"[10/14, 8:39 PM] Diejahmaidoki: IDAN KAYA YA GAJI..." GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYAR SHAFIN FARKO BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. NAGODE SOSAI DA ADDU'O'INKU HAƘIƘA HAKANNE YA ƘARA ƘWARARANI. SAI DAI ALFARMA ƊAYA NAKE NEMA A GAREKU ALFARMAR ITACE BA KULLUM ZAKU DINGA SAMU BA SABIDA YANAYIN JIKINA. AMMAN FA DA ZARAN NA WARWARE IN SHA ALLAH BABU WASA SAU BIYAR ƊINNAN A SATI ZAKU SAMESHI NAGODE NAGODE SON SO """Wazirat al sa'ada barka da safiya ya darenki ya kasance uhm""" A kunne yake mun maganar ya riƙeni ƙam kamar za'a ƙwaceni a hannunshi. A kunnen nima nace. Na kwana cike da kewa da begen abun ƙaunata. Amman yaya zanyi nasan komai mai wucewane kamar "ma ba'aiba.""" Murmushi yayi mun a kunne tare da sumbatar kunnen. Ya jani muka zauna a kujera ina kan cinyarshi muna hirarmu ina tambayarshi jikin Hajiya cike da nuna damuwata da ciwon nata wanda hakan na lura yana ƙara mishi sona da nutsuwa dani. Amman fa idanunshi akan wuyana. Hannu ya saka ya ɗago azurfar wuyana ya ƙurama kwaɗon sarƙar idanu. """Wazirat a ina kika samu wannan sarƙa amman bai ba dai siyanta kika yi ba ko?""" Yayi maganar cikin sauke numfashi mai nauyin gaske. "Ba siya nayi ba. Kyautarta aka bani a matsayin gudunmawar Aure""" Shiru yayi ya saki sarƙar ya kama ɗan kunnen ya dubi tsakiyar idanuna yace. """Waye ya baki uhm?""" "Goggo Amfana""" Kafin in rufe baki ya ƙanƙameni tsam a ƙirjinshi yana sauke ajjiyar zuchiya. Ni da tsoro ma naji sabida halin rayuwa da halin jama'a nayi tunanin wata maƙarƙashiyarce sabuwa kuma. Mun jima a haka kafin ya ɓanɓare jikinshi a nawa ya dubeni cike da farin ciki. Yaimun raɗa. """Akwai hikmar da yasa Uwata ta baki wannan sarƙar haƙiƙa kin bambamta kuma kin sake samun wani" "irin matsayi na sake ɗaura sonki a wani bigiren da babu wata mace data taɓa hawa kai""" Murmushi nayi na ɗan ja gemunshi tare da sumbatarshi. """In zaki haɗa kayanmu ki haɗa mana waje guda, sai ki zaɓa mun wanda kika fi so. Ƙanwar Hajiya Naja'atu" "zata zo anjima ta haɗa mata nata, bata sanma dake za'ai tafiyar ba jikin nata babu daɗi Hajiya maganar rashin haihuwa ta ɗauka ta ɗaura a ranta wazirat ko jiya da sambatun batun haihuwa a bakinta muka kusan kwana, sai wajajen ukun dare bacci ya ɗauketa tasha magungunanta ma ta samu bacci wallahi" "taƙi kinsan ciwon damuwa akwai wanda yake taɓa ƙwaƙwalwa to nata ya kai wannan matakinne.""" Ajjiyar zuchiya na sauke. Da gaske tausayi Hajiya ta bani dole ko maƙiyinkane ka tausaya mishi in baya haihuwa kuma yaƙi karɓan ƙaddararshi. Ciwon damuwa kuwa ko Ƴar Shuwa da mijinta dana fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan so musu wannan ciwo mai wuya ba. Allah sarki. In akwai rabo Allah ya bata. Allah kuma ya bata lafiya. Haƙiƙa duk da nawa ciwon bai kai nata "ba, nima na ɗanɗani azaba sosai kuma ciwone mara sauƙi gaskiya. Ka rabu da Hajiya tayi fama da kanta" "basai ka faɗa mata tare zamu je ba dan Allah. Kayan kuma zan haɗa mana ko zuwa yamma ne, ko dare ma. Kuma inaso in zaka fita in bika in gaisheta na kai muku abincin karyawama yana falo""" Farin cikine ya lulluɓeshi sosai yaita bina da adda'a. A hakanma ban barshi ba saida na sako mishi farfesun kaɗan yaci tukunna kafin muka jera har zuwa ɗakin Hajiya. Wallahi ni dai naji muryarta kafin mu shiga ras babu halamun ciwo. Amman shi ba lallai yaji ba da danginshi yake waya batun suna yake sanar musu zai kawoni amman ba daɗewa zanyi ba tare zamu juyo. Yana gaba ina binshi a baya muka samu ƙanwarta da Akwati turola tana haɗa ma Hajiya kayanta. "Ɗakin Hajiya gaskiya yafi nawa kyau kayan ɗakinta ƴan wajene masu tsada sosai, ɗakin ni kaina ya bani" "sha'awa sosai, kuma komai tsabtsab duk da dai mai aiki ke hidimar." """Alhaji ka shigo, kaida Amaryane? Ai Hauwa take cewa ashe tayo abinci ta kawo. Yanzu nake son in" "taimaka mata ta kintsa sai in kaita taci""" Zama yayi a gadon. Ni kuma a kujera na zauna muka soma gaisawa da Naja'atu fara'a kamar zata halakata. Hajiya kuwa dana "gaisheta hannu ta miƙo mun, na lura bata son magana duk cikin ciwonne. Hannuna na miƙa mata ta ɗaga mun halamun godiya. Shi kuma duk saiya sake shiga damuwa yana ta shafan hannunta." """Wannan ciwo Allah dai ya kawo ƙarshenshi ya bata lafiya mai ɗorewa. Dake naga kusan shekara nawa" "bai tashi ba, mu mun ɗauka ma ta warke sumul wallahi Depretion ciwone mai wuya da tsanani. Ubangiji" "Allah dai ya dawo daku lafiya. Amarya sai ayi haƙuri a ɗauki ragamar kulawa da gida har zuwa lokacin da Allah zai dawo dasu""" Murmushi kawai nayi inata adda'ar Allah yasa kada Alhaji yayi katoɓarar faɗama Naja'atu tare zamu tafi. Itama da biyu tayi maganar. Inma Hajiya na ciwo wallahi ciwon kishine duk da tana ƙoƙarin dannewa amman dai shi ɗinne wallahi. "To bari in shiga ciki zuwa anjima zan sake leƙowa""" Na faɗa tare da nufar hanyar waje. """Rigunan bacci nawa zan saka miki Yaya? """ "Naja'atu ta faɗa harda ƙara murya.""" "Wucewata nayi ɗakina na baje ɗaiɗai a ƙasa ina shan farfesuna ina nazari, dana tuno Alhaji Zaidu sai inji" "sabon farin ciki, haka inna kalli sarƙar wuyana sai inji na ƙara godiya ga Goggo Amfana." Wajajen taran safe sai naji ana buga ƙofa nasan bazai wuce Labbai ba. Ina buɗewa kuwa na ganta tare da Uzairu zuchiyata. Baki na washe cike da farin ciki da murna muka shiga har falo. """Lolo kenan kinsan Allah? Ke mai sa'ace a rayuwa. Yanzu wannan gidan gidan mijinkune duk girman" "cikinnan naki ne. Wallahi Lolo kada ki yarda kiyi irin zaman gidan Babangida, anan kam kema ki baza komarki kici karanki babu babbaka""" Uzairu zuchiyata ke magana ga farfesun da nake ci a hannunshi yana yi yana shan romo. Nan ya shiga loma. Zama labbai tayi ni kuma na shiga ciki na haɗo musu kaɓakin arziki rigi_rigi muka sake bajewa. Ga Labbai ga milo da madara anyi haɗin murtuk anata sha . """Lolo kina cin duniya da tsinke. Lolo banga kishiyarki ba? """ "Tana kwance magashiyyan gobe ma zamu tafi Jidda zata ga likitanta. Amman bata san dani za'aje ba""" """Toh ikon Allah mata ana munafurci Allah ya kyauta. Ke dai ki kwantar da hankalinki ki kula da aurenki." "Kina gani dai mu gamu bamu samu ko kamar Babangida ba, bare wannan babban gida na hamshaƙai. Gashi ɗakinki da jikinki duk ya ɗauki ƙamshi. Gaskiya duk zaki sanmun waɗannan turarukan alfarman na Mrs Bukhari gidan ƙamshi ina.""" Baki Uzairu zuchiyata ya washe. """Tabb lolo irin abinda nake da sha'awa kika samu. Inason inga ina zagaya duniya da kika ganni." Ni dai Lolo ki fitar dani kunya biki nata matsowa su Felisha suna ta shirye_shiryen tawowa. Nayi tunanin "sauke su a gidan Mum to Felisha tace Hotel zasu kama, a zo ayi bikin da za'ayi mu wuce Canada canma ayi bikin shikenan na zama mijin Baturiya. Girki kuma ina koya a wajen Maigogul dan ya karɓe ragamar girkin gidan shi yake yin komai. Amman wallahi Mum na mutuwar sonshi yana kasheta da gayu. Duk bala'in son taga ta ƙure gaye wallahi ta kasa kamo Dad yanzune ma fa yake adonshi na asali. Gashi tana shiga dashi taron kunya sosai harda gwamnoni Maigogul na ta'amali. Duk da dai suna haɗuwa dasu a" "sha'anin biki""" Labbai tace. """Koni bikin da muka shiga Abuja gwamnoni uku nagani harda Atiku Abubakar na gani. Sun saba da" "manya gaskiya.""" Muna ta hirarmu muna shewa Alhaji Zaidu ya shigo yana murmushi da yaga su Labbai. Gaza na biye dashi da jakar baya da kayan farauta a jikinshi. "Gaza har ka iso kenan ikon Allah""" "Dariya yayi ya nemi waje ya zauna, ya kalli waje ya kuma buɗar bakinshi yace." """Kutumar dumadu Lolo wai eh duk wannan gidanki ne, ji madara ga kayan more eh rayuwa? Allah sarkin" eh girma. Eh kai mata maza nan aka tawo kenan. Babban Yaya kaga wannan aminin Lolo kenan sai su kashe su eh haƙa su birne abinsu. Ni nasan eh sabida "ita ma ya eh dawo Kano. Ya bar Rakiya a eh damuwa sai ni nake ta kulin ɗinta eh wallahi""" Alhaji Zaidu ya zauna kusa da Gaza yana murmushi yana kallona. Ni kuma duk kunya ta kamani. Me yasa Gaza zai wani ɗakko kayan farauta ya saka dan Allah. """Wazirat ki ba Gaza abinci yaci zanje in kintsa zamu fita tare zan kaiki gidan suna ki dai leƙa kada ace" babu wanda yazo daga gidana. Anty Labbai ashe kune a gidan' Nan aka shiga gaisawa ya fita yana dariyar Gaza. Ni kuma nayi maza_ maza na tafi shiryawa na bar labbai na zuba ma Gaza abinci. Farin lace sol mai masifar kyau na saka ɗinkin riga da siket anyi mishi surfani har a siket ɗin. Mayafina goldin na ɗakko mai tsada na wannan zamanin. Na ciro takalmi da jaka da suka dace da mayafin. Na ɗakko gwal ɗina ƙaramar na maƙala zubuna biyu na jera a hannayena ga agogo ga awarwaro. Ina fesa turare marar ƙarfi Labbai ta shigo. Yauwa Labbai kina ganin sana'ar me ya kamata ace kin soma tunda Maman Shafa na tata sana'ar kema "saiki soma taki ai ko? """ """Wallahi Lolo ni kaina inata tunanin yafa kamata sana'ar ko babu yawa a jaraba. To ni wallahi ko man" "ƙuli sai in dinga saidawa tunda na iya matsar man a jikin tunkuza.""" "Kuma zaki iya tunda naga kina da jarumta. Nawa ne zai isheki jarin to? """ Baki ta washe tana ta murna dubu saba'in na ƙirga na bata nata. Na ƙirgi dubu ɗari nace taba Hajiya Balaraba Adama zata zo sai ta bata. Na ware wasu kuɗi nace taba Rakiya da Hauwa "Atampa na cira a cikin akwatin da Hajiya taimun na zura a leda zan tafi ma da mai jego, na ciro kala biyu" da takalmi harda sarƙa nace a kaima Rakiya sarƙar kuma ko Rahama a bata tayi zawarci dashi. "Da muka sakko na ɗiba mata su madara milo harda siga, dasu shinkafa kamar dai yadda aka saba e." Turarukan wutanma na ɗiba mata na bata lace mai kyau a cikin akwatin da Hajiya taimun. Alhaji bai jima ba ya kirani yace mu fito. "Nako ci sa'a Hajiya bata babban falo. Su Gaza sukai gaba da Alhaji Zaidu, Uzairu zuchiyata Labbai taba" ledar kayanta ya fice mata dashi. Ni kuma na raka Labbai falon Hajiya tana falo ita da Naja'atu Labbai ta gaisheta da jiki. Ni kuma nayi mata sallamar zan leƙa gidan suna daga nan kuma zan soma shiga ofice "yau.""" """To shikenan sai kin dawo. Itama yar taki zata dawo ne? """ "A_a yau zasu wuce ita da mijinta""" Naja hannun Labbai muka fita. Sai muka ji Hajiya tace. """Subhanallahi wankin kula yana shirin kaini dare, ya zama dole in ma tubkarnan hanci. Ofice?""" Idanu muka haɗa da Labbai inyi magana na lasa jikina ya mutu yayi mus wallahi. Labbai ce ta ja hannuna muka fita. Ni dai har muka kama hanyar Rano jikina a mace. Gaza sai hira yake ma Alhaji suna ta cin dariya. Ni ko saida Labbai ta zungureni ma na gane me ake ciki. Dake Gaza ne a gaban mota ni ina baya a tsakiya hankalin Alhaji Zaidu a kaina duk ɗagowar da zanyi sai mun haɗa idanu dashi. Har muka iso Rano gidan suna kenan. "Dani da Labbai dashine muka fito zuwa cikin gidan, su Gaza kuma muka barsu a mota." "Ai kuwa gidan shaƙe dam da jama'ar suna anata ɗaura tukwane, wata tukunyarma cike da jallof har an" sauketa ga kaji anata suya. """Ga Amarya ga Yaya. Sannunku da zuwa Amaryarmu ashe zaki zo?""" Cewar Zarah data rungumeni tana dariya. """Zara'una kenan. Duk kunanan. Anty Tani kema kinzo ashe? """ Ya ƙarasa ya tsugunna a wajen wasu mata su uku manya dan sun girmeshi. "Binshi nayi nima na zube, Labbai kuma tana ta gaisawa da ragowar dangin Alhaji." """Zaidu ashe saida ka ɗakkota kuka tawo? Ai data yi zamanta haihuwa da bata ƙarewa a wannan haula" kamar suna gasarta. "Yanzu jibi kusan mutum goma ke da ciki ma fa. To ku shiga Fatiman na ciki""" """Ai Anty Tani ba zama dama zata yi ba. Na dai kawota ne tayi barka taga Ƴan uwa tunda Ita Hajiya ba" "zata samu zuwa ba. Gobe ma Jidda zamu wuce""" Ta kusa da Anty Tani tace. """Wannan ciwo Alla ya yaye mata shi. To yanzu menene ya tayar da ciwon ne? Dan ba'ace kishiya ba ko," "naga ai jarumace wallahi kuma mata nawa aka kawo mata a baya ma""" Nan dai akaita maida yadda za'ayi kafin Zarah da Anty Tani sukai mana jagora zuwa ciki. Shi a falo cikin tarin ƴan gidansu ya zauna mu kuma muka shiga wajen maijego muka dubata da jinjira. Naga bata fara'a kuma batai murna da ganina ba tunda yaune haɗuwarmu ta farko ita ba biki tazo ba. Ashe ita ƴar ɗakin Hajiyace irin ta ƙuryannan sai da Zara'u ta faɗa mun na fahimceta dan wallahi Alhamdulillahi kowa yanata haba_ haba dani Anty Tani ta miƙa mun yarinyar tace in kaima Alhaji Zaid. Na shiga falon na sameshi dasu Zarah suna tattaunawa akan kasuwanci. Na miƙa mishi yarinyar ya haɗata da hannuna ya riƙe ya kalleni tare da lumshe idanunshi. "Na fahimci duk ya damu da yadda yaga yanayina wani iri, ku kuma duk wata fara'a da nake yi ta dole ce." "Hankalina yana kan furucin Hajiya wallahi. Bansan me zai biyo baya ba, bani da ilimi amman da Allah na dogara." Murmushi nayi mishi na zare hannuna na nemi waje na zauna. Cikin minti ashirin muka gama komai muka fito daga gidan kai tsaye Family house muka shiga shima mun "kai minti ashirin, kuɗi ya bani masu kauri duk tsofaffinnan na bisu na danƙa musu." Ya haɗani da Anty Khadija yace mata. """Anty khadija ga Shalelena na haɗaku tunda ke ba team ɗin Hajiya kike ba. Ko dai bakya so Anty Khadija?" """" Dariya tayi tace. """Alhaji Zaidu kenan ai baka sani ba Goggo Amfana da kanta ta ce ta haɗani da Sabuwa ƙawance." Ina da lambarta zan sata a group ɗin family na mata zallah. "Sabuwa akwai groups ɗina biyu zan sakaki zaki ƙaru sosai. Ina zuwa ko?""" Ta tashi ta shiga ciki sai gata da magungunan mata cikin leda. Nan Alhaji Zaidu ya fice taimun bayaninsu tas kana tace a group ɗinta tana koyar da yadda mace zata zama sarauniya duk wannan magungunan tana koyarwa bama ita kaɗai ba harda ƙwararrun mata daga "Sudan, da Chard, da kamaru." Nayi mata godiya muka fito ni da Labbai a ƙofar gida muka samu su Gaza muka rankaya sai kamfani. Nan Alhaji Zaidu yaita zagawa da Gaza da Uzairu zuchiyata. Ni da Labbai kuma muna ofishinshi ina ɗiɗɗiban mata maganin matannan. Tsumin sai ruwan gora muka shanye na haɗe mata su waje guda dan tsumi kala uku ta saka mun. """Gaskiya Lolo ki gode ma Allah. Wannan karon dangin miji na sonki sosai. Wannan Anty Khadijan tayi" mun wallahi da ganin yanayinta kinsan tasan kanta. "Yanzu lolo anan zaku dinga aiki? Allah mai iko wannan wai ofishinki ne""" Dariya muka yi. Basu gama zagayensu ba su Maigogul suka iso da Hajiya balataba da Cicib suna son zasu kama hanyar Dutse. Yau dai Hajiya zata je taga su Rakiya kuma ko ya zata kaya sai Allah. """Gaza ashe kazo ikon Allah Alhaji me zamu ce maka ai sai godiya.""" Cewar Cicib kenan. """Babu komai Alhaji, Baban Rahine ai abokinane""" """Ni duk kewar Rahine ke damuna Alhaji. Na barota tana ta fisge_ fisge eh ni wato da zaka eh barni sai in" "ɗakko Rahine mu zauna abinmu wallahi Allah zata yi amfani sosai zata dinga gadi""" Dariya kawai Alhaji Yayi ya riƙe kafaɗar Gaza kawai. Maigogul yace. """Shashancin banza. Kai da aka kawo aiki ina kai ina batun Rahine ai gara ka zauna kayi aikinka. """ """Hattara eh wallahi Dattijo tunda nazo wajennan kaga na eh kulaka ne? Ai tunda ka taɓo rabin raina ka" "taɓo gidan rina eh wallahi""" """Kul Baban Rahine ba'a faɗama iyaye irin wannan maganar tausasa harshe akeyi akansu. Alhaji Baba kayi" "haƙuri""" Dariya Maigogul yayi yace. """Ai babu komai gyatumarshi yake tayawa kishi fa shi yasa. Munafurcinsu ɗaya shi yasa ai daya shigo bai" "neme ni ba ma, bare ya so ganin ƙaramar uwar tashi""" Ni dai ina tsaye ina fama da kunya. Gaza ya dubi Hajiya Balaraba yace. """Ina eh wuni nace""" Ita kuwa da fara'arta ta amsa ato ai ba'a rufeta ba. Labbai ce tace. """Mu kam zamu tafi Allah ya ƙaddara saduwarmu, Alhaji Zaidu ka sake gaishe da Hajiya da jikin" """To shikenan zata ji""" "Kuɗaɗe Alhaji ya laluba ya damƙama Cicib ya danƙama Maigogul, Uzairu zuchiyata ma an bashi. Ya bani" na miƙa ma Labbai kuma naji da kauri na labbai zaiyi dubu hamsin gaskiya ko talatin haka. Tare da Maigogul da Uzairu zuchiyata da Hajiya suka tafi a mota ɗaya ya rage sai mu uku. """Yauwa Babban Yaya. Naga kamar akwai ɗakin kwana a kamfaninnan kuma naga shanya ma halamun" ana kwana ko? Madadin inje in zauna eh a gidan Ƙanwata a bani waje anan eh kawai ni zanfi sakewa eh "gaskiya""" """Na fahimta Baban Rahine. Akwai Shu'aibu ɗaya daga cikin amintattun yaranane dashi ma nake son ku" "dinga sintirin zuwa kwatano, da sauran ƙasashe siyo mota. Haya na kama mishi kuma ɗaki biyu da falone" "dan ciki da falo muka so, ba'a samu bane sabida yaso ya dawo da iyalinshi birni sunƙi dole ya barsu a" "Rano. Sai ku zauna ɗaki ɗaya. Ina zuwa bari in kirashi kuje ka kama aikinka. """ Kiran Shu'aibu yayi sai gashi da sauri. """Shu'aibu ga Baban Rahine wan Matatane zaku zauna tare a ɗakinka, shine wanda zaku dinga zuwa siyo" "motoci dashi. Sai ka nuna mishi duk abinda ya dace, ka sai mishi katifa da duk abinda yake da buƙatar" "sawa a ɗakin""" """To shikenan maigida an Gama. Baban Rahine maraba da zuwa, zamu iya tafiya""" Gaza yayi dariya yace. """Lolo a taya ni godiya, godiya dubu nace eh Alhaji sai da kai eh wallahi. Zako kaga amana wallahi""" Sa kai yayi ya wuce yana ɗaga hannaye sama. Hannuna Alhaji Zaid yaja muka shige ofishinshi. A cinyarshi yaimun masauki hannayenshi biyu riƙe dam "da ƙuguna.""" """Waye ya taɓa mun ke uhm. Hankalina kacokam yana kanki, Menene uhm faɗamun""" Ƙuguna ya matsa na lumshe idanuna. "Babu komai kawai dai yanayin jikinane ba daɗi""" Duk sai ya rikice yana cewa muje asibiti. Saida na saisaita shi ta hanyar yimai abinda na lura yafi so "sumba kenan. Tuni muka shige sama jannati mukaita shillo, da ƙyar jirginmu ya sakko." Idanu a lumshe sunyi jawur cikin muryar kasala da zabari yace. """Gashi kin kyautar dani a wajen Hajiya uhm. Kamar ni kaɗai nake kewarki uhm wazirat. Ko hotel to zamu" "tafine in muka kammala mitin ɗin uhm? Ina da mitin sannan zan gabatar da Baban Rahine za'a rubuta sunanshi zan taimaka mishi ya cike wasu takaddun, kema zan gabatar miki dasu""" Narkewa nayi a jikinshi kamar yarinya. "Yadda kake so ai haka zanyi. Ka mance kaine malallakin Sabuwa sukutum ne?, gangar jikina cike da" "kewarka abin ƙaunata""" "Murmushi yayi mun, ya sake dulmiyawa inda yafi so mun jima a cikin wannan inuwa mai sanyi da daɗi." Sai da lokacin miting yayi ya miƙe ya saisaita kanshi muka fito kai tsaye zuwa ɗakin da aka ware domin mitin ɗin. Kowa ya hallara ashe harda Gaza yana zaune da wannan ƙaddararrun kayan da bashi da wasu masu kyau da suka fisu. Zama nayi a kujerar da take kusa dana Alhaji Zaidu aka soma gabatar da mitin sai da muka yi minti talatin kana aka sallami kowa. Yace da Gaza yazo ya sameshi a ofice. Yazo suka yi cike_ciken takaddu daga haka suka tafi zuwa sallah. "Alwala na ɗaura nima nayi sallah, yana dawowa ya ɗaukeni a gaban mota sai wani lafiyayye Zangon baƙi" na masu dashi. Kuɗin ɗaki ya biya muka wuce. Muna shiga ya matseni tsam a bango. Lallai a wannan zangon baƙi munyi abu gaskiya shima yanayine mai tsayuwa a zuchiya. Raɗa yaimun a kunne harna soma bacci. """Allah yasa ajjiyata ta shiga Al sa'ada. Kin shirya cin amarci a Jidda dai ko? Kifa shirya in sha Allah acan" "zamu samo ɗiya mai suna Jidda in sha Allah""" "Kuma laɓewa nayi a jikinshi, ina na kasa magana sai bacci." Bamu muka tashi ba sai la'asar a gurguje yayo wanka ya wuce masallaci. A taƙaice sai taran dare muka baro zangon baƙinnan zuwa gida. Zukatanmu cike fes da farin ciki da wani "irin shauƙi da nutsuwa ta musamman, wallahi Allah wannan abun na sake haifar da shaƙuwa da" nutsuwar zuchiya dana ruhi. Ko da muka je gida. Ƙannen Hajiya suna gidan ita kuma tana kwance tana mun kallon biri inai mata kallon ayaba. Dubata nayi da jiki harda tsarabata nayi wucewata ciki. Nan na kira su Rakiya. Ko data ɗaga ina jiyo hayaniyar Maigogul. """Ai wallahi sai dai ka kama mata zangon baƙi taje ta kwana goben ta wuce. Ko kuma ni in bar mata" "gidan""" Cewar Rakiya. Idanu na lumshe. Haba Rakiya me yasa zaki... """Abu ta kazan... Ke lolo cikinki nake dashi ki yi mun shiru kada in haifeki mitsiyaciya. Ai da saka hannunki" "akan Auren ke da Uzairu zuchiyata dake ku tambaɗaɗɗune. Menene kike kirana to? """ Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Allah ya baki haƙuri dama Jidda zamu tafi gobe shine nace barin in sanar miki. Sannan na ba labbai saƙo "zata kawo miki. Rakiya ki dinga haƙuri dan Allah faɗanki yayi yawa.""" Guɗa ta saka tace. """Ƴata ta zama sarauniya hiye Lolo kika ce Jidda fa ta ƙasa mai tsarki? Ma'aikin Allah na madina ni Rakiya." "To shikenan Lolo kince Labbai zata kawo mun saƙo saƙon menene? """ Murmushi nayi mata nace. "Kuɗine da atampa, sai ɗankunne nace aba Hauwa"" Tsokanarta nake yi" """Ina baƙa baƙar munafuka kenan babu abinda zata samu na rantse miki da Allah. Cikin Ƴaƴanta ubanwa" ya taɓa bani wani abun. Layuza ma na kulle a ofishin Ƴan doka uban me tayi sai Allah. Sunata nuƙu_ nuƙu kinsan Hauwa da "gulma""" Rakiya tafi minti goma tana magana da ƙyar ta barni mukai sallama ina ji tana hawan Maigogul. Ni dai a daren saida na gama shirya mana komai kana nayi bacci. Da sassafe kuma shayi kawai nasha na gyare ɓarayina na fito fes cikin baƙar abaya da jaka da takalmina sai akwatin kayanmu. A falo muka haɗu da Hajiya tana tsaye harda jingina da bangi. Ganina da akwati a shirye tsab ya tsitaye mata man kai tas. Alhaji Zaidu ne ya sakko cikin shigar jallabiya baƙa mai wando yayi kyau sosai fuskarshi cike da annuri. Sai ji mukai tim Hajiya ta faɗi ƙasa tana numfashi ɗaiɗai. Kuyi haƙuri mu dasa aya anan nagode Mrs BUKHARI "[10/15, 12:53 PM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 2 Da sauri na yar da akwati na nufeta ina mata sannu. Fatana kar ta suma ace an fasa tafiyar domin ita kanta ƙurudinta kenan. Ina ganin makirci. Wallahi saita soma sambatu wai ita mutuwa zata yi tana ganin mala'ikun mutuwa bama sai anyi tafiyar ba. "Ta tashi hankalin Alhaji Zaidu, nima dai hankaalina ya tashi sabida kamar yanzu kam ciwon nata ya tashi" "da ƙarfin tsiya, ni har wata rama ta faraɗ ɗaya naga tayi fa Allah." Haka na taimaka mishi muka sakata bayan mota ƙaninshi ya tuƙamu zuwa filin jirgi tana ta ambaton "Allah ko idanu bata buɗewa. Shi kuwa Goga sai tofeta yake yi da adda'a a haka har ƙarfe tara daidai aka sakamu a bus zuwa gaban jirgi, daga nan muka haye jirgi. Awanmu goma a jirgi dake jirgin yayi tsaye tsaye sosai duk mun galabaita ƙarfe bakwai na dare muka sauka a Jidda." Daga nan muka shiga mota kai tsaye zuwa asibiti. Dakta Sameer Abbas asibitin kuɗi naga an rubuta. Hmm asibitin ya haɗu sosai. "Ni dai ina biye dasu, muna gani aka shiga da ita wani ɗaki na musamman." Ni dashi muka bi bayan Dakta zuwa ofishinshi ni dai inata kalle_ kalle gaskiya. Ina ji sunata larabci ba ƙaƙƙautawa Daktan ma har nunoni yayi ni dai naji Alhaji yace mishi wai ko Zaujati kamar dai haka ɗaliban larabci su gyara mun in na rubuta ba daidai ba. "Tare da Daktan suka fita basu suka dawo ba sai goman dare, ya dai leƙo ya miƙo mun laban a ƙaramar" "gora na sha, shi kuwa ko ruwa bai kurɓa ba abun tausayi." Suna shigowa ya dubeni yayi murmushi. Nima murmushin na mayar mishi yace. """Shalelena mu tafi masauki sai kuma gobe da daddare ma zamu dawo asibitin dan anyi mata allurai sai" "gobe da daddare zata farka ko jibi ma da safe. """ Hannu ya miƙo mun na riƙe hannun nashi na miƙe yace da Dakta. """ Doktor ma'assalama""" Sukai musabaha muka fito daga asibitin muka ɗauki Tasi. Muna bayan motar ina laɓe a jikinshi jakata na cinyarshi tsautsayi yasa nace ya miƙo mun agogona. Yana zura hannu ya zaro ambulan ɗin da Babangida ya aiko da mardiyya ta kawo mun. Take wani ruwa ya hauro mun kaina sai naji hannuna yayi sanyi har yana damshi dan masifa. Agogon ya miƙo mun nasa hannu na karɓa shi kuma ya kalleni yayi murmushi kana ya buɗe wannan ambulon sai ga kuɗi da takadda. "Kuɗin basu da kauri, takaddar ya ɗauka ya kalleni." """Saƙon waye baki buɗe ba Shalelena uhm? """ Bai yi tambayar dan yana jiran amsa ba takaddar ya warware rubutun ciki baifi layi huɗu ba ga abinda makirin ya rubuta. _Cus bazan ce ina taya murna ba dan wallahi zuchiyata ji nake tamkar zata faɗo. Ashe da gaske akwai wata ranar da zaki rayu a ƙarƙashin inuwar wani ƙaton bani Babangida kacigari ba? Duk da nayi farin ciki da baki Auri wancan ɗan akuyan Khalid ba. Daga ƙarshe ina neman yafiyarki Har abada ke ta Babangida ce_ Take naji wani zazzaɓi. """Cus, har abada ke tashi ce, cus, cus?""" Naji yana maimaitawa muryarshi da rauni linkib. Takaddar ya nannaɗe ya haɗa da kuɗin ya mayar cikin jakar. "Har muka iso zangon baƙi bai kuma magana ba, amman yana murmushi in muka haɗa idanu." Da muka sauka muka shiga zangon baƙin. Muna shiga ɗakin da muka kama ya ɗakko takaddar Babangida ya saka a shara. Waya naji yanayi yana larabci. Yana ajjiye wayar ya sauke ajjiyar zuchiya ya faɗa banɗaki naji ya saki ruwa. Nima saina bishi idanunshi a rufe yaji hannuna a fuskarshi ruwa yaci gaba da zubo mana mai zafi daidai da yanayin lokacin. Kallona yayi idanunshi sai naga sun rine yace. """Kinsan kalan kishina kuwa Shalelena? """ Kafin inyi magana ya jawo hannuna ya ɗauramun saitin zuchiyarshi da take ta bugawa. Ƙanƙameshi nayi nace. Sabida rashin mahimmancinshi yasa na mance da takaddar ma. "Da ace naso zan karanta ma in yaga ba tare da kai ka gani ba""" Fuskata ya tallafo muna kallon juna. """Shalele kada ya sake aiko takadda kisa hannunki ki karɓa bazan lamunta ba. Sannan abinda yafi komai" "ɓata mun rai shine Cus da naji ya ambaceki, Cus fa yace miki amman ke kinsan menene ma'anar cus da irin macen da ake cema cus kuwa? Matar tawa zai kira da cus. Da kuma cewa da yayi wai har abada... """ Bakinshi na toshe da abinda yafi so dole yayi shiru ya shiga sauke ajjiyar zuchiya. Saida na wanke mishi zuchiyarshi tas kana muka yi wanka tare da alwala muka fito. "Magriba da isha nayi, shi kuma isha kawai yayi yana sallamewa aka kawo abinci shinkafa kaza harda wani" "nono a kofi amman naga albasa da koren ganye a ciki dai. Ashe dashi ake haɗawa aci, na gani lokacin da muka je Umara amman ni yar da nonon nake yi sai yau Alhaji Zaidu ya zuba mana kuma wallahi da daɗi." """Shalele me kike ganin ya dace ayi ma Mama da Mama Hauwa, da Alhaji Baba? """ "Haba dai masta, baza mu ɗaura maka wata ɗawainiya ba, ai gida da ka siya mana ma wallahi ya'isa babu" "abinda zamu ce. Ga aiki ka ba Gaza shima ai zai taimaka musu""" "Hararata yayi na soyayya, nayi dariya bance komai ba, shima baice ba har muka gama cin abincin na kora" da laban shi kuma shayin da suka kawo yake ta sha. "Kayan bacci na ciro mana, a lokacin ya fita yace yana zuwa." Farar rigar bacci na saka ta tashin kai. "Na cakuɗe jikina da kullacham na matan aure da humrar matan aure, jigidar matan Auren dake ƙuguna" "na shafe da Humra danna lura yana mugun son jigidar tana ɗaukar hankalinshi, kuma yana yawan shiɗar" "ƙamshin. ( kema ki mallaki taki Hajiya wannnan jigidar akwai sirri a cikinta mai girma, in kina so kimun magana Hajiya) Na sake goge bakina da brush tas na jefa minti a bakina na haye gado ina ajjiyar zuchiya." Turo ƙofar yayi ya shigo Ya ilahi abunda ya faru a wannan daren ko na musamman ne sosai mun murje junanmu sosai Alhaji tamkar mayunwacin Zaki haka ya koma mun. Mun kasance cikin wani irin farin ciki na musamman. Bayan komai ya lafa mun tsarkake jikinmu mun dawo gado ne nace mai. "Wai me likita yace maka dangane da jikin Hajiya ne?""" Fuskata ya shafa yaimun raɗar wasu kalmomin da na kusan narkewa. Shi kuma sai dariya yake mun. Da haka muka shashantar da batun Hajiya muka shiga fallasa asirin zukatanmu kowa na faɗa ma ɗan "uwanshi yadda yaji lokacin da akayi kaza da kaza_kaza , haka mukaita birgima a gado na lura alhaji" "nason wannan birgimar sosai, kuma shima wani nau'in salon soyayyane mai tsaiwa a zuchiya Allah Daga haka mukai bacci fes zuchiyoyinmu muka wayi gari, shi ya tafi masallaci kafin ya dawo na shalla wankan" ƙananun kaya masu ɗaukar hankali. Ai kuwa saida muka yi kafi karin kumallo kafin muka koma bacci bamu muka farka ba sai wajajen goman "safe, shima ni na soma farkawa na tashi na sauka a hankali gudun kada in tasheshi yana da bashin bacci sosai bawan Allah." "Har nayo wanka, na sake saka wani riga sa siket ɗin na kanti bai farka ba." "Ga yinwa sai ɗibana take yi, na ciro gumbata ta dabino da riɗi na dinga ci, ni dai saida naci kusan rabin" bokiti lita ɗaya wallahi kafin na ɗanji dama dama na kora da laban ragowar ta jiya. Sai sha ɗayan rana Alhaji ya tashi. Yana buɗe idanu yayi tozali dani. "Murmushi na sakar mishi kawai, waya ya soma yi da masu kawo abinci kafin ya faɗa banɗaki." Kafin ya fito na gyare gadon na ciro mishi kayanshi. Ni na taimaka mishi wajen shafa mai da saka kayan. """Kinyi kyau sosai. Kayan sun karɓeki in dan tanine atampa sai dai a saka in za'a fita. Amman in ganki cikin" "irin wannan shigar nafi jin daɗi musamman in ganki babu ɗankwali. Kina sake burgeni kan wanda kike mun uhm wazirat ɗina mai sambatu uhm""" Dariya nayi mishi shima dariyar yake ta mun yana ta tsokanata. A haka muka karya cikin farin ciki sosai. Bayan la'asar yace in shirya mu ɗan fita yana da abokinshi ɗan Kano mazaunin nan jidda muje mu yawata inga gari. Ai kuwa ba shiri na shirya cikin abaya fara sol ni da kaina nasan abayar tayi mun. """To abayarma inaso gaskiya dan itama tana miki kyau uhm inaga zamu ƙara kafin mu tafi ko? """ Murmushi nayi mishi na riƙe mishi hannu muka fita. "Sai da muka fita, muka shiga tasi muka isa unguwarsu ya kira abokin nashi da lambarshi ta saudiyya sai" yake sanar mishi basa nan suna madina ya raka madam ɗinshi. """To Shalelena mu shiga gari ga prince majid park a bayanmu da ƙafa ma zamu gangara muje kisha kallo" "uhm""" Ai kuwa nasha kallo sosai gashi park ɗin babu hayaniya duk da lokacin mutane suka soma zuwa dama ance su Labaraba da daddare suka fiye fitowa da safe rana matansu na killace a gida. Mun sha soyayya harda guje_guje wallahi kamar kada mu bar wajen. Amman dole anayin Magriba muka hau abun hawa zuwa asibiti wajen Hajiya. Mun dai shiga mun dubata tana kwance ana ƙara mata ruwa tana ta bacci. Naga lokacin da muke park ma ya kira asibitin yana tambaya. Daga gidansu Hajiyan ma sun kira dan jin lafiyarta. A ɗakin ya barni yaje yayo sallah ya dawo kana muka bar asibitin akan gobe sassafe zamu dawo dan zata iya farkawa ko yaushe goben. A taƙaice mu kam sai wajajen sha biyun dare muka shiga gida. A wannan darenma kwanan nutsuwa gami da farin ciki muka yi. Sassafe muka nufi asabiti ana muƙu_ muƙun sanyi. Ai kuwa Allah cikin ikonshi da amincewarshi sai muka samu Hajiya ta farka. "Amman wallahi da gaske bata da lafiya yanzu kam na tabbatar, duk da likitocinma sun tabbatar. Sai dai" hawan jinin da take ciki yafi yawa sama da cutar damuwan cewar likitanta. Na lura bata ko so da ƙaunar ganina. Ko da na gaisheta hannu kawai ta ɗaga mun taƙi magana dani sai mijinta da take ta manne mishi. Baifa samu sukuni ba har saida akai mata allurai bayan taci abinci wajajen ƙarfe goman safe kuma ance sai zuwa gobe zata farka. Sanda abokinshi da iyalinshi suka zo ma mu muna shirin tafiyane sai kawai "muka tafi tare dasu gidan nasu, ga matar Abokin mai fara'a da son mutane tana da wayewa sosai a yadda na fahimceta." Dan ko da muka isa gidansu tana ta haba haba dani har cikin ɗakin baccinta ta shigar dani. Muka zauna ga yaranta mata guda biyu ƙanana sai shige da fice suke yi. """Amarya ikon Allah ai mu bamu da labarin Alhaji Zaidu ya sake Aure. Mu munyi tunanin ya haƙura ma da" "Auren tunda matarshi ba barin yaran su zauna take yi ba""" Saita ƙarashe tana murmushi mai ɗauke da fassarar da ita ta barma kanta sani. Cikin mamaki nace. Banganeba ita take koran matan Maman Yasmin? Ai naga Hajiya bata da matsala. Har akwati tayi mun "fa, kuma tunda aka auroni take haba_haba dani""" Murmushi tayi tace. """Hmm Amarya kenan. Kin ganni nan? Ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya ta Auri Mijinku ni na haɗa Auren." "Kinsan Allah ita ke koran matan cikin ruwan sanyi. Da wannan kirkin da kikai mata ishara dashi. Kada in cika ki da surutu bari in kawo mana abin motsa baki""" Tana shirin sakkowa daga gado nayi maza na riƙeta. "Dan Allah Maman Yasmin ki sakani a hanya. Wallahi bana fatan abinda zai rabani da mijina wallahi Allah""" Murmushi tayi tace. """Wasa kike da wuta Sabuwa baki sani ba. Hajiya Munubiya Haɗari gareta fa sosai. Ta wuce duk yadda" za'a baki labarinta. Amman zan taimakeki zan haɗaki da ita ƙanwar tawa tana nan a Abuja tana Auren wani babban mai muƙami gwamnati ne a hannunsu ma. Zata fini sanin abinda zata ce miki. Kiyi ƙoƙari ki tabbatar da kun koma kin Haɗu da Aisha kun tattauna. "Nima zan tsokata miki abinda ba za'a rasaba. Ke dai ina zuwa""" "Fita tayi ta barni illahirin mamaki ya hanani sukuni wallahi Allah. Nasan Hajiya makircinta mai girma ne," amman ban taɓa tunanin ita ke koran matan da Alhaji ya Auro ba. Lallai akwai aiki a gabana domin daga kaina in sha Allah alkadarinta saiya karye. Saina nemi kab matan da Alhaji ya zauna zaman Aure dasu na haɗa ilimin zama da Hajiya ni na ba kaina wannan aikin. Ni dai ina zaune a inda ta barni ta dawo da tiren kayan ƙwalam da maƙulashe ta dure mana. Muna ci amman munyi shiru dukkanmu da abinda muke saƙawa a zuchiyarmu. Ni na soma katse shirun ta hanyar cewa. Amman Maman Yasmin Alhaji baisan wacece Hajiya Munubiya ba. Kuma bashi da ilimin sanin ita ke "koran mishi mata ko? """ Dariya tayi naga idanta cike da ƙwalla sai tsoro ya kamani. """Sabuwa Alhaji ya yadda da Hajiya Munubiya fiye da yadda ya yadda da kanshi. Bana tunanin zai yadda" da wata mace irin dai yaddar da yayi mata. Bashi da masaniya akan hali da makircin matarshi. Haka zalika danginshi basu da masaniya akan halinta. Baki sani ba. Macace fa mai haɗarin gaske. Sannan tasan kanta tasan takunta. Aisha ta wahala har bayan rabuwarta da Alhaji Zaidu tayi jinya sosai. "Shi dake ya ɗauki yadda ya bata bawan Allah baisan komai ba, gashi da kirki da son taimako wallahi haka" danginshi gasu dai da yawa amman suna da haɗin kai son juna da sanin ya kamata. Ai shawarar da zan baki ki yagi dukiya sosai ki zauna da shirinki nayi miki imani da Allah Hajiya Munubiya "ba zata bari Alhaji Zaidu ya rayu da wata macen ba sai ita kaɗai.""" Murmusgi nayi mata cikin ƙarfafa guiwa da miƙa lamurana ga Allah nace mata. Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya. Maman Yasmin Hajiya Munubiya ƙila alkadarinta ne zai karye shi yasa Allah ya haɗa Aurena da Alhaji Zaidu. Ƙila suma sauran matan wayo take musu tayi amfani da wayewarta da yawan shekarunta ta ɓarar dasu ko? "Ni bazawarace daidai gwargwado ina da ɗan ilimin rayuwa na zauna da kishiyoyi sun kai goma, kuma ko" "wacce da irin nata makircin take zuwa. Duk da sunci nasara a kaina amman na koyi darasi sun koya mun ilimi, shi wani wuyar rayuwar matattakalar ilimin mutum ne ba tare daya sani ba, gwagwarmaya na" "taimakon mutum a tafiyarshi musamman in da Allah ya dogara.""" Murmushi tayi mun tace. """Ya kamata mu shiga Kitchen mu san abinda zamu sarrafa musu suci rana tayi. """ Tare muka shiga Kitchen har muka gama girki hira muke yi kuma hirar ta shafi hirar mata da hirar rayuwa bai ɗaya. Sai azahar muka kammala komai. A lokacin su Alhaji sun mana sallama sun tafi masallaci. "Ni na jera kayan abincin a ƙasa, ita kuma ta kunna turaren wutanta mai daɗi shima ɗan Saudiyya wanda" duk yawanci in mahajjata sunje irinshi suke siyowa yana da farin jini sosai wani mai jan murfi da kwalbarshi irin na basilin ɗin maigurguwa. Saida muka kintsa ko ina kana muka tafi yin Sallah kuma. Mun yi sallah muna zaune muna ci gaba da labari muka jiyo sallamarsu sai muma muka fita. Maman yasmin taci abinci da mijinta a faranti ɗaya. Muma tare muka ci muna hirarmu ƙasa_ ƙasa. Sai kalaman soyayya yake faɗamun. Wallahi ni dashi sai naji ina tausaya mana. Ko yaya zanyi in Hajiya Munubiya ta rabani da farin cikina? Shi ɗinma yaya zaiyi to dan tabbas na yadda yana mun wani irin so marar misaltuwa. """Amman zan dai kaika Hotel ne ka ɗakko kayanku ko? Ai anan ya kamata ku sauka ga waje ko? """ Cewar Mijin Maman Yasmin. Dariya Alhaji yayi yace. """Ina za dai mu dinga wuni muku in kuka buƙata amman na riga na biya kuɗin ɗaki na kwana goma kaga" "ai ba'ayi asararshi ba ko? Maman Yasmin ya Aisha take a gidan mijinta? """ """Aisha tana lafiya tama kusan haihuwa ta biyu. Basu daɗe da barin Jidda ba ita da mijin""" Dariya yayi yace. """Aisha kenan. Yanzu ta girma kenan. Allah yaima zuriya albarka. Ga Amarya Maman Yasmin ai zaku yi" "ƙawance ko? Kin ganta bata da ƙawa, sai nine na haɗata ƙawance da Zarah da Anty Khadija""" Murmushi Maman Yasmin tayi tace. """To gani nima na zama ƙawarta in sha Allah, zamu dinga waya. Kafin ki bar Jidda ma zamu zagaya ni da" "ita akwai gidajen Hausawa mazauna nan Jidda duk zamu zaga""" Kallona yayi ƙasa _ƙasa yace. """To ke kinji baki ci ta zama ba""" Murmushi kawai nayi. Bamu muka bar gidansu Maman Yasmin ba sai wajajen goman dare. "Koda mukai wanka muka raya daren, ai saina tashi wajajen ƙarfe ukun dare na tadda Alhaji akan sallaya" yanata tulawa. Alwala na ɗauro na fito. """Al sa'ada sallah zaki yi? """ "Sallah zanyi masta in mana adda'a Allah ya bamu rabo mai albarka da amfani """ Murmushi yayi ya shafi fuskata. """Ni ya kamata inja sallar nan""" Ai kuwa shi yaja mukai ra'aka goma sai mukai wutiri. Dana saka goshina a ƙasa nake kai ƙaran Hajiya wajen Allah. Bayan mun idar ma na jima inata adda'a. Kafin na haye gado masta ya biyoni. """Ya kamata mu nemi Jidda yanzu ai ko""" "Ƙoƙarin guduwa nayi ya danneni da ƙirjinshi, dole na bayar da kai, amarci sosai mukaita yi Alhaji ya samu" dama sai murzata yake yi kamar tunkuza. Washegari muka sake komawa asibiti jikin dai da sauƙi. Alhaji na roƙa muka je umara. "Naita ɗawafi inata roƙon Allah ya bani nasara adda'a yi nake yi babu ƙaƙƙautawa, na tsorata na tsinke," na razana da lamarin Hajiya. Hajiya kuwa ko munje asibiti sai tai ta nuna ta damu dani taita jana da hira tana mun godiya. Harda Haƙuri take bani akan ciwo ya hanani Amarci. Cikin kwana biyar ta warke ras taita roƙon sai dai a koma najeriya ita tagaji mu koma kawai. "Ni kuma naita ƙarfafa Alhaji akan a barta ta gama, warkewa tas ni wallahi har bana son mu koma gida," sai in dinga jin wani irin muguwar faɗuwan gaba da zaran ma ance za'a koma gida. Mrs BUKHARI Ayi haƙuri sai jibi Juma'a kuma kunsan jikinne babu daɗi dauriyace kawai nagode. Son so "[10/16, 11:26 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 3 BABANGIDA:. Ta ɓangaran gidan Babangida abubbuwane suke ta cukumurɗewa babu dai sauƙi sai wanda ba'a rasaba. Ita dai Hamida ta kama sana'a ka'in da na'in duk wani gulma da cece kuce in anayi babu ita a ciki. "To inama taga lokaci ita da kullum a cikin dafa zoɓo da tace kunun aya dana zaƙi take, da kwaɓa fulawa." Babangida kuma harkar baban bola ta buɗe mishi sosai harma Allah ya haɗashi da uban gida ɗan China wanda ya jawoshi sosai jikinshi ƙarfi da yaji saida ya mayar dashi kamfaninshi na siyen ƙarafuna. Kuma yana da biranch a Lagos inta kama harda Babangida ake shiga Lagos ɗin domin ya tabbatar kayan sun isa lafiya an Auna an samu komai daidai kamar yadda aka ɗauro. Inda yake siyen kayan Baban bola kuma saiya jawo Aminu harma da Aɗɗa'u ya saka a kan harkar tare da babban yaron da suke aiki tare. Da ƙyar Baba malam ya amince da hakan har saida manya suka tawo daga Ringim suka shiga al'amarin "kana Baba malam ya amince ma Aminun tare da sharaɗin Aminu daya soma Jami'a zai bar aikin. Domin gudun kada abin yayi mishi yawa ga koyarwa' ga jagorancin littattafai a makaranta, ga karatu ga sana'ar baban bola." Ta ɓangaren Ƴar Shuwa ta fake sosai akan kasuwanci ta samu dama ire iren damammakin da matan da suke bin mazan banza da Aurensu suke samu. Su fake da sana'a domin su kawar da hankula a kansu. Ta kuwa ci galaba akan Babangida musamman yanzu da bai fiye zama ba sai take cin karenta babu babbaka. Har Bamaina take zuwa ta wuni cur a wajen Sameerah. Zarah kuwa itama tana zuwa daga Abuja ta kama hotel Ƴar Shuwa taita sunturin zuwa ba tare da sanin "Babangida ba. Abokan zamanta suna ganinta amman babu wacce ta damu da'ita kowacce harkar gabanta take yi. Suna dai ganin yadda Ƴar shuwa ke tsoma biyar ta wanke goma, ga yawan cin daɗi da bala'in tara mata a ɗaki a wuni ana shewa da sunan sana'a sai in itace da girki sai dab Magrib zata soma kacaniyar gyaran waje da ɗaura girki, dake bata rabo da miyar sutu shaƙe da namomi da kifi kala kala aciki, miyar tuwonma bata fiye rasawaba dan ta sai shinƙimemen frich itama ta zuba su cola cola da su 7up harda su mondin dew na Iyabo Allah sarki iyabo ta Hamma tsuntsun soyayya aminiya a wajen uwani" ta Balbalin. "Tana ta tara kayan jirajirai masu tsada, ko gwanjon data siya masu tsadane taba ƙawarta ta wanke mata" ta goge mata a gidanta. Kayan fitar suna kuwa babu wanda bata ɗinka ta adana a cikin adaka ba. Ɗan kuɗin da Babangida yake basu na kayan haihuwa tana dai karɓane tayi godiya ba dan zasu amfaneta ba. Ta tara kuɗin masu kauri a account ɗinta sanadin Zarah dan Zarah kuɗinta take kashewa sosai akan Ƴar Shuwa. Kamar dai kullum tana zaune a Kitchen ɗinta tana kwashe tuwon shinkafa da miyar agushi data yi taji "bushasshen kifi da kayan cikin Saniya. Ga lemunta na gwaiba tayi ta zuba komai a kula taje ta jera a daining ɗaki sai ƙamshi yake yi, su Fati kuma suna zaune ta sakar musu kallon katun suna tayi babu" ƙaƙƙautawa. Kulle ƙofarta tayi kirib dan yana daga cikin sabon salon data ɓullo dashi na kulle ƙofa ko da yaushe a cewarta bata son ƙura. Tana zaune akan sallaya idar da sallar nata kenan saita gasa tagumi ta rasa ta ina zata bi diddigin sanin "halin da Sabuwa take ciki su gashi yaran basa gidan, ita ba zuwa gidan Baba Malam take yi ba bare ta" doki cikin yaran taji wani ƙarin haske. Wata zuchiyar tace. """To amman ai gidan iyayen mijin sanannen gidane me zai hana kije Ranon kai tsaye kawai?" Wata zuchiyar tace. """ Lambar kishiyarta ko lambar mijinta zaki nema kota halin ƙaƙane""" Murmushi tayi tare da gyaɗa kai daidai Babangida ya turo ƙofa da sallama ya shigo yana sauke ajjiyar zuchiya. Da gani a gajiye yake tulus. "Da sauri ta miƙe ta karɓi ledar tsarabar dake hannunshi, yara kuma suka shiga yi mishi sannu da dawowa." Saida ya zauna kana yace. """Ki ɗakko faranti ki kididdiba tsarabar ki kaima kowacce ta ɗauki nata dana yara." "Akwai kaza biyu ce bansan ya zakiyi rabon ba. """ Baki ta taɓe kaɗan tayi murmushi. """To Jannaty angode""" "Miƙewa tayi ta fita, shi kuma ya bita da idanu yana tuno yaushe rabon da su raya sunna, indai a ɗakinta" yake sai dai ya ɗau haƙuri. Da yayi ƙorafi zata ce yanayin wannan cikin data samu ne yasa sunnah ta fice a kanta. Ya zaiyi dole ya yadda da'ita akan hakanne. "Dawowa tayi ta yayyaga kajin ta kasafta ta cire musu nasu ita dashi da yara, lemo da ayaban ma duk ta" raba ta fice ta soma da ɗakin Hala sai wani taɓe_ taɓen baki na iskanci take tata yi. Har dai tazo ɗakin Sumy ita kam Sumy Amir ne ya leƙo ya karɓa ya shige. Hamida kuwa tana tsaye a gaban firiza tana ba yaro zoɓo yazo siye Ƴar shuwa ta miƙo mata wannan tsaraba. """Angode Allah dai ya ƙara buɗi""" Tana dawowa ta tarar Babangida ya haye Daining yana cin abinci. Itama can ta nufa. """Yau kaji yinwa kenan Jannaty? """ """Ki bari kawai aikinmu baya bamu damar zama wani sa'in mantawa da kanka kake yi in ba sallah data" "zama dole ba. To ya gidan ya jiki jikin? """ "Dariya tayi, shima ya ɗanyi murmushi yace." """Gobe za'a koma asibitin ko? """ """Uhm gobe ne, kuma dama inaso zan leƙa gida na kwana biyu ban leƙa ba Mama bata jin daɗi jikinta" "ɗazu ta kirani take sanar mini""" """Assha Ubangiji Allah ya bata lafiya. Zan ɗan baki wani abun ki kai mata. Gobe zan wuce Lagos in Allah ya" "kaimu a ƙalla zan kwana biyar zuwa shida acan. Sannan akwai yiyuwar wata na gaba zamu China da ogana akwai aiki daya taso a kamfanin ƙarafanshi na can""" "Haka dai sukaita hira, har lokacin bacci yayi suka kwanta kai da ƙafa dan tunda Ƴar shuwa ta shiga" wannan ƙungiya take kwana kai da ƙafa da Babangida a gado. Shi kuma sai yayi amfani da wannan "damar a ɗakinta yafi raya dare wajen bautama Ubangiji ta hanyar tsaiwar dare, karatun Qur'ani." Kullum Babangida a cikin yima yara matanshi Adda'a yake akan Allah ya karesu da karewarshi Allah kada yasa abinda yayi ma yaran wasu ayi mishi shima. Washegari ya nufi Lagos ƴar shuwa kuma ta nufi asibiti daga nan ta tafi gidansu acan ta wuni. "Mama tayi mata alƙawarin da kanta zata je ta samu aminiyar Hauwa tayi mata kwatancen gidan Sabuwa," za kuma ta karɓo mata number mijin Sabuwan a soma ta waya in bai yiwu ba kuma sai tayi takakkiya. Ai kuwa da farin ciki da annashuwa ta koma gida tana jiran Mama ta kawo mata kyakkyawan labari. (Wato ɗan tsokacin da zanyi anan shine mata mu kula mu kula sosai da irin ƙawayen da zamu riƙe a "matsayin abokai. Duk da nasan wata ƙawar baka sanin muguwace ta ƙunshe muguntarta a zuchiyarta a zahiri kuma tana maka dariya in abun murna ya sameka ta nuna ta fiki ma murna, haka zalika inna baƙin cikinne shima ta nuna ta fiki damuwa dashi. Mafita ɗaya shine mu dage muita adda'a muna faɗama Allah cewar ya Allah ga ƙawayena a cikinsu in akwai wacce babu alkhairi a tarayyarmu Allah ka rabamu cikin sauƙi. Nima in akwai wacce shiga rayuwarta da zanyi bazai zame mata alkhairi ba Allah kada ka bani ikon shiga. Allah ka kareni da dukkan abun ƙi, ka azurtani da dukkan alkhairai. Wannan ya wadatar dake" na riƙe wannan adda'ar ina ganin haskenta. Wallahi ko ƙawace nayi Sabuwa saina nemi zaɓin Allah a kanta in da Alkhairi sai zuchiyata ta nutsu da'ita "in kuwa babu alkhairi sai kuga nama kasa sakin jiki da'ita, ni dama Mijina da yarana sune duniyata gaskiya)" Gaga_gaga al'amuran gidan Babangida suka ci gaba da tafiya. SABUWA:. Kamar kullum muna asibiti tun safe da Hajiya ta warke gaskiya kuma likitocin sun tabbatar mana da "hakan. Ta matsa mu koma gida, duk da shima aiki na najeriya yana jiranshi sai waye waye yake yi da mutane." "Wayar Alhaji na karɓa na fita, dama nakanyi hakan ba dan komai ba sai don in basu waje su tattauna" zantukansu na mata da miji. Lambar wayar Labbai na soma kira ai kuwa tana ɗagawa na jiyo muryar Maman Shafa da Cicib anata gabzawa. Cicib sai tattafa hannaye yake yi yana zage zage. """Hmm Kina dai ji ko Sabuwa? Ni sai nake ganin Aure kamar bai karɓemu bane. Tun jiya ake ruwan bala'i" a cikin gidannan Maman Shafa mitsiyaciya ta hana kowa saƙat. Jiyan saida na kwaɓe muka daku har Shafa saida naima shegen duka wallahi kafin fa suka shiga "taitayinsu.""" "To wai duk wannan akan menene Labbai? """ """Akan taga ina yin mangyaɗa ana siye, ina yin ƙuli ƙuli, masu kilishi ma Cicib na kai musu tunkuza suna" siye shine take tunanin shi ya bani jarin kinji fa musabbabin wannan rigimar da aketa faman yi taƙi ci taƙi "cinyewa""" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. "Allah shi kyauta ke dai ki kula da sana'arki kawai. Ya Adama ta saro kayan kuwa? """ Na tambayeta dan mu kawar da wancan zancan. """Ta saro kaya harta koma. Wallahi ko da muka yi waya jiya tace anata siye, kuma Hajiya Balaraba ta ƙara" "mata jari kuma ita ta haɗata da mai aikinta ta rakata kasuwa""" Wani farin cikine ya lulluɓeni har ajjiyar zuchiya saida na sauke tsabar jin daɗi nace da'ita. Saura su Aisha da su Rahama so nake suyi Aure tukunna. Yanzu dai in sha Allah gida zan dinga wadatawa da komai tunda Alhaji Zaidu yace zai dinga siya musu hatsi ni sai in dinga basu na cefane kinga yawo in "sha Allah ya ƙare in duka sukai Aure sai in basu jari ko wacce ta kafa kanta itama shikenan""" Mun jima muna hira kafin na kira gidan nanma aka saka a bayyane mukaita gaisawa harda su Hauwa dasu Raliya da magazin da Sama duk saida muka gaisa. Sama ya roƙeni jari zai zuba furobishon a shagon waje na ƙofar gida na mishi alƙawarin zuwa ƙarshen wata. Su Magazin kuma nace su ɗan ƙara haƙuri shi Magazin zan tuntuɓa ko Alhaji Zaidu ko Hajiya Balaraba in za'a sama mishi aiki dan su ka basu kuɗi kayi aikin banza ba jarin da zasu wani ja ƙarshe ma su cinye a shaye_ shaye. Ina gama waya dasu na kira Maigogul nanma mun jima muna waya ina kashewa na kira wayar Mardiyya duk muka gaggaisa da yaran sai naji sanyi a zuchiyata. Na jima a zaune inata waya kafin daga bisani na koma ciki a nanne Alhaji yake sanar mun zamu koma gida Najeriya nan da jibi. Mun shiga dashi kasuwa mun yo tsaraba sosai gaskiya. Mun je gidansu Maman Yasmin mun musu "sallama ta ɗauki lambar ƙanwarta da adireshinta ta bani a takadda, nima na ɗauki lambata na bata a takadda." Ranar talata jirginmu ya dira a kano da daddare misalin ƙarfe bakwai na safe. "A mugun gajiye na shige ɓarayina, ga gidan cike da ƴan uwan Hajiya harda ƙawayenta, ni kuma babu" nawa ko ɗaya. Ko dana gaishesu sai wani mele bakinsu suke yi ni kuwa nayi shigewata ciki. Sai naga halamun kamar an shigar mun ɗaki tabbas ni dai nasan ba'a buɗe ba bar sib ɗina ba. Tsayawa nayi a gaban sib ɗin sai naga kamar dai ba'a ɗauki komai ba amman ya zamemun dole gobe gobe in duba in tabbatar komai nawa yana nan. Banɗaki na faɗa na saki ruwan ɗumi a jikina idanuna a lumshe inata tunane tunane. Bayan na fito na nemi yadi mai sauƙi na saka na shiga Kitchen na haɗa tea na ɗebi cincin na dawo falo. Zan zauna kenan naji ana buga ɓarayina nasan ba Alhaji bane. Turyan turyan naje na buɗe. Ƙawayen Hajiyane bisa jagorancin Naja'atu ai kun tuno ta mai saka rigar bacci. Da fara'a na tarbesu na juya suka shigo duk suka zazzauna muka sake sabuwar gaisuwa. """Sannu da ƙoƙari Hajiya Munubiyace dama tasa muzo muyi miki godiya bisa jinyarta da kika jajirce kika yi," "angode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma haɗe kawunanku""" Cewar Hajiya Mansa kenan Amiyar ita Hajiya. "Ayya ai babu komai abunda yayi Hajiya tabbas shi yayi ni mun riga mun zama ɗaya""" Nan dai sukai mun sallama suka fita. Ni wallahi dana gama shan shayi na nayi isha sai nabi lafiyar gado. Wajajen goman dare naji shigowar Alhaji Zaidu. A bakin gado ya zauna yana mun murmushi. """Lallai Wazirat ke baccinki kika yi ma kin mance kece da kwana ne? Kin barni a sama inata juyi?""" Murmushi nayi nace. "Ai na zaci Hajiya ke da kai tunda ni kaga tare mukaita kwana acan ko?""" Fuskata ya shafa yace. """To ita kam Hajiya ta haɗiɗiyi magunguna tayi baccinta tace a soma rabon kwana daga kanki kiyi kwana" "biyu itama tayi kwana biyu""" Jawoshi nayi ya faɗo jikina dan yadda nake jin gajiya bana jin zan iya haurawa sama. "Ai kuwa a ɗakina ya kwana, mun sha soyayya sosai na lura Alhaji bashi da wasa ta fannin mu'amala bil" haƙƙi yake yi mun. In nayi ƙorafi sai yace bana isarshi ne ai shi yasa. Washegari dai da asuba daya fice na tashi nayi mana abun kari mai sauƙi dankalin turawa da ƙwai na soya sai shayi mai kayan ƙamshi kawai. "A samanshi na jera mishi komai na kunna buna na zuba turaren wuta, na jirashi ya shigo muka karya a" gurguje yace. """Muna da aiki a ofice da yawa fa. Amman yau ki zauna ƴan Rano sun yi mun waya zasu zo uhm""" "To shikenan nagode, dan Allah da daddare inka dawo... """ Bakina ya rufe da nashi mun ɗau lokaci a haka kafin ya sakeni. """Ba sai kin faɗa ba zamu je wajen Alhaji Baba. gobe in Allah ya kaimu sai muje Dutse mu kaima su Mama" "tsarabarsu""" Ai saina ƙanƙameshi gam. Sai kuwa daya samu nutsuwa dani kafin yayi wanka ya caɓa ado ya fita. Ni kuma na koma ɓarayina na shiga binciken sib ɗina saida na fito da komai na sake jerawa. Ɗankwalin jar atampatane ban gani ba sama da ƙasa. Kuma ko ana jibi zamu tafi tabbas naga ɗankwalin. Ai take hankalina ya tashi ainun. Na gama mayar da komai kenan na jiyo dirin motar Ƴan Rano ko dana leƙa Bus guda suka ciko yaran mata da dattijai. Kaya na sake daga cikin kayan da na tafi dasu dan wallahi kayan sib ɗin duka sai naji ni bamma yadda dasu ba. Fita nayi na samesu a ɓarayin Hajiya anata gaisawa. """Amarya sannu zo ga waje ƴar albarka""" Cewar Yaya Tani kenan. Gefenta data nuna mun naje na zauna aka gaggaisa suna ta jinjinamun bisa ƙoƙarina. Hajiya na ƙara basu labarin ƙoƙarin da nayi. Kamar minti talatin da zuwansu na dubi Zarah nace. "Zarah muje mu ɗaura sanwa ko? """ Yaya Tani tace. """Hauwa aikin me take yi da ke sai kin ɗaura girki. Baki da Ƴar aikine ke a ɓangaren naki? """ Murmushi kawai nayi Hajiya tayi carab tace. """Kema kya faɗa har sau biyu na nemo mata masu aiki wallahi wai ita bata so dole na haƙura Alhaji kuma" "yace tunda bata so a barta""" Shiru Yaya Tani tayi can tace. """Ai ba'a haka ita ya kamata ace ta nemo ƴar aikinta da kanta ai bawai kishiya ce zata nemo mata ba. Ko" "ni nan bazan yadda da hakan ba, ko ɗiyata bazan yadda ayi mata haka ba. Sabuwa ya kamata ko matar Babanki kima magana ta nema miki mai aiki ta ɗan dinga rage miki aiki. Amman abinda zamu ci Hauwa zata sarrafa mana tunda zuwan na Hajiyane kuma a ɓarayinta muka yada zango kada ki damu""" Hajiya dariyar yaƙe kawai take yi. Tare da maganganun data tabbatar ta kare kanta sabida gudun zargi. "Na fahimci kamar Yaya Tani bata shiri da Hajiyane, ko kuma macace mai faɗa da bata son wargi." Duk da haka saida na ɗaura farfesun kaza guda uku suke nan a firjin cikin awa guda ta dahu dake kajin gidan gonane na juyo musu a ƙatuwar kula na kawo musu. Ai kuwa sunji daɗi sosai. Wuni sukayi ko da zasu tafi na ɗebo sabulai da man Shafawa nace akaima "Goggo amfana, ina da ragowar farfesun naman kai na cika kula dashi nace akai mata." "Bamu sake haɗuwa da Hajiya ba har saida Alhaji ya dawo, yaci Abinci ya shirya da zamu je duba su" Maigogul ne muka je falonta na duba jikin nata tana zaune tana shan fura. """Bari ina zuwa ko? """ "Ta miƙe ta shiga ciki, sai gata da leda fara ta miƙo mun wai in ba Uzairu zuchiyata." "Godiya nayi mata, na fita na ɗan basu waje ko zasu yi magana." "Ya kai kamar minti goma haka ya fito ya sameni muka wuce, muna tafe muna hira har muka isa gidan." A falo muka tarar dasu suna cin abinci Uzairu zuchiyata dai baya ciki. Maigogul da sauri ya miƙe ya nufo mu sai murmushi nake yi mishi. """Lolona ashe kuna hanya, dafa nace gobe in zan wuce Dutse zan biyo ta gidan naku mu gaisa ashe kuna" "hanya Alhaji Zaidu? """ Hannu ya miƙa mishi suka gaisa da girmamawa sosai. Sannan muka zube a ƙasan kafet ga tsaraba niƙi niƙi. Mun jima sosai a gidan kafin daga bisani mukai musu sallama suka rakomu har bakin mota. "Muma gobe zamu shiga Dutsen in sha Allah""" Baki Maigogul ya washe yace. """Allahu Akbar to ai shikenan tazo gidan sauƙi saimu tafi a jere, goben zan biyo ta gidan naku sai mu wuce" "daga nan""" "Ni dai banso yace haka ba, amman tunda Alhaji ya amsa yana iya dole na haƙura a hakan." Ko da muka dawo Hajiya ta rufe ɓarayinta sama muka haye muka raya darenmu da farin ciki. Washegari ina gaban akwatina ina haɗa kayan tsaraba Alhaji ya shigo saye da farar shadda yayi kyau sosai. Ya nemi waje ya zauna a bakin gado. Yace dani. """Wani abune ya taso mun wallahi wasu fulotaine gwamnati zata yanka a Kaduna sai yanzu ake sanar" "mun. Yana da kyau in kasance a wajen sabida zamu samu alkhairi sosai Wazirat ga maganar tafiyarmu Dutse kuma""" Zama nayi kusa dashi nace. To ai babu komai inka amince mun ba sai in bi Maigogul mu tafi tare ba in yaso in zai dawo ma dawo "tare, in kuma kwana biyu zaiyi kai sai kazo ka ɗaukeni mu dawo ko? """ Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. """To shikenan hakan ma yayi wazirat. Akwai kayan abinci da tun jiya da daddare nasa aka loda a bayan" "motar da zamu tafi dashi sai a kwashe ga keyn motar da baƙar zan tafi in kin kwashe ki ba Hajiya keyn.""" Kuɗi ya zaro a ajjihu masu kauri kashi kashi ya kasafta har Madamcy saida yace ga nata da Rita. "Yace kuma zai tura mun wasu a account in ba su Mardiyya""" "Allah ya saka da alkhairi nagode sosai. Dan Allah inaso zanje gidan kakannin su Mardiyya in dubo su," "sabida zan gaishe da Baba Malam kakansu in ka amince amman""" Shiru yayi yana kallona can dai ya miƙe tsaye. """To shikenan. Ina fatan ba a gidan Babansu yake ba ko? """ "A_a ba'a nan yake ba""" """To kije ba damuwa, jibi zan zo sai mu dawo in sha Allah. Tunda Kaduna ayau zanje a yau zan dawo inna" "gama ma Hajiya kwananta sai inzo ko? """ "Murmushi muka yi ma juna, muka sakko tare na jirashi yaje yayi sallama da Hajiya." Sai ta biyoshi ni a wajen nayi mishi adawo lafiya nayi komawata ciki naci gaba da shiri. Ya tafi bai jima ba sai ga Uzairu zuchiyata da maigogul ina jiyosu suna gaisawa da Hajiya nazo na buɗe musu muka shiga. Ko zama basu yi ba aka shiga buga ƙofa haka na koma naje na buɗe Hauwa ce da kular abinci. Godiya nayi mata na karɓa na shigo. "Maigogul ya riƙe bakinshi yana kallon ikon Allah, nima abun mamaki ya bani lamarin Hajiya yana" firgitamun lissafina. "Ga batun ɗankwalinnan dana rasa wallahi hankalina yayi mugun tashi, gashi zan kuma tafiya in bar gidan" bansan meye zai sake biyo baya ba. Allah kaɗai yasan ma mai akayi mun a ɗakin gashi bansan ta inda zan ɓulloma Alhaji da maganar ba. Amman maigogul zan soma faɗama ko zai mun mafita. Ku bani shawara dan Allah wallahi ina cikin tsaka mai wuyar fita. Mrs BUKHARI "[10/20, 8:03 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 4 "Wai me zan gani lolo, abinci ta aiko mana dashi almurar? Ohh so take ta asircemu kenan, ko tana nufin" "mu mayinwatane dan kawai munzo bakya nan ta bamu abinci mun miki kara munci? Ai kuwa wannan abinci saidai ki zabtara ki zuba a leda in zamu fita mu fita dashi ma zubar a hanya, ba zata siyemu da" "abinci ba, munfi ƙarfinta wallahi tana wasa da nine bata san kura bace tayi lafiya ba""" Uzairu zuchiyata dariya harda riƙe ciki. """To ai gaskiya ne Uzze wallahi jikina yana bani tana da muguwar nufaƙa a zuchiyarta sosai. Ki dai bi a" hankali wallahi. "Lolo nace kin yo ma su kayi nayi ƴar tsaraba kuwa? """ "E nayo Maigogul zan tafi musu dashi. Alhaji wani abunne ya taso mishi ya tafi Kaduna ku zanbi muje""" """Eh ya kirani ya tura mun kuɗin man fetur wallahi. Yanzu abinda za'ayi mu dai mun karya Hajiya ta haɗo" "mu da soyayyar kaza da fura suna mota shiryo kawai mu kama hanya. """ Sama na haura na fito da kayana na kulle uwar ɗakin saida na kalli komai tsab domin in tabbatar da a yaya na bar ɗakina kana na gangaro. Leda na samu na juye rabin farfesun da doya a ciki na ƙulle a leda muka fito. Kulolin na niƙa ma Hauwa harda godiya naima Hajiya data kafa ta tsare a babban falo tana jiran fitowarmu. Maigogul ma harda godiyarshi. Hajiya har gaban mota ta rakomu ta tafi taƙi tafiya dole haka na buɗe bayan motar Alhaji Uzairu zuchiyata ya ɗebe kayan abincin ya dawo dashi bayan motar Maigogul duk Hajiya na tsaye. Keyn motar na miƙa mata mukai mata sallama. Har motarmu ta fice a gidan Hajiya na tsaye a wajen. Muna tafe Maigogul da Uzairu zuchiyata suna ta hirarsu suna dariya ni kuma nayi shiru inata tunanin rayuwata da irin kishiyar da kuma Allah ya jarabceni da'ita. """Lolo na lura tunda muka kamo hanya kike karanta wasiƙar jaki. Shin menene matsalarki?" "Kada kiyi sake ki rasa Aurenki Hajiya tayi miki wani abunne kome? """ "Ajjiyar zuchiya na sauke na zayyanama Maigogul komai da komai da yadda muka yi da Maman Yasmin," da ɗankwalina dana rasa dan wallahi abun ya dameni sosai hankalina baya jikina akan wannan ɗankwali. Hawaye na share na sauke kaina ƙasa inajin wani irin ɗaci. """Tabb kikace me lolo. Itace ke koran matanshi fa kikace. Ita Aishan da aka baki lambarta kin nemeta ne?" """" Maigogul sai zazzare idanu yake yi. "A_a ban kirata ba tukunna. Bansan me zance mai bane ya barni inje Abuja ba shiyasa""" Ai sai Maigogul ya faka mota a kan titi tunda a lokacin muna daf da shiga dutse ne. """Lolo kwana nawa ya baki kiyi a Dutse? """ "Kwana biyu yace jibi zai zo mu tafi tare""" """To ya zama dole muje in kai ki Abuja. Ni da kaina zan kirashi in roƙeshi zaku rakani ke da Uzairu" "zuchiyata muje mu dawo a goben inta kama ma sai mu tafi tun biyar na asuba mayi sallar asuba a hanya sabida mu samu mu dawo a goben, nine kaɗai zan iya tsaya miki a duk abinda ya shige miki wallahi wallahi ta Allah bata Hajiya ba. Ke kayan tsubbuna fa ba zubarwa nayi ba. Kuma ina da tulin tarin abokai masu tsubbu wasu da rauhanai ma suke aiki fa afa bini a hankali. Lolo kada kiyi sake da adda'a kuma kita tsayuwar dare. Ke da izinin Allah asirinta saiya tonu. Ki mayar da hankalinki kan aikinki kuma ki dena shiga ɓarayinta in ta fito ki leƙo ku gaisa, ke inma zaki shiga ki tabbatar tare dashi zaku je kudun kada ta" sheƙa miki wani abun. Sannan batun ɗankwalin data turo aka ɗauka bazai wuce ƴar aikinta ta saka wannan aikin ba. In kika dage da adda'a shikenan. Zan rakaki wajen Baba Malam muyi mishi bayani ko da taimakon da zai bamu ta Allah ba tata ba. "Lallai Lolo dole kiyi shiru ki kasa magana, domin zama da makiran mata abune da bashi da sauƙi. Kada ki" "sake ki faɗama kayi nayi halin da kike ciki dan terere zata yi miki kinsanta ba'a abun arziki da'ita sam.""" Ajjiyar zuchiya na sauke. Ni kaina dama nayi niyyar in tunkari Baba Malam da lamarin nasan zai taimaka mun sosai. Motarmu muka ja muka shiga garin Dutse. Sai gamu a layinmu a ƙofar gida. Magazin na zaune a benci a ƙofar gidan yana ta busa hayaƙi ya hangomu ba shiri ya wangale get Maigogul ya shiga da motar har cikin gida. "Su Rahama duk suna tsakar gida, da ƴan ɗakin Hauwa." Ganinane yasa su Rahama duk suka miƙe suka tawo bakin motar. """Ahh mutanen Jidda kece a tafe tare dasu Maigogul mu muna shirin zuwa miki ashe ke zaki zo mana""" Cewar Rahama data buɗe mun murfin motar na fito. Layuza ta dubeni sama da ƙasa sai ciwon hassadarta ya motsa. "Wallahi kinganni na biyosu in zo in ganku. Ina Rakiya fa? """ """Kayi nayi ai tun sassafe ta fice da buhu kema fa kin sani." "Madamcy kuma sun tafi Asibiti da Sadiya da Hauwa Haihuwarce""" Maigogul ya fito yace. """Wato kayi nayi koda nace mata zanzo yau shine ta tafi kayi nayinta ko? Ai shikenan Lolo muje sama ki" "huta kinji""" "Shigewarshi yayi yana saɓa malum _malum, ko da Layuza tace mishi sannu da zuwa hannu kawai ya" ɗaga mata baiko kalleta ba. Muka bi bayanshi yuu. Magazin kuma aka barshu da tiri tirin fito da kayan abinci tare da haurowa dasu sama. """Lolo ashe kun dawo daga jiddan ya jikin kishiyar taki kuwa?""" "Cewar Raliya""" "Wallahi mun dawo Raliya jikinta da sauƙi sosai """ Sama muka haura da kayayyakin tsarabobin dana yo musu. A falo muka zube nan muka shiga ɓarin zancen yaushe gamo anata dariya da musu. """Ke Lolo Sadiya ta faɗa miki kuwa madubala yazo gidannan har kusan sau uku ma? """ Ras naji gabana ya faɗi na dubi Magazin daya dure buhun shinkafa nace. "Magazin takashin labari bani to in sha""" """Wallahi kawai ranar farko ne yazo da ledarshi shake fal da kayan shayi ya kawo ma Rakiya fa. Shine tace" mai ko zai Auri Aisha ko Sadiya tunda ke kinyi Aure. To shine bayan yayi zuwa na biyun Rakiya ta sake taranshi da maganar dai. "To zuwa na uku wajenta yazo sukaita hira a ƙofar gida in faɗa miki, amman fa yace tayi haƙuri bazai iya" "Aurenta ba kinji yadda akayi fa.""" Murmushi nayi kawai na girgiza kai. A raina nace. Allah sarki madubala Ubangiji Allah ya ɓullo maka da wacce zaka so ta fiye da yadda muka kasance a baya. Muna cikin hirarmu Hauwa tayi kiran waya Madamcy ta haifi ɗiya mace suna asibiti babu yadda take hawan jini ya rabketa. Gaza dai ya turo dubu goma gashi sun ƙare tas. Rahama ce ta miƙe tace. """Ku harhaɗo maza inje asibitin Uzairu zuchiyata ɗan Hajiya ko kai zaka ɗauki nauyin komai? """ Ta faɗa da zolaya. """Rai dai Rahama ke dai bari in auri Felisha zaku sha mamaki nifa kuɗaɗe zanta turowa ina siyan gidaje" "wallahi sabida ko ta sakeni na fita da fitata dan ba mutunci bane dasu akwai wani abokina da yake Auren Baturiya wallahi da muke hira yake faɗa mun kullum a cikin faɗa suke da kai ƙararshi kotu, muna kan" "wayarma ta fisge saida taji muryata shine ta sauke ajjiyar zuchiya""" Dariya muka tuntsire dashi dukkanmu Bana Uzairu zuchiyata yayi abun kai har nera dubu biyar ya bayar ni kuma na bada dubu ashirin Rahama ta saka kai ta tafi. Saida nayi sallah kana na rarrabe tsarabar dana kawo lokacin Maigogul ya fito yana falon yana waya da Hajiyarshi sai kashe murya yake yi yadda kuka san tsohuwar karuwa. "Har su Layuza saida na musu tsarabarsu nasa Aisha ta kai musu, sai ga Raliya ta hauro godiya." Ni dai ina yin sallar la'asar na sake kaya na fito shar dani tare da tsarabar su Mardiyya da Baba Malam. Har zuwa wannan lokacin Rakiya bata dawo ba su Aisha suna Kitchen zasu ɗaura abinci. Dubu biyar na basu nace a siyo kaza ƙatuwa a fasheta a cikin jallof ɗin. Maigogul ya tusani gaba sai gamu a ƙofar gidansu Babangida almajirai cike anata karatu Baba Malam na zaune akan kujerarshi ya hangomu mun nufoshi. """Sabuwa Maigogul kune a tafe? Lallai yau ina da manyan baƙi. Kai magajin malam shiga zaure na uku ka" "shinfiɗa mana keso maza""" Ai kuwa sai Malam ya miƙe yayi gaba muka bishi har zaure na uku. Ins hango zuwanmu gidan na farko lokacin ina ɗauke da cikin mardiyya a wannan zauren muka zauna. Rayuwa kayan Allah komai mai wucewane ada inna doso zaurukan gidannan sai inji tashin hankali dan nasan dole in shiga in tarar da ɗiban albarka da rashin mutunci iri _iri daga Malama Babba. Amman yau gani a gaban Baba Malam hankali kwance. Bayan mun gaisa sai nayi shiru shi kuma Maigogul sai ya zayyanama malam Halin da nake ciki. Ya ɗaura da cewa. """Ni da naso in mata kiranyen aljanu ma. To amma wallahi na tuba kawalcinma bana yi sam sa'ar da taci" "kenan wallahi Malam, itama Sabuwan nasan ba zata bani haɗin kai ba shi yasa ma." """Ashsha banji daɗi ba. Haƙiƙa zama da irin sheɗanun matannan akwai haɗari sosai. Amman babu komai" "zan mata rubutu gobe Babangida da yaran sai su kawo mata, ki dinga sha kina shafe jikinki in sha Allahu babu abinda zata miki yayi tasiri. Sannan ni da su Aminu zamu yi sauka mu miki adda'a sosai." Ai maganar turen aljanu shirkace Maogogul na kuma ji daɗi sosai da kace ka tuba. Abinda ya kamata shine mai zai hana da kai da iyalai ku shiga makarantar magidanta ku yi karatu abubuwan zasu kuma "sauƙi sosai """ Maigogil yace. """Dake ina da iyali kasan acan Kano Dutse shigowa nake yi duk sati in koma. Su dai sai su shiga" makarantar. Baba Malam izifi talatin cib akwaishi a kaina kuma na iya baƙi aikine dai dashi ba'ayi kuma "babu sanin fassara bare mutum yasan ma'anar""" Ya ƙarashe yana wannan dariyar ta baƙin ciki. """To ai ta kwana a gidan sauƙi in sau ɗaya zaka zauna a aji, ko majalisin karatu zaka ƙaru sosai. A Kano ga" manyan malamai suna karatuttuka da littattafai in kana so sai in haɗaka da gadon ƙaya ko Dr Sani rijiyar lemo ka dinga zuwa majilisi kana sauraren karatu. Kuma in ka shigo Dutsen ma zaka iya shigowa tamu makarantar a hakan ka dinga ɗaukar darasi da tuban zaifi tafiya da kyau yadda za'a bautama Allah bil "haƙƙi.""" """To shikenan zan dinga zuwa makarantar in na shigo. Suma su kayi nayi zan musu tayi in suna so ai sai su" "dinga zuwa wallahi mun gode Baba malam sosai""" """Maigogul ina abokinka Cicib? """ Dariya suka yi du su biyun ni kuma nayi murmushi. """Ki soma shiga ciki Sabuwa ku gaisa da Ƙarama sai ki fito mu shiga makaranta kiga yaran naki""" "To shikenan. Ga tsaraba na kawo maka""" Na ajjiye ledar na shiga cikin gidan da tsarabar yara dana Malama Ƙarama. Tayi mamakin ganina sosai kuma da fara'a sosai muka gaisa na bata tata tsarabar na fito. Bisa jagorancin Baba Malam muka shiga makarantar anata ɗaukan darasi "A ƙofar ajin su Mardiyya muka tsaya, tana tsaye tana koyarwa abun sha'awa tana hangomu ta fito da" sauri ta rugunƙume maigogul sunata dariya. """Ƴar nema"" Cewar Maigogul, murmushi Malam yayi yana kallon mardiyya." Malama da Aɗɗa'u suna aji suka hangomu ai da gudu suka iso inda muke. Duk muka ɗunguma zuwa ofishin Aminu Yana zaune yana ba wata matar Aure littafin arba'una hadith muka shigo Baki ya rufe ga murmushi ga hawaye a fuskarshi. """Ja'iri ƙaraso mana""" Cewar Maigogul yana wannan dai dariya da kuka santa ƙarasowa yayi ya riƙe hannuna. """Ummi kece kika zo mana. Yaushe kika dawo?""" Shafar kanshi nayi. "Nice Aminu ya karatu? """ Murmushi yayi ya dubi ƙannenshi suma suna cike da farin ciki. """Adda dama kinsan Ummi zata zo shine baki faɗa mana ba? """ Mardiyya tace da Aminu. """Bata faɗamun ba nima ganinta kawai nayi""" Ofishin Baba Malam muka shiga acan mukayi hirarmu na basu tsarabarsu na ƙirgo kuɗi na basu nace su sai wani Abun. """Ummi bikin Adda amman dake za'ayi komai ko dan Allah? """ "Dani za'ayi Aɗɗa'u zan zo tun saura kwana biyu soma bikin in sha Allah""" Ai sai farin ciki ya lulluɓesu. Baba malam yana kan teburinshi yana rubutamun addu'o'i a jikin takadda da zamu tafi ya miƙo mun. Nan mukai sallama dasu muka tafi akan gobe yara zasu kawo mun rubutun. Muna hanya Alhaji ya korawoni mun jima sosai muna waya. Mun isa gida mun tarar kayi nayi ta dawo suna ta cin abinci dake magriba har tayi lokacin Saida nayi sallah nazo muka gaisa da kayi nayi. Su madamcy kuwa har lokacin suna asibiti Gaza ma yazo yana can asibitin tare dasu. Da daddare ma mun kai kusan minti talatin muna waya da Alhaji kafin ya kashe wayarshi yace ga Hajiya nan ta hauro sama. Kuma Maigogul ya sanar dashi gobe zan karashi Abuja wajen Iyalan Amininshi ya amince mun inje. Ajjiyar zuchiya na sauke Ai kuwa washegari asussuba ni da maigogul da Uzairu zuchiyata muka fito da zummar nufar Abuja. """Wai maigogul me akeyi to a Abujan da zaka kwashi yara ku tafi. Ke Lolo wai meke faruwane nace miki?" "Ka mayar da ƴaƴan cikin ka abokan yawonka ko ina dan masifa kuna tare wannan dai abu da zafi yake""" "Babu komai Rakiya ai yau zamu dawo""" Tsaki tayi tace. """Allah ya tsare in kun so ma daga can ku wuce Kano ai Allah yana ganin irin zaluncin da maigogul yake yi" "mana. Ku kuma bamu bane a gabanku barinma Uzairu zuchiyata sallamammen banza. """ Maigogul zaiyi magana nace. Dan Allah maigogul kayi shiru. Rakiya dan Allah ki dinga sanyaya ranki. Wallahi ba wani abun muke "ƙullawa ba kawai gidan wata zamuje su rakiya kawai zasu yi mun""" """Au ta huɗu kuka samo mishi? Ai kuwa na rantse miki da Allah in ya ƙaro wani Auren duniya zan shige" "uban kowa ya huta.""" Wallahi dukkanmu saida muka dara """Rakiya kenan makirar mace. Allah ya shiryeki mu sai mun dawo. Kuma yau zamu dawo sai ki shirya" "tarbata ai kamar yadda Hajiya Balataba take mun ta soya kaji da basmati tana jirana. Ke kuwa koda na faɗa miki ina hanya bai hanaki zaran buhu ba.""" Motarshi ya ja Sama ya buɗe mana get muka fice. Sai a hanya muka dakata mukai sallah muka naushi hanya awanmu bakwai tafiya yankin Azaba. """Bani takaddar adireshin in gani, dan babu inda ban sani ba a garin Abuja. """ Jakata na zaro na ciro takaddar na nuna mishi ya riƙe baki. """Wuu anguwar manyan kenan. To ki kirata kafin muje a sakar mana kare""" Uzairu zuchiyata da yake ta waya ai sai dariya. """Wallahi akwai gidan da muka taɓa kai wasu mata anan Abuja ashe karene mai gadin gidan. Muna tura" get karennan ya taso mana gudun kilomita nawa kunsan muka yi? "Cicib dai har takalmi da Ɗankwalinshi sai da ya yar. Munci wuya""" Munyi dariya kamar zamu mutu Uzairu zuchiyata faɗi yake. """Wayyo cikina zan mutu. Ƙyal ƙyal ƙyal ƙyal""" "Mun jima muna dariya wallahi, baza ku gane ba ina mugun son ahalina koba komai za'ayi dariya ayi raha." Kiran Aisha nayi ringin biyu kuwa ta ɗauka da sallamarta. Gabatar mata da kaina nayi sannan nayi mata bayanin gani a Abuja ma inaso inzo gidanta. Ai kuwa ko a muryarta ta nuna jin daɗinta sosai ta sake yi mun kwatance duk da nace mata Maman yasmin ta bani adireshinta. Cikin minti arba'in sai gamu a ƙofar gidanta. Waya nayi mata tasa maigadi ya buɗe mana get muka shiga ciki. Tana tsaye da ƙaton cikinta a gaba fara kyakkyawar mace mai gashi sosai. Da fara'arta ta ƙaraso. """Ahh har da su Baba kuke. Sannunku da zuwa. Baba mu shiga ciki maraba""" Tare duk muka ɗunguma zuwa falon gidan wanda yaci kuɗi daidai gwargwado. Zama muka yi aka sake dasa sabuwar gaisuwa kafin kuma falon yayi shiru. Mai aikice ta shigo da kular abinci da komai a ƙaton faranti ta ajjiye a gabanmu tare da gaishemu cike da ladabi duk da dattijuwace. Miƙewa tayi da ƙyar tace. """Bari in baku waje kuci abinci ko""" Ta saka kai ta bi wata ƙofar. Abincin na zuba mana jalof ɗin kuskus ne da soyayyen kaza na cikin jajjagen yaji sai lemukan sha. "Maigogul na soma zuba ma, ni da Uzairu zuchiyata kuma na zuba mana tare ni dai duk hankalina ma" baya jikina wallahi komai ma dauriya da ƙarfin hali nake yi. Abincin kanshi loma uku kawai nayi na ajjiye lokalin nayi shiru ina sauraren yadda gabana ke ta aikin dokawa. """Lolo mu kam zamu je mu dawo kafin ki gama abinda ya kawoki zan leƙa abokaina." Duk abinda ya kamata kuma ya dace ki sani kada ki mance ki nutsu ki tambayeta da kyau. Taso muje "Uzzy""" Sallama sukaimun suka wuce. Suna fita Aisha ta shigo da fara'arta. """Su Baba sun tafi ne? """ "E kusan hakan zance yace inna gama in kirashi sai mu tafi dake yau zamu koma Dutse""" """Ayya. To mu shiga kiyi sallah tukunna dan labarin gaskiya da tsayi in dai labarin Hajiya Munubiyane""" Binta nayi har zuwa ɗakin baccinta mai kyau komai na cikin ɗakin ruwan hoda da ruwan maimo. Banɗaki ta nuna mun na shiga na ɗauro alwala na fito ta nuna mun gabas nayi sallah. Na jima sosai akan sallaya inata adda'a na shafa kana na fuskanci Aisha. "Na idar ke kawai nake saurare Aisha akwai magana a bakinki sosai Maman Yasmin ta faɗa mun""" """Ƙwarai akwai magana a bakina Sabuwa. Kin ganni nan? Bala'i ido da ido babu wanda ban gani ba. Dan" "ko da Alhaji ya sakeni nafi shekara guda ina jinya in faɗa miki zan iya kaiwa shekara biyu ma Amman me kike son sani akan Munubiya? """ Jikina ya sake mutuwa mus ajjiyar zuchiya na ja na sauke da tauri. Inason sanin wacce hanyar tabi ta koreki a gidan Alhaji Zaidu. Sannan da wanne salon tayi amfani har "taci galaba a kanki? """ Dariya tayi mun ta muskuta ta gyara zamanta. """Bani kaɗai ba ko Sumayya haka tayi mata ta koreta.""" Idanu na zare nace. "Ke ya soma Aura kafin Sumayya ko ita ya soma Aura? """ """Ita ya soma Aura. Itama yanzu haka tana Abujannan tana Aure a zone 2 muna zumunci dan ko da nayi" "haihuwar fari da'ita akayi komai""" Dafa cinyarta nayi nace. "Aisha ko zaki taimakeni muje gidan Sumayya mu haɗu mu tattauna baki ɗaya in babu damuwa? """ Miƙewa tayi ta buɗe cib ɗinta ta ɗakko mayafinta da jakarta. """Muje babu wata matsala. Domin Sumayya matsalar data shiga ai tafi tawa yawa.""" Miƙewa nayi babu guiwa wallahi illahirin jikina sai naji rawa yake yi. Illar rashin bincike a Aure kenan haƙiƙa ƙila da anyi bincike da za'a iya gano halin Hajiya munubiya duk da hatsabibiyace sosai. Amman ni kaina baƙin tarihin rayuwar ahalina yasa bamu damu da yin binciken Alhaji Zaidu ba. Domun yayi ƙoƙari namijin ƙoƙari da ya gama jin tarihina kuma ya aureni a hakan ba tare da nuna mun ƙyama ba sai tsagwaron so. Dafani Aisha tayi na dawo hayyacina. """Muje ko? """ "Mai gidanki baki kirashi ba ko babu matsala? """ """Ya yarje mun inje duk inda zani, ba matsala""" Fitowa muka yi ni dai jan ƙafata kawai nake yi sai naji ƙafata ta hannun hagu kamar ta samu matsala tayi nauyi sosai janta nake yi bana iya ɗagawa. Ƴar aikinta ta sanarma mun fita ta kula da yarinya tana ɗakinta tana bacci. A hankali ta dinga tuƙin ga ciki him a gaba. Muna hanya ta kira Sumayya ta tambayeta ko tana gida. """Ina gida Sista Aisha zaki zo ne? """ """Eh muna hanya tare da baƙuwa sai munzo to""" Wayar ta kashe ta dubeni tace. """Mun taki Sa'a tana gida""" Yaƙe kawai nayi mata. Muna tafe har muka iso get ɗin gidan Sumayya gidajene na sama sama guda shida a tsaye sai babban get kewaye da katanta. Ga motoci birjik a cikin haraba. Muma ajjiye tamu muka yi muka nufi gidan Sumayya Allah yasa a ƙasa take ba a sama ba. Kwankwaasa ƙofar Aisha tayi mai aiki tazo ta buɗe mana muka shiga. Gaskiya ana faluka a gidajen masu dashi dake ni ban saba da ganin irin haka ba nadai saba da falukan "faƙarahu alal lalurati ƴaƴan malam Shehu irinmu""" Ruwa aka kawo mana sai ga Sumayya ta ɓullo ta wajen Daining da dukkan Halamu Kitchen ne a wajen. """Aisha sannunku da zuwa. Baƙuwa maraba lalenku""" Gaggaisawa muka yi Aisha ta gabatar mata dani da abinda kuma ke tafe dani. Kallona ta shiga yi tana jijjiga kanta ta jima a haka hawaye suka zubo mata a kumatunta. Kalmarta ta farko itace. """Sabuwa in kina son lafiyarki da rayuwarki ki rabu da Alhaji Zaidu cikin ruwan sanyi wallahi. In kika ƙi ƙila" "ƴan uwanki ne zasu fitar dake cikin halin jinya. Dan na rantse miki da Allah Hajiya munubiya ba rabaku kawai zata yi ba saita tabbatar ta nakassa rayuwarki""" Kunji ƙudurar Allah ko? Ga ƙafata sai sake nauyi ma take yi Mrs BUKHARI Mu tara gobe in Allah ya kaimu "[10/21, 9:08 AM] BADA'AT IBRAHIM:" https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=wwc MRS BUKHARI 5 TASKAR BADI'T WANNAN SHINE JADAWALIN SHIRYE SHIRYENMU DA WANNAN TASKAR TAKE GABATARWA YAYIN DA BA'A LITTAFI DOMIN ƘARUWARMU BAKI ƊAYA MU GUDU TARE MU TSIRA TARE. MASU SON KASANCEWA TARE DA MRS BUKHARI GAREKU GA LINK NAN DUK MAISON KASANCEWA MEMBER SAI YA SHIGA A DAMA DASHI IN SHA ALLAH. ANA ƘARUWA MUNA FAƊAKARWA DOMIN AN HAƊA MALAMAI DATTIJAI WAƊANDA SUKA SAN DARAJAR MUTANE SUKA SAN ME SUKE YI. DUK DA ZAMU SABUNTA SHIRYE_SHIRYEN NAMU IN SHA ALLAH KU KASANCE TARE DANI A KULLUM RANAR MONDAY 8:00 PM A GAMA 9:30PM Shirin """""""""TARBIYYAR YARANMU""""""" MASU GABATARWA ( MAMAN KHAIRY) (ANTY BADI'AT) (KHADIJA MAI DOKI) (ANTY ZEE) RANAR TALATA 8:00AP A GAMA 9:30PM shirin """""""""AMFANIN TSABTA GA MACE""""""" MASU GABATARWA (MRS BASH) (MRS BUKHARI) (MAMAN KHAIRY) RANAR LARABA 4:00PM A GAMA 6:00PM Shirin """""""TAURARUWAR MAKO""""""""" SHIRIN DA ZAI DINGA ZAƘULO MANA MATA DOMIN SU BAMU TARIHIN GWAGWARMAYARSU A GIDAN AURE. MASU GABATARWA (HAJARA ALIYU) (OUM INTEESAR) (MAMAN SAFWAN) RANAR ALHAMIS 8:00PM A GAMA 9:300 Shirin """""""MATSALOLIN MATA DA WARAKA""""""""" SHIRIN DA ZAI DINGA ƊAUKO MAUDU'I YANA TATTAUNAWA AKAI. MUSAMMAN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI MATA. "SANNAN ZA A DINGA KARANTA TAKADDUN MASU TURO MATSALA, DA BASU SHAWARI ME KYAU""""""""" MASU GABATARWA (Ummu Inteesar) (Mum khairy) (MRS BUKHARI) RANAR JUMA'A 12: 00PM A GAMA 2:00PM Shirin """""""""ADO DA KWALLIYA""""""" MASU GABATARWA (KKhadija maidoki) (Mrs BUKHARI) RANAKUN ASABAR DA LAHADI KUMA RANAKUN HUTU IN SHA ALLAH. DOMIN KULAWA DA ME GUDA DA YARAN GIDA BAKI ƊAYA. Kina tunanin tafi ƙarfin Allah ne in mu duk tafi ƙarfinmu? Ko tunaninki babu ranar da alkadarinta ita zai karye? Sumayya soma bani labarin zamanki da Hajiya munubiya dan Allah. Baku ji yadda zuchiyata take daka "ba.""" """Hmmm Sabuwa kenan bana nufin Hajiya tafi ƙarfin Allah ya hukuntata wane mutum inji mutuwa." Ni zuwan Alhaji Zaidu wajena na farkone kaɗai bata sani ba. Zuwa na biyu tace mishi in yazo ya kirawoni a waya zamu gaisa. Da yazo kuwa yayi kiranta ya bani wayar muka gaisa cikin girma da arziki da mutunci sosai. "Tun daga wannan lokacin muke waya da Hajiya sosai, in taƙaice miki harda mamanmu suna waya a gaisa." "A dangi ana mamakin kirki da rashin kishi irin na Hajiya, da yawan dangi suna ganin nayi sa'ar da bako ke" "samu ba. Ƙalilan daga dangine suka kasa nutsuwa da kirkinta a cewarsu kirkin ya wuce misali, kuma ba'a san kishiya a haka ba a ko wanne ƙabila." A haka aka saka bikina da Alhaji Zaidu ta kirawoni tayi mun murna. Washegarin ranar da aka saka bikina muka wayi gari da mutuwar mahaifinmu ciwon ciki na faraɗ ɗaya ne yayi ajalinshi. "Sabuwa da Hajiya munubiya akayi zaman bakwai, kuma a cikin kwana bakwai ɗinnan abinci take yowa" mai yawa da kaji ta tawo dashi. Ranar sadakan uku da sadakan bakwai tayo abinci dasu masa na sadaka mai yawan gaske. Ta shiga dangina na nesa dana kusa duk aka santa suka gamsu babu ƙullin komai a zuchiyarta face alkhairi. Hmmm ashe ungulu da kan zabo ce bamu sani ba. Ita ta haɗamun lefe Alhaji ya bata kuɗin akwatuna biyar ta ƙara mun biyu suka zama bakwai. Da ita akayi shagalin biki muna manne da juna nazo na tare. Hmmmm daga lokacin ƙaddarata ta soma. Hajiya ta kawo mun mai aiki tace zata dinga biyanta duk wata na karɓa inata murna. Hajiya ta shigeni sosai bani da sirri har a kan gadona take zama tana yawan kawo mun magungunan mata masu kyau tace ta siyo mun ne. Hmmm in taƙaice miki sai da nazo nafi ba Hajiya mahimmanci fiye da shi maigidan dan cewa tayi in dena "sakar mishi jiki a turaka tsofar dani zaiyi a banza, ita sai tayi wata guda ma ba sui mu'amalar Aure ba." "Wallahi Sabuwa na biye mata kullum mu kenan a cikin rikici da Alhaji Zaidu, yadda kika san tayi mun" allura haka taita juyani son ranta. Gashi duk abinda muka yi sai tace in bata labari haka zan zauna in labarta mata komai tsab. "Watana uku a gidan ranar wata Juma'a na soma jinin Al'ada kamar wasa yau zan gama gobe ne, a_a jibi" ne. Jini yaƙi tsayawa kuma zuba yake yi sosai in faɗa miki. Alhaji Zaidu da Hajiya sukaita sunturin kaini asibiti. Wallahi Sabuwa Hajiya da kanta ita da Mamanmu "muke sunturin neman magani jini baya tsayawa. Takai ta kawo sai Hajiya ta kwantar ta tayar dani, jini fa ba wai irin na wasa ba. Yadda zaki san asirine da duk jinin da nake zubarwa a asibiti basu taɓa cewa" jinina yayi ƙasa ba bare ya ƙare a saka mun wani. Tom Alhaji Zaidu baifa gazaba jarumine sosai ya nuna damuwarshi sosai akan ciwona. Saida na shekara tim kafin wata rana kwatsam jinin ya tsaya da kanshi a hankali jikina ya shiga yin sauƙi "Hajiya da Alhaji sukaita Murna, lokacin har india aka kaini wani babban asibiti, har a injin sukutum ɗina aka sakani domin asan menene matsalar, hmm basa ganin komai." Ita da kanta ta buƙaci muje umara. Muka je muka dawo tasa Alhaji ya buɗe mun shago ita ta zaɓa mun in dinga siyar da kayan jirajirai kuma ita aka ba kwangilar gyaran shagon da zuba komai. Kasuwa ta soma tafiya kaɗan_ kaɗan A hankali naji Alhaji Zaidu na siremun inajin tsanarshi. Har Hajiya ta sani shima tun ina ɓoye mishi har ya sani. "Mukaita rikici dashi dai daga ƙarshe na tubure saiya sakeni bazan iya zama da juyi ba, tun danginshi basu" sani ba har suka sani. Suma fa saida na zagesu tas kuma nace sai an sakeni. Kinga da wannan ai ba zasu zargi Hajiya ba sun ɗauka kawai bani da kirkine dai. "A lokacin ko bacci bana iyayi kaina kullum ciwo jikina ma haka, ga jini ya dawo mun ƙaƙas." Da na tusa kuka da tambotsai dole ya sakeni na koma gida. Ba sai ciwo ya taso mun ba sai an kwantar dani sai an tayar dani. Gidajen magungunan gargajiya kam mun zagaye Kano da kewayenta kab babu sauƙi. Tun muna yi har muka haƙura muka zuba ma sarautar Allah ido gashi sai ƙarewa nake yi. Na sha wuya sosai wallahi har gobe wani sa'in inna soma jini sai in yi wata guda inayi har yanzu ban "warke duka ba abun yana jikina bai karye duka ba, ƙila dashi zan mutu ma." "Kinji abinda ya faru ko? """ "Illahirin jikina babu inda baiyi sanyi ba, kuma babu inda baya rawa. Wannan tashin hankali da yawa yake." Lallai ina wasa da wuta ban sani ba. Lallai bazan iya da Hajiya ba. A irin gidanmu inna kwanta jinya wazai iya ɗawainiya dani haka kamar yadda iyayen Sumayya sukai tsayuwar daka a kanta. Ya Allah gani gareka ya Allah kaine gatana Ubangiji Allah na dogara dakai kaimun faɗan da kanka. Aisha tace. """Bambancin labarin Sumayya da nawa ɗayane zuwa biyu." Na farko ni ba jini aka saukarmun ba. Ɗankwalina tasa mai aikin data kawo mun ta ɗauka ta kai mata. Bazan mance ba tun ranar dana saka kayan ban sake samun zaman lafiya a gidan ba. Nice zabura firgici kaina kamar ya kunce. Hankalin dangina ya tashi ainun akaita sunturin asibiti sai likitoci suce lafiyata ƙalau ni kuma ni kaɗai nasan me nake ji. Ga Hajiya bata bada wata ƙofa da za'a zargeta ba sam tayi iya yinta a kaina. Bambanci na biyu ni shagon kayan Kitchen tasa aka buɗe mun ƙaninta na zama a shagon wani sa'in kuma ina ɗan leƙawa nima. Nima ta zugani sosai akan da ƙuruciyata zan zauna ba haihuwa shikenan na kashe rayuwata. Tun abun baya damuna na soma ɗaukar zugarta gashi dama gidan ya isheni ni bana samun nutsuwa da kwanciyar hankali har sai na fita a gidan Da zaran na dawo zanji ƙwaƙwalwata na tafasa wallahi ba zata taɓa denawa ba har saina kuma fita. Ya zamana kullum nike nan a cikin gantalin fita nake dana gaji nace ya sakeni bazan iya zama dashi ba. "Haka ya sakeni, na koma gida." Ban dena jin faɗuwar gaba da razini ba har saida na kusan shekara guda ana ta jinyata. Na miki tsallake nima ita ta kawo mun Ƴar aiki ɓarayina da idanuna na kama mai aikin tana barbaɗa magani a abincin dana dafa ma Alhaji. Kunsan Allah hatta ƴar aikina saida ta kai ta kawo tsoronta nake ji. Tazo ta dena aikin ma sai dai ni inyi "abuna da kaina, kuma bana iya mata faɗa har suturuna take sakawa ta sace mun kaya, ta sace mun kuɗaɗena. Gwal ɗin kayan Aurena kuwa ban tawo dashi ba dan anyi neman duniya ba'a ganshi ba.""" Aisha ta sharce hawayenta. Ni kaina fuskata sharab da hawaye. """Shawarar da zamu baki ki rabu da Alhaji Zaidu kawai. Ki bar Hajiya ita da Allahnta""" Kaina take ya soma ciwo nama rasa abinda zance. Wayatace ta shiga ruri ina cirowa naga masta ke kirana. Sumayya da Aisha sai suka shige Kitchen suka bani waje. Muryata a dashe na amsa mishi sallamarshi jikina a mugun mace. """Wazirat lafiya menene waya taɓa mun ke to na jiki wani iri, kuma naga baki neme ni ba""" Ajjiyar zuchiya na sauke nayi murmushi a ƙoƙarina na kawar da zargin nace. Ai na barka ne ka kirani da kanka kar inzo in kira Hajiya na gefenka shi yasa. Amman ka ganni cike da "kewarka""" Murmushi yayi yace. """To ko in kamo hanyar Abujan ne in sameki uhm?""" A_a ni a su wa ai a cikin lokacin Hajiya kake. Mu yanzu ma da munyi sallah zamu kamo hanyar Dutse in "sha Allah.""" Murmushi yayi mun. """Akwai abinda kike ɓoyemun Shalelena. Ki daure ki faɗamun abinda ke damunki. Kinsan yadda nake" "sonki nake kuma son ganinki a cikin farin ciki uhm""" Ai kawai sai naji numfashina yana yin sama sama. Inason nayi magana sai nake jin kamar an zare mun harshena ya tsinke. Allah na soma ambato la'ilaha'illa'anta subuhanaka'inni'kuntuminal'zalumin shi na dinga faɗi a hankali ashe yana jina ni ban sani ba. Sai naji yayi ajjiyar zuchiya. """Menene yake damunki Shalele ki sanar dani dan Allah. Kaddai saƙon da aka turo mun da wata baƙuwar" "lamba kema an turo miki ne, ko kina da masaniya akan saƙonne, wata macece ta turo mun? Banso na ɗakko miki maganar a waya ba naso saimun dawo gida a tsanake sai muyi maganar uhm""" Sai naji gabana ya kuma yankewa ya faɗi da ƙyar nace dashi. "Wani Abunne ya faru? Ni bani da labarin komai wallahi. Kainane yake mun ciwo sai zazzaɓi da nake ji," "wanne saƙon kake maganar an turo maka? """ Ai take saiya ruɗe ya shiga aikin mun sannu sai cewa yayi mu nemi wani asibiti a Abuja muje a duba mishi lafiyata. Ni dai lallaɓashi nayi muka rabu akan zanje asibitin dan yaƙi fur. Yana kashe waya na kira Maigogul nace mishi na gama suzo Zone 2 mu tafi. Ina zaune kaina na mugun saramun. Sumayyace ta fito ɗauke da abinci. Murmishin dole nayi mata. "A_a Sumayya sallah kawai zanyi zamu kama hanyar Dutsene daga can nake""" """To shikenan muje ciki Aisha ma Sallar take yi.""" "Tare muka shiga, da ƙyar fa nake jan ƙafar tawa ta sake nauyi. Nayi sallah muka ci gaba da hirarmu nima" na labarta musu halin da nake ciki. """Hmmm ina baki shawarar ku rabu tun wuri. Sabuwa kada kiga munata ce miki ku rabu kiyi tunanin ko so" muke mu kashe miki Aurenki. Kin ganmu duk da Aurenmu a kanmu. Wallahi Hajiya munubiya muguwace "ta ƙin ƙarawa""" A_a Aisha ai gaskiya kuke faɗamun kuma in sha Allah na tattare bayananku zanyi nazarin mafitar kaina. "Ai ina ganin bama saina nemi ragowar tsofin matan Alhaji Zaidu ba bayanan bakin ku sun wadatar dani""" Su Maigogul ne suka iso. Sumayya ta ɗakko zanin gado da yajin daddawa mai yawa ta bani. Nayi musu sallama muka fito Aisha ta saka mun kuɗi a jakata ina ƙi tana ƙi dole na haƙura na shiga mota muka kama hanya. Saida mukai nisa kana na labarta musu duk labarin dana jiyo. """Tabbas ba zaku rabuba kuma daga kanki alkadarinta saiya karye. Ni nasan magunguna bafa na shirka ba" na tsari da kariya duk zan shiga jeji in tsinko miki. Lolo shawarar farko shine duk rintsi duk wuya duk bala'i kisan yaya Zaki hilaci Alhaji Zaidu ya sake miki gida. Kinga kayan sib ɗinki kwashesu za'ayi ai musu fitsari a wankesu fes da ruwan toka sai a kyautar ko ƴan uwanki ki rabemar tunda ko wani abun akayi a kanki akayi. "Kinga gidanma kada ki sake ƙafarki ta taka, kawai kisan me zaki ce da mijinki. Ko ya saki a gida daban ko" kiyi zamanki a gida muga abinda Allah zaiyi. Amman komawarki cikin gidan haɗarine ga rayuwarki Lolo. Inaji ina gani bazan barki ba. Amman fa wallahi in wani abu ya sameki narantse miki da Allah wannan matar saita raina kanta zata ga sharri zata ga bugayi ganin idanunta. Aljanu kuwa ba zasu barta ta huta ba saita haukace tuburan dan wallahi tsubbu zan koma. Kisan ya zaki faɗa ma mijinki mu zamu nuna bamu sanma komai ba. Ita Rakiya zan mata bayani yau a ɗaki inta bani haɗin kai amman. In kuma ta shiga shirme in watsar da'ita. Kuma Hajiya Balaraba ma zan sanar mata halin da ake ciki wala Allah tana "da abun faɗe""" Tun ina jin Maigogul har tunanukan kaina sukai zurfin da bana iya fahimtar me suke cewa ina dai jin muryoyinsu. "Ga batun saƙo da Alhaji yace anyo mishi shima yana buga mun kaina, ga tunanin me zance da Alhaji" dangane da raba gida ga fargaban ɗankwalina da yake hannun Hajiya tunda ina tsoron kada ta durƙusarmun da lafiyar jikina. Idanuna na lumshe hawaye sukaita wanke mun fuskata. Wayatace tayi ƙara halamun shigowar saƙo ina dubawa ilai Masta ne tare da kalaman ƙauna da zunzurutun kewata a gefenshi. Hawayen dake sakkomun ne suka sake tsananta. Amman saida na tura mishi martani na ajjiye dan gudun kada ya zargeni. Muna sharara gudu ni kuma zuchiyata nata tubkewa da warwarar mafita da yadda zan ɓulloma wannan lamarin har in shawo kan abun. Bamu muka shiga Dutse ba sai goman dare tun a hanya nake fama da matsanancin ciwon kai mai zafin gaske. Haka muka shiga cikin gidan kaina a dafe ko idanuna bana iya ɗagawa. Su mardiyyama suna cikin gidan ashe sun kawo mun rubutu kuma Baba malam yace su kwana. Gaza dasu Madamcy mai jego da Sama da rita duk suna zazzaune anata musu. Shigowarmu ce ta katse hirar da kuma yanayin da suka ganni ina tafe dafe da Uzairu zuchiyata suna tai mun sannu. """Lafiya Maigogul haɗari kuka samu ne ko wani abunne ya faru? """ Cewar Rakiya kenan Saida na zauna msigogul ma ya zauna yace. """Kanta ke mata ciwo Rakiya babu komai""" """Babu komanne aka haɗo uu mardiyya da jarkokin rubutu haka siddan? Sabida an ɗaukeni marar" "mahimmanci ko? Ko da yake baka da laifi Sabuwa itace mai haddasa wannan fitinar""" """A_a Rakiya eh kiyi shiru dan Allah eh abi komai a hankali ga yara ga surukanki. Shi eh Maigogul yana da" "kyau eh ya sanar mana abinda ke faruwa kawai""" """Zan faɗa muku duk ku kwantar da hankulanku, Lolo kije ki kwanta ki nutsu tukunna zamu yi magana" "gobe kafin ku tafi""" Miƙewa nayi na shige ciki yarana suka biyoni tare da su Rahama. A hakan na ɗauro alwala nayi sallar isha magriba munyi a hanya. Mardiyyace ce ta matso ta kama mun kaina tayi mun adda'a wallahi kamar armara kafin ta sauke hannun naji sauƙi kamar ba ni ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Aminu nace. "Tun yaushe kuka zo Aminu? """ """Tun wajen goman safe muka zo danma mun jira Malam ya ƙarashe rubutu shi da Aɗɗa'u shi yasa." Yace ɗan ƙaramin kofi zaki dinga cikawa ki sha ragowar kiyi bismillah ki shafe jikinki Ummi. Allah ya baki lafiya ummi kita Adda'a nima na tawo miki da littafin addu'o'i dana azkar na safe dana maraice. "Azkar in kika riƙeshi duk wani waraka yana cikinshi babu abinda zai cutar dake, koma zai cutar dake bazai" "yi tasiri ba. Kuma ki dinga kwanciyarki da alwala ta hannun dama.""" Murmushi nayi musu su duka wani farin ciki ya lulluɓemun zuchiyata ko iya haka naci nasara a rayuwata ko yanzu na mutu na gode Allah. Rahama tace. """Muma duk ya bamu littafin wallahi tunda akwai na hausa a gefe zamu dinga yi in sha Allah. Har Labbai" "yaba tazo tayi jiran duniya baku dawo ba shine mijinta da yamma yazo ya tafi da'ita. Ta dai ce gobe da safe zata zo ku gaisa a gurguje. In kuma baku haɗu ba Allah ya tsare hanya, ga man ƙuli ta kawo miki""" "Allah sarki ɗan uwa abun wuya. Ai kuwa naji daɗin kyautar sosai. """ Gaza ne ya shigo da jaririyarshi a hannunshi ya ajiye mun ita a cinyata. """Ki eh saka mata albarka Rakiya kayi nayi kenan eh mana rabin raina kenan fa""" Murmushin ƙarfin hali nayi na dubi yarinyar nayi mishi barka ya karɓeta ya tafi. "Sadiyace ta shigo mun da Abinci tare da malama muka ci, na samu na ɗan watsa ruwa na dawo na tarar" sunata shinfiɗar bacci har malama da Aɗɗa'u sun yi bacci. """Aminu ɗauki Aɗɗa'u kuje ɗakinsu Magazin ku yi kwanciyarku sha ɗayan dare fa." "Ke mardiyya da malama kuzo ku kwanta ta nan""" Cewar Adama kenan. Suna kan gyaran shinfiɗar Maigogul ya turo Rakiya ta kirani. Miƙewa nayi na shiga ɗakin Rakiya na zauna a kafet Maigogul da Rakiya na bakin gado. Nan Maigogul ya labartama Rakiya kab abinda ke faruwa. Shiru tayi ta shiga tunani can sai tace. """To menene matakin da kuka yanke. Komawa gidan zata yi a haka taje taci gaba da haƙuri dai ko?" Nifa Maigogul kada fa Sabuwa tace zata kaso aurenta Allah ya dubeta ya rufa mata asirinta. Ni wallahi taje kawai ta zauna a ɗakin mijinta ta dogara ga Allah. Ai asiri ƙaryane wanne irin bigene baku yi ba da kai ɗin da'itan? "Yarinya ka rabu da'ita tayi zaman aure. In ta hasalashi ya saketa ina zata shiga ta sani ne, ko kuwa gidan" "uban yaranta mai mata huɗu zata koma a matsayin ƙwarƙwara? """ Murmushi kawai nayi domin nasan za'a rina wallahi. Maigogul ya girgiza kanshi yace. """Ana ga yaƙi kina ga ƙura. Ni da kike ganina da lolo ta bar wannan auren na gwammaci komai nawa dana" mallaka ya salwanta. Ai ta shiga gidan kenan. Amman Rakiya mafita za'a nema. Ya raba musu gida kawai shine. Kayayyakin sib ɗinta nace duk a rabe ma su Adama. Amman ita zata san yadda zata lallaɓa mijinta ya sake mata gidan tunda mu ba zamu nuna ko da wasa mun san halin da ake ciki ba Tunda ita kanta lolon bata yi magana dashi akan komai ba. "Wannan mata tashi muguwar kiriminal ce wallahi. Amman fa ƙarshenta ne yazo haka nake ji Rakiya""." """Nifa wannan lamarin bai kamata ace an ɗaukeshi da zafi ba. In mijinta yazo ta bishi su tafi kada ta sake" "ta nuna mishi komai. In kuwa tayi mai magana akan uwargidanshi kwaɓarta tayi ruwa, ko ya soma zargin bata son uwargidanshine kunga wa gari ya waya ya tsinci talatarshi a laraba? Kune tunda ko umara ai dakai akaje ba da Kayi nayi ba""" """Ke ya isheki haka Rakiya ai ke sai dai a barki wallahi, da kamar ba za'a sanar miki ba ma. lolo tashi kiyi" "tafiyarki abunki""" Miƙewa nayi na fata zuchiyata kamar zata fashe. Mun fi ɗayan dare muna ta tattaunawa dasu Rahama kafin dai suka kwanta. Ni kuma na ɗauro alwala na fito nai ta sallah ina kai kukana wajen rabbil izzati na bar komai a hannunshi yaimun mafita. Saina wayi gari babu nauyin zuchiya. Ina zaune a inda nai sallah ina karanta azkar a hankali dan wasu kalmomin wuyar faɗe suke yi mun. Wasu ma sai dai in wucesu bazan rufeku ba. Na jima sosai a kan sallayar na gama na yi adda'a sai da nayo wanka na shafe jikina da rubutu bayan na sha. "Rahama fa Sadiya tun safe ban ganta ba""" """Tana ɗakin madamcy tana ma Rakiya wanka Hauwa kuma na ma Madamcy""" "To mardiyya malama kuzo muje mu dubo masu jego. Hauwa ma bamu gaisa ba da su Raliya duka""" Fitowa muka yi zamu sauka Rakiya ta fito daga waje. """Ina kuma zaku je kika taso yara a gaba lolo? """ "Ɗakin masu jego zamu je ne yanzu zan dawo""" Baki ta taɓe ta kira Marsiyya wai zata aikesu ni dai na tafi ni kaɗai. A ɗakin na tarar da Hauwa da Rahama. Hauwa na gasa ma yarinya cibi. Rahama na ninkin kaya tana zubawa a wani babban kwali irin na firich ɗinnan shine sib ɗinsu. Itama jaririya naga kayanta iyakar cikin basket ɗin jinjirayene kawai. Sai katifa da layun Gaza zagaye da ɗakin fa. Wayyo sai na ƙudurce a raina zan saima madamcy sib da gado naga Rakiya ma tana dasu. """Lolo ashe kun dawo ni sai asuba naga Maigogul da yaron Hajiya Uzairu Zuchiyata." Ince dai lafiya ko naga yaushe _yaushe kika tare da har kinzo gida? Gashi naji ance su Mardiyya sun wuce "da abu kamar magani nace ko an samu ƙaruwane? """ Murmushi nayi kawai nace. Lafiya lau sabida dai na dawo daga wata ƙasarne sai maigidan yake ganin dacewar inzo in ganku. Yauma "zai zo mu tafi""" """Ayyo Allah sarki munga tsaraba harda ta kayan abinci wallahi mungode. Rannan ma ina zaune kayi nayi" "ta leƙo ta bani dubu talatin tace inji mijinki kai nagode sosai""" Jaririyar ta miƙo mun na gaishe da madamsy da jiki. Muka gaisa da Rita wacce shigowarta kenan itama tazo taya aiki. Wajen Rakiya na koma mukai cinikin sib da gado wai sai dubu arba'in bafa wasu masu mugun kyau bane. Haka na bata kuɗin dani aka sakama Madamcy kayanta a sib Gaza da Magazin ne suka shigar da gado da sib ɗin. """Angode eh Lolo kinga dana samu kuɗi zan sai mata kafet dama na mata alƙawarin dashi zan zo mata in" "anyi eh albashin farko. Kinga shikenan ɗaki ya zama fes eh dashi. Rakiya da goshinta eh take tafe wallahi. Gata fara eh yarinyar sai dai ma rashin jin daɗina kamarta ɗaya da dattijo wallahi eh.""" Dariya muka yi kawai wajajen goman safe Alhaji ya iso Dutse sai mamaki nake yi dan a lokacin ni ina "Kitchen ina mishi abinci ne bai kuma faɗamun ya taso ba. Da asuba dai ya tasheni a bacci, daya dawo masallaci ma ya kirani mun ɗan zanta duk da bana cikin hayyacina sam wallahi tunani ya cika mun kaina sosai." Sadiya ce ta karɓa mun girkin ni kuma na faɗa wanka a lokacin fa ina jin muryar Alhaji Maigogul ya tareshi. A gurguje nayo wankan na fito hoda da kwalli kawai na murza a fuskata nabi jikina da manyan humrorin Mrs BUKHARI wanda in kana amfani dasu wallahi kafi ƙarfin duk wani turare duk tsadarshi. Su mardiyya suna wajenshi ina jiyosu suna mishi karatu. "Nayi shiru a tsaye na kasa fitowa ina tunanin ni kuwa yaya zanyi ace ban koma gida ɗaya da Hajiya ba," kuma bana gidanmu?. Maigogul ne ya shigo ya kira sunana a hankali. """Lolo jiya banyi bacci ba harda mugayen mafarkai doshin asuba da baccin na ɗan samu nayi." "In kin rasa hanyar da zaki sanarma Alhaji Zaidu ya sake miki gida, ko kuma kin faɗa bai amince ba. Ba zaki" "bishi ba sai dai in tafi dake gidana""" Rakiya da bamu san ta shigo ba tace. """Ai wallahi baka isaba saita koma ɗakinta. Duk yaran gasu a gabanmu yaushe tayi Auren? Adama ma da" "take malam madori ta zauna, labbai da take Auren Ɗan daudu ta zauna sai lolo ce ba zata zauna a gidan" mijinta da kishiya ba? "Wai me kuke nufi ne.""" Rahama ce ta shigo da sauri tace. """Rakiya ai zai iya jiyoki ba dan yara na mishi karatu ba. Mu a gidannan ba'a abun sirri. Ga Hauwa ta dage" sai taji meke faruwa sai gulma da tambayoyi take yi ta mayar damu kamar bamu san abinda muke yi ba. Ke kuma kije ki sameshi koma menene abinda zai yiwu shi za'ayi ba zaki saka rayuwarki cikin haɗariba' Sum sum sum na fita ina jiyo rikici sosai daya ɓalle a tsakanin Rakiya da Maigogul. Ina shiga falon muka haɗa idanu da Masta. Zamanshi ya gyara da kyau ya zuba mun idanu har yana ƙanƙancesu. Ina isowa daf dashi naji yayi wata ajjiyar zuchiyar da daga ji ita tayi kanta da kanta. "An gaisheku Aminu. To ku tafi kuje ku shirya ku tafi ko? """ """Baba ne zai zo ya ɗaukemu inji Malam. Ummi kima Abba godiya kinga abinda ya bamu""" Cewar mardiyya. Da take nuno mun leda shaƙe da su biskit da alawa ga kuɗi da kauri. "To shikenan kuje ciki wajen Rahama""" Da idanu muka bisu har suka ɓace kana muka kalli juna muka sakarma juna murmushi mai rai da motsi. """Wazirat daga zuwa gida sai kawai a juya mini baya uhm haka akeyi ne. Kinsan irin kewar dana shiga" kuwa? Hatta Hajiya tayi kewar motsinki a gidan uhm Mrs BUKHARI Hmmmm to mu tara gobe "[10/22, 10:33 AM] BADA'AT IBRAHIM: TASKAR BADI'T" WANNAN SHINE JADAWALIN SHIRYE SHIRYENMU DA WANNAN TASKAR TAKE GABATARWA YAYIN DA BA'A LITTAFI DOMIN ƘARUWARMU BAKI ƊAYA MU GUDU TARE MU TSIRA TARE. MASU SON KASANCEWA TARE DA MRS BUKHARI GAREKU GA LINK NAN DUK MAISON KASANCEWA MEMBER SAI YA SHIGA A DAMA DASHI IN SHA ALLAH. ANA ƘARUWA MUNA FAƊAKARWA DOMIN AN HAƊA MALAMAI DATTIJAI WAƊANDA SUKA SAN DARAJAR MUTANE SUKA SAN ME SUKE YI. DUK DA ZAMU SABUNTA SHIRYE_SHIRYEN NAMU IN SHA ALLAH KU KASANCE TARE DANI A KULLUM RANAR MONDAY 8:00 PM A GAMA 9:30PM Shirin """""""""TARBIYYAR YARANMU""""""" MASU GABATARWA ( MAMAN KHAIRY) (ANTY BADI'AT) (KHADIJA MAI DOKI) (ANTY ZEE) RANAR TALATA 8:00AP A GAMA 9:30PM shirin """""""""AMFANIN TSABTA GA MACE""""""" MASU GABATARWA (MRS BASH) (MRS BUKHARI) (MAMAN KHAIRY) RANAR LARABA 4:00PM A GAMA 6:00PM Shirin """""""TAURARUWAR MAKO""""""""" SHIRIN DA ZAI DINGA ZAƘULO MANA MATA DOMIN SU BAMU TARIHIN GWAGWARMAYARSU A GIDAN AURE. MASU GABATARWA (HAJARA ALIYU) (OUM INTEESAR) (MAMAN SAFWAN) RANAR ALHAMIS 8:00PM A GAMA 9:300 Shirin """""""MATSALOLIN MATA DA WARAKA""""""""" SHIRIN DA ZAI DINGA ƊAUKO MAUDU'I YANA TATTAUNAWA AKAI. MUSAMMAN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI MATA. "SANNAN ZA A DINGA KARANTA TAKADDUN MASU TURO MATSALA, DA BASU SHAWARI ME KYAU""""""""" MASU GABATARWA (Ummu Inteesar) (Mum khairy) (MRS BUKHARI) RANAR JUMA'A 12: 00PM A GAMA 2:00PM Shirin """""""""ADO DA KWALLIYA""""""" MASU GABATARWA (KKhadija maidoki) (Mrs BUKHARI) RANAKUN ASABAR DA LAHADI KUMA RANAKUN HUTU IN SHA ALLAH. DOMIN KULAWA DA ME GUDA DA YARAN GIDA BAKI ƊAYA. MRS BUHARI 6 Murmushi nayi mishi na ƙarfin hali. Domin kiran sunan Hajiya ke da wuya sai naji kaina ya sara mini Wallahi. Amman a haka na dake nice harda hararar soyayya nace dashi. "Kaji ka, kai da kake da Hajiya yaushe zaka zauna cikin kewa. Aina tabbatar zata kula dakai fiye da yadda" "zanyi""" Murmushi yayi mun yana ƙarema tsakiyar idanuna kallo. Shigowar Sadiya da kayan abinci ne ya katse mishi kallon. Maigogul ne ya shigo fuu yayi ɗakinshi Rakiya kuwa ta bishi nasan rikicin za'a ci gaba dayi kai Allah dai ya sauwaƙe. "Abincin zaka ci yanzu in zuba maka ne koko ba yanzu ba? """ """Ai gara inci sabida ban ko karya ba na kamo hanya ina Allah_Allah inzo in sameki. Kinsan fa jiya naji" "muryarki cike da damuwa uhm. Kuma nima akwai abinda ya faru da nace miki zan sanar miki amman sai mun tafi Kano.""" "Abincin na soma zuba mishi farfesun kazane wanda na ɗan ɗaure romon da sitati na masara., na" ƙawatashi da jan waken gongoni. "Sai farar shinkafa, sai shayi mai kayan ƙamshi." Ƙasa ya dawo daf dani ya zauna na tura mishi abincin gabanshi. Na ɗauki kofi ina zuba mishi ruwan shayi kenan Sai muka jiyo sallamar Babangida Kaci gari gabanshi gaɗi ya shigo shi taƙamarshi nan ai gidansu ne. "To ai kunga dole a falo zai zauna ko?. Muma gamu a falon Rahama ta leƙo tace ya shiga falo""" Babu guiwa ya tako yana shirin zama a kujera naji ɗumin abinci a laɓɓana Alhaji Zaidu ya ɗebo ya ɗaura a bakina. Buɗe baki nayi ya zuba mun yana murmushi. Nima murmushin nake yi. Fitowar Maigogul ne yasa su mardiyya suma suka fito. Babangida baice mana ba bamu ce mishi ba. Alhaji Zaidu sai magana ƙus_ ƙus yake yi mun inajin kaifin idanun Babangida na yawo a jikina. """Alhaji ga Baban yaran Lolo ku gaisa. Kai Babangida ga mijin Lolo ku gaisa""" Murya a shaƙe yace. """Assalamu Alaikum""" Alhaji Zaidu ya amsa mishi tare da duban Maigogul yace. """Ai Alhaji Baba bamu sanma ya shigo ba dake bamu ji sallamarshi ba sam. Ya gida Baban Mardiyya""" Alhaji Zaidu ya miƙa ma Babangida daya miƙe tsaye hannu. Dole ya miƙo nashi suka yi musabaha yace. """Mun gode da gudunmawar Aure daga bayar. Tare da Wazirat al sa'ada muka buɗe ma ambulon ɗin" "Allah ya saka da alkhairi""" """Wazirat al Sa'ada? """ Babangida ya maimaita a hankali nayi imanin bai san munji ba sai kawai yayi hanyar waje. """Ummi mu zamu tafi yaushe zaki dawo ummi?""" "To zan zo bikin Uzairu zuchiyata zamu haɗu ku gaishe da Baba malam ku yi mishi godiya""" """Ke Mardiyya zaku fito ne ko saina shigo na jawo ku ne, menene haka kun barni a tsaye ina jiranku," "wannan me kenan? In binta zaku yi gaku ga ta ai""" Da sauri suka fice Maigogul yace. """Babangida jarabar duniya. Hmm a haka ma kura tayi lafiya da dane da wallahi sai dai kaga ya" "rungumeka kun kaure da dambe Babangida bashi da daɗi sam bashi da kirki, yadda kasan a ƙofar tasha Aka haifeshi, da zasu haɗu da Gaza ma sai sun taɓa damben. Allah dai ya raba lolo da ƙaƙai ko a kotunma da yaya aka. """ Sai kuma ya haɗiye zancan shi sakamakon hayaniyar da muka jiyo a waje. Babu shiri duk muka ɗunguma waje. "Dambe ne ya kaure tsakanin Babangida da Gaza sai doki in doka suke yi, ga bakin Babangida yana jini," bakin Gaza kuma ya sha naushi ya aune. Fisgewa Gaza yayi ya nufi ɗakinshi da gudu. """Maza ku fice a guje yanzu nasan adda yaje ɗakkowa kuje dan Allah bama son fitina. Kai kullum kazo sai" "anyi rikici dakai""" Cewar Maigogul Babangida ya kama hannu Malama ya dubeni yace. """Ga abinda kika ja ai Sabuwa kina gani ai a gaban yaranki duk sanda zanzo sai an samu matsala, sabida" "ku gidanku babu tarbiyya""" Hannun yaran yaja suka fice fuu ni ko bakina na taɓe. A guje Gaza ya fito da adda Alhaji Zaidu da Maigogul ne suka cabkeshi yanata zage zagen rashin daraja. Maigogul na rungume da ƙugun Gaza carab sai fisgewa yake yi. """Da kun barni dashi wallahi da saina tsinke mishi ƙafa. Ya zai shigo har gidanmu ya dinga mun eh kallon" "banza. Allah da kun barni dashi eh. Allah ya sake zuwa kuma muka haɗu saiya rasa eh ƙafafunshi, me ma" "yake eh zuwa yayi ne, dole ne eh zai ya shigo mana eh gida. Menene bai ma eh iyayenmu na rashin mutunci ba eh""" """Haba Baban Rahine. Alƙawari fa kayi mun ka dena shaye_shaye da daba shine zaka ɗakko adda haka. Ai" "ko babu komai an haɗa zuriya dashi sai yaci albarkacin yaran. Dan Allah kada ka sake""" """Cau cau wallahi. A lafiya dai eh futu futu mugun icce. Sai ni wallahi makara motar ƙarshe, tsatsa mai" "kashe ƙarfe nake, sabon kabari mai sa a tuno Allah. Waihihuhuuuuu""" Duk saida muka dara haka Gaza ya mayar da Addarnan mu kuma muka haura sama. Sabon abinci na zuba ma Alhaji Zaidu shi kuma sai kallona yake yi. Yana cin abincin muna ɗan hirarmu sama _sama harya kammala. """To wazirat ya kamata kuma mu kama hanya ina da aiki sosai dana baro.""" "Yauwa nace ba. A cikin gidajen da kake ginawa na siyarwa kana da wani ginanne a ƙasa ne? """ Zama ya gyara yace. """Babbar magana. Uhm akwai gidaje uku a mabambanta unguwanni. Amman wanda yake ɗorayi shi har" kaya an zuba a ciki. Kinsan misali in mutum na so yafi daraja da kaya a ciki kamar tsarin da Ƴan Abuja suke yine muma nan Kano mun soma. Sai dai kiga magidanci ya lale kuɗinshi ya sai waje shi da iyalinshi sai dai kawai su ɗebo suturunsu kawai ba ruwansu da komai. Wasu kuma haya ake bayar dasu da kayan. Kamar gidaje da nake ginawa a Abuja yawanci haya nafi "sakawa.""" """To na ɗorayin inaso in mun shiga Kano kafin mu shiga gida mu soma zuwa inason zan ganine""" Kallona yayi na tuhuma yana murmushi yace. """Ko siya zaki yi ne uhm Wazirat? To shikenan zamu je ki gani ƙaramin gidane ba wani babba ba, sai dai" "yanayin tsarin gininshi yana da kyau""" Miƙewa nayi nace. To bari in fito sauran zancan ma ƙarashe a hanya. Ai kuwa na shiga ciki na haɗa ragowar kayana duk da zuchiyata tab fargabar me kaje kazo amman dole ita rayuwa sai an gwada ake dacewa ko akasin hakan. Rakiya na miƙa ma kuɗi Rahama da su Sadiya duk na basu na dubesu nace. Duk yadda ake ciki zaku ji in sha Allah adai taya ni da Adda'a. "Rahama muje ki rakani ƙasa""" Tare ma muka sakko dukkanmu Maigogul da Alhaji Zaidu suna jingine a jikin mota Gaza na riƙe da get ya wangale mana. "Kayana ya karɓa ya saka mun, nayo ma Hauwa, da Madamcy sallama Rita ta tafi aiki ita." Mota na shiga muka nufi get. """Sabuwa kima Sikari godiya wallahi ya biya eh kuɗin ragon Rabin raina harda eh kuɗin abincin suna" "wallahi""" "Allah ya saka da Alkhairi, Gaza sai ka dawo mu kam mun tafi""" Na faɗa ina dariya. """Alhaji batun Rahine a duba wallahi ni dana dawo sai naga duk ta rame har shi muzuru Uzairu duk ya" "rame har ciwo ya jiyo a ƙafa a ƙila sata ya haura yayi duba mana""" """To Baban Rahine ka tawo da Rahine harda Uzairun shi Uzairu ka bamu dan magen yayi mun kyau." "Rahine kuma saita zauna a kamfani amman fa anan zata dinga kwana""" "Ihu ya saka ya shiga kirari," """Batun albashinta fa Rahinen aiki zata yi tuƙuru""" muna dariya muka fice muka ɗauki hanya muna dai hira sama_ sama ba kamar yadda muka sababa. Can da tafiya tayi tafiya sai mukai shiru kawai kowanne cikinmu da abunda yake saƙawa. Ni tunanina ya kasu kashi kusan ukune. Na farko batun Hajiya munubiya Na biyu batun sake gida. Na ukun shine magana da yake ta cewa zamu yi dashi dan gane da saƙon da aka turo mishi. Idanuna na lumshe tare da gyara zamana. Bana son ma yayi mun wata tambayar sam sai kawai muka tafi a zuwan bacci ne ya kwasheni wallahi har muka shiga Kano idanuna biyu a baɗini a zahiri kuma bacci nake yi. Nifa ban buɗe idanuna ba har saida muka shiga ɗorayi ƙofar sabon gida. Sai naji ya tsaya ya fita a motar. Sai lokacin na buɗe idanuna da sukaimun nauyi na dubi bayanshi da gidan da fasalin unguwar. Unguwace cike da mutane ni da na ɗauka unguwace da zanga gidaje ɗaiɗaiku ajjiyar zuchiya na sauke. Shi da kanshi ya buɗe get ɗin gidan. Tabbas ƙaramin gidane kamar yadda ya faɗi. Dawowa cikin motar yayi ya sameni idanuna a buɗe. """Wazirat kin tashi ne? Ai bamma yi niyyar tashinki ba naso ne in shigar da motar ciki sai in kashe in zauna" "inta kallonki""" Murmushi nayi na farin ciki sai nayi ƙwal_ƙwal kamar zanyi kuka. Saurin riƙe mun hannu yayi cikin ƙasa da murya sosai yace. """Menene wazirat ɗina ki daure ki faɗa mun dan Allah tun jiya zuchiyata take cikin damuwa""" "Ya yanayin girman matsayina a wajenka yake Omri? """ Murmushi yayi mun mai rai da motsi. """Omri? Wannan sunan yayi mun kuma kin burgeni sosai shi Masta a barshi sai muna shinfiɗa uhm." "Menene matsalarki al sa'ada? """ Alƙawari zaka yi mun in mun shiga ciki duk alfarmar dana nema a wajenka kai mun. Kai mun alƙawari "anan tun kafin mu shiga. Sannan abun baifi ƙarfinka ko ta ko ina ba. Omri bazan taɓa neman alfarmar da nasan baka da'ita ba""" "Na ƙarashe maganar da rawar murya wasu siraran hawaye suka zubo mun.""" Babban yatsanshi yasa ya sharce mun hawayen nawa. """Dena kukan zanyi miki duk abinda kike so in sha Allah. """ Motar ya ja muka shiga gidan. Gidan yana da kyau ni ƙanƙantarshi ce ta sake burgeni ma sosai. Yana riƙe da hannuna har muka shiga falon zagaye da kujeru irin masu L ɗinnan marasa hannu na fata masu mugun tsada da gani Zaunar dani yayi a kujera. """A_a ka kaini ciki in kwanta bana jin daɗin jikinane""" Baice komai ba ya shiga dani cikin komai yana ajjiye cikin tsari da kyau gwanin sha'awa katifar dai babu zanin gado a haka na jawo fulo na kwanta. Zama yayi a gabana yana shafan kaina. """Ke nake saurare Wazirat Omri ɗinki yana jinki""" Hannunshi na riƙe gam nace. "Munyi Aurenmu cikin soyayya tare da fatan sai dai mutuwa ta rabamu ko? """ Kanshi ya gyaɗa halamar Eh. To ina fatan ni dakai mutuwa ce kaɗai ka iya mana shamaki ba dai mutum ba. Kaga shigowarnan da nayi "gidannan? To na dawo nan da zama bazan koma can gidan Hajiya ba, Allah ya hore maka ba dole sai mun zauna waje ɗaya ba. Kuma raba gida na rage zafin kishi da jin zafin juna sosai. Mu ba yara ba bare muce zumuncinsu muke kallo. In kuma kace dole sai na koma can to daga nan Dutse zan koma""" Na ƙarashe ina hawaye. Duk wannan maganar zuchiyata fa sai daka take yi mun Bansan me zan samu a matsayin amsa ba. Ya dai yi shiru yana ta saurarena da dukkan zuchiyarshi. """Wazirat nasan kina da dalili mai ƙarfi kuma zanso jin dalilinki kada kiyi tunanin ɓoye mun komai ko kiyi" "tunanin rage mun komai nake son sani""" Shiru nayi ina tunanin to ni mai zance mishi ne. Kafin in gama tunanin ya miƙo mun wayarshi yace. """Kinsan wannan lambar kuma kinsan wacece tayo saƙon? """ Amsa nayi jikina na ɓari na soma karantawa cikin zuchiyata ga abinda rubutun yake cewa. """Sabuwa bata aureka domin soyayya ba. Sai domun kuɗinka da niyyar tarwatsa maka gidanka." Sannan ƴar iska ce kayi bincike mai zurfi a kanta ɗiyarta mardiyya bata hanyar aure aka sameta ba bata san ma waye ubanta ba shine ta liƙa ma tsohon mijinta cikin. "Sannan ita da ubanta suna bokanci kayi bincike da kyau, mijinta da kwarto ya kamata sanadiyyar" rabuwarsu kenan. "Na barka lafiya.""" "Ai take hajijiya ta soma ɗibana daga wannan zaunen da nake, amman fa babu ko ɗigon hawaye a" idanuna zuchiyar sai naji ta bushe. "Lallai Ƴar shuwa ashe abinda na tare mata a rayuwa har ya kai haka, ai ni na ɗauka iya Babangida ya" isheta rayuwa ashe Aurene bata son taga nayi shi kwata kwata. """Halamu ya nuna kinsan mai rubutun ko""" E na santa farin sani ma kuwa. Abinda ta faɗa gaskiya ne face Mardiyya da tace ba yarinyar Babangida "bace ƴarshi ce.""" Na faɗa cikin rashin tsoro kawai ma duk abinda zai faru gara ya faru bana ƙarya kawai gara in sanar mishi gaskiya. """Wacece ita, a ina kuma take? """ "Kishiyata ce ta da matar Babansu Mardiyya aminiyata wacce muka yi rayuwa a gidanmu tare, aminiyar" "da ko mutum na kashe ita zata taya ni mu birne""" Zama ya gyara yana kallona cikin mamaki. """Ban gane ba, aminiyar taki ce ta Auri mijinki kuma duk da kun rabu take binki da bita da ƙulli? Ina bazan" "bar wannan maganar ba wazirat dole hukuma ta shiga cikin lamarin. Kuma dole mijinta yasan abinda ta aikata.""" Kunji a daidai gaɓar dana samu zarafin fashewa da matsanancin kuka mai tayar da hankalin duk wani masoyina. Riƙeni yayi a jikinshi tsam yana rarrashina. Ka barni inyi kuka. Shikenan babu dama ka tuba mutane su karɓeka a matsayin wankakke kenan. Bafa "mu muka zaɓi rayuwarmu ba, kuma bamu isa mun kauce ma ƙaddararmu ba. Ya Ƴar shuwa take son rayuwata ta ƙare ne ni Sabuwa da abinda zata saka mini kenan""" """Ya'isa wazirat. Ba ta turo bane dan ta ɓata mun ke ba? To wallahi kimarki da darajarki saita sake" "ɗaguwa a wajena kinsan menene dalili Shalelena?""" Girgiza kaina dake manne a ƙirjinshi nayi. """Yauwa Sabida da kika ga saƙon baki yi yinƙurin kare kanki ta hanyar layancemun ba. Sai kika karɓi" abinda ta rubuta kikace hakane face batun mardiyya data yi miki sharri akai. Al sa'ada bata san in duk kowa zai ƙi ki ni a lokacin ma zan soma sonki. A binciken da nayi a kanki tabbas banji batun Mardiyya ba. Amman a layinku akwai wani malam Habu ko ina ya samu lambata ban sani ba ya dai kirani yake faɗamun maganganu masu nauyin maimaitawa to a ciki harda batun bokancin duk ya sanar mun. Bincikena kuma ya tabbatarmun da hakanne. Ni ba jahili bane da zan ƙyamaceki dan kinyi wata rayuwa a baya. Sannan in har Allah da kaima laifi ka roƙeshi ya yafe maka me yasa zaka daka ta mutane wanda ba'a iya musu sam? Babban abinda kowa yake fata shine ƙarshenshi yayi kyau ba farkonshi yayi kyau daga ƙarshe abun ya lalace ba. "Dukkanmu masu laifine, kuma kullum a cikin saɓa ma Allah muke. Babu mamaki kin fini matsayi da" zamowa marar yawan zunubi a wajen Allah sabida kin tuba akan dukkan abinda kika aikata a baya ke wankakkiyace. Wazirat kada ki sake kuka Ƴar shuwa ko? Sai mu tsaya a gaban kotu ta nuna miki mahaifin ita mardiyyan "ba shikenan ba tunda ita jahilace. A yau kaɗai dana sanshi ban isa in kalli mardiyya ince bashi ne Abbanta ba. Sabida haka kina dani babu ke babu wulaƙanta in sha Allah. Har gida zamu je muyi sallama in gana dashi in kuma gabatar mishi da wannan saƙon""" Ruƙunƙumeshi nayi ina jin wani irin daɗi cakuɗe da matsananciyar kunyar da ban taɓa jin irinta ba a duniya. Ɗago fuskata yayi yana son mu haɗa idanu ni kuma na kasa kaina ya ɗago da ƙarfi sai nayi dariya. Shima dariyar yayi. """Faɗamun me yasa kika kawo mu nan gidan? Kinsan kuma kasancewarmu a hakan sai yayi mun daɗi fiye" "da tunaninki""" Uhm ai har abada a hakan zamu kasance. Sai dai ina fatan ragowar ɗakunan su cika da yaranmu na faɗa "maka na dawo nan da zama""" Sumbatata yayi a goshi yace. """Me kike nufi ne uhm? """ Itace alfarmar da nake nema a wajenka ka barni nayi zamana a wannan gidan naka ni kaɗai dan Allah "kada ka tambayeni dalilin ina mugun ganin darajarka da girmanka kuma wallahi mu bama ƙarya""" Shiru yayi yana kallona cike da illahirin mamaki maɗaukaki. Nima shiru nayi ina sauraren menene amsarshi. Babangida:. """Aikin banza aikin wofi wazirat al sa'ada ni zaka cema Sabuwa haka a wajena? """ Sai yayi tsaki ya shiga gyaɗa kanshi yama mance yara na bayan mota sai da yaji amon muryar Malama tana cewa a bata biskit ita ba alawa take so ba. "Idanu ya lumshe yana hango sanda aka ba Sabuwa abinci a baki, da wani irin kallon so da Alhaji Zaidu" yake binta dashi. """Ku ajjiye kayannan nace dan ubanku. Meye bana siya muku da zaku zo kuna raba kaya a mota""" Da tsawa yake maganar. Idanu ya runtse da ƙarfi. Ai kuwa ya bige wata yarinya mai tallar dafaffiyar gyaɗa. Ranga_ ranga aka ɗauki mai gyaɗarnan sai asibiti Allah ma ya so shi ƙujewane kawai sai bakinta data fasa. Gyara mata wajen kawai akayi aka bata magunguna Babangida ya mayar da'ita gaban iyayenta yayi musu bayani tare da basu kuɗi babu laifi kana yaje ya ajjiye su Mardiyya ya wuce wajen aiki zuchiyarshi nata tafasa yana ta maimaita wazirat al'asada a zuchiyarshi. Yana cikin tunaninnan ne akayi kiranshi Sumy tayi ɓari suna asibiti jini ya ɓalle mata. Babu shiri daya tashi a wajen aiki asibitin ya nufi Sumy na bacci lokacin Matar Mustapha Adeeza itace ke zaune da'ita sai Hameeda da ta kawo musu abinci da ruwan zafi zuwan nata kenan shima ya shigo. """Adeeza ya jikin nata? """ """Jiki da sauƙi an auna arziki Dr yace ba sai an ƙara mata jini ba, amman naji suna batun wankin ciki ka" sameshi a ofishinshi dai. Haka Babangida ya samu likita a ofishinshi suka yi maganar da zasu yi. Amman ina hankalinshi da nutsuwarshi baya jikinshi wannan suna da abinci da aka ba Sabuwa a "gabanshi shine babban abinda ke hautsinashi, da kamala da cikar mutuntata da dattijantakar Alhaji Zaidu." Kuma gadon da Sumy take kwance a gadon Sabuwa ta kwanta sanda akayi mata wankin ciki Sai lamura suka sake hautsinewa a ƙwaƙwalwarshi ainun. Har ya isa ɗakin Hala yana cike da baƙin ciki da takaici. Ga hayaniya da shewar mata daga ɗakin Ƴar shuwa yana jiyowa. Lokuta da dama sai yaji kamar ya rabu da Ƴar shuwa shine sassaucin da zai samu a rayuwarshi. Fuu ya fice sai gashi a tsakiyan mata a uwar ɗakinshi. """Ko wacce Ƴar iska ta fice a ɗakinnan. Marasa tarbiyya kawai""" Ai ba shiri suka shiga tururuwar fita. Ya ƙurama ƴar shuwa idanu yace. """Kinji kunya wallahi tur da mata masu taurin kai irinki.""" Ya saka kai ya fice. A wannan dare dai Babangida kusan rabawa yayi yana karanta wasiƙar jaki. Da ƙyar ya yakice tunanin Wazirat ya miƙe ya shiga jera sallolinshi kamar yadda ya saba. Yanayi yana jin wani irin yanayi mai turiri Mrs BUKHARI To sai kuma gobe "[10/23, 10:23 AM] BADA'AT IBRAHIM: Kunyi ready ku koyi skill ɗin da ke kawo kuɗi!" "Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace," ko ku iya video editing kamar professionals — to wannan class ɗin naku ne! Za ku koyi: " Voice Over (recording, editing, delivery)" " Video Editing (cuts, transitions, subtitles & more!)" Practical + Real Project Training Location: [TELEGRAM ] Payment: 9163354359 Sa'adatu Adamu Opay Send receipt via Contact: [07044292865] Registration ongoing — Limited space available! Kada ka tsaya jiran lokaci — ka shiga yanzu MRS BUKHARI 7 SABUWA:. """Nasan kina da dalili zai iya zama mai ƙarfi uhm?" To hakkinki ne ki yadda ku zauna gida ɗaya da kishiya. Kuma hakkinki ne kice ba zaki zauna gida ɗaya da'ita ba wazirat kina da wannan damar. Mata da yawa basu sani bane. Sai dai in miji bashi da halin rabawarne yake da damar da zai bada haƙuri har ku amince. Da yawa_ yawan malamai sun tafi akan cewar in kasan baka da ikon raba musu gidanma to kada ma kayi ƙarin auren. Wasu kuma suka tafi akan in da amincewarku ne babu matsala. Wasu malaman ma basa taɓo wannan ɓangaren gudun faruwar matsala da bore daga wajen nisa'u. Ta ɓangarena na amince miki zaki zauna ke kaɗai. Amman wannan gidan ai yayi miki kaɗan wazirat akwai waɗanda suka fi wannan ɗin girma da kyau da komai. "Tun farko naso dama a wannan karon in raba muku gida, to sai Hajiya ta roƙi alfarmar tana fatan tare" zaku zauna sai kawai nace da'ita eh Amman hatta Goggo amfana taso a raba muku gida haƙuri na bata dake tana da sauƙi saita yadda. "Amman faɗamun kina kewata kuwa? """ Ai kafin ya rufe baki nayi ma bakinshi riƙon alewar yara muka tafi sama jannati Bamu muka dawo ba saida muka more rayuwarmu muka wartsake ta hanyar yin wanka. Sai da muka fito na sauya kaya ya riƙoni ta baya yace. """Zamu dinga guje_guje kamar yadda ma'aikin Allah Arrasul S A W yake yi tare da Nana Aisha uwar" "muminai ya tsere mata ta tsere mishi uhm. Wanne alƙawarin farin ciki akayi mun? In ba haka ba in fasa""" Juyowa nayi na saƙalo wuyanshi nace. "Ai zamu gudanar da duk wata soyayya daka sani. Kai dai kaje masallaci anata kiraye kirayen Sallah.""" Sumbatata yayi ya fice da sauri. To dama munyi azahar a hanya Nima sallar la'asar ɗin na kabbara har ya shigo ina kan sallaya da azkar ɗina ina karantawa da ƙyar. Tsugunnawa yayi a gabana ina karantawa a tsanake yana yi mun gyara. Zamanshi yayi daf dani ya karɓe littafin ya ajjiye. """Ki dinga faɗa in na faɗa zai fi miki sauƙi""" "Ai kuwa nai ta bin bakinshi har muka gama""" """Naji daɗi sosai dana ga kina azkar. Waye ya baki littafin""" "Yaronka Aminu ne yai mun kyautarshi""" """Allah sarki. Yau zamu soma karatunmu in sha Allah kuma ba zamu dena ba, sai dai zai kasance duk" ranar kwananki ne uhm? Kaina na jingina a kafaɗarshi nace. "A ofice ba za'a dinga ƙara mun ba, ko da lokacin hutune da cin abinci. Inaso inji ina ƙira'a irin taka data" "yara""" Murmushi yayi mun ya miƙe tsaye. """Tashi muje ki rakani Rano Baba Abdullahi babu lafiya ƙanin mahaifinane a hannunshi nake""" Miƙewa nayi na kuma shiryawa muka fito tare muna tafe muna nishaɗi da farin ciki. Duk yadda na ɗauka zan sha wuya wajen ganar da Alhaji sai abun yazo da sauƙi dake yana da sani kuma yana amfani da sanin nashi baya tauye hakkin kowa. Ba irin su o_o ba. Muna tafe muna hira har muka iso Rano. """Ki shiga zan gaisa da Mutane. Kinga ga motar Hajiya ma ashe bata tafi ba""" Sakkowa nayi a hankali na ratsa almajiran dake karatu a ƙofar gidan kaina a ƙasa naita shigewa zaurukan gidan har na ɓullo tsakar gida da sallamata. Matan gida duk suka tarbeni cikin fara'a. Anty khadija kamilar mace taimun jagora zuwa ɓarayin Kawu "Abdullahi wanda yake damƙam da Ƴaƴa da jikoki, da surukai." Ina shiga muka haɗa idanu da Mandiya ta hakimce a ƙasa ga gwalagwalai ta zubasu. A kusa da'ita ta nuna mun inzo in zauna baki a washe. Da bismillah na zauna nan aka shiga gaisuwa tare da tambayar mai jiki. Anty Tani tace. """Kinga gashi can a gado mai rumfa bacci yake yi anyi mishi allura. Jikin sai godiyar Allah kinsan yanayin" "tsufa ciwon sai haƙuri. Ya kika baro gida duk kowa lafiya ko?""" "Suna lafiya Anty Tani. Allah yaba Kawu lafiya""" """Madam ashe kin dawo, shine Hauwa bata kirani ba, hala baku shiga gidan bane ko? """ Ta tambaya tana dafe da kafaɗata. "Uhm nadawo Hajiya. Bamu je gida ba nan muka yo shi yasa bata kiraki ba. """ """Ayya to maraba da dawowa bakya gidan duk sai kaɗaici koma yayane ana jin motsinki yafi wallahi""" Hajiya Amina tace. """Ke dai Hajiya munubiya akwai kyautatama kishiya. Allah ya dubeki in kina da rabo ya dubi zuchiyarki" "mai kyau da sadaukarwar da kikai ma Zaidu ya baki ɗa ko ƴa""" Duk ɗakin aka amsa da. """Ameen"" Ciki har da ni." Kiraye kirayen sallar magriba yasa aka watse a ɓarayin izuwa ɓarayin su Goggo Amfana. Ina bakin famfo ina alwala Alhaji Zaidu ya fito daga falon Goggo Amfana. """Kuna nan ashe? To ni na tafi masallaci""" Shigewarshi yayi da sauri. A kusa da Goggo Amfana nayi sallah su Hajiya suna bayanmu ita da ƴar ɗakinta mai jegon da naje suna. Muna idarwa Goggo tace. """Ashe kece kusa dani Sabuwa. Allah sarki ya kika baro iyayen to? """ "Lafiyansu Ƙalau Goggo ya jikin Kawu? """ """Kaiya jikin tsufa ciwonshi sai dai ya sassauta kawai. Yanzu Zaidu yake mun wani bayani mai saka farin" "ciki bamu gama maganar ba lokacin sallah yayi amman yanzu zaki ganshi ya dawo""" Hajiya da jin haka tayi sauri ta matso suka gaisa da Goggo da fara'arta. Itama Goggon da fara'a ta amsa. """Munubiya sai haƙuri ita rayuwa haka ta gada. Jarabawar wani sai kiga daban da jarabawar wani." A babin mutuntaka a matsayinki na babba uwargida obarol dama yana da kyau ace kin kasance gidanki "daban yake ba wai a haɗaki da abokiyar zama ba""" Carab ta tari numfashinta da cewa. """Ai babu komai Goggo ni ra'ayina nafi son mu zauna gida ɗaya domin mu taimaki juna kuma shima a" "sauwaƙe mishi wahalar. Ni nake zaɓan a kawosu sabida wanzuwar shaƙuwa a tsakani""" Shiru Goggo tayi can tace. """To hakane abun? To Allah yasa mu dace. Ke Sabuwa ki shiga wajen Khadija ƙawarki kuci abinci. Ke kuma" "sai kije wajen Huwaila ina jiran wannan yaro Zaidu yazo muna tattaunawa ne""" Miƙewa nayi nace "A tashi lafiya Goggo""" Na saka kai na fito a wajen na bar Hajiya a zaune. Na zauna a ɗakin Anty Khadija ta kawo mun dambu da lemun zaƙi kenan Goggo Amfana ta aiko Zarah tayi kirana. Da sallama na shiga falon bata ciki. Daga uwarɗakinta na jiyo tace. """Ƴarnan shigo gani nan a ciki nazo shan maganine""" Na buɗe labulen ɗakin na shiga na zauna a gabanta hannunta ta saka a kaina tace. """Naji daɗi da farin ciki da kika zaɓi zaki zauna a gida daban ba a gidan da Zaidu ya saba Auren matanshi" ya ajjiye ba. Akwai abinda nake tunani sosai akan yawan rabuwa da mata suke yi dashi sabida rashin haihuwa kawai. A nagarta irin ta Zaidu da son kyautatama duk wanda ya raɓeshi kaɗai yaci ace mace ta zauna dashi ko da baya haihuwar. To sai kiga abu yaƙi. Ya tabbatar mun yana sonki sosai nace ya baki farin ciki. Kuma wannan gida da kika zaɓa yayi kaɗan ya zagaya dake zuwa gobe ki duba a cikin gidajenshi wannene yayi miki sai ki tare acan. Kinyi dabara sosai. Akwai wani abu da kika fuskantane a zamanki da ita Hajiyan? Nasan dai tana takurama matan Zaidu sosai ala dole sai sun shaƙu da'ita a lokuta da yawa sai naita tunanin ko babu zuchiya a ƙirjinta ne. Munyi wani irin zama na girmama juna ni da yaya amman kowa na da iyakarshi. Bata matsawa ta shige mun yadda zan takura ko ace komai nawa ta sani. Haka nima bana yi mata hakan. Amman kullum muna tare hatta kaya kala ɗaya muke sakawa. Kinga wannan azurfa dana baki? Azurfarta ce tafi shekara ashirin a wuyanta da kunnenta duk wanda ya santa ya san wannan azurfa shi yasa zaki ganta da nauyi. "Mu mutan da muna ɗaura azurfa a matsayin tsarine babba, shi yasa hatta jirajirai muke ɗaura musu a" wuya ko a ƙugu maganice kuma tana maganin kambun baka sosai. Sai da ilimi ya yawaita ne komai ya canja. Da zaki mayar da azurfarnan wuyanki ta zamana ko da yaushe kina tare da'ita da yadda sonki zai ƙaru a "zuchiyar mijinki zaki yi mamaki, wannan azurfa zata zame miki garkuwa." "Duk wani abu da zai taɓaki da sunan cutarwa zai ji zafin kamar ita akayi ma.""" Sallamarshi ce ta katse mana hirarmu. Suka shigo shi da ƙaninshi mijin Anty Khadija wallahi kamar ƴan biyu tsayi kawai Alhaji yafi mijin Anty khadija da kaɗan. """Ashe tana nan. Hajiya ta karaɗe gidannan tana nemanta fa. Goggo wannan yarinyar me tayi miki ne?""" """Soyayya min indillahi nake yi mata sosai. Shi yasa na haɗata da Khadijanka nasan zasu ƙaru da juna" "sosai.""" Da kunya na gaishe da mijin Anty khadija shi kuma ya mutuntani a matsayin matar wanshi. "Goggo bari inje wajen Anty khadija""" """To shikenan Allah yayi albarka." "Neman me munubiya take yi mata ita da bata barin mutum ya sha ruwa? """ Na saka kai na fice ba tare da sanin amsar me suka bata ba. Tsohuwarnan tana zargin Hajiya bata da tudun dafawane babu hujja shi yasa. Nayi imani ba za'a rasa waɗanda suma suke zargin nata ba. "Ɗakin Anty Khadija na shiga, ina shiga na soma cin dambu kenan Hajiya ta leƙo firit babu sallama." Sai ta washe baki. """Wai ina kika shiga na neme ki na rasa a gidannan? """ "Wallahi ina wajen Goggo muna ta hirarmu sai yanzu na dawo""" Anty Khadija tace. """To ki shigo mana Hajiya sabida sauro""" """A_a ba shigowa zanyi ba ina ɗakin Huwaila in kin gama ki same ni acan""" Ta saki labule ta wuce da idanu Anty khadija ta bita sai cewa tayi """Allah ya kyauta.""" Ni dai naci dambu nayi ƙat na kora da kunun zaƙi. "Anty khadija ga nera ta dubu hamsin a bani magunguna naji daɗin waɗanda kika bani sosai. """ """Ai zaki ji daɗinsu. Akwai babban basket na amarya shi ya kamata ki siya dubu saba'inne amman ki ɗauka" a hamsin ɗin. To shikenan nagode sosai naga wasu tsumi ma da kika koya a group inaso inna samu lokacine sai in shiga "kasuwa in harhaɗo kayan nazo in daddafa in adana.""" """Bakya ra'ayin mai aiki kema kamar ni kenan? Kinga surukan gidannan duk suna da masu aikinsu sai ni" kaɗai. Kayan haɗin magungunan ma ina siyarwa harda zuma da mazar ƙwailan ma. Hajiya fa bata taɓa "siyan magani a wajena ba. Su da su Huwaila daga Senegal ake kawo musu magungunan matansu, suna kashe kuɗi sosai kuma basu fi nawa kyau ba.""" Dariya muka yi nace. To a bani komai Anty Khadija gobe sai in daddafa abini. Wallahi ƴar aikince bana ra'ayi duniyarce abun tsoro wallahi sannan naga dan dai aikina ni ni kaɗai ace "saina ɗauki mai aiki""" """Nima abinda nake gani kenan gaskiya. Shi yin aikace_aikacen gida yana ƙara lafiya sabida tamkar" "atisaye ne kake fa. Sunfi so su jibge waje ɗaya suci sui ta ƙiba""" "Mun jima muna hirarmu ni nama mance da wata Hajiya itama bata sake bibiyata ba, a ɗakin nayi sallar" isha munata hirarmu har dai Alhaji ya leƙo yace in fito. Haka na fito muka wuce wajen Goggo nayi mata saida safe nace sai nazo mata wuni. """Ai akwai meeting sati mai zuwa na bikin su Isma'il kusan su bakwai za'a Aurar gya zo ranar ko? """ "To shikenan Goggo nagode sosai Allah ya ƙara lafiya.""" Tare da Hajiya duk muka fito ta nufi motarta muma muka nufi tamu motar. Mu muka soma yin gaba tana biye damu a baya. """Wazirat can gida zamu soma zuwa zan ɗebo kayan sawata sannan zamu yi magana da Hajiya tunda bata" san ma mai ake ciki ba. Goggo Amfana tace sai dai in kai ki cikin gidajena ki zaɓi wanda ranki yake so wannan na ɗorayin yayi kaɗan. Tayi na'am sosai da hakan ai ke baki da matsala. Sannan yaushe kike tunanin mu nemi Baban Mardiyya akan batun matarshi ni ba'a waya nake so muyi magana ba ido da ido nake so muyi. Kinsan ɗazu na tura mata amsa ta godiya data faɗamun wacece ke. Hmm Wazirat sai ta sake jero wasu "miyagun maganganun masu yawa a kanki. Lallai wannan mata bata ƙaunarki sam gaskiya.""" "Bata ƙaunata na yadda. Sanda muke zaune a ƙarƙashin miji ɗaya tayi sharafi sosai Omri, amman ni" wallahi bata gabana sam. Ci gabane sam bata so nayi tafi sha'awar ta ganni ina bara tana jefamun kuɗi a "kwano. Duk sanda ka shirya sai mu je mu. Amman zan fiso muje gaban mahaifinshi mu yi mishi bayani in yaso sai shi ya kirawo mana su. """ Wasu hawayen baƙin ciki suka taru a guraben idanuna. Bamu muka isa Kano ba sai wajajen goman dare. Mun fito daga mota Hajiya tace. """Baki fito da akwatin kayanki ba. Ko Hauwa za'a kira ta shiga dashi ciki? """ Bani nayi magana ba shi ya bata amsa da cewa. """Ke dai rabu da batun akwati Hajiya ku zo mu shiga ciki""" Yayi gaba muka bishi a baya. Sai adda'a nake yi babu ƙaƙƙautawa kuma inajin tsigar kaina tana wani irin buɗewa. Wallahi ina tsallake ƙofar falon gidan sai naji kamar na taka wani abu mai tudu haka. Dana duba banga komai ba ko tsinke babu a wajen. Adda'a na tsananta yi na sake ɗaura ɗayar ƙafar tawa na shiga Hajiya ina kallonta tana murmushin muguntar ita ƙila ta gama dani. Tabbas asiri na taka babu ko kaffara. Zama na nayi a babban falon gidan sai tayi sauri ta juyo ta dubeni. """Ba zaki shiga daga ciki bane, ni bacci nake ji sosai bare in zauna muyi hirar zumunci""" """Hajiya shige magana zamu yi. Wazirat ki hau sama ki haɗamun abunda ya dace ina zuwa""" "To shikenan Omri sai ka fito. Hajiya sai da safe.""" Na haye ƙafar bene su kuma suka shige ciki. Kayanshi na haɗa mishi a akwati ƙarami. Inason ɗiban zannuwan gado a ɓarayina Allah ya sani tsoro "nake ji bansan me akayi mun a ɗaki ba. Gashi can babu zanin gado ko ɗaya, zannuwan gadon Alhaji kuma ban yadda dasu ba dukka." "Ni dai ina zaune sha ɗaya, sha ɗaya da rabi sha ɗaya da arba'in na jiyo takun Alhaji Zaidu." Ajjiyar zuchiya na sauke dana ga ya shigo da fara'a. """Muje wazirat na tsaya rarrashin yayarkine kinsan tafi son a zauna gida ɗaya kar kiga na daɗe muje ko" "Shalelen mijinta""" Miƙewa nayi shi ke jan akwatin har muka sakko ƙasa Hajiya na tsaye yau babu wannan fara'ar ta gulma. Idanunta ma naga sun gumbura kuma sunyi ja kamar kuka tayi fa. """To Sabuwa Allah ya tsare ko sai nazo ganin waje""" "To shikenan Hajiya da Alkhairi in nayi miki ba daidai ba ki yafe ni dan Allah""" Sai tayi wani murmushi mai fassarori tace. """Allah ya yafemu baki ɗaya. Sai yaushe za'a kwashe kayanki to? """ "To bazai wuce jibi ba in sha Allah zamu zo mu kwashe""" """To yanzu ba zaki shiga ɗakin ba kenan ko suturu ki ɗiba dasu zanin gado da abubuwan da ba'a rasaba?""" Murmushi nayi mata nace. "Bana buƙatar komai Hajiya nagode sosai """ Ina faɗan haka na saka kai na fita shi kuma na barshi a tsaye. Bai jima ba ya biyoni muka dawo ɗorayi a falo muka kwana sakamakon rashin zanin gado. Ranar mun gudanar da wani irin soyayya mai taushi da laushi sosai wannan dare yana daga cikin dararen da ba zamu mance shi ba. Sai dai fa sai nake jin abu kamar yana shiga jikina wallahi haka nake ji. Dana shiga banɗaki sai nake ganin kamar inuwar mutum a kaina. Idanuna na runtse gabana nata faɗuwa fat fat fat a haka na gama wankan na fito. Adda'a kuwa yi nake ban fasa ba. Ƙanƙame Alhaji Zaidu nayi ƙam na cusa kaina a ƙirjinshi. Wallahi Allah bacci ko ɗis banyi ba yaƙi zuwa. A hankali na zame jikina na miƙe na sha rubutuna na shafe jikina dashi na zauna inata adda'a sai can bacci yayi gaba dani na kwanta a jikin Alhaji da yake baccinshi hankali kwance. Washegari muka wayi garinmu cikin farin ciki sai na jini garau dani. Kafin ya dawo daga masallaci nayi wankana na shafe jikina da humrori ina zaune a falo ina jiran shigowarshi. Ai kuwa yana yin sallama naje na ɗafe shi muka yi murmushi. """Jiya ƙarfi da yaji kin samu kwanciyar ƙasa uhm?""" "Tuba nake yi kaina bisa wuyana. Yau zan tanadar mana duk abinda ya dace in sha Allah""" Hancina ya lakace yace. """To naji. Yanzu abinda yafi dacewa shine bari in shirya sai mu fita. In zagaya dake gidajannan ki gansu sai" mu nemi gidan cin abinci muci. Daga nan kuma mu nufi Kano dan wannan lamarin bazan yi wasa dashi "ba da zafi zafi ake dukan ƙarfe""" Zanyi magana ya ɗaura mun yatsanshi a leɓena dole nayi shiru. "Taimaka mishi nayi ya shirya muka rufe gidan muka fice ya zazzagaya dani gidajen na zaɓi ɗaya, daga" nan muka shiga gidan cin abinci muka ci dankali da ƙwai da shayi kana muka ɗauki hanyar Kano. Ina ji yana waya da Hajiya yana sanar mata tafiyace ta kamashi amman yau zai dawo inya dawo zai biyo ta gidanta. Goma a cikin Dutse tayi mana sai gamu a gaban Baba Malam. Yayi farin cikin ganin Alhaji Zaidu sosai. Ashe ma Baba Malam yasan mahaifinshi tare suka yi karatu a tsangaya ɗaya. Bayan an gama gaisawa muka gabatar mishi da abinda ya kawo mu. Hankalin Baba Malam sai ya tashi ainun duk sai ya shiga damuwa. """Kayi haƙuri Zaidu dan Allah. Yanzu zansa ayi mun kiran shi Babangidan da matar tashi suzo su same mu." "Duk matakin da zaka ɗauka sai ka ɗauka akai ina zuwa""" Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fita waje. Su Mardiyya ne suka fito zasu tafi makarantar boko. Suna ganinmu suka shiga murna tare da zubewa a gabanmu suka kwashi gaisuwa. """Za'a tafi karatu ba? To Ubangiji Allah ya taimaka. Bari a ƙara muku kuɗin tara""" Ya zaro dubu ɗaɗɗaya ya miƙa musu suka amsa suna godiya da adda'a mai kyau. Binsu nayi waje na jaddada musu su yi mun adda'a kada su gajiya ina cikin matsala. Sun tafi kenan wayata ta shiga ruri Adama ce. "Adama barka da safiya""" """Barka dai lolo kinga gani nan na shigo shine muke hirarki wallahi kinji dalilin kiran. Na shigo gobe zan" "shigo Kano sari in sha Allah zan shigo miki""" Yauwa Adama dan Allah ku tawo da Rahama da Sadiya na canja gida kayana dake can ɗayan gidan zaku "kwaso mun sai mu jera a sabon gidan. Ki biya musu kuɗin mota zan baki in kuka zo""" """Au har an sake miki gidan? To madallah munyi farin ciki. Nazo gidan ai nake jin me ake ciki. Babu komai" "ta Allah ba tata ba wallahi dukkan sharrinta kanta zai koma ke dai ki iya takunki kawai. Sai goben dai in mun shigo ɗin tare da Maigogul ma zamu tawo""" "Murmushi nayi nace to shikenan sai kun shigo ki gaida su Rakiya""" Da haka mukai sallama na koma zauren na tadda Malam ya dawo Na zauna ban jima ba sai ga Babangida da Ƴar Shuwa sun shigo zauren. Ganinmu yasa duk sun sha jinin jikinsu musamman ita Ƴar Shuwa da tasan abinda ta shuka ba abu bane "mai kyau sai tayi turus""" """Ai sai ku nemi waje ku zauna ko? """ Cewar Baba malam da muryar rashin wargi. Babu shiri suka zauna ni da Ƴar Shuwa sai kallon_kallo. Alhaji da Babangida ma sai kallon_ kallo Mrs Bukhari "[10/24, 6:45 PM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 8 """Kai Babangida tashi ka yo kiran Ƙarama tazo. Sabida tasan cewar nayi ma matarka iyaka da yaran" Sabuwa. To dake kai take Aure kaima dana haifa baka darajani ba bare matarka. "Kaima dana haifa baka girmama maganganuna ba bare matarka""" Alhaji Zaidu yace. """Ayi Haƙuri malam kasan ɗan yau ka haifi mutum baka haifi halinshi ba.""" Babangida ya kalli Alhaji Zaidu ƙasa ƙasa bashi dai da yadda zaiyi tunda a gaban Baba malam muke. "Kirawo Malama Ƙarama yayi suka tawo tare, aka gaisa kafin Baba Malam yace." """Malam Zaidu ba shi Babangida ya karanta saƙon iyalinshi mu saurara dukkanmu""" Ƙur Baba Malam yayi yana nazartan Ƴar shuwa da duk ta ruɗe take ta zufa. "Babangida yasa hannu ya amshi wayar ya soma karantawa da murya mai kauri da farko, daga kusa da" "ƙarshe sai muryarshi tayi sanyi, ta ƙarshe kuma sai muryarshi ta shiga rawa har tana karkatsewa""" Salati Malama Ƙarama ta soma yi tana tattafa hannunta. Hannunta ɗaya fisa haɓarta tace. """Allah mai iko da abun ikonshi. Ke yanzu Maman Fatima abinda kika zaɓama kanki kenan, ke ko wannan" "bita da ƙulli har ina? """ Babangida yana zaune jikinshi na rawa. Ranar da muka zo gidannan da Maigogul da Ci cib ne kaɗai naga Babangida a cikin irin wannan kaɗuwar sai kuma yau da Jannaty ta taro mach. Idanunshi sukai jawur sai "kallon tsana yake yi ma Ƴar Shuwa""" """Abinda zan soma dashi babba guda ɗayane kafin sauran bayanan su biyo baya. Aisha kece kika rubuta" "wannan saƙon lambar data tura saƙon lambarki ce? """ Shiru babu amsa sai rawar murya. """Ba dake ake magana ba ko saina tattakaki a nan wajen tukunna. ? """ "Babangida yayi magana da murya mai amon maɗaukakin ɓacin rai da tsawa_ tsawa.""" """Kash_ sha kada ka sake magana sai anzo gaɓar da zaka amsa naka tambayoyin. Ke Aisha kada ki bari in" "maimaita tambayata bana wasa da yarana ma bare surukata""" """Nina rubuta? """ Ta faɗa tana matsar hawaye tasan Baba malam ba mutum bane mai wasa shi yasa ta amsa. Kuma dolenta ta amsa dan ruwa ya ƙarema ɗan kadane. """To shi mijin da ba naki ba a ina kika samu lambarshi, da har kika zauna kika jero mishi wannan" "maganganun dan ki tozarta Sabuwa? """ Ƙur yayi mata Kunji tuhumar data tashi kaina. "Wato Baba malam dattijone sosai wallahi madallah da uba nagartacce kuma tsayayye, mai kaifin basira." Anan tsiyar take gashi dole ta faɗa tunda tana son aurenta. """Mamanmu ce ta karɓo mun a wajen Hauwa kishiyar Babarsu Sabuwa""" Dam naji gabana ya faɗi Hauwa kenan ita da Rakiya kowanne ya kafe akan halayyarshi dai sun ƙi sauka. Tun muna yara Hauwa ke haddasa husuma a gidannan. Damma bamu taɓa daka ta tata ba sai Layuza da take biye mata. """To shikenan ta zo da sauƙi ai ke kinsan mahaifin mardiyyan ko? Sai ki faɗama kotu in akaje kotu zata" bincikoshi saita bashi ɗiyarshi inace shi kaɗai kike so ko? Sai mijin Sabuwa yace ya rabu da'ita ko ba shikenan burinki ba dai? Kin rabata da gidanta bai isheki ba. Sabida a sanadin shashancin shi mijinki daya Auroki yake ganin hukunci zaima Sabuwa sai kika zame mishi hukuncin shi akab_ karan kankin kanshi. Shi mugu baya cika mugu sai yayi ma kanshi mugunta. Kai kuma ai kaga irin abinda ka jama haularka ko. Tun farko da baka tsangwamar yaranka ita wannan bata isa kawo wannan maganar ba ko da kuwa hakanne. "Baka tsara gidanka ta yadda matanka zasu ji shakkar ka ba, duba da yadda aka haɗu aka gina zaman" babu mutunci sam a sabgar ga rashin gaskiya zuchiyoyi fal abubuwa marasa daɗi. Kuma har gobe ina faɗan Kafi Sabuwa laifi a matsayinka na ɗan malamai ita Ƴar kawali a wancan lokacin. Sannan tambayar da nake maka. Kai ɗin a haka matanka suke sakaka ka buɗe musu ƙofa suyi duk yadda "zasu yi, haka sharia ta tsara, ko shariar gidanka ce ta tsara haka?""" Murya a dashe sosai yace. """Wallahi Malam sha'anin Aisha lamarin taurin kanta yana da yawa. Kuma ban barta sasakai ba, ina" yawan binciken wayoyinsu musamman itan. Babu abinda na taɓa gani sai dai akan ƙawaye yadda take mutuntasu yawanci abinda ke bamu saɓani kenan. Amman in sha Allah zan sake lura. "Su Mardiyya kuma. """ "Hannu Baba Malam ya ɗaga da sigar dakatarwa, dole ƙanwar naƙi kuwa ya haɗiye maganar daya jawo." """To ga Zaidu ya Aure Sabuwa dai, tare da sani haƙiƙanin rayuwarta ya kuma karɓeta tare da danginta" kab. Maigogul daka raina shi a idanunshi Dattijone mai cikar kamala da natija. Zaidu bazan taɓa cewa kada ku maka su kotu ba. Amman in kun fahimci juna ta kawo uban yarinyar anan ma shikenan. "Ke da aminiyarki ace kina bibiyar rayuwarta da irin wannan sharrin, kina mata hassada Allah na ɗaga" darajarta. Yaranta sun kasance fitila mai hasken haska ahalin da zaku tara. Ina fatan addinin Musulunci yayi fahari dasu musamman ita mardiyya da kike tunanin bata da gata. Ana Aurenta da Sauban zata koma tsangayar madina da karatunta ta tafi tare da mijinta zan ɗauki nauyin komanta har digirgir sai ta haɗo kafinma ki sake ganinta. Kuma da ba dan babu kyau umarni da saki ba da yanzu zan umarci Babangida ya sauwaƙa miki. Amman "bazan yi haka ba sabida nima na haifa kuma burina su mutu a ɗakunan mazajensu. Amman akan Sabuwa tunda na iya Rabuwa da Babba to Babangida zai iya rabuwa dake, kije ki saurari hukuncin da zai biyo bayan wannan abun da kika aikata dan ba ƙyaleki zan yi ba""" Ajjiyar zuchiya na sauke tare da share hawayen farin ciki. Zuchiyar da bata ƙullaci kowa ba Allah shi ke taimakonta. Ƴar shuwa ta muzanta gaya ta kuma tsorata sosai Haka taita kuka tana riƙe zanina akan mu yafe mata yarinya tabbas ta Babangida ce sharrinta ne kawai. Babangida kuwa tunda ya sauke kanshi bai sake samun zarafin ɗagowa ba. """Shikenan albarkacin Baba Malam mun janye sai dai dole zamu je ofishin ƴan Sanda ayi a rubuce duk" abinda ya sake biyowa baya makamancin wannan to tabbas sai anyi sharia har zuwa kotun Allah ya isa. "Sannan Baba Malam dan Allah ka yafe mata ka barta a ɗakinta kada yaronnan ya sallameta gara su zauna su gyara junansu""" Mugun kallo Babangida yayo ma Omri wallahi sai da na kusan dariya ma. Alhaji ya jima yana roƙon Malam kun san shi da kafiya da ƙyar ya janye hukuncin da yace zai yi matan. Dole Ƴar shuwa ta amince muka je tare harda Baba Malam aka saka hannu aka kashe kes ɗin ruf. Dama tun muna hanya ya riga yayi waya da abokinshi babba a Ƴan doka. "Daga nan ofishin ƴan doka muka kama hanyarmu sai Dutse, a hanya dai mukai azahar la'asar a garin" "kano tayi mana. Bamu shigo gida ba saida muka biya muka ci abinci ya kaini sito ɗin Hajiya Balaraba na siyo zanin gado da senta kafet na uwar ɗaki, dana falo kana ya zo ya saukeni a gida ya wuce wajen Hajiya." Gidan Ɗorayi na koma sai gobe zan koma wancan gidan. Na dai bashi sallahun ya tawo mun da gas kuka na da silinda haka. In ya dawo mayo cefanen kayan abinci dan wallahi kayan abincin ɓarayina sun haramta a gareni da ragowar kab abinda ke cikin ɓarayin nawa su Adama zasu tafi da kaya rigi _rigi kuwa. Nasan dai zaiyi wuya ama gas kuka asiri da tukunya baya ga su ban yadda da komai ba. Ga babbar sarƙar gwal ɗina tana gidan Allah ya soni azurfar wajen Goggo tana cikin han bagi na ɗayan gwal ɗin na wuyana. Maigogul na kira a waya ban rufe mishi komai ba kamar yadda kuka sani. """Kinyi kyan kai. Nima dani za'aje ɗiban wannan kaya Sabuwa tun a cikin gidan za'a watsa musu fitsari" kafin a taɓa. Na haɗo miki itatuwa da zaki daddafa ki dinga shansu tsarine da izinin Allah babu fa shirka ko kaɗan a lamarin. Kinsan dai ba'a faɗama Bararo magani ba ko? Shi kanshi gas kuka ki tottofeshi da adda'a kafin kiyi amfani dashi. Babu komai. "Ita kuwa Hauwa akan wannan Abun kinji na rantse saina saketa ta ɗanɗani zafin zawarci, ina na dena" barinsu Kayi nayi kaɗaima ta isheta Allah. Ita kuwa Shuwa taje dan kanta ruwa cikin cokalima ya ishi mai hankali. Abinda nake sonki dashi shine kinga tunda kin matsa gefe to sai fa dagewarki tafi ta baya Lolo. Sabida "kafin mijinki ya dawo gidanki tsab za'a iya wanko mishi kai yama fitittike yace bai sanki ba, koma yace ya sakeki bafa komai bane." Bacci bai gammu ba Lolo dole mu dage muita faɗama Allah muci gaba da tuba a bisa laifukanmu na baya. Hajiya Balaraba gobe da safe zata tawo ita da ma'aikata ai miki sabon jere ni zan biya kuɗin Lolo in sha "Allah.""" Mun daɗe muna waya kafin mukai sallama. Sai na shiga aikace_aikacen gida kuma. "Alhaji Zaidu bashi ya shigo ba sai bayan isha ya tawo mana da gashasshiyar kaza, sai kayan shayi da" biredi da ruwan gora da lemun gora. "Kazar muka ci muka baje mukaita hirarmu, kana muka soma karatu da koyon baƙi sabida yace so yake in" fahimci karatu ta yadda bazan sha wuya ba. Hanya mafi daɗi itace in iya baƙi. Bayan mun gama karatu kuma muka shiga raya dare muka wayi gari cikin farin ciki. "Kuma banji wannan irin abunda na ji jiya ba da daddare na sha rubutuna na shafe jikina dashi, kuma sai" dana tsarkake jikina na kwanta ina daga kwance inata ambaton Allah har bacci yayi gaba dani. Wannan kenan. Gaga_gaga da safe muka wuce sabon gidana gas kukan ma ko sakko dashi ba'ayi ba. Ruwan shayi na dafa mana a butar shayi na wuta dake Kitchen ɗin. Na ɓare sababbin kofuna a leda na ɗaurayesu da tafashasshen ruwa muka sha shayi da biredi sai ragowar kazar da muka bari. Muna gamawa muka tattara komai muka wuce. Mun yi waya da Hajiya Balaraba ma suna hanyar zuwa can sabon gidana dake unguwar Tarauni. Kusan minti sha biyar ne a tsakaninmu mun iso suka iso. """Wazirat to ni zan wuce office kawai Hajiya tace zan kawota amman sai da daddare. To zan zo in kawota" "in sha Allah. Me da me kuke buƙata na cefane tunda su Yaya Adama suna hanya? """ "To shikenan Allah ya kaimu, ashe fa yau a wajen Hajiya kake. Allah sarki ni, yau daga ni sai fulo kenan""" Murmushi yayi mun ya kalleni sosai. """Shalele rigima kenan. To su kayan da su Yaya Adama zasu ɗebo yaya za'ayi dasu ne uhm? Naga ga" "sababbin kaya kince Alhaji Baba ya baki uhm""" Hakane. To su Adama ne zasu raba a tsakankaninsu gaskiya kaji yadda za'ayi dasu. Kayan abinci kuma "kayan miya nake buƙata da su nama dai haka sai ruwa da lemo""" Bana so ince harda su shinkafa da mai ne ya soma zargin wani abun in kirama kaina ruwa inya fita na saka a siyo tunda akwai kuɗi a wajena. """To shikenan Abinda za'ayi zansa yara su kawo muku Shalele ni na tafi sai mun yi waya""" Da haka mukai sallama ya ja motarshi ya tafi. Gas kuka kuwa kamar yadda Maigogul yace sai da na tottofeshi fes kafin na wankeshi tas da ruwa a tsakar gidan. Hajiya Balaraba kuma tana ciki tare da ma'aikata tana basu oda. Ma'aikatan nata na tura kasuwa suka siyo mun kayan hatsi komai da komai. Da yaran Alhaji suka kawo cefane sai na tashi girki. Gaga_gaga cikin awa ɗaya da rabi aka gama komai falo ya ɗauki fasali har turarukan B4B gidan ƙamshi ta kuma kawo mini box guda kuma tace dani show glass yana tafe. """Naji labarin komai. Kinga munubiya tun muna makaranta macace mai son mulki da son kanta sosai," gata da mugunta hatta a kalaman bakinta babu alkhairi sam. Wannan dalilin yasa bana cikin sabgarta kwata kwata ai na faɗa miki. Adda'a zaki riƙe babu mamaki wa'adinta ne yayi. In kuma da rabo sai kiga kin haihu dashi ke ɗin. Allah "Ameen da munyi farin ciki Hajiya Sabuwa""" Gaga_gaga da misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga motar kaya tare da motar su Maigogul. Mu muka buɗe musu get aka zube kaya kwatsar a tsakar gida harda suturun dake sib dana akwatinan da Hajiya tayi mun dan ba kayan ciki kaɗai ba har akwatin banso wallahi. "Sai dai fa sarƙar gwal tayi layar zana basu ganta ba sam. Magazin da Ma'aru ma sun biyosu, a mata" "Kuma Adama, Labbai, Rahama, Uzairu muzuru da Gaza yace ayo gaba dashi harda sarƙa aka saka mishi a wuya sabuwa. Ƴan uwa masu daɗi sai naji sun zabtare mun rabin damuwata." """Wannan kayan gado dai zasu koma show Room in da ciko sai in yi ma Hajiya. Ragowar karikicen Kitchen" "da suturu, da kayan abinci, da waɗannan kayan fulawa na biki kuma rabon su Adama ne sai su wauwanke su shanya duk su bushe dan fitsarine linkib a jikin suturun. Kuma harda laya gata a ƙarƙashin gadon lolon muka tarar harda sunan lolo da sunan Alhaji Zaidu a cikin baka kun ganta""" Maigogul ya ciro baƙar leda a aljihunshi ya warware mana muka ga layarnan jikina yayi sanyi ƙalau "wallahi.""" Sai da suka gama wauware kaya suka kasafta tsab suka wanke hannuwansu muka shiga ciki muka baje aka soma liyafar cin abinci sai santin gidan suke yi dan gaskiya gidan yayi ga falon yayi biyun wanda na baro haka ma ɗakunan tabka tabka komai a yalwace. Ɗakina kaɗai aka saka kayan gado ragowar ɗakuna ukkun a haka aka barsu sai kafet malala a ciki kawai dama a ciki muka taddasu. Bayan magriba sai ga Alhaji Zaidu shi kaɗanshi da leda mai zane shaƙe da banƙararrun kaji da jus_jus ya "shigo, amman shi shi ɗaya yazo shi banda Hajiya ko me ya faru oho dai." Haka ya shiga cikin dangina yana ta murnar ganinsu tare da martabasu a yadda sukensu. Ya ɗan jima kafin yayi mana sallama akan sai gobe da safe zai zo. Na bar maganar gwal ne akwai gaɓar da zanyi mishi maganar in ya dawo gidana kafinnan ya nitsa. Ni da Maigogul mukai mishi rakiya zuwa gaban motarshi. """Dama akwai wasu saƙe saƙi dana sassaƙo muku a jeji da hannuna na haihuwane. Lolo sai ta dafa muku" "ku dinga sha musamman kai ka zage ka kakkaɓa muna sa ran in sha Allah za'a dace. Kasan da nayi harkar bada magungunan kurga, da amagyagya na yara, to bada taimakonma na taɓa wallahi denawa dai nayi""" Ya ƙarashe yana dariya. """Mungode sosai Alhaji Baba. Matsalar ma daga garenine ina kyautata zato zan kuwa zage in sha in sha" "Allah. Kuma wallahi naji daɗi sosai a baya ma duk na sha daga baya ne na watsar.""" """Hahahahhh babu komai. Sai dai gaskiya kullum ake so a sha shi babu fashi duk da kullum zaku haɗu" babu matsala tunda wajen aikinku guda ko. Ai haiƙan zakai ta sha za'a dace da izinin Allah. Itama fa mai ɗakina Hauwa wallahi na saketa sabida ba ma Babar Ƴar shuwa lambarka da tayi. anyi rikici "a gidan sosai, harma shi babban ɗan Hauwa Masa'u wai zai sassareni ko ya turo a sace ni. To ni dariya ma ya bani, Allah na tuba wanne iya shege ne bamu gani ba. To ita Uwar taku dai har gidan uwar Ƴar shuwa taje aka raba garin tsiya, mu dai rigima bata lafa ba har yau ɗinnan. Itama Ƴar Shuwan wai ta" "dawo gida, ko da takadda, ko hutu aka turota tayi ba dai mu sani ba. Ka dai sake haƙuri dan Allah""" Alhaji Zaidu yace. """Ashsha Alhaji Baba. Ko dan albarkacin yaran da an duba ba'a saketa ba. Ayi haƙuri a mayar da'ita dan" "Allah. Aba Mama Haƙuri itama duk a huce babu komai wallahi.""" """Ai fa baka sani ba Gaza har gidan Malam Habu ya burma dake ya raka ita uwar tashi, shi dama ba" "sonmu yake yi ba, ana faɗan ya fito yana aibatamu dawa Allah ya haɗashi da Gaza.. """ "Maigogul dare yayi ka barshi ya tafi""" """Rai a ɓace Omri ya dubeni harda hararata, amman ta gargaɗice." """ Toh hakane Alhaji da Alkhairi""" Maigogul dai ƙin bamu waje yayi tare muka koma ciki Sai wajajen goman dare Maigogul da Hajiya Balaraba suka tafi Uzairu zuchiyata yace a barshi zuwa jibi in su Adama sun tafi ya dawo. Ai suna tafiya muka dasa hirar rikicin Hauwa da Maigogul da Kayi nayi. """Ke anyi abu. Kayi nayi har waje ta ja Hauwa suka fita dambe da ƙyar maƙota suka raba. Layuza dake" bata da mutunci tace yau ɗinnan zata kama ma Hauwa gida su koma gabaki ɗayansu ke kiji neman fitina. Masa'u kuwa saida Gaza ya karza wuƙa yaga tayi walƙiya sannan ya fita a gidan. Cacar baki sukaita tatayi "da Maigogul.""" Rahama ke bamu labari. Labbai da Uzairu zuchiyata kuwa kun ga dariya wai kuwa haɗe kai suka yi sukai ta ƙyaƙyatawa. Adama tace. """Rakiya ta ƙarama rigima maggi. Wai Gaza ne yai nata Rakiya layinmu na da." Ta faɗa gidansu Ƴar shuwa shi kuma ya faɗa gidansu Malam Habu daya fito yana ƙananun iskanci Suka "raba abun kunya dai in faɗa miki dattijan anguwa dana maƙotan unguwama da ƙyar suka raba rikicin. Ƴar shuwa dai ana raɗe raɗin Babangida ya saketa amman babu tabbas gaskiya.""" Kunsan mune har biyun dare muna musu da dariya. Sai wajajen biyu da rabi Uzairu zuchiyata da Ma'aru suka shige ɗakin hagun ɗakina suka bi kafet sukai kwanciyarsu gida to babu. "Su Labbai kuma gado suka haye, ni kam sai da nayi sallah na sha maganina na shafe jikina kafin na yi" kwanciyata a ƙasa su na basu gadon sai tusa Adama take sakar mana ta cika ɗakin fal da wari. Murmushi nayi na tuno shekaru talatin baya a lokacin duk muna gida muna irin wannan gwamutsuwar ta bacci muita tusa abinmu. Rayuwa kenan. "Gaga_gaga sai da muka kwana biyu cur dasu Adama, washegarin ranar da suka zo suka tafi kasuwa ai" "kuwa Labbai ma ta samo gyaɗa mai sauƙi rabin buhu ta siyo, Adama tayi tsince_tsincen kasuwancinta su Rahama kuma suka zama ƴan rakiya da su Uzairu zuchiyata daya aro motar Mum ta wajenshi." A ranar ƴan Rano a gidana suka wuni cur mukai zumunci sunata santin waje sosai. Washegari kwana biyu kenan su Rahama suka tattare kayayyakin dana rabar musu suka kama hanya Omri yai musu goma sha tara na arziki Maigogul ya kaisu har tasha. "A kwana biyun na dafa mana magungunan haihuwa da Maigogul ya kawo mana, in Omri yazo da safe sai" ya cika kofi tam ya shanye nima yace in sha ko babu komai zai gyara mun mahaifa tunda mahaifar dama tana da matsala. Da yamma ranar da Omri zai dawo gidana a ranar da su Adama suka tafi. "Na gama komai na gyare gidana na banka ƙamshin turare, girkina na kammala na jera komai a ƙasan" kafet ina gaban mudubi sai naji anata doka get wani irin duka da rashin mutunci dai. Hular dake ajjiye a gaban madubin na saka. "Ina saye da riga da wando na kanti sun kamani tsam, fuskata na caɓa ado ga wannan azurfa a kunne da" wuyana. Sanin babu mai gadi a gidan yasa na fita a yadda nake. Ƙofarnan dukanta akeyi. "Waye yake buga ƙofa haka? """ "Hajiya munubiya ce. Kina ciki anata buga ƙofa bakya ji? """ "Sakatar ƙaramar ƙofa na ɓalle muka haɗa idanu da'ita tana tsaye da ƙawarta, ga motarsu a bakin ƙofar" gidan. Haɗa idanunmu sai naji kaina ya sara na ɗanji juwa kaɗan. """Ko zaki iya buɗe mana get mu shigo da mota? """ "Inaga sai dai ku barta a wajen bazan iya buɗe wannan ƙaton get ɗin ba""" Hajiya Mansa ke magana cike da taƙamar da zaka rantse itace a matsayin Rakiya ko Maigogul. Sai ita Hajiyace tace. """Bari mu bar motar anan. Ai ba zata iyaba""" Waje na basu suka shigo na rufe gidana nayi gaba suna bayana. Har muka shige cikin falon. Numfashi naji Hajiya ta ja mai nauyi sosai. "Ruwa na kawo musu na zauna aka gaisa babu yabo babu fallasa. Sai tambayoyin ina kayana suke to, taga" na sake wasu yaushe yaushe da Aure. "Ta leƙa Kitchen ta leƙa ɗakunan dake tsakiyan nawa, zata buɗe mun ɗaki na riƙe abun buɗewar nace." "Nan ɗakin mijinane Hajiya""" Sai ta wayance dai mukai dariya. "Ko dana basu abinci basu ci ba, bafa su daɗe a gidan ba amman a ranar na shiga sabuwar jarabawa kunji" wata ƙaddarar ko? Rimi_rimi Alhaji ya dawo muka tarbi juna cike da farin ciki muka ci abinci akai komai fa. Wallahi a wannan daren ni dai ƙaramar hauka nayi na dinga ihu ina fisgewa zan fita daga ni sai rigar bacci duk na firgice. Da Alhaji ya riƙeni sai nayi kukan kura na danna ihu in shaƙeshi da ƙyar zai ƙwace yana yi yana adda'a yana tofa mun. Wallahi kafin asuba duk na jij ji mai ciwo maƙota kuwa duk sun san abinda ke faruwa damu. Ana ƙwala kiran assalatu wallahi Allah sai naji kamar abu ya fita a jikina sai na dawo hayyacina. Ganin Alhaji duk na yakushe mishi fuska nima duk naji ciwo ga jikina duk tsami sai na fashe da kuka na faɗa ƙirjinshi. Kunji fa wata ƙaddarar. "Haka ni dashi muka rufe na ranar farko, ya shirya muka tafi aiki tare, kafin muje aikin sai da muka je naga" "likita a wani asibitin kuɗi, magunguna dai ya bani bayan ya mun tambayoyi da gwaje_gwaje, sai muka wuce wajen aiki muka wuni lafiya." "Da misalin shidan yamma muka dawo, muna shigowa ban zauna ba na shiga Kitchen. Zuwa bayan isha" na sarrafa mana shinkafa da miya. "Muka ci, na sha magunguna mu kai shirin kwanciya. A wannan daren abinda ya faru da irin ihun dana" dinga yi wallahi saida maƙota suka fito. Ya fita ya samesu ma ya kasa. Abubbuwa a haka suka ci gaba da tafiya dole saida Maigogul suka san halin da nake ciki har Baba malam. Sai aka alaƙanta hakan da aljanune suka shafeni nan kuma hankula suka tashi na shiga shaye_shayen magani afujajan. Sai Rahama ce ta tawo ta zauna dani a cikin gidannan. "Amman Maigogul da Baba malam basu zauna ba, Baba malam har sau biyu yana zuwa dubani, ina shan" rubutu "Ina sauraren Qur'ani, Alhaji Zaidu yanai mun tofi duk kwanan duniya. Ga saƙe_saƙin Maigogul da wasu" magungunan karya sihiri. "Amman wallahi ciwo sai girmama yake yi, da safe fa amma babu wata matsala sai da daddare ciwo yake" tashi. "Amman da Baba Malam yayo mun wasu rubutu ya kawo sai na dena ihunnan da fisgewa, amman fa nike" nan firgita da ƙanƙame Rahama ko Omri in ranar kwananane yazo ga mafarkai masu tashin hankali. "Kuma wani ƙudurar Allah da Hajiya da dangin Alhaji basu da masaniyar halin da nake ciki, ko da yake ita" tafi kowa sani tunda ita tayi. Sai dai duk wanda ya ganni yasan banda lafiya idanuna sun firfito sosai. A haka bikin Uzairu zuchiyata yazo ina babu dama inaji ina gani akayi shagalin da akayi bana wasa bane. Sabida rashin lafiyata babu wanda ya iya raka Uzairu zuchiyata Canada hankulan dangina yana kaina kacokam "Ita kanta Mardiyya biki ya ƙarato jikina ba daɗi sam. Gaza ma gari gari yake zuwa karɓo mun magani," amman abinda na yadda dashi lokaci Allah ya arama Hajiya. Akwai lokacin da ko ban sha komai ba zan warke da izinin Allah. "A dangin su Alhaji dai wani biki suna ina daurewa in shiga taron a hakan, tunda ba magashiyyan nake" "kwance ba, ba dan faɗawar da nayi ba babu mai gane ina cikin halin ciwo ma, Goggo Amfana ita ma ciwonta ya tashi bata gane ma wake kanta baiwar Allah. Ita kuwa Hajiya da ka kalli fuskarta sai kaganta a cikin farin cikin ganin halin da nake ciki. Kana kallon makashinka baka da abinda zaka yi mishi wata shari'ar sai Allah. Tazo gidana a ƙalla yafi sawu goma tunda ita ba za aci gaba da ɓoye mata banda lafiya ba. Har ranar da suka haɗu da Anty Tani itama tazo Rahama ke sanar mata banda lafiya. Da Hajiya tazo" sai Anty Tani tace. """Koma menene yake faruwa da matan Zaidu mu mun barma Allah ne bawai dan bamu da hankali ba""" Ƙus Hajiya tayi ba amsa. A haka bikin Ƴan Tagwayen Anty Tani yazo daf dana mardiyya Sadiya ce ta rakani muka je akayi komai dani a daddafen. Da bikin Mardiyya yazo Alhaji sai ajjiye aiki yayi ya biyoni muka tare a hotel dan kawai ya kula dani. Allah sarki bawan Allah baya nuna gajiyawarshi sam wallahi. Haka akayi bikin Mardiyya a gidansu Baba Malam. A lokacin ma na ɗan ciko na sake haske ashe ɓoyayyen cikine a jikina babu wanda yasan da bawan Allah. Kunji ƙaddara a cikin ƙaddara ko? To wannan ciki yasa nayi kyau babu laifi haka muka shiga cikin su Sa'a akayi biki. Su Adama ne akan komai ni sai ido ga ciwo ga laulayi gashi bana son shiga mutane sam. Su Hameeda sune iyayen Amarya da su Sumy da Hala duk mun haɗu dasu gaisuwar mutuncice ta "rabamu, Ƴar shuwa da danginta kuwa babu mutum ɗaya ma." Kwana biyu akayi aka gama biki duk abinda uwace ya kamata tayi to Alhaji Zaidu ya fansheni an yi mata "komai Aure na gata sosai akayi mata. Baba malam yayi rawar gani, haka shima Babangida ya fitar da'ita kunya sosai. Ta tare a gidan mijinta daya gina nan kusa da su Sa'a" Malama Babba ma naga duk ta rame tayi duhu wannan isar duk babu ita Rayuwa kenan kayan Allah. Maigogul dai kusan kullum sai yazo ya kawo magani ko yazo ganina. Ranar Juma'a ina zaune a falo na gama sheƙa amai na fito na zauna jagwab sai muka jiyo sallamar Maigogul ƙur yayi mun. """Lolo naga cikin ki kamar ya ɗaga kumburi yayi ne?" Sai ni da Rahama mukai saurin duban cikin Rahama ta latsa sai ta zabura. """Maigogul ai cikine da'ita""" """Tsarki ya tabbata ga Ubangijin kowa da komai""" Mrs Bukhari ce "[10/27, 8:49 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 9 Kunyi ready ku koyi skill ɗin da ke kawo kuɗi! "Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace," ko ku iya video editing kamar professionals — to wannan class ɗin naku ne! Za ku koyi: " Voice Over (recording, editing, delivery)" " Video Editing (cuts, transitions, subtitles & more!)" Practical + Real Project Training Location: [TELEGRAM ] Payment: 9163354359 Sa'adatu Adamu Opay Send receipt via Contact: [07044292865] Registration ongoing — Limited space available! Kada ka tsaya jiran lokaci — ka shiga yanzu Da mamaki nake kallonsu dana ji sun ambaci ciki. """Rahama abun nema ya samu zama bai gammu ba. Lolo maza ɗakko mayafinki kizo muje asibiti a duba" "cikin muga na wata nawa ne.""" "Amman Maigogul ba zaka bari muje da Alhaji ba, gashi su Rakiya da Hauwa suna hanya duk yadda akayi" "ma sun kusan ƙarasowa""" """Dake baki da hankali ba ai dole kice a faɗa ma Alhaji. Kubi komai a sannu duk abinda na tsara shi za'a bi" "ku nutsu. Taso muje maza zan faɗa mishi mun fita""" Haka Rahama ta ɗakko mun hijabina ta saka mun. Saifa data taimaka mun kana na miƙe tsaye ciwo ya cinyeni a tsaye. Asibitin kuɗi muka je aka Auna ciki wata har huɗu cib. Kuma wallahi inajin motsi kaɗan_ kaɗan haka "amman dake halin ciwo nake ciki, al'adarma da banyi ba daga ni har Rahama bamu tuno komai ba ana ta lafiyata." Muna asibiti su Rakiya sukai kiran Maigogul sun iso Kano. A lokacin Hauwa basu daɗe da dawo da Aurensu ba. Alhaji Zaidu ne ya tsaya tsayiwar daka da shi da Gaza har suka shawo kan Maigogul ya amince ya dawo da Hauwa kafin iddarta ta cika. Tasha muka wuce muka ɗakkosu ɗaya daga cikin atampar da Hajiya ta saka mun a akwati itace a jikin kayi nayi harda gyalenta to mach da ɗan ɗankunnenta ƙarami na gwal data siya daga cikin arzikin sana'ar kayi nayinta. """Baka da aiki sai yawo da Ƴaƴa raɓe_ raɓe damma kamar kumbon naka yana can canada. Jiya ma ya kira" "mun daɗe muna magana dashi.""" """Ai ke ba'a rabaki da takalar faɗa da maganganu. Shige muje muah dallah""" Motar suka shiga muka nufi gida. A falo duk muka baje Rahama ta kawo musu lemo da abinci. """To yarinyarnan lolo zamanta ya ƙare a gidannan na ɗan lokaci gaskiya dole zamu tafi da'ita dole ne" "wannan""" Da sauri na kalli Maigogul Rakiya nama cike da bakinta tace. """A wanne dalili mijinta shi ba cewa yayi ya gaji ba, shi ba nunawa yayi komai ba. Sai kaine sabida ka" "samu waje zaka ce haka? Kada ka mance yafa biya mana aikin Hajji dani dakai har da lolon zamu je. Kada kayi abinda zaka yi mana salesalin tsiya wallahi. Ka bar yarinya a gidan mijinta, ai ita makirar sai tayi" "tunanin taci galaba a kanta ma""" Numfashi yaja ya sauke. """Rakiya lolo cikine da'ita kin ganshi wata huɗu. Ganinmu da kika yi daga asibiti muke ko mijin baisan da" cikin ba. Kuma ba sani zai yi ba lalata mana shiri zaiyi dan fasa abun zaiyi kowa yaji halin da ake ciki. In labarin cikinnan ya isa kunnen Hajiya to bamu san a wanne irin hali ita lolo zata kasance ba har dama cikin. Ki duba tulin tarin dukiyar da Alhaji ya tara ko iyakar kamfanin motocinshi ai shi kaɗai arzikine jibi Gaza lokaci guda ya canja. Sukenan a sintirin shigo da motoci suke. Ke ya kike ganin in Munubiya ta samu labarin wannan cikin Sabuwa ita ya zata kasance? Wallahi a irin baƙin ranta zata iya kasheta da abinda ke cikin wa akayima asara ba mu ba? Kinji wannan "dalilin ne yasa dole lolo ta bar gidannan tun kafin Hajiya da dangin Alhaji Zaidu su ankare da cikin jikin Lolo labari ya shiga family house a cucemu""" Ai duk sai muka tsorata muka gamsu da Maigogul. Hauwa ya ƙurama idanu Ƙur saida ta sauke kanta ƙasa tsabar kaifin idanunshi. """Hauwa idan wannan labarin ya fita nasan kece dan duk wajannan babu bare. Wallahi in kika fitar a" "bakin ragowar igiyoyin Aurenki dukka""" """Bafa zata faɗa ba ma ai tayi laushi Hauwa sosai. Kuma makarantar su Mardiyya da muke zuwa babu laifi" "muna jin karatu. Rubutune Baba malam ya ɗauke mana dan mun kasa daga ni har itan, inma ta faɗa ni kaɗai na isheta riga da wando ai." Amman shi mijin lolon mai zaka ce mishi mu tafi da Lolon to ga azumi saura kwana biyu fa a soma "tafiyarmu aikin Hajji ya kusa? """ """Lolo ai ba lafiya bane da'ita yau ai anan yake ko Lolo""?" Kai na ɗaga mishi halamun eh. """ Ciwonne zaki nuna mishi yayi tsanani gaskiya ni kuma gobe sai inzo in koro mishi bayanin zamu tafi" "muyi jinyarki a gida ba shikenan ba? """ A haka aka tsayar da zancan Maigogul ya tafi ya barmu muka ci gaba da tattauna matsalolin rayuwa iri_iri har dai Alhaji Zaidu ya shigo da tsiranshi him ya kawo ma su Rakiya aka gaggaisa ya shige ciki. """Tashi ki bishi maza, kin dai ji abinda Maigogul yace miki, kibi abinda yace miki sabida rayuwarki ake" dubawa zaki iya rasa ranki in cikin kaɗai ma zaki rasa ai da sauƙi. Rahama miƙo mun wani tsinken tsiren. "Ashe haka kuke cin daɗi? """ Ni dai haka na shiga ɗaki na taddashi yayi shiru a zaune a bakin gado yana ta aikin tunani. Zama nayi a kusa dashi ya dubeni da kyau yace. """Wata rana sai labari ina fatan Allah ya baki lafiya. Goggo Amfana tace in gaisheki da jiki daga can" "wajenta nake taji labarin ciwonki. Yau tayi mun maganganun da suka tsaya mun a zuchiyata. Amman zanyi bincike da kaina in gano. Muddin abinda ta faɗa ya tabbata zuchiyata ƙila bugawa zata yi""" Ajjiyar zuchiya na sauke kawai bance mishi komai ba na fita na kawo mishi abincinshi. A wannan daren ƙaramin hauka nayi na gangan harda sambatun gangan duk saida na tashin hankalin kowa. """Wannan ciwo na yarinyarnan dole fa sai an tafi da'ita neman magani zamanku haka bazai yiwu ba." "Rahama riƙota muje ta kwana a cikinmu shima bawan Allah ya samu ya runtsa.""" Cewar Rakiya. Rahama ta riƙo hannuna muka shige ciki shi dai kusan a tafe ya kwana tsakanin ɗakinmu da ɗakinshi har garin Allah ya waye sassafe sai ga Maigogul harda Ci cib sun zo suka gabatarma da Alhaji zasu tafi dani. """To Alhaji Baba da dai an daure an barta dan Allah ai ina ganin duk maganin da za'ayi mata za'a iya mata" "anan. Ko nawane zan iya kashewa mai maganin yazo nan gidan yayi mata magani. Bana so ta bar gidanne""" "Sai ya mugun bani tausayi har rama yayi fa, ni kuma nayi likimo a kafaɗar Rahama idona ma a rufe ina" hawayen baƙin ciki. """Kana ji Alhaji? Wannan ciwon dole sai mun tafi da Sabuwa sabida lafiyarta. Mu da so samu ne ma a" "haƙura da auren kaga fa a irin halin da take ciki""" Cewar Ci cib ai Alhaji Zaidu dajin haka saiya amince a tafi dani maganan batun saki babu shi. """Amman wanne garinne za'a kaita maganin, sannan dani za'aje inta warke na dawo.""" Maigogul yace. """Ai tare da Rahama da Adama zasu tafi. Mai maganin macece maza basa zuwa gidanta kadai yi haƙuri" zasu tafi in sha Allah inta warke nan da watanni zata dawo ɗakinta ni da kaina zan dawo da'ita. Can "Agadez ne acan mai maganin take sai dai haƙuri Alhaji a yi haƙuri ƙaddarace""" """To shikenan Allah ya bata lafiya bazan yi jayayya daku ba. Duk wani gudunmawa in sha Allah zan bayar" "ko da duk abinda na mallaka zai ƙarene. Kuma zansa aita mata sauka in sha Allah. Allah ya baki lafiya ɗorarriya Shalele.""" Saida aka gama haɗamun ƴan kayayyakin da zan buƙata na shiga na sameshi a tsaye idanunshi yayi jawur yana ta kai mari yana kai gwauro. Ina zuwa saina rungumeshi na fashe mishi da kuka wallahi. Dake jarumine sai ya shiga rarrashina yana bani kalma. """Shalelena Allah yana tare dake yana sane dake. Wannan wata jarabawane Allah yake mun akan matan" da nake Aure domin ya gwada imanina. Ina hango sanda ko wacce ake fita da'ita cikin halin ciwo. Daga wannan tafiyar shikenan sai Aure ya ƙare. Gashi kema har an soma mun batun mu rabu. Allah ya bani komai na dukiya duk abinda na taɓa da hannuna Allah yana sama wannan abun albarka. Sai "ya jarabceni da rashin samun magaji, ya kuma jarabceni da rashin kwanciyar hankali." Amman in sha Allah Goggona ta haskamun wani duhu daya daɗe a rayuwa da sannu zan gano bakin zaren. "Shalelena ki kula da kanki, dan Allah duk tsanani da zafin ciwo kada ki bari a rabamu mutuwa zanyi in" kika rabu dani. Bazan ɓoye miki ba wallahi a kaf matan da na rayu dasu nafi sonki da ƙaunarki sama dasu matsayinki na "dabanne""" Saina ɗago nace. "Har Hajiyanka wacce ka yadda da'ita sama da kowa? """ Cikin ƙarfin guiwa yace. """Har ita Shalelena sabida Hajiya a halin yanzu tabbas akwai ayar tambaya a kanta. Lokacine zai bayyana" "komai""" Mun jima muna ma juna alƙawarurruka kafin daga bisani Maigogul ya ɗaukemu a mota muka tafi. A tsaye muka barshi a bakin get yana ɗaga ma motarmu hannu. Idanuna ƙur a kanshi sai nake ji kamar ƙarshen haɗuwata dashi kenan. Muna tafe ina kuka har muka iso Dutse. "Ƴan uwanane suka tarbeni dukkansu muka shiga ciki, ciwona a wannan daren yayi tsanani sosai a hakan" washegari Maigogul ya kwashemu zuwa Malam madori tare da kayan abincina da duk abinda zan buƙata har miyar situ yayi mun mai yawan gaske. Shi da kanshi ya roƙi mijin Adama akan zan zo in zauna nayi jinya anan kuma ya amince. Da Rahama muka zauna su Maigogul su kai mana sallama akan duk Juma'a zasu dinga zuwa su dubani Kunji fa halin da nake ciki. Gaga_gaga_gaga BABANGIDA:. "Abubuwa da yawa sun faru a ciki harda haihuwar Ƴar Shuwa da tayi a gidansu da Haihuwar Hala, Sumy" da Hameed kuma suma suna ɗauke da juna biyu anata laulayi. Tunda Ƴar shuwa tayi wannan abun Babangida ya korata gidansu sai dai yana ciyar da'ita yana shayar da'ita. Data haifi yarinyarta ma mace yaje ya dubasa sannan duk abinda uba yake yi yayi ƙoƙari yayi mata tsiransu sati biyu da Hala. Duk da kuɗin daya kashe wajen bikin Mardiyya hakan bai hana yayi bajinta ba. Sai dai labaran almara sun iso mushi dangane da labarin yadda sunan Ƴar shuwa ya kaya da irin manyan "matan da suka halarci bikin da irin kayan data saka, kama daga irin gudunmawar data samu, da irin abincin da akaci alhalin ansan iyayenta ba masu dashi bane." Bayan suna da ɗan lokaci Baba Malam yace da Babangida horon ya isa haka ya dawo da matarshi. Dama ƴar shuwa sun yi asirin sunyi bikon babu abinda basu yi bama akan ayi suna a gidanshi yaƙi fur gashi ita duk duniyar data samu burinta dai ta rayu a ƙarƙashin inuwar Auren Babangida. Duk da tasan a halin yanzu babu soyayya sam a tsakaninta dashi dan ko fara'a bayayi mata. Tsautsayi bayan ta dawo gidan Babangida da kwana biyu sai tafiya China ta taso mishi sunyi sallama akan daga office zasu wuce. Ƴar shuwa tana zaune a Kitchen tana soya miyar kaji ga ɗiyarta a kan cinyarta tana shan mama da misalin ƙarfe biyar na yamma. Ɗakinta yasha gyara har fenti da sababbin kayan ɗaki saida ta sake damma tana tsoron tuhuma da abinda zata yi sai yafi hakan bajinta. Kwatsam ta jiyo sallamar Zarah ta shigo suna gaisawa da matan gida. Da sauri ta ɗago suka haɗa idanu. "Fushi take yi da zarah tun ranar data kirata a waya wata budurwa ta ɗaga har suka zazzagi juna, to tun" daga ranar Ƴar Shuwa ta kashe wayarta dalilin zuwan Zarah bagatatan kenan. """Aiki kike yi my love? """ Zarah ta tambayi Ƴar shuwa. """Umm shi nake yi. Me yasa kika zo kinsan halin da nake ciki a gidannan auren sai girgiɗi kawai yake yi""" Zarah bata ce komai ba ta shige ciki itace har uwar ɗakin Ƴar shuwa kan gado. Ita kuma saida ta sauke miya ta mayar da tukunya kana ta shiga ciki. A ƙasan kafet ta ajjiye yarinyar cikin gadonta na yara dake falon ta shiga ta samu Zarah. Dake duk cikin kewar juna suke sai suka farma junansu dama shi tsautsayi baya wuce ranarshi. Ranar tonan asiri itace rana mafi tsoro tare da nadama maras amfani. Kwatsam sai ga Babangida ya dawo gida tafiya bata yiwu ba. Dake dubun ta cika ba makawa yau ƙofarta "a buɗe take, kuma shi kanshi Babangida da majalisa zai leƙa sai yayi isha sai ya shigo sai yake jin yana ɗan jin halamun mashasshara." Yana saka kafarshi ya shiga falon sai yaga yarinya ita kaɗai tana ƙananan kuka har zai ɗauketa sai yaji ihu da nishi a ciki. "Ƙirjinshi ya dafe ya duba agogo da sauran lokaci kafin magriba tayi ma, to ihun waye a ɗaki da irin" "wannan nishi? """ Sai ya soma bin hanya nishi na ƙaruwa da ihu dai har Allah ya bashi nasarar riskarsu. Ƴar shuwa tana ƙasan Zarah tana sha wa'iyazubillahi Zarah na ihu gasu tsirara haihuwar uwarsu da Ubansu. Ai take jikin Babangida ya shiga kakkarwa yana kaɗuwa yana jin wani irin juwa na ɗibarshi. Da bango ya jingina hawaye na zubowa a idanunshi. Lallai shi zina bala'ine ta ko wanne siga. Yau ga sakamakon zinar daya ta aikatawa a kan gadonshi Matarshi da mace suna maɗigo akan gadonshi na sunna yana kuma tsaye yana kallo. """Allahumma ajirni fi musibati """ Suka jiyo muryar Babangida da wani irin amo mai kauri. A zabure Zarah ta ture Ƴar shuwa tayi saurin zura doguwar rigarta ta fice a guje jakarta na falo dama ta sura ta fice da gudu. Kallon Ƴar shuwa Babangida yake yi jikinshi na rawa. Ai batai aune ba ya afka mata da duka da zagi da hauka yana yi yana tarwatsa kayan ɗakin dama yasha gyara. Harfa saida matan gida suka zo. Suna shigowa da zummar ceto in suka ga yadda take sai su koma. Amman wallahi da duka yayi duka zanin gado ta jawo ta ɗaura ta fice da gudu taga yana shirin kasheta. Fita yayi baya ko ganin gabanshi kai tsaye sai wajen Baba Malam yana zaune a kujera ya gama ɗaura alwala kenan acaɓa ya sauke Babangida a ƙofar gidan. Dubu ɗaya ya miƙa ma mai acaɓar bai tsaya neman canji ba ya tunfari Baba malam zaman daɓaro yayi a gabanshi ya ɗaura kanshi a tsakankanin cinyar Baba Malam ya fashe da kuka jikinshi na wani irin rawa na fitar hayyaci yana cewa ya yafe mishi ya tuba ya gafarta mishi. Shiru Baba malam yayi yana sauraren amon kukan Babangida yana ratsa mishi jiki. Allahu Akbar yau ɗaya sai Baba Malam ya ɗaura hannunshi a kan Babangida yace. """Dena kuka Baban masu gida. Kaita ambaton Allah inka nutsu sai ka sanar mun damuwarka""" A haka Kawu Manga yazo ya iske Baba Malam yana shafa kan Babangida ta shigar rarrashi. Ai kujera kawai ya ja zai zauna Baba Malam yace. """Manga ɗaga Babana ku je ya kwanta a ɗakina ganinan zuwa""" Da mamaki a fuskar Kawu Manga Amman babu halin magana. Haka yasa hannu ya ɗago Babangida suka shiga ciki. Baba malam yace. """Allah ka shiga cikin lamarin yaronnan ya Allah ka taɓa. """ Yana gama faɗin haka ya yafito magajin malam ya umarceshi ya bashi tawada da allo da alƙalami. Nan da nan malam ya rubuce ma Babangida wasu ayoyin Qur'ani ya wanke a ƙoƙo ya shiga mishi dashi. Babangida yana ciki a kwance idanunshi ɗaya na hawaye. Zama yayi a bakin gadon. Kawu Manga kuma illahirin mamaki ya hanashi ko da motsawane. """Babana tashi kasha rubutu ka shafe fuskarka da kanka dashi. Da dukkan halamu wani abun kaci karo" "dashi ya birgitaka tashi. """ Tashi Babangida yayi ya amshi rubutunnan ya kafa kai yasha ragowar ya muttsuke a fuska da kanshi. Malam ya kamo kanshi ya dinga mishi tofi yana hura mishi iskar a kunnenshi sannu _sannu har saida nutsuwa ta saukarma Babangida. Wallahi sai ya rungume uban ta baya ya ɗaura kanshi a kafaɗar uban. Baba malam ya lumshe idanunshi yana jin kewar yanayin sosai irin shaƙuwar dake tsakaninshi da Babangida ba shaƙuwa bace ta wasa. Wata iriyar soyayyace daga Allah a tsakaninsu ga tsananin kamanni wanda ko ƴan biyu iyakar ƙarshen kamsnnin da zasu yi kenan. """Manga kaga ɗanka ko? """ """Na ganshi Yaya kome ya sameshi oho da muka shigo baka ga yadda jikinshi yake rawaba wallahi.""" """Baba sakko ka sanar damu abinda ke damunka lokacin sallah yayi.""" A hankali Babangida ya sakko ya gurfana a gaban iyayen nashi kanshi a ƙasa. """Baba malam ka yafe mun dan girman Allah ka kuma yafe ma malama Babba a bisa saɓa umarninka da" muka yi. Haƙiƙa ruɗin abokai da kururuwar shaiɗan su suka sanya na faɗa rayuwar da bata dace dani ba. Nasan na cunkusa maka baƙin ciki mai tarin yawa amman ka yafe mini ko zan samu haske fishinka masifane da bala'i. Duk da Allah yaga zuchiyata na tuba ina mai ƙyamatar rayuwar dana aikata a baya. "Amman shirunka yana ƙona ruhina da gangar jikina a yafe mana dan Allah""" Ajjiyar zuchiya Baba malam ya sauke tare da cewa. """Menene abinda ya firgitaka Baba? """ "Muryarshi na rawa ya labarta musu abinda idanunshi suka gani""" """Assha ashsha wannan mata taka bata kyauta ba ta wani fannin. Ta wani fannin kuma kai sai ka iya ja" mata faɗawa irin rayuwar sakamakon abinda mutum ya shuka na alkhairi ba yana nufin sai sak da abinda ya aikata ba. Ballantana kuma sharri. Daka sani baka daketa ba ka rabu da'ita ina amfanin abinda ka aikata Baba ka tozarta kanka dasu "iyalanka baki ɗaya. Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba.""" Babangida yace. """Kai mun umarni in saketa dan Allah""" """Laaaa bazan umarceka ka saketa ba. Asalima a yau ɗinnan zata dawo ɗakinta ba zaka sake sakin ko" "wacce mace ba. Ka rungumi ƙaddara ka saka idanunka akan iyalanka. Ita kuma ka bata kulawa ta musamman ka kasance mai yi mata nasiha kuma kada ko da wasa ka tauye mata hakkinta domin zaka faɗa wata sabuwar jarabawar. Shi dama sharri ɗan aikene muddin ka aikeshi zai dawo, kuma in ya tashi dawowa baka san dame zai dawo ba ai. Hakkin Sabuwa daka tauye shi ya jagula lamuranka baiwar Allah ka zulunceta da yawa kayi amfani da tsoron saki da iyayenta suke yi ka wahalata. Gashi na fahimci sai dai" sonta yayi ajalinka ko ranar da suka zo da mijinta naga sonta a tattare dakai. Kayi ƙoƙarin rungumar ƙaddarar kamar yadda a baya muka rungumi ƙaddarar daka rikito mana. Kaita adda'a a cikin Ƴaƴanka Allah yasa kada wani ya jawo maka abinda ba zaka iya jurewa ba. Yafiya da kake nema Baba daga kai har Babba babu wanda ban yafe ma ba. Kai kana tunanin da ban yafe maka ba zaka kai wannan labarinne? "Na yafe maka tuni. Sannan duk abubuwan da nake yi maka sone ba ƙiyayya ba, ina horar dakaine domin" ka sake nadamar abinda ka aikata mana. Amman har gobe ina jinka a jikina. Da ɗakinnan yana magana da zaiyi kullum sai nayi tunaninka duk matsalar da zata taso a gidanka ina iya "raba dare ina roƙa maka Allah yayi maka mafita.""" Kuka Babangida ya saka mai gunji yaji soyayya da wajen Baba Malam kaɗai zai iya samun irinta. Kawu Manga yace. """Kayi shiru Baba. Haƙiƙa Yaya ka cika uban da ko wanne Ɗa zaiyi alfahari dashi. Kuma ka iya hora Ɗa" haƙiƙa na koya daga gareka. Babangida ya horu iyakar horuwa duk wannan halin ko in kula da ka kwashe "tsawon shekaru ashirin kanayi ashe kana mishi adda'a har kana damuwa da damuwarshi. Soyayyarku daga Allah ne.""" """Nagode Baba Malam kuma zan zame maka bawan da akan biyayyarka da cika umarninka zai mutu." "Nagode ƙwarai da kula da su mardiyya da kake yi nagode da tsayuwarka akan su Aminu.""" """Baba kenan babu komai. Amshi wannan kin, kin gidanane dake kusa da Wawo ba'a daɗe da gama" "gyarawa ba da ƴan haya zan zuba. Kaje ka zauna iyakar rayuwarka a ciki kamar yadda naba su Bashiru dasu Ramadan suma suke zaune. Waɗanda suka mallaki nasu sun dawo mun dashi, waɗanda Allah bai hore musu ba suna ciki har yanzu""" Kin Babangida ya karɓa ya dinga godiya yana share hawayenshi. """To bari in ƙara faranta maka wannan gida ka biya nera million uku a hankali a hankali har ya zama" "mallakinka zuchiyarka ta sake fari ko Baba? """ Dariya suka saka Babangida idanunshi cike da ruwan hawaye yake godiya. Abun sha'awa tare suka tafi masallaci hannunsu a cikin na juna tamkar abokai. Ko da suka shiga sai Baba malam ya tura Babangida akan ya basu sallah. Haka ya ba da sallar magriba su wawo dasu Ramadan suna baya mamaki duk ya kama kowa harda almajiran malam. A wannan rana dai tare da Babangida Baba Malam suka ci tuwo suna yi Babangida na mishi hira zukatansu cike da farin ciki. Sai da akayi isha Babangida yayi ma Baba Malam sallama ya tafi kai tsaye wajen Malama ya labarta mata komai. """Hukunci sai mai tsaga ido. Lallai malam a gaisheshi. To naji daɗi sosai na kuma taya ka farin ciki da kuka" "daidaita da mahaifinka. Nima inda rabo sai in koma ɗakina da izinin Allah""" Duk da girman abinda Ƴar Shuwa ta aikata cikin farin ciki da nishaɗi Babangida ya kwana. Washegari kuwa ya sanar ma matanshi zasu tashi daga wannan gidan dan haka mota zata zo da ɗaya da ɗaya ta ɗebe kayan kowa. Ya fita ya barsu suna ta haɗa kaya. Gidansu Ƴar shuwa ya wuce kai tsaye Mama tace ace ya shigo daga ciki. Ya kutsa kai ya shiga ta tusa Ƴar shuwa a gaba tai ta zagi harda duka sai shine ya ƙwaceta ma. """Babu komai Mama na yafe mata sannan ta koma ɗakinta yanzu. Gidanma tashi zamu yi yau ɗinnan sai" "ta tura a tattare mata kayanta babu komai""" Ai kuwa haka akayi a ranar suka bar wannan gida zuwa gidan da Baba malam ya basu. Sai washegari dangin matan da dangin Babangida harda su Sa'a aka zo aka taya su jere ko ina ya fito fes Ƴar shuwa kuwa fuska duk a kumbure. Tun daga wannan rana alkadarinta ya karye bata da daraja bare fawa a idanun kishiya bare miji. Babangida ko dariya bayayi mata sai dai yana sauke dukkan hakkin daya rataya a wuyanshi. Ya hanata riƙe waya ya toshe duk inda za'a sameta. Tsugunne fa bata ƙarema ƴar shuwa ba. Dan Sameerah har sabon gidan su Ƴar shuwa tazo tayi mata "hauka taji labarin ashe suna soyayya da Zarah. Ranar haka gidan ya cika da dandazon mata, Ƴar shuwa" kuwa tana kulle a ɗaki tana kuka na fitar hayyaci. Da ƙyar matan layi suka fitar da Sameerah daga wannan gida unguwa ta cika da tsegungumi. An fita daga wannan sai kuma ta shiga sabon jarabawa ƙungiyar maɗigo data shiga dai ashe harda tsafi akeyi ita dake ƙaramace a ƙungiyar bata san wannan ba manyanne suka sani. Sai ya zamana babu dama dare yayi zata ji ana kiran sunanta ana cewa in bata dawo ƙungiya ba sai an "haukatata, ko kuma an kasheta kamar yadda akaima wance da wance sai su shiga jero mata sunayen waɗanda suka fita a ƙungiya rayuwarsu ta salwanta." Abu dai kamar wasa sai lafiyar ƴar Shuwa ta soma taɓuwa yau ciwo gobe lafiya. Itace in abun ya tashi sai kishiyoyi sun daddanneta sunyi ta faman yi mata tofi tana cewa gasunan zasu kasheni. Banda rubutu da Babangida yake rubuta mata tana sha. "Abubuwan dai sai sake tsananta suke yi saida aka danganta da gidan masu magani, duk dukiyar haram" data tara saida ciwonta ya cinye tas bai bar mata komai ba Daman ance garin banza a farau_farau ɗin banza yake ƙarewa Shi kanshi Babangida saida dukiyarshi ta ƙare tas kafin Allah yasa komai ya daidaita suka fita a cikin "rayuwarta sakamakon tsayuwar Baba Malam. Sai dai ta rasa ƙafa za'a iya cewa dan ƙafarta ta hagu bata iya ɗagawa sam sai dai ta dinga janta a ƙasa, hatta kamanninta saida suka canja idanunta suka firfito ta dawo abun tausayi kamar ba ita bace wannan Ƴar shuwan mai ji da izza da taƙama ba, ta zama musaka" ƙarfi da yaji a hakannma ta Auna arziki sosai. Yau sai gaji Allah ya toni asirinta kab unguwa babu mai mu'amala da'ita cewa ma akeyi a unguwar ƴar "ƙungiyar asirice ita, inta fito zata je makaranta yara sai su gudu, makarantar dole ita kam sai dai ta" haƙura da zuwa sabida yadda ake gulmarta da yadda mata ke nuna ƙyamarsu gareta. Daidai da Zoɓo da Hamida take saidawa saida takai ta kawo ba'a siyan komai. Abinci kuwa Babangida baya iya ajjiye na wata guda a gidanshi albashin baya isarshi sai Baba malam ya tallafa mishi duk watan duniya Abubbuwa dai na jarabawa sukaita faffaruwa marasa daɗi. Wannan kenan Mrs Bukhari. "[10/28, 11:53 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 10 SABUWA:. Abubuwa sun yi sauƙi sosai dana baro wannan gida na dawo Malam madori. Ga magungunana dasu na tawo da rubutuna da dai komai. Wallahi tunda na dawo ban sake wani ciwo ba face na laulayi. Ƴan uwana naga soyayya maɗaukakiya a wajensu ko da yaushe cikin sintirin zuwa dubani suke yi. Da lokacin aikin Hajji yayi aka maye kujerata da Hauwa suka tafi suka je suka sauke farali suka dawo. Alhaji Zaidu Maigogul yana faɗamun irin damuwar da yake ciki sosai akan rashin ganina ko rashin waya dani. Amman ko da yaushe a cikin hidima dani yake a haka a haka har cikina ya isa haihuwa ranar monday na wayi gari da naƙuda zanga_ zanga su Adama suka rufu a kaina. """Allah ya raba lafiya. Aisha kirawo wayar Maigogul yace data soma naƙuda komai dare a kirashi""" "Cewar Rahama dake riƙe dani, ni kuma sai zufa nake haɓakawa." Ai cikin hukuncin Ubangiji kafin awa uku na haifo yarinyata mace ƙatuwar gaske lafiyayya kuma tana faɗowa ta fashe da kuka inya_inya. A hankali wata iska ta soma kaɗamun illahirin jikina sai nake jin tamkar an saukemun dala da gwauron dutse a kaina wallahi. "Nayi lamo ina kallon Rahama na yanke ma yarinya cibi Adama kuma tana saka mahaifa a leda, Aisha na" ƙoƙarin tattare leda da zanin da aka shinfiɗamun. """Lolo Allah mai iko wannan yarinya zata ga gata irin wanda sai an yi mamaki. Allah sarki Alhaji Zaidu ko" wanne irin farin ciki zai yi sai Allah. Murmushi nayi nace. Alhamdulillahi Rahama nagode Allah ya yasa yarinyarnan ta fito lafiya kuma da ranta gata lafiyayya. Kishiyar Adama ce ta leƙo tace. """Kaddai mai ciki ce ta haihu Adama. Muna aikace aikace sai muka ji kukan jariri? """ """Eh wallahi Hafsatu itace ta haihu ta samu mace""" """Ah Allah sarki Allah ya raya ya inganta lafiya""" Rahama tace. """Adama dubo ruwan wankan da kuka ɗaura in yayi lolo tayi wanka taji daɗin jikinta""" Ai kuwa nan da nan aka juye mun ruwa na shiga banɗaki na dinga dukan jikina da ganyen runhu ina jin wani daɗi. A bayan gidannan kafin in gama wanka naci kuka naci kuka kamar me na farin ciki da godema Allah kafin na fito. Ai kuwa takalman su Rakiya da Maigogul na gani. A hankali na shiga yarinyar tana hannun Maigogul ya rungumeta tana nannaɗe a cikin bargon farin seti na kausar. """Sabuwa ashe Allah ya nufa har kin sauka? Ga yarinya mai kama da mahaifinta masha Allah. Ko jiya sai" da shi Alhajin yazo ya duba su kayi nayi ya kawo kayan abinci. Dake ma Goggonshi Amfana ta rasu da "ƙanin mahaifinshi Kawu Abdullahi tsiransu kwana ɗaya rak.""" Zama nayi a kusa da Hauwa nace. Allah sarki tsohuwar arziki Allah ya kai haske kabarinta ya gafarta musu baki ɗaya. Lallai Alhaji yayi rashi "sosai. To Maigogul wanne suna za'a saka ma yarinyar sunan mahaifiyarshi ko sunan Goggon? """ Maigogul yace. """Ni ina ganin ki saka mata sunan Goggon tunda ita kika sani kuma ta soki sosai kuma tana da amana" "kamar ba kishiyar uwaba, ba irinsu Hauwa bane da ana binsu da Alkhairi suna bin mutum da sharri ba." "Zanyi mata huɗuba da sunanta in sha Allah. Sai ki shirya kuna haɗe arba'in zaki koma ɗakin mijinki""" Murmushi kawai nayi. Akaima yarinya huɗuba da sunan Goggo Amfana wato Hajara. Farfesu Adama ta kawo mun da shayi mai kauri naci na ƙoshi Maogogul ya ɗaukeni ni da Rahama ya kaimu asibiti a can Dutse aka duba lafiyata da lafiyar yarinya. Ananne likita tace ai na ƙaru sai an yi mun ɗinki. Ai kuwa haka akaimun ɗinkinnan Maigogul ya tasomu a gaba muka dawo. Ɗakin Adama cike da dangi suna ta cin jallof ɗin shinkafa da wake ta manja harda su Gaza da Sama da matansu duk sun tawo ɗaki dai shaƙe da mutane. """Lolo sannu ashe Allah yayi yarinya eh ta shaƙi iskar duniya? Shekaranjiya muka dawo daga kwatano, jiya" kuma Alhaji yace in dawo Dutse in duba su Rakiya ƙarama wallahi. Baki ganshi ba duk ya fita hayyacinshi wallahi lissafinshi ya kunce. Kinsan fa yayi jinya kusan watanshi "ɗaya a asibiti lokacin da asirin matarshi ya tuno ya gane duk ita take ɗaurama yaran da eh ya aura ciwo. To shine da ya kamata ya tabbatar da hakan yaita jinya a asibiti""" Hawayena na share nace. "Kuma yanzu ita Hajiyan tana ina? """ """Tuni ya eh saketa fa. Maigogul yafa san komai bai eh faɗa muku ba ashe? """ Maigogul yace. """To dama na bari ta haihu ne inta samu nutsuwa sai taji dukkan abinda ke wakana""" "Nayi mamaki sosai, sannan ko babu komai naji farin ciki da Hajiya munubiya ta fita a rayuwar Alhaji" Zaidu. Ni dai bazan iya yafe mata akan halin da ta jefani ba abadan. Haka mukaita zaman jego ni da ƴan uwana mata ko da yaushe suna tare dani su suke mun komai. Ana gobe suna sai ga Maigogul da ƙatin ƙatin ɗin tumakai har biyu da kayan abinci him sun tawo da Hajiya Balaraba. Ranar suna matan ƙauyen malam madori ne suka zo suka taya mu suna. Ni dai sai sharar hawaye nake yi ina tuno wannan sunan da ace a gidan Alhaji Zaidu akayishi irin hidimar da za'ayi bana wasa bane irin taron da za'ayi shima bana wasa bane gaskiya. Allah sarki haka ƙaddarar tazo a rubuce abu mai mahimmanci shine Alhaji Zaidu Allah ya nufa zai ga jininshi a duniya kafin ya mutu. A haka taron suna ya watse lami lafiya. Washegari kuma suka tashi da suyan nama gida duk ya kaure da ƙamshi tako ta ina. Ni dai ina daga ɗaki an zubo mun nama mai zafi ina dankwalar namannan da yajin daddawa ina korawa da kunun kanwa lafiyayye. Jego nake yi mai daɗi inci in sha in yi wanka in yi kwanciyata ƴan uwana zasu yi mun komai. Hajara kullum tana hannunsu suna lelenta ko kuma tana bayan Rahama. A zamanmu a Malam madori ƙanin mijin Adama ya ƙyalla idanu akan Rahama ya ga farar fata sai ya turo wanshi akan shi fa yana so. A lokacin shekarar matarshi ɗaya da rasuwa ta barshi da yara tara da cikin na goma Allah ya amshi abunshi. Rahama tayi na'am dashi harma an saka ranar biki. "Gidansu jere yake da gidan Adama, manomine sosai yana da arziki irin na ƙauye babu laifi sai dai fa riƙon" yara masu yawa haka ba abu bane mai sauƙi. Amman kuma dake mafaka Rahama take nema tuni ta yadda zata riƙe yarannan ta kama sana'a da zata dogara da kanta kamar yadda Adama Allah ya albarkacin kasuwancinta hakama Labbai gashi Allah ya taimaki Labbai cicib ya daina daudu sai dai muryarshi bata dawo sak ta maza ba abune ma mai wuya gaskiya. Haka tafiyar tashi sai a hankali yana dai ƙoƙartawa. Ga fuskarshi tayi duhu sosai kamar mutum ya saɓule ya warke haka fuskarshi wallahi ta zama abun tausayi sai sai yana shafa man kaɗanya ance zai rage mishi wannan ƙonewar. Ana gobe zamu yi arba'in muka tarkato Maigogul ya dawo damu Dutse muka ya da zango a gida. Naga Sama sana'arshi ta shagon saida su biskit siga madara abun babu laifi wuni yake yi a shago yana "ciniki babu laifi, magazin shima Allah ya kawo mishi tashi shiriyar mahauta yake bi yana sana'ar nama harma ya samu teburi a wata ƴar kasuwa anan yake saida nama. Kuma babu laifi yace a rana yana siyar da kaso ɗaya bisa takwas na naman balamar saniya." Ma'aru ma yana dako a kasuwa amman Masa'u gaskiya kamar ya haukace kawai gaskiya babu ragowar hankali a tattare dashi sam. Washegari muka yi arba'in a ranar Maigogul ya kira Alhaji Zaidu yake shaida mishi mun dawo daga gidan magani zai iya zuwa ya dubani jiki yayi sauƙi fes. Ina zaune ina ba Hajara Mama sai ga Maigogul ya leƙo ina kan gadon Rakiya su basanan sun tafi islamiyya. """Lolo yau ki shirya tarbar mijinki na sanar dashi kun dawo. Nasan nan da awa huɗu zaki ganshi baki ji" yadda yake kabbaraba.. Sai ki yima Hajara kwalliya tayi kyau taita ƙamshi yau dai ubanta zai gana da'ita. Yau Alhaji Zaidu zaiji ɗumin kininshi. Nasan dai naci kujerar makka ko kyautar ƙaton gida a Kano wallahi. Ina da burin in kwashe su Kayi nayi mu koma Kano dukka da zama nagaji da sunturi kuma hakanne zai tilasta mata barin kayi nayinta tunda anyi magiyar duniya taƙi ta dena. Kano yadda take da faɗi kafin a saba da mutane ma ai kinga aikine. "Maza a shirya Hajara, kiyi mai liyafar abinci ga kaji can na siyo miki""" Murmushi nayi idanuna cike da hawaye wallahi ina matuƙar son Maigogul komanshi kuma burgeni yake yi sosai. Gashi da tunani da hangen nesa ba kamar Kayi nayi yadda take nuna adankiya a kanmu ba. Ai kuwa nan na bar Aisha suna zaɓama Hajara kayan sakawa ni kuma na wuce Kitchen na wanke kajinnan na ɗaura tafashensu bayan nasa ɗanɗano da kayan ƙamshi. Risho na kunna na ɗaura tuwon shinkafa. Miyar ganye nayi mishi da kaji gundun gundun ga lafiyayyen tuwona na tuƙeshi sosai. Labbai kuma na barta tana gyaran falo har an bunka mishi turaren wuta. Ina banɗaki ina wanka Alhaji Zaidu ya iso yana zaune a falo. Ina jiyoshi yana ta faman gaisawa da su Adama. A gurguje na fito ko kwalliyar hoda kawai da kwalli na shafa na zura doguwar rigar leshi banko ɗaura ɗankwaliba dama shekaranjiya Sadiya ta yanyaramun kitson yin arba'in. Maigogul ne ya leƙo yace. """Lolo ki kintsa zai shigo ciki kawai ku zanta""" Kai kawai na ɗaga mishi. Ina tsaye ina murza kulaccham da Hajiya Balaraba ta kawo mun tun ranar suna na wajen mrs bukhari sai kawai naji ya shigo da sallama. Da sauri na juyo yana tsaye a tsakiyar ɗakin saye da waganbari mai ruwan ƙasa ɗinkin malum_malum kanshi saye da wata zanna bukhar ɗin da ɗaiɗaikun gidane babu irinta. Kun ganeta nai kala kala a jiki layi layi to itace a kanshi. Ya ƙuramun idanu ƙur yana mun lafiyayyen murmushinshi wanda nayi kewa sosai. Hannayenshi ya buɗemun yana kirana. A hankali a hankali na tattako har inda yake na shige jikinshi ya matseni tsam mukaita sauke ajjiyar zuchiyar haɓarshi na ajjiye a tsakiyar kaina. Mun jima a haka sosai sai nayi yinƙurin zamewa sai yayi sauri ya mayar dani jikinshi. Naga yayi rama sosai gaskiya. Da ƙyar na zame jikina na zaunar dashi a kan katifa hannunshi riƙe da nawa. """Wazirat al sa'ada barkanki da dawowa cikin rayuwata. A kan tafiyarki naje aikin Hajji, naje umara duk" ina roƙon Allah ya baki lafiya ki dawo mu gudanar da sabuwar rayuwar da babu takura a cikinta. Wazirat haƙiƙa ke wani ɓarayine na jikina. "Zo ki zauna in shaƙi ɗuminki mai cakuɗe da ƙamshi.""" Dole na dawo kusa dashi na zauna muka sakarma juna murmushi na kewa da son keɓewa. Wata kalma mai tsada ya raɗamun ƙasa_ƙasa. Idanuna na rufe tsabar yadda naji kunya ta kamani. "To yanzu dai bari in kawo maka ruwa da abinci ni da kaina zan ciyar dakai""" Ina yinƙurin tashi ya cabkeni carab. """Ba ƙi nayi ba tunda nayi kewar duk abinda ya fito daga gareki. Amman ki barni in zauna dake mu zanta" "wazirat. Yaufa sai dai Alhaji Baba yace banda kunya dan da matata zan tafi ko a bani ɗaki a gidannan.""" Ai kafin in yi magana sai ga Maigogul ya shigo hannunshi riƙe da jaririya tana ta kuka kamar ranta zai fita. """Lolo ga Goggo Amfana bata mamma tasha ta ishi mutane da kukan banza""" Ya dire mun yarinyar ya fice. Da mamaki da tsoro duk sun bayyana a fuskar Alhaji Zaidu har ja da baya yayi. Murya na sauke Omri kada kaji tsoro kada ka tayar da hankalinka. Kaga wannan yarinyar? To jininka ce ɗiyarka ce fid duniya wal akira da cikinta muka baro gidanka "watanta huɗu a marata lokacin """ Wallahi sai ga babban mutum ya fashe da kuka ya durƙusa yana ambaton Allah da ƙarfi. Hajara na miƙa mishi ya ƙanƙame yana ta ambaton Allah kawai. Maigogul ne ya faɗo kunsan halinshi ai mai makon yayi kamar baiji ba. Yana shigowa Alhaji Zaidu ya miƙe ya rumgemeshi Hajara na tsakiyarsu. """Hakane wannan yarinya taka ce in baka amince ba aje ayo gwajin jini." Na raɗa mata suna Hajara marigayiya Goggo Amfana. An yanka mata manyan tumakai an ciyar da Sabuwa da kyau. "Mun yi hakanne sabida gudun cutarwar makirar matarka ta da ba sabida komai ba""" Yana kaiwa nan ya fita. Alhaji Zaidu ya zuba ma Hajara idanu tana ta mutsu mutsu ta dena ma kukan sai wasa take yi da ƙafarta. Dariya yake yi yace. """Wazirat nagode da wannan irin tukuicin da kika bani. Haƙiƙa yau ranace marar misaltuwa. Ranace da ba" zata goge a cikin rayuwata ba abadan. Wazirat ina sonki ina mutuwar son Goggona. Ya mayar da idanunshi kan Hajara data soma kukan yinwa. Dole ya kawota ya ɗaura a cinyata. """Bata tasha in gani ji nake yi kamar mafarki wallahi""" Dariya nayi mishi na zaro mama na saka a bakin Hajara ta kama ta shiga tsotso shi kuma yana share hawaye. Wallahi cikin abinda yayi ƙasa da awa guda duk wata number dake wayarshi saida ya kira ya faɗama an mishi haihuwa akwai suna a gidanshi rana ita yau. Danginshi kuwa labari ya ishe musu family ya kacame da farin ciki da ta'ajibi. Ya zauna yaci abinci wallahi ya kasa har saida na dena dariya yaga dai fishi nake yi da gasken gaske shine ya zaune a hakanma Hajara na hannunshi. Abincin na zuba mishi na karɓi yarinyar na tusa shi gaba na dinga bashi da kaina. Da ƙyar yaci tuwo rabi yace shi ya ƙoshi ya karɓe yarinyar yanata kallo. """Wazirat kuma kamarmu ɗaya da'ita da gaskene munje asibitoci da dama domin a duba lafiyarmu domin" musan menene matsalarmu na dangane da rashin haihuwa. Ƙwararrun likitoci sun tabbatar mana dukkanmu lafiyarmu ƙalau kawai Allah bai yi lokacin samuwar cikin bane. Munji a wajen likitoci fin goma ba'a najeriya ba. Da wannan dalili Munubiya ta dinga cutar da yaran da basu ji ba basu gani ba. Bari in baki labarin abinda ya faru. Zuwa nayi zan duba Goggona ance mun ta samu farkawa harma tace inzo lallai tana son ganina. Bayan na shiga ne take sanar dani. """Zaidu duk wani bincike da bin diddigi da zaka yi akan matarka kayi. Ita ke ɗaurama matanka da kake" Aure ciwo. Zargina ya tabbata itace. Ka nutsu kabi kuma komai a hankali ka gano da kanka. Kada kayi mata hukunci da abinda bai tabbata. Amman ni na tabbatar maka tasan abinda yake gudana. Kada ka sake a wannan karon ka rabu da "matarka ko me zai faru kar ka rabu da'ita""" Hankalina a tashe nace. """Goggo kika ce tana da sa fa hannu a wannan abubbuwa da suke ta faruwa? Naga Munubiya macace mai" "kirki gata da biyayya""" """Kai namiji ne ba lalle ka gane makircin mata ba. Bare taka tana yin makircin da wata siga ta daban. Ka" "zauna kayi tsam kai da kanka zaka iya rabe ɗayan biyu""" Shiru nayi na bita da to sabida bana jayayya da manya. Amman ba dan zuchiyata ta yarda ɗari bisa ɗari ba. Har saida na taso a tsakankanin Rano zuwa Kano na dinga tunani game da tubka da warwarar al'amura masu dama. Sai naji ƙirjina yayi mun nauyi sosai. Bayan mun rabu daku kun tafi wazirat na shiga damuwa mai yawa. Sai Alhaji Muntada ne ya tuƙani ya kaini gida. Hajiya na zaune da ƙawayenta aikinsu kenan lissafin kuɗi na haura sama Ban jima da hawa ba ta biyoni. """King lafiya wannan damuwa haka, ko wani abunne ya faru da Sabuwane? """ Saina kalleta nace. "Iyayenta ne suka ɗauketa suka tafi da'ita sunce ma in aiko musu da takaddarta""" Nayi tsam ina kallonta. Wallahi tama kasa danne dariyarta saida ta dara kaɗan fuskarta cike da annuri can ta lulluɓe da damuwar yaudara. """To kai wanne matakin kake ganin zaka ɗauka? """ "Sai nayi tunani Hajiya yanzu kaɗaici nake so ki koma wajen ƙawayenki""" Hmmm wallahi data sauka sai ta jasu zuwa uwarɗakinta. Ni kuma saina sakko nazo na tsaya a ƙofar ɗakin. Abubuwan da naji basa faɗuwa hatta ni ba tsira nayi ba ƙarfin adda'ane yake riƙe dani kawai. To tun daga ranar na soma bin diddiginta har wajen bokan da suke zuwa a wudil saida na bisu na tambayi mutanen da suke kusa da wajen me akeyi a gidan dana ga mata nata shiga. """Wannan gidan ai gidan wani ƙaton matsafine matan da suka kwashe kayansu ne suke zuwa wajenshi." "Sai kuma masu neman duniya wato mulki.""" Wazirat ko dana dawo na soma bincike ɗakin Hajiya da ɗakina na fitar da layu sunfi ashirin. Harda wata ƙwarya ina buɗewa wallahi ƙwaryar ta soma hayaƙi. Mutum ne aka zanashi da tawada a jikin ƙoƙon aka bi ƙwaryar aka zaneta da sunana da aka rubuta da ajami. Sai wani kwaɗo da mabuɗi da jan zare zagaye dashi. Na tattaro komai na kaisu sama na kira Hauwa na tutsiyeta tare da mata alƙawarin kuɗi masu tsoka. "Kusan Hauwa ita Hajiya take ba aikin duk matana dana Aura a baya. Ita ke shiga ta saka laya, ko ta ɗakko" suturunsu da makamantan haka. Da Hauwa da mijinta na basu kuɗi masu yawa na sallamesu. Hajiya sai wajajen taran dare ta dawo tazo ta same ni a sama a gaban waɗannan kayan. Bayan na kirawo wana yazo ya gani da ƙanin mahaifinmu. Tana ganin kayan Wazirat sai Hajiya ta soma kuka ta tuba in yafe mata tasan shikenan alkadarinta ya karye ƙarshenta yazo. In yi magana na kasa sabida yadda na kaɗu takaddar saki biyu na iya miƙa mata. Kinsan Allah kamar yadda ta fita nima sai ƴan uwanane suka zo suka fitar dani zuwa asibiti? Hajiya ta cutar dani cuta mai girma. "Amman mun barta da mahaliccinmu shi yasan yadda zai yi da'ita KO? .""" "Gaskiya ne Hajiya ai shaiɗaniyace""" Nan na bashi labarin dalilin barina gidan da dalilin farkon ciwona. """Bazan yi mamaki ba a yanzu da ace a lokacin ne kika faɗamun bazanma iya saurarenki ba""" Mun yi hira sosai da sosai. Ko da zasu tafi sallah Maigogul yace in haɗa kayana zamu tafi harda su Sadiya za'aje ayi bikin suna. Ai kuwa tare duk muka rankaya harda su Adama. Sabon gida ya kaini an zuba komai da komai. Acan muka tarar da kafatanin danginshi na Rano ƴan wasu garinne kaɗai babu. Sun yi abinci jiranmu kawai akeyi. Ai kuwa muna shigowa gida ya kacame da murna ranar Hajara ta sha wahala sosai dan da daddare saida Adama ta mata wanka da ruwa zazzafa ta sha ɗauka da addu'o'i. Tunfa daga ranar jama'a sukaita tururuwar zuwa dubamu. Matan abokai ma bafa a barsu a baya ba. Yadda gidan ya ɗinke da dangin Alhaji da nawa wallahi ko keɓewa mun kasa yi sai dai Alhaji ya haɗiye ƙishin ruwanshi. Anata shirye_shiryen suna fa kuɗi yake kashewa kamar baya so Abincin sunan ma wai ma'aikatan hotel ne zasu zo suyi. Maigogul shima yace zai yi dake yaga harda maza a ma'aikatan sai ya zamana shi yake gyara musu in yaga sun kuskure yaci riga da hular girki abunshi. Ranar sunannan bazai rubutu ba wani abun ma wallahi sai ace ƙaryane amman Alhaji ya nuna bajintarshi akaina da Hajara ta ɓangaren suturu da kadara. Saniya ƙatuwar gaske su Gaza suka yanka ga tumakai wallahi har guda biyar aka yanka. Banda kaji. Suturu kuwa mun sameshi ni da Hajara ta ɓangaren dangin Alhaji dama nawa dangin kowa burinshi yayi ma Alhaji abun bajintar da zaiji daɗi. Ni yama rasa kyautar da zaiyi mun. Yace dai washegarin suna zamu wuce Dubai muje mu ci Amarci. Ai kuwa washegarin suna tun asuba su Adama da Anty Tani sukaita kasafta nama da su cincin na suna aka warema kowa nashi suka gyara mun ko'ina kafin azahar duk suka watse mu kuma wajajen bayan la'asar aka kaimu Airport ƙarfe bakwai jirginmu ya ɗaga zuwa Dubai. """Sannu wazirat masu suna sun hanani more matata sai dai inta kallonki ina haɗiye yawu uhm. Da fatan" "kin shirya Amarci da kuma bani hakkina da kyau ko? """ Idanuna a lumshe dan nayi muguwar gajiya nayi tulus nace. "Raina fansa gareka Omri sai yadda kayi dani""" Murmushi yayi mun ya dubi Hajara dake ta baccinta ranta ɗaya yace. """Baiwar Allah ita bata ma san wacece ita ba. Bata san irin so da gatan dake jiranta daga wajen dangi" zuwa wajen iyayenta ba uhm rayuwa kenan wai yau ni Zaidu wannan ce ɗiyata? Sai dai kash ba lallai inga girmanta ba yadda ya kamata ba. Amman ina roƙon Allah yayi mun tsayin ran "da zan ɗauki ɗiyar Hajara da hannuna nima inga jikina""" "Allah ya amsa mana Omrina bana son maganar mutuwa sabida ita kaɗaice zata iya rabamu.""" Murmushi kawai yayi mun nima na mayar mishi. Ƙarfe huɗun asuba gari bai waye ba muka shiga Dubai. Kafin dai Asuba har mun yada zango a ɗakin hotel da muka kama. A Dubai muka gudanar da asalin rayuwar Aure mara algus a ciki. A nanne muka fahimci junanmu sosai "da sosai, nan na ga soyayya ido da ido a baya ashe ba'ayi komai ba yanzu ne dai akeyi." Satinmu uku a Dubai muka wuce Saudiyya muka yi Umara saida muka gama aiki kafin muka ziyarci su Maman Yasmin sun kuwa ji daɗi sosai muma ziyarar tayi mana daɗi sosai. Sannan kuma muka shiga Madina wajensu Mardiyya da Sauban. Nayi farin cikin ganinta cikin kwanciyar hankali. Ta sake girma kamanninta da Babanta ya sake fitowa sosai. Abubuwan Alkhairin da Alhaji yaima Ahalina ba'a magana barinma Maigogul daya yi sama da faɗi da kaso mafi tsoka. Maigogul yana da tangamemen shagonshi na saida yadukan maza da ɗinkakkun kayan maza dama Hajiya ta buɗe mishi. "Alhaji Zaidu kuma ya narka kuɗinshi wajen ƙarama Maigogul da takalman maza, agoguna, gogul, da" "hulunan maza zanna, da irin links ɗinnan. Shagon Maigogul abun sha'awane kayane masu tsadar gaske yake saidawa hakan yasa masu kuɗi kaɗai ke iya ziyartar shagon nashi. Samfurin ɗinki kuwa sai dai a gani a wajenshi kuma kun sani." Daga Saudiya na roƙeshi inaso ya kaini wajen Uzairu zuchiyata. Ai kuwa ya amince muka wuce Canada. Hahahahhh mutuminku ya samu duniya wallahi ya sake kyau. Fatarshi ta sake wani irin laushi da kwanciya. Munje mun tadda Felisha da cikinta ƙurbibi. """Uzairu Zuchiyata an samu duniya ka manta da hanyar najeriya""" Na faɗa ina tsokanarshi. """Ka ganta ko Alhaji ta rainani wannan yarinyar. To me akeyi a najeriya tunda dai ana tura kuɗi ai" "shikenan. Kuma na ɗaura Gaza shi ke kula mun da gini da nake yi. Ni ko Lolo ina Rahine""" Dariya muka yi dukkanmu. Suma naga da ƙaton karensu suke rayuwa da magensu mai kyau. """Amman Uzairu ya yanayin zaman auren babu matsala ko? """ Alhaji ya tambayeshi. """Matsaloli ai sunfi dubu hamsin wallahi, ai ni shigo_shigo ba zurfi tayi mun. Kaga ko shekaranjiya saida" tace zata sakeni wai ita ta gaji sabida ina nuna duk inda zata shiga saina rakata. Ya mata da aure zata shirya tsirara ta tafi gidan rawa? Wallahi lauyanta ne yayi mun iyaka da son takura mata. Nima wallahi so nake mu rabu Auren turawa matsiyata ko wahala. Abinda nake ji abinda ke cikinta ne. In muka rabu fa ko yara nawa muka haifa dole in barsu a hannunta shikenan sai su zama arna. Duk da ko inanan ɗin bani "da iko a kansu kaico. Ai wallahi Alhaji kwaɗayi da son zuchiya baiyi ba. Ana zaman haƙuri da nadama dai""" Ni ko dariya kamar zan mutu wallah. Ai dama ance in da kwaɗayi da wulaƙanci. Satinmu ɗaya a Canada muka dawo gida Najeriya ƴan uwa da abokan arziki sukaita tururuwar zuwa yi mana sannu da zuwa da duba Hajara. Na zama sita a cikin familina da familin Alhaji kowa so yake ace nice ta kusa dashi. Ashe muna tafiya Dubai su Rakiya suka dawo Kano da zama gidansu na BADAWA Ko da naje gidan naga yadda suke more rayuwa na tuno rayuwarmu ta baya a ɗaki falle ɗaya duk aka haifemu kana a wannan ɗakin duk muka rayu muka girma Allah al hakim. "Gaga_gaga al'amura sukaita faruwa kwanaki, watanni, shekaru sukaita shuɗewa." Bayan wasu shekaru. Mrs BUKHARI "[10/29, 9:31 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 11 Yau dai tun safe nake shiri gida nake son zuwa naje na wuni. Jiya da yamma su Rahama dasu Labbai suke faɗa mun sun zo gida shine nima nake son ayi hirar dani. Fitowa nayi na tadda Omri a zaune yana lallatsa na'ura Hajara na gefenshi tana aikin da aka bata a makaranta. """Ranki shi daɗe irin wannan kwalliya duk tasu Yaya Rahaman ce? """ Zama nayi ina murmushi nace. "Goggona je ki ɗakko mayafinki zamu je gida""" Dariya tayi ta tafi a guje ta je ta ɗakko mayafi da takalmi. """Kin ganta sai zumuɗi take yi zata je gidansu Mamanta""" "Ai kasan zumuɗinnan duk na Maigogul ne. Sabida tana cin daɗi a wajenshi ai shiyasa""" Wata hararar soyayya yayi mun nayi saurin kama bakina nace. "Aimun Afuwa Alhaji Baba Dad""" Dariya muka yi dukkanmu. Ya miƙe ya sako malum_malum ɗinshi ya kara hula muka fito harabar gidan tare. """Mamana inna taso office zan biyo ta gidan sai mu dawo tare ko? Ki gaishe da su Mama da Alhaji Baba""" """To Abba sai ka dawo Allah ya tsare""" Bayan motata ta shige mu kuma muna tsaye. """Akwai abinda kike buƙatane kuma Wazirat? """ "A_a kayan abincin tun ɗazu nasa Amina ta saka a bayan mota, kuma akwai kuɗi a hannuna Omri""" """To shikenan sai nazo Ƴar budurwata. Ni naga kin sake kyau da haske anya kuwa ba ajjiyata bace a jikinki" "ba ki gayan gaskiya""" Dariya nayi mishi kawai na shige mota maigadi ya buɗe mana get muka fice a jere har muka zo iyakar "inda zamu rabu, yayi mun hon ya wuce mu kuma muka miƙe." Ina riƙe da sitiyarin mota ina wasa dashi a titi ina nishaɗi tare da tuno Sabuwar da data yanzu. Ni kaina wasu abubuwan inna tuno wallahi illahirin kunya ce ke kamani. Aminu ne yayo kirana. "Aminu ya dai sarkin kiran waya kenan? """ Daga cikin wayar yace. """Ummi yaushe zaki sake zuwa jikin Baba malam ya sake tsananta yanzu haka ma an fito dashi za'a mayar" "dashi asibiti ne? """ Subhanallahi jikin sake tashi yayi Aminu? Dama jibi Abban Hajara yace zamu sake zuwa mu duba jikin. In kaje asibitin ka samu ka haɗani da Malama Ƙarama a waya. Kuyi ta yi mishi adda'a jibi sassafe zamu "kamo hanya kaji Aminuna? """ """To shikenan ummin mu Allah ya kawo ku lafiya a gaishe mun da Goggo""" "Goggo zata ji zan turo maka da ɗan na kashewa inna tsaya zanje gidansu Rakiya ne""" Da haka mukai sallama ina hango fuskar wannan Dattijon arzki mai abun mamaki. Ina roƙon Allah yayi yaye mishi. A haka muka isa gida muka taddasu sai lokacin suke karyawa anata dariya ana musu. Maigogul ke soya musu doya anata juyewa a ƙaton tire ana ci ga miyar ƙwai ga shayi ya sha madara. """Ga Goggo ga Goggo. Zo taho ƴar nema""" Cewar Maigogul Hajara taje ta ruƙunƙume Maigogul suna dariya. Rakiya taja tsaki tace. """Aikin banza kai Allah ya shirya Maigogul zanga sanda in yananan zai bari inyi daraja""" Taɓata nayi nace. Haba Rakiya dan Allah ki dena kallon wannan abun a rashin daraja. Mufa muna sonku dukkanku a yadda "kuke""" Tace. """Amman da zaɓe za'ace za'ayi ai da gudu ko wacce zata sunkuceshi ko? Allah dai ya bamu lafiya. Ya shi" "Alhajin yake? """ "Lafiya lau yace a gaisheku kayan abinci yana bayan mota ma""" Saita washare bakinta. Nan muka hau gaggaisawa Maigogul har Kitchen na bishi muka gaisa yau shi yayi musu karin kumallo a gidan ma Allah sarki ya sake tsufa furfura ta sake rufe mishi ragowar baƙin gashin nashi. Dawowa nayi cikin su Adama muka buɗe hira sabuwa. Adama tayi kyau ta sake haɓaka ƙiba. Rahama goyo ne ma a bayanta na ɗa namiji wata takwas. Su Aisha Sadiya duk suna gidajen Aurensu zuwa dai ko wacce tayi daga gidan nata mijin. Su kuma su Adama sai suka biya ma Labbai suka tawo. Gaza ya zama mutum sai dai muryarshi da zubinshi bazai taɓa eh canjawa ba yananan a yadda kuka "sanshi, sigarinma yana ɗan sha gaskiya har yanzu." "Sama ma babu laifi ƙazanta ta ragu sosai yaranshi biyu, Gaza ma yaranshi biyu Anyi ma Maigogul" takwara ba don son ranshi ba sai dan son ran Madamcy dan shi yana takaicin irin kamannin ma da Rakiya ƙarama tayi da Maigogul. Bayan da aka gama karyawa sai muka shiga gyaran gidan masu wanke_wanke nayi masu shara nayi nan da nan muka kammala komai. Lokacin sha biyu tayi Maigogul ya fito tare da Hajara zasu tafi shago. Ya ci malum malum na wani yadin maza mai mugun kyau kayan gasu da ɗaukar guga gaskiya yayi kyau. Miƙewa nayi nakai mishi kuɗinshi na duk wata da nake basu. Bakinshi a washe ya amsa shima fa a ƙadamin da ake Maigogul da kuɗinshi amman baya raina wanda zai kuma samu. Rakiya tace. """Ai sai ka bada na cefane tunda dai ka samu kuɗi""" Maigogul yace. """Rakiya ho kullum na cefanannan ina fa bayarwa yanzu ai ba da bane""" Kuɗi ya ƙirga ya bata abun mamaki ohh rayuwa kenan. Maigogul yayi mana sallama shi ya tafi kasuwa tare da Hajara dan fafau taƙi zama dama ita da Maigogul babu dama ne. Muna Kitchen muna girki nake tambayar Labbai ya man ƙuli. """Ai wallahi man ƙuli sai dai ace masha Allah jari ya haɓaka ya zama babba. Cicib ma a wajena yake siyan" tunkuza da ita yake gashin tsiren dare da yake yi. Kinsan sana'ar daya koma kenan. Da rana zuwa yamma yana toya doya da kwai da kaza a wajen da daddare sai ya gasa tsire da masa ana ciniki wallahi babu "laifi.""" Adama tace. Ni da nake da shagon kayan kwalliya da su turare ba'a cewa komai ina ciniki sosai. Babu ruwana da "tenshon da sassafe nake ficewata a shago nake karyawa naci daɗi ranar girkina kuma akwai wata ƴar budurwa da take zama mun a shagon. Ga Rahama itama sana'ar turaren wuta ya karɓeta sosai wallahi ai babu abinda zamu ce dake wallahi. Su Sadiya ma anata kitso da ƙunshi da kwalliya, babu laifi gidanta" "baya rabo da mata. Aisha ma tana taɓa ɗinkin kowa dai na kan sana'arshi.""" Sallama muka jiyo kamar muryar Uzairu zuchiyata a falo. Ai kuwa sai muka ji Rakiya tace. """Uzairu zuchiyata kaine haka bagatatan? """ Duk sai muka fito Uzairu zuchiyata na tsaye da gajeren wando da riga amles ga akwatuna manya shaƙe da kaya. Suna haɗa idanu da Labbai ai sai suka soma dariya Uzairu zuchiyata harda birgima a ƙasa. Wallahi sabida mugunta har hawaye suke yi. Muma duk dariyar muke ta faman yi a haka Hauwa ta shigo da jakarta taci riga da wando da hijabi na makaranta abinta Rakiya ma shine a jikinta. """A_a dan jakar uba daga zuwa sai dariya""" Cewar Hauwa itama dariyar take yi. Rakiya da abin ya isheta tace. """Aikin banza Rahama mu zamu fita zamu je gidan suna daga can zamu wuce islamiyya mu sai mun dawo." "Muje Hauwa ko gulma zaki tsaya ji""" Suka fice Rakiya na zage_zage. """Ni naga bariki Labbai Auren turawa ko bala'i da masifa. Tsiya tsiya muka rabu ta sake ni dai kuma na" "saku na rabu da ƙaƙai. Ƙyal ƙyal ƙyal""" Muka sake ɗaura dariya kamar cikina zai ƙulle. Labbai na hawaye tace. """Garin yaya aka sakoka Uzairu zuchiyata. Ni na ɗauka iya wuya zaka yi biyayya ai? """ """Me inji akuya? Na sha gashi fa Labbai ai ni da auren dattijai inaga har abada wata ƴar budurwa zan" samu in Aura kawai tunda na fita da fitata nayi gini na tawo da kuɗaɗe ai shikenan. Yarinyar da muka haifa ta mutu. Cikin dake jikinta ne fa ya ɓare mitsiyaciyar sai ga lauyanta wai bani da ƙashin arziki kawai ita mu rabu. Wallahi daga haka shikenan ta saka hannu nima na saka. Na kuma rubutama mitsiyaciya saki uku na "islama. Ta dinga fashe fashen kaya tana shan giya tana amai. Ba shiri na bar gidan kada taje ta rataye kanta""" Habawa me zamu yi ba dariya ba. Kiran wayar Aminu ne ya katsemun dariyar na shiga Kitchen na amsa wayar. """Ummi Allah yayi ma Baba malam rasuwa yanzunnan""" "Innalilliahi, wa'inna'ilaihil'raji'un""" Kalmar da naita nanatawa kenan na fashe da kuka ina salati. Da sauri su Adama suka baibayeni nace. "Baba malam ne Allah yayi mishi rasuwa. Ku shirya bari in kira Alhaji Zaidu yanzu zamu wuce Dutse""" Ai kuwa kiranshi nayi yace to gashinan zuwa dashi shima za'aje. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso shi da Maigogul. "Motarshi Ni da Adama da Rahama, muka shiga." Motata kuma Maigogul ne zai tuƙa Labbai da Uzairu zuchiyata ne suka shiga su Sadiya da Aisha a gida muka barsu. Ni dai muna tafe ina kuka Omri na rarrashina. Ga wayata sai kira akeyi na kasa ɗagawa sai Adama Omri ya miƙa ma wayar take amsawa su Mardiyya ne suke ta kira. Mutuwar wannan bawan Allah ta dokeni fiye da tunanin mai karatu wallahi. "Da muka iso cikin unguwar, wallahi jama'a sun cika kafatanin unguwar ga motoci ma damƙam babu ma" wajen ajjiye mota sai daga titi muka ajjiye motocinmu muka ratso mutane. Ƙofar gidan kuwa ba'a magana wallahi gidan ma ya gagara a shiga sai Aɗɗa'u ne ya jamu zuwa gidan Kawu Manga dan a lokacin ne ake ƙoƙarin fito da gawar a sallaceta. Allahu Akbar wannan bawan Allah yayi mutane sai yabon alkhairanshi da halayenshi nagari akeyi. "Su Maigogul kuwa dasu aka sallaci gawar aka wuce maƙabarta duk dasu, sai da aka tafi maƙabarta ne" muka samu damar shiga cikin gidan. Cike damƙam da mata anata koke_koken al'ada. Zubewa nayi a gaban su Malama sai kuka. Malama babba ce ta dafa ni tace. """Sai haƙuri Sabuwa ayi haƙuri. Sa'a kaita ɗakin su Aminu ita da ƴan uwanta su karɓi gaisuwar acan" "Mardiyya ma da ɗiyarta tana ciki""" "Sa'a ce ta ɗagani nabi bayanta, su Adama suka mara mun banya. Ina ji wata tana cewar. Uwargidan" Babangida ce ta da uwar manyan yaranshi. A ɗakinsu Aminu na tadda su Hameeda da su Hala da Sumayya. Ƴar shuwa ma tana ciki idanun kowa jawur anci kuka an ƙoshi Mardiyya na zaune ɗiyarta na cinyarta a zaune. Da sallama muka shiga Sa'a tace Ƴar Shuwa ta sauka a bakin gado ta bani waje. Ɗingisa ƙafarta tayi ta sauka na zauna. Nan muka shiga jajantama juna mutuwar Ƴar Shuwa wallahi ta ɗago ta kalleni takasa sabida kwarjinina "da haibata ta cika ɗakin wallahi, dolen doliya ta fice a ɗakin ta koma dokin ƙofa duk ta lalace ta jeme." "Sai da maza suka dawo nan gida ya sake kacamewa da gaishe_gaishen mutuwa, su Wawo duk sun leƙo" nayi musu ta'aziyya haka ma Babangida ya leƙo. """Mun gode sosai Sabuwa. Naga su Maigogul da maigidanki ma duk dasu muka je maƙabarta Allah ya bar" "zumunci Adama mun fa gode""" "Allah sarki ai babu komai""" Na faɗa a taƙaice. Ana haka Uzairu zuchiyata ya kutso cewar in leƙo ga Alhaji yana so yayi magana dani. Fitowa nayi na sameshi tsaye shi da Babangida a kusa da turakar Baba malam. Dana iso sai Babangida yace. """Bari in koma waje Alhaji sai ka fito""" Saida ya kalleni kana ya fita. Ni kuma hankalina na kan mijina. """Wazirat kiyi haƙuri kukan ya'isa haka ki yi haƙuri dan Allah. Dama cewa nayi ko za'a siyo kayan abinci ne" "a kawo ko kuma kuɗin zan baki kya ba iyaye? """ "A_a a siyo kayan abincin. Kuɗinma sai a basu babu komai zasu riƙe a hannunsu, nima ina buƙatar kuɗi""" """To shikenan Yaya Uzairu zuchiyata zai kawo miki kuɗi zamu je dashi mu siyo kayan abincin in damƙa a" "hannun Baba Mardiyya""" Yana saka kai zai fita. Ni kuma na ɗaga ƙafata kenan zan juya sai naji marata ta murɗe sai ga jini na bin tsintsiyar ƙafata. A guje Adama tayo kaina. Ayi haƙuri yau ba yawa ina da uzirine da babu gara babu daɗi Mrs BUKHARI "[10/30, 7:20 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 12 """Lolo lafiya jini ke zuba a jikin ki fa? """ Adama ta tambaya a kiɗime dam na riƙeta dam wani irin mugun ciwo nake ji mai tsanani. """Mardiyya maza daure kirawo Uzairu zuchiyata mu fita da'ita maza aje asibiti""" Cewar Rahama da suka firfito kafin Uzairu zuchiyata yazo har Labbai ta riƙeni ida da Adama mun soma tafiya sabida Rahama ruɗewace yasa tace a kira Uzairu zuchiyata ba wani abun ba. Ai kuwa hankalin kowa ya dawo kanmu anata tambayar meke faruwa. Muna fitowa wani guda ya faɗo a ƙasa kwaɓal shikenan cikin nasan ya ɓare. A kiɗime Alhaji Zaidu da Babangida suka ƙaraso. """Meke damunta take zubar da jini? Alhaji mota zaka ɗakko maza mu kaita asibiti Sabuwa sannu""" Babangida ke magana a kiɗime shima Alhajin a kiɗime ya ɗakko mota Maigogul dai duk yadda akayi bayanan ya shiga gari. Tuni aka kaini asibiti inah ciki kam ya zube mahaifata tayi dameji sosai harma likitocin sunyi mamakin yadda mahaifar ta iya ɗaukar ciki ma. Kano muka dawo asibitin malam Aminu Kano wallahi mummunan labari ina kwance babu yadda nake ashe mahaifar tawa aka cire sukutum ta lalace ikon Allah ne yasa Hajara ma tazo duniya a yadda likitocin suka ce kenan. Nayi kuka nayi kuka sosai. Amman me? shi bawa baya wuce ƙaddararshi kuma sai dai ince Alhamdulillahi "tawa ma tayi kyau tunda ina da yara biyar to me kuma nake nema. Cire mun mahaifa shine tambari mafi muni da bazan mance dashi ba a sakamakon yawon banza da zubar da ciki, da shan ƙwayoyi. Ƙalubale a gareku yaran mata masu bin maza da yawan shan ƙwayoyin zubar da ciki ku kalli Ayar da aka saukar a" kaina ta zame muku abun tsoro. Ina kwancannan a asibiti aka mayar dani asibitin kuɗi mai kyau sosai. Haka dangi sukaita sintirin zuwa "dubiya abun mamaki harda su Sa'a da Kudidi a zuwa dubiya a bisa jagorancin su Aminu da Babangida. Amman in banda dangina babu fa wanda yasan da batun cire mahaifa, ba abu bane da za'aita yayatawa" ba. Alhaji Zaidu kuma kullum a cikin rarrashina yake tare da yi mun wa'azi. "Ba tani nake ba taka nake ji. Dole akwai buƙatar ka sake aure ko dan ka hayayyafa kaga haularka""" Na faɗa ina hawaye. Shafa kaina yake yi yace. """A baya tsawon shekaru nawa nayi a rayuwa ba haihuwar harma an cire rai da haihuwar ma sai Allah ya" "bani mamana. Shin nasan zan sameta ne ma, ko kuwa nasan ma ina haihuwar bare ince ga ranar da zanga jinina? Ke kaɗai zaki rayu dani har abada. In har zaki iya aurena a matsayin juyi, to tabbas zan rayu dake a matsayin mara mahaifa Allah ya raya mana Hajara kwana nawa ma ya ragemun nafa tsufa kece" "bakya gani""" Murmushi nayi nace. "A fuska ba. Amman zuchiyarka da ƙarfinta haka ma a. """ Sai nayi shiru muka yi dariya yace. """Ai sai kin faɗa wazirat bazan barki ba Allah""" "A kunne na raɗa mishi abinda nake son raɗa mishi. Yayi dariya sosai, sai naji sanyi a zuchiyata. Ko wanne" "bawa fa yana da tashi kalar ƙaddarar ta wani tafi ta wani ne. Kuma kowa aka ba dama yana da abun faɗe a bakinshi tabba, ko ba haka bane makaranta?" Watana ɗaya da kwana biyu a asibiti aka sallamomu muka dawo kuma gida. A lokacin ana shirye_ "shiryen Auren yaran Rahama biyu da ƴar Adama tsiran na sati biyu ne, anko ma haɗewa akayi. Ga Gaza ma wai Aure zai ƙara yaga farar bakanuwa ta sace zuchiyarshi abinka da jinin Maigogul. Uzairu zuchiyata kuma yana ta soyayya da ɗiyar ƙanwar Hajiya Balaraba wata ƴar boko wayayya, ta ganshi suka yadda da" junansu lokaci shima kawai muke jira. Bayan an sallamoni da wata biyu muka yi bikin Ƴar Adama sati na sama mukai na yaran Rahama. Kishiyoyin Rahama sun sha ruwan mamakin ganin yadda ta koma da irin bajintar da mukaima yaran na kayan ɗaki dan uban na kwance ma jinya yake yi. Mu mukai komai hatta abincin da za'aci na taron biki mu muka yi. Bayan na dawo Kano da wata guda kuma muka shiga Auren Gaza da Uzairu zuchiyata anan Kano Gidan Hajiya Balaraba akayi Auren Uzairu zuchiyata shi dai ɗan ɗakinta ne kuma ita ta haɗa mishi ma akwati Gaza kuma a gida akayi bikinshi. Amare duk suka tare a gidansu Kayi nayi rayuwa dai taci gaba da yin kyau tana shurawa a hankali a hankali. Uzairu zuchiyata yana shagon Dad tare suke gudanar da kasuwanci. Ya zuba kuɗi da agoguna suka ƙare sai ya saro da ƙudinshi aka ci gaba da harka daman shagon na ƴan gayune irinsu. Su kaɗai sun isa su baka sha'awa in siyayya kaje yi shagon irin kece wankan da suke yi ba abu bane na wasa wallahi. Babangida:. Yana zaune a tsakar gida yayi tagumi shiru gidan babu wuta sai fitila a tsakar gidan. Ƴar Shuwa ta kawo mishi abinci ta dure mishi ta kawo ruwa. Abincin ya buɗe ya saka cokali ya soma ci babu ƙorafin ba'a kawo mishi a ɗebi da kanka ba. Dake rayuwar ta mugun juya mishi baya. Kamfanin da yake aiki dasu an rufe kamfanin ƴan chinan sun sallami "kowa, ɗan wajen Baban bolanshi da yake ɗan siyan kaya shi kaɗai ne dashi a hakan ake jalautawa" kasuwar tayi baya sosai. Sai koyarwa da yake yi dai a haka ake ƙuƙutawa. """Dama nace Babansu Fatima abincinmu wallahi ya ƙare iyakar ragowar kenan yau na girke mana ko" "ɗumame ba za'a samu ba shine nace bari in sanar maka""" Kafin yace wani abun Hala ta fito ta zauna a dokin ƙofarta zafi ya isheta a cikin. """Baban Mardiyya yarannan fa dukka an korosu a school ba'a biya musu ba." """ Tun yaushe aka korosu amman? """ """Wallahi ai tun ranar Litinin fa aka korosu.""" Rai ya ɓata yace. """To amman mai yasa ba'a sanar mun bane? """ Ƴar Shuwa tace. """To ana ta batun tuwo yaushe zamu sanar maka wani batun makaranta. Yanzu kana gani yau kuɗin" "cefane ma bamu samu a wajenka ba. Aminu ne daya shigo fa ya bada kuɗin cefanen shi yasa ma akayi girkin""" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. """Babu komai gobe za'ayi biyan makaranta sai inga abinda za'ayi akan abinci da makarantar yaran. Allah" "ya ƙara rufa asiri""" """Ameen amman nace ya batun rabon gadon naku ne. Yau kusan shekarun Baba malam biyu da rasuwa" "ace har yanzu anƙi tayar da rabon gadonnan naku wawo sai wadaƙarshi kawai yake yi, harfa mota ya" "sake matanshi ya sake musu kujeru fa? """ Idanu ya lumshe tare da yin murmushi yace. """Gado ba abun dogaro bane, abinda ka tara dashi zaka dogara ai. Wawo da Bashiru sune manya idanu" mu dole zamu saka musu. Amman faful basason ayi batun rabon gadonma. Gidajen haya da shagunan haya dai su dama suke karɓan komai. Makaranta ta dawo hannun Wawo sai wata yayi goma ma bai biya "malamai ba to muna kai kuka wajen Allah babu komai wata rana sai labari.""" Shigowar Aɗɗa'u da kayansu kici_kici ne yasa Babangida yayi shiru ya zuba ma Aɗɗa'u da malama idanu. """Lafiya Aɗɗa'u daga ina a darennan kuma na ganku da kaya""" Babangida ya tambaya a ɗarare. """Dama Kawu Wawo ne yace mu dawo gidan Babanmu. Malama ƙarama ta gargaɗeshi amman yace sai" "mun dawo shine na haɗo mana kayanmu muka tawo""" Mamaki ya kama Babangida amman kuma rayuwace ai. """To shikenan ku shiga ɗakina kuyi kwanciyarku, kunci abinci ai ko? """ """Munci Baba""" """Ina shi Aminun to ya barku kuka tawo ku kaɗai? """ Cewar Sumayya Maman Amir da fitowarta kenan. """Yaya Aminu baya nan baisan ma mun tawo ba""" Tace. """To Allah ya rufa asiri""" Yaran suka shiga ciki Babangida kuma ya rufe abincin da loma huɗu kawai yayi ya fita sai gidan Wawo tunda gidan dama a jere yake katangarsu ma a haɗe. Izinin shiga wawo ya mishi a tsakar gida ya sameshi a saman kafet yana cin shinkafa da miya da latas ga zoɓo mai sanyi da ruwa mai sanyi. """Yaya dama yarane suka dawo wai kace su dawo wajena shine nace bari inji shin da gaske ne? """ Kai ya gyaɗa yace. """Tabbas ni nace su dawo hannunka kaci gaba da riƙesu zai fi. Kaga sauran yaranka ma naga an dawo" "maka da biyu mata ai gara ka haɗa da yaran Sabuwa ko? In kuma ka gaza ba sai ka turasu wajen uwarsu ba tunda attahiri take Aure""" Yawu baƙin ciki ya haɗiye yace. """Babu zancan gazawa yarana ba zasu yi zaman agolanci ba zan ci gaba da kulawa dasu wanda akayi mun" "ma nagode""" """Daga baya kenan yara kusan huɗu yanzu haka suna can suna agolanci kuma ai yaranka ne me yasa baka" "je du ka ɗakkosu ba? """ Murmushi yayi yace. """Nayi yinƙurin haka ragowar iyayen yaran sun hanani yaranne. Biyu daga cikine suka amince shi yasa aka" kawo biyun. Sannan ai su da yawansu da cikinsu aka tafi shi yasa bawai na gaza bane. Nagode mu kwana lafiya' Ya miƙe ya fita zuchiyarshi na turiri ya jima a waje yana tunanin ya zaiyi ya dinga bin ɗakuna alhalin ɗakunan cike suke da yara maza da mata. Matan suna ciki da iyayensu mazan na falo. Can yana tsaye ya tuno Kitchen ɗin gidan yana da girma sosai ma kuwa ƙaton Kitchen ne. """To sai dai ko wacce ta kwashe kayanta a Kitchen ni in koma ciki kenan. Allah ya rufa asiri.""" Shigewa ciki yayi yayi zamanshi a tabarma. Duk sunyi shiru saiga Aminu ya shigo da leda har biyu a hannunshi. """Aminu kadawo? """ """Nadawo Baba sannu da gida. Mama ina wuninku? """ Ya dubi matan uban duk suka gaisa yace. """Su Aɗɗa'u ance sun tawo ko Baba? """ """Suna ciki inka shiga ita Malama ta fito taje ɗakin Maman Amir acan zata ci gaba da kwana cikin ƴan" "uwanta. Ku kuma yaranku mazan su biyo su Aminu suci gaba da kwana a ɗakina daga gobe, damin yau tare dasu zan kwana." Zuwa gobe da safe duk ku kwashe komatsanku na Kitchen na zubarwa a zubar na adanawa a ƙarƙashin "gado a adana can ɗinne zai zama ɗakina.""" Ledojin da Aminu ya shigo dasu ya ajjiyema uban ya shiga ciki. Babangida ya buɗa ledar yaga biredai manya har uku sai sikari da madara da ganyen shayi harda kwai rabin kiret. Murmushi yayi tare da yin hamdala gami da shi ma Aminu albarka. Haka dai Babangida ya miƙa ma Ƴar shuwa ledarnan tunda itace da girki. Da safe aka sha shayi da biredi da ƙwai. Yara duk suna gida ba zuwa makaranta. Su kuma su Hamida da kwalimar fitar da kaya a Kitchen suka soma sassafe. Aminu ne ya leƙo ya tari Babangida da yake shirin fita. """Baba dama zuwa gobe in Allah ya kaimu muna son zamu bi Adda zuwa Kano. Sannan Ummi tace in zo" da takadduna tunda anan na kasa samun aiki. Koyarwar kawai nake yi kula da littattafan da nake riƙe da "ofishin Kawu Wawo ya sallameni ya saka Muntari a kujerar""" Shiru Babangida yayi kamar ruwa ya cinyeshi kamar ma bazai magana ba ba dai yace. """Haka akayi? To shikenan ragowar maganar inna dawo aiki saimu tattauna""" """To shikenan Allah ya tsare.""" Babangida ya saka kai ya tafi kasuwa yayi da Ƴar shuwa akan in sha ɗaya tayi ta turo yara su karɓa musu cefane. Haka ya tafi kasuwar tunda dai yaje har zuwa sha ɗayan yaro ɗayane ya kawo mishi wasu tukwane ya Auna amman bashi ma da kuɗin da zai karɓi kayan. Dole yaron ya tafi ya kira masu zuwa ɗiban kayan ƙarafe su biya suma suka ce sai zuwa gobe zasu biyo tanan. Dole haka da yara suka zo karɓan cefane ya ɗebi kayan ƙarafai shima ya kai aka auna aka bashi kuɗin. Da kuɗin yayi musu cefanen iyakar abinci rana yace zai taho dana daren. Yana wajen har magriba yana tubkewa da warwarewa dole dai haka ya rufe wajen ya nufi gida. A hanya suka haɗu da Mustapha ƙafarshi duk ƙura. Tafawa suka yi. """Babangida kacigari Babangida makeljacsin""" Dariya suka yi Babangida yace. """Kai dai baka da girma saina jiki wallahi""" """To ya za'ayi ya rayuwa Babangida? """ """Mustapha yanzu haka daka ganni ban basu abinda zasu girka ba ni suke jira ni kuma ban samo ba""" Mustapha ya zura hannu a ajjihu yace. """Dubu biyu ce dani da'ita nake saka ran zasu siyo gasara da sikari a dama da safe a siyo ƙosai ko" "bibbiyune aci a tashi. Bari mu raba sai mu ƙarasa gida akwai taliya sai in baka ko leda biyu ce""" "Ajjiyar zuchiya Babangida yayi, yasa hannu da godiya ya amshi kuɗin. Suka je ya bashi taliyarnan leda" biyu. Saida suka yi magriba kana ya nufi gidan. Yana shiga ya tadda kowa a tsakar gidan suna ta cin shinkafa da miya harda kaza ga lemun kwalba anata tsiyayama yara wutar nefa ta haska tsakar gidan tanwar. Da sauri Maman Fati ta shinfiɗa tabarma a gefen Kitchen har an saka labule. Ledar hannunshi ta karɓa ta shiga ciki sai gata da kofi ta ɓalle shiwebs ta tsiyaya ta miƙa mishi. """Sanyaya maƙoshin bari a kawo abinci""" """Baba sunnu da zuwa""" Yara suka soma mishi yana amsawa. "Saida ta zuba mishi abincin miyar sai ƙamshi ga kaza manyan yanka ƙirji da cinta, ga latas cakuɗe da" kabeji ta zubo a kwano daban. """Daga ina wannan abincin ina aka samu kuɗi, ni dai nasan na fita ban bar komai ba? """ """Tabbas baka bar komai ba dan hatta abincin ranan mun dai shasshafa da babu akace gara babu daɗi." Mardiyyace da bayan la'asar mijinta ya kawota duba su Aminu da jin ba'asin wai tafiya zuwa Kano da zasu yi. Ita ta kawo abincinnan a dafe harda lemun kwalba rabin kiret wallahi ta kuma bamu dubu "bibbiyu""" Shiru kamar ruwa ya cinyeshi sai hankalinshi ya tashi ya shiga wani irin yanayi da farin ciki haɗe da damuwa. Tunaninshi ya koma mishi shekarun baya sanda Sabuwa ke dafa abinci duk sanda zata je gida takai sabida tasan basu dashi. Ashe kenan haka take yaye ma Ahalinta damuwa a zauna aci ana farin ciki shi yasa duk gori bata taɓa denawa ba kenan? Gashi yau Mardiyya ta ɗanɗana mishi irin farin cikin da Maigogul da Rakiya suke shiga harma da su Uzairu zuchiyata. Ya jima yana fassara wasu yanayi na baya kana ya ja numfashi ya sauke yace. """Allah yayi mata albarka. Harta iya yo girki mai yawa ta kawo da har ya ishi gidannan? """ Ƴar Shuwa tayi mishi nuni da kular data ciko ta tawo dashi a ƙalla abincin ciki zaiyi mudu biyu. Shigen kular da Sabuwa ke cikawa takai gida a duk sanda zata je. Ashe kaima iyaye dafaffen abinci yana da daɗi da sauƙaƙewa musamman in ansan basu da hali sosai. Ashe yana daga cikin tausayawa da nuna kulawa ga ahali. Ashe yana daga cikin nuna ƴan uwantaka? Ajjiyar zuchiya ya sauke yayi murmushi. Damma Allah ya so shi bai taɓa hanawa ba sai dai gorin masifa tabbas ƙila daya taɓa hanawa ta hanu kuma ba lallai Mardiyya ta iya kawowa ba. Amman dake wannan na daga cikin tarbiyyar da Sabuwa tayi musu kuma tasan basu da hali yanzu shi yasa tayo wannan abincin ta kawo. Madallah da Sabuwa mai sabon aiki. Kiran sallah aka soma dole ya dubi su Aɗɗa'u yace su taso su tafi masallaci. """Abincin ki kai mun ɗakina acan zanci. """ Ya miƙe suka je sallah. A hanyar dawowarsu yake sanar musu ya amince suje Kano goben tare da Mardiyya. Suna dawowa kowanne ya shiga neman wajen kwanciya shi kuma ya shiga ɗakinshi. "An share an wanke an saka labule a taga da ƙofar shigowa, ga katifar yara nan ƙarama sai tabarma" babba da aka baibaye ɗakin da'ita. Abincinnan yana ci yana farin ciki har ya gama ya kora da shiwebs tare da yin hamdala. Washegari ragowar abincin aka ɗumama sai aka siyo biredi aka haɗa dashi da ruwan bunu. Duk da haka miyar tayi ragowa dayawa Ƴar shuwa ta damƙama Sumayya tunda ta fita a girki ita zata yi na rana. Sai ga Mardiyya da safe sun zo ɗaukar su Aminu sai shiri suke yi dama duk sun yi ma wanka. Da safenma bata barsu haka ba ta riƙo musu masa mai ƙuli cikin roba mai hannu babba ga ƙuli. Babangida kuma ta kawo mishi cincin mai yawa da dambun nama. Tare da Sauban suka shiga har ɗakin Babangida suka gaisheshi ta ajjiye mishi wannan kwano. """Jiya na dawo na tadda abinci akace ku kuka kawo. Sauban anfa gode Allah yayi albarka ya baku zaman" "lafiya.""" Da ameen suka amsa Ƴar shuwa ta ciko kwano da masa baɗe da ƙuli ta kawo ma Babangida tunda shi dama bai kai ga karyawan ba. Yaita ma su Sauban godiya. Da zasu tafi Sauban ya ɗakko dubu biyar ya bashi. Mardiyya ta bashi dubu biyu. Har bakin mota ya rakasu bai baro wajen ba saida motarsu ta ƙule. """Baƙar tukunya mai fidda farin tuwo. Allah mai fidda rayayye cikin matacce.""" Ciki ya koma ya zuba musu cincin da dambun nama yace su rarraba. Ya ɗakko dubu uku yaba Sumayya tunda iyaka abincin dare zata yi akwai miyar sutu ma tumaturi da ɗan "bushasshen kifi kaɗai za'a watsa a ƙara mata afki sai ayi ko da wake da shinkafane, ko shinkafa da taliya" tunda suna da'ita. Kulle ɗakinshi yayi ya musu sallama ya tafi. Su mardiyya suna tafe anata hira har suka iso Kano cikin Aminci. Sabuwa na tsaye a Kitchen taga shigowar motarsu Harabar gidan. Mrs BUKHARI Aimun haƙuri kwana biyunnan ina da uzirine shi yasa kuke ganinshi babu yawa. Afwan masoya. "[10/31, 11:22 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI" 13 Kunyi ready ku koyi skill ɗin da ke kawo kuɗi! "Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace," ko ku iya video editing kamar professionals — to wannan class ɗin naku ne! Za ku koyi: " Voice Over (recording, editing, delivery)" " Video Editing (cuts, transitions, subtitles & more!)" Practical + Real Project Training Location: [TELEGRAM ] Payment: 9163354359 Sa'adatu Adamu Opay Send receipt via Contact: [07044292865] Registration ongoing — Limited space available! Kada ka tsaya jiran lokaci — ka shiga yanzu TASKAR BADI'T WANNAN SHINE JADAWALIN SHIRYE SHIRYENMU DA WANNAN TASKAR TAKE GABATARWA YAYIN DA BA'A LITTAFI DOMIN ƘARUWARMU BAKI ƊAYA MU GUDU TARE MU TSIRA TARE. MASU SON KASANCEWA TARE DA MRS BUKHARI GAREKU GA LINK NAN DUK MAISON KASANCEWA MEMBER SAI YA SHIGA A DAMA DASHI IN SHA ALLAH. ANA ƘARUWA MUNA FAƊAKARWA DOMIN AN HAƊA MALAMAI DATTIJAI WAƊANDA SUKA SAN DARAJAR MUTANE SUKA SAN ME SUKE YI. DUK DA ZAMU SABUNTA SHIRYE_SHIRYEN NAMU IN SHA ALLAH KU KASANCE TARE DANI A KULLUM RANAR MONDAY 8:00 PM A GAMA 9:30PM Shirin """""""""TARBIYYAR YARANMU""""""" MASU GABATARWA ( MAMAN KHAIRY) (ANTY BADI'AT) (KHADIJA MAI DOKI) (ANTY ZEE) RANAR TALATA 8:00AP A GAMA 9:30PM shirin """""""""AMFANIN TSABTA GA MACE""""""" MASU GABATARWA (MRS BASH) (MRS BUKHARI) (MAMAN KHAIRY) RANAR LARABA 4:00PM A GAMA 6:00PM Shirin """""""TAURARUWAR MAKO""""""""" SHIRIN DA ZAI DINGA ZAƘULO MANA MATA DOMIN SU BAMU TARIHIN GWAGWARMAYARSU A GIDAN AURE. MASU GABATARWA (HAJARA ALIYU) (OUM INTEESAR) (MAMAN SAFWAN) RANAR ALHAMIS 8:00PM A GAMA 9:300 Shirin """""""MATSALOLIN MATA DA WARAKA""""""""" SHIRIN DA ZAI DINGA ƊAUKO MAUDU'I YANA TATTAUNAWA AKAI. MUSAMMAN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI MATA. "SANNAN ZA A DINGA KARANTA TAKADDUN MASU TURO MATSALA, DA BASU SHAWARI ME KYAU""""""""" MASU GABATARWA (Ummu Inteesar) (Mum khairy) (MRS BUKHARI) RANAR JUMA'A 12: 00PM A GAMA 2:00PM Shirin """""""""ADO DA KWALLIYA""""""" MASU GABATARWA (KKhadija maidoki) (Mrs BUKHARI) RANAKUN ASABAR DA LAHADI KUMA RANAKUN HUTU IN SHA ALLAH. DOMIN KULAWA DA ME GUDA DA YARAN GIDA BAKI ƊAYA. SABUWA: Murmushi nayi lafiyayye. Saina tsaya kawai ina kallonsu suna sauke kayansu daga mota sai dariya suke ci ko me suke tattaunawa oho. A fili nace. "Ohh ni Sabuwa Ƴar daba, mai biye_biyen club, da biye_biyen maza yau ni Allah ya azurta da waɗannan" "yara na albarka harda jika? """ Daga daf dani naji Omri yace. """Inason ganinki a cikin yanayin daba kina ciccije baki, kuma wai kin iya sara? """ Illahirin kunya saita lulluɓeni na juyo na ƙanƙameshi bana so mu haɗa idanu. """Zaki sani inna kama bakinnan naki mai daɗi da yake kiramun mata ƴar daba. Kuma in haƙuri kike so nayi" "tabbas yau sai kin mun rawar culub na gani in ba haka ba himmm.""" Dariya nayi ina ƙoƙarin zamewa yana ƙara haɗani da jikinshi. """Ina sonki sosai Wazirat ina son komai tattare dake. Kuma wallahi inason Baba Alhaji burgeni yake yi ɗan" "wanka ba. Shiga raine dashi sosai shi yasa fa Mama take kishin shi da yawa ni bana ganin baikenta""" Dariya muka saka nace. "Kayi nayi jarabar duniya""" Kafin in rufe bakina ya buge mun tare da tureni a jikinshi da gaske ranshi ya ɓaci. """Na lura bakya ji wazirat akan cewa Maigogul da kayi nayi wallahi zamu samu mugun matsala dake meye" "haka? """ Fuu ya fita ni banma taɓa ganin ɓacin ranshi haka ba sai duk na damu sukuku na fito falo na tadda mai aiki na shigar musu da jakunkunansu ciki. Duk sai suka nufoni suna kiran sunana. Dukkansu na haɗa na rungume sai ga hawaye sharshar sai muka fashe da kuka. Sauban na gefe. Omri ne yazo ya ɓanɓaresu amman Aɗɗa'una yana riƙe da wuyana. """To ayi haƙuri kukan murnane haka Aɗɗa'un Ummi ayi haƙuri kaga ƙannenka Malama da Hajara zasu yi" "maka dariya.""" Murmushi yayi tare da sakina. Har ƙasa suka tsugunna suka gaisheshi ya amsa cike da kulawa. """Ya kuka baro Baban naku da matan Baban naku?""" Aminu ne yace. """Duk suna lafiya Dady sunce a gaisheku""" """Sauban illo ya ka baro iyayenka?""" """Duk suna lafiya sunce a gaidaku""" """Muna ansawa da kyau""" Mardiyya ta sakko sabon goyonta ta miƙa ma Alhaji Zaidu ya amsa yana murmushi mai sunan Babangida kenan. Ɗayar sunan Sabuwa aka saka mata a gidan kakarta Sa'a aka barota dama kusan tun daga yaye ma tafi son gidan Sa'a sabida yadda take ji da'ita. kunji ƙudurar Allah Kitchen na shiga ni da mai aiki muka soma fito da abinci. Tare da Alhaji Zaidu aka baje akaita liyafar ciye_ciye anayi ana hirar yaushe gamo. """Ni wajen Maigogul zani ummi""" Cewar Malama. Omri yace. """Ai Hajara dai ta ture gwammatinki kai Alhaji Baba fa akwai farin jini. Sai dai yayi ƙwarƙwara da malama" "to""" Dariya muka saka dukkanmu ni kam harda ƙwarewa. Tare da yara mazan suka tafi masallaci ni kuma na ja matan zuwa ɗakina muka yi sallah. """Ya kika baro takwarata babu matsala ne a wajen wa kika barta? Ai irin wannan tafiyar da ba zaki barta" "ba kowa ai yana son ganinta. Ni nama fi son ganinta fiye daku, da Babangida kika bari a gida ni yafi mun""" Dariya suka saka na hararesu. """Ummi bakya son ganin Baban nawa? """ "Ko kaɗan kuwa""" Sai tayi murmushi kaɗan naga fuskarta ta sauya. """Allah sarki Baba ni tausayi yake bani sosai daya rasaki""" "Kinci gidanku Mardiyya kul na kuma ji""" Sai malama tace. """Ummi mun dawo gidan Baba da zama Kawu Wawo ya koromu har yana cewa Babanmu wai kangararre." "Ummi dan Allah ni zan dawo nan""" Shiru nayi ina tunani nasan in sama da ƙasa zata haɗe Babangida bazai taɓa yadda Malama dai ta dawo wajena ba. Malama kiyi haƙuri ki zauna a gidan Babanku. Ni kinga a baya duk yadda gidanmu yake haka nake son "abuna. Duk abinda kike so zan dinga miki kinji ko? """ Sai ta ɗaga kanta. "Mardiyya ki dinga leƙasu akai akai kece uwarsu kin sani ko Addana? """ """To Ummi zan dinga leƙawa""" Dawowarsu daga masallacine yasa muka rankayo muka dawo falon nan akaita hira. "Omri ya tashi ya shiga ciki nasan dama da yamma yace mun akwai inda zashi, saina bishi. Ina shiga ya" haɗe rai kicin_kicin. A hankali na isa gabanshi ya ƙuramun idanunshi sai naji gabana ya faɗi ras. Omri menene dan Allah? Sai yayi ajjiyar zuchiya. """Kukan me kike yi da kika ga yara uhm. Kina kewar rashin kasancewarki dasu a gidan Babansu ne, koko" "Baban nasu sukutum kika tuno""" Da sauri na haɗe bakinmu waje guda mun jima sosai kafin ya matsa. Kada kayi tunanin komai. Wallahi kukan na farin cikin ganinsu da girmansu ne kacal. Me akayi akayi "Babangida? In duk duniya ni dashi muka rage wallahi bazan iya komawa hannunshi ba haba omrina""" Sai kuka sabida anzo gaɓar na riga na tsokalo zuchiyar tashi. Wallahi duk sai ya ruɗe ya shiga aikin rarrashi harda ban haƙuri. Mata a kula in baki san logon mijinki ba kina ruwa. Kunga dai ya ɓige da bani haƙuri a madadin nice zanta haƙilo. """Ya'isa kishine ya hautsina mun ruwan kaina. Nama fasa fita kwanciyata kawai zanyi. Kije ki samu yara ki" "nuna musu ɗakinsu su huta sai kizo ki mun tausa uhm""" An gama ranka shi daɗe. "Sauka nayi na kaisu ɗakunansu dake jere dana juna. Na Sauban da Matarshi daban nasu Aminu daban," sai Malama a ɗakin Hajara. "Ku yi wanka ku kwanta ku huta sai zuwa magriba sai mu fita ko? """ Aminu yace. """Hmm Umminmu gaskiya kina jin daɗi wai muyi bacci fa? Da'a Dutse ne da yanzu ina can ina gararanba" "har dako yi nake yi wallahi""" Murmushi nayi nace. To ai ya ƙare yanzu kaine kayi ƙumun baki da yanzu da aikin ka a hannunka ai. Amman kace dako "koyarwarfa kai da kake riƙe da Babban ofishi""" """Hmmm ummi ai Kawu wawo ya sallameni a ofishinnan ya ɗaura ɗanshi shike kula da littattafai""" Shiru nayi. Can nace. "Shi Baban naku kuma yana gani? """ """Bashi da tacewa ne Ummi""" "Aminu kuna cikin wani hali kenan? """ """Baki koya mana ƙaryaba zamu faɗa miki halin da muke ciki in muka nutsa""" To shikenan ku watsa ruwa hu huce gajiyar Dutse. Nan na barsu na dawo na soma yima omri tausa daga tausa kuma dai kun gane... Tare muka yi baccin mune har magriba kafin muka tashi a gurguje yayo wanka ya fito. """Ku shirya inna dawo sai mu fita muci abinci a waje uhm""" Bai jira amsata ba ya fita. Saida nayi wanka nayi sallah kafin na fito. Yara suna falo duk sun sake kaya. "Kuzo mu fita Samari""" "Dariya suka yi, suka bini a baya. Omri yana mota yana jiranmu. Sauban nace ya shiga gaba ni na zauna a" "baya tare dasu. Muka je gidan cin abinci kowanne ya zaɓi abinci yaci ya more abunshi da zamu dawo aka siyo tsire da yogot nanma da akayi isha muka baje muka sha sulalewa Omri yayi ya barni, dama Sauban" ya daɗe da guduwa. Zama na gyara na fuskancesu nace. "Aminu ina jinka menene damuwar da kuke ciki? """ Kai ya sauke yayi jim. "Ka faɗa mun akwai abinda zaku ɓoye munne? """ """A_a Ummi wallahi Babane yana cikin wani hali kasuwarshi tayi ƙasa sosai, bashi ma da kuɗin siyan" "kayan Baban bola a wajen yara masu kawowa. Gashi Kawu Wawo baya yin biya akan kari. Babu abinci a gidan wallahi, shekaranjiya da jiya Adda ce ta kawo dafaffen abinci akaci a gidan""" Mamakine ya kamani nasan Babangida ba malalaci bane wajen ciyar da iyali tabbas. Jarabawace ta sameshi a sakamakon jinyar Ƴar Shuwa arzikin nashi ya ƙare. Murmushi nayi ai a tunanina in an kawo mishi abinci dafaffe bazai ci ba. Ashe in kaga ƙi gudu sa gudu ne baizo ba. A gaskiya na tausaya ace mutum magidanci mai kuɗi da ace abinci a gidanshi babu ga tarin iyali. To Aminu Allah ya kyauta zamu tallafa da abinda muke dashi in zaku tafi sai ku kai mishi. "Ku shirya gobe zamu je gida, sannan jibi kuma zamu je Malam madori kuje kuga su Rahama""" Daga haka nayi musu sallama na koma wajen mijina. Washegari sassafe yayi tafiya zuwa Abuja bayan ya karɓi takaddar Aminu yace. """Ka samu aiki Aminu a kamfanin Abokina aiki mai kyau da tsoka. Wata na gaba zaka soma zuwa tunda" kaga wata saura sati guda ya ƙare. Zaka dawo nan Kano da zama ka sanarma Babanka kaji? Ni zanyi "tafiya sati ɗaya zanyi""" """To Dady nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi""" Sallama yayi musu ya fita. Har cikin mota na rakashi na labarta mishi halin da gidansu Aminun yake ciki. """Ashsha Wazirat. To ki basu kayan abinci duk abinda kike ganin ya dace a basu su kai mishi a haɗa da" "dubu ɗari da hamsin, matan kuma ko dubu hamsin_hamsin ki basu su kama sana'a zama hakan babu daɗi sam. Ni zan wuce Allah yayi ba dake za'ayi tafiyar ba""" Mun jima a mota muna soyayyarmu kafin da ƙyar mukai sallama ya tafi. Yana fita muka shirya muka nufi gida nan muka wuni Maigogul da Uzairu zuchiyata basanan wai sun tafi China saro yaduka Allah mai iko. Sai naji gidan Babu daɗi daga Rakiya sai Hauwa sai su Madamcy Sama shi yana shagonshi dake ƙofar gida. A daddafe mukai wunin dai. Ko ince rabin wuni dan munje gidan Aisha da Sadiya. "Washegari na ɗebi kayan abinci da kuɗi da turamen zani, turare, mayafai, takalma. Kwalima sosai nayi" "musu muka nufi Dutse anan Layuza da Raliya da Qamriyya da Labbai suke Aure duk saida muka zaga na basu kayan hatsi da kwancen sutura, mun daɗe a gidan Labbai tare muka wuce malam madori da'ita." Gidan Rahama muka dira tunda itace Babba ita kuma bata da kishiyoyi sai yaran miji. Taji daɗi sosai Adama ce ta zagayo ko mayafi babu. """Lolo irin wannan kaya rigi rigi kai gaskiya mun gode dama muna da biki kice zamu fito fes damu a cikin" "kayan manyan mata.""" Rahama tace. """Ni girman su Aminu ke bani mamaki to ai ya zama saurayi sosai Aminu sai Aure, ji Malama yadda itama" "ta zama? Iko sai Allah rayuwa""" Dariya muka yi. Mun kusan biyun dare muna ta hirarmu ta zumunci a gidan Rahama duk muka kwana mijinta baya nan "yayi tafiya, ita kuma Adama ba ita ke da girki ba""" """Adama kin saki jiki sai haɓaka ƙiba kike yi wuyanki na neman shigewa"" Cewar Labbai dake ba ɗiyarta" nono. """Ke dai bari ai wannan ƙiba ta tsone ma kishiyoyina idanu sosai. Sabida ko tafiya Alhaji zaiyi ni yake" "sawa a gaban mota kinsan farar mace, ga mace mai ƙiba da cika idanu. Amman yanzu kam cikine dani" "wallahi""" "Ciki? """ "Duk muka haɗa baki, sai muka kwashe da dariya. Mu da muka zo da zummar kwana ɗaya saida mukai" "biyu, daga nan muka nufi gidan Salaha kun mance da'ita ko? Ita tana gaba can da malam madori a ƙauye" take sosai dan motarmu ta sha wuya sosai. Nanma muka kwana ɗaya na sauke mata abinda zan sauke mata na ƙara mata jari mukai sallama sai kano bayan mun sauke Labbai. Kwananmu biyu da dawowa suka shirya tafiya. "Buhun shinkafa biyu, katan na taliya biyu, kus_kus katan ɗaya, shinkafar tuwo rabin buhu, buhun" "semobita uku, sai mangyada babbar jarka yalo ɗaya na basu nace su kaima Baban. Su kuma matan uban" atampace naba ko wacce ɗaya da dubu hamsin ɗinta. Su kuma nayi musu sha tara ta arziki Sauban na bashi kuɗin mai suka tafi Hajara sai kuka take yi ita zata bisu. Dutse:. Kasancewar ba da wuri suka fita ba sai magriba suka isa ƙofar gida. Babangida na tsaye a ƙofar gida yaga suna ta fito da kayan abinci niƙi_niƙi. Saubanne ya ƙaraso ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Babangida. """Lafiya lau Sauban lallai kun sha Kano ai na zaci kwana biyu zaku yi kacal ashe ba haka bane abun." "Waɗannan kayan fa? """ Aminu yace. """Baba zamu yi maka bayani.""" Kayan duk suka shigar kana suka fito zuwa masallaci. """To Mardiyya ga abincin Babanku ko shi zaki ci? Kinga bamu san kuna hanya ba abincin kai da kai dama" "aka dafa""" "Cewar Hameeda data miƙa ma Mardiyya kular Babanta""" """A_a Mama inna je gida ko taliyar ƴan yara na dafa mana muci. Ummi tace a gaisheku duk ta bada saƙo" "ma a babbaku""" Duk sai suka washe baki Ƴar shuwa kuwa kasaƙe tayi daga zaune tana kallon kayan abincin da aka dire a tsakar gidan. Sallamar su Babangida ce tasa ta ɗago. """Wutarmu gocewa tayi ne, naga ko ina da wuta mu bamu dashi? """ Hameeda tace. """Yaya Wawo ne ya cire dama gidansu shi ke bamu wuta, yace kaja mana a falwaya kai tsaye""" """Ikon Allah wai Wawo me yake nema dani ne, malama Babba kuma duk tasan abinda yake yi kuwa? """ Ajjiyar zuchiya ya sauke duk suka zauna Sauban dai yana waje yana jiran matarshi. """Wai daga ina wannan abincin haka masu yawa? """ """Ummi ce tace mu kawo maka harda kuɗi? """ """Sabuwan tace a kawo mun, kunje kun tona mun asirin gidana kenan Aminu, Mardiyya har dake? """ Mardiyya tace. """Kayi haƙuri ta tambayemu babu matsala ko shine muka faɗa mata akwai sabida Ummi bata son ƙarya" bamu taɓa mata ƙaryaba bata koya mana ba. Baba kayi haƙuri ai kana buƙatar kayan abincin. Ga wannan kuɗinma Dady yace a kawo maka. Waɗannan ledojin nasu Mamane da jari dubu hamsin hamsin a ciki. "Aminu mimmiƙa musu ni zan tafi""" Hannu Babangida yasa ya karɓi damin kuɗin jikinshi yayi sanyi sosai tsoron Allah ya sake kamashi. """Mun gode Allah ya saka da alkhairi zan kirashi ma in sha Allah""" """Baba nima ya samamun aiki sati me zuwa zan soma zuwa can Kanon zan koma da zama""" Murmushi yayi yace. """Sabuwa tayi mun wayo ta dai ɗaukemun kai ko Aminuna? """ Sai suka yi dariya. Su Hameeda sukaita godiyar kuɗi da atampa Mardiyya dai tayi musu sallama tabi mijinta suka tafi. Babangida na gama cin abinci ya nufi gidan Malama Babba acan ya tadda wawo ma. Bayan sun gaisa Babangida yayi ƙorafinshi akan Wawo. """To Baba kayi haƙuri kaja wutar taka daban zaifi. Batun yara kuma gaskiya bai kyauta ba ta wani" ɓangaren ta wani ɓangaren zamansu a gidan bashi da amfani gara ka kula dasu yafi. Batun kuma Aminu daya cire a Matsayi tun farko ni wannan matsayin na faɗa bana Aminu bane Malam "yayi ne dan ya cusa mun baƙin ciki kawai""" Murmushi Babangida yayi yana mai nadamar kawo ƙaran ma da yayi. Kiƙewa yayi jiki ba ƙwari yace. """Saida safenku""" """To baka ce komai ba ka kawo ƙorafi anyi maka bayani ka kuma miƙe? """ Cewar Wawo sai zazzare idanu yake yi. Babangida yace. """Wawo kenan Khairan in sha Allah. Ai duk wanda yayi guga yace zai ɗebi duniya ƙarshe inya jawo bazai" "ga komai ba.""" Ya saka kai ya fice. A wannan dare Babangida da ƴar Shuwa sun kasa runtsawa shi damuwar yadda ƴan uwa suka juya mishi "baya yake ciki, da kuma mamakin yadda Allah yake jujjuya lamura wai yau shine mijin Sabuwa da Sabuwa suka rufama gidanshi asiri?" Ita kuma ƴar Shuwa nata na hassadane da ciwon wai yau Sabuwa ke cikin irin wannan daular da har dubu hamsin bata ɗauketa a bakin komai ba har zata iya raba musu su huɗu. Ga atamfa mai tsada ga hilimin kayan Abinci? Allah al hakim. Gaga_gaga _gaga _gaga Rayuwa taci gaba da garawa. "Aminu ya koma Kano yana aikinshi duk wata yana zuwa ganin gida, kuma kusan shi ya ɗauke nauyin" abincin gidan Babangida har saida Aɗɗa'u ya kawo ƙarfi shima ya samu aiki anan Dutse shine suka raba a tsakaninsu. Babangida dai tunda wannan dubu ɗari da Hamsin ta shigo hannunshi saita hayayyafa itace ta haihu ta dawo miliyoyi abubuwa suka warware da taimakon Allah ya sake buɗe kamfanin niƙa kayan Baban bola da motarsu ta sufurin kaya zuwa Lagos. Yayi gida ya tashi a kusa da su Wawo nan ɗin tunda nashi ne ya "riga da ya biya Baba malam kuɗin gidan kafin ya rasu sai ya zuba haya. Yana da ƴar motarshi ta hawa, ya" wadata iyalinshi da abinci dama haka yake tun farko Rayuwa ta daidaita tayi kyau kamar ba'ayi komai ba. Cikar kamala da Dattijantaka irin na Baba malam ya fito sak a aiyukan Babangida da mu'amalarshi. Amman me harfa zuwa wannan lokacin zuwa yau da littafinnan yazo ƙarshe ba'ayi wannan rabon gado ba. Da an yinƙuro Wawo zai yinƙura sai salwantar da hakkin marayu yake yi. Kawu Manga yayi iyakar "yinshi Babangida ya roƙeshi ya zuba idanu. Harma ake raɗe_raɗin Wawo asiri yayi musu shi yasa suka kasa yi mishi bore, suna ji suna gani yanata ɓalɓanta dukiyarsu." "Wannan kenan""" Sabuwa:. Rayuwa ta sake miƙawa Hajara har ta shiga sakandare ajin farko. Su Gaza sun hayayyafa girma yazo musu sosai. Uzairu zuchiyata shima yaranshi uku dukka Maza. Masa'u kuwa yana rihab mun kaishi hauka yake yi tuburan wallahi. "Maigogul yayi tsufa mai kyau ga shekarun amman ba wani ciwo, da ƙafafunshi yake zuwa ko'ina gaye" baifa daina ba. Hauwa da Rakiya duk sanda rikicin Rakiya ya tashi dole sai sunyi wannan faɗa musamman in Hajiya Balaraba ta kawo musu ziyara. Nasan kunata son jin ƙarshen Hajiya munubiya sai kuka ji shiru ko? "Wannan labarin ba ƙirƙirarre bane har yanzu Hajiya munubiya tana raye Allah ya ara mata lokaci, kuma" tana yawan turoma da Omri saƙo ta waya akan ya maidata ɗakinta. A wata majiyar ma mai ƙarfi naji ance bata dena bin bokaye ba. "Ƙarshen zaizo ne, in Allah yaso kuma ya barta har sai ta mutu ta koma gareshi saita girbe abinda ta shuka." A iya haka inaga labarin yazo ƙarshe Mungode da soyayya wallahi nima zanyi kewa masu son ganin hotona kona Dad ayi haƙuri dan Allah. Amman fa bazan mance da waɗanda sukaita aibatamu ba. Kuma abadan bazan mance da waɗanda sukaita mana uziri ba. "Na mance, a yanzu ina da izifi talatin a kaina, kuma na haddace wasu hadisai da dama ina iyakacin daidai" "ƙoƙarina waj kiyaye dokokin Ubangiji. Ilimin boko dai ban koma ba, sai dai Allah yayi mun arzikin samun mijin daya ɗaurani kan komai na nemanshi duk wata ƙasa da zaije dani muke zuwa, kuma duk wani meeting ina gefenshi. Na waye na goge irin gogewar da ko ƴan bokon babu abinda zasu nuna mun sai" turanci ko? Shima Uzairu zuchiyata yana zuwa muna yi inata kan koyo wallahi. Yarana dukka ni dasu munje mun yi umara na biya musu da kuɗina. ALHAMDULILLAHI LITTAFI YAZO ƘARSHE ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA DARASHIN DA MUKA KOYA. KUSAKURAN DAKE CIKI KUMA ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA. WANNE BABBAN DARASI KE KIKA KOYA TUNDA DARUSSAN SUNA DA YAWA? IN MAKI AKACE KI BA WANNAN LITTAFIN DAGA ƊAYA ZUWA ƊARI MAKI NAWA KIKE GANIN ZAI SAMU? WACCE KALMA CE TAFI BURGEKI CIKIN RUBUTUN? SON SO SAI UBANGIJI YA SAKE SADAMU A SABON LITTAFI SABUWAR TAFIYA. "CAU CAU CAU, EH WALLAHI WUYA A TYPING WUYA A KWAMENT, WUYA A EHH TO SAI EH ANJIMANKU" INJI GAZA. ฀ Mrs BUKHARI