*AUREN WATA UKU.!* *01* *©️Sameena Aleeyou… * _Rayuwa tana zuwa ma bawa ta fuskoki daban daban cikeda jarabawa had’ida K’alubale. Ashe wasu mutanen Akan k’addarosu cikin rayuwan bawa ne matsayin jarabawa. Ashe Akan jarabci ‘ya’ya da nasu iyayen kaman yanda wasu ‘ya’yan ke zamtowa jarabawa ga iyayensu. Shin su waye ka tashi ka sani matsayin ahali.? Shin a ina k’alubalen take.? A ina gwagwarmayar take..? Tabbas wasu mutane da suka zamto jigo na rayuwar d’an Adam ka iya zama babban jarabawa a gareshi. Shin muna hak’uri da jarabawarmu ko kuwa dai bijirewa muke ga d’inbin rahamar Ubangijinmu garemu..? Bari mu tsunduma cikin labarin AUREN WATA UKU dan jin yanda ta kaya tsakani wasu ahali_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.! "Kano State, Nigeria." Gida ne da za’a iya kiransa da gidan gandu sakamakon ahali guda dake rayuwa cikin gidan. K’ofofi ak’alla kuwa zasu kai takwas koma sufi. Yayye da k’anne dama makusanta na kusa wanda sukeda hakkin mallaka suke rayuwa cikin gidan. "D’aya daga cikin k’ofofin anyi cincirindo ana kallon abinda ke wakana. Dama dai abin kallo, magana harma da tsegumi basa kad’an a gidan yawa." Ba komai akai cincirindo ana kallo ba sai akwatunan da ake fita dasu sahu sahu matan da sukazo kwasan kayan suna tofin Allah tsine. "D’aya matar ta kuma janyo k’aramar akwatin da k’arfin gaske kaman zata tsinke hannun jakan. Fad’i take “Alhamdulillah Allah Ya tsami d’anmu daga k’angin gori.. Me za’ayi da gayyan tsiya. Wllhi d’anmu yafi k’arfin wann sharan. Yaro d’an dangi, inyi.. Ina dalili.? Yarinyar da kowa Ya kwana da sanin sau babu adadi kenan ana amshe sadakinta. Kawai sai shi Zubairu sabida baida mafad’i mu bari Ya aureta.. Toh wllhi sam bazata saku ba wai bindiga a ruwa ehe.. Banda ma dai bani k’asa ina can birnin Saudiya da ina zan bari wann zancen banzan yayi nisa har akaiga kawo lefe..?” Ta d’anyi fasali tana kuma wangale bakinta yanda hakwaran makka har biyu suka bayyana cikin bakin nata, ta ko wani angle walwali yake." “Aure dai mun fasa shi bama gayyan tsiya cikin zuri’armu..” Ta k’arashe d’aya matar da suke tafe tare tana tayata da fad’in “Wann gaskiya ne Hajjaju. Ai dama cewa nai kina dawowa za’a wargaza komai dama ganin babu idonki ne.” Hajiya Dudu ta cab’e “Toh na dawo sai naga uban da zai d’aura wann gantalallen auren..!” Ta k’arashe k’iiii tana janyo trolley guda. Wata mata ce da tin shigowan matan take sharb’an kuka an rasa mai bata baki ta isa da sauri ta rik’o hannun wann gabjejiyar matar. Cikin muryarta dake fita da kyar sabida kukan da taci take fad’in “Hajiya Dudu dan Allah dan Alfrman manzo Sallallahu alaihi wasallama ki rufa min asiri.. Kar ki bari a fasa auren nan.. Ki ceci d’iyata dan Allah..” Bata kai aya ba matar ta fincike hannunta tana ci gaba da huci had’ida aika mata muguwar harara ta gyara zaman mayafinta “Ke Suwaiba bari kiji na fad’a Miki wllhi idan ‘yarki itace autan mata Zubairu bazai kwashe ta ba.. Uban wa yasan abinda yasa ko wani manemi ke gudun ‘yarki.. Haka kawai a tashi a lik’a ma namu d’an.. Toh gari da yawa ga ‘yammata birjit masu jini a jika ba irin ‘yarki da ta girma ta rik’a ta tsofe gida ba.. Ke bari ma kiji cikin dangi zamu samar wa Zubairu matar aure dan gida bai k’oshi ba baza’a kai waje ba. Wajen ma ma bola shara irin ‘yarki..!” Tana ida fad’in haka ta fincike hannunta tana fad’in “Zinaru muje kinji kafin tsautsayi Ya hau kan kayan nan dan wllhi abu d’aya yayi ciwo tass sai an lale an biya.! Daga nan ma gidan Hajiya Atine muka nufa da kayan nan.. Ayyiriri D’anmu zai angwance da ‘yar dangi ba ‘yar bakin ruwa ba..” Haka suka fice suna guda suna watsa habaice habaice. Matar da suka ambata da Suwaiba ta duk’a nan wajen tana cazgan kuka hannayenta biyu aka fad’i take “Na shiga uku ni Suwaiba Ina zan saka raina inji sanyi da wann bala’ai..” Wata mata da ta d’an data dan ga dukkan alamu tafi ta tsugunnen a haife itace tai karaf ta cab’i zancen nata “Ohni Tani naga ikon Allah.. Aure ace ak’alla goma kenan ana karban sadaki ana anshewa idan ban b’ata lissafi ba.” “Yaya bai Kai goma ba..!” Suwaiba dake duk’e wajen ta fad’i cikin gunjin kuka. "Tsaki Tani tai “Kayi magana ace kishi, na baki shawari ki d’auki yarinyar nan ki kaita baki ruwan Aljanun ruwa ne suka aureta amma kink’i ji kink’i d’aukan shawarina Suwaiba.. Waima har zigaki ake ana ce Miki ni ce nan nai ma ‘yarki asiri na hanata aure.. Toh ai idan ma asirin nai mata yazo gidan sauk’i sai ki d’auki k’afa kije gidan malamai a kwance miki sammun..” Ta kece da dariya had’ida rangad’a gud’a “Ayyyiriri nanaye Ayi dai mu gani.. Mun zuba ido mun baje kunnuwa..” Ta k’arashe tana gyara d’aurin zaninta da Ya karkace." Su kaw sauran al’umman gidan dake tsaye suna bama idanunsu abinci tuni Sun soma tsegunta lamarin. * Cikin tsanaki ‘Yanmatan guda biyu ke takunsu gefen kwalta. Kallo guda zakai masu ka fahimci ‘yanuwan juna ne sakamakon kamanni ta fuskan halitta da su biyu din suke dashi. "Babban zata Kai kimanin shekaru 31 a duniya amma bazaka fahimci hakan ba sabida kyaun kira da Allah yayi mata. Sama bazakai zaton ta girme ma k’aramar wacce keda kimanin shekaru 20 a duniya har sai ka kula sosai. Sun karyo kwanan layinsu kenan suka hango wasu mata guda biyu jikin ginin wani gida Wanda garun baida tsawo sann duk ya murmushe abinka da ginin bani bani, idan da zakai tsalle d’aya zaka iya kamo katangar." Wata mata ce da d’aurin k’irji daga nan cikin gidan ta dafe katangar ta lek’o suna tattaunawa da matan nan guda biyu dake daga waje. Aiko matar dake lek’en katangar da d’aurin k’irji tana hango ‘Yanmatan ta soma yima sauran biyun magana a hankali tanai masu nuni da ‘yanmatan da idanu. Tanai masu zindensu. Gaba d’aya suka juyo suna duban ‘Yanmatan. Sun kusan cimmasu k’arama daga cikin ‘Yanmatan tace “Adda Kinga magulmatan matan nan wllhi nasan bazai wuce zancenmu suke ba. Jibi yanda suke kallon mutane kaman mayu. Su ko kunya ma basa ji da girmansu da aurensu suna halin banza. Mtsw Allah ya kyauta halin matan unguwan nan. Mazajensu suna ficewa suma suke tafiya yawon gulma.” "Babbar ta murmusa tace “Ke wa yace miki gulmarmu suke.. Nidai dan Allah bana san tashin hankali Khulsum, nasan halinki sarai.. Gaisuwar fatan baki ya wadatar..”" Khulsum tace “Wllhi Adda ko kaffara bazanyi ba zancenmu suke. Tinda muka karyo layin nan suke mana kallon k’asa k’asa kuma wllhi mata tai mana zancen banza zataji babu dad’i tinda dai matan unguwan nan basu San su rik’e girmansu ba.” Babban ta d’an tsare fuska “Ya isa Khulsumu. Kar ki sake cewa komai. Na san halinki sarai.. Kar ki ma wata mata magana cikinsu balle su samu abin tofawa.” Khulsum tace “Ahaf wllhi Adda kema kinsan halina ba yanda za’ayi mata ta gaya mun bak’a na shanye ban rama ba. Ai sai nayi ciwo ma.. Tab.!” Ita dai babbar bata kuma cewa komai ba sai girgiza kai da tai dan haka nan take ba mai yawan hayaniya bace. Koda suka iso daidai yanda matan suke Babbar ce ta bud’e murya ta soma gaishesu cikeda girmamawa. Suka amsa yayinda Khulsum ta bisu da idanu. Har sun wuce d’aya matar ta bud’e murya tace “UMMULKHAIRY..” Daidai lokacin babba daga cikin ‘Yanmatan ta juyo tana dubanta “Na’am Maman Sahal..” Matar ta murmusa tace “Ya batun aure ne wai.. Shiru shiru har yanzu ga Ummikhulsum har ta taddoki kodai tare za’a had’aku ne.?” "Kafin Ummulkhairy ta kaiga bata amsa suka sinkayo muryar Khulsum tana fad’in “Maman Sahal nace ba, idan gadon katako kikayi, to dan Allah ki canza kiyi na k’arfe kar ruma ya kama ko tsari da gara suci..”" Maman Sahal sai tai murmushi tana neman maida abun barkwanci “Oh su Khulsumu ba’aji ayi shiru.. Ai tambayan Alheri nai ba sai kin fad’a mun bak’a ba.” "D’aya matar dake lek’en Katanga tai karaf tace “Aff Lallai maman Sahal jaridu suna wuce ki kwanan nan, bakida labari har lefenta fah an kai kwanaki uku da suka shige.”" Ummulkhairy ta had’iyi abinda ya tokare mata mak’oshi had’ida aika ma ‘yaruwarta ummukhulsum mugun kallo. Ta shiga janyo hannun Khulsum zasu shige Khulsum ta kuma dogewa dan bataji bata mayar ba kaman dai yanda Maman Sahal tace. Khulsumu ta murmusa tace “Kinji abokiyar gulmar taki ta baki amsa.. Ina kika makara baki sai jaridar ba.? Ko kudin sayan ne bakida shi na ranta Miki..?” Nan fah Maman Sahal taja da baya ta Ware idanu tana nuna Khulsum da d’an yatsa “Ke kul wllhi ahir d’inki.. Koda wasa kar kimin rashin kunya ni ba sa’arki bace..” "D’aya matar ta bud’e murya tace “Wai dama Maman Sahal wa ya aikeki dogon hira da wann maras kunyar yarinyar.. Yarinyar da sam batada ta ido, ba ganin kowa take da gashin ido ba. Tanaji tana gani mata masu hankali ma yanzu ba auruwa suke ba ballantana ita maras kunya wacce bata mutunta kowa. Bazata d’auki darasi akan Yayarta ba. Kowa yayi shaidan Ummul a unguwar nan batada abokin fad’a tun tasowarta amma gashi nan ta kasa auruwa.. Sai anzo kaman za’ayi aure zance ya lalace. Ita wann kam inaga ba jinga ba saidai tayi bandaro ma.. Dan idan Har ba’a d’auki mai hankali ba banji za’a d’auki fitsararriya..”" Khulsumu kaw kafin matar nan ta rufe baki ta bata amsa da fad’in “Ai tinda mata gantalallu irinku basu rasa masu kwasan su ba bana Jin akwai kalar macen da bazata samu mijin aure ba.!” Haba Nan fah Maman Sahal da gang d’inta suka nufo Khulsum Ummul na tsakiya tana janye Khulsum tana bawa su Maman Sahal hak’uri Wanda kaman zugasu take. Fad’i suke sai sun cire ma Khulsumu rashin kunyarta. Itama Khulsum d’in sai tsalle take tana fad’in dik matar da ta fasa dukanta ta raina Wanda take zaman aure k’ark’ashinsa. Ana tsaka da wann kacaniya suka hango mata da akwatina nik’i nik’i aka sun dososu sahu sahu sai bala’i suke suna fad’in d’ansu bazai auri annoba ba. Aiko nan suka ja wani wawan birki sakamo hango su Maman Sahal da k’awayenta d’aya da d’aurin k’irji sai tsalle suke yunk’urin cakumo Khulsum ga Ummulkhairy a tsakiya sai kuka take tana rok’onsu suyi hak’uri.. Garin janye Khulsum akaI watsi ma Ummulkhairy da mayafi ya fad’i gefe had’ida fincike mata d’ankwali tuni sumarta ya bayyana. Salallami suka fara Hajiya Dudu tana masu nuni da su Ummulkhairy tana fad’in “Kunga abinda nake fad’a maku ko. Allah dai ya ceci Zubairu bazai yanka kazar wahala ba balle ya fige. wann ba matar aure bace. Sauran matan suka shiga salati suna fad’in Sun shaida. Hajiya Dudu ta kuma danna wayarta a kunne tana fad’in “Halo kai Zubairu nace wai kana ina ne haka da ka kasa k’arasowa..? Toh maza maza ka iso.. Alhamdulillahi tinda kana kusa ka gane ma idanunka. Kai sauri nace Jarababben banza..!” Tana Ida wayan taci gaba da fad’in “Alhamdulillahi ai ni naji dad’i gwara dai yazo ya gane ma idanunsa.. Da banyi da gaske ba bazai bari azo a amshe kayan nan ba.. Toh gwara ya k’araso ya gane ma idanunsa. Me za’ayi da mace mai dambe a titi..!” D’aya daga cikin k’awayen Maman Sahal kaw tana hango su Hajiya Dudu da akwatuna ta saki shewa tana gud’a tana jero baitukan ayye mama ayye mama har zuwa da aure yana raka aure da na biki mun tafi tare. Haba nan fah waje ya kuma kacamewa kan kace mai anyi caa a wajen. Mota ce k’irar Civic 2000 ta karyo layin hakan yai daidai da juyowan Ummulkhairy wacce idanunta ke zubda ruwa. Karaf idanunta suka kafe cikin na Zaubair dake rolling glass din mota. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *02* *©️Sameena Aleeyou… * Zubair yai parking idanunsa kan Ummulkhairy da tun isowar motarsa wajen ta kasa komai sai hawaye dake bin k’uncinta. Ba yau ne rana na farko da aka kawo sadakinta aka amshe ba balle wani Kayan lefe saidai a yau d’in taji wani irin abu da bata tab’a ji ba a baya. Ta sani ba wai son Zubair take ba sabida zata iya cewa zuciyarta ta k’ek’ashe da batun wani aba mai suna soyayya. Batajin ko a gaba zatayi wani abu wai shi soyayya. Tayi na’am da aurensa ne dan cikan burin mahaifiyarta kaman dai sauran aurarrakin da ake saka mata ana fasawa. Dikda hakan bazata bataji ciwon abinda ya faru cikin zuciyarta ba. Ta zaci wann shine na k’arshe. Ta zaci komai zaizo k’arshe. Ta zaci burin mahaifiyarta zai cika daga k’arshe. Sann kowa zai salama saidai abun ba haka bane. Da alama ita dai wann shine k’addararta bazata tab’a aure ba kaman yanda mutane ke fad’i akanta. Lumshe idanunta tai hawaye masu tsananin dumi suka gangaro mata. Shin yaushe ne komai zai kare.. Yaushene komai zaizo k’arshe.? Tambayar da ita kanta bata da amsar sa. Khulsum kaw ko tsayawa kula su Hajiya Dudu batai ba balle ta kula da Zubair Wanda bai jima da k’arasowa wajen ba. Sai zuba ruwan masifa take tana nuna su Maman Sahal tana fad’in duk macen da bata fasa kokawa da ita bata haifu ba. K’arasowan wasu matasa sukai k’ok’arin raba fad’an. Sai huci Khulsum take tana gyara mayafinta. Ta d’auki mayafin Ummul da akai jifa dashi can gefe ta rufa mata. Ta shiga janyo hannunta tana fad’in “Adda Ummul muje aurenki kuma in sha Allah ba fashi Akan idanunsu za’ayi saidai mata ta mutu..” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Hajiya Dudu tana fad’in “Aure ba fashi a gidan uwarki.? Mai za’ayi da mace mai dambe a titi..” Ta jiyo tana duban Zubair da ya kasa koda bud’e k’ofar mota balle ya fito “Ka daiga abinda nake fad’a maka ko.. Ka gani da idanunka.. Allah ya ceceka bazakai asaran sadaki ba.. Yo wann ai asaran sadaki ne.. Dama da na fada maka wann yarinyar ballagaza ce. Yanzu zaka yarda da batu na. Aure kaida wann ballagazar ko a k’iyama ehe..!” Ta k’arashe tana jefa kit d’in hannunta cikin boot d’in motar da tuni sauran matan sun dire akwatunan hannayensu ciki. Har lokacin idanun Ummulkhairy a k’asa suke hawaye d’aya na bin d’aya. Gaba d’aya sai jikin Khulsum yai sanyi musamman da taga yanda Zubair ke aikama Ummul wani irin kallo da ta gaza tantance na tsana ne ko na mamaki. Sunaji suna gani Hajiya Dudu ta k’arashe maganganun ta suka shige mota da sauran matan. Tuni Zubair yaja mota Sun bar wajen saima k’ura da ya bud’e su Ummulkhairy dashi. Jiki a matuk’ar sanyaye Khulsum ta kamo hannun Ummul. Saidai kafin tace wani abu Ummul ta janye hannunta ta nufi gida cikin saurin wani kukan na kuma b’alle mata. Jiki a sanyaye Khulsum ta take mata baya. Suna shigowa gidan suka tadda mahaifiyarsu zaune dirshan tsakar gidan sai cazgan kuka take. Ga Mama Tani wato kishiyar mahaifiyarsu kuma uwar gida a wajen mahaifinsu tayi bak’e bak’e a tsakar gidan sai ‘yan wak’e wak’enta na habaici take. "Ummul ta k’araso a sanyaye ta duk’a gaban mahaifiyarsu dake cazagan kuka. Jiki a sanyaye, murya na tsananin rawa Khairy ke fad’in “Umm..Umma.. Umma..” Kuka ya hanata ci gaba da magana." Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa. Cikin kuka take duban Ummulkhairy tana nunata da d’an yatsa take fad’in “Ummul na gaji.. Wllhi na gaji.. Na gaji dake.. Na gaji da wann fashe fashen auren da ake akanki.. Ummul na amso Miki rubutu.. Na Kai sunanki gaban Malamai an baki rubutu an miki addu’o’i.. Ke k’arewa har ruk’iya an miki.. Ummul anya ke ‘yaradam ce..” Ta k’arashe tana kuma fashewa da kuka. Yayinda Kan Ummulkhairi ke duk’e kukanta na k’aruwa da Jin kalaman mahaifiyarta. Khulsum kaw girgiza Kai kurum take tana duban mahaifiyar tasu cikeda mamaki Jin irin kalaman dake fitowa daga bakinta. Ita kaw Mama shewa tai harda tafi kaman ta samu tv haka take dubansu. Sai dariya take cikeda nishad’i. Khulsum ta aika mata mugun kallo kafin ta maido da dubanta ga mahaifiyarta da kuma ‘yaruwarta. “Umma dan girman Allah ki daina irin wann kalaman Akan ‘yarki.. Ke fah uwa ce Umma..” Khulsum tace ranta na tsananin sosuwa. A hasale mahaifiyarsu ta d’ago tana fad’in “Ke dalla can rufe min baki.. Mai kika sani..? Ki bari randa kika zama mahaifiya irin k’addarar da ya samu ‘Yaruwar ki ya samu d’iyarki sann ne zakiji ciwon da nake ji.. Wayyo Allah.. Wayyo ni Suwaiba laifin mi nayi aka jarabceni da ‘ya irinki Ummul.. Ke ba wani tawaya bane tattare dake d’an hasken nan baki rasa ba. Ke duk wani abin da mace zatai tink’aho dashi daidai gwargwado Allah ya baki amma a rasa Wanda zai aureki kowa da yazo sai Ya gudu.. Haba Ummul..!” Ta kuma fashewa da wani kukan.. Idan da sabo sun Saba da dramar mahaifiyarsu. Khulsum ta girgiza Kai. Tinda aka soma amsan kud’in auren ‘yar uwarta Ummulkhairy ana fasawa cikin damuwa da tashin hankali mahaifiyarsu take. Batada da burin da ya wuce taga Ummulkhairy tayi aure ta bar gidan ko ba dan komai ba sai ko dan gori da maganganu da take fuskanta Kama daga kan Abokiyar zamanta har izuwa kan ahalin gidan dama sauran jama’an unguwa. Mahaifiyar Ummulkhairy ta kasance irin mutanen nan ne masu saka damuwan maganganun mutane a ransu. A akasarin lokuta mutane suna mata kallon sakarya wacce batada wani wayo ko cikakken hankali. Sann tin Ummulkhairy tana k’arama taci burin ta aurar da ita da k’anan shekaru saidai Allah bai nufa hakan ba. Haka zatai mata wanka tai mata ado tin tanada k’ananan shekaru taita mata wak’e tana karanto baitika tana mata rawa tana fad’in saura k’iris ta aurar da ita saura k’iris ta kaita d’akin miji. Koda Mama kishiyarta zataita yab’a mata maganganu da fad’in ta jira dai taga girman ‘yar tata sam bazata tab’a tankata ba. Umma Ta kasance irin mutanen nan ne masu san Barkwanci Wanda kowa ya mata wann shaidar Wanda hakan kesa wasu ke mata kallan shashasha a akasarin lokuta. Ko fad’a Abokiyar zamanta ta tareta dashi wasa take maidashi Sam batada abokin fad’a kaf unguwar balle gidan. Hakan yasa halinsu itada Khulsum yasha bam bam. Domin kaw albasa batai halin ruwa ba. Dukda kuwa cewa Ummulkhairi ma bata dauko barkwancin ba. Sai sanyi wann kuma wajen mahaifinta ta dauko. Burin Ummulkhairi shine cikan burin mahaifiyarta. ta samu mijin da zai aureta koda bata sonsa zatai hak’uri ta zauna dashi dan burin mahaifiyarta ya cika. Burin mahaifiyarta shine Ummul d’inta tai aure ta tafi d’akin mijinta. Mahaifiyar su Ummulkhairy ta kasance itace mace ta biyu a gidan mahaifinsu. Matarsa ta fari itace Mama Tani yara uku gareta kuma duk sunyi aure suna d’akin mazajensu. Badi’a itace babba sai Salima sann autarta wacce Ummulkhairy ta girme mata da shekaru uku itama tuni tayi aure tana d’akinta. Autar Mama tani sunanta Azeema. Mama ta kasance d’aya daga cikin matan unguwar Wanda basu da aiki sai aibata duk macen da Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure ko mutuwar aure. Nan zakaji bakin Mama tana alfahari tana fad’in ita nata yaran kaf suna d’akin mazajensu kai kace wayonta ne ya kawo hakan ko dabararta. "Mahaifinsu baida wani karfi saidai basu rasa abinda zasu saka bakin salati, saida manja da mangyada yake a kasuwa dukda dai jarin ba wani mai yawa bane amma sunfi k’arfin abinda zasu saka a bakin salati daidai talaka. JINKIRIN auren Ummulkhairy ba shine ke tada hankalin mahaifinsu ba kaman yanda ake maganan aure magana yabi iska. Dukda ya kasance Dattijo kuma mai k’ok’arin danne damuwarsa ya fawwala wa Ubangijinsa lamuransa can k’asan zuciyarsa na damuwa da al’amarin ‘yarsa Ummulkhairy saidai Sam baya nuna hakan. Kullum cikin cewa yake Allah ne bai nufa ba. Ga manema Sam basu fasa nemanta ba domin kaw d’iyarsa tubarkallah ce batada makusa saidai ace d’anadam tara yake dama bai cika goma ba. Yayi imani lokacinta ne kawai baiyi ba." Gyara zamansa yai yana sauraron kukan da Umma ke ci gaba da yi tana fad’in “Abban Ummul dan girman Allah ka nemo min mafita wllhi bansan ya za’ayi na sake fuskantar mutanen unguwar nan ba. Toh ma da wani fuska zan sake fita ana nunani ana k’irga fashin auren Ummul da akai.. Dan Allah ka nemo min mafita Wayyo ni Suwaiba..” Ta k’arashe tana kuma rusa wani kukan. "Abba ya girgiza Kansa, ya kasance mutum maras San hayaniya kaman dai ‘yarsa Ummulkhairy. Shi irin mutanen nan ne da zakai abu su kauda idanu suyi kaman basu gani ba sann irin mutanen nan ne masu nuna kulawa da k’auna kan duk Wanda Allah ya hukunta kasancewarsu tare Kama daga iyalansa har zuwa kan ‘Ya’yansa da danginsa dukda kuwa k’annensa dake zaune cikin gidan basu d’aukesa bakin komai ba hasalima gaba suke dashi. Hakan baisa ya fasa masu nasiha da wasilci da zumunci ba." Cikin b’acin rai ya tsame hannunsa daga cikin kwanon tuwon dake gabansa ya katse Umma da fad’in “Haba Suwaiba! Ya isa haka nan.. Shin yau ne aka fara amsar lefen Ummulkhairy ko sadakinta..?” Batace komai ba sai gunjin kuka da take ci gaba. Ya kuma girgiza Kai “Toh tinda ba yau bane na farko sai ki kwantar da hankali dan na tabbata bazai zama na k’arshe ba tinda dai kink’i amincewa ‘yarki ta koma makaranta tai karatu kaman yanda ita Ummul d’in ke so.” Cikin zuban hawaye ta d’ago tana duban mijin nata “Yo wani karatu fisabilillahi .. Aima shekarun ta Sun wuce shekarun zaman aji.” “A ina kika tab’a ji an girma ma neman ilimi Suwaiba..? Waima dakata Suwaiba. Da kika damu kika daga hankali duka nawa Ummul d’in take ne..?” Umma ta dago a zabure jin yace nawa Ummul d’in take. Tai karaf tace “Ta fah haura talatin Abban Ummul.” Taci gaba “Yo wani ilimi zata nema ya wuce ilimin zama a gidan miji da naketa k’ok’arin bata.. Allah na tuba abu kaman jifa ko sa hannu.” Abba ya kuma katseta “Kinga Suwaiba na rabaki da wann gurb’ataccen tunani.. Ki je kina jefa kanki cikin damuwan abinda Allah bai d’aura Miki ba.. Ko an fad’a Miki bansan kina amso ma Ummulkhairy Neman Taimako bane.. Nasan komai kawai ina kauda ido ne ina Miki uzuri.. Amma ki sani kar kawar da idanun da nake bana magana yasa kije ki auka ga sab’awa mahaliccinki kiyi shirka.. Ki natsu ki san mai Kike ciki.. Allah yana sane da duk abubuwan da suke faruwa.. Addu’an da zaki mata Har sai yafi na Wanda zaki saka wani ya mata domin kaw ke mahaifiyarta ce.. Idan har da gaske so kike tai auren kaman yanda kikaci buri. Sai ki rage bacci ki tashi cikin dare ki Kai kokenki ma Ubangijin duka. Ki zubda hawaye a yanda zuban hawayen zai amfani domin kaw wajen Allah ne hawayenki keda amfani ba mutanen da zasuyi murna da ganin hawayen naki ba. Haba Suwaiba kiyita korototo kina kin shiga uku..? Da irin wann korototo da ambaton uku da kike ma kanki toh fa babu abinda zaki gani sai ukun..” Ta kuma kamo bakin zani tana share hawaye “Haba Abban Ummul dan Allah ka fad’a alkhairi..” “Kece zakiyi ma kanki karatun ta natsu ki dinga fad’in alkhairi gameda ‘yarki ko dan rayuwarta ta inganta. Domin kuwa su ‘ya’ya amana ce Allah Ya bamu kuma za’a tsaida mu a tambayemu akansu ranan gobe.” Ya k’arashe yana mai janyo kwanon tuwon sa. ** "A can d’aki kuwa Khulsum ce ta duk’a gaba ga Ummulkhairy, tayi zaman rak’umi tana fuskantar ‘yaruwar tata da tin shigowarsu gidan take aikin abu guda wato kuka." SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *03* *©️Sameena Aleeyou… * "Cikin gunjin kuka Ummul taci gaba “Mai kuma zaki fad’a mun Khulsum.. Ba dai kinyi abinda kike so ba kin tari matan nan da fad’a har Zubair ya iso ya taddamu a haka.. Toh me kuma yai saura tinda gashi ko wayata bai d’agawa.. Khulsum, Nifa burin mahaifiyata kawai nake son cikawa..!” Ta k’arashe wani kukan na taso mata." "Khulsum ta girgiza Kai “Adda Ummul dan Allah ki saurareni.. Wllhi mutumin nan bai cancanceki ba.. Ba son gaskiya yake Miki ba.. Da ace son gaskiya yake Miki da ya baki dama ya saurara daga b’angarenki, amma baiyi haka ba ya hau kan dokin fushi..”" “Har akwai Wanda ya cancanceni ne Khulsum..?” Tai maganar tana nuni da kanta cikin rawar murya irinta mai kuka. Khulsum ta girgiza Kai “Dan Allah kar ki bi maganganun Umma da mutane.. Kar ki kaskantar da kanki Adda Ummul.. Wllhi kin wuce gaban duk mazan dake fasa aurenki.. Kimarki da ajinki ya wuce nasu. Shima wann zubair din bai cancanceki ba shiyasa ya kasa ganin kimarki kaman dai sauran.” Ummul tai murmushi mai ciwo “Watak’ila banida wani kima da gaske Kulsum.. Watak’ila abubuwan da mutane ke fad’i kaina gaskiya ne.” “K’warai kuwa Ummul mace mai shekarunki batada wani kima matuk’a ba d’akin mijinta take ba..!” Muryar Ummansu ya katsesu wacce tai tsaye tana sauraron tattaunawar yaran nata. A tare suka d’ago suna duban Umma dake aika masu mugun kallo tana huci. "Khulsum ta lumshe idanunta had’ida furzar da huci “Umma wai dan Allah meyasa Baki saka farin cikin yaranki a farko.. Mutanen nan fah tuni sunzo Sun amshe kayansu, wllhi ko Zubair baizo ya tadda Adda Ummul na rabon fad’a ba bazasu bari ya aureta ba tinda sunyi furuci kuma sun amshe lefensu.. Haba sai kace ana Neman Kai da ita.. Dik anbi an tsangwameta a gida da waje duk bata huta ba.. Umma auren nan fah ba’a ce yana cikin cika cikan musulunci ba.!”" Umma ta danna mata dak’uwa “Kinci ubanki Khulsum.. Idan baya cikin cika cikan musulunci ai sunna ce mai k’arfi… Ke baki San ko gawan mace mai aure yafi daraja ba.. Cikan mutuncin mace shine a ganta a d’akinta..” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Kina jina idan baki daina korarwa ‘yaruwarki mazajen aure da wann bak’in Zuciyar naki ba wllhi kinji na rantse zan saka k’afar wando d’aya dake.. Maimakon ki duk’afa Neman naki mijin auren kin tsaya kina lalata na ‘yaruwarki koh.. Toh ahir d’inki Khulsumu aure dai da izinin Allah ina numfashi sai Ummul ta tafi d’akin mijinta ko mai zai faru kuwa.!” Ta k’arashe sai tsuma take. Khulsum ta d’ago tana duban mahaifiyar tasu da mugun mamaki. Lokaci guda ta girgiza Kai kad’an tace “Umma dan Allah a dinga Neman zabin Allah dai.. Kuma a dinga k’ok’arin furta alkhairi.. Auren nan duk yanda aka so bazafa ayi shi ba sai lokacin da Allah yace kuma yaso.” “Aw Nima rashin kunyar zaki min.. Toh bismillah.. Nace bismillah Khulsumu..” Tai k’wafa tana mai k’arawada “Rikakkiya kawai.. Bazan dai Miki baki ba dan bana fata ki Kai shekarun Ummul a gabana baki tafi d’akin mijinki ba.” Ita dai Khulsum bata ma ce komai ba dan tsanar mazan ma tai balle wani aure tin bayan abinda ke faruwa da ‘yaruwarta. ** ABUJA "Akasarin gidajen da kake iya hanga tapka tapkan benaye ne masu tsananin kyau da tsari. Yanda aka tsara su aka kuma inganta gininsu zakace a k’asar turai kake. Tapkeken gida ne da ya amsa Sunansa, ga korayen shuke shuke da ciyayi masu d’aukan idanu da ban sha’awa. Komai na gidan fari ne k’al tamkar fadar White House." A hankali yake Jin hasken ranan hantsi yana haske masa fuska sakamon baccin da ya d’aukesa a balcony d’insa saman wasu kujeru na shakatawa tin bayan da ya gabatar da sallar asuba. Sautin motoci da tsuntsaye jifa jifa suka soma gauraye masa kunnuwansa da bai cika shiri da hayaniya ba. Nan take kuwa suka katse masa baccin nasa. Tafukan hannayensa yasa ya shafe fuskarsa dasu kana ya mik’e zaune yana duba agogon dake fuskar wayarsa. A kasalce ya jefo k’afafunsa k’asa ya mik’e tsaye yana kuma stretching gabb’ansa. Kai tsaye bathroom ya shige bayan ya tura k’ofar glass da ta raba balcony d’insa da d’akin nasa. Cikin mintuna k’alilan ya shirya tsaf ya fito cikin black business suit d’insa. Kallo guda zaka masa ka tsarkake Ubangijin da ya tsara halittarsa. Koda ya sauk’o k’asa yana iya sinkayo muryar mahaifiyarsa tsakanin ma’aikatan gidan ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Ya d’an furzar da huci had’ida girgiza Kai. Wann morning routine d’in mahaifiyarsa ce. Idan da sabo duk mai rayuwa cikin gidan ya saba da wann. D’an girgiza kansa yai ba tareda ya nufi cikin gidan ba. Lokaci guda yasa Kai ya fice cikin sauri ya nufi yanda motarsa ke ajiye. Nan da nan yaja motar ya fice daga gidan a gaggauce dan Sam baiso yai arba da mahaifiyar tasa a safiyar. Bai zarce ko ina ba sai wani makeken building maiji da tsawo da kuma girma had’ida tsari. Daga saman ginin anyi rubutu da k’araffa masu ruwan zinari *MAITAMA BUILDERS*. Rubutun anyisu ne da Manyan bak’ak’e. Cikin sassarfa yake taku a katafaren ginin mai k’unshe da ma’aikata sahu sahu. Waya manne b’angaren kunnensa na hagu. Dik yanda ya shige kaw sai ya d’ibi gaisuwa Dikda ba amsawa yake ba. "Lift ya shige ya diresa a third floor. Wani hamshak’in office mai tsananin girma da tsari ya nufa, still waya yake. Nan da nan wata mata cikin shiga cooperate ta biyo bayansa." "Cikin muryarsa mai cikeda k’warjini Yaci gaba da furta “You find a way to fix this Hisham…Honestly, I’m highly disappointed. I did not expect my team members to be so unprofessional like this… Iyakacin abinda na sani shine we must cover the deal by all means possible.” Yana Ida fad’in haka ya katse kiran ba tareda ya jira amsar Hisham ba." Matar da tin isowarsa yai mata alama da hannu da ta biyosa sakatariyar mahaifinsa ne Wanda kuma ya kasance mammallakin wann shahararren Construction Company d’in wato Maitama Builders. Ta d’an risina tana gaidashi “Good morning Sir.” “Morning Jane.” Ya fad’i sanda yake kaikaitowa har lokacin idaninsa na kan fuskar wayarsa. Lokaci guda ya k’arada “Is my Dad here..?” Ta d’an girgiza Kai alamun a’a “He….hasn’t arrived yet. Sir.” Shiru yai kaman mai nazari. Securities masu tsaron gate d’in gidansu sun tabbatar masa Dad d’insa ya fita tun sassafe toh ina ya tafi idan ba Office ya taho ba. Yasan mahaifinsa mutum ne mai matuk’ar girmama aikinsa. "Jinjina mata Kai yai “Alright, let me know the minute he arrives.” Ya Fad’i yana mai nufan k’ofa." Jinjina masa Kai tai had’ida amsawa kafin ta take masa baya suka rufo ofishin Wanda ya kasance ofishin mahaifinsa. Engr Aliyu Aliyu Maitama kenan. D’ah d’aya tilo ga Engr Aliyu Maitama. Shid’in sunan mahaifinsa yaci sann same profession suke da shi da mahaifinsa. Su duka biyun Construction Engineers ne. Mahaifiyarsa ita ta tilasta masa yin karatu irin na mahaifinsa ba wai dan yanada buri ko mafarkin hakan ba. A cewarta ta ginasa Akan karatu da aiki irin na mahaifinsa ne domin kaw shine zai gaji mahaifin nasa. Wann dalili yasa harta da suna saida ta maida masa da sunan mahaifin nasa. "Second floor ya dawo ya nufin wani hanyar. Babban ofishi ne da ya k’unshi tables da dama, saman ko wanne table akwai na’urar computer bisa. Daga gefen ko’far glass d’in da zai sadaka da lobby an rubuta daga sama kad’an" *Marketing Development Department* Wani madaidaicin d’akin taro ya nufa. Daga tsakiya akwai doguwar table kewaye da kujeru a k’alla goma. Tin daga nesa employee guda ya hangesa. A guje ya shigo Office d’in yana sanar dasu “Guys guys…” kowa ya kakaito yana dubansa. Saurayin yaci gaba “Sir Haidar is here and he seems to be in a very bad mood. Let’s all behave ourselves.” Ya karashe yana daga masu gira lokacin da yake daidaita zamansa cikin kujeransa. Take kowa ya shiga taitayinsa. Ai kaw yana shigowa mutanen dake zaune saman table d’in alamun isowarsa suke jira nan suka soma kwasan gaisuwa. Bai amsa ba saima nufan kujeran dake daga tsakiya da yai. Laptop d’in da ya shigo dashi ya bud’e ba tareda ya tanka kowa ba ya shiga danne danne. Wannan ya kalli wancan wann ya kalli wann. Ganin shugaban nasu ya had’asu ya kuma samu isowa sann baice komai ba. Shiru mintoci suka shud’e kafin ya kaikaito masu da fuskar computer d’in kowa ya na gani. “This is our new marketing development plan… I suppose..” Kowa ya jinjina Kai alamun haka ne. Haidar ya gyada Kansa kafin yaci gaba “Wanda mukai discussing kuma muka b’ata lokaci sosai muna aiki akai in our last meeting.. Haka ne..?” Nan ma gyada kawunansu sukai alamun eh haka ne. "“But unfortunately, we can’t go on with this new strategy.. And do you know why..?” Ya k’arashe cikin tsananin tsarewa yana dubansu d’aya bayan d’aya. Babu Wanda ya iya basa amsa." Lokaci guda ya jinjina Kai kafin yaci gaba “Sabida bansan ya akai other company suka samu irin wann strategy d’in har suka rigamu applying cikin kasuwancinsu..” Nan kuma suka soma maganganu k’asa k’asa kowa yana duban d’anuwansa yana mamakin ya hakan ta kasance. Cikin bud’e murya ya katse k’anan cecekucensu “So tell me now.. who is selling our company..? And I’m pretty sure is someone from this department.. Kuma yanzu zaku sanar dani yanda akai abinda muka tattaunawa ya fita har wasu company suka samu.!” Kowa yaci gaba da cewa baida masaniyan yanda akai hakan ta kasance. Table d’in ya buga da k’arfin gaske. Cikin tsananin b’acin rai yake furta “Do you even realize the kind of loss we are going to suffer..? What do you want me to tell the board members..! Mai kuke so na sanar dasu..? Let me tell you this..!” Yai maganar yana nunasu da yatsa d’aya bayan d’aya “I don’t tolerate incompetency. And I don’t work with traitors. A cikinkun nan zaku nemo mai mana zagon k’asa. Before the day ends.!” Baikai aya ba sukaji an banko k’ofar zauren taron. Gaba d’aya suka juyo suna duban Wanda ya shigo. Engr Aliyu Maitama mammalakin Kampanin shine ya shigo cikin tsananin b’acin rai. Ko la’akari da mutanen dake zauren taron baiba ya k’arasa ya cakumo matashin nan cikin tsananin karaji sai sakin huci yake. Yana k’arasowa bai wata wata ba ya d’auke Aliyu da mari mai kyau.. Yana d’agowa ya kuma Kai masa wani Marin Wanda saida ya tsaga masa baki jini ya fita. Rintse idanunsa yai yana k’ok’arin nitsa zuciyarsa. Ganin haka yasa mutanen suka soma kokawan ficewa daga cikin zauren. Kowa ya kwana da sanin rashin jituwar dake tsakanin Engr Maitama da tilon D’ansa amma zasu iya cewa basu tab’a ganinsa cikin yanayi irin na yau ba. Engr Maitama ya kuma shafe fuskrsa da tafukan hannayensa yana nuna ma Aliyu fuskar iPad d’in da ya shigo dashi “Ka amsa min.. Menene wann.. What is the meaning of this.?” Aliyu bai iya furta komai ba sai sadda idanunsa k’asa da yai dan yasan haka zai faru tinda shi dai dama a idanun mahaifinsa kullum ba daidai yake ba. Mahaifinsa yaci gaba “Na zata Kai d’in kasan abinda kakeyi by now.. Na zata bazaka bani kunya ba wann karon.. Na zata zaka proving mun cewa zan iya mallaka maka ragamar jagorancin Kampanin nan in three months time.. But I was wrong.. You are not capable of anything good..!” "Cikin kwantar da murya yake furta “Dad believe me, I have no idea how our new development plan get disclosed.. I believe someone is sabotaging our company..”" “Shut up.!” Mahaifinsa ya katsesa kafin yaci gaba “Dama ta ya za’ai ka sani.. Kana can kana shashashancinka other companies are doing great..” Yaci gaba da nunasa da d’an yatsa “Ban d’auraka a matsayin Head of Marketing development department ba saida na tabbata na turaka k’asar Amurka na musamman domin ka karanci course na musamman a fannin Business Management.. Don’t make me regret this Aliyu.!” Yatsansa har rawa take sanda yake pointing D’an nasa dashi. Wani gauron numfashi Haidar yaja had’ida lumshe idanunsa cikin k’ok’arin nitsa zuciyarsa. Muryar mahaifinsa ya kuma sinkaya yana ci gaba “Our website is is.. is just a photo catalog and nothing more.. Tell me waye zai tsaya b’ata lokacinsa a nan.. A kasuwanci irin namu your website is often the first place potential costumers will go to find more "information about your company and its services. Therefore, it should be well designed and offer them exactly what they are looking for.!”" "Haidar ya kuma furzar da huci “Dad, you please listen to me first.. Na sani our company hits a bit of a marketing plateau. But that doesn’t mean we should simply give up..” Ya d’an sassauta muryarsa kafin yaci gaba “Daddy, I believe we can come up with a new marketing strategy that would help us to not just get our business back in the game but ahead of the game. Aikin da Kampanin mu zaiyi zai tabbatar da hakan.”" “Shut up.. Rufe mun baki..!” Haidar ya Had’iye k’uncinsa yana furzar da huci mai d’umin gaske. "Cikin karaji yaci gaba da nunasa da d’an yatsa “How could you have failed in accomplishing a simplest of tasks.. How could you have let our business rivals get ahead of us.. Because of your foolishness now, our company is at risk of going bankrupt.. kana can kana shashancinka other companies are doing great.. A haka ne kake tunanin ni Aliyu Maitama zan d’auki project d’in da ci gaban Kampani ya ta’allak’a a Kai ka jagoranta cikin watanni uku.. Bari kaji na fad’a maka.. I did not build this company to hand it over to a pathetic loser like you..” Yai fasali kafin yaci Gaba da nunasa “You are a disgrace to me Aliyu.. Kai baka cancanci sunana ba.. Mahaifiyarka tayi kuskure da tayi zaton zaka zamto kaman ni.. Har abada Kai bazaka tab’a zama kaman ni ba.. Kasan dalili..?” Ya k’arashe yana mai kuma takowa sosai gaban Aliyun “Sabida Kai baka saka komai a gabanka ba face shashanci… Ina nan ina Fad’i tashi to make a proper man out of you kana can kana shashanci da abokan banza.. Kana so kace mun duk kudaden da sukaita fita under your department a banza suka fita babu result a k’asa..? Ya jinjina Kai yana sakin huci “Ina sakamakon aikin..? Nace ina sakamakon aikin..?! Chacha kake da Kampanina..? Answer me, are you gambling with my company.!” Ya k’arashe yana cakumosa da hannaye biyu yana jijjigasa da iya k’arfinsa." Izuwa lokacin Zuciyar Aliyu ya gama tafarfasa. D’agowa yai sosai suna fuskantar juna shida mahaifin nasa. Lokaci guda ya murmusa kad’an kafin yace “Oh really Dad. Is that the only problem..?” Cikin huci mahaifinsa ya katsesa “Ya isheka haka.. Kar ka soma. Kar ka kuskura.” “It has always been like this Daddy.. Hatred..! Eh tsana.!” Haidar ya katsesa cikin tsananin huci. Lokaci guda yaci Gagaba “Why do you always look down on me Daddy.? Despite all the good things that I’ve done for this company.. The only thing you can see are my mistakes.. Haven’t I done everything you told me to.. Shin bana aikata duk abubuwan da kake umurta na ne. Wanne ne banayi ciki..? Tell me Daddy..!” "Idanunsa suka kuma rinewa zuwa ja, lokaci guda yaci gaba da girgiza Kai yana furta “Of course bazaka ce komai ba.! Because you don’t have the answer.. I’m sorry if I’m not as smart as you Dad.. I’m sorry if I’m not as skillful as you.. And I’m really sorry if I’m a disappointed..!”" "Cikin karaji mahaifin nasa ma ya katsesa “Yes that’s what you are.. A disappointment.. I gave you everything so you can be the best.. The best schools, the best trainings.. The best of everything.. I invested so much in you to make sure I groom you well.. Amma duk a banza.. You are nothing but a pathetic loser.”" Idanunsa na kallon k’asa yake furtawa a hankali “That’s enough Daddy. Enough please.!” Yai maganar yana murza tafin hannunsa cikin k’ok’arinsa na danne zuciyarsa dake zillo kaman zai fito daga cikin k’irjinsa sabida b’acin rai. “I don’t want see your face in my company ever again..! Get out now.. You are fired.” Mahaifinsa ya fad’i yana nuna masa k’ofa. Kansa na kife k’asa ya saki murmushi. Lokaci guda ya d’ago idanunsa ya sauk’e su tar cikin na mahaifin nasa “And do you actually think I’d give you this satisfaction..?” Ya kuma murmusawa kafin ya girgiza Kai yace “No Daddy bazan jira ka koreni ba. Kasan me..? I’m sick and tired of trying to impress you all the time.. I’m done being your puppet… I quite.. You don’t need to fire me.. To hell with your damn company… Daddy.!” Cikin huci mahaifinsa ya dago hannunsa dake rawa zai Kai masa Mari “How dare you talk to me like that..!” Rawan da hannunsa keyi yasa hannun ya gaza sauk’a saman fuskar Haidar. Sai haki yake da kyar irin na Wanda zuciyarsa yakai matuk’a wajen baci. Haidar ya finciki ID d’insa na Kampanin dake mak’ale jikin suit d’insa yai jifa dashi a wajen kafin yasa kai ya fice a fusace. A daidai k’ofa ya kusan cin karo da aminin mahaifinsa Alhaji Gimba. Kallo d’aya kurum Haidar yai masa kafin ya watsar yasa kai ya fice cikin sassarfa. Alhaji Gimba ya k’arasa shigowa cikin ofishin yana duban abokinsa dake zaune saman kujera guda yana sakin hakin b’acin rai. Cikin kwantar da murya ya soma fad’in “Abinda nake nusar dakai a koda Yaushe yana gab da faruwa Engr.” Daddy ya d’ago idanunsa masu cikeda ba’cin rai yana dubansa dasu “Kaga Gimba dan Allah kar ka mun maganan yaron nan a nan.. Na riga na Sallama shi..” Alhaji Gimba ya murmusa irinta manya “Abokina kenan. D’a d’aya tilo ai ya wuce gaban a sallamashi.. Ai Kai Sallama d’ah ba naka bane..” “I don’t care if he’s my only son.. Baka ganin abinda ya gama min yanzu ne.. Ban haifi dan da zaiga bayana ba..!” Alhaji Gimba ya kuma murmusawa had’ida girgiza kai kad’an “Yara ko dubu Allah ya baka bazaka ce ka Sallama guda ba dan hannunka baya rub’a ka yanke..” “Saidai idan bai rub’e d’in ba..” Daddy ya basa amsa a fusace. Alhaji Gimba ya tsaresa da idanu kafin yace “Wai kasan matsalar ka kuwa..?” “Ai idan Akan Haidar ne ni da Kai bazamu tab’a samun daidaito ba..” Daddy ya basa amsa Kai tsaye. "Ya d’an girgiza Kai kad’an “You are putting in a computation with your Son, and neither of you want to lose.”" Daddy yai saurin dubansa “Mai kake nufi..?” “Baka so Aliyu ya taso ya fika k’wazo Shiyasa har kullum kake gani a idanunka shi bai daidai ba.. You refuse to see his potentials. Da zaka basa dama yaron nan ba k’aramin asset bane ma Kampanin ka.. Ka bashi dama koda na k’arshe ne ka k’yalesa yai project d’in nan at least koda na k’arshe kenan kafin kace ka koresa.. Inaga dan yayi failing business plan ba yana nufin yayi failing project d’insa bane.. Ina nufin bridge project dake gabanmu..” "Da tsananin mamaki Daddy ke duban aminin nasa wann karon “Alhaji Gimba, ka kuwa ji abinda kace..? Shin ka mance cewa the company’s future defends on this very project.. Ta ya zan mallaka ma Aliyu ya jagoranta.. Do you want us all to go down..?”" Alhaji Gimba zai kuma magana Daddy ya mik’e yana gyara zaman business suit d’insa “This conversation is taking us to nowhere Alhaji Gimba.. Kamata yai yanzu ka tayani mu san mai zamu sanar da Board members sabida shashashncin d’anah.” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa. Alhaji Gimba ya girgiza Kai kurum kafin ya take masa baya. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU* *04* *©️Sameena Aleeyou… * "Tafiya yake cikin mota sautin Marin da mahaifinsa ya shata masa bai daina k’uwa a dodon kunnuwansa ba. Shi ba wai zafin Marin bane ya tsaya masa a rai, Marin nasa da yai gaban employees d’in Kampanin kuma masu aiki under department d’in da yake running shine abinda yafi komai k’ona masa rai. Ya sani shi dai a idanun mahaifinsa baya yin komai daidai sabida haka wann ba sabon abu bane wajensa. Ba a wajen aiki ba a gida ba.. Amma meyasa zai wulak’antasa gaban ma’aikatansa irin haka..? Ya cije labb’an bakinsa kad’an zuciyarsa na kuma k’una. Mahaifinsa ya tsanesa baya k’aunarsa, kai duka iyayen sa guda biyu basa sonsa basa k’aunarsa. Shi zai iya cewa tun tasowarsa baida wani good memories da both mahaifansa wato mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa tin tasowarsa cikin tilasta masa da tsaurara masa take wajen ganin yayi abinda zai burge mahaifinsa ya kumayi alfahari dashi. Saidai duk abinda yayi baya burge mahaifin nasa. Kullum cikin nuna masa baiyi daidai yake ba. Kullum cikin kusheshi yake da jifansa da kalamai masu muni. Tsakaninsa da iyayensa akwai wani Katanga da yai ma soyayya shamak’i dashi. Baisan soyayyan iyaye ba. Ya taso ne cikin tilastawa da k’ok’arin burge mutanen da bai tab’a birgewa ba a cewarsa. Yai gajeren tsaki yana mai kokarin kauda tinanin." A farfajiyan gidan yai parking motarsa jikin wani tapkeken roundabout da furanni suka k’awata tsakiyarsa ga ruwa na kwaranya daga tsakiya. Cikin sassarfa ya nufi cikin gidan har lokacin zuciyarsa bai daina masa zafi ba. Zaune ya taddata a parlornsa ta mik’e santala santalan fararen k’afafunta da suka sha ado da k’unshi . Sai faman karkad’a k’afafun nata take tana tururi ita kad’ai alamun dai isowarsa take jira. Baiji mamakin ganinta a parlorn tinda yasan kullum cikin controlling rayuwarsa take. Baice komai ba sabida ransa da yake a mugun b’ace. Har yasa Kai zai shige ya sinkayo muryarta “Ai na zaci daga can bazaka dawo nan ba tinda ka zama sallamamme .” Cak ya tsaya yana saita numfashinsa a hankali “Couldn’t you wait for me first to at least do something wrong kafin ki fara aibatani.” Ya k’arashe daidai sanda mahaifiyarsa ta k’araso gabansa ta tsaya suna fuskantar juna. Ganin ciwo a fuskarsa ya sanya yanayinta canzawa. Alamun rauni ya bayyana saman fuskarta “Haidar.. Me ya sameka.. Ina ka samo rauni..?” Ta tambaya cikin nuna kulawa. Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa. Lokaci guda ya girgiza Kai yace “Don’t act like you care Mom. Kin San hakan zai faru. Am I right.?” Ta d’an tsare fuska “Wani irin magana ne nasan haka zai faru.. Had’arin mota Kai ko me.. Tinda dai nasan baka shiga sabgan mutane balle nace fad’a Kai da wani..” “Babu ko d’aya Mommy..” Yai fasali yana mai shafa raunin da mahaifinsa yaji masa a labb’ansa “Meyasa ciwo a jikina zai d’aga miki hankali da girma na idan bai d’aga miki hankali a lokacin k’uruciya na ba.?” "Ya kafeta da idanu. Jin tayi Shiru batace komai ba yasa shi murmusawa kad’an da gefen bakinsa “Of course you don’t have the answer. Well, zaki iya kiran wann a matsayin tukuici na mahaifina. All thanks to you, your Majesty, Mommy.!”" Ta furzar da huci kad’an “Mai ya had’aka da mahaifinka..?” "“A usual stuff.. Banyi daidai ba, Dikda bana tunanin Akan wann ne kawai..” Ya d’an daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba “Nafi zaton kece kika bashi shawarin yai mun wulak’ancin da ya mun.. A naki tunanin ta haka ne kawai zaisa ki fahimci mai kike son fahimta gameda D’anda kika dasa rashin yarda da daidaito a tsakaninku tun yana k’aramin yaro. Na sani ku biyun baku zama on the same page with each other unless wann abun will hurt me deeply. Ko ba haka bane Mommy.?” Ya k’arashe yana dubanta." Furzar da huci tai had’ida girgiza Kai “It’s for your own good Aliyu.. Dik Fad’i tashin da nake inayi ne domin ka zama mutumin K’warai sann rayuwarka ta inganta.. Bazai yuwu bayan tsayin dakan da nake Akan D’ah na na zuba ido rana daya komai ya rushe ba. Aliyu ka daina kwana a gida.. Ka tsiri wasu d’abi’u da ba naka ba.. Some strange behaviors wanda a baya bakayi. A baya baka tab’a maida mun magana kan duk abunda zan umarceka.. But now.. You’ve changed.. Completely Haidar.. Ina kake kai kudaden da kake fitarwa daga kampanin mahaifinka.. So kake ka hadani fada dashi..? A nashi tunanin nice nake daure maka gindi kake abinda ka so.. A nashi tunanin nasan duk halinda kake ciki.. What he was wrong about shine yanzu Aliyun da ya sani ya banbanta da Aliyu na wanda baya boye mun komai.. D’ah na mai biyayya a gareni koda na kasance mai tsauri akanshi.. Haidar din da baya mun musu koda munada banbancin ra’ayi..” Ta danyi fasali muryarta na rawa tana kuma matsowa kusansa “Aliyu nasan ba shaye shaye kake ba tunda bakayi ba a lokacin da tak’ura da tsanani zasusa kayi. Sann bana tunanin mata ne suka d’auki hankalinka tinda shima bakayi a baya ba lokacin da ya kamata ace kayi idan kai me yi d’in ne… Toh menene ya dauki hankalinka a duniyar nan.. Haidar please..” D’aga mata hannu yai alamun dakatarwa “Kin rasa wann daman akan D’anki Mommy tuntuni.. "Ya dan juyo yana dubanta kafin yaci gaba cikin rarrabewar kalmomi “What I do with my life is none of your Business… You said it right. Ni ba wann k’aramin yaron da kike kullewa a d’aki ki hana masa lokutansa na k’uruciya ki tilasta masa cinye takardu koda baya so..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba “Kin mance ne na tuna Miki Mommy.? That unhappy little boy ya girma Mommy. Kuma zai yanda yake so da rayuwarsa ba yanda ke kike so ba.. After all, duk abinda kike yi kinayi ne sabida benefits d’inki.. Ba abu guda da kikeyi domin ci gaba na.. Kinayi ne kawai domin amfanin kanki.. Burinki shine ya mallaka min company sabida watak’ila akwai abinda kike tsoro ko kuma yake Miki barazana da rasa dukiyarsa wanda ni ban sani ba.. Shiyasa kike amfani Dani domin na zame miki makamin ki.. D’anki ba komai bane a wajenki face weapon. Yes, I am nothing to you face makaminki. Haka ne Mommy..?” Jinjina kansa yai jin bata amsa ba “Wace irin uwa ce take haka ma d’anta Mommy.? Ya k’arashe idanunsa cikin nata." Dikda zuciyarta dake harbawa bata bari tsoro ya bayyana saman fuskarta ba. Saima girgiza Kai da take “Don’t you dare question my motherhood.. You’ve no idea what it takes to be a parent..!” Ta k’arashe tana sakin huci. Jinjina mata kai yai “Eh bansan mene zama iyaye ba kuma bana so nai experiencing daidai da dak’ik’a guda. Kinsan dalili sabida ban taso naga misali mai kyau wajen mutanen da ya kamata na gani daga garesu ba.. “ Ya d’an kuma matsowa had’ida sassauta murya “Kin gama sanin duk abinda ke faruwa cikin rayuwar D’anki.. Do you know why..?” Ya tsare mahaifiyar tasa da idanu kafin yaci gaba “Because I’m not that scary little cat da kikai traumatizing d’inshi da son zuciya irin naki. Bazaki sake amfani dani domin cimma burinki ba.!” Daga haka sa kai yai ya shige cikin huci. "Tabi bayansa da kalamansa na kuma dakan dodon kumnuwanta har zuwa tsakar kanta. Salati kawai take.. Meke faruwa da ita..? Meke faruwa da D’anta. Ko zamanin yarinta zamanin da take kulle Haidar cikin d’aki mai duhu bai mayar mata da maganganun irin haka. Hasalima duk abinda zata masa shiru yakeyi. Ya koma kaman mai tsoron mutane, dik yanda mutane suke baya zama baya kuma cewa um balle um um. Akwai lokacin da har sukai zaton ko ya kurmance ne har saida aka had’a masa da therapy kafin maganarsa ya dawo. Ita tsoro abun ya soma bata. Yafi kama da aikin asiri." Yana tura k’ofan d’akinsa ya hangi Anisa ‘yar k’anwar mahaifiyarsa dake aure garin Kano tsaye closet d’insa rungume da rigarsa ta lumshe idanu. Jin an turo k’ofa ya sanyata bud’e idanunta suka kuwa had’a idanu. “What are you doing in here..? And can you explain why you are holding that..?” Yai mata nuni da rigarsa dake cikin hannunta da idanunsa. Ta saki murmushin yak’e “Na shigo na gyara maka d’akin ne.. Mommy tace kwana biyu baka kwana a gida.. Nima d’in jiya da dare na shigo garin..” Baiyi mamaki ba dan Mommy ta turo Anisa d’akinsa. Yasan kad’an ne da aikin Mommy ta turo Anisa tai mata binciken k’wak’waf cikin d’akinsa dukdai dan ta gane what’s been going on cikin rayuwarsa. “Get out.. I need to change..” Ya fad’i yana mai shigewa cikin d’akin lokaci guda yana k’ok’arin undressing Kansa. Suitcase ya ciro Anisa tana gani ya shiga ciro kayansa yana sakawa ciki. Mamaki ya cika Anisa da ganin yanayinsa. Tasan bai iya fushi ba dukda kuwa ba kasafai kake gane normal days d’insa ba. Definitely dai wani abu na faruwa dashi. Ta girgiza kai kad’an. Sauri sauri ta fito ta nufi wajen da Mommy Ke tsaye tana tsaka da salallami. Anisa d’iyar k’anwar Mommy ce mai suna Asshe dake zaune a garin Kano. Daren jiya tazo gidan dama takan d’an zo tai masu kwanaki lokaci zuwa lokaci. “Mommy wai lafiya.. Wai meke faruwa ne a gidan nan..?” Har lokacin Mommy bata amsata ba ta kasa furta koda kalma. A haka Haidar ya k’araso ya shigesu ya barsu nan tsaye suna binsa da kallon mamaki. “Aunty Kwaise..” Ta kira Mommy da sunanta kafin taci gaba “Wai meke faruwa ne.. Ina zaije shi da suitcase..?” “Ban sani ba mana Anisa. amma hala Ke zaki iya sani..” Mommy tace a hasale. Anisa da mamaki bai saketa ba tace “Mommy ta ya zan sani nida jiya jiya nazo gidan..” Mommy ta shiga janyo hannunta cikin sauri tana fad’in “Binshi zakiyi ki gane mana yanda zaije… Maza maza kafin ya b’ace kinsan yanda car keys suke ai. D’au d’aya ki bi mana bayansa. Kar barshi ya b’ace ma ganinki Anisa..” Anisa kaw tamkar wacce take jira gudu gudu tai yanda Mommy tace. Tana tafe saman kwalta cikin k’ok’arin bin hanyar da taga Haidar yabi ganin bai b’ace mata ba kaman daga sama taji an daki bayan motarta da k’arfin gaske wanda hakan yai sanadiyar da motar Haidar ta b’ace mata. A dole ta danna birki kanta ya daki jikin staring wheel. Kafin ta sami zarafin fitowa daga cikin motar mutumin da ya daki nata motar ya b’ace bashi a wajen. Mamaki ya cika Anisa ganin babu kowa bayanta da alama wanda ya mata wann aika aikan yayi gaba. Ta furzar da huci a hankali tana kuma duba bayan motar. Bin bayan Haidar da batai ba kenan dole ta koma gida. ** KANO Yau d’in yaran Mama sunzo yini daga gidan mazajensu dan tini Mama ta kirasu a waya d’aya bayan d’aya ta sanar dasu abinda ya faru na amshe lefen Ummulkhairy da akai. Dan haka washe gari kaf suka hallara. Sukai bak’e bak’e tsakar gidan suna watsa habaice habaice. Idan an Fad’i abinda ya basu dariya kaji Sun saki shewa harda gud’a. Umma kaw ta kasa ko fita tsakar gida sabida habaice habaicensu. Ko abincin rana Sun kasa fita suci kasancewar girkin Maman ne. Ta kuma hana Ummul da Khulsum fita ko k’ofa. Khulsum ta dubi agogo k’arfe d’aya saura na rana. Ta dubi Umma dake zaune ta rapka uban tagumi tana sauraron habaice habaicen Mama dasu Salima. “Umma lokacin sallan azahar yayi zan fita nai alwala..” Ta Fad’i tana k’ok’arin mik’ewa. Saurin janyota Umma tai tana aika mata mugun kallo “A haka ne zaki fita su cinyeki da habaice habaice.. Nemi waje ki zauna akwai sauran lokaci.” Ta k’arashe tana zaunar da Khulsum da k’arfin gaske. Khulsum ta dubi mahaifiyarta da tsanin mamaki “Haba Umma dan Allah shikenan har ibada ma kar muyi sabida muna tsoron maganan mutane.. Umma shikenan yau a d’aki zamu yini sabida maganganun mutane.. Umma dan Allah ina kika tab’a Jin mutane Sun fasa magana.. Kuma waye magana ya taba kashewa.? Umma komai mukai wllhi sai anyi magana gara ma ki bari mu fita muyi ibada mu rok’i Allah mafita da zaman tagumin da muke uwar d’aki.. Umma zaman mu a d’aki fah bazai sa su fasa maganganunsu ba..” Kuka Umma ta kece dashi tana fad’in “Dik ba kece kika jawo ba.. Kin tsaya kina dambe bakin kwalta.. Yo ba da dole Zubairu da yaga haka yak’i dawowa ba.. Nayi imani ba don ya hanngi Ummul na rabon fad’a ba da ya taho ya nemi afuwa ya kuma sa an maido da lefen nan dan Zubairu yaron kirki ne.. Amma jarabar fad’anki ya jawo Zubair ya kufce ma ‘yaruwarki.. Dole ma kice kar mu damu da maganganun mutane sabida ba lefenki aka amshe ba.. Wayyo ni Suwaiba wani laifi nai nake fuskantar irin wann iftil’ai..!” Ta kuma d’aura hannayenta aka tana kuka. Su Mama dake mak’ale bakin k’ofa komai a kunnuwansu. Badia ta janye labule ta lek’o tana fad’in “Gaskiya Khulsum bakida mutunci wann ai zubar mana da mutuncin gida ne dambe da k’artai a bakin layi..!” Mama tai karaf tace “Ah toh hassada take maku ku da kuka samu Allah ya rufa maku asiri kuke d’akin mazajenku bari tai abinda zai Shafa maku bak’in fenti wajen dangin mazajenku.. Yo sukaji ‘yaruwarku guda an kuma amshe lefe da sadakinta d’aya kuma tana dambe da k’artai a bakin layi ai cewa zasuyi duk zuri’arku haka kuke ke Salima me kishiya ta samu abun goranta Miki..” Haba nan fah Salima ta kuma harzuk’a ta fad’a d’akin tana kokawan janyo Khulsum tana fad’in wllhi bata isa ta kashe mata aure ba. Umma na kuka take rok’on Mama da yaranta da sukai ma Khulsum taron dangi suyi hak’uri su fice. Itakam Ummulkhairy kuka ma ya hanata katab’us yayinda Mama ke kuma ingizasu. Kan kace me ayarin yan cikin gidan Sun cika a k’ofan sashen su Ummulkhairy suna bama idanu abinci. Tuni masu jin haushin Khulsum suka goyi bayan Mama da yaranta cewa Khulsum zata b’ata masu sunan ahali bayan fentin da Ummulkhairy ke Neman shafa masu suma ak’i Neman auren yaransu. Ana wann kacaniyar mahaifinsu ya dawo daga Kasuwa. Ganin iyalansa haka yasa shi Jin kaman wani abu ya sokesa a k’ahon zuciya. A hankali ya dafe k’orjinsa yana k’ok’arin silalewa. SameenaAleeyou… *AUREN WATA UKU.!* *05* *©️Sameena Aleeyou… * K’ara Badia ta saki sakamakon hango mahaifinsu da tai yana k’ok’arin kaiwa k’asa. Nan kuma hankula suka koma kansa. Mama ta k’araso da sauri ta tallafesa tana fad’in “Malam dan Allah ka rufa mana asiri kar bak’in cikin Ummulkhairy yai ajalinka.. Wayyo ni Tani.. Sannu Abban Salima..” A haka ta k’arasa dashi madaidacin parlonsa tai masa masauk’i saman d’aya daga cikin lamusassun kujerun dake a cikin parlorn. Sai jero masa sannu take tana bangaje Umma daga kusansa. Badia ta kawo mafifici Mama ta amshe tana masa fifita tana fad’in maza ta kawo ruwa. Bayan shud’ewan wasu mintoci Abba ya soma dawowa hayyacinsa. "Gaba d’aya ya had’e matan nasa guda biyu. Ya d’an kishingid’a yana dubansu. Lokaci guda yake furta “Tani, Suwaiba..”" Kowaccesu ta amsa jiki a sanyaye. Abba yaci gaba “Bazai yuwu ku maida min gida kaman gidan kallon kwallo ba.. Ke Tani kin gayyato yaranki Sunzo kuna murnan abinda ya samu ‘yaruwarsu.. Ke kuma Suwaiba kin saka ma ranki damuwan abinda Allah bai saka Miki ba.. Ita rayuwar nan wai duka kwana nawa ne za’ayi.. Kun raba mun kan ahali kun maida min gida kaman gidan maguzawan farko.. Idan kaji hayaniya na tashi a gidan nan toh wann k’ofan ne.. Akan wani dalili..?” Ya d’anyi fasali yana dubansu kafin yaci gaba “Toh ku kula.. Ku kuma tuna cewa duk abinda Kai a wann rayuwar shi zakaje ka cimma a cen.. Bazan gushe ba ina maku nasihan kubi duniya a sannu rayuwar duka ba yawa ne da ita ba.. Bazan bari ku saka mun ciwon da bani da shi ba..” Murya a sanyaye Umma tace “Kai hak’uri Abban Ummul in sha Allah zamu gyara.. Ko Yaya..?” Tai maganar tana duban Mama. Mama ta saci idanun mijin nasu kafin ta aikama Umma harara sama da k’asa sai kuma ta juyo da duban nata ga Abba. Tai murmushi Wanda yafi Kama da yak’e “Eh in sha Allah zamu gyara mun tuba Kaji Malam..Allah ya baka lafiya.” Jinjina Kai yai yace “Alhamdulillah.. Allah ya ganar damu baki d’aya ya kuma had’e mana kan ahalinmu ya shirya mana zuri’armu.” Gaba d’aya suka amsa da Ameen. Abba yai masu izinin tafiya sai kuma ya dakatar da Umma yace ita ta tsaya. Wani birki Mama taja kaman zata dungura ta juyo tana duban Abba da yace Umma ta tsaya bayan yau girkinta ne. “Malam ban gane Suwaiba ta tsaya ba.. Ni ce da alhakin abincika yau fah ko ka mance ne..?” Tai maganar tana tururi kai kace ba itace yanzu ta gama ce ta tuba ba. Abba ya murmusa yana ayyanawa cikin zuciyarsa Mata sai a barsu wajen kishi. So tari yakan yi ma Mama uzuri dan kishi Tabbas akwai ciwo. Wani abun yasan zafin kishi ne kawai yake sanyata yi amma Tani d’insa tanada halin k’warai. “Magan zamuyi Tani ba wani abu ba..” Abba yace cikin sigan lallama. Mama ta kad’a Kai “Aiho.. Kardai garin dad’in zance a zarce a shiga hakki ehe..!” Murmusawa kurum Abba yai ba tareda yace komai ba. Saida Mama ta fice ya dawo da dubansa ga Umma. “Suwaiba..” Ya kirawo sunanta “Na’am Abban Ummul.” “D’azu a kasuwa mak’ocin shago na ke jajanta mun al’amarin auren Ummulkhairy.” Umma ta jinjina Kai alamun tana sauraro. Abba yaci gaba “Bansan ko kin gane shi ba mai babban kanti na kayan masarufi da yake jikin nawa kantin.. Wasu lokutan har rancen kaya yake bani idan na saida na mayar masa uwar kud’i hardai jarin nawa ya d’an ja baya. Mutumin kirki ne Alhaji Kamilu..” Umma ta jinjina Kai tace “Allah sarki..” Abba yaci gaba “Toh nan dai nake labarta masa al’amarin ita wann yarinya nawa Ummulkhairy.. Toh kwatsam sai ya sanar Dani yana so na bashi auren ita Ummulkhairin idan babu wani matsala.. Toooh wato gaskiya banyi garajen amsa masa ba duba da irin abubuwan dake faruwa. Ak’alla aure nawa ake sakawa na Ummulkhairy abu baya yuwa.. Sann ko sati ba’ayi ba da abinda ya kuma faruwa na amshe lefen shi yaron nan Zubairu. Amma dukda haka bazaka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji ba. Ba wann dalilin ne yasa nace ya dakata ba.. Babban dalilina shine sai naji daga bakin ‘yata idan tana sonsa.. Idan har bata sonsa JINKIRIN aurenta bazai sa na aura mata mutumin da bata so ba.. Sabida shi Alhaji Kamilun lallai lallai ya nuna mun yana son na basa dama kuma Kinga akwai ‘yar kunya a tsakaninmu… Tooooh dai gaba d’aya kaman ya d’aure ni ne.. Dan a gaskiya..” Sai ya d’anyi Shiru kuma kaman mai nazari “Bana so Ummul taga kaman na tak’ura mata da batun aure ne tinda dudu ba’a jima da fasa..” Bai kai aya ba Umma ta katsesa “Haba Abban Ummul.. Ta ya ma zakace haka.. Yo har wani lokaci zaa d’ibar mata.. Shifa lokaci baya jira. Ka duba sa’anninta duk suna d’aki daga masu yara uku hudu kai har masu shida akwai sa’anninta… Yo ai ko ta gansa ko bata gansa ba tinda har zai rufa mana asiri ya aureta ai shikenan..” "Katseta yai da fad’in “A’a Suwaiba, JINKIRIN Ummulkhairy ba zaisa na tilasta mata kasancewa da Wanda bata so ba.. Kece mahaifiyarta, ki kirata a d’aki a natse ki sanar da ita. Idan tayi na’am falillahil hamdu yau da dare sai na d’aga waya na kirasa gobe idan Allah ya kaimu sai yazo su fahimci juna.. Alhaji Kamilu mutumin kirki ne kuma yanada matan aure biyu da yara da d’an dama.. Ki kira ita Ummulkhairy ki sanar da ita a natse. Idan Sun daidaita kansu shikenan sai ai maganan aure tinda babban mutum ne ba wani Jan lokaci za’ayi ba. Hasalima Jan lokacin baida wani alfanu..”" Umma tai karaf tace “Ai ko gobe ma sai a d’aura kawai nidai ta tafi d’akinta..” Ta d’aga hannu sama tana fad’in “Oh Allah na gode maka ni Suwaiba.. Allah maji kukan bawansa mai maida asara da alkhairi..” Girgiza kai kurum Abba yai yana dubanta. Zaman Ummu a gabansa bai d’aga masa hankali ba kaman fitinar mahaifiyarta matarsa Suwaiba . Fatansa Allah ya had’a Ummul d’insa da miji na gari wanda zai kular masa da ita ya kaunaceta tsakani da Allah dama sauran yaransa gaba d’aya. Cikeda farin ciki tamkar wacce aka yaye mata kaf damuwarta na gidan duniya haka Umma ta fito tana k’wlla kiran Ummulkhairy. A daidai bakin farandar d’akin Abba ta riski Mama rik’eda farantin abincin Abban. Umma tana ganinta ta tsuke Baki tana zancen zuci Wanda sam bata san ya fito fili ba tsaban farin cikin da ta tsunduma ciki “A sirrace nema a bayyana samu.” Rangaji Mama take tana dubanta daga sama zuwa k’asa. Kafin tai murmushi mai sauti tace “Ayi dai mai mu gani wai gurguwa da auren nesa.” Ta k’arashe kaman zata bangaje Umman ta nufi parlorn Abba. Umma ta tab’e Baki ta nufi d’akinta cikeda farin cikin abin alkhairin da ya sameta dan yau d’in Ji take burinta na gidan duniya ya gama cika. ** Abuja. Cikin bacci yake Jin vibrating d’in wayarsa na kuma k’aruwa alamun wayar ta gaza yin Shiru. Yai k’ok’arin mik’ewa had’ida janye Dareen dake kwance saman k’irjinsa. Hannu yasa ya d’auki wayar dake aje gefen bedside yana ganin lokaci quart after six na safiya. Lokaci guda ya d’anyi relaxing jikin pillow yana k’ara wayar a kunnensa yana rage girman idanunsa masu cikeda bacci wanda hasken hantsi da ya soma bayyana ya tilasta masa yin hakan. “What Hisham.” Ya Fad’i yana gyara zaman wayar a kunnensa. "Daga d’aya b’angaren Hisham Yace “Haidar, Kana Ina ne.. me kakeyi..?”" Da mamaki Haidar yace “What kind of question is that..? What could I been possibly doing at this time..? Bacci nake obviously kafin ka tadani.” Hisham ya katsesa “Have you seen the news..?” “What news..?” Haidar yace cikin muryarsa mai cikeda bacci. Hisham ya furzar da huci “Lallai na yarda kana bacci.. Check your phone ka karanta labarun kasuwanci kaga abinda muka tashi dashi.” Daga haka katse kiran yai yayinda Haidar ya shiga shafa wayarsa. Tin daga saman fuskar wayan yake karo da notifications. "Notification guda d’aya ne ya d’auki hankalinsa. THE BUSINESS PRESS. Yanda aka rubuta *Top Business Scandal.* Saurin clicking yai ya shiga kan labarin. Abinda ya soma karo dashi a labarin shine hotonsa da mahaifinsa lokacin da ya cakumosa a cikin Kampaninsu yana jijjigasa yana fad’in yayi disappointing d’insa, daidai wajen akai cutting a video d’in Wanda aka fitar da hoton sosai yanda ya rik’e kwalan Haidar d’in ga jini gefen bakin Haidar. K’asan hoton kad’an an rubuta kamar haka *Owner of Maitama Builders Engr Aliyu Maitama gets into a physical fight with Son over augment.*" “Damn it..! This is not happening.” Ya furta a hankali. Sauri sauri ya mik’e ya shige bathroom dan shiryawa. Dareen dake baccinta peacefully ta soma bud’e idanunta masu cikeda bacci wanda ko shakka babu shirin da Haidar d’in keyi ne ya katse mata baccin. Ta zuba masa idanu tana duban yanda yake komai a gaggauce. Ta saki murmushi zallan k’aunarsa cikin zuciyarta. A hankali ta sakalo k’afafunta ta sauk’o daga saman gadon. Yana tsaye gaban full length mirror yana k’arisa shiri yaji ta rungumosa ta baya had’ida matsesa sosai cikin jikinta. “Good morning..” Ta furta tana mai d’aura hannayenta saman nasa ta amshe agogon da yake k’ok’arin d’aurawa taci gaba da d’aura masa “Are you leaving this early..?” Tace sanda take kaikaitowa ta dawo ta gabansa. “I have to.. I need to take care of something.. I’ll see you later..” Yace a tak’aice yana d’aukan wayarsa da mabud’in mota Ta take masa baya ganin zai fice cikin sauri. Ta kamo hannunsa guda “What about breakfast..? Your cool tea is in the fridge.. Tun asuba na had’a maka.. The way you like it.. Should I serve you..?” "D’an dubanta yai kafin ta girgiza kai “Kar ki damu, I’ll be fine..”" Ta kuma rik’e hannunsa “Does that mean ka amince da k’orafina ka fasa aje aikinka a Kampanin Daddynka.?” Tai maganar idanunta tar akansa. Ya d’anyi still yana dubanta “I don’t know… I’m not sure.. I.. must go now.. Take care..” Ya k’arashe yana shafan b’angaren fuskarta guda da tafin hannunsa. Ta janyo hannunsa ta sumbaci tafin hannun kafin ta sakar masa murmushi tana masa fatan nasara har saida taga tashin motarsa. A hankali ta lumshe idanunta had’Ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ta koma cikin gidan..” ya d’auki car keys d’insa da wayarsa ya fice a gaggauce. Yana tafe saman kwalta wayar Hisham amininsa kuma abokinsa a wajen aiki ya kuma shigowa. “Haidar this is bad.. Very bad.!” Abinda Hisham yace kenan koda Haidar ya d’aga kiran. Jinjina Kai Haidar yai "“Yanzu zaka yarda da magana na.. Someone is sabotaging the company.. And trust me, I know exactly how to catch that rat.” Shiru yai alamun yana sauraro daga b’angaren Hisham." Hisham yace “Kuma ba yanda za’ai ka kamo wann b’eran har sai kana aiki da Kampanin. Now more than ever you can’t quit your job.. You need to fix this Haidar.. You need to clear your Dad’s name.. Bazaka bari sunan Kampanin ya b’aci ba..!” “Oh Shut up Hisham..!” Ya fad’i yana mai katse kiran lokaci guda yana mai k’ara gudun motar. A can gidan mahaifinsa kaw ya tsare mahaifiyarsa ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ga ‘yan jarida sunyi chaa a bakin gate suna jiran fitowarsa. "Yaci gaba da nuna Mommy da yatsa “Call that pathetic son of yours and tell him to fix this mess immediately.. Bayan asaran da zamu tapka sabida shashashancinsa, I won’t allow him to ruin my company’s image.!” Ya k’arashe cikin tsananin huci yana mai ci gaba da zagaye katafaren parlorn nasa." "Furzar da huci Hajiya Kwaise tai, tana mai kuma dialing layin Haidar amma shiru bai d’agawa." Dad ya kuma dubanta “He’s not answering right..?” D’an lumshe idanu tai had’ida mik’ewa tsaye “Engr please calm down.” "Ya kuma katseta “Seriously Kwaise..? Are you asking me to calm down.? Ko bakiga babban abun kunyan da wann shashashan d’an naki yai bane.. Kwaise, I’m a highly respected person. A well known businessman. I have a reputation to protect.. Bazan bari wann d’an naki ya ruining d’ina ba.”" Izuwa lokacin cikin ta tunzura itama “Aw laifin Haidar kake gani..? Kai bakaga laifinka ba.. Kan wani dalili zaka cakume kwalan d’anka a bainar mutane.. Cameras all over ba dole masu Neman ganin bayanmu suyi amfani da wann damar ba.. Yanzu sai ka yarda da maganan Haidar da yace maka akwai mai maka zagon k’asa cikin mutanen da ka aminta dasu..” "Katseta yai cikin b’acin rai “This is natural in a business world. We’ve business rivals and competitors. So ba abin mamaki bane idan sunada spy cikin Kampaninmu.. Amma babban abun takaicin shine yanda muka gaza handling such situations.. And this is all your Son’s fault.. He’s weak, idiot.. A pathetic loser.. Yana can ya saka mata a ransa.. What do you expect..?”" Ya kuma jinjina Kai yana sakin huci sai yarfe gumi yake kai kace ba sanyin AC ne ke circulating cikin parlorn ba. Isowar Haidar k’ofan gidan mahaifin nasa yai tozali da dandatson ‘yan jarida. Ai kuwa kaman jira suke suka nufosa suna jefo masa tambayoyi ta ko ina. “Yallab’ai Aliyu. Da gaske ne mahaifinka ya tareka da fad’a bayan cecekuce da ya kaure tsakaninku cikin Kampanin mahaifin naka..? Engr Maitama ka amsa mana..” Da kyar ya samu ya kutsa cikin gidan sabida tambayoyi da kalaman da manema labaren keta jefo masa. Yana dosowa parlorn Daddy ya nufesa a zafafe kaman zai shak’o sa Mommy tai saurin shiga tsakani cikin k’ok’arin dannar mijinta. Sosai yake huci kaman zai kifa k’asa yana nuni da Haidar hannunsa har rawa yake. “You.. You and your entire existence is a disappointment..! Kai kayi kad’an ka lalata mun suna da sunan Company.. You better find a way to fix this mess kafin business rivals d’inmu su samu abun yawo damu kaji na fad’a maka.. Bazan tab’a bari bak’in cikinka yayi ajalina ba.. I will make sure to cut you off kafin hakan ta kasance..” Yatsanshi na rawa yaci gaba da nuna Haidar “So Kar ka sake kayi abinda zaisa na haramta maka amfani da sunana..!” Daga haka sa Kai yai ya haura sama dan a halin yau fita ma bai ganshi ba ‘Yan jaridu ta ko ina. Dan yasan K’iris abokan adawansu na kasuwanci Ke jira. Har yayi step biyu ya kuma juyo ya dubi Haidar da idanunsa suka kad’a sukai jazir “Kaje ka sallami mutanen can da ka tara mun kof’ar gida.!” Yasa kai yaci gaba da haurawa. Furzar da huci Haidar yai yasa kai zai shige. Dan yasan mahaifinsa bazai tab’a sauraransa ba. Momy ta dakatar dashi “Mom please not now.!” Ya katseta da fad’in haka. Cikin rawar murya take furta “What’s wrong with you Haidar.. Why are you doing this to us to yourself.. Meyasa ka maida iyayenka Abokan gabanka.. Why can’t you open your eyes and see my son.. Your Dad is only trying and struggling to make a proper man out of you..” “Oh really Mom.! Is he really trying to make me become a better person by pressuring me to meet all his expectations..?” Muryarsa ya soma rawa sanda yake furta “Na gaji.. Na gaji.. I’m fed up with everything around here..!” Bai kuma tsayawa sauraronta ba yasa kai ya fice yana haki da huci ga wayarsa da ta gaza yin Shiru. Kira ne keta shigo masa. Saiga Mommy ta koma gefe tana hawaye. Meke faruwa da rayuwar ahalinta.. Meke damun Haidar.. Dik yanda akai something is wrong a wani wajen.. Zama bai ganta ya zama dole ta tashi tsaye. Da wann tunanin ta nufi nata b’angaren duk jikinta a mace kaman dai ba Mommy ba. Mace mai zafi da jajircewa. Jiki a sanyaye Anisa ta k’araso rik’eda waya ta mik’a ma Mommyn tana fad’in “Ammi Ke son magana dake tana ta kiran wayarki bata samu.” Mommy tana amsar wayar ya fashe da kuka tana fad’in “Asshe ba lafiya.. Asshe gidana a hargitse yake..” Jin haka yasa Anisa komawa dan ta baiwa ‘yan uwan waje su tattauna. Sosai hankalinta ya tashi da ganin yanayin Mommy dan tinda take bata tab’a ganin ‘Yaruwar mahaifiyar nata cikin irin wann yanayi ba. ** KANO K’aton parlor ne mai d’aukeda kekunan d’inki kusan guda biyar. Yafi kama da wajen koyon d’inki. Wata mata ce da ta d’an data a shekare tsaye cikin babban zauren tana duba kekunan. Ummulkhairy ce ta soma halarta cikin d’aliban nata. Dama ita d’in da wuri take zuwa kafin lokaci yayi dan ta taimaka da share share da gyare gyare. Sallama saman bakinta ta shigo. Matar ta fad’ad’a murmushinta “Wa’slaikissalam uwar alkhairi. Dan haka take kiran Ummul d’in a akasarin lokuta. Ummulkhairy ta risina ta gaidata. Ta amsa kaman ko yaushe da sakin fuska “Uwar alkhairi kece dai kullum akan gaba kina masu wayo kina kwashe ladan. Wataran bazaki huta ba.. Jiki da jini Ummul kink’i ayi maku roster da kowa tasan ranan nata aikin.” Ta murmusa “Hajja ai nafi son na tara ladan da albarkan ni kad’ai ne..” Hajja Fannah ta murmusa “Ai kuwa da izinin Allah albarka na bibiye dake.. Kinci sunanki uwar alkhairi..” Murmusawa ta d’anyi kad’an jikinta na kuma yin sanyi da kalaman Hajja sakamakon tuno tashin hankalin da ta baro a gida. Ta mik’e da sauri gudun kar Hajja ta fahimci yanayinta ta d’auko tsintsiya zata soma shara Hajja da tuni ta karanci yanayinta ta dakatar da ita. "“Zo nan Ummul, zo ki zauna magana zamuyi kafin sauran d’aliban su k’araso. Bar sharan nan.” Tai mata nuni da gefenta saman tabarma." Jiki a sanyaye Ummulkhairi ta isa ta zauna. "Hajja ta gyara zamanta “Fad’a mun me Ya faru.?” Hajja Fannah ta jefo mata tambayar dan dama tana sane da halinda Ummul d’in ke ciki. Gidanta na bayan layin su Ummul layin da ke babban kwalta. Hajja Fannah tanada shagon d’inki da yara maza masu d’inki a shagon ta dake gaban gidan nata yayinda take koyar da ‘yanmata sana’ar d’inkin a cikin gidanta. Sunyi sabo mai tsafta da Ummul tin sanda ta soma koyon d’inki wajenta. Tana bata shawarwari had’ida kwantar mata da hankali hakan yasa Ummul ke samun sanyi wajenta, takan kai mata damuwarta su zauna su tattauna ta kuma bata shawarwari masu amfani a gareta had’ida nitsa zuciya." Ummul ta d’an share hawayen da suka gangaro mata “Hajja wllhi na gaji.. Harga Allah na gaji.. Ita fah Umma ko wanne irin mutum so take na aura babu ruwan ta ko ina san wann mutumin ko bana so.. Ita burinta kawai nai aure da farin ciki ko babu. Ni kuma a halin yanzu wllhi batun auren nan ya fita kaina ni sana’ar nan da nake nafi samun kwamciyar hankali cikinsa fiyeda komai. Shin wai ita mace ba’a mata uzuri ne a rayuwar nan..? Hajja ba biye biyen maza nake ba.. Allah shine sbiadana ina k’ok’arin tsare mutuncina.. Sann azumin litinin da Alhamis duk basa wuceni ba wai dan na Gaza rik’e kaina ba sai dan sabida nasan shi azumi garkuwa ne Hajja.. Amma ita Umma duk fah bata ganin wann. Ita kawai damuwarta mutane da abinda suke Fad’i.. Shin Hajja menene laifin wacce Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure..?” Ta k’arashe damuwa fal fuskarta hawaye na kuma gangaro mata. "Girgiza kai kad’an Hajja Fanna tai, cikeda tausayi. Ta kuma gyara zama tana duban Ummulkhairy “Ummul, shi fah d’an Adam a koda yaushe bai rasa abin Fad’i.. Sann har abada bazaka tab’a Iyar masa ba.. Mutum sai Allah..” Ta kuma gyara zamanta “Wato muna cikin wani irin Al’umma ne da k’addararka take iya zama zunubi a gareka.. Mai nake nufi da k’addararka tana zama zunubi a gareka? Macece Allah zai jarabceta da JINKIRIN aure sai kiji mutane suna cecekucen cewa ta zauna a gida tak’i aure. Idan wacce take karatu ne sai kiji ance ta rungumi boko tak’i aure.. Idan ma Sana’a take dan ta rufa ma kanta asiri sai kiji ana cewa maza ke bata kud’i ta Kama Sana’a ne dan ya zame mata garkuwa kar a zargeta.. Ita dai mace wai bazata rayu ba saida tallafin namiji. Mace ce Allah zai jarabceta da mutuwar aure sai kiji ana cewa ta kashe aurenta ta dawo gida bazaki tab’a Jin ance miji ya kashe mata aure ba sai k’alilan a’a itace dai Sarkin laifi. Kuma babban abin takaicin mutanen da tafi kusanci dasu Sune mutanen da take soma fuskantar k’alubale daga wajensu. Kowa sai ya tsangwameta a cikin gidan baga iyayenta ba baga ‘yanuwanta ba a wasu lokutan. Kinga a nan k’addararta ya zama kuskurenta.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Ummul ba ina fad’a Miki haka bane dan kiga laifin iyayenki ko wani abu mai Kama da haka. A’a ko d’aya, burin ko wasu iyaye shine da zaran ‘yarsu ta isa aure su ganta a d’akin mijinta. Kuma babu iyayen da zasu so suga auren ‘yarsu ya Mutu. Toh amma idan jarabawan Ubangiji ya shigo ciki sai ayi hak’uri a fawwala masa lamuran. Ka tsara rayuwarka yanda kake burin Ubangiji ya tafiyar maka da ita tareda fatan mafarkan ka su cika ba laifi bane hasalima Wanda baya planning rayuwarsa baisan ina ya dosa a rayuwar ba. Toh amma wasu lokutan yanda muka tsara ba haka rayuwar take zuwa mana ba. Dalili kuwa shine ba muke da hakkin tsara rayuwar ba iyakacin namu mafarkai da burika had’ida fata na gari. Ubangijin duka shike tsara mana rayuwar yanda yaso. Kuma tsarinsa a koda Yaushe shine daidai. Idan ya amsa mana addu’anmu ya tabbatar mana da burinmu da fatanmu sai muyi farin ciki mu kuma gode masa. Sann idan ya jarabcemu ya janye wann fata daga garemu bamu samu abinda muke mafarki da buri ba shima sai mu masa godiya sabida shi yasan abinda yasa ya hana mu kodai abin mai cutarwa ne a garemu. Ko kuma ya mana tanadin Wanda yafi wann.” Ta kamo hannun Ummulkhairy cikin nata “In every delay, I believe there’s khayr.. Just like your name Uwar alkhairi. In sha Allahu JINKIRINki zai zamto cikeda d’imbin alkhairi.. Babban abinda zan Miki wasiya dashi shine biyayya ma iyaye. Kar ki kuskura koda wasa ki fasa musu biyayya matuk’a bazasu ce ki sab’i mahaliccinki ba.. Idan kika rik’e biyayyan iyaye alkawarin Allah ne rayuwarki zai cika da d’imbin alkhairi kinji ko..”" Ummulkhairy ta jinjina mata Kai a hankali kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta. Hak’ik’a tana samun relief da kalaman Hajja Fannah. Inama Ummanta zata kasance mai fahimta kamar haka. Sallaman wasu daga cikin d’aliban yasata k’ok’arin saita kanta Hajjah Fannah na fad’in ta kwantar da hankalinta komai zai shige ya zama tarihi da izinin Allah. Ta mik’e tana amsa gaisuwan ‘Yanmatan da suka shigo tana fad’in yau dai Ummul d’inta zata huta Sune zasuyi shara su gyara waje. Daga can bakin Layi Alhaji Kamilu Ya aje motarsa Mama na biye dashi tana fad’in “Kai dai muje ka bama idonka abinci Alhaji.” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *06* *©️Sameena Aleeyou… * K’ofan gidan Hajja Fannah Mama ke nuna masa “Yauwa Alhaji. Nasan Kai mutumin kirki ne. Ance matanka ma ko fita unguwa basayi tsaban yanda kake kaffa kaffa da iyalanka. Toh kaga can yanda kaga mata da maza suna safa da marwa.” Alhaji Kamilu ya kuma duba k’ofan gidan wanda shaguna suka saka a tsakiya ga samari sai kai komo suke tsakanin shagunan can gefe harda shagon aski ga ‘yanmata masu sana’an koyon d’inki suna Kutsawa suna shiga gidan Hajja Fannah. Mama taci gaba “Toh wann gida dai dake gani Ummul tana ciki da ita ake wann kai komo tsakanin wad’ancan samari marassa tarbiya masu aski irin na shed’an.” Idanun Alhaji Kamilu ya sauk’a samarin da Mama Ke nuni dasu wanda suka fito shagon Aski gana ganinsu kaga samari marassa tarbiya ga wani aski da aka musu an kwashe gefe d’aya an bar d’aya. D’aya saurayin ma harda sark’a a wuyansa. Alhaji Kamilu yai Shiru kaman mai nazari. Sai kuma yace “Da zaran na aureta ta dena fita ko k’ofa dan mata na ko taron biki da suna basa zuwa babu yanda suke zuwa sai asibiti da ya zama dole.” "Mama tai ‘yar bazaurar murmushi “Toh ai Alhaji ba a nan gizo Ke sak’an ba.” Ta kuma gyara tsayuwarta “Kaga wann gida da Ummul Ke zuwa da sunan koyon Sana’a. Matar gidan ba kowa bace face gasunk’umar kawaliya. Wllhi nake fad’a maka Alhaji ta addabi kowa ta fitini kowa a unguwar nan. Mata take tarawa cikin gidanta maza kuma suna daga waje a shago. Maza take had’awa waje mata kuma cikin gidan ayita aikata masha’a ana aikata alfasha. Kuma ba zallan ‘yanmata harda matan aure a wann bad’ala da take had’awa. Na tabbata bazaka so ka auri yarinyar da ta gama watsewa wajen wann hatsabibiyar Matar wacce ko aure bata dashi zaman kanta take zaman daduro.. Wann shago da koyar da sana’a da take cikin gidanta ba komai bane face rufa rufa gudun idon mutane. Amma mu da mukaga jiya mukaga yau a unguwar kowa ya kwana da sanin Kawaliya ce. Amma idan baka aminta da abinda nake fad’a maka ba zaka iya tare mutanen unguwar nan ka tambaya Kaji idan ba zaman kanta take ba. Ko aure bata dashi babbar Magajiyar karuwaice. Kaf ‘yanmata da matan aure dake zuwa wajenta da sunan koyon sana’a, karuwanci suke fitowa su fake da san’a. Meyasa Ummul tak’i aure..? Kai bakai ma kanka wann tambayar ba. Mace har mace kyakkyawa irin Ummulkhairy ta gaza samun mijin da zai aureta.. Ai kaima kasan da walakin wai goro a miya.”" Ganin Alhaji Kamilu ya kifa kansa had’ida maida hannayensa baya irin yanda manya suke idan suna tunani yasa Mama ci gaba “Ni wllhi ganin mutuncinka ne kuma ganin Malam zai yaudareka ya lik’a maka ‘yarsa da ta gama yawon ta zubar a kororo yasa nai wann shahadar nace bari dai na sanar dakai gaskiya ka gane dalilin da Ke sa ko wani namiji mai kamala da mutunci Ke guje ma aurenta. Malam bai dubi amanar dake tsakaninku ba. Ba kalan suturan da baka masa ba amma ya zab’i ya maka lumbu lumbu dan dai kawai shima ya rabu da alk’ak’ai.. Yo shima ya gaji da ita.” Birki tai da kalamanta ganin Hajja Fannah ta fito biyeda ita Ummulkhairi ce rik’e da kayan d’inki suka shige shagon d’inki ga wani matashi ya fito daga cikin shagon ya gifta ta gefen Ummulkhairi. "Mama tai kabbara tana hamdala “Ka gani ko.. Ka tabbata ba sharri nake ba. Wai ance gani ya kori ji.. Kana nan kanata rawar k’afa zaka angwance toh aikin banza kake wai rufin d’aki da b’arawo dan k’artai bila adadi sun rigaka..” Ta numfasa had’ida gyaran murya “Toh Alhaji ni na gama nawa, Allah ya gani na fita na sanar dakai. Kuma ka gani ma idanunka. Ya rage maka ka amince ka sai ma kanka da iyalanka tikitin mutuwa dan k’anjamau ne zai maku sallama. Ka taimaki kanka kaman yanda saura suka taimaki kawunansu. Ni na Barka lafiya Alhaji..”" Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige zuciyarta fari tas. Alhaji Kamilu kuwa sai kallon k’ofan shagon yake yana jira yaga ko Ummulkhairi zata fito amma shiru. Zuciyarsa sai tafarfasa take haka yaja k’afafunsa yana sab’a babbar rigarsa da take ‘yar duk’unaso ya nufi motarsa. ** Mama tana shigowa gidan ta cire mayafi ta soma zuba ruwan bala’i “Iyi.. Kan wani dalili za’a tare ni a hanya ana mun cin mutunci kan laifin da banji ba ban gani ba.. Babu wanda ya huta a gidan nan duk akan rai guda.. Baga yarana dake gidan mazajensu ba yanzu abun har ya tsallako kaina… Toh wllhi bazan d’auki cin mutunci daga kowa ba kan ‘yar da ban haifa ba..!” Umma ta fito daga kitchen afujajan tana goge idanunta da hayak’i ya sanya mata su hawaye “Yaya lafiya.. Meke faruwa..? Wani abu ne aka miki..?” Mama taci gaba da tururi “Yo uban meye ma ba’a mun ba.. Gashi can Alhaji Kamilu yake ko ya tareni a hanya ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba saikace alhakin tarbiyan Ummul a hannuna yake.!” Cikin Umma ya bada wani irin sauti k’uuuu “Wani abu ne Ummul d’in tayi Yaya.?” “Meye kuwa batayi ba bayan ganinta a gidan Matar nan da yayi wacce kowa ya kwana da sanin Gasunk’umar magajiyar karuwai ce.. Ai bansan shashashancinki ya kai har haka ba Suwaiba.. Ni na zata da kika samu wanda zai rufa ma Ummul asiri ya aureta kinyi mata iyaka da gidan wann Kawaliyar mai zaman kanta ashe saketa kikai kamar tinkiya tana ci gaba da zuwa.. Yo a haka ne kike buri da fata ta samu mijin aure bayan kowa ya kwana da sanin ga hark’ar da Matar take d’aura ‘yanmata. Ai gashi can Alhaji Kamilu dik yanda akai yaji daga bakin mutane. ya tareni yana sanar dani dama munsan ‘yar mu yawon ta zubar take waye ya mutu waye tashi..” Ta kafe Umma da tuni duniya ya shiga juya mata kafin taci gaba “ Bari kiji Suwaiba nidai ban haifi Karuwa ba Allah ya gani ehe..!” Ta k’arashe tana mai shigewa fuuu. Umma ta soma girgiza kai tana dafe kai ta shiga bin bayan mama tana “Na shiga uku ni Suwaiba..! Yaya kar kiga laifina.. Wllhi laifin Malam ne na mata iyaka da wann koyon san’a amma shi ya k’yaleta yace dole ya koyi san’a tinda ba karatun take ba.. Amma anyi na farko anyi na k’arshe bazan bari Ummul ta kuma jaza mun ba..!” Ta k’arashe tana zaran mayafinta. Ta nufi waje a fujajan. Mama ta bud’e murya tana fad’in “Miyar tuwonki fah.. zai k’one..” “Yaya ki rik’e min ni nayi nan..!” Ta fad’i takalma a hannu ta nufi waje kaman zata tashi sama. Tana ficewa Mama ta kece da wata irin muguwar dariya. Har ga Allah shashancin Suwaiba na saka ta nishad’i. Wai Malam ya rasa da wa zai had’ata su goga a kishi saida wann shashasha ballagaza lamba d’aya wacce sam wayau da hankali basu isheta ba. Indai kishiya irin Suwaiba ne a kawo mata gomansu ma. Ta kuma kecewa da dariya tana kwaikwayon gudun Umma takalma a hannu. Ta bud’e murya tana fad’in “Kiyi a hankali dai kar ki fad’i ayi haihuwar guzuma uwa kwance ‘ya kwance.” ** Abuja. Hisham ya kuma girgiza kansa a karo na biyu yana duban Haidar dake zaune calmly kaman babu abinda Ke faruwa saima d’an tapping table din dake gaba garesu da yake da yatsarsa guda fuskarsa na duban wani b’angaren. “Haidar kamata yai muyi suing news outlet da sukai publishing labarin nan for defamation of name..” "Kaikaitowa yai yana duban Hisham, ya d’anyi still kafin ya girgiza kai “Seriously Hisham..Are we going to waste our time going against the media..?” Ya d’an girgiza kai “Don’t you think we should focus on finding the traitor that leaked the video..?”" Hisham ya d’anyi Shiru kaman mai nazari. Sai kuma ya jinina kai “Yeah you are right.. Gaskiyanka ne fad’a da media ba riba.. Wann b’eran na cikin company zamu kama sai ya sanar damu wanene uban gidansa. And I’m pretty sure shine wanda ya fitar mana da bayanan sirri na company.” Rufe bakin Hisham keda wuya wayarsa ta soma ruri. Daga Company ake kiransa. Hisham ya d’aga suna gaisa nan ya fahimci aminin mahaifin Haidar ne Alhaji Gimba mai kiran. Bayan sun gaisa ya tambayesa ko suna tareda Haidar. Saida ya dubi Haidar d’in wanda hankalinsa ya koma kan wayar salular salulansa kafin ya d’an matsa gefe ya sanar dashi eh suna tare. Magana suka d’anyi na lokaci kafin daga bisani sukai sallama. Hisham ya dawo wajen zamansa ya zauna yana tunanin ta yanda zai soma sanar da Haidar abinda Alhaji Gimba ya sanar dashi. “That was Alhaji Gimba. One of the board of directors.. Aminin Dad..” Haidar ya murmusa da gefen bakinsa kad’an jin yanda Hisham Ke masa bayanin mutumin da ya masa farin sani “What’s with the introduction..?” Yai maganar yana tsare Hisham da idanu. Hisham ya gyara zamansa cikin kujeran “He called to say ya shirya maka interview with the media tomorrow by 10am at the company.” Haidar ya kuma murmursawa da gefen bakinsa irin na Wanda takaici ya gama cikasa yana mai girgiza kai “Unbelievable.!” Ya furta a hankali. Yanzu ba Daddy kawai ba even his friends suna intruding cikin rayuwarsa. “Kan wani dalili zai shirya mun interview ba da sani ba..?” "Ya mik’e tsaye yana nuna Hisham d’in “Look, you call that man right this instant and tell him I’m not attending.!”" Hisham ya girgiza kai had’ida furzar da huci kad’an yasan halin abokin nasa yasan kayansa hakan dama zai kasance. Shima d’in mik’ewa tsaye yai “Of course you are attending..” Haida ya dubesa da mamaki “Amma kaji yanda kake min magana..?” Hisham ya kuma furzar da huci “Haidar he’s only trying to help here.” “Did I ask for his help..?!” Ya katse Hisham a fusace. “But..” “Bana buk’atar taimakon kowa.. And Much less from him.!” Ya k’arashe yana mai buga table d’in da hannunsa. Lokaci guda yasa kai zai shige. Hisham yai saurin dakatar dashi “Haidar this is the only way to save…” "“The Company’s image, right.?” Haidar ya katsesa da fad’in haka." “No.. I mean to fix this.. Ina nufin ya shafi sunan mahaifinka Haidar.. Harma da ahalinka.” “Oh c’mon.! What family.. Wani ahali kake magana..? Kafi kowa sanin banida wani ahali.” Hisham ya d’anyi still “Haidar kullum ina fad’a maka ba’a fad’a da iyaye a zauna lafiya..” “Oh shut up.!” Ya fad’i yana mai nufan motarsa. "Hisham ya furzar da huci kad’an yana mai take masa baya yake ci gaba da fad’in “Haidar kai kad’ai kafi cancanta ka jagoranci project d’in nan.. You work so hard to get to where you are now.. Bazaka bari all your efforts and hardworking su tafi a banza ba.. I know you so well, you don’t surrender. You just need a minute to cool off..”" Kaman dai badashi yake maganar ba haka yaba ma banza ajiyarsa ya isa ga motarsa cikin sassarfa. Daidai sanda Haidar ke tada motar Hisham ya bud’e murya yana fad’in “10am tomorrow at the company.” Yai maganar cikin d’aga murya dan tuni Haidar yaja motarsa ya bar wajen. Hisham ya girgiza kai kad’an dafe da kunkuminsa yabi bayan motar Haidar d’in da kallo. Yasan ba lallai Haidar ya halarci wann interview d’in sanin wanene abokin nasa. Yana tafe cikin mota yana kuma nazarin abun. Wai Alhaji Gimba ya shirya masa tattaunawa da ‘Yan jarida. How could he..! Ta yaya zai yanke babban hukunci haka ba tareda ya tuntub’e shi ba. Akan me za’a sakashi magana da media ba tareda amincewa da yardarsa ba. Duk ma ba wann ba since day one bai k’aunar mutumin sabida k’ok’arin shiga rayuwarsa musamman tsakaninsa da mahaifinsa da yake. Ya tsani a shiga rayuwarsa without an invitation. Idan bai gayyaceka cikin rayuwarsa ba kawai kar ka shiga. Ya furzar da huci a hankali yana so ya gano wani abun. ** Kano. Banda sautin keken d’inki dake tashi cikin zauren baka iya sauraron komai. Ko wacce ta bada hankali da himma wajen ganin ta zama k’wararriya a sana’ar da suke koyo. Kaman daga sama suka soma jiyo kururuwa na nufosu. Gaban Ummulkhairi ya yanke ya fad’i. Cak ta dakata da abinda take tana mai furtawa a hankali “Umma..!” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *07* *©️Sameena Aleeyou… * Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba “Sai kinyi ajalina da bak’in ciki kiji dad’i. A sau nawa zan miki iyaka da wann gidan amma kin rantse sai kin tona min asiri Ummul. Me kike nema ki zama ne wai.!” Ta karashe tana fashewa da kuka. Hajja Fannah wacce tun shigowar Umma ta sallami sauran ‘yan ajinta dakatar da Umma tai fad’in “Haba Umman Ummul ya kike kausasa harahenki akan ‘yarki. Shin baki san fushinki mai tasiri ne akanta koda baki nuna ba. Ke fah uwa ce kuma za’a tsai dake a tambayeki gameda kiwon da aka baki. Kaman yanda kikeda hakki akan yaranki haka suma sukeda hakki akanki.. Addini bai barmu kara zube ba face saida ya tsara mana yanda zamu tafiyar da rayuwarmu.. Yanzu islamiya har na matan aure sun yawaita.. Duk wanda kikaga ya zauna da duhun kai shi yaso.” "“Malama dalla ki min shiru ba wa’azi nazo kimin ba… Yo idan ma zan d’auki wa’azi sai na d’auka daga bakin ballagazar mace irinki mai zaman kanta wacce ta kasa zaman aure. Sann da kike maganar a koma makaranta yanzu kai waye kije garinmu kaf ki tambaya waye mahaifina.. D’iyar malamai nike jikan sha rubutu. Ubana Malami ne mai tak’ama da Zauren karatu, na girma ina kwankwad’an ruwan alk’alami da tawada.. Ni har an isa amin gorin ilimi nida na gajeta. Sauk’a uku nayi da k’ananan shekaru kafin a rufani akaini d’akin miji..!” Taci gaba da jijjiga tana nuna Hajja Fannah “Kuma bari kiji na fad’a miki idan ma kece kike ziga Ummul kike burin ki hanata aure kaman yanda ke kika kasa zaman aure toh Allah bazai baki nasara ba. Ummul tun tana ciki aka nema mata tsari da shed’anu irinku. Ko ana ha maza ko ana ha mata Ummul d’ina zatayi aure kaman yanda ko wacce mace mai mutunci keyi ehe..! Ke kuma shige muje kafin na kwashe miki albarka..!” Ta k’arashe tana tasa k’eyar Ummulkhairi wacce da alama ta gama saduda da sha’anin Umma." Mamaki bai saki Hajja Fannah har suka fice. Gaba d’aya ta gaza katab’us. Ita a halin yanzu ta fara tantama idan Mahaifiyar Ummul na cikin hayyacinta. Girgiza kai tai cikeda tausayin Ummul tana mai ayyanawa lallai tana cikin jarabawa. ** Khulsum da dawowarta kenan daga makaranta taji k’urin miya na k’una kan wuta duk ya cika gidan. Ga hayak’i na fitowa daga kitchen. Da sauri sauri ta shigo a tunaninta babu kowa ne amma sai ta hangi Mama zaune tsakar gidan tana gyaran k’umbarta. Bata ce komai tasa kai zata shige muryar Mama ya dakatar da ita “Toh shafaffiya maras kunya. Kin shigo kina kallo na dan rashin mutunci ko sannun fatar baki ta gagareki. Toh ai sai ki shige ki aje jakarki kije ki gaida tukunyar miyan dake k’auri kan wuta idan ba haka ba tuwon dare ya haramceku. Ahtoh dan a banza azumin da ba lada zai hau kanku daga ku har uwarku dan nikam raina guda inada gidajen ‘ya’ya ‘yan albarka da suke kame gidan mazajensu da zasu bani tuwo. Saima gidan da na zab’a naci. Banda asara har yaushe za’a ce manyan budare da suka rik’a suka rik’e a gida ana saka masu kwanon tuwo gidan mahaifinsu. Yo sadaka kuke ci sa’anninku masu mutunci dai suna d’aunansu suna aikin lada suna girka ma mazajensu tuwo.” Ta mik’e tana buge zaninta “Idan Kinga dama kar ki duba miyan girkin uwarki Suwaiba ne dan nikam na gama girka ma k’artai irinku tuwo a gidan nan. Dan dai cikina d’aya da Malam bazai gagara ba. Amma bazai yuwu da girmana a ganni ina zama bakin murhu ina girka ma gandama gandaman ‘yanmata irinku tuwo ba. Daga me yawo da sunan karatu sai mai yawo da sunan koyon san’a..” Tasa kai ta nufi d’aki “Tani ta daina girka ma k’artai tuwo wacce duk tai zuciya cikinku ta tafi nata d’akin mijin ta girka.” Ta k’arashe tana rangad’a gud’a da shewa. Khulsum ta girgiza kai kurum kafin ta aje jakar makarantarta nan tsakar gidan ta cire hijab ta nufi kitchen d’in. Shigarta keda wuya ta soma jiyo muryar Umma ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. “Ko labari na sakeji kinje gidan matar can da sunan koyon San’a Ummul saidai ki nemi wata mahaifiyar amma bani Suwaiba ba. Banda salo da fitina ke da ake gab da saka miki rana yo wacce sana’a zaki koya ya wuce zaman aure dake gabanki.” Da mugun mamaki Khulsum ke duban mahaifiyarsu “Umma.. Yanzu d’an koyon sana’ar ma hanata kikayi. Umma itafa sana’a dogaro da kai ne…” "“Ki rufe mun baki Khulsum, aure shine babban sana’ar dake gaba gareta.. Shine daraja da cikan mutuncin ‘ya mace.”" Khulsum ta saki baki da mamaki “ Umma a wann zamanin da akasarin wasu mazan basu sauk’e nauyin d’awainiyar matansu da Allah ya hukunta masu wann san’ar ba ita zata rufa masu asiri ba. Umma ko za’a baka Shi fah abu naka dad’i ne dashi.” “Idan bakiyi shiru ba Khulsum zanzo wajen naci miki mutunci.. Hanshak’iya ana fad’a kina fad’a.” Muryar Mama da fitowarta daga d’aki waya manne kunnenta ya katse Umma. Cikin d’aga murya Mama Ke ci gaba da fad’in “Hellaww ina jinki Badidi na Badi’atu ‘yar albarka.. Wai shi Tasi’un ya kawo miki Kaji kika soye mun.. Kaji D’an albark. lallai Tasi’u ya cika Surki na k’warai.. Allah dai ya maku albarka ya k’ara zaunar daku lafiya a gidajenku ya rabamu da sharrin mahassada masu san ganinmu a rana.” Kuka ya kuma zuwa ma Umma bata iya sauraron wayar da Mama keyi ba ta shige d’aki. Ita kuwa Mama tana ganin Umma da yaranta sun shige d’aki ta sauk’e nannauyan ajiyan Zuciya tana datse wayan Badi’a wacce ita kanta Badi’an ta rasa gane wasu surkulle mahaifiyarta Ke mata cikin waya. Ita da take sana’ar da ita irin uk’ubar da Tasi’u Ke bata a ‘yan kwanakin wanda ta gaza jurewa tana ce mata ita ta gaji da auren gida zata dawo sai taji tana mata wasu sunbatu wai Tasi’u ya kawo Kaji a gyare mata. Mama ta koma d’aki ta kuma danna kiran Badi’a. Kaman jira Badi’a take ta d’aga kiran “Mama wani irin abu ne inace miki Tasi’u ya dawo da hallayansa na baya yau bugun tsiya ya min saida mak’ota suka k’waceni kina kira mun wasu kaji.” Mama ta yarfe gumi “Ke Badi’a saurareni. Idan Tasi’u tsire naman jikinki yake haka zakiyi hak’uri ki zauna.. Zanzo gidan na sameki nasan yanda zamu b’ullo masa amma koda wasa kar kiyi tunanin dawowa gida.” Daga haka bata kuma tsayawa sauraron Badi’a da tuni ta fashe mata da kuka tana fad’in ita dai ta gaji. Mama kaw ta mik’e tana tunanin yanda zasu b’ullowa al’amarin Tasu’u mijin Badi’a. ** Abuja. Maitama Builders (MB). Zauren tattaunawar ta cika da ‘yan jarida abinda ya shafi b’angaren kasuwanci. Kowa shirye yake da tambayoyin da zai Engr AA. Maitama yake. Hisham ya shafi goshinsa dan interview d’in zai kasance live ne sakamakon yanda kowa ya k’agu yaji gaskiyar al’amarin bayan video da yai trending a manyan shafuka musamman shafukan watsa labarai na kasuwanci. Hisham sai kai komo yake yana duba lokaci yana add’uan Allah sa kar Haidar ya badasu. Wann shine kad’ai damarsu ta k’arshe da zata d’aga darajan Kampanin ta kuma wanketa daga daud’an da aka shafa masu. Masu gabatar da interview sun cire rai da zuwan Haidar. Sun mik’e da zummar tafiya Hisham yai saurin dakatar dasu yana sanar dasu Lallai Haidar zai zo shi. A can gidan Daddy kuwa suna zaune shida Alhaji Gimba a parlor suna duban live event d’in yanda Daddy Ke girgiza kai. Ko janye idanunsa daga screen bayayi “I told you he’s not capable of anything good..” "Alhaji Gimba ya girgiza kai “Inada yak’ini akanshi, Zai bayyana, kuma zai abinda ya dace.. Na tabbata bazai bamu kunya ba.”" Daddy ya soma k’ok’arin mik’ewa da zummar haurawa sama yana furta “This is a complete waste of time Gimba. Ni zan shige ciki..” "Alhaji Gimba yai saurin dakatar dashi “A’a Abokina.. D’an Dakata, kalli nan..!” Yai masa nuni da screen yanda aka hasko Haidar yana k’arasowa cikin hall d’in. Yayi kyau cikin shiga irinta cikakkun ‘yan kasuwa masu huld’a ciki da wajen k’asa. K’warjininsa ya cika wajen." Bakin Alhaji Gimba ya gaza rufuwa sabida farin ciki. Daddy ya jinjina Kai “I hope it doesn’t turn out to be another scandal.” Ya fad’i idanunsa akan Haidar da ake haskowa. A can Company Hisham ya murmusa yana duban abokin nasa harda d’aga masa yatsa guda alamun jinjina. Wani duba Haidar ya aika masa kafin ya wuce yanda aka tanadar masa domin zama. Yana k’arasawa mai gabatarwan ya mik’e had’ida mik’a masa hannu sukai misabiha kafin Haidar ya gyara zaman suit d’insa ya Zauna attentively. "Nan da nan aka soma gudanar da interview d’in. Yana jefo ma Haidar tambaya yana amsa sa daki daki cikeda k’warewa da sanin aikinsa nan ya jefa floor ma audiences wani ya d’aga hannu ya soma jefo ma Haidar nasa tambayar “Yallab’ai, munga wani hoto na yawo a kafafen sadarwa har wani gidan jarida ya wallafa wani labari cewa fad’a ya kaure tsakaninka da mahaifinka sabida gazawarka da kuma banbancin ra’ayi da kuke dashi. Shin menene gaskiyan al’amarin..?”." Haidar ya kafesa da idanu kafin yai clearing throat d’insa. “A ko wace ma’aikata I believe ana samun sauye sauye da banbancin ra’ayi tsakanin shugaba da ma’aikatansa. Which is what makes the company stand firm on its feet..” Babu wanda zaice bai zama impressed da yanda Haidar ke amsa tambayoyin da ake masa with so much courage and determination. Mutumin ya jinjina kai “So does that mean da gaske ne kenan kaida Mahaifinka baku samun jituwa har a wajen aiki..?” Haidar yai masa k’uri dan ya gane turosa akai yai masa tambayoyin da zasu tunzurashi. Tafukan hannayensa ya d’an had’e waje guda “I’m not here to tell a story about my personal life. But Being the son of the president of this company doesn’t make me different from others. If I don’t receive any VIP treatment it’s because that’s the company’s policy. And I believe this is why the company remains on track despite all the challenges.” Ya kuma jinjina kai. “One more question Engr. “Is it true that your company is going bankrupt.. And the economy is at the state of crisis.?” "Haidar ya d’an rage girman idanunsa kad’an yana duban mutumin, lokeci guda ya d’an gyara zaman suit d’insa “Let’s call this a business perspective. Some times failures lead to future successes. I can assure you, MB (Maitama Builders) does not… and will never fear challenges..” Ya k’arashe yana mai mik’ewa lokaci guda mai gabatarwan ma ya mik’e yana mai mik’awa Haidar d’in hannu alamun musabiha “Mun gode da bamu lokacinka da kai Rankayadade." "Alhaji Gimba ya dubi Daddy “Look, duba kaga yanda yake amsa tambayoyin with so much focus and determination. He has all the potentials and skills to take this company to a greater heights. I’m super optimistic about him.”" Daddy dai baice komai saima mik’ewa da yake k’ok’arinyi. Alhaji Gimba ya rakashi da kallo yana mamakin Allah yai baiwa wa mutum da samun d’a irin Haidar Wanda yake d’aya tamkar ga dubu amma ya kasa gani ya kuma kasa appreciating. Sosai lamarin abokin nasa ke d’aure masa kai yanaji inama nasa d’an ya kasance kaman Haidar. ** Hisham ya kuma duban Haidar had’ida girgiza kai “Ban fahimceka ba Haidar.” “Meye baka fahimta ba..?” Haidar yace yana duban Hisham d’in. D’an gyara tsayuwarsa Hisham yai “Kanaso kace min gadar zare yaso k’ulla maka da ya shirya wann interview d’in..? Kanaso kace min ya shirya hakan ne just for you to fall into his trap and create more scandals.? Kana so kace min shi kake zargi da yi ma Kampani zagon k’asa.?” “He gave me all the reasons to suspect him.” Hisham ya kuma jinjina Kai “Amma zanji mamaki idan haka ya kasance duba da kusancin shi da mahaifinka.. So what are you planning now..?” “Of course I’ll play his little game. Shiyasa ma na halarci interview d’in.” Ya k’arshe yana k’ok’arin mik’ewa. Hisham ma ya mik’e suka soma takawa. "“If that’s the case, I’ll support you Haidar har gaskiya ta bayyana.”" Ba tareda ya dubi Hisham ba yace “I’d rather do it alone. This is my battle and I’ll fight it alone.. I’ll make my Dad swallow all his words a lokacin da zan kamo wuyan mutumin da ya aminta dashi matsayin babban mak’iyinsa. Each and every insult da ya jefeni dashi sai na sashi ya cinye kalamansa. And hakan zai faru ne kawai idan ya d’aurani Akan project d’in nan. So I’ll do whatever it takes to make sure ya mallaka min ragamar wann project din.” Hisham yai still yana duban Haidar d’in “Haidar kana magana kaman fansa kake so akan mahaifinka. Haidar.. Anya lafiya kake.. Mahaifi fah ya wuce wasa.?” “Wani mahaifin kenan.. Amma wani suna ya tara..!” Yana ida fad’in haka ya bud’e motarsa ya shige. Har ya bace ma ganin Hisham bai daina mamaki ba. Al’amarin Haidar da mahaifinsa ya soma zarce tunaninsa. *** Kano. Tinda Abba ya shigo gidan hannunsa na hagu ke dafe da b’angaren k’irjinsa. Ya kuma duban Umma dake zaune gefensa ta rapka uban tagumi tana masa sannu. Ya amsa yana mai gyara zamansa bayan yasha maganin da ta kawo masa. Saida ya daidaita zamansa sosai kafin Ya soma magana “Suwaiba” Ya kirawo sunanta. “Na’am Abban Ummul.” Ta amsa duk jiki a mace ganin yanayin Abban. Abba yaci gaba “Magana nake so muyi amma ina so ki kwantar da hankalinki.” “Toh Abban Ummul.. In sha Allah zan kwantar da hankalina.. Nidai burina ka samu lafiya..” Abba ya d’an b’ata lokaci kad’an kafin yace “Ai na sanar dake yanda mukai da manemin auren Ummulkhairy. Wato Alhaji Kamilu mak’ocina a kasuwa.” Umma ta jinjina kai “Eh kwarai anyi haka..” Abba ya kuma jinjina kai “Wato Suwaiba bayan shi Alhaji Kamilu yazo yaga Ummul kwanaki uku da suka shige. Washe gari da safe kaman yanda kika sani sun taho har nan k’ofar gidana shi da wani abokinsa sun bada sadaki.. Alhaji Kamilu ya bada sadaki naira dubu d’ari a matsayin sadakin ita Ummulkhairy lakadan” Umma kam tsaban farin ciki bata tsaya taji k’arshen zance ba ta shiga gud’a tana fad’in Ummul dinta tayi goshi ‘yan bak’in ciki saidai su Mutu. Abba ya lumshe idanunsa kad’an yana jin zafin k’irjinsa na k’aruwa. Daurewa yai ya d’an bud’e murya yai mata tsawa kad’an data saurare shi. Umma ta kuma wahse baki tana gyara zama “Yi hakuri Abban Ummul.. Farin ciki na ne ya gaza b’uya. Ummul d’ina lokaci yayi. Ai ni dama tin a nan wajen ka kirawo yan uwanka a nan cikin gida suka zama shaidu aka d’aura.” “Suwaiba ki dubi girman Allah ki saurareni.” Ya kuma fad’i cikin tsarewa. Ta saka hannayenta biyu ta kame bakinta “Na tuba.. Nayi shiru Abban Ummul.. Ina sauraronka yaushe suka nema a saka lokacin biki..? Ni wllhi na ma basu wuk’a da nama su saka ko gobe ne.” Abba ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana girgiza kai kafin yaci gaba “Toh kinsan kwanakin baya kasuwa ta d’an ja mun baya har na amso bashin hatsi a nan cikin kasuwa..” Jikin Umma ya soma sanyi amma sai tace “Kasan mutane yanzu idan Sun bika bashi sunyita korortoto kenan kai kace duniya ka amsa wajensu.. Su kwantar da hankulansu lokacin biyansu yayi in sha Allah..” “Ki saurare ni Suwaiba.” “Toh Ina sauraronka Abban Ummul..” Tace tana gyara zamanta. Abba yaci gaba “Toh shekaran jiyan da suka kawo sadakin sai shi Wanda yake bina bashin hatsi Ya taho mun da buk’atan kudinsa. Lallai Lallai shima yana neman kudinsa zai amfani dasu. Kuma nima nasan yanda Kasuwa ta koma a halin yanzu. Wasu lokutan Har ka fita ka dawo ba’a zuwa saye. Godiyan Ubangiji ne kawai amma al’amarin k’asar sai addu’a. Hakan yasa na d’auka cikin sadakin Ummulkhairy na biya tinda gadarana sadakin ‘yatace. Banida hanyan biya sai wann sadakin. Na cira ciki na biya.. Yau kwatsam da naje Kasuwa Alhaji Kamilu ya tareni da batu mai tada hankali.” Ai bai kai aya ba Umma ta soma girgiza kai tana fad’in “Dan Allah. Dan tsarkin mulkinsa da buwayarsa Abban Ummul ka rufa mun asiri ka mun sutura.. Kar kace min shima ya amshe sadakinsa.. Wayyo ni Suwaiba na shiga uku na Mutu na lalace..” Abba ya kifa kansa yana girgizawa yana jin yanda Umma ke fad’in ta shiga uku ta Mutu ta lalace. Takaici da ya cika shi ganin tak’i sauraronsa sai kuka take tana jefa kanta a uku. Abba yace “Aima baki gama jefa kanki a uku ba Suwaiba sai kinji irin wulak’anci da kwance zanin da bawan Allahn nan ya mun a cikin kasuwa.!” "Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa hannayenta duka biyu dafe da k’irji yayinda Abba yaci gaba da fad’in “Tinda nake a rayuwata ba’a tab’a min irin tozarci da wulak’ancin da bawan Allahn nan ya min ba. Suwaiba, Alhaji Kamilu dai ya amshe sadakinsa ba yanda banyi ba ya bini bashin sauran kud’ad’ensa amma sai cewa yai bazai iya jira ba dan haka yasa yaran shagonsa suka kwaso kaya a nawa shagon darajan kud’ad’ensa makotanmu a kasuwa masu burin su ganmu a rana duk suna kallo. Wann wulak’anci da mai yai kama Suwaiba..”" Kukan Umma ya k’aru mik’ewa tai ta fice tana rera kuka tana fad’in Ummul zatayi ajalinta. Daga Ummulkhairy har Khulsum a tsorace suka nufo waje jin Umma na ambaton zata fad’a rijiya. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *08* *©️Sameena Aleeyou… * Yaran Umma suna kuka suna rok’onta ta sauk’o daga saman rijiya Mama na kuma ingizata “Suwaiba ko ki fad’a ko kar ki fad’a da alama dai bak’in cikin wann ‘yar naki shi zai ajalinki.. Wayyo ni Tani zanyi kewarki Suwaiba. Ashe tafiya zakiyi ki barni.. Na yafeki duniya da lahira Suwaiba.” Ta shiga rangad’a ma Badi’a da bata jima da zuwa gidan ba kira tana fad’in ta fito tayi bankwana da Suwaiba tafiya zatayi ta barsu. Suwaiba ta dena kururwar da take tana duban Mama da mamaki “Yaya bazaki hanani fad’awa ba.. Rijiya fah zan fad’a..” Mama ta kamo bakin zani tana goge hawayen da babu su “Yo ko na hanaki ko ban hanaki ba wancan ‘yar taki mai bak’in k’addara zatayi ajalinki Suwaiba. Ta shiga doka kiran Badi’a wacce bata jima da zuwa gidan ba. “Badiatu.. Badiatu! Badiatu..!! fito kiyi sallama da Suwaiba.. Suwaiba dai lokaci yayi..!” Badi’a ta d’age labule fuska a yatsine tana kuma turo kallabi gaban goshi “Toh Mama ki barta ta fad’a mana.. Idan bata fad’a ba ai bata tabbata shashasha ba.!” Khulsum ta harzuk’a “Uwa bata fi uwa ba Anty Badi’a kar ki sake gangancin zagar min mahaifiya..” Badi’a ta malamalo ashar had’ida zame d’aurin kanta tai d’amara dashi tayo kan Khulsum tana fad’in kafin uwarta Suwaiba ta fad’a rijiya sai ta fara jefata ciki taga uban da ya tsaya mata. Ai sai Umma tai tsalle ta duro daga saman rijiya ta shiga janye Khulsum wacce Baid’ia Ke k’ok’arin janyota Mama na tayata. Abu sai ya koma kaman dambe Mama ta shige ma ‘yarta Umma ma ta shige ma nata ‘yar wacce taga haik’an rijiya za’a jefata. Ummul kaw fashewa tai da wani irin kuka sosai ganin wann tashin hankalin dik sabida ita ake. Tana tsaka da kuka tana rok’onsu suyi hak’uri su daina ta hangi Abba na rarrafowa daga d’akinsa hannunsa guda dafe da b’angaren k’irjinsa. Ta kirawo sunansa cikin kid’ima tana mai nufansa. Hakan yaja hankulansu. Nan take suma sukai Kan Abba suna ambato sunansa. Tuni idanunsa sun kafe suna kallon sama baka iya ganin bak’in k’wayan idon. Sai kuma suka koma kururuwa suna neman agaji. Kaf mutanen gidan aka rasa mai kawo masu d’auki dan dik a nasu zaton wasan kwaiwayo ne da suka saba. Sukai masa caa akai kowa yana ambato Sunansa suna rok’onsa ya tashi. Umma sai masa fifita take da bakin zani yayinda Mama ta kawo ruwa cikin kofi tana mik’awa Umman. Fad’i take “Suwaiba duba mana kiga yana numfashi.” Umma na kuka take fad’in “Haba Yaya kar kiyi tunani haka. Abban Ummul na numfashi..” Taci gaba da rera kuka tana rok’onsa ya tashi kar ya tafi ya barsu. Kaf ‘yanuwansa maza dake zama cikin gidan aka rasa mai zuwa ya dubasa balle a kaisa asibiti. Dama gidan Sun gaji gaba na ‘yanubanci tin daga iyaye da kakanni. Yan wann d’akin babu ruwansu da yan wancan d’akin. Shi Abba kusan shine babba cikin mazan dake rayuwa a gidan sauran yeyyen nasu duk mata ne suna gidajensu. Shi a d’akin mahaifiyarsa shi kad’ai ne namiji. Hasalima su biyu mahaifiyar tasa ta haifesu. Daga shi sai kaw ‘yaruwarsa k’anwarsa mai suna Inna Dije. Inna Dije da mijinta basu jima da komawa garin Dutse na jihar Jigawa ba yanda mijinta ke aiki. Hasalima mijin nata d’an asalin jihar Jigawa ne amma yayi zaman Kano yanda yaga Inna Dije k’anwa ga Abba ya aureta. Sun zauna tsawon lokaci a Kano kafin iftila’in rashin tilon d’ansu ya samesu. Tin bayan rasuwar D’ansu basu kuma zaman Kano ba hakan kuma yai daidai da canjin wajen aiki da mijin Inna Dije ya samu. Sann tin bayan wann lokacin Inna Dije bata kuma saka k’afarta a garin Kano ba. Wasu dattawan unguwar masu ganin mutincin Abba su suka Kaisa wani k’aramin asibitin gwabnati mafi kusa. Mama da Umma sukai masu godiya. Jigum jigum sukai gaba d’aya suna jiran ba’asi daga wajen likitoci. Daga yanda suke zaune Mama ta kafe Umma da yaranta dake zaune daga d’aya b’angaren suna hawaye. Sai cika take tana huci dan wann dik dalilin Suwaiba da ‘yarta ke faruwa. Ta sauk’e idanunta kan Ummul wacce ta kasa daina kuka maras sauti. Kaman wacce aka sinkara ta soma furta “Wann duk laifinki ne Ummul.. Idan Abbanku ya rasa ransa ki sani alhakin mutuwarsa zai ratayu ne a wuyanki.. Kece nan kikai silan mutuwar mahaifinku..!” Umma ta d’ago tana duban Mama shaye da mamaki “Yaya ya zaki ce haka.? Ta ina Ummul ta zama Sila..?” “K’warai kuwa ita ce Sila dan bak’in cikinta da abunda ke faruwa da ita su suka taru suka haddasawa mijin mu ciwo ehe.!” Badia dake koke Koke tana ambato sunan mahaifinta ta k’arasa a guje ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad’in shegiya mai bak’in k’addara kafin ki kashe mana uba sai and fara kasheki kowa ya huta. Daidai lokacin su Azeema da Salima sauran yaran Mama dake gidajen aurensu suka iso ai nan suma suka aukawa su Khulsum. Fad’a dai yaci gaba a asibiti. Har saida ma’aikatan asibitin suka tasamma koransu. Da kyar dai aka raba bangarorin guda biyu fada. Kowa suka koma gefe suna aika ma juna mugun kallo. Can da jimawa wani Likita ya fito. Suka mik’e gaba d’aya suka nufesa. Sukai ma likitan caaa da tambayoyi kowa naso a soma amsa nasa. Mama da yaranta su Salima na yi Umma da Khulsum na yi. Ita dai Ummul ita kad’ai ce baka Jin bakinta. Likita ya zuba ma sarautar Allah idanu yana duban wann ahali Wanda majinyacin da suka kawo baya buk’atan irin wann hayaniya da tashin hankali nasu. Ya d’an girgiza kai yana k’ok’arin kwantar masu da hankali amma sai yaga kaman basa gane wann yaren. Tsawa ya daka masu yace duk suyi shiru ko su fice su bar masu asibiti. Bayan Likitan ya kebe da Mama da Umma Ya dubesu yace “Ku sani yanzu ba lokacin tashin hankali bane. Lokaci ne da mijinku ke tsananin buk’atar kwanciyar hankali. Ko kunsan mijinku na d’aukeda matsanancin ciwon zuciya mai haifar da Kumburin zuciya.!” Ai sai suka rikice Umma kuka Mama kaw mik’ewa tai dafe da k’irji “Likita kumburin zuciya fah kace.?!” Likita ya jinjina mata Kai “K’warai Hajiya.. Kuma ciwonsa ya wuce matakin farko.. Hasalima zamuyi k’ok’ari ne mu turasa can babban asibitin koyarwa dan a can ne zaifi samun kula sunada k’wararrun likitoci da ya shafi ciwon zuciya..” Umma ta share hawayen da suka zubo mata tana tuna ranan da mijin nasu yai masu wasiya da hak’uri da zaman lafiya “Likita yanzu mai zai faru da mijinmu..?” Tai maganar cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni. Sauk’e ajiyan zuciya yai yace “Kwararrun Likitocin da suka shafi b’angaren ciwon zuciya ne kad’ai zasu iya sanar daku abinda zai faru.. A halin yanzu bazan iya ce da ku komai ba.. Zuwa gobe da yardar Allah zaa tafi dashi can asibitin koyawar sai Likitocin zuciya su dubasa. Amma ku kwantar da hankulanku ba wani abin tashin hankali ana warkewa cikin k’udarar Ubangiji. Kuyi hak’uri na fad’a maku gatsau sabida Kun Kai hak’urina bango ne shiyasa. Ku kwantar da hankulanku ku had’e kan ahalinku ko dan samun lafiyan mijinku.. Please do this for your husband.” Ya k’arashe yana dubansu su duka biyu. Mama tace “Sunan maganin ka fad’a Likita.?” Ya d’an murmusa kad’an had’ida girgiza Kai “Cewa nai kuyi hakan domin mijinku.” Suka jinjina Kai a tare Likitan ya k’arada “Kar ku damu babu abinda zaku biya mutanen da suka kawo sa nan sun biya komai. Saidai idan an kaisa can babban asibitin koyarwa dole zaa bukaci kud’i ko nace kudade masu yawa.” Daga haka Sallama likitan yai masu suka fito jikkunansu duk a sanyaye. ** Abuja. Hisham ya dubi Haidar wanda ya bada hankalinsa sosai ga laptop d’in dake gabansa wanda da gani ko ba’ace kasan aiki tuk’uri yake domin achieving goals dinsa. Ya d’an Sauke ajiyan zuciya “I hope he approves the new proposal.” "Shiru Haidar yai idanunsa kan computer din har lokacin. Yeci gaba da juya pen d’in dake mak’ale cikin yatsunsa guda biyu “I know my Dad, he’s so meticulous… So everything should be done carefully..”" "Hisham ya jinina kai yana mai mik’ewa “Alright, with your permission Sir, zan koma bakin aiki na.”" “Dama ban rik’eka ba.” Haidar yace yana d’an juyi cikin kujeran da yake. Kafin Hisham yakaiga ficewa wayarsa tai ruri. Mahaifiyarsa ce mai kira. Ya fad’ad’a murmushinsa yana mai d’aga kiran. Sosai yake hira da ita cikeda so da k’auna da alamun kewan juna daga duka b’angarorin nasu. Haidar na iya sinkayo muryar mahaifiyar Hisham yanda take ta binsa da addu’o’i nagartattu yana amsa mata da ameen. Baya kasa kunne ya saurari abinda bai shafesa ba amma sai ya tsinta kansa da sauraron wayan Hisham da mahaifiyarsa. Har dai Hisham d’in suka ida waya da mahaifiyarsa Hisham na sanar da ita bazai jesa Kano anytime soon ba she shouldn’t expect him bayan bai jima da sanar da Haidar yana son daukan hutu yaje ya duba gida cikin kwanakin. Haidar ya d’an dubesa. Sai Hisham ya murmursa “Ban sanar da ita ina tafe soon ba. I want it to be a surprise.” Gajeren murmushi Haidar yai “Idan bazatan zai sanayata farin ciki.” Hisham ya jinjina kai “I hope so.. Nayi kewar Hajjata.. She’s my everything Haidar.. Ina mata son da bayada iyaka.. Na girma matsayin maraya amma bansan maraici ba sabida ita.. She’s my two in one.. Zatayi komai domin farin cikina..” "Haidar ya jinjina kansa a hankali yana jin rayuwar abokin nasa total opposite da nasa rayuwar. Amma sabida k’arfin hali irin nasa sai ya kauda tunanin yana mai ci gaba da abinda yake. Saidai da alama tunanin yak’i barinsa, Ya kasa yakicewa daga zuciyarsa. Sosai Hisham da mahaifiyarsa suka birgesa. Inama shine yakeda kusanci irin haka da nasa mahaifiyar. Ba abunda ya nema ya rasa a rayuwarsa ta duniya face soyayyar iyayensa guda biyu. Da ace dukiya shine farin cikin rayuwar duniya tabbas da ahalinsu ya cika da farin ciki. Saidai kash sab’anin haka ne cikin ahalinsu. Da ace za’a karb’e duk abinda suka mallaka na duniya a azurtasu da farin ciki kwanciyar hankali da soyayyar junarsu tabbas da sai yafi masa duk wann k’yale k’yale na duniya da suketa bautuwa akai. Ya d’an limshe idanunsa yana mai canza direction d’in tuk’insa. Can k’asan zuciyarsa yana jin akwai gibi babba cikin rayuwarsa. Har ya iso k’ofar gidan mahaifinsa yana tunanin shiga ya duba Mommy wacce sukai kwanaki basuyi koda magana ta waya ba kaman dai ba d’ah da mahaifiya ba. Ringing d’in da wayarsa tai ya dakatar dashi." Dareen ce mai kiransa hakan yasa ya fasa shiga gidan ya juya Kan motar. ** A can Kano kuwa Tuni an tura Abba babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Ana kan basa kula na gaggawa had’ida da masa gwaje gwaje da yake bukata. Mama tai saurin funcuke takardan da likita ke mik’a masu tin kafin Umma ta mik’a hannu. Sai ka ranste tasan mai aka rubuta cikin takardan ne. Ta shiga juya takardan tana dubawa “Babu damuwa Likita za’a sayo maganin Allah sa babu tsada..” Dr dai bai tsaya sauraronsu ba yasa kai ya shige. Mama ta kuma yatsina baki tana juya takardan “ Toh ma Wai Ina yaga kud’ad’en da zaa masa jinya ne wai.. Wllhi Suwaiba keda d’iyarki dai anyi annoba.. Ummul ta haddasa masa wann ciwo..” Jiki a matuk’ar sanyaye Umma tace “Kar kice haka Yaya..” Ta watsa mata harara had’ida jan tsuka kafin tai saurin tare wata nurse da tazo shigewa “Yauwa ‘yar nan dan Allah nace ba ko zaki iya duba mun mai aka rubuta takardan nan..” Nurse d’in ta amshi takardan tana dubawa “Sunayen magani ne da allurai..” Mama tace “Tooh inji dai basuda kud’i..?” Nurse d’in ta d’an kuma duban Mama “ Magunguna ne da allurai masu kud’i dan allura guda a nan yakai dubu goma.. Kije pharmacy zasu Miki bayani..” Bata kuma tsyawa sauraron Mama ba tasa Kai ta wuce. Mama ta waro idanu “Tirk’ashi toh idan jinyar Malam da tsada haka ai akwai matsala dan irin wann babban jinya kankataraf sai ya cinye d’an abinda zai bari ma yaran nasa bayan babu shi..” Ta juyo sosai tana duban Umma “Wann duk laifinki ne Suwaiba.. Ke da ‘yarki ku kuka kashe Malam a tsaye dan haka sai Kuje ku nemo kud’ad’en da zaa masa Jinya.” Cikin rawar murya Umma ke furta “Haba Yaya ki dubi yanda muke fah.. Asibiti fah muke.. Sann meyasa zaki d’aura alhakin ciwon mijinmu kaina nida ‘Yata.. Kinsan bazamu tab’a so haka ya same shi ba..” “Ke dalla rufe mun baki munafukar banza da wofi idan ba takaicin Ummul da hayagaganki ba me ya janyowa mijinmu ciwon zuciya.. Kinji na rantse Miki da Allah kije ki nemo kud’ad’en masa jinya.. Ina zaki samu bai dameni ba kawai abinda na sani shine alhakin ciwonsa na wuyanku keda Ummul.!” Jin hayaniya yasa wasu nurses k’arasowa suna masu fad’an asibiti suke ba dandali ko kasuwa ba idan hayaniya zasuyi zasu koresu. "Mama tai saurin nuna Umma “Kun ganta nan ita zaku kora itace silan ciwon mijina gashi zata k’ara masa. Tinda mijina ya aureta tsiya ke bibiyarsa, Kayan kantinsa ya daina bunk’asa ta kuma haifo masa annoba wacce kowa ke gudu.”" Nurse guda tace “Malama wann ba matsalar mu bace zan kira security yai waje dake idan bazaki mana shiru ba.” "D’ayar tace “Visiting hours ya shige mutum d’aya ne zata iya zama, ki gode ma Allah mijinku ya samu d’aki mai d’aukan mutum guda godiya ga sabuwar gwabnatinmu dake k’ok’arin inganta hark’an kiwon lafiya da yanzu dole ku nemo namiji da zai zauna.. Yanzu mace d’aya cikinku zata tafi..”" Ai bata Kai aya ba Mama ta nuna Umma “Itace zata tafi dan bamu San idan ya farka ya ganta mai zai faru ba tinda ita da d’iyarta ne silan ciwon.. Na tabbata zuciyarsa bugawa zai idan ya ganta.” Umma ta girgiza Kai tana duban Mama “Kiji tsoron Allah Yaya.” “Da tsoronki zanji Suwaiba.!” Ta girgiza Kai kurum tasa Kai ta fice tamkar kazar da k’wai ya fashe ma a ciki. A haka Umma ta dawo gida cikin jimami. Aiko tin daga bakin k’ofa take sinkayo sautin yaran Mama Salima Badia da kuma Azeema Sun saka Ummul gaba sai kwashe mata albarka suke suna fad’in ta kashe auren Azeema bai isheta ba zata kashe masu mahaifi toh wllhi idan mahaifinsu ya Mutu ta dalilin bak’in cikinta sai Sun d’auki fansa akanta. Duk fad’a irin na Khulsumu da k’ok’arin karb’ar ma ‘yaruwar tata ‘yanci yau sai ta gaza tab’uka komai sakamakon tuno halin da mahaifinsu ke ciki Wanda yake tsakanin rayuwa da mutuwa. Umma ta k’araso da sauri ta rungume Ummul. Umma kuka Ummulkhairy kuka. Kaman an jefo Mama haka ta shigo gidan tagajan magajan. Ashe koda Umma ta fice ta biyo bayanta. Nan ta tadda yaranta na d’iban albarka wa Ummul da mahaifiyarta. Mama ta cab’i zancen daga sama “Shisa nace bazan bari Suwaiba ta kwana wajen mijinmu ba. Kuma sun gama rab’ansa har Allah ya tashi kafad’unsa daga ita har ‘yar tata. Zuriyan annoba.” Azeema tace “Kinyi daidai Mama dan wllhi ko ni nan ko kan gawan mahaifina bazan bari Ummul taje ba.!” “Ya naji ana zancen gawa.. Abban ya cika ne..?” Badia tace tana dubansu. Mama tace “ Baidai cika ba amma yana hanya. Dan idan ba’a samu kud’ad’en da zaa masa jinya dasu ba nan da kwanaki k’alilan toh fah mahaifinku zai zama gawa silan wad’ann..!” Ta k’arashe tana nuni dasu Umma. Sai sann da abun ya ishe Khulsum ta mik’e idanunta na zubda hawaye take dubansu gaba d’aya “Tir da hali irin naku.. Tir da ahali irinku.. Abba na gadon asibiti kuke maganganun marassa kan gado irin haka.. Idan burinku ya Mutu ne domin ku tozarta ‘Yaruwata da mahaifiyata in sha Allahu babu d’aya daga cikin burinku da zai cika.. Allah zai tashi Abba zai basa lafiya sann rayuwar mahaifiyata harma da ta ‘Yaruwata zai inganta.” “Ke rufe mana baki k’aramar maras kunya.!” Mama tace tana huci. Badia da Azeema suka soma k’ok’arin kwance d’ankwali zasu yi d’amara. Badia na dukan k’irji take fad’in Mama ta k’yaleta ta gurji bakin Khulsum yayinda Umma ta mik’e da sauri ta tare yaranta guda biyu hawaye bai daina ambaliya a fuskarta take fad’in “Yaya dan Allah kuyi hak’uri.” Ta dubi su Salima kafin taci gaba “Ku tuna halinda mahaifinku ke ciki.. Yanzu ba lokaci ne na tada rikici ko nuna yatsa ba. Yanzu lokaci ne da ya kamata mu had’e matsayin ahali ko dan samun lafiyan mahaifinku.. Kunfi kowa sanin yanayin gidan nan yanda ‘yanubanci ya raba kan ahalin tin kan iyaye da kakkanni.. Idan bamu had’e kawunanmu ba kunfi kowa sanin babu mai yiwa mahaifinku kaf gidan nan. Dan Allah muyi hakuri duka mu nemawa Malam lafiya koda da abinda ya mallaka ne.” Mama tai saurin katseta “Ban gane koda da abinda ya mallaka ba.. Yo me ma ya mallaka da zaa masa jinya dashi.?” Umma ta jinjina kai “K’warai ya mallaki kanti. Ko Kayan ciki aka sayar da gaba d’aya kantin na tabbata zaa iya rage wani abin saura sai a nema wajen bayin Allah tinda ga yanayin ciwon nasa ciwo ne da za’a buk’aci kudade ga yanda komai ya koma a k’asar.” “Ke malama da Allah dakata.!” Mama ta katseta kafin taci gaba “Wllhi Suwaiba kinji na ranste Miki idan ina numfashi babu mai saida shagon nan.. Toh a bar ma yaran nawa mai..? Inyi.. Shikenan su koma basuda gadon mahaifinsu miji ya samu abun goranta masu ..? Toh ahir d’inki wllhi koda wasa kar na kuma jin wann batu daga bakinki.. Idan keda yaranki Baku buk’ata mu muna buk’ata dan bazai yuwu Ana shafe shekaru bila adadi ina dawainiyar Malam a barni fankinfayo ba.. Ke bari ma kiji na fad’a Miki.. Wann ciwo dai ba warkewa zai ba dan haka bazamu zubda dan abinda zai bari Akan jinyar da ba tashi zai ba. Shi fah irin wann jinyar kaf abinda ka mallaka sai ya k’are ba’a samu biyan buk’ata..” Ta d’an dakata kafin taci gaba “Toh ma ai Suwaiba keda yaranki bakuda gadonsa dan Kune kuka kashe sa.. Ku kuka jaza masa wann ciwo.. Ko a sharia duk Wanda ya kashe wani bai cin gadonsa.. Dan haka Kun fita da fitarku.! Ko ku nemo kud’ad’en da zaa masa jinya ko ya rub’e a gadon asibiti. Ta juyo ta dubi yaranta “Kusha kuruminku babu uban da ya isa ya tab’a maku gadonku ina raye ehe.!” Yaranta suka rangada shewa suna kuma ingizata. Daga Umma har Khulsum da Ummul Cak kukansu ya d’auke suka ma nemi kukan da suke suka rasa. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Wacce irin duniya muke rayuwa ciki.? Ace iyalanka daka rayu dasu ahalinka Wanda kafi kowa kusanci dasu ba damuwarsu ya zaayi ka samu lafiya ba. Ashe damuwarsu mai zaka Mutu ka bar masu ne..? Shin ina allan attajiran dake tara dukiya kota halin k’ak’a su Mutu su bar ma magadan da ko tausayinsu basa ji balle suyi masu addu’a.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Matarka da ‘ya’yanka.. Hasbunallah wa ni’imal wakil.. Muyi ma kanmu karatun ta natsu tun munada dama kafin dama ta kufce mana. Mu Gina ma kawunanmu ayyukan alkhairi. Mu d’ibi dukiyoyin mu muyi aikin alkhairi dasu tun munada dama. Mu Gina ma kawunanmu sadaka mai gudana har bayan rayuwarmu dan ba Lallai abinda ka bari su maka ba. Allah ka bamu ‘ya’ya masu albarka Wanda su kansu zasu zame mana sadaka mai gudana Ameen. Wann rana da jimami Umma da yaranta suka yini. Ummul ta dubi Umma su duka biyun idanunsu a kod’e “Umma yanzu ya zamuyi. Haka zamu bari Mama da yaranta suyi yanda suke so..?” Khulsum dake gefe ta k’ura ma waje guda idanu tace “Mai kuke tunanin a gidan da cikin Umma ma gaba suke da juna balle ‘yanuba..?” Umma ta kuma goge hawayenta dan ta d’ago ina maganar Khulsum ya dosa. Ummul ma tai saurin d’agowa ta dubi Khulsum sai kuma ta dubi Umman “Umma ko Inna Dije zamu kira mu sanar da ita halin da Abba ke ciki..?” Shiru Umma tai kaman mai nazari kafin ta girgiza Kai tace “Har yau babu Wanda yasan abinda ya haddasa gaba da k’iyayya tsakanin mahaifinki da tilon ‘yaruwarsa da suka fito ciki guda.. Mahaifinku ya b’oye mana bai sanar damu abinda ya rabasa da Dije ba.. Amma ya datse alak’a da ita kuma itama ta datse alaqa damu.” Khulsum tai saurin d’agowa ta dubi Ummul wacce keta k’ok’arin danne marayan kukan dake taso mata jikinta har rawa yake tamkar wacce ta tuna wani abu. Lokaci guda Khulsum ke ci gaba “Tin sanda Ya Fa’iz tilon d’an Inna Dije ya rasu Abba da Inna Dije basu kuma zama ‘yan uwa ba.” Take Ummul tai boasting cikin kuka mai tsanani ta mik’e ta nufi uwar d’aki. Umma ta dubi Khulsum “Maiyasa Khulsum.. Maiyasa zaki ambato mata Fa’iz… Meyasa zaki d’ago mata wann mik’i..” Sai kuma muryarta ya soma rawa. Cikin rawar murya take furta “Tinda Fa’iz ya koma ga mahaliccinsa ahalinmu bai kuma daidaito ba.. Tabbas da Fa’iz nada rai duk abubuwan da suke faruwa watak’ila da basu faru ba.. Tabbas da Fa’iz na nan a raye da yanzu Ummul d’ina ta jima a d’akinta.. Allah sarki Fa’iz ka tafi ka barmu da tarin k’alubale da iftila’i.. Tabbas rashinka babban gurbi ne a garemu.. Ka tafi da kurwar ahalinmu Fa’iz…!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka. Khulsumu ta k’araso ta rungume mahaifiyarta. Cikin rawar murya take furta “A’a Umma duk abinda ke faruwa tuntuni rubutacce ne.. Allah ya nufa hakan dole sai ya kasance.. Wann itace k’addaran ahalinmu.. Auren Adda Ummul kuma ko ya Faiz na raye ko baya raye bazai tab’a faruwa ba sai lokacin da Allah yaso. Umma kiyi k’ok’ari kiyi tawakkali da sannu Allah zai kawo mana mafita kinji Umma ta… In sha Allah Abba zai samu lafiya kuma farin ciki zai dawo cikin ahalinmu da izinin Allah.!” Umma ta rungume ‘yar tata kuka na kuma kufce mata. "Tamkar wacce aka sinkara haka Umma ta janye jiki daga na khulsum. Ta shiga girgiza Kai tana duban Khulsum d’in “Yaya tayi gaskiya Khulsumu, Anya ba wani mugun k’addara bane yake bibiyan ‘yar uwarki..? Meyasa Fa’iz ya Mutu kafin yakai ga aurenta.? Meyasa tin bayan da Fa’iz ya bar duniya duk wani maneminta basa kaiga aure maganar ke watsewa.. Shin Anya ba alak’ar Ummulkhairy da Fa’iz bane yai Ajalin Fa’iz..? .. Anya ba wann dalilin bane ya raba tsakanin ‘yan uwa biyu..? Ina nufin mutuwar Fa’iz shine ya raba tsakanin Mahaifinku da ‘yaruwarsa.. Anya ba Ummul ce tayi sanadin Fa’iz ba.?!”" SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *09* *©️Sameena Aleeyou… * Saurin rik’e bakin Umma Khulsum tai tana girgiza Kai “Haba Umma wace irin magana ce wann.. Umma magana kike fah kaman bakiyi imani da k’addara ba..Umma na zaci ciwon Abba ya dawo dake hayyacinki daga wann rashin tawakkalin.. Haba Umma saikace ba musulma wacce ta yarda da k’addara ba..” A zafafe cikin zuban hawaye Umma ta katseta “Ki gaya mun cikin abunda nace wanne ne ba haka ba..?! Ki gaya mun Khulsum..!” Taci gaba da kuka mai sauti tana girgiza Kai “Bak’in K’addaran Ummul shine yai ajalin D’an ‘yaruwar mahaifinku Fa’iz..! Bak’in k’addaran Ummul shine ya raba tsakanin mahaifinku da ‘yaruwarsa.! Bakin k’addaran Ummul shine ya jefa mahaifinku halinda ya tsinci Kansa ciki..! Bak’in k’addaran Ummul shi yake sa ko wani namiji ya guje ta..! Bak’in k’addaran Ummul shi ya jefa ahalinmu cikin yanayin da muka tsinci kawunanmu ciki..!” Kaman daga sama sukaga Mama ta d’age labulen parlorn. Ta jinjina Kai tana duban Umma “Na gode ma Allah da yasa kika furta duka wad’ann da bakinki Suwaiba.. ‘yarki Ummul itace tai sanadin Fa’iz.. Yaron kirki aka lik’a masa annoba aka rabasa da rayuwarsa.. Toh wllhi kinji na ranste Miki da Allah bazan bari ‘yarki ta kuma kusantar mijina ba balle ta lashe nasa kurwan.. Kai kaf d’inku babu mai kusantar min miji..” Khulsum dake faman sakin huci goge hawayen dake kwance saman fuskrta tai ta k’araso gaban Mama “Wllhi wllhi banga Wanda ya isa ya hanamu ganin mahaifinmu a asibiti ba..” Badia ce ta k’araso ta tsaya gaban mahaifiyarta tana murmushi tana duban Khulsum dake ci gaba da sakin huci. Lokaci guda ta d’ago hannunta dake rik’e da wayar salulanta. Take tai playin recording d’in muryar Umma da tai sanda take fad’in Ummul ce tai sanadin mutuwan Fai’z harma da ciwon mahaifinsu. Tana gama playing suka kuma sakin murmushi itada Mama. Mama taci gaba “Ko Kotu aka tafi wann kad’ai ya ishemu shaida… Badia shige mu tafi wajen mahaifinku..” Daga haka sa Kai sukai zasu shige Khulsum ta yunk’ura zatabi bayansu Umma tai saurin dakatar da ita tana girgiza Kai hawaye na fita mata dan kukan nata ya daina fita da sauti. "Khulsum ta dubi Umma. Ta rasa k’unci ne ko takaicin mahaifiyar nata ne k’unshe cikin Zuciyar “Haba Umma.. Haba Umma, kinga ga irin abinda nake fad’a Miki.. Yanzu makirar matar nan zatayi amfani da wann damar ta iya cutar da mahaifinmu.. Umma dan Allah wai sai Yaushe zaki daina maganganu marassa kan gado fisabilillahi.. Umma a gabanki matar nan da yaranta suke lissafin mai Abba zai Mutu ya bari. A bayyane take so suke mahaifinmu ya Mutu.. Umma mai zai faru idan sukai amfani da wann damar suka k’arasa mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.. Umma kin cuce mu wllhi idan Mama da yaranta suka k’arasa Abba ba kowa ne Sila ba face ke.!”" A guje Umma tabi bayan su Mama tana rok’onsu su rufa mata asiri kar sukai ma hukuma muryarta da Badia ta nad’a cikin wayarta. Takaici ya kuma Kama Khulsum dan tasan yanzu Mama da ‘yarta Badia Sun samu makamin shashantar da Umma dole su tilasta mata yin duk abinda suke so musamman da sukaji tana tsoron wai sukai recording d’in da Badia tai ma hukuma. Khulsum ta bud’e murya tana kiran mahaifiyar tasu. Lokaci guda take furta “Umma ki bi bayansu su Kai ki ma hukumar kinga ‘Yaruwata ma ta huta da muggan kalaman da kike jifanta dasu duk wayewar garin Allah.!” Tau!!! Taji sauk’an mari saman k’uncinta. Ta d’ago da mamaki tana duban Ummulkhairy data d’auketa da Marin. Lokaci guda take furta “Shin Kinsan girman mahaifiya Khulsum..! Shin Kinsan matsayin mahaifiya..? Shin Kinsan darajarta Akan ‘ya’yanta..?” Cikin huci Khulsum take duban Ummul lokaci guda take furta “Akan na fad’i gaskiya shine zaki mareni.. Mahaifiyarmu tana buk’atar mai tunasar da ita.. Mahaifiyarmu tana buk’atan mai nusar da ita..!” “Ya isheki Khulsum.!” Ummulkhairy ta dakatar da ita kafin taci gaba “A haka ne zaki nusar da ita kina d’aga mata murya kina fad’in ta cucemu mu ‘ya’yanta har Kina cewa taje hukuma su kamata.. Mahaifiyarki Khulsum.?!” Tai birki tana girgiza Kai tana duban Khulsum cikin rashin yarda “Mahaifiya ce zaki fad’a mata haka.. Ina karatunki na islamiya ya tafi..? Kin mance cewa ko nasiha za’a ma iyaye cikin kwantar da murya da lallama ake. Kin mance k’issan bawan Allah Junaid da ya keb’e kansa a wajen gari yana bautan Allah. Mahaifiyarsa tazo ta kirasa yana ibada bai amsa ba. Akai haka har sau uku a na uku tace Allah ya had’asa da sharrin ‘ya mace daga k’arshe wann bawan Allah saida ya had’u da sharrin mace. Karuwa taje tai . Bayan Allah ya wanke shi daga sharrin karuwa da ya fad’a . Daga baya mahaifiyarsa ta fad’i cewa wann bakin da tai masa shine ya kamasa.. Kinga darajan mahaifiya dukda ba sab’on Allah yake ba bautan Allah yake saida bakinta ya bisa saida yai tasiri akansa.. Wann itace Uwa Khulsum.. Ba’a wasa da al’amarin iyaye..” Khulsum ta jinjina Kai tana hawaye “Na yarda Miki ‘Yaruwata.. Shin koda ace mahaifiyarka zata apka ma b’ata sai ka k’yaleta..? Ummul sanin kanki ne rayuwar Umma akwai gyara cikinta.. Sanin kanki ne Umma bata yarda da k’addara ba.. Shin bakiji yanda ta d’aura alhakin komai akanki ba har Mama da yaranta suka sami hujja.. Ummul rayuwar mahaifinmu na cikin had’ari a wann gab’ar dole na nusar da Umma kuskuren ta..” Cikin sanyi jiki Ummul ke duban Khulsum. Sai kuma ta girgiza Kai tace “Watak’ila gaskiya Umma ta fad’a.. Itace ta haifeni.. Tafi kowa sanina..” Khulsum ta k’araso ta dafa ‘yaruwarta “Ubangijinki da ya halicceki yafi kowa saninki ‘Yaruwata.. Dan Umma tana mahaifiyarki bai zama hujja akanta ta dinga kausasa harshenta Akan k’addararki ba.. Sabida Dani dake da Umma dama duk wani mahalik’i bamuda ikon canza k’addararki.. Allah shi yake k’addara rayuwar mu yanda yake so ya kasance.. Iayakacin namu shine addu’a Allah yai mana tsari da k’addara mai muni.. Ki daina kuka ‘Adda Ummul.. Da sannu Ubangijinmu zai daidaita mana al’amranmu ya kuma bawa mahaifinmu lafiya.. Kuma na Miki alk’awari zan bawa Umma hak’uri nai mata nasiha cikin lallama da kwantar da murya.” Sai suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya. Shiru shiru Umma bata dawo cikin gidan ba. Ummulkhairy tace subi bayan Umma su dubata. Koda suka fito ma wayam basuga Umma ba. Ummul da Khulsum sukai tsaye suka jimami. Khulsum tace “Kar dai Umma tabi su Mama ne..? Mai zai faru yanzu Adda..?” Ummul ta rasa abin fad’i. Sukai tsaye suna duban mutane masu giftawa. Daga can nesa suka hango mashin d’in mijin Azeema ya nufosu ga Azeema zaune d’amas saman babur d’in. "Suka k’araso sukai parking. Ta dafe shi ta sauk’o sai karairaya take “Yauwa Habibi, da alama mun kusa mallakan mota dan na gaji da babur din nan. Kar ka damu na maka alk’awarin da an bani kaso na na gado zan biya maka duk bashin da ake binka..!” Ta k’arashe tana aikawa su Ummul wulak’antaccen kallo." Khulsum ta dubi Ummul mamaki kwance saman fuskrta. Wai mahaifin su ke kwance gadon asibiti Azeema ke wann maganar. Daga ita har mijin nata kaman sunga kashi haka suka dubi su Ummul. “Habibi bara na shiga na fito da kaya na mu tafi tinda mun hadu da Mama a hanyar asibiti.” Azeema tace bayan ta dira daga bayan Babur d’in. Haka ta k’araso ta shige ta gaban su Ummul tana watsa masu wulak’antaccen kallo. Khulsumu tai saurin Shan gabanta “Adda Azeema kinga Ummanmu tareda Mama ne.?” Azeema taja tai birki tana watsa ma Khulsum banzan kallo “Ajiyanta kika bani da zaki tambayeni ko na ganta..?” Ummul ta girgiza Kai cikin sanyin muryarta tace “A’a Azeema gani mukai ta biyo bayan Mama kuma munji kince kin hadu da mama a hanya Shiyasa muke tambayarki..” “Mahaukaciya ce ita ko k’aramar yarinya ce ita..! Tinda ku kanku kunsan cewa mahaifiyar taku b’elb’el ce sama Sama ce sai ku nemi igiya ku d’aureta a gida ko ku Sakata a turu maganin hauka…” Kafin takai aya taji saukan tagwayen maruka d’aya bin d’aya. Azeema ta malmalo wani ashar tana duban Khulsum dake sakin huci wacce itace tai Marin. Cikin huci Khulsum taci gaba “Baa haifi wacce zata ci mutuncin mahaifiyata na barta ba bari kiji na fad’a Miki..!” “Ni kika Mara Khulsumu.. Toh wllhi yau idan baki kwana cell ba wllhi ba sunana Azeema ba.. Dan uwarki Suwaiba sama sama daga kaina kin gama rashin kunya..!” Ta k’arashe tana ihu tana k’walla kiran Habibi.. Kan kace me mutane sunyi caa a wajen. Babu shiri Mijin Azeema ya ko k’araso yana fad’in wllhi baiga ballagazar da zata marar masa mata ya barta ba. Fad’i yake wllhi sai ya d’aure Khulsum.. Kan kace mai ya d’ale mashin d’insa ya bar wajen. Ummul sai kuka take tana rok’on Azeema tai hak’uri ta bari suji da ciwon mahaifinsu da kuma b’acewar mahaifiyarsu. Azeema kaw sai tsalle take tana jijjiga tana fad’in wllhi yau bataga uban da ya isa ya hanata d’aure Khulsum ba. Bakin Khulsum bai Mutu ba fad’i take wllhi Azeema ta kuma gigin zagar mata mahaifiya sai ta k’ara mata da wasu marukan. Kuma idan ta haifu kar ta fasa rufeta a gidan yari. Wasu daga cikin ‘yan gidan masu goyon bayan Azeema sai dad’a ingizita suke. Wasu kaw cewa suke Ummulkhairy da ‘yaruwarta kullum cikin jaza masu fitina suke. Idan kaji ana bala’i da rikici a gidan toh ba kowa bane face su biyun. Allah sarki Ummulkhairy idan ka ganta dole ta baka tausayi. Jim kad’an motar police ya k’araso tafiya da Khulsum. Mijin Azeema na gaba yana fad’in idan zai kashe k’arshen kud’insa sai ya k’watarwa matarsa hakkinta. Ummul kaw ganin za’a tafi da ‘yaruwarta da gaske ya sanyata saurin k’arasawa tana rok’on Habibu mijin Azeema da yai hak’uri ya taushi Zuciyar Azeema ko dan halinda mahaifinsu ke ciki a asibiti. Haka akai ayari anai masu rakiya yayinda wata ‘yarsanda ta tasa k’eyar Khulsum zuwa cikin motar su. Ummul ta kamo ‘yaruwarta tana kuka shar shar tana rok’onsu dan Allah su k’yale mata ‘yaruwarta. Sergeant d’in ta bige hannun Ummul tana tsawa wa Khulsum ta shige mota. Azeema da mijinta suka d’ale babur suka take masu baya. Durk’usawa Ummul tai a wajen wani irin marayan kuka ma taso mata. Hannayenta biyu ta d’aura akai jikinta kaw har wani irin rawa yake. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Wann wani irin jarabawa ne.. Wani irin iftila’in rayuwa suke gani.. Ba’a gama da wann ba a fad’a wann..! Ta rintse idanunta hawaye na kuma ambaliya a fuskarta. Da wanne zata fara mahaifinta dake kwance asibiti.? Mahaifiyarta da bata san ina ta tafi ba.? ko kuwa ‘yaruwarta da aka tafi da ita police station.? “Hasbunallah wa ni’imal wakil..! Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha..!” Ta furta cikin tsananin rawar murya. Ta mik’e tamkar zautacciya tana Neman ta hanyar da zata nufa. Batasan ina take tafiya ba k’afafunta kawai take jefawa. Bata tsinci kanta a ko ina ba sai gidan Hajja Fannah. Da tsananin mamaki Hajja Fannah ke duban Ummulkhairy wacce ko magana bata iya yi.. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Ummulkhairi “Subhannallahi Ummul meke faruwa..?” Ummul bata iya amsata ba saima kifa kanta da tai cikin jikin Hajja Fannah marayan kuka na taso mata. Hajja Fannah ta rungumeta sosai cikeda tsananin tausayinta. A haka suka nufi cikin gidan. Ta zaunar da Ummul saman kujera wacce ta koma tamkar mutum mutumi bata um bata um um sai hawaye dake ci gaba da gangarowa saman kumatunta. Hajja Fannah ta mik’e da zummar kawo mata ruwa ganin ta mata tambayar duniya kan ta sanar da ita meke faruwa ta kasa. Idanunta suna kafe waje guda sai zuban ruwa da suke. "Amma koda ta kawo ruwan ma kasa sha tai har lokacin idanunta na duban b’angare guda ga hawaye na kwaranyo mata. Hajja Fannah ta kyaleta bata tak’urata ba har saida suka d’ibi lokaci a haka kafin Ummul ta soma fad’in “Komai ya hargitse, sunce ni ce sila.. Sunce bak’in k’addarata da haukan mahaifiyata shi yai sanadin ciwon mahaifinmu.. Hajja Umma ta tafi bansan ina ta tafi ba.. Abba yana asibiti amma sun hanani ganinshi.. An.. An kama Khulsum… Tana ofishin ‘Yan sanda..!” Sai tai boasting cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro." Hajja Fannah ta d’an kauda fuskarta tana matsan k’wallan da suka cika idanunta. Ta jinjina kai a hankali tana shafa bayan Ummul alamun kwantar da hankali “Yi kuka Ummul.. Kukan zaisa kiji relief…” "Saida ta bata lokaci tana kukar da abinda ke k’unshe k’irjinta kafin tai gyaran murya “Let them say whatever they want. Su fad’i duk abinda suke so. Amma koda wasa kar kiyi abinda zaija miki matsala a rayuwa. We are all human beings, kuma Allah ya haliccemu daban daban. Level of tunaninmu bazai zama daidai da juna ba. Ko a makaranta ne cikin aji d’abi’un yara da halayyarsu ya banbanta. Akwai yaron da kana koyar dashi abu bugun farko ya d’auka. Wani kuma sai anyi da gaske ya gane. Akwai fast learners akwai slow learners. Malaman makaranta da suke koyar da yara suka san d’abi’unsu su zasu fad’a miki wann. Akwai yaran da suke fuskantar wani ciwo da iyayensu ma basu san suna dashi ba kaman irinsu Attention deficit hyperactivity disorder (ADHD). Sai kiga a gida anata jibgan yaro ace jaki ne baya son karatu baya gane karatu wanda ba haka bane ya samu d’an wani matsala ne da idan aka tafiyar dashi sannu a hankali yanda yake d’in idan abun ba mai tsanani ne sosai sai kiga ba sai anje ga ganin likita ba. Wata uwar fah da kanta take abusing d’an da ta haifah ko ince wasu iyayen. Kar kice d’an rik’o ko goyo a’a D’an suka haifa zasuyi abusing a nasu tunanin wai soyayya suke masa. Wani yaron tsananin matsi da tak’ura da tsanani shi yake traumatizing d’insa. Kiga uwa ta dasa ma yaranta tsoronta. Yes ta haifar da fair tsakaninta da yaranta duk wai ita a dole tarbiya take masu batasan ta kashe kanta bane a staye. Bai jima ba na gani da idona ba jiyau ba wani yaro yayi hanging kansa sabida tsoron yayi laifi. Kuma kar kice wani babban laifi a’a minor laifi ne amma sabida tsoronta da ta" "haddasa masa yasa ya d’auki rayuwarsa. Toh kinga dik ire iren wad’nn sukan haddasa ma yaro ya dinga wasu d’abi’u kaman na mai tab’in hankali tin yana k’uruciya har kawo girma. Ba’ace kar ka tsawatar ma yaranka ba amma idan aka tauna sai a d’an sake haka shi yaro yake. Sann ire iren wad’ann cututtuka na kwak’walwa akwai mutanen da dama manyan mutane da suka zama madubi ga al’umma sun fuskanta a lokacin k’uruciya idan kika bibiyi tarihinsu kafin nasarorinsu. . Akwai mutane masu special needs cikinmu ‘yanadam. Mutanen da suke buk’atan kulawa ta musamman. Ba zallan wanda muke ganinsu da nakasa ta zahiri a fili ne suke buk’atan taimako na musamman ba. Wato mutane masu disability da muke iya gani mu tantance. Akwai wasu d’abi’u da zaki kula mutum nayi wasu lokutan kaman d’an tab’in k’wak’walwa. Abun minor ne baiyi tasiri a jikinsa ba. Idan aka ja yaro jiki ko mutum mai irin wann matsalan ka tafiyar dashi yanda ya dace sai kiga abun yayi sauk’i ba sai an kaiga neman magani ba. amma mutanen da suke rayuwa dasu sai susa abun ya girma har ya koma kaman hauka. Sai kiji ance miki mutum ya koma hauka tuburan. Mutane suna hantaran shi mutum mai irin wann matsalan. Ko kiga daga an ganshi sai a fara dariya ana manna masa hauka. Mutane suna kiransa da sunaye barkatai Wawa, a’a shashasha lusari maras hankali. Dama k’wak’walwar nasa da gaske akwai d’an matsala sai kiga yayi giving up ya yarda da abinda mutane ke fad’a akanshi sai kiga ya fara abu irin na masu tab’in hankali. Irin wad’ann sune mutane masu Emotional and mental health needs. Wasu zaki samu through life experience suka had’u da wann matsalan. Wasu zaki samu stress ne ya maidasu haka. Some have history of abuse musamman idan cin zarafin da suka fuskanta a lokacin k’uruciya ne. trauma or neglect. Wasu an wofantar dasu. Dik suna contributing kiga mutum ya samu wann Matsalar. Wasu kuma biological factors ne ma’ana gadon cutan sukai ko kuma dai cuta ne kawai daga Allah. Amma a matsala irin na mahaifiyarki zai iya zama Desperation na ganin ta aurar dake ko ta halin k’ak’a zai iya haifar mata wann matsalan kinga kuma rashin tawakalli da karban k’addara yanda tazo ma Bawa ya shigo ciki. A akasarin lokuta desperate individuals sukanyi wasu bubuwa wanda normally thinking person bazai fahimta ba. Because they are desperate sukan aikata wasu abubuwa da yafi kama da hauka or illogical. A wasu lokutan Yakan sa mutum ya cutar da kansa har ma yakaiga yayi yunk’urin kashe kansa.”" Ummul ta dubeta sai ta tuna sanda Umma tai yunk’urin fad’awa rijiya zata kashe kanta dikdai sabida k’addararta. "Muryar Hajja Fannah ya dawo da ita “Ni ba likita bace sann kuma ban karanci halayyan d’an adama ba. Ina fad’a miki wasu abubuwan ne base on experience. Ni uwa ce da ta raini d’anta ba uba. Mun fuskanci k’alubale da dama a baya wanda yasa na zama exposed da ire iren matsalolin nan..” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Ko ma wanne matsala mahaifiyarki ke fuskanta Ummul kija mahaifiyarki a jiki. Kar ki tab’a hantararta koda ta kasance mai tab’in hankalin ko shashasha kaman yanda mutane ke fad’i. Iyaye ko a bola suke yawo iyaye ne. Allah yakan k’addari rayuwar wasu cikin rayuwarmu domin ya zame mana jarabawa. Kibi umarnin Allah kiyi mata biyayya cikin abinda babu sab’onsa. Kiyi k’ok’arin tafiyar da ita yanda take d’in. Na tabbata ko haukan ne, ko ganganci ne ko ma menene Allah bazai tab’a bari ki tab’e ba matuk’a kin fawwala masa lamiranki kuma baki fasa addu’a da neman zab’insa ba.” Ta kuma kamo hannayenta “Dik tsanani yana tare da sauk’i. Inada yak’inin Umma ba b’acewa tai ba. Khulsum zata dawo gida Abba kuma zai samu lafiya cikin yardar Ubangiji. Tashi muje ba zama zamuyi ba.”" Suna k’ok’arin mik’ewa sukaji sallama. Hajja Fannah tai birki tana dubansa. Tilon d’anta da aiki ya rik’e mata shi can birnin tarayya. Bai kulada budurwar dake zaune gefe saman kujera ba ya k’araso ya rungume mahaifiyarsa yana fad’in yayi kewarta. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *10* *©️Sameena Aleeyou… * Sautin kukan Ummul dake fita a hankali ne ya d’auki hankalinsa. Ya d’an kaikaito yana dubanta. Kanta a kife saman gwiwoyinta. Ya maida dubansa ga mahaifiyarsa “Hajja wacece wann..?” “Kaga Hisham jeka aje jakanka. Zuwa kai akan gab’a daidai lokacin da nakeda buk’atan hakan dikda zuwan ba zata ka min.” Zai kuma magana ta shiga turasa tana fad’in “Kaje kawai ba lokacin bayani bane yanzu.. Allah yasa da motarka kazo.” Ya jinjina mata kai yana mai nufan hanyar d’akinsa. Yana tafe yana waigowa yana duban Ummulkhairi da har lokacin kanta a kife yake. Fitowan Hisham yai daidai da mik’ewarsu tsaye. Yai mutuwan tsaye yana kallon budurwar. Fuskarta fayau alamun kuka da damuwa. Bai tab’a ganinta tareda mahaifiyarsa ba balle yayi tunin ko ‘yaruwarsu ce. Danginsu ma gaba d’aya ai suna Maiduguri so baya tunanin ‘yaruwar mahaifiyarsa ce. Yai tsaye daga gefe yana sauraron mahaifiyarsa dake kuma kwantar ma budurwar hankali. Agogon hannunsa ya duba yaji ana kiraye kirayen sallar la’asar. Ya d’anyi gyaran murya wanda yasa Hajja juyowa tana dubansa. Sai ta maida dubanta ga Ummul tace “Yanayin kinnan anya ma kuwa kin saka wani abu cikinki Ummul.” Girgiza mata kai tai. A hankali cikin Sanyin muryarta ta furta “Kiyi hak’uri Hajja na k’oshi bana jin yunwa. Bazan iya cin komai ba.” Hajjah Fannah ta fahimceta dan wani tashin hankalin ya wuce gaban komai. Dafata ta d’anyi “Maza shiga d’akina kiyi sallah. Zan shigo na sameki.” Ta jinjina mata kai tana mai shigewa jiki a sanyaye. Hisham ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta har ta shige. Ya rage daga shi sai mahaifiyarsa. Ya d’an bud’e hannayensa yana d’aga gira kafin tai masa tayin abinci “I’m still full.. Don’t worry about me.” Ya shiga nuna k’ofan d’akin yana tambaya a hankali “Hajja who is she..?” Kunnensa guda ta kamo ta shiga janyosa tana fad’in “Ban gama da kai ba zaka sanar dani dalilin da ya hanaka sanar dani kana tafe.” Ya d’an saki k’ara yana k’ok’arin dafe kunnensa “Yi hak’uri Hajjata.. Idan na sanar dake kuma ai bai zama bazata ba.” Ta murmusa tana dubansa. Su duka biyun duban juna suke cikeda shauk’i “Watau dai bazaka daina min bazata ba. Kaidak bazaka girma ba.” Ya murmusa “Na jima wann karon banzo na ganki ba shiyasa.” Suka soma sabon gaisuwa Hisham na kuma tambayarta wacece wann budurwar. Ta d’an dubesa “Naga alama ka k’agu kaji ko wacece ita. Yanzu dai kaje kayi sallah police station zaka kaimu..” Ya d’an dakata da nad’e hannun rigarsa da yake “Hajja police station kuma.. Meke faruwa ne wai.?” Ta d’an lumshe idanunta had’ida furzar da huci “Je kayi sallah Hisham.” Ya jinjina mata kai kafin yasa kai ya fice yana tunanin mai zaikai mahaifiyarsa ofishin ‘yansanda. A natse take sanar da Hisham abindake faruwa game da kama ‘yaruwar Ummulkhiairi da akayi. Mahaifinta dake kwance gadon asibiti ga kuma mahaifiyarta da suke tsammanin b’acewa tai. Saidai bata sanar dashi sanadin faruwar komai ba. Tinda ba huruminsa bane. Wann ma dole ne ta sanar dashi. Hajja ta mik’e “Jiramu a waje muna fitowa. Barin duba Ummul d’in.” Ta fad’i tana nufan k’ofan d’akin da Ummul ke ciki. Ta tadda ta ida sallar. Ta linke abin sallan kafin ta dubi Hajja dake tsaye tana jiranta. Hajja ta sakar mata murmushin k’arfafa gwiwa kafin ta sanar da ita bak’on da ta gani D’anta ne dake aiki can Abuja. Yazo hutun aiki ne. Yanzu haka yana waje yana jiransu zai kaisu police station ayi belin Khulsum sann ayi filing report na missing person idan har b’acewa Umma tai. Ummul ta jinjina kai a hankali tana ma Hajja Fannah godiya. Hajjah Fannah tace ta daina mata godiya ita ‘ya ta d’auketa. Koda suka fito Hisham na tsaye jikin motarsa yana waya. Sam ita bazama tace ta iya tantace shi ba dan har lokacin ba wai ta dawo cikin hayyacinta bane. Karfin hali ne Kauai. Tasha jin labarin ana cewa Hajja Fannah nada D’ah saurayi amma baya zama garin kano zuwa yake lokaci zuwa lokaci domin ya duba mahaifiyarsa. Duk zuwa gidan da take bata tab’a arba dashi ba sai wann karon. Back seat Hajjah Fannah ta bud’e mata ta shige yayinda ita Hajjar ta shige mazaunin mai zaman banza gefen d’anta. Suna tafe saman kwalta suna kowa yayi jigum jigum. Hisham bai saba zama haka shiru da mahaifiyarsa ba. Zai iya cewa they are best of friends shida mahaifiyarsa sabida tsananin shak’uwa dake tsakaninsu. Yau d’in duk sai yaji babu dad’i. Sai ya sata kallon Ummul ta cikin mirror yanda ya hangi Siraren hawaye basu daina sauk’a saman k’uncinta ba. Ji yai ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta. Rabin hankalinsa naga kwalta rabi naga Ummulkhairi. Hajja Fannah takai dubanta ga mirror yanda Hisham ke satan kallon Ummul. Bata kuma cewa komai ba sai d’an sauk’e ajiyan zuciya da tai. Sosai yarinyar ke bata tausayi. ** Lexus ce bak’a wul taketa kutsawa cikin k’ungurumin daji. Kai da gani kasan ba lafiya ba kaga motan manyan mutane irin wann na ratsawa cikin daji. Saida sukai tafiya mai nisa daga bakin kwalta zuwa wani k’ungurumin k’auye da yake tsakiyan daji kafin Mommy ta juyo ta dubi driver dinta tace ya fita ya basu waje zasu tattauna. Driver yai yanda Mommy tace. Juyowa tai tana Duban k’anwarta Asshe dake zaune gefenta cikin motar “Asshe kin tabbata aiki yakeyi mai kyau...” "Asshe ta murmusa ""Aunty Kwaise kenan. Ni ina zama ya ganni kishoyoyi sun sakani tsakiya. dole na kutsa nasan duk wani malami mai tashe da yake aiki kaman yankan wuka. Sha yanzu magani yanzu.”" Asshe itace kanwar Mommy dake aure garin Kano. Mijinta D’an kasuwa ne da kasuwancinsa ya zaga garin Kano harma da wasu jihohin Arewa. Su uku ne wajen mijin nasu tanada uwar gida da amarya itace ta tsakiya. Itace kuma mahaifiyar Anisa sai d’an uwan Anisa mai suna Hilal. Zaune sukai gaban gasunk’umin bokan da ya ari sunan malanta ya yafa. Sumarsa furfura ya cika kama daga kansa dake rufe cikin hulan sak’i har izuwa sajensa da ya zagaye fuskansa. Wani k’aton faranti ne gabanshi mai lallausan yashi a ciki. Hannunsa guda nad’e cikin doguwar carbin da takai tsawonsa koma tafi. D’an bukkan kuwa ko ta ina shirgi ne da tsummokara. Asshe ta gyara zama “Allah gafarta Malam itace ‘yaruwata da kwanaki na labarta maka tana so a mata aiki akan d’anta.” Hannu guda ya d’aga ya dakatar da Asshe yaci gaba da jan doguwar carbin yana furta wasu kalmomi da basu iya tantancewa. Lokaci guda yasa hannunsa ya shafi k’asan ya zana wasu layi kusan guda uku. Sai ya soma jinjina kai yana duban farantin “Naga AURE cikin rayuwar d’anki.” Asshe da Mommy suka dubi juna. Mommy ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Aure kuma Malam..?” Mutumin ya jinjina mata kai cikin tabbatarwa. “Malam anya kuwa..? Aure cikin rayuwarsa..? A gaba kenan dan a halin yanzu ko maganar mace baya so a masa balle aure da aje iyali.” Wani kwanon sha ya d’auko wanda tsatsa tai mata dabaibayi ta ko ina ya nuna mata cikin kwanon mai cikeda ruwa. Take fuskar Haidar ya bayyana. “Wann ba shine D’anki Aliyu ba..?” Mommy tai saurin jinjina kai alamun eh “Eh.. Eh shine Malam.” Ya kuma kad’a kai “Tabbas D’anki yayi Aure ba tareda saninku ba..” Mommy ta dafe k’irji cikin d’imauta “Na shiga uku Ni Kwaise..!” Ta dubi Asshe jikinta har rawa yake “Asshe tsanar da Haidar ke min har yakai yai aure ba tareda sanina ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raj’iun..!” Bokan ya katseta “Shi kansa baisan yayi auren ba.!” Suka dubi juna itada Asshe shaye da mamaki. Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Malam mai haka yake nufi ya za’ayi yayi Aure bai sani ba.?” “Koda yasan da Auren baya cikin hayyacinsa akayi Auren. Aure ne da aka k’ulla akan sihiri. Aure ne da aka k’ullashi a Fadan dodon tsafi. Aure ne da aka masa k’ulli uku mai K’arfi.. Aure ne da akayi sa dan a masa farrak’u da Iyayensa.!” Jikin Mommy ya d’auki rawa. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina “Malam.. Auren sihiri fah kenan. Na shiga uku ni Kwaise.. Haba biri yayi kama da mutum. Na fad’a Haidar baya cikin hayyacinsa. Malam wace shed’aniyar ce ta shigo rayuwar d’ah na dan ta rabamu..?” Ya kuma zana k’asa yana fesa ruwan bakinsa saman yashin “Saninta bazai miki amfani ba dan D’anki bazai tab’a bud’e baki ya sanar dake gameda wann auren nasa ba.” Mommy ta soma girgiza kai “Malam duk yanda za’ayi a karya wann mugun sihiri da aka masa. Ni kuma nayi alk’awarin ko nawa ne zan kashe domin na dawo da d’ah na cikin hayyacinsa.” Girgiza kai ya soma yana aje wani igiyan guru saman tray d’in “Abinda k’asa ya hasko min shine an bisne wann asiri a wani waje yanda ita kanta wann matar da yake tareda ita matsayin matarsa bata san yanda tukunyar sihirin yake ba. Wani wanda yakeda burin ganin bayan d’anki da ma ahalinki gaba d’aya ya mallaki tukunyar ya mata ajiya mai nisa. Dan a yanda k’asa ya hasko mun ita kanta wann matar da umarnin wani take aiwatar da komai.. Har sai wann tukunyar ya fashe kurwan d’anki da aka d’aure ciki ya kub’uta.” Zufa yaci gaba da karyowa Mommy “Na shiga uku ni Asshe waye mai burin ganin bayan ahalinmu irin haka..? Yanzu Malam ba yanda za’ayi a fasa wann tukunyar.?” Ya kuma zana k’asa sau uku sai kuma ya d’ago ya dubi Mommy “Da sihiri ake karya sihiri.. Akwai hanya d’aya tak da za’abi a karya wann sihirin.” Daga Asshe har Mommy rige rigen tambayar hanyar suke. “Wani Auren shi zai karya wann Auren.. Sabida asirin ajikin d’anki akayi..!” Mommy ta girgiza kai “Kana nufi idan yayi wani auren shikenan asirin zai karye.” Shiru yai kaman mai nazari sai kuma ya jinjina kai “Aure ne ba kaman ko wani Aure ba. Aure ne da yake k’unshe da sharudd’a.. Aure ne da za’ayisa domin warware wani auren. Aure ne da ba ko wace irin mace za’a aura ba sai macen da ta cika k’a’idodin da zan sanar daku. Aure ne da yakeda iyaka wa’adin da zai rayu. Aure ne da zai wanzu a tsakanin watanni uku tak.. AUREN WATA UKU..!” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *11* *©️Sameena Aleeyou… * Mommy da Asshe suka dubin juna cikin k’ullewan kai. “Malam sharud’a kuma.. Wasu irin sharud’a kenan..? Sann Kaman ya AUREN WATA UKU.?” Asshe ta tambaya tana dubansa. Ya kuma d’auko wasu layu da guru ya jera saman layin da ya shata akan farantin. Ya k’irga carbin dake hannunsa yace Mommy ta kama ta zab’i guda d’aya. Mommy ta d’an juyo tana duban Asshe a d’an tsorace. Asshe ta jinjina mata kai alamun tai yanda yace. Hannu na rawa Mommy tasa ta kama guda d’aya. Ya kamo daidai yanda Mommy ta rik’e bayan ta sake. Ya jinjina kai yace “Kin canki irin macen da zata warware sihirin dake k’ulle da d’anki da kanki.” Mommy da Asshe suka kuma duban juna. “Tooooh Malam wace irin Mace ce haka..?” “Itace Budurwar da maza ke so kuma suna gudunta..” Suka kuma duban juna cikin k’ullewan kai “Budurwar da maza ke so Kuma suna gudunta a lokaci guda..?” Mommy tace cikin rashin fahimta. Jinjina kai Bokan yayi “K’warai itace Budurwar da makarin sihirin da akayi ma D’anki ke jikinta..” “Malam ita wann Budurwar ya za’ayi mu tantanceta.. Ayi mana bayani..” Cewar Asshe. "Ya kuma gyara zamansa “Itace Budurwar da maneman aurenta ke guduwa. Ita ce Budurwar da sai gashi kaman zatayi aure har an kawo gab’an sai kuma wani abu ya gifta.. Ita wann irin Budurwar tanada farin jini a idon maza dan duk guje ma aurenta da mazan suke basu fasa neman Aurenta. Ita wann Budurwar itace makarin sihirin. Kaman yanda maza ke guje mata haka d’anki zai guje ma wancan shed’aniyar da ta jefesa da guban asiri koda dafin asirin yana sakashi yaji yana son kasancewa da ita. Yanda maza masu neman wann Budurwar suke guje mata haka d’anki zai guje wancan shed’aniyar matar, za kuma ta fita daga rayuwarsa fita ta har abada kaman dai yanda mazan suke fita daga rayuwar ita makarin asirin toh haka d’anki zai fice daga rayuwar wancan hatsabibiyar da ta jefesa da dafin asiri matuka ya mu’amulance wann budurwar da aka aura masa cikin watanni Uku na Aurensu.”" Ganin sun zuba masa idanu kaman basu wani fahimci mai yake nufi ba yasashi kuma gyara zamansa “Kunsan ance Aure halitta ne mai rai.. Aura masa irin wann Budurwa da na gabatar maku shine zai kashe aurensa da wancan matar da aka k’ulla ta hanyar sihiri. Amma saidai…” Sai kuma yai shiru yana dubansu. Mommy tace “Saidai mene Malam..?” Ya zana wani dogon layi tsakiyan guru da laya sai yai crossing “Rayuwa ne a tsakanin mutuwa..” Mommy ta zaro ido waje “Malam rayuwa tsakanin mutuwa. Inji ba d’a na ne zai mutu ba..?!” Ya girgiza kansa kad’an “Duk wacce kuka nemo.. Ina nufin duk Budurwar da kuka karya wann asirin dake jikin d’anki da ita zata mutu kaman yanda wancan Auren nasa zai mutu.. Shiyasa na fad’a maku Aure ne amma na watanni uku kacal.. Ita d’in ta riga ta zama MAKARIN ASIRI.. Zata mutu tareda wancan Auren. Shiyasa duk wacce zaku nemo ku sani K’addararta na tsakanin AUREN WATA UKU ne.!” Mommy da Asshe suka dubi juna. Mommy ta dubi bokan tace “Amma Malam ba yanda za’ayi a karya sihirin sai anyi Auren..? Kuma ni Malam bana so a halak’a kowa wajen ceton nawa d’an.. Dama za’ace ita wancan da tai masa sihirin itace zata mutu ba wacce ta karya sihirin ba ai da kaman sauk’i.. Malam bana son abinda zai ja min farrak’u da nawa mijin dan idan har a k’arshe yasan abunda nayi zai rabu da ni ne rabuwa ta har abada…” Ta d’an mumfasa duk zuciyarta a dame kafin taci gaba “Kuma Malam ni a gaskiya ba ko wace shara zan kawo cikin rayuwar d’a na ta rayu dashi har na tsawon watanni uku ba. Musamman da ka fad’a irin wann budurwar ai ta riga ta zama shara bola juji wanda mutane ke guje mata.” “Duk dalilan da kika lissafo su suka sa ta zama makarin sihirin dake jikin d’anki.” Ya bata amsa kai tsaye. "Mommy ta kuma girgiza kai “Kai inaa, shi kansa Haidar na san ba lallai ya amince ya zauna da macen da zan aura masa har wata mu’amala ta gifta tsakaninsu a tsakanin watanni uku.. Yanzu haka ma gaba yake dani toh ta ya zan iya janyo ra’ayinsa har ya amince da wann Auren.?”" Girgiza mata kai yai “Ba wace hanya sai wann hanyar.. Saidai kuma idan zaki hak’ura da d’anki ki sallamasa ma wancan hatsabibiyar..” Asshe tai saurin girgiza kai “Gafarta Malam gaskiya sharud’an sun mana tsauri da nauyi bana tsammanin zamu iya.. Kar garin neman gira aje a rasa ido. Aunty Kwaise tashi muje.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin mik’ewa. Bokan ya dakatar dasu da fad’in “Toh kuwa ku shirya rasa d’anku rashi na har abada..” ya tsaida idanunsa akan Mommy “Ba d’anki kawai ba harta ahalinki da dukiyar mijinki da dik wani abinda kika mallaka kike tak’amada a duniyar nan kaf zaki rasasu domin kuwa kar ki mance na sanar dake ita kanta matar da ta aure d’an naki ta hanyar sihiri ture ce a cikin rayuwarsa. Akwai babban shed’ani a sama wanda shine ummulhaba’isan komai.. Kuma bazai sarara ba sai yaga bayan ahalinki.. Dan k’asa bazata tab’a mana k’arya ba. Allah bamu alheri..!” Mushirikin Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa cikin tafiyarsa da yafi yanayi da durk’uso. Har zai shige cikin wani k’ofa nan cikin bukkan wanda yake kaman shige a durk’ushe tsaban k’ank’ancin k’ofar Mommy tai saurin dakatar dashi “Malam dakata.. Na amince..! Na amince da sharud’anka..! Na Amince zanyi ma d’a na AUREN WATA UKU..! Na amince zan kub’utar da ahalina koda za’a rasa rai..! Na amince zan kashe ko nawa domin na tabbata ban rasa masarautar da na Jima na d’ibi shekaru ina ginawa ba.. Idan irin macen da ka fad’a itace makarin sihirin dake jikin d’a na zan nemota duk yanda ta shiga ta fita.. Idan kud’i zai sayeta zan sayeta dasu domin d’a na da ahalina su tsira..!” Ta k’arashe cikin jaddada kalamanta har wani huci da tururi take fitarwa. Dattijon ya kaikaito yana duban Mommy. Sai ya kad’a ya dawo da baya da baya ya zauna a mazauninsa. Ya buga k’asan gabansa ya dubi Mommy “Ke da kanki kika zab’i nau’in Budurwar da makarin Asirin da aka jefi ahalinki ta jikin d’anki yake tattare da ita… Kar ki mance dole macen ta cika wann sharud’an idan aka samu sab’ani ko akasi ki sani tashin hankali ne maras misaltuwa biyeda ahalinki.” Ya mik’e cikin tafiyarsa da yafi kama da durk’uso. Ya d’auko wani bak’in ruwa cikin wani k’ok’o mai launin ja. Suka zuba masa idanu yanda yaketa tsifface tsiffacensa cikin ruwan. (Allah kai mana tsari da b’ata ka tsare mana imaninmu. Ameen). Har suka baro wajen bokan jimamin abun suke. Ta ya za’a soma neman irin wann matar wacce Auren Haidar ke nufin Ajalinta.? Shin wacece zata sadaukar da rayuwarta dan rayuwar nata d’an ya inganta..? Idan ma sun samu irin wann Budurwar shin Haidar zai amince da ita..? Kai abun da kaman wuya wai gurguwa da Auren nesa. Mommy ta dubi Asshe “Asshe ta ya za’a ce dole sai irin wann budurwar ce lak’anin ke jikinta.. Wai dama ana haka..?” Asshe ta murmusa “Aunty Kwaise kenan.. Kin mance akan bawa mutum lak’ani na arziki ta irin matar da za’a gindaya masa ya aura.. Wata cewa za’ayi sa’arka na tareda ita shiyasa sai kiga duk yanda irin wann matar take mutum ya tafi ya nemo. Ai a duniyar nan babu abinda ba’ayi.. Fatanmu mu samu irin budurwar da Malam yace cikin gaggawa. Mommy ta jinjina kai a hankali Tana tsaka da tunanin taji Asshe da driver suna karaton salati. Bata ankara ba sai gani tai mutum kwance gaban motar saman kwalta sun bige wata mata. Tuni Mommy ta fara salallami tana fad’in Driver ya fita ya duba matar da suka bige ko tana numfashi. ** A b’angaren su Ummul kuwa sun zaga police station kusan guda uku a na hud’u sukayi dace. Hannayen Ummul rik’e cikin na ‘yaruwarta Khulsum wanda k’araffan k’ofan cell ya raba tsakaninsu. Ta kuma share hawayenta tana duban Khulsum. Khulsum ta girgiza kai kad’an tace “Adda meyasa kika tak’ura kanki wajen nema na..? Wann hukunci na nake karb’a.. Nayi addu’a wa mahaifiyarmu cikin b’acin rai. Nace Allah yasa jami’an tsaro su kamata sai gashi ba’je ko ina ba addu’a na ya dawo kaina. Take naga ishara . Sai na zamto ni ce wacce jami’a tsaro suka Kama.. Lallai na kuma yarda iyaye ba abun wasa bane. Kuma al’amarin su al’amari ne mai girma. Ban tab’a mafarkin zuwa police station ba dukda taran rikici irin nawa sai gashi kausasa harshe da nai Akan Umma yasa nazo police station kuma har gark’ame ni anyi.. Snn ‘Yaruwata da muke uba d’aya bama bare ba itace ta zamto Sila..” Ummul ta jinjina Kai a hankali ta kuma share hawayenta “A littafin Allah mai tsarki wajaje da dama yayi umarni da a kyautata ma iyaye Khulsum. Yazo a hadisin Abdullahi bin Mas’ud yanda yake tambayan Manzo S.A.W wane aiki ne yafi soyuwa wajen Allah. Bayan sallah akan lokacinta sai biyayya ma iyaye ya biyo. Har ila yau matsayin uwa yazo a hadisin Abu Huraira wani mutum ya tambayi manzon tsira S.A.W wanene yafi cancanta yayi kyakkyawan zama dashi.? Manzo S.A.W yace mahaifiyarka. Ya sake tambaya ya sake amsa masa da mahaifiya.. Saida akayi haka sau uku yana cewa mahaifiya kafin a na hud’u yace mahaifi.. Har ila yau Manzo S.A.W ya fad’a cikin hadisin da Tirmidhi ya rawaito cewa ‘ Yardan Allah na tareda yardar iyaye haka fushin Allah na tareda fushin iyaye.’ Kinga Hakan kawai ya ishe mutum ya fahimci girma da k’ima da iyaye ke dashi musamman mahaifiya.. Shiyasa kikaga dukda abubuwan da Umma ke fad’i akaina daidai da rana guda ban tab’a fatan na sab’a mata ba. Sabida ita d’in mahaifiyata ce.. Kuma zanci gaba da mata addu’a har Allah ya fahimtar da ita. Naji dad’i da kika fahimci haka Khulsum. Kar ki damu yanzu zamu tafi kinji.. Zaki fita daga wajen nan.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. A can gaban kanta kaw Hisham sai fafatawa yake da ‘yansandan dake duty. Sun dage bazasu bada beli ba a cewarsu ba huruminsu bane. Kai da ganinsu kasan wani Abu suke son tatsa jikinsa musamman da sukaga yanayi akwai tattare dashi. Hisham ya murmusa dan shima ya d’ago jirginsu. D’an matso da fuskarsa yai kafin yace “Officer kenan. Tell me your bank details . Let’s settle this once and for all.” D’ayan ya dubi d’ayan “Mai ka maida mu.. Gurb’atattun ‘yansanda ko me..? Don’t abuse our uniform.” Katsesa Hisham yai da fad’in “Nasan matsalar ka.. Take this..” Ya k’arashe yana janyo hannun police d’in had’ida dunk’ula masa kud’i masu d’an yawa. Gajeriyar murmushi saman fuskarsa. Gurb’ataccen D’ansandan ya bud’e hannunsa yana duban yawan kud’ad’en take ya shiga washe baki harda sara ma Hisham. Ya dubi d’ayan d’ansandan wanda da gani assistant d’insa ne ya daka masa tsawa. Take ya k’ame yana amsa masa. “Maza shige ka bud’eta..” D’ansandan ya jinjina Kai ya wuce cikin sauri. Nan da nan aka fito da Khulsum. Tai tsaye tana duban mutumin da ya taimaka aka fitar da ita. Saidai ganinsu da tai tareda Hajja Fannah yasa tai zaton ko wani nata ne. Khulsum ta kariso a hankali kafin ta risina ta gaida Hajja Fannah da mutumin da ta gansu tare had’ida masu godiya. Murmushi saman fuskar Hajja Fannah ta girgiza mata Kai alamun ta daina masu godiya. Ta shiga tanbayan da fatan babu dai abinda suka mata. Ta girgiza kai tace basu mata komai ba. Ummul dai duban fuskar ‘Yaruwar tata tai da mamakin yanda yai luhu luhu alamun yasha tafi. Tasan duk yanda akai bazai wuce wann ‘yarsandar da sukazo suka tafi da Khulsum d’in bane ta mammareta. Batadai ce komai ba tinda Sun samu an fitar da ita. Gwara suyi gaggawan barin wajen kafin su bisu da wani sharrin. Asibiti suka nufa daga nan wajen Abba. Saida aka fafata da Mama kafin ta bari su Ummul suka shiga wajen Abba. Dan saida Hajja Fannah tai da gaske kafin Mama ta bari. Ya tabbata Umma bata asibiti wajen Abba. Hankulansu ya kuma tashi ga duhun dare da ya riga yayi. Hajja da Hisham suka kwantar masu da hankali da fad’in za’a sami mahaifiyarsu cikin yardar ubangiji. Hisham yace idan har bata zo asibitin a daren ba zuwa gobe zai filing missing person report ma ‘yansanda tinda ma ba’a sanar da cigiya a dokan yansanda sai after 24hrs. Bayan sunyi sallama da Hajja da nufin dik yanda ake ciki gobe idan Allah yakai rai da abun zasu tashi Ummul ta d’ago ta dubi yaron Hajja Fannah da taji ta kirasa da suna Hisham.. Cikin sanyin murya take masa godiya na taimakon da yai masu musamman da ya kasance zuwansa garin kenan ko hutu bai samu ba matslolint suka tarbesa. Murmushi saman fuskarsa ya girgiza mata kai “It’s nothing. Ki daina min godiya.. I’m glad I helped out.. Ummul- khair.” Yanda ya ambaci sunan nata da wani irin siga sai yasa ta sadda idanunta kad’an. A d’an daburce tai masa sallama had’ida komawa wajen Khulsum cikin sauri. Shi kaw kallo ya bita dashi har saida ta b’ace ma ganinsa kafin ya nufi mota yanda Hajjarsa ke jiran karasowarsa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *12* *©️Sameena Aleeyou… * Tinda suka koma gida ya gaza samun sukuni. Tunaninta ya addabesa. So yake ya tambayi mahaifiyarsa gameda ita. Sosai yaji yana son sanin labarinta. A parlor ya tadda Hajja tana had’a wasu kayan d’inkinta. Ya zauna daga gefe. Ta d’ago ta dubesa “Har kaci abincin kenan..?” D’an furzar da fuci yai kad’an yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa “Naci Hajja ya isheni..” "Ya d’anyi gyaran murya kad’an yana duban kayyayakin dake gabanta “Wai Hajja har yanzu bazaki hak’ura da d’inkin nan ba. Yanzu fah Allah ya rufa mana asiri I can take care of you , you don’t need to do all these things.”" Murmusawa tai “Ban raina k’ok’arinka ba Hisham. Amma kasan idan ba idona ne ya tafi ba ko k’arfina ya k’are bazan iya daina sana’ata ba. Sana’ar da na raineka da ita har ka zama abinda kake a yau cikin k’udirar Ubangiji. I love being independent kai kafi kowa sanin hakan.” "Ko shakka babu ta tuna masa zamansu a Maiduguri, hardships da suka fuskanta da ma duk wani k’alubale na rayuwa. Ya d’an jinjina kai ba tareda yace komai ba." Ta kuma d’agowa tana dubansa. Sai ta aje abinda take ta bada hankalinsa akansa sosai. Ta ambacesa da sunansa na yanka. Ya d’ago yana dubanta. Taci gaba “Ni a halin yanzu nafi buk’atan ka gina naka ahalin. Ka haura talatin already. Kayi karatu ka samu aiki mai kyau. Rayuwarka ta inganta Mai kuma yayi saura bayan iyali. Bazan tak’ura maka ba ko na tilasta maka amma ni a nawa tunanin ya kamata ka fara making efforts. Kaga yanda kake tafiya ka barni ni kad’ai d’in nan sai ka barni da abokan wasa.” Ya d’an murmusa dan ya d’ago mai take nufi. “Toh Hajja ki sama min Matar mana kawai a nan tinda ni dai har yanzu ban samu ba.” Tab’e baki tai tana mai ci gaba da abinda take “Idan na zab’a maka zaka amince da zab’ina ne.. Kasan ku yaran zamani ba’a maku katsalandan a wann sha’ani. Yanzu sai ku ba wa mutum kunya.” Ya kuma murmusawa “Haba Hajjata. Nasan bazaki tab’a zab’a min abinda zai cutar dani ba. So na baki wuk’a da nama.” “Ta d’an kuma tab’e baki “Na Jika dai.. Amma tina kace haka shikenan.. Ka jira kaga.. Next zuwa da zakai zaka tadda iyalinka na jiranka ne..” Ya d’an zaro ido waje “Hajja ina kika tab’a jin anyi aure Ango bai halarta ba..?” “Za’a fara akanka tinda Wakili kawai zan tura ya karb’ar maka. I already have someone in mind dama.” Ya d’an fito daga cikin kujeran cikin zak’uwan san jin yaji ko wacece “Da gaske Hajja.. Who’s she.. A ina take..?” Ta d’an dubesa “Idan lokacin yayi ka ganta.” Ya kuma murmusawa kad’an. Shiru kaman babu mai cewa komai sai Hisham yai gyaran murya kad’an “Nikam Hajja nace… Ita yarinyar nan Ummul-khair…” Hajja ta zuba masa idanu jin yanda yake maganar cikeda kulawa ga wani k’alk’ala na musamman da ya ambaci sunan Ummul dashi “Umhum ina sauraronka.” Ta fad’i still tana dubansa. “Wai dama kun jima da sanin juna ne.. Or do you have any relationship with her family.?” Hajja ta d’an murmusa “ Banda abinka Hisham yanzu ak’alla shekaru hudu fah muke nema a garin nan. Kaga ai ya kamata na saba da mutane kuma idan baka mance ba na sanar dakai ina koyar da sana’ar d’inki ma ‘yanmata. Toh Ummul tana cikin d’alibai na.” Hisham ya jinjina kansa a hankali “And she’s from around this neighborhood..?” Hajja ta kuma murmusawa kad’an dan ta lura da curiosity na d’an nata gameda Ummul. Ita idan har abinda take hasashe ya tabbata zatafi kowa farin ciki. Dan Ummul yarinyar kirkici wacce jarabawa da k’alubalen rayuwa sukai marfi ma rayuwar nata. Gyara zamanta ta d’anyi ta kaikato sosai tana duban Hisham “Naga alama dai tambayoyi ne kazo dasu wann karon.. Amma ka bari har Allah ya wayi gari lafiya kaga yanda ranar yau d’in ta kasance mai tsawo. Idan ka samu ka huta zuwa gobe da safe idan Allah ya nufemu da kaiwa sai na amsa maka duka tambayoyinka.. Maza tashi kaje ka kwanta haka ka huce gajiya kuma. Kaga nima kwanciya zanyi haka nan.” Ta k’arashe tana k’ok’arin tattare kayan. Hisham ya amshe yana linke mata su . Dan yanda ya kwana biyu baya tareda ita d’in nan dik abinda zaisa ya samu albarkanta baya wasa da wann abun komin k’ank’ancinsa. ** Sassafe Mommy ta fito da zummar komawa Abuja dan dama day trip tayi niyyan yi amma sabida accident da suka d’an samu dole ta bari sai Washe gari bayan an duba lafiyan motar an tabbatar zata iya tafiya. Ta dubi Asshe “Na bar miki wuk’a da nama amma ki tabbata wacce duk za’a samu tanada futures da qualities da zamu iya jan ra’ayin Haidar dasu in just a short time. Lafiyayya wacce batada wani cutan da zai iya shafan d’ana.” Asshe ta d’an numfasa “Bakida matsala Aunty Kwaise ai kaman yanda kikace ne a duniyar nan babu abinda kud’i bazai sai maka su ba. Ni yanzu damuwata matar da muka bige wacce har yanzu Ke asibiti gashi babu wani means of identification tareda ita balle a samu wani nata.” Mommy tace “Aff kinga ni na mance ma da batun wann matar. Yanzu tareda waye aka barta a asibiti.?” Asshe tace “Mai aikina Marka ita ta kwana da ita suna can tare yanzu haka..” "Mommy ta jinina Kai dan dama wani private hospital suka kaita “Duk abinda ake ciki dai kin sanar dani. Ni yanzu tafiya ya kamani, dan kinsan na fad’a miki Engr baisan na taho ba shima baya nan ya tafi Lagos tafiyar da ta shafi Kasuwancinsa.. So bani so ya dawo gidan ya tarar bana nan. Anisa ce kawai gidan kinsan kuma yanda take saitin da sauk’i." Asshe ta kuma jinjina kai “Zakiji komai in sha Allah Aunty Kwaise. Allah ya tsare hanya.” Suna tsaka da sallaman Hilal ya k’araso wajen. Mommy ta dubesa “Bazan amsa goodbye d’inka ba tinda har zaka zo hutu k’asar nan kuma jirginka ya sauk’a a Abuja ka kasa zuwa ka dubani.. Inji kaima kabi sahun d’an uwanka Haidar ne.?” Hilal matashin saurayi d’a ga k’anwar Mommy Wato Asshe ya d’an murmusa yana shafa kansa. Baifi sati da zuwa Nigeria ba karatu yake a k’asar Cyprus. Ya samu zangon hutu. “Haba mana Mommy ta kinsan bazan miki haka ba. Tareda Abba da matarsa muka dawo Kano daga Abuja shiyasa. Nasan duk Anisa ce ta had’ani dake. Amma kafin hutuna ya k’are zaki ganni in sha Allah. I still have 2 weeks here.” Mommy ta murmusa “Toh shikenan sai na ganka.. Ina nan Ina zuba ido.” Hilal ya murmusa yana tabbatar mata zaizo. Ya nufi wajen driver yana tambayarsa hope motar bata samu matsala ba. Mommy ta dubi Asshe ta d’anyi k’asa da murya “Oh kiji min Hilal wai Abbansa da matarsa. Kinji yaro na taya mahaifiyarsa kishi.” Asshe ta tab’e baki “Yo yarinya ce k’arama Anisa ma ta fita Kinga kuwa yaushe zai wani bata matsayi.” Mommy tai yar bazawarar dariya “Allah ya rufa asiri dai bai had’eku gida d’aya ba dan nasan da sai an kwashi ‘yan kallo tsakanin yarinyar da Anisa wataran.” Asshe ta kuma tab’e baki “Ai Anisa gaba take da Uban nasu tinda yayi wann jarababben Aure. Sun had’e kai da sauran ‘yanuwanta ‘yanmata yaran uwar gidana suna gaba da ubansu ya auro sa’arsu. Shiyasa ma bata cika son zaman Kano yanzu ba tafi son zama can Abuja wajenki to avoid seeing her father here.” Mommy tai shiru tana tuna case d’in dake nata gidan. Ta d’an numfasa “Gwara su idan sunyi gaba da Ubansu sunada dalili.” Tai maganar tana k’ok’arin shigewa mota suna kuma sallama da ‘yaruwarta. Kasancewar fitan sassafe tayi yasa ta samu isowa da wuri. Tuni tasa ma’aikata an soma dafe dafen abincin da za’a tarbi Daddy dasu. Suna zaune shida ita a parlor bayan ya ida cin abinci magazine rik’e cikin hannunsa yana dubawa. Mommy dai sai digesting maganganun da boka ya sanar da ita take. Ta rasa ta yanda za’ayi ta soma sanar da mijinta batun. Toh ma mai zata soma sanar dashi. Cewa d’ansu yayi Aure ba da saninsu ba.? Kodai mugun asirin da aka jefesa dashi.? Ko kuma auren da Malaminta yace a masa wanda shine makarin sihirin. Ta ina zata faro. Tana tsaka da tunanin kaman wanda aka jefo sa suka sinkayo sallamansa. Yau Mommy ta rasa duban tausayi take masa ne ko duban sakacinta akansa. Kallo d’aya mahaifinsa ya masa ya watsar. Ya k’ariso hannunsa rik’eda shud’in Folder mai d’aukeda logo na Kampanin mahaifinsa jiki Wato (MB). Gaisar da iyayen nasa ya soma yi daga nan yanda yake tsaye bayan kujera dan yasan he’s always not welcome. A gidan da ya kamata ya kira da home. Mommy ce ta amsa gaisuwarsa yau d’in da sakin fuska. Ga wani mugun sanyi da tayi. Mahaifinsa kaw bai samu zarafin amsa masa ba. Mommy ta d’anyi murmushin da yafi kama da yak’e tana duban mijin nata da kacaukam hankalinsa Ke bisa Magazine d’in dake hannunsa. Wani article ne ya d’auki hankalinsa yanda aka rubuta ‘FG to approve the billion dollars bridge project to Maitama Builders.’ Project din da Haidar keta fad’I tashi akai ganin an zab’esa matsayin Project Manager. Mommy ta d’anyi gyaran murya “Engr Haidar na gaidaka.” Har lokacin idanunsa naga magazine d’in “Na ganshi ai.. Sai ya fad’i abinda ya kawo shi. Yai maganar ko kallon yanda Haidar yake baiba. Haidar ya had’iyi bak’in cikin da ya tokare masa mak’oshi. Mommy dai gaba d’aya jikinta a sanyaye yake yanzu tinda Malaminta ya sanar da ita abinda Ke faruwa. Ya zama dole ta bada himma wajen had’in kan ahalinta bazata bari azzalumai suyi nasara akansu ba. Ta dubi Haidar wanda ya kafe mahaifina da ido kaida gani kasan ba kallon komai yake masa ba face tsana. Ta k’ak’aro murmushi “Haidar you heard your Dad.. Ka shigo ka gabatar masa abinda ya kawo ka nasan ya shafi aiki tinda ga company’s folder hannunka. "Bai dubi Mommy ba tinda dukansu haushi suke basa ya k’arasa yanda mahaifinsa yake. Ya aje folder d’in gefensa kad’an “This is the new proposal my team and I have been working on.. It contains all the details, the construction deliverables.. The scope and budget of the project..” Ya d’anyi fasali jin bai amsa sa ba kafin yaci gaba “You..can go through it and see, before we present it to the board of directors..”" Har lokacin bai amsa sa ba. Kaman ba dashi yake ba haka Daddy yayi. Haidar ya kuma had’iyan k’uncinsa. Duk abinda mahaifinsa zai masa akan wann project d’in ya zama dole ya shanye. Alk’awari yayi sai yasa mahaifinsa ya cinye duka kalamansa. He never backs down. He must fulfill all his promises. Zai wanke kansa zai kuma sa mahaifinsa ya cinye kalamansa sann daga k’arshe he will personally take the company down to the ground. To the last kobo. Ya ranste sai ya tarwatsa mahaifinsa da kansa. Sai matse file d’in yake cikin hannuna jijiyoyin jikinsa na kuma tashi kaikace ketata zai. Muryar Mommy ya sinkayo tana tausan mijin nata da yaji bayanan d’an nasa ya kuma sauraresa. Kaman bazaice komai ba sai yai masa nuni da hanyar da zai sadaka da study d’insa daga nan cikin parlorn. "“You can leave it over there. Maybe, I’ll go through it when I’m less busy…” Daddy yace yana mai rufe magazine d’in had’i da zame farin glasses na k’ara k’arfin gani “I just hope it is not one of your foolishness.”" Haidar ya rintse idanunsa yana jin abun har cikin k’ahon zuciyarsa. Bai kuma juyowa ya dubi mahaifan nasa ba yasa kai ya shige cikin sauri kafin zuciya ta d’ibeshi. Yana shigewa Mommy ta mik’e tabi bayansa da sauri dan wani tunani ne ya fad’o mata wanda k’ila damarta kenan akansa. A waje yanda ya aje motarsa ta cimmasa. Ta bud’e murya ta kirawo sunansa. "Kaman bazai tsaya baya, sai kuma ya dakata ba tareda ya juyo ba yana mai furzar da huci a hankali." Mommy tai saurin k’arisowa yanda Haidar ya kaikaito yana dubanta. “What now.? Kin mance ne baki bani naki insults d’in ba shine kika biyoni waje..?” Ya fad’i idanunsa akan mahaifiyarsa. Mommy tai k’ok’arin dannewa dan yanzu ta tabbata he’s not in his right state of mind. “Kaga Haidar I’m not your enemy here.. In fact taimakonka nake so nayi.. Naga yanda kake matuk’ar so kai handling project d’in nan… Kuma nima na tabbata kai kafi cancanta kayi d’in… I can be your ally until your achievement.” Murmushi Haidar yai hannayensa dafe da kunkumi yake duban Mommy. Sai kuma ya girgiza kai yace “Seriously Mommy.. You wanna be my Ally..? Since when Mommy..? Yaushe kika fara damuwa dani da abinda ya shafe ni..?” Mommy ta zuba masa idanu. Haidar yaci gaba “Kinsan meye damuwarki Mommy.. Shine ya amince na jagoranci aikin sabida personal interest d’inki. Kinsan na jima da sanin ni a wajenki ba komai bane face weapon. Makaminki.. Kuma kar ki mance na fad’a miki bazaki sake amfani dani ba wajen cimma wasu mnufofinki. Wancan Aliyun ya Riga ya mutu Mommy.. He’s long been dead.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige motarsa sai sakin huci yake. Zai bud’e marfin motar kenan Mommy tai saurin dafa hannunta saman nasa. Hawaye suka soma gangaro mata. Cikin tsananin rawar murya take furta “Haidar… What did they give you.. What have they done to you to turn you against us like this..?” Cikeda k’osawa ya zame hannun Mommy daga saman nasa “Ba hawayen da zaki zubar da zaisa na yarda dake Mommy. You destroyed that bond tin da jimawa. So kar ki saka ma kanki ciwo Mommy.. I do not give a damn about this family. I’m doing this project for my own personal interest of course. Kuma bazaki tab’a sani ba until my mission is accomplished.” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige motarsa. Mommy ta bud’e murya tace “Idan ni ce Matar Aliyu Maitama har sai kazo nan ka amince da buk’ata ta kafin ya saka hannu da sunanka saman project d’in nan.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta juya cikin gida ba tareda ta kuma sauraronsa ba. Juyowa yai yana duban Mommy yana so ya fahimci mai take nufi cikin kalamanta. Yasan mahaifiyarsa tinda ta fad’i haka tanada wani babban dalili a k’asa tana kuma so ya tank’wara shi ne yayi wani abinda take so. Zaiyi duk yanda zaiyi ya tabbata bai fad’a tarkon da take k’ok’arin d’ana masa ba. ** Kano. Waya ta ida yi da Marka yanda ta sanar da ita Matar ta farka amma bata cewa komai. Kuma bata fad’i yanda danginta suke ba balle a nemsu. Ga dukkan alamu idan ba mai tab’in kai bane k’ila had’arin ya tab’a mata kai. Hilal ne ya tuk’ota zuwa asibitin. Ta dubi Marka ta dubi matar wacce Ke ta zabga kuka saman gadon asibiti. Marka taci gaba da fad’in “Ayya Hajiya ‘yan jikokina suna gida basu ganni ba tun jiya. Wllhi duk na gaji gida nake son zuwa ga wann asibitin babu mutane sosai balle likitoci kinsan yanda asibitin kud’in nan suke zuwan likita nada k’aida da lokaci. Tak’i magana tinda ta tashi kuka take. Inaga Hajiya kawai idan likita yazo ruwan da aka d’aura mata ya kare kisa a sallameta ai kunyi naku Allah ya gani.” Hilal ya girgiza kai yana duban Matar cikeda tausayi “No Ammi. Ba haka za’ayi ba. Inaga kamata yayi akaita wajen k’wararru su sake dubata. Watak’ila ta sami wani internal injury. Kamata yayi akaita a dubata a bata all the treatment that’s needed. Idan ya kama mu mik’a case d’inta ma hukuma su zasu bincika yanda danginta suke. But we can’t abandon her not knowing ina danginta suke. Watak’ila sunata nemanta tin faruwar had’arin.” Asshe ta katsesa “Kai Hilal nayi na musulunci tinda har asibiti mun kawota. Har wacce zata kwana da ita na bari. So bazanyi treating ciwon haukanta ba. Tafiya take tsakiyar kwalta dama can k’ila da guntun haukarta.” Ta dubi Marka tace “Marka jeki abinki zan fad’awa nurses d’in da suke bakin duty da zaran likita yazo suna iya sallamarta.” Marka tai godiya da fatan samun sauk’i ta fice. Hilal ya girgiza kai zai kuma magana ta nuna masa waje “Fita mota ka sameni ina zuwa zanyi magana da mutanen asibitin.” Ba Don yaso ba ya girgiza kai ya fice. Asshe zata take masa baya kenan ta sinkayo muryar Matar tana fad’in “Lafiyata garau. Kuma duk ina sauraronku. So nake ku d’aukeni ku kaini can babban asibitin koyarwa yanda mijina yake ko zan samu na ganshi. Tani ta hana ni ganin shi tace nida Ummul mu muka taru muka saka masa ciwo.. Ta ina zan soma neman kud’ad’en da Tani tace na nemo na jinyar Malam. Tani takai mak’ura wajen makirci da zalunci.” Ta soma kokawan sauk’owa daga gado dikda drip dake d’aure hannunta. Fad’i take “Na tabbata tana can ta d’aura laifin komai akan Ummul da bak’in k’addarar da yai ma rayuwarta dabaibayi.” Asshe tai saurin k’arisowa ta dakatar da ita. Umma ta d’ago ta dubeta sai ta fashe da kuka “Wllhi lafiyata k’alau ina cikin hayyacina. Sun kasa gane banida wani buri da ya wuce naga Ummul a d’akin mijinta. Toh meyasa Tani zata d’aura alhakin ciwon Malam akaina da Ummul.?” Taci gaba da rera kuka irin na wanda damuwa ya masa dabaibayi. "Asshe ta janyo farar kujera a gefe ta zauna tana duban Matar “Sunana Hajiya Asshe, mun bigeki da mota akan hanyarmu.”" “Yaya Tani ce tace lallai lallai sai na nemo kud’ad’en da za’ayi ma mijinmu jinya idan har ina so na sake ganinsa. Ta nad’i sautin muryata cikin waya itada Badi’a sunce ko Kotu akaje ya iashesu Hujja.” Asshe ta zuba mata idanu jin yanda taketa maganganu marassa ma’ana. Labarun da yafi kama da wanda ke cikin depression. A hankali ta d’an jinjina kai ta dubi Matar “Akwai yanda yake miki ciwo ne. Kina so na kira Likita.?” Umma ta girgiza mata kai alamun a’a”Baiwar Allah ni fah lafiyata lau. Yaya Tani ce ta yanka ragon hauka ta d’aura mun dan kawai Ummul ta kasance ‘yata.” Sai ta d’anyi fasali ta kuma duban Asshe “Amma wacece ke.?” Asshe ta k’ura mata idanu tana karantarta sai tace “Toh ma sha Allah. Tinda kince babu yanda yake miki ciwo.” Tai fasali dan sosai take so taji labarin Matar musamman da taji abubuwan dake fita bakinta shan cikin Matar bazai mata wahala ba “Ki kirani maganin matsalolinki.!” Ta matso had’ida d’aura hannunta saman na Umma “Ki yarda dani zaki iya sanar dani duk damuwarki. Ni ba muguwa bace nasan zaki fahimci haka tinda bayan bigeki da mukayi bamu k’yaleki ba saida muka tabbata mun d’aukoki mun kawoki asibiti. Kuma ban barki ke kad’ai ba har saida na ajiye wacce zata kula dake. A nan muka shigo da yarona kikaji yana cewa kar mu kyaleki har sai mun tabbata kin isa ga ahalinki lafiya. Wann kawai ya isheki ki yarda mu mutanen k’warai ne ba masu cutarwa ba. Kuma a yanda yanzu duniya ta koma babu yarda tinda har ni nayi shahada na yarda dake ya kamata nima ki d’auki duk yarda ki bani. Watak’ila Allah ne ya dubeki ya had’aki da maganin matsalolonki.” Da mamaki Umma Ke dubanta “Maganin matsalolina ni Suwaiba..?” Tai maganar tana nuni da kanta. “Baiwar Allah anya kaw kinsan matsalolina..? Ai inaji kaf fad’in garin Kano da kewaye babu matar da ta kaini matsaloli tinda har na kasance mahaifiya ga Ummulkhairi.!” Asshe ta kuma gyara zama cikin son jin taji komai “Wacece Ummulkhairy.?” "Umma ta kamo bakin zaninta tana share hawayen dake kuma zubo mata “Ummulkhairi, ‘Yata da na mata lak’abi da Uwar alkhairi..! ‘Yata da naci mata buruna da dama.” Ta kuma duban Asshe sai ta girgiza kai wasu hawayen na kuma gangaro mata “Amma babu buri guda d’aya da ya cika. Kinsan dalili..?”" Asshe da ko kifta idanu batayi saurin girgiza kai tai alamun a’a. Umma taci gaba “Sabida mutane sun canfa mun ita.. Duk namijin da yazo neman aurenta guduwa yake. Kodai wani abu ya gifta a fasa Auren. Amma fah dukda wann guje mata da mazan keyi basu fah fasa neman aurenta ba. Kinsan meyasa..?” Tai tambayar murmushi mai ciwo saman fuskarta kafin taci gaba “Sabida Ummul d’ita tubarkallah ce san kowa k’in wanda bai samu ba.” Sai kuma ta fashe da kuka “Amma meyasa ta kasa Auruwa..? Meyasa duk masifa da nake fuskanta a nawa gidan Auren ta dalilinta ne.? Meyasa maza ke guje mata. Meyasa k’addararta yazo a haka.” Ta k’arashe cikin gunjin kuka. Asshe ta kamo hannayen Umma cikin nata tana k’ok’arin kwantar mata da hankali “Ki daina kuka. Shi Aure lokaci ne. Baya duba matsayi ko kyaun halitta. Wata da komai ta rasa miji wata ba komai Allah ya bata. Shi Aure kaman hab’o ne da zaran lokaci yayi sai kiga anyi..” Cikin zuciyar Asshe fal mamaki. Ganin abun take kaman almara. Abinka da mai b’atacciyar zuciya sai ta kuma gaskgata aikin bokansu. Gashi tin ba’aje ko ina kaman sun had’u da makarin sihirin dake jikin Haidar a sauk’ak’e. Sai ta kuma yarda gaskiya Malaminsu ya fad’i ta mance cewa wann duk zai iya zama jarabawa daga Ubangiji mai komai ya baka abinda kake nema d’in a kan gab’ar da kake nema. Wani shikenan sai ya kuma dulmiya cikin b’ata. (Allah kai mana tsari da shirka. Ameen) Ta saki murmushi tana duban Umma “Ummulkhairinki zatayi Aure. Aure na bajinta. Aure irin na kece raini. Auren nuna ma duniya.!” Umma ta dubeta da mamaki. Sai ta girgiza kai tace “Anya kuwa Ummul d’ina nada rabon Aure a wann duniyar.?” Asshe ta murmusa “Idan har kika aminta dani Ummul d’inki zatayi Aure..” Tai maganar cikin jaddada kalamanta. Hilal ne yai knocking ya lek’o jin shirun yayi yawa. Nan ya hangi mahaifiyarsa da patient d’in kaman sun jima da sanin juna. Mamaki ya cika Hilal. Ya d’an girgiza kai yana mamakin saurin yarda da juna da mata keda shi saikace ba Ammi bace ta gama cewa su tafi su kyale matar. Bai gama mamaki ba saida yaga Amminsa sun fito tareda Matar dan dama da ya shiga tace masa bari likitan yazo ya masu sallama tinda taga isowar motarsa. Shidai Hilal haka ya tuk’a su suka nufi gida tareda Matar dasu Ammi suka bige wacce ta zamto bak’uwar Ammin tasa. "Suna isa gida Hilal ya tareta “Ammi Wai meke faruwa ne. Meyasa kika taho da matar nan.. Ammi I thought danginta za’a nema.. Nowadays fah mutane ba abun yarda bane. This whole thing zai iya zama shiri bigeta da kukayi, kaita asibiti da duk wani maganganun da zata sanar dake. Ammi yanzu fah har gida ake ture a sace mutane. Ammi Abba sanannen mutum ne a garin nan. Iyalansa zasu iya zama target.”" “Kai dallah rufe min baki. Duka duka yaushe ka sauk’a k’asar balle ka fad’a min abinda Ke faruwa cikinta. Nafika sanin meke faruwa. Ina zuciyar taimakon taka? Inji kai ka fara cewa we shouldn’t abandon her. Toh Shiyasa na taho da ita. Kuma ko mahaifinka yazo gidan nan ba ruwanka kar ka sanar dashi komai kaji na fad’a maka.” "D’an girgiza kai yai “Fine, yanda kikace Ammi.” Hilal yasa kai yai shigewarsa." Yana shigewa ta d’aga waya tai dialing wani layi. Ana d’agawa ta soma fad’in “Hello Yunusa kanajina. Zan turo maka information kan wata mata. Yanda take zama sunan mijinta da sauransu. Inaso ka gudanar min da binciken k’wak’waf kan ahalinta da abinda Ke faruwa dasu. Bana so a d’auki lokaci. Ayi komai cikin gaggawa.” ** A can b’angaren su Ummul kuwa hankulansu yakai matuk’a wajen tashi. Dik yanda ake tunanin za’a sami Umma anje ba’a sameta ba. Hisham kaw da shi ake aiwatar da komai tuni sun bada cigiyan Umma. Yai k’uri yana duban Ummulkhairy dake ci gaba da kuka da gaske wann karon. Duk k’ok’arin ganin bata d’aura alhakin iftila’in dake faruwa cikin ahalinsu akanta ba saida zuciyarta ta raya mata hakan. Da wanne zasuji? B’acewar mahaifiyarsu ko kuwa mahaifinsu dake kwance gadon asibiti wanda har wann lokacin bai san yanda yake ba. Ga likitoci sun tabbatar masu idan har treatment d’in da ake masa yaci gaba da failing jikinsa ya kasa amsa then he must have to undergo Cardiac surgery wanda zaici mak’udan kud’ad’e ga had’arin dake tareda hakan. Hisham ya d’anyi gyaran murya cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali. Amma kaman cewa yai ta k’ara. Ringing d’in wayarsa yaja hankalinsa. Abokin aikinsa ne kuma amininsa Haidar me kira. Ba tareda ya bar wajen ba dan baisan barinta ita kad’ai farfajiyan asibitin suke yayinda Khulsum ke can wajensu mama sun hanata koda lek’a Abba ne. Daga d’aya b’angaren Sautin kuka ne yai Sallama ma Haidar. Ya d’anyi still kafin yace “Wait..What’s that noise.. Where exactly are you..?” Hisham ya dubeta sanda take k’ok’arin mak’ale kukan nata bayan taji alamun yana amsa waya “You seem to forget things easily nowadays Engr. Ka mance na tafi gida ne.” Haidar ya d’an d’aga gira yana mai jinjina kai “I hope dai lafiya ka samu gidan. I mean lafiya ka samu Hajja..?” Hisham yace “Yeah lafiya..” Ya k’arashe yana mai d’an jan kalamansa. Haidar ya kuma tambaya “So who’s making that noise.?” Ciki Zuciyar Hisham ke ayyana isa da jin kan Haidar. Wato bazai iya tanbayarsa wacece ke kuka next to him ba shine wai hayaniyar me yake ji. D’agowa yai Ya dubi Ummul wacce ke k’ok’arin tsagaita kukan nata. Ya d’an mik’e ya matsa gefe kad’an . Ya saki murmushi mai kyau yana mai d’an rage murya “Let’s call her Someone.. Someone Very special.. Ka gane I’ll call you back.” D’an tab’e yai “Let’s talk business.” Yace cikin katse Hisham d’in. Hisham ya d’an kuma satan kallanta sanda Haidar ke sanar dashi sunada ganawa ta musamman gobe a Kampani. Ya zama dole ya katse hutunsa. Hisham ya girgiza kai kad’an “Wait what meeting Haidar.?” “Tomorrow by 9:00am.. Design Architect Hisham.!” Abinda kawai Haidar yace kenan. Hisham ya soma girgiza kai cikin rashin yarda “You know I can’t make it to the meeting Haidar.. I mean I’m not the only design architect in your team...” Bai tsaya d’aukan excuse d’in Hisham ba ya katse kiran. Furzar da huci Hisham yai yana shafan fuskarsa da tafukan hannayensa. Jiki a matuk’ar sanyaye ya dawo yanda ya baro Ummul. Ta ya zai barta ya tafi a lokacinda take tsananin buk’atarsa. He needs to stay.. But what about aikinshi.. Baiso wani yai taking place d’insa. Sun jima suna aiki tuk’uru kan wann project din wanda yake da tabbacin idan ya zama a successful one ba darajan Kampaninsu kawai zai d’aga ba. Zai taimaka wajen daidaita relationship d’in Amininsa da mahaifinsa wanda a kullum yake burin faruwan hakan. Bayan haka Haidar is counting on him. Abokinsa needs him now. Amma kuma Ummul fah. Shin zai iya barinta ya tafi.? Shin waye zai kyale ciki su biyun. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *13* *©️Sameena Aleeyou… * Akan idon su Mama Hisham yai ma Ummul sallama ya rakota har wajen Khulsum. Saidai bai sanar da ita batun tafiyarsa ba. Mama da Azeema ko harma da Badi’a ko k’ifta idanu basuyi. Musamman da sukaga zankad’ed’en Saurayin dake tare da Ummul. Mama tace “Toooh shi kuma wann d’in wai waye.?” Badi’a tace “Wa ya sani masu ne Mama. Amma kaman saurayin Ummul..” Mama ta bige bakinta “A gidan uwar waye ya zama saurayin Ummul. Wann yafi k’arfin Ummul inaga dai yayi zaton mabaraciya ce ya taimaka mata musamman da yaga tana cikin damuwa.” Badi’a ta harari Mama yayinda Azeema ke hararar Khulsum tana cika. Lokaci guda ta katse Mama da fad’in “Saurayinta ne mana shine yayi belin wancan k’aramar ‘yariskar a police station bayan ta mareni.. Wllhi bazata saku ba. Ai na biya kud’in kwananta a cell amma bata kwana ba.. Toh wllhi komawa zanyi ayi duk rikicin da za’ayi. Ni da kaina na lale kud’ad’e na bawa Habibu ya biya ‘yansandan cewa su rufeta ta kwana. Wllhi komawa zanyi ko su biyani kudina ko su sanar dani dalilin bud’eta. Ai ko Kotu akaje akwai kud’in mari. Idan har ba biyana akayi ba wllhi rikicin nan bai k’are ba ehe. Ta k’arashe tana mik’ewa fuuu. Mama tai k’ok’arin dakatar da ita da fad’in “Ke ke.. Ke ina zaki Azeema..?” Ko juyowa batai ba Azeema balle ta amsa ta. Saima dialing layin Habib da tai tana k’arawa a kunne. Mama ta dubi Bad’ia bayan Azeema ta shige. Ta janyota suka keb’e “Yauwa Kinga d’aga waya ki kira Tasi’u yazo ayi maganar sayar da shagon Malam da d’an sauran abinda Ke ciki. Kinga naji d’azu likitocin nan suna bayanin aikin da za’ayi ma Malam mak’udan kud’ad’e zai lak’ume wanda ko gaba d’aya Kantin da kayan dake ciki aka sayar ba isa zasuyi ba. Kinga kafin Wann shago da abinda Ke ciki tsautsayin jinyar Malam ya hau kansu gwara mu dafe su tunda wuri dan bazai yuwu mu zuba d’an abinda zamu samu ma jinyar Malam ba wanda su kansu likitocin k’irdado suke amma ga dukkan alamu ciwon Malam ba na tashi bane. Bad’ia ta jinjina kai “Kuma ma Mama ai wanda suka fi cancanta su nemo kud’in jinyar Abba wanda sukai masa sanadin ciwon ne. Ina nufin wancan annobar da uwarta.” Tai nuni da yandasu Ummul Ke zaune. Mama ta jinjina kai “Alhamdulillahi ina jin dad’in yanda kike fahimta. Maza kirawo Tasi’un.” Tuni Badi’a ta d’aga wa ta shiga dialing layin Tasi’u mijinta. Khulsum ta dubi ‘yaruwarta Ummulkhairi cikeda tausayawa “Adda yau d’in fah duka baki saka komai cikinki ba. Dan Allah kiyi hak’uri ki tashi haka nan mu tafi gida yamma ta riga tayi.” Ummul naci gaba da hawaye ta girgiza mata kai “A’a Khulsum bazan iya tafiya gida ba. Watak’ila Umma zata zo nan wajen Abba..!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka. Muryar Mama suka sinkayo akansu “Au har yanzu Uwar taku bata bayyana ba. Ta tabbata dai Angulu ta koma gidanta na tsamiya.” Suka d’ago suna duban Mama da Badi’a tsaye kansu sai aika masu kallon wulak’anci suke. Ummul ta girgiza kai “Mama Umma b’acewa tai bamu san yanda take ba.” Sai Mama ta shiga tafe hannaye tana salallami “Na shiga uku ni Tani. Ta nan Suwaiba ta b’ullo..? Ta rasa abinda da zatai sai ta guji Malam sabida jinya ya kamasa ya zama kaya. Watau Suwaiba bazata iya jinyar Malam ba dai shine ta guje ta k’yaleni da wahalar jinya.. Yanzu da zataji labarin Malam ya cika dik yanda take zata fito tazo amsa sunar matarsa dan ta amshi rabonta na gado.” Sai sann Khulsum ta finciki hannunta daga rik’on da Ummul ke mata cikin k’ok’arin dakatar da ita. Sai huci take. Badi’a ce ta janyo hannun Mama hango mijinta Tasi’u da tayi sai buga sauri yake ya nufosu “Muje Mama kar ma kiyi hayaniya dasu balle a ba ma masu gadi hujjar koranmu. Ganin Abba ne sai a k’iyama idan sunada rabon had’uwa a k’iyamar. Khulsum ta kuma fincika zatabi bayansu Ummul ta kuma dakatar da ita. Cikin kuka Khulsum ke furta “Haba Adda Ummul. Haba ke kuwa.. Wai dan Allah meyasa kike dakatar dani.? Mutanen nan fah yaren da kawai suke fahimta kenan.” "Ummul ta jinjina kai tana kuma share hawayenta “Abinda suke so kenan Khulsum kiyita biyesu kuna tashin hankali. Ki tuna Abba dake kwance cikin asibitin nan. Ki tuna halinda yake ciki. Sann ki tuna Umma da halinda take ciki. Dan Allah ki daina biyewa Mama da yaranta. Allah ya fisu Khulsum. Mu fawwala masa komai da sannu zaiyi ikonsa akan kowa. Da sannu zai ba ma Abba lafiya ya tashi kafad’unsa kuma suna kallo. Muci gaba da yi masu add’uan shiriya har kullum domin su d’in ahalinmu ne komin lalacewarsu. Muje Khulsum, mu tafi gida mu kai kokenmu ga Rabbil izza wanda shike yaye dukkannin damuwa ya kuma kawo sauk’i da maslaha.” Tana ida fad’in haka taji natsuwa ya sauk’a cikin zuciyarta. Jiki a sanyaye suka fice daga asibitin." ** Tasi’u yau harda risinawa yake gaida Tani. A mutunce yau d’in ya fito masu dan batu ake na kud’i. "Mama kaw sai hura hanci take dan ba Wai ta masa afuwan musguna ma ‘yarta Badia yake bane. Yanzun ma dan Badi’an ta nace ne sai an sako Tasi’un cikin hidiman, ta tabbata amfani yayi da son da Badi’a Ke masa ya saye zuciyarta da kalamai har ta aminta dashi. Dan dai ita kam har yanzu bawai ta yarda da tubansa bane. Tasan tuban D’anmuzuru ne. So yake a bawa Badi’a kasonta su lak’ume tare da zaran kudi sun k’are yaci gaba da mata iya shege." Ta dubi mai sayen shagon da Tasi’u yazo dashi dan tinda Badi’a ta sanar dashi cikin waya ya taho da mai cinikinsa dan dama tuni ya tanadi mai saye tinda aka soma batun. Mama sai cika take tana batsewa tana ciniki da mai sayen shago. Tasi’u yana daga tsakiya a matsiyinsa na dillali sai gyaran waje yake. Mama ta narka masa harara ganin zak’ewarsa. “Amma dai Tasi’u ka tab’a dillanci ko..?” Cewar Mama tana dubansa a dak’ile. Tasi’u ya Washe baki “Yo Mama banda abinki meye ba’a tab’awa ai duk abinda aka samu bugawa ake baka san ta yanda wutan zai kawo ba.” Sai faman Washe baki. Ita kaw Hajiya Badi’a sai karkad’a k’afafu take tana Jin kanta. Daga yanzu ta samu makamin rik’e Tasi a hannunta. Tinda zata samu kud’i abinda yafi naira dubu d’ari aiko sai yanda tai da Tasi dole ta zama itace mijin itace mai basa doka da order. Tin yanzu ma biyayya yake mata balle ta dafe kud’ad’enta. Aka tsaida cinikin Kantin Abba. Mai saye yace gobe suzo da takardu a saka hannu.. Nan fah Mama ta soma zare idanu dan bata San yanda ya aje ba. Tasi’u yace wann ai ba abun tada hankali bane washe gari zaije yai sabbin takardu a gama komai. Yanda yake ladabi wa Mama da Badi’a kai ka ranste yaron gidansu ne ** "A can station Habibu mijin Azeema sun keb’e da sergeant d’in da suka tafi sukai arresting Khulsum dan dama budurwarsa ce, ta cika tayi fam sai hura hanci take “Ni fah ba matsala ta bace dan an mari matarka. Yo a kasheta ma mana ai banida asara. Ni wllhi ba don ka min alk’awarin aure ba wllhi kaji na ranste da bazanje nai arresting kowa" ba. Kuma kafi kowa sanin sabida kai nai. Toh ya Oga na zai yanke hukunci tazo nan tana kawo mana hauka. Ce mata akayi nan tasha ne. Ko ka d’auki matarka ka tafi ko a banza na jefata cikin cell a lakad’a mata duka dan bazan bari ta mun sanadin aikina ba. We are talking about my superiors here. Ita har ta isa tazo nan tana mana zage zage da hauka. Tasan me ake kira hukuma ma kuwa. Na ranste maka Habib idan bakai controlling d’inta ba zata gane ita k’aramar mahaukaciya ce dan yanzu zata tabbata mahaukaciyar da Dawanau ma ya kasa mata.” Ta k’arashe tana jijjiga sai sakin huci take tana tsuma tana kad’a kulkin cikin hannunta. Ya murmusa yana shafa hab’a lokaci guda yana lek’en bayansa kar Azeema ta k’araso wajen. Ya sassauta murya “Haba kurtuwata. Kema kinsan duk duniya babu macen da nake so sama dake.. Da kikaga ina biyeta amfani zata min. Yo banda abinki ni kaina sau nawa ina lakad’a mata d’anbanzan duka kuma duk akanki toh dan an mare Azeema har wani damuwa zanyi. Wllhi yanda kika san an mari wofi haka naji..” Ya kuma shafa fuskarsa yana lek’en bayansa irin yanda marassa gaskiya keyi kafin ya matso da fuskar nasa saitin fuskan ‘yarsandar “Kinga ita Azeema Ubanta na asibiti rai hannun Allah. Ta tabbatar mun mutuwa zai. Kuma da zaran ya Mutu aka raba masu d’an abinda zasu samu zan amshe komai nata. Tana mallaka min zan koreta da kud’in gadon Uban nata zan aureki Kurtuwata.” Ya k’arashe yana wani washe baki yana wani kashe mata idanu “Toh d’an yi mun murmushi mana na gani sahibata.. Inye kaga Kurtuwa Amaryar Habibi..” Ya k’arashe kaman zai rungumota. Yatsine fuska ta d’anyi had’ida turasa baya “Easy mana Alaji wajen aiki na muke.. Shikenan tinda haka kace.. Amma wllhi idan Kai ga gangancin kawo mun bariki wllhi babu abinda zai hanani cin uwarku daga Kai har matar taka kasan sharri na karanta a banza zan maida police station gidan hutun matarka.” Saurin toshe mata baki yai yana “Wllhi bama ta sanki ba har yanzu. Bata san wace budurwar tawa ba.. Kwantar da hankalinki kafin ma ta sanki ta tsufa gidan marigayin mahaifinta. amma sai na tabbata na amshe d’an abinda uban nata zai bari mata..” Ta kuma yatsina fuska kafin ta tura k’ofar ta fito tana karkad’a sandan dake hannunta sai faman d’age hanci sama take. Azeema ta bita da kallo dan haka kurum hankalinta bai kwanta da ‘yarsandar ba musamman da ta hango Habibu ya fito daga bayanta yana fad’in “Nifa Rankidade Sam bazan yarda ba wllhi sai an shiga kotu an k’watarwa matata hakkinta..!” Azeema ta k’araso gareshi ta shige jikin mijinta tana fad’in wllhi a tafi kotu kawai. Sai ya fara kokarin kwantar ma Azeema hankali da fad’in idan yana a matsayin mijinta sai an tafi Kotu. Sergeant d’in kuwa banda watsa ma Azeema wani wulak’antaccen kallo bata komai. Da kyar Habibu ya shawo kan Azeema ta amince suka bar police station d’in da sharad’in case din bai k’are nan ba. Sai aika ma ‘yarsandar mugun kallo take dan ta kula da wani kallan k’asa k’asa da Habibu ke binta dashi. ** A can b’angaren su Umma kaw d’aki maiji da lafiya aka sauk’eta. Umma ta zauna saman gado tana lotsawa tana jin taushin latifa ga sanyin AC na bugata. Ai sai Umma ta yab’e baki tace “Kai kaji taushi kaman ina saman gajimare. Tirk’ashi. Lallai masu kud’i suna sha’aninsu.” Asshe dake lab’e daga k’ofa tana karantar duk wani motsin Umma waya manne kunnenta wanda ko shakka babu da Mommy take wayan. Sauk’owa k’asa tai dan upstairs aka sauk’i Umma. Ta zauna nan parlorn k’asa tv na aikinsa waya manne kunnenta “Aunty Kwaise bakida wata matsala fah. Ni na fad’a miki na kuma yarda da aikin wann Malamin dan kaman tafiya muke da solution d’in matsalar mu. Matar nan dai da muka bige” Ta d’anyi Shiru alamun tana sauraro daga b’angaren Mommy. Sai taci gaba “A’a Haba Aunty Kwaise nasan fah abinda nake. Ai tuni nasa Yunusa yaro na ya binciko mun komai kanta. Duk wani abinda Ke wakana tsakanin ahalinta. Yazo gidan sauki tinda nan cikin Kano ne. Ai bazai yuwu mu d’ibo ko wace iri mu jajib’a ma Haidar ba koda kuwa Auren na wata UKU ne kawai. Yanzu zuwa gobe idan Allah ya kaimu zakiji duk bayanan da Yunusa zai kawo mun dalla dalla duk yanda akai. Idan ta kama a miki scanning information d’in ne a tura miki ta mail duk za’ayi Aunty Kwaise. Haba abu ne za’ayisa cikin wayewar kai. A yanda na fahimta bakin aljihu ne kawai zai bayani wann kuma nasan ba matsala bane.” Ta d’an dara tana kuma kod’a Mommy da mata kirari irin na matan Manya. A haka sukaci gaba da tattaunawar tasu. Bayan sun ida waya Asshe ta mik’e ta lek’a Suwaiba. Nan ta tadda Umma tuni ta baje saman gado bacci yayi awon gaba da ita harda su minshari. ** "Hisham yai Shiru yana sauraron mahaifiyarsa. Sai kuma ya girgiza kai kad’an “Hajja ba yanda na iya ne. Tafiyar ce ta taso mun babu shiri.” Ya d’an matso kusanta had’ida kamo hannayenta cikin nasa “Na bar amanan Ummul hannunki Hajja. Dama tare na ganku nai maku karambani ko nace zuciyata tai karambani…” Sai ya d’anyi fasali “I will come back for her Hajja.. Zan dawo, dawowa na musamman domin Ummulkhair.. Please kici gaba da kula da al’amranta har na dawo. Bazan d’auki lokaci ba wann karan in sha Allah.. Kinji Hajjata.” Ya k’arashe cikeda rauni." Dubansa ta d’anyi duka duka yaushe yazo har zai tafi. Ita kam ta fara gajiya da wann aikin nasa. A hankali ta jinina Kai “Shikenan. Allah yaci gaba da tsareka yayi maka albarka. Bazan dakatar dakai ba koda ina son yin hakan. Ummul kuma ka barta cikin aminci da yardar Ubangiji. Fatana Allah yasa kar ka d’auki lokaci mai tsawo.” Hisham ya murmusa cikeda jin dad’i yana jin zuciyarta at ease. Fitan sassafe zai wanda ba lallai ya samu ya kuma ganinta ba balle suyi sallama. Amma yayi alk’awarin da zaran ya isa zai kira Hajja ta had’asu a waya. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!”* *14* *©️Sameena Aleeyou… * Mommy ta kuma duban Daddy Wanda fitowarsa kenan cikin shirin fita Squash game. Hannunsa rik’e da jakan kayan motsa jikinsa d’aya hannun Racket ne na buga wasan. Sunada private court d’insu da suke bugawa da abokansu. "Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya a hankali “Engr, kan maganar namu..? Nasan idan har na bari sai ka dawo ce min zakai ka gaji.” Ta k’arashe da d’an shagwab’a cikeda kissa." Tab’e baki yai kad’an had’ida girgiza kai “Kwaise I thought mun gama magana. Kinga wann D’an naki na cire hannuna cikin rayuwarsa. So yayi aure ko kar yayi aure is non of my business. The only thing I care about is my company tareda ci gabanta.. “ Har ya d’an soma tafiya ya juyo “My tea should be ready kafin na dawo.. Please.” Ya k’arashe yana mai ficewa. Mommy ta furzar da huci tana girgiza kai “A’a Kwaise bazaki karaya ba. You need to do this.. You must.. Ya zama miki dole. Ta k’arashe tana neman layin Asshe. Shi kuwa Daddy zaune suke a court d’insu shida Alhaji Gimba suna hutawa daga motsa jikin da sukai. "Alhaji Gimba Ya d’an girgiza kai kad’an “Engr Ya kamata kaji maganar iyalinka.. Nima na jima da wann tunanin, inaga Aure shi ya kamata a masa.. Shi zaisa ya tara hankalinsa waje d’aya. Kasan meye idan bazaka iya zuwa ka nemar masa Aure ko ka karb’ar masa ba. I can represent you then. Zaka iya wakiltani nai komai ma Haidar. After all, nima uba ne a gare shi.”" "Daddy ya d’an dubesa, baice komai ba saima k’ok’arin bud’e bottle water dake cikin hannuna da yake." ** Washe gari Umma ta karya da karin kumallo mai kyau. Ga kaya na alfarma da Asshe ta aiko mai aiki ta kawo mata. Tai wanka ta cancand’e cikin atampar da bata tab’a mafarkin saka irinta ba. Ta dubi kanta jikin madubi tana mamaki. Ta mik’e ta shiga zaga d’akin ta yaye lalube tana kallon kyaun gidan da aka sauk’eta. A haka Asshe ta shigo ta taddata. Ta saki murmushi tana dubanta “Maman Ummul har kin shirya abinki… Na aiko Marka ta tambaya ko akwai abinda kike so..” Tai maganar tana shigowa d’akin. Umma ta girgiza kai tana washe baki “A’a babu abinda nake buk’ata.. Kin ganni na d’age labule kallon Aljannan duniya nake. Ire iren gidajen nan saidai kaita hangosu daga kwalta ashe Inada rabon bacci cikinsu.” Asshe ta murmusa tana jinjina lamarin Umma “Ai wann gidan ba komai bane gaban gidan ‘yaruwata Hajiya Kwaise dake birnin tarayya. Wann saidai a kirasa da gidan sauk’an bak’insu ko ma nace miki na ma’aikatansu.” Umma ta zaro ido waje “Gida kaman wann za’a kira gidan Ma’aikata..?” Asshe ta kuma murmusawa “K’warai kuwa.. Kinga kalli nan..” Tai mata nuni da fuskar wayarta. Umma tai k’uri tana duban hoton matar da Asshe Ke nuna mata wacce tai mata lak’abi da Matar manya cikin zuciyarta. Asshe tace “Da wa ta miki kama.?” Kafin Asshe ta rufe baki Umma tace “Da Matar marigayi tsohon shugaban k’asa Maryam Abacha.” Asshe ta jinjina kai tace “Toh wann sunanta Hajiya Kwaise Maitama. ‘Yaruwata ta ce da muka fito ciki guda. Ke da ganinta ba sai ance miki Matar manya bace.” Umma ta jinina Kai “K’warai kuwa babu shakka.” Asshe ta jinjina kai tana mai kuma gyara zama “Kaman yanda na fad’a miki Aure take so d’anta yayi kuma ta bani wuk’a da nama na zab’ar masa Matar kirki a nan gida Kano dan bata son ya auri matan dake rubibinsa a bariki wanda akasarinsu girman Turai ne. Ni kuma a yanda kika bani labarinki na tausaya miki. Dake da ‘yarki kuna cikin yanayi na k’unci da damuwa. Watak’ila Allah ne ya dubi halinda kuke ciki. Da duk abubuwan da kuke fuskanta kama daga kan kishiryarki har izuwa jama’an unguwa. Ya share miki kukanki. Zanso ‘yarki tayi Aure na gani a fad’a.. Auren da za’a bigi k’irji a kirasa Aure. Auren da duk masu jifanku da munanan kalamai sai sunyi d’an da na sani. Domin kuwa Ummulkhairinki ta amsa sunanta Uwar Alkhairi.. Ta kawo miki alheri da ma danginku gaba d’aya. Dan nayi imani katafarin illahirin danginku Ke harma da jama’an layinku babu budurwar da tayi irin Auren da Ummul zatayi. Babu wacce tai dacen miji irin na Ummul d’inki. Yaro d’an gata d’a d’aya tilo ga Attajirin d’an kasuwan da kasuwancinsa ya zaga gida Nigeria da ma k’asashen k’etare.” Ta kuma gyara zama “Ke Maman Ummul duk yanda zan miki bayanin dacen da ‘yarki tayi bazaki fahimta ba. Ke kanki guje gujen rab’arki za’a fara yi ba ma Ummul da ake gudunta ba. Domin kuwa kin zama sirkar Manyan mutane. Mutanen da ake haskosu a manyan mujallu da talabijin. JINKIRIN Ummul d’inki ya zame maku alheri. Ke fah Maman Ummul wllhi Kakarki ta yanke sak’a.” Ta d’an numfasa “Amma fah ni taimako nai niyyan yi sann tun had’uwa na farko naji na yarda dake na aminta dake. Bugu da k’ari labarinki da kika bani ya tab’a min zuciya dole duk mai imani ya tausaya miki daga Ke har ‘yarki. Kuma yanda Ummul d’inki ta juri kyara da tsangwama baisa ta lalace ba ko ta bijire ma iyayenta na kuma aminta ta cika yarinyar kirki wacce kowa zaiso ta zama Matar d’ansa. Amma idan kinaga kunada wani zab’i ko ita Ummul d’in tanada wani bazan tak’ura ki ba sai na nemasa wata dukda na masa sha’awar Ummul.” Ai kafin Asshe ta rufe baki Umma tai tsalle ta toshe mata baki “A’a haba Hajja Asshe.. Har wani zab’i Ummul kedashi.. Ina laifin wanda yaso taimakon ka ya tasamma rufa maka asiri. Ni damuwana Allah yasa ‘Yaruwar taki da d’anta su amince idan sukaga hoton ita Ummul d’in. "Asshe tai murmushin cin nasara. Lallai wann matar ta tabbata shashasha yanzu take kuma gasgata duk bayanan da Yunusa ya kawo mata akanta da ‘yarta. Wann ko ta fad’a mata mak’asudin auren ba damuwa zatayi ba. Ta murmusa a fili kafin tace “Karki damu ‘yaruwata batada matsala ita burinta kawai D’anta ya samu mata ta gari ba wad’ancan ‘yanmatan dake sonsa dan kwad’ayin abin hannun iyayensa ba. Shima D’an nata yaron kirki ne mai biyayya mai bin umarnin iyayensa. Na miki alk’awari baza’a sami matsala daga b’angarenmu ba. Amma saidai kinsan ance Aure d’an bincike ne, yanar gizo kawai zaki d’ale ya tantance Miki komai. Kinsan su manyan mutane a yanar gizo ake bikcikosu.” Ta k’arashe tana kuma dulmiyar da Umma." Umma ta shiga girgiza kai “Wllhi ni na yarda dake d’ari bisa d’ari na aminta dake sabida a zamanin nan samun mutanen kirki irinku yayi k’aranci.. Da ace Ke mai cutarwa ce tin a lokacin da kuka bigeni da mota da kunyi tafiyarku Kun barni wajen. Bakiyi haka ba kika d’aukeni kika kaini asibiti kikayi d’awainiyata kika kuma kawoni gidanki. Idan ba kin aminta dani ba na tabbata bazakiyi haka ba.” "Asshe ta murmusa “Alhamdulillah, na d’auki haka matsayin yarda da amincewarki. Yanzu ki sake kwana ki sake samun sauk’i da hutu. Mu kuma ci gaba da tsara abubuwa da yanda zasu kasance.”" Umma ta katseta “Ko dan sabida idon masu ido da hassadan masu hassada” Asshe ta jinina Kai “Kinga zuwa gobe ko jibi idan na tuntub’i ‘Yaruwar tawa aka samu matsaya sai muje asibiti a biya duk wasu kud’ad’en jinyar mijinki. Sai ki kaini kuma naga surkata Ummulkhairi. Cikin satin nan da yardar Allah magabata zasu taho daga can Abuja sai ayi maganar tsaida ranar Aure. Nafi so ayi komai a gaggauce kafin masu mugun ido su kuma jifan al’amarin da idonsu.” Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma tace “Tooh amma Hajja Asshe wani hanzari ba gudu ba. Kinga shi mahaifin Ummul yana kwance asibiti baisan yanda kana yake ba. Anya baza’a jira ya farka daga wann jinyar nashi ba.” A dak’ile Asshe take dubanta kafin tace “Haba Maman Ummul ya kike magana haka saikace ba k’arni na ashirin da d’aya muke ba. Na Miki ta bakin bature yace 21st century. Shin ita Ummul batada dangin mahaifi ne da zasu iya bada aurenta. Yaushe za’a tsaya jiran tashin mahaifinta dake tsananin jinya. Waye yasan yaushe Allah zai tada shi. Yarinya ta samu miji shikenan sai ace sabida mahaifinta ba lafiya bazatayi aure ba. A ina ake haka. Yanzu fah mazan wahala suke Shiyasa da zaran an samu gwara a kauda. Baki ganin akasarin Auren da ake yanzu daga zuwa tambaya ba bakin kowa sai kiji an d’aura ai duk sabida gudun masu neman jifanka da sharri ne balle wani abu ya gifta a fasa auren. Kinga ‘Yaruwata yanzu take so D’anta yai aure dan a cewarta yaro da kudi hannunsa ba mata had’ari ne. Kinga bazai yuwu mu tsaya jiran mahaifin ‘yarki dake jinya Ya samu lafiya ba kafin ayi auren. Kinga bazamu bari namu yaron ya lalace ba. Kawai idan wann aure bazai yuwu ba..” Saurin mik’ewa Umma tai ta daka tsalle ta tumu gaba Asshe. Ta d’ago hannaye biyu “Ki rufa min asiri kar ki k’arasa maganarki. In sha Allahu fashin auren Ummul ya k’are. An daina k’irga mata fashe fashen aure. Za’ayi aure da zaran magabata sunzo. Ayi tambaya take a d’aure tun kafin mak’iya suji labari.” Sai kuma ta fashe da kuka wiwiwi babu k’akk’autawa. Asshe ta dafata kad’an “Lafiya Maman Ummul Ya da kuka kuma keda zakiyi farin ciki burinki zai cika Ummul d’inki zatakai ga d’akin miji.” Umma ta d’ago tana murmushi ga hawaye na bin k’uncinta “Kukan farin ciki nake Hajja Asshe. Burina zai cika Ummul d’ita zatayi Aure. Zata bar gidan mahaifinta. Zan daina kwana kullum ina tashi na ganta gabana.. Wayyo ni Suwaiba Ashe wann rana zaizo..?” Taci gaba da rera kuka. Asshe ta zuba ma sarautar Allah ido ganin yanda Umma ke sunbatu tana fad’in Yaya Tani zakici goron Auren Ummul. ** A b’angaren su Mama kuwa Tasi’u yazo da wasu takardu yanda ya gabatar masu matsayin sabbin takardun shagon Abba. Harda sabbin makullai. Kai da ganinsa kaga maras gaskiya. Ya dubi Mama da Badi’a a yanda suka keb’e daga can k’asar wani bishiya wajen asibtin. “Yauwa nace mu had’u a nan sabida ‘yan sa ido. Mai saye zai iso yanzu da kud’ad’ensa naira dubu d’ari uku kaman yanda muka tsaida magana. Badi’a tace “Haba Tasi dubu d’ari uku saikace na sata.?” Tasi’u yace banda abinki abu ne ake a sirrance kuma ko ina kikaje kayan magada karyawa ake. Ku gode ma Allah ma da muka samu mai saye dan na tabbata shima rahusa yaji shiyasa bai tsnanta bincike ba amma da zaran yasan Mai shagon na numfashi bai cika ba kinsan bazai sayi gaibu ba. Ni fah taimako nake a nan.” Mama tace “Kyaleta me ta sani wann. Ni fah da kike gani so nake ayi komai a gaggauce kafin Suwaiba ta bayyana. Dan na ranste kwandala bazasu samu ba daga ita har yaran nata.” Tasi’u yace “Ah toh magana kenan.. Yauwa gashi can ya k’araso.” Yai masu nuni da mai sayen shagon Wanda Tasi’un bai jima da masa kwatance yanda zai samesu cikin waya ba. "Yana k’arasowa Tasi’u ya warware takarda “Wann takardan yarjejeniyar mallakar fili ne..” Ya saka yatsa a baki ya dangwali halshensa kafin ya d’aga d’aya takardan “Wann kuma takardun fili ne Wanda local government ta saka hannu akai, ga saka hannun sarkin Kasuwa. Kunsan ko wace kasuwa tana k’ark’ashin local government d’in da take ne.”" Ya dubi Mama “Yauwa Mama nan wajen shine wajen saka hannun magada watau masu sayarwa kenan. Nan kuma wajen saka hannun mai saye ne. Nan kuma wajen saka hannun shaidu.” Badi’a ta katsesa “Amma shi mai sayen baizo da shaidu ba.” Tasi’u ya Washe baki “Wani aiki sai Badidi ta. Banda abinki meye amfani na. Ai duk dai a rubuce ne kawai ake abin ni duk zan iya saka hannu na zame maku shaidu.. Eh ai duk abun a rubutu ne kawai.” Ya dubi mai saye yace “Mutumi na ai sai ka saka hannu ko..” Mutumi Ya amshi takarda Ya saka hannu. Tasi’u Ya kuma Washe baki yace “Ai shikenan ka mallaki shago a garin Kano.. Burinka Ya cika.. Allah yasa ma kasuwa Albarka.” Sai Washe baki yake dan dama mutumin k’auye ne irin Wanda ko cirani basa fita cikin kauye suke kasuwancinsu burinsa Ya mallaki nasa shagon cikin garin Kano nan yai gamo da Tasi’u. Tasi’u ya dubi su Mama “Yauwa Mama ga wajen da zaki saka hannu.” Mama ta dubesa a dak’ile “Banida hankali ne zan saka hannu banga kud’ad’e ba.” Tasi’u yace “Banda abinki Mama Tani waye yake yawo da kudade masu yawa irin haka. Ai sai b’arayi su bi mu. Haba shi fah kud’i d’an sirri ne.” Mutumin Kauyen yace “Wann gaskiya ne. Daga nan zamuje tareda shi surkin naki Ya amsa kud’in.” Tasi’u yace “Ahtoh tare zamu tafi takardu suna hannuna bani damk’a masa takardun Har sai ya dank’a min kud’ad’en. Ko nima baki yarda dani bane. Na tabbata da baki yarda dani ba da baki bani ‘yarki Badi’a ba.” Mama ta jinina kai “Shikenan..” Ta dubi Badi’atu tace ta nuna mata yanda zata saka hannun. Tasi’u kaman zai kamo hannayenta yake nuna mata. Yace Badi’a ma ta saka duk suka saka. Tasi’u yace su koma asibiti wajen Abba shi zai k’arisa ji da komai. Zuciyar Mama ba wai ya kwanta ba suka nufi cikin asibiti. Sam rawar k’afan da Tasi’u yake ba wai ta yarda dashi bane. Sai ta soma tunanin anya batayi gangancin barin Tasi’u su tafi su biyu da mutumin amsar kud’ad’en ba. Koda yake ya Santa ya san halinta ita ba Badi’a bace tsaf kwabo yai ciwon kai sai ta tatse. Da wann tunanin suka shige cikin asibiti. (Rayuwar Duniya kenan. A wann babi munji yanda Matan Abba Wanda ke kwance gadon asibiti sukai cinikin dukiyarsa da kuma ‘yarsa. Mama dai tayi cinikin dukiyarsa yayinda Umma tayi cinikin ‘yarsa. Fad’in Manzon Allah S.A.W cikin hadisin Abdullahi ibn Amr . ‘Duniya jin dad’i ne kuma mafi alkhairin jin dad’inta shine samun mace ta gari.’ Sahih Muslim 1467. Tabbas babban rahama ne Allah ya baka Matar kirki wacce zata tsare maka mutuncin kanta iyalanka da kuma dukiyarka Wanda suke amana a hannunta. Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu. Ameen). SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *15* *©️Sameena Aleeyou… * Mama dai ta gaza zaune ta gaza tsaye tin bayan tafiyar Tasi’u da mai sayen shagon Abba. Ta dubi Badi’a dake shafen shafen waya tace “Ke kira min Tasu’u shirun nan nashi yayi yawa.. Karb’an kud’i saikace karb’an bashi.. Maza kirasa naji ina ya makara ne wai.” Badi’a ta d’an girgiza kai “Haba Mama ko fah awa d’aya baiyi da tafiya amma kin d’aga hankali a kirasa. Nasan halin Tasi barsa da shaye shayensa amma banda sata.” Zuciyar Mama yai wani irin bugawa. Ta dubi Badi’a a zabure tace “Badi’atu ina hankali na da tunani suka tafi Har na mance Tasu’u Ya tab’a shaye shaye.. Yo ina ake dank’a amanan kud’i hannun d’an wiwi Bad’ia..!” “Mama mijin nawa ne d’an wiwi..? Ya tuba fah.” “Idan ba d’an wiwi ba d’an uwarki ne..!” Mama tace tana danna mata dak’uwa.. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina “Na shiga uku.. Na kashe kaina ni Tani. Wani b’atan basira ne ya d’ebeni na dank’a amanan dukiyar nan hannun Tasu’u.” Badi’a tai tsaki “Yo tsaban kina sauri mana a kauda shago kar ya shiga jinyar Abba ko Umman su Ummul ta dawo amsan hakkinta da na yaranta..” Mama taci gaba da safa da Marwa “A’a Tasu’u bazai tab’a min wann gangancin ba. Wllhi akan kud’in nan sai na cajesa daga hula har takalmi ba abinda ya shalleni ehe. Bayani d’aya na sani na kud’ad’ena..” Ta kuma duban Badi’a “Ki sake kiransa nace.. Ungo kirasa da nawa wayan..!” Badi’a taja dogon tsaki tana mitan Mama ta isheta. Wasu nurses suka fito suka tambayan iyalan Malam Isubu. Mama ko takansu batabi ba ita dai damuwarta kud’inta. D’aya nurse d’in da ya ganesu Ya k’araso yana fad’in “Hajiya ashe kuna nan. Muna can munata nemanku a ward.” Mama wacce gaba d’aya take a daburce ta dubesa a harzik’e tace “Toh gashi ka ganmu ai me akayi..?” Nurse d’in ya d’an tab’e baki ganin yanda ta hayayyak’osa “Dama wasu magani da drip za’a saya shine akace a sanar daku..” Bai kai aya ba Mama ta katsesa “Da uwar me za’a sayi maganin inyi.. Kai kaga mun maka kalan masu bada kud’i.? kuje ku masa abinda zaku iya mu nan bamu maganin k’wandala ehe..!” Ta dawo kan Badi’a tana fad’in ko batir d’in wayar mutuwa zai kar ta fasa kiran Tasu’u. Nurse d’in Ya kuma bud’e murya yace “Ku fah muke jira Dr zai iya shigowa round..” “Kai bana son fi’ili wai bakaga tashin hankalin da muke ciki bane?” Nurse yace “Wann matsalar ku bari idan Kun bar nan sai ku warwareta dan Allah. Yanzu dai ku sayi abinda aka ce ku saya dan a samu a ceci rayuwar majinyacin.” Muryar Badi’a yaja hankalin Mama alamun ta samu Tasi a waya. Badi’a ta juyo tana duban Mama da murmushi saman fuskarta “Ki kwantar da hankalinki Mama barin saka miki shi a speaker kiji.” Daga d’aya b’angaren Tasi’u Wanda daga jin yanda yake kana iya sauraran k’aran ababen hawa alamun yana bisa kwalta kenan. Fad’i yake cikin d’aga murya irin na Wanda ke bisa abin hawa musamman babur “Mama ina bisa hanya ne shiyasa bani iya d’aga kiran. Gasu na karb’o su.. Go slow ne ya tare mu kinsan ana fashe fashe sabida k’ara manyan titi.. Eh gani na ma kusa k’arasowa kenan.” Mama saida ta silale ta zauna dirshan a k’asa tana dafe k’irji “Yauwa yanzu naji batu” Ta marairaice murya tunanin yanzu kud’inta na hannun Tasi’u dole ta bisa a sannu kafin ta dafesu “Ayya ayya Tasu’u na.. Sannu da k’ok’ari kaji d’an albarka.. Muna nan muna jiranka.. Allah iso da kai lafiya.” Nurse da ya zuba ma sarautar Allah ido ganin Ya zo masu da muhimmin batu amma hankulansu na kan wani abu daban yace “Amma Hajiya kun saurari abinda na fad’a kuwa.?” “Mun saurara mana. Meye.? Ko so kake mu maimaita maka ka tabbatar mu ba kurame bane.” Ya d’an girgiza kai “Hajiya gaskiya ina ganin girmanki kuma ni aikina nake k’ok’arin yi a nan. Ya kamata ki dinga tantance kalamanki.” Mama ta tab’e baki dan a halin yanzu hankalinta ya kwanta taji labarin kud’ad’enta “Kaga k’aramin likita wllhi fah saidai ku k’yalesa mai aukuwa Ya auku dan nan da kake gani bamuda abinda zamu bada.” Nurse d’in yace “Ban gane mai aukuwa Ya auku ba. Ya kukeso ayi yanzu.? Kunsan cewa kud’in kwanakin da aka biya masa ma sun kusa cika. Kwanan nan za’a buk’aci k’arin kud’i musamman duba da irin jinyar da majinyacin ke fama dashi. Jinya ne babba kuma mai cin kud’i..” Mama ta dubesa galala “Au dama ba gwamnati bane Ke biyan kud’in jinyar nasa.?” Dan ita a nata zaton alfarmar gwamnati Abba ke ci tinda dai tasan tin zuwansu kwabo ba’a amsa wajensu ba. "Nurse ya girgiza kai cikin rashin yarda gajeriyar dariya na neman kufce masa “Mama kenan, a K’asar mu ta gado kike fah ko kin mance ne na tuna miki. Nothing is free in this country.”" Mama ta tab’e baki “Kai kasan me kace. Ni dai na fad’a maka gaskiya bamu maganin fici ehe.” Nurse yace “Amma ina wann mutumin da yai settling bills d’inku yake.. Ina nufin ina mutumin da ya biya kud’ad’en..?” Mama ta dubesa da mamaki “Wane mutumi kenan..?” “Wanda na ganshi nan ya rako wasu ‘yanmata biyu.. Ina tsammanin ‘ya’yan majinyacin ne..” Mama tace “Toooh..” K’irjinta na bugawa “Kar dai ace wai su Ummul kake nufi. Uban wa ya biya kud’in toh..?” Badi’a ta katseta “Wann mutumin mana da suke tare wanda har Azeema tace Miki saurayin Ummul ne kuma shine yaje yayi belin Khulsumu a police station. Ta tabbata dai saurayin Ummul ne.” Mama ta dafe k’irji cikeda mamaki. idan har Wanda aka ambata da saurayin Ummul ya biya tulin kud’ad’en nan watau mai kud’i kenan wann karon Ummul ta samo. Toh wllhi bazata saku ba wai bindiga a ruwa. Yanda sauran batun auren suka lalace shima wann haka zai lalace yabi iska. Bari ta gama da batun kud’ad’enta ta tabbata sun shiga lalitarta. Ya zama dole ta bincika tasan waye shi daga ina yazo dan tasan yanda zata b’ullo ma al’amarin amma bazata zuba ido Ummul ta k’are a gidan maik’o ba dukda wann canfi da aka mata. Nurse yace “Ku nake sauraro.” Mama tace “Yo ina kaw zaku gansa. Dama yaran karuwai ne yaje yayi abinda zaiyi dasu ne shine ya biya ladan jinyar ubansu. Sai ku jira su zo su baku dan nasan yanda Uwarsu ta tafi nata yawon suma ba zama zasuyi ba qila sun had’e a bayan gari. Ku jira Zasu zo so su kuma biyanku wasu kud’ad’en. Idan Har kuma basu samu ba sai Malam ya jira har ta Allah ta cimmasa. Idan kuma lokacinsa baiyi ba har wa’adin kwanciyar sa saman gadon asibitin ya cika sai a maidasa can gida saman katifarsa ya cika a can.” Badi’a tace “Ahtoh magana kenan..” Mamaki ya cika nurse d’in. Wai dama a duniya akwai mutane irin haka. Shikam yasha cin karo da mutane daban daban a aikinsa na asibiti amma bai tab’a cin karo da mutane irin wad’ann ba. Girgiza kai kurum yai yasa kai ya shige zuciyarsa fal tausayin Malam Isubu. ** Abuja. A fusace Daddy Ke dubanta “Wai meyasa kike son b’ata mun rai ne Kwaise. How many times do I have to tell you this.. Duk abinda ya danganci wann D’an naki bai shafeni ba..” Mommy ta soma girgiza kai “Why.? Meyasa..? Aliyu D’anka ne Engr.. He’s your flesh and blood.. Meyasa kake masa irin wann k’iyayyar haka..? Su waye suka shiga tsakaninka dashi har haka..?!” Cikin tsawatarwa Daddy ya katseta “Har sai kin tambaya waye ya shiga tsakani na dashi Kwaise.. Meyasa a kullum kike son tuna mun baya.! Kinfi kowa sanin wann D’an naki only reminds me of my sin. He reminds me nothing but my past Kwaise. Kuskure mafi muni da na tafka a baya… All because of you and your selfishness..!” Mommy na hawaye take girgiza kai ganin hannun mijin nata Har na rawa yake nunata. Cikin kuka take furta “Ni ce na maka laifi ba Haidar ba. Amma ka daina hukunta Haidar kan laifin da baida masaniya akai..” Muryarta yaci gaba da rawa “Haidar Ya taso cikin k’unci da tsangwama. A baya Nayi zaton izuwa wann lokacin zaka k’aunace sa kuma ka mance komai sann ka zama mahaifi a gareshi kaman yanda ko wani uba yake. He’s your only son our only son…” Katse ta yai ta hanyar d’aga mata hannu “This family can never be like a normal family Kwaise.. Kinfi kowa sanin haka. Farin ciki bazai tab’a wanzuwa cikin wann ahalin ba..” Cikin rawar murya tace “Nayi zaton ka yafe mun.?” Ya jinjina mata kai “Na yafe miki amma idan Har zanga d’anki sai na tuna Kwaise!” Mommy ta girgiza kai hawaye na kuma zubo mata. Tabbas an shiga tsakanin D’anta da mahaifinsa. Dan idan ba aikin asiri ba ba yanda za’ayi Ya d’auki laifinta Ya d’aura kan d’anta Wanda baida masaniyar laifin har yai masa irin wann k’iyayyar. Ta kuma share hawayenta “Meyasa kake zaune damu ni da Haidar.. To build your image a duniyar kasuwancinka.?” Taci gaba da huci “Fine.. Mun cika maka wann burin.. Kanada iyali da duniya zata d’aga ido ta kalla ta kirasu da ahalinka. Amma babu komai cikin ahalin face k’arya da k’unci.. Nothing is real here..!” “Kwaise.!!!” Ya ambaci sunanta cikin d’aga murya. Mommy na hawaye taci gaba “Eh kasuwancinka shine kawai gaskiyarka.. But your family..” “You are right… I only care about my business because it’s the only thing that keeps me moving bayan tarwatsani da kikayi years back..!” Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata. Sai kuma ta sassauta murya “I endured everything.. I even lost my own son without even realizing it. Thinking maybe wataran zaka k’aunacesa.. But than… I failed..! I failed as a mother and I failed as a wife..!” Kuka yaci k’arfinta sanda ta duk’a k’asa tana mai isarta. Ta d’an d’auki lokaci a haka kafin taji hannun Daddy saman kafad’unta. A hankali ya d’agota. Kaman wacce akace ta k’ara kuka. Ya d’an shafi fuskarsa ganin yanda take kuka sosai tana fad’in ta gaza ta ko wani b’angare. Ta gaza protecting ahalin. Rungumeta yai ta b’angaren jikinsa kad’an yana fad’in Ya isa ta daina kuka. A haka yai masu masauk’i suka zauna saman kujera. Saida suka d’ibi lokaci a haka kafin ta soma fad’in “Bazan tilasta maka ka so Haidar ba. But please just this once.. Alfarma nake nema.. Be a father to him..” Ya d’an dubeta sai kuma ya kauda kansa kad’an “Ban tab’a cewa ni ba mahaifinsa bane Kwaise. D’anki shi ya zab’i ya cire kansa daga cikin ahalin nan.” Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kafin ta mik’e sosai tana gyara zamanta “Aure nake so a masa..” Daddy ya dubeta da mamaki “Aure.? Cikin yaran Business partners dina kike so na nemar masa matan.?” "Ta girgiza kai alamun a’a “Na riga na samar masa mata a garin Kano. ‘Yar gidan mutunci wacce bata da bud’ewan ido da wayewa da yawa balle a samu matsala along the way. Ba babban Aure nake so ba, ba auren da za’a wallafa a mujalla ko a gayyato manyan mutane ba. No aure nake so ayi a sauk’ak’e. Kawu na dake can Maiduguri zai iya wakiltanka dan shi na wakilta akan komai. Ga Asshe ma a can Kanon. So dik wani necessary bincike da Ya kamata a gudanar an gudanar..”" Dakatar da ita yai ta hanyar d’aga hannu “Idan keda ‘yanuwanki kun gudanar da duk abinda ta kamata kuyi so meye nawa kuma. Ni dai kin sani bazan tab’a karb’ar ma D’anki Aure ba Kwaise. Kuma abinda ya shafi rayuwarsa ba damuwata bane. The only alak’a dake tsakanina dashi shine abinda ya shafi Kasuwancina. Kampanina da ci gabanta.” Mommy ta rintse idanunta tana jin wani zafi na ratsa cikin k’irjinta. Tasan za’a Rina haka tinda dai ta jima da sanin duk wani abinda ya danganci Haidar wofi ma ya fisa mutunci a idon mahaifinsa. Ya zama dole ta tabbata anyi auren nan at all cost. Tinda tasan wann ba komai bane face sharrin mugun asirin da aka jefesu dashi. Ta tabbata tinda Malaminsu ya sanar dasu da zaran anyi auren matsalan dake cikin ahalin zaizo k’arshe gwara tayi komai domin ta tabbata auren ya yuwu. Ta numfasa kad’an “Auren bazai yuwu ba saida yarda da amincewarku.. Ina nufin kaida Haidar..” Ya kuma dubanta da mamaki “What exactly do you mean.?” "“Ina nufin Yarda da amincewarka shine kawai zai karkato Haidar Ya amince da wann Auren. Kasan halinsa za’a iya masa auren mu daina ganinsa har abada, bazai yarda ya zauna da matar ba. Yanzu haka ma Gaba yake damu tinda gashi ya daina zama gidan nan.”" “Wanda yafi k’arfin zaman gidan iyayensa ne zai zauna ma Auren da zaki masa.? Ke kanki kinsan D’an naki baida mutunci bai ganin kowa da mutunci daga ni har Ke.” “Amma yana mutunta aikinsa.!” Mommy ta dakatar dashi da fad’in haka. Daddy ya tsareta da ido. Taci gaba da jinjina kai “Musamman project d’in nan da yaketa kai komo akai. Naga yanda ya dage yake matuk’ar so Ya jagoranci aikin.. Idan har muna so ya amince da auren zamu iya amfani da wann damar. Ina nufin zaka amince ya jagoranci aikin matuk’a zai amince da Auren. Daga baya na tabbata zai so Yarinyar kuma zasu gina family tare. Zai tara hankalinsa waje guda. A yanda matsalar..” Bata kai aya ba ya katseta “A’a dakata dakata Kwaise amma ba dani Aliyu Maitama za’ayi wann shiriritar ba..” “Engr dan Allah ka min wann alfarmar a rayuwa.. Just this once..” Ya gyara zama sosai yana dubanta cikin rashin yarda “Seriously.. Wann ai hauka ne.. Kwaise a ina kika tab’a jin anyi abu makamancin wann..? Are you asking me to put my company at risk here.?” Mommy ta silalo daga saman kujera ta duk’a gaban Daddy saman gwiwoyinta. Ta shirya sadaukar da komai domin ta ceto ahalinta. Cikin muryar kuka take furta “Zanyi ko menene Engr.. Zan duk’a a gabanka na rok’eka sabida inada yak’inin Auren nan zai zama silan shiriyar Haidar da kuma kwanciyar hankalin ahalin nan cikin yardar Ubangiji..” Saurin d’agota yai yana fad’in “You don’t need to do this Kwaise.” “A’a ka kyaleni na duka gabanka idan har hakan zaisa ka amince da buk’ata ta.” "Daddy ya soma girgiza kai “Kwaise, babu abinda zakiyi da zaisa na damu da d’anki ko na damu da al’amarin shi.. Kaman yanda ban d’auke shi da mahimmanci ba haka ban d’auki wann auren da kika dage sai kin masa da mahimmanci ba. Amma idan har haka kika zab’a ki sani I won’t get myself involved cikin nema ma d’anki aure.” Sai ya d’auki wayarsa ya shiga dialing layin Haidar. Haidar yana d’agawa Daddy ya sanar dashi yazo gida ya samesa yana jiransa." Koda Haidar Ya k’araso zaune ya taddasu a parlon. Iyayensa guda biyu. Yayi zaton magana zasuyi da Ya shafi Kasuwanci shida mahaifinsa tinda har wann ranar baice komai ba gameda proposal da Haidar ya kawo masa the other day. Har k’uri’a akai a company kan waye ya kamata ya jagoranci aikin wanda yake har kawo wann lokacin pending matter sabida shugaban kampani baiyi nasa zab’en ba. Idan Har mahaifinsa a matsayin shugaba a Kampanin Ya zab’esa ko shakka babu ya lashe k’uri’u mafi rinjaye. Idan har mahaifin nasa ya hau kujerar nak’i dole haka yana Ji yana gani aikin ya tafi k’ark’ashin kulawar waninsa. Duk shirinsa na son ganin bayan mahaifinsa da Kampanin zai tashi a banza. Like always he’s not welcome. Ya bud’e murya Ya gaishe su cikin rashin tabbacin za’a amsa masa ko baza’a amsa ba. Daddy ya jinjina masa kai had’ida nuna masa kujerar gefensa “Have a seat.” Ba musu ya k’rasa ya zauna yana satan duban b’angaren mahaifiyarsa dan a yanda Ya gansu jikinsa ya basa wani abun ake shiryawa akanshi. Ya jima da sanin su biyun tarayya suke wajen k’untata ma rayuwarsa. Daddy ya dubesa “Are you sure you can handle the project.?” Haidar yaji tambayar a bazata. Ya d’ago yana duban mahaifin nasa. Maimakon ya basa amsa kai tsaye sai ya girgiza kai yace “Do you still have your doubts.?” Mommy ta tsaresu da idanu jin Daddy ya tambayi Haidar amma sai Haidar d’in Ya amsa masa da tambaya. A cikin zuciyarta tace like father like son. Daddy ya jinjina kai “The project is to be commenced in three months time. Idan har ka shirya kuma kana so kayi da gaske zan sauk’a daga kujeran veto and give you and your team the green light… But on one condition.” Haidar ya dubesa da mamaki sai kuma ya dube mahaifiyarsa wacce tin shigowarsa ta kafesa da idanu. Ya maidoda dubansa ga mahaifinsa “What’s your condition.?” Daddy ya dubi Mommy “Go ahead Kwaise. Tell your son the condition.” Mommy da idanunta Ke a k’ek’ashe kaman ba ita ce taci kuka a while ago ba tace “Sharad’in shine Aure.. Zaka auri matar da muka zab’a maka kuma ka zauna da ita matsayin matarka.!” Tamkar sauk’an aradu haka Haidar yaji batun. Ya dubi mahaifiyarsa da tsananin mamaki Ya kuma dubi mahaifinsa. Lokaci guda yake girgiza kai alamun maganan tana kuma ringing cikin kwak’walwarsa “Unbelievable.! This is unbelievable.. What is this.. Aure.. Sharad’in Aure..? Mommy seriously..?!” Ya k’arashe yana duban mahaifiyarsa. Har lokacin ya kasa yarda. Mommy ta jinina kai “Eh Haidar.. Aure shine sharad’in idan har da gaske kana so ka jagoranci aikin..” Ya kuma juyowa yana duban mahaifinsa yana jiran ya k’aryata amma sai yaji Shiru bai ce komai ba. “Wann shine kiran.?” Ya tambaya yana duban mahaifinsa. “Abinda mahaifiyarka take so kenan. If it was to me kaima ka sani da yin aurenka da rashin yin Aurenka duk ba matsala ta bane. Talkless of wacece zaka aura. ‘Yar waye.? Daga ina take.? Duk wann ba matsala ta bane.” Meye yake ji kaman hawaye na neman cika idon shi.. Anya wad’ann mutanen sune suka haifesa? Anya akwai iyayen da zasuyi ma d’ansu mugun k’iyayya irin wann.? Abinda yakeda mahimmanci a cikin ahalin kasuwancin ahalin ne kawai Wanda za’a yi komai domin bunk’asarta. Amma duk wani abinda ya shafi ahalin baida mahimmanci musamman ma shi in particular. Muryar Mommy ya kuma katsesa “Idan an maka aure a yanda ka d’auke mu nasan zaka iya cewa an d’aura ma wofi ba lallai ka zauna da matar ba tinda yanzu ma ba ganinka muke ba. Wann dalili yasa muka zab’i gindaya maka sharud’a. “Ki gyara zancenki Kwaise kika zab’ar masa dai. Amma bani Aliyu Maitama ba. And one more thing.. I can’t gamble my company away. Idan kuma har company na zai shiga ki sani naki AUREN ma zai shiga.” Mommy ta dubesa da tsananin mamaki “Aurena kuma Engr.. Mai hakan yake nufi..?” “Hakan yana nufin it will be the end of our marriage if things go wrong with my company.. Kuma wann fake family d’in zai watse… Ina nufin babu sauran ahali.. So think carefully for the repercussions of what you are about to decide.!” Zuciyar Mommy yai wani irin bugawa kaman an sauk’e mata guduma jin irin hukuncin da mijinta Ya yanke. Yayinda Haidar ke ci gaba da dubansu cikin tsananin mamaki. Mommy ta nuna kanta tana duban Daddy “Kana so kace my marriage and the family that I spent years Ina iyaka k’ok’arin naga bai ruguje ba zai lalace..?” “Of course yes.!” Mijinta ya bata amsa. Yaci gaba “So before you make your final decision sai ki tantance wanne ne yafi mahimmanci wajenki.. Auren D’ank’i ko naki Auren.!” Haidar yaci gaba da girgiza kai yana dubansu. This is unbelievable! Ya kasa aminta wad’ann mutanen sune wai iyayensa. Ya tsaida idanunsa wanda suka rine zuwa ja kan Daddy “Really Daddy.. Is this what’s like to be born into wealthy and influential family..? Everything is about business and making money..? Da gaske Daddy..? Shin ba wani abinda yakeda mahimmanci ne cikin ahalin..?” Ya d’an d’aga murya wann karon “What are we to you..? Is that what you think of your family..? Like we are some sort of business ventures..?” Ya mik’e tsaye jijiyoyinsa na kuma tashi yana duban duka iyayen nasa “Are we supposed to..” "“Shut up!” Mahaifinsa Ya katsesa kafin yaci gaba “Don’t you dare raise your voice at me.. Da kai da rayuwarka babu guda da yakeda mahimmanci wajena. If I take your proposal into consideration, it’s because your Mom insisted.. Now get out..! Get out of my sight.!”" Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban mahaifin nasa disbelievingly. A haka ya juya ya nufi k’ofa a fusace zuciyarsa na masa mugun d’aci. Mommy ganin damarta na k’arshe zai kufce mata Ya sanyata bin bayan Haidar a d’ari tana k’ok’arin dakatar dashi. Anisa ta mik’e tana lek’en window jin irin kiran da Mommy ke ma Haidar. Nan ta hangesu sun fito daga side d’in Daddy. Haidar na tafe kaman zai kifa yayinda Mommy ke take masa baya. Mommy ta rik’esa sosai “Haidar don’t do this.. Just listen to me.. Bazai yuwu ka rasa project d’in nan ba..” Yai murmushi mai ciwo “Oh Shiyasa kika tareni ranan a nan.. Kike cewa ni da Ke zamu had’a kai.. Wann shine had’in kan naki da d’anki.. C’mon Mommy.. I always knew baki tab’a yin abinda bazakiyi benefiting a ciki ba.. What I don’t understand here shine Auren kike so nayi ko kuma dai wann project d’in ne a ranki..?” Mommy ta jinjina kai “Both Haidar.. But my top priority is the project.. Idan har baka amince da auren ba bazai tab’a baka project d’in ba. Think about it Haidar you are his only son. Tilon magajin shi. bazan tab’a bari wani Ya d’auki place d’inka a wann Kampanin ba.” Ya murmusa yana dubanta “Na sani to him I’m his failed investment. And to you… Your weapon.. Rayuwana baida wani amfani a wajenku..” Zai shige Mommy ta dakatar dashi da fad’in “Three month marriage.. AUREN WATA UKU Haidar.. Project d’in zai fara nan da watanni uku. Idan ya riga Ya d’auraka akai ka riga ka fara aikin he can’t cancel the agreement. Zaka iya rabuwa da yarinyar.. Ni dai kawai damuwata shine ya baka wann project d’in..!” Yai Shiru yana duban Mommy. Watau akan abinda take so zata iya zuwa ko wani mataki. Ya matso sosai yana dubanta “Har haka kike son project d’in Mommy..? Shin yakai ki saka naki Auren cikin had’ari ma AUREN WATA UKU. Kawai dan ya bani wann project d’in.?” Ya kuma girgiza kai “But Mommy this doesn’t make any sense. Ke kikayi kid’anki kikayi rawarki. Da kunnuwanki Kinji ya fad’a. Idan a nasa ra’ayin ne bai damu nayi Aure ba ko kar nayi. Duk ba matsalarsa bace. Kece kike son Auren kaman yanda yace.. Toh meyasa Auren Ya zama hujja.?” Mommy ta jinjina masa kai “I couldn’t just sit back and watch you lose your chance. Na kula abinda yake so kenan. Koda bai fad’a ba deep inside yana so kayi auren ne.. Kaima kasan ba don yana so kayi Auren ba bazai tab’a saka Kampaninsa on the line ba. Kayi tunani Haidar we are talking about your Dad here.. Mutumin da zai iya bada rayuwarsa ma wann Kampanin. Rana tsaka dan ina so kayi Aure sai ya amince cewa ka jagoranci aikin.. Aikin da future na Kampanin Ya ta’allak’a akansa. Think Haidar. Wllhi da ace mahaifinka baison kayi wann aure bazai tab’a yarda da sharad’in ba. Mahaifinka yana sonka Haidar kawai bazai iya nuna maka bane ko kuma lokacin nuna maka d’in ne bai ba..” “Well I don’t give a damn..!Ya soni ko kar Ya soni.. Ban damu ba kuma bana ma so naga ranar da zai so ni..” “In that case ka yarda ka amince kai AUREN WATA UKU. A lokacin da zaka fara project d’in sai ka rabu da matar ba tareda mahaifinka ya fahimci komai ba. Tinda dama Auren yake so kayi d’in. Toh kayi a wuce wajen. Dan ka rabu da matarka bazai ce meyasa ka saketa ba. Since we all believe ana aure ana rabuwa. Sann bazai tab’a yuwa A amshe aikin daga hannunka ba tinda abu ne base on agreement Wanda Ya k’unshi saka hannu daga duka b’angarorin.” "Shiru Haidar yai yana dubanta. Yasan mahaifiyarsa akan abinda take so. Sann shid’in tamkar makaminta ne da take amfani dashi wajen kare kanta. Idan Har ya amince da wann Auren za’a basa project d’in and everything he’s long been planning for zai samu damar aiwatar dasu. He can finally have the chance to ruin his Dad and his so called company. After all, the marriage is just for three months. Sann idan komai Ya wargaje auren iyayensa ma zai wargaje kowa zai kama gabansa a wann ahali da babu komai cikinsa face k’unci da k’arya. Zai d’auki matarsa Dareen suyi nesa da wann ahalin Wanda basuda hurumin saninta ko rashin saninta because bai d’auki ahalin matsayin ahali ba. Kaman yanda suma baida mahimanci a wajensu. Haka zalika bai damu yaji waye zasu aura masa ba. Dan yayi imani da zaran an basa jagorancin wann project d’in sun aura ma banza ne da wofi dan ko kamanninsa bazai tab’a bari matar ta sani ba." "“Fine Mommy.. Na amince,na amince da AUREN WATA UKU kaman yanda kikace.!”" Mommy jin abun tai a bazata. Wai Ya amince zaiyi wann Auren Wanda bata sanar dashi k’udirinta da mak’asudin Auren ba. Ta tabbata a nasa tunanin ta zab’i yayi wann Auren ne sabida project d’in da yake matuk’ar so ya jagoranta. Ta tabbata kafin ya saki Matar tama riga ta jima da rabuwa dashi idan har aikin Malaminta ya cika. Zuwa wann lokacin kuma asirin ya karye hankulan ahalinta zai dawo jikkunansu. Daga nan sai su bud’e sabon babin rayuwa mai dad’i ita da ahalinta. Ta k’araso ta rungume Haidar tana hawaye tsananin farin ciki da Ya lullub’eta. "Anisa dai sai lek’ensu take, tana mamakin yau Mommy ce harda rungumar Haidar haka. Lallai something’s going on.. She needs to find out. Saurin sauk’owa tai sanda Mommy da Haidar suka kuma shigewa sashen Daddy." "Mommy bakinta har kunne take duban mijinta “Engr, Haidar Ya amince.. Ya amince da sharad’inmu. Ya amince da batun Auren.”" Zuciyar Anisa dake daf k’ofan katafaren parlorn yai wani irin tsinkewa. A fili ta furta “Aure.? Aure kuma..?” Daddy ya d’ago yana duban Haidar Wanda ke tsaye gaba gareshi cikin parlorn Ya nad’e hannayensa kansa a karkace. Shid’in ma mahaifinsa yake duba. Irin duban nan na your days are numbered. "Cikin zuciyarsa yake furta ‘ This is the beginning of an end for you Daddy.. K’arshenka and your so called company.. Komai zaizo k’arshe a tsakanin wata uku. This project will turn out to be a great disaster for you and your company. On the day of launching the project, a wann ranan zan gayyato maka manyan bak’i Daddy.. I’ll make sure to invite EFCC for you.. All your assets will be seized. Ba a nan zai tsaya ba. You will fall in front of everyone.. I’ll make sure they sue you and your company for poor Workmanship.. Zan tabbata they impose sanctions for your company ta yanda zai zama ba kai ba shigo da wasu manyan kayan gine gine na zamani cikin k’asar nan. After all this Daddy. Ni, Aliyu Aliyu Maitama, your never wanted son will personally charge you for a series of discriminations while working under your company. Duk wasu cin mutuncin da ka mun a wann Kampanin naka sai nasa ka cinyesu gaba d’aya. I’ll make you lose everything. Alk’awari ne.!’" Muryar mahaifiyarsa Ya sinkayo tana fad’in irin farin cikin da take ciki burinta yana gab da cika. Sai kuma ya hango Daddy wanda tuni ya nufi study d’insa. Cikin sauri yabi bayan mahaifin nasa. Daddy ya d’ago yana dubansa. Haidar ya shigo cikin study d’in sosai. Su duka biyun suna duban juna. Daddy yace “What now.? Mai kuma kake nema.?” "Zama Haidar yai saman kujeran dake gaban table d’in Daddy. Ya d’auki pen ya zara plane sheet mai d’aukeda alama, adireshi had’ida sunan company dake bisa table d’in. Ya mik’a ma Daddy. Lokaci guda yake furta “You and I are both businessmen Daddy. And we know how things work a duniyar kasuwanci. Since everything here is about business Daddy. Zamuyi shi a rubuce, sann mu saka hannu to avoid business pitfalls..”" Daddy ya tsaresa da idanu yayinda Haidar yaci gaba “We will both sign this agreement tabbacin babu janye yarjejeniya daga baya.” "Daddy ya amsa takardan kafin ya ketata gida biyu “Na riga na gama yarjejeniya da mahaifiyarka. Bana magana biyu. If things go wrong, believe me your Mom will face the consequences.” Yana ida fad’in haka Ya nuna masa k’ofa." Haidar yai Shiru yana mai jinjina kansa. Har cikin ransa yake jin babu abinda zaisa Ya janye duk wasu k’udirinsa gameda wann wofin ahalin. ** A b’angaren Mommy kuwa ta kira Asshe ta sanar da ita yanda sukai da Daddy harma da Haidar. Asshe tai Shiru kaman mai nazari “Amma Aunty Kwaise na fara tsoro da lamarin nan. Ta ya zaki saka aurenki on the line..?” “Ta ya bazan saka nawa auren at risk ba Asshe.? Har yaushe zan jira na gyara ahalin bayan ga dama ya sameni. Asshe na shirya sadaukar da komai domin ceto ahalina.” Asshe ta furzar da huci “Aunty Kwaise I find it strange wai Haidar Ya amince tashi guda. Shin har haka yake son wann project d’in.. Anya son da yake ma aikin yakai yai making huge decision irin wann..? Kuma shi Engr yasan Auren wata kika shirya yi ma d’ansa.?” Ta girgiza kai kaman Asshe tana dubanta “Ta Ya zai sani Asshe..? Haidar ma na fad’a masa zai iya rabuwa da matar a wata uku ne dan na samu amincewarsa a sauk’ak’e. Amma kinsan su duka biyun Babu Wanda yasan mak’asudin auren. Dukkansu kafin su ankare aikin gama ya gama.” Asshe ta kuma jinjina kai “Ciniki ta fad’a kenan. Yanzu zamu iya zuwa asibiti mu biya kud’in jinyar mahaifinta..” Mommy ta kuma jinjina kai “K’warai.. Bana so a d’auki lokaci Asshe. Kawu Bana da mutanensa zasu zo su sameki ku tsara komai. Su karb’i auren a nad’o makarin asirin a kawota. Kud’i ba matsala bane Asshe. Zan kashe ko nawa ne domin wann buri nawa Ya cika.” "Asshe ta kuma jinjina kai “Shikenan Aunty Kwaise. Bakida matsala, zan tsaya ra’ayin daka Har Allah ya shige mana gaba.”" Mommy suna ida wayan ta fito parlor yanda ta tadda Anisa ta kifa kanta sai kuka take. Mommy ta k’araso a birkice tana tambayarta meke faruwa. Anisa ta d’ago tana dubanta dan tinda taga Haidar yazo gidan gashi taji ana batun Aure. Bugu da k’ari akan idonta Mommy ta shige d’aki tana magana da Amminta a waya Wanda ta tabbata bazai shige zancen auren suke ba. Shin iyayenta basu fahimci irin son da take ma Haidar bane. Idan har ba auren Haidar zatayi ba toh ma zaman me take a gidan. Take ta mik’e tana kuma fashewa da kuka ba tareda tace da Mommy komai ba. Mommy tabi bayanta da kallo kafin ta tab’e baki tace “Sangarcin sun motsa kenan.” Bata kuma bi takan Anisa ba taci gaba da sabgoginta dan yau Ji take tamkar kaf damuwarta na gidan duniya Ya yaye. ** "Asshe ta dubi Umma wacce ta cakare cikin tsadaddan leshi d’anubansu, Tai far da idanu “Wow Umman Ummul kinga kuwa yanda kika fito kikai kyau.. Kyaunki na asalin k’abilar Fulbe Ya kuma bayyana.. Gaskiya kud’i zasu amshe ki.. Kin ganki kuwa wa zaice kin haifi Ummul..”" Umma ta ci gaba da wahse baki tana juyi gaban madubi tana duban kanta “Allah ko Hajja Asshe.. Toh ai gwara kar na Saba tinda ba samun irin wann tufafi zanyi kullum ba.” Asshe ta kuma murmusawa “Inji waye.. Ai saidai ki dinga kyautan su ma. Ke ai yanzu kin girmi irin wad’nn ma saidai na order daga k’asar waje.. Kekam fah yanzu kin zarce sa’anninki ‘Yarki taci sunanta Uwar alkhairi ta bud’e Miki k’ofofin alkhairi.. Ke fa yanzu da matan gwamnoni zaki dinga jerawa..” “Na shige tsaran Yaya..” Umma tace tana kuma washe baki. Asshe tace “Waye kuma Yaya..?” “Tani kishiyata..” Umma ta bata amsa. Gajeren tsaki Asshe tai tace “Saidai ta soma kiranki da Yaya daga yanzu dan kin Riga kin amshe girman. Ummul d’inki ta k’wace Miki girman..” Ta aje mata hanshak’in handbag shak’e da kud’i ‘yan dubu dubu ciki tace “Wann naki ne ki razani Tani dasu.” Dan tinda Asshe ta gane Suwaiba ba kwad’ayayya bace burinta kawai shine ta burge kishiyarta harma da sauran jama’an dake tsangwamar ‘yarta su shiga taitaynsu sann Ummul d’inta Tai irin auren da yaran Tani basuyi ba ta k’udiri niyyan cika ma Umma wann buri nata. Dan sosai matar ke sakata nishad’i. Asshe ta fice tana fad’in bara ta duba Hilala ko ya shirya dan shine zai kaisu. Umma ta jinjina Kai tana kuma murmusawa. A fili take furtawa bayan Asshe ta fice “Tani kenan.. Dake da ‘ya’yanki Kun gama mana wulak’anci.. Yau idanunki zasu gane Miki abin mamaki.. Yau zakiyi nadaman duk wasu abubuwan da kika jima kina min cikin gidan nan.. Ummulkhairy da kike aibatawa Har kina ambatonta da Ummulsharri toh yau sharrinki zai koma kanki Tani.. Ki jira bayyanata.!” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *16* *©️Sameena Aleeyou… * Safiyar Washe gari gidan Hajja Fannah suka fara nufa ko an samu wani bayani gameda Umma. Saidai har kawo wann ranar babu Umma babu labarinta babu wani bayani tak’amaime da ita. Ummul sai juya wayar Umman take cikin hannunta nokia k’irar 3310 duk taji jiki ta kod’e. Hawaye suka kuma gangaro mata. Gashi sun tadda Hajja Fannah ma bataji dad’i ba kwance take lik’is dan tin bayan tafiyar Hisham jikinta ba dad’i k’ok’ari kawai take. Ummul ta dubeta tace “Hajja ko dai asibiti zamuje.?” "Hajja Fannah ta murmusa cikeda jin dad’in yanda Ummul ta damu da damuwarta “A’a Ummul, ba sai naje asibiti ba.. Zuwa anjima zazzab’in zai sauk’a in sha Allah.”" Ummul ta jinina kai suna masu mata fata da addu’an samun lafiya itada Khulsum. Khulsum ce ta soma mik’ewa yayinda Ummul ma ta mik’e suna mata Sallama da fad’in zasu biya Asibiti wajen Abba su dubasa daga can zasu k’ara komawa police station ko an samu wani batu gameda mahaifiyarsu. Ummul ta d’an dubeta “Hajja zamu iya barinki ke kad’ai naga kaman yau jikin naki da d’an nauyi.” Hajja Fannah ta murmusa tana mai mik’ewa zaune sosai dan hankalin Ummul d’in Ya kwanta “Kinji Ummul nifa zazzab’i ne ke damuna nasan kuma bazai shige typhoid d’in nan da ya sakani gana kwana biyu ba. Banison zuwa asibiti ne su tara min magani dan bana shiri da had’iye k’waya Shiyasa ko Hisham ban sanar dashi ba dan nasan yanda kika dage naje asibiti haka shid’inma zai dage. Toh kafin ku min taron dangi gashi can na dafa ruwan zogale ma inata sha dan nafi gane wann.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin nuna jarumta irinta maras lafiya. Ummul ta murmusa kad’an. Sosai take jin Matar har cikin ranta. Sun mik’e suna kuma mata Sallama ta k’araso hannunta rik’eda ‘yan kud’ad’e ta mik’a masu “Ungo nan kuyi kud’in abun hawa.” Dukansu biyu girgiza kai suke suna fad’in a’a ta barshi. Ta d’an b’ata fuska tana fad’in “Au baku d’aukeni uwa ba kenan idan har zan baku abu kuk’i karb’a.” Ta dubi Khulsum “Ungo nan karb’a maku ita Ummul ai tasan karonmu. Idan bata amshi kyauta na matsayin malamar ta ba ai ta amsa matsayin ‘Yata.” Can k’asar zuciyarta kuwa Matar D’anta ta kirata. A dole dole suka amsa dukda dama basuda ko sisin da zai kaisu asibiti wajen Abba balle Har su tafi police station maganan case d’in Umma. Suka kuma mata godiya had’ida fatan samun lafiya kafin suka fice. Suna tafe cikin adaidaita Khulsum ta dubi Ummul “Adda mai zai hana mu fara zuwa police station d’in tinda kinga asibiti ko munje ba Lallai Mama da yaranta su bari mu shiga wajen Abba ba.” "Ummul ta girgiza kanta “A’a Khulsum, koda zasu hanamu mu je d’in dai. Muji ya jikin nasa Ya kwana tinda idan muka tafi maganan neman Umma ba Lallai mu dawo da wuri ba har sai munji yanda al’amarin Ya kwana. Kinsan ofishin ‘yansanda cases da yawa. Inaji a jikina da izinin Allah yai za’a samu Umma.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irin na Wanda Ya gama karaya amma tawakkali Ya hana furta hakan." Khulsum ta jinina kai tana amsawa da Allah Ya sa a samu Umma ya kuma bawa mahaifinsu lafiya. Ummul ta amsa da Ameen daidai sansa mai adaidaita Ya diresu k’ofan asibiti. Suna dosowa haraban ward d’in suka hango Mama da Badi’a. Ga Azeema a gefe harma da mijin Azeemar Habibu. Sai wallahi tallahi suke baka ma gane mai suke fad’i dukda wai k’asa k’asa sukeyi basa d’aga murya kar ajisu a fatattake su. Azeema fad’i take “Wai kuna so kuce mun tun yammacin jiya kud’ad’en suke hannun Tasi’u kuma wayansa a kashe.?” Habibu yaci gaba da salati yana tafa hannu. Ya dubi Mama wacce ko iya cewa komai batayi. Huci kurum take. Fuskar Tasi’u ne kawai ke mata gizo cikin ido. Allah ya gani da zataga Tasi’u yanzu a gabanta zata iya shak’esa Har sai an k’wacesa. Cikeda zak’ewa Habibu yaci gaba “Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za’a ce kun kira shi Tasi’u kun dank’a masa ragamar komai irin haka. Mai zai hana baku tuntub’i ita Azeema ta kirawo nata mijin matsayin shaida ba..Wann ma ai ba magana bace tinda kud’in nan ba kud’in Bad’ia bane ita kad’ai.. Ehe kud’i ne na magada.. Kuma shago da ba shagon sata ba ya ma za’ace an sayar cikin rahusa haka. Nawa kowacce zata samu cikinku.?” Badi’a dake aika masa mugun kallo tace “Toh wai kai Malam naka a wanne.. Ko harda kasonka ne cikin gadon.?” Azeema ta katseta “Ai naga gadon na uban Tasi’u ne da kika gayyatosa Ya kwashe kud’ad’en Ya gudu. Toh wllhi na ranste da Allah bazata tab’a sakuwa ba wai bindiga a ruwa. Wllhi yanzu zan kirawo Yaya Salima tinda duk abinda ake itama bata sani ba. Na ranste da Allah sai an mana kashin hakkinmu ehe. Ko kuma wllhi na gayyato maku hukumar hisba nace Kun saida gadon mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.!” Ta k’arashe sai huci take. Habibu sai bud’e hannaye yake yana kuma ingiza Azeema. Fad’i yake Ahtoh magana kenan a fito masa da hakkin matarsa. Azeema ta Ciro waya da zummar kiran Salima kenan suka sinkayo kukan Mama. Ta kamo bakin mayafi tana matse idanunta “Ni Tasi’u zai tona ma asiri a garin nan.. Na rufa masa asiri yana d’an wiwi na d’auki ‘ya na basa a tunanina zaiyi hankali ashe ni ce ‘yar wiwi.” "“Mama ba fah kuka zakiyi ba, nemo Tasi’u Ya kamata kuyi yanda ya shiga Ya fita dan wllhi muddin Tasi’u baizo ba daga nan ofishin hukuman hizba na nufa na zayyane masu komai. Kun raba gadon mahaifinmu da ransa.!” Azeema tace tana huci." Habibu yai saurin shiga tsakiya kaman wani alk’ali “A’a a’a baza’ayi gaggawan gayyato hukuma ba tinda abin duka na gida ne. Kamata yayi a binciko yanda Tasi’u yake duk rintsi. Yanzu zan tafi yanda shi Tasi’un ya cika zama na tuntub’i abokansa tinda dai baza’a samesa a gida ba. Na tabbata baiyi nisa ba.” Ya k’arashe yana mai wucewa cikin sauri. Ummul da Khulsum suka dubi juna cikin tsananin shock. Mama da Badi’a saida shagon Abba sukai kenan ko mai hakan yake nufi.? Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Suna a haka aka zo neman kud’in magungunan Abba wanda kusan kwana biyu kenan yana skipping wasu treatments d’in masu matuk’ar mahimmanci. Mama sai ta hayyayako ta soma bala’i tana fad’in ta gaji da zaman asibiti ma jinyar da yak’i ci yak’i cinyewa. Nurse yace “Yanzu babu kud’in da za’a masa jinyar.?” Azeema tace “Kurma ne kai baka ganin tashin hankalin da muke ciki ne.. Damfararmu fah akayi..” K’arasowan su Ummul suna tambayan mai ake nema gameda jinyar mahaifinsu yaja hankulan su Badi’a. Ita kam Mama har yanzu fah bata wani gane mai ake ciki ba hankalinta kacaukam naga Tasi’u da kud’ad’enta. Badi’a tace “Kud’in jinya ake nema ko zaku biya ne tinda wancan karan ma ku kuka biya. Sai aje a sake saida jiki a kawo kud’i. Ko mazan ne babu.?” Khulsum ta dubeta Har lokacin mamakinsu bai saketa ba “Da dai a kiramu b’arayi marassa imani masu saida k’addaran mahaifinsu da ransa gwara ace jikinmu muka saida muka biya kud’ad’en jinyarsa. Kin fahimta B’arauniya matar b’arawo.!” Badi’a ta nufota a zafafe tana fad’in “Ke ni sa’anki ne dan ubanki.. Sai na gurje bakin ki yanzu a nan..!” Saida aka shiga tsakanin Khulsum da Badi’a. Nurse yace “Yanzu haka Dr zaizo babu abinda aka buk’ata.. Shin ba hanyar da za’a bi a samu a saya magungunan..?” Kaman daga sama suka sinkayo wata murya “K’warai akwai hanyar da za’a saya!” Mama dake shirin barin wajen dan batada lokacin cecekucen rashin kudin jinyar Malam da malaman asibiti burinta kawai ta isa ta cimma Tas’u. Nan tai birki jin wann murya dai tai ma me muryar farar sani. A hankali take k’ok’arin juyowa har dai ta karkato gaba d’aya. Mama ta daskare. Ta shiga mutsuka idanunta tana duban wacce take gani gaba gareta “Suwaiba.!” Ta furta cikin tsananin mamaki. Suwaiba ce fah.. Suwaiba Amaryar Malam Isubu nata take gani sanye cikin tufafi na alfarma. A gidan Uban wa Suwaiba tayi arziki dare d’aya. Karfa hausar nan da ake cewa dare d’aya Allah kan yi bature ta tabbata kan Suwaiba. Ta kuma mutsuke idanunta dan har lokacin gani take kaman gizo ne ba gaskiya ba. Wai Suwaiba shashashar matar Malam Isubu ce haka kaman wata matar shugaban k’asa ko gwamna. "Khulsum da Ummul ma da mugun mamaki suke duban mahaifiyar tasu wacce kaman an canzata. Suka dubi juna suka kuma duban Umma shaye da tsananin mamaki, cikin tsananin shock suka furta “Umma.!”" Umma taci gaba da takowa gaba garesu. Azeema da Badi’a ma da mugun mamaki suke duban Umman. Kai tsaye nurse d’in Umma ta nufa tace “Nawa ake nema..?” Nurse d’in Ya d’ago takardan na list d’in abubuwan da ake buk’ata Ya soma karantowa. Kafin Ya gama karantowa Umma ta d’aga masa hannu alamun dakatarwa lokaci guda ta bud’e tsadadden handbag d’in dake rik’e hannunta ta Ciro sabbin kud’ad’e ‘yan dubu dubu sai walk’iya suke. Mama ta zaro ido waje ganin dubabe bugun habuja suna walk’iya suna kashe mata ido. Wai Suwaiba ke fiddosu. "Ko k’irgawa batai ba ta mik’a ma nurse d’in “Ungo nan.. A saya duk abinda ake buk’ata, idan yayi canji ka rik’e canjin idan kuma akwai abinda bai isa ba ka sanar Dani.. Ko menene..” Ta k’arashe tana gyara zaman tsadaddan mayafin dake bisa kanta." Nurse ya murmusa “A’a Hajiya saidai na Miki jagora ki biya da kanki.” Umma ta jinjina kai yayinda Umma ta take masa baya. Tin daga k’afafu Mama ke dubanta Har zuwa tsadadden leshi da yan kunne da sark’a dake kwance wuyanta. Wann ko taron manyan matan gwamnoni Suwaiba taje a haka ai ta cinye taro. Akan idonsu Umma ke gudanar da komai da taimakon nurse d’in kafin daga bisani ta amso receipts ta dawo yanda ta baro ahalin mijin nata Wanda kowa shock Ya hanasa aiwatar da komai. Baga Mama da yaranta ba baga Yaran Umma ba wanda zasu iya cewa Har yanzu basu tabbatar idan mahaifiyarsu bace. Ko takan Mama batabi ba ta dubi su Ummul wacce suma kansu ta koma masu tamkar bak’uwa. Kallon rashin sani ne ko na mamaki suke bin mahaifiyar tasu dashi. Tsakiyan yaranta ta shiga wato Ummulkhairi da Ummukhulsum ta kamo hannayensu tace “Mujenku kuga mahaifinku..” Tamkar rak’umai da akala haka Umma ke janyo su Ummul da Khulsum. A haka suka zo suka shige gaban Mama da yaranta wanda suka koma kaman an dasa su. Har suka shige cikin ward d’in Mama da yaranta basu daina binsu da kallo ba. Suna shigewa Mama ta dubi Azeema tace “Ke wanke ni da mari dan ubanki.” Azeema ta dubeta a yatsine “Ban gane na wanke ki da mari ba Mama..” “Nace ki mareni na tabbata ba mafarki nake ba.. Ba Suwaiba bace Ke min gizo ba. Inji ba itace yanzu ta shige gaba na ba ko.? Ku amsa min mana.. Na shiga uku ni Tani..” Bata kai aya ba taji zafi Ya tsunkuri ‘yar yatsarta na k’afa. Badi’a ce ta take mata ‘yar yatsar cikin k’ok’arin dawo da Mama hayyacinta. Mama ta saki k’ara tana d’ingile k’afarta “Wayyo kunama ta cijen.!” "Badi’a tace “Ba kunama bane ta cijeki, take maki k’afar nai ki tabbata ba mafarki kike ba..”" Azeema tace “Mama wllhi Umman su Ummul ce. Amma nima nafi zaton canzata akai.. Mama ina ta samo kud’ad’e irin haka dare d’aya.. Kinga Har fari da shek’i ta k’ara dare d’aya. Mama kin kaw ga suturan dake jikinta. Wllhi iriinsa matar Gwamna ta saka ranan da za’a rantsar da mijinta.. Mama Ina matar nan ta samo kud’i haka wai.?” “Yo Ina zan sani ina tareda ke a nan..” Mama tace tana kuma lek’en bayan Umma a tsarace. Badi’a ta tab’e baki tace “Kar canzawarta ya zautar daku. Abu ne a bayyane matar nan dama barikinta kawai take son yi auren mahaifinmu ya taka mata burki.. Yanzu da take ganin zai Mutu shine ta baje kolinta da kyau zatai barikinta mai dalili..” "Azeema tace “Kai wllhi amma fah ta mun kyau, kinga shegen mayafin da ta watsa. Irin mai walwalin nan fah da ake talla online.. Inama ta bani aro naje dashi Bikin k’anwar Habibi na yak’i shegun danginsa.”" Bata kai aya ba Mama ta hamb’are bakinta “Kud’in shan jini da tsafin zakije a baki.. Toh Idan shaye shaye kike kije Azeema.. Kije Suwaiba ta shanyeki.. Ni nayi imani itace ta asirce Ummul mazan dake nemanta ke gudu sabida Allah Ya rufa masu asiri da sauran kwanakinsu. Shi Fa’izu dake kwanansa Ya k’are gashi ta lashe kurwansa. Yanzu kuma abun yazo kan Malam Shiyasa data mik’a sa gashi a kwance kafi gawa.. Kuma yanzu ba sai anjima ba zan fiddata daga cikin asibitin nan..” Fiuuu Mama ta shige ta nufi ward d’in yaranta na biye da ita. Bata damu da majinyata dake kwance wajen ba Mama ta shiga kururwa tana fad’in Suwaiba mayyace yar K’ungiya asiri ne na shan jini.. Ta tsafe ‘yarta Ummul tana amfani da ita tana cinye mutane kaman yanda Fa’izu d’an ‘yar uwan Malam Isubu ya mutu. Bai isheta ba yanzu ta mik’a mijinsu zata cinye.. Sai dukan k’irji take tana fad’in wllhi bazaayi ma mijinta amfani da dukiyar ‘yar shan jini irin Suwaiba ba. Sauri sauri wasu nurses da cleaners suka tafi kiran securities. Hango securities d’in da Mama tai ya sanyata had’iye kalamanta. Securities suka k’araso suna muzurai suna fad’in waye zasu fidda. Take Mama ta shiga masu nuni da Umma tana fad’in “Ga Suwaiba ita zaku kama ita zaku fidda.. Yar shan jini ce..” Ai sai Mama taga securities sun isa gaban Umma suna duk’awa suna kwasan gaisuwa lokaci guda suna tambayar ko da abinda kike so a miki Hajiya. Mama sai ta saki baki tana duban ikon Allah. Suwaiba.? Suwaibar ne Hajiya..? Umma ta murmusa tana gyara zaman mayafinta “A’a babu komai Kar ku damu. Haukar wancan Matar ne Ya motsa inaga b’allewa tayi daga b’angaren masu jinyar hauka.” Mama jin an ambaceta da Mahaukaciya ya sanyata kuma hayyak’owa. Jikinta Har rawa yake. Sauran mutanen dake wajen Wanda dama fitinan Maman a ishesu sukace da gaske ne batada saiti kullum fama ake da ita. Aiko nan take securities suka fidda Mama da k’arfin gaske sai ihu take tana tsine ma Umma. Yaranta suka bi bayanta a guje suna ambato sunanta. Umma ta zuba masu idanu har aka fice dasu kafin ta sauk’e ajiyan zuciya ta juyo tana duban yaranta Khulsum da Ummul Wanda Har lokacin kallon mamaki ko muce kallon tsoro suke binta dashi musamman bayan da Mama ta gama fad’e fad’enta. Umma ta kuma dubansu sai ta k’arasa ta rungumesu. Basu iya maida mata martanin rungumar ba. "“Ummul, Khulsum.. Ni ce fah mahaifiyarku Ummanku.. Meyasa kuke dubana kaman bak’uwar fuska. Shin ko baku shaida mahaifiyarku bace.?”" Girgiza mata kai Ummul tai “Mun shaida kamanninki Umma amma yanayi ki yafi kama da bak’uwar Fuska.. Umma mai ya canza ki cikin kwanaki k’alilan..?” Murmushi Umma ta saki kafin ta dafa Ummul “K’addararki itace ta canza ni cikin kwanaki k’alilan Ummul.. K’addaranki Wanda a baya naita Allah wadai dashi shine ya zamto mabud’in Alherinmu..” Girgiza kai Ummul tai cikin tsananin sanyin jiki “Umma ban fahimceki ba..” Umma ta kuma murmusawa “Kar ki damu ‘Yata da sannu zaki fahimci komai.. Kuzo muje..” Ta shiga janyo hannuwansu suka nufo waje yanda suka hangi Mama har lokacin huci take bayan an tilasta mata yin shiru. Mama ta zabura zata nufo Umma amma sai taga wata jibgegiyar jeep taja tayi parking gaban Umma. Mama taja wani wawan birki tana dafe k’irji. Mamaki da sanyin jiki Ya kuma sauk’ar masu Ummul. "Umma ta dubesu “Toh yarana ni zan tafi, in sha Allah zan kuma dawowa nan bada jimawa ba.”" Da tsananin mamaki suke duban mahaifiyarsu. Tasa kai kenan zata shige mota Ummul tai saurin kamo hannunta. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai “Umma.. Ina zakije ki bar Abba cikin halinda yake ciki..? Umma ina kikaje kika barmu mu nata nemanki.. Shin Kinsan abubuwan dake faruwa a nan.. Umma wai meke faruwa.. Umma meke faruwa ne..?” Dafata Umma tai “Da sannu zaki fahimci abinda ke faruwa Ummul.. Zan rok’i alfarmarku. Kar ku bar kusan mahaifinku.. Ku zauna ku kula dashi.. In sha Allah daga yanzu duk wani abinda za’a kashe sabida jinyar mahaifinku bazai zama matsala ba. Na barku lafiya yarana..” Ummul na kuka ta kuma kamo hannunta “Umma shin kinsan kalan tashin hankalin da muka shiga na rashin ganinki.. dan Allah kar ki tafi ki barmu.. Umma..” saidai tuni Umma ta cire hannunta daga rik’on da Khulsum tai mata ta shige mota. Ummul ta kuma yunk’ura tana ambato Umma amma saiji tai Khulsum ta rik’on hannunta had’ida dakatar da ita “K’yaleta Adda.. Wann ba Umman mu bace.. Idan ma itace banida haufi an canzata dare d’aya.” Fad’awa jikin Khulsum Ummul tai wani irin kuka na kufce mata. Mama kaw zuba masu idanu tai tana mai kuma tabbatar da zarginta cewa Suwaiba dai K’ungiyar asiri ta fad’a. Umma tana shigewa cikin motan ta dubi Asshe dake zaune gefe. Ta d’an yi adjusting mayafin “Hajja Asshe Ya kikaga k’warewata..? Kinga kaw yanda na razana Tani na haukata ta na gigitata.? Gaba d’aya fah ta birkice..” "Asshe ta murmusa tace “Ai ma fah bama ayi komai ba, wann ai sharan fage ne. Sai randa aka kai lefen Ummulkhairi, ranan ne zaki kashe kishiyar ki da k’unci. Dan ina mai tabbatar miki sai ta had’iyi ranta. Kaf abinda ta miki kan Ummulkhairi sai kin rama. Ranan biki kuma a fice da gawarta.”" "Umma ta zaro idanu “Na shiga uku, bazan so Yaya ta Mutu ba ai…”" Asshe ta d’an murmusa kad’an had’ida dafe kafad’ar Umma guda “Bazata Mutu ba ma sai taga Nasaranki da na Ummul. Kuma ko yanzu kin tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro.. Ni so nake ki kece raini a kamfatanin layinku.. Duk masu aibata Ummul d’inki sai Sun shaida auren gata da za’a mata..” Nan fah Umma ta shiga wage baki zuciyarta na mata dad’i. Karfa ku mance mijin Umma na kwance gadon asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa. Amma Har yanzu burin Umma shine Ummul d’inta tayi aure kota halin k’ak’a ko ba dan komai ba sai dan ta birge Mama da sauran jama’an unga sabida abinda suka jima suna mata kan Ummul. ** A b’angaren su Ummul kuwa tinda Umma ta shige bak’ar Jeep d’in nan mai lullub’e da tint suka kasa komawa cikin asibiti wajen Abbansu dan haka su Mama da Azeema sukai caa a haraban asibiti suna nunasu suna cewa ga ‘ya’yan mayya. A dole suka fice daga asibitin suka dawo gida. Ummul ta zuba tagumi Khulsum ma da kalan nata tagumin. “Adda anya ba gaskiya Mama take fad’i kan Umma ba.. Anya Umma ba wani k’ungiyar asirin ta shiga ba..!” Tai maganar kaman mai tsoron furtawa. Ummul tai saurin d’agowa tana dubanta “Haba Khulsum ta ya zakiyi irin wann tunanin..?” “Adda abinda idanun mu suka gane mana fah kenan… Ina Umma ta samo dukiya irin wann tsakanin kwanakin nan..? Sann meyasa ta tafi ta k’yalemu..? Meyasa bata damu ta bar Abba cikin halinda yake ba.. Adda kifa duba kiga yanayin da Abba yake ciki amma Umma tana a matsayin matarsa ta saka k’afa ta tsallake shi har da shigewa shirgegiyar Jeep d’in nan. Ga ado da tayi irin wanda bata tab’a yi ba. Wata matace zatayi wad’ann abubuwan alhalin mijinta na kwance cikin tsananin jinya. Wllhi ko baki fad’i ba Kema kanki nasan zuciyarki bai kwanta ba Adda kuma akwai irin tambayoyin da nakeyi kwance cikin zuciyarki.” Sauk’e wani irin ajiyan zuciya Ummul tai sai kuma ta jinjina kai tace “Kinyi gaskiya… Akwai tarin tambayoyi k’unshe cikin zuciyata Wanda zanso Umma ta amsa min su.. Amma ko ma menene kar muyi gaggawan yanke hukunci da abinda idanu mu ka iya gani.. So tari abubuwan da idanun mu ke iya gani a zahiri ba haka suke a bad’ini ba.. Mu tsaya Har muga gudun ruwan Umma mu kuma ji abinda ke faruwa.” Khulsum taja wani irin gauron numfashi ba tareda ta kuma furta komai ba. ** Abuja. Laptop ne gabansa waya manne kunnensa yana duban wasu sketches na manyan bridges iri daban daban. Ko ba’ace ba da Hisham yake wayan. Da alama shi ya turo masa sketches d’in da suke tattanawa akai. Bayan Sun gama magana shiru yai yana nazarin abinda ke gabansa. Sai kuma ya rufe laptop d’in ya k’ura ma waje guda idanu. Dareen da waya ke mak’ale kunnenta ta kuma lek’ensa kafin ta koma da baya tana rage murya had’ida matse wayar jikin kunnenta sosai “How would I know.. He’s been acting strange lately..” Daga d’aya b’angaren muryar mutumin ya katseta “What are you there for idan har bazaki iya karantar yanayin da yake ciki ba..?!” "Ta d’an rausayar da idanu had’ida furzar da huci “Look, I see him everyday but I can’t grasp his mood. Ba ko yaushe asiri yake tasiri ba. Kar ka mance Shi mutum ne Wanda tun kafin sihiri ya jefesa yakeda wahalan sha’ani.”" Mutumin yace cikin tsawatarwa “Kalla Dareen. Ban kawo ki cikin rayuwar Haidar dan kiyi holewarki dashi ba. Kinfi kowa sanin dalilin da yasa kike tare dashi. Idan Har bazaki min amfani ba. Zan tarwatsaki da kaina.. Kinsan inada makamin da zan tarwatsaki a hannuna tinda har yau baki san yanda na bisne sirrin da Ya rufe Aurenki da Haidar ba.” "Lumshe idanunta tai had’ida bud’esu “Fine, zanyi iya k’ok’arina na fahimci mai yake shiryawa. Amma karkayi gangancin rabani da Haidar domin zan tashi wutan da kaima baka isa kashewa ba.!”" Ya murmusa “Kar ki mance I’m the one calling the shots here. Kibi umarnina ki zauna lafiya.!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran. Furzar da huci ta kumayi kafin tai k’ok’arin kintsa kanta ta fito parlor yanda Haidar ke zaune. Murmushi saman fuskarta ta zauna gefensa “Love..” Ta fad’i tana shigewa jikinsa. Sai kuma ta d’ago fuskarta tana dubansa “Is something bothering you..? You seem preoccupied… Is it about work..? Ko kaje duba Mommy ne..?” Tambayan da ta masa na k’arshe yasa ya dubeta sai kuma ya maida dubansa wani b’angaren “I’m fine..” Ya fad’i a tak’aice ba tareda ya kuma cewa komai ba. A ‘yan kwanakin ta kula magana ma sai ya zama dole yakeyi. Ya koma mata tamkar bak’o cikin gidan dukda dama a iya zamansu bata isa tace ta sansa kaman yanda tasan tafin hannunta ba dukda kuwa Auren sihiri da tayi dashi. Mik’ewa yai ya nufi sama ba tareda ya kuma ce mata komai ba. Hannayensa sakale cikin aljihun sweatpants d’in dake jikinsa. Tabi bayansa da kallo har ya haye sama kafin tai saurin janyo laptop d’in ta bud’e. Sannu a hankali take bin duk wasu abubuwan dake fuskan computer d’in tana karantawa. Aiki yake sosai kan project d’in da takeda masaniya yanata fad’i tashi akai. Toh kodai mahaifinsa ya basa go ahead ne.? Idan har mahaifinsa ya amince ya jagoranci aikin dole akwai wani abu a k’asa. Ba yanda za’ayi mahaifinsa ya amince masa cikin sauk’i.. She needs to find out meke faruwa. ** Yau kwanaki biyu kenan Umma bata kuma waiwayowa ba. Hankalin Mama kaw gaba d’aya ya gaza kwanciya. Damuwarta kawai shine tasan yanda Suwaiba ta samo irin wann arziki da ta gani tareda ita. Gaba d’aya ta ma mance da batun Tasi’u da halinda kud’ad’en shagon Abba ke ciki. Yau d’in ko asibiti wajen Abba ta gaza komawa. Tare take da yaranta Badi’a da Azeema yayinda suka baro Salima can wajen Abba. Tunanin Mama d’aya idan ta fice Suwaiba na iya zuwa gidan wajen ‘ya’yanta Shiyasa ko k’ofa ta gaza fita. Mama da yaranta Azeema da Badia Suna tsaka da aibata Suwaiba ‘yar k’ungiyar asiri gaban su Ummul suka soma jiwo hayaniya daga waje. Wann Ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Azeema tai saurin tare wani yaron cikin gidan da ya shigo a guje rik’eda gudan dubu a hannunsa yana ihun murna. Azeema ta rik’esa tana tambayarsa meke faruwa waje. Yaron yace “Umma ce.. Umman su Khulsum itace tazo da k’atotuwar mota tanata rabon kud’i a waje..” Mama dasu Azeema suka dubi juna. Babu shiri suka nufi waje a fujajan yayinda su Ummul ma duban junan sukai itada Khulsum. Take suma suka take ma su Mama baya. Mama da yaranta suka wani irin birki Har saida ya rage saura k’iris Mama bataci tuntub’e da wani yaro da ya nufo gida a guje yana ihu yana d’aga kud’insa sama. Daskarewa Ummul da Khulsum ma sukai suna duban kayan al’ajabi. Ikon Allah. Da gaske Umma ce ta fito cikin wann bak’ar shirgegiyar mota tana rabon kud’i ma Al’umman unguwar. Mutane kaw sai fitowa suke kusufa kusufa daga lungu da sak’o suna amsan kud’ad’en da Umma ke rabawa. A haka Umma ta k’araso gaban Mama. Ta murmusa tana dubanta “Tani ya muka sameku..” Mama ta kuma bud’e baki tana duban Umma jin irin gaisuwan rainin da tai mata. Wai Tani ya muka sameku.. Tani fah.. yau Suwaiba bata kirata da Yaya kaman yanda ta saba ba. Tani fah ta kirata dashi gatsau. Waima Yaushe "Suwaiba ta sami ‘yanci cikin gidan. Dan lokacin da aka aurota daga rugarsu babu kalan uk’uban da bata gallaza mata ba ga wauwauta ga shashashanci had’ida mugun k’auyanci da sukai mata dabaibayi.. Wai har Suwaiba ne ta waye yanzu.. Lallai ta yarda da hausar nan da ake cewa Shege na k’auye.. Idan bak’auye ya samu faraga yafi d’an birni iya shege.. Eh Tabbas yanzu ta shaida wann da idanunta.. Dan barikin da Suwaiba take a yanzu ko goggan d’an birni Wanda aka haifesa tsakiyar wayayyu bazai ba. Ko ita kanta bata tasa k’afa ta tsallake mijinsu dake kwance yana jinya ta tafi ta barsa ba. Sai yanzu take ganin ashe ita jaririya ce a bariki tinda ita saida shagon Isubu kawai tayi, tanata kumfan baki tana fad’i tashi ta raba gadon Isubu tun yana raye dan kar Suwaiba da yaranta su samu. Ashe Suwaiba kallon k’aramar ‘yar iska take mata. Ita a daidai wann gab’ar ma ta baje Rumfar barikinta." Muryar Umma ne Ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin da yai nisa ciki “Yauwa Tani nace ba ga wann ki kula da Abban Ummul sosai.. Naga Salima wajensa. Bansan mai kike a nan ba da har yanzu baki tafi wajensa ba. Idan akwai abinda ake buk’ata kina iya sanar Dani dukda dai duk wani abinda ya kamata a bayar an bayar. An canza masa d’aki ma ya koma b’angaren kud’i. Kira Salima zata sanar dake komai tinda tareda ita akayi duk wasu sauye sauyen. Tai maganar tana mai Ciro kud’ad’en cikin hamshak’in jakanta. Yacce kasan matar gida na bawa ‘yar aikinta sak’o. Mama tai sakare tana duban Suwaiba. “Ungo amshi mana..!” Umma tace tana mai kamo hannun Mama had’ida damk’a mata kud’ad’en ciki. Lokaci guda Umma tasa kai tana taku d’add’aya sai juya ma Tani mazaunai take. Kusan silalewa wajen Mama tai har saida Azeema ta tallafeta. Kasa motsawa Khulsum tai har Umma ta shige ta nan gabanta rik’eda hannun Ummulkhairi wacce ke biye da ita tamkar rak’umi da akala. Bata iya dawowa hayyacinta ba saida ta sinkayo muryar Mama na fad’ida Azeema ta rik’eta sosai bata iya tsayuwa kan k’afafunta. Cikin sauri Khulsum ta nufi bayansu Umma k’afafunta Har hard’ewa suke. Tana shigowa ta sinkayo muryar Umma dake rik’eda hannun Ummulkhairi tana fad’in “Ba sai Kin d’auki komai ba. Maza tashi muje direba yana jiranmu..” Katseta Khulsum tai da fad’in “Ina zaki Kai ‘Yaruwata Umma..?” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *17* *©️Sameena Aleeyou… * Katseta Khulsum tai da fad’in “Ina zaki kaita Umma..?” Muryarta Ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da furta “Umma shin abinda mutane ke fad’i gaskiya ne..? Umma dan Allah wacece ke..? Ina asalin Ummanmu da muka sani..?” “Banida lokacin Miki bayanin komai a yanzu Khulsum.. A halin da ake ciki ‘yaruwarki nazo d’auka..” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Ummulkhairi. Cikin azama Khulsum ta rik’e Ummulkhairi tana girgiza mata kai tana hawaye “A’a Adda kar ki bi Umma.. Adda dan Allah kar kije..” Dubanta Umma tai a yatsine kafin direba ya bud’e mata owners corner saida ta dubi yaranta na d’an lokaci kafin taceda Ummul idan kin gama kya shigo muje.” Daga haka ta fad’a mota kayanta. Khulsum ta kuma share hawayen da suka gangaro mata. Hannayenta cikin na Ummul take fad’in “Adda dan Allah kar ki bi matar nan.. Bamu san Ina zata kaiki ba.. Watak’ila rad’erad’in da mutane suke da gaske ne Adda.. Kinga Umma dai an canzata gaba d’aya bamu San Wacece ita ba a halin yanzu.” "Khulsum na hawaye take girgiza kai lokaci guda taci gaba “ Adda Ummul, Mai zai faru idan da gaske wajen matsafa zata kaiki.. Mai zai faru idan wani abun ya sameki.?”" "Ummul ta zame hannunta daga cikin na Khulsum tabi bayan Umma aka bud’e mata mota ta shige. Tana kallon Khulsum dake tsaye wajen hawaye na gangaro mata yayinda itama Ummul d’in hawaye ne ke gangaro mata. Ta rintse idanunta cikin zuciyarta take furta ‘Kiyi hak’uri ‘Yaruwata. Ya zama dole nayi wann. Babu abinda zai sameni face Allah ya k’addari faruwan hakan.. Dani dake mun San yanayin Umma a d’abi’a da halayya. Munsan matsalan mahaifiyarmu, Abu ne mai sauk’i a rud’eta.. mahaifiyarmu ce, ya zama dole na bita na gano hak’ik’anin abinda ke faruwa da ita. Domin kaw bazamu bari ta auka ma halaka ba munaji muna gani. In sha Allah komai zai daidaita K’anwata..’ Ta k’arashe tuanin nata wasu hawayen na kuma gangaro mata." A daidai gate d’in wani gida mai matuk’ar kyau da tsari motar tai horn. Khulsum da tuni ta d’ale acab’a tabisu a baya ba tareda saninsu ba. Tana ganin gidan da akai parking tace ma me mashin ya ajeta daga can nesa dan sai ta karanci gidan kafin ta danna kai ciki. Allah ya gani bazata bari mahaifiyarsu ta bada ‘yaruwarta ayi tsafi da ita ba. Driver na Ida parking Ya fito ya bud’e masu k’ofofin. Zuciyar Ummul sai tsinkewa yake tana duban Umma wacce ta koma mata tamkar bak’uwa. Umma ta dafata tana murmushi “Ki saki jikinki Ummul d’ita. Ban kawo ki yanda za’a cutar dake ba. Domin kaw ni mahaifiyarki ce. Tin haihuwarki burina shine rayuwarki ya cika da d’imbin alkhairai kaman dai yanda sunanki yake.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba “Kinga nan gidan.. Gidan da za’a share mana hawaye ne.. Gidan da za’a cika mana burinmu da yardar Ubangiji. Kukanmu yazo k’arshe Ummul.. Taho muje..” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Ummul. Amma sai Ummul ta tarje. "Umma ta juyo tana dubanta “Ummul ya kika ja kika tsaya, kinga nasan damuwarki bai wuce tafiya da mukai muka k’yale ’yaruwarki Khulsum ba. Sanin halinta, sanin duk abinda aka saka da ita sai ya lalace shisa bamu taho da ita ba.. Shige muje kinji.”" Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta “Umma gidan da za’a cika mana buri fah kikace… Umma Ashe har akwai mahaluk’in da zai cika ma wani mahaluk’i burinsa..? Umma idan kinga burin d’an adam ya cika ya bar duniyar nan ne..” Bata Kai aya ba Umma ta hanb’are mata baki “Ke ke meye haka.. Daina kira mana mutuwa a nan.. Nidai bazan Mutu ba sai burina ya cika in sha Allahu. Shiyasa nace da yardar Ubangiji. Kuma burina shine na ganki a d’akinki dik rintsi.. Koda k’arshen abinda zan aiwatar kenan a rayuwana..” "Jikin Ummul ya kuma yin sanyin Jin kamar mahaifiyarta ta riga ta zauce. Cak tai tsaye tana duban mahaifiyarta, ta rasa tausayin kanta ne ko tausayin mahaifiyarta take. Muryar wata mata ce ya dawo da Ummul daga duniyar tunanin da ta tafi “Ummul d’inmu ta iso..!” Ta fad’i kyakkyawan murmushi saman fuskarta." Ummul ta karkato tana duban matar wacce keta faman fad’ad’a murmushinta. Kafin tai wani aune ta k’araso ta rungumeta tana fad’in finally sun had’u. Lokaci guda kuma ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad’in maza ta shigo ta shirya mai hoto yanzu zai iso bada jimawa ba. Tambayarta kanta take Wacece wann matar..? Ina Umma ta santa..? Hoto kuma..? Wane irin hoto..? Meke faruwa ne wai..? Anya zata iya jurewa..? Anya batai gangancin biyo Umma ba kaman yanda Khulsum tace.. Amma idan mutanen suka cutar da mahaifiyarsu fah.. Zuwanta shine daidai ko dan tasan wani hali Mahaifiyarsu ke ciki. Jikin Ummul sai rawa yake yayinda Asshe taci gaba da janyota Har suka shige cikin gidan Umma na biye dasu baki har kunnenta. * A b’angaren Khulsum kaw tinda ta shigo gidan ta rasa wani b’angare suka shige. Nan ta hangi wani section daga farko. Ganin k’ofan wajen a bud’e Ya sanyata nufan k’ofan cikin tunanin nan su Umma suka shige. Saidai tana shiga wayam bataga kowa ba. Shiru alamun babu kowa. A hankali cikin sand’a ta soma jada baya zata fice. Saidai tana cikin sand’an da baya da baya taji ta bangaji mutum. A tsorace ta juyo zuciyarta na tsinkewa dukda bata bari tsoron Ya nuna saman fuskarta ba saima sauk’e huci da take. "Wani matashin saurayi ta gani ya zuba mata ido, hannayensa hard’e. Yana binta da kallo mai d’aukeda alaman tambaya." Taci gaba da huci tana hura hanci basu daina duban juna ba. “Ina ‘yaruwata.. Mai kuka mata.. Su waye ku.?” "Hilal ya girgiza kai kad’an “Excuse me, what are you talking about..? Wait, Who are you..? And what exactly are you doing in here.?”" Gajeren tsaki tai had’ada sa kai zata shige. Hilal ya kuma tare gabanta Yana girgiza yatsa alamun bazai barta ta fice ba har sai ta amsa masa tambayoyin sa “Oh wait. Dakata dakata. Ai bazaki fita ba sai kin sanar dani wacece ke. Daga ina kike..? Kuma mai ya shigo dake b’angare na.?” Ya d’an girgiza kai ganin har lokacin hararsa kurum take. A tunaninsa sabuwar mai aikin Amminsa ce a gidan. Ya katse shirun da fad’in “You must be new here? Basu fad’a miki masu aiki basa shigowa b’angarena ba saida izinina.?” Kallonsa tai daga sama zuwa k’asa jin ya kirata da mai aiki “Kaga Malam ka bani hanya na wuce. Banida lokacinka balle na tambayoyinka. Watak’ila ba kai nazo nema ba.!” Ta k’arashe kaman zata bangajesa ta shige. Ya d’an matsa Ya bata hanya ganin da gaske bangajesa zatayi. Lokaci guda yabi bayanta da kallo “Who’s she.? She doesn’t sound like mai aiki.” Ya d’an girgiza kai har lokacin yana duban k’ofan “She’s so tough.” Ya fad’i yana mai tab’e baki had’ida girgiza kai. * Suna shigewa d’akin Ummul ta juyo ta dubi matar amma bataga Umma tareda ita ba. Nan fah tsoronta Ya ninku. Asshe ta murmusa ganin har lokacin jikin Ummul bai daina rawa ba “Ki kwantar da hankalinki Ummulkhairi. Ki saki nan gidanku ne kinji.. Ga bathroom ki shiga kiyi wanka duk abubuwan buk’ata zaki samu cikin band’akin.” Asshe tasa kai zata fice kenan Ummul tai saurin kamo hannunta “A’a dan Allah kar ki cutar dani.. Dan Allah kar cutar da mahaifyata.. Na San tanada nata irin matsalar amma ita d’in ba mai kwad’ayin abin duniya bace.. Bansan mai ya sameta ba har ta mance damu da mahaifinmu dake kwance gadon asibiti ta zab’i wann rayuwar.. Kiji tsoron Allah kar ki cutar damu.. Na rok’eki..!” Ta k’arashe tana mai duk’awa gaban Asshe tana kuka sosai. Tallafota Asshe tai ta d’agota cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali take fad’in “Ki kwantar da hankalinki Ummul banida wani k’ulli cikin zuciyata taimakonku nai niyya.. Kar ki min mummunan fahimta..” Ummul taci gaba da kuka har lokacin jikinta rawa yake “Dan Allah kar ki cutar damu kar ki cutar damu..” Ganin gaba d’aya ta birkice yasa Asshe daka mata tsawa da fad’in “Ke ki mun shiru.. Yi mun shiru dallah.. Kar ki mun shashashanci a nan.. Shige maza kiyi wanka kafin masu kwalliya da mai hoto su iso..” Tai maganar tana k’ok’arin tura Ummul cikin bathroom Ummul tana tarjewa tana fad’in “A’a dan Allah.. Dan Allah a’a..!” Daidai lokacin Khulsum ta k’araso ta finciki hannun Ummul daga rik’on da Asshe tai mata “Sakar mun ‘Yaruwata.!” Ta fad’i da k’arfin gaske tana fincikan Ummul. Asshe tai tsaye tana duban Khulsum wacce tuni ta soma tambayar Ummul koda abinda ya sameta “Adda sun Miki wani abu ne.. Muje zo mu gudu.. Zo mu tafi..!” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Umma tana fad’in “Babu yanda zaki kaita.. Sakar mun ‘ya..!” Da mamaki Khulsum da Ummul suke dubanta. Khulsum tace “Umma Allah bazai baki damar cutar da ‘Yaruwata ba sabida tin tasowarta biyayya take Miki. Dani da ‘Yaruwata zamu tafi.. Zamu fice daga rayuwarki Umma idan Har haka kike so..” Muryar Khulsum ya soma rowa sosai “Umma me ya sameki..? Su waye wad’ann..? Menene gaskiyan rad’e rad’in da mutane suke akanki.. Umma shin kin manta da k’alubalen da ahalinmu suke fuskanta..? Shin har akwai abinda Yafi Miki ahalinki mahimmanci..? Umma Abba yana kwance a asibiti tsakanin mutanen da suke mafarki da burin ganin bayansa.. A daren da kika zab’i ki tafi ki barmu Har kusan kwana nayi a police station.. Duk ina kike Umma.. Ina kike sanda mahaifinmu yake tsananin buk’atarki kusan shi.. A kullum muna fita mu fuskanci mutane da maganganun da suke jifanmu dasu.. Yanzu kin zagayo kin d’auke ‘Yaruwata kin kawota nan ayi tsafi da ita.!” Bata kai aya ba taji sauk’an mari a k’uncinta. Ta d’ago tana duban Umma dake sakin huci. Lokaci guda take nuna Khulsum hawaye na gangaro mata “Ke baki san komai ba.. Baki san abinda ke faruwa ba.. Zo ki fice… Shiyasa tin farko ban gayyatoki ba dan nasan ke dai kam ba’a k’ulla alkahiri dake.. Zo ki fice..” Muryar Asshe ne ya katse su. Ta dubi Khulsum tace “Kar ki Fad’i abinda baki Sani ba yarinya. Duk fad’i tashin da mahaifiyarku keyi akanku ne da mahaifinku. Ina kuke a lokacin da kishiyar mahaifiyarku ta koreta tace taje ta nemo kud’ad’en da za’ayi ma mahaifinku jinya..?” Khulsum ta kaikaito tana mata wani irin duba “Wacece ke..? Me kike nema daga wajen mahaifiyata..?” “Ki kirani Sirkar ‘yaruwarki Ummul.. Domin kaw nan bada jimawa ba Ummulkhairi zata zamto matar D’ana.!” Da mugun mamaki dukansu suke duban matar da kuma Umma.. suka kuma juyowa suna ma Umma wane irin duba Wanda su kansu basu san duban me suke mata ba a halin yanzu. “Sirka..! Matar D’ah..!” Khulsum ta nanata tana duban Asshe da Umma kafin ta kuma juyowa ta dubi Ummul wacce ita kanta cikin rud’ani da duhu take. "Umma ta jinjina kai “K’warai kinji da kyau.. Wann matar da kike gani k’anwa take wa mahaifiyar mijin Ummul d’ita.. Wnn karan bazan bama wani k’ofa Ya lalata auren Ummul d’ina ba, ba ke ba Khulsum ba Tani da ‘ya’yanta ba ba kuma sauran munafukan mutanen layinmu ba.. Dan haka zo ki fice..!”" Ta k’arashe tana k’ok’arin rab’a hannun Khulsum dana Ummul amma sai taji wann karon Ummul ta rik’e hannun ‘yaruwarta k’am tak’i saki hawayen dake idanunta sun kafe sun daina zuba. Ummul ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tasu cikin rashin yarda “Har yanzu wann ne damuwarki Umma.. Ki aurar Dani kota halin k’ak’a..? Shin Umma rashin aurena ne kawai k’alubalen da muke fuskanta a rayuwa..?” Muryarta Ya soma rawa sosai “Abba yana cikin wann yanayi.. Ahalinmu suna cikin wann jarabawa amma ke damuwarki har yanzu guda d’aya ne Umma.. Shin Umma bakida sauran matsaloli na rayuwa ne sai wann..? Umma iyakacin kiman da nake dashi kenan a wajenki a matsayina na ‘yarki..? Iyakacin kiman da mahaifina yake dashi kenan a wajenki matsayinsa na mijinki.. Umma ina zaki kai girman hakkin Abba.. Ta Ya zaki shirya aurar da ‘yarsa yana kwance cikin wann hali.” Khulsum na hawaye ta katseta “Ta Ya zata shirya sayar masa da ‘Ya dai.. Adda dan Allah kizo muje.. Muje mu nemi agaji daga hukumar hisba wllhi Umma bata a hayyacinta..” Ta k’arashe tana kuka sosai. Ummul na hawaye take girgiza kai “kiyi hak’uri Umma.. Ki yafe mun amma.. amma Bana tunanin wann karon zan iya Miki biyayya.. Kiyi hak’uri zanbi ‘Yaruwata mu tafi.!” Tana ida fad’in haka ta janyo hannun Khulsum “Muje Khulsum..!” Umma ta dubi Asshe hawaye na k’ok’arin ciko idanunta “Kin gani ko kinga abinda nake fad’a Miki.. Wann ‘yaruwar tata ta kora mata mazan aure sunfi abinda suka fi da wann bak’ar Zuciyar nata. Kin gani hassada take da ita.. Toh wllhi wann karon ban shirya jin kunyan duniya ba.!” Tana huci take duban su Ummul da k’iris Ya rage basu fidda k’afafunsa daga cikin d’akin ba. Umma ta bud’e murya tace “Ummulkhairi.! Idan kika saka k’afa kika fice daga d’akin nan.. Ki mance kinada mahaifiya Suwaiba..! Wllhi wllhi idan Har ki kai sanadin da mutanen nan zasu ce sun fasa auren nan toh Babu ni babu Ke kuma ke ba ‘Yata bace daga wann lokacin.. Ki nemi wata mahaifyar amma ba ni ba..!” Ta k’arashe tana sakin huci. Cak Ummul ta tsaya ta kasa koda motsa k’afarta guda. "Gani haka yasa Asshe bud’e murya “Ba sai kin mata baki ba! Baza kuma a mata dole ba. Yardarta da amincewarta shi zaisa ayi wann Auren.” Ta maidoda dubanta ga Ummul “Har yau ba’a biya kud’in surgery da za’ayi wa mahaifinki ba. Anyi masa komai, an canza masa d’aki. Yana samun duk wani kulawa saidai kud’in aiki ne kawai yai saura.. Kinsan dalili..?”" Ummul ta dubeta cikin tsananin sanyin jiki “Sadakin ki shine kud’in da za’a biya ai ma mahaifinki aiki Ummulkhairy..” "Asshe taci gaba da takowa gaban Ummulkhairy, su duka biyun suna duban juna “Nasan za’a iso wann gab’ar. Shiyasa ban bari an biya kud’in aikin ba. Har sai nida Ke mun gana da juna. A halin yanzu, ki sani Aurenki shi kad’ai ne zai ceci mahaifinki. Domin kuwa sadakinki da zamu biya shine kud’in da za’a masa aiki a ceci rayuwarsa.. Wuk’a da nama na hannunki... Yanzu idan kika ce baki amince ba. Ni kuma zan janye komai ku nemi wani hanyar da za’ayi wa mahaifinki aiki..”" Umma ta kuma bud’e murya ganin Asshe tayi nasaran dakatar da Ummul. “Wacece matsalar ahalinmu Ummul. Kece matsalar mu. K’addararki shi yai silan kwanciyar mahaifinki.. Idan Har akwai wacce tafi cancanta tai sadaukarwa mai girma wa mahaifinku.. Toh ki sani kece kika fi cancanta Ummul.!” "Khulsum ta soma girgiza kai tana duban Ummul “A’a Adda, dan Allah karki amince.. Akwai na gari da yawa. Na Allah basa k’arewa.. Dan Allah kar ki amince da wann auren na rashin galihu Wanda ko sanin mijin bakiyi ba.” Ta k’arashe tana ci gaba da janyo hannun Ummulkhairy alamun tazo su tafi. Amma sai taji Ummulkhairy ta doge. Lokaci guda take girgiza kai tana duban Khulsum “Kiyi hak’uri Khulsum.. Na zab’i ceto rayuwar mahaifina koda shine abinda zanyi na k’arshe a rayuwata. Zanyi auren.. Zan auri ko waye Umma ta kawo dan na ceci rayuwar mahaifina.. Gaskiyar Umma ne. Watak’ila idan nayi auren komai zai zo k’arshe. Watak’ila matsalar ahalinmu zai k’are. Watak’ila ni ce matsalar kaman yanda Umma tace.”" Khulsum na hawaye take girgiza mata kai alamun a’a. Cikeda k’osawa Umma ta dubi Khulsum. Kinji abinda tace “Ita d’in ’ya mai biyayya ce ba irinki ba. Sakar min hannun ‘ya kafin ki mata sanadin abun alheri da ya sameta.” Khulsum ta girgiza kai tana duban Umma. Lokaci guda ta soma jada baya. Tana duban Ummul hawaye na gangaro masu su duka biyun. ** A can gida kaw Mama tana zaune tsakar gida ta rapka tagumi ga su Azeema da Badia sai dadd’age Kayan masarufin da Suwaiba ta kawo suke. Yaran Salima suna gefe an had’asu da Kayan mak’ulashe. Babu yanda Mama batayi ba kar su tab’a Kayan Suwaiba Kayan Shan jini amma babu wacce ta kula mama cikinsu sai Salima wacce ta tayata da tagumi. Gashi Salimar ta basu labarin irin kud’ad’en da Umman ta kashe a asibiti. Amenity ma aka maida Abba executive room kula ake basa na musamman. Su Azeema kam har so take washe gari yayi ko Umma zata sake zuwa ta rok’eta Aron tufafin kece raini taje bikin dangin mijinta da suke dashi a satin. Mama ta kuma sauk’e kakkauran ajiyan zuciya tana tuna Suwaiba a baya Suwaiba fah data maidata bora cikin gidan farkon aurota wai itace yanzu duniyar nan ta juya akeyi da ita. Gashi har ‘ya’yanta na cikinta sun fara son Suwaiba da tarayya da ita. Ikon Allah Lallai ta yarda babu mayaudariyar aba irin duniya. Yanzu zata rud’eka ka zata tanayi dakai anjima kad’an ta sake ta Kama wani a Barka bakin Tasha. Ita yanzu haka tanaji tana gani Suwaiba zata ci gaba da zuba mata bariki a gida. Lallai bataci ta zama ba. Ya zama dole ta san abinyi. ** Abuja Saukowa yai cikin shirin fita waya manne kunnensa “Family dinner?” Ya d’an girgiza kai yana ci gaba da sauk’owa “This is not part of the agreement Mommy. You know we can’t stand each other.” "Shiru yai alamun yana sauraro daga mahaifiyarsa “Fine, I’m on my way there. Amma wann zai zama na k’arshe.” Daga haka katse kiran yai." Dareen ta k’araso tana dubansa “Going somewhere.?” Tace tana mai kamo hannayensa murmushi saman fuskarta. “To my Mom’s” Ya fad’i a tak’aice sai kuma ya k’ara da “Don’t wait for me for dinner.. Maybe I’ll be back late.” Ya fad’i yana shafan b’angaren fuskarta guda. "Ta d’an jinjina kai “Haidar, don’t you think it’s high time you introduce me to your family. After all, we’ve been married for months now.”" Hannayenta ya kamo cikin nasa “I don’t think it’s necessary. Those people mean nothing to me. I don’t even consider them family.. Na rubuta yarjejenyar rabuwa dasu. Rabuwa ta har abada.” "Tai masa k’uri tana dubansa, Ya d’an janyota cikin jikinsa suna fuskantar juna sosai “You.. And only you.. You are the only family I have.”" Murmushi ta saki zuciyarta zallan k’aunarsa. Ta shafi gefen fuskarsa tana fad’in “And I’ll love you till my last breath.” Ya murmusa had’ida manna mata light kiss. Lokaci guda Ya kuma mata Sallama kafin ya fice. Tabi bayansa da kallo cikin d’aurewar kai. This is not like him. Ya canza gaba d’aya. Mutumin da ya tsana ai masa zancen iyayensa shine yanzu yake zuwa wajensu akai akai.. Sann mai yake nufi da ya rubuta yarjejeniyar rabuwa dasu..? Shin Wai meke shirin faruwa ne..? Haidar ya canza gaba d’aya wani sabon kusanci na neman shiga tsakaninsa da ahalinsa.. At the same time yana cewa ya kusa datse duk wata alak’ar dake tsakaninsu. What exactly is going on..? Kasa nemo amsar da Tai ya sanyata k’arasawa saman kujera ta zauna tana kuma fad’awa duniyar tunani. ** Ita dai tana Jin yanda makeup artist d’in keta faman zuzuta kyaun da tai amma bata tanka ba. Dan physically ne kawai take wajen amma tinaninta da hankalinta basu a wajen. Duban fuskar nata take cikin madubi Wanda dukda makeup d’in ba mai tsanani bane. Amma abinka da wacce bata saba ba sai take ganin kaman an canza mata kamanni ne . Dama tin can ita ba gwanar kwalliya bace balle yanzu da take tsaka mai wuya. Bata tab’a tsammanin Umma zata "tafi da nisa har haka ba. Tana jin sanda su Umma da Aunty Asshe suka shigo sai faman zuzuta kyaun da tai suke. Lafaya ne Wanda kallo guda zaka masa ka tabbata Ya amsa sunansa kalan peach Wanda Ya dace da skin color d’inta da bai cika haske ba haka nan kai tsaye baza’a kirata bak’a. sai black long sleeve shirt daga ciki, an kwantar da lallausar bak’ar sumarta da Ya sha gyara daga gefe." Asshe ta k’araso da sauri ta mik’ar da ita tsaye “Wow! lallai za’a haifo mana Fulata shuwa. Yauwa ‘yar albarka Uwar alkhairi.. Maza muje masu hoto suna parlor suna jiran fitowarki.” Ummul ta d’ago ta dubi Umma amma sai taga Umma ta kauda kanta gefe alamun bazata saurare ta ba. Cikin sanyin jiki ta soma jan k’afafunta tana biyeda Asshe wacce ke rik’e da ita. Can k’asar zuciyarta bata komai sai ambaton Allah domin ya shiga lamuranta. Suna fitowa parlorn suka tadda masu d’aukan hoto har kusan mutum uku. Tai tsaye tana duban masu hoton wanda k’arasowarta kawai suke jira komai nasu ya zama ready. Ji tai kaman kar ta k’arasa wajen amma sai maganar Aunty Asshe ya fad’o mata “Kud’in Aurenki shine kud’in aikin mahaifinki” Ta d’an d’aga k’wayan idanunta sama cikin k’ok’arin hana hawayenta zuba. Tamkar kazar da k’wai ya fashe ma a ciki haka take takowa cikin parlorn. Ta k’arasa ta zauna yanda masu d’aukan hoton ke nuna mata. Lokaci guda zuciyarta na karanto mata ‘Komai da kike gani na faruwa akwai dalilin faruwarsu Ummulkhairi.. Ita rayuwa jarabawa ce gaba d’ayanta. Allah yayi tanadi wa masu hak’uri kaman yanda yayi alk’awari.. Watak’ila kasancewar Umma a matsayin mahaifiya a gareki shine babban k’alubalenki a rayuwa.. Kiyi hak’uri kiyi mata biyayya.. Har abada bazaki tab’e ba.’ Da wann batu na zuciyarta taji k’warin gwiwa na d’an zuwa mata. Umma ce mai nuna mata styles d’in da zatayi har gyara mata zama take tana fad’in tai murmushi kyaunta ya bayyana. Kuji fah. Izuwa lokacin Ummul ta daina mamakin Umma sai addu’a da take wa mahaifiyar nata cikin zuciyarta. Aka d’auki hotuna aka gama dikda cikin idanunta akwai alamun hawaye a duka hotunan amma kam tayi kyau TabarakAllah ma sha Allah inji Aunty Asshe. Fad’i take d’ansu yayi dacen mata. Bayan Asshe da Umma sun keb’e Umma tace “Toh yanzu meye abu na gaba Hajja Asshe.?” Asshe tace an tura ma mutumin da zai wanke hoto can Abuja ya kai ma ‘yaruwata. Yau zasuga Amaryarsu Ummulkhairy a hoto kafin su ganta a zahiri. Umma ta lumshe idanu had’ida sauk’e ajiyan zuciya. Lokaci guda ta d’aga hannuwa sama “Ubangiji kasa an dace.. Allah yasa Ummul d’ina ta dace.. Allah na rok’eka ka jefa k’aunarta cikin zukatansu a kallon farko..” Asshe ta murmusa ta dafa Umma “Anma dace in sha Allahu. Kinsan dai ance wai gani ya kori ji Shiyasa za’a aika masu hotunan Ummul su gani su shaida amma ‘Yaruwata da D’anta basuda matsala. Yanzu Abu na gaba sai maganan kai lefe da saka rana.. Inaso duka ayi su a gobe ne. Amma kafin nan dole mu samu magabatan Ummul ayi magana.. Kinaga dangin mahaifinta zasu amince su bamu aurenta.?” "Umma tai shiru kaman mai nazari. Cikinta ya bada wani sauti k’uuu.! Ita sai yanzu ma ta Tina da za’azo wann gab’ar. Ta soma ‘yan kame kame. Sai kuma ta nusa tace “‘yanuwansa basa jituwa dashi abinki da gidan da ‘yanubanci ya raba kai. Yaruwarsa mace ce guda d’aya tak, kuma itama Sun raba gari tinda jimawa. Kuma mace ai bata bada aure. Kaf ‘yanubansa ne gidan Wanda ba wani ganinsa da gashin ido suke ba..” Idanun Umma suka kawo ruwa murna na Neman komawa ciki take duban Asshe “Toh.. toh.. Yanzu mai zai faru idan suka k’i amincewa su bada auren Ummul..?”" Saurin katseta Asshe tai “Haba Suwaiba kin faro abu da zafinki kar ki badani mana… Keda kike da babban makami.. Bakiga yanda kika aje Kishiyarki a yanda ya Kamaceta bane..? Ai kud’i Sune jigon rayuwar nan Suwaiba. Idan kud’i na aiki toh na tabbata Miki zasu bada auren Ummul ba tareda wani b’ata lokaci ba dan nayi imani kaf d’insu fama suke da rayuwar nan ta yau..” Umma ta jinjina Kai “Kuma fah kince wani abu dan ko yau d’in nan da naje nai rabon kud’in ina ganin Baballe ya amshe Wanda na bawa D’ansa ya soke a aljihu.. Kunya ce ta hanasu nasan suma da Sun shiga layin rabon kud’in..” Asshe tace “Ah toh kin gani ko. Ke fah yanzu sai abinda kika ce a wann gidan.” Ta k’arada “Ita kuma Ummul zata zauna a nan a mata ‘yan gyare gyare na amare.. Mai gyara na musamman na d’auko daga can gida Maiduguri.Kuma kinga dai yaro ne d’an gayu Wanda rabin rayuwarsa turai ne Ya saba cin karo da matan turawa da wayayyun mata da suka goge. Kinga kuwa dole duk wacce zata je matsayin matarsa ta wanku da kyau ta kuma k’ara samun gogewa gudun kar a samu matsala dukda ko a haka aka kai masa Ummul na tabbata baza’a samu matsala ba amma kinsan ance idan kanada kyau ka k’ara da wanka. Kinsan sha’anin d’an yau.” Ta d’an gyara tsayuwarta “Sann zamanta a can gidan naku wani tsautsayin na kuma giftawa Wanda bazamuyi fata ba. Kinga Har kawo wann lokacin kishiyar ki batasan abinda ake shiryawa ba.” Umma tai karaf tace “Ai Kinga wann ‘yaruwar tata da ta fice ko bala’inta kad’ai Ya isa ya iya jawo wani matsalan tinda kinga a nan take ce mata su gudu. Toh kafin ta koma can na shafa cikin dare naji sun gudu gwara ta zauna a nan asiri na a rufe a kula da ita idon masu ido bai ganta bakin masu baki bai tofa ba.” Asshe ta jinjina kai “Cikin kwanaki k’alilan komai zai kammala da yardar Ubangiji Ummul d’inki ta shige d’akin aurenta mafarkin ki ya zama gaskiya.” Umma sai ta fara hawayen farin ciki tana fad’in shikenan burinta yana gab da cika. Allah zai cika mata wann buri nata daga k’arshe. Asshe ta girgiza kai kafin ta fice ta bawa Umma waje tai mai isarta. A haka Ummul ta k’araso ta tadda Umma wacce itama hawaye ne kwance saman fuskarta. Ta k’urawa mahaifiyarta ido. Sai kuma tasa bayan hannunta ta share hawayen dan taji kaf tattaunawar da su Umma sukai. “Alfarma d’aya zan rok’eki Umma.” Ta fad’i cikin rawar murya. Umma ta dubeta wann karon hawaye ne saman k’uncinta. Ummul taci gaba “Ki kaini wajen Abba na gansa nai masa Sallama kafin ku killaceni a wann gidan.” Umma ta jinina mata kai tana sakin murmushi ta kamo hannayen Ummulkhairi “Zamuje Ummul. Zamuje kiga mahaifinki. Sann zan baki labarin duk abubuwan da suka faru dalla dalla tin daga lokacin da Tani ta fatattake ni naje na nemo kud’ad’den jinyar mahaifinku.” Bayan Umma ta labarta komai dangane da had’uwarsu da Asshe da irin duk wani taimako da Asshe Tai mata. Da buk’atan Asshen na nema ma d’ansu aurenta. Jinina kai Ummul tai ba tareda tace komai ba dan kalamai sun k’are saman harshenta. Abinda yai mata saura hawaye ne Wanda suma d’in batada tabbaci idan basu kusan k’arewa ba. Driver ne ya d’aukesu Ya kaisu Har asibiti wajen Abba. Mama dake zaune a haraba tana hangosu ta mik’e cikin sauri ta nemi wajen b’oyo ta b’uya yayinda Ummul da Umma suka shige d’akin. Umma ta dubi Ummulkhairy tace “Zan barki ki gana da mahaifinki Ummul. Ku biyu.” Ummul ta jinjina mata mai tana goge hawayen da suka kwararo mata. "Ummul zaune gaban gadon mahaifinsu Wanda idanunsa ke lumshe, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata, abubuwan da suke faruwa da ahalinsu sai gifta mata suke a k’wayar idanu. Ta d’aura hannunta guda saman na Abba. Cikin rawar murya take furta “Abba tinda ka kwanta komai bai k’ara daidaita ba.. Umma ta canza Abba..” Sai kuma tai shiru tana share hawayenta “Abba koda bana nan… Ban sani ba ko zamu sake had’uwa ba ko bazamu sake had’uwa ba. Abba ka yafe wa mahaifiyata a bayana. Dan Allah ka yafe ma Umma.!” Kuka ya hanta ci gaba da magana." Da k’yar kukan nata Ya tsagaita kafin taci gaba “Abba bazanso wani wanda ba kai ba ya aurar dani. Watak’ila Umma ta hana maka wann damar ne domin ceto naka rayuwar.” Muryarta yaci gaba da rawa “Abba banida wani zab’i.. Rayuwarka na kan gab’a a nan.. Watak’ila wann shine maslahan ahalinmu. Watak’ila komai zaizo k’arshe. Watak’ila ni ce matsalar. Watak’ila idan nayi nesa daku zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu tsakanin ahalin. Abba zanyi duk wata sadaukarwa sabida ahalina. Ka yafe mun Abba. Kuma ka yafe wa mahaifiyata .” Ta k’arashe tana mai kifa kanta gefen Abba hawaye na kuma kwararo mata. Mama dake lab’e bayan window ta waje taji duk abinda Ummul tace. Wato Suwaiba ta shirya aurar da Ummulkhairi ne a sirrance..? Shin wann shine dalilin canzawan Suwaiba..? Aiko idan haka ne sai taga ta yanda za’ayi wann aure.. Idan Suwaiba tasan wata bata San wata ba. Toh amma ta ya zata b’ata auren tinda Suwaiba bata nuna masu mijin Ummul d’in ba.? Kar dai Suwaiba ta samo attajiri ne ma Ummul d’inta.. Idan har al’amra sukaci gaba da tafiya a haka kenan fah Suwaiba zata zamto sarauniya a gidan. Sai abinda tace. Harta ‘ya’yan cikinta su Azeema sai Sun gagareta. Tin yanzu ma komai ya canza balle abubuwa suci gaba da tafiya a haka.. Uwa uba Har kawo wann lokacin basu saka Tasi’u a idonsu ba... Dawowan Suwaiba dik shi ya karkata masu hankali ta kasa aiwatar da komai gameda b’cewan Tasi’u. Toh inaga Abubuwa sunci gaba da tafiya a haka.? Yanzu ita fah zata tashi a tutan babu kenan ga Suwaiba ta dawo da sabon sauyi.. Mama ta koma gefe saman benci ta zauna had’ida buga uban tagumi. Kallo d’aya zaka mata ka fahimci duniyar tai mata atishawan tsaki. Sai faman sauk’e tagwayen ajiyan zuciya take tana canza salon tagumin ta. Babu babban abinda ya bata takaici kaman da ya kasance yanzu dik abinda suke ci daga wajen Suwaiba ya fito.. Shikenan Suwaiba fah ta amshe girman nata. Abinda yai saura kawai shine Suwaiba ta umarceta ta soma kiranta da Yaya. Saiga Mama na hawaye tana fad’in har abada bazata bari Suwaiba tai nasara akanta ba. Idan abinda zata aiwatar k’arshe shine hana yuwan auren Ummulkhairi ta shirya yi. Da dai ta bari Suwaiba tai galaba akanta gwara tai komai dan nasara nata ne da yaranta ba na Suwaiba da nata ‘ya’yan ba. Da wann tunani ta mik’e tagajan magajan domin kaw zama bai ganta ba. * Kan Ummul na kife gefen mahaifinta tana ci gaba da cazgan kuka mai ban taisayi. Umma ta k’araso ta dafata. Ummul batace komai ba Har Umma ta ta k’araso wajen. "“Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan mahaifinki ba har sai ranan Aure gudun kar wani abu ya gifta. Kindai san matsalarki da abubuwan da mukaita fuskanta a baya na fashe fashen Aurenki. Wann karon ban shirya ba ma wani k’ofa ya lalata Aurenki ba. Naga Tani bata nan a nan, zan zauna wajen Abbanku Har Tani ta dawo. kuma zan karanto masa komai koda bazai bud’e idonsa ba na tabbata kunnuwansa da zuciyarsa zasu saurareni.”" Ta murmusa tana duban Ummul “Na tabbata a yau mahaifinki ya farka ya ganki a d’akin Aurenki zaifi kowa farin ciki sann wann kad’ai Ya isa ya zama silan yaye damuwar dake k’unshe cikin zuciyarsa.” Dubanta kurum Ummul Tai ba tareda ta iya cewa komai ba. Har yanzu dai a idon Umma itace matsalar ahalinsu da k’addararta. Ta kuma juyowa ta dubi Abba hawaye suka kuma gangaro mata. A hankali ta isa ta tofa masa addu’o’i kafin tasa kai ta fice jiki a mace. ** Abuja.. Zaune suke gaba d’aya a nan lambun dake farfajiyan gidan. Mommy Daddy harma da Anisa. Mommy dai bata sama bata k’asa gaba d’aya kana ganinta zaka hango tsantsan farin cikin da take ciki. Ta dubi Anisa tace maza ta sami one of the mades su shirya wajen cin abincin mutum guda. Daddy ya dubeta “Are you expecting someone.?” Mik’ewar da Anisa zatai ta hango shi ya nufo garden d’in. Looking handsome as always. Zuciyarta yai wani irin yankewa. "Mommy ta fad’ad’a murmushinta tana nuni da Haidar dake k’arasowa “Oh! He’s here already.” Ta maido da dubanta ga mijinta “Ya kamata mu rinka samun lokaci irin haka na musamman domin ahali. After all, amarya za’a kawo mana very soon.”" Baice komai ba yaci gaba da abinda yake. Dan yanzu ya kula Kwaise batada zance sai na auren D’anta. Haidar ya k’araso Mommy na masa sannu da zuwa. Sai nan nan dashi take. Wani sabon kula da soyayya take nuna masa abinda bata masa a baya ba. Kaman tayi ma wofi haka ya d’auki abun tinda yasan ba dan Allah take ba. Koda Anisa ta kawo plate karb’a Mommy tai tana k’ok’arin serving d’insa sai haba haba dashi take tana tambayarsa me za’a zuba masa. "Cikeda k’osawa Haidar Ya rik’e hannunta Ya amshi plate d’in “Mommy please that’s enough, I can do it myself. I’ve been doing it since childhood.”" "Jikinta ya d’anyi sanyi ta soma Tina ita dai tin tasowarsa tin yarinta bata tab’a tambayarsa yunwan cikinsa ko lafiyarsa ba. Masu aiki da Nannies Sune suka San lafiyarsa, cinsa ko shan sa. Har yayi ciwo ya gama bata san yayi ba kuma ba matsalar ta bane. The only abu da take tambaya ta kuma tada hankali akai shine karatunsa na boko da sakamakon da zai birge mahaifinsa. Idan kuwa bai kawo sakamakon da zai birge mahaifinsa ba ranan zai wuni ne a d’aki mai duhu kuma a kulle cikin tsananin horo." Mommy ta gyara zama ganin table d’in Ya b’ata shiru sai sautin cutlery dake tashi cikin plates. Ta d’an murmusa tana duban Haidar “Ya labarin aiki.. Ina nufin sabon project d’in naku.. Kun fara ne.?” "Yasan so take tai creating hiran da zai had’asa magana da mahaifinsa. Ya d’an girgiza kai kad’an “Still ironing out the details..” Ya d’ago yana dubanta sosai tinda yasan tasan komai “In a couple of months, Mommy. Let’s say two to three months.”" K’arasowar wata mai aiki rik’eda k’aton frame a rufe Ya katse Mommy. Mai aikin ta k’araso cikeda ladabi ta tsaya nan bayan Mommy rik’eda frame d’in tana sanar da ita security ne Ya shigo dashi. Mommy ta jinjina Kai tana mai nuna mata yanda zata ajiye. Ta maidoda dubanta ga Ahalinta tana kuma fad’ad’a murmushinta “Na had’a mana wann cin abincin ne a tare domin na gabatar mana da wani mihimmin abu. Musamman gareka Haidar.” Ta k’arashe tana mai isa jikin frame d’in. Ta shiga bud’ewa sannu a hankali tana mai furta “Kyakkyawar Amaryar mu. Matar D’anmu Haidar. Sirkarmu wacce zata zamto silan dunk’ulewar ahalinmu.” Cak ya tsaya da abinda yake. Lokaci guda yana mai matse fork and knife dake rik’e cikin hannunsa. Bai iya janye idanunsa daga saman plate d’in ba haka nan bai dubi hoton da mommy ke nuna masa ba wacce ta ambaceta da matarsa. Girgiza kai Daddy yai yana tunanin matarsa ta zauce da wann auren da take yunk’urin yima d’ansu. Ya d’auki tissue had’ida goge bakinsa. Ya dubi Mommy kafin yace “Are you in your right state of mind. What’s the meaning of this Kwaise.?” "Mommy tace “Gani ya kori ji Engr. Matar Haidar ce. Idan ba a hoto ba nasan bazaije ya ganta ba har sai Randa aka kawo mana ita gidan. So kafin a kawota yak’i amincewa yace gaibu na auro masa. Gwara na samu dalilin kafa hujja. Look kalla kaga, zasu dace da Haidar.. Asshe ta iya zab’e.” Ta k’arashe sai duban hoton take tana murmushi." Daddy dai kallon wacce ta samu matsala yake mata. Lokaci guda ya girgiza Kansa “I’m done here.” Yai maganar yana mai barin wajen. Zuciyar Anisa yaci gaba da bugawa tana mai duban hoton. Cewa da Mommy tai Asshe ta iya zab’e shine keta yawo cikin kumnuwanta. Mai kenan hakan ke nufi.? Amminta ce ta zab’o wa Haidar mata.? Mahaifiyarta ta turota gidan ne dan taci amanarta ta nema ma Haidar auren wata daban a garin Kano.? Ko kuwa mai Ammi take nufi da ita.? SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *18* *©️Sameena Aleeyou… * "Haidar ya k’arisa gaban mahaifiyarsa yana mata duban mamaki. Ya jinjina Kansa kad’an har lokacin dubanta yake “Had I known, akan wann abun kika kirawoni nan. I wouldn’t have wasted my time coming here.” Yai maganar yana nuni da hoton Wanda ko kalla baiba. Daga haka sa Kai yai zai shige amma sai yaji kaman Wanda aka ce ya juya ya dubi hoton." Bazai iya ce ga kamanninta ba ko wani abu mai Kama da wann. The only thing he noticed cikin hoton shine k’wayar idanunta masu cikeda rauni ga kwantattun hawaye ciki. Yanda kasan magen dake cikeda tsoro. Ya janye idanunsa ba tareda ya kuma ceda Mommy komai ba yasa kai ya fice. Mommy tai saurin bin bayansa cikin k’ok’arin dakatar dashi. "Anisa kaw kasa janye idanu tai daga barin duban hoton. Ita wann d’in wacece.? A ina Amminta ta samota.? Maiyasa Mommy ke yunk’rin had’a aurensu da Haidar Dikda cewa Haidar d’in baya so. Cikin azama ta mik’e tana Jin kuka na zuwa mata. Ta gaji ta gama zaman gidan, bazata zauna a kawo wata cikin gidan da sunan matar Haidar ba. Gwara ta tafi ta koma gida dik abinda Ammi zata k’ulla ta k’ulla Akan idonta dan tayi imani bazata bari wann auren ya tabbata ba. Idan ma anyi it won’t last long. She promised. Table knife d’in dake hannunta ta jefa jikin hoton Ummul Ya kuwa samu daidai tsakiyar fuskar hoton. Sai sakin huci take ta mik’e ta shige cikin gida kaman zata fashe." Tana shiga ta soma kiran layin mahaifiyarta. A zuciya take had’a kayanta cikin suitcases. Ammi tana d’agawa Anisa taci gaba “Wow congratulations Ammi. Aikinki yana kyau. So wann shine dalilinki na turo ni gidan nan..? Ki nemar wa Haidar auren wata can garin Kano.. Wato baki so na zame Miki matsala cikin abinda kike shiryawa shisa kika tarkaso ni kika turo ni nan..?” Ta jinjina Kai tana mai ci gaba da huci “Ammi I thought plan d’in shine nazo nan dan na Sami kusance da Haidar da kuma ahalinsa.? But what did you do Ammi.. You sent me here for you to carry out whatsoever your plan might be. Zan dawo gobe goben nan.. Zan dawo garin Kano. Kuma ina mai tabbatar Miki na shirya b’ata dik wani shirinki Ammi.” Ta k’arashe cikin huci. Daga d’aya b’angaren Asshe ta katseta “Idan ke shashasha ce ki dawo Anisa. Abinda baki sani ba shine wann auren da kikaga na dage ina nemar ma Haidar ba ji ba gani ma ke nake Anisa.” Baki sake Anisa ta girgiza Kai “Wane irin ma ni kike Ammi bayan gashi na gani da idona kin turo picture d’in yarinyar da kike nemar ma Haidar Aurenta. C’mon Ammi mai kike nufi.?” Asshe ta murmusa kad’an “Bazaki fahimci komai ba sai nan gaba kad’an Anisa. Amma wann auren kaman fansar Haidar nake nemar Miki dashi. Idan har ba’ayi wann auren ba bazaki tab’a iya samun Haidar ba Anisa. Har abada.” Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ammi auren da kike nemar ma Haidar fansa kaman ya.? Ammi mai hakan yake nufi.? Ni fah ban fahimci komai ba.” Asshe ta kuma jinjina Kai “Bazaki fahimci komai a halin yanzu ba Anisa. Amma nan gaba kad’an zaki gane duk abubuwan da nake fad’a miki. Idan har kina so Haidar ya zama naki sai kin bada goyon baya d’ari bisa d’ari ma wann auren. Ki bawa Aunt d’inki k’warin gwiwa akan auren d’ari bisa d’ari. Idan har kina son D’anta sai kinso wann auren Anisa. Ke idan an kawo matar ma ki shiga jikinta sosai ki tabbata ta samu kusanci da Haidar.” “Ammi kin kuwa ji abinda kike fad’i. Ammi how can I possibly do that.? Maganar mutumin da nake so the most fah ake a nan. Ta ya zan so ya samu kusanci da wata bani ba.?” "Asshe ta murmusa kad’an “Ni mahaifiyarki ce, kuma nafi kowa so ki kasance cikin farin ciki Anisa dan haka kiyi abinda nace idan har da gaske kina sonsa. Nan bada jimawa ba zai zama naki. Amma fah sai kin tabbata wann auren nasa ya yuwu.”" Anisa ta girgiza Kai kad’an “Ammi wai meyasa dole sai anyi auren. Can’t he just marry me instead.?” “Ke bana son shashanci kika auresa yanzu kashe kanki zakiyi.. Na fad’a Miki Fansar Miki shi zanyi da wann auren wai meyasa mik’ewa shashanci ne.?!” Da mamaki Anisa tace “Kashe kaina kuma Ammi dan na auresa.?” "Asshe Jin ta kusan yin b’aranb’arma ya sata sassauta murya tace “Anisa ni mahaifiyarki ce, kuma ki yarda dani I want nothing but the best for you. So idan nace ki yarda dani ma ke nake wann yak’in ki yarda kawai. Zaki mallaki Haidar. Zai zama naki Watak’ila nan da watanni k’alilan kinji koh. So ki kwantar da hankali ki and trust your Ammi.”" "A hankali Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya “Shikenan Ammi, if you say so. I trust you, hundred percent.”" Bayan sun Ida wayar zama Anisa tai tana tunanin maganganun mahaifiyarta. Ta ya zata goyi bayan wann auren.? Abun da kamar wuya. Ta mik’e jiki babu wani k’wari ta shiga unpacking kayanta. ** "Yana tsaye k’asan shower ruwan na sauk’owa tin daga cikin sumarsa har zuwa jikinsa, saurin bud’e idanunsa yai Wanda suke a lumshe sakamakon hoton fuskar yarinyar da ya gaza b’acewa a kwanyarsa da kuma k’wayar idanunsa. Ba wai fuskar nata yake gani cikin k’wayan idanunsa ba. Dan bazaice ga kamanninta ba. A’a kwantattun hawayen da shi kad’ai ne yai noticing a hoton yake gani. Sau d’aya tak ya kalla, maiyasa ya kasa cire hoton cikin idanunsa, meyasa duk rufe idanun da zai sai yaga idonta masu d’auke da hawaye.. Maiyasa ta amince da aurensa.. Meyasa hawayenta kawai ya iya noticing.? Shin dole aka mata.? Shin Wacece ita ma.? Shin tasan shirin Mommy Akan auren cewa AUREN WATA UKU zasuyi kuma dalilin auren shine mahaifinsa ya mallaka masa project. Shin tasan duka wad’ann ta amince da aurensa.? Is she that lowlife.? Wacece zata amince da irin wann wulak’antaccen auren. Does she have any idea who he really is.? Does she even know what she’s getting herself into.? Tambayoyi da yawa Wanda idan ba ita ba babu mai amsa masa. Take yaji zuciyarsa ta soma raya masa ‘Maybe she’s aware of everything.. Maybe kaman yanda Mommy tai deal dakai Akan auren haka itama tai deal da ita.. Mommy zatayi komai dan abinda take so. He knows his mother har cinikin auren zatayi. What if wann yarinyar cinikin aurenka tayi" da Mommy.? Take yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi. Ji yai ya kuma tsanarta. Ya tsani mutumin da zaiyi komai sabida kud’i da abin duniya. Sauri sauri ya fito daga shower d’in dan baiso yaci gaba da tunanin. Yana fitowa ya tadda Dareen har ta kwanta. Ya k’arasa shirinsa kafin ya isa gefe ya kwanta. Saidai kwanciyar sa da kad’an ya soma sinkayo sautin Dareen a hankali kaman na mai kuka. "Ya d’an mirgino yana dubanta, nan yaga har kaman shesshek’a take. Side lamp ya kunna ya mik’e daga kwamcen da yake “Hey.” Ya furta a hankali." "Jin bata amsa ba ya sanya shi matsawa kusanta ya mirgino da ita, nan yaga hawaye Sun wanke mata fuska. Baison ganin hawaye tin yana yaro. Watak’ila hoton yarinyar can da ya gaza b’ace masa a k’wayar ido ma sabida hawayen da ya hango ne cikin idonta. He hates to see people cry.. A nashi tunanin ba abu k’arami bane zaisa mutum kuka. A lokacin yarinta duk irin abubuwan da yai going through baya iya kuka koda yana son yi. So he believes idan har baiyi kuka lokacin yarinta lokacin da ya kamata ace yayi ba dukda irin abubuwan da ya fuskanta a rayuwa Lallai ba Abu k’arami bane zaisa mutum kuka." “What’s wrong.?” Ya tambaya cikin kwantar da murya idanunsa tar kanta. "Dubansa tai sai kuma ta girgiza Kai “Haidar I don’t know.. Ban sani ba, I.. I just feel like I’m losing you somehow..”" "Zuba mata ido yai tausayin ta fal k’irjinsa. She’s right, a kwanakin kaman ya nesanta Kansa da ita. Above all, wann auren shirin ko yace auren yarjejeniya da Mommy ke yunk’urin yi masa yasa ya d’auke masa hankali da tunani.. He feels like he’s not being fair to her.. Koda ace bai mata irin son da take mishi. She’s still his wife kuma ta cancanci kula na musamman daga wajensa. Hannayenta ya rik’e cikin nasa suna fuskantar juna. Yayinda Dareen taketa addu’an Allah yasa tarkonta ya d’anu. Bata isa tace ga weak point d’insa ba tinda tasan shi mutum ne da ba kasafai ake iya karantar yanayinsa ba. What she’s sure about shine shi Mutum ne mai tausayi wanda ta fahimci haka from his actions, especially towards mutane masu rauni. Yanada tsananin zafi saidai a wasu lokutan tausayin masu rauni da yake dashi yakan rinjayi zafin sa. Da wann takanyi amfani ta tatsa duk wani information gameda rayuwarsa. Ta kula yanzu kaman ya daina sanar da ita abubuwa da dama. Ya fara komawa kaman dai Haidar d’in da ta soma sani daga farko kafin aikin aisiri yai tasiri akansa. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in." “I have been dealing with so many things lately… That I even lost sight of what’s more important.. I mean you..!” Gajeren murmushi saman fuskarsa ya kuma rik’e hannayenta cikin nasa yaci gaba da fad’in “But I’ll make it up to you.. Just choose a place from the map.. Let’s go for a vacation.” "Surprisingly take dubansa “Really, vacation..? Na zab’a duk yanda nake so from the map.?”" Murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake jinjina mata kai “Just mention the place.. Any place you have in mind.” “OMG.! I love you.. I love you so much..” Ta fad’i tana mai fad’awa jikinsa sabida murna. “I’ve never been to Cuba. Let’s go to Cuba. Zan duba mana best Resort da sukeda shi.” Ta fad’i murmushi saman fuskarta. "Shid’inma murmushin yai kafin ya jinin Kai “Alright Cuba, Lets explore Cuba then.”" Rungumesa ta kumayi zuciyarta na raya mata ta mance komai ta daina binciken komai tabi mijinta suje su sha soyayyarsu. "A b’angaren Haidar kaw cikin zuciyarsa yake ayyana wann shine maslaha. A daidai lokacin da Mommy zata kawo masa yarinyar can matsayin mata zata shafa ne taji baya nan.. Bazai dawo ba sai bayan wani lokaci, zai timing lokacin da zasu fara gudanar da project d’in kafin ya dawo k’asar." ** Kano Da tsananin mamaki Hajjah Fannah ta dubi agogo Jin da gaske buga mata k’ofa ake. K’arfe shad’aya na dare har ta gota. Ta fito da kyar dan har kawo lokacin bata wani Jin k’arfin jikinta. Khulsum ta gani tsaye k’ofar gidan ga alamun hawaye saman fuskarta. “A’ah! Khulsum. Lafiya? Ina kika fito cikin Daren nan..?” Khulsum bata iya amsa mata ba sai ma wani sabon kukan da ta fashe mata dashi. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Khulsum suka shige cikin gidan. Ruwa ta soma kawo mata tace ta sha ta samu natsuwa. Ta d’an dubeta “Khulsum ina Ummul..? Meke faruwa ne wai.. Inji ba wani Abu bane ya kuma faruwa.?” Khulsum ta saka bayan hannunta ta share hawayen “Hajja Adda Ummul ta tafi.. Umma ta saida ita.. Tabi Umma.. Ta amince da auren da Umma ta shirya mata.. Ta zab’i tayi biyayya ma Umma bisa auren da ta shirya mata a bayan idon mahaifinmu.. Su d’in basuda wani banbanci da Mama da yaranta masu burin ganin bayan Abba..!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka. Hajja Fannah ta dubeta da mamaki “Aure kuma Khulsum. Aure Ummul zatayi.?” Khulsum ta jinjina mata Kai har lokacin jikinta a mace yake. Sai Hajja Fannah ta nemi duk wani ciwon da takeji ta rasa. Taci buri ma d’anta Wanda ko shakka babu shima ya auka ma soyayyar Ummulkhairin. Saidai kana naka Allah na nashi kuma na Allah shine daidai. Jiki a sanyaye ta dubi Khulsum “Wanene mijin da zai auri Ummul.?” Khulsum ta girgiza mata Kai tana mai tab’e baki “Bana tsammanin ko ita kanta Umma da ta had’a auren ta sansa.” "Sauk’e ajiyan zuciya Hajja Fannah tai, wani irin batu ne ita kanta Umman nasu bata san mijin da ta nemo ma Ummul ba. Ta yaya haka zai kasance.? Ummul ta wahala a rayuwa bazataso ta kuma fad’awa wani wahalar ba. Lokaci yayi da za’a dakatar da mahaifiyar Ummul. Idan ahalin su Ummul bazasu iya dakatar da Suwaiba ba zata nemi taimakon manyan Unguwa musamman mai Unguwa da commette d’insa asan halinda ahalin Malam Isubu ke ciki ayi k’ok’arin dakatar da Suwaiba tun kafin mai aukuwa ya auku." Ta dubi Khulsum tace “Kici abinci ki kwanta ki huta na Miki alk’awari in sha Allah zanyi iyaka abinda zan iya dan naga mahaifiyarku bata salwantar da rayuwar Ummul ba da izinin Allah. Khulsum ta jinjina mata Kai ba tareda ta iya cewa komai ba. Hajja Fannah dai mamaki ne ya kasa saketa. Sai sak’awa da warwarewa take tana tinanin toh waye mijin da Suwaiba ta kawo ma Ummul Wanda ita kanta bata sanshi ba. A haka ta kwana cikin daren tareda zullumin idn har auren Ummul ya tabbata batasan ta yanda zata soma sanar da tilon d’anta Wanda ta jima tana binsa da batun aure yana kaucewa sakamon k’azafi da mahaifinsa ya jefasa dashi tin yana d’an watanni uku a ciki. Daga k’arshe Hisham ya samu macen da take tunanin zasu samu daidaito sai ga kuma abinda ke shirin faruwa. Tabbas Zuciyar D’anta zai karaya. Washe gari ma Khulsum wajen mahaifinta ta yini dan ko ta kan ahalinta bata kuma bi. A cewarta dukansu basuda banbanci da juna. * Washe gari masu kawo lefe Sun samu isowa gidansu Ummulkhairi. Tin daga bakin layin ake k’irga motocin dake shigowa domin kawo lefen Ummulkhairi. Su Azeema sukai layi suka jeru nan tsakar gidansu suna duban masu shigo da lefe. Tin suna k’irga akwatuna har dai suka hak’ura da k’irge suka zuba ma sarautar Allah idanu. Azeema ta tab’a Salima tace “Yaya Salima anya wann ba kwari suka saya gaba d’aya ba..!” Salima ta sauk’e ajiyan zuciya “Ni na ma rasa abin fad’i.” Gajeren tsaki Badia tai “Mtseww aikin banza.. Wann da gani kasan kayan haya ne ba lefe ba..” Tana ida fad’in haka ta d’age labulen d’aki ta shige. Azeema ta dubi Salima tace “Kin ganni nan wallhi baza’ayi hidimar nan babu ni ba.. Gwara na shiga a dama Dani dan nasan duk rintsi sai an sallameni da atampa da jaka da takalmi na samu na yak’an dangin Habibu. Salima ta tab’e baki “Amma Azeema matsalarki kad’an ce..!” Tana ida fad’in haka itama ta fad’a d’akin mahaifiyarsu. Duk suka zuba tagumi suna Jin yanda hayaniya ke ci gaba da tashi. Zancen guda d’aya ne Ummul tayi dace. Azeema kaw tuni ta nufi bakin farandar Umma yanda ake baje kolin kayan lefen Ummul. Sai zuzuta kyaun kayan take tana fad’in ‘yaruwarta tayi goshi.. Umma ta dubeta tace “Kar ki damu Azeema dake za’a tafi kai amarya.” Azeema ta daka tsalle tana fad’in “Wllhi Umma ni har zaman d’aki ma sai na mata ai.. Irin wann kayan bajinta kayan alatu haka. Kai ina ma nice mai sa’a irin Ummul..” Anzo yanda Umma take so. Taji ana ambaton Ummul d’inta da mai sa’a.. Umma ta shiga washe baki tana jin yanda mutane ke fad’in K’warai Ummul tayi goshi ita d’in mai sa’a ce. Haka akaita shigo da zuk’a zuk’an akwatina da sunan lefen Ummulkhairi. Kan kace me labari Ya karad’e unguwa. "Umma naku fah ba’a sama ba’a k’asa, uwar amarya da kanta. Duk magulmatan unguwar masu tsegumin Ummulkhairi ta kasa auruwa Sun dawo b’angaren Umma. Mama taga tijara a wann ranan, dan tuni Umma ta amshe girman nata kama daga cikin gida har zuwa wajen mutanen unguwa Wanda a baya suke aibata su." Uwa uba da sukaga su Hajja Asshe matsayin iyayen mijin da zai auri Ummulkhairi dan tuni d’aya daga cikin kawayen Asshe ta soma bada bayanin ko su waye su. Hakan ya kuma sanyar ma kowa gwiwa dan mijin Asshe dai ba b’oyayyen mutum bane a birnin Kano da kewaye. Hakan Ya kuma tabbatar masu Umma dai ba hark’ar shan jini ta fad’a ba kaman yanda duk sukai zato a baya. Allah ne ya kashe ya basu. Lokacin su ne yayi. Azeema sai kallon Hajja Asshe take sanda taji tana yabon surkarsu Ummul. Sai duban dank’ara dank’aran gwal d’in dake zube wuyarta da awarwaron dake hannunta take. Ga wani k’amshin ‘yan gayu na musamman da matan suke. Dan Asshe ita da K’awayenta suka kawo lefen. ** Yanda Mama taga rana haka taga dare. Ko asibiti wajen mijinta ta kasa komawa tinda taga an kawo lefen Ummulkhairi. Ta mik’e ta shiga safa da marwa a d’an tsukikin d’akinta tana neman hanyar da zatabi ta hana yuwan wann aure. Wani tunani ya fad’o mata. A fili ta furta Dije. Dije ce kawai zata sa wann aure Ya watse. Cikin sauri ta isa tana bubbuga k’afar Badia wacce tinda Tasi’u Ya b’ace ta dawo kwanan gida. "“Badia, ke Badia.. Tashi mana..!”" Badia ta mik’e tana mutsuka idanu da kyar “An fara shagalin bikin ne..?” “Shagalin bikin Ubanki..!” Mama tace tana danna mata dak’uwa. Badia taja tsaki tana turo baki gaba “Haba Mama ni wllhi na zata shagali aka soma inata mafarkin mun tafi Kai amarya an raba mana motoci matsayin tukwici kin wani kama kin tashen.” Mama ta kuma danna mata harara “Dan ubanki murna kike wann annobar zatai aure bayan ke ga naki auren yana sama yana k’asa. Allah kad’ai yasan yanda wann macucin mijin naki ya gudu.. Ba abun muyi k’ararsa ba mu tona ma kanmu asiri…” Badia tace “Mama Tasi fah ba guduwa yai ba. Ni na tabbata yana can yana juya mana kud’ad’enmu sai yayi arziki kaman mijin da zai auri Ummul kafin ya dawo. Na fad’a Miki ko jiya fah Munyi waya dashi.” Katseta Mama tai tana mai kuma danna mata wani ashar d’in “Ashe ke babbar shashasha ce. Yacce kika san Suwaiba ce ta haifeki.. Ba dan ina tsoron tonuwar asirina ba ace na saida gadon mijina tun kafin ya mutu wllhi da na maka k’arar wann d’an iskan mijin naki a Kotu..” Badia ta shek’e da dariya “Toh ai saidai ki maka k’arar wofi Mama. Dan Tasi dai ba ganinsa zakiyi ba sai Ya zama hamshak’in Mai arziki ya dawo mana da kud’ad’en mu.. Wai baki so muyi arziki kaman nasu Ummul ne..” “Idan kika sake kira mun Ummul a nan zan zagi gawa ka k’i kabarin uban nan naki dake kwance. wann aure kuma ba yinsa za’ayi ba dan alwashi na d’auka. Bani wayarki..” Ta k’arashe tana mik’a mata hannu. "Badia ta dubeta sai kuma ta mik’a mata “Mama me zakiyi da wayata, ni dai dan Allah kar ki kira Tasi ki zagesa dan nasan halinki..”" Bata amsata ba sai ta mik’a mata nata wayar “Ungo nemo min lambar Dije.. Allah Sa dai bata canza layi ba..” Badia ta dubeta galala “Mama Inna Dije kike nufi ko wa..?” “Dije k’anwar Ubanku Isubu kira mun ita..” Badia tace “Mama me zaki fad’a mata a tsohon daren nan.. Sanin kanki ne Inna Dije da Abba harma da ahalinsa sun raba gari tun da jimawa..” Mama ta jinjina kai “Waye sila..?” Badia tai k’uri tana dubanta. Mama taci gaba “Suwaiba da bakinta ta fad’a cewa ‘Yarta Ummul ita tai sanadin barin Fa’iz duniya dan haka zan kira Dije na sanar da ita komai na kuma kunna mata recording d’in da kikai a wayarki lokacin da Suwaiba ke fad’in Ummul ce tai Sanadin Fa’iz.. Sai muga ta yanda za’ayi ai wann aure tinda naga su ‘yan uwan mahaifin naku an rufe bakinsu da kud’i.. Dije ita kad’ai ce zata saka birki ma wann aure..” Ta k’arashe tana kecewa da dariyar cin nasara. Tana ayyana yanda za’a wayi gari da labarin an fasa auren Ummulkhairi. Saidai duk Neman wayar Inna Dije da suke basu samu ba cikin daren. Akan dole Mama ta hak’ura da niyyan washe gari idan Allah ya kai rai zata nemi wani hanyar dan bazata hak’ura ba. Duk rintsi sai ta cimma Dije an wargaza shirin wann auren. ** "Khulsum ita kad’ai ta kwana wajen Abba. Tana zaune gefensa hawaye na gangaro mata. Hannunta saman nasa “Abba.. Abba na Kai hak’uri. Allah ya jarabceka da cuta kaman yanda ya jarabceka da ahalinka. Abba Allah masu imani yake jarabta. Ina rok’onsa da ya baka lafiya ya kuma baka ikon cin jarabawa.” Taci gaba da kuka tana mai kwantar da kanta gefe da mahaifinta. A hankali taji kaman Abba na motsi. Khulsum tai saurin d’agowa tana dubansa, sai taga kaman bakinsa na motsi. Ta matsa kusa dashi cikin sauri tana kai kunnenta saitin bakinsa dan jin abinda yake son fad’i." Tai saurin d’aura hannayenta saman nashi “Abba gani a nan. Khulsum ce Abba.” Amma sai taji kaman yana ambaton Ummulkhairi cikin maganan da bai iya fita sosai. "“Ummulkhairi.!” Khulsum ta nanata a hankali. Cikin sauri ta dubi Abba “Abba zanyi k’ok’arin dakatar da ita. Bazan bari Umma ta cimma makahon burinta Akan ‘Yaruwata ba. Abba zan dakatar Adda Ummul kaji..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin mik’ewa. Sai kuma ta juyo ta dubi mahaifin nasu Wanda babu kowa wajensa sai ita. Toh idan ta fice wani abun ya taso fah,.? Ko ma wani abu ya samu Abba.? Kasa ficewa tai sai komawa da tai ta zauna tana tinanin taje ta dakatar da ‘yaruwarta ne ko kuwa ta zauna da Abbanta ne.? A hankali ta lumshe idanunta tana jin wani abu mai ciwo na tasowa daga cikin k’irjinta. Batajin har abada zata kuma iya kiran ahalinta da sunan ahali. Nan taci gaba da sak’awa tana warwarewa taje ta sanar da Ummul Abba ya ambaci sunanta ne kokuwa ta k’yaleta da makauniyar biyayyan da take k’ok’arin yima Umma." ** Asshe da gogaggun k’awayenta Sun samu hallarowa da Kayan lalle nik’i nik’i. Dan dama sassafe aka taho da Ummul d’in gidan. Umma tace saidai azo gidan mahaifinta a d’auketa kaman yanda yake a al’ada bayan an d’aura aure. Mama ta zuba ma sarautar Allah ido ganin matan nan harda masu algaita suke tafe suna masu rakiya. Sai Asshe ta isa ta kamo hannun Umma suna tik’an rawa tare ta b’alle bandir ‘yan dubu dubu ta shiga lik’a ma Umma. Su Maman Sahal magulmata Unguwa da sauran ‘yan cikin gidansu Ummul kaw fitowa sukai suna tayasu tik’an rawa sai damben kwasan kud’ad’en da Asshe ke lik’awa suke tsakaninsu da masu algaita. "Mama ta kuma rapka uban tagumi. Ikon Allah yanzu Isubu na kwance gadon asibiti Suwaiba take wann bariki a cikin gidansa. Idan sunanta Tani wann aure baza’ayi ba. Ta mik’e ta cikin k’ok’arin dakatar da masu algaita tana fad’in irin fashe fashen auren Ummul da bak’in k’addara da yake biyeda rayuwarta. Idan har suna nema ma d’ansu lafiya kar su had’asa da annoba. Sai aka maida Tani Mahaukaciya dan babu Wanda ya d’auki zancenta. Iyayen ango kam ma ko kallo bata ishesu ba suka sa aka fito masu da Amarya Ummul Asshe na shafa mata lalle da kanta da turare iri daban daban, harda wasu tufafi irin na al’adansu da suka zo dasu aka rufa ma Amarya Ummul." Bayan komai ya kammala Asshe ta juyo ta dubi Tani “Munyi abinda ya kawo mu a yanzu. Sai kuma mun zo tafiya da Amaryar mu..!” Har zata shige ta kuma juyowa ta dubi Tani “Sai hak’uri haka zakiyi ta cin karo damu cikin gidan nan idan ba amaryarmu muka d’auke muka ba.!”Daga haka sa kai sukai suka fice k’awayen Asshe na raka Tani da wulak’antaccen kallo. Su Baba Dauda da Baballe k’annen mahaifin Ummul suka take ma Asshe baya kaman zasu bangaji Tani. Nan suke sanar da Asshen indai Ummulkhairi ce Sun bawa D’ansu duniya da lahira Allah basu zaman lafiya Ya kad’e fitina. "Asshe ta murmusa tana gyara mayafinta kana ta dubi Baba Dauda tace “Ma sha Allah. Alhamdulillah, naji dadin wann batu kuma akwai sauran aikenku na nan tafe..”" Baba Dauda suka dubi juna suna washe baki. Asshe taci gaba “Iyayen Aliyu zasu iso nan bada jimawa ba. Zasu kawo kudin aure da duk wani abinda ake buk’ata na Al’ada. Babu b’ata lokaci nake so a d’aura auren nan..” "Baba Dauda yace “Alhamdulillahi.. Shikenan, komai ta kankama.. Allahu Akabar.. Oh ashe dai yarinyar nan zamu ga ranan aurenta.. Isubu dai Allah yayi yana kwance yana jinya za’a aurar da d’iyarsa.. Allah Ya k’ara rufa mana asiri. Ai shi auren shine mafi a’ala a gareta.”" Baballe sai gyada kai yake yawa k’adangare “Wann gaskiya ne.. An samu maslaha kan matsalar yarinyar nan daga k’arshe. Yau ko farkawa Yaya Isubu yai yaga Ummulkhairi bata gidan zaifi kowa farin ciki. Musamman idan yaji d’akin mijinta ta tafi.” Asshe ta jinina kai tana kuma bud’e handbag d’inta. Nan ta ciro kud’ad’e ta mik’a masu “Ga wann kuyi amfani dasu ku canza tufafin jikinku. Dan Allah ko ready made sai ku saya dan wllhi duk wari kuke. Kun San Manyan mutane ne zasu taho amsar auren D’anmu. Bai kamata aga sirakanmu cikin daud’a ba. Baballe yana wage baki yake fad’in “Wann na jikina ai sabuwa ce Hajiya. Fitar sallah ce..” Yana maganar yana d’ago rigar jikinsa. Kaman zasu kwanta gaban Asshe haka suka sa hannu suka amshe kud’ad’en suna mata godiya. Akan idon Mama komai ya auku. Ta dubi Badia dake gefenta “Ki shige muje dan ubanki.. Wllhi bazan zuba idanu a aurar da Ummul ba. Tinda mutanen nan basu jin bari ko da k’afa ne zan tafi garin Dutse na sami Dije da wann labari tinda na gaza samun wayarta.. Wllhi idan ina numfashi baza’ayi wann aure ba..!” "Badia ta kuma riketa “Mama na yaushe, baki alk’alami fah ya Riga ya bushe. Mutanen nan babu abinda zaisa su fasa aura ma D’ansu Ummul.. Kina ganin yanda Hajiyar can ta gwasaleki dan girman Allah kawai ki hak’ura aci hidiman biki damu..”" Mama ta kuma danna mata ashar “Bazan bari Suwaiba da munafukan k’annen mahaifinku Su aurar da Ummul ba.. Dije kuma idan taji recoding din da zan kai mata zata waiwayi gida ko dan ta amsar ma D’anta hakkinsa.. Kinga dole wann aure Ya watse kaman yanda sauran suka watse.!” Badia tace “Idan kuma kika kira Inna Dije reshe ya juye da mujiya fah Mama..? Ina nufin idan Inna Dije tazo ta fahimci kin saida kaf abinda D’anuwanta ya mallaka kin ci gadonsa tin yana raye fah.. Um um fah Mama.” Mama ta kuma harzuka “A gidan uwar naci gadon nasa bayan wann shegen mijin naki ya gudu da kud’ad’en. Ai saidai a kama mijinki..” “Ta Ina za’a kamasa tinda babu Wanda yasan yanda yake yanzu. Ke fah za’a kama Mama..” Badia ta fad’i haka cikeda gargad’in mahaifiyar tata. "Mama na huci take fad’in “Dije bazata san wann batu idan ba kece da shegen bakinki kaman ta’adin wuk’a zaki sanar da Dije ba. Ki zuba min idanu kiga yanda zan kassara auren Ummulkhairi, idan na gama da wann sai naji da D’aniskan mijin nan naki maras mutunci. Dik yanda zai gudu wllhi sai na nemo sa na amshe kud’ad’e na idan yaso auren naki ya mutu..!” Tana ida fad’in haka tasa kai fuu ta koma cikin gida tana sakin huci. Bataga ta zama ba dole tayi shirin tafiya garin Dutse. Ameen" Badia kaw tab’e baki tai had’ida koma cikin gida akaci gaba da hidima da ita. ** Misalin k’arfe 4:30pm ‘Yanuwan Mommy Maza masu karb’an auren suka samu isowa gidan su Ummulkhairi ciki harda mijin Asshe. Ba tareda wani b’ata lokaci ba suka soma gudanar da abinda Ya had’asu. A yammacin wann rana aka d’aura auren Ummulkhairi Yusuf tareda angon ta Aliyu Aliyu Maitama bayan cika cikan k’ulla aure sun tabbata. A nan k’ofar gidan mahaifinta. Cak Hajja Fannah tai tsaye daga waje tana sinkayo sunan mijin da ya auri Ummul wanda masu algaita keta faman nanatawa. Aliyu Aliyu Maitama. Sunan da har abada bazai tab’a shafewa a duniyarta da na d’anta ba koda kuwa tayi k’ok’arin kauda sunan. “Aliyu Maitama.” Ta nanata a hankali. Sai kuma ta sake fad’in “Aliyu Aliyu Maitama.?” Shin Aliyu da ta sani ne ya Auri Ummul ko kuma d’ansa ne.? Ko kuma wasu daban ne basu ba. Take rayuwar ta na baya ya soma dawo mata. Rayuwarsu a gida Maiduguri. AUREN WATA UKU da tayi da Aliyu Maitama. Rabon da suka samu a tsakanin WATA UKU Wanda yak’i aminta da wann rabon tin yana ciki baizo duniya ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Meke shirin faruwa.? Bata Ida tunanin ba ta hango motoci ‘yan d’aukan amarya Sun samu k’arasowa. Zuciyarta ne ya kuma yankewa. Koda ace shekaru sunja bazata mance kamannin K’anwar kishiyarta Kwaise ba wacce da ita aka k’ulla komai. Bakinta na rawa ta furta “Asshe..!” Ji tai k’afafunta na Neman gaza d’aukarta. Da gaske Asshe k’anwar Kwaise take gani ana mata kirari da uwar ango Aliyu Haidar Maitama. Kenan Ummul d’an Kwaise ne ya aureta.? Kenan Ummul D’anuwan D’anta Hisham da suka had’a uba d’aya ta aura.? Ta ya zata soma sanar da Hisham Ummul d’an Uwansa da baisan dashi ba ta aura.? Bata kuma sanin meke faruwa ba.? Bata kuma sanin ina take jefa k’afafunta ba sai ganin kanta da tai cikin gidanta. Zama dirshan tai wani irin kuka na taso mata. Meke shirin faruwa da ita. Badai baya ne ke k’ok’arin dawowa cikin rayuwarta ba. Ta jima da binne bayanta. Ta kumayi alk’awari bazata waiwayi baya ba. Sann uwa uba bata shirya sanar da D’anta Hisham asalinsa ba. Sosai jikinta ke rawa sanda ta soma tuno rayuwarsu na baya. ** Mama da Tunda taga manyan mutane da sunan sunzo shaida auren Ummulkhairi bata iya jura zama ba. Nan tai azaman tafiya garin Dutse dan ta sanar ma Dije abinda ke faruwa. Koda an d’aura auren tasan idan ta isa ga Dije ta kuma kunna mata rikodin d’in nan dole a warware auren koda kuwa an d’aura. Sann a yanda tasan zafin Dije ko birnin Sin aka Kai Ummulkhairi sai ta bita ta fanshi mutuwar tilon d’anta. Tashan mota ta nufa. Tana tafe tana tsaka da wann tunani ta hangi Mutumin k’auye da akai cinikin shagon Malam dashi ya kuma saya shagon. Cikin Mama ya bada wani irin sauti na tsoro. “Yauwa Yallab’ai gatan can.. Itace Tani Uwar gidan Malam Isubu. Kuma itace ta saida mun shago.” Mama taja wani irin wawan birki tana duban ‘yansanda da suka nufota. Zuciyarta sai tsinkewa. Ta yunk’ura zata gudu saidai babu hali. Mutumi ya k’araso yana fad’in babu yanda zata gudu sai ta masa kashin kud’ad’ensa. Mama ta fara kururuwa tana fad’in ita wllhi bataci kudi ba Tasi’u ne ya gudu da kud’ad’en. Bakauye yace baisan wann zance ba shidai kawai a tafi ofishin ‘yansanda. ** "Sauri Khulsum take kan faman zabgawa gashi ko taro batashi balle sisi, da k’afa taketa nik’owa ga uban nisa. Alla alla take ta isa ta dakatar da wann aure. Ji rai Sam bazata bari Umma ta salwantar da rayuwar ‘yaruwarta sabida san zuciya irin nata. Burinta kawai ta cimma Ummul kafin Umma ta aurar da ita." "Hilal daketa faman zabga gudu dan ya samu ya cimma kwatancen da Amminsa ta masa, bai fata a d’aura auren bai isa location d’in ba. Auren d’anuwansa Haidar wanda shi kanshi Haidar d’in bai samu halarta ba. Bai fata ace shima ya rasa auren ko dan ya samu abun goranta ma Haidar cewa shi ya karb’ar masa aure." Kaman daga sama Khulsum taji a wanketa da tab’o. Taja tai birki tana duban jikinta yayinda Hilal ya buga uban tsaki ya bud’e motar ya fito yana duba yanda tayun motarsa suka b’aci da tab’o. Allah ya gani ya tsani datti ya b’ata masa mota. Da datti ya tab’a masa Mota gwara ya b’ata masa kaya. Hilal irin wad’ann mutanen ne da zasu iya yini maka suna aikin k’alk’ale abin hawansu dan shi bai yarda car wash sun iya wanke mota ba. “Whattt.!” Ya furta da k’arfin gaske yana zagaye motar daga duk’e yana duban yanda duk tab’o ya wanke tayun Motar zuwa fuskar mota. “C’mon this is not happening.. I spent half of the day ina wanke motar nan.. What the hell..” Muryar Khulsum dake tsananin huci ne ya dakatar dashi “Malam kai ta mota ma Kake.!” Tai maganar cikin sakin huci. Hilal ya d’ago yana duban mai maganar kasancewar idanunsa rufe suke cikin bak’in gilashi hakan yasa bata hangi k’wayar idanunsa ba. “You again.?” Ya furta yana mai nunata. Sai ya zame glasses d’in dake idanunsa Wanda hakan ya bawa Khulsum daman ganesa. Da gaske wann d’an rainin hankalin take sake gani gabanta Wanda ya kirata da mai aiki a gidan da Umma ta Kai Ummul. “Makaho ne kai.. Ko bakaga aika aikan da ka mun bane.?!” Ya shiga binta da kallo sama da k’asa dan tsaf ya ganeta tun a kallon farko. Ita ce dai intruder d’in da ya kama a b’angarensa 2 days back. “Kece zan tambaya ko makauniya ce ke.. Why do you keep on getting on my way.? Are you stalking me..?” Har lokacin idanunsa akanta. Khulsum ta kuma tunzura. Ta soma takowa kusansa tana sakin huci kai kace rufesa da duka zatai. Hilal sai ya soma matsawa da baya. Khulsum ta nunasa da yatsa bata daina sakin huci ba “Kayi sa’a sauri nake banida lokacinka balle na fad’a.!” Kafin ta rufe baki suka soma sinkayo wata murya tana rok’on ‘yansandan da suka tasata Gaba tana fad’in su mata rai wllhi ta tuba kar su tafi da ita. Tasi’u zasu nemo shine b’arawo shine ya gudu da kud’d’en. Khulsum ta juyo da mamaki had’ida furta “Mama.!” Aiko Mama tana Jin haka ta bud’e murya sosai tana fad’in “Khulsumu ki ceceni kar ‘yansandan nan su tafi dani.. Wllhi ba guduwa zanyi ba ba tashan mota zan tafi ba.. Wllhi banci dukiyar mahaifinku ba.. Ke shaida ce Khulsum ni ce nan ke kula da mahaifinku.. Kar ki bari a tafi dani babu mai kula da Abbanku bayan ni..!” ‘Yansandan suka tasa k’eyarta cikin mota suna fad’in ta shige suje station. Ta Adana duka bayananta tai masu a can.. Mama na kururwa tana duban Khulsum tana fad’in ta ceceta aka jefata cikin motar ‘yansanda. Khulsum ta yunk’ura zata bi bayansu tana fad’in su dakata amma inaa Sun wuce. Ta nufi kwalta a guje tana yunk’urin tare abin hawa saidai babu Wanda yai yunk’urin tsaya mata. Kaman daga sama taga motan d’an rainin hankalin nan yaja ya tsaya gabanta “Shiga muje.. shiga mubi bayansu kafin su b’ace mana..” Tai tsaye tana dubansa kaman mai tunanin shiga. Hilal ya kuma danna mata horn alamun tai sauri ta shiga kar su rasa motar ‘yansandan. Sauri sauri ta bud’e marfin motar ta shige tana fad’in subi bayansu. Nan da nan Hilal ya kwashi motar suka bi hanyar da motar ‘yansandan tabi. ** A can gidansu Ummul kaw Sanda aka soma buga algaita ana shelan an d’aura auren Ummulkhairi sai jikin Umma ya d’auki rawa. Duniyar ta shiga juya mata. Gani take kaman ba gaskiya bane. Kaman d’aya ne daga cikin mafarkan da ta saba. Wai yau an d’aura auren Ummul d’inta.. Ummul tayi aure. Sai Umma ta yanki jiki ta fad’i hankulan mutane suka yo kan Umma. SameenaAleeyou… *AUREN WATA UKU.!* *19* *©️Sameena Aleeyou… * Ruwa aka kawo za’a yayyafa ma Umma Asshe ta dakatar dasu ta bud’e bakin jaka ta shiga lik’a ma Umma kud’i had’ida umartan matan da ke gefe da su rangad’a ma Umma gud’a cikin kunne. "Aiko firgit Umma ta mik’e tana tambayan da gaske ne an d’aura auren Ummul, Ummul d’inta dai. Sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in bata tab’a tsammanin zataga wann rana nan kusa ba." Masu lallashi nayi masu tausayi nayi masu murna nayi harma da masu takaici. "Toh komai akace d’an lokaci ne, shi kuma aure baka tab’a yinsa sai lokacin da Allah Yace. No matter how hard you try or how many relationships make. Zai faru ne kawai a lokacin da Allah ya nufa. Yau dai Allah ya k’addari za’a d’aura auren Ummulkhairi bayan tulin fad’i tashi da mahaifiyarta taitayi dan dai taga ‘yar tata tayi aure. Dukda irin kawo sadaki ana janyewa saka rana ana d’agawa harma da amshe lefe yau Allah ya nufa ya kuma k’addari za’a d’aura auren." "‘Ya’ya musamman mata tamkar k’wai suke hannun iyayensu. Babu Iyayen da zasu so wani abu na k’i bisa tsautsayi ko tilastawa ya fasa wann k’wai da suke rik’e dashi cikin kula da kaffa kaffa. Tabbas burin ko wata uwa koma iyaye in general shine da zaran ‘yarsu ta Kai gab’an aure su kaita d’akin mijinta cikin salama da aminci. Saidai wasu lokutan insecurity yakan rinjayi confidence da muke dashi akan yaranmu Wanda hakan ka iya zama babban threat a garemu. Tsoron zamansu a gabanmu babu aure, tsoron maganganun mutane da abinda ka iya zuwa yazo yakan sa mu mance wani b’angare mai mahimmanci Wanda yake tamkar foundation idan babu shi tamkar anyi gini bisa iska ne . Shine neman zab’in Allah da fawwala masa lamra. Idan tsoron ya rinjayi raunin har aka mance wann gab’a mai mahimmanci hakan ka iya jefa rayuwar yaran cikin had’arin da yafi zamansu gaban Iyayen. Wani auren death sentence ne iyaye suka jefa yaransu ciki ba tareda sunyi la’akari ba. Da yawa auren yayi ajalinsu. Wasu ma anyi tsafi dasu sabida ba’a nemi zab’in Allah ciki ba tun farko." ‘Ya’ya amana ne hannun iyaye sann sunada hakkoki Akan iyayensu kaman yanda iyaye keda hakkoki Akan nasu ‘ya’yan. Mu fara k’ok’arin sauk’e nauyi da hakkokin yaranmu Wanda shine tarbiya na farko da zamu basu ko dan nan gaba su sauk’e namu nauyin hakkin dake kansu. Bazai yuwu ka haifi d’a ka wofantar dashi ba kai tsammanin zai girma da tausayinka. Da yawan yaran da muke ji muke gani suna zama abin gudu cikin Al’umma mu bincika yaya tarbiyansu ya samo asali. Wasu tun suna yara iyayen sun d’ebe masu albarka da harsunansu. Wasu iyayen basu san cin yaran ba basu san karatunsu ba balle maganinsu Wanda duk nauyi ne da ya rataya kan iyaye. Ko a d’abi’ance Yaron da ya taso cikin kula da soyayya ba daidai yake da yaron da aka wofantar dashi ba. Akwai jarabawa. Idan kayi iya naka Allah ya jarabceka wann kuma jarabawa ce da yake jarabtar bayinsa dashi. Ba’a yarda ka d’auki ‘yarka ka bada aurenta ma ko wane irin mutum ne yazo Neman auren nata ba dan kawai kana hanzarin ka kauda ita gabanka. Shiyasa addini ya bada tsare tsare cikin Neman auren Kansa kafin aje ga auren. Uwa uba a nemi zab’in Allah cikin duk abinda ake nema. Allah ya shirya mana zuri’a ya azurtamu da yaranmu da samun abokan rayuwa na gari. Ameen. Umma naku fah kan kace me ta ware. Har wani cakarewa tai cikin tsaddan leshi da Hajja Asshe ta kawo mata a d’inke. Kayan da Ummul zatai fitan biki ma Hajja Asshe ta kawosu a d’inke masu d’an karen kyau da tsada. Dik wani buk’ata da amarya zatai amfani dasu Asshe da k’awayenta Sun kawo. "Hajiya Hadiza k’awarta ta dubeta bayan Sun keb’e “Amma fah kawata kin bani mamaki, ko a mafarki ban tab’a hasashoki tsakankanin talakawa ana damawa dake ba. Wai fisabilillahi ya akai kuka amince da wann aure tinda nasan duk yanda tsiya yake ba’a ganinku wajen.”" "Murmusawa Asshe tai tana duban Umma yanda taketa shige da fice cikeda farin ciki. Ta kuma duban k’awarta Hadiza “Hadiza kenan, kin fad’a daidai. Duk yanda tsiya da talauci yake bana zuwa wajen. Toh amma babu yanda muka iya ne. Dole ce ta Kama sai anyi auren.”" Hadiza ta girgiza Kai kad’an “Toh amma gida bai k’oshi ba yaya za’a kawo waje. Ina nufin ga Anisa ‘yarki dan me baki had’a auren da ita ba tinda tana zaune itama ba mijin har yanzu.?” Asshe ta kuma murmusawa “Tinda kikaji na Miki amfani da kalmar dole ki amince kawai dolen ne. Ni fah kaza ce Hadiza bani k’wai na saida zakara. Ke kinfi kowa sanin haka. Yanzu dai ki bari a gama hidiman nan idan mun natsu na sanar dake komai.” Hadiza ta jinjina Kai a hankali har lokacin mamaki bai saketa ba ganin yanda Asshe ta shiga cikin talakawan nan ana damawa da ita. K’awarta ce tun secondary school ta Santa farin sani. Asshe da zuri’arta worshiping money suke inji su Hadiza. Mutane ne da zasuyi komai Akan duniya da abinda ke cikinsa. Shiyasa ta sha mamakin ganin wann al’amari. Kaman yanda Asshe tace da ita akwai dalili ta tabbata akwai dalilin. ** A can police station kuwa motar ‘yan sanda na shigewa na Hilal ma ya sako kai. Sauri sauri Hilal ya take mata baya ganin ta nufi hanyar da aka shige da Mama sai kururuwa Maman take tana fad’in wllhi bata ci kud’ad’en ba. Mama taci gaba da fad’in “Wayyo Khulsum ‘Yata ki cece ni ki ceci Mamanki kar a rufeni. Idan aka rufeni babu mai kula da Abbanku dake kwance gadon asibiti Khulsum.” Khulsum ta samu zarafin dakatar da ‘yansandan ga bak’auye a gefe yana fad’in kwarankwatsa sai an karb’ar masa hakkinsa. Baici nanin ba nanin bazata cisa ba. Takardun bogi suka kawo masa ya saka hannun. Sarkin kasuwa yace baisan da zancensa ba. Idan sama da k’asa zasu had’e sai an fitar masa hakkinsa. Police ya dubi Khulsum yace “Ke kuma fah.?” Mama tai saurin bud’e murya tace “‘Yata ce. “ "Tsananin mamaki sai ya hana Khulsum furta koda kalma. Wai yau Mama ce ke kiranta da ‘yarta. Ikon Allah, Ashe har akwai ranan da Mama zata danganta kanta da jinin Ummanta. Bata kaiga furta kalma ba ta hango Habib mijin Azeema da police woman d’in da kwanaki suka kawota nan police station d’in. Sai wani mannewa take jikinsa. Mama ganin Khulsum tayi shiru ya sanyata duban yanda Khulsum d’in ke duba." Ta zaro ido waje tana kuma mutsukesu. Waye take gani haka.? Habibu ne mijin Azeema Sun fito daga wani ofishi yana faman gyara kwalan rigarsa sai washe baki yake ga wata ‘yarsanda gefe sai kashesa da kallo take kaman zata shige cikinsa. Ta dafe k’irji tana furtawa da k’arfin gaske “Na shiga uku mai nake gani.! Habibu..!” Hankalin Habibu da ‘yarsandarsa ya dawo kansu. Mama ta soma nunasa da yatsa “Habibu mai zan gani mai kake a nan..? Amanan Azeema kake ci da wann ‘yarsandan.?” “Madam ki iya bakinki police station kike ba Tasha ba.” ‘Yarsandan ta fad’a cikin dakatar da Mama wacce tai sokoko tana kallonta. Habibu ya wayance “Haba Mama ya kike magana haka.? Nan fah police station ne. Zuwa nai inata fafutuka ina fad’i tashin yanda za’a samu a kamo mana Tasi’u mana Mama..” Ya dubi mutanen dake wajen ya kuma dubi ‘yansandan da suka kamota “Meke faruwa a nan.. ya na ganki da ankwa.?” Sai Mama ta soma kuka “Habibu ka ceceni.. Kamo ni sukai.. Ka fad’a masu waye yaci kud’in shagon Malam. Kai shaida ne wllhi banci ba. Habibu kar ka bari a rufe ni.” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Khulsum “Ni kuma zan bada shaidan kece kika sayar da shagon koda kuwa Kotu za’a je na shirya zuwa.!” Mama ta kaikaito tana duban Khulsum “Fitsara zaki min a nan Khulsum.? Inji kin biyo ni ne dan ki taimakeni ki bada shaida kaina.” “K’warai kuwa Mama. Zuwa nai dan na bada shaida akanki na kuma tabbata kin biya abinda kika aikata wa mahaifina Wanda yake kwance baida ikon kare kansa balle dukiyarsa.” "Mamaki ya cika Hilal. Ya dubi wann ya dubi wancan “Wait. D’an dakata, wai dama ba zuwa nan kikai dan ki taimaki matar nan ba.. I thought I heard you call her Mama or something.. Is she not your Mom.? Ba naji ta kiraki ‘yarta ba. Ta ya kike bada shaida mai muni kan mahaifiyarki.. Are you going to let them arrest your mother just like that..? Don’t tell me we came all the way here just for you to make sure anyi arresting Mamanki..”" “Malam kar ka sake kiran wann matar Mamata. Ni ba uwata bace. Kuma ka fad’i daidai zuwa nan nai na bada shaidan abinda ta aikata kafin wancan surkin nata yayi amfani da damarsa ya fiddata.” Ta k’arashe tana nuni da Habib dake tsaye gefen budurwarsa ‘yarsanda wacce ya kawo ta kama Khulsum d’in lokacin da ta mari Azeema. “Amma nafi uwarki da ta saida ‘yar Malam Isubu yana kwance. Gwara ni shago kawai na saida.” Mama tace tana huci. Hilal ya kuma duban Khulsum da mamaki Wanda kalaman Mama ya haifar mata da sanyin jiki. Bakauye ya kafe sai an rufe Mama idan ba kud’ad’ensa aka lalo aka basa na. Haka dole aka jefata cikin cell Habib na kwantar mata da hankali da fad’in zai iya k’ok’arinsa yaga ta fita. Khulsum kaw bata kuma fahimtar komai ba tun bayan maganan da Mama ta fad’a mata. Take taji wani irin kuka na zuwa mata. Tabbas Mama ta fad’i gaskiya gwara ita Akan Umma. Ita abun duniya kawai ta saida amma Umma fah mutum ta saida. ‘Yarta da ya kamata ace ta zamto tamkar lu’ulu’u a hannunta. Abu mafi daraja fiyeda shago da abinda ke cikinsa Umma ta sayar. Ko kusa baza’a had’a laifin Mama da Umma ba. Bata San yanda take jefa k’afafunta ba tafiya kawai take tana kuka. Tana Jin wani abu mai kama da k’iyayya Wanda shine zata iya cewa iyakacin alak’arta kenan da mahaifiyarta. Tana tafe gefen kwalta Hilal na biyeda ita cikin mota. Yaci gaba da fad’in “You know you are unbelievable.. Da nasan Akan wann dalilin kika taho all the way to police station da ban b’ata lokaci na na kawoki nan ba. Because of you na rasa d’aurin auren d’an uwana.” “Malam idan baka Kama gabanka ba duk abinda na maka Kai ka saya da kud’inka.. Da ace baka b’ata min jiki ba Watak’ila da ban tsaya na b’ata lokacina wajen ji da kai ba balle har nayi gamo da Mama. Watak’ila da na samu damar dakatar da auren zalunci da ake yunk’urin yima ‘Yaruwata..”Ta fad’i tana ci gaba da sakin huci ga hawaye dake ci gaba da gangaro mata. “Blame your step mother then.” Hilal ya bata amsa Kai tsaye. Khulsum taci gaba da tafiya tana hawaye. "Hilal yai parking ya fito ya tare gabanta “No I can’t just leave you here. After all, Ni na kawoki nan. Idan wani abu ya sameki I’ll blame myself for the rest of my life. Please get in the car. Ki bari na maida ke yanda na d’aukoki. At least.”" Bata amsa shi ba sai kukan da take ci gaba da yi dan mugun takaicinsa take. Ya d’an waiga yana duban mutane masu giftawa sai kallonsu suke. "Ya d’an kuma gyaran murya “Look, I don’t want people to think that I hurt a girl. Dan Allah ki shiga.. At least ki bani dama na fitar dake daga nan.. Dare ya soma yi duba ki gani.. And is not safe for you to walk alone a babban kwalta irin haka.”" Cikin kuka Khulsum ke dubansa “Na tsaneka.! Na tsani mugayen ahalinka da sukai amfani da raunin mahaifiyata suka sayi ‘Yaruwata da sunan aure.!” "Hilal ya zuba mata ido “Look, bansan meke faruwa tsakanin ahalinmu ba. But the only abu da zan fad’a Miki shine my cousin is a good person.. He has his faults as human. But I can assure you he’s a good person.” Ya d’an tab’e baki “Idan yar uwarki ta kasance matarsa abun kiyi mata murna ne.”" Takaici ya hanata furta koda kalma tasa kai tana ci gaba da tafiya. Hilal ya kuma tareta “Yamma yayi sosai ki shiga na kaiki gida. That’s idan Kinaso ki cimma ‘yaruwarki kuyi Sallama kafin a tafi da ita. Dan na tabbata kawo wann lokacin an d’aura auren. Tinda bakiyi nasaran dakatar da auren ba. Watak’ila zakiyi nasaran samun dama kuyi Sallama idan har kika shiga mota ta.” Ya k’arashe yana nuni da motar. Bata k’aunan abinda zai kuma had’ata da d’aya daga cikin wann ahalin. Toh amma gaskiya ya fad’a idan batai saurin cimma Addanta ba Watak’ila bazata samu suyi Sallama ba za’a tafi da ita. Saida ta rakasa da harara kafin ta nufi motar. Hilal ya d’an tab’e baki yana bud’e mata marfin motar “Sorry to say a daidai yanda na d’aukeki zan ajiyeki. Kinga ko ba komai na rage Miki hanya.” Ta kula nema yake ya dad’a tunzurata hakan yasa bata kuma bi takanshi ba balle ta amsa shi. Saidai suna isowa bakin babban kwalta da zai shigar da kai layinsu suka hango motocin amarya na ficewa. Alamun Sun makara amarya ta riga ta hau hanya. Hilal ya tab’e baki kad’an “Looks like someone didn’t make it on time. Unless zaki bi bayansu.” “Ajiyeni a nan.” Ta fad’i tana k’ok’arin bud’e motar. “Are you serious.?” Hilal ya fad’i yana k’ok’arin juya kan motar cikin k’ok’arin bin bayan motocin. Da mamaki Khulsum ke dubansa ta kuma jan marfin motar ta jita a rufe alamun ya rufe daga wajensa. “Malam ka ajiyeni a nan nace ko na maka ihun b’arawo.!” "“You and I both know this is what you want. Kiyi Sallama da ‘yaruwarki. Just admit it.” Ya d’an dubeta sai yai murmushi da gefen bakinsa “Don’t worry, I’ll do you a favor and take you to your sister. After all, Nima can na nufa..” Ya maida idanunsa ga kwalta “Kar ki damu ba sai kin biya kud’in abun hawa ba. A simple thank you will be okay.”" Bai kuma cewa komai ba yaci gaba da tuk’a motan. Izuwa lokacin ta rasa ma mai zatce ma wann d’an rainin hankali. Shiru tai tana duban titi yanda Hilal taketa fifila gudu da ita. ** Abuja.. "Zaune yai gaban mahaifinsa yana sauraronsa yanda Daddy yaci gaba da fad’in “I will be meeting with our international clients in Nairobi.. Daga can zan wuce Cape Town, southAfrica gameda business alliance da muka fara a can months back.” Ya gyara zaman glasses d’in dake mak’ale idonsa kafin yaci gaba “Maybe it will take me two to three weeks before I return..” Ya k’arashe yana ci gaba da duba documents d’in dake gabansa." Haidar ya jinjina Kai yana duban mahaifinsa “So why are you telling me all these Daddy.? Are you.. Do you want to hear from my own perspective.? I mean regarding the alliance.?” D’agowa yai had’ida d’an zame glasses d’insa yana duban Haidar d’in sosai. “I did not send you to those expensive schools dan kawai ka dawo na saka ka a gaba naita kallonka. But unfortunately it is unfolding.. Watak’ila ba kai bane wann D’an da zanyi alfahari dashi. By now ya kamata ace na huta. Ya kamata ace Kai ke wakiltana a tafiye tafiye irin wann. Saidai Kai d’in banida k’warin gwiwa akanka. It is enough da na amince ka jagoranci project d’in cikin gida..!” Ya kuma dubansa sosai kafin ya k’arada “You are a complete failure to my name Aliyu!” Ya k’arashe yana maida glasses d’insa. "Haidar yai murmushi mai ciwo yana jinjina Kai “Is this the kind of legacy you wish to leave behind for your Son.?” Ya jinjina Kansa zuciyarsa na kuma masa d’aci kafin yaci gaba “I wouldn’t be surprised of course. But You know what Daddy. No matter how insignificant you keep insisting I’m to you.. You can’t deny the fact that your company needs me.. And you need me too.. Kuma shine dalilin da yasa ka kirani kake sanar Dani duka shirye shiryenka.. So Daddy, deny it all you want. But the truth is that I’m very much important to you.. And your company is nothing.! Absolutely nothing without me.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e zuciyarsa na masa zafi." A daidai k’ofan fita daga sashen ya had’u da Alhaji Gimba na shigowa. Alhaji Gimba na ganinsa ya fad’ad’a murmushinsa. Bai damu ba idan Haidar bai gaishesa ba. Shi dai bazai tab’a cire hope Akan Haidar d’in ba. Alhaji Gimba yaci gaba da fad’in “Congratulations to you and your team. Naji dadin wann al’amari kuma inada yak’inin company bazatayi danasanin zab’en gwarazan da zasu jagoranci wann aiki irinku ba..I trust you and your team.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba “Wann aikin kampani ne so ina shawartanka kar ka bari wani matsala da kake dashi tsakaninka da mahaifinka yasa kai ma aikin rik’on sakainan kashi ko ka yanke hukunci cikin fushi. Na yarda da Kai amma tunasarwa yanada kyau. The company’s future relies on your hand Aliyu. And we have high expectations of you.. Let’s set our differences aside so we can reach our common goal. Ko dan mu ba ma abokan Adawa kunya.” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa. "Tinda ya soma magana Haidar da hannayensa ke sakale cikin aljihu yake dubansa lokaci guda yana nazarinsa “Trust me, it’s just a matter of time before we find out who the real traitor is.”" Murmushi Alhaji Gimba ya kuma sakar masa kafin yai nuni da parlorn “Baringa mahaifinka. Have a good evening.” Ya fad’i yana mai shigewa cikin parlorn. Lumshe idanunsa kad’an Haidar yai had’ida furzar da huci “Fake life fake people. Everything around this family is fake nothing is real.” Lokaci guda yasa kai ya shige cikin sassarfa zuciyarsa na masa wani irin k’una. Ya fito daga sashen mahaifinsa kenan ya hangi k’atuwar mota ta shigo cikin gidan shak’e da kaya ta nufi nasa b’angaren. Yabi motar da kallo kafin ya nufi hanyar sashen nasa. Nan ya hangi Mommy da Anisa sai nuna ma masu interior d’in yanda zasu jera kayayyakin suke. Ga tsaffin Kayan duka an fito dasu. Yai tsaye yana dubansu da mamaki. Can Anisa ta hangosa. Sai ta matso kusan Mommy tai mata rad’a a kunne “He’s here Mommy.” "Mommy ta d’ago tana tambayan wane kenan. Ganin Haidar ya sanyata fad’ad’a murmushinta. Ta k’arasa da sauri ta kamo hannunsa “Haidar my son, today is the happiest day of my life.. An d’aura aurenka yau Haidar.”" Sai yaji abun banbarakwai. Shi ya ma mance da wani batun aure da yarjejeniya. Wani irin duba yake mata irin na da gaske take.? Da gaske auren suka masa sabida son zuciya irin nasu. Mommy taci gaba da fad’in “Wann shine Mafarin had’in kan ahalinmu da yardar Ubangiji. Cikin ikon Allah komai zai daidaita.” Bakinta ya gaza rufuwa har mamaki Anisa take yanda Mommy ke matuk’ar d’aukin wann aure. Taci gaba da nuna ma Haidar kayayyakin “Look duba kaga. I know you have high taste so I ordered everything to your taste.” Ta saka hannu ta tallafo fuskarsa “Yau d’in ina Jin na cika wani gurbi na zama uwa a gareka D’ana. Burin ko wata uwa kenan taga D’anta yakaiga cikan kamala.” K’ok’arin cire hannun Mommy daga fuskarsa yake Jin tana wasu irin sunbatu “Mommy will you please stop.! Enough of this drama.” Ya dakatar da ita kafin yaci gaba “Quit the act already! Stop acting like you care.. Like you are responsible.! Like you are doing your motherly duties wad’anda kika makara bakiyi ba tun a baya. It doesn’t suit you at all Mommy.!” Ya k’arashe jijiyoyinsa har fitowa suke. “Haidar.” Ta ambaci sunansa kaman mai shirin kuka. "Dakatar da ita ya kumayi “Mommy you and I both know ba auren tsakani da Allah bane. Ba don ci gaban rayuwana matsayina na d’anki kikai ba. You are doing all this for your own advantage.” Ya d’anyi fasali “Mommy my day is bad enough, thanks to my Dad. bazan bari ki k’ara mun wani akai ba.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga gidan a gaggauce." Jiki a matuk’ar sanyaye Mommy ta juyo. Anisa ta k’araso ta taddata. “Mommy seems like ke kad’ai kike son auren nan a gidan nan. Shin bazaki hak’ura da auren nan ba kawai tinda Wanda akayi dominsa baya so. Kawai ki d’aga waya ki kira Ammi ki sanar da ita an fasa tin kafin a kawo matar cikin gidan nan. Dan na tabbata wann auren ba mai d’orewa bane.” "Mommy ta harereta “Ke dalla rufe mun baki. Bansan shashanci, Wann aure da kika gani mutuwa ce kawai zata raba matar da Aliyu. Idan kinga auren ya Mutu ki tabbata matar ta Mutu ne.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige tana neman layin Asshe dan Jin mai ake ciki." Anisa ta tab’e baki tana mamakin wann irin al’amari. ** Kano… Dik maganganun da Hilal keyi cikin motar ba sauraronsa take ba. Hasalima bazata iya tantance mai yake cewa ba da za’a tambayeta. Damuwarta kawai su isa ga ‘yaruwarta tai k’ok’arin shawo kanta su gudu tinda babu idon Umma. K’aran bud’e gate ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da tai nisa ciki. Zuciyarta sai tsinkewa yake tana addu’an Allah ya bata ikon shawo kan Addarta Ummul cikin sauk’i. Tana ji a jikinta wann aure babu wani alheri cikinsa. Hilal yana Ida parking tai saurin kama handle tana kokawan bud’ewa. Ya tsareta da idanu “Easy kar ki balla min marfin mota bayan kin b’ata min da tab’o..” Bata amsa shi ba dan bata da lokacinsa. Tana Jin sanda motar ta fita a lock tai saurin bud’ewa ta fito. Sauri sauri ta nufi cikin gidan har kaman zatai tuntub’e. Hilal ya bita da kallo had’ida tab’e bakinsa kad’an kafin ya nufi bangarensa. A daidai mashigar gidan Khulsum taji ance da ita “dakata..!” Cak taja ta tsaya sakamon muryar taji ya dakatar da ita. Umma ta gani ta tsaya tayi k’ebebe rik’e da kunkumi tana duban Khulsum d’in. “Umma..!” Khulsum ta fad’i mamaki kwance saman fuskarta. Umma ta jinjina kai “K’warai ni ce nan.!” Tai maganar tana kuma k’obarewa bakin k’ofa. “Umma.. Me kike a nan..?” Khulsum ta tambaya cikeda mamaki. “Ke zan tambaya mai kike a nan..? Wani munafuncin ne Ya kawoki..? Awho kinzo ne ki kashe mata auren Tun kan ta tare ko..?” "Mamaki Ya hana Khulsum furta koda kalma sai duban Umma da take. Da k’yar ta iya furta “Umma a ina uwar amarya ta tab’a yima ‘yarta rakiya d’akin miji.. Haba Umma fisabilillahi, bayan auren rashin galihu da kikai ma ‘Yaruwata shine saida kikai mata rakiya. Shin baki gudun maganganun mutanen ne Umma..?”" “Allah tsari gatari da saran shuka.. Aure auren gata nai ma d’iyata irin Wanda kaf lungun ku ba’a tab’a samu ba. Ki koma ki tambayi ‘yan lungun naku kiji wani irin aure akaima Ummul. Aure na bajinta auren da na tabbata bazaa daina kambabasa ana labarinsa ba. Ke harta da masu shigewa saida suka shaida.. Kuma ban rako Ummul ba saida zuciyata ta tabbatar min zaki iya zuwa… Gashi kaw kin zo d’in kaman yanda nai tunani.. Zuwanki na sani ba Alheri bane.. Dan na tabbata kaman yanda nai alwashin aurar da Ummulkhairi haka Kikai alwashin lalata mata aure. Tinda ba yau kika saba korar mata maza ba. .Ke ni fah akan auren nan wllhi Khulsum sai mu raba gari dake.!” Ta k’arashe tana sakin huci. Khulsum ta jinina kai a hankali tana duban mahaifiyar tata “Umma kin kaw ji abinda kike fad’i..?” Tai maganar cikin rawar murya. “K’waraiii kuwa.. Wllhi sai kiyi yamma nai gabas muddin kikai yunk’urin lalata auren ‘Yaruwarki Wanda Babu kalan fad’i tashi da banyi ba dan ya tabbata. Tsaf zan yafeki Khulsum muddin kika kawo mishkila.” Hawaye suka gangaro ma Khulsum “A’a Umma. Abun bai tsanani haka ba. Har kullum ke mahaifiyata ce banida tamkar ke.. Bazan b’ata auren Adda Ummul ba.. Na Miki alk’awari Umma.. Amma dan Allah alfarma d’aya nake so kimin..” Yanda Umma ke dubanta a dak’ile sai ka rantse ma wata tsararta take jifa hararan. “Umma dan Allah ki bari nai Sallama da Adda.. Na rok’eki..!” Ta k’arashe tana had’e tafukan hannayenta biyu waje guda alamun rok’o. Umma bata amsa ba sai k’ofan waje da ta shiga nuna mata “Fita.. Wuce ki fita.. Wllhi idan ni na haifeki kuma na haifi Ummul bazakiyi Sallama da ita ba.. Shige ki fita nace kar na bud’e idanuna na ganki..” Khulsum ta dubi mahaifiyarta da mamaki “Umma kin Sallamanin kenan..?” “Idan haka kika d’auka.. Kije duniya da yawa..” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Khulsum ke nanatawa cikin zuciyarta. Wai mahaifiya ke fad’a ma ‘yarta haka.. Anya Umma ita ta haifesu..? Anya akwai iyaye irin Umma..? Anya mutum zai d’auki D’ah a cikinsa tsawon watanni tara Ya haifosa duniya yaci gaba da rainonsa rana tsaka Ya k’isa sabida wani buri nasa na duniya..? Anya akwai irin wad’ann iyayen..? A iya saninta harta dabba yasan dadin d’ansa. Meyasa tasu mahaifiyar ta zama haka..? Shin dama ana jarabtan bawa da iyayensa..? Ashe ba iyaye bane kawai ake jarabtarsu da yaransu ashe Yaran ma akan jarabcesu da nasu iyayen.. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. A hankali take ja da baya hawaye na gangaro mata tana duban Umma. Umma kaw bayan ta tabbata Khulsum ta fice cikin gidan ta koma harda ce ma maigadi idan wann yarinyar ta dawo ya koreta. "Suna zaune parlor itada Asshe bayan k’awayen Asshe Sun watse. Asshe ta dubi Umma tace “Yarinyar nan taki akwai fitina, sam batai halin ‘yaruwarta Ummul ba.”" Umma ta tab’e baki “Ai mutane biyu ne mabanbanta halayya. Fitinanniya ce ga taurin kai tsiya da masifa yacce kikaga k’anwar Ubanta. Bata rage ma Dije komai a d’abi’a ba.” Asshe tace “Wacece Dije..?” Kafin Umma ta kaiga bata amsa suka sinkayo wata murya daga k’ofa “Ni ce nan Dije k’anwa d’aya tilo ga Isubu..!” Daram.! Daram!! Daram.!!! Haka k’irjin Umma ya bada wann sauti cikin sakan guda. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *20* ©️Sameena Aleeyou… * "Inna Dije taci gaba da takowa cikin parlorn. Yayinda Umma keta faman k’ifta idanu, zuciyarta bata daina tsinkewa ba." Daidai saitin Umma Inna Dije ta k’araso ta tsaya. Umma ta kasa d’ago idanu ta dubi Dije. “Dole ki kasa d’ago idanu ki dubeni Suwaiba. Idan Har kinada sauran kunya bazaki dago ki dubeni ba..” Umma ta soma girgiza kai hawaye na zubo mata Har lokacin bata d’ago idanunta ba. Fincikota Dije tai tana fad’in “zo nan.. Yau sai naji uban da ya tsaya miki a garin nan Suwaiba har kike buga wasanki da sunan wauta da shashancin gangan..!” Ta kuma janyo Umma a zafafe. Hajja Asshe tai saurin raba tsakaninsu “Inaga dai ya kamata ayi komai gaban idona.!” Ta k’arashe tana duban Inna Dije data cakumo Umma. Umma ta k’walalo idanu waje Jin zaa kwance mata zani gaban Hajiya Asshe. Ta had’e hannu biyu waje guda alamun rok’o “A’a Dije.. Kar kiyi haka.. Wann matsala ne da ya danganci ahali..” Inna Dije ta murmusa tana duban Umma “Dole kice matsala ce da ya danganci ahali Suwaiba.. Sabida bakiso a bankad’o sirrikanki gaban sirakanki ko..? Kin masu rufa rufa kin aura masu ‘yarki da lak’anin mahaifinki ya fad’a kanta cewa ita d’in bazata tab’a aure ba.. Sabida wani babban Dalili Wanda nida ke muka binne hakan tinda jimawa..!” Umma ta zaro idanu waje tana duban Inna Dije da Jin wani batu Wanda ta kasa fahimtar ina ya dosa.. Asshe ma idanu waje take duban Umma da Inna Dije cikin tsananin d’aurewar kai “Wa.. Wani batu kenan..?!” Dije ta murmusa cikeda cin nasara. Cikin zuciyarta take ayyana lokaci yayi lokacin d’aukan Fansan rasa tilon D’anta Fa’iz da tai a dalilin Ummulkhairy. Umma ta kuma girgiza Kai “Dije wa.. Wani dalili ne wann.. Kuma.. Wani magana muka tab’a binnewa mu biyun Wanda ni ban sani ba.?” Dije ta murmusa “Suwaiba kar ki fara mana dramarki a nan.. Dan kinsan tar nake kallonki.. Kin shashantar Dani Karon farko na rasa Fa’iz dalilin ‘yarki bazan kuma bari ki shashantar Dani ba..!” Umma ta kuma girgiza Kai hawaye na Neman b’allo mata.. Zatai magana Asshe ta dakatar dasu “Wai meke faruwa ne..?” “Abinda yake faruwa shine D’anku ka iya zama gawa na gaba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu..!” Asshe ta mik’e tana kuma zaro idanu dafe da k’irji “Na shiga uku gawa fah..! Haidar ne zai zama gawa na gaba..?!” Dije ta dubeta sosai tace “K’warai kuwa.. Domin Ummulkhairy da kike gani ba mace bace..!” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Shine abinda Asshe take nanatawa tana ganin duniyar na Neman juye mata “Ba mace ba..? Mecece toh..?! Na shiga Uku ni Asshe me na aura ma D’an ‘Yaruwata..?!” Umma na kuka take girgiza Kai tana duban Inna Dije jin irin sharrin da ake ma ‘yarta akan idonta “Dije kiji tsoron Allah..!” “Idan banji tsoron Allah ba tsoronki zanji ko tsoron mushurikin mahaifinki wanda ya maida Ummulkhairy yanda take a yanzu..!” Izuwa lokacin kan Asshe ya gama k’ullewa.. Ta dubi Umma dake duk’e wajen tana hawaye tace “Ke Suwaiba..! Fad’a mun.. Meke faruwa..? Wacece ‘yarki..?” Umma bata iya cewa komai ba sai kuka tana girgiza Kai.. Inna Dije ta kuma murmusawa “Ai bazata iya sanar dake komai ba domin kuwa batada amsar baki.. Amma ki tambayeni ni zan sanar dake komai.. zan sanar dake Wacece Suwaiba da badak’alan data k’ulla a doron k’asa..!” Asshe ta d’ago tana duban Inna Dije cikin tsananin shock. Lokaci guda Inna Dije taci gaba “Yarinyar da kuka aura ma D’anku ba mace bace.. Domin kuwa a lokacin da Suwaiba ta samu cikinta ba cikin ‘Ya mace tai fatan samu ba.. Mahaifin Suwaiba ya kasance gasunkumin malamin tsubbu ne Suwaiba ta tafi wajensa amsar taimako a lokacin tana d’auke da cikin Ummulkhairy kan cewa ya bata lak’anin haifo d’a namiji... Sabida Sun mance Allah shi kad’ai yake halitta mahaifinta bai isa ya sauya halitta ba.. Wann dalili yasa aka haifo Ummul a idon duniya mace ce mai kyau son kowa k’in Wanda ya rasa.. Amma a zahiri ne kawai. A magana ta auratayya namiji bazai tab’a amfana da Ummul ba domin kuwa ita d’in an tsafeta tun a ciki.. Hakan na nufin Ummulkhairy bazata tab’a aure ba.. Idan kuma tai toh fah duk mijin da ta aura zai mutu. Idan bai Mutu kafin ta kaisu ga aure ba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu toh zai mutu idan wata alak’a ta auratayya ta gifta tsakaninsu.!” Duniyar Asshe ya shiga juyawa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Meke shirin faruwa dasu.. Shin ta yaya zata sanar dasu suma auren warware asiri kawai na watanni uku sukai da Ummulkhairy Wanda sai ya mu’amulamceta wann sihirin da aka masa ya karye.. Ta ina zata soma sanar da ‘Yaruwarta abinda ke faruwa.. Lallai tana tsaka mai wuya..! Muryar Umma ne ya katse mata tunanin yanda take fad’i cikin kuka “Haba Dije..! Dije kiji tsoron Allah.. Ki tuna akwai mutuwa.. Dije har zaki iya tsara wann babban k’arya kan D’iyar D’anuwanki.. Dije baki tsoron hakki.. Baki tuna yau idan babu mahaifin Ummul ita amanace a gareki..?!” “Rufe mun baki annamimiya..! Ke Har akwai maci amana irinki ne Suwaiba.. Kin mance Ya aurenki ya kasance ne na tuna miki Suwaiba..?” "Umma ta kuma kifa kanta a k’asa kuka na kuma zuwa mata. Lokaci guda Dije taci gaba “Talla kike kawowa cikin gari a lokacin Tani da mahaifiyarmu wato sirkarta kenan basu jituwa mahaifiyarmu tana so Yayana Isubu ya k’ara aure kafin ta bar duniya sabida yara mata da Tani ke haifa masa. Mahaifiyarmu tana son samun jika namiji daga wajen D’anuwana Isubu.. Ke Suwaiba kika yaudari Tani kikace a garinku mahaifinki malamin zaure ne kuma yana bada lak’anin mallaka, Tani ta biyeki kika kaita Har rugarku da sunan tana neman lak’anin mallaka. Shakuwa ya shiga tsakaninku kika d’auki Tani tamkar Yaya. Tani ta daukeki tamkar k’aramar k’anwa ta baki dukannin yardarta. Kika zamto mata ingiza mai kantun ruwa.. Kika zaga Tani kikaci amanarta. Maganin bakin jini keda Ubanki kukaita tura ma Tani Wanda zaisa mijin Tani ya tsaneta ya soki. Haka ne..?”" Idanun Umma suka kuma firfitowa waje tana jin sirrikanta kaf Dije na fito dasu. Dan wann b’angare da Dije take fad’i bata da haufi gaskiya ne. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Amma nayi nadama kuma mahaifina ya daina wann aikin kafin ya bar duniya Dije. Ke shaida ce mahaifina bai Mutu yana wann mummunan sab’o ba. Dije Allah Algafur ne kuma mai rahama.” “Ke yimin shiru! yau ne kika san Allah Suwaiba.? Ashe kinsan da haka kika rufe ido kika doge sai kinga auren Ummul kaman lokacin baya da kika doge wajen ganin kin haifo d’a namiji.? Kaman yanda burinki na farko bai ta bata ba Suwaiba haka burinki na biyu ina nufin ganin ‘yarki Ummul a d’akin aure kaman ko wace ‘ya mace bazai tabbata ba.!” Dije na huci taci gaba “Kusanci da yarda da Tani ta baki da shi kikai amfani kika aure mata Miji. Mahaifiyarmu babu irin soyayyar da bata Miki ba Dik a tinaninta zaki haifo mata jika namiji.. Wanda hakan yasa kukaje kukaita tsibbace tsibbacenku keda mahaifinki dan ki haifo d’a namiji..Idan kin mance na sake tuna miki da cikin Ummul mahaifiyarmu ta bar duniya bataga abinda kika haifa ba Wanda ta k’wallafa ran D’a namiji zaki haifo.. Bayan mutuwar Inna wato mahaifiyarmu mahaifinki ya Mutu shima. Daga nan ne Tani ta fara cuzguna Miki… Kika koma mata tamkar baiwa.. Duk abubuwan da kikai a baya basu isheki ba Suwaiba har saida kika saka mutanen da basuda hakki ciki.. Idan ni na rasa Fa’iz Watak’ila sabida tsanar da na Miki a baya.. Su wad’ann mutanen mai suka Miki kika jangala masu Ummul...? Suwaiba dole ki haukace da son ganin ‘yarki tayi aure kota halin k’ak’a tsoron kar tsafin da mahaifinki ya jefi ‘yarki dashi a lokacin da kike d’auke da cikinta ya tabbata.!” Girgiza Kai kurum Umma take tana hawaye ganin Dije ta d’aureta ko ta ina.. Babu bayanin da zatai ta wanke kanta. Dije taci gaba “Ke fah akan cikan burinki Suwaiba babu Wanda bazaki ci Amanansa ba. Koda kuwa wann mutumin ya Miki halarci kaman yanda Tani ta Miki..!” Asshe ta shiga jinina Kai bakinta yana furta “Tabbas haka ne..! Sai yanzu nake fahimtar komai.. Tani taso nusar Dani gaskiya na rufe idanuna.. Ashe ita ce mai gaskiya.. Tabbas na Miki rana Suwaiba.. Babu abinda ban Miki amma kika zab’i ki b’oye mun wann bala’i dake k’unshe jikin ‘Yarki.. Da niyyan taimako na nema ma D’an ‘yar uwata auren ‘yarki.. Ashe ke akwai k’ulli cikin zuciyarki.. Kin cika butulu Suwaiba.!” Muryar Asshe ya soma rawa hawaye na gangaro mata “Ki sanar Dani mai zan fad’a ma ‘Yaruwata da ta aminta Dani Akan Tilon D’anta ta mallaka min wuk’a da nama.! Ki sanar Dani Suwaiba..!” Ta k’arashe kuka na kuma b’allo mata. Umma na girgiza Kai tana hawaye take fad’in “Ki yarda dani Hajiya Asshe.. Wllhi cikin maganganun Dije akwai Wanda sam ba gaskiya bane.. D’anta had’arin mota shine ajalinsa amma ba auren Ummul d’ina da Ya tasamma bane.!” “Wani gaskiya kike dashi da har zan yarda dashi..?” Asshe ta katseta cikin d’aga murya. Lokaci guda taci gaba “Wann auren babu yanda zaije..! Bazan saka rayuwar D’an ‘Yaruwata Akan layi ba.. Za’a Warware wann aure tun kafin ‘yarki ta bar gidan nan.. Zan kira ‘Yaruwata na sanar da ita komai.. Ita zatai umarni ma D’anta ya datse auren Amaryar da aka aura masa wacce ko saninta bai ba..!” Tana ida fad’in haka ta mik’e zata nufi sama.. Umma ta bita a guje ta duk’a gabanta ta kamo k’afafunta tana kuka sosai take fad’in “Ki rufa mun asiri dan girman Allah Hajja Asshe.. Dan Allah kar ki bari a warware wann aure.. Dan Allah kar ki bari a maida sadaki.. Wllhi Ummul mace ce kaman ko wace ‘ya mace.” Asshe ta fuzge k’afarta “So kike na kashe D’ah na Akan cikan makahon burinki Suwaiba..! Aure dole a warware..!” Tana ida fad’in haka ta kuma fuzge k’afar ta ta nufi sama a fujajan kaman zata kifa. Hannu biyu Umma ta saka aka tana kuka maras sauti tsoron kar Ummul taji muryarta tasan abinda ke wakana. A fili take furta ta shiga uku ta Mutu ta lalace. Daga yanda Dije ke tsaye tana dubanta murmushi ta saki. Cikin zuciyarta take furta “Da kyau Dije.. Fansan ran Tilon D’anki kike d’auka.. Aima baki shiga uku ba tukuna Suwaiba.. Dan yanzu ne aka fara buga wasan.. Ba ke kad’ai bace kika iya buga wasa.. Saima kin ci karo da duk tanadin da na miki.. "Asshe tana haurawa zama tai gijif saman gado tana jin wani irin tashin hankali na ziyartarta. Yanzu ta ina zata fara b’ullo ma wann al’amari..? Mai zata soma sanar da ‘yar uwarta bayan d’inbin kud’ad’en da ta asma daga wajenta..? Ta sanar da ‘yaruwarta d’iyan mutane masu mutunci mai irin matsalar da boka yace a aura ma Haidar ta samu dukda kasancewansu talakawa amma sunada dattako. Sabida Hajiya Kwaise bata amince D’anta ya kasance da d’iyar matsiyata marassa dattako k’ark’ashin kalmar aure ba koda kuwa na tsawon watanni uku ne kacal. Shin ta yaya zata soma gabatar da wann ahali masu dabaibaye da matsala Wanda tashin hankali yai ma rayuwarsu marfi, dangin tsiya dangin matsafa. Ba’a nan ta tsaya ba Ita kanta yarinyar an tsafeta tin a ciki.. Sann ita d’in barazana ce ga rayuwar Haidar. Ta rintse idanunta tana jin tashin hankalinta na kuma ninkuwa.. Meyasa Tai komai a gaggauce..? Meyasa bata saurari Tani ba..? Meyasa Tai zaton kishi ne kawai da Hassada yasa Tani gaza zaune wajen ganin auren bai tabbata ba..? Ta Ware idanunta sanda zuciyarta ke ambato mata . ‘Mutuwar Kwasko kenan Haidar zaiyi da wann yarinyar da kika aura masa. Shin AUREN WATA UKU zaki ambaci auren ko Auren ajali.? Tabd’ijam! Wann shi ake kira cuta ta d’au cuta.!’" Ta kuma mik’ewa tsaye zufa na kuma tsartsafo mata. Zuciyarta ta shiga amsa mata d’imbin tambayoyin da sukai karan tsaye cimma Zuciyar nata ‘Me kike tunani a auren da aka faro bisa umarnin boka..? Me kike tunani a auren da ba’a nemi zab’in Allah cikinsa ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a d’aukesa umarni daga Allah ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a ginasa bisa ginshik’in auren ba..? Ma’ana ba’ayi sa domin cika sunnar ma’aiki (SAW) ba. Dole abubuwa su biyo baya.. Dole bazaku ga da kyau ba. Kaman yanda kika rufe ido kikai ma ‘yar mutane auren Mutuwa da D’anku haka nan wann matar da kika d’auketa shashasha tai auren mutuwa ma d’anku da nata ‘yar. Tirk’ashi. Lallai yau akeyinta. Asshe taja wani irin gauron numfashi tana mai kuma mik’ewa tsaye daga zaune. Lokaci guda take furtawa a fili “Me zan aikata ni Asshe.. Me zan sanar da ‘Yaruwata..? Zata fahimci k’arya naita shera mata kenan ina amsar mak’udan kud’ad’e hannunta..? Shin waye zai fanshe kud’ad’en da na amsa hannun Kwaise da sunan AUREN WATA UKU ma d’anta. Shin ma ta ina zan iya mayar mata da kud’ad’en da ta bani na yak’in nemo ma Haidar matar wata uku..? Dan nayi imani nawa mijin ba biya zaiyi ba dan shi mutum ne da mata bata cin kud’insa sai wacce yake yayinta. Nida ‘Yaruwata kuma k’ar tasan k’ar ne akan kud’i. Zamu iya samun matsala ta tarwatsewar ahali akan kud’ad’en da ta tafka asara ba tareda ta samu biyan buk’ata ba. Uwa uba taji auren mutuwa na shirya ma tilon D’anta Wanda ita kanta ta saka nata Auren cikin had’ari domin ta ceto sa daga mugun asirin da aka jefesa dashi. Mijina will come to know everything. Duk abubuwan da na aikata harda zuwa wajen boka da AUREN WATA UKU da na k’ulla Wanda Ya k’unshi kisan kai. Zai rabu dani rabuwa ta har abada. Even my children will leave me. Kowa zai gujeni na zama banida tsuntsu banida tarko. Kishiyoyina su samu abun yawo Dani. Lallai ina tsaka mai wuya ni Asshe. Suwaiba ni ta cuta a duka wann al’amari. Gashi garin k’ok’arin gyara ahalin ‘Yaruwata ni zan tarwatsa nawa ahalin da farin cikina. Toh amma rayuwar Haidar ake magana a nan.” Ta shiga girgiza kai tana mai furtawa a hankali “A’a.. A’a bazan bari hakan ta kasance ba.. Haidar’s life is at stake here.. Bazan bari a kai masa ajalinsa ba.. I need to do something immediately.. I need to come up with something… I just.. Can’t sit back and do nothing.. Amma me zanyi..?” Batakai aya ba wayarta ta soma ruri Hajiya Kwaise ke kira. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *21* *©️Sameena Aleeyou… * Jikin Asshe Ya kuma yin lak’was dan gani take kaman Kwaise ta riga ta san komai. Cewa Ajalin D’anta zata kai mata matsayin makarin asirinsa.. Har wayar ta kusa tsinkewa kafin Asshe ta iya tattara daidai gwargwadon natsuwan da yazo mata a wann lokacin. Murya a raunane ta d’aga kiran “Aunty Kwaise..” Daga d’aya b’angaren Mommy ta kaste ta “Asshe duk yanda za’ai Amaryar wata uku ta iso Abuja a gobe.. Asshe a yanda na hango tsananin k’iyayya a idon Haidar Ya kuma haifar min da tsoron rasa D’ana. I can’t afford to lose him Asshe. Haidar shi kad’ai ne D’ah na zanyi komai zan sadaukar da komai nawa dan na kub’utar dashi da ahalina daga sharrin shed’aniyar can. Asshe bana so a sami wani mishkila. Ki kula da matar wata uku da kyau tamkar k’wai a hannun yaro tinda kinsan amfanin ta wajenmu. Rayuwar d’ana tamkar yana had’e ne da nata rayuwar. Har sai lokacin da zata karya wann asiri da aka jefesa dashi. We need to make sure ta iso a gobe cikin k’udurar Ubangiji.” “Amma.. Amma.. Aunty Kwaise..” "“Asshe Babu wani Amma.. I cant afford to lose my son completely… Just do as I say.. The house is set. Everything is ready. Isowarta kawai ake jira na rik’e Haidar a gida kaman yanda yake bisa yarjejeniyar mu dashi. Engr ma cikin satin nan zai tafiya, Business trip. Akan Auren Haidar na hana kaina bin mijina tafiyar da zai d’aukesa makonni kinga kuwa na shirya ma wann aure. Na shirya karya asirin da akai ma Haidar.” Mommy ta k’ark’are wayar nata tana kuma jaddada ma Asshe lallai lallai kar a samu wani matsala." Asshe Tai sakare tana duban wayar. Zama Tai gijif cikin gado zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Shikenan.. Ta faru ta k’are wai anyiwa mai dami d’aya sata yanzu mi zatayi..? Ba tada ikon canza komai a halin yanzu. A dole ta nad’e Ummulkhairy ta kaita ma Yayarta Kwaise. Yanzu ita meye abinyi. Anisa ce ta fad’o zuciyarta. A fili ta furta “Anisa.. Anisa zata taimaka min na aiwatar da komai ba tareda Haidar Ya cutu ba sann ba tareda ‘Yaruwata ta fahimci komai ba. Lallai zaman Anisa a can shine kawai rufin asirina. Toh amma idan Anisa taje ta tafka wani shashancin fah.? Kuma kenan zaki sanar da Anisa komai.?” Ta soma girgiza kai a hankali “A’a Anisa doesn’t need to know about everything. Kawai umarni zan dinga bata daga nan.” A hankali ta shiga jinjina kai kafin ta nufo k’asa. Nan Asshe ta tadda Inna Dije ta titsiye Umma sai ta fito mata da Ummulkhairy ta tafi da ita. Umma sai kuka take tana rok’on Mama Dije ta rufa mata asiri kar ta tona mata Auren Ummul ya mutu tun a daren aurenta kafin tafiyarta. Cikin gunjin kuka Umma taci gaba “Dije ki dubi girman Allah ki rufa mun asiri.. Wanda kika tona min ma Ya isheni wllhi.. Yanzu idan auren Ummul Ya Mutu Tun a daren yau da wani idanun zan kalli mutanen unguwarmu da dangi baki d’aya… Dije idan kina ma Allah kar ki d’auki Ummul.. Kar ki tafi da Ummul..” Kaman daga sama muryar Asshe ya katse su “Babu yanda za’a tafi da Ummul domin kuwa a halin yanzu mutum d’aya keda iko da Ummul shine mijinta..!” "Gaba d’aya suka juyo suna dubanta, daga Umman Har Mama Dije." Asshe taci gaba da sauk’owa daga bene cikeda k’asaita. Ta k’araso gaban Inna Dije dake tsaye gaban Umma wacce ke duk’e kaman mabaraciya tana Koke Koke. Dije ta zuba ma Asshe idanu. Su duka biyun suna duban juna. kowacce tana sak’awa cikin zuciyarta. Murmusawa Dije Tai tana kuma duban Asshe da kyau “Da gaske..? Bayan duk abubuwan da kika ji… Kin amince a kaima D’anki ajalinsa..? Oh! D’an ‘yaruwarki..? Haka ne..?!” "Asshe ta murmusa tana ma Dije irin duban da biri yake ma Ayaba “Ko mai zai faru a halin yanzu.. Ummul tana k’ark’ashin ikon mu ne.. Sadaki D’anmu Ya biya Wanda Ya tabbatar da wanzuwan igiyoyi Har guda uku da suka mallaka masa cikakken dama da iko akan Ummul. Duk wani abinda zai biyo baya, hukunci zai zamana yana wajenmu.!”" Sosai Mama Dije ta tsareta da idanu tana ji akwai wata a k’asa. Dan ta tabbata wann aure ba auren Allah da Annabi bane.. Duk yanda akai akwai wata shiryayya. Idan auren tsakani da Allah ne bayan duk abinda ta sanar ma Asshe a gaban Suwaiba wacce take mahaifiya ga Ummul ba yanda za’ai Asshe ta amince akaima D’ansu mace irin Ummul. Umma harda sujudusshukur tayi dan farin ciki. Ta shiga d’aga hannaye sama tana mik’a ma Allah godiya “Alhamdulillah..! Alhamdulillah Allah abin godiya.. Allah gatan bawansa.. Kai amma dai annamimi baiji dadi ba.. Zakaran da Allah ya nufa da cara ko fah ana Muzuru ko ana shaho sai yayi.. Kuma wllhi idan rana ta fito tafin hannunki bata isa ta rufesa ba Dije..! Tani ma ta buga Dani ta barni balle ke..!” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye harda rangad’a gud’a. “Bada garaje ba Suwaiba..!” Muryar Asshe ya dakatar da ita. Umma ta waro idanu waje dafe da k’irji tana duban Asshe. Sai kuma ta soma girgiza Kai “A’a dan Allah.. Ki rufa mun asiri Hajja Asshe.. Ki dubi girman Allah kar ki bari mak’iya suyi dariya.. Wllhi duk abinda kikaji daga bakin Dije ba komai bane face sharrin mak’iya..” Asshe ta dafa Umma tana murmushi “Kin yarda cewa aure rai ne dashi..?!” Umma ta jinjina kai tana duban Asshe. Asshe taci gaba “Bazai Mutu ba sai kwanakin Sa ya k’are.. Haka ne..?” Nan ma a sanyaye Umma ta jinina Kai. Asshe ta juya ta basu baya daga Umma har mama Dije lokaci guda tana taka parlorn nata a hankali take ci gaba da fad’in “Bari muce auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..!” Dummm! Haka k’irjin Umma ya buga. Jiri ne taji na neman aikata k’asa. Ta dafe garu tana furta “Ban ban.. Ban fahimceki ba Hajja Asshe.. Mai Kike nufi da cewa auren Ummul zai rayu ne na wani d’an lokaci..?” Assshe ta juyo tana dubansu “Ina nufin zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal.!” Dije ta gyara tsayuwarta sosai tana duban Asshe makirin murmushi kwance saman fuskarta. Cikin zuciyarta take furtawa ‘Eh Lallai.. Da alama yanzu ne wasan zai d’au zafi.. Bari dai mu gani..!’ Muryar Umma ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. “Ban.. Ban gane tsawon watanni uku kacal ba.. Me kike nufi Hajiya Asshe..? Me kike nufi da auren Ummul zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal..? Ki min magana dan Allah.. Ki sanar Dani mai kike nufi..?!” “AUREN WATA UKU..! Ina nufin AUREN WATA UKU kawai mukayi ma D’anmu da ‘yarki.. Bayan wata uku.. ‘Yarki zata dawo gareki.. Sai ki shirya mata wajen zama bayan wata uku..!” Duniyar Umma ya shiga juyawa sama na koma mata k’asa… Ta girgiza kai tana jin hankalinta na neman gushewa da gaske. Cikin rawar murya Umma ke furta “Amma.. Amma meyasa haka Hajiya Asshe.. Shin wani irin aure kukai ma D’anku da ‘Yata… Meyasa na wata uku kawai..?” “D’an ‘Yar uwata yana aiki ne k’ark’ashin Kampanin Mahaifinsa. Mahaifinsa zai basa wani k’wangila ne na tsawon watanni uku kawai idan yayi aure.. Bayan wata uku zai gama wann kwangilar.. Daga nan kuma bamuda buk’atar ‘yarki dan kwangilar ta k’are.. Kin fahimta..?” Ta k’arashe tana duban Umma sosai. "Umma na girgiza kai cikeda rashin yarda take duban Asshe “Amm.. Amma.. Amma.. Bamu yi haka dake ba.. Wann zalunci ne.. ‘Yata ta jima, ta d’auki lokaci batayi aure ba.. meyasa kuka zab’i cutar mun da ‘ya.. Ummul.. Ta wahala a rayuwa, ta fuskanci k’alubale na gujewan manema.. Ta fuskanci k’alubale da dama.. Bata cancanci irin wann auren ba.. ‘Yata ta cancanci aure na gaske.. Aure mai d’orewa ba mai rabewa ba.. Shin Auren Kwangila kukaima D’anku da ‘yata..? Hajiya Asshe kin cuceni.!”" “Ban cuceki ba hasalima taimakon ki nayi.. Idan baki mance ba sadakin ‘yarki shine kud’in jinyar mijinki.!” “Wani irin taimako ne wann..? Wane irin taimako ne haka.. Wann zalunci ne ba taimako ba..” "A zuciye Asshe ta katseta “Kar ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki.. Magana akan cuta.. Shin tsakanin ni da Ke waye ya cuci wani..? Ni da naima D’ana auren cikan buri da ‘yarki ko kuma keda kika cuceni kika sakani a tsaka mai wuya, nai jagoranci wajen aura ma d’an ‘Yaruwata wann ‘yar taki mai lullub’e da Illan asiri da farar k’afa.. shin ki fad’a mun… Tsakanin mu biyun waye ya cuci wani..? Rayuwan d’ana yana tsaka mai wuya a nan.. Idan Haidar Ya Mutu ‘yarki ce Sila.. Shin banyi adalci ba da nace zata zauna na tsawon watanni uku..?!”" Umma taci gaba da hawaye tana duk’e wajen. Asshe taci gaba “Ki gode ma Allah.. ‘Yarki bazata fuskanci tozarci na mutuwan aure a daren aurenta ba.. Ki gode ma Allah bayan duk abubuwan da kikayi ‘yarki zata zauna k’ark’ashin Inuwan aure na tsawon watanni uku.. Ki gode ma Allah bazaki fuskanci dariya da gori harma da wulak’anci idan har auren ‘yarki Ya Mutu a daren yau ba.. Domin kuwa duk wani Sirrinki da naji sai na bankad’e.. Kuma Kinsan me..?” Ta k’arashe tana mai duk’awa gaban Umma dake duk’e tana hawaye “Zaki amar da duk wasu kud’ad’en da na kashe wajen nema ma D’an ‘Yaruwata auren ‘yarki. Kaf ko kobo bazan bari yai ciwon kai ba.. Kin shirya biya.?” Ta k’arashe tana tsare Umma sosai da ido. Inna Dije ta k’arada “Daga nan kuma sai kiyi bankwana da Mijinki Suwaiba bayan kin rasa yaranki. Dan bayan abinda Ya faru ki sani zan d’auke D’anuwana na masa jinya bazan barshi tsakanin mata guda biyu da Babu Allah cikin zukatansu ba..!” Umma ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Dije da Asshe “Dan Allah.. Kar ku jefa rayuwata cikin garari.. Kuji tsoron Allah.. Kuji tausayin rai.. Ku tuna kuma iyaye ne.. Kuma burin ko wace uwa ta kai ‘yarta d’akin miji.” “Kar kiyi mana maganan zama iyaye a nan.. Domin kaw baki tab’a zama uwa ga ‘ya’yanki ba Suwaiba.. Kuma yau zaki fara girban duk abinda kika shuka..!” Dije ta k’arashe tana sakin huci. Asshe ta gyara tsayuwarta “A tsakanin watanni ukun ma inada sharud’a.. Dan Kinsan a daren nan zan iya kashe auren ‘yarki Suwaiba haka ne..?!” Ta k’arashe tana duban Umma kannare da idanu. Umma ta share hawayenta tana kuma jinjina kai a hankali kaman marainiyar mage. Asshe ta jinjina kai “Shradina shine bazakiyi magana da Ummul ba har na tsawon watanni Uku. Ina nufin iyakacin wa’adin zaman da zatai da D’anmu. Keda had’uwa da ita kuma sai kwangilar D’ana Ya k’are randa Ya cika aikinsa ya warware auren.. Ni kuma zan d’auko ‘yarki da kaina na kawo miki ita cikin mutunci. Kin amince..?” Umma ta d’ago a raunane tana duban Asshe jin da gaske dai Auren wutin gadi Ummul tayi ba kaman yanda taci mata buri ba. Sann ga wasu dokoki da sharud’a Wanda aka gindaya na datse alak’arta da ‘yarta “Dan Allah kar kiyi haka.. Kiyi hakuri… Kar ki rabani da Ummul.. Wllhi Ina son ‘Yata..” “Na zata kinfi so tayi aure tayi nesa dake… Ko ba haka bane..?” Asshe ta katse ta. Umma ta kuma rintse idanunta tana hawaye. Muryar Inna Dije ya katseta “Burinki Ya cika Suwaiba.. Mata mazan ‘yarki tayi aure.. Amma aure mai gibi.. Wanda bada jimawa ba angulu zata koma gidanta na tsamiya..” Ta murmusa kafin taci gaba “Inama zanga Tani na bata wann babban Albishir..!” Umma ta shiga d’ago hannaye daga duk’e tana rok’on Dije “Dan girman Allah ki rufa mun asiri Dije.. Kar abinda Ya faru yau ya fita ko ina.. Dan Allah Ku rufa mun asiri.. Wllhi na amince zanyi duk abinda kukace.. Amma kafin nan dan Allah ku barni nai Sallama da Ummul.. Ku barni nai Sallama da ‘Yata..!” Dije da Asshe suka dubi juna kafin Asshe ta jinina kai “Kinada minti talatin kacal kiyi Sallama da ‘yarki.. Sann ki aje wann a ranki.. Kaman dai yau nan da watanni uku zaki sake had’uwa da ‘yarki.. Watak’ila had’uwa ta Har abada..” Umma ta shiga jinina kai tana godiya. Jiki Babu laka ta mik’e ta nufi sashen da aka aje Ummulkhairy. Umma tana shigewa Dije ta juyo tana duban Asshe duban irinta gogaggu. Dukansu biyu suka tsare juna da idanu. Kai da gani zaka fahimci wann ta naima wann kallon biri ne waccan tanai ma d’aya kallon ayaba. Ko wacce irin duban da take ma juna kenan. Dije ta murmusa tace “Kin d’auki kasada mai girma ma d’anki dukda na sanar dake ga abinda Ya samu nawa d’an.. Meyasa..? Meye dalinlinki..?” Asshe ta murmusa irinta gogaggun wayayyu “Aw.! Baki yarda da hujjata bace..? Cewar auren kwangila na tsawon watanni uku mukai da ‘yarku.?” Murmushi Inna Dije Tai “Kar kiyi zaton wayewarki zaisa ki shashashantar Dani kamar yanda kika shahsantar da Suwaiba.. Ni ba Suwaiba bace.. K’ar nake kallonki.. Dan haka Ki sanar dani meye asalin dalilinki.. Dan babu wanda zaiji abinda na fad’a Ya kuma amince D’ansa ko wani nasa yai tarayya da Ummul.. Bayan jifa na asiri dake jikinta ita d’in barazana ce ga rayuwarsa.. Anya akwai wacce zata amince wani nata Ya zauna da Ummul matsayin matar aure..? Ko da yake ba d’anki da kika haifa bane.. D’an ‘Yaruwarki ne.. Tabbas akwai banbanci.!” Ta k’arashe shu’umin murmushi saman fuskarta. Asshe ta murmusa “Jifa na asiri..? Toh kodai kece kikai jifan.. Dan idan Har Zan amince D’an ‘Yaruwata ya auri ‘yarku mai tawaya na asiri.. Bana jin akwai wacce zata tona ma ‘yar D’an uwanta asiri irin haka.. Kaman dai yanda kikai ma Ummul.. Da ni dake dukanmu ‘Yanuwa ne ga iyayen Ummul da kuma Haidar.. Haka ne..?” Dije Tai shiru tana duban Asshe. Ta kula su duka biyun Sun k’ware a iya buga wasan. Tabbas kuskure kad’an zatai gaban matar nan ta sha k’asa.. Koda wasa bazata bari hakan ta kasance ba. Gwara ta gyara d’amararta da kyau. Murmusawa Dije tai tace “Af! K’warai haka fah.. Magana ake na gwaggwani da Innoni.. Wanda yafi nuna kula ga nasa.. Tabbas shi zai d’auki kambin.. Mai zai faru idan na tafi na samu ‘yaruwarki na sanar da ita ga abinda kika shirya ma D’anta… A bayan idonta..?” Ta k’arashe tana tsare Asshe da idanu ga muguwar murmushi saman fuskarta. Asshe ta d’an d’auki lokaci tana dubanta. Dukda bugu da zuciyarta keyi bai hanata tattaro natsuwarta ba dan bata so ta bama Dije k’ofan da zata d’ago rauninta. ta murmusa tace “Wai ance da D’an gari akanki gari.. Kin tab’a jin an shiga gari yak’i Anci yak’in ba tareda taimakon D’an gari ba..? Ina nufin kinada masaniyar wace irin yarda ce tsakanin ‘yanuwa biyu.?” Ta k’arashe tana tsare Dijen da idanu itama..” "Su dukansu biyu suna duban juna. Asshe ta murmusa ganin Dije bata bata amsa ba. Ta k’araso ta dafa Dije kad’an “A shawarce “Kowa ya tsaya a masarautarsa , Ina nufin kiyi yanda kikaso da Suwaiba harma da D’anuwanki.. Kar ki shiga tsakanina da ‘Yaruwata.. Dan nasan bazaki so yin wasa da wuta ba..”Ta k’arashe murmushi saman fuskarta." Dije ta murmusa “D’iyar mak’eri bata shakkan wuta.. Hasalima ta saba wasa da wuta.. Kiyi tunani kan abinda na sanar dake. Domin kuwa kaman yanda kika amshi bak’oncina cikin gidanki ba tareda kin gayyaceni ba. Toh ina mai tabbatar Miki zan kai ziyara ma ‘yaruwarki ta birnin tarayya.. Ina nufin mahaifiyar surkinmu.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Shiru Asshe tai zuciyarta na kuma bugawa. Lallai wann matar babbar barazana ce a gareta. Dan tabbas idan ta tafi ta samu Kwaise ta sanar da ita abinda ke faruwa toh fah tata ta k’are. Sosai tai nisa cikin duniyar tunanin yanda zata b’ullo ma wann Dijen wacce ta zamto babban threat a gareta. Inna Dije ta gyara zaman mayafinta “Kiyi tunani da kyau.. Ni zan tafi.. Dare yana yi.. Amma kafin na tafi ki zuba mun lambobinki a nan.. Sabuwar k’awata..” Ta k’arashe tana duban Asshe da ta zama deep in thoughts. Asshe ta dubeta irin duban baki kai ki shiga jerin matsayin kawayena ba.. Sai kuma ta murmusa abinka da gogaggiya “K’awa..? Oh haka ne… Ta bayan fage..!” Ta k’arashe maganar tana Shafa kwantattun gwalgwalan dake zube wuyanta zuwa kunnuwanta da hannayenta. Dije sai dubanta take tana jinina barikin matar nan. Watau bazata fad’a mata matsayinta da baki ba saidai yanayin shigarta da suturan dake jikinta Ya tantance hakan. Lokaci guda ta d’auki wayarta ta mik’a ma Inna Dije “Zuba min lambobinki a nan..” Inna Dije ta murmusa kafin ta dubi wayar kaman zata amsa sai kuma ta tabe baki tace “Baki tunanin ban Saba da rik’e irin wayoyin nan naku ba.. K’awa..!” Ta k’arashe tana juya mata gajiyayyar wayar dake rik’e hannunta harda d’aurin robber ring jiki. "Asshe ta murmusa tace “Gashi Ba hand sanitiser kusa, bara na sanar dake da baki sai ki juye a naki wayar.. Ya Miki..”" Dije ta jinjina kai “Kar ki damu.. matuk’a bazaki lank’wasa harshe ba.. Anyi alimantari an samu na zama cikin Al’umma.. Kar ki mance lambobin gaske zaki bada dan idan ba haka ba. Zan riga ki isa wajen ‘yaruwarki.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. A haka dai sukai exchanging phone numbers kowa tana watsa ma juna bak’ar magana da sako a dunk’ule. Inna Dije zata fice Asshe ta dakatar da ita “Ina Miki ta’aziyar D’anki.. Ina kuma fata hakan bazai faru da nawa D’an ba..” Inna Dije ta murmusa “Fata mai kyau.. Allah yasa.. Idan kuma fatanki bai amsu ba.. Sai ki tanadi farin k’yalle nan da watanni uku.. Watak’ila akwai cin gumba gidan k’awata..” Suka sakar ma juna murmushi Wanda yafi kama da yake. Kafin daga bisani suka kuma yin Sallama. Asshe ta juya idanu cikeda k’osawa Har Inna Dije ta fice. Zama Tai cikin kujera tana mai furtawa a fili “Oh ni Asshe wasu irin mutane na jajib’o mana ne wai.. Ita Suwaiba nayi zaton abin nata a shashanci da wauta kawai ya tsaya ashe Shegiya wawiyar gangance ‘yar boka. Ga Tani daga can gefe mai cinye gadon miji yana raye.. Ita kuma wann Dijen da alama itace tafi kowa hatsabibanci cikin ahalin domin kuwa idan har banyi da gaske ba zata zame min babban barazana..!” Ta mik’e cikin sand’a ta nufi d’akin da Umma ke ban kwana da Ummul d’inta. Jikin k’ofa ta mak’ale tana sauraron tattaunawar ‘ya da Uwan. Umma tai k’ok’arin saita kanta tana duban Ummul dake dubanta cikin rashin yarda hawaye kwance saman k’uncinta. Sosai Umma ta sha mur kaman ba ita ba. Cikin zuciyarta kaw k’ok’arin danne raunin nata kawai take dan k’arfafa gwiwar ‘yar tata. Cikin kakkausan murya ta ambato sunan Ummulkhairy snn taci gaba “Ina so ki mun alk’awari guda d’aya Ummulkhairy.. Watak’ila shi kad’ai ne alfarmar da zan nema daga wajenki.!” Ummul ta kuma duban mahaifiyar tata jiki a matuk’ar sanyaye. Murya na tsananin rawa take furta “Umma kin wuce ki nemi alfarma wajena.. Kar ki mance ke mahaifiyata ce.. Ko me kike so nayi matuk’a bai sab’a wa Ubangijina ba zanyi… Dan cikan burinki… Zan zan Miki Umma..!” Ta k’arashe cikin sautin kuka. Dukda kuka da yazo ma Umma amma sai tayi k’ok’arin danne kukanta “Ummulkhairy kar ki neme ni… Kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Ko a waya kar ki kirani.. Ki min alk’awarin.!” Da tsananin mamaki Ummul ke duban mahaifiyarta. Ta shiga girgiza kai cikin rashin yarda “Umma.. Mai hakan yake nufi..? Umma zaki yanke duk wata alak’a dani ne..?” Umma ta jinjina mata kai alamun eh “K’warai Ummul.. Kuma kema kimin alk’awarin yanke alak’arki damu.. Ina nufin da d’aukacin ahalinki na tsawon watanni uku.. Kimin wann alk’awarin..!” Ta k’arashe tana duban Ummul d’in. Girgiza kai Ummul keyi tana duban mahaifiyarta “Umma.. Kin kaw ji abinda kike fad’i mun..? Umma yanke alak’a da iyayena harda mahaifina dake kwance yana jinya..? Umma Anya..” Katseta Umma tai “Na tsawon watanni uku kacal.. Dan Allah ki mun wann Ummul..!” Ta k’arashe tana kamo hannayen Ummul d’in alamun rok’o hawayen da taketa k’ok’arin dannewa na kwaranyo mata. A hankali Ummul ta zame hannayenta tana girgiza kai “A’a Umma.. Baki tunanin Kin tafi da nisa Umma.. Bazan iya ba.. Bazan iya abinda kike nema daga wajena ba.. Bazan iya yanke alak’a da ahalina ba.. Menene dalilinki Umma..?” "Umma taci gaba da matsan k’walla. Sai kuma ta mik’e tana huci “Wann Shine kad’ai abinda na nema daga wajenki Ummul.. Kar ki nemeni, kar ki tako yanda nake Har na tsawon watanni uku.. Idan kuma kika nemi ni ko kika tako yanda nake kafin wata uku ban yafe miki ba.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice kuka na kuma b’alle mata." Ummul Tai zaune tamkar wacce aka dasa. Ta nemi kuka ta rasa. Sai ta shiga tambayan kanta Wacece ita..? Meyasa rayuwa yazo mata a haka..? Shin ita kad’ai ce take fuskantar k’alubale irin nata..? Shin Anya Umma itace ta haifeta..? Anya uwa takan haifi ‘ya tayi watsi da ita irin haka.. Tin daga tasowarta Umma bata tab’a damuwa da al’amarin rayuwarta ba. Ta mata aure a wulak’ance. Daga k’arshe ta datse alak’a da ita ba tareda dalili ko hujja ba.. Anya ana samun irin wann uwar.. Anya ko a labarai ta tab’a cin karo da uwa irin Umma..? Ta shiga girgiza kai tana duban d’akin da aka ajeta. Lokaci guda ta mik’e tana takawa a hankali. Daidai gaban madubi taja ta tsaya tana duban kanta cikin madubin. Take zuciyarta Ya shiga karanto mata wacece ita. Tin daga lokacin k’uruciyarta har kawo girmanta. Duban kanta take cikin mirror hawaye na zurarowa daga cikin idanunta d’aya na bin d’aya. A hankali ta silale a wajen cikin kuka maras sauti tana jin tamkar bata a duniyar. ** Umma ta kusan ficewa kenan taji an damk’o hannunta an janyota wani d’akin. Asshe ta gani tsaye tana sakar mata murmushi “Kinyi abinda ya kamata.” Jinjina kai Umma tai tana duban Asshe “Ki sani da ace nasan irin auren da zakuyi ma D’anku da Ummul kenan tun farko da ban amince ba. Amma saidai idona Sun rufe Allah Ya barni da iyawata a lokacin da na Shafa’a da neman zab’i daga gareshi. Watak’ila wann shine hukunci na.” Ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba “Nayi abinda kuke so.. Na yanke alak’a na wucin gadi da Ummul kaman yanda kukai auren wucin gadi da ita.. Alak’ata da ‘yata zai dawo ne bayan sharud’anku Sun cika.. Wann lokacin kuma.. Nayi alk’awarin sabanta alak’ata da ‘Yata.. Nayi alk’awarin bata kulan da ban bata ba tsawon rayuwarta.. Nayi alk’awarin nuna mata soyayya irin Wanda na hana mata a matsayin uwa tsawon rayuwarta… Na..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Da k’yar ta iya saita kanta kafin taci gaba “Iyakacin abinda zan rok’a daga wajenki shine ki kula mun da Ummul .. Dan Allah kar kici amanata Asshe.. Ke kad’ai na sani cikin ahalin da Ummul zata shiga na watanni uku… Dan Allah Ki kular mun da ita.. Kuma ki rike amanata kar ki tab’a tona sirri na ma Ummul… Kar ki sanar da ita AUREN WATA UKU tayi kuma inada masaniya. Dan Allah kimin wann..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka hannayenta had’e waje guda alamun rok’o. Asshe tab’e da baki take duban Umma babu ko alamun tausayi. Cikin zuciyarta take ayyana dan ma baki san dalilin auren ‘yar taki shine ta karya sihiri ba. Sann auren yana nufin ajalinta. Ki gode ma Allah itama ta zama barazana ga rayuwar Haidar Wanda hakan zaisa ki sake had’uwa da ‘yarki bayan wata uku. Dan bazan tab’a bari Haidar ya kusanci wann ‘yar taki ba. Ta murmusa kad’an “Kin kware wajen iya wasan kwaiwayo Suwaiba.. Ban Miki alk’awarin komai ba… Dan bayan amanata da kikaci bansan mai zai faru a tsakanin wata uku ba..!” Cikin zuban hawaye Umma ta shiga jinjina kai tana k’ok’arin mik’ewa. Jiki a matuk’ar sanyaye tasa k’afa zata fice Asshe ta kuma dakatar da ita. Umma taja ta tsaya Har lokacin hawaye take. Asshe ta k’araso tana duban Umma daga sama zuwa k’asa. Lokaci guda tasa hannu ta shiga janyota da k’arfin gaske . A haka suka isa gate. Suna isowa gate tai jifa da Umma gaban securities. Asshe ta shiga nuna masu Umma “Ko me kamannin matar nan kar ku bari ta kuma shigowa gidan nan..” Umma dake watse k’asa kaman kayan wanki ta d’ago idanunta da kyar tana duban Asshe dan yanzu ta daina mamakin abubuwa. “Asshe…” “Shiiii..!” Asshe ta dakatar da ita tana mai d’ora yatsa ta guda saman labb’anta “Duk draman da akayi mijina baida masaniya Suwaiba.. Ni Ina son mijina kuma ina daraja aurena.. Ni ba irinki bace wacce ta watsar da mijinta dake kwance yana jinya sabida cikan burinta. Bazan bari mace irinki ta lalata mun aure ba.. Dan haka bake ba ni. Dama kema kinsan hanyar jirgi ba daidai bane da na mota. Ni da Ke ba d’aya bane. Ciniki Ya had’amu kuma ta k’are. Babban goro sai magogin k’arfe bayan wata uku zaki sake haduwa da ‘yarki idan d’anmu Ya gama kwangilarsa dan ita ba ajinsa bane. Zaren ba kalar yadin bane. Tashi ki fice kafin nasa su fitar dake..!” Ta k’arashe tana nuna mata k’ofa. Jiki Babu k’wari Umma ta mik’e tana ganin duhu na gauraye mata k’wayan idanu. Ta shiga had’e hanya tana takawa da kyar tana jin wani abu mai zafi na yawo cikin k’irjinta.. A haka Umma ta fice daga gidan ga duhun dare ba tareda tasan ina take zuwa ba. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *22* *©️Sameena Aleeyou… * A b’angaren Inna Dije kaw koda ta fice sai ta tadda Khulsum a yanda tace ta zauna ta jirata. Dan dama lokacin da Umma ta kori Khulsum daga wajen Ummul Inna Dije ta had’u da ita a k’ofan gidan tana kuka. Nan take sanar da Inna Dije ga yanda sukai ita da Ummanta hakan yasa Inna Dije Tai mata umarni da ta jirata Har ta shiga ta fito zasu tafi tare. Basu zarce ko ina ba sai asibiti wajen Abba. Inna Dije ta k’ura ma D’anuwanta dake kwance idanu. Ta shiga jinjina kai tana mai furtawa a fili “Lallai Yaya ka gamu da jarabawan shed’anun Mata.. Amma da izinin Allah ba macen da zata saka samun damar cutar dakai cikinsu.. Bazan bari hakan ta kasance ba.. Na maka alk’awari D’anuwana.” Ta k’arashe tana dafe hannunsa guda. Khulsum dake zaune gefe ta goge hawayen da suka gangaro mata tana jin ciwon abinda mahaifiyarta da abokiyar zaman mahaifiyar nata sukai ma mahaifinta Wanda Babu mijin da Ya cancanci mata Irinsu. "Mama Dije ta matso ta rungume Khulsum tace “Kar ki damu Khulsumu. In sha Allahu mahaifinki zai samu lafiya, zan d’auke shi daga nan.. Zamu tafi gaba dayanmu.. Zamu fara sabuwar rayuwa gaba d’ayanmu tare.. Su kuma Suwaiba da Tani ko waccensu zata girbi abinda ta shuka ne..”" Khulsum bata iya cewa komai ba sai kauda fuskanta gefe da Tai tana mai kuma goge hawayen dake zubo mata. Dan Allah ya gani dukda Umma ta kasance mahaifiyarta sai taji sam bata ko k’aunar a ambato mata sunan mahaifiyar tata musamman bayan rabuwar da sukai a daren yau d’in. "Mama Dije sai duban Khulsum take tana sak’a abubuwa cikin zuciyarta ‘Tabbas sai ta cika Zuciyar Khulsum da tsanar mahaifiyarta.. Suwaiba zata rasa yaranta gaba d’aya.. Bayan ta rasa Ummul zata rasa Khulsum ma. Zata rasa ahalinta gaba d’aya dan mijin ma ta rasa shi kenan rashi na Har abada.. Sai ta tabbata rayuwa yayi k’unci ma Suwaiba, k’uncin da sai ta gwammaci mutuwa da wann rayuwar… Kaman yanda ta rasa Fa’iz d’inta D’anuwanta tilo Ya kuma k’ullaceta sabida soyayyan Suwaiba da ya rufe masa ido. Ta rasa soyayyan D’anuwanta na tsawon shekaru zata tabbata tayi amfani da wann damar ta dawo da shak’uwa da soyayya dake tsakaninta da D’anuwanta.. Snn zata rattaba Auren Ummul ya Mutu kafin wa’adinsa ya cika. Bayan auren ya Mutu ta bi ta sanar da Ummul irin auren tozarci da Suwaiba tai mata. Sai ta kwance ma Suwaiba zani kasuwa gaban ‘ya’yanta. Dik irin biyayya da Ummul ke ma Suwaiba sai ta tabbata ta masu farrak’u bayan ta kashe wulak’antaccen auren da tai ma Ummul. Suwaiba zata zama batada tsuntsu batada tarko. Zata rasa kowa tin daga kan Yayanta Isubu da zata masa jinya a yanzu wanda makahon soyayyan da yake ma Suwaiba ya hanasa ganin aibun Suwaiban har dai suka sami sab’ani mai muni duk sabida Suwaiba har izuwa kan yaranta guda biyu Ummulkhairy da kuma Ummulkhulsum.. Wann alwashi ne da ta d’auka ma kanta. Ta saki murmushi a hankali tana jin zuciyarta na mata sanyi al’amara suna tafiya mata yanda take so." ** Ikon Allah ne ya kawo Umma gida. Tana isowa ta hangi fitilan d’akin Tani a kashe. A nata tunanin Tani ta kwanta bacci tinda tasan kaman yanda Dije tace bazata kuma barin d’aya daga cikinsu ta kusanci Abba ba tasan bazata bar Tani ta zauna can asibiti wajen Abba ba. Hakan yasa ta shiga sand’a a hankali alamun bata so Tani taji dawowarta. "Kaman Wata b’arauniya haka ta shige d’akinta cikin sand’a tana addu’an Allah yasa ta tadda Khulsum na bacci. Saidai koda ta shige d’akin babu Khulsum Babu alamunta. Umma ta silale ta zauna da kyar tana duban gadon yaran nata da angle din da ko wacce ta Saba kwanciya.. Sai ta tuna irin rabuwar da sukai da Khulsum duk Akan Auren Ummul. Datse alak’a tai tsakaninta da ‘yarta Khulsum. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un tana cikin hayyacinta ta aikata makamancin wann abu. Sai ta soma tunanin toh ina Khulsum ta shige.? Take zuciyarta ta bata amsa da fad’in tana wajen mahaifinta a asibiti kaman yanda kika koreta daga gareki. Khulsum bata da wajen zuwa da ya shige wajen mahaifinta. Umma ta silale a hankali hawaye na kuma b’alle mata. Sai tana jin wani abu da yafi yanayi da tashin hankali na ziyartarta… Yau dai Babu Ummul a cikin gidan, wacce a kullum idan ta bud’e idanu ta ganta cikin gidan Babu aure zuciyarta ke mata ciwo, hankalinta ke tashi. Haka zalika taita kausasa harshenta Akan k’addarar ‘yar tata. Meyasa bataji ciwon ya tafi ba..? Meyasa duk tulin damuwar da Tai a baya Wanda a nata zaton ganin Ummul ne a gida ba tareda aure ba ya haddasa mata. Meyasa taji babu abinda ya ragu a k’uncin da takeji cikin ranta sai ma abinda ya k’aru..? Meyasa..? Meyasa abubuwa suka kwabe meyasa auren Ummul da tai zaton zai zamto mabudin farin cikin ta da na ahalinta meyasa bai zama haka ba.. Meyasa auren Ummul ke barazanan zama mabudi da Mafarin tarwatsewar Ahalinta.. Ta rintse idanunta wasu hawayen masu tsananin ciwo suna zubo mata. Saida Umma tai kuka mai isanta ita kad’ai cikin d’aki with no shoulder to lean on. Babu wanda zaiji sautin kukan nata balle Ya lallasheta.. Ita kadanta cikin d’aki tasha kukanta. Dakin ya mata girma, daren ya mata tsayi… Haka Umma taci kukanta a d’aki cikin dare tamkar marainiyar kenwa." ** Washe gari sassafe ake shirin tafiya da Amarya Ummulkhairi gidan mijinta dake Abuja. Asshe ta fito taci uwar gayu yayinda Ummul ta kasa fitowa sai shesshek’ar kuka take Wanda ya riga ya zame mata jiki. Tin Daren jiya take aikin abu d’aya Akan dole Asshe ta tilasta ma cin abinci ma saida tai da gaske kafin ta saka ruwan shayi a cikinta. Kallo guda zaka mata ta baka tausayi. Asshe sai sababi take tana fad’in haka za’a Kai amarya a k’anjale jiki duk yunwa kaman wata kazar mayu. Cikin ranta kuwa addu’a take Allah yasa Ummul tafi haka lalacewa ko dan kar idon Haidar da hankalinsa ya sauk’a kanta. A haka suka fito da k’yar bayan Asshe ta sanar da Ummul kar ta mance kud’in Aurenta shine kud’in jinyar mahaifinta dan haka tafiya gidan Miji ya zame mata dole idan har ba so take su janye komai ba. Ummul na hawaye take janyo k’afafunta. Tabbas wann auren sadaukarwa ne ga illahirin ahalinta. Bayan datse alak’a da ita da Umma tai a daren jiya na tsawon watanni uku na farkon aurenta bata jin Umma zata tab’a yafe mata idan tace ta fasa wann aure. Ta rintse idanunta zuciyarta na tausarta da cewa irin nata k’addaran kenan. Watak’ila hakan shine alkhairi ga d’aukacin ahalinta. Idan tai nesa dasu Watak’ila farin ciki da kwanciyar hankali zai wanzu cikin ahalin irin Wanda basu samu a baya ba. Fitowar da zasuyi da zummar shiga mota kenan suka sinkayo wata murya. “Ku dakata ku dakata. Direba a dakata ga pasinja d’aya.!” Ta k’arashe tana kuma mak’ale k’aramar jakar Ghana must go d’inta a hammata sai faman buga sauri take. Asshe ta zaro ido tana duban matar nan shaye da tsananin mamaki “Dije.!” Ta furta da k’arfi. Inna Dije taci gaba da sakin murmushi tana duban Asshe “Haba k’awa ban gane wasa tare ci banban ba. Haka kika shirya tafiya da ‘yarmu babu wani nata. Ce Miki akai batada dangi ko tsawa akai ta fad’o da zaki rufeta ki kaita kamar wata maras gata.” "Ummul tai saurin yaye rufin kanta hawaye na kuma b’alle mata “Inna Dije.” Ta furta a hankali tana duban Dije. Dije tai saurin k’arasawa ta rungumi ‘yar D’anuwanta “Ni ce nan Goggonki Ummul.. Innarki Dije, bazan bari a kaiki gidan miji kamar maras gata ba. Shige muje.!” Ta k’arashe tana mai shigar da Ummul cikin mota." Har lokacin mamaki Ya kasa sakin Asshe. Watau matar nan ta ranste sai ta tona mata asiri. Inaa bazata bari hakan ta kasance ba.. Kafin Tai aune taji Inna Dije ta janyo hannunta ta jefata cikin mota. Fad’i take “Direba tada mota muje birnin tarayya ba nan kusa ba.” Asshe ta matse hannun Inna Dije da k’arfi tana k’ok’arin fiddota waje amma sai taji Inna Dije ko gizau bata motsa ba. Saitin kunnen Asshe take rad’a mata “Kar kiyi wann ganganci dan tsaf zan kwance Miki zani a Kasuwa. Kama daga kan mijinki da kishiyoyinki Har izuwa kan ‘yaruwarki. Dan haka cikin salama ki shige mu tafi.!” Ta k’arashe tana firfito da idanu waje. Asshe ta had’iyi abinda Ya tsaya mata a mak’oshi da k’yar. Cikin sigan rad’a take tambayarta “Fad’a mun nawa kike so.?” "Inna Dije ta murmusa, cikin sigan rad’a ta bata amsa da fad’in“Ki bari mu isa can zamuyi ciniki a tsanake.” Sai ta murmusa tana k’are ma Asshe kallo harda kashe mata ido “Kar ki damu k’awalliya zamu sha hirarmu ta k’awaye a mota.” Ta k’arashe tana d’aka ma Asshe bugu a cinya harda kecewa da dariya. Ta dubi driver tace yaja mota su tafi kar rana yai masu a hanya. Driver kaw yai yanda tace dan dai Asshe kam ta kasa katab’us cikin motan. Abun matar Ya koma bata tsoro. Ta d’auki Suwaiba shashasha amma wann kam ko shakka babu gogaggiya ce . Tanaji tana gani suka d’auki hanya tareda Dije babu kuma yanda ta iya. Abinda take tsoro ne yake gab da aukuwa. Mai zai faru idan wann matar da ta zame mata k’arfen k’afa ta bud’e baki ta sanar da uwar Haidar komai. Ta tabbata Kwaise zata iya d’aureta Har igiya yayi saura sann asirinta gaban miji da kishiyoyi harma da yaranta Ya tonu. Lallai Ya zama dole ta san yanda zata b’ullo ma wann matar. Idan ta kama ta b’atar da ita tun akan hanya ne kafin su isa zatai hakan. Dole ta canza salon yanda zata tunk’ari wann mahaukaciyar Matar da burin fansan ran D’anta Ya rufe mata ido. Haka dai Asshe taita sak’awa tana kwancewa cikin mota. Gaba d’aya kallo d’aya zaka mata ka gane a birkice take." ** A b’angaren Umma kaw sassafe da rabon fad’an yaran Mama ta tashi. Badia da Azeema sai tona ma juna asiri suke Azeema na fad’in sai Badia ta nemo B’arawon mijinta yanda ya shiga ya fita. Yayinda Badia ke fad’in gwara nata mijin a sata Ya tsaya ita kaw Azeema ba Wanda baisan Habibu k’aton kwarto bane Wanda baya raina mai d’ankwali. Nan dai akaita fad’a Umma na k’ok’arin rabiya amma inaa saida dai akai chaa a k’ofan b’angaren nasu kaman ko yaushe ana bama ido abinci. Azeema taci gaba da fad’in “Oho dai gwara ni mijina baiyi sanadin rufe uwata a police station ba. Hasalima fad’i tashi yake ba dare ba rana dan ya fidda mahaifiyarmu da wann macucin mijin naki ya jefata ciki.. Kuma wllhi idan Har baki fito da Tasi ba zan tona miki asiri wajen Jami’an tsaro dan ba Mama bace kawai ta saka hannu a takardun bogin da mijinki ya kawo na saida Shagon Abba harda ke macuciya azzaluma.!” Haba nan fah Badia ta janyo Azeema dambe ya kaure tsakaninsu. Umma ta shiga tsakiya tana k’ok’arin rabiya aikaw akai jifa da ita gefe. K’um kakeji jini ya b’alle a goshin Umma. Ta dafe kanta dake juya mata tana shafan jinin dake zubowa daga goshinta. Da rarrafe Umma ta bar wajen ta shige d’aki dan ba mutan gidan kawai ba har mak’ota lek’ensu suke suna Allah wadai irin wann ahali. Saikace ba jiya akai auren Ummul ba wacce kowa yake tunanin sabida ita ahalin suka gaza samun kwamciyar hankali. Sai gashi yau an wayi gari babu Ummul da akai mata lak’abi da annoba cikin gidan amma da tashin hankali suka wayi gari kaman dai ko yaushe. Umma ta matse bakinta tana jin kukan gaske mai k’arfi na taso mata musamman da taji abubuwan da mutane ke fad’i. Ta kuma shafan goshinta taga jini. Ta rintse idanunta tana tunanin ‘ya’yanta a daidai lokacin da jini ke fitowa daga goshinta. Ta aurar da Ummul bisa son zuciyarta sann ta kori Khulsum. Ummul take hangowa tana share mata jinin goshinta cikin tsananin nuna soyayya da kulawa yayinda take hango Khulsum tsakiyan Azeema da Badia tana k’ok’arin k’watar wa mahaifiyarta hakkin rauni da sukai mata a goshi. Umma ta fashe da wani irin kuka mai ciwo. Lallai mutum baya gane kiman wani ni’ima da Ubangiji yai masa baiwa dashi sai ya rasa wann abun. A haka Umma taci kuka da suntumemmen goshi ita kad’ai a d’aki. "Rayuwa kenan ko babu rabuwa akwai mutuwa. Mu zama masu godiya ga d’imbin rahamomin ubangijinmu garemu tun kafin daman hakan ya kufce mana. Tomorrow is not promised. Mu so juna muyi hakuri da juna. Mutanen da Allah ya albarkace mu dasu cikin rayuwarmu. Walau iyaye, ‘ya’ya, miji, mata abokan zama da sauransu. Rayuwar duka batada tsawo. Abinda hak’uri bai kawo shi ba tashin hankali bazai bayar ba. Allah ya mana muwafak’a duniya da lahira. Ameen." ** A can b’angaren Mama Tani kuwa yanda taga rana haka taga dare a police station. Fuskarta ta kumbura suntum sakamon Mari da tasha hannun tsagerun ‘yanmatan da aka had’asu cell d’aya. Sallah ne kawai yake ceton Mama daga bugun da take sha hannun tsagerun nan. Saiga Mama tana sallah cikin cell harda nafilfili. Har bata fatan ta ida sallah gudun kar su ci gaba da cutar da ita. Yara k’anana Har tausa suke sa ta masu idan batayi ba taci bugu. Ta kula ko neman agaji take wajen ‘yansandan basu kawo mata d’auki musamman wann matar da ta gansu da Habibu. Ta nemi a fitar da ita zataje fitsari. Da k’yar da sid’in goshi aka fitar da ita tinda bata jima da fita alola ba. Addu’a take Allah Ya had’ata da Habibu Ya sanar da ita yaushe za’a fiddata. Kaman daga sama ta bayan d’akin da aka kaita fitsari yanda band’akin suke a jere ta soma jin maganganun ta wata ‘yar window. Muryar Habibu takeji daga window d’in yana kwantar ma ‘yarsandar hankali da fad’in shi fah ba taimakon Mama Tani zai ba. Dama yayi zaton zai cimma Tasi’u ne kafin abubuwa su lalace. Dan haka bazai jefa kansa a uku ba dan wann bakwaiye Ya rantse har kotu sai an tafi. K’arshe gidan Kasu Tani zata tafi babu ranar fita. ‘Yarta kuma babu amfanin da take masa saima cike masa d’aki da tai dan haka a yau d’in nan zai rubuta mata takarda tinda Tasi’u Ya gudu da kud’ad’en. Aure zaiyi Ya saka amaryarsa a d’akin. Sai ga Mama tana sakin fitsarin jikinta. Ta kama k’arfen window ta d’ale tana dubansu “Habibu.. Irin cin amana da yaudara da zakai ma Azeema kenan..! Amma Habibu Allah Ya tsine maka albarka. Ka cuceni ka cuci Azeema. Habibu Allah bazai barka ba. Kan wann kilakir ka wulak’anta Azeema.?” Kafin takai aya taji sauk’an tagwayen Mari a fuskarta. ‘Yar sandar Habibu ce tai mata Marin “Ki iya bakinki kisan a ina kike.” Cewar budurwar Habibu Yayinda Habibu ke mik’a mata farar takarda “Tazo gidan sauk’i tinda kina kusa. Ga wann ki bawa ‘yarki idan gantalinta Ya d’ebota ta nan tinda ba mutuncinki suke gani ba balle suzo dubiyanki. Kar na koma gida na tadda tsummokaranta cikin d’akina. Sak’o na baki ki sanar da ita. Gyara zan fara a gaggauce dan amarya ta zan aje ciki.” Ya k’arashe yana kashe ‘yarsandarsa da murmushi. Mama sai Tai mutuwar tsaye tana juya takardan da Habibu Ya mik’a mata cikin hannunta. Bata san meke wakana ba har saida ‘yarsandar da tai mata rakiya fitsari ta tasa k’eyarta. Fitsarin da ta juyesa jikinta kenan ba tareda taje band’aki ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Meke faruwa da ita da yaranta? Daga wacce miji Ya bata sak’on sakinta ta hannun mahaifiyarta sai wacce miji Ya cuta ya kuma gudu Ya barta. Sann a dalilinsa aka kame uwarta aka gark’ame. Shin wann wace irin rayuwa ce. Sai ga Mama tana kuka shar shar da hawaye hannaye biyu aka “Wayyo ni Tani naga takaina.! Habibu kaji tsoron Allah. Ka tuna ko mutuwa na kunyar idon uwa. Yanzu da wani bakin zan goranta ma Suwaiba ni Tani. ‘Yar Suwaiba ta tafi d’akin Miji ni nawa yaran Sun dawo a jere. Wllhi bazata saku ba. da na koma na fuskanci tozarci yo gwara na Mutu a nan.!” Ta kuma kurma kururwa. Tsawa budurwar Habibu ta daka ma abokan aikinta cewa su shige da Tani cikin cell d’inta su gark’ame. ** Abuja "Tsaye suke a can construction site d’insu, yanda zasu gudanar da babban project na Kampaninsu." Dukansu sanye suke da kaya irinta k’wararrun Engrs. Reflective safety jacket kalan d’orawa mai ratsin bak’i sai safety helmet mai d’aukeda tambarin kamfaninsu daga gaban *MB* Su kusan hud’u sunyi tsaye gaban wani tapkeken sketch. Design Architect Hisham sai kwararo bayani yake yayinda sauran ke jinjina Kai kowa yana fad’in abinda ya k’ware akai. Hisham na hankalce da Haidar Wanda Sam hankalinsa bai tare dasu. Excusing Kansa yai ya k’araso yanda Haidar ke tsaye jingine jikin mota. Shima d’in cikin shiga irin tasu yake saidai shi babu jacket saman rigarsa sai ko helmet. Hisham yai masa k’uri hannayensa zube cikin aljihun jeans d’insa. D’an k’arasowa yai kusan Haidar d’ in had’ida jingina jikin motar. Ba tareda ya dubi Haidar d’in ba ya soma fad’in “This is not like you Engr. Ban Saba ganin ana aiki jikinka a mace ba.. I expect to see Haidar mai jajircewa da na sani dan ban tab’a tsammanin Dad d’inka zai mik’a maka ragamar aikin nan cikin sauk’I ba.. Snn kaji yanda abokinsa yake yabawa team d’inmu baice komai ba baiyi yunk’urin dakatar dashi ba kaman yanda ya saba a baya. Kawo yanzu sun hango future ma Kampanin tareda kai. Zan iya ce maka na hango yau d’in a k’awayar idanunsa. Ko bai furta maka ba he’s proud of you..” "Furzar da huci kad’an Haidar yai yana mai gyara tsayuwarsa hannayensa zube cikin aljihunsa yake duban masu tonon k’asa daga gefe “But unfortunately I’m not a perfectionist, a workaholic like my Dad.” Ya karkato yana duban Hisham sosai “Ban damu ba yayi alfahari dani ko kar yayi. I don’t give a damn..”" "Hisham ya d’an girgiza Kai yana duban Haidar d’in “So tari mukan kasa ganin blessings da Allah ya mana baiwa dasu har sai mun rasa. Ka gode ma Allah Haidar ka girma da iyayenka biyu a raye kuma suna tareda kai. In my own case is a different story. Ban samu daman sanin mahaifina ba. Ban samu daman had’uwa dashi ba.” Ya d’anyi fasali kafin ya murmusa “But it’s fine I’m not complaining. Alhamdulillah, At least I have my Mom with me. And to me" she’s more than enough you know.” Ya kuma murmusawa yana jinina Kai “Bazamu iya k’irga d’inbin ni’imomin Ubangijinmu garemu ba.” Dukda sanyi da jikin Haidar yai sai ya kauda Kai gefe dan shi gani yake da mahaifinsa da babu shi duk d’aya ne gwara ma ace babun Watak’ila bazai masa irin k’iyayyan da yake masa a yanzu ba. Duban abokan aikinsu yai kana ya kauda zancen da fad’in “Komai ya kammala saura fara aiki. Soil test ya rage. You take care of the report while I’m away..” Hisham ya zuba masa ido shaye da mamaki. Ya d’an girgiza kai “While you are away.? What does that mean..? What do you mean by that.?” "Murmushi Haidar yai “It’s good to take a break, don’t you think.”" Har lokacin dubansa Hisham yake da mamaki “Seriously.! Ina zaka Haidar.?” “To Cuba. Jirgina gobe da safe ne in sha Allah..” “Business trip.?” Hisham ya tambaya yana dubansa. “Am I using business terms here.? Bakaji mai nace maka bane. Vocation zan tafi of course.” Hisham ya d’an Ware idanunsa. Kafin ya soma magana Haidar ya dakatar dashi “Don’t even start.” Hisham ya jinjina Kansa a hankali “Bazaka saurareni ba na sani. But why Cuba.? Jiya fah nake gani a labarai Hurricane killed at least 6 people there… Couldn’t she think of a better place.” Ya tambaya yana duban Haidar d’in tinda yasan wann bai wuce aikin Matarsa Dareen ba wacce yayi imani tarayyarta da Haidar d’in Babu wani alheri tinda aure ne da Har yau iyayensa basuda labari. K’ok’arin bud’e motarsa ya soma “Zamuyi magana kaikam..” Har ya bud’e motar zai shige Ya juyo ya dubi Hisham murmushi saman fuskarsa “C’mon haka zaka barni na tafi bazaka min fatan alheri ba. What if this is the final goodbye. What if hurricane ya ritsa dani a can.?” Hisham ya k’araso ya d’an punching muscle d’in Haidar guda “You shut up jerk.!” Dariya sukayi su duka biyun kafin suka rungume juna Hisham na fad’in zasuyi aikinsu tareda nasara cikin yarda da ikon Ubangiji. A haka sukai sallama kowa naji a cikin zuciyarsa zasuyi kewan juna. Hisham yai tsaye yana bin bayan motan Haidar da kallo. Murmushi ya saki yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa tinda ba wani aiki mai tsanani da zasu fara yanzu zai tafi Kano. Ya kuma sakin murmushi sanda yake hango beautiful innocent face d’inta a k’awayar idonsa. Ya shirya tafiya neman aurenta wann karon. Ya shirya sanar da ita abinda yakeji gameda ita. Even though he’s not expert a wann b’angaren but zaiyi iya k’ok’arin sa ya tabbata bata kufce masa ba. He’s been rejected so many times wanda hakan yasa neman aure da ‘yanmatan suka fita Kansa. But wann karon ya shirya yak’in Neman auren Ummulkhairi da duka k’arfinsa. Ya kuma sakin murmushi mai kyau zallan k’aunarta na d’awainiya dashi. ** "Yanda Mommy keta faman shiga da fice saida abun yai mugun d’aure ma Anisa kai. Mommy fah tarba na musamman taketa faman shirya ma masu kawo Amaryar Haidar. Jikin Anisa gaba d’aya ya mace, zuciyarta ta karaya ganin yanda Mommy keta d’aukin wann aure. Ta tabbata ko wacece matar Haidar ta gama samun gurbi mai girma cikin zuciyar Mommy dan sosai take son wann aure. Ita gani take Ammi b’ata lokacinta kawai take dan Mommy bazata bari Haidar Ya rabu da matar nan ba cikin watanni k’alilan kaman yanda Ammin nata ta sanar da ita." Suna jin shigowar Mota Mommy tai saurin mik’ewa tana fad’ad’a murmushinta. Lokaci guda ta dubi Anisa tace maza su sauk’a k’asa ga matar Haidar ta iso. Saurin rik’o Mommy Anisa tai tana murmushi da yafi Kama da yak’e “A’a haba Mommy. D’an dakata mana kefa uwa ce. Ki bari ni na sauk’a. Ma shigo miki da ita.” Bata jira cewar Mommy ba ta nufi k’asa tana mai rausayar da ido had’ida furzar da huci dan wani mugun takaici ne Ya cika mata zuciya yacce kasan ‘yar gwal za’a kawo gidan. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *23* *©️Sameena Aleeyou… * "Mommy ta gaza zaune ta gaza tsaye. Zuciyarta sai harbawa yake, ta rasa sukuni ne zuciyar nata ya samu sakamakon kawo makarin asirin Haidar da akayi kokuwa yarda da amincewan Haidar Wanda batada tabbas akai ne. Koma dai tsoron abin ya k’unshi rasa rai ne. Sai ta fara tuhumar kanta anya bata kasance mai son zuciya ba. How could she kill another person’s child for her own to survive. Saurin girgiza kai tai dan bata son irin tunanin nan su shige kanta. Dole ne yasa tayi hakan. Ance so so ne amma son kai yafi. She needs to save her only son no matter the cost, koda kuwa Ya k’unshi rasa rai ne. Da wann tunanin zuciyarta ya samu natsuwa. Tai zaune cikin kujera tana jiran shigowarsu." Inna Dije na rik’e da hannun Ummul gam take k’are ma katafaren gidan kallo Wanda ta masa lak’abi da fadan shugaban k’asa. "Suna shigowa wani irin k’amshi ne da zatace hancinta bai tab’a karo da irin shi ba tsaban dad’i shi ya daki hancinta, nan ta hangi wata hamshak’iyar mace wacce kallo guda zakai mata ka tabbata tayima babu bugun girma. Tana ganin Asshe jik’akk’iyar mace wayyaya sai taga ashe gaban Hajiya Kwaise Asshe ba komai bace. Kama daga yanayin suturan dake jikinta muhallinta harma da gogewar fatar ta. Dije ta jinjina kai tana kuma tabbatarwa. Waima Tani bataga wann daula da Ummul ta shiga ba kenan koda kaw ace na wutin gadi ne. Dole Tani ta zauce ta haukace." Mommy ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in su k’araso su k’araso bismillah. Yayinda Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa. Har lokacin kanta rufe yake cikin mayafi. Daga yanda take zaune saman carpet tana jin yanda su Inna Dije dasu Aunty Asshe suke gaisuwa da muryar wata mata mai yanayi da shige dana Aunty Asshe. Nan gaisuwar tasu ta sauya salo zuwa yaren k’abilar shuwa arab tsakanin Asshe da ‘yaruwarta. Ita dai Inna Dije tinaninta da k’wak’walwarta sun gaza tantance tsananin kyau da tsarin gidan. Sai juye juye take tana mamakin koda ace auren kwangila na wata uku d’ansu zai da Ummul meyasa sai Ummul a wann irin arziki da suke dashi. Meyasa basu nemo mace da Babu aibu tattare da ita ba sai Ummul. Itafa wann aure Sam bata amince iyaka cin gaskiya Asshe ta sanar dasu ba. Dik yanda akai akwai wata a k’asa. Tunaninta ne Ya katse sanda taga matar ta k’araso gaban Ummul murmushi fal saman kyakkyawar fuskarta. Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa sanda taga hannun matar saman nata. Lokaci guda Mommy ke ci gaba da fad’in “Welcome my daughter. Sannu da zuwa cikin ahalinmu. I can’t believe this is happening.. Finally Matar Aliyu na ta iso.” Sai ta k’arashe tana rungume Ummul daga zaune. Anisa da Tai mutuwar zaune tana dubansu. Sai ta rausayar da ido cikeda k’osawa tana mai aika ma Amminta wani kallo wacce itama jiki a sanyaye take duban Mommy dake rungume da Ummul tana ayyana farin cikinta a fili. "Mommy kaw cikin zuciyarta take ayyanawa ‘Zan kula dake a tsawon watanni uku da zakiyi damu. Sabida kin cancanta. You are my son’s savior. Kin sadaukar da rayuwarki dan rayuwar nawa d’an Ya inganta koda ace bakida masaniya akan hakan. This is the least I can do for you bayan sadaukarwa mai girma da kika mana. Zan baki dukkan soyayya da kulawa Har kawo lokacin da zaki warware mugun k’ullin da akai ma D’ana harma da ahalina.’ Ta k’arashe tinanin nata idanunta harda guntun k’walla. A hankali ta saka hannu ta yaye rufin da akai ma Ummul. Wani ikon Allah Sai Zuciyar Mommy ya kuma karaya. Fuskar yarinyar take kallo.. She looks so innocent and totally naive. She couldn’t help but to feel guilty.. Meyasa rauni Ya cika zuciyarta a kallon farko da Tai ma fuskar yarinyar a zahiri. Tai k’ok’arin saita kanta tana fad’ad’a murmushinta “Barka da zuwa Ummulkhairi, d’ago ki kalleni.. Sabuwar Mamanki..!” Ta k’arashe tana mai tallafo fuskar Ummul wacce ta kasa d’ago idonta ta dubi matar amma jin kalamanta na k’arshe yasa ta soma k’ok’arin d’ago idonta masu cikeda rauni hawaye tab cikinsu." Dubanta Mommy take Har lokacin tana rik’eda hab’arta murmushi saman fuskarta. Sai Ummul taji kuka da gaske na zuwa mata musamman da taji matar ta ambaceta da sabuwar Mamanta. Shin tasan Ummanta ta datse alak’a da ita ne..? Mommy ta soma girgiza mata kai alamun banda kuka. Ta shiga share mata hawayen tana fad’in ta daina kuka ta saki ranta kaman tana cikin Ahalinta. Mik’ewa Anisa Tai cikeda k’osawa tana rausayar da ido. Ta dubi Amminta ta furta a hankali “I’m tired of this drama.!” Tana fad’in haka tasa kai ta shige. Su Inna Dije Anci an sha an masu tarban girma ta kuma yarda Lallai Ummul gidan girma ta arziki ta shigo dan ko matar nan bata masu tarba da kayan arziki ba tarban fuska da ta masu da yanda ta amshi Ummul kawai sun isa ta shaida gidan girma da arziki Ummul ta shigo. Koda yake amma Asshe ta sanar da ita Auren na wata uku ne sann ga dalilin auren cewa kwangila suke so a bama d’ansu a kampanin mahaifinsa mahaifin nasa yace bazai bada ba har sai ya kawo masa mata ma’ana Har sai yayi Aure. Shin duk akan AUREN WATA UKU matar nan tai masu irin wann tarba ta kuma karb’i Ummul hannu bibbiyu kaman ‘yarda ta haifa.. Anya kuwa..? Ita fah duka abubuwan dake faruwa Sun fara kwance mata kai. Ji take ta gaza fahimtar komai. Koda sukazo tafiya da Ummulkhairi b’angaren Haidar Mommy ce ta rik’e Ummul da kanta tace ita zatai ma ‘yarta rakiya. Kan Inna Dije Ya kuma d’aurewa. Suka dubi juna itada Asshe. Asshe ta k’ifta mata ido alamun kar tace komai. A haka dai aka bama Inna Dije ma nata masauk’in nan cikin gidan da nufin washe gari idan Allah yakai rai zasu koma Kano itada abokiyar tafiyarta Asshe. Ita kad’ai a d’aki sai sak’awa da warwarewa take. Ta d’au d’amarar kafin su bar gidan kafin su koma garin Kano sai tayi yanda tasan ta fahimci duk abubuwan dake wakana. Batai ma Ummul rakiya zuwa garin ba sai don su koma tare da Ummul d’in. Amma yanda taga Uwar mijin Ummul na kaffa kaffa da ita tana nan nan da ita bata tsammanin Auren zai Mutu a sauk’ak’e. Abu guda ne zai kashe auren nan shine kawai ta bud’e bakinta ta sanar da matar cewa ajalinta D’anta Asshe ta kawo mata cikin gida. Ta mik’e da zummar fitowa nan taga Asshe tsaye gabanta. Girgiza mata kai Asshe Tai tace “Koma ki zauna Tun muna mu biyu.” Inna Dije ta dubeta da mamaki. Sai kuma Tai ‘yar bazawarar murmushi “Aw baki so mu kasance mu uku ne. Ina nufin ni da Ke da kuma ‘yaruwarki wacce kikai mata rufa rufa ki aura ma D’anta ajalinsa. Kar ki tausareni da abun duniya dan yanzu na fahimci kema gaban ‘yaruwar taki almajira ce. Sunan mijinki ne kawai kike tink’aho da tak’ama dashi amma da alama Babu abinda auren naki ke tsinana Miki. Da alama yayinki ya k’are wajen miji dole ki nemi hanyar neman kud’i kota halin k’ak’a.” A zuciye Asshe ta dakatar da ita “Kar ki kuskura ki bada shaida kan abinda bakida masaniya. Ina shawartanki kar kiyi gangancin shiga tsakanin ‘yanuwa guda biyu. Ina nufin nida ‘yaruwata.” Ta k’arashe maganar nata tana sakin murmushi kamar ba itace ta sha mur ba. "Lokaci guda Asshe ta k’araso ta dafa kad’an Inna Dije guda tana sakin murmushi “Ki kwanta a saman gado irin Wanda baki tab’a mafarkinsa ba. Ki yada gajiya, kafin ki d’auki hanyar gida gobe dan ba Lallai ki sake karo da irin wann gadon ba. Kar ki mance ‘yarku wata uku kacal zatai a gidan nan.!” Ta k’arashe tana k’irga uku da yatsunsa. Lokaci guda ta zaunar da Dije saman gado sai itama ta zauna a gefenta “Ya kamata mu tab’a hira ta k’awaye kafin safiya.. Baki tunani.?” Ta k’arashe tana kashe ma Dije ido. Daidai lokacin Anisa ta shigo da tea cups guda biyu." Asshe ta fad’ad’a murmushinta “Yauwa ‘yar albarka. Kin kawo mana shayin nida k’awata.” Anisa ta jinina kai tana mai ajewa gaba garesu. Asshe ta d’auko ta mik’a ma Dije “Ga shayin gidan shugaban k’asa. Irin wann ganyen shayin a gidan shugaban k’asa kawai kike gani ki sha ki kafa tarihi ki goranta ma sirakanki ina nufin Tani da Suwaiba.” Ta k’arashe tana kurb’an wanda ke d’aya hannun nata. Ganin Dije ta k’ek’ashe ido tana dubanta Ya sanyata sakin murmushi “Aw na zaci k’awa kika d’aukeni. Kindai san k’awar arziki bazata baki guba ba. Ko dama k’arya kike da kika kirani k’awa.?” Ta murmusa tana kurban shayinta hankali “Ashe k’aryar gogewa kike Dije.” TaI maganar tana kuma kurban shayin. Harda lumshe ido tana fad’in “Wani abu sai a fadan shugaban k’asa.” Ta shanye nata tana k’ok’arin janyo na Inna Dije da niyyan shanyewa Inna Dije Tai saurin rik’e hannunta ta amshe tea d’in. Inna Dije na murmushi tace “Yo Dije nake muricin kan Dutse . Idan baki sani ba ban fito ba saida na shirya. Ba wani barikinki da gogewarki da zai bani tsoro.” Ta k’arashe tana kafa kai ta soma kurb’an shayi tana lumshe ido. Kan kace me Inna Dije ta zube kan gado bacci yayi awon gaba da ita. Asshe ta kece dariya tana jinjina k’ok’arin ‘yarta Anisa da ta kawo wann plan d’in. Lokaci guda ta gyara ma Inne Dije kwanciyarta tana furta “K’awata ki sha bacci lafiya. Keda bud’e ido kuma sai gobe da safe in sha Allahu.” Ta k’arashe tana kuma kecewa da dariya. A haka Anisa ta kuma shigowa ta tadda Amminta “Gobe da safe jirgin Daddy zai tashi. Mommy zata masa rakiya zuwa airport. Sai kiyi amfani da wann dama Ammi ki fitar da matar nan daga gidan nan da zaran Mommy ta fice. Kinga hakan na nufin bazata samu zarafin sanar da Mommy abinda kike tsoro ba wanda kika kasa sanar dani.” Ta k’arashe tana tab’e baki had’ida rausayar da ido Wanda d’abi’anta ne. Bakin Asshe Ya gaza rufuwa dan farin ciki bata tab’a tsammanin zata samu solution na yanda zatai da matar nan cikin sauk’i ba. Ta dubi Anisa tace “Ni yau kin gama min komai. Ina Miki kallon marar wayau ashe zaki iya had’a plan irin wann. Lallai na yarda banyi ganganci ba da nace You’d become my eyes here.” "Anisa ta murmusa “I’m your daughter after all, Ammi.”" Asshe ta jinina kai “K’warai yau kin gama tabbatar min. Kuma na yarda zakiyi kaman yanda nace. Koda wasa kar ki bari D’anuwanki Haidar Ya samu kusanci da yarinyar nan. Kiyi duk irin makircin da kikaga Ya dace ki tabbata basu samu kusanci ba a tsakanin watanni uku.” Anisa ta girgiza kai kad’an “Amma Ammi meyasa kika canza ra’ayinki akan yarinyar bayan da kince mun na zama mabudin k’ulla shak’uwa tsakaninsu da Haidar.. Ammi what’s with all the mystery behind this marriage.. Ke yanzu kin nuna baki so amma a b’oye ba tareda kin bari Aunty Kwaise ta fahimci haka ba. Ita Aunty Kwaise tana son auren tana son yarinyar da duka zuciyarta. And at the same time baki so wann matar tayi magana da Aunty Kwaise..” Ta k’arashe tana nuna Inna Dije dake zube saman gado tana bacci. Ta kuma girgiza kai “Ammi wai menene b’oyeyyen al’amarin gameda Auren Haidar.?” Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya ta kamo hannayen Anisa “Ki yarda dani Anisa. Zan fayyace miki komai amma ba a daidai wann lokacin ba. Akwai lokacin da zaki fahimci duk abubuwan da nayi. Iyakacin abinda zan fad’a Miki a k’arshe shine zaki mallaki Haidar da izinin Allah. Amma fah sai kinyi aiki tuk’uru Anisa. Kar ki bari Ya kusanci yarinyar nan. Daga k’arshe zamu nemo mafita.” "Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya “Shikenan Ammi zanyi yanda kikace. After all, bana son auren tin daga farko. Yanzu zan d’auko makaman yak’i na da kika sa nai watsi dasu daga farko.” Ta kuma murmusawa kafin tace “Tinda inada ke Ammi, I know I’m not fighting a losing battle.”" Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta tabbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige. Asshe ta janyo ma Inne Dije k’ofa kafin ta fito daga b’angaren bak’in ta nufi wajen ‘yaruwarta daketa faman neman layin Haidar bata samu. Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k’arara saman fuskar Mommy. "“Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.?”" Mommy ta furzar da huci kad’an “Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso.” Asshe ta jinina kai kad’an “Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak’ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k’afafunsa.” Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take “What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I’m scared.. Tsoro nake kar duk efforts d’ina su tafi a banza.” "Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado “A’a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k’ok’arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D’anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak’inin hak’armu zata cimma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk’ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k’afa akan yarinyar zai k’ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai ki tunk’aresa da batun.”" Mommy ta girgiza kai “Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji.” Asshe ta jinjina kai “Na fahimceki Aunty Kwaise. Shiyasa nake k’ok’arin fahimtar dake abinda na hango.” Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d’aya batada wani kuzari “Asshe.” Ta kirawo sunanta in a serious tune. Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras gaskiya. "Mommy taci gaba “Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.?”" Asshe tai Shiru zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar ‘yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya. “Asshe.!” Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna. Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai. Hakan yai mugun tada hankalin Mommy. Bata San sanda ta mik’e ta k’araso wajen ‘Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa. Asshe na hawaye take bama Mommy hak’uri tana girgiza kai. Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai “Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma meyasa kike bani hak’uri.. Wani laifi ne kika min..?” Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba “Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise..” Mommy ta girgiza kai “Laifi.. Wane irin laifi..?” Anisa da isowarta jikin k’ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana sauraron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu’a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd’add’en aure da sukai ma Haidar. Muryar Amminta ta sinkayo tana fad’in “An sace komai Aunty Kwaise. Kayan lefe na gani na fad’a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b’arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zarafin fad’a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta.” Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali “Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud’in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu. Akan auren nan har property na na d’aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak’in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinyar su fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d’an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a sauk’ak’e. Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za’a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k’afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k’are mata kallo taga me take dashi haka da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita. A b’angaren Asshe kuwa sauk’e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb’o ta coge kud’ad’e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had’a ba k’aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta amaryarsa yarinyar Sa’ar Anisa ke cinye kud’in harta da yawon k’asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d’inta da auren d’an ‘yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab’a bari Kwaise tasan gaskiyan al’amari ba. Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad’ai. Ji take tamkar cin fuska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za’a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d’inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad’an kafin ta nufi sama. Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had’ida juya ido “Seriously.! Da gaske kina nan kina k’unk’ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud’e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab’in cincin dan ba mijin da zai bud’e wann fuskar naki.!” Ta k’arashe tana fincike rufin fuskan Ummul. Damm! Haka k’irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *24* *©️Sameena Aleeyou… * Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa. Ta sani bata tsammaci farin ciki cikin Auren ba. Kaman yanda bata tab’a mafarkin akwai wani rayuwa mai dad’i gaba gareta ba. Saidai tafi zaton tashin hankalin daga wajen mijin. Tinda mutum ne da ko saninsa batai ba. Sann shima bata tunanin ya santa. Ta d’ago a sanyaye tana duban Anisa dake ci gaba da aika mata mugun kallo. Anisa bata daina sakin huci ba ta finciko Ummul ta tadata tsaye “Tashi makira. Sai wani sanne fuska kike tinda kikazo. Irinku kunfi kowa iya makirci.” Ta shiga zagaye Ummulkhairi dake tsaye tana k’are mata kallo. Sai ta tab’e baki dan ido ba mudu ba yasan kima. Dukda nad’e take cikin lafaya tasan ko kusa bazasu zo d’aya ba. Hasalima Anisar bazata nuna mata komai ba face farin fata. "Anisa ta rausayar da ido cikeda takaici. Tai tsaye gaban Ummul wacce Har lokacin ko motsawa batai ba “Kar kiyi tunanin zaki tadda farin ciki a wann gidan dan kinyi nasaran saye zuciyar Mommy. Bariki ji na fad’a Miki wani abu. Mommy mace ce da take tamkar Hawainiya.. Babu wuya ta canza launi. And Haidar.?” Ta kuma sakin murmushi tana ci gaba da zagaye Ummul “Hello, I’m sorry to say sai kin gwammaci mutuwa da auren wann miskilin. Bansan dalilinki na amince ma aurensa ba amma ina mai tabbatar Miki Kinyi babban ganganci. You’ve made a grave mistake, because Haidar Maitama would never ever fall for someone like you.!” Ta k’arashe muguwar murmushi saman fuskarta ga wani wulak’antaccen kallo da take bin Ummul d’in dashi." Saida ta gama juye ma Ummulkhairi buhu buhun wulak’anci kafin tasa kai zata fice. Ummul ta sakar mata murmushi tace cikin sanyin muryarta “Baki sanar Dani sunanki ba.” Anisa ta kalleta a dak’ile “Mai sanin sunana zai miki.?” Ummul ta kuma murmusawa “Sanin suna nada mahimmanci ko dan hakkin zamantakewa. Allah yasa hakan ba matsala bane.” Anisa ta tsareta da ido tana kallon salon makirci daga wajen wann bagidajiyar. sai kuma ta girgiza kai tana rolling eyes “I don’t have your time.” Har tasa kai zata fice ta sinkayo muryar Ummul “Ina tunanin tinda har kika tako yanda nake kinada lokaci na.” Tai maganar murmushi saman pale face d’inta da taci kuka. Anisa ta kuma dubanta da mamaki. Wanda mamakin Ya hanata magana. Bata tsammaci maganganu irin wad’ann daga bakin bagidajiyar Amaryar Haidar ba. Ganin tayi sakare yasa Ummul kuma murmusawa ta k’araso kusanta “Ni sunana Ummulkhairi.. Watak’ila nasan kin sani Shiyasa baki tambaya ba.” Har lokacin sassanyar murmushi ne saman fuskarta Wanda ba k’aramin tunzura Anisa ya kuma yi ba. Ganin Anisa tayi Shiru yasa Ummul katse shirun da fad’in “Yauwa gwara da Allah yasa kika shigo.. Dan Allah ina ne band’aki wllhi tun d’azu nake so na tashi nayi sallan isha amma bansan ta ina zan shiga ba.” "Hararta Anisa tai daga sama zuwa k’asa “Ina Miki kashedi, kar ki kuskura ki shiga d’akin cen. Dan wann d’akin d’akin Haidar ne.” Ta k’arashe tana nuni da d’akin." Ummul ta murmusa kad’an “Ok haka na nufin wancan kenan zan shiga.” Tai nuni da d’aya k’ofar. Takaici ya kuma cika Anisa ganin da gaske Ummul bata d’auketa da zafi ba. Taja tsaki tana juya ido kafin tasa kai zata fice. Ummul Tai saurin dakatar da ita “Kinga.” Anisa ta juyo tana dubanta a dak’ile. “Na gode.” Tai maganar har lokacin kyakkyawan murmushin ne saman fuskarta wanda ko shakka babu k’ok’arin b’oye tashin hankalin dake saman sa take. Wani tsakin Anisa ta kumayi kafin tasa kai ta fice a fusace. "Sauk’e ajiyan zuciya Ummul tai tana mai hamdala cikin zuciyarta. Dan da dai tai tozali da mijin da aka aura mata, gwara taita karo da wann figaggiyar. Dan idan fad’a da tashin hankali ne zata iya cewa cikinsa ta girma. Amma miji bata san mai zata tarar ba. Bata san wani irin k’alubale zata fuskanta tare da shi ba. Haka zalik’a zuciyarta Sam ya gaza natsuwa dukda kwantar mata da hankali da mahaifiyarsa tai. Ta kuma sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin tasa kai ta nufi d’aya d’akin hagu da wanda Anisa tai nuni dashi matsayin na Haidar." Kaman mai tsoron shiga haka ta tura k’ofar. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Sai addu’an neman samun salama had’ida natsuwa take cikin zuciyarta take. D’aki ne mai matuk’ar kyau da tsari komai na ciki sabo ne dal da alama. Tai tsaye sororo tana duban d’akin dan ita dai bata San ta ina zata fara ba. Abinda ta soma tunowa shine gadon baccinsu ita da ‘yaruwarta Khulsum. Shikenan Sun rabu. Ta rabu da kowa nata kenan kaman yanda Umma ta umarceta. Shikenan ba ita ba danginta. Wani hali Abba yake ciki.? Yaya yanayin k’arfin jikinsa.? Umma ta mata iyaka dasu gaba d’aya tace ko a waya kar ta nemesu idan har ita ta haifeta. Sai taji k’afafunta Sun gaza d’aukarta. Nan ta silale wajen kuka na zuwa mata gadan gadan. ** Kano… Har ta kwanta wajajen misalin k’arfe shad’aya na dare taji ana buga mata k’ofa. Ta mik’e da kyar tana mamakin waye haka cikin daren nan. Bata kawo kowa ba sai Khulsum tinda ita ce tazo mata cikin dare irin haka a kwanan baya. Ta k’araso tana tambayar wanene lokaci guda tana ci gaba da fad’in Khulsum kece nan wajen. Ga tsananin mamakinta muryar D’anta Hisham taji. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa. “Hisham.!” Ta furta a hankali Hisham yace “Hajja ni ne.” Ta bud’e k’ofan tana dubansa da mamaki “Lafiya kai kuma cikin daren nan.. Watau bazaka daina irin wann tafiyar naka ba ko.” Murmushi Hisham keyi yana duban mahaifiyar tasa “Haba Hajjata tarban da za’a min kenan. Hajja ko shigowa gidan banyi ba fah balle na sha ruwa balle mujega gaisuwa.” K’wafa tai tana dubansa kafin tasa kai ta shige tana ci gaba da sababin yanda ya maida tafiyan dare d’abi’arsa. Hisham ya maida k’ofan ya rufe kafin ya take mata baya yana fad’in Allah ya huci Zuciyar Mamanshi tuba yake. Sukai zaune a parlor suna gaisawa bayan ta gama sillesa tas kan yanda ya maida tafiyar dare jiki musamman duba da yanayin hanoyin a yanzu. Hisham ya tsareta da ido. Shi sai lokacin yake hango rama tattare da ita. Ta d’an kuma dubansa “Waima mai Ya dawo dakai ne.? Inji baka jima da komawa bakin aikin ba. Kai da kanka kace kunada babban project a kampanin ku zaka tara hankalinka waje d’aya. Toh me ka dawo yi.?” “Hajjah..” Ya kira sunanta a hankali. Sai ta d’ago ta dubesa ganin sosai ya tara hankalinsa. “Wani abu ya faru ne da bana nan.?” Tambayar da yai mata sai taji tamkar yana sane da cewa Ummul tayi aure ne kuma ba kowa ta aura ba face D’anuwansa da suke Uba d’aya. Ji tayi kaman d’an nata Ya riga yasan sirrin da ta jima tana b’oye masa. Ta girgiza kai a d’an daburce “Mai ka gani.. Kaga ni bacci nake ka katse min. Ko ma meye mayi magana da safe. Tashi kaje ga abinci a kitchen sai kai warming kaci tinda kai ka so zuwa cikin dare. Idan bai maka ba kasha ruwan shayi dama abinda ka Saba kenan.” Hisham Ya girgiza kai. Tana k’ok’arin mik’ewa yai saurin k’arasawa Ya rik’e hannunta “Hajjah you look sick. Kinyi ciwo ne sanda bana nan..?” Ta sauk’e ajiyan zuciya jin ba Ummul ya tambayeta ba wanda ba grin Allah da zai waye suyi waya bai tambayeta ita ba. Yaso karb’an lambar wayarta ma sai Hajjan ta sanar dashi Ummul batada waya. Yaita mamakin ya za’ace budurwa kaman Ummul ba waya a hannunta. “Eh.. eh nayi dan zazzabin nan da ake fama dashi. Amma bai wani tsanani ba. Shiyasa ma ban sanar dakai ba gudun kar ka tashin hankalinka ka d’ago k’afa kazo. naji sauk’i Alhamdulillah.” Hisham Ya girgiza kai “Haba Hajjah. Har kiyi ciwo ban sani ba.. Hajja a duniyar nan sabida wa nake neman duk abinda nake nema. Hajja sabida kece.. Lafiyarki na gaba da komai da kuma kowa. You are my number one priority kin sani..” ya kuma girgiza kai “Da ace wani abu ya faru dake da bazan tab’a yafe ma kaina ba.” Ya k’arashe fuskarsa fal damuwa. Sai ta k’ura ma d’an nata ido ganin yanda hankalinsa ya matuk’ar tashi a sabida ita. Koda duka duniya zasuyi rejecting d’insa zata so shi ta k’aunace shi domin kuwa Hisham d’inta definition ne na d’a na gari a idonta. Ta d’an dungureshi “Silly. Ba abinda zai sameni da izinin Allah sai naga ‘ya’yanka.” Ya murmusa yana duban mahaifiyar tasa cikeda so da k’auna “And very soon zaki gansu in sha Allah. Dan wann karon na d’au d’amaran neman aure da gaske. Bazan koma ba sai na tabbata an bani ita.” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Take annurin fuskarta ya d’auke cak. Ta soma k’ok’arin kauda fuskarta dan bata so su had’a ido. Hasalima bata san ta yanda zata soma sanar dashi labarin Auren Ummul ba. Shin da wanne zata fara.? Cewa Ummul tayi aure ko kuma D’anuwansa da baisan yana dashi ba ta aura. Shin mahaifinsa tasowa yai daga kabari kokuwa dai yana raye tintinin. Zata mik’e Hisham yai saurin dakatar da ita ganin gaba d’aya yanayinta Ya sauya tashi guda “Hajja na fad’i wani abu ne da bai dace ba.?” Girgiza masa kai tai “Hisham kaje ka kwanta dare yayi.” Tana fad’in haka ta mik’e ta shige d’aki ta barsa nan wajen yana sak’e sak’e. Fatansa Allah sa dai lafiya ba wani abun bane ya faru. Jiki babu wani kuzari Ya mik’e Ya nufi nasa d’akin. ** Washe gari Inna Dije bata Ida warwarewa ba sai a cikin mota bayan Sun d’auki hanya sunyi nisa. Ita kad’ai sai layi take dan baccin bai saketa ba. Haka Asshe da Anisa suka turata cikin mota. Ko zarafin Sallama da Ummul basu barta tayi ba. Saida sukai nisa Abadan kafin Inna Dije ta ida warwarewa. Ta dubi Asshe dake gefenta da mamaki tana kuma duban cikin motar. Asshe ta karyi goron dake hannunta dan galibi idan zatai tafiya mai tsawo da goronta cikin jaka. Ta murmusa tana duban Inna Dije “Barka da safiya K’awalliya.” Inna Dije ta kuma dubanta da mamaki sai lokacin take tuno duk abubuwan da suka faru. Asshe ta murmusa had’ida mik’a mata goro “Karb’i ki karya kumallo.” Inna Dije kallon mamaki kurum take ma Asshe Har lokacin. Ta dubi goron da take mik’a mata “Kin bani k’waya cikin dare yanzu zaki had’a min da goro ki k’arasa kasheni. Makira algunguma.!” Asshe ta dara kad’an “Haba K’awalliya wasa fah ake bugawa. Da sauran lokaci ai ba’a gama ba. Kika sani ko anjima ki lallasa ni.” Inna Dije tace “Ina muke..?” Asshe ta kuma karyar goronta “Kar ki damu mun kusa isa gida nasa a shirya Miki karin kumammalo mai kyau gudun kar kiyi mutuwar bakin al’muru.” Inna Dije ta girgiza kanta Wanda Har lokacin nauyi Ya mata “Yanzu sabida rashin imani naki Asshe shine kika bugar dani ko sallan asuba banyi ba kika nad’oni kika saka cikin mota.. Toh ina jakan kayana.?” Asshe ta tab’e baki “Buhun tsummokaranki zakice. Wari suke min a mota nai watsi dasu. Kar ki damu sabbi suna jiranki idan mun isa. Yanzu bari a samu waje a tsaya kiyi sallah tinda kin dawo hayyacinki.” Inna Dije sai kallon mamaki take ma Asshe dan ta fara zarce tunaninta. Koda suka iso Kano kai tsaye gidan Asshe suka nufa. Inna Dije ta samu ta saka abu cikinta sann tai wanka aka bata tufafi ta canza. Asshe ta k’araso tana dubanta lokaci guda tana tinda ransa Suwaiba ta soma zuwa gidan. Murmushi ta sakar mata ganin ta shirya tsaf “Ko kefa K’awalliya. Kin ganki kuwa..” Inna Dije ta d’aga mata hannu alamun dakatarwa “Ke ni fah ba Suwaiba bace. Babu wani makircinki da zai bani tsoro. Bazan bari na sake fad’awa tarkonki ba. Mijina baisan nayi tafiya ba a nasa tunanin ina tare ne da d’a uwana. Ni ba ballagaza bace kaman Suwaiba.” Asshe ta murmusa “Ashe duk kanwar ja ce.” “Mai kika ce.?” Inna Dije ta katseta. Asshe ta kuma murmusawa “A’a K’awalliya cewa nai idan kin gama Hilal sai ya kaiki masaukin ki.” Zata fice kenan Inna Dije ta janyota. Saitin kunnenta take rad’a mata “Kinyi kuskure tinda kika kaini naga gidan. Watak’ila kin lashe wasan a wann karon. Amma ki kiyayi karawa na gaba. Abun bazai miki da kyau ba. K’walliya.” Ta k’arashe harda kashe ma Asshe ido. Sai Asshe ta murmusa su duka biyun suna k’are ma juna kallo. “Kar ki damu na Miki alkawarin babu had’uwa na gaba. Dan kafin wann lokacin zan tabbata ‘yarku ta fice daga rayuwar D’anmu. K’awalliya.” Asshe tace tana mai ficewa. Lokaci guda ta kira Hilal Tai masa umarni da yakai Inna Dije Asibitin koyarwa. ** Cikin sand’a Umma ke takowa ta nufi k’ofan d’akin Abba tana addu’an Allah yasa kar ta tadda Dije. Ai kaw tana tura k’ofan a hankali taga Babu kowa sai Abba dake kwance shi kad’ansa. Tai k’uri tana dubansa sai taji hawaye na neman ciko idonta. Rayuwarsu na baya taketa tunowa da yanda burin son ganin ta aurar da Ummul ko ta halin k’ak’a ya rufe mata ido. Ta share hawayen da suka zubo mata tana neman afuwan mahaliccinta cikin zuciyarta. Cikin sand’a tamkar mai tsoron kar wani ya ganta ta shigo d’akin. A d’arare ta zaune gefe dashi. Tana hawaye take furta “Abban Ummul ka yafe mun. Na tapka kuskure mai girma. Kuma nasan ni ban cancanci yafiya ba.. Amma..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Saida tai mai isarta kukan da ba sauti kafin taci gaba “Bazan gushe ba Ina maka addu’an samun lafiya mijina.. Hak’ik’a duniya makaranta ce kuma naga izna akan hakan. Duk abubuwan da na aikata Sun dawo gareni harda tukuici. Kaico na.. Kaicon irin wann rayuwa. Kaiconki Suwaiba.!” Ta k’arashe tana toshe bakinta dan kuka ne na gaske ke zuwa mata. Shigowar Khulsum kenan ta hangi Umma zaune gaban gadon Abba tana shesshek’ar kuka. Khulsum Tai saurin k’arasowa ta raba tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta. Umma ta d’ago jiki a sanyaye tana duban Khulsum wacce itama d’in ita take duba saidai babu d’igon annuri a fuskarta. “Khulsum..!” Umma tace cikin tsananin rawar murya. Khulsum ta girgiza mata kai “Umma me kikeyi a nan.. Dan Allah ki tashi ki fita kafin Inna Dije ta shigo ta taddaki. Dan yau ta sanar Dani zasu dawo tareda ‘Yaruwata wacce kikai mata auren rashin galiho. Inna Dije tace bazata bari aci amanan mahaifinmu dake kwance ba. Tace bazata dawo ba sai tareda ‘Yaruwata wacce kika rabamu da ita sabida son zuciya irin naki Umma.” Khulsum ta k’arashe hawaye na gangaro mata yayinda Umma ma ke hawaye tana jinjina kai. Dan a halin yanzu ita dai kam tasan batada wani hujja ko kalamai da zatai amfani dasu dan ta wanke kanta. Ta kuma san sai yanda k’arfin Dije ya k’are wajen ganin ta rabata da ahalinta. “Umma dan Allah ki tashi ki fice.. Bamu neman wani tashin hankali a nan..” Khulsum ta sake fad’i cikin rawar murya. Jiki a sanyaye Umma ta mik’e sai ta ajiye ‘yar kular da ta shigo dashi na abinci Wanda ta kawo ne ma Khulsum d’in. Duban foodflask d’in Khulsum Tai ganin Umma takai k’ofa tai saurin dakatar da Umma kafin ta d’auki kular ta mik’a mata “Kin mance wann Umma. Idan dan Abba kika kawo baici.. Idan kuma sabida ni kika kawo kiyi hak’uri nima bana buk’ata. Ci na ko shana bai tab’a damunki ba Umma. Abu d’aya ne damuwarki a gidan duniyar nan shine ki aurar da ‘Yaruwata.” Tai murmushi mai ciwo “Auren da kikai ikirarin kin rabu dani akan shi Umma.. Wacce Har zaki mata irin wann kalami bana tunanin akwai sauran damuwar da zakiyi da ita Umma.. Haka ne.?” Ta k’arashe tana duban mahaifiyar tata. Har lokacin Umma bata iya cewa komai ba sai hawaye. Khulsum ta share hawayen da suka zubo mata kafin ta kuma nuna ma Umma k’ofa “Idan Inna Dije tazo nan ta sameki Umma kinsan abin bazai kyau ba. Ki dubi girman Allah ki duba jinyan da mahaifina ke ciki dan Allah ki fita ki tafi Umma..” Umma ta jinjina kai tana hawaye ta nufo waje. Khulsum tai saurin bin bayanta rik’eda kulan abincin tana k’ok’arin dakatar da ita. Daidai lokacin motar Hilal tai parking.. Aiko Inna Dije tana hango Umma da Khulsum tai saurin fitowa ta nufosu. Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Saida tai ma Umma tas kafin ta janyo Khulsum tace maza su shige wajen Abba. Khulsum ta kaikaito ta dubi Umma tana kuma sharan k’walla. Haka Umma taci gaba da tafiya kaman kazar da k’wai ya fashe ma. Hilal da akai komai gabansa bayan Umma yabi da mota dan sosai ta basa tausayi. Ya fito ya gaida Umma bayan yayi parking gefen kwalta. Umma ta ganesa d’an wajen Hajiya Asshe ne da ba yau suka fara had’uwa ba. Hilal Ya rok’eta ta shiga mota ya kaita gida. Da fari k’in amincewa Umma tai saida Hilal yai da gaske dan ta kula idan har bata shigan ba bazai k’yaleta ba. Yai saurin bud’e mata backseat ta shige kafin ya dawo mazauninsa Ya shige had’ida tada motar. Har k’ofan gida yakai Umma kafin Ya juya. Maimakon ya koma gida sai ya koma asibitin. Room number d’in Abba ya tambaya a reception suka sanar dashi. Ya isa yai knocking. Har lokacin Khulsum kuka take bayan Inna Dije ta sanar da ita sab’anin halinda ta baro Ummul ciki. Cewa da gaske Suwaiba ta saida ta ne ma wasu irin mutane marassa imani balle mutunci. Ba yanda bataiba ganin k’ok’arin ta dawo da Ummul amma mutanen sunce kudi suka sa sukai sayi Ummul. Ko Kotu za aje bazasu iya kashe auren Ummul ba tinda tak’ama suke da kudi . Yacce kasan zamanin cinikin bayi haka aka saida ‘yaruwarta a wulak’ance. Knocking d’in ne Ya d’auki hankalinsu. Inna Dije ta mik’e tana tambayan wanene. Ga mamakinta Hilal ta kuma gani. Ya sakar mata murmushi yana gaisheta had’ida tambayarta mai jiki. Ta amsa tana tambayarsa lafiya. Ko wani mantuwa ne Asshen Tai. Hilal Ya girgiza kai alamun a’a. Sai ya k’ara da “Em.. Da Allah dama nace.. Emm yarinyar nan da na gani d’azu..” Dan shi dik had’uwar da suke da Khulsum kusan sau uku bazaice ga sunanta ba. Inna Dije ta katsesa “Wace kenan..?” Hilal yace “Emm.. K’anwar Matar Haidar.” Dan ya tabbata ta haka kawai za’a ganeta. Jin haka yasa Khulsum lek’owa tana dubansa dan taso d’ago muryar. Ai kuwa shi d’in ne dai. Ta galla masa harara cikeda takaici musamman da Inna Dije ta sanar da ita yanda sukai da danginsa akan ‘yaruwarta Ummul. Hangota da Hilal yai sai ta sakar mata murmushi Ya d’ago mata hannu alamun gaisuwa. Inna Dije da Tai k’ebebe bakin k’ofa tace “Toooh mai kake nema wajenta.?” Hilal Ya rasa abun fad’i. Sai ya soma ‘yan kame kame “Em.. Dama akwai wani sak’o ne da zan bata.. Idan hakan na matsala.” "Ta dubeshi a dak’ile, sai Ta juyo ta dubi Khulsum, ta kuma duban Hilal “Minti goma. Minti goma na baka. Kuma kar kuyi nisa Ku tsaya bayan lambun d’akin nan yanda zanke hango ku ta window ehe..” Ta dubi Khulsum tace “Zo kije ina kallonku ta window.”" Har lokacin hararsa kurum Khulsum take. Kaf danginsu ta tsanesu. Suka jera suna tafiya har suka isa zuwa wajen wani dogon kujera na shak’atawa. Hilal Ya nuna mata kujeran “Bismillah..” “Kaga Malam ba zuwa nan nai dan na saurareka ba. Zuwa nai na baka sak’o ka fad’a ma azzaluman danginka. Ni UmmuKhulsum ‘yaruwarta sai na raba wann auren k’etar da sukai ma d’ansu da ita. Ka fahimta.!” Hilal ta girgiza kai kad’an dan sai yanzu yake jin sunan nata “Ki rik’e sak’on ki dan bazan isar ba. Kinsan dalili.?” Ya tsareta da ido yanda take huci kafin yaci gaba “Ni ba maras kunya bane. Kuma Ina daraja iyayena.” "Ganin irin duban da Khulsum ke masa ya sanya shi saurin d’aga hannayensa biyu alamun surrender “Look, I’m not implying anything here. Kar ki dauka da wani manufa. Quite the contrary.” Ya jinjina kai kafin yaci gaba “But honestly, abinda kikaima mahaifiyarki d’azu ba daidai bane. Ko meye mahaifiya tayi ta cancanci a saurareta…. Ko dan girman hakkin da take dashi akan D’anta. Nasan kin sani amma tunasarwa yanada kyau.”" “Malam kai baka san komai ba. Kar ka bada shaida kan abinda Bakada masaniya.” Ta fad’a hawaye na gangaro mata dan ita kanta tana jin ciwon abun cikin ranta. "Hilal Ya jinjina kai “Matsayin iyaye musamman mahaifiya Ya wuce a k’ullacesu. Barin baki wani labari gajere. Ya d’an kuma takowa ya zauna saman kujerar. Lokaci guda yaci gaba “A lokutan baya inada kusanci sosai da Abba na. Baya iya bacci ba tareda ya ganni ba.. Ko baya gidan mahaifiyata idan yazo Ya tadda ban dawo makaranta ba sai ya jira na dawo kafin ya tafi. Gidan stepmom d’ina da gidanmu isn’t that far. So takai ta kawo ko sallan asuba Ya fito sai ya biyo har gidanmu Ya tadani mun tafi tare. Toh wann tashi na da asuba da Abba yake sai yasa gaba d’aya naji bana son kusancina dashi a ganina tak’ura min yake yana yanke min bacci na.” Ya d’an murmusa yana girgiza kai “Back in the day, Haidar cousin d’ina yakan zo gidanmu yai kwanaki . Abin sosai yake birge Haidar yanda yake ganina tareda Abba na. What he’s been denied his whole life.” Ya girgiza kai “I know I shouldn’t be telling you all this amma ta kama ne shiyasa nake sanar dake.” Hilal yaci gaba “Bama son fita sallan asuba but Haidar yana mun sha’awan wann opportunity d’in na kasancewa da Abba na. Ko naji Abba yazo tada mu tafiya masallaci bana tashi sai na barsa yai knocking har ya hak’ura ya tafi. Amma sai Haidar Ya tadani dole yace mubi Abba masallaci ba tareda munyi alwala ba tinda shine bama sonyi wai mu gudun kar baccinmu Ya tafi. A haka za’ayi sallah damu idonmu a rufe muna bacci, idan mun dawo gida sai muci gaba da baccinmu.”" Ya d’an dubeta ganin ta zuba masa ido “Hey ba wai fah bama yin sallah bane idan mun dawo gida. Quite alright zamuci gaba da baccinmu ne bayan mun dawo masallacin. idan mun tashi da safe sai muyi alwala muyi sallah mai alwala. Wai mu munyi dabara baccinmu bai gudu ba.. Crazy right.” Ya fad’i murmushi saman fuskarsa yana jinina kai. “That was then nake fad’a Miki. Lokacin k’uruciya.. Idan ban mance ba Babban Yayana Haidar kanshi bai rufa ashirin ba balle ni.” Ya fad’I haka tamkar wacce ta tsile shi. Hilal ya murmusa yana jinjna kai “I Guess a halin yanzu k’anan k’annena yaran third wife d’in Abba sun k’wace Fada na wajen Abba. Na daina ganinsa often musamman a gidanmu. And ya daina zuwa tadani sallan asuba. Ya zama everyday idan zan tashi sallan asuba sai na tuna Abba da yanda yake zuwa ya tadani koda baya gidanmu.” Ya d’ago ya dubeta “Moral of the story kar kayi wasa da damar da ka samu. Sometimes we don’t know the value of what we have in hand until we lose it. So please ki saurari mahaifiyarki tin kinada daman hakan.” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda ta mik’e yana fad’in “Barin tafi before you attack me da irin wann kallon da kike mun.” Khulsum ko janye k’afarta ta kasa jikinta yayi mugun sanyi da maganganun Hilal. Har ya soma tafiya ya juyo ya dubeta nan yanda ya barta tsaye “Kar fah wataran kiyi Haidar yaji labarin nan a bakin ki since he’s married to your sister now. My cousin will definitely kill me idan yaji na bada labarin k’uruciyarsa ma k’anwar matarsa. sallan da muka dingayi babu alwala.” Ya k’arashe yana murmushi. Har ya soma tafiya ya kuma juyowa “And.. kar ki damu zaki jima baki ganni ba daga yau. Cos I’ll be flying back to school in a couple of days. I hope zakiyi tunani kan abinda na fad’a Miki.. Goodbye.” Ya k’arashe yana d’ago mata hannunsa mai rik’eda mabud’in mota. Jiki a sanyaye Khulsum ta silale ta zauna saman kujeran tana dubansa yana tafiya har ya b’ace ma ganinta. Ba wai bata so ta aminta da kalamansa bane. Saidai har k’asan Zuciyarta bata in zata iya komawa ga Umma. Akan idon Inna Dije komai ya auku. Ta murmusa kad’an. Cikin zuciyarta take ayyana lallai idan hasashenta ya tabbata D’an Asshe son Khulsum yake ko shakka babu ta samu makamin da ta yak’i Asshe dashi cikin sauk’i tinda a halin yanzu Khulsum a hannunta take. Tsaf tasan ta yanda zata b’ullo ma Asshe bariki. Ta kuma sakin murmushi tana jinina Kai a hankali. A fili take furta “Asshe bariki kin shigo hannu.!” ** Hisham ya dubi mahaifiyarsa Wanda Ya kula gaba d’aya ranar kaman tana avoiding d’insa ne musamman da ya d’ago mata zancen Ummul. Bai kuma mata maganar ba sai shirin fita da yai da yammaci. A parlor ya taddata tana zaune tana kallon tv. Ta dubesa da mamaki “Ina zaka.. Kaida ba wasu abokai gareka a garin nan ba.” Ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an “Emm.. Gidansu Ummul na nufa Hajja.. Inaso naji ya jikin mahaifinta..” Bata san sanda ta mik’e tsaye ba. Ta soma girgiza kai “A’a Hisham.. Koda wasa. Ba kai ba mutanen nan har abada kuma.. Ka cire Ummul a ranka.” Hisham Ya girgiza kai cikin rashin fahimta “Hajja ban fahimceki ba.. Wai meke faruwa da Ummul d’in ne..?” Ganin mahaifiyarsa bata amsa shi ba ya sanya shi sakin murmushi mai ciwo “Kinje nema min aurenta kaman yanda kikace.. Suma sunyi rejecting d’ina kaman dai sauran ko.. Haka ne Hajja.” Yaci gaba da jinjina kai idonsa na kuma rinewa zuciyarsa na kuma karaya “Hajja I love Ummul. I sincerely do.. I want to build a family with her.. Ahalinda a kullum kike min fata da burin ki gani.” Katsesa tai “Ya isa na ce ka cireta a ranka. Kuma ko hanyar da Ya danganci ahalinta kar ka kuma bi.” Girgiza kai yake cikin rashin yarda “Hajja ki gafarceni.. Not that I’m being to pushy about this.. Kece kika fara saka mun hope akanta.. Yanzu da zuciyana ya tabbatar mun Ya kamu da sonta why the sudden change of mind.? Hajja Wai meke faruwa ne dan Allah.?” Ya k’arashe cikin rawar murya. “Abinda yake faruwa Hisham shine Ummul ta haramta a gareka.! Ummul tayi Aure.! Ita d’in matar wani ne a yanzu..!” Duban mahaifiyarsa yake cikin tsananin shock.! SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!* *25* *©️Sameena Aleeyou… * "Ya girgiza Kai kad’an disbelievingly “Hajjah.. Ban.. Ban fahimceki ba. Aure.? Ummul tayi aure..?” Ya kuma girgiza Kai “Ina nufin, wane irin aure kuma.?”" “Zauna.” Ta fad’i tana nuna masa kujeran dake gefensa. Jiki a matuk’ar sanyaye Hisham ya ja k’afafunsa ya isa ya zauna had’ida zuba ma mahaifiyarsa ido. "“Hisham, ba wann karon bane ka fara Neman aure baka samu ba. Ka kai sadaki, har an saka rana a wasu lokutan amma daga k’arshe an hanaka. Toh ina so ka saka ma ranka wann bazai zama na k’arshe ba. Kuma shi aure da kake gani nufi ne na Allah. Matar mutum kuma bazata wuce shi ba. A kullum hud’ubar da nake maka kenan. Kar ka saka damuwan rejecting d’inka da akeyi cikin zuciyarka. Lokaci ne kawai baiyi ba amma idan lokaci yayi zakayi Aure. Abinda yasa na maka sha’awan Unmulkhair ba komai bane face aminta da nayi da hankalinta, tarbiyarta da kuma addininta. Kaman yanda yazo cikin hadisin Abu Hurayrah Wanda bukhari ya rawaito ‘Manzon Allah (SAW) yace ana auren mace sabida abubuwa guda hudu, sabida dukiyarta, sabida nasabarta, sabida kyaunta ko sabida Addininta. Sai Manzon Allah SAW yace Na horeku da ma’abociya addini hannunka zai samu riba.’ Wann yasa nai maka sha’awar Ummulkhair.” Ta kuma daidaita zamanta cikin kujeran kafin taci gaba “Bugu da k’ari kaida Ummul kunada k’addara mai kamanceceniya. Dukanku Kun fuskanci k’alubale na lalacewar neman aure kafin akaiga auren. Toh amma a ko yaushe shi mutum ya zama mai d’aukan k’addara da hak’uri da jarabawar Ubangiji a yanda tazo masa. Duk iyaye burinsu kenan. Farin cikinsu kenan suga ‘yarsu ta natsu a gidan aure. Haka zalika idan namiji ne suga yayi archiving a rayuwa sann ya zama mutum mai cikan kamala yayi aure. Shi aure abun so ne ba abun gudu bane ba abun k’i bane. Hasalima ya inganta a hadisin Anas dan Malik wanda Bukhari da Muslim sukai ittifak’i akai. Cikin hadisin Manzo SAW ya tabbatar Aure sunnarsa ce kuma wanda ya k’yamaci sunnarsa baya tare dashi. Toh kaga kuwa aure sunnah ce mai girma kuma koyi ne da Manzo SAW. Yayi umarni ma samari da suyi aure ga Wanda Allah ya bama ikon yi. Domin shi aure yana tsare gani da kuma kamewa. Ga Wanda baida hali kuma yayi azumi domin shi azumi garkuwa ne. Hadisin Abdullahi bn Umar wanda Bukhari da Muslim suka rawaito shi.” Ta d’an numfasa “Toh kaga duk wad’ann hadisan suna nuni da aure ba abun k’i bane aure ginshik’i ne na ko wani Al’umma. But you can’t force it. Kuma ka nemi zab’in Allah cikin duk abinda ka sa gaba. Kana so kana buri kana kuma fatan kayi. Cikin aure akwai tarin albarka kuma ibada ne. Allah ya halicci ‘yan Adam jinsu biyu domin su samu natsuwa da juna. Kaga wann natsuwar sai ta hanyar aure za’a samu. Kai hak’uri d’ana, Kai hakuri da jarabawarka. Kai hak’uri da Ummulkhair. Ka cireta a zuciyarka ka nemi wata daban. Allah yasa haka shi yafi zama maka alkhairi da mu baki d’aya.”" Sauk’e ajiyan zuciya Hisham yai yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Sai ya kifa Kansa na d’an lokaci. Ya d’ago yana duban mahaifiyarsa broken “Hajjah.. Hajjah wanene Ummul ta aura.?” Tambayar da ya haifar mata da fad’uwan gaba. Ta girgiza Kai kad’an “Shin baka d’auki k’addara bane.? Are you having doubts kan abubuwan da na sanar dakai.?” Girgiza mata Kai yai a hankali ba tareda da ita cewa komai ba. Hajjah Fannah ta jinjina Kai “Sanin waye Ummul ta aura baida wani alfanu wajenka. She’s someone’s wife now. Ka cireta gaba d’aya a ranka kuma kar ka waiwayi baya.. Ka min wann alk’awarin D’ana.” D’agowa ya kumayi ya dubeta. Sai yai murmushi mai ciwo “Kamar yanda kika ce Hajjah.. Zanyi kaman yanda kikace..” Ya mik’e yana kuma shafa fuksarsa “Inaga zan koma bakin aiki ko zuwa… Gobe idan Allah ya kaimu. If that’s with you.” Ya k’arashe jiki a mace. Sosai tausayin shi ya cikata. A hankali ta jinina masa Kai “Hakan yayi D’ana.. Allah ya tsareta da tsarewarsa ya baka dukkan kariya. Ya saka maka albarka cikin duk abinda ka sa gabanka.” Ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata kafin yasa kai ya shige. Sauk’e ajiyan zuciya tai tana jin ciwon da D’an nata ke ji har cikin zuciyarta. Shin har yaushe zata ci gaba da b’oye masa.? Shin sai yaushe zata sanar dashi gaskiyan lamari gameda mahaifinsa.? Shin rufe masa da tai tayi daidai..? Shin yaushe zata sanar dashi gameda Ahalinsa.? Shin Anya wann ba alama bace a gareta na cewa ya kamata ta fayyace ma D’anta komai. Musamman da yanzu d’an uwansa ya auri Ummul.? Anya ba baya bane yake hunting d’inta..? Bayan ta datse duk wani alak’ar da take da tabbacin zaisa su waiwaya.. Meyasa kwatsam abubuwa ke neman sauyawa..? Shin Ummul zata iya kasancewa dalilin da zaisa su waiwayi baya.? Ta kuma girgiza kai cikin sauri. A fili take furta “Bana fatan hakan. Allah ya gani tsakani da Allah naso Ummul tamkar ‘yarda na haifa a cikina. Watak’ila iyaka lokacin da zamuyi kenan a tare. Tabbas ya zama dole na datse alak’a da Ummul da duk wani abinda zai had’a d’ana da Aliyu Maitama.” ** Abuja… Tsaf suka fito cikin shirin fita. Doguwar rigar abaya Anisa ta bata ta saka. Da shike kaf dogayen rigunan Anisa ta rage fad’insu hakan yasa ya kama Ummul sosai sai yafi kyau a jikin Ummul d’in saidai tsawo da ya d’an mata yawa sakamakon Anisar ta fita tsawo. Sai faman yatsina fuska Anisa take tana mata kallon wulak’anci. Mommy kaw suna fitowa ta mik’e ta isa ga Ummul wacce tuni ta sadda kanta k’asa. Murmushi saman fuskar Mommy take fad’in “Ki saki jikinki ‘Yata. Ki zabi duk abinda kike so. Ko menene.” Ta dubi Anisa “Ki tayata ta zab’i kaya masu kyau Wanda zasu k’ara fito da kyaunta. And make sure you take good care of her.” Anisa ta kauda Kai gefe tana rolling ido. Kuji Mommy fah wani wai ta kula da ita saikace watchdog d’inta or something.? “I’m talking to you Anisa kina kallon wani wajen. Kinsan bana san shashancin nan naki..” Mommy tace ba walwala. Anisa ta juyo fake smile saman fuskarta “Ok Mommy. Kaman yanda kikace .. I’ll take good care of your daughter in- law for you. I promise.” "Mommy tace “She’s my daughter, not daughter in-law..”" Anisa ta kuma kauda Kai tana fuzar da huci. Sai yanzu ta yarda da kalaman Haidar idan ya kira Mommy good actress. Tayi imani ba a banza take ma wann kucakar makahon so irin haka ba. Yarinyar da gaba d’aya duniyarsu ya banbanta. Su d’in gaba d’aya ma ba d’aya bane. Wai Hajiya Kwaise Maitama ke treating ‘Yar talaka haka. Wllhi idan za’a Mutu bazata tab’a yarda auren nan na Allah da Annabi akayi ba. Kuma ko menene ke rufe cikin auren she vowed to find out about it. Sai ta binciko to the core. Credit card Mommy ta mik’a ma Anisa bayan ta tambayeta zatai driving ko driver ya kaisu. Anisa tace no zata tuk’asu. Murmushi Anisa ta sakar ma Ummul harda bud’e mata front Seat gaban Mommy. Dan Mommy ta tabbata zata kula mata da sirkarta. Cikin zuciyarta kaw cewa take ‘I’ll play your little game Mommy har na gano bakin zaren komai.’ A haka suka d’auki hanya. Suna tafe Anisa ta d’aga waya ta k’ara a kunne “Hello Girlfriend kina ina..?” Ta murmusa “Toh ki bar duk abinda kike let’s go shopping.” Ta kuma darawa “Ok just wait there yanzu zaki ganni.” Tana Ida fad’in haka ta katse kiran. Tai parking ta dubi Ummul “Ke koma baya zan d’auki k’awata” Ummul ta dubeta sai ta murmusa. Kaman zata fita sai kuma ta fasa. Ta juyo ta dubi Anisa “Amma ba a gidan baya Mommy tace na zauna ba. Kiyi hak’uri bazan iya sab’a umarninta ba.” Ta k’arashe murmushi mai k’untata ma Anisa saman fuskarta. Hararta Anisa tai kafin taja motar. A haka suka k’arasa kusan wani k’aton gini mai gidaje iri guda a jere. Can wata budurwa ta fito cikin shigar Wando sai top bajajje wanda bai matseta ba sai d’ankwali d’aure kanta. Tana k’arasowa Anisa ta bud’e motar ta fito suka tafi a guje suka rungume juna suna kiran juna Girlfriend. Da mamaki budurwar ta tsaya tana kallon wacce ke zaune gaban motar. Ta juyo ta dubi Anisa “Neesa wacece kuma wann..?” Anisa ta rausayar da ido “Kinsan a duniya ba abinda ke burge bakauye irin zaman gaban mota. Kedai shige muje Leenah we gonna shop the entire city..” Ta k’arashe tana d’aga mata card d’in mommy dake hannunta. Leenah ta shige backseat sai labari suke itada k’awarta Anisa. Tanata k’are ma Ummul kallo wacce batabi ta kansu ba. Can Leenah Ta bangaji Ummul ta mik’a hannunta jikin radio na motar ta k’ure kid’a. Har lokaci Ummul batabi ta kansu ba. K’arshe hannu tasa ta cikin mayafi ta toshe kumnuwarta dan ita dama ba mai sauraron irin wad’an wak’ok’in na turawa bane. Sanda suka isa ma gaba sukai suka barota baya. Har sun d’an yi nisa kafin Anisa ta rausayar da ido ta juyo ta dubeta. Nan ta hange Ummul na kokawan d’alewa escalator. Sai kuma ta dubi Leenah “I can’t believe this is happening to me. I can’t believe we are hanging out da bagidajiya irinta. Dubi abinda take neman wani ya mana video yace tare muke. Anjima mu ganmu ana tagging d’inmu. Nidai yau Mommy ta kashe ni. Wann da kyar idan ba daga kauye aka d’aukota ba dan ba dai cikin birnin Kano ba.” Ta k’arashe tana furzar da huci. Daidai sanda Ummul ta k’araso “Kuyi hakuri takalmin ne nakeji kaman zai kadani.” Leenah da Anisa suka dubi juna suka dara a tare. Kafin Anisa tace “Malama karkiji Mommy ta ce na kula dake. If you go missing babu wanda zai b’ata lokaci wajen nemanki dan da alama this is your first time in a place like this.” Leenah ta tab’e baki sai kuma ta nufi wani wajen cikin sauri tana ambaton sunayen designers. Anisa ta rausayar da ido tana duban Ummul da Leenah ta barsu nan tsaye tare “Baiwar Allah. We are here already. Select what you want.. Ko shima sai na tayaki.?” Ta k’arashe tana kuma rausayar da ido had’ida furzar huci. Tuni Anisa ta tafi wajen k’awarta Leenah. Suka kyale Ummul ita kad’ai. Saida suka jida kaya nik’i nik’i suka tadda Ummul tsaye da wasu dogayen riguna da basu wuce uku ba. Duban juna suka kuma yi kafin Anisa tasa hannu ta finciki Kayan dake hannun Ummul. Ta d’aga kayan sama ta Ware tana gani Leenah na tayata “What.! Are you kidding me..? Wann shine iyakacin abinda kika iya zab’a tuntuni.?” Ta girgiza Kai tana kuma duban Kayan. Leenah tace “Wai zallan jallabiya ta zab’a. Ina zata dasu.. Ba azumi ake ba balle nace ittik’afi zata shiga.” "Anisa ta girgiza Kai tana duban Ummul take d’aga rigunan “Baiwar Allah. We are shopping with Hajiya Kwaise Maitama’s card, we can buy the whole mall if we want.. And hello! You are married to Haidar Maitama. So get used to spending a lot.”" Leenah baki sake take duban Anisa Jin ta kira budurwar da suke tare matar Haidar. Saurin janyota tai suka matsa daga kusan Ummul. "Leenah ta dubi Anisa “Wait, did I hear that right..? Wann d’in matar Haidar.. Haidar Maitama da na sani. Our long time crush..?”" Anisa ta juya ido “You heard it right. Wai wann d’in matarsa ce. Amma bana tunanin auren mai d’orewa ne dan dai tin jiya da aka kawo masa ita gidan he didn’t show up. Mommy ce kawai mai son Auren Amm Wanda akai domin shi baisan anayi ba da alama.” Leenah ta jinina Kai “No wonder. Dan dai wann hanyar da Haidar yabi ma bata isa bi ba.” Sai ta kuma gyara tsayuwarta tana duban Anisa “But what about you girlfriend. I know you love your cousin so much. Does that mean.. You give up..” “Giving up is not in my vocabulary Leenah. You should know better. Kawai lokaci na d’ibar masu. I have to study my target well before I strike.! But trust me sweetheart hakan zai faru ne kafin ta samu kusanci da Haidar.” Ta k’arashe makirin murmushi saman fuskarta. Leenah ta murmusa “Then do it fast sweetheart. Kinga irin wadnn makiran babu wuya sun saye Zuciyar namiji.” Dubanta Anisa take fuska a yatsune. Tai nuni da Ummul wacce mata me kula da kantin keta faman nuna mata wasu kalolin designs din. Anisa ta murmusa ta kuma duban Leenah “Haidar Maitama ya fada soyayya da wann bagidajiyar. You know what Leenah. I hate to burst your balloon but what you’re imagining is never ever going to happen.” Ta k’arashe tana kuma rausayar da ido. Leenah ta murmusa “Lallai Neesa toh barikiji na fad’a miki. You’ll remember this moment idan baki tashi tsaye tun yanzu kin kawar da ita ba. Ina nufin tun kafin Haidar ya zame Miki k’alubale wajen kauda ita.” Shiru Anisa tai sai kuma tace “I don’t want things to reach the point where I have to stain my hands.” Leenah ta murmusa “Then hire someone to do the job for you.. I can’t wait to get my hands dirty..” Ta k’arshe tana kashe mata ido. Juyawa tai ta kalli wani cream yanda aka rubuta do not apply on face. It contains strong fragrances that might irritate your facial skin. Ta murmusa ta kuma duban Anisa “Hey Girlfriend. Daga nan ya kamata mu ziyarci beauty Spa.” Tai maganar tana d’auko cream d’in ta nuna ma Anisa. A tare suka dara kafin suka k’arasa wajen Ummul suka ci gaba da tayata shopping kaman babu abinda ke faruwa. Har cewa Anisa take ita tasan taste d’in Haidar so zata zab’a ma Ummul kaya to taste d’insa. Ita dai Ummul bata tankasu ba amma jikinta ya bata wani abun suke shiryawa. Daga nan Beauty Spa suka tsaya. Ummul ta dubi Anisa “Mai zamuyi a nan.” “Face treatment sweetheart.” Ta bata amsa tana unbelting kanta daga cikin kujeran. “Amma ba abinda ya samu fuskata ni..” Ummul ta bata amsa. Gajeren tsaki Anisa tai “Beauty treatment ake magana ba sai kinji rauni ba. Dan Allah bani son stinginess naku na talakawa. Mommy card ta bayar mu k’arar dashi akanmu idan munso.” Ummul ta murmusa had’ida girgiza Kai ganin Anisa ta fice zata rufeta a mota. Koda suka shiga Ummul na hankalce dasu. Anisa da Ummul ake ma gyaran fuskar yayinda Leenah ke tsakani tana jira ta cika aiki kaman yanda suka tsara itada k’awarta Anisa. Ana fara face massage cikin dabara Leenah ta dauko wann cream din ta zuba cikin bowl din da aka kwaba kayan gyaran fuska na Ummul. Tana gama zubawa ta fice dama idon Anisa a lumshe suke sakamakon abinda aka daura mata saman idon. Ummul ta murmusa a hankali dan taga sanda Leenah ta matse tube din ciki. Aiko nan Ummul ta soma kokawan mik’ewa a birkice jin ana juyata mata fuska alamun bata saba ba. Aiko nan bowls d’in suka fado k’asa saidai basu zube ba. Ummul tai saurin d’aukan na Anisa wacce idonta ke lumshe sai faman tsaki take Bagidajiyar nan na bada ita. Ummul ta mik’a ma mai mata gyaran fuskar robar gyaran fuskan Anisa yayinda mai gyaran fuskar Anisa ta Sunkuya ta d’auki na Ummul dake k’asa tana ce da ita ba komai ta daina basu hakuri. Anisa ta rausayar da kwayar idonta dake rufe. Takaicin Ummul fal zuciyarta wani b’angare na zuciyarta kuma cikeda farin ciki zata toya ma Bagidajiyar Amaryar Haidar fuska tun kafin ya ganta. Bata Ida tunanin ba taji wani k’aik’ayi mai gauraye da k’una saman fuskarta. Aiko nan Anisa ta saki k’ara tana tsalle tana ihu tana tambayarsa mai suka saka mata a fuska. ** Royalton Cayo Santa Maria resort. Cuba… Tana kwance tana facing view na ruwa. Zuciyarta na mata sanyi. Rayuwar Jin dadi da bata fata wani abu ya katse mata shi. Nan ta bud’e WhatsApp dinta da ta kwana biyu bata waiwaya ba. Sak’onni ne sukaita shigo mata daga wani number da tai saving da . *Shadow.* Kaman jira yake ta kunna nan k’ira ya soma shigowa. Dareen taja garen tsaki. Tasan babu abinda zai tambayarta face mai suke Cuba a daidai wann lokacin bayan kwana biyu bata basa wani update kan Haidar d’in ba. Ganin bazai daina kiraba yasa ta d’aga ba don taso ba. Tana d’agawa ta fara da “Shadow shadow. Looks like kana biye damu dik yanda muka je. Just like your name.. Before you ask. We are here on our third honeymoon. Oh! I forgot to put my cellphone on DND mode.” Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta “Who is Shadow.?!” Zuciyar Dareen yai wani irin tsinkewa tamkar statue haka ta kafe ko motsawa ta kasa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *26* *©️Sameena Aleeyou… * Ko motsawa ta kasa. ‘Yan hanjin cikinta tuni Sun kad’a. A hankali ta zame wayar daga kunnenta bayan ta katse kiran. Muryarsa ta kuma sinkayowa Ya daki dodon kunnwanta a karo na biyu. “I think I ask you a question. Who were you talking to on the phone. Who the hell is Shadow.?!” Juyowa tai tana dubansa yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa. Alamun yana jiran amsarta. Abinka da gogaggiya sai tai murmushi “Shadow.. Inuwa.. Asalin sunansa Inuwa.. He’s.. He’s my cousin.. My cousin that I told you about lokacin auren mu.. Ka tuna..?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido. Kansa ya soma juyawa. Sai yaji ya soma wani tunani wanda bazai iya cewa ga specific abinda yake son tunowa ba. Sai ya zama lost and confused. Dan shi bazai iya cewa ga abinda ya faru lokacin auren nasu ba. Iyakacin abinda yakeda tabbaci akai shine sunyi aure. But baya iya tuna komai in detail. "Dareen taci gaba “Cousin dina da na baka labari. Wanda yake so na ni bana sonsa. Because my heart belongs to you tun kafin mu had’u.” Ta kuma murmusawa “Yaron Uncle dina. Shine ya kira wai mu gaisa har kaji ina kiransa Shadow ina kuma ce masa ya daina damuna because ina tareda lovely husband d’ina, enjoying our third honeymoon.” Ta k’arashe tana d’aura duka hannayenta saman kafad’unsa makirin murmushi saman fuskarta." Kansa ne Ya kuma Ji ya cunk’ushe sai ya rasa wane tunani yake guda d’aya. Wani abu yake son tunawa amma bai sani ba. Ya kuma kasa tuna komai. Tinda Dareen ta d’aura hannayenta saman kafadunsa sai ya kuma Ji ya zama confused. Sai ya zama baya tunanin komai cikin kwakwalwarsa baya kallon kowa cikin k’wayar idonsa sai ita. Dareen ta karkatar da kai tana dubansa har lokacin murmushin ne saman fuskarta “Shall we go now.?” Girgiza mata kai yai cikin rashin fahimta “To Where.?” Ta kuma murmusawa tana mai tallafo fuskarsa da tafukan hannayenta “You seem to forget things easily nowadays My love.. Har ka mance. Jiranka nake ka fito mu tafi Spa and fitness.. I thought kace zaka gym.” Shiru yai kaman mai nazari sai Ya karisa saman drawer ya d’auki wayarsa had’ida jefata cikin aljihun wandon three quarter dake jikinsa. Har ya soma takawa ya juyo ta dubeta “Don’t answer his calls again.” Ya fad’i cikeda gargad’i. Saurin jinjina masa kai tai “I’m blocking his number right this instant.” Baice da ita komai ba yasa kai ya shige ba wai dan ya aminta da labaran da ta basa ba sai don Ya k’asa tuna komai. Bayansa tabi da kallo murmushin saman fuskarta ‘Bazaka tab’a sanin waye Shadow ba Haidar.. Shadow has been shadowing you for a long time now.. Maybe tun kafin na shigo rayuwarka. But one thing I’m sure of shine Shadow made a huge mistake da har ya bari na shiga rayuwarka. Because I’ll protect you from him. Kuma bazan tab’a bari ya cutar dakai ba for as long as we are together..’ Ta k’arashe zancen zucin nata tana take masa baya dan tuni Haidar ya fice. Motsa jiki yake da iyaka kuzarinsa da k’arfin sa ko zai iya tuna wani abu amma ya kasa. Why couldn’t he remember a thing.? Meyasa yake ji kaman brain d’insa na barazanar tarwatsewa.? Meyasa yakeji kaman chest d’insa ya masa nauyi. Meyasa yakeji like he’s lost in his own world. Rintse idanunsa yai yana kuma tuk’a keken motsa jikin da iyaka k’arfin sa. ** Abuja.. Suna fitowa Leenah ta mik’e a birkice tana duban fuskar k’awarta da ya koma jazir abinka da farar fata. Fuskar tayi rod’i rod’i duk tayi jazir kaman k’osan da ya sha wuta cikin mai. “OMG.! Girl.. What happened to your face…?” Leenah tace tana zaro ido waje. “Just shut up Leenah..! This is all your fault..” Anisa tace tana sakin huci. Lokaci guda tasa kai ta nufi mota. Daidai lokacin Ummul ta fito fuskarta ta k’ara kyau sai wani shek’i na musamman da fuskar nata keyi. Sosai gyaran ya amsa fuskarta. Leenah ta saki baki tana duban Ummulkhairi. “But..But.. Wait.. How’s this possible..?” Leenah tace cikin rashin fahimta. Murmushi Ummul ta sakar mata kafin tasa kai ta shige ta nufi mota. Leenah tabi bayan k’awarta Anisa cikin sauri tana tambayarta me Ya faru. "Juyowa Anisa tai tana dubanta da toyayyan fuskarta “You know what Leenah, I don’t want to listen to you. Just get in the car and let’s get out of this place..!” Ta k’arashe tana furzar da huci had’ida rausayar da ido." Saurin rik’ota tai ta dawo da ita baya “Hey hey easy.. Wai mai ya faru ne.. For as far as I know ba ma Ke na zuba cream din ba. How did it end up on your face..?” Anisa ta rausayar da ido “Because She outsmarted you Leenah.. Isn’t it obvious..? You are so useless.!” Ta k’arashe cikin huci tana juya ido. “Hey easy don’t take it out on me. She’s the culprit. She switched the bowls.” Cewar Leenah tana nuni da Ummul dake zaune cikin mota. "Anisa ta rausayar da ido “That’s because you are stupid. You know what Leenah, I feel like punching your ugly face.”" Leenah ta shafa fuskarta “Hey don’t be mean. I spent so much on this beauty..” Ta k’arashe tana Shafa fuskarta da murmushi. "Rausayar da ido Anisa tai tana sakin huci. Zata shige Leenah tai saurin kamo hannunta. “Girl, if she can do something terrible like this, with that innocent looking face. Then believe me she’s dangerous.. She’s a wolf in sheep’s clothing. You need to eliminate her out of the picture.. As soon.. As possible..!” Ta k’arashe tana firfito da ido waje." Tururi kurum Anisa take “Believe me Leenah. I won’t play fairly this time around..She wants battle? then I’ll give her war..Just watch and be amazed.!” Ta k’arashe tana sakin huci. Leenah ta girgiza kai “You need to change your ways Neesa. Ki fito mata a musulma. Make sure you win her trust first before you make your move.” Anisa ta rausayar da ido “I don’t think I have that kind of patience. I can’t stand her one bit.” “You have to Neesa. You must put up with her. That is idan har kina so ki kawar da ita cikin sauk’i.” Anisa tai Shiru without saying a word. Murmushi Leenah ma ta saki amma sai murmushin ya rikid’a Ya koma dariya dan sosai fuskar Aminiyar nata ya bata dariya yanda ya sauya halitta lokaci guda. “What’s got you laughing..?” Anisa ta tambaya a hasale. Leenah ta soma k’unshe baki tana nuni da fuskar Anisa “Seriously Girlfriend you look like a monster.” Ta dubi Ummul da ko kallon yanda suke batayi tace “Ita kuma makirar tayi kyau jibi yanda take glowing.. Awwn I’m jealous of her skin..” Ta k’arashe tana dafe fuska. Tsawa Anisa ta darara mata tana fad’in ta shige mota su tafi ko ta tafi ta barta nan wajen. "“Oh hey. Easy girl, I’m just joking.. You are still more beautiful than her.” Leenah ta fad’i tana take ma k’awarta baya." Haka suke tafe Mota Leenah na kuma tunzurata da surutanta har dai aka sauk’e Leenah a destination dinta shak’e da kayyayakinta da sukai shopping. Mota ya rage saura Ummul da Anisa. Ba mai ce da kowa komai har suka iso gida. Ummul ta dubi Anisa Tai mata godiya wann murmushin Wanda sam Anisa bata k’aunar gani saman fuskarta. Suna shigowa cikin gidan suka tadda Mommy zaune da wasu mata masu sanye da rigar kampani na tailoring a first parlor. Ma’aikatan gidan da kusan ko yaushe suke cikin shiga ta uniform suka soma amsan kayyakin hannunsu suna masu sannu da zuwa cikeda girmamawa had’ida ladabi. "Ita dai Ummul duk ba wai ta Saba da irin wad’ann abubuwan bane. Musamman idan taga manyan mutane suna girmamata suna gaisheta koda kuwa masu aiki ne. Sam batajin dadin irin abun. Sosai abun ya bata mamaki da safe kafin su fita yanda Anisa ta dinga masifa ma babban mata dake kitchen wai dan kawai bata kawo mata abinda ta buk’ata kan lokaci ba. Tana jin wacce ta amsa Kayan hannunta tana tambayarta “Ma’am, should I take these to your section..?” Kasancewar akasarin ma’aikatan gidan hiring d’insu akai daga registered company na masu aikace aikacen gida da Office ba hausawa bane ba sosai suke hausa ba." "Sai Ummul tai sakare tana dubanta. Ba wai dan bataji mai tace bane, kawai sabo ne da irin rayuwar da Sam batai ba. Rayuwar da gaba d’aya ya banbanta daga irin rayuwar da ta girma ciki tai wayo ciki." Mommy ce ta bata amsa da fad’in ta kai mata su side dinta. Wato b’angaren Haidar. Maid din ta amsa da “Yes Ma.” Cikeda risinawa. Mommy ta k’araso ga Ummul wacce tuni ta risina tana gaisheta. Bata amsa gaisuwar ba sai kamo hannunta da Tai tana fad’in suje ga masu d’inki zasu gwadata su d’auki measurement dinta. zasu d’inka mata atamfofi da laces daidai size d’inta. Anisa ta saki baki tana kallon ikon Allah musamman da ta ga babban tailoring company da Mommy ta kira Wanda a garin ma ba ma kowa suke d’inki ba sai ka cika elite. Ko ita kanta Anisa basu tab’a mata d’inki ba sai gashi wai zasuyi ma wann kucakar. Zuciyar Anisa ta kuma tunzura. Tsanar Ummul ya kuma cika mata zuciya. Ko ta kanta fah Mommy bata bi ba balle taga abinda ya samu fuskarta. Cikin k’unan rai ta nufi d’aki tana tuanin sabon hanyar da zata bi ta b’ullo ma Ummul dan bata tunanin zata iya hak’uri da Ummul d’in kaman yanda Leenah ta bata shawari. ** Kano… Da kyar Mama ta amince ta fito wajen ganawa da mutane yanda Umma ke jiranta a nan police station da akai detaining dinta. Umma ta zuba tagumi tana duban Mama yanda ta jeme ta rame duk tsawo da jiki irin na Tani duk ta lalace cikin k’ank’anin lokaci ta zama abun tausayi. Banda Uwar harara Mama bata aika mata komai. “Kinzo ne kimin dariya Suwaiba.? Kinzo ne dan kiji dadin ganina a k’ask’ance..?” Muryar Mama ya soma rawa “Ki amsa min Suwaiba. Kinzo ne dan ki min dariyar abubuwan dake faruwa dani..? Ina nufin ‘Ya’yana Sun jirge gida. Badia miji ya gudu Ya barta ita kuma Azeema miji ya koreta.. Ni kuma gani a nan cikin k’ask’anci da tozarci.. A yayinda ke Allah ya cika miki burinki. Ummul d’inki tayi aure.. Aure na gani a fad’a irin Wanda nawa ‘ya’yan basu samu ba.. Mutanen unguwa sun bar nunaki da baki sun koma nuna ni nida nawa ‘ya’yan.. Mijinmu kuma yanzu na k’ark’ashin kulawarki.. Ya zama naki ke kad’ai.. Haka ne Suwaiba..?” Ta k’arashe kuka na b’alle mata yayinda Umma ma kukan take. Cikin zuciyarta cewa take Allah sarki Yaya baki san tashin hankalin da kike ciki mai sauk’i ne gaban Wanda nake ciki. Baki san wani irin aure Ummul Tai ba. Baki san cewa Aure ne mai k’ayyadadden wa’adi ba. Baki san Aure ne da aka k’ullasa bisa yarjejeniya na tsawon watanni uku.. Aure mai gib’i auren da zan jima ina d’an dana sanin yi ma Ummul irin wann auren Har tsawon rayuwata. Sann Mijinmu banida ikon taka yanda yake. Muryar Tani ya kuma katseta cikin karaji sanda ta soma janyo Umma tana fad’in “Tashi ki tafi Suwaiba. Ki tashi nace ki tafi kuma kar ki sake takowa yanda nake.!” Kuka Umma take tana girgiza kai “A’a Yaya.. Dan Allah ki saurareni.. Wllhi ko d’aya banzo nan dan abubuwan da kika zayyano ba.. Yaya ki saurareni..” Sai Umma ta rungume Tani tana kuka.. Su duka biyun kuka suke Wanda yafi kama da kukan nadaman rayuwa. Mama ta fincike jikinta daga rik’on da Umma tai mata. Zata sa kai ta shige Umma ta kuma rik’o hannunta “Yaya dan Allah ki saurareni.. A halin yanzu bamuda kowa sai mu biyun..” Mama Tani ta goge hawaye da bakin zaninta Wanda yai duk’un duk’un “Yayane Suwaiba..? Ki sanar Dani yayane..?” Umma ta goge hawayenta da bakin mayafi “Yaya yanzu ba lokaci bane da zamu rik’e juna abokan gaba. Lokaci ne da zamu fahimci dukkanmu masu kuskure ne.. Kuma Allah yana sonmu da ya nuna mana kura kurenmu tun a nan gidan duniya.. Saura ya rage namu mu d’auki darasi ko mu bijire.” "Jikin Tani ya kuma yin sanyi wasu hawayen na zubo mata yayinda Umma taci gaba “Yaya babban abinda ya jefa mu cikin halinda muka tsinci kanmu shine son kanmu, rashin tawakkali da yin abu dan mu burge mutane Wanda Har yasa mun mance su waye mu. Mun mance auren mu, mun mance ‘ya’yanmu da Allah ya dank’a mana amanarsu. Mun mance mijinmu da yakeda girman hakki akanmu.. Sabida son zuciya irin namu.. Mun mance mu masu kiwo ne kuma za’a tambayemu bisa abinda aka bamu kiwo.. Yaya duk mun mance wad’ann mun saka son zuciya a farko.. Wanda shi ya kai mu ga halinda muka tsinci kawunanmu.” Ta kuma jinjina kai tana hawaye “Watak’ila Ummul tayi aure.. Amma ba irin auren da naci mata buri ba.. Dije ta rabani da Khulsum kaman yanda ta rabani da mijinmu.. Nida ke bamuda wani maraba Yaya. Yanda kike rufe a nan babu walwala nima a b’angare na haka take.. Kullum ina kulle ne cikin d’aki Babu walwala.” Ta kuma share hawayenta yayinda Tani ta katseta “Wani irin aure ne Ummul Tai Wanda baki ci mata buri ba Suwiaba.?”" Tambayar da ya haifar ma Umma fad’uwan gaba. Koda Ummul AUREN WATA UKU Tai bazata so ta sanar da Tani ga irin auren ba. Hasalima bazata iya ba. Batada wann k’warin gwiwar. Girgiza mata kai tai “Ki yarda dani Yaya na tapka babban kuskure..” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka. Mama ta jinjina kai “Na yarda da duka abubuwan da kika fad’a Suwaiba.. Mun tapka kuskure.. Kuma idan bamu had’e kawunanmu yanzu ba bazamu tab’a k’wato mijinmu daga hannun Dije ba. Tazo Har nan ta min d’iban albarka ta kuma jaddada min tinda naci amanar d’anuwanta dake kwance nida fita a gidan yari sai Randa jakin Baba yayi k’aho. Zata tabbata ban samu wani k’ofa da zan tsira ba. Sann yarana sun guje ni. Salima ce kawai ke zuwa nan ta dubani. Amma Azeema da Badia Wanda nake gark’ame nan sabida su sun wofantar dani Suwaiba..” Ta kamo hannayen Umma “Suwaiba dan girman Allah ki taimaka min kafin a tafi Kotu. Sunce cikin satin nan za’a shiga Kotu da mutumin k’auye mai kudi. Dan girman Allah Suwaiba ki taimaka ki nemo kud’d’en nan a fitar dani.. Naga Sirakan Ummul masu hannu da shuni ne. Ki taimaka min Suwiaba ko wajensu kije ki nemo kud’ad’en nan ki fitar Dani a nan..” Ta k’arshe tana tsare Umma da ido. Zuciyarta na tabbatar mata hanyar da zata bi kenan ta samu ta fita daga wann tuggun. Ta nuna ma Suwaiba nadamarta a fili Har dai Suwaiban Tai mata hanyar fita.. Dum!! Haka k’irjin Umma ya buga dan ita kanta bata isa tace ga kalan sirakan Ummul ba. Uwa uba rabuwar da sukai da Asshe Wanda Asshe tai mata iyaka da gidanta. Tani ta tsare Umma da ido. Cikin zuciyarta take ayyana tinda na sauko da kaina Suwaiba dole kimin abinda nake so. Ta haka ne kawai zan samu na fito har na fahimci mai kike b’oye min gameda auren Ummul. "“Ke nake sauraro Suwaiba, zaki min wann alfarmar.?” Mama tace tana tsareta da ido." Zuciyar Umma ya kuma tsinkewa. Ta d’ago tana duban Mama cikin sanyin jiki… SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *27* *©️Sameena Aleeyou… * Umma ta girgiza kai a hankali “Kiyi hak’uri Yaya.. Bazan iya Miki alk’awarin komai ba a halin yanzu.” Tai maganar ba tareda ta iya duban fuskar Mama Tani ba. A dak’ile Mama ke dubanta “Suwaiba.. Kina nufin bazaki taimake ni ba..? Kenan kema kin zab’i a tura ni kurkuku kaman Dije.?” Umma tai saurin d’ago kai tana girgizawa alamun a’a. Tani ta gyara zama “Toh idan ba haka ba yaya ne.? Bakida wani maraba da Dije Suwaiba.. Banyi zaton haka daga wajenki ba Suwaiba..” Sai ta fara hawaye “Bayan ke banida kowa Suwaiba.. ‘Ya’ya na Sun guje ni.. Mijina na kwance jinya ta cinyesa.. Ke da nake zaton zamu taru mu rufa asirin juna kema kin juya mun baya Suwaiba.?” Sai ta fashe da kuka tana fad’in bata zaci haka daga Umma ba. Lokaci guda Mama ta mik’e tana huci “Tinda haka kika ce Suwaiba.. Shikenan kije abinki.. Kije kici arzikin sirakanki ke kad’ai. Ni kuma in sha Allahu babu ni babu Ke Suwaiba. Kar ki sake tako inda nake idan har ba taimako na zakiyi ba.” Tasa kai zata shige Umma tai saurin mik’ewa ta tareta “A’a Yaya. Dan Allah kar kice haka.. Ni ahalin yanzu banida kowa nima sai ke. Bamuda kowa sai mu biyun.. Amma..” Katseta Tani tai “Amma me Suwaiba.?” Tai maganar tana tsare Umma da ido. Gaba d’aya Umma ta daburce bata San mai zata sanar da Mama Tani ba. Bata san ta yanda za’ayi ta sanar da ita cewa itama ta riga ta k’are mata ba. Tai saurin jinjina kai “Toh. Toh.. Yaya.. In sha Allah zan nemo hanyar da zaki fita..” Mama ta jinjina kai “Yanzu naji batu Suwaiba. Kar ki mance fitowa zanyi muyi yak’in k’wato mijinmu daga hannun azzalumar ‘yar uwarsa wacce babu komai cikin zuciyarta face burin fansa dan nayi imani ba tsakani da Allah Dije ke ma Isubu jinya ba. Shi kansa yasan halin Dije Shiyasa tun yanada lafiya ya mata iyaka da yanda yake. Ko dan wann Suwaiba bazamu bari Dije ta rab’esa ba. Ki nemo kud’ad’en bak’auye a biyasa na fito mu k’wato mijinmu uban ‘ya’yanmu. Ta haka ne kawai ahalinmu zai kuma samun daidaito. Kin fahimta.” Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai “Na fahimta Yaya. Nima zanso muyi jinyar mijinmu mu samu ladansa. Kuma kuskure ne mun riga Munyi amma munyi nadama. Kuma Allah mai afuwa ne mai yawan gafara.” “Yauwa dai Suwaiba ko ke fah. Nasan kinada fahimta Shiyasa munafukai basu tab’a samun nasaran shiga tsakaninmu ba. Ni ‘yaruwa na d’auke ki Suwaiba ba kishiya ba. Kuma ‘yan sa’insa da sab’ani da muke samu a baya zama ne Ya kawo haka. Dama shi kansa rayuwar zo mu zauna ne zo mu sab’a. Harshe da hakori ma suna samun sab’ani ballantana mu ‘yan adam.” Umma ta jinjina kai “Haka ne Yaya. Zanyi iyaka kokari na in sha Allahu. Allah ya mana jagora.” Mama ta murmusa had’ida amsawa da “Yauwa yanzu naji batu Suwaiba. Ina nan ina saka tsammani. Na d’aura duka yardana akanki Suwaiba.” Ta k’arashe cikin yanayi na tausayawa. "A hankali Umma ta jinjina kai duk jikinta a mace haka sukai Sallama da Tani. Tana ficewa Tani ta kece da dariya. A fili take furta “Saidai ba Suwaiba matar Malam Isubu ba. Muje zuwa, da kanki zaki fiddani ni kuma na fidda ‘yar naki a gidan auren nata. Tinda ‘ya’yana basu zauna d’akin miji ba naki ‘yarma bazata zauna ba. Abun yazo gidan sauki dan da alama akwai abinda kike b’oyewa gameda auren. Bazan yi k’asa a gwiwa ba har sai na shak’a iskar ‘yanci dan na cimma burina.” Ta kuma murmusawa daidai sanda wata ‘yar sanda tazo maidata cell dinta." Umma tana tafe tana lazimi da tinanin ta yanda zata b’ullo ma al’amarin Tani. Zatai iyaka yinta dan ta taimaki Tani tinda ta tabbata idan yau mijinta ya farka Ya gansu sun had’e kawunansu kuma sunyi nadaman duk abubuwan da suka aikata a baya zaifi kowa farin ciki kuma Watak’ila fushin da yake dasu ya gushe. Watak’ila hakan ya zama silan yafe masu duk wasu kurakuren da sukai sanda yake kwance. Toh amma ina ta nufa..? Ina zataje .? Wajen waye zata je ta samo kud’ad’en da za’a fidda Tani.? Asshe kawai ta fad’o ranta. Dan idan ba Asshen ba bata kuma san wajen waye zataje ba. Toh amma sanin irin rabuwar da sukai da Asshe sai ya kuma haifar mata da sanyin jiki. Asshe ta bada umarni ma masu tsaron gidanta cewa ko mai kamanninta suka gani kar su bari ta shiga. Uwa uba had’e kan da Dije da Asshen sukai mata kafin a tafi da Ummul. Ta tabbata idan Har Dije ta k’ulla aminta da Asshe zuwa wajen Asshe had’ari ne. Dan idan har Dije ta fahimci Matan Isubu Sun had’e kai. Wato ita Suwaibar da Tani wani sabon wuta zata kunna masu. Snn abinda take k’ok’arin b’oye ma Tani gameda auren Ummul kuma shikenan ya tashi daga sirri. Dan tayi imani Dije bazata so taga wann had’in kan ba Wanda yake nufin rugujewar shirin duk wani fansarta akansu. Dole tai taka tsantsan. Dole tabi komai a tsanake idan har tana so ta taimaki abokiyar zamanta Tani ta fita daga kurkuku. Da wann tunanin ta sallami mai adaidaita ta shigo gida. Saidai tana shigowa abinda Tai karo dashi ne Ya mugun bata mamaki. Dije ta gani tsaye tsakar gidan ga kayan abinci da kwanaki Suwaibar ta kawo lokacin sunayi da Asshe lokacin yak’in auren Ummul jirge gaban Dije ta kirawo yara tana fad’in maza su fidda mata kayayyakin su kai mata cikin adaidaita dake jiranta k’ofar gidan. Umma ta saki baki tana kallon ikon Allah “Dije.. Lafiya mai nake gani haka..? Ina zaki kai mana kayan abincin.?” Kallonta Inna Dije Tai daga sama zuwa k’asa “Makauniya ce ke.? Bayan shahshanci kuma idonki Ya rufe ne Suwaiba.? Tafiya dasu zanyi. Tinda na tabbata da kud’ad’en da kika saida d’iyar D’anuwana kika sayi kayan abincin nan. Ko ma ince su suka baki. Kaman yanda kika sani da zaran an sallamesa daga asibiti ko gidan nan bazai taka ba balle yayi karo da wani tashin hankalin da tsautsayi. Dutse zan wuce dashi ya samu hutu da jinya a can. Kayan abinci kuma zamu buk’ata.” Ta k’arashe tana d’aura ma yaro guda kwalin taliya akai. Umma ta girgiza kai “Amma Dije mai zamuci.? Kar ki mance ba ni kad’ai ce a gidan nan ba. Akwai Badi’a sann akwai Azeema. Idan kika kwashe komai mai zaki barmu dashi.?” Dariya Inna Dije tai harda shewa kafin tace “Lallai Suwaiba. Yau kece mai fafutakan abinda yaran Tani zasu ci.? Saikace ba kece Tani ke hana naki yaran abincin da ubansu Ya kawo ba. A cewarta bazata girka ma k’artan banza Wanda suka ki aure abinci ba.? Ikon Allah sai gashi yau ke Suwaiba kece kika nemo abinci kika ba ma yaran Tani da suka k’i zaman aure harma girka masu kike. Yaran da ko ganin mutuncinki basayi. Lallai na yarda kin tabbata shashasha Suwaiba.” Umma ta girgiza kai “Dije rayuwar duka nawa take. Ciyar da rai lada ne dashi balle ‘ya’yan mijina Wanda jarabawar rayuwa ya fad’a kansu suka baro gidan mazajensu. Babu mahaifinsu a gidan Babu mahaifiyarsu. Gatansu Allah sai ni kad’ai da na rage masu cikin gidan kuma in sha Allahu bazan wofantar dasu ba. Idan Allah ya bani dama da iko na zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa ‘ya’yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba.” Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai “Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu. Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga wann abincin Ya haramceku daga ke Har su.” Ta k’arashe tana sunkuman kwalin taliya. Kaman daga sama taga Azeema da Badia kanta ko wacce tana sakin huci. Shigowarsu gidan kenan. Azeema ta nuna mata kwalin taliyar “Ajiye.” Ta fad’i cikeda gargadi. Inna Dije ta dubeta da mamaki “Ke Azeema ni zaki ma rashin kunya.” “Zaki ajiye ne ko zaki jira na tayaki ajewa.” Cewar Badia tana shan d’amara. Inna Dije ta saki baki da mamaki “Ke Badi’a.. Ni zaku ma d’iban albarka ina kanwar Ubanku.?” “Allah yasa k’anwar uban kikace ba uban ba. Rashin kunya kuma ai mai sauk’i ne wann. Billahillazi akan abincin nan sai mu tara Miki na jaki a nan mu bama idon mak’ota abinci dan kinsan dai wann ba bak’on abu bane a wann k’ofar.” Azeema tace tana kuma shan d’amara. Har lokacin mamaki take baki bud’e “Ni Dije zaku daka ke Azeema.! Eh Lallai! Ai idan bakuyi ba baku cika jinin Tani ba. Ba laifinku bane Kunsha a nono.” “Wllhi Inna Dije zakici bugu a banza dan kin fad’a da bakinki nida kunya dama munyi hannun riga. Ke d’in banza tinda na tafi na tari fad’a da budurwar Habibu mai tak’ama da uniform da bakin bindiga banga uban da bazan taresa ba. Ke mu fah fad’a ma rancenta muke ko ya kikace Badia.?” Badia ta dubi Inna Dije da bakinta ya gaza rufuwa sabida mamaki “Inna billahillazi idan baki kira yaran nan sun maido da abincin da suka fitar ba wllhi Kinji na ranste Miki kaf takaicin duniya da Tasi’u Ya juye mun zan juyesu akanki. Dan wllhi yanzu a haka hannayena k’aik’ayi suke.!” Inna Dije ta jinjina kai “Eh na yarda dole ku kasa zaman gidan aure dan babu Wanda zai zauna da shed’anu Irinku. Me za’a tsammata daga wajen yaran da uwarsu ke tsare a gidan gyaran hali.” “Saki nawa aka Miki.? Yaji sau nawa kikayi da wayonmu kafin ki zauna gidan auren.?da wayonmu muna rakaki kome. Naga gado mukai wajenki” Badia tace tana fincikan kwalin taliya dake hannun Inna Dije. Inna Dije ta jinjina kai tana duban Umma da ta zuba ma sarautar Allah ido. K’wafa tai tasa kai zata wuce Badia da Azeema suka shiga janyota suka nufo waje suna fad’in saita maido kayan abincin da ta sace ta saka a keke napep. Haka Azeema da Badia suka tirsasa ma Inna Dije ta dawo masu da kayan abinci. Suka k’araso da kayan suka jirge gaban Umma. Har lokacin ko waccensu da d’amara a kunkuminta. Azeema taci gaba da nuna ma Umma kayan abincin “Kema kiji da kyau bamu k’wata abincin nan sabida Ke ba sai don yunwar cikinmu. Kici gaba da girkawa kina bamu.” Umma bata ce komai ba har suka gama maganganun da zasuyi. Dan tun bayan abubuwan dake faruwa kaman abun nasu k’aruwa yai. Cikin Zuciyarta tabi su da addu’ar shiriya. Ta d’au alwashin zatai hak’uri dasu kuma bazata fasa masu nasiha ba har lokacin da abubuwa zasu daidaita da taimakon Allah. ** Abuja… Anisa taci gaba da juya kwalaben turare da Mommy ta bata tace ta kaisu ma Ummul. Waya ta d’aga ta kira Amminta. Asshe na ganin wayar Anisa Tai saurin d’agawa “Ina sauraronki Anisa meke faruwa.? Shin Haidar yazo gidan.?” Anisa ta rausayar da ido “No Ammi he hasn’t shown up until now. And I don’t think zaizo gidan anytime soon.” "Asshe ta jinina kai “Toh ina sauraronki, wani abun ne Ya faru.?”" Anisa taci gaba da juya kwalban turaren “Ammi Kince duk abinda ake ciki na dinga sanar dake.” Asshe tace “Eh K’warai. Remember you are my eyes there.” Anisa taci gaba “Ammi Mommy ta bani wasu kwalaben turare guda biyu.. Kaman turaren black khumra amma banaji suna k’amshin khumra.. Tace na bama Ummulkhair.. Lallai Lallai na bata na kuma sanar da ita had’in khumra ne na musamman Mommyn Tai mata kyautar su.” Ai Asshe bata San sanda ta mik’e daga zaunen da take ba. Ta soma tuna lokacin zuwansu wajen boka sanda za’a masu aiki akan makarin asirin Haidar. Boka Ya basu wani turare mai launin bak’i ya kuma ce lallai lallai duk matar da za’a karya asirin jikin Haidar da ita sai ta zamto tana amfani da wann turaren domin kuwa turaren tamkar shine kuran k’arfe da zai janyosa zuwa gareta Har dai sihirin Ya lalace. Idan kuwa haka ne bazata bari Ummulkhairi Tai amfani da turaren ba tinda ita d’in barazana ce ga rayuwarsa. Baki na rawa Asshe tace “Turaren humra.? Kar ki bata su Anisa..!” Anisa tace “Meyasa Ammi.?” “Na fad’a Miki no asking questions Anisa. Just do as I say. Ki zubar ki zuba turaren Khumra cikin kwalban ki bata. But koda wasa kar ki bata wann turaren idan har kina son ki mallaki Haidar.” Anisa ta kuma juya ido “But Ammi what if Mommy ta ba ma Bagidajiyar nan turaren da zata mallaki Haidar ne since she wants her for her son. What if I use it instead.. Kinga sai ya soni bai sota ba..” K’iris Ya rage Asshe bata kurma kururuwa cikin waya ba jin nata ‘yar zata zama makarin asiri “Ke Anisa. Zan tsine miki albarka idan kikai amfani da turaren nan.. Wai ke wace irin shashasha ce. Nace duk abinda nace kiyi kawai kiyi zan miki bayanin komai daga baya.. Just dispose it and replace with natural Khumra. Kin fahimceni.?” Ta k’arashe cikeda gargadi. Anisa ta furzar da huci dan ta gaji da wann mysteries d’in “Ok fine Ammi. As you wish.” Ta k’arshe tana katse kiran. Taci gaba da juya turaren kafin ta nufi d’aki ta nemo wani kwalban ta juye turaren ciki ta wanke kwalban kafin tai yanda Amminta tace. Can k’asan kayanta ta b’oye turaren da Mommy ta bata Wanda zuciyarta ke raya mata turaren da zaisa Haidar yaso Ummul Mommy ta bayar a kai ma Ummul d’in tinda tana mata makahon so. Idan kuwa Har hunch dinta ya zama gaskiya ita ce wacce zatai amfani da wann turaren dan Haidar ya so ta. ** Gaba d’aya Ji take bata kyauta ba tin bayan abinda Ya faru tsakaninsu da Anisa. Musamman da taga yanda fuskar Anisar Ya b’aci. Ita a halin yanzu ba abokin fad’a take nema ba. Hasalima Tun farko batada abokin fad’a dukda kuwa masu nemanta da fad’an sunada yawa kama daga cikin gidansu har izuwa mutanen unguwa. Khulsum ce ta fad’o ranta wacce a ko yaushe idan an taresu da fad’a ita ke d’aukan fad’an. Tayi nata Tai na Ummul d’in. Ta murmusa a hankali. A fili ta furta “Nayi kewar ki fitananniyar ‘Yaruwarta.” Ta share hawayen da Ya gangaro mata. tunanin mahaifinta ne Ya fad’o mata sai ta tuna alk’awarin Inna Dije gareta a lokacin da suka kawota cewa kar ta saka damuwan mahaifinta a ranta domin kuwa zata kula dashi cikin yardar Ubangiji. Umma ta fad’o ranta. Sai ta lumshe ido a hankali tanajin kuka na zuwa mata. Kalaman Umma na k’arshe a gareta su take tunawa cewa kar ta nemeta kar ta nemi kowa cikin danginta Har na tsawon watanni uku koda kuwa a wayan salula ne. Meyasa Umma zata yanke mata hukunci mai tsauri irin wann. Shin ko haka take a al’adarsu idan anyi aure sai bayan watanni uku kai magana da ahalinka.? Bata jin hakan ne. Ta lumshe idonta wasu hawayen suka kuma gangaro mata. Tana a haka taji ana knocking a b’angaren ta. Ta mik’e Tai k’ok’arin kintsa kanta kafin ta nufi k’ofa. Ga mamakinta Anisa ta gani tsaye tana sakin huci. Ummul ta sakar mata sassanyar murmushi had’ida bata hanya “Bismillah shigo.” Anisa ta watsa mata harara kafin tasa kai ta shigo. Sai faman yatsina yank’wanannen fuskarta da bai Ida warkewa ba take. “Ba zama nazo yi ba. Ban kuma zo dan na rama abinda kika min ba dan naga kin sha jinin jikinki. Sak’o Mommy ta bayar a kawo miki.” Tai maganar tana mai aje turaren saman centre table. Ummul ta katseta “Ni ban miki komai ba Anisa. Ke shaida ce keda k’awarki ku kuka shirya abunku.” Ganin Anisar ta tsareta da ido Ya sanyata samun k’warin gwiwar ci gaba “Ni bana nemanki da fad’a. Kuma ki yarda dani har cikin zuciyata banji dad’in abinda Ya sameki ba.” “Oh please shut up! Spare me your false sympathy.” Taci gaba da takowa gaban Ummul. Tana huci take nuna fuskarta. Muryarta ya soma rawa alamun kuka “Just look at my face.. Look at what you did to me. Kalli yanda fuskata ta lalace.. This is what you want right.? Farin ciki kike ko..? Na sani tun farkon zuwanki gidan nan baki sona.. Amma ban tab’a tunanin zaki min abinda kika min ba. Leenah ita ce ta zuba miki cream din ba ni ba. Meyasa kika zab’i b’ata nawa fuskar… It was Leenah’s plan and not mine. Bansan ta shirya Miki haka ba amma ki zab’i cutar dani. Look duba kiga abinda kika min.” Ta k’arashe cikin kuka. Jikin Ummulkhairi yai sanyi. Ta soma girgiza kai “Anisa ki yarda Dani banji dad’in abinda ya samu fuskarki ba. Amma ki sani shi rayuwa abinda ka shuka fah shi ke dawo maka. Idan khairan khairan idan sharri sharri. Ya kamata ki d’auki darasi cikin abinda Ya faru.” “You are not in a position to dictate to me what I should do with my life. Idan kuma shawari ne ban nema ba. We are not even friends to begin with.” Ta k’arashe tana juya ido. Ummul ta kuma girgiza kai “Ni bance mu zama k’awaye ba. Amma ki sani bana neman abokin fad’a.” Anisa ta kafeta da ido sai kuma ta marairaice fuska ta k’arasa saman kujera ta zauna tana Shafa fuskarta. Ta d’ago tana duban Ummul da idonta masu zuban ruwa “You are right you know. Duk abinda ka shuka a duniyar nan shi yake dawo maka. At first I hate you Ummul.. Bazan b’oye Miki ba. Ina kishinki musamman ganin yanda daga zuwanki gidan nan hankalin Mommy da soyayyarta gaba d’aya ya koma kanki.” Ta mik’e Tai tsaye gaban Ummul da idonta masu zuban ruwa “I’m not a bad person Ummulkhair. I’m so sorry for everything I did to you.. I don’t want us to fight anymore.. Ko bamu zama kawaye ba I believe we can get along and live in peace..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Ta mik’a ma Ummul d’in hannu murmushi saman fuskarta “Mu mance komai mu zauna lafiya.” Sosai Ummul tasha mamaki da sabon sauyin Anisar. Amma sai ta murmusa ta mik’a mata hannu sukai musabaha. Anisa Tai saurin hugging d’inta tana fad’in fad’a tsakaninsu Ya k’are tayi alkawari. Ta dubi saman dining table yanda abinci suke nan a jere alamun tinda aka kawo ma Ummul d’in bata ko tab’a ba. Ta murmusa ta dubi Ummul “Don’t tell me you still haven’t eaten. Koda yake zaman kad’aici Babu dad’i. Come zo muje. Barin tayaki cin abincin.” Ta janyo hannun Ummul suka nufi dining table. Anisa tace da Ummul ta zauna ita zatai serving d’insu. Ta zuba abinci ta shirya table. "Nan suka zauna suna facing juna itada Ummul d’in. Ganin Ummul ta matsar da table knife gefe yasa Anisa murmusawa tace “Ya kamata ki koyi cin abinci to our level. You must keep your table manners. And that includes the use of utensils. Kar ki mance ke sirkar gidan nan ce a yanzu. Hakan na nufin, your social status has changed. You" "should learn how to mingle with upper class people. Mijinki Haidar mutum ne da ya girma cikin wayayyu sann yake hulda da wayayyun mutane, so you must adopt our lifestyle.” Anisa ta k’arashe tana gyara zamanta ta d’aura napkin saman laps d’inta. Sai faman kwarkwasa take." Ta dubi Ummul tace tai irin zaman da Tai. Murmushi Ummul Tai had’ida yin yanda Anisa tai. Anisa tace “Good. Haka wayayyun mata ke zama bisa table especially in public. Yanzu ki d’auki fork and knife muga.” Ummul ta kuma murmusawa dan harga Allah dariya Anisa ke bata. Nan tai yanda Anisar tace. Anisa ta girgiza kai "“No, fork should be in your left and knife in your right. Like this.” Ta k’arashe tana nuna mata." Murmushi Ummul ta kuma yi. Sai ta girgiza kai wann karon “ Amma addininmu harma da al’adarmu basu koyar damu cin abinci da hannun hagu ba. Shed’an shi yake cin abinci da hannun hagu.” Anisa ta kauda fuskarta gefe tana juya ido. She had no other option than to put up da wann Bagidajiyar. Sai ta juyo ta murmusa “Of course you are right. Kinyi gaskiya. Na gode da kika tunasar dani.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. A haka sukaci abinci Har Ummul Tai mata rakiya sanda zata tafi. Sai mamakin canzawar Anisar Ummul d’in take. Amma cikin ranta taji dad’i da suka shirya da Anisar dan harga Allah bata neman abokin fad’a. Anisa tana shigowa ta tadda Mommy zaune a parlor alamun tana jiran shigowarta. “Mai ya tsaidake can.? Shin kin bata turaren da na baki ki bata ko kin tsaya shashancinki ne.” Mommy ta tambaya tana duban Anisar . Murmushi Anisa tai “Na bata Mommy. Tace ta gode sosai. Taji dadin kyautar dan tin kafin na bar wajen ta shafa.” Annurin fuskar Mommy ya k’aru jin tayi amfani da turaren. Anisa taci gaba “Na tsaya na tayata cin abinci ne Mommy. Sai kuma na mata hira..” Ta k’araso ta zauna kafin taci gaba “Da alama kad’aici na damunta. Dan ko abinci bata wani iya ci. Kar kiga yanda taci abinci sosai da muke tare..” Ta kuma muskutawa “Em Mommy nace why not gobe Ummul ta shigo muci abinci gaba d’aya tare. Zata d’an rage kewa kuma zata k’ara samun daman sakewa damu tinda har yau Haidar baizo ba..” Mommy ta murmusa “Da alama ku biyun Kun fara sabo sosai. Sai ki samu ma’aikatan kitchen ku shirya komai.” "Anisa ta murmusa “Okay Mommy..” Ta mik’e tana murmushi. Har ta soma tafiya ta juyo “Em.. Mommy nace, can I invite my friend over..?” Sanin ba ko wani shirgi Hajiya Kwaise ke bari a kawo mata cikin gida ba Shiyasa ma ta tambaya." Mommy ta jinjina kai “Of course you can..” Tai maganar tana murmushi zuciyarta fari sol tinda Anisa ta sanar da ita Ummul tayi amfani da turaren da ta bata. burinta Ya kusa cika. Haidar d’inta zai dawo gareta. ** Saida Anisa tai shirin kwanciya kafin ta d’aga waya ta kira Leenah. Tana tsaye gaban mirror tana cleansing soyayyan fuskarta da auduga taci gaba “I told you Leenah. Yarinyar nan sai tayi nadaman soyan fuska da tai. Zamanta a gidan nan yazo k’arshe. Kedai kizo da wuri ki sha kallo. Kar ki damu na karba Miki katin gayyata daga wajen Hajiya Kwaise Maitama dan kinsan da k’a’ida ake shigar mata gida. Matsalar kawai I need someone who can help me to carry out my plan .” Leenah ta murmusa “Girl I’ve got your back. Just say the word kiga aiki da cikawa.” “Oh shut up Leenah! As if your tiny brain is capable of helping me out.. last time I checked stupidity dinki ne yasa fuskata ta soye.” "Leenah ta murmusa “Haba Neesa trust me we re not going to repeat the same mistake.. You need me. After all, I’m the only one you can count on.”" "Shiru Anisa tai “Fine. But wait , if you screw up my plan Leenah. I swear I’m going to kill you myself.”" Leenah ta murmusa “I’m on it girl. Kar ki damu zamu shirya komai ta yanda yarinyar zata bar gidan a gobe. I give you my word.” Jinjina kai Anisa take tana sakin murmushi lokaci guda tana duban fuskarta a mirror. A fili take furta “Tomorrow I am going to get rid of my problem. Goodbye to you. Ummul..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya had’ida duban kanta cikin mirror. ** Bayan ta Ida shirin baccinta alwalwa ta d’auro ta soma jero nafilfili tana kai kokenta ga Rabbil Izza. Kama daga kan sabon rayuwar da ta tsinci kanta ciki zuwa ahalinta da ta baro Har dai izuwa kan wann k’addararren aure da Ubangijinta Ya jarabceta dashi. Auren da batada tabbaci akan makomarsa auren da har kawo wann rana bata san kalan mijin ba bata kuma da tabbacin mijin Ya san da ita. Dan dik kyautatawa da d’imbin alherin mahaifiyarsa gareta bata tab’a jin a ranta ta samu sukuni cikin fargaban abinda ka iya zuwa yazo cikin auren. Addu’a ta dingayi Allah ya shiga al’amarinta. Idan har akwai alheri a cikin auren. Idan har zamanta alheri ne a gidan Allah Ya kawo mata komai cikin sauk’i. Haka zalika idan Babu wani alheri Allah Ya sauk’ak’a mata ya kawo hanyar da zata bar gidan cikin sauk’i. Ta jima sosai tana kai kokenta wajen Ubangijin da Babu abinda yafi k’arfin buwayarsa. A nan kan sallayarta bacci yai gaba da ita. ** Cuba.. Bacci yake yana jin Kansa na juya masa cikin baccin. Nan kuma ya soma mafarki da mahaifiyarsa. Mommy ya gani durk’ushe gabansa tana kuka hannunta rik’eda farin takarda. Tana fad’in mahaifinsa yayi canceling project d’insa. Saurin amsar takardan yai daga hannunta saidai yana ware takardan yaga sab’anin abinda Mommy tace. Domin kuwa takardan sakin mahaifiyarsa ya gani wai Daddy ya saki Mommy. Juyowa yai bayansa yana huci kaman zai shak’e Daddy yana fad’in maiyasa zai saki mahaifiyarsa. Daddy bai basa amsa ba saima nuni da yai masa da bayan wata mace tana tafe tana jan akwatinta. Jikin Haidar yai sanyi sanda Daddy ke fad’in ‘Mahaifiyarka ita ta saka nata Auren cikin had’ari dan wanzuwar AUREN WATA UKU. Ka tuhumi kanka Aliyu.!’ Daga haka ya farka daga baccin duk ya had’a zufa. Nan yaga yamma ne sosai a agogon Cuba. Around karfe shida na yamma. Ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa yana mamakin baccinsa a daidai wann lokaci. Ba bacci bane yafi basa mamaki kaman mafarkin da ya tsinta kansa da yi cikin barcin. Meyasa hankalinsa ya tashi sanda yaga Mommy na kuka a cikin barcinsa. Baya son ganin hawaye. Baya so yaga ana kuka amma ya sani hawayen Mommy bai tab’a damunsa ba. Meyasa ya tsinci kansa yana mai damuwa da hawayenta cikin barcinsa. Meyasa zuciyarsa tai zafi da yaga mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa.? Wann shine abinda yake fata yake buri tsawon rayuwarsa ahalin ta ruguje ta lalace. Meyasa hankalinsa zai tashi bayan abinda yake buri ne Ya faru cikin barcin nasa. Ya furzar da huci a hankali yana kuma shafan fuskarsa. Can k’asan zuciyarsa ji yai yana son kiran Mommy amma wani b’angare na zuciyarsa na kuma tunzurasa gameda al’amarin iyayen nasa. Why would he even care. Toh su rabu mana for all he cares. Yai gajeren tsaki kafin ya mik’e yana neman Dareen yanda ya hangeta cikin pool tana waving d’insa tana fad’in he should join her. ** Washe gari ta kama Alhamis hakan yasa Ummul ta tashi da azumi dan dama azumin litinin da alhamis basa wuceta hasalima Sun zame mata jiki. Anisa ce ta shigo Tai inviting b’angaren Mommy kaman yanda Mommyn ta buk’ata a Cewar Anisa. Ummul ta shirya tsaf kafin suka jera suka nufo b’angaren tareda Anisa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *28* *©️Sameena Aleeyou… * A parlour suka tadda Mommy. Tana ganinsu ta fad’ad’a murmushinta. Ummul ta k’araso ta zauna daga can bakin carpet ta gaida Mommy. Bayan Sun gaisa Mommy ke ce da ita ta dinga shigowa b’angaren tana cin abinci tare dasu duk sanda take son hakan sabida zaman kad’aicin babu dad’i. Murmushi kurum Ummul tai dan harga Allah sosai take jin nauyin Mommy dukda k’ok’arin janta jiki da take. Nan take mata godiyan turaren da Anisa ta kai mata injita. Mommy ta murmusa tace Babu komai. Cikin zuciyarta kaw dad’i ne ya mamayeta. Daga k’arshe burinta yana gab da cika. Haidar ya gama gudunsa duk yanda zaije amma tanada yak’inin aikin Malaminsu zai tasiri akansa. Anisa ce ta janyo hannun Ummul tace ta taso su duba ma’aikatan a kitchen. Aiko kaman wacce take kan k’aya ta mik’e tabi bayan Anisa. A kitchen d’in ma saida ta janyo Anisa suka keb’e ta d’an mata nasiha kan wulak’anta d’an adam koda na k’ark’ashin ka ne. Musamman da taga yanda duk ta birkita ma’aikatan da tsiwa. Anisa ta kauda fuska tana rausayar da ido. Cikin zuciyarta fad’i take ki gama duk wani kilibibinki bayan abinda na shirya Miki kin zama tarihi a gidan nan. Zuwan Leenah yasa Anisa barin kitchen d’in dan security personnel sun kira daga can gate sun sanar Anisa tanada bak’uwa. Hakan yasa bata bi takan Ummul ba ta fice. Ummul na tsaye gefe ta hangi madara kan wuta yana gab da zuba. Cikin sauri ta isa ta d’auki abun motsawa tana juya dan hanasa zuba. Chef d’in da bata jima da barin wajen ba ta k’araso da sauri tana bama Ummul hak’uri da fad’in urgent call ta samu daga gida Shiyasa ta tafi amsa kiran. Ummul ta murmusa had’ida girgiza mata kai “Laa babu komai kar ki damu nima nayi kewan aikin ne. Ban Saba zama haka nan bana aiki ba. Duk sai ina jin ba dad’i.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Dan ta lura cikin ma’aikatan wann wacce ta d’an manyanta mai kula da sauran ‘Yanmatan dake kitchen din ita kad’ai taji tana hausa sosai. Matar ta d’an murmusa “I’m the chief chef here. I’m the one supervising and monitoring the kitchen staff. Kar ki damu munada yawa a nan.. Zamuyi komai kan lokaci in sha Allah.” Ummul ta murmusa kad’an “Amma zan d’an iya tsayuwa a nan na tayaku da wani abun..?” Matar ta kuma murmusawa “I’m afraid you can’t. Idan Madam tazo taga mun baki aiki zai iya shafan namu aikin musamman ni.. Kar ki damu zamu kula da komai a nan.. Kije kawai.” Ba don Ummul taso ba ta jinjina kai ta nufi k’ofa matar sai sakar mata murmushi take. Tafiya take a katafaren gidan tana waige waige. Tabbas batada tabbaci idan bata b’ace hanya ba. Tana tafe tana tinanin ta ina zata bi nan ta hangi wani k’ofa tabi k’ofar. Wata ma’aikaciyar gidan mai sanye da uniform ta gani. "Budurwar ta tambayi Ummul “Ma’am, are you looking for someone.. Do you need something..?”" Ummul ta dubeta sai tace “Hanya nake nema dan Allah.” Budurwar ta murmusa “Oh that’s the way to the main house Ma’am.” Ta k’arashe tana nuna ma Ummul b’angaren dama. Ummul ta jinina kai a hankali kafin Tai mata godiya tabi hanyar da budurwar ta nuna mata. Tana tafe taga wani k’aton hoto manne a wani madaidaicin parlorn mai kaman waiting. Ta gane Mommy a hoton dukda k’uruciya da ya nuna a fuskar Mommyn. Gefe da Mommy wani mutumi ne mai Kamala da bata tantance ba amma tanada tabbacin shine mai gidan kenan. Tsakiya dasu wani yaro ne Wanda duka duka bazai gaza shekaru 10 ba. Kansa an tara masa suma irin mai laushin nan da cika. Ga kamannin iyayensa d’auke a fuskarsa. Yanda yaron ya b’ata rai cikin hoton ga fuskarsa da Ya buya cikin sumar kansa sosai abun yaso bata dariya musamman da taga kaman ita yake harara. Kai da gani kasan camera yasha harara kaman dai Wanda aka masa dole. Muryar su Anisa da ta soma jiyowa ne Ya janyo hankalinta. Ta nufi hanyar da take sinkayo muryoyin. Nan ta kuma cin karo da wani hoton a wani dogon corridor. Saidai wann hoton matashi ta gani tsaye gaban wani k’atoton zanen gine gine hannunsa rik’eda wani k’aramin abu kaman kara yana nuna ma mutanen dake zaune saman kujeru bayansa zanen dake gabanshi. Ko ba’ace ba zaka fahimci ma’aikata ne. Matashin yana sanye da suit saidai fuskarsa bai bayyana cikin hoton ba sakamakon Ya bada baya alamun yana bayani gameda hoton dake gaba gareshi. Bata san dalili ba amma kallo guda Tai ma mutumin dake cikin hoton zuciyarta ya yanke. Ta tsinci kanta da fad’uwan gaba dukda ba wai ganin fuskarsa tai ba. A haka tana nan tsaye su Anisa suka k’araso suka taddata. Anisa da Leenah suka dubi juna kafin Anisa ta k’araso murmushi saman fuskarta. Tai tsaye gefen Ummul dake duban hoton. “Aliyu Haidar Maitama. D’a d’aya tilo ga Engr Aliyu Maitama da kuma Hajiya Kwaise Maitama.” Abinda Anisa kenan tace Wanda ya kuma haifar ma Ummul fad’uwan gaba. Kenan wann shine Aliyu.. mijinta.? Sai ta kuma jin zuciyarta na bugawa da sauri. Musamman da Zuciyar nata ta ambacesa da mijinta wanda ko shakka babu da kokonta zuciyar nata ta raya mata. Anisa ta murmusa tana ci gaba da kallon hoton “Mutumin da manyan mujallu ke rubibin hasko fuskarsa yana guje masu. Da matuk’ar wahala kiga hotonsa koda cikin mutane saidai a bazata.” Ta kuma murmusawa “But If you read papers definitely zaka iya sanin fuskarsa. Dan bana tunanin wann d’anuwan nawa has any social media account.” Ta kuma murmusawa tana girgiza kai “I guess my cousin is allergic to camera. He is the weirdest person with high standards I’ve ever known.” Ta juyo ta dubi Ummul “Shall we.. Abinci is ready ke muke jira ranki dad’e.” Ummul ta murmusa kad’an “Saidai ni Ina azumi yau d’in..” Anisa da Leenah suka dubi juna. Anisa tace “Azumi ba cikin watan azumi ba.” Ummul ta kuma murmusawa “Yau d’in alhamis ne akwai falala cikin yin azumi a wann ranar.” Leenah ta kauda fuska gefe tana rausayar da ido cikeda k’osawa yayinda Anisa ta murmusa “Wow. A gaskiya kin burgeni Ummul. Zan so na koya daga wajenki.” Batace da Anisa komai ba sai murmushi da tai. Anisar ta janyo hannunta tana fad’in suje she can wait in her room idan bazata zauna a table din ba. Nan d’akin Anisa suka baro Ummul d’in yanda Anisar da Leenah suka nufo teburin cin abinci. Mommy ke tambayarsu ina Ummul d’in. Anisa ta waiga kaman wacce take nemanta “Oh mun fito tare daga d’akina.. But where has she gone.?” Tai maganar fuskarta d’aukeda alamun tambaya. Leenah tace “I think naga komawarta cikin d’akin. Maybe ta mance wani abun.. Or she’s Probably using the bathroom.” Mommy bata ce komai ba taci gaba da cin abincinta. Can wayarta yai ruri ta tashi daga table din tabi wani k’ofan tana amsa kiran. Leenah da Anisa suka dubi juna suna murmushi daidai lokacin Ummul ta fito. Su biyu ta tadda a table d’in. Anisa ta fad’ad’a murmushi sanda taga fitowarta “Har kin fito. Sorry we left you alone. Gashi na mance ban kunna miki Kayan kallo ba. You must be bored.” Ummul ta girgiza kai “A’a kar ki damu babu komai. Ina so na koma ne naga garin da hadari na bar wasu Windows a bud’e.” "Leenah ta girgiza kai “Haba Ummulkhair kan wann zaki wahalar da kanki. Umarni kawai zaki bawa ma’aikata su miki.. Wai ko Har yanzu baki gane matsayinki bane a gidan nan.? Kinga koma abinki kiyi zamanki yanzu zamu shigo nasan kunya kikeji. Bazaki iya zama ki saka surkarki gaba tana cin abinci ba dikda ita Mommy normal ne wajenta abinki da civilized woman.” Ta karkato sosai tana duban Ummul “Kinada babban sa’a Ummul. Mata da yawa suna burin ina ma ace sune a matsayinki. Wayayyun mata Wanda suka had’a komai na rayuwar duniya. If I were you, bazanyi wasa da wann damar ba.” Ta kuma murmusawa “Kar ki damu a hankali zaki koyi irin rayuwar.” Ta k’arashe tana sakar mata murmushi kafin Ta mik’e tana fad’in “I’ll ask one of the maids ta rufe windows din.” Bata jira Cewar Ummul d’in ba ta wuce b’angaren ma’aikatan cikin sauri Kai kace itace ‘yar gidan. Anisa ta dubi Ummul d’in da murmushi." Ummul Tai tsaye kaman mai tunanin wani abu. Magaganun Leenah take kuma nanatawa cikin kanta. Sai tanaji tamkar wani sak’o Leenar ke son bata a dunk’ule. Allah sarki da ace Leenah tasan ita wann auren ba da son ranta akai ba. sadaukarwa ne kawai ga ahalinta da bata fad’i abinda ta fad’i ba.. Ta d’anyi still a wajen sai kuma ta juya ta koma d’akin Anisar dan gabatar da sallar la’asar da aka soma kira. Bayan Sun gama cin abinci suna zaune suna hira nan d’akin Anisa gaba d’ayan su ukun. Da alama harta Leenah ta saki jiki da Ummul. Har kana iya jiyo shewan Leenah da Anisa alamun hira ta masu dad’i. Ita dai Ummul saidai tai murmushi idan an fad’i wani abun bakajin muryarta. Suna tsaka da hiran suka soma sinkayo muryar Mommy tana doka kira ma ma’aikatan gidan. Anisa Tai shiru tana fad’in “Kai ku saurara kuji.. Meke faruwa.? Kaman muryar Mommy nakeji cikin fad’a.” Gaba d’aya suka saurara aiko nan suka sinkayo muryar Mommy tana fad’in kaf ma’aikatan su hauro parlornta. Anisa tace maza su tashi suje suji abinda ke faruwa. Suka mik’e gaba d’ayansu suka nufo parlorn Mommy yanda suka tadda ta had’a assembly ma gaba d’aya ma’aikata tana tambayar waye ya shigar mata d’aki cikinsu. Wann ya dubi wancan wancan Ya dubi wann. Kowa yace bai shiga ba tin gyaran safe. Mommy ta d’ago wani d’an box hannunta. Cikin tsimewa taci gaba da fad’in ta tadda jewelry drawers d’inta a bud’e kuma an d’auki sark’ar dake cikin box d’in hannunta. Waye ya d’auka.? Anisa ta zaro ido waje “Mommy sata cikin gidan nan..? This is something unusual.. Abu ne da bai tab’a faruwa ba.” Mommy taci gaba da jinjina Kai “If there’s one thing I hate shine rashin gaskiya. Abu ne da akayi shi a cikin gida. And that’s why dole a fito da koma waye yayi satan. If it takes ayi searching every angle na cikin gidan nan ne za’ayi. Kayan kowa cikinku kaf sai an bincika.” Ta k’arashe tana duban ma’aikatan. Anisa ta jinjina kai “K’warai Mommy a duba ko ina cikin gidan nan. I’ll search the employees section myself.” Mommy ta dubi babba cikin ma’aikatan wacce tafi aminta da ita Tai assigning d’inta da suje su duba su caje kaf b’angaren ma’aikatan. Daga b’angaren ma’aikata Anisa tace su nufi b’angaren Ummul tinda Mommy kaf gidan tace a duba. Su Mommy da Ummul suna tsaye tareda sauran ma’aikatan a parlor wayan Mommy yai ringing. Anisa ce mai kira duk jikinta a sanyaye. Mommy tace “Ehen I’m listening to you. Kun samu sark’ar.?” Anisa ta jinjina kai a hankali kaman Mommy na kallonta “Eh mommy mun samu..” Mommy taci gaba da jinina kai “Cikin kayan waye kuka samu tsakanin maids d’in. Ki sanar da security guda d’aya a kira ‘yansanda. Wacce duk tai satan must be punished kuma zata bar gidan nan a yau.” Anisa ta kuma fad’i a sanyaye “Mommy you need to come see it yourself.. Ban san yanda zan sanar dake ba.. Amma Ya kamata ki gani da idonki.. I’m still in shock..” Mommy ta girgiza kai kad’an “Anisa.. Ban fahimceki ba.. Mai kike nufi.?” Shiru ne Ya biyo baya alamun Anisa na sanar da ita abinda ke faruwa. Ta juyo ta dubi Ummul wacce damuwar abuja ke faruwa Ya nuna a fuskarta “Kin tabbata da abinda kike fad’a Anisa.?” Jinjina kai Mommy tai a hankali kafin ta nufo k’asa. Sosai taji mamakin ganin sark’ar cikin d’akin Ummul. Toh amma Ya hakan ta kasance.? Ma’aikaciyar ta girgiza kai “Hajiya gaskiyar kenan. Nima naji mamaki sosai da abinda muka gani.” Mommy ta girgiza kai “Ummulkhair bata jima da zuwa gidan nan ba. Amma inada tabbacin bazatayi abu makamancin wann ba.” Anisa Tai Shiru kaman mai tunani “Nima dai Mommy ban zaci haka daga wajenta ba. Dukda yau ce rana ta farko da ta jima b’angarenki..” Shiru Mommy tai tana juya maganganun Anisa. Tabbas yau ne rana na farko da Ummul ta jima irin haka a b’angaren ta. Sann lokacin da suke cin abinci batazo teburin cin abinci ta zauna tareda su ba. Anisa ta kuma duban Mommy kafin tace “Mommy bazanso hakan ta kasance ba.. Yarinyar nan ba saninta mukai ba. Ammi ce kawai ta Santa da background d’inta.. I’m sorry to say kinsan talakawan nan gold diggers ne. Ammi used to tell me this.” Ta kuma duban Mommy sosai “What if Ammi batai bincike mai zurfi kan ahalin Ummul ba.. Kuma d’azu da naje zan shigo da Leenah na ganta ta fito ta hanyar parlorn ki na sama. I thought kece kika aiketa wajen or something. Kuma one of the maid ta sanar damu taga Ummul wandering around the house.” Shiru Mommy tai tana juya maganganun. Sai kuma ta girgiza kai “I still find it hard to believe Ummulkhair zata iya aikata abu makamancin wann. But koma menene we’ll find out about it. Je ki kira Ummulkhair da ita da maid din da tace miki ta ganta tana zagaya gidan.” Anisa ta jinjina kai “Yes Mommy.” Lokaci guda tasa kai ta fice tana sakin muguwan murmushi zuciyarta fal nishad’i. Ba’a jima ba Ummul da maid d’in da Tai mata kwatancen hanya harma da Leenah suka k’araso. Anisa na tafe gaba garesu. Zuciyar Ummul yaci gaba da tsinkewa ba don tsoro ba sabida tasan akan gaskiya take ba abinda zai bata tsoro saidai a duniyarta ba abinda ta tsana irin a danganta ta da sata. Sata abu ne mai ciwo ace an danganta ka dashi. Koda ace ta fito gidan da basuda arziki Allah ya masu arziki da wadatan zuci wanda shine babban arziki. tayi imani basuda abinda zata sata. Sanda Mommy ta d’ago sark’ar tana nuna mata sai taji kuka yazo mata. Mommy ta k’araso ta dafata “Bance kin d’auka ba Ummul. So nake kawai ki amsa min tambayata dan haka ne zai wanke ki. An samu sark’ar a cikin d’akinki.. Ta Ya haka ya kasance.?” Ummul ta girgiza kai “Ki yarda Dani Mommy. Ni ba b’arauniya bace. Ban kuma d’auka ba. Sann bansan Ya akai ya zo d’akina ba. Gaba d’aya ranar ina zaune cikin gida ban ma shigo b’angarena ba.” Leenah tai kaf tace “But wait kince zaki zo ki rufe Windows d’inki sabida hadari da kika gani gudun kar ruwa ya shiga miki.. Kodai lokacin ne kika fito kika kawo sark’ar kika ajiye a d’akin ki.” Ummul ta dubi Leenah cikeda mamaki dan ta ma kasa cewa komai yayinda Anisa Tai karaf tace “A’a Leenah. Ai Ummul bata zo ta rufe Windows d’in ba.. D’aya daga cikin ma’aikata ne tazo ta rufe Windows d’in.” Leenah ta tab’e baki “But samun sark’ar a nan proves otherwise.” Ummul taci gaba da girgiza kai tana hawaye take fad’in ita ba b’arauniya bace. Leenah tace “Prove it then.. So kike a d’aura ma wani sharri bayan ga abinda aka gani.” Mommy ta aika ma leenah wani kallo ganin irin kukan da Ummul keyi. Hannayen Ummul Mommy ta kamo tace “Idan kina son sark’ar Ummul zan baki ita kyauta. Kar wann yasa ki d’aga hankalinki. Ni ban kawo a raina zaki min sata ba. Duk abinda kika d’auka nawa tamkar naki ne. Ke matar Haidar ce idan har zance kin min sata kaman nace Haidar ya mun sata ne. Duk abinda kika d’auka gidan nan ba sunansa sata ba. Case closed.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana goge ma Ummul d’in hawayen dake gangaro mata. Cikin zuciyarta cewa take ke d’in makarin asirin d’ana ne ko mai zaki min zan shanye har na samu Haidar ya dawo gareni. Da mugun mamaki Anisa da Leenah suke duban juna baki sake. Wai shin wane irin makahon so Mommy ke ma yarinyar nan Wanda hankali bazai d’auka ba. Wai Hajiya Kwaise ce ta zama very soft haka. Matar da sunyi imani irin sanin da suka mata yanda ta kama b’arawon nan sai Ya d’and’ani kudarsa. Matar da sam bata yarda da wani shit ba. Ummul ta girgiza kai ba don bata d’auki maganganun Mommy da mahimmanci ba sai don bazata bari a mata shaidan sata ba. Amma ta ya zata wanke kanta. ta ina zata fara hakan.? D’agowa Tai tana dubansu gaba d’aya da idonta mai zuban ruwa. Sai ta dubi Mommy ta kuma girgiza kai “Ban d’auka ba. Kiyi hakuri Mommy ban raina k’ok’arin ki na kula dani da bani duk wani kariya ba. Amma hankalina zaifi kwanciya idan har aka tabbatar banida laifi.” Leenah da Anisa suka kuma duban juna suna mamakin ta Ya za’ai ta fidda gaskiyar. Ummul Tai tsaye tana k’are ma gidan kallo. Cikin zuciyarta kaw addua take ‘Ya Allah banida wani wayo sai abinda kayi dani. Ya Allah ina tawassili da azumin dake bakina Wanda nakeyi dan neman yardarka. Allah ka wanke baiwarka mai rauni daga wann sharri da aka k’ulla mata.’ Anisa ta katseta da fad’in “Ummul Mommy ta aminta dake inaga ya kamata ki bar zancen a haka. I think You don’t need to prove your innocence.” "Mommy ta girgiza kai “No, if she wants to prove her innocence bazan dakatar da ita ba. After all, I want to know who the real culprit is.”" Zuciyar Anisa Ya kuma tsinkewa. Leenah ta dubeta a tsorace itama. Nan ta fara wak’an tafiya gida. Mommy tace babu mai tafiya sai gaskiya ya fito. Ta dubi Ummul tace suna sauraronta. Ta bayyana gaskiyarta. Ummul ta jinjina kai a hankali kafin ta d’aga kai tana k’are ma gidan kallo. Can k’ofan shigowa sashen ta hangi security camera. Leenah ta rausayar da ido tace “Ummul bakida wani hujja please don’t waste our precious time here. I really need to leave now. Is getting late already.” Juyowa Ummul tai ta dubi Leenah tana murmushi “A’a inada hujjar da zan kare kaina.” Leenah ta girgiza kai “So.. Where is your proof then.?” Ummul ta girgiza kai “Kiyi hak’uri ban fahimci mai kike nufi ba.” Leenah tai murmushin rainin hankali tana duban Ummul a wulak’ance “Common English bakiji har kina tunanin kinada wani intelligence da zaki iya canza abinda idonmu ya gani.? Is this a joke or something.” Jinjina mata kai Ummul Tai “K’warai inada shi koda harshena bai iya furtawa ba.” Ta d’aga hannu Tai mata nuni da cctv camera. Taci gaba “Na tabbata shi zai tantance na fita daga sashen Mommy ko ban fita ba. Haka ne.?” Leena tai Shiru sai muzurai dan batai zaton wann bagidajiyar zatai tunanin cameras ba. Batamayi zaton tasan da zaman cameras din ba. Ta juyo ta dubi Anisa cikeda tsoro. Sai Anisa ta kashe mata ido alamun ta kwantar da hankalinta she had everything under control. Mommy ta jinjina kai “K’warai akwai cameras a wasu hanyoyi da zai sadaka da d’akuna cikin gidan nan. Shi zai tabbatar mana idan Ummul ta shiga d’akina ko bata shiga ba.” Anisa ta jinjina kai tace k’wari a duba footage. Saidai koda aka duba cameras na cikin k’waryar gidan kawai aka duba kuma da alama duk Sun samu fault dan haka ba’a ga waye ya shiga d’akin ba. Leenah ta rausayar da ido cikeda k’osawa tana fad’in Ummul batada sauran hujja. Ummul ta girgiza kai tace “Na cikin k’waryar cikin gida kawai aka duba mai zai hana a duba na waje. Shi zai tabbatar ya kuma tantance waye ya kawo sark’ar b’angarenta. Leenah ta dubi Anisa wacce izuwa lokacin ta gama razana dan zallan cameras na cikin gidan Tai tampering banda na haraban gidan tinda bata kawo abun zai kawo haka ba. Mommy ta jinjina ma tunanin Ummul dan koda aka duba footage na haraban gidan Ya hasko wata maid din gidan sanye da uniform dinta ta nufi bangaren Ummul da sark’ar rike hannunta saima juyasa take tana waige waige. "Leenah ta rausayar da ido “See, this doesn’t prove you innocent Ummul. It could be an alibi so that no one would suspect you. I’m sure this is pretty mandated. Bakinku d’aya kawai bata mana lokaci kike a nan.”" Mommy ta daka mata tsawa da fad’in Tai masu shiru. Sai kuma ta juyo sosai tana duban Leenar dan ta kula zak’ewarta da k’ok’arin ganin ta d’aura laifin kan Ummul yayi yawa. Mommy ta girgiza kai kad’an tana kuma duban Leenah “Waye ya baki daman saka hancinki cikin al’amarin gidan nan.?” Leenah ta sha jinin jikinta. Ta dan matsa gefe tana bama Mommy hakuri. Take Mommy tasa akai mata kiran maid din. Ba’a jima ba Maid din ta bayyana gaban Mommy wacce ta tsareta sosai da ido. Sai rawa jikinta keyi dan tsoro. Cikin murya mai tsoratarwa Mommy ke tambayarta waye ya bata umarni da ta kai sark’ar d’akin Ummul. Maid din taci gaba da sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ta d’ago tana dubansu a tsorace. Anisa ta Zare mata ido. Sai ta girgiza kai ta shiga nuna Ummul d’in tana fad’in ita ta bata umarni taje ta b’oye mata sark’ar a b’angarenta bayan ta d’auko. Cikin harshen turanci mai aikin tai maganar. "Leenah ta murmusa “My hunch was right, after all. Gashi Ummul Vicky ta bada shaida akanki. Bakinku d’aya. Shin har yanzu kinada sauran hujja.?”" Mommy ta kuma tambayar Vicky tabbata Ummul ce ta bata umarni. Vicky tace eh haka ne. Girgiza kai Ummul take tana dubanta kafin ta k’araso gabanta “Kika ce ni na baki umarni.?” Sai ta d’ago tana duban Ummul d’in dan bataji mai tace ba sabida ba hausa take ji ba. Ummul ta kula mai aikin bata jin hausa. Sai ta murmusa a hankali tana hamdala cikin zuciyarta dan da alama duk yanda mugun zaibi yaga Ya kulleta sai Allah ya bata k’ofan fita sabida batada hakki. Taci gaba da duban Maid din tana mai ci gaba da furta “Amma baki jin yaren da nakeyi. Haka zalika nima bana jin yaren da naji kinyi magana dashi. Shin ta Ya akai har na k’ulla cinikayya dake.? Ta ya akai har kika iya d’aukan umarni daga bakin wacce baki jin mai take fad’i.?” Shiru sai kallon Ummul da take cikin rashin fahimtar mai take cewa. Mommy ta jinjina kai cikeda gamsuwa da yanda Ummul ke fayyace komai dalla dalla. Mommy ta dubi Leenah tace “Yanzu kika mana proving a nan cewa Ummul bata jin turanci haka ne.?” Cikin sanyin jiki da daburcewa Leenah ke duban Mommy ganin table na k’ok’arin turning. Mommy taci gaba da jinjina kai “Idan haka ne bana tsammanin zata iya dogon magana har su shirya wani plan da Vicky wacce sam ba hausa take ji ba.” Kowa ya shiga jinjina al’amarin yayinda zuciyar Ummul Ya cika da hamdala. Anisa ta sake baki tana kallon ikon Allah yanda Bagidajiyar nan zata kamasu gidadancin da suka raina. "Leenah ta janyo Anisa gefe tana mata k’usk’us “Oh Girl, this is not happening.. What’s she doing.? My goodness! Is she a detective now.? I never imagine zatai irin wann tunanin maiyasa kika bada aikin ma wann maid d’in da batajin hausa.” Tai maganar tana satan duban Ummul. Kafin ta kuma kwantar da murya daidai kunnen Anisa “I thought you said you’ve everything under control.. looks like it’s gonna backfire.. Hajiya Kwaise bazata yafe mana ba Neesa. Oh no.. I’m scared. Mai zai faru idan tasa ‘yansandan su tafi damu.? This is all your fault Neesa. I shouldn’t have involved myself in your plans.”" Anisa ta furzar da huci Har lokacin k’usk’us suke yayinda Mommy ta tistiye Vicky tana tambayar sai ta sanar da ita waye ya bata order. Leenah ta kuma tambayar Anisa “Girl what do we do now.? Your grand plan turned out to be brainless. Are you that stupid Neesa. Didn’t it occur to you hakan zai iya faruwa.?” “Oh shut up Leenah.! Banyi tunanin haka ba. You know why.? Because your stupidity is contagious.. Ke kika shafa mun shashancinki.” Ta k’arashe daidai lokacin da idon su Mommy gaba d’aya yayo kansu dan Vicky direction d’insu take duban sanda Mommy ta titsiyeta. Mommy taci gaba idonta kan su Anisa “Tell me Vicky. If you don’t want to go to jail alone. Who’s your accomplice. Who ordered you to frame my daughter in-law.? Tell me now.!” Mommy ta k’arashe cikin tsawatarwa. Ganin haka yasa Anisa yin alama ma Vicky da yatsarta tana nuna mata Leenah cewa tace Leena ce. "Hannu na rawa Vicky ta nuna Leenah “It’s her.. She payed me to do a clean job. But believe me madam, I only accepted her offer because I desperately needed the money.. Please don’t fire me. Have mercy on me.!” Ta k’arashe cikin kuka tana duk’awa gaban Mommy." Leenah ta saki baki cikin tsananin shock jin yanda aka aza mata laifin komai tashi daya. Ta soma girgiza kai tana duban Vickey “Me.? Hey excuse me.! What crap are you talking about.? Why would I do such a thing.. What could be my motive. I have nothing against her..!” Tai maganar tana duban mutanen dake wajen cikin k’ok’arin kare kanta. Leenah ta tafi ta shiga jijjiga Vicky tana fad’in ta bud’e baki ta fad’i gaskiya cewa ba ita ta sakata ba. Vickey ta nuna credit alert da Leenah tai mata dan dama da account d’in Leenah akai payment d’in sabida account din Anisa yak’i transfer kuma ba cash a hannunta. Leena tace akwai kud’i cikin account d’inta bari ta tura ma Vicky. Nan Anisa tace Tai payment d’in 100k zata bata daga baya. Hakan yasa da Vicky ta nuna kud’in da ya shiga account d’inta sunan Leenah ya fito. Vicky taci gaba da fad’in ta tura kud’in ne zuwaga mahaifiyarta dake jinya dan sayen magani. Shiyasa ta amsa tayin da Leenah Tai mata cewa taje ta aje sark’ar a d’akin Ummul. Leenah ta saki baki ta juyo tana duban Anisa wacce Tai kaman batasan meke faruwa ba. Zata kuma magana Anisa ta dakatar da ita da fad’in “Oh shut up Leenah.! Bansan haka halinki yake ba. Bansan zaki k’ulla ma Ummul irin wann sharrin ba I shouldn’t have invited you here in the first place.” Leenah ta saki baki tana duban ikon Allah jin yanda k’awarta Anisa Tai incriminating dinta ta kuma aza mata laifin komai tashi guda. Leena baki na rawa take furta “But.. But wait..” "“Oh Leenah kowa yaga evidence da sunanki. Ke kika biyata Tai aikin without my knowledge. Amma nasan dalilin da yasa kikai haka k’awata. You did it out of your concern for me. A tunanin ki zaki rama min abinda Ummul ta mun a SPA ne Shiyasa kikai haka, right.?”" Leenah ta kasa cewa komai sai duban k’awarta Anisa da take da tsananin mamaki. Anisa ta juyo ta dubi Mommy “Mommy dan Allah kiyi hak’uri. I know Leenah.. I know my friend is not a bad person. Misunderstanding aka samu.” Tai briefing Mommy kan abinda Ya samu fuskarta duk akan Leenah ta d’aura laifin Har abinda ya faru a spa. Sam bata nuna ma Mommy tasan da plan d’in Leenah na k’ona fuskar Ummul ba Wanda ya juya nata fuskar. Anisa taci gaba “Mommy Leenah thought she was doing it for me. Ta zaci hakan da Tai tamkar ta rama mun ne. Kinsan kishi irin na k’awaye. Kishi take da Ummul zata k’wace mata k’awancenmu. Musamman da yau da tazo taga yanda nake da Ummul d’in.” Ta kuma duban Ummul “Ummulkhair please forgive my friend.” Muryar Mommy ta sinkayo tana fad’in “Dama nasan za’a rina. A yanda taketa k’ok’arin d’aura laifin ma Ummul. She’s the real perpetrator. I dont care if she’s your Friend. Criminals are not welcome in my house. And this won’t go unpunished. She must pay for what she did to my daughter.” Ta dubi d’aya daga cikin ma’aikatan gidan tace ta kira mata ‘yansanda. Matar ta jinin kai “Right away Madam.” Vicky sai kuka take tana fad’in a mata rai. Yayinda Leenah mamaki ya hanata katab’us. Sai jan k’afafun Ummul Vicky take tana fad’in ta yafe mata. Tsawa Mommy ta daka ma Vicky da fad’in “Shut your mouth and get up from there! You are leaving this house right this instant. I don’t have room for criminals like you in my house.” Ta kuma jaddada mata sai ta fara mik’asu ma hukuma daga ita Har Leenah. Duk sai jikin Ummul yai sanyi. Yarinyar ta bata tausayi. Da alama cikin ma’aikatan tafi kowa k’arancin shekaru. Sann taji cewa da tai kud’in da ta amsa wajen Leenah ta aika wa mahaifiyarta dake jinya ne. Sai ta tuna nata mahaifin dake kwance yana jinya. Ta tuna mak’asudin zuwanta gidan itama yarda da auren da Tai sabida ta ceci mahaifinta dake jinya ne itama. Sann sadakinta shine kud’in jinyar mahaifinta. Tabbas kowa zai komai dan ya ceci iyayensa. Sai taji kaman batada wani maraba da Vicky. Cikin sauri Ummul ta juyo ta dubi Mommy kaman zata fashe da kuka take fad’in Mommy tai hakuri ita ta yafe masu kar a kirawo ‘yansanda. Da kyar Mommy ta hak’ura da kiran ‘yansandan sabida rok’on da Ummul Tai mata. Amma kam ba don Ummul d’in ba da daga Leenah Har Vicky sun kwana ofishin ‘yansanda. Mommy ta bada umarni ma babba cikin ma’aikatan gidan cewa a raka Vicky waje da kayanta ta koreta. Ita kuma Leenah ko me kamanta securities suka kuma bari ta shigo gidan a bakin aikinsu. Harda Anisa akaima Leenah rakiya waje. Sai kallon mamakin cin amanar da Anisa Tai mata take ma Anisar. Anisa ta dubeta bayan Sun rage saura su biyu “Let me call you a cab for you..” D’aga mata hannu Leenah tai alamun dakatarwa “Ki barshi bana buk’ata. You know what Neesa ban tab’a zaton zaki ci amanata irin haka ba. Ta ya zaki d’aura min laifin da banyi ba. You planned the whole thing. Sann kin d’aura min laifi kaman wata sakarai. You know what? I think you’re right. I’m stupid and that’s why I remain loyal to you.” Tana gama fad’in haka tasa kai ta shige kaman zata tashi sama ba tareda ta kuma bi takan Anisa ba. Juya ido Anisa Tai had’ida furzar da huci kafin ta koma cikin gida. "Nan ta tadda Mommy ta had’a kaf ma’aikatan gidan tana kafa masu warning. Ta dafa kafad’an Ummul tace “She’s my Son’s wife. I expect each and everyone of you to treat her with absolute respect, Including you Anisa.” Tai maganar tana duban Anisa da shigowarta kenan kafin taci gaba “The same respect da zaku bama D’ana Haidar. Bana so makamancin abinda ya faru yau Ya kuma faruwa. Do I make myself clear.?”" Gaba d’aya suka jinjina mata kai hadida amsawa cikeda risinawa ** Bayan Ummul ta koma sashenta tana zaune saman darduma Ida sallarta kenan Anisa ta shigo da murmushi saman fuskarta. Ummul bata nuna mata komai ba dan itama wann sassanyar murmushin wanda a baya Anisa ta d’aukesa shashanci da gidadanci a halin yanzu shakkar wann murmushin take shine dai saman fuskar Ummul. Ta zauna tana tambayarta an sha ruwa lafiya. Ummul ta amsa mata da sakin fuska. Nan Anisa ta soma bata hakurin abinda Leenah Tai tana mai kuma tabbatar mata Lallai Babu hannunta cikin abinda Leenah da Vicky suka k’ulla mata. Murmushi Ummul ta kuma yi “Babu komai Anisa kar ki damu. Suma ban k’ullacesu ba. Daga k’arshe Allah Ya bayyana gaskiya. Ba wayona bane ba kuma dabarata bace. Allah ne Ya dube ni da rahamarsa Ya wanke ni daga k’agen da aka so min. Na kuma gode masa da Ya wanke sunana daga k’agen sata. Ina kuma fata ya shiryi duk masu tunani irin nasu damu baki d’aya.” Anisa ta jinina kai “You are a good person Ummul. You have a clean heart that’s willing to forgive and forget. Yanda kika wanke kanki cikin hikima ya burgeni. I wish zan zama kaman ke.” Ummul ta murmusa “Duk wanda ya dogara ga Allah Allah ya isar masa. Kuma duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai samar masa mafita. Ba yin kaina bane Allah yakan wanke bayinsa da akai masu k’age ba tareda sun aikata laifin ba. Kaman yanda Ya wanke Ummuna Aisha (RA) daga k’agen da azzalumai suka mata. Kaman yanda Ya wanke Annabi Yusuf (AS) daga k’agen da aka masa. Kaman yanda Ya wanke bayinsa muminai da dama daga k’agen da aka masu. Kaman haka yanke wanke bayinsa da basuda hakki. Na gode masa da ya wanke ni daga k’agen da aka min ba tareda hakki ba. Amma ni Ummulkhair banida wani wayo. Saidai Inaso mutane irinki da Leenah su fahimci English is just a language and not a means to measure one’s intelligence or education. Snn duk wani wayewar da yai karo da koyarwar addininmu da d’abi’u da kyawawan al’adunmu ba sunansa wayewa ba.” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Baki sake Anisa ke kallonta “So you can speak English.?” Ummul ta murmusa “Ba sosai ba abinki da Wanda taje makaranta na gwabnati.” A hankali Anisa ke jinjina kai “Na yarda da duk abubuwan da kika ce. A yau kin kuma tabbatar min da haka. “ Ta kamo hannayen Ummul “Mommy tayi zaton ni zan koya miki abubuwa musamman zamantakewan rayuwar civilized world. But it turned out ni ce wacce ke koyo wajenki. Yau na raina duk wani exposure na Ummul.” Ummul ta girgiza kai “A kullum ko wani shafi na rayuwar mu darasi yakan bude mana dan mu koya. Kullum cikin koyo muke a duniyar nan. Kaman yanda muke had’uwa da mutane iri daban daban.” Ta d’an murmusa “Nima ina koyo daga gareki Anisa.” Shiru Anisa Tai sai kuma ta saki murmushi da yafi kama da yak’e. Tin daga wann rana Ummul ta samu sanyin abubuwan da Anisa ke mata. Sai ta koma kaman tana shakkan Ummul d’in koda bata nuna a fili ba. A kwanakin da alama Anisa ta maida makaman yak’inta. ** Kano… Batai k’asa a gwiwa ba dukda fargabn abinda ka iya zuwa yazo ta nufi gidan Hajiya Asshe. Juyin duniya Umma tayi amma masu gadi sun hanata shiga sabida dokan da Asshen ta basu tin kwanakin baya. Asshe na kitchen tana had’a ma maigidanta abinci kasancewar ranar yake dawowa daga tafiya kuma gidanta yake. Mai gadi yai Sallama ya sanar da zuwan Umma wacce babu yanda basuyi ba amma tak’i barin bakin gate din tace sai ta gana da Hajiyar. Zuciyar Asshe ya tsinke yanzu idan matar nan ta tada mata hargitsi a k’ofan gida har mijinta ya iso ya tadda wann al’amari mai zata ce masa. Oh! Ita kam dai ta d’ebo ruwan dafa kanta. Wann wasu irin ahali ta kwaso masu ne wai ita Asshe. Bata gama da fitinan Dije ba ga Suwaiba da tai tunanin ta ajeta yanda ya kamaceta yanzu ta dawo. Toh uban mai ta dawo zata mata.? Fuuu ta nufo gate tana huci dan wllhi bazata bari d’aya daga cikin watsatsun matan nan su mata sanadin aurenta da take lallab’awa ba. Tana fitowa ta shiga janyo Umma tana fad’in yau hukuma ce zasu mata iyaka da ita muddin bata bar mata k’ofan gida ba. Umma bata tafi ba bata fasa rok’on Asshe tana fad’in ta dubi girman Allah ta saurareta. Hilal daga sashensa yake jiyo haniya yak’i k’arewa daga gate. Babu shiri ya bar abinda yake ya nufo gate d’in. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *29* *©️Sameena Aleeyou… * Asshe taci gaba da janyo Umma tana fad’in kodai ta bar mata k’ofar gida ta mik’a mata ma ‘yansandan dan ta gaji da fitinan fitinannun mata Irinsu. Wanda tin had’uwar ta dasu Masifan yau daban na gobe daban. Umma taci gaba da girgiza kai “Idan kina ma Allah ki tsaya ki saurareni Hajiya Asshe.” “Na saurareki na saurari mi inyi.? ‘Yarki ce nace Miki akwai wa’adin da na d’ibar Wanda zan dawo da ita gareki. Amma a halin yanzu ni Asshe banida wani sauran alak’a dake da sauran zuri’arku. Na gode ma Allah da yasa auren Ummul ba mai d’orewa bane. Mi za’ayi da zuri’arku dangin masifa dangin mayu dangin matsafa.. Zo ki wuce.. Idan kika kara minti d’aya k’ofar gidan nan ki kwana ofishin ‘yansandan” Ta k’arashe tana hankad’a Umma da iyaka k’arfinta Wanda saida ta kaita k’asa. Daidai nan Hilal Ya fito ya taddasu. Ya isa da sauri yana ma Umma sannu had’ida tambayar bataji ciwo ba. Umma ta d’ago tana girgiza masa kai alamun a’a. Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyarsa “Ammi what’s the meaning of this.? Kan wani dalili zaki aikata abu makamancin haka..? Mai yayi zafi..? Wai meke faruwa ne ma.?”Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa. Asshe na huci take furta “Babu ruwanka Hilal. Ba abinda ya had’aka da Matar nan zo ka shige gida.” Hilal ya girgiza kai “Ammi matar nan sirkar Haidar ce.. ‘Yarta Haidar ke aure.. We are practically family now.” Bai kai aya ba Asshe ta k’araso a guje ta toshe bakinsa “Allah tsari gatari da saran shuka. Allah mana tsari da had’a iri da wann zuri’a.. Shige gida kar na sake jin bakinka.” Ta k’arshe tana nuna masa k’ofa. Girgiza kai Hilal Ya kumayi “Ammi I’m sorry. Bazan iya barin Umma a nan ba har sai na san abinda ke faruwa.” Baki sake Asshe ke dubansa “Umma.?” Ta nanata a fili. “Umma ka kirata.? Toh sunanta Suwaiba. Kanwar uwarka ko na ubansa da zaka kirata da Umma.?. Ka sake kiran mahaukaciyar nan Umma sai naci maka. Zo ka shige kafin Abbanka Ya k’araso.” Ta k’arashe tana janyo Hilal yana tirjewa haka Har ta shigar dashi cikin gidan ta janyo k’ofa tana fad’in masu gadi kar su bari Suwaiba ta zo koda kusan gate din ne. Mamaki Ya cika Hilal. Shi Ya kasa gane wann irin al’amari ne wann da kuma abindake tsakanin mahaifiyarsa da da Umma. After some hrs da faruwan hakan. Tsaye yai bayan mahaifiyar tasa sanda take lek’e daga window ko zata hango Umma. Cikin zuciyarta tana addu’an Allah yasa mayyar ta tafi dan bata fata mijinta ya dawo ya tadda Suwaiba kofan gidan balle asirinta ya tonu. "Ya girgiza kai kad’an yana kuma takowa kusan mahaifiyarsa. Aiko a firgice ta juyo tamkar maras gaskiya. Ta dafe k’irjinta tana fad’in “Haba Hilal, halin Anisa na lab’e ka koya kaima. K’iris zuciyata bata buga ba.” Ta k’arashe har lokacin hannunta dafe da k’irji. Sai kuma ta canza maganan da fad’in “Lek’e nake naga ko Abban naka Ya iso.. Gashi dai da alama har yanzu bai iso ba.. Lallai da alama zai dare.” Ta kuma duban Hilal tana tsimewa “Waima mai ya shigo da Kai nan ne. Mai kake nema.?”" “Dama na shigo ne na fad’a Miki zan d’an kwanta kafin la’asar tinda naga har yanzu Abban bai iso ba.” Ta jinjina Kai tana dubansa “Idan ya iso zan tada Kai.” Ta fad’i tana nufan k’ofa yayinda Hilal ya take mata baya. * Fitowan Hilal sallar la’asar bayan an Ida sallah a masallaci a hanyar sa ta dawowa gida ya hangi Umma tana sallah jikin wani gini dake manne da karantar gidansu. Kasancewar akwai interlocks wajen. Mamaki ya cika Hilal. Ikon Allah yanzu dama ashe matar nan bata tafi ba. Lallai ba k’aramin Abu ya zaunar da ita ba. Ya k’araso gefenta daga can ya tsuguna kan k’afafunsa har ta Ida addu’arta. Hilal ya tayata shafawa. “Umma.” Ya ambaci sunanta daga nan yanda yake tsugune kaman dai yanda yaji Khulsum na kiranta. Umma ta d’ago ta dubesa sai ta sakar masa murmushi “Hilal d’an albarka.” Ta fad’i tana dubansa dan bazata tab’a mance alkhairan yaron ba koda kuwa ita mahaifiyarsa suna buga dabi. Kaman yanda nata yaran basuyi halinta ba haka zalika Hilal baiyi halin mahaifiyarsa ba a cewarta. Hilal ya gaisheta kafin ya k’arada “Umma mai kikeyi a nan.? Mai ya zaunar dake nan.?” Ya dan numfasa kiyi hak’uri da tambayar da zan Miki “Shin akwai wani matsala ne tsakaninki da mahaifiyata.? Meke faruwa tsakanin ku biyun.?” Umma ta girgiza Kai kad’an “Babu komai Hilal. Amma Kai hakuri bazan bar k’ofar gidan nan ba har sai mahaifiyarka ta saurareni.” Hilal ya zuba ma sarautar Allah ido yana tuno yanda sukai da Amminsa. Ya d’an kuma girgiza Kai “Amma.. Kiyi hak’uri da tambayarta da zan Miki.. Wani abu ne kike nema wajen mahaifiyata.? Ki sanar dani dan Allah idan wani Abu ne da zan iya taimakawa.” "Umma ta kuma murmusawa “A’a Hilal. K’arshen abinda zanyi shine na saka ka cikin matsalolinmu. Kai d’in kanada zuciya mai kyau. Ina rok’on Allah yasa D’anuwanka dake auren Ummul d’ina ya zama mai kyaun hali da d’abi’u irin naka..” Ta k’arashe cikin rawar murya irin na mai kuka hawaye na gangaro mata dan a koda yaushe cikin tunanin Ummul d’inta take da halinda zata iya kasancewa ciki. A gaggauce tai k’ok’arin goge fuskarta kafin ta kuma duban Hilal tace “Mahaifiyarka nake son magana da, sabida wajenta nazo. Domin dani da mahaifiyarka munada alak’a mai kyau.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta." Mamaki ya kuma cika Hilal. Kansa ya kuma k’ullewa. Tabbas wad’ann mata wato Amminsa da Umma al’amarinsu abin dubawa ne sann yanada rikitarwa. A b’angare guda mahaifiyarsa tana ikirarin datse alak’a da Umma da ahalinta. A b’angaren Umma tana fad’in itada mahaifiyarsa sunada alak’a mai kyau. Shin na waye zai d’auka cikin su biyun.? Juyin duniya Hilal yayi Umma ta hakura ta koma gida amma fir fir tak’i ta kafe lallai lallai sai Asshe ta saurareta. Ganin yamma nayi yasa Hilal d’aukan mota ya fice daga gidan. Dan yasan watak’ila maganarta kawai Umma zata saurara ta amince ta bar k’ofar gidansu. A bakin ward din ya hangeta tana k’ok’arin shiga. Sauri sauri ya k’arasa ya cimmata. Kaman Wanda aka jefo shi haka Khulsum taga Hilal gabanta. Da mamaki take dubansa. “It’s a good thing that I found you here. You need to come with me.” Abinda kawai Hilal yace kenan. Khulsum ta girgiza Kai cikeda mamaki “Malam lafiya.?” Yai gajeren tsaki “Wai ke ko yaushe haka kike ne. Abun fad’a baya Miki kad’an ne.?” Ya kuma girgiza Kai “I need you to come with me right away. And please you alone. You don’t need to inform that aunt of yours… She might stop you.” Dan bai mance ba kwanakin can da suka shige ita ce ta hana Khulsum bin Umma Akan idonsa. Daga haka sa Kai yai ya soma tafiya yana fad’in tai sauri ba lokaci. "Takaici ya cika Khulsum, mai wann D’an rainin hankalin ya d’auketa da zaice tazo ta bisa. Ina ma zata bisa.? Mai ya maidata.?" Ganin ya soma tafiya ya nufi mota yasata bin bayansa da sauri tana fad’in “Kai Malam.. D’an dakata.? Kana tunanin kai waye.? Mai ka d’auke ni.. Mai ka maidani da zaka tako har yanda nake kace nazo na bika kuma kar na sanar da Innata.. Ce maka akai..” "Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren fahimtar da tai masa “Hey cut it out will you.!” Ya katseta da fad’in haka kafin yaci gaba “Seriously, is that what you think of me.?” Har lokacin da mamaki yake dubanta kafin yaci gaba “If that’s what I wanted I’d have gone straight to a hotel or club, and not a hospital.” Ya dan girgiza Kai “Look, ni ba irin wad’ann mutanen bane. And I’m not kidnapping you.. Idan na zo nan kawai nazo ne sabida mahaifiyarki dake zaune k’ofar gidanmu through out the day. Idan Ammi na ta fito ta taddata wajen it would be a disaster. Idan akwai girman mahaifiyarki da kike gani kike ji a cikin Zuciyar ki koda kad’an ne zaki taho tare Dani dan na tabbata ke zata iya sauraronki.” Ya k’arashe yana bud’e motar." Jikin Khulsum yai sanyi ta dubesa da mamaki “Umma ce take k’ofar gidanku.?” Hilal ya zuba mata ido yana dubanta. Baice komai ba sai tada motar da yai “Zakije ne ko nai tafiyata.?” Ta hareresa sai kuma tai still a wajen kaman mai tunani. Shin ta sanar da Inna Dije ne.? Toh amma idan ta sanar da Innah Dije wani wutan zata kunna tinda tasan Ummanta da Inna Dije basa jituwa. Sann Inna Dije zata iya hanata zuwa. Tana tsaka da tunanin taji sautin horn ya cika mata kunne alamun Hilal na jiran decision dinta. Harara ta b’alla masa kafin ta bud’e marfin motar ta shige. Ya soma driving babu mai ce da kowa komai cikin su biyun har suka iso k’ofar gidansu Hilal. Can Khulsum ta hangi Umma rakub’e jikin gini tana lek’en gate din gidansu Hilal kaman wata mabaraciya. Sosai abin ya mata ciwo ganin mahaifiyarta a haka. Hilal na Ida parking ta fito ta nufi Umma. “Umma.!” Khulsum tace daga nan yanda take tsaye kusan Umma. Umma ta d’ago tana dubanta. Khulsum tai saurin k’arasowa ta duk’a gaban Umma “Umma Mai kike a nan. Dan Allah mai kike haka a nan.? Umma wann fah zubda mutunci ne. Dan Allah ki tashi ki bar k’ofar gidan nan. Duba fah kiga mutane masu shigewa suna kallonki.. Umma dan Allah ki tashi haka nan.” Hawaye Umma ta soma tana girgiza Kai “A’a Khulsum bani tafiya sai Hajiya Asshe ta sauraren.” Khulsum ta juya ta dubi Hilal dake can jikin motarsa yana tsaye. Shid’in ma su yake duba. Ko ba’a ce ba damuwan halinda Umma ke ciki ne saman fuskarsa dukda baya iya sauraron mai uwa da ‘yar ke cewa. Khulsum ta maidoda dubanta ga mahaifiyarta “Umma matar nan tareda ita ina nufin keda ita kuka k’ulla auren ‘Yaruwata. Bansan dalilinta na juya Miki baya ba. Bansan meye ku biyun kuka bisne ba. Bansan meye a tsakaninku ba. Amma ke mahaifiyata ce kuma bazan so ki walak’anta ba. Dan Allah Umma ko mai kike nema wajen matar nan kiyi hak’uri ki bar k’ofar gidan nan.” Umma ta kuma girgiza Kai tana hawaye “Khulsum idan na tafi mai zanje nace da Tani. Na mata alk’awarin zan nemo kud’ad’en belinta. A nan ne kawai nake da yak’inin zan samu kud’in fiddo Tani Khulsum.” Baki sake Khulsum ke dubanta. Da mamaki tace “Umma wai dama kan kud’ad’en belin Mama kike nan.?” Umma ta jinjina mata Kai alamun eh. Shiru Khulsum tai na d’an lokaci kafin ta dubi mahaifiyar tata tace “Umma kece zakiyi belin Mama. Wai Mama Tani dai da ta saida shagon Abba.?” Umma ta kuma jinjina mata Kai “Dukkanmu masu kuskure ne Khulsum. Tani ta salwantar da dukiyar Malam ni kuma na salwantar da rayuwar ‘yarsa. Cikin mu biyun idan akwai Wanda tafi girman laifi toh ni ce Khulsum. Ni yafi cancanta na tafi gidan kasu ba Tani ba. Idan har zan zuba ido ni ina shak’an iskan ‘yanci yayinda Tani ke gark’ame kurkuku bana tsammanin nayi ma kaina adalci. Sann bana jin ‘yancin iskan da nake shak’a a mak’oshi na. Tani ta tuba Khulsum. Dukanmu mun gane kurakurenmu. A halin yanzu bamuda wani buri da ya wuce mu koma ga mijinmu mu kula dashi mu masa jinya mu samu aljannarmu.” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Jikin Khulsum yai sanyi. Tasan mahaifiyarta tanada zuciya mai kyau Wanda da yawan mutane suna amfani da wann damar su shashashantar da ita. Kaman dai yanda takeda kokonto Akan tuban Mama Tani. Dan tasan kad’anda aikin Mama ne ta shashantar da mahaifiyarta ta samu ta fito daga prison. Muryar Umma ta kuma sinkayo sanda ta tallafo fuskar Khulsum d’in cikin zuban hawaye take fad’in “Nayi kewarku Khulsum daga ke har ‘yaruwarki. Ina zaman kad’aici a gidan.. Babu ke.. Babu Ummulkhair.. Babu mahaifinku.. Tani ma bata nan.” Tai shiru tana tinanin daga ita sai su Azeema Wanda suka maidata wofi cikin gidan barikinsu kawai suke bugawa. Su fita sanda suka so su dawo sanda suka so. Idan tai masu abincin da bai musu ba su mata tatas. Har wankin kaya Badia ke sakata. A cewarsu idan batai ba zata fice ta bar masu gidan uba tinda gidan na ubansu ne. Ganin tayi shiru ta tsunduma tunani yasa Khulsum kamo hannayenta “Umma.” Ta kirawo sunan Umman a hankali. Umma ta d’ago tana duban Khulsum. “Zaman kad’aici yasa kike so ki fiddo Mama Tani.?” Shiru Umma bata ce komai ba sai hawaye dake kuma gangaro mata. Khulsum ta janyo mahaifiyarta ta rungume sai dukansu biyun suka fashe da kuka. Cikin muryar kuka Khulsum ke fad’in “Umma kiyi hak’uri ki koma ki zauna. Nayi ma Abba alk’awari bazan sake barin kusansa ba bayan abinda ya faru.” Cikin rawar murya taci gaba da fad’in “Umma ba zama da Inna Dije na zab’a ba. A’a zama da Abba na na zab’a. Inna Dije bazata kuma barinki kije kusan mahaifina ba Umma. Zanfi kowa so naga ahalinmu ya kuma cika amma a halin yanzu Abu ne mai matuk’ar wuya Umma. Ki koma kici gaba da addua ma Abba har Allah ya bashi lafiya iyakacin soyayyar da zaki nuna masa kenan a halin yanzu. Da sannu Allah zai duba Zuciyar Wanda yai tuba na gaskiya ya yaye masa matsalarsa kinji Umma na.” Ta k’arashe cikin rawar murya. Umma ta shiga jinjina mata Kai a hankali har lokacin tana hawaye. Cikin zuciyarta kaw cewa take ita kanta bazata so ta bar Malam k’ark’ashin kulawar Dije kawai ba. Gwara ace Khulsum d’in na tare dasu. Zatai hak’uri kuma zataci gaba da addua kaman yanda ‘yar nata ta shawarceta. Hannunta Khulsum ta kamo suka nufo Motan Hilal. Hilal na ganin su ya isa ya bud’e back seat Khulsum suka shige tareda Umma hannayensu rik’e cikin na juna suna Jin d’umin juna da suka jima basu samu hakan ba. Ta mirror Hilal yake dubansu yanda suka shige jikin juna. Kan Khulsum na kwance gefen kafad’an mahaifiyarta yayinda Umma ta rik’e hannun Khulsum d’in k’am cikin nata tamkar kar wani Abu ya rabasu. Murmushi ne yaji out of nowhere na zuwa fuskarsa. Shi a duniyar sa duk yanda yaga shak’uwa da soyayya mai tsafta tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ba kowa yake hasashowa ba face D’an Uwansa Haidar. A kullum addu’arsa kenan yaga irin wann bond d’in tsakanin Haidar da iyayensa. Har gida Hilal ya kawo Umma. Khulsum ta fito taima Umma rakiya zuwa cikin gida ta kuma tausarta had’ida kwantar mata da hankali amma fah dukda haka bata ji cikin zuciyarta zata iya baro Abba ta dawo ta zauna da Umma musamman idan ta tuna abinda matan Abban nata suka masa. Tana fitowa ga mamakinta ta tadda Hilal na nan na jiranta. Daga can yanda take tsaye ya zuba mata “Rankidad’e jirana ake gida muje mana.” Ta had’e fuska sosai “Toh ce maka nai ka jirani. Kai tafiyarka mana.” Tace tana canza hanya. Furzar da huci yai kad’an ga wayarsa da ta kasa shiru sakamakon kira da Mahaifiyarsa ke jero masa. Yasan bazai wuce Abbansa ne ya iso ba. Baisan mai zaice mata ba dan shi dai bai iya k’arya ba amma muddin ya sanar da ita Umma ya kawo gida ya taro match ne tsakaninsa da Ammi. "Ya k’arasa da mota gaban Khulsum yai rolling glass “Zaki shiga ne ko sai na fito na shigar dake da k’arfi.? Be thankful, albarkacin Umma kikace idan na maidake.alk’awari na daukar mata zan maidaki yanda na d’aukoki.” Yace a mugun tsare." Khulsum ta dubesa dan yanzu gadararsa da k’arfin halinsa ya daina bata mamaki. Bata son dogon hira dashi dan kaf zuri’arsu haushi suke bata. Sann ga magarib ya k’arato hasalima batasan yanda za’ai ta koma ba tinda ba kud’in abun hawa wajenta. Ta kauda fuska gefe cikeda takaici zata bude backseat ya saka motar a lock. Fitowa yai daga mazauninsa yana fadin “You must be kidding. D’azunma albarkacin Umma kikaci na barki kika zauna baya.” Ya bud’e mata front seat “Shige muje.” Ta hararesa kafin ta shige. Tana shiga ya sakar mata murmushi had’Ida kashe mata ido kafin ya zaga ya shige. Takaici ya kuma cika Khulsum. Suna tafe babu mai cewa komai. Khulsum ta saci kallonsa. Yanzu wai godiya ya kamata ta masa ko hakurin kuskuren fahimtar da tai masa zata basa.? Kai ina ita dai bazata basa hakuri ba dan bataga laifin da tai masa ba. Ta saci kallonsa suka had’a ido. Sai ta wayance dan bata so ya fahimci tana dubansa. tai kaman bata kalli b’angaren da yake ba. Saida tai gyaran murya da kyar kafin tace “Idan kana jira na baka hak’uri ne kan abinda ya faru ni dai bazan baka ba. Abinda Kai kuma shima Kai ka saka kanka shima bazan maka godiya ba.” Ta k’arashe tana kauda fuska. Hilal ya murmusa “Guilty conscience.? Kar ki damu na yafe miki.” Yace idonsa naga kwalta. Bata amsa shi ba sai kuma tace “Toh mai za’a tsammata daga wanda yake sallah babu alwala.?” Ya kuma murmusawa “Allah yasa dai ba kece mai karb’an tuba ba balle ki k’i karb’an nawa tuban.” Ta kuma hararsa “Ka fad’a ma wann D’anuwan naka mai sallah babu alwala ‘Yaruwata musulma ce bazata zauna dashi ba. Ni Khulsum sai na datse wann auren.” Hilal ya jinjina Kai “Why not ask your sister to tell him. After all su biyun sunfi kusa a halin yanzu.” "Ya d’an dubeta a kaikaice kafin ya k’ara “And remember they say, Wanda ya shiga tsakanin mata da miji shi zaiji kunya.”" Ta hareresa musamman da taga murmushin dake bisa fuskarsa. Yana ida parking tasa hannu ta bude marfin motar a fizge ta fice. Ko kallon yanda yake bataiba balle tai masa sallama balle ya samu arzikin godiya. Bayanta yabi da kallo yana murmushi. Cikin zuciyarsa yake jin yanzu yanada k’wakk’waran dalilin da zaisa ya k’ara delaying lokacin komawarsa makaranta koda hutunsa ya k’are. Bazai tafi ba har sai ya tabbata baida wani pending matters. Saida ta b’ace ma ganinsa kafin yaja motarsa ya bar wajen. ** Cuba… Waya manne b’angaren kunnensa na dama. Dareen na hankalce dashi tinda ya soma wayar. Daga d’aya b’angaren Hisham yaci gaba “You know I still can’t get over her. I don’t know why.. But I find it difficult to forget about her. Dukda cewa mun hadu ne na d’an wani lokaci. Nayi tunanin zan cireta a zuciyata cikin sauk’i kaman yanda na cire sauran. But then I realise she’s different. So different.” Ya d’anyi fasali “Haidar na kasa hana zuciyata tunanin matar wani. I dream about her every night. And worse part d’in shine zuciyata tak’i ta karbi k’addaran. Haidar ji nake zata dawo gareni.. Astagfirullah.” Ya k’arashe jikinsa duk a mace. Sosai Haidar yaji tausayin abokin nasa. Shi ire iren abun nan ba layinsa bane. Hasalima bai tab’a soyayya ba. Dareen ma bazaice ga yanda akai har ya fara sonta ya aureta ba. So baisan wani shawari zai ba ma abokin nasa ba. Ya d’an numfasa kafin yace “Just.. Just try to distract yourself.. Engage in activities that require your full attention… Like work.. Zaka gani in no time zaka mance da ita. And you’ll find someone better than her.” Hisham ya d’an furzar da huci “What if my mind gets stuck here Haidar.? What if I couldn’t move on.? What if banida wani future dangane da abinda ya shafi Aure.? What if this is my destiny.?” Haidar yai shiru cikin sanyin jiki ba tareda ya iya cewa komai ba. "Hisham yai murmushi mai ciwo “Sorry I shouldn’t be telling you all this. Kayi tafiya ne dan ka rage damuwar dake kanka bai kamata na k’ara maka da nawa ba. Anyways, I guess this is life for us. Ba ko yaushe muke samun abunda muke so ba.” Ya d’an murmusa kafin yace “Let’s talk business maybe this will keep me busy.” Yai maganar da gajeren murmushi kafin yaci gaba “Ya kamata ka dawo haka work is getting hampered because you are not here. Komai so yake ya tsaya. And kasan lokaci baya jiranmu.”" Ya d’anyi gajeren tsaki “I’m still on my vocation. Zanje Pennsylvania daga nan.” Daga d’aya b’angaren Hisham Ya girgiza kai “Wai kana nufin hutun naka bai k’are ba.. Ko wani business d’in kakeda a can US d’in.?” Gajeren tsaki ya kuma yi “Ka kira ne dan ka bani haushi.? What business kuma.?” Hisham Ya murmusa kad’an “Alright fine. Yanzu dai Ya kamata ka dawo. Kaga we need to meet up. Ina nufin our team members. We’ve got a lot of things to discuss.” Tsakin ya kuma yi dan ya kula da gangan Hisham ke son tunzirashi “Maiyasa zan dawo. Mai zan dawo na maka when you can schedule a zoom meeting. I just hope ba shirme da shiririta bane cikin meeting d’in ba. Because you know my time is precious.” "Hisham ya murmusa kad’an “Look Haidar, you and I both know dawowarka nada mahimmanci. Magana muke kan project d’in da bamu tab’a handling babba kaman shi ba. Kuma a matsayinka na Wanda ragamar kula da aikin ke k’ark’ashin ka ya kamata ace by now ka ziyarci site not just once or twice. Cikin k’ank’anin lokaci zamu fara. Sann any moment any time Dad dinka zai iya dawowa k’asar nan. Mai kake tunani idan ya dawo Ya tadda baka nan.? The story will definitely change. And all our hard workings will go to waste.. Haidar you need to forget about your tour to America and come back as soon as possible.”" “I don’t take orders from you Hisham. Let Aliyu Maitama do his worse. I do not give a damn.!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran kafin yasa kai ya fice cikin huci saikace Hisham d’in na ganinsa. Zuciyarsa na masa zafi dik sanda aka ambata masa mahaifinsa. Sunan da dik sanda aka ambata sai yaji k’una cikin zuciyarsa at the same time babu yanda ya iya wann sunan dai yake amsawa. Babban kuskuren da mahaifiyarsa Tai shine saka masa sunan wann mutumi da Tai Wanda duk duniya babu Wanda Ya tsana sama dashi. Dareen ta fito daga mab’oyarta tana bin bayansa da kallo Har ya b’ace ma ganinta. Zama tai tana k’ok’arin figuring out maganganun da taji ya tattauna cikin waya. A b’anegarn Haidar kuwa can bakin beach yaje ya zauna tunanin duniya na damunsa. K’iyayyan mahaifinsa ne zalla cikin zuciyarsa. Lokaci guda maganganun Hisham na yawo a kwanyarsa. If he wants to take his Dad down dole yaje yayi aikin koda baya son komawa. Rashin komawarsa na nufin zai iya rasa chance d’insa na k’arshe akan mahaifinsa. Dan kaman yanda Hisham yace ne idan har Dad d’insa ya rigashi komawa Nigeria toh fah zaiyi replacing d’insa da wani ne. He promised to make his Dad swallow all his words sann baya jin zai janye wann k’udirin nasa. Gajeren tsaki yai yana tunanin abun yi. Mommy ce ta fad’o ransa. Yai scrolling kan sunanta. Kaman mai tunanin wani abu ya jima sosai kan lambarta had’ida k’ura ma sunanta ido. Saida ya furzar da huci kad’an dan baida wani option kafin yai dialing layin. Sunanta Ya fara ambata tana d’aga wayan in the way he does sanda yake k’arami. Sai Mommy taji hawaye ya ciko idonta. Idan Ya kirata da wann sigan lokacin k’uruciyarsa ta kullesa ne a d’aki taurin zuciyarsa bazai bari Ya rok’eta ta bud’e sa ba sai ya ambaci sunanta da wann sigan. Tai k’ok’ari Tai ta maza ta share hawayen da suka gangaro mata “Haidar ina ka shiga tsawon sati biyu.? Mai kake nufi Dani Haidar..? Mai kake nufi da Amaryarka dake zaman jiranka tsawon sati biyu. Shin ka cika alk’awarin da ka d’aukar min.?” Da ta ambaci amaryarsa sai yaji abun Ya masa wani banbarak’wai. Girgiza kai yai kad’an “Alk’awari d’aya na d’aukar miki Mommy shine bazan saketa ba sai ta cika wata uku kaman yanda yake a Yarjejeniyar. Amma ban miki alk’awarin zama da ita cikin watanni ukun ba.” Mommy ta zaro ido waje kaman yana ganinta. Idan baizo ba ai Babu amfanin auren. Ya zama wofi kenan. Katse shirun Tai da fad’in “A’a Haidar kar mu fara wann wasan dakai. I mean what about the project.? Muddin mahaifinka ya rigaka saka k’afa cikin gidan nan kasan sauran Haidar. All our efforts and sacrifices zasu tafi ne a banza . Haidar ka tuna na k’ulla auren nan ne dan mahaifinka ya amince ya baka project din nan.” Katseta yai da fad’in “To hell with everything Mommy.” Mommy ta mik’e tsaye tana jin zufa na keto mata. Sai muryarta Ya soma rawa “A’a Haidar.. Haidar kar kace haka.” "“You know what Mommy, you are too demanding. Yes na yarda zan auri yarinyar chan or whatsoever da kika kawo kika ce na aura because I wanted to manage the project. But zama tareda ita under same roof ban miki wann alk’awarin ba. It’s suffocating already da na amince da auren.”" Mommy taci gaba da girgiza kai jin duk sadaukarwan da tai da duk wasu k’ok’arin ta zasu tashi a banza. Sai ta soma hawaye “Yanzu da gaske ka hakura da aikin Aliyu.? Mai zai faru Dani Haidar.? Mai zai faru da nawa auren.? Yanzu bazaka amince da AUREN WATA UKU dan ceto auren naka mahaifiyar ba.” Cikeda k’osawa yake tattare naman goshinsa “Quit the act Mommy. Your victim card won’t work on me. You brought this to yourself. You should blame yourself.” Cikin kuka Mommy ke fad’in “Haidar cikin satin nan Mahaifinka zai dawo k’asar nan. Na tabbata idan Har ya rigaka dawowa zaka dawo ka tadda bana nan. Idan har ni na haifeka zaka dawo Aliyu.. Zaka dawo ka ceci Aurena kafin mahaifinka ya sauk’a k’asar nan..” Tana ida fad’in haka ta katse kiran ba tareda ta jira cewarsa ba. Ya lumshe idonsa kad’an yana tuna mafarkin da yai tareda iyayen nasa a kwanakin baya.. Yai gajeren tsaki wani b’angare na zuciyarsa na fad’a masa mafarki is the opposite of reality. Ya kuma yin gajeren tsaki zuciyarsa na kuma tunzura shi gameda al’amarin iyayen nasa. Meyasa yakeji gaba d’aya shidai baida wani alk’ibla a rayuwarsa. Like his life’s a complete messed up. Baisan mai yake son yai ba. Baisan mai yake ji ba. A haka ya mik’e yana tafiya baisan wani direction zaibi ba. ** Abuja.. Mommy yau din mafarki tai Haidar ya dawo suna zaune parlor Kansa kwance saman cinyarta suna hira na d’a da uwa da basu tab’a irinsa ba. Tinda tai wann mafarki ta tashi da farin ciki ga dukkan alamu shirinta mai tasiri ne Akan Haidar din. A b’angare guda ga Daddy ya mata waya ya sanar da ita nan da kwanaki biyu zuwa uku zai dawo da izinin Allah. Gaba d’aya sai tana ji kaman lokacin dunk’ulewar ahalinta ne yazo. Burinta yana gab da cika. Tuni tasa akai mata kiran Ummul ta sanar da ita Mijinta na nan tafe. Yacce kasan wacce takeda tabbacin dawowar Haidar d’in ta dauko mai gyara na musamman irin nasu na shuwa aka soma yi ma Ummul sabon gyara. Wani sabon kula na musamman Mommy ke bawa Ummul. Hankalin Anisa idan yayi dubu ya tashi. Babu shiri ta fita ta nufi gidansu Leenah dan bazata iya kallon wann kayan tashin hankali ba. Bazata bari Haidar ya dawo gidan ya cimma Ummul ba. Leenah ta dubeta a dak’ile “So da kika taso kika zo nan mai kike so na miki.?” Anisa tace “Leenah let’s forget about everything. Nasan ban kyauta ba amma dole ce ta saka ni d’aura miki laifin. Da ace na d’auki laifin da yanzu bana gidan. Leenah I have no one to turn to but you. You just can’t abandon me you know.” Ta k’arashe tana duban kawar tata kaman zatai kuka. Shiru Leenah tai na d’an lokaci kafin tace “Neesa I’m not doing this. I won’t allow myself to fall into your trap again. I’m not that stupid.” "Anisa ta kamo hannayen Leenah “Girlfriend please mana. Zamu bari wann low class d’in ta shiga tsakanin abotanmu ne.? Tayi mana guda biyu bazamu bari tayi na uku ba. Think, yanzu idan muka kyaleta ji zatai tayi nasara akanmu. And remember, we never back off for a fight.”" Shiru Leenah tai kafin tace “This is your battle Anisa. You should fight it alone.. Kin gane.” "Sai kuma ta faurzar da huci kad’an ganin Anisa ta tsareta da ido “Fine, naji.. What do I get in return dan wann karon shiri babba zamuyi wanda bazata iya tsallakewa ba.”" Anisa ta jinjina Kai tana murmushi “Idan har kika taimaka min na zama matar Haidar komai mai sauk’i ne Leenah. I promise not to let you end your life Washing clothes with bleach just to keep them white.” Leenah ta jinjina Kai tana murmushi “Lokaci yayi da zakiyi abinda kike tsoro Anisa.” Anisa ta dubeta cikin rashin fahimta “Kaman yaya..?” Leenah tace “Your ultimate goal is to get rid of her for good. Right.?” Anisa ta jinjina Kai “K’warai kuwa.” Leenah ma ta jinjina Kai “Good..! Then make her disappear for good..” Anisa ta kuma girgiza Kai “But how.?” “Kill her Neesa.! Poison her once and for all.” Anisa ta zaro ido waje “A’a Leenah.. What what if our plan fails again..? Kaman dai sauran..?” Leena ta dubeta “Anya da gaske kin shirya Anisa..?” Anisa ta dubeta a d’an tsorace “Mai a zai faru idan bataci poison din ba.?” Leenah ta murmusa “Ba ko wani poison bane ake ci Anisa. Wani shak’ansa ake a iska. A hankali yake lalata lungs kafin a ank’ara sai gawan mutum. Kinga irin wann babu wanda zai zargeki.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. Anisa ta murmusa “Yayi. Yanzu ya za’ayi mu samu.?” Leenah ta murmusa “Wann mai sauk’i ne ki bar min komai a hannuna. Nasan kudi bazai zame miki matsala ba.” Anisa taita murna tana mata godiya. Akan haka suka rabu washe gari suka had’u a mahad’a. Leenah ta ciro wani mistitsin kwalba cikin jakanta ta mik’a ma Anisa. Anisa hannu na rawa ta amsa dan kwalban da wani ruwa mai kaman acid ciki. Anisa na juya kwalban Leenah ke mata bayanin yanda zatai amfani dashi. “Cikin turaren da take yawan amfani dashi zaki zuba kad’an. Muddin tana shak’an wann turaren bazata wuce kwanaki uku tana numfashi ba.” Murmushi Anisa tai. Cikin zuciyarta take fad’in Yazo gidan sauk’i dan ta kula Ummul tana yawan shafa turaren humra da ta kai mata a kwanakin baya Wanda ta sauya turaren da Mommy ta bata dashi. Tabbas zata zuba mata a ciki. Leenah ta dubi Anisa had’ida gyara zamanta “A baya nayi zaton Hajiya Kwaise bazata tab’a bari D’anta ya auro d’iyar talakawa ba. Nafi tunanin iyayen Haidar zasu nema masa aure ne daga babban ahali. A well known and influential family. Like business partners d’insu ko d’iyar manyan ‘yan siyasa kodai d’iyar masu mulki. Amma na sha mamaki yanda ta auro ma d’anta wann yarinyar.” Anisa ta jinjina Kai “Ba ke kad’ai kike mamaki ba Leenah. Shiyasa zuciyata ke tabbatar min akwai wani Abu a k’asa k’ark’ashin wann auren. Massive love d’in da Mommy ke nuna ma yarinyar yafi komai d’aure min kai. Ko ni nan da nake tamkar ‘yarta sann mahaifina is a successful businessman banyi zaton zata bari d’anta ya kawo mata ni matsayin sirka ba sanin ko wacece ita. Nafi zaton zata tafi da nisa sai gashi ta k’are a ‘yar talaka. Ke da ganin wann al’amari kinsan akwai lauje cikin nad’i. And believe me I vow to find out whatsoever she’s hiding.” Leenah ta jinjina Kai “Ta haka ne kawai zaki fahimci komai Neesa. Idan kika kashe yarinyar.” Anisa ta jinjina Kai tana tabbatar da kalaman Leenar. Daga bisani godiya tai ma k’awarta Leenah sukai sallama Leenah na fad’in sai taji result. Koda Anisa ta koma gida cikin hikima da dabara ta zuba wann ruwan lungs poison da Leenah ta bata cikin turaren Ummul. Ta dawo d’aki tai relaxing tana sakin murmushin nishad’i. Nan da kwanaki biyu zuwa uku mataalarta zai kaw. Saidai a fidda gawan Ummul daga gidan. Dan ta tabbata wann karon Ummul bazata haye tuggunta ba. A fili take furta “Mommy ki gama duk wani shirin da zaki mata. Haidar gawar Amaryarsa zai dawo ya tadda.” Tana Ida fad’in haka ta fashe da dariya. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *30* *©️Sameena Aleeyou… * "Tinda jirginsu tai landing a Nigeria Dareen ta rasa sukuni. Ta kula akwai mihimmin abinda yasa suka yanke hutun nasu suka dawo gida Nigeria. Toh amma rashin sanin mak’asudin dawowar tasu shi yafi komai d’aure mata kai. Da fari tayi zaton project d’insa yasa ya dawo amma daga bisani ta kula kaman dai abun nada alak’a da ahalinsa ne musamman ma mahaifiyarsa. Meyasa duk irin aikin da suka tabbata anyi kan Haidar d’in da iyayensa kaman bai wani tasiri tsakaninsa da mahaifiyarsa ba. Kaman dai Har yanzu shid’in koda bai nuna ba can k’asar zuciyarsa yana kwad’ayin Ya mata biyayya. Dan taga call history nasu a wayarsa shida mahaifiyarsa. Kuma tinda sukai wann wayar ya yanke decision d’in dawowa gida. Tabbas ya zama dole ta koma wajen Dodon kobuku ta sanar dashi halinda ake ciki. Tana so aimata aiki na musamman akan mahaifiyar Haidar wacce take ji a jikinta ita d’in nema take ta zame mata barazana. Sann wann zuwan da zatai bazata bari Shadow ya sani ba. Aiki ne da za’a mata ita kad’ai. Ya kamata ta saka rana ta tafi gida Ilorin dan ta gana da Dodo Kobuku. Ta k’arashe tunanin tana kallon fuskar Haidar dake kwance yana baccin gajiyan hanya. Fuskar tasa tayi fayau tamkar Wanda baida wata damuwa. Ta murmusa zallan k’aunarsa takeji na bin duk wani vein na jikinta. Ta Shafa fuskarsa a hankali. Can k’asar zuciyarta take furta ‘You are mine Haidar Maitama. Ni kad’ai na. I won’t allow anybody to come between us. Not Shadow, not even your own parents. Idan shiga tsakaninku is not enough zan b’ullo maku ta wani hanyar. Idan ta kama na kashe rai ne akan ka zan kashe. Koda mahaifiyarka ce dan na kasance dakai zanyi Haidar. Kaid’in nawa ne. Ni kad’ai.!’ Ta k’arashe tana tsura masa ido." ** "Tin farar safiya take gidansu Leenah, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Zuciyarta ya cika da tsoron abinda ka iya zuwa ya zo. Yau kwanaki uku kenan da ta zuba poison din cikin turaren Ummul. Ta tabbata izuwa wann lokaci komai zai iya faruwa dan gaba d’ayan ranan ma bataji d’urin Ummul d’in ba. Ta dubi Leenah dake zaune hankalinta kwance tana kallon American movie ta k’araso ta zauna kusan Leenah zuciyarta sai tsinkewa yake “Hey.! What if she’s dead by now.? Ko kuma ta shirya min wani makircin tinda kinsan makira ce ta gaske..!” Anisa tace duk a tsorace." "Murmushi Leenah tai tana jefa popcorn a bakinta “You know what Neesa, you should stop being paranoid idan ba haka ba a banza zaki sa ko wani Abu ya sameta a zargeki. And if that happens believe me I won’t come to your aid. So ki kwantar da hankalinki ki tashi ki koma gidan ki tabbatar da abinda ya sameta.” Ta k’arashe tana duban Anisa." "Jikin Anisa har lokacin a mace yake sanin ko wacece Ummul d’in tinda ta tsallake tuggunsu har guda biyu. Idan ta tsallake wann din ma ba abin mamaki bane. Babban abinda yafi bata tsoro shine wann ya k’unshi kisan kai ba kaman sauran ba. Bata kuma cewa komai ba sai zama da tai can gefe tana ci gaba da tunanin abin yi. Dan tsoronta d’aya ji take kaman idan ta koma gida Ummul zata kamata, reshe zai kuma juyewa da mujiya kaman ko yaushe. Da kyar ta iya tashi tai Sallama ma Leenah ta nufo gida duk jikinta a mace." Daga can nesa tai tsaye tana hangen sashen Ummul amma bata shiga ba dan har lokacin zuciyarta bai daina bugawa ba. Sauri sauri ta nufi nata d’akin tana tambayan maids ko Ummul ta shigo. Nan wata maid ke sanar da ita bataga shigowarta ba. Da haka Anisa ta nufi d’aki duk a tsorace take. Tana shiga ma kwanciya tai saman gado ta sanar sa maid d’aya ko Mommy ta neme ta tace mata ta dan kwanta bata Jin dadi. Kwanciyarta da kad’an ta hango mota bak’a k’irar Mercedes GWagon. Gabanta yai wani irin tsinkewa dan wann motar tasan ta Haidar ce. Yaushe Ya dawo.? Da gaske shine ciki.? Kodai idonta ne ke mata gizo.? Da gaske Haidar ne Ya dawo.? Take taji jirin gaske na neman kada ita sanda ta diro daga saman gado. Ta isa jikin window a guje dan tabbatar ma idonta. Shid’in ne dai looking handsome as always a cewarta. Gani tai ma ya k’ara k’warjini da kyau. A hankali ta furta “Haidar… Mai ka dawo yi..? Meyasa bazaka jira ta cika ba.? Meyasa zaka dawo yanzu..?” Ji tai tana son sanin halinda Ummul ke ciki kafin Haidar Ya cimmata. Sauri sauri tai nufin fitowa daga d’akin sai kuma taja ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu zuciyarta na kuma bugawa. A hankali ta koma da baya ta zauna zuciyarta bai daina bugawa ba. A b’angaren Haidar kaw tsaye ya hange mahaifiyarsa gaban tsohon hotonsu Wanda akai tun yana k’aramin yaro d’an shekara 10 Wanda bayan shi baya tunanin sunada wani family picture tare. "Hawaye take tana Shafa hoton, at same time tana ci gaba da furta “I want nothing but the best for you.. I know I’ve never been a good mother to you.. But please give me a chance Haidar.. Ka bani dama na gyara kurakuran da nai a baya. Just this once..” Kuka ya hanata ci gaba da magana." D’an kauda fuskarsa yai cikeda k’osawa dan yasan hakan bazai wuce d’aya daga cikin acting d’inta ba. Yasan bazai wuce ta hangi motarsa ne ko taji shigowarsa shine tazo gaban picture d’insu take wann wasan kwaikwayon nata in order to gain his sympathy. “Nice performance Mommy.! I’m here already. I guess the show is over.” Yace yana k’arasa shigowa parlorn. Mommy ta juyo cikeda mamaki tana dubansa. Ta kuma mutsuka idonta. Sai taji murmushi na zuwa saman fuskarta. “Haidar.. My Son..!” Ta furta cikin rawar murya hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba. Sai Ta isa da sauri ta rungume shi kukanta na k’aruwa. Tsam ta rik’e sa cikin jikinta. Tana hawaye take furta “I knew it.. I knew You’d come back to me.. To your family. Nasan zaka dawo garemu Haidar.. Nasan bazaka bani kunya ba. Sabida kai d’in D’ana ne..” Duk sunbatun nan da take ji yake ta cika masa kunne. Yai k’ok’arin cireta daga jikinsa da k’arfin gaske. “Don’t get it wrong Mommy. Idan na dawo na dawo ne kawai sabida project d’in amma ba sabida ke da k’udirinki ba.” Yace yana duban mahaifiyar tasa dake tsaye gabansa tana kuka cikin sanyin jiki. Mommy ta jinjina kai “Even so Haidar. I’m glad ka dawo sabida project d’in. Nafi kowa farin cikin dawowarka. Your wife is waiting for you Aliyu.. She’s been waiting for you for the past two weeks..” Bata kai aya ba suka soma sinkayo hayaniyar wata ‘yar aikin gidan tana ihu tana kiran Mommy. Gaba d’aya Haidar da Mommy suka juyo a tare sanda maid din ta shigo tana haki. Anisa da hayaniyar ya sanyata fitowa ba shiri ita ta tari maid din da tambayar meke faruwa ta shigo haka tana ihu. Cikin haki take sanar dasu ta shiga kai abinci section d’in Ummulkhair amma ta tararta a kwance lifeless. Mommy da taji batun bagatatan saurin k’arasowa tai tana jijjiga mai aikin tana tambayarta mai take cewa. Mai aikin ta kuma nanata binda tace. Babu shiri Mommy ta fice ba tareda ta bi takan kowa cikinsu ba ta nufi sashen Haidar. Yayinda Anisa taji kama an yaye mata duka damuwarta. Daga k’arshe dai burinta Ya cika. Yanda Mommy taga Ummul kwance k’asa tamkar maras numfashi sai ya kuma gigitata. Ta shiga jijjigata tana ambaton sunanta. Mik’ewa tai cikin kuka tana fad’in ma’aikatan gidan su kira ambulance amma kafin tai wani aune sai ganin Haidar tai ya ciccib’i Ummul d’in Ya nufi motarsa da ita yana Anisa ta isa ta bud’e mata bayan motar. Mommy ta biyo bayansu cikin sauri Har lokacin hawaye take. Anisa jikinta duk a mace ganin Haidar ya d’auki kucakar nan ya sakata motarsa harma cewa yake ta bud’e masa motar. ‘Kan uba toh wllhi ka d’auki wofi domin kuwa fanko ce wajen gawa ce Babu rai.’ Ta fad’i haka cikin zuciyarta. Mommy ce ta shiga bayan motar ta d’aura kan Ummul saman cinyarta yayinda Anisa tai maza ta shige gaban Motar Haidar ke driving. Yanda hankalin Mommy ya tashi dole ta baka tausayi. Dan kuka take da gaske tana fad’in Ummul ta tashi kar ta tafi ta barsu ga mijinta Ya dawo gareta. Daga Anisa Har Haidar d’in sumbatun Mommy ya cika masu kunnuwa cikin motar. Allah Allah suke a isa asibiti ko sun huta da sunbatun Mommy. Suna isa Ya kuma d’aukanta suka nufi cikin asibitin da ita. Take Likitoci suka amsheta aka nufi ER da ita. Nan suka zauna suna jiran ba’asi daga Drs. Har lokacin Mommy kuka take yayinda Anisa ke addu’an Allah yasa a fito da sakamako mai dad’in sauraro a kunnuwarta ma’ana ta mutu. Ganin Mommy bazata daina kuka ba yasa Haidar mik’ewa Ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kukan da Mommy take irritates him musamman idan yaji tana ambaton yarinyar ta tashi mijinta ya dawo gareta. Gaba d’aya ji yake zuciyarsa a cunk’ushe. Meyasa ma bazai tafi ba.? Zaman me yake a asibitin.? He did what he had to do sanda yaga yarinyar kwance lifeless. Ya kawota asibiti. Toh zaman mai zaici gaba da yi.? Yai gajeren tsaki sanda ya kuma duban Mommy dake ci gaba da matsan hawaye. Wani b’angare na zuciyarsa na sanar dashi ka zauna ko dan mahaifiyarka. Ya kuma yin tsaki wai shi Haidar ke yin abu dan mahaifiyarsa matar da bata da wani buri bayan taga ta k’untata masa. Ya kuma yin gajeren tsaki yana mai duban k’ofan ER din. Can gefe ya matsa dan baya son sauraron kukan da Mommy take. Anisa sai satan kallonsa take da duk wani motsinsa. Wayarsa ce ta soma ruri Ya fito da ita daga aljihu nan yaga Dareen ke kiransa. Bai amsa ba sai Ya maida wayar aljihu Har ta k’arashi ringing d’inta. Hankalin Anisa sosai ya kuma tashi ganin Haidar baibi takan wayarsa ba sann ga damuwa k’arara Ya nuna saman fuskarsa. Mai hakan yake nufi .? Ba dai Haidar damuwa yai da wann kucakar ba Wanda ko wayarsa Ya kasa amsawa. Dan ita duk a nata tunanin damuwar halinda Ummul ke ciki ne ke d’awainiya da Haidar d’in tsaban abinda ta raya ma ranta kenan. Zuciyarta sai wani irin k’una yake mata tana ci gaba da addu’an Allah yasa a fito masu da gawan Ummul kowa ya huta. A can gidan Haidar d’in kuwa hankalin Dareen yayi dubu Ya tashi. Haidar d’inta ne ke ignoring calls dinta yau. Mutumin da ko important meeting yake zai excusing kansa ya d’aga kiranta musamamn da taga an d’auki lokaci bai returning call din ba. Ita kad’ai sai safa da Marwa take tana jin zuciyarta na mata d’aci. Tana a haka taga wayan Shadow na shigo mata. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *31* *©️Sameena Aleeyou… * Tana d’aga kiran ta sinkayo muryarsa daga d’aya b’angaren “I heard that you’re back in the country.. Ya akai banji hakan daga bakinki ba..?” Shiru batace dashi komai ba sai hucin da take dan gaba d’aya zuciyarta a cunkushe take tinda ta kasa samun Haidar a waya. Muryar Shadow ya kuma dakan dodon kunnenta “Dareen are you sure you are not hiding something from me.?” "“Toh mai zan b’oye maka. Yes mun dawo amma ban samu chance na sanar dakai hakan ba. After all, jiya ne kawai muka dawo k’asar. Is not as if na shafe kwanaki ne da dawowa bakaji daga gareni ba.”" Katseta yai “Don’t you dare take me for a fool. I know you so well. Na sani idan kina shirya wani abun.. Let me warn you Dareen. Idan kika shirya wani abu a bayan ido na believe me zaki d’and’ani kud’arki.” Tai murmushin takaici “Is that a threat.?” Murmushin shima yai “You know me so well. I don’t keep people around with threats. Idan har zanyi abu lokaci d’aya nakeyi ke kinfi kowa sanin hakan.” Yai gyaran murya kafin yaci gaba “Ina Haidar..?” Ta kuma furzar da huci “How would I know.? Ya fita bai sanar Dani ba.” “You should know Dareen. Because that’s what you are there for. Ban ajiyeki tareda dashi ba just for you to have fun with him kin fahimta.” “Oh excuse me! You don’t own me.. And you are not the one calling the shots here. Ni ce nake rayuwa da Haidar a halin yanzu… Barazana kawai kake da kake cewa tulun da aka d’aure kurwar Haidar aka shata layin k’iyayya tsakaninsa da iyayensa na wajenka.. Kuma bari kaji from now henceforth bazan bari ka cutar da Haidar ba. Babban kuskuren da ka tapka shine da ka min sanadin shiga rayuwarsa. A halin yanzu Haidar dani are one.. He’s my husband da nake sonsa da duka zuciyata.. Bazan bari kai ko wani ya cutar dashi ba. So if I were you zan maida makaman yak’ina.” Murmushi yai daga d’aya b’angaren “Haka kika ce.?!” Bata bashi amsa ba sai sakin huci da take. Ya kuma murmusawa “Fine. Zamu gani tsakanin mu biyun Who owns Haidar..!” Yana Ida fad’in haka ya katse kiran. Dareen taci gaba da kallon wayar tana sakin huci. ** A can asibiti kaw suna nan zaune jiran tsammani Mommy ta dubi Anisa wacce dama saura su biyu ne zaune wajen “Idan likitocin Sun fito kimin magana.” Jinjina mata kai Anisa tai had’ida amsawa. Tabi bayan Mommy da kallo wacce hankalinta ke ga wayar salularta. Mommy tana ficewa wani corridor d’in ta soma waya da ‘yaruwarta Asshe. Nan take sanar da Asshe abinda ke faruwa. Baki har na rawa Asshe ke tambayarta “Haidar..? Haidar fah..? Ina Haidar Haidar yana lafiya.?” Dan ita duk a tunaninta aikin gama ne Ya riga Ya gama tsakanin Haidar da Ummul. Mommy ta girgiza Kai kad’an “Asshe Haidar lafiya yake. Hasalima shi yai driving namu to hospital. Amma meyasa kike tambayar lafiyar sa.?” Sauk’e ajiyan zuciya Asshe tai tana jin gumi da ya tsartsafo mata na bin jikinta yana sauk’a. Lokaci guda tai k’ok’arin saita kanta “Toh amma Aunty Kwaise is possible asirin ne yai aiki. Is possibile amfanin yarinyar ya kare ne. Tinda ita d’in makarin asiri ce.” Kaman Asshe na ganinta haka Mommy ta girgiza kai “Ta ya hakan zai kasance bayan Haidar shigowarsa gidan kenan. Babu wata alak’a data shiga tsakaninsa da yarinyar. Ko kin mance mai Malam Ya sanar damu. Har sai wata alak’a ta auratayya ta gifta tsakaninsu kafin ta karya asirin.” Daga d’aya b’angaren Zuciyar Asshe yaci gaba da tsinkewa. Toh ko dai Anisa tayi shashashancinta ne ta bama yarinyar turaren bata zubar ba kaman yanda ta umarceta. Kodai har mai aukuwa ya auku ne ba tareda Kwaise tayi la’akari ba. Wann abu da d’aure kai yake. Toh amma idan Har illan dake jikin yarinyar bai shafi Haidar ba kaman yanda Dije ta sanar da ita. Ta iya yuwa da gaskiyar Suwaiba Dije fansarta kawai take son d’auka kan yarinyar da uwarta tinda gashi yarinyar ce ke kan gargarar mutuwa kaman yanda bokansu Ya sanar dasu ba Haidar ba. Idan Har hakan ta kasance zatafi kowa farin ciki. Muryar Mommy ya kuma katseta “Kaina Ya k’ulle gaba d’aya Asshe. Shin idan yarinyar nan ta mutu a haka wann na nufin asirin dake jikin D’ana Ya karye ne kokuwa dai Har yanzu da asirin jikinsa.?” Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Aunty Kwaise bakida tabbacin idan Haidar bai shiga b’angaren yarinyar nan ba a tsakanin shigowarsa gidan. Kinsan abu ne da aka had’a da asiri kuma wann turaren da Malam Ya bamu ya tabbatar mana shi d’in tamkar magnet ne Wanda zai janyo Haidar zuwa gareta..” Mommy tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta girgiza kai “Asshe al’amarin nada rikitarwa amma inada tabbacin a lokacin da muka tsinceta kwance k’asa kaman gawa a wann lokacin Haidar ya soma sanyata a idonsa.. Tabbas tayi amfani da turaren inada tabbacin hakan amma bana tunanin amfani da turaren kawai zaisa ta Mutu kafin Haidar ya samu kusanci da ita.” Haidar da isowarsa wajen kenan yai tsaye Cak yana sauraren kalaman Mommy na k’arshe. ‘Turare.? Mutuwa kafin shi Haidar ya samu kusanci da yarinyar.?’ Ya nanata kalaman da yaji Mommy tace cikin zuciyarsa.? A razane Mommy ta juyo tana dubansa duk a birkice. Kana ganinta kaga maras gaskiya. Tai saurin canza maganar da take cikin wayar tana mai katse kiran. Ta k’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa “Em.. Em.. Haidar ashe kana nan baka tafi ba..? Na zata ai ka tafi..?” Ya girgiza mata kai kad’an alamun a’a “Ina nan Mommy.. Naje sallah ne. Why.? Is there something I should know.?” Yai tambayar yana tsareta da idonsa. Tai saurin girgiza masa kai alamun a’a. Ya jinjina Kansa a hankali ba tareda ya nuna mata yaji koda word d’aya daga wayan da ta gama ba. Ya d’an ci gaba da takowa kusanta har lokacin Mommy a tsarge take. Haidar na hankalce da ita. “Any news about the girl’s condition.?” Ya tambaya yana tsare Mommy da ido. Zuciyarta Ya kuma tsinkewa tana tuhumar kanta mai hakan yake nufi.? Kenan Haidar Ya damu ne da Ummul.? Bata kai ga samo amsa ba suka hango wani Dr ya fito daga ER d’in. Mommy ce ta nufe shi cikin sauri tana tambayarsa Ya jikin Ummul. Yayinda Anisa ma ta taso daga yanda take zaune ta nufo su. Haidar kaw daga can yanda yake tsaye yana karantar yanayin Mommy. Meyasa take nuna damuwa gameda yarinyar bayan ga abinda yaji a waya kaman mutuwa take nema ma yarinyar.? Meye nufin Mommy akan yarinyar.? Mecece manufarta na aura masa yarinyar.? Tunani daban daban cikin zucjuarsa. Muryar Dr ya sinkayo yana fad’in “She’s still not out of danger. A halin yanzu bazamu iya bada shaida akan komai ba. Anything can happen.” Ya numfasa kafin ya dubi Mommy “Is she your Daughter.?” Kafin Mommy ta bada amsa Anisa tai tsulum ta bud’i baki tace “No she’s not her daughter.” Mommy ta k’ara da “She’s my Son’s wife.. Dr meke faruwa da ita ne.?” Dr ya d’anyi Jim sai yace “Where’s her husband then.? I’d like to speak with him.” Mommy ta juyo a d’arare tana duban direction din da Haidar yake. Anisa ma shi take duba tana jira taji yayi rejecting hakan amma sai taji akasin hakan. Abun mamaki muryar Haidar suka sinkaya yana fad’in “I’m here. I am her husband.” Daga Anisa Har Mommy cikin tsananin shock suke duban Haidar Wanda tuni ya soma takowa kusansu. Dr yace “May I have a word with you.?” Haidar ya jinjina masa kai alamun eh “Sure.. After you.” Ya k’arashe yana alama ma likitan da hannu. Dr ya jinjina masa kai kafin yasa kai ya nufi ofishinsa Haidar na take masa baya. Daga Mommy har Anisa mamaki ya hanasu rufe baki. Babu Wanda ya tasammaci haka daga Haidar. Ko ita kanta Mommy da takeda yak’inin maganin bokansu ka iya tasiri akan Haidar tinda ya sanar dasu turaren da suka ba ma Ummul ta dinga amfani dashi zai janyo Haidar gareta batai zaton abun zaizo da sauk’i haka ba. Kenan Watak’ila d’aukanta da yai cikin hannunta har ya shak’i turaren.? Gaba d’aya kan Mommy ya k’ulle ta rasa fahimtar tunanin da take. Gaba d’aya duk abubuwan dake wakana Sun k’ulle mata kai. Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana tinanin kiran k’awarta Leenah dan sanar da ita halinda ake ciki. ** Dr ya dubi Haidar kafin yace “Amma kana ina har ake barazanar d’aukar rayuwar matarka..?” Haidar ya jinjina kai lamun nuna rashin fahimta “Ban fahimceka ba Dr. Barazanar d’aukar rayuwarta kaman yaya.?” Dr ya jinjina kai yace “Sakamakon gwaje gwajen da mukai mata na gaggawa ya tabbatar cewa she’s being poisoned… Guba ne da ta shak’esa ta numfashi Wanda ya harba huhunta. Most likely cikin turare aka saka guban.” Haidar yai shiru yana had’a maganganun Likitan da wayan da yaji Mommy nayi. Sai girgiza kai kad’an yace “Turare.?” Dr ya jinjina kai alamun eh kafin yaci gaba “Irin wann guban akan sanya shi ne cikin wani scent da mutum ke amfani dashi slowly yake lalata lungs d’in mutum ba tareda an ankara ba. Shi irin wann guban anfi amfani dashi ne idan ana so mutum ya samu slow and painful death. Fortunately guban baiyi wani tasiri jikin matarka ba. But we can’t say she’s completely out of danger har sai mun mata minor aiki a lungs d’insa munyi flushing sauran wann guban to prevent it from spreading. Muna buk’atan saka hannunka Shiyasa na buk’aci ganinka a sirrance. Sann abu ne da Ya danganci criminal act kaga dole ai taka tsantsan tinda ba’a tantance waye perpetrator din ba. Koda tana k’ark’ashin kulawarmu a asibiti rayuwarta na cikin had’ari Har sai an kama mutumin dake k’ok’arin ganin bayan rayuwarta.” Shiru Haidar yai Zuciyarsa Ya kasa aminta da abinda Likitan nan ke fad’i da maganar da yaji Mommy tayi cikin waya. Idan ya had’a maganan Mommy da maganan Likitan nan. The whole thing yanada alak’a da turare kaman yanda yaji Mommy tace sann ta ambaci mutuwa a ciki. Ga turare ga mutuwa. Ga kuma abinda Dr ya sanar dashi cewa anyi poisoning yarinyar ne ta cikin turare. Toh idan Har Mommy kashen yarinyar takeda niyya meyasa ta aura masa ita.? Meyasa zatai poisoning d’inta.? Shin kodai Mommy shi take so tai poisoning shine ta b’ullo ta wann hanyar ta aura masa wann yarinyar ta saka poison din cikin turarenta dan shima ya shak’a su hadu su Mutu gaba d’aya tinda gashi ta matsa sai yazo ya zauna da yarinyar. Shin wann shine shirin Mommy na k’arshe akan shi ta kashe shi ba tareda kowa ya zargeta ba.? Shin har haka Mommy ke masa k’iyayya.? Shin Anya Mommy ita ta haifeshi.? Anya shi d’aya ne daga cikin wann ahalin.? Muryar Likitan ne Ya dawo dashi daga duniyar tunanin da Ya tafi yanda Likitan Ya d’an murmusa dan dik shi a tunaninsa Haidar tunanin aikin da za’ai ma matarsa a lungs yake kar aje a tab’a mata lungs dinta sabida sanin Had’arin irin aiki da Ya danganci organs. "“Look Engr. It’s just a minor surgery. We call it Minimally invasive thoracic surgery.” Ya d’an numfasa kafin yaci gaba “Is a way of performing surgery in the chest through small incisions, without making large cuts in the body, and it does not require spreading apart of the ribs. We use camera and instruments to get to the lung through small incisions in between the ribs. Kaman ma ba’ayi wani aiki ba haka jikin matarka zai zauna. But it’s necessary a dakatar da guban daga yad’uwa cikin jikinta.” Ya k’arashe yana mik’a ma Haidar pen da form." Haidar ya jinjina kai a hankali kafin ya karba yai signing a yanda aka buk’aci Ya saka hannu. Har lokacin ya kasa yarda da abinda ke faruwa. Ya dubi Dr yace “Dr I want this to stay between us please. Ban jima da dawowa k’asar ba so bansan waye ke farautar rayuwar matata ba da kuma dalilinsa. I need to investigate first.” Dr ya jinjina masa kai “Bakada matsala Engr. If you excuse me. Zan koma bakin aiki.” Haidar ya jinjina masa kai kafin suka mik’e a tare suna masabaha cikin mutunta juna. Sanda Haidar Ya fito ya iske Mommy da Anisa duk sunyi tsuru tsuru alamun suna jiran ba’asi. Babu ya Mommy. Kallo d’aya zaka mata ka fahimci a hargitse take. Ta k’araso da sauri tana tambayarsa Ya jikin Ummul mai Drs suka ce.? Haidar bai kaiga bata amsa ba dan har lokacin mamakin matar yake Wanda Ya girma ya sani matsayin mahaifiyarsa. Wayar Mommy ne yai ruri Daddy ke kiranta nan ta matsa gefe tana amsawa dan ita Har ta mance ranan Daddy ke dawowa Nigeria. Bayan ta Ida wayar ta dawo garesu tana duban Haidar Wanda ya tsareta sosai da ido kaman mai tuhumar ta. A d’an daburce tace “That was your Dad. Gaba d’aya na mance yana hanya sabida tashin hankalin nan da muka tsinci kanmu ciki. Driver yana hanya zaizo Ya tafi dani.. Yanzu yarinyar ce bansan da waye zamu barta ba.” Anisa tai karaf tace “I’ll stay here with her.” "Ga mamakinsu muryar Haidar suka sinkayo “No, I’ll stay with her. Kuna iya tafiya Mommy. After all, abinda kike so kenan na dawo na zauna da ita. Right.?” Ya k’arashe yana tsare Mommy da ido." K’ak’aro murmushi Mommy tai tana jinjina masa kai alamun eh. Yayinda Anisa tai mutuwar tsaye tana kallon abun mamaki wai Haidar zai zauna a asibiti da wann bagidajiyar.? Ikon Allah. Wai meke shirin faruwa ne.? Anya Haidar bai kamu da son bagidajiyar nan a kallon farko ba.? Sai tai saurin girgiza kai alamun a’a tana mai kwaban zuciyarta da irin wann tunani maras kan gado. Abu ne da bazai tab’a faruwa ba ko a mafarki. Haidar would never ever fall for someone like her. Muryar Mommy taji tana fad’in suje driver yana close Daddy na gida na jira. Anisa tabi Mommy jiki duk a mace sai waigowa take tana duban Haidar da Ya tsaya kaida fata wai shi zai zauna wajen Ummul. Gaba d’aya mamaki ya kasa sakin Anisa. Suna isa gida ta shige d’aki tana faman safa da marwa tana tunanin kiran Leenah dan ta sanar da ita halinda ake ciki. Bata Ida tunanin ba taga wayar Haidar na shigo mata. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sai tana ganin kaman Haidar Ya fahimci cewa ita tai poisoning Ummul. Da kyar ta iya d’aga kiran zuciyarta sai harbawa yake dan tsoro. Daga d’aya b’angaren Haidar yace “Kina jina. Kije d’akin yarinyar nan ki tattaro mun duk wani perfume dake d’akin ki kawo mun shi asibitin right this instant. Ina jiranki..” Ya k’arada Kar ki bari Mommy ta ganki ko ta fahimci wani abu. Understood.?” Anisa da zuciyarta bai daina tsinkewa ba a d’an daburce take jinjina kai “Oh ok.. Zanyi yanda kace.” Jinjina kansa yai kaman tana ganinsa kafin ya k’ara tabbatar mata da yana jiranta yanzu yanzu. Daga haka katse kiran yai Anisa kaw gijif ta zauna cikin kujera shikenan asirinta Ya tonu Dr ya sanar da Haidar guba aka saka ma Ummul cikin turare. Yanzu mai zatai..? Taje ta fasa turaren ne ko ta kai masa ne.? Amma idan ta kai masa ta kama kanta ne.. A fili ta furta “Oh no Neesa.. This is not happening. You screwed up again.!” Ta kuma rintse idonta tana tunanin abin yi. Cikin sauri ta d’ago wayarta . Jikinta har na wani irin kyarma ta shiga neman layin Leenah dan samun mafita. Leenah tana zaune taga kiran Anisa na shigo mata. Ta saki murmushi a hankali kafin ta furta “My stupid friend is calling again.” Ta kuma sakin murmushi kafin ta d’aga wayar. A birkice Anisa ta soma fad’in “Leenah komai Ya lalace.. Our plan didn’t succeed.. I’m afraid I messed up everything again..!” “Girl calm down..! Just… What are you trying to tell me..?” Leenah tace cikin dakatar da Anisa. A tak’aice Anisa ta bama Leenah labarin duk abinda ke faruwa Har kawo yanzu da Haidar Ya bata tax na kawo masa duka turaren da suke d’akin Ummul. Anisa ta k’arada “Leenah what if he he suspects me.. What if he finds out about the truth cewa ni ce nan na zuba poison din..?” Leenah ta rausayar da idonta “Here you are being paranoid again Neesa. Ta ya zai zargeki idan ba kece kika basa k’ofa ba. Base on abinda kika ce. Idan har Haidar ya baki tax na kai masa turaren hakan na nufin Ya yarda dake ne.” Anisa ta katseta “Nifa Leenah mafita na kiraki ki bani ba wai kimin narrating abinda na gama baki labari ba. What if I destroy the perfume..?” "Murmushi Leenah tai “Idan kikai destroying turaren shine kin basa room na suspecting d’inki… You know what Neesa, You always call me a moron. But you are the one acting foolish here. Idan har kika lalata turaren nan no doubt Haidar zai zargeki. Idan kuma ya zargeki ki tabbata sunana bai fito ba. Sabida nida kike gani inada burin aure da samun family of my own bana mafarkin karasa rayuwata a jail.” Ta numfasa “But wait.. A yanda kika bani labari Haidar yace kar ki bari mahaifiyarsa yasan kin kai masa turaren.”" "Anisa ta jinina kai alamun eh kaman Leenah na ganinta kafin Leenah taci gaba “Then let him suspect his mother.. Incriminate her. After all, kin sanar dani turaren da kika zuba poison din ma Ummul ciki turaren da Mommy ta baki ki bata ne kika canza da wani. Ya zo gidan sauk’I Anisa. Mahaifiyarsa itace ta bada wann turaren mai guba aka zuba ma matarsa ciki.!”" Dummm.! Haka k’irjin Anisa ya buga. Leenah fah cewa take tai incriminating Mommy. Mahaifiyar Haidar..? A hankali Anisa ta soma girgiza kai… SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *32* *©️Sameena Aleeyou… * Anisa taci gaba da girgiza Kai tana duban wayan. Mommy fah.? Ta ya zata soma d’aura ma Mommy laifi.? Bayan kasancewar ta mahaifiyar Haidar ita d’in fah ‘yaruwa take ga mahaifiyarta. Idan Abu ya lalace ba rasa Haidar kawai zatayi ba harda zumuntar iyayenta zata b’ata. Amma mai zatayi..? Ita kad’ai tana sak’awa da warwarewa ta kuma kiran Leenah dan ta gaza samun mafita. Leenah ta rausayar da ido tace “Haba Neesa ya kike abu kaman wata bagidajiya.” “Ban kiraki just for you to insult the hell out of me ba Leenah. Na fad’a Miki hujjojina if things go wrong. It will definitely be the end of me Leenah..!” "Leenah ta kuma rausayar da ido irin yanda Anisa take kaman dai Anisa na kallon ta “Toh banda abinki Anisa. Abun nan fah a bayyane take turaren da mahaifiyarsa ta ba ma matarsa akwai poison ciki ke meye naki a ciki.? Idan akwai wacce za’a zarga bazai wuce Hajiya Kwaise Maitama ba. Unless kuma zaki b’ullo ta wani hanyar kisan yanda zakiyi ki kutsa cikin d’akin da Ummul take ki k’arasata amma fah wann yafi had’ari Anisa because you would easily get caught. Hanya d’aya shine ki kyale mahaifyarsa ta d’auki laifin nan because he already grows suspicious of her idan har zaice ki aiwatar da Abu ba tareda saninta ba. Kuma kinsan me matar nan fah mahaifyarsa ce he would forgive her, definitely. Even if she’s convicted sabida ita d’in mahaifiyarsa ce amma ke fah kika kuskura kika bari ya kamaki kashinki ya bushe Neesa ba hannun Haidar kawai ba harda hannun uwarsa.”" "Anisa ta jinjina Kai idanunta na kuma k’ek’ashewa “You are absolutely right Girl. After all, Haidar baya son wann auren tai masa. Akwai tarin tanbayoyi da ya kamata yai ma mahaifyarsa.” Ta k’arashe tana sakin murmushin cin nasara. Lokaci guda ta katse kiranta da Leenah ta soma shirin fita. Nan taga wayar Amminta na shigo mata." Ta rausayar da ido kafin ta d’aga kiran mahaifiyarta “Yes Ammi. I guess labari ya isa miki.” Tace tana kuma juya ido. Daga d’aya b’angaren Asshe tace “Da uban wa kiketa waya ina nemanki..?” Anisa ta kuma juya ido “Abinda kika kirani kice kenan kawai Ammi.?” “Ke bani son shashanci.. Wai meke faruwa ne a gidan Aunt d’inki da banji daga gareki ba. Ko kin mance na barki a can ne matsayin ido na. Ki sanar Dani meke faruwa tsakanin Haidar da yarinyar can. Shin kin bata wann turaren ne da nace ki zubar.?” Anisa ta murmusa “Of course ban bata ba Ammi..Kuma na canza turaren kaman yanda kika umarceni.. Amma saidai..” Zuciyar Asshe yaci gaba da tsinkewa tinda tasan kalan shashancin ‘yar tata “Amma me Anisa..? Meye kika aiwatar ba tareda sanina ba. C’mon tell me.. Meye kika aiwatar.?” Juya ido Anisa ta kumayi a hasale ta katseta “Nayi poisoning turaren da na canza mata dashi..” Ta juya ido tana jan tsaki “She’s like a cockroach Ammi. Duk irin tuggun da nake k’ulla mata taki mutuwa kaman dai kyankyaso.!” K’iris ya rage Asshe bata saki wayarta ba. Baki na rawa take furta “Anisa kece kika zuba guba ma mutum..?Anisa waye ya aikeki.. Are you that dumb.? Bance Miki ki bar min komai ba zan kula da komai..? Bance miki kar ki yanke wani hukunci on your own ba.? Anisa kanki Kalau zakiyi kisan Kai kan namijin da baisan kinayi ba.?” Tsaki Anisa tai “There you go again Ammi. Very soon nida Haidar zamuyi aure as soon as wann makirar is out of the picture. And please do me a favour Ammi. Duk abinda zaki ji ko ki gani naki ido.” Tana Ida fad’in haka ta katse wayan. Asshe na k’ok’arin dakatar da ita amma inaa tuni ta kashe. Tuni Anisa tayi kaman yanda Haidar ya umarceta. Sanda ta kawo masa turarukan asibiti sai ta dubesa da mamaki “Amma me zakayi da turare a asibiti.? Kodai Ummul d’in ce ke so.. Amma idan itace ke son a kawo mata definitely zai kasance wann ne.” Ta k’arashe tana juya kwalban turaren cikin hannunta ga damuwa saman fuskarta kai kace zallan tausayin Ummul din ke d’awainiya da ita. Haidar ya tsareta sosai da ido sai ya girgiza Kai kad’an “Meyasa kikace haka.?” “Because it’s her favourite.” Ta dan murmusa cikeda makirci tana nuni da tausayi sann taci gaba “Mommy ce musamman ta bata turaren nan. Ummul tana son turaren sosai. Allah sarki Allah ya bata lafiya. At first bama wani jituwa amma daga baya I have become fond of her sabida tanada zuciya mai kyau. Kowa yana sonta a gidan especially Mommy.” Ta k’arashe tana share guntun hawaye da ya gangaro mata. Ba wai yana sauraron surutan da Anisa ke masa bane tinda yaji key points din da yake son ji ya daina gane mai take cewa sabida ta cika masa kunnuwa. Dakatar da ita yai da fad’in “You can go now. And don’t say a word to Mommy. Are we clear.?” Anisa ta jinjina masa Kai tana mai tabbatar masa bazata sanar da Mommy komai ba. Bai kuma bi ta kanta ba yasa Kai yai shigewarsa. Anisa tabi bayansa da kallo yanda ya shige hannunsa rik’eda turarukan cikin dan jaka. Murmushi ta saki dan ta tabbata ko gwaji akai aka gano turare mai d’auke da guba ciki Mommy ce zata rufta. Sann ne zata b’ata sunan Ummul a wajen Mommy dan ta tabbata idan har aka d’aura ma Mommy laifi zata tsani Ummul ne taji ta fita akanta. Zatai amfani da wann daman ta cire ma Mommy son Ummul cikin zuciyarta tinda dama ita kad’ai ke son wann jarababben aure. Zuciyarta wasai ta dauki hanyar gida. ** Tsaye Haidar yai gaban gadon da Ummul ke kwance bayan an fito da ita daga surgery. Yai mata k’uri yana dubanta. Tanbayoyi da dama cikin zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake jero tanbayoyin da baida amsoshinsu ‘Who are you..? Maiyasa Mommy zata farauci rayuwarki.? Shin Mommy ta kawoki ne dan ki zame mata hanya mafi sauk’i wajen ganin bayan rayuwa na.. Kina sane da shirin Mommy akaina.? Da yarda da amincewarki ki ka zab’i ta cutar dake dan kawai ta cimma burinta akaina ko kuwa dai kema victim din Mommy ne.?’ Daidai lokacin Dr ya turo k’ofa ya shigo. Ganin Haidar tsaye ya saka Ummul gaba wacce ke kwance unconscious saman gado. Ya saki murmushi “Engr da alama kana ji da matar nan taka sosai. Kar ka damu in sha Allah bazata wuce kwana biyu bata bude ido ba. Alhamdulillah the surgery was successful and we can now say she’s out of danger in sha Allah.” Har lokacin dubanta Haidar yake. A hankali ya kaikaito ya dubi Likitan “Har sai an Kama Whosoever is responsible an kuma tsaresa sann ya biya abinda ya aikata.” Daga yanda yake maganar zaka fahimci tsananin son daukan fansa cikin muryarsa. Mommy kawai yake hangowa cikin idonsa zuciyarsa na tabbatar masa wann shine daidai lokacin da ya kamata ya d’auki fansar duk abinda matar nan ta jima tana masa. Sann lokaci yayi da zata fayyace masa komai idan ma sato shi tayi duk sai ta fad’a. Bazai barta ba sai ta fayyace masa komai gameda gaskiyan lamarin da ya danganci rayuwarsa. Dr ya jinjina Kai yana duban Haidar din dan dik shi a nasa tunanin tsananin soyayyar da Haidar keyi ma matarsa yasa yaketa k’ok’arin ganin ya kamo mai laifin. Ya dan numfasa “The laboratory test for the perfume would take less than 24hrs. Zuwa gobe da safe in sha Allah zamu tantance wane turare ne mai guba cikinsa.” Haidar ya jinina masa Kai Dr ya k’arada “Engr.. Emm nace are you spending the night here with the patient.?” Sai ya k’ara da “Kar ka damu if you have some matters to attend to kana iya tafiya.. You can be sure she’s in good hands.” Ba tareda ya dube Likitan ba yace “I’ll be staying here Doc.” Ya k’arashe yana mai zama saman soft sofa dake can gefe da gadon. Gani yake kaman zata bud’e ido ta soma amsa masa tarin tanbayoyinsa. Dr ya murmusa kafin ya jinina Kai yai Sallama ma Haidar ya fice. Haka Haidar yai zaune ya sakata gaba yana kallo. Yana ganin wayoyi na shigo masa amma baida lokacin daukan ko d’ayansu. Shi dai burinsa safiya tayi hunch d’insa ya tabbata Akan Mommy. ** Dareen sai safa da marwa take tana kuma duba time. Bai tab’a kaiwa irin wann lokacin bai dawo gida ba. Tinda sukai aure bai tab’a kwana waje ba. Ko aiki ya rik’esa a Office komin dare sai ya dawo gida ya kwana. Toh wai meke faruwa ne. Wane irin al’amari ne wann..? Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son sanin wani hali Haidar ke ciki. Hakan yasa ta yanke shawarin zuwa gidansu Haidar din kawai. Komai ta fanjama fanjam. Idan ma zasu hadu da iyayen Haidar for the first time ne ita kam gwara taje tasan meke faruwa dashi tinda gashi baya ko daga wayarsa. Wata Zuciyar kuma ta soma raya mata toh kodai Shadow ne ya Sace Haidar to teach her a lesson tinda ga irin rabuwar da sukai a waya da Shadow d’in. What if Shadow ya cutar da Haidar.? What if wani Abu ya samu Haidar.. No bata fata.. She wouldn’t be able to take it idan wani Abu ya samu Haidar d’inta. Jikinta na rawa ta soma kiran layin Shadow “Tell me. Do you have Haidar.. Did you kidnap him.. Ka sanar Dani mai kayi ma Haidar..?” Ta k’arashe hankalinta duk a tashe sai rawa jikinta keyi. Murmusawa Shadow yai cikeda k’asaita daga d’aya b’angaren “Har kin sare ne..? Da wuri haka.?” Ta dan furzar da huci kad’an hankalinta na kuma tashi. Sai ta sassauta murya tace “Please don’t do anything to him.. Dan Allah kar ka cutar da Haidar.. Na yarda daga yanzu zanyi duk abinda kace amma dan Allah kar ka cutar min da Haidar..!” Ta k’arashe kaman mai shirin kuka. Shadow yai wata dariya irinta basawa “Dareen Dareen.! Yanzu kin tabbata I have both you and Haidar wrapped around my fingers. You don’t want to mess with me Dareen.” Ta lumshe idonta a hankali tana mai sadda kai kasa kaman yana ganinta “Forgive me.! It won’t happen again.. Please don’t do anything to Haidar.. Nayi alkawari bazan sake sab’a umarninka ba ko gaban Dodo akaje.” "Yai murmushi cikeda k’asaita “Good girl. Now that you realise your place, I want you to tell me where the hell is Haidar.?”" Mamaki ya cika Dareen. Ta girgiza kai kad’an “What do you mean.. Kana so kace min you don’t have Haidar.?” “I wouldn’t be asking you the same question if I have him.. Dareen wai meke damunki ne.? Shin amfanin ki Ya k’are wajen Haidar ne.? Are you that insignificant to him.? Do I need to replace you with another woman for me to push through with my plans.?” Saurin katsesa tai “No please.. Wllhi amfanina bai k’are ba.” “Then what the hell is the problem..?!” Kaman kunnenta zasu fice sabida sautin maganar. Jikinta na rawa take fad’in “Na fara zargin mahaifiyar Haidar ke yunk’urin rabamu.. Watak’ila ta gano cewa Haidar din yayi aure a b’oye ba tareda saninsu ba. Duk wasu calls da yake da ita yake tun muna Cuba. Idan ka mun izini zan tafi gidan su Haidar yanzu mai faruwa ta faru. Let them find out about me and Haidar.” Shadow ya daka mata tsawa da fad’in “Don’t you dare show your face to Kwaise Maitama.! This is not part of the plan. Bazasu san dake ba har sai ahalin Ya tarwatse ya lalace. Har sai sud’in sun yak’i junansu da gaske. Idan Har kika nuna kanki yanzu fad’an zai dawo kanki ne. Let them fight each other. Let them hate each other. Let them go down together… I am warning you kar ki kuskura ki nuna ma Kwaise fuskarki.. You know me Dareen. No body double crosses me. And I have no patience with people who screwed up.!” Ya k’arashe yana sakin huci. Ta jinina kanta a hankali “Got it. I won’t go there.. But what about Haidar.. I’m starting to worry.” “You are useless.!” Ya fad’i yana mai sakin gajeren tsaki kafin Ya katse kiran. Dareen ta koma ta zauna jikinta duk a mace. Yanda taga dare haka taga rana dan bata iya bacci ba. Ita dai tafi tunanin mahaifiyar Haidar ta fahimci wani abu gameda Haidar din sann bata zauna ba. ** "A can asibiti kaw wayar Mommy ne Ya tada dashi. Yai gajeren tsaki yana mik’ewa zaune daga nan saman sofa yanda ya kishingida ya soma k’ok’arin bud’e idonsa da yai masa nauyi. Gaba d’aya ji yake kaman an masa duka, dan a tak’ure a nan wajen ya kwana. Yakai dubansa gareta Har lokacin idonta a lumshe suke ga nauran oxygen mak’ale hancinta. Ya kuma duba wayarsa dake ci gaba da vibrating. Har lokacin Mommy ce mai kira. Bai d’aga ba har ya k’arashi ringing. Ya jima baiyi bacci da Ya makara irin haka ba. Ya duba yaga calls da dama ciki Harda na matarsa Dareen Wanda akasarin missed calls daga ita Ya samu. Harda tex message ta tura masa wanda bai bi takansu ba. Ya mik’e yana stretching arms d’insa. Ya shafi sumar kansa da duka hannayensa biyu. Nan wayar Mommy ya kuma shigo masa." Gajeren tsakin ya kuma yi “She won’t stop calling.!” Ya furta a hankali. Tsaban haushinta da yake ji sai ya jefa wayar a aljihu. Ya d’auki mabudin motarsa ya nufi k’ofa a gaggauce. Har ya isa k’ofa ya kuma juyowa ya dubeta. Har kawo wann lokacin da zaka tanbayesa ya kamanninta yake bazai iya tabtancewa ba. Abu d’aya ya sani shine baida burin da ya wuce ta tashi ta amsa masa tulin tambayoyin sa. Dan alk’awari yayi sai ya hukunta Mommy da duk wani Wanda yakeda saka hannu a tarwatsewar rayuwarsa. Ya furzar da huci kad’an kafin Ya janyo k’ofar Ya kulle. Yana tafe Mommy na kuma kiransa bai daga ba har ya shige mota ya soma tuk’i. Abubuwa fal cikin zuciyarsa. Anisa da bacci Ya kaurace a idonta tin daren jiya ta window ta hango motar Haidar Ya shigo gidan. Ta mik’e da sauri tana lek’ensa. He looks exhausted. She couldn’t believe it wai Haidar wajen bagidajiyar cen ya kwana kuma a asibiti. Ta lumshe idonta tana jin zuciyarta na mata ciwo. She couldn’t bear the thought of it. Suitcase d’insa da dake cikin motar Wanda bai unpacking ba tun bayan dawowarsu daga Cuba 2days back ya bud’e motar ya Ciro. Kai tsaye section d’insa ya nufa. Yai tsaye yana k’are ma gidan kallo Wanda a halin yanzu yarinyar ke rayuwa cikin gidan. Tin daga haraban sashen har zuwa parlor a gyare ne. Sai k’are ma gidan kallo yake dan shi mutun ne da baya shiri da k’azanta. Da yawan cleaning ladies na gidan da ake canzawa sabida shi ake canzawa. "Dukda an canza fasalin gidan hakan bai hanasa nufan k’ofan dakinsa ba. Saidai yana murda handle d’in ya jita a rufe. Sai ya lumshe idonsa kadan. Ya mance shid’in bak’o ne a gidan a halin yanzu. Ya d’anyi gajeren tsaki, ya d’ago yana duban k’ofan d’aya d’akin. He had no other option. Hakan yasa ya nufi k’ofan d’akin. Yai still kaman bazai bud’e k’ofan ba sai kuma ya murda handle d’in had’ida tura k’ofan d’akin. D’akin ma kaman dai ko ina a gyare yake. Ya tabe baki kad’an dan ba abin mamaki bane dan yaga babu datti yanda yarinyar ke zama tinda ya sani ma’aikatan dake gidan sunfi ahalin cikin gidan yawa amma dukda haka shi zai iya cewa b’angaren nasa bai tab’a kasance masa cikin gyara da zuciyarsa ta aminta dashi irin haka ba. Suitcase d’insa ya bud’e ya dauki abun buk’ata kafin ya nufi bathroom. Nan ma the same komai a gyare. Idonsa suka sauka kan inners dinta dake shanye a band’akin. Yai saurin janye idonsa sirirn tsaki na kufce masa. Sauri sauri ya sakar ma Kansa shower yana mai lumshe idonsa cikin k’ok’arin haramta ma idonsa abinda ya gani. Koda yai wankan ya mance babu towel cikin wann jakan. Ya d’ago kai yana duban bathrobe din dake mak’ale nan cikin bathroom d’in. Ya jima sosai yana bin bathrobe din da kallo wai shi Haidar zai amfani da somebody else’s bathrobe. Shi da ko towel d’in matarsa Dareen bai tab’a" amfani dashi ba. Ya lumshe idonsa a hankali yana furzar da huci. Akan dole ya d’auki bathrobe din Wanda baida haufi na yarinyar ne ya zira jikinsa ba don yaso ba. Sanda ya fito daga bathroom din Anisa na nan lab’e jikin k’ofa tana lek’ensa. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa ganin Haidar da gaske wanka yai a d’akin Ummul sann abunda yafi tada mata hankali harda bathrobe d’in Ummul d’in ta gani d’aure jikinsa. Dan bata mance ba zuwansu shopping tareda Ummul suka sai wann bathrobe din Wanda saida tai masu kauyanci akan bata iya amfani dashi ba. so definitely nata ne. Ji tai kuka na Neman balle mata. Ji tai k’afafunta suna barazanar gaza d’aukarta. Ta koma da baya a hankali had’ida jingina jikin garu. Ta soma tuhumar kanta anya batai gangancin saka ma Ummul poison din nan ba.? Anya wann ciwo da Ummul take bazai sanadiyan samun kusamcinta da Haidar ba. Ya zama dole ta yi duk yanda zatai ta tabbata Ummul da Haidar basu samu kusanci ba. Ta lumshe idonta da k’arfin gaske tana Jin bugun zuciyarta na karuwa. Da kyar da iya ficewa daga sashen cikin k’ok’arin maida hawayen da suka gaza Jin lallashinta. A b’angaren Haidar kaw bayan ya shirya nan ya tada sallan asuba da bai ba. Alamu sun nuna a spot din da yai sallah a wann wajen take sallah dan bayan hango Al’Qur’ani mai tsarki da yai saman drawer harda cazbaha a gefe. Ji yai zuciyarsa yayi wani irin tsinkewa sanda ya hango Qur’anin dan shi dai zai iya cewa rabonsa da ya d’auki littafin Allah mai starki ya karanta tin kafin yayi aure. Sai ya soma wasu irin tunanin da bai zai iya cewa ga abinda yake son tunawa ba. Yaji zuciyarsa ya cika da guilt din da bazai iya cewa na menene ba. Zuciyarsa yaji na masa d’aci. Yanaji kaman babu komai cikin rayuwarsa face tarin yaudara da k’arya. Yana tsaka da tunanin wayarsa ta soma ruri daga asibiti ake kiransa. Haidar ya daga kiran suna gaisuwa da Dr. Nan Dr ke sanar dashi sakamakon gwajin turaren Sun fito shi ake jira. Haidar ya jinjina Kai yace gashi nan zuwa right away. Sauri sauri ya nufo waje zai nufi motarsa ya hangi Anisa na zuwa. Bai damu yabi ta kanta ba yaci gaba da tafiya direction d’in motarsa. Anisa tai saurin cimmasa “Good morning…” Ta fad’i murmushi saman fuskarta. Bata damu da rashin amsa mata da bai ba ta k’arada “How’s your patient.?” Wani irin duba yake mata sann ya girgiza Kansa kad’an yana rage girman idonsa “What patient.?” Anisa ta dubesa da mamaki dan da alama a yan kwanakin yana mance abubuwa cikin sauri. Ta ya za’a ce majinyacin da ka kwana kana kula dashi ka mance dashi da safe..? Toh kodai ba asibitin ya kwana ba.? Something is definitely off. Sai ta k’ak’aro murmushin yak’e “I mean your wife..” Haidar dake k’ok’arin bud’e mota Cak ya dakata da abinda yake. Ya kaikaito sosai yana duban Anisa “Don’t… you dare call her my wife.! You don’t have the right.” Ya fad’i cikeda gargadi. "Anisa ta dan kauda fuska tana mai rausayar da ido “Fine, I won’t call her your wife again..” Ta dan girgiza Kai “" Are.. you leaving already..? I thought you just got here..?” Ta fad’i tana dubansa. “Why..? Do you have problem with that.?” Ta girgiza Kai “Mommy ce tace idan ka fito I should let her know because tayita kiran wayarka bata sameka ba.. And she prepares breakfast for you.” Tin sanda ta ambaci Mommy yanayin sa yai mugun canzawa. Ya gyara tsayuwarsa sosai yana duban Anisa “Tell her I’m ok.!” Har zai shige mota ya kuma juyowa ya dubi Anisa “No. Go tell her anything prepared by her..Is contaminated.!” Yana Ida fad’in haka ya bud’e motar ya shige had’i da fuzgan motar. Anisa tabi bayan motar da kallo tana sakin makirin murmushi. Ta tabbata Haidar zargin mahaifiyarsa yake. A fili take furta “Well done Neesa.! Yanzu ne zaki shana yanzu ne zaki bak’anta Ummul a idon Hajiya Kwaise. I have to make it looks like Ummul brings nothing to this family but bad lucks. Knowing Kwaise Maitama duk abinda zai shafi mutuncinta da na ahalinta musamman a idon abokan kasuwancinsu zatai komai dan ta kawar da wann abun.! Kamar haka zata kawar dake Ummul.!” Ta k’arashe tana sakin murmushin cin nasara. ** Yana isa asibiti Likitan ya nuna masa sakamakon da suka samu cikin wann bakin turaren humra akwai deadly guba da aka zuba ciki Wanda baida haufi shine Ummul ta shak’a Watak’ila na tsawon kwanaki. Huci kurum Haidar yake yana hango fuskar Mommy k’iyayyar da yake mata na ninkuwa cikin zuciyarsa. yana tuna sanda Anisa ta sanar dashi musamman Mommy tai ma yarinyar kyautar turaren. Ya jinjina Kansa kad’an kafin ya daga wayarsa yana dialing layin Hisham. Hisham yana daga wayar ya soma da “Huh.! Finally you are returning my calls.. I’ve been trying to reach you since yesterday.. Wai ina ka shige ne.?” “Find me a lawyer Hisham.. A very good one..!” Hisham ya girgiza Kai cikin rashin fahimta “Lawyer kuma.. Mai zakai da Lawyer.. Wait are you having a court case..?” “Looks like.” Haidar ya bashi amsa Kai tsaye. Hisham ya dan girgiza Kai “Then what about your family lawyer.. I mean..” “Wann ahalin ba nawa bane. Ka nemo mun Lawyer Hisham .. A very good one.” "Jin Hisham yayi shiru yasa Haidar fad’in “Look, idan bazaka yi bane. Fine zan nema da kaina.”" Hisham yai saurin dakatar dashi “Haidar wait.. What’s going on..? Wai meke faruwa ne.. Tinda ka dawo bamu hadu ba.. Yanzu ka kira kana maganar Neman Lawyer.. Waima kana ina ne yanzu.. Zan zo na sameka..” Bai Kai aya ba ya soma sinkayowa ta cikin wayar ana sanar da sunan wani Likita da ake nema a ER. Hisham yace “Are you in a hospital.? Haidar meke faruwa ne wai.. Mai kake a asibiti.. Waye ba lafiya.?” “You ask too many questions Hisham.. You know what.! Calling you is pointless.” Hisham bai bari ya katse wayar ba yace ya sanar dashi asibitin da yake gashi nan tafe. ** Sanda Hisham ya iso mamaki ne ya cikasa jin Haidar k’arar mahaifiyarsa zaiyi. Bai tsaya a nan ba har sai ya tabbata an gark’ame ta a gidan kasu. Hisham yaci gaba da girgiza Kai cikin rashin yarda “No Haidar.. You are insane.” “You are the one who’s sick in the head if you think I’m going to let that woman get away with everything she’s done..!” Haidar katse Hisham cikin karaji. Yau d’in ran Hisham a bace yake sosai da abokin nasa. Ya sani yana hak’uri da Haidar yana masa uzuri a lokuta da dama sann yana nusar dashi kan mahimmanci iyaye amma bai tab’a tunanin Haidar zai tafi da nisa irin haka ba. “Ce mun kake na nemo lauyan da zai tsaya maka ka kulle mahaifiyarka Haidar..? Haidar mhaifiya fah..! Shin kasan matsayin mahaifiya a wajenka.?!” “Kar ka sake ambaton wann matar da mahaifiyata domin mahaifiya ta gaske bazata tab’a yunk’urin halak’a D’anta ba.!” Girgiza Kai Hisham keyi “Ko meye mahaifiyarka tai maka matsayin ta da darajar ta ya wuce duk yanda kake tunani.” “Well I don’t give a damn.!” Haidar ya fad’i cikin karaji. Daidai lokacin d’aya daga cikin Likitocin da sukai ma Ummul surgery a jiya yazo wucewa. Hango Haidar da yai ya k’araso suna gaisawa had’ida tambayarsa jikin matarsa. Bayan Likitan ya shige Hisham ya dubi Haidar da mamaki “Matarka akaima aiki..? Wai Dareen ce a kwance a asibiti.?” "Haidar ya d’ago yana duban Hisham sosai “Not Dareen, actually.!”" "Cikin rashin fahimta Hisham ke girgiza Kai “Wait.. If not Dareen, then who.?” Ya kuma girgiza Kai “Wait a second. Haidar don’t tell me aure ka sakeyi secretly ba tareda sanin iyayenka ba.?”" “Throw that question to Kwaise Maitama. Ina ganin itace tafi cancanta ta baka wann amsar..!” Yai maganar yana sakin huci yana ci gaba da takowa kusan Hisham “Kasan dalili.?” Su duka biyun duban juna suke. Haidar na sakin huci yayinda Hisham ke binsa da kallon mamaki. Haidar yaci gaba “Well that woman da na girma na sani matsayin mahaifiyata ta kawo wata mata cikin rayuwata dan tayi amfani da ita ta kasheni. Wann matar da kake ta k’ok’arin karewa Hisham ta sa nayi signing agreement dan kawai ta cimma burinta akaina.” Hawayen zafin zuciya na gangarowa daga idonsa guda yake ci gaba “Kasan dalilin da yasa wad’ann mutanen suka amince na jagoranci project d’in.? It’s because I signed the marriage agreement Hisham.! Kasan dalilin da yasa na tafi Cuba.?” Hawaye suka ci gaba da zubo masa yayinda jikin Hisham yai matuk’ar yin sanyi. Haidar yaci gaba “That’s the reason Hisham. Wann shine dalilin.!” Ya jinina Kansa yana ci gaba da duban Hisham da ya zama speechless “Tell me Hisham. Wace irin uwa ce take ma D’anta haka. Tell me.. Wad’ann mutanen su suka haife ni..? Tell me akwai iyayen da zasuyi ma d’ansu irin wann k’iyayyar..? Tell me..! Answer the damn question.!” Ya k’arashe idanunsa na kuma rinewa Kai kace zai shak’o Hisham d’in ne. Cikeda tausayawa wann karon Hisham ke dubansa. Jiki a sanyaye yake waigawa dan ya tabbatar babu idon mutane kansu ganin Haidar d’in ya fice a giya. A hankali yake furta “Calm down Haidar.. Just try to calm down please.” Ya k’arashe yana kamo Haidar d’in had’ida zaunar dashi saman kujeran dake gefensu. Haidar ya had’e duka hannayensa biyu a shafe fuskarsa da tuni ta koma jazir. Hisham ya zauna gefensa yana k’ok’arin digesting maganganun. Tausayin abokinsa ne fal zuciyarsa. He couldn’t believe Haidar yayi going through duka abubuwan da ya sanar dashi. Shi yana ta murna Mahaifin Haidar da Haidar sun soma samun jituwa tinda gashi har ya amince ya basa jagorancin project d’in da suka jima suna fad’i tashi akai ashe ba haka bane. Ashe sun tilasta masa signing yarjejeniyan aure ne. Ya kasa yarda da abinda yaji. Marriage is a serious commitment abinda kullum mahaifiyarsa ke sanar dashi. Ya za’ace iyayen mutum sun masa irin wann auren.? Ya kasa yarda da abinda yaji. Sosai tausayin abokinsa ya cika zuciyarsa. Sun d’auki lokaci a haka kafin Hisham ya soma fad’in “I’m sorry Haidar. I didn’t know kayi going through duk abubuwan da kace. Kai hakuri Haidar.” Haidar ya dubesa sai ya dan girgiza kai “Na riga na gama yanke hukunci. I’ll have that woman arrested. Ta haka ne kawai zan San komai. Duk wani k’ulli dake rufe.” "Hisham ya zuba masa ido sai ya d’an girgiza Kai kad’an “No Haidar, ka nutsu kai tunani akai. Wann al’amari ne da ya danganci ahali. you can’t involve the authorities.. I mean it might turn out to be a scandal..”" “Well I don’t give a damn. Wann ahalin ya riga ya lalace.!” Hisham ya girgiza Kai “No Haidar. Wann Abu ne da zai shafi rayuwarka. Ba rayuwar ahalinka kawai ba..” Yai maganar cikeda nuna kulawa. “My life is already a circus Hisham.” Haidar ya basa amsa Kai tsaye. Hisham ya d’an lumshe ido had’ida girgiza Kai “No Haidar. You have no idea what you are talking about.. Haidar na taso not knowing wanene mahaifina. Ban San me ya faru a shekarun baya ba. Bansan menene tsakanin mahaifina da mahaifiyata ba.. Bansan meyasa ta b’oye min shi ba. Iyakacin abinda na sani shine ta sanar Dani ya Mutu. Ko danginsa tak’i ta nuna mun. Rashin sanin mahaifina da asalinsa yayi affecting dina Haidar. And I am the one paying the price. Rashin sanin asalina ya janyo min setback da dama a rayuwa. Ka yarda dani.” Ya k’arashe cikeda kulawa. Ya d’ago yana duban Haidar sosai “Haidar bana so irin abinda ya sameni ya sameka. Please mubi komai a hankali.” Girgiza masa Kai Haidar yai “At this point ban damu ba Hisham.! I’m so tired of everything.!” Rufe bakin Haidar keda wuya suka hangi Mommy da Anisa na fitowa daga mota. Haidar ya kafe Mommy da ido yana jinina Kai. Lokaci guda yake fad’i ma Hisham “Don’t let that woman escape. I’ll be back soon.” Yana ida fad’in haka ya nufi motarsa cikin sassarfa. Hisham na bin bayansa yana tambayarsa ina zai je shi amma inaa ko zarafin amsa shi Haidar bai samu ba sai ma fuzgar motar da yai ya bar wajen. Hisham ya dawo da baya yana girgiza Kai yasan shawo kan Haidar ai abu cikin lallama ba k’aramin aiki bane. ** A can company kuwa Daddy ya dubi Alhaji Gimba Ya kuma girgiza kai “Ni Aliyu Maitama ne zan d’auki k’afa na tafi asibiti duba yarinyar da Kwaise taima Haidar auren wasan yara da ita Gimba.? What for..?” “Because she’s family. D’anka yana aurenta.. Inaga ta cancanci muje mu dubata.” Alhaji Gimba Ya basa amsa kai tsaye. "Daddy ya kuma girgiza kai “If it were up to me, ban damu Haidar yai aure ko kar yai aure ba in the first place. Dan haka ban damu da sanin halinda Haidar ka iya kasancewa ciki ba balle yarinyar da kwaise tai masa auren shiririta da ita. Iyakacin abinda yake gaba na shine my business and my company. As long as matsalolinsu bazai affecting d’aya cikin biyun nan ba. Ban damu ba Gimba.!”" Kafin Daddy ya rufe baki Sakatariyarsa ta shigo a birkice tana nuna masa tablet din dake hannunta “Sir I’m sorry but you need to see this.” Ta k’arashe tana nuna masa fuskar tablet d’in yanda Daddy yaga hoton Haidar an had’a da wani hoto na amarya amma babu fuskar amaryar sai na Haidar. Saman article din an rubuta *Shahararren D’ankasuwan nan Engr Aliyu Maitama yayi auren sirri ma tilon D’ansa. Kawo wann lokaci Babu Wanda yasan wacece Amaryar ko ‘yar waye. Shin Aliyu Maitama ya aura ma D’ansa ‘yar d’aya daga cikin abokan adawarsa na kasuwanci ne dan ya ceci Kampaninsa?* “Damn it.!” Daddy ya furta a hankali. Ya juyo yana duban Alhaji Gimba “Ka gani ko.! kaga abinda nake fad’a maka ko. Wann yaron brings nothing to me but trouble.” Alhaji Gimba Ya girgiza kai yana kallon labarin “Yanzu zaka yarda da batu na da nace da kai mu tafi asibitin. Rashin nuna damuwarka zai janyo hankalin press garemu. Idan son samu ne yarinyar tana warkewa ka kira koda kwaryakwaryar walima ce tsakanin business partners dinmu ka sanar da Auren D’anka.” Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad’in bazai bari Haidar Ya tarwasta shi ba. A fusce ya fice Alhaji Gimba na take masa baya. ** A can asibiti kuwa Haidar ne ya k’araso da yan sanda har guda biyu. Hisham na ganinsa da yansanda ya mik’e yana girgiza kai “No.. This is not happening.! Haidar mai kake shirin aikatawa.?” Duk k’ok’arin Hisham na ganin Ya dakatar da Haidar bai nasara ba har saida Haidar d’in Ya kutsa kai cikin recovery room da aka aje Ummul. Hisham yai wani irin burki zuciyarsa na bugawa sakamakon hango mutum da yai kwance saman gado. Dukda na’urar oxygen dake saman hancinta bai hana zuciyarsa bugawa sau uku a jere ba. Ji yai Ya kasa jurewa Har saida k’afafunsa suka kaisa gaban gadon. A daidai lokacin da Anisa harma da Mommy suke duban Haidar cikin tsananin mamaki Wanda shigowarsa dakin kenan ga yansanda biye dashi. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *33* *©️Sameena Aleeyou… * Da tsananin mamaki Mommy ke duban Haidar. Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta “Haidar meke faruwa. Why are the police here..? Who are they here for.?” Haidar da Har lokacin dubanta yake. Wane irin duba da za’a iya fassara sa kai tsaye da duban k’iyayya Ya k’araso daidai gabanta. Ya d’auki dak’ik’ai a haka kafin Ya rank’wafo da kansa saitin kunnen Mommy “Isn’t it obvious? They are here for you Mommy. Sunzo ne su tafi dake.” Mommy ta dago cikin tsananin mamaki tana dubansa. Ta girgiza kai cikin rashin yarda tana kuma duban ‘yansandan. Sai ta kuma duban Haidar cikin k’ok’arin tantance shin mafarki take ko kuwa da gaske ne hakan ke faruwa. Haidar ne ya kawo yansanda su tafi da ita. D’anta da ta haifa. Tilon D’anta da take duk wani fad’i tashi sabida shi a rayuwarta yau ya kawo yansanda suyi arresting dinta. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Bata tab’a tsammanin za’a kawo wann gab’ar ba. Duk k’iyayya da Haidar ke masu daga ita Har mahaifinsa bata tab’a tsammanin k’iyayyar zai tasiri irin haka ba. “Aliyu.!” Ta ambaci sunansa cikin sanyin jiki “Ni ce ka kawo ma ‘yansanda su tafi dani.?” Ta k’arashe maganar nata tana nuni zuwa gareta da ‘yar yatsarta cikin tsananin shock. Haidar da Ya kafe ta da ido lokaci guda yake jinjina kai “Remember this is a hospital Mommy. You can’t make a scene here. Ki fita ki tafi tareda ‘yansanda a tsanake.” Mommy ta kuma girgiza kai tana jin hawaye na k’ok’arin ciko idonta. Ta tuna shekarun baya lokacin da ta haifi Haidar. Bata raine shi ba haka bata tab’a shayar dashi drop na nononta ba. Ko zai kwana yana kuka a matsayin jariri bata tab’a attempting lallashin shi ba irin yanda uwa keyi ma jaririn ta. Bata tab’a rungume Haidar yaji d’umin mahaifiyarsa ba. Ta tuna Asshe tasha nusar da ita cewa hakan zai iya yin tasiri tsakanin dangantakarta da D’anta domin kuwa a wann lokacin ake samun bond na uwa da D’ah. Wann shak’uwa soyayya da tausayi dake tsakanin D’ah da uwa a wann lokacin ake building d’insa. Ba birgewa bane sabida gayu da zamani kice bazaki shayar da D’anki da kika haifa ba wai gudun kar jikinki ya lalace. Kar ki losing figure dinki koh. Toh ki sani wann ba wayewa bane ba kuma birgewa bane. Ba birgewa bane kice ke bazakiyi d’awainiyar komai ma D’anki da kanki ba sai Nannies. At least ki samu lokaci na musamman tsakaninki da D’anki koda bazaki masa wasu hidindimu na d’abi’a ba. Ke uwa ce mai k’ok’arin k’ulla alak’a mai kyau tsakaninki da D’anki. Mommy ta dago tana duban cikin idon Haidar Wanda sanda yake jinjiri bata bar shi ya kalli cikin nata idon ba. Bata hango tausayinta ba bata hango soyayyarta ba balle jin k’anta sai akasin haka. Saiga hawaye suna gangarowa daga idon Mommy. “Haidar ni mahaifiyarka ce. Ni ce na d’auki cikinka tsawon watanni tara.” Bai bari takai aya ba ya dakatar da ita “Ki aje duk wani bayananki Mommy. Wann labarin da kike bayarwa akwai ayan tambaya akansa a halin yanzu. Kuma kinsan me? Whatsoever you’re hiding sai na binciko sa this is just the start.” Ya dubi ‘yansandan “You can take her with you officers.” ‘Yarsandar macen ta soma k’ok’arin matsowa da sauri Anisa ta shiga tsakiya tana hawaye take girgiza kai “Don’t touch her.! Don’t you dare come near her. Do you really know who you are arresting.?! This woman here is Hajiya Kwaise Maitama. You just can’t arrest her. Kudin zaku iya rasa aikinku gaba d’aya.!” Haidar ne Ya matso kusan Anisa yana sakin huci Anisa ma na hawaye take dubansa cikeda firgicin yanayin da taga Haidar din ciki. "“Who the hell do you think you are to interfere.? Get out of the way now. Or else..!” Bai kai aya ba Mommy ta katsesa “She’s my niece, and she has every right to interfere.! Unlike you she’s not ungrateful.. Wane irin D’ah ne zai kawo wa mahaifyarsa yansanda..?!”" Jinina Kai yake yana duban Mommy “Since you went ahead and brought it up.. Are you really my real mother.? Da gaske kece mahaifiyata kodai sato ni kikai.? Tell me now Kwaise Maitama. Who are my real parents.? Where are they.? Did you kill them and kidnapped me.? Answer me now.!” Ya k’arashe idonsa na kuma kadawa. Mommy ta kasa furta komai sai hawaye dake neman ciko idonta jin danta data dauki cikinsa tsawon watanni tara ta haifosa duniya na kokonto idan ita ta haifesa. "Haidar yaci gaba da jinjina Kai jin bata basa amsa ba “Of course you don’t have the answer. But I promise you, koda baki amsa yanzu ba zaki amsa a ofishin ‘yansanda.” Idonsa na kanta yaci gaba “Officers take this woman with you right now.!”" Yarsandan ta kuma matsowa Mommy taci gaba da girgiza Kai “No Haidar. Baka cikin hayyacinka..” Ta dubi yarsandar dake kokarin kamo hannunta ta aika mata wani kallo “You are doing this to lose your job. Do you have any idea who I am.?!” Yarsandar ta d’anyi gyaran murya “I’m sorry Ma’am but we have the warrant for your arrest.” Ta k’arashe tana k’ok’arin warware mata takardan hannunta. Mommy zata kuma magana Haidar ya katseta “Ki adana duka bayananki har a isa ofishin ‘yansanda. Zaki sanar dasu yanda akai kika Saka guba a turaren da kikai niyyan Kasheni dashi ta hanyar gayyato wata mace cikin rayuwana da sunan aure.!” Mommy ta saki baki wann Karon cikin rashin fahimta “Turare kuma.? Mai.. Ni.. wane irin turare.?!” Ta k’arashe tambayar cikin rashin fahimta yarsandar na k’ok’arin janyota ta daka mata tsawa da fad’in “I am Kwaise Maitama. You just can’t arrest me.! Idan gayyata ta ofishin ku kuke zan iya tafiya a nawa motar amma baku Kai kuyi arresting dina a k’asar nan ba. Even your superiors sunyi kad’an.!” Ta k’arashe tana sakin huci ta fito asalin a Kwaisenta. “And do you think you are above the law.? Just because you are rich and powerful.?!” Haidar ya katseta. D’aya Dansanda namijin ya tare gaban Haidar yana dannarsa “Calm down Engr. If that’s what she wants let’s do it her way then.” Ya dubi Mommy cikin risinawa yace “We are sorry Hajiya. We understand that you are an important figure in the society. Zaki iya zuwa ofishin mu a motar ki tareda rakiyar abokiyar aikinmu guda d’aya. I hope that’s ok with you.” Ya k’arashe cikeda risinawa. Takaici ya cika Haidar ganin yanda ikin tsaro ya lalace wai idan kanada matsayi da mukami cikin Al’umma treatment dinka daban ne. Idan kuwa haka ne zai tabbata kudi da influence da Hajiya Kwaise keda shi baiyi tasiri a shari’an da zasuyi da ita ba because he waged a war on her. Sai yanda k’arfinsa ya k’are. Haka suka fice salim alim dan Mommy dai bata so taja idon mutane da hankali kanta. Anisa na biye dasu tana hawaye tana ci gaba da rok’on Haidar. Duk dramar nan da suka gama Hisham na tsaye gaban gadon ta har dai suka fice gaba d’aya d’akin ya rage saura su biyu Hisham da Ummul dake kwance saman gado ido a lumshe. "Hannu yasa ya share hawayen da suka zubo masa. A hankali ya soma furta “You know, when I first met you.. I told myself… Hisham, this is the time.. You’ve finally found her… Your soulmate.. The love of your life.. After all the rejections.. All the heartbreaks..” Muryarsa ya tike sanda ya kuma share hawayen da suka Zubo masa “Daga k’arshe ka hadu da ita. But it turned out to be the worse of all..!” Ya kuma murmusawa yana girgiza Kai “Do you know what’s the funniest thing.. And yet the saddest.. I never got the chance to tell you how I feel about you.. It was all a dream.. Kuma zai tabbata a matsayin mafarki Wanda bazan tab’a farkawa ba.”" Ya hade hannayensa biyu alamun rok’o wasu hawayen na gangaro masa “You are now married to Haidar.. My best friend. He’s like a brother to me you know. Kuma zan iya sadaukar da komai nawa for him if I had to.. Koda kuwa rayuwana ne.. so Please ki daina zuwa mun a mafarki na.. Please..!” Ya k’arashe wasu hawaye masu ciwo na kuma gangaro masa. A hankali ya soma janyo k’afafunsa da k’yar cikin k’ok’arinsa na ficewa daga d’akin. Aiko yana ficewa yai bursting cikin wane irin kuka yana mai k’unshe bakinsa. Kai da gani kasan direct daga zuciya kukan ke fita. ** Motan Mommy da su Daddy suka gani ya fice daga hospital ga na ‘yansanda biye dasu ya sanyasu cikin tsananin shock da mamaki. Uwa uba da sukaga motar Haidar biye dana su Mommyn. Daddy ya dubi Alhaji dake gefensa “What.. What’s the meaning of this..? Motar Kwaise nake gani tareda ‘yansanda.!” Ya share gumin da yaji na tsartsafowa daga goshinsa “Kwaise da D’anta bazasu tab’a barina ba sai sunga bayana Gimba.!” Alhaji Gimba ya girgiza kai “Kar kayi magana haka Engr. Bamu san abinda ke faruwa ba. Let’s follow them and find out.” Ya k’arashe maganar yana mai sanar da driver da yabi bayan motocin su Mommy. Girgiza Kai Daddy yake sanda yaga sun nufi hanyar headquarter na yansanda “What.! No way Gimba.. I can’t be seen there.. Bazai yuwu a haskoni a ofishin ‘Yansanda ba it will be a disaster for our business. Kai kasan hakan.!” Yaci gaba da girgiza Kai yana fad’in karshen zamansa da Kwaise harma da D’anta yazo. Wani Kayan tashin hankalin shine suna isowa kusan kofan ofishin suka hangi masu nad’an rahotanni kowa na jefo masu tambayoyi cikin son sanin mai ahalin ke ciki. Daddy ya shafe fuskarsa da duka hannaye biyu yana girgiza Kai. Sai wani irin huci da yake furzarwa. Ya dubi Alhaji Gimba “Saida nace maka zuwa police station ba shawari mai kyau bane. Kaga abinda nake sanar dakai. Our company is handling one of the top government infrastructure project at the moment. We can’t afford to lose credibility a idon gwabnati.!” "Alhaji Gimba ya furzar da huci kad’an dan shima abun na neman fin k’arfinsa. Ya dubi Daddy yace “I’ll take care of the media. Zan tabbata basu publishing wani labari ba. Wancan labarin Auren Haidar da suka daura, I’ll make sure they take it off.. Ka shiga ka samu ahalinka.. Bamu San meke faruwa ba. Su d’in suna buk’atar ka.”" Da kyar da sud’in goshi Alhaji Gimba ya shawo kan Daddy ya amince ya nufi ofishin yayinda aka barshi nata kokarin ji da Media. Daddy yana shiga akai directing dinsa zuwa ofishin daukan bayanai yanda akai detaining Mommy ana koro mata laifukan da ake tuhumarta dashi ga Haidar tsaye a gefe ya kafeta da ido Kai kace shike interrogating din nata. “D’ansandan yaci gaba “Maiyasa kikai yunk’urin kashe yarinyar.? Shin kinsan turaren da kika bata turare ne mai d’aukeda guba.” "Zuciyar Mommy yaci gaba da tsinkewa. Shikenan boka ya sakata a uku. Ashe guba ya bata matsayin turaren da zai janyo Haidar zuwaga Ummul. Meyasa ta kasa yarda cewa boka mak’aryaci ne.? Dama da ake cewa boka makaryaci ne bata yarda ba amma yau ta yarda. Wato ya bata turare mai guba ciki idan Ummul ta shak’a ta Mutu shikenan sai ita kuma tai zaton asirin dake jikin D’anta ne ya karye kaman yanda Bokan yace. Zatai zaton tsafin Boka ne yai aiki. Ashe ba haka bane annamimin guba ya saka cikin turaren Wanda zai ajalin Ummul shikenan ita kuma ta hau kan aikinsa ne yai tasiri. Kai Kaicon rayuwa cikin b’ata. Gashi nan Boka mushuriki mak’aryaci ya sakata a uku, ya kulleta cikin bala’in da bata san yanda zata wanke kanta a idon mijinta da D’anta ba." Muryar Daddy suka sinkayo “Kisa Kwaise.?!” Mommy tai saurin juyowa tana duban Daddy hawaye na kokarin ciko idonta take girgiza masa Kai alamun a’a. "Daddy ya dubi ‘Yansandan “Would you please, excuse us.?”" "‘yansandan suka mik’e cikeda risinawa suna fad’in “Sure Sir, of course.!”" Haidar dake tsaye gefe jinjina Kai yake yana duban Daddy bayan ‘Yansandan Sun fice “Matarka tayi attempting kashe ni ta hanyar wann yarinyar da ta auro ta kawo cikin gidan da sunan matata.. Shiyasa ta dage sai nazo gidan na zauna tareda yarinyar. Tayi poisoning d’inta cikin turare sabida motive dinta kawai shine taga bayana. Wann matar ba ita ta haifeni ba.. Kuma yau zata fad’i a yanda ta sato ni.!” Daddy ya Kai k’ololuwa cikin b’acin rai a hasale ya maida dubansa ga Haidar “Ka daina maganar shiririta a nan.! Kwaise is your real biological mother. She gave birth to you. She’s your mother.!” "Ya maida dubansa ga Mommy “Tell me Kwaise, meke faruwa a nan.. Meye wann yaron yake fad’a..?!”" Mommy taci gaba sa girgiza Kai tana hawaye “Engr bansan komai ba. Wllhi bansan turaren da na baiwa yarinyar matsayin kyauta akwai guba ciki ba. Why would I poisoned her.. What could be my motive.? You need to believe me. Ina son yarinyar nan like my own. Kowa a gidan shaida ne. Ita kanta Ummul shaida ce.!” Daddy yaci gaba da girgiza Kai yana dubanta “You brought that girl into our family Kwaise. Bansan dalilin ki na dagewa sai kin aura ma D’anki wann yarinyar ba.” “Her motive’s quite clear. To use her and get rid of me without being detected. Maybe she realises that I’m no longer useful to her. That I stoped being her weapon. She couldn’t use me to get what she wants. So she decided to get rid of me…” Yaci gaba da jinina kai “When I was a child she used to call me…A useless child. Yes useless.! D’ah maras amfani. Haka kike kirana Mommy… Banida amfani cikin rayuwarki.. Yanzu da kika tabbata banida wani amfanin da zan miki.. I couldn’t be what you wanted me to be.. I couldn’t make you proud.! I couldn’t be just like him. Haka ne.?!” Ya k’arashe yana nuni da Daddy hannunsa har rawa yake jijiyoyin jikinsa na kuma mik’ewa. Daddy ya katsesa “Enough.! I’ve had enough of you and your Son Kwaise. I won’t allow your problems to affect my business in any way.!” Haidar na huci yake dubansa “Is this about your business again Daddy..?” Yaci gaba da huci yana duban mahaifin nasa “This is about me and my life Dad..!” “Of course I do not give a damn about you and your chaotic life.!” Daddy ya katsesa da fad’in haka cikin tsananin huci. "Haidar na girgiza Kai cikin rashin yarda yake duban mahaifin nasa. Ya saki murmushi mai ciwo “Those words ain’t new to my ears. But I want you to keep this in mind. You can use all the power and influence you have. Amma ina mai tabbatar maka, your wife won’t get acquitted until she answers all my questions.! Until she pays for all the crimes she’s committed.!”" Bai Kai aya ba Daddy ya daura masa Mari maiji da lafiya su duka suna huci yayinda Mommy tai saurin mik’ewa ta shige tsakaninsu tana kuka sosai. Haidar na jinjina Kai yake duban iyayen nasa “All I ever wanted is a quite and happy life. Away from all this chaos. Yana maganar Mommy tana dubansa hawaye na gangaro mata. Ta rasa tausayin waye take ji cikinsu gaba daya. Haidar yaci gaba “Amma Idan wann shine Abu na k’arshe da zanyi a rayuwata zanyi. Na ranste sai na isa k’arshen komai. Mark my words.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga room d’in. Mommy ta dubi Daddy “Engr we need to stop him. Da gaske yaron nan ba cikin hayyacinsa yake ba.” “Ki min shiru Kwaise. This is all your fault you know. I’ve warned you.. Na Miki gargadi amma bakiji ba. I knew nothing good would come out of this marriage da kika dage sai kinyi ma d’anki. Ga abinda nake Miki gargadi akai amma bakiji ba.” Mommy ta girgiza Kai “Ka yarda dani Engr wllhi ban saka guba ma yarinyar ba.” “Just shut up Kwaise.! Meke tsakaninki da wann yarinyar is absolutely none of my business..” Ya kuma matsowa yana nunata da yatsa yana sakin huci “Na gargadeki cewa idan har wann watsattsen auren da kikai ma wann D’an naki ya shafi Kasuwanci na ki kuka da naki auren.!” “Har yanzu barazana kake mun da Aurena.” Mommy ta katsesa. Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye “Shin meye matsalar.? Auren da nai ma Haidar ne matsalar kokuwa dai har yanzu akan Fannah ne da abinda ke cikinta.!” Cak Daddy ya tsaya ya dago yana dubanta yana jinina kai “You are right Kwaise. You are absolutely right. You should be grateful ban miki korar kare ba bayan abinda kika mun.!” Mommy taci gaba da hawaye tana duban mijinta nata yanda yaci gaba “Bayan abinda kika min nayi hakuri na zauna dake da abinda kika haifa tsawon shekarun nan.!” “Nasan albarkacin Haidar naci kake zaune Dani kawo wann lokacin.!” “Will stop with your guilt tripping Kwaise.! Idan kinsan da haka kar ki bari na tuna Miki abinda kika aikata mun a baya.!” Mommy na hawaye taci gaba “Meyasa baka barmu munyi tafiyarmu ba nida Haidar idan har zaka rik’esa ka kasa accepting dinsa tsawon shekarun nan.?!” Taci gaba da hawaye “Na sani nayi kurakurai da dama a baya. Kuma babban kuskuren da na kasa yafe ma kaina shine k’iyayyar da na nuna ma Haidar a lokacin da na haifosa ka k’i accepting dinsa.” Daddy Yaci gaba da jinina kai yana huci yayinda Mommy taci gaba da hawaye. “How do you expect me to accept your child bayan kinsa na sheganta D’an wata.? Ta ya kike zaton zan rayu da naki D’an na bude ido na ganshi yana girma bayan akwai wani D’an nawa can Wanda na sheganta sa da bakina. A kullum na bude ido naga D’anki Kwaise ba komai yake tuna mun ba face mummunan kuskuren da na tapka. Kuskuren da na zartar da hukunci akansa ba tareda bincike ba.!” Ya jinjina kai kafin yaci gaba “Dik randa naga Haidar sai na tuna akwai D’anuwansa can wanda naki accepting d’inshi tun yana ciki. Ta ya kike zaton naki D’an zai girma da soyayya na.? Ki gode ma Allah da na bama D’anki sunana.” Cikin kuka Mommy tace “Haidar D’anka ne dole ya amsa sunan ka.” “Amma kin haramta ma wani D’an nawa Ya amsa sunana Kwaise.!” Ya katseta da fad’in haka jikinsa Har rawa yake. Hawaye yaci gaba da gangaro ma Daddy “Na tuna miki zaluncin da kika mun ne.?! Kwaise kin kawo wani k’ato yayi fyade wa Matana a cikin gidana.. Da aurena akanta da cikina a jikinta Wanda kika sa na Sheganta shi tin yana ciki baizo duniya ba. Kinsa na rabu da matata a WATA UKU na farkon aurenmu. Kinsa na tura Fannah gidan Yari ta raini cikinta a can ta kuma haifesa a can. A gidan Yari ta haifi D’ah na da na sheganta sabida son zuciya irin naki Kwaise.!” Mommy tai bursting cikin kuka tana girgiza kai take fad’in “Wllhi Allah shine shaida na ban basa umarnin ya aikata ma Fannah wani abu ba. Sharri kawai nace Ya mata. Allah shine shaida na babu fyad’e a plan d’in.” “Just shut up already.! Kar ki sake ambatan sunan Fannah da wann bakin naki.!” Daddy ya katseta. Haidar Ya banko k’ofar Ya shigo cikin wane irin yanayi yake duban iyayen nasa “Wacece Fannah..?!” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *34* *©️Sameena Aleeyou… * "Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy “Kina iya sanar da D’anki zunubanki idan kinso. I’ll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D’anki ku min sanadi ba .” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice." Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga mahaifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k’afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata “Tell me Mommy. Wacece Fannah.?” Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D’an nata kafin ta jinina Kai “She… She was your Dad’s wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu.” Haidar ya jinina Kai a hankali “So Daddy yanada wata matar a baya.?” Mommy ta jinina Kai a hankali. "“What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.?”" Mommy ta girgiza Kai a hankali “I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba.” “Meyasa kika nemeta.?” Ya kuma jefo ma Mommy tambaya. Ta d’ago tana dubansa “Dan na nemi yafiyarta.” Ya kuma jinjina Kai “So tell me Mommy. Mai kika aikata mata.?” Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai “Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin… Watak’ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D’ah na.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido. Waiwaye… Years back..! "Borno State, Maiduguri." Hajiya Kwaise zaune saman kujera a madaidaicin parlorn ta Wanda ya tsaru iyaka tsaruwa a wancan lokacin. Kuka take sharshar da hawaye a lokacin da taji sautin wayar landline na gidan na kururuwa. Ta mik’e da kyar ta isa ta daga wayar. Daga d’aya b’angaren muryar Aliyu Maitama ta sinkayo “Kwaise an d’aura auren.. An daura auren.. An daura aurena da Fannah..” Yanda yake maganar zaka fahimci kaman Wanda aka saka shi dole haka yake maganar. Bata k’arasa sauraro ba ta saki wayar ya fad’i kasa tana mai kuma rushewa da kuka. A haka Asshe ta k’araso ta sameta. Asshe k’anwarta da tin bayan da Kwaise tai aure rik’on Asshe ta dawo hannunta dama ba wani girme mata sosai tai ba kuma su biyu iyayensu suka Haifa. Mommy ta dago tana duban Asshe cikin rawar murya “Asshe Aliyu yayi aure.. Aliyu ya auri d’iyar leburan dake aiki k’arkashinsa Wanda block na gini ya fado ya fasa masa Kai ya rasa ransa dalilin haka. Asshe Aliyu na ya aure ‘yar wann mutumin..!” Ta kuma rushewa da kuka. Asshe ta dubeta cikeda tausayawa “Aunty Kwaise mijinki loves you. Wllhi koda ace yayi aure bazai daina sonki ba. Ni fah ban taba ganin wacce mijinta ke mata irin Son da Uncle Engr ke Miki ba. He loves you dearly. Zai komai dan farin cikin ki Aunty Kwaise. Keda kanki kin fada Aurensa da wann yarinyar Fannah k’addara ce kawai batada kowa bayan mahaifinta da ya Mutu ta dalilin aiki k’ark’ashin ma’aikatan mijinki da yake. Wllhi na tabbata dan ya taimaketa ya aureta. Ba wai dan yana So ba ko dan ya daina sonki. Idan ba so da mijinki ke Miki ba. Mutum kaman Engr Aliyu matashi mai tashen kud’i ga k’uruciya ga dama na rayuwa da ya samu ai da tuni ya cika gidan nan da mata sai yanzu da k’addarar hakan tazo. Dan Allah kar ki saka wani Abu a ranki.” Mommy ta dago tana share hawaye “Asshe bazaki taba ganewa ba. Namiji Akan mace sunansa namiji bazakiyi shaidarsa ba. Nidai bazan iya sharing Mijina da wata ba balle wann bagidajiyar ‘yar lebura.” Asshe ta furzar da huci “Toh ya kike so ai yanzu.?” Mommy bata iya bata amsa ba sai mik’ewa da tai ta shige k’uryar daki wani sabon kuka na taso mata. Haka ta yini a daki bata aikin komai sai kuka. Asshe ke Lek’ata lokaci zuwa lokaci. Ko abinci Mommy ta kasa ci ranan. Can dare taji shigowar motar mijinta. Nan ta Mike da sauri tana lek’en window. Hangosa tai tareda Amaryar sa tana biye dashi kanta a k’asa. A haka suka shigo har parlorn gidan. Koda Daddy ya shigo ya tadda Mommy juya masa baya tai. Ya k’araso jikinsa duk a mace “Kwaise. My love..” Sai ya kasa ci gaba da magana yayinda kukan Mommy ya karu. A hankali ya isa ya rungumeta ta baya. Su duka biyun hawaye na gangaro masu. Cikin kwantar da hankali yake furta “Wann shine k’addarar mu Kwaise. Allah ya k’addari Fannah zata shigo cikin rayuwarmu. Yarinyar abun tausayi ce bata da kowa sai mahaifinta da ya rasu sakamakon aikin da yake k’ark’ashina. Mommy na hawaye take girgiza Kai “Ba hurumi na bane na tuhumeka dan ka k’ara aure Aliyu. Addini ya halatta maka auren mata d’ai d’ai har hudu idan kanada hali. Kawai alfarmar da zan rok’a daga gareka shine Kai Adalci tsakaninmu.” Ya murmusa yana dubanta. Ya saka hannunsa ya share hawayen da suka gangaro mata “I love you Kwaise.. So much..! Ban tab’a son wata mace sama dake a rayuwata ba. Ki tayani addu’a Allah ya bani ikon yin Adalci tsakaninku because.. I’m not sure idan son da nake Miki zai barni na kamanta adalci.. Kwaise ba kece cikin tashin hankali ba. Ni ne cikin tashin hankali.. Because son da nake miki baida match da ko wace mace. When it comes to you wayona baida yawa Kwaise.” Mommy ta tsaresa da ido kafin ta k’ak’aro murmushi ta riko hannayensa “You can do this in sha Allah mijina. I’m here for you.. Tashi na shiryaka amarya tana jira.” Kaman rak’umi da akala haka Daddy ya Mike Mommy ta shiryawa tsaf harda su fesa turare kaman ba ita ce ta yini kuka a daki ba. Koda suka fito suka tadda amarya ma Mommy bata nuna komai ba. Asshe taita mamakin canzawan ‘Yaruwar tata. A haka rayuwa ke tafiya masu Mommy bata nuna komai ga Daddy ya saki jiki ganin hankalin Kwaise ya kwanta. Ya maida hankali kan bunk’asa k’aramin kampaninsa a nan birnin Maiduguri da Kewaye. Watan Fannah biyu a gidan ta fara nuna alamun masu juna biyu. Kwaise da kanta ta dauketa ta kaita asibiti akai mata gwaji aka tabbata tana d’aukeda karamin ciki na tsawon watanni biyu. Sosai Mommy ta nuna marnanta har kaman tafi Fannah murna. Lokacin Daddy na cuku cukun Kai Kasuwancinsa tsakanin Abuja da wasu jihohi Mommy da kanta tai masa Albishir na cikin da amaryarsa ke dashi sanda sukai waya tinda shi a wann lokacin ya rage zaman Maiduguri. Farin ciki wajen Aliyu Maitama baya misaltuwa. A wann lokacin yai ma matan nasa kyauta ta sabuwar mota dal ‘yar yayi a wancan lokacin. Ya kuma d’ebesu gaba daya suka tafi Umra suka gode ma Allah da kyautar da yai masu dan a lokacin aurensa da Kwaise kusan shekaru biyar kenan babu rabo saida Fannah ta shigo sai gashi ta samu daga shigowarta. Bayan dawowar su daga Umra Daddy ya tafiya ta kasuwanci da zai d’aukesa kusan wata guda. Asshe ta dubi Mommy wacce keta faman sakin murmushi tana gustiran Apple. Ta d’an girgiza Kai tace “Kenan kin yarda ta rigaki Haifa masa Magaji Aunty Kwaise.? Ni fah kirkikin da kike ma matar nan tai yawa. Ke kaman bakijin kishi irin na mata da ake fad’a.” Murmusawa Mommy tai “Asshe kenan. Sarai nasan abinda nake kuma lokaci yayi da zan executing plan dina. Trust me.” Asshe ta girgiza Kai “Toh amma Aunty Kwaise mai zakiyi yanzu.?” “Wann cikin da Aliyu Maitama ke rawar k’afa akansa da Kansa zai sheganta sa tin a ciki kafin a haifosa. Zai ma Fannah korar wulak’anci. Wann cikin kuma Engr Aliyu Maitama bazai taba accepting dinsa ba.” Asshe ta girgiza Kai “Amma ta ya zakiyi hakan.?” Mommy ta kuma gyara zama “Uban Fannah labourer ne a kampanin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila’ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya ganta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake aiki k’ark’ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka masa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan ance har gobe yana mutuwan sonta.” Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya “Toh ya abin zai kasance.?” Mommy ta kuma murmusawa “Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K’anwata.” Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta “Kaman ya kenan Anty Kwaise.? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan.” Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu Maitama zai dawo gari ya kamasa a d’akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne.” Ta k’arashe tana sakin murmushi. Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin Fannah yai ba tareda kowa ya gansa ba. Fannah da fitowarta kenan daga band’aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet da gajeren wando. Jikinta ya d’auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had’ida toshe bakinta da k’arfin gaske. Fannah tana kuka tana k’ok’arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta. Daddy ya dawo cikeda d’oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b’angaren ta d’aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k’ato rungume da matarsa dake d’aure da towel ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa. Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad’in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amincewarta ba fyade yai mata. Daddy ya shak’osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b’acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d’aure jikinta. Ta dawo ga Daddy tana fad’in “Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba.” Daddy ya dubeta da mamaki “Dama ya Saba zuwa.?!” Mommy ta jinjina Kai kaman gaske “Ai idan Baka nan yakan zo. Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa.” Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace “A’ah.. Wann mutumin ai mak’ocin su k’awata Baana ce. Kuma ta…” Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana. Mommy tace “Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?” “Ta sanar dani shi d’in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu… Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!” Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k’arfin ta “Haka ne.? Wann D’an iskan saurayinki ne.?!” Ya tambaya yana dubanta. Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa “Ki amsa min..! Haka ne..!” Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad’in “Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk’ar so. Kuma mahaifinta ya min alk’awarin bani ita.. Amma ‘yanuwanta Sun karya wann alk’awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu’amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..!” Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b’arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka. Daddy ya ci gaba da huci “Ga b’arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la’akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk’a sa ma shayibu yana fad’in bari yaje ya duba section d’insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d’insa na cikin gidan an kwashe kud’ad’en ciki. Koda aka mik’a Auwalu ma ‘yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud’ad’en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud’ad’en dan su gudu su bar gari. Daddy bai saurara daga b’angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar. Sosai take kuka duk’e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari.” Yana ida fad’in haka ya mik’e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari. ‘Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad’in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k’ila da an fara k’irga ma abinda ta haifa watanni. "Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k’ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu." Sam bata San Daddy ya shigo ba take b’arin zance. Daddy ya dubeta da mamaki “Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!” Sai Mommy ta mik’e tana girgiza Kai “A’a Engr dan Allah ka saurareni.” “Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud’e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma mata..? Kece kika shirya komai..?!” Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai “Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba..” Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa. Mik’ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d’inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d’aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab’akar da tai sabida halin k’unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu’amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k’unci hopping idan ta haihu zuwan D’an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa “See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d’an da zakai alfahari dashi.” Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin. Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik’e cikin hannunta baiba balle ya karb’e sa. Sai ma mik’ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D’anta sai hidiman bunk’asa Kasuwancinsa da yake. K’unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d’awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D’anta da Daddy yai take. Ta duk’ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d’an matsayin D’a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta’allak’a ga bunk’asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad’ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab’a ganin k’ok’arin Haidar ba har kawo girman sa. Wann kenan. (Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan ‘ya’ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da ‘ya’yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa). * Ci gaban labari.. Haidar ya share hawayen da suka zubo masa “So that’s the reason why he hates me.!” Ya fad’i haka Kansa a kife. Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata “No Haidar.. Your Dad doesn’t hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That’s just.. his way of punishing me.!” “Well I don’t care.!” Ya fad’i haka yana mai buga teburin gabansa da k’arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad’in “I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.!” Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake. Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai “I’m sorry my Son.. I’m sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!” Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d’agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa. "Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta “Serving jail sentences won’t be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won’t rest until I see you locked up in jail.. Koda zaki k’arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don’t want to see your face ever again.!” Ya k’arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik’e ya nufi k’ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k’ofa ya fice cikin tsananin huci.." SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *35* *©️Sameena Aleeyou… * Bayan Daddy ya turo mata lawyer d’insa aka basu waje dan su gana. "Lawyer ya dan dubeta sai ya jinjina Kai yace “I don’t want to say this, but a halin yanzu farkawar matar D’anki ne kawai zamu iya cewa zai kub’utar dake Hajiya. Sabida ba zargi ake ba keda kanki kika tabbata kin bata wann turaren.”" Mommy ta girgiza kai “Kana so kace baza’a iya granting bail dina ba a halin yanzu.?” Yai shiru kaman mai nazari “I’m afraid yes. Laifin babban laifi ne.. Kuma akwai evidence a hannu. Zai matukar wahala. But still nothing money can’t buy in this country. Akwai hanyoyi da dama da za’a bi dan a rufe case din. Amma abun shine kince baki so ai amfani da kudi wajen siyan freedom d’inki.” Bai Kai aya ba tai saurin jinjina masa Kai “It will only complicate the situation even more. Ni a halin yanzu bana son duk wani abinda zai hadani fad’a da Haidar. Idan har nai amfani da kudi ko wani k’arfi nawa D’a na zai k’ara k’ina ne kan wanda yake. I want to make things right with my son..Ba wani hanya da za’a bi wanda rashawa bazai shiga ba.” Lawyer yai shiru sai kuma ya girgiza Kai “Saidai idan ita yarinyar ta farka tayi withdrawing charges. Let’s pray she wakes up soon.. Shine kawai mafita.” Mommy taja gauron numfashi had’ida jinjina Kai. Ta k’udiri niyyan bazatai wani abun da zai kuma b’ata ta a idon ahalinta ba. A haka dai sukai sallama da Lawyer aka kaita detention cell dinta. Ta d’ago ido tana duban cikin cell d’in. Sai ta tuna lokacin da tai ma Fannah sharri itama kurkuku aka kaita. Hawaye suka gangaro ma Mommy. Tabbas ta kuma yarda duk abinda ka shuka a rayuwa zai dawo maka harda riba. Sai gashi nata D’an ya turata kurkuku bayan ta tura Fannah da jaririn da baida laifin komai kurkuku. Dirshan Mommy ta duka wajen hawayen nadama na gangaro mata. Anisa ce ta k’araso k’ofan cell d’in hawaye tab idonta. Ta duka tana duban Mommy “Mommy..!” Anisa tace cikin murya irin ta mai kuka. Mai ta dago tana duban Anisa. Yayinda Anisa taci gaba da share hawaye tana fad’in “Mommh you will get out of this place soon. I’m sure of it.. Zaki fita in sha Allah. We all believe you are innocent.” Ta k’arashe tana mai kamo hannayen Mommy. "Mommy ta murmusa tana duban Anisa “I hope so Anisa. Muyi addua Allah ya tashi Ummulkhair na tabbata bazata barni a nan ba, ita d’in tanada zuciya mai kyau.”" Wani k’atutun bak’in ciki ya tokare ma Anisa mak’oshi Jin Mommy na yabon Ummulkhair dikda kaman itace sanadiyar kasancewarta cikin halin da ta tsinci kanta ciki. Anisa ta jinjina Kai sai kuma tace “But Mommy Meyasa abubuwa suke faruwa tinda Ummul ta shigo cikin ahalin nan. I don’t want to think about it amma I couldn’t help.. Tinda ta shigo cikin ahalin nan problems keep piling up.. Misfortune after misfortune.. It’s like she brings bad luck with her… Mommy I’m only concern about you..!” Ta k’arashe wasu hawayen na gangaro mata. Ganin Mommy tai shiru kaman nazari yasa Anisa ci gaba “Mommy what if.. What if she’s a curse or something.. hasn’t this crossed your mind..? Mommy Ammi ce kawai fah tasan asalin Ummul..” Mommy tai shiru tana nanata maganar Anisa cikin ranta. Kuma fah Boka ne yace ta auro ma d’anta mace irin Ummul. The same Boka da ya bata turare mai guba ciki. Maganganun Anisa akwai k’amshin gaskiya tinda Ummul dai dama duk namijin da yazo nemanta gudu yake hasalima Shiyasa Boka yace ta aura ma d’anta dan ta zamto makarin asirin da akai ma d’anta. Anya batai gangancin kawo irin wann macen cikin rayuwar D’anta ba.? Anisa ta kafe Mommy da ido makirin murmushi saman fuskarta. Plan dinta na tafiya yanda ya kamata. Sannu a hankali sai ta fitar da Ummul daga rayuwarsu. Ganin Mommy na k’ok’arin maidoda dubanta gareta ya sanyata ta kuma canza fuska ta koma kalar tausayi. Ta kamo hannayen Mommy “Mommy I’ve brought food for you. Nasan bazaki ci abincin nan ba. Bai kamaceki ba. Mommy you don’t belong here. You are Hajiya Kwaise Maitama.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin tunasar da Mommy wacece ita dan da alama kaman Mommyn ta mance. Murmushi Mommy tai tana duban Anisa “Thank you Anisa. Thank you for being here for me.” Anisa ta murmusa “Anything for you Mommy.” A haka dai sukai sallama da Mommy tareda alk’awarin kullum zata zo ta dubata har dai al’amra su daidaita. Anisa tana fitowa daga station taga wayar Leenah na shigo mata. Gabanta ya yanke ya fad’i. Leenah kuma a daidai wann lokacin.? Rage speed din motar tai kafin ta daga wayar tana mai rausayar da ido “Girlfriend what’s up.!” Ta fad’i zuciyarta na mata wasai dan wani dadi take ji Mommy ta soma fad’awa tarkonta. Leenah ta murmusa daga d’aya b’angaren “Da alama duniya tana Miki dadi kawata.” Anisa ta murmusa “Keda kika sani. Shawarin ki yayi kawata dan komai ya tafi just as we planned.” Leenah ta kuma murmusawa “Tinda nayi nawa part d’in kuma kwalliya ta biya kud’in sabulu. It’s your turn to return the favor Neesah.” Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta murmushin fuskarta na gushewa “Wha.. What do you mean. What favor.?” “Oh c’mon Neesa. Everything has a price in this life.. You said it yourself..” Ta kuma murmusawa “Wait.. Na tuna miki ne.? Well bari na tuna miki statement dinki “Leenah idan kika taimakeni Nima zan taimakeki. Zan tabbata baki k’arashi rayuwarki washing white cloths with bleach.. Just to keep them white. Now it’s the time Neesa.” Anisa tai murmushi Wanda yafi Kama da yak’e “Idiot.! Ba yanzu nace zan Miki hanyar arziki ba. Until I become Mrs Haidar Maitama.” Dariya Leenah ta fashe dashi “Don’t try to be funny Neesa. I want those money now. Kuma yanzu dole zaki bani.” Cikeda mamaki Anisa tace “Wait.. Are you trying to betray me.?” Leenah ta girgiza Kai “No I’m just being honest here. What if I open my mouth..? Mai zai faru idan na sanar da Kwaise Maitama wacece dalilin tafiyar ta jail.? Meye kike tunanin zai faru.?” Anisa ta kuma girgiza kai cikin rashin yarda “Are you trying to blackmail me Leenah..?” "“You can take it that way Neesa. But I want money in exchange for my silence.! 1million, Anisa.”" Anisa da ta kasa rufe baki girgiza Kai ta kuma yi “Leenah are you crazy. Ni.. ni ce kike blackmailing..? Ni Anisa.? Your very own best girl.?” Dariya Leenah ta fashe dashi “Oh Neesa. Kinsan matsalarki. You are too dumb. Baki fahimtar komai.. Na baki nan da three days kiyi abinda nace ko na bud’e baki na. I know you wouldn’t like that.” Murya na shaking Anisa ke fad’in “No Leenah you can’t do that to me. Leenah 1M fah kike magana in three days.. A ina zan samu..? Kin sani sarai Abba na Alhajin mak’o ne kudi basu fita hannunsa saida bayani.. Ko mahaifiyata ma bata ci balle ni..” "“I don’t care Neesa. After all, a gidan Aliyu Maitama kike zaune. Idan sata zakiyi ki bani kudi ban damu ba. Kuma ki sani wann phase one muke. Next kudin zai ninka na farko.!” Tana ida fad’in haka ta katse kiran." Dole Anisa ta nemi waje tai parking tana nanata maganganun Leenah. Yanzu ya zatai da Leenah.? Just when she thought abubuwa suna tafiya mata yanda take so Leenah ta bijro mata da wani batu. Yanzu ya zama dole ta nemo kudade ta ba ma Leenah dan tai shiru.. Bazata bari Leenah ta bata mata shirinta ba. But me zatai..? Ta ina zata samo miliyan d’aya cikin kwanaki uku.? Ta shafe goshinta tana dukan steering wheel da k’arfin gaske tana fad’in I hate you Leenah.! ** Dareen na ta faman safawa da marwa tana kuma duban labarin Auren Haidar cikin wayarta da yazo mata a bazata. Ga hoton Haidar amma babu fuskar amarya. Ta rasa gane wani aure ne Haidar yai kokuwa dai aurensu da ita ake nufi a wann labarin tinda babu Wanda yasan da auren nasu.? Ta kuma furzar da huci tana shafe goshinta. Things are getting messy. Komai na Neman ya kufce mata. No banda Haidar.. Batai shirin rasa sa ba.! Juyowar da zatai ta gansa tsaye gabanta cikin wani irin yanayi da bata tab’a ganinsa ciki ba. “HISHAM!” Ta furta a hankali. Hisham yaci gaba da takowa gareta. Saida ya iso zuwa gabanta kafin yaja ya tsaya. Suka kwashe dak’ik’ai a haka “Call me SHADOW. Kaman yanda kika saba.!” Ta furzar da huci tana girgiza Kai sai kuma ta d’ago fuskar wayarta tana nuna masa “You did this.. right.? Kai ka shirya labarin nan.. I thought kace ba yanzu bane lokacin da iyayen Haidar zasu san Dani..” Fincikar wayar yai had’ida jifa dashi “Of course ni na fitar da labarin kaman yanda na fitar da sauran.. Kaman dai ko Yaushe. Amma kinsan me? wann matar da kike gani da sunan matar Haidar ba ke bace.. Ni kaina bansan wacece ita ba sai bayan da na sa aka fitar da labarin.!” Yaci gaba da huci yana duban Dareen “Haidar has another wife now.!” Dareen ta kasa rufe baki sabida mamaki yayinda Hisham yaci gaba da jinjina Kai yana huci “Yes he has another wife..! That imbecile brother of mine has another wife..! Kuma wann matar ba kowa bace face macen da ban tab’a son wata mace kaman ita ba a duniyar nan.. He’s taking everything away from me kaman ko Yaushe. My Father..! My life… And now the love of my life UMMUL..!” Ya k’arashe sai sakin huci yake. Dareen ta kuma girgiza Kai “But.. But.. Ta ya hakan ya kasance.?” “Because you are an imbecile. Incompetent.. He’s just a man.. But you couldn’t handle him.” “Ta ya hakan zai zama laifina idan kaima da kake amininsa baka San da labarin Auren ba.?” "“Because he doesn’t tell me everything. Har sai ya zartar da hukunci yake sanar dani.. Kaman dai tafiyar ku Cuba, aurensa da iyayensa suka masa dama abubuwa da dama.. I had to find out about them all bayan abubuwan Sun wakana.!” Ya dago yana duban Dareen sosai “Amfaninki shine ki samu kusanci dashi fiyeda ni, ki rayu dashi under same roof dan musan mai yake ciki.”" Taci gaba da jinjina Kai “Does Haidar love her..? Yana son matar da iyayensa suka aura masa..? Tell me pls Hisham.” Ta k’arashe tana fito da idonta waje. Hisham ya kareta da ido sai kuma ya girgiza kai “Don’t think of going near her.!” Yai maganar cikeda gargadi yana nunata da D’an yatsa kafin yaci gaba “Kar ki kuskura Dareen. I love Ummul.. She’s the love of my life. Kuma zanyi komai to take her back from Haidar.!” Dareen ta d’ago tana dubansa “What about Haidar.. you know I love him too.” Hisham ya jinjina Kai “You can’t make any move sai abinda nace. Ummul ta shigo ciki ya zama dole na bincika naji meye asalin labarin aurenta da Haidar. Ta haka ne kawai zan iya d’auketa daga gare shi. After all ban yarda da zamanta tsakanin azzaluman mutane irin ahalin Maitama ba. Tin ba aje ko ina ba sun soma yunk’urin kasheta. I need to take her away from them. Wann auren na Haidar da Ummul bazai je ko ina ba.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice kaman zai kifa. "Zama yai cikin mota bayan ya fice yana tuna duk wani shirinsa akan Ahalin Maitama. Ahalin da suka tarwatsa masa rayuwa, ahalin da ya ranste sai ya tarwatsa su tin sanda yasan ko shi waye. He vows to take them down for ruining his Mom’s life. Zai komai Akan mahaifiyarsa. Zai d’aukar mata fansa koda Abu na k’arshe kenan da zai a rayuwarsa. Ya ranste sai ya mayar masu da duk k’uncin da suka fuskanta a rayuwa ta dalilinsu. Sai yanzu yake gano dalilin Hajja na b’oye masa waye Ummul ta aura. Dama ta sani kenan. Ta San Dan azzalumin tsohon mijinta ne ya auri Ummul.? Ya jinina Kai a hankali yana ayyana bazai tab’a bari ta fahimci akwai alak’a tsakaninsa da ahalin Maitama ba. Bazai tab’a bari ta fahimci yasan wani Abu ba har sai ya k’arashi fansarsa akansu. Idan kuma na numfashi Ummul zata dawo gare shi. Meyasa shine gaba da Haidar amma komai nasa Haidar ke samu. Shi ya kamata ya fara zama D’a wajen mahaifinsa bai zama ba Haidar ya zama. Yanzu Ummul da ya fara ganinta wacce shi ya kamata ace ya aureta sai gashi Haidar ya rigasa samunta. No way.. Bazai bari hakan ta kasance ba. Bayan fansarsa da yake so Akan ahalin he needs to fight for Ummul. Ita din tashi ce.! Cikin sauri ya tada motarsa had’ida barin wajen." * A hankali Ummul ke k’ok’arin bud’e idonta har ta sauk’e su tar kan Likitan dake tsaye gabanta. Ta yunk’ura zata mik’e amma sai ta kasa. Muryar Likitan ta sinkayo yana fad’in “Ah sorry. Bazaki iya mik’ewa a yanzu ba. Sannu ko…” Ummul taci gaba da rage girman idonta tana dubansa a hankali tana kuma duban d’akin da take. Ta dubi hannunta taga drip.. Ta girgiza Kai kad’an “Aaaah… Ina ne nan..? Ina nake meke faruwa dani.?” Dr ya murmusa “I’m Dr Faruk.. Ni ne Likitan da ya kula dake da aikin da aka miki..?” “Likita..? Aiki..?” Sai ta yunk’ura taji zogi kad’an wajen hak’ark’arinta. Dr ya jinina Kai “Mun Miki aiki dan fitar da guban da kika shak’a cikin lungs dinki..” “Guba.! Lungs..!” Ta fad’i cikeda mamaki tana duban Dr Wanda ya soma duba file din dake hannunsa “There’s nothing to be worried about.. the poison is completely out of your system in sha Allah. Akwai maganin da zamu dauraki akai na dan wani lokaci.” Ummul ta katse sa cikin girgiza Kai “Amma Likita dan Allah waye ya kawo ni nan.. Meyasa banga kowa ba.?” Dr ya murmusa “Ina ta jira naji kinyi tambayar nan dan yanda mijin nan naki ya damu dake na kwana biyu banga irin haka ba. A nan yake kwana kwanaki biyun nan da kikai a kwance.. Yanzu haka ma gida ya tafi nasan nan bada jimawa ba zaizo musamman idan yaji labari mai dadi cewa kin farka.” Ya k’arada akwai yanda ke Miki ciwo ne.?” Ummul bata samu zarafin amsa sa ba sai mamaki da ya cika ta wai mijinta kuma a nan yake kwana. A hankali ta furta “Mijina.?!” Wayar Dr ne ta soma ringing ya dubi Ummul “Please excuse me. I have to answer this… Akwai wani Dr da zai shigo anjima ya dubaki. Zai instructing dinki gameda abubuwan da suka kamata ki fara ci.” Bai tsaya sauraronta ba ya fice cikin sauri yana amsa kiran dake shigo masa. Har lokacin mamaki ne ya cika Ummul. Toh wane irin guba ta shak’a..? Sann wani Miji Likitan nan yake magana akai.? Bata Kai ga samo amsa ba Anisa ta turo k’ofa ta shigo gaba d’aya ta rasa sukuni. Bata san ya zatai da Leenah ba. Bata tab’a tsammanin Leenah zata zame mata tashin hankali irin haka ba. Wato dama plan d’in Leenah kenan da tace ta incriminating Mommy. Shine ta tasta kudi jikinta. Yanzu idan ta bud’e baki ta fad’i abinda ya faru Tabbas kashin ta ya bushe. Hango idon Ummul da tai a bud’e ta sanyata k’arasowa cikin sauri tana fad’in “OMG.! Finally you are wake.. Oh thank goodness.!” Ta k’arasa tana mai kwantowa jikin Ummul dake kwance had’ida bata light hug. Anisa ta kuma duban Ummul tana mata sannu. Murmushi Ummul take sakar mata tana amsawa. Anisa taci gaba “We were so worried about you Ummul. We all thought you were going to die.. Especially Mommy. Kai Alhamdulillah kin tashi.” Ummul ta k’ak’aro murmushi kad’an. Sai kuma ta fara lek’e kaman tana Neman wani. “ “Ina Mommy.. Tare kuke da Mommy.?” Ummul ta tambaya. Take Anisa tai rau rau da ido had’ida girgiza Kai “Ummul to be honest with you Mommy is in jail right now.. And it’s all because of you.” Ummul ta dubeta da mamaki “Mommy kuma a jail..? Kuma dalilina.. Wai meke faruwa ne Anisa.?” Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya kaman gaske “Turaren da Mommy tai miki kyautar sa an tabbatar akwai guba ciki Ummul.” Shaye da mamaki Ummul ke dubanta “Guba kuma.?” Anisa ta jinjina mata Kai alamun tabbatarwa “And that’s why you ended up here in a hospital. Mommy kuma aka tura ta jail.” Ummul ta soma girgiza Kai “A’a Anisa… Wani Abu ba daidai bane a nan.. Mommy bazata tab’a saka mun guba ba. Tana sona sosai ni shaida ce.. Bata tab’a min wani Abu na cutarwa ba.. Meyasa zata saka min guba.” Anisa ta jinjina kai “Nima dai abinda nai tunani kenan. Mommy tana sonki Ummul sosai.. She’s shown nothing to you but immense kindness. She defended you so many times.. She loves you tamkar itace ta haifeki. Bazai tab’a yuwa ta cutar dake ba. Idan ma har akwai guba ciki Tabbas bata sani ba.” Anisa ta dafa hannayen Ummul dan babu yanda ta iya dole tayi convincing Ummul ta janye k’ara Akan Mommy ta haka ne kawai zata samu ta rabu da Leenah cikin ruwan sanyi tinda idan Ummul ta janye k’ara ko ta sanar da Mommy bazai amfanin komai ba sann Mommy bazata yarda da Leenah ba tinda dama kwanakin baya Leenar ce ta k’ulla ma Ummul sharrin sata balle yanzu idan taga da taimakon ita Anisar ta fice a jail. She needs to play her card well. Cikin kwantar da murya take ci gaba “Ummul janye k’ara da zakiyi akan Mommy shi zai fidda Mommy daga jail a halin yanzu.” Cikin rudani Ummul ke girgiza Kai “Wai wani k’ara kike magana Anisa..? Dama babu wani k’ara.. Koda Mommy da gaske tayi niyyan kashe ni wllhi bazan tab’a yin k’ararta ba. Mommy uwa ce a wajena.!” Ta kuma duban Anisa a daburce “Ina Likita..? Ya kamata na tafi daga nan.. Ina so na tafi na samu Mommy please..!” Ta k’arashe tana yunk’urin mik’ewa. Anisa tai saurin dafata “A’a Ummul a hankali. Bakida k’arfi har yanzu.. Mu jira Likita yazo..” Bata Kai aya ba wayarta ya soma ruri Leenah ce mai kira. Cikin zuciyarta ta furta ‘Damn it.’ Ta dubi Ummul tana sakin murmushi “Zan amsa kiran nan ina dawowa.” Ummul bata iya ce mata komai ba dan ita har lokacin mamaki take wai Mommy na jail dalilinta. Bata da burin da ya wuce ta fita daga asibitin taje ta samu Mommy. A hankali ya turo k’ofan d’akin ya shigo. Nan ya hangeta kwance saman gadon wann karon idonta a bud’e suke tar. Kullum a rufe yake ganinsu amma yau d’in a bud’e ga gansu. Ya kasa janye idonsa daga cikin nata idon. Ummul kaw ganin wann mutumi da ya shigo tayi zaton d’aya Likitan ne da Dr ya sanar mata cewa wani Likitan zai shigo ya dubata tinda ba sanin kamannin Haidar tai ba. Tin kafin ya ida shigowa ta soma fad’in “Dr dan Allah ku Sallameni.. Wllhi naji sauki. Wani abu ya Sami Maman mijina.. Ya kamata naje na dubata.. Bazai yuwu na kyaleta cikin halin da take ba. Dan Allah ka cire min drip din nan na tafi na samu Mommy tana buk’atata a daidai wann lokacin.” Ta k’arashe tana k’ok’arin cire drip din dukda ba iyawa tai ba ganin ya kareta da ido ko motsawa bai yi. Haidar yai sauri ya rik’e d’aya hannun nata da take k’ok’arin cire drip din dashi. “Ke.!” Ya daka mata tsawa. D’agowa tai tana dubansa sai kuma ta dubi yanda ya tamke mata hannu da k’arfin gaske ga wani irin huci da yake. "Bata iya fad’a ba, ba d’abi’arta bane. Khulsum bata nan balle ta k’wace ta kaman yanda ta saba. She needs to stand up for herself." Ta d’ago ta dubesa tana huci har lokacin rik’e yake gam da hannunta bai kuma da niyyan sakar mata hannu. Sai ta soma tuno yanda Khulsum ke fad’a. “Malam sakar min hannu..!” Ta fad’i tana firfito da ido waje. Bai sake ba sai tsareta da ido da yai har lokacin yana kuma matse hannun nata cikin nasa. Hakan ya kuma tunzura Ummul dan ta kula wann Likitan baida mutunci. “Ka sakar min hannuna Malam. Ni matar aure ce. Idan ka bari mijina ya shigo nan ya sameka ka kuka da kanka..!” Tai maganar tana ci gaba da kiciniyar k’wace hannunta amma ta kasa. Kwanto da fuskar yai kusan nata “Call him.! Go ahead and call that husband of yours.!” Sosai tsoro da tashin hankali suka bayyana saman fuskar Ummul. K’irjinta yaci gaba da bugawa. Ana a haka Likitan da bai jima da fita ba ya kuma turo k’ofan ya shigo. Hangosa da Ummul tai yasa ta soma fad’i cikin rawar murya “Yauwa Dr. Dan Allah ka ceceni hannun wann abokin aikin naka.. Dan Allah ka sallame ni daga wann asibitin yanzu.. Ya kamata na tafi naji sauk’i.” Tai maganar da kyar dan d’an magana da firgicin da tai har wajen aikinta ya soma mata zafi. Dr da bai wani saurareta ba dan maganar nata ba fita sosai yake ba. Ya fad’ad’a murmushinsa ganin Haidar “A’a Engr kaji kiran Madam kenan dole ka taho Akan k’afafunka.. Matarka is finally awake.!” Zuciyar Ummul yai wani irin tsinkewa tana duban Likitan Jin kalaman sa. ‘Matarka.’ Ta nanata cikin zuciyarta. Ai sai taji kaman Cak numfashinta ya d’auke. Ta kasa juyowa ta dubi mutumin da Likitan ya kirata da matarsa. Sai ji da tai hannunsa na sakin nata a hankali. Haidar ya dubi Dr sukai masabaha kafin ya k’arada “Sallama nake so Dr as soon as possible.” Dr ya d’anyi jim “Da wuri haka. Ya kamata mu ajeta a nan for observation. Wait I’ll be back.. Dr Charles needs to see her first.” Yana ficewa Haidar ya isa ya zame drip din. Batai aune ba sai ji tai ta sunkuceta cikin hannunsa. Ummul ta kasa gane meke faruwa. Ta rasa ihu zatai tsalle zatai saima taji tamkar wacce aka d’aureta. Har lokacin cikin mamaki mai gauraye da tsoro take. Ji tai yawun bakinta kaf ya k’afe. Bata tsammanin akwai jijiya mai motsi cikin jikinta a wann lokacin. Bai direta ko ina ba sai cikin motarsa. Anisa da fitowarta kenan daga wani hanya taga kaman bayan Haidar take gani ya gifta mutum cikin hannunsa. Zuciyarta yai wani irin yankewa kar dai Ummul ce.? A hanzarce ta nufi d’akin Ummul saidai tana zuwa bata tadda kowa ba sai gado. Nan Anisa ta fito a guje tana kwalla ma Likita kira. ** Suna tafe saman kwalta ta kasa tantance wace duniya take ciki har kawo wann lokacin. Ta kasa duban b’angaren da Haidar yake. Iyakacin abinda ta sani shine anata falfala gudu da ita saman kwalta. Da wutsiyar ido Haidar dake falla gudu dasu saman kwalta ya dubeta. Nan yaga har lokacin a tak’ure take harda kaman rawar d’ari da take. Ya maida dubansa ga kwalta ba tareda yace komai ba. Har lokacin Ummul bata dubesa ba. Ta kuma kasa furta koda kalma. Kana ganinta zaka fahimci har wann lokaci ba daidai take ba. Haidar ya karya kan motar suka shiga wani close da babu gine gine sosai saiko gida je da basu wuce uku ba. Ga yawan bishiyoyi da shuke shuke. A daidai k’ofan wani madaidaicin gida Wanda kaman tsakiyar forest yake tsaban yawan bishiyoyi da shuka dake kewaye da wajen yai parking. D’ago Kai tai cikeda tsoro tana duban gidan dake tsakiyan jeji a idonta dan sai wann lokacin taji kaman an Zare electric shock d’in da aka saka mata. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *36* *©️Sameena Aleeyou… * A tsorace ta d’ago tana dubansa. “Can you walk.?” Ya tambaya yana dubanta itama shi take duba. Ganin bata ce masa komai ba sai ma rawa da jikinta keyi alamun dai batada strength har lokacin yasa bai kuma yin wata wata ba ya fiddota daga cikin motar. Ganin haka yasa ta soma girgiza masa kai tana fad’i cikin rawar murya “A’a dan Allah.. Ina ne nan… Ina ka kawo ni..?!” Cikin muryarta da bai fita sosai take maganar. “Shut up. Just shut up.!” Ya fad’i still tana cikin hannunsa. A haka ya tura k’ofan parlorn suka shige. Ko ina an rufe da farin kyalle alamun dai babu mai zama cikin gidan. Wani d’aki ya bud’e ya ajeta saman gado. Ta d’ago a tsorace tana dubansa had’ida girgiza Kai ganin na k’ok’arin ficewa. Da tangadi ta nufo k’ofa tana fad’in “Dan Allah.. Kar ka barni a nan.. Ka Kaini wajen Mommy dan Allah ina buk’atan ganinta.” "Haidar ya d’auki lokaci yana dubanta kafin ya tako zuwa gabanta “Look, I don’t intend to keep you here for good. If you cooperate with me.. Bazaki jima a nan ba zaki tafi.!” Yana ida fad’in haka ya janyo k’ofan ya rufe kirif." Ummul ta duka a wajen tana dukan k’ofan da d’an sauran strength dinta tana fad’in dan Allah ya bud’e ta ya barta ta fita. "Shiru babu agaji ba taimako, Haidar bai bud’e ta ba sai sautin tashin motarsa da taji. Ta rarrafa da kyar ta isa jikin window nan ta hangi hancin motarsa na barin wajen. Wani irin kuka ta fashe dashi tana Jin zazzabi mai zafi na sauko mata." ** Anisa ta dubi Dr “Dr wann ai kidnapping ne. We need to see your security footage.” Dr ya murmusa “How is that a kidnap.? Haidar shi ya d’auke matarsa.. He’s her legal Husband.. So wann ba kidnapping bane.” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa. "Anisa ta furzar da huci “But still you are her Dr. And it’s your duty to call him and tell him exactly the consequences of what he’s done.. I mean, she’s still recovering.. She needs to stay here at the hospital.”" Dr ya dubeta still murmushi saman fuskarsa “If you excuse me Miss. I have some patients to attend to.” Ya k’arashe yana mai shigewa. Anisa taci gaba da huci “Ahhhg! Imbecile.!” Ta fad’i tana sakin huci. Wayarta ne ya soma ringing. Ta duba taga Leenah ce. Gajeren tsaki tai had’ida kin d’agawa. Leenah ta kira har kusan sau uku Anisa bata daga ba sai ta turo mata SMS. _Remember you only have 2 days_ Tsaki Anisa tai tana sakin huci. Yanzu ya zatai ga wann D’an zafin Kan ya d’auke Ummul wacce take tunanin itace last alternative d’inta. Kodai Hilal ne zata kira.? Ta d’anyi gajeren tsaki kafin ta soma Neman layin Hilal. Bugu biyu Hilal ya d’aga “How’s my fish brain sister doing.?” “Zanci k’aniyarka Hilal.” Anisa tace a hasale Jin ya kirata da sunar tsokanar da ya saba kiranta tin yarinta fish brain. Hilal ya dara “Hey easy. Nayi kewar tsokanarki ne. How have you been.. Bazaki zo bane sai na tafi.?” Ta dan rausayar da ido had’ida furzar da huci “Yaushe zaka koma school din.?” “Nayi postponing akwai abinda nake a nan.” Ya bata amsa Kai tsaye. Anisa ta dan zaro ido “Kuma Abba na sane da haka.?” Hilal ya dara kad’an “He doesn’t need to know.. Wani Abu kawai zan k’arasa sai na tafi.” "Anisa ta jinjina Kai “Hey Hilal, brother… Alfarma nake nema.”" Hilal ya kuma d’an darawa tinda yaji ta fara kashe murya tana kiransa brother yasan abu take nema wajensa “Fad’a kawai meye kike nema wajena.?” Anisa ta furzar da huci “Money Hilal. Kudi nake nema wajenka.” Hilal ya kuma darawa teasingly yake fad’in “Kuda kuke Abuja gaki ga shugaban k’asa ina zan samo kudi a state na baki.” “Hilal I’m being serious here. Da gaske kudi nake nema. And it’s urgent.” “Ok fine. Nawa kike nema.?” “1M..!” Ta fad’i kaman mai tsoro. Dariyar rainin hankali Hilal yai “What.! Are you kidding me Neesa.. 1 million a wajen D’an makaranta irina..? You’ve got to be kidding me. Why not ask Abba. shine D’an kasuwan bani ba. And hey I’m not his manager.” Anisa tace “Haba Hilal. Nasan kanada hanya Shiyasa na kiraka.. Wllhi ina tsananin buk’atar kudin nan. Look zan biyaka da zaran na samu.” Hilal ya d’anyi Jim Jin tayi sounding serious. Shima sai ya daina wasa “Wait Anisa. Be honest with me.. What have you got yourself into..? Gambling kika fara..? Dan nasan dai ba business din da kike. Kodai kinje kin hadu da wasu scammers ne.?” Anisa ta rausayar da ido “Hilal dan Allah ka taimaken mana nasan Abba naji dakai wllhi na rantse maka da Allah matsala nake ciki. Haba Hilal meye amfanin ‘yanuwa ma junansu idan bazasu rufa asirin juna ba. Nasan Mommy zata bani idan tasan ina nema amma bana so ta sani. Kasan masu kudin nan the moment suka gane abun hannunsu ya rufe maka ido akwai matsala.” Hilal ya d’anyi jim “Anisa ni fah kudin dake account dina pocket money na ne. Kuma idan har na baki su yanzu za’azo a shiga tsakiyan semester ne ina nema. And kinsan Abba komai da lissafi yake bazan zo masa da labarin rashin kudi ba tinda yasan ya sallameni. Cewa zai wasa nake da kudi sai naje nai ko aikin k’arfi ne a can na ci da Kaina.” Anisa tace “But you are his favourite.” “Even so Neesa. Kinsan yanda mahaifinmu yake idan aka zo maganar kudi.” Zata kuma magiya Hilal yace “Fine… Zan tura miki.. Amma ko da wasa kar ki bari ko Ammi tasan na baki banso na hadasu fad’a da Abba.” Anisa tai alaman zipping bakinta da yatsa kaman Hilala na kallon ta “An gama my dear Brother. That’s why I so much love you.” Da haka Anisa taita gwada Hilal tana fad’in irin son da take ma tilon dan uwan nata. Gama wayar da zatai ta waigo gabanta yai wani irin fad’uwa samakon ganin mutum da tai tsaye bayanta. Taci gaba da yatsina fuska tana dubansa “Malam lafiya.? Wanene kai.?” Huci kurum Hisham yake yana dubanta kaman zai shak’ota. Yaci gaba da jinjina Kai yana fad’in “Nasan kece.! Kece kika tassama kashe Ummul.!” Anisa ta zaro ido waje ganin stranger da ko saninsa batai ba yana fad’in laifin da ita da Laila suka binne. Ta soma girgiza kai tana fad’in “No.. I don’t know what you are talking about Malam. Meyasa zanyi yunk’urin kashe Ummu. What could be my motive.? Wait why am I even explaining myself. I don’t even know you. Excuse me.” Tasa kai zata shige. “You are the only person with the motive to kill her.. Because you love Haidar.. Haka ne.?” Ya k’arashe yana tsareta da ido. Anisa taja Birki tana dubansa shaye da mamaki. Sai ta soma girgiza kai kad’an ganin dai guy d’in nan da gaske ya sansu “Mai kake nufi..? Wanene Kai.?” “Na tuna miki ne. Kwanakin baya lokacin da motar ki tabi bayan motar Haidar. Cikin k’ok’arin bin bayansa da kike dan ki gano yanda yake zuwa. Someone hit your car and stopped you from following him.. That someone.. Was me.. Ni ne na bigi bayan motar ki na hanaki bin bayan Haidar.” "Anisa ta soma tuno kwanakin baya Mommy tasa ta bi bayan motar Haidar dan gano yanda yake zuwa amma sai tai accident a hanyar ta wata mota da bata tantance ba ta bugi bayan motar ta Wanda hakan Ya hanata bin bayan Haidar.. Kenan wann mutumin ne Ya bigi bayan motarta. Ta d’ago a d’an firgice tana dubansa “Wait.. Kaman nasan fuskarka.. Wait… Aren’t you friends with Haidar.?” Ta dan murmusa tana girgiza kai “Oh now I understand.. Are you his watchdog.? Trying to play best friend of the year.? Wow you try..” Ta d’anyi shiru tana dubansa “Don’t you think… you are over reacting.. I mean, matar abokinka kake karewa irin haka.”" Hisham Ya fahimci Anisa shashasha ce kuma zata zamto makami mai k’arfi da zai amfani da ita wajen k’watan Ummul daga wajen mortal enemy d’insa Haidar. Anisa ta murmusa tana dubansa “Or maybe it’s the other way around.. Mai kake tunanin Haidar zai yi.? if he finds out that his coworker or should I put it this way… His friend is in love with his wife… Kodai ku masoya ne dama tintinin.?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido. “Think whatever you want to think.!” Ya k’arashe yana matsowa kusanta kaman zai shak’ota tana k’ok’arin matsawa baya. Anisa taci gaba da Zare ido “Malam idan baka k’yaleni ba zan maka ihun b’arawo.!” Yaci gaba da jinjina Kai “Go ahead and shout! Let see waye yakeda abun fad’i ma ‘yansanda.” Sai kuma tai shiru tana ci gaba da Zare ido. Hisham yaci gaba “If you dare think of hurting Ummul.. Believe me I’ll deal with you myself.!” Cikeda tsoro had’ida mamaki Anisa ke dubansa. Sai kuma ta girgiza Kai tace “And… who are you to Ummul.? Dan ban yarda kana son kareta ne kawai dan kana abokin Haidar ba.” Kallon shashasha yaci gaba da yima Anisa dan da tasan lokacin da ya bugi bayan motarta Ya hanata bin bayan Haidar ba don Ya kare Haidar yai ba sai dan ya hanata gano Matar Haidar da Ahalin Haidar d’in basu san da ita ba wato Dareen da wann doluwar bata tsaya tana bata bakinta ba. “Idan kika sake yunk’urin cutar da ita .. Sann ne zaki san ko ni waye.” Anisa ta murmusa tana dubansa “Ta Ya zan cutar da ita balle Har ka bata kariya bayan an riga an d’auketa.” Hisham Ya dubeta ya kuma girgiza kai da mamaki “Kina so kice mun Ummul bata asibitin nan.?! Is she kidnapped or something.? Waye ya saceta.?” Anisa ta kuma murmusawa “One question at a time. Wanda ya fimu kusanci da ita daga ni har kai shi ya saceta.. Ina nufin mijinta..!” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. Zuciyarta na tabbatar mata abokin Haidar son Ummul yake ba tareda sanin Haidar d’in ba. Amma ita idan har haka Ya tabbata ribanta ne dan zasu had’a team mai k’arfi wajen ruguza tsakanin Ummul da Haidar. “Ina Haidar Ya kaita.?” Ya tambaya yana duban Anisa. "Anisa ta murmusa “Why not ask him.. After all, abokin ka ne… Kasan me.? Although Haidar never introduce his friends to his family na rasa gane ya akai nasan fuskarka matsayin abokinsa… Koda yake wann Dan uwan nawa bamuyi zaton ma nada abokai ba.. Maybe kaima d’in dan wajen aikinku d’aya ne Shiyasa.. Im sure na tab’a ganinka ka kawo masa wasu takardu da Ya danganci aikin company gida.”" “Shut up.” Hisham ya katseta jin tana sunbatun da babu Wanda Ya tambayeta. Yaci gaba da dubanta “Kina jina.. Yes ina son Ummul. With every fibre of my being. Hasalima ni na fara sonta kafin ta zama matar Haidar.. You and I are going to help each other out. Ina so ki tabbatar min cewa my secret is safe with you kaman yanda naki ya zama safe dani. That is idan kina so mu raba su biyun.. Ki mallaki Haidar na mallaki Ummul.. Zan iya tabbatar Miki with my help.. Haidar will be yours forever..” Anisa ta zaro ido waje “Da gaske kake.. Let’s team up then.. Zanyi komai.. In fact kokari kullum nake dan burina Ya cika.” “Your wish has been granted..” Ya fad’i yana jinina kai. Take sukai exchanging phone number cikin k’ok’arin yanda zasu fara zartar da plan dinsu na k’ok’arin raba Haidar da Ummul. "Tsaye Hisham yai a dakinsa na sirri Wanda hotunan Daddy Mommy harma da Haidar sune kawai a cikin d’akin an mammannasu jikin wall. Had’ida dangin magazines masu d’auke da labarun Maitama Builders. Da duk wani article da ya k’unshi scandals wanda sukai popping a labarun kasuwanci wad’anda suka danganci Kampanin Maitama da ahalinsa. kaf shi yake fitar da scandals d’in. Yai tsaye gaban hotunansu yana kallo lokaci guda yake furta “Why Ummul.? Why her..? Menene dalilinku na kawo Ummul cikin wann messed family din naku.!” Yakai dubansa kan hoton Mommy, lokaci guda yaci gaba “Kwaise Maitama ya kikaji zaman kurkuku.? you are the one who instigated everything.! You should suffer the consequences.. All the hardships nida mahaifyata had to experienced. Kece kika jawo.!” Yaci gaba da jinjina Kai “It is your fault that I had to search for people who would accept me all my life..?!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa. Yaci gaba da jinjina kai “You are now in Jail… Ke d’in yanzu kina tsare a kurkuku.. Abin takaicin kuma D’anki ne Ya kaiki. Did you know that… I was born in a prison..? Did you know that I grow up thinking ni ba kowa bane but a son of a criminal..?! Yai maganar cikin tsananin sakin huci kafin yaci gaba “This is the perfect time for me to ruin your life completely kaman yanda kika lalata nawa. Yanzu ne lokacin da ta kamata na fitar da labari akanki. Kinyi yunkurin kashe matar D’anki. Ya kika ji labarin Kwaise.? Abun zai matuk’ar k’ayatarwa musamman a shafukan labarun kasuwanci. Dan na tabbata Aliyu Maitama ba korar wulakanci kawai zai Miki ba muddin kika bata masa suna irin haka a duniyar kasuwanci. Zai tabbata dake da D’anki da kika koreni sabida shi naku rayuwar ya daidaice fiyeda yanda nawa rayuwar da na mahaifiyata ya daidaice. Saidai kashh.! Ummul ta shiga cikin wann ahalin naku. She shouldn’t get involved..! She shouldn’t.!” Yaci gaba da jinjina Kai yana sakin huci “Kaman yanda nai alk’awarin tarwatsaku haka nai alk’awarin fitar da Ummul daga wann ahalin naku. Sai na rabaka da Ummul Haidar domin kuwa ita d’in tawa ce.!” Ya k’arashe yana duban hoton Haidar da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja." ** Ba shi ya dawo gidan ba sai yamma lis. Tana nan kwance k’asa zazzabi Ya gama lullub’e ta. A hankali Haidar Ya tura k’ofan d’akin hannunsa rik’eda manyan ledodi. Hangota da yai kwance saman rug ya sanyashi saurin sakin ledojin Ya k’arasa gareta. Ya kai hannu ya tab’a goshinta ganin sai rawan d’ari take. Nan yaji jikin nata zafi k’au. A hankali ya furta “Oh no she’s burning up. What do I do..?!” Ya furta yana dubanta gashi ya mance magungunanta a pharmacy din da ya saya. Wani tunani ne yazo masa yai saurin d’agota daga k’asa Ya daurata saman gado ya shiga janyo bargo yana rufa mata ganin sosai take rawan sanyi.. Ya soma rurrufe windows trying to keep her warm. dan dik shi a tunaninsa haka ne zai sauk’ar mata da zazzabin ta daina jin sanyi. Amma sai yaji kaman zafin jikin ya karu ga rawan sanyin da take ya karu. Yai tsaye yana kallonta yana tunanin abunyi.. Ko room heater zai fita Ya nemo Yai warming dakin dashi..? Ya nufo waje sauri sauri yana tunanin nemo room heater. Cak kuma yaja Ya tsaya kaman Wanda aka dakatar dashi. “Dr Faruk.” Ya furta a hankali kafin ya soma jinjina kai “Yes I need to call him..” Ya k’arashe yana mai Ciro wayarsa daga aljihun jeans d’insa. Nan ya soma dialing layin Dr. Dr yana dauka Haidar Ya soma sanar dashi cewa jikin Ummul yayi zafi sann Ya mance bai taho da maganin ba. Meye first aid da ya kamata ya soma bata. Dr Faruk ya murmusa daga d’aya b’angaren. Soyayyar Haidar ga matarsa na kashesa “A cool shower will help.. And she should wear lighter and more breathable clothing.” "Haidar ya jinjina kai yana nanatawa “A….. cool shower.. Ok, cool shower..”" Dr ya kuma amsawa yana mai fatan samun sauk’i ga matar Haidar d’in. Haidar yai masa godiya kafin yai hanging up. Dawowa d’akin yai Ya ganta nan yanda ya barta saman gado tana rawar sanyi. Yai saurin k’arasawa Ya yaye bargon da ya rufa mata. Ya soma k’ok’arin rage mata tufafin jikinta amma sai ta takure jikinta waje guda tana fad’in Ya kyaleta dukda rawan sanyi da take. "Cikeda takaici Haidar yai jifa da hulan da ya zame daga saman kanta “Fine then, take the shower like this.” Ya k’arashe yana mai dagota daga saman gadon Yayinda Ummul ke k’ok’arin tattaro sauran strength da ya rage mata tana janyewa daga jikinsa tana fad’in ina zai kaita ya kyaleta." Bai tsaya amsata ba Ya nufi bathroom da ita cikin hannunsa. Taci gaba da k’ok’arin turasa Haidar na rik’eda da ita yana fadin “Stay here and take a shower. You are burning up.” Ya k’arashe cikin k’ok’arin tsaida ita kan k’afafunta amma sai ta soma k’ok’arin zubewa a k’asa sakamakon rashin karfi. Bai bari takai kasa ba yai saurin k’arasowa ya rungumeta cikin jikinsa a daidai lokacin hannunsa ya tab’a switch na shower din ai kaw nan ruwan ya soma zubowa kawunansu su duka biyun. Sauk’an ruwan da taji saman jikinta a bazata ya sa ta sakin ajiyan zuciya Wanda yasa Haidar yai mata cover da arms d’insa kaman mai tsoron kar ruwan Ya cutar da ita. Ya shigar da ita sosai cikin k’irjinsa ruwan naci gaba da zubowa kansu. Yana jin yanda ruwan ke ratsa dumin jikinta zuwa nasa jikin. A hankali Haidar ke lumshe idanunsa yana jin harbawan da zukutansu keyi kaman a tare. Sun d’auke minutes a haka kafin yaji temperature dinta na sauka a hankali. A haka Ya fito da ita daga bathroom din su duka biyu jikkunansu a jik’e. Cikin kayan da ya shigo dasu Ya Ciro towel sabo Ya rufa mata. Ya d’auki hand towel din yana tsane sumarsa. Lokaci guda yake furta “Change those clothes before you catch cold.” Yana ida fad’in haka yasa zai fice yayinda Ummul ta mak’ale sosai cikin towel din da ya rufa mata. Tabbas zazzabin da takeji ya dan sauka. Sanda taga haikan zai kuma ficewa ya kulleta a wann dakin tai saurin bud’e murya tace “Dan Allah ka dakata.” Haidar Ya tsaya Cak sanda yaji muryarta. Ganin Ya tsaya yasa Ummul ci gaba “Meyasa ka kawoni nan ka kulleni..? Dan.. Dan Allah.. Ka fitar Dani daga kurkukun nan.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya. Juyowa yai yana dubanta sai ya dawo da baya. Yai tsaye kanta hannayensa hard’e yayinda Ummul ta soma k’ok’arin jada baya. Sai taji ya soma fad’in “Who are you.? Meyasa kika yarda da auren mutumin da baki taba sani ba. Is that even possible.?” Shiru tai ba tareda ta iya amsa masa tambayarsa ba sai bugun zuciyarta dake karuwa. “Did Mommy buy you with money.? Nawa ta biya ta sayeki dan kawai kizo cikin rayuwana.?!” Ya k’arashe cikin d’aga murya. Ta soma girgiza kai tana hawaye. Abinda baison gani a rayuwarsa. Yai gajeren tsaki yana kauda fuska gefe jin bata amsa shi ba sai hawayen dake gangaro mata. “Fine.. Since you don’t want to talk. Enjoy your stay here. Dan bakida ranan fita a nan.!” Ya k’arashe yana mai jifa da hand towel din da ya gama tsane sumarsa dashi zuwa gefenta Wanda saida ya dan firgitata. Da taga haik’an da gaske zai kuma ficewa ya sanyata saurin fad’in “Nayi ne sabida Iyayena.!” Tai maganar cikin rawar murya irinta mai kuka. Haidar Ya kaikaito yana dubanta. Ya tako zuwa gabanta “Kin amince da auren mutumin da baki tab’a sani ba sabida iyayenki .? Are you that desperate.?!” Ta girgiza masa kai tana hawaye “Kud’in aure na.. Shi…. Shine kudin jinyar Abba na… Sann mahaifiyata…” Ta kasa ci gaba da magana sakamakon rawa da muryarta keyi. Haidar ya kafeta sosai da ido. Ya dan d’ibi dak’ik’ai a haka kafin yace “So I was right. Mommy sayenki tayi da kudi.. Nawa ta sayeki dashi.?!” Ya k’arashe maganar zuciyarsa na masa zafi. Ta rintse idanunta sosai hawaye na zubo mata. Ba yanda ta iya dole ta fad’a ma Haidar mak’asudin aurensa koda zai kawo karshen zamansu. Ita dai burinta taje ta fidda Mommy daga kurkukun da ake k’ok’arin kaita. Zatai komai dan ta kub’utar da Mommy matar da tun shigowarta gidan bata nuna mata komai ba face zallan k’auna. Muryar Haidar ta kuma ji cikin tsananin huci yana fad’in “You sold yourself to her.. You don’t deserve to go free.!” Yana maganar yana jinjina Kansa. Lokaci guda yasa kai ya fice rai bace. Kallo d’aya zaka masa ka fahimci abun ya masa zafi sosai. Ummul ta kuma runtse idonta wasu hawayen na gangaro mata. Can dare ta kuma jin shigowarsa dan har tayi zaton bazai kuma dawowa ba. Wann karon bai ko kalli yanda take tak’ure ba ya aje mata wasu ledodi. D’aya na abinci d’aya na magani. Baice da ita komai ba ya nufi k’ofa. Yana k’ok’arin fita ta rarrafo garesa tana rok’onsa “Dan Allah ka fitar Dani daga gidan nan.. Wllhi tsoro nakeji.. Dan Allah kar ka barni a nan..!” Ta k’arashe tana had’e hannu alamun rok’o. Wani kallo ya watsa mata kafin yasa kai ya fice yana mai rufe d’akin. Ummul tai lamo a wajen tana mai lumshe idonta Wanda kuka ya zame masu jiki. Ga dare ga jeji. Bata jin komai sai kukan tsuntsaye. Addu’a kawai take tana kai kukanta ga Rabbil Izza da Ya jibinci lamuranta. ** Washe gari Haidar bashi yazo gidan ba sai wajajen azahar. Ta Ida sallah kenan taji tsayuwar motarsa. Ga yunwa da ya azalzaleta. Tin bayan abincin da ya kawo mata bata kuma saka komai cikinta ba. Tai saurin mik’ewa ta Lek’a window dan tabbatar ma idonta ko shi d’in ne. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sakamakon tuno abinda ya faru jiya. Tai saurin komawa da baya tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. Sanda Haidar ya turo k’ofan kanta a k’asa. Ya dan d’auki lokaci tsaye daga k’ofan yana dubanta. Janye idonsa yai daga barin dubanta yana k’ok’arin shigowa d’akin dan shima a b’angarensa yana shigowa Ya soma tuna kasancewar da sukai tare k’asan shower a jiya. Yai gajeren tsaki yana mai shigowa dakin. “Have you taken your meds.?” Ya fad’i kaman baya so. Daga nan yanda yake tsaye. Jin bata amsashi ba yasa shi yin gajeren tsaki ya isa ya janyo ledan maganin yana d’aga ko wani maganan Wanda a rubuta dose jikin ko wanne. Nan yaga dai tasha duka. Cikin ko inkula Ya aje mata ledan abinci kafin ya tako zuwa gabanta “Ke.!” Ya fad’i yana dubanta. “Sunana Ummulkhairi.” Ta basa amsa daga nan yanda kanta ke kife. Bai ambaci sunan nata a fili ba dukda zuciyarsa ya maimaita the moment she closed her lips. Takarda ya mik’a mata “Sign these papers.” Ya fad’i cikeda umarni. Ta dubeshi ta dubi takardun da yake mik’a mata. Sai ta girgiza kai kad’an “Na menene..?” “You want be free. Then sign these..!” Ya kuma fad’i yana mik’a mata. A hankali tasa hannu ta karbi takardun tana dubawa. Dukda ba wai ta fahimci bayanan da suke kan takardun sosai bane. Ta gane takardu ne daga Kotu Wanda idan ta saka hannu tamkar tayi k’arar Mommy ne kai tsaye. Bata San meyasa Haidar ke fad’a da mahaifyarsa irin haka ba. Mahaifiyarsa fah yake yunk’urin kaiwa prison. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Anya yasan k’ima da darajan mahaifiya.? Waye yake fad’a da iyayensa sai tab’ebb’e. Ta d’ago a d’an tsorace tana dubansa “Bazan iya ba.. Bazan iya kai Mommy gidan Yari ba.!” Ya duk’o da fuskarsa kusan nata “Why.? Are you even related to her.?!” Yanda yake maganar tamkar fuskokinsu zasu hade waje guda. Ummul na iya jin huci da tururin numfashinsa saman fuskarta mai cikeda tsoro. Ya damk’o hannunta da iyaka k’arfinsa yana fad’in she should sign the papers. Batajin tana da k’arfin da zatayi kokawa dashi amma abu guda da ta sani shine har abada bazata kai Mommy prison ba. Wani dabara Ya fad’o mata kawai sai ta fashe da kuka tana k’ok’arin rik’e b’angaren da akai mata aiki alamun na mata ciwo. Haidar yai saurin sakinta yana kallon yanda take kuka tana kama wajen. A d’an daburce Ya soma fad’in “I.. I didn’t mean to hurt you… This is your fault you know. Da ace kinyi abinda nace it wouldn’t have to be this way. Wait let me see..” Ya soma k’ok’arin janye rigarta ai sai ta zaro ido da gaske ganin zai dage mata riga. Ta soma turasa cikin tsananin k’idimewa tana fad’in “Ai Ya.. Ya ya daina.. k’alau nake yanzu ka gani..!” Ta mik’e tsaye kan k’afafunta kaman wacce aka razaneta cikin k’ok’arin nuna masa lafiya take ba ciwon dake damunta. Ya tsareta sosai da ido. Wato kukan da take acting ne kawai ba ciwon da take ji. Da taga da gaske zai d’age rigarta ta daina acting d’in. Women are so good in acting kaman dai mahaifiyarsa. Sai shima ya mik’e tsaye yana binta da kallo daga sama Har k’asa. Ya kula har lokacin kaman rawa jikinta yake. Ai kuwa idan Har haka ne Ya gano lagonta. Zaisa tai signing papers din cikin sauk’i. Ya soma takowa gareta tana k’ok’arin jada baya. “Kodai ki saka hannu a takardun nan a dad’in rai… Ko kuma…” Yana maganar yana k’ok’arin balle botiran rigarsa. Bai kuma fasa nufota ba. Ta soma girgiza kai hawayen gaske na zubo mata “A’a dan Allah..!” Cikin rawar murya take maganar har saida Haidar Ya cimmata. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba ganin ya mata rumfa “Zaki saka ne ko na sakaki kisa da k’arfi..!” Ya fad’i fuskarsa dab nata. Dukda zuciyarta dake tsananin bugu bata fasa girgiza masa kai tana fad’in “K’ima da darajan mahaifiya Ya wuce ai fad’a da ita balle a kaita kurkuku duk girman laifinta.!” Bakinta dake fitar da kalaman yaketa kalla zuciyarsa na kuma masa zafi da kiran Mommy mahaifiya da take dan shi a idonsa Mommy bata canci a kirata mahaifiya ba. Jinjina kai yake yana huci “You think I’m playing here right.?!” Batai aune ba taji ya rufe bakinsa da nata. Hankalin Ummul yakai k’ololuwa wajen tashi. Al’amarin da ko a mafarki bata tab’a hasasho kanta ciki ba sai gashi na k’ok’arin faruwa da ita. Numfashinta ne Ya soma fita sama sama… Take taja wani irin numfashi ta zube masa a wajen. Ya duk’a yana jijjigata yana fad’in ta tashi ta daina wann wasan kwaikwayon. Shiru bata tashi ba har dai Haidar Ya soma tunanin ko sumar gaske ne tai. Ya tashi ya fice cikin k’ok’arin kawo ruwa ya yayyafa mata aiko yana ficewa Ummul ta mik’e a guje dikda rawa da jikinta keyi ta isa ta rufe k’ofan dan dama ya bar key d’in jiki. Da mamaki ya juyo yana duban k’ofan. Ta dai k’ara shashantar dashi a karo na biyu. Ya girgiza Kansa k’adan yana mamakin yanda Ya fad’a tarkon yarinyar Har sau biyu dikda matsalan saurin yarda da yake dashi gashi har sau biyu ya yarda da acting da Ummul tayi. Lallai da alama wann yarinyar zata basa matuk’ar wahala kafin ya samu ya cimma burinsa na tura Mommy prison. Sai kuma yaji gaba d’aya jikinsa ya sake kaman baida sauran kuazari. Ya isa saman kujera ya zauna gijif had’ida kishingid’a. Ya lumshe idanunsa bugun zuciyarsa na k’ok’arin daidaita. ** Police headquarters. Barr ya dubi Daddy da Mommy ya dan girgiza Kai “Zamu iya making abun Ya zama kaman illegal detention tinda Haidar ya b’oye matarsa babu Wanda yasan yanda take.” Daddy yace “So does that mean they would let her off the hook.?” "Kafin Barr yakai ga bada amsa Mommy ta katsesu “No.. I don’t want money or power to speak for me.. Iyakacin abinda nake so shine D’a na ya dawo gareni.. I’ll plead guilty, if that’s what it takes… Zan amsa laifin gaban Alk’alai zan tafi prison for Haidar to forgive me.”" Daddy ya dubi Barr yace ya dan basu waje. Bayan Barr ya fice ya tsare Mommy sosai da ido kafin ya soma girgiza kai cikin rashin yarda “You don’t know what you are talking about Kwaise. Do you really want to get convicted.? That ungrateful Son of yours doesn’t even care about you..!” Mommy na hawaye take jinjina kai “Yes.. Zanyi idan hakan zai kawo maslaha cikin rayuwar Haidar. Na rasa shi a farko.. I can’t lose him again.” "Daddy yaci gaba da girgiza kai “You know you can’t appear in court da aurena akanki, bearing my name… Mai kike" tunanin sunana zai zama a duniyar Kasuwanci.?!” Mommy na kallon Daddy take girgiza kai “Then end it Engr.!” Da tsananin mamaki Daddy ke kallonta. Duk juran zaman da tai a gidansa dukda rikon ko inkula da yake masu daga ita Har Dan nata bata tab’a zab’an rabuwa dashi ba daidai da rana guda sai gashi yau tana fad’in haka kai tsaye. “It has always been… an empty marriage that’s hanging by threads… Watak’ila sabida Haidar ka barni na zauna. Saidai a bangarena na zama lost between zama Mata ko Uwa.. Watak’ila na zab’i na zauna ne Thinking one day komai zai wuce ahalin Ya daidaita… Na Had’iye komai sabida D’ah na da mijina. I even named him after you… I turned myself into a monster a k’wayar idonsa ba tareda nayi la’akari ba. Na tilasta masa ya zamo abinda nake so thinking watarana zaka k’aunacesa zakai alfahari dashi kaman yanda ko wani uba yake… Ya kai matsayin da Har na mance cewa ni Uwa ce dik cikin k’ok’arin ganin burina na had’e kan ahalin Ya cika. But then I realise wann burin nawa bazai tab’a cika ba… Dik abinda naso ma nawa D’an na hana ma D’an wata ya samu.. Na rabaka da D’anka da matarka… Ta Ya zanyi zaton zan samu wann farin cikin da nake fad’i tashi akai tsawon rayuwata..? I am so selfish.” Kuka ya hanata ci gaba da magana yayinda jikin Daddy yai matuk’ar yin sanyi. "Mommy ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba “Na gode da hakurin da kai Dani tsawon shekarun nan. For letting me stay koda sabida D’anmu. Na gode da ahalin da ka bamu koda bai zamto kaman ko wani ahali ba. Koda cike yake da tarin k’alubali.” Taci gaba da jinjina Kai “I give up Engr.. I’m tired.. Na gaji.. Iyakacin abinda nake so a yanzu shine D’ana Ya dawo gareni. The wealth, the name.. Duka na hakura dasu. Na zab’i D’ah na.. Na rasashi daga farko bazan kuma sake rasashi a karo na biyu ba.!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata." Daddy ya kauda fuskarsa gefe yana k’ok’arin maida hawayen dake yunk’urin ciko idonsa. Bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yai ta fice cikin sauri. Mommy ta kuma rintse idonta wasu hawayen na gangaro mata. A halin yanzu ta gama aminta bokan da suka je wajensa itada Asshe mashahurin makaryaci ne. Tinda gashi turaren da Ya bata ta bama Ummul yasa ta fad’a uku. Dama ita bata tab’a yarda da aikin boka ba ko can baya Asshe ce ta ingizata sukaje. Sann she was desperate ta dawo da D’anta gareta. Bazata gushe ba zataci gaba da rok’on Allah Ya yafe mata kaucewa da tayi dan Tabbas taga aya. Zuciyarta na cikin natsuwa da aminci matuk’a Haidar d’inta na tareda Ummul. Ta aminta da hankali da natsuwar Ummul. Tanada yak’inin D’anta bazai tab’e ba cikin ikon Allah matuk’a na tareda Ummul. Da wann tunani Zuciyar Mommy ya dan samu natsuwa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *37* *©️Sameena Aleeyou… * Bayan shud’ewan awanni ta mik’e da kyar dan a tunaninta ya tafi musamman da taji sam babu d’uriyarsa. Window ta lek’a a hankali kaman mai tsoron kar a ganta. Ga mamakinta shi ta hango zaune k’asar wata bishiya Ya bada baya ma yanda take tsaye daga cikin d’akin. Tsuntsayi ta gani kaman dangin tattabarai Sun taru gabansa sai watsa masu abinci yake suna ci. Wasu Har kaman zasu d’ale saman hannunsa. Kai da gani zaka fahimci yana cikin annashuwa da jin dad’in abinda yake. Juyowa yai yana watsa ma sauran abincin nan ta hango kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Abinda bata tab’a gani ba. Zuciyarta yai wani irin yankewa tai sauri ta koma da baya had’ida jingina jikin gini. Ta d’auki lokaci a haka. Kafin ta kuma rintse idonta sakamakon tunowa da tai da yanayin da suka kasance ciki bada jimawa ba. Bata San dalili ba amma sai taji hawaye Sun ziraro mata. Ta jima nan a haka kafin ta bud’e lumsassun idonta da suka jike da hawaye. Ta kuma leka window amma sai taga bata gansa ba wann karon. Babu tsintsayen shima baya nan. Babu ko alamunsa. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin tai k’ok’arin saita kanta. Bata San ya za’ai tai escaping kurkukun da Haidar ya boyeta ciki ba. Bata san hanya ba bata kuma san idan zata iya isaga Mommy ba. Saidai abinda take da tabbaci akai shine zata fice tinda tai saa makulin na tareda ita. Zata fice kodan taje ta ceci Mommy. Har abada bazata bari Mommy ta tafi prison saboda ita ba. Sauri sauri ta isa k’ofa ta murda makullin ta soma k’ok’arin fitowa a hankali cikin sand’a. Tana tafe tana waige waige ga tsoro da Ya cikata. Saidai tana zuwa k’ofan da zai fitar da ita waje taji gam an rik’e hannunta. K’iris Ya rage bata saki k’ara ba amma sai taji an toshe bakinta. Ta d’ago idonta masu cikeda tsoro tana duban Haidar dake huci yana dubanta. A matuk’ar tsare yace “Are you trying to escape.? Where do you think you are going.? Answer me.! Guduwa kike so kiyi..?” Girgiza kai take hawaye naci gaba da gangaro mata. Haidar yaci gaba da janyota yana fad’in bazata bar wann gidan ba Har sai tayi abinda ya umarceta. Da k’arfin gaske Ya tura k’ofan d’akin Ya jefata ciki. Cikin rawar jiki Ummul ra soma k’ok’arin rarrafowa tana fad’in “Dan Allah kar ka sake rufeni.. Dan Allah Kaji tausayi na ka kyaleni na tafi.. Na maka alk’awari bazan zauna cikin rayuwarka ba.. Dan..!” “Shiiii..!” Ya mata alama da yatsarsa saman labb’ansa. Ya duk’a gabanta yanda take nan duke tana hawaye cikin rawar jiki. Sai ta soma k’ok’arin matsawa baya ganin Ya duk’o gabanta suna fuskantar juna. Ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba. Haidar ya dan d’auki lokaci yana dubanta kafin ya kauda kansa gefe. Hannu yasa ya kamo hannunta cikin k’ok’arin hanata ci gaba da matsawa. Tsoro Ya hango sosai saman fuskarta. Sai ya soma sassauta rikon da yai mata a hankali. D’ankwalinta da ya fad’i gefe ya d’auko. Ummul taga Ya kuma nufota taci gaba da k’ok’arin matsawa Har saida ta isa jikin gado. Ga mamakinta bai mata komai ba sai rufa mata D’ankwalin da yai. Ya kuma duk’awa gabanta suna fuskantar juna. Ta sadda kanta kasa tsoron dake fuskarta bai gushe ba. "A hankali ya soma fad’in “Look, you can call me a monster, but I don’t hate you… And..that doesn’t mean I like you either.. Kuma idan har kikayi abinda na sakaki.. Believe me, I’ll let you go..”" Ta dago raunannun idanunta tana dubansa. Sai Ya jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa. Dubansa take shima ita yake duba. Sai ta sadda nata idon a hankali tana mai girgiza masa kai alamun a’a. Cikin sanyin murya mai gauraye da rauni take furta “Ubangijina Ya bani umarni da nai maka biyayya cikin abinda bai sab’a masa ba. An shar’anta wa mace neman al’jannah a k’ark’ashin mijinta. Kaman yanda shima namiji nashi aljannar yana k’ark’ashin mahaifiyarsa. Ka sani Mommy da kake k’ok’arin turawa kurkuku naka aljannan ta wajenta aka ce ka nema.?” Shiru baice komai ba. Ummul ta goge hawayen da suka gangaro mata kafin taci gaba “Shin akwai D’an Adam din da zai wasa da aljannarsa.?” Cikin k’arfin hali Tai maganar dukda zuciyarta dake bugawa. Katseta Haidar yai da fad’in “Shut up.!” Ya katseta yana mai nunata da yatsa kafin yaci gaba “Who do you think you are.?” Ya kuma girgiza Kai yana rage muryarsa cikeda gargad’i “You don’t have the right to speak to me that way.?” Sai ta tsinci zuciyarta da ba ma Haidar amsa da fad’in ‘Ni matarka ce.!’ Kaman Wanda yaji amsar da Zuciyar nata ta bayar sai yaci gaba da jinjina Kai had’ida furta “Kiyi gaggawan yin abinda na umarceki for your own freedom. You don’t want to live with a monster as a husband.!” Ya k’arashe yana tsareta da ido. "Girgiza masa kai tai “Kai ba mugu bane. Kana kuma da zuciya mai kyau.. Wanda har zaiji tausayin dabba Ya bata abinci bana jin zaik’i jin tausayin mahaifiyarsa wacce tai sanadiyar zuwansa wann duniyar, ta rainesa har kawo girma..”" Katseta yai da fad’in “Enough.! Ya isheki haka.. You don’t know anything..! Ke baki san komai ba gameda wann matar.!” Sosai Ummul ta razana da yanayinsa. "Haidar yaci gaba cikin tsananin huci “Yes you might be right.! Watak’ila tayi sanadiyan zuwana wann duniyar. Amma naso ace ta barni na Mutu ina yaro da rayuwar k’unci da ta bani.! Yes. Watak’ila ta raine ni kaman yanda kikace. But I was sacred the whole time!” Yaci gaba da jinina Kai yana duban Ummul da idanunsa da suka kad’a sukai jazir “She raised me while degrading me.. While insulting me.. She raised me locking me up in a dark room. Forcing me to eat papers. She raised me punishing me for her sins.!” Yaci gaba “Because of her.. I grew up feeling low self esteem, feeling insignificant… I had a hard time living in myself..!” Yaci gaba da huci yana jinjina akai “And for years… It took me years to overcome the fear and the trauma..!” Ya matso da fuskarsa kusan nata “Did you know na girma ina shakku da kokonto if she’s really my real mother.? Do you know how it feels ka girma cikin shakku da kokonton sanin wanene kai.?!”" Suka dauki lokaci a haka suna duban juna hawaye na gangaro ma Ummul. Haidar ya matso kusanta had’ida sassauta murya “So don’t act like you know everything.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma yunk’urin rufeta ba. Tana jin sautin tashin motarsa. Tai saurin Lek’awa nan taga Ya fuzgi motar ya bar wajen a guje. Tabi bayan motar da kallo Har ya b’ace ma ganinta. Sai ta tsinci kanta da masa addu’an kasancewa cikin aminci. Jiki a sanyaye ta dawo da baya ta zauna saman gado had’ida rapka tagumi. Ta rasa mai zuciyarta ke ji gameda al’amarin Haidar. Idan ta fahimcesa kaman dai ya amo da abinda ke masa ciwo a zuciya ne. Har k’asan zuciyarta bata jin shid’in mugu ne. Sai ta stinci zuciyarta da tausaya ma rayuwar Haidar d’in. Dan bayan abinda ya gama amo mata ta fahimci alak’arsa da mahaifyarsa ya samo nakasu ne tun yarintarsa. Sosai taji tana son sanin asalin wanene Haidar. A wata fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k’addara mai kamanceceniya musamman a b’angaren abinda ya shafi alak’arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad’o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata. Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba. ** Hisham yai tsaki a karo na ba adadi. Da alama amfanin Dareen ya k’are cikin rayuwar Haidar. Da alama Anisa ce kawai yanzu zatai masa amfani wajen cimma burinsa. Idan kuwa har amfanin Dareen ya k’are baiga amfanin zamanta da Haidar ba. Watak’ila idan asirin da Dareen tai masa ya karye Haidar zai fito da Ummul daga yanda ya b’oye ta. Bazai iya jure rashin sanin ina Haidar yakai Ummul ya b’oye ba. He knows Haidar so well. Idan zai Mutu bazai tab’a sanar da kowa ga yanda ya b’oye Ummul ba. Shi mutum ne da ke aiwatar da abubuwansa ba tareda shawarin kowa ba. Shi mutum ne da baida kusanci da kowa face zuciyarsa da abinda ta raya masa. Idan kuwa har haka ne Dareen batada wani amfani. Da ita da dodon nata k’arya suke. Tinda asiri baiyi wani aiki ba ya kamata ya gwada tactics d’in Anisa. Watak’ila ta haka zai samu ya mallaki Ummul. Shi Akan ya rasa Ummul ya yarda zai iya abandoning mission d’insa na ganin bayan mahaifinsa wato Engr Aliyu Maitama da ahalinsa. Da wann tunanin ya mik’e yana huci yana ayyana a cikin zuciyarsa bazai tab’a bari ma Haidar Ummul ba. Soyayyarsa ga Ummul ne last abu da ya kamata ya tabba bai bari Haidar ya rigasa samu ba. Hajja ta saka masu albarka dashi da ita. Ummul bata cancanci miji irin Haidar ba. Bata cancanci zama cikin ahali irin na Maitama ba. Akan ya mallaketa ya yarda ya rasa komai. Ya isa ya janyo wani drawer. K’asan drawer d’in ya daga tile guda sai ga wani bak’in tulu an rufe samansa da jan kyalle. Dama shi yake ajiye da wann tulun Wanda hakan yasa ya rik’e Dareen a tafin hannunsa. Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i dukda da ita da sunanta da sumarta da na Haidar aka had’a akai asirin amma batada say dan bata san ina Hisham ya b’oye tulun ba. Shiyasa a kullum take bin Hisham a sannu dan Dodon tsafi ya sanar dasu duk randa wann tulun ta fashe asirin zai karye sann Haidar zai rabu da ita zai nuna bai ma tab’a saninta ba. Koda Hisham yaji haka sai yai wuf ya d’auke tulun ya b’oye dan ya samu ya rik’e Dareen cikin hannunsa ta dinga yin duk abinda ya Umarceta. Wann dalili yasa Dareen batada say sai abinda Hisham ya fad’i sabida Tulun na wajensa ya masa b’oyo mai nisa kaman yanda Dodo ya sanar da ita. Hakan yasa Dareen ke bin Hisham a sannu gudun kar ya fasa wann tulun ya karya asirinta na kasancewa matar Haidar. Sauri sauri ya fito daga gidan nasa tulun rungume cikin hannunsa. Dareen na tsaye haraban gidan tana faman safa da marwa ta hangi Hisham na zuwa. Tai tsaye Cak tana dubansa k’irjinta na bugawa. Bata Ida razana ba saida ta hangi hannun Hisham rungume da bakin tulun da Dodo ya k’ulla aurensu da sumarta da sumar Haidar ya rufe cikin wann tulun ya kuma tabbatar mata matuk’a wann tulun na nan yanda yake aurensu da Haidar babu abinda zai samesa sai mutuwa ce zata raba. Ta nufo Hisham cikin rawar jiki tana fad’in “Finally ka zab’i ka dank’a min ajiyan makullin aurena da Haidar.!” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Dakatar da ita Hisham yai da fad’in “Stay right there.!” Dareen taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Cikin rawar murya take furta “Hi….Hisham.. What’s going on..?” Murmushi Hisham yake da gefen baki “You are no longer useful to me.. Kuma kinsan abinda nake da mutanen da basuda sauran amfani wajena.. I dispose them.. Just like this..” Ya k’arashe yana k’ok’arin sakin tulun. Dareen ta zaburo tana k’ok’arin yowa Kansa “No Hisham don’t do this.. Please kar ka aikata min haka.. Kar ka tsinka igiyan aurena da Haidar.. Wllhi I truly love him..!” Dariyar rainin hankali Hisham yai “Love.? Did you just say love.. How is that relevant.? Ta ya zakiyi soyayya da mutumin da bashi a hayyacinsa. bai san dake ba ko ince baisan da Aurenki ba.? Ko kuma nace idan ma ya sani auren na fluctuating cikin kansa.” Dareen ta girgiza Kai tana hawaye “Watak’ila baisan ya akai Aurenmu ba amma nayi alk’awarin kare wann auren till my last breath. You can’t break our marriage Hisham.” Ya kuma murmusawa har lokacin bak’in kwaskon na cikin hannunsa “Na tuna miki yanda akai kuka hadu ne.?” Ta kasa cewa komai sai hawaye dake gangaro mata. Hisham yaci gaba “Wani rana ne a airport. Zamu tafi wani construction work Lagos muka hadu dake a jirgi. Tinda naga yanda kike kallon Haidar na tabbata kin kamu da sonsa. Kinyi ta k’ok’arin shige masa amma sai kika lura bazaki samu chance dashi ba. Har dai kaman kinyi giving up. Ni na sameki nai Miki proposing idan kina son Abokina da gaske. Kika kuma tabbatar min zaki iya komai dan kawai ki mallakesa. Na baki zab’i cewa zaki mallakesa amma zaki min aiki a jikinsa. Zaki zame min tamkar spy wacce zata dinga nado min komai na duk abinda yake ciki a rayuwarsa domin Nima na cimma burina Kansa. Dani dake muka had’a k’arfi da k’arfe. Ni na nemo Miki sumar Haidar muka had’a da naki sumar muka Kai gaban dodon tsafinku aka k’ulla aurenku da Haidar kaman yanda Dodon ya buk’ata. Ya kuma tabbatar mana duk yanda Haidar yake zai bayyana matsayin mijinki.. Zaki bayyana masa matsayin matarsa.. Haka ne.?” Taci gaba da girgiza Kai tana hawaye. Hisham yaci gaba da murmusawa “Kiyi gaggawan b’acewa daga cikin rayuwar Haidar. Dan idan kika jira na fasa kwaskwon nan Haidar sai ya kusa kashe ki da hannayensa kafin ya mik’a ki ga hukuma.” Dareen na huci take dubansa “Na ranste da Allah baka isa ba Hisham. Baka isa ka rabani da abin kaunata Haidar ba.!” Ta k’arashe tana kokawan k’wace bakin kwaskon daga hannun Hisham. A daidai lokacin Haidar ya k’araso. Hisham na hangosa yaci gaba da kokawan k’wace kwaskon daga hannun Dareen yana fadin “Allah ne ya toni asirinki mushirika. Ni dama na jima da fahimtar ba tsakani da Allah kike zaune da abokina ba. Kuma yau sharrinki zai koma kanki dan sai na fasa wann kwaskon da na ganki dashi. Yau Haidar zai fahimci gaskiyar abinda naita nusar dashi akanki.!” Aikaw garin kokawan k’wace kwasko ya fad’i k’asa ji kake tasss ya fashe. Sai ga bak’in hayak’i na tashi. Dareen ta saki k’ara tana soshe soshe yayinda Haidar ya Kama Kansa da yai wani irin sara masa. Ya duk’a nan wajen yana rik’e Kansa had’ida sakin k’ara da bai san yana yi ba. Nan ya kwanta wajen tamkar sumamme. Hisham yayo Kansa a guje yana jijjigasa yayinda Dareen ta k’araso tana haki ta dubi Hisham dake jijjiga Haidar Wanda da alama ya sume. Ta nuna Hisham da yatsa “This is far from over Hisham. Ko ince shadow ka tsammaci dawowa ta dan nice zan dawo maka a matsayin Shadow.!” Murmushi Hisham yai mata da gefen baki “Kafin ki dawo na Miki alk’awarin na d’auke abinda nake son d’aukewa daga wajen Haidar. Bazaki sameni cikin rayuwarsa ba.!” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda. Da baya da baya ta dinga tafiya har ta shiga gidan a guje ta soma tattara ya nata ya nata. Hisham ya d’auki Haidar ya shigar dashi cikin gidan ya kwantar sa saman kujera. Bayan ficewar Dareen. Bayan shud’ewar wasu mintoci Haidar ya soma bud’e idonsa da sukai masa nauyi yana jin kaman abin da a kullum yake ji ya masa nauyi a k’irjinsa anyi lifting masa. Wani cunkushewa da yake ji zuciyarsa da kwanyarsa suna masa sai yaji kaman an d’aga masa Abu mai nauyi da aka ajiye cikin k’irjinsa. Tilon abokinsa Hisham ya gani zaune gefensa yana danna masa towel saman goshinsa. Hisham na ganin Haidar ya bud’e ido ya sakar masa murmushi yana hamdala “Alhamdulillah Haidar ka tashi.!” Sosai Haidar ya mik’e yana k’are ma Hisham kallo “Meke faruwa Hisham. What just happened.?” Hisham bai Kai ga basa amsa ba ya hangi hotonsa da na Dareen mak’ale a parlorn ta mak’alk’ale cikin jikinsa. Ya juyo yana duban Hisham zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Sai ya mik’e ya isa jikin hoton yana kallo sosai. A hankali komai yake dawo masa. Tin daga had’uwarsu a airport da irin shige masa da taso yi bata samu k’ofa ba. Dan har wajen aikinsu a Lagos ta bisu. Da tsanar da yai mata. Ya kuma tuna Tabbas yayi zaman aure da ita auren da bazai ce ga yanda aka k’ulla ba. Auren da wani lokaci Ya tuna da ita wani lokaci Ya mance da ita. Idonsa naga hoton yake furta “Ya akai na k’are da auren yarinyar nan Hisham.?” Hisham ya mik’e yana mai furzar da huci. Ya dan tako kusan Haidar d’in su duka biyu suna kallon hoton kafin Hisham yai gyaran murya “Tambayar da na jima ina maka Haidar. Ka mance.?” Hisham yaci gaba “Tun a fari ban San ya akai haka ta kasance ba Haidar. Sanin irin k’iyayyar da Kai ma yarinyar a haduwarku ta farko a airport. Ka tuna.? Ganinka kawai da ita nai matsayin matarka bansan ya akai k’iyayyar da Kai mata ya rikid’a ya koma soyayya ba. Soyayyar da har ta kaiku ga aure. Auren da bayan ni ko iyayenka baka sanar masu ba kuma nima ka haneni na sanar masu.” Haidar yai shiru kaman mai nazari dan yasan duk anyi haka. Idonsa ya kada sosai yake duban hotonsu da Dareen yana tuna irin rayuwar da sukai Wanda sai gashi yana son tuno Abu ko tambayarta wani Abu sai ya kasa ko ya mance “How is this possible Hisham.?” Hisham ya girgiza Kai kad’an “Baka a hayyacinka ne Haidar.. Kaga wann..” Ya k’arashe yana nuna masa bakin tukunyar da ya fasa. Haidar ya tako yana duban abun da mamaki. Abun da shi bai tab’a believing ma anayi ma mutane ba balle yayi tasiri akansa. "Hisham yaci gaba “Kwanaki uku kenan bamu hadu da Kai ba. Naje asibiti wajen d’aya matarka dake kwance asibiti a tunanina zan sameka can ban sameka can ba. Hasalima Likita ya sanar Dani ka d’auki matarka kun tafi babu Wanda yasan ina kuke. So sai nayi tunanin nan gidanka ka kawota maybe ka had’ata da matarka Dareen. So da nazo sai na tadda Dareen rik’eda wann kwasko da kake gani tanata wasu sunbatu more like rituals, kaman ma yare take dan ban fahimci mai take cewa ba. So sai jikina ya bani wani Abu ba daidai bane. Musamman yanda taketa ambaton sunanka ga yare tanayi ga kuma wann tukunyar cikin hannunta. Koda ta ganni ta razana sosai nan na fahimci my hunch was right. Shine kaga ina kokawan fasawa har Allah ya taimakeni nai nasaran fasa wann kwaskon Wanda ko shakka babu na tsafin ta ne.”" Hisham ya numfasa dan har lokacin Haidar bai iya cewa komai “ Ka gode ma Allah Haidar da ya maida mata sharrinta kanta.” Yai maganar yana mai dafa Haidar d’in. Haidar baice komai ba sai komawa parlor da yai ya zauna saman kujera ya k’ura ma waje guda ido. Har lokacin bai dawo daidai ba da alama. Hisham ya dafasa kad’an “Is not easy.. Abinda kake going through ba abu bane mai sauk’i Haidar. Ace ka zauna da mace ak’alla tsawon watanni shida ba tareda sanin ya akai ka aureta ba akwai tashin hankali… Amma na maka alk’awari zata biya abinda ta aikata maka abokina. I’ll look for her yanda ta shiga ta fita.. we can’t let her get away with what she did to you..!” Ya mik’e yana jinjina Kai alamun tabbatarwa. Lokaci guda yasa kai ya fice da zummar neman Dareen. Kai kace da gaske Har zuciyarsa ya damu da Haidar d’in ne. Haidar ya bisa da kallo har ya bace masa ba tareda yace komai ba. Ya jima zaune wajen yanata kallon hotonsu shida Dareen. Bazai ce ga abinda yake ji ba. Saidai wann nauyin da a kullum k’irjinsa ke masa yaji kaman anyi lifting abu mai nauyin. Like he’s free from captivity. Amma freedom da bazaice ga makomarsa ba. Jiki babu k’wari ya mik’e ya fice daga gidan ba tareda ya jira dawowar Hisham ba. A b’angaren Hisham kaw ficewa yai cikin k’ok’arin cimma Dareen dan yasan ta yanda zai bullo mata kafin tai gangancin b’ata masa shirinsa. Saidai koda ya fita bai cimma Dareen ba ga wayarta bata shiga. Yaita buga tsaki yai saurin dawowa ga Haidar dan ya samu yaji ina yakai Ummul ya b’oye. Saidai yana dawowa yaga wayam babu Haidar babu dalilinsa. Ya buga tsaki yana naushin kujera da hannunsa “Damn you Haidar.! Damn you.!” Yayi duk abinda zaiyi ne dan ya gano yanda Haidar ya b’oye Ummul amma da alama Haidar ya fice ya tafi ba tareda ya jira dawowarsa ba. Bayan duk abinda yai ma Haidar d’in still yai zab’i yaita yin abubuwansa ba tareda ya sanar dashi ba. Haka ya dinga tsaki shi bai cimma Dareen ba bai kuma tadda Haidar ba. Ficewa yai yana dialing layin Anisa. ** A b’angaren Haidar kaw koda ya k’araso gidan zama yai a veranda dake nan wajen gidan. Bai bi takanta ba bai nemeta ba sai zama da yai ya daura hannayensa saman k’afafunsa Kansa kife tamkar maras lafiya ko Wanda ke cikin yanayin damuwa. Ta window ta hangi motarsa. Tai mamaki Jin bataji shigowarsa ba yau d’in. Tai saurin mik’ewa ta yafa mayafin doguwar rigarta ta nufo waje. Nan ta gansa zaune ya kifa Kansa ga tsuntsayen da yake basu abinci Sun kewayesa amma ba abincin yake basu ba. Sosai taji mamakin ganinsa haka sai ta soma takowa cikin sand’a kaman mai tsoro ta k’araso Sallama saman bakinta. Amma sai taji shiru bai amsa ba. Ta d’anyi gyaran murya tace “Ka mun izinin…. Zama.?” Nan ma shiru bai amsa ta ba. Sai dai kawai tai ta maza ta zauna daga can gefe dashi tana satan kallonsa ganin bazai amsata ba. Har lokacin Kansa a kife yake. Bai d’ago ba bai ce da ita komai ba. Ta dan sha jinin jikinta sai ta soma kallon yanda tsuntsayen suketa kewayesa alamun suna jira ya basu abinci. Ta saki murmushi a hankali tace “Kaman dai… Kai suke jira..” Yanda tai maganar zaka fahimci k’ok’ari take ta had’a kalaman saman harshenta. Nan ma shiru bai ce komai ba. Ta d’an k’ara satan kallonsa still yana nan yanda yake. Ta maida kallonta ga tsuntsayen “Bari ni na baku…. idan zakuci nawa.” Tai maganar murmushi saman fuskarta. Har lokacin yana nan yanda yake. Mik’ewa tai tana satan kallonsa har lokacin yana nan yanda yake. Ta tafi ta dauko sauran abincin da Haidar ya kawo mata na ranan da ya gabata. Ta k’araso a d’arare tana watsa masu sai suka fara tashi sama suna guduwa. Ta d’anyi rau rau da ido tana kallonsu “Kaga ni basa son na basu.. dan Allah ka amsa ka basu.. Kaga guduwa suke..” Tai maganar kaman zatai kuka tana duban Haidar Wanda sai a lokacin ya dago fuskarsa yana dubanta. Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i gani da tai fuskar nasa cikin wane irin yanayi da zatace bata tab’a ganinsa ciki ba. Ga idanuwansa Sun kad’a sunyi ja sosai. Duk sai jikinta yai sanyi. Ta sadda nata idon a hankali tana tuhumar kanta mai ma ya kawota yanda yake.? Wata zuciya tace ta haka ne kawai zaki iya fahimtarsa idan har kina son sanin wanene shi. Wata Zuciyar ta gargad’eta ‘Anya baki tafi da nisa ba Ummul.?’ Sai ta soma k’ok’arin janye jikinta da nufin barin wajen amma sai taga hannayensa saman nata. Ta d’ago a d’an razane tana dubansa. Shid’inma ita yake duba. Wann karon fuskarsa ya zama pale sosai tamkar ta marassa lafiya. Batasan ya akai ba sai ji tai ya rungumeta sosai cikin jikinsa had’ida kwanto da Kansa saman kafad’arta. Zuciyarta yaci gaba da harbawa. Har lokacin Haidar na nan rik’eda ita idanunsa a lumshe. Yayinda jikin Ummul ya gama yin sanyi. Kaf nauyinsa ya d’aura mata saman kafad’arta. Ta kasa katab’us ta kasa koda motsawa Haidar kaw bai saketa ba. Sun jima sosai a haka kafin taji yana sassauta rik’on da yai mata. Ya soma k’ok’arin mik’ewa tsaye fuskarsa a matuk’ar tsare kaman ba shine ya gama rungumarta ba. Kauda kansa gefe yai kad’an yayinda Ummul tai k’asa da fuskarta cikin sanyin jiki. Saida ya mik’e tsaye sosai ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa kafin ya dubeta “Let’s go.” “Na’am.!” Ta fad’a a dan daburce had’ida dagowa tana dubansa. “Pack your things we are leaving..” ya fad’i yana nufan mota. Mamaki ya cika Ummul. Allah mai iko.. Toh kodai Addu’arta ne suka fara karbuwa.. Allah yasa haka ne. Allah yasa Zuciyar Haidar ne ta karkata ga mahaifyarsa kaman yanda take ta addu’a. Cikin sauri ta mik’e tai yanda yace. Tana karasowa yasa hannu ya bud’e mata front Seat ta shige a d’arare. Tana addu’an Allah yasa ba wani wajen zai kaita ba. Ita dai addu’a kawai take cikin zuciyarta tinda suka baro wann gida dake tsakiyan daji a cewarta. Ganin sun nufi gari yasa hankalinta ya soma kwanciya. Bata Ida mamaki ba saida taga sun doso wani dogon gini mai d’aukeda ‘yansanda tin daga waje. Suna isowa yace ta fito. Tai yanda yace tana biye dashi suka shige cikin ginin. Haidar ya nuna mata wajen zama kafin ya k’arasa yai magana da wasu ‘yansanda. Dawowa yai yanda take ya zauna daga gefe. Sai faman rabe raben ido take tana duban wajen. Can ta hango Mommy tafe ta nufo yanda suke. Cak Ummul ta mik’e k’walla na ciko idonta yayinda idon Mommy ma ke k’ok’arin zubda k’walla. A hankali Ummul ta furta “Mommy.!” Tuni Ummul ta soma takowa zuwaga Mommy su duka biyun hawaye ke zubo masu. A yayinda suka cimma juna kuwa sai suka rungume juna suna masu bursting cikin kuka. Mommy ta tallafo fuskan Ummul tana duba murmushi saman fuskarta “I knew you’d come…” Shiru tai tana duban Ummul d’in kaman wacce ta tuna wani abu. Dan ita dai Mommy har kawo wann lokacin gani take turaren da boka ya basu ne mai guba ciki Wanda ya tassama ajalin Ummul. "Hannayen Ummul ta kamo, tana mai kuma k’ak’aro murmushi “Are.. You here to withdraw the charges against me..? Zaki janye k’aran dake kaina..?”" Saurin girgiza Kai Ummul tai “A’a Mommy dama babu wani k’ara.. Dan Allah kar ki fad’i haka.. Ina Jin kaman laifi na ne da aka ajeki nan… Kiyi hak’uri banzo da wuri na fiddake ba Mommy..!” Ta k’arashe cikin rawar murya. Murmushi Mommy ta kuma yi tana mai rik’e hannayen Ummul cikin nata sosai “Baki mun komai ba Ummul face alkhairi… Just like your name.. Ke d’in alKhairi ce.!” A hankali Ummul ta sadda idanunta k’asa. Allah sarki sai ta soma tuna kalaman da Mama da yaranta harma da mutanen unguwa ke jifanta dashi wani sa’in harda nata mahaifiyar cewa sunan bai kamaceta ba babu wani alheri tattare da ita sai akasin sa. Mommy takai dubanta ga b’angaren Haidar Wanda ke tareda ‘yansanda ga lawyer d’in Mommy ya iso suna kula da al’amarin. Ko kallo Mommy bata ishesa ba. Sanda ya k’araso yanda suke Ummul kawai ya duba fuska a matuk’ar tsare “Let’s go..” Har ya juya zai soma tafiya sai ya kuma juyowa ya dubi Mommy “Your driver will be here to pick you.” Ya maida dubansa ga Ummul “Don’t waste my time.!” Yana ida fad’in haka yasa kai yai shugewarsa cikin sassarfa. Ummul ta bisa da kallo jiki a sanyaye sai kuma ta juyo ta dubi Mommy. Jinjina mata Kai Mommy tai murmushin k’arfin hali saman fuskarta “Just go. Go with your husband.. Don’t worry about me I’ll be fine.. Ya k’ira driver zai zo ya d’auke ni. Tashi kije kinji. Allah ya tsareku yayi maku albarka.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Jiki a sanyaye Ummul ta mik’e. Mommy ta bita da kallo zuciyarta na mata sanyi. Ficewar su Ummul da kad’an ta hangi Daddy na shigowa. Sosai mamaki ya cika Mommy ganin Daddy yana shigowa. Toh mai ya kawosa.? Ta zaci zai rabu da ita kaman yanda ta basa zab’i. Ta zaci zai zab’i Kasuwancinsa da reputation d’insa sama da ita da D’anta da a kullum yake ikirarin basuda wani amfani cikin rayuwarsa. Take kuma zuciyarta ta soma raya mata toh kodai zuwa yai ya tabbata ya yanke sauran alak’arsa dake na har abada.? Kodai zuwa yai ya tabbata bazaki koma gidansa ba daga nan.? Dukda bugun zuciya da tunanin ya haifar mata hakan bai hanata kauda fuska tai kaman bataga zuwan Daddy ba. Ya k’araso yana mai gyaran murya. Dan ya tabbata taga zuwansa amma tai biris dashi. “Barrister called….. and told me you are free now.” Ya fad’i daga nan yanda yake tsaye. "Ta kaiakito da kyar tana dubansa, bata ce komai ba sai ta kuma kauda fuska." Daddy ya had’iyi abinda ya tsaya masa “Shall we go now.?” Ya fad’i a hankali. Bata tashi ba sai ta girgiza kai “Haidar ya kirawo driver na zaizo ya d’auke ni..” Da mamaki Daddy ke girgiza Kai “Kwaise did you hear yourself.? Ya inace miki ki tashi mu tafi kina ce min Haidar ya kira driver..” Mommy ta kaikaito sosai suna fuskantar juna daga nan yanda take zaune “You shouldn’t be here in the first place.. Kai babban mutum ne dake jagorancin babban kampani.. Bai kamata a ganka a waje irin nan ba. It won’t be good for business and your reputation.” “Enough Kwaise. Nasan ina kalamanki suka dosa.. But this is not the right place to talk about that.. Ki tashi mu tafi gida then we talk..” “Kai hakuri kaje kawai Engr. I don’t want to go with you..” Mommy tace cikin Shan k’amshi. Mamaki ya mugun cika Daddy. Shine Kwaise take turning d’insa down. Ya baro tulin ayyuka tinda Lawyer d’inta ya kirasa ya sanar dashi halin da ake ciki cewa Haidar yazo da matarsa kuma an janye k’ara Akan Mommyn. "Yai mugun tsarewa “Haka kika ce.? Fine, ki sani duk direban da yazo ya d’aukeki a bakin aikin shi.”" Ta dubesa da mamaki “Zaka koreshi aiki dan yazo d’aukata.?” “Of course I’ll have him fired.” Ya bata amsa Kai tsaye. Mik’ewa tai “Shikenan ni zanje na shiga motan haya..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa. Yai saurin dakatar da ita “Umarni nake baki a matsayina na mijinki.. Idan har zaki bawa matar D’anki umarni da tabi mijinta Ashe ke ya kamata ki fara bin umarnin naki mijin.” Yanzu kuma ta nan ya b’ullo.? Kenan ya jima da zuwa station din Akan idonsa tace ma Ummul tabi Haidar. Ba don taso ba sai dan babu yanda ta iya haka tabi bayansa kaman rak’umi da alkala. Har suka iso gida daga ita har Daddy fuskokinsu babu walwala babu mai cewa da kowa komai. Abun sai mamaki yake ba ma Daddy wai Kwaise ke banza dashi irin haka. Matar da tsawon zamanta a gidan tin bayan abinda ya faru batada buri face taga itada D’anta sun samu attention d’insa. Koda suka isa gida basu tadda motan Haidar can ba. Addu’an mommy d’aya Allah yasa ba wani wajen Haidar ya kuma kai Ummul ba. Suna isa Mommy ta bud’e k’ofa ta fice. Daddy yai saurin fitowa had’ida dakatar da ita. “Kwaise what’s with the attitude.? This is not like you..? Ya kike Abu kaman wata yarinya. Abinda bakiyi ba a k’uruciya.. Akan Haidar kike duka wad’ann abubuwan.? Ina Haidar d’in.. Ina yake a nan..? I can’t believe you are risking everything… And even our relationship for him.. D’an da bai damu dake ba.” "Juyowa tai tana dubansa, sai tai murmushi wann karon “Did you say our relationship.?” Ta dan kuma girgiza Kai “I thought all you care about is your business.”" "Cikeda mamaki ya girgiza Kai “Kwaise, amma kinji yanda kike mun magana.?”" "A hankali ta sadda kanta k’asa “Tuba nake. Allah ya huci zuciyarka Engr…. Idan akwai abinda kake buk’ata kafin ka koma company.. I’ll have it prepared for you..” Dakatar da ita yai da fad’in “No, bani buk’atar komai.!” Yanda yai maganar zaka fahimci ya gama tunzura amma sai Mommy ta murmusa ta dubesa." “Thank you… for driving me home..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana mai shigewa. "Daddy ya bi bayanta da kallo. Maiyasa ya d’auki shawarin Alhaji Gimba da yace yaje ya dawo da Kwaise gida.. Dan lokacin da Lawyer d’insa ya sanar dashi halin da ake ciki gameda batun case din Mommy suna tare a company da Alhaji Gimba kuma shi ya basa shawarin da yaje ya d’auki iyalinsa ya maidata gida, ya tafi da Kansa shi kad’ansa ko driver bai bashi shawarin d’auka ba. Gashi nan ya baro abinda yake dik irin mahimmanci da yake ba ma aikinsa yazo kwaise tana masa abinda batayi da ba. Ko shiga gidan baiba yai komawarsa company." "Anisa duniya sabuwa, tana zaune parlorn Mommy ta mimmik’e k’afafu tana bawa ma’aikatan gida umarni da order Kai kace itace Madam din gidan Mommy tai Sallama. K’iris ya rage Anisa bata saki glass cup d’in dake rik’e ciki hannunta ba." SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *38* *©️Sameena Aleeyou… * Zumbur Anisa ta mik’e tana duban Mommy cikin tsananin shock. Gaba d’aya sai ma ta daburce ta rasa mai zatai… Kaman wacce aka sinkara ta tafi a guje sai kuma taja ta tsaya gaban Mommy murmushin da yafi Kama da yak’e saman fuskarta “Mommy.. Are you free now… Omg! I’m so happy you are free.. Thank goodness you are free Mommy..!” Ta d’anyi rau rau da ido tana duban Mommyn “Can I.. Please hug you..?” Tai maganar kaman zatai kuka. Sosai Mommy ta tsare tana dubanta Wanda har saida yasa Anisa Shan jinin jikinta. Zuciyarta ya cika da tsoro da fargaba. Gani take kaman asirinta ne ya tonu… Kar dai Mommy ta gane gaskiya ne cewa ita ta zuba ma Ummul guba cikin turare ta kumayi incriminating d’inta.. Tsoro da fargaba suka hanata motsawa.. Mommy ta juye mata Kwaise matamar ta wacce bata d’aukan wani shit. Har ta gama saduda kwatsam ta hangi Mommy na sakar mata murmushi. Bugun Zuciyar Anisa ya soma yin k’asa. Mommy ta bud’e mata hannaye “Silly girl.. Come here.” Tai maganar murmushi irinta manya saman fuskarta. Anisa ta k’araso da murmushi ta rungume Mommy a d’an d’arare tana fad’in tayi kewarta.. Gaba d’aya gidan ba dad’i sabida bata nan.. Mommy ta harareta “Ke tafi can rufe mun baki.. Ai Shiyasa na ganki zaune kin nad’e k’afa bak’e bak’e kina cin Duniyarki da tsinke.” Tai maganar tana mai shigewa lokaci guda tana ceda Anisar tai mata kiran d’aya daga cikin ma’aikatan ta. Har Mommy ta shige Anisa bata dawo daidai ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Meke faruwa.? Waye ya fitar da Mommy.. Toh kodai Haidar ya fito da Ummul ne daga yanda ya b’oye ta.? Tunani daban daban cikin kanta.. Wayar Hisham ne taga ma shigo mata. Tai saurin d’agawa tana barin wajen. Daga d’aya b’angaren Hisham yace “Tell me what’s going on there..? Is Haidar there..?” "Anisa ta rausayar da ido had’ida furzar da huci “No, Haidar is not here but My Aunt Hajiya Kwaise is here.. She’s free now..”" "Tsaki yai yana fad’in “Well I don’t give a damn about your Aunt, and much less about her freedom. Tell me is Ummul there..? Do you know her whereabouts..?”" Anisa ta murmusa tana kuma rausayar da ido “I don’t care about Ummul or whatever.. And much less her whereabouts.. All I care about is Haidar.. I don’t care if she never shows up.. I don’t care if she dies matuk’a Haidar zai dawo gareni..” “Shut up.!” Hisham ya katseta kafin yaci gaba “Kina ji.. Idan har Hajiya Kwaise is free that only means Haidar ne ya fitar da ita ko Ummul.. Kuma jikina na bani idan har ba Ummul bace tai escaping daga fursunan da Haidar ya b’oye ta toh kuwa Tabbas Haidar zai bayyana a gidan anytime soon.. Use your brain and do something useful ki gano mana ina yaje ya b’oye Ummul.. Idan kikayi wann kin gama naki.. Leave the rest to me.. Zan kula da komai.. Na Miki alk’awari zan d’auke Ummul daga rayuwar Haidar.. And Haidar is all yours..” "Anisa sai ta fara dariya dan murna tana fad’in “Seriously, are you for real.. Zan mallaki Haidar.”" Furzar da huci Hisham yai cikeda takaicin Anisa dan ya kula shashasha ce lamba d’aya. Bai tsaya sauraron sakarcin Anisa ba ya katseta da fad’in kar tai gigi b’ata masa shiri.. Muryarsa ne ya sark’e sakamakon hango motar Haidar da yai k’ofar gidan Haidar d’in yanda suka zauna da Dareen dan dama Hisham bai bar area din ba sabida zuciyarsa bata daina raya masa Haidar ko Dareen d’ayansu ka iya waiwayan gidan ba. “He’s here..” Anisa ta girgiza Kai cikin rashin fahimta “Who’s there..?” “Haidar.. Haidar Maitama of course..” Anisa ta zaro ido kaman yana ganinta “You mean Haidar my cousin.. Toh kasan mi.? Do something to distract him..” Hisham yace “What do you mean..?” "Anisa tace “I don’t know.. Just do whatever is necessary.. Think of something.. Something that will lead you to yanda ya b’oye Ummul.. And hey, don’t think of following him.. Kasan zai iya gane ana binsa, you know how he’s.. Just ka gane.. Ka samu chance ka lalata motarsa kodai Kai wani abin. Yanda dai zaka samu yai leading dinka zuwaga mab’oyar Ummul.”" Shiru Hisham yai yana sauraron shawarin Anisa. A hankali ya soma jinina Kai “Seems like k’wak’walwarki na aiki.. I know exactly what to do.” Ya k’arashe yana katse kiran murmushi saman fuskarsa. Anisa ma murmushin tai tana kallon kanta jikin mirror haida ziga kan nata “You are genius Neesah.. Kedin akwai kwanya.” Ta k’arashe tana kuma murmusawa tana duban kanta. A b’angaren Hisham kawa tsaye yai daga nan mab’oyarsa yanda yake iya hangar motar Haidar dake lullub’e da bakin glass. Sam bai iya hangar cikin motar. A cikin motar kaw juyowa Haidar yai yana dubanta bayan ya ida parking. Nan yaga ta kwantar da kanta jikin seat had’ida lumshe ido kaman na mai bacci. Ya d’an d’auki lokaci yana dubanta kafin yai unlocking motar. Har zai fice sai ya kuma juyowa yana dubanta. Yai gajeren tsaki kafin ta soma k’ok’arin kwantar mata da kujeran yanda zataji dadin kwanciya.. Yanda ya kwanto da fuskarsa harma da jikinta kusan nasa cikin k’ok’arin kwantar mata da kujeran yasa numfashinsu sark’ewa waje guda. Yai tsaye cak da abinda yake yana kallon fuskarta wanda yai kusa dab da nashi. A daidai lokacin Ummul ta bud’e lumsassun idonta ai kaw sai cikin na Haidar. Su duka biyun fuskokinsu kaman zasu had’e. Bugun Zuciyar Ummul ya k’aro.. Tsoro ya bayyana cikin idonta masu yalwan haske a cikin nasa idon. Ta zaro idon sosai tana k’ok’arin mik’ewa amma sai taji ya d’aureta da Seat belt ya hanata mik’ewa. "Kwanto da fuskarsa ya kuma yi kaman mai shirin sunbatarta yayinda zuciyar Ummul yaci gaba da bugawa. A hankali ya zame fuskarsa. Saitin kunnenta yakai bakin nasa, murya can k’asa yace “Relax, I’m not kidnapping you.. And I’m not going to lock you away again.. Just wait for me here….I’ll be back in a bit.” Yana ida fad’in haka ya matsa baya yana mai daidaita zamansa cikin kujera had’ida yin gyaran murya kad’an. Idonsa na kallon ta yake fad’in “Bansan daga ina Mommy ta d’aukoki ta kawo ki cikin rayuwata ba. At first I was angry at you.. Sabida Mommy ta sayeki da kudi ta kawo ki cikin rayuwata.. Watak’ila dan ta cimma wani manufar ta akaina dake…” Ya d’anyi fasali still yana dubanta “My life is a complete chaos.. I know I’m a monster.. And maybe that’s what she raised me to be.. But believe me, I don’t want to hurt you..” Yaci gaba da kallon ta yana jinjina Kai “Kin amince da aurena ne sabida mahaifinki dake jinya.. Haka ne..?”" Ta jinjina masa Kai a hankali cikin sanyin jiki. Haidar yai shiru kaman mai nazari yana dubanta. Sai ya kauda fuskarsa kadan yana jinjina Kai a hankali “Even though I have an unhealthy relationship with my parents.. I know parents are important.. And they play a pivotal role in their children’s life.. Koda ace ni ban samu haka ba..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana duban Ummul “Kuma mutane masu kyakkyawan alak’a irinki da iyayensu would do the same.. So I won’t judge you for doing what you did… The only person who’s to blame here is my Mom for taking advantage of the situation… Ta duba halinda kike ciki na buk’ata tai amfani da damarta akanki da family d’inki..” "Saurin d’agowa tai tana dubansa zuciyarta na bugawa.. Ba Mommy bace Kai tsaye ta buk’aci haka daga wajenta.. Ummanta ne da Aunty Asshe k’anwar mahaifyarsa.. Shin ta yaya zata sanar dashi idan akwai mai laifi a nan ba kowa nace face nata mahaifiyar, wacce take tsananin son taga tayi aure ta bar gabanta koda Aunty Asshe bata buk’aci wani abu daga wajensu ba." Kafin ta samu wani k’warin gwiwar magana ta sinkayo muryarsa yana fad’in “I’ll set you free and go far away from here..!” Daga haka bud’e motar ya fice ya nufi cikin gidan. Yayinda Ummul tai mutuwar zaune maganganun Haidar na dukan dodon Kunnuwarta.. Haidar zai sawak’e mata yai tafiyarsa.. Zai fice daga rayuwar Mommy.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un… Mommy bata cancanci haka ba.. Iayakacin abinda take fata da buri shine alak’arsa da Mommy ya inganta ba wai yai nesa da ita ba. Ya zatai..? Mai zatai ta dakatar da Haidar kar ta tafi ya k’yale Mommy..? Sai tai lamo cikin kujera had’ida lumshe idanunta hawaye na ziraro mata. A b’angaren Hisham kaw yana ganin Haidar ya fice ya shige gidan sai ya lab’ab’o a hankali cikin sand’a. ‘Yar k’aramar wuk’a ya ciro cikin aljihun sa. Ya rarrafa jikin motar yanda babu mai iya ganinsa. A hankali ya isa jikin birki ta k’asar motar ya b’allata da wuk’ar hannunsa. Yana gama abinda zai ya kuma lab’abawa ya fice daga wajen ya koma mab’oyarsa yana jiran fitowar Haidar. Muguwar murmushi saman fuskarsa yake duban motar daga nan yanda yake lab’e. A fili yake furta “Let’s see Haidar.. Bari dai muga ina ka Kai Ummul ka b’oye.. Kaida kanka zaka kaini yanda ka b’oye Ummul sabida motarka ta buga..!” Ya k’arashe murmushin bai bar fuskarsa ba. Jim kad’an Haidar ya fito daga cikin gidan hannunsa rik’eda suitcases harda laptop bag alamun dai abubuwan amfanin sa ya d’auka. Hisham na huci yake duban Haidar sanda ya isa jikin motan. Akan idonsa Haidar ya zuba stuff d’insa bayan motar ya bud’e mazaunin driver zai shige a nan Hisham ya hango kaman mutum cikin motar.. Daidai lokacin kuma Ummul ta soma k’ok’arin mik’ewa zaune nan Hisham ya hangota cikin motar. Zuciyarsa tai wani irin tsinkewa. A fili ya furta “Ummul.? No.. No no this can’t be.. She can’t get hurt..!” Yana maganar cikin tsananin daburcewa har bai san sanda Haidar yaja motar ya bar wajen ba. Cikin rikicewa Hisham ya shige nashi motar daga can yanda ya ajeta. Yana driving yake dialing layin Anisa. Tana d’agawa Hisham ya fara cikin sakin huci “I know where Ummul is.. Tana cikin motar.. Tana tareda Haidar.!” "Anisa tace “So, come up with something.. Kidnap her and runaway.”" A hasale yace “Shut up. Just shut up.! Kece kika bani shawarin na shirya ma Haidar accident ta haka ne zai leading dina to where he hides Ummul.. Na d’auki shawarinki and tempered with his brakes. And now.. Komai ka iya faruwa da Ummul.. Damn you..! I shouldn’t have listened to your advice..!” Cikin daburcewa Anisa ke fad’in “Idiot..! I didn’t say you should temper with his brakes.. Kawai cewa nai Kai causing masa minor accident ka dan bigi bayan motarsa or something.. Amma ni bance Kai causing babban accident ba.. Do you even realize they can both die in that car..!” Sai ta fara kuka tana fad’in “Wayyo Haidar.. If something bad happens to Haidar wllhi bazan tab’a yafe maka ba.. And you will answer to me..!” Hisham ya daka mata tsawa da fad’in “Shut up. Shut your trap..! I can’t lose Ummul. Bazan rasata ba.. Kuma idan wani abu ya sameta you’ll be the one to pay the price.!” Bai kuma tsayawa sauraron Anisa ba ya Katse kiran yana mai dukan steering wheel da iyaka k’arfinsa yana tsaki. ** "A b’angaren Daddy kuwa tinda ya koma Office tunanin abinda Mommy ke masa ne ya sha masa Kai. Da fari ta basa zab’i cewa zai iya datse aurensu Idan yaso.. And now tana nuna masa kaman dai zaman D’anta kawai take a gidan. Kaman dai shid’in baida wani mahimmanci wajenta. Ya sani yaso Kwaise da duka zuciyarsa, hasalima bai tab’a son wata mace kaman yanda yaso Kwaise ba.. Amma bayan abinda ta masa.. Bayan rabasa da matarsa da sheganta cikin D’ansa da tasa yai yaji ta fita masa a rai. Ba ita kad’ai ba ko wace mace ma ta fice masa.. Yaji baya mararin wani abu mai suna soyayya because he was betrayed by macen da ya nuna mata zallan soyayya. Wanda hakan yasa ya d’ibi kwaise ya watsar sann bai kuma yunk’urin sake wani aure ba. Kaman yanda tace Kasuwancinsa shine kawai a gabansa shine rayuwarsa shine komai nashi.. Bai kuma damu ba idan Kwaise bata nuna damuwarta akansa ba. Hasalima yanda taketa Neman attention d’insa zuwa gareta da kuma D’anta tun bayan abinda ya faru sai hakan yake kuma tunzura shi yake nuna mata da ita da d’an nata basu gabansa hasalima babu abinda ya baiwa rashin mahimmanci irin su… But why’s he feeling this way now..? Meyasa yake ji yanzu da Kwaise ta fara nuna masa baya gabanta abun ke masa zafi sosai..? Meye dalili.. Meyasa yake Jin ciwon hakan bayan abinda yai buri kenan tsawon shekarun nan. Ya d’an furzar da huci yana aje pen d’in dake hannunsa." Alhaji Gimba daketa Sallama Daddy baisan da zuwansa ba sabida nisa da yai cikin duniyar tunani k’arasowa yai ya zauna kujera mai kallon na abokin nasa. Daddy ya d’anyi gajeren tsaki “Yi hakuri Gimba banji shigowarka ba..” Alhaji Gimba ya murmusa “Ina kuwa zakaji shigowata Madam ta caza maka Kai..” Yai maganar cikin barkwanci irinta abokai. Daddy ya kuma yin gajeren tsaki “Don’t please.. Don’t bring her up here.. Let’s talk business..” Girgiza Kai Alhaji Gimba yai yana juyi cikin kujeran “Abokina kenan. Kana nan a Aliyun ka da na sani.. You know your son Haidar takes after you.. Bai bar maka komai ba.” Daddy ya kuma yin gajeren tsaki “Are we going to talk about this issue again..?” “K’warai bazaka iya guje ma hakan ba.. Sabida sud’in ahalinka ne.” "Daddy ya kuma lumshe idonsa cikeda k’osawa “Gimba please, my day is bad enough coming to add to it.. Kar ka min maganan D’aya cikin biyun nan..”" “Abinda nake fad’a maka a kullum shi zan sake tunasar dakai. Bakada Wanda ya fi maka su.. Sud’in ahalinka ne..” "Daddy ya kuma yin tsaki “Gimba, please get out before I ask my secretary to escort you out.!” Ya k’arashe yana nuna masa k’ofa." "Murmushi Alhaji Gimba ya kuma yi “Seems like your pride is speaking for you again Abokina.” Ya kuma gyara zamansa “Shi rayuwar nan Engr wllhi kyauta ce. Yau dubu nawa basuda daman rayuwa irin namu. Ba wai k’uruciya muka fisu ba.. Ka juya ka duba environment d’inka sosai kaga masu irin shekarun ka guda nawa ne.? A ajiye maganan arziki na kudi da dama na rayuwa, ka duba masu arzikin lafiya irin naka guda nawa ne.? Ka duba masu ahali irin naka guda nawa ne.? Shin kasan wani ya tara arzikin amma baida lafiyan jin dadin arzikin..? Shin kasan wani ya tara dukiyar amma baida Magaji.. Shi da za’a amshe duka dukiyar da ya mallaka dan a mallaka masa irin D’an daka mallaka K’wara d’aya tak da ya fiye masa duk wani arzikin gidan duniyar nan da za’a basa..”" "Daddy ya girgiza Kai kad’an “So, what are you trying to imply here.. That I’m ungrateful..?”" Alhaji Gimba ya katsesa “Because you are stuck in tha past.. And that destroy your present.” Ya dan gyara zamansa “Kuma kasan ina matsalar take.. A naka tunanin bayan abinda ya faru dakai a baya Kasuwancinka shine abinda yai keeping d’inka moving.. Amma ba haka bane.. Wann ahalin da a kullum kake ik’irarin basuda mahimmanci cikin rayuwarka sune sukai keeping d’inka moving forward.. Your wife and your Son.. Amma ba business d’inka ba kaman yanda Kai kake tunani..” Ya d’an numfasa yana jinjina kai “Your company is your distraction not your source of happiness.. Wann ahalin da a kullum kake tashi ka gansu sune sukai healing wann gurbin ciwo dake cikin zuciyarka.” Katsesa wann karon Daddy yai “Quite the contrary… Ganinsu a kullum da nake shi yake tuna mun baya.. And maybe that’s why I feel trapped in the past.. Watak’ila da ace bani ganinsu things would’ve been different..” "Alhaji Gimba ya girgiza Kai yana murmushi “So tari zamu so abu amma ba alkhairi bane wajenmu.. Sann so tari zamu k’i abu amma alkhairi ne a tattareda mu. Watak’ila D’anka daka rasa tun kafin yazo duniya ba alkhairi bane cikin rayuwarka, Watak’ila D’anka Haidar da Allah ya bar maka shi Watak’ila shine alkhairi a gareka. Barinyi maka tuni da wani k’issa na Annabi Musa (AS) da malaminsa Khidr Wanda a k’auli mafi rinjaye shima Khidr Annabi ne. A cikin tafiyarsu da sukai Wanda Annabi Musa(AS) ke Neman ilimi wajen Khidr sunga wani yaro a hanyarsu kuma Annabi Khidr ya kashe yaron Wanda har Annabi Musa ya gaza hak’uri ya tambayesa meyasa zai kashe ran da baiji ba bai gani ba. Koda suka zo rabuwa Annabi Khidr ya amsa ma Annabi Musa (AS) amsoshin tambayoyinsa da ya gaza hak’uri akansu. Shi wann yaron da ya kashe Iyayensa mutanen kirki ne shi kuma yaron Allah ya k’addari idan ya girma zai lalace kuma iyayen nasa suna matuk’ar sonsa zasu jarabtu dashi har ya lalatasu dan haka Allah ya masa umarni da ya kashe wann yaron.” Ya dan numfasa yana kallon Daddy da jikinsa yai sanyi sosai “Karatun da zaka d’auka a nan wani sa’in abu ba alkhairi bane wajenka sai Allah ya d’auke maka shi cikin rahamarsa. Watak’ila wann D’an daka rasa tun yana ciki Watak’ila zaka jarabtu dashi sai Allah ya maka sauyi da wani d’an Wanda ka kasa gani ka kuma kasa appreciating d’insa.” Ya dan kuma gyara zamansa “Ina ka bar tawakkali..? Ina ka bar imani da k’addara Abokina.?”" Daddy ya dubesa a sanyaye da idanunsa da suka kad’a ba tareda yace komai ba. Alhaji Gimba yaci gaba da jinjina Kai “You need to let go of the past and accept what you have kafin lokaci ya k’ure maka.. Kafin kai nadama maras amfani Abokina.” Ya mik’e yana fad’in “Zan koma bakin aiki kafin kasa sakatariyarka ta koreni.. Kai tunani kan abinda muka tattauna dan lokaci baya jiranmu..” Daga haka ficewa yai ya kyale Daddy nan zaune yana juyi cikin kujera. ** A b’angaren su Haidar kaw suna tafe saman kwalta. Gudu yake sosai yana tunanin ahalin da ya girma dasu matsayin iyaye. Wani b’angare na zuciyarsa na tunanin Dareen da abinda tai masa. Meyasa rayuwar sa haka.? Meyasa abubuwa suke zuwa masa yanda suke zuwa..? Meyasa rayuwarsa gaba d’aya batada alkibla tun tasowarsa.? Why.. Why.. Why.?! Tambayoyin da zuciyarsa ke ta nanata masa kenan ga gudu da yakeyi saman kwalta har baisan gudun nasa ya shige misali ba.. K’ok’arin danna birki yake amma batayi.. Ga gudu da yake gashi sun fara ratsa tsakiyan motoci.. A razane Ummul take dubansa tana tambayarsa meke faruwa.. Haidar yaci gaba da k’ok’arin danna birki yana fad’in “The brakes.. Is not working..!” Ummul ta soma salati tana karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. A daidai lokacin Haidar yai k’ok’arin kauce ma wata mota Wanda hakan yasa nasu motar ta bar saman kwalta ta fad’a gefen titi.. Haka motar ta dinga juyi har saida ta isa jikin wata bishiya.. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *39* *©️Sameena Aleeyou… * Sosai Mommy ke kuka sanda suka iso asibitin Anisa na biye da ita itama matsan k’wallan take. Hankali tashe Mommy ta nufo hospital staff d’in tana tambayar yanda su Haidar suke. A daidai nan su Daddy da Alhaji Gimba suka fito daga wani k’ofa. Dan dama sanda accident d’in ya faru company aka k’ira aka sanar dasu. Daddy yai tsaye yana dubanta yanda take kuka sosai Anisa nata kokarin kwantar mata da hankali bayan hospital staff d’in sun sanar dasu Haidar da matarsa suna cikin ER Likitoci na kula dasu. Wayar Daddy ne ta soma ruri. Daga Kampani ake kiransa. Dafe goshinsa yai yana mai lumshe ido sanda yake amsa kiran. Ga dukkan alamun ba labari mai dad’i yai receiving cikin wayar ba. Alhaji Gimba Ya dubesa had’ida girgiza kai kad’an “Akwai wani abu ne.?” D’an furzar da huci Daddy yai “There’s been an emergency at the company..” Alhaji Gimba Ya girgiza Kai kad’an “Emergency..? Mai ya faru.?” Furzar da huci Daddy ya kuma yi “Ban sani ba Gimba.” Shiru Alhaji Gimba yai yana dubansa. Tunanin sa d’aya Engr zai iya tafiya ya bar asibitin musamman da yake Haidar ne a asibitin sanin irin alak’ar dake tsakanin Engr d’in da ahalinsa. And especially da yake matsala ne ya kunno a Kampaninsa. Ya sani da za’a ba ma Engr zab’i tsakanin Kampaninsa da D’ansa he’d always choose his company. A halin yanzu ahalinsa suna buk’atar sa fiyeda ko yaushe. Adduarsa Allah yasa kar Engr Ya tafi ya bar ahalinsa cikin yanayin da suka tsinci kansu na jarabawa. Yana tsaka da tunanin kaman daga sama ya sinkayo muryar Daddy “You go… and take care of things there.” Alhaji Gimba Ya dubesa da mamaki cikin gaza b’oye farin cikinsa na decision d’in da Engr ya dauka na tsayuwa a asibiti wajen ahalinsa. Hakan na nufin Engr ya zab’i D’ansa sama da kampaninsa da Kasuwancinsa for the first time. Cikin sauri ya soma jinjina Kai “Kar ka samu damuwa abokina.. zan je na kula da komai a can.. You stay here.. Your family needs you.” Ya k’arashe cikin k’ok’arin k’arfafa ma Daddy gwiwa Wanda Sam k’arfin halinsa ya hana ya nuna tsananin damuwarsa. Kai dubansa ga yanda su Mommy ke zaune yai bayan Alhaji Gimba ya shige. Anisa sai k’ok’arin calming d’inta take da kalamai masu kwantar da hankali cewa Haidar harma da Ummul zasu samu lafiya. Mik’ewa Anisa tai tana duban Mommy wacce har lokacin bata cewa komai sai hawaye dake gangaro mata “I’ll.. bring you some water Mommy.” Ta k’arashe tana mai shigewa. Bayan Anisa ta shige k’uri Daddy yaima Mommy k’uri daga nan yanda yake tsaye. Yana kallon yanda take cazgan kuka mai tsuma zuciya. Tin bayan abinda ya faru tsakaninsa da Kwaise zai iya cewa bai sake Jin ya damu da wani damuwa da ya danganceta cikin zuciyarsa ba musamman idan abun ya shafeta ita da D’anta ne. Amma yau d’in sai yaji har k’asan zuciyarsa na jin zafin kukan da Kwaise take. Har cikin zuciyarsa yana so ya k’arasa gareta ya rungumeta cikin jikinsa amma sai yana jin bazai iya hakan ba. Lumshe idanunsa yai yana mai barin wajen cikin sauri dan Sam bai son sauraren kukan da take. It hurts him a lot. A can waje kuwa koda Anisa ta fita sun samu sun keb’e da Hisham. Ta kuma dubansa a hasale “You know your IQ doesn’t work at all. Waima how many gb akan nan naka..?” Katseta yai kaman zai mak’ureta “Don’t you dare insult me. It was your idea from the very start.. Kece kika kawo shawarin a shirya masa hatsari.. If there’s someone to be blamed here that should be you.” Anisa na huci take nuna sa “Kai addu’a kar wani abu ya samu Haidar.. Dan wllhi idan wani abu ya samu Haidar sai na tona maka asiri.!” "Murmushi Hisham yake da gefen baki “If that’s a threat, I suggest ki ajiye sa zuwa anjima har muji wani yanayi Ummul ke ciki. Dan na miki alk’awari idan har wani abu ya sameta.. Zakiyi d’andanasanin sanina..!” Ya k’arashe jijiyoyin fuskarsa suna mimmik’ewa." Anisa ta zaro ido tana duban Hisham cikeda mamakin irin son da yake ma Ummul. furzar da huci tai hadida rausayar da ido dan bazata basa daman ganin gazawarra ba “Let’s not waste time pointing fingers at each other.. Bazai taimakemu ba.. I thought da ka shirya hatsarin zaka d’auki Ummul ka gudu da ita.. I thought you said you wanted to be with her so badly. Maiyasa kai wasa da damarka. Maiyasa baka saceta ba kowa Ya huta.?!” Ta k’arashe tana huci. "Murmushi yake da gefen baki yana dubanta “You think I’m stupid.?” Ya kuma murmusawa yana duban Anisa “To tell you the truth, I was the anonymous person da ya k’ira company ya sanar da hatsarin nasu.” Ya jinjina Kai yana ci gaba da murmushi “Ina gefe ina kallon komai har yan kwanakwana suka kawo masu dauki.. Daidai da dak’ik’a guda ban bar wajen ba. I had to make sure sun samu taimako na gaggawa right away.!”" Ya kuma murmusawa yana kallon Anisa da ta zama confused tana duban makirci da ya dama nata. Hisham yaci gaba “Alak’a mai kyau mai tsafta mai cikeda yarda nake son k’ullawa da Ummul Wanda Babu algus cikinsa. And believe me na shirya hakan. Bazan tab’a bari ta zargi soyayyar da nake mata ba.. She will come to me willingly.. And she will accept me ba tareda wani ya tilasta mata ba.. Kin fahimta.?!” Anisa ta tsaresa da ido sai kuma ta girgiza kai “I hope it happens very soon.!” Tana ida fad’in haka tasa Kai ta shige tana huci. A yanda ta bar Mommy nan ta sameta har lokacin matsan hawaye take cikin yanayi mai nunida tsananin tashin hankali. Anisa tai saurin sauya fuska had’ida daura damuwa saman fuskarta. Ta isa ga Mommy jiki a sanyaye ta zauna gefenta tana mai b’alle bottle water d’in da ta shigo dashi. Ta mik’a ma Mommy a hankali tana fad’in “Mommy have some water.” Girgiza mata Kai Mommy tai cikin zuban hawaye “I can’t Anisa. Bazan iya ba.. Bazan iya saka komai a bakina ba tareda sanin halinda Haidar da Ummul ke ciki ba.!” "Anisa ta maidoda hannunta baya cikin sanyin jiki. Ta d’aura hannunta guda saman na Mommy tana k’ak’alo hawaye “Mommy I know you are strong.. In fact, you are the strongest woman I know.. And you are my inspiration.. But sometimes even the strong ones feel vulnerable.. Because we are human beings…” Anisa tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sai ka rantse har cikin zuciyarta Abinda take fad’i haka ne. Taci gaba “Tada hankali da damuwa dole ne.. But what they need the most now it’s our prayers.. Addu’o’in mu suke buk’ata fiyeda komai Mommy.. Especially you.. Sabida ke uwa ce.. Mommy kiyi ma Haidar Addu’a.. In sha Allah zasu samu lafiya daga shi har Ummul kinji Mommy.”" Hawaye na gangaro ma Mommy sai ta rungume Anisa kuka na kuma zuwa mata. Anisa ta saki murmushin cin nasara da gefen baki. A fili kuwa fad’i take “I’m here for you Mommy.. I’m here..!” A haka Anisa taci gaba da k’arfafa ma Mommy gwiwa Har kawo zuwa fitowan wani Dr daga hanyar da zai sadaka da ER. Yana tafe yana zame safar hannunsa. Cikin sauri Mommy ta mik’e Anisa na biyeda ita suka nufi Likitan. Daddy Wanda shima yaga fitowan Likitan zai nufesa kenan yaga Mommy ta rigasa. Sai yaja Ya dakata Ya tsaya daga bayansu. “Dr how’s my son and his wife..? How are they doing..? Can I see them now.. Can I see my son now.. Please tell me..” Ta k’arashe cikin tsananin kid’imewa. Dr ya dan girgiza Kai yana duban yanda ta rikice sosai. Ga mutum mai shekaru da Ya d’an soma ja is not good for their health. Karaf Likitan ya had’a ido da Daddy dake daga gefe. A hankali Daddy ya girgiza masa kai had’ida masa alama da ido alamun kar Ya fad’i wani abinda zai k’ara mata tashin hankali. Dr ya dan murmusa yace “Kar ki samu damuwa Hajiya.. D’anki harma da matarsa na Miki alk’awari suna samu kyakkyawan kulawa. And fortunately matarsa ta riga ta farka tana d’akin hutu. Shima munada yak’inin in a couple of hours zamu turasa d’akin hutu cikin yardar Ubangiji. There’s nothing to be worried about.” Relief ya nuna saman fuskarsa Mommy. Ta soma jinjina kai “Da gaske Dr. Yarana are out of danger.. Zasu samu lafiya.. Ta dubi Anisa dake sakar mata murmushin nuna jin dadi “Zasu samu lafiya in sha Allah.” Ta juyo ta dubi Likitan dake nan tsaye gabansu “Zamu iya ganin Ummul.” Dr ya jinjina mata kai a hankali “Of course you can.. This way please.” Ya k’arashe yana nuna mata hanya. Mommy ta jinjina kai tana mai shigewa Anisa na biyeda ita. Bayan Sun shige Dr da Daddy suka keb’e a ofishin Likitan. "Dr ya dubi Daddy yace “To be honest, I couldn’t tell your wife the real condition of your son.”" "Daddy ya zuba masa ido. Sai Ya girgiza kai kad’an “Tell me his condition, Dr.”" "Dr ya jinjina Kai kad’an “He’s lost a lot of blood.. But.. Zamu iya cewa he’s responding well. That’s why we moved him to the ICU… Amma..” Sai ya d’anyi shiru yana duban Daddy kafin ya girgiza Kai kad’an yaci gaba “Komai zai iya faruwa.. Because the first 24hrs is critical.. Let’s just pray he wakes up before then. Otherwise, we don’t know what might happen.” Ya k’arashe yana duban Daddy hadida girgiza Kai alamun hope d’in kad’an ne." Daddy yai shiru cikin tsananin sanyin jiki tamkar Wanda yai nisa cikin duniyar tunani. Muryar Dr ya sinkayo yana fad’in “Muna buk’akan jini da za’a k’ara masa cikin gaggawa.” Daddy ya dubi Likitan jiki a mace sai Ya jinjina kai “Go ahead Dr.. Just do your job..” Likita ya girgiza Kai kad’an “Unfortunately bamuda irin jininsa a nan. Mun samu shortage na jinin due its high demand. Ba don muna buk’ata cikin gaggawa ba da zamu iya jira tinda jini da baida wahalan samu. A halinda ake ciki any delay zai iya janyo matsala.” Daddy ya furzar da huci kad’an. Dan shi dai Haidar D’ansa ne amma bai tab’a sanin lafiyarsa rashin lafiyarsa balle wani blood type d’insa. Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Dr.. What’s his blood type then.?” Dr ya sanar da Daddy blood group din Haidar. Shiru Daddy yai kaman mai tunani. Dr zai kuma magana Daddy ya dubesa had’ida katsesa cikin sauri “I have same blood type with him.. I hope zaku iya d’iban nawa.” Dr ya jinjina Kai yana mai sanar da Daddy su k’arasa lab dan suyi aune aune. A can d’akin da Ummul take kaw. Shigowar Mommy yai daidai da bud’e idonta. Ta soma k’ok’arin Ware idanunta da suka mata nauyi. Tsaf ta sauk’esu akan Mommy dake karasowa gaban gadon nata. “Mommy..!” Ummul ta furta cikin murya irinta marassa lafiya. Mommy ta sakar mata murmushi ta k’araso tana dafa kanta daga nan yanda Ummul d’in ke kwance “‘Yata.. Alhamdulillah kin farka. Ya karfin jikin naki..? Mai kike ji yanzu.?” Ummul ta dubi Mommy tana k’ok’arin tuno abinda Ya faru. Take ta tuna sansa Haidar yace birkin motarsa bata aiki. Ta tuna yayita k’ok’arin ya tsaida motar bai iya ba. Ta tuna sanda motar ta bar saman kwalta Haidar Ya mata rumfa da jikinsa cikin k’ok’arin ganin yayi saving dinta wani abu bai faru da ita ba.. Ta tuna jini da ta hango Ya wanke fuskar Haidar da ya bar saman seat d’insa yai mata rumfa cikin k’ok’arin kareta. Ga idanunsa a lumshe tamkar baya numfashi. Tinda taga Haidar a wann yanayin bata kuma sanin ina kanta yake ba sai farfadowa da ta ta ganta a gadon asibiti. Ta soma girgiza kai hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar.. Ina Haidar yake..? Dan Allah ku fad’a mun ya samu sauki.!” Ta soma k’ok’arin mik’ewa tana fad’in “Dan Allah ku kaini wajen shi.. Dan Allah ina so naga Haidar.. Please Mommy..!” Saurin rik’eta Mommy tai itama din hawaye take. Bata bari Ummul d’in ta bar saman gadon ba take fad’in “Haidar yana can likitoci na kula dashi Ummul. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Kema ba k’oshin lafiya ne dake ba. Look duba kiga ga bandage a goshinki da hannunki.” Cikin zuban hawaye ta katse Mommy da fad’in “A’a Mommy banjin ciwon komai.. Ni Haidar kawai nake son gani dan Allah..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka. Anisa dake gefe juya ido rai cikeda takaicin Ummul. Cikin zuciyarta take fad’in ji wani iyayin banza. Sai wani neman ganin Haidar take bata ta kanta. Yaushe ma suka San juna ita Haidar d’in. Makirar banza. Ta kuma juya ido ganin Mommy ta rungume Ummul dake kuka sosai cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali dudka Mommyn ma hawaye ke zubo mata. "A can b’angaren Daddy kaw bayan an ida d’iban jininsa an k’ara ma Haidar duban Dr Daddy yai “Doc, I want this to" stay between us.. Bana so Matata ta San ni na bama Haidar jini… Ko shi Haidar d’in idan ya farka.” Dr ya jinjina cikin tabbatar ma Daddy baida matsala da hakan. "Daddy ya jinjina kai had’ida masa godiya kafin Ya k’ara da “Can I please, see him now..?”" Dr ya jinjina kai “Sure.. But it should be quick.” Daddy ya jinjina kai yayinda Dr Yai masa jagora zuwa cikin ICU bayan an basa wani rigar kariya da hula harma da nurse mask kafin ya nufo yanda Haidar ke kwance na’ura ta ko ina. Tin daga nesa jikin Daddy yai matuk’ar sanyin yanda ya hango Haidar kwance cikin buwayar Ubangiji. Yana takowa yana tuna Haidar d’in tin haihuwarsa. Gwagwarmayar rayuwa da Ya fuskanta musamman dasu iyayensa. Ya tuna a lokutan baya sanda yake rige rigen kawo masa sakamakonsa na makaranta da kyauttukan da aka basa amma daidai da rana guda bai tab’a kalla ba balle Ya yabesa. Ya tuna banda hantara tsana da kyara babu abinda ke tsakaninsa da D’an nasa. Ya tuna irin k’ok’ari da yake a company kan duk wani aiki da aka d’aurasa ba dan komai ba sai dan ya tabbata baiyi failing mahaifinsa ba. Still nothing was enough. Ya tuna auren da Kwaise Tai masa Wanda bai saka hannunsa ba balle Ya halarta matsayinsa na tilon D’ansa dukda sanin aure wani gab’a ne mai mahimmanci a rayuwar D’an adam. Haka yaita tuna rayuwarsu na baya Har kawo tattaunawarsu da Alhaji Gimba da yanda Alhaji Gimba yace dashi yai tunani Ya gyara alak’arsa da iyalensa tun kafin Lokaci ya k’ure masa dan Lokaci baya jira. Saiga hawaye na kwararowa daga k’uncin Daddy. Yakai hannunsa dake tsananin rawa yana k’ok’arin Shafa kan Haidar. Sosai muryarsa ke rawa sanda ya soma fad’i a fili “Aliyu..!” Ya furta a hankali yana shafa kan Haidar d’in. For the very first time da ya tab’a ambaton Haidar da sunan from his heart tin bayan da aka rad’a masa sunan. Daddy yaci gaba “My Son.!” Nan ma karo na farko da Ya ambacesa da D’ansa kai tsaye. Yaci gaba “Shin kasan a ranan da aka haifeka a lokacin da mahaifiyarka ta nuna mun kai a wann rann na samu k’arfin komawa bakin aiki.?” Ya murmusa hawaye na kuma gangaro masa “People might think kasuwanci na da Kampanina sune abinda sukai keeping dina moving.. But the truth is that you were the one that kept me going.. You brought me back my strength koda ban nuna hakan ba.” Ya shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa kafin yaci gaba “Meyasa na hukunta ka cikin laifin da ba naka ba Wanda baka da masaniy akai.?” Ya dan numfasa yana kuma shafa kan Haidar d’in “I was so angry at your Mom… That I didn't even realize I wasn't only a husband who’s been hurt and betrayed… I was also a father.. Na mance ni mahaifi ne da Allah Ya dank’a mun amana da kiwo Wanda zai tsaidani Ya tambayeni kan wann kiwon.. Nayi abubuwa cikin fushi.. Na d’auki tsangwama da kyara na d’aura akan ka just because you’re Kwaise’s Son.. Fushi yasa na mance you are also a part me.. My soul… my flesh and blood..” Ya lumshe idonsa hawaye suka kuma gangaro masa “Bai kamata na barka ka shiga cikin matsalolinmu ba. Why are You the one who's suffering the consequences... It shouldn't be this way.. If there is one thing I regret the most shine sake da damata da nai cikin shekarun da Allah Ya albarka ce ni da kai matsayin D’ah…. Forgive me son… Ka yafe mun D’ah na..!” Ya k’arashe kuka na neman cin k’arfinsa. Saida Yai masa addu’o’in samun sauk’i kafin ya baro d’akin duk jikinsa a mace. A hanyar ficewa suka had’u da Mommy. Daddy ya bita da kallo saidai batace da shi komai ba tasa kai ta shige. Jiki babu k’wari yaja k’afarsa Ya bar wajen. A yanda Mommy taga Haidar sosai hankalinta Ya tashi. Haka ta kwantar da kanta gefensa tana kuka tana fad’in irin k’aunar da take masa tana fad’in kar Ya tafi ya barta. Hannun Ummul taji saman k’afadarta wacce itama ta kasa hakuri har saida likitoci suka hakura suka barta ta shigo dan taga mijinta. Ummul na k’ok’arin bama Mommy baki amma sai ta kasa sai k’unshe bakinta tai dan sosai taji kuka na zuwa mata musamman yanda taga Haidar na kwance idanunsa a lumshe ga na’ura ta hanci ta baki. "A hankali kukan Mommy ke tsagaitawa, ta sa hannu tana shafan sumarsa. Murmushi da hawaye saman fuskarta take fad’i da Ummul “Tin lokacin da yake ciki rayuwarmu ta sauya. Na shiga matsansncin damuwa.. And maybe that’s why he was so tiny lokacin da na haife shi… Amma dukda haka he was strong, a fighter..” Ta kuma murmusawa tana hawaye “Sann Koda ya zama cikakken mutum mai cika ido da kyaun k’ira bai huta ba.. Tin haihuwarsa baisan wani farin ciki ba.. And that’s all my fault..” Ta k’arashe tana share hawayen da suka zubo mata. Taci gaba “Meyasa nake ji kaman laifuka na yake biya..?”" Saurin girgiza mata kai Ummul tai “Kar kice haka Mommy.. Bawa baya wuce k’addararsa a rayuwa. Duk abinda ke faruwa muk’addari ne daga Allah. Wasu abubuwan suna faruwa ne cikin rayuwarmu domin su zamto mana darasi. Ubangijinmu zai jarancemu ta ko wata fuska. Muyi ma Haidar addu’a Allah Ya tashi kafad’unsa Ya basa lafiya..” Mommy ta jinjina mata kai tana mai rik’e hannun Ummul d’in cikin nata. Ummul ta kamo hannayen Mommy sosai tana fad’in “Muje ki huta Mommy. Zan tsaya a nan na kula da Haidar..” Mommy ta jinjina mata kai a hankali tana mai goge hawayen da suka zubo mata. Haka Ummul ta rik’o hannunta har suka fito dikda itama ga rauni jikinta. A nan k’ofa suka had’uda Anisa. Ummul ta mik’a ma Anisa hannun Mommy tana fad’in ta kula da ita tana buk’atan hutu. Anisa ta jinina kai tana fad’in “Ummul is right.. You need to have some rest Mommy.. this isn’t good for your health.. Haidar bazai so ya farka yaga kema ba lafiya ba.. Muje Mommy..” Ta k’arashe tana rik’o Mommyn wacce da gani tafiyar kawai take. Suna shigewa Ummul ta koma cikin ICU d’in. Ta jima tana kallon Haidar dake kwance tana tuno yanda had’arin nasu Ya kasance. A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata. Ta janyo kujera ta zauna nan gaban gadon nasa. Kallonsa take tana tuna yanda aurensu Ya kasance Wanda ko sanin wanene shi balle kamanninsa batai ba farko. Ta tuna lokacin da ta shak’i poison Dr ya sanar da ita yanda Haidar Ya kula da ita. Ta tuna d’auketa da yai Ya kaita wann gidan Ya kulle.. Ta tuna yanda yai fitar da Mommy da kansa daga hannun ‘yansanda Wanda a baya ya dage sai an kulleta a prison. Ta tuna tattaunawarsu kafin Had’arin Ya faru yanda yace mata bazai saceta ba kuma bazai sake rufeta ba sann zai sawwak’a mata tai tafiyarta shima zai tafi zai tafiya mai nisa far from everyone and everything. Ta tuna sanda hadarin ke faruwa yanda ya finciki seatbelt d’insa yai tsalle daga nasa kujeran yai mata rumfa cikin k’ok’arin kareta. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Bayan mahaifinta bataji akwai wani D’an adam da Ya tab’a ba ma rayuwarta mahimmanci irin haka. Ta bud’e lumsassun idanunta masu zuban ruwa tana kallonsa. A hankali ta soma k’ok’arin kai hannunta dake rawa ta d’aura saman nasa hannun. A hankali take furta “A lokacin da Umma ta shirya aurena da kai na shiga damuwa da tashin hankali na rashin sanin wanene zata aura mun.” Ta kuma goge hawayen da suka gangaro mata “Ban tsammaci farin ciki ko wani rayuwa mai inganci cikin auren ba kama daga mutanen da shafin rayuwa zata had’ani dasu Har zuwa mijin.” Ta k’ura masa ido hawaye na kuma gangaro mata “Shin kasan kowa gudu na yake.? Ni Ummulkhairi ban tab’s tsammanin akwai wani D’anadam da zai fifita rayuwata sama da nashi ba. Koda ace akwai ban tab’a tsammani daga wajen mutum irinka ba. Wanda na tabbata ka fini a komai sau babu adadi. Sann mu biyun duniyar mu sun banbanta. Haka ne.?” Ta kuma jinjina kai tana hawaye “Dole ce tasa na danne nawa raunin gaban Mommy dan na bata k’warin gwiwa.. Amma kasan me..? Banida wani k’warin gwiwa.. Dan Allah ka tashi kaji.. Ka tashi..!” Ta k’arashe kuka na neman b’alle mata da gaske. Tai k’ok’arin saita kanta kafin ta kuma dubansa murmushi da hawaye saman fuskarta “A koda yaushe kana kiran kanka Monster.. Ni kuma ina fad’a maka kai ba mugu bane.. Mugu bazai tab’a zama mai kyakkyawan zuciya wanda ke saka damuwar wasu sama da nasa irinka ba. Yau d’in na kuma yarda da haka bayan abinda ka mun.. Watak’ila da baka zab’i ka bani kariya ba Watak’ila da ni ce zan kasance nan a kwance ba kai ba..!” Ta share hawayen da suka ziraro mata. Ta kuma daura yatsun hannunta saman nasa “Ina tareda kai.. Zaka samu lafiya cikin k’udurar Ubangiji.. Allah Ya baka lafiya…SweetMonster..!” Ta k’arashe tana mai kwantar da kanta gefensa kad’an. ** Kano… Hilal na Ida parking Ya juyo ya dubi Umma dake zaune bayan motar. Murmushi Ya saki kad’an “Umma mun iso..” Umma ta sauk’e ajiyan zuciya tana dubansa “Hilal.. Na haneka kak’i ji.. Mai zai faru idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata.?” Ya d’an girgiza kai kad’an “Ammi bazata sani ba Umma. Taimako nayi niyyan yi kaman yanda kema taimakon kikayi. Ina addu’an Allah Ya had’a mu cikin lada.” Umma ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an tace “Ameen Hilal d’an albarka. Mu k’arasa ko.” Hilal Ya jinjina kai yana mai fitowa had’ida bud’e ma Umma k’ofa. A daidai lokacin motan Ashshe dake biye dasu ba tareda saninsu ba ta iso wajen. Ta bama driver umarni da yai parking can gefe dasu. Sai huci take tana ayyana gidan Uban wa Suwaiba alak’ak’ai zata kai mata D’ah.? D’aga kan da zatai taga sun nufi cikin Kotu. Asshe ta zaro ido waje tana d’ora hannaye biyu a k’irji “Na shiga uku ni Asshe mai Hilal yake a Kotu.?!” Batasan sanda ta finciki marfin mota ba tabi bayansu a fusace. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..! *40* *©️Sameena Aleeyou… * “Ke Suwaiba dakata.!” Ta furta da k’arfin gaske daga nan yanda take tsaye bayansu. Gaban Umma ya yanke ya fad’i. Ta kasa juyowa sai furtawa da Tai cikin zuciyarta ‘Asshe.!’ Shi kaw Hilal da tsananin mamaki Ya juyo yana dubanta “Ammi.!” Ya furta cikeda mamaki. Asshe taci gaba da jinjina kai tana huci “Baka tsammace ganina ba koh..? Nace baka tsammaci ganina ba koh..?” Hilal Ya d’an lumshe ido kad’an ya k’araso yana k’ok’arin janye mahaifiyarsa “Ammi please don’t make a scene here.” A hankali yake maganar yana k’ok’arin janye ta. Ta funcuke hannunta tana nunasa Umma da d’an yatsa “Kina jina Suwaiba kurwar zuri’ata kur..! Idan na sake ganinki kusada d’a nah.. Kinga nan.” Ta nuna mata kotu dake gaba garesu “Wllhi a nan za’a rabamu.!” Hilal yai saurin katseta “Ammi Umma bata tilasta mun zuwa wajen nan ba.. Nazo ne da rad’in kaina..” “Rufe mun baki kai kuma kafin na Sallamaka da gaske kabi daji.!” Umma ta k’araso cikin sauri tana girgiza kai “A’a Asshe dan Allah kar kice haka.. Wllhi Hilal yaron kirki ne mai biyayya.” Da mugun mamaki take duban Umma “Kul.! Ahir d’inki kar ki sake ki sake saka mun baki ina magana da D’ahna. Suwaiba ke har zakiyi magana akan biyayya..?!” Umma ta sadda kai k’asa a sanyaye. Asshe taci gaba “Kina jina idan har baki sakar mun kurwan D’ah ba wllhi sai na maidake abin kwatance a garin nan.! Ban haifo muku D’ah dan yaji da matsalolinku da gurguntaccen ahalinku ba ehe.!” Ta dubi Hilal “Kai kuma idan ni ce na haifeka ka saka k’afarka a kotun nan.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige mota fuuu kaman zata tashi sama. Hilal Ya dubi Umma yace “Kiyi hak’uri Umma bansan Ammi na biyedamu ba..” Umma tai saurin girgiza masa kai alamun a’a “Kar ka damu Hilal kabi umarnin mahaifiyarka. Ni zan shiga na saurari k’aran Yaya Tani. Idan bata ganni a kotun ba zatai tunanin na kuma watsar da ita ne.. Inada yak’inin Allah zai kawo yanda za’a biya mutumin nan kudinsa Tani ta dawo gida.” Hilal Ya jinjina Kai a hankali “Umma biyan kudin bazai zama matsala ba in sha Allah.. Na Miki alk’awarin baza’a sake zaman Kotu akan wann batun ba.” Kaman daga sama suka sinkayo murya “Zaman Kotu da Tani yanzu aka fara dan sai na karb’ar ma D’anuwana hakkinsa rabon gadonsa da Tani tai yana raye. Idan banci taran Tani ba ba sunana Dije ba.!” Tsaf Hilal ya gane Inna Dije ita ce dai Kanwar Abbansu Khulsum dake wajensa a asibiti sann koda aka sallame su Khulsum d’in ta tabbatar masa gidan Inna Dije dake Dutse zasu wuce da Abba yanda zaici gaba da jinya. Gaisar da Inna Dije yai yana mai k’arasowa gareta “Ni zan biya taron Innah.. A kashe wutan maganar nan kowa ya huta.. Kar ki manta ku ahali ne kai juna Kotu ba naku bane musamman yanzu da Abba yake cikin wann yanayi.. Inna Idan Abba ya farfado daga jinyarsa yaga ahalinsa suna fad’a da juna irin haka mai kike tunanin zai kuma samunsa.?” Shiru Babu Wanda yace komai daga Inna Dije har Umma. Hilal ya samu k’warin gwiwan ci gaba “Rashin lafiya irin na Abba baya buk’atan tashin hankali irin haka. Salama da kwanciyar hankali yafi buk’ata ta. Na tabbata idan Abba ya tashi yaga ahalinsa sun had’e. Suna k’aunar juna sun mance duk abinda Ya faru a baya. Sun kuma yafi juna wann kad’ai sai yafi maganin da Likita zai bashi.” Ya k’arashe yana duban Inna Dije. Sai kuma ya soma saka hannu a aljihu “Zan biya ko nawa ne idan hakan zai kawo maslaha da zaman lafiya cikin ahalin.” Inna Dije na murmushi ta dakatar dashi “A’a haba.. Idan na karbi kudi hannun surki na mai na zama kuma.” Tai maganar tana fad’ad’a murmushinta. Sai ta soma mutsuke ido tana janyo bakin mayafi tana share hawayen da suka soma zubo mata bagatatan “Na jima banji kalaman da suka ratsa zucuyata irinta yau ba. Tabbas Babu komai cikin k’iyayya da gaba. Tabbas D’an uwana ya farka yaga ahalinsa sun dunk’ule waje guda shine babban maganin da yake buk’ata. Laidai kam bakai halin mahaifiyarka ba. Al basa batai halin ruwa ba. Ubangiji ya maka albarka. Lallai ka cika D’ah na gari da kowa su iyaye zasuyi buri da mafarkin samu. Da ace duniyar zata cika da mutane irinka masu k’ok’arin ganin Sun wanzartar da zaman lafiya tsakanin Al’umma da rayuwa ta canza. Haka Inna Dije taita sharb’an kuka tana fad’in ta tuba ta canza halinta. Taita saka ma Hilal albarka har ya bar wajen. Mamaki ne ya cika Umma matuk’a da al’amarin Inna Dije dare d’aya dai kokuwa rana d’aya tak Inna Dije ta sauya. Ta ya za’a ce kalaman Hilal da basu shige a k’irga ba Sun karkata Zuciyar Dije. Kai abun da mamaki matuk’a. Har Umma ta dawo gida mamakin wann kayan al’ajabi take. A nan tsakargida ta yada zango ta kwab’e hijabinta ta lank’aye saman gajeren katanga dake tsakargidan. A haka Badia da Azeema suka shigo tsakar gidan suka taddata. Duban Umma sukai a tare suka dubi juna da mamaki ganin sunata Sallama bata amsasu ba. Suka k’araso a tare cikin sauri suka zube gabanta. Badia ta kamo hannun Umma cikin nata a dan firgice “Umma Mama ta Miki wani abin ko.? Umma saida muka fad’a Miki Mama tuban d’an muzuru tai.” Azeema ta cab’e “Umma mun fad’a Miki gaskiya Mama bazata tab’a saduda ba.. Mun santa kuma munsan halinta tinda ita ta haifemu ta kuma rainemu.. Duk abinda Mama take acting kawai take dan ta samu a fiddata ta shak’i iskan ‘yanci ta fito taci gaba daga yanda ta tsaya.” "Badi’a tace “Umma fad’a mana, Mama ta miki wani abu ne..? Ki fad’a mana Umma idan ta Miki wani abu ne zamu fuskanci Mama koda ta kasance mahaifiyarmu. Dan munyi alk’awari bazamu sake bari wani ya cutar dake muna kallo ba. Koda baki haifemu ba mun Miki alk’awari zamu kasance ‘ya’ya masu biyayya a gareki.” Ta k’arashe tana duban Umman cikeda kulawa hannunta cikin na Umman." "Umma ta murmusa hawayen farin ciki na gangaro mata. Ta dubi Azeema ta kuma duban Badi’a. Hannayensu su duka biyun ta kamo ta rik’e cikin nata. Ta girgiza Kai a hankali “A’a yarana, Yaya Tani bata mun komai ba.. Kuma ina nan Akan bakata in sha Allahu. Zanyi iyaka k’ok’arina wajen ganin ta dawo garemu. Wani al’amari da ya d’aure mun Kai ya faru.”" Badia da Azeema suka dubi juna da mamaki “Wani al’amari kuma Umma.? Wane irin al’amari kenan. Mai ya faru.?” Cewar Azeema tana duban Umman cikeda kulawa. Umma ta jinjina Kai tace “Yau da na tafi sauraron k’aran Yaya na gamu da Innarku Dije.” Suka kuma duban juna da mamaki “Inna Dije.?” Azeema ta nanata. Umma ta jinjina Kai “K’warai Dije dai k’anwar mahaifinku.” Badia tace “Allah yasa dai ba wani abin tai Miki ba Umma.” Umma ta girgiza Kai “A’a ko kad’an bata mun komai ba.” Nan take ta labarta musu taryan taryan yanda sukai da Inna Dije. Ta k’arada “Har cewa tai ina iya zuwa naga mahaifinku a Dutse dik sanda nake buk’atan hakan..” Daga Azeema har Bad’ia ido suka zuba mata. Azeema ta mik’e k’afa tana girgiza Kai cikin yanayin salon da take idan bata gamsu da abu ba “Aaaa haba Umma. Wllhi matan nan wasa kawai da hankalinki suke. Wai Mama da Inna Dije ne dare d’aya suka zama salihan bayi.. Kaji ‘yan rainin hankali. Kut wllhi k’arya suke.” Duban da Umma tai mata yasa ta kame bakinta kad’an “Ai afuwan Ashe munce zamu k’ok’arta mu rage wasu abun. Yo baki ya saba aita sorry damu Umma in sha Allahu munata k’ok’arin saita halayyan namu koda salihanci baya mana dad’i. Amma dai wllhi idan bindiga za’a saka mun bazan yarda mata guda biyun nan tuban k’warai sukai ba. Haba Mama ce fah da Inna Dije ake magana a nan.” Badi’a ma girgiza Kai tai “Gaskiya Umma Nima zuciyata bata amince da wann canzawa da Inna Dije tai tashi guda ba. Kaman yanda har yau na kasa amincewa da tuban Mama. Umma suna amfani ne kawai da Zuciyar ki mai kyau dan su cimma wani buri nasu.” Umma tai shiru tana tunani. Ta sani Dije tanada masaniya kan abinda Tani batada masaniya akai tinda Akan idon Dije akai auren Ummul. Babban fargabanta shine kar Dije tai amfani da abinda ta sani gameda auren Ummul ta tarwatsa sabon alak’an dake tsakaninta da abokiyar zamanta Tani. Kaf fad’in danginsu Dije ce kad’ai takeda masaniya kan cewa Ummul AUREN WATA UKU tai. Mai zai faru idan tai amfani da wann damar ta tarwatsa mata ahalin da take k’ok’arin had’ewa kaman yanda tai alk’awari a baya. Fargabarta d’aya dik randa Ummul tasan da saninta tai mata AUREN WATA UKU ‘Yarta zata tsaneta sann zatayi danasanin duk wani biyayya da tai mata matsayinta na mahaifiyarta. Ta lumshe idonta tana addu’an Allah ya kawo mata mafita ya daidaita komai kafin komai ya lalace. Azeema ta d’an tab’ata “Umma kar ki damu. Idan ma Inna Dije wasa take bugawa ki bita a haka. Kinada manyan ‘yan wasa tareda dake. Kinada goalkeeper kinda defender. mu nan zamu tayaki buga wasanta. Umma alk’awari muka Miki bazamu tab’a barinki ke kad’ai ba. Mu ‘ya’yanki zamu tare Miki duk wani fad’a.. Umma a d’an zaman nan da mukai dake kinyi hak’uri damu. Kinyi mana abubuwa da mahaifiyarmu batai mana ba.. Kin zama uwa ta gari a garemu nida ‘Yaruwata. Umma mu kuma munyi miki alk’awarin zama ‘ya’ya masu biyayya a gareki.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. "Umma ta dubi Azeema ta kuma dubi Badi’a. Sai taji k’walla Sun ciko idonta. Allah sarki rayuwa, tayi addu’a Allah ya bata ikon gyara kuskuren da tai kan ‘ya’yanta guda biyu Ummulkhairi da Ummukhulsum. Ya kuma bata ikon zama uwa ta gari ga ‘ya’yan mijinta guda biyu Azeema da Badi’a. Sai ga hawaye na gangaro mata." Badi’a ta kamo hannun Umma “Umma Watak’ila tunanin ‘yanuwan mu kike Ummul da Khulsum. Haka ne.?” Sai Umma ta lumshe idonta hawaye na kuma gangaro mata. "Azeema ta kamo d’aya hannun Umman, murmushi saman fuskarta “Umma, nasan kina hango fuskokin Ummul da Khulsum cikin namu fuskokin.. In sha Allahu watarana ‘yanuwanmu zasu rik’e hannayenki kaman yanda nida Badi’a muka rik’e hannayenki yanzu..”" Umma ta murmusa hawaye na kuma gangaro mata. Ta shiga jinjina Kai a hankali “In sha Allahu yarana. Wataran ahalinmu zai cika da alkhairi.. Wataran zamu had’u gaba d’aya cikin alkhairi. Wataran komai zai wuce ya zama labari.” Suka jinjina mata Kai a tare murmushi saman fuskokin su. Umma ta janyosu ta rungume tana mai lumshe idonta. Addu’anta d’aya Allah ya had’e kan ahalin mijinta ya kuma bashi lafiya. Suna a haka suka sinkayo Sallamar Inna Dije. A tare Badia da Azeema suka mik’e zaune suna duban Inna Dije dake shigowa haraban tsakar gidan cikin yanayin da zasu ce bata tab’a ganinta ciki ba. Idan ma Sun tab’a Watak’ila tun kafin ta rasa farin cikinta tilon D’anta Fa’iz. Mik’ewa Baida tai cikin huci “Da wanne kika zo Innah.?” Umma tai saurin kamo Badia ta zaunar cikin k’ok’arin dakatar da ita. Azeema tace “Ai dai gwara mu tambayeta Umma dan idan da tashin hankali tazo bamu maraba da ita. Kaf fad’in gidan nan a halin yanzu babu k’ofan da yakai k’ofan nan zaman Lumana dan haka bazamu bari a kawo mana tashin hankali ba.” Ta k’arashe tana watsa ma Inna Dije mugun kallo. Umma ta girgiza Kai kurum ganin irin kallon da Azeema ke yi ma k’anwar mahaifin nasu. Ta sani Sun canza sosai Sun rage wasu abubuwan sosai. Amma wasu abubuwan sai a hankali su daina dan haka ga duk Wanda ya san su waye su a baya dole yai masu uzuri. Umma ta murmusa tana mai janyo Azeema kusanta “K’warai d’iyata k’ofan mu ya zama k’ofan zaman lafiya da lumana cikin yardar Ubangiji. Hakan yasa Innarku shigowa cikin lumana.” Ta k’arashe tana duban Inna Dije wacce ta koma tamkar salihar mage “Haka ne Dije.?” "Inna Dije tai saurin d’agowa ta dubi Umma sai ta jinjina Kai a hankali “K’warai Suwaiba. Babu abinda yafi yafiya, zaman lafiya da lumana.”" Umma ta jinjina Kai kafin ta maido da dubanta ga Badia da Azeema “Ku gaisar da k’anwar mahaifinku.” Suka dubi juna suna yatsina fuska. Umma ta tsare sosai tana dubansu alamun tana jira su aiwatar da abinda ta umarcesu. Murya can k’asa Badia tace “Wllhi darajan Umma kikaci.!” Zuciyar Dije yai wani irin tsinkewa jin wai yau ita ake ce ma taci darajan Suwaiba shashashar matar D’anuwanta. Ta had’iyi abinda ya tsaya mata sanda ta sinkayo muryoyin yaran D’anuwan nata suna gaidata da k’yar. Ta amsa masu a Mutunce da sakin fuska kaman dai ba Inna Dije ba. Umma tace Badia ta kawo ma Inna Dije abinci sann Salima ta gyara mata d’akinsu ta kwana ciki tinda tace washe gari take komawa Dutse. Sosai Inna Dije ta saki jiki ta nuna musu komai ya shige. An bud’e sabon shafin rayuwa na zaman lafiya da k’aunan juna tsakani da Allah. Harda ba ma Umma zab’i tai idan tana so a dawo da Abba gida cikin ahalinsa. Umma ta murmusa had’ida girgiza Kai kad’an “A’a Dije zamansa a can yafi. Kinga har yanzu akwai abubuwan da bai sani ba. Kaman auren Ummul da Tani dake tsare. Kuma kinga shi mutum ne majinyaci shiga damuwa ko tashin hankali ba nasa bane.” Muryarta ya soma rawa sanda taci gaba da fad’in “Yau a k’alla watan Ummul guda da aure harda ‘yan kwanaki.. Dije kinfi kowa sanin auren Ummul mai k’ayyadadden wa’adi ne.. Nafi so idan wa’adin ya cika Ummul ta dawo garemu kaman yanda Hajiya Asshe ta tabbatar mana sann a lokacin Tani ta dawo sai mu fuskanci Malam gaba d’aya matsayin ahali.!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka. Inna Dije ta matso gareta ta dafata kad’an “Suwaiba Hak’ik’a kurakurai mun riga mun taptapka a baya. Gyaran da zamu masu kenan shine mu gyara gaba.” Umma ta jinjina Kai a hankali tana duban Inna Dije itama Inna Dijen Umma take duba ko wanne da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa. ** Hilal yana isa gida kaman jira take ta soma kiransa. Ya murmusa kad’an yana mai lumshe ido dukda jikinsa Ya basa ba kalamai masu dad’i zaiji cikin wayar ba. Ya d’aga yana jiran da mai zata fara. “Wai Kai dan Allah a sau nawa zance maka ka daina shiga al’amarin ahalina..? Shin bakada wani abin yi ne? Ko kuma dai ka zama wakilin wanzar da zaman lafiya ne.?!” Ya murmusa kad’an yana mai relaxing cikin kujerar motar “I’d rather become a Peacemaker and a unifier da ace na zama mafad’aci..” Kafin yakai aya yaji an finciki marfin motar an fuzge wayar. Ba kowa bace face mahaifiyarsa. Khulsum wacce batasan meke faruwa ba daga d’aya b’angaren taci gaba “Ni Khulsum Ina maka gargadi na k’arshe da ka daina shiga hidiman ahalina dan zaman lafiyarka da naka ahalin.!” Asshe dake huci ta katseta “ Ke mai kika ce.?!” Ta fad’a da mamaki tana duban Hilal da Ya zuba ma sarautar Allah ido. Khulsum kaw tinda taji muryar mahaifiyar Hilal cikin wayar sai ta katse kiran a daburce zuciyarta na tsinkewa. Asshe ta dubi Hilal da tuni ya fito daga cikin motar “Mai ya had’aka da yarinyar nan Hilal.? Nace mai ya had’aka da ita.?” Ta shiga salati tana dafe k’irji “Na shiga uku ni Asshe Sun ranste sai Sun lasheka.! Ka amsa min Hilal!” Ta k’arashe kaman zata rufesa da duka. Daidai lokacin Motar mahaifin Hilal Ya shigo gidan. Yanda sukaga yanayinsa daga ita Har Hilal d’in Ya d’aga masu hankali. Musamman yanda sukaga Ya nufosu a zafafe ga wane irin kallo da yake bin Hilal d’in dashi. Yana k’arasowa yace su biyosa parlornsa. Asshe ta dubi Hilal Wanda shima ita ya duba cikin tunanin yanayin da yaga mahaifinsa ciki. Suna shiga ya nuna ma Hilal saman carpet gabansa “Zauna nan.!” Ba musu ya isa ya zauna yana kokarin gaida mahaifin nasa Wanda ko amsawa bai ba. Abinda bai tab’a masa ba tun tasowarsa. Mamaki ya kuma cika Asshe dan tasan Hilal dan gaban goshin mahaifinsa ne Tun tasowarsa. A Cewar sauran ahalin gidan baya laifi idon mahaifinsa. Jiki a sanyaye tace “Alhaji lafiya.. Meke faruwa.?” “Ki tambayi wann D’an naki.!” Ya k’arashe cikin huci yana nuni da Hilal. Ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Hilal. Asshe ta kuma duban mijinta duk hankalinta a tashe da yanayinsa. Ta kuma duban Hilal. “Hilal.? Meke faruwa ne wai..?” Kafin Hilal yakaiga bude bakinsa mahaifinsa ya katsesa “Meye dalilin da yasa ka bar karatunka.? Meye dalilin da yasa ka bar makaranta wann karon.?!” Salati Asshe ta soma cikin tashin hankali tana girgiza kai “Hilal.! Makarantar ka kuma bari wann karon ma..? Na shiga Uku ni Asshe.. Hilal asirina kake so ka tona.. Meke damun rayuwarka ne.. Abubuwan da bakai a k’uruciya ba kake so kayi yanzu.?” “Gwara ki tambayesa idan ma shaye shaye Ya fara. Dan wann karon idan ya watsar da karatunsa sisin kobona bazai sake ciwo akansa da sunan karatu ba. Makaranta na nawa aka canza masa.? Sa’anninsa daga masu aure sai masu ‘ya’ya shi Har yanzu baima san ina nasa rayuwar ta dosa ba. Shi ba kasuwa ba shi ba wani sana’an hannu ba shi ba karatun ba. Sanin kanki ne sauran yarana sai Sunyi zaman yaran shago kafin na barsu suyi wani karatu amma shi da yake gata Ya masa yawa gashi nan bai san mai yake ciki ba.!” Cikin tashin hankali Asshe take duban Hilal “Kace mun hutu kake Har yanzu.!” “Makarantar su sun jima da soma karatun wann zangon. Daga gidan Alhaji Halilu nake akwai nasa yaran a makarantar nasu. Muna labari yara sunata hutu yake sanar Dani ai Sun tsufa can Cyprus. Gashi nan ki tambayeshi.!” Ya k’arashe yana nuni da Hilal d’in cikin b’acin rai. Asshe ta fashe da kuka ta mik’e tana nuna Hilal da yatsa tana fad’in bayanta yake son gani. Sai sann Hilal ya katseta “Ammi I didn’t dropout.. Ok.. Ni bar makaranta ba..” “Idan ba bari kai ba mai ya hanaka komawa.?!” Ta tambaya tana kuka. Ya dubi mahaifinsa cikin kwantar da kai “Abba ba makarantar na bari ba.. I Only take.. half a semester off..” Mahaifinsa ya katsesa “Akan mai zaka jingine karatunka na wani lokaci.. Akan mai..? Mai kake yi a nan d’in.?!” Zuciyar Asshe ya kuma tsinkewa kar dai sabida matsalolin zuriyan Suwaiba Hilal ya shashantar da karatunsa. “Tambayarka nake.?!” Mahaifinsa Ya kuma katsesa. “Abba.. Aure nake so a nema min kafin na koma.” Daga Asshe Har Mahaifin nasa da mamaki suke dubansa. Asshe baki sake tace “Aure.? Aure Hilal.? ‘Yar wa kake nema.?” "Muryar Mahaifin Hilal d’in ne ya katsesu “ ‘Yar waye yake nema ba shi bane matsalar. Matsalar shine bazan masa aure bai koyi komai a rayuwarsa ba. Kodai ya koyi san’a na basa jari yayi aurensa ko kuma yayi karatu. Amma bazan nema masa auren ‘yar kowa baida sana’a ko aiki ba. Son da nake masa bai kai na sangartasa Har haka ba. Nima nawa iyayen ba haka suka mun ba. Dan haka bazanyi ma nawa d’an kisan gwani ba. He must learn to take responsibilities. Kuyi shawari da D’anki. Kodai ya kama Sana’a ya hakura da karatun yayi auren ko kuma ya ci gaba da karatu kafin yayi auren.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e zai fice. Sai kuma ya juyo ya dubi Hilal “Kana jina, ka dawo da duka kud’ad’en da na baka da sunan makaranta. K’wandala ban yarda ka bari wajenka ba. Kar ka bari na sake maimaita maka ka dawo mun da kud’ad’ena.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice." Asshe taji duniyar na juya mata. Ta k’araso gaban Hilal dake duk’e wajen “Ina jinka.. Wace yarinyar ce ta d’auke maka hankali haka..? ‘Yar waye.. Waye mahaifinta a garin nan.?!” Ya d’ago yana murmushi mai ciwo yana duban mahaifyarsa “Ammi is that really what matters now.? Kar ki damu kinfi kowa sanin ko wacece ita da kuma ahalinta..!” Yana ida fad’in haka ta mik’e ya fice cikin sassarfa. Zuciyarsa fal damuwan yanda zaiyi Ya maidama mahaifinsa kud’ad’ensa kafin wa’adin da ya basa Ya cika. Yana ficewa Asshe ta mik’e tana tunanin abun yi. Wacece ta d’auke mata hankalin D’a haka.? Khulsum.! Sunan da zuciyarta ya raya mata kenan. Ta soma girgiza kai tana zagaya parlorn. Suwaiba ta gama da ita da halinta dole ta nemo hanyar da zata raba Hilal da wad’ann harababbun mutane kafin su gama da ita. Dije.! Ita ce ta fad’o ranta. Dije ce kawai zata zamto makamin da zata yak’i Suwaiba da ita. Saurin ficewa tai ta nufi nata sashen. Saidai tana isa ta tadda wayar Anisa na shigo mata. Labarin hadarin su Haidar da Anisa ta sanar da ita ya kuma jagula mata lissafi. Asshe ta shafe goshinta tace “How’s my sister doing Anisa..? Yaya ‘yaruwata take.?” Anisa takai dubanta ga Mommy wacce Daddy ke rik’e da ita Sun nufi mota. Da kyar ya shawo kanta zai kaita gida ta dan huta Tai sallah. Saida yai mata alk’awarin dawowa da ita asibitin ma kafin ta amince ta bisa. Ta numfasa daga nan yanda take tsaye tana wayar “Your sister needs you Ammi.. Gata nan ta kasa barin asibiti. Ta kasa cewa komai ta kasa cin komai sai kuka da kiran sunan Haidar take. Ammi ya kamata ko mai kike ki bari ki zo Abuja.. Ki raba Haidar da annobar da kika lik’a masa kafin tai ajalinsa.. Dan tinda ta shigo ahalin tashin hankali ne ke kunno kai na yau daban na gobe daban. And worse part d’in shine ta lashe Zuciyar Mommy bata ganin laifinta. Tana mata wani irin soyayya da bazai bari ta bud’e idonta ta gane cewa ita d’in annoba ce kuma had’ari ce ga rayuwar Haidar.. Ammi only you.. Ke kad’ai ce zaki iya raba wann jarabbabben aure da kika nemar ma Haidar. Dan idan ba kece kika bud’i baki kikace Ummul annoba ce Mommy bazata tab’a yarda ba.!” Zufa yaci gaba da karyo ma Asshe dan yanzu wani masifan da ya b’ullo mata ya wuce gaban tasa k’afa ta tsallake. A halin yanzu ba rayuwar Haidar bane kawai akan layi harda rayuwar nata d’an Hilal. Dan tayi imani tsautsayi da masifa ke bibiyan Suwaiba da ahalinta.. Bazata tab’a bari Hilal dinta Ya fad’a cikin wann bala’i ba. Nan take ta sanar da Anisa zata kira Mommy amma bata jin zata samu zuwa duba Haidar a daidai wann lokacin domin kuwa wani wutan zata kashe. Dole ta saka ma Suwaiba birki. Anisa tace da mamaki “Ammi yanzu ita Ummul d’in Har tanada ‘yaruwa da Hilal ya k’yalla ido kanta.? Ammi wai mai kika gani so special gameda mutanen nan ne kam da kika jajibo mana su..? Ammi yanzu kina so kice mun Abba yace Hilal ya maida masa kud’ad’ensa.?” Asshe tace “Wann ba matsala ta bace Anisa. Tinda nasan D’anuwanki kobon mahaifinku bazai ciwo ba zai maida masa. Da ace kece sai na damu.” Anisa ta katseta “Ammi you are wrong.!” Asshe tace da mamaki “Mai kike nufi.?” Anisa taci gaba “Ammi.. Bana jin Hilal yanada kud’ad’en maida ma Abba yanzu.” Tai maganar kanta staye. Da mamaki Asshe tace “Kan mai zaki ce haka.. Kinsan wani abu ne..?” “Ammi Hilal ya tura mun kud’ad’en dake account d’insa.!” Da mamaki Asshe tace “Ke ban fahimceki ba mai kike nufi..?” Take Anisa ta labarta komai yanda Leenah taita karb’an kud’ad’e wajenta ita kuma tana tambayar Hilal. Asshe ta koma ta zauna gijif saman gado tana dafe kai “Kin kashe ni Anisa..!” Take zuciyarta ta soma ayyana mata Yanzu idan Hilal bai maida masa kud’ad’en ba dole k’arshe zai fad’i gaskiya cewa ma Anisa ya bada. Idan aka isa nan.. Magana zai fito fili.. Komai zai bayyana. Mijinta zai San ta tafi gidan boka. Aunty Kwaise zata San ta ha’inceta akan auren Haidar da Ummul. Wani b’angare na auren da ‘yaruwarta bata san dashi ba zai bayyana. Snn ‘yarta Anisa zata shiga uku. Gaskiya zai bayyana cewa ita ce sanadin rufe Aunty Kwaise da akai. Ahalin zai tarwatse .. Bazata bari hakan ta kasance ba.. Bazata bari ba. Gaba d’aya Asshe ta daburce ta susuce. Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. Daga ita Har Anisar kuka suke. Ko wanne na jingine laifi ga d’aya b’angaren. Anisa na kuka take fad’in “Ammi.. Mommy bazata sake stanata ba ma sai taji cewa had’arin da ya samu Haidar inada hannu ciki..!” Cak hawayen Asshe suka k’afe “Na shiga uku.! Anisa mai kika zama..? Kin lalata komai kin b’ata komai keda nace kar ki aiwatar da komai ba tareda umarni na ba.!” Anisa na kuka take fad’in “Har yaushe zan jiraki Ammi.? Har tsawon wani lokaci zaki d’iba kafin ki fitar da Ummul daga rayuwar Haidar.. Duk abinda na aiwatar sabida son Haidar nayi. Ammi I couldn’t wait for you to act.. I had to do it my way.. And I ended up screwing everything up as always.!” Ta share hawayenta tana huci “But there’s no going back Ammi.. Abinda ya faru ya Riga ya faru. Idan kikai wani abu foolish ko kika tona asirina wajen Mommy. Ba ni kad’ai Mommy zata yak’a ba Ammi.. ‘Yaruwarki will wage a war against you zata tsaneki ne.. ‘Yaruwar da ta rik’eki har kawo Aurenki.. ‘Yaruwar da ta d’aukeki Aminiya abokiyar shawari. The best solution shine ki bar min komai a hannu na.. Ki tsaya a kano ki kashe wutan da Hilal ya kunna.!” Tana ida fad’in haka ta kashe kiran. Wani irin kuka Asshe ta fashe dashi duniyarta tai mata d’aurin goro. Ta d’aura hannu biyu akai tana fad’in ‘ya’yanta biyu zasuyi ajalinta. Cikin duka abubuwan data aiwatar Bata tab’a tsammanin zai backfiring da yaranta tsamo tsamo ciki ba. Mik’ewa Tai tana tunanin kuka bai ganta ba. Take ta danna kiran Dije. Dije tana ganin kiran Asshe tai wata murmushi da gefen fuska. Cikin zuciyarta take ayyana kin kira akan gab’a. Saida ta Lek’a ko ina ta tabbata babu mai ganinta kafin ta d’aga kiran. Babu b’ata lokaci Asshe ta sanar da ita dalilin kiran. Inna Dije ta sanar da ita tana gari ta tsammaci ganinta washe gari kafin ta juya Dutse tinda dama a washe garin take shirin komawa. Da wann sukai sallama. Washe gari kuwa kaman yanda suka tsara. Bayan Inna Dije tayima su Umma Sallama cikin mutunci ta nufi gidan Asshe.. Asshe ta dubeta ta kuma gyara zama “Ni da ke munsan sirrikan juna.. Haka ne.?” Dije ta murmusa “K’walliya munsan abinda muka sani dai.” Asshe ta furzar da huci “And we have common enemy here.” “A’a a’a yimin da yaren da nafi wayo.. Mai kike nufi.?” Ta k’arashe tana fiddo idonta waje. “Ina nufin munada mak’iyiya guda d’aya.. Ita ce Suwaiba.!” Inna Dije ta murmusa “Anzo wajen.. Ai ni a halin yanzu kallon ‘yaruwa Suwaiba take min ba mak’iyiya ba.” Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ban fahimceki ba.. Kina so kice mun keda Suwaiba Kun sasanta..? Kin yafe mata duk abubuwan da tai maki a baya.. Ciki harda mutuwan tilon D’anki.?” Inna Dije ta murmusa tana kurban soft drink d’in da aka tarbeta dashi “Waye yace miki Dije tana yafiya..?” Ta kuma gyara zama “Ni da kike gani bana mantuwa kuma bana yafiya. D’aukan fansa farilla ne. Na bama Suwaiba abinda take son gani ne a yanzu dan ta haka ne kawai zan cimma burina kanta.!” Asshe ta jinjina kai “Toh idan kuwa haka ne bakida Wanda kike dashi da zai taimaka Miki ki kai Suwaiba k’asa kaman ni. Nikeda makullin auren Ummul a hannuna.! Nikeda makullin tashin hankalin da zai tarwatsa Suwaiba ya kaita k’asa.. Ni keda makullin AUREN WATA UKU.!” Ta k’arashe idonta tar cikin na Inna Dije. Murmushi Inna Dije take tana dubanta “Maiyasa kika kirani.?” “Kiranki nai mu taru mu had’a k’arfi da k’arfe mukai Suwaiba k’asa. Dan bazan tab’a bari nawa ahalin Ya tarwatse sabida ita da zuri’arta ba. Bazan bari Alakan D’ana da mahaifinsa Ya samu nakasu ba. Bazan bari Na rasa mijina ba. Bazan bari na rasa D’ahna ba. Bazan tab’a bari D’ana ya auro jinin Suwaiba ba. Bazan tab’a bari na had’a zuri’a da Suwaiba ba.!” Ta k’arashe tana huci. Inna Dije ta murmusa “Idan kina so na taimakeki fayyace min komai.” Taryan taryan Asshe ta karanto mata yanda Tai da mijinta harma da D’anta Hilal da kudin da ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa dan ya rufa mata asiri da cewa da maifin Hilal yai Ya maido masa kud’ad’ensa Har kawo auren da Hilal d’in yace yana son yin Wanda ba kowa yake so ba face ‘yar Suwaiba. Inna Dije ta sauk’e ajiyan zuciya “Idan Har kina so kiyi ma Suwaiba da ahalinta iyaka da zuri’arki zab’i d’aya kike dashi a nan.” Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Wane zab’i kenan.?” “Ki fitar da Tani kishiyar Suwaiba daga kurkuku.!” Asshe ta d’ago da mamaki tana duban Inna Dije “Tani kuma.? Meyasa zan fitar da ita.. Maiyasa zan fitar da matar da Suwaiba ke fad’i tashi wajen ganin ta fitar da ita.? Maiyasa zan taimaki Suwaiba.?!” Murmushi Inna Dije tai tana mai fitowa kad’an daga cikin kujeran “Banida tabbaci kan tuban Tani. Da gaske ne ta canza kokuwa wasa da hankalin Suwaiba take kaman yanda nai. Tani a halin yanzu Babu abinda take buri kaman ta shak’i iskan ‘yanci.. Ina mai tabbatar Miki idan har Tani tasan cewa kece Kika fiddata Babu abinda zaki umurceta ta gaza miki shi. Zaki mallaki Tani a tafin hannunki.!” Ta k’arashe shu’umin murmushi irinta gogaggun mata saman fuskarta. Asshe tai shiru kaman mai nazari. Tabbas fitar da Tani zai mata amfani ta wata fuskar bayan mallakar Tani da zatai. Zata jifi tsuntsu biyu d dutse d’aya. Zataja layi ma D’anta Hilal da hakan.. Tinda ta tabbata ba zaiso mahaifinsa yasan cewa ya tura ma ‘yaruwarsa Anisa kud’ad’en makarantar sa ba. Idan Hilal yai alk’awari baya tab’a sab’awa musamman tsakaninsa da ‘yaruwarsa. Yana k’aunar ‘yaruwarsa da zai iya zaban ya shiga matsala sabida nata asirin ya rufu. Idan ta fitar da Tani hakan na nufin ta samu igiyan d’aure Hilal. Ta murmusa tana duban Inna Dije wacce itama can k’asan zuciyarta da nata manufan akan fidda Tani da take so Asshe tai. “K’warai na fahimceki kuma na amince. Idan Har fitar da Tani daga kurkuku na nufin rugujewar Suwaiba na amince zan fitar da ita.” Inna Dije ta jinjina kai “Suwaiba bazata san kece kika fidda Tani ba. Zan ci gaba da shashantar da ita.. Abin zai kasance kaman dai ni ce nai ma Tani hanyar fita daga kurkuku. Hakan zaisa Suwaiba ta kuma yarda da sakin jiki Dani. A sauk’ak’e zamu kaita k’asa.” Asshe ta murmusa tana jinjina kai.. Nan take suka shirya komai da yanda zasu gudanar da komai. ** Bayan kwanaki uku da faruwan wann al’amari Tani ta shak’i iskan ‘yanci. Duk a tunanin Umma Inna Dije ce Tai hanya aka fidda Tani ba tareda tasan cewa Asshe ce ta biya Bakauye kud’ad’ensa harda tara. Tani taita kuka tana godiya ma Suwaiba da Dije da alk’awarin zama da kowa lafiya. A b’angaren Hilal koda mahaifinsa Ya tutsesa da maganar kudi Asshe tai karaf tace taimako yai ya fidda sirkar Haidar da aka lak’a ma sharri daga gidan kasu. Taci gaba da matsan hawaye tana fad’in “Alhaji ni bansan wane irin Zuciyar taimako Hilal keda shi ba. Kaf kud’ad’en yayi amfani dasu wajen d’aukar ma surkar Haidar Lawyer da biyan tara. Ina laifin Ya sanar damu ko iyayen Haidar ko shi Haidar d’in halinda ake ciki.. Ni yanzu na yanke shawarin zan d’aga koda k’adarata..” Katseta yai da fad’in “Ba sai kin saida komai naki ba.. Dama so nake nasan mai yai da kud’ad’en.” Ya dubi Hilal “Taimako abu mai kyau ne koda ace wasu ka taimaka ba Dangin matan Haidar ba. Amma ka sani komai yanada tsari da hanyar da ya kamata abi a aiwatar duk kyaunsa.. Kud’ad’en nan da kai taimako dasu ka kai munzanin da zaka iya nemansu. Ka d’aukesu matsayin bashi na baka. Zaka tafi kasuwa kai aiki tuk’uru ka nemesu da guminka sann ka biyani kud’ad’ena.” Yana ida fad’in haka Ya mik’e ya fice yana sab’a babbar riga. Hilal ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai lumshe ido. Ya bud’esu ya dubi Amminsa cikin mamakin yanda ta tsara zance ma mahaifinsa. Kafin yai wani magana ta dakatar dashi “K’warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud’ad’en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Kuma nasan ko mai zai maka bazaka tab’a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba ‘yar Suwaiba.! Ka nemi ‘yar gidan ko waye ka aura amma ba ‘yar Suwaiba ba.!” Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa “Kinyi haka ne dan ki d’aureni Ammi..? Sabida haka kika zab’i taimaka masu.?” “Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark’an Suwaiba da zuri’arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai na sa kud’i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi ‘yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda ‘yar Suwaiba ehe.!” "Ya girgiza Kansa “Kiyi hak’uri Ammi.. You don’t have to go this far.. Kimarki ya wuce haka a wajena.. Maganar aure kuma ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice." K’arshe dai Asshe ciwon k’arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar. ** Abuja.. Yau kwanan Haidar ak’alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk’ufa addu’a gareshi da rok’ar masa sauk’i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Ummul ke kwana wajensa. "Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na’urar nasara Sun masa k’awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido." "Mommy taci gaba “A lokuta da dama mukan mance wasu ni’imomin da Allah yai mana na d’an lokaci ne ba mai tabbata ba… Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman ‘ya’ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a’a shekaru nawa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk’e nauyin da aka d’aura maka na hakkoki..?” Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni “Ina rok’on Allah yasa da sauran rayuwar da zamuyi tareda Haidar a gaba.. Ina rok’on Allah Ya tashi kafad’unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib’icin Al’amaransa..” Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata “Ina rok’on Allah Ya nuna mun zuri’ar Haidar kafin na bar wann duniyar Ummul.. He’s all I have.. I can’t lose him..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka." "Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k’ok’arin k’arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar zai tashi cikin yardar Ubangiji.. Zakuyi rayuwa irinta D’ah da mahaifiya mai cikeda albarka da aminci.!”" Ta d’ago tana duban Ummul wacce itama d’in Mommyn take duba hawaye fal idonta. "Ta kuma kamo hannayen Ummul cikin nata “Na fad’a zan k’ara fad’a, kin amsa sunanki Uwar alkhairi.. Kinzo da d’imbin alkhairi cikin ahalinmu.. Ummulkhair.!” Ta ambaci sunanta cikin wane irin siga mai nuni da yarda da aminci. Ummul ta d’ago ta dubi Mommy a sanyaye jin yanda ta ambaci sunanta. Mommy taci gaba “I entrust my son to you.. Please take care of him.. Be patient with him.. Don’t let go of his hand.. Help him find his way.. Nasan zaki iya.. Allah ya zama maku jagora Ya albarkaceku rayuwarku da zuri’a ta gari.”" Sai Ummul ta sadda idonta k’asa cikin jin nauyin Mommy. Mommy ta murmusa kad’an tana dubanta kafin tace “Tashi ki shiga alwalanki.. Ni zanje na samu Daddynku naga sak’on sa yana jirana a reception.” Ummul ta jinjina kai a hankali tana mai amsawa kafin ta mik’e ta nufi bathroom. Koda Mommy ta mik’e sai ta nufi jikin gadon Haidar.. Ta dafa goshinsa tana dubansa. A hankali ta furta “My handsome Boy. Allah ya baka lafiya.” karanto masa addu’o’i samun sauk’i tai. Ta sumbaci goshin nasa cikeda so da k’auna kafin ta fice. Tana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idon Haidar. A hankali yatsarsa guda ke motsi.. Ya soma k’ok’arin bud’e idonsa da suka masa nauyi. A haka Har ya bud’esu tar yana kallon sama.. Komai ya soma dawo masa gameda had’arin da sukai. Ya tuna sanda motar ta sauk’a saman shoulder.. Ya tuna tsallen da yai ya rufe Ummulkhair gudun kar wani abu ya sameta. A hankali ya kai hannunsa ya zame na’urar dake hancinsa lokaci guda ya furta “KHAIRY.!” A daidai lokacin Ummul ta fito daga bathroom. Haidar na jin an tab’a k’ofa ya kuma lumshe idonsa kif. Ummul takai dubanta garesa. Batasan ko idonta bane amma sai taga kaman ya motsa daga kwancen. Ta nufi jikin gadon nasa Tai zaune saman kujeran da take kusan yini akai tana dubansa dake nan jikin gadon. A ‘yan kwanakin da sukai asibitin.. Tagumi tai da hannayenta biyu had’ida tsura masa ido daga nan yanda yake kwance. Ta shiga tuno kalaman Mommy a gareta wanda tamkar amanar Haidar d’in ta damk’a hannunta. Sai ta tsinci kanta da shakku da kokonto musamman da ta tuna kafin had’arin ya faru ya furta mata cewa he’d set her free.. Zai sawak’a mata. A b’angaren guda ga Mommy tace don’t let go of his hand..! Mai zai faru idan k’addara bai bata daman sauk’e alk’awarin da ta d’aukar ma Mommy ba.? A wani b’angare na zuciyarta tana tunanin aurenta ya k’are a daidai wann gab’ar bayan ta d’aukar wa mahaifiyarta alk’awarin bazata waiwayi gida ba har sai ta cika watanni uku da aure. Wani k’alubale zata fuskanta bayan ta koma gida.? Shin ta Ya zata fuskanci Umma da sauran ahalin gidansu idan har aurenta Ya Mutu. Auren da ga yanda Ya kasance Tun farko.. Tabbas batasan yanda zata fuskanci Umma ba muddin aurenta Ya k’are kafin aje ko ina.. Ita duk ba wann ba. Ko kiran waya Umma ta haramta mata mai zai faru idan ta koma da sunan auren ta Mutu.? Ta lumshe idonta a hankali tana furtawa cikin zuciyarta ‘Allah duk yanda kayi daidai ne.! Ka shiga al’amari na ka zamto majib’icin lamrana.!’ Ta bud’e lumsassun idonta ta zuba su tsaf akan Haidar dake kwance. Sosai k’irjinta ke bugu sanda Takai hannunta dake tsananin rawa mai d’aukeda damshin ruwan alwala tana shafa goshinsa zuwa sumarsa a hankali. Abunda tasan ko bindiga za’a saka mata idan idonsa biyu ne bazata tab’a iya yin hakan ba. Tamkar electric shock haka Haidar yaji sauk’ar hannun nata saman goshinsa. Har lokacin bai nuna alamun farkawa ba. "A hankali taji tana samun natsuwa, bugun zuciyarta na daidaita bata daina abinda take ba." Ta tsinci kanta tana mai sakin Murmushi a yayinda take dubansa. Har lokacin bata daina shafa goshinsa zuwa sumarsa ba “Kasan mai..!” Ta furta a hankali had’ida gyara zamanta. Ta d’aura hannunta saman yatsunsa a hankali “Kanada sa’a. Kai d’an gata ne.. Ina nufin kanada mahaifya da take matuk’ar k’aunarka..!” Ta k’arashe maganar cikin sanyin jiki tunowa da nata mahaifiyar da tai da kuma irin rabuwar da sukai bayan tayi aure. Ta jinjina kai a hankali tana share hawayen da suka gangaro mata. Sai ta d’an tsura masa ido kad’an “Kanaga zan iya sauk’e nauyin alk’awarin da na d’aukar ma Mommy.?” Sai ta d’an girgiza kai “Na tabbata da idonka biyu zaka ce.. Ke! Get out of my face.! You don’t want to have a monster for a husband.!” Tai maganar cikin tsarewa ita a dole tana kwaikwayonsa. "Sai kuma ta bama kanta dariya. Ta murmusa kad’an tana mai tsura masa ido tsananin tausayinsa kwance cikin k’irjinta. Tai raurau da ido Kaman mai shirin kuka tace “Watak’ila You are a bit of a Monster, but you are also sweet.. So sweet…. Sweet Monster.!” Taci gaba da sakin sassanyar murmushi tana dubansa “Na gode da ka ceci rayuwata.! Na gode da rayuwata ta kasance mai mahimmanci a wajenka. Allah ya baka lafiya.!” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa. K’ok’arin zame hannunta daga nashi take amma mai .? Sai ji tai gam Haidar ya tamke hannunta cikin nasa." K’irjinta yai wani irin bugawa. Ta zaro ido waje tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. Ta kasa juyowa ta dubesa sai rawa da jikinta yake. SameenAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *41* *©️Sameena Aleeyou… * Duk sai ta daburce ta rasa mai zatai. Ta kasa furta komai sai duban juna da suke su duka biyun… A haka aka turo k’ofan d’akin.. Ba kowa bace face Mommy. Ganinsu a haka yasa Mommy saurin k’arasowa murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. Farin cikinta ya gaza b’uya. "“Haidar. My son.! Alhamdulillah.. Haidar ka tashi..!” Sai kuka ya b’alle ma Mommy. Ta d’aga hannayenta sama tana fad’in “Alhamdulillah.! Allah na gode maka da ka tashi D’ah na. Allah na gode maka..!” Hawaye na gangaro mata tafukan hannayenta tallafe da fuskan Haidar din duka b’angare biyu taci gaba “I can’t believe you are finally here with us again son.. You know, I don’t mind losing everything.. But.. Amma bazan iya rasaka ba Aliyu… Bazan iya jure rashin ka ba..!” Ta daga hannayenta guda biyu sama “Allah na gode maka daka tayar min da D’ahna… Allah na gode maka for giving me such a blessed opportunity to be with my son again..!” Ta k’arashe tana mai rungumo kansa daga nan yanda yake a kwance. Dole duk Wanda ke duban Haidar da mahaifiyarsa su basa tausayi." Ummul ta share kwallan da suka zubo mata. Ta janye jikinta ta matsa gefe kad’an cikeda farin ciki musamman yanda taga farin ciki Ya mamaye Mommy. Mommy ta dubi Anisa da shigowarta kenan tace maza ta kirawo Likita. Cikin sauri Anisa wacce itama farin cikinta had’ida mamaki Sun gaza b’uya ta shiga jinjina akai tana fad’in “Sure Mommy. Right away.!” Koda Likita ya shigo tambayoyi ya soma masa yanda ya fara da tambayarsa meye sunansa. Shiru Haidar baice komai ba sai kallon da yake binsu dashi d’aya bayan d’aya. Zuciyar Mommy yai wani irin yankewa ganin irin duban da Haidar ke masu tamkar Wanda bai tab’a saninsu a rayuwarsa ba. Duba irinta rashin sani. Mommy ta soma girgiza Kai tana duban Haidar tana duban Likita “Dr.. Meke faruwa da D’anah..? Why can’t he say anything..?” Dr yai k’ok’arin calming Mommy kafin ya dan soma ‘yan dube dube dangin su ido da k’irji ma Haidar dake nan kwance yana musu kallon rashin sani musamman Mommy. Mommy ta dubi Haidar ta kuma dubi Dr “Likita sanar Dani meke damun D’ana.?” Dr ya girgiza Kai kad’an had’ida furzar da huci kafin ya maida dubansa ga Mommy “I’m not sure if he’s having a temporary memory loss.. But there are some testes he has to undergo ta haka zamu iya fahimta matuk’a baiyi magana ba har na tsawon dak’ik’ai.” Mommy ta lumshe idonta hawaye suka gangaro mata. Taci gaba da duban Haidar tana hawaye take girgiza Kai.. Ta rungume kan Haidar cikin k’irjinta hawaye naci gaba da gangaro mata. Mai zai faru idan Haidar ya mance ta.? Mai zai faru idan D’anta bai kuma tuno ko wacece ita ba. Just when she thought rayuwa ta basu daman kasancewa tare a karo na biyu kwatsam wann tashin hankalin ya Kunno Kai.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Cikeda tsananin tausayi Ummul ke duban Mommy da Haidar hawaye na gangaro mata. Allah sarki Mommy ta jira farkawan D’anta ta sanar dashi how much she loves him sai gashi ya farka amma ba Lallai ya kuma sanin ko wacece ita ba.. Kai Lallai rayuwa abar tsoro ce. Anisa ce ta kamo hannun Ummul itama guntun hawaye ne cikin idonta “Let’s go Ummul. Let’s wait outside.. Mommy needs some time with her Son alone.” Ummul duban Anisa kawai take tana Jin zuciyarta na wani irin yankewa.. Tamkar rak’umi da akala haka tabi Anisa suka fice daga d’akin. Kan Mommy na kife gefensa tana hawaye taji hannun Haidar saman nata. “Mommy.!” Taji ya furta a hankali cikin murya irinta majinyata. Ta d’ago tana dubansa yayinda Idanun Haidar ke kallon sama. “Aliyu..!” Ta furta a hankali tana dubansa “Ka.. Kana iya magana..? Ka gane ni..? Ka.. Ka ambaci Mommyn ka.!” Still idanunsa na duban sama yake fad’in “Even back then.. Lokutan da kike hukunta ni bisa laifin da ba nawa ba ban tab’a mance ki ba Mommy.. And do you know why.?!” Ya k’arashe yana mai karkato da fuskarsa suna fuskantar juna shida ita. K’walla ne tab cikin idonsa yayinda hawaye suka ci gaba da gangaro ma Mommy. Haidar yaci gaba “Because you are my mother.! Ban tab’a tunanin rejecting d’inki matsayin mahaifiya ba. Haka ne.?” Mommy taci gaba da hawaye yayinda Haidar yaci gaba da jinjina Kai siririn hawaye na gangaro masa “Koda ace wann D’an talikin yaron babu abinda yake mafarki da buri sama da soyayyar ki da kulawarki.. Not once have I ever looked down on you..!” Ya lumshe idonsa siririn hawaye ya gangaro masa. Mommy ta lumshe idonta hawaye suka gangaro mata. Tana tuna rayuwar k’unci da ta ba ma d’anta ba tareda tayi la’akari ba. Haidar yaci gaba da jinjina Kai yana duban mahaifiyarsa “Dukda duka wad’ancan abubuwan da kika mun.. Dai dai da rana d’aya Mommy ban tab’a danasaninki matsayin mahaifiya ba.. Ban tab’a hanaki yanke wani hukunci na rayuwata ba.! You dictated my whole life.. Karatuna..! Aikina.! Daga k’arshe har aure na Mommy… Kece kika zabo matar kika kuma yi a lokacin da kike so koda auren ya kasance k’ark’ashin yarjejeniya.! Koda ban kasance wann D’an da kike so mahaifinsa yayi alfahari dashi ba. Ban tab’a taka wani dokanki ba sabida ina ganinki matsayin mahaifiya.!” Suka ci gaba da duban juna hawayen Mommy na k’aruwa. "Haidar ya maida dubansa ga duban sama “Amma daga lokacin da na dubeki da kallo na k’ask’anci.. Na Miki kallon tir da zama mahaifiyata. Na kulle ki a kurkuku Mommy.. Na fad’a Miki kalamai masu tsanani Wanda duk rayuwar da mukai lokutan baya ban tab’a fad’a Miki irinsu ba.!” Sai ya d’an girgiza Kai kad’an “Ummulkhair..!” Ya furta a hankali kafin yaci gaba “Thanks to her na fahimci ke d’in Mahaifiyata ce. Kuma ba’a tab’a iyaye irin haka a zauna lafiya.!” Ya Kuma duba Mommy kafin yaci gaba “Na fad’a Miki kalaman ne cikin b’acin rai bayan kin sanar Dani labarin yanda kika salwantar da ahalin mahaifina... D’anuwana ko ‘yaruwata dake ciki bai zo duniya ba da kuma matar mahaifina da batada hakkin komai..!” Yaci gaba “Na mance cewa dukanmu ‘yanadam ne.. And we all have our shortcomings. Na mance cewa we all make mistakes and We are far from being perfect…!” Yaci gaba da duban Mommy daga nan yanda Yake kwance “Watak’ila na shiga hurumin da ba nawa ba..! She was right Mommy… Khairy was right, I shouldn’t have looked down on you.! I shouldn’t have locked you up in jail..! I shouldn’t have said all those horrible words to you.” Ya d’an karkato sosai yana duban mahaifiyarsa. Hannunsa na matuk’ar rawa ya d’aura saman na Mommy. Mommy ta dago da idonta masu zuban ruwa tana duban Haidar da kuma yanda ya d’aura hannunsa saman nata." “Please forgive me Mommy..!” Ya k’arashe muryarsa na shaking sosai. The sincerity in his voice was clear. Sai Mommy ta rungumosa daga nan yanda yake kwance saman gadonsa. Cikin kuka take girgiza Kai tana fad’in “Baka mun komai ba Aliyu.! Tun tasowarka ni ce na cuzguna maka na bak’anta maka rayuwa sabida son zuciya. ! Tabbas abinda mutum ya shuka shi yake girbewa. Na cutar da Fannah da abinda ke cikinta dan na samu dawamammen farin ciki a cikin gidana. Shi kuma alhaki kwikuyo ne. Sai na samu akasin haka tsawon shekarun nan. Ban samu wann farin cikin ba. Bakada laifi ta ko wace fuska Haidar kuma banji ciwon abinda ka mun ba sai ciwon abinda ni na jima ina maka. Na aza maka nauyin zunubaina bisa kafad’unka ba tareda hakki ba.” Ta numfasa hawaye na kuma gangaro mata “Aliyu D’anah ina matuk’ar k’aunar ka.. Ina rok’on Allah ya bud’e Zuciyar D’ah na ya mun kwatankwacin kaunar da nake masa.!” Ta k’arashe hawaye da murmushi saman fuskarta. Ya rik’e hannun Mommy cikin nasa sosai “I would pick my mother to be my mother again in any and every life time.. Farin ciki ya gaza b’uya a fuskar Mommy cewa da Haidar yai zai zabe ta matsayin mahaifiya a kowace rayuwa ya yaye mata wani burden da take kwana ta tashi dashi. Daddy dake daga k’ofa Akan idonsa komai ta faru.. Murmushi out of nowhere ya subce masa ganin ahalinsa cikin yanayi mai ban sha’awa da bai tab’a gani ba. Kasa shiga d’akin yai sai ya juya ya fice yana jin zuciyarsa na masa wasai.. Koda ace baida k’warin gwiwan tunk’aran ahalin nasa a yanzu. Ganinsu haka cikin farin ciki Ya wadatar masa. Yana Jin wani annashuwa da sakinah da ya jima bai tsinci kansa ciki ba tsawon shekarun. Koda ya isa company ma Alhaji Gimba ya fuskanci relief da farin ciki da abokin nasa ke ciki. Alhaji Gimba ya murmusa yana duban Daddy alamun da magana a bakinsa. Kafin yakai ga furtawa Daddy ya katsesa “A fad’a maka Haidar ya farka..?” Yai maganar har lokacin dai murmushi ne saman fuskarsa. Alhaji Gimba ya kuma murmusawa “Ka fad’a mun wann the moment labarin ya same ka. Har ka mance.?” Daddy ya d’an shafi goshinsa “Aff haka fah..” “Ya baka zauna can ba.! Ai da kayi zamanka.. I have everything under control here.” “Kwaise tana can.” Ya fad’i jikinsa a dan sanyaye wann karon. Dan har kawo wann lokacin Mommy bata daina sha masa k’amshin da ta tsira ba. Kallo guda zaka masa ka gane duk baya wani hayyacinsa. Shiru Alhaji Gimba ya d’an yi kafin ya numfasa yace “Ka k’ara mata lokaci abokina.. Ita mace fah duk girmanta sunanta mace. Kuma su mata rauni ne dasu… Ba wuya an janye wayonsu da kalamai da kyautatawa.. Nan da nan sai kaga Sun sauk’a daga dokin fushi.. Amma fah idan aka kaisu mak’ura kalamai da lallama basa aiki nan take.. Toh fah wann karon kaine zakayi hakurin da ita.” Daddy ya dan dubesa sai ya furzar da huci a hankali.. Ya kishingida cikin kujera yana mai lumshe idonsa. ** A can asibiti kuwa Hisham ne yaje duba Haidar. Yana zaune gaban gadonsa ya k’ura masa ido fuskarsa fal damuwa. Haidar yai gajeren tsaki “Kasan dai bana so ayita kallo na.. It irritates me..” Hisham ya Kai masa punch a damtsensa maras ciwo. Haidar ya dan saki k’ara yana fadin “You are such a jerk you know.!” "Hisham ya girgiza Kai “You are the real jerk here Haidar.! This isn’t a joke.. I mean, You almost killed yourself in that accident.. I know you so well.. Idan ranka ya baci tuk’i kake ba tareda kana sanin ina kake zuwa ba.!”" “Kana tunanin akwai b’acin ran da zaiza nai yunk’urin kashe kaina..? Hisham akwai wata cikin motar nan. And she happens to be my wife.!” Saida Hisham ya dago ya kallesa jin ya ambaci Ummul da matarsa. Haidar yaci gaba “You know me.. I wouldn’t put someone in harms way.. Koda ace ni mutum ne da ya yak’i ahalinsa tsawon rayuwarsa…” Yana jinjina Kai yake fad’in haka kafin yaci gaba “Abinda nake tunani shine… the accident was planned. Someone planned it.!” Gaban Hisham ya yanke ya fad’i amma sai ya dake . Ya dan girgiza Kai kad’an yana karantar Haidar d’in “What do you mean.? Kana so kace kana zargin wani da shirya maka had’arin.? Kamar ya kenan Haidar.?” Ya dan rage girman idona still yana duban Haidar d’in “Wait don’t tell me har yanzu zargin ahalinka kake da yunk’urin kasheka.. My goodness Haidar.. Wai har yaushe zaka watsar da wann tunanin ne..? Sai yaushe zaka watsar da makaman fad’anka Akan ahalinka. Until when Haidar.?!” Ya k’arashe cikeda nuna kulawa kaman dai ko Yaushe. Haidar ya tsaresa sosai da ido “Someone tampered with my brakes.!” Hisham ya dan girgiza Kai “But.. who could have done that.? I mean all your life you thought ahalinka sune mak’iyanka.. Dukda cewa kanada b’oyayyun mak’iya masu son ganin bayan ahalinka da family business dinku.. Ina nufin masu kai maka suka a company da media.. But basu tab’a yunk’urin kasheka ba.. “ Katsesa Haidar yai da fad’in “What if I have a new enemy..? What if someone’s holding a grudge against me..? What if someone wants to take their revenge on me.!?” Cikin sakanni Zuciyar Hisham ke bugawa dan gani yake Haidar Ya gama ganosa ne. Daidai lokacin akai knocking a k’ofa.. Mommy ce ta shigo fuskarta d’aukeda murmushi. Hisham ya mik’e cikin k’ok’arin bama Mommy da Haidar waje. Ya gaida Mommy had’ida mata sannu da jikin Haidar kafin ya maida dubansa ga Haidar. Sallama Yai masa tareda fatan samun lafiya had’ida k’arawa da zasuyi magana. Mommy tabi bayansa da kallo fuskarta d’aukeda murmushi. Shi d’aya ne abokin da zata iya cewa ta sani na Haidar.. Dukda ba wani saninsa tai sosai ba tasan wajen aikinsu d’aya kuma he’s very fond of her son.. Tasan duk Wanda zai hak’uri da halayyan Haidar Ya zauna dashi irin haka sai Wanda yake masa soyayya na gaskiya tsakani da Allah. Tana ji Har cikin ranta he’s a good influence for her son. Farin cikin Mommy gaba d’aya ya gaza b’uya. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tamkar k’wai hannun jariri haka take ririta Haidar. Gaba d’aya jinsa yake Awkward dan shi tun tasowarsa zai iya cewa babu wata alak’a mai kamanceceniya da wann tsakaninsa da mahaifiyarsa. Ya d’an soma yunk’urin mik’ewa Mommy ta k’araso da sauri tana k’ok’arin taimaka masa take tambayarsa mai yake so. A hankali yake furta “Is ok Mommy.. I can manage..” Mommy ta gyara masa pillow ya kishingid’a sosai. Tana dubansa tana sakin murmushi… Gani tai sai kalle kalle yake kaman yana neman wani abin ko yana so ya tambayeta wani abu. Ta matso ta dafa hannunsa kad’an “Akwai abinda kake so ne Son.. Should I call the Dr for you..? Kana jin wani ciwo ne..?” Ya d’an girgiza kai kad’an “Where is she..? Why isn’t she here..?!” Magana yai a hankali amma bai san Ya fito fili ba. Mommy ta girgiza Kai kad’an tace “Wace kenan..?” Ya dan dubi Mommy kaman bazai ce komai ba sai Ya tsinci bakinsa kai tsaye da furta “Khairy..!” Farin cikin Mommy ya k’aru. Sai tace “Oh.. Ai Sun tafi tareda Anisa ta kaita gida. Nace ko zata d’ebo maka wasu kayyakin da zaka buk’ata. Amma nasan Watak’ila ma suna hanyar dawowa.” Baice komai ba sai Ya d’an kuma yunk’urin mik’ewa alamun yana son sauk’owa daga saman gadon. Mommy tai saurin tallafosa tana tambayarsa mai yake so. Ya d’an dafa gadon yana fad’in “I need to use the bathroom..” Mommy ta soma k’ok’arin dafa masa tana fad’in bari ta taimaka masa. Ya girgiza Kai cikeda kokari mai nuni da jarumta “You don’t have to worry Mommy.. I can manage..” Ta girgiza kai a’a Haidar Bakada wani k’arfi fah.. Duba ka gani..” Daidai lokacin su Ummul da Anisa sukai sallama. Mommy tai hamdala tana fad’in “Gwara da Allah Ya kawo ku. Maza k’araso Ummul ki taimaka ma mijinki..” "Haidar yai saurin katseta “I said I can manage, Mommy..”" Girgiza Kai Mommy tai “So kake ka fad’i ka kuma jin wani ciwon…?” Ta k’arasa ta kamo hannun Ummul da tai sororo ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba. Ta dank’a mata hannun Haidar cikin nata “Assist your husband.” Bata tsaya sauraron komai ba ta janye Anisa da tai mutuwan tsaye nan wajen tana kallon yanda Mommy ta saka hannun Ummul cikin na Haidar.. Bata ankara ba sai ji tai Mommy tana janyota tana fad’in ta shige su basu waje. D’akin ya rage saura Ummul da Haidar. Ya kuwa tsareta da ido fuskan nan a murtuk’e kaman ba shine ya gama jajenta ba. Ta had’iyi abinda ya tsaya mata da k’yar dan tinda yai regaining consciousness bayan gaisuwa da tai masa basuyi wani magana ta fatan baki ba. Takai idonta kan hannunta yanda Mommy ta had’e da na Haidar waje guda. A hankali ta soma k’ok’arin zame hannun amma sai taji ya matse hannun ya hanata abinda take k’ok’arin yi. Ta d’ago ta dubesa ita d’in yake duba har lokacin babu wani walwala saman fuskarsa. Hannunta taji ya janyo ya zagaye bayansa dashi ya d’aura saman waist d’insa.. Ta kuma dubansa cikin fad’uwan gaba. Har lokacin bai janye ido daga barin dubanta ba.. Bata kuma ankarewa ba saiji tai ya d’aura hannunsa guda saman kafad’arta yayinda hannunta guda ke saman waist d’insa irin dai yanda ake taimaka ma maras lafiya idan zai tafiya.. Maimakon ta soma takawa sai shine dai yai yunk’urin tafiyar Kai kace itace maras lafiyan. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Don’t look at me like you’ve seen a ghost… They say monsters don’t die early.!” Yai maganar kaman ba shi ba saida ta dan dago ta dubeshi tana mamakin kar dai yaji kiransa monster da ta dingayi sanda yake kwance unconscious. Sai ta tsinci kanta da Jin kunya ta sadda kanta k’asa. A haka suka ci gaba da takawa Zuciyarta bai daina yankewa ba. Addu’a kawai take cikin zuciyarta Allah ya bata k’warin gwiwa.. Aiko suna shigewa bathroom din ta soma k’ok’arin janye jiki daga nasa.. Cikin in ina take furta “Zan.. Zan jiraka a k’ofa..” Juyawan da zatai ta kunna musu shower akansu.. Haidar ya janyota jikinsa gaba d’aya “What if I fall..?” Ya fad’i yana mai manne goshinsu waje guda su duka biyun idonsu a lumshe. Sosai Ummul ta rintse idonta tana Jin yanda karan hancin Haidar ke gogan nata ga ruwa dake zubo musu. “Amma.. Amma.. Naji kaman kace ma Mommy zaka iya..” Ta fad’i da kyar cikin k’ok’arin ganin ya k’yaleta ta fice. Amma sai taji ya kuma had’e fuskokinsu waje guda. Murya na rawa ga ruwa dake jik’asu tace “Mai.. Kake aikatawa..?” “I’m rebuilding my life..!” Ya furta a hankali saitin kunnenta kafin yaci gaba “Isn’t this what you want..?” Tai saurin ware idonta tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa. Haidar yaci gaba “Isn’t this what you promised Mommy… That you’d help her son…rebuild his life… Are you scared now..?” Yai maganar yana mai kuma rungumeta cikin jikinsa. Cikin sigan rad’a yaci gaba “Are you sure you are ready to invade my sick world..? Don’t you think you are taking too much of a risk..? Are you not scared of a monster..?” “But you are not a monster…!” Ta furta cikin rawar murya. “What makes you believe… That… I’m sweet…?” Yai maganar d’umin numfashinsu na gaurayuwa da juna. Kaman zai sumbaceta. Har lokacin idanun Ummul suna lumshe. Ga heartbeat dinta dake k’aruwa. Ta kasa furta komai sai k’ok’arin cire jikinta daga nasa da tai dan ta gama amincewa yanzu kam duk wasu maganganun da tai sanda yake kwance yaji komai. “Zan… zan jiraka a k’ofa ta fad’i tana mai tamke tufafin dake jikinta cikin tsananin rawar murya. Kaman zata kifa haka ta fice tana had’e hanya. Haidar yabi bayanta da kallo murmushin da ba lallai ka fahimta ba saman fuskarsa. Ummul kaw tana ficewa ta jingine jikin k’ofa tana maida numfashi. A b’angaren su Mommy kuwa Asshe ta iso gari dan haka Kai tsaye ta taho asibitin yanda ta tadda ‘Yaruwar tata. Suna zaune saman wani kujera a wani hanya da zai sadaka da hanyar dakin Haidar d’in. Asshe taci gaba “Aunty Kwaise yarinyar nan annoba ce.. Tsautsayi ke bibiyarta.. Ya kamata ayi gaggawan datse aurenta da Haidar… Allah na tuba bamusan dalilin da yasa boka yace mu aura masa mace irinta ba..” Anisa da karyo kwananta kenan zata nufi d’akin Haidar ta sinkayi tattaunawar iyayen nata. Ta zaro ido waje tana dafe k’irji “Boka.!” Ta furta a hankali. Lokaci guda ta gyara tsayuwarta ta lab’e sosai. Mommy ta girgiza Kai tana duban Asshe “A’a Asshe na yada batun boka tuntuni kuma na k’aryatasa kaman yanda Ayoyin Alk’ur’ani mai tsarki ya k’aryatasa a wajaje da dama. Asshe ba shakka munyi kuskure a yanda muka faro Auren Haidar da Ummul.. Amma na gode ma Allah da ya nufeni da tuba ya kuma bud’e min ido na na gane gaskiya dalilin shigowar Ummul cikin rayuwarmu. Sann inada yak’inin Auren Haidar da Ummul Alkhairi ne Asshe. Domin shigowar Ummul cikin ahalinmu shi ya fargar damu gaba d’aya.. Ita d’in ta zamto tamkar wani igiya mai k’arfi da ta had’e ahalinmu waje guda ta d’aure Asshe. She’s an Element of Union.. Na shafe skaru sama da talatin ina fad’i tashi da ganin na had’e kan ahalina sai gashi cikin watanni biyu na zaman Ummul tareda mu Allah ya jefa wann had’uwan ahalin da soyayyar d’ana da mijina da nake buri. Kuma in sha Allah Ummul ko Haidar cikin su babu Wanda zai San ga Manufar aurensu daga farko. An Gina auren ne bisa sharad’in boka domin a raba Haidar da wancan Hatsabibiyar da tai masa sihiri Wanda a halin yanzu ma bana tunanin suna tare.” Anisa ta zaro ido waje tana Jin sirrin Auren Ummul da Haidar Wanda ba yanda batai ba Mahaifiyarta ta sanar da ita. Dama wann shine dalilin da yasa Kwaise Maitama ta auro ma D’anta D’iyar talakawa da taita mamaki daga farko.? Dama wann shine dalilin da yasa Mommy hak’uri da Ummul da nuna mata unconditional love.? Tirk’ashi Lallai yau akeyinta. Mommy taci gaba “Asshe kimin alk’awari babu Wanda zai San wancan manufar tamu na farko domin na riga na bisne wancan manufar na lullubesa da tuba na gaskiya. Ummul da Haidar zasu rayu a k’ark’ashin inuwar aure tsawon rayuwarsu cikin yarda Ubangiji aure mai cikeda d’imbin albarka ba AUREN WATA UKU mai k’ayyadadden lokaci Wanda Boka mak’aryaci yaima Ummulkhair alk’awarin mutuwa ciki ba.!” Anisa sai ta sake baki tana fito da ido waje.! Mutuwa..? Shiru tai tana sauraron yanda Mommy ke zayyano sharud’an boka gameda auren cikeda nadama. Anisa ta kasa rufe baki dan mamaki. Kenan An auro Ummul ne dan ta zamto makarin asirin da akai ma Haidar. Sai yanzu ta gane manufar turaren da Mommy ta bata ta bama Ummul. Sai wann lokacin take fahimtar komai.. So Mommy isn’t as innocent as she thought.. So duk wann soyayyar da Mommy take ma Ummul na k’arya ne tana mata so ne out of guilt tinda ta kawo ta cikin rayuwar D’anta ne dan ta kasheta ta kuma ceci nata D’an. Muryar Mommy ya kuma dawo da Anisa daga duniyar tunanin da ta tafi. Mommy ta kuma kamo hannayen Asshe “Asshe Alhamdulillah ahalina Ya fara daidaita cikin ikon Allah. Bazan kuma yin wani abu da zai tarwatsa min wann farin ciki da na jima ina fatan samu ba. Haidar da Ummul harma da Engr bazasu San ga manufar auren ba… Asshe idan suka sani ahalina zai kuma tarwatsewa Watak’ila yai rushewar da baiyi ba a baya… Kimin alk’awari kaman yanda muka shirya komai daga farko tare zamu bisne wann magana kuma bazamu sake d’agota ba har abada.” Ta k’arashe tana duban Asshe. Asshe Tai shiru tana duban ‘yaruwar tata dan dik yanda Anisa ke sanar da ita irin makancewar da Mommy wajen nuna ma Ummul so bata kuma gaskatawa ba sai yanzu “Amma… Aunty Kwaise..” “Babu amma Asshe. Inada yak’inin kafin a sallami Haidar daga asibitin nan shida Ummul zasu k’ulla alak’a mai kyau tsakaninsu.. Zasu k’aunaci juna a hankali. Domin da zaran an sallamesa ni Kwaise zan shirya gagarumin bikin na gaske. Za’ayi komai cikin mutunci da karramawa kaman yanda yake a al’ada. Za’a sallami Haidar ne tareda bikin tafiyarsa da matars in sha Allah. Ni da kaina zan tafi wajen dangin Ummul muyi masu gaisuwa a k’ulla alak’a da zumunci mai tsafta..” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. A hankali Anisa ta soma jada baya.. Shigowan da batai ba kenan ta soma tafiya jiri na neman kada ita. Tana fita ta soma neman layin Hisham. Bugu biyu a na uku Ya d’aga. “Tell me your location.” Abinda kawai Anisa tace kenan… Hisham na sanar da ita location d’insa tasa kai zata fice sai kuma taja birki ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu. Ji tai ta k’agu ta tunk’ari Haidar da Ummul ta sanar dasu irin Auren yaudara da Mommy ta k’ulla tsakaninsu. A b’angaren su Ummul kuwa tana nan lamo jingine jikin k’ofan bathroom taji motsin tab’a k’ofan alamun zai fito. Tai k’ok’arin saita kanta tana mai taimaka masa da bud’e k’ofan. Suka dubi juna sai ta kauda fuskarta kad’an. Gaba d’aya saima ta rasa mai zatai musamman da taga yanda yake dubanta daga nan yanda yake tsaye dafe da garu. Baice da ita komai ba sai soma takowa da yai. Ta yunk’ura da zummar magana saiji Tai ya kuma kamo k’ugunta had’ida tallafo kafad’an ta guda. Sukai tsaye nan haka suna duban juna. "A haka Anisa ta turo k’ofa taci karo dasu rungume da juna suna duban juna ga jikkunansu duk a jik’e. Takaici yakai Anisa k’ololuwa. Banda sakin huci bata komai. Wai Haidar Maitama ne dai take gani rungume da wann kucakar harma kaman ya makance a shauk’in kallonta baisan an tab’a k’ofa ba balle Ya kula da Wanda Ya shigo. A zuciye Anisa ta janyo k’ofar ta fice, kukan da ta rasa na takaici ne ko na kishin Abun k’aunarta Haidar ne na kufce mata." Haka ta fice tana kuka shar shar take driving. Da alama duk wani effort dinta a banza yake tafiya dan duk k’ok’arin taga Haidar da Ummul basu samu kusanci ba kaman k’ara rura wutan abun take. Koda ta isa location d’in Hisham bata daina kuka ba. Hisham Ya tsareta sosai da ido had’ida bata lokaci dan ta fitar da k’uncin dake ranta. Ganin dai kukan Anisa bazai k’are ba dan tinda tazo yanda yake kul take ta kasa cewa komai. Hisham yai tsaki kad’an “Ke enough please. Ya isa haka mana.! Wai meye kikazo kika saka ni gaba kina kuka.? Ok dama kin nemi sanin yanda nake ne kawai dan ki cika mun kunnuwa da sautin kukan ki. Ai da baki b’ata mana lokaci ba daga ni har Ke tinda idan kinyi a waya ma zanji.” Anisa ta d’ago tana huci “We can’t let them be happy while we are stuck here just.. Freaking miserable you know..! Wllhi na tsani Ummul.. Na tsaneta.. Na tsani Mommy da taima Haidar AUREN WATA UKU.. Auren karya asiri da ita.. I hope she dies kaman yanda Boka yace.!” Da mugun mamaki Hisham ke kallonta.. Ya girgiza Kai cikin rashin Fahimta “Mai kike nufi..?!” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *42* *©️Sameena Aleeyou… * Anisa ta d’ago fuskarta da Ya jik’e sharkaf da hawaye “Ina nufin ko ban kashe Ummul ba Boka ya mata alk’awarin mutuwa.!” Ta k’arashe tana kecewa da wani irin dariya mai sauti. Hisham Ya daka mata tsawa da fad’in “Cut the crap.! Wai meye yake faruwa ne.? Wani boka kike magana.?!” "Sosai Anisa ke dubansa kafin ta mik’e suna fuskantar juna “Your beloved Ummulkhair.. Hajiya Kwaise Maitama my Aunt ta kawota cikin rayuwar D’anta Haidar ne domin ta karya asirin dake jikinsa da ita.. Meaning, Auren Haidar da Ummul an ginasa ne bisa k’arya, yaudara da kuma cin amana… Aure ne mai k’ayyadadden wa’adi..! AUREN WATA UKU.! Sann daga k’arshe mutuwar Ummulkhairy shine cikan AUREN WATA UKU.!”" Hisham dake dubanta babu k’ifta ido Ya kuma girgiza kai “Ki min bayani dalla dalla.. Ban fahimci komai ba..!” Ya k’arashe kaman zai shak’o wuyarta ga wani irin huci da yake. Sosai Anisa ta razana da yanayinsa sai ta mik’e tana girgiza Kai “I think it was a wrong move to come here.!” Hisham ya daka mata tsawa da fad’in “Kina tunanin zan barki ki tafi ne ba tareda kin fayyace min komai ba.. Mai kike nufi da AUREN WATA UKU.?!” Anisa ta kuma daidaita tsayuwarta tana duban Hisham cikin ido. Taryan taryan ta karanto masa sirrin Mommy da mahaifiyarta da taji Wanda ta jima tana zargin akwai wani b’oyayyen al’amari mai tattareda sark’ak’iya gameda auren. Shiru Hisham yai yana kallonta bayan ta gama karanto masa kafin taci gaba “Amma idan har Haidar yayi wani aure ba tareda sanin ahalinsa ba.. Auren da Mommy ta kawo Ummul cikin rayuwarsa dan ta warware shi toh wacece matar da Haidar Maitama da ya aura a sirrance.? Meyasa babu Wanda ya Santa.?” “Except me.!” Cewar Hisham daga nan yanda yake zaune. Anisa ta waigo da mamaki tana dubansa “You.? Ta yaya..?” “Because I’m his only friend.. Na san wani b’angare na rayuwarsa da ahalinsa basu sani ba. Dareen..!” Anisa ta dubesa da mamaki tana girgiza Kai “Dareen.? Wacece Dareen.?” “Ita ce matar da ta aure Haidar da asiri kuma inada tabbacin ita ce Hajiya Kwaise Maitama taima Haidar Auren karya asiri da Ummul d’ita dan ta rabasu..!” Yaci gaba da huci “Why Ummul..? Meyasa ita..?” Cikin zuciyarsa yake furta ‘No.. Banyi asiri ma Haidar dan macen da nake so ta zamto makarin asirin ba. Wai meke faruwa ne.? Could this be my Karma.? Na yi asiri ma Haidar dan ya kasance da wata mace sai gashi the only mace da nake so ta zamto makarin wann asirin.. But asirin Ya riga Ya karye.. Amma what if Ummul ta mutu sakamakon Auren Haidar kaman yanda Boka yace.?’ Sai Ya soma girgiza kai a fili yana furta “No I can’t lose her.. I need to protect her from this marriage at all cost.!’ Anisa ta girgiza had’ida katse masa tunanin nasa “Wai mai kake fad’a ne..? Wacece wann Dareen d’in.. Where is she..?” “She’s nowhere to be found.. Haidar ya rabu da ita a ranan da zaiyi accident d’in.. Amma idan har muna son cimma burinmu na raba Haidar da Ummul.. Dole mu dawo Dareen cikin rayuwar Haidar.!” Ya k’arashe yana duban Anisa. “You must be crazy..! Bayan ya rabu da rak’ai so kake ta dawo..? So kake idan Ummul bata Mutu ba ni na mutu.?!” Ta k’arashe tana firfito da ido waje. "Makirin murmushi saman fuskar Hisham yake fad’in “For once in your life, use that tiny brain of yours..!” Ya k’arashe yana mata lamu da yatsunsa alamun yana nuni da k’ank’ancin kwakwalwarta kaman yanda yace." Anisa ta galla masa hara tana duban yanda yake Kallonta with that infuriating half smile on his face. A kufule tace “ Toh mai babbar kwanya make me understand. Har lokacin murmushin ne saman fuskarsa. Ya dan kauda fuska ga barin dubanta “Abun shine zamu dawo da ita ne domin ta tarwatsa yarda da aminci da Ummul tayi ma ahalin Maitama.. Zamu dawo da ita ne domin mu bud’e idon Ummul ta fahimci dalilin kawota cikin ahalin da Hajiya Kwaise Maitama tayi. Zamu dawo da ita ne matsayin matar da Haidar yai zaman daduro da ita ba k’ark’ashin kalmar aure ba..Zamu dawo da ita ne domin mu b’ata image d’in Haidar da ahalinsa a idon Ummul.. Zamu dawo da ita ne domin mu nuna ma Ummul cewa gaba d’aya ahalin Maitama Sun yaudara ta ne. Su d’in macuta ne mayaudara kuma azzalumai Wanda zasuyi komai sabida cikar burinsu..!” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Dareen ta sani a halin yanzu bazata sake mallakan Haidar ba.. Dan haka zatai komai domin ta tarwatsa masa farin cikin dake k’ok’arin shigowa cikin rayuwarsa Wanda ya rasa hakan tsawon rayuwarsa.. Kinga idan har Ummul ta fice daga rayuwarsa you can have Haidar all to yourself .. Isn’t that genius..?!” Ya k’arashe da murmushin saman fuskarsa. Anisa sai ta soma murmushi tana jinjina Kai “Wow.. tunani mai kyau.. I must admit kwanyarka na ja… Toh amma yanzu.. A ina zaka samo Dareen or whatever.?” Murmushi kawai Hisham yake yana duban Anisa tareda jaddada shashancinta. Dan Hisham dai bai sanar da ita cewa tareda Dareen suka k’ulla komai ma Haidar ba. Komai d’aurawa yai kan Dareen. Bazai ba ma Anisa reason ko wani k’ofa da zata samu abun threatening d’insa dashi ba. Bazai tab’a bud’e ma Anisa cikinsa tasan ko wanene shi da asalin manufarsa Akan Haidar da ahalinsa ba. “Kar ki damu zan kula da wann.. Kedai kije kici gaba da monitoring komai acan.. Ki saka mana ido kan Haidar da Ummul kiga ina relationship d’insa ya nufa.. Sann ki saka mana ido Akan Kwaise Maitama.” Anisa ta jinjina Kai “Kar ka damu da wann.. Zan kula da wann b’angaren.” Ya jinjina Kai suna Sallama da Anisa. "Bayan Anisa ta fice shid’in ma gidansa ya nufa ya isa jikin hotunan Haidar da Ahalinsa Wanda yai crossing da red pen gaba d’aya. A fili yake furta “Ban jure duk wani wahala a banza ba..! Banyi duk wani fad’i tashi na ganin na zama cikakken architect a banza ba.. Nayi haka ne to easily invade your lives.. Nayi haka ne domin na fanshe duk wani k’uncin da kuka jefamu ciki nida mahaifiyata..!” Ya kuma gyara tsayuwarsa yana huci “I’m resourceful today because you rejected me Aliyu Maitama.!” Yai maganar yana duban hoton Daddy Wanda shima yayi crossing. Yaci gaba “I’m who I’m today sabida na girma cikin wahala, k’unci da takaicin zama D’anka..! Ka yarda dani wann D’an da ka sheganta da bakinka tun yana ciki baizo duniya ba shi zaiyi ajalinka da duk wani farin cikin da kake tunanin ka samu a wann duniyar.!” Ya maida dubansa kan hoton Mommy Wanda shima anyi crossing da red pen. You’re the one who instigated all this chaos.. Kece kika tada duk wani k’ura.. Daga k’arshe kin kawo Ummul d’ina ciki.. Saidai d’iyar ‘yaruwarki Anisa ta mutu amma ba Ummul dina ba.. Sai na raba wann D’an naki da Ummul d’ita duk wuya duk rintsi.. Ummulkhair is mine.. Wllhi na ranste sai na d’auketa daga wajenka Haidar.!!” Ya k’arashe yana huci yana duban hoton Haidar dake daga tsakiyan na iyayensa Wanda shima anyi crossing anja layi da jan alk’alami." ** Su biyu ne cikin d’akin yana kwance daga saman gadon yayinda Ummul ke tsaye gefe tana fito da shirts daga cikin suitcase d’in da suka shigo dashi itada Anisa. Mommy ce ta d’aureta nan wajen tace Lallai ta nema ma Haidar rigar da zai canza dan tasan halinsa tinda Ya farfado bazai taba yarda ya zauna da kayan asibiti ba. Sai fito da t-shirts din take amma da alama Wanda take fito da Kayan dan ya gani yai selecting baida niyyan yin hakan. Dan ko kallo bata ishesa ba balle kayan da take cirowa. Ta lumshe idonta a hankali tana tunani cikin zuciyarta ‘Mai zanyi yanzu ni Ummul. Bai kallon b’angaren da nake.’ D’ago idon da zatai sukai ido hudu. Sai ta daburce gaba d’aya.. Ta suri t-shirt d’aya ta d’ago sama tana nuna masa “Wann yayi.?” Yanda tai maganar fuskarta d’aukeda murmushin da yafi kama da yak’e sosai zai baka dariya. Kai da gani kasan maganar zuwa mata kawai yai ba tareda ta shirya yinsa ba. Bai bata amsa ba Har lokacin dubanta yake da rikitattun idanunsa. Ganin bai daina kallonta ba bai kuma ce komai ba Ya sanyata aje rigar ta kuma d’auko wani ba tareda ta kalla mai ta d’auko ba ta shiga nuna masa “How about this one..? Duba kaga.” Wann karon sosai ya dad’a tsarewa yana duban abinda take nuna masa Wanda da alama ita kanta bata San mai take nuna masa ba. Ta kasa daina murmushin yak’en da take sai juya abin dake hannunta take idanunta naga Haidar Wanda yai k’ok’arin mik’ewa alamun zai nufo yanda take. Bugun Zuciyar Ummul Ya k’aru ta yunk’ura zata nufosa tana fad’in “A’a ka dakata.. Zan taimaka maka.” Bata rufe baki ba abinda ke cikin hannunta tana nuna ma haidar wanda a tunaninta riga ce ta fad’o k’asa.. Dubawan da zatai nan taga shorts ne ashe take ta faman nuna masa. Bama tasan da gajeren wandon cikin jakar ba. Anisa ce ta saka a sace dan kawai ta had’a Ummul d’in da Haidar fad’a tinda tasan Haidar mutum ne da baya so ana kutsa masa kai cikin rayuwa without an invitation. Ummul ta runtse idonta sanda ta d’auko gajeren wandon cikin hannunta.. Tai saurin b’oyesa a bayanta tana tuhumar kanta ‘Daga ina wann yazo. Mai kika aikata Ummul.?’ Bata Ankara ba sai jin hannayen Haidar tai ya kewayeta. Bakinsa kusan kunnenta yake furta “Who gave you the right to touch my things.?” Ta kasa cewa komai sai zuciyarta dake ci gaba da bugu. Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa Haidar ci gaba sanda yake Zare shorts d’in daka cikin hannunta har lokacin tana rungume cikin jikinsa “I hate it when others invade my private space.!” k’arashe yana zare wandon cikin hannunta. Daidai lokacin Anisa ta turo k’ofa ta shigo Mommy na biye da ita. A tunanin Mommy Anisa ta nemi izinin shiga an bata Shiyasa ta kutsa kai. Anisa tai saurin cin birki had’ida cewa “Kuyi hakuri na shigo kaina tsaye. I’m sorry.!” Mommy tai saurin janyota suka nufi k’ofa tana fad’in “Ke ai bansan Randa zaki bar wann shashancin naki ba.” Haidar ya dan matsa baya kad’an yana dafe garu had’ida ciza labbansa kad’an sabida raunin da suke jikinsa Har lokacin. A hankali ya furta “It’s fine Mommy.. You can come in.” Ya k’arshe maganar sanda yake kishingid’a saman gadonsa ta majinyata. Ummul ta rintse idanunta tana jin kaman k’asa ya tsage ta shige. Ko d’agowa ta dubi Mommy ta kasa. Yayinda Anisa ke ta faman aika mata harara cikeda k’iyayya k’asa k’asa. Mommy ta karance yanayin da Ummul ke ciki sai ta bata aike wajen nurses d’in dake reception dan tana son magana da Haidar alone. Ta dubi Anisa ma ta aiketa can waje wajen driver d’inta. D’akin ya rage saura ita da Haidar. Mommy ta tsaresa sosai da ido. Duba irinta ta tuhuma. Ya d’an dubi mahaifiyar tashi sai ya d’an sadda idonsa kad’an ba tareda yace komai ba. Sosai Mommy taji dad’in hakan da Haidar yai alamun dai gradually yana sauyawa tinda tasan girmamawa ce yasa shi sadda idanunsa. Ta janyo kujera ta zauna kusan gadonsa gefen kansa. “Haidar.!” Ya d’ago ya dubeta jin ta kirasa in a serious tune. Mommy taci gaba “Kar kaga laifin Ummul dan an had’o kaya an kawo maka.. Ni ce na sakata yin hakan.” Ya d’anyi shiru sai kuma yace “But Mommy ba sai anje cikin kayana ana bincike ba.. You could’ve sent your driver ya saya ko a boutique.. Since I won’t be staying here for too long..” Mommy ta murmusa jin yanda yake ta kwanakwana yana maganar. Wai Haidar ne bai fad’a mata magana kai tsaye ba yaketa faman kwana.. Hakan na nuna mata Ya fara gudun b’acin ranta. Ta d’aura hannunta guda saman nasa tana murmushi “I know Haidar.. Zan iya yin hakan amma na zab’i matarka taje ta bincika cikin kayanka ta d’auko maka kaya.. Kasan dalili.? Sabida ita d’in matarka ce.. Bata da wani shamak’i da duk wani sirri naka.” Sai ya dan lumshe ido kad’an ba tareda yace komai ba. "Mommy ta kuma gyara zamanta “Aliyu, my son.”" Haidar Ya d’ago Ya dubeta. "Mommy taci gaba “Kaman yanda Ubangiji Ya bamu daman kasancewar D’a da mahaifiya a karo na biyu.. Ina so ka nuna godiyarka ta hanyar kasancewa miji ga Ummulkhair.. Bani so na kuma tilasta maka wani abu musamman abinda ya danganci yanke hukunci ga rayuwarka.. Amma na maka alk’awari wann shine zai zamo abu na k’arshe da Ya danganci yanke hukunci cikin rayuwarka Wanda zan buk’ata daga gareka, in sha Allah.. Please do this for me Haidar.. For the last time.. Ka bama kanka dama da Ummulkhair.. Just this once.. Na maka alk’awari.. Daga k’arshe idan bai working ba I won’t force it..” Ta dan murmusa tana dafa hannunsa “Inada yak’inin ma Khair in sha Allah.” Ta k’arashe tana duban D’an nata." Haidar ya dan dubeta cikin yanayin da bazaka iya fasalta abinda ke cikin zuciyarsa kai tsaye ba. Mommy ta kuma murmusawa kafin ta mik’e “Ni zan wuce gida na duba Aunt d’inka Asshe da gajiyan hanya.” Haidar baice komai ba sai jinjina mata kai da yai. Yai mata fatan kasancewa lafiya. Da haka Mommy ta fice zuciyarta fari sol. Cikin buwayar Ubangiji D’anta Ya soma dawowa kan turba. Bayan tafiyar Mommy daga bisani Ummul ta shigo. Aiko tana shigowa saiga Anisa ta take mata baya. Tai Sallama ma Haidar kafin ta juyo ta dubi Ummul “Ummul kema ya kamata mu tafi koh.. You know they don’t accept visitors here.” Kaman wanda aka zaburesa haka ya juyo yana duban Anisa jin tana fad’in Ummul ta tashi su tafi. Anisa tai murmushin da yafi kama da yak’e ganin irin duban da Haidar ke aika mata “Hos..Hospital rules.!” Ta fad’i cikin sauri da k’ok’arin kare statement d’inta. Har lokacin wani irin duba Haidar ke aika mata “She’s not a visitor.. You can leave.” Ya fad’i a tak’aice. Cikin sanyin gwiwa Anisa ke jinjina kai “Haka ne na mance..She’s your wife.. I.. am the visitor here.” Tai maganar cikin k’ok’arin danne k’uncin dake taso mata ga murmushi mai ciwo saman fuskarta. Ummul dai ta dubi Anisa ta dubi Haidar. Anisa taima Ummul saida safe had’ida fatan samun sauk’i ma Haidar.. Tasa kai zata fice Haidar Ya dakatar da ita "“Do yourself a favour and quit coming around. As you mentioned, visitors ain’t welcome.!”" Da mamaki Anisa ke dubansa jiki a matuk’ar sanyaye yayinda Ummul ma ke binsa da kallon mamaki. Anisa ta k’ak’aro murmushi mai ciwo tana jinjina Kai “As you wish..Dear Cousin.” Ta k’arada “Get well soon.” Ta k’arashe tana Kai dubanta ga Ummul wacce sosai damuwa ya nuna saman fuskarta. Anisa na ficewa tai bursting cikin kuka. Gudu gudu ta fice daga asibitin. Ummul ta maidoda dubanta ga Haidar Wanda ke k’ok’arin zame rigar dake jikinsa sai faman tamke fuska yake sabida zafin rauni da basu gama sake shi ba. Sam bama ta kula da abinda yake ba dan sosai korar da yai ma Anisa yai mata zafi. Kaman zatai kuka. Cikin sanyinta ta soma fad’in “Haba mana.. Mai ka aikata ne ..? Meyasa zaka Kori Anisa. Laifi ne dan an nuna damuwa akanka.?” Kallan Yanda tai da fuskarta kaman mai shirin kuka Haidar yake. ‘How dare she interferes! Who does she think she is?’ Cikin zuciyarsa yake zancen saidai Ya kasa furta komai. Bai ce da ita komai ba sai k’ok’arin sauk’owa daga gadon da ya soma. Sai sann Ummul ta kula babu riga jikinsa. Ai sai ta d’an daburce ta soma k’ok’arin kare idonta da tafin hannunta tana sadda Kai k’asa ga Haidar dake nufota. Ta soma matsawa baya tana fad’in “Wai mai kake aikatawa ne. Da.. Da cewa Kai na baka waje zaka canza..” Bai amsata ba bai daina nufota ba har suka isa jikin gini. Hannu yasa ta bayanta Wanda ya sanyata saurin d’agowa a matuk’ar tsorace tana dubansa zuciyarta bai daina bugawa da sauri ba. Sun d’an d’auki lokaci a haka kafin Haidar ya mik’a hannunsa sosai ya d’auki riga cikin suitcase d’insa dake daga gefen Ummul saman drawer. Ganin ya d’auki rigar ya soma takawa a hankali ya sanyata lumshe ido had’ida sauk’e ajiyan zuciya a hankali. Shi kaw Haidar na hankalce da ita yana kallonta ta wutsiyar ido. Murmushi ya saki da gefen bakinsa kafin ya dan saki k’ara yana rik’e gefen ribs d’insa Wanda yasa Ummul saurin Ware idonta. Bata san sanda ta nufosa da sauri ta mik’a hannayenta ta tallafosa tana masa sannu had’ida tambayarsa ko ciwo yake ji. Haidar bai daina ciza labb’ansa yana tamke ido had’ida sakin k’anan k’ara alamun yana jin pain har saida suka isa saman gadon. Ummul ta kuma dubansa a kid’ime bayan ta taimaka masa ya d’an kishingid’a “Kana jin ciwo ne.? Kana so na kiraka maka Likita.? Kaga barin kirawo su.” Ta k’arashe tana k’ok’arin dirowa daga saman gadon amma sai taji Haidar ya rik’o hannunta. Cak ta dakata da abinda take ta juyo a sanyaye tana dubansa. Ya d’an sha mur ganin tana duban fuskarsa kafin ya sakar mata hannun “Why would you call them.? Bayan gaki nan a nan.!” Ya k’arashe maganar yana d’aura mata rigar saman hannunta. Ta dubesa ta dubi rigar da ya saka cikin hannunta da mamaki. Sai ta d’an girgiza Kai kad’an alamun bata gane mai yake nufi ba. Mai zatai da rigarsa. Sai shima ya d’aga mata gira had’ida yi mata alama da ido da ta saka masa rigar. Sai Ummul ta soma girgiza Kai “A’a bazan iya ba.. Ka saka rigarka da kanka.” "Bata Kai aya ba ya bata amsa da “But I can’t move my arms.. It hurts.. And since you are my caretaker, Ke yafi kamata kiyi. Haka ne.!” Ya k’arashe yana tsareta sosai da ido." Sukai shiru su duka biyun suna duban juna kafin Haidar ya k’ara da “I thought kin d’auki alk’awari ma Mommy.. Cewa zaki iya shiga cikin rayuwata..? Here.. Do it.!” Ya k’arashe cikin sigan rad’a yana mai kuma dank’a mata rigar cikin hannunta. Ummul tai rau rau da idanu tana dubansa kaman zata sakar masa kuka tace “Amma..Toh.. Amma ya akai ka cire wancan.?” Har lokacin muryarsa k’asa k’asa “It’s just a patient wear.! Hakan na nufin zan iya cirewa cikin sauk’i..” Ya k’arashe yana tsareta da ido. D’an rausayar da ido kad’an tai tana mai satan kallonsa. Har lokacin idon Haidar na kanta alamun yana jiran ba’asinta. Sai Ya kashe mata ido guda alamun yana jira. Ta d’an gyara zamanta tana duban gefe da gefe. Ta kai idonta kan hospital gown da ake sanyawa wa marassa lafiya Wanda Ya cire. Tace “Amma.. amma Na zata saka rigar asibitin ma dokace.” Kafin tai shiru ya bata amsa da fad’in “You should understand by now that I don’t follow rules.!” Ya k’arashe yana mai tsareta da ido. Wanda hakan Ya kuma sanyata maida idonta k’asa. D’akin Ya d’anyi shiru banda lugude Babu abinda k’irjinta keyi. Ta Ya zata soma sanya masa riga.? Haidar ya soma k’ok’arin saka rigarsa yana hankalce da ita sai faman juya yatsun hannunta take. Sarai yasan tunani take. A hankali yake zira hannunsa still yana kallonta. Out of nowhere ta sinkayo muryarsa “Kenan k’arya kike da kika ce kin dau ma Mommy alk’awarin shiga rayuwata.?” Shiru batace komai ba sai sadda kanta k’asa da tai kaman wata maras gaskiya. Dak’ik’ai suka gifta babu mai cewa komai cikinsu. “Zamanki a nan baida amfani.. You shud also leave please.” Ya fad’i yana k’ok’arin saka rigar da kansa. Ta soma girgiza kai tana dubansa cikin d’an daburcewa. K’ara ya saki kad’an alamun ya fama ciwonsa. Ba shiri Ummul ta k’araso da sauri ta rik’e hannunsa da rigar tana masa sannu had’ida tambayarsa ko ciwo ke masa. Duk ta daburce a hankali take zira masa rigar Har saida ta fitar masa da hannunsa. Idonsa kyam a kanta Har ta gama zira masa rigar ta gyara masa pillow ya kishingid’a. Zata mik’e Ya rik’o hannunta. Ta kaikaito suna duban juna. “You should.. also change.. You can’t sleep with…those cloths.!” Yai maganan yana nuni zuwaga kayan jikinta da idonsa. Ta k’ak’aro murmushi “Kar ka damu.. Zan iya.” Bai kuma cewa komai ba sai tab’e bakinsa da ya d’anyi. Tana kallonsa daga nan yanda take zaune ya tada sallan isha har ya sallame. Can wani ma’aikacin asibitin Ya nemi izinin shigowa Ummul tai masa iso. Nan ya shigo yana turo wani keke irin Wanda ake d’aura abincin majinyaci. Iyakacin k’ayaddajen abincin da majinyacin zaici aka shigo dashi harda dose din maganin da zai sha na wann lokacin. Mutumin zai soma b’alle magani Haidar ya dakatar dashi “Just leave it from here. Kana iya tafiya.” Ya jinjina masa kai kafin ya dubi Ummul Ya bata wani k’aramin card Wanda zata karbi abincinta dashi a cafeteria. Ita dai Ummul sai juya card d’in take tana mamakin asibiti kaman a turai. Dole ma ace ba’a buk’atan d’an tayin jinya tinda duk wani kula za’a baka. Ga na’ura dake indicating musu abubuwa da dama Wanda daga yanda suke zasu fahimci hakan. Haidar yai gyaran murya kad’an Wanda hakan Ya dawo da hankalinta gareshi. Yai mata alama da ido da ta k’araso ta zauna. Ba musu ta k’araso saidai idonta a k’asa dan ita dai tinda ta sanya masa riga ta kuma kasa had’a ido dashi. “Can I take my drugs…now.?” Yai maganar yana mai kai dubansa ga agogon bango dake manne d’akin. Alamun yana nuna mata lokacin shan maganin zai shige. Sai ta dubi magungunan ta girgiza kai “Ban.. Ban san ya zanyi ba.” Ya tsareta da ido sai yace “Come close.. I’ll show you.” Da dan dubesa sai ta d’an matso kusansa kad’an. Shi kaw har lokacin ya tsareta sosai da ido “Closer.!” Ya furta a hankali. Ta kuma dubansa sai ta d’an kuma matsowa.. Saida ya tabbata ta matso kusansa sosai kafin yace ta d’auko parantin maganin ya nuna mata. Ita dai jinsa kawai take amma da ganinta zaka fahimci a tsorace take. Ta d’auki glass cup da bottle water da mutumin ya shigo dashi ta soma tsiyayawa hannunta sai rawa yake alamun nervousness. A haka take yunk’urin kai ruwan da maganin bakinsa Har lokacin hannunta bai daina rawa ba. Shi kaw Haidar sosai ya tsareta da ido. Charaf yai grabbing hannunta. Wanda hakan Ya sanyata d’ago ido tana dubansa a d’an tsorace. Shid’inma ita yake kallo “Just.. relax..!” Ya fad’i yana mai kai hannun nata saitin bakinsa har lokacin idonsa akanta. A haka dai ta ko k’arta ta basa maganin. Akazo maganar abinci zata tashi nan ma yace bazai iya moving arms dinsa ba she should feed him. Haka dole ba yanda ta iya ita ta basa abinci. Ko wani motsi nata kan idon Haidar. Ranar dai ta zamto tamkar personal nurse d’insa. Dan duk wani abu da suke na kula da majinyaci baya bari suyi ita takeyi saidai Wanda yafi k’arfinta ko layin ma’aikatan lafiya ne kawai. Dik yanda taso ta zille ma Haidar Ya kasa barinta. Can dare tana kishingid’e saman sofa shi kaw sai kallonta yake daga nan saman gadonsa ta majinyata. Nan yaga ta tak’ure waje guda ta k’udindune cikin hijab dinta. A hankali Ya mik’e daga saman gadonsa da kyar. Ya tako zuwa yanda take. Zama yai gefenta yana k’are ma fuskarta kallo. Kallo irin Wanda bai tab’a tsayawa yai mata ba. Hannu yasa yana zare Hijab d’in hakan yai daidai da juyin da zatai. Take yaji wani abu ya tsargar masa kaman electric shock. Nan yake binta da kallo head to toe. Ya jima sosai yana k’are mata kallo kafin ya karkatar da ita kad’an Ya kwanta nan gefenta kasancewar kujerar mai fad’i ne sosai. Ya matso da ita cikin jikinsa Ya janyo abin rufuwar Ya rufa musu. ** A can gida kuwa yanda Anisa taga rana haka taga dare. Sai kai komo take a d’aki ita kad’ai tana safa da marwa. Ta lallaba ta tafi d’akin da aka sauki Amminta. Ta tsaya tana kallon mahaifiyar nata dake sharan bacci tana tunanin hirarsu da Mommy da ta sinkaya a asibiti gamed auren Haidar da Ummul. Kodai ta tashi Ammi ne ta sanar da ita taji komai. Tasan komai a halin yanzu.? Toh Amma Hisham yace ta bar masa komai.. Ya mata alkawarin zai cire Ummul daga rayuwar Haidar ko ta halin k’ak’a.. Idan ta sanar da Ammi wani abu yanzu shirinsu da Hisham ka iya b’aci. Bazata bari hakan ta kasance ba. Sauri sauri ta koma nata d’akin. Ta kagu gari ya waye ta bullo da wata hanyar da zata samu taje ta duba Haidar da Ummul tinda Haidar dai ya mata iyaka da asibitin. ** Asubahin fari ta farka tana mamakin yanda bacci mai nauyi ya dauketa itada take yawan farkawa cikin dare. Nan tajita cikin jikin mutum kuma. Zuciyarta ta tsinke. Ita tsoro ma abin ya bata dan Sam bata kawo a zuciyarta majinyaci irin Haidar ka iya mak’alewa gefen kujera har yayi bacci irin haka ba. Ta yunk’ura a tsorace zata tashi sai ta sinkayo muryarsa yana sakin ‘yar k’ara had’ida rik’e gefen hak’ark’arinsa. Su duka biyu duban juna suke kasancewar akwai hasken dim-night cikin d’akin. Tai saurin mik’ewa tsaye daga kan kujerar tana kuma kallonsa. Ganin da gaske na cikin pain dan har lokacin bai daina tamke ido yana dafe hakarkarinsa ya sanyata saurin duk’awa gabansa tana tambayarsa “Da zafi ne.? Na bige maka ciwo ko.? Dan Allah kai hak’uri wllhi ban kula bane.!” Ta k’arashe maganar kaman mai shirin kuka. Sai Ya daina tamke idon da yake yana Ware idanunsa a hankali yana kallon yanda take magana kaman itace cikin pain d’in. Ta d’an saci kallonsa “Kai hakuri zan tabbata na taho da abin rufuwa yau in sha Allah.” Ya tsareta sosai da ido kafin ya girgiza kai kad’an had’ida lumshe idonsa “It’s fine..” Ya fad’i a tak’aice. Ya mik’e a hankali yana fadin “I.. Will use the bathroom.. It’s subh prayer time already..” Ta jinjina masa Kai a hankali “Kana buk’atan taimako na.?” “No I.. Can manage.” Ya fad’i yana dingisawa har ya nufi hanyar bathroom din. Yana shigewa ta zauna had’ida sauk’e deep breath. Hannunta na rawa ta janyo mayafin da ya rufesu dashi. Sai ta runtse idonta da sauri wai yau ita Ummul ke bacci mayafi guda da Haidar.. Kunya ne.? Damuwa ne? tsoro ne? Duk sai ta ma rasa mai ke mata yawo cikin zuciyarta. A b’angaren Haidar Shima haka nan ya lumshe idonsa a bathroom abubuwa fal zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake tuhumar kansa ‘What’s wrong with you Haidar.? Why are you so soft with her..?’ Take zuciyarsa ta shiga tuno kalaman mahaifiyarsa garesa ‘Ka ba ma kanka dama da Ummulkhair.. Kamin wann Haidar koda shine abu na k’arshe da zan buk’ata wajenka.’ A fili yake furta “Sabida Mommy. You are doing it for Mommy and because of Mommy.. Kaman yanda ta buk’ata.” Da safe kuwa su duka biyun yanayinsu ya dan sauya bayan baccin da sukayi tare musamman ma Ummul wacce ta kasa had’a ido dashi. Gaisuwa ma k’asa k’asa tai masa. Haidar nata karantarta. Sassafe take shirin tafiya gida dan ta samu ta kintsa kanta kafin ta dawo. Zata fice ta sinkayo muryarsa “Khairy.!” Cak ta tsaya tana sauraron sunan da ya kirata dashi. Haidar yaci gaba “Don’t take long.. And.. kar ki sake ki zo da wani abin rufuwa asibitin nan.” Sai ta dubesa da mamaki “Amma maiyasa.?” Ya tab’e baki kad’an “Hospital rules.!” Ta jinjina Kai a hankali tace “Shikenan bazan zo dashi ba” Haidar ya jinjina mata Kai sihirtaccen murmushi saman labb’ansa. (Kunji wani salon wayo wajen Haidar. Wai asibiti ta hana zuwa da abin rufuwa daga gida.) Ita dai Ummul Haka ta fice tana mamakin wann wane irin asibiti ne masu tarin dokoki da k’a’idodi. Bayan ficewar ta da kad’an Anisa tai knocking a k’ofa. Duk a tunaninsa Ummul ce ta dawo. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Ga mamakin sa Anisa ya gani rik’eda jakan kaya. Ya tsareta sosai da ido alamun yana jiran ba’asi tinda yasan ya mata iyaka da asibitin. Ta k’ak’aro murmushi tana masa gaisuwar da bata samu amsa ba. "“What are you doing here? I thought I made it clear to you…” Saurin katsesa tai ta hanyar d’ago masa jakar Kayan “Kayan Ummul… Mommy ce ta Aiko ni na kawo..” Sai ta d’an saci kallonsa “And.., I…wanted to check how you’ve been holding up.. Laifi ne hakan..? After all, we are cousins.”" Katseta yai “I just don’t want you here.. Don’t you get it” Kuka ta fashe dashi tana mai barin d’akin. Ta rasa mai tai ma Haidar yake mata irin wann kiyayya.. Toh kodai ya fahimci da saka hannunta ne a had’arin da ya samesa.? Dole ta nemi Hisham su san ta yanda zasu bullo ma al’amarin. ** Hisham ya dubeta sai kuma ya girgiza Kai yana murmushi “Kar ki bani dariya mana Neesa. Quite alright Haidar na zargin had’arin mota da ya samu shiryayyen abu ne.. Amma ina mai tabbatar Miki ba kece yake zargi ba.” Anisa ta dubesa ta d’an girgiza kai “Ta Ya ka tabbatar da haka.? Sann waye yake zargi.?” Hisham Ya murmusa “Wani hujja yakeda shi da zai zargeki.?” Shiru bata basa amsa ba. Hisham yaci gaba “A kalaman Haidar cewa yayi yana zargin wani ne dake boyayyen agenda akansa. Waye keda dalilin ganin bayansa.?” Shiru bata amsa ba. “Dareen.! Ita ce kawai takeda motive na hallak’a Haidar tinda ta rasa shi bazata bari wata ta same shi ba. Haka ne.?” A hankali Anisa ke jinjina kai. Hisham yaci gaba da murmusawa “Which is why dole na cimma Dareen kafin Haidar Ya cimmata..” Ya kaikaito sosai yana duban Anisa “Duk abinda nakeyi.. Everything is calculated. Ki bar mun komai kaman yanda na fad’a.. Aikinki kawai shine ki saka ido akan Haidar da kuma Ummul.” Ta rausayar da ido “But it is not as easy as it seems. Haidar is making it difficult.” Ya kurbi drink dake hannunsa had’ida d’age kafad’unsa kad’an ya tabe baki “You must do it. You don’t have a choice. Find a way to keep an eye on those two” Ta shiga jinjina kai a hankali tana furzar da huci. Basu ida maganar ba wayar Hisham tai ruri Haidar ke kiransa. Ya murmusa yana duban wayar “Speak of the devil… he shows.!” Ya furta a fili kafin ya d’aga kiran. Bayan Sun gaisa irinta abokai Haidar yace “I sent you an email.. Since you can’t come to visit.” Ya murmusa “Haba abokina ba haka bane.. Kasan asibitin naku ne na turawa. Komai d’an k’aida.. And work’s been too demanding lately.. Musamman da yake baka nan. On the other hand ga neman Dareen da nake. Kasan bazan tab’a barinta ba sai na nemota ta biya abinda ta aikata ma abokina. “Speaking of Dareen. Are you free?” Shiru kaman bazai amsa ba Ya soma yan kame kame Haidar Ya katse sa “You know me. I don’t take no as an answer. Ina jiranka.” Daga haka katse kiran yai. Duban Anisa yai yana huci. Cikin zuciyarsa yake ayyana Ya tsani yanda Haidar keyi kaman wani boss d’insa bayan cewa ko a haife ne shine gaba da Haidar d’in.. Anisa ta katse shirun da fad’in “See Kai gashi yana nemanka amma ni cewa yake anyi restricting zuwan visitors.” Hisham Ya furzar da huci “Kinsan meye matsalar?” Anisa ta girgiza kai alamun a’a. “Bazai yuwu Ummul ta ganni wajen Haidar ba all our plans zasu lalace ne. No Ummul bazata ganni wajen Haidar ba. It will be a disaster.” Anisa ta murmusa “But this is the perfect time da ya kamata ka visiting Haidar because Ummul bata wajensa ta tafi gida. I believe ma Shiyasa ya samu chance na kiranka. Hisham yace “You sure.?” “Hundred percent.!” Ta basa amsa tana mai jinjina kai. “Perfect! Yanzu abinda zaayi kiyi maza ki tafi gida ki rik’eta ki hanata barin gida Har sai nayi alerting naki. Ma’ana sai na bar wajen Haidar.” Anisa tace “An gama Barinyi sauri na tafi kafin ta fito nasan sai ta tsaya tayi wanka tayi wasu abubuwan.” Daga haka sukai sallama da Hisham. Shi Ya nufi asibiti wajen Haidar ita kuma ta nufi gida wajen Ummul. A can gida kuwa Mommy sai nan nan da Ummul take tana fad’in maza maza ta gama shiryawa driver ya maidata. Mijinta majinyaci ne bai kamata ta barosa shi kad’ai ba. Asshe kanta sai mamaki take ganin yanda Mommy keyida Ummul. Lallai Anisa tayi gaskiya da tace idon Mommy ya rufe akan Ummul. Gani take kaman an canza mata ‘yaruwar tata da gaske ne. Gaba d’aya Mommy ta tashi daga Aunty Kwaise da ta sani ta koma wata abu daban. Ita kanta Asshe lamarin tsoro Ya fara bata. Ta zuba ma sarautar Allah ido ta kasa katab’us. A haka Anisa ta iso gidan ta taddasu sai karantar Mommy take tana ganin yanda take ingiza Ummul tayi ta tafi wajen mijinta. Makirin Murmushi Anisa tai tana jinjina kai dan har ta hasasho ta yanda zata tarwatsa Auren Haidar da Ummul. Muddin ta fayyace ma Ummul komai zata fahimci Hajiya Kwaise Maitama azzalumar mace ce ba soyayyan gaskiya take nuna mata ba. Kawai tana mata duk abubuwan da take ne don amfanin kanta da D’anta. Tabbas Ummul zata tsani Kwaise da tsinann auren da tai ma da d’anta Wanda boka Ya had’a. Ta k’arashe tunanin tana mai kecewa da Makirin murmushi. A k’ofan fita daga sashen Mommy Anisa ta cimma Ummul. Suka sakar ma juna murmushi had’ida gaisuwa. "Anisa ta k’arada “Ba dai har zaki wuce ba.?” Kafin Ummul ta kaiga bata amsa ta kuma sakin murmushi tana mai dafa kafad’an Ummul d’in “It’s fine, Ya kamata ki tafi kin baro mijinki shi kad’ai… I Miss having you around Ummul.. Kinsan bahaushe yace sabo turken wawa”" Suka murmusa a tare kafin Anisa ta mik’a mata jakan hannunta “Ga wann kar na rik’eki da surutu.” Ummul ta d’an girgiza kai kad’an cikin rashin fahimta “Ta mecece.?” “Kayanki ne a ciki. Nayi tunanin na kai miki su asibiti sanin cewa zaki buk’ata amma sai mijinki Ya koreni dasu.. Kamar dai ko yaushe.” Ta k’arashe tana mai k’ak’aro murmushi. Jikin Ummul Ya d’anyi sanyi “Kiyi hak’uri Anisa…” "Saurin dakatar da ita Anisar tai “No no.. You don’t have to apologise for his behaviour. Kar ki samu damuwa.. Nasan Haidar since childhood.. He’s rude, arrogant, short tempered.. and sometimes unpleasant to be around.. Ki yarda dani, idan da sabo na saba da halin d’anuwana..”" Da mamaki Ummul ke dubanta dan ko ba auren soyya sukai da Haidar ba sosai taji zafin kalaman da take fad’i kansa. Amma sai ta danni zuciyarta ta murmusa “Baki tunanin kalaman da kike sunfi kama da cin fuska.?” Shiru Anisa batace da ita komai ba. Ummul ta murmusa had’ida dafa kafad’ar Anisa “Kar ki damu banyi fushi ba. Dan dik abinda kika lissafo gameda shi kwalliya na d’aukesu. Domin kaw sosai suke k’ara masa k’warjini da birgewa.” Ta k’arashe murmushin nan nata dake tunzura Anisa saman fuskarta. Murmushin da yafi kama da yak’e Anisa ta k’ak’aro “Of course. Haka ne.. Let me walk you to the car..” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Ummul d’in suka nufi mota. A hanya Anisa ke ci gaba da fad’in “Mutanen gidan nan sunyi kama da mutanen kirki koda ahalin ya kasance birkitaccen ahali mai tarin gib’i.. Haka ne.?” Ummul ta dubeta cikin rashin fahimta. Anisa ta murmusa “Ko wani d’an adam yanada sirrikansa.. Amma akwai wasu abubuwan da sirri baida muhalli cikinsu. Kamar dai Aure. Haka ne.?” Ummul ta kuma girgiza kai tana karantar yanayin Anisa. Tana danganta maganganun Anisa da tunanin kodai Anisa tana so ta sanar da ita cewa tasan yanda akayi aurenta ne.? Amma batada wani sirri da ta b’oye ma Haidar gameda aurensu face iyaka da Umma tai mata da d’aukacin ahalinta Har na tsawon watanni uku ciki harda mahaifinta dake kwance yana jinya. Bata Ida tunanin ba ta kuma sinkayo muryar Anisa daidai sanda suka isa jikin mota. “Kina tunanin kinsan ahalin gidan nan ne Ummul.? Ko kina tunanin kinsan mijin da aka aura Miki ne.? Ina shawartar ki kar ki zak’e da yawa.. Don’t get too attached. Be warned.!” Cikeda gargadi tai maganar kafin ta murmusa “Akwai abubuwa da dama dake cikin duhu. Ina fatan a lokacin da duhun nan zai yaye miki Ummul bazaki sameni cikin wad’anda suka ci amanarki ba. And you can count on me dan ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace ce.” Ta k’arshe tana murmushi had’ida bud’e mata marfin mota “A cikin gidan nan trust no one but yourself Ummulkhair. Tabbas Wani Auren nasara ne. Amma Wani Auren halak’a zai kaika.! Allah Ya tsare hanya.” Ta k’arashe da murmushi. Tana ida fad’in haka ta juya ta shige cikin gida zuciyarta na mata fari k’al. Dan ta tabbata ko ba komai ta cika shakku cikin zuciyar Ummul. Wani abu ma sai randa k’wai Ya fashe gaba d’aya. Tabbas Anisa tayi nasaran jefa mata waswasi da shakku cikin zuciyarta. Shin da gaske ne ita d’in ta zak’e da yawa.? Batasan mai Anisa take son sanar da ita ba. Sann koda wann auren tun usul bata tsammaci farin ciki ko wani abunda yai kama da wann cikinsa tun farko ba. ta tsinci kanta cikin tsananin shakku da rud’ani Wanda bataji irinsa a baya ba. Sann sosai taji tana buk’atan sanin mai Anisa take son sanar da ita musamman gameda mijinta Haidar. Haka har ta isa asibiti tunanin da take kenan jikinta duk a sanyaye. * Asshe bata iya kwanaki garin ba ta tarkasa ta dawo Kano dan sosai ta firgita da lamarin ‘yaruwarta dole ta dawo gida ta samu ta shawo kan matsalar kafin komai Ya ida kwance mata musamman da idonta ya tabbatar mata idan ‘yarta Anisa bata k’arashi rayuwarta gidan yari ba toh kuwa ba shakka zata k’are a turu ganin irin abinda take wanda yafi kama da hauka tuburan duk dan akan Haidar. Da fari ta saka ma Ummulkhair guba a turare sann ta d’aura alhakin kan Mommy har ta tafi jail tai kwanaki dik akan haka. Yanzu ga had’arin mota da ta shirya ma Haidar wanda k’iris bai rasa ransa ciki ba. Lallai ya zama dole tasan abinyi.. Dole ta raba wann jarabebben aure na Ummulkhair da Haidar wanda ta zamto silarsa a farko ko dan ta ceto ‘yarta Anisa. * Kano.. "Sun had’e su uku a parlorn Hajiya Asshe. Mama Tani wacce bata jima da shak’an iskan ‘yanci ba, Inna Dije sai kaw Uwar gayya Hajiya Asshe." Tani ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Inna Dije “Dije kina nufin kice wann matar ita tayi belina ba sirakan Suwaiba ba.? Sann so kike kice mun duk zaman dad’I da naga kinayi da Suwaiba a halin yanzu dama ba na gaskiya bane.? Dije wai meke faruwa ne.?” Inna Dije ta murmusa tana duban Tani “Tani banda abinki.. Wann ma ai sirkar Suwaiba ce. Kuma ke a tunaninki ni Tani zan tab’a yafe ma Suwaiba da ‘yarta Ummulkhair ne. Kar ki mance a dalilin bak’in k’addarar Ummulkhairi na rasa tilon D’ana Fa’izu.! Kuma ke kinfi kowa sani Tani. Dije bata yafiya sai d’aukar fansa.! Yau d’in nan zan sanar dake wace kalan Aure Suwaiba taima ‘yar D’anuwana dake kwance yana jinya wanda zai zamto Miki makami da zaki kori Suwaiba da Auren cin amana da tai miki. Tani na san komai Suwaiba zata Miki a halin yanzu. Duk wani halacci na k’arya da zata Miki bazaki tab’a mance bak’in cin amana da ta miki na aure Miki miji bayan kin aminta da ita da tayi ba. Haka ne?!” Tani tai shiru tana duban Inna Dije wacce ke sakin huci. Tani sai ta girgiza kai a hankali “A’a Dije. Yo ni a halin yanzu wani makami nakeda shi Wanda zan yak’i Suwaiba dashi bayan yarana da a kullum nake goranta mata cewa sunyi aure suna d’akin mazajensu gasu nan duka sun dawo gida daga wacce miji Ya koroto sai wacce miji Ya gudu Ya barta. K’arewa ma Suwaibar ke kula dasu a lokacin da nake gark’ame gidan gyaran hali. Na sani abinda Suwaiba ta min bazan tab’a yafe mata ba ko mutuwa Malam yayi amma a halin yanzu banida abinda zan yak’i Suwaiba dashi kina gani yarana ma sun koma k’ark’ashin tutar Suwaiba.. Toh mai yai saura.?” “Malam Isubu Yayana shine kad’ai ya miki saura Tani. Dan Dikda kasncewarki ‘yar ta’adda mai saida hakkin miji da ransa da sunan gado ta’addacin da Suwaiba tayi yafi naki kuma dik randa D’anuwana yasan mai Suwaiba ta aikata a lokacin da yake kwance ya rabu da ita kenan rabuwa ta Har abada.. Kuma idan mutuwar auren yaranki ne Ya tsaya Miki ki taya Suwaiba sharan d’aki yanda Ummul zata zauna dan nan da wata d’aya jal Ummul zata dawo gida ta jone da naki yaran.!” Tani ta girgiza kai “ban fahimceki ba Dije.? Mai kike nufi.? Wane irin Aure Suwaiba taima Ummul.?” Carab Asshe ta cab’e “Auren mutuwa.! Auren warware sihiri.! Auren WATA UKU.!” Take Tani ta mik’e a zabure tana dafe k’irji “Na shiga uku ni Tani. Auren mutuwa..?!” SameenaAleeyou*AUREN WATA UKU..!* *43* *©️Sameena Aleeyou… * Inna Dije ta jinjina kai “K’warai kuwa kaman yanda kika ji.” Wata ‘yar bazawarar dariya Mama Tani tai irin Wanda bai kai ko ina ba “Haba haba Dije. Dani dake munsan Suwaiba.. Koda ace shashasha ce lamba d’aya bazata tab’a abinda kike fad’a mun ba. Koda ace mafarkin Suwaiba da cikan burinta shine taga Ummul dinta a d’akin aure ko wane iri ne. Dije munsan Suwaiba bazata tab’a gigin jefa ‘yarta a halak’a Har haka ba.!” Asshe ta murmusa tana duban Tani “K’warai kuwa da saninta bazata jefa ‘yarta a auren halak’a kaman yanda tayi ba. Burin Suwaiba shine ‘yarta Ummul tayi aure ko ta halin k’ak’a ko wani iri ne matuk’a sunansa Aure. Tabbas da ace Suwaiba tasan wani irin Aure ta jefa ‘yarta ciki da nadaman da zatayi sai tafi wanda take ciki yanzu.” Ta numfasa kafin taci gaba “A Yarjejeniyar da mukai da nida Suwaiba shine ‘yarta Ummulkhair Auren Kwangila tayi mai k’ayyadadden wa’adi Wanda wa’adinsa watanni uku ne. Sam ban sanar da Suwaiba ga asalin sahihin manufar Auren ba. Hasalima ban sanar da kowa bayan ‘Yaruwata da muka shirya Auren tare sai ku da Ya zama dole na bude maku cikina dan bazan iya wann yak’in ni kad’ai ba. A halin yanzu Babu abinda nake so kaman Ummul ta fice daga rayuwar ‘Yaruwata tinda na kula Ummul ta riga tayi tasiri a zuciyarta. Ba haka na shirya abun ba.. Domin kuwa a halin yanzu ‘Yaruwata mahaifiyar mijin Ummul Auren gaskiya take son D’anta yayi da Ummulkhair ba AUREN WATA UKU kaman yanda muka faro daga farko ba.” Tani ta dubeta da mamaki sai ta girgiza kai “Toh mai kike so muyi a nan.? Ta yaya zamu raba auren da bamu muka k’ulla ba.?” Inna Dije ta murmusa “Mu kad’ai ne zamu iya datsen Auren sabida mu keda kusanci da Ummul da kuma Mahaifyarta Suwaiba. Hajiya Asshe batada abokin tarayya domin kuwa ‘yaruwar tata da tai komai domin ita asirin Suwaiba yayi tasiri akanta tinda gashi ta makance da soyayyar Ummul ma d’anta. A halin yanzu Suwaiba ta aminta da mu Tani. Da wann aminci mu kuma zamu yi amfani mu tsinke Auren ‘yarta sann mu d’au fansar duk wasu abubuwan da tai mana.!” Tani tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta girgiza kai kad’an “Amma idan Har Ummulkhair Auren mutuwa tayi mai zai hana mu kyaleta ta Mutu cikin wann aure kinga Babu babban fansa da zamu d’auka kan Suwaiba tamkar ta rasa ‘yarta da ta k’wallafa rai akanta tin haihuwarta. Musamman ma ke da kika rasa tilon D’anki ta dalilin bak’in k’addararta.” "Dije tai ‘yar bazawarar dariya wann karon “Idan dan wann ne da na jima dayi Tani. Idan kashe jinin Suwaiba shine fansar ran Fa’izu ai Khulsum tana nan gabana da tuni na b’atar da ita. Kar ki mance ‘ya’yan Suwaiba duk yanda naje nazo ‘ya’ya na ne.. Sann ai mutuwar Ummul bazai mata ciwo ba musamman idan a gidan Aurenta ta Mutu. Hakan na nufin burin Suwaiba na aurar da Ummul Ya cika kenan. Ai bari kiji Tani Ummul ta dawo gida sann tasan duk wani badak’ala da mahaifiyarta ta tafka da sunan Aurar da ita sai yafi komai yi ma Suwaiba ciwo. Dik randa Ummulkhairi tasan cewa Mahaifiyarta ta siyar da ita ne domin ta zamto makarin asiri da sunan Aure zata tsani Suwaiba, zatayi danasanin kasancewarta mahaifyarta sann zatayi nadaman duk wani biyayya da ta jima tana mata. Ba a nan kawai ba, Mijinki Yayana zai tsani Suwaiba zai guje ta Ya rabu da ita rabuwa ta Har abada kai kowa nata sai Ya guje ta. Dan babu Wanda zaiji abinda Suwaiba ta tapka bai kyamaceta ba. Yanzu kin fahimci manufata.?” Ta k’arashe tana tsare Tani da ido." Makirin Murmushi Tani ta saki irin Wanda ta jima batayi ba tin kafin a gark’ame ta a gidan gyaran hali “Lallai dole na jinjina Miki Dije. Wann shiri naki Ya shiryu Ya kumayi daidai da fansar da na jima ina so na daukan kan Suwaiba amanata da taji ta aure min miji bayan na aminta da ita.! Har na hango idon Suwaiba a lokacin da Malam zaiji cewa Matar sonsa Suwaiba ta mik’a yarsa mafi soyuwa ayi tsafi da ita.!” Ta kece da wata iriyar muguwar dariya Dije na tayata. Asshe ta dubesu tana murmushi “Toh ni babu abinda zance sai hamdala tinda dukkanmu mun samu matsaya guda shine mukai Suwaiba k’asa warwas. Abinda zamu maida hankali yanzu akai shine ku kuje kuci gaba da shashantar da Suwiaba kuna nuna mata cewa Lallai kuna tareda ita dan taji dadin sakin jiki daku ta yarda cewa tuba na gaskiya kukayi. Nima kuma zan maida hankali ga ‘Yaruwata da shirye shiryen da take na tariyar Ummul da Haidar da zaran an sallami Haidar d’in daga asibiti. Bazamu bari ayi wann bikin tariyar ba. A daidai wann lokacin zamu k’addamar da duk wani shirin mu sann mu lalata komai. Zan raba D’an ‘Yaruwata da zuri’ata da annobar da na kawo mana cikin zuri’a. Sann ku kuma zaku d’auki fansar ku akan Suwaiba. Duk kun amince da haka.?” Gaba d’aya suka jinjina kai suna masu jaddada k’udirorinsu. ** Abuja… A hankali yake takowa cikin parlorn bayan kiran da Ya samu daga Hajiya Kwaise Maitama cewa tana nemansa. Koda Hisham yaji sak’on nemansa da Hajiya kwaise keyi baiji ko d’ar ba cikin zuciyarsa sann baiyi k’asa a gwiwa ba ya amsa gayyatar nata. Cak Ya tsaya tsakiyar katafaren parlorn na alfarma bayan one of the maids ta masa iso. Wann shine ya kamata ace Ya kasance rayuwarsa amma Hajiya Kwaise ta masa denying. Ta koresa a gidan mahaifinsa tin yana ciki baizo duniya ba. Ya d’aga kai yana kallon wani hoton Haidar da ba’a jima da kafawa a parlorn ba. Shi kansa Haidar baisan da hoton ba dan yana asibiti Mommy tasa aka saka hoton. A Office aka masa hoton bayan ya gama gudanar da wani presentation. Yayi kyau sosai k’warjininsa sosai ya bayyana cikin hoton. Wani irin k’atutun bak’in ciki ya tokari Hisham. Wann duka rayuwarsa ne amma ta sace komai daga gare shi ta baiwa D’anta shi kad’ai. Ya tsane su gaba d’aya. Kuma babu Wanda zai ragar masa cikinsu. Yana nan tsaye wata maid din ta k’araso ta k’araso ta cika centre table da kayan motsa baki. Ta kuma tanbayesa ko yana son tea ko coffe. Ya girgiza mata kai had’ida fad’in kar ta damu abinda ta kawo ya wadatar. Tai excusing kanta ta fice. Har lokacin Hisham na nan tsaye gaban hoton Haidar ya had’e hannayensa ta baya yana kallon hoton. Sallaman Mommy yasa shi kaikaitowa yana dubanta. Kaman ko yaushe Hajiya Kwaise Maitama ta sauk’o zuwa parlorn cikin shigarta ta alfarma. A da saidai ka hango izza da isa a tattare da ita amma a halin yanzu annuri fari’a da walwala kake hangowa a kyakkyawar fuskarta. A sanda take takowar nan Hisham kaw cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kece sila.. Kece silar komai.. Baki cancanci yafiyana ba Kwaise Maitama.’ Ta k’araso da murmushinta tana nuna ma Hisham wajen zama “Bismillah zauna mana.” Shid’inma murmushi ne saman fuskarsa ga kwantar da kai da yake irinta girmamawa Wanda zaka ranste Har cikin ransa ne. Saida ya duk’a Har k’asa ya gaida Mommy cikeda risinawa da girmamawa Wanda hakan sosai ya kuma birge Mommy ta kuma jin ta aminta sosai da tarayyarsa da D’anta. Ta amsa da sakin fuska tana fad’in Ya tashi ya hau kujera ya zauna. Hisham yai yanda Mommy tace cikeda girmamawa ba. Mommy ta dubesa bayan ta tambayarsa mutanen gida da aiki. Hisham yace “Kowa lafiya Mommy. Aiki kuma mun gode Allah.” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa. Mommy ta murmusa tana fad’in Masha Allah. Dak’ik’a ya dan gifta kafin tace “Arc. Hisham ko.?” Hisham ya murmusa “Hisham d’in dai Mommy.” Itama murmushin tayi “A’a gwara dai na baka title dinka. I heard that you are one of our best architects a nan M&M Builders.” Cikin raha da k’ok’arin sako barkwanci take maganar wanda a baya ba d’abi’arta bace. Hisham Ya dan murmusa “K’ok’ari kawai muke Hajiya.” Itama ta murmusa “Toh ma sha Allah. Allah ya taimaka.” Hisham Ya amsa da Ameen. Mommy ta dan gyara zama kafin tace “Hisham wata ‘yar alfarma nake buk’ata daga wajenka.” Ya d’ago Ya d’an dubeta sai Ya girgiza Kai “Alfarma kuma Mommy.. Wace iri kenan.?” Wani folder ta dauko gefenta ta mik’a masa tana fad’in ya duba ya gani. Hisham ya saka hannu biyu ya amsa. Mommy taci gaba a sanda yake warware folder d’in “Plan ne na gida. Ina so ka duba kai nazari akai.” Hisham Ya ida warware folder d’in yana dage takardun yana gani. Mommy taci gaba “I want to surprise your friend.. My son.” Hisham ya dago ya dubeta “You mean Haidar.?” Mommy ta jinjina masa kai “He’s my only son.. Our only son nida mahaifinsa.” Tai maganar da murmushi saman fuskarta Wanda yake nuni da tsananin k’aunar da take ma D’an nata. A cikin zuciyarsa Hisham yace ‘Sabida kinyi sanadin raba d’ayan d’ansa da ahalinsa.’ Amma a fili sai Ya murmusa “Okay.. And mai za’ayi da wann.?” “Nasan kanada masaniyar cewa tsawon lokaci alak’an Haidar da halinsa akwai babban tangarda ciki since you are his best friend and possibly his only friend nasan kanada masaniya kan wann.” Hisham ya jinjina kai a hankali “Haka ne Mommy.. And believe me burina shine Haidar ya shirya da ahalinsa.” "Mommy ta kuma jinjina kai “Hakan yasa na gayyato ka domin ka min wann aikin. After all, layinka ne.”" Hisham Ya kuma jinjina kai kafin Mommy taci gaba “Wann plan na gidan da na dank’a maka shine gidan da muka fara zama cikinsa nida Mahaifin Haidar wato Engr Aliyu Maitama a lokacin da muka dawo Abuja.. Ina so Haidar da matarsa Ummul su tare a wann gidan da zaran an sallamesa daga asibiti. Na dank’a maka ragamar komai duk wasu gyare gyare da sauye sauye Wanda yayi daidai da ra’ayin Haidar ayisu kafin bikin tariyarsu da zaran an sallamesa daga asibiti. Kai abokinsa ne nasan kasan ra’ayinsa tsare tsarensa. Inaso ayi komai to his taste ta yanda zaiji dadin bazatan. Duk wani abinda ake buk’ata don’t hesitate to let me know. Kar ka mance na sanar da kai wann din Bazata ne. So ko Boss dinka a Office ina nufin Mahaifin Haidar banso ya sani.. Is our little secret for your dearest friend.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. K’ak’aro murmushi Hisham yai dukda mutuwar zaune da yai yana sauraron Hajiya Kwaise kafin ya shiga jinjina kai “Bakida matsala Mommy. Haidar tamkar D’anuwa na d’aukesa ba aboki kawai ba. Zanyi komai to the best of my ability in sha Allah.” Mommy ta murmusa tana dubansa. Yanda yace D’anuwa Ya d’auki Haidar ba aboki kawai ba sosai Ya hakan Ya haifar mata da sanyin jiki. Bata san dalili ba amma sai taji tunanin Fannah da abinda ke cikinta yazo mata. Watak’ila da ace Fannah ta haife abinda ke cikinta idan Ya fito namiji da yanzu Sun taso tare haka da D’anuwansa Haidar tamkar dai abokan. Sai ta tsinci kanta da addu’an Allah Ya bayyana mata Fannah Ya kuma sa ta haifi abinda ke cikinta ko Haidar d’inta zai samu D’anuwa ko ‘yar uwa. Daga bisani mik’ewa tai tana ce ma Hisham Ya saki jikinsa kaman a gida yake Yaci abubuwan da aka kawo masa. A haka Mommy ta bar parlorn duk jikinta a mace sakamakon tuno Fannah da abindake cikinta da tayi. Yayinda Hisham yai mutuwar zaune yana jin shirin Kwaise Maitama. Wai shi Hisham shine zai gyara ma Haidar gidan da zai zaman aure da Ummul d’insa sann gidan ma ba ko wane gida ba. Gidan Mahaifinsa da ya fara zama ciki lokacin da yazo garin. Idan akwai Wanda yafi kowa cancanta da zaman aure tareda Ummul a wann gidan ba kowa bane face shi. Shine babban d’an mahaifinsa sann shine ya fara son Ummulkhair tun kafin Kwaise tai mata k’adararren auren nan da D’anta. She’s so selfish. Ta ya zai fara wann aikin ma.. Just how.? Muryar Anisa yaji a kansa wacce mamaki ya cika sai waige waige take “What are you doing here.? Who invited you.?” Duban Anisa yai sai Ya murmusa “Mu gaisa mana kafin duka wad’ann..” Anisa taci gaba da ‘yan waige waige kafin tai k’asa da murya tace “Is this also part of your games.?” CCTV camera dake mak’ale a parlorn Ya kalla sai Ya murmusa Yace “Neesa long time no see. Ko dan dik rashin lafiyar abokina ne ya b’oyeki kema..?” Mamaki Ya cika Anisa tana duban Hisham dake kurb’an drink din dake hannunsa. Lokaci guda Ya mik’e yai k’asa da murya “Zan iya samun rakiyarki..? To my ride.?” Anisa ta murmusa ta biye wasan Hisham “Sure.. Of course.” Hisham ya nuna mata hanya “After you.” Sa kai sukai suka fice a tare. Suna isa jikin motar Hisham yace “Get in.” Ta dubesa da mamaki “Ban gane ba.. Are you a kidnapper now.?” “Just get in Neesa.. We need to talk.. Somewhere else.” Ba musu ta bud’e motar ta shige kafin Hisham ya shige mazaunin driver ya tada motar suka fice daga gidan. Tinda suka fice daga Hisham ke zabga gudu saman kwalta zuciyarsa na tafarfasa musamman idan Ya tuna aikin da Kwaise Maitama ta basa wai shi Hisham sai zai renovating gidan da Haidar da Ummul d’insa wai zasu zauna. Anisa ganin gudu ba na k’arau ba Hisham na yunk’urin hallak’asu cikin motar ta soma k’ok’arin dakatar dashi “Ka dakata Hisham.! Wai meke faruwa ne.? Why are you so furious.? Where are you taking me to.?!” A harzuk’e ya buga kan steering wheel ya dubeta yace “I don’t know Neesa.! I just don’t know maybe to hell.!” Yanda Yai maganar yana huci gashi bai daina gudu ba yasa Anisa kuma razana ga wata mota gaba garesu Wanda k’iris Ya rage Hisham bai daki bayan motar ba “Hishaamm.!” Ta k’arashe tana daka masa tsawa daidai sanda Hisham ke taka birki a tsakiyar titi. Rufin asirin Allah Babu wata mota bayansu. Ya d’ago yana dubanta cikin huci. Itama d’in hucin take tana dubansa “Just what do you think you are doing.? What’s gotten into you.? Are you trying to kill us or something.?! Meye haka.? Kaga saidai tafi hell d’inka kai kad’ai but I won’t allow you to take me with you..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin fincikar marfin motar. Hisham Ya furzar da huci kad’an yace “All right.. I’m sorry..” Ta juyo tana dubansa fuska a tamke. Parking yai gefen hanya kafin ya shafi fuskarsa yace “I can’t stand your Aunt Neesa. I just can’t.!” “Mai tai..? Mai ma ya kaika gidan in the first place. I thought your friend is still in the hospital. So why were you there anyway.?” Ya dubeta sosai “Kirana tayi ta bani wani aiki.. Aikin da zaifi mun ciwo sama da ko wani aiki a rayuwata.!” Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Aiki.? Wane irin aiki kuma..? For all I know my Aunt doesn’t take part a ayyukan company.” Folder din dake hannunsa ya mik’a mata. Anisa ta girgiza kai “Meye wann.?” “Karba ki gani.” Ta karba ta shiga bud’ewa “Dukda ba Layina bane amma Wann ai kaman plan ne na gida.? Mai hakan yake nufi.?” “Hakan yana nufin ni ne mutumin da Kwaise Maitama ta d’aura ma alhakin gyaran gidan da Haidar zai angwance da Ummul d’ita ciki.!” Anisa ta zaro ido tana dubansa “No you can’t be serious.? You know you are such a joker.” Hisham ya dubeta sosai “I’m being serious here Neesa. Hajiya Kwaise Maitama ta d’aura alhakin gyaran gidan hannun aminin D’anta.! Ya gyara zamansa kadan yana jinjina kai “Hakan na nufin zanyi mastering ko wani lungu da sak’o na cikin gidan a saukake. Idan naso na d’auke Ummul d’ita na gudu da ita a randa aka kai masa ita wann gidan.. Sann kuma na cinna ma gidan wuta your beloved Haidar na ciki bayan na gudu da abar k’aunata. Kwaise Maitama zata hadiye ranta da zaran ta rasa tilon D’anta. Haka ne.?!” Ya k’arashe yana fashewa da dariya. Anisa ta girgiza kai “You are insane Hisham. Kar ka mance a Yarjejeniyarmu Babu cutar da both parties ina nufin Haidar da Ummul. Rabasu shine agenda d’in haka ne.?” Ya murmusa kad’an “Just kidding sweetheart. Ki kwantar da hankalinki Haidar dinki is safe matuk’ar Ummul dita tana lafiya. Abun shine Hajiya Kwaise ta kawo mun hanya mafi sauki ne da zan d’auke kayata na gudu. Idan Har na kasance Wanda zai renovating wann gidan ke kuma ya kamata ki zamto event planner. Baki tunanin abin zai k’ayatar.?” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda. Shiru tai kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai “Yes. K’warai ka kawo shawari. Idan Har zaka kasance mai gyara gidan da zasu zauna ni yafi cancanta na zamto wacce zata shirya shagulgulan bikin tariyar. Kaga a sauk’ak’e zamu rufta komai mu lalata komai.. Duk shirin Mommy na ganin Ummul da Haidar sun tabbata ma’aurata zamu lalata shi. Ko wannenmu ya kasance da abun k’aunarsa haka ne.?” Hisham Ya kuma murmusawa “Perfect.! Ni yanzu aiki na ya shigo hannu saura kiyi naki k’ok’arin ta dank’a Miki ragamar jagorancin shagalin bikin tariyar.” Anisa ta murmusa kafin tace “Bikin da Aunty Kwaise Maitama bazata tab’a mancewa dashi ba. Bukin da zamu gayyat manyan bak’i ciki harda Dareen.. Tsohuwar sirkar ta da basu tab’a had’uwa ba.!” Suka kece da dariya suna ci gaba da ayanna manufofinsu. ** Hospital.. Haidar ya dubeta dan ya kula yanayinta a kwanakin ya d’an sauya gashi in less than 2weeks za’a musu sallama. Ta k’araso ta bashi magungunansa fuskarta Babu wani walwala. Zata mik’e Ya kamo hannunta. Ta juyo ta dubesa still babu wani walwala tattareda ita. Ganin Ya tsareta da ido ya sata sauk’ar da idonta kad’an. “Khairy…!” Ya ambato sunanta a hankali. Still bata d’ago ta kallesa ba saima hawaye da taji na yunk’urin zuwa mata. Zuciyarta cike yake da tarin abubuwa. Ga maganganun Anisa Wanda ta sanar da ita kwanakin can ga kewar ahalinta da ta baro gida da ya addabeta. Tana nan tana lissafin watannin da Umma ta d’ibar mata ta waiwayi gida wato watanni uku bayan aurenta. Dukda cewa bai shige sauran sati biyu watannin su cika ba ji take kaman bazasu cika ba. Majinyacin Mahaifinta da bata san wani hali yake ciki ba. ‘Yanuwanta musamman ‘yaruwarta Ummukhulsum da ko bacci bai rabasu a baya sann da ita kanta Umman koda itace ta bata wann sharad’in. Tayi kewarsu gaba d’aya sann ta k’agu ta gansu taji daga garesu. “Look up Khairy.. Kalleni..” Yai maganar softly. Sai ta d’ago ta dubeshi. Hawaye Ya hango kwance cikin idonta. “Are you crying.?” Ya tambaya yana k’ok’arin kai hannunsa had’ida d’ago hab’arta kad’an. Baisan Ya akai ba saiji yai hannun nasa a kasan idonta . Gently ya shiga share mata hawayen dake mak’ale cikin idonta Wanda tuni sun ziraro k’asa. Ai kaw kaman wacce ke jiran dalili sai ta soma kuka maras sauti. Haidar yai mata k’uri yana kallonta. A hankali Ya furta “Come here.” Ya janyota zuwa b’angaren jikinsa. Kaman wacce ke jira nan ta soma kuka sosai kanta cikin k’irjinsa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *44* *©️Sameena Aleeyou… * Sun d’auki lokaci sosai a haka Har saida kukan nata Ya tsagaita yayinda Haidar yaci gaba da Shafa kanta zuwa bayanta a hankali cikin k’ok’arinsa na calming dinta. D’akin yai shiru tana nan kamo cikin k’irjinsa sai zukatansu dake bugawa kusan a tare. Bata San dalili amma sosai ta samu natsuwa da kwanciyar hankali tattareda shi. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Nayi kewarsu..! Nayi kewarsu sosai..?” Ya kuma shigar da ita k’irjinsa. Ba ra’ayinsa bane bin diddigin matsalolin mutane. Baisan dalili ba amma sai yaji yana son jin nata matsalan “Su waye kikayi kewarsu.?” A hankali take furta “Abba.. Umma.. Khulsum.. Da sauran ‘yanuwana..!” Ta k’arashe wani kukan na zuwa mata. Haidar yaci gaba da Shafa bayanta yana kokarin kwantar mata da hankali. D’akin yai shiru har kaman bazai ce komai ba sai kuma yace “Then… give them a call..” Shiru bata ce komai ba.. Shima saida yai maganar ya tuna duk zamansu shidai bai tab’a ganinta da waya ba sann bai tab’a ganin ta kira kowa ba. Ya d’an kamo arms dinta Ya d’ago ta kad’an “Where is your cell phone… Do you have one..?” Shiru kaman bazata ce komai ba sai kuma ta girgiza kai a hankali. "Mamaki Ya cika Haidar. ‘Ta Ya za’a ce mutum baida wayar salula. Is this even possible.?’ Ya dan girgiza kai kad’an, Kasancewar shi kansa mutum ne da bai cika son magana da bin diddigin al’amari ba yasa shi jinjina Kai a hankali. Sai Ya mik’a hannun Ya d’auki nasa wayar. Sai gani Ummul tai yana mik’a mata nasa wayar." “Here..! You…. can use mine.. If that’s.. ok with you..” Ya k’arashe yana dubanta sosai. Ta dubesa sai ta dubi wayar. Jikinta ya kuma yin sanyi sakamakon tunowa da kalaman Umma ‘Kar ki neme mu koda a waya ne har sai kin cika watanni uku a gidan aurenki . Sai ta girgiza kai a hankali. Cikin rawar murya tace “Ban rik’e lambobinsu akai na ba..” "Wann karon ma da mamaki yake dubanta sosai. Dukda shima bai tab’a damuwa ya kiyaye lambobin ahalinsa ba tin yaranta yasan hakan nada alak’a da rashin jituwa da k’alubale da ya fuskanta da iyayensa tin yarinta. Amma ita tanada alak’a mai kyau da iyayenta ga dukkan alamu, musamman mahaifinta dan bai mance ta sanar dashi sabida shi ta amince da aurensa. Amma sai bai ce komai ba ya jinjina Kai a hankali." Kallonta ya kuma yi dan shidai baisan wani aba lallashi ba a rayuwarsa sann bai iya ta ba. Sai ya "kamo hannunta cikin nasa ya kuma kwantar da ita gefen kafad’arsa, yatsun hannunta cikin nasa. Calmly yake fad’in “You know, I’m not used to seeing you like this.. Murmushi yafi Miki kyau.” Ya k’arashe kaman ba daga bakinsa maganar ya fito ba." Sai taji Murmushin ya kufce mata out of nowhere. tai saurin kare fuskarta da tafukan hannayenta. Hannu yasa ya d’ago fuskanta kad’an suna duban juna. Ya tsareta sosai da ido kafin yace “Do you feel better now..?” Ya tambaya fuskarta tallafe cikin tafukan hannayensa. D’an lumshe idanunta tai kafin ta jinjina masa kai a hankali. Shima ya jinjina nasa kan. Su duka biyun murmushi ne saman fuskokinsu. ** "Anisa ta shigo a guje tana nuna ma Mommy Pages na different professional event planners. Ta murmusa tace “Yauwa Mommy ya kikaga wann. The event should be grand and super elegant. Ya kamata ayi komai to perfection. I’ll be the coordinator.. And trust me, it will definitely be a sight to behold.!” Ta k’arashe tana juyi gaban Mommy had’ida juya ido. Cikin zuciyarta kuwa cewa take ‘Dan na miki alkawari Mommy, akwai abubuwa da dama da zasu faru a wann rana Wanda idaniya bazasu tab’a mancewa ba.’" Mommy ta tab’e baki tana dubanta sama da k’asa “Toh ce Miki akayi shiririta zaayi wajen ne.? Bani son shashashan cin nan naki.” Anisa ta turo baki kad’an “Haba Mommy.. I’m just being concerned here… Kuma kinsan abu idan aka ce biki toh a nan wayota da basirata Ya k’are.. Mommy kinsan bazaki iya dealing da wani headache na event a yanzu ba. Kuma Haidar cousin dina ne Ummul kuma I consider her friend. Ni ce yafi cancanta na shirya shagalinsu Mommy. Just assign me to do the work please.. Please Mommy. And kuma kinsan abu na zamani sai d’an zamani.. Gwara a shirya komai daidai da zamani da yayi.” Ta k’arashe tana juya ido da rangwad’a Wanda d’abi’ar ta ce. Mommy ta kuma girgiza kai yayinda Anisa taci gaba da mata magiya tana fad’in ta dank’a mata ragamar shirya shagalin. "Murmushi Mommy tayi had’ida girgiza kai kad’an “Fine, naji Anisa.. Amma kinsan bani so a samu wani mishkila.”" "Anisa harda ‘yar tsallenta tana fad’in baza’a samu mishkila ba, kama daga shirya wajen taro, live entertainments har zuwa guests list." Mommy ta murmusa tana duban Anisa tana jin dadin yanda kowa ke marmarin biki. Batai k’asa a gwiwa ba taci gaba da kiran k’awayenta da matan abokan kasuwancin Daddy tana sanar dasu. Sann hakan wani dama ne da zai goge scandal din da yai erupting kwanakin baya. Labarin da wani gidan jarida ya wallafa cewa Engr Aliyu Maitama yayi ma d’ansa auren sirri da ba’asan ko wacece Amaryar ba. A wann rana zata gabatar da Ummulkhair matsayin matar D’ansu Haidar ga duk abokan alk’allarsu dama sauran jama’a gaba d’aya. Anisa kaman ta zuba ruwa a k’asa ta sha dan murna. Haka ta kirawo Hisham tana sanar dashi plan dinsu Ya tafi yanda suka tsara. Mommy dai ta dank’a mata ragamar jagorancin shagalin bikin. Sann Gidan Haidar da Hisham ke renovating nan ne venue kaman yanda Mommy ta buk’ata . Hisham yai muguwar murmushi yace komai Ya tafi daidai.. A ranar wann shagalin zasu striking plan d’in su. Ranan da Kwaise Maitama take tunanin farin cikin ahalinsu zai soma wann ranar komai zai wargaje. A haka ko wani b’angare suka ci gaba da gudanar da shirye shirye yahinda b’angaren Haidar da Ummul sabo da shak’uwa ke dad’a shiga tsakaninsu. A b’angaren su Tani ma suna nan suna nasu tanadin dan Hajiya Asshe ta sanar dasu ‘yaruwarta Hajiya Kwaise na shirya gagarumin bikin tariyar Ummul da Haidar Wanda suma a nasu shirin wann ranar zasu k’addamar da shirinsu. Zasu fayyace ma Ummul komai gameda mahaifiyarta da wulak’antaccen auren da tai mata. Zasu jefa rayuwar Suwaiba cikin garari a wann ranar. Zasu d’auki duk wani fansarsu dake kan Suwaiba. A b’angaren Ummul dad’i da k’arin sakin jikinta da Haidar yanada alak’a da tsananin farin ciki da take ciki. Watanni uku Sun kusa cika zataga ahalin ta kaman yanda ta d’aukar ma mahaifiyarta alk’awari cewa bazata waiwayesu ba har sai ta cika watanni uku da aure kaman yanda mahaifiyar tata ta buk’ata daga gareta. Shi kuwa Haidar dukda shiryawa da yai da mahaifiyarsa saidai har kawo wann lokacin bai saka mahaifinsa a idonsa ba. Daddy bai kuma dawowa asibiti ya dubasa ba. Abun bai basa mamaki ba tinda yasan shidai tsakaninsa da mahaifinsa Babu komai face tsangwama tsana da kuma kyara. Amma saidai a wann lokacin abun bai masa ciwo sosai kaman a lokutan baya sanin cewa da yai ko Babu komai a halin yanzu yana tareda soyayyar mahaifiyarsa da k’aunarta. Uwa uba idan Ya kalli Ummul sai yaji duk wani k’unci dake zuciyarsa ke ciki ya yaye.. Bai sani ba ko tsananin sabon da sukayi a yanzu ne ke haifar masa da hakan Wanda a baya idan aka ce zai zauna da ita under same roof zai musa. Sai gashi a halin yanzu Har bacci suke cikin mayafi guda. Ya lumshe idanunsa a hankali murmushi na kufce masa. A reception wani staff na asibitin Ya bata wani shud’in folder mai d’aukeda logo na Maitama Builders daga fuskarsa. cewa wani abokin aikin Haidar d’in ne ya bari a bashi. Ita dai ta amsa folder d’in ta nufi d’aki dashi. Hisham Wanda shine ya kawo folder d’in yana lab’e yana kallon Ummul Har ta shige da folder d’in. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Saura kad’an.. Saura kad’an na d’aukeki Ummul.. Saura kad’an mu kasance tare.. Saura kad’an ki kasance da masoyinki na gaskiya.’ Yana ida fad’in haka yaja Pcap d’in dake kansa ya kuma rufe face dinsa dashi kafin ya fice daga asibitin. Haidar yai zaune yana duban folder d’in Wanda ke k’unshe da wasu bayanai da wani waje na rattaba hannu gameda babban aikin da suke gab da farawa da zaran ya fito daga asibiti. Long awaited project dinsu. Project d’in da yai alwashin kai mahaifinsa k’asa warwas dashi. Project d’in da yai niyyan ruguza Maitama Builders dashi. Project d’in da Ya jima yana tanadin duk wani fansa nasa kan iyayensa musamman mahaifinsa Wanda Har kawo wann lokacin basu fuskanci juna ba. Shiru yai yana juya folder d’in cikin hannunsa a hankali yake furta “You deserve this Daddy.. You deserve this.. I can’t backdown now.. Ka cancanci haka Daddy.!” Ummul ta dubesa da d’an mamaki ganin irin hucin da yake. Ga wani yanayi da Ya shiga tinda ta kawo masa wann folder d’in Wanda ta jima bata gansa cikin irin yanayin ba. Tai k’ok’arin zama gefensa a d’arare. Ta dubesa kaman mai tsoron magana “Lafiya kake..? Kaman naji magana kake.? Ko.. Akwai abinda zan iya taimakawa dashi.?” Tai maganar a sanyaye. "Kallonta yayi, wann karon irin kallon da yake mata a baya kafin su saba da juna . Ya kafeta sosai da ido sosai Wanda Ya soma bama Ummul tsoro Har saida taji dama bata tambayesa ba." Jiki a sanyaye tace “Kai.. Hak’uri.. Ba nufi bane nai maka shishigi a almarinka..” Tana k’ok’arin mik’ewa taji ya kamo hannunta. Ta lumshe idanunta cikin k’ok’arin saita kanta. Bugun zuciyarta na sassauta a hankali. Ya dawo da ita Ya zaunar kafin ya kuma d’ago folder d’in yana gani. Idonsa na kan folder d’in yake furta “He sees me as a failure.” Yai murmushi da za’a iya kira da murmushin takaici “That I create a circus out of his business life.” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “I’ve been planning.. To take him down.. To take Aliyu Maitama down.. To ruin him.. To bankrupt his business.. The business he valued all his life more than his own son..” Fuskarsa tai jazir haka idanuwansa sanda yake maganar. Ya d’ago yana duban Ummul dake dubansa cikin wane irin yanayi mai kama da tausayi. "Haidar yai murmushi yana juya folder d’in, irin murmushin nan da ake kira da murmushin takaici “He values this more than everyone around him. Tell me, shin nayi laifi idan nace zan kaishi k’asa.?”" Sai Ummul ta shiga jinjina kai tana dubansa “K’warai kuwa.. Ka tapka kuskure. Kuskure mai muni. Dik yanda kaje kazo shine mahaifinka… Wanda kasancewarsa hakan Ya haramta maka fad’a dashi..” "Katseta yai da fad’in “You don’t know anything.!” Ya sassauta murya “If only you knew the kind of hell he made me went through tin daga yarinta na, har kawo girma na.. Har zuwa aiki da nayi a k’ark’ashin kampaninsa. Ki yarda dani wann aikin da zanyi shine zai zamo aikina na k’arshe k’ark’ashin kampanin sa. Sann shine fansar duk wani wulak’anci da cin zarafi da na fuskanta a wann kampanin.!” Ya k’arashe yana kuma tamke folder d’in cikin hannunsa." “Kar ka bari fushi yai maka jagora..” Bata Kai aya ba ya dakatar da ita. “O c’mon Khairy.!Stop minimising the issue here. Don’t act like I’m making a big deal out of it.!” Yaci Ya k’arashe maganar a zafafe. "Dukda zuciyarta dake bugu hakan bai hanata k’ok’arin tattaro courage dinta ba, ta d’aura hannunta saman nasa, tana dubansa da fuskarta mai cikeda rauni “Duk abinda Ya faru dakai a baya. Na d’auka mun riga mun wuce wann. Na d’auka ka goge duk wani k’unci na rayuwar da ka fuskanta a baya da yafiya.. Su d’in iyayenka ne ba ma’asumai ba. Girman hakkinsu akanka Ya shige ka nemi fansa akansu..”" Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa “You always talk about hakkinsu.. Have you ever bothered talking about hakkin ‘ya’ya. Shin su basuda hakki ne kan mutanen da suka zamto sanadin tsintar kansu a wann duniyar..?” Shiru tai tana dubansa. “Answer me. Basuda hakki.?” “Eh.. Su.. su..” "Katseta yai “Why are you stuttering now..? Kin kasa furta kalma d’aya sabida kinsan gaskiya nake fad’a. Sunada hakki and they will be questioned kan wann hakki na yaransu.” Yaci gaba da jinjina kai “Shin kinsan most of children da suka tsinci kansu a yanayi na Allah wadai are victims of circumstance. Wasu sun fuskanci abuse and negligence from their own parents. And don’t you think this can cause behavioural issue in the children later in life.?” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Idan kayi shuka zaka bashi ruwa zaka kula dashi Har wann shukan ya girma ka girbi amfaninsa. Kaman haka idan kayi shuka baka kula dashi ba zaka samu akasin amfani mai kyau. Kaman misalin haka ne tsakanin ‘ya’ya da iyayensu.” Ya dan rage girman idanunsa yana dubanta “Wait a minute, do you really think you can change the dynamic of this family.?”" "Ummul ta jinjina kai a hankali “Bank’i maka duk abinda kace ba. Shiyasa na sanar dakai tin daga farko. Iyayenmu ma suna kuskure. Sann kuma idan akwai wad’anda zamu fi ma uzuri sune Iyaye.” Ta d’an gyara zamanta “Jinin Daddy shike yawo through your veins tun a fari.. Sann daga baya da ka samu had’ari ka rasa jininka jininsa ke yawo cikin jikinka a karo na biyu..!” Ya kaikaito yana dubanta da mamaki. Ummul taci gaba da jinjina Kai tana sakin murmushi. Lokaci guda taci gaba “Zan sanar dakai wani sirri da baka sani ba. Sabida tsananin k’aunarka da yake Ya zab’i a ajiye hakan matsayin sirri a wajenka harma da Mommy. Bai zab’i ka sani ba, sabida yayi ne don soyayyar da yake maka.”" “What do you mean.? What secret are you talking about.?” Ya tambaya cikin rashin fahimta. "Ummul taci gaba “A lokacin da mukayi accident Daddy ne ya bada jininsa aka k’ara maka. Cikin yardar Ubangiji, You are alive today sabida jinin Daddy na yawo through your veins.” Ta k’arashe murmushi had’eda k’walla tab idanunta." "Haidar ya shiga girgiza kai “No. no, no way… No, this can’t be… You must have got this wrong.. Tsakanina da mahaifina babu komai face k’iyayya, kyara da hantara.. I’m the last person da Daddy zai baima jininsa. Na sani bazai tab’a ba koda mutuwa zanyi.. Ta Ya mutumin da ko zuwa Ya dubani baiba zai bani jini. I almost lost my life amma.. Bai damu yazo Ya dubani ba. Ta Ya zai bani jininsa.?”" “Amma yayi hakan. Idan Har hakan na cikin wani hakkoki naka akansa toh ka tabbata Ya cika wann hakkin. Kana iya karb’an hospital report d’in and see for yourself.” Cewar Ummul. Haidar ya girgiza Kai “Well I don’t need his blood.! Knowing my Dad.. Akwai manufar da yasa yai hakan.! Watak’ila to throw it own my face cewa ya bani jini.. I’m alive sabida jininsa dake yawo through my veins.!” Ya k’arashe yana huci. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali “Bazai tab’a zama haka ba sabida Daddy bai zab’i wani daga cikin ahalinsa yasan hakan ba. Musamman ma kai.” Batai k’asa a gwiwa ba ta kuma daidaita zamanta “Dalili shine Ina zaune lambun can na shak’atawa dake bayan offices din likitocin kwanakin baya. Nan na tsinci zancen likitan da abokin aikinsa yana sanar dashi kwanaki da suka rasa jini kala kaza a asibitin mahaifin patient d’in shi Ya bada jininsa kuma ya zab’i hakan Ya zama sirri tsakanin ahalinsa. Sunan hamshak’in D’an Kasuwa Engr Aliyu Maitama da suka ambata yasa na fahimci kai suke nufi.” Ta d’an numfasa “Ba nufi bane naji zancensu. Sann banso ka sani ba tinda Daddy ya zab’i ya zama sirri. Amma idan hakan zai kawo maslaha cikin ahalin banida zab’i da Ya shige na sanar dakai.!” "Jikin Haidar Ya d’anyi sanyi Dikda k’ok’arin b’oye hakan da yaketayi, yayinda Ummul ta kuma daura tafukan hannunta bisa nasa “Daddy yana sonka.. Yana matuk’ar k’aunarka.. Dan Allah ka janye duk wata maganar fad’a da d’aukan fansa akansa.. Shid’in mahaifinka ne… Idan baka zamto jigo na hab’aka masa kasuwancinsa ba bazaka tarwatsa ba. Kar ka mance mutane da yawa Sun dogara da aikin da suke a wann Kampanin dasu da iyalansu. Kai tunani idan ka tarwatsa Kampanin mutane nawa zai affecting.? Mutane nawa zasu rasa ayyukansu sakamakon durk’usar da Kampanin da kayi. Mutane nawa zasu koma basuda aiki basuda abinda zasu rufa asirin kansu da iyalansu dashi. Tin daga shugaban Kampanin Wanda Ya kasance mahaifinka Wanda yake da girman hakki akanka matsayinsa na mahaifinka koda bai kasance ahugabanka wajen aiki ba. Sauran manyan ma’aikata masu hannun jari Har zuwa kan k’anan ma’aikata… Ina zaka kai girman hakkokinsu.?”" Ya d’ago Ya dubeta cikin yanayin da zata iya cewa bata tab’a ganinsa ciki ba. A hankali taci gaba “Nasan kai mutum ne mai saka sharri da alkhairi. Wanda duk yanda Ya zauna Ya tashi alkhairansa bazasu gushe ba. Jajirtacce Wanda jajircewarsa takanyi tasiri cikin duk abinda yasa gabansa. Mai taimakon Al’umma ba mai durk’usar da ita ba.” “What if duk abinda kika fad’a akaina ba haka bane.! What if na aikata kudirina da abinda na jima ina shiryawa.?! Kina tunanin zaki iya dakatar dani.! Just Who do you think you are.?!” Ya k’arashe yana mai tsareta da ido. Cikin zuciyarta tace ‘I call you sweet monster for a reason. You are not like other monsters out there.’ A fili kuwa cewa tayi “Kanada zuciya mai kyau. Inada yak’inin kyakkyawar zuciyarka bazata bari ka aikata akasin abinda na fad’a ba.” Haidar Ya kuma d’agowa ya dubeta. Sai Ya dan lumshe idonsa kadan “Khairy please get out now. I need to be alone.!” “Amma…” “I said leave.!” Ya katseta a zafafe "A hankali ta mik’e, ta d’an dubesa kafin ta soma tafiya cikin sanyin jiki." Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Just.. go home. I don’t need you here.!” Ya k’arashe ba tareda ya dubeta ba. Ta juyo ta dubesa a sanyaye sai ta jinjina kai a hankali. Lokaci guda tasa kai ta fice cikin sanyin jiki. "Bayanta yabi da kallo Har ta fice kafin ya maida dubansa ga folder d’in kalamanta yaketa k’ok’arin yakishewa ganin basuyi tasiri cikin zuciyarsa ba. Ya d’ago hannunsa yana juywa yana bin veins d’insa da sukai rud’u rud’u sukai kore shar yana tuna kalamanta sanda take sanar dashi Daddy ya basa jini. Jinin Daddy ke yawo through his veins. A hankali Ya lumshe idanunsa hoton abubuwan da mahaifinsa Ya jima yana masa na yawo a kwanyarsa, zuciyarsa da kuma lumsassun idanunsa." Koda dare yai Haidar kasa bacci yai sabida rashin Ummul. Baisan yayi sabo da ita Har haka ba. Room nurse din dake kula dashi kuwa cewa yai ya fice ya bar masa d’aki he can take care of himself. Gaba d’aya gani yake room nurse baisan komai ba bai iya komai kaman ita ba. Abubuwa ne da dama fal zuciyarsa. Koda yazo bacci haka yaita juyi yana tunaninta. Yakai dubansa ga kujerar da suka kwana tare ranar farko da ya farka. Ya lumshe idanunsa. A fili yake furta “I’m not the type that share his problems with others.. I don’t know how I do it with you.” Ya d’anyi shiru still yana duban wajen. A hankali ya furta “It feels so empty to go to bed without you.!” Ya rasa haushinta ne ko haushin kansa ko kewarta yake. ** A b’angaren Ummul kuwa Mommy taso ta fahimci wani abu musamman da taga Ummul d’in bata koma asibiti wajen Haidar ba . "Washe gari da safe koda Ummul ta shigo gaida Mommy sai Mommy ta dakatar da ita bayan Sun gaisa. Ta nuna ma Ummul d’in gefenta saman kujera “K’araso nan ki zauna daughter, magana nake so muyi.”" Ummul ta jinjina Kai had’ida amsawa kana tai yanda Mommy tace. Anisa dake k’ok’arin saukowa downstairs nan ta sinkayo zancensu. Ba shiri ta lab’e jikin staircase tana sauraronsu. Mommy taci gaba yayinda kan Ummul ke kife k’asa “Bana so na zamto irin iyayen nan masu kutsa Kai a al’amari gidan ‘ya’yansu. But when it comes to Haidar you and I are team. Haka ne.?” Ummul ta jinjina Kai a hankali. Mommy taci gaba “Kuma zamuci gaba da zama team wajen ceto rayuwarsa daga halak’a. Tinda ni mahaifiyarsa ce ke kuma matarsa. Mu duka d’in yanada matuk’ar mahimmanci a wajenmu. Haka ne.?” Nan ma jinjina Kai ta kumayi a hankali. Wann karon sai Mommy ta d’aura hannu saman nata “Ummulkhair.!” Ummul ta d’ago a raunane tana duban Mommy. "Mommy taci gaba “Nasan kina hak’uri da Haidar. Amma dan Allah ki k’ara. I have this strong feeling, with you by his side, Haidar zai mending ways d’insa. Kuma mun fara ganin hakan cikin ikon Allah..” Ta dan numfasa “Bazan tambayeki mai ya hadaku ba dan wann ba hurumi na bane. Sann dik hukuncin da kika zartar har kawo zuwa lokacin da zaki sauk’o bazan tak’ura miki ba. And always remember kina tareda yarda da kuma k’aunata a gidan nan. Tashi kije, Allah shi muku albarka gaba d’aya.”" Ummul ta jinjina kai a sanyaye kafin ta mik’e ta fice jiki ba laka. Anisa da ta gama nad’e komai murmusawa tai. Cikin zuciyarta take furta ‘You are so selfish Mommy. Kedai kawai d’anki. Toh bari dai mu gani idan hak’arki zai cimma ruwa.’ Da dare ta iske Ummul a sashenta. Anisa ta saki murmushi tana duban Ummul “Da alama jikin D’anuwana kuma mijinki da sauk’i sosai tinda gashi har kin rigashi dawowa.” Tai maganar tana murmushi sai kuma ta k’arada “Kodai kema koroki yai kamar dai yanda ya koroni.?” Ta k’arashe tana d’aga gira d’aya. Tinda Anisa ta soma magana k’irjin Ummul ke bugu. Anisa ta kuma murmusawa “Saidai kuma nasan mahaifiyarsa zatai iya k’ok’arinta ta kuma maida masa ke koda kuwa korarki yayi. Sabida ita d’in kanta kawai ta sani. She’s so selfish.” "Ummul ta dubi Anisa da idonta da tuni sun kad’a. Murmushin ne dai saman fuskar Anisa. Ta matso dab kusan Ummul ta dafa kafad’arta “Hajiya Kwaise Maitama bata tab’a son talaka ba sann bazata tab’a so ba, ita d’in mace ce da bata so wani talaka ya rabeta balle har ta aura ma D’anta. Ki yarda dani, she’s just toying with you Ummul. She’s using you. Ki yarda dani amfani dake kawai take dan ki toshe gibin da ta jima da bud’ewa cikin ahalinta da kanta.” Anisa tai maganar babu ko alamun d’ar tattareda ita." "Ta d’ago idanunta masu cikeda k’walla tana duban Anisa. Sai Anisa ta karkad’a yatsa a saman fuskar Ummul d’in “No, I’ll do the talk today because, ni keda abin cewa.” Taci gaba da murmushi tana duban Ummul “Mommy is a very dangerous woman who’s capable of doing anything to protect her interest. She brought you into her son’s life not because she loves you for him. But because, she wants you to do what she couldn’t do.” Taci gaba da jinjina kai alamun tabbatar da kalamanta “She wants you to do the job for her. To knock some sense into her son. She brought you into his life to cleanup her mess. Ki nutsu kiyi tunani Ummul a koda yaushe Mommy zancen Haidar take miki. Ya za’ai ki shawo mata kan Haidar. Shin ta tab’a tambayarki idan kina cutuwa a zaman da kike da D’anta.? Ko ta tab’a tambayarki menene naki damuwar.? Shin ta tab’a tambayarki ko kinada wata damuwa da ya danganci ahalinki.? Bata tab’a ba. Koda yaushe maganar d’aya ce ‘Haidar.’ Haka ne.?”" Izuwa lokacin idanun Ummul sun soma zubda ruwa. Anisa ta dafata kad’an “Kar ki bari Mommy tayi amfani dake dan cimma wata manufa nata. Ke macece mai k’ima. Kar ki bari wann matar ta watsar dake gaban D’anta.” Ta kuma dafa Ummul “Kiyi weighing maganganun da na fad’a miki sai ki tantance. Abu guda nakeda tabbaci akai shine ban tab’a miki k’arya ba.!” Tana ida fad’in haka tasa Kai zata fice. Har ta Kai k’ofa ta kuma juyowa “Save yourself while you still can. Run as fast as you can.. Ki ceci kanki daga wann auren da da baida tabbatacciyar makoma.” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice tana sakin murmushi. "A hankali Ummul ta silale k’asa kukan da taketa k’ok’arin dannewa na zuwa mata gadan gadan. Meyasa takejin zuciyarta ta gamsu da duk abubuwan da Anisa ta fad’a. Meyasa takeji kamar dai itace ta b’ace cikin k’ok’arin lalumo ma Haidar hanyarsa. Meyasa takeji kamar dai kowa amfani da damarsa yake akanta.? Ba auren soyayya tayi ba sann bata tsammaci wani abu mai kama da farin ciki cikin auren ba. Musamman idan ta tuna yanda akayi auren Wanda sadakin auren Ya kasance kudin jinyar mahaifinta. Koda ace Mommy ba har zuciya take nuna mata so ba, koda ace manufar Mommy shine ta shigo rayuwar Haidar dan tai guiding d’insa bata jin Mommy tanada wani laifin cikin hakan tinda tin farko ga yanda akai auren. Sann A d’an zaman da sukai da Haidar kai tsaye bazata ce ta kamu da soyayyarsa ba. Amma tana jin damuwarsa Har cikin ranta. Saidai dukda wad’ann tunani can k’asan zuciyarta tana jin sosai take so ta gano manufar Anisa dan ta tabbata idan Babu wani boyayyan al’amari Anisa bazata samu k’warin gwiwa irin haka ba. Ta d’au d’amarar gano bakin zaren komai cikin ikon Allah." A ‘yan kwanakin Mommy ke zuwa wajen Haidar ta yini dashi sann ko zancen bata kumayi ma Ummul ba. Iyaka damuwa Haidar yakai k’ololuwa. He misses her so much. Baisan ta yanda zai sanar da Mommy ba. Ya kula ma kaman Mommy punishing d’insa take da rashin Ummul d’in. Da Haidar yaga abin ba na k’are ba Har ana shirin sallamarsa batazo ba dole ya tambayi Mommy Ina take mai take gida.? "Mommy ta dubesa a dan tsare “Hutawa take gida, ka kyale nurse room dinka ya kula dakai. After all, aikinsa ne. An biyasa domin yayi hakan.”" “But Mommy he doesn’t do anything right.. And I don’t want him touching my things.” Ya k’arashe fuskarsa duk a dame. “Oh kasan da haka kai mata mugun hali.?” Mommy tace a dake. Sai Ya d’ago a d’an firgice “Mommy mugun hali kuma.? ita tace Miki na mata wani abin.?” Yanda yai tambayar ya tabbatar ma Mommy D’anta Ya fara nitso a tekun soyayya bai sani ba. Ta kifa kai ta murmusa kafin ta kuma d’agowa a tsare ta dubesa “Nasan ka mata wani abin ne amma wann ji da kan naka bazai bari ka amince kayi ba.” Ya lumshe idonsa kadan had’ida furzar da huci “Mommy I didn’t mean to hurt her feelings.. Believe me.” "Dakatar dashi tai “Ba ba’asi na nema ba.” Sai ta kuma dubansa wann karon a d’an sanyaye “Haidar, ni na haifeka nasan halinka tun k’uruciya. Nasan abubuwan da kai going through a rayuwa. Tin kana yaro baka bari a gane lagonka dukda tarin k’alubale da ka fuskanta. Jarumtarka baya bari a gane raunin ka. Amma ka sani even the strong people need help sometimes.”" Sai ya dubi Mommy a d’an sanyaye wann karon. Mommy taci gaba da jinjina kai “I know your psychological wounds are much deeper.. But I believe they’ll heel in time with Ummulkhair by your side.” Haidar ya kuma duban Mommy without saying a word. Mommy taci gaba “Ba gazawa bane to Own up to your mistakes and apologies when necessary. Even if it hurts..” Ta murmusa tana dubansa “Kana so matarka ta dawo wajenka.?” Sai ya dubi Mommy har lokacin baice komai ba. Saima kaikaitar da fuskarsa da yai. “Shikenan zan sa driver ya kawota. But I have my conditions.” Yai saurin duban Mommy “Mommy conditions kuma.? You.. just call her my wife fah.” Dariya Ya kusa kufce ma Mommy tai k’ok’arin gimtsewa “Toh so kake na kawo maka ita ka wulak’anta ta. Ai dai naga ni na biya sadakin ba Kai ba.” Ta kuma gyara zamanta “Conditions dina sune Bazaka sakata fushi ba. And you must kill that prideful behaviour of yours. Kayi alkawari.?” Ya marairaice fuska “Mommy do I have to promise.?” “Aw! Toh kaga ni saida safe.. Room nurse d’inka na jira.” Ta mik’e tana k’ok’arin d’aukar jaka. "Saurin kamo hannunta yai “Ok, fine. I promise.” Ya fad’i kaman Wanda aka masa dole." Mommy ta k’unshe dariyarta dan sosai draman Haidar d’in Ya bata dariya. Ga abu kana so amma ka kasa fitowa kai tsaye ka furta. Wani abun sai Aliyunta. Ta tuna da fari da kyar Ya amince Ummul ta zauna wajensa sai gashi yanzu da kanshi yake nemanta. ‘Sannu a hankali ma zaka kawo kanka wajen Ummul d’ita Haidar.’ Mommy tace a zuciyarta. Ba Mommy ce ta maida ma Haidar matarsa ba sai ana gobe sallamarsa. Dan so take ta wana Haidar kad’an yanda idan ta mayarsa da Ummul zai shiga taitayinsa. Sa’arsa d’aya ma dan jinya yake. * Yana nan kishingid’e saman gado yana duban yanda taketa fito da kayayyakin daga hospital wardrobe d’in tana shiryawa cikin suitcase. Fuskarta babu yabo babu fallasa. Dan tinda ta dawo bata yarda sun koma kaman da ba musamman idan ta tuna maganganun Anisa. Ta k’udiri niyyan gano koma menene ke b’oye da izinin Allah tinda tasan a shashanci irin na Anisa haka kawai bazata shirya zance irin haka ba face tanada k’wakk’waran hujja. Ta dan saci kallonsa tana linke Kayan. Nan taga ya kafe ta da ido. Tai saurin janye idonta. "Mik’ewa yai Ya soma takowa a hankali. Ta bayanta ya tsaya had’ida rungumota, Ya rik’e hannunta da kayan cikin nasa. Ummul ta lumshe idonta a hankali jin hannunta saman nasa. A hankali yake k’ok’arin linke kayan ba tareda ya saki hannunta ba. Har lokacin idanun Ummul a lumshe suke tana jin kwalla na k’ok’arin ciko idonta. A hankali Ya d’aura hab’arsa saman wuyarta had’ida lumshe idanunsa. Wasu abubuwa yake mata Wanda k’afafuwansu ke barazanar gaza d’aukarsu. Rigar dake cikin hannunsu Ya silale Ya fad’i k’asa… Ta soma k’ok’arin cire jikinta daga nasa amma saiji tai ya rik’eta tsam. Murya can k’asa yake furta “I wanted to hate you.. I tried to hate you.. But I couldn’t..!” Ya d’anyi fasali yana mai ci gaba da sinsina wuyarta. K’amshinta da yai missing. Har lokacin idanun Haidar a lumshe suke. Yayinda hawayen da Ummul ke k’ok’arin makalewa suka shiga zarya." “I can’t get you out of my mind Khairy… Please stay.. right here..And don’t let go.!” "Hawaye shar suka soma ambaliya a fuskarta. Ta shiga cikin rud’ani matuk’a. Ta rasa da waye zata yarda cikin ukun. Mommy ce, ko Anisa ce ko kuwa Haidar ne." SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *45* *©️Sameena Aleeyou… * Zame jikinta tai daga nasa tana mai goge fuskarta. Lokaci guda ta k’arasa saman sofa ta zaune tana mai ci gaba da goge hawayen da ya wanke mata fuska. Ya d’anyi still a wajen yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takowa a hankali zuwa yanda take. Har lokacin babu walwala a fuskar Ummul. Haidar ya zauna daga gefenta ba tareda ya dubeta ba. Dak’ik’ai suka gifta. Ya soma tuno kalaman Mommy da tace he should own up to his mistakes. Ya dan lumshe idonsa kadan. Har Ta cire ran bazai ce komai ba ta sinkayo muryarsa “Are you.. Still mad..?” Ta dan dube shi. Sai taji yace “Do you want me to apologise.?” Nan ma batace komai ba sai d’an dubansa da tai. Haidar ya dan furzar da huci wann karon yana janye idanunsa daga barin dubata “Oh no Khairy. You are not going to give me that silent treatment.” Nan ma bata ce komai ba. Sai ya mik’e a dan fusace “Ok fine.. Dama kawai baki dawo ba idan bazaki ce komai ba.!” "Mik’ewa tai itama cikin fushi “Da gaske, haka kace…?” Sai ta nufi k’ofa da zummar ficewa. Haidar yai saurin dawo da ita." Ta d’an kalleshi “Ni ka sakar mun hannu.” “Idan ank’i fah.?!” Ya fad’i yana tsareta da ido sosai. Sai ya dan sassauta rik’on da yai mata “Wai duk mema genesis na fushin nan ne .? Kan project d’in nan ne right.?” Ta dan kallesa da wutsiyar ido. Kaman Wanda ya fama mata wani mik’i tace “Waye yake fad’a da mahaifinsa.? Waye yake d’aukan fansa kan mahaifinsa.!” “Oh no please.. Not again.” Ya fad’i yana kame Kansa kad’an. Sai kuma ya dubeta a fusace “Maybe he pushed me into becoming this monster.. Don’t you think.!” Sai ta girgiza Kai tana dubansa “A’a saidai idan hakan d’in ka zab’a. K’walla suka ciko idonta tana dubansa. Ta rik’o hannayensa cikin nata “Shin zakaci gaba da rayuwa a bayanka ne.? Meyasa zaka bar kanka rufe cikin kurkuku.. Wann k’uncin da kake ji cikin zuciyarka ba komai bane illa kasa karb’an k’addararka da kayi. A wasu lokuta Allah "yakan saka mana jarabawar mu su zamto mutanen da suke da alak’a ta jini damu. Mutane mafi kusanci damu. Bamu ke zab’an ahalinmu ba, kuma hakan Rahamarsa ce.” Ta d’an numfasa kafin taci gaba. Allah ya jarabci salihan bayinsa Annabawansa da ahalinsu. Kaman Annabi Ibrahim (AS) Allah ya jarabce shi da Babansa. Kaman Annabi Yusuf (AS) Allah ya jarabce shi da ‘yanuwansa. Kaman Annabi Yaqub (AS) Allah ya jarabce shi da ‘ya’yansa. Kaman Annabi Nooh(AS) Allah ya jarabce shi da D’ansa. Kaman Annabinmu fiyayyen halitta(SAW) Allah ya jarabcesa da Uncles d’insa. Duka wad’annan Annabawa masu daraja sun fuskanci jarabawa daga cikin ahali. Ashe lallai muma zaa jarabcemu daga cikin namu ahalin. Wad’ann k’alubale da jarabawa suke k’arfafa imaninmu..Sann Allah shike shiryar da Wanda yaso..” Daga haka bata kuma cewa komai ba taci gaba da tattare kayyakin da take." Haidar ya koma ya zauna had’ida zuba mata ido ba tareda ya kuma cewa komai ba. A hankali yasa tafukan hannayensa ya shafi fuskarsa. ** "Koda suka dawo gida maganganun Anisa suke yawo a kwanyarta, tayi k’ok’arin ta yakice tinanin amma ta kasa. A lissafi saura kwanaki uku kacal ta cika watanni uku da aure. Hakan na nufin alk’awarin da ta d’aukar ma mahaifiyarta yana gab da cika. Ya kamata ta waiwayi gida. Tana buk’atan sanin wani hali ahalinta ke ciki. Musamman majinyacin mahaifinta. Tinanin kalaman Anisa suka ci gaba da dukan kwanyarta. ‘Shin Mommy ta tab’a tambayarki wani abu gameda ahalinki.?’ Tai saurin rintse idonta ta mik’e da zummar ficewa taji muryar Haidar daga bathroom yana kiranta. Ta isa jikin closet din kafin ta d’anyi gyaran murya ta amsa. Haidar yaci gaba “Could you please pass me my towel.”" Ta shiga bin closet din da kallo tana duban yanda komai yake cikin tsari. Nan ta hangi towel d’in dan sama kad’an anyi folding an jerasu cikin open shelf cabinet. Ta ciro towel din mai dan girma tai knocking a k’ofan bathroom din “Ga.. Gashi nan na kawo maka.” Muryarsa ta sinkayo “The door is open.. you can come in.” Ta zaro ido waje jin abinda yace. Sai ta soma girgiza kai ita kad’ai “A’a.. A’a kawai ka karb’a.” Ta k’arashe tana mai tura hannunta dake rikeda towel d’in ta tsakanin k’ofar. Bata ankare ba saiji tai ya had’e da hannunta Ya janyota cikin bathroom d’in. Ummul ta rintse idonta sosai sai ta fashe masa da kuka. ta shiga dukan k’irjinsa “Mai kake aikatawa ne.. Dan Allah ka… k’yaleni na fice. Please..!” For the first time da taji sautin dariyarsa. Cak ta tsaya da abinda take still ta kasa bud’e idonta. Haidar murmushi yake Har hak’waransa na bayyana “Okay.. Open your eyes now.. You are here already..!” Ummul ta mak’e kafad’a tana kuma dukan k’irjinsa “A’a nidai bazan.. bazan bud’e ba.” "“Okaaaay.. Let’s see now..” “Trust me, I’m gonna make you open those eyes.” Har lokacin murmushi mai sauti mai bayyana hak’wara yake. Abinda Ya jima baiba na tsawon lokaci." “Wai.. Mai kake k’ok’arin aikatawa.?” Bai amsata ba yaci gaba da niyyansa. A yayinda Ummul ke k’ok’arin zillewa bata ankara ba sai ji tai Haidar Ya janyota sun fad’a cikin jacuzzi tub d’in a tare. Ummul ta ja numfashi tana mai fiddo kanta waje had’ida shafe ruwan da Ya jik’a mata fuska. Ta kafesa da ido baki a ture kaman zata fashe da wani kukan. Haidar ya kashe mata ido daya “See. I told you zansa ki bud’e idonki.” Ta soma k’ok’arin mik’ewa yayi saurin kamo hannayenta “Ina kuma zakije bayan kin riga kin jik’e.” Baki a ture tace “Ba kaine ka jik’ani ba... Kuma kasan Mommy ta gayyacemu cin abincin dare. Ya kamata naje sashenta da wuri dan na taimaka da wasu abubuwan..” “Kar ki damu Mommy bazata ce komai ba..” Ta d’an hararesa baki a ture “Kuma na riga na shirya.. kasa na jik’e gaba d’aya.” Ya dan tab’e baki kad’an had’ida lifting shoulders d’insa “Shikenan sai ki sake wani wankan.” Ya matso saitin kunnenta yana mai rage murya “Let’s bath.. Together..” Turasa tai da duka k’arfinta ta tashi . Murya na rawa ta shiga nuna masa forehead d’insa da hannunta “Kaga duba kaga.. akwai abu kusan idonka..” Yakai hannunsa goshinsa sai Ummul tai amfani da damar ta tashi a guje ta zille masa. Wann karon itake masa dariyar. "“Don’t worry, I’ll get you next time.” Ya k’arashe yana mai mata alama da yatsarsa." Anisa da tin shigowarta sashen ta soma sinkayo kaman sautin mutane nan ta sad’ad’ kaman mai shirin satan wani abu. Ta lab’e yanda take sinkayo sautin. K’iris Ya rage Zuciyar Anisa bai buga ba. Kasa jurewa tai dole ta fice daga sashen. Tana ficewa ta d’auki waya ta kirawo Hisham. Cikin tsananin huci take fad’in “No way Hisham. I can’t wait till that day.. I’m losing my patience here. Na tsani wann kucakar.. She’s driving me crazy.. Ji nake kaman naje na shak’eta.” “You will not do anything foolish.” Ta katsesa “Na gaji Hisham.. Bakaji yanda suke dariya cikin nishad’i ba. They were having a good time.” Ta saki kara tana fad’in “It’s so irritating.. Ka gane we can’t let those two be happy while we are stuck here.. just freaking miserable. We need to act fast.!” Hisham dake ci gaba da sakin huci Ya katseta cikin tsawa “Just shut up Neesa.! Na gaya Miki bazaki aikata komai ba ba tareda umarnina ba. Na dan lokaci ne. Haidar bazai taba samun dama akan Ummul dita ba. So just trust me.!” Ya k’arashe idanunsa ba kuma kad’awa in rage. A fusace ta katse kiran tana kuma ci gaba da zagaya d’akin zuciyarta naci gaba da tafarfasa. Sautin nishadin Haidar da Ummul Ya kasa barin kwanyarta da kunnuwarta. Ta saki k’ara kad’an tana durk’usawa wajen. A hankali take furta “I hate you.. I hate you Ummul.!” * Koda Ummul ta koma nata d’akin murmushi ne Ya kasa barin fuskarta. Ta Tina sanda sukai juyi cikin jacuzzi tub tare sai ta lumshe ido a hankali tana sauk’e sassanyar ajiyan zuciya. Wata doguwar riga silk kalan peach da ya zauna a jikinta sosai ta d’auko ta saka ta yane kanta da mayanin rigar. Ba makeup a fuskarta sai d’an man leb’e amma sosai tai kyau. Fatarta da bai cika haske ba sann bai cika duhu ba ya k’ara murjewa yayi kyau. Kwantattun sumarta irinta asalin k’abilar fulani da ta d’auko daga mahaifiyarta sun kwanta sunyi luf tin daga gaban goshinta Har zuwa gefen fuskarta. Kallo d’aya zaka mata kaso sake kallonta. Kalan rigar sosai ya tafi da Kalar jikinta. Abinda bata saba ba sai ta tsinci kanta da duban kanta a madubi. Kunya da dariyar kanta suka zo mata lokaci d’aya. Harga Allah zata iya cewa ta mance da wata damuwar gidan duniya da batun Anisa. Shi d’in kawai take hangowa a duniyar ta Wanda takeji tamkar su biyu ne ciki. Parlor ta sauko tana jiransa dan yace ta jirasa zasu shiga sashen Mommy tare. A b’angaren Haidar kuwa bayan Ya d’auki file din ya jima yana juyawa yana tinanin maganganunta kai tsaye sashen mahaifinsa Ya nufa. Daddy yana zaune study Haidar yai Sallama Ya shigo. Daddy ya d’ago ya dubi Haidar da idanunsa dake rufe cikin farin gilashi na k’ara k’arfin gani ga wad’anda shekaru Ya d’an ja masu. Tin daga yanda Daddy ya amsa masa Sallama jikin Haidar Ya d’anyi sanyi. Dan yanayin amsa masa da yai yasha bambam da irin yanda yake amsa masa a baya. Sun d’auki lokaci suna duban juna kafin Daddy ya nuna masa kujera mai kallon table d’insa yace ya zauna. Haidar ya k’arisa ya zauna. Shiru Ya dan ratsa tsakani kafin Haidar yai k’arfin halin cewa “Daddy.. Barka da dare.” Daddy ya amsa masa had’ida jinjina Kai. Sai Haidar ya aje folder d’in saman table din Daddy. Daddy ya girgiza Kai kad’an kaman Wanda yake avoiding k’wayan idon Haidar d’in “What’s this for.?” Haidar yai clearing throat d’insa “Yarjejeniyar project d’in ne Daddy.. Tareda resignation latter.. Na janye ragamar kula da kwangilar.. Sann.. Na aje aikina na company.” Daddy sai Ya d’ago yana dubansa sosai wann karon. Haidar sai Ya mik’e kansa a kife “I.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an da kake fata da buri na zama ba..” Ya soma k’ok’arin ficewa daga study d’in mahaifinsa ya dakatar dashi. “Aliyu.!” Daddy ya ambaci sunansa. Ya d’ago Ya dubi Daddy. Da ido Daddy yai masa nuni da kujeran “Koma ka zauna.” Haidar ya komo ya zauna har lokacin Kansa a kife. Cikin tsawa da fad’a kaman yanda ya saba masa a lokutan baya ya soma fad’in “Ni kake ce ma ka aje aikinka..?” How dare you.? Who do you think you are...! Kai har ka kai ka dubeni kace min ka aje aikinka.? Kai har ka isa.?!” Da a lokutan baya ne da ya amsa ko ya maida ma mahaifinsa martani cikin daga murya. Amma ga mamakin Daddy sai yaji ya soma magana a natse “I’m sorry.. But I can’t do it Daddy.!” Ya fad’i k’walla suna ciko idanunsa. Cak mahaifinsa ya tsaya yana dubansa. Haidar yaci gaba da girgiza Kai “I can’t destroy you.!” Daddy ya koma ya zauna yana duban Haidar d’in sosai cikin tsanani shock. “My plan was… To use this so called project and destroy you.. I wanted to show you the kind of monster you created in me.. But then I couldn’t.. I couldn’t destroy the hands that raised me koda ace mun kasance munada alak’a mai rauni cikeda tarin k’alubale.” Yaci gaba da girgiza kai. Sai murmusa kad’an wann karon “I just want to be free from this prison. I.. I don’t want to keep on living my life tied to all this rage and hatred.. I want live a normal life.. To start a family of my own..” Muryarsa yaci gaba da rawa “I.. I’m sorry Daddy.. I’m sorry idan ban kasance wann d’an dake fata da burin samu ba.. I’m sorry idan ban kasance wann D’an da zakayi alfahari dashi ba.. Believe me.. I truly.. am sorry..” Baikai aya ba Daddy dake ta k’ok’arin danne hawayensa sai ya zame farin gilashinsa ya kauda fuskarsa kadan yana goge hawayen da suka mak’ale masa a ido. "Kaman daga sama Haidar ya sinkayo muryar mahaifinsa “Aliyu, my son..”" Da mamaki Haidar ke duban Mahaifinsa Jin ya ambacesa da D’ansa abinda bai taba ji daga mahaifin nasa ba. “Shin ka tambayi kanka koda ka farka daga coma meyasa baka ganni wajenka ba.?” Shiru Haidar baice komai ba. Daddy yaci gaba da jinjina Kai har lokacin bai kalli b’angaren da Haidar d’in yake ba “Sabida bazan iya kallonka a ido ba.. Bazan iya ambatan kaina da mahaifinka because I.. I haven’t been a good father to you.. And I treated you badly..” Daddy ya kifa Kansa hawaye na gangaro masa “Fad’an da kaji ina maka a yanzu borin kunya ce kawai sabida ni d’in ban sauk’e wani nauyi da hakki na mahaifinka dake rataye wuyana ba. Hadisi ne guda cewa ko wannen mu mai kiwo ne kuma za’a tambayemu gameda wann amana na kiwo da aka dank’a mana. Bazan iya duban idanunka na nemi gafararka ba Haidar… Bazan iya ba..!” Saiga alamun kuka cikin muryar Daddy. Haidar ya mik’e jikinsa a matuk’ar sanyaye ya tako har zuwa gaban kujeran da Daddy ke zaune bisa. Duk’awa yai gaban Daddy Wanda har lokacin Kansa na kife yana d’igar da hawaye. Haidar ya daura hannayensa biyu saman hannayen Daddy dake bisa laps d’in Daddyn. Shiru ne ya ziyarci wajen baka iya jin alamun komai face motsin zuciya. Daddy ya rik’e hannayen Haidar tsam cikin nasa “I’m sorry son.. I’m sorry.. Please forgive your Dad…” Hawaye suka gangaro ma Haidar dake duk’e gaban Daddy hannayensu cikin na juna. "Mommy da ta nufo k’ofan dan ta sanar da mijin nata gayyatar D’ansu da matarsa dinner matsayin maraba da dawowa gida ma Haidar d’in koda bazai nuna kulawarsa kaman yanda ta tsammata ba, nan ta riski wann babban al’ajabi. Rana mai d’inbin tarihi.. K’afafun Mommy suka kusan gaza d’aukarta.. Hawaye suka shiga zarya a k’uncinta.. Sai Mommy ta fad’i k’asa tana mai sujada na godiya ga Ubangijinta. Tama rasa mafarki ne take kokuwa dai a farke take. Haidar dinta da mahaifinsa take gani cikin yanayi da bata tab’a tsammanin zata gansu ciki ba. Allah buwayi gagara misali. Mommy ta kuma yarda cewa lallai duk Wanda ya dogara ga Allah toh fah Allah ya isar masa. Itakam babu abinda zata ce saidai taci gaba da gode ma mahaliccinta Wanda ya yaye duhun dake cikin gidanta da ahalinta ya yalwatasu da haskensa. Ta saki turban boka da suka d’auko daga fari ta rik’e turba na gaskiya sai gashi komai yana gudana cikin sauk’i. Lallai wann wani rahama ne daga Ubangijinta. Lallai wann izna ce ga tababbu masu bin hanyar b’ata. Wanda ya gane Allah shi yake yi ba boka ko Malam ba shi keda babban rabo duniya da lahira. Bata san sanda ta koma da baya ba ta nufi d’akinta ta maida k’ofa ta rufe ta fad’a saman gado tana kuka sosai. Kukan farin ciki wann karon. Kukan da ya goge Wanda ta jima tanayi a baya Kama daga zuciya har k’wayan ido. Alkhairin Allah yaci gaba da haska gidanta da ahalinta." Haidar yaci gaba da girgiza Kai yana rik’eda hannayen Daddy gam cikin nasa “Daddy ka daina bani hak’uri. We are all human beings.. We make mistakes. What’s important is that we learn from those mistakes.” Yaci gaba da jinjina kai a hankali “Ni yafi cancanta na nemi yafiya a gareka Daddy. Idan inada hakki akanka hakkinka dake kaina yafi girma. Duk yanda naje nazo banida madadinka.. I should’ve been more understanding with you. Cikin zuciyarsa yake tuno sanda Ummul take fad’a masa ‘A rayuwa wasu lokutan Allah yakan saka mana jarabawarmu ya zamto people that are tied to us by blood.’ Sai Haidar ya mik’a hannu ya d’auko folder d’in project da ya shigo dashi. Ya daura saman hannun Daddy suna kallon cikin fuskan juna. Murmushi gauraye da siraran hawaye saman fuskar Haidar yake fad’in “Daddy I can walkway from this Business because it’s my choice.. But I can’t walkway from you. Do you know why.?” "Sosai Daddy yake kallonsa yana hawaye. Haidar yaci gaba da jinjina Kai “Because you are my Father.. Allah chose you for me… We are tied to each other by blood because haka Yake so ya kasance.” Yaci gaba da jinjina Kai yana murmushi “Daddy jininka shi yake circulating cikin jikina daga farko.. A karo na biyu Kai ka bani jininka, you couldn’t walkaway from me either. Sabida ni d’in D’anka ne.”" Daddy sai ya janyo kan Haidar ya rungume cikin jikinsa. Muryarsa na rawa yake fad’in “Allah ya maka albarka Aliyu.” ** A lambum dake bayan sashen Mommy aka shirya cin abincin daren. Hasken wutan lantarki ya karad’e ko ina tamkar ba dare ba. An shirya teburin gwanin ban sha’awa ga barbecue stand daga gefe. Suna cikin shirya plates saman teburin itada Anisa Anisa tai excusing kanta sakamakon kira da ya shigo wayarta. Nan Ummul ta hangosa na tahowa. Sassanyar murmushi saman fuskarsa. Ta shagala sosai da kallonsa kaman yanda shima ya shagala da kallonta dan sosai tai masa kyau. Yana k’arasowa sai ya tsaya daga bayanta ya dan rungumota had’ida rank’wafo da kansa kusan kunnenta “You look.. Gorgeous.!” Ya fad’i cikin sigan rad’a. Ummul ta soma k’ok’arin turesa daga jikinta tana ‘yan waige waige “Mai kake aikatawa ne wai.. Idan wani ya ganmu fah.?” Bai saketa ba ya kuma rad’a mata “So what.! Can’t I hug my wife.?” Ta waiga ta dubi Anisa dake can gefe tana amsa waya. Ta kuma duban ma’aikatan kitchen guda biyu dake gefe gaban BBQ stand. Kaman zatai kuka tace “Dan Allah ka bari akwai mutane wajen nan fah nan..” Juyawa yai ya dubi kitchen staff d’in. Sai ya dan murmusa “Is that problem.? fine. Zo muje.” Bai jira amsarta ba ya shiga janyo hannunta. Suka nufi yanda ma’aikatan ke gashin naman. Haidar yace musu suna iya tafiya zasu kula da barbecue d’in. Ma’aikatan suka amsa masa cikeda risinawa suna duban yanda Haidar ya janyo Ummul dake fad’in ita fah bata iya amfani da irin wann abin gashin ba. Yace kar ta damu tare zasuyi. Sosai suka birgesu kaman kar su daina kallonsu. Abu ne da zasu iya cewa basu tab’a ganin ya faru gidan ba. Basu tab’a ganin Haidar cikin farin ciki irin wann ba. Su dai kam Sun shaida zuwan Ummulkhair gidan Alkhairi ne. Anisa ta juyo baki sake tana duban ikon Allah Haidar da Ummul gaban barbecue stand sai zuba soyayya suke. Gwiwoyinta taji sun sake kamar wata maras laka. A haka Mommy ma ta k’araso wajen ta taddasu. Farin ciki maras misaltuwa ya kuma gauraye zuciyarta. Zuwan Mommy wajen yasa Ummul janye jiki ta kyale Haidar shi kad’ai. Haidar na fad’in ta mik’a masa bbq cutting board sai sann ya kula ta silale ta bar shi shi kad’ai.. Ba kowa wajen ma sai shi kad’ai. K’ila Sun shige yin wani abin cikin gidan. Ya dan tab’e bakinsa kad’an. Amma sai yaga wani hannu na mik’o masa abinda yake nema. Haidar yabi hannun da kallo. Ga mamakinsa Daddy ya gani. Kyakkyawan murmushi saman fuskar mahaifin nasa. Haidar yasa hannu ya amshi board d’in had’ida godiya ma Daddy. Jinjina Kai Daddy yai. Sai Haidar yaga Daddy na nad’e hannun long sleeve shirt din dake jikinsa alamun zai tayasa. Sai Haidar ya girgiza Kai “No Daddy you don’t have to.. Ya kamata kaje ka zauna.. I.. I’ll serve you some.” Ya fad’i awkwardly dan abu ne da bai saba faruwa ba koma bai tab’a faruwa ba tsakaninsu. "Murmushi ne saman fuskar Daddy ya dafa kafad’an Haidar din “No Son, let’s do it.. Together.”" "Haidar yai murmushi yana tuna lokacin yarantarsa wann shine mafarkinsa. To make memories with both his parents… To strengthen their bond. Ya samu kusanci sosai da mahaifinsa. To have some quality time together.. To build something together. To play sports, video games, go horse riding da dai sauransu. Sai ya murmusa yana duban mahaifin nasa sosai. Kaman mafarkinsa ne yake zama gaskiya. Yana k’ok’arin yanka naman saman board din Daddy ya dafa hannunsa wana hakan Ya dakatar da Haidar. Suka dubi juna sai Daddy yace “Be careful Engr, this is not a construction side.”" "Su duka sai suka d’an dara kad’an. Daddy yace “You know Son, if I were to turn back time.. Da munyi aiki tare hand in hand.. Like professional Engrs.”" Jikin Haidar Ya d’anyi sanyi Ya fahimci abinda sukeyi a yanzu d’in Ya K’wadaitar ma mahaifinsa inama lokacin da sukeda damar kasancewa tare a company sunyi ayyuka tare tare babu tsangwama babu hantara. Gashi yanzu Ya sanar da mahaifinsa Ya aje aikin company meaning ba lallai su sami irin wann damar ba. Muryar Daddy ya kuma sinkaya “Bana so na tak’uraka. Da na rok’eka wani alfarma.” Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy.. Ka wuce wann.” "Daddy ya murmusa “Haidar, I can understand you, if you… don’t want to manage the project due to.. your personal" priorities.. But please kar ka aje aikinka.. Kar ka bar Kampanin… Let this be the last abu da zan buk’ata ka mun.” "Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy, I’m your son.. Hakkina ne matsayinka na mahaifina nayi maka biyayya cikin abinda bai sab’a ma mahaliccina ba. Kuma wann bazai zama abu na k’arshe da zan maka ba. Umarni kawai zaka bani a koda yaushe.. Kuma na maka alk’awari bazan aje aikina ba in sha Allah. Bazan bar company ba. Together we will take the company to greater heights.!” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa." Sai Daddy ya kamo k’afafunsa Ya rungume “Thank you son. Allah ya maka albarka.” A haka Mommy ta k’araso wajen ta iskesu. Farin cikinta ya ninku. Itakam a halin yanzu tana jin babu sauran abinda zata nema da ya shige taita gode ma Ubangijinta da ya cika rahamarsa ga ahalinta. "Bayan cin abincin suna zaune itada Haidar a parlor. Haidar ya kuma murmusawa ya dubeta “You know Mommy," After all these years it's today that I feel like… I'm part of the family.” Mommy ta rik’e hannayensa cikin nata. Kyakkyawan murmushi saman fuskarta “We gonna have some family bondings to makeup for all the time we've lost… Kuma.. Zamu fara da shagalin bikinka. Aurenka da Ummul ta cancanci biki na gaske irin na ‘yan gata.” Ya dan girgiza Kai yana murmushi “Mommy na kasa yarda bisa yarjejeniyar Wata uku na amince da auren Khairy.. Dan kawai Daddy ya bani wann project d’in.” “Shiii.” Mommy ta dakatar dashi “Babu wann maganar Haidar.. An rufe shi har abada. D’ago baya irin haka baida wani amfani. Bazaka sanar da Ummul wani abu mai suna auren yarjejeniya ko AUREN WATA UKU ba.” Sai ya d’an dubeta can k’asar zuciyarsa yana jin zuciyarsa ta katsa samun natsuwa har sai ya sanar da ita.. Sabida a halin yanzu Aure yake so ya gina da ita bisa zallan gaskiya. Ya d’an dubi Mommy “Mommy I want to build my marriage with her base on trust and transparency. Bana so daga baya tazo ta fahimci cewa na aureta ne bisa yajejeniya zuwa wani k’ayyadajjen lokaci. I want her to hear it from me first kafin taji daga wani waje.” Mommy ta jinjina Kai “Na fahimceka Haidar.. Amma kafin nan ka d’an dakata har a gama wann bikin tariyarku can gidanku da na saka nan da kwanaki biyu kacal. Idan yaso sai ka sanar da Ummul yanda al’amarin ya kasance..” Sai ya d’anyi jim kafin kuma ya jinjina Kai a hankali “Shikenan Mommy. Idan hakan kike so.” "Ta murmusa cikeda jin dad’i. Burin ko wasu iyaye shine su samu ‘ya’ya masu biyayya a garesu. Lallai mai rai kar ya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa. Who would’ve thought za’a zo lokacin da Haidar zai d’auki umarnin mahaifyarsa ba tareda jayayya ko nuna k’in amincewa ba.? Ya ke ‘Yaruwa da Allah ya Miki jarabawa da D’an da kika haifa, kar ki tab’a yanke k’auna daga rahamar Ubangijinki domin kuwa shid’in rahamarsa mai yalwa ne. Kar ki karaya, kici gaba da mik’a lamuranki ga Ubangiji. Duk Wanda Allah ya zama majib’icin al’amarinsa shi keda babban rabo." Haidar ya mik’e da zummar mata sallama ta dakatar dashi. “Yauwa nace ba sai abu na gaba..” Haidar ya jinjina kai yana sauraron Mommy. “Kanaji.. Ummul zata dawo nan sashena da zama har sai anyi bikin an kai maka ita.” Wann karon zaro ido yai kaman wani abin tausayi ya langab’e kai “Haba mana Mommy does it have to be this way.. I just came out of hospital fah..I’m still a patient.” “Mommy ko kin daina tausayina ne.” Ya kuma fad’i a marairaice. Dariya yaso bata amma ta gimtse tace “Ba tausayinka na daina ba. So nake kai d’aukin d’iyata idan an kai maka ita.. Waima dakata shin kai ka biya sadakin nan ne.?” Haidar ya sauk’e ajiyan zuciya kaman wani maraya “Shikenan Mommy.. Saida safe.. Amma please a k’yaleta ta kawo min coffee.” “Naji… Just coffee..” Tai maganar tana jaddada masa. Ta k’arada “Jeka Allah bamu alkhairi.” Haka ya fice duk jikinsa ba kuzari. Shi fah maganar gaskiya wann gadara da Mommy take masa da mata akan sadaki ya fara isansa. Shidai kawai gwara ya biya Mommy sadakinta ya huta. Bayan ficewar Haidar shiryawa tai ta nufi sashen Daddy. A parlor ta iske shi. Daddy ya dubeta da mamaki. For days yana k’ok’arin shawo kanta daga fushin da take dashi sai gashi yau ta kawo kanta har yanda yake. Murmushi yai cikin zuciyarsa yake ayyana lallai sai a bar uwa da D’anta. D’anta shine rauninta. Ta k’araso kanta a k’asa. Kaman mai shirin zama sai kuma ta silale gabansa. Ta kifa kanta tana hawaye. Cikin rawar murya irinta mai kuka take fad’in “Engr ka yafe min.. Ka yafe mun duk abubuwan da nai maka.. Na shekarun baya da na kwanakin nan..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Daddy ya duk’a shima suna fuskantar juna. Sai ya rungumota zuwa jikinsa. Kamar wacce take jira kukanta sai ya k’aru. Shima ya saka d’an yatsarsa ya goge kwallan da ya mak’ale masa cikin ido. “Is Ok Kwaise. Ya isa haka.. Dukanmu ‘yan adam ne masu kuskure. Mafiya alkhairi sune masu tuba. Bayan tsawon shekarun nan idan akwai Wanda yafi cancanta ya nemi yafiya ni ne. I supposed to be the head of this family.. Amma duk sai na bar Miki nauyin.. Kece kika jajirce Akan wann ahalin Kwaise.. You never give up despite the challenges.. Kin tsaya Akan k’afarki ganin cewa ahalinki bai watse ba. Kinyi abinda ni na kasayi Kwaise.. Thank you for not giving up on us..” Murmushi ne gauraye da hawaye saman fuskarsa. Sai suka rungume juna wani kukan na kuma zuwa ma Mommy. ** A b’angaren Haidar kuwa koda ya koma sashensa zama yai shi kad’ai a balcony d’insa yana tunanin rayuwarsa. Da yanda shigowarta cikin rayuwarsa Ya canza komai lokaci guda cikin ikon Allah. Yana jin wani shauk’i can k’asar zuciyarsa Wanda bai tab’a jin hakan ga wata mace ba. He wants to build something special with her.. base on trust and transparency wanda hakan ke nufi dole ya sanar da ita wasu abubuwan daga past d’insa musamman abinda ya danganci personal rayuwarsa. Aurensa da Dareen Wanda ko family d’insa basu sani ba har ya faru ya k’are da kuma yanda nasu auren da ita Ummul d’in Ya kasance. Yarjejeniya sukai da mahaifiyarsa zata shigo rayuwarsa a matsayin matar wata uku dan kawai Ya mallaki project d’in da yai niyyan tarwatsa mahaifinsa dashi. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furzar da huci. Shigowa Ummul Tai rik’eda kofin coffee da ya buk’ata a hannunta. Ta mik’a masa cikeda risinawa. Ya amsa yana mata godiya. Sai ya nuna mata gefensa “Come sit here... let’s talk.” Haka kurum taji gabanta ya fad’i sai ta d’an girgiza kai kad’an “Magana kuma.?” Haidar ya jinjina Kai bayan ya sipping coffee din “Kar ki damu yau magana zamuyi ba akan kowa ko komai ba... Magana ce akanmu.. Let’s talk.. about us.” Ya k’arashe yana kashe mata ido d’aya gajeren murmushi saman fuskarsa. Bugun zuciyarta Ya dan karu musamman da taga yanda yake binta da kallo. sai ta k’arasa a d’an sanyaye ta zauna a yanda Ya nuna matan. Dak’ik’ai suka d’an shige kafin Haidar Ya aje coffee din dake hannunsa bisa teburin gefensa. Ya gyara zamansa Ya karkato sosai yana facing dinta gwiwarsu na gogar juna. Sai ta d’an sadda idonta kad’an ganin irin yanda ya tsareta. Hannayensa ya d’aura saman nata dake bisa laps dinta. Ummul ta dubi hannayensa da Ya d’aura bisa nata dake bisa cinyarta. Sai ta d’ago ta dubesa a d’an sanyaye. “Khairy..!” Ya ambace sunanta kaman yanda Yake kiranta. “You came into my life to make it better.. You’ve changed all areas in my life..” Ta dube shi sai ta dan murmusa “Bani nayi ba duka yin Allah ne..” "Ya jnjina kansa “Kece sanadi...” Yaci gaba da jinjina Kai hannayenta cikin nasa “I.. know there’s still a lot.. to do.. But you showed me the way Khairy..” You made me want to be a better son… You made me wanna wake up and reflect. You made me wann be.. a better business man, take my brand far.. And above all, you made me believe,.That I can be a better person. Thank you.. For coming into my life.” Ya k’arashe labarin na neman sauya direction." Jiki a sanyaye ta soma k’ok’arin zame hannunta sabida zuciyarta dake bugawa cikin sauri. “Dare yayi.. Ya kamata ka kwanta ka huta… Kaifa patient ne.” Ya kamo waits dinta ya zaunarta saman laps d’insa. Cikin sigan rad’a yake fad’in “Wa yace miki ni patient ne har yanzu.? Bari ma na nuna miki na warke.” Ta zaro ido tana k’ok’arin turasa “Kaga.. Ni tafiya ma zan..” Bata kai aya ba ya rufe bakinta da nasa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *46* *©️Sameena Aleeyou… * Da kyar ta samu ya k’yaleta yai mata rakiya har k’ofan parlorn Mommy. Suna isowa ta zame jikinta daga nasa. Sai ya mik’a mata k’aramar paper bag d’in dake hannunsa. Ta d’an girgiza Kai “Ta mecece.?” “Don’t open it yet sai kin shiga.” Ya fad’i yana kashe mata ido d’aya . Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya soma tafiya yana waving dinta kaman kar ya tafi ya barta. Ta girgiza Kai kurum tana binsa da kallo a haka har ya shige. Anisa tana nan ta kasa ta tsare tana jiran dawowarta dan kusan komai Akan idonta ya faru. "Sam Ummul batasan da mutum a parlorn ba sai muryar Anisa da ta sinkayo. Batada lokacin sauraron maganganun Anisa hakan yasa tuni tasa kai ta nufi upstairs ba tareda ta tsaya sauraron maganganun Anisa ba. Amma sai Anisa ta bud’e murya tace “Auren Haidar Maitama might seem to you like a golden opportunity na samun nasarori da Jin dad’in rayuwa.. Musamman duba da irin rayuwar da kika baro cikinta… But what if, this golden opportunity comes at a very high price.?”" Ummul taci gaba da k’ok’arin dannar kanta. Dan a yanda ta tsara ba a wann lokacin zata fuskanci Anisa ba. Ta gama shirya lokacin da zata tunk’ari Anisa da kalamanta. Sai ta bud’e lumsassun idonta a hankali taci gaba da tafiya ba tareda ta juyo ta dubi Anisa ba. Anisa ta take mata baya tana ci gaba da fad’in “Abinda yasa kikaga na dage miki Ummul dan inada gaskiya ne. Bana so ki saki jiki cikin auren da zakiyi danasani a gaba. Kuma ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace ce.. Ba komai cikin wann auren face k’ask’anci.” Ummul ta dubi Anisa da murmushi saman fuskarta. Sai kuma ta maida k’ofan d’aki ta rufe ba tarda tace komai ba. Dan Sam bazata bari ta b’ata shirinta ba. Anisa taci gaba da sakin huci dan ta tsani wann silent treatment din da Ummul ke bata dan bata mance karonsu da Ummul d’in ba. Tasan she’s sharp and smart dik yanda akai wann shirun da take tana murmushi wani abin take shiryawa tinda Tasha lalata mata shiri ba d’aya ba. Taci gaba da sakin huci ita kad’ai. Ummul tana shigewa d’aki ta lumshe idonta tana karanto addu’o’in samun sauk’i da sukuni cikin zuciyarta dan sosai take Jin maganganun Anisa har cikin k’ahon zuciyarta da b’argonta. Ta isa saman gado ta zauna gijif sai ta dubi ‘yar jakan da Haidar ya bata. Ta soma k’ok’arin bud’ewa. Nan taga wayar salula ce ta yayi mai d’ankaran kyau. Da alama komai an saka cikin wayar. Kaman daga chaji har zuwa simcard. Taita juya wayar kafin ta kunna. Sak’o ne ya fara mata Sallama _I've bought a new book.. and open a brand new page… together with you_ Taita karanta sak’on yayinda jikinta ya kuma mutuwa. A b’angare na kunnenta guda kalaman Anisa ke mata yawo a d’aya b’angaren sak’on Haidar cikin yanayin muryarsa na mata yawo. Ta rasa wanne d’aya zata saurara sai ta toshe duka kunnuwanta biyu kuka na zuwa mata. Ganin koke koke da tunanin bazasu fishheta ba kawai sai ta mik’e ta d’auro alwala ta soma Kai kukanta ga Mabuwayin Sarki da babu kaman shi. Tana bisa darduma tayi lamo tana duban wayar kira na shigowa Wanda tasan kiransa ne tinda lambarsa ne kawai kan wayar. Bata bi takan wayar ba haka akaita kira har dai ya hak’ura. K’arshe ya tura sakwanni Wanda suma batabi takansu ba. Duk Haidar sai ya damu ya fara tunanin ko bataji dad’in kyautar da yai mata bane. Kodai ya mata wani abin ne. Washe gari da safe Fashion designer tazo har gida da manyan bridal dress catalog dan amarya Ummul ta zaba yanayin rigar da za’a mata. Anisa ita ke tayata zabe. Ummul sai duban Anisa take tana mamakin wai wacce ke mata gargadi da kashedi da auren Haidar sai gashi itace mai zakewa wajen zaba mata Kayan da zata saka. Aka nuno wani farin gown mai dankaran kyau Anisa tace “Yauwa perfect. I think this one is ok.” Kaman daga sama suka sinkayi wann muryar nasa daga bayansu “This is too revealing.. My wife can’t wear this.” Ya fad’i cikeda gadara hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa yasa kai ya shige upstairs gaida Mommy ba tareda ya dubi ko yanda Ummul d’in take ba. Ta bisa da kallo duk jikinta a sanyaye. Toh ko dai fushi yake da ita sabida yayita kiranta a Daren jiya bata d’aga ba har sakwanni ya turo bata amsa shi ba. Gaba d’aya sai taji babu dadi. Anisa na hankalce da ita da Haidar d’in. Lokaci guda tana mamakin wai Haidar ke cewa kaya is too revealing dik girma da tasowa cikin gogaggun wayayyu da yai. Lallai ta yarda ya fara nisa cikin soyayyar wann Bagidajiyar. Idan batai sauri ta rabasa da wann Bagidajiyar ba haka zata maida mata Haidar d’inta Bagidaje irinta. Haka har aka gama zaben rigunan ita dai bama tace ga rigar da aka tsaida ba. Duk tunaninta na kan Haidar.. Bata san ta damu da fushinsa har haka ba. Abinda yafi bata mamaki shine ko ta kanta bai sake bi ba.. Bai nemeta bata ma sake saka shi a idonta cikin gidan ba. Ta d’auki wayar kaman zata kira layin sa amma sai ta kasa. Haka kaman wasa har ranan da ake saka ran ranan ne Mommy ta tsaida dan shagalin bikinsu bata saka Haidar idonta ba. Wani abinda ya k’ara bama Ummul mamaki shine Anisa batai k’asa a gwiwa wajen shirya komai ba. Ita Mommy tasa ta kaita saloon aka gyara mata gashi sann ta d’auko mai lalle da makeup artist har gida. Kaman wata maid of honor haka Anisa ta zak’e tana mata komai. Ummul bata daina karantarta ba. Cikin wata farar doguwar riga da dinkin ya zauna jikinta ta shirya. An mata dauri na zamani da irin fabric d’in rigar Wanda da gani zaka san an b’arar da kudi wajen sayensa da d’inkasa. Ba’a cika mata kwalliyar ba amma tayi kyau har ta gaji. Duk Wanda ya kalle ta sai yaso sake kallonta. Haka masu kwalliyan da shiryata sukaita santin kyaun da tayi. Ita dai Ummul gaba d’aya ranan ta kasa gane kanta gaba jinta take ba daidai ba. Something feels wrong. Sai kawai ta danganta hakan da fushin da Haidar keyi da ita. Koda akace ta fito su d’auki hoto da Haidar sai rashin nutsuwar da take ciki ya ninku. Zuciyarta yaci gaba da bugu. Yanda kasan bata tab’a sanin shi ba haka takeji. Da kyar ta iya fitowa k’irjinta sai bugu yake. Tin daga saman bene masu camera ke haskota har zuwa saukowarta parlorn basu daina d’aukarta hoto ta ko wani angle ba. "Anisa ta dubeta ta saki murmushi “Relax Ummul, ki natsu a Miki hotuna masu kyau dan wad’ann hotunan a manyan mujallu zasu fito.. Mrs Haidar Maitama.” Ta kashe mata ido guda tana fad’in a d’auke su tare." "Mommy ta k’araso tana dubanta kwalla kaman zai zubo mata ta k’arasa ta rungumeta “Kinyi kyau daughter.. May yours be among the best.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. Nan aka d’auke su hoto. K’wallan da Ummul take makalewa ya gangaro. Mommy tai saurin goge mata tana girgiza Kai “A’a Ummul, yau fah ba ranan kuka bane.. Bana so hawayen nan ya bata Miki kwalliya.” Ta waigo cikin k’ok’arin danne nata kukan tana tambayar wai ina Haidar d’in ne.?" Anisa da takaicin acting Mommy ya isheta sai ta juya ido tana furzar da huci. Tana k’ok’arin barin wajen ta hango Haidar na shigowa cikin shiga ta farar shadda k’al babbar riga harda hula. Shigan da zata iya cewa bata tab’a ganinsa ciki ba. Sosai ya amshe sa dan ba Anisa kawai ba harta ita Ummul d’in saida ta shagala da kallonsa. Ya k’araso aka musu su uku da Mommy. Ta shige tsakiyar su ta rungumesu su duka biyun akaita kashe musu pictures. Daga bisani aka soma yima amarya da ango. Masu hoto suna bada direction. Aka ce ta d’aura hannunta guda saman chest d’insa sai ta d’an d’ago tana dubansa. Duban irin na mai yake nufi.? Ita fah har kawo wann lokacin bai mata magana ba gashi duk yanda aka ce ya rik’e jikinta kafin ma ace yayi. Wann fah shine mutumin da a baya he’s allergic to cameras. Ummul bata Ankara ba saiji tai ya d’ago hannunta ya d’aura saman chest d’insa. Anisa taji wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata makoshi. Ga wani kallo da suke bin juna dashi. A hankali take calming kanta cikin zuciyarta ‘Patience Neesa.! Patience.!! Na yau ne kawai.. Daga rana mai kaman ta yau ta zama tarihi a rayuwar Haidar dinki.’ Ta kuma murmusawa ‘I can’t wait for things to get chaotic.’ ** A can waje kuwa zabga zabgan bak’aken jeep d’in sukai parking. Motar farko Hajiya Asshe ce ta fito sai Inna Dije daga d’aya b’angaren. D’ayar motar kuwa daga can seat din ‘yanuwan Ummul guda biyu ne Badi’a da Azeema yayinda Umma da Mama Tani ke daga tsakiya. Suka neri suka fito sahu sahu. Kallo guda zakai ma Umma ka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki. Tayi tsuru tsuru da ido ko motsi mai kyau bata iyawa. Badia da Azeema kuwa kasa rufe baki sukai ganin irin gidan da Ummul wai take aure ciki.. Ummul fah. Wacce kowa ke gudunta cikin ahalin su. Wann maras sa’an.. Wacce ake mata lak’abi da mai farar k’afa.. Wann wacce maza da yawa ke guje ma Aurenta.. Allah mai iko. Gashi daga sauk’an su wasu ma’aikata masu uniform suka taho suna masu sannu da zuwa cikin harshen turanci cikeda ladabi suna amsan jakkunansu. D’aya daga ciki tai directing nasu zuwa masauk’i. Sukaja suka tsaya wann ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Asshe ta furzar da huci kad’an ganin duk sunja sun tsaya suna duban tsoro ma juna “Ku taho muje mana. Wai ko Baku gaji bane.?” Sai Inna Dije ta murmusa da shike ita ta tab’a zuwa lokacin auren Ummul. Tace “Kunga ba masu yankan kai bane ko Shan jini. Ku taho muje..” Sai Mama Tani wacce ta kasa gasgata wata duniya ma tukunna take ta janyo Inna Dije tana rad’a mata “Ke Dije.. Da gaske kike.? So kike kice min nan shine gidan da Ummul take ko kuma dai matar nan ta shanshantar damu ne gaba d’aya Kama Suwaiba. Dije nan fah fadan shugaban k’asa ne. K’ur’ani shine a talabijin nake gani.!” Ta k’arashe harda dangwala yatsa saman harshe. Inna Dije taci gaba da janyo Mama Tani tana fad’in “Kin dai gani da idonki.. Na tabbata bazaki so ki bar Ummul cikin wann daula ba. Duk bala’in da za’ayi bazamu fice daga gidan nan ba saida Ummul.” Cikin sigan rad’a suke ma juna magana. Duk maganar da sukeyi ita dai Umma bama tasan mai ke faruwa ba jefa k’afafunta kawai take tana tuna kalaman Asshe a gareta tana tuna a daidai wann rana sukai AUREN WATA UKU da tai ma Ummul da d’ansu zaizo k’arshe. Azeema da abin ya fara bata tsoro ta dan jada baya tana janyo ‘yaruwarta Badia. Tai k’asa da murya “Badia nifah wllhi naga gidan zama.. Wllhi bazan koma Kano ba ina nan tareda ‘Yaruwata.!” Badia ta dara kad’an tace “Toh kiyi yaya da Habibinki kuma idan ya dawo miki.?” Azeema ta galla mata harara “A’a Mak’iyi dai ba Habibi ba. Ai ni idan kinga na fice a gidan nan saidai idan fadan shugaban k’asa zan tafi..” Badia ta kuma darawa daidai sanda suka isa guest section din. Asshe ta dubesu tace su saki jiki su huta ga abinci dama tuni an jere musu idan da akwai abinda suke buk’ata ga ma’aikata zasuji dasu. Zata shiga cikin gida ta sanar da isowarsu. Inna Dije ne kawai ta amsa mata yayinda Mama Tani ta rakata da harara duk cikin acting ne da suke dan su shashantar da Umma. Badia da Azeema kam basu tsaya sauraronta ba suka tashi suka soma zaga gida suna kallon aljannar duniya a cewarsu. Bayan ficewar Asshe jikin Umma yaci gaba da rawa. Ba tareda ta dubesu ba take fad’in “Yau ne.. Yau ne tai alk’awari.. Wa’adin auren zai cika.. Yau d’ansu zai sakar mun Ummul d’ita.. Zan d’auki Ummul d’ita mu tafi.. Shine kawai abinda ya kawoni..!” Mama Tani da Inna Dije suka dubi juna.. Tani tuni shiga bud’e buden kayayyakin abincin da aka jere musu Wanda da yawa ma bama ta tab’a ganin irinsu ba. Da ta ga dai bata gane wasu abun ba sai ta d’auki Wanda takeda tabbacin naman kaza ne ta soma gwagwiya dama Tani da kaza. Tana ci tana Zare ido kaman za’a k’wace. Ta dafa Umma “Shiyasa na rakoki ‘Yaruwata. Kinga wann mata mai zubin akwati (Wai Asshe) kina ganinta kinga makira.. Wani abin take shirya Miki.. Ni da tuni kin sanar Dani ga yanda auren Ummul ta kasance ai da tuni anyita da wajewa an gama komai.. Haba Tani fah nake.!” Ta k’arashe tana kurban wani abu da bata tabbata kunu ne ko madara mai ‘yan’yan itatu ciki ba. Ta lumshe ido tana fad’in “Dole ace masu kudin nan kunci rabonku na Aljannah ehe.!” Inna Dije ta harareta sai ta dafa Umma tace “Suwaiba mu duka muna nan tare da ke bazan bari aci zarafin ‘yard’anuwana ba. Kafin su wulak’anta Ummul zamu d’auketa mu tafi dan kinsan masu kudin nan su wulak’anta D’anadam ba komai bane wajensu. Tinda auren ma a wulak’ance suka nema dan haka a wulak’ance zasu nemi rabuwa bacin haka meye dalilinsu na gayyato mu a wann rana da sukai alk’awarin kashe Auren. Kinga Suwaiba tashi ki shiga band’aki kiyo alwala.. Muje na nuna miki yanda ake amfani da irin bandakinsu kinsan ni na tab’a zuwa.” Ta k’arashe tana mai kamo Umma suka nufi band’aki. Ta nuna mata yanda zatayi kafin ta dawo ga Tani. Ta kafe ta da ido “Ke kuma Tani ba sallah ba salati kin fara ciye ciyen abubuwan da cikinki bai saba da irinsu ba.. Idan cikinki ya tsure kika kasa zuwa wajen shagalin bikin tozarta Suwaiba da ‘yarta saidai na kulleki a d’akin nan dan nidai billahillazi bazaki b’ata min shiri ba ehe..” Mama Tani ta saki gyatsa mai k’arfin gaske tace “Yo ka iya ibada ciki bai d’auka ba. Ibadanki ma maje ina Dije.. Yo naga k’eta ce da fansa ya kawo ki nan..” Inna Dije ta galla mata harara yayinda Mama Tani ta shek’e da dariya. ** "Jikin Mommy ya d’anyi sanyi. Ta kuma duban Asshe “Asshe kika ce harda Mahaifiyar Ummul akazo..? Asshe ina Jin nauyi.. Ina matuk’ar Jin nauyin bayin Allahn nan.. Mu ya kamata mu fara zuwa musu ba su ba.. Kuma a yanda na shirya da anyi bikin tariyar zamu d’unguma mu tafi gaba d’aya mu gaida iyayen Ummul da danginta musamman iyayenta.. Mu kuma musu godiya sann a k’ulla alak’a da zumunci mai kyau.. Munada shirin zuwa gaba d’ayamu.. Ni, Haidar harma da Engr da Kansa. Sun cancanci haka Asshe.. Dama kawai na buk’aci wasu daga cikin danginta suzo ne dan itama taji dad’i kar taga ba danginta ko d’aya wajen shagalin. Dan farin cikin Ummulkhair.” Duk jikin Mommy a sanyaye take maganar." Asshe ta furzar da huci kad’an tana mamakin dan dai Mommy batasan waye Suwaiba ba. Da bazata d’aga hankalinta kan wann shashasahar matar ba. Ta dan girgiza Kai “Aunty Kwaise ke ya kamata ki musu godiya ko su ya kamata su Miki godiya.? Yau kece zaki duk’a kiyi godiya ma talaka Aunty Kwaise.? Aunty Kwaise Anya kece kuwa ba’a canza ki ba.?” Asshe ta k’arashe tana bin‘Yaruwar tata da kallon mamaki. "Sai Mommy ta dubeta ta shiga jinjina Kai “K’warai kuwa ni ce Asshe. Saidai ba Kwaisen da kika sani a baya bane.. Wancan Kwaise da kika sani capitalist, maison mulki, izza da d’agawa ta tafi kuma bazata sake dawowa ba. Wann Kwaise ce da ta fahimci duniya da rayuwa. Kwaise ce mai Neman dacewa da tsira duniya da lahira.”" Asshe ta furzar da huci kad’an sai kuma tace “Aunty Kwaise nidai.. Da an kashe auren nan kawai mu basu d’iyarsu kaman yanda muka tsaro daga farko kawai a huta.. Aunty Kwaise wa’adin ya cika.. Kawai mu basu ‘yarsu kawai and save Haidar..” Ta k’arashe cikin rawar murya. Mommy sai ta d’an girgiza Kai kad’an cikin rashin fahimta “Save Haidar kuma Asshe. Kaman ya save Haidar.. If there’s someone to save here is Ummul. Balle ma boka makaryaci ne kinga dai yanda Al’amra suka kasance bayan mun bar hanyar b’ata mun kama hanyar gaskiya. Kinga bana ma so ana d’ago wann maganar kije ko da akwai abinda suke buk’ata sann kizo kimin iso na gaishesu.” Asshe ta kuma fruzar da huci “Wai Suwaibar zakije gaisarwa Aunty Kwaise.? Matar nan fah ko a ‘yar aikatau d’inki bata isa tazo ba.” Izuwa lokacin Zuciyar Mommy ya soma tunzura. A fusace ta dubeta wann karon “Matar da ta haifo Ummulkhairi idan ta kama na duk’a gabanta na mata godiya ne zanyi haka Asshe. Domin kuwa tinda Ummulkhair ta shigo rayuwarmu banda alkhairi babu abinda muke gani. Ke shaida ce a gabanki komai ya faru Asshe.. For years ina kuka kan ahalina.. Ahalin da na ruguza da hannu na.. Akan idonki Haidar da baisan hawa ba baisan sauk’a ba ya d’auki burden din da ba nasa ba tsawon rayuwa. Shin ba Akan haka bane muka tassamma kauce hanya.? Yau sai gashi cikin ikon Allah Haidar ya zauna da iyayensa lafiya. Ahalin da na jima ina mafarki ya dunkule waje d’aya. Ummul ta shigo ta farfado da duk wasu kyawawan d’abi’u da muka mance dasu ta cika gidan da nargartanta da alkhairanta.. Kinga kuwa ko duk’awa nai na mata godiya ban fad’i ba. Mahaifiyar Ummul ko wace iri ce Asshe tanada k’ima da mutunci a idona. Danginta ko yaya suke mun zama d’aya irrespective of our social differences. I expect you to do the same with them. Kin fahimta.!” Ta k’arashe cikeda umarni like a big sister. Zuciyar Asshe yaci gaba da tafasa. Ta kula Aunty Kwaise tsaf zata iya zab’en dangin Ummul ta mance ita ce danginta ta asali. Gaba d’aya itakam kaman an canza mata ‘Yaruwa. “Magana nake Miki Asshe..!” Mommy ta kuma tsawatar mata. Sai Asshe ta jinjina Kai da kyar tana k’ok’arin k’wak’ulo hawaye. Cikin muryar kuka take fad’in “Aunty Kwaise yanda kike magana kin fara bani tsoro.. Aunty Kwaise karfa k’warin gwiwar da kike dashi Akan yarinyar nan yasa ki mance komai.. Aunty Kwaise ni fah amana ce wajenki.. Iyayenmu Sun bar Miki amanata.. Banida wacce ta fiki kaf fad’in duniya.. Aunty Kwaise dan Allah kar ki tab’a mance hakan.. Idan kika rabu dani bansan ya zanyi ba… Duk abinda nakeyi kawai dan na damu dake ne.” Jikin Mommy ya d’anyi sanyi. Sai taji dan dafa Asshe “Haka ne Asshe. Idan ba mutuwa ba babu abinda zai rabamu ‘Yaruwata. Likewise banida wacce ta fiki. A lokacin kuka da lokacin dariya duk muna tare. Ta dalilinki Ummulkhairi ta shigo rayuwarmu Asshe.” Bata k’arasa sauraronta ba zuciyarta ya shiga tafarfasa. Dole dai sai ta ambaci wann mayyar yarinyar. Gaskiya ta fara yarda da batun su Dije yarinyar mayyace dan gashi ta lashe Zuciyar ‘yaruwarta. Sauri sauri Asshe ta nufi kiran Dije da Tani. Suka keb’e tana sanar dasu tsarin yanda zasu tarwatsa wann biki. Asshe ta rik’e kunne tana duban Tani da Inna Dije alamun kashedi “Kunaji biki ne na manyan mutane. Biki ne da zai samu halartan manema labarai. Dole ‘Yan jarida zasu sanin ‘yar gidan wane hamshak’i tilon D’an Aliyu Maitama yake Aure. Inaso da zaran manema labarai sun soma jefo muku tambayoyi ku fara amo duk abinda muka shirya.” Tani ta chab’i zancen da fad’in “Zan fed’e musu daga buzu Har fata. Zasuji wacece Ummul da kuma yanda auren Ya kasance. Wayyo wayaga Tani cikin talabijin tana bayani.” Asshe ta furzar da huci had’ida yin gajeren tsaki. Ta dubi Inna Dije alamun tana jiran nata ba’asin. Dije ta murmusa “Ita ce tayi sanadin mutuwan tilon D’a na Faizu sabida bala’in farar k’afarta. Maza bila adadi sun mutu ta dalilinta.” Asshe taci gaba da jinjina kai tana sakin murmushin cin nasara. ** Su Badia tuni Sun nufi cikin gidan suna fad’in a kaisu wajen Ummul. Da kyar Anisa ta kyale su suka shige wajen Ummul d’in a Cewar Anisa ana gyara mata kwalliyarta dan tuni ta canza zuwa wani shigan. Sai kallonsu take tana yatsina fuska tana toshe hanci wai dik warin talauci suke. Azeema tana hankalce da ita jira take su fito daga wajen ‘yaruwarsu Ummul suji da ita. Suna shigewa katafaren bedroom d’in suka tafi a guje suka rungume Ummul. Ummul wacce ta gansu a bazata sai ta mik’e cikin tsananin shock tama rasa mafarki take ko gaskiya. ‘Yanuwanta take gani. Sai ta rungumesu ta k’ank’ame tana mai fashewa da kuka. Saida tai mai isarta suna bata baki suna fad’in kar ta bata kwalliyarta. "Ummul ta kuma dubansu dan ta kasa yarda “Azeema, Badia.. Wai dan Allah kune.?”" Azeema ta murmusa tace “K’warai kuwa mune ‘Yaruwa. Kawo hannunki ma ki kuma tabbatarwa. Ta had’e hannuwansu su duka uku waje guda. Ummul ta murmusa tana share guntun hawayen da ya digo mata da tissue “Ina Abba na.. Ya jikinshi..? Ina Khulsum da Anty Salima.? Meyasa basu biyoku ba..? Ina Mama da Umma.?” Azeema da Badia suka dubi juna sai Badia ta kamo hannun Ummul tace “Abba jikinsa da sauk’i sosai Ummul.. Yana tashi yana zama saidai maganar ne da sauki. Sann har fita dashi waje yasha iska anayi. Abubuwa ne dai har yanzu ba kasafai yake ganewa ba. Likitoci sunce sai a hankali..Kinsan ciwo idan ya had’u da shekaru.” Ummul ta jinjina Kai a hankali tana addu’an samun lafiya ga mahaifinta. Azeema taci gaba “Anty Salima tana tana gidanta yaranta ba lafiya kyanda suke gaba d’ayansu. Amma tace muce Miki tana tayaki murna kuma taso zuwa Allah bai nufa ba. Mun taho da Mama da Inna Dije.. Da..” Sai Badia ta dan dubeta dan Umma ita ta rokesu cewa ko sunga Ummul cikin gidan kar su sanar da ita zuwanta tukuna. Basu kawo wani abu ba dan Umman ta kwana biyu cikin wane irin yanayi. Ummul sai bata tambayesu Umma ba dan tinda sukace Mama ta taho sai tayi tunanin Umma ke tare da Abbanta. “Khulsum fah.? Meyasa batazo ba..? Har yanzu tana fushi dani koh.?” Ta tambaya jikinta a sanyaye. Murmushin da yafi kama da yak’e sukai. Badia tace “A’a ko kad’an bata fushi dake Ummul…” Ta d’anyi fasali sai kuma tace “Ummul ki yafe mana duk abubuwan da muka Miki a baya..” Azeema ma ta saka baki suna rok’on Ummul yafiya. Dadi gauraye da farin ciki Ya mamaye Ummul. Ta kamo hannayensu tana fad’in komai Ya wuce Allah Ya yafesu gaba d’aya. Nan ta soma tambayarsu labarin gida. Badia ta d’an numfasa tace “Abubuwa da dama Sun faru a lokacin da baki nan.. Kedai sai mun samu lokaci kawai.. Yau ranar ki ce bani so wann hawayen yaita b’ata Miki kwalliyarki na ‘yan gayu.” Cewar Badia tana k’ok’arin gyara mata fuskar. Azeema tace “Wai Ummul kece kika zama haka.? Kin ganki kuwa.? Saikace wata shahararriyar ‘yar gayu irin Wanda muke gani wayoyin mutane ana turawa..” Ta mik’e tana zaga d’akin Wanda Ya amsa sunansa wajen kyau da girma “Dank’ari mak’ari wani aikin sai amale. Rayuwa kenan Ummul kiga yanda Allah Ya sauya miki rayuwa lokaci guda.. Tabbas kinyi hak’uri kuma kinga ribar hak’uri.. Sai na tuna Zubairu dasu Hajiya Dudu irin tijaran da suka zuba lokacin da suka amshe lefenki dashi Zubairun. Ai wllhi yanzu kam saidai Zubairu yazo a direbanki.” Ta k’arashe suna darawa daga ita Har Badi’a. Ummul ta murmusa had’ida girgiza kai “A’a Azeema ni duk wad’ann kayan kyalekyalen basu dameni ba matuk’a akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya..” “Chab ai kudi sune kwanciyar hankali wllhi.. Yo ina cikin wann daular k’aryar bak’in ciki Ya tunk’areni ai.” Azeema tace tana mai hayewa saman gadon. Anisa ce ta banko k’ofa ta shigo tana fad’in maza su fice za’a k’arisa shirya Ummul. Azeema ta kuma harararta Tai k’wafa. Ummul ta kamo hannayen ‘yanuwanta tana sanar dasu kar su koma masauk’i su jirata nan parlor tana fitowa. Koda suka fito parlor Azeema dai bata zauna ba sai zagawa take tana bama idonta abinci a cewarta. A haka Anisa ta k’araso daidai sanda Azeema take tab’a wani k’aton flower vase. Anisa ta rausayar da ido tana fad’i a fili “Dealing with Ummul is already giving me a headache. Now I had to deal with these local champions.?” Ta rausayar da ido tana furzar da huci. “Excuse me.!” Ta darara ma Azeema tsawa. Azeema ta juyo da mamaki tana dubanta. "Anisa taci gaba da nunata a wulak’ance “That flower vase worth your entire family.. Tell me, idan kika fasa zaki iya biya ne.?”" Badia ta d’anyi k’asa da murya taceda Azeema tazo ta zauna su jira fitowar Ummul. Ta dubi Anisa tace “Kiyi hak’uri bazata fasa ba. Hararsu take daga sama zuwa k’asa kafin taja dogon tsaki ta shige tana toshe hanci. Azeema ta yunk’ura zata bi bayanta Badia Tai saurin rik’ota. “Ki k’yaleni na shayar da wann mai k’irar zabon mamaki Badia.” Badia ta girgiza kai “A’a Azeema yau ranar farin cikin Ummul ne bazaki b’ata mata da wani abu ba. Musamman fad’a da dangin mijinta.. Ki kyaleta kawai karma ki kulata.” Azeema Tai k’wafa “Wllhi darajar Ummul taci da nayi wasan kura da ita dan dama hannuna k’aik’ayi yake kwana biyu. Ban saba da wann salihancin ba.” Badia tace “Naji dai bazakiyi ba..” Ta k’arada inata so na tambayi Ummul ina surkin namu mu gaisa.” Daga can Azeema ta hango Haidar na tahowa dukda bata sanshi ba amma kallo d’aya ta masa ta gane shine angon. Sai ta shiga tab’a Badia tana fad’i a hankali “Ke wllhi gashin can yana zuwa.. Shine ango. Shine surkinmu.. Na shiga uku Badia kiga irin mijin da Ummul ta samu bayan duk k’alubalen da ta fuskanta saikace tauraron fina finan Hindiyan nan. Ummul ta had’a komai Badia kawai ta nemi lahira. Gaskiya na yarda da karin maganar nan da ake cewa Wani JINKIRIN alkhairi ne. JINKIRIN Ummul ya zama Alkhairi Badia. Wllhi ta amsa sunanta Ummulkhairi.” Jin Azeema duk ta zauce yasa Badia take mata k’afa kad’an dan ya kusa k’arasowa yanda suke. A hankali take furta “Ke meye haka wai. Ni dan Allah ki natsu saikace wacce kikai gamo sai sunbatu kike. Ki mata fatan alkhairi kawai.. Kinga gashi nan ya iso da alama d’akin da Ummul take zai shige.” Kafin Badia ta rufe baki Azeema ta mik’e ta hau d’aga masa hannu “Sirkinmu.!” Haidar ya juyo da mamaki sai ya shiga ‘yan waige waige yana tunanin kodai ba dashi ake ba. Azeema ta kuma nunasa da yatsa “kaidai sirkinmu.” Ta k’araso yanda yake bata daina washe baki ba “Mu ‘yanuwan Ummul ne.. Ni k’anwarta ce.. Waccan kuma dake zaune Yayarta ce Babanmu d’aya ai da Ummul..” Badia dake zaune daga saman sofa takaici ne ko kunyar abinda Azeema take ta ma rasa wanne ne d’aya take. Sai sukaga Haidar Ya murmusa ya fasa shigewa d’akin Ya nufo yanda suke. Anisa da k’arasowarta wajen kenan mamaki kaman ya kasheta ganin da gaske Haidar Maitama kema kucakan nan sannu da zuwa kuma fah ransa a sake. Wai anya ba’a canza shi ba kuwa. Tana tsaka da tunaninta ta sinkayo muryar Azeema tana fad’in “Sunana Azeema. Ni ce ta hud’u wajen Abbanmu ai.. Daga Ummul sai ni ke biye mata..” Haidar Ya jinjina kai har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Ya nuna Badia yace “And.. you are..?” "Sai Badia da Azeema suka dubi juna. Azeema ta k’araso da sauri tana rad’a ma ‘yaruwarta “Adda Badia, kinsan dai mudai boko rakiya mukayi dan na tabbata Har yau ko shakeki za’ai da kyar ki iya rubuta sunanki. Su Ummul da Khulsum ne masu kwakwalwar ganewa. Turanci fah yake miki.. Tambayarki yake Ya kike.. Kice masa you are fine. Haka nakeji ake fad’a. Kar ki masa shiru zaki disga Ummul.”" Badia tace “You fine.” Sai Ya d’an murmusa kawai yace “I’ll check on.. Khairy.. Sannunku da zuwa once again.” Azeema taci gaba da waving d’insa har ya shige. Badia ta fuzgota tana fad’in “Ke dan Allah wai meye haka ne.? ki kama kanki mana.” “Mutanen da muke gani a tv mun gansu a zahiri Har gaisar damu yake kice na kama kaina.. Ke Nifa yanzu ko unguwarmu na koma wllhi ba ma kowa zanke magana ba ehe… Kiji wani sunan yan gayu da yake kiran Ummul dashi.. Kai wllhi na Miki murna ‘yaruwa Kekam taki addu’ar ta amsu.” Badia ta girgiza kai “Allah Ya baki lafiya Azeema.” Azeema ta kyalkyale da dariya tana amsawa da Ameen. Anisa da takaici Ya cikata furzar da huci Tai tana barin wajen. Dik yanda zatai bazata bari sunan wad’annan Almajiran ya shiga guest list ba tin daga waje zata sa securities suyi watsi dasu. Ana shirin fita wajen event Anisa tai kicibis da Azeema a dan wani lobby. Sai kawai ta k’ara wayarta a kunne alamun tana amsa kira “I need to double-check the guest list because ba ko wasu shara bane za’a barsu su shiga. You know is a high class event.” Ta k’arashe tana aika ma Azeema harara. Zata wuce Azeema ta cakumo wuyarta ta dawo da ita baya “Toh ya ne.! nace ko kinada abin cewa ne.?” Ta k’arashe tana tunkud’a drink din dake hannun Anisar ai kaw ya zube ma Anisa a jiki ya b’ata mata expensive gown dinta. Mamaki ya hana Anisa rufe baki ganin bata ko tanka Azeema ba amma tai mata wann d’ibar albarka. Girgiza Kai Anisa take tana fad’in “No this is not happening.. Not my dress..!” Ta dubi Azeema dake nad’e hannu riga Kai kace zata d’aga wani abin ne tace “You ask for it.!” Tai maganar tana sakin huci tana k’ok’arin Kai ma Azeema Mari amma sai caraf Azeema ta rik’e nata hannun ta kuma d’auketa da maruka har biyu masu kyau. Anisa ta kuma zaro ido cikin mamaki. Saima Azeema ta soma bata tsoro ta fara tunanin jada baya zata gudu Azeema ta kuma jawota tana fad’in “Ashe k’aryar tashanci kike k’aramar maras kunya ba yanda zakije.” Anisa taji rik’on manyan yan dambe ta soma kokawan k’wace kanta tana fad’in “Let go.. let me go.. What are you doing you witch.. I said let me go.” "Wani d’aki mai kaman store Azeema ta turata ta janyo k’ofar da k’arfin gaske Wanda taga har wani d’an haske ya kawo daga wajen rik’ewar mai d’aukeda alamun wajen danna yatsa, sann harda wasu lambobi jiki. Bata tab’a ganin irin k’ofar ba. Sai ta d’an matsa da baya ganin k’ofan na haske." Anisa ta fara girgiza Kai tana bugun k’ofan tana fad’in ta bud’eta. K’ara Anisa ta saki tana Kama Kai sanin cewa da tai k’ofan Smartdoor ne. A fili take fad’in a taimaketa tana buga k’ofan. Azeema kuwa shek’ewa da dariya tai jin Anisa tanata ihu daga cikin d’akin sann ta kasa fitowa. Sauri sauri Azeema ta bar wajen tana kyalkyale dariya ga wayar Anisar da ya fad’i nan wajen sanda take k’ok’arin turata d’akin. Tasa k’afa ta kuma cilla wayar a gefe tai wucewarta abinta. Sai nishad’i takeji tayi maganin zabuwar can. Anisa taci gaba da bugun k’ofa tana neman d’auki ga wayarta can a gefe Hisham sai kira yake no response. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *47* *©️Sameena Aleeyou… * Da kyar Anisa ta samu d’aya daga cikin ma’aikatan gidan wacce k’ofan ke amfani da fingerprint dinta tazo ta budeta. Duk ta galabaita kwalliyar ma duk yaji jiki a fuskarta. Ba’a maganar daurin kai da tuni ta kwance. Haka ta fito a firgice tana neman wayarta. Can ta tsinceta gefen madubin console daga k’asa. Sauri sauri ta fice ma’aikatan na mata a dawo lafiya ko ta kansu bata kuma bi ba. Tana driving take dialing layin Hisham duk a d’imauce take. "Hisham yana d’agawa Anisa ta soma jero masa tambayoyi a gigice “Hish.. Hisham.. Tell me I didn’t screw up like always.. Tell me I’m not late.. Tell me, we can still execute our plans…I.. I’m just few minutes away from the venue.!”" Ga mamakinta muguwar murmushin nan taji Hisham yayi. Yaci gaba da fad’in “Do you think I’d let your stupidity ruin my plans.? I always have plan B for every situation Neesa.” Ya kuma murmusawa kafin yaci gaba “Too bad idan bakiyi sauri ba zaki iya rasa kallon show d’in.. The fall of Maitama’s.. The biggest scandal of their lives is just about to erupt.!” Ya k’arashe yana shekewa da dariya. Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Mai kake nufi.?” Ya kuma murmusawa “You wouldn’t want to miss the show.!” Yana ida fad’in haka ya datse wayarsa yana dariya. ** A can filin taro kuwa Haidar matsawa gefe kad’an yai sakamakon kiran Amininsa Hisham da ya shigo masa. Cikin nuna tsananin damuwa tamkar gaske Hisham ke fad’in “Banida wani zab’i ne Haidar dole na bar duk abinda nake na tafi gida na duba jikin Hajja.. Jikin nata ya d’anyi nauyi ne Haidar. Dan Allah Kai hakuri. Nasan ya kamata ace ina tareda kai a rana mai matuk’ar mahimmanci irin haka a wajenka.” Haidar ya girgiza Kai “Amma ka saurari kanka.? Maiyasa zaka bani hak’uri.. What’s more important than lafiyar Hajja.. Iyaye first kafin kowa Hisham.” "Mamaki ya kusa kashe Hisham jin yau wai Haidar ke d’aukan al’amarin iyaye da mahimmanci. Lallai ya yarda rayuwar Haidar ta fara d’aukan saiti bazai tab’a bari wann ahalin su dunk’ule waje d’aya ba. Sai ya dan jinjina Kai yace “Haka ne Haidar.. A gaishe mun da amarya ace mata ina nan zuwa gaisuwa da cin girki in sha Allah. Allah sa ta iya abincin gargajiya kasan nan nafi wayo ni, dan mijinta dai bature ne..!" Gajeren tsaki Haidar ya d’anyi “Kai komai sai ka saka wasa ciki. Ka gaisar mun da Hajja sosai. Idan tana iya amsa waya ka had’amu mu gaisa.. In sha Allah zan samu time nazo na dubata.” Katse kiran yai bayan Sun gama kafin ya nufo wajen motar yanda Ummul take. Amarya da ango na k’arisowa media suka masu chaa suna nema ji ta bakinsu. Saidai securities basu wani basu chance ba balle su samu daman magana dasu.. Sann tuni Mommy ta hana wani d’an jarida shiga wajen taron Wanda hakan ba k’aramin tada hankalin Asshe yai ba. Shirinsu na barazanar rugujewa. Hannunta rik’e cikin nasa suke tafe. Haidar kaw tin sauk’owarsu a mota yake karantarta. "Tafiya take tana ganin kaman duniyar na juya mata, ji take kaman dai wani babban al’amari ke shirin faruwa da ita. Gani take kaman duk illahirin jama’an dake wajen ita suke kallo. Jiri ya d’an d’ebe Haidar yai saurin tarota ta fad’o jikinsa. Cikeda kulawa ya rik’eta sosai “Are you.. ok..?”" Sai ta d’an jinjina masa Kai. Har lokacin rik’e yake da ita. Cikin rashin gamsuwa ya dan girgiza kai “But.. You almost fell..” Ganin yanda ya rik’eta ga idon mutane akansu duk sai taji kunya ya cikata. Tai saurin girgiza Kai tana yin k’asa da kanta shi kaw na dad’a rank’wafo da Kansa dan ya saurari abinda take cewa. “Kar ka damu k’alau nake.. Inaga takalmin ne kawai da ban.. Ban saba tafiya da irinsa ba.” Ta fad’i duk a dan daburce cikin k’ok’arinta na ganin ya k’yaleta. "Maimakon ya sakarta saima sake rik’eta da yai, ya kuma girgiza Kai yana kallonta sosai “You look pale.. You sure you’re fine.?”" Jinjina masa kai kurum tai ba tareda ta iya amsa sa ba. Sai Ya k’arada “Have you had lunch.?.” Shiru batace dashi komai ba saima yan waige waige da ta soma kanta a k’asa dan gani take kaf mutanen dake wajen su kawai suke kallo. Muryarsa ta kuma sinkayowa “Wait.. Have you been skipping your meals..?” Sai tai k’arfin halin girgiza masa kai. Ganin dai idan bata amsa sa ba bazai daina jefo mata tanbayoyi baz Da kyar ta iya furtawa a hankali “Lafiya nake… Naci abinci… Kawai kar ka damu.. Ina so na zauna.” Bai kuma cewa komai ba sai d’an jinjina Kansa da yai ba wai dan ya gamsu ba. Ya sakalo hannunta suka k’arasa wajen da aka tanadar domin su. "Bayan an sanar da zuwan amarya da ango, manyan bak’i da sauransu.. Nan aka soma gudanar da shagalin biki.. Asshe ta fito da niyyan gabatarwa kwatsam taji microphone baya aiki. Ta kalli microphone da mamaki tana kuma jijjigasa domin kuwa da kamar wuya abu irin haka Ya faru wajen taron da ya amsa sunansa ya kuma samu halartar manyan bak’i na musamman. Bata ida juya speaker ba taji sautin tafi ta bayanta. Juyawan da zatai da tsanani mamaki sai gani Tai k’atoton screen d’in dake bayanta wata budurwa ta bayyana." Yayinda hankalin kowa yayi wajen. Dareen taci gaba da tafi cikin screen tana takawa. Lokaci guda take fad’in “Surprise.! Surprise.!! Ga Wanda basu sanni ba sunana Dareen.. Kuma Mata ga Haidar Maitama wacce mahaifiyarsa ta k’uduri niyyan raba Aurenmu.” Wann ya kalli wann wancan Ya kalli wann. "Dareen taci gaba “Wann taron bikin da ake, an ginasa ne bisa cin amana, yaudara da kuma zallan k’arya.. An ginasa ne dan tarwatsa wani Auren. An ginasa ne dan a kashe nawa Auren da Haidar.. Haka ne Hajiya Kwaise Maitama.?”" "Mamaki Ya hana Mommy motsi sai kallon screen din da take, yayinda Dareen taci gaba “Saidai abinda baki sani ba Hajiya Kwaise wann Auren da kikayi ma Haidar dan ki raba namu Auren bazai dore ba bazai je ko ina ba domin kuwa an gina auren ne bisa zalunci.. Dan kawai a raba masoya guda biyu. Ina nufin ni da masoyi na Haidar..” Taci gaba da murmushi “And now more than ever Aurenmu da Haidar bazai tab’a mutuwa ba Kinsan dalili Mommy.?”" Zukata sukaci gaba da bugawa. Mamaki da al’ajabi yaci gaba da bayyana tsakanin fuskoki. Yayinda video d’in Dareen yaci gaba “I am pregnant.! I am three months pregnant.. I am carrying your grandchild Hajiya Kwaise.. Your son’s child. Ina d’aukeda juna biyun Haidar har na tsawon Watanni uku.!” "Ba Haidar da yai mutuwar zaune yana duban Screen din ba, ba Ummul wacce ta koma tamkar mutum mutumi tana kallon abinda ke faruwa tamkar ba zahiri ba baga Mommy da ta koma tamkar hoto a wajen.. Baga su Tani da suka maida kawunansu k’anun alhaki ba sakamakon ganin abinda ke wanzuwa kan idonsu. Kai duk wani mahaluk’i dake wajen Daskarewa yai yana kallon ikon Allah.." "Dareen taci gaba da murmushi cikin video d’in “Haidar my love.. I am carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. You are going to be a father my love.. Zamu zama iyaye.. Ba haka naso na sanar dakai ba sai dan naga an shiga tsakaninmu da yawa.. Na sani this is going to affect your family business somehow.. But believe me, I didn’t mean to jeopardize your business.. Please forgive me my love.” D’iff screen din ya d’auke." A daidai lokacin Anisa ta k’araso ta tadda wann babban shiri da Hisham yai. Cak Anisa ta tsaya tana sakin murmushi tareda jinjina ma shed’anancin Hisham. Asshe ta mik’e a firgice ta nufi yanda MC da sauran masu kula da event suke tana fad’in “What’s this.. What’s the meaning of this.. Who’s in charge of the event.. Wai meke faruwa ne.. Ya akai haka ta kasance..?” Kowa yace bai san Ya akai aka sabotaging event din ba. Baga securities ba baga MC’s da sauransu ba. "Anisa ta saki murmushi sanda ta hangi Azeema. Ta shiga shafa b’arin fuskarta yanda shatin yatsun Azeema suka bayyana sakamakon marin da ta mata. A zuciyarta tace ‘Baki mari banza ba. Zan nuna miki barikin gaske.. Anisa nake, I always get what I want.’ Ta kuma murmusawa. Lallai dole tayi amfani da wann damar. Sai ta k’araso tana kuka tana rik’e Mommy tana fad’in “Mommy ni ce wacce ta kamata tai coordinating komai a wajen nan kaman yanda kika amince mun, amma wancan munafukar ta kulleni a gida sai yanzu na samu na k’araso.. Ma’aikatan dake cen gida sune shaiduna.. Mommy I’m sure bakinta d’aya da duk Wanda sukai sabotaging event din nan.. Ita ta taimaka musu ta rufeni a d’aki dan su samu saukin executing plan dinsu. Mommy ki yarda dani da shirinsu suka taho wajen nan.” Tai maganar tana nuni da Azeema." "Duk jijjiga Mommy da Anisa take Mommy bata iya cewa komai ta koma tamkar hoto, ko motsi k’akk’wara bata kuma yi ba tin bayan da Dareen ta bayyana cikin wann faifayin. Sai kawai AnisaTa tafi aguje zata shak’o Azeema tana fad’in she’s working with the people that sabotage the event. Ta shiga kiran securities tana fad’in su kama Azeema ita zata fad’i wad’anda take ma aiki wad’anda suka sakata ta kulleta a d’aki sabida kar ta samu damar halarta wajen event din." "Haba nan fah Azeema ta shiga kururwa tana fad’in ita wllhi bata san komai ba bata san kowa, sann bata aiki ma kowa. Mama Tani ganin securities sunyo kan ‘yarta ta nufesu cikin k’ok’arin k’watan ‘yarta tana fad’in su rufa mata asiri kar su kulle mata ‘ya ta d’and’ani zaman gidan yari bazata so wani nata ya kuma d’and’ana ba. Gaba d’aya taro ya yamutse ya hargitse ya rikice." "Kasa komai Haidar yai har lokacin idonsa na kan screen d’in dikda ya d’auke. Har lokacin Dareen yake hangowa cikin screen d’in. Wacce rabonsa da ita tin ranar da suka samu had’arin mota shida Ummul, exactly two months back kenan.. Kalmarta na cewa tana d’aukeda Juna biyu shine yaci gaba da duka dodon kunnensa." Wajen taro ya yamutse ya watse. Masu tsegumi nayi masu nad’an rahoto nayi domin kuwa abun nema ne ya samu. Asshe ce ta janyo Mommy wacce har lokacin bata komo daidai ba duniyarta na nema juya mata sama ya koma k’asa. A daidai lokacin Umma da Inna Dije suka take masu baya. Can wani k’aramin lambu na shak’atawa dake daga cikin gidan ta baya kad’an Asshe ta k’arasa da ‘yaruwarta tana k’ok’arin zaunar da ita Umma ta k’araso ta rik’o hannun Asshe tana kuka “Ina zakuje.. Ina zaku gudu kuje ba tareda kun sanar dani makomar Auren D’anku da ‘Yata ba.?!” Sai Mommy ta d’ago tana duban Umma dukansu biyu hawaye ne saman fuskokin su. Daga can nesa Anisa ke hango su kawai sai ta saki murmushi ta koma da baya. A can wajen taro kuwa Mik’ewa Ummul tai ba tareda tasan ina take jefa k’afafunta ba. Caraf Anisa tasha gabanta. Ta dan girgiza Kai kad’an tana duban Ummul d’in “This is life of the rich.. Surrounded by scandals.!” Ta d’ago gajiyayyun idanunta tana duban Anisa. Sai Anisa daketa k’ok’arin k’wak’ulo hawaye ta isa ta rungume Ummul. Ta fashe da kuka tana fad’in “I’m here for you Ummul.. I’m here for you. Ciwon ‘ya mace na d’iya mace ne.” "Ummul bata motsa ba sann batace komai ba sann babu wani abu mai alamun kuka ko hawaye cikin idonta. Idanun ne kawai a bud’e amma ita kanta bata san wace duniya take ciki ba. Anisa ta dubeta tace “Ummul mu bar maganan scandal din da matar Haidar tayi.. Na fad’a Miki, rana irin wann nake tsoron zuwanta.. Su d’in Sun jima suna b’oye abubuwa.. Taho muje.. Muje.. Ki gani da idonki ki kuma ji da kunnuwanki.. B’oye b’oye ya k’are.” Ta k’arashe tana janyo hannun Ummul wacce har lokacin bata um bata um um. Tafiya kurum take Anisa na janyota. Anisa ta kauda fuska gefe tana wata muguwar murmushi Wanda idan ba ita Anisar ba ko wanda suke shirya abubuwa tare ba lallai wani ya fahimta ba. Daga can gefe da yanda su Umma, Mommy, Asshe da kuma Inna Dije suke suka ja suka tsaya." Umma taci gaba da girgiza Kai tana fad’in “Ba haka mukayi dake ba Asshe.. K’warai nasan yau ne wa’adin Auren zai cika Shiyasa da kuka shirya biki jiki na ya bani bikin mutuwar Auren kuka shirya..! Wacece wancan matar kuma meyasa kukayi ma D’anku AUREN WATA UKU da d’iyata? shin kunyi masa Auren domin mahaifinsa ya basa wani kwangila wajen aiki ne. Ko kuma dai Kun masa AUREN WATA UKU da d’iyata dan ku raba Aurensa da wancan matar tasa ce.?” Mommy taci gaba da girgiza Kai tana hawaye. Yayinda Inna Dije ta k’yalla ido ta hango su Ummul sai ta dubi Umma ta fara fad’in “Kar kiyi wani dramarki na k’arya a nan Suwaiba. Kowa ya kwana da sanin zakiyi fin haka idan Akan Auren da kika kudiri niyyan yima Ummul ne..!” Taci gaba da huci “Kina so ki ce mun ba da hannuwanki kika saida musu Ummul ba.? Kina so kice kin mance tsananin son da kike Ummul tai aure ko ta halin k’ak’a zaki iya jefata cikin ko wani irin Masifa da sunan Aure.! Suwaiba harta ‘yarki Ummul tasan zaki iya mata ko wani irin Aure matuk’a zatayi Aure ta bar gabanki..! Ta shiga nuna Asshe tana fad’in “Wann matar ta sanar Dani komai Suwaiba.. Ta sanar Dani yanda kika wulak’anta d’iyar D’anuwana kika saida musu ita dan a karya asirin da wancan shed’aniyar matar D’an nasu ta masa.! Ta sanar Dani yanda kika basu Auren Ummul domin ta zamto makarin asiri.! Ta sanar Dani cewa Boka shine ya basu lak’anin cewa su nemo ma D’ansu mace mai irin matsalar Ummulkhairi wacce maza ke guje ma Aurenta. Irin wann budurwar ita ce irin macen da za’a karya asirin da akai ma D’ansu da ita.. Ta sanar Dani yanda idonki ya rufe kikayi ma Ummul AUREN WATA UKU.. Auren mutuwa..!” Baki na rawa Umma ke girgiza Kai “Auren mutuwa kuma Dije.?” Inna Dije ta d’aga mata hannu alamun dakatarwa “Har haka kika tsani Ummul Suwaiba..! D’anuwana yana kwance yana jinya kika d’auki Ummulkhairi kika saidata dan ta zamto makarin asiri kamar yanda Boka ya fad’a ajalin Auren na tareda ajalin Ummul cikin watanni uku. Kaman yanda Auren D’ansu da wancan shed’aniyar zai Mutu haka Ummul zata Mutu tare da wancan Auren.!” Sai Umma ta d’ago cikin tsananin daburcewa Jin Dije tana zayyano kalaman da batasan dasu ba dan a nata iya sanin Auren kwangila sukayi ma Ummul da D’ansu wanda Auren zai faru ne kawai na tsawon watanni uku dan mahaifinsa ya basa kwangila. Umma taci gaba da girgiza Kai bakinta ya kasa furta koda kalma. Mommy da hawaye suka wanke mata fuska sai ta soma girgiza kai. Murya na tsananin rawa take furta “Wann duk haka ne kafin mu gyara niyyarmu.. Bayan da muka fahimci Allah shi keyi ba Boka ba. Wllhi tuni mun mance wancan shirin namu kuma Aure na tsakani da Allah nake fata da burin Haidar yayi da Ummul. Ita d’in Alkhairi ce ga ahalina.” Anisa ta juyo ta dubi Ummul wacce har lokacin ko motsi batayi sai kallon Ummanta da Mommy da take ga wasu hawaye suna sauk’owa zuwa k’uncinta ba tareda ta iya koda k’ifta ido ba. “Yau kin yarda dani Ummul.. Bayan tsawon lokacin da na d’iba ina k’ok’arin fahimtar dake soyayyar bogi da Mommy ta jima tana nuna miki.? Matar nan ‘Yaruwar Mahaifiyata ce nasansu farin sani na kuma san zasu tafi da nisa koda zasu kashe rai ne dan su samu biyan buk’atansu.. Na fad’a miki idan ranan tazo zaki yarda ni kad’ai ce na zauna dake bisa zallan gaskiya a cikin gidan.” Bata kuma tsayawa sauraron Anisa ba. A hankali ta soma takawa zuwa yanda suke duk sai suka juyo suna dubanta. Kai tsaye gaban mahaifiyarta ta tafi ta tsaya. Umma ta d’ago idonta mai zuban ruwa tana duban Ummul tana girgiza Kai. Har lokacin idon Ummul Akan Umma “Wann shine dalilin ki Umma..? Wann shine dalilin da.. Yasa.. Kika hana na waiwayi gida sai bayan Watanni uku..? Haka ne Umma.?” Muryarta yaci gaba da rawa . Yayinda Umma taci gaba da girgiza kai tana hawaye tamkar wacce aka d’aure harshenta. Duk sunyi shiru sai zuban hawaye. Mommy ma ta kasa tsaida nata hawayen. Ummul taci gaba “Na kasance inada kurakurai na amma ba ni na zab’i k’addarata ba..” Muryarta yaci gaba da rawa “Umma nayi k’ok’arin na kasance ‘ya mai biyayya a gareki.. koda a wasu lokutan Babu Wanda zai fahimceki nakanyi k’ok’arin na fahimceki.. Sabida ke d’in mahaifiyata ce..” Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye “Duka rayuwana k’ok’ari nake naga na faranta ma mutanen dake kewaye dani.. koda hakan na nufin na mance kaina.. Na kasance banida wani fata nawa..” Taci gaba da girgiza Kai “Auren karya sihiri..! Auren mutuwa..! Auren wata uku..!” Sai ta soma girgiza kai sosai “Ki gafarceni Umma.. Ki gafarceni..!” Umma tai yunk’urin bin bayanta amma inaa ta wuce cikin gidan a guje tana kuka sosai. Mommy tai saurin rik’o Umma tana fad’in ta kyaleta abi komai a sannu. Ummul shiga cikin gidan kawai take ba tareda sanin ina take zuwa ba har saida ta isa wani bedroom.. Tana shigewa ta maida k’ofan ta rufe ta silale nan wajen tana mai fashewa da wani irin kuka. Sam bata kula da Haidar dake zaune shattered k’asa a d’akin ba. K’afafuwansa mik’e a k’asa ga babbar rigarsa a gefe. Sosai take kuka tana girgiza Addu’a take cikin zuciyarta Allah yasa mafarki take. Allah yasa zata farka daga wann mummunar mafarkin.. Mahaifyarta.. Ashe har mahaifya zata iya jefa ‘yarda ta haifa cikin irin auren da ta jefata.. Shin har haka Umma take so ta bar cikin rayuwarta.? Umma ta mik’ata ayi tsafi da ita.!’ Sai ta rintse idonta sosai tana jin wani irin tashin hankalin da bata tab’a tsintar kanta ciki ba. A haka Haidar Ya rarrafo gareta. Duk a tunaninsa maganganun da Dareen tayi ne Ya jefa Ummul cikin wann yanayi baisan idan maganganun Dareen Ya jefata cikin rud’ani da firgici bai kama k’afan abinda taji mahaifiyarta ta aikata mata ba. Haidar ya shigar da ita cikin jikinsa tana kuka shid’inma k’ok’ari ne kawai. Sosai Ya matseta cikin jikinsa yana fad’in “Let it all out.. Na cancani duk hukuncin da kika mun amma kafin ki hukuntani.. Zan so ki saurareni.. Hear me out first please..!” Tana nan cikin jikinsa su duka biyun suna zaune k’asa. Saida tayi mai isarta kafin ta soma furtawa a fili “Labarin duka k’arya ne.. Babu wani gaskiya cikinsa...” Haidar Ya kuma matseta cikin jikinsa “Akwai abu d’aya da yake gaskiya cikin labarin.. Shine soyayyarmu.. The love that I have for you Khairy.. I.. I love you.. I love you with everything I am..” Jin kalaman take har k’wak’walwarta. Ta cire jikinta daga nasa tana dubansa. Sai ta girgiza kai “Shin kana sane da cewa AUREN WATA UKU suka mana.?” Haidar da baisan da batun warware sihiri ba. Saidai yanada masaniyar AUREN WATA UKU na yarjejeniyar project da sukai da Mommy. Sai Ya soma k’ok’arin kauda fuskarsa kaman yana avoiding kallon idon Ummul d’in. Mamaki Ya cika Ummul. Ta dan girgiza kai kad’an “Kasan da labarin AUREN WATA UKU.?” Sai Ya lumshe idonsa a hankali Ya shiga jinjina kansa alamun haka ne. Kawai Ummul sai ta soma girgiza kai tana ja baya gareshi.. Tsoro ne firgici ne ta ma rasa mai takeji.. Haidar ya soma girgiza kai cikin kid’emewa yana k’ok’arin nufota “But you need to listen to me first Khairy..” Dakatar dashi Tai ta hanyar d’ago masa hannu. Muryarta na tsananin rawa “Kar ka masto yanda nake.. Kar ka k’araso yanda nake.. Gaskiya ne.. Cikin labarin gaba d’aya ni kad’ai aka shashantar..!” Haidar bai fasa nufota ba yake fad’in “Khairy please listen to me.. Please hear me out first.. Allah shine shaida na.. Nayi niyyar sanar dake komai yau d’in nan.. Ciki harda Aurena da Dareen da kuma yanda namu Auren Ya kasance.. Dan Allah ki saurareni.. Na sani ni mai laifi ne.. But ki saurareni first.” Jikinta Har rawa yake bata daina k’ok’arin dakatar dashi da hannunta ba “Kar ka k’araso yanda nake.. Bakada sauran abinda zaka sanar dani dan naji komai.. Auren.. Ya cika watanni uku a yau d’in nan… Ya cika wa’adinsa.. Ba abinda yai saura.. Lokaci yayi da zamu fice daga rayuwar juna.” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa ta isa k’ofa. Haidar ya tafi da sauri yai ma k’ofar lock. Yaja Ya tsaya. Huci take tana dubansa shima d’in huci yake yana dubanta. “Ka bud’e min k’ofa na fice ni ba matarka bace dan wa’adin Auren Ya cika.. Ko baka gani bane.!” “Ank’i a bud’e d’in baza’a bud’e ba.. Nace ki saurareni first kafin ki yanke duk wani hukunci.. And one more thing.! Kar ki sake cewa ke ba matata bace.!” Taci gaba da huci zuciyarta na mata rad’ad’i tasa hannu zata bud’e k’ofan Haidar Ya cire d’an makullin Ya jefa bayan gado. Ummul ta d’ago tana dubansa cikin wane irin yanayi da bai tab’a ganinta ciki ba “Ka bud’e mun k’ofa na fice..!” “Baza’a bud’e ba.! Ank’i a bud’e d’in.. Na ce ki saurareni muyi magana.” Rintse idonta Tai ta toshe kunnuwarta sai ta fashe da kuka sosai “Bana so.. Bana so na saurari komai daga gareka..! Kawai ka bud’e mun k’ofa ni na fice.. Na tsaneka..! Na tsani ganin wann fuskar taka balle sauraron muryarka.!” Sosai kalamanta ke masa zafi.. Sosai zuciyarsa ke masa zafi.. Bai bari takai aya ba ya k’araso da sauri ya rufe bakinta da nasa.. Ta shiga turasa da duka k’arfinta amma kaman zugasa take. Duk iya k’ok’arinta na ganin ta hana Haidar abinda yake k’ok’arin aikatawa ta kasa. Haka Ya rik’e bridal gown dinta ya k’eta da k’arfin gaske. "Ba a haka yaso zuwa mata ba. Ba haka yaso su shimfid’a tarihin soyayyarsu ba. Sam ba nufinsa bane ya saka mata force amma bazai iya jurewa ba, bazai iya jure kalamanta a garesa ba.. Idan hakan shine masa saura dan ta sauraresa zai aikata." Taci kuka har ta gode Allah. Sabon tsanar Haidar da illahirin ahalinsa Ya kuma ruruwa cikin zuciyarta. Hannayenta ya rik’o cikin nasa yana shafa sumarta a hankali.. Idanunta a lumshe suke gashin idon duk Sun jik’e da hawaye still hawayen basu daina fitowa daga lumsassun idonta ba. Yaci gaba da Shafa gaban goshinta zuwa farkon sumarta da gumi yasa suka dada kwanciya luf. A hankali ya lumshe idanunsa ya sumbaci goshin nata “I.. I’m sorry Khairy… I didn’t mean to.. force myself on you.. But you forced me to..” Shiru yai ganin har lokacin idanunta a lumshe hawaye basu daina ziraro mata ba. "“Please don’t hate me.. Don’t hate me Khairy.. I grew up thinking.. My life was a complete mess.. Ba wani abu da yake gaskiya cikinta.. Duka k’arya ce kawai.. But then you came.. And changed everything..” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Idan akwai abu d’aya da yake gaskiya cikin rayuwana.. It is you Khairy.. Kece..!” Sai Ya d’an murmusa yana k’ok’arin maida kwallan da suka ciko idonsa “You know, For the first time in my life.. I experience true happiness.. You filled the emptiness inside me Khairy.. With you, I feel complete..” Sai ya d’ago yana dubanta sosai siririn hawaye ya gangaro masa “Punish me all you want.. But don’t say na rabu dake Khairy..I.. I just.. can’t bear the thought of it..”" Sai sann ta d’ago masa hannu alamun dakatarwa. Dan yanda kasan garwashin wuta haka takejin kalamansa. Ta bud’e lumsassun idanunta a galabaice. Ba tareda ta dubesa ba ta yunk’ura zata tashi sai taji zafi sosai daga k’asanta. Ta rintse idanunta tana jin wani kukan na zuwa mata.. Ba kukan physical wounds din dake jikinta take sai na rad’ad’in da zuciyarta ke mata. Haidar yai k’ok’arin taimaka mata ganin tana so ta mik’e amma sai yaji muryarta cikin kuka “Kar ka tab’a ni.. Na rok’eka kar ka sake d’aura koda d’an yatsa a jikina.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin mik’ewa. Ya zuba mata ido yana dubanta zuciyarsa zallan k’aunarta da tausayinta ne. Yanaji yana gani yana son taimaka mata Babu hali. A haka ta lallab’a ta bud’e k’ofan da take tsammanin bathroom ne. Nan kuwa taga shid’in ne ta shige Haidar na binta da kallo har ta b’ace ma ganinsa. Ya lumshe idanunsa yana mai furzar da huci had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Ya maidoda dubansa kan bridal gown d’inta da Ya b’aci da stain. Ya kuma lumshe idanunsa yana jin wani abu kaman tsanar Kansa can k’asar zuciyarsa… A hankali ya furta “Oh no.! What have you done Haidar.!” Ya furzar da huci zuciyarsa na tuhumar sa ‘What if she hates you.’?.. Saurin girgiza Kansa yai bai so ma ya tuna. He needs to save their marriage at all cost. A b’angaren Ummul ma tana shigewa bathroom din wani sabon kuka ta fashe dashi. Zata iya cewa ita dai batasan wani abu soyayya ba sai akanshi.. Koda ace an gina Aurensu ba akan soyayya ba ta tsinci kanta da aukawa ma soyayyarsa.. A fili ta furta “labarin ya k’are ne Tun kafin ya fara dan na tsaneka Haidar.!” Ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. ** "A can gidan Hisham kaw cikin huci Ya mik’e kaman zai shak’o Dareen dake tsaye gabansa yake fad’in “You damn fool.. Na fada miki so nake ki sheganta wann tsinannen cikin jikin naki, kan wani dalili zaki jingina kanki da kalmar Aure tareda Haidar.. Auren da Boka ya Miki alwali… Auren da akai Haidar bashi a hayyacinsa. Tsakaninki da Haidar babu wani kalma mai sunan Aure a tsarina.! Wann shegen dake cikinki shege ne shid’in shege ne dole ki sheganta shi kaman yanda Kwaise Maitama ta shegantani ina jariri d’an wata uku a ciki.. Ina so tarihi ya maimaita mata Kansa cikin ahalin Maitama Akan jikan Kwaise Maitama. Taji zafin samun jika shege kaman dai yanda ta shegantani. Kin fahimtaaa..!” Ya k’arashe kaman zai shak’e wuyanta sai wani irin tururi yake." "Girgiza kai Dareen take tana huci tana Shafa cikinta “No.. No way Hisham.. Bazan tab’a abinda kake fad’I ba, bazan tab’a sheganta D’a na da Haidar ba.. Koda ace Aurenmu bai kasance kaman ko wani Aure ba wann cikin da Aure aka same shi.. Kuma shine abu kad’ai da zai maida Aurenmu da Haidar.. Ka cire wann a ranka.. Duk abinda zai faru Babu abinda zai hanani komawa ga masoyi na Haidar tareda D’anmu dake cikina. Zamu Gina ahalinmu as it should be.!”" Kaman daga suka sinkayo muryar Anisa “Wann kuma k’arya kenan.. Zancen banza kenan. Ban aikata komai ba ban sadaukar da komai dan wata kucaka irinki ta mallaki Haidar ba.!” Dareen ta juyo cikin tsananin mamaki tana duban wacce Tai maganar “And you.. Ke kuma wacece..?!” Anisa taci gaba da takowa “Ki kirani masoyiyar Haidar da ta sadaukar da komai tayi duk wani fad’i tashi dan ta mallakesa..!” Dareen ta juyo tana duban Hisham da mamaki “Hisham.. Wacece wann.. And what is she saying.?” Anisa ta katseta “Kar ki tambayesa. I am his accomplice.. Mu biyun tare muka shirya dawowarki cikin rayuwar Haidar dan kawai mu raba Haidar da matar da Mahaifiyarsa ta aura masa. Ki kirani masoyiyar Haidar sann ki kira Hisham da masoyin Matar Haidar. Mu biyun are team.” Ta murmusa “Ki yarda dani amfaninki Ya k’are kinyi abinda muka kawo kiyi Dikda naji wani babban kwafsi.. Ki sani koda ace cikin jikinki na Haidar ne bakida wajen zama cikin rayuwarsa. Haidar nawa ne ni kad’ai.!” Dareen ta juyo tana wani irin duba na cin amana ma Hisham dan batasan da zancen wata Anisa ba sai kawo wann lokacin. Ta soma girgiza kai tana jada baya “Lallai ka cika shed’ani Hisham.! Ka cika babban mayaudari.. You are a Demon.! Na kasa yarda na Barka kayi amfani dani dan cimma bak’in burinka akan Haidar a karo na biyu..! Amma ka sani wann shine zai zama na k’arshe.. Zan tafi yanzu.. Zan sanar da Haidar komai duk wani mugun k’ullinka akansa ko dan D’ansa dake cikina.. Bazan tab’a bari ka sake cutar da Haidar ba.. Zan sanar dashi komai koda zan rasa shi..!” Tana ida fad’in haka ta fice a guje. Hisham Ya soma k’ok’arin binta a guje yana kiran sunanta yana fad’in ta dakata.. Anisa tuni ta take masa baya. Koda suka fito Sun tadda Dareen Har ta bud’e gate ta fice.. Anisa ta shige mota tace da Hisham maza Ya shige su bi bayanta. Hisham Ya shige suka soma bin bayan Dareen dake gudu a k’afa tana saka hannu tana neman abun hawa. Saidai akai rashin sa’a babu alamun mutane a layin balle abun hawa. Dareen taci gaba da gudu a galabaice tana k’ok’arin tsere musu.. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *50* *©️Sameena Aleeyou… * "Wasa wasa an shafe sati uku da mutuwar Auren Ummul da kuma Haidar. A wann lokacin Daddy ya shafe a k’alla sati guda da dawo daga SouthAfrica, kuma labarin scandal din da yai erupting wajen bikin tariyar Haidar d’in Ya cimmasa. Hankalin Mommy duk ba’a kwance yake ba sanin mijinta mutum ne da ko kad’an baiso wani abu ya shafi Kasuwancinsa. Yanda rayuwar ahalinta Ya soma daidaita bata fatan abinda zai kawo musu wani mishkila ko sab’ani. Ga mamakinta sai Daddy ya tari abun bisa lumana ba kaman yanda Ya saba a baya ba. Dan ko zancen bai bata k’ofan ta masa ba dikda taso yi masa. Bai canza ko kad’an daga irin kulan da yake bata ba tin bayan da suka daidaita tsakaninsu. Hasalima k’ara janta jiki yai yana fad’in irin kewarta da yai. Ta d’an dubesa a sanyaye tana so suyi zancen sai Ya kuma janyo hannayenta yace “Kwaise na gaji da tafiye tafiyen nan. Inaga lokaci yayi da zan mik’a ma yaron nan ragamar kasuwancin.. Koda wani portion ne. We are not getting any younger.. Shekaru k’aruwa suke..”" Mommy ta jinjina kai duk jikinta a sanyaye. Alamun shigowar mota sukaji. Daddy ya lek’a window sai Ya murmusa yace “Ina tunanin Yaronnan ne … Na kira shi yana company.. Na sanar dashi Ya bar aikin da yake yazo gida magana zamuyi.” K’irjinta ya bada dam.! Dan tuni jikinta Ya bata ba magana mai k’aramin mahimmanci bane zaisa ya kirawo Haidar ya bar aikinsa yazo gida dan kawai suyi magana. “Let’s go downstairs..” Ta sinkayo muryar Daddy yana k’ok’arin nufan k’ofa. Jikinta babu wani k’wari tabi bayansa. A parlor suka iske Haidar Har ya k’araso yana jiran sauk’owa mahaifin nasa. Haidar ya risina ya gaida iyayensa. Duk suka amsa masa da sakin fuska saidai kallo guda zakai ma Mommy ka fahimci tana cikin damuwa. Daddy ya dubi Haidar cikeda kulawa “Aliyu.” Ya kirasa da asalin sunansa. Haidar ya amsa cikeda girmamawa. Daddy yaci gaba “Na dawo na taradda abubuwa marassa dad’in gani da kuma sauraro. Garin yaya al’amra suka lalace har haka.?” Haidar ya jinjina Kansa a hankali sai yace “Daddy Kai hak’uri.. Ban.. san abubuwa zasu zama haka ba.. Amma tuni nasa jam’ian bincike su binciko yanda Dareen take.. Kai hak’uri Daddy.. Idan duka wann ya saka Kasuwancinka cikin had’ari..” Daddy ya sauk’e ajiyan zuciya kad’an sai ya girgiza kai yace “Ba wann nake son ji ba.” Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yaci gaba “Ba batun Kasuwancina da abinda zai shafesa nake son ji ba.. A’a naka batun nake son ji.. Al’amarinka da iyalinka. Because you matters to me more than any business.” Haidar yaji wani abu can k’asar zuciyarsa. Yau Daddy ya zab’i ya fifita al’amarinsa sama da Kasuwancinsa da a baya yake d’aukakawa. Jikin Mommy yai sanyi musamman da taga Haidar yayi shiru. Duka laifin nata ne. Gwara ta sanar da Daddy yanda al’amarin ya kasance. Jiki a sanyaye Mommy tace “Dama..” Haidar bai bari takai aya ba yai karaf yace “Daddy scandal din da ya faru ya.. janyo sab’ani tsakanina da Ummulkhair.. Kuma har ta kaiga na mata saki.. d’aya.” "Sai Mommy ta dubi Haidar cikeda tausayawa.. Ta fahimci yasan duk abinda tai amma ya zab’i ya rufa asirinta. Bazai bari mahaifinsa yaji ga abinda ta aikata ba gameda AUREN WATA UKU. Allah sarki D’a da uwa. Sai taji girma , k’ima da soyayyan d’an nata ya k’aru a kwayan idonta. Fatan ta Allah ya albarkaci rayuwarsa Ya daidaita al’amarinsa da iyalinsa." "Daddy ya dan numfasa sai ya dubi Mommy yace “Rankidad’e, can I have a moment with my son.?” Ya k’arashe yana dan mata alama da ido." Mommy tace “Badai cireni akai daga cikin ahalin ba.” Ya dan murmusa kad’an “Waye ya isa ya cire ran gida cikin ahalinta. Magana ce tamu. Men talk.” Ta d’an murmusa “Kace dai kawai wariya. Toh bara na baku waje dama inada abinyi.” Ta k’arashe tana mik’ewa. Daddy yai gyaran murya kad’an yace “Haidar banji dad’in abinda kai ba dukda sanin saki a musulunci ba haramun bane amma sai idan Ya zama dole akeyi. Idan akace daga samu sab’ani za’a dinga saki da ko mu nan iyayenka bamu kawo har wann lokacin muna tare ba. Kai shaida ne.. Kaga k’alubale da iftila’i na rayuwa da mukaita fuskanta. Amma dukda haka muka jajirce. Har hakuri ta kawo mu yanda muke yau. All marriages have ups and downs but this decision should not arrive easily.” Sai Daddy ya mik’e tsaye kaman Wanda ya tuna wani abu “Kaga tashi muje.. Akwai yanda nake so ka rakani.” Haidar ya jinjina Kai yana amsawa. Suka jera suna tafe shida mahaifinsa. Ta window Mommy ta hangesu sun jera Sun fice. A ranta tace ko ina D’a da mahaifin suka nufa sai Allah. Ta murmusa tana jin dad’in yanda sabo ya fara shiga tsakaninsu. Koda suka fito Haidar ya tambayi Daddy ko Yai masa kiran driver d’insa amma sai Daddy yace a’a shi Haidar d’in zai tuk’a motar. Nan ma cikeda girmamawa Haidar ya amsa masa. Daddy ya shige mazaunin mai zaman banza yayinda Haidar ya shige wajen driver. Suna tafe Daddy yace dashi gidan Alhaji Gimba suka nufa. Kai tsaye Haidar ya d’auki hanyar gidan aminin mahaifin nasa. Koda suka isa Daddy yace da Haidar yai parking daga waje. Nan ma yabi umarnin mahaifinsa. Suka fito Daddy na d’an gaba kad’an yayinda Haidar ke take masa baya. Sai Haidar yaga Daddy ya nufi masallacin k’ofan gidan Alhaji Gimba. Suka gaggaisa da mutane ya tambayesu Ya Sheikh bai fito ba. D’aya daga cikin mutanen yace “Ai zai wahala Ya Sheikh ya fito yau sabida tun jiya yake cewa bai gane jikin ba.” Daddy yai masa fatan samun lafiya. Ya kuma yi ma mutanen Sallama Wanda kusan dukansu Dattijai ne kaman sa da ma Wanda suka fisa. Da alama duk sun saba dashi dan tare suke d’aukan karatu a nan masallacin tsakanin sallar magrib da isha wajen Imam ya Sheikh. Sun fito tareda Haidar kenan saiga Alhaji Gimba. Nan suka tsaya suna gaisawa. Haidar ya dan matsa gefe ya basu waje. Alhaji Gimba ya dubi Daddy ya dan girgiza kai “Lafiya dai naga ka taho tareda Haidar..?” Daddy ya dan sauk’e ajiyan zuciya yace “Lafiyan zance ba lafiya ba tinda kanada masaniyar abinda ya faru lokacin bikin tariyarsa da iyalinsa.. Tinda Har business competitors dinmu sun so suyi amfani da wann su sokemu.” Alhaji Gimba ya jinina Kai “Haka ne.” Daddy yaci gaba “Toh Wato abinda ke faruwa shine.. Wann abu da ya faru har ya haifar da matsala tsakanin shi Haidar d’in da iyalinsa.. Kuma kaga abu da yara tashi d’aya yayi saki.. Kasan da yawan samarin nan ba’a zama a fahimtar dasu menene ma Auren kansa kafin su shigesa which is wrong.. As a parent musamman ma Uba inaga yanada kyau idan D’anka yakai munzanin Aure ya kuma zo maka da batu na Aure idan Har zaka nemar masa Auren ‘yar wani. Ko dai kai ka zaunar dashi ka fahimtar dashi menene Auren kokuma ka kaisa yanda za’a zaunar dashi a sanar dashi Auren tareda hakkokinta da hukunce hukuncenta.. Dan nima har yau ina nadaman wasu kurakuren da nayi a baya kuma bana fata irin haka ya faru da D’a na. Idan ka duba da yawa yanzu Shiyasa zakaga mace macen Aure yayi yawa dan shiga cikin Auren kawai ake ba karatun sanin hukunce hukuncenta.. Shine kaga na kawo shi nan dan Sheikh Imam ya fahimtar dashi wasu abubuwa. Sai kuma akai rashin sa’a Sheikh yau bai fito majalisi ba.” Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Wann gaskiya ne Abokina. Ina ma iyaye da yawa zasuyi yanda kayi da an rage wasu mace macen Auren da babu gaira babu dalili. Amma tinda yanzu Sheikh baya nan ni zan zaunar dashi mu d’an yi magana ta fahimta.. Kasan kai zai iya jin nauyinka a wasu abubuwan.. Sann idan son samu shima kasa ya dinga zuwa d’aukan karatu ko ba lokacin da muke ba.. Akwai lokacin da aka Ware dan samari kaman shi. Lallai yanzu Babu mai zama da jahiltan addini sai Wanda yaso.” Daddy ya jinjina Kai “Wann haka ne.. Toh zan bar maka shi. Zan kira driver yazo ni ya d’aukeni.” Alhaji Gimba yace “Akwai driver na ai sai ya kaika.” Nan sukai sallama Daddy ya sanar da Haidar shi zai tafi "A d’an wani hut dake haraban gidan suka zauna yayinda Alhaji Gimba ya soma jan Haidar d’in da hiran Kasuwanci kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Haidar, ni aminin mahaifinka ne nasan kasan da wann.”" "Haidar ya jinjina Kansa a hankali. Alhaji Gimba yaci gaba “Kaman yanda musulunci yace abokan iyayen mu iyayen mu ne. Idan sunga munyi wani abu ba daidai ba zasu iya kiranmu su mana gyara.. Idan ma ta kama su tsawatar mana duk zasuyi.. Haka ne.” Nan ma jinjina kai Haidar yai. Alhaji Gimba yace “Ma sha Allah. wato Haidar, mahaifinka ya sanar Dani abinda ke faruwa, ba wai dan ya bud’e min sirrinka ba sai dan so da yake a samo maslaha.”" Haidar yai shiru yana sauraronsa. "Alhaji Gimba yaci gaba “Wato shi Aure wani abu ne da yakeda mahimmanci Haidar a rayuwar Al’umma gaba d’aya. Dalilai da dama suna sawa ayi aure haka dalilai da dama Suna sawa Aure ya mutu Wanda ba’a so. Daga cikin dalilan mun sani Aure ibadah ne bautan Allah ne kuma d’abbaka sunnnar Ma’aiki (SAW) sann duk Wanda ya d’auki aure matsayin ibada bautan Allah zai samu dacewa da tsira harma da farin ciki a cikinta. Hakan nan Aure yana sa kamewa daga fad’awa tarkon zinace zinace. Kaman yanda yazo a hadisin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara yarda a garesu. Yanda Manzo (SAW) yace yaku taron samari ga Wanda ya samu iko daga cikinku yayi aure. Shi aure yana tsare gani sann yana kame al’aura. Har yake cewa ga Wanda bai samu hali ba toh yayi azumi. Shi azumi garkuwa ne.. Sann dalili na gaba samun nagartacciyar Al’umma. Ta hanyar Aure ake haihuwa a samu Al’umma nagartacciya. Bazamu fad’ad’a ba amma kaga ko wad’ann muka d’auka Sun ishemu dalili. Haka zalika shi Auren nan ba’a barmu kara zube ba saida aka koyar damu yanda zamu zauna cikinta ta fuskar shari’a da koyarwar addini. Ta yanda d’aya bazai zalunci d’aya ba a cikin zamantakewar. Domin kuwa addinin musulunci addini ne mai kyau da tsari da kuma adalci. Haka zalika idan rabuwar Aure ta kama dole, Wanda ba’a fata toh nan ma saida aka koyar damu yanda zamu rabu bisa kyautatawa da mutuntawa.” Ya dan gyara zamansa kafin yaci gaba “In Islam, it is believed that married life should be filled with mercy, compassion and tranquility. Sann Zaman aure zo mu zauna ne zo mu sab’a.. Ko harshe da hakori watarana ana samun mishkila.. Toh idan an samu sab’ani ba haka kawai ake saki ba sabida girman al’amarin.. Akwai hikima da musulunci ya saka saki hannun namiji. Dan idan mace ne zakuyi fad’a sau d’aya amma tana iya cewa ka saketa sau dubu. Kaga tunaninta da naka ba d’aya bane.. Hangen nesanka da nata ba d’aya bane.. Kai ko a halitta ta fuskar k’iran jiki kaida ita ba d’aya bane. Ita haka Allah ya halicceta mai rauni kai kuma mai jurewa. So idan al’amara irin wann suka taso endurance dinka da tolerance d’inka ya kamata yafi nata. Idan an samu rashin fahimta ko matsala a zamantakewa a tsakanin. Kuyi k’ok’arin samo maslaha tsakaninku ba sai third party ya shigo ba, idan kukai trying a tsakaninku still ba’a samu maslaha ba sai a saka manya ciki dan amfani manyan kenan. Bama a fata har takaiga zuwa gaban manya toh amma idan ya zama ba mafita sai a mik’a matsalar gaban magabata. Idan ya gagara a mik’a matsalar gaban jagororin Al’umma wato malamai. Idan shima baiyi working ba toh fah ka sani duk yanda ake son wani Auren rabuwan shi yafi alkhairi. Sann idan Allah ya k’addari ba sauran zama dole za’a rabu.. Toh sai a rabu cikin mutuntawa da kyautatawa..” Ya dan gyara zamansa “Shin ya ma ake sakin.? Saki yana" "nufin furtawa. Intention na saki ba saki bane. Idan kace ma matarka zan sakeki, wann ba saki bane.. I intend to divorce you, this is not a divorce. I think we should get separated, this is not a divorce either.. It has to be a statement or a verb. In the sense that Na sakeki, .. Or you are divorced. Shikenan ta saku. Shi da yayi sakin yanada chances na kome guda biyu, idan yayi na uku babu kome Har sai ta auri wani mijin bashi ba. Idan miji ya saki matarsa sau d’aya, meaning one down two to go. Sann Anfi so matar ta zauna gidan mijin tayi iddarta. Akwai hikima da musulunci yace ayi hakan. Dan a wann zaman zai iya maida matarsa kuma ta maidu ba sai anje ana biko da sauransu ba. Menene Iddah.? Shine waiting period after the divorce. Ga macen da batada juna biyu iddah period dinta shine 3 monthly cycles.. If she’s too old like If she’s in her menopause ma’ana wacce ta daina Al’ada ko kuma yarinya k’arama wacce bata fara ba their iddah period is 3 months.. Idan mata mai juna biyu ce kuma iddarta shine ta haihu.. And this may be 2 months, 3months, 7months.. Depending on her pregnancy.” Sai ya dan gyara zamansa “Now, it is prohibited for a man to divorce his wife a lokacin da take al’ada, or when she’s in the state of purity yet he had intercourse with her in that state of purity. An hana saki a wad’an nan lokutan. Wann shine saki na bidi’a. Innovated divorce. Mafi rinjaye Sun tafi akan it is sinful but valid. Ma’ana kuskure ne hakan amma matar ta saku. Idan mutum zai saki matarsa. God forbid, yet they had intimacy few days, few weeks ago. Musulunci yace he waits until she gets her menses. Idan tai tsarki ba’a samu intimacy ba sann sai ya saketa. Kaga zai wahala ma yayi sakin idan har zai jira wann lokacin. Amma da yawa hakan baya faruwa sabida mafiya yawan sake sake cikin b’acin rai akeyi. Akwai hikima cikin duk abinda musulunci yayi umarni ko yayi hani..”" Yaci gaba da bayani kan hukunce hukunce da hakkoki Haidar na saurarensa.. Har ya fara tuna nashi sakin da matarsa Wanda sun samu intimacy kafin ya saketa. Ya lumshe idonsa kad’an yana karanto istigfari. Har saida ya sinkayo muryar Alhaji Gimba yana tambayarsa “Be open with me Haidar. Shin kana son matarka.?” Haidar ya jinjina masa kai “I love her with my life Uncle… But..” “There’s no but if you truly love her..” "Jiki a sanyaye Haidar ya girgiza Kai yace “I choose to be the problem Uncle.. I choose to carry the burden..” Ya dan girgiza kai a hankali “Mahaifiyata ta wahala sosai.. Tanada kurakurenta, but.. I can’t let her carry it all alone.. Bazan iya barinta ita kad’ai ta fuskanci matsalar ba sabida ita din ta fahimci kuskuren ta kuma ta tuba.” Yaci gaba da jinjina Kai “I choose to be her shield in this.. Idan hakan na nufin sitirta kuskurenta, even if it would destroy me.!” Ya k’arashe cikin yanayi mai ban tausayi." Alhaji Gimba ya dubesa cikeda tausayawa. Yanada masaniya gameda family issue da ahalin Aminin nasa suka fuskanta. Yau Haidar ne yake sacrificing farin cikinsa sabida mahaifyarsa lallai rayuwa ta sauya kuma Haidar ya cika D’an da za’ayi alfahari dashi. Sai yaci gaba da jinjina Kai a hankali murmushin saman fuskarsa yake duban Haidar d’in. "“Idan na fahimceka Haidar, kayi komai ne sabida mahaifiyarka. Kuma duk d’a nagari irin haka zaiyi.. Ba ina nufin sakin ba.” Ya d’anyi gyaran murya “Ka zab’i ka sadaukar da farin cikinka sabida mahaifyarka.. Amma rabuwa da iyalinka bazai zama mafita ba. Bansan menene wann kuskure na mahaifyarka da Kake son sitirtawa ba, ka sani duk Wanda Ya rufa asirin wani musulmi Allah zai rufa nasa ranar gobe balle Mahaifiya. Saidai akwai hanyoyi da dama da ake bi dan shawo kan matsala. You can’t let yourself be destroyed in the process.. Because Destruction is not the solution and it will never be. Mahaifyarka sai tafi shiga tashin hankalin idan har hakan yai destroying d’inka. You are a man, and you supposed to act like one.. Be brave enough to face your problems..Kar ka guje ma matsalolinka dan idan ka guje masu zasu bibiyeka ne har k’arshen rayuwarka.” Ya dan numfasa “I’ll ask you this question again, do you love your wife.?”" "Dubansa kurum Haidar keyi, ya shiga jinjina Kai ba tareda ya iya furta koda kalma ba." "Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Then what are you waiting for, go and reconcile with your wife. Kaje ka dawo da iyalinka.”" Sai Haidar ya d’anyi shiru yana tunanin irin k’iyayyar da ya hango a kwayar idanun Ummul. Ya sani a halin yanzu Babu abinda tafi tsana Watak’ila sama dashi. Jin yayi shiru yasa Alhaji Gimba murmusawa yace “Bansan Aliyu da rashin k’warin gwiwa ba dukda ance rauni na cikin soyayya.” Ya k’arashe cikeda barkwanci. "Sai Haidar ya d’an k’ak’aro murmushi yana jinjina Kansa “In sha Allah Uncle, zan dawo da ita. Kuma bazan tab’a sarewa ba. Na gode k’warai.. Allah ya saka da alkhairi ya k’ara girma.”" Alhaji Gimba ya murmusa “Yanzu naji Zaki na magana. Allah ya maka albarka ya mana jagora.” Haidar ya amsa da Ameen had’ida k’ara godiya ma Alhaji Gimba. Alhaji Gimba ya mik’e suka jera zuwa motan Haidar a tare tamkar yana ma Haidar d’in rakiya. "Haidar bai tab’a tsammanin rana irin wann zata zo ba. Mutumin da a baya yake masa kallon tarayyarsa da mahaifinsa babu wani alfanu. Mutumin da yai masa mummunar fahimta a baya. Sai gashi yau wann mutumin ya zamto tamkar mutumin da ya jefa masa igiya cikin rijiya mai duhuwa yace ya kama ya fito. Tabbas zaka k’i wani abu wann abun alkhairi ne a gareka, zaka so wani abu wann abun sharri ne a gareka." Fatan alkhairi Alhaji Gimba ya kuma yi ma Haidar d’in. Ya kuma ce a duk lokacin da wani abu ya shige masa duhu ko yake nema shawari his door is always open yazo ya samesa matsayin Uba a wajensa. Godiya Haidar ya kuma masa cikeda girmamawa kafin ya wuce. Tinda ya fito daga gidan Alhaji Gimba yake ji kaman ya k’ara masa k’warin gwiwa ne.. Yayi alk’awarin zai jira Ummul Har tayi healing koda zai d’aukesa tsawon shekaru ne.. Amma yau da Alhaji Gimba ya nusar dashi zai iya wasa da damarsa sai yaji bazai iya jira ba. Zai tafi yayi yak’in dawo da Ummul cikin rayuwarsa da taimakon Allah. Washe gari sassafe yai shiri da zummar d’aukan hanya garin Kano. Ya shigo ya gaida iyayensa sann ya k’arada "“Daddy, Mommy.. Ina so zan tafi garin Kano yanzu.. Zanje na dawo da Khairy.”" Farin cikin Mommy ya gaza b’uya. Duk a ‘yan kwanakin ta kula ko zancen Haidar baiso a masa sai gashi yau yace zaije ya dawo da matarsa. Suka saka masa albarka tareda fatan alkhairi. Daddy ya dakatar dashi. Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yace da Haidar ya jirasa a mota yana nan fitowa. Mommy tace “Engr. Ya naga ka tsayar dashi..?” "Ya murmus “With your permission Rankidad’e, I’m going with him.. I want to be a father to my son..”" Har k’walla saida suka ciko idon Mommy. Ta tuna farkon Auren Haidar da Ummul d’in Daddy cewa yai ba hannunsa ba ruwansa tayi yanda take so da rayuwar D’anta. Yau sai gashi ya saka kansa tsamo tsamo a al’amarin Haidar d’in. Ta murmusa tace “Toh kodai nima nayo muku rakiyar ne.?” Daddy ya girgiza Kai yana d’aura wristwatch d’insa “A’a wann tafiya ce tamu ta maza. Daga baya sai kiyi naki.” Murmushi kawai Mommy tai ta musu fatan sauk’a lafiya baida dacewa. ** Koda suka isa garin Kano sun samu an kaisu Har k’ofar gidan Malam Isubu mai Manja kaman yanda aka fi saninsa. "A farfajiyan gidan aka saka masu tabarma daga nan k’ofan su Ummul d’in dan Tani bata bari ‘yanuwan Mahaifin Ummul da suke uba d’aya Wanda suka amshe kudi hannun Asshe farkon Auren Ummul d’in sun shiga cikin maganar ba, sanin abinda ka iya zuwa yazo. Dukda maganan na maza ne amma kamawa take Shiyasa tazo wajen tinda tasan da cewa akan kudi ba abinda su d’in bazasuyi ba. Sann basu san da mutuwar Auren Ummul d’in ba. Bayan sun gaisa Nan take sanar dasu Daddy har kawo wann ranan basu saka Ummulkhairi a idonsu ba. Sun bincika duk yanda ya kamata amma babu labarinta." Haidar ya dubeta cikin shock “Khairy bata nan..? Toh ina take.?” Tani ta sauk’e ajiyan zuciya “Duk yanda ya kamata mu bincika gidan ‘yanuwa da zuri’a mun bincika amma Babu labarinta. Tin a lokacin naso mu koma mu sanar daku halinda ake ciki amma mahaifiyarta tak’i hakan. Ta d’auki duk laifin ta aza ma kanta..A cewarta wann hukuncinta ne take karb’a.. Sannan har rana mai kaman wann Mahaifin Ummulkhairi dake cikin jinya baisan Aurenta ya mutu ba.. An dai sanar dashi tayi Aure a haka yana jinyar amma baisan da wann labarin ba dan jinyar tashi abu ne da ya danganci zuciya. Likitoci suna bada shawarin ba komai za’a sanar dashi kai tsaye ba duba da irin yanayin jinyar. Sann baisan da cewa mu kanmu bamu san yanda Ummulkhairi take ba.” Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban Daddy “This is all my fault Daddy.. Duka laifina ne.. Daddy idan na rasa Khairy.. Bansan ya zanyi ba..” Ya k’arashe cikin tsananin nuna damuwa. Daddy bai kaiga furta kalma ba Azeema ta fito da murmushi saman fuskarta. Kai tsaye ta furta “Bazaka rasa ‘Yaruwata ba Sirkinmu Dangayu. Domin kudin kuna son junanku.. Naga haka a k’wayan idonku.. ‘Yaruwata..” Bata kai aya ba Khulsum ta fito da sauri dan dama tin baya dawowar su Umma daga Abuja suka d’auko Khulsum da Abba daga gidan Inna Dije. Tani ta kuma d’inke bakin Inna Dije da fad’in idan taji fit wani abu ya fita daga bakinta ya karad’e dangi gameda Auren Ummul toh ta tabbata itama nata Auren ya Mutu kenan sann itada D’anuwanta Malam Isubu har abada. Khulsum ta girgiza kai tana duban Azeema “Kiyi shiru Azeema..” Duk sai suka maida dubansu ga Khulsum da Azeema. Azeema tace “Khulsum ki k’yaleni na sanar dasu.. Baki gani ne Yayanmu naso ya maida matarsa.. Meyasa bazaki bari a sanar dasu ba..” Khulsum na huci tace “Sabida ‘Yaruwata tace bata so a sanar dashi.. Sabida ita d’in bazata tab’a komawa gareshi ba.” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata. "Haidar da baisan tuni ya mik’e tsaye ba ya isa gaban Khulsum yana girgiza kai “Kinsan yanda Khairy take..? Tell me, where is she.. Where can I find her.?”" Ta dubesa sai ta kauda fuskarta gefe tana share hawaye. "Haidar ya kuma jefo mata tambaya “Please tell me, kinsan yanda take..? Ina take.. Dan Allah ki sanar dani..”" Azeema tace “Bazata sanar dakai ba. Dan nima bata sanar Dani ba.. Kaf gidan nan babu Wanda ta sanar dashi. Nima abinda yasa naji tana waya ne na lab’e na saurara nan naji da Addarmu Ummulkhairi take waya.” Mama Tani ta mik’e tana duban Khulsum “Ke Khulsumu meke faruwa..? Yanzu dik irin d’aga hankalin nan da kikaga munyi munata neman Ummulkhairi dama kinsan yanda take.. Shine kika kyalemu cikin duhu.. Muna nan muna tunanin Har yanzu fushi kike da ita Shiyasa baki tada hankali wajen neman ina take ba Ashe kina sane..” "Kuka Khulsum take tana girgiza kai “ ‘Yaruwata bata sanar Dani yanda take ba.. Amma nayi waya da ita kuma ta sanar dani cewa tana nan lafiya kar na damu ta kuma tambayeni jikin Abba.. Sann tace na kula da Umma kuma na nemar mata yafiyar Umma.. Sann..” Sai ta dubi Haidar da yai mutuwar tsaye yana dubanta, taci gaba “Sann tace ko ka zo nemanta kar na sanar dakai cewa munyi waya.. Dan har abada bataso ta sake ganin ko mai kamanninka..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka." Cikin wane irin yanayi Haidar ke furta “No please.. Don’t do this.. Please tell me.. Tell me idan ta sanar dake yanda take.. Ko kuma.. Ina layin da ta kiraki dashi..” Duk a daburce yake. Khulsum ta girgiza kai “Ta rufe lamban bai fito ba..” Ya lumshe idanunsa yana dafe kai “No.. There has to be something.. Just think please.. Or maybe we can try to retrieve all the calls from your line.. And see if we can track the number..” "Ganin duk ya daburce yana neman ficewa hayyacinsa yasa Daddy d’an yin gyaran murya yace “Haidar, taho nan ka zauna.. Abi komai a sannu..” Ya dubi Khulsum yace “ ‘Yanmata jeki abinki ko.” Khulsum ta risina ta tana mai jinjina kanta kafin ta shige tana share ragowar hawayen da suka zubo mata. Azeema na take mata baya." Tani ma ta dawo mazauninta ta zauna. Daddy ya dubi Haidar yai gyaran murya “Haidar ina so ka natsu ka kuma natsa zuciyarka. Yanada kyau mubi komai cikin lumana dan tada hankali bazai tab’a kawo mana maslaha ba. Idan har Ummulkhair tana cikin k’oshin lafiya wann ma abun mu gode ma Allah ne. Kuskure ne an riga anyi shi dama kuma shi gyara sai a hankali.” Tani ta jinjina kai “Wann gaskiya ne.” Daddy ya kuma jinjina kai kafin yace “Amma yaya jikin Maigidan..? Yana asibiti ne Har yanzu kokuwa..? Mai likitoci suka ce gameda rashin lafiyar nasa.?” Tani ta dan gyara mayafinta “Toh jiki Alhamdulillah zamu ce. Sann asibiti kuma sai jikin ya d’anyi tsanani ake zuwa.. Yana nan a gida. Saidai maganar ne ba sosai ba.. Amma yakan fahimci wasu abubuwan.. Rahotannin asibitin nasa duk yana wajen d’iyarsa Khulsumu dan kusan tareda ita akai jinyar nasa gaba d’aya. Ba abinda zamuce ma yarinyar saidai Allah shi mata albarka.” Daddy ya jinjina Kai yana fatan lafiya ga Abban kana ya mik’e yace “Ko zamu iya ganin shi.?” Tani ta jinjina kai “Eh yana d’aki yana kwance. Mu k’arasa. Bismillanku..” Tai gaba Daddy da Haidar na biye da ita suka nufi wata ‘Yar k’aramar k’ofa da zai sadaka da d’akin Abba. Suka d’an tsaya daga waje kafin Tani ta shiga ta tadda Umma ciki nan take sanar da Umma su Haidar da mahaifinsa zasu shigo su gaida Abba dama tuni Tani d’in ta sanar da ita zuwansu. "Umma ta gyara zamanta ta dan gyara Abba ma kafin ta rufe kanta da mayafi, Har rabin fuskarta saida ta rufe sabida surkunta." Tani Tai masu iso. Daddy ya soma d’an rage tsawonsa ya shige d’akin Haidar na biye dashi. Suka gaisa da Umma suka tambayi mai jiki kafin Tani ta d’an matso kusan Abba tana sanar dashi ga Surkin Ummul da mai gidanta zasu gaishe shi. Allah sarki Abba sai ya soma k’ok’arin mik’ewa jin an ambaci Maigidan Ummul d’insa da surkinta. Daddy yai saurin taimaka masa yana masa sannu da jiki dukda muryar Abban ba wani sosai yake fita ba. Bayan sun gaisa da Daddy sai ya fice amsa wayarsa dake ruri. Cikin muryarsa da bai fita sosai irinta majinyaci mai Jin jiki Abba yace “Ina Maigidan Ummulkhairina.?” Haidar ya k’araso cikeda risinawa yana gaida Abba zuciyarsa ya kuma cika da tausayin Khairy da ahalinta. Sai Abba ya soma k’ok’arin d’ago hannu yana mik’a ma Haidar alamun yana so suyi masabaha. Haidar yai saurin tallafo hannun Abban ya rik’e cikin nasa suka gaisa. Sai yaji Abba ya rik’e hannunsa gam yana fad’i da kyar “Kaine Aliyu mijin Ummulkhairi na..?” Sai Haidar ya jinjina kai a hankali “Eh.. Eh Abba ni ne..” "Abba yaci gaba “Ina matuk’ar son ‘Yata Ummulkhairi, tanada zuciya mai kyau.. Ka rik’e mun.. Ita da amana kaji koh..”" "Dukda tausayin Abba had’ida wani abu mai kama da rauni da Haidar keji yana taso masa tin daga can k’asar zuciyarsa bai hanasa jinjina Kai cikin sauri, ya soma furtawa cikeda k’warin gwiwa “In sha Allah Abba.. Zan rik’eta… Zan rik’e Khairy amana.. Na maka alk’awari.!”" Abba ya murmusa had’ida jinjina kai sai kuma yace “Ina Ummulkhairi.. Maiyasa bata biyoka ba..? Na jima ban ganta ba. Ina kewar.. ‘Yata sosai.” A nan ne kuma jikkunansu gaba d’aya yayi sanyi. Babu ya Haidar Wanda ya gama d’aukar ma majinyacin mutumin alk’awarin kular masa da ‘yarsa wacce baisan ina take ba. Sai Tani Tai karaf tace “Ai.. ai laulayi take… K’aramin juna gareta shiyasa bata samu zuwa ba.” Ita kanta Tani da tai maganar saida taji banbarak’wai. Yayinda Umma tai saurin dubanta da idanunta masu cikeda rauni. Shi kaw Haidar sai ya sadda kansa kad’an. A haka dai Har suka fito zasu tafi. Baffanin Ummul guda biyu da suka amshi kud’ad’e hannun Asshe suka bada Auren Ummul d’in nan suka jeru suna jiran fitowar su Haidar ganin hamshak’iyar motar da ke k’ofar gidan nasu. Sai jinjina lamarin suke suna fad’in albarkacin bakinsu gameda mijin Ummulkhairi da mahaifinsa Wanda Tani ta hana su gana dasu a cewarsu. Ai ko suna ganin fitowar su Haidar suka k’arasa kaman zasu kwanta suna mik’o ma Daddy hannu alamun musabaha. Daddy da Haidar suka tsaya suna gaisawa da mutanen cikeda girmamawa. Nan sukai introducing kawunansu matsayin K’annen Mahaifin Ummulkhairi kuma Wanda suka bada Auren ita Ummulkhairin. Nan suka sake sabon gaisuwa na musamman suka kuma cikasu da goma na arziki daga Daddy har Haidar din babu wanda aka bari baya. Kowa kokari yake yayi alkhairi daga aljihunsa. Alkhairin da ya bar su Baffah Ado cikin tsananin al’ajabi. An masu kyautan ban girma sai kawai suka fara wasa Ummulkhairi cikin gidan suna cewa ta kawo alkhairi. Wacce a baya suka kyamaceta da k’addararta Har cewa suke tana bata sunan zuri’a da muguwar bak’ar k’addararta yau sai gasu nan suna rigen kiranta jininsu. Rabon da su shiga sashen su Ummul su duba D’anuwansu tinda Abba da Khulsum suka dawo daga Jigawa can gidan Inna Dije. Yau sai gasu nan tsamo tsamo suna kiran Abba Yayansu. Tani kaw ta masu d’add’aya tana fad’in maza aci arziki. Ummulkhair da suke ambato da Ummulsharri a baya yau sai gashi suna k’aryata harsunansu dan cewa suke ta amsa sunanta Uwar alkhairi. ** Bayan Haidar ya kai Daddy masauk’i nan suke tattaunawa da Daddyn gameda ciwon Abba. Daddy yace “Inaga ko zakaje Asibitin ku tattauna da Likitocinsa na nan. Sai a duba hospital report din nashi kaji shawarwarinsu.. Idan yaso ko can Abuja ko dan ta kama a fitar dashi abroad ne sai su sanar dakai.” "Haidar ya jinjina Kai “Ina da wann plan din Daddy.. Hospital din da na kwanta lokacin da na samu had’arin mota is a prestigious hospital, sunada likitoci k’wararru daga k’asashe da dama sunada advanced technology.. In fact is a foreign hospital.. Because a yanda naga jikinsa ba Lallai Likitoci su bamu shawarin a fita dashi kai tsaye matuk’a akwai solution a nan.. Duba da process din da za’a bi. Dan Ga dukkan alamu yana jin jiki sosai. Amma zan tuntub’i Likitocin nasa kaman yanda kace.”" Daddy ya jinjina kai “Good.. Yayi kyau.. Toh ai inaga ni zan bi jirgin yamma na koma. Zan turo Sadis (Daya daga cikin trustees d’in Daddy ne a wajen aiki) sai ya tayaka ku kula da al’amran.” Haidar ya dan murmusa yana risinawa “A’a Daddy da ka barshi. Zan kula da komai by myself.. Financially da dik wani abinda ya kamata.” "Murmusawa Daddy ya d’anyi yana jin dad’in yanda D’an nasa ya zama responsible. Sai yace “Even so, Sadis zaizo ya tayaka da wani abin. Jirgin yamma nake son bi.” Ya k’ara maimaita ma Haidar d’in." Sai Haidar yai saurin jinjina kai “I’ll call the airport right away” Ya fad’i yana mai ficewa. Daddy ya jinjina masa kai. Haidar bai bar garin ba saida ya tabbata an shirya duk wani abinda ya kamata gameda tafiyan Abba zuwa prestigious hospital din da za’ai treating d’insa. Umma tace fir saidai Mama Tani ta tafi tareda Abba ita zata zauna da yaran. Haidar ya musu goma na arziki dukda cewa da Umma take ya daina d’awainiyar nan musamman idan ta tuna abinda ke faruwa na rashin Ummul. A cikin zuciyar Haidar kaw cewa yake baiyi rabin abinda Khairy ta musu shida ahalinsa ba. Cikin zuciyarsa yana kewarta sosai.. A koda Yaushe k’aunarta k’aruwa masa yake. Kafin ya bar garin da yamma yana zaune saman tabarma a haraban gidan dan tuni ya zama D’an gida. Azeema sai zuba masa surutu take ta d’auko wani tsohon album d’in Abba tana nuna masa hotunan Ummulkhairi harda Wanda take sanye da uniform na makaranta. Ya jima yana kallon hoton. Sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Azeema taci gaba da basa labarin k’uruciyarsu Har ta gangaro kan samarukan Ummul da ake saka musu rana a fasa. Har kan Zubairu da su Alhaji Kamilu da yanda kowa ya zata Zubairu zata aura sabida yanda Zubair d’in yaso Ummul. A nan ne fah sukaga Haidar ya had’e rai tamau. Badia sai mintsilin Azeema take tana fad’in Tai shiru haka nan amma inaa Azeema sai zuba take yawa kurna. Mama Tani ta kawo masa abinci tana fad’in su Azeema su kyalesa haka nan yaci abinci. Azeema ta dubeta ta dubi tuwon. Tuwon gero ne da miyar yauk’i. “Haba Mama ya zaki bashi irin wann abincin. Na tabbata bai ma tab’a gani ba.” Haidar kam ma iya cewa baima abindake faruwa ba. Dan tinda Azeema tai mentioning Zubair tsohon saurayin Ummul ya rasa sukuni.. Sai ya dan dubi Azeema ya girgiza Kai kad’an yace “Amma ina Zubair yanzu.. Yayi Aure.?” Azeema ta saka ma bakinta sakata tana Zare ido. Badia ta rankwafo had’ida rankwashin Azeemar kad’an ta rad’a mata “Kin gani koh. Ke baki san kishi irin na maza bane kinzo kina labarin tsaffin samarukan Ummul. Yanzu gashi kinsa mutumin na miki wasu tambayoyi. Haba Azeema mutumin nan fah ji yake kaman Ummul ta kufce masa kenan tinda sun rabu.. Idan baki basa k’warin gwiwa ba bazaki basa dalilin rura wutan tashin hankalinsa ba.” Azeema tai murmushin da yafi Kama da yak’e ta dubi Haidar tace “Wann ai tsohon labari nake sanar dakai Yayanmu. Zubairu ya jima da auren ‘Yaruwarsa wacce ake so a had’asu tuntuni..” Ta shiga tura foodflaks din abincin da aka kawo masa tana fad’in “Kaci abincinka Sirkinmu. Tuwon nan idan yai sanyi babu dad’i.” Badia ta harareta tana girgiza Kai ta janyo Azeema suka bar wajen tana rad’a mata “Kedai wacce tai jegonki bata farse wann bakin naki ba.” Azeema ta kuma kame bakin ta tana fad’in “Wllhi na sani… Duk yanda akai Inna Dije ce.” Suka dara a tare Badia tana fad’in Allah ya shiryi Azeema. * Kafin ya tafi saida ya k’ara tuntuban Khulsum ko ta sake samun kira daga Ummul. Khulsum tace bata sake kiranta ba. Su kansu saida Haidar ya basu tausayi. K’arshe haka ya hak’ura ya bar garin ba don yaso ba. ** "Idanunsa na duban window yake ci gaba da fad’in “It’s been three months Hisham. Wata uku babu Khairy.. And Dareen is nowhere to be found. I feel lost, tiny and insignificant in this world..”" "Hisham ya sauk’e ajiyan zuciya “I believe everything happened for a reason.” Ya dan furzar da huci had’ida girgiza Kai “I have never met your wife Haidar.. Amma abinda na kula shine kana k’aunarta sosai, because ban tab’a ganinka cikin yanayi na soyayya irin haka ba..” Ya dan numfasa “Kuma koda ka kasance mutum da bai cika bud’e al’amransa ba jikina yana bani ba k’aramin abu bane ya shiga tsakaninku.”" Sai Haidar ya dubesa amma baice komai ba. "Hisham ya jinjina Kai kad’an “Whatever is the case Haidar, know that I’m here for you.. And you can always count on my support.” Ya jinjina Kai alamun tabbatarwa. “Idan zakaje kaci gaba da Neman matarka ni zance naci gaba da" "nemar maka Dareen. Ko ba don ka hukunta Dareen ba sai dan D’anka dake cikinta. Ko ya kayi Haidar, that child she’s carrying is still yours.. Kuma baida laifin komai.. Bazaka hukunta shi da laifin mahaifyarsa ba.”" Haidar ya tsaresa sosai da ido wann karon sai ya girgiza Kai yace “Are you even sure that child is mine.?” Shiru Hisham bai amsa shi ba saima tunani da ya soma cikin zuciyarsa ‘Bastard! Zaka sheganta wann D’an kaman yanda Ubanka ya shegantani a ciki.! Kai din baka rage ma Ubanka komai ba Haidar.’ "Hisham ya sinkayo muryar Haidar sanda yaci gaba “Wha if babu wani ciki. What if k’arya take, tinda iyakacin tarayyata da ita k’arya ne kawai.!”" "Hisham ya dan furzar da huci yana mai d’aga gira sama “Bazan k’i maka ba. Kuma bazanga laifinka ba.. Because you’ve been fooled and betrayed. Amma Kai tunani Haidar.. Kayi rayuwa na Aure da Dareen koda ace rayuwar ta k’arya ce. You were once husband and wife.. You cannot deny that. So ba abin mamaki bane idan tana d’auke da gudan jininka.. I mean, if you neglect that child zai tashi ne da tsanar koma waye mahaifinsa.. Meyasa ‘ya’ya zasu biya kuskuren da iyayensu suka aikata..? Hakan ba adalci bane.” Yanda yake maganar tamkar yana digging ma Haidar past d’insa ne." Hisham yaci gaba “You can’t let that child pay the price Haidar.. You know exactly how it feels mutum ya girma babu soyayyan iyayensa. You can’t make that child a victim. You can’t let that happen to your own child.!” Ya k’arashe cikin tsananin k’warewa tareda tono ma Haidar bayansa. Yanda ya girma da tunanin iyayensa basa sonsa duk sabida wani kuskure da mahaifyarsa ta aikata. Ya rintse idanunsa yana jin kamar dai duniyar ta dad’a juye masa. Sann gaskiya ne abinda Hisham ke fad’i. Because shi Kansa Haidar d’in was once a victim. Bazai bari tarihi ya maimaita Kansa cikin ahalinsa ba. Hisham ya tsaresa da ido cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kai da ahalinka bakuda daman yin wani farin ciki a wann rayuwar. A lissafi Ummul ta cika watanni uku tin bayan da k’addararren Aurenku ya k’are.. Hakan na nufin ta fice daga iddarka.. Ni kuma yanzu zan tafi na gina nawa soyayyar cikin zuciyarta…All my sacrifices are finally going to pay off’ A fili k’arasawa yai ya dafa Haidar kad’an fuska fal damuwa. Cikeda kulawa yake furta “Haidar bazan Barka ka koma irin rayuwar k’uncin da ka fuskanta a baya ba. Ka tafi ka nemo matarka yanda ta shiga ta fita.. Ni kuma zan tafi na nemo maka Dareen yanda ta shiga ta fita ko dan wann innocent soul d’in dake cikinta.” Ya k’arashe damuwa sosai saman fuskarsa. Haidar bai iya ce masa komai ba sai shafe fuskarsa da yai da tafukan hannayensa. A haka Hisham ya tattari files d’in da ya shigo dasu ya fice fuskarsa d’aukeda mugun murmushin da ba kowa ke iya fahimta ba. Cikin zuciyarsa yaci gaba da ayyana Ummul tasa ce a halin yanzu. Da wann farin cikin Hisham ya taho garin Bauchi zuciyarsa fari k’al da nufin ya tafi Neman Dareen a zahiri kuma wajen Ummul yazo da niyyan k’ulla soyayyarsa. Babu Wanda yasan da zuwan nasa. Hajja batai mamaki ba dan dama ya saba mata irin wann zuwan na bazata. Saidai ta kula wann karon da wani irin farin ciki yazo maras misaltuwa. Suna cikin gaisawa da Hajja yake tanbayarta “Hajja nace ina Ummul kuwa..?” "Bata kaiga basa amsa ba suka hango Ummul da fitowarta kenan daga babban parlorn da Hajja ke sana’arta na d’inki, nan suka hangota tana tafiya da kyar tana dafe garu tana kame kanta dake matuk’ar juya mata.. Kafin suyi wani aune jiri ya kusan kaita k’asa. Hajja ta nufeta hankali tashe ta tallafota tana ambaton sunanta dan tuni idanunta sun soma juyawa." SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *51* *©️Sameena Aleeyou… * "Bud’e ido tai sai gani tai fanka na wainawa saman kanta, ta yunk’ura zata tashi sai taga igiyar drip daure hannunta. Nan ne ta fahimci saman gadon asibiti take. Ta waiga kad’an sai taga wani mutumi da ko shakka Babu Likita ne tsaye daga gefe hannunsa rik’eda file kansa kife kaman yana rubutu." Hankalinsa naga abinda yake ta sinkayo muryarsa yana mata sannu. Ya k’arada “Malama Ummulkhair right.?” Ta jinjina kai kad’an. “Kina Jin wani pain..? Akwai yanda ke Miki ciwo.?” Ya k’arashe yana mai janyo kujera had’ida zama gefen gadon. Ta d’an girgiza Kai sai ta dafa kanta kad’an “Kaina na d’an juya min sann yana ciwo.” Sai ta dan tab’a gefen cikinta kad’an tace “Ciki na na ciwo kad’an ta gefe.” Ya jinjina kai “It’s normal to experience such pains in early stage lokaci zuwa lokaci.” Bata gano abinda yake nufi ba amma tana Jin heartbeat dinta na k’aruwa da sauri. Kaman yasan tana jiran Karin bayani ya soma jero mata wasu tambayoyin. “Amma… Yaushe rabonki da kiga al’adarki.?” Yai tambayar fuskarsa na nuna alaman tsananin kulawa. Sai ta kalleshi da mamaki. Ganin irin duban da ta masa yasa shi d’an sakin murmushi “Kinga kar ki ba ma tambayar wani manufa na kula kaman.. Baki fahimci meke damunki bane bayan kin d’ebe watanni cikin yanayin..” Kanta ya kuma k’ullewa.. Ta d’an girgiza kai “Dr.. Meke faruwa dani..? Dan Allah Ka mun bayani..” Ta fad’i duk a d’an tsorace Jinjina kansa yai yana kuma tabbatar da hunch d’insa. Sai Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Kar ki damu ba wani abin tashin hankali bane.. Amma ki amsa min tambayata first. When last kikaga menstrual period d’inki.?” Sai ta soma tunani.. Ita zata iya cewa damuwa da tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki yasa ta ma mance wani abu wai shi menstrual period. Ta girgiza kai tace “Ni.. ni … Ni ban sani ba..” Ta basa amsa tana d’an kauda fuskarta. Dr ya rage girman idanunsa had’ida girgiza kai kad’an cikeda mamaki “Is it possibile.?” Ta d’an dubesa fuska d’aukeda alamun k’osawa wann karan dan Likitan Ya fara hawa kanta da tambayoyinsa marassa kan gado. Sai Ya dan tab’e baki kad’an yace “Ina mijinki.?” "Tambayar ya kuma tunzurata, ya fama mata gyambon dake cuziyarta, ta kuma jin wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi. A kufule tace “Bani dashi.!”" Sai ya kuma girgiza kai cikeda mamaki “Baki dashi kuma..? I.. thought mutumin can da ya kawoku keda mamarki mijinki ne..” “Na fad’a maka bani da miji.. Ni Ummulkhairi banida wani miji..!” Ta fad’a kaman zata fashe da kuka. "Likitan ya dan jada baya kad’an yace “Ok.. Ok easy..” Sai ya soma bud’e file d’in dake hannunsa yana duban file d’in yake fad’in “Amma sakamakon gwaje gwajen da muka Miki Ya tabbatar kina d’auke da juna biyu har na tsawon watanni uku which is why kikaji Ina miki tambayoyin da nake miki.. Amma sai na fahimci wann shine karonki na farko shiyasa Har juna biyun Ya shafe tsawon wann lokacin a jikinki tareda kin fahimta. Although pregnancy is not typically visible at 3 months, especially in a first pregnancy.. Most women begin to show in the second trimester, around 16- 20weeks.. However,…” Aya yai ma kalamansa sanda ya d’ago yana dubanta dan idanunsa naga file din dake rik’e hannunsa yaketa wad’ann bayanan da sam babu mai saurarensa balle fahimtarsa ga dukkan alamu." Abu d’aya zata iya cewa taji cikin kalaman nasa shine juna biyu bayan wann kalman bata sake fahimtar komai ba… Dr ya dan girgiza kai yana dubanta “Hello.. Are you with me..?” Ya fad’i cikin k’ok’arin dawo da ita daga duniyar da ta b’ace ciki. Dubansa take tana girgiza kai tana jin kaman duniyar ke juya mata “Ju..juna.. biyu..!!” Ta fad’i labb’anta Har rawa suke. Ta kuma girgiza kai cikin rashin fahimta “Mai.. Mai hakan.. yake.. Nufi Dr.. Ni.. Ni Ummulkhair.. Juna biyu..?” Ta k’arashe tana nuni zuwa gareta hannunta na matuk’ar rawa haka ma muryarta. Dr ya jinjina Kai alamun tabbatarwa “Of course. You are 3months pregnant.” Sai ta soma girgiza kai “A’a.. A’a baku gwada daidai ba Likita… Dan Allah ka sake gwadawa.. ni banida komai..” Cikin tsananin damuwa mai gauraye da tashin hankali take maganar. Dr ya shiga nuna mata sakamakon yana fad’in “Gwaji na jini mukayi wanda ya tabbatar da hakan.. Ina shawartanki da ki rage stressing kanki sann ki rage shiga damuwa ko dan lafiyarki da lafiyar abinda ke cikinki… I’ll prescribe some medications for you.. Sai a kiyayesu..” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa. Kuka ta fashe dashi tana girgiza kai “A’a Dr.. A’a..Dan Allah ka cire mun cikin.. Wllhi bana so.. Dan Allah ka ceceni..” Shima wann karon a kufule yake dubanta “Bakiyi kama da maras Kamun kai ba da nace ta wani hanyar daban kika samo.. Amma ko ta ina kika samu ki sani bama cire ciki a nan.. Excuse me..” Ya k’arashe yana k’ok’arin ficewa yayinda Kukan Ummulkhairi Ya karu Wanda hakan yasa Hajja dake daga bakin k’ofan d’akin shigowa ba shiri. Dr ya dubeta “Yauwa.. Akwai magunguna da zan rubuta mata dan Allah sai a kula ta sha su akan kari..” Hajja ta jinjina kai “Eh akwai yarona da Ya kawomu yana waje.. Zai sayo magungunan.” Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya fice. Hajja Tai sauri ta k’arasa ga Ummul dake cazgan kukan kamar wacce aka aiko mata sak’on mutuwa. “Ummulkhair.. Jikin ne..?” Ta tambaya cikeda damuwa. Shiru Ummul bata bata amsa ba sai kuka da take tana girgiza kai. Hajja ta dubeta sai ta dubi takardan dake aje saman drawer dake gefen gadon. Nan taga pregnancy test ne kuma ya nuna positive. Ji Tai tamkar jinin jikinta Ya k’afe. Taji kaman an d’add’aure jijiyoyin jikinta.. Ummulkhair juna biyu ke gareta.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Duk abinda ke faruwa da Ummul tono mata nata bayan yake.. Tamkar dai reputation ne na abubuwan da suka faru da ita shekarun baya.. Dama a yan kwanakin taso ta fahimci hakan saidai tayita kore tunanin abin dan guje ma tono nata bayan. Sabida duk abinda zaisa ta waiwayi baya guje masa take. Saidai ga dukkan alamu duk yanda kaso guje ma wani abin sai Ya tono kansa a wasu lokutan.. "Hajja ta fad’a duniyar tunanin abinda Ya faru da ita shekarun baya. Auren ta da Mahaifin Uban cikin Ummulkhair wato Aliyu Maitama kuma mahaifi ga tilon D’anta Hisham.. Sai kuka da muryar Ummul ta sinkayo tana fad’in “Dan Allah Hajja nikam bani son wann cikin.. Dan Allah kar ki bari na haifosa.. Dan Allah kisa likitocin nan su ciresa.. Ki taimake…” Batakai aya ba Hajja Tai k’arfin halin tattaro k’arfinta ta rufe bakin Ummul da k’arfin gaske “Kul. Ko da wasa kar na sake jin kalamai masu kama da wann daga bakinki Ummulkhair.. Da iliminki da karatunki.. Da addinininki..? Haba Ummul this is not like you.. Ba haka Ummul d’in da na sani take tunani ba.. Mai hak’uri a duk halinda ta tsinci kanta ciki.. Kinyi hak’uri a lokacin da kika fuskanci k’alubale na JINKIRIN Aure da fashe fashen Aure. Kin karb’i k’addararki kuma in sha Allah kin dace da jarabawa. Toh ki sani yin Aure ba yana nufin k’alubale da jarabawa Sun k’are bane. A’a wani sabon babi na karatu da jarabawa ne rayuwa ta kuma bud’e miki.. Shi kansa zaman auren karatu ne kaman yanda mutuwar Auren zai iya zama jarabawa a gareki. Ki sani ba akanki aka fara mutuwar Aure ba haka zalika ba akanki za’a daina ba… Kowa da yanda rayuwa take zuwa masa.. Kowa da irin k’addararsa a rayuwa. Kowa akwai abinda aka sanya masa jarabawarsa da k’alubalen sa cikinsa.” Ta dan numfasa sai Ta kamo hannayen Ummul cikin nata wacce Har lokacin hawaye ke kwaranya mata “Duk abinda kikaga Allah Ya hukunta ma bawa, Allah yasan dalilin da Ya k’addari aukuwar hakan.. Taho nan..” Ta k’arashe tana rungumo Ummulkhairin daga zaune.. Sosai Hajja ta rungumeta zuciyarta fal tausayinta. Cikin zuciyar nata take fad’in ‘Ko ni da suka sheganta nawa cikin ban ciresa ba.. Dan haka Bazan tab’a bari makamanciyar tunani irin wann yayi tasiri a zuciyarki ba.’ A fili kuwa murmushi take tana rungume da Ummul d’in “ ‘Ya’ya rahama ne.. Kyauta ne mai girma Wanda Allah kad’ai ke bama wanda yaso cikin bayinsa.. Insha Allahu zaki haifo abinda ke cikinki lafiya kuma zai zamto mabudin alkhairi da sauyin rayuwa mai inganci a garemu baki d’aya..”" Cak Hisham dake daga bakin k’ofa hannunsa rik’eda ledan maganin da Dr yai prescribing ma Ummul yaja Ya tsaya sakamakon kalaman da yaji na fita daga bakin mahaifiyarsa.. K’iris Ya rage ledan dake hannunsa bai sunce Ya fad’i k’asa ba… Mai hakan yake nufi..? Ummulkhair ciki ne da ita..? No.. No way.. Allah yasa ba Daidai yaji ba. Babu wani ciki tattare da ita.. Haidar bazai masa haka ba..! Watanni uku Sun cika ta fita daga iddan Haidar bazai yuwu ace ciki ne da ita ba.. It can’t be… It definitely cannot be. Bai sadaukar da komai dan ya rasata daga k’arshe ba..! Jikin Hisham yaci gaba da rawa a daidai sanda ya kuma sinkayo muryar mahaifiyarsa tana tabbatar da juna biyun dake jikin Ummulkhair.. Zufa yaci gaba da karyo masa ta ko ina.. Da baya ya soma komawa ba tareda ya iya shiga d’akin ba. A nan cikin d’akin kuwa Hajja duk ta zak’u sai d’auki take. Bata san dalili ba amma sai ta tsinci kanta cikin matsanancin farin ciki gameda samuwar cikin. Ji take tamkar zatayi jika nata na kanta dan ‘ya ta d’auki Ummulkhair koda a zahiri abinda ke cikin nata Ya kasance tsatso kuma jika ga mutanen da suka zamto silan durk’ushewar rayuwarta. A b’angaren Hisham kuwa tashin hankali maras misaltuwa Ya shiga. Bayan dawowarsu gida can k’uryar d’aki Ya k’ule ya shiga dunk’ule hannunsa yana sakin huci.. Ya bigi garu da hannun nasa yana furtawa a hankali cikin karaji “Damn you..! Damn you Haidar..! How dare you..!How could you do this to me.!” Yaci gaba da sakin huci gumi na tsartsafo masa. Ji yake da zaiga Haidar gabansa da Ya shak’esa da iyaka k’arfinsa. Yana nan a haka wayar Ania Ya shigo masa.. Ya dubi wayar yana ci gaba da sakin huci kaman bazai d’aga ba. Sai Ya koma ya zauna ya janyo wayar ya daga ba tareda Ya daina sakin huci ba. Yana d’agawa daga d’aya b’angaren Anisa tace dashi “Ango ka sha k’amshi.. I know by now ka fayyace ma Ummulkhair irin soyayyarta dake lullub’e cikin zuciyarka.. Watak’ila Har an fara zancen saka muku rana. Toh nima dai Albishir na kira na maka dukda nasan kace ya kamata mu daina kiran juna tinda hak’armu na raba tsakanin Ummul da Haidar ya cimma ruwa.. Na kiraka ne na sanar dakai cewa Aunty Kwaise taje Har Kano ta d’aukoni ta dawo Dani gidanta.. Kuma kasan mai yanzu treating dina take da kyau har wani respect naga tana bani da kula na musamman.. Yanzu bata min kallon shashasha kaman yanda take min a baya.. Na tabbata bazai jima ba zan saye zuciyarta kamar yanda Ummul ta lashe zuciyarta. In no time zata aura min d’anta dan wllhi sosai ta d’aukeni da mahimmanci wann karon.. Finally burina zai cika Hisham.!” Ta k’arashe tana ‘yar tsallan murna. “Shut up.! Shut the hell up.!!” Hisham ya daka mata tsawa kafin yaci gaba cikin huci “Kina jina idona idon tsinannen Haidar d’in nan sai kashesa..!” A d’an tsorace Anisa ta waro ido waje kaman Hisham d’in na kallonta tace “Excuse me.. Mai kake cewa.. Kan wane dalili zaka kashe Haidar dina..?” “Shut up Neesa..! Kar ki sake ambato min sunansa..! That Imbecile made sure ya bar wani babban dalili da zai hana k’arewar alak’a tsakaninsa da Ummul..!” Anisa ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ban fahimceka ba.. Alak’a kamar ya..?” “He made sure ya bar gudan jininsa tattareda ita..! He ruined all my plans.. All our plans. Duk abinda muka jima muna shiryawa zai zama aikin banza..!” Anisa da taji maganar a bazata cikin rashin fahimta tace “What do you mean..? Mai kake nufi ya bar gudan jininsa… So kake.. Kace min like.. Ummul is pregnant..?” Hisham ya furzar da huci “So kike na maimaita miki.. He made sure he impregnated her kafin ya rabu da ita.. I hate him..!” Anisa ta soma girgiza kai “A’a.. We can’t let this happen.. Haidar can’t find out about this.. No one should find out bout this.. She can’t be pregnant.. She can’t give Haidar a child do you understand Hisham.. Dole muyi komai domin kawar da wann cikin.. No matter the cost..!” Hisham baice komai ba sai huci da yake ci gaba da furzarwa. Anisa cikin tsananin damuwa da tashin hankali taci gaba “Hisham wann cikin shi zai sake k’ulla igiyoyin Auren Haidar da Ummul da mukayi komai domin tsinkasu. Idan har muka bari wann ciki ya tabbata har aka haifosa kashinmu ya bushe.. Dan zamu rasa komai.. Dole muyi komai domin kawar dashi kuma kaine zakayi dan kaine kake tareda ita..” “Mai kike nufi..?” “Ina nufin duk yanda za’ai mu cire wann cikin.. Bazai yuwu a haifosa ba..” “How..? Ta ya hakan zai kasance.?” Anisa tace “Kawai ka kaita asibiti a cire ko ka saka mata magani cikin wani abin sha ta sha Ya fice.. Is as simple as this.” "Wann karon murmushi Hisham yai kafin yace “Lallai na yarda kin cika mai k’wak’walwar kifi Anisa. Ta ya kike zaton zanyi duk abinda kika ce ba tareda Sun zargeni ba.. You must be stupid.!” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Look, Daga mahaifyata har Ummul sunyi matuk’ar yarda dani bazanyi wani abu da zai rusa wann yarda nasu da na samu ba..”" Anisa ta furzar da huci “Toh idan ba haka ba ya zamuyi..? Ai gwara mu markade wann cikin ma fiyeda shegen can dake cikin Dareen Wanda muka markade. Dan wann shine babban barazana a garemu.. Hisham duk yanda za’ai cikin nan bazai zo duniya Ya tarwatsa mana farin cikinmu ba.!” Hisham Ya furzar da huci “I need to think of something.. Amma banda zubar da cikin.” "Cikeda k’osawa Anisa tace “Har kanada wani abinda zakai tunani akai bayan wann cikin threat ne a garemu..” Ta girgiza kai cikin tashin hankali “Hisham, we can’t afford any further miscalculation… We need to act now tun munada dama akan cikin nan.. Tun yana k’arami.. Yanzu ya kamata mu b’arar dashi. Idan ta kama na taho yanda kake ne zan taho just to carry out the job.”" A zuciye yace da ita “I love Ummulkhair kin fahimta.. I want to build my relationship with her based on trust.. Bazan tab’a bata wani room da zata zargeni ba.. So tinda nace ki bar min komai ki bar min nasan abinda zanyi.. The bottom line shine Ummul bazata tab’a komawa ga Haidar ba..!” Bai jira cewarta ba ya katse kiran yana ci gaba da sakin huci. Ya jima zaune wajen yana sak’e sak’e cikin zuciyarsa da yanda zai b’ullo ma al’amarin. Ya shafe fuskarsa yana jin tsanan Haidar na ninkuwa cikin zuciyarsa. A b’angaren Ummul kuwa wani kula na musamman take samu daga Hajja wacce takeji tamkar dai jika zata samu. Duk yanda Ummul ke nuna bata son cikin bai hana Hajja d’aukin cikin ba. Sann dukda samuwar cikin ya haifar mata da tuno nata bayan bai canza yanda take ji gameda cikin a zuciyarta ba. Duk wani abinda tasan yanada kyau ga mata masu juna biyu sauri take taima Ummul. Haka zalika duk abinda tasan mata masu juna biyu naso kokari take ta mata koda Ummul d’in tana nuna bata so. ** A parlor Hajja ta tsinci magungunan da aka bama Ummul ko d’aya bata sha ba ta ajesu. Hajja ta girgiza Kai ta d’auki ledar maganin ta nufi d’aki yanda takeda tabbacin Ummul na kwance nan dan tinda suka komo daga asibiti da labarin cikin yau kusan kwanaki uku kullum zama take a d’aki tana aikin kuka abinci ma sai Hajja tayi da gaske take ci. Hajja ta turo k’ofan d’akin tana juya magungunan kaman mai k’irgensu take fad’in “Ummulkhair wai baki sha maganin nan ko d’aya ba tinda aka baki su..?” Da kyar Ummul dake ta kwance lamo hannunta guda saman cikinta ta mik’e tana goge ragowar hawayen da suka gangaro mata tanayi tana avoiding idon Hajja dan tasan bata son kuka da shiga damuwar da take. A hankali ta furta “Hajja ni wari suke min bana so.” D’an girgiza Kai Hajja tai kafin ta zauna gefenta kad’an “Banda abinki Ummul magani ai ba’a shansa dan dad’i.. Shi wann maganin folic acid ne kuma magani ne mai amfani sosai ga mata masu juna biyu wanda ake so su fara shansa tin ciki na k’arami sabida matuk’ar amfaninsa ga jaririn dake cikinsu. Da yawan mata masu juna biyu idan an basu magunguna makamancin wann sai su aje bazasu sha ba Wanda haka barazana ne ga lafiyar jaririn dake cikinsu.” Cikin murya irinta mai kuka ta katse Hajja “Amma ni bana son jaririn Hajja… Bana so na haifosa dan Allah..” Ta k’arashe cikin rawar murya "Hajja ta girgiza Kai had’ida kamo hannayen Ummul “Na haneki da fad’in kalmar nan Ummul.. Ke din nan bada jimawa ba zaki zama mahaifiya da izinin Allah. Duk abinda kike furtawa ki sani na tasiri Akan D’anki. Zama iyaye ba abu bane mai sauk’i. Daga zaran ance yau Kin zama uwa toh ki sani rayuwarki ta canza, dole ki zama mai kula da taka tsantsan kan abubuwan da kike furtawa musamman kalaman da suka danganci ‘ya’yanki dan bakin mahaifiya sosai yake tasiri. Sann duk wani decision da zakiyi making da ya danganci rayuwarki ki sani dole wann D’an nada wani kaso na hakki a cikinsa.. Ke din wani nauyi ne da amana yake gab da hawa kanki wanda yasa nake tunanin lokaci yayi da zaki waiwayi gida Ummulkhair.”" Ummul ta d’ago a d’an razane tana dubanta. Sai ta soma girgiza Kai “A’a.. Dan Allah a’a Hajja.. Bazan iya ba.. Bazan iya tunk’aransu a haka ba.. Wllhi bazan iya ba.. Dan Allah ki barni a nan nidai bani so su ganni da wann cikin..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka. Hisham da fitowarsa kenan da niyyan yima Hajja Sallama dan a ranan yake son komawa Abuja kafin ya ida shirya yanda zaiyi da cikin Ummul nan ya lab’e bakin k’ofa yana sauraronsu. Cikin zuciyarsa yake fad’in wato Hajja ta shirya mayar da Ummul gaban iyayenta kenan. Komawan Ummul gida kuma na nufin Haidar zai sameta. Ai kuwa bazai tab’a bari hakan ya kasance ba. Bazai tab’a bari Ummul da Haidar su sake crossing path ba tareda ya samo solution d’in yanda zaiyi da D’an Haidar dake cikinta ba.. He needs to make his move fast kafin Hajja ta b’ata masa komai.. Komawa Abuja bata gansa ba har sai ya samo ma Kansa mafita. Sai ya samo makomar cikin Haidar dan bazai tab’a bari duk sadaukarwar da yai su tafi a banza ba. Komawa da baya yai yana tunanin abun yi. Dole ya dakatar da Hajja. Kai tsaye waje ya fice yana kiran Anisa a waya. Nan yake la barta mata zancen Hajja da Ummul da ya sinkaya. Anisa ta mik’e tsaye a firgice tana girgiza Kai “No… No way Hisham… We can’t let this happen.. Kaga abinda nake fad’a maka ko.. Wann shine abinda nake tsoro.. Idan har Ummul ta koma gida toh kuwa shakka babu tamkar ta koma hannun Haidar ne dan a halin yanzu Haidar baida wani aiki sai zarya tsakanin Abuja to Kano. Bazaka bar Ummul ta isa Kano da wann cikin ba. Do whatsoever it takes ka dakatar da aukuwar hakan.. Hisham dole cikin nan ya salwanta dan cikan burinmu. Bamu tafi da nisa har zuwa nan da wani d’an tayi ya ruguza mana shiri ba.” Hisham ya bud’e marfin motarsa ya shige yana shafa Kai had’ida furzar da huci “Kaina ya k’ulle Neesa.. I don’t know what to do anymore.. Knowing Hajja bazatai k’asa a gwiwa ba har sai ta damk’a Ummul ga iyayenta.” Ya kuma furzar da huci yayinda Anisa taci gaba cikin hasala “Toh ai duka laifinka ne. Da ace ka d’auki shawarina ka tistiyesa da bamu kawo wann gab’ar ba.. Da ba wann zancen muke yanzu ba.” “Are you insane Neesa. Bakisan had’arurrukan dake tareda abortion bane ko me.? Ta ya zan jefa rayuwar Ummul cikin had’ari bayan duka abinda nake dan na mallaketa ne. Wann banzan Haidar d’in ne ya b’ata komai da ya kasa hak’uri har saida ya tabbata ya d’irka mata ciki. Idona idonsa sai na shak’esa tinda ya keta gonata dan Ummul tawa ce ni na fara saninta tun kafin ya santa. Ni na fara sonta tun kafin ya sota. Ni na fara niyyan Gina rayuwar Aure mai tsafta tareda ita kafin shi da uwarsa su k’ulla Auren yaudarar da yai da ita.. Idan sunana Hisham Haidar ya gama rayuwar Aure da Ummulkhair.!” Anisa ta furzar da huci “Duka wad’ann bazasu taimakemu ba Hisham. We are running out of time. We need to act now kafin Ummul ta isa Kano.!” Hisham yai shiru yana sakin huci yana fidda tururi shi kad’ai. Idonsa naga kallon gabansa daga nan yanda yake zaune cikin motar. Bai kuma ceda Anisa komai ba sai huci da yake fiddawa har saida Anisa tai tunanin ko ya aje wayar ne. Anisa ta kuma ce “Hello.. You there.?” Gungun matasa rik’eda makamai dangin dogayen wuk’ak’e da Hisham ya hanga ya sanyasa sakin murmushi. Duk abinda matasan suka gani sai Sun saresa da makami ba mutum ba dabba. Kai ko abin hawa suka gani a layin sai sun rabza masa makaman hannuwansu. Lokaci guda yace da Anisa “I have a plan.” Ya fad’i yana mai sakin murmushi kafin yaci gaba “I will surely ruin Hajja’s plan of taking Ummul back to her parents.” Cikeda k’osawa Anisa tace “Meye shirin naka.?” Hisham ya murmusa “‘Yan sara suka.!” Cikin rashin fahimta Anisa tace “Yan sara suka kuma.?” Hisham Ya kuma murmusawa “Just wish me well..!” Yana ida fad’in haka ya katse kiran ya mik’e da sauri ya fice daga motarsa. Aiko yana ficewa daga motar matasan nan suka k’araso a guje suka dinga dukan motar da makamai har saida suka farfasa glass. Shi ko Hisham a guje ya shige gida dan kar su saresa ko suyi ajalinsa. Yana shigewa ya sad’ad’a a hankali ya shige kitchen. Wuk’a ya d’auka zuciyarsa na bugawa da sauri. Ya rintse idanunsa yana bama kansa k’warin gwiwar abinda yai niyyan yi “I have no other option. Bazan iya barinki ma Haidar ba Ummul..!” Ya fad’i yana mai dab’a ma Kansa wuk’ar a gefen cikinsa. Ya rintse idonsa da k’arfin gaske sabida azaban zogin da yaji. Ya tafi da sauri cikin d’ingishi yana danne gefen cikinsa yanda yai stabbing Kansa jini na fita. Waje ya fito had’ida jefar da wuk’ar cikin hanyar ruwa har lokacin matasan basu daina ta’addanci da tada hankalin Al’umma a wann layin ba. (Allah ka shirya mana Al’umma.) A gigice ya turo k’ofar gidan yana bin garu yana rik’e gefen cikinsa yana tamke ido alamun zogi. Lokaci guda yake rangad’a ma Hajja k’ira da k’yar. Daga Hajja har Ummul a birkice suka fito jin irin yanayin da Hisham d’in ke ambato Hajjan sann sunji hayaniya ya kacame unguwar Wanda hakan yasa Hajja zama tareda Ummul a d’aki dan kar ta razana. Jini suka gani na bin gefen cikin Hisham da tuni ya galabaita yana fad’in “Hajja.. They stabbed me.. Help me..!” Dukansu jikkunansu rawa ya d’auka. Hajja ta shiga salallami cikin tsananin kid’ima “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Mai zan gani.? Hisham..!” Sai ta fashe da kuka ta nufesa a kidime tana fad’in “Sun caka ma d’ana wuk’a sun saresa.. Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raji’un..!” Ummul ma duk ta kid’ime sai aka rasa mai bama wani baki cikin ita da Hajja ga Hisham dake kwance shame shame yana nishi. “Hajja su waye suka caka masa wuk’a.? Mai ya faru dashi..?” Sai kuma ta nufi k’ofa a guje tana fad’in zata nemo agaji. Duk jikinta rawa yake. Shugaban committee na unguwar ne da wasu maza kusan biyu suka biyo bayan Ummul suka shigo gidan. Duk a rikice. Suna shigowa suka nufi yanda Hisham yake kwance shame shame ga Hajja gefensa sai hawaye take tana k’arfafa masa gwiwa da fad’in zai sami lafiya in sha Allah. Shi kuwa sai nishi yake mai nuni da yana jin jiki “Hajj..Hajja ki yafe mun.. Ki yafe mun Hajjah.. Mutuwa zanyi..!” Ta kuma matsan k’walla hannunsa rik’e cikin nata gam take fad’in “Ka daina fad’in haka D’ana. Zaka samu lafiya..” muryarta Ya sarkafe sai rawa da jikinta yake.. Daidai lokacin yan committee suka ciccibi Hisham da zummar kaisa asibiti. Hajja da Ummul suka take masu baya cikeda tashin hankali. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *52* *©️Sameena Aleeyou… * A gaggauce aka wuce da Hisham Emergency yanda aka soma kokarin ceto rayuwarsa. Idan kaga Hajja sai ta baka tausayi. Batada kowa sai tilon D’anta Wanda bata fata ta rasa shi. "Ummul ma karfin hali kawai take dan sosai daga Hajja har Hisham sosai suka bata tausayi. Mutane ne masu mutunci, karamci da sanin darajan D’an adam. Bata fata wani abun tashin hankali Ya samesu. Suna tareda ita a lokutan k’uncinta da tashin hankalinta dan haka Ya zama dole ta aje nata damuwar da tashin hankalin ta ji da nasu damuwar. Fatanta Allah ya tashi kafad’un Hisham ya bashi lafiya sann ya sassauta ma Hajjah." Jiki a sanyaye Ummul ta k’araso yanda Hajja ke zaune bayan an shige da Hisham surgery. Hajja ta d’ago ta dubeta sai ta k’ak’aro murmushi na karfin hali tace “Ya kamata ki koma gida haka nan ki huta kema ba k’oshin lafiya ne dake ba. Stress ba naki bane.. Ya kamata ki samu hutu.” Ummul ta kamo hannayen Hajja tana girgiza kai “Bazanje ko ina ba Hajjah.. Ina nan tareda Ke in sha Allah.. Har sai munsan halinda Yayana Hisham ke ciki.” Hajja ta k’ak’aro murmushi tana duban Ummul d’in. Sai ta goge hawayen da Ya gangaro mata “Shi d’aya Ya rage mun.. Yazo cikin rayuwata a lokacin da nai zaton Babu wani k’ofa na haske da zai kuma budewa cikin rayuwata.” Sai ta d’an murmusa “I named him Hisham. Meaning generous. Sabida Ina so ya girma da zuciya mai yalwa. Zuciya mai son bayarwa da taimakawa cikin duk halinda ta Sami iko..” Ummul ta jinjina kai cikin kokarin k’arfafa ma Hajja gwiwa “Shid’in ya dace da sunansa Hajja. Tabbas yanada zuciya mai kyau mai kwad’ayin taimako ba tareda ta nemi wani abu in return ba. Ni shaida ce akan irin taimakon sa a gareni.. Shid’in D’a ne da ko wace uwa zatai Alfaharin samun irinsa. You are blessed to have him as a child Hajja.. A lokutan da wasu ‘ya’yan sukan zama jarabawa ga iyayensu wasu ‘ya’yan abun alfahari ne da sanyin idaniya ga iyayensu. Ked’in Lallai kinada sa’a Hajja.. Babu abinda yafi buk’ata daga gareki a halin yanzu face addu’o’in ki gareshi.” Ta k’arashe murmushi da siririn hawaye saman fuskarta. Hajja ma murmushi take tana hawaye tana jin dadin kyawawan shaidan da akai ma tilon D’anta musamman idan ta tuna mahaifinsa ya ciresa daga cikin ahalinsa Tun baizo duniya ba. Sai jikinta ya d’anyi sanyi. Ta soma jinjina Kai a hankali tana fad’in “A koda Yaushe fata na shine na kasance mahaifiya da zai alfahari da ita. Mahaifiya da zata sauk’e nauyi da hakkinsa da ya ratayu wuyanta..” Sai Muryarta ya soma rawa “Ina tsoro Ummul.. Ban sani ba.. Ko na gaza a wani fannin domin shid’in Ya girma baisan mahaifinsa ba..” Tausayinta ke ninkuwa cikin Zuciyar Ummul. Tai saurin girgiza kai “Ke mahaifiya ce da ko wani D’a zai alfahari Ya kirasa da mahaifiya Hajja.” Sai ta murmusa “Meyasa ma Ya Hisham bazai zama mai kirki ba bayan ya kasance D’anki.?” Murmushi Hajja Tai dan ta kula so take ta dan kwantar mata da hankali. Ummul ta matso jikin Hajjan tana kuma fatan sauk’i ma Hisham. Tana kwance jikin Hajja takai hannu a hankali tana Shafa nata cikin. Batasan labarin Hajja ba. Sann bata san abinda ya faru da mahaifin Hisham ba. Amma Hajja ta zama tamkar inspiration d’inta. Ita d’in ta raini D’a kaman Hisham. D’an da kowa zai alfaharin samun kaman shi. Sai taji k’warin gwiwa na shigarta akan cikinta. For the first time da taji tana so ta haifo abinda ke cikinta koda bazata tab’a sanar da mahaifinsa ba. Koda bata k’aunar mahaifinsa.. Zatai komai ma D’anta da izinin Allah. Zata zama masa uwa ta zama masa uba kaman yanda Hajja ta jajirce akan D’anta. Anyi aiki ma Hisham kuma aiki yayi kyau cikin ikon Allah. Hajja ta shigo ta tadda shi tareda ‘yan committee suna jajanta masa abinda ya faru da tambayarsa yanda abin ya kasance. "Hisham dake kwance da d’inkakken ciki nan yake labarta ma yan committee cewa yaje taimakon wani yaro ne suka soka masa wuk’a. Hajja ta lumshe idonta tausayi da k’aunan D’an nata na ninkuwa cikin zuciyarta. Allah sarki, shidai kamar ko Yaushe cikin taimakon Al’umma yake. Ashe silan tsautsayin da Ya auka masa taimako yaje kaman yanda tai tsammani." Ta k’araso suna gaisawa da shugaban committee yanda yake sanar dasu ana kan k’ok’arin kama yaran dan a hukuntasu sabida rashin hukuntasu da ake yasa suke abinda suka so cikin Al’umma. Hajja ta girgiza kai tana amsawa. Ta k’arada “Allah dai ya shirya mana zuri’a amma al’amarin dad’a ta’azzara yake.” Shugaba ya girgiza Kai yace “Sai ka rasa ina matsalar take. Shin iyayen ne ko kuwa dai halin yau da muka tsinci kanmu ciki ne. Wai nan abinda suka fito sunayi na tada hankalin Al’umma sunansa shara. Ko mai suka gani sai Sun lahanta.. Yara k’anana samari da basu wuce ace suna makaranta ba.” Hajja ta jinjina kai “D’an yau ne ka haifesa baka haifi halinsa ba.” Ya jinjina Kai “Tabbas akwai jarabawa a wasu lokutan kuma sakaci na iyaye. Mutum karma ka haifo yaran da bazaka iya kula dasu ba yaran da bazaka iya basu tarbiya. Tarbiya Ya k’unshi kula da d’aukan nauyi tareda sauk’e wasu hakkoki da suka ratayu wuyan iyaye. Sai kaga mutum matansa hud’u d’akuna hud’u gareshi wani ma gidan haya ne. Kai shekaran jiya aka kawo mana wani case d’aki d’aya aka raba da labule aka aje mata biyu labule ne kawai Ya rabasu. Ina addini cikin wann al’amarin. Ga yaran nan haifo su ake ba mai zuwa makarantan islama balle na boko.. Ta ya za’a ce kana mutum mai hankali da Allah Ya halicceka da k’wak’walwa bakada tsari a rayuwarka.? Haka zakiga yaran Sun girma wasu ma a mak’ota suke kwana dan babu d’akin kwanansu a gidan mahaifinsu. Yarinya budurwa ace ita zata nemo ma kanta abinci ubanta mahaifi na nan da rai amma baisan yaya d’iyarsa take cin abinci ba. Kuma zaki samu bai fasa aure ba bai fasa haifo wasu yaran ba.. An bar yara kara zube an jefa rayuwarsu cikin garari Tun suna k’anana. Ta ya za’a tsammaci Al’umma mai nagarta da irin wann tauye hakki da ake ma wad’ann yaran da tuni Sun zama victims of circumstances.” Hajja ta jinjina Kai “Haka ne Suhaga.. Da yawa an sha’afa da hakkin yara na iyayen kawai ake hangowa. Tabbas iyaye sunada girman hakki akan ‘ya’yansu wanda bayan biyayya ga Allah da manzonsa sune suka biyo baya. Amma sai muna mance kafin mu Gina irin wad’ann yaran sai mun fara sauke nauyi da hakki nasu dake rataye wuyanmu Wanda za’a tambayemu akai. Dole mutum yai k’ok’arin Gina yau dinsa da kyau dan gobensa Ya inganta. Allah ya iyar mana da tarbiyar yaranmu ya bamu ikon sauke nauyi na zama iyaye da ratayu wuyanmu gwargwadon iko.” Suka jinjina kai suna amsawa da Ameen. Ummul dake mak’ale daga k’ofa ta juya da baya a hankali ta nemi waje ta zauna tana tunanin nan zuwa wani lokaci kadan wann nauyin zai hau kanta. Cikin zuciyarta take addu’an Allah Ya iya mata Ya dafa mata Ya bata ikon sauke nauyin dake gab hawa kanta. ** Gaba d’aya hankulansu ya karkarta ya koma ga jinyar Hisham. Daga Hajja Har Ummul Sun aje zancen tafiyar Ummulkhair Kano. Zuciyar Hisham fari tas dan dama wann dalili yasa yai ma kansa abinda yai. Ya d’auki wann risk din dan ya karkatar da tunaninsu da hankulansu. Sunyi waya da Haidar ya sanar dashi cewa Sun tafi da mahaifiyarsa can wani k’auye ne garin magani Shiyasa bai samu komowa bakin aiki ba. Sam Hisham bai sanar da Haidar cewa shine baida lafiya ba. Haidar yai shiru yana saurarensa sai kuma yace “Amma.. Meyasa baza’a kawo ta nan Abuja Asibiti ba Hisham. Idan ta kama a fitar da ita meyasa bazaa fitar da ita ba..? I see no reason da zaisa ka dauki mahaifyarka ka kaita wani jeji da sunan neman magani.. Meye amfanin karatun ka ne wai.?” Hisham Ya k’ak’aro murmushi “Engr kenan. Kasan ku yan bokon nan kunyi imani da boko amma ita Hajja tafi son na gargajiyan kuma kasan ance magani dace.” Yana maganar yana tamke fuskarsa sabida zogi da yake ji. Haidar Ya jinjina kai ba tareda yace komai ba. Hisham ya k’arada “Nace.. Ya labarin Ummulkhair kuwa..? How have you been coping..?” Haidar ya dan lumshe ido had’ida furzar da huci kadan “Every minute passes by feels like a century…” Cikeda nuna kulawa Hisham yace “Haidar I’m sorry.. I’m so sorry brother bana tareda kai a irin wann lokaci mai matuk’ar wahala.” Haidar ya katsesa “You have your own problems to deal with Hisham.” Ya danyi fasali kafin yaci gaba “Abu d’aya da nakeda yak’ini is that I will find Khairy… I will definitely find her no matter the cost… I will never give up.!” Yanda yake maganar with so much courage and determination sosai ya haifar ma Hisham fad’uwan gaba. Ya had’iyi miyau da kyar kafin ya k’ak’aro murmushi yace “I trust you Abokina. The word giving up has never been in your vocabulary.. Keep searching until you find her.” Haidar baice dashi komai ba sai duban Anisa dake tunkaro yanda yake da yai. Taci Uwar ado kaman mai zuwa gidan biki. Sai yace da Hisham “We talk later..” Daga haka sukai sallama ya katse kiran. Anisa ta k’araso tana ci gaba da k’wark’warsa hannunta rik’eda k’aramin paranti. Fuska d’aukeda murmushi Tai masa sallama. Ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta aje masa tray din tana fad’in “Sannu da hanya. Mommy tace yanzu sauk’ar daga Kano.. Ya hanya..? Ya ka baro su Ammi.?” A tak’aice ya amsa mata sai gani tai ya mik’e yana amsa waya Wanda ga dukkan alamu aiki Ya Shafa. Baiko bi takan ta ba ya fice yana amsa kiran. Anisa tabi bayansa da kallo kaman zata rusa ihu. Ko kallo fah bata ishesa ba.. Tazo tana tarbansa amma ko kallanta bai ba balle yaci abinda ta kawo masa. K’atutun bak’in ciki Ya tokare mata mak’oshi sanda ta waiga ta kalli k’atoton hotonsu shida Ummul Wanda akai masu a ranar bikin tariyarsu an kafa a parlorn kaman ka kirasu su zo. Nan taji k’walla ya ciko idonta ta mik’e ta isa jikin hoton. Cikin zuciyarta take fad’in ‘Meye ta fini dashi Haidar.? Meyasa bazaka mance da ita ba.? Meyasa bazaka hak’ura da ita ka so ni ba. Wllhi zan maka komai matuk’a kaso ni.. Ni Kai kawai nake so.. Dan Allah ka fahimce ni.’ Ta k’arashe zancen zucin nata tana Shafa hoton daidai fuskar Haidar. Mommy dake daga jikin staircase tanata kallonta tana karantarta daga nan yanda take tsaye. A hanakali Mommy ta soma takowa cikin parlorn. Anisa ta waigo da sauri tana duban Mommy. Murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar ma Mommy. Mommy ma ta maida mata Martanin murmushin. “Sannu da sauk’owa Mommy.” Anisa tace tana risinawa. Da murmushi saman fuskar Mommy ta amsa “Sannu Daughter.” Sai takai dubanta ga parantin dake aje saman side table “A’ah! Ina Aliyun.. Har ya fice ne wai.?” Anisa ta jinjina Kai Jiki a sanyaye “Ya fice ko ruwa bai sha ba Mommy..” Ta marairaice fuska “Mommy I’m worried about him.. Bakiga yanda ya fice ba duk bashi a hayyacinsa. Ina fata a samu Ummul very soon..” Ta k’arashe tana kai dubanta go hoton Haidar da Ummul fuskarta fal damuwa. Mommy taci gaba da takowa tana jinjina Kai a hankali. Ta isa jikin pic din itama. Idonta naga hoton take fadin “Wherever she is. I hope she’s safe.” Anisa ta jinjina Kai. Cikin zuciyarta tace ‘Tana d’aukeda jaririn ciki. Jikanki da bazan tab’a bari ki sani ba. A fili kuwa sai ta kuma marairaice fuska tana duban Mommy cikeda kulawa “But.. Mommy mai zai faru idan bata dawo cikin rayuwar Haidar ba. Haka nan.. Zai k’arashi rayuwarsa a gantale Mommy..? It’s been three months now.” Tai maganar kaman zatai kuka. Mommy ta tsareta da ido sai ta d’an girgiza Kai kadan had’ida furzar da huci “I don’t know Anisa.. Bayan yarinyar can da tai masa asiri bana jin Haidar Ya taba son wata mace except Ummulkhair..” Ta danyi fasali “Ban sani ba.. Kodai zai so wata a gaba kodai ni ce zan sake aura masa wata.” Anisa tai sauri ta dubi Mommy “Mommy kina nufin zaki sake aura ma Haidar wata matar idan Ummul bata dawo ba..?” Mommy ta dubeta sai tace “Why not.! Idan har a baya lokacin da bai daukan magana na da mahimmanci Ya amince da zab’ina Maiyasa yanzu bazan sake zab’ar masa mata ba. Matsalar kawai ban san wace zan zab’o masa mai hankali kaman Ummulkhair ba..” Anisa ta sha jinin jikinta kanta a k’asa. Mommy ta kafeta Da ido sai ta gyara zama tace “But.. I have someone in mind already.. Saidai ban sani ba ko zata amince dukda itama inada iko akanta..” Anisa ta d’ago a zabure tana duban Mommy. Murya har na rawa take furta “Mommy.. I don’t think akwai macen da zata guje ma auren Haidar duk had’uwar ta da isarta.. He’s every girl’s dream.” Mommy taci gaba da dubanta murmushi saman fuskarta tace “You think so.?” Anisa ta jinjina Kai “Hundred percent sure.!” Mommy ta kuma jinjina Kai “Anisa what if.. Kece wann yarinyar da nai sha’awa ma D’ana Haidar..” K’iris ya rage Anisa bata yanki jiki ta zube k’asa ba dan a bazata taji maganar Mommyn. Tama kasa yarda da abinda kunnenta yaji mata. Ta girgiza Kai cikin rashin yarda tana duban Mommy “Mommy… Ni..? Kike so Haidar ya Aura.?!” Mommy ta jinjina mata Kai “Why not.!” Mommy tace cikeda kulawa. Ta k’arada “You are his cousin sann ko da ace Ummul ta dawo gidan Haidar nasan baza’a samu matsala daga wajenki ko wajenta ba.. I’m sure ku biyun zaku fahimci juna… But I’d have to ask you this question. Do you love Haidar..?” Anisa wacce ta koma tamkar statue baki sake take duban Mommy. Ta kasa gaskgata abinda ke faruwa. Mommy ta kuma jefa mats tambayar sai Anisa ta fashe da kuka. Mommy ta kamo hannunta tana girgiza Kai “A’a Anisa meye kuma abun kuka. Kinga idan baki sonshi bazan tak’ura ki ba zan nema masa wata can daban..” Mommy bata Kai aya ba Anisa ta shiga jinjina Kai tana murmushi “Mommy kukan farin ciki ne.. I never thought a day like this would come… I mean… Not this soon… Mommy I.. I can’t believe it… My dream is finally coming true.” Da tsananin mamaki Mommy ke dubanta sai ta girgiza Kai kadan tace “Do.. You love Haidar.?” “I’ve always loved him Mommy.. I love him since childhood…” Mommy tace “Aw..! wai so kike kice tuntuni kina son Haidar..?” Taci gaba da jinjina Kai yayinda farin cikinta ke ninkuwa. Tin ina yarinya nake son shi Mommy.. Kawai kun kasa fahimta ne.. But he’s the love of my life..” Mommy taci gaba da jinjina Kai tana dubanta “Does your Mom know..? Asshe tasan kin jima kina son Haidar..?” Sai a nan ne Anisa ta d’an ja jinin jikinta.. Sai ta girgiza Kai alamun a’a “Kawai.. Ni kad’ai na rik’e abuna cikin zuciya.. Ko Hilal bai sani ba.” Mommy ta jinjina Kai kaman mai nazari sai kuma ta sakar ma Anisa murmushi “Yazo gidan sauk’i had’aku aure bazai wahala ba.” Anisa ta d’an dubeta. Fuska dauke da alamun tsoro “Amma.. Mommy what if Haidar rejects the idea.. What if yak’i aminta da Auren.?” Murmushi Mommy ta kuma sakar mata “Kar ki damu. Yarona Haidar mai biyayya ne.. Ko a baya baya sab’a umarni na balle yanzu.. Kawai muyi fatan naki iyayen su amince musamman ma Amminki tinda har yanzu bamu koma kaman da ba.” Anisa ta waro ido tace “Haba Mommy dani da Ammi fah ke d’in duka uwa ce a wajenmu.. And a halin yanzu Ammi dalilin da zaisa zumuncinku ya sak’e k’ulluwa take nema kinga kuwa zatafi kowa farin ciki da wann had’in.. Abba kuma kinsan baida matsala tinda ba kudinsa zaa karb’a ba.” Mommy taci gaba da duban Anisa mamaki bai saketa ba. Lokaci guda take jinjina Kai “Shikenan.. Zan samu Asshe da maganar..” Cikeda zak’ewa Anisa tace “Toh Mommy shi kuma fah..? Ina nufin Haidar..” Ta k’arashe cikeda sakarci. Mommy ta jinjina Kai “Haidar bazai zama matsala ba dan haka kar ki samu damuwa kinji.” Anisa ta daka tsallan murna ta nufi hanyan kitchen a guje tana rangada ma ma’aikatan kitchen k’ira tana fad’in duk su fice zatai ma mijinta abincin dare. Mommy ta bita da kallo har ta shige kafin ta jinjina kai kadan tace “Sannu a hankali.” Daren ranan Anisa bata sama bata k’asa. Sai kai komo take da sunan tana shirya ma Haidar dinner. Mommy ta shigo kitchen din tana dubanta fuska d’aukeda murmushi “Iyye lallai.! Ashe d’iyar tawa gwana ce wajen girki.” Mommy tace tana bude dishes din da Anisa Ke shiryawa. Anisa ta wani murmusa tana sadda kai alamun kunya. Mommy ta kuma murmusawa “Yau kuma Mommyn taki kike jin kunya..? Kinga ni ba wata surkunta tsakaninmu ki saki jikinki Dani fiyeda yanda muke a baya.” Anisa ta kuma murmusawa “Shikenan Mommy.. I’ll be open with you.. Ina so ki kaunaceni kaman yanda kika k’aunaci Ummul koma fiyeda ita.” Mommy ta jinjina Kai “Ko ba Haidar ni mamarki ce Anisa. You shouldn’t be hiding things from me haka ne..?” Anisa tai saurin jinjina Kai cikeda jin dadi. Mommy tace “Good. And if you want anything.. Don’t hesitate to let me know kinji koh.” Nan ma da sauri Anisa ta jinjina kai kafin Ta k’arada “Mommy ni kin gama min komai a rayuwar nan… Ina jin babu wani abu da zan nema kuma da Ya wuce Auren Haidar. Duk duniya ke kadai kika fahimci mai nake ciki. For so long Ina dakon soyayyarsa Babu Wanda Ya fahimta. Sai Allah Ya share mun hawaye yasa kika fahimta.. Thank you Mommy.” Mommy ta dafa kafad’arta “Anything for my Daughter..” Anisa na wangale hak’wara tasa kai zata shige cikeda jin dadi. Mommy ta tsareta da ido sai ta dan riko hannunta alamun dakatarwa “Ina kuma zakije Daughter..?” “Zanje na sake kwalliya ne kafin Haidar ya shigo.” Mommy ta girgiza mata Kai alamun a’a “Bana so kina rawar k’afarnan a gabansa sai ya rainaki. Ki dinga jan ajinki matsayinki na mace. And kar Ki mance Haidar baisan da zancen ba tukuna.” Anisa tai raurau da idanu had’ida tab’e fuska kadan. Ta dubi Mommy kaman zatai kuka “Amma Mommy zaki sanar dashi.?” Hannunta Mommy ta kamo “Taho nan kiji.” Suka zauna saman kujera. Mommy ta dubeta tace “Anisa nasan kinsan al’amarin aure ba abin wasa bane. Balle Haidar dake fuskantar k’alubalen rashin Ummul. Matuk’a muka tunk’aresa da irin wann batu a daidai wann gab’ar za’a iya samun matsala ne. Kinsan sa yanzu sai ya kwance mana ya koma Haidar d’insa na da. Sann Daddy ma bazai yuwu muzo masa da batu irin wann a daidai wann lokaci ba. Kowa zaiga rashin dacewar hakan musamman da yake Mahaifin Ummul na nan asibiti a Abuja. Ya kamata mu bar komai har sai an sallamesa sun koma can gida Kano ta yanda ba wani tashin hankali da zai bullo mana. A tsanake zamu tunk’ari lamarin. Kedai kawai ki kwantar da hankalinki kiyi duk abubuwan da na umarceki tinda kinada yarda da amincewata ki k’addara tamkar kin Auri Haidar an gama.” Anisa ta danyi jim sai kuma ta jinjina Kai tace “Gaskiya ne Mommy. And its a once in a lifetime in sha Allah. Kuma so nake Aurenmu Ya karad’e ko ina dan babban biki nake so Mommy.” Mommy ta jinjina Kai tana duban Anisa murmushi saman fuskarta. ** A haka Anisa taci gaba da mafarkinta na kasancewa matar Haidar cikin kwanciyar hankali sanin cewa tana tareda yarda da amincewar Mommy. Ba abinda yake gabanta a halin yanzu tamkar taga wann mafarki nata Ya zama gaskiya. Dole ta dad’a daure belt dinta da kyau dan ta tabbata Ummul bata dawo ba. Burinta bai wuce taga wann ragwababben uban Ummul d’in Ya bar garin ba. A can b’angaren su Ummul ma Hisham yanata samin lafiya saidai da yaga hankulansu zai karkata zuwa wani abin daban sai ya b’ullo da wani abin wanda zai dauke hankulansu. A haka aka kwashe kwanaki satuttuka Har aka soma k’irga watanni. Kowa da abinda yake burin cimmawa. Ummul na nan tana rainon cikinta. Hisham bai fasa kudirinsa da shirinsa ba. Haidar bai fasa neman Ummul ba. Mommy ta maida hankali kan Anisa yayinda Anisa taci gaba da mafarkin cikan burinta. Abba yanata samun lafiya. Daddy nata zarya tsakanin SouthAfrica da Nigeria kasuwancinsa na dad’a bunk’asa a k’asashen k’etare. Cikin Ummul nata girma cikin k’oshin lafiya. Saidai tinda cikin Ya fito ta kuma rok’on Hajja da cewa dan Allah ta barta tai rainon cikin gabanta ko dan guje ma abinda zaije yazo cikin ahalinta. A b’angaren Haidar kuwa dukda ayyuka da suka sha gabansa bai fasa k’udirinsa na nemanta ba. Dan tinda tafiye tafiyen Abba ya k’aru Sai ayyukan cikin gida Nigeria suka dawo wuyan Haidar gaba d’aya. Kusan shi yake kula da ragamar Kampanin. * Watan Abba uku a Abuja aka sallamesa daga asibiti. Tuni Haidar Ya kira Sadis ya sanar dashi tinda dama duk wani hidindimun asibitin Sadis d’in keyi. "Kai tsaye gidan Daddy suka taho. Abba har tafiya yake da sanda, idan ka gansa bazaka gane sa ba ya samu lafiya da kula cikin ikon Allah. Sai son barka. Mama Tani da Abba ne a bayan motan yayinda Azeema ke zaune mazaunin mai zaman banza Sadis na tuk’awa." Koda suka iso gidan Mommy da kanta ta tarbesu. Tuni tasa an shirya musu sashen bak’i sai haba take dasu Anisa kaw sai cika take tana batsewa dikda cikin zuciyarta fal annashuwa ne an sallami nakasashen uban Ummul zasu fice daga rayuwarsu gaba d’aya su huta. Suka raka juna da mugun kallo itada Azeema dan dukansu basu mance karonsu da juna ba. Anisa taja dogon tsaki ta juya Azeema ma Tai shigewarta tana kad’a kai. Tinda suka iso gidan jikin Abba ba a sake bane. Ya kuma duban Mama Tani yace “Tani wai shin bazai yuwu mu tafi gida a yau d’in nan bane sai mun kwana gidan sirakanmu. Ni fah sabida naga Ummulkhairi na amince na taho.. Amma ina ganin rashin dacewar hakan. Abin zai yawa ai.” Dukda k’irjin Mama Tani dake bugawa sai tai k’arfin halin cewa “Haba Malam.. Daga sallamanka asibiti sai ka hau hanya.. Ai dai ka jira ka d’anji k’arfin jikin.” Shiru yai kaman mai nazari sai Ya girgiza kai “A’a Tani.. A Ina kika taba jin Uba yaje gidan sirakansa Ya saki jiki.. Wann ai bai tsari ba… Iyakacin karamci da duk wani taimako mutanen nan Sun mana. Kuma na shaida Ummulkhair tayi sa’an miji da iyayen miji masu dattaku da sanin darajan d’an Adam. Kinga bazan so ni kuma suga namu rashin dattakun ba.” Tani ta d’an murmusa “Haba Malam. Kamawa fah take. Ba don jinya da Allah ya jarabceka dashi ba da hakan bazai kasance ba. Fatanmu Allah ya k’ara maka lafiya su kuma ya biyasu Ida mafificin alkhairi.” Sai Ya dubeta kaman Wanda Ya tuna wani abu “Na shafe watanni banga Suwaiba ba..” Wai ance kishi dole saida Mama Tani taji zuciyarta ya d’an sosu. Sai Tai kokarin kauda tunanin tace “Malam a yau kawai sau uku kai waya da Suwaiba.. Kai hakuri zaka ganta ne da zaran mun koma gida. Kasan Suwaiba da kunya da surkunta bazata iya zuwa nan ta duba ka ba Shiyasa bata zo ba amma ai nakan had’aku a waya tin bayan da likitoci suka ce zaka iya amsa wayan talho haka ne.” Abba ya jinjina Kai a hankali sai kuma yace “Ummulkhairi fah.? Kince bata iya fita ko k’ofa sabida junan da take d’auke dashi. Likita yace mai tattare da had’ari ne. “ Ya d’anyi fasali “Amma ai zan iya ganinta yanzu.. Zan iya zuwa Har yanda take ko Tani.” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa da sandarsa. Mama Tani ta rasa ta ina zata b’ullo masa. Mai zata sanar dashi gameda Ummul da Aurenta.? Ganin yana k’ok’arin mik’ewa yasa Tani saurin kamo hannunsa “A’a Malam ka dakata ka dan huta kaci abinci.. Ai.. Ai nan gidan sirakan Ummulkhairi ne.. Ba.. Ba nan bane Gidanta Shiyasa baka ganta ba.” Ta fad’i cikin k’ok’arin had’o kalaman tanayi tana kauda fuska gefe. Abba ya tsareta sosai da ido dan yasan matar tasa sosai. Ya sani idan tana had’o zance. “Tani.” Ya kirawo sunanta cikeda kulawa. Ta d’ago ido a sanyaye ta dubesa “Na’am Malam.” “Ina Ummulkhairi..?” Ya jefo mata tambayar. Tani ta d’an sosa keyarta “Tana gidanta Malam. Dan Allah ka kwantar da hankalinka. Kaji mai likitan nan yace sam shiga tashin hankali ko damuwa ba naka bane… Kaga lokacin sallan la’asar ta gabato barin taimaka maka ka d’auro alwala.” Ta fad’i tana mik’ewa. Bayan ta masa rakiya ban d’aki ta nuna masa yanda zaiyi nan ta dawo d’akin tana waya da abokiyar zamanta Suwaiba. Ko shakka Babu matsalan suke tattaunawa. Sam Tani bataji fitowar Abba daga Band’aki ba sai muryarsa ta saurara yana fad’in “Tani… Mai nake ji kina cewa? Za’a sami Ummul da izinin Allah..? Tani meke faruwa..? Ina Ummulkhairi…?” Ya k’arashe tambayar jikinsa na rawa daga nan yanda yake tsaye. Har sandarsa rawa take. Murmushin da yafi kama da yak’e Mama Tani tai. Ta k’araso tana fad’in “Wai Har ka fito bakai kirana ba.” Abba ya girgiza Kai ba alamun wasa “Baki amsa min tambayata ba Tani. Da waye kike magana a waya? Sann meyasa kikace za’a samu Ummulkhair.?” “Da Suwaiba nake magana Malam. Kuma tambayata take ko kun gana da Ummul tinda tasan kana matuk’ar son ganin Ummulkhairin.. Shine take ce min an sameta a waya nace za’a sameta in sha Allah.” Ta k’arashe cikin k’ok’arinta na gamsar dashi. Abba yai shiru kaman mai nazari dan Sam baijin zuciyarsa ta natsu da maganganun Tani d’in. Bayan yayi sallah Tani ta taimaka masa suka fito parlor yaci abinci Ya sha magani. Nan Mama Tani ta soma waige waigen neman Azeema. Ta mik’e tana fad’i ma Abba bari ta nemo Azeema cikin gidan. Dan Sam zuciyarta bai kwanta ba da rashin ganin Azeemar tinda tasan sam ita da Anisa d’iyar k’anwar Hajiya Kwaise had’uwarsu baya dad’i. Ficewar Mama Tani da kad’an aka soma k’wank’wasa k’ofar. Abba ya mik’e kad’an daga kishingid’en da yake. Ya bud’e idanunsa yana duban k’ofan yake fad’in “Bismillah.” Wata budurwa ce ta turo k’ofan da Sallama saman bakinta. Abba ya gyara zamansa yayinda murmushin Anisa Ya k’aru tana tambayar Abban ko zata iya shigowa. Abba ya jinjina Kai yana bata izinin shigowa had’ida amsa gaisuwarta. Anisa ta risina yawa mutumiyar arziki tana kuma yima Abba sannu da jiki had’ida fatan samun lafiya. Harda addu’o’i ta jero masa. Abba ya amsa cikeda jin dad’I musamman da yaga yanda yarinyar ke girmamasa sai ta tuna masa da Ummul d’insa. "Anisa taci gaba da risinawa tana fad’in “Abba ni sunana Anisa, kuma k’anwa nake ma sirkin ka Aliyu.. Sann munyi zaman dad’i da Ummul dan har mun k’ulla k’awa ce da Ya zarce Ya koma tamkar ‘yanuwan juna..”" Abba yace “Allah sarki.. Toh.. Ma sha Allah.. Ai ga dukkan alamu halayyanku ne yazo d’aya da Ummulkhair.. Dole kuyi abota.” Anisa taci gaba da murmusawa tana kuma sadda Kai. Sai ya dan gyara zamansa kad’an yace “Amma.. Nace ina ita Ummulkhairin.. Har yanzu ban ganta ba… Ina so naga d’iyata.. Ina so naga yanayin jikin nata.” Anisa ta waro ido tana dubansa. Sai ta d’an waiga baya kad’an tace “Ban gane baka ganta ba Abba.. Wai har yanzu basu sanar dakai ba.?” Abba ya dubeta da mamaki “Akwai wani abinda Ya kamata na sani ne gameda Ummulkhairina..?” Anisa ta soma girgiza kai “Abba ai Ummul ta jima bata nan.. Idan ban b’ata lissafi ba mun d’ebe a k’alla watanni shida bamusan yanda take ba..” Abba ya girgiza Kai cikin rashin fahimta yana dubanta “Ban fahimceki ba yarinya.. Kina nufin b’acewa Ummulkhairi tai baku san yanda take ba.?” Anisa sai ta fara hawaye murya na rawa take fad’in “Abba Auren Ummul da D’anuwana Aliyu Ya k’are… Ta tafi babu Wanda yasan ina ta tafi..” Daidai lokacin Mama Tani da Azeema suka shigo suka tadda Abba na dafe k’irjinsa ga Anisa duk’e wajen tana kuka. Mama Tani ta soma salallami ta isa ta tallafi Abba dake k’ok’arin kaiwa k’asa yayinda Azeema ta tafi a guje ta shak’o Anisa tana tambayar mai tai ma mahaifinta. Tani taci gaba da jijjiga Abba tana fad’in “Malam meke faruwa..? Lafiya na Barka.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Malam.!” Ita kuwa Azeema tuni ta shak’e Anisa tana fad’in sai ta sanar da ita mai tai ma mahaifinta.. Hayaniyar yaja hankulan mutanen gidan. Mommy ta shigo a fujajan tana tambayar meke faruwa.? Azeema taci gaba da mak’ura Anisa tana fad’in ko ta fad’a mai tai ma mahaifinta ko itama ta shak’eta sai ta daina numfashi. Jikin Anisa yaci gaba da karkarwa. Fad’i take “Mommy ki yarda dani wllhi babu abinda nayi.. Gaishesa na shigo yi Ya tambayeni Ummulkhair ni kuma na sanar dashi bata nan.. Mommy bansan Mahaifin Ummulkhairi baisan meke faruwa ba.. Wllhi iyakacin gaskiyata kenan.” Azeema ta kuma yowa kanta tana fad’in “K’arya kike bak’ar munafuka shak’esa kikayi..” Mommy ta daka musu tsawa da fad’in “Ya isheku dukanku..!” Ta dube Azeema tace “Maza kirawo Sadis a koma asibiti.” "Sai suka sinkayo muryar Abba yana fad’in “A’a ba sai an koma asibiti ba.. Magana guda nake son ji!” Ya dubi Tani dake hawaye yace “Tani, ina Ummulkhairi..? Shin gaskiya ne Aurenta Ya k’are ta tafi babu Wanda yasan ina take.? Shin wann ne dalilin da yasa na kasa ganin Ummulkhair.? Shin wann ne abinda kuketa b’oye min keda Suwaiba.? Wann ne dalilin da yasa Suwaiba ta kasa zuwa ta dubani tsawon watannin nan.? Tani mai kuka aiwatar lokacin da nake kwance..? Wane irin Aure Suwaiba da ‘yanuwana sukaima Ummulkhair da zaisa ta guji gida bayan mutuwansa.?”" Sai kukan Tani ya k’aru yayinda jikin Mommy yai sanyi. Tai k’arfin halin k’arasowa. Ta dubi Abba sai ta dubi Tani.. Tace “Abban Ummul.. Dan Allah kar ka yanke hukunci Har sai ka saurareni… Duk abinda ke faruwa ko ince abinda Ya faru.. Babu wani mai laifi face ni.. Duka laifina ne…” Daidai lokacin Haidar Ya shigo. Kafin Mommy ta k’ara furta wani kalma Haidar yai karaf yace “Abba duka laifi na ne.. Ni nayi AUREN WATA UKU da Ummulkhair.! Ni nayi Aure mai k’ayadadden wa’adi da ita. Auren da zai Wanzu na tsawon Watanni uku. Ni na tilasta mata ta Aureni dan ta Sami damar biyan kud’in jinyarka.! Na saka sadakin Ya zama kudin da za’a maka aiki dashi muddin ta amince da Aurena.. AUREN WATA UKU.. Dan na cimma burina na mallakan wani aiki k’ark’ashin kampanin mahaifina..” Muryarsa ya soma shaking “It is all my fault.! Duka laifina ne ni Aliyu.. Umma da Mommy duka basuda laifi.. Laifin nawa ne… Da nai irin wann wulak’antaccen Auren da Ummulkhair..” Cikin tsananin shock Abba ke dubansa. Ya soma takowa yana dogara sandarsa Har ya k’araso gaban Haidar Wanda tuni ta sadda idanunsa k’asa. Abba yaci gaba da girgiza Kai yana ma Haidar kallon k’iyayya “Kai.. Har ka isa.. Har ka isa ka saka rayuwar ‘Yata a matsayin farashi.?!” Hawaye suka soma gangaro ma Abba sanda yaci gaba “Waye kai..? Wa ya baka ikon wulak’anta rayuwar ‘Yata irin haka.! Ka amsa min waye ya baka dama.!” Haidar ya rintse idanunsa rad’ad’in da yakeji a zuciyarsa na ninkuwa. Abba yaci gaba da jinjina kai “Shiyasa ka d’aukoni ka kawo ni nan.? Dan ka goge zumubinka ne.? Ka amsa min.!” "Parlorn yai shiru sai hawayen dake gangaro ma Mama Tani, Mommy harma da Azeema." "Abba yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar dake tsaye gabansa kansa kife. Yaci gaba da nuna Haidar da hannunsa mai rawa “ Ka sani, rayuwar ‘Yata baida farashi.! Gwamma ace na rasa nawa rayuwan.! Yata tana da daraja.. Tanada k’ima.. Kuma ta wuce ayi irin wann wulak’antaccen Auren da ita. Zan tabbatar maka da hakan.!” Yaci gaba da jinjina kai yana haki da kyar. Lokaci guda ya dubi Tani yace “Ki shige mu tafi bamuda wajen zama a wann gidan.!”" Jiki a sanyaye Mama Tani da Azeema suka nufi hanyar d’aki yayinda Mommy ke k’ok’arin shawo kan matsalar amma ko kallo basu ishi Abba ba daga ita Har Haidar d’in balle Ya tanka musu. A haka suka fito zasu wuce Haidar yai saurin kiran Sadis a waya ya sanar dashi Ya d’aukesu komin dare ya tabbata sun isa kano cikin k’oshin lafiya da izinin Allah. Bayan tafiyarsu a waje Mommy ta iske Haidar. Ta zauna gefensa su duka biyun ba mai cewa komai. A hankali Haidar Ya furta “It’s so painful and tiring Mommy…” Ta janyosa jikinta tana Shafa sumarsa kadan “This too shall pass” Haidar yace “Yaushe ne duka wad’ann zasu wuce Mommy.? It’s one challenge after another.” Mommy ta jinjina kai “Wann sunnar rayuwa ce Haidar. Haka rayuwa ta gada. You cannot expect life to be hundred percent perfect.. Dole yau idan anyi dariya wataran zaayi kuka… Yau gareka gobe ga waninka.. Tsanani yana tareda sauk’i.. Duka wad’ann zasu zo su wuce.. All you need to do is put your trust in Him.. Ka saka yardarka wajen Allah shi kad’ai. Da sannu zai yaye mana duka matsalolinmu Ya cika ahalinmu da alkhairi.” Anisa ta hangesu daga saman bene tana murmushin cin nasaran kauda iyayen Ummul daga cikin picture d’in. Tinda taga Mommy bata nuna mata b’acin ranta gareta ba ya kuma tabbatar mata Mommy ta aminta da ta d’ari bisa d’ari. Yanzu ta tabbata zatai maganar Aurensu da Haidar dan dama tayi hakan ne dan ta samu ta kauda su a wuce wajen. * Koda su Abba suka isa Kano bai gane gidansu ba. Dan tuni an sauya fasalin gidan an d’aga gini na zamani gaba d’aya gidan hasken lantarki irin manyan fitilun solar d’in nan sun haske gaba d’aya layin. Ya dubi Tani da mamaki ganin ta nufi wann gidan da Ya sauya fasalin unguwar gaba d’aya yace “Nan kuma ina kika kawo ni.?” Azeema ta d’an dubesa tace “Abba gidanmu ne fah.. Baka gane ba.” Rai bace ya dubi Tani yace “Mai nake gani Tani.? Me hakan yake nufi.?” Jiki a sanyaye Tani tace “Malam mu shiga mana tukuna.. Dare yayi sosai..” Abba ya girgiza Kai cikin b’acin rai “Bazan shiga ba.. Bazan shiga wann gidan da aka ginasa da kudin da aka sayi Ummu ta ba.. Ki shiga ciki ki kirawo mun Suwaiba da duk wani ahalina dake cikin gidan. Ni Malam Isbusu na gama kwana a wann gidan.!” "Tani ta furzar da huci kad’an yayinda Sadis Ya k’araso yana rok’on Abba da yai hak’uri Ya shiga gidan. Dan motan Sadis d’in ma da fari bai yarda ya shiga ba saida Sadis Ya sanar dashi ba kobon ahalin Haidar jikin motarsa kafin Ya amince Sadis Ya kawosu Kano. Da kyar, har saida Sadis da Azeema suka kirawo ma Abba Dattijan unguwan da yake jin nauyinsa suka saka baki kafin Ya amince Ya shige cikin gidan. Ya kuma sanar da illahirin ahalinsa cewa basu ba Haidar da danginsa. Ko mai kamannin Haidar baiso Ya sake gani yazo yanda yake. Hakan yasa dole Haidar janye jiki da gidan musamman duba da irin yanayin rashin lafiyar da Abban ke fama dashi. Masu lalura irin wann dole lallab’asu ake had’ida guje ma duk abinda zai b’ata ransu." Haidar ji yake tamkar Ya zama hopeless.. He’s tired and exhausted.. Ji yake Duk wani k’warin gwiwar sa da k’ok’arinsa sun gama k’arewa musamman yanzu da ya tabbata Abba baya b’angarensa. Ya tabbata koda Khairy ta bayyana zai matuk’ar wahala abubuwa su zo masa da sauk’i. Furzar da huci ya kumayi a karo na Babu adadi yana duban hotonsu da aka musu ranar aure dake aje gefen bedside lamp d’insa an saka cikin k’aramin frame. "Ya d’auki hoton had’ida k’ura ma hoton ido. Cikin wane irin siga yake furta “where are you Khairy..? Do you hate me this much.? Haven’t I suffered enough.” Ya girgiza Kai kad’an “Ya isa haka Khairy. I’m exhausted..! Please, enough with the punishment. I can’t bear the pain anymore. I can’t Khairy..!” Ya k’arashe yana shafa fuskarta saman hoton. Ya d’an d’auki lokaci yana duban hoton kafin Ya mik’e kaman Wanda aka zaburesa. Shiryawa yai Ya fito Ya nufi sashen mahaifinsa." Mommy da Daddy duk suna zaune parlor. Daddy na kallon news channel yayinda Mommy ke k’ok’arin mik’ewa tana fad’in zata shiga ta kwanta nan sukaji sallaman Haidar. Suka dubi juna da mamaki kafin Daddy ya bud’e murya yace “Haidar.? Is everything all right.?” Haidar yace “Lafiya Daddy.. I’m sorry na shigo dare yayi.” Daddy ya girgiza Kai “No.. No problem.. K’araso shigo mana.” Haidar yaci gaba da takowa Mommy na hankalce dashi. Ya zauna daga kusan k’afan Daddy. Ya gaida iyayen nasa. Bayan sun amsa Mommy ta k’arada “Inji dai lafiya.?” Ya d’an murmusa kad’an “Lafiya Mommy.. Dama wata ‘yar magana na shigo muyi.” Mommy ta tsaresa da ido “Kuma maganar baza’a iya yinsa da safe ba sai cikin daren nan.?” Daddy yace “Haba Kwaise ki kyalesa muji binda yake tafe dashi mana.” Ya dubi Haidar “Ina saurarenka meke faruwa.?” “Daddy dama akan Kasuwancinmu dake can SouthAfrica ne.. Ina so wann karan na tafi SouthAfrica a maimakon Kai and take care of our Business there.. If that’s ok with you.” Daddy yana dubansa yake jinjina Kai “Of course that’s totally fine with me. In fact abu ne da nake matuk’ar so kuma yake cikin tsarina.. But duba da yanayin da kake ciki yasa ban kawo maka wann bukatar nawa ba…” Da farko Mommy ta nuna k’in amincewarta a cewarta bata so D’anta yai nesa da ita musamman yanzu da rayuwa ta koma masu tamkar sabuwa. Da kyar Daddy da Haidar sukai convincing dinta da fad’in ba zuwa can zai Ya zauna gaba d’aya ba. Kaman yanda Daddy yake tafiya lokaci zuwa lokaci haka shima zai yi.. Kuma hakan zai d’an basa dama yai taking break regarding abubuwan dake faruwa. Da kyar Mommy ta amince ita kuwa Anisa hankalinta ne Ya tashi ganin mutumin da tayi komai dominsa zai kufce mata Ya tafi wata uwa duniyar. Saida Mommy ta lallabeta da fad’in ba jimawa Haidar zai a SouthAfrica ba sann da zaran Ya dawo maganar bikinsu za’ayi. Kar ku mance Har kawo wann lokacin Anisa da Mommy ne kawai ke zancensu ko Haidar d’in baisan da labarin ba balle akaiga sako iyaye maza cikin maganar. Idan Anisa ta tuna tana tare da yarda da amincewar Mommy kawai sai taji Har ta mallaki Haidar an gama hakan yasa ta kuma kwantar da hankalinta dan tasan dik daren dad’ewa dole Haidar ya dawo ya aureta kasancewarta zab’in mahaifiyarsa. Dukda zatai kewar fuskar da take matuk’ar so amma idan ta tuna Mommy tace da zaran ya dawo sai maganar aurensu ne tinda by then ya mance da batun Ummul sai Anisa ta tsinci kanta cikin annashuwa. Aka bar Anisa da k’irga kwanaki tin bayan tafiyan Haidar. Daga lissafin kwanaki har ta shiga satittika ta soma k’irga watanni. Hisham na sanar da ita update gameda Ummul da cikinta. Tin bayan da ya warke ya komo Abuja bakin aikinsa sann shi yaima Haidar rakiya har zuwa Airport sanda Haidar d’in zai tafi SouthAfrica. Hisham ya sanar da Anisa da zaran Ummul ta haife cikin zai salwantar da abinda ta haifa ya rufe Shafin Haidar cikin rayuwarta. A lokacin da Haidar ya cika watanni uku a SouthAfrica a lokacin yake sanar da Mommy shirinsa na dawowa gida. A wann lokacin kuma Aurensu da Ummul ya cika watanni tara da mutuwa. Haka zalika Ummul ta shiga watan Haihuwarta. Tinda Mommy ta shelanta labarin dawowar Haidar Anisa ta gaza zaune ta gaza tsaye Angonta zai dawo. Tuni ta fidda Ankon bikinta tsakanin kawayenta. Ko sanar ma Mommy batai ba dan ma kar Mommyn ta dakatar da ita. Dan a halin yanzu kam ta gama shiri ta kuma lashi takobin zama matar Haidar Maitama. Duk wann bidirin da take iyayen nata kansu basu da labari. A cewarta saidai suga IV musamman Amminta wacce har kawo lokacin basu koma normal da mahaifiyar Haidar ba. Bazata bari sab’anin dake tsakaninsu ya mata sanadin farin cikinta ba. Gwara kawai idan an gama komai Ammi taga IV. * Illahirin ma’aikatan gidan suna kitchen suna aikin abincin sauk’an Haidar. Mommy na tsakani tana directing nasu yanda take so komai Ya kasance perfect. Yayinda Anisa ke zaune gaban make-up artist da ta kirawo Har gida ana tsara mata make-up d’in tarban Angonta Haidar. Ga wata Uwar bridal gown da taci yanda kasan wata amarya. Ranta fari sol kaman yanda rigar tata take. At last mafarkinta zai zama gaskiya. Daga k’ofan d’akin sukaji ana knocking. Anisa sai tsuka take dan a zatonta d’aya ne daga cikin ma’aikatan gidan. A hasale tace “Wai wayene wajen.?! Na fad’a muku I don’t want anything before dinner.. Bazan saka komai a bakina ba sai Mijina yayi landing.!” Aka ci gaba da turo k’ofan ana tafe hannu. Cak Anisa ta ja tai turus. Ba shiri ta ture hannun mai make-up zuciyarta naci gaba da bugawa. Ta mik’e a firgice had’ida juyowa tana duban wacce ta shigo. K’iris Ya rage Anisa bata kife k’asa ba. Jikinta ya d’auki kyarma ta shiga nunata da dan yatsa “You.!!!” SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *53* *©️Sameena Aleeyou… * “Surprise.! Surprise.!!” Ta furta tana duban Anisa daga sama zuwa k’asa murmushi saman fuskarta. Anisa ta dubi makeup artist d’in tace ta basu waje. Lokaci guda ta tako zuwa gabanta tana huci take fad’in “Mai kike a nan Leenah..? What exactly do you want from me.?!” Leenah taci gaba da murmusawa tana duban Anisa “Haba Amarya.. Ai ba’a san amare da fushi ba. Kar ki b’ata kwalliyarki..” Ta karada “Kashh kinga Har kin fara jurwaye tun ango bai gani ba.!” Ta kamo bakin rigarta ta soma k’ok’arin gyara ma Anisa kwalliyar tana fad’in “Ki adana guminki Anisa dan ba’a fara wasan ba balle ki jik’e da gumi.” Anisa ta kai hannu fusace ta bige hannun Leenah tana huci “I don’t have time for your stupid games Leenah.! Just tell me once and for all Mai ya kawoki gidan nan a daidai wann lokacin.?!” Leenah ta kuma murmusawa tana duban Anisa sai ta isa ta zaune saman sofa ta d’aura k’afa d’aya bisa d’aya “Kar ki damu I’m not here to blackmail you.. Nazo tayaki murna ne. Girlfriend… Ko ince .. Mrs Haidar Maitama.! Oh! Na mance. Soon to be..” Ta k’arashe tana fad’ad’a murmushinta. Anisa ta had’iyi abinda ya toshe mata mak’ogoro “Kinga Leenah ki tashi ki fice. Ba Wanda ya gayyaceki.” “This is where you are wrong Neesah.!” Leenah tace tana dubanta. Sai ta kuma murmuswa “Amma Hajiya Kwaise tasan duk abubuwan da kika aikata..? Ina nufin kin sanar da ita kece kikai sanadin rufeta a cell..? Kaman yanda bana haufin kece kikai sanadin had’arin motar da D’anta ya kusa rasa ransa ciki.!” Anisa bata bari Leenah takai aya ba ta k’araso ta shiga janyeta tana fad’in ta tashi ta fice ko ta kirawo mata securities. Leenah ta finciki hannunta tana huci itama take duban Anisa wann karon “Kin zata zan barki kici banza ne.? Yanzu ba sai anjima ba zan wargaza duk wani shirinki Anisa. Dan sai na sanar da Hajiya Kwaise wacece ta zuba ma Ummul poison ta kuma d’aura mata blame d’in.” Tana ida fad’in haka tasa Kai zata fice Anisa tai saurin fincikota ta maidota baya. Ta marairaice fuska kaman zata fashe da kuka take fad’in “Oh no.. Sorry Leenah.. Please don’t expose me.. Tell me how much money do you want.?” Tana ida fad’in haka sai ta kece da dariya tana kuma duban Leenah wacce itama da mamaki take dubanta. Anisa ta dubi Leenah daga sama zuwa k’asa tace “Haka kike so nayi right.? Toh kinyi k’arya Leenah. Bazaki tab’a ganin haka daga wajena ba. Kina tsammanin Mommy zata yarda dake ne.? Idan bata yarda dake ba a baya meyasa zata yarda dake yanzu Leenah.? Kar ki mance kinada tabon sharrin sata da "kikai ma Ummul a idon Mommy. And hello.! Last time I checked, Mommy ta miki iyaka da gidan nan. You might be charged with trespassing sweetheart.”" Shiru Leenah bata ce mata komai ba. Anisa tai murmushin cin nasara “Ko mai zaki sanar da Mommy Leenah kin riga kin makara domin a halin yanzu Mommy ta aminta Dani d’ari bisa d’ari.!” Taci gaba da zagaye Leenah tana fad’in “You can go ahead and tell Mommy everything Leenah. It’s my word against yours. Kije ki ce mata Ni Anisa ni na canza turaren da ta bani na bama Ummul na kuma zuba guba ciki.! Ni Anisa ni nayi sanadin jefata a cell har ta shafe kwanaki.! Ni Anisa ni nayi sanadin had’arin motan da Haidar ya kusa rasa ransa ciki dan kawai naga bayan Ummul.! Ni Anisa ni nayi sanadin mutuwan Auren Ummul da Haidar sann zan tabbatar Ummul da abinda ke cikinta basu dawo cikin rayuwar Haidar ba.!” "A daidai nan sukaji an bud’e k’ofar d’akin. A tare suka waigo suna ganin waye ya bud’e, ba kowa bane face Mommy cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinta ciki ba." Jikin Anisa ya d’auki rawa sai ta fashe da kuka ta nufi Mommy tana nuna mata Leenah take fad’in “Mommy kisa securities securities Ki koreta. Kin mata iyaka da gidan nan tin lokacin da ta k’ulla ma Ummul sharrin sata.. Kuma wlhi ni yanzu ba kawata bace babu abinda ya hadani da ita.” Anisa bata Kai aya ba taji sauk’an Mari maiji da lafiya a k’uncinta. Ta d’ago a firgice tana duban Mommy wacce fuskarta ya gama rinewa haka ma idanunta. Anisa ta dafe k’uncinta bata daina kallon Mommy da mamaki ba. Murya na rawa take fad’in “Mo..Mommy..” Nan ma bata Kai aya ba Mommy ta kuma d’auketa da wani marin. Tana kuma tasowa ta sake Kai mata wani Marin..Sai Anisa ta duk’a a k’asa tana kuka tana dafe duka b’angaren fuskanta. Ta soma jada baya cikeda tsoron Mommy. Leenah tasa k’afa ta take k’afar Anisa dake daga zaune tana jan jiki Wanda hakan ya hanata motsawa. Leenah na k’are mata ma Anisa dake duk’e kasa dafe da fuskanta tana bin Mommy harma da Leenah da kallon tsoro. Baki na rawa Anisa tace “Waht’s… going on here…?” Leenah ta katse ta “Hm Anisa kenan. Kin zata ke kad’ai ce kika iya buga wasan.?” Sai ta murmusa kafin ta saka hannu ta Ciro kwalban turaren da Mommy ta bama Anisa dan ta bama Ummul Wanda bata ma Ummul d’in ba suka canza da mai guba. Baki sake Anisa ke dubanta tana duban kwalban turaren. Ya akai ya isa hannun Leenah.? Sai ta tuna lokacin da Ammi ta dauketa suka tafi Kano ta bar turaren nan d’aki cikin wardrobe bata tafi dashi ba. K’ila Leenah ta shigo ta bincika ta samu kenan. Muryar Anisa na rawa ta d’ago hannaye ta had’e waje guda tana duban Mommy “Mommy Kar ki yarda da duk abinda Munafukar nan zata sanar dake.. Wllhi Mommy sharri take mun ni bansan komai ba. Bakin ciki take mun taga zan auri Haidar.” "“Idan kika sake magana sai na d’aukeki da wani Marin.! Maras mutunci kawai. Ai da Haidar ya aureki Anisa gwara ya k’arashi rayuwarsa a haka.!” Mommy ta katseta tana ci gaba da huci. Lokaci guda Mommy ta k’araso gabanta “Banida lokacin sauraran sauran makircinki bayan Wanda naji da kunnuwana. Abu d’aya zan tambayeki yanzu Anisa, ki fad’a mun ina Ummul take.?!”" Anisa na hawaye take ci gaba da girgiza kai “Mommy dan Allah ki min rai.!” “Zaki fad’a mun yanda Ummul take ne ko sai nasa anyi k’asa k’asa dake.!” Daidai lokacin suka sinkayo muryar Haidar da shigowarsa gidan kenan. “What is going on here.?.. Mommy did you mention Whereabouts d’in Khairy..?” Suka waigo gaba d’aya suna dubansa yayinda Haidar yaci gaba da shigowa d’akin. Idanun Mommy naga Anisa dake duk’e tana kuka taci gaba da nunata da yar yatsa “Gata can Haidar.! Anisa ta jima tana k’ulla abubuwa a cikin gidan nan ba tareda mun Kai hankulanmu kanta ba. Anisa da muka dauka shashasha wacce bamu bama al’amarin ta mahimmanci… Anisa itace ta k’ulla ta kuma wargaza a gidan nan.!” Cikin rashin fahimta Haidar ke girgiza Kai yana duban Mommy ya kuma dubi Anisa. Sai ya kara duban Mommy yace “Mommy.. Ban fahimceki ba..” Mommy taci gaba da jinjina Kai “Yau zaka fahimci komai Haidar. Kaman yanda watanni k’alilan baya na soma fahimta.” Taci gaba da jinjina Kai “A lokacin da na soma zargin Anisa sai na tafi Kano na dawo da ita gidan nan dan na tabbatar da zargina akanta na kuma Kamata red handed. Na karanci Anisa na tsawon watanni yanda na fahimci ita d’in ta jima tana sonka.. Sann duk abubuwan da ta aikata da sunan soyayyar da take maka ne..!” Da mamaki Haidar ke girgiza Kai “Ni kuma.. Anisa.. Anisa ke sona. Did you hear yourself Mommy..?!” Mommy ta jinjina Kai “I couldn’t believe it either har saida na gano abubuwan da ta tapka in the name of tana sonka. Bayan na gano haka sai na nuna mata ina tareda ita d’ari bisa d’ari.. Na nuna mata tanada goyon bayana zan maka umarni da ka aureta.. Nayi wasa da tunaninta kaman yanda ta jima tanayi da namu. Nan na binciko yanda wann kawar tata take dan ban mance wani rana da suka k’ulla tuggu ma Ummul su biyun har naima kawar tata iyaka da gidan nan.” Mommy taci gaba da jinjina Kai “Anisa itace ta zuba ma Ummul poison a turare dan ta kasheta slow dead sann ta d’aura blame d’in akaina.! Anisa itace tai sanadin had’arin motan da ya auka muku kaida Ummul duk dan ta kashe Ummul ta cireta daga cikin rayuwarka.! Anisa ita ce tai sanadin mutuwan Aurenka da Ummul Wanda bana haufi bakinsu d’aya da wancan azzalumar da ta aureka ta hanyar sihiri.. Anisa tasan yanda Ummul take tsawon lokacin nan.! Sann..” Sai Mommy tai shiru tana ci gaba da huci “Sann tana saneda cewa.. Ummul is pregnant har ta shiga watan haihuwarta.. Duka Anisa na sane da wann tsawon lokacin nan.!” Gumi ne ke gangaro masa tin daga tsakiyar sumarsa har zuwa goshinsa.. Ga jijijiyoyin jikinsa dake kuma mimmik’ewa.. Ya saki k’aramin briefcase din dake hannunsa. Yayinda yaga wani duhu ya gifta k’wayar idonsa.. Anisa ta soma jada baya tana hawaye take girgiza Kai ganin Haidar gaba d’aya ya rikice ya sauya mata. Cikin rawar murya tana jan jiki tak fad’in “ No Haidar please.. Haidar..! Haidar dan Allah ka yarda dani.. I did everything out of love… I didn’t mean to harm you or Mommy.. Wllhi nayi komai ne sabida ina sonka.. Kuma.. Kuma wllhi ban tab’a had’a baki da Dareen ba… Sann..” Bata Kai aya ba Haidar ya shak’ota da iyaka k’arfinsa yana wani irin huci “I will kill you..! I swear I’m going to kill you.!” Wane irin huci kurum yake yana shak’e wuyan Anisa har saida Mommy ta soma k’ok’arin janyesa. Baza’a kira abinda ke tsartsafowa daga cikin idanunsa hawaye ba saidai ruwan tururin k’unan zuciya. “Tell me..! Tell me. Where is my wife..?!” Yai maganar gumin dake tsartsafowa ta ko wani kofan sumar dake jikinsa naci gaba da gangarowa. Anisa ta soma sosa wuya da kyar tana tarin azaba take fad’in “Zan fad’a maka.. Please let go..!” “Tell me now..!” Ya kuma fad’i yana fidda huci kaman zaki. “Ta.. Tana Bauchi…” Mommy ta dubeta da mamaki “Bauchi.?” Anisa taci gaba da jinjina Kai ga gumin azaban da ya wanke umburarren fuskarta da ya sha tafin Mommy ba adadi. “Bauchi wajen wa.? Mai ya kaita Bauchi.?” Cewar Mommy. Anisa taci gaba da jinjina Kai daga durk’ushe kaman Marianiyar Kenyawa “Wajen mahaifiyar Hi… Wajen mahaifiyar Hisham.” “Hisham..!” Mommy ta maimaita cikin tsananin mamaki da rud’ani dan tama rasa tuna waye Hisham. Yayinda Haidar yai mutuwar tsaye yana nanata abinda Anisa tace cikin kwanyarsa. “Waye Hisham kuma.?” Mommy ta tambaya. Anisa ta yarfe gumi da hawayen da suka gauraye mata fuska “Hisham Abokin Haidar.. Bansan dalilinsa ba amma ya jima yana bibiyan Haidar da ahalinsa da sharri. Kuma.. Kuma bakinsa d’aya da Dareen tare suke k’ulla komai tin kafin na had’u da Hisham.. Hisham has been shadowing Haidar for quit some time.. Tin kafin Ummul ta shigo rayuwarka.” Kalmar Shadow da Haidar yaji ta ambata sai Ya tuna masa wani rana Ya taba jin Dareen tana waya da wani mai suna Shadow koda Ya tambayeta sai tace Uncle dinta ne. Muryar Anisa Ya kuma dakan dodon kunnensa “Sann koda Ummul ta shigo rayuwarka sai akalar yakinsa Ya koma ga k’udirin raba tsakaninku. A cewarsa shi ya fara ganin Ummul ya kuma fara sonta kafin Haidar….Ni kawai.. Kawai nayi tarayya da shine dan na cimma burina na mallakan Haidar kamar yanda yake so ya mallaki Ummul.. Kuma ya d’au alwashin raba Haidar da Ummul ko ta wani hali.” Juyawan da Mommy zatai b’at suka nemi Haidar a wajen suka rasa. Anisa ta soma k’ok’arin mik’ewa tana Neman gafaran Mommy. Mommy ta nunata da dan yatsa “Kika kuskura kika motsa daga yanda kike sai nasa an canza Miki kamanni da bugu. Munafuka azzaluma.!” Leenah ta dubi Mommy tace “Amma ai ni zan iya tafiya..?” Bata rufe baki ba sai ganin wasu mata guda biyu sanye da Kayan ‘yansanda Sun shigo d’akin ma’aikaciyar gidan na directing nasu. Mommy ta nuna musu Anisa da Leenah tace “Arrest them.” Anisa ta saka hannu biyu aka ta kurma ihu tana fad’in “Mommy ki min rai.. You can’t send me to jail.. I’m your niece.. You can’t do this to me Mommy.. Wayyo na shiga uku ni Anisa.” Leenah ta katseta “Ba ke kika shiga uku ba Anisa ni kika jefa a uku.. Allah ya isa ban yafe Miki ba. Yau ga yanda bak’in shashancinki da son zuciyarki ya kaimu.. Wayyo ni Leenah guba kawai na kawo ba ni na zuba ba ma Ummul ba.!” ‘Yarsanda ta tasa k’eyar Leenah tana fad’in “Ki k’arasa bayaninki a station. Move.!” Ta k’arashe tana hankad’eta. Haka aka tasa k’eyar Anisa da Leenah aka wuce dasu police station. * "Tinda ya fice yake sharara gudu saman kwalta. Waya manne kunnensa na hagu. Sadis yake kira. Sadis na d’agawa Haidar yace “I need a plane ticket to Bauchi. Right this instant.!” Bai kuma tsayawa sauraren Sadis ba ya katse kiran yana ci gaba da tururi. Fuskar Hisham kurum yake hangowa. He trusted him. He believed in him. How could this be possible.? Hisham.! Hisham fah.. Mutumin da ba komai a tsakaninsu face zallan gaskiya, yarda da amana.! Is it a crime to trust someone.? Ta ya haka zai kasance.?! Yaci gaba da girgiza Kai yana ganin abun tamkar dai a mafarki ne. Not his Hisham. His best friend. Mutumin da ya aminta dashi sama da kowa a duniya ciki harda iyayensa kafin alak’arsa dasu ta gyaru. Ya lumshe idanunsa yana mai kuma Waresu tar a daidai lokacin da ya shigo Company. Securities na gaishesa ko zarafin amsa su bai ba ya tambayesu ko Hisham yazo Company. Nan suke sanar dashi bai shigo ba gaba d’aya ranan. Haidar ya jinjina Kai kafin yasa kai ya nufi cikin building d’in kaman zai kifa k’asa. Duk Wanda ya gansa basa hanya kawai yake. Yanayi ne da zasuce Sun jima basu gansa cikin irinta ba. Ko a zamanin baya da yake samun sab’ani da mahaifinsa bai shiga cikin irin yanayin da suka gansa. Kai tsaye Office d’in Hisham ya nufa. Ya soma takowa cikin Office d’in yana tuno farkon had’uwarsu da Hisham. Motarsa ce ta tsaya masa a wajen gari Hisham helped him out daga nan suka k’ulla zumunci nan Hisham yake sanar dashi Neman aiki ya kawosa Abuja and he’s an architect. Haidar yace ai kuwa he’s in the right place, because his Dad owns a Construction Company dan haka yasa ma ransa tamkar ya Sami gurbin aiki k’ark’ashin Kampanin mahaifinsa mai suna Maitama Builders. Nan take yai going through takardun Hisham ya kuma ga ya cancanta hakan yasa babu b’ata lokaci Hisham" ya Sami gurbin aiki a kampanin. Hisham yai ta murna harda hawayen murna yana fad’in Allah ne ya amsa kokensu shida mahaifyarsa ya turo Haidar cikin rayuwarsa dan ya jima yana neman aiki bai samu ba. Shi maraya ne mahaifinsa ya rasu tun yana k’aramin yaro. Mahaifyarsa ta sha wahala sosai sann tayi d’awainiya dashi tun yana k’aramin yaro. Ya gode Allah yanzu zai share mata hawayenta da izinin Allah. Tabbas bazai tab’a mance halaccin Haidar gareshi ba. Ire iren kalaman Hisham kenan Wanda yasa a ko Yaushe yake ma Haidar nasiha gameda bin iyaye. Hisham tolerates Haidar a cewarsa bayan Hajjarsa baida Wanda ya fiye masa Haidar. Wanda hakan yasa suka k’ulla abota sosai har ta zarce ta koma amintaka. Haidar ya yarda dashi dan hardly ka gansa da wani aboki idan ba Hisham d’in ba. Haidar ya numfasa had’ida d’aukan wani k’aramin hotonsu da aka saka cikin k’aramin frame suna tsaye a wani construction site aka musu hoton ba tareda saninsu ba. Cikin shiga irinta k’wararrun magina. Idan ka gansu gwanin ban sha’awa. Hisham yaji dad’in hoton ya k’aunaci hoton wanda hakan yasa ya aje hoton cikin frame ya jera shi a Office d’insa. Idanunsa Sun kuma rine sosai yake duban hoton yana tuno duk rayuwarsu tare daki daki da tsawon lokacin da Hisham ya kwashe yana munafurtansa. Wayar salulansa Ya Ciro yakai kan number d’in Hisham yana kallo. Yana ji kaman ya daki wayar lambar ta tarwatse. Lokaci guda yai dialing zuciyarsa naci gaba da tafarfasa. Bugu biyu a na uku Hisham Ya d’aga duk a birkice yake tambayar Haidar yaushe ya dawo k’asan. Haidar yace “I just landed. Ya naji muryarka haka.? Is everything all right.? Nazo company baka nan..?” Hisham ya kuma Shafa goshinsa yana furzar da huci. Bai sani ba sai ji yai bakinsa na furta “Ina Teaching hospital can Bauchi.. Na kawo ‘Yaruwata” ‘Traitor.!’ Haidar ya furta a zuciyarsa yana fidda huci. A fili kuwa karfin hali yai Yace “ ‘Yaruwarka kuma.. Dama kanada ‘yaruwa.? I thought Hajja ka kai..?” Yana maganar yana k’ok’arin dannar kansa dan bazai ba ma Hisham wani k’ofa da zai gane yasan meke faruwa ba har sai ya isa yanda yake Ya cafkesa da hannayensa. Sai dunk’ule hannunsa guda yake yana murzawa sabida yanda zuciyarsa ke masa zafi. Hisham Ya rintse ido yana tuhumar kansa meyasa zaice ma Haidar ‘yaruwarsa Ya kawo. Tsaban a birkice yake baisan yayi sub’utan baki ya furta haka ba. Ya rintse idanunsa da k’arfi ya soma kame kame “Eh.. Eh.. ‘Yaruwa ta nesa ce.. Sun rabu da mijinta tana zaune gaban Hajja toh ga haihuwa yazo mata.. Tin safe muke asibiti Har yanzu bata sauk’a ba..” “Haihuwa.?!” Haidar yace zuciyarsa na tsnanta bugu yana tuna cewa da Anisa Tai Ummul na wajen Mahaifiyar Hisham kuma ta shiga watan haihuwarta. Haidar bai k’arasa sauraren Hisham ba ya fice yana huci idanunsa suna kuma rinewa kaman zai kifa k’asa.. Mota Ya shige Ya nufi hanyar airport. Yana tafe hanya wayan Sadis ya shigo masa. Nan Sadis d’in ke sanar dashi jirgin Bauchi ta riga ta cika kuma gab take da tashi. “I don’t care Sadis.! Just make sure a space is created for me in that plane. I must fly to Bauchi right this instant.” Yana ida fad’in haka Ya katse kiran yana ji kaman bazai isa ba. "** Bauchi," A can TH kuwa b’angaren masu haihuwa hannayen Ummul rik’e cikin na Hajja ta gama galabaita sosai. Hawaye take tana girgiza kai take duban Hajja “Ki kira min Umma dan Allah.. Dan Allah Ki kaini wajensu.. Ki kaini naga Abba na.. Ki kaini na nemi yafiyarsu Hajja.. Mutuwa zanyi.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Dan Allah kar ki barni na Mutu a nan ban nemi yafiyar iyayena ba.. Hajja ki kaini wajen Umma da Abba.. Bazan iya ba mutuwa zanyi.. Abba na tuba.. Umma dan Allah ku yafe mun.. Nayi kuskuren kaurace muku.. Na tapka kuskure ku yafe mun dan Allah.!” Ta kuma kankame hannun Hajja. Cikin rarrabewar kalamai take furta “Dan.. Allah.. Kice.. Su yafe mun.. Ki sanar dasu ina k’aunarsu.. Ki rok’ar min iyaye na gafara Hajja ko zan samu sassauci da rahamar Ubangiji..” Ta kuma rintse idanunta “Bayana.. Hajja.. Wayyo Umma na ki yafe min.. Bayana.!” Jikinta ya kuma sakewa nishin ma ya daina fita. Hajja nata k’ok’arin kwantar mata da hankali tana fad’in “Bazaki Mutu ba in sha Allah Ummul.. Zaki haihu lafiya da izinin Allah.. Zaki rok’i Umma da Abba yafiya da bakinki. Ta kuma ficewa a kid’ime kiran likitocin dan sun sanar da ita basuga wani complication da zai iya hana Ummul din haihuwa da kanta ba Shiyasa basuyi yunk’urin yin cs ba. Hisham Ya nufo Hajja a birkice yana tambayarta ko Ummul ta haihu. Hajja ta girgiza kai tana fad’in Likitocin zata kira dan ita kanta lamarin Ya soma bata tsoro. Gwara kawai suzo idan ma aiki zasu mata sai su mata amma ta riga ta galabaita. Hisham Ya shafe fuskarsa yana girgiza kai yake fad’in “No.. No Hajja.. Please tell me Ummul is going to make it alive.. I can’t lose Ummul.. I lost her once bazan bari ta sake kufce min ba..!” Ya kuma dafe Kansa a kidime kaman sabon kamun hauka yake fad’in “Wai ina Doctors din suke ne…! Which kind of incompetency is this.. Meyasa tuntuni ma basu cire cikin ba.. I don’t give a damn wether the child survives or not matuk’a Ummul zata kasance cikin k’oshin lafiya ban damu a rasa wann jaririn ba.!” Cikin tsananin shock Hajja ke dubansa. Ta sani Ya tab’a son Ummul kafin tayi aure amma maganganun da ke fita daga bakinsa ya haifar mata da tsoro da rud’ani.. Gani Tai kaman na Hisham dinta ba.. Kaman wani ne daban take gani tsaye gabanta. Kasancewar halinda ta baro Ummul din yasa ta janye jiki ta shige bata bi ta kansa ba. Amma tsoron da mamakin bai bar jikinta ba. Bayan shud’ewan wani lokaci Hajja da likitoci guda biyu suka nufi kan Ummul yayinda Hisham yaci gaba da safa da marwa daga waje yakai Mari Ya Kai gauro yana fad’in bazai rasata ba. Yana tsaka da safa da marwansa yaji wata murya daga bayansa ta ambaci “SHADOW.!” Zuciyar Hisham Tai wani irin tsinkewa. Yaji kaman an aje masa guduma. Jinin jinka kaw tamkar Ya tsaya Cak Ya daina circulating. Da kyar ya soma k’ok’arin karkato jikinsa. Juyowan da Hisham zai yayi ido hud’u da Haidar cikin yanayin da bazai iya fasaltawa ba.! *Toh fah.! Yau dai ga Shadow ga Haidar ga kuma Ummul akan gwiwa. Ko Ya za’a wanye.?* SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *54* *©️Sameena Aleeyou… * "Girgiza Kai Hisham yake a hankali ganin yanda Haidar ke fidda wani irin huci yana dubansa da rinannun idanunsa. Yasan duk yanda akai Anisa must have screwed up kaman dai ko yaushe. A hankali Hisham ya soma takowa ga Haidar Wanda har lokacin dubansa kurum yake without uttering a word. Hisham ya soma ware hannayensa a hankali tamkar mai shirin yin surrender “Whatever it is that’s in your mind, I hope you listen to me first.. I know by now your cousin Anisa ta gama b’ata sunana a idonka.. Haidar nasan matarka Ummulkhair even before you met her.. Saidai bansan itace matar taka ba har sai bayan da kuka rabu a lokacin da na fahimci ‘Yaruwarka Anisa na neman rayuwarta..!” Ya dan numfasa yayinda Haidar ke dubansa fuskarsa na kuma rinewa. Yana kuma dunkule hannuwansa zuciyarsa naci gaba da zogi had’ida tafarfasa." "Hisham yaci gaba “Haidar ko mai Anisa ta sanar dakai ka sani nayi ne to protect you, your wife and your child of course.. Anisa zata kashesu kaman yanda ta kashe Dareen.. Anisa is a maniac Haidar.. Zata iya aiwatar da komai dan cikan burinta.. Dan ta mallakeka she can go to any extent… She ran Dareen over while pregnant with your child.. I fear the same would happen to Ummulkhair da abinda ke cikinta Shiyasa na barta wajen da zata zama safe from any" "danger.. Yanda Anisa bazata cimmata cikin sauk’i ta kashesu ita da abinda ke cikinta kaman yanda ta kashe Dareen da abinda ke cikinta..!” Bai Kai aya ba yaji sauk’an naushi a bakinsa Wanda saida ya kaisa k’asa. Haidar ya saka duka hannayensa biyu ya cakumosa yana fidda huci fad’in “The nerve of you.. Bastard.! Are you that shameless.! Tell me.. Tell me who are you..?! Ka fad’a mun waye Kai waye Kai..? Mai ya kawoka cikin rayuwana..? Answer me.!!!” Ya k’arashe yana kuma shak’e Hisham kaman zai aikasa lahira. Huci Haidar yaci gaba da yi idanunsa suna kuma rinewa, yaci gaba da jinjina Kai yana duban Hisham “I couldn’t care less if it’s about business. All the scandals.. Alla the damages and losses..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana fitar da huci “But you’ve crossed the line The moment you involved my wife you Bastard.!” Ya k’arashe yana kuma kaima Hisham naushi a hanci. Ya kuma cakumo wuyan Hisham d’in yana wani irin huci “How dare you look at my wife.! How dare you hear her voice.! How dare you go near my wife you Bastard.!” Ya k’arashe yana gwaran hancin Hisham da goshinsa saida ya kaisa k’asa." Kasancewar wajen Amenity ward ne yasa ba zirga zirgan mutane sosai. Da kyar Hisham ke nishi daga nan yanda yake duk’e k’asa . Haidar ta kuma cakumosa Ya mik’ar sa tsaye. Ruwa ne ke tsartsafowa ta ko wani mahudan gashi dake jikin Haidar. “How could you..! I gave you everything..My trust..! My friendship… I gave you job.. I even called you brother..!” Da kyar Hisham ke iya furta “Ha.. Haidar wllhi ka yarda dani.. Ka yarda dani this is all part of Anisa’s plan. The moment da naji shirinta akanka sai na fahimci kaida ahalinka kuna cikin had’ari sabida ita… Ita da bakinta ta fad’a tayi attempting kashe Ummul lokacin da ta zuba mata guba cikin turare.. Nasan baka mance wancan lokacin ba.. Kaga idan Har tayi attempting kasheta tun a fari ashe rayuwar Ummulkhair harma da jaririnka dake cikinta kusan ‘Yaruwarka Anisa na cikin grave danger.. Anisa ita ta aikata maka komai kuma I’m very sure bakinta d’aya Dareen and that’s why she killed Dareen.. Because sunyi tarayya itada Dareen wajen son abu guda. And that’s you.! “ Cikin d’acin rai Haidar ya kuma Kai ma bakinsa naushi hawaye har tsartsafowa daga idonsa yake. Ya shak’e Hisham sosai yana fad’in sai ya kashesa tinda yaje kusan matarsa. Dariya Hisham Ya soma yana girgiza kai “But she’s no longer your wife Haidar..! Saurara Kaji da kunnuwanka..!” "Daidai nan yaji sautin kukan jariri ya daki dodon kunnensa ya karad’e wajen gaba d’aya. Cak Haidar ya dakata da abinda yake.. Yayinda Hisham yaci gaba da murmusawa jini na bin bakinsa da hancinsa “That must be your newborn baby, Haidar.. You ended that marriage yourself nine months back.. Haihuwar D’anka ya tabbatar da cewa Ummulkhair ta gama Aurenka Haidar.!”" Duban Hisham Haidar yake kaman mutum mutumi.. A hankali ya sake wuyan rigar Hisham Ya d’ago yana duban matar dake tunk’aro yanda suke ga jariri sabon haihuwa rungume cikin hannunta.. Idonta naga jaririn dake hannunta.. Murmushi saman fuskarta take furta “Hisham.. Ummul ta sauk’a lafiya.. Alhamdulillahi..!” Birki tai ma kalamanta sakamakon hango fuskar Hisham da tai jina jina.. Sam bata kula da matashin dake tsaye gefen Hisham yana kallon jaririn dake rungume cikin hannunta cikin wane irin yanayi ba. A yayinda Hajja ke nufo D’anta dake duk’e wajen fuskarsa na d’igar da jini a daidai wann lokacin Haidar ke nufota yana duban nasa D’an dake rik’e cikin hannunta.. K’arasowar da Hajja zatai sai ganin hannun wani matashi tai yana k’ok’arin amsar jaririn dake hannunta. Hannayen kawai ta kalla zuciyarta yai wani irin yankewa. Zuciyarta na bugawa take duban hannayen Har zuwa fuskarsa yayinda Haidar ke duban jaririn. Cikin rawar murya yake ke furta “My child..!” Cak Hajja ta d’ago tana duban matashin. Take zuciyarta yai wani irin yankewa dan ba kowa ta hango ba face Aliyu Maitama da kuma matarsa Kwaise. Tai tsaye Cak ba tareda ta iya wani katab’us ba har saida Haidar ya amshi jaririn cikin hannunsa. Ya k’ura ma jaririn ido yanajin k’walla na ciko idonsa. Kyakkyawan yaro mai kamanninsa sak kaman an tsaga kara. Ya sumbaci yaron yana lumshe idanunsa. Har lokacin ko motsi Hajja ta kasa yayinda Haidar ya nufi k’ofan da yaga matar ta fito rungume da yaron ba tareda ya kuma bi takan Hisham da mahaifiyarsa ba. "A hankali Haidar ya tura k’ofan D’akin. Can ya hangota tana kwance saman gadon asibiti, idanunta a lumshe suke tamkar na mai bacci." A hankali ya furta “Khairy..!” Sann ya soma takowa gareta jaririn na mak’ale cikin hannunsa. Ya k’araso har gaban gadon da take kwance. Ya k’ura mata ido sosai yana dubanta. Fuskarta yayi fayau dukda d’an jiki da ta k’ara Wanda bai wuce yanada nasaba da haihuwan da tai ba. It’s been nine good months rabonsa da ita.. Ji yai k’afafunsa na barazanar gaza d’aukarsa. Ya zauna saman kujeran dake gefen gadon. Har lokacin rungume yake da jaririn idanunsa naga Ummul wacce ke kwance tamkar mai bacci. Siririn hawaye Ya gangaro masa. Ashe da ciki ya saketa.. Ta tafi tayi rainon cikin ita kad’ai Har ta haifi jaririnsu ba tareda shi ba.. He wasn’t there for her.. She did it all alone by herself.. Bazai tab’a yafe ma Hisham ba da Ya b’oye Khairy tsawon lokacin nan. He denied him the right to know Khairy was carrying his child koda ace Ya saketa. Bazai taba gajiyawa ba har sai Hisham Ya biya abubuwan da Ya aikata masa. Ya sauk’e idanunsa kan jaririn dake cikin hannunsa. Ya k’ura masa ido sosai idon yaron a bude suke yana iya kallon cikin k’wayan idon yaron. A fili ya furta “My Son… Dad is here.. I won’t allow that Maniac to go near you or your Mom. Dad is here to protect you both.” Ya k’arashe yana sumbatan goshin yaron. Lokaci guda Ya maida dubansa ga Ummul dake kwance har lokacin idanunta a lumshe suke. "Cikin wane irin yanayi ya soma furta “I’m sorry.. I’m sorry I wasn’t there for you.. I’m sorry you had to go through all this alone..” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “I should never have.. divorced you.. I should never have gave that maniac a chance to go near you. This is all my fault.. Amma, ina so ki sani… I.. I never stopped loving you Khairy.. Ko lokacin da na furta Miki kalmar saki ban daina sonki ba.. You are always right here.. In my heart.!” Ya k’arashe yana nuni da b’angaren k’irjinsa." ** A can waje kuwa gaba d’aya hankalin Hajja a tashe yake. Ganin Haidar ya haifar mata da shiga wani irin yanayi Wanda yasa har ta kasa tambayan Hisham mai ya samu fuskarsa. Abinka da gogagge sai ya nufo Hajja yana fad’in “Hajja akwai abubuwa da dama da ya kamata ku sani daga ke har Ummul. Na b’oye muku ne to save Ummulkhair.. Sabida Rayuwarta dake cikin had’ari.” Dubansa kurum Hajja take ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Hisham yaci gaba “Ummul abokin aiki na ne tsohon mijinta Hajja.!” Kaman sauk’an aradu haka taji maganar. Ta d’ago a daskare tana duban Hisham cikin tsananin shock. Jiri Ya kusan kaita k’asa.. Ta girgiza kai kad’an “Ka.. Ka ka ce.. Wann wann mutumin abokin aikinka ne..?” Ta k’arashe hannunta na tsananin rawa kaman yanda muryarta ke rawa. Ta ci gana da nuni da hanyar da Haidar yabi. Hisham yaci gaba da jinjina Kai “He’s not only my colleague Hajja.. He’s my Friend.. Haidar is my friend.. Sann Haidar shine mijin Ummul.. Ban jima da sanin hakan ba. Haidar Ya tareni da fad’a Hajja kafin ya saurara yaji daga gareni.. Akwai abubuwa da dama da Ya kamata Haidar Ya fahimcesu. Wasu mata sunyi tarayya wajen soyayyarsa sann Sun tarwatsa rayuwarsa.. Ni taimakon Abokina kawai nake Hajja amma bai fahimta ba… Hajja Haidar is a good person.. I can’t let those two women ruin him..” Ya k’arashe cikeda nuna tsantsan damuwa. Gaba d’aya Hajja a birkice take.. Ta kasa yarda da abinda takeji. Ta Ya haka zai kasance.. Ta Ya ‘yanuwan suka kasance abokan juna.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. K’iris Ya rage bata zube k’asa ba sabida jiri da Ya kusa kada ita. Cikin sauri Hisham Ya tallafota yana tambayarta lafiya meke faruwa da ita. Bata iya amsa Hisham ba. Hasalima bata kuma fahimtar meke wakana ba. Bata san ina take zuwa ba. Ita dai kawai ji take k’afafunta suna motsawa. K’arshen tikatiki tik.. Bata da sauran wajen gudu.. Ya zama wajabi ta dakata ta fuskanci bayanta. Ta Ya zata soma fuskantar Aliyu Maitama da ahalinsa..? Ta Ya zata soma sanar da tilon D’anta ga asalinsa da ta jima tana b’oye masa.? Ta Ya zata iya sanar dashi abokinsa D’anuwansa ne da suka had’a uba d’aya.? Ta Ya zata iya karya alk’awarin da ta d’aukar ma kanta cewa bazata tab’a jingina D’anta da Aliyu Maitama ba.? Ji Tai Hisham Ya kamo hannunta yana girgiza kai yake tambayarta “Hajja dan Allah meke faruwa ne wai..? Hajja meke damunki..? Gaba d’aya kin sauya lokaci guda. Tin sanda kika ga tsohon mijin Ummul.. Ina nufin Abokina Haidar.? Hajja kin sanshi ne.?” Ta d’ago ta dubesa cikin wane irin yanayi “Hisham. Kaini gida..!” Ta furta da kyar. Hisham yai mata duban mamaki “Gida kuma Hajja? Hajja Ummul fah tana asibitin nan ba’a sallameta ba.” Sai taji kuka na zuwa mata gadan gadan ga shivering da jikinta keyi kaman an saka mata electric shock “Hisham ka tashi ka kaini gida ina so na kasance ni kad’ai.. Ka kaini gida Hisham.!” Hisham ya jinjina Kai ya kamo hannayenta ya mik’arta tsaye “Shikenan Hajjah.. Zan kaiki gida.. Just calm down.. Breath.! Inhale exhale.!” Ya fad’i cikin k’ok’arinsa na calming dinta. Ya rik’o hannunta suka nufi mota hawaye naci gaba da gangaro mata. Hisham ya kauda fuska gefe ya saki wata muguwar murmushi a zuciyarsa yace 'I'll never let you win Haidar.! Musamman yanzu da na tabbata Ummul ta gama aurenka. Ka tsaya kaga yanda zan mallaketa cikin sauk’i. Ka tsaya kaga yanda ‘Yaruwarka Anisa zata d’auki nauyin zunubaina.! I know exactly how to cover all my tracks.. You just wait and see.!’ Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushin nan nasa. * "Yaron yana rik'e cikin hannunsa yana jijjigasa waya manne kunnensa na hagu ""Yes Sadis, ka shigo asibitin.? Don't let him escape.! Ka tabbata bai kufce maka ba Sadis.""" "Daga d'aya b'angaren Sadis ya kaste Haidar da fad'in ""Ga plate number dinsa ina gani..Positive. I can see his car clearly yana fitowa daga asibitin.. It's him.""" Haidar yaci gaba da jinjina Kai yana jijjiga yaron dake cikin hannunsa “Good Sadis.! Make sure that Bastard doesn’t escape. I’ll call the cops now.” Daga haka katse kiran yai. Daidai lokacin Ummul ta fara motsa jikinta alamun tana yunk’urin farkawa. Still idanunta a lumshe suke.. Cikin wane irin kasaltacciyar murya take furta “Umm.. Umma.. Umma na.. Umma na..!” Haidar ya k’ura mata ido ba tareda ya furta komai ba. Ga jaririn rungume cikin hannunsa. "A hankali ta soma bud’e idonta da suka matuk’ar nauyi har ta sauk’e su tar akan Haidar. Sosai ta razana da ganinsa, alamun tsoro Ya nuna saman fuskarta.. Bata ma kula da jaririn dake rik’e cikin hannunsa ba. Ta soma k’ok’arin matsawa baya daga nan yanda take kwance saman gadon tana fad’in “Mai.. Mai kake a nan..? Ya akai kasan ina nan..?”" Idanunsa suna kuma rinewa zuwa ja yaci ga a da takowa zuwa gaban gadon nata “How could you..? How could you have done this Khairy..? How could you have kept something so serious like this..? Ta ya zaki b’oye mun abu mai girma irin wann.? What kind of punishment is this..?” Ya numfasa zuciyarsa na kuma masa zogi. Sai ya sassauta murya kad’an still yana iya sauraran tsananin b’acin rai cikin muryar nasa “Khairy.. How could you have trusted that imbecile..? Ki fad’a mun saceki yayi..?! Answer me now.!” Ya k’arashe cikin dacin rai Har hawaye na gangaro masa. Kuka ta fashe dashi itama. Ta soma k’ok’arin saukowa daga saman gado. Ta nufi k’ofa tana kuka dukda tangadi da take. Haidar yai sauri ya tare k’ofan. Ta d’ago ta dubeshi cikin kuka. Da kyar ta iya furta “Ni Ka.. Ka k’yaleni na wuce.. Na tsaneka bani son ganinka.. Ka..!” Sai ta duk’a a wajen tana kuka sosai. "Shima duk’awan yai gabanta sirirn hawaye na gangaro mishi ga yaron na kuka cikin hannunsa. Cikin rawar murya mai cikeda sanyi wann karon yake furta “No Khairy.. I can’t… I won’t let you go..! How.. Can I let you go when you are so close to me..? I went insane looking for you, you know.! Ta ya zan bari ki sake guje mun.. Just how Khairy..?!”" Haidar na hawaye Ummu na kuka haka ma jaririnsu kuka yake. Ta dubeshi ta dubi jaririn ba tareda ta daina kukan ba. Saima sadda idonta k’asa da Tai tana mai ci gaba da kukan. Har cikin bargo da tsokarsa yake jin rad’ad’in kukan nata. Ji yake kaman Ya janyota cikin jikinsa Ya lallasheta amma baida wann ikon a halin yanzu.. Ya tuna months back batada masauk’i sai cikin jikinsa. He couldn’t believe shi da Kansa ya furta ma Khairy kalman saki. Kalman da gashi Ya haifar masu da barrier tsakaninsu. Ya lumshe idonsa yana jin zuciyarsa na masa ciwo… A hankali Ya Ware idonsa sanda yaji kukanta na k’aruwa “Please don’t cry… Ki daina kukan nan haka..!” Yaci gaba da dubanta yana jinjina kai “I’ll kill for every tear..” Batace da shi komai ba sann bata dubesa ba bata kuma fasa zubda hawaye ba saima abinda Ya k’aru.. A daidai nan yaron Ya kuma calla k’ara daga nan cikin hannun Haidar. Ya mik’e tsaye yaci gaba da jijjiga yaron yana fad’in “See.. You are making him cry as well..” Yaci gaba da jijjiga yaron yana fad’in “Oh c’mon champ.. hush now.. Don’t cry..” Yaci gaba da jijjiga yaron yana lallashinsa a haka Ummul ke satan kallonsu. Har yaron yai shiru.. Wayar Haidar ta soma ruri.. Yai saurin cirowa daga aljihunsa. mommy ce mai kira. Ya d’aga kiran cikin sauri yana ci gaba da jijjiga yaron da d’aya hannun. Ummul tana jinsa yana waya da Mommy yana sanar da ita tayi jika cikin tsananin farin ciki maras misaltuwa. Haidar yaci gaba “You have a grandson Mommy.. A beautiful Grandson.” Daga d’aya b’angaren Mommy sai ta fashe da kukan farin ciki. Fad’i take gata nan zata shigo jirgi ta taho Bauchi. Haidar yace ta bari idan Allah yakai rai da safe sai su taho gaba d’aya da Daddy. Mommy taci gaba da girgiza Kai tana fad’in “No Haidar.. I can’t wait till morning.. I can’t wait to see my grandson..” Cikin muryar kuka mai gauraye da joy take maganan. Shid’inma dauriya kawai yake amma ji yake kaman yayi kukan musamman da Mommy tace “Na kasa yarda rana irin wann zaizo Haidar… Zanga D’anka.. Ma sha Allah. TabarakAllah…! Alhamdulillah is all I can say..” Ta d’anyi still kafin taci gaba “What about Ummul..? How is she.. How is my daughter Haidar..?” Sai sann Haidar Ya dan waiga ya dubi Ummul wacce ke kwance ta basa baya hawaye naci gaba da gangaro mata. “She’s fine Mommy.. I mean.. She will be fine..” Mommy tace “What do you mean she will be fine.. Ina take..? Can I talk to her.. please put her through.. I want hear her voice.. I want to know how she’s doing.?” "Haidar ya dan furzar da huci lokacin da jaririn Ya fara yan k’anan kuka. mommy ta sinkayo sautin yaron daga cikin waya. Annurinta ya ninku, yayinda k’walla ta kuma ciko idonta “Is that my grandson.. Is that his voice..?”" Haidar ma murmushin yake yana duban yaron “Yes Mommy.. It’s your grandson.. He wants to hear your voice I guess. I’m putting you on speaker.” Yasa Mommy a speaker yana yana duban yaron yake fad’in “Guess who’s on the line Son.? It’s Grandma. Say hi to granny.!” Cikeda farin ciki yake maganan gwanin ban sha’awa. Mommy tace “Hello my cutie.. Is that you..? Is that your tiny voice.? How’s my little love doing..? Oh c’mon don’t cry.. Is the little one hungry..?” Cikeda farin ciki da ya gaza b’uya take maganganun. Haidar sai murmushi yake yayinda Ummul ke saurarensu daga nan yanda take kwance har lokacin hawaye ke gangaro mata musamman da ta sinkayo muryar Mommy tana magana ma jaririn. Mommy tace da Haidar Ya bata Ummul. Sai Haidar Ya d’an waigo kadan yana duban Ummul da ta basu baya. Kuka take maras sauti. Ya d’anyi gyaran murya yace “She’s.. still asleep Mommy..” "Mommy ta jinjina kai “Kyaleta tana buk’atan hutun.” Ta k’ara da “Haidar, nace ya batun aurenku.. Mecece makomar aurenku da Ummul.?” Jikinta duk a sanyaye Tai tambayar cikeda shakkun amsar da zata samu daga gare shi." Lumshe idonsa yai kad’an had’ida furzar da huci daidai lokacin wata mata mai sanye da kayan nurses ta dan manyanta matar ta shigo. Ta dubi Haidar dake rik’eda jariri ta kuma dubi Ummul. Kallon na mamaki ko tuhuma take ma Haidar ganin bataga mutanen da suka taho da Ummul ba. Kafin tai magana Haidar yai saurin furta “I’m the father.” Sai ta saki murmushi matar tace “Ba shakka naga kama.. Congratulations to you.” Ya jinjina mata kai had’ida mata godiya kafin ya sumbaci yaron Ya mik’a mata. Ta amshi yaron tana nufan Ummul. Ficewa waje Haidar yai yana amsa kiran Mommy. Mommy ta sake nanata masa tambayar da Tai masa. "Furzar da huci Ya kuma yi yana shafa kansa kad’an “All that I’m sure Mommy.. Shi ne I won’t give up my wife.. I’ll never give up Khairy.. I won’t give up my little family.. I will do everything I could to make sure ahalina bai tarwatse ba.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “If Khairy is the architect of our love Mommy.. Then I’ll be the Engr.. If she’s the one that designed our love.. Then I’d make sure it is well built.. I will be the protector of that love.. I know it won’t be easy.. It will be difficult.. But then, I won’t give up.. Never..!”" Mommy ta goge hawayen da suka gangaro mata. Murmushi ne saman fuskarta amma can k’asan zuciyarta zallan tausayin D’an nata ne. Ta shiga jinjina kai tana fad’in “May Allah be with you Son… Ina rok’on Allah ya had’e maka ahalinka kaman yanda Ya had’e mun nawa.” Haidar Ya amsa da Ameen Mommy. Yai mata godiya Tai masa fatan alkhairi da nufin washe gari idan Allah yakai rai jirgin sassafe zasu biyo itada mahaifinsa. ** A can waje kuwa Sadis bai fasa bin bayan motan Hisham ba har saida ya cimmasa. A dole Hisham yai birki yai parking. Hajja ta soma karanto salati tana waige waige ganin Mota ta sha gabansu ba shiri. “Hisham meke faruwa.. Waye wann meyasa yake bibiyanmu.?” Hisham da k’irjinsa bai daina bugawa ba girgiza kai yake yama kasa ficewa daga cikin motan. Fad’i yake cikin rawar murya “I.. Ya.. Yaron Ogana ne a wajen aiki.. Ogana da nake aiki k’ark’ashin Kampanin sa.. Engr Aliyu Maitama mahaifin Abokina Haidar.!” Cikin wane irin shock Hajja ta d’ago tana duban Hisham fiyeda Wanda ta shiga lokacin da taga Haidar. “A..Aliyu Maitama.. K’ark’ashin sa kake aiki..?!” Ta fad’i cikin birkicewa. Hisham Ya jinjina kai “Eh Hajja k’ark’ashinsa nake aiki kuma na tabbata shi Ya turo a kamani a tunaninsu ni macuci ne kaman yanda Haidar yai zato.. Hajja abun is complicated amma na tabbata komai zai fito fili idan suka tabbatar banida laifi kuma ni taimakon Abokina kawai nake.” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un shine abinda take nanatawa cikin zuciyarta. Bata sake fahimtar komai ba sai tsintar kanta da Tai a station dan tuni an kama Hisham anyi dashi ofishin yansanda. Hisham Ya kamo hannayen Hajja cikin nasa daga nan yanda yake rufe cikin cell. Ya kwantar da murya sosai “Hajja I’m innocent.. Ban sace Ummul ba.. Ban kuma raba Haidar da Ummul ba.. Hasalima ban tab’a sanin Ummul abokina Haidar take aure ba har sai bayan da suka rabu.. Sann a wann lokacin na san ‘yaruwarsa Anisa tana neman rayuwar Ummul da abinda ke cikinta kaman yanda tayi ajalin rayuwar tsohuwar matar Haidar da abinda ke cikinta..!” Hajja bata fahimtar komai sai hawaye dake gangaro mata tana duban D’an nata cikeda tausayawa. Ta ya fara aiki k’ark’ashin kampanin mahaifinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D’anuwansa ya zama abokinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D’anta ya fad’a gidan da taita k’ok’arin nisanta shi dashi ya fad’a cikinsa tsamo tsamo..? Ta ya duka wad’annan abubuwan suka faru. This a too much of a coincidence. Muryar Hisham ta sinkayo yana fad’in “Hajja ki daina kuka.. Banida laifin komai Hajja ta.. Your son is innocent.. I’m sure Haidar would understand so as his father. Su d’in mutane ne masu nagarta.” Hajja ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Silalewa Tai nan wajen tana kuka sosai. Kuka mai tab’a zuciya. ** Washe gari jirgin safe su Mommy suka biyo zuwa Bauchi. Haidar kuwa asubahin fari Ya baro masaukinsa Ya nufo asibitin dan dama bai yarda ya bar asibitin ba saida ya samar ma Ummul da jaririnsu room nurse da zata kula dasu dan ko nawa zai kashe a kular masa dasu tinda shi dai bazai yuwu Ya kwana dasu ba. Cikin tsananin damuwa mai tattareda tashin hankali Ummul ta kuma tambayar nurse din “Ina Hajja.. ina Hisham meyasa ban sake ganinsu ba tin jiya..? Ki fad’a mun.. Haidar ne yace ki rufe ni a nan Ki hanani fita..? Dan Allah Ki sanar Dani.. Ina Hajja da Hisham..?” “Suna yanda Ya kamata ace nan suke.!” Haidar da shigowarsa kenan da kaya nik’i nik’i na jaririn da na mahaifiyar jaririn Ya fad’i haka. Nurse din ta sauk’e ajiyan zuciya tana ma Haidar sannu da zuwa. K’ok’ari taketayi Ummul ta saka ruwan tea a cikinta ko jariri zai samu ruwan nono amma tak’i sai tambayarta take ina Hajja da Hisham. Nurse din Suka gaisa kafin Haidar Ya shiga aje kayayyakin dake hannunsa matar tana sanar dashi Sun sha fama da ‘yar rigimarsa daren jiya dan cewa Tai saidai a barta ta fice. Ta dubi Ummul murmushi saman fuskarta ta kuma dubi kofin tea dake aje gefe sai ta dubi Haidar tace “Kuma tak’i ta saka komai cikinta balle wann babban mutum din ya samu isasshen abinci.” Ta mik’a mata mug din “Ya kamata ki shanye wann.. Mu a Likitance ruwan nono shine farkon rigakafi ko wane jariri ke buk’ata.” Ummul ta galla mata harara. Dariya taso bama nurse din amma ta gimtse tace “Daure dai ki shanye wann.. Ni kinga ma tafiyata.” Ta mik’e tana ma Haidar Sallama. Bayan ficewarta Haidar ya maidoda da dubansa ga Ummul wacce ta nannad’e jikinta cikin mayafi. Ya dan furzar da huci kad’an kafin yace “Kiyi hak’uri ki sha.. Take one more sip.. Please.!” Kauda fuskarta gefe ba tareda ta dubi yanda yake ba. Ga jaririn tuni ya soma mutsu mutsu yana cilla k’afafu sai tsotsan hannunsa yake alamun yunwa. Haidar ya kuma furzar da huci yana shafe fuskarsa “Look Khairy.! Idan baki sha ba zan tako har wajen na baki da kaina kuma kinsan zan aikata..!” Ta dube shi a dak’ile “Ni kuma sai na tsaya wani k’ato ya bani abinci a baki.. Allah ya sawak’e mun. Idan ka mance ne dai na sake tuna maka.. Ni Ummulkhair ba matarka bace. AUREN WATA UKU mukayi kuma ya k’are.!” Haidar ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida furzar da huci. Yasan dole zai sha fama ba kad’an ba. Yakai dubansa ga yaron da tuni ya b’ige da kukan yunwa ga Ummul ta had’e rai sosai ta kauda fuska gefe. Dik yanda take son ta d’auki D’anta ta basa abincinsa ta lallashesa yai shiru ta kasa sabida tsananin k’iyayyar mahaifinsa dake kuma tunzurata. Sosai kukan jaririn ke mata zafi amma ta kasa koda motsawa sabida Haidar dake wajen. K’arasowa yai ya d’auki yaron ya shiga jijjigasa yana lallashinsa. Sai ya saka ma yaron lip d’insa na k’asa aiko tuni ya capke ya soma tsotsa kaman ya samu abinci. Ummul ta saci kallonsu yanda Haidar ya saka bakinsa ma yaron sai jijjigasa yake. Hawaye suka gangaro mata. Daidai nan sukaji Sallama a k’ofa. Haidar ya bada izinin shigowa. Wa zata gani.? Mama Tani ce da ‘yanuwanta guda biyu Azeema da Badia. Suka tafi a guje suka rungume Ummul suna kuka. Yayinda Haidar ke gaisawa da Mama Tani ya mik’a mata jaririn yana musu sannu da hanya. Dan dama Tun a daren jiya ya tura Sadis ya tafi Kano d’aukosu. Asuba Sun kamo hanya shisa sukayi isowan safiya. Haidar ya fice wajen Sadis ya basu waje. Sosai Ummul ke kuka tana tambayan sauran ahalinta. Ta dubi Azeema tace “Ina Khulsum..? Maiyasa bata biyoku ba..? Itama tana fushi dani ko.? Umma da Abba duk fushi suke dani ko.?” Hawaye suka ci gaba da gangaro mata tana girgiza kai take fad’in “Bazan iya dubansu cikin ido ba.” Cikin tsananin rawar murya take maganar. Azeema ta murmusa tana share ma Ummul d’in hawayen da suka gangaro mata “Dukanmu muna fushi dake ‘yaruwa.. Shin wak’e gudun danginsa a lokaci mai mahimmanci irin wann…? Amma Kar ki damu zamu iya yafe Miki ko dan zuwan Sabon D’anmu.!” Ta k’arada “Kinga d’ago ki gani.. D’ago kiga da wa muke tare.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. D’agowar da Ummul zatai sukai ido hud’u da Khulsum. Rabon su da su saka juna a ido Tun lokacin Auren Ummul d’in a gidan Hajiya Asshe ranan da mahaifiyarsu tai ma ‘yanuwan Farrak’u a k’ok’arinta na ganin Auren Ummul Ya tabbata. Hawaye suka ci gaba da kwaranya musu.. Khulsum tana k’arasowa gaban Ummul kukan Ummul d’in Ya k’aru sosai. Murya na rawa Khulsum ta furta “Adda Ummul..!” Sai sukai bursting cikin kuka sosai su duka biyun. Suka rungume juna suna yin mai isansu. Har saida Mama Tani tace zasu tasa mata sabon maigida da kukan da suke dan tuni bacci ya d’auke jaririn cikin hannunta. Ana haka su Mommy harma da Daddy sukai sallama tareda jagorancin Haidar. Gaishe gaishe aka soma kan Ummul na kife k’asa tin shigowar Mommy da Daddy. Mama Tani ta mik’a ma Mommy yaron tana fad’in ta rigata ganin angon nasu. Sukaita ‘yar bankwanci a tsakani Mommy tana fad’in ma sha Allah ta sumbaci goshin yaron. Sak Haidar dinta sanda yake jariri. Su Azeema kaw ficewa sukai bayan Sun gaisar da iyayen Haidar. Mommy ta mik’a ma Daddy dake zaune saman farar kujera yaron. Ya amsa yaron kyakkyawan murmushi bisa fuskar Daddy. Haidar yana gani Daddy na ma yaron addu’a ya tofa masa. Ya mik’a ma Mommy yaron bayan ya jero ma jaririn da mahaifyarsa add’u’o’i. Har kawo wann lokacin Ummul bata iya d’ago fuskarta ba. Daddy ya dubi Haidar yace suje daga waje. Ba musu Haidar yabi bayan mahaifinsa. Bayan ficewar su Mama Tani ma ta zame jiki ta fice tana ce da Mommy bari ta barta ta gana da sabon Angonta dan gashi da alama har ya kori Daddy. Mommy ta murmusa tana jinjina barkwancin Mama Tani. Mik’ewa Mommy tai rungume da yaron cikin hannunta ta dawo kusan Ummul wacce tinda Mommy ta nufota k’irjinta ya tsananta bugu. Ta kasa koda motsawa balle ta dubi Mommy tin bayan gaisuwa Wanda shima da kyar ta iya. Ta sani tana fara magana kuka ne zai biyo baya. Mommy ta kwantar da jaririn cikin baby crib d’insa dake gefe. Ta kuma matsowa sosai kusan Ummul. Sai Mommy ta d’aura hannayenta saman na Ummul. Ummul na ganin hannun Mommy saman nata hawaye suka shiga gangaro mata. Mommy ma kuka ne taji na zuwa mata. Sai kawai ta rungumo Ummul cikin jikinta tana fad’in “Taho nan ‘Yata..!” "Mommy ta rungumeta sosai cikin jikinta yayinda Kukan Ummul ya k’aru, Mommy na ci gaba da lallashinta." ** A can waje kuwa taryan taryan Haidar ya karanto ma Daddy komai gameda Abokinsa Hisham da irin cin amanar da yai masa bayan ya aminta dashi. Sann ya sanar da Daddy baida haufin duk wani scandals da failures da Kampaninsu ta fuskanta da saka hannunsa ciki. Daddy yaita jinjina lamarin domin kuwa zai iya cewa bai tab’a tsayawa ya tantance kamannin matashin ba cikin employees d’insa dukda kuwa cewa suna tareda Haidar kusan ko Yaushe a company. Ya dubi Haidar yace ai sai su wuce police station din snn ya kuma ce da Haidar d’in ya kirawo company lawyer d’insu cikin gaggawa. Dole Hisham nada Ubannin gidan da suka turosa kampaninsu domin Ya musu zagon k’asa. Tuni Sadis ya jasu suka nufi station yanda Hisham ke gark’ame. * Hajja na gaban Kanta tana magiya ma ‘yansanda da su saki D’anta dan bata fata Aliyu Maitama ya tadda su a station d’in. Alk’awari tai ma kanta bazata tab’a jingina ma D’anta sunan Aliyu Maitama ba koda kuwa shine abu na k’arshe da zatai a rayuwarta. Ba yanda batai su bata belin Hisham ba amma sunk’i sunce sai Wanda yai filing complaint akansa yazo idan D’anta nada lawyer yana iya kiransa. Hajja ta kuma marairaice fuska “Rankaidade ka dubi girman Allah ka min alfarmar nan.. Ka dubi soyayyar dake tsakanin D’a da mahaifiya ka bani belin D’ana.. Ko nawa zan kokarta na biya in sha Allah.” "Shi kaw Hisham addu’a yake daga nan cikin cell yanda yake gark’ame kar a bada belinsa har sai mahaifinsa Aliyu Maitama yazo station d’in. Aiko kaman daga sama ya hango Haidar da Sadis ga Daddy na biye dasu. Hisham ya saki murmushi da gefen bakinsa. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Bingo.! Daga k’arshe dai, korarren D’an zai had’e da mahaifinsa. Bari dai mu gani Aliyu Maitama.. Ya zakai da wann D’an naka da ka sheganta… The Son you never noticed dikda jimawansa yana aiki k’ark’ashinka.!’" A haka suka k’araso cikin station d’in waya manne kunnen Daddy dake magana da company lawyer dinsu. Cak Hajja ta had’iyi kalamanta. Tai mutuwar tsaye nan wajen. Ta ina zata mance wann murya dukda muryar ta manyanta a halin yanzu.. Ta tuno muryar a lokacin da ya jajanta mata rashin mahaifinta kuma leburansa a Kampaninsa. Ta tuno muryar a lokacin da yai alk’awarin Aurenta bayan rashin mahaifinta. Ta kuma tuno muryar a lokacin da ya furta mata kalman saki ya kuma sheganta jaririn cikinta. Ta tuna sanda ya turata kurkuku har ta haife D’anta a gidan yari. Yau gashi nan zai kuma tura D’an da yai sanadin haihuwarsa a gidan kasu zuwa gidan kasu. Ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na bugawa cikin sauri. "Cak Daddy ya ja ya tsaya, ya dakata da wayan da yake a daidai sanda ya shigo cikin ofishin yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa ba tareda yasan dalili ba." SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *55* *©️Sameena Aleeyou… * Officer yana hango su Haidar yace “Yauwa Hajiya.. Ki adana duk wann magiya da kike. Gasu nan sun iso su yafi cancanta ki roka ba mu ba.” Ya k’arada barkanku da isowa.” Zuciyar Hajja yaci gaba da harbawa daga nan yanda take tsaye gaban kanta. A hankali Daddy ke takowa kusan matar yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa. A b’angaren Hajja ma hakan ce ta kasance. Ta kasa koda motsawa balle ta waigo. Addu’a kawai take cikin zuciyarta Allah Ya kawo mata da sauk’i. Ji take tamkar numfashinta zai bar gangan cikinta haka nan k’afafunta tamkar bazasu iya d’aukanta ba. Tana jin officer yana fad’in “Ga mahaifyarsa nan tun safe take mana magiya a nan.. Tak’i barinmu mu huta.. Cewa take lallai lallai sai mun bata belin D’anta.” Haidar ne ya katse D’ansandan da fad’in “Idan D’anki nada lauya kuna iya gabatar dashi k’arshen gata da zaki masa kenan. Dan sai nayi sharia da D’anki with every means and resources da nake dashi.!” Ya k’arashe yana aika ma Hisham dake tsare cikin cell mugun kallo kaman zai shak’o sa. Har lokacin jikin Daddy a matuk’ar sanyaye yake dan matar tak’i juyowa ta dubesu Har wann lokacin. Sai Ya d’anyi gyaran murya yace “Sannu Baiwar Allah.!” Zuciyarta taci gaba da harbawa tana sanar da ita ‘Bakida sauran zab’i da Ya wuce ki fuskanci baya Fannah. Komai yazo k’arshe.. Yau dai gaki ga Aliyu Maitama.. Ki juya ki fuskance shi.. Dole ki juya koda zaki tuna masa bayansa da ya k’yamata. Just turn and face the reality.!’ Lumshe idanunta Tai hawaye suka gangaro mata kafin ta soma k’ok’arin waigowa cikin wane irin yanayi. Daddy ya daskare nan wajen. Ya kasa gaskgata abinda yake gani. It’s her.. It’s really her… Ta ya zai mance kamanninta bayan ya shafe tsawon shekaru yana nemanta.? Ta Ya zai mance wann fuskar nata koda ace sanin k’uruciya yai mata. Fannah..! Fannah ce.. Fannah matarsa da ya d’aukar ma Marigayin mahaifinta alk’awarin rik’eta bisa amana. Fannah da Ya datse igiyan Aurensu da jaririn cikinsa cikin jikinta. Cikin da Ya fidda shi daga cikin ahalinsa tun kafin ya shak’i iskan duniya. Fannah da Ya tura fursuna da jaririn cikinsa. Cikin tsananin rawar murya Daddy ya furta “Fann.. Fannah..!” Sai tai bursting cikin kuka ba tareda ta iya furta komai ba. Haidar ya dubi Daddy cikin tsananin shock sai ya kuma dubi matar. Ya sake duban Daddy da mamaki “Fannah kuma..?! Daddy… Fannah naji kace..?!” Ya kuma girgiza kai kad’an cikin rashin fahimta ko rashin aminta “Fannah.. Your exwife.. Matar da.. Matar da Mommy ta jima tana nema..? Daddy ita ce wann..?!” Ya k’arashe yana nuna Hajja cikin tsananin shock. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta. Har lokacin cikin tsananin shock shima yake “Eh Haidar..! Ita ce.. Ita ce Fannah.. Matata..! Matata da muka rabu tsawon shekaru na kuma nemeta ban sameta ba.!” Daga nan cikin cell Hisham ke girgiza kai fuskarsa na nuni da tsananin mamaki yake furta “Hajja.. Hajja meye nake ji haka..? Meye suke cewa haka..?!” Ya dubi Haidar Har lokacin da mamaki samar fuskarsa tamkar gaske “Meye nake ji haka..? Ta Ya mahaifiyata ta zama matar mahaifinka..?!” Sai sann Daddy yakai dubansa ga Hisham zuciyarsa na tsananta bugu. Bai san sanda ta soma takawa ya isa har gaban k’arafunan cell da Hisham ke rufe ciki. Daddy ya k’ura masa ido without saying a word. Su duka biyu shida Hisham kallon juna suke cikin ido.. A hankali Daddy ke bin Hisham da kallo k’walla tab idanunsa tin daga fuskarsa har izuwa k’afafunsa yanda yaga k’afafun Hisham d’in Sun jeru da nasa k’afafun suna kallon juna. Sai Daddy ya k’ura ma yatsun k’afafunsu kallo. Babu abinda ya raba k’irar halittar k’afafunsa da na matashin. K’wallan dake kwance cikin idanun Daddy suka d’igo suka sauk’a saman k’afan Hisham. Sai Daddy ya juyo yana duban Hajja dake kuka sosai shid’in ma hawaye ke gangaro masa. Yana dubanta yake nuni da Hisham yatsarsa Har rawa take “Is.. Is he my son..? Shi ne D’ana.. da kika tafi yana ciki..!” Sai Hajja ta kuma fashewa da kuka ba tareda tace komai ba. Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Hajja. Ya tamke k’arafan cell sosai yana kuma girgiza kai mai cikeda nuna rashin amincewa “Hajjah.. Mai nake ji haka..! Mai haka yake nufi..? Mai Mahaifin Haidar yake cewa..? Hajja mahaifin Haidar .. Shine mahaifina..? Har lokacin ta kasa cewa komai sai kuka yayinda Daddy yaci gaba da duban Hisham hawaye naci gaba da gangaro masa. Haidar da yai mutuwar tsaye yana duban abin al’ajabi cikin wane irin yanayi yake girgiza kai “No.. No.. No way.. This can’t be.. No this can’t be happening..?” Hawaye suka ci gaba da gangaro ma Hisham. Cikin wane irin yanayi yake furta “Hajja please answer me.. Is he my father..? Da gaske shine mahaifina..? Hajja shekara da shekaru ina tambayarki ina mahaifina..? Ina danginsa.. Ce min kike ya mutu all these years.. Ce min kike baida kowa baida dangi.. Hajjah.. Ta Ya mahaifin Abokina Ya zama mahaifina..? Hajja ki sanar Dani dan Allah.. Hajja zuciyata tana nauyi.. Dan Allah Ki sanar Dani bazan iya d’auka ba.!” Hawaye ne ke ci gaba da gangaro ma Daddy yai saurin shigar da hannunsa cikin k’arafan cell d’in Ya tallafi fuskar Hisham dake kuka sosai. Cikin rawar murya Daddy ke furta “My son.. My son.. You really are my son.. I’m your father.. Your father is alive.. He’s very much alive.. Mahaifinka na raye D’anah.!” Sai Hisham yai bursting cikin kuka yayinda Haidar yaci gaba da dubansu cikin tsananin shock. ‘Yansandan ma duk mamaki da al’ajabi ne Ya cikasu. Kowa a wajen mamaki yake. Sai babba cikin ‘yansandan ya fito yana gyara d’amararsa yace “Inaga an sami rashin fahimta a nan..! Da alama rikicin na cikin gida ne.. Inaga bai kamata mu bar wann k’araffan su zama shamak’i tsakanin D’a da mahaifi da suka shafe shekaru basu tare.” Ya k’arashe yana mai bud’e cell. Kaman jira Daddy yake sai Ya shige Har cikin cell d’in Ya rungume Hisham sosai cikin jikinsa. Girgiza kai kurum Haidar yake yana duban Daddy da Hisham yana jin tamkar dai duniyar na juya masa. Ya kasa yarda da abinda idonsa ke gani.. Ta Ya mutumin da yaci amanarsa zai zama D’an mahaifinsa.. Ta Ya zai soma kiran wann bak’in k’umurcin D’anuwa. Just what is this.? Meye yake faruwa haka.? Bazai iya jure tsayuwa nan wajen ba. Bai san sanda Ya fice daga wajen cikin wane irin yanayi ba. ** A can asibiti kuwa an rasa gwani wajen tarairayar sabon jariri da mahaifiyarsa tsakanin Mommy da Mama Tani. Dr ne Ya shigo ya duba jariri da mahaifiyarsa nan yake sanar dasu a ranar zaayi Sallama. Mommy ta kuma daukan jaririn ta mak’ale shi cikin hannunta tana fad’in zasu fice lambun dake bayan d’akin Ya samu vitamin d’in dake cikin hasken ranar hantsi a cewarta. A wasa Mama Tani ke fad’in su dai basu saba da jegon turawa ba. Jariri a d’aki yake har yai kwanaki bakwai. Mommy ta murmusa tace gwara dai su fice taji dumin mai gidanta koda na dan lokaci ne tinda gashi har zaayi Sallama. "Sai jikin Mama Tani Ya d’anyi sanyi Har taji ba dadi dan ta kula sosai yaron ya shiga ran Kakar tasa gashi Haidar da Ummu basu tare balle ta Sami kusanci da yaron. Sauken ajiyan Zuciya Mama Tani tai tana addu’an samun maslaha a al’amarin ma’auratan cikin zuciyarta. Musamman idan ta tuno wani rikicin da suka baro gida wato Abba. Ta maido da dubanta ga Ummul bayan Mommy ta fice tace “Yauwa Ke Ummu, nace ba.. Kinga dai a halin yanzu ke uwa ce.. Abinda aka sani ga uwa kuma shine sadaukarwa.. Ummul inaga tinda Allah yasa kin haihu lafiya sann yanzu rabo Ya tsaga tsakaninki da yaron nan Aliyu.. Bakiga yanda Ya shiga damuwa da tashin hankali ba sanda baki nan, yaro mai k’aunarki ga dattaku da sanin yakamata ba irinsu mijin Badia Tasi’u barawo da mijin Azeema Habibu gantalalle. Ni inaga zaifi kyau a maida aurenku tinda ga rabo a tsakani.. Yaro Ya girma tsakanin iyayensa biyu yafi.. rabuwar sai dole. Idan Har ke d’in kika sauko daga dokin fushi kika amince a maida auren Abbanku mai sauki ne..” Bata Kai aya ba ta soma sinkayo kukan Ummul." Taci gaba da girgiza kai “Ni dai a’a dan Allah Mama. Wllhi bani son komawa gidan Haidar.. Ni ko ganinsa bani son yi..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Mama Tani ta jinjina kai a hankali “Shikenan kiyi shiru Ya isa haka.. Kinji gashi ana Sallama a k’ofa.” Ta k’arashe tana bada izinin shigowa. Ga tsananin mamakinsu Asshe suka gani. Mama Tani ta mik’e tsaye tana gyara daurin zani tana huci “Toh gayyan tsiya gayyar Allah tsine.. Waye Ya gayyatoki.?” Ga mamakinsu cikin sanyi Asshe ta dubi Mama Tani tace “Kiyi hak’uri mu gaisa kafin duk wani tashin hankali.. Hasalima no ban zo nan da wani tashin hankali ba.” Mama Tani ta rakata da harara “Yo ai ke ganinki babu alkhairi Sam Sam. A hankali Asshe ta jinjina kai “Komai kika fad’a akaina bazan mayar Miki ba. Wanda nayi tuba domin shi Ya sani.” Ta dubi Ummul dake zaune saman gadon ta kuma duban Tani tace “Wajen Ummulkhair nazo idan kinmin izini.” Mama Tani ta kuma gyara daurin zani “Toh ban miki izini ba.. ki kwashe k’afafunki ki fice tin muna mu biyu..” Ummul Tai saurin girgiza kai tana duban Mama Tani “Kiyi hak’uri dan Allah Mama.. Kiyi hakuri ki kyale Aunty Asshe.” Shek’ek’e Mama Tani ke dubanta “Awho na fice na k’yaleki da ita a d’aki ta shak’eki kaman yanda wancan muguwar ‘yar tata taso kashe ki.” Asshe ta share hawayen da suka gangaro tana mai zama gefen Ummul. Harara Mama Tani ta rakata dashi Tai mata nuni da k’ofa tace “Ba nisa zanyi ba.. Ina nan daga k’ofa ina gadinki.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice tana aika ma Asshe mugun kallo. "Bayan Mama Tani ta fice Ummul ta bud’e murya ta gaida Aunty Asshe. Saiga Asshe na hawaye. Ta kamo hannayen Ummul tana rok’onta gafara. Taci gaba “Tabbas a wann ranar da za’a Miki aure ni da kaina na baki zab’i cewa sadakinki shine zai zama kudin jinyar mahaifinki.. Idan akwai Wanda Ya tilasta Miki auren Haidar ba kowa bane face ni.. Ummulkhair, Haidar baida masaniya a duka abubuwan da muka aikata nida mahaifiyarsa.. Kaman yanda mahaifiyarki ma bata sani ba.!”" Cikin wane irin yanayi Ummul ta d’ago tana duban Aunty Asshe hawaye na gangaro mata. Asshe taci gaba da jinjina kai tana hawaye “Haidar baisan da labarin Auren karya sihiri ba kaman yanda mahaifiyarki bata sani ba.! Ummul batada laifi cikin AUREN WATA UKU da muka shirya. Mahaifiyarki uwa ce kawai kaman ko wace uwa. She wants nothing but the best for her daughter. Tana son ‘yarta takaiga d’akin Aure kaman ko wace ‘ya mace.. Tana so ta sauk’e wani nauyi ne kawai da Ya rataya a wuyanta matsayinta na mahaifiya. Tana so ta cike wani gurbi nata na zama uwa a gareki. Da saninta da hankalinta ba mahaifiyar da zata d’auki ‘yarta ta sakata cikin halak’a.. Mahaifiyarki tana matuk’ar k’aunarki Ummulkhair..!” Asshe taci gaba da girgiza kai tana duban Ummul “Mahaifyarki Bata san da Auren karya sihiri ba.! Mahaifiyarki bata san da AUREN WATA UKU ba har sai bayan da akai auren. Idan akwai mai laifi ni ce da na b’oye mata. Ni nayi amfani da rauninta na shashantar da ita Har ta d’auki ‘yarta ta jefata cikin irin Auren da Babu Uwar da zata saka ‘yarta. !” Tinda Asshe ta soma magana kuka kawai Ummul take ba k’akk’autawa. Tausayi da soyayyar mahaifiyarta ya cika zuciyarta. Asshe taci gaba “Ni na datse soyayya da shak’uwa dake tskanin ‘ya da mahaifiya. Ni nayi umarni ma mahaifiyarki cewa ba ita ba ke Har sai bayan tsawon watanni uku. Ni ce nan na tilasta mata ta sanar dake haka amma ba rad’in kanta bane. Ni na saka shamak’i a tsakaninku.. Yau gashi ‘yansanda Sun saka shamak’i tsakani na da tawa ‘yar.. Anisa tana tsare kurkuku.. Da zargi masu nauyi akanta na attempting kasheki da taso yi..!” Ta kuma kamo hannayen Ummul hawaye naci gaba da gangaro mata “Zunubaina ke bibiyata.. Tabbas duk abinda ka shuka a rayuwar nan zai dawo gareka. Ya rage naka ka shuka khairan ko sharran. Ummul dan Allah ki yafe mun ki yafe ma ‘Yata Anisa ko zamu samu sassauci.!” Ummul taci gaba da kuka sharshar da hawaye yayinda Asshe ma taci gaba da zuban hawaye. Ta goge hawayen kafin taci gaba “Anisa tayi yunk’urin kashe ki ne sabida soyayyar da take ma Haidar.. Ina sane da duka abubuwan da Anisa take Wanda hankali bazai Kama ba amma na adana a raina sabida soyayyar dake tsakanin Mahaifiya da ‘yarta.. Na mance ba’ayi ma Allah wayo.. Kaman yanda naso raba wata uwa da ‘yarta gashi nan Nima yanzu za’a rabani da nawa ‘yar.. Nabi son zuciyana Ya rufe mun ido.. Nayi komai ne sabida soyayyar da nake ma yarana Haidar da kuma Anisa. Ki sani Ummulkhair.. Haidar baida masaniya akan Auren karya sihiri.. Eh Tabbas da yarda da amincewarsa aka k’ulla AUREN WATA UKU sabida wani manufa na shi kan iyayensa a baya amma baisan da labarin karya sihiri ba. Ya d’auki girman laifin ne kawai domin Ya zamto shield ga mahaifiyarsa.. Ya datse igiyan Auren ku ne ba don yana son yin hakan ba sai don ya zamto garkuwa a idonki dama sauran jama’a ga mahaifiyarsa.. Ya d’auki laifin mahaifiyarsa ne don ita d’in mahaifiyarsa ce.. Ko wane D’a na gari zai sadaukar da komai nasa sabida mahaifiyarsa.. Ciki harda soyayyarsa.. Kuma na sani wann shine mafarkin ki da burinki ga ahalin Haidar Tun bayan da kika shigo rayuwarsu.. Kina kwadayin kiga alak’arsa da iyayensa ta gyaru tayi kyau.. Toh Tabbas ta gyaru kuma tayi kyau.. Saidai tazo at a huge cost. The cost of your marriage.!” Ta kamo hannayen Ummul cikin nata su duka biyun hawaye na gangaro musu tace “Ki yafe ma Haidar domin shi d’in masoyinki ne. Ni na raini Haidar da hannuwana Tun yana k’uruciya.. Na kalle shi Har tasowarsa.. Kuma ban tab’a ganin shi cikin soyayya irin Wanda na gani akanki ba.” Sai suka soma sinkayo kukan jaririn daga window. Asshe taci gaba da jinjina kai tana duban Ummul “A wasu lokutan mukan rufe idon mu ne mu Dole ce kawai da K’addara suke sa ‘ya’ya su girma ba tareda iyayensu biyu ba matuk’a suna raye.Ki koma d’akin mijinki ko dan wann D’an k’aramin alhakin da baisan hawa ba baisan sauk’a ba. Kar ki bari ahalinki ya tarwatse. Kar ki hana ma D’anki abinda Haidar Ya rasa lokacin k’uruciya.. Kar ki bari tarihin abinda Ya faru da mahaifinsa Ya maimaita kanshi..!” Ta sauk’e ajiyan zuciya murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. A hankali ta mik’e tana gyara fuskarta “Zanje naga jikana.. D’an Haidar dina.!” Tana ida fad’in haka ta mik’e ta fice. Yayinda Ummul Tai bursting cikin kuka. Asshe tana fitowa taci karo da Haidar a lobby cikin wane irin yanayi tamkar Wanda ruwa Ya shanye shi. Cikin sanyin jiki take dubansa. Ta ambato sunansa a hankali “Haidar.!” Bai iya cewa komai ba sai kawai Ya rungume Asshe. Jikin Asshe ya kuma yin sanyi ganin yanayin nasa. Ta rungume shi cikin jikinta hawaye na kuma gangaro mata “I’m here.. I’m here Haidar.. Your Aunt is here.!” Sai kawai yai bursting cikin kuka. Kuka sosai yake kaman k’aramin yaro kukan da zata iya cewa bata tab’a jin yai irinsa ba tun tasowarsa matsayinta na Uwar goyonsa. Cikin rawar murya Asshe ke furta “Wann ba Zaki na bane.. Zakin da na raina baya kuka.. Na raini Jarumi.. Jarumin da ba’a ganin rauninsa balle a gano lagnosa.!” Tana maganar tana tuna yarintar sa sabida Sam baya kuka a yarinta sann ba wani abu da yake basa tsoro bayan wofantar dashi da iyayensa sukai a lokacin da Ya kamata su jasa jiki. Saman wani kujera suka zauna ta dan waje. Haidar ya saka tafukan hannayensa ya share fuskarsa da ta rine ta koma jazir. Cikin wane irin yanayi yake furta “When will all this end..? Yaushe ne komai zai wuce.? Meyasa rayuwa ta kasance haka..?!” Aunty Asshe ta jinjina masa kai “Wann sunnar rayuwa ce Haidar.. Jarabawa basu k’arewa Har sai an bar gidan jarabawa wato duniya.!” Haidar yaci gaba da girgiza kai “Na kasa yarda.. Na kasa yarda da abinda ke faruwa.. Mutumin da nafi tsana a halin yanzu Ya zama D’anuwana..! How is this possible Aunt.?! Ta ya zan kalli wann mutumin na kirashi da D’anuwa..? Just how.?!” Cikin rashin fahimta Asshe ta girgiza kai “Wane D’anuwa kake magana Haidar..? Meke faruwa.?” "Yaci gaba da jinjina Kai “Daddy yana can reuniting with his long lost son. Su d’in Sun hadu da juna.. Daga k’arshe dai, D’a da mahaifin sunga juna.. I don’t know how Mommy would take it.. Bansan ya iyaye na zasu d’auka ba.. Amma abinda na sani shi ne wann mutumin bazai tab’a zama D’anuwana ba.!”" Muryar Mommy suka sinkayo tana fad’in “D’an uwa.. Wane D’anuwa kake magana Haidar.?!” A tare Haidar da Aunty Asshe suka juyo suna duban Mommy. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *56* *©️Sameena Aleeyou… * Haidar yai shiru yana duban Mommy. Ba huruminsa bane ya zamto mutum na farko da zai sanar da ita gameda al’amarin. This is something for his Dad to decide. Kaman yayi shishigi ne idan Ya soma sanar da ita. Mommy ta kuma jefo masa tambayar ganin yayi shiru ba amsa. "“Haidar, nace wane D’anuwa kake magana.?”" Asshe ta dubi Mommy sai ta dubi Haidar. Sai ta d’an murmusa kad’an tace “D’anuwansa Hilal dake makaranta yake magana…“ Mommy dai kallonsu take bawai ta gamsu ba.. Wayar Haidar ce ta soma ruri. Daddy ne mai kira sai Ya mik’e Ya dan matsa gefe yana amsa kiran Daddy yayinda Aunty Asshe ta k’araso ga ‘yar Uwar nata jiki ba wani kwari dan har kawo lokacin ta kasa sakin jiki da Mommy kaman a baya. Daga d’aya b’angaren Daddy yaci gaba “Kana jina Haidar.. Sadis yana hanya zai taho ya d’aukeku kaida mahaifiyarka.. Ina so kuzo ku sameni a nan masauk’i.” Haidar ya dan lumshe idonsa kadan Ya waresu yana duban Mommy dake zaune gefen Aunty Asshe tinda shidai yasan kwanan zancen. Bazai wuce kan Sabon D’an Daddy bane da mahaifiyarsa. Sai Ya dan furzar da huci kad’an yace “Ok Daddy.. Kaman yanda kace.” Yana ida wayan Ya dawo yanda ya baro su Mommy. A tare suke dubansa itada Aunty Asshe. Sai gani sukai ya duk’a gaban Mommy daga nan yanda take zaune saman kujera. Jikin Mommy ya kuma yin sanyi da al’amarin Haidar. Hannayenta ya kamo cikin nasa yana dubata. Lokaci guda yake furta “You are the most precious to Me Mommy.. And.. Whatever happene know that I’m here for you.. And I got your back.” Ya jinjina Kansa kad’an kafin ya k’arada “I love you Mommy. So much.” Har lokacin jiki a sanyaye Mommy ke dubansa musamman da taji ya matse hannun nata sosai cikin nasa sanda yake maganan. Ta jinjina masa kai a hankali tana jin k’walla na ciko idonta. “Nima Ina sonka D’ana.. Ina matuk’ar k’aunarka.!” Ya murmusa kad’an had’ida mik’ewa tsaye. Aunty Asshe ma murmushin tai cikeda farin ciki. Ta goge hawayen da suka gangaro mata ta mik’e tana fad’in zata shiga ciki taga jariri sabon angonsu. Bayan ta shige Haidar Ya rik’o hannun Mommy suna tafe sanda yaga isowar Sadis. Suka nufi motar hannunta na sakale cikin nasa. Ita dai Mommy bata san ina ake zuwa ba sai ji tai Haidar na fad’in “Mommy akwai yanda zamuje yanzu.. Daddy yana can yana jiranmu.. Ina so Ki kwantar da hankalinki.. Kuma ki sani ina tare dake.” Ya k’arashe yana bud’e mata owners corner.” Duban Haidar kurum take ba tareda ta iya furta koda kalma ba sai k’irjinta dake tsananta bugu ba tareda sanin dalili ba. Tana gani ya bud’e front Seat Ya shige yace da Sadis suje. Sadis yaja mota suka fara tafiya. Tinda suka soma tafiya saman kwalta Mommy bata iya cewa komai ba. Har kawo bud’e musu wani tampatsetsen gate da akai. Suka shige cikin tsantsararren Villa Suite d’in Sadis Ya nemi waje yai parking. Haidar ne Ya bud’e ma Mommy k’ofan motar. Tai zaune daga cikin motar tana dubansa “Haidar.. What is this place..? Ina muka zo.. Wajen wa muka zo.?” Sai Ya murmusa “Mommy masauk’inku da Daddy muka zo.. Daddy yana ciki yana jiranki.” “Amma.. Ummul da Jikana suna can asibiti.. Bai kamata mu taho mu barosu ba.” Ya jinjina Kansa a hankali yana kamo hannunta “Kar ki damu Mommy zamuje mu d’auko su.. But for now.. Daddy needs to see you first. Let’s go.” Ya k’arashe yana kamo hannunta suka nufi building d’in. Tamkar rak’umi da akala haka Mommy ke biyeda Haidar Har suka isa k’ofan parlorn. Daddy ne zaune daga saman kujera dake daga centre… Hajja Fannah tana daga can gefe yayinda Hisham ke zaune daga saman carpet gefen k’afafun Daddy kansa kife kaman mutumin arziki. Sosai Haidar Ya rik’e hannun mahaifiyarsa cikin nasa idonsa kan Daddy Sam bai kula da Hisham dake zaune daga gefe ba. Zuciyar Mommy yaci gaba da bugawa sanda suke shiga cikin parlorn musamman da ta hangi Hisham abokin Haidar wanda D’anta Ya aminta dashi Ya kuma ci amanarsa. Sai Mommy ta soma girgiza kai tana nuna Hisham “Haidar mai wann criminal d’in yake a nan. He should be arrested. He supposed to be in jail.. Dashi da Anisa Sun had’e kai sunyi yunk’urin kasheku kaida Ummul..” Ta dubi Daddy “Engr mai wann azzalumin da Ya kusa halaka mana D’anmu da iyalinsa yake a nan.?” Daddy ya mik’e da sauri Ya nufota “Calm down Kwaise.. That’s exactly why I asked Haidar to bring you here..” "Hannayen Mommy Daddy ya kamo yai k’ok’arin zaunarta saman kujerar dake fuskantar Wanda Hajja Fannah take. Idon Hajja Fannah akansu har Daddy yai masauk’i ma matarsa saman kujera, sai Hajja Fannah ta sauk’e idanunta k’asa a hankali tana mai kifa kanta." Sam Mommy bata kula da matar dake zaune daga kujera mai fuskantar nata ba idanunta naga Hisham tana fad’in saidai a kira yansanda su tafi dashi. Daddy ya kamo hannayenta cikin k’ok’arin calming dinta “Kwaise ki natsu ki saurareni..!” Sai Mommy tai shiru tana dubansa. Daddy yaci gaba “Akwai abubuwa da dama da Ya kamata ki sani harma da Haidar.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Kin tuna Fannah..? Ina nufin tsohuwar Matata Fannah.?” Sai jikin Mommy ya kuma yin sanyi. Ta soma jinjina kai a hankali “Matarka Fannah da nai ajalin Aurenku a tsakanin watanni Uku tak.! Matarka da na koreta da jaririn cikin wata uku sabida son zuciya.!” Muryarta yaci gaba da rawa hawaye na gangaro mata yayinda Hisham ke mata wani irin duba na tsana daga nan yanda yake zaune gumi na karyo masa kaman ba AC bane cikin parlorn. Yau dai da kumnuwarsa yake jin Kwaise Maitama tana amo laifukan da ta aikata masa shida mahaifiyarsa. Mommy taci gaba sanda ta kamo hannayen Daddy sosai cikin nata “Engr da ita nake kwana da ita nake tashi.. Banida burin da ya wuce na ganta na kuma nemi yafiyarta.!” Ta k’arashe cikin kuka yayinda Hajja Fannah taci gaba da zubda hawaye daga can yanda take zaune saman kujera. Daddy ma hawaye ne ya digo masa sanda yake jinjina kai yana duban Mommy “She’s here Kwaise.. She’s right here with us.. Fannah is here with us.. Ba ita kawai ba.. Harda wann jaririn cikin nata da ta fita dashi.!” Dumm! Haka k’irjin Mommy ya buga. Ta d’ago gajiyayyun idanunta tana duban Daddy dasu “Fannah..! Fannah da D’anta suna nan a nan..?!” Ta tambaya cikin rawar murya. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana karkatar da fuskarsa b’angaren da Hajja take. Cikin wane irin yanayi Mommy ke kaikaitowa tana duban yanda taga Daddy na duba. Cak ta mik’e tsaye tana dubanta “Fann.. Fannah..!” Ta furta a hankali still tana dubanta. Sai Hajja ta d’ago idonta mai zuban hawaye tana duban Mommy. A hankali Mommy ta soma takawa har ta isa ga Fannah. Ta zuba mata ido tana kallonta. Sai ga Mommy na k’ok’arin duk’awa gaban kujeran da Hajja Fannah take. Bata bari Mommy ta duk’a ba itama ta sauk’o daga saman kujeran. Su duka biyu suna durkushe gaban juna. Mommy ta kai hannayenta masu shaking ta d’aura saman na Hajja Fannah. Daddy ya dubi Haidar da Hisham yace su taho tareda shi. Haidar yakai ma Hisham wani irin duba kaman bazai bi bayan Daddyn ba sai kuma yasa kai yabi bayan mahaifin nasa. Parlorn Ya rage saura Hajja da Mommy. Sosai suke kuka su duka biyun an rasa mai bama wani baki. Saida sukai ma isar su kafin Mommy ta iya bud’e baki ta soma sanar da Hajja Fannah irin nemanta da tai sanda bata nan. Da irin nadaman da Tai bayan abinda ta mata sai kuma ta soma neman gafaran Fannah d’in. Hajja Fannah ta girgiza kai tana hawaye “Ta Ya zan iya yafe Miki bayan kin so ki maimaita tarihin abinda kika min akan Matar D’anki Ummulkhair? Yarinyar da kika so hallak’ata ta hanyar sihiri dan ki ceto naki D’an.!” Ta k’arashe hawaye naci gaba da ganganci mata. Saurin girgiza kai Mommy take tana hawaye “Kafin na gane kuskure na.. Kafin nayi tuba na gaskiya.” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Tai k’ok’arin nitsa kanta kafin ta dubi Hajja tace “Zan karanto Miki komai.. Irin zaman da na fuskanta nida D’ana a gidan Engr Aliyu Maitama bayan tafiyarki da jaririn cikinki.. Shigowar Ummulkhair cikin rayuwarmu da yanda Allah Ya sauya al’amarin ahalinmu bayan mun zab’i mubi turba mik’akk’iya.. Nasan idan kikaji komai Watak’ila ki Sami gurbi cikin zuciyarki ki yafe min Fannah.!” Taryan taryan Mommy ta soma karanto mata abubuwan da suka faru tin bayan barinta gidan. ** A can d’aya parlorn kuwa Daddy ne zaune daga saman kujera yaran nasa guda biyu suna daga saman carpet ko wanne yana daga nashi angle din. Kan Hisham a kife cikeda ladabi ya risina gaban Daddy ko iya d’ago ido ya dubi Daddy cikin ido bayayi yayinda Haidar ke ci gaba da aika masa kallon k’yama da tsana. Da kyar ma Haidar d’in ya amince ya zauna a parlorn saida Daddy yai da gaske dan cewa yai bazai iya jure zama Inuwa guda da betrayer irin Hisham ba Wanda ko fuskarsa baya k’aunar Ya sake gani balle Ya sauraresa. Cikin dacin rai Haidar yaci gaba da nuna Hisham yana fad’in “Everything make sense now Daddy. Wann azzalumin ya rab’i ahalinmu ne domin Ya tarwatsa mu. Sai Ya fara da company kafin ya gangaro kan Matata Shiyasa yai amfani da shashancin Anisa ta zamto mataimakiyarsa. Everything is clear now.. There’s nothing like coincidence.. Ya riga ya jima da shirya komai Daddy.!” Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Haidar “I can’t believe you Haidar.! Na kasa yarda zaka tafi da nisa Har haka. Throwing such acquisitions on me.. Haidar we’ve been friends for quite some time now.. Ka sanni kasan abubuwan da zanyi da Wanda bazanyi ba.! Ta Ya zansan ku ahalina ne sann na zab’i cutar daku.?” Ya waigo yana duban Daddy “Duk Wanda Ya sanni tareda Haidar yasan irin soyayyar da nake masa matsayin aboki Wanda Har ya zarce abota. mun koma tamkar yan uwa.!” “Shut up.! Kar ka sake kirana Danuwanka.. Kuma ka saka a ranka sai na sa ka biya duka abubuwan da ka aikata.!” Haidar Ya dakatar dashi. Daddy dake shafe goshinsa mik’ewa yai tsakiyan su biyun “Enough.! Ya isheku haka.!” Ya dubi Haidar “Ka daina cewa D’anuwanka yanada wani laifi a company dan Bakada wani proof akai.!” Cikin tsananin shock Haidar ke duban Daddy. Ya girgiza Kai kad’an “Seriously Daddy.! Are you taking his side now.?” “Bana d’aukan b’angaren d’aya cikin ku biyun.. K’ok’ari nake a samo maslaha.” Daddy ya fad’i haka a dan zafafe. Haidar yaci gaba da girgiza kai cikin rashin yarda yana duban Daddy “The only solution here… Is for this snake to pay for all he’s done.!” "Hisham ya katsesa “I didn’t commit any crime Haidar. On the contrary, ni taimakon ka kawai nake but you’re blinded by your anger..!”" Cikin huci Haidar ke fad’in “Ban buk’aci taimako daga wajen wani ba.. And Much less from you..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana huci “ Ka yarda dani zaka biya duk abubuwan da ka aikata.. You mark my words.” “Haidar.!” Daddy ya daka masa tsawa kafin yaci gaba “Idan k’ara akan Company na ne.. Na janye.. And I expect you to do the same.!” Cikin tsananin mamaki Haidar ke duban Daddy. Cikin rashin yarda yake girgiza kai “Seriously Daddy. Are you going to trust this traitor sama da D’an daka rayu dashi tsawon rayuwarsa.? Daddy Anisa tana can a tsare kuma tayi confessing cewa tare suka aikata duka laifukan da ake tuhumar ta dasu… Daddy Anisa tayi rabin girmanta a gidanka koda ace baka shiga al’amran gidan a baya amma kasan Anisa a matsayin ‘ya somehow.. Daddy Anisa might be stupid but I’m very sure she couldn’t have planned to kill someone ba tareda taimakon wani Wanda Ya fita wayo ba… Daddy this coward here amfani kawai yai da Anisa ya juya mata baya.!” “And this is where you are wrong.! Because you refuse to listen to him. You refuse to hear his side of the story.. Abinda Anisa Tai confessing kawai ka dauk’a.. Mai Anisa da k’awarta sukai confessing Haidar.? Cewa sukai su biyun Sun saka ma Ummulkhair guba cikin turare haka ne.? I don’t remember her mentioning my Son’s name cikin bayananta.!” Haidar yaci gaba da duban Daddy kurum yana girgiza kai cikin rashin yarda yayinda Hisham yaci gaba “Daddy zan fi so a tafi can. Gani gashi ga Anisa a warware komai..!” "Ya juyo yana duban Haidar cikin yanayi na ban tausayi “Haidar, I know we grow up quite a bit differently.. Ka girma with both your parents around you.. Ina nufin mahaifi da mahaifiya tareda kai. Ka girma cikin asali.. Amma ni kuma a nawa b’angaren, is the other way around.. Na girma ban san mahaifina ba balle danginsa.. Fatherless Son..! Wasu suna kirana D’an mace.. Wasu Har ce mun suke banida mahaifi banida asali.. I spent my entire life searching for people who would accept me.” Yanda yake maganar dole ya raunana maka zuciya." Tausayin Hisham Ya cika Zuciyar Daddy da jin irin kalubale na rayuwa da Ya fuskanta.. Sai yana jin duka laifinsa ne. Muryar Hisham Ya kuma sinkayowa sanda yaci gaba “ Na fuskanci k’iyayya.. Kyama daga wajen wasu mutanen na nemi aurarraki an hana ni duka sabida laifin da ban san dashi ba amma haka baisa na zab’i zama mutumin banza ba.. Ba Ina yabon kaina ba kafi kowa sanin ni wane irin mutum ne Haidar.. Idan zaka min adalci a tsawon zamana da Kai k’ok’ari nake naga ka zama mutum nagartacce ta hanyar gyara alk’arka da iyayenka..” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Idan duka wann akan Ummulkhair ne.? Akan ta kake nema ka rik’e ni da gaba ka mance Abotanmu da duk wasu alkhairai dake tsakaninmu.? Haidar bansan Ummulkhair kake aure ba har sai bayan da kuka rabu dukda cewa na santa kafin ta aureka hasalima na rigarka saninta… Zaka iya tambayar koma waye koda ita Ummulkhair d’in ne. "Banida tsoro Akan gaskiyata.” Yaci gaba da jinjina Kai tamkar gaske “Zan iya cewa bayan rabuwarku a hanya na tsinci Ummulkhair wacce take tamkar ‘yaruwa a gareni koda babu Kai.. Har kawo lokacin da na taimaketa bansan kaine mijinta ba. I helped her out na kuma kaita wajen Mahaifiyata dan tace mun bata son komawa can gidansu Kano.. A lokacin da nasan kaine mijinta. Wani rana ne da ‘Yaruwarka Anisa tazo company nemanka. Bata sameka ba sai ta Sami Office d’inka a bud’e ta shige. Ni kuma na taho zan shigo Office d’inka sai naga mutum tsaye ciki rik’eda k’aramin hoto cikin yar k’aramar frame. Ta rik’e hoton cikin hannunta tana maganganu masu firgitarwa. Tana fad’in sai ta kashe matar dake jiki kaman yanda ta kashe Dareen ta bigeta da mota. Sai na shigo cikin Office d’in hankalina a matuk’ar tashe jin irin kalaman da take. Idan baka mance ba ni dai ban wacece matarka ba balle nasan kamanninta. If you can still recall hoton da aka muku a ranar tariyarku da Ummul shine hoton da ka saka cikin k’aramin frame ka aje a Office d’inka. Kuma a wann ranar da Anisa takai maka ziyara Office a wann ranar ka aje hoton cikin Office d’inka kafin zuwan Anisa. Haka na nufin nima a wann ranar naga hoton matarka. Na kuma fahimci Ummulkhair da na taimaka kake Aure. Sai nai barazana ma Anisa da fad’in zan mik’ata ga hukuma koma na sanar da kai amma sai Anisa ta rokeni da na dubi girman zumuncin dake tsakanin mahaifyarta da mahaifiyarka kar na bata zumunci nayi hakuri ta tuba. Bazata kuma kashe matar Haidar ba.. Hasalima bata san duniyar da matar Haidar take ba. Tinda ta hadani da girman Allah sai na mata afuwa ban sanar dakai ba. Inata mamakin ashe kaine mijin Ummulkhair. Ban nuna maka na san matarka ba sabida ina so na tabbatar da gaskiyar Anisa akanta. Kar na bayyanata ta kasheta d’in kaman yanda tace ta kashe Dareen da mota. Sai na soma bibiyar Anisa duk dan nai protecting d’inka da matarka dake gaban mahaifiyata musamman da na fahimci ka saki matarka da juna biyu wanda kaima baka sani ba. Toh a cikin bibiyan manufar tuban Anisa da nake na fahimci k’arya take bata tuba ba tana nan akan bakanta na neman Ummulkhairi dan tayi ajalinta. Cikin k’unan zuciya nake sanar da Anisa bazata tab’a cimma burinta akan ahalin Abokina ba, bazan bari ta gansu ba balle tai ajalinsu musamman da nasan cewa gida d’aya kuke rayuwa kaida Anisa hallaka Ummulkhairi da abinda ke cikinta bazai mata wuya ba tinda she tried once. Tayi k’ok’arin poisoning dinta daga fari... Ni kuma sai nai tunanin zamanta wajen Hajja da abinda ke cikinta zaisa Sufi samun tsira da kwanciyar hankali tinda dama Ummulkhair tamkar ‘ya take wajen Hajja su biyun ba bak’in juna bane. Tamkar uwa ce da ‘ya. Sosai na razana da al’amarin Anisa tinda kasan ance kaidin mata yafi na shed’an. Gashi Anisar ta fad’a ta kashe Dareen da jaririn cikinta a ranar bikin tariyarku da Ummul d’in. Idan kaje ka duba motar da Anisa ta shiga a ranar bikinku zakaga anyi had’ari da motar ta sanar Dani ta aje motar a gida ta rufe ba Wanda Ya sake bi takan motar sabida yawan motocin dake gidan ba Lallai hankali yakai kan wann motar da aka rufe da bakin k’yalle ba. Kaman yanda aka mance da wann motar kaman haka zata kashe Ummulkhair da abinda ke cikinta kuma a mance dasu a cewarta. Kaji yanda akai Anisa tasan Ummulkhair na Bauchi wajen mahaifyata ta kuma san tana d’aukeda juna biyu.!” Kuma a jiya da mukayi waya ka tambayeni ban b’oye maka ba. Ce maka nai ina Bauchi na kawo K’anwata da mijinta ya saka asibiti zata haihu. Da ace inada mugun nufi da bazan fad’a maka haka kai tsaye ba Haidar. Na fad’a maka haka ne dan bazan so na tashi hankalinka ba dan ka sanar Dani isowarka k’asar kenan daga SouthAfrica. Dama a tsarina shine da zaran Allah Ya sauk’eta lafiya na sanar da Hajja dama Ummulkhair komai kaima kuma na sanar maka asan matakin d’auka kan Anisa.!”" Ya dubi Daddy cikin sanyin jiki “Daddy wann itace iyaka gaskiyata duk yanda zaaje. Bazan ce kar D’anuwana yai sharia Dani ba. Amma banida gaskiyar da ta wuce wann.!” Haidar yaci gaba da girgiza kai cikin tsananin takaici yana duban Hisham “And you expect me to buy those lies..! Are you that shameless.. Are you that coward..! Don’t you have conscience.?! Why can’t you just admit to the truth.!” “Enough Haidar.!” Daddy ya dakatar dashi kafin yaci gaba “Ya fad’i nashi sai ka bar ma hukuma aikinsu suyi bincike su zartar da hukunci.!” Cikin sanyin jiki Haidar ke duban Daddy. Yana girgiza kai yake fad’in “I can’t believe this Daddy.. Na kasa yarda ka aminta da D’an da ka had’u dashi yau d’aya sama da D’an da ka rayu dashi tsawon rayuwarsa.” Ya jinjina Kai a hankali still yana duban Daddy “Dama mai zan tsammata.. He’s always been your favorite even before you met him.. A sabida rashin shi ka azabtar Dani shekara da shekaru.. A sabida rashin shi ka kasa kallona a matsayin D’a..” Hawaye suka soma gangaro ma Haidar sanda yaci gaba “A sabida rashin sa na rayu cikin duhu ni kad’ai a cikin gidan mahaifina..!” Wann karon cikin sanyin murya Daddy ke furta “Haidar Ya isa haka.” Haidar yaci gaba da nuna Hisham jijiyoyin goshinsa Sun mimmike fuskarsa tayi ja sosai yake ci gaba da furta “This is the truth Daddy.! Duk a sabida rashinsa ne….!” "A hasale Daddy ya katsesa “Then blame your mother..! Ita ce silar faruwar komai..! She created all this chaos..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana duban Haidar “You should be grateful ka girma kana ganin duka iyayenka biyu. D’anuwanka Ya girma baisan mahaifinsa ba..!” Muryar Daddy ya soma rawa sosai, hannayensa har b’ari suke sanda yaci gaba da nuna Hisham idanunsa naga Haidar “I kicked him out tin yana ciki baizo duniya ba.! I kicked my son.. My flesh and blood out of his very own home Haidar..! A sabida haka zan bashi duk wani kariya da yake buk’ata daga yanzu har k’arshen rayuwata Wanda ban bashi a baya ba.!”" Abinda Hisham yake son ji. Anzo daidai gab’ar da yake so a iso. Ya saki murmushin nasara cikin zuciyarsa. ‘Da kyau.. Da kyau Aliyu Maitama. Ka zab’i turban gaskiya da ka zabi ka bi bayana da mahaifyata.’ Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban mahaifinsa. A daidai lokacin Mommy da Hajja Fannah suka k’araso parlorn. Haidar ya waigo ya dubi mahaifyarsa. Sai ya isa ya kamo hannunta “Let’s go Mommy.! We are not welcome here.!” Yai maganar yana duban Daddy. Daddy ya lumshe idonsa kadan ba tareda Ya furta komai ba. Mommy ta waigowa ta dubi Hisham ta kuma dubi Haidar. A haka Har suka fice. Suka nufi yanda Sadis ya aje motar. Mommy ta kula da yanayin Haidar d’in tinda suka fito. Ta kuma ga yanayin rabuwarsa da mahaifinsa. Sai Tai gyaran murya kad’an sanda suka zauna saman kujerun shak’atawa suna jiran zuwan Sadis. “Aliyu kana lafiya.?” Ta tambaya tana dubansa. Sai ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata. Ya dafa hannunta guda “As long as kina cikin k’oshin lafiya nima ina lafiya Mommy na.” Ta murmusa tana dubansa sai ta jinjina kai a hankali “Haidar… My Son..” Ya d’ago yana duban mahaifyarsa. Mommy taci gaba “Kai hakuri da mahaifinka.. Kai masa uzuri a wann lokacin. He just met his Son… So zaka iya ganin abubuwa da dama da zaisa kaga kaman baya sonka ko yafi Son sabon D’ansa da basu tab’a had’uwa ba. A’a ko d’aya ba haka bane. Yana son duka ‘ya’yansa saidai it is natural mutum yai d’okin sabon abu. Misali kai kanka da aka maka haihuwa just yesterday kaji kana d’aukin wann D’an. Toh kaman haka nake so kai ma mahaifinka uzuri duk abinda zai faru kaji koh.” Haidar yai shiru yana sauraron mahaifiyarsa kafin ya jinjina Kai yace “Na gode Mommy.” Ta jinjina masa kai murmushi saman fuskarta “Ina cikin farin ciki maras misaltuwa a yau d’in. Inaji tamkar na sauk’e wani kaya mai matuk’ar nauyi akaina.. Na nemi yafiyar Fannah kuma ta yafe mun. Alhamdulillah.. Ko yanzu na bar duniya Ubangijina Ya cika mun wasu manyan burika nawa. Ya daidaita tsakanin ahalina Ya kuma sake had’ani da Fannah mun fahimci juna ta kuma yafe ni. Sann Ya nuna mun gudan jininka.. jikana. Ba abinda zance sai godiya. Hak’ik’a duk Wanda Ya dogara ga Allah toh Ya isar masa.” Ya kalleta tausayin ta da k’aunarta tab zuciyarsa. Sai Ya murmusa cikeda jin dadi yana mai danne k’uncinsa tareda ayyana farin cikinsa ganin mahaifiyarsa da yai cikin farin ciki. ** A b’angaren su Hajja kuwa bayan ficewar su Mommy sai itama tace tafiya zasuyi. Dama ta tsaya ne domin su gana da Kwaise kuma fahimci juna itada Kwaise sun yafi juna dan haka ba zama zatayi ba. "Hisham Ya dubi Daddy sai Ya sadda kai cikeda risinawa yana satan kallon Hajja ganin tana binsa da wani irin kallo tamkar kallon tuhuma ko kallon rashin yarda. Ya sadda kai sosai gaban Daddy yace “We.. will go ahead, Sir.!” Yai maganar kaman yanda yake kiransa a Office." Sai Daddy ya murmusa yace “No more Sir. It’s Daddy.. Ka kirani Daddy kaman yanda D’anuwanka Haidar ke kirana.” Murmushi Hisham yai yana kuma sadda kai “Ok.. Daddy.” "Daddy ya jinjina Kai kafin ya k’arada “Come here.” Ya k’arashe yana bud’e masa hannayensa alamun Ya taho su rungumi juna. Aiko Hisham Ya taho sukai hugging juna Daddy ya dan bigi kafad’arsa kad’an yace “Da kyau my Architect. Baka samu passion din naka a sama ba..It runs in our blood.. After all, your Dad is an Engr.”" Murmushi Hisham yai kafin ya kuma yima Daddy Sallama Ya dubi Hajja cikeda risinawa yace “Hajja.. Zan jira a waje.” Bata amsa shi ba sai kallon da ta bishi dashi. Hisham Ya fice yana mai shan jinin jikinsa dan yaga irin kallon da mahaifiyar tasa Tai masa. Daddy yai gyaran murya bayan ficewar Hisham. Ya d’an tako kad’an “Fannah.!” Ya ambaci sunanta da tausassar murya. Ta d’ago ta dubesa kad’an sai Tai saurin sadda idonta kad’an tana jin zuciyarta na harbawa. "“Thank you.! Na gode da kika yafe ma Kwaise. Na gode da kika yafe mun kika fahimceni.. Sann na gode da kika raini D’ana cikin aminci ya girma ya zama mutumin K’warai.. Nasan bai zama mai sauki a gareki ba. Amma dukda haka kinyi iyaka kokarinki wajen ganin kin basa tarbiya kuma kin providing masa.. Ina nufin duk wasu d’awanniya da Ya kamata ace nauyi ne na mahaifi.. cinsa shansa, lafiyarsa.. Karatunsa da sauransu.. Na gode.”" Ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an “Ka daina min godiya.. Haka ne Ya kamata… Idan ba damuwa ni zan wuce.. Ina so na biya asibiti na duba Ummukhair.” Daddy ya jinjina Kai “Ok.. Is alright..” Ya fad’i yana dan jinjina Kai. Tana shirin mik’ewa yai saurin mik’ewa daga kujeran da yake kai yace “Can I..” Sai ya d’anyi shiru kaman wanda ya tuna wani abu sai kuma ya k’arada “I mean.. see you out.?” Sai ta girgiza kai kad’an “A’a karka damu.. I can walk myself to the door.” Ya jinjina kai kad’an. Har ta fara tafiya Ya kuma dakatar da ita. Ta lumshe ido a hankali kafin Tai k’ok’arin juyowa. Daddy yai gyaran murya cikin k’ok’arin had’o kalamansa. “Em nace ba.. Idan bazaki damu ba ina so na tafi tareda Hisham.” Sai ta murmusa kad’an “He’s a grown Man now.. Kuma Abuja wajen aikinsa ne..” Daddy ya katseta “Eh haka ne.. Amma ina so Ya zauna tareda mu a can gidana wann karon.. So that.. I can get know my Son better..” Ta jinjina masa kai kad’an “Duk yanda kai daidai ne. Kaman yanda kace.. he’s your son.” Tai saurin k’arawa da “Ni zan wuce. Allah bamu alkhairi..” Bata jira amsarsa ba tasa kai cikin sauri. Daddy ya sauk’e deep breath had’ida zama cikin kujera. A waje ta iske Hisham jikin mota. Yana ganin isowarta yai saurin nufan k’ofan motar da zummar bud’e mata. Sai yaga bata shige motar ba ta kafesa da ido sosai. Wane irin kallo da idon da zai iya cewa bai tab’a gani daga gareta ba tin tasowarsa. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *57* *©️Sameena Aleeyou… * Ganin bata shige motar ba yasa jikin Hisham macewa sosai. Cikeda kulawa yace “Hajja ta akwai wani abu ne..? Kodai Daddy ne ya sanar dake wani abu.?” “Akwai abinda ya kamata ya sanar Dani ne.?” Ta tambaya a dake tana dubansa. Sai ya dan sadda idonsa kad’an “A’a… Kawai dai.. Just asking..” “Hisham.” Ta ambaci sunansa a tsare. “Na’am Hajjata.” Ya amsa cikeda kulawa. “Meyasa ka b’oye mana komai idan Har abubuwan da kake fad’a gaskiya ne..? Meyasa ni baka sanar Dani ba..? Anya akwai wani abu mai kama da coincidence cikin labaranka.?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido sosai. Sai ta murmusa yana girgiza kai “Hajja ke kika raineni.. Kuma kinsan ni wane irin mutum ne.. Hajja zafin kishi ne kawai ke d’awainiya da Haidar.. Kuma zan tabbatar masa I’m not after his family.. Hajja ki yarda Dani nayi komai ne sabida Haidar.. Yeah quite alright naso Ummul a baya kema shaida ce Hajja.. Kuma da ace tun a lokacin da na riski labarin Auren Ummul kin sanar Dani asalina da ba wann labarin muke a yanzu ba. Hajja b’oye min da kikai Shiyasa Allah Ya hadani da Haidar D’anuwana Har na hadu da ahalina da kuma mahaifina.. You should never have kept this from me Hajjah.. As they say no secret remain hidden forever..” Jikin Hajja yai sanyi sai ta fara tuhumar kanta tana jin da gaske itace mai laifi da taita k’ok’arin b’oye masa. Hisham na hankalce da ita yaci gaba “I don’t know who’s the real victim here.. Ni ne victim d’in.. Ko kuma D’anuwana Wanda muka Gina abota mai tsafta tare.?” Yai murmushi mai ban tausayi kafin yaci gaba “We were so closed Hajja.. We looked up to each other like brothers ba tareda munsan cewa Mu d’in ‘yanuwan juna bane.. Ashe shak’uwarmu da abotan mu ba daga sama Ya samo asali ba Ashe jini ne.. Amma a halin yanzu Haidar baida babban mak’iyi sama Dani.. Banida zab’i da Ya wuce na wanke kaina daga duk wani zargi..” Ta d’anyi Jim tana dubansa sai tace cikin sanyin jiki “Amma.. Amma kayi wani furuci da Ya bani tsoro da mamaki a ranar da Ummul zata haihu.. Naji da kunnuwan kana cewa baka damu ba koda za’a rasa jaririn matuk’a Ummul zata zama safe.. Kalamai be da ban tab’a jin makamancin su daga gareka ba.” Sai Ya dan jinjina Kansa a hankali “K’warai nayi wann furucin.. Watak’ila cikin dimauta da ganin irin yanayin da Ummul ke ciki.. Ya kamata ki min uziri a nan.. Sabida zuciya batada k’ashi.. Kar ki mance irin soyayyar da nai ma Ummul.. A lokacin da take yunk’urin haihuwa tsakanin rayuwa da mutuwa take.. Hajja ko kece aka baki zab’i tsakanin Ummul da jaririn dake kokawan fitowa nasan Ummul zaki zaba ba jaririn ba..!” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Hajja kema zargina kike kaman Haidar..? Na kasa yarda Hajja.. You raised me yourself.. Kinsan komai akaina.. Ni din tarbiyarki ne kuma rainonki.. Ta Ya Daddy da muka hadu yau d’aya tak zai yarda dani amma mahaifiyar da ta raineni ta kasa yarda dani.?” Furzar da huci kad’an Tai tana kauda fuska gefe. Ta soma girgiza kai “Ban sani ba Hisham.. Ban sani ba ko na tauyeka ta wani waje.. Ban sani ba.. Ko dai nayi kuskure da na zab’i nisantaka da mahaifinka..!” Sosai muryarta ke rawa sanda take maganan. “Ban sani ba kodai na gaza.. Ban sani ba Kodai wani abu daban na raina..!” Ta k’arashe muryarta na rawa irin na mai kuka. Zuciyar Hisham yai wani irin tsinkewa. Hawayen da ya gani na fitowa daga idon mahaifyarsa Ya haifar masa da shiga tashin hankali. A duniyarsa ba abinda baya so kaman b’acin ran mahaifiyarsa. Zaiyi komai sabida ita. Hasalima duk wani fansa da Ya jima yana dauka sabida ita ne sabida soyayyar da yake mata ne Har saida Ummul ta shigo cikin picture d’in. Saurin k’arasawa yai ya rungumeta “Hajja ki daina kukan nan.. Baki san hawayenki sunfi komai tsada a Duniyar nan ba. I’ll set whole world on fire just for your tears.. Dan Allah Ki daina kuka Hajjata..” Ta d’ago tana dubansa shima ita yake duba. Ya kamo hannayenta “Na Miki alk’awari zan wanke kaina Hajja.. Kuma ki yarda dani dan halak kika raina. Zan fito da evidence da zasu tabbatar da iyakacin gaskiyata.” Ya k’arashe yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa. Daga nan bud’e mata marfin mota yai ya taimaka mata ta shige kafin suka d’auki hanyar Asibiti. ** Suna isa asibiti suka iske ana shirin sallamar su Ummul. Hajja ta mak’ale Ummul cikin jikinta tana fad’in “Ki yafeni ‘Yata na tafi na barki a lokacin da bai kamata na tafi na barki ke kad’ai ba.” Ummul ta murmusa “Nasan babban al’amari ne zaisa ki tafi ki barni. Na gode ma Allah da yasa kuka kasance cikin k’oshin lafiya.” Hajja ta kuma rungumeta tana amsar jaririn. Duk wann abin gaban su Mommy ke faruwa. Sai mamaki suke suna fad’in ashe Ummul ce zatai sanadin sake had’uwarsu. Mommy ta kuma kamo hannayen Ummul tace Lallai ta cancanci sunanta Uwar Alkhairi kuma element of Union. Gashi dai duk dad’ewa da sukai suka shafe shekara da shekaru suna neman Hajja basu sameta ba sai ta dalilin Ummul. Tabbas ita d’in alkhairi ce ga ahalinsu. Nan Su Mama Tani suke ta mamakin al’amarin harma da Ummul d’in musamman da sukaji cewa Haidar da Hisham ‘yanuwan juna ne da suka had’a uba d’aya. Mama Tani tace ashe abin duk ahali ne. Mommy ta karada “What a small world.” Addu’a sukai gaba d’aya kafin suka d’unguma suka fito dan tuni an sallamesu. Hajja Fannah ta rok’i alfarma a bar Ummul ta kwana d’aya can gidanta idan yaso washe gari sai su d’auki hanyar kano tinda ga almuru Ya sako kai ga kuma jariri danyen haihuwa. Bai kamata su d’au hanya cikin dare ba. Mommy tace eh gaskiya ne hakan yayi Mama Tani ma duk sunyi na’am da shawarin idan ka dauke Haidar Wanda sam ba hakan yaso ba musamman idan Ya tuna cewa gidan mahaifiyar Hisham Khairy and his Son zasu. Aka zo shiga Mota Hajja na rik’eda Ummul suka nufi motar Hisham yayinda Mommy ke rik’eda jaririn. Ga kuma Haidar Ya k’araso da bak’ar Land Cruiser din da Sadis ke ja tin zuwansu garin. A daidai gefen motar Hisham Haidar yai parking. Ga Ummul tsaye tsakiya hannunta cikin na Hajja. Mommy na daga bayansu rungume da jaririn. Ummul ta kalli motar Hisham da tin fitowarsu ke jiran karasowarsu ta kuma dubi Motar Haidar da k’arasowarsa wajen kenan. Sai kawai tasa kai ta nufi motar Hisham. Daga nan cikin mota Hisham da Haidar ke aika ma juna kallo ta tsakankanin glass. Sai Hisham Ya sakar ma Haidar sihirtaccen murmushi alamun shi Ummul ta zab’a tinda gashi ta nufo motarsa. Idanun Haidar suka kad’a sosai sanda yake duban Hisham. "Mommy ta waiga ta dubi Haidar, ta kuma dubi Ummul da tuni ta nufi motar Hisham. Sai ta dubi jaririn dake cikin hannunta. Ta kuma duban Haidar. Sai taji tausayin D’an nata sosai. Kawai sai ta nufi motar Haidar da jaririn." Har ta isa jikin motar Hisham sai ta waigo ta dubi Mommy wacce tuni ta nufi motar Haidar. Tausayin Mommy ne taji sosai cikin zuciyarta. Ta dubi Hajja tace “Kiyi hak’uri Hajja.. Zan taho tareda Mommy.” Hajja ta murmusa had’ida jinjina mata kai “Ba komai ‘Yata Allah hadamu a gida lafiya.. Je ki taho tareda Mommyn ki.” Ummul ta jinjina mata kai kafin ta nufi motar Haidar zuciyarta na tsinkewa. Hisham Ya had’iyi abinda ya tsaya masa a mak’oshi. Ummul tana isa jikin motar Asshe taceda Azeema ta shigo su zauna tare. Aiko kaman jira Azeema take ta shige bayan motar ta zauna tsakiyar Asshe da Mommy. Sai wage baki take yau gata zaune tsakiyar gogaggun mata wayayyu yan boko. Ba yanda Ummul ta iya dole ta shige front Seat gefen Haidar. Su Mama Tani dasu Badia harma da Khulsum suka shige motar Hisham tareda Hajja gaba d’aya suka dunguma suka nufi gidan Hajja dake nan cikin garin Bauchi. "Koda suka iso gidan, su Mommy na ficewa kafin Ummul Tai wani aune tana k’ok’arin ficewa saiji Tai Haidar ya locking motar." Ta lumshe idonta kad’an had’ida sauk’e ajiyan zuciya. Ba tareda ta dubesa ba tace “Ka bud’e min mota na fice.” "Shima a dake yace “And who’s holding you.? Go ahead.. get out.. After all, bani na kawoki cikin motar ba.”" A kufule ta juyo tana dubansa da mamaki “Karma kai tunanin wani abu daban. Sabida Mommy kawai na shigo motar nan.!” Murmushi yai da gefen baki “Really.. Sabida Mommy.? Toh Mommy ta fice kema sai ki fice.” Kaman zatai kuka take dubansa “Wai mai keke nema wajena..?!” A fusace ya matso da fuskarsa dab kusan nata “You..! Ke nake nema Khairy..! You and my Son.!” Muryarta ya soma rawa tana girgiza kai “Duk abinda ka mun bai isheka ba.? Kayi AUREN WATA UKU dani.. Kuma ka cika Wa’adin Auren kuma..” Bata kai aya ba ya katseta “Kar ki sake nanata min wann kalmar. AUREN WATA UKU.!” Tai murmushi da yafi kama da murmushin takaici. Sai ta d’ago hulan sanyin jaririn dake rike cikin hannunta “Kaga wann shi zai dinga tuna maka da kalmar AUREN WATA UKU..!” Ta k’arashe tana kuma fincikan marfin motar. Har lokacin motar a rufe take ta kuma juyowa a kufule. Sai ta sassauta murya tace “Dan Allah ka bud’e min na fice.. Please..!” Tai maganar kamar mai shirin kuka. Har lokacin muryarsa a dake “Khairy.. Look up.. Look here.. Look into my eyes and tell me you don’t love me.. Ki kalli cikin idona ki fad’a mun baki sona..!” Kasa d’agowa tai ta kallesa saima shesshek’ar kukanta da Ya soma jiyowa. "Haidar ya sassauta murya wann karon “You can’t.. Bazaki iya ba.. Because you too love me.! I know you do.! Stop punishing yourself.. Stop punishing me.. Stop torturing our love.. Stop being stubborn Khairy..! Look, Our life will be good as it was.. I promise you.! Those days.. Those beautiful days kin tuna..?! Ya k’arashe cikin sigan rad’a sihirtaccen murmushi saman fuskarsa." Katsesa ta da fad’in “Dan Allah ka bud’e min na fice.. Na rok’eka.” Ta k’arashe tana had’e hannayenta biyu alamun rok’o hawaye naci gaba da gangaro mata. Hisham na daga gefe yaga fitowar kowa daga cikin motar amma baiga ta fito ba. Duk ya damu. Sai tambayar kansa yake cikin zuciyarsa uban mai Haidar yake mata da zai kulleta cikin mota Ya hanata fita. Yana tsaka da tunanin yaga ta fito ta nufi cikin gidan tana matsan hawaye. Yabi bayanta da kallo Har ta shige kafin Ya maida dubansa ga Haidar da fitowarsa kenan shima daga motar. Hisham Ya nufosa yana tambayar mai Ya ma Ummulkhair. Dubansa Haidar yake without saying a word sanda Ya jingina jikin mota had’ida folding hannayensa saman k’irjinsa. "Hisham Ya dan furzar da huci ganin irin duban da Haidar d’in ke masa. Sai Ya sassauta murya ya soma fad’in “Look Haidar, don’t think otherwise… Ummulkhair kaman k’anwa take a wajena.. Kasan yanda big brothers suke.. So protective.! Ka kira hakan da kulawa na Babban Yaya.” Ya k’arashe yana daga masa gira d’aya." Har lokacin Haidar bai daina dubansa ba. Ga mamakin Hisham murmushi yaga Haidar ya sakar masa. “You are a coward.! Wanda yake aikata laifi sann Ya b’uya a bayan mace. Ta Ya zaka daura nauyin zunubanka akan Anisa. What kind of a coward are you.?!” Ya k’arashe cikin k’unan rai. Hisham ya murmusa kad’an “You know what your problem is.. You are being jealous for no reason.. Bazan tilasta maka ka yarda dani ba.. Amma na maka akawari zan wanke kaina.. Dear Brother.!” Sosai wann karon Haidar ke huci Ya matso da fuskar sa dab kusan na Hisham “You can fool them all you want.. But you can’t fool me. Zan kama ka a cikin hannuna Hisham ka yarda dani.!” Hisham Ya dan lumshe ido “Haidar…” Dakatar dashi Haidar yai “You might be my father’s Son.. But you will never.. Never be my Brother..!” Yaci gaba da jinjina Kai still yana duban Hisham d’in “And let me make this clear to you.. You will stay the hell away from Khairy and my Son..!” Bai tsaya sauraron amsar Hisham ba yasa kai ya shige. Hisham yabi bayansa da kallo muguwar murmushin nan saman fuskarsa. ** "Koda suka isa gidan sallah sukai kafin suka hadu gaba d’aya tsakar gida gwanin ban sha’awa sai hira ake kowa Ya yafi kowa an zauna inuwa guda. Mai yafi yafiya da zama lafiya dadi a duniya. Gaba d’aya ‘Yanmatan kitchen suka shige sanda sukaga Hajja ta mik’e zata daura girki. Nan suka karbe ragamar girkin daga hannun Hajja sukace ta huta zasuyi komai.Azeema, Badia harma da Khulsum idan ka d’auke Ummul mai jego dake daga d’aki." Aunty Asshe ce ke tsaye daga k’ofan tana duban ‘Yanmatan yanda suke ta k’ok’arin daura girkin sai raha suke tsakanin junansu suna tuno lokutan k’uruciya sanda suke kwaba girki a gida. Sai Tai tsaye tana dubansu tunanin nata ‘yar dake tsare ofishin yansanda Ya fad’o mata. Tasa bayan hannu ta goge hawayen. Jiki a sanyaye ta shige wajen Mommy da Mama Tani yanda Mama Tani d’in ta cikata da labarai na barkwanci. Wayar Mommy na parlor saman kujera yayinda suketa fira saman darduma a veranda. Daddy sai kiran Wayar yake Mommy kam bama ta sani ba tana can Tani ta cikata da hira. Hajja ce ta fito daga d’aki wajen Ummul nan ta hangi wayar sai ruri. Taje da zummar dauka ta kai mata wayar nan taga mijinta ke kira wato Daddy. Zuciyarta yai wani irin yankewa..Sai tai saurin matsawa da baya. Saima ta fice daga parlorn cikin sauri ba tareda ta tab’a wayar ba sabida zuciyarta da Ya tsananta bugu. Koda Daddy bai samu wayar Mommy ba sai ya kira na Haidar dake tareda Sadis daga waje saman wani d’an dakali. Nan Daddy ya buk’aci ya hadasa da mahaifiyarsa idan suna tare. Haidar ya mik’e Ya nufi cikin gidan yanda Ya taddasu gaba d’aya kasan rumfar dake tsakar gidan. Mama Tani da Ummul na daga ciki tana taimaka ma Ummul d’in da wanka. Jaririn kaw na rik’e cikin hannun Hajja shima an masa nasa wankan Mommy tana fad’in a kwantarsa cikin mosquito net d’insa. Hisham tsaye daga gefen Hajja yana kallon jaririn da murmushi saman fuskarsa lokaci guda yake tambayar “Hajja wai an masa suna kuwa..? Ya kamata dai na samu takwara.” Muryar Haidar suka sinkayo yana fad’in “Aliyu..!” Gaba d’aya suka juyo suna dubansa. Haidar yaci gaba daga nan yanda yake tsaye “Sunansa Aliyu..!” Gaba d’aya sai murna Ya kacame waje Ya dauka ana Allah Ya raya Aliyu. Another Aliyu in the Family.. Aliyu the 3rd. Hajja Fannah ta mik’a shi ma Mommy tana fad’in Allah Ya raya musu BABA ALI. Haidar Yaci gaba da takowa Har gaban Hisham da takaici Ya nuna k’arara a fuskarsa. Yayinda hankulan mutanen dake wajen Ya tafi ga murnan sunan Aliyu da aka sake sakawa cikin ahalin Haidar kaw yai tsaye gaban Hisham da tuni yayi mutuwar tsaye wajen like a loser. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Haidar hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa. Ya dan rank’wafo da Kansa saitin kunnen Hisham “He’s named after his Dad.. He will grow up like a Lion.. Just like his Dad.!” Hisham ya had’iyi abinda yai masa tsaye a mak’oshi yanaji kaman ya shak’o Haidar amma ba hali. Haidar yaci gaba “ I had a great Victory.. Like a Lion… I beat you Hisham.!” Yaci gaba da murmushi yana jinjina kai “I won.. You are the loser..” Ya gyara tsayuwarsa Ya tsaya k’yam gaban Hisham Har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Har ya juya zai soma tafiya sai kuma ya juyo yace “You should change your last name.. You must be eager to bear the name Aliyu Maitama.!” Ya k’arashe still da murmushi lokaci guda ya tsime had’ida sa kai ya bar wajen. Ai Hisham bai kuma k’ara Minti d’aya tsaye wajen ba ya fice a gaggauce zuciyarsa na masa d’aci. Ummul ma a sama taji wai Haidar yayi ma jaririnta suna ya kumayi ma Kansa takwara. Takaici ya cikata.. Sabida tsaban gadara ko sanar da ita bai ba yama kansa takwara. Tana Jin sai shelan sunan suke a tsakani bata ko bi takansu ba. Bayan Mommy da Haidar Sun keb’e nan yake sanar da ita Daddy nata nemanta a waya baya samunta. Mommy tace “Af aiko inaga na baro wayar can yanda nai sallah..” Aiko batai shiru ba Daddy ya sake kiran layin Haidar. “He’s calling again.” Haidar yace yana kokarin daga kiran. Ya sanar da Daddyn suna tare da Mommy sann Ya mik’a mata wayar yana mai bata privacy. Bayan sun gaisa Daddy ke tambayarta ina ta shiga yaketa nemanta duk a dame yake maganar. Murmushi Tai kafin tace yai hak’uri hira ce tai dad’i. Daddy yace “Ya kamata ki taho masauki haka nan.. Is getting late already.” Daidai lokacin Hajja Fannah ta taho da abincin da ta kawo ma Haidar sai ta aje gefen Mommy ganin ba Haidar wajen. Mommy ta dubi Hajja Fannah sai tace “Nidai idan ka min izini zan kwana nan gidan Fannah.” Cak Hajja Fannah ta dakata da abinda take sanda ta jiyo abinda Mommy tace. Bata ida mamaki ba saida ma taji Mommy ta saka wayar a speaker. Tana jin sanda Daddy ke fad’i daga d’aya b’angaren “Shikenan ni kuma sai ki barni gauro a nan.” Mommy ta murmusa kad’an “Toh ka k’ara mana kawai Engr… Kaga idan bani nan inada mataimakiya..” “Aw haka ma kika ce.. Shikenan zan k’ara amma sai idan kece kika samo min matar.” Mommy ta dan ware ido “Ina ka taba ji an nemo ma miji mata.?” Daddy ya murmusa daga d’aya b’angaren “Za’a fara akanki.. Na baki wuk’a da nama Kwaise ta.” Hajja Fannah da gaba d’aya ta gaza sukuni daga nan yanda take duk’e. K’afafunta Har rawa suke.. tana k’ok’arin mik’ewa taji Mommy ta kamo hannunta gam ta hanata barin wajen. Mommy ta d’ago ta dubeta bayan sun gama waya da Daddy. "“Fannah nasan nayi kasalandan ma rayuwarki.. Amma bakida gidan da Ya wuce gidan Aliyu Maitama. A baya nayi zaton cewa zamana ni kad’ai a gidan Aliyu Maitama shi zai kawo min dawamammiyar farin ciki Shiyasa nayi duk yanda zanyi naga na rabaku.. Ashe abun ba haka bane.. Sai gashi bayan tafiyarki na rayu ni kad’ai amma Babu farin cikin da naci buri.. Ba abinda yafi komai kawo farin ciki a rayuwar nan kamar ka tsarkake zuciyarka.. Ka zauna da kowa tsakani da Allah.. Shi kuma Allah sai Ya saka maka nutsuwa farin ciki,harma da kwanciyar hankali a zuciyarka..!” Ta kuma kamo hannayen Hajja Fannah “Kaman yanda na zamto silan raba Aurenki da mijina a baya ina so ki bani dama na zamto silar maida Aurenku a yanzu.!”" Hajja ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Mommy yayinda Mommy taci gaba da jinjina Kai murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta “Na san bazaki ce a’a ba dan mijina d’aya ne tamkar da dubu. Ki yarda Dani.. Ina son mijina.. Ina matuk’ar k’aunarsa… This is the hardest decision of my life.. Amma bazan ja da hukuncin Ubangiji ba. Ina rok’on Allah Ya had’e kawunan ‘yayanmu Ya bamu ikon kyautata ma juna tareda yima mijinmu biyayya.” Sai suka rungume juna kukan Hajja Fannah na k’aruwa. Asshe dake kallonsu daga nesa murmushi Tai tana mai goge hawayen da Ya gangaro mata.. A cikin zuciyarta take cewa ina ma ita da nata Abokan zaman zu zamto haka. Bayan da Haidar Ya dawo wajen Mommy sai Tai masa tayin abincin da Hajja ta kawo masa. Tab’e baki yai kad’an had’ida girgiza kai “I’m good Mommy.” Ya kuma duban Mommy da kyau “Mommy nace are you sure this place will accomodate you all..?” Yai maganar yana daga ido yana duban gidan cikin wane irin yanayi. Mommy ta jinjina kai “Eh mana. K’warai kuwa.. Kaga dukanmu mata ne haka nan zamuyi squatting.” Da mamaki Haidar ke duban Mommy “Mommy keda kanki kike using word din squat.?!” Mommy ta kuma murmusawa tana duban gidan “Mamaki kake Hajiya Kwaise Maitama zata kwana cikin gidan da bai kai darajan d’akunan ma’aikatan ta ba..?” Ta kamo hannayen Haidar cikin nata “Haidar my Son. Shi dan adam bai gane cewa shi ba koman komai bane until life humbles us.. Mu d’auki rayuwa da sauki dan mu d’in daga turb’aya muke kuma cikinta zamu koma.” Haidar ya jinjina Kai a hankali “Haka ne Mommy..” sai karada “But Mommy.. Kinaga Khairy da Baby zasu iya kwana a nan..? I mean anyi yawa a gidan.. The place is too crowded.. Plus I don’t like the vibe here..” Mommy ta saki baki tana dubansa. Sai ta dunguri keyarsa wann karon “Rufe min baki ban son iyayi. Kai a dole kayi D’a ko.. Aiko dukanmu nan daka gani haka dai zamu kwana a nan har Allah ya wayi gari da izininsa. Naga ta yanda zakai kinibibin idan ka bud’e ido ka ganka Abuja Baba Ali na wajen uwarsa a Kano.” Ya dan furzar da huci kad’an “Mommy ni fah.. Gaskiya bazan iya komawa Abuja ba tareda an maida Aurenmu da Khairy ba..” Shiru Mommy tai tana dubansa. Sai ta girgiza kai kad’an “Haidar ni a nawa shawarin. Da ka bar maganar maida Auren nan ba yanzu ba.. Ummul bata jima da haihuwa ba… Ga abubuwan da suka faru.. Ga iyayenta can gida da zataje ta fuskanta.. Give her some time to recover.. Sai ai komai cikin lumana.” Duban Mommy ya d’anyi fuskarsa duk a dame “But Mommy..” Ta katsesa “No buts Haidar.. This is the right thing to do.. Yanzu ma ni abinda nake so da kai ka kira can station din da Anisa ke tsare ka bada umarnin a saketa.. Kawo wann lokacin nasan ta gane kurenta.” Ya d’anyi jim yana duban Mommy. Sai Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa “Mommy kiyi hakuri.. ba wai bana so a saki Anisa bane.. It breaks my heart seeing Aunty Asshe like this.. Mommy akwai Wanda nake so na kama ne.. Kuma through Anisa kawai zan kama shi.. But I promise you da zaran bincike Ya kammala Anisa will be free.” Ta jinjina kai a hankali tana dubansa. Sallama yai ma Mommy kafin ya tashi ya fice ya nufi nasa masauk’in. ** Washe gari kaman yanda suka tsara sassafe Sadis ya kwashesu suka d’auki hanyar Kano. Tuni Daddy ma Ya tasa kan ‘ya’yansa Haidar da Hisham suka bi jirgi zuwa Abuja. A Cewar Daddy akwai gabatarwa na musamman da zaiyi a Company gameda ‘ya’yan nasa musamman Hisham Wanda daukacin ma’aikatan Kampanin suka sansa da ordinary employee a baya. A halin yanzu zai koma ne matsayin D’a ga mai jagorancin Kampanin. Ba yanda Haidar ya so sabida Daddy dole yabi umarnin mahaifin nasa ya tafi tareda su. * Umma na zaune tsakar gida taji Sallama Ya kacame ko ina. Ta mik’e cikeda farin ciki tana ganin masu shigowa. Mama Tani dasu Azeema ne suka soma shigowa.. Su Azeema dasu Khulsum suka haye jikin Umma suna fad’in sunyi kewarta. Umma ta dubesu jiki a mace ganin bataga Ummul tareda su ba. Cikin rawar murya take tambayarsu “Ina Ummulkhair..? ina ‘yaruwarku.?!” "Bata rufe baki ba ta hango Ummul na shigowa cikin matuk’ar sanyin jiki, kanta kife ga jariri sabon haihuwa nad’e cikin hannunta. Mommy da Aunty Asshe na biye da ita." Umma ta mik’e cikin matuk’ar sanyin jiki tana duban Ummul dake shigowa. Tuni Umma ta soma tafiya ta nufi Ummul. Tana k’arasowa gareta taja ta tsaya kukan da taketa k’ok’arin dannewa yana kuma fizgarta “ ‘Yata.. ‘Yata Ummulkhair..!” Sai Umma tai bursting cikin kuka yayinda Ummulkhair ma kuka ya kufce mata. Asshe ce ta amshe jaririn daga hannun Ummul wacce tuni ta zube k’asa gaban Umma tana kuka sosai. Sai Umma ma ta duk’a ta rungumeta ‘ya da uwan suka b’ige da kuka mai ban tausayi.. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *58* *©️Sameena Aleeyou… * Kan Ummul bisa cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro mata yayinda Umma ke ci gaba da Shafa kanta a hankali itama d’in hawaye ke gangaro mata. “Nayi kewarki… Nayi kewarki sosai Ummata.. Dan Allah Ki yafe mun..!” Umma taci gaba da Shafa kanta a hankali murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta “Baki na goma kenan kike neman gafara na Ummul.. Ni mahaifyarki ce kuma na yafeki tun kafin ki nemi yafiyata.. Babu abinda yake tsakanin ‘ya da uwa face yafiya da afuwa.!” Sai Ummul ta sake bursting cikin kuka mai tsuma zuciya. Daidai nan Mama Tani ta shigo da Baba Ali dake yan k’anan kuka tana sanar da Umma tafiyar su Hajiya Kwaise da Hajiya Asshe.. Umma ta amshi jaririn tana lallashinsa lokaci guda take ce da Ummul maza ta mik’e ta kintsa kanta ta kula da yaron kafin Abbanta ya shigo. Ummul ta d’ago ta dubi Umma tana goge ragowar hawayen dake fuskarta. Murya a sanyaye tace “Umma da gaske Abba ya samu lafiya Har ya fara fita kasuwa.?” Tai maganar tsantsan farin ciki na nunawa a fuskarta. Umma ta murmusa “K’warai kuwa. Abbanki ya samu lafiya.. Nan bada jimawa ba zai shigo da yardar Allah.” Sai Ummul ta mik’e jiki a sanyaye tana tunanin yanda had’uwarsu da mahaifin nata zai kasance. Wanka sukai ita da jaririnta dan tuni Mama Tani ta d’aura ruwa bisa murhu tin isowarsu. Yaron Ya samu bacci da yaji ruwan d’umi. Umma ta saka yaron gaba tana kallonsa sassanyar murmushi saman fuskarta. Yau ga D’an Ummul dinta nan tana gani za kuma ta sab’asa a baya ta goya da izinin Allah. A haka Mama Tani ta shigo ta taddata. Su duka biyun suka tasa yaron gaba suna kallo. Mama Tani Tai saurin bud’e net d’insa tana k’ok’arin rufa masa Umma tace “Yaya naga dare baiyi ba da an kyalesa da gidan sauron nan tuk’uri ne dashi.” Mama Tani ta rufe gidan sauron ruf tana fad’in “Um um Suwaiba gwara dai mu killacesa jikan Manyan mutane ne wann.. Ina mai baki labari gobe zakiga Hajiya Kwaise sassafe gidan nan matuk’a tana garin nan.. Muddin taga alamun cizon sauro jikinsa na tabbata bazata bari ya kuma kwana gidan nan ba.” Ta gyara zama tana kame hab’a “Umm Suwaiba am.! mu muka sha kallo yanda ake taltala yaron nan da kyar Ubansa Ya amince a taho dashi nan.” Ta k’arashe tana gyara zaman net d’in sosai. Umma ta murmusa tana girgiza kai kad’an. Sai suka dubi juna itada Mama Tani sanda suka hangi ‘ya’yansu ras zaune daga parlorn Umman. Mama Tani ta girgiza kai tace “Wato Al’amarin Allah sai a bar masa kayansa Suwaiba. Duk Wanda yace zai shishigi ko k’atsalandan a hurumin Ubangiji toh fah Tabbas sai Allah Ya nuna masa iyakarsa. Yanzu dai ki duba kiga yaran nan yanda muka ci musu burin zaman gidan miji gasu nan ras a gabanmu yanzu. Ba wai basu je gidan mijin ba sunje amma sai Allah Ya dawo mana dasu gabanmu dan mu hankalta mu kuma dauki darasi. sabida a lokacin da mukaci musu burin zama gidajen mazajensu bamu nemi zab’in Allah ba sann mun zata iyawan mu shi zaisa su samu mazajen aure kuma su natsu a gidajen Aurensu. Ashe ba iyawan mu bane ba kuma wayonmu bane.” Umma ta jinjina Kai “Wann gaskiya ne Yaya. Allah yasa hakan ya zamto izna a garemu da masu hali irin Wanda mukayi a baya.” Mama Tani ta amsa da Ameen Suwaiba. A b’angaren Ummul kuwa sabon tashin hankali ta shiga dan tinda Abba ya dawo daga kasuwa yak’i ya dubi koda yanda take balle ya amsa gaisuwarta. Ko jaririnta bai kalla ba balle ya amshe sa. Tai kwance lamo saman cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro mata “Umma Abba yak’i ya min magana. Yak’i amsa gaisuwata.. Yak’i ya dubi jaririna.. Umma Abba bazai tab’a yafe min ba..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya. Saurin toshe bakinta Umma tai “Kul Ummul. Kar ki sake magana irin haka..Kiyi ma Abbanki uzuri dan tinda ya farka daga jinyar nan nasa al’amarinsa sai a hankali. Musamman idan ya hau dokin fushi. Masana sun alak’anta hakan da magunguna masu k’arfi da yake sha ga kuma ya hadu da girma. Ki basa lokaci a hankali zai sauk’o ya huce kinji koh. Maza tashi ki daina kukan nan haka.. Kici abinci ki sha ruwan d’umi kafin Babban mutum ya tashi a nasa barcin.” Ummul ta mik’e zaune tana goge hawayenta tana tunanin irin soyayya da shak’uwar dake taakaninta da mahaifinta yau an wayi gari itace Abba take gaishesa ya juya mata baya ba tareda ya dubi koda yanda take ba balle ya amsa gaisuwarta. Jiki a matuk’ar sanyaye ta nufi band’aki nan cikin d’akin Ummanta. Dan a gyaren gyaren da Haidar yasa akai ma gidan harda band’aki akai masu gaba d’aya kowa cikin d’aki aka kuma kawata ginin gidan kaman ba shi ba. Zama tai ta saka abincin gaba ba tareda taci ba. A haka Umma ta shigo d’akin ta taddata zaune saman pillow kaman yanda ta shirya mata wajen zaman. Umma ta soma da lallashi amma Sam Ummul bata iya cin abincin ba har dai Umma ta dan soma mata fad’a maimakon taci abincin kawai sai ta b’ige da kuka. Ta kasa yarda wai ita Ummulkhair d’in Abbanta Abba ke fushi da ita irin haka. A haka Khulsum ta shigo rik’e da waya tana fad’in “Adda Ummul ga Ya Haidar a waya yace a baki.” Ko sauraron Khulsum batai ba balle ta amshi wayar. Khulsum ta dan furzar da huci tace dashi “Tak’i ta amshi wayer.” Umma ta tsare sosai tace maza ta amshi wayar. Ba don taso ta amsa Umma da Khulsum suka fice suka barta rik’e da wayar ba tareda tace dashi komai ba. Mugun takaicinsa ne ya kuma taso mata. Ita gani take duk laifinsa ne Abba ke fushi da ita. Watak’ila da bai amince da Auren Wata Uku da yai da ita ba tun a fari da duk wad’ann abubuwan basu faru ba. Duka laifin na Haidar ne da ya amince zai AUREN WATA UKU da ita. Maganan duniya Haidar ya mata tak’i ta amsa. Yayi magiyar yayi lallab’in duk bata amsa shi ba har saida suka sinkayo kukan Baba Ali alamun ya tashi a bacci. Dan ta k’ara basa haushi sai kawai ta barshi yanata suararon kukan D’ansa cikin wayar. Har lokacin ba abinda tace sai kukan yaron dake k’aruwa. Zuciyar Haidar yaci gaba da masa zafi. Ya sani intentionally ta kyale yaron yana kuka dan yaji zafi. A zuciye yace “Khairy wai ina karatunki ya tafi ne.? Ta ya kike punishing k’aramin yaro for his Dad’s mistake.?!” Bata amsa shi ba har lokacin sai hawaye dake gangaro mata. Haidar ya jinjina Kai yana Jin zuciyarsa na masa zafi sosai “Fine Ummulkhair.!” For the first time da taji ya ambaci sunanta kai tsaye ba kaman yanda Ya saba fad’a ba. Haidar yaci gaba “Do as you wish.! Mommy tana nan cikin garin Kano bata dawo Abuja ba.. Zata zo ta d’aukar min D’ana zai iya rayuwa da baby formula.. Bazan bari tarihin abinda ya faru Dani ya maimaita Kansa Akan D’ana ba..!” D’if ya kashe wayar ba tarda ya kuma cewa komai ba. Aiko yana kashe wayar kaman ance nan ta b’ige da kuka sosai jaririn nayi itama tanayi a haka Umma ta shigo ta taddasu. ** Washe gari kaw su Mommy da Aunty Asshe suka zo duk a tunanin Ummul sunzo su tafi da Baba Ali ne kaman yanda Haidar yace. dan tayi zaton Haidar ya sanar da Mommy kaman yanda yace amma sai bataga hakan daga Mommy ba. Kayyaki ma taga ta kawo musu ita da jaririn da wasu abin buk’ata. Nan take sanar dasu washe gari zata bi jirgin safe ta tafi Abuja kafin ran suna. Umma sukaita mata godiya da san Barka. Mommy ta dubi Ummul dake zaune daga mazauninta kanta a k’asa. Ta murmusa tace “Toh Daughter ni zan wuce gobe in sha Allah. Na samu urgent call daga Daddynku. Duk dai bazai wuce magana akan yaransa ba ga kuma case din Anisa da ba’a warware ba har yanzu. Naso na tsaya ayi suna kafin na koma.. But still idan na samu dama zanzo ayi suna Dani idan kuma ban samu Aunty Asshe zata wakilceni in sha Allah.” Ta jinjina Kai a hankali ba tareda ta iya cewa komai ba. "Mommy ta kuma murmusawa tana duban jaririn dake baccinsa peacefully tace “Gameda batunku keda Haidar.. You have the final say here.. Kin cancanci hakan. Dan a baya an Miki dole. Idan aka sake Miki dole wann karon ba’a Miki adalci ba… He’s my son.. Ina son shi fiyeda komai a rayuwar nan.. Amma hakan ba yana nufin zan sake fifita shi sama da komai kaman yanda nayi a baya ba.” Mommy ta dan numfasa kafin taci gaba “ I couldn't manage to change him for years.. Amma cikin buwayan Ubangiji you came and changed him.. Ina nufin kece sanadi.” Mommy taci gaba da jinjina Kai tana duban Ummul “Ki sani, You are the most precious truth in his life.. But still zab’i naki ne Ummulkhair.. Bazan sake tilasta Miki kasancewa da D’ana ba kaman yanda nayi a baya.. Sabida ke d’in ma ‘ya ce a wajena.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Ta k’arasa ta sumbaci Baba Ali dake bacci kafin ta kuma yima Ummul Sallama. Har Mommy takai k’ofa Ummul ta mik’e cikin sauri tana duban Mommy. Ta ambaci Mommy a hankali." Mommy ta juyo tana dubanta. Sai Ummul ta isa da sauri bata san sanda ta fad’a jikin Mommy tana hawaye. Mommy ta rungumeta sosai tana bata baki tareda mata fatan alkhairi. A haka dai suka sake wani sallaman. Ummul ta kuma yarda kaunar dake tskaninta da Mommy daga Allah ne ba wai dan ta kasance mahaifiyar Haidar ba. Dan ita dai tin farkon haduwarsu tin kafin ta saka Haidar a idonta Allah ya jefa mata k’aunar matar.. Matar da tai defending dinta a gidan da babu kowa nata cikinsa gidan da mijin da taje domin sa ya gujeta. Koda ace Mommy da manufa ta nuna mata so a fari itakam bataji son da take ma Mommy ya ragu ba ko kadan. ** Abuja… Isowan Mommy gidan ta hangi sashen Haidar a bud’e ana fiddo da wasu kayayyaki. Mamaki ya cika Mommy. Ta dubi d’aya daga cikin ma’aikatan ta tambayesa lafiya meke faruwa meyasa suke fiddo da wasu kayayyakin. Kafin ma’aikacin ya bata amsa ta hangi Hisham ya fito daga sashen sai stretching hannayensa yake yana Ware su alamun duniya tana masa dad’i. Mommy ta zuba masa ido tana duban ikon Allah. Daidai nan Hisham ya k’araso yana mata sannu da zuwa. Bata iya amsa shi ba sabida mamaki da ya daure mata Kai. Can ta hangi Daddy na k’arasowa da murmushi saman fuskarsa. Ganin Daddy sai Hisham ya koma ga ma’aikatan yana ci gaba da nuna masu abubuwan da yake so da Wanda baya so a sashen. Daddy na mata sannu da sauk’a bata iya amsa shi ba sai nuni da tai da sashen Haidar cikin tsananin shock “Engr. Meke faruwa..? Ya naga ana fidda wasu kayayyakin Haidar daga sashensa.?” Sai Daddy ya murmusa “Banda abinki Kwaise Haidar kam ai yanzu bak’o ne a gidan nan.. Ko kin mance tin bayan bikin tariyarsa saidai yazo mana bak’unta..” “But still.. Sashen sa ne.. Akwai sections da yawa a gidan nan.. Meyasa na Haidar..?” Cewar Mommy har lokacin a shock take. "Murmushi Daddy ya kumayi “Haba Kwaise is just a section.. Ba wani abu bane dan D’anuwansa ya zab’i ya zauna a nan. Hisham da Kansa ya zab’i wann section d’in.. Ni kuma ganin yanzu Haidar ba mazaunin gidan nan bane yasa nace zai iya amfani da wann b’angaren. After all, nan ne ya kamace shi ba b’angaren bak’i ba.”" “Amma Engr.. Haidar ya sani.? Kasan yanda yake. Kasan yanda baya so ayi invading space d’insa ba tareda saninsa ba..” Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta yana fadin “Is ok Mommy..” Yai maganar kyakkyawar murmushi samar fuskarsa. Ta waigo tana dubansa murmushin ne saman fuskarsa. Yana k’arasowa ya bud’e mata hannaye alamun hug. Sai ta fad’a’da murmushinta suka rungume juna yana fad’in “welcome Mommy.. Ya hanya.. Ya kika baro Little Haidar.?” Daga Mommy har Daddy murmushi sukai Mommy tana fad’in ba ko kunya D’ansa kawai yake tambaya. Su duka ukun raha ne saman fuskokin su yayinda Mommy ta Ciro wayarta tana nuna musu hoton littile Haidar yanda Ya k’ara wayau. Daddy na fad’in dashi yake Kama ga hancinsa da sumarsa ya d’auka. Mommy na cewa hasken fatanta da manyan idanunta ya d’auka. Haidar ya saka iyayen nasa gaba yanda ko wanne yake fad’in jikan nasu dashi yake kama. Sai murmushi kurum Haidar yake. Hisham na tsaye daga gefe rik’eda hoton Haidar da Ummul Wanda aka musu ran bikin tariyar su ya fito dashi daga sashen Haidar d’in. zuciyarsa sai faman tafarfasa yake. Basu Ankara ba sai karan fashewan abu sukaji. Hisham ya saki hoton ya fad’i k’asa ya fashe. Suka juyo gaba d’aya suna duban Hisham Wanda tuni ya d’uka yana k’ok’arin tattare hoton yake fad’in Haidar yai hakuri bai sani bane. A garin k’ok’arinsa na tattare hoton glass ya yanka masa hannu. Daddy ya k’arasa da sauri ya rik’o hannun Hisham d’in yana duba yankan da yai. Hisham yana fad’in Daddy ya bari ba komai it’s nothing serious. Tuni Daddy ya rikosa ya nufi cikin gidan dashi yana fad’in “You are bleeding Son.. Are sure ba sai anje asibiti ba. Come We need to clean your wound.” Ya k’arashe suna nufan cikin gidan. Mommy da Haidar suka bi bayansu da kallo kafin Mommy ta kamo fuskar Haidar “Son..” Saurin girgiza mata Kai yai ya kamo hannayenta murmushi saman fuskarsa “I’m fine Mommy.. Don’t stress yourself..” Ya rik’o hannunta yana fadin “You just arrived.. Ki shiga ki huta..” Saida ya tabbata ya mata rakiya har cikin gidan kafin ya dawo yana duban hotonsu shida Khairy Wanda Hisham ya fasa. Duk’awa yai ya d’auki fasasshen hoton yana kallo. Daga bayansa ya sinkayo muryar Hisham “I’m sorry Haidar.. It wasn’t my intention to break your photo..” Sai yai aya har lokacin Haidar bai tankasa ba. "Hisham ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa “Koda yake dan na breaking hotonku bazai zama matsala ba.. After all, kayi breaking auren naku da kanka.”" Haidar ya had’iyi abinda ya tok’are masa mak’oshi. Ya mik’e tsaye ba tareda ya dubi Hisham ba. Yayinda Hisham yaci gaba da sakin muguwar murmushinsa silently dan ya tabbata ya tarwatsa Zuciyar Haidar da kalamansa kaman yanda ya tarwatsa hoton aurensu. Ga mamakin sa murmushi yaga Haidar ya sakar masa. Ya tako zuwa gaban Hisham d’in k’adan. Saida dak’ik’a ya gauta Haidar na duban Hisham na sakin murmushi kafin yace “You can do your worse Hisham. Amma bazaka tab’a iya raba tsakanina da Khairy ba.. Kasan dalili..?” Sai ya nuna masa fuskar wayarsa dan D’ansa ne Akan fuskar wayar. “Wann kawai ya isheka amsa. Kuma ka yarda dani.. Zan kawo k’arshen karyarka da fuska biyunka.. Sai nayi unmasking dinka.!” Yai maganar yana jinjina Kansa alamun tabbatar da kalamansa kafin yasa kai ya shige. Hisham ya bisa da kallo yana shafa hab’arsa muguwar murmushinsa saman fuskarsa. Washe gari da safe Haidar da ya fito cikin shirin fita Office kaman yanda Daddy ya buk’aci yaran nasa da su shirya da wuri sabida gabatarwa na musamman da zai musu a company nan ya iske iyayensa saman dining table. Ya k’araso ya gaishesu Mommy tace ya zauna suyi breakfast.. Ba musu Haidar ya zauna.. Zai soma serving Kansa Daddy yace ya jira D’anuwansa ya shigo. It would be rude a fara breakfast ba tareda an jirasa ba musamman da yake bak’o ne shi a gidan. Da mamaki Haidar ya dubi Daddy sai ya aje serving spoon din cikin sanyin jiki. Mommy ta dubi D’anta cikeda tausayawa tasan an fara kaisa mak’ura da al’amarin sabon D’an mahaifinsa. Hannunta ta d’aura saman nasa cikin k’ok’arin calming d’insa. Sai ya murmusa yana girgiza mata Kai alamun ba komai she shouldn’t worry. Time Haidar ya duba saman agogonsa dake daure hannunsa na hagu. Ya dan furzar da huci kad’an.. Yana tapping yatsunsa a hankali saman table d’in.. Ba jimawa gogan ya shigo cikin shirinsa tsaf irin shirin da bai tab’a irinsa a baya ba idan zai tafi office. Da ka gansa kaga D’an manya. Ga wata expensive suit da ya saka da wata tsadaddiyar cover shoe bak’a sai shining take. Ga k’amshin turaren TomFord dake tashi jikinsa. Irin dai turaren Haidar yau shi ya saka. Haidar ya kauda fuska gefe yana sakin murmushin takaici. Ba shakka wann banzan competing yake dashi a halin yanzu. Daddy ya mik’e da murmushi yana tarban D’ansa sanda Hisham d’in ya duka yana gaida Daddy cikeda ladabi. Daddy ya kamosa ya mik’arsa tsaye yana tambayarsa how was his night. Hisham ya amsa yana wani sadda Kai k’asa yawa mutumin arziki. Haidar ya kuma yin murmushin takaici yana kauda fuska. Hisham ya k’araso ya duk’a yana gaida Mommy.. Ta amsa masa da sakin fuska tana fad’in bismillah ya zauna suyi breakfast. Hisham ya zauna a kujera mai kallon na Haidar murmushi saman fuskarsa yake fad’in “Good morning bro… I hope I didn’t keep you waiting.?” Mik’ewa Haidar yai yana fad’in “I’ll.. Go ahead..” Mommy ta dakatar dashi “Haidar ka tsaya kaci abinci mana.. You can’t go to work with an empty stomach.” Haidar ya dan girgiza Kai “Kar ki damu Mommy zanci a Office.” Daddy yace “Koma ka zauna Haidar..” Ba don yaso ba ya komo wajen zamansa. Hisham ya murmusa yana duban Haidar sanda yake cakalan chips da fork “You shouldn’t be skipping your breakfast "Brother.. Because, they say breakfast is the most important meal of the day… Haka ne Daddy.?”" Daddy ya jinjina Kai da murmushi saman fuskarsa “K’warai haka ne. Gwara ka dinga fad’a ma wann D’auwan naka dan bai son abinci tuntuni.” Hisham ya murmusa yace “K’warai ni zan bada shaidan hakan.. Dan baida abokin da ya fini..” Banda murza fork and knife din dake hannunsa ba abinda Haidar keyi sabida takaicin da ya turnikesa. Bai tunanin zai iya hakurin zama waje d’aya da mayaudari irin Hisham. Washe gari ma Daddy yasa yaran nasa su shirya cikin manyan kaya wann karon. Cikin su biyun babu Wanda yasan nufin Daddy. Bai kuma sanar dasu ina suka nufa ba.. A haka dai suka d’auki hanyar Airport cikin shiga ta manyan kaya. Basu zarce ko ina ba sai birnin Maidguri yanda sukai rakiya wa mahaifin nasu ya amso aurensa da tsohuwar matarsa a karo na biyu. Saidai amarya bata biyosu Abuja ba ta buk’aci ango ya bari sai daga baya ta tare dan abubuwan komai ya faru ne cikin sauri. Ga dangi da bata gama zagawa ba. Taso Hisham Ya zauna nan Maiduguri tareda ita amma sai Daddy ya nuna yana buk’atan Hisham d’in can Abuja kusansa. Farin ciki wajen Hisham baya misaltuwa. Shidai Haidar bai um bai um um.. Sam baijin haushin matar amma yasan D’anta bak’in k’umurcin maciji ne. Snn koda suka dawo gida ya jaddada wa mahaifiyarsa tana tareda goyon bayansa duk abinda zai faru. Mommy ce ta kwantar masa hankali da fad’in babu abinda zai faru da izinin Allah sai alkhairi domin Auren da mahaifinsa yai ma zabinta ne. Bayan ficewar Haidar daga wajen Mommy Daddy ya shigo. Duban Mommy yai da murmushi saman fuskarsa. Zatai magana yai saurin daura d’an yatsarsa saman lips dinta. Yai gyaran murya kad’an sanda ya rik’o hannayenta cikin nasa “You don’t have to say a word Kwaise. Yau d’in ni zanyi maganar.” Murmushi ne saman fuskokinsu suna duban juna hannayensu cikin na juna. Daddy ya dan sassauta murya kafin yace “Do you know that.. you are the pillar of this family..” Murmushi Mommy tai had’ida girgiza Kai kad’an “Kai Engr.. Kar fah ka mance ni fah matar Engr ce so nasan matsayi da amfanin pillar a gini.. I might be the scaffolding that keeps the pillar upright.. But you are the pillar my Engr.” Daddy yai murmushi mai bayyana hakwara kad’an kafin yace “Lallai na yarda ke matar magini ce. Amma a wann ahalin you are both the scaffolding and the pillar Kwaise.. Behind every successful man is a woman. Do you think I'd be Aliyu Maitama that I am today if it weren't for you..?” Yaci gaba da murmushi yana dubanta “Hak’ik’a Allah Ya gama min duk wani gata da Ya bani mace ‘yar aljannah irinki. Thank you for everything Kwaise.. Allah ya miki albarka..” Ta sadda idonta kad’an tana mai amsawa da Ameen mijina. ** Washe gari sassafe a station ya musu. Idan kaga Anisa sai ta baka tausayi. Ta fice a hayyacinta ta shiga makarantar ta natsu. Ga mahaifinta yace ba ruwansa ya cire hannunsa akanta sann idan Asshe ma ta taka k’afa taje yanda Anisa take a bakin Aurenta. Asshe tanaji tana gani an mata farrak’u da ‘yarta kaman yanda tai ma Umma da ‘yarta Ummulkhair a baya. Tabbas sharri d’an aike ne. Duk yanda ka tura shi zai dawo gareka. Hisham dai Ya gama k’ulle Anisa cikin case din ko ta ina. Sam bai bar wani k’ofa da zargi zai hau kansa ba. K’arshe Daddy da Haidar suka buk’aci belin Anisa Daddy ya bada umarni da a rufe case din gaba d’aya .. Saidai ana tsaka da processing release papers d’in Anisa sukaji sauti daga bayansu na fad’in “Bada garaje ba. Babu yanda wann macuciyar zataje har sai ta biya kisan yar mu da tai.!” A tare Daddy da Haidar harma Hisham suka waigo suna duban mutanen da suka shigo station d’in. Daddy ya girgiza kai yana dubansu cikin rashin fahimta “Su waye ku.?” Mutumin yace “Mune iyayen Dareen da ‘yarku ta kashe.!” Sabon tashin hankali da ba’a saka masa rana. Ga dai iyayen Dareen Sun bayyana Sun kuma d’au alwashin sai an karb’ar ma ‘yarsu hakkin kasheta da akai wanda hakan ke nufin ba ranar fitar Anisa daga gidan kasu babu kuma ranar rufe case. Sann ba ranar yanke hukuncin shari’a har sai angano gawan Dareen. Anisa ta amsa laifin ta na cewa ita ta bige Dareen da mota sabida soyayyar da take ma Haidar dan ga shaida an samu a gidan Aliyu Maitama motar da Anisa tai amfani dashi ta bige Dareen. A halin yanzu case ake na kisan Dareen Wanda duk wani evidence yake pointing zuwa ga Anisa. Itace prime suspect. Ita keda babban dalilin kashe Dareen sabida son da take ma Haidar kaman yanda ta tassama kashe Ummulkhair. Allah sarki Anisa dole ta baka tausayi dan ba wanda zai fiddata daga cikin wann masifa da take ciki sai Allah. Ta saduda ta koma ga Ubangiji. Shi kawai take ambata da ya kawo mata d’auki. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *59* *©️Sameena Aleeyou… * Safiyar ranar Alhamis Haidar ya fito cikin shirin fita Office. Can wajen motoci ya hangi Hisham na zab’en motar da zai d’ale. Saida ya hangi fitowar Haidar kafin yai murmushi ya isa jikin farar SUV da Haidar ke hawa time to time ya dafa motar yana duban Haidar murmushin nan nasa saman fuskarsa “How about this ride.. Baka tunanin zai dace Dani..? Dear brother..!” "Haidar baice dashi komai ba ya nufi motarsa. Har ya isa jikin motar ya d’ago yana duban Hisham da murmushi saman fuskarsa “Bazaka tab’a zama kaman Haidar Maitama ba, no matter how hard you try.. Kasan dalili..?” Ya tsare Hisham sosai da ido “You are nothing like me.!” Yana ida fad’in haka ya saki murmushi kad’an kafin ya juya zai shige motarsa. Sai kuma ya juyo kaman Wanda ya tuna wani abu. Ya dubi Hisham yace “Make sure you don’t" lose track of time.. You don’t want your Boss to arrive first before you.!” Ya k’arashe yana nuni da agogon dake daure hannunsa. Lokaci guda yasa kai ya shige mota yaja motar ya fice daga gidan. Takaici ya cika Hisham. Ya bigi tayar motar da k’afarsa guda tsanar Haidar na kuma ruruwa cikin zuciyarsa musamman idan ya tuna yana sama dashi wajen aiki. Da takaicin Haidar ya nufi Company. Yana tafe hanya Daddy ya kirasa ya sanar dashi ya zama in charge bazai Sami shigowa company ba ranar. Haba nan fah kan Hisham ya kuma fashewa yana jinsa sama da Haidar.. Alla alla yake ya isa Company ya nuna ma Haidar kasawarsa tinda gashi Daddy shi ya k’ira ya bar masa ragamar komai a hannunsa. Yau sai ya wulak’anta Haidar ya k’ask’antar dashi a company. Allah yasa ya Riga Haidar isa ya wulak’anta sa. Haidar kaw bai isa Company ba Daddy ya kirasa yace ya juyo zuwa gida. Ba musu ya dawo ya tadda mahaifin nasa. Farar shadda mai dankaran kyau da tsada Daddy ya basa yace ya sauya shiga zasu wani wajen. Ba musu Haidar ya amsa yai yanda Daddy yace duk a tunanin Haidar Maiduguri zasu sake komawa tinda bai jima ba sukaje suka amso auren Daddyn. Wann karon ma airport suka nufa saidai ga mamakin Haidar maimakon Maiduguri wann karon Garin Kano suka nufa. Suna isa Sadis ya isa ya d’aukosu. Shidai Haidar sai aika ma Sadis kallon tuhuma yake yayinda Sadis ke ta faman k’unshe dariyarsa dan shima Sadis d’in cikin shiga ta manyan kaya yake. Haidar bai ida Shan mamaki ba saida yaga Sadis ya dire su k’ofan gidan su Ummulkhair. Ga tsirarun mutane da basu shige a k’irga ba zaune k’ofar gidan. Can ya hangi mahaifinta yayi shiga ta manyan kaya shima. Kan Haidar ya kuma d’aurewar.. Toh kodai bikin radin sunan little Haidar ake bacin haka bai tunanin Abba zai barsa ya tako k’ofar gidansa balle har ya basa wajen zama. Haidar ya saci kallon Daddy da mamaki sai yaga Abba ya mik’e ya nufosu ya tarbi Daddy suna masabaha. A hankali Haidar ya janyo Sadis ya rage murya sosai yace “Now you tell me.. What is going on.?” Sadis ya murmusa “Baza’a ji a bakina ba Ango.” Haidar ya girgiza kai “Ango.?” Sadis yace “Kashh.! Ka jini da sub’utan baki.. Kaga gashi can Daddy na mana alama da hannu.. Mu k’arasa.” Jiki ba wani k’wari Haidar ya soma takowa da jagorancin Sadis dan gani yake kaman Abba zai fatattake sa kaman dai yanda ya saba. Ga mamakin Haidar baki har kunne Abba ke nuna masa wajen zama “Bismillah Aliyu.. Taho ka zauna.. Ga Imam din ya k’araso.” Haidar ya zauna bugun zuciyarsa na k’aruwa. Bai k’arasa Shan mamaki saida yaji da kunnuwansa Daddy na nemar masa da a sabunta aurensa da Ummulkhair. Abba yai na’am da batun a take Daddy ya fiddo sadaki ya bayar aka samu cika cikan aure. Sadaki siga da kuma shaidu nan take a sabunta Auren Haidar da Ummulkhair cikin abinda yai saura na wancan Auren. Tuni Sadis ya mik’e yana rabon goro da alawa. Tsananin shock ya hana Haidar furta koda kalma har saida Abba ya mik’a masa hannu sukai masabaha ya kuma tayasa murna sann ya jaddada masa amanar ‘yarsa Ummulkhair a karo na biyu. Daddy ya tabbatar masa in sha Allah zasu rik’e amana dan Ummulkhair ‘ya ce wajensa kaman Haidar. * Koda Abba ya shigo gida sai yasa aka masa kiran Ummulkhair. Kanta a k’asa ta k’araso ga Abba. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yai gyaran murya kad’an “Ummulkhair.” “Na’am Abba.” Ta furta a hankali. Abba yaci gaba “A yau na maida aurenki da mijinki Aliyu kaman yanda na Sami yarda da amincewar ki.. Ki sani ke ‘Yata ce banida burin da ya shige na ganki cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Burin ko wani mahaifi shine rayuwar yaransa ya inganta. In sha Allah zaki kasance cikin aminci kaman yanda kika kasance mai biyayya a garemu. Na jarabta mijinki ta hanyoyi da dama a lokacin da baki nan kuma Tabbas Aliyu yaci jarabawa dan na gamsu da hankalinsa tarbiyarsa dattakunsa da kuma irin k’aunar da yake Miki. Hak’ik’a bani tunanin akwai wani Wanda ya cancanci zama mijinki sama da Mahaifin D’anki. Allah ya muku albarka ya albarkaci zuri’arku ya kuma zaunar daku lafiya.” A hankali ta amsa da Ameen Abba. Abba ya jinjina Kai kafin yaci gaba “Gameda maganar tarwarki gidan mijinki mahaifiyarki ta buk’aci da an dan bada lokaci ki Sami k’arfin jikinki jariri Aliyu ma ya dan yi kwari. Tuni nayi magana da mahaifin mijin naki ya kuma samu mijinki da batun kuma an samu daidaiton fahimta. Ina fata hakan kema ya miki.” Ta kuma sadda kanta kad’an “Duk yanda kukayi daidai ne Abba.” Ya kuma murmusawa cikeda Jin dadin biyayyarta a garesa shi mata albarka ya kuma kafin ya sallameta. Cikin gida ya kacame da guda da murna. Ga murnar radin suna ga murnar sabon Aure. Murna ta ko ina sai son barka. Saidai Sam Amarya Ummulkhair bata bari Angonta ya sakata a idonsa ba har ya Kama hanyar Abuja a washe gari. Koda shima din bai nemi ya ganta ba. ** Isowarsu Abuja Kai tsaye company ya nufa dan yasan can zai Sami Hisham. Hisham sai cika yake yana batsewa. Haidar yanaji yana bada umarnin kar a bar kowa ya shigo ya damesa yanda kasan shine shugaban kampanin. Haidar bai tsaya sauraron kowa ba ya tura k’ofar ya shige. Idon Hisham naga computer din dake gabansa ba tareda ya dubi Wanda ya shigo na ya soma fad’a yana fad’in waye ya shigo masa office ba izinin sa. D’agowar da zai suka had’a ido da Haidar. "Murmushi Haidar ya sakar masa sai yace “Tuba nake Mr CEO, na shigo ba tareda izini ba.”" Murmushi Hisham d’in ma yai kafin ya nuna ma Haidar wajen zama “Welcome brother. Bismillah have a seat.” Haidar ya girgiza Kai kad’an “Ba zama nazo yi ba. But thanks anyway..Nazo ne na baka wann.!” Yai maganar yana saka hannu a aljihun sa. Sai ya Ciro goro da alawa na Aure. Tinda Hisham yaga haka zuciyarsa ke tsinkewa. Haidar ya aje masa goron da alawan saman table d’insa. "Hisham Ya girgiza Kai kad’an cikin rashin fahimta “What are.. we celebrating, Brother.?”" Har lokacin murmushi ne saman fuskar Haidar “Ka tayani murna. Jiya an maida aurena da matata UMULKHAIR.! Don’t you think is enough reason for us to celebrate.?” Kaman sauk’an aradu haka Hisham yaji batun. Ya saki baki da hanci cikin tsananin shock yana duban Haidar. Sai kuma Haidar ya janye alawan. Sosai Ya matso da fuskarsa kusan na Hisham. Ya rank’wafo suna duban juna cikin ido. Murya a dake yake furta “Goro shi ya kamaceka dan na tabbata kana jin d’aci a ranka fiyeda dacin goron nan. !” Ya sakar masa murmushi yana jefa candy din a bakinsa ya kashe ma Hisham ido guda sann yaci gaba “Enjoy the bitterness of those kola nuts.” Daga haka sa kai yai ya fice. Har lokacin Hisham bai dawo daidai ba. Ya kasa yarda da abinda yaji. Wai dama tafiyar da Haidar da Daddy sukai ba tafiya bace ta kasuwanci. Tafiya ce ta Auren Haidar d’in. Lallai ma Daddy yama raina masa hankali.. Shi yana nan yana k’ababa yana murnan Daddy ya fara sakar masa ragamar company Ashe munafuntarsa yai.. Ashe ya tafi ne dan ya karb’ar ma d’ansa Auren Ummul d’insa da yai komai dan ya tabbata ya rabasu da Haidar d’in. Yaci gaba da huci yana jinjina kai. A zuciyarsa yake furta ‘You don’t want to play fair Haidar.! Idan haka kake so.. I can play dirty as well.. Yanzu wasan zai fara kawai ka jira ka gani.’ Ya k’arashe zancen zucin nasa yana sakin huci idanunsa na kuma kad’awa. Sauri sauri ya fito daga Office d’in ya nufi elevator. Wata staff tai saurin dakatar dashi sanda zai shige elevator din “Em excuse me sir. That’s Mr Haidar’s private elevator.” Huci Hisham yake yana dubanta “Ke kinsan ni waye.? Kinsan da waye kike magana.?!” Yanda yake mata maganar cikin tsananin tsawatarwa ya janyo hankulan sauran mutanen. Hisham yaci gaba da huci yana furta “I am Hisham Maitama.! I own this company.. I can fire you right this instant if I want.!” Sai ta soma basa hakuri tana neman hanyar tsira. Yaci gaba da duban mutanen wajen kaman wani zararre “Sunana Hisham Aliyu Maitama. The Eldest Son of Engr Aliyu Maitama. Did you all get it.! Ni ne Hisham Maitama. Hisham Maitama.. Everything here is mine. I own this company.! Dukkanku ku saka wann a cikin kawunanku.!” Yana ida fad’in haka yasa Kai ya shige cikin k’unan rai. Shi d’ayansa yana driving yana buga steering wheel yana furta “Damn you.! Damn you Haidar.! Damn you..!” Waje ya nema yai parking yana maida huci. Sai k’ullawa da sak’awa yake yana neman ta yanda zai b’ullo ma al’amarin. Dan Alk’awari Ya dauka bazai taba saduda ba. A fili Ya futa “ANISA.!” Anisa dai ita kad’ai ce card d’in da zai sake amfani da ita. Kai tsaye motarsa ya shige ya nufi jail din da Anisa ke tsare. Sosai Anisa taji mamakin wai Hisham Ya kawo mata visit. Hisham Ya tsareta da ido yanda ta rame tai duhu duk ta fice hayyacinta kaman wann Anisa ‘yar gayu da Ya sani ba. Ta dan rausayar da ido had’ida furzar da huci. Wanda saida tai wann d’abi’ar nata ma Hisham Ya tabbata ita d’in ce. “Mai ya kawoka wajena.?” Ta tambaya tana dubansa. Hisham Ya murmusa “Alkhairi.!” Ta dan girgiza Kai kad’an “Kai har akwai wani alkhairi tattareda kai Hisham. Bayan duk abubuwan da ka mun. I’m in this situation because of you.” Hisham ya dakatar da ita “No Neesa. You are in this situation because of your stupidity. Kinga duk ba wann ba.. Idan Har kika amince da batun da nazo Miki dashi ki yarda dani you’ll be set free..” Tai murmushin takaici “Now I understand everything. Kai din ka jima da sanin Haidar d’an mahaifinka ne. Kaidin fansa kawai kake nema kan Haidar da Aunt dina Shiyasa kai amfani dani. Shiyasa ka b’oye min komai naka baka sanar Dani cikinka ba kaman yanda ni na sanar dakai nawa. Ashe amfani Dani kawai kake dan ka cimma burinka.” Taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Kayi amfani dani a karo na farko bazan bari ka sake amfani dani ba Hisham.. Dareen was right kaman yanda kai amfani da ita ka jefar da ita gashi nan Nima na faruwa akaina.. Ban tab’a ganin azzalumin mutum macuci irinka ba Hisham.. Kuma nayi alk’awari ma Haidar sai yanda k’arfina Ya k’are wajen bankado gaskiya da bayyana true color dinka. Bazaka sake samun dama akaina ba Hisham.!” Murmushi yai kad’an had’ida gyara zamansa “Neesa kenan. Kina magana kaman baki san wane irin serious crime ake tuhumar Ki dashi ba.. Tuhumarki ake da kisan kai Anisa. Bana jin akwai Wanda zai iya wankeki daga wann babban tuhuma da ake Miki koda kuwa Haidar ne.” Ya kuma gyara zama “You are alone in this Anisa. Ahalin ki Sun juya Miki baya.. Ina nufin mahaifinki da mahaifiyarki.. Sann Haidar da kika dogara dashi ki yarda dani yana yin komai ne to win Ummulkhair back.” Ya kuma karkacewa yana gyara zamansa “For your information Neesa.. An maida Auren Ummulkhairi da Haidar kinga kuwa Haidar baida sauran dalili da zaisa Ya taimaka Miki Ya cireki daga cikin wann tuggu.” Anisa ta saki baki da mamaki tana dubansa “An maida Auren Ummul da Haidar.?” Ya dan tab’e baki kad’an kafin Ya kuma gyara zamansa “Abu d’aya zai cireki daga wajen nan Anisa shine Ki amince zaki Aureni..!” Kaman sauk’ar aradu haka taji batun. Ta d’ago da mugun mamaki tana dubansa “Ni Aneesa kake cewa na Aureka.?!” Hisham ya murmusa “Ba don Ina sonki zan Aureki ba Anisa.. Sai don kawai ina so na taimaka Miki na cireki daga cikin wann k’ulli mai wuyan warwarewa da kike ciki.!” Girgiza kai Anisa take tana dubansa cikin shock “You have no shame Hisham.. You are a demon.! Baka da zuciya cikin k’irjinka.. Tir da D’anAdam irinka..! Ta nan ka b’ullo..? Toh ka sani ni Anisa bazan tab’a auren mutum irinka ba.. Never.!” Hisham ya mik’e yana gyara zaman suit d’insa “Think about my offer Neesa.. Wann shi kad’ai ne hanyar tsira da Ya rage Miki if you don’t want to rot in here.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *60* *©️Sameena Aleeyou… * A parlour Hisham ya iske Daddy after dinner. Mommy na zaune gefensa suna tattauna yanda auren Haidar ya kasance. Da yanda Daddy da Abba suka shammacesu gaba d’aya da al’amarin auren. Ya shigo da Sallama saman bakinsa. Suka amsa masa da sakin fuska Dddy yana masa iso da ya shigo ciki ya zauna. Can bakin carpet Hisham ya zauna had’ida risinawa kaman dai yanda yakeyi gaban Daddy a ko Yaushe. Daddy ya dubesa cikeda kulawa dan ya kula da yanayin D’an nasa kaman dai babban Al’amari ke tafe dashi koda bai furta ba. "“Son, lafiya dai koh..? Inji komai lafiya..?”" Hisham ya jinjina Kansa kad’an “Lafiya Daddy.. Dama..” Sai ya d’anyi fasali ba tareda yaci gaba ba. Mommy ta soma k’ok’arin mik’ewa tana fad’in “Bari dai na baku waje.” Hisham yai saurin dakatar da ita da fad’in “No Mommy.. You should also stay.. Please...” Mommy ta dan yi still sai tace “Shikenan ba damuwa.” Ta koma mazauninta. Hisham ya dan gyara zamansa kad’an sanda Daddy yace “Muna sauraronka.” “Daddy dama.. Ina so na nemi Auren Anisa ne idan babu damuwa. Idan hakan ya muku.. Ina nufin both you and Mommy.” Da mamaki Daddy da Mommy suka dubi juna. Mommy ta girgiza Kai kad’an “Wace Anisar.? Kana nufin Anisa my niece.?” Hisham ya jinjina Kai kad’an “Eh Mommy.. Idan har babu wani damuwa.” Daddy ya katsesa da fad’in “Ka kuwa san mai kake fad’a Hisham.. Auren Anisa fah kace. Anisa dake facing court case.?” Hisham ya jinjina Kansa cikeda risinawa “Eh Daddy.. Kasancewar akwai court case akanta bazai hana Aurenmu ba. In fact wann shine dalilin da yasa na yanke hukuncin neman Aurenta. Dan na fitar da ita daga cikin situation d’in da ta tsinci kanta ciki Wanda ba komai bane face jarabawa daga Ubangiji.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Daddy Anisa tayi kuskure amma ta fahimci kuskuren ta kuma ta gyara.. Dukanmu munga yanda tai repenting bayan ta fahimci kuskurenta.. We shouldn’t abandon her.. Ina nufin dukanmu munyi kuskure a baya.. Kuma mun yafi juna. Bai kamata mu kyale Anisa ita kad’ai cikin wann ba. Daddy ni zan Auri Anisa matuk’a hakan yayi muku.” Muryar Haidar suka sinkaya Wanda shigowarsa parlorn kenan yana fad’in “Did I hear that right.? Zaka nemi Auren Anisa.?” Yai tambayar cikin tsananin shock yana duban Hisham d’in. Hisham ya murmusa had’ida jinjina Kai yana duban Haidar d’in “Eh Haidar.. You heard that right.. Ina so zan Auri cousin d’inka Anisa… I hope kaima na Sami goyon bayanka D’anuwa.” Murmushin takaici ne ya kufce ma Haidar “You are unbelievable.! You really have no shame.! Ta nan ka b’ullo..? Zaka auri Anisa..Just what are you up to this time around.? Mai kake shiryawa Hisham.?!” Daddy ya dakatar da Haidar “Haidar ya isa haka.. Kar ka fara.” Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy “Daddy don’t tell me har yanzu baka gane wann makaryaci mai fuska biyun ba..! Daddy I’m sure idan ya shirya Auren Anisa wata manufa yake dashi amma ba don yana son Anisa ko yana so ya fiddata daga situation da take ciki ba Wanda shi ya jefata.. Daddy this monster here only think of himself.. If he says he wants to marry Anisa that’s because yanada wata manufa da yake so ya cimma.! I’m very sure he’s up to no good.!” “Enough Haidar.!” Daddy ya dakatar dashi kafin yaci gaba “Kai a rayuwa ba’a yafiya aka yafe maka.? Meyasa kullum kakeda negative thought Akan D’anuwanka Wanda ba abinda yai maka face alkhairi..! Ka fad’a mun abu d’aya da yayi na cutar dakai..! Idan aka Ummulkhair ne ya maka bayani ya kuma janye idon shi Akan iyalinka a lokacin da ya fahimci Kai take aure. Sann na d’auka an rufe wann babin a jiya da aka maida aurenka da iyalinka.! Yanzu yazo da batun yana Neman Auren Anisa kace ba haka ba.! Toh mai kake so yayi Haidar.? Ka sanar Dani mai kake so ya aikata kuma.!” "Shiru Haidar yai ba tareda ya kuma cewa komai ba. Yayinda Hisham ya soma bama Daddy hakuri cikin kwantar da murya da k’ok’arin kwantar masa da hankali. Ya dubi Haidar da idanunsa suka kad’a sosai. Ya sassauta murya “Haidar, ina fata mu samu daidaiton fahimta watarana. I hope a day will come.. Ranan da zaka sake amincewa Dani. Ka amince bani nufinka da komai face alkhairi.” Ya dan numfasa “Ka yarda Dani, da kyakkyawan manufa nace zan nemi Auren Anisa. Amma idan kanaga bata cancanci miji kaman ni ba.. Ba matsala sai na hakura.After all, ba yau ne rana na farko da na fara neman Aure ana rejecting dina ba.”" Kalamansa sai ya tuno ma Daddy labarin da Hisham d’in ya basu lokacin da yaita Neman aure ana rejecting d’insa sabida rashin cikakken asali. Wanda Daddyn yake ganin hakan kaman laifinsa ne. Now is the right time for him to be a father to his son. Daddy ya dubi Hisham yace “Ya isa haka Son. Just don’t mind your brother. A hankali wataran zai fahimceka. Idan Kana so ka auri Anisa zan nema maka Aurenta. Ba Anisa kawai ba. Kai Ko ina kake so kaje neman Aure ni mahaifinka Aliyu Maitama zan tsaya maka.. Ko ‘Yar gidan waye kuwa. Ba Wanda zai sake maka gorin asali.” Hisham ya murmusa cikeda Jin dadi. Kaman zai kuka yake furta “Thank you Daddy..! For the first time in my life.. Naji a raina Nima inada mahaifi kaman ko wani D’a.” “Ya kamata kaji haka koda yaushe. Because your Dad will always be here for you kaji koh.” Girgiza Kai kurum Haidar keyi kafin yasa kai ya fice daga parlorn dan bazai jure kallon Kayan bak’in ciki irin wann ba. Mommy ta mik’e tabi bayansa. Daddy ya dubi Hisham yace “Amma wani hanzari ba gudu ba.. Kanaga za’a bada belin Anisa cikin sauk’i musamman yanzu da iyayen yarinyar can Dareen suka bayyana kuma suke Neman hakkin Ran ‘yarsu.?” "Hisham ya jinjina Kai “K’warai Daddy. Da ace Anisa bata amsa cewa da ganganci tabi kan Dareen da mota ba Tabbas da abin yafi zuwa da sauk’i. Babban abinda zaisa a bada belin Anisa a halin yanzu shine rashin ganin gawar Dareen Wanda ganin gawar Dareen ne kad’ai zai tabbatar da mutuwar ta. Kaga zamuyi amfani da hakan a court. Da taimakon k’wararren Lauya kotu zata amince ta bada beli koda za’a ci gaba da Shari’ar. Daddy ita kanta Anisa da ta bige Dareen batada tabbacin Dareen ta Mutu ko bata Mutu ba tinda bataga gawar ta ba balle ta tabbatar kaman yanda ta fad’i a statement dinta. So bazai yuwu a yanke ma Anisa hukunci ba tareda k’wakk’waran dalili ba. Anisa ta cancanci second chance kaman kowa a rayuwa Daddy. Kuskuren da ta aikata bazai zama dalili da zaisa a juya mata baya ba. Daddy idan ka amince min zan tsaya tsayin daka har sai na tabbata Anisa ta Sami freedom din data cancanta. Dan rashin adalci ne a barta a rufe ba tareda an tabbatar da ta aikata laifin kisan ba. Idan har daga baya wani abu ya bayyana.. Ina nufin aka samu gawan Dareen ko wani k’wakk’waran dalili da zai tabbatar da mutuwar Dareen.. Ka yarda dani Daddy ni da hannuna zan mik’a Anisa ma hukuma, Alk’ali yai hukunci koda bayan ta zama matata. Zan kuma d’auki hakan matsayin k’addara Daddy dan D’anadam bazai wuce k’addararsa ba. Daddy I believe Anisa ta cancanci Rayuwar farin ciki mai cikeda ‘yanci a Gidan Aurenta koda na dan lokaci kad’an ne. Ina fata ta Sami wann opportunity d’in a rayuwa ta samu wann experience din koda na dan lokaci kad’an ne.. Balle ma in sha Allah baza’a sameta da laifin kisan ba.” Ya k’arashe cikeda kulawa." Mommy dake tsaye bayan parlorn duk sai jikinta yai sanyi. Sai ta rasa tausayin waye zataji. Anisa dake tsare ne ko kuwa Hisham d’in ne dake kokarin nema mata ‘yanci Wanda take ji kaman dukkansu sunyi failing Anisar sai Hisham ne zai sadaukarwa mai girma ga d’iyar ‘Yaruwar tata. Daddy ya dafa kafad’an Hisham “I’m proud of you Son. Kanada zuciya mai kyau kuma mai yalwa. Allah ya maka albarka da wann sadaukarwa mai girma da kake k’ok’arin yi. Amma ina so ka fara tuntubar mahaifyarka da batun. Munyi waya ta kuma sanar Dani gobe ‘yanuwanta zasu mata rakiya zuwa nan Abuja. Yanada kyau kaji nata ra’ayin da shawarin.” Hisham ya amsa da “Shikenan Daddy zanyi kaman yanda kace in sha Allah.” Daddy ya amsa da “Maddallah. Allah yayi jagora.” Hisham ya sake amsawa da Ameen kafin yai Sallama ma Daddyn ya fice zuciyarsa wasai. Washe gari kuwa Hajja ta samu tarewa zuwa gidan mijinta Engr Aliyu Maitama a nan birnin tarayya tareda rakiyan tsirarun ‘yanuwanta. Daddy yaso ya raba musu gida ita da Mommy amma sai Mommyn harma da Hajjan suka zab’i zaman tare a gida d’aya. Hakan yasa tuni aka gyara ma Hajjan nata sashen a nan cikin gidan. ** Anisa bataji mamakin ganin Haidar ya kawo mata ziyara ba dan tasan izuwa wann lokacin labari ya isa masa cewa Hisham naso ya aureta. "Haidar ya tsareta sosai da ido kafin ya gyara zamansa yace “Tell me, is it true… Da gaske ne wann D’aniskan ya miki tayin aurensa.?”" "Ta furzar da huci kad’an had’ida rausayar da ido “Believe me I couldn’t believe it either.. I mean how shameless of him. Ta ya zai soma cewa zai aureni bayan ukuban da ya jefani ciki..! Ka yarda dani, Ya b’ullo ta wann salon ne bayan da yaji an maida Aurenka da Ummulkhair. Na tabbata wani abun yake son shiryawa.”" Haidar yai shiru kaman mai nazari “And you.? What are you suggesting.?” Anisa taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Zan amince da Tayinsa. Zan aure shi.” Da tsananin mamaki Haidar ke dubanta “Did you hear yourself. Kin kuwa ji mai kika fad’a.? Zaki amince ki amshi tayinsa.? Zaki amince ki aure shi..? Are you going to let him use you for the second time.?!” Murmusawa tai kad’an “You might know Hisham as a friend.. Amma ni na sanshi ne a matsayin mugu. Hisham is a very coning person. Idan yace zai Aureni kaman ya sadaukar da wani portion ne na soyayyar da yake ma Ummulkhair. Knowing Hisham bazai tab’a sadaukarwa mai girma irin wann ba ba tareda ya samu wani babban outcome ba. Idan har yace zai Aureni ka yarda dani akwai wani shiri babba da yake kullawa ta k’ark’ashin k’asa. Kar ka mance Hisham ya kawo mace cikin rayuwarka har ta aureka kukai rayuwar aure ba tareda ka ankare ba. Wanda duk zai aikata abu makamancin wann ba k’aramin shed’ani bane. So na sani Hisham ba mutum bane da za’ayi under estimating d’insa. Duk abinda yake yi is well calculated. Amma ka yarda dani aurena da yace zai yi wann karon shine babban miscalculation mafi muni da zai tapka a rayuwarsa. Ni ba wann shashashar Anisa da ka sani a baya bane. Bazan Auri Hisham dan na bashi dama yai amfani Dani ba. Saidai ni nayi amfani dashi. Wann karon zai tone ramin da zai rupta ne a ciki da Kansa ba tareda ya ankare ba. Zan tabbatar mishi da cewa ni mace ce kuma yayi kuskuren underestimating dina. Ni yafi cancanta na bayyana asalin waye Hisham sabida Dani yai amfani. Kuma aurensa da zanyi shi zai bani dama na samu duk wani kusanci dashi sann na yaye rufin fuskarsa kowa yasan waye shi. Ka yarda dani Hisham bazai tab’a barinku ku samu peace ba kaida Ummulkhair matuk’a yana nan a kura lullub’e da fatan akuya.” Haidar ya girgiza Kai kad’an “No.. No Anisa. I won’t let this happen. Ina nufin bazan bari ki jefa rayuwarki cikin had’ari ba dan kawai asirin Hisham ya tonu. Kin kuwa san mai ake nufi da kalmar Aure.? Ta ya zaki amince ki auri mutumin da ke kanki kinsan ba mutum bane. Anisa Aure is a life time commitment.. Ke ‘Yaruwata ce kuma k’anwata. Koda ace bamu had’a alak’a ta jini ba bazan bari wann devil d’in ya kusanceki ba balle har akai ga maganar Aure. Aure is serious commitment. Na d’auki al’amarin Aure da wasa a farko naga yanda ya juya mun. Bazan barki ki d’auki wann path din ba. Bazan bari kiyi gambling da rayuwarki ba dan kawai kina so ki tona asirin Hisham.” Ya dan furzar da huci yana jinjina Kai kad’an “Akwai ways da yawa da za’a Kama shi. Yanzu haka nasa ana bincike kan iyayen Dareen.I believe a hankali through wad’ann mutanen zamu samu wani haske gameda gaskiyar al’amarin mutuwar Dareen ko nace b’acewarta. If she’s alive ita kad’ai ce zata iya kawo k’arshen yaudarar Hisham.” Anisa ta murmusa “And what if she’s dead.? Zan tabbata ne kawai a nan gidan yari babu ranar fita. Sann Hisham bazai tab’a biyan duk abubuwan da ya aikata ba. Uwa uba bazai tab’a bari ku Sami kwanciyar hankali ba kaida Ummulkhai.” Ta dan numfasa “Na gode da kulawarka a gareni D’anuwa. Amma Hisham ya wuce tunanin mutum.. Bana tunanin akwai wani bincike da zaisa a Kama Hisham dumu dumu dan shi d’in k’wararre ne. Sann baya barin wani shaida da zai tracing back to him. Abu d’aya da zaisa a Kama Hisham shine abi ta hanyarsa. Ina nufin makirci.! Aurensa ne kawai zaisa na samu kusanci dashi.” Taci gaba da jinjina Kai a hankali “I might not be innocent. Kuma nasan in one way or the other dole zan biya abubuwan da na aikata a rayuwa. Tabbas ni nake driving motar. Ni na bige Dareen da Mota but under the influence of Hisham. Ka yarda dani bansan ina hankalina yake ba lokacin da na bige Dareen maganganun Hisham ne kawai suke yawo a kwanyata. K’ok’ari kawai nake na dakatar da ita kar isa gareka kaman yanda Hisham keta tunzura ni da na dakatar da ita. Dan idan ta isa ta sanar dakai komai zaka tsaneni koma ka hukunta ni. Ashe amfani kawai yake Dani dan na zame masa garkuwa na aikata laifin da zai amfani ya rufe bakina dashi. While I’m stuck here Hisham bazai tab’a biyan abubuwan da ya aikata ba. Ina buk’atan ficewa a nan dan na tabbata ya biya duk abubuwan da ya aikata.” Haidar ya furzar da huci kad’an yana jinjina Kai “Idan haka kika zaba. Fine.! Kowa yanada ‘yancin yin yanda yaso da rayuwarsa. Amma bana so ki saka ma ranki sabida ni Haidar zaki sadaukar da farin cikinki da rayuwarki ki auri mutum irin Hisham. Idan duk abinda kike fad’a gaskiya ne Anisa. Then Do it for yourself.. For your own freedom.. For you to clear your name...!” Yana ida fad’in haka ya mik’e yai ficewarsa. Anisa ta bisa da kallo har ya bace mata. Ta lumshe idanunta hawayen nadama suka gangaro mata. ** A cikin satin maganan Auren Anisa da Hisham ya kankama. A b’angaren Hajja sai bata kawo komai a ranta ba tafi alak’anta hakan da Jin k’ai da taimako da D’anta ya saba tsakanin Al’umma tinda d’abi’ar taimako shaidarsa ce. Sann hankalinta ya kwanta da maganan Ummulkhair musamman da yake an maida Auren Ummul d’in da D’anuwan Hisham d’in wato Haidar. Ga Hisham ma zai nasa auren ya samu natsuwa. Itakam maganar Auren sosai tai na’am dashi dukda can cikin zuciyarta bata Jin wani abu mai Kama da farin ciki gameda auren. Sann Sam bata samu natsuwa hundred percent ba sai kawai tai k’ok’arin kawar da tunanin dan tasan bazai shige aikin shed’an ba tinda shi Sam baya fatan a k’ulla alkhairi musamman a batu irin na Aure. Bugu da k’ari bayan series of Aure da D’an nata yake nema a baya ana hanasa idan tak’i wann sai ya zama kaman tayi butulci ne ma Allah. Tuni ta bar ma Allah lamarin ta kuma nema zab’insa ciki. Ko wane aure yana zuwa da nasa k’alubalen. Waye zai tab’a tunanin wai ita Fannah D’anta zai auri d’iyar Asshe k’anwar Hajiya Kwaise.? Waye zai tab’a tunanin zata dawo gidan Aliyu Maitama suyi rayuwa mai tsafta da Hajiya Kwaise.? Lallai rayuwa cike yake da sauye shayen lamra. Allah ka sauya mana sharri zuwa alkhairi. Ameen. Cikin k’ank’anin lokaci aka aiwatar da komai dan tinda akazo da batun auren sai Anisa ta samu sassauci daga wajen iyayenta musamman Abbanta Wanda dama shi yaima Amminta iyaka da ita matuk’a tana tsare a police station. A cewarsa bai haifi ‘yar da zata d’aga masa hankali ba. Ba kaman da Abban Anisar yaga D’an Aliyu Maitama ne mijin Anisar. Abun duka gida ne.. Hakan yasa babu wani dogon bincike balle jan lokaci. Balle ma shi ina ruwansa baijin ko kashi Anisa ta kawo zai fasa aura mata da dai ta zame masa masifa da tashin hankali cikin gidansa. Can Kano gidansu Anisa akaje ka d’auro Aure ko gida Abbanta bai bari taje ba daga cell yace a wuce da ita d’akin mijinta. Taron biki ma bai bari an masa a gida ba. Mommy ce ta had’a yar k’aramar biki can Abuja. Da kyar Abban Anisa ya bari Asshe ta halarta bikin yar nata. Bayan biki da kwanaki biyu Daddy yace da Hisham wann karon shi zai tafi SouthAfrica dan ya kula da kasuwancinsu na can. Ya d’auki matarsa su tafi can musamman da yake an dage sauraron k’aran Anisar har sai bayan watanni hud’u masu zuwa. Sam Hisham bai k’i tayin Daddy ba. Sati guda kawai sukai a Nigeria ba tareda Anisar ta tare da angon nata ba tinda sud’in ma tafiya ne. bayan bikin suka tattara suka nufi southAfrica. Tafiyar da zai d’auke su tsawon watanni uku. "Da wutsiyar ido yake duban Anisa sanda suka zauna saman kujerun jirgin. Ya saki wann muguwar murmushin nasa kafin ya rank’wafo kad’an cikin k’ok’arinsa na d’aura mata seatbelt “Babe, I can’t wait jirgin nan tai landing. A hannu zan sureki na fara nuna miki soyayyar da ban samu daman nuna miki a Nigeria ba.”" Banbarakwai haka taji abun. Ta watsa masa wani irin mugun kallo kafin tai ‘yar bazawarar murmushi na nuni da takaici “Kar mu raina ma kanmu hankali Hisham. Nida Kai munsan babu komai cikin auren nan face k’arya. So we shouldn’t expect anything from this marriage. Dan ina mai tabbatar maka ni Anisa bazan tab’a barinka ka tab’a koda d’an yatsana ba cikin watanni uku da zamuyi tare. Kuma ka saka ma ranka.! AUREN WATA UKU shi mukayi. Ina cika watanni uku a lokacin da muka dawo Nigeria zan rabu da k’addararren aurenka.!” Hisham ya tsareta da ido. Sai ya murmusa yana daidaita zamansa saman seat din. Irin Wanda ya kware a shed’ana yake fad’in “A naki wauwautan Anisa kinyi zaton wasa da hankalina kike..! Kinyi zaton kin Aureni ne dan Ki samu dama akaina ki bankado duk wasu sirrika na. Haka ne..? Kina tunanin a watanni uku da zamuyi matsayin mata da miji zaki iya samun dama akaina ki bankad’o duk wasu sirrika nawa.? Har haka kike son Haidar.? Dan na tabbata sabida shi kikai sadaukarwa mai girma kika amince da aurena.!” Yai maganar yana shafe hab’arsa yana mata wane irin duba. Har lokacin murmushi ne saman fuskarsa “Lallai kin tabbata sokuwa Anisa idan har kikai tunanin zaki iya outsmarting dina by marrying me.!” Ya k’arashe yana kamo hab’arta suna fuskantar juna. Murmushin itama ta sakar masa dan bazata bari ya gane ta karaya ko abu mai Kama da haka ba. Ya dan girgiza Kai yana dubanta “Bazaki tab’a yin hankali ba balle wayo Anisa. Idan amfani dake a karo na farko ya fi min sauki a lokacin da ban Miki farar sani ba. Meyasa amfani dake a karo na biyu lokacin da na sanki kaman tafin hannuna zai min wahala.” Ya d’anyi gajeren tsaki had’ida yin ‘yar bazaurar dariya irin Wanda ake ma Wanda aka raina masa wayau kafin yace “Ki yarda dani daga k’arshe kece zaki kasance da Haidar ba Ummul ba. Idan kika bi plan dina daga karshe Haidar zai tabbata naki.” Ya k’ank’ance idanunsa yana dubanta kaman zai sumbaceta “Mai zai faru idan na saka Miki rigar bomb. Zaki kira Haidar ki nemi taimakonsa.. Sann shi kuma zaizo ya ceceki like a real hero.?” Murmushi yaci gaba da yi yana dubanta yayinda Anisa ke ci gaba da masa kallon mamaki tama rasa a wani aji zata aje Hisham. "Hisham yaci gaba “Zaku kasance a wann d’akin da na kulleki da rigar bomb ku biyu. Bomb din zai tashi daku biyun. Zaku k’one tare.. Ku biyun zaku Mutu tare kaman dai asalin masoya.. Sann ni kuma, Zan Auri matar K’anina sann na kula da bayansa ina nufin marayan D’ansa da bzawarar matarsa kaman dai D’anuwa na gari..!” Ya k’arashe yana murmushi mai bayyana hakwara." "Matsawa ta soma k’ok’arin yi daga gefensa yai saurin rik’o hannunta ya matseta cikin jikinsa. Ya rank’wafo da bakinsa saitin kunnenta. A hankali yake furta “Kaman haka inada hanyoyi da dama da zanyi amfani dasu dan cikan burina. So I’m warning you Anisa, do not teste my patience.!” A hankali kuma ya soma sakin hannun nata yana sakar mata murmushi. Saima ya shiga k’ok’arin gyara mata mayafinta yana fadin “Hey wifey.. Did I scare you..? Im just kidding.” Yai mata rad’a a kunne da fad’in “bazan kasheki ba.. Zan barki kiyi rayuwa mai tsawo da Haidar d’inki.. Happy.?” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda da murmushi saman fuskarsa." Anisa batace komai ba sai tsaresa da ido da tai dan dama Tabbas tasan Aurenta da Hisham yayi yanada shiri fiyeda Wanda yafi wann ma. Ta shirya ma aukuwar komai. Alk’awari tai bazata sake bari Hisham ya kuma samun damar cutar da Haidar da Ummul ba. Even if it will cost her her life. ** Tin bayan tafiyan Hisham da Anisa k’asar SouthAfrica Haidar bai kuma bi takan Ummul ba. Mommy dai ta sanar dashi idan Ummul d’in tayi Arba’in zata tare nan Abuja. Abinda Ya bama Mommy mamaki shine sam bai wani nuna d’okinsa ba balle damuwarsa. Sai bata kawo komai a ranta ba tinda tasan Watak’ila yayi d’okin ne har ya gaji. Sosai Ummul ta damu da halin ko in kula da Haidar yai da ita tin bayan aurensu a karo na biyu. Tanaji zaizo gidan Ya gaida su Umma yaga D’ansa Ya tafi amma ko sunanta bai ambata balle Ya buk’aci ganinta. Ranar wata juma’a ma haka tanaji su Azeema suna shelan zuwansa. Tana daga d’aki tana jinsa Har hira suke yana wasa ma D’ansa amma koda Azeema tace bari ayi masa kiranta sai Ya mik’e abinsa yana fadin Azeema ta shige cikin gidan Tai masa kiran ‘yan samari Wanda zasu shigo da aike. Hankalin Ummul idan yayi dubu Ya tashi. Wai ita Haidar yake basarwa irin haka.. Toh mai Tai masa ne da tsanani.. Kodai Ya daina sonta ne.? Tambayar da taji ya haifar mata da fad’uwan gaba. Sai taji k’walla na yunk’urin ciko idonta. A nan d’aki Mama Tani ta shigo ta isketa tana rera kuka dan dama duk idan Haidar yazo gidan sai iyayen mata su shige k’ofan Abba su bar masu filin tsakar gidan. Mama Tani ta dubeta da mamaki “A’ah! ke kuma kukan me kike..? Ina Haidar d’in.. Wai Har ya tafi ne.?” “Nima ban sani ba Mama.” Ta bama Mama Tani amsa cikin kuka. “Ban gane baki sani ba.” Cikin kuka taci gaba “Mama Haidar ya daina sona ko yazo gidan nan wajen D’ansa kawai yake zuwa amma ko gaisawa baya tsayawa muyi.” Maganganun ta suka so bama Mama Tani dariya amma sai ta gimtse tace “Toh ke ba haka kike so ba. Inji a nan kike kumfan bakin ke ba don kina sonsa kika amince da komen gidansa ba. Ke bari kiji na fad’a Miki maza irin Aliyu ba’a ja musu aji dama kad’an k’adangarun nan na bariki masu d’ingilallun buje ke jira akansu. Ahtoh.!” Badia dake daga parlor ta dage labule ta lek’o tace “Ahtoh Mama fad’a mata dai. Tana nan tana wauwauta taji ana shafe Fatiha a Abuja.!” Ummul ta kuma tunzura da kalaman Badia. Sai ta kuma fashewa da kuka. Mama Tani ta aika ma Badia dak’uwa “Kinci gidanku Badia. Ke bakinki bazai fad’i alkhairi ba. Kiji da naki matsalan wann gantalallen mijin naki ya gudu Ya barki ba tsuntsu balle tarko. Ke ba mai aure ba ke ba sakakkiya ba.” “Haba Mama Aure ni da Tasi’u kuma ai ko a k’iyama.!” Cewar Badia. Mayafi Mama Tani da dauka tana fad’in zata dubiya layin bayansu. Badia tace da ita a dawo lafiya. Mama Tani na tafe can k’asan babban kwalta ta hango ana ihun b’arawo sai jibgan mutumin ake ana masa ihun b’arawo mutane kaw sai tururuwa suke. Kaman Wanda aka ce Mama Tani ta kutsa nan ta hangi Wanda ake ma ihun b’arawo ba kowa bane face Tasi’u mijin Badia. Tasi’u dai da Ya gudu da kudin Bakauye da takardun bogi na shagon Abba ya kuma jefata a uku. Mama Tani ta dafe k’irji tana salallami “Na shiga uku mai zan gani ni Tani.?! Tasu’u.!” Tasi yaji muryar da Ya sani yana tunanin samun rahama daga jibgan da yake sha sai Ya soma k’ok’arin rarrafowa ga Mama Tani yana fadin “Mamana Mamana takaina kimin rai wllhi akasi aka samu ba ni ne b’arawon ba.!” Samarin dake wajen suka dubi Mama Tani sukace “Baaba D’anki ne.?” Mama Tani ta zaro ido waje tana dafe k’irji “Ni Tani haramiya.! Allah shaida ban haifi b’arawo ba. Wllhi ba D’ana bane nima nan a sanadiyan wann kafuri na tafi gidan kasu bada hakki ba.! Kucimin uwarsa da kyau amma kafin nan ku dakata.!” Ta waiga gefe ta dubi yaran da aka tasosu daga makaranta ta amshi paper da pencil hannunsu ta mik’a ma Tasi’u tace “Rubuta.! Rubuta ma ‘yatsa rasidi dan ubanka!.” Tasi yana haki yake girgiza kai “Mama kimin rai wllhi ina son Matata hasalima abinda Ya shigo dani layin nan kenan dan na maida matata kawai tsautsayi Ya hau kaina aka soma ihun b’arawo ni kuma na karyo kwana kenan na taka sawun b’arawon amma wllhi bani ne b’arawon ba.!” Mama Tani ta jinjina kai “Sanin gaskiyanka sai Allah Tasu’u. Amma ko hakan d’in ne ba abinda zance sai Alhamdulillahi.! kaji yanda akeji. Kaman yanda ka gudu da kud’i ka barni a tsaka mai wuya banci nanin ba nanin ta cini. Ba kunya ba tsoron Allah ina Uwar matarka. Da tsufa na geme geme na tafi kurkuku k’anun yara suka shassahata ma wann fuska tawa Mari sabida Kai. Toh kaman haka kaima yau ka taka sawun b’arawo. Wann sai Ya zama wa’azi gareka damu baki d’aya Tasu’u.!” Samarin sukaci gaba da girgiza kai suna fad’in “Karya yake bakinsu d’aya da b’arawon wllhi sai munyi ajalinsa a nan ehe.!” Mama Tani tace ku dakata kar kuyi ajalinsa. ‘Yata ta shafe shekara da watanni tana zaman gaibu da aurensa ba tareda ansan yanda yake ba. Bazata kuma yin takabansa ba bayan tsawon lokacin da ta diba babu sanin makomar aurensa. Tasu’u wllhi sai ka sakar min ‘ya.!” Ta k’arashe tana dangwala masa paper. Bai rubuta ba hakan yasa samarin nan sukaci gaba da dukansa. Tasi’u da yaji bugu kaman zai Mutu sai yace su dakata su daina dukansa zai rubuta ma ‘yar Mama Tani Badia takardan saki da sharad’in samarin zasu mik’asa ga hukuma bazasu kashesa ba. Ya gwammaci su kira ‘yansanda su mik’a shi ga ‘yansanda da dai su masa dukan kisa wajen. Samarin sukace yaci darajan Mama Tani Ya rubuta takardan sakin su kuma zasu basa kariya bazasu bari a illatasa da bugu ba har ‘yansanda su iso. Haka kuwa akai Tasi Ya rubuta takardan sakin Badia Wanda Ya zame masa kariya daga dukan da yake kwasa. Mama Tani ta amshi takardan sakin tai hamdala kana tai godiya ma samarin tasa kai ta shige tana fad’in ta gode Allah da Ya kawo k’arshen auren ‘yarta Badia da miji irin Tasi’u. ** Kwanci tashi babu wuya wajen mai duka. A ranar da Ummul ta cika kwanaki arba’in da haihuwa Abba yace Ya cika alkawarinsa yau zata tafi ga mijinta. A zaton Ummul Haidar zai zo amma sai taga baizo ba. Aunty Asshe ce kawai tazo sann Abba bai bari wani daga gida Ya mata rakiya zuwa Abuja ba. A Cewar Abban tinda ba sabon aure bane kome ne ba sai an Tara mutane an mata rakiya ba. Daga ita sai Aunty Asshe da jaririnta suka nufi Abuja. Ummul taci kuka har ta gode Allah. Tarba mai kyau suka samu daga wajen iyayen Haidar baga Mommy ba baga Hajja ba an rasa waye yafi d’okin zuwan Ummul da jaririnta. Tuni an gyare musu masauk’i a b’angaren Mommy amma sai Hajja ta rok’i alfarmar Ummul ta zauna a nata b’angaren ta k’arashi bik’inta dan dama Mommy tace bazata tare gidan Haidar ba sai ta cika watanni uku da haihuwa. Koda Hajja ta buk’aci Ummul da ta zauna a b’angarenta Mommy cewa Tai hakan yayi dama ‘yarta ce. A b’angaren Haidar kaw da mugun mamaki yake duban Aunty Asshe yana jin wani sabon turanci wai Khairy bazata tare gidansa yanzu ba. "Ya girgiza Kai kad’an still yana duban Aunty Asshe “Aunty, wai kina nufin akwai wani watanni biyu nan gaba da zan sake jira.?”" Aunty Asshe tace “K’warai kuwa. Zancen kake so muyi Haidar. Mommy tace ‘yarta bazata tare da d’anyen jego ba sai ta cika watanni uku da haihuwa.” Girgiza kai yake disbelievingly “Unbelievable.!” Ya furta a hankali yana jinjina kai kafin ya gyara zamansa kad’an ya bud’e murya yace “Aunty ni kuma sai na zauna Har tsawon watannin nan ba mata.? Tsakani da Allah an min adalci kenan.? Seriously this is unfair fah.!” Yai maganar duk a gajiye. Ya dan fito daga cikin kujerar yana dubanta “Aunty you need to talk to Mommy. Knowing Mommy tinda tace sai Khairy sai ta cika watannin nan bazata bari ta tare d’in ba. Please Aunty do something.. Ki rarrashi sister dinki ta amince ta bani matata mu tafi. Aunty wllhi hakuri na gab yake da k’arewa.!” Ya k’arashe kaman wani maraya. Aunty Asshe dai tausayinsa taji kai har kunya saida Haidar yasa taji. Tinda Ya iya budan baki yace mata hakurinsa ya kusa k’arewa tasan an kusa wajen. cikin zuciyarta cewa take ‘Gata ake maka Haidar dan Mommy so take a gyara maka matarka sosai kafin akai maka ita. Ta yanda bama zakai tunanin ta haihu ba.’ A fili kuwa cewa Tai “Kai hakurin shekara sanda bata nan balle yanzu da watanni biyu ne jal bai cika wata biyu ba tinda Anci kwanaki arba’in already.” Girgiza kai yake yana furta “Aunty wancan lokacin daban. Nasan babu auren a wancan lokacin amma yanzu da aure. Thank goodness wann karon ba Mommy ce ta biya sadakin nan ba balle ta hanani Matata... Mommy Sam ta daina tausayi na Aunty. Kawai gwara na nemar ma kaina mafita.” “Ban gane ka nemar ma kanka mafita ba mai kake nufi Haidar.?” Aunty Asshe ta tambaya tana duban Haidar dake k’ok’arin mik’ewa. “Mommy taita ajiye ‘yarta amma Aure zanyi Aunty. Ki shirya zaki had’a mun lefe ko Mommy bata sani ba.” Ummul dake mak’ale jikin k’ofa tana sauraron su zuciyarta yai wani irin tsinkewa taga wani irin duhu ya gifta k’wayan idonta. Wani hajijiya Ya kusan aikata k’asa. Bata san sanda ta k’unshe bakinta ba cikin kokarinta na hana kukan dake zuwa mata. Muryar Aunty Asshe ta sinkayo tana ceda Haidar. “Dakata dakata.. Wane irin aure kuma Haidar.? Mai yai zafi.?” “Khairy da Mommy bakinsu d’aya Aunty.. Idan kuma kema zakiyi joining team din nasu ne fine. I’m used to fighting my battles alone.” Ummul bata ida k’arashe sauraron hirar Haidar da Aunty Asshe ba ta janye jiki da kyar ta fad’a kan gado tana rera kuka mai dalili. Shikenan itakam da gaske Haidar baya sonta. Badia tayi gaskiya da tace tana nan tana wauwauta zataji an shafa fatihan Aurensa a Abuja. Ashe dama aurensa yake nema Shiyasa Ya wofantar da ita bai kuma bi takanta ba. Kuka ya kuma b’alle mata. A haka Mommy ta shigo ta isketa. "Da mamaki Mommy ke dubanta. Ta girgiza kai kad’an “Ahah.! Ummulkhair, kuka kuma.. meke faruwa.?”" Tai saurin gyara zamanta tana k’ok’arin Had’iye kukan nata. Mommy ta zauna gefenta tana karantar ta sai tace “Lafiya kike kuka Ummulkhair.?” Shiru bata iya amsa Mommy ba tanata k’ok’arin danne kukanta. Ganin haka yasa Mommy yin shiru tana nazarinta. Sai ta tuna Haidar bai jima da ficewa daga gidan ba cikin yanayi na rashin walwala da fushi. Sann koda ta tambayesa abinda ke damunsa bai sanar da ita komai ba. Koda Mommy ta tambayesa bazai kwana nan gida ba sai ce ma Mommy yai no kawai zai tafi can gidansa Ya kwana da safe zai shigo. Ta tsare Ummul d’in sosai da ido kafin tace “Kunyi Sallama da Haidar d’in ne.?” Ambato sunansa da Mommy tai yasa ta kasa danne kukan kawai sai ta fashe da sabon kuka. Ganin haka yasa Mommy tsareta da ido tace “Fad’a min Haidar Ya Miki wani abun ne.?” Tai saurin girgiza kai “A’a Mommy.. Kawai.. Kawai ina kewan gida ne.” Mommy ta d’anyi still dan tasan bata fad’a bane kawai amma kukanta nada alak’a da Haidar. sai Mommy ta soma lallashinta ta k’arashe da fad’in “Gobe in sha Allahu YâGumsu zata taho daga Maiduguri.. Zata tayaki da kula da Baba Ali… Barin duba Hajjan taku.” Ta k’arashe tana mik’ewa. Da kai kawai Ummul ke iya amsa mata dan ita bama tace ta fahimci maganganun Mommy ba tsananin tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki. Mommy ta fito tana sababin Haidar zaizo gidan Ya sameta dan ita bata yarda baima Ummul komai ba. Ta kula a yan kwanakin ‘yan halin nasa ne suka motsa. Tai k’wafa tana fad’in “Ai shi dama mai haki baya fasawa.” Aunty Asshe ta dubeta “Wai lafiya Aunty Kwaise keda waye haka.?” Mommy ta kuma yin k’wafa “Banda Haidar… Na rasa mai Ke yawo akansa cikin kwanakin nan.. Jibi dai yau Ummulkhair tazo gidan nan ya d’age kafafunsa yayi tafiyarsa. Allah kad’ai yasan wani bak’in cikin Ya tura mata Ya fita yai tafiyarsa. Kuka sosai na shiga na tadda tanayi..” Murmushi Aunty Asshe Tai ba tareda tace komai ba. Mommy ta dubeta baki sake “Aw dariya ma abin ya baki?” Aunty Asshe ta kuma murmusawa “Toh idan ba memanmu kukeda fitina ba Aunty Kwaise Kun dakemu kuma kukan ma so kuke ku hanamu.” Mommy tace “Ban fahimceki ba. Haidar d’in yace an masa wani abin.?” “Eh mana mun d’auko matar mu Kun k’wace a nan.. Ni yanzu duk laifina ma yake gani yace da na d’auko masa matasa da straight can gidansa na wuce da ita da ba’a masa fin k’arfi ba a nan.” "Mommy tace “Aw wai duk wann fushi da kumburi da yake akan ba’a kai masa ita bace.? Ai kaw saidai ya fashe dan kumburi, ba ta yanda za’ayi akai masa yarinya da d’anyen jego. Kema dai Asshe so kawai kike ki biye ma rigimar Haidar amma ina aka tab’a haka. Yoh idan acan gida Maiduguri ne ai sai ta kwashe watanni ma bai sakata ko a ido ba.”" Aunty Asshe ta murmusa “An rage al’adun nan fah yanzu Aunty Kwaise a duba al’amarin yarona kar azo ana cewa bamu kyauta ba. Iyaka hakuri fah munyi kar kuma a k’ure mana hakuri. Dan takaiga mun fara maganar k’arin aure.” Galala Mmmy ke duban Aunty Asshe “Haidar d’in ne ke maganar karin aure.?” “K’warai kuwa.” Aunty Asshe tace tana karanto ma Mommy yanda sukai da Haidar d’in. Girgiza Mommy tai had’ida tab’e baki “Rigima ce kawai irinta Haidar.. Kuje can kuyita auren naku ‘Yata tana nan sai na tabbata Martabanta Ya inganta.” Daga haka Mommy bata kuma bi takan Aunty Asshe da rigimar Haidar ba. ** A b’angaren Ummul kuwa sosai ta damu da zancen Auren Haidar gashi ta kasa sanar da kowa damuwarta. Ga Haidar kaman ya k’ara janye jiki da gidan. Ko ya shigo gaisuwa kawai ke kawosa saiko duba D’ansa sam baya bi takan Ummul har kawo wann lokacin. Iyaka damuwa da tashin hankali Ummul ta shigesa. Da kyar ta iya sanar da Hajja halinda take cik. Hajja ta lallasheta da fad’in ta cire damuwar Auren da Haidar yace zaiyi a ranta. Ta maida hankalinta ga karan kanta. Ta natsu ta kwantar da hankalinta. Dan ita tama fi so lokacin da Haidar zai ganta ya kasa ganeta. Ga gyara mai aminci da take samu daga Hajja harma da YâGumsu wacce da alama ba don kula da Baba Ali kawai Mommy ta kawota gidan ba harda kula da Uwar Baba Alin. YâGumsu sunada dangantaka da Daddy dan mazaunin Kaka take ga Haidar. Gyara na kankaro mutunci da dawo da martabar d’iya mace bayan haihuwa YâGumsu ke mata. Gyara tin daga ciki Har kawo fatarta daga waje. Kan kace mai Ummul tayi kyau ta k’ara haiba. Ga wani haske da shek’i na musamman da take ba’a maganan wani musulmi k’amshi da tuni yabi jikinta Har zuwa suman kanta. Ita da kanta jinta take ta canza kama daga matantakanta har zuwa gangar jikinta. Wasu lokutan sai ta d’auki wayarta tana duban layin Haidar kaman zatai dialing sai kuma ta tuno kashedin Hajja na cewa ta maida hankalinta ga karan kanta ta mance da zancen Auren Haidar. Cikin zuciyarta take furta ‘Toh ma ni ina ruwana.. Ba sai yaje Yata auren nasa ba. Dama ni sabida Abba da Mommy na amince da aurensa.’ Ta Kai dubanta ga YāGumsu da shigowarta kenan rik’eda Baba Ali yaron ya girma yayi wayau ga kyau da ya k’ara kaman D’an turawa bazaka ce d’an wata biyu bane. Ga shiga rai wajen duk Wanda ya d’ora ido kansa. A haka suka doshi watanni uku suna samun kula da tarairaya daga ita har jaririnta. Tayi k’ok’arin kauda tinanin Haidar cikin zuciyarta kaman yanda Hajja ta shawarceta. Ita zama ta iya cewa ta mance da Haidar d’in balle wani zancen aurensa. Sosai ta natsu ta kwantar da hankalinta. Idan tana tareda Baba Ali ba k’aramin d’ebe mata kewa yaron yake ba. Ya shiga ranta yanda baka tsammani. A sama ranan ta stinci hirar YâGumsu da Mommy. Yâ Gumsun na shirya Baba Ali bayan ta masa wanka take jajen uban Babagana kaman yanda take kiran Baba Alin. Mommy tace “Ai zaman Lagos ya auresa yanzu yana can kudu bai Faye zaman nan d’in ba.” Abinda Ummul ta sinkaya kenan taji kanta na juyawa. Wai zaman Lagos ya auresa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Toh kodai Haidar aure yai ya aje matar a Lagos ba tareda saninta ba. Toh kodai ya b’oye ma Mommy zancen Auren nasa ne kaman yanda yace da Aunty Asshe zata had’a masa lefe ko babu sanin Mommy.. Idan ba haka ba maiyasa zai tare garin Lagos.? Sam bama ta kawo tunanin aiki ko wani abu zai iya kaisa Lagos ba. Haka ta yini d’aki tana faman sak’e sak’e. Duk yanda taso ta yakice tunanin ta kasa. Haka ta shige band’aki taci kukanta ita kad’ai tana mai tausayin kanta. ** Kwance take da hantsi d’akin Mommy. Idanunta a lumshe irin na mai bacci.. Baba Ali na cikin cradle d’insa dake nan d’akin Mommy shima baccin yake. Haidar da shigowarsa gidan kenan Kai tsaye d’akin Mommy ya nufo yana nemanta. Cak yai tsaye yana dubanta zuciyarsa na wane irin fuzga.. Ta masa kyau har ta gaji ga wani k’yalli na musamman da fuskarta keyi. Shi zai iya cewa rabon sa da ita ya mance.. A hankali yake takowa cikin d’akin kaman mai tsoron kada ya tadasu daga baccinsu. Yai tsaye akanta yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Ya furta “sleeping beauty” a hankali kafin ya zauna nan gefenta yana kuma k’are mata kallo tin daga fuskarta har zuwa d’an yatsarta. Ga wani musulmin k’amshi mai sauk’ar da nitsuwa da yai ma k’ofofin hancinsa Sallama tinda ya zauna kusanta. Bai san sanda ya rank’wafo sosai yana shak’an k’amshin nata. Idanunsa a lumshe yake shak’an dadd’an k’amshinta Wanda ya sauk’ar masa da natsuwar da ya mance yaushe rabonsa da yaji irin haka. Kaman a mafarki Ummul ke Jin hucin numfashin mutum saman wuyarta. Tai saurin bud’e idanunta masu cikeda bacci. Nan kaw sukai ido hud’u da Haidar fuskarsu dab na juna har tsinin hancinsu na had’ewa. Zuciyarta yai wani irin yankewa. Dan ita dai rabon ta da Haidar zata iya cewa ta mance.. Ta d’anyi yunk’urin mik’ewa a firgice amma sai Haidar yai saurin rik’o ta ya hanata mik’ewa. Ya tsareta sosai da rikitattun idanunsa. A hankali ya furta “I’ve missed you Khairy.. I’ve missed everything about you..!” Yai maganar yana mai kuma shigar da Kansa wuyanta “Your smell..! Your skin..! Your lips..!” Ya k’arashe yana gangaro da bakinsa zuwa labb’anta. Sosai ta rintse ido tana Jin hawaye na ciko idonta sanda ta tuna daga Lagos ya dawo can wajen matarsa. Sai taji kuka ma zuwa mata da gaske. Tai ta maza ta taresa daga jikinta kukanta na k’aruwa “Ni dai ka k’yaleni.. Ka koma can wajen matar taka.. Nida D’ana bamu buk’atarka.” Cak Haidar ya dakata yana dubanta cikin rashin fahimtar ina kalamanta suka dosa. Ya dan girgiza Kai kad’an “Wait.. What do you mean… Na koma wajen matata.?” Cikin kuka taci gaba “Eh wajen matarka da ka baro can Lagos.. Ni dai kawai ka koma wajenta ka kyalemu.” Izuwa lokacin dariya maganganun nata suka so basa. Yai k’ok’arin gimtse dariyarsa “Kinga.. Saurareni Khairy.” Ta mak’e masa kafad’a cikeda shagwab’a “Ni dai kawai ka koma. We don’t need you here” Ya jinjina kansa “Tinda bazaki saurareni ba shikenan.. Kece dai baki buk’atana amma D’a na yana buk’atana.. I’m sure he missed his Dad.” Ya k’arashe yana nufan gadon Baba Ali. "Annurin fuskarsa ya k’aru sanda ya Ciro yaron daga cikin gadonsa. Yana kissing d’insa yake fad’in “Hello Son, Wakey wakey.. Dad is here..” Yai maganar sai kissing yaron yake yana mai cillasa sama yana fadin ya tashi daga bacci su gaisa. Haka ya fice da yaron cikin hannunsa sai masa wasa." Aka bar Ummul da matse matsen k’walla. Ficewar Haidar da Baba Ali da kad’an taji sak’o ya shigo wayarta. Ta janyo wayar tana dubawa zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Kuka ta fashe dashi sosai ta nufo downstairs a guje tana ambaton Mommy cikin kuka. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *61* *©️Sameena Aleeyou… * Mommy taci gaba da jijjigata tana tanbayarta lafiya meke faruwa. Ummul ta kasa furta komai sai kuka da take tana girgiza kai. A haka su Hajja da Yaa Gumsu suka shigo suka taddasu. Sud’in ma bakin Mommy suka bi suna tambayar meke faruwa. Mommy tace “Yanda kuka ganni a nan tambayar da nake mata kenan.” Ta kuma duban Ummulkhair “Ina Baba Ali wani abin ne Ya faru.?” Cikin kuka Ummul ke fad’in “Baya nan Mommy.” Suka saki baki gaba d’aya. Mommy ta girgiza kai kad’an “Ban gane baya nan ba.. Wane irin bayi nan.? Inji tare na barku a d’aki kuna bacci.?” Murya Har na sark’afewa take fadin “Mommy Haidar Ya tafi dashi.” Mommy tace “Haidar kuma..?” Ummul ta kuma jin kai cikin sauri bata daina matsan hawaye ba “Ya shigo ya d’auki Baba Ali ya tafi dashi.. Mommy dan Allah Ki kirashi.” Ta k’arashe cikin shesshek’ar kuka. Da mamaki suke duban juna gaba d’aya. Mommy ta girgiza kai tace “Haidar kuma Ya tafi da Baba Ali..? Toh ina zai kaisa.? Yaushe ma ya shigo gidan.?” Yaa Gumsu ta dubi Mommy tace “Ah ah.! wai ba jiya nakeji kina cewa yana birnin ikko ba.?” Mommy tace “Dama akan yau jirgin safe zai biyo yazo shi Abuja. Amma bai sanar Dani ya taso ba.. Sann yaushe ma ya shigo gidan..? Sam banji alamunsa ba.” Yaa Gumsu taceda Ummul K’ila dai mafarki take amma basuga shigowan Haidar gidan ba. Ummul na kuka take fad’in ba mafarki take ba a shiga d’akin a duba babu Baba Ali Haidar ya tafi dashi. Mamaki Ya cika su Mommy gaba d’aya. Yaa Gumsu da Hajja suka nufi sama duba Baba Ali amma wayam bashi a makwancinsa. Mommy ta shiga dialing layin Haidar amma baya shiga. Neman duniya anyi ma Haidar wayarsa baya shiga. Ran Mommy idan yayi dubu ya b’aci k’wafa kawai take tana fad’in Haidar zaizo Ya sameta. Akan wani dalili zai d’auki yaro jariri mai shan nono ya fice dashi Har tsawon sa’o’i. Abu kaman wasa ba Haidar ba Baba Ali sann wayoyin Haidar kaf a rufe suke basa shiga. Lamo Ummul tai saman cinyar Hajja hawaye naci gaba da gangaro mata ga k’irjinta da tuni Sun ciko sai ciwo suke sakamakon ba mai sha. Ita bama physical pain d’in bane Ke damunta psychological pain din Ke dawainiya da ita. Tana jin Hajja na fad’in Tai hakuri haka ta daina kunan nan tinda dai Haidar ba cutar da Baba Ali zai ba. Cikin zuban hawaye tace “Hajja wa ya sani yaci abinci ko bai ci ba.? Koma kuka yake.? Waye zai hada masa abincinsa.? Waye zai canza masa diaper.? Hajja ni nasan kawai wajenta yakai shi..” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Hajja ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Wajen ita wa.?” “Wajen matarsa.” Ta bata amsa kai tsaye cikin rawar murya. Muryar Mommy suka sinkaya tana fad’in “Wajen matarsa.? Wace matar kenan.? Haidar d’in keda wata matar.?” Ummul taji kukanta na k’aruwa sai ta mik’e zaune tana jinjina ma Mommy kai “Eh Mommy.. wajenta yakai Baba Ali.” Hajja ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Ummulkhair kinkuwa ji abinda kikace yaushe Haidar d’in yai aure bamu sani ba..” Cikin kuka Ummul ke fad’in “Hajja da gaske aure yai.. Gashi Ya turo mun sako cewa Ya d’auke dansa kuma nasan ma matarsa zai kaisa.” Hajja ta girgiza kai kad’an had’ida murmusawa “Banda abinki Ummulkhair a ina Haidar zai tafi yai aure duk bamu sani ba..? Kuma har ya d’auki Baba Ali ya kaishi ma matar .?” Mommy tai k’wafa tace “Toh wa ya sani masa ne yanzu. Zai aikata tinda yayi a baya ba da sanin namu ba..” Ta d’aga waya da zummar kiran Aunty Asshe ko zata Sami wani bayani gameda Haidar d’in tinda tasan d’an gidanta ne amma sai Aunty Asshen ta riga kira. Mommy tace da Hajja “kinga ma Asshen na kira” Ta daga wayar tana jin da mai Aunty Asshe ta kirata. Aiko tambaya Aunty Asshe ta soma ma Mommy meke faruwa ne Haidar Ya mata waya yana tambayarta yanda ake had’a baby formula da canza diaper. K’wafa kawai Mommy take kafin tace “Zan kira kika rigani.. Kinsan yaron nan zuwa yai Ya d’auki D’ansa Ya kuma kashe wayoyinsa.. Wato iyakacina yake son nuna min.!” Hakuri ta fara ba Mommy tana fad’in “Kinga yace ma I should keep it a secret. Kawai so yake ya kasance da D’ansa.” “Dan yana so ya kasance da D’ansa shine sai Ya d’auke sa yai tafiyarsa Ya kashe wayoyinsa.. Waye Ya tab’a hanasa kasancewa da Dan nasa.?” Mommy ta kuma fad’i cikin fad’a. Aunty Asshe tace “A’a Aunty Kwaise banda son kai mana. Watak’ila bai Sami breathing space bane a gidan shisa ya fice dashi.. Keda Ummul kun suffocating min yaro. Ni dai dan Allah dake da d’iyarki ku daga masa k’afa haka nan yasha iska.” Gajeren tsaki Mommy tai tace maza Asshe ta kira mata shi. Daga haka katse kiran Tai. Sai fad’a take har saida Ummul taji ba dad’i dan bata tab’a ganin fushin Mommy irin haka ba. Har Daddy ya dawo gida ba Haidar ba dalilinsa. Daddy ma fad’a yai tayi yana fad’in wane rashin hankali ne zaisa Haidar Ya d’auki yaro jariri mai shan mama Ya fice dashi. Daddy yasa akai masa kiran Ummul. Duk sai jikin Ummul ya kuma yin sanyi wai yau ita Daddy yake kira sashensa. Gaba d’aya iyayen suna had’u parlorn Daddy. Mommy da Hajja ga Daddy daga nasa kujeran. Ta risina daga can gefe tana goge ragowar hawayen dake gangaro mata tana janyo mayafinta zuwa fuskarta. Ta risina sosai ta gaida Daddy da kyar. Mommy kam har lokacin huci kawai take ba walwal saman fuskarta. Daddy yaci gaba “Ummulkhair nasan kin d’aukeni kaman Abbanki.. Bazan bari wani abu na cutarwa ko rashin adalci Ya faru dake ba.. Kaman yanda nai alk’awari ma Abbanki.. Ki sanar Dani akwai wani matsala ne tsakaninki da Haidar.. Tinda nasan ba k’aramin abu bane zaisa Aliyu Ya d’auki jariri Ya fice dashi Har tsawon lokacin nan.” Ummul bata iya bama Daddy amsa ba sai hawayen dake ci gaba da gangaro mata. Mommy tai karaf tace “Wai har sako yake tura mata zai kai D’ansa ga sabuwar matarsa sabida shi ga shafaffe da mai.!” Daddy ya girgiza Kai cikin rashin fahimta “Sabuwar matarsa kuma.? Yaushe Haidar d’in yai aure.?” “Oho masa mana.! Iyakacina yake son nuna min tinda na hanasa matarsa bari yaje yai wani Auren Wanda ban isa da shi ba.!” Mommy tace cikin b’acin rai. Hajja tace “A’a fah Aunty Kwaise. Auren nan mai yuwa hasashen Ummul ne kawai amma Haidar bazai aikata abu makamancin wann ba.” Mommy tace ba maganar hasashe zai aikata dan ya nuna mata iyakarta. Daidai nan Haidar yai Sallama rungume da Baba Ali cikin abin goyo dake d’aure daga kafad’a zuwa k’irji. Hannayensa kuwa rik’e suke da manyan bags mai k’unshe da manyan teddies da dangin kayayyakin wasa na yara. Zuciyar Ummul yai wani irin tsinkewa. Yayinda iyayen nasa suka zuba masa ido gaba d’aya suna dubansa. Ga dai Baba Ali sai baccinsa yake peacefully rungume cikin k’irjin Babansa. Babu Wanda ya amsa masa gaisuwar nasa cikin iyayensa sai kaw Hajja. Mommy kam mik’ewa Tai ta isa garesa fuu fuska a matuk’ar tsare ta hau kwance belt din da ya rik’e yaron tana fad’in “Bani shi nan.!” A hankali Haidar ke furta “Mommy I’m sorry.!” Ya fad’i yana mai shan jinin jikinsa. Bata sami zarafin amsa sa ba ta koma mazauninta tana jijjiga yaron cikin hannunta. Daddy yai masa alama da hannu yace yazo Ya zauna. Ba musu Haidar Ya isa yanda Daddy ke nuna masa ya zauna a sanyaye. Daddy yai gyara murya yace “Aliyu.” “Na’am Daddy.” Haidar ya amsa a sanyaye. Dan yasan idan Daddy ya ambaci sunansa kai tsaye akwai bayani. Daddy yaci gaba “Have you realized what you’ve done.? Wani dalili zaisa ka dauki yaro jariri ka fice dashi ka rabashi da mahaifiyarsa Har na tsawon sa’o’i.?” Haidar yace “Daddy nayi kuskure Im sorry.. But I just wanted to spend time with my son.” Mommy tai karaf tace “Mu zaka fad’a ma kana son spending time da danka.? Ka cire yaro a nono na tsawon sa’o’i.. Kai ko tausayin uwa da D’an bazaka ji ba.! Harda turo sako kana wani cewa ka kaisa ma sabuwar matarka ko.? dan ka nuna min ni ban isa ba.!” Haidar ya dubi Mommy da mamaki “Mommy sabuwar mata kuma..? Ni Haidar.?” “Auho karya ma aka maka kenan..!” Daddy yace “Shi fah al’amari na aure ba abin wasa bane Haidar. Bai kamata ka maida wann word din abin wasa ba. Kai ya kamata kafi kowa sanin hakan.” Cikin d’aurewar kai Haidar yace “Daddy meyasa zanyi wasa da al’amarin AURE. Idan akwai Wanda zaifi daukan al’amari na Aure da mahimmanci that person should be me. Because I once joke with it kuma naga yanda Ya juya mun.” Mommy tace “Shi kuma sak’on da ka tura ma Ummulkhair na menene.?” Haidar Ya dan saci duban Ummul dake zaune daga gefe saman carpet d’in yace “Mommy ni ban tura ma Khairy wani sako mai kama da haka ba. Eh quite alright na shigo wajenta na tadda tana bacci.. I didn’t wanna wake her up sai na d’auki Baba Ali na fice dashi to spend time with him..” Ya d’anyi k’asa da murya yana fadin “I wanted so badly to be with my family.. Shiyasa na fice dashi zuwa toy store..” Ummul ta dubesa da mamaki jin ya b’oye ma iyayensa ce masa da tai ya fice bata son ganinsa bata buk’atarsa. Mai hakan yake nufi.? Shin hakan yana nufin tsananin son da Haidar ke mata ne yasa ya b’oye kalaman da ta furta masa matsayinsa na mijinta ga iyayensa kodai wani dalili ne na daban.? Muryarsa ta sinkayo yanda yaci gaba “Na tura mata text cewa ina tareda D’a na ne so that she shouldn’t worry.” Mommy tace “Ai sak’on da ka tura d’in bazai karya ba.” Daddy yace duk akan sak’o ake wann rikicin. Ina sak’on yake.? Mommy Ta dubi Ummul cikeda confidence ita a dole sune akan gaskiya ba Haidar ba tace ta nuna sak’on da ya tura mata na cewa yakai ma matarsa yaron. Nan ne fah gaban Ummul ya fad’i dan ita dai bama ta karanta sak’on da Haidar d’in ya tura mata ba. Kawai dai bayan ficewarsa da Baba Ali da taga ya tura mata sako kawai sai ta saka ma ranta ya tafi dashi ne kaman yanda tace ya koma yanda ya fito bata bukatarsa tinda taji yace his son needs him and he missed him. Bugu da k’ari da taga Ya d’auki tsawon lokaci bai dawo da Baba Alin ba kawai sai ta saka ma ranta haka d’in ne. Jiki ba kwari ta mik’a ma mommy wayar sanda ta kai daidai kan sak’on. Daddy kaw yace da Mommy “Read it loudly.” Jiki a sanyaye Mommy ke duban sak’on. Daddy yace “Ke muke sauraro Kwaise. Nan kotu muke. Ki karanto a warware matsalar yarana. Murya a sanyaye Mommy tace “Na’am Engr.” Sosai Daddy ya tsareta da ido had’ida jinjina mata kai alamun ta karanta sak’on. A hankali Mommy ta soma karanta sak’on kowa naji _”I will spend time with my son.. Na kosa watannin da Mommy ta d’ibar mana su cika. Na kosa mu kasance tare mu ukun.. Kaman dai ahali. I love you so much Khairy. And I can’t wait to be with you again.!”_ Tinda Mommy ta soma karanta sakon jikin kowa yai sanyi Babu kaman Ummulkhair. Ga kunya da Ya gama lullub’e ta kaman k’asa ya tsage ta nitse ciki. Abinda Hajja dai ta fad’i Ya tabbata hasashen Ummul Ya raya mata wann tunani gameda mijinta. Hajja ta kula da yanayin da Ummul d’in ta tsinci kanta ciki gaban sirakanta sai kawai ta mik’e ta amshi Baba Ali hannun Mommy ta k’arasa ta kamo Ummul tace suje ta bama yaron abincin sa. Ai kaman jira take sum sum tabi Hajja kanta sanne a k’asa suka nufi k’ofa. Haidar Ya saci kallonta daidai sanda suka iso kusan k’ofa zasu fice. Ya kashe mata ido guda yana matse murmushinsa. Harda furtawa a hankali “Mission accomplished.” Labb’ansa ne kawai suka motsa. Ta kuma sadda idonta cikin saurin tana ayyanawa cikin ranta wato Haidar da nufi yai abinda yai. Tabbas hak’arsa ta cimma ruwa tinda gashi an isa gaban Daddy. Gashi ya sata jin kunya da alama shi ko ajikinsa. Dan a iso gaban Daddyn ma yai abinda yai. Sauri sauri ta fice biyeda Hajja tana jin wani sabon kunya na kuma lullubeta. Haidar ya mik’e shima cikeda risinawa Ya kuma bama iyayen nasa hakuri kan kuskuren da yai tareda alkawrin irin hakan bazai kuma faruwa ba in sha Allah. Ya k’arasa ya tattari toys d’in da ya shigo dasu Ya fice yabi bayansa su Ummul da kayan wasan. Daddy ya tsare Mommy da ido. A matsayinsa na D’a namiji idan ya fahimci abinda ke faruwa dai Matarsa ne Tai fin k’arfi ma D’an nasa ta aje masa mata da D’a tak’i bari su tare gidansa Tun bayan da suka d’auro auren Haidar d’in da iyalinsa a karo a biyu. Ya jinjina Kai yana duban Mommy wacce ta d’an sha jinin jikinta. Jiki a sanyaye tace “Engr wai lafiya kake ta kallona haka.?” Daddy yace “Dole na kalleki Kwaise kin shigo da k’ara kotu ashe kece dai mai laifin.” Mommy ta marairaice fuska tace “Ni ce kuma mai laifi Engr..?” Daddy yace “Eh mana.. Laifinki mana. Ni na rasa zaman me iyalin yaron nan suke a nan..? Meye manufarki na aje masa iyali a nan...?” Mommy tace “Engr naga haihuwa fah tayi..” “Toh dan ta haihu sai ki hana ma yaro iyalinsa.? Harda wani watanni da kika d’ibar musu.. A wani aya ko hadisi kikaji hakan.?” Mommy ta girgiza kai kad’an “A’a Engr ba ko d’aya.. Amma ai..” “Babu wani amma a nan Kwaise. Ki kyale yaro ya tafi da iyalinsa haka nan.” “Engr naga wai watanni ukun da na d’ibar musu saura sati biyu ne kawai su cika.” Cewar Mommy a sanyaye. Daddy yace “Su cikite sati biyun a gidansu. Kar iyalin yaron nan su kuma kwana gidan nan. Ki barsu haka su tare yau d’in nan. Kinga dai abinda ya faru hannunka mai sanda D’anki yai Miki. He wants his family next to him. Ya kuma baki matsayin ki as mahaifiyarsa da Ya biyo ta hanya mafi sauk’i da zaki fahimcesa.” Mommy ta jinjina kai “Yanzu yau d’in su tafi Engr.?” Daddy ya kuma gyara zamansa cikin kujera “Toh mai zasu miki a nan d’in Kwaise.?” Mommy tace “Wai dama gani nai idan suka cika watanni ukun sai mu kira namu shagalin taron sunan da bamu samu munyi ba.” “Tafiyarsu bazai hana muku taron sunanku ba Kwaise.” Daddy ya bata amsa yana mai daukan remote control na tv cikin hannunsa. Mommy tace a sanyaye “Shikenan Engr.. Idan haka kace.. Barinje na sanar dasu su shirya.” Ta dan kara duban Daddy da Ya maida hankalinsa kacaukam ga TV tace “Na kawo maka shayin ne.?” Daddy ya girgiza Kai yace “No barshi zuwa dare.” Sai ya k’arada “Kimin kiran yaran nan Haidar da Ummulkhair.” Mommy ta amsada “Toh Engr.” Kafin ta fice. Nasiha mai ratsa zuciya Daddy ya musu gameda zamantakewa kafin ya saka musu albarka Ya sallame su. A ranar dai Mommy ta hakura ta sakar ma Haidar matarsa harma da D’ansa. Kafin dare ta tura wasu daga cikin ma’aikatan gidan suka tafi can gidan Haidar d’in suka gyare ko ina tsaf. A d’aki Hajja ta zaunar da Ummul Tai mata nasiha da Ya danganci aure da zaman aure. Ta k’ara nusar da ita mahimmanci communication tsakanin ma’aurata dan da yawan aurarrki Sun lalace ne sakamakon rashin daidaiton fahimta Wanda lack of communication Ya haifar. Ta k’ara nusar da ita gameda dabarun kula da miji da jawo hankalinsa sann tace duk abinda Ya shige mata duhu a gidan Aurenta she should call her kai tsaye. Koda Ummul ta shigo yima Mommy Sallama kanta a k’asa. Dan yau d’in wani mugun nauyin Mommy din ne ya k’aru a idonta. Mommy tashi mata albarka had’ida jero masu add’uo’i na kariya. Ta rungume Baba Ali cikin hannunta tana jin kaman su bar mata yaron kaman kar su tafi dashi. Sosai yaron Ya shiga ransu kaf gidan jimami da begen tafiyan Baba Ali suke. Haka ba don Mommy taso ba ta mik’a sa ma Yâ Gumsu tana fad’in kullum a kawo mata maigidanta yini. Ummul harda d’an hawayenta sanda suka fito daga b’angaren Mommy dan gaba d’aya yau d’in sosai jikinta yai sanyi jin yanda kowa ke mata nasihohi masu tsayawa a rai. Suna ficewa Haidar Ya shigo wajen Mommyn dan mata nasa sallaman. Ta d’an d’aure fuska ba tareda ta dubesa ba. Ya k’araso ya duka wajen k’afafunta. Hannayenta ya kamo cikin nasa yace “Har yanzu fushi kike Dani Mommy.? Haba Mommy na.. I said I’m sorry fah.!” Ta dubesa a dak’ile “Kaga Haidar ka tashi ka wuce. You can’t keep them waiting.” Ya dan marairaice fuska “Amma Mommy haka zan tafi without your blessings.” Kunnensa ta kama kad’an taja tace “Dan albarka.! Tashi kaje Allah Ya muku albarka. Allah ya kare ku da dukkan sharri..” Haidar ya amsa da “Ameen Mommy na. I love you.” “Maza tashi kaje haka nan..” Tace tana mai gyara zamanta. Ya murmusa yana jin k’aunar mahaifiyar nasa na dad’a ratsa zuciyarsa. Har ya kai k’ofa ya sinkayo muryarta tana furtawa a hankali “I love you more.. May you always be protected.” Murmushi ya saki kafin ya fice yana furta Ameen Mommy na a hankali. ** Koda suka iso gidan sai jikin Ummul Ya kuma macewa. Ta soma tuno abubuwan da suka faru watanni shabiyu baya. Yaa Gumsu tace da ita ta shiga da k’afar dama sanda sukai stepping a main door din gidan. Haka nan Ummul ke taka cikin gidan tana jin wani bak’on al’amari na faruwa da ita. Gidan yana nan a sanin da Tai masa sai wasu yan sauye sauye da baza’a rasa ba. Tinda ta shigo d’akin zuciyarta ke tsinkewa. Taci gaba da tuno abubuwan da suka faru a wann d’akin bugun zuciyarta na k’aruwa. Takai dubanta ga gadon dake d’akin sai tai saurin rintse idonta. Sai tana jin kaman lokacin ne komai ke faruwa. Alamun tab’a k’ofa da taji Ya sata saurin waigowa. Haidar ta gani tsaye daga k’ofa Ya hard’e hannaye yana dubanta. Tai k’ok’arin janye idonta daga gareshi sanda Ya soma takowa zuwa gareta. Ganin sai Ya tuna mata abubuwan da Ya faru tsakaninsu a wann d’akin. Sabon haushinsa da takaicin abinda Ya mata Ya taso mata. Ta janye jiki cikin sauri tana mai k’ok’arin ficewa daga d’akin amma sai Haidar yai saurin rikota. Ta d’an dubesa ba walwala “Ni ka kyaleni.” Ya d’ago gajiyayyun idanunsa yana dubanta “Khairy wai ban baki tausayi ba..” Hararsa ta d’anyi “Aw kaine ma abin tausayi ko ni da kasa naji kunya gaban Daddy.?” Ya murmusa kad’an yana dan ciza lip d’insa na k’asa kad’an “Aw wai ke dama baki karanta sak’on ba kika tada hankali Harda kai k’arata gaban Daddy.?” Kaman zatai kuka tace “Ai kai ka shirya hakan dama. Duka laifinka ne.” Ya kuma murmusawa “How am I at fault here.? Ni sak’on da na tura daban sak’on da kika sanar dasu Mommy daban. I don’t remember telling you nayi wani aure ko inada wata mata ba.. Ban san ina kika samo wann idea d’in ba.” Hararsa ta kumayi “Da kunne na naji kana fad’a ma Aunty Asshe ai. Har cewa kake zata hada maka lefe ko mommy bata sani ba.” Ya dan fito da idanunsa waje “Aw.! wai dama kina lab’e kina jin duk hirarmu da Aunty Asshe.?” Ya dan tsareta da ido “Wait.! Were you eavesdropping?” Ta kuma dubansa kaman zatai kuka wann karon “Ni wann kawai naji fah.. Kuma ban damu ba dan zaman Lagos Ya aureka. Ban damu da kai ba kaman yanda baka damu dani ba. Kuma ni sabida Mommy da Abba kawai na amince da aurenka.!” "Sosai taso basa dariya sai Ya dan murmursa yana yana shigar da ita jikinsa “Wow someone’s jealous..! Tell me, do you love me this much.?” Ya k’arashe teasingly bai daina matseta cikin jikinsa ba." Tab’e baki Tai kad’an tana kauda fuska. Ya kamo hannunta yana fad’in “Taho nan kiji.” Ta d’an cije tak’i tabi bayansa. Ya kaikaito yana dubanta cikin marairaice fuska “Please don’t give me this attitude Khairy.. Not tonight please.. Wllhi na yarda you are not an easy woman. I’ve been trying tirelessly to win you back for the past 12 months.. Dan Allah kiyi hakuri yau kam ki saurareni kinji Khairy na. Wllhi na tuba.!” Yanda ya marairaice yana maganar dole ya baka dariya. Ta kuma tsuke fuska kaman bazata bisan ba sai ta tuno jawaban da Hajja Tai mata kawai sai ta tsinci kanta tana mai take masa baya. Suka k’arasa yai musu masauk’i saman chaise-longue. Tsareta da ido yai yana dubanta. Ta d’an dubesa sai ta kauda fuska “Nifa ban son yawan kallo..” “If only you know how much I missed you Khairy..” Ya fad’i bai janye idanun nasa daga barin dubanta ba. Batace dashi komai ba sai kauda fuska da ta kumayi. Haidar ya kamo hannayenta cikin nasa “I don’t know where to start.. Na rasa da wanne zan fara..” Ta dan dubesa a dak’ile “Fara da labarin matarka ta Lagos.” Ya dan murmusa “Khairy are we going to talk about this again.? Wai ni dakata.. How many times do I have to explain myself.?” Ta tabe baki kad’an “Idan ba mata kake dashi a Lagos ba Meyasa zaman can ya aureka..?” Ya dan furzar da huci kad’an sai Ya Ciro wayarsa ya nuna mata fuskar wayar. Hoton road construction ne ya bayyana a fuskar wayar. Ummul ta dubi wayar cikin sanyin jiki. Haidar yaci gaba “Aiki ke kani Lagos. Akwai road project da Kampaninmu keyi a Lagos.. And I’m in charge. So idan kinji na tafi Lagos site nake. Happy.?” Ya k’arashe yana dubanta. Ya dan murmusa “Ai bansan Har haka aka damu dani ake kishi na ba..?” Cikin inina take furta “Ni.. Ni ba kishi nake ba.” Tana maganar tana avoiding k’wayar idonsa irin Wanda kunya ya lullub’e. "Murmushi Haidar keyi kafin ya kamo hannayenta cikin nasa. Ya d’anyi gyaran murya kad’an “First, zan fara da baki hakuri Khairy.. Na sani ban kyauta ba in many ways. For the past few months na baki sarari ba wai dan na dena sonki ba. Sai dan Ki samu breathing space.. I thought I was suffocating you Khairy..!” Ya dan kamo hannayenta cikin nasa “Na baki space ne ba don na daina sonki ba sai don kiyi healing.. Because time is the only remedy I believe… But believe me it hurts.. It hurts more than you can ever imagine… Ki yarda dani.. A daddafe nayi watannin nan.. But then I had no choice but to punish myself.. For you..”" Ta d’ago ta dubesa da idanunta da suka cika da rauni wann karon. Haidar ya dan numfasa “Now that we are finally together zan cike miki wann gurbin Khairy... I promise to make it up to you.” Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta “Thank you for choosing me .. Thank you for being my wife again.. I promise you won’t regret choosing me.. I might not be a perfect husband.. but I’ll try my best to be the best.. Best Partner for you.. And best Dad for your kids.. Our kids.!” Ya kuma matse yatsunta cikin nasa “And this time around Aure mukai na Har abada ba AUREN WATA UKU ba.. Ba Aure sabida wani manufa ba.. Ba Aure dan Daddy ya mallaka min wani project ba. I love you so much Khairy.. And from now henceforth I want you to know that you are my FOREVER.. Mrs Haidar Maitama.” Hawayen da take mak’alewa suka digo saman hannun Haidar. Fuskarta Ya kamo yana dubanta “Forgive me Khairy..! Forgive your Sweetmonster.” Murmushi take tana dubansa hawaye na gangaro mata “Na yafe maka.! Na yafe maka mijina.. Na yafe maka tin sanda Aunty Kwaise ta sanar Dani gaskiyar al’amarin.. Na yafe maka because I always believed you are a good person.. Na yafe maka because I love you.!” Ta k’arashe cikin yin k’asa da muryarta. Kallonta yake kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yana duban yanda lips dinta ke furta kalaman so a gareshi. Bai san sanda Ya janyota jikinsa ya rungume ba. Idanunsa a lumshe yake furta “I love you more.. I love you more.!” Ya k’arashe yana kuma shigar da ita jikinsa. Jin zancen na neman canza salo Ya sata k’ok’arin janye jikinta tana fad’in zataje ta duba Baba Ali. Haidar bai saketa ba yaci gaba da rikitata da kalolin k’aunarsa yana fadin “But his Dad needs you more.. Besides Yaa Gumsu is there to take care of him.” Kaman zata sakar masa kuka take fad’in dan Allah yai hak’uri Ya kyaleta taje ta duba su ta barsu shiru tuntuni. Shima kaman zai kukan yake fad’in idan ta tafi wajen Baba Ali shi waye zai kula dashi. Ta kuma marairaice fuska “Toh ai shi Baby ne.. Kai fah babba ne.” Yaci gaba da shafa sumarta yana duban fuskarta “But I’m your big baby.” Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Haidar ya janye hannayen suna duban juna cikeda so da kauna. "“Tell me, am I not your big baby.?”" Ta yunk’ura zata kuma shigar da fuskarta cikin jikinsa ya tallafo fuskarta yana tsareta da idanunsa. Ta kuma marairaice fuska zatai magana taji ya kuma had’e bakinsu waje guda. Da kyar Ummul ta samu ta kwaci kanta daga hannun Haidar. Ya d’ago idanunsa da tuni Sun k’ank’ance yana dubanta. Da kyar ya iya d’ago yatsun hannunsa guda uku yana mata alama “3 minutes.. Minti uku kacal na baki.!” Ya furta daga nan yanda yake kishingid’e yana maida numfashi. Lumshe idanunta Tai bayan ta fito daga d’akin tana mai sauk’e ajiyan zuciya. Haidar k’arshe ne Ya kware wajen mantar da ita duk wani b’acin rai da fushi da Ya jefata ciki a baya. A hankali ta furta “I love you.. I love you so much my bigbaby.” Ta tadda Baba Ali baccinsa yake Yaa Gumsu na bisa darduma da alama sallah ta ida. Bata ko bari Ummul ta zauna ba ta fatattake ta da ta koma wajen mijinta ta karada idan Baba Ali na nemanta zata kirata a waya. Cikeda kunya Ummul ta fice ta koma nata d’akin. Kasancewar bata tadda Haidar a d’akin ba ya bata daman fad’awa bathroom tayo wanka. Tsaye Tai gaban wardrobe tana nema tufafi mai sauki da zata sauya. Tana nan a haka taji hannun mutum ya zagayeta Ya rungumeta ta baya had’ida manna mata kiss a dokin wuyarta dake da dashi da dumin ruwan da Tai wanka. Tai wani irin jan numfashi a dan firgice. Ya kaikaito da ita suna duban juna. A dan shagwab’e tace “Ka bani tsoro.” "Ya d’an Ware ido “Really I scared you..?” Yai maganar yana janyota jikinsa sosai. Lokaci guda yai kasa da murya “Tell me, ta Ya na baki tsoro..? By… hugging you.. Or.. by… kissing you.?” Yai maganar cikin kashe murya yana kuma shigar da ita jikinsa." Kaman zata sakar masa kuka tace “ All..!” Ya kuma shigar da ita jikinsa yana mai ci gaba da sumbatar wuyarta yake furtawa a hankali “I want you to scare me too.. with your sweet kisses.. Warmed hugs.. And your sincere smile..!” Ya k’arashe cikin kasheta da wani irin salo mai wuyan fasaltuwa. Cikin k’ok’arin janye jikinta take fad’in Ya kyaleta ta saka kaya. Ya tsare fuska yana dubanta “Do you need it.?” Cikeda kunya ta rufe bakinta da tafukan hannu tana zaro ido. Kashe mata ido yai kafin yace “Zo muje.?” Ta girgiza masa kai “To where..?” “To my bedroom obviously.. I have cloths for you there.” Zata kuma magana ya duk’a gabanta yana mai kwantar mata da gadon bayansa. Itakam dariya ma abin ya bata ganin Ya duka ya juya mata baya “Wai mai kake ne.. Meye haka.?” “What..? D’ale mana.” Yace yana nuna mata gadon bayansa. Murmushi mai bayyana hakwara take. Ta d’an girgiza kai kad’an tana nuni da kanta “Wai ni ce zan d’ale baya.?” Ya d’ago gira da ido yana dubanta “Oh mamaki kike.? Of course I’ll give my wife a piggyback to my bedroom.” Itakam dariya da kunya duk sai Ya rufeta musamman da ta d’ale bayan Haidar d’amas ya nufi bedroom d’insa da ita. Saida suka isa d’akin ta raina wayonta dan Haidar dai bai aje mata wani kayan sakawa ba kaman yanda yace. Kaman zata masa kuka take tambayarsa ina kayan nata suke. Ya dan tsuke fuska yana dubanta “It’s not.. necessary.. You don’t need it.. You’ll be fine like this..” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda. Kaman zatai kuka take fad’in ita dai tak’i wann wayon. Haidar Ya janyota jikinsa yana lallashinta da fad’in yayi alk’awarin zasu sharing nasa kayan kafin wayewar gari. Nan kuma suka soma sinkayo kukan Baba Ali. Ummul ta dubesa tana girgiza kai “Ka gani koh.. Yanzu ya zanyi na fita a haka.. Daga corridor fah nake sinkayo kukan nasa.. Wayyo Allah na nasan zagawa take dashi dan yai shiru.. Ta ya zan soma fita a haka.?” Ya kamo hannayenta “Relax Khairy.. You stay here.. I’ll go check on them. Ok.” Ya karshe yana dubanta. A hankali ta jinjina masa kai. Ta koma tai zaune tana k’are ma d’akin kallo. A haka Haidar ya shigo da Baba Ali cikin hannunsa idanun yaron tar a bud’e da alama hira zaiyi. Sai cillasa Haidar yake shi kaw yaron sai k’ekata dariya yake. Haidar Ya diresa saman gado yana ci gaba da masa wasa. Ya kwanta ringingine ya dora yaron saman k’afafunsa yana cillasa da k’afafu. D’a da uban duk dariya suke mai cikeda nishadi. Ita kam Ummul sai suka zame mata tv dan sosai suka birgeta. Ganin Haidar ya shagala da wasa da D’ansa yasa ta fice nata d’akin ta sako tufafi mai sauk’i. "Haidar ya dubeta sama da k’asa sanda ta turo k’ofan d’akin. Ya dan tsuke fuska yace “Mrs Aliyu, what’s the meaning of this..?”" Ta dan girgiza Kai “Mai fah.?” "Ya mata nuni da bakinsa zuwa kayan jikinta “I mean, do you really have to wear that..?”" Ta dan rausayar da ido dan tasan rigimace kawai irinta Haidar. Sai Ya dan kashe murya yace “But still.. you look spicy..!” Ya k’arashe yana kashe mata ido. Ya dan bud’e mata hannu yace ta k’araso. Cikin tsanaki take takawa har ta isa garesa. Yai mata masauk’i zuwa b’angarensa guda yayinda Baba Ali Ke cikin d’aya b’angaren nasa. Ya had’esu gaba d’aya ya rungume. Ya dan lumshe idonsa kadan “Finally we are together.. The three of us.!” Ya fad’i yana sumbatar su biyun. Sosai ta shige cikin jikin mijinta ga D’anta daga d’aya b’angaren. Mai kuma zata nema a duniyar nan. A hankali take furta kalmar godiya ga Ubangijinta da ya cika rayuwarta da d’imbin albarka. Haidar ya dubeta yanda Tai lamo gefen kafad’arsa “Mrs Maitama.” Ta amsa murya a mak’oshi kafin ta dan d’ago ta dubesa. Haidar yaci gaba “Put him to sleep now.. Let’s have our own time..” Ya k’arashe yana mika mata Baba Ali. Ba musu ta amshesa ta soma kiciniyar basa abincinsa. Haidar ya rik’e rigar nata yana mai fad’in “Allow me.” "Batai yunk’urin hanasa ba. Batai yunk’urin dakatar dashi ba har ya saka ma yaron abincinsa a baki da basmala. Haka Haidar yai zaune ya sakasu gaba yana kallon yanda take feeding jaririnsu gwanin bansha’awa. Sosai ya shagala da kallonsu suna k’ara birgesa Har Baba Ali ya samu bacci. Bayan ta shimfid’a Baba Ali Haidar ya umarceta da ta d’auro alwala tazo suyi sallah. Haka kuwa akai. Ya jasu sukai sallah raka’a biyu kaman yanda yazo a sunnah. Sukai addu’o’i da duk wani abinda Ya kamata suyi. Bayan nan ne fah ta yarda lallai Haidar na buk’atan nasa lokacin. Dukda tsananin son kasancewa dashi take a wann daren bai hanata tuno wahalan da ya bata a kasancewarsu ta farko. Haidar ya kula da hakan. Cikin lallama da dabara yake sanar da ita it will be different from the other time. Gently yake biyeda ita. Saida ya tabbata ta mallaka masa kanta, zuciyarta, ruhinta da gangan jikinta gaba d’aya. A haka yai leading nasu zuwa wata duniya da basu tuna kowa cikinta sai su biyun. Kaman yanda yace zai kasance na daban haka d’in ne ta kasance. Ta yarda yayi kewarta ya kuma nuna mata tsantsan k’aunarsa gareta. He made sure wann daren zai tabbata na musamman a tarihin rayuwarsu.." A kwanakin soyayya sukaita nuna ma junansu Babu kaman Haidar da gaba d’aya ya sake rikicewa akanta. Idan suna tare basu tuna komai basu tuna kowa sai su biyun wasu lokutan kukan D’ansu Baba Ali ke dawo dasu wann duniyar. Sunyi nisa cikin faranta ran junansu suka sinkayo sautin kukan sa. Ummul Tai yunk’urin zame jikinta daga nasa tana fad’in zataje ta duba Baba Ali. Rik’eta Haidar yai yana kuma shigar da ita jikinsa. A hankali yake rad’a “Do you know why he’s crying..?” Ta dan girgiza Kai “No.. He’s hungry.. probably..!” Haidar ya kuma matseta cikin jikinsa “Cewa yake he wants a sibling.” Cak suka daina sinkayo kukan yaron. Haidar yaci gaba da rikitata da salon k’aunarsa yana fadin “See I can read his mind.. You don’t need to go check on him.. Just stay and give him a sibling..” Da dabara Ummul ke zame jikinta Har ta samu ta zille masa. Saida ta kai k’ofa taji ya rik’o hannunta. Ya manneta jikin k’ofa had’ida d’ago hab’arta kad’an suna duban juna “I love you Khairy.. I love you so much.” A hankali bakinta itama ke furtawa “I love you too.. I love you my sweet.. sweet..!” Bata k’arasa ba Haidar yai karaf yace “Your sweet mons…” Bata bari yakai aya ba tai karaf tace “My sweetlove..” Ta k’arashe tana mai manna masa kiss a lips d’insa. Daga haka ta zame ta fice cikin sauri tana murmushi ma Haidar da tuni Ya daskare yana shafa lips d’insa. ** Tarewarsu da sati biyu ake bikin sunan Baba Ali a nan Abuja. Su Mommy suka hada nasu taron nan gidan Daddy. Ummul tayi waya da yanuwanta duk zasu samu halarta harda Babbar Yayarsu Aunty Salima wacce tuni ta baro yaranta gida wajen Mama Tani dan yaran ne kawai zasu samu halarta banda iyayen. "Sadis ne Ya tafi ya d’aukosu ana gobe taron sunan. Azeema na gaba yayinda Khulsum, Badia da Aunty Salima ke baya. Aunty Salima tana hankalce da Sadis da Azeema tin tasowarsu Har kawo isowarsu. Ko ba’ace ba zata iya cewa ta fahimci meke wakana tsakanin su biyun." Sanda suka iso Salima ta tsare Azeema da ido bayan sunyi Sallama da Sadis Sun nufi cikin gidan. Salima ta girgiza kai kad’an tana duban Sadis dake kuma waigowa yana satan duban Azeema. Itama Azeema sai murmushi take tana waigawa. Salima ta tsareta da ido tace “Ke Azeema.. Wai meke faruwa ne a nan..?” Azeema tace “Me fah Aunty..?” Salima Tai mata nuni da Sadis da tuni Ya nufi mota tace “Shi nake nufi.” Murmushi Azeema ta saki tana wani juya ido “Laa wai Sadis.. Ba komai fah Aunty Salima.. Kawai mutunci muke.” Salima ta jinjina kai tana fad’in “Eh lallai fah mutunci.. Toh idan Tai tsami munji mun gani.” Ta k’arashe tana take ma Khulsum baya. Badia kaw dake nan daga waje tin bayan isowarsu tana nan zaune gefen flowers dake jikin k’aton shataletalen dake tsakiyar gidan. Wayar Ummul take amsawa yanda take sanar da Ummul d’in Sun iso amma Sun sauk’a gidan Daddy. Ummul kaman zatai kuka take fad’in meyasa basu taho sun sauk’a gidanta ba. Badia tace “Ayya ‘yaruwa kiyi hakuri wllhi tin kafin mu taso Mommy ke ta waya tana fad’in tuni an shirya mana masauk’i.. Kinsan bazamu iya ce ma Mommy a’a ba.” Daga d’aya b’angaren Ummul kaman zatai kuka tace “Toh shikenan.. Gobe muma in sha Allah da wuri zamu shigo.. Idan mun zo Zan rok’i Mommy nasan zata amince mu taho tare.” Badia tace “Toh shikenan Allah Ya kaimu goben. Kinga bara na shige ciki sauk’armu kenan.” Sukai sallama da ‘yaruwar tata a daidai sanda wata k’atuwar b’akar jeep ta shigo gidan. Badia ta soma tafiya kenan taji wata murya na babban mutum mai cikeda kamala na mata Sallama. Ta waigo cikeda girmamawa tana amsawa. Dan idan dai bai kai Abbanta a shekare ba zaiyi kusansa dukda hutu da jin dad’i na b’oye tsufa. Bayan ta gaida mutumin sai Ya k’arada “Allah sa dai ‘yar gidan ce ke.?” Ta d’an girgiza kai kad’an “A’a ni ba ‘yar gidan bace. Amma ciki zan shiga yanzu.” Ya murmusa yana jinjina kai “Toh da Allah idan kin shiga kimin iso wajen Maigidan. Dan nayita neman layinsa bana samu.” Ta d’anyi jim sai tace “Toh.. Wanene zance.?” Mutumin yace “Kice Alhaji Gimba ne.” Ta jinjina kai tana mai amsawa kafin ta shige. Alhaji Gimba yabi bayanta da kallo murmushi saman fuskarsa yana jin wani abu na fuzgarsa. Koda Daddy ya fito ya tadda Alhaji Gimba tambayar da Ya soma yi ma Daddy shine wacece wann yarinyar da Tai masa iso.? Daddy ya d’anyi jim sai Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Bansan wacece ciki ba amma dai ina tsamman d’aya daga cikin ‘yanuwan Matar Haidar ne..” Sai Daddy ya dan girgiza kai “Amma meke faruwa..? Allah yasa dai lafiya.?” Alhaji Gimba yai saurin girgiza kai “Lafiya sai alkhairi.. Kawai dai.. Naga iri gidanka ne abokina.” Da mamaki Daddy ke dubansa. Sai Ya girgiza kai kad’an yace “A’a Gimba.. You can’t be serious. Bazaka mana haka ba.” Alhaji Gimba yace “Wllhi I’m serious Abokina.. Ai kasan ban tab’a zuwa maka da magana makamancin wann ba. Ba irin k’ok’arin da bakayi ba ganin na sake aure Tun bayan da na rasa iyalina amma banyi ba. Yau nazo maka da irin batun da kake son ji kana nema ka k’aryatani.” Daddy ya girgiza Kai “Ni ba k’aryataka zanyi ba amma matar d ka d’auko d’in ne ban tsammaci haka ba. Bayan kasancewarta k’aramar yarinya ka fad’a mun ta Ya zamuje muna zubda gwiwoyin mu a yanda Haidar keyi. Ta ina zamu fara jera kafad’a muna surkunta a yanda Haidar keyi.?” Alhaji Gimba Ya murmusa yace “Abokina kenan. Naga dai ba haramci cikin abinda nake son aikatawa sai alkhairi in sha Allah. Sann Tafiyar Haidar daban namu daban.. Kaman yanda kaje ka nemo ma Haidar haka zaka tafi a nemo min matuk’a na samu yarda da amincewar yarinyar. Daddy ya girgiza Kai yana fad’in “Gaskiya Gimba ni baza’ayi wann kayan kunyan dani ba. Kaje can ka nemi aurenka ba hannuna.” Alhaji Gimba Ya dan dara yana kuma fad’in lallai sai Daddy ya shige masa gaba a neman auren da yake. Washe gari ta kama ranar taron sunan Baba Ali da Kakaninsa na Abuja suka shirya. Sann ranar mutanen SouthAfrica wato Hisham da Anisa ke dawowa gida Nigeria. Hisham Ya kaikaito Ya dubeta sanda jirginsu Tai landing a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport. Shu’umin murmushin nan nasa ne saman fuskarsa “Mai ciki. Tashi ki daina baccin haka mun iso.” Wani Uwar harara Anisa ta watsa masa tana jin kaman wani haraswan zata kuma dan tayi amai cikin jirgin yafi sau uku. Huci take tana fad’in “Na tsaneka Hisham..! Allah ya isa fyaden da ka dinga mun.!” Hisham yaci gaba da murmushi yana shafa hab’arsa “Daga baya kenan… Na Miki na k’arfi sau d’aya amma duka sauran da yarda da amincewarki akayi..!” Cikeda gargadi yaci gaba “Kuma bari kiji na fad’a Miki wllhi kikayi gigin cire cikin nan ko kika bari wani abu ya samu cikin nan..!” Sai ya girgiza Kai yana dubanta “I don’t know what I might do to you Anisa.!” Murmushin takaici Anisa take tana dubansa “I can’t believe I’m three months pregnant with your child Hisham. A monster like you bai cancanci zama mahaifi ba.!” Murmushi Hisham ya kumayi yana dubanta kafin ya sakalo hannunta cikin nasa “You won’t do anything foolish Anisa..! You will face them and act cool..!” Ya k’arashe yana mai finciko hannunta suka nufi arrivals. Can ya hangi Mota mai d’aukeda plate number na Company d’insu. Ya rik’o hannunta yana fad’in our ride is here. Babu wata wata suka shige bayan motar Hisham na kuma jero ma Anisa warnings. Tana fad’in yayi kad’an ya sakata yin abinda batai niyya ba. Haka akaita shera gudu dasu sai masifa suke tsakaninsu sam bama su kula da waye driver din nasu ba dan p cap ne akansa. Saida akai nisa sukaga driver ya canza hanya ya d’auki wani hanyar.. Hisham ya fara fad’in “Lafiya..? Wane hanyar kake bi.. Hey who are you.. Why can’t you turn back..!” Hisham ya k’arshe yana k’ok’arin fizgoshi saidai tuni driver d’in ya murda AC din motar take wani abu kaman hayak’i ya gauraye cikin motar. Suka soma tari gaba d’aya idan ka d’auke driver d’in da hancinsa ke rufe da nose mask.. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *62* *©️Sameena Aleeyou… * "Suna zaune gaba d’aya parlorn Hajja a sama, hira suke na yaushe rabo cikeda nishad’i. Ga gidan tuni Ya soma cika sakamakon taron da zaayi da yamma. Dan har wasu dangi daga Maiduguri Sun samu hallara. Koda Haidar Ya Lek’a yaji hayaniyar mutane sai bai haye saman ba yai zamansa a parlorn k’asa. Wayarsa ya Ciro Ya tura mata sak’o." Ana tsaka da hira sak’on Haidar ya shigo ma Ummul. _I’m hungry_ Ta karance sak’on sai ta soma waige waige. Ta tura masa reply _Where are you_ Ya mayar mata da amsa _Downstairs.. Waiting for you_ Mik’ewa Ummul Tai da zummar barin wajen Salima tace ina zata suna tsaka da hira. Ummul ta d’an juya ido tana mata alama da k’asa. Badia tai gyaran murya tace “Haba Aunty Salima sai kin mata tonon silili ne. Wajen Oga Haidar zata.” Salima ta jinjina kai “Haka kuma. Toh a dawo lafiya..” Murmushi kawai Ummul tai tasa kai ta fice. Tana ficewa kuwa Salima ta dawo kan Azeema tana fad’in sai ta fad’a meke tsakaninsu da Sadis d’in can. Nan Badia ta saka baki tana fad’in itama ta kula tsaf da su biyun. Azeema kaw sai cewa take ita ba komai tsakaninsu fah sai mutunci. Ita dai Khulsum kallonsu kawai take jikinta duk a sanyaye ba tareda tasan dalili ba. Bata san meyasa ba amma haka kurum taji tunaninsa Ya zo mata. Tinda ya koma makaranta bata sake ji daga garesa ba. K’ila ma Ya mance da ita. Saurin kwaban zuciyarta tai da fad’in ‘Toh ke ina ruwanki dashi.. Meyasa zakiyi tunaninsa Har haka.. Ya mance da ke kema ki mance dashi.’ Saurin mik’ewa Tai ta bar wajen cikin k’ok’arin kawar da tunanin. A parlor Ummul ta iske Haidar. Sanye yake da jampa ruwan k’asa harda hula. Ya turo hular saman fuskarsa had’ida kishingid’a cikin kujeran. Tai tsaye tana dubansa murmushi saman fuskarta. A hankali take takowa Har ta iso kusansa. K’amshin ta ne yai masa Sallama. A hankali yasa hannu Ya janye hular. Ya bud’e lumsassun idanunsa yana dubanta. Tayi kyau cikin leshi golden brown color. Dinkin sosai yai mata kyau Ya zauna jikinta kaman wacce bata jima da haihuwa ba. Ya bud’e mata hannayensa daga nan yanda yake kishingide “Come here.” Ta d’an fito da ido tana dubansa. Sai ta soma ‘yan waige waige. Haidar yace “What..! Taho mana.” Ta d’an langab’e kai kad’an “Wasa kake.. Ka mance ina muke ne.” Gyara zamansa yai kad’an had’ida furta “Fine.. Kin sama min mai zanci.?” Yai maganar yana mai janyo hannunta. Ta d’an girgiza kai “Gidan gaba d’aya cike yake.. Barin kira kitchen naji mai suke dashi.” Tabe baki yai kad’an “Banson abincin Chefs din gidan nan.. Sun Faye cika yaji…” Ta d’an marairaice fuska “Toh ya kake so ayi Rankaidade.? Mu fah bak’i ne a nan. Kai hakuri kaci haka.. Idan munje gida sai na girka maka abinda kake so.” Cikin sigan lallashi take maganar. Sosai suka birge Hajja har taji dama bata sauko parlorn ba dan kar ta katse musu soyayyarsu. Ummul ta d’an matsa baya kad’an daga kusan Haidar tana ma Hajja sannu da sauk’owa. Haidar ma gaisar da Hajja yai kafin daga bisani Hajja ke musu tayin Burabusko miyan taushe da ta dafa ma Daddy. Ta k’arashe tana fad’in Ummul ta taho ta kawo ma Haidar. Haidar ya dan shafa kansa kafin ya katse hanzarin da fad’in “But.. I don’t eat Burabusko..” Hajja ta dan murmusa tace “Lallai kace zamu maida Kai Yerwa Haidar. Ya zaace Kanuri bai cin Burabusko.? Kuma naga favorite din Daddy kenan. Ya kamata ace ka iya ci.” Daga k’ofa suka sinkayo murya na fad’in “My brother is more Shuwa arab… Abincin larabawa yake ci.” Gaba d’aya suka waigo suna duban mai maganar ba kowa bane illa Hilal.. Ya kara girma da k’warjini kaman ba shi ba. Ya k’araso cikin parlorn yana gaida Hajja da Ummul lokaci guda Ya k’araso ga Haidar suka gaisa Hilal na hugging d’insa kad’an na yaushe rabo. Hajja ta shige ta basu waje abinta bayan tayi ma Hilal lale da zuwa. Haidar ya dubi Hilal “Kai kuma daga ina kaman an jefo ka.?” “Daga gida Kano.. Tare muke da Ammi.. I arrived in the country yesterday.” Haidar ya jinjina Kai yana tambayarsa ya sch. Allah sa dai ya tab’uka abin arziki wann karon. Ya k’arada “Kasan ban tab’a ganin unserious human being irinka ba. Gaba d’aya baka d’auki rayuwarka da mahimmanci ba Hilal.” "Hilal ya Dara kad’an “Sanin da ka mun da ne D’anuwa. Well, I can finally say it with full chest.. I’m a graduate now. Kana magana da cikakken accountant ne a nan.”" "Jinjina Kai Haidar yake yana dubansa “Idan gaskiya kake fad’i, I’ll hire you.”" Suka dan murmusa gaba d’aya. Hilal na fad’in Lallai shi D’angata ne gashi daga dawowa ya samu aiki. Ummul da ta b’ace b’at kaman bata a wajen muryar Hajja ta sinkayo tana fad’in maza ta taho ta shige kitchen dinta dake bangarenta ta samar ma Haidar abinci. Dan ta kula kaman abincin matarsa yake son ci. Hilal yai karaf ya dakatar da Ummul da fad’in “Addarmu ina Baby yake.? Ni fah shi nazo gani.. Naji ance takwara akai ma Yaya na Haidar. Meyasa ba’a min ba. Haidar ya dalla masa harara “Waye zai maka takwara.? Ba dai ni Haidar ba.” Hilal na murmushi yake Shafa Kai “I’m a changed person fah.. Zaka sha mamaki. Ni fah yanzu na zama responsabile Human being.. Na jima da daina sallah ba alwala..” Haidar ya kuma aika masa wani duba dan baiso a d’ago yarintar su gaban Ummul. Murmushi Ummul take tana fad’in bari ta kawo masa yaron. Saidai kafin tai shiru ta hangi su Khulsum dasu Badia suna sauk’owa downstairs ga Baba Ali cikin hannun Khulsum d’in. Sam Khulsum bama ta kula da mutumin dake zaune gefen kujeran Haidar ba. Shi kaw Hilal mutuwar zaune yai yana dubanta. It’s been long.. So long rabonsu da su saka juna a ido.. Ta k’ara masa girma da kyau.. Saidai ya hangi wani abu mai Kama da salihanci saman cute grumpy face dinta. Sam bata kula ba sai wasa take ma Baba Ali. Bataji sanda Ummul ke introducing Hilal masu Aunty Salima. Bata Ankara ba sai sinkayo muryarsa tai yana fad’in “May I please.. see him..” Cak ta dakata da abinda take bugun zuciyarta na k’aruwa. Ta ina zata mance muryarsa. Ta d’ago a hankali tana dubansa. Shi d’in ne dai.. Saidai wann karon ya k’ara mata girma fiyeda sanin da tai masa a baya. Wann sumar tasa mai laushi da tsantsi irinta asalin k’abilar shuwa arab ya tara shi wann karon. Harda jiki ya k’ara saidai girman yasa ya k’ara duhu kad’an. Har Hilal ya amshi Baba Ali daga hannunta bata dawo daidai ba. Sam bama ta kula har su Azeema Sun wuce sashen Mommy ba. Gaba d’aya sai ta daburce.. Ga Hilal kusan k’ofa yake tsaye rik’eda Baba Ali yana fad’i ma Haidar yaron dashi yake kama ba da Haidar ba. Harda cewa za’a basa yaron he’s his Godfather. Ai kawai sai Khulsum tabi bayan Ummul ta nufi kitchen. Ummul ta dubeta da mamaki yanda ta shigo duk a daburce “Ke kuma fah.? Mai kikeyi a nan.. Na zata kun tafi sashen Mommy gaba d’aya..” Kasa amsata Khulsum tai sai ma dibi dibi da take. Ummul dai d’an tabe baki tai kadan Ta d’auko carrots zata pilling Khulsum tai karaf ta amshe tana fad’in zata fere mata. Ummul ta tsareta da ido yanda take komai sauri sauri ba natsuwa. Ta aje chopping board din dake hannunta tana kuma tsare Khulsum da ido “Khulsum.” Ta k’ira sunanta cikeda kulawa. Khulsum ta amsa tana dubanta. “Fad’a mun.. Meke faruwa ne.?” Khulsum ta d’an girgiza Kai “Ba.. Ba komai.. Mai kika gani Adda Ummul.?” Ummul ta jinjina Kai “Idan zaki b’oye ma wani nidai kinsan bazaki b’oye min ba.. Ki fad’a min meke faruwa.?” “Da gaske ba komai fah Adda Ummul..” Daidai lokacin suka soma sinkayo kukan Baba Ali daga parlor. Ummul ta zame apron din dake jikinta tana nuna Khulsum “Ni dake bamu gama ba.. K’arasa fere mun carrot d’in ki yankasu k’anana ina zuwa.” Daga haka Ummul ta fice sauri sauri. Ta tadda Hilal ya mika yaron ma Babansa yana fad’in ya kamata ya sanshi dan shine Godfather d’insa. Ba maganan k’iwa tsakaninsu. Haidar ya amshe yaron yana fadin “Come to Paapa.” Ya shiga jijjiga yaron yana fad’in yai shiru Maama is here. Daidai sanda Ummul ta zauna gefen Haidar tana k’ok’arin amsar yaron. Yanda gaba d’aya attention d’in iyayen ya koma kan yaron sosai hakan ya birge Hilal ya kuma basa sha’awa. Sai ya dan murmusa yana k’ok’arin barin parlorn. Hanyar da yaga ta nufa yabi. Nan ya hangeta tsaye cikin kitchen din tana dicing carrots. Ya jima yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa kafin Ya soma takowa cikin kitchen din a tsanake. Sam bataji alamun mutum ba sai taji gyaran murya daga bayanta yana fadin “Hello.. Excuse me..” Ta dan razana Wanda hakan ya sata saurin aje knife d’in da take yanka carrots din dashi had’ida rintse idanunta alamun ta razana. Hilal ya dan leko yana duban fuskarta. Murya a hankali yace “Sorry..! I didn’t mean to scare you.” Huci Khulsum keyi ba tareda ta dubesa ba. Lokaci guda tana dunk’ule knife din cikin hannunta. A fusace ta waigo tana fad’in ya kuwa bazataji tsoro ba mutum yana shiga waje ba Sallama kaman goyon yahudu. Tana maganar a fusace tana juya wuk’ar dake cikin hannunta. Kallon yanda take juya wukar kawai Hilal yake ya d’ago hannayensa sama alamun surrender lokaci guda yake jada baya yana fadin “Easy.. Easy..!” Yanda yake ja da baya kaman zai auna a guje sai ya kuma tsorata Khulsum. Ta soma waigawa baya tana duba mai ya gani yake shirin guduwa. Hilal bai daina jada baya ba ai kawai sai itama ta nufo k’ofa a guje dan ta zata wuta ne ya gani a kitchen din ko wani abu mai Kama da haka. Kafin tai aune Hilal ya tare k’ofan kitchen d’in wanda hakan ya hanata k’arasawa. Bai daina nunata ba bai daina daukan saiti na gudu ba bai daina furta easy ba. Ta kuma waigawa cikeda tsoro wann karon “Wai meye ne.. Meye ka gani.?” Ya nuna mata hannunta mai rik’eda knife “Pleae keep that away..” Yai maganan yana rik’eda k’ofar kitchen din gam. K’afarsa d’aya na waje d’aya na kitchen din. Sai ta d’ago wukar dake cikin hannunta tana kallo. Gajeren tsaki tai had’ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ta koma bakin aikinta. Hilal ya murmusa kad’an kafin ya kuma takowa gareta. Wann karon Sallama yai. Kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa da kyar. Hilal ya k’arada “You haven’t changed a bit.” Ya fad’i da murmushi saman fuskarsa. Bata ko dubesa ba balle ta kulasa. Saima ci gaba da tai da abinda take. Ya dan langab’e Kai yana dubanta “Wai ko darajan gaisuwa bazan samu ba balle sannu da zuwa.?” Ta dan dubesa a dak’ile sai ta tabe baki had’ida janye idonta “Wanda yai Sallama idan zai tafi shi ake ma sannu da zuwa.” "Hilal ya dan murmusa dan ya tuna sanda zai tafi bai mata sallama ba. Dikda lokacin itama tana Jigawa gidan Inna Dije amma ko a waya bai kira ya sanar da ita tafiyarsa makaranta ba. Sann tinda ya tafi bai sake nemanta ba. Alk’awari yai ma Kansa zai natsu yai abinda ya kaisa once and for all ya k’arasa karatunsa ko dan ya share hawayen Amminsa ya kuma tabbatar ma Abbansa bazai sake asaran kudi Akan karatunsa ba. Above all, zaiyi ne ma Kansa ta yanda idan yazo ma Abbansa da batun Aure zai tsaya ya sauraresa." Gyaran murya ya d’anyi yace “Lallai ban kyauta ba amma kiyi hak’uri.” Ya d’anyi shiru kafin ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da ya haifar mata da sanyin jiki. “Khulsum.” Ta d’ago ta d’an dubesa. Hilal yaci gaba “Tafiyar da nai ba Sallama yanada dalili wanda nasan idan muka samu time na miki bayani zaki fahimta.Ki yarda Dani nayi hakan ne for us.” "Sai ta d’an kuma dubansa. Yayinda Hilal yaci gaba da jinjina Kai “Believe me, Ban manceki ba daidai da dak’ik’a guda. A koda Yaushe kina nan a nan..!” Ya k’arashe yana nuni da b’angaren k’irjinsa yanda zuciyarsa take bugawa. Yayinda Khulsum taci gaba da dubansa jiki a sanyaye. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Hilal yaci gaba “I never stopped loving you my cute cute miss grumpy.!”" Daidai lokacin sukaji alamun ana shigowa kitchen d’in. Khulsum tai saurin juyawa tana ci gaba da yanka carrot din sanda Ummul ta shigo kitchen d’in. Shi kaw Hilal saurin daukan glass cup yai yana fadin “I.. I will have a glass of water.!” Ya k’arashe da murmushi yana daukan ruwan gora dake wajen. Ya dubi Khulsum ya kashe mata ido yayinda Khulsum d’in ma ta bisa da wani kallo sihirtaccen murmushi saman fuskarta. Ita dai Ummul dubansu kawai take. Ta dubi wann ta dubi wancan har Hilal ya fice sai waigowa yake yana duban Khulsum. Bayan Hilal ya fice Ummul ta tsare Khulsum da ido wacce ke ta faman sakin murmushi a hankali. Ummul tai gyaran murya tace “Toh ai ya fice sai ki daina wann murmushin da kike.” Khulsum ta dan zaro ido “Na’am Adda Ummul..!” Tsareta Ummul tai da ido sai ta murmusa tana aje Kayan miyan dake hannunta cikin roba a sink “Zama kimin bayani ne dalla dalla yarinya. Bari dai mu k’arasa da kitchen din nan.” Dan darawa Khusum tai tana fad’in “Adda Ummul ba fah abinda kike tunani bane.” Ummul tace “Toh ni mai kikaji nace.. Kin Kama kanki tin baaje ko ina ba yarinya..” Khulsum ta sanne Kai tana dariya. Bayan Sun gama girkin ne kuma suka soma shirin shagalin. Tuni masu kwalliya Sun iso sunyi mata light make-up da ya matuk’ar mata kyau. Shima Haidar d’in saida ya k’ara shiryawa sabida pictures da zasuyi da jariri. Haka kowa ya dinga santinsu dan ba k’aramin kyau sukai ba. Daga bisani Ummul da jaririnta sukaita hotuna da ‘yanuwa da abokan arziki. ** Wasa wasa har rana ta kusa k’arewa su Hisham basu iso ba. Har akaci taron shagalin suna aka watse basu Anisa ba dalilinsu. Izuwa lokacin hankulansu ya soma tashi dan tuni anyi conforming jirginsu ta jima da landing. Ana haka wayar Sadis ya shigo ma Daddy yanda yake sanar da Daddy sun kalla daga security footage na airport Hisham da Anisa Sun shiga wata mota mai d’auke da fake plate number na Kampaninsu. Akwai possibility din kidnapping dinsu akai daga Airport. Daddy yaci gaba da karanto Innalillahi wa inna’ilaihi ilairaji’un. Daidai lokacin da su Hajja da Mommy harma da Aunty Asshe suka shigo parlorn a kid’ime dan tare Sadis da Hilal suka tafi airport binciko abinda ke faruwa kuma tuni Hilal ya kira mahaifiyarsa yayi updating d’inta. Aunty Asshe kuka kawai take tana fad’in anyi kidnapping su Anisa ne dan ance tun rana jirginsu ta sauk’a ga kuma shaida wani mota da ba’a tantance ba ya d’auke su. Kwantar musu hankali Daddy keyi da fad’in in sha Allah ba komai dan idan ma kidnappers ne dole zasu kira su nemi ransom kuma ko nawa sukai demanding zai bayar dan ya ceto yaransa. Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy “Na tabbata this is one of his games Daddy.. There’s nothing like kidnapping here.. Hisham shi ya shirya wann wasan kwaikwayon. And he used Anisa as a bait.!” "A fusace Daddy ya daka masa tsawa da fad’in “Ka rufe mun baki Haidar.!” Cikin b’acin rai Daddy yaci gaba “Your brother is kidnapped.. Ba shi kad’ai ba harda iyalinsa wacce ta kasance Yaruwarka.! And you are here blabbing nonsense..!” Yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar cikin rashin yarda “For once in your life Aliyu, call a truce with your brother.! If you can’t do anything to help. Then just shut your mouth and get hell out of my house.! Fitar mun a gida nace.!” Ya k’arashe yana nuna ma Haidar k’ofa cikin tsananin b’acin rai." Idanun Haidar Sun kad’a sunyi ja yake duban Daddy. Meyasa Daddy bazai yarda dashi ba.! Meyasa idonsa ya rufe Akan d’aya D’ansa.?! Ya soma girgiza Kai yana jada baya lokaci guda ya fice daga parlorn kaman zai kifa. Mommy tabi bayansa da kallo tana kiransa amma inaa bai tsaya ba. Hajja kaw tashin hankalinta ne ya ninku. Duk yanda taso ta hana zuciyarta yarda da abinda Haidar ke fad’i gameda D’an nata meyasa taji yau d’in kaman ta yarda da Haidar. Addu’a take a cikin zuciyarta Allah yasa Haidar kuskuren fahimta kawai yake ma D’anuwansa. Allah ya bayyana Hisham da Anisa cikin k’oshin lafiya ya warware komai ya kuma kawo k’arshen matsalolin Ahalinsu. Haidar na fitowa sashen Mommy ya nufa kaman zai kifa. Ya shige su Salima a parlor Wanda tuni suma sunyi jigum jigum dan sunga ficewar su Mommy dasu Aunty Asshe hankali tashe. A d’aki ya iske Ummul tana bama Baba Ali nono. “Tashi mu tafi.!” Ya fad’i babu walwala. Ta dan dubesa da mamaki. Dan tin shigowarsa bata gane yanayinsa ba. “Ban.. Ban gane ba.. Na tashi mu tafi kuma.? Amma meyasa zamu tafi yanzu.?” “Kar ki bata mun rai Khairy.! Ki tashi nace mu tafi.!” Ya kuma fad’i cikin tsananin b’acin rai. Itakam sai taji k’walla na zuwa mata. Ga Baba Ali da tuni ya rigata fara kuka ciresa da tai yana tsaka da shan nono. Haidar ya amshesa ya izasa bisa kafad’a “Ki same mu a mota.. Kar ki bata lokaci.!” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa. Mamaki da tsoro suka cikata. Haidar ya juye mata tashi daya. Tasan bai iya fushi ba amma mai ya bata masa rai irin haka. Toh kodai ta masa laifi ne.? Bata ida tunanin ba ta sinkayo sautin horn kaman zai daga gidan alamun ita yake jira. Kuka ta fashe dashi tana mai zira mayafinta. Koda ta nufo k’asa hankulan su Khulsum bai ta b’angaren da take. Hakan yasa ta nufi k’ofa tana danne kukanta. Khulsum da ta hangeta tai saurin mik’ewa ta nufeta tana ambaton sunanta. Bata iya amsa ta ba sai kawai tasa Kai ta shige cikin sauri wani kukan na kuma zuwa mata. Hakan ya janyo hankulan sauran ‘yanuwan . Wann ta kalli wann wancan ta kalli wann gidan dai da alama ba lafiya. Aunty Asshe ta fice tana kuka.. Su Mommy sun fice hankula tashe yanzu ga Ummul ta fito tana kuka. Badia ta rapka tagumi tana fad’in “Oh ni Badi’atu yau meke faruwa ne a gidan nan.?” Salima tace “Gaskiya ba lafiya.. Toh amma meke faruwa ne.?” Badia ta tsaida wata ma’aikaciyar gidan tana tambayarta meke faruwa a gidan. Matar ta girgiza kai tace “Naji securities da suke gate suna cewa yaron Alhaji da zai dawo daga SouthAfrica aka kidnapping together with his wife Anisa.” Azeema ta saki baki tace “Anisa dai.?” Sai ta rangad’a guda tana fad’in Alhamdulillah an gama taro lafiya ba Anisa dan ta iso kafin a gama taron da ta wargaza komai. Salima ta girgiza Kai tace “Kedai bazakiyi hankali ba Azeema. An ce Miki an sace mutane kina shewa. Toh gashi bata zo d’in ba amma taro ya tashi ba dad’i. Ki gaya min hankalin waye ke kwance.?” Azeema ta tabe baki tace “Wllhi Anty Salima dan dai baki zo bane lokacin bikin tariyar Ummul da ke kanki sai kin tsani wann anisar.” Salima ta girgiza Kai “Toh yanzu dai duk ba wann ba. Mu had’a hannaye mu tayasu da addu’a Ubangiji ya bayyanasu cikin aminci.” Suka amsa da Ameena gaba d’aya. ** Koda suka isa gida a d’aki ta k’ule tana share share hawayenta bata bi takansa ba. Har saida ta soma sinkayo kaman muryoyi daga parlorn. Hilal yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar “I just don’t get you Haidar.. Kasan bazan iya abinda kake fad’i ba. Anisa ‘Yaruwata ce and she’s been kidnapped.. I can’t just sit back and do nothing.!” A zafafe Haidar ya katsesa “Well Anisa ita ta jefa kanta cikin mess d’in nan.. I warned her not let that maniac use her.. but what did she do.?She went ahead and married him.. Now she’s trapped. Dama na fad’a amfani kawai zai da ita. Ni na tabbata ba kidnapping dinsu akai ba. Hisham zai iya shirya komai ta yanda Zai looking kaman sace su akai dan ya cimma wani manufa nasa.!” Hilal yaci gaba da girgiza Kai yana duban Haidar “Ya kake magana kaman ba Nigeria muke ba. Yanda satan mutum ya zama ruwan dare.? Mai zai faru idan real kidnappers ne suka d’auke su.?” "“Tell me akwai abinda zaka iya yi ne idan ma sacesu d’in akai.? Ka fad’a mun zaka iya tracking motar da suka shiga..? Tell me, Did the kidnappers call.? Did they ask for ransom.?” Yaci gaba da girgiza Kai yana duban Hilal “ Babu ko d’aya Wanda hakan yake tabbatar da wasan Hisham ne kawai.! That imbecile is using Anisa as a bait.! I warned her from the very start amma tak’i taji. She thought she could outsmart him.!”" "Hilal ya furzar da huci yana girgiza Kai “Kai hakuri brother, a wann b’angaren Nima ban yarda da kai ba.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice cikin sauri." Juyowan da Haidar zai ya hangi Ummul tsaye bayansa tana hawaye. Lokaci guda itama take girgiza kai “Da gaske ne.? Da gaske ne an sace Yaya na Hisham da Anisa.?” Cikin huci yake furta “Kar ki sake kiran wann D’aniskan Yayanki. He’s nothing to you.!” Taci gaba da zuban hawaye “Meyasa kake nuna masa k’iyayya irin haka.? Meye ya maka da tsanani.? Shid’in fah D’anuwanka ne.. Kan wani dalili kake masa irin wann kiyayyar.?” Cikin huci ya juyo yana dubanta “Do you want to know the reason.? Kece Khairy.. That maniac is obsessed with you.! Do you know that.!” Ta soma girgiza Kai tana dubansa “Baka fahimta bane.. Na san shi tun kafin na aureka amma babu komai tsakaninmu.. Ya taimaka min a wajaje da dama taimakon da bazan tab’a mancewa ba. Shi d’in mutumin kirki ne bai kamata ka masa irin wann mummunar fahimtar ba.!” Cikin kuka take maganar. Yaci gaba da jinjina kai yana dubanta da idanunsa da suka rine “Ya aikata duka abinda ya aikata Miki ne for a reason. And that’s to win your heart. And he’s doing what he’s doing now for a reason. To separate us.!” Taci gaba da zuban hawaye tana girgiza Kai “Meyasa kake fad’in haka.?! Meyasa kake furta wani yana sona.! Of all people D’anuwanka.! Ni fah matarka ce.!” “You too don’t believe me. Do you.?” Ya tambaya yana dubanta cikin sanyin jiki idanunsa na kuma rinewa. K’arasowa tai kusansa ta kamo hannayensa “My love.. Please don’t misunderstand me.. You are being paranoid for no reason. You are being jealous for no reason.. Hisham is your Brother.. And he’s married to your cousin now.. Hisham bazai taba irin tunanin da Kai kake ba. Shed’an ne kawai yake raya maka haka dan baiso ku samu daidaiton fahimta da D’anuwanka.!” Murza hannayensa yake yana huci “Kema baki yarda dani ba Khairy..! Kin zab’i ki yarda da wancan banzan sama dani.! Haka ne.?!” Ya k’arashe yana dubanta. Ta dan furzar da huci zata kuma kamo hannayensa ya dakatar da ita “Get out Khairy..!” “Amma..!” “I said get the hell out of my sight.!” Ummul taci gaba da girgiza Kai tana hawaye “Why do I feel like I don’t know you.! Meyasa bazamu samu daidaiton fahimta ba.?” “Idan Akan wann banzan ne ni da ke bazamu tab’a samun fahimta ba.!” Izuwa wann lokacin sosai take hawaye tana dubansa. Cikin murya irinta mai kuka taci gaba “Idan duk abinda kake zargin Hisham dasu gaskiya ne maiyasa bai ida nufinsa akaina ba lokacin da ya samu dama.?! Ya taimaka min a lokacin da ka cika wa’adin AUREN WATA UKU...! Ya bani shelter a lokacin da na fice daga gidanka bansan wajen zuwa ba.! Ya kaini ga mahaifiyarsa a lokacin da na kasa tunk’aran nawa mahaifiyar.!” “Khairyyy.!” Haidar ya dakatar da ita da fad’in haka har ruwa na fita daga idonsa. Yaci gaba da nunata da yatsa “Kar ki sake maimaita min kalmar AUREN WATA UKU..! Kar ki sake jingina abinda ya faru tsakaninmu da wann D’aniskan.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga gidan a fusace. Duk’awa Ummul tai wajen sabon kuka na zuwa mata. * Yana ficewa bai zarce ko ina ba sai wajen Sadis. "Sadis ya dan shafi fuskarsa da tafukan hannayensa “Kai ma Daddy uzuri Haidar, Shi har yanzu gani yake yayi failing Hisham as a father. Har yanzu gani yake bai biya Hisham ba.”" Murmushin da yafi Kama da takaici Haidar yai “Growing up as a Maitama has never been easy.. Idan akan wann sunan ne naso ace shi ya girma as Maitama ba ni ba.!” Sadis ya dan furzar da huci “Amma Maganarka zai iya zama da k’amshin gaskiya Haidar. Hisham zai iya sakawa a sacesu shida Anisa idan duk ya aikata abubuwan da suka faru a company ba tareda an ganosa ba” Haidar ya jinjina Kai “My point exactly amma cikinsu ba Wanda ya fahimta. Meyasa Hisham ya dage zai cire Anisa daga mess d’in da shi ya jefata ciki.? Idan ba yanada wani babban shiri ba bazai tab’a amincewa ya auri Anisa ba. Ya wuce duk yanda mutum yake tunani.. Amma koma menene shirinsa ka yarda dani Sadis sai na kawo k’arshen k’aryarsa.” Sadis ya dan furzar da huci “How do you plan to do it.. Ina nufin har yanzu babu wani call ko wani abu mai Kama da haka.” Jinjina Kai Haidar yake “I don’t know how.. But I’ll surely bring hm down.. ka yarda dani Sadis. Zanyi unmasking Hisham.!” Ya k’arashe yana jinjina Kai alamun tabbatar da kalamansa. Wayar Sadis ne ya soma ringing. Sai ya d’anyi excusing Kansa ya matsa yana amsa kiran. Bayan ya gama amsa kiran ya dawo ga Haidar. Ya d’an furzar da huci kad’an yace “That was Azeema. Tambaya take gameda case d’in.. Duk hankulansu a tashe yake.” Jinjina Kai Haidar yai “Could you do me a favor.” Sadis ya jinjina Kai “Ina sauraronka.” Haidar yaci gaba “I’ll stay here tonight.. Ka Kai mata sisters dinta gidan..Tana buk’atar su kusa da ita.” Jinjina Kai Sadis yai yana fad’in zai k’ira Azeema ya sanar da ita. ** Washe gari Sadis ke sanar da Haidar ba wani developments gameda case d’in bacewar su Hisham. Har yanzu ba wani k’ira ko wani abu mai Kama da haka daga kidnappers d’in. Jinjin Kai Haidar yai kad’an “I wonder what that maniac is planning.” Bai Kai aya ba wayarsa ta soma ringing. Ganin ba suna yasa shi juya wayar cikin hannunsa. Har ta kusa tsinkewa sann ya d’aga. Cikin wane irin murya mai gauraye da tashin hankali ya sinkayo muryar Hisham yana fad’in “Haidar you need to help me.! Help my wife.. And my unborn child..! Zasu kashe mu.. Dan girman Allah ka basu duk abinda sukai demanding brother.. Please.!” Girgiza Kai Haidar yake cikeda mamaki dan tuni an katse wayar d’if. Ya soma dialing layin amma bata zuwa. Sadis ya dubesa “Lafiya.?” Haidar ya d’ago yana duban Sadis “It was.. Hisham.. I clearly heard his voice Sadis.” Sadis ya girgiza Kai kad’an “Did he say something.. Maybe abind ya samesu ko yanda suke.?” Girgiza Kai Haidar yai yana duban Sadis d’in “Cewa yake zasu kashe shi.. Zasu kashe Anisa da unborn child dinsu..” Sai ya girgiza Kai had’ida sakin murmushin takaici “I knew I was right.. Ba wani abu mai Kama da kidnapping a nan. D’aya ne daga cikin wasannin Hisham. Cewa yake na bama kidnappers d’in whatever they demand.!” Ya mike yana huci “I told you Sadis.. Hisham is playing a game here.! Idan da gaske sacesu akayi meyasa ba’a kira Daddy ba aka kirani.? How does this make sense.?” Sadis ya girgiza kai “Amma meye demand d’in nasu.?” Haidar ya girgiza Kai “Ya kashe wayar bai fad’i wani demand ba.” Kaman jira kaw suke nan wayar Haidar ta kuma ringing da wani layi. Muryar Anisa ya sinkayo wann karon “Haidar..! Dan Allah kazo ka ceceni.. Zasu kashe ni wllhi.. I’m bleeding already.. Haidar I’m pregnant.!” “What.!” Ya furta a hankali kafin yace “Anisa don’t let him use you. Just tell me what’s going on.? Ina Hisham ya kaiki..? Meke faruwa.?” Muryar wani Mutumi ya sinkayo wann karon “Don’t act foolish Engr.! Do not involve anyone in this matter.! Ba ‘yansanda ba ba ahalinka ba. Ba kudin mahaifinka muke nema ba.! Kai kawai muke so ka kawo kanka.! Mun baka less than 24hrs idan baka kawo kanka zuwa adireshin da zamu tura maka ba komai zai iya faruwa da ‘Yaruwarka harma da abinda ke cikinta.!” Wani irin huci Haidar yake zufa na tsartsafo masa “Ta nan ka b’ullo Hisham.! Haw could you use Anisa as a bait.! Why can’t you confront me coward.! You don’t need to use anyone.!” “You have less than 24hrs.. Lokacinka ya fara kirgawa daga yanzu.!” Cewar mutumin. D’if yaji an katse kiran. “I’m going to end this once and for all.” Cewar Haidar yana mai mik’ewa a zafafe. Sadis ya taresa “Haidar wait.! Ka dakata. Ya kamata a fara sanar da gida sann ayi reporting ma yansanda. Bazai yuwu ka kai kanka ba dan kawai sun buk’aci haka. For all we know zai iya zama dakwai muggan makamai tareda su.” Murmushi yai yana jinjina Kai “This is my chance Sadis. Wann shine damata Akan Hisham.!” Ya k’arashe yana mai nufan k’ofa. Sadis ya kuma taresa “Toh idan kaje sukai trapping d’inka fah.? Burin Hisham ya cika na ganin bayanka. You need to think first Haidar. Kar Kai abu cikin gaggawa.” Jinjina Kai Haidar yake yana dubansa “I have a plan Sadis. And you will help me in carrying out my plan.! Bazaka sanar da kowa ba musamman ahalina. Idan na buk’aci backup kaida yansandan kunsan yanda zaku sameni.!” Ya k’arashe yana jinjina Kai. Sadis ma jinjina masa Kai yai kafin suka soma tsara yanda zasu tunk’ari lamarin. * Yinin ranan Haidar bai dawo gida ba bai kuma kira ba. Cikin zuban hawaye take duban Addarta Salima bayan Sun keb’e a d’aki. Yayinda Aunty Salima taci gaba “Duka laifin naki ne Ummul. Akan wani dalili zakiyi jayayya da mijinki kan wani daban. Ummul sufah maza ba son jayayya balle ma Akan wani namijin.” Cikin zuban hawaye Ummul ke girgiza Kai “Aunty Salima ni fah ba jayyaya nake dashi ba. Hisham fah D’anuwansa ne kuma yana auren ‘yaruwarsa Anisa.. Akan wani dalili zai dage Hisham sona yake.? Idan ma fushin ne ni ya kamata nayi. Maimakon yai tunanin yanda zai ceto ‘yanuwansa hannun azzaluman da sukai garkuwa dasu amma zuciyarsa sai ingizasa take Akan Hisham. Mutumin da babu wani abu na sharri da ya tab’a shiga tsakaninsu tun suna a matsayin abokai kafin su fahimci su d’in ‘yanuwan juna ne.” Sauk’e ajiyan zuciya Salima tai “Yanzu dai addu’a kawai shi zamuyi Allah a bayyanasu cikin aminci ya kuma warware duk wani abinda ya shige duhu.” Ta janyo mata plate din abinci tana fad’in taci abinci haka nan tin Daren jiya bataci komai ba. Yaronta zai buk’aci abinci idan bataci ba shima bazai samu ba. Da lallama Salima ta tasa Ummul gaba kafin ta samu ta saka abinci cikinta. * Bayan la’asar Hidar ya shigo gidan da sallama. Yanda ya tadda Duk yanuwan nata suna parlor idan ka d’auke Salima dake kitchen. Ga Baba Ali hannun Azeema. Suka gaisa da sakin fuska. Sann suka masa jajen bacewar su Anisa da addu’an Allah ya bayyanasu. Haidar ya amsa da Ameen yana amsan Baba Ali dake hannun Azeema. Nan yake tambayarsu Khairy fah.? Azeema ta basa amsa d fad’in tana ciki. Jinjina Kai yai kafin yasa kai ya shige sai wasa yake ma yaron. Saida ya tsaya a k’ofan kitchen suka gaisa da Salima da sakin fuska harda ‘yar zolaya yake mata yau Addar tasu ce da kanta a kitchen. Salima kaw ta d’an murmusa kafin itama ta masa jaje. Da haka ya nufi upstairs wajen Ummul rungume da D’ansa. Sanda Haidar ya tura k’ofan d’akinta ya tadda tana saman darduma alamun tana sallah. Ya zauna daga gefe har ta sallame. Bata juyo ta dubesa ba sann bata ko motsa daga yanda tai sallan ba. Yasan za’a rina.. Ya kwantar da Baba Ali saman gado kafin ya k’araso gareta. Rungumarta yai ta baya yana mai lumshe idanunsa. Itama d’in lumshe idanunta tai hawaye suka gangaro mata. “Take care of our Son Khairy.. Take care of yourself for me.. I love you both so much.!” Yana ida fad’in haka ya manna mata kiss a cheek dinta kafin ya isa ga Baba Ali daketa cilla k’afafu daga nan saman gado yanda yake kwance. Ya saki murmushi yana duban yaron “Maybe I named you Aliyu for a reason.! Allah ya maka albarka. Son.” Ya k’arashe yana mai sunbatan yaron. Yai tsaye yana duban Ummul da har lokacin hawaye take “Sadis zaizo ya kaiku gidan Daddy.. Ki kula min da Mommy.. Tell her that I love her.. Kuma ina neman yafiyarta..!” Ummul tai saurin waigowa tana dubansa ga hawaye na kuma ziraro mata. Shid’in ma ita yake duba. Bata san dalili ba sai taji illahirin jikinta yayi mugun sanyi. Ta nemi kalma d’aya a bakinta ta rasa. Sai taji kaman an d’aure harshenta.. Tanaji tana gani Haidar ya fice ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Aiko yana ficewa ta rungumi D’anta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. ** "Bayan sun had’u gaba d’aya parlorn Daddy. Mommy, Hajja, Aunty Asshe, Ummul, Hilal.. Harma da Daddyn Kansa." Daddy ya dubi Sadis da shgowarsa parlorn kenan. Jikin Sadis d’in duk a sanyaye. “Sadis what’s the meaning of this.? Meye manufarka na tara mu a nan..? Ka fad’a mun kidnappers d’in Sun kira ne.? Did they ask for ransom.? Tell me.. Nawa suka nema.?” Sadis ya jinjina kansa a hankali “Eh Daddy sun kira.” Daddy ya juyo ya dubi su Mommy Wanda suma gaba d’aya tashin hankali ya kuma bayyana saman fuskokinsu. “Ai sai ai gaggawan sanar da jami’an tsaro.. Nawa suka nema.?” Cewar Daddy muryarsa har na hadewa. Sadis ya girgiza Kai daga nan yanda yake tsaye “Ba kudi suka nema ba Daddy.” Da mamaki Daddy yace “Ba kudi suka nema ba.. Toh me suka nema.?” “Haidar..! Haidar suka nema.. Sun kirasa Sun buk’aci kodai yakai musu Kansa kodai su kashe Hisham da Anisa harma da jaririn cikin Anisar. Sann sunce kar ayi gangancin involving jami’an tsaro.” Girgiza Kai Mommy take zuciyarta na wani irin harbawa yayinda Ummul ta soma ganin parlorn na juya mata. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *63* *©️Sameena Aleeyou… * Ummul bata sake fahimtar komai ba sai tsintar kanta Tai jikin Hajja tana mata fifita saman fuskarta. Take ta soma tuno abinda ke faruwa. Ta tuna irin sallaman da sukai kafin ya tafi.. Sai tana ganin abin kaman ba a zahiri yake faruwa ba.. Ta kasa furta komai ta kasa motsawa Har lokacin bata ida dawowa hayyacinta ba. Tana jin k’irjinta na mata nauyi kaman an aje mata abu mai nauyi. Muryar Mommy ta da soma sinkayowa daga can b’angaren parlorn kasancewar parlor ne mai girma sosai. Hakan Ya kuma tabbatar mata a zahiri abin ke faruwa. Haidar ya kai kansa ma ‘Yantadda. Mommy fad’i take “Engr dan Allah ka dakatar dashi.. Ka dakatar da Aliyu.. Kar Ya kai kansa ma ‘Yantadda.. Wllhi zan bada nawa rayuwar fansar nasa.. Engr I can’t lose my Son.. Bazan iya rasa Haidar ba.. He’s all I have.. You need to stop him please.. Please Engr do Something.. Not our Son please..!” Saurin rik’ota Daddy yai ya shigar da ita jikinsa yana fad’in “Haba Kwaise ke fah musulma ce Ya kamata ki natsu ki ambaci Allah… Addu’a zamuyi in sha Allah komai zaizo cikin sauk’i.. Zamu bi komai cikin tsanaki.. Babu abinda zai samesu gaba d’aya kinji.!” Yanda yake maganar zaka fahimci k’arfin hali ne kawai amma ba daidai yake ba. Hilal ma rik’e yake da mahaifyarsa yana k’ok’arin calming dinta. Gaba d’aya gidan Ya kuma hargitsewa. Ganin haka yasa Sadis saurin zamewa daga parlorn. Wayar Haidar Ya soma kira yana ‘yan waige waige. Haidar dake tsaye jikin motarsa yana gyara zaman kwalar rigarsa nan yaga wayar Sadis na shigo masa. Ya d’aga yana tambayarsa Sadis ya ake ciki. "Sadis Ya dan girgiza Kai yana rage muryarsa kad’an “Haidar are you sure about this..? I mean, things are really getting messy here.”" Daga d’aya b’angaren Haidar ya jinjina Kai “There’s no going back Sadis.. I need to do this.. I need to catch Hisham in the act..” Sadis ya dan furzar da huci “But you are putting me in a difficult situation.. Idan wani abu ya sameka ahalinka zasuga laifina.. Musamman ma Daddy.” “This is my decision not yours Sadis.. Sun sani idan nai making mind dina bana canzawa.” "Sadis Ya kuma furzar da huci “But.. Are you aware of the danger of what you are doing..? I mean, this look like a suicide.. You should have let the police handle the matter.”" “No Sadis.. This is something I need to do it alone.. Kar ka nuna musu komai sai na isa wajen. I’m hanging up now.!” Daga haka katse kiran yai yana saita shirt button d’insa dake daga wuyar rigar. Wanda a zahiri button ne kawai. Idan ba ka sani ba Sam bazaka kawo ‘yar k’aramar spy camera bace dake nad’e hoto da murya. A fili Ya furta “It is now or neve.!” Lokaci guda Ya shige motarsa ya d’auki hanya. * A can cikin daji kuwa iyaka laushi da buguwa Hisham da Anisa sunyi. Tsananin bugu ya haifar ma Anisa bleeding shi kuwa Hisham Har kaman sumewa yai ga k’afafunsa da suka koma tamkar basu motsi. Ruwan sama da Ya soma sauk’a shi ya dawo da Hisham hayyacinsa. Yaci gaba da tari jini na bin goshinsa hancinsa harma da bakinsa. Ya bud’e bakinsa da kyar yana fito da harshensa yana lasan ruwan dake saukowa dan rabonsa da Ya saka wani abu a cikinsa tin jiya da aka kawo su wann daji da tin shigowarsu ba abinda suke karb’a cikinta sai bugu da nau’uka na azaba. Ga mutanen basu ce dasu komai ba sai azabtar dasu da suke. saiko wayar da sukai ma Haidar. "Cikin tsananin jin jiki Hisham ke furtawa da kyar “Have mercy.. Have mercy.. Su waye ku..? Mai kuke nema wajenmu..! Look, mahaifina attajiri ne.. ku fad’i ko nawa kuke nema.. I.. I mean whatever amount kuke so.. Mahaifina zai baku.. Amma dan Allah ku kyalemu mu tafi haka..!”" Gardin dake tsaye kusan kan Hisham ya buga masa k’asar bindiga akai nan jini yaci gaba da fita daga sassan jikin Hisham. Ya saki k’aran azaba sanda mutumin ya kuma buga masa wani abu kaman guduma a sangalalin k’afafunsa. Lokaci guda ya manna masa shocking wire gashi dama cikin cakwab’i na ruwa yake kwance shame shame nan Jikin Hisham ya soma vibrating yana sakin wani irin gurnani na azaba. Anisa kaw cikin jin jiki take fad’in “Ku taimaka min.. Ku taimakeni zan Mutu.. Wayyo Allah na.. Wayyo Ammi.. Na shiga uku.. Mara na ciwo yake mun.. Zan m… Zan mutu..!” Bata Kai aya ba taji an buga mata wani abu kan cikin Wanda Ya sanyata sakin k’aran azaba siririn jini na kuma bin k’afafunta.. Hisham Ya waiga a galabaice yana duban Anisa ga jini dake bin k’afafunta. Cikin wane irin yanayi yake furta “No.. No please.. Not my child.. She’s pregnant.. Please let her go.. Don’t kill my child.. Please spare my child.!” Wata murya suka sinkayo tana fad’in “You should have thought about this a lokacin da kuka kashe nawa D’an.!” Zuciyar Hisham Tai wani irin tsinkewa.. A hankali ta furta “DAREEN..!” Dareen taci gaba da tura wheelchair din da take zaune bisa har ta k’araso yanda Hisham ke kwance tamkar Wanda yai paralyze. Jikin Anisa Ya d’auki rawa daga nan yanda take kwance shame shame.. Ta soma k’ok’arin jada baya cikin tsananin tsoro tana cije keb’e sabida azaba. Har lokacin jikinta karkarwa yake tamkar wacce taga fatalwa. Dareen ta dubeta sai ta shek’e da dariya “Ina zakije Anisa..? Tsoro kike kinga fatalwa.? Kun zata Kun kashe Dareen koh..? Kun zata Dareen ta tafi bazata dawo ba ko.? Sabida Kun cika marassa kunya harda zuwa ku aure juna.?!” Sai ta kuma darawa “But you two look perfect together..! Ku biyun Kun dace da juna.!” Cikin jin jiki Anisa ke tamke ido tana girgiza kai lokaci guda take furta “Dan girman Allah kiyi hakuri Dareen..! Wllhi ba abinda kike tunani bane.. Ban auri Hisham dan ina son kasancewa dashi ba..! Wllhi he tricked me too..! He betrayed me kaman yanda yaci amanarki.. Na amince da Aurensa ne dan na kawo k’arshen yaudararsa da fuska bayinsa.. Cikin da kika gani jikina ma wllhi fyade Ya mun bada son raina bane..!” Bata kai aya ba taji sauk’an Mari maiji da lafiya a fuskarta Wanda Ya k’ara had’a mata jini da majina. Dareen taci gaba da huci tana duban Anisa “Sa’anki d’aya Anisa ni mace ce da bata yarda aci zarafin wata mace ta hanyar fyade ba.! Because I believe babu macen da ta cancanci aci zarafinta ta hanyar fyade komin munin halinta.. Ba don haka ba da wad’ann k’artan zansa suyita sukuwa akanki sai tsinannen dake cikinki Ya fita fit.! Amma da nau’ukan azaba sai na ciresa kafin Haidar ya iso nan.!” Dareen ta kuma bud’e murya tace “Kelly.!” Take wann k’aton Ya k’araso gabanta yana risinawa. Nan tabasa umarni da Ya zana Anisa da murd’add’iyar bulalar dake hannunsa. Kan kace me Kelly ya shiga nade bulalar dake hannunsa Ya shiga zuge Anisa dashi tana sakin k’aran azaba dan ko motsawa bata iyayi. Hisham Ya zaro ido waje daga nan yanda yake karb’an nasa hukuncin. Cikin tsananin rawar murya Hisham ke fad’in “Please don’t Dareen.. Don’t kill my child please..! Anisa is pregnant with my child.. She’s three months pregnant.. Ina son cikin nan fiyeda komai a duniya Dareen.. Ki kasheni idan kina so.. Ni na miki laifi.. But please sapere my child..! Let the child live please.. Kiji tausayin jaririn dake ciki Wanda baida hakki..!” "Wani kafurin dariya Dareen ta kece dashi tana duban Hisham “Unbelievable..! Ban iso kanka ba cikakken D’aniska.! Ni zaka duba kace I should spare your child.?! Did you spare my own child Hisham..?!” Ta kuma kecewa da dariya kafin taci gaba “Wai ni kake ce na tausaya ma jaririn cikinka da baida hakki..? Ka mance lokacin da kai da wann k’aramar doluwar kuka murk’ushe nawa jaririn da tayun mota.?! Ka gaya min Hisham nawa jaririn shi hakkin uban wa yaci cikinku.?!” Taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Gwara ma wann shegen dake cikinta iyayensa tsinannu ne azzalumai Watak’ila zunubinku Ya shafe shi.. Amma ni nawa jaririn fah.? Cikin innocent Haidar ne Hisham..! Haidar shine uban jariri na..! mutumin da ka tarwatsa masa rayuwa kai destroying d’insa from the root..! Uban cikina is innocent..! shi aka zalunta cikin gaba d’aya labarin.!” Taci gaba da jinjin kai tana duban Hisham “Kamar yanda zan k’araci rayuwata saman wheelchair sabida murkushe mun k’afafu da kukai da mota, kaman haka zan tabbata ka zama paralyzed for the rest of your miserable life Hisham..! Kaman yanda kuka kashe D’ana da Haidar yana watanni uku kacal a ciki..! Kaman haka zan kashe wann cikin naku mai watanni uku a ciki..! Haidar zai k’araso nan Hisham.. Zaka bud’e baki ka sanar dashi komai..! Ina nufin komai..! Duk abubuwan da kai masa a rayuwa..! Duk shiga rayuwarsa da kai..! Duk tarwatsa masa rayuwa da kai.. Zaka bud’e baki ka karanto zunubanka gaban Haidar..! Ko d’aya bazaka bari ba sai ka fad’a taryan taryan..!” Ta k’arashe tana mai kiran d’aya gardin tace Ya sake mana ma Hisham igiyan shocking." ** "Cikin zuban hawaye take duban Hajja, da kyar take furta “Dan Allah Hajja kice mun bai kai kansa ma ‘Yantadda kaman yanda suka nema ba..” Ta rintse idonta hawaye na gangaro mata “Yau Aurenmu yake cika watanni uku cif a karo na biyu.. Hajja dan Allah kice mun zai dawo gareni kice mun ba AUREN WATA UKU muka sakeyi ba..! Ya mun alk’awari wann karon Aure mukai na Har abada.. Dan Allah kice zai dawo gareni.. Idan na rasashi nima mutuwa zanyi Hajja..!” Ta k’arashe tana kame k’irjinta tana kuma rintse idonta dake ci gaba da zuban hawaye.!" Hajja Tai k’ok’arin maida nata hawayen tana jijjiga Ummul take fad’in “Ki daina maganganu irin haka Ummul. Ba abinda zai samu Haidar.. Ba abinda zai samesu gaba d’aya da izinin Allah. Haidar zai dawo gareki Babu zancen AUREN WATA UKU tsakaninku.. Zakuyi rayuwa mai tsawo tare in sha Allah kinji koh.. Kici gaba da ambaton Allah kinji koh. Da sannu zai kawo mana sauki cikin al’amarin.!” Ta k’arashe hawayen da take ta k’ok’arin dannewa na zubo mata itama. Mommy da Aunty Asshe ma an rasa mai bama wani baki Hilal na tsakiyansu Ya rungumesu dukansu biyu shima hawayen yake Ya kasa jurewa. Aunty Asshe fad’i take “Ina yawan kiran Anisa shashasha kun sani..? Amma lokacin da akai Aurenta sanda zasu tafi SouthAfrica.. Kun san mai tace min da muka keb’e a d’aki.? Ce min Tai Ammi ki yafe min.. Nasan na sakaki bak’in ciki da dama because of my stupidity..!” Asshe yaci gaba da hawaye tana jinjina kai “Sai tace min I’ll make it up to you Ammi..! You will be proud of me..! Ammi Ina sonki..! Kice ma Abba ya yafe min.. Kuma kice ma Hilal ina son shi.. And I thank him for always having my back.!” Ta k’arashe cikin kuka yayinda Hilal ma ta matse hawayen da suka gangaro masa. Mommy kam bata iya cewa komai ba sai hawaye dake ci gaba da gangaro mata tana tuna randa ya dage sai an basa matarsa da D’ansa Sun tafi.. Ta tuna irin draman da akai kafin ta amince Ya d’auki iyalinsa su tafi.. Ta tuna saida ta aje masa mata na tsawon watanni uku kafin ta basa matarsa.. Ta tuna sanda ya shigo ya mata Sallama da kalamansa na soyayya a gareta. Ta tuna yanda yaita bata hakuri yana fadin bazai tafi ba sai ya daina fushi dashi kuma sai ta saka masa albarka. Sai Mommy ta rintse ido hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata “My prayers are with you Son.. Allah bazai basu dama akanka ba.!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Daddy kuwa yana daga waje bakin parlorn shida Alhaji Gimba yanda Alhajin Gimban keta k’ok’arin kwantar ma abokin nasa hankali. Duk k’arfin hali na Daddy saiga hawaye na gangarowa daga idonsa. Ya kuma d’agowa yana duban Alhaji Gimba. Cikin zuban hawaye Daddy yaci gaba “Gimba my two Sons.. Yarana guda biyu wanda nai failing dinsu tin suna yara ko ince Tun suna ciki basu zo duniya ba..! Wad’anda Allah ya bani su cikin tausayinsa da jin k’ansa da kuma rahamarsa amma sai nai masa butulci ban nuna godiya a gareshi ba.! Guda d’aya na sheganta shi da harshena na koreshi tin yana ciki.. Ya girma babu mahaifi..! Guda d’ayan kuma.. Ya girma gaba na amma banyi appreciating d’insa ba. Ya girma tamkar Babu mahaifi sabida wofantar dashi da nai akan idona..! Yau gashi dukansu biyu suna hannun barayin Daji Gimba.. Su biyun sunyi abota tin basu san sud’in ‘yanuwa bane. Amma abotan Ya koma k’iyayya a lokacin da Ya kamata sufi son junansu bayan sun fahimci Sun had’a mahaifi guda.. Gimba inaji kaman ni na haifar da conflict d’in dake tsakanin yarana guda biyu.. I failed them both.. And now.. Ban sani ba.. Ko dai na sake ganinsu ko ba na sake ganinsu ba..! Gimba kana ganin Har yanzu Ubangijina hukunta ni yake akan laifuka na na baya.?!” Ya k’arashe yana girgiza cikin zuban hawaye. Alhaji Gimba Ya girgiza kai “Kar kayi magana irin haka abokina. Duk abinda Ubangiji Yayi daidai ne. Ba’a saka ayar tambaya. Tsarki ya tabbata gareshi mai mulkin sammai da k’assai mai juya al’amara yanda yake so. Idan yaso Yayi mana rahama idan yaso Ya azabtar damu duka iko nashi ne akan halittunsa. Sann duk halinda muka tsinci kanmu ciki rahamarsa ne.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Ka daina dawo da kurakuren da kai baya kana azabtar da kanka dasu. Mu dukanmu ‘yanadam ne kuma masu kuskure sann mafiya kyawun masu kuskure cikinmu sune masu tuba. Wanda mukai tuba na gaskiya dominsa Ya sani sann shi d’in mai yawan gafara ne mai jin k’ai.” Ya dan dafa hannun Daddy “Tabbas idan Munyi imani za’a jarabce mu.! Kai hakuri abokina kai tawakkali. Ka saka ma ranka wann rajabawa ce daga Allah.. Muyi addu’an Allah Ya kub’utar dasu Ya dawo mana dasu lafiya..” Daddy ya amsa da Ameen yana mai waigawa ko zaiga Sadis amma bai gansa nan wajen ba. Alhaji Gimba Ya gyara zama yace “Kuma Haidar kawai suka nema yakai kansa.? Sann meyasa baayi gaggawan sanar da jami’an tsaro ba dan a samu a shawo matsalar da wuri.” Daddy yai saurin girgiza kai “A’a Gimba rayuwar yarana are at stake here.. Kaga ita Anisa ma cewa sukai juna gareta kaga dole abisu yanda suka buk’ata kasan yanda wad’ann azzaluman mutane suke gudanar da al’amaransu sam babu Allah a ransu Gimba. Yanzu mistake kad’an zaayi su hallak’a min yara gaba d’aya. Watak’ila idan Haidar yaje su nemi Ransom mai tsoka.. Ni ko rayuwata suka nema ba Kampanina da abinda na mallaka ba zan basu dan su sako yaran nan Gimba.” Alhaji Gimba Ya tsare Daddy cikeda tausayawa. Sai yana tuna lokutan baya da Daddy ke cewa kampanin sa Ya fiye masa Haidar. Yau gashi yana ce zai sadaukar da komai nasa dan ya ceci Haidar ciki harda rayuwarsa. Ya dan numfasa sai kuma yace “Amma akwai alaman tambaya a nan Abokina.. Meyasa zasu buk’aci Haidar Ya kai kansa..? Meyasa Kai tsaye basu nemi Ransom ba.? I’m sorry to say this.. Abokina Anya baza’a duba maganar Haidar ba.? Banso na saka maka zargi ko shakku akan D’anka musamman da shike baku jima da kasancewa da juna ba.. Amma..” Daddy yai saurin dakatar da Alhaji Gimba yana girgiza Kai “Haba Gimba kar kace kaima ka yarda da shirmen Haidar. Haidar zafin kishi kawai ke d’awainiya dashi amma d’an uwansa bai nufinsa da komai face alkhairi. Masu garkuwa su suka sacesu. Kasan mutanen nan da salo salo na yaudara.. Kar ka mance sukan sace mutum su nemi kud’in fansa Wanda yakai kudin ma suyi garkuwa dashi..” Sai ya d’anyi shiru kaman Wanda Ya tuna wani abu “Haidar shine in charge na sabon kwangilan titi da mukeyi a jihar Lagos.. Kasan Kampani da dama sun nemi kwangilar basu samu ba.. Kanaga garkuwa da akai da yaran nan nada alak’a da wann kwangilar tinda gashi basu nemi ransom ba sai Haidar..!” Alhaji Gimba yai shiru sai kuma ya jinjina kai kad’an “Everything is possible here.. Amma Kai tsaye bazamuyi saurin yanke hukunci ba.. Saidai dole mu saka abinda kace into consideration. Allah dai ya bayyana mana su cikin aminci.. Daddy ya amsa da Ameen yana jinjina kai. ** Kutsawa yake cikin dajin yayi tafiya da baida wani nisa daga bakin kwalta. Kasancewar ba daji bane sosai hakan yasa Sadis bai sha wahalan samun layin Haidar ba. Bakin kwalta Haidar ya bar motarsa Ya sauk’a d Ya fara tafiyar k’afa. Nan yake sanar da Sadis ya kunna tablet d’in da sukai connecting spy camera din dake button din wuyar rigar Haidar d’in dashi. Akwai app da sukai installing cikin tablet d’in yanda kowa zaiga live streaming abinda ke faruwa. Spy Camera d’in dake jikin button d’in wuyar rigar Haidar zata dinga nade komai yanda su kuma zasuke gani cikin tablet d’in. Lokaci guda Sadis ke fad’in an gama. Daddy yana gefe nan cikin parlorn yana amsa waya bayan Alhaji Gimba Ya fice zuwaga majalisunsu zai sanar dan a tayasu da addu’a. Ga security ya kuma zama very tied a gidan. Har lokacin su Mommy jigum jigum suke. A haka Sadis ya shigo parlorn rik’eda tablet d’in yace dasu gaba d’aya Haidar yana so suga abinda zai kunna musu. Take hankulansu ya dawo ga Sadis. Daddy ya katse wayan da yake ya k’araso yana tambayar Sadis meke faruwa.? Mai Haidar yake so su gani.? Take Sadis ya kunna tablet d’in ya kam video na sirri da Haidar ke nad’a Wanda ke mak’ale gaban rigarsa kaman button. A haka Haidar yaci gaba da kutsawa. A daidai jikin wata bishiya yaji alamun fito. Yaja Ya tsaya yana waige waige. Can ya hangi wasu k’artai guda biyu Sun fito daga bayan wata k’atuwar bishiya. Daga nesa sukai masa umarni da “Hands in the air.” Haidar ya d’aga hannayensa sama alamun surrender. Kartan suka k’araso guda d’aya yai searching Haidar dan ya tabbatar bai d’auke da makami. Yayinda guda d’aya yake lek’en bayan Haidar d’in dan ya tabbata shi kad’ai yake babu jami’an tsaro. Ya dubi Haidar yace “Are you sure you are alone.?” Haidar ya jinjina Kai “You can be sure I’m alone.!” Suka amshi cell phone d’insa kafin sukai blindfolding d’insa. Tafiya kad’an sukai idanun Haidar suna rufe. Sai yaji alamun kaman ba mutanen wajen. Abinda kunnuwarsa suka soma sinkayowa shine gurnani da kuka kaman na mutanen dake cikin azaba. Anisa wacce ita ta soma hangosa fad’i take “Haidar..! Haidar please help.. Help me.. Zasu kashe ni…!” Cak Haidar yaja Ya tsaya ga idanunsa a rufe.. A hankali Ya furta “Anisa..!” Cikin sauri Ya zame abinda suka rufe masa ido dashi. Ya nufo Anisa dake kwance jini na bin k’afarta. Cikin tsananin shock yake furta “What happened to you..? Mai Hisham ya aikata Miki..? Ina Hisham yake..? Su waye wad’ann..? Come.. I’ll save you.. We need to leave this place..” Ya k’arashe yana k’ok’arin d’agota. Saidai bai rufe baki ba ya sinkayo muryar Hisham dake baje cikin chakwabi na laka. Sam bai ma zata mutum bane wajen Ya zata curin k’asa ne ko wani abin. Da kyar Hisham Ya d’ago hannu yana fadin “Brother please don’t leave me here.. Dan Allah kar ka barni a nan.. Zasu kashe ni wllhi..!” Girgiza kai Haidar yake yana duban Hisham cikin rashin yarda “Wai meke faruwa ne haka a nan..? Meye kake shiryawa ne Hisham..? Meye ka aikata ma kanka.. Mai ka aikata muku.. Mai zakai gaining cikin duka wann wasan.?” Cikin murya irinta mai kuka Hisham ke fad’in “Ka yafe mun Haidar..! Ka tausaya mun ka fitar Dani a nan.. Wllhi kasheni zatayi..?” “Zata kasheka..? Ita wa..?” Daga bayansa Ya sinkayo murya tana fad’in “Banyi alk’awarin kashe ka ba Hisham Har sai kayi confessing duk wasu abubuwa da kayi ma Haidar da ahalinsa.!” Cikin wane irin yanayi Haidar ke juyowa Har ya sauk’e idanunsa tsaf akanta. “Dareen.!” Ya furta cikin tsananin shock yana duban Dareen dake zaune bisa wheelchair. “You.. you are alive.?” Haidar ya kuma fad’i yana dubanta. Dareen ta saki murmushi “Im alive Haidar my love.. I am very much alive.. Burin wad’ann azzaluman na ganin sun kashe ni sun rufe baki na bai cika ba.! Sunyi k’ok’arin takeni da mota dan kar na isa gareka na tona asirinsu wajenka.. Sunyi nasaran takeni da mota amma basuyi nasaran kasheni ba kaman yanda sukai nasaran kashe mana jaririnmu mai watanni uku a ciki..! Haidar I was carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. The only abu da zan dinga gani na tuna soyayyarmu.. Wad’ann azzaluman Sun kashe min shi.. Kaman haka nayi alk’awarin tatse tsinannen D’ansu dake cikin Anisa dan su d’in basu cancanci zama iyaye ba.!” Girgiza kai Haidar yake yana dubanta tashin hankali k’arara saman fuskarsa. Lokaci guda Ya daga hannaye sama a hankali kaman mai surrender. Fad’i yake “You don’t need to do this Dareen..! You don’t need to torture them like this.. You don’t need to kill their child.. Just let them go please.. Let Anisa go.. She’s bleeding..!” A fusace Dareen ta katsesa da fad’in “No Haidar.! They killed our child..! These two monsters killed our child.. Na kiraka ne kaga fansar d’aukan ran D’anmu da sukayi sann wann Devil din yai confessing duk abubuwan da Ya maka. Wanda ya hana na sanar dakai ta hanyar amfani da Anisa ta bigeni da mota..! A yau shi da bakinsa zai fad’i komai akan fuskarka Haidar. Zai fad’i duk abinda yai maka da ahalinka..!” Ta mik’a hannu ta cakumo Hisham dake layin azaba “It is game over for you.! Start talking Bastard.! Ka fad’a masa yanda ka kawoni cikin rayuwarsa ta hanyar sihiri dan ka tarwatsa tsakaninsa da iyayensa.. Talk.!” Ta k’arashe tana turasa gaban Haidar yanda Hisham Ya zube gaban Haidar yana nishi. Zamu iya cewa ba D’anadam guda dake motsi parlorn Daddy. SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *64* *©️Sameena Aleeyou… * Har lokacin duk’e Hisham yake gaban Haidar yana fidda numfashi da kyar. Ya kaikaito yana duban Dareen dake zaune saman wheelchair gefensa. A hankali yake jinjina kai yana dubanta “So this is your plan..? To exact revenge.?” "Cakumosa Dareen ta kumayi tana huci “No, this is not revenge but a Karma.. This is exactly what Karma looks like..! When you feel you are at the lowest of your life..?” Ta murmusa “You think you are Smart Hisham.? Well I’m ten steps ahead of you.. Filthy Bastard..! Tell him now.. Tell him everything.! And when I said everything.. I mean every.. Thing..!”" Haidar yaci gaba da duban Hisham yana girgiza kai da idanunsa da tuni Sun kuma kad’awa “I know you’ve always known… Ka jima da sanin cewa kai din.. d’an mahaifina..? Sann dalilin da Yasa ka shigo rayuwata kenan.. Haka ne..?” Hisham Ya jinjina masa kai yana dubansa. Murmushi saman fuskarsa “That’s right Haidar.” Haidar ya jinin kai kad’an “But why me.. Meyasa ni..? What have I done to you..?” “Because ta hanyarka ne kawai zan kutsa cikin ahalin ka na kuma tarwatsa ku..! Nayi rantsuwa matuk’a ina numfashi your family will never be whole.. I vowed to be shadowing each and every step you take in life.! Nayi rantsuwa sai na tarwatsa ku.!” Yaci gaba da jinina kai yana duban Haidar “Na kawo Dareen cikin rayuwarka dan na samu saukin tarwatsa ku.!” A fusace Haidar Ya katsesa “But that family you tried so hard to break has already been broken.. Wann ahalin Ya riga Ya tarwatse tin kafin zuwanka.. Kuma kasan mai..? I’ve paid the price..! Na girma Ina biyan wann farashin.. Ka sani.?!” Hisham yai saurin katsesa“No Haidar baka biya komai ba..! Baka biya komai ba kan irin rayuwar da na fuskanta..!” Hisham yaci gaba da hawaye yana duban Haidar d’in “I grew up in a misery..! I grew up watching my Mom suffering.. Suffering from the misery your parents inflicted on her..! Before you judge me.. Ina so ka saurari nawa b’angaren labarin.!” Cikin huci Haidar ke dubansa “Nothing justifies what you did Hisham.. Kai dan adam ne kaman kowa and you had your chance to do what’s right..!” "Hisham ya girgiza Kai “Mai zakace ga D’an da aka haifesa a kurkuku..? Mai zaka ce ga yaron da Ya taso cikin kyama da tsangwama..? Mai zakace ga yaron da Ya taso ba tareda yasan mahaifinsa ba.. Mai zaka ce ga yaron da aka turasa kurkuku sabida rashin galihu sann a wann kurkukun yasan cewa a nan aka haifesa..? Mahaifinsa shi ya jefa mahaifiyarsa a wann kurkukun da Ya zamto tushensa.. Sann.. Sann Matarsa ita ce silar aukuwar komai..!” Yaci gaba da jinjina kai yana duban Haidar “Yes Haidar a kurkuku nasan cewa a nan ne aka haifeni.. A nan nasan labarina.. Da asalina da aka rufe tun kafin nazo duniya..!” Ya share hawayen da suka gangaro masa kafin yaci gaba “Kaman yanda ka sani sunana Hisham..! Na taso na tsinci kaina ni kad’ai wajen mahaifiyata, babu mahaifi, babu D’anuwa ko ‘Yaruwa… Babu tak’amaimen ahali… Mu biyu ne tak.. Daga ita sai ni.. Na taso cikin kyara da tsangwama daga wajen mutane da dama.. Tin ina yaro tin bani fahimtar kalaman da mutane ke jifarmu nida mahaifiyata dasu Har dai nakai munzanin da na soma gane abubuwa. Babban kalma na aibu da ake jifana dashi shine rashin Uba.. Wanda har ta Kai na soma jefa ma Hajja tambayoyi gameda nawa mahaifin. Amma sai ta ce mun Ya rasu.. Idan nace ina danginsa sai tace mun baidasu.. Idan na tambayeta nata dangin sai ta ce mun na daina yawan tambayoyi inada ita kuma tana k’aunata. Daga baya na fahimci Ahalinta Sun koreta ne sann suna gudunta.. Tabbas ita d’in korarriya ce cikin danginta dan nima lokacin da naso tunk’ararsu sun koreni tin kafin na tunk’aresu. Babu mai so ace ya rab’e mu balle Har ya samu wata alaka damu.. Duk yanda na shiga korata ake ana jifana da kalamai na aibu.. Na shiga rud’ani da damuwa musamman idan na daga ido na kalli mahaifiyata sai naga mutumiyar kirki.. Nayita jefa ma kaina tambayoyi meyasa muka zama abin gudu abin kyama bayan kyawawan D’abi’u da mahaifiyata take dasu Wanda take k’ok’arin d’aurani akai.. Zan iya cewa kaf cikin mutanen da suke hantaranmu suke kyaranmu babu Wanda bazai so ace Ya samu D’a mai natsuwa irina ba.. Duk yanda mukaje korarmu ake.. We had nowhere to go.. Mahaifiyata tana iya k’ok’arinta taga ta samar mana abinda zamu rufa asirinmu dashi.. But it was not easy.. Tayi ko wani irin aikatau dan ta turani makaranta.. Ta hana kanta abinci dan rayuwana Ya inganta.. Ita d’in uwa ce kuma uba a wajena… A wani gida da take aikatau yanda muka samu saukin tsangwaman da muke fuskanta a nan ta turani boarding school da" "dan kudin da take samu a wann gidan.. Wani rana na dawo hutu na tadda Maigidan yana kokarin yaci zarafinta… Da yaga haikan bazata bashi kanta ba sai Ya soma zage zage yana jifanta da kalamai masu muni yana cewa waye a gari baisan wann D’an nata ma ta hanyar banza ta same sa ba.. Dan haka Dole ta basa kanta dan ya mata sutura ita da D’anta..! I was only 16 then.. Zuciya ta debeni ganin yana kokarin nufo mahaifiyata dake neman hanyar tsira.. Nai jifa da jakar makaranta na na rarumi wani katako a wajen na kwada masa akai.. Take jini Ya balle yai kwance wajen tamkar maras numfashi.. Ganin haka yasa hankalin Hajja Ya Tashi.. Jikinta na matuk’ar rawa take furta Hisham ka kashe shi.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ka tashi ka gudu kafin wani Ya cimmaka.. Ka fita daga nan ka gudu.. Na soma girgiza Kai ina hawaye fad’i nake A’a Hajja bazan tafi na k’yaleki ba.! A dole Hajja tasa na fice daga gidan. Koda matan mai gida suka shigo suka tadda mijinsu haka sai suka kira ‘yan sanda suka sanar dasu cewa mai masu aikatau wato Hajja ta ita tayi yunk’urin kashe masu maigida bayan tayi k’ok’arin seducing d’insa bata samu yanda take so ba. Dama Sun jima da sanin ita d’in ba mutumiyar arziki bace sann tanada criminal record. Hajja batai wata wata ba ta amasa laifin da fad’in ita ta illata mutumin Wanda Ya kwashe watanni kwance asibiti baisan yanda kansa yake ba. Da naga za’a tura Hajjata kurkuku sai na fito na amsa laifin aka turani gidan yari da k’anan shekaru.” Hisham yaci gaba da jinina kai yana duban Haidar “Hajja ta shiga cikin yanayi na tashin hankali da d’imauta. Bamuda kowa bamu da komai bamuda mai tsaya mana. Allah ne gatanmu. A kurku na hadu da wani mutumi wanda Ya kwashe shekaru da dama a kurkukun. K’alilan ne suka fisa jimawa cikin kurkukun. Bansan dalili ba amma Allah Ya jefa kaunata Zuciyar mutumin. D’abi’a ce a kurkuku duk sabon zuwa dole a masa sannu da zuwa. Sann wann sannu da zuwa d’in ba komai bane face bugu na fitan hankali wasu lokutan Har stabbing mutum ake. Na bugu iyaka buguwa a hannun sauran inmates d’in. Toh bayan naci bugu ne hankalin wann mutumin Wanda yana d’aya daga cikin masu fad’a aji tsakanin prisoners Ya kai kaina. Ya kirawo ni ya bani abinci naci ya kuma ce daga wann bugun na farko da aka mun kar Wanda ta sake tab’a koda d’an yatsa na. Da wann na samu saukin gwale gwalen azaban gidan kasu. Mutumin ya tanbayeni labarina na sanar dashi cewa k’ok’arin kare mahaifiyata nake shine dalilin shigowata gidan kasu. Koda yaji abinda Ya faru sai naga ya jinina Kai yace mun nayi daidai. Bansan wani tunani yake cikin zuciyarsa ba sai naga ya ciro wani hoto cikin aljihunsa yana kallo. Idona yakai kan abinda yake kallo sai naji k’irjina yayi wani irin bugawa. Dan koda kuruciya Ya nuna a fuskar Hajjata Tabbas na gane ita ce. Hannuna na rawa nake nuna hoton nace ‘Ina kasan Hajjata.?’ Sai Ya dubeni da mamaki Ya girgiza kai ‘Hajjarka.?’ Na kuma jinjina masa kai ‘K’warai Hajjata.. Mamata.. Mahaifiyata..’ Sai naga mutumin ya tashi sosai yana dubana ‘Kai.. Kai D’an Fannah ne..?’ Sai na jinina masa kai nace k’warai ni D’anta ne.’ Sai mutumin yace dani ‘Ina mahaifinka.?’ Sai na girgiza masa kai nace ‘Mutanen gari suna cewa bani dashi.. Amma Hajjata ta sanar Dani Ya rasu Tun kafin a haifeni..’ Sai naga mutumin yana jinina kai. Ni kuma sai na tambayesa ya akai yasan Hajjata sann me hotonta yake wajensa.? Ya gyara zama yana dubana sai Ya sanar Dani shi tsohon masoyinta ne da wasu masu k’arfin iko suka rabasu. Ya kuma dubana yace ‘Mahaifinka na nan Hisham.. Mahaifinka bai Mutu ba.. Sann kaga wann gidan Yarin a nan aka haifeka.. Kaidin tamkar ka dawo Tushenka ne ko ince k’addara ta kuma kawoka ciki wann kurkukun dan kasan bak’in zaluncin da aka muku kaida mahaifiyarka Tun kafin kazo duniya.!” Hisham yasa hannu Ya share hawayen da suka zubo masa yayinda hawaye sukaci gaba da zarya a fuskan Haidar. Lokaci gida Hisham yaci gaba “A nan ne wann mutumin Ya bani labarin duk abubuwan da suka faru baya.. Auren Aliyu Maitama da Mahaifiyata da yanda Matarsa Hajiya Kwaise Tai amfani da shi wann mutumin wato tsohon masoyin mahaifiyata ta tarwatsa auren mahaifyata da Aliyu Maitama ta kuma sa Ya koreni daga cikin ahalinsa tun ina ciki banzo duniya ba sann Ya daure mahaifiyata Har ta haifoni a gidan Kasu.. Mutumin yaci gaba da sanar Dani ‘Ni na biya kurakuraina tsawon zaman da nayi a gidan yarin nan.. Sann ni da ka gani bazan tab’a fita daga gidan yarin nan ba sabida kwanakina k’ayaddu ne a halin yanzu. Kwanaki k’alilan suka rage mun kaman yanda Likita yace sabida ciwon daji na huhu da nake fama dashi. Watak’ila wann hukuncin abinda nai ma mahaifiyarka ce. Had’a baki da akai dani aka ci amanarta. Ni tawa ta riga ta k’are kuma na girbi abinda na shuka. Saura Ya rage naka Hisham.. Ka tafi ka dauki fansa. Ka dauki fansa wa mahaifiyarka.. Ka tarwatsa ahalin da suka zalunceta.. Kasa su biya abinda suka aikata mata..! Wasiyata a gareka kenan..! Fansa..! Ka d’au wa mahaifiyarka da kai kanka Fansa..!’ Yana ida fad’in haka ya soma tari sosai yana kame k’irjinsa.. Ba’a jima ba yace ga garinku ya mutu. Tin daga wann lokacin, tinda wann mutumin ya bani labarin abinda Mahaifina da matarsa sukai ma mahaifiyata sai naji a duniya banida sauran buri da ya wuce d’aukar Fansa.. Sai naji kaman amfani na kawai na girma na d’auki fansa ne.. Fansar duk abinda akaima mahaifyata da irin rayuwa na k’ask’anci da muka fuskanta ta dalilin wann k’age da aka mata. Nayi rantsuwa sai na tarwatsa wann ahalin koda shi kad’ai ne abinda zanyi a rayuwata. Shekaru biyu na rayuwata na b’ata a gidan yari kafin daga bisani aka fiddo ni. Koda na fito ban nuna ma Hajja na san wani abu dangane da baya ba. Ban nuna mata na san asalina ba. Saima na daina tanbayarta gameda asalina da dangin mahaifina. Daga nan sai na maida hankali kan aikin k’arfi da karatuna fafa. A lokacin Hajja ma ta soma sana’ar d’inki. Sai muka bar k’asar Borno gaba d’aya muka dawo makwabciyarta Yobe. Mun jima a yobe kafin muka dawo Kano. A nan na maida hankali na karanci b’angaren Architecture sabida mutumin can ya sanar Dani mahaifina Engr ne na gine gine sann sana’arsa kenan. Sai na fuskanci idan ina so na kutsa cikin ahalin na musu lahani kwatankwacin Wanda suka mana nida mahaifiyata dole ya zama inada wani makami da zanyi amfani da shiga jikinsu dashi. Nayi dedicated lokaci sosai ganin na zama mai kwazo a fannin. Ban" huta ba har saida na zama cikakken Architect kuma kwararre. Duk wani labarai da ya danganci Kampanin Mahaifina wato Maitama Builders baya wuceni. A nan ne na fahimci ta hanyarka ne zanfi samun saukin shiga cikin kampanin harma da ahalin.I became Woolf in Sheep’s clothing and befriended you in order achieve my goal.” Ya kuma duban Haidar yana jinjina kai “Kaji dalilin da yasa na kutsa cikin ahalinku. Sann na kawo Dareen cikin rayuwarka dan ta zame mun kaman spy. Ta dinga sanar Dani duk wani hali da kake ciki musamman tsakaninka da iyayenka.. Dareen ita ta jefeka da asiri Haidar dan ta kasance da kai saidai na goya mata baya sabida k’udirin da nake dashi akanka da ahalinka.. Na amshi tukunyar da Tai maka asiri na b’oye a wajena ne sabida nasan duk daren dad’ewa wataran zan karya wann asirin da hannuna. Kuma hakan ce ta kasance na fasa wann tulun da ta d’aure kurkwarka ciki bayan da na fahimci ka auri Ummulkhair..!” Haidar na hawaye yake huci yana dubansa “Don’t you dare mention my wife you psycho.!” Hisham ma hawaye yake yana jinina kai “Dole na ambaceta Haidar..! Kasan dalili..?” A fusace Haidar yace “You are obsessed with her.!” "Hisham ya girgiza kai “No Haidar.. Na Sani na so Ummulkhair Tun kafin ka aureta.. Amma a baya ne..! I’m not capable of loving..!” Hisham ya basu labarin had’uwarsu da Anisa da yanda akai suka tabbata AUREN WATA UKU na Ummul da Haidar yazo k’arshe, yanda Ya d’auki Ummul Ya kaita ma Hajja har stabbing kansa da yai da duk wani k’ulli da yai dan ya tabbata Ummul bata koma wajen Haidar ba. Yaci gaba da jinjina kai yana duban Haidar “Na fahimci ba Ummul nake so ba. You are the one I’m obsessed with Haidar. You are like my trigger.. Kaidin kana tuna min duk wani abu da nai going through ne a rayuwa Wanda iyayenka sukai sanadiyan jefani da mahaifiyata ciki. Na fahimci duk abubuwan da nakeyi inayinsu ne kawai dan na k’untata maka..! Amma bayan da na fahimci Anisa na d’aukeda juna biyu.. Bayan da na fahimci zan zama mahaifi.. Sai ya zama ba abinda nake so irin wann D’an.. Wann cikin dake jikin Anisa.. Haidar Allah shine shaidana na zubar da makaman yak’ina da kai tun a SouthAfrica.. Na kuma dawo gida Nigeria da zuciya d’aya.. Da niyyan na Gina rayuwa mai kyau da ahalina.. Ina nufin Anisa da abinda ke cikinta.. Koda Anisa bata sona.. Na saka ma raina a hankali zan koya mata sona.. Sann Watak’ila zuwan wann D’an dake cikinta zai iya canza k’iyayyar da take mun.. Amma like they say abinda ka shuka shi zaka girbe.. Na yarda abinda na shuka shine nake girbewa.. Na yarda ba komai a cikin fansa face tarin nadama da danasani. I lost the child..! I lost my child.. Kuma na sani.. Idan Hajja taji abubuwan da na aikata In the name of revenge bazata tab’a yafe mun ba. And she will despise me.. Zata tsaneni.. Koma na rasa mahaifyata gaba d’aya kaman yanda na rasa D’ana..!” Ya juya ya dubi Anisa wacce ta fice a hayyacinta sabida galabaita. Ya dawo da dubansa ga Haidar “Please save my child Haidar.. Please he’s your nephew.. Save him please..! Ban damu ba idan Dareen ta kashe ni a nan.. But please you need to save Anisa and the child..!”" Kafin Haidar yai wani motsi sai gani sukai Dareen ta zaro bindiga. Tai pointing Anisa dashi tana fad’in “Da ita da abinda ke cikinta zasu mutu Hisham..! I don’t give a damn about you or your wife.. And much less your unborn child.. Dukanku uku ina nufin your little family.. Matarka da D’anka dake ciki zaku Mutu yanzu a nan.. Ka zaba da waye zai fara tafiya cikinku..?” Haidar Ya soma girgiza kai yana duban Dareen “No Dareen.. Please don’t do this.. Just let them go please.. It is me that you want.. I’m right in front of you.. And I’m not going anywhere.. I’m coming with you.. Just let them go please..!” Dareen ta harba harsashi sama ta saki k’ara tana fad’in “No Haidar.. These two destroyed our own little family.. Sun kashe mana D’anmu kuma sun tarwatsa mu.. Basu cancanci rayuwa ba..!” Ana haka suka soma jiyo sautin motar ‘yansanda tana nufo wajen. Dareen ta waigo ta dubi Haidar da mamaki “Did You call the police..? You betrayed me Haidar..!” Ta soma kuka tana girgiza kai yayinda kartan guda biyun suka soma k’ok’arin janye wheelchair d’in Dareen suna fad’in “Ma’am we need to leave right away.. The police are heading our direction.. We can’t afford to get caught..!” Dareen ta saki kara tana tarjewa take fad’in “No..! I’m not leaving.. I’m not going anywhere without Haidar..! No.. Bazan tab’a barin Haidar ba.. He’s mine..! Shi din nawa ne..!” Daidai lokacin ‘Yansanda sukai masu kawanya suna fad’in Dareen da yaranta suyi surrender.. Girgiza kai Dareen take tana dubansu. Cikin huci take furtawa a hankali “If I can’t have you Haidar.. Then no one will have you.. Zan kashe ka kuma na kashe kaina.. Zamu kasance a eternity tare da D’anmu gaba d’aya.. Zamuyi forming ahalinmu a can..!” Tana ida fad’in haka Tai saitin Haidar da bindiga tana fad’i da k’arfin gaske “I love you Haidar..!” Tauuu.!!! Ta saki harsashi. Hisham Ya saki k’ara yana ambato sunan Haidar da k’arfin gaske..! Daidai lokacin signal d’in Ya d’auke daga nan yanda suke kallo cikin parlorn Daddy. Bayan labari mai firgitarwa had’ida tsoratarwa da suka gama saurara. Tabbas harsashin kaman ta hudo cikin camera d’in ne ta samesu gaba d’aya.! SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!* *65* *©️Sameena Aleeyou… * *END* Haidar ya tallafo Hisham Wanda tuni Ya mik’e dukda k’afafunsa dake masa rawa Ya tare ma Haidar harsashi a lokacin da Dareen ta harba. Harsashin ta samu Hisham a bayansa maimakon ta Sami Haidar. Tuni jini ya soma ambaliya. Girgiza kai Haidar yake yana duban Hisham dake furtawa cikin galabaita “I’m a failure… A worthless son and a cruel brother… Forgive me Haidar… Ka yafe mun.. Kace ma Hajja ta yafe mun..! Ka rokar mun gafaran iyayena Wanda na zamto jarabtu a garesu.. Dan Allah ka yafe mun brother..!” Girgiza kai Haidar yake “What have you done Hisham..? Mai ka aikata.. Mai ka aikata ma kanka..?” Ya k’arashe yana girgiza kai yana kuma ce ma police d’in suyi maza su kirawo ambulance. Dan tuni Hisham Ya fice hayyacinsa. Haidar na rik’e da Hisham ga Anisa ma can kwance unconscious. Su duka biyun Sun fice hayyacinsu a haka ambulance ta k’araso aka sakasu ciki. Ya waiga Ya dubi Dareen dake kwance kasa jini na bin kanta dan a lokacin da ta harba harsashin da nufin Ya samu Haidar take ta D’ana ma kanta. Aka rufeta da farin k’yalle dan tuni tace ga garinku su kuwa yaran nata ‘yansanda tuni Sun kama su. Ana isowa asibiti aka wuce da Hisham da Anisa zuwa ER dan ceto rayuwarsu. Haidar na zaune wajen Daddy ya k’araso. Ya tsaya daga nesa yana duban Haidar d’in ga wasu kwantattun hawaye saman fuskarsa. Juyowar da Haidar zai sukai ido hud’u da Daddy. Sai Ya mik’e tsaye yana jin hawaye na k’ok’arin ciko idonsa shima. Daddy na k’arasowa suka rungume juna shida Haidar sai kawai Daddy yai bursting cikin kuka. Fad’i yake “I’m sorry.. I doubted you… I’m sorry son.. Please forgive me..! Ka yafe ma Babanka..! For he’s not perfect..!” "Haidar ya rik’e hannayen Daddy suna duban juna. Ya girgiza kai kad’an “No Daddy, ka daina rokona gafara..” Sai ya d’anyi shiru yana duban Daddy “I just wanted the truth to come out.. amma ban rik’e ba Daddy.. Kasan dalili..? Sabida kai din mahaifina ne..!” Daddy sai Ya kuma rungume Haidar hawaye na kuma gangaro masa." Haidar ya dan shafe fuskarsa da tafukan hannaye yace “Hisham da Anisa suna ciki.. Hisham is undergoing a surgery.. He took a bullet for me Daddy..” Katsesa Daddy yai da fad’in “I don’t know Haidar.. Ban sani ba idan ina so na sake ganinsa bayan abubuwan da naji ya aikata maka.. Meyasa zai cutar dakai.. You haven’t wronged him in any way.. Ni nai masa laifi why would he take it out on you..! Meyasa bai hukuntani ba ya zab’i ya hukuntaka..? Meyasa zai shiga rayuwarka Ya tarwatsa maka..!” "Girgiza kai Haidar yai “No Daddy.. Please don’t talk like that.. Dan Allah kayi ma Hisham uzuri ka yafe mishi… He’s gone through a lot in life.. As they say zuciya batada kashi.. Mu duka mun hukunta sashi da kurakuren sashe. Mu d’auki hakan matsayin k’addara da jarabawar ahalinmu..” Ya dan jinjina Kai kad’an yana duban Daddy “Koda mantuwa ya kasance mai wahala.. Mu yafe ma juna.. At the end, we are all family.. And that’s what matters..” Ya k’arashe yana k’ak’aro murmushi." Daddy ya share hawayen da suka gangaro masa yana duban Haidar d’in. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa “Kanada zuciya mai kyau Haidar.. Madallah da D’a irinka..! Madallah da kyauta irinka..! Hak’ik’a nayi kuskure da na kasa ganinka a gabana..? Hak’ik’a samun D’a irinka babban kyauta ce Aliyu.. A lokacin da wasu ‘ya’yan suka zamo jarabawa ga iyayensu wasu kuma sanyin idaniya ne.. Nayi zaton kaine jarabawa na.. Nayi zaton D’an da na rasa a baya shi zai zamto sanyin idaniya a gareni. Ashe ba haka bane.. Ashe wasu kyautan basuda farashi a duniyar nan..! Allah ya maka albarka Aliyu..! Allah ya haskaka rayuwarka da d’imbin alkhairai..! Kaman yanda ka zamto D’a na gari a gareni ina fata ka zamto Uba na gari ga ‘ya’yanka wad’anda zasuyi alfahari dakai sann su zamto sanyin idaniya a gareka..” Ya k’arashe yana kuma hugging Haidar. Haidar ya share k’wallan da suka gangaro masa yana mai rungume Daddy. * A b’angaren su Mommy kaw tuni anyi rushing Hajja zuwa asibitin sabida jininta da Ya hau har ta rasa consciousness. Farkawan da Hajja zatai sai ganin Mommy tai zaune gefenta. Mommy ta matso tana mata sannu. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai “Ta ina na ragesa..? Nayi iyaka kokarina ganin na tayar da D’a na gari.. Na sadaukar da komai nawa wajen inganta rayuwarsa.. Na zata na basa duk wani tarbiya da kulawa.. Ashe ni din na gaza… Ni ba uwa ta gari bace..!” Ta k’arashe cikin rawar murya kuka na cin k’arfinta. Hannayenta Mommy ta kamo tana girgiza kai “Kar kiyi magana irin haka Fannah..! Tabbas ke uwa ce ta gari.. Sann kin bama Hisham duk wani kulawa.. Kin sauk’e nauyi da hakki da Ya rataya a wuyanki irin Wanda ni ban sauk’e akan nawa D’an ba..” Hajja na hawaye tace “Meyasa zai min irin wann sakayyar..? Ta ina na tauye shi.? Tsawon rayuwata nayi zaton mutumin kirki na raina.” Mommy ta jinina kai “Wann shi ake kira jarabawa.. Haka Allah yaso Ya sanya sashe cikinmu matsayin jarabawa ma junanmu.. A baya ban kasance uwa ta gari ba amma an jarabci D’a na Haidar da samun uwa irina… Sann yayinda ke kika zamto uwa ta gari sai aka jarabceki da samun D’a irin Hisham Wanda Ya girma da burin fansa Ya kuma rufe Miki k’udirinsa.. Amma dukda haka ba yana nufin Hisham ba yaron kirki bane.. Shi d’in d’a ne mai biyayya ga mahaifiyarsa.. Kaman dai yanda yai defending mahaifyarsa Har ya tafi kurkuku a sabida haka. Rashin sa’a akayi Ya hadu da Wanda Ya karkata masa zuciya zuwa burin fansa a gidan kasu. Kuma kuskurenki d’aya ne a nan rashin sanar da Hisham asalinsa da bakiyi ba da bakinki har dai wani mugu Ya rigaki sanar dashi Ya kuma daurasa akan tarbiyar yanda zai fuskanci al’amarin. Shiyasa a duk wani abinda Ya shige ma yaranmu duhu musamman idan wann abun mukeda hakkin sanar dasu. Lallai mu Ya kamata mu sanar dasu domin tarbiya namu ne hakkinmu ne.. Nauyi ne da ta rataya a wuyanmu.. Baza mu so wani daban waje yaje Ya basu nasa tarbiyar ba.” Ta kuma kamo hannayen Hajja “Kar kiyi ma Hisham baki.. Kar ki hana masa yafiyarki da albarkanki.. Ke d’in uwa ce kuma babban jigo na rayuwarsa. Hisham ya tuba ya kuma gane kuskurensa. Muyi fatan Allah Ya yafe mana baki d’aya ya kuma iya mana abinda mu bamu iyawa. Allah yasa iyaye da dama su d’auki darasi cikin irin rayuwar da mukayi da namu yaran.” Hajja ta amsa da Ameen tana jinjina kai cikin matuk’ar sanyin jiki. * Bayan da Anisa ta farfado ne su Aunty Asshe harma da Ummul da Hilal suka k’araso. Kai tsaye d’akin hutu da Anisa take Aunty Asshe da Hilal suka nufa yayinda Ummul Tai tsaye tana dubansa Ya basu baya yana amsa waya. K’walla tab idanunta. Juyowar da zai sai sukai ido hudu.. Ji take kaman ta tafi a guje ta haye jikinsa sabida farin ciki.. Ya kaste wayar da yake Ya tsareta da ido sihirtaccen murmushi saman fuskarsa. Sai Ya bud’e mata hannaye alamun ta taho. Ta soma waige waige dan ta tabbatar ba mai ganinsu. Haidar ya kuma murmusawa yana tayata waige waigen “Taho mana.. There’s no one here..” Ya fad’i yana daga mata gira. Ai bata san sanda ta tafi a guje ta rungumesa kaman ma ta mance Baba Ali dake cikin hannunta. Ya had’esu duka Ya rungume.. Ummul kam sai ta saki kukan da taketa k’ok’arin dannewa. Haidar Ya kuma matsesu gaba d’aya had’ida lumshe idanunsa “It’s over.. It’s finally over.!” Ya Baba Ali dake cikin hannunta “Come here Little Lion.. Come to Paapa..!” Ya k’arashe yana daga yaron sama tuni yaron Ya shiga kyalkyale dariya alamun yayi kewan Babansa. Ummul ta tsare su da ido tana jin shauk’in k’aunarsu gaba d’aya. A can d’aki kuwa wajen Anisa Hilal Ya sakata gaba ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba Kai kace ba ‘yan biyu suke ba. Kace Ya girme mata ne. “Kinsan me kin tabbata mai kwakwalwar kifi Anisa.. Why would you get married to that psychopath.. Are you that stupid..? Bansan shashashancinki yakai wann peak din ba.!” Anisa ta juya ido da kyar had’ida furzar da huci “Ammi please… tell him to leave..” Aunty Asshe ta hararesa “Bakada hankali ko Hilal.. Baka ganin halinda ‘Yaruwarka ke ciki ne.. Idan bazaka iya taimakawa da komai ba ka wuce ka fita.. Kar ka sake stressing dinta.” Hilal Ya furzar da huci “Amma Ammi ni fah gaskiya kawai nake fad’i..” A fusace tace “Rik’e gaskiyar taka bamu so..” Ta k’arashe tana k’ok’arin kai spoon din oath bakin Anisa. Sai lallaba Anisar take tana fad’in tasha ko kadan Likita yace ba abinci a system dinta. A haka su Mommy da Hajja suka shigo. Mommy ta k’arasa ta d’anyi hugging Anisa daga nan yanda take kwance saman gado Tai mata sannu da jiki da fatan samun sauk’i. Sai suka fice gaba d’aya su ka bama Anisa da Hajja waje. Bayan Hajja ta mata sannu da jiki. Hannaun Anisa ta rik’e cikin nata “Ina mai baki hakuri on behalf of Hisham.. He manipulated you and made you go through a lot… Kiyi hak’uri Anisa.. Kuma idan baki son zama dashi ki sani kinada goyon bayana.. Allah ya baki lafiya..” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin janye jiki. Har ta kai k’ofa ta sinkayo muryar Anisa “Hajja..!” Juyowa Hajja Tai tana dubanta. Anisa tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata “Im not innocent.. I’m also being punished for my sins… Abinda na shuka nima nake girbewa.. Wad’anda sukafi cancanta a nemi yafiyarsu sune Ummul da Haidar… Ina fata su yafe mana kuma Ina fata Allah Ya yafe mana gaba d’aya.!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Hajja ta dawo da baya ta rungume Anisa daga nan yanda take kwance. Sai Anisa ta shige jikinta tana matsan hawaye. Ta d’ago ta dan dubi Hajjan “How’s… he doing..?” Tai tambayar tana mai janye jikinta daga na Hajja. Ganin Hajja ta mata k’uri sai yasa ta dan sadda kai ta k’arada “I mean.. Hisham.. What’s his condition.. What did the Doctors say..?” Hajja ta sauk’e ajiyan zuciya “Sunyi nasaran cire harsashin sann aikin yayi kyau according to them.. But they insist something might remain irreversible in his life.. Sabida harsashin ta kuskuri k’ashin bayansa... Hakan na nufin zai iya zama saman wheelchair har k’arshen rayuwarsa.. sunce a jira farkawarsa.. Sann a shirya ma aukuwar komai.” Ta jinina kanta kad’an ba tareda ta kuma furta komai ba. Jikinta duk a mace. Hajja ta d’auko oath d’in taci gaba da bama Anisa tana fad’in Tai kokari ta shanye. ** Koda Hisham Ya farfado kuwa iyayensa guda biyu basu tunk’ar d’akin da yake ba. Haidar ne yaita basu baki yana fadin suyi hakuri su yafe ma Hisham su kuma shiga su dubasa. Dik da shima Haidar d’in bai iya shiga Ya duba Hisham d’in ba. Ya yafe masa amma baijin su biyun zasu iya zama in good terms like before. Daddy kaw darajan Haidar Hisham yaci Shiyasa zai shiga ya duba halinda yake ciki. "Kwance Daddy ya hangi Hisham saman gado, Ya jima sosai yana dubana yana tuno farkon had’uwarsu matsayin d’a da mahaifi. Ya tuna yanda yaita k’aryata Haidar akan Hisham d’in. Ya tuna irin yardar da Ya basa had’uwarsu ta farko cikin k’ok’arinsa na gyara kuskuren da yai ma Hisham d’in da mahaifiyarsa a baya." Juyowar da Hisham zai ya hangi Daddy tsaye yana dubansa cikin yanayi da zai iya cewa bai tab’a ganin fuskarsa ciki ba. Sai Hisham yaji Daddy ya furta “SON.!” Hisham ya d’ago da mamaki yana duban Daddy. Gashi dai ya ambacesa da D’a amma fuskarsa a matuk’ar daure. Hisham yaci gaba da hawaye yana duban Daddy. Yayinda Daddy yaci gaba “Kasan na baka wann title d’in a karon farko da na d’aura ido akanka matsayin D’ana.?” Hisham ya jinjina Kai a hankali yana mai ci gaba da hawaye. Hawaye suka gangaro ma Daddy har lokacin fuskarsa a matuk’ar daure. Daddy yaci gaba “Shin kasan Haidar shekara nawa yayi ina kallonsa a gabana amma ban tab’a basa wann title d’in ba..?” Muryar Daddy ta soma rawa “Kasan shekara nawa na kwashe ina hukunta Haidar a sabida rashinka..? Kasan shekara nawa nayi ina denying masa sunan da shi ya cancanta fiyeda kai..?! Did you know that I never doubted you.. Not even once.. Ka san na yarda da kai a karon farko.?” Yaci gaba da girgiza kai yana duban Hisham “Why..? Meyasa..?” Kuka ya hana muryar Daddy fita. A haka ya silale wajen yana dafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana jin zuciyarsa na masa nauyi. Hisham ma kuka yake yana fad’in Daddy ya yafe masa. Saida sukai mai isansu su duka biyu Hisham naci gaba da rok’on Daddy gafara kafin Daddy ya mik’e ya daidaita tsayuwarsa yana duban Hisham d’in with a straight face “Duk abubuwan da ka mun a Company.. All the damages you’ve caused… All the scandals.. All the setbacks zan iya yafe maka kuma zan d’auki hakan matsayin hukunci "gameda kuskuren da na aikata maku kaida mahaifiyarka a baya, musamman kai.. Koda rayuwana ka nema duka zan d’auki hakan matsayin hukunci na.. But not at the expense of my Son’s life.. Ran Haidar yafi mun duk abinda na lissafo maka ciki harda nawa rayuwar. Da ace na rasa Haidar a wann had’arin motar da ka shirya masa da bazan tab’a yafe maka ba.”" Cikin zuban hawaye yake fad’in “Nasan ban canci yafiyarku ba.. And I know I’ll have to earn for it..” “Is that why you took a bullet for him..? Kana tunanin hakan da kai ya wadatar.?” Daddy ya katsesa. Kafin yaci gaba “Koda bakayi hakan ba Haidar zai yafe maka. Kasan dalili.?” Daddy yaci gaba da jinjina Kai “Sabida yanada zuciya mai kyau Wanda babu k’udirin fansa cikinta sai d’imbin alkhairi.” Hawaye suka kuma gangaro ma Hisham kansa kife a k’asa. Girgiza kai kurum Daddy yai kana yasa kai ya fice cikin sauri dan bai fata zuciya ta debesa Ya furta wani kalma out of anger. A k’ofa suka had’uda Hajja tana shigowa. Suka dubi juna duk jikkunansu a mace musamman Hajja. Sai kawai tasa kai ta shige dan bayan abinda Hisham Ya aikata gaba d’aya nauyin kowa take cikin ahalin. Kasa duban mahaifyarsa a k’wayan ido yai. He failed her as a son.. Bayan duk wani fad’i tashi da Tai akansa. Bayan duk wani sadaukarwa irin sakayyan da zai mata kenan.? Hajja kuka Hisham kuka. Sai taji bazata iya jure tsayuwa kusansa a d’akin ba. Tasa kai zata fice amma sai ta tuna kalaman Mommy a gareta da wann Hisham ya samu sassauci wajen mahaifiyarsa. ** Kishingide suke saman sofa ta shige jikinsa sosai. Hannunsa zagaye da ita yana shafa sumarta kaman mai k’irga kitson dake kanta. A hankali ta furta “Ka yafe mun..! Na maka kuskuren fahimta.” Mik’ewa yai zaune had’ida cireta daga jikinsa. Ummul ta bisa da kallon mamaki yanda ya tsare sosai yasha mur. Sai ta d’an girgiza kai kad’an “Bazaka yafe mun ba ko..?” Tai maganar kaman mai shirin kuka. Ya jima sosai yana dubanta sai ya tabe baki kad’an “No.” Yai maganar yana mai gyara zamansa cikin kujera harda hard’e hannayensa a k’irji. Sosai ya sha mur fuskarsa babu alaman walwala. Tai rau rau da ido “Toh ka fad’a mun mai zanyi ka yafe mun..” Ya dan saci kallonta da wutsiyar ido yanda ya hango damuwa k’arara saman fuskarta. Ya saki murmushi kad’an. Bata ankara ba sai jinsa Tai cikin jikinta. ya shigar da fuskarsa cikin wuyanta sosai. Cikin sigan rad’a yake furta “Maybe I can forgive you..” Ta dan fito da ido waje “Da gaske.?” Ya jinjina Kai kad’an “But only If you tell me… You love me.. like hundred times.. That’s the only way.” A hankali take sakin sihirtaccen murmushi tana kashesa da wani irin duba “That’s just it.. Shikenan.?” Haidar ya jinjina mata kai yana fadin “Umhum..!” Sai ta matso sosai saitin kunnensa ta rada masa “But I love you more than love itself..And when I tell you I love you.. I’m not saying it out of habit.. I’m reminding you that… You are my life..!” Baisan sanda ya rufe bakinsa da nata suka lula wata duniyar. ** Months later… "An fara shirye shiryen auren Hilal da Kulsum, Azeema da Sadis da kuma Badia da Alhaji Gimba. Dan Alhaji Gimba bai k’asa a gwiwa ba har saida ya tabbata ya samu soyayyar Badia da amincewar ta. Matarsa ta jima da rasuwa kuma d’a d’aya gareshi Wanda tinda Ya tafi turai karatu bai kuma waiwayowa gida ba aure ma can yayi. Ya auri baturiya ‘yar k’asar Poland. Suna can da yaransu har biyu saidai shi Alhaji Gimban yaje Ya duba su idan yaji kewa amma sam basu zuwa Nigeria Shiyasa a lokacin da Daddy yake nuna halin ko inkula akan Haidar Alhaji Gimba yake ganin kuskuren abokin nasa. Mu zamto masu godiya ga d’imbin rahamar Ubangijinmu garemu domin abinda kake rainawa wani shi kawai yake fata da burin Allah Ya basa. Bamu gane mahimmancin wani ni’ima da Allah yai mana sai mun rasa wann abin. Allah kasa mu zamto bayinka masu godiya a gareka da kuma karban k’addara a duk yanda tazo mana." ** Khulsum ta rok’i alfarmar iyayenta da su bari ta tafi can Jigawa wajen Dije. Koda aka fara bikin ma Abba da Umma basu nemi ta dawo ba sai Inna Dije Tai mata nata bikin a can. Aure kawai aka d’aura a Kano amma tana can wajen Inna Dije. Sosai Inna Dije taji dadin hakan Har saida tai hawaye sabida farin ciki. Hak’ik’a Khulsum ta girmamata ta bata darajan uwa taji dadin wann karramawa sosai. Taita godiya ma abba da Umma tana hawaye. Umma tace ta daina godiya Hak’ik’a ita d’in ta zamto uwa ga Khulsum a lokacin da ta gaza zama uwa gareta. Abin farin cikin shine Allah Ya dad’a had’e kan ahalinsu kuma ya cikasu da alkhairi. Umma da Mama Tani suka had’e kawunansu suna kukan farin ciki. Yau yaransu gaba d’aya sunyi aure. A baya lokacin da sukaci musu buri na ganin sunyi ko wani irin aure ko ta halin k’ak’a sai Allah Ya barsu da wayonsu. Yanzu da suka fawwala masa al’amarinsu sai Ya zamto majib’icin al’amarinsu. Ya kawo ma ‘ya’yansu mazajen aure na gari a lokaci guda. Lallai Ubangiji Ya cika abin godiya. An sha biki lafiya a lokacin cikin Ummul Ya tsufa Baba Ali nada shekara d’aya da wata uku a duniya. Tai zaune a playing room d’in Baba Ali tana duban yanda Haidar Ya baje ma yaron kayan wasa dangin building block da motoci irin na construction.. Harda helmet ya d’aura masa yana fad’in “Da kyau my little Engr let’s build a house for Maama..” Ummul ta kuma dubansu tana sakin sassanyar murmushi. Wayan Haidar ne ta soma ruri Ya daga yana amsawa. Da alama wayar nasa aiko ya Shafa. Tinda Ummul taga haka sai ta d’anyi kicin kicin da fuska dan tasan bazai wuce kira na gaggawa Ya samu daga Lagos ba sabida taji sanda ya ida wayan Ya kira Sadis yace ya masa shatan PJ a ranan zai tafi Lagos d’in bazai jira jirgin safe ba. Ya k’araso gabanta ya dan langab’e kai yana duban yanda ta cika Tai fam. Ya duka gabanta hadida d’aura hannayensa saman laps dinta “Maman Biyu.. What’s wrong.. Why the long face.?” "Ya dan hararesa kad’an bakinta a ture, kaman zatai kuka tace “Nasan tafiya zaka kumayi.. Bayan duka duka yaushe kazo.”" Haidar ya dan murmusa yana mai kamo yatsun hannayenta cikin nasa “Duk sabida haka ake fushi ana bata kwalliyan da aka mun.?” Sai Ya bata dariya ta dan murmusa tana mai kuma turo baki “Amma ai baka jima da zuwa ba.. Kuma kace wann karon zaka jima kafin ka koma.” Jinjina mata kai yai “Kiyi hak’uri.. Dole ce tasa zanje suna buk’atana a can. But I’ll only be there for a while.. Bazan jima ba In sha Allah. Da zaran na gama abinda yakaini zaki ganni.. Tashi muje ki tayani i shirya jaka.” Ya k’arashe yana mai taimaka mata ta mik’e da kyar. K’arasawa yai Ya d’auki Baba Ali suka nufi dakinsa gaba d’aya dan shirya jaka. Ummul tana fiddo masa kayan yana shiryasu a suitcase ta d’an dubesa. Kaman bazatai magana ba sai kuma tace “Dazu Munyi magana da Anisa a waya take ce mun basu ganka ba har yanzu.. Yau kuma satinsu guda kenan da dawowa daga Germany.. Kowa yaje Ya duba Hisham saura kai..” Haidar Ya katseta “K’arata ta kawo miki banje na duba mijinta ba..?” Saurin girgiza kai Ummul Tai “A’a ba haka bane” Ta bar abinda take ta matso yanda yake “Dan Allah ka yafe ma D’anuwanka.” Ya dubeta kad’an sai Ya girgiza kai “Na yafe masa tuntuni.” "Ta jinjina kai “Kai kokari ka mance komai ku gyara alak’arku.. Haka ne kawai zai tabbatar da yafiyarka a gareshi.. Ina so ka min wann alfarmar mijina, kaje ka duba D’anuwanka kafin ka wuce Lagos.. Please mijina.!” Ta k’arashe cikin sigan lallashi tana kuma kamo hannayensa." "Haidar Ya dan furzar da huci kad’an “Fine, zan biya na duba shi.. Yayi miki..?”" Ta murmusa cikeda jin dadi tana jinjina kai “Yayi min.. Na gode sosai.” Tsareta yai da ido. Sai Ya tallafo fuskarta da tafukan hannayensa.. Ya kannare ido sosai yana dubanta “What have you done to me Khairy..? You convince me on most impossible things..” "Ta murmusa tana kashesa da wani irin kallo mai kashe masa jiki. Ta sakala hannayenta saman kafad’unsa, ta langab’e kai “You love me so much that you can’t say no to me.” Tai maganar tana kashe masa ido.. Sai Ya janyota jikinsa Ya lumshe ido “Of course I do.. I do love you..!” K’arshe duk’awa yai saitin zungureren cikinta ya soma zance da cikin “Hey twins, Papa is going on a short trip.. While I’m away, be good kids and don’t give too much stress to Maama… I love you.” Ya k’arashe yana sunbatan cikin. Ummul kaw sai dariya take dan so tari idan Haidar na zance da cikin jikinta sosai abin ke bata dariya. Sai ka rantse da wani cikakken mutum yake magana. Ba wai taga banbancin rainon cikinta na farko lokacin bata tareda Haidar da wann da take tare dashi. Taga gata da soyayya irin wana batai zaton na faruwa da gaske ba. Ita kam ba abinda zatace ma Ubangijinta sai godiya. Fad’insa ne tsanani yana tareda sauk’i sann duk Wanda ya dogara gareshi toh ya isar masa. Tafiyan Haidar da kwanakin da basu shige biyu ba ta fara labour. Ai kaw koda aka tafi asibiti cikin ikon Allah bata d’auki dogon lokaci tana labour din ba ta haifo d’iyarta ma sha Allah. Ba’a kuma jimawa ba namiji Ya biyo baya. Ma sha Allah tabarakallah. Allah mai kyauta da k’ari, buwayi gagara misali." Zo kaga farin ciki wajen d’aukacin ahalin. Abin baa cewa komai sai son Barka. Shi kansa Uban gayyan wato Haidar kai kace ba’a tab’a masa haihuwa bane. Kowa na farin ciki da son Barka. Wann karon Umma da kanta saida ta wanko k’afa tazo Abuja. Tsaban farin cikin da Abba ya shiga ma tuni yace Umma da Mama Tani duk su shirya su tafi. Yara biyu lokaci guda ba k’aramin kyauta bane. Taron suna yaga jama’a . Harta da Inna Dije saida tazo.. Su Badia da Azeema dake a nan Abuja gidajen su yake tuni akai komai dasu. Khulsum ce dai aka sha fama da Hilal dan ciki gareta kuma karami irin mai saka laulayin nan. Da kyar dai saida Aunty Asshe ta saka baki Ya amince suka biyo jirgi suka taho gaba d’aya. Gaba d’aya dangi duk sun hallara. Abin fah ba’a cewa komai sai son barka. Ranan suna da safe Hajja ta had’e kan ‘Yanmatan gaba d’aya dan d’abbaka wani al’ada na ahalinsu. ‘Yanmatan a gida da sirakai sukan hadu su girka ma mai jego abinci wana zata ci. Aka had’a Anisa da yanke Albasa. Idon Anisa sai hawaye yake sai mita take tana fad’in ita bata saba da wann aikin wahalan ba. Fad’i take “Wayyo idona yaji.. I can’t open my eyes.. Wai dole dai sai mu zamuyi aikin nan gida cikeda ma’aikata.” Azeema ta harareta “Ni fah gaskiya duk kin cika mana kunne. Masu abin mita ma basuyi mita ba sai ke.?” Tai maganar tana nuni da Khulsum da Badia dan dukansu biyu juna garesu. Anisa ta galla mata harara da idonta da yai jazir Ya jik’e da hawaye “Ina ruwanki dake nake.? Ai duk laifinki ne. Sabida kinajin haushina kika sa aka hadani da yanka albasa. Toh ai sai kizo ki karisa.. I’m not doing it again..!” Ta k’arashe tana aje wukar had’ida goge ido. Azeema ta tabe baki “Toh ke me zaki iya ma idan ba yanka albasa ba. Ba iya girkin kikayi ba balle ace kiyi. Dan haka dole ki yanka albasa.” Badia ta lallashi Anisa da fad’in kar ta biye ma Azeema k’ila itama fitinar masu k’aramin ciki take bata sani ba. Azeema ta zaro ido tana fad’in ita batada komai. Aunty Asshe ce ta lek’o tana musu sannu da aiki. Ta dubi Khulsum tace kar tayi stressing kanta musamman da yake cikin jikinta na sakata laulayi sosai. Kawai sai Anisa ta fashe da kuka tana fad’in “Wayyo Ammi idona.. Wayyo yaji..” Aunty Asshe ta galla mata harara “Meye haka ke kuma.. banson sakarcin banza.” Anisa ta kuma turo baki tana fad’in “Ammi wllhi bakiji ba kaman idona zasu fice.” “Toh su fice din mana. Haka dai zakiyi.” Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Why are we torturing ourselves.. Is there not a machine for doing this..?” Aunty Asshe tace “Machine din kenan hannunki..” Ta dubi su Azeema tace su karo mata lawashin duk ta yanka. Kuma Mijinta na ida jin k’arfi zasu tattara su tafi gidansu kuma zata hana ya d’aukar mata wata mai aiki. Anisa tace “Ammi kawai kice baki sona.. Dama Hilal kikafi so gashi kin hana matarsa aiki.” Aunty Asshe tace eh d’in ba’a sonta d’in. Ta dubi Khulsum tace maza ta fito kitchen din haka Anisa ta had’e aikin Khulsum d’in da nata duk tayi. Khulsum tana fad’in zata iya Azeema na turota waje tana fad’in “Wllhi Ammi dazu ma bakiga ba yanda take tangad’i kaman zata fad’i k’asa saida na tarota.” Aiko nan Aunty Asshe tace maza maza ta fito haka ta huta. Anisa sai ta kuma fashewa da kuka tana ma Azeema Allah ya isa data sa aka had’ata da wahala. Dan ko bayan aurensu da Hisham a SouthAfrica ba girki take ba. Sann da suka tafi Germany jinya ma ba girki take ba. Yanzu da suka dawo ma gidan Daddy suke. Azeema da baki baya shiru ta galla mata harara ta karo tulin albasa ta dangwala gabanta tana fad’in “Allah dai yasa surkarki ce ta sakamu. Kuma baa isa ace baza’a ayi aikin sirka ba.” Ta kekace da dariya tana fad’in “Maza ayi biyayya aci gaba da yanka albasa aci gaba da murza ido aci gaba da hawaye.” Gaba d’aya saida ta basu dariya. Kawai sai Anisa ma ta fashe da dariyar ga ido jazir fuska sharkaf da hawaye. "Yara sunci sunan Mommy da Abba. Ta ko wani b’angare farin ciki ke circulating. Da yamma aka sha walima na alfarma a nan gidan Daddy. Bak’i maza da mata. B’angaren mata daban na maza daban. Musamman aka d’auko babban malami yai wa’azi sosai kan mahimmanci tarbiya da kula da yara. ‘Ya’ya rahama ne kuma kyauta ce da babu mai yinta sai Allah. Sann duk Wanda aka danka masa kiwon d’a Tabbas amana aka dank’a masa Wanda Allah zai tsayar dashi Ya tambayesa gameda wann amana da aka basa. Yaya ya tafiyar da amanar.? Ya sauk’e nauyi da hakkoki da suke kansa.? Mu sani kafin mu samu nagartattun ‘ya’ya Tabbas sai mun zama iyaye masu nagarta kuma ababen koyi. K’addarar mu tana tafiya da jarabawar mu. A lokacin da muka kamanta namu k’ok’arin muka kuma had’a da neman taimakon Allah sai kuma mukaci karo da jarabawa, toh fah mu sani wasu mutanen Allah yakan k’addarosu cikin rayuwarmu ne matsayin jarabawa. Ya Allah kasa mu zama ‘ya’ya masu biyayya ga iyayenmu sann ka sanya mu cikin iyaye masu nagarta. Ka azurta Al’umman Mamzonka (SAW) da samun ‘ya’ya na gari wad’anda zasu zamto" sanyin idaniya kuma sadak’atuljariya a garemu baki d’aya. Allah ka iyar mana abinda mu bamu iyawa. Ya Allah duk wata uwa da take nema ma ‘ya’yanta shiriya Allah ka shirya mata su. Masu neman haihuwa Allah ka azurtasu da salihan ‘ya’ya wad’anda zasuyi alfahari dasu dama Al’umma baki d’aya. Ameen thumma Ameen.! ** "Haihuwan ‘yan biyu yazo ma Haidar da tarin nasarori na rayuwa. A lokacin Daddy yai stepping down daga matsayinsa na kasancewa shugaban kampani kuma mai jagoranci kampanin. Yanda Ya d’aura D’ansa Aliyu ya zamto shugaba kuma mai jagorancin Kampanin. Sann Ya bar zab’i hannun Haidar gameda aikin Hisham under his company. Idan har Haidar ya amince zai iya barin Hisham yai aiki a company, idan kuma bai amince ba Hisham bazai koma company ba. A Cewar Daddy bayan yafe masa da yai wann shine hukuncinsa." Gagarumin taro aka gudanar yanda Haidar ya karbi lambobin yabo da karramawa dama. Ciki harda aikin da ya gudanar na bridge project da ya jagoranta a lokacin da yai yarjejeniyar AUREN WATA UKU da Ummul. Wann gadar ta zamto kaman itace mafarin komai. Sanda ya fito domin bada speech d’insa bai k’asa a gwiwa ba har saida ya fad’i mahimmancin wann project d’in a garesa da yanda Ya zamto silan canza direction na rayuwarsa harma da Company’s future. Wann project d’in zai tabbata na musamman cikin jerin ayyukan da yayi. Daddy ya k’araso sukai masabaha bayan zauren taron ya kacame da tafi da fatan alkhairi. "Murmushi saman fuskar Daddy yake furta “Congratulations Son, ina tayaka murnan d’imbin nasarori da ka samu. Ka cancanci fin haka. Nasan bazanyi danasanin dank’a maka ragamar company ba. Inada yak’inin zaka kai Company zuwa matsayi mai girma cikin yardar Ubangiji.” Ya kuma duban Haidar sosai yana jin k’walla na ciko idonsa. Sai ya kuma tuno lokutan baya yanda yaita nuna gazawar Haidar d’in da kasawarsa. Muryar Daddy yaci gaba da rawa sanda yake furta “Today I want to tell you this Son. I am so proud of you.. Ina alfaharin zama mahaifinka Aliyu..! Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa." Haidar ma murmushin yake sai yai hugging Daddy “Thank you Daddy.. Thank you for trusting and believing in me. In sha Allah bazan baka kunya ba.” Daga nan manema labarai sukaci gaba da hasko Haidar as the New President of Maitama Builders suna neman ji ta bakinsa. Daga bayansa Ya sinkayo murya na fad’in “Congratulations brother..! Ka cancanci wann matsayin.!” Juyowar da zai sukai ido hud’u da Hisham dake dogara sanda alamun ya fara takawa da sanda bayan da Ya dawo jinya daga Germany. Murmushi Haidar Ya saki sai ya mik’a Hisham hannu suka gaisa “Thank you… Brother.!” Haidar yace hannunsa cikin na Hisham. Hawayen farin ciki suka gangaro ma Hisham dan wann shine rana na farko da Haidar Ya kirasa da D’anuwa Tun bayan da suka san cewa sud’in ‘yanuwan juna ne. Hisham yaci gaba da murmushi yana jinina kai “Ina rok’on Allah yai rik’o da hannayenka sann yai maka jagoranci… D’anuwana.” Haidar ya kuma murmusawa had’ida jinjina kai “Na gode D’anuwa.. I hope very soon zaka samu lafiya sann ka dawo bakin aiki. Muyi aiki hand in hand.. like before.. cikin aminci da yarda.” "Hisham Ya d’ago da mamaki yana dubansa “Does that mean zaka barni naci gaba da aiki k’ark’ashin ka, Mr President.?”" Murmushi Haidar Ya kuma “It’s your company Hisham. Kasancewana shugaba bazai canza matsayinka ba matuk’a zakayi aiki bisa gaskiya da amana.” Hisham sai Ya rungume Haidar yana hawaye yake furta “Thank you brother.. Thank you for accepting me back in the company. Na gode maka matuk’a.” Haidar ya rik’e hannayen Hisham cikin nasa “Together we will take the company to greater heights… Together we will make Daddy proud.!” Hisham yaci gaba da jinjina Kai murmushi saman fuskarsa “Together brother.!” Sai suka rungume juna. Daddy dake gefe yana kallonsu sai Ya goge hawayen da suka gangaro masa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Who would’ve thought wad’ann yaran nasa guda biyu zasu sake zama k’ark’ashin Inuwa guda.? Godiya ta tabbata ga mahaliccinsa da Ya cika ahalinsa da alkhairi bayan sun fuskanci tarin k’alubali da jarabawa. Tabbas when there is life there is hope. Mai rai kada ya zamto mai d’ebe tsammani ga rahamar Ubangijinsa. Domin shi d’in shine mai sauya al’amara a lokacin da yaso. ** Tsaye yake gaban makeken hoton bridge d’in Wanda akayisa cikeda kwarewa da kuma fasaha. Da yawan mutane suna masa lak’abi da ‘heart shaped bridge’ sabida unique shape da wann gadar ke dashi kaman shape din heart. A zuciyarsa yake furta ‘It started with this da alk’awarin cikin watanni uku da alk’awarin AUREN WATA UKU. She came into his life and everything changed. Ya gina bridge d’in with so much love. Kaman yanda wann bridge d’in Tai linking Manyan hanyoyi guda biyu kaman haka Tai linking zukatansu. And that’s why he named the bridge in his heart ‘Bridge of Love.’ Ya waigo yana duban Baba Ali dake guje guje tsakanin ‘yanuwansa twins dake zaune cikin toys dinsu suna wasa. Ummul ce ta k’araso tana k’ok’arin hana Baba Ali guje guje tsakanin yaran gudun kar ya fad’i kansu dan already yaja k’afan wann yaja kunnen wancan. Muryar Haidar ta sinkayo yana fadin “Let him be love… So yake su tashi suyi wasan tare.” Ta dan dubesa “Amma idan Ya fad’i kansu fah. Gaba d’aya sakalta yaron nan kake.” "Murmushi Haidar yai yana janyota jikinsa “What do you expect.? He’s my namesake, after all.”" Ta dan dubesa “kuma sai na bari yaci min zalin iyaye..? Ina nufin yarana manyan sunane dasu. Abba ne da Mommy guda a wajen.” Ya jinjina Kai kad’an “Haka kuma.. Toh amma kinga shi suna biyu yaci. Shifa takwaran Daddy ne kuma takwaran Babansu..” "Ta d’an tsaresa da ido “Wait, what are you implying here.? So kake kace ni kad’ai ce bare a tsakani.?”" D’an tabe baki Haidar yai yana jinjina kai “Kind of..” Sai ya rad’a mata “If you don’t want us to gang up on you kawai Ki haifo naki takwarar..” Zaro ido waje Tai tana turasa “No way.. Nak’i takwarar..” ta k’arashe tana jifa masa teddy. Su duka biyun dariya suke. A haka Baba Ali ya k’araso da gudu ya haye wuyan Haidar. Ai kuwa sai Ya shiga cillasa yana masa kalan wasan da shi kad’ai yake masa. Yaron Ya shiga k’ek’yata dariya yayinda Haidar Ya kwanta da baya Ya d’aura Baba Ali saman k’afansa ya janyo twins zuwa cikinsa. Ummul Tai zaune tana dubansu zuciyarta fari tas. A hankali ta furta “Alhamdulillah.!” *TAMMAT BI HAMDILLAH.!* *A nan na kawo k’arshen wann littafi mai take AUREN WATA UKU. Fad’akarwar dake ciki ina rok’on Allah Ya had’amu daku baki d’aya wajen lada. Kurakuren dake ciki Ubangiji Ya yafe mana.* "*Masoyan Sameena masu bibiyan labarnta, duk yanda kuke ku sani Sameena tana sonku kuma tana ji daku. SAIDAKU masoyan Sameena. Ubangiji ya bar k’auna. Taku Har kullum..*" SameenaAleeyou