[5/10, 8:41 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 ✨ *_JALALA_* ✨ 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_ALHAMDULILLAH TSARKI YA TABBATA GA UBANGIJIN DA YA HALICCI SAMMAI DA ƘASSAI, YA HALICCI MUTUM DA ALJAN YA YI WUTA DA ALJANNA, SARKI MABUWAYI WANDA BASHI DA KISHIYA BAI HAIFA BA BA'A HAIFESA BA, YANDA NA FARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA INA ROƘON UBANGIJI DA YASA NA GAMA LAFIYA_* *_Special tnx to my people, masoya masu ƙaunata a ko yaushe yauma dai gani da sabon salo mai tafiya da zamani, labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi da dama, ku kasance dani a cikin wannan labarin._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Pg 1 to 2_* *KWARA STATE.* *_IFELODUN local Government_* *_IYABO QUARTER'S NEAR OMUPO WORD_* "Sauyin rayuwa kan nuna maka alamun ka hankalta, amma ina mamakin mutane da basa gane azancin duniya, duniya tamkar waina ce dake bisa kasko takan iya juya mutum a duk sanda taso, shiyasa ko yaushe nake fatan Duniya ta muku juyin alkairi, domin bana fatan abinda zai shiga tsakanin ku har ya samu damar rabaku tamkar jinina haka nake jinka *_NAMEER_* so nake ku kasance tsintsiya maɗauri ɗaya har ƙarshen numfashinku, *_HISHAM NAMEER_* ba iya Amini yake a wajen ka ba tamkar ɗan uwa na jini haka yake tunda a hannuna ya tashi tun bayan mutuwar mahaifansa, Soyayyar ku da abotarku tun ta yarinta ne, duk da a zuciyata bana jin akwai abinda zai iya rabaku saboda tsantsar ƙaunar dake tsakanin ku, amma wasiyya da nasiha ta dole ce a gareku, abotarku tana da ƙarfin da tafi jini tasiri, nasan dole ne kuyi nasara akan maƙiyanku ina matuƙar alfahari daku ina muku wannan nasihar ce saboda ita mutuwa bata da notice haka kuma bata ƙwanƙwasawa bawa ƙofa, zan iya komawa ga mahallicina a ko wani lokaci." Kallon Nameer Hisham yayi tare da sakin numfashi yace. "Abba Ina mantawa da cewa Nameer Abokina ne, kallon jinana kawai nake masa, yana kyautata min Abba, yakan yaƙi da duk wata damuwar da yaga ta tunkaro ne, karka manta Abba, Ammi ta kasance ta bamu tarbiyya iri ɗaya, ta bamu abinci a baki tare, ta share mana hawaye tare, to ta yaya zan ɗauke sa iya Aboki kawai? ya wuce wannan matsayin Abba, domin ƙaunar da nake masa ta kai ga zan iya mallaka masa komai a rayuwata domin kuwa yafi min komai mahimmanci ina matukar alfahari da Nameer Abba shine jigon rayuwata na basa duk wata yardata." "Abba Hisham fa ɗan uwana ne ka daina shakku akanmu domin kuwa zamuyi ƙargo har abada, igiyar Amintar mu tana da ƙarfin da bazata taɓa tsinkewa ba ni da Ɗan uwana Hisham mutu ka raba Abba, zamu bawa maƙiya kunya ka kwantar da hankalinka a kanmu Abba." "Hmmm! Ni ma shaida ce Abban Hisham domin kuwa yarana basu taɓa ko da cacar baki bane bare faɗa, lokacin Office na ƙurewa kuyi maza kar ƙananan ma'aikata su gaji da jiranku Allah ya muku albarka ya tsare min gabanku da bayan ku." Murmushi Hisham yayi tare da cewa. "Ameen Ammin mu, mun gode sosai sai mun dawo." "Sai mun dawo Ammi." Shima Nameer yayi Maganar cikin fara'a, da adawo lafiya Ammi da Abba suka amsa, kafin ko wannensu ya ɗauki jakar aikinsa suka fita tare, Murmushi Ammi tayi kafin ta mayar da kallonta ga Abba tace. "Abban Hisham, shaƙuwa da ƙaunar junan da suke yiwa junansu har yayi yawa, ina jin Nameer a jikina tamkar ni na haifesa, Abban Hisham, mutane sai saka maka albarka suke bisa ɗaura Nameer a matsayin shugaban Companyn ka *_ HISHAM RICE MILL LIMITED_* madadin ka bawa Ɗanka Hisham ka kyauta sosai na tabbata kuma zai tsare maka dukiyar ka da mutuncin Companynka, Allah ya jiƙan iyayen Nameer mutane ne na ƙwarai da suka san haƙƙin makwabtaka." Numfashi Abba ya saki yace. "Na lura yafi Hisham nutsuwa da sanin abinda yake zaifi mai da hankali ga cigaban Company shiyasa na basa dan haka ki daina gode min abinda ya kamata nayi, Nameer shima ɗana ne." "Hakane to Allah yayi jagora, bara naje na bawa TUTU key ɗin store ta ɗauko coffee na kitchen ya ƙare." "Okay kina iya tafiya." Abba yayi Maganar yana maida glass ɗinsa idanunsa tare da ɗaukar jarida ya cigaba da karantawa itama Ammi bedroom ɗin su Nihal ta nufa. Tafe suke a ƙas sun fito daga ofishin Jaridar Aminci, suka hango cincirindon mutane, a gefen hanya, duban Basmah tayi tace. "Basmah meke faruwa a can.?" "Kaji wata tambayar rainin wayo, mu fito tare sannan ki tambayeni aljana ce ni ko boka da zansan abinda ke faruwa a wajen." "To sarkin ɓakar magana, ni bara na ƙarasa wajen naga abinda ke faruwa." Kanta Basmah ta girgiza tare da cewa. "Kina da matsala *JIDDA* baki san meke faruwa a waje ba ki kai kanki saboda kawai kina ƴar jarida mai tarar kasada ko ke gaki mai son ɗauko rahoto." "Bani da lokacin ki idan zaki iya zuwa ki biyoni idan bazaki iya ba, mu haɗu a gida." Tayi Maganar tana saka kai tabar wajen, bakinta Basmah ta taɓe tare da bin bayanta, ko da Jidda ta isa wajen a cike yake babu masika tsinke jama'ar wajen ta dinga ketawa har ta samu ta shiga tsakiyar wajen da ƙyar, wata ƴar matashiyar budurwa ce baje ƙasa, da alamu bata motsi, yayin da jama'ar dake Wajen suka zuba mata idanu babu wanda yayi yunkurin taimakon ta, jikinta duk ya kuje da alamun yaguni da sauri Jidda ta sunkuya a kanta tana furta. "Subahanallah! Meya faru da ita, kun zuba mata idanu bazaku kaita asibiti ba idan ta mutu a wajen nan fa.?" Wani daga cikin wadanda ke tsaye a wajen ne yace. "Ta yaya zamu sanya hannu a jikinta bayan muna kallo aka wurgota daga mota, mun sanya hannun mu a cikin masifa kike so, idan taimakon ta kike son kiyi to ki fara kiran Police tukunna." Ɗago idanunta Jidda tayi a zuciye tace. "Amma dai Allah wadarai wallahi kuna kallon mace wurge gefen titi ku gagara taimaka mata, idan ƙanwarku ce zaku zuba mata idanu haka ba tare da taimako ba, mtsss! Wai kuma har kana da bakin bani shawara, ku kauce ku bani ni zan rungumi kasadar idan yaso masifar da kuke gudu ni ta kasheni." Tayi Maganar tana miƙewa tare da kwaɗawa Basmah kira, duk kaucewa gefe sukayi suka bata hanya babu wanda ya ce komai a cikin taron, Basmah ƙarasowa tayi ta tsaya a gabanta tare da cewa. "Gani kiran me kike min.?" "Taimakon ta zamuyi Basmah domin kuwa tana buƙatar taimako ta zubar da jini da yawa Sannan bata motsi zata iya rasa rayuwarta muddun muka tafi muka barta a hannun wadannan marassa imanin." "Hmmm! Jidda ba rashin imani yasa basu taimaketa ba, karki musu mummunar fahimta domin kuwa rayuwa ta lalace, a sanadin taimako sai ka shiga cikin wata masifar banga laifin su ba, ko da ma suna da laifi to laifin ɗaya ne na rashin kiran jami'an tsaro da wuri, karmu taɓa wannan yarinyar idan har taimakonta zamuyi to police ya kamata mu kira kamar yadda wannan bawan Allah ya faɗa miki." "Kinga Basmah bazan tsaya har sai an kira Police sunzo ba! Kafin a kaita asibiti rayuwarta zamu ceta bama bukatar jira idan zaki taimaka to idan bazaki taimaka ba kija baya zan iya ba tare da taimakon ki ba." Tayi Maganar cikin masifa tana fita sarari da kallo Basmah ta bita domin kuwa ko yaushe bata gajiya da mamakin taurin kai da kafiya irin na Jidda ba, sam ba'a juyata inda ta sanya kanta nan kawai takeyi tana kollonta ta taro adaidaita, da ita da mai adaidaitan suka kama yarinyar suka sanya ciki kafin Jidda ta shiga ta tallafota jikinta, Basmah kanta ta kaɗa tare da shiga cikin adaidaitan, harara Jidda ta watsa mata tare da cewa. "Nayi zaton ai imaninki ya gushe ashe har yanzu da saura." Tayi Maganar dai-dai mai adaidaitan yana ja. "Bazaki fahimce ni bane, yanzu da kika ɗauketa kina zaton asibiti zasu amsheta ba tare da Police bane.?" "Bazasu amsheta ba na sani, shiyasa ma na turawa Ahmad text cewa kinyi accident muna IBUNKU OLU CLINIC wataƙil ya rigamu isa kinga police ɗin ma aishi zai jiramu." "What! Jidda meye kikayi haka." "Ceton rayuwar mace ƴar Uwar mu shi nayi ko akwai laifine ayin hakan." "Ƙwarai kuwa akwai babban laifi ma, akan me zakiyi ƙarya dani ki faɗa masa gaskiya mana zaki wani ɗaura min mungun abu." "Koma dai mai zaki faɗa kiyi haƙuri ni ne na miki laifi amma kin sani muddun na sanar dashi gaskiyar abinda ke faruwa ba zuwa zaiyi ba." Tsuka Basmah taja cikin ɓacin rai tace. "Dole ki bani haƙuri ai tunda kin cuceni." Tayi Maganar dai-dai suna shigowa asibitin, shima Ahmad dai-dai yayi parking ɗin motarsa ya fito a gigice turus ya tsaya ganin Basmah sun rungumo wata, wajen su ya ƙarisa da sauri yace. "Jidda ya haka kince Basmah tayi accident kuma naga kin rungumo wata ga Basmah tsaye lafiya.?" "Ahmad bamu lokacin Doguwar magana dan Allah ka sanya hannu a duba wannan baiwar Allah, kafin mu maka bayani, a gefen titi muka tsinceta cikin wannan halin." Ahmad zaiyi Magana Basmah ta katsesa da cewa. "Kar ka mata gardama domin kuwa kasan mayya ce ita, ka sanya hannun." Numfashi Ahmad ya saki kafin likitoci suka taho da keken marassa lafiya aka turata, ganin Ahmad da kayan Police a jikinsa, bayansu yabi ya cike dukkan wata takadda rashin sanin sunanta yasa ba'a rubuta sunanta ba kafin sukayi emargency da ita. Bayan an shiga da ita ne Ahmad yayi kan Jidda da faɗa na ɗaukar wannan kasadar, ita dai bata kulasa ba, suna nan tsaye har doctor ya fito duban Ahmad yayi yace su samesa a Office bayansa sukabi tare da zama doctor ya dubi Ahmad yace. "Wannan marar lafiya da kuka kawo, gaskiya ta zubar da jini da yawa, muna da jinin da yayi dai-dai da nata kasancewar tana neman jini cikin gaggawa yasa bamu muku magana ba muka sanya mata da alamu faɗowa tayi daga sama ko dai something haka ta kuje sosai amma dai Alhamdulillah! Babu matsalar buguwar kai, mun mata allurar bacci sannan akwai zazzaɓi a jikinta zata iya farkawa ko wani lokaci zakuje receiption ku biya kuɗin jini, ga kuma takaddar magani zaku saya." Hannu Ahmad ya sanya tare da amsa yace. "Thank Doctor." Tashi yayi ya fita bayansa suka biyo, Jidda ce tace. "Akwai kudi a account ɗina ni zan biya wannan taimakon da kayi da jikinka ma kaɗai ya wadatar na gode sosai." "Hmmm! Jidda kece zaki biya kudin kika ce, Karki manta ɗawainiyar mahaifiyarki da ta ƙaninki kuɗin hayar gidan ku duk a kanki suke, dan haka idan ba'a ƙara miki ba baza'a rageki ba, ni zanje na biya da aljihu na." Numfashi Jidda ta saki tana ganin darajar Ahmad sosai musamman yacce yake tausayawa rayuwarta. "Hakane Ahmad na gode sosai, yanzu yaya za'ayi da kwana a wajen yarinyar kaga fa Ummana ba lallai ta amince na kwana ba infact ma bazata yarda ba."? "Karki damu Jidda, zan kira A'isha sai tazo su kwana zuwa gobe ta dawo hayyacinta sai musan ahalinta, kuna iya tafiya zanje na gama komai kafin Aisha tazo ni sai na wuce." Murmushi Jidda ta yi tace. "Na gode Ahmad Allah ya maka abinda kayiwa wannan yarinyar sai goben." Tayi Maganar tana yin gaba, Basmah duban Ahmad tayi tare da sakin murmushi tace. "My Dear ina matukar girmama Soyayyar mu, kai Mutum ne na Musamman a rayuwata, ina sonka matukar Soyayya." "Hmmm! Basmah idan ban kyautata miki ba waye zan kyautatawa, kinfi ƙarfin komai a gareni Basmah dan haka ki tafi kuje huta zan shigo anjuma." "Shikenan farin ciki na bye." Tayi Maganar cike da soyayya tana bin bayan Jidda. 💫💫💫💫💫💫 "Na rantse da Allah sai naga bayan zuri'ar Iyabo bazan taɓa gushewa ba sai naga ƙasƙantarsa da tozarta sa, koda kuwa zanyi yawo tsirara, nasan zuwa yanzu saƙona ya fara ƙwanƙwasa musu ƙofa, sai na sanya su a cikin *_JALALAR_* da sai sun roƙi mutuwa da kansu, *TUNDE* muddun kai jinina ne to tabbas bazaka gushe ba har sai ka ɗauki bashin gabar da ke tsakanin mahaifinka *Babawale* da *Iyabo*, kadda ka saurara musu nima kuma bazan saurara musu ba, na sanya mutanena a cikin Companyn su suna sanya min ido akan dukkan abinda zaije ya dawo acikin Companyn to yana tafin hannuna dan haka karka saurara." *Mama Bisola* tayi Maganar cike da tsantsar wutar fansar dake ruruwa a cikin zuciyarta da tsanar familyn Iyabo. "Mamabisola karki manta cewa babu mutanen dana tsana a wannan duniyar sama da su Iyabo ba kuma zan gushe ba har sai naga bayansu, daga ƴaƴansa zan fara da wannan tsintaccen yaron da ya ijiye ya basa yardarsa fiye da matar sa da ɗansa, wallahi Mamabisola sai na sanya su kuka a tsakiyar titi." "Haka nake so Tunde kaje kana tare da Sa'a." "Na gode Mamabisola, zan wuce wajen Bola." "Ka dawo lafiya." Mamabisola tayi Maganar cike da ƙaunar Tunde, yana fita Wemimo dake gefe zaune ta dubi Mamabisola cikin harshen yarbanci tace "Mamabisola, ina mamakin yadda Iyabo ya bawa wannan dan Hausan Amana sunansa Nameer ko, meyasa ya basa shugaban Kamfanin sa bayan ga Hisham ɗansa.?" "Hmmm! Wamimo ke kanki hakan zai baki mamaki har yanzu ban gano wani ƙwaƙƙwaran dalili da yasa yayi hakan ba, duk da cewa yaron abokin ɗansa ne, amma ni na sani sai yaci amanarsa domin kuwa Hausa babu amana." "Hakane Mamabisola, amma Mamabisola, gani nayi kinfi MamaIyabo yawan yara naki yaran Uku ne, ita kuma MamaIyabo nata yaron ɗaya ne Iyabo amma har kikayi sake dukiyar MamaIyabo ya yaɗu ku naku ya lalace, meyasa Mamabisola, meyasa kuka sake haka."? "Hmmm! Wamimo bazaki fahimta ba, amma maigidan mu shine wanda ya cuce mu ni da yarana, shi ya bawa Iyabo ƙyautar Companyn sa na Auduga, wanda bai shiga cikin gado ba, wanda shine yanzu iyabo ya gyarasa ya maida shi Hisham rice mill limited, wanda a yanda Ademola yake sanar dani a ko wani wata suna samun kuɗi sama da 50m ni kuma gani ni da ƴaƴana muna zaune bama samun rabin abinda suke samu, dan haka Wamimo na ɗaura aniyar tozarta rayuwar Iyabo da iyalinsa, wacce hanya ce zaki iya taimaka min."? Numfashi Wamimo ta saki tare da cewa. "Huuuu! Mamabisola, ni kuwa nake da hanyar taimaka miki, zamuje wajen sarkin aljanu domin ya tarwatsa dukiyar su rasa komai ya kike gani zamuje."? Girgiza kanta Mamabisola tayi tace. "No Wamimo, bazai yiwu zuwa wajen Sarkin Aljanu yanzu ba domin kuwa mai gidan mu *ABDULWASI'U* yayi kafi a jikin yaransa idan mukayi tsafi yanzu zai iya dawowa kanmu, da badan wannan kafin ba, da na juma da hallakar da Iyabo, sai dai taimako ɗaya zaki min ki shiga ki fita wajen sarakan tsafi ki samo min makarin kafi idan har aka samu to tabbas zan hallaka Iyabo da tsafi." "Za kuma a samu tabbas ni ne nake tabbatar miki da wannan, zan fara bibiyar Sarakan tsafi kuma sai na kawo wannan makarin." "Idan kika min haka Wamimo bazan taɓa mantawa da ke ba, kije ki bincika ni kuma zan cigaba da jifansu da makaman sharri." "Baki da matsala Mamabisola, ni yanzu zan shige sai gobe zan fara nawa aikin." "Na gode Wamimo muje na rakaki." Mamabisola tayi maganar tana tashi har bakin get ta raka Wamimo kafin ta koma cikin gida. ***************************** A bakin ƙofar gidan su Jidda suka rabu da Basmah kasancewar gidan su Basmah yana gaba da nasu Jidda, sallama sukayi da nufin sai gobe zasu haɗu, kafin Basmah ta shige ita kuma Jidda ta shiga cikin gida, Umma ta samu zaune a tsakar gidan gefenta kuma AbdulRahman ne yana mata wanke wanke zama tayi tana cewa. "Wash Umma na gaji sosai yau." Murmushi Umma tayi kafin tace. "Ai dole ki gaji jiddatul kair tun safe fa kika fice, kece sai yanzu gabannin magaruba, meya tsayar dake ne haka ke da kika saba dawowa 4:00pm.?" "Hmmm wallahi Umma wani matsala ne ya faru a hanyar mu ta dawowa, wata yarinya ce aka bigeta da mota to shine muka taimaka ni da Basmah aka kaita asibiti yanzun ma daga asibitin muka dawo shiyasa nayi dare." "Subahanallah! Amma dai haɗarin da sauƙi ko.?" "Ehh Umma da sauƙi sosai ma, amma dai mun baro asibitin bata dawo hankalinta ba, amma likita yace zata farka lafiya." Gyaɗa kanta Umma tayi tace. "To masha Allah, Allah ya bata lafiya, ki cigaba da taimako Jiddatul kair insha Allah kina tafe da gagarumar nasara a rayuwarki, nakan jin daɗi harma nayi alfahari idan naji kin taimakawa wani, Allah ya miki albarka ya rabaki da sharrin maƙiya." "Ameen Umma." "Adda Jidda sannu da dawowa." "Yauwa abdulrahman kana taya Umma aiki ne, magaruba ta gabato, ka tashi kaje kayi alwala ka tafi masallaci bara naje na ijiye mayafi na sai nazo na ƙarisa wanke wanken." "To Adda." Yayi Maganar yana tsame hannunsa daga ruwan wanke wanken, ya ɗauki buta Jidda tashi tayi taje ta ijiye mayafinta da jakarta kafin ta dawo ta idda wanke wanken, ita ta tuƙawa Umma tuwon kafin aka kira sallah sukayi alwala sukayi sallah bayan sun idar ne ta ɗauki Alqur'anin ta ta hau karatu bata idda karatun ba har sai da tayi sallar isha'i" "Jiddatul kair tashi kije ki sako mana tuwo muci, naga alamar Abdu bazai shigo yanzu ba." "Ina ga sun tsaya karatu ne, bara naje na ɗauko." Tayi Maganar tana tashi taje ta ɗauko musu tuwan masara miyar ɗanyar kuɓewa, zama tayi ta ijiye tuwon tare da Bismillah suka fara cin abincin babu wanda yayi magana har suka kammala cin abincin suka wanke hannu sannan Jidda ta fitar da kwanukan ta dawo." "Umma wai nikam dama haka yaruba suke basu da kirki." "Jiddatul kair meyasa kika min wannan tambayar wani abin suka miki na rashin kyautatawa.?" "A'a Umma wacce nace miki an bigeta da mota mun kaita asibiti ita suka gwadawa rashin imani domin kuwa Umma Yarinyar ta juma sosai wurge tsakiyar titi cikin halin rayuwa ko mutuwa sun cika a kanta Umma amma babu wanda yayi tunanin taimaka mata sai ma idanu suka zuba mata tamkar tv suna kallon ta hakan ya ƙona min rai sosai Umma." "Jidda a gaskiya Bayarben mutum, bashi da daɗi ta wani fannin amma ta wani fannin kuma yafi kowa daɗin mu'amala, domin kuwa ba duka aka taru aka zamo ɗaya ba, basu da matsala ta fannin mu'amala domin kuwa suna kyautatawa talakan da suka fisa ƙarfi, nayi zama cikin su sosai na fahimci ɗabiun su suna da zumunci da kyautatawa ga maƙwabci, amma nayi mamaki da basu taimaki wannan Yarinyar ba." "To dai gashi basu taimaketa ba, ni har na fara ma jin haushin wannan yaren Yaruba basu da im............ "A'a jiddatul kair kul kika ƙarisa, ko kin manta Mahaifiyata Yaruba ce kike ƙoƙarin aibata su.?" "Ban manta ba Umma sanin hakan ma yasa ni ƙwarin gwiwwa da hujjar rashin imani irin na Yaruba domin kuwa na sani da Hausawa ne ko Fullo ko Kanuri bazasu taɓa yasar da ɗansu ba komai girman munin halinsa, na sani Umma da mahaifinki yana raye bazaki tagayyara haka ba, Umma nasan zakiji zafin maganganuna domin kuwa uwa ba abar wasa bane sai taki mahaifiyar bata da tausayi." Idanun Umma cikowa da hawaye sukayi tabbas maganganun ƴarta akan mahaifiyarta gaskiya ne sai dai har cikin ranta tana jin zafi da ciwo idan taji an aibata mata uwa bata taɓa zaton rayuwa na juyawa mutum baya haka ba sai a tsakanin waɗannan shekaru 18 da suka gabata numfashi ta saki kafin ta cewa Jidda. "Jiddatul kair ki tashi ki bani waje." "Amma Umma y....... "Ki tashiii ki bani waje nace miki! Bana son maganar banza babu ruwanki tsakanina da mahaifiyata koma me ta min a rayuwa uwata ce koda mahaukaciya ce ina alfahari da ita, koda kuwa kasheni tayi ta dawo dani ina sonta zuciyata kuma bazata jurewa munanan maganganu akanta ba, ki kiyaye muddun bakya son fushina ya sauka a kanki." _____________________________________ Share and comment my fan's🥰 *UMMU NASMAH CE✍🏻.* *_FOR MORE INFORMATIONS_* *_08147537180_* [5/11, 7:21 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. https://chat.whatsapp.com/JdppMXgnPBL1ZTAKjpSrYs *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_FREE BOOK ONE_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Pg 3 to 4_* "Kiyi haƙuri Umma Allah ya huci zuciyarki, banyi zaton maganar zata ɓata miki rai haka ba, ke uwace gareni fushinki masifa ce a gareni ki yafe min insha Allah bazan kuma wata magana marar daɗi akan Mama ba." Umma ba tare da ta dubeta ba tace. "Naji na kuma yafe miki Allah ya muku albarka." "Ameen Umma na gode." Tayi Maganar dai-dai Abdu na shigowa gefensu ya zauna, Jidda ce ta dubesa tare da cewa. "Abdullahi sai yanzu ka dawo daga sallar." "Na tsaya Liman ya ɗaura min karatu ne shiyasa na juma, ina abinci na."? "Abincin ka yana madafa." Ta basa amsar tana miƙewa ta shige ɗakinsu, Abdu Umma ya kalla yace. "Umma kamar wani abu yana damun Adda naga kamar ranta babu daɗi."? Numfashi Umma ta saki tace. "Yanayin rayuwa ne Abdu ba ko wani lokaci bane bawa yake cikin farin ciki, kaje ka ɗauki abincin ka." "To Umma." Yayi Maganar yana miƙewa yaje ya ɗauki tuwon nasa kafin ya shiga ɗakin da Jidda ta shiga tana zaune tsakiyar katifa tayi shuru cikin tunani da damuwar rayuwa sallamar sa shine ya dakatar da ita daga tunanin da ta tafi, ta amsa sallamar zama yayi yana sanya hannunsa cikin aljihun sa ya zaro dubu biyar ya miƙa mata. "Gashi Adda." Kallon kuɗin tayi ba tare da ta amsa ba tace. "Gashi kamar yaya kuɗin waye.?" "Uncle Abdulra'uf ne ya bani yace na kawo miki ko kina da wata buƙata kiyi amfani dasu." "Abdulra'uf ya baka ka kawo min, na roƙesa kuɗi ne ko kuwa ya ganni cikin tozartacciyar rayuwar da har zan fara roƙo, banyi wannan lalacewar ba Allah ya min ni'ima da har ya bani damar karatu na samu aikin yi, ka mayar masa da kuɗinsa kace bana buƙata." "Amma Adda gani nayi kamar babu kyau mai da hannun kyauta baya, uncle Abdulra'uf fa sonki yake Adda ba laifi bane idan ya miki kyauta sanin kanki ne yana tausayawa halin da muke ciki, kefa macece komai kece kike mana namiji ma yaya ya ƙare da nauyin gida bare kuma mace dole ne a tausaya miki Adda gashi ni bana da ƙarfin da zan iya neman kuɗi a yanzu bani da lafiyar ɓargon jiki sannan ga ƙafata janta nake hmmm! Adda........... "Ya isa haka Abdullahi, ka daina min wannan Maganar mace ma mutum ce kamar kowa duk abinda Namiji zaiyi zamu iya dan haka ka daina jin damuwa a kaina, kaje ka mayar masa da kuɗinsa kamar yadda na umarce ka, bana buƙatar abinda zai fito daga garesa na yafe zan iya ɗaukar nauyin rayuwar mu sannan ka sani idan shi Abdulra'uf yace maka yana sona to tabbas yayi kuskure domin kuwa bazanyi kuskuren da mahaifiyata tayi ba, na amincewa Yaruba dukkan su macuta ne basa da imani." "Amma Adda ya kamata ki duba wann......... Cikin sauri ta ɗaga masa hannu. "Ka tashi ka fita min daga ɗaki Abdullahi idan ba so kake na ɓata maka rai ba." Ganin ranta ya ɓaci yasa Abdullahi tashi ya fice da kwanon tuwonsa yana mai da kuɗin aljihun sa. Tsuka Jidda taja tare da jawo bargo ta kwanta tana rufe jikinta. Washegari da safe, Tutu da kanta ta musu breakfast ita da Peju kukun gidan su, a daining table suka jera abincin kafin Tutu ta shige bedroom ɗinta tabar Peju tana kimtsa kitchen ɗin Ummi ta turawa saƙon sun kammala breakfast ɗin kafin ta shige tollet wanka. A hankali ya buɗe idanunsa yana duban agogon bangon dake manne a bangon ɗakin idanunsa ya lumshe tare da duban Nameer da ke bacci har yanzu bashi da niyyar tashi, ƙafafunsa ya ziro ƙasa tare da sanya takalmin dake gefen bed ɗin, ya sauƙa, towel ya ɗauka tare da shigewa tollet, ya juma sosai kafin ya fito ƙugunsa ɗaure da towel ya rataye ɗaya kuma a kafaɗarsa da alamu wanka yayi, a dressing mirror dake gefen bed ɗin ya zauna tare da sanya hannu ya kaɗowa Nameer ruwan gashin sa a fuskarsa yana sanya towel ɗin ya hau tsame ruwan kansa, cikin azama Nameer ya buɗe idanunsa, jin sauƙar abu kamar ruwa a fuskar sa, a kan Hisham ya sauƙe idanunsa kanne masa ido Hisham yayi tare da nuna masa agogo da hannu yace. "Raise your eyes and look at 11:00 am this weekend Abby is home, breakfast on time is a must." Numfashi Nameer ya saki tare da jawo ƙaramin filon dake tsakiyar su ya jefi Hisham dashi yana cewa. "Saboda yau weekend ne shine zaka min irin wannan tashin na razanarwa wai Hisham yaushe zakayi hankali ne, ko sai randa kayi Aure ne.?" Wani irin kallon off and down Hisham yayiwa Nameer kafin yace. "Aure! Ni hmmm! Idan mafarki kake ka tashi kayi sadaka, natsani Soyayya, bare kuma Aure da yake ginshikin Soyayya, dan haka ka daina sani a wannan layin." Murmushi Nameer ya saki yana tashi ya jingina da jikin bed ɗin tare da cewa. "Ba'a cikawa so baki Hisham, domin kuwa so tamkar iska yake ba'a sanin shigarsa ba'a kuma ganinsa sai dai a jisa a zuciya idan ta ɗauro ma ya taho a makance, sannan baya shawara da zuciya idan zai shiga gareta faɗawa kawai yake, dan haka ba'a cikawa So baki, ta iya yiwa ka faɗa tekun Soyayyar da bazaka taɓa iya fitowa ba komai iya ruwan da kayi." "Idan har za'a danganta so da iska to tabbas kuwa za'a iya dakatar da shigarta domin kuwa sai ka ja numfashi kafin iska ya samu damar shiga jikinka kaga kuwa za'a iya ɗaukewa So numfashi dan haka zan iya kare kaina daga faɗawa wahalar SO." "To ai kai Hisham kayi mantuwa, ba'a taɓa iya rayuwa babu numfashi muddun zaka ɗauke numfashinka na awa guda to tabbas zaka rasa rayuwarka ta har abada, ba'a gujewa so kamar yadda ba'a gujewa mutuwa duk tserenka dasu wallahi sai sun cimmaka." "Musu da kai ai wahala ne Nameer domin kuwa duk inda gaskiya take kauce mata kake muddun a fagen so ne, tamkar malamin Soyayya haka kake, ina tausaya maka domin kana cikin wahala duk da har yanzu bamu ga gwanar taka ba duk wannan lectures ɗin." Yayi Maganar yana tashi ya je drowar gajeren wando boxer ya sanya tare da farar vest Nameer ne ya mai da masa amsa da cewa. "A fagen so ba'a kuri na tabbatar maka wata rana sai Soyayya tayi wasa da rayuwar ka a gaɓar da bakayi zato ba." Kafin Hisham yayi magana Tutu ta turo door ɗin Room ɗin bakinta ɗauke da sallama Hisham amsawa yayi yana cewa. "Autar Abba, Abba yayo kira ko."? Dariya Tutu tayi tare da cewa. "Yeah abinda kuka sani ne ai, yana can yana ta faɗa wai baku fito da wuri ba, yace ku fito yanzun nan daining." "Kingan ni nan na gama shiryawa ga dai makararren da zaki faɗawa Aku sarkin magana ni kaga fitata sai ka fito." Yayi Maganar yana zarar wayoyinsa tare da sanya takalmi ya fice, Nameer duban Tutu yayi tare da cewa. "Ya akayi kika ƙura min ido tamkar kinga baƙo." "Hmmm! Dole ai na ƙura maka ido ko yaushe kai sai kayi let akan komai kana dai kallon Yaya Hisham akan lokaci yake komai nasa baya wasa da lokaci saɓanin kai." "Kema fa kinsan dole na makara domin kuwa jiya munja dogon dare, dan haka bai kamata kimin ƙorafi ba, kije kawai ina fitowa nan da 10minute, sannan zamu fita by 12 tunda yau ba ki da school." Numfashi Tutu ta saki tare da riƙe kunkuminta da kyau tace. "Bazan fita da kai ba yau Yaya Nameer, gajiyar jiya ma bata gama barin jikina ba bare kuma na kara biyeka, sannan ka dinga ɗaga ƙafa gudun fahimtar wani abu ga ahali, kayi maza ka fito kasan Abba baya jurewa jira." Tayi Maganar tana fita daga room ɗin numfashi Nameer ya saki tare da tashi ya shiga tollet. "Good morning Abba." "Morning my soon wannan sarkin makaran yauma dai still ko."? "Ummm Abba kaima fa kasan Nameer abinda aka saba ne kullum." Yayi Maganar yana kallon Ummi tare da cewa. "Good morning Ummina." "Morning Hisham, da alamu dai yau uba da ɗa sun haɗewa ɗana baki, to kuwa baku isa ba muddun ina zaune anan baku isa kun tsige min yarona ba." Dariya Tutu tayi kafin tayi Magana, suka jiyo Muryar Nameer daga step yana cewa. "Yeah! Uwata maganin kukana faɗa musu dai ni ai nasan muddun Ummina na kusa babu wanda ya isa tureni." "Hmmm! Masu uwa mu kuma ai marayu ne mararsa gatan uwa." Hisham yayi magana yana murmushi, Abba shima murmushi ya saki yace. "Chaptern ya isa haka, Tutu kiyi seving ɗin mu." Miƙewa Tutu tayi tare da jawo plas ɗin abincin ta yi seving ɗin kowa, sanin halin Hisham ba komai yake so ba yasa Tutu dubansa tare da cewa. "Yaya Hisham me zakaci.?" "Zuban chief's." Kanta ta girgiza tare da sanya masa ta tura masa gabansa, kafin tasa nata, breakfast suka fara cikin soyayya da ƙaunar junansu babu wanda yayi magana har suka gama breakfast ɗin, Hisham ya riga kowa tashi, ya koma tsakiyar falon ya zauna, kafin Abba ya biyo bayansa. "Hisham." Abba ya kira sunan sa ɗago idanunsa Hisham yayi tare da amsawa. "Na'am Abba." "Wannan week ɗin kaje gidan Mamabisola kuwa ka gaishe ta."? "Banje ba." "Meyasa."? "Haka kawai." "Hisham bana son sakarci da iya shege, Mamabisola uwa ce gareni bana son kana ɗaukarta tamkar wata bare." "Hmmm! Abba ni fa bazanje inda za'a dinga zagina ana kallona banza ba, kaine take dole a gareka bani ba, dan haka ni babu abinda zanje nayi a gidan ta, kawai ka ƙyaleni." "Hisham........... "Dan Allah Abba kabar wannan maganar, please." Ya katse Abba cikin ɓacin rai fuskarsa a haɗe domin kuwa ya tsani yaji ana zancen Mamabisola. "Hisham katseni zakayi ina magana saboda iya shege, to bara kaji tunda har Mamabisola ta zamo dolena to kuwa kaima ta zamo dolenka, ni da WALE uba ɗaya muke bani da ɗan uwan da ya shigesa, dan haka ya zamo wajibi ka girmama mahaifiyar sa." "But Abba........ "Hisham...." Ummi ta katsesa tana ƙarisowa wajen ta zauna tare da cewa. "Hisham bana jin daɗin abinda kake yiwa Mamabisola, karka manta su fa jikinka ne dole ne ka girmama su domin kuwa baka da ɗan uwan daya wucesu, baka ganin yadda Tunde ke girmama mahaifinka ko wani weekend sai ya zo ya gaishe sa cikin girmamawa kuma baya taɓa zuwa hannu haka sai yazo masa da abin arziki sai kaine zaka wulaƙanta nasa Iyayen ka kiyaye, jiya ta kirani ai Mamabisolan tana sanar dani rashin mutuncin daka tafka masa, a Company." "Rashin mutunci kuma Hisham ɗin ya yiwa Tunde, Ramata."? Abba ya tambayi Ummi cike da mamaki. "Ƙwarai kuwa wai yaje Company da takaddunsa zai nemi aiki saboda inda yake aikin babu salary mai kyau, amma yaron nan Hisham sai cewa sakatariya yayi bazai gansa ba, hakan yaɓatawa Mamabisola rai shi kansa Tunde cewa yayi bazai koma ba." "Yo ina zai koma yaje ɗan uwansa ya wulaƙanta sa, HISHAM anya kana son farin ciki na kuwa, Nameer!." Abba yayi Maganar yana kwaɗawa Nameer kira, Nameer dake zaune a daining shida Tutu ne ya juyo tare da amsawa yana miƙewa ya taho garesu gefen Abba ya zauna yace. "Lafiya Abba naga ɓacin rai a fuskar ka.?" "Dole ai kaga ɓacin rai a fuskata tunda ku baku da mutunci." "Abba me kuma mukayi.?" "Dole ai ka tambaye ni wato saboda Tunde yaje Company neman aiki shine bari a wulaƙanta sa ko aƙi ganinsa bare aji meke tafe dashi." Numfashi Nameer ya saki tare da cewa. "Tunde kuma yaushe yaje Company, wallahi ban sani ba bani da labari."? Kallon Hisham daya haɗa rai Abba yayi tare da cewa. "Oh ashe kai ɗaya kayi tsiyar ya maka kyau, Nameer zan kira Tunde Monday zaizo company lallai ku gansa kuma ku amshi takaddunsa, ku tabbatar kun basa aiki a gurbin daya kamata wannan umarnina ne." "Shikenan Abba insha Allah abinda kace haka za'ayi Allah ya huci zuciyarka." Nameer ya yiwa Abba maganar cikin sanyin kalami tare da girmamawa, duban Hisham dake kumbura Abba yayi yace. "Ba kumbura zakayi ba, ka fashe, sannan duk uzurin dake gabanka tsakanin yau da gobe ka ijiye sa kaje ka gaishe da Mamabisola idan ba haka ba ni da kaine." Hisham shuru yayi ba tare da yace wa Abba komai ba, saima tashi da yayi yabar wajen, Da kallo Nameer ya bisa ganin ransa a ɓace yasa Nameer bin bayansa, kanta Ummi ta girgiza dai-dai Tutu na ƙarisowa ta zauna jikin Ummi. "Hmmm! Abban Hisham, ni fa lamarin Hisham da Mamabisola yana bani tsoro, domin kuwa Hisham da gaske baya sonsu a shekaru irin na Hisham ya wuce ace sai an turasa yaje ya gaishe da Mamabisola, amma Abban Hisham menene duk hakan anya kuwa rayuwa zata yiwu a haka babu fahimtar juna tsakanin su, sune fa gatansa bashi da jinin daya wuce su a yau muka mutu dole sune zasu zame masa katanga." "Ramata ni kaina wannan lamari na Hisham yana bani tsoro duk da Mamabisola ta taka muhimmiyar rawa wajen cusawa zuciyar Hisham tsanar su, a duk lokacin da zaka nunawa yaro ƙiyayya tun yana ƙaraminsa to tabbas zai tashi da haushinka, Ni da ɗan uwana Wale mun kasance cikin ƙaunar junanmu sai dai ita Mamabisola sam bata son hakan bata ƙaunar shaƙuwa dake tsakanina da Wale dalilin kenan daya sanya tabar gidan mu na gado ta koma gefe, tunda Baba ya mutu Mamabisola ta ɗaura min tsana har yau na kasa fahimtar laifin dana mata sai dai bana fatan hakan ya faru dasu Hisham shida Tunde, wato rashin zumunci da gaba." "To Allah ya kyauta ya gyara lamarin, bara naje na gyara Room ɗin ka, ke kuma ki tashi ki tattara daining ɗin." Ummi tayi Maganar tana tashi ta haura Room ɗin Abba. Abba hannu yasa ya ɗauki jarida. Dafe kansa Hisham yayi sosai ransa ya ɓaci, da faɗan da iyayensa suka masa, drowa ya buɗe tare da ɗauko sigari zai kunna, Nameer daya shigo ne yayi saurin sanya hannu ya fisge karan sigarin yana cewa. "Wai da gaske bazaka daina shan sigari ba Hisham.?" Idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur Hisham ya ɗago ya kalli Nameer tare miƙa masa hannu cikin ɓacin rai da kaushin murya yace. "Bazan daina ba, miƙon Abina!." "Bazan bayar ba, ka ƙwace da ƙarfi." "Nameeeer!" "Hishammmm! Bazan bada ba, ka zauna muyi magana." Shima Nameer ya masa maganar cikin tsawa dafe kansa Hisham yayi tare da zama yana kallon Nameer, kafaɗarsa Nameer ya dafa cikin taushin murya da alamun kwantar da hankali ya ce masa. "Cool down Hisham, ka nutsu, ba komai ake ɗauka da zafi ba, ka fahimci Abba mana gaskiya yake faɗ......... "Nameer! Ya isa bana son jin komai akan wadannan mutanen, ni ba ƴan uwana bane bana ƙaunarsu Nameer, ko dasu ko babu su zan iya rayuwata, meyasa dole sai nayi mu'amala da mutanen da basa ƙaunata Abba ya kasa gane hakan, Nameer ni kai ne ɗan uwana kaine rayuwata ka ishine rayuwa a matsayin jigo, idan kana kusa dani bazan nemi agajin kowa ba, ina jinka tamkar numfashina, akwai ka ƙyaleni bana buƙatar su." "Hmmm! Hisham jigo baifi jini ba, ko ka manta da karin maganar Hausawa, jini yafi ruwa kauri, duk yadda zan kai ga ƙaunarka bazan maye gurbin jininka ba, ka yiwa Abba biyayya, dan Allah, kasan Abba bazai cutar da kai ba, ka shirya anjuma muje gidan Mamabisolan." "Nameer Meyasa zaka tursasa zuciyata yin abinda bana so, ka sani bana iya musu da kai, tamkar Yayana na gaba dani haka nake kallonka." Numfashi Nameer ya saki yace. "Na sani Hisham, shiyasa nake son kayiwa Abba biyayya, meyasa baka sanar dani zuwan Tunde Company ba.?" "Saboda nasan zaka sauraresa har ka basa aiki shiyasa ban sanar da kai ba, sannan ka sani ina kan bakata baza'a bawa Tunda Tunde aiki a Companyn mu ba, maganar zuwa gidan Mamabisolan kuma tunda ka matsa zanje." Yayi Maganar yana saka kai ya kwanta saman bed ɗin, numfashi Nameer ya saki, domin kuwa har cikin ransa baya jin daɗin yadda Hisham ke jin tsanar Mamabisola, tollet ya tashi ya shige yabar Hisham kwance. ********* Da shirinta ta fito bayan ta gamawa Umma duk wasu ayyukan ta, a baranda ta samu Umma zaune, kallonta Umma tayi tace. "Ina zuwa kika fito cikin shiri bayan yau baki da aiki weekend ne.?" Sunkuyawa tayi tare da cewa. "Umma zamuje asibiti ne mu dubo wacce na ce miki moto ya bigeta mun kaita asibiti, ni da Basmah zamuje." Kanta Umma ta girgiza tace. "Ai na manta da zancen ma shaɗaf, to Allah ya tsare hanya ina mata sannu da jiki, amma ki dawo da wuri karki juma." "To shikenan Umma." Tayi Maganar tana miƙewa ta fice a ƙofar gidan nasu ta ga Abdullahi shida ABDULWASI'U suna zaune wajen shagonsa, kanta ta kawar tare da tsayawa ganin ta tsaya yasa Abdu tashi ya nufota. "Ina zakije Adda.?" "Zanje asibiti ina fatan ka mayarwa da wannan mutumin kuɗinsa.?" "Ehh na maida masa kin bawa Umma kuɗin cefene ne.?" Dafe kanta Jidda tayi tace. "Kash kaga wallahi na manta ita kuma Umma bata tuna min ba." Tayi Maganar tana sanya hannu taja zif ɗin jakarta dubu da dari biyar ta bawa Abdu tace ya kaiwa Umma na cefene amsa Abdu yayi tare da mata a dawo lafiya kafin ya shiga cikin gidan ABDULWASI'U cike da so da ƙauna yake kallon Jidda sai dai bata basa fuskar da zai mata magana ba, tunda yace yana sonta ta daina koda gaishesa, yana kallonta Basmah ta ƙariso da mai adaidaita ta shiga suka bar wajen. "Dama nayi hasashen yanzu zaki ƙariso shiyasa ma na fito, jiya na kwana da tunanin halin da wannan yarinyar ta ke Allah dai yasa ta dawo hankalinta." Jidda tayi maganar tana duban Basmah, numfashi Basmah ta saki tare da cewa. "Ai kuwa mun kwana da damuwa ɗaya, domin nima da ita na kwana a raina." Basmah tayi Maganar cike da tausayawa Yarinyar daidai sun iso harabar asibitin IBUNKU OLU CLINIC fita sukayi Jidda ta biya kuɗin kafin suka shiga basu sha wata wahala ba suka hango Aisha ƙanwar Ahmad zaune a bakin room ɗin da aka kwantar da Yarinyar, bayan sunyi sallama Aisha ta amsa Jidda ce tace. "Aisha sannu, ya mai jikin dai, ta farfaɗo kuwa, wai ma ya kike zaune a waje."? "Jikin nata da sauƙi sosai tama farfaɗo, likita ne a ciki shiyasa na fito waje, Aunty Basmah ina wuni."? "Lafiya Aisha sannu da ƙoƙari, Allah ya saka da alheri, amma jikin babu wata matsala tana gane mutane.?" "Ba matsalar komai tana gane mutane dan sanda ta farfaɗo naji tana kiran Abioye dana tambayeta waye ita sai tace Auntyn ta ne." Girgiza kanta Basmah tayi tace. "Okay to alhamdulillah." Tayi Maganar dai-dai likita na fitowa, shiga sukayi suka sameta zaune jingine jikin gadon asibitin. "Sannu baiwar Allah, ya jiki." Sukayi maganar kusan a tare da kallon rashin sani take binsu kafin cikin raunanniyar murya ta amsa da. "Jiki da sauƙi." "Hmmm! Allah ya ƙara afuwa." Cewar Jidda kafin Basmah tace. "Baki gane mu ba ko, mune waɗanda muka kawo ki asibitin nan sanda moto ya bigeki, sannu ya jikin dai."? Kafin tayi Magana Aisha tace. "Sune suka ceci rayuwarki, sai ki gode musu." Kanta ta girgiza tare da cewa. "Na gode sosai tabbas da badan ku ba da wataƙila labarin mutuwa ake yanzu na gode ƙwarya da kuka ceceni daga hannun wannan azzalumin, da yanzu rayuwata ta lalace, wayyo! Abioye kizo ki koma dani imo state bazan iya rayuwar wannan garin ba." Tayi Maganar cikin matsanancin kuka, cike da tausayin ta, Jidda ta zauna a bakin bed ɗin cikin tausayawa ta fara rarrashinta. "Ya Isa haka ki daina kukan ba lafiya gareki ba nutsuwa da hotu kike bukata naga duk kina firgice har yanzu, waye azzalumin kin sansa ne sannan su waye iyayenki da alamu kinsan wanda ya bigeki.?" Kafin tayi Magana Basmah tayi saurin cewa. "Haba Jidda meye haka na jera mata wannan tambayoyin Yarinyar da take gadon asibiti, kwance babu ƙwarin jiki kike aikin jarida akanta, kya bari ai ta samu sauƙi a sallamata kafin ki jero mata wadannan tambayoyin." Tsuka Jidda taja tare da cewa. "Ƙanwata rabu da ita, naga jikin naki da ƙwari, wanda ya miki wannan aikin yana bukatar a hukunta sa, ki faɗa min waye ne."? Kanta Yarinyar ta girgiza idanunta na kuma zubo da hawaye tace. "A'a bazan faɗa ba idan na faɗa miki yayi alƙawarin tozarta rayuwata ta yacce zan gwammaci mutuwa fiye da rayuwa, ina tsoro shi ɗan masu ji da mulki ne a ƙasar nan." Numfashi Jidda ta saki cikin ƙunar rai tace. "Kalli ƙwayar idanuna ki gani akwai tsoron wani basarake ko mai kuɗi a cikin su, ki kalla da kyau ko akwai rashin amana da ƙwarin gwiwwa a tattare dani, ki kalla da kyau shin zaki iya yarda dani."? Idanunta Yarinyar ta saka cikin na Jidda ita dai Basmah tana tsaye tana kallon ikon Allah a wajen Jidda. "Ban hango tsoro ko rashin amana a tattare da ke ba, na yarda da kai sai dai shi ɗin hatsabibi ne zai iya cutar da Rayuwarki kema muddun kikayi ƙoƙarin taimakona." "Wai shin waye wannan ya tsorata rayuwarki haka na faɗa miki ki yarda dani babu abinda zai samu Rayuwarki sai ma ƴanci da zaki samu muddun kika bani haɗin kai ki faɗa min waye shi sannan kema menene sunanki ya........... "Jidda wai mey........... "Ya isa Basmah ki daina katseni ki barni na kai aya, na ce ki faɗa min waye wanda yaso kasheki waye wannan wanda bai san mutuncin mace ba, wani dabban ne ki faɗa min." Jidda tayi maganar cikin tafasar zuciya, a tsorace cikin rawar baki yarinyar tace. "Na....na......na... Nameer ab..dulzahir, Iyabo masu Companyn *_HISHAM RICE MILL LIMITED_* shi..shi...shi ne yaso yamin fyade NAMEER." Wani razana Jidda da Basmah sukayi lokaci guda har Aisha sanda Maganar ta soki zuciyarta Basmah ne tace. "Whatttttt! Ke Nameer Abdulzahir Iyabo kike faɗa, Iyabo dai wanda muka sani shahararren attajirin da babu kamar sa a wannan jihar tamu, shi kike faɗa, capp lallai kam babu yadda zakiyi Jidda muddun Nameer Iyabo ne babu abinda zaki iya a kansa." Tayi Maganar cikin yanayin mamaki da damuwa domin kuwa zata iya rantsuwa da Allah NAMEER bazai ɗauru ba ba kuma zai kamu ba, murmushi Jidda ta saki na takaici tace. "Yaruba Man nawawo, oh Rapping, rapping ɗinki zaiyi, Mema sunansa Nameer ko menene.?" Aisha ce tace. "Nameer, gaskiya Aunty Basmah ta ke faɗa miki Nameer hukuma ko wata ƙungiya bazasu iya kamasa ba saboda ƙarfin kuɗi da iko na Alhaji Iyabo." "Ko waye ubansa sai ya kamu domin kuwa case ɗin fyaɗe, dawamammene akan dukkan wanda ya aikata ko yayi ƙoƙarin aikatawa, komai kuɗi da ikon ubansa sai ya tozarta tunda shi ɗan Akuya ne mai dabbar zuciya." ______________________________________ Sai tambaya ta ake Ummu Nasmah littafin Free ne ko na kuɗi muna son zamuyi payment sorry sister Book One Free ne idan kin matsu sai kinyi payment Saboda kunfi bukatar silent group marar hayaniya to Ummu Nasmah tana da special group wanda zakiyi karatu cikin nutsuwa babu yawan posting ko damunku da ture turen abubuwa idan kina buƙata sai min magana 08147537180 *UMMU NASMAH CE✍🏻* *For more information 08147537180* [5/12, 7:10 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *Masha Allah JALALA FAN'S son so nake muku fisabilillah ina jin daɗin comments ɗinku* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *Free Book One* *_Page 5 to 6_* "Hmmm! Jidda ki tsaya iyakar matsayin ki, karki jawowa kanki da Mahaifiyar ki rigimar da bazaku iya ɗauka ba, Iyabo ba ƙaramin mutum bane a ƙasar nan ya wuce duk tunaninki daga Nigeria har ƙasashen duniya sunansa ya fantsama, dan haka ki riƙe mutuncin ki ki ƙyale wannan maganar." Murmushin takaici Jidda ta saki cike da jin haushin maganar Basmah tace. "Kin bani mamaki Basmah ban taɓa zaton bakya kishi da abinda ya samu mace ƴar Uwar ki ba, idan ƙanwarki aka yiwa haka zakice abar Maganar ne, na tabbata ko da mutuwa zakiyi zakice sai kin ƙwato mata ƴancinta, amma da shike ita wannan ba jininki ba ce shine kike cewa abar Maganar, wallahi bazan bar maganar ba koda zan mutu ta sanadiyyar haka sai na ƙwato mata ƴancinta, sai ya fuskanci hukunci komai gata da ikon ubansa Allah yana tare da mai gaskiya nayi imanin bazai bari na tozarta ba zai kareni, na ɗauki wannan kasadar." "Hmmm! Jidda kenan yau ni kike faɗawa baƙar magana Saboda kawai na ce miki ki kula, Jidda tunda har kika min kuskuren fahimta a tsawon zamana dake tun yarinta, shekaru ashirin da biyu muna tare ai shekara ashirin da biyu ba kwana ashirin da biyu bane, idan wani yamin abinda kika min yau bazanji haushi ba, sai dai ki sani bazan fasa faɗa miki gaskiya ba saboda ina ƙaunarki bana ƙaunar abinda zai taɓa rayuwarki, amma idan kin zaɓi rayuwa a cikin tsoro da fargaba, bazan iya hanaki tafiyar da rayuwar ki yadda kike so ba amma ki sani bazaki iya faɗa da ahalin Iyabo ba." Basmah tayi Maganar cikin ɓacin rai tana saka kai tabar room ɗin, yarinyar ce ta share hawayen ta tare da duban Jidda tace. "Gaskiya take faɗa miki bazaki iya ja dasu ba domin kuwa suna da ƙarfin da bamu da kwatansa, ni na barsu da Allah kema dan Allah kibar maganar bazan yafewa kaina ba muddun wani mummunan abu ya sameki a dalilina." "Ƙwarai kuwa gaskiya ne Aunty Basmah ta faɗa miki Aunty JIDDA dan Allah mubar wannan maganar mu barsu da Allah shine mai sakayya akan duk wanda aka zalunta dan Allah." Aisha tayi Maganar cikin sanyin jiki, shuru Jidda tayi kafin zuwa can ta dubi yarinyar tace. "Meye sunanki.?" "Hajara." Ta bata amsa a taƙaice. "Okay ki amshi wayar Aisha ki kira wani daga cikin gidan ku, bara naje na dawo." Kanta Hajara ta ɗaga kafin Jidda ta tashi ta fice, Basmah ta hau dubawa cikin asibitin babu ita babu alamunta hakanne ya tabbatarwa Jidda Basmah gida ta koma, kanta ta kaɗa tare da ficewa ta tari adaidaita tace ya Kaita police station. A bakin station ɗin mai adaidaita ya sauketa ta basa kuɗinsa kafin ta shiga ciki, First Dpo taso gani suka ƙi barinta ta gansa, hakanne yasa ta shigar da ƙarar NAMEER ABDULZAHIR IYABO, a tsorace ɗan sandan ya ɗago ya kalleta tare da cewa. "NAMEER kike tuhuma da Case ɗin fyaɗe? Bazamu amshi Case ɗin nan ba." Murmushi Jidda ta saki tare da ɗauko id card ɗin ta na aikin jarida ta nuna masa tare da cewa. "Dama nasan zaiyi wahala ku bari a shigar da ƙara a kansa, sai kamar yadda ka gani a wannan ID CARD ɗin ni ƴar jarida ce wanda mutanen wannan ƙasar suke riƙe jaridar mu a ko wacce rana dan haka muddun baku amshi wannan ƙaran ba to wallahi zakuji mummunan labari akan wannan Police station ɗin naku, yadda ko wannenki sai ya rasa aikinsa." Tayi Maganar tana ja gefe ta tsaya shuru ɗan sandan yayi a tsorace kafin ya miƙe cikin sanyin jiki ya nufi office ɗin Dpo Abbas Marafa, yayi nocking kafin dpo ya basa umarnin shiga, shiga yayi tare da sara masa. "Sargent Bala ya akayi."? "Sir wata matsala ce take shirin faruwa." "Matsala kuma Sargent Bala, ta mecece."? "Wata ƴar jarida ce ta shigo yanzu take shigar da ƙara akan NAMEER ABDULZAHIR IYABO." "Whatt! Nameer to wani laifi take zarginsa dashi."? Dpo yayi Maganar cike da mamaki domin kuwa bai taɓa jin wanda ya kawo ƙorafin ya'yan gidan ba sai yau kowa albarka yake musu da godiya saboda kyautatawarsu ga talakawa musamman NAMEER. "Sir akan Case ɗin fyaɗe ne wai ya yi ƙoƙarin yiwa wata yarinya fyaɗe yanzu haka Yarinyar wai tana gadon asibiti kwance tana jinya." Dafe kansa Dpo yayi tare da cewa. "First time da aka fara kawo case mummuna akan ahalin Iyabo, is okay ka ɗebi jami'an mu kuje asibitin ku fara tabbatar da maganar ta, idan ya tabbata to wajibine aje ayi arresting ɗin NAMEER saboda kace yarinyar ƴar jarida ce gudun ɓatawa wannan station ɗin suna da kuma kare kakin mu ya zamo wajibi mu amshi Case ɗin, kana iya tafiya." "Yes Sir." Sargent Bala yayi Maganar yana ficewa numfashi Dpo ya saki har yanzu bai daina mamaki ba. "Allah ya kyauta." Shine abinda Dpo ya furta ya cigaba da aikinsa. Ko da Sargent Bala ya fito harara ya watsawa JIDDA tare da cewa. "Ana ganin mutum Allah ya rufa masa asiri za'a fara tunanin ta yadda za'a tona masa, to ta Allah ba taku ba insha Allah sharrinku a kanku zai ƙare." Yayi Maganar yana fita ya haɗa jami'ai huɗu ya kuma leƙowa yace. "Sai kizo muje asibitin mu tabbatar da ƙaryar taki." Bakinta Jidda ta taɓe tare d da bin bayansa asibitin sukaje Sargent Bala da kansa ya yiwa Hajara tambayoyi ta kuma tabbatar da cewa lallai Nameer shine yaso mata fyaɗe, hakan yasa Sargent Bala da Jidda da sauran Police ɗin suka nufi IYABO Estate. A bakin get ɗin farko na gidan Soja suka tare su duk da ganin motar Police ne, har sai da suka nuna takaddar ijinin da aka basu, sannan suka barsu suka shige, zuwa get na biyu wanda yake ɓangaren su Nameer, mai gadi shine ya buɗe musu get ɗin suka shiga, kafin suka fito tare da bawa maigadi umarnin ya shiga ya sanar da cewa ƴan sanda suna neman NAMEER, da ganinsu alaramma mai gadi bai yarda dasu ba sai dai ba tare da tsoro ba ya nufi cikin babban falon nasu kasancewar yasan ƴan sanda sun saba zuwa neman alfarma gidan, JIDDA da kallo take bin girma da tsaruwan gidan yanda akayi asarar dukiya wajen ginasa, bakinta ta taɓe ko kaɗan gidan bai burgeta ba. A falo mai gadi ya samu Ummi da Tutu, Ummi ce ta dubi mai gadi tace. "Alaramma ya akayi akwai abinda kake bukata ne.?" "A'a Uwar gida babu abinda nake buƙata Police sukazo wai suna son ganin Oga NAMEER, sai dai Uwar gida a yanda na gansu kamar ba lafiya ba." Murmushi Ummi ta saki tace. "Meye abun damuwa saboda Police suna bukatar ganin NAMEER sun saba zuwa neman alfarma dan yauma bana rabe abinda ya kawo su kenan, ke Tutu jeki yiwa NAMEER magana yaje ya samesu." Girgiza kanta Tutu tayi cike da tsarguwa da rashin yadda tace. "No UMMI nima hankalina bai kwanta da yaya Nameer ya fita ya samesu ba gaskiya domin basu saba zuwa wajen sa, wajen Abba suke zuwa kai tsaye, dole dai akwai wata damuwar to amma wacce irin damuwa ce zaisa Police suzo neman yaya NAMEER, Ummi muje mu fara jin meya kawo su tukunna." "Ƙwarai kuwa Uwar gida gaskiya Tutu take faɗi domin kuwa naga harda wata yarinya budurwa suka shigo sai famar haɗa rai take da alamu dai babu alkairi a tare da ita." Alaramma mai gadi yayi Maganar cikin kulawa, Tutu ce tace. "To kinji Ummi muje dai mu duba kafin a kira su yaya NAMEER ɗin." "Gamu ko ba'a kira mu ba." Sukaji muryar NAMEER ya doki kunnen su gabaki ɗayansu idanu suka ɗaga suka kalle su suna sanye cikin gezna baƙa iri ɗaya sun kafa baƙar hula sosai shigar ta musu kyau tamkar ƴan biyu haka suka fito, Ummi murmushi tayi tace. "To gara da kuka zo kuwa, daru nake da wadannan rigimammun, wai Police ne sukazo nemanka, shine ƙanwarka ta ce baza'a kiraka ba sai anje anji abinda ya kawo su wai basu saba zuwa neman alfarma wajenka ba, wajen Abban ku suke zuwa, shi kuma wannan ustazun ƙaryar yace min bai yarda dasu ba wai harda wata mace suka taho, to koma dai menene ai banga abin tsoro ba, domin kuwa marassa gaskiya su ke razana ba masu gaskiya ba, kunji abinda yake faruwa." Hisham ne yace. "Zancen banza zuwan Police gidan nan kuma har wani abun mamaki ne, ƴan maula ne karnuka, ƙashi kawai suke nema da zarar an jefa musu zasu ƙara gaba, muje NAMEER bani da lokaci." Kansa NAMEER ya girgiza kafin yace. "Ƴan sanda sune ƙashin bayan al'umma Hisham sam mummunar magana akansu bai dace ba, da babu su bazaka iya tafiya kaje inda kake so cikin kwanciyar hankali ba, dan haka ka dinga faɗar magana mai kyau a kansu." "Faɗa masa dai domin kuwa naga alamar Hisham ya tsani Police da yawa, kuje ku samesu kuji abinda yake tafe dasu." Ummi tayi maganar. Bakinsa Hisham ya taɓe tare da yin gaba, bayansa NAMEER yabi yana cewa. "Muje Alaramma." Bayan NAMEER shima yabi suka fita, Tutu miƙewa tayi zata bisu Ummi ta dakatar da ita da cewa. "Ina zakije, ba aiki na sanya ki ba, maza shige kije ki cigaba da aikin dana saki.?" "Ummi ki bari naje naji tukunna sai na dawo na ƙarisa aikin." "Bazan bari ba, bana son shashancin banza ki shige kije kimin abinda na saki." Bakinta Tutu ta tura tare da shigewa kitchen. A bakin motar Police ɗin suka tsaya, Nameer ne ya dubi Sargent Bala tare da sakin murmushi yace. "Sargent Bala kaine kuma baka kirani ba, meke faruwa domin kuwa yadda na ganka dole akwai Magana kai ɗaya ka saba nemana yau kuma na ganku ku shida."? Shuru Sargent Bala yayi cike da fargaba da tsoron yadda zai sanar da NAMEER abinda ya kawo su, HISHAM ne yace. "Kai Magana ake maka ko kurma ne kawai, mtsss ko da yake ba sai kayi magana ba, neman kuɗi ya kawo ku ba." Hisham yayi Maganar yana sanya hannunsa cikin aljihu ya zaro rafar 500 ya wurga musu tare da cigaba da cewa. "Gashi sauri muke bamu da lokacin ɓatawa, muje NAMEER." Hisham yayi Maganar cikin gadara da iko gami da wulaƙanci, cikin jin zafin abinda HISHAM yayi Jidda take bin kuɗin da kallo tare da ɗago kanta ta furta. "Tirrr! Allah ya wadaran mutumin da zai wulaƙanta ɗan adam akan wasu ababen duniya, himm! Wai ɗan sanda jagoran al'umma ake wulaƙantawa ake jefa masa kuɗi saboda sun lalata mutuncin kakinsu da son abun duniya har ake musu kallon ƙasƙantattun mutane kare ake jefawa abu ba mutum ɗan Adam ba, gashi kuma kun sunkuyar da kanku kun kasa faɗa musu abinda ya kawo ku, to sunce su sauri suke basu da lokacin ɓatawa tunda ku kuma kuna da lokacin jiransu sai mu samu waje mu zauna mu jira har su dawo ko."? Jidda tayi maganar tana jefawa Hisham mungun kallo Nameer sai yanzu ya ɗago idanunsa ya kalleta, Hisham kuwa murmushi ya saki zaiyi Magana NAMEER ya ɗaga masa hannu tare da cewa. "Sargent Bala ɗago idanunka ka kalleni ka faɗa min meya kawo ku." Sai yanzu Sargent Bala ya ɗago kai tare da cewa. "Ranka ya daɗe ƙara aka shigar akanka shine Dpo ya mana umarnin muzo muyi arresting ɗinka." "Ƙara kuma aka shigar a kaina? Waye ya shigar da ƙara a kaina kuma akan me yake tuhumata.?" Sargent Bala Jidda ya nuna da yatsa tare da cewa. "Wannan itace ta shigar da ƙorafi akanka, akan Case ɗin fyaɗe, kayi haƙuri ranka ya daɗe muje office sai ka ƙarisa jin Case ɗin." Wani irin hasala HISHAM yayi tare da jefawa Jidda kallon tsana domin kuwa tun a maganganun ta na farko ya fuskanci tacacciyar marar kunya ce. "Whattttttt! Kai kasan abinda kake faɗa kuwa NAMEER ake tuhuma da Case na fyaɗe, hmmm! Da alamu ku mahaukata ne da kuka debo ƙafa kuka sako wannan Yar tashar a gaba wai kunzo kama Nameer, to bara kuji ko da NAMEER ya aikata wannan case ɗin bazai kamu ba, bare kuma ɗan uwana bazai taɓa aikata wannan ƙazamin aikin ba, mtsss nonsense! Let go NAMEER." "Hmmm! Ɗan tasha shi ke gane ɗan tasha, ashe kuwa kaine cikakken ɗan tasha tunda har ka gane ƴar tasha hmmm! Wasu dai ba mutane ba domin kuwa sam basa gane gabas bare kuma yamma." Jidda tayi maganar tana taɓe bakinta, Hisham hannu ya ɗaga zai ɗauketa da mari, Nameer yayi saurin riƙe hannunsa yana girgiza masa kai. "Nameer meyasa zaka riƙe hannuna akan wannan daƙiƙiyar jaka ƴar matsiyata, waye ita meye ta ke taƙama dashi da har zata tako ƙafarta cikin gidan nan ta taka mu, tabbas kinyi kuskuren da baki taɓa irinsa ba a rayuwar ki, tunda har kika fara tunanin taɓa ɗan uwana to ki fara ƙirga ranakun tashin hankalin ki, duk wanda ya taɓa ɗan uwana na rantse da Allah sai naga ƙarshen sa, wallahi sai na tozarta rayuwarki da ta ahalinki, daga yau kin shiga komar HISHAM ABDULZAHIR IYABO iyayenki ma kwanciyar hankali sai ta gagaresu zaki ga yadda ake tsantsar tozarci ƴar matsiyatan talakawa." ______________________________________ *Share and comment my fan's i really love You* *UMMU NASMAH CE✍🏻* *_For more information 08147537180_* [5/13, 7:10 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_JALALA FAN'S INA ƘAUNAR KU INA JIN DAƊIN SHARHINKU ALLAH DAI YABAR ƘAUNA MU CIGABA DA GASHI_* *_FREE BOOK ONE_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 7 to 8_* Murmushi Jidda tayi tare da harɗe hannunta a ƙirji tana yiwa Hisham kallon mahaukaci Nameer ne yace. "Ya isa haka Hisham, meye haka meya kawo iyaye cikin wannan maganar, iyaye suna da mahimmancin da taka su mungun haɗari ne a rayuwa, koda basu haifeka idan sun kai girman haifar kamarka to iyayenmu zamu kirasu, karna kuma jin ka zagi iyayenta, please Hisham ka dinga dannar zuciyar ka." "Da ka barsa ya cigaba da zagin domin kuwa mahaukacin kare shike haushi, Malam Hisham dan Allah karka fasa tozarta ni, idan kuma ka fasa to baka amsa sunan gidan ku ba, idan kai mahaukaci ne ni kuma likitar mahaukata ne zanyi maganin haukarka, karka fasa." Jidda tayi maganar tana jan doguwar tsuka tare da juyawa ga Sargent Bala ta cigaba da cewa. "Idan kunga dama ku kamasa idan kunso ku ƙyalesa, ni kuma bazan fasa ƙudiri na a kanku ba ku tuna da wacece ni." Tayi Maganar tana juyawa tabar wajen ba tare da ta tsaya taji me Sargent Bala zai ce ba. Wani irin hura zuciyar Hisham yake tunda yake a tarihin rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa a gabansa ya faɗa masa magana yadda ta masa cikin tsawa mai rikitarwa Hisham ya jawo kwalar Sargent Bala yace. "Waye ita! Dame ta dogara waye ya ɗaure mata gindi ƴar uban waye Minister ne ko shugaban ƙasa ko gomna ka faɗa min na rantse da Allah sai na tozarta ta sai na bambance mata tsakanin aya da tsakuwa, sai na zamo sanadiyyar lalacewar rayuwarta idan ban aikata hakan ba ni ba jinin Iyab.............. Saurin toshewa Hisham baki NAMEER yayi yana janye hannunsa daga rigar Sargent Bala, cikin taushin murya NAMEER yace. "Cool down Hisham ba komai ake ɗagawa hankali ba, kar ƙaramin abu ya tayar maka da hankali ma, kayi haƙuri ka koma ciki ni zanje station ɗin rago shike tsorata marar gaskiya kuwa gumi yake bana da matsala ko jin zafin akan Sargent Bala yazo tafiya dani aikinsa yake ka barsa yayi aikinsa kaje ka sanar da Abba abinda yake faruwa, muje Sargent Bala." "Bazai yiwu ba Nameer mutuncika ya wuce ka shiga cikin motar Police, bazai yiwu ba hakan ba mai yiwuwa bane, Sargent Bala kaje ka cewa Dpo ni Hisham nace NAMEER bazai zoba, ku fice ku bar gidan nan ko na sunce muku karnuka suyi maganinku." A ɗan tsorace Sargent Bala ya ɗago ya kalli Hisham domin kuwa yasan zai aikata duk abinda ya furta NAMEER ne yace. "Sargent Bala kuje zanzo a motar gida ɗan uwana baya son na shiga motarku bazan shiga ba amma zanzo karka sanar da Dpo sakonsa domin kuwa baku da laifi aikinku kuke kuje." Kansa Sargent Bala ya ɗaga tare da bawa sauran Police ɗin umarnin su tafi, NAMEER kallon Hisham yayi tare da cewa. "Baka cika bibiyar jarida bane shiyasa baka santa ba, tabbas zata iya ɓatawa station ɗin su suna muddun basuyi abinda tace ba, ba ƴar kowa bace face ƴar Jaridar Aminci mataimakiyar shugaban Aminci na santa domin kuwa na juma ina son na kai mata ziyara sai dai kuma gashi ita ta riga kawo min, naji daɗin hakan sosai." Cike da rashin fahimta Hisham yace. "So whatt! Idan ƴar Jaridar ce, tukunna ma ya akayi kasan wani abu a kanta kana da alaƙa da ita ne.?" "Hmmm! Yanzu ba lokacin tambaya bane Hisham, ka koma ciki ka sanar da Abba abinda ke faruwa ni zanje station ɗin sannan karka fasa zuwa gidan Mamabisola kamar yadda muka shirya dan Allah kaje." "Ta yaya zan Barka ka shiga cikin station kai ɗaya sam bazan iya barinka ba tunda ka dage sai kaje sai dai mu tafi tare babu gidan Mamabisolan da zanje muje kawai." "Bazamu tafi ba tare da ummi tasan abinda ke faruwa ba, kaje ka sanar da ita ta yadda zata fahimta ka tabbatar hankalinta bai tashi ba." Kansa Hisham ya girgiza tare da juyawa cikin gidan cikin wani irin mungun yanayi, yana shigewa NAMEER ya buɗe mota da sauri sauri ya shiga tare da jan motar ya fice. Falon ya koma cikin sanyin jiki tare da zama gefen Ummi, Ummi cike da mamaki take dubansa tare da cewa. "Lafiya Hisham ka shigo haka cikin wani irin yanayi, ina shi NAMEER ɗin yake, kun fasa zuwa gidan Mamabisolan ne.?" Ummi ta jefa masa tambayar daidai Tutu na shigowa falon ta zauna gefen su. "Tambaya uku Ummi kika min ajere sai dai kafin na baki amsar ki, ina da bukatar wata amsa daga gareki, Ummi meyasa ya sanda basu da amana meyasa basu san mai basu ba, Ummi shin dama muna da maƙiya ne wadanda zasu iya mana mungun ƙazafi, ana niyyar tozarta min ɗan uwana! Kuma wallahi bazan bar hakan ba sai na sanya duk mai hannu cikin wulaƙanta min ɗan uwana cikin JALALAR da bazasu taɓa iya fita ba, wannan yarinyar da ta samu zarrar kai ƙarar ɗan uwana Police station da mungun ƙazafi harma ta tako cikin gidan nan take faɗa min Magana son ranta Hmm Ummi! Sai na hana rayuwarta bacci a yayin da ni zanyi bacci a cikin zuciyarta, na rantse da Allah sai tayi danasanin taɓo ni, ta tsokono rigimar da bazata iya ba, wuta ce wacce zata babbakata ta ɗauko bazan taɓa ƙyaleta ba." Tunda ya fara Maganar Ummi take kallonsa cikin rashin fahimta da tashin hankali, tafi kowa sanin ɗanta mutum ne mai zafin zuciya da saurin fushi, bai cika yafiya ba, ba kuma a dannarsa ya dannu numfashi Ummi ta saki cikin yanayin damuwa tace. "Hisham yanayin maganganun ka da yadda ka hasala ya ɗaga min hankali domin kuwa hakan na gwada min cewa ƴan sandan da sukazo sun tafi da NAMEER, hmmm! Wani laifi NAMEER ya aikata wanda har zai kai Police su zo su tafi dashi, NAMEER ɗane mafi soyuwa a cikin zuciyata bazan taɓa bari wani mummunan abu ya samesa ba, rayuwata ne shi, bazan bar wani abu ya samesa ba, dan haka sanar dani wani laifi ake zarginsa dashi, nasan sharrin magauta ne domin kuwa kaf ƴaƴana babu mai jawo rigimar da zata tada hankalin mu." "Yaya Hisham meya faru da Yaya Nameer dama ni hankalina bai kwanta da zuwan wadannan Police ɗin ba, yanzu ina yaya Nameer ɗin." "Me yake faruwa ina daga sama ina jiyo hayaniyar ku, Hisham me nace maka ɗazu ba cewa nayi ka shirya kaje ka gaishe da Mamabisola ba ina shi NAMEER ɗin yake."? Suka jiyo Muryar Abba daga saman step yana tsaye, numfashi Hisham ya sauƙe tare da ɗaga kansa yace. "Abba ƴan sanda sun kama NAMEER wai suna zarginsa da Case ɗin fyaɗe." "Whattttttt!" Abba ya furta da ƙarfi Ummi wani irin sarawa kanta yayi itama tace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Nameer ɗin nawa shine aka yiwa wannan ƙazafin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga Uku, Abban Hisham Case ɗin fyaɗe fa babban Case ne." "Ƙwarai kuwa babban Case ne, hmm! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Bana tunanin cewa NAMEER zai aikata wannan laifin, Case ɗin fyaɗe." Abba yayi Maganar cikin tashin hankali, yana sauƙowa tsakiyar falon, Hisham runtse idanunsa yayi kafin yace. "Abba ka kira a sakar min ɗan uwana, wannan yarinyar da ta masa ƙazafi wallahi Abba bazan ƙyaleta ba." Zama Abba yayi yana kallon Ummi da hankalinta yayi mungun tashi har gumi take haɗawa ya cewa Hisham. "Wacce yarinya ce takai Case ɗin.?" "Abba wata ce naji ma suna cewa ƴar Jarida ce, har ikirari take cewa muddun Police ɗin basu amshi Case ɗin ba sai ta yi sanadiyar aikinsu, na rasa gane wacece ita da me take taƙama ƴar uban waye, kuma kamar tsoronta Police ɗin sukeji, ni dai Abba ka sanya a sako min ɗan uwana." Numfashi Abba ya saki yace. "Bazai yiwu ba Hisham, a yanzu bani da ikon sanyawa a saki Nameer Case ɗin fyaɗe babban Case ne da duk gatanka baza'a iya fitar da kai ba, idan naje na ce a saki NAMEER tamkar na zubar da mutuncin gidan nan ne domin kuwa duniya ɗauka zatayi ɗana yayi laifi nayi amfani da ƙarfi da dukiyata na sanya an sakesa bare kuma Case da ƴan jarida aciki dan haka mu ƙyale Nameer gaskiyar sa ta fitar dashi." A wani irin zabure Ummi ta miƙe tare da cewa. "Me kake nufi Abban Hisham! Kana nufin mu bar Nameer ya tozarta a ɓata masa suna ƙarshe ya ƙare rayuwarsa a gidan yari bayan kana da hanyoyin da zaka saka a sakesa, meyasa zamu barsa a wulaƙance, ko dan saboda ba ɗanka na cikinka HISHAM aka kama ba, ina ƙaunar Nameer fiye da yadda nake jin Hisham a cikin raina ji nake tamkar ni na shayar dashi nono bazan taɓa bari ya tozarta ba, Abban Hisham ya zamo wajibi a kanka ka sanya a sako min ɗana." Abba kallonta kawai yake tare da miƙewa shima yace. "Hmmm! Mata kenan duk girman ku, hankalin ku kaɗan sam baku da dogon lissafi a tunaninki kin fini son Nameer ne, ko da kaso ɗaya a cikin goma na Soyayyar Nameer da nakeji a raina baki ɗauki ɗaya ba, domin kuwa Soyayyar da nake masa yasa na sanya wasiyyar koda bayan raina ne a raba dukiyata biyu a bawa NAMEER kaso ɗaya sauran kaso ɗaya kuma iyalina suyi tarayya a kai ki faɗa min idan ba Soyayya ba me zaisa nayi haka, shin yanzu kina jin kin fini sonsa ne, ki faɗa min."? Bakinta Ummi ta toshe tare da silalewa ƙasa ta zauna tana sakin wani irin kuka mai cin rai Hisham kuwa zuciyarsa tafasa take, cikin wani irin yanayi na damuwa ya dubi Abba. "Abba kana nufin bazaka sanya a saki ɗan uwana ba, ina bazai yiwu ba Abba ka sake tunani ya zamo dole ɗan uwana ya kwana a gida yau zanje Police station ɗin kafin fito ya zamo wajibi a kanka mu dawo tare da Nameer, ki daina kuka Ummi bazan taɓa bari NAMEER ya wulaƙanta ba zanyi duk yadda zanyi ya fito ko da kuwa babu ƙarfin Abba." Yayi Maganar yana saka kai zai bar wajen Abba ne ya kira Sunansa. "Kai Hisham ka dakata karkaje ka aikata wani kuskuren." Juyowa HISHAM yayi a fusace tare da cewa. "Kuskure! Hmmm! Domin gyara wani kuskuren dole sai an tafka wani kuskuren, tunda baka da karfin dawo da Nameer ni zan nemo wannan ƙarfin." Yayi Maganar tare da ficewa Abba na kiransa ko sake waiwayowa baiyi ba, Tutu share hawayen fuskarta tayi tare da miƙewa ta haura sama. Hisham yana fita Police station ɗin ya nufa abun baƙin ciki da takaici Nameer ya iske a cell yana zaune tamkar wani marar galihu idanunsa ya runtse cike da baƙin ciki, wajen Sargent Bala ya nufa tare da tsayawa a gabansa yace. "Sargent Bala waye ita meye sunanta ka bani bayani akanta har adress ɗin ta ina bukata." Yayi Maganar yana watsawa Sargent Bala kuɗi, kuɗin Sargent Bala ya ɗauka tare da ɗago kai ya dubi Hisham. "Jidda Muhammad Bello, cikakkiyar ƴar Jarida, ƴar unguwar ORA layin igbaja gida mai number 234." Numfashi Hisham ya saki tare da kuma cewa. "Ina Dpo ina son magana dashi." "Dpo yana ciki zaka iya shiga." Kansa Hisham ya kaɗa tare da shigewa nocking yayi kafin Dpo ya basa izinin shigowa. Shiga Hisham yayi tare da tsayuwa ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa Dpo dubansa yayi cike da mutuntawa yace. "Hisham Barka da zuwa Bismillah ka zauna mana." Kujerar Hisham ya duba tare da takowa ya zauna yana cewa. "Barka Dpo kayi mamakin ganina ba." "A'a banyi mamaki ba duba da ɗan uwanka yana station ɗin nan, nasan dole zakazo sai dai bansan da wata bukatar ka shigo office ɗina ba.?" "Ka san bukatar da ta shigo dani, belin NAMEER nake bukatar ka bani, duk da kunyi kuskuren ijiyesa a inda yafi ƙarfin zama." "Sorry Hisham da ace zamu iya bada belin NAMEER to da bazamu je mu kamasa ba, kayi haƙuri bamu da damar sakin NAMEER har sai bincike ya tabbatar cewa bashi da laifin da ake zargin sa, saboda Case ɗin sa mai girma ne." Cike da mamaki Hisham ke kallon Dpo tare da cewa. "Whatt! Dpo kasan abinda kake faɗa min kuwa, Dpo wannan itace kawai alfarmar da zaka mana a rayuwa karka manta Matsayin da kake kai yanzu silar arzikin mu ne, sannan ka saka a ranka muddun NAMEER ya fito zaka haura wannan matsayin, well idan ma bazaka iya kyauta ba, ka faɗi farashin ni zan biya ko nawa kake bukata, koma ya za'ayi NAMEER ya fita daga wannan kurkukun da kuka jefasa." Murmushi Dpo yayi yace. "Ka kasa fahimta ta Hisham, tabbas kun min rana domin kuwa ko wani irin matsayi na kai kune sila sai sakin NAMEER kan iya jawowa na rasa aikina gabaki ɗaya, karka manta Case ɗin fyaɗe ake tuhumar sa dashi wanda gata da faɗa aji gami da dukiyarka bazasu taɓa ƙwatarka ba, da fito da NAMEER zai yiwu to da mahaifinku shine mutumin da zai fara kirana, naso ace ina da halin taimakawa NAMEER da sai na fi kowa farin ciki.'' "Hmm! Okay na fahimta idan kai bazaka iya ba akwai na gaba da kai, sai dai ka sani ka yiwa kanka babbar asara." Hisham yayi Maganar yana tashi tare da ɗaukar wayarsa ya fice numfashi Dpo ya saki tare da bin ƙofar da kallo ya furta. "Ikonku da kuɗinku bazai taɓa fitar da NAMEER ba sai dai gaskiya da tsantsar bincike ya fitarsa, kana da matsala Hisham zafin rai gami da izza sun maka yawa uwa ba ƙasƙantar da Mutum." Dpo yayi Maganar yana mai da kansa ga aikin sa. Ko da Hisham ya fito bakin cell ɗin ya tsaya cikin ɓacin rai murmushi Nameer ya saki tare da cewa. "Wai damuwar me kake ne Hisham, akan wannan ƙaramin lamarin kake damuwa.?" "Ƙaramin lamari wannan kake ƙaramin lamari, wankin hula na shirin kaimu ga dare amma kana kiransa ƙaramin lamari, Hmm! Gaskiya ko waye ya shirya wannan tarkon yayi dogon lissafi akanmu, ina zuwa." Hisham yayi Maganar yana juyawa zai bar wajen, yaji muryar NAMEER. "Ina Ummi da Abba ina fatan hankalin su bai tashi ba." "Hmmm! Kaima kasan dole hankalinsu zai tashi." Yayi Maganar yana saka kai ya fice daga Police station ɗin motarsa ya shiga yaja karfi babu inda ya nufi sara Ora cikin mintuna kaɗan ya samu damar shiga unguwar baisha wahala ba wajen gane layin igbaja, kasancewar yasan wajen, parking yayi a ƙofar gida mai 234 tare da harɗe hannunwansa. ********* A tsugunne taga Basmah gaban Umma cikin sanyin jiki ta ƙarisa domin kuwa tasan duk yadda akayi Basmah ƙarar ta ta kawo, ƙarisawa tayi tare da zama gefe tana cewa. "Umma sannu da hutawa." A hasale Umma tace. "Sannun gidan ubanki, nace sannun gidan ubanki, Jidda ashe dama mahaukaciya ce ke ban sani ba, so kike ni ki kasheni ki raya iyayen wasu, ina kiranki da sunan Alkairi kullum sai kuma gashi kina niyyar Kawo min masifa ina ke ina faɗa da ahalin Abdulzahir Hmm! Tabbas cikakkiyar mahaukaciya ce ke Jidda." Idanunta Jidda ta runtse tare da jin haushin Basmah cikin sanyin murya tace. "Umma mahaukaciya kuma, kenan Umma saboda su masu kuɗi ne shine sai mu bari su zalunci talakawa muyi shuru Umma kefa kikace na taimaki duk wanda na gani yana bukatar taimako, muddun ina da halin taimaka masa meyasa zan gani nayi shuru bayan zan iya bata gudunmawa Umm........ "Ki rufe min baki dan ubanki! Da nace ki taimaki al'umma cewa nayi kisa Rayuwarki a cikin haɗari, ita yarinyar bata da iyayene da zasu kai ƙara sai ke gwali, duk masifar da muka shiga a baya bai isa haka ba Jidda har sai kin ƙara ɗauko min wata masifar so kike bakin ciki ya kasheni da badan wannan Yarinyar Yar albarka Basmah tazo ta sanar dani ba da shikenan sai ki jawo mana masifa, to muddun ni ce uwarki, ki cire hannunki a cikin wannan Case ɗin." Kanta ta sunkuyar ƙasa tana sauraren faɗan mahaifiyarta kafin ta ɗago tace. "Kiyi haƙuri Umma." "Ba haƙurinki nake son ji ba, ki fita daga cikin wannan faɗan da babu ruwanki tashi ki bani waje." Umma tayi Maganar tana tashi ta shige ciki, ɗago idanunta tayi ta kalli Basmah tare da girgiza kai zatayi Magana sukaji muryar yaro. "Assalamu alaikum wai inji wani a waje Jidda ƴar tasha tazo ko shi ya shigo da kansa." "Jidda ƴar tasha! To fa a gidan nan kuwa.?" Jidda tayi maganar cike da mamaki, Basmah ce ta taɓe bakinta tare da cewa yaron. "Jeka tana zuwa." "Yaje ina zuwa zakice bakiji sunan daya ambata ba Jidda ƴar tasha, gani nayi gidan nan babu ƴar tasha." Shidai yaron bai tsaya ba yayi ficewar sa, Basmah cewa tayi. "Idan har lissafina dai-dai ne kinje gidan Iyabo idan har kinje Kuma an kama NAMEER to babu shakka Hisham ne yazo ƙofar gidan nan kuma ya aiko a kiraki da Jidda ƴar tasha." Zaro idanunta Jidda tayi tare da furta. "Hisham! Kuma a gidan mu.?" _________________________________________ Share and comment my fan's🥰 *_For more information 08147537180_* [5/14, 8:40 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE* *_PAGE 9 to 10_* "Yess HISHAM kinyi mamaki ne.?" "Ƙwarai to me zai kawosa ƙofar gidan mu it means ma a ina yasan gidan mu waya gwada masa."? "Hmmm tambayar rainin hankali, ke ta yaya kika san gidan su, sannan kinfi kowa sanin abinda ya kawosa." "Wai ke Basmah meyasa bakya gane Annabi ya faku ne, haba dalla sanin gidan su ai ba ɓoyayyen abu bane saboda mahaifinsa mutum ne wanda ya sanu a ƙasar nan." Numfashi Basmah ta saki tare da cewa. "Haka zalika kema a matsayinki ta babbar ƴar jaridar Aminci gidanku bazai ɓuya ba kinga kuwa kunyi ɗaya yana da kyau ki daina wannan zancen banzan ki fita kiji da me yazo kafin ya shigo ya ɗagawa Umma hankali dan kin san zai aikata." "Mtsss! Zan fita kuwa na koya masa hankali yacce bazai ƙara tunanin kallon ƙofar gidan nan ba tunda mahaukaci ne shi." "Ke kin kirasa mahaukaci ke kuma Umma ta kiraki mahaukaciya to bari muga ke dashi waye mai asalin cutar haukar amma dai ki kula gudun faɗawa ramin da bazaki iya fita ba, munje ni na shige gida." Harara Jidda ta watsawa Basmah tace. "Wallahi babu ramin da zan faɗa ban fito ba, shi dai wannan ƙaramin tsageran bai isa jefani wani rami ba, ke ko da kuwa da kuskure na faɗa wallahi sai nayi tsalle na fito, ki kuma saka ido kiga yadda zan koyawa rayuwarsa hankali." Taɓe bakinta Basmah tayi tace. "We'll idan ke baki koya masa ba shi ai zai koya miki." "Mungun bakinki ya biki Basmah naga alamar kamar kina ɗaure masa gindi ne." "Oho koma dai mai zaki faɗa bazai dameni ba." Basmah tayi Maganar tana ficewa bayanta Jidda tabi a fusace. Yana tsaye jikin mota idanunsa manne da glass ya harɗe hannunsa, Basmah gefe ta tsaya tana jiran fitowar Jidda babu jumawa kuwa ta fito ko inda Basmah take Jidda bata kalla ba ta nufi Hisham tare da tsayawa a gabansa tace. "Ban taɓa ganin Mutum marar daraja ɗan adam ba irinka me kazo yi ƙofar gidan mu."? Bakinsa Hisham ya taɓe tare da ɗaga ido ya kalli gidan kafin yace. "Ina gidan yake wannan kangon kike kira da gida hmm! Ko da yake zaki kirasa gida saboda tsoho bai mutu yabar komai ba, wannan ɗin ma hayace zaman notice." A fusace Jidda tace. "Ya isheka haka Malam duk abinda zaka faɗa min ka tsaya iya kaina karka kuma sako iyayena ciki, domin kuwa naga kai rayuwa kake irin ta dabbobi." Ɗan murmushi Hisham yayi tare da sanya hannu ya shafa gashin kansa kafin yace. "Rayuwa irin ta dabbobi, Hmm! Shi yasa nazo na gwada miki halin dabbobin, ba dai ke ƴar tasha bace har kina da zarrar sawa a kama ɗan uwana yanzu zaki shiga masifar da zaki kasa fita a cikin sa, ba dai kin sokeni a ƙirji ba, to ni idan nazo sokarki ba iya ƙirji zan tsaya ba sai na huda har cikin zuciyarki za kiga yadda ake tashin hankali." "Barazana kazo kamin ne naji tsoro naje na sanya a saki wannan ƙaton dabban da baisan darajar Mace ba." Dariya sosai Hisham yayi kafin yace. "Hisham baya bazarana aikinsa kawai yake aiwatarwa sai dai dama sharaɗina ne kafin a fara yaƙi dole sai na faɗi abinda zai biyo baya, domin kuwa da zarar an fara yaƙin da kanki zaki fara neman sanin me zai faru gobe, we'll ki fara tunanin gobenki domin kuwa zaki shiga baƙar cakwakiya ki fara nazarin rayuwarki inma ki mutu domin rayuwar ahalinki inma ki rayu cikin baƙin ciki da takaicin rayuwa." Cikin hasala Jidda tace. "Me kake nufi da maganganun ka me zaka yiwa ahalina, rayuwata ne su taɓa su tamkar taɓa rayuwata ne, ka ciresu cikin wannan faɗan domin basu san komai ba, tsakanina da kaine mu kashe kanmu mu biyu." "Rayuwarki ne su, ni kuma nawa ahalin da kika saka cikin tashin hankali ba rayuwata bane, Hmm! Lokaci shine zai gwada miki abinda nake nufi ki ijiye a ranki NAMEER dole zai dawo gida inma yau inma gobe koma jibi, tabbas zai dawo daga ranar kuma da kikaji labarin an sakesa to daga wannan ranar lokacin fargaba da tashin hankalin ki zai fara bazan ƙara waiwayowa kanki ba har sai NAMEER ya dawo gida." Yayi Maganar yana sakin murmushi tare da shigesa cikin mota yaja da ƙarfi yabar wajen da kallo Jidda ta bisa cikin ƙunar rai ta furta. "Banza Dabba sai muga ta yadda NAMEER ɗin zai fito." "Hmmm! Ni kam na wuce gida Allah ya tsayar haka." Basmah tayi Maganar tana kallon Jidda, hararar Basmah Jidda tayi tare da shigewa ciki. ********** "Wai dariyar me kikeyi ne Wamimo.?" Gyara zamanta Wamimo tayi tana kuma sakin dariya tace. "Hmmm! Mamabisola ai dole nayi dariya wannan abun farin ciki da ya samemu, Hmm! Ɗan riƙon dai ankamasa yana can hannun shegun a rufe." "Waye kenan Wamimo ban gane wanda kike faɗi ba."? Mamabisola tayi Maganar cike da rashin fahimta, Wamimo dubanta tayi tare da cewa. "Au wai har kin manta, yaron da ɗanku Iyabo ya ke riƙe dashi mana Nemeer shi nake nufi." "Whatt! Wamimo da gaske kike yana Police station, kar dai tarkon mu ya kama kurciya."? Dariya Wamimo tayi tace. "Ƙwarai kuwa muɗin na wasa ne an faɗa miki ke dai kawai zuba ido kiga yadda wasan zai kaya." Dariya Mamabisola ta saki tare da cewa. "Kinga Wamimo tashi ki rakani gidan Iyabo ai dole muje mu masa jaje da kuma bugan ciki, ga mayafina kusa muje." Tayi Maganar tana ɗaukar mayafin Wamimo ma tashi tayi suka fice tare. ********* Zaune yake yayi shuru yana mamakin wannan ƙazafin da aka ƙulla masa a iya saninsa bashi da abokin gabar da zai masa wannan mungun ƙazafin, numfashi ya saki tare da dafe kansa yana kallon ruwan dake gefensa, tsayawa tayi jikin cell cike da tashin hankali idanunta na zubar da hawaye tace. "Yaya NAMEER yanzu kaine a nan ƙasƙantaccen wajen, wai me yake faruwa ne yaya Nameer na kasa fahimtar komai waye zai maka wannan ƙazafin, rayuwata ne kai bazan iya juran ganinka cikin matsala ba."? Murmushi Nameer yayi yana zuba mata idanu kafin ya miƙe tsaye ya taho jikin cell ɗin. "Bani da maƙiyi dan haka bana zargin kowa, bansan dalilin da yasa nazo wajen nan ba, sai dai na ɗauki hakan a matsayin jarabawa ce Ubangiji ya ɗauro min, a matsayina kuma na musulmi dole nayi imani da ƙaddara,Tutu ina da gaskiya dan haka bana tsoron wajen nan ina da yaƙinin gaskiya ta zata fitar dani, na sani kina jin zafin acikin zuciyarki amma kiyi haƙuri ki danne damuwarki insha Allah komai zai wuce, me Abba yace sanda yaji Maganar.?" "Yaya Nameer meyasa sai lokacin da yazo daf zaka sanar da Abba Soyayyar mu za'a katse mana numfashi, yaya Nameer ina son kowa ya sheda Soyayyar mu, amma hakan ta kasa faruwa ko yaushe mukayi yunkurin hakan sai matsala ta shigo tsakani, mtsss! Ko yaya Hisham kaƙi bari yasan Soyayyar dake tsakanin mu sai rufaffiyar Soyayya muke wanda bata da alƙibila ina cikin tashin hankali." Tayi Maganar cikin kuka mai cin rai bakinsa Nameer ya cije tare da cewa. "Tutu tambayar da na miki baki bani amsar ta ba, kin tsaya kina min tambayar da zata ɗaga min hankali a halin da nake ciki yanzu bai kamata ace kina min magana akan goben Soyayyar mu ba, kamata yayi ki mai da hankali wajen ganin ta yaya zan fita daga wannan masifar, kin san ina sonki kuma bazan taɓa juyawa Soyayyar ki baya ba, ko kina shakku akan soyayyata ne ko baki yarda dani bane.?" "A'a Yaya Nameer na yarda da kai yarda marar misaltuwa, Kawai ina jin zafin matsalolin da ke shan gaban Soyayyar mu ne, amma na fahimta kayi haƙuri zanyi ƙoƙari naga duk yadda za'ayi ka fita, Abba shima yana can cikin tunani da nazarin mafita kuma nasan yaya Hisham bazai barka cikin wannan halin ba dole zai fitar da kai daga nan ko da babu hannun Abba, Ummi ma tace ka kwantar da hankalinka komai zai daidaita." "Hmmm! Ba komai Tutu ki koma gida idan kin koma ki sanar da Ummi cewa karta ɗaga hankalinta ina nan lafiya kuma insha Allah zan fito." "Shikenan ka kula min da kanka." Kansa Nameer ya kaɗa kafin Tutu ta juya ta bar wajen, bata juma da fita ba Dpo ya fito, cell ɗin aka buɗe masa ya shiga tare da zama Nameer dubansa yayi tare da sakin murmushi. "Nameer Abdulzahir Iyabo, har ga Allah banji daɗin zamanka a inda kafi ƙarfin zama ba dole ta kama babu yadda na iya." Murmushi Nameer yayi tare da cewa. "Karka damu a sake na ke ban takura ba, kasan ai ko wani ɗan adam komai gatansa ƙarshen mutuwa ce, yaje yayi rayuwa a ƙarƙashin ƙasa inda ba tabarma bare filo, ina tunawa da wannan kullum shiyasa bana jin wata damuwa dangane da zamana a nan Malam Dpo." "Hakane kayi daban da ɗan uwanka, kai mutumin kirki ne." "Ɗan uwana ma mutumin kirki ne fahimtar sa ne kawai bakuyi ba, jeka kai tsaye kan abinda ya shigo da kai nan ka ijiye maganar ɗan uwana a gefe." "Hmmm! Okay we'll, Meyasa ka aikatawa yarinya fyaɗe shin baka san illar hakan bane laifi ne da zai iya kaika kurkuku na tsawon shekaru.?" Dariya Nameer yayi tare da cewa. "Bansan wannan maganar ba, wataƙila wani mai suna Nameer ɗin kuke nema amma wannan Nameer ɗin yasan darajar mace ba zai aikata abinda kuke zarginsa dashi ba meye hujjar ku daya tabbatar cewa ni ne mai laifin.?" "Ba'a yiwa Police tambaya cikin tambaya Malam Nameer, ka bani amsar tambayata." "Hmmm! Ikon Allah na amsa maka tambayarka kafin jefo tawa tambayar ko a ruɗe kake ne, Malam Dpo kasancewata anan bashi zai baka damar min tsawa ba, karka manta halacci." "Hakane bazan manta halacci ba, sai a bangaren bawa ƙasata gudummawa to bazan ɗagawa kowa ƙafa ba, har yanzu bamu gama tabbatar da hujja akanka ba shiyasa ma muka ijiyeka cikin kulawa babu horo." "Okay kuje ku cigaba da binciken idan har kun tabbatar ni ne criminal ɗin is okay ku karya ƙasussuwana karku raga min sai dai fa Malam Dpo idan ya tabbata Nameer bashi da laifi ɗan uwana bazai taɓa ɗaga muku ƙafa ba sai dai idan ni ne na dakatar dashi." Nameer yayi Maganar yana sakin murmushi shima Dpo murmushin yayi kafin yace. "Shikenan hakanma yamin." Shima yayi Maganar yana tashi ya fice daga cell ɗin Sargent Dogo yazo ya kulle. ************ Tun daga get ɗin gidan ake bawa Mamabisola girmamawa har ta iso get ɗin da zai sadata da part ɗin Iyabo, kallon Wamimo tayi tace. "Munzo ki nutsu domin muna bukatar makamin da zamu kuma hurawa Case ɗin wuta kin fahimta.?" "Na fahimta kuma zan baki mamaki." Murmushi tayi sannan suka shige part ɗin, sallama sukayi Ummi dake zaune tayi tagumi tana share hawaye jefi jefi Abba na gefenta shima yayi shuru Ummi ta amsa sallamar ƙarisowa sukayi Abba na ganin Mamabisola ya miƙe cikin girmamawa. "Mama sannu da zuwa." Ummi tayi Maganar tana zamewa ƙasa ta zauna kasancewar al'adar su ce idan babba na zaune a sama su suyi ƙasa, murmushi Abba yayi tare da zama gefen ƙafar Mamabisola cikin girmamawa yace. "Sannu da zuwa Mama kece tafe ai da kirana kikayi nazo da baki wahala wajen zuwa ba." "Babu komai Iyabo, zuwan ai dole ta kama yanzu ina zaune nake jin maganar da ta ɗaga min hankali shiyasa nace banci ta zama ba, dole nazo naji gaskiyar zancen, wai yaron nan da kake riko yayi laifin fyaɗe an kamasa.?" Numfashi Abba ya saki tare da jin ƙunar rai wato ma har maganar ta fara zagayawa gari kansa ya girgiza tare da cewa. "Ehh Mama da gaske yana hannun hukuma sai dai NAMEER bazai aikata wannan laifin ba, ina tunanin sharri ne kawai amma insha za'a san yadda za'ayi a wankesa mai gaskiya baya taɓa faɗuwa ƙasa Mama." "Hmm ni kaina nayi mamaki ace yaro mai hankali da nutsuwa ya aikata wannan mungun aikin, to Allah ya fidda sa, amma dai......... Sallamar Hisham itace ta dakatar dasu daga maganar, shi kansa bai kula da Mamabisola ba sai da ya shigo tsakiyar falon Sannan ya ganta idanunsa ya runtse muryar sa a dakile ya risina tare da cewa. "Ina yinin ku." "Da bami wuni ba zaka ganmu dan ƙwal ubanka, dama ai nace zamu haɗu ne komai daɗewa, idan arziki bai haɗamu ba tsiya ta haɗa mu, wato shine Tunde zaije Company neman aiki kasa a koresa kamar kare kai ga isasshe mai gadara da Companyn ubanka ko? Tunde dai ɗan uwanka ne babu abinda zai goge hakan ka fifita bare sama dashi, ina magana kana wani haɗe fuska kamar wanda na kashe maka uwa, to bara kaji wallahi ka gyara wannan shegen baƙin halin naka." Ransa Hisham ya haɗa tare da kawar da kansa gefe yaƙi tanka mata ganin yayi shuru ne Mamabisola ta cigaba da cewa. "Ina magana kamin shuru ka maisheni mahaukaciya." Miƙewa Hisham yayi tare da cewa. "Bani da amsar da zan tanka miki, ƙorafin da kika kawo wajen Abban bai isa ba sai kin biyoni har gida Tunde bai cancanci zama ɗaya daga cikin ma'aikatan mu ba, saboda mu muna ɗaukar masu ƙwazo ne da hazaƙa kuma masu riƙon amana Tunde bashi da ɗaya a cikin wadannan idan kin manta bara na tuna miki, Tunde sata yayi a Companyn da ya baro na makudan kudade, dan haka bama bukatar barawo a Companyn mu." Yayi Maganar cikin izza tare da saka kai yabar wajen, Mamabisola wani irin ɓacin rai taji wanda ya sanya har tayi danasanin zuwa domin kuwa da tasan zatazo HISHAM ya faɗa mata magana tabbas da batazo ba, Abba ne ya nisa tare da cewa. "Kiyi haƙuri Mama jikan naki ne na rasa yaya zanyi da zafin kansa kullum cikin faɗa nake masa amma tamkar wanda nake ƙara tunzura sa, kiyi haƙuri dan Allah, mun gama magana da Nameer cewa Monday za'a ɗauki Tunde a Company, to sai wannan jarabawar ta shigo amma insha Allah idan komai ya daidaita Tunde zai kawo takaddunsa a basa aiki a gurbin da ya kamata kiyi haƙuri dan Allah Mama." ''Hmm! Ba komai Iyabo ni kaina nasan halin Hisham, karka damu yanzu a wacce matsaya ake wani ƙoƙari kake wajen ganin yaron nan Nameer ya kubuta."? "Ehh gaskiya har yanzu banyi wani yunkuri ba domin kuwa bani da ƙwarin gwiwwar da zan fara tunkarar matsalar Saboda Case ne mai girman gaske, amma insha nasan dole Hisham zai samo evidence da zamu iya kare sa, insha Allah zuwa anjuma zan kirasa sai muji abinda ya samo insha Allah duk abinda ake ciki zan sanar dake." "Duk dai yadda za'ayi ka tabbatar ya kubuta domin kuwa yaron kirki ne mai amana, sannan karka yanke hukunci ba tare da ka sanar min ba." Murmushi Abba yayi tare da cewa. "INSHA ALLAH babu abinda zanyi ba tare da saninki ba kece uwata a yanzu ya zamo wajibi nabi umarnin ki." "Hakane Iyabo shiyasa nake alfahari da kai domin kuwa kaine gatana a yanzu, sannan ka jawa Hisham kunne ya kiyayi faɗa min duk maganar da tazo bakinsa sannan ka tambayesa wani irin laifi muka aikata masa daya tsanemu haka, mu zamu koma." Kafin Abba yayi Magana Ummi tace. "Babu abinda kuka masa Mama kawai tsiya ce irin tasa insha Allah zan masa magana bazai kuma mayar miki da martani ba kiyi haƙuri." Bakinta Mamabisola ta taɓe tare da cewa. "Nayi hakuri Hmm! Ramata ina da yaƙinin cewa kece kike kitsawa Hisham duk abinda yake min domin kuwa kema ba ƙaunar uban Tunde kike ba ko an faɗa miki ban gane take takenki ba ne." Ɗan zaro idanunta Ummi tayi zatayi Magana Abba yayi saurin katseta tare da cewa. "Karkice komai ki shige sama." Kanta Ummi ta kaɗa tare da bin umarnin Abba ta haura kafin ya dubi Mamabisola da Wamimo da ta nutsu tana sauraren su ya cigaba da cewa. "INSHA ALLAH za'a masa faɗa muje sai drever ya sauƙeku." Kanta ta girgiza tare da yin gaba Abba yabi bayansu. ********** Misalin goma da rabi na dare Jidda ta yi shiru a ɗaki tana nazarin maganganun HISHAM duk da bata jin zai iya aikata abinda yake faɗa mata, amma zuciyar sa ta girgiza da maganar sa sosai tana son ahalinta fiye da komai a rayuwarta bata jin zata iya jurewa ganinsu cikin tashin hankali, numfashi ta saki tare da ɗaukar wayarta ta kira Aisha ringing ɗaya Aisha ta ɗaga. "Kina asibitin ne." Daga can Aisha tace. "A'a na dawo gida tun ɗazu, saboda ƙanwar mahaifiyar Hajara tazo shiyasa na taho." "Okay kina da numbern nasu ne ina son zanyi magana da ita hajaran ne."? "Kai gaskiya Aunty Jidda babu numbern nasu nan domin kuwa banyi seving ba, nima ina son kiransu naji ya jikin nata na duba wajen calling banga numbern ba, amma dai tahota jikinta da sauƙi sosai harma ta zaga harabar Asibitin." "Okay to shikenan ba damuwa da safe naje asibitin mun gode da ƙoƙari Aisha Allah ya biyaki ki gaishe da Ikko da Ahmad." "Zasuji na gode Aunty Jidda sai da safe." Aisha tayi Maganar tana katse kiran. Numfashi Jidda ta saki tare da saka kanta ta kwanta ganin dare yayi har 10:30pm. Sai dai me bacci ya gagari idanunta tunani da tsoro duk ya cika mata zuciya tana son ahalinta fiye da komai a rayuwarta su kuma ya'yan masu kuɗin nan ba imani garesu ba su tozarta talaka ba abun mamaki bane, numfashi ta saki tare da tashi ta ɗauro alwala ta hau sallah. Washegari da safe bayan sunyi karin kumallo ne Umma ta dubi Jidda tare da cewa. "Jiddatul kair." "Na'am Ummana." "Jidda dan Allah na roƙeki ki cire hannunki cikin wannan Case ɗin fyaɗen dan Allah na roƙeki a matsayina ta mahaifiyarki, ki barmu mu zauna lafiya, ina da hawan jini ga suger, bana bukatar tashin hankali, har yau ciwon baƙin cikin mahaifin Abdullahi bai wankewa zuciyata ba, ki barni dashi ma kaɗai ya isheni." "Kanta Jidda ta girgiza tare da cewa. "Shikenan Umma insha Allah na cire hannuna zanje na janye ƙarar farin cikin ku yafi min komai a rayuwata." Tayi Maganar cikin sanyin jiki cikin zuciyarta ta fara saka, ita da take da niyyar zuwa asibitin taga yadda hajaran ta kwana sannan ta biya Police station ɗin taji ya ake ciki, amma gashi Umma na ƙoƙarin dakatar da ita, amma koma yaya ne bazan bar wannan Case ya tafi a banza ba, tayi Maganar zucin tana sakin ijiyar zuciya Umma ne tace. "Shikenan jiddatul kair Allah ya miki albarka, yau zaki fita ne ko zamu a gidane."? "Ehh Umma zan fita yanzu zanje gidan su Basmah na bata haƙuri jiya ta tafi cikin fushi akan wannan case ɗin." "Hakan yana da kyau Basmah masoyiyarki ce ta haƙiƙa, idan kinje kya gaishe da babarta ta ko." "Insha Allah zataji Umma bara na ɗauki hijabi na na tafi." Da adawo lafiya Umma ta mata kafin Jidda ta miƙe ta shiga ciki ta ɗauki hijabinta ta fita, ko da ta fito ABDULWASI'U yana tsaye ƙofar gidan su da niyyar aikawa tazo tsayawa tayi tana dubansa kafin tayi Magana yace. "Dama jira nake Abdu ya fito na aikesa yamin kiranki." "Okay sai kuma gashi na fito meke faruwa.?" Murmushi ABDULWASI'U yayi kafin yace. "Kamar kuma naga sauri kike ai." Cike da fara gajiya da maganganun sa tace. "Eh idan ba damuwa zan iya tafiya idan na dawo na saurari abinda kake da niyyar faɗa ko." Tayi Maganar tana saka kai tabarsa tsaye kansa ABDULWASI'U ya girgiza ya rasa meyasa Jidda bata ƙaunarsa duk da kyautatawa da biyayyar da yake yiwa iyayenta, numfashi ya saki ya koma bakin shagonsa. Jidda kanta tsaye mai adaidaita ta tare tace masa IBUNKU OLU CLINIC zai kaita can ta nufa, ta shiga mai adaidaitan yaja suka nufi hospital ɗin, bayan ya Kaita ne ta basa kuɗinsa 200 naira kafin ta shiga cikin asibitin darect ɗakin da Hajara take Jidda ta nufa domin kuwa tun jiya hankalinta yaƙi kwanciya ji take tamkar wani abun zai faru da Hajara maganganun HISHAM sun tayar mata da hankali tanajin zai iya komai domin ganin ya kuɓutar da wannan azzalumin ɗan uwan nasa, a tsaye taga wasu mata su biyu wanda bata sansu ba cikin tashin hankali gadon da Hajara ke kwance ta kalla wayam babu kowa cikin sauri tace. "Waye ku ina Hajara wacce take kwance a gadon nan jiya, an sallameta ne."? Ɗaya daga cikin matan ne ta kalli jidda tare da cewa. "Mu ƙannen mahaifiyar Hajara ne, ba sallamar mu akayi ba, Hajara aka nema aka rasa tun jiya cikin dare anyi nema anyin nema kaf cikin asibitin nan da unguwar nan har gida an kira da sauran ƴan uwanmu amma Hajara bata nan hankalin mu yana tashe bamu san ina Hajara take ba." Dafe kanta Jidda tayi tare da furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. "What ba'aga Hajara ba to ina ta shiga karfa a saceta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un." ______________________________________ *Ina kallon SHARHINKU my fan's ina jin daɗin hakan sosai Allah yabar ƙauna.* *Aunty Fauziya Auwal ƴar mutan jingau na gode sosai da kulawar ki Allah yabar zumunci Allah ya baki isasshen lafiya ya raya miki zuri'arki bisa tafarkin Manzon rahama.* Share and comment my fan's. *UMMU NASMAH CE✍🏻* *For more information 08147537180* [5/15, 7:22 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_PAGE 5_* Ƙanwar mahaifiyar Hajaran ne wacce suke kira da Baba jummai tace "Ba'a ganta ba, mun rasa ya zamuyi tun daren jiya muke nan cikin tashin hankali abun kamar almara." Numfashi Jidda ta saki tare da cije bakinta cikin zuciyarta take saƙa cewa. (To waye zai sace Hajara garin yaya za'ace da bakinta da hankalinta an sace ta anya kuwa wannan abinda zai yiwu ne, to amma idan da gaske saceta akayi garin yaya hakan ta faru? ko dai Hisham ne, kai ina bazai yiwu ba babu ta yadda Hisham zai iya saceta a cikin wannan asibitin dole yasan idan aka nemeta aka rasa su za'a zarga, to amma fa hatsabibi ne Hisham zai iya aikatawa ta wata fuskar domin ba imani garesa ba, sai dai kuma ba Teddy bace ita bare ya saceta cikin sauƙi, Hmm! Lallai akwai lauje cikin naɗi, bai zamo lallai ace Hisham bane saboda dole yasan su za'a zarga, kai zaima fa iya aikata sacetan yadda yake jin kansa tamkar sarki.) Tayi Maganar zucin tana sakin numfashi kafin ta dubi Wacce tayi Maganar tace. "To amma garin yaya kuna tare da ita cikin room daya har a ɗauketa baku sani ba, sannan abun mamakin ma ta yaya akayi bakuji motsinta ba a matsayin ku na majiyantan ta dole dai idan har tasan saceta za'ayi tayi ƙoƙarin kururuwa, gaskiya kunyi sakaci.?" Baba larai ce wacce suke tare da Baba jummai tace. "Ba sakaci mukayi ba, ƴar nan Saboda cikin dare ma misalin 3:00pm na farka har na bata ruwa tasha, tashin mu sallar asuba muka nemeta muka rasa munyi tunanin ko gida ta koma muka kira ummanta muka tambayeta tace batazo ba muka duba cikin asibitin nan gaba ɗaya babu ita hakanne ya sa hankalinmu ya tashi kaf cikin dangi da abokan arziki da aka san zata iya zuwa an tambaya amma bataje can ba tabbas sace ta akayi, maganar bacci kuma shi bacci ai ɓarawo ne bamu da laifi." "Hmmm! To an sanar da Police station ne sannan ina shi doctor dake kula da ita, sannan ina mahaifiyarta.?" Jidda tayi tambayar cikin sanyin jiki, Baba larai ne ta kuma magana. "Doctor ya je station zai sanar da abinda ya faru yanzu ma haka suna can tare da Mahaifiyar Hajaran." "Okay wani statin ɗin ne.?" "Wanda dai kika kai ƙarar wadanda suka yi ƙoƙarin mata fyaɗen can yace mana zaije tun ɗazu muke jiran dawowarsu muma." "Okay muje station ɗin." Jidda tayi maganar tana ficewa daga room ɗin bayanta sukabi kafin suka tari adaidaita zuwa Police station ɗin. Ko da isar su Police station ɗin sun sami Mahaifiyar Hajara da doctor zaune gaban Dpo daya fito harabar station ɗin cikin cell ɗin kuwa Nameer ne zaune, Jidda inda Nameer ke kulle ta kalla tare da cewa. "Dpo wannan ɓatan Hajara akwai lauje cikin naɗi ta yaya za'ace ana wannan case ɗin a nemeta a rasa mutum ce fa ba dabba ba ba kuma mahaukaciya ba, bare ace rashin hankali yasa ta fice, ya kamata a binciki gidan Alhaji Iyabo ina zargin su da sune zasu sace Hajara domin rufe babin wannan Case ɗin." Murmushi Nameer dake cikin cell ɗin yayi yana tsura mata idanu ko kaɗan baiji zafin maganar ta ba, Dpo ne yace. "Nima zargin da nake kenan, sai dai koma waye yayi wannan aikin zamu ganosa very soon." Yayi Maganar yana miƙewa tare da nufar cell ɗin ya dafa ƙarfen ƙofar yana duban Nameer dake zaune yana sauraron su yace. "Ina kuka kaita domin nasan tana wajenku."? Murmushi Nameer ya saki tare da cewa. "Tunda kasan tana wajen mu mai zai hana kaje ka ɗaukota, Abbas Marafa kana zaƙewa da yawa fa ka fara ƙoƙarin fusatar dank dan Allah ka dinga kulawa kana tauna harshen ka wajen min tambaya, ina nan rufe ko kun buɗeni ne, bare naje na saceta."? Dpo zaiyi Magana Jidda tayi saurin cewa. "Ba'a buɗeka ba amma abokin cin mushenka yana can yana shawagi kamar tsuntsu, zai iya aikata hakan a madadinka saboda imaninsa yayi ƙaranci, zai iya komai domin ganin ya kuɓutar da kai, ɗan uwanka bashi da imani kamar dai Kai ɗin nan." "Okay na fahimta Hisham kike nufi ko? let go ku kamasa sai ya muku magana da bakinsa idan shine bazai ɓoye muku ba, ɗan kanfai ne Hisham yana dai-dai da ƙugun kowa, gaskiya kina ƙoƙari wajen shigar da kanki cikin matsalolin da ba naki ba, zakiyi danasani kuma zakiji kunya a duk sanda gaskiya ta bayyana." Nameer yayi Maganar cikin murmushi, Jidda bakinta ta taɓe ta kuma cewa. "Wacce gaskiyar zan gani bayan wannan, hmm! Akanku dai bazan taɓa jin kunya ba bare kuma nayi wata danasani, a duniya babu wanda na tsani gani a rayuwata sama da kai da ɗan uwanka kuma tabbas sai kun fuskanci hukunci." Tayi Maganar a fusace Dpo ne yace. "Ba damuwa kuna iya tafiya zamuyi bincike kuma zamu samota nan da zuwa awa ashirin da huɗu, kai kuma Nameer zaka gane kuskuren ka." Kanta Jidda ta girgiza mahaifiyar Hajara ne tace. "Ranka ya daɗe dan Allah ku rufa min asiri ku nemo min ƴata, ita ɗaya Allah ya bani dan Allah ku rufa asiri bazan iya zure rasata ba." Jidda ce ta riƙota tana cewa. "Kiyi haƙuri Mama insha Allah Hajara Zata dawo cikin ƙoshin lafiya ki daina kukan kinji.?" "Naji Jidda na gode sosai kina ta ƙoƙari akan Hajara tamkar ƴar Uwarki ta jini Allah ya biyaki da mafificin alkairi." "Ameeen Mama wannan yiwa kaine muje, Baba larai mu tafi ku hau adaidaita ku mayar da Mama gida insha Allah komai zai daidaita ." Tayi Maganar tana riƙe da ita suka fita tare, DOCTOR shima hannu ya bawa Dpo sukayi musabaha kafin ya tafi. ********** Abba ne ya dubi Hisham da yake cin abincin tamkar yana cin magani yace. "Hisham kamin shuru tun ɗazu nake magana ni ɗaya ko baka jina ne?." Ɗago idanunsa Hisham yayi ya kalli Abba dake riƙe da cup ɗin block tea a hannunsa kafin yace. "Ina jinka Abba me kakeso na ce maka Abba akan wannan lamarin kace babu ruwanka mu jira gaskiyar Nameer ta fitar dashi, to kuma meye amfanin sanar da kai wani abu, kabar maganar kawai." "Hisham! Hisham! Tambayar ka fa nake kake min zancen banza munyi magana da commissioner jiya ina son sanin wani evidence kake dashi domin kuwa commissioner yace dole sai anje kotu muna bukatar barrister shiyasa nake son ji daga bakinka domin kuwa zaman Nameer cikin cell yana ɗagawa mahaifiyar ku rai dani kaina." "Abba na gama tsara komai Nameer zai fito cikin aminci kabar komai kawai a hannuna, sai dai Abba ina bukatar 5million daga gareka ina son buga wasa ne dasu." Ummi ne ta ture plat ɗin abincin dake gabanta tace. "Wasa Hisham, 5million ne zaka buga wasa dashi saboda baka da hankali, ka dinga hankali da rayuwa Hisham, baza'a baka waɗannan kuɗaɗen ba, sannan ka tashi muje ka kaini naga yarona Nameer." Hisham murmushi ya saki yace. "Ummi kin sani bana wata aba wasa, wannan shine wasa na na farko da zan buga dan haka Abba kai nake saurare." "Hmmm! Hisham kuɗi ba matsala bane, damuwata yanzu............... "Nameer ya fito haka zakace." Ta katse Maganar Abba tana shigowa gabaki ɗayansu juyawa sukayi suka mai da kallonsu kanta, Ummi ce tayi murmushi, shima Hisham murmushin ya saki tare da cewa. "Aunty Halima kece.?" "Eh Hisham ni ne." Tayi Maganar tana zama a daining ɗin tare da cigaba da cewa. "Yanzu nake samun labarin abinda ke faruwa da NAMEER shiyasa ma na taho cikin gaggawa, ta yaya za'ace da kuɗin mu da ƙimarmu da darajar mu, muna da ƙarfin iko a ƙasar nan gabaki ɗaya harma da tsallakenta, ace Nameer ya kwana a police station, wannan ƙasƙantar da ahalin mune, Hmmm! Yaya ya zamo wajibi muyi amfani da kuɗin mu da ƙarfin ikon mu NAMEER ya fito, kuma duk wanda ya masa wannan ƙazafin na rantse da Allah bazan ƙyalesa ba sai na hukunta sa." "Hmmm! Yes Aunty Halima magana kikayi mai kyau, Amma Abba shi bazai yarda da haka ba, yafi yarda da gaskiyar ce, Aunty Halima a yanzu bama bukatar kashe ko sisi ko neman alfarmar wani akan case ɗin Nameer na gama komai Nameer zai fito gobe." "Kamar yaya me kake nufi Hisham."? Abba yayi Maganar yana ɗan zaro ido. "Ina nufin Nameer zai Fito gobe, Aunty Halima nasan Ummi bazata bar Abba ya bani 5m ba, amma nasan zan iya samu a gareki." "Zan baka kuɗin da kake bukata Hisham, zakaji alart, amma ta yaya zaka fitar da Nameer daga cikin wannan haɗarin."? "Hanya ce mai sauƙi Aunty Halima, kuma na gama samun hanyar, nasan amfani akayi da wannan yarinyar wajen ganin an tozarta mu shiyasa nima nayi amfani da ita wajen ganin na kuɓutar da ahalina, muje Aunty Halima." Hisham yayi Maganar yana ture plat ɗin abincin tare da miƙewa, ummi ce ta dubesa tace. "Hisham meka aikatawa ƴar mutane."? Aunty Halima ne ta cewa Ummi. "Muddun Nameer zai fito to kawai ki sanya idanunki, muje Hisham." Itama aunty Halima tayi Maganar tana tashi suka bar wajen ita da Hisham Ummi duban Abba tayi tace. "Abban Hisham, kana jin abinda yaron nan yake faɗi kayi shuru karfa ya ƙara jawo mana wata fitinar bamu gama da wannan ba, ga kuma Halima tabi bayansa." "Hmmm! To me zance Ramata, nasan dai ko mai Hisham zaiyi bazai cutar da yarinyar ba, sannan na yarda da maganar sa amfani akayi da Yarinyar ki ci abincin ki kawai zanyi magana dashi a nutse." "Shikenan Allah ya kare." Da ameeen kawai Abba ya amsa. Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Hisham ya dubi Aunty Halima tare da cewa. "Aunty Halima, naje na sace yarinyar da tace Nameer ne yayi ƙoƙarin mata fyaɗe, yanzu haka gareta nake son muje tare da ke." "Hisham da gaske ka ɗauko yarinyar, amma garin yaya ka ɗauketa ba'a ganeka ba."? "Aunty Halima wannan abu ne mai sauƙi a gareni zan iya ɗaukar ko wacce irin kasada akan Nameer bazan yafewa kaina idan na kasa fitar dashi a wannan halin daya shiga kawai muje." Yayi Maganar suna nufar parking space bayansa Aunty Halima tabi suka shiga mota, tunda suka shiga babu wanda ya kuma magana har suka shiga gidan gonar Abba parking sukayi suka fito tare fa shigewa can ciki wani ɗaki Hisham yasa key ya buɗe, Hajara ce zaune tayi shuru jin an buɗe ƙofar ya sata firgita ta ɗago kanta ido huɗu sukayi da Hisham, murmushi ya saki tare da shigowa ya zauna gefenta, Aunty Halima ma shigowa tayi tana kallon Hajara kafin tace. "Yanzu wannan yarinyar ne ta yiwa Nameer sharri.?" "Itace Aunty Halima." Hisham yayi Maganar yana kallon Hajara hannu yasa ya ɗauketa da wawan mari wanda sai da taga taurari Uku, da yatsa ya nunata yace. "Waye ya biyaki kuɗi domin ki tozarta ahalina ki ɓatawa gidan mu suna waye shi."? Fuskarta Hajara ta dafe da shatin yatsun Hisham suka bayyana a kai idanunta kuma sai hawaye yake kanta ta girgiza tace. "Babu wanda ya sani ba sharrin na masa ba tabbas yaso min fyaɗe." Murmushin gefen baki Hisham ya saki Aunty Halima ne tace. "Okay bazaki faɗi ba kenan okay kin zaɓi ki wahala akan ki tonawa wanda ya saki asiri ko, Hisham ka ɗauko belt ka bigeta har sai jini ya fita a jikinta karka ƙyaleta har sai ta faɗa." "No Aunty Halima ba dukanta zanyi ba, akwai sistern ta zansa a mata fyaɗen idan yaso sai ashiga kotun da dalili wallahi aunty Halima da gaske nake zansa ayiwa ƴar Uwar ki Zainab fyaɗe muddun baki faɗa min gaskiya yanzu ba kuma na sanya a tozarta mahaifiyarki." Wani irin firgita Hajara tayi jikinta na rawa bakinta na karkarwa tace. "A'a dan Allah karka min haka karku taɓa Zainab bata san komai ba dan Allah ka rabu da ita." "Hmmm! Idan ita bata san komai ba to ke ai kin sani kece kaɗai zaki iya ceton ta ki faɗa min waye ya sanyaki.?" "Idan na faɗa maka zaka ƙyale Zainab idan har zaka rabu da ita zan faɗa maka gaskiya."? Numfashi Aunty Halima ta saki tare da cewa. "Gaskiyar muke bukatar ji muddun mukaji gaskiyar zamu rabu daku." "Nameer bai sanni ba bai taɓa ganina a cikin rayuwarsa ba, tabbas kuɗi aka biyani domin na masa sharrin da xa'a ɗauresa na tsawon shekaru." Kansa Hisham ya girgiza tare da cewa. "Waye ne ya sanyaki.?" "Tunde shine ya biyani dubi ɗari biyu domin nayi wannan aikin dan Allah ka rabu da ƴar uwata na tuba bazan kuma ba kayi haƙuri." Murmushi Hisham ya saki aunty Halima kuwa bakinta ta riƙe cike da mamaki. "Tunde! Hmmm! Ni nasan za'a rina wai an sace zanin mahaukaciya, tom riƙe wayar nan na mai da layi na no number ki kira Tunde kar kuma ki nuna masa cewa kina cikin damuwa kuyi Magana dashi." Hisham yayi Maganar yana dannawa Tunde kira tare da sanya handsfree, ringing ɗaya kuwa ya ɗaga saurin sanya recording. "Hello dawa nake magana." "Ni ce Hajara Tunde." "Hajara! Ina kikaje akace kin ɓata har muna zargin ko Hisham ne ya saceki domin mungun wayo garesa zai iya tunanin mune muka ɗana musu wannan tarkon kina dai lafiya ko.?" "Ina lafiya Tunde babu wanda ya sace ni kawai guduwa nayi daga asibitin, ƙarin kuɗi nake bukata wanda ka bani sunyi kaɗan domin kuwa ba ƙaramin kasada na ɗauka ba, idan ba haka ba zan tona asiri." "Haba Hajara yanzu 200k ne tayi kaɗan, kinga yanzu kina ina zan zo na ƙara miki 50k hakan yayi.?" "Yayi zan sake kiranka anjuma." katse kiran Hisham yayi tare da sakin murmushi ya dubi Aunty Halima yace muje. "Dan Allah karku tafi ku barni anan tunda na faɗa muku gaskiya ku sakeni." Juyowa HISHAM yayi ya kalleta tare da cewa. "Kamar yadda na miki alkawari bazan cutar da ƴar Uwarki ba tunda kin faɗa min gaskiya sai dai fa ki sani ke bazan sakeki ba sai kin gane kuskuren ki zaki gane wanda aka biya ki taɓa." Yayi Maganar yana saka kai ya fice bayansa Aunty Halima tabi tana dakawa Hajara harara, ko da suka shiga mota Aunty Halima cewa tayi. "Meye ribar Tunde idan ya tozarta Nameer.?" "Babu wata riba da zasu samu kakarsa ce maybe ta sakasu, shi Abba har yanzu ya kasa fahimtar su waye Mamabisola, kawai ƙiyayyace da hassada take damunsu a rai." "To Allah ya kyauta amma dai ya kamata yaji wannan voice ɗin ko.?" "A'a Aunty Halima bazai ji ba bana son abinda zai tayar masa da hankali bare ma yadda Abba yake ɗauka duk duniya bashi da gatan daya wuce su, sanin halin da ake ciki kan iya tayar masa da hawan jininsa zan kashe Case ɗin ba tare da su Abba sun san komai ba." "Hmmm! Hisham naji daɗi da kayi hakan Allah ya shirya su su kuma, amma daga nan Police station zamuje ko."? "A'a gidan ki zan sauƙeki daga nan Police station sai gobe ki turo kuɗin yau gobe nake son zanyi amfani dashi." "Okay baka da matsala." Har bakin get ɗin gidan ta ya sauƙe ta kafin ya yi shigewarsa yana murmushi domin kuwa shi ya juma da fahimtar Mamabisola ba ƙaunar su take ba shuka take a idanun makwarwa wanda har yanzu ita bata fahimci Hisham yasan abubuwan da take ƙulla musu ba. _____________________________________ Share and comment my fan's *UMMU NASMAH CE✍🏻* *For more information 08147537180* [5/16, 8:31 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_FREE BOOK ONE_* *PAGE 13 to 14* Isar ta cikin gidan Ta samu Umma sunkuye tana tsintar shinkafa, sallama tayi Umma ta amsa tana ɗago kanta. "Kin dawo."? "Eh Umma na dawo bamma samu Basmah ba sai na biya gidan su Zainab." "Tana ɗakin ki ma ai tana jiranki, ta juma a ciki da alamu dai kamar tana cikin damuwa na tambaye ta ko akwai abinda yake damunta sai tace babu wai abbanta ne yake asibiti jikinsa ya tashi sai kije ki sameta ki rarrasheta." "Subahanallah! Jikin Abban ne kuma ya ƙara tashi bara naje na sameta." Jidda tayi maganar tana tashi da sauri ta shige ɗakin nata, tana zaune tayi shuru hawaye na biyo idanunta ko kaɗan bata kula da shigowar Jidda, ta yi nisa sosai a cikin tunani, sai ji tayi ta dafa kafaɗarta. "Basmah abun har ya kai ga kuka, jikin Abban babu daɗi ne.?" Numfashi Basmah ta saki tana goge hawayen fuskarta tace. "Jidda jikin Abbana ba daɗi, dole sai an masa cs ana neman dubu arba'in, mu kuma bamu da ita bamu da wanda zai bamu, ga kuɗin hayar gidan namu ma ya kare suna bukatar Kudi masu gidan, salary na kuma na wannan watan kuɗin makarantar su hafiz aka biya, gacar Mama ta shiga cikin damuwa." "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati! Lallai dole hankalinki ya tashi Basmah, yanzu ina zamu samu wannan kuɗin ko Abba a fara masa cs ɗin 14k ne kawai a cikin account ɗina, bansan kuma ina zamu samu 26k ba, mutanene yanzu basa taimako kowa kansa da iyalansa ya sani, bashi ma ba kowa bane zai baka wani ma yana da shi sai ya gama jin sirrinka yace maka babu, amma yaushe ne za'a masa cs ɗin." "Sunce jibi zasu masa, bansan inda zan samu kuɗin nan zuwa jibi ba, shiyasa kikaga hankalina ya tashi Abba bashi yake da shi ba, kaf ƴan uwansa babu wanda zai taimaka masa wallahi, suna da kuɗi sai dai basa taimakon sa, abinda yake sani kuka kenan." "Karki damu Basmah akwai Allah muyi addu'a insha Allah, Allah zai kawo hanya, gobe ai muna da aiki idan yaso sai muje mu tambayi accounter bashi zuwa ayi salary idan yaso sai su bamu aron 26k ɗin sai mu haɗa da 14k ɗin wajena in akayi salary sai su cire 10k cikin kuɗina kema su ciri 16k karki damu Allah ya bawa Abba lafiya." "Ameeen, amma Jidda bazan amshi kuɗin ki ba, kema kina fama da ɗawainiyar gidan ku, dan haka ki bari muje mu nemi bashin 40k ɗin insha Allah zan biya amma bazan sakaki cikin wahala ba." Numfashi Jidda ta saki tare da girgiza kanta ta ɓata ranta. "Saboda ni Abba bai haifeni ba ko shiyasa bazan masa ɗawainiya ba, idan kika min haka baki min adalci ba, tamkar mahaifina haka nake masa kallo yadda baki isa hanani yiwa Ummana abu ba, haka baki isa ki hanani na yiwa abbanki abu ba, dan haka karki sake cemin komai ki share hawayen ki kukan ya isa haka insha Allah Abba zai samu lafiy." "Hmmm! Shikenan Jidda Allah yabar zumunci, amma asibiti kikaje ko nasan karya kika yiwa umma ba gidan mu kikaje ba, wato har yanzu baki fita a cikin wannan sha'anin ba ko Jidda.?" "Basmah na faɗa miki bazan fita ba dole sai na taya Hajara kwato ƴancinta yanzu haka maganar da nake da ke an sace Hajara." "An sace Hajara, kamar yaya sai kace wata kaza." "Da gaske ansace ta kuma ni gaskiya wannan Hisham ɗin shi nake zargi babu wanda zai sace Hajara sai shi Saboda ya kuɓutar da ɗan uwansa." "Amma abun da mamaki Jidda Hisham bazai sace Hajara ba domin yasan dole shi za'a zarga, Allah ya bayyana ta, amma dai Jidda ina ƙara faɗa miki ki fita cikin wannan Case ɗin bana son ki jawa kanki matsala." "Hmmm! Naji mubar maganar, ki tashi muje mu taya Umma aiki sai mu koma asibitin." "Okay." Basmah tayi Maganar tana tashi suka fita. ************ "Wai Tutu bazaki daina wannan damuwar ba, zafa ki sawa kanki ciwo." "Hmmm! Samira dole fa na shiga cikin damuwa, gani nake kamar yaya Nameer baya sona, yaƙi bayyana Soyayyar mu, harta ga yaya Hisham da suke ƙaunar juna yaƙi bayyana masa akwai wani abu tsakanin mu, hankalina yana tashi idan na tuna da hakan zuciyata sai ta dinga tsinkewa ina matukar son yaya Nameer Soyayyar da ban san iyakar ta ba." Numfashi Samira ta saki tare da dafa kafaɗar Tutu tace. "Tutu ni kaina kullum ina wannan tunanin Soyayyar da kike yiwa yaya Nameer kamar shi baya miki, da Yaya Nameer yana sonki Tutu to wallahi da zai bayyanawa kowa Soyayyar ki, bazai ɓoye ba anya ma kuwa ba da gaske Nameer shi ya yiwa wannan yarinyar fyaɗe ba Tutu."? "A'a Samira na rantse da Allah Yaya Nameer bazai aikatawa wata mace fyaɗe ba, domin kuwa Mutum ne mai ƙyanƙyami bare kuma wannan Yar talakawa, da zaiyi lalata da wani to da dani zai fara saboda yadda na sake masa jiki nasan yaya Nameer mutum ne shi mai tsananin sha'awa, amma hakan bazai sa ya zalunci ƴar wata ba, na fi kowa sanin waye shi." Bakinta Samira ta taɓe tana yiwa Tutu kallon mahaukaciya kafin tace. "Na sani Soyayyar da kike yiwa yaya Nameer bazai taɓa barinki ki faɗi aibunsa ba, wannan Soyayyar ita take cutarki, da ita yake amfani yake cutarki ya kasa bayyanawa duniya yana sonki, soyayyar gaskiya ba'a ɓoye ta, ko da an ɓoyeta ita da kanta take bayyana kanta, ya mayar dake mahaukaciya sai wasa yake da tunaninki, Allah ya ganar da ke Tutu yasa ya aureki." "Ba karesa nake ba Samira nasan halin yaya Nameer nasan abinda zai aikata da wanda bazai aikata ba, wallahi bazai yiwa wata fyaɗe ba, ki yarda Samira ba halinsa bane, Hmm! Amma ke ba lallai ki yarda ba, Samira kece kaɗai wacce kika san wannan sirrin nawa muddun asirina ya tonu to kece zan zarga, dan Allah ki ɓoye min sirrina, ki bari har shi ya bayyana Soyayyata." "Bazan taɓa tona miki asiri ba Tutu domin kuwa na san menene amana, amma ina baki shawari muddun yaya Nameer ya dawo gida ki tabbatar Soyayyar ku ta bayyana idan ba haka ba zaki tura mota ta tashi ta barki da ƙura." Samira tayi Maganar tana miƙewa tare da ɗaukar mayafinta ta kuma cewa. "Ni kinga tafiyata Allah ya fiddo miki dashi." Kanta Tutu ta girgiza tare da tashi ta raka Samira har bakin get kafin ta dawo a falo ta tarar da wayar Hisham tana ringin hannu tasa ta ɗauka taga Sadiq ya bayyana a screen ɗin wayar bata ɗauki kiran ba ta haura bedroom ɗin su nocking tayi Hisham dake zaune yayi shuru yana saƙa da warwara akan Tunde, yace. "Yes come." Turo door ɗin tayi ta shigo cikin sanyin jiki gefen Hisham ta zauna sai kuma idanunta ya ciko da hawaye, sanin hawayen fuskarta yasa HISHAM sanya hannu ya share mata hawayen cike da ƙaunar ƴar uwarsa domin kuwa a rayuwarsa ya tsani abinda zai ɗaga mata hankali su biyu kawai Ummi ta haifa bashi da wani yaya ko ƙani itace ƴar uwarsa guda ɗaya tilo. "Tutu wai meyasa bakya jin rarrashi ne, ba nace miki Yayanki Nameer zai dawo gobe ba, ko baki yadda dani bane, kin damu akan Nameer sosai Tutu dole kuma ki damu domin kuwa Nameer shine hasken gidan mu, ɗan uwa ne na gari bazan bari wani abu ya cucesa ba zan karesa da jikina da kuma rayuwata." Kanta Tutu ta kaɗa tare da miƙa masa wayarsa. "Ya Sadiq ne yake kiranka." Amsa yayi tare da cewa. "Okay kije ki wanke fuskarki." "To Yaya." Tayi Maganar tana tashi tabar wajen kiran Sadiq Hisham yayi Ringing ɗaya ya ɗaga. "Malam kazo airport ka ɗaukeni." "Whatt airport, serious." "Yeah da gaske wallahi ina jiranka ko su Daddy basu san dawowata ba." "Shegen gari, okay gani yanzu dama kuwa akwai game gobe." Yayi Maganar yana katse kiran tare da tashi ya zari key ɗinsa ya fita. *********** Motoci huɗu ne sukayi parking a police station ɗin, da sauri Soja ya fito ya buɗe wata baƙar mota Abba ne ya fito hannunsa riƙe da waya shida commissioner bayansa masu tsaron nasa suka bi har cikin Police station, gaba ki ɗaya ƴan sanda miƙewa tsaye sukayi cikin girmamawa, kujera aka ɗaukowa Abba, zama yayi shima commissioner aka kawo masa kujerar ya zauna. Commissioner ne yace "Ku buɗe Nameer." Cike da bin umarni Sargent Dogo yazo ya buɗe, miƙewa Nameer yayi ya fito tare da nufar Abba Abba yana ganin Nameer ya miƙe suka rungume juna cikin soyayya da kulawa kafin Abba ya zauna Nameer gefen ƙafar Abba ya jawo kujera ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaɗar Abba. "Nameer ka takura da zaman nan ko.?" "No Abba ban takura ba rayuwa ce ba inda bata kai mutum Abba ina ummina ita kawai nake tunani nasan zata fi kowa damuwa." "Hmmm! Umminka ta damu ƙwarai Nameer sai dai ɗan uwanka yana kwantar mata da hankali, munyi magana da commissioner gashi nan yace dole ne sai an kaika kotu, zamu nemi lauyer insha Allah zan tsaya domin ganin ka samu adalci." "Abba bani da damuwa da zuwana kotu har yanzu bana jin koda tsinkewar zuciya saboda nasan ban aikata laifin da ake zargina dashi ba, Abba ina tunanin Hisham yayi fushi dani ko tun shekaran jiya daya zo bai kuma dawowa ba." "Ka sani Hisham bazai taɓa fushi da kai ba Nameer kasan zuciyar sa bazai iya jure ganinka cikin wannan halin bane sannan ya sanar dani baya son ƙara ganin fuskar Dpo wata ƙila hakan yasa yaƙi zuwa amma yana can yana ƙoƙarin ganin ya kuɓutar da kai." "Idan ka koma Abba kace masa ina kewarsa." "Shikenan zan isar masa da sakon." Commissioner ne ya tambayi Sargent Bala Dpo tare da basa umarnin ya shiga ya sanar dashi sunzo babu ɓata lokaci ya shiga kiran nasa. Babu jumawa Dpo ya fito cikin girmamawa ya sarawa commissioner tare da gaishe da Abba shima cikin girmamawa kafin ya zauna, commissioner ne yace. "Dpo ya ake ciki game da case ɗin Nameer me kuka tattara ga binciken da kukayi."? "Sir har yanzu muna kan bincike bamu kammala ba shiyasa ma bamu kai case ɗin kotu ba tukunna, amma binciken asibitin dai ya nuna cewa an ya kushe ta sosai ma'ana anyi kokawa da ita sannan kayan jikinta duk sun yaga, kuma the Best ma mun samu agogon hannun Nameer a jikinta wanda maybe bai san ya maƙale a jikinta ba domin kuwa doctor sunce a jikinta suka samu sanda aka kawota asibitin wannan agogon dai shine yake tabbatar mana da cewa Nameer shine yayi ƙoƙarin keta mata haddi, sannan ita yarinyar ma ansaceta jiya, sai dai sir Hisham muke zargi da saceta saboda shine kawai zai iya hakan duk da zargi muke, yanzu ma niyyar zuwa wajensa muke sai kukazo." Commissioner duban Nameer yayi tare da cewa. "Amma har yanzu 2days a wannan binciken kawai kuka tsaya, Dpo ganin agogon Nameer a jikin ta tabbas hujja ce sai dai fa ku sani za'a iya masa sharri saboda mahaifinsa babban mutum ne kuma yana da maƙiya shiyasa nake son kuyi bincike da kyau, dan haka na baka zuwa yau da gobe ka tabbatar ka gama tabbatar da gaskiyar binciken, maganar Hisham kuma kuna iya zuwa kuyi binciken ku duk da ba lallai ace shi ɗin bane." "Shikenan Sir insha Allah zanyi yadda kace." Numfashi Abba ya saki tare da cewa. "Commissioner ina son idan ta tabbata za'a kai Nameer kotu, to karku sanar da Hisham ranar Shari'ar." "Meyasa."? Commissioner yayi tambayar yana kallon Abba. "Saboda zai iya ɓata komai." "Shikenan, zamu iya tafiya." Duban Nameer Abba yayi yace. "Zan koma Nameer insha Allah komai zaizo cikin sauƙi dan Allah karka ɗaga hankalinka." "Insha Allah Abba ka cewa Ummi ina gaisheta kuma nayi kewarta, Abba Tutu kace injini tayi haƙuri karta sa damuwa a ranta ta dinga cin abinci." "Saƙon duk zai isa garesu ka kula Nameer." Abba yayi Maganar yana tashi suka fita kafin Sargent Dogo ya mayar da Nameer cikin cell, shuru Nameer yayi yana nazarin maganganun su Abba, cikin ransa yace. (Meyasa Hisham ya iya wadannan kwanakin baizo ya ganni ba, me yake shiryawa tabbas Hisham ne ya ɗauke wannan yarinyar domin ganin ya kuɓutar dani to amma ko ta ina Case ɗina a dabaibaye yake ta yaya Hisham zai iya warwarewa, nasan halinsa sarai zai iya aikata komai domin idan ya yanke hukunci baya jin Muryar kowa, lallai na kuɓuta Dpo bazai shaba a wajen Hisham, nasan yanzu yana can yayi target ɗin Jidda zai kuma iya aikata mata duk abinda ya kudurta a ransa sai dai bazan so hakan ba.) Ya yi maganar yana sakin numfashi, jingina kansa yayi jikin cell ɗin tare da yin shuru. ********** "Yau tsawon kwana biyu babu labarin ki ko wayarki na kira baya tafiya." Gyara zamanta Wamimo tayi tace. "Naje ƙauye ne kinsan na kira yata dake ƙauyen Agunjin, nace idan taji labarin wani shahararren matsafi wanda yake karya kafi ta min magana, to ranar da mukaje gidan Iyabo da ke bayan na koma gida shine sai ta kirani take cewa wani mai tsafi yazo shi, kuma aikinsa yana yi sosai yana karya kafi, to shine fa naje ƙauyen naso dawowa a ranar to layi yayi yawa a wajen matsafin shiyasa na kwana biyu, babu network ne ma a ƙauyen shiyasa ban kiraki ba." "Wamimo da gaske kike min wannan Maganar.?" Mamabisola ta tambayeta cikin zakuwa. "Ƙwarai kuwa na samu ganawa da matsafin na kuma masa bayanin ki, yace dole sai kinzo da kanki ya duba ya gani idan aikin zai yiwu." Numfashi Mamabisola ta saki tace. "Hmmm! To ki shirya jibi muje Wamimo Allah yasa aikin nan ya yiwu ina son ganin bayan Iyabo ina son ganin dukiyar sa ta tarwatse ina son ganin ya rasa komai a rayuwarsa idan hakan bata kasance ba hankalina bazai taɓa kwanciya ba." "Karki damu Mamabisola wannan aikin sunansa ya yiwu domin kuwa ance wannan matsafin bai taɓa aiki bai yiwu ba, indai yayi aiki to tabbas sai aikin yayi, yanzu bara naje kasuwa anjuma zan dawo." "Shikenan kije dawon." _______________________________________ *Share and comments my fan's🥰* *_UMMU NASMAH CE✍🏻_* *For more information 08147537180* [5/17, 7:36 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *BAZAN FASA GODIYA GA JINJINA TA A GAREKU BA MASOYA NAJI DAƊIN YADDA KUKA AMSHI LITTAFIN NAN HANNU BIYU, KO WANI GROUP NA SHIGA COMMENTS NA GANI AKAN JALALA LALLAI KUN ƘARFAFA MIN GWIWWA KUNCE NA DAGE WAJEN TYPING, INSHA ALLAH ZAKU CIGABA DA NISHAƊI CIKIN WANNAN LABARIN BA'A MA FARA KOMAI BAI YANZU WASAN ZAI FARA, JALALA FAN'S HAR NA RASA ABINDA ZANCE MUKU TSABAR FARIN CIKIN SHARHINKU, ALLAH YA BAR ƘAUNA.* *_FREE BOOK ONE_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 13 to 14_ Washegari da safe bayan Hisham sun kammala breakfast ne wajajen 11:30am ya ɗauki wayarsa tare da duban Abba yace. "Abba zanje Company yau saboda naga yadda abubuwan suke tafiya." "Okay hakan yayi, amma baka sanar dani halin da ake ciki ba, ina yarinyar da ka ɗauke ɗin, Dpo ya fara zargin kaine ka saceta kuma yana gaf da tunkaro ka domin tuhumar ka sai ka shiryawa tseratar da kanka." Murmushi Hisham ya saki tare da cewa. "Nayi mamaki ai da basu zo da wuri ba, nasan dama dole ni zai zarga, karka damu Abba dai-dai nake dashi." Ummi ce tace. "Hisham wai Meyasa baka tsoron rayuwa ne kai wannan duniyar fa abar tsoro ce Hisham amma kai sam bata baka tsoro, meye ribarka idan ka ɓoye wannan yarinyar, to kaje ka buɗe ƴar mutane muddun kana gudun ɓacin raina idan ba hakaba sai na saɓa maka yau naga shashancin banza." "Ummi bazaki fahimta bane amma ni naga ribar da zan ɗauka, kin sani Ummi idan na yanke hukunci *_KO UMARNIN ZUCIYATA BANA BI_* dole sai na aiwatar nake samun sukuni, *_ƊABIAR ƊANKI NE KIN SANI_*." "A Wannan taƙin kuwa zan taka maka burki da ƙanin ubanka, kaje ka sau yarinyar nan dai na faɗa maka." Duban su Abba yayi yace. "Hisham na yarda da kai bana kuma jin zaka bani kunya kaje ka binciki yarinyar da kyau sannan ka sake cikin ƙoshin lafiya ta koma ga iyayenta." "Ya haka Abban Hisham, kamar fa ɗaure masa gindi kake akan me zaka basa ƙarfin gwiwwa bayan kasan ɗanka ba ji yake ba, mutumin da ya kashe kansa da girman kai da izza harshi ne Mutum, Allah ya yiwu Nameer albarka shi sam bashi da wannan ɗagawar taka, ta inda ya fika morar Rayuwar Duniya kenan, amma ka zauna kana bin Bayan yaro kuma kasan halin zuciyarsa sarai, wannan ba gata bane." Ummi tayi Maganar tana hararar Hisham murmushi Hisham ya saki ganin ummi na neman rikice masa ya sashi saurin fita, Abba murmushi yayi yace. "To ai ya fita faɗan sai ya ƙare ko." Shima Abba yayi Maganar yana tashi a wajen, bakinta Ummi ta taɓe tana kallon Tutu tace. "Ke kuma meye yake damunki kin hana rayuwarki sukuni tunda Nameer ya bar gidan nan, wai ke bazakiyi tawakkali ba, ko ce miki akayi Nameer ɗin bazai dawo bane, to ki daina wannan damuwar bana so." "Ummi gidan ne duk babu daɗi babu yaya Nameer." "Insha Allah Yayanki zai dawo mu cigaba da addu'a, sai ki tattare daining ɗin." "To Ummi Allah yasa." Da ameeen Ummi ta Amsa tare da tashi ta haura sama. Hisham yana cikin tuƙi yaji shigowar kuɗin da Aunty Halima ta masa alƙawari, wayar ya ɗaga ya kira Sadiq Ringing ɗaya ya ɗauka, daga nan Hisham yace. "Mu haɗu Aminci News by 1:00." Ya katse kiran Companyn ya shige ya je ya duba abubuwan da ke tafiya, Salisu ya aika BANK ya ciro masa wannan kuɗaɗen ya dawo, ya juma sosai cikin Companyn shine bai baro Companyn ba har sai da yayi Sallah kafin ya kira Sadiq yace su haɗu yanzu gashi nan zuwa, ya zari key ɗinsa ya fice daga Companyn. A bakin ofishin Jaridar ya samu Sadiq yana tsaye da alamu saukesa akayi parking Hisham yayi tare da fitowa hannunsa riƙe da baƙar jaka ya nufo Sadiq yana dariya hannu ya basa sukayi musabaha. "Kaddai ka juma kana jirana." "Ina ban juma ba yanzu Ib ya sauƙeni ya akayi me zamuyi a ciki."? "Muje kawai Sadiq kai dai ka min video record akan duk wata tattaunawar da zamuyi a wajen ta, muje amma karka fara ɗaukar har sai na taka maka ƙafa." Hisham yayi Maganar tare da yin gaba Sadiq yabi bayansa. "Jidda dama na sani ba lallai mu samu rancen kuɗin nan ba, Hmm! Bansan ya zanyi ba, Abbana yana cikin matsala ina son na ceci rayuwarsa babu wanda zai masa idan bani ba." Cikin kulawa Jidda da alamun damuwa Jidda tace. "Hmmm! Basmah akwai Allah kuma zai taimaka karki damu bari mu koma gida insha Allah bazamu rasa abin yi ba." "Any................. .. "Assalamu alaikum." Sallamar Hisham ta katse Maganar da Basmah zatayi gabaki ɗaya idanu suka ɗaga suka kalli bakin ƙofar, ganin Hisham yasa Jidda sakin murmushi domin kuwa tasan yauma haukar ce ta kawosa. "Ameeen wa'alaiku mussalam." Shigowa sukayi Hisham ya harɗe hannunsa tare da tsayawa a gabanta. "Bana hana maƙiyi abu biyu wajen zama da kuma ruwan sha." Murmushi Hisham ya yi yace. "Kina nufin mu zauna kenan."? "Kwarai kuwa." Zama sukayi Sadiq da Basmah dai kallon ikon Allah suke, Hisham gyaran murya yayi tare da cewa. "Hisham ya faɗi domin kuwa ya gagara cire ɗan uwansa daga cell, shiyasa na dawo gareki durƙusawa wada ba gajiyawa bace neman taimako ne." "Hmmm! Ashe dama matsiyaciya tana da rana duk da nasan ungulu bata jimar banza meke tafe da kai shin yauma kazo kamin barazanar ce akan wancan dabban ɗan uwan naka, kayi ikrari har yanzu ka kasa cikawa." "Hmmm! Ko da zancena na farko ya nuna ba tashin hankali bane ya kawo ni." Yayi Maganar yana taka kafar Sadiq. "Meya kawo ka to.?" "Neman alfarma ina son ki cire hannunki a wannan Case ɗin kije Police station ki nuna ke baki san komai ba, infact ma sharri yarinyar take yiwa Nameer, ba kyauta zaki min ba biyanki zanyi manyan kuɗaɗen da zasu saya muku gida abar na haya kiyi tunani ba gaggawa nake ba." Kallon Hisham Jidda tayi wato ma ya raina mata wayo ya rasa mafita shine zai bata cin hanci, saboda tsinannen ɗan uwansa ya kuɓuta. Za tayi Magana Basmah ta taka ta tare da sunkuyawa dai-dai kunnenta ta mata raɗa. "Dama ce mai kyau da zamuyi amfani dashi wajen samun kuɗin da muke nema, ki amshi tayinsa da zummar zakiyi aikin mu amshe kuɗin banza, amma a zahiri baza kiyi aikin ba, ki duba halin da Abbana yake ciki ki cecesa Jidda kimin wannan taimakon, ba wai zakiyi masa aikin bane kuɗin kawai zaki amsa kuma ki ƙi yin aikin Please Jidda." Shuru Jidda tayi zuciyarta na kai kawo. _Anya kuwa hakan zata yiwu, to amma Basmah tana bukatar taimako, zanso ace na taimaka mata amma ba ta wannan hanyar ba, domin kuwa amsar cin hanci babban laifi ne duk da ba aikin zan masa ba, ko da yake koda na amsa babu wani laifi domin kuwa bazan taɓa take gaskiya ba, gaskiyar Basmah zan amsa na nuna masa bashi da yawo._ Murmushi Jidda ta saki kafin tace. "Amma dai anyi faɗuwar baƙar tasa ko nace faɗuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance, ka bada maza ina kurin ina barazanar shin ka fasa tozarta nin ne, hmm an dai ji kunya, ba damuwa nawa ne farashin." Murmushi Hisham ya saki yace. "5million babu tayi idan sun miki shikenan idan basu miki ba zan koma da kuɗina." Murmushi Jidda itama ta saki tace. "Ciniki ya faɗa zanje na ƙaryata Hajara, Ɗan uwanka zai fito nan da dare." jakar ya ijiye mata tare zazzage duka kuɗaɗen a ƙasa yace. "Ga su nan, Sadiq muje." Hisham yayi Maganar yana miƙewa Sadiq dake ɗaukar dukkan abinda ke faruwa ya tashi suka fice tare, Jidda duban Basmah tayi tace. "Anyi banyi kuskure ba kuwa Basmah zuciyata bata kwanta da Hisham ba, anya kuwa babu wani abu a ƙasan zuciyar sa.?" Numfashi Basmah ta saki tace. "Babu komai Jidda karki wani damu kawai ɗan uwansa yake son ya fitar a cikin matsala, ya gagara ne kawai yaga bashi da wata mafita sai wannan, kuma ni a ganina wannan dama ce mai kyau tunda dama Umma tace ki cire hannunki a cikin wannan Case ɗin kinga kin samu riba biyu kenan, ga kuɗi ga kuma bin umarnin Umma kije kawai ki cire hannunki kalas magana ta ƙare." A fusace Jidda ta kalli Basmah tare da cewa. "Whatt! Kinsan abinda kike faɗi kuwa na cire hannuna fa kikace, amma sanda kike so na amshi kuɗin me kika cemin ko kin manta na tuna miki, ba cewa kikayi na amshi kuɗin naƙi masa aikin ba, shine yanzu zakiyi ƙoƙarin turani ga hallaka, to wallahi tashi zan naje har gidan su na mai da masa da wanannan kayan tsiyar tasa, domin kuwa bazan taɓa ganin gaskiya na take ta ba, bazai yiwu ba, kai amma nima mahaukaciya ce dana biye miki na amshi kuɗin nan, yanzu dana amshi wannan kuɗin naje gida na cewa Umma ina na samesu, kin san dai sai ta bincike ni ƙarshe ma raina yayi mungun ɓaci kin kaini kin baro Basmah." Tayi Maganar cikin ɓacin rai sai yanzu ma taji haushin kanta da ta amshi wannan kuɗin shikenan zai rainata ya dinga mata kallon ƙasƙantacciya mai kwaɗayin abun duniya. "Jidda baki fahimce ni bane Abbana yana cikin matsala kin sani sannan zaki cecemu ne idan kin amshi kuɗin kina gani fa cikin office ɗin nan abamu aron kuɗin sunsan za'a cire wannan kuɗin cikin salary namu amma sukace babu kuɗi a ƙasa kuma akwai kuɗin bawai babu ba, to ina zamuje a bamu, muna ganin dama tazo kuma muna bukata sai mu barsa, Jidda muje mu yiwa Umma bayani a nutse zata fahimce mu, sannan....... Hannu Jidda ta ɗagawa Basmah tace. "Sannan na daure na cire hannuna a cikin Case ɗin ko? To impossible." Jidda tayi maganar tana tashi ta fice daga office ɗin nata, numfashi Basmah ta saki tare da dafe kanta tasan halin taurin kan Jidda sarai dama ba lallai ta amince ta cire hannunta a case ɗin ba. "Ban taɓa ganin Hisham ya nemi alfarma a wajen wata ba sai yau ban taɓa ganin an faɗawa Hisham baƙaƙen magana yayi shuru ba sai yau, tabbas kana ƙaunar Nameer fiye da kowa a wannan duniyar, sai dai nayi mamakin da ka shanye maganganun wannan yarinyar." Murmushi Hisham ya saki tare da cewa "Hmmm! Hisham baya jewar banza kamar yadda ta faɗa, ba Nameer yasa naje mata da wannan buƙatar ba domin kuwa ina da hujjar da zai sanya Nameer ya fito yanzu haka Police station zamu wuce tare da Nameer zamu fito." "Ban fahimta ba Hisham me yasa to kaje wajenta shin meye manufar, sannan shi kuma wannan video record ɗin da kasa nayi fa."? "Ka sanya idanu kayi kallo Sadiq zaka fahimci manufata, wannan shine wasan da nace maka zamu buga kuɗina zai dawo Naira biyar bazaiyi ciwon kai ba, ko da kuwa ta kashe wani abu daga ciki na rantse da Allah dai ta biya." "To Allah ya kyauta." Sadiq yayi Maganar a takaice babu wanda ya sake magana har suka isa Police station ɗin. Shigar su cikin station ɗin, Hisham darect cell ya nufa Nameer na zaune ya haɗa kansa da bango yaji muryar Hisham. "Hmmm! Wata ƙila ɗan uwana yana cikin damuwa nasan dole izuwa yanzu ka fara gajiya da zaman wajen nan." Kansa Nameer ya ɗago ya dubi Hisham kafin yace. "Sadiq Barka da zuwa yaushe ka dawo ƙasar.?" Murmushi Hisham ya saki domin kuwa ya hango fushi Nameer yake dashi ya kuma san fushin bazai wuce akan rashin dawowarsa station ɗin ba, Sadiq ne ya amsa da. "Jiya shigowata sai kuma nake jin labari marar daɗi." Kafin Nameer yayi Magana Hisham yace. "Kayi haƙuri nasan fushi kake dani akan rashin dawowata, nayi hakan ne saboda bana son ganinka a cikin wannan halin nayi alkawarin bazan dawo station ɗin nan ba har sai da hujjar da zata kuɓutar da kai." "Bana fushi da kai Hisham sai dai ina fushi da zuciyar ka, saboda ta cika rashin haƙuri zafinta yayi yawa, nasan Kaine ka sace wannan yarinyar meyasa zakayi haka Hisham kuskure ne babba ka tafka bana son ka shigo haɗari saboda ni, da ka shiga cikin tashin hankali Gara ace na rasa rayuwata." "Ina zuwa Nameer Sadiq muje wajen Dpo tukunna." Yayi Maganar yana juyawa domin kuwa bashi da amsar da zai bawa Nameer, ko inda su Sargent Bala yake Hisham bai kalla ba ya wuce office ɗin Dpo, babu wanda ya kulasa kasancewar sunsan halinsa nocking yayi Dpo ya basu damar shigowa sosai Dpo yayi mamakin ganin Hisham mutumin da yake da niyyar zuwa garesa sai gashi ya kawo kansa, zama Hisham yayi tare da sakin murmushi yace. "Nasan dama dole akwai ranar da ɗan tsakon Police zaiji kunya sai ga kuma ranar tazo, har abada ahalin IYABO masu Nasara ne ko da alfarma ko babu." Murmushi Dpo yayi yace. "Na fahimta, wani tsuntsun tarkon ka kuma ya kama Hisham Abdulzahir.?" "Ba tsuntsu ba dai sai dai tsuntsuwa domin kuwa na farauto tsuntsuwar kuma har na samu kwamishon farauta, ita tsuntsuwar da kuke nema tana gareni." "Hajara tana wajenka kenan, ehh tabbas ƴar Jaridar nan tayi gaskiya da tace kaine zaka sace yarinyar, meye ribarka da hakan.?" "Hmmm! Ita Zabiyar har ta hasashoni kenan, we'll ribar na kawo maka yanzu idan ka shirya amsa sai na gabatar maka." Numfashi Dpo ya saki tare da cewa. "Hmmm duk tsuntsun da yaja ruwa ka sani dole sai wannan ruwan ya dakesa, gabatar." "Shikenan zan kuwa jawo babban ruwan da zai dake ku amma ni tuni na zillewa wannan ruwan." Yayi Maganar yana ɗauko wayarsa a aljihu ya danna recording ɗin da yayi na Hajara ya ijiye, gaba daya shuru sukayi suna sauraron recording ɗin, Sadiq sosai yasha mamaki musamman da yaji wai Tunde ne yasa ayiwa Nameer wannan ƙazafin, Dpo kuwa wani irin gumi ne ya keto masa, domin kuwa duk binciken da sukayi nunawa yake Nameer ne ya aikata bayan recording ɗin ya ƙare ne Hisham ya kashe tare da mayar da wayarsa aljihu ya saki murmushi. "Ya kamata ka cire wannan kakin naka domin kuwa sam wannan aikin bai dace da kai ba tunda har ka gagara gano gaskiya, Dpo na faɗa maka shiga komar Hisham ba abu bane mai sauƙi, amma zan kyaleka za kuma mu cigaba da bawa karnuka ƙashi, sai dai fa dole ne a wannan karon kamin wani aiki sannan a rufe babin Case ɗin Nameer gaba ɗaya kamar ba'a taɓa yiba bana bukatar ko Abba yasan da labarin Tunde ne ya haɗa wannan tarkon, sai kuma aikin da nace zaka min, idan ka amince zan ɗaukaka darajar ka ta hanyar samun ƙarin girma." Shuru Dpo yayi tare da ɗago idanunsa ya kalli Hisham. ____________________________________ Share and comment my fan's. *UMMU NASMAH CE✍🏻* *For more information 08147537180* [5/18, 7:34 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE📘* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *Page 17 to 18* "Hisham ka sani akan gaskiya ta nake aiki, kamar yadda ka buƙata za'a rufe Case ɗin Nameer ba kuma za'a tuhumi Tunde ba kamar yadda ka bukata, sai dai ban san wani aiki zaka bani ba, idan har babu cutarwa a ciki ƙofata a buɗe take." Kallon Dpo Hisham yayi kafin ya saki numfashi yace. "Yarinyar nan wannan ƴar tashar da ta sanya ku kama Nameer nake son kuje ku kamota ina zaune ina jira ku jefata cell yayin da kuka fitar da Nameer wannan shine aikin da zaka min Dpo." "Ban fahimta ba Hisham ta yaya zamu kamata bayan bamu da hujjar yin hakan ka sani doka ce baza'a kama mutum ba har sai da hujjar da take nuna yayi laifin da za'a kamasa ita kuma wannan yarinyar bata da wani laifi." "Ita kuwa take da laifi ko sanya bakinta wajen yiwa Nameer ƙazafi wannan ma babban laifi ne kuma idan mun so zamu shigar da ƙara akan hakan kuma dole ku amsa, bar wannan ma tunda nace a rufe wannan babin Case ɗin, ni ina da cikakkiyar hujjar da za'a kamata domin kuwa naje mata da cin hanci kuma ta amsa har Naira miliyan biyar a hanuna da zummar zatazo ta ƙaryata kanta, wannan babban laifi ne a dokan ce sannan hukuncin wanda yayi wannan kora ne daga wajen aikinsa, ta muku furucin cewa zata iya sawa ku rasa aikin ku, to wannan kalmar zata dawo kanta domin kuwa ita zata rasa aikinta." Yayi Maganar yana amsar wayar Sadiq ya kunna recording ɗin ya miƙawa Dpo amsa Dpo yayi kafin Hisham ya cigaba da cewa. "Wannan shine shaidar gani da ido naje na gwada muku gaskiyar ta ne ta yadda zaku fahimci wacece ita ba tasan ina da hujjar da zan saka a saki Nameer ba, nayi hakanne saboda ku san wacece ita dan haka hukunci yana gareku." Numfashi Dpo ya saki yana duban video ɗin murmushi ya saki tare da cewa. "Mutum mungun ice, Hisham ko da baka nemi na kama Jidda ba, dole ne a kamata bara a kira Sargent Dogo suje suyi arresting ɗin ta, ina kuka baro ta.?" "Tana can ofishin su, sannan a taho min da kuɗina." Waya Dpo ya ɗaga ya kira Sargent Dogo babu jumawa kuwa ya shigo umarni ya basa da ya haɗa Police Uku suje suyi arresting ɗin Jidda, a office ɗin su sannan su taho da kuɗin da aka bata." Sarawa Dpo Sargent Dogo yayi tare da furta. "Yes Sir." Yayi Maganar yana ficewa, takaddar belin NAMEER Dpo ya bawa Hisham. *********** Jidda tunda ta fita daga office ɗin take tsaye a waje duk sai taji babu daɗi ta gwammace da bata amshi wannan kuɗin ba, zuciyar ta sai ayyana mata take taje ta mayar masa da kuɗinsa, juyawa tayi zata shiga office ɗin nata da niyyar ɗaukar kuɗin taje ta mayar wa Hisham taji kuwwar motar Police a bakin ofishin Jaridar tasu, juyawa Jidda tayi tare da tsayawa tana nazarin me kuma ya kawo Police wannan office ɗin. Sargent Dogo ne suka shigo su Uku basu kula Jidda ba duk da Sargent Dogo ya ganta, darect ofishin shugaban nasu suka shige yana zaune suka shigo, miƙewa Manager yayi cike da mamaki yace. "Yallabai lafiya kuwa."? Sargent Dogo ne yace. "Lafiya bata cika kawo mu ba, amma da zaka bamu dama zamu sanar da kai abinda ya kawo mu." "Ina sauraronka meke tafe daku." Sargent Dogo wayar Sadiq ya miƙawa Manager bayan ya kunna video record ɗin, nutsuwa Manager yayi yana kallon videon wani irin ɓaci ransa yayi Jidda da suke yiwa kallon mai ƙwazo da gaskiya yau itace take neman ɓatawa ofishin su suna ta rasa inda zatayi almundahana sai a ofishin su, numfashi ya saki cikin ɓacin rai yace. "Kuje ku kamata zanzo office ɗin naku yanzu." Manager yayi Maganar cikin tashin hankali domin kuwa yasan wannan video ɗin ya fita jaridar su ta gama yawo, fita sukayi daga office ɗin Manager har yanzu Jidda tana tsaye har Basmah ma ta fito Sargent Dogo a gabanta ya tsaya tare da cewa. "Munzo mu tafi da ke ne.?" Zaro idanunta Jidda tayi zuciyarta ta tsinke tace. "Whatt! Ku tafi kuma laifin me na aikata.?" "Idan munje zakiji umarni ne aka bamu mu tafi dake office." Kanta Jidda ta ɗaga ta kalli Basmah kafin tace. "Basmah karki sanar da Umma abinda yake faruwa ko da ban dawo ba." Tayi Maganar tana shigewa gabansa Yar sanda mace ce ta rufa mata baya, Basmah shuru tayi cikin tashin hankali wani irin laifi Jidda zatayi wanda har za'a kamata bata shiga harkar kowa ba'a taɓa rabata faɗa da wani ba. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!." Shine abinda Basmah ta furta cikin tashin hankali marar misaltuwa. *********** Ko da suka isa Police station ɗin Sargent Dogo da kansa yaje ya sanarwa Dpo sun taho da ita, bayan sun gama tattaunawa ne da Hisham tare da alƙawarin da Hisham ya yiwa Dpo na zai sakar masa da Hajara muddun ya rufe masa Jidda na tsawon kwana Uku babu beli, yayi Maganar yana sakin murmushi tare da miƙewa Dpo shima miƙewa yayi suka fito tare, Jidda tana tsaye cikin tashin hankali taga Hisham da Dpo idanunta Jidda ta zaro tare da furta. "Kaine!?" Dariya Hisham ya yi tunda take ganinsa bata taɓa ganin yayi dariya ba sai dai murmushi sai gashi yanzu yana dariya. "Yeah ni ne kinyi mamaki ne ko kin manta Ungulu bata jimar banza kina zaton zaki taka Hisham ne ki taka banza, ba'a taɓa ja da Hisham aci bulus ki shiryawa kare kanki domin kuwa nayi alƙawarin tozarta rayuwarki." Nameer a zabure ya miƙe jin furucin Hisham yana mamakin me Jidda tayi aka kawota nan. Bakinta Jidda ta cije tare da cewa. "Kayi nasarar jefani cikin tarkonka Hisham amma ka sani wannan shine mafi girman kuskure da kayi a rayuwarka." Shima murmushi yayi yayin da Dpo da kansa ya buɗe Nameer kusa da ita Hisham ya tsaya daf har yanzu bakinsa na ɗauke da murmushi. "Na faɗa miki bazan waiwayo gareki ba har sai NAMEER ya fita daga komar hukuma, idan Banda ke jahilace wawiya marar lissafi, an faɗa miki Hisham zai nemi taimakon ƙaskantacciya irinki ne, bari kiji wannan abin da na miki yanzu ƙofa na ƙwanƙwasa miki ba'a buɗe ƙofar ba tukunna kin sokeni a ƙirji kuma na faɗa miki idan na tashi sukanki a ƙahon zuciyar ki zan sokeki, wannan jifan da na miki mutum biyu zai samu na farko ke da kuma mahaifiyar ki domin kuwa itama sai taji ciwo kamar yadda kika saka tawa Mahaifiyar taji ciwon rufe mata ɗa da kika saka akayi, wasan ya fara daga yanzu mu buga mu gani tsakanin ni da ke waye zai faɗi." Wani irin huci Jidda take sosai ranta ya hasala wato tarko Hisham ya ɗana mata da wadannan kuɗaɗen, zatayi Magana Manager ɗinsu ya shigo tare da katseta yana wurga mata takaddu guda biyu Basmah ce a bayansa cikin tashin hankali, idanunta sai zubar da hawaye yake duk abinda ya samu Basmah lallai itace sila. "Baki isa kin ɓata mana sunan ofishin mu ba, kin san girman laifin da kika aikata kuwa amsar cin hanci almundahana a office ɗin mu a matsayinki na ƴar jarida da kece zakiyi kira da a daina, wannan takaddun na korarki ne daga aiki mun koreki karki sake doso mana office bama bukatar ki." Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo daga idanun Jidda babu wanda zai yarda da ita ko mai zata faɗa, shikenan ta rasa aikinta ta rasa damarta ta rasa hanyar da take taimakon ahalinta yaya zasuyi da me zasuci abinci. Ɗagowa tayi ta kalli Hisham tare da girgiza kanta tace. "Kaji daɗi ko, kaji daɗi ka zuba ruwa a ƙasa ka sunkuya ka shanye amma na rantse kayi danasanin taɓa min aikina." Tayi Maganar dai-dai zuwaira na tura ta cikin cell ɗin murmushi HISHAM ya saki Nameer ne ya dubi Dpo tare da cewa. "Wai me kuke aikatawa ne haka macece fa ita akan me zaku tozarta ta, wannan ba adalci bane Hisham meyasa Meyasa baka yafiya Dpo ka bani belin ta." "Bazai yiwu ba domin kuwa bazataci banza ba, amanar ƙasarta taci dan haka dole a hukuntata, babu ruwanka a cikin wannan Case ɗin Nameer." "Da ruwana Hisham bazan zuba idanu ku wulaƙanta mace ba." Dpo ne yace. "Sorry Nameer ko da za'a ba da belinta ba yau ba." Numfashi Nameer ya saki tare ficewa a zuciye, hannu Hisham ya bawa Dpo sukayi musabaha, yana amsar kudaden sa kafin suka bi bayan Nameer shi da Sadiq. "Manager me kake bukata naga kamar kana da abin cewa?" Dpo ya jefa masa tambayar bayan fitar su Hisham. "Sunan Jarida ta, karta ɓaci dan Allah ka rufa min asiri kar aji wannan Case ɗin Please Dpo kasan ni bani da laifi, idan wannan video ya fita tabbas zan samu matsala." "Hakane Manager baka da laifi gaskiya ne insha Allah babu abinda zai faru zanyi magana da Hisham ɗin insha Allah zai goge video ɗin." "Na gode Dpo." Manager yayi Maganar yana hararar Jidda. Basmah kuwa sosai take kuka hankalinta yayi mungun tashi, Dpo ne ya kalleta tare da cewa ta fice tabar masa wajen cikin tsoro Basmah tabar wajen. Jidda tunda ta shiga cell ɗin ta haɗa kai da gwiwwa cikin matsanancin tashin hankali, idan Umma taji wannan labarin tasan hawan jininta sai ya tashi, hawaye ne ya biyo idanunta taja numfashi tare da furta. "Hisham! Hisham! Hmmm.!" Sai kuma ta daki bango da hannunta zuciyarta na tafasa tana jin wani irin haushi da tsanar Hisham. ************ Basmah a wajen station ɗin ta tsaya tare da kiran Ahmad tace yazo yanzu su haɗu a ƙofar gidan su, kafin ta katse kiran tana tare adaidaita sahu ta hau, yama rigata zuwa a tsaye jikin babur ɗinsa ta samesa, mai adaidaita ta biya kuɗinsa tare isowa wajen Ahmad yana ganinta ya tabbatar ba lafiya ba domin kuwa idanunta sunyi jajur alamun tasha kuka. "Basmah lafiya ko jikin Abban ne.?" "A'a Ahmad, Ahmad! Nasa Jidda a cikin masifa banyi zaton zata shiga cikin wannan balain ba, mai zan cewa ummanta me zan ce mata innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!." "Basmah ki nutsu ki tsayar da kukan ki faɗa min meke faruwa." Cikin shashshekar kuka take sanar da Ahmad abinda ya faru, numfashi Ahmad ya saki tare da furta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ashsha! Basmah garin yaya kika bata wannan gurguwar shawarar, kin san hakan babban laifi ne, a yanzu rayuwa ta sauya ba kowa bane yake yadda yayi taimako saboda zaka taimaki mutum ne sai shi kuma ya jefaka cikin masifa yanzu ina ranar wannan taimakon, yanzu tana can police station ɗin kenan.?" "Tana can ina cikin tashin hankali Ahmad bansan wacce irin masifa Jidda zata faɗa ba, nayi kuskure Ahmad ka kuɓutar da Jidda dan Allah." "Hmmm! Babban kuskure ma kuwa amma ita kanta Jidda tasan bazaki mata haka saboda ta tozarta ba, na tabbata zata miki kyakkyawar fahimta, yanzu bamu da damar da zamuje muyi belin Jidda dole ne sai ta kwana, gobe zanje Police station, yanzu abinda zai faru muje gidan nasu wajen Umman ni zan fahimtar da ita." "Amma Jidda tace bata son Umma tasan tana Police station hankalinta zai tashi tana da hawan jini." "Karki damu nasan yadda zan fahimtar da ita." Kanta Basmah ta ɗaga kafin suka nufi gidan su Jidda Basmah ce ta fara shiga ta samu Umma zaune cikin barandarta, amsa sallamar Basmah Umma tayi tana cewa. "Basmah kece yanzu bakije wajen aikin naku bane yau."? "Naje Umma ni da Ahmad zai shigo ku gaisa." Murmushi Umma tayi tace. "Ai sai kice min keda suruki na ne, kije ki shigo dashi Umma tayi Maganar tana ɗaukar hijabinta ta sanya a jikinta, da sallama Ahmad ya shigo suka gaisa Umma tace ya zauna a tabarma zama Ahmad yayi kansa a sunkuye. "Barka da rana Umma fatan mun sameki lafiya." "Lafiya lau Amadu ya aikin naka da can gidan naku." "Komai lafiya Umma." "Masha Allah! Allah ya muku albarka, Basmah yau ke kin tashi da wuri kenan kinbar ƴar Uwar taki a can."? Kanta Basmah ta sunkuyar ƙasa idanunta ya ciko da hawaye Ahmad ne yayi saurin cewa. "Umma dama ai munzo mu miki bayani dan gane da jiddan, amm Umma dan Allah ki nutsu ki saurare mu karki ɗaga hankalinki." Cikin tsinkewar zuciya Umma tace. "Amadu wani abunne ya faru da Jidda ko accident tayi ta mutu ne."? "A'a Umma ki kwantar da hankalinki babu abinda ya samu Jidda tana lafiya, kawai ƴar hatsaniyar da suka samu da wannan yaron ɗan gidan Iyabo HISHAM shine yayi report ɗinta a police station bayan an gano ƙazafi aka yiwa ɗan uwan nasa shine fa Police suka kamata, amma Umma ba wata matsala ba ce insha Allah gobe zanje nayi belinta, dan yanzu bazai yiwu su bani belinta bane da tuni mun dawo tare da ita amma insha Allah gobe zata dawo sai kuma musan yadda zamuyi mu kashe Case ɗin." Umma idanunta ta runtse tare da furta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati! Subahanallah! Tana Police station wato da nace ta cire hannunta a case ɗin bata cire ba, sanda ta jawo min masifa, da Jidda taji magana ta da wannan tashin hankalin bai sameta ba abinda nake kiyaye mata kullum kenan bata da gata ta daina shiga cikin rigimar da bata shafeta ba, Amadu yanzu goben zata dawo kana jin kuma case ɗin zai iya mutuwa, kai ɗan sanda ne ka taimaka min Amadu kuje gidan Alhaji Iyabo ku bawa yaron haƙuri idan ta kama ni naje da kaina ne ma sai naje." "A'a Umma ba sai kinje ba nima zan iya komai Jidda zata dawo insha Allah ki kwantar da hankalinki, Basmah ki zauna tare da Umma ni zanje asibiti sai na sanar da Mama abinda ke faruwa kar ta jiki shuru ki kula da ita." Kanta Basmah ta ɗaga tare da tashi ta raka sa waje tsayawa sukayi Basmah tace. "Ahmad baka sanar da Umma cewa ankori Jidda a aiki ba." "A'a bai kamata ta sani yanzu ba hankalinta zai tashi fiye da yanzu dan haka karki sanar da ita mu jira har mu kashe case ɗin tukunna ke dai ki kula da ita tunda kinga tana da hawan jini damuwa kuma shine first abinda yake tayar da hawan jini ki tabbatar bata shiga cikin damuwa ba, ni bara naje." "Shikenan zanyi abinda kace amma dan Allah gobe kayi belin Jidda da wuri." "Insha Allah! Ahmad yayi Maganar yana tafiya komawa ciki Basmah tayi cike da zullumi. _____________________________________ *Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ *FOR MORE INFORMATION 08147537180* [5/19, 9:19 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* _Ina miƙa sakon ta'aziya ta ga Hajiya Aisha Lawwali Allah ya jikan mahaifinki Alhaji Lawwali Isa Jalo Allah yasa can yafi masa nan yasa mutuwa ta kasance hutu a garesa idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da imani Allah ya karbi bakon cinsa._ *_bazan gajiya da jingina gareku ba JALALA FAN'S a duk inda kuke ina muku fatan alheri sharhinku yana isowa gareni._* _Kuyi hakuri jiya na samu mistake ɗin page, page ɗin jiya shine 15 to 16 ba 17 to 18 ba na yau shine zai kasance page 17 to 18 mistake na samu._ *FREE BOOK ONE📚* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 17 to 18_* Ciki Basmah ta koma gefen Umma ta zauna tayi shuru. "Basmah da yawan yara suna faɗawa cikin masifa saboda kujewa maganar iyaye da sukeyi a ko yaushe uwa takan nunawa ɗanta hanyar da zai samu nasara ne a rayuwarsa, babbar musibace kin bin maganar iyaye na tabbata da jidda taji maganata to tabbas da bata shiga wannan halin da take ciki yanzu ba hankalina yana tashe." "Kiyi haƙuri tabbas Jidda tayi kuskure amma na tabbata ita bata ɗauki hakan akan zai zamo mata matsala ba, ki yafe mata Umma ki yi addu'a Allah ya fitar da ita daga sharrin Hisham." "Ameeen Basmah amma duk wanda baiji bari ba zaiji hoho, ina mata addu'a Allah ya tsareta." "Ameeen Umma." Basmah tayi Maganar cikin sanyin jiki. *********** A parking space sukayi parking kafin suka fito tare dukkan su har Sadiq cikin falon suka shiga Abba da Ummi suna zaune yayin da Tutu ke kitchen tana abincin rana, sallama sukayi Ummi ta ɗago kanta ganin Hisham da Nameer yasa Ummi miƙewa da sauri. "Alhamdulillah! Nameer welcome." Tayi Maganar cikin farin ciki, shima Nameer cikin dariya ya tafi da gudu ya rungume Ummi. "Welcome Ummi nayi missing ɗinki." "Nameer kaine alhamdulillah! Allah na gode maka." Tayi Maganar tana sakinsa, zama dukkan su sukayi NAMEER ya dubi Abba yace. "Masha Allah! ABBA dama na faɗa muku mai gaskiya baya taɓa tozarta ba gashi na dawo ba." "Hakane Nameer, Hisham da wani hujja ka cire Nameer daga wannan haɗarin."? Murmushi Hisham ya saki tare da cewa. "Tunda ya fito ai zance ya ƙare." Hisham yayi Maganar a takaice yana tashi yabar wajen gudun kar Abba ya kuma jefa masa wata tambayar. Kasancewar Abba ba mutum bane mai yawan ƙwaƙƙwafi yasa shi basar da maganar cikin farin ciki suke hira har Sadiq. Tutu da ke cikin kitchen ne take jiyo tamkar Muryar Nameer, shuru tayi ta kasa kunne tabbas dai Muryar Nameer ɗin take jiyowa, da sauri ta fito tsayawa tayi turus tana kallonsa wani irin farin ciki ne ya lulluɓe mata zuciya, da sauri ta ƙariso kusa dashi. "Yaya Nameer hmmn alhamdulillah! Yaya Nameer ka fito Wayyo daɗi." Dariya Nameer yayi tare da ɗaga mata kai. "Na dawo Tutu kin rame da yawa ko dai fargaba na ne ya ramar da ke haka.?" "Yaya Nameer ai dole na rame gidan ne duk babu daɗi babu kai." "Gashi ai na dawo bara na haura sama nayi wanka 2days ban samu na watsa ruwa ba." "Shikenan sai ka fito." Tayi Maganar tana komawa kitchen Sadiq duban Nameer yayi yace. "Nima gida zan koma zuwa yamma in kun fito zamu haɗu." "Okay shikenan na gode Sadiq." "Ba komai." yayi Maganar yana yiwa Ummi sallama. A kwance ya tadda Hisham ya na famar zuƙar sigari hancinsa Nameer ya toshe tare da ƙarisawa da sauri ya wafce sigarin. "Haba Hisham haba dan Allah, ka min alƙawarin ka daina shan sigari amma kuma ka karya min alƙawarin Hisham why.?" Yayi Maganar yana take sigarin a ƙasa idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur Hisham ya ɗago ya kalli Nameer maganganun Jidda suna ƙara faɗo masa yaji zafi da ƙunar maganar. _Amma dai anyi faɗuwar baƙar tasa ko nace faɗuwar guzuma ƴa kwance uwa kwance, ka bada maza ina kurin ina barazanar shin ka fasa tozarta ni ne, Hmm andai ji kunya._ _kaji daɗi ko, kaji daɗi ka zuba ruwa a ƙasa ka sunkuya ka shanye amma na rantse sai kayi danasanin taɓa min aikina_ Da ƙarfi ya furta. "Har yanzu bata rusuna ba, har yanzu kuri da baki take min, ni ne take cewa zanyi danasanin taɓa mata aikinta, lallai sai na ƙasƙantar da rayuwarta ƙasƙanci mafi muni, sai na sanya mata tsorona wanda sai ta gwammaci ganin mahaukacin zaki da ganina." Tsuka Nameer yaja yana zama bakin bed ɗin. "Mtsss aikin banza yanzu duk wannan haukar da jan idon da kake akan Jidda ne, Hisham wai Meyasa kake biyewa ruɗin zuciyar ka ne, yanzu duk wannan tozarcin da ka mata bai isheka ba har akwai wani abinda kake shirin mata wanda yafi wannan muni da aikinta fa ka rabata, Hisham ka rabu da jidda ka dakatar da wannan faɗan haka ya isa." "Bai isa ba Nameer! Yanzu ma aka fara! Ka sani idan na yanke hukunci *KO KAINA BANA SAURARA* bazan ƙyaleta ba sai naga ƙarshen rashin kunyarta." "Shikenan Hisham karka fasa, ni kuma zan kareta domin kuwa ta shiga wannan Case ɗin ne akan gaskiyarta kuma ni ta burgeni domin kuwa ba ta goyon bayan zalunci, idan yaso idan ka ɗebo masifar ka haɗa harda ni." Bakinsa Hisham ya cije tare da cewa. "Hmmm! Bata goyon bayan zalunci kuma ta amshi rashawa, Hmm! Na fahimci tun farko baka ga laifinta ba ai ba sai ka sanar min ba, ina jin haushi da takaicin zuciyar ka da bata nuna maka masoyanka, kafi ɗaukar maƙiya a masoya, tirr." "Naji amma ka sani Hisham ba'a taɓa cin nasara akan maƙiyi ta hanyar zafin rai da hasala ka sani idan ka jawo maƙiyinka jikinka babu shakka gobe masoyinka zai zamo, HISHAM dan Allah na roƙeka a karo na biyu ka daina shan sigari dan Allah cuta ce gareka ka kiyaye lafiyarka Hisham bana ƙaunar ciwo ya kwantar da kai, domin kuwa sai na fika cutuwa." "Naji." Yayi Maganar a takaice, kansa Nameer ya kaɗa tare da ijiye wayoyinsa ya shiga wanka ya juma sosai a tollet ɗin kafin ya fito ya samu Hisham tuni har yayi bacci Kasancewar zafin da ake na damina yasa Nameer ko mai bai shafawa jikinsa ba turaruka kawai ya fashe jikinsa dasu kafin ya sanya boxer da vest ya kwanta a bayan Hisham, bai juma da kwanciya ba shima bacci ya kwashesa kasancewar gajiya da rashin samun bacci na kwana biyu da baiyi ba, Ummi jinsu shuru ya sata haurowa bedroom ɗin nasu da kanta gaba daya suna bacci murmushi Ummi ta saki cike ƙaunarsu zama tayi a gefen su tana zuba musu idanu. "A ko da yaushe na ɗaga idanuna na kalleku sai naji wani farin ciki marar misaltuwa, damuwata sai ta kau, kaine jigona Nameer rashin ka gareni zaizamo macewar farin ciki na, a duk sanda ka shiga damuwa nima ji nake tamkar zuciyata ta fashe kaine haskena Nameer farin cikin gidana, tun kana ƙanƙaninka kake kore duk wata damuwata baka taɓa bari wani ya ɗaga min yatsa sai ka karya wannan yatsar, ina jin farin ciki a duk sanda kake nunawa ɗan uwanka hanyar dai-dai, kaine control ɗin Hisham domin kuwa baka taɓa bari ya aikata ba dai-dai ba, ta yaya zan kasa sonka a cikin raina Nameer bayan kafi kowa ƙaunar ta ni da ƴaƴana, muddun ina numfashi bazan taɓa barin rayuwarka ta shiga cikin matsala ba." Ummi tayi Maganar tana sakin murmushi. Idanunta ne ya sauƙa akan karan sigarin da Nameer ya ƙwace ya kashe, numfashi ta saki tare da miƙewa ta ƙara musu ƙarfin Ac jin garin da zafi, kafin ta fice domin tasan Hisham ke shan sigari tayi faɗan tayi nasihar amma ya gagara, abun ya zame masa kamar masifa. ************ Da misalin ƙarfe 4 na yamma Tunde ya fito yana jiran su Mamabisola a parking space. Da shirin su na tafiya ƙauye Mamabisola da Wamimo suka fito duban Tunde Mamabisola tace. "Kayi sauri mana ka jamu mu tafi kar dare ya mana a hanya." "Ku shiga muje ai na fito nima." Yayi Maganar yana shiga motar, suma shiga sukayi har tunde zai ja motar kiran wayar Hisham ya shigo wayarsa. "Hisham kuma."? Ya furta yana kallon Mamabisola. "Ka ɗaga kiran muji meke faruwa." Kiran ya ɗaga tare da kara wayar a kunnen sa yana danna handsfree. "Ina jinka Hisham." Daga can Hisham daya ke zaune bakin bed Nameer yana kwance har yanzu bai tashi daga baccin ba yace. "Ka ƙara buɗe kunnenka da kyau domin kaji abinda zan faɗa maka da kyau." "Wai me ya faru ne Hisham."? "Kafi kowa sanin abinda ya faru, jifan da kuka yiwa Nameer ya faɗi ƙasa domin kuwa bai samesa ba, wai shin ance maka taɓa ɗan zaki wasa ne, ina neman mutuwa ne, kuma ka nema ka fara tseratar da rayuwarka domin kuwa nayi alƙawarin sai na baka kashinka a hannunka." Idanunsa Tunde ya zaro ya kalli Mamabisola kafin yace. "Me kake nufi Hisham ban fahimta ba."? Murmushi Hisham ya saki tare da cewa. "Zaka fahimta domin kuwa tsuntsuwar da kuka aikowa Nameer tana hannun Hisham sannan inda ka faɗo kayi waya da ita a gabana kuma na naɗi komai, kazo Amar garden ka sameni by 5:00pm idan ba haka ba zan tona maka asiri duniya tasan waye ku kai da wannan kakar taka lallai kazo ka sameni." Hisham yayi Maganar yana katse kiran bai jira amsar Tunde ba, a gigice Tunde ya kira layin Hisham, switch 📴 ya kashe wayar gaba ɗaya. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Mama kina jin abinda yake faɗi asirin mu ya tonu ya gane, Hajara ta tona mana asiri, Hmm! Meye abun yi Mama.?" Numfashi Mamabisola ta saki cikin tashin hankali ta furta. "Lallai idan har IYABO yaji wannan maganar to tabbas naji kunya domin kuwa bai san zagon kasan da nake masa ba, wannan yaron ya zamo min ciwon ido a rayuwata ya zamo wajibi na ɗauki mataki a kansa, abinda za'ayi mu fasa zuwa ƙauyen sai gobe kaje da gaggawa kaji mai zaice ni kuma zansa a min maganinsa." "Okay shikenan Mama ku fita daga motar bara naje wajen Oga Wale muyi shawara dashi domin kuwa bazan yarda naje wajen ni ɗaya ba." "Shikenan kaje Allah ya baka Nasara." Tayi Maganar suna fita daga motar da ƙarfi yaja motar yabar gidan wani irin tashi hankalin Mamabisola yayi, sai kaiwa da komowa take Wamimo ne tace. "Mamabisola Akwai matsala wannan yaron shiya kamata a kawar idan ba haka ba shi zai ga bayan mu." "Naga alamar haka Wamimo domin kuwa tuya muke muna mantawa da albasa, lallai dole ne Hisham ya mutu." "Ƙwarai kuwa mutuwa ce ta dace dashi ki barmin komai a hannuna ni zan nemi wanda zai kashe mana shi cikin sauƙi ba tare da an zargi kowa ba." "Hakan yamin duk yadda zanyi domin naga ƙarshen Hisham na rantse da sarkin da ya busa min numfashi bazan taɓa yadda na faɗi warwas ba sai dai muyi mutuwar kasko. ______________________________________ *SANARWA bazan dinga posting Asabar da Lahadi ba weekend ina da uzuri a wannan ranakun, duk weekend baku da posting.* _Share and comments my fan's🥰_ *UMMU NASMAH CE✍🏻* *For more information 08147537180* [5/20, 8:20 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* _Tnx for comments my fan's i love You so much🥰_ *FREE BOOK ONE 📚* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 19 to 20_* Mamabisola tayi Maganar cikin hasala da tashin hankali domin kuwa dukiyar Iyabo ba ƙaramin ƙona mata rai yake ba. "Haka nake so karki damu burunki sai ya cika, kiyi haƙuri mu koma ciki." Kanta Mamabisola ta ɗaga tana huci suka koma cikin falon nata. Gudu kawai Tunde yake shararawa a tsakiyar titi tamkar mashayin da yasha giya ya bugu, masu abin hauwa sai kauce masa sukeyi yayin da masu Allah wadarai akansa suna yi, ikon Allah ne kawai ya kawo Tunde shagon Wale parking yayi ya fito a fusace shi kansa Wale ganin Tunde haka sai da ya razana sa. Zama Tunde yayi yana huci dubansa Wale yayi yace. "Tunde lafiya kuwa meke faruwa.?" "Hmmm! Ina kuwa lafiya wale ina cikin tashin hankali da masifa.?" "Tashin hankali da masifa kuma Tunde, faɗa min me akayi.?" "Wale Hisham ya gano duk shirin mu ya gane mune muke musu zagon ƙasa, meye abun yi yanzu haka yace mu haɗu a Amar garden lallai ko ya tona mana asiri wayar da nayi ranar da Hajara a gabansa nayi." "Kaga idan har Hisham ya gano to tabbas bazai ƙyale ka ba, sai ya zamo barazana ga rayuwar ka, Hmm! Tunde kaje ku haɗun duk abinda zai faɗa maka marar daɗi to ka danne zuciyar ka, sannan Hajara taci amanar mu ya zamo wajibi ta mutu domin kuwa barinta babbar hujja ce ga Hisham zamu iya sa ko Nameer ya sanya Hisham ya goge wannan record ɗin saboda wawa Nameer muna nuna masa nadamar mu shikenan mun gama dashi, yaushe yace ku haɗu."? Numfashi Tunde ya saki yana dafe kansa yace. "By 5:00pm." "Okay to kaje babu abinda zai maka na cutarwa a yanzu ni na sani." "Okay shikenan amma hankalina ya tashi tabbas Hajara ta tafka babban kuskure kuma zata girbi abinda ta shuka, na tsani na buɗe idanuna na kalli Iyalan Iyabo suna cikin walwala, ka duba yanda suka sanu sukayi suna a duniya, ni kuma mahaifina har ya mutu babu wanda ya sanshi, haka IYABO ya barsa ya mutu a wulaƙance Wale bazan taɓa barinsu suyi nasara ba a rayuwar su ko ta halin yaya sai sun ƙasƙanta." "Hmmm! A hankali ake dukan ƙarfe har yayi laushi Tunde dan haka a juri zuwa rafi." "Bani ruwan sanyi nasha zuciyata hura take." Tunde yayi Maganar cikin matsanancin damuwa, tashi Wale yayi yaje ya kawo masa ruwan. ************ Tun biyar saura Nameer ya shirya cikin ƙanana kaya, ya fito Hisham dake zaune a falo shi da su Tutu da Ummi ne ya cewa Nameer. "Ina kuma zakaje haka, ka fito da key ɗin mota."? "Unguwa zanje." Tutu ne tayi carap tace. "Yauwa Yaya Nameer sauke ni a gidan su Samira." "Okay ɗauko mayafinki ina mota, Ummi bara naje yanzu zan dawo." "Allah ya dawo da kai lafiya amma dan Allah ka dawo da wuri tunda ka dawo dai kasan bamu zauna munyi hira ba ko, ina bukatar lokacinku dukkan ku." "Ba matsala Ummi insha Allah a gida zanyi sallar magaruba." "To Allah ya tsare." Da ameeen Nameer ya amsa yana fita, bai juma ba tutu ma ta biyosa a baya, da kansa Nameer ya tuka motar suka fita. Sunyi nisa da tafiya Nameer yace. "Farin ciki na, kinga yadda kika rame kuwa, ashe dai kina yina da yawa." Murmushi Tutu ta saki tace. "Yaya Nameer ai ba iya rama kawai nayi ba zuciyata ma so tayi ta buga gaskiya dai naga masifa, yauwa Yaya Nameer wai ina maganar mu ta kwana ne, ya kamata zuwa yanzu ace Soyayyar mu ta bayyana amma har yanzu banga alamun hakan a tattare da kai ba, Soyayyar da nake maka yaya Nameer ta wuce misali." "Na sani tabbas kina sona fiye da komai a rayuwarki Tutu, sai dai fa ki sani na faɗa miki idan lokaci yayi dole Soyayyar mu zata bayyana har yanzu akwai sauran lokaci tukunna." "Wani irin sauran lokaci meka rasa wanda zai hanaka Aure kana da kuɗi to meyasa lokacin baiyi ba.?" Tayi Maganar dai-dai sunzo kofar gidan su Samira, parking yayi tare da cewa. "Lokacin ne dai baiyi ba, bana son doguwar magana, kije idan na dawo ma karisa Maganar." Kanta Tutu ta kaɗa tare da cewa. "Shikenan zan jiraka kazo ka ɗaukeni." "Okay." Yayi Maganar Tutu na fita motar ya yiwa key tare da shan kwana yabar layin, darect kofar gidan su Jidda yayi parking, yaro ya hango ya kirasa tare da cewa ya shiga yace wa mamar Jidda tayi bako. Yaron ya ɗan juma da shiga kafin suka fito da Basmah har bakin motar Nameer ganin Nameer yasa Basmah razana tare da zaro idanunta a tunaninta yazo ne shima ya ciwa Umma mutunci cikin nauyin baki Basmah tace. "Kaine! Kazo ne kaima ka rama abinda Jidda ta maka, Umma tana da hawan jini dan Allah na rokeka, karka ɗaga mata hankali ka dubi darajar mahaifiya ka kalleta a matsayin uwa dan Allah." Murmushi Nameer yayi yace. "Ko ɗaya ni banzo na ɗagawa wani hankali ba, ina son ganinta zanyi magana da ita." "Shikenan muje." Basmah tayi Maganar tana yin gaba Nameer yabi bayanta, a baranda Basmah ta shinfida masa tabarma kafin ta shiga ta yiwa Umma magana babu jimawa suka fito tare da Umma, a bakin kofa umma ta zauna cikin girmamawa Nameer yace. "Barka Umma ina yini." "Lafiya alhamdulillah! Basmah ta ce min kaine wanda Jidda tasa aka kulle ko, kayi haƙuri ina baka hakuri Jidda yarinya ce, tayi hakanne bisa kuskure duk da bansan meya kawo ka wajena ba amma banga tashin hankali a tattare da kai ba." "Hakane Umma ni sam banga laifin Jidda akan kamani da akayi ba, nasan tayi komai ne akan gaskiyarta, nima zuwa nayi na baku haƙuri akan abinda ɗan uwana yasa aka mata ba kulleta bane matsalar aikinta da yasa ta rasa, saboda nasan insha Allah gobe ina zuwa Dpo zai saketa, kiyi haƙuri Umma insha Allah zan samowa Jidda aiki mai kyau wanda yafi wanda ta bari." Idanunta Umma ta zaro tace. "Bayan kamata da yasa akayi harda aikinta yasa ta rasa yanzu an kori Jidda daga wajen aiki innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Wannan ɗan uwan naka yana da zuciya kuwa a ƙirjinsa, kasan mutum nawa aikin Jidda yake taimakawa kuwa, itace ci da sha na gidan nan, ita komai na makarantar ɗan uwanta suturar da muke sawa a jikinmu duk da aikinta muka dogara meye ribarsa idan ya toshe mana hanyar ci da sha ɗinmu, ashsha wannan yaro bai kyauta ba, amma babu komai bakin da Allah ya tsaga bazai hanasa abinda zai ci ba Allah ya shiryesa." "Umma Hisham ba mutumin banza ba ne, zuciyar sa ne tayi yawa amma bayan haka ɗan uwana mutumin kirki ne, zuciyarsa na hasala akaina muddun za'a ɗaga min yatsa to wallahi Hisham bazai iya riƙe kansa ba, na ji daɗi da kika masa addu'ar shiriya, ki ƙara hakuri gobe ƴarki zata dawo kuma insha Allah kamar yadda na faɗa zan sama mata aiki mai kyau." "Bakomai Allah ya mana mai kyau kaima Allah ya maka albarka." "Ameeen Umma." Nameer yayi Maganar yana ciro kuɗi dubu hamsin a aljihun sa ya ijiye a gaban Umma Basmah dai tana zaune tayi shuru ga damuwa da tunanin abbanta. "Ga wannan Umma kwayi wata bukatar da ita." Kanta Umma ta girgiza tace. "A'a yaro ka barshi bama buƙata muna da komai." "Ba'a mai da hannun kyauta baya Umma ni ma ɗanki ne ki amsa kimin addu'a albarkar ku ita muke bukata." Wani irin kaunar Nameer Umma taji take taji ya burgeta domin kuwa da alamu yaron yana da dattako da mutunta na gaba dashi murmushi Umma tayi tace. "To na gode sosai Allah ya saka da alheri, Allah ya maka albarka." "Yauwa Umma haka nake so ameeen na gode ni zan koma." "To ka gaishe da mutanen gida." Tashi Nameer yayi ya fita cike da farin ciki da ƙaunar Umma matar sam bata da hayaniya ko kaɗan matar kirki tabbas wannan ƴaƴanta sunyi sa'ar samun uwa ta gari. Basmah har bakin motarsa ta rakasa. "Nameer mun gode sosai nayi zaton kamar yadda Hisham yake kaima haka kake sai gashi kunyi banbanci sosai kai mutumin kirki ne na gode sosai da kulawarka garemu dan Allah ka dakatar da faɗan dake tsakanin Jidda da Hisham." "Hmmm! Karki damu Basmah insha Allah komai zaizo ƙarshe, shima Hisham mutumin kirki ne zafin zuciya ne kawai ya masa yawa, wanda yake zaune dashi kullum shi zai faɗi waye Hisham." "Hakane mun gode." Murmushi Nameer yayi dubu talatin ya ɗauka ya bawa Basmah, amsa tayi cikin farin ciki tana godiya tana kallon Nameer yaja motarsa yabar ƙofar gidan, murmushi ta saki maganar Jidda ne ya faɗo mata a rai _Insha Allah Basmah Allah zai mana zamu samu kud'in aikin da za'a yiwa Abba."_ Numfashi ta saki ta koma ciki ta nunawa Umma kuɗin murmushi Umma tayi ta ƙara mata dubu ashirin tace ta haɗa aje a yiwa Abba aiki sosai Basmah taji daɗi, sun juma sosai a wajen suna zancen kirkin Nameer. ************* 5:14pm Zaune Hisham yake a Amar garden shida Sadiq, Motar Tunde tayi parking a parking space, Cike da zullumi Tunde ya fito yasan babu inda Hisham yake zama sai wajen coffee nan ya nufa kamar yadda yayi zato kuwa haka ya samu yana wajen, da ke zuciyarsa yayi ya nufi teburin da suke, zama yayi a kujerar da babu komai hannu ya miƙawa Hisham. "Ƙazanta ne bawa hannu mai datti hannu mai tsafta, Tunde good job." Murmushi Sadiq ya saki yace. "Good Tunde gaskiya ka yi bazata da yawa amma abun mamakin Tunde kana zaton zaka wurgawa zaki Dutse ya samesa, mtsss! Kayi kuskure Babba." Murmushi Hisham ya saki yace. "Maybe ya manta ne, amma yanzu zan tuna masa da Zaki zai yi faɗa, kai ɓarawo ba iya satar ka iya ba kenan harda tuggu, da naso da na tona maka asiri Tunde ta hanyar kunnawa Abba wannan record ɗin, sai dai bazanyi haka domin kuwa bana bukatar ɗagawa Abba hankali a yanzu, amma fa ka sani dole ne wannan video record ɗin yaje ga Abba, Saboda zan sanar dashi ne ta hanyar da hankalinsa bazai tashi ba, saboda yasan waye ku ƙazantar da kuke rufe masa zai bayyana kasan meyasa na kiraka saboda na baka saƙo ka kaiwa wannan tsohuwar kakar taka, kace mata Lulluɓin biri zai yaye ta fara neman hanyar tsira domin kuwa asirinta ya kusa tonuwa." Wani irin suya da raɗaɗi zuciyar Tunde ke yi, bakinsa ya buɗe yace. "Hish............ Mari Hisham ya ɗauke sa dashi bai dasa aya ba yace. "Karka kuskura ka ambaci sunana da wannan ƙazamin bakin naka, ka sani bana bukatar jin Muryar ka a nan, kuma ka tuna da wannan ko wani Aji akwai malaminsa sai dai amma Malaman suna suka tara, wani malamin hoti ho ne baya sanin ana kallon sa, kaje ka faɗawa Tsohuwar kakar ka, malamin zamani yazo ta shirya sauyawa wannan tsohon malamin Aji, ka ce mata komai gudunta bazata kamo gobe ba, dole sai ta jira yazo da kansa, mu gobe ne munfi ƙarfin yau, kowa da burinsa, haka zalika muma da burin mu, ku naku burin shine ganin bayan mu, yayin da mu namu burin shine mu tunbatsa a duniya labarin mu ya zaga ko ina, baku isa kuma ku toshe wannan hanyar ba dole ku kallemu ku barmu ko baƙin ciki ya zamo ajalinku, ka faɗa mata cewa shuka take a idon makwarwa tar Hisham yake kallonta da idanunsa, tashi ka fece ko na karya maka muƙamiƙinka ɓarawon banza." _____________________________________ Share and comments my fan's🥰 *UMMU NASMAH CE✍🏻* _For More Information 08147537180_ [5/23, 7:31 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE📚* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 21 to 22_* Tunda Tunde ya dawo ya sanar da Mamabisola abinda ke faruwa hankalinta ya kuma tashi damuwarta ta ƙaru sai kaiwa da komowa take ta kasa samun nutsuwa, hankalinta duk a kaɗe ta wacce hanyar zata toshe wannan ɓarakar meyasa Hisham yake son ya shiga rayuwarta ne, numfashi ta saki tare da samun waje ta zauna. "Tunde lallai Hisham zai zamo karan da zai tsokale mana ido muddun mukayi wasa." "To amma Mama ya kike ganin zamuyi kar fa asirin mu ya tonu shi nake tsoro." Girgiza kanta Mamabisola tayi tace. "Ka daina jin tsoron yau muji tsoron gobe kamar yadda ya faɗa saboda bamu san da me zata zo mana ba, tunda har Hisham ya fita daga Police station bai tona asiri ba to a wannan wasan ruwa tasha, bazai fasa wannan ƙwan ba, ka bari zansan yadda zamuyi dashi kafin ƙwan yayi wari zamu aikasa shida hujjar gaba daya, yaro ne shi bai san wuta ba sai ya taka." "Amma dai Mama karki ja lokaci muna bukatar ɗaukar mataki akan Hisham da gaggawa, saboda matsala ne shi a garemu yasan abinda muke shirya musu." "Karka damu tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya sai ayi dubu ba'a fito ba dani yake zancen." Tashi Tunde yayi yace. "Okay shikenan." Yayi Maganar yana barin falon, da kallo Mamabisola ta bisa cike da ƙaunarsa tanayin komai ne saboda shi. *********** Washegari da misalin 12 na rana motar Nameer tayi parking a police station ɗin, har ciki ya shiga cikin Sa'a kuwa ya samu Dpo yana nan waje hannu ya basa sukayi musabaha suna dariya. "Ɗan sanda abokin kowa." Cewar Nameer murmushi shima Dpo yayi yace. "Nameer Abdulzahir jiya akayi belinka yau har kazo belin wata." Dariya Nameer yayi yace. "Harma ka fuskanci abinda yake tafe dani kenan, to Allah yasa dai za'a baka belin nata amma Dpo ni fa a nawa tunanin Hisham shiya yaudari yarinyar nan ta iya yiwuwa gadar zare ya ƙulla mata, kasan halin Hisham zai iya aikata komai domin ganin ya tozarta yarinyar nan da zaka min alfarma tunda babu wani na sama da kai da yasan wannan Case kawai a rufe Case ɗin ya zamo baya da file a cikin Police station ɗin nan saboda hakan tamkar ɓata mata suna ne." Girgiza kansa Dpo yayi. "Impossible a rufe file ɗinta, because an riga da an buɗe zan baka belinta amma dole zamu cigaba da bincike a kanta wannan shine abinda zan iya yi maka." Murmushi Nameer ya saki wai Police ne zai cigaba da bincike akan rashawa. "Dpo in dai akan rashawa ne bai kamata aji bakin ku ba saboda kune kukafi kowa cin hanci da rashawa a ƙasar nan, sorry amma ka sani dole ne za'a rufe file ɗinta, ni ba Hisham bane komai da lissafi nake yinsa, kasan me da ace Hisham kuka rufe na rantse da Allah bazai kwana ba domin kuwa ni nafi Hisham basira da lissafi nake komai iya basirar Hisham a neman fitar dani wajen commissioner of police kawai ya tsaya amma ka sani akwai baban commissioner Minister governor da sauransu, shi kansa Abba bai so fitar dani bane saboda gudun abinda al'umma gari zasu faɗa akansa sannan yasan ina da gaskiya dole zan kuɓuta bawai dokar banza ta gwamnati bane tasa ban fito ba, amma ka sani a wannan karon file ɗin zai rufu ba kuma za'a ƙara buɗesa ba har abada." Murmushi shima Dpo yayi yace. "Okay shikenan a rufe file ɗin mu gani na baka nan da 24hr." Bakinsa Nameer ya taɓe yana girgiza kansa tare da kallon agogon dake saƙale a hannunsa. "No 10minute 24hrs is over, hmmm bara muga." Nameer yayi Maganar yana ɗaga waya ministan Jiha ya kira ringing ɗaya ya ɗaga bayan sun gaisa Nameer ke sanar dashi abinda ke faruwa da kuma bukatar sa, kafin suka katse kiran, bai 5minute ba da katse kiran commissioner ya kira Dpo tare da umarnin a rufe Case ɗin Jidda a sallameta, Dpo yaso magana amma commissioner ya hanasa magana numfashi Dpo ya saki yana kallon Nameer shi kuwa Nameer murmushi ya saki tare da miƙewa tsaye yana cewa. "Na faɗa maka ni ba Hisham bane da zan dage wajen neman alfarmar ka, dama ɗaya kawai nake bawa Mutum a rayuwarsa da zarar yayi wasa da wannan damar zanbi ta kansa na shige gargadi ne wannan Dpo, nafi Hisham tsauri zafin zuciya kawai ya fini da gaggawa, kuje ku sako yarinyar mutane." Cikin ɓacin rai Dpo yaje ya buɗe Jidda dake zaune tana sauraron su a cikin cell, domin kuwa a bakin cell suke tsaye, fitowa Jidda tayi a kwana ɗaya har ta faɗa idanunta kuma sun zurma bata jira Nameer ba ta fito waje tana fitowa Ahmad yana shigowa da babur ɗinsa numfashi Jidda ta sauƙe tare da nufar Ahmad da sauri, tsayawa tayi gaban babur ɗin daya kashe. "Ahmad ina Ummana tayi fushi dani ko, Allah yasa bataji labarin na rasa aikina ba, bazata iya jurewa hakan ba, Allah yasa baku faɗa mata ba, Hisham ya cuceni Ahmad ya min mungun illa bazan taɓa kyalesa ba wallahi sai ya girbi abinda ya shuka." Gyara tsayuwar sa Ahmad yayi yana kallon Jidda kafin yace. "Waye yayi belinki.?" "Ni ne nan." sukaji muryar NAMEER daga bayansu juyowa Ahmad yayi duk wanda yake cikin kwara state kuma yake ganin gidan tv to tabbas yasan Nameer ko da kuwa bai taɓa kallonsa a zahiri ba. "Nameer Abdulzahir Iyabo, Barka amma nayi mamaki ace ɗan uwanka shine yasa ta cikin wannan halin amma kai kuma kazo ka fitar da ita duk da itace tayi sanadiyar shigarka cell, hmmm! Sorry da tambayar da zan maka Nameer meyasa kayi belinta."? "Bani da amsar tambayar ka saboda nima bansan dalilin ba, Jidda muje na mayar da ke gida saboda na yiwa Mahaifiyar ki alƙawarin cewa zan dawo mata da dake a wannan lokacin." Juyowa Jidda tayi cike da mamaki tace. "Ummata ka yiwa alƙawarin zaka dawo mata dani gida, kunje gidan mu ne kun gwada mata rashin mutuncin ku, meya kaika gidan mu, Meyasa zakuje ku ɗagawa mahaifiyata hankali meye laifina saboda na nemawa talaka ƴar uwata ƴanci, meye laifin hakan, anfi bukatar a tozarta talaka ne saboda shi talaka bashi da ƴanci meyasa yawancin masu kuɗin mu azzalumai ne marassa iman........... Bata ƙarisa ba Nameer ya katseta cikin tsawa mai firgitarwa. "Ya isheki haka! Nima ɗin talaka ne kamarki, wataƙila ma ke kin fini wadata tunda har kina da aikin yi a wannan lokacin, Masu kuɗin mu ba duka suka haɗu suka dawo azzalumai ba, akwai na gari a cikin su, domin kuwa ni Alhaji Iyabo yamin sutura a rayuwata, iyayena ƙasƙantattun talakawa ne marassa gata da ƴanci a rayuwa wadanda abinda zasu saka a bakin su ma yake gagararsu, wannan mai kuɗin shine yamin riga da Wanda domin ya suturta rayuwata, karki sokesa Jidda gara ni ki sokeni sunmin hallacin da babu wanda ya taɓa minshi a rayuwata ciki harda jinina, domin kuwa ya ɗaukoni ya sani a jikinsa ya mai dani ɗan da ya haifa a cikin sa dani da Hisham bamu da banbanci a wajensa." Gabaki ɗayansu shuru sukayi musamman Jidda da tayi suman tsaye tsabar mamaki da ƙin yadda da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, cike da mamakin tace. "Kai ba ɗan Abdulzahir Iyabo bane, me kake son faɗa min Nameer.?" Kansa Nameer ya ɗaga mata idanunsa na ƙoƙarin ciko da hawaye ya dubi Ahmad yace. "Ƙwarai ka ijiye Babur ɗinka muje na baku mamaki Ahmad." Mashin ɗin Ahmad ya yiwa key tare da duban Jidda yace. ''yana da kyau muje mu saurari labarinsa Jidda domin kuwa na kaɗu sosai da jin Nameer ba ɗan Alhaji Iyabo bane." Kanta Jidda ta kaɗa tare da bin bayan Nameer motarsa suka hau ya Nameer ya jasu har unguwar Ile-Ire unguwa ce ta talakawa sosai infact ma kamar ƙauye haka unguwar take yawancin gidajen unguwar irin gidajen lakan nan ne na da can wasu gidajen ma babu gini sai rufin langa-langa, wani dogon layi sukabi mai yawan kwatoci, a ƙofar wani tsohon gida na laka rabinsa duk ya rushe fitowa sukayi Nameer ya musu jagora har cikin gidan, wani ƙaramin dakali da yasha ƙura Nameer ya kaɗe da kansa suka zauna gabaki ɗayansu kallon gidan suke ita Jidda tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin tsohon gida lalatacce irin wannan ba. Nameer numfashi ya saki tare da dubansu mamaki ya hango ƙarara a idanunsu. "Kuna mamakin wannan gidan ko, shine gidan mahaifina a nan aka haifeni anan na fara rayuwata bari na baka labarina yadda zaku fahimci cewa Alhaji Iyabo wato Abbana yamin Rana a rayuwata. *_SHEKARU 27 DA SUKA GABATA_* Ruwa ake sosai tamkar da bakin ƙwarya garin duk ya narke yayin da Ruwan ke tafiya da iska, zaune nake takure a gefe yayin da ɗakin mu ke yoyo kwanon ɗakin duk ya huje gefen gabar ɗin ɗakin mu yafi ko ina yoyo kwano Mamana tasa take tare ruwan dubanta ta mayar gareni da nake takure tace. "Babana yunwa kakeji ko, kayi haƙuri bari Babanka ya shigo muga me zai dawo dashi bani da abinda zan baka Babana kayi haƙuri kaji." Kaina na kaɗawa Mamanmu nace. "Mama yunwa nakeji sosai gashi Baba yaƙi dawowa, ni dai Mama ko garin rogo ne ki bani zansha ko ba Suger." Zama Mamanmu tayi gefena ta kamo hanuna tace min. "Babana bani da komai na faɗa maka nima raina baya jin daɗin halin da kake ciki na yunwa, kayi haƙuri kaji insha Allah yanzu baban naka zai dawo." "To Mama Allah ya dawo dashi lafiya." Nayi Maganar cikin sanyin jiki, yunwa kuma tamkar zata kasheni, hanjin cikina kuwa ji nake tamkar sun naɗe, ga feshin ruwa dake shigo mana bayan yoyon da ɗakin keyi kana kallon Mamana a wannan lokacin zaka fahimci tana cikin damuwa. Muna nan zaune Baban na ya dawo duk ya jiƙe jikinsa sai karkarwa yake yana layi, idanunsa sunyi ja, babu komai a hannunsa hakanne ya tabbatar min Baban mu bai dawo da komai ba, zuciyata ne ya tsinke domin nasan daƙyar idan ba da yunwa zan kwana ba, duk da nasan iyayena suna bakin ƙoƙarin su wajen ganin ban kwana da yunwar ba, ko da su zasu kwana da ita, zama yayi gefe har yanzu jikinsa rawa yake ko magana baiyi ba, Mama ne tace. "Baban Nameer lafiya kuwa, ya akayi ka bari ruwan nan ya dakeka haka, ka tashi ka sauya kayanka ko sanyin zai ragu maka.?" Kansa Baba ya girgiza cike da damuwa yace. "Ba sanyin bane damuwata Usaina abinda zaku ci shine damuwata kun wuni baku ci ba, bazai yiwu ku kwana baku ciba, ban samu komai ba nayi iya yina amma babu abinda na samu yau babu kasuwar Raken da ƙyar na sai da sanda ɗaya naira 70 kinga itace kawai a hanuna." Numfashi Mamana ta saki ta dubi Baban mu tace. "Kaga Baban Nameer kayi haƙuri INSHA ALLAH komai zai wuce rayuwar taƙaitacciya ce, kuma kaga ai ita kasuwa dama Sa'a ce idan ba'a samu ba yau gobe za'a samu, idan ruwan ya tsagaita, sai ka fita ka sayowa Nameer garin Hamsin Suger na ashirin, ya samu yasha yunwar ta damesa mu zamu iya haƙuri shi kuma yarone bai san babu ba." Kansa Baban mu ya kaɗa yace. "To Allah ya iyar mana." Ni dai ina zaune ina kallon su, shi kansa Baba kana kallon sa zaka fahimci shima yunwar yakeji amma haka ya danne tasa, kayan jikin nasa ya sauya yazo ya zauna kusa dani yana lallashi na, ko kafin a gama ruwan tuni har bacci ya ɗaukeni, sai ji kawai nayi Mama na tashi na nasha garin ashe har an gama ruwan Baba yaje ya sayo min, haka na tashi nasha garin da Mama ta jiƙa min ita kuwa da Baba haka suka kwana da yunwa. Washegari da safe ma da zan tafi makaranta Mama da kanta ta fita taje ta amso min bashin Taliya a wajen iya mai Taliya da Ɗanwake dake bayan layin mu ta samin a plast na tafi dashi makaranta. Ko da na dawo daga makaranta na samu Mama ta mana buragandu shi naci nasha ruwa, na fita wasa na, da la'asar lis Hajja Anti ta shigo gidan mu makwabciyar mu ce suna shiri sosai da Mama duk da ƙarancin shekaru na a wannan lokacin ina iya fahimtar wasu abubuwan, tazo ne tana sanar da Mama cewa akwai wanda take musu aiki ta mata magana ta cikiya musu ƴar aiki wanda zata dinga musu wanke wanke da shara kawai, shine taga halin da muke ciki tace ko Mama zataje ta dinga yi sosai hakan ya yiwa Mama daɗi sai dai bata amince mata ba tace sai ta sanar da Babana, akan wannan maganar sukayi sallama da Hajja Anti akan tana sauraran Mama. Ko da Baba ya dawo Mama ta sanar dashi ransa bai so ba, sai dai yadda Mama ta kafe da kuma hujjojin ta na amfanin da aikin zai mana yasa Baba amincewa, da wayar Baba Mama ta kira Hajja Anti take sanar da ita Baba ya amince, tace washegari zata zo suje wajen da Uwar ɗakin nata. ____________________________________ _Wannan littafin Book one Free, Book two ba Free bane Paid ne, to akwai Costomers ɗina da suka saba sayen Book ɗina sunce abasu account number zasu fara payment, so da 300 nace so amma duba da yadda ake ciki na tsadar rayuwa yasa na barsa a 200 ba ga Costomers ɗina ba har ga all fan's ɗina ga account number wanda yaga zaiyi payment_ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike, falyakum khairan auli yasmut._ *Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ *_For More Information 08147537180_* [5/24, 7:56 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. https://chat.whatsapp.com/JwLvHkW5qmbBQd6JEgDjMV Gashi masu cewa a saka su a group ɗin JALALA sai suyi joining mata zallah dan Allah Banda maza please kar namiji ya shigo dan Allah *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, sannan sorry akwai abinda na manta ban sanar da ku ba cewa akwai wacce ta bada rabin kuɗin Mutum shabiyar tace sadaka, an samu Mutum 8 sun ciko kuɗin dan haka kema ƴar uwata idan kina son shiga cikin wadanda zasu samu wannan sauƙi akwai sauran dama na Mutum 7 zaki iya cika Naira 100 kacal ki ganki a Paid group amma damar Mutum bakwai ne kawai ya rage idan kin samu kin shiga cikin wadannan Mutum bakwai ɗin to fine_ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut, siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai da kuma a baka labari gara ka bayar._ *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 23 to 24_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 Kamar yadda Hajja Anti tace Washegari da safe tazo ta ɗauki Mama da yake ranar weekend ne bamu da makaranta hakan yasa Mama kama hannuna muka tafi tare, bana mantawa a lokacin ina da shekara goma sha ɗaya ne a duniya aji na biyar a primary school dake nan unguwar Ora, duk da ƙarancin shekaru na ganin gidan da muka shiga sai da ya burgeni, sosai yamin kyau tunda muka shiga na fara tsalle ina cirar flower ɗin da sukayi ado dashi a gidan, Mama ce ta kamo hannuna tana zaro min ido tace. "Kul ka ƙara cira musu flower Babana sojaji zasu kamaka su maka bulala ka gansu can suna kallon mu ka bari kaji Babana ba kyau yiwa mutane ɓarna." Dubana na kai ga sojojin dake zaune bakin get ɗin, dama kuwa ni gwanine wajen tsoron soja, cikin sauri na ƙanƙame Mama har muka shiga part ɗin nasu muka shige babban falon gidan ban kuma taɓa wani abun ba, a falon muka zauna har lokacin ina maƙale jikin Mama, bamu juma da zama ba Ummi ta sauƙo daga sama, kana kallon matar zaka fahimci matar mutunci ne domin kuwa fuskarta a sake take, a kujera ta zauna tare da duban Hajja Anti tace. "Hajja Anti yau kece a gidan nawa, wata sabon gani, sannu baiwar Allah." Ummi tayi Maganar tana kallon Mama, cikin girmamawa Mama ta gaishe ta kafin Hajja Anti tayi dariya tana cewa. "Aunty Ramata kwana biyu sai a hankali, amma wallahi ina da niyyar zuwa na gaishe ki, ranan munyi magana da Aunty Luba take cemin kina son ƙarin ƴar aiki, to shine na samo miki wannan baiwar Allah, nasan zata iya abinda kike buƙata, na kira Aunty Luba take cemin na kawota kawai darect wajen ki idan ta miki sai a ɗauketa." Murmushi Ummi ta saki tace. "Eh tabbas munyi magana da ita ina bukatar mai goge goge da sharan falon nan, idan har kun yaba da halinta da tsaftar ta, to ai ni bani da matsala sai ta fara aiki kawai." "Ehh gaskiya bata da matsala ko kaɗan tana da tsafta sosai." Duban Mama Ummi tayi tace. "Baiwar Allah na ɗauke ki aiki dan Allah ki riƙe min amana, menene sunan ki."? Kanta Mama ta ɗago tace. "Insha Allah zaki sameni mai riƙe amana sunana Fatima amma ana kirana da Maman Nameer." Murmushi Ummi tayi ta kalleni hannu ta miƙo min tace. "Ayya wannan shine Nameer ɗin ko, zo kaji yarona." Sakin Ummi nayi na tashi naje wajenta akan cinyar ta ta ijiye ni da gudu na hango wani ƙaramin yaro ya fito daga wani room ya faɗa a jikin Ummi ko da ganin yaron nasan zan girmesa da wajen shekara biyu Ummi ne ta dubesa tace. "Kai HISHAM ina ka shige tun ɗazu lami na jiranka zata sauƙe ka a gidan Mamabisola."? Ransa Hisham ya haɗa cikin ƙunƙuni yana tura baki yace. "Ummi ni bazani ba babu inda zanje ni ball zanyi." Yayi Maganar yana kama hannuna yace. "Kazo muje muyi Ball, Abbana ya kawo min sabuwar Ball daga Indonesiya zo muje mu buga." Murmushi Ummi tayi cikin mamaki tace. "Ikon Allah lallai Nameer da Sa'a ka shigo gidan nan yau har Hisham ne zaiga baƙo bai masa hali ba yace suzo suyi wasa, to kaga Nameer kuje kuyi wasan kaji banda faɗa, kai kuma karka kuskura ka masa wani abun nasan halinka kaga ɗan uwanka ne, sunan sa Nameer." Dariya Hisham yasa yana tsalle yace. "Ummi ina sonsa bazan dakesa ba Ball zamuyi, mu tafi Nameer." Yayi Maganar yana jan hannun Nameer suka fita, da kallo Ummi ta bisu tana murmushi kafin tace. "To Maman Nameer zaki fara aiki yau falon nan da can ɗakin baƙi zaki dinga mopping sai wanke wanke kina iya farawa zamu baki dubu goma a wata 10k." Cike da farin ciki Mama tayi dariya tace. "Na gode sosai Hajiya kin taimakeni na gode." Murmushi Ummi tayi tare da tashi ta haura sama bata juma ba ta fito hannunta riƙe da kuɗi ta bawa Hajja Anti, anan Hajja Anti tabar mu ta tafi. Ƙarfe shabiyu na rana Mama ta gama aikin, a ɗan wannan wuni har sabo ya shiga tsakanina da Hisham tunda nazo bamu rabu ba, har sai da Mama tazo tafiya, sosai Hisham ya haɗa ransa yace sai ya bimu, da ƙyar da lallashi Ummi ta rarrashesa kafin muka koma gida. Ko da muka koma bayan Baba ya dawo Mama ta ke sanar dashi yadda sukayi a gidan aikin da albashin da za'a dinga bata sosai hakan ya yiwa Baba daɗi yasan komai yaya wata wahalar zata ragu. ************ Haka rayuwa ta dinga tafiya kullum sai Mama taje gidan aikinta yayin da shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Hisham, duk kuɗi da ikon su Hisham hakan baya hana wata rana ya biyo Mama ya kwana a gidan mu, haka duk weekend dani Mama take zuwa, sai ya zama Mama da Ummi suma suka shaƙu sosai, Ummi tana kyautatawa Mama dai-dai gwargwado, bana mantawa akwai ranar da mai gadin su Ummi na part ɗin su ya ijiye aikin, hakan yasa Mama neman alfarmar Ummi akan a ɗauki Baba ya maye gurbin mai gadin, babu musu Ummi ta sanar da Abba yace a kira Baba yazo suyi magana, ko da saƙon ya isawa Baba baiyi ƙasa a gwiwwa ba yazo a ranar da yazo shima Baba a ranar ya fara aiki, hakan tasa Abba bawa Baba wani ƙaramin part dake cikin gidan yace mu dawo da zama tunda aikin Baba na kwana ne, baiyi musu ba Baba duba ga Irin kyautatawar da suke mana. Numfashi Nameer ya saki tare da juyowa ya kalli jidda yace. "wannan shine dalilin da yasa muka baro wannan gidan muka komo gidan ALHAJI IYABO da rayuwa, ba iya nan labarin ya tsaya ba Ahmad. Ni sawa Ahmad yayi cike da mamaki yace. "Na matsu naji ƙarshen labarin ahalinka Nameer." Kanta Jidda ta kaɗa itama tace. "Tabbas rayuwar ka abar tausayi ce Nameer dole ka sakawa Alhaji IYABO da alkairi menene ya faru bayan dawowarku gidan Alhaji Iyabo.?" Numfashi Nameer ya saki ya cigaba da cewa. "Bayan mun dawo gabaki ɗaya Hisham sai ya tare a Wajen mu babu abinda yake mayar dashi part ɗin su sai har idan tare dani zamu shiga, Abba hakan sosai ya masa daɗi domin kuwa a yanda suka san Hisham bai taɓa aboki ba, asali ma duk yaron da yazo gidan korarsa yake amma sai gashi lokaci ɗaya Hisham yayi sabo dani, wannan dalilin yasa Abba yamin transfer daga Makarantar gomnati da nake ciki zuwa privet inda Hisham ke karatun aka ijiye mu waje guda, duk abinda zai taɓani Hisham baya so haka nima bana yadda wani ya ɗaga masu hannu, a haka rayuwar mu ta tafi har muka girma muka shiga jami'a komai namu tare yake tafiya duk wanda yasan Hisham to yasan ni, haka kuma ake min kallon ɗan Alhaji Iyabo domin kuwa ya maidani ɗansa komai tare yake mana haka Ummi duk abinda zata yiwa Hisham sai ta min wani lokacin takan hana Hisham ni ta bani amma hakan bazai sa Hisham yaji haushi na, ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwata itace ranar da muka wayi gari da mummunan tashin hankali ranar talata, ni da Hisham bamu kwana a part ɗin mu ba kasancewar Abba yace mu kuma wajen su, cikin dare wuta ta tashi a part ɗin su Mamana, wajen misalin ƙarfe 2 na dare, kwalala da ihun sojojin gidan shine ya tashi kowa dake cikin gidan, yayin da ake ta watsawa part ɗin ruwa sai dai ina tamkar ƙara hura wutar ake, har abin kashe gobara da Abba ya ijiye anyi amfani dashi amma a banza, hankalina sosai ya tashi bansan sanda hawaye ke zubowa daga idanuna ba, fire service aka kira ko da sukazo sukayi nasarar kashe wutar da sauri aka shiga part ɗin sai dai kash ƙaddara ta riga fata domin kuwa su Mama sun ƙone rai yayi halinsa nayi kuka tamkar zan bisu haka shima Hisham yaji mutuwar, ko wanka ba'a samu an musu ba kasancewar sun ƙone sai ruwa kawai aka yayyafa musu aka musu sallah, ranar babu wanda hankalin sa bai tashi ba da mutuwar su Baba, bayan anyi sadakar Uku, ne Abba da Ummi suka ijiye ni suka min nasiha sosai da nuna min mahimmancin haƙuri inda Abba yace min. (Baka rasa iyaye ba NAMEER kai mai iyaye biyu ne, muma iyayenka ne baka da banbanci da Hisham a wajen mu, bazamu bari kayi maraici ba duk gatan da uba zai nunawa ɗan da ya haifa zan nuna maka shi NAMEER ka cigaba da yiwa iyayenka addu'a Allah ya musu rahama.) Wannan Maganar ta Abba sosai tamin daɗi domin a lokacin da iyayena suka rasu ina da shekara ashirin ne a aduniya tun daga wannan ranar kuwa na cigaba da rayuwata a wajen Abba da Ummi da zuri'arsu domin kuwa dangin mahaifina babu wanda ya kuma nemana har sai da sukaga na kawo ƙarfi sannan suke nemana saboda ina da abinda zan basu, wannan shine tarihina. Kallon Jidda yayi ya cigaba da cewa. "Ki faɗa min Jidda ta yaya za'ace dukkan masu kuɗi azzalumai ne, Abba Mutum ne na gari kuma na kwarai." Numfashi Jidda ta saki. "Ƙwarai kuwa na yadda da maganar ka Nameer, kayi haƙuri bansan cewa Hajara sharri ta maka ba sai jiya da daddare Dpo ya faɗa min." "Ba komai Jidda nasan yanzu haka Umma tana can hankalin ta a tashe muje na sauƙe ku." "Nameer ina tsoron komawa Umma a wannan lokacin da wani baki zan faɗa mata cewa na rasa aikina, dashi muka dogara nasan dole hankalinta zai tashi." Murmushi Nameer yayi tare da cewa. "Karki damu Jidda Umma mutum ce mai tawakkali a kallo ɗaya da na mata, na kuma gama hukunci tunda Hisham yasa kikayi asarar aikinki ni zan baki babban matsayi a COMPANYN MU *_HISHAM RICE MILL LIMITED_* zaki samu salary sama da wanda kike ɗauka a aikinki na baya." Zaro idanunta Jidda tayi a firgice tace. "Whattttttt! Hisham rice mill limited, hmmm! Sorry Nameer bazan taɓa iya haɗa inuwa ɗaya da Hisham ba domin kuwa nayi rantsuwa da Allah sai na masa rashin mutuncin da bai taɓa cin karo dashi ba a rayuwarsa alkawari na ɗauka." ______________________________________ Like comments and share my fan's. _Jalala fan's kun rage comments ya dai ban fa gane ba wai shin bacci kukayi ne to dan Allah ku farka_ *UMMU NASMAH CE✍🏻* _for more information 08147537180_ [5/25, 7:55 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE📚* *_Page 25 to 26_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 "Ashsha haba Jidda banji daɗin wannan maganar taki ba, wannan faɗan naku ya kamata ya tsaya haka meye amfanin rigimar, fitina fa a kwance take meyasa zaku ta da ta, halinku yazo ɗaya da Hisham shiyasa bazaku taɓa daidaitawa ba, muje na sauƙeki." Ba tare da jidda tayi Magana ba ta shige gaba, bayanta sukabi motar Nameer ɗin suka shiga, a hanya Ahmad ya sauƙa shi kuma Nameer ya shige da Jidda har ƙofar gidan su yayi parking tare suka shiga cikin gidan da Nameer, Basmah ce kawai a tsakar gidan tana shara, ganin Jidda yasa Basmah tahowa da gudu ta rungumeta. "Alhamdulillah! Sannu Jidda." Murmushi Jidda ta saki tana kama hannun Basmah tace. "Ina Umman take.?" "Umma ta fita makwabta can gidan su Indo." Numfashi Jidda ta saki ta dubi NAMEER. "Umman bata nan, na gode Nameer, ka fitar dani daga cikin cell bazan manta da hakan ba." "Bakomai idan ta dawo kwa gaishe ta." Basmah ce tace. "Zataji insha Allah Nameer mun gode." Kansa Nameer yasa ya fice zama Jidda tayi bakin ƙofa Basmah ta ijiye tsintsiyar ta taho kusa da jidda ta zauna." "Har kunyar kallon idanunki nake, na miki laifi nine sanadiyyar faɗawa halin da kika shiga gashi kin rasa aikin ki, wallahi banyi da nufi ba, nayi ne saboda neman mafita na ciwon Abba da nasan tarko Hisham ya ɗana miki wallahi da bazan fara kuskuren saki ki amshi kuɗin ba." Murmushi jidda ta saki tace. "Karki damu Basmah ni nasan bazaki taɓa cutar da rayuwata ba, hmm! Abba mahaifi nima nake kallon sa zan iya komai domin ganin ya samu lafiya dan haka karki saka a ranki naji haushinki, ko ɗaya sai ma sonki da na ƙara ji a raina ƙawata ki kalli idona ki cigaba da faɗa min abinda ya dace dani a rayuwata, Basmah da Jidda abu ɗaya ne. Jidda bazata taɓa jin kunyar Basmah ba dan haka Basmah ma karta kuskura taji kunyar Jidda." Dariya Basmah tasa tare da rungume Jidda, tace. "Dama na sani Jidda bazata taɓa jin haushin Basmah ba, za'a yiwa Abba aiki." Cike da farin ciki Jidda. "Kai haba a ina aka samu kuɗin.?" "Nameer jiya da yazo wajen Umma ya bata 50k ni kuma 30k shine Umma ta cika kuɗin aikin tun jiya da daddare na kai kuɗin yanzu su muke jira su saka ranar da zasuyi aikin, Jidda gaskiya da alamu wannan Nameer ɗin yana da kirki yafi wannan Hisham ɗin." "Hmmm! Haka naga alamu amma har yanzu zuciyata bata amince dashi ba saboda mayaudara ne, dan haka karki kuskura kiyi saurin sakin jiki dashi, aikina kuma dana rasa karki damu haka Allah ya hukunta, shi kuma Hisham dani yake zancen zan bambance masa tsakanin aya da tsakuwa." "A'a Jidda dan Allah ki fita a harkarsa babu ruwanki dashi wannan fa ɗan tasha ne bazaiji kunyar wulaƙanta ki ba." "Mubar maganar Basmah domin kuwa bazan hanu ba, bari naje na watsa ruwa kafin Umma ta dawo." "Shikenan nima idan kin fito zanje asibiti na dubo Abba." "Shikenan bara na fito ɗin.'' ************ Lumshe idanunsa Hisham yayi yana zugar sigarin sa hankali kwance, shi kuwa Sadiq shisha ma yake zuƙa, yasar da karan sigarin yayi ya takesa, tare da sanya hannu ya ɗauki coffee ɗin dake gabansa a hankali yake kurɓar coffee ɗin. "Hisham da zan baka shawara da kaci nasara a yaƙinka tsakaninka da wannan yarinyar nasan maganar da ta faɗa maka a police station har yanzu shine yake damunka a ranka, duk nasan babu abinda ta isa ta maka, amma yana da kyau ka koyawa rayuwarta darasi." Ijiye coffee ɗin Hisham yayi tare da mai da kallonsa ga Sadiq yace. "Wacce irin shawara zaka bani ina jinka." "Hanya ce mai sauƙi Hisham, shi yaƙi ɗan zamba ne ba ɗan fito na fito ba, ba'a taɓa cin nasara ga maƙiyi ɓaro ɓaro, yaƙin sunƙuru yafi aika saƙo ga maƙiyi, yanzu fa zamani ya sanda a da ana yaƙi ne da takwabi amma yanzu zamani ya kawo bindiga idan har bindigar ma ta gagara, sai kawai a tashi bom." "Kasan bana fahimtar irin wadannan murɗaɗɗun kalmomin tafi kawai kai tsaye ka faɗa min abinda yake ranka." "Hisham ka yaudari yarinyar nan da zummar Soyayya ka tusa mata sonka a cikin ranta ta yadda zataji bazata iya rayuwa ba tare da kai ba, ina son Soyayyar ta kusa kaiku ga Aure ma'ana har rana asaka randa za'a ɗaura Auren kace ka fasa aurenta ka fito ka nunawa duniya cewa tana da cutar da ke karya garkuwar jiki, sannan ka saye dukkan likitocin garin nan ta yadda Maganar ka zata Tabbata, idan ka mata haka to ba dukan zuciyar ta kayi ba kasheta kayi, domin kuwa ba ita ba hatta ƴan uwanta sai baƙin ciki ya kusa kashe su." Waro idanunsa Hisham yayi tare da saki dariya har yana dukan teburin gabansa "Nice idea Sadiq tabbas wannan ce kaɗai hanyar da zan gama mata wulaƙancin duniya, bansan meye Soyayya ba amma wannan karon zan buga wasa da ita domin kuwa idan wasa akan maƙiyi ne ba ƙaramin daɗi yake min ba, ka zuba idanunka ka kalli yadda wasan zai fara." "Nasan zaka iya shiyasa na kawo maka wannan shawarar amma karka yadda kowa yasan Game kake bugawa a Soyayyar ta, ka nuna musu Soyayyar gaskiya ne, hatta Nameer dasu Ummi su ɗauka son na gaskiya ne, amma karka sanar da kowa har sai ta amshi tayinka." "Kana da basira Sadiq shiyasa nake son saka cikin lamurana, an gama." Yayi Maganar yana mikewa tare da ɗiban wayoyinsa yace. "Bari na shige Company sai mun haɗu da daddare." "Okay sai mun haɗun." Har Hisham zai fita Sadiq yace. "Sorry ya maganar yarinyar nan ne Hajara ya kamata ka bawa Dpo ita fa ta horu ai 5days tana rufe cikin duhu." "Anjuma insha Allah idan muka haɗu zamuje a fitar da ita wannan ya isheta darasi." "Okay limamin zamani mai hukunci da zamani." Sadiq ya masa kirarin yana dariya m Shima Hisham fita yayi yana dariya yabar Sadiq yana zuƙar shishirsa. Nameer daga gidan su Jidda gida ya dawo da yaso ya shige Company sai yaji bazai iya zuwa Companyn ba, babu kowa a falon Tutu ta tafi school Ummi kuma sun fita unguwa da drever, bedroom ɗin su ya shige tare da zama bakin bed ɗin ya dafe kansa, tun lokacin da sukaje wani program a Companyn Zeen global concept ya ga jidda tun lokacin hankalin sa ya koma kanta a ko da yaushe tunaninta yake yayi bincike sosai akanta ya tabbatar da a Aminci take, sati biyu da haɗuwar su a Zeen global concept, tazo gidansu da Police akayi arresting ɗin sa, numfashi ya saki tare da furta. "Wannan lokacin ya kamata na furta mata soyayyata itace macen da ya kamata na aura zuciyata ita take so, ya zamo wajibi na shiga jikin mahaifiyarta hakan zaisa Jidda ta soni." Ya furta yana lumshe idanunsa, wayarsa ce tayi ringing, Hisham ya gani hannu yasa ya ɗauki wayar. "Ya akayi."? Daga can Hisham yace. "Kana ina ne yazo office ɗin ka sakatariyar ka tace baka shigo ba kuma naga tun safe ka fita."? "Gani a gida na dawo kaina ke ciwo bazan iya shigowa ba, ɗazun station naje na amso belin jidda." "Whatt! Belin Jidda kuma, well shikenan ka samu kasha magani sai na dawo." Hisham yayi Maganar daga can yana taɓe bakinsa tare da katse kiran duban sakatariyar yayi yace. "Bazai samu shigowa ba, duk wanda yazo ganinsa ki turo sa office ɗina, ina da abu mai muhimmanci da zanje nayi yanzu." Sakatariyar ce tace. "Sir akwai wanda ya kawo file ɗin sa yace a bawa Oga Nameer idan ya shigo." "File kuma okay let me See." "Okay Sir." Sakatariya tayi Maganar tana ɗauko file ɗin ta miƙawa Hisham amsa yayi tare da buɗe file ɗin, idanunsa ya ɗago ya kalli sakatariya yace. "Yaushe aka baki File ɗin, shi Tunde da kansa ya kawo file ɗin ko wani ya aiko."? "Yes Sir da kansa ya kawo ɗazu kafin ka shigo nace ya kai maka office ɗin ka, yace a'a na riƙe kawai na bawa Oga." Murmushi Hisham ya saki yace. "Okay ba damuwa ki cigaba da aikinki zanje da file ɗin." Shigowar Tutu gidan babu kowa hakan ya sata haurawa sama har zata buɗe bedroom ɗin Ummi taji motsin mutum a bedroom ɗin su yaya NAMEER, fasa shiga bedroom ɗin Ummin tayi ta nufi na su Nameer nocking tayi Nameer dake kwance yana aiki da system ɗinsa yace. "Yes come." Shigowa Tutu tayi ganin Nameer ne kawai ya sata zama bakin bed ɗin.. "Ina yaya Hisham ɗin na ganka kai ɗaya.?" "Yana Company ya akayi har kun tashi daga school ɗin kenan."? "Eh, Yaya Nameer am....... Katseta yayi da cewa. "Um um, kinga I love you, kinsan Nameer bashi da wata mata bayan Tutu, wai ma na tambayeki naga sai ƙara kyau kike meye sirrin ne." Murmushi Tutu ta saki cike da ƙaunar Nameer tace. "Waye sirrina bayan kai, Yaya Nameer ji nake nafi ko wacce mace Sa'a domin kuwa babu wanda ya kaini dacen samun jarumin saurayi." Murmushi kawai Nameer ya saki yace. "To naji sarauniyata, time ɗin dawowar Hisham yayi zamu fita da yamma ki shirya." "Okay I love you." Ta furta tana murmushi. "I love You too." Shima Nameer ya furta yana kanne mata ido, fita Tutu tayi cike da farin ciki domin kuwa a duk sanda ta kalli Nameer farin ciki ne yake gauraye zuciyar ta, bata juma da fita ba kuwa Hisham ya shigo ko takalmin sa ba cire ba ya zauna tare da miƙawa Nameer file ɗin Tunde. Amsa Nameer yayi tare da buɗe file ɗin sanda ya karanta tukunna kafin ya dubi Hisham. "Amma ai ko kai zaka iya Sumit ɗin file ɗin idan kasa hannu ai shikenan ka basa office ɗin da ya kamata yayi aiki ba sai ni ba." "Okay na fahimta, kuma nasan hakan sai dai karka manta ni ya fara kawowa file ɗin office ɗina, kuma na yanke hukuncin bazamu ɗauki ɓarawo aiki ba, dan haka baza'a ɗaukesa ba." Murmushi Nameer yayi yace. "Amma karka manta Abba ne ya bada umarnin mu ɗaukesa dan haka ya zamo wajibi Tunde yayi aiki a Companyn mu, bayan shima zan ɗauki Jidda itama aiki a cikin Companyn saboda kaine ka mata asarar aikinta dan haka ya zamo wajibi ni kuma na biya bashin da ka ɗauka rigimar ta ƙare." Murmushi Hisham ya saki yana sunkuyawa ya zare takalmin ƙafarsa bai cewa Nameer komai ba, ganin yayi murmushi yayi shuru yasa Nameer cewa. "Nayi magana kamin shuru baka faɗa min ra'ayinka akan hakan ba.?" _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [5/26, 8:10 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 27 to 28_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 "Au wai Hisham banza kayi dani nayi maganar kayi min shuru." Agogon hanunsa da ya cire ya ijiye tare da juyowa yace. "Meyasa zaka damu dole sai kaji ra'ayina ba dai kai ka gama yanke naka hukuncin ba to meye nawa a ciki." Tashi Nameer yayi ya zauna tare da cewa. "Ina son jin ra'ayinka ne saboda bana son rigima bana son su fara aiki ka dinga ɗaga mana hankali a Company, nasan halinka sarai Hisham." Dariya maganar ta bawa Hisham tare da juyowa yace. "Oh saboda ni ne masifaffe zan ɗaga muku hankali ko, to ai abinda baka sani ba Nameer saboda ka ɗauki Jidda aiki ni wannan ba matsala ta bace abu ɗaya ne dai bazan yadda ba dole sai anyi kafin a ɗauke ta aiki shine cike dukkan wani doka na Company dole sai an tantance ta, bayan duba takaddunta ana bukatar sai an mata interview kasan wannan wajibi ne a cikin Company, sannan shi Tunde da kake magana a kansa kamar yadda ka faɗa bazanyi jayayya da maganar Abba ba, to shima sai ya cike ƙa'idojin Company idan har sun cancanta za'a gani." "Hmmm! Haba Hisham nifa ba yaro bane, kawai kace zaka koresu a wajen interview tunda kaine mai interview a cikin Company kaga kace sun faɗi ai ba wani abu mai wahala bane a wajenka, musamman Jidda da kake jin kamar ka kasheta." Sosai Hisham yayi dariya cikin zuciyarsa ya furta. _Nameer baka san shirina akan Jidda bane shiyasa kake kallon kamar bazan bari tayi aiki a Companyn mu ba, wannan dama ce mai kyau ka kawo wanda burina zai cika cikin sauƙi muddun Jidda tayi aiki a Companyn mu._ Numfashi ya saki har yanzu dariyar yake yace. "Nameer ka fahimce ni, ni fa yanzu bani da matsala tsakanina da Jidda, bashin gaba ce kuma an fanshe, babu bashi tsakanin mu yanzu, ta kulleka na kulleta Final, karka damu ka shigo ayi interview tare da kai tunda kana min kallon maƙaryaci." "Ba kallon maƙaryaci nake maka ba Hisham sanin hali ne yafi sanin kai nafi kowa sanin waye kai." "Okay shikenan babu kuma abinda zance maka yanzu." Hisham yayi Maganar yana ɗaukar towel ya shige tollet, tashi Nameer yayi ya fita falo, Ummi ya gani yanzu, murmushi ya saki yace. "Ummi yaushe kika dawo." "Kuna ƙuryar ɗaki Nameer yaushe zaku san dawowata." Zama yayi yana murmushi yace. "Shigowa ta babu kowa shiyasa ma na shige bedroom." "Nameer wai ya Maganar Aure ne, na fara gajiya fa da ganinku haka just 35yrs ai ya kamata ace zuwa yanzu kunyi haihuwar fari."? Dariya Nameer ya saki tare da cewa. "Kai Ummi nawa shekara 35 take da har za'a gaji damu, insha Allah Ummi Auren nan yana zuwa nan kusa kusa amma fa nawa bansan na Hisham ba, dan shi ko zancen Soyayyar ma baya so." "Ƙyaleni da ɗan ƙwal uba, Auren nan dai sai yayisa ko na masa Auren dole." "Haba dai Auren dole ai yanzu an shige wannan zamanin da ake yiwa mata Auren dole bare kuma maza." "Naji to kai surukar tawa a ina take.?" Murmushi Nameer yayi yana jin Jidda cikin ransa yace. "Ummi na dai ganota amma ban furta mata ra'ayina ba, amma Ummi ina sonta sosai so beautiful ce yarinyar." "To marar kunya ko kunyata baka ji, to dai kayi gaggawar sanar da ita karka tsaya kallon ruwa ƙaton kwaɗo ya maka ƙafa, amma dan Allah Nameer ku nemi Aure a gidan mutunci saboda mace ta gari itace ƙashin bayan al'umma daga gareta ake samun ƴaƴa na gari, yana da kyau ku kula." Numfashi Nameer ya saki yana jinjina kansa yace. "Hmmm! Hakane Ummi insha Allah bazamu ɗauko macen da za'a kuka da ita ba." "To Allah yayi jagora ya muku albarka." Tayi Maganar dai-dai Hisham na sauƙowa, kusa da ita ya zauna yana cewa. "Ummi jiya Abba yake cemin zai tafi Istanbul by tomorrow, kuma zai kwana biyu it's true."? "Eh insha Allah gobe zai tafi suna da meeting da zasuyi acan so shima tafiyar ta taso masa ne kawai lokaci guda, bayan haka ai ya juma baije Istanbul ba." "To Allah ya kaimu, maganar wannan Yarinyar Hajara da na rufe a gidan gonar Abba ya za'ayi da ita na miƙawa hukuma itane ko kawai na ƙyaleta tayi tafiyar ta.?" "Subahanallah! Hisham dama baka saki yarinyar nan ba, ni Hisham mai yake damunka ne, kana da hankali kuwa ka ɗauki yarinya mace ka je ka ɓoyeta saboda ubanka ya ɗaure maka gindi, bana fa jin daɗin abinda kake Hisham ka dinga kiyayan ɓacin raina, yanzu dan ubanka idan Tutu aka yiwa abinda ka yiwa wannan yarinyar zakaji daɗi, tashi ka tashi kaje ka ɗauki ƴar mutane ka mayar da ita gidan ubanta." Idanunsa Hisham ya runtse yana jin faɗan Ummi, a rayuwarsa ya tsani faɗa da tsawa. "But Ummi........ "Kul kamin wata magana cewa nayi ka tashi kaje ka saki ƴar mutane." Nameer ne ya miƙe tsaye tare da cewa. "Allah ya huci zuciyarki Ummi kiyi haƙuri ni bara naje da kaina na maida ta gidan su, a wani room ka rufeta.?" Ɗago idanunsa Hisham yayi ya kalli Nameer kafin cikin ɓacin rai yace. "Ka tambayi mai gadi zai nuna maka key ɗin room ɗin yana hannunsa." Yayi Maganar yana tashi yabar wajen, harara Ummi ta watsa masa tana cewa. "Kai dai Allah ya shiryeka, ina sane da baka daina shan sigarin nan ba ai dan uwarka shasha wanda baisan ciwon kansa ba, kana ganin ɗan uwanka yanda yake tafiyar da rayuwar sa cikin nutsuwa da albarkar kowa amma kai Banda kai sai zafin ran tsiya da bazai amfanar da kai komai ba ga shegen taurin kai." Shi dai Hisham baiyi magana ba ya shige a zuciye. "Ummi dan Allah kiyi haƙuri ki daina masa faɗa haka, kinsani Hisham haka Allah ya hallice sa a haka ya taso bazai sauya ba, dan Allah Ummi ki daina wallahi raina suya yake min idan kina zaginsa." "Umhum ai kune masu ƙara tunzura sa dole ya cigaba da ganin abinda yakeyi dai-dai ne, zaka shige ne ko kaima sai na ɓata maka rai." "Allah ya huci zuciyarki Ummi." Yayi Maganar cikin girmamawa yana fita, tsuka Ummi taja cikin ɓacin rai, tana jin haushi da takaicin wannan sigari da Hisham ke sha tayi faɗan tayi zagin amma abu ya gagara, ga sigari illace ga kayan cikin Mutum musamman Huhu tana saurin lalata sa. _Allah ka shirya min Hisham, Allah ka fitar masa da wannan sigarin a ransa._ Tayi zancen cikin zuciyarta tana sakin ijiyar zuciya. A zama yayi tare da dafe kai cikin matsanancin ɓacin rai, tebur ya buga tare da cewa. "Rabon da Ummi ta zageni ko ta min faɗa harna manta a rayuwata, amma yau Ummi ke zagina, kuma duk wannan matsiyaciyar yarinyar ce sanadi, JIDDA na tsaneki na tsaneki I hate you!." Yayi Maganar da ƙarfi yana runtse idanunsa. Ya juma sosai yana huci har Nameer ya dawo sai kusan isha kafin ya ɗan saki har suka ci abinci, Hisham fuskarsa tana ɗaure ita dai Ummi bata kulasa ba, ko Nameer bai yiwa sallama ba ya yi ficewarsa, shima Nameer wanka yayi ya ɗauki Tutu suka fita. ************ A bakin railway ya ɗauki Sadiq sunyi nisa da tafiya Sadiq yace. "Ina zamuje ne, can gidan gonar Abba ne.?" Girgiza kansa Hisham yayi Yace. "No ba can zamuje ba Nameer yaje yayi handling ɗin wannan Case ɗin." "To ina kenan zamuje."? "Kai Sadiq ka cika yawan tambaya kasan dai duk iskancina bazan je na sayar da kai ba ko, Ora zamuje, gani nayi ya kamata mu fara buga Game ɗin nan yau." Dariya Sadiq ya saka tare da cewa. "Au har ka gama playing ɗin yadda game ɗin zai kasance kenan, to menene tsarin."? Kansa Hisham ya girgiza tare da sakin murmushi yace. "Ka zuba idanunka zaka gani, Hisham ne fa ko ka manta ne.?" "Ina kuwa zan manta Hisham, ai nasan saƙar ka shiyasa wani lokacin nake tsoron ka, amma dai ka taka a hankali gudun zamewa kasan wani sa'in bama fahimtar akwai santsi a waje har sai mun jimu a ƙasa, ya kamata mu dinga tafiya da waiwaye." "Karka damu Sadiq duk santsi wajen akwai takalmin da ya fi ƙarfinsa muje zuwa zakaga ƙarshen wasan." Dariya Sadiq yayi basu kuma magana ba har sai da suka yi parking a ƙofar gidan su Jidda, duban Hisham Sadiq yayi yace. "Hisham wai kiranta za'ayi ne.?" "No shiga gidan zamuyi da kanmu." "Shiga kuma Hisham ba tare da neman izini ba." "Karka damu biyoni kawai." Kansa Sadiq ya kaɗa tare da fitowa daga motar key Hisham ya yiwa motar kafin suka nufi gidan su Jidda kansa tsaye Hisham ya shiga da sallama Umma ne ta amsa Jidda kanta na sunkuye tana ɗaurawa Abdu karatu, Basmah ma tana gefe, Umma cike da mamakin su sun shigo musu gida kai tsaye duk da Umma bata san Hisham ba, kamar wanda akace Basmah ta ɗago kanta taga Hisham na doso su a zabure Basmah tace. "Hisham." Ai Jidda saurin ɗago kanta tayi cikin mungun mamaki taga Hisham miƙewa tayi tsaye tayi tace . "Hisham meya shigo da kai gidan mu.?" _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_[5/27, 7:59 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko Please._* *FREE BOOK ONE📚* *_Page 29 to 30_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 Murmushi kawai Hisham yayi bai kuma tsaya ba ya cigaba da tahowa, cikin azama Jidda ta taho zata tare gabansa Umma ta daka mata tsawa. "Karki kuskura! ki dawo ki zauna a inda kike.'' "Hisham ne fa Umma ta yaya zan barsa ya shigo mana gida ya cima mutunci, kinsan kuwa yanda na tsani ganin wannan mutumin, wallahi Umma da ganin wannan gara nayi karo da mungun maciji, shine fa mutumin daya tozarta ni shine mutumin da baya ƙaunar yaga asirin mu ya ruhu shiya rabani da aikina Umma saboda kawai yaga mun tozarta, wannan maƙiyin Allah ne." Kanta Umma ta jinjina domin kuwa ta fahimci yadda Jidda take jin zafin Hisham a cikin ranta. "Na sani Jidda, dan haka ki koma ki zauna haka na ce miki." Shuru Jidda tayi tana cije bakinta zuciyarta na tafasa ta koma ta zauna, Basmah ma daga inda take ta zauna Umma kuwa nuni ta yiwa Hisham da tabarma tace. "Ga waje ku zauna." Zama sukayi Hisham ya dubi umma tare da cewa. "Barka da dare." "Barka yaro kaine Hisham ko, Allah yasa ba wani kuskuren muka sake maka ba."? "Ko ɗaya Umma babu wani kuskure da kuka min ni ne ma na muku kuskure, Umma ba tashin hankali bane ya kawo ni, nazo ne na baki haƙuri a matsayin ki na uwa na tabbata zaki fahimce ni, nasan ba lallai Jidda ta yadda dani ba, saboda tana kallon na yaudareta a baya da nufin na saduda wanda hakan yasa ta faɗa tarkona har na samu hujjar da na rufeta a police station, Umma a yanzu ba yaudara ba ce ta kuma kawoni gidan ku ke uwace kuma kin girme mu idan har yaudara ce ta kuma kawoni na tabbata ke zaki fahimci hakan, Umma jiya mun zauna da Nameer munyi magana ya nuna kuskurena akan abinda na yiwa Jidda, kuma na fahimta na gane cewa ita bata da laifi gashi kuma na cutar da ita da yawa, jiya banyi bacci ba tunani da damuwar zaluncin da na mata su suka dameni da tunanin anya kuwa Jidda zata yafe min, ban tunkaro Jidda nazo gareki saboda ke uwace zaki gane zafin da nakeji a raina ita Jidda ba lallai ta fahimce ni ba, dan Allah ku yafe min, maganar aikinta kuma da ta rasa munyi magana da Nameer zata kawo takaddunta mu duba insha Allah zamu ɗauketa aiki, Umma zafi da ciwon abinda Jidda tasa aka yiwa ɗan uwana shine yasa idanuna rufewa harna mata haka, bana iya riƙe kaina muddun aka taɓa Nameer, amma yanzu na fahimci kuskure na aikata ga Jidda kuyi haƙuri, wannan shi ya kawo ni." Shuru Umma tayi tana sauraren Hisham sosai Maganar sa ta shiga jikinta kuma bata hango yaudara ko rashin gaskiya a tattare dashi ba, tsantsar gaskiya da nadama ta hango a idanunsa, numfashi ta saki kafin tace. "Na saurari maganganun ka Hisham, ni kaina bazan ɓoye maka da farko naji zafin ka, amma tun sanda ɗan uwanka yazo gidan nan yake bani haƙuri ya kuma tabbatar min kai ba mutumin banza ba ne na yarda dashi, saboda Mutum ne na ƙwarai shi, sai kuma yanzu da kazo na tabbatar da hakan wannan akasi ne daya faru kuma Allah ya ƙaddara sai anyi hakan ni na fahimce ka, ita kanta Jidda tun farko da nace ta janye jikinta a cikin Case ɗin da taji maganata dama hakan bata faru ba, ni na yafe maka kuma ita ma jidda ta yafe maka." "Wallahi ban yafe masa ba Umma kuma bazan yafe masa ba har abada! Da wannan mungun maƙaryacin zaki yadda macijin sari ka noƙe, da kake zancen zaku ɗauke ni aiki a Companyn ku, ce maka akayi mahaukaciya ce ta yayeni da zan yi aiki a ƙarƙashin ku, Allah ya tsari gatari noma ko kwarya ta fashe wallahi akwai sauran zane, kuma ka sani ina nan akan bakata sai ka girbi abinda ka min." Jidda tayi maganar tana huci, Umma da kallo ta bita shi kansa Hisham dama yasan bazai ci nasara cikin sauƙi ba, miƙewa yayi tare da cewa. "Umma ranta ne a ɓace har yanzu tana jin haushi na bata gama hucewa, kiyi haƙuri, zan cigaba da baki haƙuri har sai kin haƙura, muje Sadiq Umma na barki lafiya." "Ba komai na gode Allah yayi muku albarka, ka gaida ɗan uwan naka." "Zaiji insha Allah." Hisham ya amsa suna ficewa, Umma kallon Jidda da sai cika take tana batsewa tace. "Jidda meyasa zuciyar ki bata da kyau ne wani lokacin Jidda idan babu haƙuri duniyar zata zauna ƙalau ne, ita kanta duniyar ma fa ƙalilan ce ko yaushe ina nuna miki mahimmancin haƙuri Jidda, da kike cewa bazaki amshi aikin su ba, so kike mu koma halin da muka shiga a baya ne Kafin ki samu aiki, idan bakiyi danni ba, ko dan Abdu zakiyi saboda kuɗin makarantar sa, kin sani bani da wani yaro Babba Namiji kece jigona dalilin kenan da yasa na dage kikayi karatu, duk rintsi da wahala sai da na tabbatar kin samu ingantaccen ilimi da ingantaccen kwali, kema kin sani babu irin wahalar da bansha ba a rayuwata." Numfashi Jidda ta saki idanunta na ciko da hawaye tace. "Na sani Umma kuma bazan taɓa mantawa ba, amma Umma ki sani Hisham yaci mutunci na a rayuwa, Umma mayaudari ne zai iya fakewa da wannan hanyar saboda ya ƙara cutar dani, baki san waye Hisham bane shiyasa kika yarda dashi cikin sauri amma ni bazan taɓa yarda dashi ba, idan har kince dole sai nayi aiki a ƙarƙashin su zan miki biyayya Umma amma sai dai ni nasan dole sai wani mummunan abun ya faru, duk wanda ya haɗa hanyar sa da Hisham dole sai ya taka ƙaya." Jidda tayi maganar hawayen yana biyo idanunta tare da tashi tabar wajen Umma duban Basmah tayi tace. "Basmah kinfi kowa sanin waye Jidda dan haka ina son ki bani gudummawa wajen ganin Jidda ta amshi wannan aikin, bamu wata madogara da ta wuce amsar aikin muddun muna son mu cigaba da rayuwa cikin rufin asiri kema shaida ce kan wahalar da muka sha a rayuwa." "Na sani Umma kuma insha Allah zanyi iya bakin ƙoƙarina domin ganin Jidda ta amshi aikin bara naje na sameta." "Shikenan Basmah na gode." Umma tayi Maganar cikin sanyin jiki, kafin Basmah ta tashi tabi bayan Jidda. Sunyi nisa da tafiya HISHAM yace. "Sadiq meka fahimta a zuwan mu gidan nan shin ka hango nasara kuwa.?" "Eh to kusan haka amma dai akwai ƙura, kaima tunda muka fito naga kamar ka sare, ko da zakayi nasara akanta to zata baka wahala da alamu tana da taurin kai yarinyar sannan ƙwaƙwalwarta yana ja sosai sai ka taka a hankali." Iska Hisham ya fesar daga bakinsa kafin yace. "Naga alamar haka, Sadiq kasan kuwa yadda nake jin zuciyata kamar ta fashe tsabar baƙin ciki sanda na ƙasƙantar da kaina a gabansu, matsiyacita wadanda basu wuce bayina ba, Sadiq lallai duk wani baƙin ciki da zuciyata ta ƙunsa ya zamo BASHIN GABA tabbas zansa Jidda cikin JALALAR da sai ta gwammaci mutuwa fiye da rayuwa, sai tace meyasa ma tazo duniya, ban taɓa tsanar mutum irin yadda na tsani Jidda ba, kamar yadda tace da ganina gara ganin baƙin maciji da ni a gareta to kuwa na gwammaci ganin mutuwata sama da ita, hmmm! Sadiq wannan yarinyar ta ɓallo ruwan da bazata iya taresa ba, kuma nayi alƙawarin sai ta soni sai nayi wasa da zuciyar ta kamar yadda sarakuna suke wasa da Doki sai ni tsalle a cikin zuciyarta ina tafe ina zaneta kamar yadda ake yiwa bayi, zan kunna mata wutar da bazata iya kasheta ba a zuciyarta, na rantse sai na koya mata soyayyata, ko da kuwa zansha wahala kafin hakan ta kasance." Numfashi Sadiq ya saki yana sakin murmushi yace. "Na godewa Allah da yasa abinda ta maka baisa ka zuciya ba, ka sani sai ansha wahala ake samun nasara ba'a taɓa cin galba akan masoyi cikin sauƙi ka sauƙe ni anan zanje unguwa." "Unguwa kuma to na kaika mana sai na shige, nima gidan Aunty Halima zanje." "Karka damu Hisham, ka sauƙe ni kawai." Kansa Hisham ya kaɗa tare da yin parking Sadiq ya sauƙa, yana fita yaja motar yabar wajen murmushi Sadiq ya saki yana bin motar da kallo sanda yayi nisa wata farar mota tayi parking a gaban sa, buɗe motar yayi ya shiga, yana shiga ya ɗaga kai ya kalli Tunde sai suka saki murmushi Tunde ya ɗagawa Sadiq babbar yatsa alamun jinjina👍🏼 "Banyi zaton zaka iya buga wannan wasan haka ba, sanda Mama ta kiraka baka wannan kogilar cikin tsoro da tunanin kai Aboki ne a wajen Hisham wanda ya yadda da kai, sai gashi ga baro ƙasar da kake saboda amsar wannan kogilar, a yayin da kasa Hisham wasa da zuciyar wata kai kuma bai san wasa kake da rayuwar sa ba, da alamu dai zamu ci Nasara akan ahalin Iyabo ta dalilinka, hmm tabbas zamu kauda hankalinsa da wannan yarinyar akan mu, Hisham wawa ne na ajin farko marar lissafi." _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [5/31, 9:01 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE📚* *_Page 31 to 32_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 Murmushi Sadiq ya saki yana duban Tunde kafin ya girgiza kansa yace. "Idan har Hisham wawa ne to kuwa tabbas kowa ma dake wannan duniyar wawa ne, Hisham fa ba gaɓo bane kamar yadda kake tunani komai da lissafi yake yi, tabbas ni zan iya wofintar da tunaninsa saboda yadda bazai taɓa ankara zan cutar dashi ba, yarda ce zata sa na iya kai Hisham ƙasa ba wauta ko rashin lissafi ba, idan wayo ne da kuma lissafi Hisham ya fini nesa ba kusa ba dan haka ko yanzu karka ɗauka cewa Hisham ba'a ankare yake ba, takun mu ya kamata mu iya." "Hakane na fahimta, Mama tana son zatayi Magana da kai." Kansa Sadiq ya girgiza. "No Bazanyi Magana da ita ba ba kuma zan haɗu da ita ba, ina yin komai cikin tsaro ne, bana bukatar wani ya fara fahimtar akwai alaqa tsakanina da ku, kaima kanka ina haɗuwa ne kawai da kai ba tare da motar gidan ku ba, dan haka duk abinda take son tattaunawa da ni ta sanar dakai kai ka zamo ɗan saƙo." "But ko waya bazaku iya kuyi ba, ko da baku haɗun ba.?" "A wannan lokacin hanyar sadarwa ma ba cikakken tsaro bane da ita saboda abu mai sauƙi ne a bibiyi da wadanda kake waya dan haka bazanyi waya da ita ba, sannan ka jaddada mata cewa muddun muka kammala wannan mission ɗin ta cire HISHAM RICE MILL LIMITED a cikin lissafin ta domin nine wanda zai mallakesa kamar yadda na faɗa muku zamu kawo ƙarshen gaba ɗaya wadannan mutum huɗun, Hisham Ummi Abba da kuma Tutu saboda sune suke da gadon IYABO, to tabbas zan iya tsayar da numfashin su, ka tabbatar mata Company nawa ne, idan kuma aka ci amanata to tabbas kuma bazan barku ba sai na kawo ƙarshen ku, da lissafi nake komai cikin nazari nasan tunda kukaci amanar Alhaji Iyabo to abu ne mai sauƙi a wajen ku kuce zakuci amanata, to ina ankare cin amanata gareku tamkar kun ɗebi tafasasshen ruwa ne kun watsa a jikin ku, magana ta da kai a yanzu tazo ƙarshe." Sadiq yayi Maganar yana buɗe motar ya fita numfashi Tunde ya saki tare da jan motar yabar wajen, ko da ya koma gida yadda sukayi da Sadiq ya sanarwa Mamabisola, murmushi ta saki Tunde ne yace. "Mama wannan mutumin bashi da hankali idan har muka basa Companyn ai shikenan mu mun tashi famfam saboda Company shine fa ƙarfin arzikin su, shiya kawo musu dukkan kuɗin da suke alfahari dashi yanzu gaskiya Mama bazai yiwu mu basa wannan Companyn ba." "Tunde kenan kai yaro ne shiyasa ba komai zaka fahimta ba, Tabbas HISHAM RICE MILL LIMITED shine babban Companyn su amma ka sani suna da ƙananun Company a jahohi daban-daban, sannan akwai wani babban Companyn nasu a Indonesiya NAMEER COTTON LIMITED ana ji dashi Company ne na AUDUGA suna kuma sarrafashi ta hanyoyi daban daban, suna yin atampopi da sauransu, dan haka mu barsa da wannan Companyn domin kuwa Sadiq shine garkuwar da zai iya kai Hisham ƙasa mu kuma dama Hisham shine matsalar mu domin kuwa idanunsa suna kammu." "Okay to shikenan Mama, yace bazaiyi magana da ke ba kuma bazaiyi waya da ke ba, saboda tsaro duk saƙon da kike son isar masa yace ki faɗa min ni na isar masa idan muka haɗu." Dariya Mamabisola tayi sosai kafin tace. "Tabbas kansa yana ja, yana tafiya da lissafi na fahimci karatun nasa da alamu kuma zai kawo hadda, ba damuwa ka zamo ɗan saƙo." "Okay ya maganar zuwa ƙauyen da zasuyi da Wamimo."? "Tunde zan tsagaita tukunna naga takun Sadiq idan akwai nasara Bama bukatar tsafi, mu jira muga iya tseren sa tukunna itama Wamimo na sanar da ita hakan." "Shikenan Allah yasa tseren yayi gudu dan ina bukatar ganin ƙarshen su cikin gaggawa." Yana rufe bakinsa wayarsa tayi ringing dubansa ya kai ga wayar Nameer, Mamabisola ya kalla. "Nameer ke kira." "Ka ɗauka kaji abinda zai ce maka." Wayar ya ɗauka yayi sallama sun ɗan juma suna waya kafin Tunde ya katse yana kallon Mamabisola yace. "Kinji wai na kawo takadduna gobe za'a min interview." "Okay ba damuwa kaje ɗin, bara na je na kwanta." Mamabisola tayi Maganar tana tashi tabar falon. *********** Dariya Aunty Halima tasa tana duban Hisham tace. "Wai da gaske kake Hisham." "Allah kuwa Aunty Halima, da gaske nake ina son haɗa Sadiq da Tutu Aure, saboda amanarsa da kuma hankalinsa, Sadiq yana bani gudummawa sosai a cikin al'amari na, amma ke ya kika gani." Numfashi Aunty Halima ta saki tace. "To wani hanzari ba gudu ba, Kamar Tutu tana da wanda take so domin kuwa ni ta taɓa cemin tana da wanda take so, kaga kuwa bazamu mata Auren dole ba, wanda take so shi zamu ɗauka mu bata." Cike da mamaki Hisham yace. "What Aunty akwai wanda Tutu take so ya akayi mu bamu sani ba daga ni har Nameer babu wanda ta sanar hakan kuma bana tunanin ta sanar da Ummi dan da Ummi ta sani zata sanar damu, amma Aunty waye tace miki wanda take so ɗin."? "No bata sanar dani waye bane gaskiya ta dai cemin tana da wanda take so, amma kafin kayi magana da Sadiq ka fara zama da Tutu tukunna." "Okay shikenan hakan zanyi zan samu lokaci nayi magana da ita, dare yayi zan koma gida Aunty sai da safe." "Allah ya tashe mu lafiya ka gaishe da Ummin naku, ka cewa Nameer ina neman sa." Tunda Hisham ya dawo gida har yayi wanka ya kwanta tare da jawo system ɗinsa ya hau aiki, ƙarfe 10:30 har zuwa wannan lokacin Nameer bai dawo ba, ture system ɗin Hisham yayi tare da miƙewa ya fito falo Ummi da mai aikinta kawai Hisham ya gani suna kallo zama yayi yana Zama mai aikin ta tashi tabar wajen. "Ummi ina Tutu.?" "Tutu kuma ba sun fita da Nameer ba wai sunje zatayi shopping." Shuru Hisham yayi tare da kallon agogo yace. "Amma ya kamata ace zuwa yanzu sun dawo 10:35 fa Ummi, Hmm mtsss bai dace Nameer ya kai har wannan lokacin da Tutu ba." "Hisham meye damuwarka ba dai da ɗan uwanta ta fita ba, bana son shirmen banza." "Allah ya huci zuciyarki Ummi, bawai wata fassara dabam nayi ba, yauwa Ummi wai nikam Tutu ta sanar da ke akwai wanda take so ne ma'ana zata aura.? "Tutu kuma to ai bamma taɓa jin tace min ta fita zance ba, bani da labari gaskiya amma me ka gani."? "No Ummi ba komai kawai na tambaya ne." "Hisham." "Na'am Ummi." "Hisham kana ɓata min raina abinda kake min Hisham bana jin daɗinsa." "Ummi ni kuma me nake miki ummi.'' Yayi Maganar cikin tashin hankali, numfasawa Ummi tayi tace. "Sigari, sigari da kake sha Hisham shine yake ƙona min raina na ce maka bana so amma Hisham kaƙi bari kafi so ko yaushe raina ya dinga ɓaci ko.?" "Kai Ummi kin razana ni, nifa sigarin nan idan ban shata ba ji nake tamkar bani da lafiya musamman ma idan raina yana ɓace sai nasha nake samun sukuni, kawai ki cigaba da min addu'a idan da rabon zan daina sha is okay, kuma idan banda ke ma Ummi bafa sigarin da zata fito a jikina na matsiyacita nake sha ba, babu wanda ya isa yace ina shan sigari sai wanda ya sani,sigarin ma ai kala-kala ce." "Hmmm! Ikon Allah ina nuna maka gabar kana kai yamma zakayi, yanzu Hisham idan bata fito a jikinka ba ai dai bazata fasa cutar da lafiyar ka ba ko, Hisham ka sani ina maka tsananin ƙaunar da bazan iya jure rashinka ba, dan Hisham ka daina shan sigarin nan she is dangerous to why zaka nace da shan abinda kasan cutarwa ce ga rayuwarka, ka bari bana so." "Shikenan Ummi kiyi haƙuri insha Allah zanyi ƙoƙarin naga na rage, idan bansha bane Ummi bana jin daɗi, musamman idan ina cikin damuwa amma insha Allah zan rage." "Allahu yasha Hisham." "Ameeen Ummi Abba fa ya kwanta ne.?" "Ehh ya kwanta tun ɗazu kasan gobe sammako zaiyi zuwa Indonesiya, na Companyn Nameer." "Eh ya faɗa min, Ummi dai kina ji da Nameer baki cewa Companyn mu sai Company Nameer." "Ya za'ayi bazanji dashi ba, shi da baya ɓata min rai duk abinda na hanasa hanuwa yake, amma kai fa Hisham ba ka jin maganata." Tayi Maganar dai-dai Tutu na shigowa da sallama kusa da Hisham ta zauna tana cewa. "Ummi mun dawo." "Ta ganki ai, nayi zaton ai kwana zakuyi acan." "Kai yaya Hisham daɗinta ma dai da Yayana na fita, ba da wani ba." "Ki fita da wani mana dan ubanki idan ban karya miki ƙafa ba." Daga nesa Nameer yace. "Umhum ai nasan za'a rina, kai dai a duniya babu wanda kake sauƙe fushinka a kansa sai Tutu." Dariya Hisham yayi yace. "Au dama haka kake ɗauka, na ma kusa na aurar da ita na huta." Ummi dariya tasa tana kallon Hisham tace. "Ikon Allah mutumin da bai aurar da kansa bane yake tunanin aurar da wata yo Hisham gaka ƙaton tuzuru bakayi Aure ba sai auta na zaka takurawa ai kuwa baka isa ba, ka fara auren tukunna kafin ka saka wani yayi." Dariya Nameer tare da ƙarisowa ya zauna yace. "Yauwa Ummi faɗa masa dai, Malam ka fara fito da mata tukunna." "Au wai taron dangi zaku min akan nace wannan ƙaramar alhakin tayi Aure, to kai mai bakin banga taka matar ba." "To idan ba tsoro ba, nan da wata biyu kowa ya fito da tashi matar da zai aura mana." Cewar Nameer, dariya Hisham yayi yace. "Na kuwa yarda Ummi ki zamo shaida, alƙawari kuma mukayi, da dai bani da niyyar Aure amma tunda yanzu ka hasala ni zan kuma baka mamaki." "Wannan alƙawarin kuwa zan kasance mai tuna muku." Itama Ummi tayi Maganar, dukkan su dariya sukayi, Hisham ya juya ya kalli Tutu yace. "Naje gidan Aunty Halima ɗazu muke tattauna magana akanki take cemin kince mata akwai wanda kike so zaki aura, waye ne.?" Da sauri Nameer ya juya ya kalli Tutu, itama shi ta kalla tare da sakin murmushi ta juya ga Hisham. _____________________________________ *Masu min VTU Please ku daina bana son vtu ga account number na saka a jikin page ku ɗauka ku turo kuɗin ku ta ciki, idan baki da account ban tsananta ba nace kiyi snap ɗin katin mtn ki turo, to meye na yin VTU, duk wanda ta sake min VTU transfer ɗin katinta zanyi na mayar mata, dan haka dan Allah ku daina idan kin turo kuɗi kuma ki tabbatar da kin turo min shaidar biya bana so muzo muna wallahi tallahi da ke, yau kwana uku Mutum biyu sukace sun turo na ce ni ban gani ba su kawo shaidar biya sunce wai yayi delete a wayarsu, ni kuwa har yau banga alart ɗin su ba, ta yaya alart zaiyi delete a wayar Mutum idan bashi ya goge ba dan Allah idan kun tura ku turo shaidar biya.* _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [6/1, 8:25 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *Page 33 to 34* *_WRITING ON 01/03/2022_* "Yaya Hisham Yaushe Aunty Halima ta faɗa maka hakan.?" Tayi Maganar tana kallon Nameer girgiza mata kai Nameer yayi alamun karta sanar da Hisham, girarta ta ɗaga masa alamun meyesa, Muryar Hisham taji yace. "Malama ina ruwanki da ranar da ta faɗa min tambayar ki kawai nayi sai ki bani amsa." "Okay sorry, amma yaya Hisham nifa cikin wasa na yiwa aunty Halima wannan maganar, bansan ta ɗaukesa serious ba, ni bani da wani saurayi, da kuma da Ummi ta sani." Murmushi Hisham ya saki tare da cewa. "Wa yaga sarkin baƙin jini yarinya mai shekara ashirin wai bata da manemi, to ai shikenan ni hakan ma yamin daɗi domin kuwa zan sadakar da ke cikin sauƙi." "Yaya Nameer kana jinsa ko wai ni zai sadakar, wallahi nafi ƙarfin ayi sadaka dani ina nan Allah zai kawo min miji na gari.'' Dariya Nameer yayi tare da miƙewa yana cewa. "Wannan faɗan ni yafi ƙarfina, kunga ma shigewata dan wallahi bacci nakeji." Ummi ne tace. "Kana da gaskiya Nameer nima tashi zanyi naje na kwanta kwa ƙarita ku biyu." Ummi tayi Magana itama tana tashi tayi bedroom ɗin ta shima Nameer shigewa yayi Tutu tana tura bakinta itama ta tashi bakinsa Hisham ya taɓe tare da jawo wayarsa ya kira Sadiq Ringing ɗaya ya ɗaga. "Ya akayi Hisham.?" "Mtsss! Kai dai Sadiq barni, kasan wata cacar da muka sanya da Nameer.?" "A'a sai ka faɗa min." Numfasawa Hisham yayi yace. "Musu muke akan maganar Aure cikin haka har mukayi muƙabalar fitar da matar Aure cikin wata biyu, Ummi itace alƙali, anya kuwa ban ɗauko dala babu gammo ba." Daga can Sadiq yasa dariya tare da cewa. "Haba Hisham babu wani dala daka kinkima, she is gentleman so beautiful, kaga kuwa kana da damar sace zuciyar Jidda cikin sauƙi, sai dai inda gizo yake saƙar babu Auren Jidda cikin mission ɗin ka." "Wannan ba damuwa ba ne, Sadiq wannan itace damar da Hisham zai gwada ƙarfin sa'ar sa, dan haka ka zuba ido kaga yadda zan ɗauko zuciyar shegiyar a tafin hannuna 3week komai ready insha Allah." "Okay hakan ma yayi, sai mun haɗu gobe." "Allah ya kaimu." Hisham yayi Maganar yana katse kiran murmushi ya sanya tare da furta. "Ina zan samu phone number ɗinta, hmmm! Okay Idi maye shi zan bawa wannan aikin zuwa gobe zai antayo min numbern nata." Murmushi ya kuma saki tare da kiran idi maye aikin ya yi basa da adress ɗin Jidda sannan ya katse kiran. Can kuwa Nameer tunda ya shiga yake kai kawo ya na tunanin ta ina zai fara aika saƙon sa ga Jidda iya nazarin da yayi akan rayuwarta macece mai kafiya da kuma ji da kai, numfashi ya saki tare da zama yayi tagumi, yana jinta a ransa fiye da kima baya jin cewa akwai macen da ya taɓa kaunarta kamarta, tabbas rasa Jidda gareshi tamkar tarwatsa rayuwarsa ne a ko yaushe zuciyar sa tana harbawa ne da sunanta, jigo ce ita a cikin rayuwarsa, a fili ya furta. "Bazan taɓa yarda na rasaki ba Jidda ko ta halin yaya sai na mallakeki ke tawace zanyi yaƙi da kowa a kanki, komai tsanani komai wahala Jidda bazaki kaucewa rayuwata ba ke tawa ce nima kuma naki ne." Yayi Maganar yana ɗaukar wayarsa ya kirata bata ɗaga ba, wajen sau biyu, sai kawai ya kira ummanta yana kira kuwa cikin Sa'a Umma ta ɗauka cikin girmamawa Nameer yace. "Umma Barka da dare, kiyi haƙuri na kira a wannan lokacin." Daga can Umma tace. "Ba komai Nameer komai a kamawa take, Allah dai yasa lafiya." "Lafiya alhamdulillah Umma, dama na kira numbern Jidda ne bata amsa kiran ba, maybe bata san number na bane, dama zance mata ne gobe ta taho da takaddunta na makaranta Companyn mu za'a mata interview, muna saka ran ɗaukarta aiki insha Allah." Cikin farin ciki umma tace. "Alhamdulillah! Gaskiya naji daɗin wannan kiran naka Nameer ɗazu kuwa ɗan uwanka ma Hisham yazo ya bamu hkr yace ka nuna masa abinda yayi bai kyauta ba, mun gode da gudumowarka garemu insha zatazo ta Allah ya maka albarka." "Ameeen Umma na gode sai goben." "To Allah ya tashe mu lafiya na gode." Katse kiran Nameer yayi cike da mamaki ya furta. "Hisham kuma yaje gidan su Jidda, kai anya kuwa Hisham zaije ya basu haƙuri kai mtsss ba Hisham bane gaskiya." Yayi Maganar Hisham na shigowa. "Kayi mamaki ne Nameer saboda Hisham yana da ɗagawa ko bazai iya bawa talaka haƙuri ba, to kayi kuskuren fahimta domin kuwa a wannan lokacin Hisham ya yadda yayi kuskure, ni ne naje na basu haƙuri ka daina mamaki." "But Hisham lallai kuwa idan har da gaske ne Hisham ya fara sauyawa." "Haka kuke so ku ganni ai shiyasa na sauya saboda kuyi farin ciki." "Hakane na kira Tunde gobe zaizo interview itama Jidda na kirata zata zo gobe Company." "Allah ya kaimu goben." Hisham yayi Maganar a takaice. *********** Washegari bayan sunyi breakfast suka raka Abba har airport sanda jirgin su ya tashi tukunna suka shige Company, da misalin sha ɗaya da rabi, Tunde ya shigo, a office ɗin Nameer ya zauna kasancewar yasan halin Hisham, bai wani juma da zuwa ba Jidda ta kira Nameer cewa ta shigo Companyn, security ya kira yace ya shigo masa da Jidda office ɗin sa, tare suka shigo da Basmah Jidda tasha doguwar riga marun color tayi rolling ɗin gyalen a kanta duk da Jidda ba gwanar makeup bane sosai tayi kyau, da sallama suka shigo tunda suka shigo Nameer ya tsurawa JIDDA ido tamkar zai cinyeta sosai ta masa kyau kujera ya nuna mata tare da cewa. "Basmah sannunku da zuwa Bismillah ku zauna." Zama sukayi, Jidda ba tare da ta kalli Nameer ba tace. "Sannu aiki, jiya Umma ta isar min da saƙon ka, ga takaddun nawa." "A'a bani zan amshi takaddun ba Hisham ne, wannan bangaren sa ne shike tace ma'aikata." "Hisham kuma, to amma namee........ Hannu Nameer ya ɗagawa Jidda tare da cewa. "Hisham ya sauya ba yadda kika sanshi a baya bane, karki yanke hukunci ki jira har yazo tukunna." Nameer yayi Maganar yana ɗaga waya ya kira Hisham yace yazo office ya samesa su jidda sunzo, kafin ya ijiye wayar, jefa jifa Nameer suna taɗi da Basmah ita dai Jidda tayi shuru, kusan 30minute babu Hisham baizo ba, har aka doshi awa ɗaya, Jidda sosai ranta ya sosu domin kuwa ita a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da jira cike da hasala ta miƙe tace. "Tashi mu tafi Basmah." "Ta tashi ku tafi kuma meyasa." Kallon Nameer tayi kai tsaye tace. "Saboda banzo dan a wulaƙanta ni ba." "Haka zalika kuma babu mai wulaƙanta ki." Sukaji muryar Hisham ta doki kunnen su gaba daya juyowa sukayi suka kallesa murmushi ya saki ya ƙariso yana cewa. "Sorry kun gaji da jirana ko, akwai waɗanda suka juma kafin ku su na tsaya na sallama amma har kin ƙosa da yawa." Shuru Jidda tayi tare da komawa ta zauna dariya Hisham yayi tare da dafa dest ɗin da take zaune ya kanne mata ido yace. "Kamar dai har yanzu haushina kikeji ko, we'll da ma kinyi murmushi domin ko yaya kika juya yanayinki kyau kike ƙarawa, zan iya ganin takaddun naki." Yayi Maganar yana ɗaga mata gira, idanunta jidda ta runtse cike da jin haushin sa tace. "Bani na fara zuwa ba, sai ka fara sallamarsa tukunna." Murmushi Hisham yayi tare da juyawa ya kalli Tunde. "Au wai dama wannan shagiri girbau ɗin yana nan ne shima, hmm! Wai Tunde baka da zuciya a ƙirjinka ne, da ace ni ne kai ko inda Companyn nan yake bazan kalla sai dai ina kare ya cinye zuciyar, sai dai fa mu anan bama ƙyale ɓarawo muddun ya saci abummu, hannu muke cire masa, miƙo min takaddun naka ɗan uwana Tunde." Yayi Maganar yana sakin murmushi wani irin ɗaci Tunde yaji a zuciyarsa sosai ransa ya ɓaci ji yake tamkar ya tashi ya cakwamo Hisham, idanunsa ya runtse. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [6/2, 8:20 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 35 to 36_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 Murmushi Hisham ya kuma saki ganin ran Tunde yayi mungun ɓaci nauyin jiki ya sa ya kasa miƙo masa takaddun nasa. "Hannunka yayi nauyi ne bazaka iya miƙo min takaddun ba, au ko nazo na ɗauka da kaina ne." Teburin gabanta Jidda ta daka da ƙarfi tare da miƙewa a hasale, gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallonta har Hisham ɗin, gaban Tunde ta ƙarisa ta ɗauki takaddun nasa ta matso kusa da Hisham. "A rayuwata na juma banga mutum irinka ba, nayi tsammanin cewa ni ne kaɗai kake wa wannan wulaƙancin ashe kowa baifi ƙarfin wulaƙanci a wajen ka ba, ta yaya zai iya miƙo maka bayan ka ci masa mutunci, ka gyara rayuwarka Hisham domin kuwa baka kan turba mai kyau, saboda yazo neman aiki wajenka bashi zai baka lasisin wulaƙanta sa ba, ga takaddar ni na miƙo maka idan ma hannu ɗaya bazai baka sau biyu ni na haƙura da nawa shi dai ya samu." Murmushi Hisham ya saki yana kallon Jidda. "Haka zalika ke ma ɗaukar damuwar wani ki ɗaura a kanki baya baki wahala, shi wannan ɗin da zaki ari faɗansa to ɗan uwana wannan faɗan cikin gida ne yana da kyau ki kawar da kanki, amm me ma kikace idan ma hannu biyu bazai bani na karɓa ba ke kin haƙura da naki, Hmm! Ko sau dubu hannunki ya miƙo min ni mai amsa ne a gareki saboda ina neman afuwarki, gaskiya ke macece ta musamman ƙwarin zuciyar ki na burgeni." Yayi Maganar yana amsar takaddun Tunde yace masa. "Interview room idan na gama dashi zan kiraki.'' Yayi Maganar yana fita NAMEER ne ya dubi Tunde yace. "Ka tashi kaje kayi haƙuri kasan halin Hisham muma haƙuri muke dashi." Kansa Tunde ya haɗa yana dariya zuci domin kuwa shi a yanzu kallon biri yake yiwa Hisham, tarkon da suka ɗana masa zaiyi wuya ya tsallake sa tashi yayi yabi bayansa Jidda ne tace wa Nameer. "Nameer wai shi Hisham haka rayuwarsa take, ya kamata ku dinga masa burki bai kamata ku barsa ya tafi a haka ba, da zan samu dama wallahi da zan saisaita rayuwarsa." Numfashi Nameer ya saki, yana kallon Jidda yayin da yakejin ƙaunarta na nunkuwa a zuciyarsa, kafin yace. "Zaiyi wahala ki iya gyara Hisham tunda har muka gagara sanyaya masa zuciyar sa to babu wanda zai iya, kuma baku fahimci Hisham bane, shifa baya taɓa shiga harkar wani, idan kinga Hisham ya shiga harkarki to tabbas kece kika taka masa gonarsa baki san waye Tunde bane da bazakiyi gaggawan shiga faɗansu ba, su ɗin ƴan uwane na kusa iyayensu gindinsu ɗaya." "Kai ai kullum a cikin kare Hisham kake, Nameer halin ka mai kyau ne da ace Hisham kamarka yake to da tabbas sai yafi kowa jin daɗin rayuwarsa, kasan meye ina tausayawa matar da zata auri Hisham domin kuwa zata sha wahala kafin ta fuskanci waye shi." Murmushi Nameer ya saki yace. "To ni kuma tawa matar wani irin tausaya mata akeyi."? Murmushi itama Jidda tayi tace. "Ai kai Nameer duk matar da ta aureka to tabbas tayi sa'ar miji na gari, za kuma taji daɗin rayuwarta." Dariya Nameer yayi yace. "Gashi kuma wacce nake so ita bata san ina yi ba, ina sonta sosai soyayya ta haƙiƙa Soyayyar gaskiya ji nake tamkar bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, ita ɗin rayuwata ne." "To amma meyasa bazaka sanar da ita Soyayyar da kake mata ba, kana da kyawawan halin da Mace bazata ƙika ba, ko wacce Mace ka furtawa kalmar so na tabbata bazata furta maka kalmar ƙiyayya ba." "Shikenan lokaci shine alƙali, Allah yasa maganar ki ta tabbata, ta soni Kamar yadda nake sonta." Jidda batayi magana ba Hisham ya kira waya yace Jidda ta ƙariso, kallonta Nameer yayi yace. "Hisham yace ki ƙarisa, kije sakatariya zata saka a kaiki." "Okay to shikenan Basmah ki jirani ina zuwa." Tayi Maganar tana tashi ta fita, kafin ta fita ma Nameer ya kira sakatariya tana fita ta samu security ya nuna mata, inda zatayi, tana zuwa ta shiga room ɗin babban room ne ma'aikata ta samu sosai a wajen, hakan ya nuna mata ba room ɗaya bane a ciki, wani ɗan korido ta bi, kanta ta ɗaga taga wani room an rubuta BUA INTERVIEW ROOM, rasa inda zata samu Hisham ya sakata sakin numfashi ta tura room ɗin wani mutumi ta samu zaune cikin office ɗin sallama tayi ya amsa. "I'm sorry, Hisham nake nema." Murmushi ya saki tare da tashi yaje ya rufe room ɗin yana murmushi ya juyo tare da doso Jidda yana cewa. "Wow she is beautiful, ƴan ba sai kin sayarwa Hisham ba, idan aiki kike nema kawai ki bani hadin kai kin samu just 11minute ma is okay.'' Yayi Maganar yana matsota Jidda ganin da gaske neman rungumeta yake ya sata yin baya cikin tashin hankali, take baya tana cewa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Auzubillah! Allah ya tsare ni daga sharrinka Hisham fa nake nema dan Allah ka buɗe min ƙofa na fita ni ba Yar iska bane ka matsa min na shige." Dariya ya sanya yace. "Gaki kamar Mace mai wayo ashe wawiya ce, just 11minute fa kawai ya isa." Hisham jin Jidda shuru bata shigo ba ya sashi kiran Nameer yana tambayar sa ina jidda cike da mamaki Nameer yace ai tun ɗazu security ta kawo ta, ijiye wayar Hisham yayi cike da mamaki ya fito, room ɗin da yake cikin yana kallon wanda Jidda ta shiga, har zai shige sai ya jiyo tamkar Muryar mace tana kuka cikin room ɗin khabeer alkanawi, bakin room ɗin yaje ya tsaya tare da sanya hannu yayi nocking jin nocking yasa khabeer saurin juyawa sai kuma ya juyo ya kalli Jidda da har ya ɓarka mata rigarta, a zatonsa security ne daga inda yake tsaye yace. "Waye ne.?" "Hisham." Amon Muryar Hisham ta doki kunnen sa, cikin ɗaga murya a gigice Jidda tana kuka tace. "Hisham! Ka taimake ni! Zai keta min mutunci na." Cike da mamaki HISHAM ya toshe bakinsa tare da furta. "What Jidda, khabeer buɗe ƙofar nan." Bakinsa khabeer ya toshe tare da ɗaura hannunsa a ka, cikin mungun tsoro, da gudu Jidda ta buɗe ƙofar, har tana bige Hisham wajen fitowa ta ƙanƙame jikinta sakamakon yagewar da rigarta yayi, kallon Jidda Hisham yayi tare da juyawa ya kalli khabeer, ƙafarsa yasa zai shiga room ɗin sai kuma ya tsaya cikin zuciyarsa ya furta. _me zaisa na taimaka mata, to wai ma meya aikata mata anya kuwa ba fyaɗe ya mata ba._ Yayi Maganar yana juyawa ya kalli Jidda rigarta daya yayyage ya ke kallo rabin ƙirjinta duk a waje idanunsa ya runtse tare da mai da kansa gefe, Rigarsa ta sama ya cire tare da miƙa mata ta amsa cikin sauri, da wani irin mungun kallo yake bin khabeer idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine yaga ana ketawa mace haddi............. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [6/7, 7:22 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 37 to 38_* Idanunsa ya kuma runtsewa tare da ware su akan khabeer da yayi tsuru_tsuru yana kallon sa a mungun fusace Hisham yayi kan khabeer tare da shaƙo wuyansa wani irin naushi ya kaimasa a cikinsa tare da jidesa da ƙafarsa ya faɗi warwas a ƙasa, ƙara kai masa naushi yayi a bakinsa, wani irin ƙara khabeer ya danna tare da yunƙurowa zai tashi Hisham yasa ƙafa ya kwashesa, yayin da Jidda ta ke gefe takure hawaye na cigaba da biyo idanunta tabbas tayi danasanin zuwa wannan ma'aikatar da ace tasan haka zata faru da ita da babu abinda zai kawota, shi kuwa HISHAM ya dage sai dukan khabeer yake, ya gagara ramawa domin kuwa yasan yana wani yunkuri zaiyi asarar aikinsa, jin ihunsa yasa ma'aikatan wajen zuwa suka taru a kansa, ƙoƙarin ƙwacesa suke amma sun gagara, da ƙyar suka kwacesa daga hannun Hisham, wani irin huci Hisham yake tamkar mayunwacin zaki, Nameer da Basmah a gigice suka taho wajen sanda security suka sanar dashi, Gaban Hisham ya tsaya tare da cewa. "Hisham meyake faruwa, da girman ka Hisham kasa hannu a jikin ma'aikacin ka why.?" Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur Hisham ya ɗaga tare da nuna masa JIDDA da hannun sa gabaki ɗaya juyawa sukayi suka kalli Jidda itama idanunta sunyi jajur da sauri Basmah taje ta riketa tana cewa. "Innalillahi! Jidda meya sameki, ke da.......... Bata ƙarisa maganar ba idanunta suka sauƙa akan rigarta da ya yage sai yanzu ta kula da rigar Hisham dake jikinta, a fusace Basmah tazo ta tsaya a gaban Hisham. "Me kuka aikata mata, me ka mata Hisham, dama kun kirata da sunan bata aiki ne saboda ku wulaƙanta ta, macece fa ita, Meyasa baka yafiya ne Hisham." "Ya isheki haka, ba dai Hisham ya aikata wannan mungun aikin ba, duk tsiyata ban taɓa tunanin ketawa Mace haddinta ba, ki juya ki yiwa wannan ɗan bunsurun wannan tambayar da kike min." Hisham yayi Maganar cikin tsawa yana ɗaukar wayarsa Police ya kira yace suzo su tafi da khabeer Idanunsa shima Nameer ya runtse wani irin ɗaci da baƙin kishi ne yaji ya sarƙafe masa wuya, a fusace idanunsa a rufe yasa hannu ya finciko khabeer da ƙarfi tare da haɗasa da jikin bango, take goshin khabeer ya fashe jini ya biyo fuskarsa, wuyansa ya kuma shaƙowa wani irin gurnani khabeer keyi idanunsa duk sun firfito waje alamun wahala, shi kuwa Hisham kansa ya dafe tare da neman waje ya zauna yana jin zuciyarsa na hura, yama kasa yiwa NAMEER magana, Basmah tana ƙanƙame da Jidda duk hankalinsu na tashe, ƙarar motar Police da sukaji shiya ƙara ɗagawa Khabeer hankali, duk alokacin yana jin a ransa cewa kashesa Nameer zaiyi, jin motar Police yasa Hisham tashi da sauri ya wani irin kwashe khabeer rigib yayi a ƙasa, ƙafarsa Hisham yasa ya taka ƙafar khabeer da ƙarfin gaske ji kake ƙafar tayi ƙas, ya ɗaga ƙafarsa zai kuma takesa Police ya yi saurin rike Hisham ƙoƙarin ɗaga khabeer sukayi ya tsaya da ƙafarsa abu ya gagara, hakan ya tabbatar da cewa Hisham ya karya khabeer, Police ɗin ne yace. "What Hisham ka karyasa fa, duba kaga wannan ƙafar tasa bata tsayuwa." "karaya huɗu naso yayi ba ɗaya ba, duka hannayensa da ƙafofin naso su karye, ɗan matsiyaciya bunsurun banza! Wannan tsinanne ne la'anannen Ubangiji, ku fice da shege daga wajen nan, dan uwarsa an faɗa maka cewa nan Companyn tsinannune irinka kwarton banza kaji kunya kuma kayi asara, ɗan shegiya, tauren banza." Hisham yayi Maganar cikin tsawa, dubansa Police ɗin yayi yace. "Kabi a hankali mana Hisham meyasa kai ka fiye zafin zuciya ne, komai sannu muke binsa dole sai mun san abinda ke faruwa kafin mu tafi dashi." "Ba zafin rai kawai nake da shi ba harda zafin hannu, bayan zafin hannu ma harda na ƙashi na rantse da Allah idan baku fita dashi ba zan illata sa yadda ko likitocin duniyar nan zasu taro a kansa bazasu iya gyarasa ba, dan haka ku fice da tsinanne, tunda ba Companyn ubansa bane." Hisham ya kuma maganar yana huci, Nameer ne ya girgiza kansa yace. "Sargent Bala ku shige dashi can office ɗin naku zan biyo bayan ku, sannan karku sassauta masa fyaɗe yaso aikata mana a cikin Company juya kaga yadda yaci zarafinta." Kansa Sargent Bala ya kaɗa tare da juyawa ya kalli Jidda keyar khabeer ya kaɗa sukayi gaba, Police ɗin suna fita Hisham ya dubi ma'aikatan dake tsaye a wajen da yawa idanunsu yana kan Jidda baiyi magana ba yaja hannun Jidda ya shige da ita room ɗin daya fito yana huci, tunda Hisham ya riƙe mata hannu Jidda taji tsikar jikinta ya zuba wani abu ya taso mata daga ƙafarta har cikin ƙwaƙwalwarta, bai jira su Nameer sun shigo ba ya rufe ƙofar da ƙarfi idanunsa sunyi wani irin kaɗawa har abun tsoro idan ya ɗago ya kalleki. "Ki faɗa min, ya miki fyaɗe ne karki ɓoye min meya miki."? Kanta Jidda ta ɗago hawaye na tsiyaya ta kallesa kuka ne yaci ƙarfinta madadin ta masa magana sai ta fashe da kuka, kansa Hisham ya dafe yana cije bakinsa, ya bigi teburin gabanta. "Oh my god, hmmm! Ya lalata miki rayuwa ko, ki faɗa min gaskiya mana, ya miki fyade ko."? Ita dai Jidda taƙi magana sai kukanta take ta fama, cike da jin haushi ya daki bango gefensa cikin ɓacin rai ya furta. "Kuka! Kuka! Kuka! Wannan wanne irin munafurci ne, uban meye ya kaiki office ɗinsa nan aka kiraki ne, kin sani a gaba sai kukan munafurci kike min, bayan ya gama lalata rayuwarki duk macen da ta rasa budurcinta to ki sani ta rasa kimarta da mutuncinta har ma da kimar iyayenta, gashi kema kin shiga wannan jerin waɗannan Mutanen, khabeer ya hallaka miki rayuwa ya cuc............. "Ya isa haka Hisham! Ka barni da abinda ya dameni, ka barni nayi kukana a duk sanda na haɗa hanya da kai masifa nake gani duk da kayi ƙoƙarin ƙwatata a hannun wannan azzalumin, amma babu alkairi a tarayyata da kai Hisham, bana bukatar aikin na haƙura zanje na riƙe talaucina Allah bazai hanani yadda zan kula da ahalina ba, da kake kiran fyaɗe! Fyaɗe! Waye yace maka ya rabani da darajata, kana ina akayi da zaka yanke hukunci bisa son ranka ko ka yarda ko kar ka yarda ni ban rasa mutunci na ba, babu abinda ya min Allah ya kwace ni a hannunsa, akwai CCTV Camera kaje ka duba ka gani idan yamin fyaɗe, ka daina yanke hukunci da son ranka ka buɗe min ƙofa nabar wannan Companyn." Iska ya fesar daga bakinsa yace. "Babu Alkairi a tare da ni kakace, Hmm! Ƙarya kike duk inda na shige alkairi ne ke bin bayana, ki sani babu sharri a tare dani, da kuma akwai sharri a tare dani da banzo na ceceki ba kije ki kwanta kiyi tunani, kije mun ɗaukeki aiki." Hisham yayi Maganar a zuciye yana ɗaukar takaddun ta ya fita dasu, numfashi Jidda ta saki hawaye na biyo idanunta. Nameer ganin Hisham ya buɗe ƙofar ya fito a fusace ya sashi shiga da sauri Basmah na biye dashi, Jidda Basmah ta riƙe har yanzu itama ranta na ɓace, Nameer ne yace. "Kiyi haƙuri Jidda nasan Khabeer bai miki fyaɗe ba, ya dai kuskureki, amma na miki alkawari sai ya gane kuskuren sa, muje na kaiki gida da kaina." Kanta Jidda ta girgiza tana jan majina tare da sanya hannu ta share hawayen ta, tace. "Bazan koma gida a haka ba Umma bazata ji daɗi ba, zanje kawai gidan su Basmah na sauya kaya." "Okay to muje sai na sauƙeki a gidan su Basmah." Kanta ta girgiza tare da tashi suka fita. Hisham tunda ya fita daga interview room ɗin motarsa ya shiga tare da wurga takaddun Jidda a bayan motar, darect Joint ya nufa, baiyi wani parking ɗin arziki ba ya fito, ko motar bai rufe ba, sai security ne ya taho da sauri ya rufe masa motar, teburin da babu kowa ya samu ya zauna tare da runtse idanunsa, abubuwan dake faruwa ne suke dawo masa a cikin idanunsa. _Aduk sanda na haɗa hanya da kai masifa nake gani, babu Alkairi tarayyata da kai_ Da ƙarfi Hisham ya furta. "Kaga ƴar shegiya, bazaki san tsakanina da ke babu Alkairi ba sai sanda na karya miki zuciya a ranar zaki tabbatar da haɗuwata da ke masifa ce, zan tabbatar miki da wannan furucin naki sai na sanyaki cikin masifar da bakiyi zato ba, tabbas zan ɗaukeki aiki domin shine damata da zan jawoki jikina." Yayi Maganar yana zarar sigari, leta ya ɗauka a gefen table ya kunna sigarin, zuƙa yayi tare da lumshe idanunsa, sai kuma ya saki murmushi. "The game is ready, wasan yanzu za'a fara." Hisham yayi Maganar bakinsa ɗauke da murmushi, Sadiq ya dannawa kira 4 miss Call bai ɗaga ba ya juma sosai yana shan sigarinsa ko ruwa bai sha ba a wajen kafin ya tafi. ************ Tsakiyar dare wajajen 2 na dare idanun Jidda suka buɗe bacci ya gagareta zullumi da tsoron duniya suka shiga zuciyarta rayuwa ta lalace mutane duk sun zamo marassa imani, an maida fyaɗe ruwan dare, ko dan saboda ba'a hukunta masu aikata wannan laifin ne shiyasa laifin ya yawaita an maida mutunci mace ba komai ba, numfashi Jidda ta saki tana tuno abinda ya faru, _yanzu da Hisham baizo ya ceceni ba da yaya kenan da yanzu na rasa mutunci na_ tayi Maganar zucin tana sakin numfashi tare da furta. "Duk munin halin Hisham ya taimakeni domin kuwa da badan shi ba da yanzu rayuwata tana cikin tasku, lallai ya taimakeni, ashe dama Hisham zai iya taimakon wani, lallai yadda na ɗaukesa ba haka yake ba, meyasa ma na faɗa masa magana marar daɗi bayan shine ya taimake ni, bai dace na kirasa da masifa, wannan kalmar bata dace ga mutumin daya taimaki rayuwar ka ba, nayi kuskuren faɗa masa wannan kalmar ya zamo lallai na basa hakuri, mtsss! To amma Hisham yana da jiji da kai da isa muddun na basa haƙuri to zai rainani ne, amma ai durƙusawa wada ba gajiyawa bane, kai ina anya zan iya bawa Hisham haƙuri kuwa."? Ta yiwa kanta tambayar tare da yin shuru tana nazari ringing ɗin wayarta ta ji, duban wayar tayi taga bakuwar numbern hannun ta sa ta ɗauki wayar tare da cewa. "Hello da wa nake magana."? Daga can taji ance. "Hisham." "Hisham kuma." Jidda ta furta cike da mamakin ina ya samu numbern ta. "Eh Hisham kinyi mamaki ne.?" "Ƙwarai kuwa gani nayi babu haɗin danga da garahunu." Daga can Hisham yayi murmushi tare da cewa. "Ayya to ai muddun ɓera zai shiga turken mage ki sani dole wannan magen tazo neman wannan ɓeran wataƙila sata ɓeran yayi kinsan ba'a raba ɓera da sata." "Au ni ce ma ɓerar, amma dai kaci mutunci na, ni zaka kira da ɓera, me na sata a Companyn naku Banda bala'in da na gani." Dariya sosai Hisham yayi kafin yace. "Ayya Malama ɓera meye na jin haushi saboda na kiraki ɓera, shifa ɓarawo dole ne ya amsa sunan ɓera." Cike da hasala JIDDA tace. "Malam wai me kake nufi da ni ne, ka kirani tsakar dare kana neman faɗa min baƙar magana, idan Mutum ɗan mutunci ne zai kira Mace cikin wannan daren ne." Dariya ya kuma mata har tana jiyo sautin dariyar tasa yace. "Haka kuma idan Macen yar mutunci ne ko da an kirata tsakiyar dare bazata ɗaga ba, kinga kuwa marar mutunci ne ya haɗu da ƴar Uwarsa marar mutunci." Kanta Jidda ta riƙe cike da jin haushi taja doguwar tsuka tare da katse kiran tana furta. "Banza." _____________________________________ *Kuyi haƙuri da jina shuru da kukayi kwana biyu, hidima ce tasha min kai, ina muku fatan alheri masoya na ina kuma godiya da ƙaunar da kuke gwada min.* _Akwai wadanda suka cemin zasu biya kuɗin JALALA amma basa son group na dinga tura musu ta PC to gaskiya idan ta pc kike so 500 zaki biya._ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [6/8, 9:58 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 39 to 40_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 Tunda Hisham ya amshi takaddun Jidda kusan 14days babu wani sako sai dai abinda ya bawa Jidda mamaki yadda lokaci ɗaya shaƙuwa ta shiga tsakanin Umma da Hisham domin kuwa a kai akai yake zuwa gidan nasu ko Nameer bai shaƙu da Umma ba yadda Hisham ya shaƙu da ita kayan Abinci da wasu abubuwan buƙata na gida haka Hisham ke kawo wa su Umma, harta Basmah yanzu mutunci ne sosai ke tsakanin ta da Hisham yanda Hisham ke yiwa Umma biyayya kamar mutumin kirki ke kyace itace ta haifesa, maganar Khabeer kuwa tuni su Nameer suka Kaisa kotu, zama ɗaya aka yankewa Khabeer shekara bakwai a gidan yari na yunkurin fyaɗe da ya yiwa Jidda da taran Naira dubu ɗari wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yiwa Jidda ba, sai dai har yanzu akwai guntun faɗa tsakanin Jidda da Hisham, Soyayyar Jidda kuwa ko yaushe ninkuwa yake a zuciyar Nameer yayin da ya kasa sanar da ita ko nuna mata alamun yana sonta. Yau Jidda tana zaune ita da Basmah tace wa Basmah. "Basmah wai yaushe ne zaki koma gidan ku, kinga tunda aka yiwa Abba aiki suka dawo gida ya kamata ace kin koma, nasan Mama idanu kawai ta zuba miki taga gudun ruwanki bazata ji daɗi ba." "Au korata kike wai Jidda." "Ko ɗaya Basmah gidanku gidan mu ne kamar yadda kike kallon gidan mu a naku, nasan dai Mama bazata ji daɗi bane da zamanki anan dole zata buƙace ki." "To gobe INSHA ALLAH sai na koma." Da Allah ya kaimu Jidda ta amsa dai-dai Nameer na sallama a cikin gidan nasu fuskarta a sake Jidda ta amsa kafin ya shigo, kujera ƴar tsugunne Jidda ta basa ya zauna. "Sannu da zuwa Yaya Nameer." Cewar Jidda murmushi Nameer ya saki tare da cewa. "Yauwa sannu Jidda ke da Basmah ne.?" "Eh wallahi yaya Nameer, ya aikin jiya da daddare ai na kiraka sai Hisham ya ɗaga wayar yace baka kusa." "Eh tabbas bana kusa Basmah, ya akayi da wani labarin ne." Murmushi Basmah tayi tace. "A'a ba komai kawai dama gaisuwa ce, kuma na jika shuru kwana biyu shine Umma tace na kiraka naji ko lafiya." "Ayya Allah sarki Umma na, bana gari kwana biyu naje Abuja." Jidda ne tace. "Gashi kuma Umman bata nan taje unguwa." "Ba wajenta dama nazo ba, takaddun ki na dawo miki dasu, gobe zaki fara aiki, a ƙarƙashin Hisham, office ɗin Khabeer da ya bari wannan gurbin muka baki kece zaki tace ma'aikata na fannin goge shinkafa, ina fatan zaki iya aikin."? Numfashi Jidda ta saki tare da cewa. "Zan iya mana sai dai banso ace an ajeni a ƙarƙashin Hisham ba." "Shine yake da alhakin tace ma'aikata, kuma shine ya baki wannan gurbin bani da ikon da zance masa meyasa domin aikinsa da ya juma yana yi." Basmah cewa tayi. "Ke dai kawai Jidda kice Allah yasa hakan shi yafi alkairi." "Wannan shine gaskiya Basmah." Cewar Nameer, kanta Jidda ta girgiza tace. "To Allah yasa hakan yafi alkairi, jiya Abdu ya dawo yace yaje zai biya kudin makaranta sai suka ce masa, ai an biya masa wani yaje last week ya biya, nasan kaine ka biya kudin." Cike da mamaki Nameer yace. "A'a gaskiya bani bane infact ma bansan lokacin biyan school payment ɗin nasu yayi ba, to amma waye ne zai biya masa har 39k.?" Cikin mamaki sosai Jidda tace. "Ba kai bane to waye ne ikon Allah." "Sai Allah amma dai ko waye ne wata rana zai bayyana, ni bara naje muna da meeting yanzu." "To shikenan mun gode yaya Nameer gobe insha Allah zan fito da wuri." "To Allah ya kaimu kya gaishe da Umman idan ta dawo." Yayi Maganar yana fita, Jidda cike da mamaki ta dubi Basmah tace. "To waye ya biyawa Abdu kuɗin makaranta.?" Shuru Basmah tayi tana tunani kafin tace. "Anya ba Hisham bane, kin fa san yanzu ya sauya, daga yadda kika sanshi." "Gaskiya ne ya sauya tun sanda ya taimake ni lokacin da khabeer yaso keta min mutunci na, daga ƙwayar idanunsa yadda ransa ya ɓaci na tabbatar da ya sauya, da Hisham yazo har gidan nan yace nayi haƙuri da abinda yamin na yarda ya sauya sai dai ba'a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa." "Hakane yanzu ni bara naje nayi wanka sai nazo muje gidan ko." "To shikenan sai kin fito." Tayi Maganar tana jingina da jikin bango. ********** "Wai Hisham ya kuke ciki ne da Jidda har yanzu zuciyarta bata fara yarda da kai bane, ya kamata zuwa yanzu ta fara yarda da kai, ka sani alƙawarin ku da Nameer na fitar da matar Aure sati biyu ya rage karka yadda ka kasa cika alkawari."? "Sadiq komai taurin zuciyar ta na tabbata zuwa yanzu tana jina a ranta kasan meye dalilina."? Kansa Sadiq ya girgiza yace. "No sai ka faɗa." "Dalilina shine komai bushewar zuciyar ta, tunda har na sunkuya a gabanta da mahaifiyarta na bata hakuri dole jikinta yayi sanyi, domin kuwa tasan abune mawuyaci wanda zaisa ni Hisham na bata hakuri, sai kuma Khabeer da ya saukaka min aiki, domin kuwa cetonta da nayi a hannunsa wannan kaɗai ya isa ta yarda da ni, uwa uba kuma tallafawa uwarta da nakeyi da wannan nakasasshen ƙanin nata, abu ɗaya ya rage min kuma shima sa ido kayi kallo, na tabbata nan da sati ɗaya zan bijiro mata da soyayyata kuma ina tabbatar maka ko shawarar wani bazata nema ba zata amince sani, ina tabbatar maka sai nasa rayuwarta a cikin taskun masifar da bata taɓa zato ba." "Shege abokina gaskiya ƙwaƙwalwarka naja, kayi aiki mai kyau wasa yazo tsakiya." Cewar Sadiq, sai kuma yace. "Hisham ni wai Company nawa kuke dashi ne."? Ɗago idanunsa Hisham yayi cikin mamaki domin kuwa ta yaya Sadiq zai masa wannan tambayar akan kadarorinsu kafin yace. "Meyasa kamin wannan tambayar Sadiq, me hakan zai amfanar dakai." Murmushi Sadiq ya saki _wato Hisham ya zargi wani abu a ransa kenan, ina bazaka taɓa gane santsin da nake ƙoƙarin yarfawa ƙafarka ba sai randa ka buɗi idanunka ka ganka a ƙasa warwas a ranar zaka fahimci kai mahaukacin kare ne_ Sadiq yayi Maganar cikin zuciyarsa kafin yace. "Me kuwa zai amfaneni dashi Hisham, jiya ne ina zaune a wani Joint ni da Abba naji wani yana cewa, kuna da Company biyar a ƙasar Rasha, to shine abin ya bani mamaki domin ni bansan kuna da Company a Rasha ba, yadda nake da kusanci da kai ya kamata ace na sani, amma kuma sai naga kamar tambayar bata maka daɗi ba." Murmushi Hisham yayi yace. "Bawai banji daɗi bane abunne ya bani mamaki da ka min wannan tambayar domin kuwa a sanina bamu da Company a rasha, infact ma idan muna dashi,ai bai zamo lallai sai na sanar da kai ba komai kusancin dake tsakanin mu, Sadiq asirin ciki sai hanji sanin sirrin dukiyar mu, wannan tsakani na da ahalina ne, dan haka babu wannan layin tsakanina da kai Sadiq mu tsaya iya abotar mu." Numfashi Sadiq ya saki domin kuwa ba haka yaso ba, yaso ace ya bigi cikin Hisham amma ba komai lallai wata rana sai na sani kafin na aika ka lahira murmushi ya saki tare da cewa. "To shikenan Allah ya baka haƙuri, yanzu ya za'ayi ina son zan shige Abuja gobe." "Okay kana buƙatar kuɗi kenan, muje POS sai na baka, nima zan shige ne muna da meeting." Tashi sukayi suka shiga mota, a POS ɗin suka tsaya Hisham ya cire 50k ya bawa Sadiq kafin ya saukesa a ƙofar gidan su ya shige Companyn nasu . ********** Washegari da safe Nameer da Tutu ne kawai suke breakfast Ummi tana azumi bata fito daining ɗin ba, shima Hisham da azumi ya tashi, yana can bedroom ɗin su bai fito ba. "Yaya Nameer kullum ji nake tamkar na jawo sati huɗin da kuka yi alkawarin fitar da mata kai da yaya Hisham, gashi har mun cinye sati biyu." Spoon ɗin da ke hannun Nameer ya ijiye tare da xubawa Tutu ido yace. "Ban fahimta ba, meyasa kikeji tamkar ki jawo wannan watan yazo da wuri.?" "Hmmm! Saboda a wannan lokacin ne zaka fitar dani a matsayin matar da zaka Aura, duniya zata san Soyayyar dake tsakanina da kai, ina kwadayin wannan ranar shiyasa nake gaggawar tazo ta, i love You so much Yaya Nameer, bansan Irin Soyayyar da nake maka ba, ina burin ganina a ƙarƙashin inuwar aurenka." Numfashi Nameer ya saki, tare da runtse idanunsa. _Ta kasa fahimtar bata ra'ayina, ta kasa gane bana jinta a raina yanzu, ya kamata zuwa yanzu ta fahimci haka ba sai na faɗa mata da bakina ba, Jidda itace zaɓina itace muradina, kuma ya zamo wajibi na aureta komai rintsi komai wahala sai na mallaketa kiyi haƙuri Tutu bazan iya aurenki ba, bazan yiwa Soyayyar Jidda kishiya ba, itace muradina ba ke ba._ Nameer yayi Maganar zucin idanunsa na runtse, plat ɗin abincin ya ture daga gabansa tare da miƙewa zai bar wajen ba tare da ya yiwa Tutu magana ba, kallon sa tayi tace. "Ya ka tashi baka ce komai ba, ko akwai wata matsala ne.?" Murmushi Nameer yayi yace. "Matsala kuma Tutu, Allah ya rabamu da ita, lokacin aiki ne yayi, Allah ya nuna mana lokacin." Yayi Maganar a takaice yana barin wajen numfashi Tutu ta saki tana sakin murmushi, ko kaɗan bata fahimci Nameer baya sonta ba. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [6/10, 4:54 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 41 to 42_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 Hisham ya riga Nameer fita Company, ko da yaje ya samu tuni har Jidda ta isa, a bakin office ɗinsa ya tarar da ita zaune murmushi Hisham ya saki ko kaɗan Jidda bata kula da shigowar sa wajen ba, sai ji tayi mutum ya sunkuyo kanta har tana jiyo hucin numfashin sa idanunta ta runtse tsikar jikinta ya zuba, ƙamshin turarensa ne ya tabbatar mata da Hisham ne, ganin ta runtse idanunta yasa Hisham sakin murmushi yana ƙarewa ƙaramin bakinta kallo, murmushi ya saki tare da cewa. "ke meye na runtse idon ko ance miki sunbatarki zanyi dallah Malama buɗe idanunki." Jidda da idanunta ke runtse ne tace. "Ka matsa kusa dani malam akan me to zaka ranƙwafo kaina kamar wanda zai bani magani." Kansa Hisham ya ɗaga har yanzu fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna a gefen ta, mutane tsirarun da suke wajen ne suka bi Hisham da kallon mamaki domin kuwa tunda suke dashi basu taba ganin yayiwa wata murmushi ba ko ya tsaya kusa da wata sai yau Hisham duban Jidda yayi yana dariya yace. "Kinsan me kuwa Jidda, gaskiya ke kyakkyawa ce babu ƙarya duk wanda yace miki mummuna sai dai maƙiyi, matsalar ki ɗaya." Hisham yayi Maganar yana taɓe bakinsa, dubansa Jidda tayi tare da sakin murmushi domin kuwa maganar tasa dariya ta bata." "Hmmm! Ikon Allah to meye kuma matsalar tawa yanzu ni ɗin har na fika matsala.?" "Ƙwarai kuwa kin fiye izza da ji da kai ga shegen taurin kai, sai dai fa ahakan ma kina burgeni." Ɗan zaro idanunta Jidda tayi cike da mamaki ta kalli Hisham. "Ni ce nake burgeka Hisham ni ɗin."? Jidda ta masa maganar cike da mamaki, dariya Hisham ya sanya har dimple ɗinsa na loɓawa yace. "Yeah meye Kuma abun mamaki just wanted you to impress me, so why should be surprised? or do you want me to tell you I love You." Zaro idanunta Sosai Jidda tayi tana mamakin anya Hisham ne, kafin tace. "To ikon Allah gani nayi kamar ba Hisham ɗin da na sani ba, dole nayi mamaki, cewa kayi fa ina burgeki, so Hisham......... "Ya isa haka Jidda karki ce komai tabbas rashin jituwa ya faru tsakanin mu a baya amma hakan bashi yake nufin bani da hali mai kyau ba, zan ƙara baki haƙuri a karo na biyu Jidda be patient and forget what happened in the past and take that Hisham that you know now is not a new one." Wani irin sanyi taji jikinta yayi tunda ta ke da Hisham bai taɓa burgeta ba irin na yau lallai yau ta yarda da maganar Nameer Hisham mutumin kirki ne mune bamu fahimce sa yadda ya kamata ba, murmushi Jidda ta saki tace. "Hisham ko Ubangijin da ya hallice mu muna masa laifi kuma ya yafe mana to meyasa mu bazamu yafewa junanmu ba, Hisham daga yau na manta da abinda ya faru a baya, a yanzu na ɗaukeka sabon abokina, komai ya wuce." Murmushi Hisham ya saki cikin zuciyarsa ya furta _lallai ko da kin manta abinda ya faru a baya, to tabbas tarihi zai maimaita kansa da kaina zan tuna miki da wannan mantuwar da kikayi yayin da zaki tafi da ciwon zuciya na bakin ciki, wata kila ma hakan ya zamo ajalinki wannan alƙawarin na ne._ kafin yayi murmushi yace. " Naji daɗi da ya kasance kin manta komai Jidda, tabbas kin samu sabon abokin da zai tare miki wani bangon, zamu ciza kuma zamu hura tare barka da samun sabon aboki." Dariya Jidda tayi kafin kuma ta ɗan haɗa ranta cikin zolaya tace. "Amma tsaya Malam na tambayeka, ta yaya zaka iya abota da mai izza, jiji da kai, shegen taurin kai, ta yaya zaka iya answer me idan har kana son nayi aiki a Companyn nan yau."? Dariya sosai Hisham yayi, kafin yace. "Yess! Shiyasa nace kina burgeni ai, taken mace kenan izza da ji dakai wannan na mace mai aji ne, taurin kai ɗin ne dai Hisham zai sauya miki shi." Murmushi Jidda tayi ta girgiza kanta ganin yau wai Hisham ke dariya abun kamar almara, bakinta ta taɓe tare da mikewa tsaye tana cewa. "Kafin Hisham ya gyara Jidda sau ɗaya na tabbata ita ta gyarasa sau goma, muje ka kaini office ɗina na fara sanin abubuwan da suke gabana." Murmushi yayi tare da cewa. "Dole dai sai kin fara shiga office ɗina na gama sanar dake ayyukan ki sannan na haɗaki da wanda zasu nuna miki yadda aikin mu yake tafiya dole sai kin zagaya Kinga yadda muke harkokin mu, dan haka muje office." "Okay." Jidda tayi maganar tana tashi, tare suka shiga office ɗin, suna zance kamar abokan da sukayi shekara da sabawa. Nameer bai shigo office da wuri ba har wajen 12:30 tunda yazo ya shiga office ɗin sa bai fito ba, tare da sanar da sakatariyar sa duk wanda yazo neman sa tace bazai ga kowa ba yau, shuru yayi cike da tunani da zullumin yanda zaiyi ya rabu da Tutu, idanunsa ya runtse tare da miƙewa tsaye kaiwa da komowa yake a office ɗin sa duk damuwa ta ishesa. _meyasa Kan Tutu baya ja ne, meyasa bazata fahimci baya ra'ayinta ba, duk wannan kuskure na ne da na fara sonki Tutu, Hmm Jidda itace muradina, ina sonta fiye da komai a rayuwata, meyasa na kasa sanar da ke soyayyata Jidda ya kamata ki fahimci ina sonki fiye da yadda uwa ta ke son ɗanta, kece alƙibilata Jidda, I love you so much, i love You so much Jidda, Hmmm! Mtsss ya zamo wajibi na bayyana miki soyayyata idan ba haka ba ciwon sonki zai illata zuciyata, yaya zanyi da soyayyar Tutu ya zanyi na rabu da ita cikin sauƙi, Hmm! Lallai ya zamo wajibi ki cire Soyayyata a ranki a baya Tabbas na soki amma a yanzu babu ɗigon sonki a zuciyata, na yadda da kalmar hausawa da suke cewa so tsuntsu ne yakan tashi daga wannan bishiyar ya koma wata._ dafe kansa yayi tare da neman waje ya zauna, wayarsa ce tayi ringing duban wayar yayi yaga Dear murmushi ya saki tare da ɗaukar wayar ya kara a kunnensa. "Hello Jidda." Daga can Jidda tace. "Gani a bakin office ɗin ka, sakatariya ta hanani shigowa, kace mata wai baka bukatar ganin kowa yau meyasa.?" Numfashi ya saki yace. "Bawa Sakatariyar wayar." Miƙa mata wayar Jidda tayi ta amsa umarni ya bata da tabar Jidda ta shigo, bawa Jidda wayar tayi tace zata iya shiga shiga Jidda tayi da sallama, Nameer yana zaune ya dafe kansa kusan bakinta Uku tana sallama baiji ba ya lula duniyar tunani, zama Jidda tayi tare da buga teburin dake gabansa a ɗan razane Nameer ya ɗago kansa ganin Jidda ya sashi sakin numfashi tare da cewa. "Har kin shigo."? "Eh tunanin me kake haka ina ta sallama bakaji ba, da alamu Dai yau kana cikin damuwa."? "No babu wata damuwar da nake da, kawai yau stress ɗina ne haka, ya akayi.?" "Wannan file ɗin ne Hisham yace na kawo maka ka duba." Amsa Nameer yayi ya buɗe file ɗin, kafin yace. "Zanyi aiki a kansa kafin na dawo miki dashi sai ki nemi mai file ɗin idan ya dace da muyi aiki dashi." "Okay to shikenan bara na koma office." "Da wuri haka, tun bamuyi hira ba, dama fa neman ki nake akwai Magana mai mahimmanci da nake son mu tattauna, amma yanzu nasan lokacin aiki ne, mayi maganar wani lokacin." "To shikenan ba damuwa bara naje ni." Kansa Nameer ya haɗa kafin Jidda ta fita. ********** Inda suka saba haɗuwa yauma dai nan suka tsaya, Tunde ne ya dubi Sadiq yace. "Mama tace har yanzu taji shuru babu wani motsi, babu wani harin da ka aikawa Hisham meyasa."? Murmushi Sadiq ya saki tare da cewa. "Ka ce mata yaƙin sunƙuru nake bana bukatar kai hari cikin gaggawa, ka sanar da ita cewa ta yadda dani ne yasa ta bani wannan aikin dan haka ta saka ido kawai tayi kallo, ta yaya kuke tunanin na kai masa hari, wato na fargar dashi cewa ana neman rayuwarsu ne, ina bazan taɓa barin ya fahimci hakan ba nafi bukatar na kaisa ƙasa kafin ya ankare." _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [7/6, 8:07 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE📚* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *_Page 43 to 44_* Dariya Tunde ya saka kafin yace. "Hakane amma kasan bana bukatar ɓata lokaci, kusan kullum sai na faɗa maka wannan kalmar, kawai ka aika masa makamanka." "Okay tunda haka kuke bukata kun matsa zan jaraba, amma duk abinda ya biyo baya ku kuka da kanku domin kuwa ni zan iya zillewa, zan saka aiki tunda naji next week ne zaka fara aiki, zan nemo guba, da za'a sawa Nameer a jus ko copee ta kansa zamu fara, zan sanar da kai yadda aikin zai kasance, guba ce mai haɗarin gaske dole sai ka kula." "Takan Hisham ya kamata mu fara ba Nameer ba domin kuwa nameer bashi da gadon IYABO Hisham shine jininsa dan haka shine zai zamo abin harin mu na farko da jinin Iyabo ya kamata mu fara yaƙi ba ɗan riƙo ba." Tunde yayi Maganar cikin rashin gamsuwa da maganar Sadiq tsawa Sadiq ya dokawa Tunde tare da cewa. "Karka kuma bani umarni domin kuwa ba sayata kukayi ba, idan har ka kuma bani umarni to kuwa zan ijiye muku aikin ku sannan kuma na zamo Mutum na farko da zai tarwatsa aniyarku, kunsan waye Sadiq yana da kyau ku kula, da ƙwaƙwalwata zanyi aiki ba da daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarka ba, zan kama gabana yanzu idan kaje ka sanar da tsohuwar kakar taka yadda mukayi yanzu, tabbas Nameer shine first target ɗin mu." Sadiq yayi Maganar yana buɗe murfin motar da sauri ya fice ya tokare fuskarsa da kula posingcap, numfashi Tunde ya saki tare da jan motar ya nufi gida, Wamimo ya tarar a falon nasu babu Mamabisola zama yayi gefen kujera mai biyu cikin harshen yarbanci su gaisa da Wamimo kafin yace. "Mo ni Mama?" Ya tambayi Wamimo cikin harshen yaruba, kitchen Wamimo ta nuna masa tace. "O wa ni ibi idana ounjẹ bayi nduro fun ọ" "Okay bara naje na sameta kawai." Tunde yayi Maganar yana tashi ya shiga kitchen ɗin tana wajen gas tana tafasa ruwan Lipton, Tunde ya tsaya gefenta ransa a haɗe. "Na ga ka haɗa ranka meye Sadiq ɗin ya maka.?" "Babu abinda yamin Mama sai dai da alamu bamu samu abokin aiki ba, domin kuwa baya amsar umarni daga garemu wanda a wannan tsarin mune muka ɗaukesa aiki kuma ya zamo wajibi ya ɗauki umarninmu." "Ban tari numfashinka ba Tunde, amma ka sani aikin kai da kai muke da Sadiq bani gishiri na baka Manda ne dan haka nemosa mukayi akan gaɓar da ta dace, ƙwaƙwalwarsa na ja sosai dan haka muje dashi a yadda yake so mu bukatar mu burin mu ya cika, da zarar burinmu ya cika to ƙofar rago zamu masa." "Okay sai yanzu na fahimci karatun, yace da Nameer ya kamata a fara bansan dalilinsa na hakan ba, amma koma menene ke na fahimce ki." "Tunda ka fahimce, kaje kawai mu barsa da ƙudirinsa." "Shikenan Mama ko part ɗina ban shige ba nazo nan bara naje." Tunde yayi Maganar yana sakin murmushi, itama Mamabisola murmushin tayi kafin Tunde ya bar kitchen ɗin. *********** Jidda ganin ta tashi aiki da wuri ya sata biyawa gidan su Basmah, dan ta sanar da ita ranar zata koma gida, ta samu kuwa ta koma, Abban Basmah ta shiga ta gaisar kafin ta shige ɗakin Basmah tana zaune tayi shuru da alamu tunani take ga wayarta kuma a gefe ana kira bata lura ba zama Jidda tayi tare da dafa kafaɗar ta tace. "Ke tunanin me kike haka ga wayarki kuma majnunun naki yana kira."? Tsuka Basmah taja tana kallon wayar tata tare da jan doguwar tsuka cike da mamaki Jidda tace. "Basmah Ahmad ne fa yake kiranki kika ja tsuka lafiya ko kunyi faɗa ne."? Kanta Basmah ta girgiza tare da cewa. "Faɗa kuma kema ai kin san bamu taɓa faɗa da Ahmad ba, kawai dai wayar ce yau bana son yi har kun tashi daga wajen aikin ne."? Kanta Jidda ta ɗagawa Basmah tace. "Eh na dawo 5:00pm suke tashi daga aiki ga ko wanne ma'aikaci." "Jidda ina son na ijiye aikina na jarida nazo na nemi aiki a Companyn ku nima, saboda bana jin daɗin aikin babu ke." Ɗan zaro idanunta Jidda tayi tace. "Basmah kinyi shaye-shaye ne da kike faɗar wannan maganar." "Jidda sai nayi shaye-shaye ne zanbar aiki a Aminci, just ce miki nayi na gaji bana son aiki dasu, ina bukatar sauyi, fine babu wani laifi tunda ba Companyn ubana bane da zan tabbata anan ke ko Companyn ubanane idan na gaji zan iya sauya waje bare wannan da bani da alaka ta kusa ko ta nesa dashi." "Amma ai komai yaya ne bai kamata ki bar aiki a ƙarƙashin Aminci ba, aikin jarida yana da matukar muhimmanci, ko nima ba'a son raina nabar aiki dasu ba, amma idan kina ganin hakan yafi miki shikenan sai ki fara tuntubar Nameer kiji." Numfashi Basmah ta saki tare da cewa. "Ba Nameer zan tuntuba ba, Hisham zan tuntuba saboda shi mutumin kirki ne, infact ma hankalina yafi kwanciya dashi." Dariya Jidda ta saki tace. "Au har Hisham ne yafi Nameer kirki, impossible kawai dai son ranki kike faɗa Malama." "Ke nifa Hisham burgeni yake wallahi, gayen yayi arayuwa kina ganin handsome guy, kinga kamar fa yadda Nameer ɗin ya faɗa ne a baya HISHAM mutumin kirki ne kawai rashin fahimta yasa muke masa kallon wani bahagon mutum amma ni yanzu na fahimci waye Hisham." Taɓe bakinta Jidda tayi tace. "Hmmm! Hakane nima na fahimci hakan amma duk da Hisham bazai kai Nameer kirki ba, ke Kinga ni wannan chapter ta isheni haka dama jikin Abba nazo gani, kuma tunda jikin da sauƙi tashi ki rakani nayi gida." Jidda tayi maganar tana tashi, tashi itama Basmah tayi Jidda ta shiga ta yiwa Mama sai da safe kafin Basmah ta rakata har waje. ********** Da daddare Jidda tana zaune suna hira da Umma taji wayarta tayi ringing dubanta ta kai ga wayar taga Hisham, murmushi ta saki tare tashi ta koma ɗaki tana ɗaga kiran. "Hello." Jidda tayi maganar tare da yin shuru daga can Hisham yace. "Hi ƙawata ya akayi kin koma gida lafiya."? Murmushi Jidda tayi tace. "Na koma lafiya, ya naka gajiyar aikin."? Murmushi Hisham yayi yace. "Gajiya kuma sai kace mace, no ni ban gaji ba, amma ina fatan kinji daɗin aiki da Companyn mu ko.?" "Eh to da dai da ne sai nace aiki da Hisham babu daɗi amma da Hisham ya sauya lokaci guda aiki dashi yafi komai daɗi, naji daɗin fara aiki a ƙarƙashin ka.'' Ɗan dariya Hisham ya saki yace. "Masha Allah kice Hisham ya ciri tuta, kin san meye Jidda.?" "A'a sai ka faɗa." Gauron Numfashi ya saki tare da ɗan hura iska a Speaker wayar, yace. "Ke macece ta musamman, kina abubuwa da yawa wanda ba ko wacce mace ta ke dashi ba, ke ta dabance da sauran mata, kina burgeni sosai Jidda, gaki da kyau ga ado ga diri ga kyawun sura ga ilimin addini dana zamani, bakina yayi kaɗan ya lissafo ingancinki shiyasa nace ke macece ta musamman Jidda." Murmushi Jidda ta saki sosai taji daɗin maganganun Hisham. "Duka wannan yabon ni na cancanci amin sai na ke ga kamar bani da wannan abubuwan da ka lissafo." "Bazaki fahimci hakan bane ke, amma ni na hango abinda ke baki hango ba, bara na barki haka dama na kira naji kin isa lafiya ne, ki gaishe da Umma." "Shikenan zataji na gode." "Okay bye." Hisham yayi Maganar yana katse kiran murmushi Jidda ta saki tare da lumshe idanunta ta furta.. _Hmmm! Hisham kai mutum ne na musamman wanda ya zauna da kai shine kawai zai fahimci hakan._ Tayi Maganar tana sakin numfashi tare da tashi ta dawo wajen Umma. "Ke dawa kike waya ne.?" Cewar Umma Jidda zatayi Magana yaro ya shigo yace. "Wai Jidda tazo inji Abdulra'uf." "Abdulra'uf kuma na masa meye jeka ce ina aiki bazan samu fitowa ba."? Umma ne tace. "Kai yaro kace tana zuwa." Da sauri Jidda ta kalli Umma cikin mamaki, Umma cewa tayi. "Kalleni da kyau ja'ira yo meye laifin Abdulra'uf da zaki dinga nuna masa ƙiyayya gani nayi wanda yace yana sonka ya fi maƙiyinka komai lalacewarsa, maza kije ki sauraresa baki san inda alkairinki yake ba, yaron arziki da yake mutunta naki ke kice zaki nuna masa ƙiyayya, wannan ba tarbiyya ta bace." Bakinta Jidda ta tura tace. "Ni fa Umma bana sonsa, dan haka banga dalilin da zaisa na dinga tsayuwa dashi ba muna ɓatawa juna lokaci, kawai Umma ke babu ruwanki a tsakanin mu." Abdu ne yace. "Amma fa Adda gani nayi Abdulra'uf bashi da laifi yana da sana'ar sa, kuma mutumin kirki ne, yana da cikakken ahali, ina ga wannan ake bukata a neman Aure." Harara Jidda ta watsawa Abdu tace. "Kai kuma wa ya saka bakinka a cikin wannan maganar, ko Maganar ne.?" "Ya fiki gaskiya ki daina masa tsawa, ki tashi kije kiransa maza." Miƙewa Jidda tayi ranta a ɓace ta yayiɓi Hijab ɗinta zata fita taji Umma tace. "Au saboda zaki wajen maƙiyinki shiyasa bazaki kimtsa ba, zaki fita haka to maza ki dawo ko ɗan powder ki goga a fuskar ki." "Kanta Jidda tasa ta fice ba tare da ta juyawa ba kanta Umma ta girgiza ta cewa Abdu. "Rabu da ita sai dai ta fita ko bata so, ni banga laifin yaron nan ba da tabi ta ɗaura masa tsana, yaron da tun yana ƙanƙaninsa ubansa ke tahowa dashi a hannu ƙofar gidan ga, nasabar sa duk an sani amma tsabar iya shege irin na jiddatul kair tabi ta ɗaura masa karan tsana, na rasa dalilin da yasa bata sauraron samari duk wanda yazo zance wajenta sai tasan yadda tayi ta koresa, ni wannan lamari harya fara bani tsoro, shuru kawai nayi ina kallonta ta mai sheni shasha bansan sonta shi Abdulra'uf yake ba." "Hmmm! Umma ni fa na rasa me yake damun Adda, ko fa zancen Aure bata so a mata." Abdu yayi Maganar yana kallon Umma. "Barni da ita zan daidaita ta ne, ka tashi kaje ka karɓo min kamu a wajen Iya." Amsawa da to Abdu yayi yana tashi ya fita. Ko da Jidda ta fita ta samu Abdulra'uf tsaye jikin gidan Alhaji Barau da ke manne jikin gidan nasu, tsayawa Jidda tayi tare da sallama ta kawar da kanta gefe fuskarta a haɗe daga wannan sallamar Jidda bata kuma magana ba, ko arzikin gaisuwa bai samu ba, numfashi ya saki ganin Jidda bata da niyyar magana yasa shi nisawa yace. "Da ganin fuskar ki baki so kika fito, kiyi haƙuri idan na takuraki ba laifina bane laifin zuciyata ne, na kasa cireki a cikin zuciyata, ina sonki, amma na rasa dalilin da yasa kike nuna min ƙiyayya, Meyasa haka Jidda.?" Sai yanzu Jidda ta ɗago kanta ta kalli Abdulra'uf tace. "Naji daɗi da kamin wannan tambayar, ba ƙiyayya nake nuna maka ba, bana son na yaudareka saboda bana jin zan iya Auren ka, kayi haƙuri ba wai ina faɗa maka wannan maganar ba ne saboda kaji zafi a ranka bane, a'a ina faɗa maka gaskiyar abinda yake raina ne, bana jin sonka na Aure a cikin zuciyata karmu yaudari juna dan Allah kayi haƙuri ka nemi wata Please." "Hakane na juma da fahimtar bakya sona sai dai idan na zauna ina yawaita tunanin cewa ko wani mungun hali nake dashi wanda bazaki iya aurena ba saboda shi, kokuwa saboda ni talaka ne shiyasa, ki amsa min wannan tambayar abinda ya kawo ni ƙofar gidan ku kenan yanzu."? "A'a ko ɗaya Abdulra'uf baka da wani mungun halin da za'a ƙika saboda shi halinka mai kyau ne, haka kuma ni ba yar kowa bace dan haka bazan ce sai mai arziki zan aura ba, sonka ne kawai banayi ka fahimta kayi haƙuri kaje ka nemi wata zaka samu wacce ta fini idan har bakaji daɗin maganata ba, dan Allah kayi haƙuri." "Ba sai kin bani hakuri ba Jidda ba komai Allah ya haɗa kowa da rabonsa, amma ki sani ina jinki a cikin zuciyata bazan taɓa daina sonki ba Jidda Allah ya baki miji na gari wanda zai riƙeki bisa gaskiya da amana, ni zan tafi ki gaishe da Umma." "Na gode da ka fahimce ni kaima Allah ya baka wacce ta fini." Jidda tayi maganar tana komawa ciki. ************** Bayan sati guda Damuwa da soyayyar Jidda ta hana Nameer sakat duk sanda ya kasance shi ɗaya babu abinda yake sai tunaninta, zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa, sai yayi yunkurin sanar da ita Soyayyar sa sai yaji ya kasa hakan, yayin da tsananin shaƙuwa ta shiga tsakanin JIDDA da HISHAM ya zamo tamkar abokinta na yarinta, zuciyarta ɗaya take jin Hisham sai dai shi kuwa har yanzu cikin zuciyarsa tsanar JIDDA ce a cikin ta, yana sake mata ne kawai saboda burin samun cikar ƙudirinsa akanta. Yau takama asabar ranar weekend yana zaune shi kaɗai a falo ya kira JIDDA, da sanar da ita zasu haɗu ya fitar da abinda ke ransa ko zai samu sukuni, ringing ɗaya ta dauka, daga can tace. "Barka da safiya Nameer." "Barka Jidda ina fatan yau kina free ina son zamu haɗu ne da ke a inter room garden." Numfashi Jidda ta saki kafin tace. "Okay ba damuwa amma lafiya kuwa sannan zan iya zuwa da Basmah."? Murmushi NAMEER ya saki tare da cewa. "Zaki iya zuwa da Basmah, wannan kiran alkairi ne Jidda fatana dai mu haɗu yau ɗin." "Okay da misalin ƙarfe nawa zamu haɗu."? "By 4:30pm." Nameer ya faɗa a takaice, murmushi Jidda tayi tace. "To shikenan sai mun haɗun ka gaishe da ummin ku." Da zataji Nameer ya amsa kafin ya katse kiran dai-dai Hisham na sauƙowa ya zauna gefensa yana cewa. "Ya kake zaune kai ɗaya, ina Ummi da Tutun suke.?" "Tutu ai tana da school yau, Ummi kuma bata juma da shiga bedroom ɗin ta ba, ya akayi alkawarin mu fa ya kusa Malam kuma har yanzu banji motsinka ba." Murmushi Hisham ya saki tare da cewa. "Karka damu da motsina ka jira yau zakaji kyakkyawan labari domin kuwa a yaune zan kiraka kaga matar da zan Aura." "Serious Hisham."? Nameer ya tambayesa cike da mamaki. "Yeah serious kasan dai ban taɓa ɗaukar alƙawari ban cika ba ko, duk da soyayya bata gabana haka kuma har yanzu banga kalar matar da tamin ba, ko wannan da zan fitar manage zanyi da ita." "Hisham ni fa kana bani mamaki ta yaya zaka auri abinda baka so, wacce Yarinyar ce zatayi gangancin Auren mijin da baya sonta, karka zalunci Yarinyar mutane Hisham, idan baka sonta Please karka yaudareta tukunna ma a ina ka samu yarinyar tell me.?" Dariya Hisham yayi yace. "Tell me! Tell me! Hmmm! Nameer koma wacece ka jira zaka ganta, sannan maganar Soyayya ko yaudara da kake, ita ta gani kuma zata iya ɗauka, dan haka babu ruwanka da rayuwata a wannan sabgar kowa ya iya ruwa zai fito ko teku ya faɗa." Hisham yayi Maganar yana tashi zai bar wajen, magana Nameer yake masa amma Hisham bai ma tsaya ya sauraresa ba ya fice, numfashi Nameer ya saki tare da furta. "Wacce yarinya ce Hisham ke shirin kai rayuwarta ya baro, mtss! Allah ya rufa asiri, to ni kuma ya zanyi da matsalar Tutu ya zataji idan na fitar da wata a matsayin matar aurena ba ita ba, anya zuciyar ta zata iya ɗaukar wannan ƙaddarar."? Ya tambayi kansa yana dafe da kansa, ya juma sosai a falon yana saƙar zuci kafin yabar falon. ********** Jidda cikin shiri ta fito da la'asar dai-dai lokacin da sukayi alkawarin haɗuwa da Nameer yayin da ya rigata zuwa wajen yana zaman jiranta, tare da Basmah suka fito, cike da mamaki Jidda ke kallon Hisham da ta gansa tsaye a ƙofar gidan su jikin motarsa. "Hisham kaine kazo babu kira.?" Hannunsa Hisham ya harɗe tare da cewa. "Au dama doka ce idan zanzo wajenki sai na kiraki a waya."? "Ko ɗaya babu wata doka kawai naga ka saba kirana ne idan zakazo." "Okay yau kuma ban kira ba, Umma tana ciki ne ina son zan sanar da ita zamu fita unguwa da ke.?" "Unguwa kuma yanzu Hisham baka ga fita zamuyi da Basmah ba ne ko baka ganta bane, ina da alƙawari da Nam......... Bata kai ƙarshen maganar ba Hisham ya katseta da cewa. "Listen to me, I told you, we will go out or I will not go out with you tell me."? Kanta Jidda ta girgiza tare da cewa. "Ni fa bance baka kai ka fita unguwa dani ba cewa nayi akwai wanda yake jirana yanzu haka.'' Fuskar sa Hisham ya haɗe tamau tare da kallon Basmah yace. "Ki koma gida Basmah ki cewa Umma na fita tare da Jidda plaza zata tayani sayayya kiyi haƙuri Basmah bazamu daɗe ba yanzu zamu dawo." Yayi Maganar yana buɗewa Jidda gaban mota kallon Basmah Jidda tayi da ta ke kaɗawa Hisham kai kamar ƙadangare kafin ta buɗe motar ta shiga ita kuma Basmah ta koma cikin gida duk abinda ke faruwa ABDULWASI'U yana ƙofar shagonsa yana kallon su, domin kuwa shi gani yake Jidda irin su Hisham take harin Aure ba irinsa ba talaka shima Hisham motar ya shiga ya ja suka ɗauki hanya, sun ɗanyi nisa da tafiya wayar Jidda tayi ringing hannu tasa cikin jakarta ta ɗauko wayar zata amsa kiran HISHAM yayi saurin kwace wayar daga hannunta ya kashe ba tare da ya duba mai kiran ba cikin aljihun sa ya jefa wayar, Jidda ko da bata ga mai kiran ba tasa Nameer ne yana can yana jiranta yaji shuru. "Hisham why are you turning off my phone when you are calling me?" Kansa Hisham ya girgiza. "I do not need to know, Jidda I want you to give me peace of mind when I need you ." "Ka fiye rigima Hisham, muje na ga inda zaka kaini." "Kinyi kyau fa sosai tamkar ɗanyen gold haka kika fito." Murmushi Jidda ta saki. "Ka iya tsara zance Hisham, yanzu ina muka nufa." Murmushi Hisham ya saki yace. "Karki damu zaki gani yanzu." Yayi Maganar yana kashe mata ido, kafaɗarta Jidda ta ɗaga alamun to, suna zance jefi jefi har suka shiga babban Mall ɗin Alhassan Ɗan Iya da ke titin Darasawa, parking Hisham yayi tare da fitowa itama Jidda fita tayi tabi bayan Hisham, wani office ya shiga tana tsaye a bakin office ɗin bai juma ba ya fito suka shige ciki tunda Jidda tasa ƙafarta a wannan wajen wani irin sanyi ya ratsata idanunta ta zaro tana kallon abun mamaki yanda aka ƙawata wajen da kyawawan furanni, mai launin ja da kore, ga wasu irin wuta da suke bada hasken ja da kore. "Wow." Jidda ta furta a fili, murmushi HISHAM yayi Jidda bata ankare ba taga Mutum ya durƙusa a gabanta tare da buɗe akwatin zobe da ke hannunsa zoben azurfa ne mai kyawun gaske an masa ado da zanen love. "I LOVE YOU JIDDA I WANT YOU TO MARRY ME, I REALLY LOVE YOU, HELP ME RESPOND TO MY LOVE, I LOVE YOU." Tamkar saukar aradu Jidda taji maganar idanunta ta zaro tana bin Hisham da zoben dake hannunsa kallon mamaki. "Hisham, are you in love with me?." "Yeah Jidda i really love you." "No Hisham you are dreaming, I do not have a position to loving me, bani da wannan matsayin ko wacce kwarya da abokiyar burminta." Kansa Hisham ya kaɗa cikin nuna tsantsar damuwa yace. "Ki taimakeni ki amshi soyayyata muddun ba so kike rayuwata ta shiga cikin haɗari ba, babu ruwan so da sani matsayi ko iko Jidda, ki taimakeni ki soni dan Allah." "No Hisham babu soyayya tsakanin m........ Katseta yayi da cewa. "Please JIDDA ki taimakeni ki amshi soyayyata wallahi ina sonki na juma da soyayyarki a cikin raina please kiyi seving ɗin rayuwata I love You Jidda." Runtse idanunta Jidda tayi ta sani babu Macen da Hisham zaice yana so ta ƙisa, itama idan tace bata sonsa a yanzu wallahi tayi ƙarya girgiza Kanta tayi tare da miƙo masa yatsarta zoben Hisham ya sanya mata a yatsar kafin ta ɗago yatsar tana kallon zoben idanunta na runtse ta furta. "I accept your Love Hisham, I love You too. " Miƙewa daga tsugunnen da yake Hisham yayi yana sauƙe ijiyar zuciya mai nauyi a fili ya furta. "Yes! Jidda thank I love you so much." Ya furta cikin farin ciki tare da zagowa gabanta ya ciro wayarsa selfie ya ɗaukesu dukkan su suna dariya ita dashi suna kallon juna, kana kallon picture ɗin kasan dukkan su suna cikin farin ciki, nuni Hisham ya yiwa Jidda da kujerar dake gaban ƙaramin table ɗin da ke ɗauke da kayan alatu na ci dasha ya mata alamun ta zauna, zuwa Jidda tayi ta zauna har yanzu murmushi ta ke. Shi kuwa Hisham picture ɗin ya turawa Nameer ta Whatsapp tare da rubuta masa. _surprise she is my wife to be, My first Love JIDDA._ Yayi sending yana sakin murmushi, tare da tura masa text ta message yace ka buɗe Whatsapp ɗinka na aiko maka da saƙo mai mahimmanci. Nameer dake can yana zaman jiran JIDDA a cikin inter room garden, sai duba agogo yake har 5:30pm babu Jidda wayarta kuma ya kira yafi sau goma switch off ya kira Basmah ma wayarta baya tafiya, jin shigar text cikin wayarsa ya sashi duba sakon Hisham ya gani, data ya buɗe cikin minti goma sai sakon nasa na Whatsapp ɗin ya shiga, Nameer kansa tsaye ya shiga kan saƙon picture ya gani rubutun ƙasan ya fara karantawa kafin ya buɗe picture ɗin. _Surprise She is my wife to be, My first Love Jidda._ Murmushi Nameer ya saki ko a zuciyarsa bai kawo Jiddar sa bace ya furta. "Wai dama da gaske Hisham yake ya fitar da matar aure, cap waye ce tayi gangancin shiga rayuwar Hisham." Yayi Maganar yana saka hannu ya buɗe picture ɗin, a wani irin firgice ya miƙe tsaye ganin Hisham tsaye da Jiddar sa da yake zaman jira yanzu cikin nishaɗi suna dariya. "Whatt! Jidda no impossible ba Jiddana bace." Nameer yayi Maganar cikin tashin hankali yana goge idanunsa wai ko sune suke masa karya. _____________________________________ *_ALHAMDULILLAH NA GODE SOSAI DA ADDU'OIN KU MASOYA DA KUMA UZURIN DA KUKA MIN NA DAKATAR DA WANNAN LABARIN DA NAYI NA WASU KWANAKI HAR ALLAH YASA YAU NA DAWO, ALHAMDULILLAH! JIKIN MAMA YAYI SAUƘI SOSAI ADDU'A TA KARƁU NA GODE SOSAI JALALA POSTING BA KAMA HANUN YARO INSHA ALLAH I LOVE YOU MY FAN'S🥰_* *MUSAMMAN JALALA GROUP DA ƳAN UWANA SHAƘIƘAINA ƳAN ƘUNGIYATA KAINUWA WRITER'S INA GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU, NA GODE NA GODE DA KULAWARKU GARENI MASU KIRANA DA MASU TURO MIN SAƘO NAJI DAƊI SOSAI ALLAH YABAR ZUMUNCI.* _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [7/7, 8:22 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. https://chat.whatsapp.com/KoKE4o7opsRG4PfMLrKO2J Mutane sai tambayata LINK ƊIN group ɗin JALALA suke to yau dai gashi na sake muku link ɗin amma group ɗina yana da doka, sannan ina haɗa namiji da Allah da yayi haƙuri karya shiga min group dan Allah na haɗaka da Allah🙏🏼 *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 45 to 46_* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 "Ta yaya hakan zata faru soyayya tsakanin wuta da auduga, no bazai taba yiwuwa ba domin kuwa babu ta yadda wuta zata jitu da Auduga a waje guda, na tabbata dole sai wannan wutar ta ƙoneta, ya akayi haka Hisham da Jidda soyayya." Ya furta maganar a kiɗime cikin munguwar mamaki. _yeah serious kasan dai ban taɓa ɗaukar alƙawari ban cika ba ko, duk da soyayya bata gabana haka kuma har yanzu banga kalar matar da tamin ba, ko wannan da zan fitar manage zanyi da ita_ Ya maimaita maganar Hisham ta ɗazu a cikin zuciyarsa yana neman warware kalaman nasa amma ƙwaƙwalwarsa ta gaza fassara kalaman Hisham, ko cikin mafarki kai ko a zahiri aka ce masa yau HISHAM da Jidda zasuyi jituwar da soyayya zata shiga tsakanin su wallahi sai ya ƙaryata, runtse idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur yayi tare da buɗesu ya dafe kansa dake sara masa ji yake tamkar ya kurma ihu da ƙarfi ko nauyin da zuciyar sa ta masa zata ragu. "Meyasa ƙaddara zaki min haka, meyasa kika haɗa soyayyar mace ɗaya a zukatan ƴan uwa masu ƙaunar junan su, wannan wacce irin mummunar ƙaddara ce, I love Jidda, bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, why Hisham zaka rabani da farin cikin rayuwata why, bazan iya jure rayuwa ba tare da ita ba, HISHAM! Why.!?" Yayi Maganar cikin ƙaraji yana dunƙule hannunsa ya daki teburin gabansa idanunsa ya runtse tare da cije lebensa idanunsa sun dawo tamkar gauta wato Jidda shanyasa tayi ta tafi wajen Hisham ta ma manta da yana jiranta, yayi Maganar zucin zuciyar sa tamkar zata fashe, sakon Hisham ya ƙara dubawa bai san sanda hawaye ya biyo idanunsa ba, hannunsa na karkarwa zuciyar sa na ƙuna ya yiwa Nameer reply da _congratulation Bro na tayaka murnar samun Mace ta gari, ko cikin mafarki ban taɓa zaton soyayya zata shiga tsakanin Hisham da abokiyar faɗansa JIDDA ba, ashe Alkairi ne tsakanin ku, naji daɗin haɗuwar ku Allah ya sanya muku alkairi._ Ya tura saƙon zuciyar sa na harbawa da ƙarfi hannunsa ke tura saƙon amma zuciyar sa tamkar zata fashe haka yakeji, numfashi ya saki tare da kifa kansa jikin kujerar da yake zaune hawaye ya cigaba da zirarowa daga idanun sa, ga wani kwallon da ya tsaya masa na baƙin ciki ya tokare masa ƙirji ya juma sosai kansa yana kife kafin ya ɗago ya share hawayen sa miƙewa tsaye yayi tare da kwasan wayoyinsa ya fito daga wajen motarsa ya shiga yaja da ƙarfi cikin matsanancin tashin hankali ga kansa dake mungun sara masa. ******** Zama yayi a gabanta ya fuskance ta tare da dafe kumatunsa ya zuba mata idanu yana lumshe idanunsa. "Kallon yayi yawa idan dai ba haɗiye ni zakayi ba." Jidda tayi maganar tana sakin murmushi, murmushi shima Hisham ya saki yace. "Kinsan meye kuwa."? "Ban sani ba har sai ka faɗa." Numfashi Hisham ya saki tare da cewa. "Banyi zaton zaki amshi soyayyata cikin sauƙi ba Jidda, hmm! Jidda tun sanda na fahimci cewa ke macece mai adalci da riƙon amana da kuma tallafo damuwar wani daga ranar na fara jin Soyayyar ki a raina da farko banyi zaton cewa soyayya bace na ɗauka cewa kawai burgeni kike, sai da zuciyata ta fara matsa min da tunaninki da kuma yawan kallonki a cikin idanuna da kuma mafarkin ki da nakeyi ko yaushe yasa na fara gaskata zuciyata sonki take, Soyayya kuma ba ta wasa ba, i love You so much Jidda, hmmm! Na miki abubuwa da yawa na rashin kyautawa hakan yasa nake jin zaiyi wahala ki amince da soyayyata, meyasa kikayi saurin amincewa dani Jidda?." Tunda ya fara Maganar ta tsura masa idanu tana kallon sa har sai da ya kai ƙarshe kafin tayi murmushi tace. "Hisham babu ruwan so da ɗabia dan haka ka daina tambayata dalilin Soyayyarka a gareni abinda dai na sani ina sonka a koma yaya kake ni zan iya rayuwa da kai a haka." "Hmmn! Hakane Jidda na sani babu ruwan so da ɗabia amma kuma ki sani akwai ɗabiar da so ke gujewa, musamman ni da............ Saurin dakatar da Hisham Jidda tayi da cewa. "A'a Hisham karka tuna baya mu kalli gaban mu da kuma tunanin yaya zamu tafiyar da goben mu, ina sonka Hisham soyayya ta gaskiya." Murmushi Hisham ya saki sun juma sosai a wajen suna fira cikin nishaɗi har sai 5:59 sannan Hisham ya dawo da Jidda gida bayan ya gama mata sayayya. Jidda na shiga gida Hisham ya saki numfashi tare da sakin murmushi wayarsa ya ɗauka ya kira Sadiq yana ɗagawa yace su haɗu a gida kafin ya katse kiran ya ja motar. *********** Tutu tana zaune a falo taga shigewar Nameer kamar mai tangaɗi yana riƙe da kansa da sauri Tutu ta miƙe tsaye tare da cewa. "Subahanallah! Yaya Nameer meya sameka.?" Bai ko kulata ba ya haura sama da ƙyar bayansa Tutu tabi da sauri, kusan tare suka shiga bedroom ɗin nasa, a saman bed ya zube yana runtse idanunsa har yanzu ƙirjinsa zafi yake masa ga ɗaci da yakejin zuciyar tasa na masa, idan ya runtse idanunsa sai ya ga hoton Hisham da Jidda da sauri ya buɗe idanun nasa a firgice tare da furta "Ni!." Da ƙarfi cikin ƙaraji har sai da tutu ta tsorata da sauri tace. "Yaya Nameer meya sameka, hankalina ya tashi Yaya Nameer please meke faruwa."? Idanunsa da suka gama rinewa ya ɗago ya kalli Tutu wani irin haushinta yaji bakinsa ya cije bai kulata ba ya juyar da kansa gefe, cikin tashin hankali Tutu ta kuma fuskantar Nameer ta sunkuya a gabansa tace. "Yaya Nameer please meyake damunka, dan ka faɗa min hankalina ya na tashe."? Cike da jin haushin ta Nameer ya daka mata tsawa yace. "Get out Tutu." "Yaya Nameer na fita kace, kana cikin damuwa zaka ce na fita na baka waje, ta yaya zan iya barinka cikin wannan damuwar, idan kana cikin damuwa zuciyata bazata taɓa samun sukuni ba, bazan bar nan ba har sai ka faɗa min abinda ya sameka." Cikin tsawa ya kuma ce mata. "I told you to get out of this room! And don't make me worry more, Get out." "Nameer........... "Please! I say get out." Yayi Maganar cikin tsawa yana yunƙurowa tamkar zai kai mata duka, a firgice Tutu tayi baya tare da tashi ta fice da sauri tana kuka, Nameer kansa ya dafe. "I love you so much Jidda, how can I own you? why Hisham you will come between me and my happiness, why."? Ya furta hawayen na kuma biyo idanunsa. Tutu tana fita falo ta zauna a saman kujera tana rera kukanta, cikin munguwar damuwa da tashin hankali ta furta. "Why are you expelling me from you Yaya Nameer, what is happening to you? Your concern lifts my spirits, I love You so much Yaya Nameer, i love You." Ta furta cikin tashin hankali tana cigaba da kukanta, tana cikin kukan Hisham ya shigo tsayawa yayi cak yana kallon Tutu tare da furta. "Ke kukan uban me kike yi me aka miki.?" Jin muryar Hisham yasa Tutu miƙewa da sauri ta faɗa jikinsa tare da kuma sakin kuka mai sauti. "Tutu tambayar ki fa nake wht happening.?" Cikin kukan tace. "Yaya Nameer yaya Nameer ne yaya Hisham yana can." "Nameer kuma meye Nameer ɗin ya miki dukanki yayi."? Hisham ya mata tambayar a takaice. Hawayen ta ta share tana sauke ijiyar zuciya tace. "A'a ni ba dukana yayi ba, shine dai yana can ya shigo cikin damuwa har hawaye yake idanunsa kuma sunyi jajur da na bisa bedroom ɗinku ina tambayar sa meya samesa shine yamin tsawa wai na fita na basa waje, hankalina ya tashi Yaya Hisham saboda ban taɓa ganinsa a cikin irin wannan mummunan yanayin ba." Numfashi Hisham ya saki cike da mamaki yace. "Nameer kuma yake cikin damuwar da har zata sanya sa kuka, kuma ban sani ba kai mtsss bara dai na je na gani." Yayi Maganar yana cire Tutu daga jikinsa ya haura bedroom ɗin da sauri, Tutu numfashi ta saki har yanzu tana cikin tashin hankali wayarta ta ɗauka ta kira kawarta Samira tace tazo zasuyi magana kafin ta katse kiran tana zama ta zuba tagumi. A firgice ya tura bedroom ɗin nasu ko sallama baiyi ba turus ya tsaya ganin Nameer cikin yanayin da Tutu ta sanar dashi. _Da gasken kuwa hawayen yake_ Hisham ya furta cikin zuciyarsa kafin ya ƙaraso kusa dashi da sauri ya zauna yana dafa kafadarsa jin an da fa kafadarsa yasa Nameer saurin ɗago rinannun idanunsa ya zuba a cikin na Hisham da baisan ma shigowarsa ba. "Nameer dama ashe zaka shiga damuwa ka shigo ɗaki kayi kuka kai ɗaya, ni bazaka sanar dani ba yaushe ka fara ɗaukar damuwarka taka kai ɗaya, ba raba damuwar junan mu muke ba why zaka ɓoye min why Nameer.?" Hawayen dake fuskarsa Nameer ya sa hannu ya goge tare da girgizawa Hisham kai yace. "No Hisham babu wata damuwa da take damuna, kawai kaina ke ciwo sosai jin kan nake tamkar zai rabe gida biyu, sai kuma tsinkewar zuciya da ke damuna jima nake kamar na tattara kayana na gudu." Numfashi Hisham ya saki tare da cewa. "A'a Nameer wannan damuwar taka ba ta ciwon kai ba ne, tsinkewar zuciya kuma meye ma'anar sa, amma ka tashi muje asibiti a maka gwajin bp." "Gwajin BP kuma Hisham me zai haɗani da Bp ni da ba wata damuwa bace gareni, please Hisham ka ƙyaleni da wannan maganar na samu nutsuwa tukunna idan kaina na ciwo kafi kowa sanin bana son damuwa please dan Allah." "Nameer ni fa nace maka wannan damuwar ba ta ciwon kai bane akwai dai abinda yake damunka wanda ni kake ɓoye min, ciwon kai bazai saka tsinkewar zuciya ba Nameer, kuma ɗazu munyi waya da Hassan abokinka yace min ya shigo gari ya nemi layinka baya tafiya sai ka taɓa sa." Cike da fara gajiya da maganganun Hisham ga shi haushin sa yakeji yau yace. "Hisham na ce maka kaina ne yake ciwo Final babu abinda zan ɓoye maka a wannan duniyar, Please kabar ni haka." "Okay shikenan amma dai kasha magani, ni fita ma zanyi na bar maka bedroom ɗin, zanje garden zamuyi magana da Sadiq gacan ƙanwarka a falo ka sanyata kuka." Hisham yayi Maganar yana tashi ya fita, da kallo Nameer ya bisa zuciyarsa na masa ƙunci komawa yayi ya kwanta tare da runtse idanunsa da ƙarfi. _Hassan ya dawo tabbas ya dawo akan gabar da nake buƙatar sa, shine zai warware min wannan matsalar da na ke ciki na MAHAUKACIN SO, ita kuma Tutun kuka ta ke hmm! Ya zataji kenan idan ta fahimci cewa bazan iya Auren ta ba, me zai faru idan har su Abba suka fahimci akwai alaqar Soyayya tsakanina da Tutu kuma suji cewa bazan aureta ba, wanne irin hukunci Abba zai yanke min?._ Nameer ya furta cikin zuciyarsa yana jin jikinsa duk babu daɗi shi kansa bai so ace ya rabu da Tutu ba sai dai babu yadda ya iya da zuciyar sa JIDDA itace kaddararsa da ke biye dashi tamkar Inuwa bayajin zai iya haƙura da Jidda. *********** Sadiq na zaune cikin mota shi da Tunde kiran Hisham ya kuma shigo masa waya daga kiran yayi tare da ce masa ya basa 10minute gashi nan karasowa kafin ya ijiye wayar yana duban Tunde yace. "Na faɗa maka kayi hankali da gubar nan domin kuwa tana da hadarin gaske, ka tabbatar yarinyar da zakuyi aikin tare mai basira ce, muddun Nameer yasha wannan gubar babu makawa bazai ƙara minti biyar ba a duniya, idan muka kashe Nameer to mun kashe ƙarfin Hisham da hasken sa, domin kuwa cikin duhu da tunani zai fara rayuwa yayin da hankalinsa zai rabu biyu gefe guda na ga ciwon rashin Nameer gefe guda kuma na ga tunanin ɗaukar fansa akan Jidda ina fatan ka fahimta, idan kuma har ka yadda wata matsala ta samu to ka sani babu ruwan Sadiq akanka damuwar zata tsaya domin kuwa na faɗa maka zan iya zillewa." Kansa Tunde ya kaɗa yace. "Yes na fahimta, insha Allah gobe komai zai kammala, zanyi aiki cikin basira da kwarewa babu wata matsalar da zata samu." ''okay fatan Nasara." Sadiq yayi Maganar yana fita daga cikin motar ya shiga nasa tare da jan motar yabar arean wajen. A parking space na ciki part ɗin su Hisham yayi parking ɗin motarsa tare da fitowa yana kiran Hisham, garden ɗin ya nufa bayan Hisham ya sanar dashi yana garden ɗin, yana zaune a ƙasa kan darduma, fuskarsa cike da fara'a kana ganinsa zaka fahimci yana cikin farin ciki zama Sadiq yayi gefen sa, ganin Hisham na murmushi ya sashi cewa. "Daga ganinka kana cikin Happy, me ka samo mana, Allah yasa wata hajace mai nauyi."? Dariya Hisham ya sanya yana cewa. "Wa ya ce maka samuwa ce, wannan ba samuwa ba ce waken gizo ne dai zaisha wuta harma ya babbake, domin kuwa Allah ya kai damo ga harawa, kaga kuwa ɓarna dole ne, burina ya cika akan wannan bahamagiyar yarinyar domin kuwa ta faɗa tarkona, na kusa biyan bashin gaba, kasan shi bashi tamkar adashe yake muddun kaci to sai ka biya wallahi, ko kafi uwarka kokari, tabbas ta faɗa tarkon da zai zamo tabon baƙin cikin da bazata taɓa mantawa dashi ba har karshen rayuwarta." Dariya sosai Sadiq ya sanya ko da Hisham bai fayyace masa inda ya nufa ba, kalama ya basa a dunƙule, ya fahimci Jidda ce ta faɗa tarkon sa, Sadiq duban Hisham yayi yace. "Ni dama nasan dole zata faɗa tarkonka, domin kuwa babu Macen da zata kalleka tace bata so, amma mubar wannan maganar tukunna mu dawo kan lamarin Mamabisola ina son muyi magana akan Tunde." Dago idanunsa Hisham yayi ya dubi Sadiq cike da mamaki yace. "Mamabisola kuma Sadiq, meyasa zaka min magana a kansu why SADIQ kana da Alaqa da su ne wanda har zai sa su baka wani saƙo, ko ka fara shiga sabgar su ne."? A ɗan firgice Sadiq ya ɗago ya kalli Hisham _kar fa nayi wasa Hisham ya gano wani abu na shiga Uku, ko da yake ina bazai taɓa fahimtar komai ba idan kasan wata ai baka san wata ba Hisham na fika iya buga wasa._ Sadiq yayi Maganar zucin yana sakin murmushi kafin ya ɗago ya kalli Hisham yace "Kana zargina da wata alaqa dasu ne saboda kawai zanyi magana da kai akansu.?" "Ko ɗaya Sadiq bana zargin ka kuma bazan taɓa zargin ka ba domin kuwa nasan bazaka cutar da ni ba.?" Numfashi Sadiq ya saki yace. "Kasan wani abun mamaki kuwa Hisham.?" Kansa Hisham ya girgiza yace. "A'a babu abinda zan sani har sai idan ka sanar dani sai dai nayi mamaki sosai da kai da bakinka kace zamuyi magana da kai akan Mamabisola." _____________________________________ *ANAN ZAMU DASA AYA HAR SAI ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH INDA ZAMU DAWO SALLAH DA SATI ƊAYA NASAN ZUWA WANNAN LOKACIN AN GAMA HIDIMAR AIKIN NAMA MA'ANA DAI MUN TAFI HUTUN SALLAH BANSO ACE NA TSAYA BA SABODA RASHIN TYPING DA NAYI KWANA BIYUN NAN, TO SAI DAI BABU YADDA NA IYA DOLE NE MU TAFI HUTUN SALLAH SABODA AYYUKA INSHA ALLAH ANA GAMA HIDIMAR SALLAH ZAMU DAWO POSTING BA KAMA HANNUN YARO HAR SAI MUN DASA AYA A KARSHEN LABARIN.* _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan aul yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [7/18, 7:20 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE 📚* *_PAGE 47 TO 48_* "Ba fa wata magana ba ce ta ɗaga hankali Hisham mamaki na ke yadda Mamabisola ta lalata rayuwar Tunde ta barsa ya ke abinda ya ga dama a rayuwarsa, ina wannan yaron A'lameen ɗan gidan Alhaji Dage yaron da ya kashe wannan almajirin har aka kaisa prison na Abuja kafin mahaifinsa ya shiga ya fita aka fito dashi."? Shuru Hisham yayi yana tunani kafin yace. "Okay na gane Dagash zaka cemin sai nafi ganewa na ganesa meya faru.?" Numfashi Sadiq ya sauƙe kafin yace. "Tare na gansa shi da Tunde wajen sau uku ina ganinsu tare nan a ShopRite na gansu nan kuma a Sudan Markey sai kuma yau na gansu tare a mota kasan abokin ɓarawo ɓarawo ne Hisham, ni fa wannan lamari ya fara bani tsoro kuma tashin hankali na yanzu Tunde ya shigo Companyn ku." Tsuka Hisham yaja yace. "Mtsss ni nayi zaton wani abun zaka faɗan to Sadiq ni ina ruwana dashi idan yaga dama yaje ya shiga cikin Yan shan jini ma dan Allah mubar wannan maganar mu dawo kan maganar wannan jakar yarinyar." "Jakar yarinya kuma Hisham JIDDA itace jakar."? "Kwarai kuwa Jaka ma ta bugawa a jarida yo idan Banda mahaukaciya yanzu ita idan akace zanso yar matsiyata irinta sai ta yarda, ban taɓa raina basirarta ba sai yau wallahi." Dariya sosai Sadiq ya saki tare da cewa. "Shege abokina wato dai yanzu kai murna kake ka samu karenka ya tsotsi ƙashi karfa reshe yayi ƙoƙarin juyewa da mujiya dan itama yarinyar naga so beautiful, ka dai taka sannu Hisham." Tsuka Hisham yaja yace. "Mtsss! Tsiyata da kai kenan wani sa'in ba'a tadin arziki da kai wallahi, yo ni ko baki Ammi tamin zanso wannan Yar talakawa ne, da dai nayi rayuwa da wannan Yarinyar ta aure na gwammaci na mutu gauro yanzu dai ba wannan ba, ta faɗa tarkona meye next takun da zanyi mata kasan fa wani sa'in kaine madubina a wannan harkar saboda ba wai shiga sabgar mata nake ba ka sani." "To naji abinda ya kamata kayi yanzu shine ka ƙare dagewa wajen ganin ka kama zuciyar ta ma'ana ya zamana cewa bata jin ko wanne ɗa namiji a ranta sama da kai taji bazata taɓa iya rayuwar Aure da wani ba idan ba kai ba, ka ƙara kwantar da kanka gareta da nuna mata kulawa Hisham zakaga yadda zata mace a akanka idan har ta kai wannan matakin a Soyayyar ka to da shine zaka iya yiwa rayuwarta illa." Duban Sadiq Hisham yayi tare da cewa. "Kana nufin kenan har yanzu ban gama samun makaman da zan yaki JIDDA dasu ba."? "Kwarai kuwa Hisham makami ɗaya kawai ka riƙe da sauran rina a kaba tukunna yanzu ta fara sonki yana da kyau ka riƙe zuciyar ta." "Na fahimta Sadiq insha Allah kuma sai na baka mamaki domin kuwa bazan taɓa daina jin ciwon tozarta Nameer da JIDDA tayi ba har sai na wulaƙanta rayuwarta sannan ne zan huce zuciyata taji cewa da gaske Hisham bazai taɓa bari a wulaƙanta Nameer ba." "Hakan ma yayi domin kuwa ana tauna ƙasa ne saboda aya taji tsoro." Sadiq yayi Maganar yana kallon Hisham sun juma sosai a wajen da Hisham kafin Sadiq ya tafi. Da daddare bayan sunyi deaner Ummi ta koma tsakiyar falo shi kuwa Hisham bedroom ɗin su ya shige saboda yana da aikin da zaiyi ya rage daga Nameer sai Tutu a daining ɗin, idanunta Tutu ta ɗaga ta kalli NAMEER da take lura dashi tunda aka fara cin abincin shi bai wani ci ba yafi mai da hankalinsa ga tunani da alamu yana cikin matukar damuwa. "Kayi haƙuri yaya Nameer dazo nazo na takuraka da tambaya kana cikin yanayin da baka bukatata a lokacin kayi haƙuri zuciyata ce ta gaza samun nutsuwa da halin da na ganka a ciki a zatona ni abokiyar shawararka ce babu abinda zaka iya ɓoye min a matsayina na matar da zaka Aura." Kallonta yayi sai kuma tausayinta ya kamasa sosai _tabbas da tasan abinda yake zuciyata bazata so na furta mata shi ba, tabbas RASHIN SANI YAFI DARE DUHU_ Nameer yayi Maganar zucin har zuwa lokacin idanunsa na kanta, numfashi ya saki tare da cewa. "Ba ɓoye miki damuwata nake ba, kawai ina cikin yanayi marar daɗi ne yau shi yasa bana so kowa ya kasance kusa dani nafi bukatar kadaici a wannan lokacin karki damu ba wata damuwa ce ta ɗaga hankali ba infact ma komai ya shige." "Amma yaya Nameer zaman mu cin abinci fa ina lura da kai baka wani ci abinci ba, sai ma tunani da kake yi wannan kaɗai ya isa ya nuna damuwar da kake ciki mai girma ce, Please farin ciki na tell me." Kansa ya girgiza yace. "Tunda na ce miki kibar maganar nan ta wuce to ki barta ba gashi ba yanzu kallonki ya san yani cikin nishaɗi, ke ta musamman ce Tutu i love You so much." Murmushi Tutu ta saki sosai taji daɗin maganganun NAMEER a gareta kafin tace. "Shikenan na bari amma ka sani bana son sake ganinka cikin damuwar nan, domin farin cikin ka shine nawa, kasan dai irin matukar Soyayyar da nake maka numfashi ma wuya zai bani muddun babu kai cikin rayuwata domin kuwa rayuwar duhu zata min irin duhun da ko tafin hannu baza'a iya kallo ba, yau idan na tuna cewa gobe ne alkawarin ku na neman matar Aure da kuka yiwa Ammi zai cika sai naji wani irin farin ciki domin kuwa gobe ne kowa zai ji labarin Soyayyar mu harta Abba da baya ƙasar nan sai mun kirasa mun sanar masa." Dariya Nameer ya saka tare da cewa. "Saboda baki da kunya Jidda sai ki sanar da Abba Soyayyar ki." Nameer yayi Maganar cikin dariya Tutu idanunta ta zaro cike da mamaki tace. "What JIDDA kuma yaya Nameer wacece kuma JIDDA da har zakayi sha'afan da zaka kirani da sunanta wani irin mahimmanci ta ke dashi a rayuwarka."? Tayi Maganar tana haɗa ranta tamau. Kansa Nameer ya dafe bai san ma ya ambaci Tutu da sunan Jidda ba, tsabar Jidda ce kaɗai take yawo a cikin ransa numfashi ya ɗan saki tare da cewa. "Sorry Farin ciki na, babu wani mahimmanci da take dashi a rayuwata kawai dai sunan ne yazo bakina, Kinga mubar wannan maganar yanzu ina son zan haura akwai aikin da zanyi." Kanta Tutu ta kaɗa tare da cewa. "Okay shikenan amma dai hankalina bai kwanta da wannan Jiddar ba dan harma naji na tsaneta tun kafin nasan waye ita." Murmushi kawai Nameer ya saki tare da tashi yace. "I love You." Yayi Maganar yana haurawa sama murmushi Tutu ta saki ta bisa da kallo cike da so da kauna kafin ta tashi tayi wajen Ummi. Ko da Nameer ya shiga ya samu Hisham zaune a saman kujera mai biyu dake tsakiyar bedroom ɗin, tollet Nameer ya shige yayi wanka ya fito tare da sanya boxer da vest ya zauna yana ƙoƙarin jawo system ɗinsa yaji muryar Hisham. "Nameer wai bakaga sakon da na turo maka bane ta Whatsapp."? Kansa Nameer ya ɗago ya kalli Hisham tare da cewa. "Bakaga sakon da na maido maka ba kenan halan baka buɗe data bane." "Eh ban buɗe ba gaskiya, kayi mamaki ko da kaga Jidda na fitar a matsayin matar da zan aura."? Numfashi NAMEER ya saki yana jin wani ɗaci na taso masa a zuciyarsa kafin yayi murmushin ƙarfin hali yace. "Babu abun mamaki ai Hisham shi Allah ba yadda baya lamarinsa naji daɗi da ya kasance Jidda ka fitar domin kuwa ko shakka bana yi kayi dacen mace ta gari, amma Hisham Soyayyar gaskiya kuwa kake yiwa Jidda anya babu wani manufa a ƙasan ranka karfa ka zalunci Yarinyar mutane."? Murmushi Hisham ya saki kafin yace. "Nameer kana ganin zan cutar da Jidda ne meyasa zakayi wannan tunanin, hmm! Nameer har cikin zuciyata nake jin Soyayyar Jidda ina sonta sosai." "Ban yarda ba Hisham ko ka manta abinda ka faɗa min ko matar da zaka fitar bawai kana sonta bane manage kawai zakayi da ita ko ba haka ka faɗa min ba." Dariya sosai Hisham yayi yana ture system ɗin sa gefe yace. "Malam ni fa wasa nake maka wai dama serious ka ɗauki maganar gaskiya she is funny." Numfashi Nameer ya saki yace. "Okay Allah ya sanya alkairi nima insha zakaga tawa." "Allahu yasha" Hisham ya furta yana maida kansa ga system ɗin sa. ********** Cike da farin ciki Jidda ta shiga gidan nasu babu kowa tsakar gidan hakan ne ya bata damar faɗawa ɗakin ta domin kuwa tasan Basmah na ciki tana zaune tana ninke kaya Jidda ta faɗa jikinta tare da rungumeta ta baya tana dariya juyowa Basmah tayi tare da cewa. "Lallai yau da alama ta samu wannan farin ciki haka." Dariya Jidda ta kuma saki tare da sakin Basmah ta zauna a tsakiyar katifar tace. "Basmah yau dai nima nayi tsuntuwa domin kuwa burina ya cika na samu irin namijin da nake burin aura, zancen da nake miki harma ya furta min kalmar I love You." "Ban fahimta ba naga da Hisham kuka fita a can ɗin kika gamu da saurayin."? Kanta Jidda ta girgiza tare da cewa. "A'a shi ɗin dai Hisham." Da ƙarfi zuciyar Basmah ta buga tare da dafe ƙirjinta idanunta suka firfito waje da karfi ta furta. "What! JIDDA Hisham shine yace yana sonki.?" Ta jefa mata tambayar ƙirjinta na harbawa da ƙarfi, dariya Jidda tayi tace. "Ƙwarai kuwa Hisham ɗin, Basmah bazan ɓoye miki ba nima fa na kwana biyu ina jin sonsa a raina kawai ina dannewa ne saboda ban san me gobe zata haifar ba, nayi mamaki da baki fahimci hakan ba keda kikafi kowa sanin waye ni." Gumine ya ketowa Basmah tamkar zata danna ihu haka taji zuciyar ta, jikinta duk ya mata nauyi hankalinta ya tashi. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_[7/19, 8:18 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE 📚* *_Page 49 to 50_* Jidda ganin Basmah ta kwabe fuska har tana haɗa gumi ya sata cewa. "Basmah meye haka kin wani haɗa rai sai kace wanda na faɗa miki ranar mutuwarki, har kina haɗa gumi akwai matsala ne."? Saurin girgiza kanta Basmah tayi tace. "Yo Jidda ba dole na haɗa gumi ba naji kinzo min da wata magana tamkar almara, meye zai haɗaki soyayya da Hisham, har kin manta halinsa kin manta waye Hisham kin manta kalar rashin mutuncin sa, da zakiyi gangancin shiga rayuwar sa."? Murmushi Jidda ta saki tare da cewa. "Hmmm! Basmah kenan meye aibun Hisham, ke fa da bakinki kike cemin ashe Hisham mutumin kirki ne mune bamu fahimce sa ba, yanzu kuma kice zaki tuno da baya, we'll munin halinsa ba abun gudu bane domin kuwa irinsu suna bukatar macen da zata nuna masu rayuwa shiyasa banji tsoron shiga rayuwar sa ba, ina son Hisham Basmah bazan iya rabuwa dashi ba kiyi haƙuri mace ma tana gyara miji ki fahimta, ina da yakinin Hisham bazai juyawa rayuwata baya ba, na kawo miki labari mai daɗi shine zaki sa gwiwwata ta sare madadin ki karfafa min gwiwwa akan abinda nake muradi." Numfashi Basmah ta saki zuciyarta na hura har yanzu hankalinta a tashe yake _Wannan wacce irin masifa ce yaya Hisham zai min haka ni da nafi kowa muradinsa ni da nake da shirin shiga Companyn su domin samun kusanci dashi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Jidda meyasa zaki min haka_ Basmah tayi Maganar zucin cikin matsanancin tashin hankali kanta ta girgiza tace. "Shikenan Jidda Allah yasa haka yafi Zama Alkairi, yanzu ya kukayi dashi kin tabbatar Soyayyar gaskiya yake gwada miki.?" "Ƙwarai kuwa Basmah na tabbatar ɗari bisa dari, ina labarin Ahmad ne kwana biyu bamu haɗu ba." Bakinta Basmah ta taɓe "Yana nan lafiya jiya ma sai da ya tambayeki." "Ayya dan Allah idan kunyi waya kice masa na gode da mantawa da yayi dani, bara naje wajen Umma bata san na dawo ba." Kanta Basmah ta girgiza kafin Jidda ta fita tana fita Basmah ta mike tsaye. "Na shiga Uku ni Basmah duk adana soyayyar Hisham da nake amma sai da aka min ƙofar rago, Hmm why Jidda, mtsss bazan iya haƙura da Hisham ba kiyi haƙuri Jidda dole sai na kwaci soyayyata." Tayi Maganar cikin huci tana riƙe kunkuminta. ********** After two days Companyn cike yake da ma'aikata kasancewar yau take ranar aiki Monday kowa yana harkokin gabansa, Yau lokaci a kure Hisham ya shigo Companyn, darect office ɗin Jidda ya nufa yaga ko tazo, ya samu ta shigo amma tayi office ɗin mr John hakan ya sashi juyawa ya koma nasa office ɗin, Tunde kuwa tun shigowarsa ya nufi Wajen Zainab ya sameta zaune ita ɗaya a wajen da suke goge shinkafa, gefenta Tunde ya zauna. "Ya akayi Tunde ka shiryawa aikin ne."? "Kwarai kuwa na shirya shiyasa ma kika ganni anan Zainab bana son matsala a aikin nan duk yadda za'ayi ki samu ki zuba wannan gubar a tea ɗin da Nameer zaisha bana son kuskure." "Kuskure Hmm kaima fa Tunde idan har baka yarda dani ba bazaka bani wannan aikin ba dan haka karka damu aiki zai tafi yadda kake bukata." "Shikenan ga nan gubar ki kiyaye." Tunde yayi Maganar yana miƙa mata kwalbar gubar amsa Zainab tayi kafin tace. "Nan da 30 minute ina jiran alart ɗina yana shigowa zan aiwatar da aikin." "Karki damu zakiji" Tunde yayi Maganar yana tashi yabar wajen murmushi Zainab ta saki tare da furta "akan kuɗi ba abinda bazan iya aikatawa ba, kayi haƙuri Nameer kuɗi yafi min komai a rayuwa." Kansa tsaye Sadiq ya shigo office ɗin dubansa Hisham yayi yana sakin murmushi yace. "Nayi zaton bazaka zo ba ai Bismillah ka zauna." Zama Sadiq yayi yace "Ai kasan muddun ka kirani zanzo, Allah dai yasa lafiya ka kirani da sanyin safiya kasan ko breakfast banyi ba." "Mtsss! Kiran dole ya kama Sadiq, bara na kira sakatariya tasa a kawo maka tea ko da bread ne ka fara kafin muyi maganar ko." Kansa Sadiq ya girgiza yace. "Bar tea ɗin tukunna sai mun gama tattaunawa." "Okay Sadiq ni har yanzu akwai Yarinyar da ka fitar a matsayin zaka Aura.?" "Wannan wacce irin tambaya ce Hisham da ina da budurwa ai da ka sani bani da ita, amma meyasa kamin wannan tambayar."? Numfashi Hisham ya saki yana gyara zamansa yace. "Saboda ina son ka nemi ƙanwata Tutu, amma fa sai idan kaji ta maka babu dole." Murmushi Sadiq ya saki yace. "Kai ka isa kamin dole ne Hisham, ka sanni sarai bana ɓoye maita ta, Tutu ba Macen da za'a ce ba'a so bane Hisham sai dai ka gane Soyayya tana buƙatar haɗuwar jini, amma ita ka tuntubeta ne."? "A'a ban tuntunbeta ba tukunna nafi bukatar na fara ji daga gareka, na tabbata ita bazan samu matsala da ita ba, Sadiq kai Mutum ne na ƙwarai da kowa zaiso haɗa zuri'a da kai shiyasa na yiwa ƙanwata kwaɗayin samun ka a matsayin mijin aurenta." "Karka damu Hisham kaje ka tuntunbeta idan har ta amince ni bani da matsala, waye zaiki haɗa zuri'a daku Hisham sai dai marar rabo." Dariya Hisham ya saki yana ɗaukar sigarinsa ya saka a baki tare da kunna mata wuta kafin yace. "Kai kuma bazaka zamo cikin marassa rabo ba ko, ya labarin wannan shegen ne Dawud."? "Kai dalla bar zancen ɗan iskan nan ka sanya a kawo min tea ɗin na samu na bawa hanjina hakkinsa, sigari dai ta zamo maka ɗabia Hisham." Dariya yayi yana ɗaga waya ya kira sakatariya yace tasa a kawo tea da bread kafin ya dubi Sadiq yace. "Ba ɗabia ta zame min ba rayuwa ta zame min musamman idan ina cikin damuwa nafi jin daɗin ta." "Kuma kafi kowa sanin illarta ba." Yayi Maganar dai-dai Sakatariya na shigowa da tea ta ijiye a tebur ɗin kafin ta juyawa, jawo tea ɗin Sadiq yayi tare da bread ɗin a hankali ya fara sha suna hira da Hisham har ya gama shan tea ɗin yana ijiye cup ɗin cikinsa yayi wani irin juyawa idanunsa ne suka firfito waje ya fara wani irin gurnani a ɗan gigice Hisham ya miƙe yana yasar da sigarin hannunsa ya take tare da furta. "Subahanallah! Sadiq meke faruwa, me yake damunka what kumfa a bakinka Sadiq!''? Hisham yayi Maganar da ƙarfi yana zagowa ya tallafo Sadiq cikin tashin hankali magana ma ta gagari Sadiq saboda shakewar da wuyansa yayi, idanunsa ya zazzaro numfashin sa sai sama sama yake yana neman daukewa, security Hisham ya dannawa kira cikin gaggawa suka shigo office ɗin kafin kace me zance ya karade Companyn Jidda da Nameer kusan tare suka shigo Nameer shiya kira Police ya sanar dasu, cikin gaggawa kuwa sukazo akayi asibiti da Sadiq yayin da sai shidewa yakeyi kowa da ke cikin Companyn ya shiga cikin tashin hankali, Tunde ma ya shigo sai hankalinsa yayi matukar tashi kar fa ace gubar nan Sadiq yasha, tare suka dunguma zuwa asibitin Nameer da Hisham har Jidda, Take likitocin suka ruhu a kansa, Hisham sosai hankalin sa ya tashi, sai kaiwa da komowa yake ya gagara samun nutsuwa, likitocin sun juma sosai kafin suka fito, doctor yace su Hisham su samesa a office. Koda sukaje likita ya tabbatar musu guba yasha mai haɗarin gaske kuma shine last abincin da ya ci tare da cewa suna bukatar suga last abinda yaci, a firgice Hisham ya miƙe tare da furta. "What! Last abinda Sadiq yaci shine tea kuma a office ɗina yasha, ta yaya hakan zata faru, kaga Doctor tukunna a wani hali Sadiq yake ciki.?" Doctor ne yace. "Muna bukatar sauran tea ɗin ko cup ɗin da aka sha tea ɗin domin mu gwada muga irin gubar da akayi anfani dashi a yanzu dai haka Sadiq yana halin rayuwa ko mutuwa gaskiya saboda dole sai mun san kalar gubar gubar kafin mu san treatment ɗin da zamu masa na ainihi duk yanzu ma munyi iya bakin ƙoƙarin mu, amma bamu muku alƙawarin zai rayu ba gaskiya." Numfashi Hisham ya saki tare da dafe kansa Nameer ma sosai hankalinsa ya tashi guba a cikin Companyn su waye yake ƙoƙarin kaiwa rayuwarsu farmaki, wato Hisham aka so kashewa lamarin ya sauƙa akan Sadiq waye ne. "Hisham ya akayi haka guba kuma a Companyn mu, Hmm! Lamarin ya bani mamaki sosai, ya kamata Police suje suyi bincike." "Ni kaina mamakin da nake kenan Nameer sakatariya ce ta kawo tea ɗin itace first target ɗin da za'a zarga, Inspector Lawan yana can Companyn zaiyi duk abinda ya dace ni aka so kashewa ba Sadiq ba, doctor muje da nurse ta ɗauko kuma cup ɗin." Hisham yayi Maganar yana miƙewa jikinsa a sanyaye cike da mamakin yadda hakan ta faru. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* _Mai ra'ayi shi zai saya please bana son ƙananan magana idan har ba saya zakiyi ba dan Allah karmu ɓatawa juna lokaci karki biyoni pc kiyi zamanki a inda kike muddun ba Book zaki saya ba, falyakum khairan auli yasmut siyan na gari mai da kuɗi gida anayi da kai yafi ba'ayi da kai._ *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [7/20, 8:35 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE 📚* _Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._ *_Page 51 to 52_* Numfashi Nameer ya saki cike da tunani gabaki ɗaya Companyn suka koma sun sami Police suna ta famar bincike, inspector Lawan da kansa ya dage wajen binciken, Zainab sosai ta shiga cikin tashin hankali domin kuwa ta rasa ya akayi akayi sauyin cup ɗin har Sadiq yasha gubar duk da bata san akwai alaqa tsakanin Tunde da Sadiq ba, cikin tashin hankali Tunde ya nufi Zainab ganin an tsawaita bincike tana nan tsaye itama cikin tashin hankali ya iske ta. "Bana faɗa miki cewa kar a samu kuskure ba, meyasa zaki min wannan shirmen kinsan rayuwar waye kuwa kika sanya cikin hadari, yana da matukar muhimmanci a rayuwata, kin riga kin aikata kuskure amma ki sani karki kuskura a san cewa kece kika sanya wannan gubar idan har akayi ƙoƙarin ganoki babu shakka kafin a iso gareki zan ɗauke numfashin ki." Yayi Maganar yana nuna mata yatsa tare da barin wajen cikin hanzari, numfashi Zainab ta sauƙe tana huci ta furta. "Babu wanda ya ganni da zan aikata haka kuma babu wanda ya isa ya gano ni ko shatin yatsata bai taɓa cup ɗin ba bare nayi tunanin tashin hankalin rayuwa." Tayi Maganar tana sakin murmushi, can kuwa nurse da police ɗaya suka koma da cup ɗin tea ɗin asibiti inda darect sukayi lap da shi domin gwada launin gubar, Duk binciken Police ɗin ya ta'allaka ne akan sakatariya da Esther wacce itace ta haɗa tea ɗin. Sosai sakatariya ta shiga tashin hankali, Inspector Lawan ne ya sasu su biyun a gaba sukayi asibitin za'a gwada zanen yatsunsu, shi kansa Hisham lamarin ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba wunin ranar haka sukayi shi cikin bincike da tashin hankali sai Nameer bai yadda an sanar da Abba abinda ke faruwa ba. Dukkan su babu wanda ya samu damar barin cikin Companyn har sai da suka kai 6:30pm kusan kiran magaruba dan har sai da Police suka dawo da sakatariya da Esther tukunna, Hisham Jidda ya ɗauka ya Kaita gida. ******** Ƙafafuwan sa ya tankwashe a gabanta yayi shuru, yayin da ranta ke ɓace cikin hasala tace. "Wace shegiya daƙiƙiyar ka bawa wannan aikin, idan har Sadiq ya rayu ba lallai ya ƙyale mu ba, domin kuwa cewa zaiyi gangancin mu ne, koma yace da gangan muka aikata masa hakan saboda ya nemi wani abu daga cikin dukiyar da muke hari, ya kamata yarinyar nan ta fuskanci hukunci, a wannan karon idan har Hisham ya gano akwai hannun mu cikin sanya wannan gubar wallahi sai ya tarwatsa rayuwarmu." Kansa Tunde ya girgiza tare da cewa. "Mtsss! Mama ban taɓa zaton cewa Zainab zata min ganganci ba, sai dai ki sani bazata taɓa bari a gane itace ta aikata ba, asirin mu bazai tonu ba, baƙin ciki na ɗaya ne Mama na tarwatsewar mission ɗin nan banso ace Nameer ya tsallake wannan tarkon ba, naji baƙin ciki sosai, Mama karki damu wannan gubar bazata bar Sadiq ya rayu ba bare ya zamo barazana a rayuwar mu shine ya tabbatar min da ƙarfin gubar duk wanda yasha yace bazai rayu ba dan haka karki damu Sadiq tasa yazo karshe." "Amma Sadiq yana da mahimmanci a aikin mu rashin sa wata matsalar ce fa, waye zamu samu na jikin Hisham wanda zai iya mana wannan aikin shine babban tashin hankali na, domin Sadiq shine jigon aikin mu." "Hmmm! Na sani Mama amma ki sani bazamu rasa ba, gari da yawa maye bazai ci kansa ba, ke dai ki cigaba da addu'a, sannan Mama dole fa sai kunje kauyen nan da Wamimo domin kuwa bazamu iya kaisu ƙasa ba dole sai mun haɗa da asiri." Shuru Mamabisola tayi tana tunani kafin ta ɗaga kanta tace. "Shikenan, zan nemi Wamimo zamu san yadda za'ayi kaje ka ci abincin ka." Kansa Tunde ya girgiza tare da tashi yabar wajen, bayan ya fita ne Mamabisola ta miƙe tsaye cike da tunanin yadda zata bullowa lamarin domin kuwa taga lamarin yana shirin fin ƙarfinta muddun tayi wasa kwabarta zata mata ruwa. "Lallai dole Wamimo tazo muje ƙauyen nan na Agunjin." Tayi Maganar tana sakin numfashi cike da damuwa wayarta ta ɗauka ta kira Wamimo sukayi magana akan tafiyar sun juma suna waya kafin sukayi sallama. ********** "Meyasa zaka sawa kanka damuwa haka bayan Police suna nan suna bincike, dole kasan zasu gano wanda ya aikata wannan aikin bazai tsira ba tunda akwai CCTV Camera."? Kansa Hisham ya girgiza yana kallon Jidda cike da damuwa yace. "Har yanzu baki fahimci damuwata ba Jidda, damuwata rayuwar Sadiq ne idan Sadiq ya mutu ta wannan dalilin bazan yafewa kaina ba domin silata hakan ta faru dashi, Sadiq wani tsagi ne na rayuwata Jidda, mutumin kirki ne da babu ruwansa bashi kyashi ko mugunta bare kuma hassada, gashi can a tsakanin rayuwa ko mutuwa babu tabbacin zai tashi, da ace zansan wanda yayi wannan aikin babu makawa sai na kashe sa kafin aje ga hukuma, ina jin zafin halin da Sadiq ya shiga da wani ido zan kalli mahaifinsa tun ɗazu na gagara komawa asibitin da akace Alhaji Sagir mahaifinsa yaje." "Insha Allah ina da yakinin babu abinda zai samu Rayuwar Sadiq insha Allah zai tashi, rayuwarsa tana hannun Ubangiji ne ba na likita ba faɗa ne kawai nasu, amma ainihin sanin gaibun yana hannun Ubangiji, ka daina ɗagawa kanka hankali insha Allah komai zai tafi normal." Bakinsa Hisham ya cije tare da cewa. "Hmmm! Jidda rayuwata aka nema bata Sadiq ba domin kuwa ni nace akawo min tea ba tare da sanin waye zai sha ba kinga kuwa ni aka so kashewa ya faɗa kan Sadiq." "Karka ce haka waye kake dashi maƙiyi a wannan Companyn da zai nemi rayuwarka naga zaman lafiya kuke da kowa cikin mutuntawa da ƙaunar juna tunda na fara aiki ban taɓa ganin Company mai haɗin kai daya burgeni irin Companyn ku ba." Murmushin takaici Hisham yayi yace. "Kin manta kenan da fyaden da Khabeer yaso miki kuma a cikin Companyn namu, a hakan ne kike yabon mutanen cikin ta, ɗan adam ba abin yadda ba ne Jidda, ina da makiyin da zai iya neman rayuwata." "Ban fahimta ba waye wanda zai iya neman rayuwar ka a cikin Companyn.?" "Tunde.?" "What!?" Jidda ta furta tana zaro idanunta cike da mamaki. "Ƙwarai kuwa, meyasa zakiyi mamaki ko kin manta abinda ya faru ne a baya na Case ɗin Hajara ko kin manta da shine ya sanya Hajara ta yiwa NAMEER sharrin fyade duk wanda zai maka sharrin fyaɗe to tabbas zai iya kasheka." "A'a ban manta ba, amma wannan bashi zai baka hujjar cewa Tunde zai nemi rayuwarka ba, zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya, idan baya ta wuce babu amfanin a tuno sa, amma naga kai kamar baka manta ba, alkairin baya ake tunawa ba sharrinsa ba." "Kina da saurin manta maƙiyi Jidda da wannan zuciyar taki wata rana za'a cutar da ke, ki shiga gida ana kiran sallah nima zan shige." Yayi Maganar yana buɗe mata murfin motar, kanta Jidda ta girgiza tace. "Dan Allah ka samu nutsuwa insha Allah babu abinda zai faru sai Alkairi." Tayi Maganar itama tana fita daga cikin Motar da kallo Hisham ya bita ba tare da yace komai ba har ta shiga gida, kafin yaja motar sa yabar wajen ransa cunkushe da damuwa. Ko da Hisham ya koma gida ma ya samu Nameer dasu Ummi a falo a zaune suna ta jajanta maganar, inda Nameer ya hana Ummi sanar da Abba maganar gudun kar a ɗaga masa hankali baya ƙasar, ranar haka suka kwana cikin yanayin rashin jin daɗi musamman Hisham da yakejin zafin abinda ya faru da Sadiq shi Nameer tashin hankalin ma biyu ya zame masa ga na zullumin rashin Jidda ga kuma na abinda ya faru a Companyn nasu, haka dai suka kwana ba daɗi washegari sammako Hisham yayi zuwa asibitin sai dai zuwan sa yayi bala'in ɗaga masa hankali domin kuwa ya tarar da mahaifiyar Sadiq da ƙanwarsa sai ihu suke Allah ya yiwa Sadiq rasuwa Hisham jingina bayansa yayi da jikin bango ya runtse idanunsa bai san sanda hawaye ya biyo fuskarsa ba, gagara magana yayi idanunsa na lumshe hawaye na cigaba da biyo idanunsa, Nameer a haka ya ƙariso ya samu Hisham gaban Safiya ƙanwar Sadiq ya ƙarisa tare da cewa. "Me yake faruwa karki cemin Sadiq ya rasu.?" Kanta safiya ta ɗaga tana kara sakin kuka cikin rawar murya tace. "Yaya Sadiq ya rasu, mun shiga Uku." Tayi Maganar cikin matsanancin kuka kansa Nameer ya dafe tare da furta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Baku shiga Uku ba safiya akwai Allah ki daina kukan." Yayi Maganar yana tashi yaje ya tsugunna a gaban Alhaji Sagir, yace. "Alhaji......... Hannu Alhaji Sagir ya ɗaga wa Nameer tare da tashi yabar wajen, shuru Nameer yayi tare da tashi ya nufi Hisham. "Hisham ka yi haƙuri Please ga police sun shigo." Idanunsa Hisham ya ɗago ya kalli Nameer tare da juyawa ya kalli Police ɗin, room ɗin da gawar Sadiq yake suka nufa ganin Alhaji Sagir yana huci yasa Hisham bai tunkari inda yake ba. Inspector Lawan sun juma sosai cikin ROOM kafin suka fito da umarnin za'a iya ɗaukar gawar Sadiq, Hisham inspector Lawan ya nufa tare da dafa kafadarsa yace. "Munyi duk wani binciken da zamuyi bamu samu wata hujjar da ta nuna wanda yayi amfani da gubar nan ba, guba ce mai haɗarin gaske wanda duk wanda ya shata rayuwarsa bazata tsira ba, sakatariya da Esther babu hannunsu cikin aikata wannan masha'ar, sannan mun koma Companyn naku da daddare mun ƙara bincike har CCTV Camera dake Companyn sai da muka duba amma bamu ga komai ba, bamu da wata hujjar da zamu kama wani da laifi amma zamu cigaba da binciken ma'aikatan ku ɗaya bayan ɗaya.'' Kansa HISHAM ya girgiza yace. "Na gode Inspector Lawan, tabbas duk wanda yayi wannan aikin babu shakka ya juma yana harin mu yayi komai ne cikin dabarar da baza'a iya gano sa ba, kuyi kokarin gano wanene zan baku duk wani haɗin kan da kuke bukata." Hannu inspector Lawan ya bawa Sadiq kafin yabar wajen, gawar Sadiq aka fito da ita a motar asibitin akayi gida dashi, shima Hisham yabi bayansu tare dashi akayi sallar jana'izar Sadiq bayan sun dawo ne daga makabarta Hisham ya sunkuyawa gaban Alhaji Sagir yana basa hakurin abinda ya faru, a wannan lokacin ya saurari Hisham harma suka zauna waje daya aka cigaba da karɓar gaisuwa. Tun da Tunde yaji labarin mutuwar Sadiq hankalinsa ya tashi sai dai ko da wasa baije wajen amsar gaisuwar ba gudun kar Hisham ya zargesa. *********** Dariya ta sanya da jin labarin mutuwar Sadiq madadin tayi jimami, cike da mamaki Wamimo take kallonta ita da Tunde kafin Wamimo ta nisa tace. "Mamabisola meyasa kike dariya madadin kiyi alhinin rasa abokin aiki, wannan kisar fa kune kuka yisa."? Dariyar ta kuma saki tace. "Ba dai mu ba, shi dai ya kashe kansa waye ya kawo gubar idan ba shi ba, shine ya bada ajalinsa da hannunsa, dan ni tunda nazo duniya ban taɓa sanin akwai wannan gubar ba, duk makirci na." "To amma Mama meyasa kike dariya.?" Tunde ya jefa mata tambayar, Zama tayi tare da kallon sa tace. "Ina dariya ne saboda na samu hanyar durƙusar da IYABO, da wannan mutuwar da Sadiq yayi a Companyn su zanyi amfani wajen ganin na durkusar da Companyn su, duk wani bincike sunyi basu samu hujjar wanda yayi wannan kisan ba, da Wannan zan tunzura Alhaji Sagir ya shigar da Companyn ƙara kotu domin bin kadun jinin ɗansa, zan nuna meyasa meyasa aka rasa duk wata hujja, hakan na nuna kenan anyi shirin kashe masa dane shiyasa aka goge hujjar da zata nuna wanda ya aikata kisan ni nasan yadda zan tunzura zuciyarsa harya hasala ya maka *Hisham rice mill limited* a kotu, yayin da su kuma basu da wata hujjar da zasu kare kansu." Tayi Maganar tana sakin murmushi, gabaki ɗayansu dariya suka sanya tare da kallon juna suna jinjinawa Mamabisola. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [7/22, 7:56 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE 📚* _Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._ *_Page 55 to 56_* Kallon Hisham Abba yayi ya kalli takaddar sammacin kansa ya girgiza tare da cewa ɗan sakon. "Okay kana iya tafiya Allah ya kaimu Monday." Kafin ya dubi HISHAM da yayi Matukar kaduwa yana gigice har yanzu hawayen yake. "Hisham baka da hankali, yanzu Hisham ayi kisan kai a cikin Companyn mu baku sanar da ni ba saboda rashin hankali, yanzu wannan gangancin da kukayi kasan irin asarar da zai haifarwa Company kuwa.?" Kansa Hisham ya kaɗa sai yanzu ya samu damar fashewa da kuka cikin kukan yace. "Bashi bane damuwata Abba, na amince nayi asarar komai a rayuwata muddun ɗan uwana zai kasance tare dani har abada, Abba lafiyar Nameer shine damuwata Abba mu nema masa lafiya kana jin abinda likita yace ɗan uwana bazai wuce wata biyu ba a duniya, bazan iya kirga wannan kwanakin ba Abba kace min mafarki ne, kace kunnena karya yake min Abba." Yayi Maganar cikin wani irin kuka mai ɗagawa mai sauraro hankali. Tausayin sa ne ya kama Abba, ya jawo sa jikinsa tare da rungumesa Ummi ma kukan ta kuma sanyawa tana neman waje ta zauna. "Rayuwa zata mana tsanani Hisham rashin Nameer a rayuwar mu tamkar rasa jigon jikin mu ne, bazan iya jurewa rashinsa na kwana goma ba bare kuma na tsawon rayuwa, Abban Hisham mu ɗauke Nameer daga wannan asibitin mu fita dashi waje watakila su zasu iya ceto mana rayuwarsa na shiga Uku idan na rasa Nameer." Ummi tana kuka take wannan maganar, a wannan lokacin duk wanda ya zo ya wuce yaga wannan ahalin sai ya tausaya musu, kusan gigita Abba sukayi suka kuma tayar masa da hankali, ƙasa yayi tare da Hisham suka zauna cikin sanyin murya Abba yace. "Ya ya kuke son nayi da rayuwata da wanne zanji da tashin hankalin ku ne ko da ciwon Nameer ko kuwa da fargabar wannan takaddar da tazo gareni, so kuke ku haukata ƙwaƙwalwata, Ramata da girmanki kike abu tamkar yarinya karama madadin ki rarrashi Hisham shine zaki sanya kuka kamar shi kina kin shiga Uku, ku sani babu yadda muka iya da ƙaddara a yau Ubangiji yaga dama zai ɗauki Nameer kuma babu yadda zamuyi dole muyi haƙuri dan Allah ku kwantar da hankalinku mubi komai a sannu ko nima zan samu nutsuwar da zan san Abin yi." Kanta Ummi ta ɗaga tana cigaba da kukan Abba zame Hisham yayi daga jikinsa ya tashi ya koma wajen Doctor. Ko da ya shiga sun tattauna sosai akan matsalar NAMEER tare da neman shawarar Doctor ko akwai inda yake ganin idan sunje zasu samu Nasara sai dai ina Doctor ya tabbatarwa da Abba sai dai suyi haƙuri domin kuwa duk inda zasuje wannan result ɗin za'a basu, haka Abba ya fito cikin sanyin jiki daga office ɗin, wajen Nameer ɗin suka koma dukkan su Abba ya zauna gefensa, ya zuba masa idanu cike da tausayin sa, ya taso tun yana yaro a hannunsa bai taɓa ɓata masa rai ba komai cikin ladabi da girmamawa yake masa, ko yaushe tunaninsa da burinsa akan yadda zai kare masa ahalinsa, yadda yake kula dashi ko Hisham ɗan da ya haifa a cikin sa baya masa wannan kulawar, da ace akwai inda za'a bawa Nameer rayuwa tabbas da komai nisan wajen sai yaje ko da dukiyarsa ne gaba daya zai iya kashewa domin ceto rayuwar Nameer, numfashi ya saki shi kaɗai yake zancen zucin Ummi kuwa tana rike da hannunsa. Itama Tutu a gigice ta shigo asibitin ko da Ummi ta sanar da ita abinda ke faruwa da Nameer ihu Tutu ta sanya sosai hankalinta ya tashi Abba ne ya mata nasiha sosai kafin ta risina tabar kukan amma har yanzu tana ijiyar zuciya, Nameer bai farfaɗo ba har wajen karfe biyar na yamma, tunda ya buɗe idanunsa yake ƙarewa ɗakin kallo, akan Hisham da ya takure a gefe yayi shuru Nameer ya sauƙe Idanunsa. "Hisham." Ya kira sunansa ɗago idanunsa Hisham yayi tare da tashi da sauri ya nufesa kusa dashi ya zauna sai kuma yaji kuka yazo masa sai yanzu Hisham ya samu damar sakin kuka mai sauti yana kifa kansa a jikin Nameer idanunsa Nameer ya runtse cikin sanyin jiki yayi Magana. "Tabbas kukan ɗan uwana gareni ya tabbatar da cewa mummunan abu na faruwa ga rayuwata, Abbana ka faɗa min me likita yace yake damuna karka ɓoye min Abba ka faɗa min zan rungumi kaddara tunda ni musulmi ne nasan bazan kaucewa kaddarata ba." Wani irin tausayinsa ne ya kuma shiga zuciyar Abba shima hawayen ne ya ciko a idanunsa saurin mayar dasu Abba yayi gudun karya karyawa Nameer zuciya, Abba cikin tashin hankali da yanayin damuwa yace. "Ba wata matsala bace fa Nameer likita yace zaka samu lafiya...... Saurin ɗago kansa Hisham yayi tare da katse Abba da cewa. "A'a Abba karka ɓoye masa cutarsa kasa ya sanya rai ga abinda ba lallai bane ya tabbata, yana da kyau yasan cutarsa, domin ko ba komai zai san tanadin da zai yiwa goben sa, Nameer ba kai kake cikin damuwa ba mune, cutar a jikinka take amma mune muke jin zafin ciwon, mune muke cikin tashin hankali da masifa domin kuwa rasaka garemu masifa ce Nameer babbar masifa ma, zan shiga cikin kuncin rayuwa komai zai ƙwace min muddun na rasaka, kaine fitilar rayuwata ta yaya zan koyi rayuwa ba tare da kai ba, likita yace kana ɗauke da *KANSAR ƘWAƘWALWA* yace bazaka wuce wata biyu ba a duniya zaka mutu, amma nasan karya yake zaka rayu, zamu cigaba da rayuwa tare bazaka mutu ka barni ba sai dai ni na mutu na barka." Yayi Maganar yana kuka har da majina idanunsa sunyi jajur, idanunsa Nameer ya runtse madadin ya shiga cikin tashin hankali sai murmushi ya saki tare da kamo hannun Hisham, gaba ɗaya da mamaki suka kallesa ganin murmushi a fuskar sa madadin tashin hankali. "Wai kuka kake Hisham saboda Yar wannan maganar, ni fa mai rai ne dole ne wata rana zan mutu Meyasa zaku damu akan abinda yake kan kowa, dukkan mu zaman jiran mutuwar muke, dan haka ku daina damuwa, idan na mutu ba ga ka nan ba Hisham, zaka kula mana da Abba da Ummi da Tutu bazaka bari suyi kukan rashina ba, ku daina damuwa Ubangiji ya gama tsara lamarinsa a kaina karkuyi fushi da ikon Ubangiji muyi haƙuri sai mu ci jarabawar mu, ummina Abbana ku daina kuka muddun kuna son na cigaba da dariya kafin lokacin mutuwata." Hawayen fuskarta Ummi ta goge tare da kamo hannunsa tace. "Hakane Nameer insha Allah ma zaka rayu, zamu cigaba da nema maka inda zaka samu lafiya." Abba shima nasiha ya dinga yiwa Nameer yayin da sai murmushi yake yana jansu da tadi har Hisham ya ɗan sake, Tutu ma duk kukan da take sai da Nameer yasa tayi dariya. Ranar Hisham ne ya kwana tare da shi a asibiti, washegari da safe Ummi ta taho da breakfast ita da Tutu, wajen sha biyu na rana Mamabisola tazo asibitin, bata samu Abba ba sai Ummi da Hisham, cikin girmamawa Ummi ta bata waje. "Sannu da zuwa Mama." Ummi tayi Maganar cikin girmamawa, da yauwa Mamabisola ta amsa tare da cewa. "Yanzu nake jin labarin abinda ke faruwa da Nameer, Iyabo ya kiran yake sanar dani, Allah ya basa lafiya." Da ameeen Ummi ta amsa kafin Mamabisola ta kuma cewa. "Ramata garin yaya wannan mahaukacin ɗan naki yayi gangancin sakewa ma'aikata har akayi kisan kai a cikin ma'aikata, hmm! Iyabo yace min mahaifin yaron da aka kashe ya shigar da Companyn ku ƙara kuma wannan duk gangancin y'ay'anki ne, zaku samin Iyabo cikin masifa dan yanzu ma gashi hankalin sa ya tashi." Nameer dake kwance ne ya ɗan zaro idanunsa yana kallon Hisham, kansa Hisham ya girgizawa Nameer yana hucin maganganun Mamabisola, Ummi ce mata tayi. "Bamu da hakkinsu insha Allah babu abinda zai faru, gaskiya zatayi halinta." Murmushi Mamabisola ta saki tare da cewa. "Abinda zai ceci wannan Company hujja ce kawai kuma ance babu ita ku dai kun jawowa IYABO masifa, to dama Ramata ya ya za'ayi abinda kika haifa yayi albarka shima Iyabo ai yasan abinda ya debowa kansa, ni kinga tafiyata." Tayi Maganar tana tashi ta fita daga room ɗin, numfashi Ummi ta saki tare da kallon Hisham da ke famar huci, zaiyi magana ta ɗaga masa hannu. "Duk abinda yake cikinka ka mayar dashi, Mamabisola Tana da ikon da zata dakeni ma bare duka, uwa na ɗauketa dan haka bana son naji kayi wata maganar a kanta." Shuru yayi tare da mayar da kansa gefe Nameer ne yace. "Alhaji Sagir ne ya shigar da Company ƙara.?" "Eh Nameer nayi mamaki kwarai domin kuwa shi da bakinsa yace ya yafe." Shuru Nameer yayi ya kasa magana domin kuwa maganar ta ɗaga masa hankali. Hisham ne ya tashi ganin kiran Jidda yasan ta jisa shuru ne shiyasa ta nemesa bata san abinda ke faruwa da Nameer ba, fita waje yayi ya amsa wayarsa, Abba bai dawo asibitin ba har wajen la'asar lis ko da Ummi ta tambayesa inda yaje yake sanar da ita yaje sun gana da Chief judge ne akan karar da Alhaji Sagir ya shigar ya ce har Alhaji Sagir yaje ya samesa amma yana nan kafe akan lallai sai an shiga kotu, kanta Ummi ta jinjina tare da tambayar Abba yaya za'ayi. "Hmmm! Wallahi ban sani ba Ramata sai an shiga kotun dai musan abinda zai faru wadannan yaran ne suka min shirme da tun fari sun sanar dani da na yiwa tufkar hanci tun wuri, kai Nameer yaya jikin naka.?" "Da sauƙi Abba, kayi haƙuri Abba ba laifin Hisham ba ne, ni ne na hana a sanar da kai abinda ke faruwa gudun kar mu ɗaga maka hankali bamuyi zaton lamarin zai rincabe haka ba, dan har munyi magana da Alhaji Sagir ɗin ya tabbatar mana da ya yafe, yaushe sukace za'a shiga kotun."? "Akan Monday sukace amma na samu Chief judge na roki alfarmar a daga shari'ar zuwa ka samu lafiya, yanzu sai last this month zamu shiga kotun, maybe shawara ya sauya gani yake bazai iya haƙuri ba, Doctor ya bamu sallama zamu iya komawa gida yanzu." "To Abba maganar Hisham da Jidda fa."? "Yau da daddare Alhaji Bawa zai kawo sakamakon binciken da yayi, mu jira sa tukunna." Kansa NAMEER ya kaɗa shi dai Hisham yana ji baiyi magana ba Ummi kuwa haɗa ranta tayi cike da haushi basu fi minti sha biyar ba, suka haɗa komai suka taho gida. Hisham bayan ya sauƙe su ne ya juya da kan motarsa zuwa gidan su Jidda a ƙofar gida ya tsaya ya kirata a waya kusan minti goma da kiranta ta fito sanye da Hijab har ƙasa motar ta bude ta shiga tana duban Hisham. "Zuciyata har ta fara dukan Uku Uku ɗazu da naji shurun yayi yawa, gashi weekend ba aiki bare nasan halin da kake ciki, ya jikin yaya Nameer ɗin, meke damunsa.?" Numfashi Hisham ya saki yana jingina kansa da site ɗin motar kafin cikin damuwa yace. "Ina cikin tashin hankali Jidda makiya sun sako rayuwata a gaba, ga tashin hankalin Nameer na fara saduda da rayuwa Jidda, babu makawa makiya sunci galba a kanmu, domin kuwa ina ji a jikina za'a rufe Companyn mu, ga kuma Nameer yana tsakiyar rayuwa da mutuwa, bashi da lafiya Doctor ya tabbatar mana da cewa KANSAR ƘWAƘWALWA ke damunsa yace Nameer bazai haura wata biyu ba a duniya zai mutu, rayuwar nan babu komai a cikin ta Jidda sai tarin bakin ciki." Wani irin razana Jidda tayi tare da furta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Hisham me kake faɗa min, Yaya Nameer ɗin ne yake cikin wannan halin, kai ina faɗar likita ai ba faɗar Ubangiji bane, a dai sauya wani asibitin aji su kuma me zasu ce.?" "Hmmm! JIDDA kenan lokacin da likita yace Sadiq yana halin rayuwa ko mutuwa ai haka kikace kuma yazo ya mutun, kawai dai Jidda ina cikin tashin hankali, mtsss Hmm! Nazo na ganki ne kawai na tafi kije kawai kaina yana ciwo zanje na kwanta." "Amma Hisham ina bukatar lokacinka fa, daga zuwa sai tafiya." "Please JIDDA ki barni na tafi, wallahi jiri nakeji na juma anan bazan iya kai kaina gida ba, nazo ne na ganki ko zan samu sukuni." Kanta Jidda ta kaɗa tace. "Shikenan ka gaishe da yaya Nameer ɗin insha Allah gobe zanzo na gaishe sa." Da zaiji Hisham ya amsa sanda Jidda ta shiga gida kafin ya tafi. ****** Ko da daddare Nameer yana kwance a gefen Abba Shi kuma Hisham yana zaune kan kujera Alhaji Bawa ya shigo shida Alhaji Ahmed, tashi Nameer yayi ya zauna Abba duban Hisham yayi yace yaje ya kira Ummi tashi yayi yaje ya kirata suka dawo tare itama gefen Abban ta zauna tana cewa su Alhaji Bawa. "Barkan ku da zuwa Alhaji Bawa Alhaji Ahmed Barka." Cikin fara'a suka amsawa Ummi Nameer da Hisham ma gaishe su sukayi har suna tambayar NAMEER jikinsa, Abba ne yace. "Alhaji Bawa tun dazu na ke sauraron zuwan ka, Allah dai yasa binciken da kukayi akan Yarinyar an samu sakamako mai kyau." Shuru Alhaji Bawa yayi sai Alhaji Ahmed ne ya nisa yace. "To Alhaji maganar gaskiya dai anje anyi bincike da farko yaron wajena Kabiru na aika unguwar su Yarinyar ya min bincike, sanda ya kawo min sakamakon ban daddara ba na koma da kaina na sake bincike shima Alhaji Bawa da kansa yaje yayi binciken abun mamaki gabaki ɗaya sakamako ɗaya muka samu babu wani sauyi, da farko dai ita Yarinyar bata da wani aibu kowa Alkairi yake faɗa a kanta tana da riƙon addini ga girmama manya, mahaifin yarinyar bahaushe ne haka kuma mahaifiyarta bahaushiya ce mahaifiyarta ne yaruba, Alhaji IYABO, akwai babbar matsala gaskiya, dangin mahaifiyar Yarinyar duk mijin da ya auresu farko sai ya rasa rayuwarsa, gaba daya haka suke, ita na mahaifiyar Yarinyar yafi tsananta domin kuwa maza huɗu ta aura duk basa wuce sati da Auren suke mutuwa, shine dalilin da yasa aka kyamace ta tabar cikin Yan uwanta ta dawo gefe ta zauna, wannan itace matsalar Alhaji Iyabo, duk wanda ya auresu da fari mutuwa yake, sannan kakar Yarinyar uwar mahaifiyarta kenan ance cikakkiyar ƴar bariki ce, amma ita yarinyar bata da matsala, wannan shine abinda muka binciko kuma mun tabbatar da gaskiyar lamarin haka yake." Kansa Nameer ya dafe, Abba numfashi ya saki kafin ya kalli Hisham da yake kallonsu hankali tashe domin kuwa a yanzu yana jin Soyayyar Jidda sama da komai a rayuwarsa yana jin cewa zai iya rayuwa da ita a ko wani hali, ya ijiye duk wata ɗaukar fansa da yayi niyya a gefe, a yanzu da gaske yake jin Soyayyar ta, ƙirjinsa ya dafe dake dukan Uku Uku Muryar Abba yaji yana cewa. "Subahanallah! Alhaji Ahmed, gaskiya wannan ba irin da za'a aura ba ne, bazai yiwu Hisham ya auri wannan Yarinyar ba, menene amfanin auren da babu jin daɗin rayuwa, sati ɗaya miji ya mutu, no Hisham kayi haƙuri da wannan Yarinyar ka nemi wata ka dai ji da kunnen ka, Nameer ka basa shawara ya nemi wata, Ramata kema ki faɗawa danki babu Aure tsakanin sa da wannan Yarinyar, Alhaji Bawa na gode sosai." _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_ [7/25, 9:13 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE 📚* _Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._ *_Page 57 to 58_* Idanunsa Hisham ya kuma runtsewa tare da cije lebensa yana jin maganar Abba tamkar yana zuba masa ruwan zafi a jikinsa, Muryar Ummi ne ya kuma dukan kunnen Hisham. "Dama ni ai Abban Hisham da ka saurareni tun fari baza'a kai zuwa wannan lokacin ba zamu rabasa da yarinyar amma tunda yanzu yaji da bakinsa zai haƙura dole ai." Numfashi Alhaji Ahmed ya saki tare da tashi suka yiwa Abba sallama, shima Abba tashi yayi ya rakasu har ya dawo Hisham bai ce komai ba, Abba ne yace masa. "Muna magana Hisham kayi shuru tamkar baka wajen, bakaji abinda ake magana bane.?" Abba ya jefa masa tambayar sai yanzu Hisham ya ɗago idanunsa da sukayi jajur ya kallesu tare da cewa. "Ina jin ku Abba, to me zance muku, ni na amince ko wacce irin mummunar kaddara Jidda ta ke ɗauke dashi ni na amince zanyi rayuwa da ita a haka, Abba Ƙaddara rayuwa bata nufin karshen mafarkin Rayuwa, Jidda kaddarata ce ko iya soyayyar ta da nakeji a raina ya nuna min cewa Jidda kaddarata ce, da farko ba son gaskiya nake yiwa Jidda ba Abba a nufina na kona zuciyarta da soyayya domin ɗaukar fansar abinda ta yiwa ɗan uwana Nameer sai Ubangiji ya juya lamarin sa ya sanya min Soyayyata na haƙiƙa a raina bazan iya jagorantar rayuwata ba dole sai da ita Abba, ba dole ace kaddararta da ta ahalinta ɗaya ba ne, kayi haƙuri bazan iya bin umarninka ba akan rabuwa da Jidda, ina son Jidda na amince idan na aureta na mutu ko ba komai zan mutu cikin farin ciki da cikar muradina, *KO BAKU AURA MIN ITA BA DOLE SAI NA AURE TA, BA ZAN TAƁA RABUWA DA ITA BA KO MAI ZAI FARU KO DA HAKAN YANA NUFIN KARSHEN NUMFASHI NA NE.* Yayi Maganar a zuciye yana tashi ba tare da tsayawa sauraren abinda Abba zaice ba zai bar wajen, Muryar Nameer ya dakatar da shi. "Tabbas ƙaddarar rayuwa bata nufin karshen mafarkin rayuwa Hisham na yarda da wannan maganar taka, sai yanzu na fahimci ƙaddarar ciwo na, da alamu Ubangiji yana nufin ni ne zan fanshi rayuwar ɗan uwana, bani da doguwar rayuwa a wannan duniyar, wata biyu ne ya rage min zanyi amfani da wannan kwanakin domin ceto Soyayyar ɗan uwana, zan kasance mijin Jidda na farko domin bawa Hisham farin ciki na tsawon rayuwa, zan auri Jidda idan na mutu ka samu damar kasancewa da ita a matsayin mata ba tare da wani tsoron mutuwa ba, Abba ni zan auri Jidda idan na mutu Hisham ya kasance da ita na har abada." Tunda suka fara Maganar Abba ke bin Hisham da kallon mamaki duk da yasan zuciyar Hisham amma bai taɓa tsammanin zai iya kallon idanunsa ya ce zai juya masa baya akan mace ba, kafin Abba yayi Magana Ummi tace. "Akan wannan matsiyaciyar Yarinyar zaka sadaukar da rayuwarka Nameer wa ya ce maka bazaka rayu ba, zaka samu lafiya Nameer a wannan asibitin kawai mukaji furucin su bamu ji na wasu asibitin ba, zamu je asibitin Doctor Barde shima zai ƙara gwadawa bazamu tsaya ba har sai ka samu lafiya, kai kuma Hisham a wannan karon bazan ɗauki iskancinka ba, tabbas zan koya maka hankali, dole ka rabu da ita dan ubanka ai ba tsoronka mukeji ba bare ka juya mu yadda ranka yake so shasha." Ummi tayi Maganar cikin ɓacin rai, shi dai Hisham bai ce komai ba bayan wannan maganar da yayi, Nameer zaiyi magana Abba ya ɗaga masa hannu tare da cewa. "Ya isa haka, duk ku tafi ku bani waje, ya maka kyau Hisham na gode iyakata ka nuna min kaje kayi abinda kake so kaje maza ka nemi wasu iyayen da kake dasu bayan mu su nema maka Auren mu ai bamu isa da kai ba ." Wani irin sanyi jikin Hisham yayi, kansa ya girgizawa Abba tare da cewa. "Kayi haƙuri Abba wallahi kun isa dani, ka fahimce ni Abba ina son Jidda wallahi bazan iya rabuwa da ita ba Please Abba ka taimakeni ka Aura min ita ko da ita ko babu ita bazan taɓa tsallake wa'adin da Ubangiji ya min ba a duniya mu yarda da ƙaddara nas............... "Ka shige ka bani waje Hisham!." Abba ya dakatar dashi a zafafe cikin tsawa, idanunsa Hisham ya runtse tare da barin wajen cikin kunar rai, bayansa Nameer yabi da sauri Ummi Abba ta duba tare da cewa. "Nasha faɗa maka cewa mu daina biyewa Hisham muna masa duk abinda yake so amma kaƙi saurarana, duk abinda Hisham yayi a wajen ka daidai ne yau ga irinta nan ya nuna maka bazai yadda ya rasa abinda yake so ba, saboda ka saba masa da samun duk abinda ya nema." "Ramata karki ɓata min rai da maganar banza, ko yanzu ma ba hanasa abinda yake so nayi ba, rayuwarsa nake son karewa da ace Yarinyar nan bata da wannan tabon mutuwar to da tabbas zan aura masa ita, sannan ko yanzu idan har aka samu ƙaddarar da zata sauya wannan tabon mutuwar to tabbas zan aura masa yarinyar." Cike da mamaki Ummi ta ke kallon Abba. "Abban Hisham har akwai wata kaddarar da zata sauya mutuwa, oh na fahimta saboda muradin danka ya cika ka yarda ya aureta ko da zai rasa rayuwarsa, hakan Soyayya ce, kai fa kace ya haƙura da yarinyar yanzu kuma ka sauya maganar me yaja hankalinka haka.?" "Ni ne Ummi ni ne naja hankalinsa, da ku rasa mu gabaki ɗaya gwara a rasa ɗaya dole dai ni mutuwa zanyi, ki yarda da ƙaddara Ummi, Doctor Sabo bazai faɗi result ɗin karya ba akan ciwo na, ko da asibiti ɗari zamuje amsar dai ɗaya ce waye kika ga mai KANSAR ƘWAƘWALWA ya yi doguwar rayuwa ya kamata mu yiwa kanmu hisabi idan rai ya ɓaci mu kai zuciya nesa Ummi Hisham yana son Yarinyar nan ya kamata ki barsa ya aureta, Ummi auran Jidda da zanyi shine kawai zai ceto Hisham daga mutuwa, ban taɓa neman alfarma a wajenki ba Ummi, amma yau zan nema, idan har kika min haka Ummi shine zai tabbatar min da kinfi kowa ƙaunata a duniya, kuma zan mutu ina farin cikin wannan alfarmar da kika min dan Allah Ummi." Hawaye ne ya zubo daga idanun Ummi, tare da takawa taje gaban Nameer ta tsaya. "nasan alfarmar da zaka nema a wajena Nameer bazan iya ba, bazan iya kallo kasa rayuwarka a cikin haɗari ba, duk da yanzun ma Rayuwar taka acikin haɗari take, Nameer ina ji a jikina zaka samu lafiya." "A'a Ummi bazan samu lafiya ba kin sani na sani, kawai kimin wannan alfarmar." Kanta Ummi ta kaɗa tace. "Shikenan zan maka zan bar Hisham ya auri yarinyar nan ne kawai saboda kai Nameer amma Allah ya gani har cikin zuciyata bana kaunar ta, amma da sharadi ɗaya har sai mun koma asibiti an tabbatar da cewa bazaka rayu ba, sannan ne zan iya barinka ka ɗauki wannan kasadar Nameer." Ummi tana faɗin haka ta juya da sauri tabar wajen tana kuka, Nameer wajen Hisham ya koma. Yana zaune yayi shuru. "Hisham na faɗa maka wannan gardamar zan rabata ni zan auri Jidda tunda dama ai ba jumawa zanyi a duniyar ba, kaga idan na mutu shikenan ka samu damar zama da ita na tsawon rayuwa." "Hassan tun ɗazu yake kiran wayarka." Hisham ya masa maganar tamkar baiji mai yace ba. "Magana fa nake maka Hisham ba damuwata kiran Hassan ba." Idanunsa ya ɗaga ya kalli Nameer kafin ya girgiza kansa. "Hmmm! Maganar taka ce bata da daɗin ji Nameer, wa yace maka nidin mai tsawon rayuwa ne, kasan ƙaddarar mutuwa tace, kaga Nameer idan Allah yasa kana da tsawon kwana duk wahala da ciwo sai ka tashi kayi Rayuwar da Ubangiji ya diba maka, ka barni na ɗauki kaddara ta Jidda kaddarata ce kuma ni zan ɗauki kaddararta." "Hisham kenan kaga mun gama magana da Ummi muddun kana son Auren Jidda to dole ne sai na fara rabaka da kaddarar da take cikin ahalin Jidda." "Ka tashi muje gidan su Jidda na tabbatar da abinda kunnena yaji." Kansa Nameer ya kaɗa yace. "Shikenan zamu iya zuwa Hisham hankalina ya kasa kwanciya akan karar da Alhaji Sagir ya shigar da Company, watakila a gama shari'ar bana raye, ko mai zai faru Hisham karka bari Companyn mu ya wulakanta, ka kankaro mutuncin Abba, kayi ƙoƙarin ganin ka kare mana Company." "Nameer shi kansa Abba bazai bari Companyn sa ya wulakanta ba, yafi Alhaji Sagir karfi da iko a cikin ƙasar nan, nasan a wannan lokacin Abba zai tauna tsakuwa dan aya taji tsoro wallahi Nameer bana jin tsoron wannan kotun da za'a shiga, ni nasan wanda ya je ya saka Alhaji Sagir ya shigar da Company ƙara, ba kowa bane face Mamabisola, tar na ke kallonta da idanuna, burinta ɗaya mu rasa komai a rayuwa bazan taɓa tona mata asiri ba, nafi so shi Abba ya fahimta da kansa." "Me kake nufi Hisham waya faɗa maka cewa itace tasa Alhaji Sagir ya shigar da ƙara kotu."? Miƙewa tsaye Hisham yayi tare da goya hannunsa a baya yace. " *MAI GADIN GIDAN TA* Shine ya sayar min da wannan jaridar akan kuɗi Naira dubu ɗari b." A razane shima Nameer ya miƙe yace. "What! To amma meyasa zai fitar mata da sirri muddun gaskiya yake fadi baya tsoron abinda zaije ya dawo, kai mtsss to meye tsakanin ta da wannan kisan tasan wanda yayi kisan ne da har zataje ta zuga Alhaji Sagir.?" "A'a bata sani ba kawai dai ta shiga ciki ne saboda ta samu taga mun wulaƙanta, shine ita burinta zai cika." "Kai lamarin da mamaki Hisham, to Allah ya kyauta, ka tashi muje gidan su Jiddan." _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *FREE BOOK ONE 📚* _Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma mun kusa zuwa karshen Free zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180._ *_Page 59 to 60_* Bakinsa HISHAM ya taɓe ransa duk a cunkushe ya ɗauki wayarsa tare da cewa Nameer suje. Abba bedroom yabi Ummi ya dinga rarrashinta da ƙyar ya samu Ummi tayi shuru. Ko da sukaje unguwar su Jiddan Hisham kansu tsaye suka shiga, Umma ce kawai da Basmah a tsakar gidan Jidda tana dakin ta, darduma Umma ta shimfida musu Basmah hankalinta duk yana kan Hisham tana jin baƙin ciki da kunar rasashi duk da a ranta ta saka sai ta ƙwaci Soyayyarta, bayan sun gaisa ne Umma ta fahimci kamar suna cikin damuwa, nisawa tayi tace. "Nameer kamar akwai abinda yake faruwa ko, naga kamar duk jikinku yayi sanyi.?" Numfashi Nameer ya saki tare da kallon Hisham kafin yace. "Umma tabbas akwai abinda ya kawo mu sai dai fa Umma ban san ta yaya zamu fara miki maganar nan ba ina jin nauyin maganar." "Nauyi kuma Nameer ni ai uwa ce, ku faɗa min damuwarku babu komai." Ganin Nameer na wala wala yana jin nauyin tambayar yasa Hisham cewa. "Umma magana ce akan neman aurena da Jidda, Abba yasa anyi bincike akanku, kuma ankawo masa sakamako marar daɗi, har hakan yasa iyayena suna son min katanga da Jidda, Umma da gaske ne duk wanda ya auri zuri'arku Auren farko sai ya mutu? Umma ance ke maza huɗu kika aura duk basa fin sati da Auren suke mutuwa, ance dalilin da yasa kenan kika bar cikin Yan uwanki kika dawo gefe, sannan kuma ance mahaifiyarki ƴar bari............ "Ya isa haka Hisham wadannan tambayoyin ma kaɗai sun isa, domin sune matsalar mu ba sauran ba." Tunda Hisham ya fara magana Jidda ta fito take jinsa har Nameer ya dakatar dashi hankalinta ne ya tashi gumi ya keto mata bata san sanda hawaye ya biyo idanunta ba, umma kuwa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta hau furtawa a cikin zuciyarta shikenan ranar da take tsoron zuwanta tazo numfashi Umma ta sauke kafin tace. "Hisham idan har iyayenka sun maka katanga da Jidda to kabi umarninsu domin kuwa bazasu cutar da kai ba saboda duk wanda zai soka yaso farin cikin ka a duniyar nan bayan sune, *_Wannan ba ƙarya aka faɗi akanmu ba tabbas ƙaddarar da ke cikin zuri'ar mu ne sai dai bani da tabbas idan Jidda tana ɗauke da wannan kaddarar saboda ita jinin gidan ubanta ne ba gidan mu ba, duk da acikin ya'yan mata da ke gidan mu da yawa sun gajemu dole a guje mu Hisham, tabbas mazan aurena huɗu suka rasa ransu babu za'ida aciki, Hmm! Ance muku goggona tana rainon ƴan bariki ko shine tambayar da Nameer ya dakatar da kai ga yinta gareni ko, shima gaskiya ne babu ƙarya a ciki, kaje ka yiwa iyayenka biyayya ka rabu da Jidda zata iya rayuwa ko ba Aure, ko da ta rasa mijin Aure, ai shi Aure Sunna ce ba farilla ba, farilla ce dole ba Sunna ba, manyan malaman Musulunci sunce idan mace batayi Aure ba har iya tsawon rayuwarta ba haramun bane kuma Allah bazai tambayeta akan meyasa batayi Aure ba, na gode da KULAWARKU da soyayyar da kuka nunawa yata Hisham da kuma ɗawainiyar da kukayi gareni, kaje ka yiwa iyayenka biyayya Allah ya muku albarka ya baku mata na gari_*." Umma tayi Maganar cikin sanyin jiki, Wani irin kuka Jidda ta sanya sautin kukan ta shiya dawo da hankalin su Hisham gareta, dubanta Hisham yake cike da tausayi Muryar Nameer sukaji yace. "Umma dama munzo mu tabbatar da gaskiyar maganar ne, bani da lafiya umma, munje asibiti sun tabbatar da cewa ina da Cutar KANSAR ƘWAƘWALWA sunce bazan haura wata biyu ba a duniya zan mutu, nayi magana da mahaifiyar mu cewa ni zan ɗauki kasadar Auren Jidda, tunda dama ni mutuwa zanyi dan haka zan aureta idan na mutu Hisham ya auri matar sa, a ina dangin mahaifin Jidda suke Umma zamuje mu nemi aurenta." "Subahanallah! Nameer abinda ke faruwa da kai kenan innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Amma Nameer wannan ba ɗaukar kasada ba ce zakayi faɗar likita ai ba faɗar Ubangiji ba ne Nameer insha Allah zaka samu lafiya." "A'a Umma karki hanani, babu wanda ya taɓa kamuwa da cutar nan ya rayu, ki duba kiga yadda take kuka ko hakan ya isa ya nuna miki ƙarfin soyayyar da suke yiwa junansu ina da halin taimakawa ɗan uwana bazan barsa ya shiga wani hali ba, ki mana addu'a da fatan Alkairi kawai." Tunda Nameer ya fara Maganar Hisham yaji wani kishi yazo masa ya tsaya a wuyansa, idanunsa ya runtse, yana ji Umma tace. "To shikenan Nameer Allah yasa haka yafi Zama Alkairi, amma fa ka sani bazan waiwaici bayana ba, bana son tuna abinda ya wuce, akwai baffan ta a cikin garin Gombe sai dai kuje wajensa ya baku Auren Jidda amma bazan iya faɗa muku inda Ahalinta suke da zama ba saboda babu Alkairi a tsakanina dasu." Kansa Nameer ya girgiza cikin zuciyarsa ya furta _tunda har aka samu baffan ta to tabbas za'a samu cikakken ahalinta._ "Shikenan ba damuwa idan mun gama magana da Abba zamuzo sai a bamu numbern wayar baffan nata mu zamu koma." Nameer yayi Maganar yana tashi shima Hisham tashi yayi sukayi sallama da Umma jidda da Basmah bayan su HISHAM sukabi suna tsaye jikin Mota har yanzu Jidda hawaye take sun juma suna tattaunawa akan lamarin, Nameer ya tabbatar da cewa shine zai raba wannan gardamar sai dai ita Jiddan har cikin zuciyarta bata amince da lamarin ba, cikin jimami suka rabu da Jidda. ********** Acikin kwana shida da maganar Abba da Hisham da kuma Nameer sunje asibiti huɗu da Nameer manyan asibitin da suka fi dukkan asibitin da ke cikin garin har result ɗin sa aka tura India suka ƙara bincike amsar dai ɗaya ce bazai rayu ba bazai gaza wata biyu a duniya ba, Hisham da Umma sosai suka kuma shiga cikin tashin hankali sai dai babu yadda suka iya da kaddara dole suka haƙura, sai a wannan lokacin Abba da Ummi suka amince da Nameer ya auri Jidda duba da yadda Hisham ya shiga tashin hankali akan Jiddar, shima Hisham da kyar ya amince Nameer ya auri Jidda dan har cikin ransa yake jin kishin hakan duk da Nameer ɗan uwansa ne, Abba yace gara ayi auren cikin gaggawa kafin wata biyun ta cika. A cikin wannan satin Abba ya tura su Alhaji Bawa sukaje har gida suka samu Umma ta musu kwatancen inda zasuje su sami Baffan Jidda Malam Aminu da ke zaune cikin jihar Gombe tare da basu numbern wayarsa, ko da suka dawo Abba da kansa ya kira Malam Aminu ya masa bayanin abinda ke faruwa, cikin mutuntawa da kulawa Malam Aminu yace Allah ya kawo su lafiya, Abba Nameer yasa yaje ya yankawa su Alhaji Bawa ticket ɗin jirgin Gombe washegari su tafi. Haka kuma akayi washegari suka tafi Gombe harda Nameer, wuni guda suka gama abinda ya kaisu suka dawo, inda Malam Aminu ya bawa Nameer Auren Jidda sai dai shi baya da masaniya akan neman Jidda da Hisham dan Abba yace kar a sanar da Malam Aminu a nuna masa kawai Nameer shine yake neman auren nata, ansa ranar auren wata ɗaya tal, inda Malam Aminu yace shima zaizo Kwaran a ɗaura Auren kawai anan, ko da suka dawo suka sanar da Abba yace hakan yayi sai dai Umma ita bata ƙaunar shigowar Jidda cikin ahalinta a haka aka ijiye maganar auren. ********** Sosai Basmah ta ke dariya ita kaɗai a cikin daki, shuru tayi na wasu mintinan sai kuma ta kuma sakin dariya tare da furta. "Allah mai iko rana ɗaya sai ya baka dama tabbas Hisham zai zamo nawa." Tayi Maganar tana dariya text ne ya shigo wayarta hakanne yasa Basmah Daga wayar ta buɗe sakon zama tayi ta fara karanta sakon. _Bana son kusan ko ni waye shiyasa na ɓoye number ta na turo miki wannan text ɗin, nasan kece aminiyar Jidda ta haƙiƙa, wacce kike ɗaukar damuwarta amatsayin naki, to shawara zan baki ki bawa Jidda akan Auren da take niyyar yi da Nameer nan ba da jumawa ba babban kuskure ta ke kokarin tafkawa rayuwarta, Nameer ƙarya yake bashi da wata cutar KANSAR ƘWAƘWALWA, wannan shirinsa shi da likitotin daya saya saboda bukatar ya mallaki Jidda, bashi da wannan cutar dan haka idan har ta auresa to ta tabbatar ta rasa Hisham na har abada NAMEER MUNGUN MACIJI NE WANDA BASHI DA ALKIBILA, dan Allah ki sanar da Jidda ku san yadda zaku dakatar da wannan Auren ni musulmi ne wallahi na miki rantsuwa da Allah Nameer bashi da wata cuta ƙarya ne, idan kuma wannan maganar da na faɗa miki ƙarya ne to na yadda bala'in Ubangiji ya sauƙa a kaina, shida abokinsa Doctor Hassan suka kulla wannan makircin saboda cikar ƙudirinsa na mallakar Jidda ya gama bincike akan Mahaifiyar Jidda shiyasa ya ɓullo da wannan makircin saboda yasan ta nan ne kawai burinsa zai cika._ Miƙewa tsaye Basmah tayi a firgice da ƙarfi ta furta. "What!!! Nameer ɗin." _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to insha Allah Book One ya kusa zuwa karshe, alhamdulillah tuni masu niyyar saya sun fara saya kema ƴar uwata karki sake ayi babu ke bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne 200 kacal karki sake a buga wannan cakwakiyar babu ke, duk yadda zaki kai ga hasashen yadda labarin yake ina tabbatar miki bazaki taɓa hasashen dai-dai ba, domin kuwa labarin a sarƙe yake warwaresa a wajen readers abune da bazai yiwu ba dole sai kun tsumayi alkalami._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 💑 *_JALALA_* 💑 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 *_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_* *_The writer of_* -Sauyin Rayuwa. -Nasmah ko Nasirah. -Sara da Sassaqa. -Indo a Birni. -So Bai San Jini Ba. -Ruɗanin Zuciya Biyu. -Akan Ƴar Uwata. -Doctor Hassan. -Gelle Ɓingel. -Ƙauyenmu. -Hatsabibiya Saude. -Aminaina ko Ita?. -Ƙullalliya. *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Special tnx to my people masoya masu ƙaunata masu bibiyata ako da yaushe, yanzu ma gani tafe muku da sabon salo sabon labari mai tafiya da zamani labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi a cikin sa ku kasance dani domin jin yacce cakwakiyar zata ƙarke, idan kinsan kina da ra'ayi akan wannan labarin to ki fara bibiya tun daga farko kar sai nayi nisa kice min daga farko please._* *_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻 *END OF BOOK ONE LAST FREE PAGE 📚* _Wannan littafin ba free bane na kuɗi ne Book one shine Free kuma wannan page ɗin shine last free page zamu shiga Book two inda zaku cigaba da karatun wannan littafin akan 200 kacal ban tsawwala ba farashin da zaku iya biya na sanya dan Allah idan har kina son wannan littafin kina bibiyar sa kizo ki biya kudin ki, ki cigaba da karatun sa akan farashi ƙalilan, karki yadda ki kasance cikin ɗaya daga cikin masu cin hakkin wani 08147537180 Ummu Nasmah na maraba da masoyanta, wannan shine damar da zaku nuna min soyayya ta hanyar sayen wannan littafin._ *_Page 61 to 62_* Cike da tsantsar mamaki Basmah ta nemi waje ta zauna _ta yaya za'ace NAMEER zai ci amanar Hisham wannan ba maganar da hankali zai ɗauka bane, amma kuma ai ana iya komai akan Soyayya, to tunda nima zan iya cin amanar Jidda meyasa shi Nameer zan kasa yarda da zai ci amanar Hisham, ko da yake kusancin dake tsakanin Hisham da Nameer yafi ƙarfin kusancin dake tsakanina da Jidda_ numfashi Basmah ta saki a fili ta furta. "Hmmm! To ma wai waye ne ya turo min wannan sakon a idan gaskiya ne a ina ya samu wannan sirrin waye Hassan ya kamata nasan waye shi Hassan domin sanin dabiun sa shine zai tabbatar min da waye Nameer a zahiri dai Nameer mutumin kirki ne to amma ta yaya cikin sa zai kasance baƙi, to ma meyasa zan faɗawa Jidda wannan saƙon ni ai wannan babbar dama na samu bazan taɓa bari Jidda tasan wannan maganar ba, domin kuwa Auren Nameer da JIDDA shine zai bani damar samun Hisham a matsayin mijin aurena, lallai wannan babbar dama ce gareni." Tayi Maganar tana sakin murmushi tare da jingina kanta a jikin bango. Tun ɗazu ta ke kuka tamkar ranta zai fita taki tayi shuru idanunta yayi jajur, Ummi tayi tambayar duniya ta faɗa mata abinda yake damunta amma taƙi sai kuka kawai take tayi rarrashin duniya kuma taki tayi shuru, Hisham ne ya shigo yana waya shima duk fuskar sa ta faɗa dan tunda aka saka ranar auren Nameer da Jidda zuciyar sa take tsinkewa ga fargar mutuwar da aka Nameer zaiyi nan da wata biyu, ganin Tutu nata kuka ya sashi katse wayar tare da nufar su yana cewa. "Ummi meke faruwa kuma, meya sameta."? Numfashi Ummi ta saki dai-dai Abba na shigowa shi da Hisham tace. "Umm ka ganta tun ɗazu take wannan kukan nayi tambayar duniya ta faɗa min abinda ke faruwa taƙi, nayi rarrashin ma kuma taƙi tayi shuru bansan meke damunta ba." Zama gefenta Hisham yayi tare da dafa kafadarta. "Tutu kalli idona ki faɗa min meke damunki ko Allah zaisa na iya share miki hawayenki, faɗa min."? Kuka ta kuma fashewa dashi jikinta na rawa daƙyar ta buɗe bakinta tace. "Yaya Hisham da gaske zaka share min hawayena."? "Eh zanyi maganin damuwarki idan har bata fi ƙarfi na ba, faɗa min menene matsalar."? Idanunta ta ɗaga ta kalli Abba kafin ta sunkuyar da kanta. "Yaya Hisham idan har ana son na cigaba da farin ciki a cikin gidan nan to a fasa Auren Yaya Nameer da Jidda, ni ya Aure Ni." A firgice Hisham ya ɗago kansa ya kalli Ummi ya kalli Abba da Nameer da suma suka zaro idanunsu suna kallon Tutu. "Tir ƙashi." Hisham ya furta yana mai da kallonsa ga Tutu kafin ya miƙe tsaye yace. "Tutu kinsan abinda kike faɗi kuwa, kin haukace ne, Nameer ba matsayin uwa ɗaya uba ɗaya ya kamata ki ɗaukesa ba, ya fasa auren Jidda ya aureki ke gaki uwarsa kin basa umarni ko, to yaƙi bin umarnin naki uwarsa tsine masa albarka ya shiga duniya, dan Allah Ummi kiji wani rashin hankali wai bazata ƙara farin ciki ba muddun bai aureta ba, to sai ki mutu da baƙin ciki wawiya." Hisham yayi Maganar a fusace tamkar zai kai mata duka, Nameer kuwa wani irin tsinkewa zuciyar sa yayi ko da wasa baiyi zaton Tutu zata birkice haka ba, numfashi ya saki tare da jinginuwa da bango ya kasa magana Ummi ce tace. "Wai dama wannan uban kukan da kike duk na wannan shashancin ne Tutu, kin manta da lalular da Nameer yake ɗauke dashi ne bai kai wata biyu ba ya rage masa a wannan duniyar bama da wani kwanciyar hankalin farin ciki daga mu harshi Nameer ko wani wayewar gari da fargabar mutuwar sa muke tashi, ita kanta Jiddar da zai Aura kin sani Tutu ba wai da san ransa zaiyi Auren ba, kinsan dalilin aurenta da zaiyi, amma kuma ke yanzu sai ki ɓullo mana da wannan shashancin, karna kuma jin kinyi wannan Maganar." Kukan Tutu ta kuma fashewa dashi cikin tashin hankali ta hau cewa. "Ni fa Ummi na yarda na auresa a haka ko da kwana ɗaya nayi tare dashi, zanyi farin cikin ganin wannan ranar na tsawon rayuwata, Ummi wallahi ina son yaya Nameer, shima fa Ummi yana sona ku tambayesa mana kuji, mun fa juma muna soyayya Ummi karku hana mu farin ciki Ummi wallahi muna son junan mu." Kansa Nameer ya dafe jin ta fasa masa taya amma da ke namijin duniya ne sai yayi fuska tamkar baiji zancen ba, Hisham da Abba ido suka Daga suka kalli Nameer. "Nameer kana jin abinda Tutu ta ke faɗa, da gaske ta ke kuna son junanku kai da ita.?" Ɗago kansa yayi ya kalli Hisham shima tare da nuna kansa da yatsa cikin yanayin mamaki yace. "Wai ni ɗin ne nake soyayya da Tutu, wannan wacce irin magana ce kike haka, nifa kallon ƙanwar da muka fito ciki ɗaya na ke miki Tutu, anya kuwa yau kina cikin hankalin ki, Hisham da ace ina soyayya da Tutu kaine mutum na farko da zan fara sanarwa ko da ban sanar dasu Abba ba, kaima ka sani, ina ga yau dai Tutu bata cikin hankalin ta akwai abinda ke damunta." Kansa Hisham ya gyada tare da cewa. "Tabbas haka ne Nameer da bazaka ɓoye min ba, barni da ita idan kin haukace ne to ni kuma zan kaiki asibitin mahaukata ko tausayin halin da yake ciki bakya yi, yanzu na taka miki wuya." Da wani irin mungun mamaki Tutu ta ke bin Nameer da kallo tana matsowa garesa hawaye na daɗa gudu a fuskarta tamkar saukar aradu taji maganar tasa, sanda tazo daf dashi cikin kuka da wani irin sautin Muryar da ya fara dashewa itama ta nuna kanta da yatsa sai kuma ta fashe da kuka. "Yaya Nameer ƙarya nake! Karya nake kace meyasa meyasa zaka min wannan wasan Please yaya Nameer yanzu ba lokacin wasa bane loka..... Ba ta kai ƙarshe ba Hisham ya ɗauketa da mari sai da taga duhu ya gifta ta cikin idanunta har sai da ta shiɗe, da yatsa ya nunata. "Idan kika ƙara wata magana sai na ballaki wallahi shige kibar falon nan." Yayi Maganar yana nuna mata hanya da gudu Tutu ta haura sama tana kuka tamkar ranta zai fita, ɓoyayyen numfashi Nameer ya saki cikin zuciyarsa yana godewa Allah da babu wanda ya fahimci komai a cikin su Hisham haƙuri ya bawa Nameer yana ta famar faɗa Ummi ita kasa magana ma tayi shima Abba kansa ya kaɗa tare da furta Allah ya sawwaka ya shige bedroom ɗinsa. A saman bed ɗinta ta saki kuka mai ban tausayi ita kaɗai tasan irin matsanancin soyayyar da ta ke yiwa Nameer ashe dama soyayya kan dawowa ƙarya, meyasa Nameer zai juya mata baya ya ƙaryata soyayyar ta _kin faɗa min gaskiya naki na ɗauka Samira kullum kina faɗa min ni ne na ke son yaya Nameer shi bana gabansa amma naki yarda, a zatona ko da dukkan mazan duniya zasu juyawa mace baya yaya Nameer a matsayin sa na babban wana da nakejin zai iya tare min komai a duniya shi bazai min haka ba wannan wacce irin munguwar ƙaddara ce_ tayi Maganar zucin hawaye na cigaba da zuba daga idanunta ƙirjinta kuma tamkar zai fashe haka take ji tana jin Ummi na murda handle ɗin kofar bedroom ɗin nata tana kiranta tayi shuru tamkar bata ji ba domin haushin kowa takeji a cikin gidan karar shigowar saƙo ta ji a wayarta, hawayen idanunta ta goge tare da jawo wayar ta buɗe sakon a hankali ta hau karantawa sanda ta gama karantawa ta miƙe a firgice tare da mutstsika idanunta wai ko bata karanta bane ƙara maimaita karantawa tayi, sakon dai da aka turowa Basmah ne sai dai ita ana mata gargadi da karta kuskura tabari ayi Auren gumi ne ya yankowa Jidda hawayen dake zuba a idanunta suka kafe zama tayi dabas a tayels tare da furta. "What! Yaya Nameer ɗin lamarin nasa har ya kai haka.?" idanunta ta ɗaga ta kalli agogo karfe tara na dare numfashi ta saki tare da dafe kanta tana jin wani irin jiri na kwasarta, wayar ta ta ɗaga cikin nauyin jiki ta kira Nameer ɗin kusan miss Call 8 bai ɗaga ba, saƙo ta tura masa. _Na sani bazaka ɗaga wayata ba yaya Nameer, ashe bani kaɗai ka cuta kaci amana ba, harda mutumin da ya baka yardarsa fiye da kowa a wannan duniyar, Hmm! Soyayya mai juya tunanin marar lissafi, ashe soyayyar Jiddan har ta kai ga kaci amanar mutumin da yafi kowa yadda da kai a wannan duniyar labari ya iso domin kuwa Ubangiji baya bacci baya bari a zalunci bawansa dan haka Allah ya toni asirinka ashe dama baka da Cutar KANSAR ƘWAƘWALWA ka daurawa kanka masifa saboda neman biyan buƙatar kanka, muddun ina numfashi to wallahi sai na tona maka asiri bazan taɓa bari ayi wannan Auren ba._ Ta tura saƙon tana kuma sakin kuka mai sauti tare da tsanar rayuwa ace ka yadda da mutum ya cuceka. ******** Yana ganin kiran nata yayi banza yaƙi ɗauka, Hisham ya na can gefe da system a gabansa saƙon ya shigo wayar Nameer bakinsa ya taɓe tare da ɗaukar wayar ya buɗe saƙon, yana gama karantawa ya miƙe a firgice tare da furta. "What! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!." Ya furta a firgice, Hisham ɗago kansa yayi da sauri ya dubi Nameer tare da cewa. "Lafiya Nameer meya faru kake wannan salatin.?" END OF BOOK ONE KU BIYONI MU TARA A PAID GROUP ANAN NE KAWAI ZAREN LABARIN ZAI WARWARE. TAMBAYA shin yaya Shari'ar da za'a shiga tsakanin Alhaji Sagir da Companyn su Hisham zai kaya shin burin Mamabisola a kansu zai cika? Mai zai faru tsakanin Basmah da Jidda aminan da suke son Namiji ɗaya shin Basmah zata samu damar Auren Hisham? Shin da gaske ne Nameer baya ɗauke da wata cuta, idan har haka ne meyasa zai ci amanar Ahalin IYABO da suka mai dashi mutum duniya ta sanshi, sannan yaya zaiyi da kaddarar ahalin Jidda na mutuwar mijin da ya Auresu na farko, sannan yaya Hisham zaiji idan har ta tabbata Nameer yaci amanar sa ya zumuncin su zai kaya." Shin idan Abba ya fahimci cewa Nameer ya ha'ince sa zai cigaba da rikesa a matsayin Ɗa kuwa.? Waye ya turowa Basmah da Tutu wannan saƙon, waye kuma Hassan.? Duk amsar wadannan tambayoyin suna sarkafe a cikin Book two domin kasancewa dani a cikin wannan cigaban labarin biya 200 kacal ki cigaba da karatu cikin nutsuwa. _____________________________________ _Kamar yadda na faɗa Book one shine free Book two kuma PAID to alhamdulillah Book One yazo ƙarshe wannan shine last free page, idan kina bukatar jin karshen wannan labarin to maza garzayo ki biya kuɗin ki bamu tsawwala ba farashin ƙalilan ne muddun kina da niyyar saya, masoya sai azo a nuna min soyayya ta hanyar sayan wannan Book ɗin son so fisabilillah masoyana._ *0666081848 Gambo Ibrahim GT Bank bayan kin tura sai kiyi screenshort ki turo min evidence of payment ta wannan numbern 08147537180 da zarar na gani za'ayi adding ɗinki PAID GROUP tuni an fara payment ban tsawwala ba farashi ne na saka dai-dai da yadda zaku iya biya 200 idan baki da account number sai ki turo hoton katin mtn ta wannan numbern 08147537180* *Like Share and comments my fan's🥰* _UMMU NASMAH CE✍🏻_