🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:01 KANO STATE. *Unguwar kwanar ƴan dadawa* Tafe take tana ƙwambo,ta ɗage kafaɗarta ɗaya irin yadda nigogi keyi,jikinta sanye da wata ƙatuwar riga irinta maza da wando shima ƙato,kanta sanyeda pcap,zariyar wandon harkusada gwiwar ta,ƙafarta sanyeda wani ƙaton boot na maza baƙi, duk ya tsufa yasha faci,kayan jikinta kuwa sunyi uban squeezing,se ƙwambo take tana hura hanci,tafiyarta ma tanayi rana ɗage kafa ɗaya kamar namiji,hannunta riƙeda ƙaramin bucket fari wanda ake cewa fallasa na talla,shaƙe yake da awara me miya. Tana tafiya tana ɗage kafada irin yadda maza keyi,duk inda ta gitta yara da manya sekaji ana kANDE mai awara,ita kuma tana ɗaga hannu kamar wata ƴar siyasa tana faɗin "eh mana,dawa dai, kuhuta kawai". Tana kawo wa wata chamber samari guri ya kaure da ihu suna faɗin zaa kand, zaa kand,itakuwa se wani ɗage kafada take tana ƙwambo,tana basu hannu suna kashewa kamar yadda maza ke gaisawa da junansu. Cikin karkace baki kamar namiji tace "eh maza yane?, ya ake ciki ne eye?,kun haɗo min balance ɗina ko yaya?" Ɗaya daga cikin samarin yace "ai tuni na cake miki uwar kuɗin ki zaa kand, d one nd only ƙanwar maza in the ƴan daddawa village" wani juyowa tayi ta kallesa ta karkace baki ita adole namiji ce tace "zakarius asswear zan bubburma maka hannu a hanci,see zis tsamius want to read me nonsenseus eh,tsohon waye yake a village din iye? Zakarius zafa mu raba tawun(town) da kai fa,Allah wlh, Ni kar ka sake cewa unguwar mu village garama kawai ka mata zigidir ka kirata local getto yafi yawwa", tafada tana wani dire bokitin awarar ta. Tamika maka hannu tace "giv me zaa yastazey(yesterday)balans",miƙa mata kuɗin yayi,ta amsa ta gyara p cap dinta ta laƙwato miyau tafara ƙirga kuɗinta. "Wan,su,siri,foo,fai,sis,sabin,ess,nai,sen" haka ta dinga fillila ƴan hamsi2 tana kirgawa ita adole turanci take,samarin wurin sunmata yuuu da ido suna kallon ɗan bakinta kamar gidan tsutsa gashi jajur wai ita anan namiji ce,kaf faɗin unguwar batada ƙawa duka maza ne abokan hurɗarta,acewarta ita ƙanwar maza ce sbd haka itama namiji ce ba ragguwa ba,ƙawarta ɗaya ce layuza,itama sbd tsananin haƙurinta da juriya yasa suke ɗasawa,saboda tun suna yara ita kaɗai ce take jure wahalar bala'in kande shiyasa har suka girma suna tare,kuma bata sauyaba duk ko yadda suke da mugun banbanci in person. Iyayen layuza sunyi2 suraba wannan abota saboda yadda kande ke tafiyar da rayuwarta kamar ba mace ba, komi nata a tsaitsaye take yinsa tamkar namiji kasancewa duk yayyenta su takwas maza ne,ita kaɗai ce mace,se yaran kawunnanta mata biyu. Wani siririn saurayi ne yazo chamber yana wani hura hanci,tana tafiya yana kakkaɓe wandonsa da hankacif,ta inda ta ajiye bokitin awarar yabi ze wuce,be Ankara ba ta finciko rigarsa ta baya da hannu ɗaya tadawo dashi inda take tsaye tace "kai yane? Bakaga manyan guys bane zaka wani taho siii kamar dodon koɗi kana nema ka yimin tamola da bucket of my awaras" cikin broken english dinsa yace "hey u mara foka, liv my t-shirt alone,wat do you say,i will eat ur fada, daughter of air kawai". Cikin ƙaraji tace "hey wat do u nufi iye? Is me ka kira dota of air iye? Hey gayis ku cafa min shi anan gurin,Ni ze nunawa karyar turanci harda zakigina,kamar ni zaa soja of gidan ustazu habu me kayan koli,zecewa dota of air,nice ƴar iska,dama ɗan iska kace dana maka afuwa,gayis oya ku tara masa na yashi abaka" aikuwa rana rufe baki ɗan kanzaginta zakarius ya fizgo wnn lamushshsem saurayin yafara talle masa ƙeya,yana faɗin "hu are u iye?,do u know zaa soja of ƴan daddawa getto iye,zis is zaa kANDE, me awara and zaa one nd only soja of zis tawun". Dasauri wani saurayi ya taso yana cewa "easy zaa kand, baki gane wnn bane eh?". Cikin hura hanci ita adole uban daba tace "hey Boris don't firgita me, don't do yawa,kawai ka bari nasa zakarius da duna sumasa ɓalli-ɓalli a hammata,Allah wlh yanzun nan se nasa su mayar dashi kangaroo hannuwa aɗage" tafaɗa tana keɓe baki gefe. Boris yace "dawa de zaa kand wnn fa she is jikan mai unguwa Bello,kin mantashine?, tun muna yara aka kaishi bauci karatu gurin ƴan uwansu,baki gane shiba?".su adole se sunyi turanci,dama haka suke duk ƴan gang din kande Mayun turancine,dolema kayi turancin nan na dole inde kana tare da kande. Se lokacin taƙare masa kallo tace kai "Bello sagalo, innalillahi wai wnn Bello sagalo ne wanda yake shan majina muna yara, innalillahi yee gurin ya kaure da ihu,Bello sagalo haka akayi ta ihu ana kashewa,suna tambayar sa yakaratu, yanata zuba musu ƙarya yace ai yagama degree dinsa a harkar noma,shi yanzu she is piropeshonal farmer ne in d ƴan daddawa tawun. Kallonsa kawai suke suna ta ihu yana basu labarin ƙarya bayan ance musu almajiranci aka kaishi,amma se gashi yana ce musu shi yagama degree dinsa,se zabga musu turanci yake. Kande ta daga murya tace "oya kip kwayet,oya zakarius ɗauko min awarar cen kowa yasiya kuma yau ba bashi wlh, asawata(mamanta) tace kitty zatakai hospital bcos of she is not well,sbd haka kowa yau seya biya zeci". Boris yace "dawa de zaa kand wlh yunwa nakeji kuma banda ko ƙarfanfan yau,yau emti nake alqur'an,atemaka abani har gobe" kallonsa tayi tace "yawa kake zakarius eh,meye haka ne,Allah yau sede Kaci tuwon asawarka,kanaji fa nace kitty ba lfy yau Allah no loan of my awaras". Nan danan aka wawashe awarar suna tsaka daci Bello jikan me gari yace "kawarmu amma awarar nan wlh da dadi" cikin jin haushi tace "kai sagalo wlh zansa zakarius yamaka askin rabin hanci,dan me dafa muku tuwo agidanku wanene kawarku?, ni am soja,zaa one nd only soja of gidan ustazu habu me kayan koli,ko kace zaa kand,da nayi niyyar nayafe maka kuɗin awarar amma nafasa,kuma wlh dan ma awarar ta shekaran jiyace datafi hk daɗi". Duk kallon ta sukayi jin abinda tafaɗa wai awarar ta shekaran jiyace,masu lashe hannu duk aka tsaya ana kallon. Sauran guda huɗun da ta rage tace zakarius ya ɗauka ya cinye tabashi kyauta. Wato ita kande haka take duk bala'i seta faɗi gsky sede a mutu. Gata da kyauta,abunta baya rufe mata ido sam. .......... Hanyar gida ta nufa bayan tagama haɗa kan ƴan cinikinta,tana tafe tana wakar bobmali tana wani buɗa kafaɗu,duk inda ta gitta zakaji ana zaa kand tana Sa'a de mutanena, tana ɗaga hannu kamar meneman ƙuri'a. Dede wani gida madedeci yasha suminti taja birki ganin maza na fitowa daga zauren gidan nasu da alama yanzu aka idar da sallar azahar,dama idan aka aka zauna ɗaukar karatu agurin babanta se anyi sallar azahar sannan ake watsewa, gefe taja tana fito se wani kallo mazan da suka kasance samari da magidanta harma da tsoffi suke mata,wasu na mata kallon tir da ita batayi halin ubanta ba wanda yakasance babban malami a unguwar kuma liman. Yayinda wasu suke mata kallon marar kamun kai kuma marar hankali,wasu ma kallon da suke mata ma'anarsa aboye take. Ganin sungama wucewa ne tazo tana bouncing tashige cikin gidan itama,a zauren ta haɗu da babanta mlm babu me kayan koli,tana shiga tace "Sa'a de dagus, zaa imamu sannunka de da hutawa" kallonta yayi murmushi kwance akan fuskarsa cikin Muryar ustazai yace "a'a ya kande,ainafin daga gurin tallar ake ne?" "Dawa de dagus,dagacen nake kuma an siyar,duk da na faɗa musu ta shekaran jiyace amma haka suka lamushe suka caken balans ɗina,kasan innata akwai iya sarrafa hatsi,duk taurin kan hatsi yana tsoron masifar inna,shiyasa kaƙi kara aure dagus,hehehe Kai dagus nawa,zaa imamu sekayi Allah wlh" tafaɗa tana keɓe baki gefe tare da sheqewa da dariya ganin yadda baban nata sauke tabaransa yana mata kallon ƙasan ido. Cigaba tayi "wai dagus ina zawarar nan taka ne batula iye? Kasan fa cikar nan tana bala'in ƙaunarka iye, she is love you lodi lodi asswear,yawa kake imamu,kawai karufe ido kayi wuff da batula,kadena tsoron inna ni na tsaya maka,kalli batula ƴar caras da ita eyane" ganin tana neman gurin zama yasa cikin lallashi yace "ainafin yake uwata kisamu kishiga daga ciki ki kai kuɗin tallar naki,seki samu ki watsa ruwa ajikin ki ko yaa kande" sheqewa da dariya tayi tamiƙe ta ɗauki bokitinta tace kai innata Allah yasa de ƴar aljanna ce,duk ta rikita mana zaa imam da bala'in ta,imamu guda amma yana tsoron matarsa hehehe" takara sheqewa da dariya tana fito. Ball take da duk abinda yatari gabanta,tana faɗin "asswear Sena saka ƴan gidan nan adashen robobi,tunda kun zama non living things,ko Ina se kun karkasa kaya sekace gidan kutare, ƴan yawa kawai, Alqur'an inde bazaku zama living things ba sede kuyita siyan sabbin kaya,dan kullum Sena fasa wanda nagani a tsakar gida", wata matace tafito daga ɗakin ta tahau durawa kande zagi ganin tayi mata fatali da sabon bahonta data jiƙan kayan wanki,gashi se yararin ruwa yake da alama ya fashe ne. Ko kallon inda take kande batayiba ta afka ɗakin innarta ko cire takalman ƙafarta batayiba,wani baƙin cikin ne ya tokarewa umma amaƙoshi ganin ko kulata kande batayiba duk irin manyan ashariyar datake sauke mata,ga sabon bahonta agefe ruwan ciki yagama tararewa aƙasa sbd babbar hujewa da yayi,ƙwafa tayi ta juya ɗakinta inda tabar baƙuwarta. Aɗakin su kande kuwa, tasamu innarta ta idar da Salla takalleta tace, "uwar masu gida ya akayi naga bokiti, incede ba bashi kika rabar da awarar ba yauma?" "Ga balans ɗinki nan yau ba arnen dana baiwa bashi,kowa seda yaban ƙudina,kuma na gaya musu awarar shekaran jiyace datayi cimbi amma dashike hannunki na daurine sunsiye harda lamushe hannu,kai inna hoo ke,hoo ke ga masifa ga iya girki,ga kyau kamar birin wasa,zaa inna ta,matar imamu,kin mallake mana liman guda duk masifarki amma yaƙi kara aure,yafita gari ana girmama shi,amma daga shigo gida seya koma kamar zakaran da ruwa yayiwa bugun dawa,kai inna Allah de yasa kishiga aljanna" tafaɗa tana shafa ƙatuwar magen dake kwance akan gadon innarta ta,duka inna ta kaiwa kande ta goce tana dariya tace "zanci ubanki fa uwar masu gida,nikike fadawa Allah yasa zan shiga aljanna? Yo idan aljannar ta ubankice kice karya sakani". "Sa'a de inna kema kin san idan aljanna a hannun dagus take da tunkan ki sheqe ma ze wullaki cikinta,Kodan jarabar ki,ni jiyama batula ta tareni a hanya tace ina imamu nata,harda sabulu tabani" da gudu inna ta biyo kande aikuwa takwasa aguje se dakin kakarta Amo,kan ta shige ɗakin tasakeyin ball da bahon umma na ɗazu aikuwa yarabe biyu,ko waiwayawa batayiba ta afka ɗakin Amo kakarta, cikin ihu irinta bebaye Amo tace "na shiga uku takwara, waya biyoki ne kike neman kayar dani?". Acen waje kuwa inna wani aikin takama ta fita batun kande,dan tasan ko giyar wake tasha bazata fara binta ɗakin Amo ba wacce yaran gidan suke kira da gwaggo,dan ko bazata bari ta daki kande ba koda lefin me tamata balle yanzu da suke ba'a. Tana cikin haɗe kayan wanke wankenta Sega umma ta fito daga ɗaki ta rako baƙuwarta kallon banza sukayiwa inna suyi hanyar zaure, umma se sakewa inna habaici take., Ko ci kanku inna batace musu ba,sukayi hanyar waje suna ƙus-ƙus,cikin ƙasa da murya umma take cewa,"dan Allah lami ki tabbatar kinje min gurin nan,wlh kullum na kalli waccen shegiyar me suffar maza banajin na gamsu,sonake talalace takoma kamar karya,ganin ta ahaka be isheniba sonake takona magajiyar" takarasa tana kashewa lami ido,shewa sukayi suka tafa. Koda umma tadawo daga rakiya tasamu bahonta adagargaje wata ashariya me rai ta lailayi tana sakewa,"wani ɗan kaza kazane ya dagargaza mata sabon bahonta,wane tsinanne ne,ɗebabbe,tanbaɗaɗɗe", tanayi tana karasawa kusada inna,tana zuwa ta duƙa ta dau fasasshen bahon nata tana bangaje inna ai kafin tayi motsi ba biyu inna ta kwashe ƙafarta Sega umma aƙasa kamar an juye buhun dawa,ihu tasaki dede Lokacin da ƴarta Ikilima ta sanyo kai,ganin uwarta aƙasa tana zabga ihu ga inna agefe kamar batasan abinda akeyiba dan ko kallon inda umma take tule aƙasa bata kallo kamar ba ita ta juyeta aƙasanba. Aguje Ikilima ta rugo tana faɗin "innalillahi umma sannu,garin yaya kika faɗi,gashi dan baƙin hali bawanda yatemaka miki" tafaɗa tana zabgawa inna harara, cikin kururuwa umma tace "ga baƙar muguwar data kwashen ƙafa nan,sbd nayi magana akan tsinanniyar ƴarta me suffar maza,ta fasamin baho,wayyihuhu kashin aguɗina ze balle,yiiiihiii duwaiwaina". Cikin masifa Ikilima tasani ummanta tayo kan inna tana zage zage da niyyar tureta,aikuwa tana sakin umman tasake tafiya rijib tazube aƙasa tasake ƙwallah ihu,ko waige Ikilima batayiba burinta ta ture inna wacce ke tsaye tana kallon yadda Ikilima ta zaburo kamar zatayi faɗa da Sa'arta, tana zuwa gaban inna taja ta tsaya kamar an riketa takasa tureta sbd wani irin kwarjini da taga innar tayi mata,dede lokacin kande ta fito daga ɗakin Amo tagama cika cikinta da fura. Duk abinda ake tanajinsu, tana zuwa ta kwashe fuskar Ikilima da wani mari, tasa ƙafa fa kwashe kafar Ikilima tahau jibagarta sekace soja ya kama kwarto,ihu Ikilima keyi da kururuwa itada ummanta,sunata aikawa kande zagi da jafa'i kala2. Ihunsu ya janyo hankalin sauran ƴan gidan aka firfito ana kallon wnn dramar,aka rasa wanda ze kwaci Ikilima a hannun kande,seda tanata lilis sannan ta kyaleta,inna kuwa aikinsa taci gaba da yi kamar bata gurin,kande tana gama jibgar Ikilima tasa kai tayi hanyar waje tana buɗa kafaɗa da hura hanci. Seda ta fice sannan aka fara cece kuce, ana mayarda yadda akayi,umma se kururuwar ankashe mata ƴa take,tana jifan kande da munanan alkaba'i. Amo kakar su kande tana ɗaki tana kallo batasan ma me ake ciki agidan ba, kasancewarta bebiya ce,se akusa cinnawa gidan wuta da bala'i batasan anayiba. Kallon da takeyima in za a kasheta batasan me ake cewa ba,sede tayi ƙuru da ido tana kallon hoto tunda bajin abinda ake faɗa take ba. Wai wacece kande ne. _Ina masoyan MOMSANI ina wanda suka daɗe suna jiran wnn zazzafar tafiyar ta labarin kANDE,zaa kanwar maza,zaa soja,zaa kAND,to albishirinku yaude Allah ya nufa kuma yakawomu acikin wnn daddaɗan labarin me suna kANDE,bakijiba ne nace kANDE zaa tomboy_ _shin dake akayi daddaɗar tafiyar nan ta labarin Asma'u da Muhammad Mahii ,SAURAYIN YAYATA,kin karanta labarin SIRIKATA,ko a'a,to albishirinku yauma momsani tasake dawo muku da wani daddaɗan labarin me dogon zango wato kANDE THE TOMBOY,in Sha Allah hajiyata bazakiyi nadamar karanta wnn labarinba_ _zazzafar tafiyace me ɗauke da zazzafan darasi,tare da nishadi,haɗi da ban tausayi,tattareda zazzafar soyayya,gamida cin amana dakuma butulci,bazan cika baki ba,bakuma zan cikaku da surutu ba,amma in Sha Allah karki bari ayi wannan mysterious journey din batare dakeba_ *kANDE littafin kuɗi ne akan farashi me sauki, Naira ₦400 kacal,idan kin shirya ki tura kudinki fa wnn asusun0591819457 SADIKA IBRAHIM gt bank,seku tura shedar biya ta wnn layin 07088282153,se na jiku masoya,i promise u will never regret* Magoya ƴan amana Sena jiku,mom sani tana jiran ganin kauna daga gareku,love you all😘 Share fisabilillahi 🤲 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:02 Bismillahirrah manirrahim. Mlm Hamza shine sunan mahaifin malam habu me kayan koli mahaifin kande,yanada mata biyu Amina da Hafsatu, Amina (Amo)itace uwar gidansa ta Daɗe bata haihuba har seda mlm Hamza yakara aure ya auro ƴar uwarsa Hafsatu ta haifi yaro namiji ana cemasa Musa,ko shekara beyiba Allah ya baiwa Amina ciki, tahaifi namiji itama aka sanya masa Abubakar, shekarar sa biyar Hafsatu takara haihuwar namiji aka sanya masa Mudassir. Suna zamansu lfy daga baya Amina tafara wani irin ciwon kai da kunne harya kai tana ficewa a hayyacinta,idan ciwon ya taso seyayi kwana uku batasan inda kanta yake ba,anje asibiti sun kasa gano ainahin meyake damunta,haka aka koma na Hausa duk de bata canza zani ba,dg baya tafara wasu ƙuraje ajikinta kamar ƴan zufa, daga baya aka gane ashe baƙon dauro ne yakamata, duk da cewa bashida alaƙa da ciwon kanta,amma tunda aka gano baƙon dauro ne aka tashi tsaye da magani,daga wnn ciwon seya zamto batajin magana sosai,bakinta ma dakyar idan tayi magana ake gane abinda take faɗa,tun ana zuwa asibiti abu yaƙi sauki har daga baya idonta ma ya fara wani fari2,seya zamto bataji,bata gani,bata magana,hakan yasa tabar wasiyyar riƙon Abubakar a hannun Hafsatu,dan ta sakawa ranta ciwon bana tashi bane,iyayen Amina sunso su ɗauketa amma nlm Hamza da Hafsatu suka hana,Hafsatu na iya bakin ƙoƙarinta da Amina,mlm Hamza yana kan neman magani baya gajiya,cikin hukuncin Ubangiji aka kwatanta musu wani me maganin gargajiya hardana iska acen kura,datemakon Allah aka fara samun sauki,idonta ya washe haka tafara magana amma da ƙarfi,kunnenta yafara budewa ta yadda sekayi magana da karfi sannan zataji. Wannan shine dalilin zamowar Amina bebiya,daga baƙon dauro takoma bebiya,bayan tasamu sauki sukaci gaba da zamansu da Hafsatu lafiya har lokacin kuma Abubakar na hannun Hafsatu ta haɗa da ƴaƴanta ta rike. Kwatsam aka wayi gari Hafsatu ta rasu ba ciwo ba komi,daga baccin dare bata farka ba, Amina da mlm Hamza sunyi matukar yin baƙin cikin rashin Hafsatu daga baya suka dangana,se rikon yaran duka yakoma hannun Amina wacce suke kira da Amo. Musa, Abubakar, Mudassir sun kasance ƴan uwa masu son junansu,sunada hadin kai sosai,sam bazakace suɗin ƴan uba bane,saboda suna da haɗin kai,manoma ne kamar mahaifinsu, suna noma da kiwo sosai hakan yasa sukeda rufin asiri sosai. Sunyi karatu boko zuwa matakin secondary,daganan Abubakar yakoma cikin kasuwar ƴan kaba yana sana'ar hatsi da kayan lambu da kayan koli,Allah yasanya masa albarka aciki,Abubakar wanda akasuwa ake kiransa da mlm habu me kayan koli yanada tarin ilimin addini,ɗan izalane na gaske,hakan yasa da dare yake koyarda magidanta harma da samari agida,da karancin shekarunsa aka basa limami. Shida ƴan uwansa suka sake gyare gidansu suka mayar dashi sashe huɗu inda kowansu yayi aure,aka barwa Amo da mlm Hamza shashe ɗaya,mlm habu duk yafi ƴan uwansa hali,hakan yasa yake temaka musu sosai,duk rabin ɗawainiyar gidan shine,sbd mahaifinsu yanzu baya aikin komi, zaune yake agida sbd jikin girma,sun bude masa shagon hatsi anan cikin unguwa,baya zuwa ko ina kullum yana shago kusada gida. Matar mlm habu me suna A'isha mace ce me kirki da faram2,amma masifaffiyace sosai ta gaske inde aka shiga harkarta to ba mutunci,tanada kyauta sam bata da munafunci da shiga abinda be shafeta ba, itace ta fara haihuwa acikin gidan ta haifi namiji aka sanya masa sunan mlm Hamza,akwai kishin sauri sosai tsakaninta da matan su Hamza da Mudassir,sam basa sonta sun haɗe mata kai,kullum cikin zuga mazansu suke akan sun zauna basuda ƙwaƙƙaran aiki se noma,gashinan habu ya amshe girma da ragamar komi,sugasu su biyu shikuma shikaɗai amma yafisu arziki,akan haka Musa yataɓa sakin matarsa Zabba'u, wacce takasance sumumu kasau, batada hayaniya sam amma muguwa ce,ko alama bazata nuna fushi ko ɓacin rai afuskarta ba amma seta bada mamaki ta hanyar abinda zata aikata,batada mutunci,amma sam ba a ganewa,tunda aka mata saki ɗaya sbd iyalan mlm habu dashi kansa daga nan seta cenza takunta, ganin faɗan zahiri ba riba seta koma yi ta bayan fage. Seta zuga matar Mudassir Hadiza,dake ita Allah yamata bakin tsiya,batada kunya ko kaɗan,idan faɗa yahado ku duk abinda ya fito abakinta faɗa take yi kanta tsaye,sam bata ganin girman A'isha,ta tsani A'isha ga jan faɗan tsiya duk yadda ka kaiga hkr seta ƙureka ka tanka ta. Hakan yabaiwa Zabba'u damar aiwatar da yaƙinta ta hanyar Hadiza. Abangaren Mudassir tun baya ɗaukar zigar matarsa Hadiza hartaci galaba akansa ya fara adawa da ɗan uwansa,sam baya ganin ƙoƙarin mlm habu akansu. Gashi su har lokacin Allah be basu ƴaƴa ba,seda A'isha ta haifi maza shida ajere, sannan haihuwa ta tsaya mata,Hamza,Hamis, Ibrahim, Musa, Mudassir,dan sefa yayiwa ƴan uwansa takwara sannan Aminu,bayan Hadiza matar Mudassir tasaka an riƙe bakin mahaifar A'isha ta hanyar asiri acewarta dan ita komi nata ba sirri,idan ranta yaɓaci seta furta mugun alkaba'i tare da cewa mutum seya gani,hakance ta kasance tacewa A'isha seta gani akan sunyi faɗa ranar sunan Aminu. Alokacin ne kuma matar Musa ta haifi mace aka samata sunan Hafsatu,wata shida tsakani Hadiza ta haifi mace itama,Musa yayi2 da Mudassir yasaka sunan Amina amma ƴaki,sbd Hadiza tace muddin ya yarda aka sakawa ƴarta sunan amo to sede ya saketa kuma ba inda zata da ƴar sede ya kaiwa Amo bebiya da akayiwa takwara ta shayar da ita,shikuwa ba wacce yake ƙauna aduniya bayan Hadiza da ƴarsa,haka aka sanya wa yarinyar suna Hulera sunan uwar Hadiza kenan. Alokacin ne mlm habu yarasu yayi ciwon kwana biyu yarasu. Kwatsam Sega A'isha da ciki,hakan ya firgita Hadiza matuƙa dan tayi tunanin A'isha tagama haihuwa,a tunaninta A'isha bazata kuma haihuwa ba har ta mutu,hakan yasa ta sakankance kawai sede suka farga da tsohon ciki ajikin A'isha,haka tasake haihuwar ƴan biyu maza, alokacin ne akayi tashin hankali dan kiri kiri su Hadiza suka nuna baƙin cikinsu afili wai da gangan take haihuwar maza sbd ta cinye dukiyar gidan, alokacin ne suka raba gari tadena mu'amala dasu kwata2 bayan ta sauke musu kwandon hauka da shika-shikan rashin mutunci,dan ƴan uwanta masifaffu ne suma haka akayi baram baram,sam malam habu bayajin daɗin wnn rashin jituwar ta matansu,daga lokacin A'isha bata shiga harkar kowa acikin su,sbd akan fuskarta suka fada mata basa ƙaunarta itada mijinta da ƴaƴanta kuma in Allah ya yarda seta gani,hakan yasa ta tayarda bala'i sede mlm habu ya cenza mata gida sbd abinda facalolinta sukace, shikuma yace bame rabashi da ƴan uwansa, duk abinda yasamesa ko ƴaransa daga Allah ne bawanda ya isa ya cutar dasu se abinda Allah ya tsara masa. Dama shine yake taka mata birki take rage wani abun,amma dan ta ita kullum se anyi bala'i agidan,ƙiri ƙiri se a dokar mata yara amma mlm habu yahata magana,ranar da ƴan biyu suka rarrafa sukaje sashin mama suka zubar mata da gasara kashesu ne kawai Hadiza batayiba, dake tana sashen itama, A'isha na sallah sede ta dinga jin ihunsu ga ƙarar duka alamar dukansu ake,tana zuwa mama dake bakin ƙofar shashen tashige toilet da sauri, Hadiza ko bataga zuwan A'isha ba tayi nisa se zabga musu tsintsiyar kwakwa take a hannu,aikuwa kamar walƙiya A'isha tayi wani irin tafiyar yaji da Hadiza, duk kibarta seda A'isha ta kaita kasa tanata jibga, daƙyar aka raba wnn faɗan lokacin Hadiza tayi laushi se kuka take an fasa mata baki da hanci, se bayan anrabasu sannan mama tafito daga toilet tana sallallami, ko kallonta A'isha batayiba ta kwashi yaranta wanda suke ta ajiyar zuciya. Aikuwa aranar Hadiza bata kwana agidan ba dan wani ƙaton macijine yashige ɗakinta kan gado ya fasa kai se huci yake. Daga kan twins inna bata kuma haihuwa ba, kullum addu'ar ta Allah ya bata mace,tanason ƴa mace arayuwarta, gashi ba halin ta ɗauki yaran facalolinta yanzu se suce tanason ta kashe musu ƴaƴa. Ahaka Zabba'u takara haihuwar mace aka sanya mata siddiqa se Maryam, Hadiza kuwa bayan Hulera ta kara haihuwar Asiya, se Ikilima. Mama kuwa daga baya Allah yabata namiji,kusan tare suka kara haihuwa da A'isha wacce batasan tanada cikiba har seda yayi girma ajikinta,bata faɗawa kowa ba segashi sun haihu tare da Zabba'u wacce yaran gidan suke kira da Mama,aranar Hadiza har suma takusa yi saboda baƙin ciki. Zabba'u bata wani damuba ganin ta haifi namiji itama,amma sam aƙasan zuciyarta bataso A'isha wacce yara ke kira da inna tasake haihuwa ba,amma bakomi zasu gani,Hadiza de ita nata baƙin cikin afili yake amma bawanda yasan me mama take ciki tunda ita mijin nata yaƙi ɗaukar zuga. Kasancewar inna a asibiti ta haihu wnn karon daga ita se mijinta, dan ƴan uwanta ma seda aka sallamota sukaji haihuwar, ba wanda yasani har uwar mijinta Amo hakan yasa seda suka dawo snn ƴan gidan sukasan ma haihuwa tayi kuma mace,ƴan uwan A'isha ƴan bala'i ne basuda mutunci haka suka dinga kiɗe kiɗe suna shewa da guɗa an haifi kANDE,ranar suna yarinya taci suna Amina,anyiwa Amo takwara ba zaman lfy lols,seya kasance kamar ba suna biyu akeyi ba,ƴan uwan Aisha sun cika gida an kashe kuɗi anyi ɓarna sosai da kuɗi da abinci da nama, sam bazakace wai ana wani suna a sashen Zabba'u ba,dan da gayya ƴan uwan Aisha suke wani abun dan niyyar su ana tankasu se sun ci uwar mutum. Wannan yaƙara girmama baƙin cikin Hadiza kuma taci alwashi sosai akan seta lalata rayuwar ahalin A'isha,inda mama Zabba'u ko ajikinta tunda de ta haifi namiji to ai angama komi,yaro yaci suna Abdullahi. Tare kande da Abdullahi suka taso se suka tashi kamar twins, sam basaji ko kadan tare suke zuwa makaranta Arabic da boko kullum se ankawo kararsu ko sun daki yaran mutane ko sunyi wani abun,gasu da ƙoƙari amma sam basaji,kullum mlm habu na hanyar makarantar su,shekararsu biyar amma sam basaji,a lokacin umma takara haihuwa ta haifi Ikilima,daga lokacin se haihuwa ta tsaya musu duka matan gidan. Kande irin yaran nan ne da ake kira gifted, duk abinda aka karanta mata sau ɗaya yashige kanta kenan ba maimaici,nan take take ɗauke abu a kanta,tanada zuciya sosai batason reni,gata yarinya amma ƙoƙarin ta har tsoro yake baiwa inna da mlm, shekararta biyar amma tana iya karanta duk ayar da aka janyo acikin Kur'ani,sbd idan mlm habu na koyarwa a zaure itada Abdullahi suna gurinsa,hakan yasa duk yadda wasa ze dauke mata hankali baya hanata ɗauke abinda taji an karanta koda ba ita ake gayawa ba. Kande ta tashi cikin tsananin soyayyar uwa da uba,ga yayye maza kowa kande, sunan da kakarta tasaka mata kenan Amo,itace take kiranta da kande ko kuma tace takwara,A'isha (inna) kuma tace uwar masu gida,wnn suna yana ƙonawa umma da mama rai,gabaki ɗaya sun tsani yarinyar ganin duka ƴan gidan kowa yana son kande, hatta ƴaƴansu ba wanda ya dakko baƙin halin uwarsa. A cikin yaran Zabba'u siddiqa ita tafi kowa sanyi,yarinyar batada hayaniya sam,ga ilimin addini, baruwanta. Yaran umma kuwa kusan dukkan su basu da hayaniya bakamar itaba,Ikilima ce kawai tayo halin uwarta. Matan kusan duk sunyi aure, Hafsatu, Maryam,yaran Zabba'u duka sunyi aure, siddika ce kawai ta rage se Abdullahi autan mama. Yaran umma ma Hulera da Asiya duk sunyi aure suma. Kaf unguwar ansan gidansu kande gidane na ƴan izala masu ruko da addini,dan su Hamza daga malamin islamiyya se alaramma,se wanda ke kasuwa gurin kasuwanci,suka sunada aikin yinsu,bame zaman banza, twins kuwa suna jami'a. Ko daga waje duk wanda ze shigo gidan to ina kande shine abinda ze furta,duk ta dusashe tauraron sauran yaran gidan,tun mama na damuwa harta gaji ta saki,umma ce kullum cikin wahala, batada aiki se jifan kande da inna da mugayen alkaba'i,inde akan inna ne bata furta alheri. Haka baba Musa komi ya samu kande,ko yace wnn na uwar masu gidane, Abdullahi ko kamar bashi ta haifeshiba ganin tasa tazo ɗaya da kande hakan yasa yaron ya tattare kayansa ya koma ɗakin inna. Ankai ruwa rana sosai da mama, dan ta kafe akan ɗanta baze zauna agurin innaba, duk ƴaƴa maza da Allah yabata amma se ɗan gudalenta za a ɗauka awani baiwa inna,hakan yajanyo baba Musa yace idan takara tayarda zancen abakin aurenta,dan shi yana ƙaunar ɗan uwansa mlm habu,kuma sam baya ɗaukar wargi, hakan yasa baya iya hanasa ɗan uwansa duk abinda ya nema,duk da cewa bashi ya nuna yanason ya rike Abdullahi ba amma ganin yaron nason zama agurin inna yasa yake jin nauyin amsarsa,dan gani yake kamar idan Abdullahi yabar gurin inna mlm habu zeji ba daɗi. Mama tanaji gana gani aka rabaga da ɗanta,bata wani damu sosai ba dan tasan inna ba maƙetaciyar mutum bace,dan kular da ze samu agunta ko ita wacce ta haifeshi se haka. Kwatsam wata rana aka baiwa kande scholarship daga makarantarsu zuwa babbar makarantar nan ta m.m. Haruna English academy, alokacin shekararta goma,tagama primary zataje secondary,dan jumping aka dinga yimata, ga haddar izu talatin akanta na Kur'ani. Haka akayi ta murna agidan ana tayata farin ciki,inna kuwa har sadaka seda tayi. Yayyenta maza kuwa kowa seda yabata kyauta. Ranar ta ta farko a school....... 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:03 Bismillahirrah manirrahim. Tun ranarta ta farko a makarantar tayi kawaye yaran masu kuɗi,tasaje da yaran masu kuɗi itama saboda irin kalarsu gareta,farace sosai,tanada tsayi ba lefi,gata da hanci da manyan ido,idan tana magana bakinta kamar bashi ke motsi ba,siraran lips ne da ita,fuskarta oval shape,sumar hanta tana da tsayi sosai,ga saje daya biyo ta gaban kunnen ta,tanda 1 side dimple, kyakkawar gaske ce,yarinyace amma jikinta a murje yake sosai,fatarta tanada matuqar kyau,snn gashin ta ba baƙi bane wuluk,akwai ruwan golden brown aciki hade da baƙi suffarta daban take kamar ba ɗiyar hausawa ba. Ga ƙoƙari kamar alhuda-huda,komi aka fada mata sau daya ya zauna akanta kenan koda ba a ajinsu bane,hakan yasa satinta uku aka fara shirin yimata promotion zuwa j.s.s. 3,ranarda takoma gida tana murna tare da takaddar gayyata izuwa ha mlm habu,koda su umma sukaji labari nanfa bala'i ya tashi akan sede asaka Ikilima da saddiqa da Abdullahi a m.m. Haruna,duk da cewa siddika tana shekarar ƙarashe ne amma haka umma ta dinga bala'i,mama de uffan bata cewa,tagaji da yiwa inna hassada tunda kullum Sa'a a gefen inna da iyalanta yake. Kwatsam rana tsaka aka dawo da kande dg school tafaɗi,sunkaita clinic na makaranta an dubata har drip ansaka mata amma sam taƙi ta farfaɗo,hankali tashe inna ta shinfiɗe ta,anata shafa mata ruwa taki farfaɗo wa, Amo kuwa banda ihun kuka ba abinda take,murya a sama irinta bebaye take faɗin,duk wanda yake son ganin bayan jikarta karya bari ta ganosa dan seta yi masa rashin mutunci,haka taketa zabga bala'i tana ihu irin ta kurame. Haka mlm habu yadawo ya samu autarsa unconscious,addu'a kawai yake tofa mata,haka ya karanta wasu manyan surori aruwa yace inna ta shafe mata jiki,yin hakan ko keda wuya ta farka,kamar robot haka ta miƙe tsaye batareda jikinta ya lanƙwashe ba,a tsorace inna ta matsa tana zare ido cike da faɗuwar gaba,duk yayyenta dake ɗakin ba wanda be tsorata ba ganin yanayin da ta farka aciki. Fuskarta tayi kore sosai,jikinta ma haka,idonta yakoma ɓaki duka ko ƙwayar fari babu,cikin buɗaɗɗiyar murya kamar ta maza tace "lahuhu irmati gidigam gam,abukanwatur fadurma gim gam" kamar wata bokanya haka take furta wasu irin dalamisai,jikinta banda jijjiga ba abinda yake,bakinta har wani hayaƙi yake fitarwa, nan take dakin ya fara jijjiga kamar ze ruguje,cikin ɗaga murya mlm habu ya fara karatun suratul baƙara,yi yake da karfi, nan take su Hamza suka ɗauka,da karfi suke karatun, Amo na gefe se tsandara ihu take kamar ana yankata, ta tsula fitsari yakai sau biyar,sun rungume itada inna se kuka suke, Amo se ihu take tana gwalanci wai nan addu'a take. Ihu kande tafara yi tana jijjiga kamar ba mutum ba,cen tayi wata irin gigitacciyar ƙara wacce duk maƙotansu seda sukaji,gashi marece ne anata kiraye-kirayen sallar magrib, ihu take tana susar jikinta kafin takara yanka wani ihu me karfin da yafi na baya tazube aƙasa ta zauna kamar ƴar bori, still su mlm habu basu dena karatunba sema wasu manyan ayoyi da suke sake janyo wa,kamar a mafarki tafara rera karatun tare dasu,idan suka cenza aya itama tacenza har suka yi shiru,amma ita seda takai ƙarshen aya. Zuciyar mlm habu akarye cike da firgicin wannan sabon al'amari daya riskesu yau,amma Cikin dakiya ya buɗa muryarsa babu wasa yace "wanene kai? Me kake yi ajikin ƙanƙanuwar yarinya irin wnn? Ko ta yimaka wani laifin ne da ka zaɓi shiga cikin jikinta,kuma ga dukka alamu sun nuna cewa kai ɗin musulmi ne". Cikin wata babbar murya marar hayaniya akace "Assalamu alaika ya Imam Abubakar bin Hamza,Tabbas ni muslumi ne kamar yadda kaji,kuma sunana Muhammad Arun ɗan Sarkin aljanun baihak,ni musulmi ne,kuma ni ɗin na kasance ajikinta tun tana cikin cikin mahaifiyarta,sannan ni ne wanda nake bata kariya bisa umarnin kakana muzgar". Jikin inna da Amo banda rawa ba abinda yake,yayyenta ma dauriya kawai suke,domin abin babu daɗin gani kwata kwata halittar jikinta ya sauya kamar wani ƙaton gardi, ga wasu jijiyoyi sun ratsa mata a damtsen hannunta,gashi daga ita se vest da leggins. Jinjina kai Malam habu ya yi yace "tabbas nagani kuma naji kai ɗin musulmi ne,amma shin me wannan yarinya ta aika maka,ko ta cutar da kai ne dayasa ka bayyana akanta ko kuwa?". "Babu ɗaya daga cikin biyun tambayoyin ka,wato zancen gsky naso nayi zamana shiru batareda na nuna wata alamar cewa ina tare da itaba,amma hakan baze taɓa yiyuwa ba,anyiwa goɗiya wani mummunar sihiri wanda akaso bayan tagama wulaqanta tayi mummunar mutuwa. An sadaukar da jini ga baƙaƙen aljanu an tura su jikinta da mummunar niyya,kuwa hakan yakusa yin tasiri sakamakon bama tare da ita a lokacin ,munyi wata doguwar tafiya zuwa ƙasar misra domin gabatar da wani yaƙi acen tsibirin asgarul mundal, sannan mun nasaka fararen rauhanai a domin bata kariya da kuma gadinta kafin mu dawo,amma se akayi rashin Sa'a baƙaƙen aljanun da aka turawa goɗiya sunfi ƙarfinsu,hakan yasa sukayi nasara akansu har suka raunatasu,duk da cewa mun bar wani kariya ajikinta hakan yasa sukayi kwanaki bakwai suna fama kafin su sami nasarar shiga jikinta ta hanyar wacce tayi mata turensu,tabata ɗan wake taci,acikin ɗanwaken akwai wani magani wanda ya karya garkuwar da muka bari atareda ita,a jiya ne muka sami nasara akan baƙaƙen aljanun da suka addabi tsibirin da mukaje yaƙi,cike da azama muka dawo gareta kwatsam se mukayi arba da shugaban baƙaƙen aljanun da muka nema muka rasa a fagen yaƙi, yana shirin ɗaukar rayuwar goɗiyarmu,wanda da hakan ta kasance to tabbas da sede mu mutu atare da ita, domin rayuwar mu gaba ɗaya sadaukarwa ce ga ahalin goɗiya. Kakan goɗiya ya taba temakon kakana alokacin da yayi ɓadda kama amatsayin ɗan Adam kuma almajiri, lokacin kakana ba musulmi bane,amma karamcin da kakanta yayi masa yataɓa zuciyarsa,har ya amshi musulunci,a dalilin haka yasa yake bibiyar ahalinsu. kakanta ya temaki kakanmu, yana saurayi a lokacin batareda ma yasan cewa aljani yatemaka wa ba,a hannun kakanta Abu Rayyan kakana ya amshi musulunci,hakan yasa kakana ya tara iyayenmu yabasu labari kuma ya umurce su da amsar musulunci tare da faɗa musu lalle su kasance masu baiwa ahalin Abu Rayyan kariya har ƙarshen rayuwarsu. Mun kasance tare da mahaifin goɗiya kafin faruwar wani babban al'amari, daga baya kuma muka koma gareta tun acikin cikin mahaifiyarta,. Tabbas makashinku na tare daku, tabbas anaso a salwantar da rayuwar goɗiyarmu hakan yasa muka riƙe baƙin aljani Gandamul arzu bawai dan bazamu iya galaba akansa ba, a'a sedan munaso ya bayyana ajikinta akan idon ku,yaso tserewa tun da sa'ar da mukayi arba da juna aɗazu,amma na riƙesa sakamakon munaso kufara hukunta sa da kanku da ayoyin Allah,ya yi iya yinsa dan ganin be iso nan ba,sbd yasan karonsa da mlm ba zeyi masa kyau ba amma sam bamu basa damar yin hakan ba. Niyyarsa ya aiwatar da abinda aka aikosa yakama gabansa batareda ya iso gidan nan ba amma bamu basa damar guduwa ba. Shine wanda ya fara bayyana ajikinta sakamakon ruwan addu'a da aka shafa mata, seda muka tabbatar kun ƙonasa da ayoyin Allah ta yadda baze ƙara moruwa ba kafin muka barsa ya fita,fita ta har abada bakuma ze ƙara gigin shafarta ba". Se yanzu ta sauke numfashi idanunta arufe,cikin sanyin jiki malam yace in Sha Allah babu abinda wani mahaluki ya isa ya yi agaremu face abinda Allah ya tsara mana. Tabbas munji daɗi kuma muna gdy bisa kariyar da ka kasance kana baiwa ƴarmu,amma kasani mudin bil adama ne babu wani haɗi tsakanin mu daku, muna godiya matuqa amma dole zaka bar jikin wnn yarinya,idan kayi duba da ƙarancin shekarunta sbd haka ina gamaka da Allah akan kayi haƙuri ka barta". Ido rufe kuma cikin wata murya wacce ta fi ta farko ƙarfi da firgitarwa tace "wannan ne kuma bazamu iya yi muku alqawarin aikatawa ba,zamu tafi yanzu,bazamu kuma bayyana ba,kuma zamu ɗauki mataki dede gwargwadon abinda aka aikata wa goɗiyar mu,sannan zamu aikata wani al'amari atareda goɗiya wanda muka tabbatar shine kariya agareta kuma zaman lafiyar kowa aciki harda ku,duk abinda zata aikata kar wanda ya ƙalubalanceta akai,tabbas komi yanada lokacinsa, kuma idan lokacin da muka dibarwa hukuncin da zamu yanke ya kai to tabbas komi ze bayyana. Mlm Abubakar bin Hamza tabbas kaiɗin mutumin kirki ne,ka kasance me aikata alheri akoda yaushe,kuma me saka sharri da alheri,saboda haka karka ce zaka ɗauki wani mataki akan hukuncin mu,zamu tafiiii amma kusani muna tare da goɗiya akoda yaushe,domin nauyin kare ta yana rataye a wuyan ahalinmu,wannan alƙawarine. NATAFIIIIIIII...., KUMA ZAN DAWOOO...." Wata babbar hamma kande tayi kafin ta tafi yaraf ta kwanta kamar ta mutu, wani nannauyan bacci ne ya yi awon gaba da ita. A lokacin sallar isha'i ake kira,jikin malam habu amatuqar sanyaye yatashi tasake tofe kande ta addu'o'i,wacce banda gumi ba abinda take,dukama wanda yake ɗakin ya haɗa uwar zufa. Se a sannan inna da Amo wanda idonsu yajiƙe sharkaf da hawaye ya kumbura suka saki junansu,kaka Amo kamar abin tsafi duk abinda ya wakana taji raɗau kamar ba bebiya ba. Zuciyoyin duka wanda suke cikin ɗakin ɗauke da tambayoyi masu yawa amma kowa ya bari har lokacin daya dace kafin ya furta. Haka mazan suka fito daga ɗakin jiki a sanyaye,akan idon mlm habu yaga gittawar mutum da gudu ya yi hanyar waje. Girgiza Kai kawai mlm habu ya yi dan sarai ya gane ko wanene,kawai shiri ya yi,kuma yasawa ransa koma menene da yaddar Allah baza ayi nasara akansu ba. Haka kande ta share kwana biyu batasan inda kanta yake ba,kullum se malam yamata tofi aruwa ashafe mata jiki. Yau kamar a mafarki inna tana sallar azahar taga wani abu kamar inuwar mutum ya tsaya adede kan kande. 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:04 Bismillahirrah manirrahim. Kafin inna ta karasa setaga kamar wannan inuwar ta faɗa ajikin kanden. Saurin miƙewa tayi bakinta ɗauke da addu'o'i ta nufo inda kanden take akwance,tana zuwa dede lokacin kande ta buɗe idonta wanda sukayi jajir jini ya kwanta acikinsu kamar an zuba mata,baka ganin farin cikin idon ko kaɗan,tana gani tar amma idon yayi mata nauyi. "Alhamdulillah" shine abinda inna ta furta tana kama hannun kanden datake miƙa mata. Jikinta yayi mata nauyi sosai bata iya motsa ko ɗan yatsan ta,kuka inna keyi ƙasa ƙasa,ta janyo wayarta keypad tana dannanwa mlm habu kira, alokacin shi kuma ya shigo cikin gidan hannunsa ɗauke da wata gora ta ruwan addu'a, Kasancewar an idar da sallar ya sallami ɗalibansa masu ɗaukar karatu,tare suka shigo da twins wanda suka dawo sbd ciwon kanden. Dasauri mlm habu yakarasa shiga ɗakin yana tofa mata addu'o'i,ahankali yace "mamana", bakinta yamata nauyi sosai amma ta ɗaga idon ta wanda yake nan gwanin tsoro sbd yadda ya koma ta kallesa,hakan yabashi tabbacin ta dawo cikin hankalinta, Sake tausasa murya ya yi bayan ya janyota daga kwance ya mayar jikinsa ta jingine dashi ya sake cewa "kingane wacece wnn?" Yafada yana nuna inna dake durƙushe kusada gadon tana hawaye,ganin yadda fuskar ƴar ta ta ya kumbura sosai bakinta abushe idonta babu daɗin kallo. Jinjina kai tayi a hankali alamar ta ganeta, "waɗannan fa?" Ya nuna su twins wanda suma hawayen suke,dan akwai shaƙuwa me tsanani tsakaninta dasu kamar ba saƙonnin ta ba,duk ma yayyen ta maza suna matuƙar ƙaunarta,sake jinjina kai taji a hankali,amma ba magana. Hamdala mlm da inna sukayi,gorar ruwan addu'a mlm ya ɗakko ya yi bismillah ya kafa mata gorar abaki,ba musu ta amsa ta fara sha da sauri, sefa tayi rabi kafin ya cire mata ta huta,sannan ya sake miko mata ta amsa seda ta shanye tas,kaɗan ta bari ya zubaa hannu ya shafa mata afuska sannan ya ajiye gorar. Lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta fara yinƙurin amai,da sauri inna ta miƙo mata wani ƙaramin baho aikuwa tafara sheqa wani irin amai baƙiƙirin dashi,harda wasu abubuwa kamar kwalba, aman babu kyan gani,ga wasu abubuwa kamar tsutsa se motsi suke,seda takusa yin rabin bahon kafin aman ya tsaya mata,takoma jikin mlm tana sauke wani wahalallen numfashi,ba jimawa wani baccin ya sake kwasheta. Shimfiɗeta mlm yayi yasake tofeta da addu'a kafin suka sake fita. Seda takai la'asar tana bacci kafin ta farka,cikin ikon Allah koda ta farka idonta ya fara washewa kuma harta iya tashi da kanta ta zauna, Amo na gefe se zare ido take,dazarar taga kande zata kallo ta setayi maza ta ƙara damƙe carbin ta,murya asama take istigfari,dan wlh tsoron bala'i kanden ke bata,ganin take har yanzu al janun na nan basu tafi ba. Inna ce tashigo ta kamata suka shiga toilet takai mata ruwan zafi wanda mlm ya yi mata tofi aciki,inna tayi mata wanka dan har lokacin jikinta babu ƙarfi. Tea me kauri inna ta haɗa mata da ruwan addu'a wanda mlm ya yi mata shi dayawa komi nata inde naci ne ko nasha to da wnn ruwan za'ayi mata amfani,har wanka. Duk wannan abin da ake yi umma bata leƙo sashen ba ko sau ɗaya,mama de ta shigo sau ɗaya ta tsaya daga bakin ƙofa tace Allah y kafa afuwa tayi gaba,ko takalma bata cireba balle tashi ɗakin. Duk da inna taji zafin abinda suka mata amma taji daɗin yadda mama tazo ta duba jikin ƴarta,koba komi de tazo,tafi umma wacce ko bakin ƙofar sashen bata leƙo ba. Seda kande ta shafe sati ɗaya kafin ta fara magana, maganar ma me ban mamaki dan kamar wata namiji haka take magana tana wani karkace baki gefe,da farko abin dariya ya baiwa inna hartana cewa "haba uwar masu gida,daga buɗe baki kuma se shegan taka,meye haka kamar namiji?" Tafaɗa tana murmushi. Cikin cijewa kande tace "yo inna da mecece ni ɗin,ai ni namijice kawai totally,kallifa duka yayyena maza ne" tafaɗa tana nuna su Hamza da su Hamis da twins dasuka kalli juna., saboda haka nima namiji ne kuma soja zan zama in Sha Allah. Ya Musa yace "haba auta ke mace ce,kuma kyakkawar yarinya,ƴar autar inna da malam,jikar Amo kallifa ji sumarki me kyau da ita ga tsayi". Kallonsa tayi tace "Allah ko ya Musa,wannan gashin shiya sake saka wa nake kama da mata ko? To yau base gobe ba zan askesa,Sena je an aske mini shi". Kamar wasa tafara acting kamar namiji,duk kayan da inna ta ɗakko mata ta sanya setace sam bata sonshi, ita sede anemo mata riga da wando su zata saka. Tun Inna na kallon abun a matsayin wasa har tafara jin haushi,cikin fusata tace "zanci ubanki fa,ki tashi ki saka kayanki,tun ɗazu kin sauna da ɗaurin zani,karki bari raina ya ɓaci", se mafifa inna take. Nan take idon kande ya cenza tayi tsaye ƙiƙam taki motsi ta sunkuyar da kanta gashinta ya zubo ya rufe mata fuska,inna tayi magana har ta gaji amma shiru babu amsa,ganin hakan yasa ta sakko ta fara lallashi da ban baki,amma shiru kamar tanayi da dutse. Matsowa inna tayi ta dafa kande tana yimata waƙa kamar yadda take mata idan tayi fushi, amma ko alamar zata motsa babu,janyota inna tayi da niyyar rungumeta amma taƙi janyu wa,sema ji tayi kamar ba mutum take jaba, kamar gini haka ta maƙale agurin, cikin tsoro inna ta saketa taja da baya,aguje ta ruga zuwa zauren gidan tana ƙwalawa mlm kira, jikinta banda rawa ba abinda yake. Arikice ta fada zauren inda mlm ke tsakiyar karatu da ɗalibansa,da sauri ya tashi yana tarota,cikin sauri kuma ya janye ta sukayi cikin gidan yana tambayar ta meya sameta harya firgita ta haka,inna banda rawa ba abinda jikinta yake se nuna masa hanyar ɗakinta take,ta kasa magana hawaye se zuriya yake akan fuskarta. Hanyar ɗakin ya nufa da ita,amma ta cije a waje taki shiga,baiwar Allah Inna banda rawa ba abinda jikinta yake. Sakinta mlm ya yi yashiga ɗakin yaga kande a halin da take,bakinsa ɗauke da addu'a yake nufarta,haka mlm ya shafe tsawon lokaci aɗakin kafin ya fito yana sharce gumi. Yana fitowa Sega kande abayansa tana faɗin "inna yunwa nake ji wallahi,dan Allah kiyi mana ɗan wake", jikin inna be dena rawa ba ta kalli malam,jinjina mata kai ya yi alamar bamatsala. Cikin ɗari2 inna tace "to auta in Sha Allah,zoki amso mana fulawar", inna ta fada tana miƙo mata naira dubun da mlm ya bayar,cikin murna ta yi hanyar waje daga ita se ɗaurin zani a ƙirji ko ɗan kwali babu akanta,ga dogon two color hair dinta dakenan har kusada mazaunanta yanata tashi iska na kaɗa mata shi,kamar ba ƴar hausawa ba,da sauri mlm yace "a'a uwata kawo na bayar a amso muku", haka tundaga wannan ranar kande ta koma me siffar maza. Bawai jikinta bane ya koma siffar mazan, a'a,tana nan a yadda take,kawai de gabaki ɗaya yadda take gudanar da al'amaran rayuwarta ne ya koma na maza,inna batasan ya akayi ba se ganin kan kande tayi an aske mata rabin sumarta, normally sumarta ta kai har ɗuwawu amma kawai se wayar gari akayi an yanke Mata fiye da rabi yakoma kamar na namijin ba indiye. Shigarta da komi nata sak namiji, school ma ta dena zuwa,ɗan karatun ta da ake taƙama dashi aka nemeshi aka rasa,bayan fatiha babu abinda kande ke karanta wa daidai,a fannin boko kuwa ɗum,kai ya koma kamar na kifi bata gane komi,tunrancin da yazamewa bakinta kamar yaren ta na usuli shima aka nemesa aka rasa,komi nata kamar an juya mata shi,tamkar yadda ake juya riga daga Dede takoma baibai. Ada ta kasance me yawan son turanci,har bayan samun matsalar ma bata dena son yin turanci ba,amma fa kafurin broken english take kwaɓawa,baƙaramin ciwa turanci zarafi take ba,idan ta kwaɓa wani turancin se dariya ta kusa kashe mutum,amma ita ko ajikinta,ta fuske,ita adole turancin gaske take. Ga baki daya rayuwarta tayi juyin waina acikin tanda,yayyenta maza abun ya yi musu ciwo sosai,gashi sun kasa samun wata gamsashshiyar amsa daga iyayen nasu,sude sun san tun sa'adda tasamu matsalar jinnu din nan bata kuma samun kanta ba,kullum da abinda zata fitar sabo arayuwarta. Tun ranarda sukayi ƙungiya sukayiwa inna ƴar tsure tare da jefa mata wata nannauyar tmby wanda yakusa zautar da jin ta,har girgizar da tayi sanadiyar tambayar su ya bayyana afili,nan take ta fatattakesu sbd rashin gamsashshiyar amsar da zata baiwa ƴaƴan nata. Hakan yasa suka juya tmbyr izuwa kan mlm,tabbas shima ba ƙaramin jijjigashi tambayar tayi ba,amma dayake namijin gaske ne shi be nuna ya firgita da tmbyr ba. Cikin dakiya mlm yace "Hamza me kace?,me kuke son sani gameda lalurar ƴar uwarku ne?bayan komi akan idon ku ya faru,kuma duk abinda aljanin yafada kunji da kunnenku". Maimaita tambayar Hamis ya yi cikin kwantar da murya yace "am mlm dama cewa mukayi,menene gaskiya akan abinda muka ji aljanin kan auta ya faɗi?shin wanene Abu Rayyan,menene dalilin da ya sanya gabaki ɗaya rayuwar auta ya cenza,kuma munga baka ɗauki kowanne mataki ba,kamar ma abinda take yi yanzu baya damunka,gashi mutanen unguwa harsun fara gutsira zantuttuka akan sabon tsarin rayuwar da ta ɗakko a yanzu,sam sekace ba ƴarka ba,komi nata ya sauya,mlm dubi yadda takoma sak namiji,kuma ma dakanka ne kabata kuɗi tasai irin tufafin da maza suke sakawa,wanda kaine ka koyar damu cewa duk namijin da yake kamanceceniya da mata to yanada babban zunubi agurin Allah (s.w.a),haka ma ga macen ta take kamanceceniya da maza,harfa yanke gashin kanta tayi,wanda yin hakan a addini shima haram ne,gashi yanzu bata tsoron kowa,shekaran jiya nan naga ta kama Ikilima tamata shegen duka seda ta yimata targaɗe a hannu,mlm dan Allah kafaɗa mana menene asalin abinda yake faruwa wanda mu bamu sanshi ba,kuma wanene ABU RAYYAN* a iya sanin mu kune iyayenmu,kuma aduk cikin kakanni mu bamusan wani me suna abu Rayyan ba,mlm kai masani ne wanda Allah yabashi baiwar ilimummuka me tarin yawa,kuma abinda take yi Sam ko a addini be dace ba,idan ma sbd aljanun kanta ne ai Allah ya baka sani ta yadda zaka magance komi batareda an bar wani aljani ya sauya mata rayuwarta hakaba,ka gafarcemi mlm idan na faɗi abinda ya sosa maka rai,bada nufi bane ". Dogon numfashi mlm yaja kafin yace "duk naji abubuwan da ka faɗa kuma tabbas maganganun ka gaskiya ne,amma abunda nakeson ka sani,duk wata cuta Allah be halicce ta ba har seda ya fara saukar da maganinta, sannan idan ka lura gaba ɗaya rayuwar auta maƙiya ne a kewaye da ita wanda nasani kuma kun sani,tun kafin bayyanar wannan aljanin atare da ita ansha neman nakasta rayuwarta wanda ku ƙila a yau kuka san wannan,akwai aljanun da zaman su atareda mu bil adama babu alheri wanda hakan kesa muke yin duk yadda zamuyi araba wanda suka shafa dasu,akwai kuma nau'in aljanun da zaman su atareda mu wata kariya ce daga Ubangiji* Tabbas rayuwar auta ta sauya kuma babu wani wanda hakan kewa daɗi daga Ni har mahaifiyarku,kuma duk yadda zakuji ciwon sauyawarta baku kai mu ba tunda mune muka kawota duniya,kuyi hakuri kubata lokaci,idan kun lura harda kuruciya a lamarin uwata,in Sha Allah komi ze dedeta da izinin Allah* Ni nasan abunda baku saniba,wanda in Sha Allah idan lokacin kusani ya yi tabbas ba makawa se kun sanshi,rayuwar auta akwai wasu manyan sirrika wanda lokaci ze bayyana su,kuyi hakuri ku bata lokaci,kuma ina roƙon ku kar wanda ya hanata abinda take ko ta nema,inde befi ƙarfin ku ba ina neman alfarma abata,sannan Abu Rayyan bakowa bane kawai zancen aljanin ne,nagama magana kutashi kuje Allah ya yi muku albarka". Sam mlm be basu damar yin wata magana ba,kuma tabbas sunajin cewa akwai abinda mlm be faɗa musu ba,amma kamar yadda yace komi lokacine suna fatar lokacin nan ba anesa yake ba,dan duk wanda yasan auta ada yarinya me hankali ga ƙoƙari ga son karatu,to ba ze yadda itace ta koma yadda take a yanzu ba,yarinya ƙarama me shekaru goma zuwa sha ɗaya,sam kamanninta ya sauya,babu wata cikakkiyar nutsuwa atare da ita,ga rashin kunya,duk wani ilimi da take dashi yanzu babu ya gudu,takoma kamar jaka, bata da mutunci sam,ga ƙarfi kamar ba mutum ba,ba wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa ko ya ɗagawa innarta,duk mutanen gidan yanzu shakkar ta ake, ƙaramar yarinya amma ta addabi kowa,musamman umma da ƴarta Ikilima wanda suke nuna sam basuda alaƙa da ita,mama de dama ba shiga shirgin kande take ba,tun bayan da ɗanta Abdullahi yakoma sashen ta shikenan burinta ya cika,dama ba dan Allah ya barshi a gurin inna ba, barazanar da mlm Musa mijinta yamata ne yasanya ta kyaleshi acen,amma yanzu tunda ya dawo gurinta ba abinda ya shalleta dasu. Abdullahi ya gudu shashen uwarsa mama ne tun ranar da kande ta tayarda aljanu, yaji tsoro sosai ya kwashi kayansa yakoma sashen uwarsa wanda har yau wata na biyu da faruwar abin be dawo ba,tun Inna na magana da mlm har suka hakura,mlm Musa ma be ce ya koma ba hakan ya yi wa Mama daɗi kuwa, ɗan ta ya dawo gare ta. Tun daga lokacin kuma Abdullahi ya fita harkar kande ya dena kulata,itama bata damu ba ta fita iskar sa. Dama acikin unguwar mace ɗaya ce ƙawarta layuza maƙota ne dasu inna,layuza tanada haƙuri sosai bata cika yin fushi ba,duk masifa da bala'in kande tana shanye wa, Allah ya ɗora mata ƙaunar kande,hakan yasa suke ƙawance,. Tunda ɗabi'un kande suka sauya iyayen layuza suka hanata hulɗa da kande anna ta kafe ta ƙiji,kusan kullum tana hanyar zuwa gidansu kande,. Layuza tana tallar dafaffen dankali, kasancewar basu kai su kande hali ba,hakan ke burge kande sosai,ita tallah mugun birgeta yake,a ƙa'idar gidansu mlm habu yaro baya tallah,saboda sunada rufin asirin su,amma rana tsaka kande ta tayarda bala'i ita tallah zata fara,tun mlm da inna suna ganin abu wasa har ta fara kuka tana tirje tirje ita se an yimata sana'a ta fita tallah. Haka mlm badan yaso ba ya goya mata baya,seda ta zaɓi abinda zata dinga tallar ma,awara ita kadai take so,haka mlm yabata kuɗi taje tasiyo rabin mudu,inna tayi mata awara,ranar da ta fara ɗauka taci wankanta jikinta sanye da wasu riga da wando ƴan dai dai na maza tasha cover shoe dinta babban size wanda yafi ƙarfin ƙafarta,ta ɗauki bokitin ta fito tana ƙwambo tana buɗa kafaɗa dede umma na baiwa Ikilima sako a ƙofar shashensu da alama aikene ake bata,wata irin dariya suka kece da ita kamar zararru,yi suke sosai suna nuna kande wacce ta tsaya sororo tana kallonsu fuskarta a murtuƙe,dake sashen umma dana inna suna kallon juna,sashen mama ne ke cen kusada na Amo suma suna kallon juna. Cikin hura hanci kande ta dubesu tace "da uwar uban wa kuke ne?" Dariyace ta sake kama su ganin yadda ta karkace baki kamar wata ƴar daba,umma wnn sauyi na kande ba ƙaramin daɗi yake mata ba,tana rokon Allah ya dawwamar da ita haka har ƙarshen rayuwarta,ko dama yadda ake ji da kande agidan ba ƙaramin ci mata tuwo a kwarya yake ba,kowa agidan idan ka cire umma da mama son kande yake,har ƴaƴansu mata da sukayi aure sunason kande, har mijin umma Mudassir idan ana zancen Ikilima batada ƙoƙari a makaranta seyace tadinga zuwa gurin kande tana koya mata,hakan na baiwa umma haushi,amma yanzu a kalli kanden ita kanta batasan komi ba balle ta koyawa wani. Cikin fusata ta ajiye awararta agefe ta fisgo Ikilima ta buga kanta da ƙofar shiga sashen nasu,ihu umma ta ƙwallah ganin take kan Ikilima ya fashe jini ya fara fita,juyowa kan umma tayi bayan ta sake Ikilima ta faɗi kasa dafe da kanta tana ihun itama,ai umma na ganin yadda idon kande ya juye tana mata wani kallo kamar zaki yaga nama ai aguje ta koma cikin shashen nata ta afka ɗaki ta rufo ƙofar se zagi take aunawa kande amma ta rufe kofar. Daukar bokitin awarar ta tayi takara gaba,awaje ta haɗu da layuza ɗauke da tiren dankalinta, murmushi tasakarwa kande cikin murna ta matso tana faɗin "laa ashe dagaske kike,kai aikuwa ji yadda awarar tayi kyau dagani zatayi daɗi" fuska amurtuke kande tayi gaba se banka sauri take,ko saurarar layuza batayi,itako baiwar Allah se sauri take tanaso ta cimma kande amma takasa. Haka sukaje gurin da layuza take zama da tallar ta bakin wata secondary school suka zauna,adede lokacin ne aka tayar dasu break,haka ɗalibai suka fito kamar kiranye sukayo kan bokitin awarar kande suka yanyane kowa nason ya siya,duk da kuwa ba ita kaɗai bace me awarar. Seda tagama shan kanshinta sannan ta taso tabuɗe bokitin awarar ta ta tafara basu suna bata kuɗi,tun daga ranar aka dena siyan awarar kowa seta ta,seta siyar sannan seta koma kan tiren dankalin layuza ta zauna,nan ma a yanyame ayita siya,tas suke siyarda komi,har inna ta kara hannun yimata awarar. Daga gurin tallar yau gungun wasu yara maza wanda suma tallar suke kaiwa amma ba'a taba kallonsu har se idan ta kande ta ƙare,kullum abun na basu haushi,yau suka haɗa plan akan su tare su kande su musu shegen duka ta yadda gobe bazasu kara kai tallah gurin ba. Tofa suwaye waɗannan masu rabon shan wahalar??? Muhadu a next pg. 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:05 Bismillahirrah manirrahim. Sun ɗanyi nisa da tafiya kawai Sega matasan yara maza kusan su biyar,ko wanne da ƙatuwar bulalar darbejiya a hannunsa,sun tari gabansu kande gadan gadan,aƙalla yaran zasuyi shekaru sha biyar biyar,ba wata wata wanda yafi Kowane tsayi acikin su ya laftawa layuza bulalar hannun sa,yana zare mata ido. Hannu yasa ya ture kande wacce ke tsaye ƙiƙam tana masa wani kallo,sauran yaran mutum biyu suke rirriƙe mata hannuwa suna faɗin ita hukunci ta na daban ne,su zata nunawa shigar maza to sune maza na ainahi, sbd duk da shigar maza da kande keyi hakan be hana agane cewa ita mace bace da kallon farko. Dauda shine sunan yaron daya fara dukan layuza kuma ya ture kande,wanda suka riƙeta kuma da zakariyya,da Buhari,gefe kuma wani yaro ne kamar wawa hancinsa duk majina,ya sake baki,cikin sakalta se kallonsu yake, ɗauke da tiren dafaffiyar gyaɗarsa,ko inda ake rigimar be matso ba yana gefe yana kallo sake da baki. Dauda ya ɗaga bulalarsa ze sake dukan layuza wacce harta fara kuka, kamar wata jarumin namiji haka ta fizge hannuwanta da suka rirriƙe,kamar kaji haka suka biyo hannun kamar an januosu suka haɗe,gib goshinsu ya daki na juna,ihu sukayi suna faduwa ƙasa kowa ba laluba kansa dan sun bugu sosai. Juyowa Dauda ya yi aiko sejin saukar bulala ya yi ajikinsa, dukansa kande take kamar Allah ya aikota, sekace uwarsa gashi ya fita tsayi ta haɗa da su zakariyya da Buhari se jibga take,tuni sukayi buɗu2 da jikinsu agurin, se susar jiki suke suna kuka,seda tayi musu duka sosai kafin ta yarda bulalar wacce duk ta karye ajikinsu. Bello ko harararsa batayiba amma yamaƙale ajikin bishiya yanata rusa kuka,fuskarsa tayi dameji da hawaye, ga majina yarara tanabin hancinsa har zuwa cikin bakinsa,se kuka yake jikinsa na makyarkyata. Juyowa kande tayi ta kallesa ai tuni ya ƙara ɓare baki Yana kuka,fadi yake tayi hakuri karta dakesa, dan Allah karta dakesa,wata irin dariya ta kwashe da ita tana kallonsa tace "kai sagalo na dakeka ne kake wannan kukan?" Saurin girgiza Kai yayi kamar ze tsinke wuyansa yace "a'a baki dake niba,amma kar ki dakeni dan innarki fa baffanki yuuu wayyo Allah na" dariya take sosai ganin yadda yake kuka sosai yana suɗe majinarsa,sak dolo. Daka masa tsawa tayi tace "ya suna ka?" Seda ya shanye majinarsa yace "Bello",zuwa tayi inda yake tariƙe kunnensa tace "daga yau sunanka Bello sagalo kaji" tafaɗa tana zare masa manyan fararen idonta, dasauri ya jijjiga kai yace "eh naji na yadda dan Allah karki dakeni". Juyowa tayi kansu Dauda daketa kuka tace "duk kufaɗa min sunanku", da sauri zakariyya yace "sunana Zakaria" , "nikuma sunana Buhari",nide sunana Dauda " Seda ta sake dingure masa kai tace "daga yau sunanka Dauda duna, kaikuma zakariyya zakarius,kai kuma Buhari boris,kunajina ko" tazare musu ido. Kamar puppet nata haka suka dinga gyaɗa kai,tace "oya zaa goo,maza2 kutashi kubar nan arnaye kawai"tafaɗa tana cije baki. Aguje suka bar gurin tare da kayan tallar su, Bello wanda tasaka wa sagalo kuwa ko tiren dafaffiyar gyaɗarsa be dauka ba ya ruga aguje. Allah ya yiwa kande wani irin kwarjini,ko babban mutum baze iya kallon ƙwayar idonta kai tsaye ba balle yara ƴan uwanta. Dariya take itada layuza sunata nishadi suna mayar da yadda abin ya kasance har suka kai ƙofar gidansu kande,dake gidansu ne farkon isa,ta shige layuza tayi gaba tana murna ta siyarda dankalinta,ga yadda kande ta tare musu faɗa. Wasa2 seda aka jera kwana biyar inde kande taje gurin tallah tofa su zakariyya zakarius sede suyi cimbi,bame kallon sashe da suke balle asiya, sede sunaji suna gani kande tasiyar da tallarta,takoma kan tallar kowa na gurin seta siyar masa bandasu, nan da nan tayi suna agurin kande me Sa'a,kowa kande ɗalibai kande masu tallah kande,malaman makarantar ma harsun san labarin kANDE me Sa'a. Ana haka yauma kamar kullum sun biyo hanya kawai Sega su zakarius da uban tallarsu akai,Dauda awara yake da yaji, zakarius kuma shinkafa da mai Buhari kuma doya da ƙuli me mai da albasa, Bello sagalo kuma dafaffiyar gyaɗa. Ja tayi tana kallonsu da niyyar duk wanda ya matso inda take seta zubar masa haƙura. Amma kawai seganin tayi sun zube aƙasa suna bata haƙuri,dan Allah tayi hakuri tayafe musu ta temaka ta cire ƙofin da tayi musu aka dena siyan Kayan sana'ar su,kuka suke wiwi suna roƙonta,nan danan zuciyarta ta karye tauasayinsu ya kamata,mace koya takaiga taurin zuciya mace ce kuma me rauni,balle yarinya kamar kande. Amma ta dake tace "dalla arnaye ku tashi kun wani riƙen kafa,oya ku ajiye kayan tallar acen", ta nuna musu gaban itacen durumi kusada wani masallaci, dassauri suka kai kayan sana'ar suka ajiye,ana idar da sallar azahar kamar anyiwa mutane kiranye suka fara tsaya wa suna siyan abinda su Dauda duna suka ajiye,kan awa daya ansiyarda kaf abincin da suka ajiye,aikuwa banda ihu ba abinda suke,suna kiran se kande me Sa'a,bata rai tayi tace ita sede su dinga ce mata zaa kand ko kuma zaa soja da turancin literature kenan.,aikuwa suka dinga fasa mata kai suna kambabata se wani hura hanci take ita adole boss. Tundaga wannan ranar tare suke tafiya tallar su,duk shiriritar kande basa tafiya se tazo,sedaga baya suka san ashe duk a unguwa ɗaya suke,kawai layine kowa da nasu,kullum seta siyar da awararta sannan take siyar musu da tasu,agidan iyayen kowannen su an san labarin zaa kAND zaa SOJA zaa ƙanwar maza me Sa'a. Daga baya sauransu suka dena tallar kowa ya koma makaranta,dama ana cikin hutun yajin aikine a makarantun gwaunati,a lokacin kuma aka ɗauki Bello sagalo jikan me unguwa,aka kaishi cen garin bauci gurin ƴan uwan babansa almajiranci. Kande kuma atafau taki komawa school,har school authority dinsu sunzo dubata,Kuma sun aiko da letter akan ana buƙatar ta a school dan zasuje wani debate na state kuma sunada cikakken yaƙini da hope me yawa akan kande cewa idan akaje debate din nan da ita to ba makawa zasu lashe,sbd turancinta ma is totally different,kamar ba a Nigeria take karatuba. Amma wat shock dem the most shine zuwan wasu malaman makarantar da aka wakilta domin zuwa duba kanden shine ganin yadda takoma, sam dafarko basu yadda cewa itace takoma total tomboy ba,abin ya basu tsoro matuƙa,sannan yadda sukaga tayi biris dasu kamar batasan inda suka fitoba ya ƙara basu mamaki,dan se wani cijewa take tana shamusu ƙamshi,ga wani kafurin turanci da take suburbuɗo wa kamar bata taɓa sanin hanyar ajin school ba. Wani ƙarin abin mamakin ma seda sukaga Ikilima ta shigo tanata rusa kuka,fuskarta kamar tumatir sbd jaa dan itama farace,kuka take tana faɗuwa tana tashi,yauma de tsautsayi yasake haɗata fada da kande. A hanya taga kande da bokitin awarar ta ta dawo tallah,se tafiya take tana buɗa kafaɗa tana shan ƙamshi sak de irin yara marasa ji din nan, buɗar bakin Ikilima se cewa tayi,"a'a ƴar daudu an dawo daga aikin banzan? Allah yasa ba ƙwaƙwuleki akeyi agun tallar ba yasa kika nace kullum se kinje,duk gidanmu bame tallah seke,mtwss aikin banza", tafaɗa tana yin gaba kamar wata babbar mace,Ikilima a lokacin bata wuce shekara 7 ba,amma sbd tsabar rashin kunya da manyance idan tayi magana seta baka tsoro,kuma hakan ya samo asali ne daga yadda umma take,duk nauyin zance bata jin kunyar fadarsa agaban Ikilima,kuma abakin ta Ikilima taji cewa wai kande ƙwaƙwuleta ake agurin tallah. Cikin wani irin fusata kande ta fizgo Ikilima wacce tayi hanyar gida, jikinta sanye da uniform din sabuwar private school din da mlm yasaka su itada Abdullahi, kamar jaka haka kande ke fizgarta har zuwa gaban wani kanti, ba tsoro tare da ita tacewa me kantin "bani razor blade yanzun nan", miƙo mata ya yi tabashi kuɗi yana cemata tayiwa yarinyar ahankali kartaji mata ciwo,danshi ya dauka rikon wasa ne tayi wa Ikilima bawai rigima suke ba. Da karfi ta janyo Ikilima har wani ɗan lungu daba mutane sosai,fizge hular kan ta tayi tasanyata atsakanin cinyoyinta da karfin bala'i ta askewa Ikilima kai tas,se kyalli yake kamar silba, kuma ta kwashi gashin ta zuba mata a jaka,Ikilima zuwa lokacin kamar zata shiɗe sbd kuka,se mulmula take akasa tana ihu, fuskarta gwanin ban dariya,kallonta kande tayi tace "now we luk zee same,duka mun koma maza dagani harke, nonsenseus kawai arniya" tasa kai ta wuce tabar Ikilima agurin. Riƙe haɓa sukayi dukansu daga mlm har teachers din bayan sungama jin jawabin komi abakin Ikilima wacce tasha aski kamar namiji,se kuka take sherɓawa,haƙuri mlm yabata yace tashiga ciki zaizo yasamesu itada kanden yaji meya haɗasu,dan Ikilima bata faɗi gskyr me tacewa kande ba,cewa tayi haka kurum kande ta kamata tamata aski. Gogar kuwa tana gefe tana hura hanci taƙi cewa komi. Anyi anyi da ita har malam seda yasa baki amma ta turancesa tsaf da haukarta,kuma tace wlh idan aka matsa mata seta koma sede anemeta arasa,gatade yarinya sosai amma kalaman bakinta abin tsoro ne,sanin matsalar ta yasa Malam ya basu haƙuri da cewa suje kawai daga baya ze lallaɓata ta dawo. Ya faɗa musu haka ne kawai dan su tafi,amma yasan tunda ta kafe to no way out,Kuma ajikinsa yakeji yafara nadamar hukuncin da ya yanke a kanta. Aranar ko anyi bala'i sosai agidan dan umma wando ta sanyo tazo sashen inna wai yau ko abata kande tamata aski ko kuma su daku da inna,mama na side dinta tanaji amma ko leqe balle tabada hakuri,haka aka dinga bala'i harda Amo,se daga murya take tana faɗin idn umma ta taɓa mata takwara seta saka itace ta sheme ta🤣da kyar mlm ya kashe wutar nan,dan alokacin baban Ikilima baya gari yayi tafiya Haka kande ta cigaba da rayuwa ba boko ba islamiyya,tunda ƙananun shekarunta ta sami wannan nakasun, yayyenta wani lokaci har kuka suke wa mlm akan araba ta da duk wani aljani da yake tare da ita ko an samu sauƙin wani abun,dan su acewarsu duk abinda yasameta to haka Allah ya ƙaddara mata,babu tsumi babu dubara,amma be dace abarta da wannan aljanin da yake iƙirarin kare ta yake ba yana lalata mata rayuwa da future nata ba. Duk wannan sauyin marar daɗi daya samu kande hakan be hana an cigaba da jifan rayuwarta da mummunar nufi ba,ga hassada da ƙeta kala kala,sam rayuwarta ce ba a so yanzu. Duk da cewa ansan babu hanyar ratsa jikinta da wani sihiri hakan besa an saduda ba,dama jaki de akoda yaushe sunansa jaki, kuma duk yadda akayi dashi seyaci kara. Haka kande ta cigaba da gudanar da rayuwarta har kawo yanzu data girma tazama cikakkiyar budurwa,babu abinda ya sauya sema gaba da yake kara yi,gashi bata ƙaunar sabon kaya,sede taje gwanjo ta zaɓo abinta,gata da tsafta da ibada,amma kayanta kamar an ƙwato abakin kura,sam bata ƙaunar guga, takalma kuwa idan ta ƙadan masa to in Sha Allahu seya dagargaje yadena ɗinkuwa sbd wahala sannan zata dena sakawa,kuma har yau bata dena tallar awararta ba. Ga awarar tasu da farin jini,amma duk yadda kuka kai da kwaɗayi idan bata tashi fita tallah ba to sede ka mutu, bata siyarwa acikin gidan,dole sede ajirata har sanda ta fito tallarta,kuma ba kowa take siyarwa ba,taga dama ma idan ta fita tayi gun almajirai ta basu bokitin awarar tace su raba,duk maitar me siya kuwa sede ya hkra. Idan kuma awarar ta kwana seta faɗawa me siya,tace ta jiyace inzaka siya ka siya in bazaka siyaba ka bari ehe. Kamar de yau da ta kai chamber su ta samari seda ta faɗa musu ta shekaran jiyace idan zasu siya to idan kuma bazasu siyaba su suka sani,lols. *_cigaban labari*_ "Mama me kikeso kicemin ne?, kina nufin wai har yanzu taurarinta sunfi na duka ƴaƴana haske? haba mama kefa babbar bokanya ce wacce ba abinda ya gagareki, atemaka asan yadda akayi aka dusasar da hasken nata,dan Allah yasani idan ina ganinta jinake kamar na haɗiyi zuciya,na tsani wannan yarinyar daga ita har uwarta,uwarta ita tamini katanga da auren mlm na ƙare a auren ɗan uwansa,gashi nan har yau banida tsuntsu bare tarko, mama kitemaka min bazan iya ƙara jurar faɗuwa ba,baze yuwu uwarta tayi galaba akaina kuma ƴarta taƴi akan ƴaƴana ba,ko ma jini nawa ne zan bayar,wannan karon a shirye nake mama,Ajuji ya ja kwananki mama me tukunyar sharri,". Ta cikin madubin wata mata ce zaune da baƙaƙen kaya, ba'a ganin fuskarta sbd doguwar rigace ajikinta baƙa me hula hoodie,ya rufe mata fuska ba'a iya gane ainahin kalarta baƙace ko fara,sbd ba wata gaba ta jikinta dake waje. Magana tafara kamar haka muryarta na amsawa bibbiyu.......... ______________????? Shin wacece wnn matar ta gaban madubi?, Akan suwa take magana? Tauraron wacece ta dusashe nata dana ƴaƴanta? Wacece wnn matar tacikin madubi? Muhadu a next pg. # 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:06 Bismillahirrah manirrahim. Wacce aka kira da Mama ta cikin madubin ce ta fara magana muryarta na amsawa bibbiyu da sauti me firgitarwa "dolene zaki bada cikin jikin yaranki kamar yadda aka saba,sannan a yau base gobe ba kije ki nemo mahaifar baƙar karya tare da ɗan da karyar ta haifa ki binne su da ransu,ki tabbatar kowa be ganki ba,muddin wani ya ganki to kome yafaru dake ke kika janyo wa kanki,kisani wannan aikin bama buƙatar kowa ya ganki ko da kuskure,in ba haka ba komi ze lalace duka abinda kika yi ze komo kanki". Batareda ta sake samun damar sake magana ba madubin ya yi duhu cen kuma ya washe yakoma normal mirror,miƙewa tayi ta cire doguwar rigar da ta sanya baƙa me hula,fuska wacce ya bayyana seda wayar ɗakko rahoto ta kusa faɗuwa,guess whoo,mama😱 _*Nigerian elite special force*_ General Asim,"munsamu wani hint gameda wadannan ƴan mata tara da aka sace,majiya me ƙarfi ta sanar mana anfita dasu ne da sunan za'a basu aiki a Saudiyya,amma a zahiri ba haka bane,ƴan mata uku kawai aka kai saudiyya suma da niyyar karuwanci aka kaisu bayan an yaudari iyayensu,sauran kuma Uganda aka kai su,wasu kuma south Africa for prostitutional purpose* Sannan ba iya ƴan mata suke safara ba,harda yara ƙanana suke safara suna kaisu ƙasashen waje,wasu kasuwancin sassan jikinsu ake, wasu kuma ana training dinsu ne dan su zama high assassin's, hacker's,gays etc". Numfashi wanda aka kira da G.Asim ya sauke,har yanzu fuskarsa tana kallon wajene be juyo ya kalli me basa jawabin ba,ingarman namijine me ƙirar sadaukan maza,girmansa ma kawai ya isa ya firgita me kallonsa,yanada faɗi jikinsa ko ina amurɗe,ya goya hsnnuwansa abaya,jikinsa sanyeda kakinsu na special elite force,yanada yalwar suma me tsayi baƙi siɗik,dan har ɗaurers ya yi ta baya, hannunsa daya goya wasu irin jijiyoyine kwance akansu muscles ta ko ina,hannun kawai zaka kalla kasan ba baƙin mutum bane haka kuma ba fari bane,fatarsa chocolate color ce,sak Ethiopian. Wani ne yasake shigowa office din yasara musu kafin lieutenant general Habib yace masa "ya akayine Captain Abdul?" Wata takarda wanda aka kira da Captain Abdul ya miƙa masa yace wannan saƙon general ne"amsar envelope ɗin L.G Habib ya yi yace "tnk u captain" seda yasake Sara musu kafin ya fita,har lokacin G.Asim be juyoba. Tabbas abinda L.G Habib yake faɗa ya ɗauki hankalinsa amma babban abinda yafi damunsa a yanzu shine be wuce yacce yakama matarsa ta aure tana zuba masa poison a abinci ba,matarda sukayi auren soyayya amatsayinta na ƴar uwarsa,duk da cewa da farko be wani damu da ita ba,amma daga baya haka kurum yaji duk duniya ba wacce yake so da ƙauna irin Meerah. Shiko wace irin rashin Sa'a ce dashi har haka,ace aure har biyu amma babu matar arziki a cikin,shi yasani ba duka aka taru aka zama ɗaya ba dole acikin dubu akwai ɗaya zakka amma a ina? wani guri? "Hmmmmmm" ya sauke gauron numfashi yana juyowa tare da sanya hannuwansa acikin aljihun wandon kakin jikinsa. Subhanallahi wa bihamdihii,fatabarakallahu ashanil khaliqiin,wani irin halitta ne me wata irin fuska wacce kai tsaye bazakace ga daga jinsin daga yakasance ba, wani irin sassanyan kyau ne dashi me sanyaya zuciyar me kallonsa,kyakkawa ne ainun,shi ba fari ba shiba baƙi ba,haɗaɗɗene wanda ya amsa sunan sa me kyau,kai tsaye zaka iya kiransa da giant rocky hanmson. Fuskarsa meɗan tsawo da faɗi,laɓɓansa jajaye ne pure red,manyan piercy silver eyes,darked brows,pointed nose,he's just damn hamson,_General Asim Al-Amin Muhammad_ the general commander na elite special force,bangare na musamman wato (ALPHAH). Kallonsa L.G Habib ya yi yace "abokina kana lfy kuwa?anya kana bacci acikin kwanankin nan?kalli yadda idonka ya sauya,nd u look so pale,tun shekaran jiya kake cikin damuwa amma ka ƙi kafaɗa min,pls tell me my friend ko Meera ce?" "Hmmm, exactly Habib meerahhhh" sekuma ya yi shiru,ya sunkuyarda kai don wani irin zafi zuciyarsa keyi,jiyake kamar yanzu ne yaganta tana zubawa. "Ehen tell me ok?" Cikin lallashi Habib yake tmbyr sa, kuma ga dukkan alamu damuwar babba ce tunda har yakasa faɗa kai tsaye, "calm down bro,kasan barin kashi aciki baya maganin yunwa,pls tell me friend,kasan koda yaushe problems told is half solved always umm,so kafaɗa mini menene ya faru da meerah". Cike da jin ƙwarin gwiwa yace "L.G i caught meerah red handed poisoning my food, she's trying to get rid of me,5 wat bloody reason huh? I loved nd care 5 her,cherish her,na bata full asset to do wat ever she want with her lyf nd my wealth, or giving her freedom is a crime? Habib pls tell me am i not worth to be loved huh?* Habib nakasa ganewa kaina gaba ɗaya ya kulle, menene atare da ni dayasa mata basa sona? Aure biyu duka ba dan Allah suka aure niba,duka kowa da tashi matsalar da ta sanya suke tarayya dani,kowacce she's after my lyf for wat reason for goodness sake?" Jikinsa har rawa yake idanunsa nan take suka kaɗa sukayi jajir,dasauri Habib ya tashi ya ɗakko ruwa me sanyi acikin deep freezer din dake office din yazuba a glass cup y miƙowa Asim,ba musu ga amsa ya kafa kai seda ya shanye,kara zuba masa Habib ya yi har sau uku har ruwan ya ƙare kafin Habib ya daga kafaɗar sa yana matsawa a hankali,jan ajiyar zuciya kawai Asim yake kafin Habib ya fara magana cikin taushin murya. "Haƙiƙa Sameerah ta aikata babban kuskure,kuma dole fa fuskanci hukunci,yanzu abinda nakeson sani shine tasan ka ganta ne a lokacin da take zuba maganin?" Girgiza Kai Asim ya yi idonsa a lumshe, yace "kwana na biyu anan ba koma gida ba,tun ranar da naganta banyi making any sound ba na baro gidan,kuma na kashe wayata,kasan baze yiwu naje gidan hjy kwana ba dole zata gane akwai matsala,das y I decided to stay here at d office,tunda i have everything her just lyk home,hjy ma kiranta kawai nayi nafaɗa mata aiki ya riƙe ni bazan samu zuwa gurinta ba". "gud,yanzu abinda za muyi shine ka kunna wayarka", ba musu Asim ya ɗakko wayarsa ya kunna,tana gama loading saƙonnin barkatai suka fara tseren shigowa,kafin kiran meerah ya biyo baya,alamar ya ɗauka Habib ya masa ba musu ga ɗauka yasa a handsfree "oh tank goodness u on ur phone honey,Ina ka shiga ne haka,kabarni da tunani duk ka tsorata ni, are u ok babe,pls talk to me,I was so worried dabaka nan,U scared me love" Sauke numfashi ya yi bayan ya kalli Habib alamar kaji makira ko,ido Habib ya masa alamar yy magana, seda yaja numfashi kafin yace "hey meerah am alive ok,ban mutuba kamar yadda kikaso" cikin daburcewa tace "am eh na'am baby wat do mean?wat are you saying?" Gabanta na mugun faɗuwa, murmushi taji ya yi tacikin wayar yace "relax bay am just kidding u" wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke har seda Asim da Habib suka kalli juna,cigaba da magana ya yi "wani aiki ne ya tsareni kwana 2,it's urgent shiyasa nayi zamana har komi yazama steady amma don't worry ok,Ina lfy ina nan dawowa soon prepare something delicious for me nd my kiddo,see you soon I have a big surprise for you". Thumb Habib ya nuna masa kafin yace raɗawa Asim wata magana a kunne,kallonsa Asim ya yi yace "baka ganin ya yi sauƙi yin hakan,da wlh niyyata na azabtar d ita Sosai,amma bakomi wannan shawarar ma tayi,tank u so much friend,barinje zuwa gobe zamuyi magana akan ƴan matan nan". Sallamar juna sukayi Asim ya nufi hanyar gidansa tare da convoy na mototinsa da security ɗinsa. Wani irin gidan naga an nufa a unguwar Nassarawa GRA,gaban wani gida me kamar na president suka nufa,tun kafin su karasa wasu sojojin ne suka buɗe masu tangamemen gate din, danna hancin motocin sukayi zuwa cikin ƙaton mansion ɗin,sojoji ne birjik acidan na security,seda suka wuce gate biyu bayan na farkon,duk gate din da suka wuce wasu daga cikin motocin zasu tsaya,har suka dangana dana ƙarshe kafin motarsa ta shige ita kaɗai,aguje wata farar siririyar mace ta rugo jikinta daga ita se wata half lassy gown shoulderless brown wacce tasake fito da ainahin kalar farinta, Dede sanda ya fito daga cikin motar tana zuwa ta ɗane ajikinsa rana ihu kamar ƙaramar yarinya,kanta ta tufƙesa amma sbd yadda ta ɗanesa aguje har seda naɗin ya warware,dogon gashinta ya bayyana,kyakkawa ba sosai ba,farinde ya haskata amma kuma ba munanna nace.,fuskar nan tasha make up,jikinta amurje alamar hutu,amma bayan ƙirjinta babu abu me tsoka a jikinta, siririya ce sosai. Yana tsaye ƙiƙam kamar zuma rock beyi hugging nata back ba,kuma be hanata rungumarsa ba fuska ba walwala yace "meerah am tired pls let me take a shower" shagwaɓe fuska tayi tana buga ƙafa a ƙasa "nide nide bakamayi missing ɗina ba ko?" Gaba ya yi ya barta tsaye agurin, sbd yadda ransa ke ƙuna. Sororo tabisa da kallo meye haka kuma?kode bashida lfy ne,sharewa tayi tabi bayansa,wani irin ƙaton gidane wanda kamar ba hannu ne ya gina shi ba,komi na wajen gidan fari ne,tundaga fenti har tiles,bayan ya saka password na ƙofar ya buɗe ya sanya kai yashige,waw wat a heaven,hakama main falo na cikin gidan,komi fari ne ta torch din brown, curtains,sofas,karfet,dining,komi na falon set ne. Wani abu ya taka kamar scale me ɗan faɗi kawai abun ya yi sama dashi,ashe abun zagaye yake da glass lift ne daga ƙasan zuwa saman benen dake falon,ga matakala nan ga lifter se inda ka zaɓa kabi. Tana kallonsa ya haye sama,taɓe baki tayi aranta tace mtwsss mutum se shegen faɗin rai yau de ka gama yawo useless kawai,tasake jan tsoki a fili,ta wuce ta ƙara gyara dining ɗin,tanemi guri fa zauna jiransa tana latsar wayarta,dan bazata bisa ba,tasan duk wannnan shan ƙamshin baya hanasa zuwa idan buƙatarsa ta ciyosa,kuma tasan highess hakurinsa kwana2 ne komin fushinsa seya nema,shiyasa idan taga yana irin wnn shan ƙamshin take fita harkarsa idan ta ciyosa dole yazo ya yi biyayya. Yauma kafin ta aikata abinda tayi niyya na bashi abinci me guba seta samu ya biya mata buƙatar ta tukuna. Acen ɓangaren G.Asim kuwa,wani irin haɗaɗɗen falo yashiga wanda faɗar irin kyawu da haɗuwar falon ma ɓata lokaci ne,komi na falon light red ne da purple,se sofa arsh, se karfet purple gawata ƙatuwar cinema kamar mutanen ciki zasuyi magana. Agajiye ya wuce ya haye steps ɗin da ze sada shi da bedroom ɗinsa,tun a bakin ƙofa yafara zubar da kayan jikinsa, toilet ya miƙeya rufo. Sefa ya kwashe lokaci me tsawo kafin ya fito sanyeda bathrobe,gashinsa se ɗihar da ruwa yake,wani irin shining fatarsa take kamar ta mace. Seda ya ɓata lokaci me tsayi kafin ya koma main falo daya bar meerah,tunda ya fara sakkowa daga matakalar benen ta zuba masa na mujiya, ganin yadda ya haɗe cikin wasu irin riga da 3quater din wando,se baza ƙamshi yake,yana tafe ya na waya da hjyr sa,kamar zata cinyesa haka yakeji. Seda ya yi waving hannunsa akan fuskarta kafin ta san ya iso inda take tsabar yadda ta shagala da kallonsa, hannunsa zube acikin aljihunsa yace "ƴar ƙauye me kike kallo haka" murmushi tayi aranta tanajin anya batayi gaggawar yanke hukunci ba kuwa,yanzu wnn giant rocky din zata sheqe batareda ta gama jin ɗaɗin ta dashi ba. Afili kuma wani irin lust look tafara aika masa,kafin tasaka hannu ta zuge zip ɗin half gown din jikinta tana miƙewa tsaye,nan danan rigar ta fadi kasa,tsayayyune na shanunta suka bayyana acikin Black lassy bra ɗinta,tareda fant dinsa wanda yake nan dashi da babu duk ɗaya. Tasan Asim sarai tasan baya wuce irin wnn tarkon..... 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:07 Bismillahirrah manirrahim. Cikin wani salo na jan hankali ta fara tako wa zuwa gabansa,tana karaikaraya jikinta kamar macijiya,kallonta yake sosai irin kallon ƙurillar nan,kallon da be taba yimata irinsa ba na tsawon shekaru biyu da sukayi da aure,tiny waist nata yake ƙarewa kallo,be taba sanin haka kwankwason meerah yake ba, dama ashe ya ɗade yana kara kaina acikin ƙasusuwa,lafaffen cikinta ya kalla yadda yake flat kamar se haɗe da bayanta kamar batacin abinci,farace sosai meerah,juyowa tayi tana juya masa mazaunai cikin salo tazame ɗan fant wanda yake so transparent,kallon ass dinta ya yi kaɗan ya rage dariya bata kubce masa ba,duk yadda ransa yake a ɓace amma wannan karairayar ta meerah dariya take son bashi,acen baya idan tana masa irin hakan yana shiga yanayi na buƙata koda gangar jikinsa bataso seyaji zuciyarsa tana fizgarsa akanta,amma tun ranar da ya ganta tana zuba masa abu a cikin abinci be sake jin wani abu atare da ita ba. Hasali ma ji yake kamar an tayar dashi daga wani bacci me nauyi,betaba ganin munin siranta ba se yau dayake kallon Meerah agabansa kamar tv,ita nan wai ƙoƙarinta na taja hankalinsa ne,azuciyarsa ya ce let's play d game b4 I hit u ryt straight to ur...be gama tunanin ba yaji tana shafa ƙirjinsa in sexy way. Lumshe ido ya yi kamar abin ya fara shiga jikinsa, murmushin samun nasara tayi tana cigaba da shafa shi,mamakin ƙarfin halin ta yaƙara kamasa ganin yadda ta zage tana sarrafa shi,to ko dai dama ba kashe shi take son yi ba,Kode ya yi judging nata wrong ne,wata zuciyar tace masa amma me zaka kira kwalbar poison ɗin da ka gani da idonka a hannunta da sanda ta buɗe ta zuba ta kara zubawa,shima misjudged zaka kirasa ko me,duk a zuciya yake wnn tunanin yayinda meerah taji nisa wurin ganin ta tayar masa da hankali,dan har ta cire bra ɗinta ta yar,se goga masa ƙirjinta take. Biyeta ya yi yana taya ta abinda take,seda tayi nisa sosai ya fahimci ba abinda take buƙata kamar shi,ta rufe ido tana jiran taji dumus amma shiru,sema jin da tayi yana cewa "am hungry bay come nd serve me pls" arikice ta buɗe idonta ta hangosa zaune agaban dining yana danna wayarsa kamar ba shine yagama hargitsa ta ba, hankalinsa kwance kamar bashiba, saurin sauke ƙafarta datayi hanging akan hannunta tayi,jikinta na rawa ta taso ta nufosa,kallonta ya yi tana nufosa kamar zata karye,tana zuwa ta faɗo kansa tana neman haɗe bakinsu muryarta na rawa tace "pls honey don't do dis to me huhh, pls ko sau ɗaya ne,am badly in d mood u know,kasanni bana jure wannan point din pls" ta fada tana neman kai bakinta kan nashi. Kawar da kansa ya yi yana cewa "pls meerah ba abinda zan iya am hungry ok?" Ya buga mata tsawa,tasan yadda yake baya wuce tayin sex amma ji yadda yake wani yaƙunata akan takawo masa kanta,ranta ne ya ɓaci cikin haushi ta bar jikin sa ta ɗauki kayanta ta haye sama tana juya masa flat ass dinta,tasan baya wuce irin wannan tayin,tasan dole nema ze biyota shiyasa ta tafi,amma wata irin muguwar sha'awa ce ke taso mata,ba abinda take buƙata kamar tajita ajikinsa. Tana shiga ɗakin tasaka dim light ta shige toilet ta watsa ruwa yazo ta shafe jikinta da wasu turaruka masu ƙamshi da tayarda hankali,bata sanya komi ajikin taba ta haye gadon ta kwanta,tana jiran tsammani amma har tsawon 3mint shiru tun tana jurewa harta fara tunanin anya lfy kuwa,miƙewa tayi ta sanya wata rigar net shara2 rigar kamar bathrobe ta sakko ƙasa,baya falon amma taga takarda akan dining ɗin,wani wawan tsuki taja ko takan takardar bata bi ba ta kwalaws me aikinta kira,jiki na rawa ƴar aikin ta fito wacce ta kasance Christian ce,duka bazata wuce sa'ar meerahn ba, "follow me" shine kawai abinda ta ce takoma sama,ƴar aiki Dinah data sunkuyar da kai meerah na hayewa sama ta bita da wani kallo tana sakin wani irin murmushi,aguje ta faɗa toilet ɗin falon ta watsa ruwa ta sake tahowa aguje daga ita se towel ta haye sama bedroom ɗin meerah dede sanda Asim yake sakkowa daga lifter yaga hayewar Dinah me aiki dg ita se towel kuma hanyar ɗakin Meerah ta tafi. Mamaki ne ya kamasa,saboda yasan Meerah sam bata shiri da ƴan aiki ko ɗakinta bata bari su shiga balle nasa,to me Dinah zataje yi kuma ko kayan babu ajikinta harda gudu,saurin bin bayanta ya yi yagani kar yazo wani mugun abun zata je yi. Saboda sauri ko ƙofar bata rufeba,tana shiga tasaki towel din nata abakin ƙofa sbd gargaɗin Meerah ne a irin wannan lokacin bata zuwa mata da komi ajikinta,kanta aƙasa kamar bataso ta shiga ɗakin,Meerah da take ma matuqar matse tayi saurin fizgo Dinah ta turata kan gadon tabita ta danne tana haɗe bakinsu,sunyi nisa banda nishinsu ba abinda ke fitowa daga ɗakin ga ƙofar bata gama rufuwa ba. Sandarewa Asim ya yi a tsaye yana kallon wani abu wanda ko a mafarki akace masa hakan ta faru to seya ƙaryata sbd irin sanin da ya yiwa Meerah,sam bata da sauƙi akan ƴan aiki wani lokaci har seya mata magana akan yadda take tozarta su,amma yau idonsa ya gane masa abinda be taba zato ba. Meerah ce kwance share2 Dinah ta kifa kanta ajinta banda ihunsu ba abinda ke tashi,gaba ɗaya sun fice a hayyacinsu,har ya shigo cikin ɗakin ya tsaye musu aka basu san ya shigo ba. Wata wawuyar kick y baiwa Dinah wacce tabuga uban goho kanta acikin ƙugun Meerah,wani irin ihu suka ƙwallah atare sbd azabar da ta ratsa kowanne su,ita Dinah sbd azaba gabanta harya fara jini sbd wasu kafuran takalma ne aƙafarsa na aiki,shurin da ya mata direct ya seta dede v.hole nata data baje awaje se dripping yake sbd yadda suka tayar wa kansu da sha'awa,hakan yasa haƙuranta suka haɗe harta gartsawa Meera wani cizo me zafi acikin nata hole ɗin data wangale ana lashewa, azaba tasaka kowaccensu saka hannuwa bibbiyu suna dafe gabansu tare da tswala ihun azaba. Se sannan suka gansa akansu ya kunna wata irin ƙatuwar wato cigars wacce turawa ne sukafi yawan amfani da ita,kallonsu yake a sheqe, kowacce tana neman abin sitirta jikinta, amma sun kasa tashi sbd yadda kowacce headquarter dinta tad'auki wata irin raɗaɗi da azaba,Meerah jitake inama kasa ta buɗe tashige sbd wata irin kunya data kamata,bata san hana gidan ba,duk tunaninta ya fitane,yayinda Dinah take kukan wahalar da zata sha a hannun ogan nata. Waya ya ɗauka yi magana kafin ya sauke wayar still idonsa akansu,se baiwa cigars dinsa wuta yake harya yi rabinta, kwankwasa kofar akayi kai tsaye yace come in,yasa ƙafa ya wurgawa Dinah towel dinta tunda Meerah ta yafawa jikinta bargo,wasu murɗaɗɗun sojoji ne suka shigo ɗakin suka sara masa,kallon su y yi yanuna su Meerah wacce tamiƙe zaune kanta aƙasa,ashe shigewa bargon da tayi rigarta tasanya, "get dem" abinda yace kenan kawai yasa kai ya fita,yanajin ihu su,musamman Meerah tana zunduma musu zagi tana faɗin kar wanda ya taɓa ta, sukuwa sojoji ba mutunci umarnin oga suke bi. Yana zaune afalon ƙasa se kaɗa ƙafa yake yakunna wata cigars se bata wuta yake,sojojin suka sakko Dinah na gaba se rafsa kuka take, yayinda aka saɓo Meerah akafaɗa se ihu take tana dukan wanda ya saɓo ta,zagi iri iri ba wanda bata ɗura musu ba. Agabansa suka ajiye su,takaddar ɗazu na hannunsa yana juyawa miƙo mata ya yi,seda ya busar da hayaƙi me yawa kafin yace, "i try my very best to be nice to u,nakama ki da idona kina zuba min guba a cikin abinci,wanda na tabbatar wancen abincin ma akwai same poison a cikinsa, naso sakinki in a peaceful way Amma abinda kika aikata yanzu yasaka nacenza ra'ayina,Sena hukuntaki dede 1da abinda kika aikata mini"kallon guards din ya yi yakaɗa musu kai,sake kwashe su sukayi suka fita dasu,Meera se ihu take tana roƙon ya yafe mata, wa Sherin sheɗan ne amma ko kallon inda take beyiba sema sake busa hayaƙin sa ta yake. KIAMBA ISLAND PHILIPPINES. Wani irin ƙasurgumin daji ne dake gaɓar tekun phillipines,daji ne me matuƙar haɗari wanda ƴan daba suka ƙwacesa suka mayar dashi sansanin aikata miyagun ayyukansu. Cikin wani underground building suke zartar da meeting ɗin nasu,mutane ne wanda kallo ɗaha zaka musu ga tabbatarwa manyan mutane ne su ɗin,sbd shigar dake jikinsu, tattaunawa suke akan yadda ake samun gagarumar riba a harka smuggling da safarar mata da yara,babbar me kawo ribar kuwa sune kidnapping da human part trafficking. Babbar me hannu jari a cikin wannan harƙalla kuma me kaso hamsin a duka wannan harƙallolin itace *Annabella de'cruz* ƴar nan ƙasar ta phillipines ce,matashiyar mace ƴar kimanin shekaru arba'in,afuskar duniya itadin ƴar kasuwa ce me manyan hannun jari a companoni da dama a ƙasar,ko wannan dajin na KIAMBA ISLAND ma itace jagorar amshe shi yazama mallakin ƴan daba. Acikin wannan underground building din Allah ya yi yawa da munanan ayyukan da ake aikatawa aciki,komi na Anna na ƙasar phillipines anan ake yinsa,duk wani mummunan abu acikin kiamba dark island ake yinsa. Agurin ana ƙera duk wani nau'i na muggan makamai,miyagun ƙwayoyi,har asibitin da take safarar sassan jikin ɗan Adam da jarirai a wannan tsibirin yake. Bayan sun gama tattaunawa akan ribar da suke samu sekuma aka koma kan yadda sabon jami'in hana sha da fatauci miyagun ƙwayoyi ya musu karan tsaye acikin garin,duk wasu manyan yaran Anna dake jigilar yimata aiki acikin garin manila ya damƙe su,hakan yasa kowa ke kawo shawarar yadda za'a ɓullo masa,sbd yanada kafiya, da dagewa akan aikinsa,Asalinsa ɗan ƙasar Dubai ne,ya yi karatunsa a Dubai har ya zuwa matakin aikinsa a yanzu, kasancewar mutum me gsky da dagewa akan aikinsa yasa aka dinga masa sauyin gurin aiki har Allah ya sa aka kaisa ƙasar phillipines agarin manila. Tunda ya fara aiki yake yiwa ƴan daba manya da ƙanana ɓarna,har sanda aikinsa ya faɗa kan babbar kura Annabella de'cruz,the red dragon,shine takenta a duniyar miyagu. KANO NIGERIA. Wanka kande ta fito,yau wani irin nishadi take ji ta siyi sabon kaya a gwanjo, wani wando ne 3quater me faɗin gaske,se wata rigar polo irin ƙatuwar nan,da alama ta ƙaton mutum ce,tsaf tagama shirinta,ta ɗakko sabon covershoe ɗinta kauce buba ta ƙwama,ga wata pcap,fara amma Takoma brown ahakan ma tasha wanki ne agurin Amo dan ita keyiwa kande wanki,guga ne bata iya ba kuma kande batayi,ahaka take burma kayanta duk squeezing ɗinsu,wata doguwar Zariya ta ɗakko ga ɗaure ƙugun wandon dan ya mata yawa,idan kaga yadda tayi dressing seka ɗauka wani ƙaramin mahaukaci ne,zaka rantse batada gata acikin gidan Kano. Fitowa tayi tana ƙwambo se karkaɗe jiki take ita adole yau ta yi wankan sabon kaya. Kallonta inna tayi kamar tayi dariya amma ta maze tace "a'a auta wannan gayun fa,se ina haka,amma kin yi kyau" cikin shan ƙamshi tawani cira kai gefe tana karkace baki tace "Sa'a de inna ta,zaa tufar idon mlm habu me kayan koli,seke inna Allah wlh" murmushi inna tayi tana juye miyar data gama soyawa akan awarar, ɗaukan bokitin tayi tana tafiya tana kallon wankan data ɗauka yau,yau dolene ma tayiwa su zakarius ƙwambo,a zaure ta tsaya ta kalli mlm wanda har ɗalibansa sun fara zuwa,tace "Sa'a de dagus,dawa de zaa imamu,Ni zan ware eh,kawai se na dawo asa mana albarka" "Allah ya miki albarka ya shiryeku keda ƴan uwanki mamana,Allah ya bada Sa'a kinji? Dan Allah banda faɗa da doke doke". "Dawa de dagus,Allah bar mana kai zaa imamu namu,Amin Amin tsoho ni na shige,see you in zaa aftanu(afternoon)tasa kai fa fita, ɗaliban mlm se kus kus suke suna mamakin yadda akayi malami kuma liman kamar mlm habu amma ya haifi irin wannan ƴar. Tana fitowa waje ta sake cenza yanayin tafiyarta,har wani ɗage kafa ɗaya take tana zauɗewa gefe ɗaya,wasu yara ne sukace zaa kand me awaraaa,kallonsu tayi tace "saa de yara kuhuta kawai,kai kutaho yau ko inna zata tabo gajimare ne Allah sede na saka mata lada,Alqur'an yau sadaka zanyi" aguje yara suka taso da almajiri haka ta dinga raba musu awarar nan,gashi tayi kyau tayi manya tasha miyar jajjage amma haka kande ta dinga kyautar da awarar nan,tana cikin baiwa yara se masifa take tana zata yayyarfawa yaro hannu a ƙeya batason turereniya,wani hannu ne taga ya miƙo shima abashi bin hannun tayi da kallo tace "aaa dawa de kirezi man,kaima kasan yunwa ashe,hhhh yo ai na ɗauka mahaukata basa cin food, Allah yasin kuwa,kai atafawa yunwa raf raf", yara se tafi suke suna ihu,ta dakko awara ta baiwa mahaukacin wanda yake ta kallonta kamar ze cinyeta,ganin yaƙi tafiya yasa ta kallesa tace "yade kirezi ko ta mama kaɗan ne?" Jijjiga kai ya yi alamar eh, amshe ta hannunsa tayi tace "bar nan dan asawarka,bari gobe idan akayi wata Sena ƙara maka idan da kuɗin ka acikin jarin awarar ɗan dusa da tsaki kawai". Seda ta rabe awarar tas sannan tabaiwa wani yaro bokitin awarar tace ya kaiwa innarta. Chamber su ta wuce,tana zuwa tun daga nisa ta cenza tafiya tana "yoo yoo maza,ya ake ciki ne,hi gayis y me news ne" ihu suka ɗauka ganin ta da wata sabuwar shiga kuma basu santa da kayan ba,se wani juyi take tana breakinh dance tana faɗin "yoo yoo zaa kand, zaa soja is me, I am zaa 1"wani juyi tayi acikin burma burman kayanta kawai se kicibis suka haɗe da wannan mahaukacin da ta amshe awararta a hannunsa,kallon ƙurilla yake Binta dashi kafin ta wani cii birki agaban sa tace ...... 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Not edited Free page:08 Bismillahirrah manirrahim. "yoo yoo zaa kand, zaa soja is me, I am zaa 1"wani juyi tayi acikin burma burman kayanta kawai se kicibis suka haɗe da wannan mahaukacin da ta amshe awararta a hannunsa,kallon ƙurilla yake Binta dashi kafin ta wani cii birki agaban sa tace "arna yane? Kai kirezi r u in zaa ur hankali kuwa? Tun dazu na lura da kai se folowin ɗina kake,yane iye hw market ko kaima wankan ya maka ne?" Tafaɗa tana tsaresa da manyan idonta. Juyawa kawai ya yi yawuce yana tafiya yana waiwayenta, zakarius ne yace "zaa kand wannan ai ya kwana2 a unguwar nan,kusan kullum yana unguwar nan ya daɗe sosai, kawaide baki taɓa ganinsa bane" taɓe baki tayi kafin tace " wai ina sagalo ne yau bezo cika chamber ba Wetin hapin dashi ne eh?" Duna ne yace "dawa de zaa kand,wai bakisan cewa ƙojensa yana asibiti ba?,ai shekaran jiya tsohon sa yaje yasha tamasa over kawai yazo yasamu babar sagalo ya sauke mata rabin bulo atsakar baya,ai yasin baban sagalo bulkumi ne,shi har yau beyi hankali ba,tun muna yarafa yake kwalɓewa har yau be dena ba,kullum idan yashawo kayarsa seyazo ya tarawa babar sagalo gajiya,arne kawai, ga babar sagalo 50inch shine kawai ta fara nuna masa itama fa arniya ce,yadda yake wani figigi kamar taliya ƴar murji Allah ɗaukar amarya kawai tamasa ta dinga maka arne da ƙasa kan azo akawo masa agaji ya wulla second barzahu arne kawai". Dariya kawai kande ke ƙyaƙyara,dan ita har ga Allah babar sagalo ta birgeta data sumar da baban,tun suna yara yake shaye2 daga su wiwi abun ya yi yawa har giya sha yake,kuma idan ya dawo gidan ya kwara mata amai haka zata wanke tana kuka,amma bawan Allahn nan ba wacce ya rena irinta,abu kaɗan duka,badama tayi magana seya zare belt ya yita laftar baiwar Allah,gata irin matan nan ne masu jiki da tsawo sosai gata fara dan ita Bello sagalo ya biyo,baban Bello kuwa baƙi ne wuluk,gashi kamar taliya ƴar murji ta bakin duna,sirirne sosai,auren gida aka musu da babar sagalo baya sonta shiyasa yake wulaqanta ta,ansha zugata tadena zama yana dukanta abanza amma setace bakomi wata rana ze dena,haka za ata zugata amma bata ɗauka,ko agaban su Bello da ƙannensa ne seya mata duka ba abinda ya dame shi,ansha kai ƙararsa gurin babansa me sunguwa yasa akamasa aɗaure amma take tayita kuka tana bada haƙuri wai asakesa ita ta yafe masa,haka me unguwa yashe cewa ze raba wnn auren taje ta auri wanda yasan darajar ta amma tayita kuka tace ita abarta da mijinta tanason sa,wannan dalilin yasa me unguwa ya ɗauke Bello yakaishi bauci gurin yayan baban su Bello,dake shi makamin tsangaya ne,se aka kai Bello domin ya yi karatu yadena ganin wannan taladdancin da babansa yakewa uwar amma har kawo yanzu be dena ba. Shekaranjiya cikin rashin Sa'a yadawo abuge yazo yafara jibgar ta,to dama tafara gajiya kuma tafara ɗaukar shawarar mutane na cewa tadena zama yana dukanta agaban yara,idan ba haka ba zasu ɓatawa yaransu tarbiyya tunda dukansu mazane,haka zasu tashi kamar yadda sukaga ubansu,aiko yana fara lafta mata belt cikin zafin rai ta warto gaban rigarsa tayi sama dashi kamar ta ɗaga ƴar kaza ta haɗe shi da bango ta dinga makawa,tun yana ihu har ya fara bata hkr, amma ina tayi zuciya seta ta fasa masa kai taga yadena motsi sannan ta yasar dashi aƙasa,ko ajikinta tasaka hijabi tafita ta kira me napep tasakashi takaishi asibiti tace musu santsin ya kwashe shi yafaɗi. Tunda takaishi tabari asibitin takoma gida,shine ta tura Bello da kuɗin magani da komi shine yake jinyar babansa ita taƙi zuwa,dalilin rashin ganin Bello kenan. Seda tagama dariyar sannan tace "yakamata muyiwa sagalo solidarity muje muga jikin lamison tsohonsa hhhhhh", tasake sheqewa da dariya se dariyar halin gidansu sagalo suke yi. Washe gari haka fa sake ɗibar wani wankan wanda yafi na jiya ban dariya,ta shafe fuskarta da basilin se shining take kamar takaddar tsire,tayiwa inna da mlm sallama ta tafi asibiti zasuje itada su duna su gaisar da baban sagalo daganan zata wuce kasuwa tasiyo waken soyar awararta. Itama innar shiri take zata tafi gidan Hafsatu tayi miscarriage,Maryam kuma tana asibiti tana naƙuda cikinta be isa haihuwa ba watanta biyar kenan,amma naƙuda fa taso mata me tsanani,shine inna take shirin tafiya dubasu. Awaje kande taga su duna suka fada mata an sallamo baban sagalo yana gida,gidan suka tafi suna sake dariyar abinda ya faru,sallama suketa har ita duk sunƙi shiga su adole maza mazansu faɗa gidan mutane haka kawai ba. Ƙanin Bello ne yafito yace wai yaya yace su shigo kawai dan yanaji muryarsu ya gane su. Shiga sukayi kande ce agaba se wani ɗage kafada take tana baje baya da burma burman kayanta ga fuska se shining take gwanin ban dariya tasha p cap ga sumarta data yanke tabarta dede kafaɗa ta tattare ta cusa cikin p cap ɗin,bayan su gaisarda babbar su Bello kande tace "dawa inna kina wuta alqur'an, ashe kinyiwa zaa fazaa lamiso dukan dawa?kai inna kin birgeni Allah wlh,yo dama inna yadda kiken nan da arnen kyau a kamata ya yi ace fazaa yana biye dake sau da ƙafa kamar yaron aikin ki Allah kuwa,Kinga inna ta alqur'an dagus tsoron ta yake" tajuyo kan baban su sagalo dake kwance an laulaye masa kai da bandeji tace "ahh cau cau fazaa ka daku alkur'an, innalillahi irin wannan rawani haka kallifa yadda aka mayar dakai kamar sarki kasha rawani amma na bandeji wayyihuhu inna tamu dawa de inna kincikawa fazaa aiki alkur'an Kinga kema kinyi free da duka kamar masara,da seki zauna ya yita miki jibgar dawa,amma yanzu ai kinsamu lafiya kema kai cau cau inna Sa'a de inna Allah bar mana ke alkur'an" dariya kamar ga kashe su zakarius dasu duna tun suna kumshewa har suka fara yin abunsu har Bello dariyar yake kamar ba iyayensa akewa iskanci ba,babarsu Bello itama dariyar take,dama ita tun ainahi kande birgeta take,duk yadda ake tsinewa halin kande ita batayi yarinyar birgeta take sosai gata kyakkawa ga ƙarfi kuma zamanta dasu sagalo besa sun lalace ba daga su har ita,hakan yasa ita se kawai Allah ya ɗora mata son yarinyar,baban sagalo kuwa da kande ta saka masa fazaa lamiso yana kwance se wurga idanuwa yake ga fuska a suntume baya iya magana sbd ya jibgu,ya yi gum da baki. Kallonta tayi tace "kande ina innarki ne? Yau ba tallar awarar ne?" Keɓe baki gefe kande tayi tace "inna anacen gida nabarota tana shirin zata tafi ashibanci yi ashibanci mana waifa su yaya Hafsatu ne sukayi ɓari shine taketa shirin zuwa gaishesu harda kama agwagwarta ta yanka tayiwa yaya Hafsatu miya wai tamayarda kwaɗayi kijifa inna da iyayi,duk da de yaya Hafsatu da yaya mero basuda damuwa amma ai mama ba godewa inna zatayiba,sede ma azageta ita kuma yaya Maryam tana asibiti tana naƙuda kuma batakai lokacin haihuwar ta ba" "Assha subhanallahi abu beyi daɗi ba Allah yabasu lfy" "amin" kande ta amsa tana ciro ɗari biyar tabaiwa inna tace asiyawa fazaa lamiso lemu,ta cewa su Bello ita zata ware kasuwa zata tafi,tamusu sallama ta fito,babar sagalo har zaure ta raka kande tana dariyar shigar da yarinyar tayi da yadda take tafiya ita bata yadda ba itama namiji ce. AGRA INDIA. SITHABARAN HOSPITAL. Dr Joshi shine in charge na duba duk wata mace me ciki,ya iya aiki sosai ya kware sosai akan sanin abinda ya shafi mata musamman masu ciki. Zaune yake a office ɗinsa yana rubutawa wata mace me ƙaramin ciki magani,wayarsa ce tayi ƙara cikin faduwar gaba ya ɗauki wayar yana miƙa wa matar takaddar taya gama rubuta mata maganin da zata je pharmacy ta amsa, nan da nan jikinsa ya jiƙe da gumi,yana picking call ɗin hoton ƴarsa ya bayyana an saka mata wuƙa awuya cikin tsananin firgita yake baiwa mutumin haƙuri akan karya cutar da yarinyar duk abinda suke so ya amince ze yi,dariya ƴan daban suka kece da ita wanda yasawa yarinyar wuƙa a wuya yacire yana cemasa ya kalli babban screen din dake bayan su, wani mutum ne ya bayyana wanda aƙalla ze iya yin shekaru hamsin da takwas,amma sbd kuɗi da suka zauna masa hakan yasa yake kama da ƴan 30y. Fuskarsa da kansa dake da farin gashi ne kawai yake nuna ya manyan ta amma jikinsa amurje yake kamar matashi, yanada kyau sosai,jikinsa sanyeda wata irin suit se walwali take kamar an shafa mata gold,yana zaune agaban wani babban teburi aɗakin taro,kallon Dr Joshi ya yi yasaki wani wild smirk yace cikin harshen indianci "idan kana buƙatar ƴarka ta dawo gida safe nd sound dolene ka yarda da deal ɗin da muka kawo maka,dole ne kayi mana gwajin magungunan mu akan mata masu juna biyu,dole kuma duk cikin da yakai wata biyar kasan yadda kayi ya lalace domin wannan jinin miscarriage ɗin muke da buƙata a tara mana,idan kayi hakan ina me tabbatar maka seka zama shararren me kuɗin da duk fadin india babu me irinsa,namaka alkawarin wannan,sannan zan saka asibitin ka yazama lamba ɗaya da duk duniya zata san da zamansa,kaide kawai kabi sharaɗin da zamu gindaya maka,ina binka da lalama ne kawai saboda ƙwarewarka a aiki shine jarinda nakeson amfani dashi a wannan harƙallar,amma ba dan hakaba da kota ƙarfi Sena saka kayi abinda nake da buƙatarka". Banda gumi ba abinda yake zuba ajikin Dr Joshi,Amma ba yadda ya iya inde yana buƙatar zaman lafiyar iyalansa dole ya aikata abinda suka so. Yana cikin wannan tunanin wasu manyan manyan mutane suka shigo sanyeda kayan likitoci suka ajiye masa wasu akwatuna suka juya suka fice. Kallon wayar yayi inda yaji ana masa magana "wannan sune allurorin na baƙin case sune muke buƙatar ka gwada su akan duk wata me tsohon ciki,su kuma na jan case din sune magungunan da zakana basu suna sha,se farin case suma allurai ne,duk macen da ka tabbatar cikinta ya kai wata biyar ko shida to akansu ne zaka yi amfani da wannan allurar,sannan zamu riƙe ƴarka dake gurin mu,har seka aiwatar da aikinmu na tsawon shekaru daya kafin musaketa" kafin ya yi wata magana sukayi saurin disconnect na kiran bisa umurnin na cikin babban screen din wanda ko sunan sa Dr Joshi be sani ba. Wani irin kuka Dr Joshi keyi,ƴar sa shekararta goma sha huɗu,yarinyace ƙarama kuma ita kaɗai yakeda,tabbas bayason ya rasata, haka kuma bayason aikata wannan mummunar aikin da suka sanya sa akan al'ummar da basu ji ba basu gani ba,sbd yasan allurorin yasan haɗarin su. Su wadanda akace ya yiwa masu tsohon ciki illarta shine zata sakarwa jaririn cikin cutar kansa me hadari,wanda zata iya illata har uwar ba wai yaron kadai ba,idan akayi babbar Sa'a shine za a haifi cikin amma baze zo da lfy ba, daganan se su kawo wani magani wanda shine maganin cutar wannan shine kasuwancin da suka kulla da asibitoci da dama a faɗin duniya,wani kuwa tun aciki yake mutuwa kokuma daga uwar har yaron su mutu,kuma se sun zaƙulo babban likita me cikakkiyar ƙwarewa da sanin kan aikinsa sannan suke kai masa wannan farmakin,duk kuma wanda ya bijire ko masa barazanar za akasheshi ko kuma akashe wani nasa da haka wasu suke yadda wasu kuma tayin farko idan sukaji maƙudan kudade kai tsaye suke amincewa. Ita kuma ta masu cikin wata biyar itace wacce zata lalata cikin har se an kwashe musu,to jini ɓarin ake siyarwa wasu kamfanoni masu yin mayukan fata dana bleaching,ba iya nan ba har matsafa suna siyarwa. Haka Dr Joshi ya yanke shawarar kawai ya kashe kansa akan ya aikata wannan mummunar aikin da ɗaukar alhakin al'umma Gara kawai yakashe kansa,dan yasan ƴarsa dake gunsu ma ba zasu barta lfy ba,bama ze kuma ganinta ba,gara kawai yakashe kansa,wayarsa ya ɗauka ya yi video akan duk abinda ya faru da duk wani details akan harƙallar ya turawa wani abokinsa dake aiki a Dubai,ko minti biyar beyiba saƙo ya shigo wayarsa da sauri ya duba atunanin sa abokin nasa ne,amma se ganin wani vedio ya yi daya jijjiga duniyarsa. <><><><><><><> Kande tana tafiya amma jitake kamar ana binta idan ta waiwaya kuma bata ganin kowa,tun tana shiru harta ci birki tana faɗin "ko wane arne ne yake bin bayana kawai yayo waje na gansa,in ba hakaba zan ci me ɗumama masa tuwo Allah wlh" se mafita take ita kaɗai amma ba wanda ko gittawa ya yi a hanyar,cigaba tayi da tafiyarta ta nigogi tana masifa,amma still tanajin takun mutum alamar ana biye da ita,kamar bazata juyo ba tayi kamar bata damuba kawai ta juyo da sauri aikuwa idonta ya faɗa akan wannan mahaukacin yana dab da ita. Cikin ɗan firgita da yadda ya ke dab da ita tace "kai kirezi dan fazaan ka kasha Omo ne iye, y are u follow me,are u mad?" Sekuma tace jini kuma ina tambayarasa bayan mahaukacin ne. Daukar wata sanda tayi tace "ware kabar nan dan me dafa muku tuwo agidanku,bar nan kona maka ɗaukar amarya na jibga a ƙas" bawan Allah ganin ga ɗakko bulala ai aguje ya ruga ya barta se Bala'i take ita kaɗai Acen gida kuwa mama ce tazugo umma wai an hana ƴaƴanta su Hafsah haihuwa se cinye musu ciki ake tanata kuka,aikuwa umma dake ba hankali ne da itaba ta dinga yada magana acikin gida amma inna bata kulata ba sema ɗauko kwanon silbarta data zuba miyar da tayiwa Hafsatu tayi ta ajiye aƙasa tana kullo kofar sashen ta. Umma ganin inna tamata banza cikin jin haushi tace "Allah wadaran maye me cinyewa mutane ƴaƴa" cikin zafin rai inna ta waiwayo ta kwashe fuskar umma da mari dede lokacin da Mudassir ya sanyo kai cikin gidan. 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Not edited Free page:09 Bismillahirrah manirrahim. Salati Mudassir yasaki yana fizgo umma daga riƙon da inna ta mata se fyalla mata mari take,cikin ɓacin rai yace "yau base gobe ba zamu bar gidan nan,Ni dama na daɗe da sanin ba'a son zamana da iyalina acikin gidan nan,kullum se kande ta kama Ikilima ta daka,yau kuma abin yakoma kan matata to ni bazan ɗauka ba,maza Hadiza tafi ki fara harhaɗe mana kayan mu". Turo baki gaba umma tayi tace "nide gsky wnn gidan ko wutafa baka ja mana ba,Allah ya gani ba zan iya kwana acikin zafi ba,Ikilima ma jikinta baya son sauro kasani" Mama dake laɓe abayan ƙofar sashen ta tayi tsuki ganin faɗan beyi nisa ba takoma ɗaki. Umma tuni tayi gaba tabarsu nan suna kayan haushinsu, itade ko gobe idan Hadiza zata dinga shiga hanyarta to baza ta gaji da gyara mata zama ba itama,a zaure ta haɗu da mlm habu wanda duk abinda ake yana jinsu,har abinda Hadiza tace yana ji, murmushi kawai ya yi don yasan ko sama da ƙasa zasu haɗe Hadiza bazata iya barin gidan nan ba,sallama inna ta masa yace mata adawo lfy yabata wani ruwa acikin gora guda biyu yace idan taje ta baiwa ko waccensu, in Sha Allah inde matsalarsu ba daga Allah bace shafar jinnu ce ko wani al'amari na Ubangiji to in Allah yaso bazasu kuma ɓarin ciki ba,dan idan be manta ba Hafsatu ɓari na biyar kenan tayi,ita kuma Maryam ɓarinta biyu wnn ne aketa murna harya kai wata biyar se kuma gashi naƙuda ta taso mata da alama shima ɓarinsa za'a yi. Amsa inna tayi ta fice,a waje taga baba Musa tayi masa sallama ya tsare mata napep tana ya barshi amma seda ya biya me napep ɗin,yanata yi mata gdy da sa albarka itada mlm habu,dan duk sanda irin haka ta samu yaran nasa itace take ƙoƙari dasu,duk shirin umma da mama,mama bata bari umma taje gidan su Hafsatu ba wanda yasan dalilinta,ita ma umman bata sani ba,ko a kwalar rigarta ma abin baya damunta dan ita ba mutum bace me son zuwa unguwa dama,mama ta fake da cewa tunda uwar asugwui na zuwa wai inna take nufi su suyi zaman su base sunje ba,da wnn mama ta hana umma zuwa gurin su Hafsatu. Amma ita idan fitar ta ta kamata tana zuwa gidajen ƴaƴan umma batareda ta sani ba. Kande a hanyarta ta dawowa daga kasuwa tana shirin tsallaka titi amma an tsayar da kowa daga masu ababen hawa har masu tafiya aƙafa,wasu irin maka makan motoci ne na sojoji baƙaƙe suketa wucewa aguje, tana tsaye agefe tana kallo,se masifa take wai an hana su wucewa saboda wasu banzaye masu baƙaƙen kaya,wai su sojoji,wanda tasan yanzu idan zasu ga bomb ba wanda ze tsaya guduwa za suyi "mtswwww*,taja wani dogon tsuki tana cewa "ai wlh idan jarumin soja na gaske akeson gani abari nazama soja za aga jarumta, duk wani bomb ko wata AK47,dasu igwa,dasu gurnet,dasu tiyagas da waye bazasu bani tsoro ba,kai woo ni woo ni,zaa kand zaa ƙanwar mazaje su ustazu Hamis dasu ya Musa,zaa 1 nd only soja of gidan ustazu habu me kayan koli yihuuuu cau cau" ta fada tana wani jijjiga ita bata yadda ba itama namiji ce kuma soja ce, kallonta na kusa ta ita sukayi suka kwashe da dariya. Ihun mutane suke yi ganin wani mahaukaci ya karto aguje ta cikin jerin motocin nan yanaso ya tsallaka,cikin rashin Sa'a motar ta bigeshi,ai aguje kande ga saki kayan hannunta aƙasa ta ratso cikin mutane tana "kai ku kauce" har ta iso gaban mahaukacin nan wanda yake ta juya kansa daya ɗan fashe ga gwiwar hannunsa ma ta ƙuƙƙuje,saurin tsallaka wa tayi inda mahaukacin yake zaune se yamutsa fuska yake alamar yanaji zafin ciwon nasa,tsugunnawa tayi ta kama kan nasa ta ɗago tayi saurin yago gefen burmemiyar rigar jikinta ta ɗaure masa kan nasa,mutane anci dafifi ba wanda ya isa inda suke se kallo ake ana mayarda yacce akayi,gasu tsakiyar titi ga rana,ga motocin nan dole suka dakata saboda basu gama wucewa ba mahaukacin ya ratsa har aka buge shi. Kallonsa tayi tace "kai kirezi ina zaka je ne bakada farin tuwo ne acikin kanka iye?wai ƙwaƙwalwa ce farin tuwo,kana kallo kowa an saka masa pause saboda lakwaye zasu wuce amma ka wani taho aguje, inama zakaje ne,ba a area na baroka ba meya kawo nan?kar de sake biyo ni kayi?aiko gashinan ka samu riba Dilla miƙe kirezius kawai" se masifa take masa tana turancesa kamar yana fahimtar me take faɗa,kama masa hannu tayi ta miƙar dashi tace "taho na kaika gefe ka huta". Wani soja ne ya fito cikin baƙaƙen kaya fuskarsa sanyeda face mask ya rike wata bindiga abar tsoro yana zare jajayen idonsa yace "hey u bunch of lunatics,bazaku tashi agurin ba?bakwa gani kun tsare mana hanya ne?" Juyowa kande tayi tana kallonsa kamar bazata ce komiba sekuma ta tsaya tamasa kallon sama da ƙasa tace "me i no wasa da ragwayen sojoji lyk U,kuma kaine benci ba ni ba ɗan renin hankali kawai, ɗan wulaqanci ku bige mutum ko sannu baku ce masa ba sannan kawani taho ciki agaba kamar tankar miyau dawasu idonka kamar gautar ɗaci kanaso ka karanta min nonsenseus,eh r u mara foka living things kawai, ni bana tsoron ka ehe ,i no tsoronka" daga hannu cikin ɓacin rai ze mareta mutane se kallo akw,wasu ma tafiya suke amma sun tsaya kallon yacce zata kaya tsakanin wannan yarinyar me shigar maza,dan bazasu ce itama mahaukaciyar bace duba da yadda take tsaf tsaf,kawai shigar ta ce ta maza. Tana tsaye ƙiƙam ko gezau batayiba mahaukacin nan kuwa hana tsaye a bayanta se ɓoye fuskarsa yake alamar tsoro yakeji,ya rirriƙe mata riga ta baya,ganin za'a mareta da sauri ya kama hannunta yana ja alamar ta zo su gudu amma kande da taurin kai ta fizge rigarta tace "Dilla cen cikamin rigata,idan tsoro kakeji koma gefe kayi kallo,ko kuma ka hau legediz Benz dinka ka ja saɓa,wannan kurtin sojan besan ni bane,nima fa banaji Allah wlh, Nima soja ce daka ganni anan kawai wannan kayan ne bana sakawa",ta fada tana juyowa kan wannan sojan,dede sanda ya sauke hannunsa caraf aka cafe hannun,juyowa ya yi yaga wanene wannan me rabon shan wahalar,saurin ƙamewa ya yi yana sarawa wanda ya riƙe hannun nasa,yace "sorry boss,wannan mahaukatan ne suka tsayar damu,sun shiga kan hanya" yafaɗa har lokacin yana ƙame" Kallon kande da taja daga wanda ya fito yanzu ya yi,yana sanye cikin wasu irin kaki na sojojin ciki wato elite force,ya ɗaure gashinsa da band baƙi,fuskarsa rufe da mask iya idon sa ne abuɗe,kallonta yake yadda take wank hura hanci taja ƙafa ɗaya baya ɗaya agaba ta dunƙule hannu kamar zata kai naushi, irin tana jiran kora kwana,matsowa ya yi kusada ita cikin wata exotic voice yace "sorry ƴan mata,bakuji ciwo ba ko?" "Normal kawai oga,beji ciwoba ai bani aka bigeba wannan kirezin ne" tafaɗa tana wani karkace baki gefe tana hura hanci tare da nuna mahaukacin wanda har lokacin idonsa aƙasa yana ɓoyewa abayan kande, se wani sunkwi da kai yake. Ƙura masa ido general Asim ya yi wanda sunansa yake rubuce agaban rigar kakin jikinsa,har lokacin be cire mask ɗin ba,kallon mahaukacin yake sosai kafin ya juyo kan kande yace "cool down soja girl yi hkr naga beji ciwo sosai ba ma,amshi wannan ki siya masa maganin ko a chemist ne" yafaɗa yana mikawa wannan sojan na ɗazu hannu, kuɗi ya miƙo masa masu yawa ya amsa yana miƙawa kande,amsa tayi tana wani ci cijewa ta ƙirge 5k ta miƙa masa sauran tace "wannnan ma sun isa,zan siya masa harda abinci ma,1k kuma na siyi waken soya na dana zubar nasan yadda ake yunwar nan wasu sun kwashe" kallonta kawai yake be amsaba ta ajiye akan wata mota dake kusa dasu tace "censa yakkaɓai na sara maka,naga kamar kai nagari ne,mazan fama Allah tsare gaba da bayanka, banda wasu masu neman dukan talakawa,censa yakkaɓai" yafaɗa tana sara masa,amma wai yakkaɓai zatace masa. Shide yana tsaye yana kallon ikon Allah tajanyo hannun mahaukaci wanda g.Asim keta ƙarewa kallo sukayi gaba, mutane se kallon kande ake ana mamakin ƙarfin halin ta,haka ta dinga tsara mutane tana wucewa janye da hannun mahaukaci wanda yake ta rawar jiki kamar yanajin tsoron mutane. Komawa mota su g.Asim sukayi suka ƙara gaba. Haka kande ta kai mahaukaci wani chemist aka wanke masa ciwo se yatsina fuska yake,kande na gefe tana yi masa sannu cen tace "Dilla jishi ƙato da kai se wani kwaɓe fuska kake,bawani zafin kirki nasani, kuma ma wai ina ƴan uwanka ne suka barka se galantoyi kake layi2 kwararo2,koda yake ma kaida kake kirezi ina zaka sani" haka ta dinga ɓaɓatu me Chemist nata dariyar yadda take wani buɗe kafaɗa take ita adole najimi ce. Ana gamawa ta biya kudin taje bakin masallaci ta siya masa shinkafa da wake me mai,ta siya masa kifi soyayya ta saka aciki ta sai nasa fanta ta haɗa ta kawo masa,ko wanke hannu be jiraba ya zurma hannu yafara kai loma hannu baka hannu ƙwarya. Kallon sa take seya bata tausayi tace "oo kirezi anji gumama, kai wlh yunwa arniya ce baruwanta da hauka ko kai yaro ne,kawai kowa farmaka take,kai yunwa Allah gama mana dake arniya kawai" idan ba gizo idon ta ya yi ba kamar murmushi mahaukacin nan ya yi,amma se taga kamar idonta ne,yana gamawa ta zuba masa ruwa ta ɗau gorar da ya shanye fanta ta watsa maganin da me Chemist ya basu ta zuba ruwa ta jijjiga yana narkewa cikin dabara ta baiwa mahaukacin nan aiko ya amshe ya shanye ba musu ta kalle sa tace "kai kirezi a haka de kamar me hankali, duk yacce akayi da kai ba wata damuwa,kuma dan Allah duk ƴan uwanku aka rasa wanda ze kula dakai,nagade ba ka duka balle suce, yaude nayi aikin lada,dole ma na faɗawa su zakarius". Seda ta ga ya fara bacci aƙasan bishiyar mangoro da suka zauna sannan ta tashi tace "barin ware nide,gashi bakada suna to korezi se anjima na saɓe". Hartayi nisa mahaukacin nan be dena kallonta ba,idonsa cike da hawaye. Bayan inna ta gama kulawa da hafsatyta mata duk wani abinda yakamata tamata sallama ta wuce asibitin mlm Aminu Kano gurin Maryam wacce take nan rai a hannun Allah, ta kasa haihuwar abin dake cikin kula ga haihuwar,duk ta galabaice ta fice a hayyacinta, tana ganin inna ta fashe da kuma tana rike hannun innar tace "kuyafemin inna mutuwa zanyi,dan Allah kice mama da baba su yafe min,momy da Abba kuma ku yafe min dan Allah mommy kicewa Aliyu shima ha yafemin" tana gama faɗa tafara salati,da sauri inna ta ciro ruwan addu'ar da mlm yabata ta kafawa Maryam abaki wani ya shiga wani ya zube haka har tasha kusan rabi,mintinan goma tsakani tafara wata irin jijjiga kamar convulsion ya kamata da sauri mommy sarakuwar Maryam ta fita ta kira nurses suna zuwa sukace kowa yafita abasu guri. Kafin awa daya Maryam ta haifi abinda ke cikin ta ashe twins ne gasunan kamar ƙadangaru haka aka nannaɗe acikin tsumma aka baiwa daddyn Aliyu dan shi Aliyu mijin Maryam baya gari yana hanyar dawowa. Tasamu bacci,acen inna ta wuni har dare, koda kande ta koma gida bataga inna ba agurin mlm ta tare se addabar sa take da sheri kala2 tana masa zancen bazawararsa batula,anan unguwar take tana mugun son mlm habu,hakan yasa duk inda taga kande yi take kamar ta mayar da ita cikin ciki. Se dare kusan taran tare inna ta dawo,koda ta dawo ta samu kande tayi bacci a ɗakin Amo. Zaune take agaban madubinta na tsafi ta saka doguwar rigarta baƙa wacce take sawa idan zasu gana da bokanya mama,cikin ɓacin rai da murya me firgitarwa mama tace "Zabba'u babu yadda za'ayi aikin ki ya yi kyau bayan kin zauna kina bacci,an toshe mana duk wasu hanyoyi da zamu kuma samun galaba akan ƴaƴanki,daga yanzu bazamu kuma samun damar sadaukar da jininsu wa dodo ba,sannan ƴarki siddiƙa ba abinda zamu iya yi mata,na gargaɗeki akan karki yadda kowa ya ganki alokacin da kike birne mahaifa da kuma jinjirin karyar nan,kin karya mana doka saboda haka dole ki karɓi hukuncinki" Cikin matsanancin firgicin mama take cewa "kitemakeni yake mama Ajuji yaja da zamaninki yake mama me tukunyar Sheri,wallahi bansan yadda akayi hakan ta kasance ba,bansan wanda ya ganni ba a sanda nake aiwatar da aikin,seda na tabbatar kafa sun kau kafin na aiwatar da aikin,sannan bansan taya aka toshe mana hanyoyin baiwa dodo Ajuji jinin su Hafsatu ba,mama kitemaka min,abani wani aikin komin hatsarinsa inde ƴata siddika zata dawo cikin nutsuwarta to koma meye na amince zanyi". Ɗago kai mama bokanya tayi baka iya hango fuskarta sam,se wani abu jaa sosai kamar garwashi wanda yake nan kamar idonta,cikin muryarta me rarrabuwa tace" babu wani aiki da zaki aiwatar da ze ceci ƴarki,tun farko mun gargaɗeki amma shashancinki da banzan tunanin ki yabaki cewa ke kaɗai ce me jiran duhun dare domin aiwatar da buƙatarki,saboda haka a yanzu de babu abinda zamu iya miki,karki kuma nemana idan ba abu me muhimmanci kika zo dashi ba" Jiki a sanyaye mama ta rufe madubin ta na tsafi,kuma ta duƙufa acikin tunanin neman mafita,tabbas ko ya zatayi seta ga bayan A'isha,tunda suka taso a rayuwa itace matsalarta, tunani tafarayi rahuwarta ta baya. FLASH BACK.. Zabba'u mama da A'isha Inna,maƙotan juna ne kafin suyi aure,tun suna yara ba wani jituwa suke ba Allah be haɗa jininsu ba sam,haka kawai Zabba'u ta tsani A'isha batareda wani ƙwaƙƙwaran dalili ba,irin tsanar nan ta rashin haɗuwar jini marar tushe. Islamiyyarsu ɗaya, Zabba'u ta girmi A'isha,amma A'isha na gaba da ita a makarantar islamiyya,saboda ƙoƙarin A'isha itace head girl a lokacin,wata rana tana tsaron latti abakin gate itada ƴan uwanta prefect Sega Zabba'u da tawagar ƙawayenta ƴan salon tsiya kai ba kokari,haka sukazo kansu tsaye zasu wuce amma prefect din nan sukace dole se an musu bulalar latti,nan fa faɗa ya ɓarke harda dambe A'isha na gefe duk masifarta bata fiya dambe ba,dan irin mutanen nan ne masu zuciya da nacin faɗa,kuma inda tasaka maka hannu seta fitar da jini,hakan yasa bata fiya dambe ba. Tafiya tayi ta sanarda shugaban makarantar alokacin yana meeting da wasu malamai da alarammomi akan musabaƙar da za'ayi yana basu sunayen ɗalibai masu hazaƙa,acikin malamai baƙin fuskar da sukazo makaranta harda mlm habu,acikin ɗaliban kuwa harda A'isha,da sauri shugaban ya tashi ya biyo bayanta, haka ma mlm habu,koda sukaje sun samu Zabba'u tacire hijab ɗinta se tiƙar dambe take da prefects ɗin,yaranda tama girmesu,aikuwa nan da nan shugaban makaranta ya tattara su zuwa Ofishin sa, aka tmby meya faru nan fa kowa ya hayayyaƙo tana bada bayani,kowa nason ace shine me gsky, A'isha na gefe batace komi ba,buga musu tsawa shugaban makaranta ya yi kafin ya juyo kan A'isha yace "head girl Muna sauraron ki meya faru?" Nan ta kwashe yadda akayi ta fada cikin nutsuwarta kanta a sunkuye, nan shugaban makaranta ya baiwa wani malami bulala yace ya zane masa su Zabba'u,aiko agaban baƙin malaman nan aka zanesu se sharɓar kuka suke amma Zabba'u ko gezau batayiba duk da yadda bayanta ke raɗaɗi dan sun daku, kuma shugaban makaranta ya fi ga musu faɗa harda ce musu manyan kawai,da ƙannen bayansu suke faɗa,A'isha na gefe tana murmushi, Zabba'u kamar ta tashi ta shaqe A'isha har lahira,bada ita akayi faɗan ba amma duk t fi jin haushin A'isha akan kowa. Bayan sati ɗaya aka fara zaban ɗaliban da zasuje musabaƙar state,A'isha ce farko acikin list ɗin,bayan an watse daga assembly Zabba'u tasamu shugaban makaranta tace masa itama tana son shiga,haka ya sanya sunanta aka haɗasu da wasu malamai wanda bana makarantar ba suna musu rehazal da testing ɗin karatunsu don jin wanda ya zama colified aje dashi musabaƙar,A'isha ta haye tare da wasu maza biyu,dama mutum biyar ake buƙata,amma Zabba'u ko zango na farko bata wuce ba,gashi ta nace seta yi abinda A'isha tayi sbd sanya wa rai wahala,duk wannan abin da takeyi ustaz habu farin malami me zazzaƙar murya tare da cikakkiyar ƙwarewa akan iya sarrafa karatun Alkur'ani shine yatafi da imanin Zabba'u. Duk wannan naci da fafutukar shi take wa,amma kamar ma besan tanayi ba,dan ko kallon fuskarta bayayi. Haka Zabba'u tazama discolified a cikin masu zuwa musabaƙar nan, antafi kuma makarantar su itace taciyo wa Kano ta ɗaya,har kyautar maka da kuɗaɗe masu yawa A'isha ta samo,haka aka dinga murna aka shirya walima akaci aka sha,A'isha ta baiwa abbanta kyautar kujerar hajjin da aka bata. Kawayen Zabba'u babu wacce batasan irin mugun son da take wa ustaz habu ba,har kirari mata tare da canza mata suna,ZAHAB shine sunan da tamayar wa kanta,ba wanda ya fahimci abinda ake yi,daga ɗalibai har malamai balle shi kansa uban gayya mlm habu,kwatsam aka kawo cingum da alawa anata raba wa ɗalibai wai anyiwa ustaz habu baiko da A'isha head girl,.... Aranar har wata iskar bala'i Zabba'u ta hau,aguje ta damƙi wuyan A'isha wacce take zaune a aji se tsiya ake mata wai dama soyayya suke da ustaz habu amma ba wanda yasani,ƙawayenta sun sata agaba da zolaya ita kuma se sunne kai take tana dariya,ba zato Zabba'u ta shaqi wuyanta,anyi anyi arabasu amma abu yaci tura,se ihu ɗalibai keyi, wasu kuwa aguje sukeje sukazo da shugaban makaranta,kamar haɗin baki sefa ustaz habu shika yazo makaranta kasancewar ba ana yake koyarwa ba,aikuma wani irin karfi ne yazo wa A'isha tayi wani irin kukan kura ta ɗaga Zabba'u sama duk da girman jikin ta amma A'isha sefa ta kaita ƙasa,haka tasamu sa'ar Zabba'u ta dinga naushin baki da hancinta seda ta zubar mata da jini bana wasa ba,koda shugaban makaranta da ustaz habu suka ƙaraso ai Zabba'u ta dena iskoki ta koma ihun neman agaji,ihu take iya ƙarfinta tana faɗin arabafa da A'isha mahaukaciya ce,dakyar da bala'i ustaz habu ya sanya hannu ya fizgo A'isha daga kan Zabba'u wacce tayi laushi,fuskarta ta haɗe da jini,bakinta hanci,idonta duk sun kumbura suntum. Se fizge2 A'isha keyi tana sake kaiwa Zabba'u cafka amma mln habu ya riƙe hannunta sosai,har seda ta gaji dan kanta ta tsaya tana mayarda numfashi fuskarta tayi jajur,se huci take,haka aka ƙara tara wani taron a ofishin shugaban makaranta,anyi anyi da Zabba'u wacce keta rusa kuka ta faɗi abinda A'isha ta mata harta sameta da faɗa amma taƙi faɗa se kuka take rafsawa. Wani mlm ne yaje ajinsu Zabba'u da nasu A'isha ya kira mutum uku2,ƴan ajinsu A'isha aka fara tmby meya haɗa Zabba'u da A'isha fada,sukace sude suna zaune kawai sukaga Zabba'u aguje ta damƙi wuyan A'isha ta shaqe ta,sunyi sunyi su raba amma sun kasa shiyasa sukazo suka kira shugaban makaranta. Ƴan ajin su Zabba'u aka tmby ko sun san abinda ya faru,nan fa kowa ya fara zare ido,seda shugaban makaranta ya daka musu tsawa kafin suka fara inda inda, shugaban makaranta yace wa malamin ɗazu ya ɗakko bulala ya zane masa su,cikin tsoro sukace zasu faɗa. Babbar ƙawar Zabba'u Hairatu itace tafara bayani,"um dama wai,am um mlm wallahi tsaya kaji,dama Zabba'u ce take son mlm habu,shine yau kawai se muka ji wai an musu baiko da A'isha". Dumm haka gaban kowa ya buga harda Zabba'u wacce ta dunƙule agefe se gumi take,ga kuka tana kan yi. 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Not edited Free page:10 Bismillahirrah manirrahim. Tunda aka faɗi abinda ya haɗasu kunya ta kama Zabba'u,duk setaji ta muzanta,ace tana faɗa akan namijin da bemasan tanayi ba, mlm habu kuwa tashi kawai ya yi ya bar makarantar ma gabaki ɗaya,A'isha kuwa wani irin tuƙuƙin baƙin cikin ne ya kamata wato akan masoyinta ma aka mata wannan renin wayon ko,shi kuma harda wani tashi ya fita kamar munafuki ai zezo gida anjima ya sameta. Haka shugaban makaranta de ganin ba wani abin arziki bane ya janyo faɗan se son rai irin na Zabba'u da kuma Sherin zuciya,hakan yasa ya tilasta Zabba'u ta baiwa A'isha hakuri ko kuma tazo da iyayenta gobe,ai da sauri ta bata haƙuri,don gidansu ba wanda ze goyi bayanta idan sukaji abinda ya faru,wata kila ma asaka wani malamin ya kuma zaneta. Sallamar kowa shugaban makaranta ya yi,ya rage daga shi se Zabba'u se malamin da aka tura kiran ɗakibai ɗazu,nasiha sosai shugaban makaranta yamata,tarefa ƙara lurar da ita muhimmancin kamewa agurin mace,duk da cewa dan taso wani ba lefi bane amma abinda tayi na jan faɗa lefine,idan kuma ta duba shi wanda take faɗan dan shi bemasan tanayi ba. Godiya ta masa kamar abin kirki,duk taji ta muzanta,tun daga ranar bata kuma zuwa makaranta ba,har aikawa shugaban makaranta ya yi akace lafiyar ƙalau,kuma tace ace ita ta haƙura da makarantar gaba ɗaya. Haka akasha bikin A'isha da ustazu habu, watansu biyar da aure,Musa ya yi aure shima,se bayan ankawo amarya ne A'isha taga ashe Zabba'u ce,itama Zabba'u data ga A'isha amma seta nuna kamar batasan inda A'isha ta fito ba,dafarko A'isha tayi binta da lalama tana girmamata matsayinta na matar wan mijinta amma daga baya ta tattara ta dena tunda taga abin na Zabba'u ba hankali aciki. Baran ma da Mudassir ya yi aure,mama ta janye Hadiza matar Mudassir suka haɗe kai iskanci ba wanda A'isha bata gani,har kawo yanzu bata canza zani ba. Sauke dogon numfashi tayi afili tace "A'isha kin aikata babban kuskure na shiga rayuwata da zame mini katanga da duk wani cikar burina, kuma zan nuna miki kin aikata babban kuskure, Ni dake shega ka fasa. *_Bayan wata huɗu_* Kande ce take tafiya tana ƴan waƙe waƙenta,tasha wata burmemiyar rigar me botira agaba,yau kam Amo harda guga tamata,ta fesa turare se tafiya take tana ɗage kafaɗa,hannunta riƙeda kuɗi da wani ƙaramin bakko zata kasuwar ƴan kaba, yau komai na kayan miya basu dashi,waken soyar ta ma ya ƙare shine aka ɗau na agwagwa za'a tafi kasuwa siyyya. Gitfa wasu ƴan mata tayi,suka kalleta suka kwashe da dariya, ɗaya tace wa sauran "Allah na tuba,yanzu wannan wai mace ce amma duk ta lalata jikinta da tafiyar maza,ita adole namiji ce", ɗayar ma tace "waifa soja take kiran kanta"hhhhhh suka kuma sheqewa da dariya,ta ukun kuwa tace nide birgeni take wlh,ga kyau,wannan idan zata nutsu wallahi mace ce me zati da diri" ta farkon ta kuma cewa ke dilla cen matsa,ina wani kyau anan wacce kullum take wuni cuɗanya da maza,mtwsss" ta biyun ma ta kuma cewa "kyau iya kyau amma na banza ba mashinshini,ni wnn anya ma akwai nonon arziki aƙirjinta kuwa?" Ta fada tana kama haɓa, wata dariyar suka kuma sheqewa da ita suna tafawa. Juyowa kande tayi afusace ta nufosu tana wani irin huci,tsayawa sukayi dan ganin me zata musu ita kaɗai sukuma har rai uku,tana zuwa ba wata2 ta haɗa kansu guri ɗaya dukansu,da wacce ke tsakiya da waɗanda ke gefe da gefe ta haɗe musu kai ji kake gub,agigice ta tsakiyar ta yanka ihu ta kwasa aguje kamar ta gigice, sauran biyun kuma suka tsugunna ko wacce tana dafe kanta dan sun gumu ba lefi, kallonsu tayi a sheqe ta nuna ɗayar tace "kikace ko akwai nonuwa akirji na ko?, to maza miƙe ko laluba kiji" tafaɗa tana finciko hannun budurwar wacce ta fasa ƙara tana bawa kande hakuri,fadi take "dan Allah dan Annabi kiyi hkr wlh Sherin sheɗan ne,dan Allah kiyi hkr,ni wlh bazan kuma shiga harkarki ba dan Allah kiyi hkr ",kande kuwa ta rike hannun budurwar chaf tace aifa seta taba kirjin taji ko akwai nono. Seda budurwa nan tagalabaita saboda kuka,fuskarta duk tayi kace2 da kuka sannan ta saketa dan ɗayar tuni itama ta cikawa bujenta iska,tace "arniya ƙaramar ƴar iska kawai" ta juya ta tafi gun aikenta. Tana tafiya tana tuna yadda ƴan matan nan suka rikice musamman wacce ta ruga aguje kamar ta gigice se murmushi take ita kaɗai,abin ya bata nishadi,shafar ƙirjinta tayi wanda take mance ma wai akwai wata halitta agurin, rintse ido tayi jin ta taɓa wasu halittu masu matuqar laushi,madedeta dan sunfi ƙarfin hannunta,amma yanayin yadda jikinta yake bata da faɗi ta sama se ta ƙugu ga yacce take tafiya a ƙobare hakan yasa bakowa ne ze iya gane yanayin cikar halittarta ba,uwa uba kuma shigarta,amma duk wannan abin bisa tilastawar inna yasa take saka half vest acikin burma burman kayan nata,wnn ma yaƙara temakawa gurin ɓoye cikar ƙirjin nata,wanda idan ba ido kasanya mata ba ma sam bazakace tanada su ba. Hura hanci tayi ta daki ƙirjin nata tace "munafukan abubuwa arnaye me zanyi daku ma,ni dama baku fito ba yasin,bakkuda wani use agun soja" ta wani cuno baki gaba,tana sake yin doro da bayanta irin karma akuma lura akwai su agurin. Sam kande ita a yanzu halittar mata akanta bata birgeta,zata iya rantse wa tana mantawa ita mace ce se idan tazo kama ruwa ko yin wanka,dan tunda Allah ya sa ta girma ta cika mace bata taɓa yin jinin al'ada ba,shekarunta ashirin da ɗaya,zata iya rantse wa ma tamanta mata suna wani abu wai al'ada,dan idan inna tana al'ada ƙaryar mutum yagane,ko lokacin sallah ya yi seta waske,mlm habu ne kaɗai ze iya sanin tana cikin halin rashin tsarki,hakan ya ƙara sanya wa kande ta manta da wata aba wai al'ada,balle a yanzu da inna ta dena yi kwata2. A dede wani lungu wanda ze sada kande da kasuwa taga wani me baro a kwance aƙasa yanata sheqa amai,jikinsa banda rawa ba abinda yake,da sauri kande ta matsa kusa dashi tace "subhanallahi sannu mlm, bakada lfy ne?" Be iya ce mata komi ba, ya jingine da bangon gurin yana mayar da numfashi,jikinsa se rawa yake idonsa ya yi ja sosai,daganinsa yanajin jiki,ga barronsa a gefe,da sauri ta tashi taje gaban bore hole ɗin dake kusada su ta ɗebo ruwa a wani bucket data gani agurin ta kawo masa tana masa sannu,ya amsa ya wanke fuskarsa ya zuba akan sa,duk ya bata tausayi,a ranta tace oo Allah neman halak da wuya,kalli wannan babban mutum dashi amma yana na barrow,ko lafiya bashida ita amma ya fito neman halalinsa,* kande mutum ce me tsananin tausayi,ita kanta batasan tana da tausayi ba,wani abin ma bata sanin tanayi. Gdy mutumin ya mata ya miƙe bayan yaɗanji karfin jikin sa,yaja barrow dinsa harya fara tafiya Jiri ya ɗebesa yafaɗi agurin a sume,da gudu ta tashi ta ruga ta isa inda yake a kwance ta na irin kiran bawan Allah,wasu masu barrow ta hango a tsallaken titi ta tallafo kansa tana bubbuga kumatunsa tana kiran bawan Allah bude idonka amma baya cikin hayyacinsa, tashi tayi ta ruga tsallaken ta kira masu barrow nan tace ga wani ɗan uwansu cen ya faɗi ya suma kamar ma bashida lfy ne,da sauri kuwa suka biyota zuwa inda yake kwance aƙasa a sheme,suna zuwa suka gansa da sauri ɗaya ya tsare musu napep suka kamashi daƙyar suka sanya aciki,dake sunada yawa se mutum uku suka shiga napep ɗin biyu abaya suka rikeshi se ɗaya ya shiga kusada direba suka tafi asibiti,sauran kuma suka zauna suka ajiye wa wanda suka tafi asibiti barrow ɗinsu,kande tana tsaye tana kallonsu har suka ƙulewa ganinta,jiki a sanyaye ta tashi ta shiga kasuwa tayi siyayyarta ta juyo hanyar gida,har lokacin fuskar mutumin nan me barrow bata bar idonta ba,duk tausayinsa dama talakawa ya rufe ta,ita de tasan su bamasu kuɗi bane,amma sunada wadatar da abinda zasuci daa na bukatar yau da kullum be gagaresu ba,harma wani kan iya jingina dasu shima ya wadata. Tana tafiya tana tunanin halin tsadar rayuwa da yadda talaka kullum yake shan wahala,kamar ance ta ɗaga kai kawai idonta ya faɗa cikin na mahaukacin ta data sanya wa suna kirezi. Ta daɗe bata ganinsa,kusan sati biyu rabon da ta gansa,amma da kullum yana biye da ita duk inda zata to seta gansa agurin, ta danganta hakan da kila dan tana bashi abinci ne,se kuma a ka ɗauki sati biyu bata gansa ba se yau. Suna hada ido aikuwa ya sinne kai kamar ya yi rashin gaskiya,tsallaka titi tayi tashareshi ta nufi hanyar gida,kamar yadda tayi tsammani kuwa yana bayanta yana binta a hankali,amma suna da nisa da juna,wata kwana tashiga,ta ɓoye ta ɓace masa,ai kuwa aguje ya rugo ya biyo kwanar shima yana dube dube alamar ita yake nema. Be ganta ba kawai ya kwaɓe fuska ya ɓata rai ya juya ze wuce kawai ya ganta a bayansa tace masa "woooooo" ,kamar ba mahaukaci ba seda ya firgita dan babu zato ya ganta akusa dashi,dariya ta fara ƙyaƙyata wa ganin yadda kirezi ya firgita se zare fararen idonsa yake,a sace ya saki murmushi shima se kuma ya kwaɓe fuska ya sauke kai alamar fushi yake,dariya take seda tayi me isarta yatsare ta da manyan idanuwansa yanata kallonta,baƙaramin kyau tayi ba yadda take sheqa dariyar,1 side dimple dinta kamar a zuba abu aciki ya zauna tsabar yadda ya loɓa, kallonta yake sosai ya shagala,ji yake kamar ya shafa kyakkyawar fuskarta,gashi ta ta sharɓa basilin ga hasken rana yana haske fuskarta se wani walƙiya take kamar wacce take amfani da glowing products. Gimtsewa tayi tace "hi kirezius Ina ka shige ne?,2 sleep I no see u,were u go, eh" na sha ma ƴan uwanku ne suka kwalfeka,ashe de har yanzu kana nan a layi kana gararamba". Ko mi be ce mata ba se sunkuyarda kai da yayi,kama hanya tayi tace "kai kirezi yau banda ko asi kawai ka ware nima nayi nan",ta kama hanyar gida,kirezi kuwa yau duk inda kande ta saka ƙafa shima seya saka,tayi2 ya tafi yaƙi,duk inda ta wuce se an kauce ganinta da mahaukaci,ko ita kaɗai ba me tarar hanyarta balle yau an ganta da mahaukaci,har gida ya bita,a ƙofar gida Ikilima ta fito taci kwalliya da alama fita zatayi,se yauƙi take tana wani gyatsine,tayi kyau abinta itama fara ce kyakkawa,yanzu ta gare shiga shirgin kande tauda de taga ba riba,koda yaushe idan ta haɗo su itace take shan wuya,kuma ba wani mataki da ake ɗauka shiyasa tayiwa kanta karatun ta nutsu. Ai tana hango kande da wani rusheshen mahaukaci ta tsallara ihu aguje ta koma cikin gida tana ihu,malam dake zaure da dalibansa da sauri suka fito waje dan ganin abinda ya tsorita Ikilima haka,ai kwa darewa suka farayi suma ganin kande da wani ƙaton mahaukaci. Tsayawa tayi tana cewa "kirezi tsaya anan barin gani ko inna ta gama tuwo,kuma kana cinyewa ka kama gabanka tom", kamar me hankali yako tsugunna agurin,mlm habu yana tsaye yana kallon ikon Allah. Juyowa tayi zata shiga gida taga mlm da ɗalibansa sunyi cirko2 suna kallonta. Sallamar ɗaliban mlm ya yi bisa dole,kafin ya janyo hannun kande yashiga da ita cikin gida,ɗaki ya kaita ya nemi guri ya zauna ya ƙura mata ido,kallonta yake sosai itama kallonsa take cikin ido,kallonta mlm yake yana karanta wasu addu'o'i itama kallonsa take ido cikin ido,sosai mlm yake addu'o'in nan,idonta ne yafara tara jini nan take idonta yakoma kamar an zuba nuna mata jini,saurin rintse ido tayi gumi na karyo mata ta ko'ina. Cikin buɗaɗɗiyar murya ta fara magana hankali kwance,tace.... # 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Not edited Free page:11 Bismillahirrah manirrahim. Cikin buɗaɗɗiyar murya ta fara magana hankali kwance,tace "malam Abubakar bin Hamza,meyasa ka kasance me gaggawa ne a wasu lokuta? Tabbas kai ɗin cikakken ɗan Adam ne, gaggawar ka ta kuma tabbatar mana da hakan,idan baka mantaba abaya shekaru sha ɗaya da suka shuɗe mun taɓa faɗa maka akwai sirri dunƙulalle a tattare da goɗiya,to a yanzu sirrikan sun fara bayyana tabbas wannan mahaukacin ba mahaukaci bane, cikakken mutum ne me hankali,kuma ba ƙaramin mutum bane,sannan ta dalilinsa ƙofar sirri zata buɗe,mun baka gajeren haske,sauran kuma kaine da kanka zaka nemo,tabbas kai ɗin ubane na gari,kuma kaso abinda bakada alaqa kota kusa bare nesa,tabbas zakaga sakamako,mahaukaci sunansa A'ZAM(ma'anar sunan the greatest),ka tunkaresa kai tsaye kuma ka nuna masa kasan yanada hankali,tabbas zakasan duk wani abu da kake da buƙatar sani,dukkan wani sirri ze bayyana,amma ko ka sani lokacin bayyanar sirrin wa goɗiyar beyi ba,kai kaɗai kake da damar sanin wannan sirrin,.. malam Abubakar bin Hamza tabbas zakaga sakamakon alherin ka,ka bar damuwa da yanayin rayuwar goɗiya,tunda kayi hkr na tsawon shekaru to haƙiƙa ribar ka akusa take,komi ya kusa zuwa ƙarshe,sannan sirrin cikin gidan nan ma ya kusa bayyana,duk ka zuba ido zakayi kallo kuma zakayi mamaki,abinda ka sani da wanda baka sani ba duka zasu fito fili,Ni zan tafiiii,kuma zan dawo kamar de yadda aka saba". Hamma me tsayi kande ta yi kafin ta lumshe idonta a hankali kuma ta kwanto a jikin mlm, maida hannunsa ya yi ya rungumeta idonsa na zubar da hawaye masu zafi,tabbas shi yasani dole wata rana abinda yake gudu ze faru,amma be ɗauka abin a kusa yake ba,ji yake kamar bayason wannan ɓoyayyen sirrin ya bayyana,inama wannan abin da suka binne ze iya zama sirrin da har abada baze bayyana ba,inama inama,amma ba yadda ya iya,shi yasani dole ne abinda yake gudu seya faru,yasani wata rana dole hakan zata kasance. Kallon kyakkyawar fuskar ƴar tasa ya yi wacce ta jiƙe sharkaf da gumi,jikinta duk ya saki,juyowa ya yi ya kalli inna wacce ta takure se sharbar kuka take,tunda aljanin kande ya fara magana ta shigo ɗakin,dan ta zaga ne sanda mlm ya shigo hannunsa riƙe da kande, fitowar ta ne ta gansu acikin yanayin da kande bata hayyacinta. Itama taji duk abinda kande ta faɗa ko ace iskanta ya faɗa. Shimfiɗera mlm ya yi,seda ta kai kusan magrib tana bacci kafin ta tashi a gajiye, jikinta duk ya mutu,akasalance ta kalli inna da Amo wanda suke zaune akan ta hannun Amo da carbi,se ja take tana zare ido,duk a tsorace take,kamar ace kyat ta fece aguje. Inna kuma hannunta riƙe da wayarta keypad ta kunna kira'a sun ajiye a gefe. Da sauri kande ta tashi zaune,tace subhanallahi inna karfe nawa ne,kallon juna inna da Amo sukayi kafin inna tace "karfe Shida da hamsin ne auta, ya akayi ne?,me za'a kawo miki kici?", saurin miƙewa tayi tana faɗin "innalillahi,inna garin yaya nayi bacci me yawa haka kuma baki tashe ni ba,wlh wani mahaukaci ne yaketa bina, kullum duk inda naje seya bini,ko dan ina bashi abin ci ne,yau ma har gida ya biyoni,nace zan duba ko kin gama abinci in bashi,ashe kwanciya nai, kai innalillahi,Allah sarki kirezi kilama ya tafi" tayi maganar a shagwaɓe kuma sak muryarta tun tana yarinyar ta kafin ta haɗu da lalurar iska. Kallon Amo inna tayi,itama haka,duk da cewa Amo bataji me kande ta ce ba sbd kunnenta,amma yadda kanden ta kwaɓe fuska cike da shagwaba yabata mamaki,balle inna da ta ji abinda tace da kuma yanayin yadda muryarta ta fita,cikin ɗan murna wacce ta fara kama inna tare da tunanin ko addu'ar su ce ta karɓu ta ce "mahaukaci kuma auta a ina kika samo sa ke kuwa?" Kamar an mintsineta tace "Allah wlh kuwa inna,wani kirezius ne ya mini ta kaska,duk inda na dire legediz dita seya ɗora tasa agun,bansan shi bafa, amma ya nanemin,duk inda naje yana biye,shine yau ya biyo ni harnan da alama tsumagiya ce ta fyaɗosa,dan be taba biyoni har gidaba se yau," ta dubi inna wacce jikinta ya yi sanyi murnar ta ta koma ciki ganin yadda ta kuma komawa kanden ta me kamar maza,ta kuma cewa "ya ake ciki ne tuffar dagus akwai tuwon ne na ɗan sanmasa ya lomata shima?,kila ma ya tafi yaganni shiru kamar an aiki bawa garinsu, Allah sarki kirezius" ta fada tana sakkowa daga kan gadon. Acen waje kuwa bayan mlm ya fita,da sauri ya leqa waje dan tabbatar da abinda aljanin kande yace,wayam ba kirezi ba alamarsa, jinjina kai Malam ya yi,tabbas wannan mahaukacin akwai ayar tmby akansa,amma tunda yake bibiyar yarinyar sa yasan dole da manufa,kuma dole ze dawo,yanzu dole shima yasaka ido sosai akan ƴarsa. * Niger state minna* _mariga way_ Tafiya suke amotar sunata mayarda zance akan yadda sace sacen mutane yazama ruwan dare,kawai se a ɗauke mutane ayi daji dasu kamar dabbobi,wasun su suna ganin lefin gwaunati ɗari bisa ɗari kan taɓarɓarewar tsaro,ga tsadar rayuwa kullum rayuwa daɗa ƙunci take,kullum talaka shine a wahala amma dan ɓacewar basira da rashin lissafi da talakan de za'ayi amfani asakasu su yaƙi junansu,su kashe junansu,hallau acikinsu ne ake samun waɗanda sunfi ma masu garkuwa da mutanen bala'i wato informants. Wasu suka suna ganin kawai mafiya aksarin kidnappers son zuciya da dogon buri ne yake sanya su faɗawa cikin harkar,sunyi nisa sunata tattaunawa akan matsalolin rayuwa,ba zato sukaji direbansu yaja wani wawan birki yana salatin duk da yazo bakinsa, faɗi yake "yau munshiga uku tamu ta ƙare kowa yayi ta kansa,se a sannan kowa ya lura da abinda ke faruwa agurin. Motoci ne iya ganine hange,duk an fitar da mutane an tarasu aguri ɗaya kamar shanaye,wasu mutane ne sun rufe fuskar su da baƙin abu,jikinsu sanyeda kayan sojoji,mashinansu kusan guda hamsin fake agefe daya,wasu mahaukatan bindigogi ne ahannun su,se fitar da mutane suke daga cikin motocinsu suna tattara su gefe ɗaya,cikin sanɗa direban wannan motar ta saulale ya fice daga motar yabar fasinjoji sunata sallallami,direban nan yana sanɗa acikin ciyayi yanason ya samu ya gudu,ba zato yaji bindiga akansa an ɗana masa ana cemasa ya miƙe ko a harbesa. Cikin tsananin firgita ya miƙe tsaye yana haɗa me bindigar da Allah karya kashe shi,wlh yanada iyalai da marayu wanda suka dogara da shi,kaɗashi akayi tare da sauran fasinjojin da ya kwaso har inda aka tara mutanen da aka fara kamawa,yana juyowa idonsa akan wanda ya sanya masa bindiga,cikin tsananin mamaki yaga ɗaya daga cikin Mutane da ya ɗakko ne, wanda dashi akayi ta zancen ƴan garkuwa da mutane,ashe shima ɗaya daga cikin su ne. Kusan duk motocin da aka kama acikin fasinjojin akwai kidnapper aciki,sune suka Sanar da ƴan uwansu nakan hanya cewar motoci sun taso da yawa,kasancewar ranar cin kasuwar mariga ne,har sukayi nasarar kame mutane da yawan gaske,mafiya yawancinsu ƴan kasuwa ne,wasu da kayan da zasu kai don cin kasuwar,wasu kuma da uwar kuɗaɗe ajikinsu don zuwa cin kasuwa,amma cikin hukuncin Ubangiji duk anyi garkuwa da su. Seda ƴan bindigan nan suka haɗa mutane masu yawan gaske,kafin suka kaɗasu zuwa daji,bayan sun amshe musu kuɗaɗe da kayan abinci,haka suka tasa ƙeyar jama'a da dama. Ga tafiya ba karama ba,wasu a hanya sukayi ta suma,wasu harbinsu akayi saboda sunyi yunkurin guduwa. Seda sukayi tafiya me nisan gaske wacce ta shafe awoyi da yawan gaske kafin su isa wani ƙaramin gari inda ƴan bindigan sukeda zama,haka aka dinga amsar numbobin iyalan bayin Allahn nan ana kiran su ana sanar musu anyi garkuwa da ƴan uwansu,duk wanda akayi cinikin sa haka za'a waresa gefe,haka suka dinga cinikin mutane kamar dabbobi. Wadanda ba a samu cikakken bayani agurin ƴan uwansu ba,da waɗanda sukace su basu da kowa suma aka waresu gefe,su nasu hukuncin na daban ne,mafiya yawansu saida sassan jikin su ake,wasu kuma kashesu ake,wasu kuma se ajuyar da tunaninsu suma su koma ƴan bindiga. ******* _United Arab Emirates _ DUBAI. _Durah jungle _ Dubai special force vanguard. Wasu manya manyan sojoji ne da hukumar soja ta dubai suka ware waɗanda ake baiwa horo na musamman,a wuri na musamman,durah jungle wani sansanin soja ne dake nesa da garin sosai,su waɗannan sojojin bakowane lokaci ake fita dasu aiki ba,duk wani aiki me mugun haɗari shine aikinsu,kamar shiga ƙungiyoyin manya manyan daba irinsu, ISIS, mafias,ko kuma manyan sindicates wanda suka gagari duniya,irin wannan aikin ake tura su domin kawo ƙarshensa,chief commanda RAYYAN RAHMAN,shine tsaye yana kallon yadda atisayen ke wakana, tabbas lokacin da yake jira ya kusa ƙaratowa,shi da wasu zaƙaƙwuran sojoji irinsa wanda suka wahala kuma suka bautawa ƙasar su,sune suka fitar da wannan reshen na sojojin sirri tare da goyon bayan shuwagabannin kasar na ƙwarai. Ofishin sa ya koma ya fara fitar da list na sunayen waɗanda za'a tura domin zama ɗaya daga cikin ƙungiyoyin dabar da sune a jadawalin su a yanzu,su waɗannan ƙungiyoyin sun gagari duniya ta fannoni daban daban,a kuma ƙasashe mabanbanta,acikin ƙasashen da za'a tura waɗan nan sojojin akwai Dubai ɗin kanta se phillipines,China,south Africa, Russia,Ghana da kuma linjeriya kasarmu ta gado🤣. _Nigeria,Kano state_ *Sannu kaji mamuda, jiki ya yi kyau ai alhamdulillah,kaida muka kawoka ranga ranga kamar zaka sheqa, baka fa san waye akanka ba,Allah sarki wata yarinya ce me shigar maza shigar ta ta gwanin ban dariya,ita ce tazo tace mana ga wani me baro cen ya faɗi,shine fa muka rankayo aguje ashe kaine,ai yarinyar nan ta temaka wlh,da wata ce guduwa zatayi taga mutum a kwance kamar bashi da rai,uhum kaide mamuda Allah ya kara afuwa,wai nace mamuda bakada ƴan uwa ne,ni har yau kwananka biyu amma banga kowa yazo da sunan dubiya ba da ga fanni ka?" "Wlh jabir kacika ɗan banzan surutu,haba mutum yana kwance bashida lfy amma ka sanya shi agaba se famar ratattako batu kake babu birki,sekace an buɗe dam din ruwa,haba dan Allaha" "Kaiko lurwanu daɗi na da kai kenan ka cika saka ido da yanƙwana mutum,haba kalli fa yadda ƴan matan cen suka kakkallo ni, se wani faɗa kake min acikin jama'a dan na tambayi mamuda ƴan uwansa,naga ai gsky na faɗa,tunda muka kwaso shi ranga ranga muka kawosa nan bawani daga nasa da sukazo da sunan duba jikinsa,kuma dan na tambaya shike nan nayi lefi haba du Allah du Annabi lurwanu". Se cecekuce samarin suke a tsakaninsu,wanda aka kira da mamuda kuwa yana kishingiɗe akan gadon marasa lafiya ya lumshe idonsa,ƙala be ce musu ba amma duk abinda suke fada yana saurare,har suka gama faɗan nasu kuma suka koma fira. ..... Moscow, Russia.... Wani irin gidane cable front acen cikin wani guri wanda ya yi nesa da cikin garin Moscow ɗin,kusada wani madedecin tafki,wasu manyan security ne suke shawagi agurin,duka ƙofofin gidan masu password da thumbprint ne,wasu manyan motocine kusan guda goma sha ɗaya suka parker a waje gidan,biyar agaba biyar abaya,se wata golden lemo a tsakiya,kusan atare ƙofofin motocin suka buɗe banda ta tsakiyan wacce ta kasance lemo. Kusan mintuna asirin kafin aka buɗe daya daga cikin ƙofofin lemo din,wani ingarman namijine ya fito daga cikin motar,jikinsa sanyeda wasu simple Pakistan wear farare tas,se wani madedecin makawuya daya naɗa akan hular kansa wacce take baƙa, ƙafarsa sanye cikin takalma sau ciki baƙake,hannunsa sanyeda wani danƙareren agogo me matuƙar tsada,fararen yatsunsa sanyeda wani zobe baƙi me fuskar zaki,ya riƙe wata sanda kamar da gold me shegen kyau se walwali take,saurin buɗe masa lema akayi saboda snow ɗin da ke sauka agurin. Fuskar mutumin kadai idan ka kalla seka kuma kallo,mutum ne majiyi ƙarfi, ingarman namiji ne sosai,fatarsa har wani yello take,fuskarsa cike da beard me ɗaukar idon me kallo,yanada kyau me suna kyau*wild king Rolex*kenan,tafiya ya fara cikeda izza irinta maza majiya ƙarfi,duk inda ya gifta se securityn wurin sun rungume hannunsu ɗaya a ƙirji tare da sunkuyarda kansu. Yana zuwa gaban main entrance na shiga gida kofar tayi scanning na idonsa,bakinsa ɗauke da fito ya danna kansa cikin falon wanda ya ɗauki ɗumi me daɗi da ƙamshi,wata matace zaune fara me dogon gashi ta juya baya,hannunta ɗauke da wata ƙatuwar mage fara me kyau. Takawa yake yana nufar inda take zaune,bakinsa yana fito,yana isa inda take gaban wasu duwatsu masu ci da wuta irin room heater ɗin nan na jikin bango amma wannan wasu irin duwatsu ne masu kyau da sheqi kamar normal dutse suna fitar da zafi de ɗumama daki. Hannu yasa yana shafar dogon gashinta me kala biyu baƙi da roɗi roɗi kamar fari kamar milk,ko gezau bata motsa ba,ya cigaba da shafar sumarta har zuwa dogon wuyanta,hannu yasa ya juyo da kanta da ƙarfi ya juyo da fuskarta...ba zato wayar ɗauko rahoto ta faɗi saboda ganin fuskar matar nan.. Jama'a kande ce faaaaa, a Moscow😱😱😱 End of free pages kuma book 1. ************************* Shin menene ainahin asalin kande? Wanene wannan mighty wild king Rolex din? Wanene chief commander RAYYAN RAHMAN? Wani lokaci yake jira? Wanene mamuda me barrow wanda ke kwance a asibiti? Wanene general Asim? Wanene mahaukaci kirezi? Wai ma suwanene mlm habu da inna? Wani sirri suka sani akan kande,wanda aljanin kanta yake yawan nanatawa? Meye alaqaar da aljani yace akwai tsakanin kande da kirezi? Wani mission ne RAYYAN RAHMAN ze tura special force ɗinsa? *Duka wannan amsoshin suna dunƙule acikin littafin kande kashi na biyu wato book 2.* # love # hate # crime # black money # soccery # betrayal # illegal trafficking # smuggling # comedy # romance # momsani✍️ _Ina masoyan MOMSANI ina wanda suka daɗe suna jiran wnn zazzafar tafiyar ta labarin kANDE,zaa kanwar maza,zaa soja,zaa kAND,to albishirinku yaude Allah ya nufa kuma yakawomu acikin wnn daddaɗan labarin me suna kANDE,bakijiba ne nace kANDE zaa tomboy_ _shin dake akayi daddaɗar tafiyar nan ta labarin Asma'u da Muhammad Mahii ,SAURAYIN YAYATA,kin karanta labarin SIRIKATA,ko a'a,to albishirinku yauma momsani tasake dawo muku da wani daddaɗan labarin me dogon zango wato kANDE THE TOMBOY,in Sha Allah hajiyata bazakiyi nadamar karanta wnn labarinba_ _zazzafar tafiyace me ɗauke da zazzafan darasi,tare da nishadi,haɗi da ban tausayi,tattareda zazzafar soyayya,gamida cin amana dakuma butulci,bazan cika baki ba,bakuma zan cikaku da surutu ba,amma in Sha Allah karki bari ayi wannan mysterious journey din batare dakeba_ *kANDE littafin kuɗi ne akan farashi me sauki, Naira ₦400 kacal,idan kin shirya ki tura kudinki fa wnn asusun0591819457 SADIKA IBRAHIM gt bank,seku tura shedar biya ta wnn layin 07088282153,se na jiku masoya,i promise u will never regret* Masoya ƴan amana Sena jiku,mom sani tana jiran ganin kauna daga gareku,love you all😘