hakane muna waya mamu ke fada min cewa ya kamata mu shigo mu duba hjy don jikin nata a lokacin babu dadi gaskiya. Nace mamu naso hakan saidai yaya din ne nasan a yanzu yana da wuya ya barmu mu shigo Nigeria zan dai gwada tambayan shi mu gani. Ki daiyi kokarin hakan koda bazai bari kizo din ba don yasan kin damu da al,amarin kema. Don duk iyalan su Aliyu sunzo har na habbib dubata kinga ya kamata ace kuma din kunzo idan da halin hakan ai. Hakan da mukayi da mamu yasa na buga mai waya bayan mun gaisai ne ya tambayi yaran da kowa nake rokon sa akan ya barmu mu shigo tunda muna hutu mai tsawo mu duba hjy da jikin. Tunda naji yace zahra ina kike son zuwa da yaran nan yanzu tafiyan ku a yanzu haka kinsan abune mai wahala gareku dani ma. Yaushe zan dawo nan bayan kin san abubuwa sun min yawa a nan nace na bar aiyuka na zo daukan ku zai zama wani matsalan kuma. Nace sai inzo dagani sai Abbana sauran in barsu da maria a nan har in dawo . Da sauri yace kina da hankali kuwa zahra yaran ne zaki bari da yar aiki harsu hudu zahra kina da tunane kuwa ? Yaya kayi hakkuri don Allah nima banyi wanan tunanen ba na fada gani nayi dai hakan bai kamata ba ace komai nisan wuri hjy tana cikin wanan halin kuma ace kai naka iyalin basu zo ba . Wanan zahra matsalanane ban son zuwan ku kasan nan don irin abubuwan dake tasowa daga baya idan kunzo tunda har yanzu bawai hjy ta fasa halin ta bane kema kin sani. Shiru nayi ban iya magana sai can nake fadi a sanyayye a gaida kowa a gida ya amsa shima cikin wani yanayi da zasuji. Wayan na kalla jin ta kashe ina sauke ajiyan zuciya a hankali tare da furta kai ni wanan lamarin Allah dai yai muna mafita akansa . Don wani fannin idan na duba gaskiya yaya ya fada kan matsalolin dakan taso daga wurin hjy din idan ta ganmu a kasan. Koda mamu ta tuntubeni da maganan fada mata yadda mukayi dashi nayi tace kuma ya fadi gaskiya don hjy bata fasa halin nata ba gaskiya. Ko tana asibitin nan mun tafi gaida ita bamu dawo a cikin dadin raiba don sai da suka taba fitina da hjy maryam a can. Cewa tayi maryam din tana farin cikin barinta gidan har tana gallazawa danta don taga bata nan tana wullakanta mata da dacewa Nura. Nace kin gani mamu balle nida suke hake dani kan wanan amaryan tasa suna fadan wai muke asiri muka shiga tsakanin su . Salma ke fada min hakan wai hjy sabuwa taje asibitin gaida ita ranan kuma da bata hakkuri kan abinda ya faru a tsakanin su shine suke maganan wai sun fahinci aiki saka hannun ne akai masu har hakan ya faru. Kaji kuma wai sai yaushe ne hjy zata daina irin wanan halin na daukan wani ne yake jufanta da zaman lafiyan data kasa nemawa kanta a gidan tane ? Mamu ai kinsan wanda bai barwa Allah lamarin sa a kullun ganin yake kowa yana aikata irin abinda yake aikatawane a kanshi. Tace hakane baida kin nuna mai sha,awan son zuwan dubata din ba kuma yanzu yasan da hakan bawai laifin ki bane. Mun bar wanan zancen shima bai sake maganan kan hakan ba dani har aka sallamo hjy bawai don taji sauki din ba suka dawo gida da ita don zaman asibitin babu dadi. Jin hakan yasa su gaba daya dawowa a lokacin don sanin halin hjyn dana hjy sabuwa dayayi saboda hakan ne ya dawo garin. Suna dawowa gida da ita ya bude part din mu suka shiga a nan aka gyara mata dakin da zata zauna a ciki. Gaba daya kowa ya fita zancen wata samira da yanzu suka kara ganin bbakinta sosai a gidan suna ganin itace mussababin jefa mahaifiyarsu a wanan halin duk da yawan kula da hjy sabuwa keyiwahjyn a yanzu . Na kokarin ganin ta wanke yarta daga wurin su da mahaifiyar su din ko abubuwa zasu zo da sauki a garesu. Washe gari da dawowan hjyn gida daga asibiti merry ta sauka kasan ita da yarta Queen wace tazo masu a bazata. Basu ba harshi yayi mamaki matuka da ganin merry din Nageria a wanan lokacin don baisan da cewa zasu zo kasan ba shima. Itako merry da biyu ta zo garin don ta sada Queen data dameta da son sanin dangin mahaifinta wanda a yanzu taga dacewan yin hakan a garesu. Sai gashi kuma wani abokin karatun su daya san yaya umar din yana fada mata irin masana,antar dashi umar din ya buda yanzu a Nageria. Wanan abinda taji ne ya tayar masu da hankali sosai ta gane yanzu umar din yana boye mata wasu abubuwa daya dangance shi. Idan bata dauki mataki ba sannu a hankali zai gujesu daga ita har yar tasu nan gaba idan ta kyale hakan zai iya haifar masu da matsala. Duk da yanzu tasan umar din yana da wasu yaran da ya haifa bayan nata yar wanda hakan yana matukar kara bakanta mata rai sosai. Da zata shigo gidan gaba daya ko ina na gidan gaba daya ya canza mata sai bin dayan part din dats ga an gina takeyi da kallo wanda ita a ganin ta ginan da akayi din take ganin bai dace ayisa a cikin gidan ba ma. Da tako dadaya suka shigo gidan a daidai lokacin da umar din yake zaune da yan uwan shi suna karyawa da safe tare da yin magana kan matsalan mahaifiyar su din don samun mafita. Takon da sukaji din ne ya shagaltar dasu kallon mai shigowa a lokacin sai merry din suka gani tare da yarta kamar a mafalki a lokacin. Gaba daya kallon su da mamaki ya koma gareta ga wani shegen shigar banza da tayi dan bujen data sako iya cinyarta ya tsaya mata. Sai Queen itama shigen shigar mahaifiyan nata tayi ga kansu dake nuna suna cikin halin takaban mahaifin ta da aka aske shi gaba dayan su suna kuma saye da bakaken kaya a jikin su. Kunya da nauyi suka lulube yaya umar a lokaci guda na wayan shigar banzan da merry din har yarsu suka shigo dashi a lokacin. You are wellcome Aliyu dake washe baki yanace masu sannun su da zuwa a lokacin. Hannu ta dan daga mai mai alaman amsawa tana nufin gurin mijin nasu takai mai hug itako Queen ja tayi ta tsaya tana binsu da kallon mamakin kamanin su da ubanta a lokacin. Dan hannu habbib ya daga mata tare da fadin zo nan yar mu kece kika girma hakan bamu sani ba yana dan murmushi. Jin umar bai mayar mata da martanin huging din ta ba har lokacin yana zaune a guri daya. Dan dagowa tayi da mamaki a idon ta tana kallon shi yace daga ina suke haka ne ? Tambayan ya bata mamaki yace eh dole in tambaye ki don bayi dake kan zuwan naki ba. Maganan nasa ya bata mata rai sosai saidai ganin yan uwan shi a gurin yasa ta dake tana fadin mamaki muke son baka ai. Kayan su da driver gidan yake jawowa zuwa ciki yasa suka maida hankali a banda umar da yake jin har yanzu a ranshi ya muzants sosai da hakan. Mikewa yayi zuwa cikin dakin shi har lokacin merry tana duke ta da dafa kujera tana mamakin sauyawan komai a ranta. Key din dakunan gidan ya fito dasu a hannun shi ya nufi wani daki yana kokarin budewa don a saka kayan a ciki dasuka zo dashi. Yana budewa ya dawo falon sai lokacin ya samu daman rungumar yarsa Queen a jikin shi yana maijin dadin zuwanta nan kasan shi na haihuwa. Jan Queen din yayi zuwa wanan dakin yana fadin tazo suje taga dakin da zata sauka a cikin har lokacin yana makale da yar tashi a jiki yayin da merry da kowa na falon ke binsu da kallo. Ko wani tunane yayi a lokacin har sun kai kofan dakin sai ya juyo yana kallon merry din tare da miko mata hannu alaman tazo mana garesu. Hakan yasa ta dan sauke ajiyan zuciya kadan ta tako a hankali zuwa gare su ya hada ya rungume su zuwa cikin dakin. Daya bayan daya su Aliyu suka watse a falin cike da takaicin auren wanan zurian da dan uwansu yayi a rayukan su saidai ba wanda ya iya yiwa dan uwanshi maganan hakan. Ya dan jima a dakin yana nuna mata bacin rai kan irin shigar da tayi zuwa nan din wanda bai boye mata jin haushin ta ba. Koda ya fito ya samu babu su umar din a lokacin falon gidan haka yasa ya san sun tafine wurun masu aikin shi ya nufa yana fadin a shirya masu abinda zasuci a lokacin. Wanka tayi ita da yarta bayan sun daidaita da mijin nata ko yanzuma bata sauya zani ba wani tsinanen rigan ta kara sakawa a jiki shima dai bakin ne kamat wancan din na farko. Falo suka fito harshi zuwa dining don karyawa tunda tafiyan safe sukayi zuwa garin kano din. Saida suka karya ne ya kaisu gurin hjy dake zaune a dakin ta bata san ma da zuwan su kasan ba a lokacin. Hjy da ke zaune shigowan su saida ta dan zabura don kaduwan da tayi da ganin nasu kamar wasu babbakun aljannu take ganin su a hakan kai aske. Shima kanshi ya zama mai dole ne tunda sunzo din a hakan ba yadda ya iya dasu don bai taba yin nadama irin na wanan ranan ba a rayuwan shi a kan auren merry din. Yanzu ga abin har ya shafi yarshi na wanan akidar tata na shigan arnan da suka gawurta sosai itako merry din ko a jikin ta . Wani kallo sukewa juna da hjyn duk da ya fada masu irin matsalan daya samu hjyn a lokacin saidai hakan baisa merry din ta nuna wani kulawa a gareta ba. A tsaye kamar dokin dake ciwon ciki suka gaishe ta babu alaman wani girmamawa irin na al,adan mu ga sarakuwar nata a lokacin. Yayin da yar jikan nata da aka tsorata da kowa tun kan tazo ta kara makewa cikin jikin mahaifin nata. Duk da yana kokarin basarwa yana fadin taje yau ga grany din ta ta gani wacce ta haifeshi . Hakan baisa yarinyar ta yarda taje gun hjyn ba sai ma kara boye kanta da takeyi kan hakan da yake kokatin nuna mata mahaifiyar tashi. Tunda merry taga baida niyar fita dasu daga dakin ta juya ta fita zuwa falo kallon shi hjy tayi a cikin wani irin yanayi na ban tausayi tana fadin babawo yar nan taka tana da akidar musulunci kuwa a rayuwan ta ? Yace mama mai kika gani kan hakan kokarin da nakeyi ke nan akoda yaushe don ta fahinci addinin mu. Ido hjy ta runtse a karo na farko take ganin gaskiyan kawu a yau kan abinda yake shan fada mata koda yaushe game da dan nasu. Har ya fita da yarshi daga dakin tana zaune saman keken dake taimaka mata da ka sai mata don zuwa ban daki da dan motsa jiki saboda kwanciya kada yai mata yawa. Falo suka samu merry dake bin ko ina da kallo na gidan wayan shine ya dauki kara ya dauka ya fita don ganin mai kiran nasa. Bai jima da fita ba hjy sabuwa da yarta suka shigo falon a lokacin don gaida hjyn saidai ganin merry da yarta a falon yasa suka tsaya suna kallonta da mamaki . Itama merryn ido ta tsura masu tana mamakin dalilin shigowan su gidan haka kai tsaye. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:22 - 🀐🀐🀐: Suna shiga dakin bayan sun karewa merry da yarta dake zaune falo tana ta waya kallon kwam suka shiga dakin da mamaki da gulman dake cin su a rai. Don basu samu damar kebewa ba saboda ba lokaci a gurin da zasu samu magana kafin shigan su dakin da hjy take jinya a ciki. Itama hjy zaune take da imanin ganin merry a hakan daya cika mata zuciyar ta da mamaki da tsana har lokacin da suka shigo dakin. Amsa masu sallaman su tayi har lokacin tana zaune saman keken da aka tanadar mata don zama da laluran kewayawa a dakin. Gaisawa sukayi ko karasawa basuyi ba hjy sabuwa ke fadin hjy jummai wanan ta zaune a falon ku da yarta wacece ita. Naga wata katuwar arniya tayi kane kane zaune a falo tana busan iska a gidan nan kamar wata yar gida har yaya akayi wanan kafirar ta shigo gidan nan haka ? Dan runtse ido hjy tayi daga zaune tana mai jin dacin kalamin hjy sabuwa a ranta ga nauyi da kunyar fada masu itacr matar dan nata ai da takeji tun shigowan su da hjy sabuwa ta fara magana. Idon ta bude a hankali tana bude baki da kyar ta iya furta matar gidan ke nan ai hjy . Itace kafiran da yake aure a can kafin Alh ya aura mashi wanan yar ta wurin maimuna daga baya. Wanan din itace matar Umar din dama abu haka kamar ginan dare ba wani kyau ba fasali a tare da ita ko kadan. Gane min hanya dai ta fada tana sauke wani nauyayyen ajiyan zuciya a tare da ita. Sai lokacin samira da tun shigowan su tsana da kishin merry ya baibaye zuciyan ta a lokaci daya don yadda suka sameta a falon da ita ake mata rowan shigowan shi tana matar gidan saiga kafira ta gani a zaune tayi kane kane a cikin sa. Jin an anbaci itace matar umar din ta kara jin wani kin merry din da yarta har cikin kokon ranta lokaci guda. Yanzu wanan abar itace dear yake aure har yake iya fifitata dani dama wanan mai zubin samudawan farko ga kira da kama kamar suffan namiji. Aike dai batu ne bai faduwa hjy sabuwa tace tana kaiwa zaune ga gulma nacin ta tace. Me tazoyi a nan kuma yanzu tana fada tare da kallon fuskan hjy jummai tana son jin abinda ya kawo merry din kasan. Yadda kuka ganta haka na ganta da safen nan nima rabonta da kasan nan tun tana dauke da cikin yar nan nata da zo muna a bazata tun wansn lokacin bata dawo ba sai yanzu. Ikon Allah hjy sabuwa ta fada tana gyara zaman ta don taji labarin da dadi a kunnuwan ta sai kallon hjy jummai takeyi don jin tayi shiru ga labarin data dauko basu din na merry da yarta. Jin shirun yai yawa tace dole ne Alh sani yai ma dansa haka jummai wanan irin abu hakan babu fasali ai kazantane ga kowa. Uhumm kawai hjy jummai ta iya fada a lokacin don yanzu ta fara fahintar hjy sabuwa ta fara gane zama da su da takeyi ya hana ta sake wani zance mai zurfi kan iyalin nata. Magana sosai suke sakewa kan merry da umar din tana jin su kala bata furta masu ba har suka gama don kansu tana fadin zata koma dama kwana biyu bata zo dibata ba yasa ta shigo yanzu. Koda suka fito merry bata falo tana ciki da yarta sun kwanta sun so su kara mata kallon kurulla sosai saida bata wajen a lokacin. Part din samira suka koma nan suka yada zango hjy dake fadin tana sauri sai gata har azahar a gidan suna kule kule da yarta a gidan. Ya Umar bai dawo gida ba sai bayan la,asar don sun tafi wani gona nasa dake wudil duba shanayen da ake masa kiwo a ciki. Dawowan nasa yayi daidai da tashin merry da yarta da suke barcin gajiya tun safe da suka shige daki. Suna zaune suna cin abincin da aka hada masune ya shigo gidan a gajiye don ranan da ya kwaso a can wurin zagayen da yaje din. Queen ne ta taso a guje zuwa taron daddy nata tana fadin tayi missing din shi tun safe daya fita. Rugumar yarinyar yayi tare da dagata sama yadda ya saba mata idan tayi mai hakan yana shafanta yace miss you too dear tare da mayar da hankalin shi ga merry dake zaune a gurin dining. Saida ya iso wurin ya sauke yarinyar ta hanyar zaunar da ita saman kujera ya dan kaiwa merry din kiss kafin ya zauna tare da tambayan ta yaya suke ? Dan bata rai tayi kafin tace dashi not bad saidai kewan Us da sukeyi kawai don yanayin nan akwai zafi da yawa sosai. Daga kai yayi ya kalli AC dake aiki a falo har biyu yana fadin kada ki manta da kema nan kasan kine ai ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun wajen. Kasanane saidai ba zama dole in fadi hakan ba yanzu tunda ina da shedan zama yar kasan America yanzu don acan aka haifeni. Kaga na samu riban kasa biyu ke nan a rayuwana hira sukaci gaba dayi a wurin suna cin abinci gwanin bannsha,awa . Yana kkatin nuna masu kulawan shi a kansu don bakuntar da suka kawo mai har kasan shi duk da yasan zuwan nata ba a banza tayo shi ba haka. Saidai ya saka mata idone yaga iya gudun ta da abindaya kawo ta din don yasan zata fada da bakin ta saboda sanin halin ta dayayi. Can sun kusa gamawa takira sunan shi ya dago yana kallon ta take fadin ya bata mamaki daya iya boye mata abinsa a yanzu. Aje spoon din dake hannun shi yayi yana kallin ta a cikin mamaki tare da fadin me yayi mata har ya bata mamaki din shi a zaton shi wani abune can merry din taji game dashi kuma . Omar can you imagin idan nice har na iya yima hakan na boyema wanan sirin nawa kana da kudin da zaka zo nan kasan kayi wani abu dashi ka kasa fada min in baka shawara akai wai sai kazo kasan nan da barayi da mayaudara sukai yawa ka gina company ba tare da sani ba Omar ? Ajiyan zuciya ya sauke don jin abinda ta fada mai ya dan murmusa tare mayar da kanshi saman makirin kujeran da yake zaune akai kafin yace. Merry nayi mamakin da har kikai saurin matawa hakan ko kin manta tsakani na dake kotu ta raba muna komai da muka samu a tare. Baka manta da zancen ba ke nan ta fada tana kallon shi ya bude baki zai bata amsa takon tafiya ya tsayar dashi ga abinda yai niyar fada a lokacin. Sin mayar da hankalin su ga kofan falon samira ce ta shigo taci kwaliyan dogon rigar shadda a jikin ta mai aikin stones har kasa sai sheki takeyi. Hakan yana daga cikin abinda suka kitsa da uwarta kafin ta tafi dazun don hakane ta fara aiwatar da shirin ta a yanzu. Tana zuwa direct wurun shi ta nufa duk da zuciyar ta na mata dardar karya tsuka ta a gaban merry din da yarta data same su a zaune. Ga wani irin uban kishin merry din data gamsu a tare yanzu yana cin zuciyar ta tun kallin farko datayi masu dosowan ta wurin. Dan dafashi tayi cikin karfin hali da daurewa cikin kissan mata tana kai goshinta a daidai saitin fuskan shi tana fadin ka dawo ashe duk da bata san fitan shi gidan ba a ranan. Na dawo ya bata amsa cikin karfin hali yana dagowa daga yadda yake zaune yai balance saman kujeran a lokacin da suke magana da merry kan abinda ya kawo ta kasan. Merry dake zaune imani da mamaki ya kasheta a lokaci guda sai kallon mamaki takewa Samira din tare da tambayan kanta ita wanan wacece gare shi kuma haka. A yadda tasan mijin nata da kamun kai da rikon addinin shi baya wanan akidar da wata mace idan ba ahalin shi ba. Umar daya dago daga zaunen yana gyara zaman shi yace ga matana merry da yarta Queen sun zo yau daga America. Yana nunawa samira din su merry da hannun shi cikin dakewa tace au wanan ce kafiran da ake fadi kana aure ashe, tana maganan tana kallon merry din da yarta. Who is dis woman merry ta tambaye shi tana kallon shi don san jin ko ita waye a gare shi kafin ya fada samira tace his third wife. Da sauri merry tayi wani zabuwa a inda take zaune sai kuma ta koma ta zaune tana sauke numfashi ba merry kadai ba har Queen da take yarinya a cikin su kallo tabi samira dashi lokacin. No no no you can't be my father wife he's only marry my mum and twin's mother right Dad tana kallon fuskan uban nata. Dan murmushi yayi kafin yace right my Queen wanan tana fakewa a gidan nan ne da sunan uwata OK ? Kai yarinyar ta gyeda mai alaman gamsuwa yayin da su duka suke kallo umar din da yai wanan maganan with one mind a fuskan shi. How comes merry tace ya bata amsa da as you can see now yana kokari tashi daga wurin don duk a matse yake a lokacin dama merry din ta dakatar dashi wurin wanka yake son yi yaji sanyi a jikin shi. Yasan baza a rasa wace zata biyo shi ba hakan yasa ya rufo kofan nasa yai masa key lokaci guda tare da sauke ajiyan zuciya. Sai a lokacin muka fado mai a rai zama yayi bakin gadon yana kokarin balle aninan rigan shi yana kiran layin mu duk da yasan lokacin dare ne can sosai. Kiran na batun katsewa na daga idona yana cike da barci a lokacin da sallama a bakina ya amsa min. Kun kwantane ya tambayeni nace eh yau banjin dadin jikina nida Abdulsalam may ke damun ku ya tambaya da sauri . Na bashi amsa da sanyi ne yai yawa ya saukar muna da zazzabi sai ciwon kai da mura da kowa ke fama dashi. Kun tafi asibiti ya tambaya nace nakai yaran dai don har babana kwana biyun nan duk baijin dadi shima. Shine baki fada min ba da mukai waya jiya dake nace naga ba wani sosai bane ai a jiyan yasa ban fada ba. Idan jikin ba sake ku ba ku koma asibitin a gobe idan Allah ya kaimu muji mai zasu ce har sanyin ya sauka hakane daya fara ba mutane wahala. Sanyi ake sosai a nan yaya bama fita ko ina duk kwanakin nan muna gida rufe sai yau da muka fita zuwa asibiti din. Idan har sanyin zai maku illa haka gara ku dawo nan ku karasa hutun ku don tsaron lafiyan ku ya fada. Ya jikin hjy na tambaye shi cikin kulawa yace da sauki tana gida an sallamota tun jiya fadin hakan da yayi ya gagauta mikewa tsaye yana fadin zan kira da safe inji jikin naku. Daga haka ya kashe wayan nasa wanka ya shiga a gurguje don yana son leka hjyn su a lokacin tunda ya dawo bai lekata ba ya samu merry falo ta tsare shi da magana. Barin falon shi aka tsaya kallon kallo tsakanin merry da Samira kowa nawa dan uwa kallon tsana. Banza kawai samira tace tana jan tsuki tare da juyawa zata bar wurin taji merry tace mata mara fuck you bich . Hakan yasa ta juyo da karfi itama tana fadin fuck you too yar iskan banza kawai kafira mai fitsari tsaye nan zagi ya kaure a tsakanin su kowa na aikawa dan uwa zagin daya zo mai a baki lokacin sunawa juna kallon tsana. Hjy dake daki tun tana dan jin yaniya kadan kadan ta fara jin sauti na tashi ga muryan samira daya karade gidan . Haka yasa tayi kokarin hawa keken ta da dabara sai ta fado kasa daidai zata hau din wani kara ta sake mai karfi saida fitsari ya zubo mata duk ta bata jikin ta dashi don zafin da taji. Gashi ta kasa dagawa daga inda take duk kokarinta na son ta dago da kanta da takeyi din ta kasa hakan. Gasu kuma muryan su da duk ya karade gidan do hayaniya sule sosai a falon har wanda ke wajen haraban gidan zai iya jinsu a lokacin. Koda umar ya fito bai tsaya ba a gurguje ya saka kaya duk da doguwan rigan jallabiya ya sakawa jikn shi yana sauri ya leka mahaifiyar shi a lokacin da tun shigowan shi bai samu lekata ba. A lokacin ne kuma yake jiyo hayaniyar matan nasa a falon da sauri ya karasa fita falon nan ya same su suna abinda sukeyi kamar zasu buga a tsakanin su. Wani irin tsawa ya buga masu tare da nunawa samira kofan fita daga falin bata fita hakana ba sai da tace dashi . A kan wanan kafiran matan naka mai fitsari a tsaye kada ka daka min tsawa don Allah dama wata mace ce ba wanan abin banza da kake takama wai mata ba gareka. Duk da merry batajin me take fada tasan bakar magana take fadi game da ita shiya bata kyale ba tana jefa mata irin zagin su na yan America mai zafi. Juyowa yayi wurinta yana fadin zatayi shiru ko sai ranta ya baci itama yana fadan haka ya wuce zuwa dakin da hjyn ke ciki. Tun a kofa yake jiyo nishinta ya shiga da sauri yana fadin mama lafiya yadda ya same ta kwance a kasa ba saman gado ba ba saman kujeran ta ba. Yasa shi fadin mama lafiya ya hakan ya faru dake cikin kidima yake magana hankali tashe. Hjy babu bakin magana har lokacin sai wani irin kugin wahala da take fitar wa kawai takeyi a dakin kokarin daga ta yayi sai lokacin yaga abinda tayi wanda yasa dakin yake bashi a lokacin. Hakana cikin dauriya ya daga ta yana kalon irin yanayun da take ciki rausayin mahaifiyar nasu ne ya kara tsarguwa a ransu lokaci guda daukan ta yayi zuwa bayi ya hada ruwa tare da duk yadda zaiyi ba tare daya wani wuri na jikin ta ba ya gyara ta ya fito bayan ya barta ta takara inda babu halin tabawa a gareshi ya fara gyaran dakin da kasan zuciyar shi cike da tausayin mahaifiyar tasu don yasan wanan na daga cikin jerabawan ta da Allah ya aiko mata. Bayan ya gyara dakin ya fesa kamshi sosai ya koma ya samu ta gama haka ya daukota zuwa dakin ya azata saman gado sai faman sannu yake mata a lokacin. Fita yayi da sauri zuwa falo ya hadu mata abinci da kanshi duk da yasan an bata abinci a lokacin sai yanzu yake tunanen ina mai aikin da aka dauka don kula da hjyn kawai a gidan ta tafi ? Koda ya dawo dakin bai samu tambayan ta daga ta yayi ya bata abincin taci sosai kafin ya kawo magani ya bata tasha. Sai barci mai nauyi ya dauke ta duk da magariba ya gabato a lokacin ya dan dade dakin zaune yana tunane a ranshi ranan ba kalan tunanen da baiyi ba a zuciyar shi. Kafin ya fito zuwa haraman yin sallah babu kowa a falo daya fito son haka kai tsaye dakin shi ya nufa ya dauro alwala ya fito zuwa sallah. Bai fito massalacin ba sai baya isha,i takwas da wani abu dakin mahaifiyar shi ya leka ya samu har lokacin tana kwance tana barci saboda maganin da tasha. Ya dan dade tsaye wurin kafin yaji motsi daga kofan alaman mutum a wurin ya leka dakin wanan matar ne ke dan rabe rabe mai kula da hjyn a cikin dan daure fuska yake fadin ina kika je kika barmin mahaifiyata ciwon ta ya tashi. Mun daukoki ne dan laluranta sai ki tafi ki barta a cikin matsala badon Allah ya kawo ni ba yau ban san abinda zai kasace da ita ba. Jin yayi shiru tace Alh ba laifina bane hakan nima sai da nai gudun hakan amma hjy tace in tafi wurin aiken da taimun a gafarceni Alh hakan ba zai kara faruwa ba insha Allahu. Kala baice mata ya fita daga dakin yabar matan tana sauke ajiyan zuciya a dakin ita kadai sai hjy dake kwace sharkaf da ita. Barci nake da safe bayan na karya nasha magani na dan koma barci don har yanzu jikin nawa bai gama warwarewa ba a lokacin. Karan wayana dake gefe ya tayar dani tun ban dauka ba na gane shine ke kirana a lokacin ko kuma mamu don sune masu yawan kirana ko wani lokaci . Dan dama dama salma da Atika da yanzu zama ya dawo dasu kano ita da mijin ta dake aiki karkashin yaya a yanzu . Dauka nayi da sallama ina gaidashi kamar kullun tambayana yayi karfin jikin mu nace mai da sauki dukkan mu Abdulsalma yana falo babana kuma Fauziya ta goyashi yayi barci. Ok bakuje asibitin ba ke nan yau ya tambaya ? Saida na dan marairaice muryana kafin ince naga munji sauki ne yaya look zahra idan yaran nan basuji sauki don Allah ki mayar dasu asibitin nan please. Nace zan kaisu yaya idan naga hakan Allah ya sauwaka yace na amsa da amin sai kuma ya danyi shiru nidai ina sauraren shi sai naji yace dani. Idan kun kara jin sauki zuwa next week zanso ku shigo Nigeria kodan sanyi da yai yawa a can don yaran nan . Allah ya kaimu na iya bashi amsa dashi tare dayin shiru yace ko akwai wani abinda kuke bukatane ? Babu komai na kara bashi amsa ku kula da kanku don Allah kada ki bar yaran nan su dinga fito ko kofan gidane. Na kara amsa mai da toh yaya kawai alaman dai wani abu yana damuna a likacin shima haka ya kashe waya yana mamakina a ran shi. Nima ta bangarena mamakin shine fal a raina yadda dan kanshi yanzu yayi shawaran zuwan mu gida. Jin hakan danayi daga gare shi yasa na fara shirin duk wani abinda nake bukata tare damu na hada a shirina har ina mamakin kaina da kayan dana hada don tafiya. Kamar yadda yace din hakane don munyi waya dashi da kwana biyu saiga abokin shi yazo ya amshi pasphots din mu don shirin tafiya. Abinda ya dan kara kaimu wani lokaci shine babana da yanzu nake goyo saida akai mai nasa shirin shima ranan Friday da dare muka daga zuwa Nigeria nida yarana ina dokin zuwa gida inga yan uwa da abokan arzikina. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:22 - 🀐🀐🀐: Tsakanin merry da Samira sai harara yanzu don tun ranan basu kara haduwa ba irin hakan merry taso ta tayarwa yaya da hankali ya nuna mata ba shike gaban shi ba don shi yanzu yana fama da jikin mahaifiyar shi ce. Don tun wana ranan yaya ya mayar da hankali sosai a gurin hjyn su komai zai shiga yai mata shi tun lokacin daya fahinci babu jittuwa a tsakanin ta da matar da suka aje mata mai kula da ita. A bangare merry har lokacin zuciyar ta na cike da kuna zancen samira bayan wacan da take tausan zuciyar ta akanta yanzu kuma ya kara auro wata mara mutunci. Ai gara da Fatema bata taba mata rashin mutunci ba duk haduwan su da sukeyi wanan haduwa daya tayi masu rashin mutunci daga ita har diyanta. Gashi bai bata dama ba da zatai mashi magana don yace shi zancen mahaifiyar shine yanzu a zuciyar shi ba zancen banza. Wanda tasan hakan don batayi zaton halin da hjyn tasu take ciki yakai haka tsanani ba saida sukazo taga halin da matar ke ciki yasa ta dan tausaya mata duk da har yanzu akwai kallon tsana da matar ke aika mata. Suna a hakan kwatsam sai gamu mun sauka garin ba tare da sanin kowa akan zuwan namu ba lokacin. Abin kallo muka koma garesu dan tana daki da yarta take jin hayaniyar shigowan mu gidan don yara harka dasu ba bace yake ba. Saukan yamma mukayiwa kano shida mansur da yake jin dadin kasancewan su tare a yanzu don kwazon shi da nuna wayewan shi da shishigin shi ya shigewa umar din a jiki sosai. Ko mamu ban fada mata shigowan mu ba sai dai ji kawai sukayi mun shigo garin ranan a bakin murja dana bugowa waya ta samu labari. Don nakira murja ta hannun damana da nomban Nageria tana dauka tace wai kina inane haka naga nomban naija nace muna cikin ta ina son ki zo gidan kafin mu karaso ki mun gyara don Allah. Ihun murna ta dan sake tare da fadin ashe muna da manyan baki kasan nan bari yanzu in shirya kafin ku iso. Shine take fadawa Amma da mama hadiye har mamu taji take fadin ban fada mata zamu shigo ba sam bata sani ba ita. Merry bata san da shigowan mu ba Queen ce dake jin motsin yara ta dan saci jiki tafito daga dakin nasu shine ta samu yaran tare da mahaifin su a falo ina daki tare da murja a lokacin. Sam ban san merry na garin ba sai murja ke fada min taji ana fadin merry ma tana kasa nan tazo akace sai dai har yanzu bataje can gidan mu ba don naji Amma na fada kan hakan. Tana kasan nan fa murja na tambaya cikin mamaki murja tace min wallahi nima haka naji ita da yarta akace. Dan jim nayi ina tunane kafin ince bai fada min hakan ba kuwa kodai wani dalili yasa ya taramu a nan din wanan lokacin na tambayi kaina. Saidai zan share hakan kamar yadda bai fada min ba nima ido zan saka masu a kasan zuciyana kuma ina tunanen irin zaman da zamuyi a wanan gidan mu uku din. Tambayan ta nayi hjyn su fa tana inane tace min a gidan nan naji akace take mana don nima tun shigowana ban samu ganin ta ba nan na nufo kai tsaye. Shine ya shigo dakin nawa yana dauke da babana sai Sultana dake makale da jikin shi ganin shi yasa murja zata bar dakin yace no ki zauna fita zanyi yana miko min yaron da har yanzu bai gama warwarewa daga ciwon da yayi ba. Mama fa tana inane wai na tambaye shi tana dakin ta ai, a nan gidan take ne na kara tambayan shi yace tana wancan dakin na farkon shigowa inda Amma ta taba zama. Mikewa nayi ina fadin ai ban sani ba har na shigo ban shiga na gaida ita ba cikin nuna kula nake maganan. Wanda hakan yai mai dadi har cikin ranshi saidai bai nuna hakan a fili ba fita yayi daga sultana dakin. Mun fito zuwa dakin nida murja saidai tun a kofa bashi da tsami ya tare mu dake fitowa daga dakin. Haka muka daure muka shiga nan muka samu mai kula da ita tsaye akan hjy tana faman kawar dakai gefe da alama dagata take son yi a lokacin. Jin sallaman mu yasa ta dakata da abinda takeyi din da sauri muka karasa bakin gadon muna gaida ita ta amsa da kyat badon ta shedamu ba a lokacin. Dan shirune ya biyo a dakin sai can nacewa matar ya naga haka take fadin tayi najasa ne nake son in kaita bayi in gyara ta kuma na kasa dagata ni kadai. Dan shiru nayi a wurin kafin ince ai ba sai kin kaita bayi ba a yadda take din nan . Yaya za aiyi idan ba a kaita bayin ba matar ta fada tana bata fuska da gani ta gaji da wanan aikin don da wahala sosai gaskiya. Nace leda za a samo yanzu bari kiga yadda zaki dinga yi leda murja tafi ta samo min da sauran abin bukata irun deltol da kamshi dasu handglove. Muna dakin har ta dawo nasa matar ta debo ruwan dumi a bayi a lokacin na shiga gyarawa hjyn jiki dagani sai matar a daki. Tana kallon yadda nake komai har zanin gadon dana gyara a cikin dubara duk da hjyn na sama kwance sai nayi dabara irin yadda asibiti suke gyara duk a kan idon matar nayi shi. Ta sauke a jiyan zuciya tana fadin wanan ai hanyar sauki ne yafi wanan cicibar da muke mata zuwa bayi kullun. Nace yafi sauki da za a samu allurai yanzu ai mata zai taimaka mata sosai yadda jikin nata zaidan yi karfi taji dadin sa. Wanan sai idan Alh ya dawo matar tace noce No bari a rubuta kawai sai a sayo yanzu ai mata har na fita daga dakin hjy sai bina da idanu takeyi kawai bata iya magana. Ban kuma sa wanan matar tasan ni ko wacece ba ga hjyn sai bina takeyi da kallon mamaki har na fita daga dakin. Saida nayi wanka na dan ci wani abu na fito dauke da ledan magani a hannu na zuwa dakin hjy muka hade da yaya da dawowan shi gidan ke nan tun fitan shi. Gaidashi nayi tare da dan tsayawa yake tambayana inda zani nace dakin hjy. Na shiga dakin bayan ya wuce tana kwance a yadda na barta da farko saidai wanan karon barci na samu tanayi. Tambayan matar nayi ko taci abinci bayan fitana tace kwana biyun nan tunda ta fama wajen ta rage walwala da komai. Abu mai ruwa nace ta hado ko kunu ko tea a bata sai ta hado tea don dare yayi ba kunnu a lokacin. A hankali na dinga daga ta har tayi daidai a yadda nake son taji dadin shan tea din sai likacin ta dan bude idanuwan ta gaida ita nayi da sannu mama ya jikin ? Ta gyada min kai kawai na mika hannu na karbi shayin ina dan bata kadan kadan ga kyale a gefe ina goge mata baki dashi idan ya dan zubo kada ya bata mata jiki. A daidai wanan lokacin ya shigo dakin dauke da babana sai queen da sultana dake tare dashi gefe da gefen shi sun saka shi tsakiya. Yana tafe yana Kallon mu da mamaki karara a fuskanshi yadda nake rungume da ita ina bata shayi tana sha a hankali har ya karaso wurin. Da sauri matar ta shiga gaidashi tana fadin yau wanan yar uwar takula da tazo ta taimaka muna sosai wallahi nan dai ta shiga lissafamai taimakon da nayi mata wurin gyara hjyn. Dan murmushi yayi yana fadin wanan baki santa ba ko tace yawa ne daku har yanzu ban gama fahintar ku ba ai Alh. Nice na katse zuban da take mai na fadin dama allura nake son yi mata wanda zai dan taimakawa karfin jikin nata. Yace hakan yana da kyau dama ina tunanen ko mu mayar da ita asibitin ne saidai likita ya zo ya dubata yace ba abinda zasuyi mata yanzu kuma sai bayan wata uku suga aikin da sukai mata din. Ba matsala idan zan gana da doctor din dake dubata don wata course mate dina ta fuskacin irin matsalan nan sai dai ita faduwa tayi a bayi . A lokacin na samu experice akan irin matsalan don an dan bamu hit game da case din nan shiyasa na sayo wanan alura na gwada yi mata duk da baikai wancan din danake so karfi ba. Yace a sanyayye is ok idan kinga ba matsala ga hakan ai zaki iya mata mu gani ba bata lokaci na fara hada alluran hjy na kwance sai kifta ido takeyi tana son magana ga ciwo na cinta kuma ko hannunta aka daga sai tayi kugi mai nauyi na ciwo. Dan daga ta mukayi da taimakon shi na cilla mata alluran a jiki muka mayar da ita a hankali muna mata sannu sai gyada muna kai take iyawa. Mun dan dade tsaye a gurin ta kafin mu fito daga dakin don barcin da mukaga ya fara daukanta a lokacin. Tare muka fito dashi har yaran shi din muna fitowa merry ne a zaune saman kujera ido ta kura muna tana bin mu da kallo har muka karaso inda take. Fuskanta yana a daure na sakar mata murmushi ina fadin maman Queen you are welcome na tare ta da fadi kafin ta kare min kallon tsanan da take jefo muna daga ni har shi. Sai lokacin dataji gaisuwan da nai mata ta da ce dani yaushe muka shigo kasan ne nace yau din nan . Faith ta fada min kune kuka zo dazun nace karya take ashe gaskiya ta fada . Tambayan mahaifiyat ta da yan uwanta nayi tare da fadin ya karin hakkurin rashin mahaifinta tace sun gode sai ban tsaya falon ba na nufi hanyar dakina nan na barsu tare a falon ban shiga daki ba saida na leka dakin yarana na samu sunyi barci ko sai fauziya da maria ne zaune suna hira. Fauziya kinsan hjy tana gidan nan kuwa nake fadawa yarinyar ta dago da sauri tana kallona da mamaki naci gaba da fadin . Tana gidan nan bata da lafiya sosai don nima ban dauka ciwon har yakai haka ba gaskiya. Da safe sai ku shiga ku gaida ita don yanzu tayi barci na fada ina fitowa har na kai kofa na juyo ina fadin. Maria sai kin kula min da yaran nan sosai wanan karon don bamu kadai bane a gidan nan yanzu gaba dayan mu muna gidan nan ko yanzu na bar sultana da babana a falo tare da baban su duk da nasan zai shigo min dasu nan idan sun gama. Tace insha Allahu zan kula kamar yadda kikace hjy banda matsala kan hakan don nasan maria tana aikin ta da kyau yadda ya dace tayi. Saidai dole in kara fada mata don bamu taba haduwa haka ba gaba dayan mu lokaci guda don hakan ban san abinda zai iya biyowa baya ba nan gaba a gidan. Duk da ganin hjy yasa zuciyana shiga cikin wani yanayi hakan bai hanani kuma tunanen ko me yasa yaya ya hadamu haka a guri daya ba wanan karon abinda bai taba yi ba tun bayan dana fara haihuwa dashi. Kara tsabatace jikina nayi bayan na shiga daki don yanzu babu abinda nake ji sai barci don haka ina fitowa na fara shirin kwanciya kawai. Lokacin ne yaya ya shigo dakin nawa da yaran sa har lokacin Queen tana biye dashi a baya kallo daya nai masa naga yanayin da fuskan shi ke ciki nasan ran shi a bace yake lokacin. Karbi yaron nan barci yake ji yace min nasa hannu ina karban yaron yake kara fadin ina ga har yanzu jikin nasa bai sake shi bane ko ? Kafin mu taso lafiyan shi kallau saidai idan zaman jirgine ya taba shi yanzu din muryan Queen ne ke fadin daddy a nan zai kwata da maman shi ya bata amsa da eh. Sai yarinyar tace itama a gurin baby din zata kwana tare dashi tana fadi tana dan jawo kafan yaron dake jikina. Naji yace No kije gun mamakin tana can tana jiranki ku kwanta ta tabure mai fuska tana fadin ita tare da baby zata tsaya nan. Da kyar ya lalashe ta suka fita ban kwanta ba saida na koma dakin naga maria ta rufe masu kofa na dawo na kwanta zuciyana cike da tunane. Washegari ina sallame sallah na kira fauziya ta dawo dakina ta tsare min yarana na nufi dakin hjy in duba su. Na shiga da sallama dakin aka karba min wanan matar ne tana zaune saman sallaya inda ta idar da sallah muka gaisa nake tambayan ta jikin hjyn tace jiya sun samu barci sosai kuwa. Nace da son samu ne a yanzu mama sai muyi mata wanka a bata abinci zaifi tasha magani kafin a kara wani allura zuwa anjima. Tana mikewa take fadin ai tunda gani hjy ba matsala dama takan min nauyi ne na kasa daga ta ni kadai yasa muke tsaikon komai. Ban dakin zamu shigane nace yawan motsawan da takeyi shike kara fama wurun ciwon nata a yanzu ba irun nomal wankan mu ya dace da ita ba sai dai a dinga goge jikin yadda zata dinga jin dadin sa kamar yadda kikaga nayi mata jiyan. Ganin zata bata lokaci na shiga bayin na hado ruwan dumi na dauko tawul na fito na samu tana kokatin cire rigan na taimaka mata muka gyara mata jikin na cire wanan zanin gadon na saka mata wani cikin dubura hjy sai bina da idanuwa takeyi kawai tana kallo na ga sannun maman da muke mata akai akai tana amsawa. Kitchen na nufa don duba dan abinda zata iya ci mai sauki na samu babu kowa a kitchen din a lokacin. Ruwa na dora a gas din sai bin kitchen din nakeyi da kallo har na dan dama mata kunun bature dana gani a kitchen din na fito. A kofa muka hadu da yaya ya dawo daga masalaci yana saye da brown jallabiya mai sulbi a jikin shi sai tasbaha dake hannun shi yana ja. Gaidashi nayi da kwana ya amsa min tare da fadin kun tashi lafiya ya gajiyan tafiya nace tafiya yabi lafiya ta falka ke nan ya tambaya da nufin hjyn tasu. Nace eh har munyi wanka zata samu abunda tace tasha magani yanzu don haka ya dace ta samu ealy morning. Tare muka shiga dakin dashi na samu matar ta gyara ko ina na dakin tana saka kamahi don haka na umurce ta tayi kafin in fita. Aje abindana shigo dashi nayi na fita na barsu a dakin falo naje na duba table da karami sai na danyi mai dabara ya koma kamar na asibiti na dawo dauke dashi ina fadin ki kama min wancan gefen mu daga ta dakyau. A cikin dabara muka dago ta ta dan kai zaune yana tsaye duk abunda mukeyi ya kura muna idanu kawai bace uffan ba har lokacin da muka fara bata abincin tana karba kamar ba hjy jummai ce ba a kwance haka mutumba a bakin komai yake ba a gurin Allah idan ya tashi ikon shi ga bawan sa. Yau hjy ce haka a hannuna sai yadda mukayi da ita babu bakin magana din tunda nazo banji tayi magana da bakinta ba hakan yasa na dago ina tambayan shi wai tana magana kuwa yaya ? Ajiyan zuciya ya sauke da alama yayi nisa a cikin tunane lokacin yace tun lokacin data fama ciwon nan jikin nata ya kara rikicewa haka ai. Zata samu lafiya da yarda Allah na bashi amsa ina mayar da hankali a gurin ta magani na dauko muka bata tasha muka mayar da ita ta kwanta tana lumshe ido sai ga hawaye yana gangarowa a fuskanta a hankali. Haba mama kada kuma ki saka damuwa a ranki wani ciwo yazo ya shige ki kuma. Fita naga yayi a dakin saida naga ta dakatar da hawayen na bar daki ina fadawa matar su kwanta su dan huta zuwa goma zan shigo in mata allura . Godiya matar ke mun tana saka min albarka nayi murmushi na fita daga dakin zuwa nawa part din. Daki na koma wanka na shiga don na samu har lokacin yaran suna barcin su a dakin Fauziya ma tana kwance a inda tayi sallah. Wanka nayi na shiya sai ga maria ta shigo dakin tana gaida ni zata dauki yaran tayi masu wanka kamar yadda ta sabayi masu a can. Sultana ta fara dauka a lokacin fauziya ta falka itama hakan ya tayar da babana daga barci. Kafin takwasa duk mun shirya mun hadu a dakina inda na kara jawa kowa kunne da zaman gidan da zamuyi tare da wasu duk da bamu saba da hakan ba tun farko. Alhamdullahi duk sun gamsu da warning din da nayi masu maria na umurta data fita zuwa kitchen ta duba idan masu aiki basu fito ba ta hadawa yaran abin karyawa. Bata jima ba ta dawo tana fadin sun fito na amsa mata fita tayi zuwa dakin su ta gyara masu zuwa tara da wani abune na fito tare da yaran har lokacin babu kowa a falon gidan. Dakin kwanan shi muka nufa tare da yarana su duka hudun nayi sallama a kofa kafin ya karba mu gaidashi mukayi da kwana yana kallin yaran cikin kulawa daga inda yake zaune har lokacin da alama bai riga da yayi wanka ba don jallabiyan da nagani a jikin shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:22 - 🀐🀐🀐: Zaune muke gaba dayan mu a dining yaya umar ya fito daga dakin shin a cikin shitin shi yaran suka mike a inda suke suna gaida shi yana daga su daya bayan daya yana saukewa. Baifi minti biyar da zama damu ba sai ga merry ta fito da yarta fuskanta babu yabo babu fallasa a tare da ita. Yarta ne tazo wurin shi yana subantanta suka gaisa kamar yadda yarinyar tayi hakama uwar tayi don sai da suka danyi hugging din junan a gaban mu. Zama sukayi suma don karyawa a lokacin nice na fara gaida ita ta amsa bawani sakin fuska har lokacin tana gaidashi. Muka fara cin abincin gaba dayan mu sai maria ce bata cikin a lokacin don har fauziya tana gurin zaune. Kamar yadda ta saba shigo masu da kasaita ko wanan karon haka ta shigo muna tana tako dadaya dole hankalin kowa ya koma ga kofan don ganin mai shigowa banda yaya dake dauke da abbana sai Queen dake gefen su tana saita dauki Abba din ta rike shi. Farinta na maine na fara hangowa sai gashin dokin da tai kitso dashi ya sauko mata har a baya sai wani cin chewing gun take a bakinta irin na yan bariki sosai din nan. Itama dai kamar yadda muke kallon ta gaba dayan mu har yaran hakane take kallon mu da mamaki itama. Take iskancin data shigo dashi ya gushe lokaci guda yanayin ta gaba daya ya canza ta shiga dan kame kame kamar zatayo wurin mu ta fasa shiga dakin hjy a lokacin sai kuma ta juya ta shiga dakin da hjy din ke ciki. Bani da nake ba hausa ba har merry dake kabila saida ta harbo jirgin ta na daburcewan da ta shiga a lokaci guda don ganin mu. Tsaki merry taja tana fadin pulish lady tana tsamanin kowama kamar tane haka ? Banyi magana ba saima Allah ya taimakeni a daidai lokacin wayana yayi kara hakan yasani tashi a lokacin na barsu a wurin zaune tare da yaran. Murjace ta kirani a lokacin na shige daki ina karba wayan bansan me zata fada min ba na rigata fadin ke murja yanzu naga wanan matar da yaya ya aure wallahi. Dariya murja ta kwashe dashi tana fadi wai dama ke baki santa bane ko a photo nace ina zan santa nida ba wani dadewa nayi a kano sosai ba. Ai bama zaki santa ba din don ba,a kanon suke da zama ba dama suna lagos duk dadewan nan sai yanzu da mahaifisu yai ritayane suka dawo nan tunda komai ya kare masu. Suna dawowa kuma tana ganin yaya ta leke mai saishi take so nace amma murja wanan tsohuwace fa sosai don dai jikintane baya nunawa kawai. Tace tsohuwa ko ta gaske ma don bakiga kannen ta maza bane ai da kin gaskanta tsofan nata sosai. Yanzu kuma haka yaya yake zama da ita murja bakina ya subbuce da fadin hakan a lokacin don mamakine fal a zuciyana sosai. Dariya ta kara kwashewa dashi tana fadin haka ko yake zaune da abinsa ba gashi har ta buge mahaifiyar shi ba tana kwance ba,ai komai ba koda yake su basu son a fadi hakan ai. Nan murja ta kara ban labarin fadan nasu tana kwashewa da dariya sosai nake fadin don Allah murja barni da abin haushi mana haka. Shi yaya wani irin zuciyane dashi haka da har mace zata nakasama uwa kana zaune da ita baka dauki mataki ba uwa fa ba wasa bace murja. Ke bafa laifin yaya din bane don kawune ya tauye shi kan daukan mataki kinsa aiko bai dauka ba yan uwan dasun dauka yanzu. Laifin kawune da ya hana kowa magana ke abinda baki sani bafa shine a yadda naji Amma na fadi ranan . Babu ruwan yaya da uta tunda ta shigo gidan shi suna nan sai bare baren kudi suke a kanshi don dai kawai a jawo hankalin shi gareta. Zuwan merry ma kasan nan ba karamin fitina aka kwasa ba a tsakanin har hjyn ta fama ciwon ta take rabke haka. Humm Allah ya kyauta nace mata tace amin dama na kirakine in fada maki su mama zasu shigo wurin ku tare da Amma yanzu. Nace kai ai da su barni in je don yanzu idan sunje yaya ba zai bari in tafi gida ba kuma kin dai san halin shi murja. Tace sunce zasu shigo su gaida yaran da akace basu da lafiya ina ganin yaya din ya fada masu hakana. Shigowan Queen dauke da Abbana dakin sultana na bayan ta tana fadin ta basu babyn su ya katse min wayan da murja da mukeyi. Zama yarinyar tayi a nan tare damu yaron yana shan nono sai faman jagulan shi take da gani tana sha,awan yara kanana sosai . Tana nan tare damu har wani lokaci a dakin yayin da suke dan surutun su wani lokaci in basu amsa don gaba daya yanayi jinsa nake babu dadi a tare dani a lokacin. Sallaman su yan gidan mune da fauziya ta sheko da gudu tana fada min shigowan su yasani fitowa daga dakin. Bayan sun gama mamakin girman da Fauziya din ta kara tare da yarana suka shiga dakin hjy don su gaida ita da jiki. Sun samu ranan ta dan samu sauki sosai tana kwance idon ta biyu ba barci takeyi ba suka fara gaida ita a daidai lokacin na fadon dakin da sallamana don murnan ganin su. Amma da yanzu tsofa ya kara takureta sosai sai lalaba rayuwa da akeyi tana ganina ta washe baki tana murna sai fadi take masha Allahu A ruwa kece haka kin zama wata dirkekiya dake sam barka . Nace Amma ke kuma ga tsufa yana batun rufe muna ke a yanzu da mukafi bukatan ki a tare damu . Nan dai muka shiga gaisawa dasu a dakin kafin in koma wurin da hjy take kwance ina tambayan lafiyan jikin nata yayin da dakin gaba daya yai tsit ana sauraren mu. Ina fadin ya kamata ta samu abinci taci yanzu don Allah ki daina barin ta sai lokacin da za a gama abinci ace a lokacin za,a bata abinda zataci. Mamu da tun shigowan ta batai magana ba tace gaskiya kan yunwa ma ai kanta ciwone sai lokacin matar ke fadin ai na gode da zuwan yarnan taku sosai don ita ta taimakemu a daren jiya da zuwan su ta shiga dawainiya da hjy sai gashi yau ta tashi jikin da sauki sosai. Da ai tun ranan data fadi din nan jikin nata har jiyan ba dadi sosai wallahi sai mama hadiye ke fadin hjy ki bar motss jikin tunda motsawan shike kawo matsala irin haka. Shine ai wanan yar taku ta fada ko wanka a nan saman gadon tai mata sabanin da can da sai mun tafi bandaki da ita munyi ko hakan ai sai ya jawo fitina. Aikin sune hakan ai dadin karatun ke nan wallahi kinga abin yazo da sauki bama sai likitan da ake daukowa yazo din ba tunda ga fatima Allah ya kawo kasan. Wai dama ba a nan suke zaune bane ke nan matar mai suna Asabe ta tambaya tare da fadin gaskiya na gansu kamar kabila har yaran don basu jin hausa. Wai baki santa bane matar mai gidan nan ne fa yar uwanshi da aka aura mashi a can suke zaune da yaran su duka kasan waje. Ikon Allah kaga mace kan wallahi Allah ya inganta rayuwan ku dana auren ku gaskiya kan Alh yayi dacen mace mai mutunci da tarbiya bakuga yadda takeyi ba da boyar Allah nan tunda tazo. Ai shine dama haka duniya ta gada ai shi da na kowane don baka san ta inda zai taimaka maka ba watarana Amma ta fada tana mikewa tare da fadin Ina yaron da aka haifa din bamu sanshi ba mun daiga yan biyu a waje. Tare da Amma da mama muka fito daga dakin muka bar mamu da hjy maryam a gurin hjy suna kara mata sannu da jikin. Sai lokacin naga Nura autan su yaya yana gaidani yana zaune tare da yaran da Fauziya suna turanci kai katako kamar yadda yanzu nake kiran shi tun bayan aurena da yaya yace har yanzu baki daina kirana da wanan sunan ba. Ina zan daina tunda bana karfen kake ba na dan tsaya muka kara gaisawa da yaron a wurin kafin in juya na kaisu dakina . Nan muka kara gaisawa sosai dasu muna yaushe rabo sai mama hadiye ne ke tambayan ace merry ma tana gidan ai. Nace eh mama a nan muka sameta ban ma san da zuwan ta ba saida muka zo garin na sani murja ce ta fara fada min tana nan amma shi bai fada min ba. Fita nayi zuwa kitchen na sa aka hado masu abin motsa baki kafin in koma dakin na nufi dakin merry a cikin karfin hali irin nawa na kwankwasa kofan nata. Kusan sau uku kafin ta amsa da who is dat nace it,s me Fatima kamar ba zata bude ba sai can naji ta bude kafan nayi mata yaya lokaci ban jira amsawan ta ba nace. Parents din mu ne suka shigo duba jikin hajiya naga ya dace su gaisa da ita shine na zo fada mata. Sai ta danyin jimmm a wurin nace zaki iya masu biyayya koda bakiso saboda martaban yarki da take jinin su hakan zai sa su soku sosai a jiki. Ina fadin haka na bar wurin ba tare da tsayawa in saurari amsan da zata ban ba don irin kallon da take min a lokacin gashi da gani tasha kuka don idanuwan ta da suka nuna alaman hakan. Dakin na koma inda na samu su mamu sun shigo suna zaune saman kujera ga abinda aka kawo masu ba wanda ya taba a cikin su. Sai fadi suke su zasu tafi nace haba maman ikilima tun yanzu zaku tafi tace yaya na iya da wanan mai alkunyan wai da ita ba zata shigo dakin ba tace. Mumu na kalla ina fadin ba zaku bari har a dan jima ba hjy maryam da sai kallon manyar jakkunan dake zube daga can gefen gadona ta juyo tana fadin Alh ne kawai a gida sai murja da Nafisa suma yanzu da mun koma zasu fitone sukace. Muryan merry ce dake shigowa ya hana kowa wani magana merry ta shigo tana saye da wani bakin dogon riga a jikin ta mara hannu rigan sai gurin hannun da akaiwa dan tattara kamar kwalliya. Gaida su ta fara tana tsaye suna binta da kallo hjy maryam da mamu suna tambayanta ina Amina saini ce suna tambayan Queen ce don haka suke kiranta nan. Ta ce tana waje da sauran yaran a falo tun dazun bata tsaya ba kawai ta juya ta fita daga dakin tana mai jin zafin su a ranta don gaba daya kowa a wurin ta mai laifi ne gare ta. Don sune suka jawo mata bacin ran da take ciki a yanzu wanda auren mu da yaya yayi take ganin da hadin bakin duka yan uwan shine akayi shi. Basu dade ba suka fito har mama hadiye sai Amma ce da zata tsaya damu har aya umar din ya dawo gida . Sai da suka biya dakin hjy sukai mata sallama kafin mu rakasu har waje nida maria ina fadin sai mun shigo suka tafi. Ban koma daki ba kitchen na hada ma hjy abinci mara nauyi nakai masu dakin nan muka tsaya muka bata tare da matan kafin in fito na bata magani tasha. Dakina na koma na samu har Amma tayi barci yasani fitowa zuwa wurin maria a nan na dan zauna don kada mu tayar da Amma danaga ta samu barci sosai a lokacin. Daga dakin na yara na tskayi sallaman su murja na fito da sauri na tare su muka dunguma zuwa dakin hjyn da a yanzu zaune muka sameta tana zufa nace su kunna Ac sanyi ya gauraye dakin tukunna zata fi jin dadi. A haka har muka share kwanaki a gidan ba ruwan wani da wani a cikin a na zamane kawai a tsakanin mu kowa yana jin kansa. Kwatsan da wani safiya nake jin dan hayaniyar yaya da merry tun suna rigima a hankali har aka fara jin muryoyin su . Nidai ina dakina ban fito ba sai wani tsawon lokaci da maria ta shigo take fada min wai taga merry ta fita tana ganin kamar tafiyan ke nan tayi don da kayan su suka tafi. Sai zuwa yamma kuma muka ganta ta dawo a rikice wai bataga Queen ba inda sukaje shiga jirgi. Gaba daya hankalin mu gidan ya tashi sosai da wanan labarin batan Queen daya riskemu a lokaci daya. Duk abin nan da akeyi amaryan yaya tana part din ta ta kure shiyanta da sauti gamu sai faman buga waya akeyi ko ina tun munayi mu kadai har abu ya karde unguwa ga baki daya security suka zo sai lokacin ne baba balarabe ya shiga yai fada sosai kan abinda ta aikata din ya fito yana fada sosai har saida merry dake tsaye a gefena ta jingina da jikina don kukan dayaci karfin ta. Babu mai iya kama wani a cikin mu a lokacin duk hankali tashe muke a gidan gaba dayan mu ga baki daya . Naga karfin halin wanan samiran don har mukaci muka sude muka koma ciki wanan matar bata ko leko mu ba kowa na fita da ita a baki a gidan. Sai can cikin dare muna zaune a falon mu zugun zugun merry duk ta fice a yanayi ta sai ga su yaya Aliyu sun dawo da yarinyar wai a nan cikin airport aka sunce ta ta samu wuri ta boye don bata son bin mahaifiyan ta zata zauna da yan uwanta a nan. Shi umar ma a lokacin bai garin yayi tafiya kasan south Africa wani business shida Nasir sai ta waya muke communicating dashi kawai. Merry data gigice lokacin da aka shigo da yarinyar sai zubewa tayi sumay a lokaci daya kafirci baiyi ba wallahi. Ranan munga tabara a wurin merry irun na kafirai da basu san Allah ba mahaifiyar ta ko ta kira yafi a kirga a ranan. Sai lokacin muka samu kwanciyar hankali kama yarinyar nayi naje nayi mata wanka na bata tea mai kauri tasha sai barci. Wayewan gari tun karfe shidda gidan namu a cike yakw da mutane yan barka da arziki da Allah ya kiyayye wanda ya nuna hadun kai ga musulmai gare ta. Har wani kungiya na kirstan aka turo muna gidan wai daga kungiyar su na kiristoci na kasa da kasa sukazo sun so tafiya da merry din da yarta kawu balarabe yayi tsaye ya hana hakan. Kuma sai abin yaso ya koma wani rikici a lokacin don sunyi tsaye sai abasu su su wuce dasu kawu balarabe yai tsaye sai uban yarinya ya dawo ya yanke hukunci da kanshi. Dole ba yarda zasuyi suka barta suka tafi don kawu balarabe fitananen mutum ne sosai kowa yasan shi da fitina. A wanan lokacin ne na zama kamar nice yar uwan merry din ko da yaushe muna tare ina bata magana duk ta fita cikin hayacin ta saboda fargaban data shiga na yar nata. Kwanan yaya biyu ya juyo ya dawo saboda halin da yarsata shiga na bata hankalin shi yayi kololuwan tashi a can duk da an fada mai anga yarinyar saidai bai yarda da hakan ba. Dawowan shi yasa mutane suka fara tururuwan zuwa masa jajen abinda ya faru da yartasa daga ciki kuwa har samira da mahaifiyar ta dako leke basu leko yiwa kowa barka da arziki ba da farko. Ance abin duniya baya boyuwa don dai basuyi sa, an zuwa gidan ba saboda sun samu Amma da mama hadiye da tun faruwan abin suna gidan basu koma gida ba don tare muke dasu a gidan. Gaisuwa suka fara sai jajen batar yar da suka fara mai a lokacin mama hadiye tace wai mamaki hajiya sabuwa wai me yasa kuke daukan mutane wasu iri kamar kunfi kowa dabarane ? Kallon mama kowa dake falon yayi har da bakin dake nan a lokacin hjy sabuwa daba kyale ba tace akan me zaki fada muna haka hadiye ? Dole in fada maki do naga kuna son mayar da kowa wawa a gidan nan saboda kunyi na farko ga hjy kunji dadi. Ina nan ake kururuwan batar yar nan a gidan nan har wanda bamu sani ba ya shigo gidan nan taya mu bakin cikin abinda ya faru damu. Amma yarki tana gidan nan bata leko kowa ba a gidan nan karshe ma sai kidan farin ciki data saka muna a gida sai yaya balarabe ne ya shiga ya tsawata mata. Hakan baisa ta tako zuwa wurin uwar yar nan ta nuna bakin cikin ta ba gare ta ai na dauka ko akuyan muce ta bata yanzu tunda samira tana karshin inuwar shi tare da ita za ai zaman bakin cikin nan. Yanzu kuzo don ganin ido saboda kunga umar ya dawo wai kunzo taya mutane bakin cikin abinda ya faru ko kunya babu don kun mayar damu bamu san abinda mukeyi ba ko mai ? Hadiye akwaiki da wani magana yarshi ce ta tabata don haka shi muka zo yiwa tanzanko ba wani ba . Wurin wa kike son muzone da wurin kishiya ko wa zamu zo din bamu gaji dukawa kishiya ba kema kin sani balle yar cikina ta tabi kishiya don son suna. A take falon ya dauki hayaniya a wurin inda yan uwan hjyn su yaya suka karbe zancen ya zama nasu sai hayaniya ya tashi a falon . Mikewa yaya yayi dauke da Abbana dake jikin shi yana rike da hannun Queen da sauran yaran dake biye dashi bayan shi suka fice daga falon. Hayaniyar da yai yawa a falon yasa merry ta juyo inda nake zaune a kusa da ita tana tambayana meke faruwa ne wai na fara mata bayani abinda kowa ya fada a gurin. Tace thank you mama da cewa wa mama hadiye da tai magana sun dauka kowa baida hankali da wayau sai su, . Sun dauka zasu iya dumping din kowa a yadda suke son yi kome wanan matar ita da yar is devils they are very weaked in action. Ba a daiyi ta da dadi ba a ranan don rayuka sun baci sosai a gurin samira tana taya uwar ta fadawa yan uwan hjy dake falon magana mai zafi. Ga merry ta matsa min da tambayan me ake fada dole na koma hankalina ya kasu gida biyu a lokacin. Sai bayan sun fitane sun koma part din su hjy sabuwa kecewa samira bance ki dagawa duk dan iskan dayaso ya kawo maki gani gani a gidan nan ba kaf. Don basu da yadda zasuyi dake sai gani sai hange gida daine baki barin sa koshi dan iskan mai akidan turawa zai dawo haya bada dadewa ba zamu kamashi a hannu dumu dumu ya gama duk kwanaye kwanaye shi muna nan zai sake ki zakice na fada maki wanan maganan ai. Amma umma baki ganin hakan da mukeyi duk da bai magana zai iya zama muna matsala tunda ba duka muka gama rufe bakin su ba jifa yanzu wanan gwaggon nasa data kawo wanan maganan a gaban sa. Kyale yar iska idan na koma gidan boka zan bada sunan ta tunda tana ganin ita takai a yanzu. Gaba dayan su sai nagama dasu kaf wallahi dani suke wasa basu san sabuwa ba jina sukeyi kawai. Umma ni abinda yafi damuna a yanzu shine wanan matar tashi Fatima don ko ita kafiran kamar wanan fatiman ta shige mata a gaba a gurin shi. Nima nayi wanan tunanen a yadda na ganta ta kara zama wata hamshakiya shegiya sai wani kyau da haske take karawa kamar itace mai dukiyan. Yo yar banza dole ta haska tun yanzu ta cika mai gida da yan yayaye haka masu zubin turawa ko larabawa dasu can jifa ko hausa yaran nake ganin basaji. Itama dole a satin nan mu kaita a sakarwa yar iska warin jaba kyauta da suran da take takama dashi duk ya tashi a banza yaji ya tsaneta ga baki daya. Wanan maganan yaiwa samira din dadi sosai tace mama ko nawa ne indai har hakan zai faru da ita zan bada don a shirye nake inyi komai kan wanan yar iskan yarinyar . Tunda tazo garin nan nake a cikin fargaba da tsoro daduk nayi arba ds ita wallahi sai naji gabana ya fadi uku uku ban san meke sa ina jin hakan ba a kanta da duk naga wanan yarinyar. Wata rana kece zata koma tsoro ai uwarta ba sheri ta iya ba jummai ta samu sakarai ta kasa natsuwa ta juya yan banza yadda takeso sai kishin hauka da girman kai irin nata. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:22 - 🀐🀐🀐: Yaya umar tun fitan shi gidan su ya nufa tare da yaran shi da suke tare a lokacin , part din kawu suka nufa don yanzu sai suke jin gidan babu dadi gare su idan sun shigo. Tun bayan barin hjyn su gidan na yan wani watannin dasuka shude gaba dayan su, gidan babu dadin zuwa gare su hakan kesa da sun shigo sai su nufi part din Amma sai wani lokaci sukan dan leka su mamu a part dinsu su gaisa. Tunda ya shigo ya zauna suka gaisa da kawu bai kara magana ba yana zaune yaran nata dan surutu a tsakanin su sai can kawu ya dago kai ya kalle shi tare da fadin lafiya kake na ganka haka yau. Dan murmushin yake ya sakarwa kawu tare da fadin babu komai daddy yana kara lumshe idanuwan shi a hankali. Ko har yanzu zancen bacewar yarinyar ne ka saka a ranka ko kana zaton wasune suka dauketa da niyyah yin hakan. No ba abinda nake wa tunane ke nan ba Amma wanan fitinar dai da mama ta dauko min a gidanane ya fara damuna . Fitinan me ke nan saudaki kake nufi ta jawo maka a gida kuma bayan wanan zancen batar yar taka ? Ya gyara zama tare da hade hannayen shi ya dan furzo da iska daga bakin shi yana fadin wanan yarinyar da ke zama a gidana . Yanzun haka na barsu ita da uwarta a gidan suna masifa dasu gwago hadiye tana kokatin tara min mutane a gida. Dan murmushi manya kawu yayiwa dan nasa yana fadin umar ke nan ai dama duk wanda ya sai lariya yasan zatai yoyo . Ka taba ganin inda irin wanan hadin na mata zallah yai albarka abin son raine fa aka hada ba don Allah akayi shi ba. Amma yanzu duk me ya kawo wanan zancen har suke wanan fitinan suna kokarin tayar maka da hankali kaida gidan ka. Nan dai ya koro mashi abinda ya faru har fitina ya kaure a tsakanin su kawu yace ban san har sai yaushe wa yan nan mutanen zasu gane talala na sakar masu a gidan ka. Wanan iya shegen shi jummai take son in barta tanayi a gidan nan sun dauka hakan wani wayewa ne ko burgewa a idon jama, a. Basu san hakan zubarwa mutum kima da ajinshi yake ga duk wanda yaga suna aikata irin wanan rayuwan . Ina dadi wai ace mahaifiya taje gidan yarta tana wanan sayar da halin haka kamar ba wa yanda suka samu irin tarbiyan mu ba a nan. Na dauka hakan daya faru a tsakanin su da ita jimmai zai sa nadama da natsuwa yazo masu a rayuwan su sai dai ashe su a wurin su ba haka abin yake ba. Daddy wa yan nan mutanen babu nadama a tare dasu abinda sukaiwa hjy sam su ko a jikin su ma don ko gaida ita sai wanan taga dama take shigowa ta dubata . Gaba daya iyalina babu wanda ta sanda yazo a gidan balle harta kalle su da idon mutunci sai fadan nan nasu dasu mama na gane komai da takeyi da sanin mahaifiyarta take yin sa. Don kalaman ds mahaifiyar ta jefawa su mama cikin zancen nasu ya nuna itace ke dora yarinyar a hanya ma. Gashi gurin raba su fada da marry har hjy ta fado ta fama ciwon jikin ta tun ranan bamu gane kanta ba na kira likita mu mayar da ita asibitin yace ko mun koma da ita can babu abinda zasu iya mata a yanzu. Allah ya taimaka zuwan Zahran nan kasan tun ranan da ta sauka ta rubuta magani da allura tare da bata taimakon daya dace muka fara ganin sauki sosai a gare ta. Kawu dake kasa zaune yana wasa da Abbana daya rarafa zuwa wirin shi da sauri ya dago kai yana fadin madallah. Al,amarin Allah ke nan yau yarinyar nan fatima ce maiba jimmai taimako har ta yarda ta karba daga gareta din. Yarinyar da jimmai ta tsana har bata iya boye hakan a gaban kowa lalai lamarin ubangiji baida kadan. Ko yanzu bukatana ya biya don ubangiji ya wankeni ga abinda nake son jimmai ta gane akan rayuwa. Shi da na kowane balle mutum baka san a inda Allah zai turo ya taimake ka ba kaga yanzu sam babu wanda ya taba kawo hakan mu saman ma ita jimmai din data dauki duniya da girma takw ganin kaskancin yarinyar akoda yaushe. Gashi yau wa yanda take ganin su din ne wata tsiya a wurin ta sun kasa taimaka mata dako sannu balle kallon arziki. Dama irin haka yakan kasance sai Allah ya jarabe ka ta yarda zai nunawa mutane irin hikiman shi a ko yaushe. Sai yanzu umar da yai shiru yana sauraren zancen mahaifin nasa ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin . Ni kaina daddy ranan na dade ina irin wanan tunanen wanda ita kanta hjy naga alaman nadama a fuskanta lokacin da zahra ke rungume da ita tana bata abincin. Murmushi sosai kawu yayi a fuskan shi yana fadi kuma a fili Allah yasa hakan ne a zuciyar ta . Yanzu ina son ka kara kwantar da hankalin ka kan zancen batar yarinyar nan kada ka zargi kowa a kan hakan don a bakin yarinyar cikin hikima zakaji komai da ya faru da ita ba sai an saka zargin kowa ba. Sai zancen wa yan nan mutanen naga abin nasu ba zancen nadama a cikin shi don haka duk hukuncin da kaga ta dace zaka iya dauka a kansu sai dai ina mai kara baka shara ka kara hakuri har gaskiya ya gama baiyana kanshi kowa ya fahinci manufan mu kan hakan. Insha Allahu ya furta a sanyayaye ba tare da ya dago kanshi ya kalli mahaifin nasa ba in a son ranshine yaso wanan karon ayita ta kare a tsakanin shi da wa yan nan mutanen. Saidai a yanzu dole yabi ra, ayin mahaifen nasa kan hakan daya bukata a wurin shi yanzu. Bai fita gidan ba bayan yabar wurin kawu din saida ya biya da yaran part din su mamu suka gaisa ya dan jima a wurin mamu suka dan taba hiran batan Queen da tayi. Ya dawo gida babu kowa a falo ga yaran dake a takure don sun ki cin abincin da kawu yasa a kawo masu da suka zo wurin shi . Na idar da sallah azahar ke nan na dan kwanta in huta don merry bata barni kwanakin nan na samu natsuwa ba da tabaran ta irin na kafirai idan masifa ys yasame su. Yaron ya shigo ya shimfide a kusa dani yana fadin gashi yayi barci kuma akwai yunwa a cikin sa. Yanzu jan sai ya falka kuma ai tunda naga barcin nasa yayi nisa sosai abawa sauran suci kada suma suyi barci a hakan. Yana kai kofa ya juyo yana fadin merry dazun take fada min irin kokarin da kikai mata lokacin da wanan abin ya faru da Queen. Kai haba ai dole mu rausaya mata son bata san kowa ba a nan bayan mu idan duk muka juya mata baya da wanne zataji a ranta. Dan murmushi kamar yadda yake ga al,adan shi ya sake yana murda kofan dakin y fita nema sauke ajiyanzuciya nayi na sauko ina gyarawa yaron kwancia kafin in fito daga dalin . Kula sosai nake ba hjy kuma alhamdullahi tana samun a banci a kai dakai sai hakan ya kara taimala mata wurin jin sauki . Bayan kwana biyu ne merry ta kara zancen tafiyan ta sai dai yaya ya nuna mata bai yarda ta koma mai da yar shi ba wanan shine kuma sabuwar fitinan daya kara kunnu kai a gidan namu kuma. Ashe tun wancan ranan da mukaji suna fitina akan hakan ne har yakai yar taji uban na fadin ba za, a tafi da ita ba ta bar mashi yarsa a nan. Shine dalilin da har Queen din taga zasu bar kasan nan tare da mahaifiyar ta ta gudu ta boye a ban daki akai ta neman ta taki fitowa. Sai gashi kuma a yanzu din kuma wanan irin rikicin ya kara aukuwa a tsakanin su haka yasa ya dauke Queen bada sanin kowa ba ya turata Abuja gidan habbib dan uwan shi. Merry na falkawane bata ga yarta ba ta tayar damu da kururuwa da tashin hankali dole kowa na gidan ya fito don jin abinda ke faruwa. Banda ya umar da bai leko falon ba inda merry ke birgima da ihu dauke mata ya da akayi wanda tasan aikin umar din ne hakan. Nice dai na koma mai kaunar nata a yanzu don haka na shiga dakin yaya din don ganin halin da yake ciki bai fito ba. Samun shi nayi yana shiryawa hankalin shi kwance yana kuma waya a lokacin. Jin motsin shigowan mutum ya tsaya yana kallona bai kuma daina wayan nasa ba a lokacin. Maganan da yayi ne yasa na fahinci yasan inda yarinyar take a lokacin wayan ya kashe ya juyo yana tambayana lafiya ? Queen ce kuma wai ba, a gani ba yanzu ihun uwarta ya tayar damu daga barci nake fada mashi. Tana gurin na kawai ya fada a takaice tsayawa nayi ina kallon shi da mamaki ganin babu fuska kan hakan na juya na fita daga dakin zuwa falo. Nan na samu merry tana kira a waya haka ya bani daman nufar dakin hjy don in duba su da kwana. A zaune na sake su dakin suna magana duk yanayin su baya a cikin dadi a lokacin kara sallama nayi na shiga dakin . Mun gaisa nake mata ya karfin jikin nata ta amsa min a kasalance da sauki bari na dan dawo yanzu sai sha magani. Wanan karon Asabe ce tayi magana tana fadin mun tashi da zancen shan maganin sai ga kururuwan wanan matar ya tayar muna da hankali. Dan murmushi nayi ina fadin mama kin san tsakanin da da mahaifi dolene hankalin uwar ya tashi haka . Wanan dalilin yasa bata son zuwa da yar kasan nan don kada ta san kowa daga bangaren mahaifinta take nisanta ta da kowa nasa. Ashe kuma bata tsira da hakan ba don yar ta nace sai a kasan nan zata zauna yanzu tare da yan uwanta. Ni wanan abinda mai ya kama fitinan matar nan tunda tazo ya isheni a gidan nan babu kwanciyan hankali sam ga zuwan nata. Sai yanzu nake hango gaskiyan Alh daya nace kan sai umar yayi aure a gida a lokacin har ina ganin laifin shi kan hakan hjy ta fada a cikin takaicin abinda ke faruwa din Kafira kafira wa yan nan mutane ai basu da dadi wallahi kansu kawai suka sani kan komai halin su yan akidan su don haka muka zauna dasu a kaduna. Fita nayi daga dakin a daidai lokacin da merry ta rike yaya kan ya bata yarta don ashe tun cikin dare ya fada mata muddin tace sai ta tafi da yarinyar shiko zai dauke yarshi a wurin ta. Ni dai hankalinane ya tashi kan fitinan danaga suna yi din gata, tana ta barazanan kai karan shi ga hukuma yana fadin sai ta dawo. Kawu na kira nake sheda mai abinda ke faruwa a gidan yace zaiyi magana da yay din da ita merry. Karan da naji tayi ya kara firgitani na fito da sauri ina ganin yadda yaya ya hankadeta yana fita daga gidan. Nikan wanan abin ya isheni nayi dana sanin zuwa kasan na samu merry din a nan do hutun namu sam baiyi dadi ba ga laluran hjyn su ga fitinan matan yaya din ko yaushe sai na kwanmace ace ina can abina yafi mun wanan zuwan haka a gidan sarka. Zuwa nayi wurin merry din ina bata hakkuru wani tsawa ta daka min tana dadin in barta duk abinda akai mata nima da sanina ai. Mamakine ya kamani jin furcin merry din a gabana ban iya furta komai ba na juya na koma dakina na barta a wurin. Tun wanan lokacin ban kara shiga tsabganta ba duk da ina jin yadda suke kwasa cikin kwana biyun nan. Rikici sosai sukeyi don har kotu suke da merry din dukda tana gidan nasa zaune ga samira idan zamu hadu kiyayyanane karara a fuskan ta babu sassauci a gareta. A karshe kotu tace zata ba yar tasu dama ta fadi inda take son zama a tsakanin su. Wanan case din nasu ya kara kawo cecekuce ga mutane suke ganin illan auren matan da ba addinin su ba don gujewan irin wanan fitinan. Karshe dai Queen ta zabi zama nan wurin mahaifin ta hakan yasa yan uwan merry shigowa har kasan nan kan case din nasu. Sosai sukai rikici dashi kan ya basu yarsu ganin fitinan yaki karewane yasa suka dauki yar su suka tafi suka bar Queen tare da mahaifinta. Ganun hjy ra samu sauki soai don har sun koma wurin likita ya dubata ya yaba da nasaran da aka samu sosai. Ya kara diban masu lokacin da zasu dawo a kara dubata again maganin da zasu saya ya tsaya ya sawo a hanya suka nufo hanyan gida. Saida ya shigo da mahaifiyar har dakin ta inda ya samu mun gyara dakin nida maria sai kamshi ke tashi a dakin. Abinci maria ta shigo masu dashi bayan sun dan huta tana ajewa na shigo dakin dauke da abinsha ina gaidasu da dawowa. Wanda yanzu idan na gaida hjyn tana karba min sai dai babu sakewa a tare damu dagani har ita ko wani lokacin don ba sabawa da hakan a tsakanin mu . Nikan na gama na fito daga wurin su na koma dining muka zauna cin abinci da yarana har maria da yanzu na mayar da ita yar gida sosai tare damu don irin kokarin maria din da kula ga rikon amana. Ban farga da shigowan Samira din falon ba don ranan bata saka takalmanta mai yawan sauti ba ta shigo. Sai jin muryan ta mukayi a kanmu tana huci take fadin ke yar aiki da cewa maria . Duk juyowa mukayi muna kallon ta ta nunani ta sake fadin nace kada ki kara shanya min kayan yaran ku a wurin dakina baki ji ba ko. Wanan ne karo na farko da wani magana ya taba hadani da ita tun zuwa mu kasan da muka same ta a gidan. Nace amma ke baki da wayau ko hankali ko yanzu akan shanyi kawai zaki shigo muna nan da kashedin bar maki shanyin tufafi a kusa da part din ki. Ko part din kine ta tambaya a gwatsale a cikin izgili a, a gidan ubankine nan din aikun sani. Gaba dayan mu muka juya don jin muryan Nafisa data shigo gidan bada sanin kowan mu ba duba jikin mahaifiyarta da aka kai asibiti. Ke kuma asuwa a cikin wanan maganan ko yanzu kuma kin fara kamun kafa da itane an gama zagin ta koda yake banyi mamakin yin hakan daga gareki ba don har manyarki ma haka suke nunawa bayan an gama bata ta da farko. Duk wanda zai batani wata kila nayi masa ba daidai bane har ya fusata dani kada kuma ki manta Nafisa yar uwan hauhuwa nane na jini. Ba abin mamaki bane don ta shiga magana na a yanzu kinsan ba, a raba anta da jini ai nake fadi a cikin zafin rai. Ta juyo tana kallona kafin tace wai mamaki ke yanzu kina ganin kin samu wuri da har kike ganin kina iya taka kowa tau ki sani kijawa yar aikin nan naki kunne kada in karas ganin kayan yaran nan a gefen part dina don ba za,a tare min iskaba don isa da mallaka da ake takama dashi. Isa da mallaka kan ai dole tayi shi a gidan nan tunda gida gidan mijinntane gidan diyan ta kuma nafisa ta fada. Wani mahaukacin dariyan yan iska ta kwashe dashi tana fadin ke yanzu bakiji kunya fadin wa yan nan maganganun ba haka Nafisa ? May ye baku fada ba akan wanan da farko daga ke har kowa naki sai yanzu ne kuma take mutum a wurin ki. Ikon Allah ke yanzu wanan haukan ne ya turoki nan ina dai ni ban ma san da zamaki gidan nan ba don dake da babu duk dayane a gare ni don haka dani da yarana mu fita a idon ki. Gida dai na uban su ne don haka ke kinyi kadan kice mun ga abinda za,ayi a gidan nan sai dai bari maigidan ya dawo muji idan ya raba gidan yaba kowa nasa kason ne ban sani ba. Muryan hjyce ke dan tashi tana kiran Nafisa daga dakin da take a cikin damuwa a daidai wanan lokacin ne samira din taja wani tsuku mai karfi tana fadin aikin banza yiwa kare wanka duk a tafin hannuna kuke gaba dayan ku gidan nan. Ta juya ta fita nan ta barmu da mamakin ta ina girgiza kai dalili daya zuwa biyu ya hana na bata amsa daidai da abinda tazo dashi. Kudun hjy ta sake shiga wani hali kamar wancen na baya sai kuma yaran dake wurin tun shigowan ta sun kura mata ido a tsorace don basu saba ganin hakan ba isan ba a kasan nan ba yanzu. Don Allah kuyi hakkuri wallahi kusan kwana biyar bamu da wuta layin mu a wahalce na samu har na karasa wanan din da fatan zaku fahince ni yanuwa nagode kuyi hakkuri don Allah. 17/11/2021, 07:22 - 🀐🀐🀐: Bayan Nafisa ta shige gurin hjyn su samira ta kada kai cikin izza da isa ta juya ta fita daga part din kowa na binta da kallon mamaki. Ta na shiga part din ta ta wani sauke numfashi tare da sake dafa kirjin ta tana fadin ashe zan iya kuwa . Waya ta dauko tana kiran mahaifiyar ta kira uku ta dauka bata jira sallaman ta ba ta fara fadin umma wallahi nayi duk yadda kikace in masu. Koke fa da kin zauna kina wani kumshe a daki kamar wata matsoraciya dake nina fada maki kada ki ragawa kowa koshi maigidan da kuke zaman shi ya kawo maki wani gani gani ki face shi tas. Da mamaki take tambayan mahaifiyar amma umma sai nake ganin shi ai ba daidai bane in masa rashin mutunci tunda kinga neman shiga muke a zuciyar shi. Shiga ai mun rigada mun shiga samira kedai kawai ki zura ido kiga yadda za a kwasa dashi a karshen aikin kawai. Ko yanzu me yake iya tabukawa a kanki sai dai ido kawai duk wani kulli kuma da aka aiwatar a kanshi zamu walwale komai da sannu. Sun dan dauki lokaci suna tataunawa da yar nata kafin su gaji su kashe wayan don kansu . A bangare na tana ficewa na girgiza kaina tare da kallon abincin dake gaba ina ci ina dan sakw murmushi a fuskana wanda ni kadai nasan ko na meye a lokacin. Fauziya ce ta kawar da shirun tana fadin wanan matar kamar mara hankali komai nata ita fadane wallahi. Ni tun ranan dana fara ganinta na gane tana da masifa don mun fita da yaya waje take bin mu da harara bata san na ganta ba a lokacin. Eh dole ne tayi haka ai don babu abinda zata gwada a gun hjyna na kishi ga yaran nan da tsone ido jama,a duk wanda ya gansu sai yayi magana kan su dole hakan ya kara mata takaici a kansu. Maria ke nan nace da ita nima kaina wanan abin yana min zafi don mutum wani baka san bakin shi ba sai zuwan mu nake dana sanin zuwa da yaran nan kasan nan a wanan lokacin. Duk da nasan babu abinda zasu iya masu sai Allah don a tsaye nake kan diyana tun dana haife su don gudun irin hakan. Na dade wurin zaune har lokacin na kasa tsayar da magana daya a raina wanda zanyi amfani dashi wurin nuna ma wanan samira din nima na iya kamar kowa. Daki na shiga nayi alwala na gabatar da sallah a zahar da ake kiran sallah a ko ina dadina da kasata ke nan mu sanman arewa zaka ji abinda zai tunatar ma da addinin ka ta ko ina sai dai idan baka da niyar daukan darasi ga hakan. Waya da nakeyi da anty Ramla ne ya dauke min hankali har lokacin shan maganin hjy yayi ban sani ba saida salma da ban san da shigowan ta gidan ba. Muryan ta naji kamar daga sama tana fadin madam kece kwance haka a kasa da alama dai tun idar da sallah baki mike ba. Ga hjy can tana zaman jiran maganin ta nace barin duba mata ke a nan na mike ina murmushi tare da fadin yaushe kika shigo gidan nan ne ? Ban dade da shigowa ba don a hanya sallah ta riskeni ma mun gaisa na nufi bakin mirro dina na dan gyara muka fito tare da ita zuwa dakin hjyn don dubata. Da sallama muka shigo dakin mun samesu a zaune dukan su har hjyn dake saman gadon dakin zaune gaida ita nayi tare da tambayan ta jikin ta. Da sauki kawai ta bani amsa tare da fadin naga har lokaci yana shigewa baki zo kin ban maganin ba. Sai na dauka wanan dan tsantsamin da kuka yi da samira ne yasakaki bacin rai har kikaki zuwa ki ban da mamaki na juyo a inda nake tsaye nace waye samira hjy don ni harga Allah ba wai na rike sunan ta bane hakana. Nafisa ce a hasale take fadin kishiyar ki mana wanan yar iskan mai rainin wayau tana ganin kamar tafi kowa zata iya taka kowa duk lokacin da taso. Salma ce ta tambaya da fadin anyi wani abinne kuma da ita a gidan nan bayan wancan sai mama Asabe ta amsa da fadin ai ita fitinan ta basai da wani dalili ba. Kawai wai don me aka shanya kayan yara a kusa da bangaren ta shine fadan data shigo nan tanayi da yar uwa dazun. Dake fatima take fadan hakan kodawa lalaima wanan ta samu wuri da yawa ni na rasa gane mai yaya ke jira har yanzu da ita bai sallame ta ba. Salma ke nan da wani magana ina zai sallame ta tunda Alh yana son yaga iyakata da sune a yanzu. Na fahinci komai Alh ne ya hana su daukan wani mataki akan abinda sukai min don kawai yaga iyakata dasu kawai. Wa yan nan ai ba abin a barsu bane don wani dalili na kawu kisan kai fa suka tashi yi a nan badon Allah ya gyara abin ba . Nan dai na shiga masu bayanin halin da hjy take ciki duk hankalin su ya tashi sosai nake fadin wanan likitan yaso ya cuta mata da wanan maganun da yake mata amfani dashi don bashi ya kamata ace tasha ba tun faruwan abin. Mama Asabe ke fadin ai mun gode da zuwan ki don tun randa kuka sauka kasan nan muke samun barci da dare sabanin da can da muke kwana a zaune don zafin ciwon. A ikon Allah wai yau Fatima ce tasan wanan aikin haka mama har kina fada lokacin data fara karatun nan kan baki yarda da hakan ba. Ai karatun yana da amfani sosai musanman na diya mace yanzu wanan dawai niyar haka ai sai mace yar uwarka zata taimaka mata. Ni dai har na gama na fita daga dakin dauke da dan salma da take goyo a lokacin ban kuma ji hjy tayi wani magana ba kuma. Yaya bai dawo gida ba sai bayan sallah isha,i suka shigo gidan dashi da habbib dakin mahaifiyar su suka fara shiga suka duba jikin ta tare da dan zaunawa da yan uwan su suna dan hiran ciwon uwar tasu. A lokacin Nafisa ta sako zancen abinda ta samu samira tanayi muna a gidan wanda banso hakan ba don matakin da nake son dauka a kanta lokacin. Saboda na kula ba a part din ta ake girki ba gaba daya ake girkawa a part din mu akai mata tun bayan zuwan yaya garin ta hana mai aikinta yin girki taba masu aikin umurnin su girka su kai mata nata a can idan sunyi. Duk da ran yaya ya baci dajin haka sai bai yarda ya nuna bacin ranshi a gurin ba ya hade abin a ranshi yana jin daci a zuciyar shi. Tun da yamma na ba masu aiki umurnin kada su kara girka komai da samira a part dina da duk wani aiki da zata umurta suyi mata shi na hana ta ba shuganan su umurnin hakan. Koda yaya ya shigo bai nuna min komai ba har yayi wanka ya fito suka zauna cin abinci dashi da habbib na fito ina gaida habbib din tare da tambayan shi iyalin shi . Yace ai suna gari tare dasu ya shigo dazun dan washe baki nayi ina fadin ashe zamu hadu dasu wanan karon ma ke nan. May ya hadaki da wanan yarinyar har ta shigo nan fada dake zahra yaya ya tambayeni cikin katse mu ga maganan da muke da yaya habbib a lokacin. Wace yarinya ke nan na tambaye shi ina kallon fuskan shi da mamaki sai ya habbib ne yace samira yake nufi man. Fuska na daure don jin hakan tare da kawar da kaina gefe ina fadin ina ruwana da tsabganta kawai dai tazo tana karanta min hauka a nan ne dazun. Ya kara tambaya a kan me tazo fada nan din saboda an shanya kayan yara wurin bangareta da maria tayi wanki da safe. Wanan akwai yar iska tana ganin har ta samu wurin yin hakan ga yayan mu kome habbib ya fada a hasale . Abinci naga yaya ya fara zubawa kamar bai damu da zancen ba a lokacun hakane ya ban haushi na mike zuwa dakin yarana na barsu a gurin zaune. Adduan kwanciya nayi masu kafin na juya zuwa dakina na fara kimtsawa don in kwanta sai dai tunawa da ban ba hjy magani ba yasa ni fita lokacin. Yana zaune dakin wanan karon na samu su salma sun tafi ita da nafisa gida gaidasu nayi har lokacin babu walwala a tare dani. Hjy magani za a sha nace da ita bayan na nufi wurin maganin kai tsaye ba tare da najira cewan ta ba na fara ballan maganin ina hada mata don tasha. Har na gama bata maganin ban yi magana ba a dakin nayi masu saida safe na fito zuwa dakina kwanciya nayi don banda ra,ayin zuwa wurin shi ranan. Can barci ya fara daukana naji shigowan shi dakin tare da kunna wutan dakin ya gauraye da haske lokaci guda. Takowa yayi zuwa bakin gadon da nake kwance ga yarana sultana da Abbana sai Fauziya da muke kwana tare wani lokaci yauma a dakin ta kwanta. Tashi muje daki ya fada a daidai lokacinda yazo ya tsaya a kaina ya fada yana mai tsareni da idanuwan shi. Na dauka ai wacan mai fada a kan ka dani ce zata kwana dakai yau din na fada ciki ciki dan murmushin iya fuska kawai yayi yana fadin mene ? Shiru nayi mai ban kara magana ba ina gyara kwanciyana ki tashi mu tafi idan zata kwana tare dani ai ba sai kin sani ba don da baki ganni nan ba yanzu yana fadin haka ya juya ya fice daga dakin. Na dade wurin kwance kamar ba zan tafi dakin ba can dai dole na mike na same shi a dakin bai kwanta ba koda na shigo yana zaune da wayan shi a hannun shi sai dai har ya gama wayan ban iya fahintar maganan da yakeyi ba a lokacin. Wuri na samu na kwanta kafin inji hannun shi saman jikina ban hanashi komai ba saidai bai samu taimako daga bangarena ba har ya gama abinda yake dani. Washe gari bayan munyi sallah muka kwanta bamu fito da wuri ba don na fahinci yau hutu yake ba inda zai tafi ke nan . Don tun zuwanmu kasan ba zance naga ya yini tare damu ba ko yaushe yana zirga zirgan harkan business din shi zuwa wurare daban daban don zuwan nawa ya taimaka mashi sosai ta fanin hjyn shi da sauran abubuwa. Can cikin barci nake jiyo muryan Samira a kofan dakin tana masifa wanda ni na manta da dokan dana ba masu aiki a kanta. Ta turo mai aikin ta karban abinci su kace madam ta basu umurnin kada su kara saka mata abincin ko wani aiki shine dalilun wanan ashar din da take dura min da farar safiyan nan haka. Yun kurawa nayi da niyar tashi in fita don in same ta in bata amsa sai naji yaya ya rikeni daga inda yake kwance yana fadin ina zakije kuma ? Dan jiyowa nayi na kalleshi ina fadin wurin wanan mara hankalin kada ta firgita min yara da safen nan kuma don duk sun tsorata da fitinan ta tun zuwan mu garin nan. Is Over ki kyaleta kawai tayi haushinta ta gaji ta tafi idan kin fita abin ba zai kare ba kuma yanzu yace. Amma dai yaya kana jin irin kalamin da take fada min marasa dadi haka da safen nan yace nace ki barta ko bakiji bane wai. Hakan yasa na koma na kwanta na lafe ban tashi ba sai shi da yaji hayaniyar yayi yawa ne ya fita daga dakin ina kallon shi. Tana tsaye a tsakiyan falon sai masifa takeyi ido rufe jin kara bude kofan ne yasa ta juyowa tana fuskantar kofan. Jallabiya ce fara a jikin shi sai takalman daya zura a kafafun shi ya fito fuska daure yake kare mata kallo a cikin tsana. Itama kallon shi takeyi sai taji dan nauyin ci gaba da masifan da takeyi din tana fadin ashe kana cikima dama wurin ku nazo don matarka ta hana wai a ban abinci dayi min aiki shine nazo jin dalilin hakan. Ke dakata idan ta bada dokan hakan laifi ne ko kin manta cewa nan din gidan tane ita da yayan ta tana da ikon yin komai da taso da kowa. Don haka ki bace min daga nan tun baki hadu da bacin raina ba a yanzu mara hankali kawai zaki shigowa mutane da sassafen nan kina karanto muna hauka . Ban gane abinda hakan ke nufi ba ke nan nidin may ye matsayina kake nufi a gidan nan yanzu. Zaki iya shiga ki tambayi wace ta kawo ki gidan ai tana cikin gidan nan ko yanzu kuma don kinyi mata rashin mutuncin alakan hakan ya yanke a tsakanin kune kuma . Kofan fita ya kara nuna mata yana fadin ki fita tun kan ranki yafi nan baci a gidan nan yanzu. Ganin da tayi babu wasa ko kadan a fuskanshi yasa ta juya ta bar dakin da sauri dan saura kiris hawayen da take boyewa ya zubo mata a wurin. Na shiga uku take fadi a ranta har hannun ta na rawa wurin daukan wayan ta ta kira mahaifiyar ta da sauri take kira tayi sa, a ta daga wayan. Samira me kuma ya faru da safen nan yanzu kuma umma wallahi yau mutumin nan ya gama dani a gaban kowa a gidan nan. Gaban kowa fa ya fada min maganganu masu zafi har yake fadin wai zaman mahaifiyar shi nake gata nan daki inje in tambaye ta. Gida na matar shine da yaran ta don haka tana da iko akan komai dake gidan bani ba. Ke nan umma may yake nufin da wanan maganan nasa yanzu yana nufin dama zaman wanan matar ke nan nakeyi a gidan ba nasa b, , , Samira ki natsu ki min bayanin komai yadda zan fahinta kina hada min magana cikin magana bana ganewa. Umma abinda ya faru ke nan nake fada maki ni wanan abin gaskiya a yanzu ya fara isata gaskiya. Ke gani nan zuwa yanzu tunda yana gidan sai da muka kashe duk abinda ke gare mu zaki wani ce wai kin fara sarewa da zancen haka. Dakin ya shigo lokacin har na mike zaune ina sauraren abinda suke fadi daga falon jin shigowan shi yasa na mike tsaye ina kokarin saka hijjab dina a jiki. Ina kuma zaki tafi yanzu yaran basu falka ba don babu kowa a waje a cikin su har maria ya fada. Zan duba hjy ne kada taga yau ban lekota ba har lokacin nan lokacin shan magabin ta ya dan gwauta kadan na bashi amsa ina fita daga dakin. Bina yayi da kallo har na bace mai da gani ya sauke ajiyan zuciya tare da girgiza kan shi don yana ganin wautana kan abinda baikai na fushi ba na dauki zafi dashi haka. Kai ya kara girgizawa yana kokarin cire rigan jikin shi don shiga ban daki ya watsa ruwa a jikin shi ya fito zuwa duba jikin mahaifiyar su. Ban shiga wurin hjyn ba saida nayi wanka na gyara jikina tsab na fito inda kusan lokaci daya muka shiga don banbdade a ciki ba shima ya shigo suna gaisawa tare da tambayan yadda take jin jikin nata yanzu. Hjy bata kai ga bashi amsa ba muryan hjy sabuwa ya katsesu tana fadin ina mara kunyar yake yana ganin yanzu yafi karfin mutane don ya samu daurin gindi a wurin iyayyen shi yasa kake son taka kowa yadda kakeso. Har kan wanan yarinyar kake kokarin wullakanta yar uwan ka ka fifita agaolan gidan ku da aka cinna maku da sunan mowan gidan ka komay ? Hjy kin ban mamaki kina gidan nan har umar ya tsaya yana fadin wanan magana ga yar uwan shi baki kwabe shi ba tana fada ra sawo kai dakin sai taja ta tsaya don ganin mu da tayi a dakin don bata zaci hakan ba a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA 17/11/2021, 07:23 - 🀐🀐🀐: Shiru dakin yayi ana sauraron abinda hjy sabuwa da ta fado dakin babu ko sallama take fadin magana iya son ranta. Babu wanda yai mata magana daga cikin wa yanda ta sama a dakin ita da kanta taji nauyi da kunyan kanta lokaci guda sai kuma ta fara dan kame kamen zancen. Ina gida yanzu wanan yar ta kirani take sheda min wai umar ya ci mata mutunci tunda safen nan akan matar shi. Shine ya mike tsam daga inda yake zaune ya nufi hanyar fita daga dakin ba tare da yama tsaya sun gaisa da ita ba. Fita zakayi ne mama Asabe take tambayan shi bai juyo ba yake bata amsa da fadin ina da abin yi ne yanzu. Amma kasan wurin ka nazo aiko don kaji abinda ya kawo ni gidan nan yanzu ai. Juyowa yayi da mamaki a fuskanshi yake fadin wai dani kike magana hjy ? Itama kallon mamaki take mai don babu alaman wasa ko girmamawa a gareta ko kadan a fuskan shi. Eh matar kace takai karan ka gareni nazo jin dalilin faruwan hakan don zancen mata ba a san namiji da daukan bangare daya ba. Har kana fadin wani zance dani kaina na kasa fahintar may hakan ke nufi a zuciyana. Matata fa kika ce hjy ki dai ce yarki dake zama a gidan nan ko zaifi sauki matata kan ai ga daya nan a gaban ki yanzu kina ganin ta. Ke zahra ko kece kika kai kara a wurin tane don ban fahinci zancen nata ba har yanzu gaskiya. Eh lalai kana da gaskiyan ka don ba laifin ka bane idan kayi hakan a yanzu saboda alama ya nuna baka cikin hayacin ka gaskiya. Zaki iya fadin hakan tunda yarki na son ta lalata min gida da fitina don kawai taga tana cin albarkacin wani a wurina. Saidai ina son ki fada mata cewa zaman ta a gidan nan yana gab da karewa idan bata fita harkan iyalina ba. Don ba zan lamunci a wullakanta min matana da yayana ba ko kadan a zauna lafiya ko yanzu taci albarkacin mahaifiyata ce da take zama gidan nan donta. Koda yake ku din baku sanda hakan ba tunda ko ita sin bataci ragowa a wurin ku ba sai kokarin nakasa muna ita da kukeyi ba dan Allah ya gyara zancen ba. Jummai kina jin abinda danki ke fada mi a gaban ki baki yi yunkurin hana shi fada min wanan maganganun da yake fada min ba. Ashe taimako yana iya komawa tsiya kefa da kanki kika bukaci hada wanan alakan don a ceto maki danki daga hannun wanan matar tasa da kika tsana. Sai haihuwan da take zubawa a gidan don ta mallake dukiyan shi ita da uwarta da wasu can daban da baki son hakan ya faru dashi. Ashe kin san bakifi karfin daki bama tukun balle matar tashi da alama ya nuna duk ta gama dake da diyan nakima. Ai ashe don ni kika dauko yarki kika kawo ta gidan nan ban sani ba don ni bansan ma da wata aba bacan dana nazo wai matar mijina don banga alaman hakan ba a gidan. Ke fitsarara kada ki soma kawo min rashin kunyar ki da ake fadan kina dashi nan don gida kika sama na rashin mutunci. Sabuwa dama kece daidai dani ba yarki ba don haka yanzu ki kauda yarki kizo ki share daki mu zauna dake sai mu kara ina ganin haka zai fi don kece daidai dani wurin daukan fansa ba lusarar yar nan da kika aje muna a gida ba kamar ba mace ba don ko gaba na mata bata dashi. Kutumar uban nan har iskancin naki yakai ki kalli tsaba idona ki fada min haka kwarai kuwa tunda ke baki ji kunyar fada mi magana irin haka a gabana ba. Aiko ta kara tasowa tana kokarin kaiwa gareni da sauri yaya yace hjy muddin hannun ki ya kai a jikin matana wallahi sai na daure ki a garin nan karyan masifa kikeyi ana kyaleki ne dama. Muryan hjyn su yayane data fashe da wani irin kuka lokaci guda a dakin ya mayar da hankalun kowa a wurinta . A daidai lokacin samira ta fado dakin tana fadin wallahi babu mai wullakanta min uwa ya zauna lafiya a cikin ku. Don uwa bata fi uwa ba ehhe ki daina kukan munafunci ki tsaya a gyara zance zaki sakawa mutane kukan munafunci don zancen ya tsaya a, , , , Saukan mari da tajine a fuskanta har biyu lokaci guda ya hana ta karasa maganan da take son fada. Yaya ne da take tsamanin ya bar dakin yaga shigan ta ya dawo a daidai lokacin da take wanan magana ga mahaifiyar su. Hanyar fita ya nuna mata ita da uwar yace ku fice min daga gida yanzu nan ba sai an jima ba har hjy sabuwa zatai magana ya kara daka mata tsawa saida ta firgice don tsoro. Mai hakkuri ance ranshi bai iya baci ba don yau kan ko mahaifiyar shi ta sheda hakan don bai ragawa hjy sabuwa ba ko kadan ranan tsaye yayi yana umartan yan aikin shi da su tabbatar basu kara shigo mai gida ba. Sai kuma ga hjy sabuwa ta zube a kasa tana rokon shi ya rufa mata asiri ya dubi zumuncin su ya bar samira a dakin ta. Zumunci zumunci fa kika ce hjy ko kin manta ke da bakin ki kika fada babu wani zumunci a tsakanin ku sai na zaman unguwa daya dasu mama. Yanzu hat zaki kira min wani kalman zumunta a tsakanin mu dama talala na sake maku don inga iya gudun ku saboda albarkacin mahaifiyata da kukaci na bar yarki a gidana tana zama. Yanzu ko kun kaini bango ta yadda ban kaunar kara ganin kowan ku a gidan nan . Dama ance yar mace bata taba zama mace ta gari do gashi kin nuna min baki san darajan iyayyen wasu ba balle naki . Kun duke ta kuna ganin kamar kun daki banza ba wani matakin da za, a iya dauka a kanku do kawai an maku dubaiyan da baku san ana maku ba sai gashi kuma har zaku maimaita hakan a gaba gun matana a yanzu. Kin dauka idan idon mama ya rufe da abinda kuke dura mata nawa dana yan uwana zai rufene hjy. Da har zaki dauko yar ki mai ciwo ki kawo min har gidana wai da sunan aure watau duk mu taru mu halaka bayan ta gama halakanta da taimakon ki. Baki hjy ta bude tare da fadin sheri kuma zakai muna umar don kaga muna rokonka ko may ? Habbib dake tsaye tare da iyalinshi dana Aliyu yace eh ai dole ki roke shi kan cuta azzaluman mata mun dade da sanin komai kyale ki mukayi muga iya gudun ki gidan nan ai. Ko kin dauka idanuwan mu muma a rufe yake kamar yadda kuka rufewa mama gaskiyan abinda ke damun yarki taki aurowa a lagos din. Shine do cuta zaki kwaso sheri ki haro dan uwan mu dashi har gida wai da sunan kin taimaki mahaifiyat mu da yarki. Hjy dake wani kukan takaici da bakin ciki a zaune ta wani dafe kirji da karfi tana fadin na shiga uku dama yar nan bata da lafiya ashe sabuwa kika rufe min. Abin nasu kamar hadin baki don sai jin muryan yan uwan haihuwan hjyn su yaya mukayi suna fadin dama ai saida muka fada maki bakiji ba hjy a lokacin . Yanzu ba don Allah ya gyara ba da kin cuci zurian ki da kanki anty wanan maganan nake fada maki a kullun kuke gabin zafina a cikin mu. Akan wani ra,ayi naki can na banza zaki cutar da rayuwan yaran nan ki halaka mashi zuria irin wanan ranan ake gudu dama ranan nadama ga bawa. Godiya mu ga Allah a kullun da yake kawo muna dauki akan komai kafin wani abin ki yakai ga samun mu. Yanzu gashi kin biyewa hjy sabuwa har auren ki na shekara da shekaru yakai ga samun tangarda wanan son zuciya dame yai kama haka don Allah ? Gida duk ya kidime da yayan mutane shikan yaya yana gama magana da hjy sabuwa tun lokacin ya juya ya shiga part din shi ya rufo. Haka nima naja kafa zuwa part din mu yarana na samu zaune a falon maria ta hadesu a guri daya suna kallo. Zama nayi a cikin su a daidai lokacin da su Aisha da Rukkaiya suka karaso ina masu sannu da zuwa. A cikin alaman mamaki suka karba min tare da fadin wanan abin mamakin dame yai kama hakane wai ? Rukkaiya tace mu dai gamu muda ba,a so din dai mune na kwarai a yanzu ai don da bakin suke magana akan irin taimakon da kike mata a yanzu . Koma dai meye ai naka sai naka ba don Allah ya gyara yaya yana da natsuwa ba da yanzu ya dade da kwasan wanan cutar ko tunda auren nasu ai yakai wata biyu ko uku yanzu tana gidan nan zaune. Wana ma wani iri rashin zuciyane ace mutum ya nace kan abu idan ba yasan cutar da yake son yi ba a gurin. Ni wanan zancen ma gaba daya duk ya kashe min jiki wallahi wai mutane mai yasa basu da imani ne yanzu Aisha ke fadi. Sai yanzu nai magana tun zaman su wurin ina fadin rayuwa haka take zuwa da kalubali mai tarin yawa ga bawa sai idan Allah kareshi a cikin ikon shi sai ya kawo mashi komai da sauki . Abinda hjy take nuna min da farko ne nake jin zafin hakan amma yanzu na daina rikon abin a raina ko kadan don dai jini ya riga da ya gauraye da ruwa. Don ko yanzu na bar gidan nan sunana ba zai taba kankaruwa a cikin zurian dakin hjy ba dole sai ance nice uwar yaran nan jikokin ta. Kwarai kuwa Rukaiya tace dole ne kan a fadi hakan dan ma hjy ta godewa Allah rabon yaran nan bai kasheta ba yara kusan nawa ta nuna bata kaunar auren iyayyen su da diyanta. Allah ya riga daya tsago sai zurian dakin ta sun fito daga jikin mu ai dan ni kiri kiri hjy ta kira sunan uwana ta hada dana ubana ta zagesu tas a gabana wallahi. Wanan idan ba kakai zuciya nesa ba kina ganin mai zai faru a wurin saukin abin ma yaran nata basu dauki wanan halin nata ba a ran su da ai zumunci ta dade da lalacewa ko a family mu. Gulman me kuke yi haka kuka kashe murya haka don da gani zaman gulma kuke a nan muryan yaya habbib ne yake fada muna haka . Juyowa mukayi muna kallon shi da dan murmushi a fuskan ko wacen mu sai matar shi ke fadin kai yaya mu hiran abinda ya faru mukeyi ba gulma ba. Kun gaisa da hjy ne da kuka zo nan kuka zauna ya fada yana tsare mu da idanuwa ma,ana umurni yake basu a lokacin. Dakin ne baida dadin shiga yanzu yaya ana cikin wanan tashin hankalin haka yasa bamu shiga ba sai dan zuwa anjima idan an rage yawa. Yadda ya juya yasa ta fadin Aisha tashi mu dubata kada muma namu ya same mu yanzu a gurin shi. Ni dai ina jin su suna mikewa na mike nabi bayan su zuwa dakin da hjyn ke ciki duk da muna jin hayaniyar yan uwanta a dakin. Mun samu har su salma sun shigo don labarin abinda ya faru da safen ya isa kunnen yan uwa sai zuwa gidan suke don jin ba,asin zancen. Sallaman mu ya dawo da hankalin su kofan dakin muka shigo mu uku muna gaida su mama Asabe take fadin au a tare kuke da maigidan ashe ? Tare muke mama Rukaiya ta fada tana neman wurin da zata tsuguna a dakin don ba wani fili a dakin don tarkacen hjy dake dakin yanzu. Sun gaida hjy tana amsa masi cikin yanayin rashin dadin zuciyan da take a lokacin take tambaya da ina yaran suka barsu ne ? Aisha tace suna gida wurin mama muka barsu da zamu zo mun biya can suka ce zasu tsaya a nan da cewa gidan kawu ke nan. A dan dakile ta amsa don jin abinda Aisha ta fada din da alaman hakan bai mata dadi ba kasan ranta. Fatima sannu da kokari fa muna ta jin kokarin da kikeyi da jikin hjy wurin asabe Allah ya saka da alheri ya baku masu rama maku hakan. Dakin ne ya amsa da amin ina fadin hjy dazun ko kin sha wanan maganin dana hada sai mama asabene tace . Ina fa yan nan ta dauko ke nan zata sha wanan bala,in yazo muna tunda safen nan ai sabuwa batayi ba wallahi. Don Allah Asabe ku daina ganin laifin su nifa har gobe inda gaskiya yake nake fada sam sabuwa wuri ta samu a nan . Allah dai ya kare komai bai kai ga faruwa ba a tsakanin su amma mama komai gaskiya ai hjy sabuwa tafi mama laifin don ta boye mata gaskiyan halin da yarta ke ciki don cuta da zalunci kawai salma ke fada. Magani na hada na kara bawa mama Asabe don taba hjy din a wanan lokacin na fita zuwa dakin yaya don na samu yaya habbib shi kadai a zaune falon shi bai fito ba. Dakin na tura na shiga da sallama na hango shi kwance yana rigingine fuskan shi yana kallon saman dakin. Dan juyowa yayi ya kalli kofan kafin ya kawar da kai ya koma a yadda yake da farko na karaso ina fadin yaya ka kwanta kabar yaya habbib a falon shi kadai zaune. Yana gidan nan ne har yanzu ya tambaya har lokacin kamar bason mu hada idanuwa dashi ne. Zama nayi a gefen shi ina fadin lafiya na gabka haka yaya ina tambaya tare da kallon shi a yadda yake din kwance. Yace da kyat No ba komai sai yai shiru nima dai shirun nayi na dan lokacin kafin yace Zahra na amsa da na,am ina kallin shi. Kada ki dauki wanan abin daya faru da zafi kice zaki rike shi a ranki don Allah . Da sauri nace haba yaya a kan me zan dauki wanan zancen da zafi bayan Allah ya karemu daga sherin hjy da yarta. Hannu ya daga min yana mikewa daga kwancen yake fadin nasan kalaman hjy sabuwa da mama ta fada a kanki suna da zafi sosai. Don haka nake rokon ki kan kiyi hakkuri da duk abinda hjy tayi maki kada kice zaki dauki wanan abinda zafi a ranki. Yanzu bada bane yaya hjy nasan uwatake a gareni kuma sarakuwata don haka don mahaifiya taiwa yarta abu saita dauki zafi da ita. Ajiyan zuciya naji ya sauke mai dan sauti yana fadin idan kin min hakan kin kyauta min matuka kuma ina alfahari dake akoda yaushe don nasan daddy bai min zaben tumun dare ba. Ko nace ina dan kallon shi ina murshi yace kinfi kowa sanin wanan hadin namu ai daga Allah yake kawun ki idda sunna yayi kawai . Au goron da zaka ba kawu a yanzu ke nan yace gaskiya na fada yana kokari tashi tsaye ta hanyar dafani ya mike tsaye. A tare muka fito dakin har lokacin yaya habbib yana gurin zaune wanan katon tare da yaran yake fira jin fitowan mu yasa ya dago kai yana kallon mu. 17/11/2021, 07:26 - 🀐🀐🀐: Sun dade tare a falon bansan may suke zance a kai ba don ina daki tare dasu Aisha muna hira inda suke ban hiran abubuwan da hjy take yi masu na rashin dacewa gare su. Ban furta komai ba sai kara kwantar masu da hankali a kanta kamar yadda nima mamu take yawan yi min nasiha da kada na nuna abun yana damuna don dan ta bazai ji dadin hakan ba idan na nuna. Rukkaiya kan cewa take ita kan gaskiya ba zata iya shanye wani abu a ranta ba don da gangan ake maka cin fuska don kawai danta yana auren ka sai ka zama abin ki ga mutum ? Sai bayan la,asar yaya habbib ya bugo waya yana fadawa matar shi ga driver nan a waje yana jiran su don yaran sun fara damuwa lokacin. Sai da suka shirya sun dadauki abinda suke so a dakin nawa ban hanasu don sun nuna ra,ayi akan abina nasan Allah zai musaya min da wanda ya fishi idan na basu da zuciya daya. Muka fito zuwa dakin hjy don su sallameta a zaune take lokacin tana shan ferfesun kaysn cikin rago. Nafisa tana tsaye a kanta da ruwa rike a hannun ta tana bata jin sallaman mu shigowa yasa suka mayar da hankalin su gare mu. Mun mata yaya jiki yayinda take dan dago kai tans fadin ashe kuna gidan nan har yanzu eh yanzu zamu koma don yaran nacan su damu mu dawo. Ke nan ba za,a kawo su su ganin basu ko don kuna gudana da yayan ko hjy ta fada tana kai cibin da take shan ruwan miyan a bakin ta. Can muka fara zuwa gaida daddy shine suka lekawa mama don sun saba da ita yasa muka barsu can tare da ita don lokacin an bugo waya ana wanan fitinan da safe. Na fahinci may Rukkaiya take nufi yasa nayi saurin fadin hjy Nafisa ashe kin shigo ban sani ba ? Tace ummm ke dai fatima na shigo dazun bayan azahar da nake jin abinda wayan nan marasa mutuncin sukayi yau . Don ni ina kuryan Amma ina barci banji me ke faruwa ba sai dana tashi Amma ke labarta min hakan. Wallahi naso na shigo a lokacin da yau sun kara raina kansu wallahi don wana karon ba zan kyalesu ba Allah. Umm tashi mu tafi Rukkaiya tace tana hararan gefen da Nafisa din take . Jin hakan nace Nafisa ke nan wa yan nan ai sai irin su yan duniya don babu mutunci a tare dasu ko kadan. Na fahinci babu shiri a tsakanun su da samira do haka nake kokarin a rabu lafiya a dakin don yanzu sam bansan me yasa bana son tashin hankali ba ni. Ganin sun fara fita daga dakin yasa nace barin dawo Nafisa in baki labari ta amsa da ai ina nan don kilama a gidan nan zan kwana yau. Nace kice dai yau mune da bakuwa a gidan nan ashe mara masu Aisha baya nayi ina fadin sai yaushe kuma zan ganku ? Muna nan ai tunda an kawo mu jiya ne don haka sai kin gaji da ganin mu har bakin mota na raka su suka tafi ni kuma na koma ciki. Dakin nayi niyar shiga zancen dana sama sunayi ya hanani shiga dakin Nafisa ce ke fadin ai nasha fada maki wallahi fatima tafi su kirki dan dama Aisha don ita bata fitowa fili ta tsulawa mutum tsiya kai tsaye. Uhumm ni kaina canzawan yarinyar nan yana ban mamaki don da farko na dauka makircin sune take min don mijin nata ya gani. Amma yanzu na fara sarewa da al,amarinta don yadda akai wanan maganan sabuwa ta tona min asirin duk abinda mukayi tare da ita amma bata canza min fuska ba saima goyon bayana da tayi a gurin. Jin hakan yasa na fasa shiga dakin naja kafana nabar kofan dakin zuwa part din mu zuciyana cike da tunanen maganan nasu. Lalai mamu tayi gaskiya da take fadin duk abinda zataiwa hjy bazata taba son mu a ranta ba don kiyayyan mu ya riga da ya shiga ranta ko mai kankare shi sai Allah. Tunanen ba zai kare ba na tashi zuwa gun maria don ganin halin da suke ciki don yinin ranan na barta da yaran tana dawainiya dasu. Na sameta tana goye da babana da yai barci a bayanta sai sultana da take shiryawa don fauziya tana bayi tanawa yaran wanka lokacin saboda yamma dayayi. Har zuwa lokacin da yaya ya dawo gida baya cikin walwala tare dashi na fahunci hakan ne ta hanyan rashin cin abincin dare da baiyi ba sai ruwan shayin daya sha ya kwanta a lokacin. Ban matsa da tambayan shi haka nazo na kwanta na tashi don da safe ma muryan shine a inda yake karatun kur,ani ya tayar dani . Kallon shi nake da mamaki da bai tayar dani inyi sallah ba a ranan haka kuma banji lokacin da akai sallah asuba ba a ranan . Ki tashi kiyi sallah lokaci yana kurewa sanyin ruwan sama ya hanaki tashi kiyi sallah akan lokaci. Ban iya magana ba lokacin don raina da nake jin babu dadi saboda rasa sallah asuba danayi a ranan. Ban tsaya dakin ba fita nayi zuwa dakina na shiga bandaki kodana idar da sallah ban daga ba wurin ina zaune sai faman tunanen rayuwa nake a raina. Merry ce ta fado min a rai tausayin ta ya kamani don raba da da mahaifi sai Allah nasan kuma wucen merry ta bar queen a kasan nan bawai ta bar zancen bane. Saidai matakin da zata dauka ne ban san yadda zasu kaya karshe ita da mijin nata ba a karshe. Mikewa nayi don jin ruwa ya kara saukowa a lokacin hakan yasani fita daga dakin zuwa wurin maria don in duba halin da suke ciki. A daki na same su bata yarda tabar yaran sun fito koda falo ba don ruwan da ake shekawa a safiyan . Tana ganina ta fara gaidani kamar yadda nake kiranta da maman kid's haka na ambata mata ina zama nake tambayan ta ya suka kwana tace lafiya sai dai Abbanane jikin shi da dare ya danyi zafi kadan. Tabashi magani da safen nan taji zazzabin ya sauka nace a jikin shi nace ai da bakuyi mai wanka ba yanzu. Ina daki har ta shirya yaran suka fito cin abincin sai lokacin na tuna ban leka hjy ba ranan . Koda naje na same shi dakin suna hira nayi sallama na shigo Nafisa tana kwance saman dogon kujera har lokacin tana barci bata tashi ba. Mama Asabe ne ke fadi ai nace hjy yau bamu ganki ba tun dazun dan murmushi na sake a fuskana ina fadin Abbana ne baida lafiya yau na dan tsaya dubashi. May ya samu yaron kuma ta sake tambayana, hjy kuma tana fadin waye ake kira haka cikin yaran ? Bani kadai ba har yaya saida ya dan kalli mahaifiyar tashi don jin tambayan da tayi a lokacin. Kafin wani cikin mu ya bada amsa sai mama Asabe tace karamin wanda ake goyo shine da wanan sunan. Ikon Allah sunan shi wa ke nan ake kiran sa da Abba shiru nayi ina mamakin ta a raine sai shine ya bata amsa da Abubakar yake ai. Sunan mahaifinta ke nan ka sakawa yaron ashe ai na fada maki tun lokacin da aka haifeshi Abubakar na saka mai. Amma ai baka fada min sunan mahaifinta bane ka saka mai ko zaiyi magana mama Asabe ta amsa da fadin ko ba sunan shi bane tunda haka sunan yake sai ta kirashi da Abbanta don sunan mahaifintane haka ? Umhumm kawai hjy tace tana kawar da kai gefe daya ganin haka yasa na mike don barin dakin sai mama Asabe ke fadin. Allah dai ya bashi lafiya da dukkan musulmi baki daya muka amsa da amin ina barin dakin. Wanka na shiga na fito na tsaya shiryawa hakan ne ya dan daukeni lokaci har yakai ga shigowa dakin ban gama shiriba. Fuskana babu walwala ina mai jin zafin maganan hjy datayi kan yarona ko adduan samun lafiya bai samu ba a gurin ta. Yana shigowa ya kalleni ganin yanayi na yake fadin ni zan fita akwai inda zamu tafi da Nasir yau. Kayi break ne na tambaya daga inda nake zaune a gaban mirrow na yace yanzu dai zan fita nayi ina son zanje gida yau in gaida kawu na fada. Ki bari sai idan na samu lokaci mu shiga tare don ina son zuwa mu zauna dashi nima amma kasan mamu bataji dadi ba tun shekaran jiya ban lekasu ba . Kina magana kamar wace ke cikin bacin rai mana ta fada a daidai lokacin daya kai kofan dakin . A kan me raina zai baci zancen mama kikewa wanab daure fuskan kaima a kanshi zaka hanani zuwa gida na tambaya. Kafin ya bada amsa nace akan me zan daure fuska tunda bani tayiwa maganan haka ba kuma ai da zaka saka sunan bakai shawara dani ba da sai ince a saka na kawuna. To ni na saka na surikina amma ai ba aso ka saka din ba ya dan kalleni ya girgiza kai yana fadin Allah dai ya raya min yarana yasaka masu albarka. Ya juya ya fita bin bayan shi nayi da kallo tare da jin wani takaici a raina naso yau in je gida in duba su mu dan kebe da mamu kan abubuwan da suka faru. Ban fito ba don na karbi dana muka kwance tare a dakin haka yasa ban fito ba sai wajajen sha biyun rana ko shi sultana ce ta shigo da kuka dakin na falka. Muka fito tare zuwa falon lokacin ne maria ke fada min kamar taga merry ta shigo gidan nan don taga wasu mata sun fito part din ta dazun. A raina nace nasan za a rina shigowan Atika ya dauke min hankali ban kara bi ta kan zancen merry din ba koda gaske ne ita din ce. Don Atika dana gani saboda koda mukazo kasan tun lokacin mun samu tana bauchi sunyi bukin kanen mijin ta su biyu a can. Mun jima da Atika a dakin muna hira kafin mu fito zuwa cin abinci a falo sai lokacin na tabbatar da zuwan merry din da muke kwankwanton zuwan ta garin. Da fara, a a fuskana na yi mata sannu da zuwa ta amsa min da kyat ganin haka yasa na share ta don ni ba lokacin ta nake dashi ba yanzu. Ban kuma koma dakin su hjy ba don saboda cin fuskan da tayi min saboda kawai sunan mahaifina dataji yaron dashi. Bayan mun gama cin abinci na kai Atika dakin don ta gaida ita da jiki suna zaune sunyi shiru a dakin da gani kowan su yayi zurfi a tunanen wani zance ne muka shigo dakin. Sai mama Asabe ke fadin kai bukar ya jikin naje dubashi akace kuna barci tare dashi a dakin. Na dan juya ina kallon ta tare da fadin yaji sauki ai mama nagode komay hjy ta gani can tace an fada ma maza na rakin ciwo ne halan mai rakin ciwo. Dan murmushi nayi kawai ina fadin wanan kawatace tun na yarinta yanzu suna garin nan ne da mijin ta zaune. Ohh itama yar bauchin kuce ashe Nafisa da tunda muka shigo sai a lokacin tayi magana take fadan haka. Na dan juya inda take ina fadin kin tashi ke nan don iyakata da ita dan guntun murmushi kawai tunda na fahinci tsanata a garesu har zuciyan su yake. Ashe merry ta dawo ne Nafisa ta fada yanzu na tashi na ganta nima na bata amsa a takaice muka daga muka bar dakin. Karfe biyar bayan Atika ta tafi ne sai gashi ya dawo wanan karon su ukunsu suka shigo gidan inda suka yada zango a dakin da mahaifiyar su take. Sun dan jima a dakin shi ya fara fitowa ya same ni a daki tare da fauziya muna ba Abba magani don jikin shi da ya kara zafi lokacin.. Har yanzu jikin nasa da zafi ke nan ya fada lokacin daya shigo yana karasowa inda muke . Na dan dago kai ina fadin yanzu ya kara zafi kuma shine nake bashi magani . Dukawa yayi ya karbi yaron a hannu na yana fadin bari ayi sallah mu kaishi asibiti a dubashi bandai yi magana ba har ya gama da yaron zai fita nake fadin ashe merry tana tafe ne ? Merry ya juyo da mamaki yana tambaya fuskan shi dauke da mamakin jin haka. Tazo ne ya tambaya yana kallon fuskana da mamaki sai kuma ya juya yana fadin humm ya fita. Nikan sai ban san dalilin jin zuwanta bai kwantar min da hankalina ba don haka nake faman kafa kafa da yarana a gidan na saka ido ga duk wani motsi nasu. Zuwan ta da kamar sati biyu a gidan kowa na zaman sa ba ruwan wani a tsakanin mu don baka sanin ma tana gidan sai idan ta fito za a ganta. Gashi ta rame ta kara duhu sosai da gani bata cikin yanayin dadin rai yanzu. Kai ranan dai yawan mafalkin da nakeyi marasa dadi yasa na yanke hukunci fadawa mamu cikin daren nake waya da mamu ina fada mata nifa hankalina bai kwanta da zuwan merry din nan ba, . Don haka kawai nake jin faduwan gaba tunda na ganta garin nan ga yawan mafarki da nakeyi mara dadi. Mamu ta tambayeni da ita kike yawan mafalkin kodawa nace hankalina daine bai kwanta ba mamu. Nasan halin bakaken fatan America wurin daukan famsa sai nake ganin kamar shi tazo yi a kan yarana da sauri mamu tace Don me zaki fadi haka sayadi ina ruwanki da maganan su da zata dauki fansa gun yaran ki kuma. Mamu nidai hankalina bai kwanta ba da wanan matar tunda har naji gabana yana faduwa haka tunzun ta gaskiya a cikin daren nan zan kawo su yanzu daya shiga sallah. Ki bari zanzo da kaina tare da Nura mu dauko su a daidai lokacin ta yadda ba wanda zai gane hakan zan ma kawun ki bayanin komai yanzu. Inji mai zai fada kada in kwaso yaran bada sanin shi ba. Haka kuwa ya faru don ba wanda yasan fitan su gidan har da maria suka fice gidan koda ya dawo yana tambaya cewa nayi kawu ya aiko aka kwashe su dazun bayan fitan shi. Don me aka dauke su da yamman nan nace ban sani ba ya dai aiko yana son yaran su zo mai ne kawai yace. To amma kuma idan daddy zai kwashi yaran zai kira ko ya fada amma haka ka, , , sai kuma yai shiru ya juya ya fice daga dakin. Nikan ganin merry tana gari yasa nake rufe kofana da wuri na shige abina daki in kwanta. Da kyat na samu Abbana yayi barci ranan sai fitina yake min bayan na samu yayi barci, bayan dan fitinan daya taba shiga barcin can cikin barcina nake jin hayani ana dukan kofana da karfi kafin in bude idona da kyau ina saurare kofan aka kara duka da karfi sosai na mike zaune ina kokatin kunna autan dakin don inga haske. 17/11/2021, 07:26 - 🀐🀐🀐: Jin bugun kofan yayi yawa yasa na fara addua, can naji murya da alama ba hausawa ke magana ba a yadda nake jin muryoyin su a lokacin. Suna fadi a cikin turancin lagos dana kwarai meke na break d fucking door now. Wanda aka ba umurnin karya kofan ya fara kokarin dukan kofan da karfi yana son balla kofan kota karfin tsiya. Ina tsaye kuryan daki ina jero duk addu,an daya zo min a bakina a lokacin can naji dayan yayi wani kara yana fadin shit he don't shoot me wooo. Jin hakan yasa na kara matse yarona gam a bayana ina jero adduan ina ji ina gani ga kofan ya kusa budewa don ba karamin duka sukewa kofan ba lokacin. Wani karan na kara ji mai karfi wanda ya tayar min da hankali sosai don ina jin sautin tankar na yaya umar a lokaci. Ina saman bakina ga hawaye yana zubo min wanda bansan inda suke fitowa ba a lokacin. Shiru naji a lokaci guda a daidai lokacin da Abbana yaji matsan da nayi mai yaiwa hadi da karan dukan kofan ya tayar dashi a lokaci guda. Ya fara kuka babu kakautawa a lokaci daya ina kokatin rufe mai baki yanayi kamar zai shude a lokaci daya. Kukan nasa yai min yawa yasa na sauke shi ina kokarin bashi nono ko zaiyi shiru . Sai dai ina zuciya irin ta yara yazo mai a lokacin sai kuwa yake don ya tsorace ga baki daya. Shawara nayi na shage ban daki dashi in lalashe shi a hankali na tura kofan ban dakin na rufo na fara lalashin yaron da kyat na samu ya kama nonon sai faman ajiyan zuciya da yake saukewa lokaci guda . Ina cikin bathroom din cike da tsoro don ba komai nake jawa ba sai wullakancin da sukewa mata a yadda nake jin labari shi nafi kawowa a raina. Can gabanin asuba naji ana sake dukan kofan dakin tare da kiran sunana inda na tabbatar da muryan yaya habbib ne dana su kawu. Sai wasu muryoyi danake ji na daban suna fadin a karya kofan mana aga halin da take ciki idan basu harbe ta ba. Tunda ga shedan harbi a kofan kuna gani sai naji an kara kiran sunana da karfi haka yasa na taso a inda nake da sauri zuwa wurin kofan na fara budewa. Da kawu balarabe na fara arba haka ya kwantar min da hankali na nufesu ina kuka sosai naji muryan mama hadiye na fadin a kama yaron kada ya fadi kawu kuma yana fadin bakidai ji ciwo ba ko Fatima ? Kai kawai na iya girgiza masu ina kwantawa a jikin mama hadiyen cikin tashin hankali. Can kuma na dago da sauri ina fadin yaya fa mama ina yaya yake don ban ganshi a cikin su ba yasa nake tambayan shi. Ya na nan naji kawu balarabe ya bada amsa yana kawar da kai da sauri tare da fadin hadiye ku zauna da ita a nan zamu koma asibitin yanzu. Mama wake asibiti don Allah ku fada min ina yaya yake ko shine ke asibitin ne mama ina tambayan ta wasu hawaye na kara zubo min lokacin. Kwantar da hankalin ki ki kama yaron nan dake kuka yanzu idan gari ya kara wayewa zai dawo ai. To nace ina kaiwa zaune har lokacin ina raba ido ga mutanen dake tsaye a kaina fuskokinsu babu dadi a yanayin su suna tsaye kowa ya kura min idanu suna kallona. Dan dukawa nayi ina kallon yatlron dake shan nono don ajiyan zuciyan danaji yayi da karfi lokaci guda saboda kukan daya sha din. Wani sautin kuka naji an sake wanda yasa na mike tsaye zubur da yaron dake makale da nono a bakin shi yana sha kamar ba gobe. Sai lokacin nasan da hjy maryam a wurin don jin muryanta da nayi tana fadin don Allah ku bata hakkuri karta koma daga muna hankalin Fatiman kuma. Lokacin har nakai tsayeni na nufi hanyar dakin hjy inda nake jiyo koke koke a dakin hjy ce ke fadin na shiga uku na lalace sun kashe min jigon dakin nawa yau. Wa aka kashe na jiyo ina tambayan mama hadiye danaji ta dafani da sauri mama tace ba a kashe kowa ba fatima rudun hjy ne kawai. Yanzu me aka dauki ran mutum ne sai akashe mutum akashe banza don kawai imani ya kawo a zukatan jama,a. Allah ya jikan ka umar Allah yabi maka hakkin ka ga duk wanda ke da hannu a cikin aikin nan. Idona naji ya fara rufewa a lokaci guda daga haka ban kara sanin inda nake ba sai falkawa nayi nagani daure da ruwa karin ruwa a hannu na ana kara min. Bude idona da sukai min nauyi nayi har wani yaji suke min saboda halin masifan da muke fuskanta a ranan. Kallon dakin nayi na fahinci a asibiti nake kwance har lokacin ban san karin ruwa ake min ba saida na daga hannu na a lokacin naji karin ruwan da ake min din. Zubur nayi kokarin mikewa zaune don tuna abinda ya faru damu da zancen hjy danaji har nakai ga sumewa sai yanzu na farfado daga suman danayi din. Muryan su Amma naji suna fadin subbahanallahi hadiye ku kamata don Allah kada ta fama ciwon ta. Sauke idona nayi kan Amma dake magana ina fadin don Allah Amma ku bari in tashi ina son ganin yaya umar yanzu don Allah Amma ki taimakeni in ganshi kofa sau gudane zan natsu wallahi. Umar yana nan A ruwa saidai shima a kwance yake yana jin jikin shi don sun mashi rauni a lokacin da suka shigo gidan. Innalillahi wa ina alaihim raji,un Amma sun jinwa yaya ciwo wa yan nan mutanen wasu irin mutane ne su marasa imani. May mukai masu suka zo muna a wanan dare haka harda bindiga suna harbi kamar munyi masu wani laifi a rayuwan mu. Shigowan yaya habbib tare da wani likita yasa na mayar da kallona garesu ina fadin din Allah yaya habbib ka kaini wurin yaya ina son ganin yaya insan halin da yake ciki don Allah. Za a kaiki zahra ki kwanta ki huta shima din yana dakin hutu a yanzu haka ba a son a dame shi. Tau tau yaya don Allah a kula dashi da kyau tunda kana wurin nan kada wani abu ya same shi. Za a kula dashi insha Allahu ai ya samu sauki sosai yanzu barci kawai yakeyi daya samu. Idona na mayar na lumshe hakan bai hana hawaye biyo gefen idanuwana ba a hankali suke gangarowa daga cikin idanuwana. Barci ne ya kara daukeni a hakan sai lokacin yaya habbib suka fice daga dakin shida likitan da suka shigo a tare. Yana ganin nayi barci yasa shi fita dakin ranshi babu dadi a lokacin muryan mama hadiye ne yaji a bayan shi ya dakatar dashi daga tafiyan da yakeyi. Ya juyo yana fadin mama ana kan bincikin har yanzu ba a gane komai ba don kin san suma a bangaren su ai ba karamin shiri sukayi ba kafin su diro masu din gidan. Allah dai ya tona asirin kowaye ke da alhakin wanan abin da gagawa mama hadiye tace tana hawaye. Yanzu yaya ake ciki zancen shi umar din kai ya girgiza yana fadin har yanzu dai bai farfado ba sai dai yana numfashi kamar yadda yakeyi tun dazun. Nan dai zuwa safe idan munga halin da yake ciki zamu nemi transafer zuwa Abuja mu gwada can mu gani. Allah dai ya tada kafa ya bashi lafiya ita Fatima din sai zuwa yaushe za a sallameta ne don naga kamar dan damuwa ne kawai ke damun ta da firgici. Eh to yanzu dai likita ke fada min cewa sai nan zuwa safe itama idan anga yadda jikin nata ya kasance. To Allah ya kaimu mama tace tana juyawa zuwa dakin da nake kwance a ciki ta samu amma ta shiga yin alwala don yin sallah la,asar da yayi. Tana fitowa itama mama din ta shiga don dauro alwalan tayi sallah fitowan ta yayi daidai da zuwan mamu da hjy maryam tare da kawu. Abincin dake hannun Nura ya aje yana kallona suma din hankalin su a kaina yake mama ta fito take masu sannu da zuwa. Suka karba tare da tambayan ta yaya mai jikin tace da sauki don ta farfado dazun sai dai damuwanta shine a kaita tana mijin ta don Allah. Innalillahi suka furta Hjy maryam tace wanan daukan alhakin dame yai kama don Allah mutum a gidansa yanzu bai tsira ba wanda ke kan tafiyan ma haka ba a barshi ba. Imani da tausayi ya fice a zukatan mutane sai son kai da son duniya shine abinyi a yanzu ido rufe. Umar dai ba wani mai rigima bane balle ace wani abu ya hadashi da wani akai mai haka. Yanzu ai ba sai kayiwa mutum komai ba zaiyi kokarin rabaka da duniya kawai lokacin muke da Allah ya fada shine ya fara gabato muna ubangiji yasa mufi karfin zuciyan mu dai suka karba da amin. Dakin yai shiru sai kukan Abbana dake tashi kawai wanda su mamu suka shigo dashi don yadan sha nono idan na falka. Don tunda na fadi aka daukoni sai aka mikawa mamu shi a can ya wuni gidan mu wurin su mama din duk da kowa ranan ranshi babu dadi kowa babba da yaro daya shafe mu yana cikin tashin hankaline. Asibitin kuma yana cike da yan uwa da abokan arziki har ma da wa yanda ba,a sani ba a lokacin. Kawune ya kawar da shiru ta hanyar tambaya wai shi fa tun safe da abin nan ya faru baiga wanan yarinyar ba da akace itama tana kasan kuma ai dole tana cikin gidan ai da abin ya faru ko ? Wa ke nan Alh hjy maryam ta tambaya tana kallon kawu din yace dayan matar tashi mana ai naji ana fadan tana kasan nan ko ? Laila kuwa merry din tun ganin safe da nayi mata a gidan ban kara ganin ta ba mama hadiye ta fada. A jiyan zuciya mamu tayi tana fadin yarinyar nan sayadi kamar mai duba a jiyan fa ta kirani muna waya da yamma take fada min. Cewa ita dai gabanta sai faduwa yakeyi tun zuwan merry din kasan nan danayi mata fada kan hakan . Sai cewa tayi ita tasan ko waye merry din don halin black American da nakeji merry din tana dashi sak. Don haka ita dai bata yarda yaran nan su zauna a gidan ba dole Allah zata kawo min su su kwana biyu a waje na. Nace ta bari sai Alh ya dawo zan fada mai zuwa dare kuma ta sake kira tana fadin taji shiru shine ta bugo min don gaba daya ta kasa natsuwa da hakan . Nace ban fada ma Alh ba do bai dade da dawowa gida ba a lokacin shine fa tace gasu nan yanzu zata saka akawo su idan daga baya zanwa Alh bayanin zuwan nasu. To zuwan nasu ne yasa na manta in fada ma Alh don yaran sun shagalar dani wallahi sai gashi kuma mun tashi da wanan maganan yau na tashin hankali haka. Lalai akwai ayan tambaya a nan don wanan magana yayi kama da batar ita merry din su hjy ya kamata a tambaya ina ita merry take aji ko a gidan ta kwana itama jiyan da abin ya faru. Gidan ta kwana yaya don na ganta da mukazo da idona sai hjy maryam tace tabbas tana gidan don itace ma ta ke kururuwan da Alh balarabe yace a daina kuka haka. To ina wanan yarinyar ta shiga yanzu ko dai tana gidan ne don taga kowa hankalin shi yana ga wa yan nan kamar an fita batunta an ware ta daban. Bani tunanen haka Alh inji hjy maryam yanzu dai habbib ya kamata ka sanarwa komai don a bincika inda take din ko ya sani shi. Ina zai sani tunda shine tsaye a kan komai tunda aka wuto da umar asibitin nan yake nan ban sa ya koma gida ba har yanzu ma mama hadiye ta fada. Kawu yace to amma dai kun san wanan maganan ba abin kyalewa bane don dole ne mu san halin da yar mutane take ciki kasa ta salwanta kuma. Ko tana daki don bakin ciki ta kulle kanta don shi kafiri bai san yarda da kaddara ba idan tazo mashi. Waya kawu ya dauko daga aljihun shi yana neman layin habbib din ya fara kira sai kiran ya shiga. A daidai lokacin ne kukan da Abbana keyi ya falkar dani daga barcin na bude idona sai akan su kawu din da matan shi dake tsaye a kaina lokacin. Kallon yaron dake miko min hannu zuwa wurina don ya karbi abincin shi sam yaki sakewa a gidan mamu dukda mariya da fauziya dake gidan tare da yan uwan shi a lokacin. Kawu yace min sannu Fatima ya karfin jikin kuma da sauki kawu na bashi amsa sai hawaye. A daidai lokacin ya dauki wayan suka fara magana da yaya habbib a waya kan zancen merry din da ba,a gani ba a lokacin. Ya juyo yana gab da fita dakin yana fadin ku mikashi mana ta bashi nono tunda ta tashi tun safe yake wanan kukan saboda firgitan da yayi. Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin ita kuma mamu ta miko min Abba din dake kuka ta hanyat shi fidar dashi saman gadon da nake kwamce din. Ita ta gyara muna kwanciya da yaron duk su mama d hjy suna kallon mu gwani ban tausayi damu lokacin. Kawu sunyi magana da yaya habbib yace shima ta fado mai a tai da bai ganta ba asibitin tun dazu. Dkn Allah ayi kokarin nemo inda take kada yar mutane ta salwanta kuma muna cikin garin nan. To daddy ya amsa yana dauko wayan shi kake a cikin aljihun yana neman wani ashe hjy yake kira don ya tambayeta ina merry din take ne . Hjy jiki na rawa ta dauki wayan tana zaton za ace wani abu game da yaya umar don haka tayi saurin daga wayan don gani layin habbib din ke kiranta dan jin halin da umar din ya ke ciki a lokacin. Saidai sabanin jin bayanin komai daga gareshi da tayi yake tambayan ta ko merry na gidan do bata asibiti tunda suka zo nan. Ina zan sani tunda ba nan take shigowa ba balle mu sani don Allah idan nafisa na kusa ta duba muna ita a bangaren ta ko tana gidan. Nafisa ta kalla kafin tace ni ba wanan ba yanzu wani hali dan uwan naka yake cikine wai kun barmu nan a duhu haka babu labari. Yace mama sai dai addua ga yaya gaskiya don yanzu shi yafi bukata a gare mu tunda har harbi biyu sukai mai da kafa da kirji kinga dole ya shiga wani hali a yanzu. Shiru tayi ba tare da ta kara furta komai ba sai can ta kalli Nafisa tana fadin wai ki duba mashi wanan yar waje din ko tana gidan nan. Nafisa tana kunkumi ta mike zuwa part din don dubawa sai dai tana zuwa ta tura kofan ta sameshi a bude babu kowa a ciki ta dan duba har bathroom nan ma bata a ciki ta fito ta bude wardrove din dakin dakin sai dan daidaikun kayan merry din ta gani a ciki. Alaman dai babu mutum a cikin dakin na dan wani lokaci ke nan ta fito ta fadawa hjy abinda ta gani a dakin. Hjy dasu mama sukace ta duba waje ta tambayi masu gadi ko sunga fitan ta . Masu gadin sun tabbatar mata ba, a dade da kai maigidan asibiti ba ta fito wata bakar motace tazo ta dauke ta da yar jakkar kayan ta. Komawa tayi ta fada masu habbib hjy ta kira take fada mai komai kawu dake gefen shi yace shike ban zancen yarinyar nan ya tabbata kan matar nan da alama fansan yarta tazo dauka gareshi dama. 17/11/2021, 07:26 - 🀐🀐🀐: Bai bata lokaci ba wurin kiran dansandan dake kula da case din yana bashi bayani kan zargin merry da kuma batan da tayi. Dansandan yace gasu tafi don du kara daukan bayani kowa dake gidan lokacin da abin ya faru. Cikin yan mintina suka shigo asibitin a nan suka samu yaya habbib don jin karin bayanin kiran da yai masu din. Kara maimaita masu bayanin dayayi mai a waya yayi suna rubutawa a takarda kafin su ce suna son duk wanda ke gidan a wanan daren zasu gana dasu daya bayan daya. Wake cikin asibitin nan a cikin su eh akwai matar maigidan wace ke kwance a yanzu da take jin jiki sai kuma dayan maigadin da aka harba dayan kuma ya mutu tun a lokacin da abin ya faru dashi. Ok ko zamu iya ganin wani daga cikin su a yanzu dansanda yace yana tambayan likitan sai a lokacin likitan ya dan gyara tsayuwa yana fadin. Da zaku barsu har zuwa gobe don lokacin hankalin su yadan fara kwantawa suna cikin dan hayacin su zaifi sai ku dauki duk bayanin da kuke so a garesu. Ba matsala dansandan yace ko akwai wasu da zamu iya gani bayan wa yan nan din yaya umar yace eh akwai wani mai kula da duk wani al,amarin gidan tare da matar shi da suke a gidan lokacin da abin ya faru. Ok yana ina yanzu ya habbib yace zamu iya samun shi a gidan yanzu don ko yaushe shi yana gidan bai faye fita ba. Zamu iya zuwa yanzu mu ganshi idan ba damuwa ya fada yana kallon habbib din yace No problem zamu iya zuwa mu ganshi ai da haka suka bar asibitin a tare. A dakin da nake kwance kawu ya shigo bayan sun fito sallah magariba ya samu su mamu a zaune inda suka idar da sallah yake fadin dare ya soma zaku fito ne mu koma gida. Yaron fa a nan zamu barshi kodashi zamu koma gidan hjy ta tambaya tana kallon mamu don son jin amsan da zata bayar. Kafin mamu tai magana kawu yace a barshi nan mana tunda an samu tana dan cikin hayacin ta yanzu. Nima shina gani don ko munje dashi ba zai ci komai ba kamar yadda yayi dazun . Kawu ya dan matso kusa dani yana fadin fatima mu zamu tafi yanzu dare yayi mun bar yara a gida . Ina son ki kwantar da hankalin ki insha Allahu mijin ki zai samu lafiya da yardan Allah kuma yan sanda suna nan suna binciken wanda keda alhakin aikata haka . Da kyat na bude baki ina fadin kawu don Allah kayi magana a cire min ruwan nan inje inga yaya umar din dakon da yake. Zakije fatima kiyi hakkuri kema yanzu ba dadi kike ji ba har ruwan ya kare sai a rakaki ki ganshi ki mashi addua don yanzu adduan mu yake bukata fiye da komai. Ina jin hakan na runtse idanuwana ina jin zuciyana kamar zai fashe a lokacin nasan yaya umar yana cikin wani yanayi mai muni ke nan a yadda kawu ke nufi. Ban kara bude ido ba har barci ya daukeni a hakan yadda nake ina tunanen halin da mijina yake ciki. Jin an dauki yaron dake manne a jikina yasa na falka firgigit ina bude idanu a tsorace sai nake ganin kamar mutanen ne suka kara dawo min a lokacin. Ganin mama hadiye tsaye a kaina yasa na maida idanuwana rufe muryan yaya Ahmed naji yana fadin sannu fatima ya jikin naki. Sake bude idanuwa nayi a hankali ina fadin da sauki salma ne ta matso bakin gadon tana fadin ya jikin fatima kai na gyada mata kawai ina datse bakina don yadda nake ji a lokacin . Ina jin Ahmed na fadin har yanzu dai ba,a samu bayanin wa yanda sukai wanan abin ba ko ? An sani ba kowa bane merry ce na bashi amsa don tun lokacin data zo garin nan zuciyana ya bani hakan kuma shi kanshi yaya na fada mai abinda nakeji game da ita akan yarana. Kowa dake dakin ya dauki salati sai mama ke fadin ki bar fadin haka fatima tunda zato kikeyi don Allah . Ba ita kadai yanzu ake zargi ba ai har hjy sabuwa da yarta suma ana zargin suna da hannu a cikin wanan abin ai. Tunda ta fadi sai yaga abinda zatayi mai tunda yai masu haka a gaban kowa kinga ko dole a zarge ta itama. Allah dai ya tona asirin duk wanda yai wanan abin Ahmed yace aka amsa da amin gaba daya. Juyowa nayi a hankali na kalli salma ina fadin salma kinga yaya din wani hali yake ciki nace su bari in tafi in ganshi anki bari in tashi. Fatima kiyi hakkuri kema kina cikin taki laluran ga ciki a jikin ki dake maki wasa sanadin wanan abin ga kuma halin da kike ciki. Ba zaki fada min halin da yayan ki ke ciki ba kema salma ku fada min mana don Allah idan ya mutu ne in sani. Wallahi bai mutu ba fatima yana dai cikin wani haline mara dadi don har yanzu baisan a inda yake ba. Kuma likitoci basu bari a shiga inda yake sai yaya habbib da daddy da akace ya shiga dazun ya ganshi. Zubur na mike zaune ina kokarun cire karin ruwan da ake min wanda yakici yaki cinyewa har yanzu don rage karfin ruwan da sukayi bai sauka sosai da sauri. Sai subbahanallahi may kikeyi haka Fatima ina, zaki don Allah, don Allah ki natsu ke kanki baki da lafiya fa. Shine abinda wa yanda ke cikin dakin suke fada min cikin tashin hankali suna kokarin kamani su kwantar dani. Ku barni in inje in ganshi ko akwai abinda zan iya mashi a yanzu don Allah na fada ina karasawa da kuka . Tausayi na basu naji mama na fadin ni banga dalilin da zaisa a hanata ganin shi ba dama don ganin shi shine kwanciyar hankalin ta a yanzu. Jin abinda mama tace na juya gare ta ina fadin don Allah mama ku barni in ganshi don Allah saka hijab mu tafi inda yake saidai likitocin basa yarda kowa ya shiga dakin da yake ciki gaskiya. Muma da muka tafi ta taga muka tsaya mukai mai adduan Allah ya bashi lafiya tana gaba ina binta a baya muka karasa har emergycy dakin babu kowa sai shi dake kwance ga na,ura saukan numfashi makale a hancin shi sai ruwa da ake kara mai. Innalillahi na fara ambata sai dai duk da halin rudun da nake a ciki bai hana inyi nazarin yadda abin yake ba. Juyawa nayi ina fadin mama ko zan iya ganin likitan dake kula dashi don Allah ? Eh to habbib ne tare da wani likita abokin shi suke tsaye a kanshi dama ya Ahmed ya fada yana karasowa kusa. Amma idan kina son ganin shi ai za a iya masu magana a yanzu sai a hadaki dasu ko , ? Da sauri nace don Allah yaya idan ba damuwa zanso in gansu akwai maganar da nake son yi da likitan a yanzu. Ya juya tare da fita wurin komawa nayi ina kara nazarin halin da yaya yake a ciki lokacin. Saiga yaya ya dawo yana fadin likitan yace naje tare dashi da salma muka shiga office din nan ya nuna muna wurin zama yana fadin lafiya dai hjy kike son ganina hope ba wani matsala bane kuma yanzu. Dago kai nayi ina fadin doctor idan babu damuwa zanso muyi magana insan abinda kukai ma mara lafiya amfani dashi da irin ci gaban da kuke ganin ana samu gareshi yanzu. Wani kallo likitan yayi min yana kokarin cire glass din dake saye a idon shi. Amma malama ke din wacece da zaki zo min da wanan maganan ya fada cikin daure fuskan shi aka kwankwasa kofa za a shigo office din. Hakan ya hanani furta mai komai har wanda ya shigo din danaji yana mai sannu da zuwa amsawan maishi yasa na juyo daga inda nake zaune don ji muryan wanda na sani. Shima anyi sa,a ya juyo yana kallon mu a cikin mamaki lokaci guda muke ambatan sunan juna. The guy yace Fatima kece ko gizau idanuwa na ke min don na bincika an fada min kin koma second degree din ki a can London kuma. Kai na gyada mai ina fadin hakane yanzu ma mun zo kasan nan don duba sarakuwata da bata da lafiya shine wani tsautsayi ya samemu a nan din. Likitan ne ya karba da fadin kan isue din dana kiraka ke nan yanzu don abin ya shige min a duhu ni kaina. Innalillahi ya furta tare da fadin how comes hakan ya faru is a long story sai dai da alama kasan ta a yadda naga kun nunawa juna. Kallo na The guy yayi yana fadin wanan da kake gani aida nasan tana nan da ban baro Abuja nazo nan ba don duk abinda zan iya itama iam sure zata iya fiye dashi ma a yanzu. Mu daina wanan magana muyi zancen mara lafiyan nan please don i am sure muna gab da rashi a yanzu saboda awowin daya dauka a hakan. Nan na fara gin ma likitan tambayoyi yana min bayani sai na tuno da wani hikima da aka koya muna indan an harbi mutum. Nan nayi masu bayani take likitan ya mike yana fadin shaf na manta da wanan idea din da kika kawo kiran doctor habbib yayi yana masa bayani sai yace gashi tafe. A tare dani muka shiga da yaya dakin theater din aka yi mai duk wani abinda ya dace a lokacin kusan duk wani dan uwa na jiki yana tsaye a gurin an zubawa sarautan Allah ido kawai. Ni kaina hankalina ba a kwance yake ba alwala nayi na tayar da sallah nakai kukana ga ubanginjin talikai mai jin roko da biyan bukatun bayin shi. Ina sallamewa na zauna addua a gurin can kuma tunane ya dauke min hankali na yanzu idan yaya ya tafi ya barmu ni yaya rayuna dana yarana zasu kasance daga baya. Ban kaiga karasa tunanen ba naji ana kiran sallah asuba don haka na mike don yin nafila. Saida aka tada kabbara a masalacin dake cikin asibitin na mike don gabatar da sallah na idar kenan ina lazimi naga likitoci da sauri sun shiga dakin da yaya din yake kwance. Da sauri na mike tsaye zuwa dakin saidai na samu sun rufe kofan hakan yasa na tsaya sanin shiga lokacin aikin su dokane. Tunda ba aiki nake a gurin ba ina tsaye ina shawara naga wani nurse zai shiga dakin da sauri yana rike da kayan aiki a hannun shi. Ban tsaya ba na jefa kaina a dakin nima a rikice suke su duka suna gani na dayan yace don me na shigo masu daki lokacin aikin su. Ban damu da tambayan da yake min ba hankalina yana gun yaya da sauri na karasa ina fadin ya miko min spoon ko seazors kada yai mai alluran nan yanzu. Nawan shi nagani wurin miko min abinda na bukata din da sauri na dauko na bude bakin yaya na saka mai tare da toshe hancin shi sai naji ya ja wani irin ajiyan zuciya lokaci guda a hankali numfashin shi ya fara dawowa . Dakin yayi tsit kowa na kallin ikon Allah duk idanuwan likitocin yana kanshi har ni a lokacin sai na,uran da aka makala mai ke aiki cikin dakin nima duban na,uran nakeyi a hankali ya koma daidai na zare almakashin dake bakin shi. Addua na fara jero mai na samun sauki a wurin Allah don yana cikin wani yanayi wanda ba,a son mutum ya kai a lokacin. Juyawa nayi ina fadin ko za,a samo wani allura na fada don shine daidai aimai a lokacin ba wanda suke niyar mai ba a yadda yaken. Alluran nan yana da wuyan samu gaskiya a yanzu wani ya fada min yake fadin basu faye sayoshi ba a kasan nan don ba kowane zai iya sayen shi ba. Dayan likitan ne ke fadin yana ganin yana dashi a gurin shi daya sayo zaiwa wani mutum a lokacin kuma sai mutumin ya rasu. Likitan mai duba yaya yace yayi sauri ya dauko muna nan ya juya ya fita dakin yayi tsit muna ksllin yadda numfashin shi ke tafiya a hankali har wanan likitan ya dawo da maganun a cikin wani kula don ba, a barin shi inda babu sanyi. Karba doctor yayi suka fara shawaran mill nawa zasu mai ina jin hakan nace give him five is ok for him now. Kallona sukayi dukkan su basuyi magana ba don the guy ya riga ya fada masu su yarda dani da duk shawaran da zan basu nasan aikina sosai. Anyi alluran da kamar minti goma sha sai numshin ya koma normal sosai har zaka iya jin dan hantsari daga gare shi. Sai lokacin na sauke a jiyan zuciya na juya ina fadin thanks tare da nufar hanyan fita daga dakin don kafafuwana ba zasu iya daukana ba a lokacin. Na fito daga dakin idanuwan kowa a kaina don na samu har hjyn su tazo an kamota tana wurin da duk yan uwanta da na kawu sai wasu fuskoki da ban sani ba. Rasa wanda zan amsawa tambayan da suke min nayi don kowa na son jin halin da yake ciki saboda hankalin su gaba daya ya tashi a lokacin. Da sauki na fada na nufi empty kuran dana hango na zauna don ba zan iya tsayuwa ba a lokacin gashi nima ba lafiya ne a jikina ba. Abbana mama hadiye ta kawo min don in bashi nono karban yaron nayi duk ya langabe nasan yayi kukane har ya gaji don bai sansu ba. Habbib suka shigo tare da Aliyu don tunda sukai sallah suka tafi gida daga can sai gashi an kirasu kan anga likitoci na shiga dakin da sauri har nima ina cikin dakin ba wanda ya san meke faruwu a ciki. Bayan sun gaisa da mutane suke tambayan halin da dan uwan nasu ke ciki ake fada masu nice dai na shiga don su suna waje tsaye lokacin da abin ya faru. Yaya habbinb ya tako zuwa inda nake zaune mun gaisa yayi min yaya jikin na amsa mai da sauki ya gyara tsayuwa tare da tambayan hakin da ake ciki ina mai bayani. A lokacin sauran yan uwa suka matso don jin halin da ake ciki na fara mai bayani sai ga likitan dake dubashi ya fito daga dakin nan kuma suka koma gareshi akai mai caaaa da tambaya. Wanan ba wani abin mamaki bane a kasan mu yadda masu jinya kan tasa likita gaba da tambayan halin da mara lafiyansu ke ciki. Nunani yayi yana fadin yanzu itace likitan nasa ai don ta karantu a wanan fannin sosai fiye da tsamanin ku. Zuwan ta nan ya tai maka muna sosai don a halin yanzu numfashi ya koma daidai yadda muke so. Nan dai likitan ya kara kwantar masu da hankali sosai sai a lokacin hankalin kowa ya kwanta don ana ganin sauki a gareshi. 17/11/2021, 07:26 - 🀐🀐🀐: Ganin sauki sosai ga yaya hankalina ya dan fara kwantawa sai dai a kasan zuciyana tunanen wanda yai mashi wanan aika aika yake min yawo a rai. Don zuciyana ta kasa tsayawa wuri daya a tsakanin abu uku da nake zargi nafarko dai itace merry da nake zargin tazo daukan fansan yarta a kanshi . Sai na biyu itace samira da mahaifiyar ta da ake zargi suna iya aikata hakan don abinda ya faru a tsakanin su yan kwanakin da suka shude. Wanda yan uwa da abokan arziki sunfi zargin hakan garesu don tun da yaya habib yaji abindana fada bai yarda ba shi sai cewa da yayi merry tsorone da fargaba kila yasata ta bar kasan a gigice. Shi yanzu bukatan shi shine asan inda merry da ake nema ta shiga tun daren jiya din ba,a ganta ba kada dai kuma wani abu yazo ya faru da ita nan gaba a kuka dasu daga baya kan hakam. Ni kawai jin su nakeyi don sanin wacece merry a yanzu da nayi don sanin halinta akan komai da yadda wayewan ta yakai a America din. Dole na gyagije ga nawa ciwon muna fuskantan nasa don ni nawa tsorone da fargaba ya saukan min da ciwo na dan lokaci guda dama. Saidai duk da na gyagijen bai hana kaga damuwa da tashin hankali a tare dani idan ka kalleni sau daya saina baka tausayi a yadda na koma. Hjyn su yaya ita kanta ta fita daga hayacin ta sosai don nan gurin shi itama ta wuni a ranan duk da ga yan uwanta sun mata kara don sun cika asibitin sosai. Amma hakan bai hana hjyn zama asibitin ba itama da ka ganta bata cikin hayacin ta ko kadan a lokacin kowa hankalin shi yana a tashi da faruwan al,amarin. Yan sanda sai aikin su na bincike kan case din sukeyi basu gane komai ba sai washe garine da dayan mai aikin wanda bai mutu ba ya farfado suka samu dan haske gareshi kan al,amarin. Don yan sanda najin ya farfado suka garzayo dakin da yake suna mashi tambayoyi yadda abin ya faru a gidan. Yake fada masu da misalin karfe biyun da wani abu na dare suna kwance sukaji harbi bindiga. A inda ya gane ba hausawa bane don turancin yaji suna yi akan harbin da daya su yayi ogan su na mashi fada kan hakan yana fadin madam tace damu bata son a harbi kowa a gidan nan kai gashi yanzu ka harbi maigadi kilama ya mutu. Yaran kawai tace mu kwashe koda ba duka bane ko daya muka samu mu dauko mata kazo zaka batawa mutane shirin su kuma. Yace oga yana da bindiga fa a hannun shi shi yasa na harbe shi kada ya harbe mu mutumin yace ina jin haka sai na shiga cikin tarkacen dake dakin na kara lafewa sosai. Sun kai su nawa a naka ganin da suka shigo gidan dansanda ya tambaye shi . Yace zasu kai su takwas ko fiya da hakan do su kasu kashi kashi a gidan don har wajen gida wasu sun tsaya daga cikin su. Nima dai rabon wahala yasa na fito wajen da niyar in gudu a lokacin danaga hankalinsu ya dauke a cikin gidan injin karan harbe harbe na fito da niyar gudu. Sai dai ban san akwai biyu ko uku a waje ba lokacin ne suka harbeni sai dansanda ya dakatar dashi da fadin. Kafin ka suma bakaji wani karin kalamin da zamu rike a matsayin huja ba a bakin su sai mutumin ya girgiza kai alaman baiji komai ba. Dansanda yayi mai godiya bayan yan rubuce rubucen da yayi a takarda a lokacin ne saurayin ke fadin yallabai na tuna da wani kalma danaji sun fada kwarai a lokacin. Da suke fadin we should rush mu bar garin nan yau komai dare kada a kama mu sai dayan yake fadin Samuel fa da aka harba yace dashi zamu tafi. Don barshin a nan risk ne gare mu don za,a iya gane hakan ta hanyar shi don haka zamu tafi dashi ke nan. Dan nazari dansanda ya tsaya yayi kafin ya mike yanawa saurayin godiya tare da fatan samun sauki ya fito ya leka a dakin da yaya yake kwance. Bayan tafiyan dansandane kowa ke fadin albarkacin bakin shi kan abinda saurayin dake muna wanki ya fada wanda daga kauye ya shigo gari neman kudi dama nasir ya dauke shi aiki a gidan. Ban furta komai ba don magana yana dan fara dauko kamahin gaskiya sai nake jin ko a can gidan mu da yaran suke zaune kamar basu tsira ba a hannun makiyan. Don zasu iya cin masu can su dauke su tunda sunyi niyar yin hakan a kan yaran nawa haka ya jawo hankalina kasuwa gida biyu a gurin tunane yanzu. Zuwan mamu da kawu ne ya dan kwantar min da hankalun don sun samu labarin abinda mai wankin mu ya fada tun suna gida. Kawu ne yakw fadin in kwantar da hankalina tunda har Allah yasa mi sanin gane wani abu mara kyau yana shirin faruwa da yaran naji a jikina kuma har hakan ya faru . Sai in godewa Allah in dage dayin addua don addua itace takobin mumuni Allah ya kara tsarewa insha Allahu Allah zaibawa yaya lafiya ya tashi da yardan ubanginji. Wanan kamar kina nunawa ubangiji rashin godiyane yau da ace wanan abin ya zama sanadin rasa umar fa ? Ashe ba zaki zamo mai tawakkali ga jarabawan ubangijin ki ba fatima ? Jin kalamin kawu yasa na dago kai ina kallin shi tare da kokarin share hawayen dake zubo min a lokacin. Bayan kawu ya mike don shiga yaga dan nasa ya rage wurin dani da mamu sai Amma dake lazumi tana sauraren mu . A hankali nace mamu yaran basu damun ki ko a can don nasan su da fitina idan basu ganin dayan mu tare dasu. Saida mamu ta sauke ajiyan zuciya take fadin basu fitinan komai tunda ga sadiya nan da maria suna gani yau daine ita yar fitinan ta matsa da kiran mummy mummy ina jin maria tana lalashin ta itama kanta maria ai abin ya bugeta sosai don bata a cikin dadin rai duk yinin yau din. Sai lokacin Amma data shafa addua take fadin yo ina zataji dadi wanda kake tare dashi yana a cikin wani hali haka mara kyau. Mamu n fada maku ni zuciyana tafi karkata gun merry din nan don yarta da yaya ya karbe a hannun ta yanzu. Kada kice haka sayadi don zato zunubine koda ya zama gaskiya don haka ki daina wanan zargin. Sai ya kasance ita bata ma san da wanan zancen ba sai wani ya taka sawunta yai wanan aikin . Abin ne da kama ai dole yar nan tayi zargin hakan don biri yai kama da mutum gashi an nemeta an rasa a garin nan tun jiya. Wata kila tsoron taji kamar yadda habbib ya fada ai ana kan bincike dai insha Allahu gaskiya zata baiyana komai daren dadewa. Fatan mu dai Allah ya tayar da kafadan shi ya bashi lafiya yasa hakan ya zamo mashi kaffara a yanzu. To Amin Amma ta fada tana kawar da kai tare da fadin ni dama auren sadauki da kafiran nan bai taba kwanta min a rai ba sai ace ranon yar nan daine kawai ya kaishi ga auren ta . Amma wanan ai ba macen nunawa tsara bane a fage don banga wani abinda yaja shi gareta ba. Aurene gwaggo Allah ya kaddaro akwai aure a tsakanin su da rabon yar nan da kika fada yanzu. Idan ba wani abuba ai sai ya bata yar ta karata can da ita ta bar dan nan ya zauna lafiya Ammake fadan hakan. Amma wai kin san sai da wanan matar ta saka aka kwace wa yaya komai a can da farko kamar zasu rabo dashi sai gasu kuma sun kara dinkewa daga bayan nan. Ke yar nan ki bar wanan zancen aka kwace mashi dukiya kuma yake zaune tare da ita ? Kwarai Amma don kawai kara aurena da yayi daga bayan nan taimakon yaya guda shine tun farko sunyi alkawari a rubuce cewa ga addinin shi ya yarde mashi ya kara aure . Kuma ta amince da hakan saidai lokacin da tasan da zancen aurena dashi ta kaishi kara kotu dole kotu ga al,adansu nacan ta raba dukiyan sa biyu ta bata rabi. Bata san da yana dabaran turo arzikin shi gida ba daga bayan nan kuma da ta sani ta biyo shi har kasan nan da jidali wai a cewan ta tare da ita suka samu arziki don me zai munafunce ta yayi hakan ba tare da sanin ta ba. Rikincin gangan ke nan wanan ta zama Sarka mai rikucin gangan arziki nasa sun hada karfi ne tare da ita ? Gwaggo kin san su ga al,adan su ai haka abin yake na miji baida halin yin wani abin ba tare da sanin matar shi ba irin namu na nan. Yau ina mahaukaciyar uwar shi tazo taji wace tafita famkama da abin danta ita da da anyi zance zatace ni uwar maza ne masu arziki kuma ? Yoni wanan jahilci ko hauka za a kirawa jimmai yau dai idan umar ya fadi ya mutu ke A ruwa kin fita kaso a cikin abinda ya bari shine kawai bakin ciki da hassadan jummai dama dake. Amma ni ban taba tunanen irin wanan ba a rayuwana idan za a barmin shi yafi a bar min tarin arzikin da hjy ke hange. Affa ke kika san wanan Aruwa rikicin jummai ai ba sai da dalili ba abin ya zake mata a jiki don ita bata bar kowa ba. Duk da wanan abinda ya sameta baisa jummai yin nadama ba don dazun nan kuna ciki wurin yaron nan take fadin wai dama ana son ya tafi a mamaye abinda ya tara. Har abin yaso zama masu fada da hadiye shine dalilin dana tura hadiye gida dazun . Don ba zamu taru anan ana sayar da hali ba mutane suna tafiya damu a baki. Kai halin hjy sai ita duk da bawan Allah nan yana cikin wanan halin bautan ubagiji zukatan mutane baya a kwance take wanan furcin. Mamu ne ke fadin wanan magana tana kada kai taci gaba da fadin wa take zargin ya aikata hakan yanzu gareshi ? Na nisa tare da fadin ni zancen hjy bai taba damuna a yanzu matar da taje neman wace zata kifar da mutuncina a gidan yaya don kawai kiyayya irin nata. Mai kuma zatayi ko ta fada a kaina yanzu inji zafin shi a kwance take amma zuciyar ta na cike da sheri. Kawai lamarin hjy sai addua a gareta idan tana da rabon shiryuwa Allah ya gyara halin ta. Na dauka wanan abin da ta sameta a yanzu zai sa ta yin nadama sai gashi har yanzu zuciyar hjy bai saduda ba ga yawan aikata sheri gana tare da ita . Kafin wanan abin ya faru na fito da safe na samu mama asabe waje tana kuka nake tambayan ta. Da farko bata so fada min ba saidana matsa da nuna mata damuwa na take fada min ita ta gaji da halin hjy. Don duk dawainiyar da take da ita bata ganin haka wai jiya don tace a kiran in duba ta take fadin ta fahinci akwai makircin da muke kokarin kulla mata nida ita. Don taga yadda take shige mun idan na shigo tana wani yabona to ta sani duk kilibibin da nake kallona kawai take don ta gane nufinmu a kanta. So nake kawai na karasa nakasata sai nace mata haba hjy wanan wani irin magana ne yarinyar nan fa itace fa silar samuwan saukin ki a yanzu. Sai cewa tayi dani koda banzo ba idan Allah ya nufa zata warke ne ta tsani ki ta tsani duk wani ahalin ki jin hakan da nayi nace . Wa,iyazu billahi hjy mai yai zafi hakan uwar jikokin kine fa kike aibantawa hakan. Nice shedaniya kike nufi da kike kore min shedan komai to bari kiji indai a kan wanan yarinyar da tayi sanadiyar barina dakin aurena kike kokarin karata a gaba ki sani bani bake asabe. Dama nasan ba don Allah kike min abinda kike min ba don wani manufa takine kawai don da ba zaki goyi bayan yarinyar nan ba haka alhalin kin san irin kuntata min da sukeyi da ita da uwarta. Mama asabe ta kare da fadin yanzu FFatima ya dace duk irin kokarin da nake da hjy tace min wai ba don Allah nake kulata ba . Don haka ni na gaji wallahi tafiyata zanyi ba zan iya wanan abin ba gaskiya jiya sai abinda hjy ta manta bata fada min ba. Nace mama don Allah kiyi hakkuri kada kice zaki tafi don yaranta yadda suka daukeki bazasu ji dadin hakan ba idan kin tafi. Hjy halinta sai ita wallahi ya kamata ace iyanzu kin saba da wanan halin nata ita da kanta zata dawo ta nemeki ai . Tunda ba zata iya yiwa kanta wani laluran ba dole sai an taimaka mata bamu rufe baki ba mukaji muryan ta tana kiran mama asaben. Amma tace ke ki duba min wanan abin mamakin don Allah wai mutum na kokari da kai kake masa wanan bala,in haka don wani dalilin naka can. Ganin su kawu sun mike daga inda muke iya hangen su a zaune suna magana sunyi cikin dakin da yaya yake kwance da sauri. Saurin mikewa mukayi lokaci guda don bamu san abunda yake faruwa ba a dakin suka mike zuwa dakin nasa. Kusan nice a gaba wurin shiga dakin a tsartsaye na samu su kawu suna gaida yaya din da yake kwance yana bin kowa da idanuwan shi. Sai dai duk gaisuwan da suke mashi bai amsa ba sai binsu yake da idanuwan shi kamar wanda bai karkare farfadowa ba a lokacin. Zuwan mu kusa dashi yayi daidai da karasowan su hjy gurin hjy tana ririke a hannun yan uwanta. Ganin su yasa muka dan tsaya a bayansu kada sai gaidashi da jiki sukeyi mai ina gefe tare da mamu da Amma sai hamdala nake ga ubangijin talikai daya rufa muna asiri yaya ya samu lafiya. Ganin ba za,a sarara ba a lokacin yasa na karasa bakin gadon na fara fadin yaya sannu ya jikin ? Sai lokacin ya dan juya kanshi yana kura min ido kafin yayi kokarin budan bakin shi yana son yin magana. Sai dai ya kasa sai kuma ya lumshe idanuwan shi a hankali ganin hakan da yayi ne wani kuka ya kubce min lokaci guda. Bani kadai ba kusan matan dake dakin hawaye suke a lokacin Amma na fadin saudaki sannu ya jikin kuma tana share hawaye . Jin muryan Amma din yasa ya kara bude idanun shi a hankali yana kallon mu ya kara dago ido ya kalleni a karo na biyu. Kuka nake yayin da iyayyen mu maza ke fada dani akan in daina kukan sai ya dan saki dan murmushi kadan ya lumshe idanuwan shi. Muryan likitan shine ya shigo yana fadin haba a rage yawa a dakin don ba,a son a dameshi da yawa hakan zai iya kara jefa shi cikin wani damuwa. Jin yadda nake kuka yasa likitan dago kai yana fadin why doctor fatima kin san aikin ki kece kiba da muhinmiyar rawa wurin taimaka muna kan maigidan naki har muka kai ga nasara. Dakin yayi tsit yayin da wasu matan suke ragewa kamar yadda likitan da kawu balarabe suka umurta. 17/11/2021, 07:26 - 🀐🀐🀐: Dan juyo kanshi yayi kadan tare da kokarin mika hannayen shi gare ni lokaci guda sai kuma ya kasa yin hakan don jikin shi da yayi mai tsami a lokacin. Ganin hakan kawu sani ya fara fadin Alhamdullahi da alama aiki yayi kyau ke nan tunda har ya iya sheda matar shi a yanzu. Jin hakan hjy ta fara kiran sunan shi da babawo ya jikin naka ya kake ji yanzu ? Kawu yana ganin hakan ya gane mai hjy take nufi yasa ya bar dakin ta hanyar yiwa matan shi dake wurin nuni da kofa ba bata lokaci suka bi bayan shi suna Allah ya sauwaka tare da adduan kara samun lafiya gareshi. Dakin ya saura daga ni sai hjy da yan uwanta a tsaye mun zuba mai ido duk da ba magana yake iya yiba a lokacin sai numfashin da yake mayarwa a hankali. Ganin yadda suke basu ko nuna alaman cewa sun san dani a wurin ba yasa na yanke shawaran fita daga dakin lokaci guda duk da ina son kara duba yadda jikin nasa yake a lokacin. Wurin Amma na koma na zauna basu fito ba saida nurse tazo tayi masu magana suka bar dakin duk muna zaune a inda muke tare da Amma sai kara kwantar min hankali da takeyi. Shigan likitan ne ya sa a kirani nazo da sauri yake fadin mara lafiya ne yace a kira mashini ina shiga hjy da suke daga gefen mu suka taso sai dai likitan ya rufe kofan babu halin shiga gare su. Banji dadin yadda na samu yaya ba a wanan shigar don numfashin shi ba kamar dazun ba da muka barshi. Isa nayi bakin gadon da yake kwance hankalina a tashe na kai hannuna saman goshin shi lokacin ne ya bude idanuwan shi a hankali yana kallona. Ido ya dan kura min kamar bai ganeni ba sai kuma naga ya sakar min murmushi a cikkn karfin hali da daurewa na kara matsawa kusa dashi. Hannuna dake saman goshin shi yake kokarin lalaba a hankali gane hakan da nayi yasa na kai hannuna da sauri na kama nasa. Ji nayi ya rike hannun nawa sosai ya furta zahra na amsa da hawayen dake zuba a fuskana. Stop crying yace min a daidai lokacin da likitan ya budewa yaya habbib da Aliyu kofan suka shigo. Zahra zan tafi in barki da dawainiyar yaran mu ke kadai kiyi hakkuri da hakan zahra haka Allah ya nufa da ra, , , sai ya dan fara shakuwa. Gaba daya rudewa sukayi Aliyu kan kasa zama a dakin yayi ya fito yana kuka wanda hakan ne ya jawo hankalin sauran mutanen dake waje. Saida shakuwan ya lafa mai yake fadin habbib ko kasan merry ce ta saka ai min hakan dan yarta . Wani kuka ne na sake sakewa mai sauti ga hannayen shi rike cikin nawa ya rikesu gam habbib yake fadin mun san da hakan bros don Zahra ta fara fadi. Habbib i can't survive don haka komai ritsi kada ku bata queen ka hada ta da yan uwanta ku rike min su amana bazan rayuwaba habbib. Bros ka daina fadan insha Allahu zaka warke habbib ke fadi innallilahi nake iya fada a lokacin sai kalman shahada da nakeyi a fili a cikin gigita. Dago idanu yayi ya kalleni idon shi gaba daya sun canza kala irun yanan da ake jefawa bawa yayin barin shi duniya sun sauka a idanun shi a lokacin . Hakan dana ganine ya kara rikitani sosai yaya habbib yake fadin in fita dakin kada in kara daga masu hankali. Kaina girgiza naki fita dakin don koma nace zan fita din hannayen mu yana sarke da juna yana murmushi jin fadan da yaya ke min a fuskan shi na kara kai dubana gareshi a lokacin idanuwan shi sun kara canzawa ga baki daya. Allah ya ban hikimar kara furta mai kalman shahada sai naji ya karba min daga haka naji hannayen shi sun sake lokaci guda a take na kira sunan shi da karfi. Saidai ina Allah ya riga da yayi ikon shi ya karbi abinsa lokaci ya cika babu sauran magani ni din dai da hjy ta tarewa ganin shi take hana in shiga dakin. Allah ya nufa yaya zai cika a hannuna ta faru ta kare sai mu yanzu tamu ta rage shikan ya tafi abinsa ubangiji ya bamu cikawa da kyau da imani idan tamu tazo. Likitan ne yayi dan aune aune yaja zanin ya rufe yaya umar a gaban idon mu muna ganin abin kamar a mafalki mai rabawa ya raba tsakanin mu da yaya umar din. Ban samu kukan ba lokaci daya idanuwana suka kankance ina gani dishi dishi likitan yace yaya habbib ya kamani. Fitowan mu yasa kowa ya gane abindake faruwa gurin Amma yaya habbib ya kaini itama Amman kuka take sosai hhaka yasa yaya habbib kiran su kawu yana sheda masu abindake faruwa. Kafin wani lokaci labarin ya zagaye yan uwa da abokan arziki yaya Ahmed ne ya kaimu gida shida salma da Amma gaba dayan mu kuka muke sosai a lokacin. Dare yayi don haka aka bari sai safe a kawar da yaya zuwa makwancin sa gaba daya lokacin ban san a inda nake ba don rudewa. Hankalin kowa yana a tashe da wanan mutuwan mai girgiza zukata dayazo muna lokaci guda ga zancen merry dake ta yawo har an fara neman ta a ko ina a cikin fadin kasan nan. Ba karamin jama, a yaya umar ya samu ba da sukai masa sallah da rakiya zuwa gidan gaskiya ga sheda na alheri da sai a yanzu muke jin irin alheri da taimakon al,umma da makwabta da yaya yakeyi idan yazo Nigeria ashe. Dama ba a fadin halin ka sai bayan ranka kowa ke fadin albarkacin bakin shi a kanka Allah ya bamu ikon cikawa da imani Amin. Karfe goman safiyan jumma,a aka kawar da yaya zuwa makwancin sa nayi kuka kamar raina zai fita banci bansha sai idan an tsareni don dole zan dan kurba ruwan kunu a cikina. Da akai kwana uku yaya habbib yazo akan in koma gidan mu in zauna kada a bar gidan babu kowa don masu zuwa gaisuwa haka yasa muka kwasa muka koma can dani da manjo da Amma da suke tare dani a kowani lokaci. Iyakata da mutane shine idanu idan kaji maganata sai yara suna kusa dani tunane babu wanda banyi a lokacin ji nake dama mu duka aka harbe da zaifi da barin na da yaya yayi a duniya ni kadai. Sannu a hankali har na dan fara sabawa da rashin yaya a tare damu inda abin yazo min da sauki har yaran da yake shi yaya mai yawan tafiyane a lokacin da yake a raye haka yasa ko yanzu sai nake ganin kamar tafiya yayi zai dawo. Hakama yaran kan dameni da tambaya yaushe ne daddy su zai dawo kamar yadda suka saba tambayana idan yayi tafiya. A wansn zaman makokin da akayine aka samu aka shawo kan kawu ya mayar da hjy dakinta tunda Allah ya raba akan wanda suke fitina a kanshi. Da farko kawu ya kafe akan har abada bazata dawo gidan shi ba tunda har yanzu bata saduda ba ko bayan mutuwan yaya saida ta tafka wani tsiyan ma. Don kawai na aiki driver da motar yaya din ba kuma aiken shi nayi haka kawai ba shine yazo min da maganan akwai wasu takardun yaya da zai tafi ya karbo nace ya dauki motar ya fita da ita don sheda. Shine aka fada mata tunda safe tayi min tas a gidan tana fadin sai a bari a raba gadon yaya da muke kwadayi nida uwata da yan uwana. Wanan maganan ne yakai kunnen kawu yazo gidan yaiwa hjy tas akan ta fita harkata ta barni inji da abinda ya dakeni na rashin mijina. Wanan abinda tayine yasa kawu cewa ba zai mayar da ita gidan shi ba saida aka taru dattijan unguwa suka bashi hakkuri da kyar ya yarda da sharadin ba zata kawo mai wani tashin hankali ba a yanzu kuma. Gidan ya rage dagani sai yarana sai yan aikin dake gidan yaya habbib da yaya umar dama Nasir babban abokin yaya suna tsaye a kan mu bamu nemi komai mun rasa ba a rayuwan mu tankar yaya yana raye. Mun cika kwana arba,in cif da yake inada karamin ciki wanda hjy sai daga baya ne take jin zancen cikin jikina din tayi fadan hakan kamar tsiya . Inda take fadin wai da gaiya nake zuba haihuwa haka a gidan yaya dan kawai gadon mijina ga gadin nan dukiyar ai anbar muna muci. Ni dai tashin hankalin yai min yawa na hjy don kulun safiya da irin fitinan da zata fito dashi duk kashedin da kawu yai mata kafin ta koma bai hana hjy tsula halin ta ba garemu. Kamar ba dan cikin ta ta rasaba a lokacin gaba daya abinda ya bari a duniya ya rufe mata idon ta sai tsakure tsakuren maganan da takeyi. Nazo ma kawu da zancen komawa na school tunda yaya dai ya tafi ke nan ba zai taba dasowa gare mu ba kuma gara in nemi na kaina don in kula da yarana da suke kanana tun yanzu . Don gaba daya ban gane mai ake ciki da dukiyan shi ba kodan ban sawa kaina damuwa da hakan bane a lokacin oho ? Saida kawu ya tambaya aka fada mai mudfin zan kula da kaina in tsare mutuncina zan iya komawa can in kammala har zuwa lokacin da zan haihu don dama idda ya saura min kuma ga ciki a jikina. Aiko hjy najin zan koma London da yara ta samu kawu da zancen bata san wanan maganan ba har idan zan koma ne ma sai dai idan za a hadani da wani muje tare don ita sam bata yarda in koma ni kadai ba saboda ba,a san abinda ya bari acan ba. Kawu yace a kausashe jummai kina da hankali kuwa kin ko san abinda kike fada kuwa da alama dai kamar kin dan motsu. Tace da hankalina sarai Alh yardane kawai banyi da ba da ko wace mace ba matarshi bace tayi sanafin barin shi duniyan nan don me yanzu zan yarda da wata kuma. Kiran habbib yayi bayan ta fita don kawu bai kara kulata ba yace suzo yana neman su bayan sunzo ne yake fada masu bukatana. Sai habbib din yace nima nayi tunanen hakan gareta tun farko sai dai ban sani ba ko tana da daman yin hakan ga addini tunda tayi nisa ga karatun nata. Kawu yace to ba wanan ba dazun muka gama magana da mahaifiyar ku ta nuna bata yarda Fatima ta tafi ita kadai ba don ba,a san abinda ya tara a can ba kada ta tafi tayi rub da ciki dasu ita kadai. Innalillahi suke maimaitawa tare da fadin kai haba mama koma mai yaya ya bari a can ai ko fatima taci abinsu ita da diyanta taci bana wani ba. Ku kuka san da hakan kawu ya fadi lamarim mahaifiyar ku a yanzu sai addua don abin nata kara yawa yakeyi ko yaushe. Kafin su fita suka aje magana kan za,a bincikeni yaushe ne zan koma don su sani a shiryawa tafiyan mu don sun amince na koma harda yaran gaba daya can har zuwa lokacin da zan kara sakewa . Naji dadin wanan halarcin da sukai min din don dama yadda za a rabani da yarana nake ji dashi nake kwana nake tashi a raina. Sai gashi abin yazo min da sauki sosai ba bata lokaci na shirya na koma London nida yarana inda za a dinga kulawa damu a karkshin oga mansur mijin Ramla. Mun tafi mun bar hjy da tarin dukiyan da take fada a kanashi inda bata san can ma dan nata ya bar arzikin da bata taba tsamanin irin sa ba gareshi. Don aikin yaya ba karamin samu sukeyi ba wanda yake harkan international samu yake kamar ba gobe a kullun. Sosai na mayar da hankalina ga karatuna inda nake tare da maria sai manjo da na wuto da ita don kara debe min kewa. Hakan baiwa hjy dadi a ranta ba sai jefa magana takeyi tana fadin wai rashin tsoron Allah yasa aka turani in koma don ansan abinda aka kitsa na koma na wawashe abinda aka bari a can tunda nan babu halin ci a gareni. Itace tace nayi ta haihuwa kamar bera dama mun san abinda muka shirya a kanshi merry sawun barawo kawai ta taka. Duk da ina samun kulawa a bagare daban daban daga yan uwa da abokan arziki na yaya umar hakan bai hanani kewan mijina ba muna tsaka ga exam din shiga matakin karshe na haifo dana mai kama da ubanshi sak wanan ba inda ya ragewa yaya umar shi wurin kama. Tun fitowan shi na fara kiran shi da habibi da kuma wanan sunan oga mansur yayi mai huduba watau umar faruq. Gida basu samu labarin haihuwana da wuri ba don nina hana a fada ba saboda komai ba sai don in dan samu natsuwa don hjy na iya tayar da fitinan in dawo tunda na haihu ayi suna a nan gida. Ban damu da fadan kowa ba a yanzu idan ma har koyone na koyi halin boye sirina a wurin uban diyana. Tunda labarin haihuwana yazo kunnen hjjy ta dan bada lokaci sai kuma ta matsa sai in dawo gida a raba gado tun tana boye hakan da farko tana fadin in kawo yaron dana haifa su gani har dai ta gaji ta fara fadin in zo asan inda kowa yake zaifi. Kin dawowa nayi nace duk abinda sukayi daidai ne a gareni ba don komai naki dawowa ba sai don yarana da nake jin kishin kishin din za, a rabani dasu wai idan muka dawo gida haka yasa na share kowa nayi zama tare da yarana a can . A haka na samu labarin wai hjy dai zaman yaki ta tare yanzu a gidan mu kuma tana amfani da babbar motar da yaya yake amfani dashi. Duk wanan bai dameni in dai ina tare da yarana hankalina yana kwamce gasu da jikjn girma sunyi wani girma hausa ma ya fita bakin su. Kodana kara karatuna na samu aiki a can ta hanyar oga mansur mutumin kirki da bai gazawa damu ga business da mukeyi nida mamu ina shiga kashe ina saro kaya in turo nan kano yaya Ahmed yana kula min da sana,a ta. Bani nazo gida ba saida na share shekara biyar da watani a can koshi don ciwon Amma da aka buga min bata da lafiya na shigo. Lokacin na kara bunkasa na zama wata wayyaya dani ko dole yanzu yaji shakkan takani kamar yadda ake min a baya. Don a karskashin WHO nake aikina idona ya bude sosai bani daukan raini a gurin kowa a yanzu. A bangaren merry kuwa tunda ta samu ta bar Nigeria a furgice bayan barin ta gidan lokacin da abin ya faru ta koma America a firgice tana nadaman abinda ta aikata din har labarin rasuwan yaya yazo mata gashi bata san inda yakai mata yarta ba ya rasu kuma. Gashi taji labarin ana neman ta a Nigeria ido rufe kan zargin kisan mijin ta da tasa yan bundiga suka zo har gida sukai mai. Wanan dalilin yasa ra boye kanta ga kowa bata yarda ta kara waiwayan yar nata ba ga rashin ya ga rashin mijin da tayi don bata san abin zai kai ga kisan shi ba. Hakan ya jawo mata gaba da yan uwan mahaifiyar ta da suka bata shawaran ayi kidnaping din yaran sai ya fito mata da yarta a bashi yaran shi sai gashi plan din ya basheta. Mun iso Nigeria mun samu Amma abin ba dadi don jikin ya matsa mata sosai tun rasuwan yaya data saka damuwa a ranta. Muna da sati biyu da zuwa Allah ya karbi rayuwanta mukayi wani babban rashi tsohuwar arziki a cikin mu. Duk da Amma tsohuwace saida wanan mutuwan nata ya taba kowa na halin don anji mutuwanta sosai a gidan. Saida komai ya lafane sai ga yaya habbib ya tsiro da wani zance wai yana son a daura muna aure dashi ya maye min gurbin dan uwan shi. Wani sabon tashin hankali kuma ke nan don hjy naji ta hau bakin ta da bala,i ga kuma matar kawu balarabe da ta fito da nata bala,in ina muka fito nida mamu. SARKA MAI RIKICIN GANGAN ina wuta su sakani na dawo bauchi wurin gaisuwan umma da ta rasu na samu wanan fitinan kuma duk ina jin su ban samu ba kowa amsa ba. Sai ji sukayi kawai na koma na bar kasan koshi da kyat kawu ya yarda na koma don shi ya amince da zancen yaya habbib din. Har London yaya habbib ya biyoni da zancen na nuna mashi hakan ba zai yuyu ba saboda me ya tambaya nace ko ya manta da wace yake aure yar uwata ce ita. Ko bayan hakana yasan zancen da ba zai taba yuyuwa garenu bane don hjyn shi bazan sake zama a karkashin ta ba har abada. Wanan amsan dana bashi yasa shi har zuka wai idan hakane sai dai in bashi yaran su dama suna daga min kafane don haka tunda ban yarda ba zasu dauki yaran su yanzu . Nan kuma na nuna mai bai isa ba muka rabu baram baram dashi babu dadi haka yasa na samu sa,ida ga lamarin su. Iyakata nazo mu kwana biyu da yara mu koma ina kula da abina tunda Allah ya hore min abinyi yanzu ban damu da dukiyan yaran ba don da aka raba cewa hjy tayi saidai su su rike na yaran a wurun su har yara su girma. Wanan shine labarina mai cike da rikici har mai rabawa yazo ya rabamu da yaya hjy bata barni na huta ba saida taga na fita zancen komai da yaya ya bari a duniya kafin ta dan sarara min. Ina rokon duk wanda na batawa rai kan wanan littafin da ya yafe min sai mun sake haduwa a wani littafin kuma kurakuren mu Allah ya yafe muna baki daya. Ina kara mika gidiya ga dinbin masoyana da so da kaunar da suke nuna min da hakkuri da halina banda abinda zance a kullun sai godiya a gare ku da fatan alheri. Yau gashi sanadin rubuta novel rayuwana yakaini inda ban taba zato ba a sanadin ku na tsuci kaina a kasan Europe. Masayona ku tayani yiwa wanan boyar Allah da a sanidiyarta Allah ya ingata rayuwana ku tayani yi mata godiya tare da addu,a ita da ahalin ta a baki na godewa kowa da kowa ina godiya a gareku har kullun masoyana ubangiji Allah ya rufawa kowa asiri a rayuwan shi Amin. SARKA FADI KIRICE MAI RIKICIN GANGAN