[15/07, 6:25 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ• πŸŒ•LELEWALπŸŒ• πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹ πŸŒ•πŸŒ• STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin. MARUBUCIYAR:- ZUHRAA HAMRAH IGIYAR RAYUWA NOOR IMAAN and RUWAN SAMA. FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763 SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar kauna. JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™. EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“ (Home of exquisite writers') Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai. β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€” 1 1 ..... 1️⃣ Gabad'aya tunaninta ya tafi ne ga wani shud'dd'en lokaci chan a rayuwarta, tayi zurfi sossai cikin tunani har bata san ana kwala kiran sunanta ba seda aka ta'ba ta, firgigit tayi tana kallon wacce ta ta'batan, cikin fad'a baaba lami tace "Anya kekam bilkisu ba aljannu bane a kanki? Mutum shi kad'ai se ya zauna yayi zurfi cikin tunani ayi ta kira bazaki ji ba? Da kankantar shekarun kin nan wani irin tunani kikeyi haka?" Murmushi da be kai zuci ba bilkisu tayi cikin sanyin murya irin nata tace "yi hakuri baaba" tsaki er tsohuwar tayi tana ci gaba da mitanta ta nufi katifarta "nan kam ai kin fi kowa kwarewa eeh fannin bada hakuri ba se ki je hajjiya yasmeen ke nemanki". Cikin sanyin yanayi na rashin hayaniya bilkeesu ta mike wadda ita a ganinta hakan sauri ne take abinda ke konawa masu gidan rai kenan musamman Yasmeen da sahla se su ce iskanci ne, fita tayi daga 'bangaren nasu na masu aiki ta nufi chan cikin gida dukda yadda zuciyarta ke luguden bugu sbd sanin se ta sha zagi da fad'a kila harda rankwashi wurin Anty Yasmeen hakan be hanata tafiya cikin natsuwa ba, da sallama ta tura kofan parlorn kasan. Had'add'en parlor ne babba sossai me set d'in kujeru har uku kuma a hakan ba wadda ya takure wani chan tsakiyar parlorn ta hango fahad da khalil suna buga PS kallo d'aya ta musu ta wuce ta nufi stairs da ya kasance had'add'e shima ta haura kanta kasa har ta isa tsakiyar parlorn saman da shima yake yanayi da parlorn kasan tsawa taji an daka mata a firgice ta d'aga kai ta zubawa sahla idanunta masu ruwan zaiba da d'igon baki a kan farin na hagun. Sahla da ta harzuka da kallon ta jefa mata trow pillow tana furta "dan uwarki parlorn na gidanku ne da zaki shigowa mutane kai tsaye ba sallama ba gaisuwa?" Dukawa tayi tace "kiyi hakuri Anty sahla nayi sallama sede baki ji bane ku......." a harzuke sahla tace "you are very stupid ni sa'ar uwarki ce ai da zaki na min magana kina kallon tsakiyar kwayar idona" Shiru kuma tayi bata kara magana ba, sanin halinta na baza ta sake magana ba kuma yasa sahla cigaba da aika mata zagi kala kala. Ita ta rasa me tayiwa en gidan nan da suka tsaneta haka, duk cikin masu aikin gidan ba wadda suka tsana kaman ita komai tayi bata burgesu, duk wahalansu da take sha ba me mata Sannu bare na gode, maganan sahla ne ya katse mata tunaninta "kin 'bace min da gani ko se na mike na taka ruwan cikinki?" Da sauri ta mike ta nufi d'akin Yasmeen, da sallama ta shiga sede Yasmeen dake zaune tana danna waya ko d'agowa batayi ta kalleta ba bare ta sa ran amsar sallamanta. "Anty Yasmeen gani" Shiru ta mata taci gaba da abinda takeyi seda ta shaaka don kanta tace "Don ubanki bance kar na dawo na samu inner wears d'ina a toilet nan ba?" Hawaye ne cike tab da kwayar idanunta wadda suka kara musu sheki, cikin rawar murya tace "Anty na ga sunyi stain ne and wannan kaman sirrinki ne ke ya kamata ki...." bata karasa ba taji saukan rankwashi a kanta runtse idanunta tayi wadda hakan ya baiwa hawayen ciki damar zuba. "Wuce kije ki d'auka ki wanke min maza maza, har ke Kin isa ki gayamin abinda ya kamata nayi? Shegiya me kama da aljannu da shegen turancin karyar da kika d'aurawa kai" cewar Yasmeen, da sauri ta wuce hawayenta na kara yawa d'auko panties d'in tayi ta fito, daga nan saman ta bud'e wani kofa wadda ya kasance stairs ne daga bakinshi har kasa ta gangara wurin tap da suka saba wanki da wanke wanke se kuma irin girkin taro haka ruwa ta tara ta hau wankewa bayan ta shiga laundry room dake nan wurin ta d'auko sabulu da omo. Cikin tsantsan kyankyami da take dashi wadda ko ita kanta jininta da kyar take wankewa bare na wata, cikin bakin ciki ta fashe da kuka, wani irin rayuwar rashin 'yancin kai ne wannan? Haka rayuwarta zata kare? Cikin muryan kuka ta furta "Ammiee..... Abbiena me yasa kuka yi saurin tafiya kuka barni?" Se kuka.... ~~~~~~~~ Wayarshi kirar iPhone 11 pro max ce hannunshi yana kallon porn kaman yadda ya saba yayinda d'ayar hannun ke rike da glass d'in wine me tsananin tsada sossai ya shagala da kallon wadda har be san an shigo ba se ji yayi an fisge wayan, a Zafafe ya d'ago se suka had'a ido da wata had'add'iyar babe da yayi d'azu wani kasalallen murmushi ya saki tare da janyo hannunta jikinshi yana shunshunata yace "hey hind banyi zaton zaki zo ba ai". Cikin karairaya irin na matan bariki ta sa hannu tana shafa wuyanshi zuwa kirjinshi da ya kasance naked tace "na isa? Duk garin nan wace babe ce da ta isa ta amsa sunanta zata ji Kira irin naka na manyan harka taki amsawa Ai babu shegiyar" wani irin dariya yayi ya kur'bi giyar hannunshi ya tsiyaya mata a baki ta kuwa had'iye tana me shafashi nan take suka shagala suna yi suna kuma kallon sex video da dama yake kallo. Allah ya shiryamu ya shirya mana zuriah. ~~~~~~~~~ A matukar gajiye ya bud'e motanshi kirar Hyundai Elantra ze shiga yaji ance "barrister Aayan" seda ya runtse ido yayi kaman ze yi kuka da fuskanshi kan ya juyo ya Kalli abokinshi dake kiranshi "what again shaheed?" Dariya shaheed ya fashe dashi yana nuna shi yace "ka ga fuskanka kuwa kaman irin baby da uwa ta hana wasan kasa" had'e rai yayi yace "in ba ka da abin fad'a shaheed na wuce na gaji hutu nake bukata" mika mishi file d'in hannunshi yayi yace "case d'in rape da kace zakayi handling d'in nan ne ka san jibi za'a fara sauraran shari'ar ya kamata ka duba In kaje gida" kar'ba yayi ya had'a da blazer d'inshi ya watsa sit d'in baya kan ya shiga motar ba tare da ya kuma tankawa shaheed ba ya ja ya fice don ya san yace ze kara magana se ya kuma rikeshi da wani surutun. Direct gidanshi ya nufa dake malamre nan jimeta dukda gida yake shirin shiga sede hankalinshi in yayi dubu a tashe yake na tunanin abinda ze je ya tarar, mazajen aure na nufan gidanjesu ne cike da farin ciki da jin daad'i sbd natsuwar da ako yaushe suke samu da iyalansu amma banda shi, ya gwammaci rayuwarshi kan aure da wannan da yake ciki. Da wannan tunani yayi horn a bakin ash iron gate d'inshi me gadi yazo da sauri ya bud'e mishi da adu'ar shiga gida a bakinshi ya shiga yayi parking bayan ya d'an tsaya sun gaisa da me gadin, kallon inda motanta yake yayi tana nan kenan bata fita ba, sit d'in Baya ya bud'e ya kwaso abubuwanshi ya nufi cikin gidan da sallama a bakinshi ya tura kofan parlorn sede hautsatsiyar karni da ya tareshi ne yasa ya kasa karasawa, tana zaune kaman kullum gaban extension wire hannunta rike da wayanta tana dannawa tana dariya. Kallon jikinta yayi tun kayan baccin da ya fita ya barta dashi wadda jiya ma dasu ta yini rintse idanunshi yayi ya kuma bud'ewa sun kad'a sunyi ja ranshi a hautsine ya kalli tsakiyar parlorn komai d'ai d'ai ba kimtsi ba komai cups ko ta Ina sbd bazata iya dafa abinci ba tana dannan waya ta gwammaci ta sha wannan ta sha wanchan suma da kyar, wani irin bala'i ne wannan. Be san sadda ya fara sana'ar tashi ba wato taunar Lips musamman In ranshi na a matukar 'bace, idanunshi na kan 'yarsu kwaya d'aya sahar dake da 3 and half years tana bacci ita d'inma kayan baccinta da ya sauya mata jiya ne jikinta kenan ba'a mata ko wankan safe ba, ga fuskanta duk jirwayen hawaye da suka bushe alamun kuka ta sha har ta gode Allah uwar taki kulata. In da sabo yaci ace ya saba da halin Zaheera, yana matukar bakin cikin ganin matar aurenshi a haka, lumshe ido yayi ya kuma bud'ewa kan ya sa kafafunshi cikin parlorn direct kan sahar yayi ya d'auketa suka haura sama ita kuwa zaheera ko motsinshi ma bata ji ba se murmushi take tana chatting, yana shiga room d'inshi da niyyar kwantar da ita ta farka tana ganinshi ta saki murmushi tace "Daddy..." murmushi shima ya kakalo yace "baby har kin tashi?" Kai ta gyad'a se ta marairaice tace "mi nyaman nyamdu daddy"(zan ci abinci daddy) murmushi ya mata yace "toh first of all ayi wanka kan abinci right?" Kai ta gyad'a. Ya d'auketa zuwa toilet d'inshi dake wanke tas sbd kan yayi wankan safe yake wanke abinshi in ya fito ya gyara gadonshi ya share d'aki ya fice in yaci sa'a normal ze dawo ya samu d'akin nashi kaman Yadda ya bari but in har be ci sa'a ba jujun zaheera suka kawota d'akin toh fah kan ya dawo bola albarka. wanka ya ma sahar ya fito da ita cikin towel seda ya shafa mata mai kan yaje room d'inta ya d'auko mata riga da pant yazo ya sa mata se surutu take zuba mishi yana biye mata, a tare sukaje kitchen na saman ya had'a mata tea me kauri tare da soya mata kwai guda biyu ya kawota parlor kan su zauna ma ta kusa shanye tean sbd yunwar da take ji da kanshi yayi ta bata kwan har ta koshi, baki ta shangala mishi tana buga ciki tace "daddy pim pim" yana murmushi yace "toh se d'ume?"(se mene) tace "a wannam banchilili"(ayi mini banchilili). Yace "toh ha mi yiwa minfu mi nyama se en wad'a"(to bara nayi wanka nima naci abinci se muyi) tsalle ta fara ya mike ya barta nan ya wuce room d'inshi yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya tunaninshi gabad'aya na ga kan matakin da ze d'auka kan zaheera, ga wannan yarinyar ba karamin shiga hakkinta take ba, ba ma ita ba yanzu yadda ta barta a parlon da yunwa da komai tayi bacci da wani mugun ne ya shigo ya sa'beta yayi gaba bama Zata sani ba fa tunda bama taji shigowanshi da d'aukan samha zuwa haurowansu ba. Ya gama yanke ze samu ummie da maganan zaheera for the last time tunda kullum hakuri ake bashi ace kuruciyace zata dena, In taki sa mishi hannu wurin gyarata toh fa dole yayi wani aure don ba me aikin da ze ajiye gidanshi, sahar kuma for now play class ze samu ya saka ta ko ba komai zata na cin abinci me kyau in har me tsada ne. Car key ya d'auko ya sauko sbd rashin ganin sahar sama tana nan tana wasanta da Teddy's d'inta tana ganinshi ta kwala mishi kira wadda hakan ya sa zaheera farga da zuwanshi ta d'ago tana sosa kanta da ya daskare sbd rashin gyara tace "au ashe ka dawo?" Be kalleta ba yace "uhmm" ta'be baki tayi ta maida kanta kan wayarta shi kuwa hannun samha ya kama suka fice. ~~~~~~~~~~ Kaman daga sama taji muryan hajiya tana cewa "samun wurii, wato sbd Yasmeen ta sakaki wanke en waennan kayan shine kike rusa wannan uban kuka? Wai me ya kawoki gidan nan ne In ba aikatau ba sbd mutuwar zuciya irin na iyayenki, Toh kuwa sede kiyi kukan jini gama mata kije closet na akwai kayan wankina cikin basket dama Adamu zan bawa amma tunda gaki Ai shikenan" cikin ladabi tace "Toh hajiya" ta cigaba da wankin hawaye na kwaranya kan fuskanta, ba abinda yafi tsaya mata a rai irin yadda suke cin mutuncin iyayenta da suke kwance a cikin kabarinsu ta san da Abbienta na nan ko Ammienta babu wadda ze bari a turota aikatau gidan irin waennan mutane marasa tausayi sede ma ita ta saka ayi. Hawayenta ta share ta mike taje ta shanya panties d'in Yasmeen daga nan ta kuma komawa saman zuwa d'akin hajiya Allah ya taimaketa bata had'u da kowa ba ta d'auko basket d'in ta nufo kofar se tajishi a kulle kuma murd'awa tayi da gaske dai an kulle kuma ba key jiki juyowa tayi tabi ta cikin parlorn anan ta ga sahla rike da keys d'in tana juyawa bata ce mata komai ba ta sauka parlorn kasa anan ta ga hajiya na zaune da wata bakuwa, bakuwar ta gaisar tayiwa hajiya sannu kan ta fice. Babban abinda ya sa ta tsani bi ta nan sbd yaya Aadil ne part d'insu na nan daga inda yabi zuwa baya hajiya kuma ta hana bin ta cikin kitchen da ko wani kaya In ba kayan da dama a cikin kitchen d'in suke ba, aiko abinda ta tsani gani shi idanunta da kunnuwanta suka jiyo mata, had'a idanun da sukayi yasa tayi saurin ta'awizi tana neman tsarin Allah da sharrinshi, iskanci a filin Allah. Seda ya mata kiss kaman ze cinye bakin kan ya d'aga mata hannu tana godiya ta fice akan zasuyi waya, kallon bayan Bilkeesu yayi tare da lashe baki yace "in har sunana Aadil Sadeeq Chubado se na koya miki hankali, ba ni kike kyama ba?" Yayi wani irin dariya kan ya juya ya koma part d'inshi dama rako hindu yayi bayan sun gama masha'arsu ya cika ta da kud'i. Sarai ta jishi sede bata tanka ba se ma kara sauri da tayi zuwa backyard d'in nan ta sunkuya wankin hajiya, tana cikin yi aka kira magrib bari tayi tayi alwala nan bakin pampon ta nufi part d'insu tana shiga taga Indo cikin murna ta rungumeta tace "indo yaushe kika shigo ban ga wucewarki ba?" Itama indo cikin farin cikin ganinta tace "ban jima sossai ba wuraren biyar haka" Bilkees tace "kila lokacin naje d'auko kayan hajiya, sannu da zuwa ya mutanen gida?" Tace "suna nan kalau" bilkeesu tace "bara nayi sallah se muje wurin wankina Ina yi muna hiran yaushe gamo" sallaya ta shimfid'a ta tada sallah itama indo toilet d'insu ta fad'a tayi alwala ta fito ta tada nata sallahn a gefen bilkeesu inda baaba lami ma na chan tanayi. Bayan sun idar tana ninke sallaya indo ke tambayarta "banga su grace ba" Tace "suna kitchen da rana ma seda muka kwasa da blessing ganin abinda en gidan nan ke min yasa su ma suke neman maidani jaka" dariya indo tayi tana ajiye khimar d'inta Don ita yawo take ba wani khimar a gidan sa'banin bilkeesu da seda hijabi take fita daga d'akinsu, tace "me ya had'aku?" Baaba lami da take ta lazaminta bata tankasu ba se binsu da tayi da ido har suka fice Bilkeesu na cewa "wai fah kayan miya aka kawo dayawa a lokacin ma gyaran d'akin Anty Yasmeen nake kuma ga na su khalil da ban gyara ba Sannan ga wankin jibgin inner wears d'in Anty Yasmeen wai ta sameni wai hajiya tace In zo muyi gyaran kayan miya". Dariya sossai indo ke yi sbd yadda bilkisu ke kwaikwayar maganansu itama se murmushi take kaman bata da wani damuwa Alhalin kasan ranta duhu ne baki kirin, indo tace "Toh me kika ce musu?" "Ke ma Ai kin san abinda zance, cewa nayi bazanyi ba" wani dariyar indo ta fashe dashi tace "yanzu da da gaske hajiyarce ta aikosu fah?" Ta'be baki tayi tace "na san karyarsu na kuma san ba aikosun zatayi ba". Seda suka isa wurin wankin nata da hasken security light d'in gidan ya haska ko Ina tarwal kaman rana kan indo tace "bara naje nayiwa hajiya sannu da gida ta san da dawowata" Kai kawai bilkeesu ta d'aga mata yayinda ta ci gaba da wankinta, kaman daga sama taji ance "Ke" Da sauri ta d'ago a firgice ta matsa jikin gini ta mannu tana kallonshi da idanunta dake kara sashi jin tsantsar kwad'ayi da sha'awarta. "Ki je d'akina akwai plates da na ci abinci yanzu ki fiddo ban son kazanta" dakewa tayi don baza taje ba sede hajiya ta kila ta yadda ta saba In ya aiketa d'akin shi taki zuwa, kallon wurin tayi ba kowa so quit se ta fara ambaton Allah cikin dakiya tace "ba aikana ba kenan, as you can see wanki nake" matsota ya fara a harzuke yace "kee!! Wai me kika d'au kanki ne? Ina sa'a dake da kullum zan sakaki aiki kice bazakiyi ba? Kin kuwa san waye ni?" Hannunta ze rike ta fisge ta matsa tana cewa "Wallahi bazan je ba In ka ga dama sa wuyana gabas ka yanka" a zafafe ya kuma nufota ihu ta kwala se ga baaba lami bayanta ta riketa tana cewa "lafiya Alhaji Aadil?" Lip d'inshi na kasa ya taune yana aika mata sakon harara ya juya ya fice. Kuka ta fashe dashi tana furta "ya zanyi ne da rayuwata? Ya suke so nayi dan Allah?" Cike da tausayinta baaba lami tace "Bilkisu na d'aukeku kaman 'ya'yan da na Haifa a cikina bazan ta'ba son wani mummunan abu ya sameku ba musamman ke da Aadil ya sawa ido, bakya ganin kaman komawanki gidanku shi yafi alkhairi?" wani irin murmushin takaici ta saki kan tace "hmmm baaba kina ganin akwai banbanci tsakanin gidanmu da nan ne? Gani nake ma gwara nan zasu iya min in hakura amma chan fah? Gwara duka da gallazawar hajiya akan na mama, gwara barazanar Aadil akan na shu'aib gwara hantara da kyara irin na Yasmeen da sahla akan ummu hadiyya da Zainab gwara anan khalil da fahad suna bani girma akan yasir da yassar, a nan ban ta'ba ganin mahaifinsu ba bare ya bada gudumawa kan abinda ake min amma a chann......." kuka ne yaci karfinta wadda ya hanata karasawa...... *Amm a wannan Karon bazaku samu yadda kukeso ba sbd abubuwa da suka d'an min yawa maybe inyi typing sau hud'u a sati maybe sau uku In na samu sarari kuma kullum In Shaa Allahu. Fatana dae kawai shine inga ruwan comments* πŸ–€GureenjoπŸ–€ [15/07, 6:26 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ• πŸŒ•LELEWALπŸŒ• πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹ πŸŒ•πŸŒ• STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin. MARUBUCIYAR:- ZUHRAA HAMRAH IGIYAR RAYUWA NOOR IMAAN and RUWAN SAMA. FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763 SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar kauna. JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™. EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“ (Home of exquisite writers') Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai. β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€” 2 ......... 2️⃣ 2 Dafa kafad'unta baaba tayi dukda kuwa tsawo da bilkees ta fita cike da tausayawa tace "Daga ranar da na fara ganinki bilkeesu na san akwai murd'dd'iyar abu cikin rayuwarki, kwarai na kasance me matukar tausaya miki Allah ya kawo miki mafita" rungume baaba kawai tayi tana me ci gaba da hawaye cikin rawar murya tace "kwarai kuwa baaba rayuwata bata da wani abu face duhu me matukar sarkakiya tabbas a Baya nayi farin ciki sede ya wanzu a rayuwata ne na lokaci kankani, na gode kwarai da kulawarki watarana zan baki labarin bilkees.." tana kai nan ta d'ago ta share hawayenta tare da sakin murmushi tace "baaba bara na karasa wankin nan kar dare ya min". Da mamaki baaba ke kallonta kaman ba itace ke kuka yanzu ba, ta jinjinawa matukar dauriya da shanye damuwa irin na bilkisu, ita ma murmushi tayi kan ta wuce, bata kai ga kulewa ba indo ta dawo kallonta bilkees tayi tace "se yanzu? Ko wani aikin aka saki?" Girgiza kai tayi tace "na tsaya kallon dramar ya Aadil da yayanshi ne" bilkees na me cigaba da wankinta tace "ya zo ne?" Indo tace "har ma yayi zuciya ya fice kuma fah da 'yarshi yazo baki ga kyaunta ba" d'an kallonta bilkees tayi tace "zuciya kuma?" Indo na tsoma hannunta cikin wankin Don tayata tace "eh kin san ya tsani halin Aadil na bin mata so yana kokarin shigowane yaga wata karuwa da ta fita daga gidan nan shine fah yazo ya haushi da fad'a hajiya kuma ta shiga ta kareshi Toh ko zama be yi ba ya fice". Girgiza kai bilkees tayi tana cewa a zuciyarta 'ashe ba ni kad'ai bace na kyamaci wannan hali na ya Aadil' a fili kuwa cewa tayi "oh watana uku a gidan nan amma Allah be yi na ga wannan yayan nasu ba" waro ido indo tayi tana cewa "ashe fah baki ta'ba ganinshi ba duk ya fi su kyau da hankali har Anty Sumayya da Anty Rufaida kuwa ga 'yarshi Masha Allah In kin ganta" murmushi bilkees tayi tana cewa "wata rana zan ganshi Ai tunda Ina gidan". Daga nan ta kauda hiran en gidan suka koma na kauyen su indo se labari take bata tana dariya, kusan 8pm suka gama wankin, bilkees na da tattare parlorn kasa inda anan suke cin abinci hakan ya sa indo d'auka musu dinner d'insu ta wuce shiyarsu na masu aiki da ya kasance da d'akuna manya biyu kowanne da kewaye an zagayeshi Sannan tsakiyar ya kasance kaman zaure da aka sa mishi tiles. 'Daki d'aya ya kasance su su uku indo, bilkees da baaba kowacce da katifanta kuma su ne masu share share na cikin gida, se baaba lami dake girkin abincin gargajiya a duk sadda suke marmari ko Alhajinsu ya dawo, d'ayar d'akin kuma na grace da blessing sune masu aikin duk wani abincin da ya shafi turawa. Da sallama ta shiga parlorn Allah ya taimaketa sun haura Don chan take jin muryoyinsu suna hira, a tsanake ta tattare parlorn tsab duk wasu kwanuka dake dining wadda suka ci abinci suka wargazar ta kai kitchen ta goge dining d'in tare da share parlorn, a gajiye ta mike da ta gama aikin sbd bayanta da ya kama lumshe ido tayi ta kuma bud'e komai normal se ta ja kofa ba tare da ta kashe wuta ba sbd su Fahad da zasu sauko zuwa d'akinsu dake parlorn kasan In sun gama hira. Seda tayi Alwala a tab kan ta wuce d'akinsu hira ta samu baaba nayi da indo yayinda abincinsu ke zaune suna jiranta ba tare da tayi sallar da tayi Niyya ba tayi joining d'insu suka ci abincin, dake a ka'idarta In tana cin abinci In ba ya kama dole ba bata ta'ba iya magana hakan ya sa sede ido take binsu dashi tana gamawa kuwa ta mike ta kurkuro baki tazo tayi sallah tare da gabatar da shafa'i, kasancewar tana tashin dare yasa batayi wutiri ba kan ta idar indo ta tattare inda suka ci abincin kwanukan se gobe in sun tashi fita zasu fita dashi sbd tsoron sharrin mutan gidan. Hamma ta saki tana kallon indo dake son fara janta da hira tace "ke wallahi bacci nake ji kaman me bazan iya biyewa surutun kin nan ba" kwanciya tayi tana jin yadda indon ke mita bayan ta gama adu'o'inta na bacci ta shafa tace "baaba se da safe" baaba da ita ma ta kwanta tace "Allah ya tashe mu lafiya d'iyar albarka" sossai bilkees taji daad'in sunan se ta lumshe ido kawai tana tuno mahaifiyarta, a lokaci d'aya tana dariyar indo sbd ganin ta kashe wuta itama ta kwanta sbd ba me biye mata ayi surutu har da hawayenta, kan kace me bacci ya sureta sbd wahalan da ta sha na aiki. ~~~~~~~~ Abinda ya faru kuwa ta 'bangaren Aayan yana danna horn na shigowa gidan nasu yaga wata ta fito da wani irin shiga na Allah wadai cikin takaici da jin haushi yake kallonta har ta fice, gaba yayo da motarshi ya sauke glass yana kallon baba lawalli dake gaisheshi sama sama ya amsa ya d'aura da "wan chan bakuwar hajiya ce?" Girgiza kai yayi yace "a'a Alhaji karami wurin Me gida Aadil ta zo" had'e rai yayi yace "tun yaushe?" Me gadin yace "tun bayan la'asar ranka ya dad'e" lip d'inshi ya taune yana me lumshe ido yace "shikenan baba" ya ja motar ya karasa shigowa cikin gidan. Sossai ranshi ke 'baci In ya tuna wai a gidansu cikin gidansu kaninshi ke masha'a ba tare da Ummie ta tsawatar mishi ba, In basa tsoron idon alumma Ai ya kamata su ji na Allah da ya ara musu rai da lafiya da kuma kud'i suke yadda suka so bare kuma mahaifinsu da ba mazauni bane in ya ji wannan labari ze iya yanke jiki ya fad'i sbd matsananciyar hawan jinin da yake dashi, me yasa basu da tausayi haka?. Hannunshi rike da na samha ya tura kofar babban parlorn Aadil dake tsaye daga gefen kofan yana magana da ummie da ta hakimce tana kallon tv yayi arba da dama shi yake nema Ai kuwa be yi wata wata ba ya tsinka mishi mari wadda ya sa yasmin dake danna waya mikewa tare da kama baki tana zaro ido, sahla dake saukowa ai da sauri ta koma yayinda ummie ta kafa mishi ido cikin 'bacin rai. A zafafe yace "Aadil kai kam wani irin dabba ne? Me ke damunka? Ko shaye shayen da kakeyi ya fara ta'ba maka kwakwalwane ban sani ba? How many times did I warned you in zaka bi matanka kasan inda zaka je kabi ba cikin gidan nan ba?" Huci kawai Aadil ke yi idanunshi sun kad'a sunyi jajir ba Don yana tsoron wan nashi ba ba abinda ze hanashi rama marinshi. Ummie ne cikin masifa tace "me haka Aayan? Akan wani dalili zaka gaura mishi irin marin nan? Na sha fad'a maka hakuri zaka na yi da Kanin kan nan har yanzu fah yaro ne yaushe ya gama mallakan hankalin kanshi da ya san abinda yake me kyau ko marar kyau? Toh ka fita idanuna In rufe akan wannan shine last da zan ga ka d'aga hannu ka mareshi In ba haka ba zan iya sa'ba maka akanshi" cike da takaici yake kallon ummien a sanyaye yace "me yasa a ko yaushe kike goya mishi Baya ne ummie? Baki ganin irin Girman zunubin da yake aikatawa? Idan Allah ya tashi tambayanki amanar da ya baki me zaki ce mishi ummie?". Ajiyar zuciya ta sauke tana tahowa gareshi tace "Son ka fahimceni ba fa wai ki nake ka ma kaninka fad'a ba sede ka duba....." katseta yayi da "shikenan ummie he should do what ever he felt like doing" ya kausasa murya yana kallon Aadil "but ba a gidan nan ba sbd baza ka 'bata future d'in kannenmu dake tasowa In zuba maka ido Ina kallo ba useless boy" yana kai nan ya juya rike da hannun ershi ya fice ummie na kiranshi ko tsayawa be yi sbd ranshi dake tsananin suya. Mota kawai ya ja ya fice direct mafiyas ya nufa dake cikin yola, a tsanake ya danna horn har sau biyu kan me gadin ya leko ya koma kuma ya bud'e gate d'in sbd gane shi da yayi, a mutunce suka gaisa ya karasa kutsawa ciki tare da samun wuri yayi parking, part babba dake tsakiyar flat house d'in ya nufa ya kwankwasa, ba 'bata lokaci aka bud'e "oyoyo uncle Aayan" yarinyar da ta bud'e ta fad'a tare da rungumanshi sede ganin samha yasa tayi ihu tana kwala kiran sunan kanwarta da kaninta "mu'azzam, Salma guess who is here?" Da gudu suka karaso suna me tureta ganin Sahar yasa suka fara murna. Aayan dake murmushi yace "a matsamin to kan yanzu na juya da ita mu koma inda muka fito" cikin harshen fulatanci suma duk da fulatancin suke magana da sauri suka matsa ya shiga, Aisha ta tsaya gaidashi kawai ta ga Salma ta d'auke sahar dake ta dariyar ganinsu tayi d'aki da gudu mu'azzam ya bita Ai itama da gudu ta bisu tana kwala kiran ta rigasu da d'aukanta. Murmushi kawai Aayan ke yi yaji rabi da kwatar damuwar da ya kwaso ya kau, "A'a Barrister lafiya kuwa da irin wannan ajiyar zuciyar?" Kallonta yayi sanye take da khimar alamun sallah ta idar cewa yayi "Adda wallahi ba lafiya ba I'm tired of zaheera and Aadil" Tace "zo zauna" zama yayi ta wuce kitchen d'inta ta had'o mishi abinci a tray da ruwa da kuma drinks tazo ta ajiye gabanshi akan center table, ba tare da 'bata lokaci ba ya d'iba a plate ya fara ci rabonshi da kwakwaran abinci tun jiya. Cike da tausayawa take kallonshi har ya gama ci ya ajiye plate d'in, "ka ci gaba da hakuri barrister komai me wucewa ne" yace "magananku kenan maman Aisha daga ke har ummie kullum hakuri hakuri ni kam zaheera ce kad'ai mace a duniya? I'm very tired of her habit Ina kuma ganin lokacin d'aukan mataki na yayi dama chan she wasn't my choice sbd ummie kawai na aureta but look..." ajiyar zuciya ta sauke tace "A kullum Ina tayaka da adu'a Allah ya shige maka gaba a duk lamuranka barrister ya kara maka jumriya da hali irin na zaheera but abinda baka sani ba shine akwai fah sharad'in da aka gindaya tsakanin ummie da First Lady kan a aura maka zaheera wadda kai baka da masaniya......" Bata karasa ba yace "to hell with their sharad'i, I don't care abinda kawai na sani shine duk hukuncin da na gama yankewa idan time yayi zan aiwatar" saninshi da kafiya yasa ta ajiye maganan gefe tace "d'azu naji ka ambaci Aadil wani abin kuma yayi?" Seda ya tauni lip sossai ita dae ta zuba ido tana kallonshi sbd hakan da yayi ya nuna Aadil ya kaishi makura sossai, "could you imagine yaron nan mata yake kaiwa har cikin gida yake abinda yaga daama ba tare da ummie ta tsawatar mishi ba?" Salati ta saki tana me gyara zama a lokaci d'aya tana al'ajabin irin son da ummie ke wa aadil Anya kuwa wannan soyayyace me d'aurewa? A sanyaye hawaye na gangaro mata tace "since when baka ta'ba fad'amin ba?" Yace "last three weeks naje gidan na ga wata na shiga side d'inshi I followed her sbd sanin ba family bace ko one of masu aiki ganin shigar dake jikinta but to my biggest surprise Ina shiga na gansu rungume da juna yana shafata yayinda d'ayan hanunshi rike da wine yana sha nayi musu fata fata na koreta inda nan na samu ummie da maganan se ta nuna min ta sani Ai Aadil yaro ne be girma ba, saurayi me almost 25 years take cewa yaro fah" Dafe goshi yayi na mintuna yana jin yadda yayar tashi ke kuka ci gaba yayi "and also today zan shiga naga fitan karuwar, I even slapped him but maimakon ummie taga gyara nake kokarin yi kasancewana babba na miji se cewa tayi zata sa'ba min na kuma ta'bashi" salati Adda sumayya take ta nanatawa wace irin uwa ce wannan? Muskutawa Aayan yayi yace "ba kuka zaki mishi ba adu'a zaki mishi In Shaa Allahu kan Abba ya san da maganan nan zan san yadda zanyi da Aadil" share hawayenta tayi tace "Allah ubangiji ya shirya mana zuri'ah" ya amsa da "Ameen" tace "Toh barrister ka d'auki me aiki mana ko don sbd sahar tana cutuwa fah sossai" yace "I know play class zan sa ta, you know I hate maids d'innan wallahi" Tace "but akwai fah masu hankali" seda ya ta'be baki kan yace "what ever, kira yaran nan please ki ba sahar abinci mu tafi almost 10" yayi maganan yana duba had'add'iyar wrist watch d'inshi. Kiransu tayi dukkansu suka fito sahar tazo da gudu ta rungumeta itama rungumeta tayi tana cewa "oyoyo my baby" ta d'auketa zuwa kan cinyarta, kallon Aisha tayi tace "sa min abinci kad'an a plate in bata" sakawa tayi tana dariya hirar da mu'azzam ke ma uncle Aayan na zane Salma da akayi yau a school sbd fad'a a class shi kam da ake ba labari murmushi kawai yake yana rike da hannun salma Dake son kaiwa mu'azzam duka, Adda dake kokarin bawa layla abinci tace "Ai ke kam salamatu ko borkono nayi taci da cikinki albarka" wadda hakan ya sa en uwanta kwashewa da dariya se ta hau kuka. Aayan dake murmushi yace "uhm uhm ku dena sa salmahta kuka Ai abu aka miki kika rama ko?" Kai ta gyad'a tace "ba ita bace ta ce min wai salamatu" dariya suka kuma kwashewa dashi aiko mu'azzam bud'an bakinshi yace "hajiya salamatu" ya kwasa da gudu ta kuwa bishi, girgiza kai Aayan yayi yana murmushi dramar yaran nan se su, sahar da ake ba abinci se kokarin zillewa ta bi su take. Bayan Adda ta gama bata abinci ta dubeshi "yaushe ne EDDn zaheeran?" Yace "In next three weeks tace min she was even saying ita bazata iya wannan haihuwa haihuwan ba sbd a gidansu bata ga ana haka ba so tana haifan na cikinta zata juya mahaifa" zaro ido Adda tayi tace "and kayi shiru kai kuma?" Kafad'a ya d'age yace "damuwanta" tare da mikewa ya rike hannun sahar, yace "bari mu wuce, gud night" mikewa tayi ita da Aisha suka rakosu bakin mota seda suka shiga kan Addan tace "Allah ya tashemu lafiya" ya amsa da Ameen ya ja motan ya fice. A sanyaye ta bi shi da kallo har me gadi ya rufe gate d'in ta san shi da son yara dukda be fiye surutu irin nasu ba but yana son yara, aiko idan har zaheera ta kuskura ta juya mahaifannan she will definitely push him inda ba wadda ze so a familyn, ajiyar zuciya ta sauke tana furta "I most stop her". ~~~~~~~~~~ Juyi take cikin bacci tana fidda wani irin numfashi da sautin kuka kad'an kad'an wadda duk alamu suka nuna cikin bacci ne hakan ke faruwa sanadiyar mafarki da take, sossai tayi jigib da zufa a hankali sautin kukanta ya cigaba da karuwa kaman an mitsineta tayi wani irin zabura ta mike zaune tana ambaton sunan Allah, shafa fuskan ta tayi tana goge hawayen da ya gama jike mata kumatu ko bata duba time ba ta san karfe biyu ce daidai sbd wannan ba shine karon farkon mafarkinta da tashinta hakan ba. Kusan zata ce ta saba sbd tunda tayi turning 12 take irin wannan mafarki tun bata saba mikewa tayi nafila ba har ta fara a ko da yaushe idan hakan ya faru se ta mike ta kaiwa Allah kukanta sbd ta kasance me matukar damuwa da se Allah ne kad'ai ze iya fiddata, mikewa tayi a sanyaye tana gyara d'aurin d'an kwalin kanta, da lalu'be ta fad'a toilet ta d'auro alwala ta fito ta kuma lalu'bawa ta shimfid'a sallaya ta sa khimar ta tada sallah raka'a biyu tayi a na karshe ta jima cikin sujjada tana zub da hawaye tare da yiwa Allah kirari ya kawo mata haske cikin rayuwarta ya bayyana mata yayanta a duk inda yake. ~~~~~~~~~ A daidai wannan lokaci Aadil ke wani had'add'en bar wurin wani partyn friend d'inshi gabad'aya wurin duhu ne hasken er kad'ance sbd fitila marar haske da suka saka kowanne saurayi a wurin rungume yake da buduruwa Suna rawa da shafe shafe, sossai Aadil ke enjoying moment d'in sbd a rayuwarshi yana matukar son party mussaman irin wannan cikin dare ga harka ko ta Ina. Dukda en mata biyu da suke rungume dashi tunaninshi da hankalinshi gabad'aya na ga Bilkees ne, yana mamakin irin kyaun fuskanta wadda ze so ganin cikin ya yake amma munafuka kullum cikin hijab take tana mishi bakin ciki, ya ayyana hakan a ranshi, be san me yasa komin daad'in mace se yake ji a jikinshi kaman bazata kai bilkees ba, he has one and only wish yaga ya samu yarinyar nan yayi yadda yake so da ita wadda soon yake saka ran hakarshi zata cimma ruwa, wani mugun murmushi ya sake wadda yayi mugun kara mishi kyau sbd shi d'in kyakyawa ne na sossai, Sannan ga dala abinda ke jan en mata gareshi kenan, wadda ya mayar kamar rigar sawa a rana ze kwanta da mace har uku ko a kwalar riganshi gobe wasu ze nema. ~~~~~~~~ A daidai wannan lokacin barrister Aayan ya gama duba case da ze fara gabatarwa jibi wadda hakan ya nuna mishi dole gobe ya ziyarci familyn yarinyar ya kara fuskantan abinda ya shige mishi duhu, rufe system d'in gabanshi yayi ya mike ya shige toilet alwala ya d'auro yazo ya wuce inda ya kebance don sallah a cikin d'akin nashi bayan ya saka jallabiya ya tada sallah, raka'a biyu ya gabatar bayan ya sallame ya had'e kai da gwiwa yana adu'a hawaye na zuba mishi, cikin sanyin murya da zub da hawaye ya furta 'maami...' da sauri ya share hawayen ya mike ya cire jallabiyar ya koma gadonshi bayan ya sa hannu yayi switching light ya janyo sahar jikinshi tare da rintse ido hawayen shi na cigaba da gangara duk kuwa da yadda yake son dannewa. Mutuniyarshi kuwa na chan tana aikin dannan wayanta bama ta san halin da yake ciki ba, ko da ya dawo dama ba magana ta mishi ba shima kuma be neme ta ba se samanshi da ya hauro ya shiga harkokin gabanshi...... πŸ–€GureenjohπŸ–€ [15/07, 6:26 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ• πŸŒ•LELEWALπŸŒ• πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹ πŸŒ•πŸŒ• STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin. MARUBUCIYAR:- ZUHRAA HAMRAH IGIYAR RAYUWA NOOR IMAAN and RUWAN SAMA. FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763 SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar kauna. JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™. EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“ (Home of exquisite writers') Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai. β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€” ..........3 Cikin baccin da ya kuma d'aukanta kan sallayar take jin kiran sallah sama sama, a hankali ta bud'e idanunta tana me mikewa zaune, ta d'an jima kan ta mike zuwa toilet ta kuma yin alwala tazo ta tashi ba-ba lami da indo se da taga tashinsu kan ta tada raka'atainil fajr, a natse take komanta yadda daga gani zaka fahimci ilimin addini ya ratsata, bayan sun idar da sallahn asuba kowa ya fice Don fara Ayyukansa. Indo Zata haura sama bilkees tayi saurin riketa tana furta "Da karambanin kin nan bazan barki hawa sama ba kije ki tashesu ni In shiga uku, gyara kasan bara na haura" harararta indo ke yi ko kulata batayi ba ta haura ta share saman tas ta kuma yi moping. cikin lokaci kankani wurin ya d'auki kamshi da haske, a natse ta leka d'akin sahla ganin bacci take yasa ta wuce toilet d'inta ta fara shirin wankewa. Tab ta kunna tare da tura bucket don tarar ruwan da zata sa omo don wankewa, a yayinda ruwan ke zuba idanunta kuma suna kanshi hankalinta gabad'aya ya tafi ga tunanin hasken rayuwarta da har yau bata san inda yake ba, kaman an kunna mata kaset haka mafarkinta ya ci gaba da dawo mata. Kasurgumin daaji ne me cike da duhu ba abinda kake ji se kukan tsuntsaye daban daban........ kafafune guda biyu na namiji da mace suna gudu cikin zafin nama namijin ke jan hannunta yana kuma waiwayen baya, cike da tsoro da fargaba, tuntu'be taci ta fad'i hawaye na zuba cikin tsantsar gajiya da kishirwa ga wani bala'in yunwa dake azalzalanta ta kalleshi ta furta.; "yaya na gaji..." Baya ya kuma kalla Jin alamun motsi yasa ya duka cikin haki yace "oya hau bayana Bilkees yi sauri karsu taddamu" hawa tayi ya mike ya cigaba da gudun da dukkan alamu gudun na ceton rai ne ba shi ya tsaya ba se bakin wani rafi.. Ya ajiyeta yana duba kafanshi da ya fashe duk kayoyi sun shiga, kallonta yayi yayi murmushi wadda har kumatunshi na dama ya lo'ba, cikin tausayawa ta rike kafarshi tana kuka; hannayenta ya kama ya mikar da ita yana furta "hey me na kukan? I'm fine" zatayi magana suka ji gudu ta bayansu da sauri ya janyota bayan wani bishiya da ganyayyaki suka rufeshi tare da danna mata baki. d'aga kan da ze yi me ze gani!! maciji ne daidai wuyanta yana shirin sarinta cikin zafin nama ya juyata ta dawo kirjinshi macijin yayi azamar sakin dafinshi a daidai kafad'unshi, idanunshi ya runtse da karfi sbd azabar zafi wadda se lokacin ta lura a take ya fara had'a gumi kan kace kobo ya yanke ya fad'i wani irin ihu ta kwala tana kiran "yaayaaa"........ A firgice ta dawo daga tunaninta jin zuban sassanyar ruwan sanyi a fuskanta a rud'e take jan numfashi sbd shid'ewar da ta so yi sbd ruwan a bazata ya zo mata, sahla dake tsaye rike da bowl tace "iskancin banza iskancin wofi, wato tsabar salon wulakanci Ina cikin bacci kika kunna ruwa da gangan yake ta zuba har yayi sanadiyar tashina wadda kin san ba komawa zanyi ba sbd ke bazaki samu daman baccin ba shine kike bakin ciki?". Zata yi magana sahla tace "shut up bloody fool wuce fitar min daga toilet kuma wallahi bashi kika ci se naci ubanki yau" fita tayi jikinta a sanyaye runtse idanu tayi ta kuma bud'e sun kad'a sossai sbd a rayuwanta ta tsani ruwan sanyi tunda tayi wani ciwo sanadiyar azabar ruwan sanyin Mama take tsoron sanyi, kallon kayan jikinta tayi In ta zauna dashi to tabbas se bala'e'iyar mura ta kamata kasa ta nufa Don chanza kaya, Tana gama sauka parlorn taji an fisgota zuwa lungun stairs an danne bakinta......... A firgice ta zare idanu a lokaci d'aya tana shirin kwacewa sbd warin giya da ya kusa sumar da ita, ba tantama Aadil ne, cike da 'bacin rai ta sa hannu biyu ta hankad'ashi da iya karfin da Allah ya bata; aiko ya tafi luuuu ya buga keyarshi da tsinin ginin stairs abinka da tsautsayi ga kuma jiki luwai luwai na en hutu abu kam ya hud'a mishi keya se jini, cikin azaban zafi ya sa hannu ya ta'ba wurin tare da dawo da hannun zuwa ganinshi waro ido yayi yana kallonta ita kuwa ta daskare a tsorace. A take ya fara gani bibbiyu, ga dama chan a shaye yake tatul, luuu ya tafi ya zube kasa dukda haka be fasa yi mata kallon 'you are dead' ba . Sahla da ta biyo sahunta Don ganin In ta barta taci bulus ne ta kwala kara tana kiran sunan yayan nata, zuwa lokacin ba karamin rawa jikin bilkees yake ba ta san yau ta gama kad'ewa har ganyenta hawayen idanunta ne suka gangara a sadda Sahla take kwala kiran sunan "ummie! ummie!!" Cikin karaji Ummien da tun ihun sahla na farko ta fara kokarin fitowa ce ta amsa tana gangarowa daga stairs, kallo d'aya zaka mata ka san bata wani samu baccin kirki ba, ko me yasa? Allah masani. Da sauri ta karasa gangarowa cikin tashin hankali tace "sahla me ya sameshi??? Maza maza Kira shu'aibu da lawwali a kama min shi a sa mota mu tafi asibiti, Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun". Da gudu sahla ta fita ba tare da ta damu da kayan bacci ne jikinta ba, sbd a lokacin bacci ya kwashe Aadil wadda su a zatonsu suma yayi sede basu san giya ce ta fara aikinta ba. Sanin bala'in mutan gidan yasa driver da me gadin baro abinda sukeyi da wuri suka shiga parlorn, a take suka d'auke shi da kyar zuwa motan ummie, sahla ta haura ta d'auko mata key da khimar ta fice cikin sauri a lokacin kusan 6:30am. Dukar da kanta tayi ganin irin kallon da sahla ke jefanta dashi a hankali ta matso gabanta tare da sa hannu ta rike kunnenta. "Dan ubanki me kika mishi??" Shiru bilkees tayi kanta kasa ta san yau ta kad'e har ganyenta tunanin abinda zata ce takeyi bata hankara ba se jin saukan mari tayi akan kuncinta, a razane ta d'ago ta zuba mata idanu hannunta dafe da kunci. karfa kuyi mamaki In nace muku bilkees ta girme ma sahla da almost year, idanunta ya kad'a sossai ranta wani irin kuna da tafarfasa yake "me mutanen gidan nan suka d'auki kansu ne?" Tayi maganan ne a zuciya ba tare da sanin a fili tayi shi ba se jin wani saukan marin tayi. "Har se kin tambaya?" Tayi wani irin dariya kan tace "dan ubanki har kin isa ki ce min me muka d'auki kanmu? Bayan ji ma wa na ciwo da kikayi? Wallahi bilkeesu In har Ina da rai kuma kina gidan nan se na kaskantaki kaskancin da baki ta'ba tunani ba, wawiya jaka, yau se kin yabawa aya zakinta a hannuna kan mommy ta dawo, shegiya me kama da mayu wuce muje." A Baya ta bita har waje ta kirawo me bawa flowers ruwa, ta kuma kira baaba lami da indo cikin fisge kai da nuna isa tace "yau gabad'aya na hanaku aiki, duk wani aikin da kukeyi ku tabbatar kun bar wa er iskar yarinyar nan yau ita zatayi, kuma na rantse In kama wani na tayata ku ga..." tana kai nan ta juya ta fice. Lumshe manyan idanunta tayi na mintuna ta kuma bud'e hawayenta suka gangaro da sauri ta sa hannu ta share tare da sakarwa su baaba laami dake aika mata kallon tausayi murmushi, juyawa tayi ta koma parlorn kasan ta shige d'akinsu fahad. ~~~~~~~~ Tunda ya dawo sallahn asuba be kwanta ba se cigaba da duba wannan case d'in yake yana mamakin maza marasa Imani masu yiwa mata fyad'e, Me yasa bazasu nemi mata karuwai da suka kai kansu ba se waenda suka killace kansu? Tabbas shi kuwa se ya d'aukawa yarinyar nan fansa Don se inda karfinshi ya kare kan wannan shari'ah. Bayan ya gama d'an abinda ze yi ya shiga wanka cikin mintuna da basu wuce 40 ba yayi ya fito a shiryenshi tsab cikin blue suit da er ciki fara tare da blue black tie, blazer d'in na rike a hannunshi ya d'auko brief case d'inshi ya fito har seda ya fito ya tuna sahar kallon time yayi a tsadaddiyar wrist watch d'inshi ze makara In yace se ya tsaya mata wanka da nemar mata abinda zata ci dukda shi cikakken lawyer ne me zaman kanshi. "sahar" ya kira sunanta da sauri ta kalleshi dama ita ba me baccin safe bace duk inda 6 yayi ta farka. Yace "ina ummanki?" Tace cikin fullancinta da maganarta da ba fita yake sossai ba "tana bacci, Abbie zan bika" tayi maganan cikin turo baki irin na shagwa'ba'bbun yara, yace "Toh mamana zo muje". Da gudu ta mike ya rike hannunta suka shiga d'akin zaheera se 'bata fuska yake sbd zarnin fitsarin toilet d'inta da ya tabbata ya kai sati be ga wanki ba, karamar drawer d'in sahar ya nufa ya d'aukar mata kaya suka fito zuwa mota ba tare da ya kalli ko ta 'bangaren da zaheera take tana kwasar baccinta ba; Sbd ya san ko tashin duniya ze mata ba tashi zatayi ba bare har su saka ran samun breakfast, gidansu ya nufa da ita daga bakin gate ya sauka tare da d'aukanta da kayanta zuwa bakin gate ya sa hannu ya kwankwasa lawwali ya leko ganinshi yasa ya washe baki "aaa Alhaji karami barka da safiya" yace "Yauwa baba Barka dae, dan Allah taimaka ka mika min ita cikin gida na so in makara ne, kar In shiga kuma In zauna". "A'a to to ba damuwa Allah ya tsare" yayi maganan yana kar'banta kasancewar bata da kyewya yasa ta je, har tana yi ma babanta bye bye, shima byee ya mata bayan yayi pecking d'in kumatunta ya juya ya fice, rufe gate d'in baba yayi ya nufi cikin gidan. ~~~~~~~~~ Da d'akinsu fahad ta fara, d'aki ne me d'an yalwan fad'i da gado na katako irin na yara, gadon farkon an saka zanin gado blue me zanen spider man yayinda d'ayar ya kasance me red zanin gado da zanen Ben 10, a gefe kuma kwabar kaya ne guda biyu shima d'aya red da fari d'ayar ma blue da fari, se kafet me kalolin nan uku da aka kawata d'akin dashi se karami na takawa da aka saka daga chan daidai kofar toilet. Standing fans guda biyu da Ac ne kawai a d'akin bayan kayan gadajensu ba karamin kawatuwa d'akin yayi ba, fahad dake kan na farkon ta fara tashi suka shiga toilet ta had'a mishi Ruwan wanka ta fito da kanshi yayi sbd baya yarda a mishi kan ya fito ta fidda mishi uniform d'inshi wando three quarter blue da milk shirt me guntun hannu, da karamar tie haka ma na khalil yana fitowa ta d'aga khalil shi kam ita ta ta mishi suka fito se ma surutu yake mata sbd yanayin da take ciki yasa sama sama kawai take amsa shi, ta shafa mishi mai ta saka mishi uniform bayan shorts da ta sa mishi. White Socks da black boots d'inshi ta d'auko ta sanya mishi dama tuntuni fahad ya saka nashi, kowannensu ta d'auko mishi school bag d'inshi ta mika mishi "ya fahad aje a ci abinci a tafi school kar a makara". dayake shegen son girma ne da fahad hakan yasa take tsokanarshi da yaya sbd ba yadda be yi khalil ya dinga ce mishi yaya ba yaki, suna fita ta hau gyaran d'akin seda ta share ta shiga toilet d'insu ta wanke ta kunna musu Ac ta sa fan d'insu a chargy tana shirin fitowa se ga khalil rike da hannun sahar. Kallonta bilkees ta tsaya yi da murmushi sbd yarinyar ba karamin sha'awa ta bata ba kyakyawa sossai ga gashi Masha Allah, maida kallonta kan khalil da ya fara magana tayi. "Bilki ga Baby sahar nan itama wai se an mata wanka an sa mata uniform" rike hannun layla tayi dake hangala mata baki ta dubi khalil ba tare da ta damu da kiranta bilki da yayi kai tsaye ba sbd ta san yayyunsu sun hanasu ce mata wani Aunty, tace "toh je ka karka makara" kallon sahar tayi da ke cewa "Anty nima zan je ki min wanka In bisu". Shafa kanta tayi tace "right away baby, sede fah In nayi miki wanka kika tafi school a haka zane ki Antyn school zatayi kinaso ta zane ki?" Shagwa'be fuska tayi tana make kafad'a tace "uhm uhm" Tace "yauwa baby girl muje muyi wanka mu wanke kai kanki yayi datti" turo baki tayi bilkees ta d'auke ta zuwa toilet tayi mata wanka ta nad'o ta towel se surutu take zuba mata nan da nan bilkees ta sake tana jin son yarinyar a ranta. ~~~~~~~~~~ A asibiti kuwa seda doctor ya aske daidai inda ya ji raunin kan ya d'inke aka bashi gado ya fito ya samu ummie dake safa da marwa yace "hajiya ciwon nan ba wani ciwo bane na har chan an ma mishi d'inki yanzu dae matsalar itace shaye-shayen da yakeyi In har baku mishi fad'a ya kiyaye ba nan gaba Ina jiye muku tsoron halin da ze fad'a na tabbatar Alhaji sadiq chubado ba sanin hakan yayi ba da kila ya d'auki mataki". Cikin masifa tace "Ina ruwanka? Nace Ina ruwanka da saninshi da rashin saninshi, aikinka shine ka dubamu ka rubuta magani ba'a sa da saka ido ba" ta kama tafiya tana mitar "In ba ma nigeria ba mutum na aiki a karkashinka yana ci gaba dakai amma ya nemi ci ma fuska". girgiza kai yayi ba Don yana ganin girman Alhaji sadiq chubado da Barr. Aayan Sadiq chubado ba da ya jima da dena yiwa familynsu aiki sbd sauran yaranshi amma ba komai aje zuwa ya juya ya fice cike da kunan rai. ~~~~~~~~~~~~ Zaune yake a wani karamin tsakar gida kan kujeran tsuguno inda mutanen gidan ke zaune kan taburma uwar da yayar mace se kuka suke yayinda uban ya zabga tagumi tare da zubawa yarinyar da bata wuce 12 years ba ido, idanunta a kafe wuri d'aya ko juyasu batayi. cike da tausayawa yace "kuyi hakuri inna haka Allah ya kaddaro mata tata rayuwar, In Shaa Allahu se inda karfina ya kare wurin kwatar mata en cinta bana bukatar ko naira biyar d'inku akan wannan aiki burina kawai ku yarda a kaita asibiti a duba ta, kunga rashin sake maganan nan babban abu ne ba'a sani ba ko ya bita har abada". Ajiyar zuciya baba ya sauki yace "d'an nan me yasa kake son taimakonmu haka?" Aayan yace "Saboda Allah" baban yace "yaro ka gama magana, Allah ya saka maka da alkhairi ya biyaka yaji kan iyaye, Allah ya baka masu Jin kanka haka, bara na shirya muje" Da Ameen Aayan ya amsa yana murmushi, zaro wayanshi yayi ya shiga kiran Dr. Basheer Abdulbasid, ringing biyu ya d'auka cikin zolaya yace.. "Kaga barrister dodon en iska" murmushi kad'an Aayan yayi yace "likita bokan turai, ya aiki?" Yace "Da godiya ka Kira jin ya jikin kaninka ne? Cikin rashin fahimta Aayan yace "kanina kuma?". Dr. Basheer yace "au baka sani ba? Brother d'inka na nan ban san taya ya ji rauni a kanshi ba, he was drunk sanda suka zo har d'inki na mai". Aayan yace "subhanallah was it that bad?" Dr. Yace "da sauki dae, ya ne to kiran me aka min? I know you baka kira seda dalili" Aayan yace "gani nan zuwa patient zan kawo, raping d'inta akayi wadda tun daga ranar bata iya magana se de ta kurawa wuri d'aya ido I think shock ne zan kawota ka taimaka pls gobe akwai shiga court". Dr. Basheer yace "subhanallah!! To Ina jiranku se kun karaso" suka ajiye wayan kan nan innan ta sa khimar ta sanyawa yarinyar me suna Aisha, baban ne ya kamata suka fito suna ba yayar amanar gidan, da kanshi ya bud'e musu Baya suka shiga ya zagaya ya shiga ya ja se asibitin. Direct office d'in Dr. basheer sukayi inda shi kuma ya kamata suka fita bayan yayiwa iyayen jaje, Aayan ma ya mike yana cewa "Ina zuwa baba" ya fice, d'akin da Dr. basheer ya fad'a mishi su ummie suka ya nufa, yana shirin tura kofar yaji Aadil na furta. "Na rantse randa na kama yarinyar nan se na mata fata fata, ummie daga na rungumeta shikenan se taji min wannan rauni? Ba ma wannan ba kin kuwa san yadda nake valuing hair styling na? Yanzu kwalkwal zata sa nayi?". Ummie tace cikin fad'a "nace maka ba ruwanka da yarinyar nan Aadil, In zakayi neman matanka ka nema waje gasu birjik me had'inka da wata banza me aiki? Ka kiyayeni na gayama Sannan na rantse In baka rage shaye shayen kan nan ba duk randa mahaifinku ya sani ba ruwana". Girgiza kai Aayan yayi wace yarinyace kuma Aadil ke kokarin wulakantawa? Kwafa yayi tare da knocking kofan ba tare da ya jira izini ba ya tura ya shiga, ummie ne ta kalleshi da mamakin wadda ya gayamishi, Ita Allah ya gani tana takaicin ganin duk wani ci gaba 'ya'yan zara'u ke samu amma nata babban da ya kamata ya yi abin kirkin se shegen shaye shaye da bin mata kaman wacce akayiwa baki. Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake murmushi tace "Son wa ya Fad'amaka muna nan? Kila sahla ko? Ta d'aga maka hankali a banza gashi har ka baro aikinka". Yana zama yace "No wani aiki ne ya kawoni asibitin se kuma basheer yake gayamin kuna nan se nayi branching, ya jikin?" Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata wuya wai wani branching se kace shara suke, Aadil da tun shigowarshi ya lumshe ido kaman me bacci ne yayi juyi kaman cikin bacci ya fuskanci gini tare da bud'e ido wani irin haushi da tsanar Aayan ke taso mishi. Ummie ce ta daure tace "da sauki" mikewa yayi yace "Toh ummien mu In ya tashi a mishi sannu da jiki kuma a ja mishi kunne kar ya kuskura ya fara abinda ze yi da na sani sbd ba ruwana da shi waye...." yana kai nan ya fice. Taune lip ummie tayi tana hararar iska, Allah kasa yana shiga motan ta kife dashi. ~~~~~~~~~~~ Yana komawa ya samu Dr. basheer ya ko gama duba ta ya rubuta wasu magunguna inda ya tabbatar mishi ko yaushe zata iya fara magana kaman yadda yayi tunani she was shocked ne beyond extent, ta de ci gaba da shan maganin anytime zatayi magana. Godiya sossai ya mishi suka mike suka fito seda ya saya maganin ya maida su gida, suna ta shi mishi albarka kan ya wuce police station inda yaron yake sede duk yadda ya so yaron yayi magana kiyawa yayi se kawai ya kyaleshi ya wuce office. πŸ–€GureenjohπŸ–€ [15/07, 6:26 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ• πŸŒ•LELEWALπŸŒ• πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹ πŸŒ•πŸŒ• STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin. MARUBUCIYAR:- ZUHRAA HAMRAH IGIYAR RAYUWA NOOR IMAAN and RUWAN SAMA. FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763 SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar kauna. JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™. EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“ (Home of exquisite writers') Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai. β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€” ..........4 Duk inda tayi se Sahar ta bi ta a baya kaman jela, sossai ta debe mata kewa har ta samu ta gama duk ayyukan gidan cikin sauri, duk d'akunan gidan seda ta gyara banda na Aadil da Alhaji, bawa flowers ruwa shine na karshe wadda zatayi zuwa lokacin 11 da wani abu, ai tana d'auko tiyo sahar ta fara tsalle cikin murnan za'ayi wasan ruwa sede ganin bilkees ta dukufa bawa flowers d'in ruwa tana baya baya dasu a wahalce yasa ta turo baki gaba tana kallonta. Nan da nan ta fara jero atishawa hawaye na zuba a idanunta a takaice kan ta gama bawa flowers nan ruwa wasu kananun kuraje sun fito jajir a fuskanta, da kyar ta daddafa ta zauna tana lumshe idanu, cike da tausayawa sahar ta dafa ta "Anty baki da Lafiya?". Bilkees tace "eh sahar amma nayi sauki" sahar tace "a'a Anty Daddy fah ya hana karya yace Allah na hukunta me karya gashi har yanzu kina kuka..." Share fuskanta tayi tace "Toh baby sahar na dena, zo muje" kama hannunta tayi suka wuce kitchen don d'aukan breakfast d'inta sede ga mamakinta kitchen d'in ba wani sauran kwano da ya nuna akwai abu ciki an wanke su tas an maida komai muhallinshi, kallon blessing dake 'bare garlic kan bowl tayi tace "blessing Ina abincina?" Ba tare da ta kalleta ba tace. "Anty sahala tace kar a ajiye miki" da mamaki take kallon blessing bayan duk wahalan ayyukan nan da ta sha yau kuma a ce mata ba abinci!! A sanyaye ta juya sahar ta bi bayanta d'akinsu ta nufa tana zuwa ta kifu kan katifarta tare da fashewa da kuka, kuka sossai takeyi har jikinta na rawa ita kam rayuwar nan ta isheta haka, duniyar da ba iyayenta ba yayanta da ta tabbatar zuwa yanzu ta mance sunan shi, ba wani jin daad'in rayuwa se gallazawar waennan family biyu to ina zataje taji sanyi?. In ta koma gidan mahaifinta azabanshi yafi nan, bata san wasu en uwansu ba bayan su uncle Mukhtar da iyalanshi bare tace zata gudu wurinsu, ba karatun kirki ke gareta ba bare tace zata dogara dashi ta gina kanta, dafata da taji anyi ne yasa ta tsagaita kukan tana me d'agowa a lokaci d'aya tana share hawayen fuskanta tare da jan majina, idanunta sossai ya sauya kala ya kankance. Ba-ba laami ce cikin tausayawa tace "kiyi ta hakuri bilkisu komai na duniya me wucewa ne, ki mikawa Allah lamuranki sbd komai kika gani daga gareshi ne watarana se kiga kaman komai be faru ba, nan gaba zakiji daad'in rayuwa in Shaa Allahu, kalli kiga yadda yarinyar nan ke kuka sbd ke". Da sauri ta juya shap ta mance da sahar ganin yadda fuskanta yayi jage jage da hawaye yasa ta janyota jikinta ta rungume, hawayenta na kuma zuba, indo tace cikin hawaye itama sbd saurin kuka da take dashi tace "ga abincinmu ni da ba-ba mun rage miki". Murmushin karfin hali ta saki tana kar'ban kwanon da indo ke mika mata tace "na gode ba-ba dake da indo bazan ta'ba mancewa da ku ba har abada" ba-ba da se yanzu ta lura da kurajen fuskanta tace "subhanallah me ya sami fuskanki haka?". Bilkees tace "ba-ba jinina ne be son flowers, I'm allergic to them" indo tace "wayyo sannu Akwai ciwo ko?" Girgiza kai tayi tana kuma murmushi tace "ai na bar inda suke shikenan kuma a hankali kurajen zasu tafi" d'ago sahar tayi tace "tashi ki ci abinci sahar na san kina jin yunwa kema" da sahar suka ci abincin suna er hira tsakaninsu. Bayan sun gama ci ta d'auko comb da kifiya da kuma man kitso dayake ta iya kitso, tsefewa sahar kai tayi da wayo da dabara sbd lura da tayi sahar na tsoron kai, cike da kwarewa ta yi mata kalabanta madaidaita wadda yayi kyau sossai, kan ma su gama sahar tayi bacci hakan yasa ta gyara mata kwanciya ta shige toilet ta watso ruwa cikin en kayanta da suka fara kod'ewa ta za'bo wani doguwar bakin riga wadda ummu hadiya ta bata ya d'an d'ingile mata haka ta sa tare da d'aura gyalen a kanta. Tana sa khimar aka banko kofan a tsorace ta d'ago sbd indo da ba-ba lami duk sun fice Don kama wasu ayyukan tuntuni, hajiyace ta shigo a masifance ta nufi Bilkees ta kwasheta da mari ta kuma kara mata cikin fad'a tace. "Ke har kin isa? Kina kaskantacciya me aiki ki jima d'an gida ciwo? Bilkisu don't you dare try me baki san da wadda kike tare ba, daga randa kika sake cutar min da d'a na rantse se na lahira ya fiki jin daad'i, zan kira ita uwar taki inji In ita ta aikoki yin hakan don ban cike da halin iskanci In bazakiyi aikin ba ki kama gabanki". Kallon sahar dake kan gadonta tayi har zatayi magana se kuma ta watsa mata harara tayi gaba, a hankali bilkisu ta sulale kan katifar ta zauna dabas zuciyarta na wani irin kuna, cin kashin nan har Ina? ~~~~~~~~~~~ Tsaye yake jikin windown office d'inshi da ya yaye hannunshi zube cikin aljihun wandonshi yayinda idanunshi da suka d'an kad'a ke kafe wuri d'aya, kallo d'aya zaka mishi ka san yayi nisa ba kad'an ba cikin tunani me zurfi, dafa kafad'anshi yaji anyi wadda hakan ya saka shi juyowa a matukar harzuke se suka had'a ido da shaheed. Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "yaushe ka shigo?" Shaheed yace "taya zaka san sadda na shigo bayan kayi zurfi cikin tunanin da bashi da anfani? Allah abokina wannan tunanin ba shine mafita ba dubi idanunka" lumshe zara zaran idanunshi masu tafiya da natsuwar en mata yayi ya kuma waresu kan shaheed a lokaci d'aya ya kama lip d'inshi na kasa da yake red sbd yawan sawa da yake a baki ya hau tauna a hankali. Se da ya mula don kanshi zuwa lokacin har shaheed ya je karamin fridge dake office d'in ya d'auki maltina ya bud'e ya fara sha yace "Toh shaheed ya zanyi? Wacce irin mata ni kuma Allah ya bani? Duk wani irin hukuncin da Allah ya tanadar tsakanin miji da mata na mata, first of all na mata fad'a ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, shaheed na kaurace mata amma ta kasa fahimta sbd kanta ba na mutane bane, na kai karanta wurin iyayen mu mata amma ba wani sauyi, yanzu haka zan iya ce maka na kai sati rabon da magana me karfi ya had'amu amma a banza bata sauya ba, ya take son inyi da ita ne?" Ya karashe a raunane, shaheed yace "Toh barrister kayi auren mana kawai ko ka samu natsuwar zuciya" tsaki yayi yana dafe kanshi dake sarawa yace "ba auren bane matsala matar ne, banga macen da ta min ba shaheed har yau Sannan Ina tsoron sake za'ben tumun dare kaga garin neman gira se a zo a rasa ido". Shaheed yace "ka cigaba da adu'a Allah ya za'ba maka abinda yafi alkhairi In auren ne se kaga ka zo kayi amma a gaskiya kana kokari zama da kazamar mace a wurin irinka me tsantsar tsabta kaman azaba ne" ya karashe yana sake kurawa Aayan d'in ido, "Aayan alamu sun nuna baka jin daad'i me kuma ke damunka bayan matsalar zaheera?". Yace "nothing just headache" shaheed yace "maybe stress ka kuma zo ka sawa kanka tunani, sorry why not kaje gida ka huta kaga gobe kana da case" ba tare da ya musawa shawaran shaheed ba ya fara tattare abubuwanshi dukda har kasan ranshi ya san in yaje gidan ma wani Karin 'bacin ran ne, sallama sukayi da shaheed bayan ya sallami sakatariyarshi da masinjanshi ya ja motar ya bar harabar wurin zuwa gida. A tsaye a tsakiyar parlorn kasa ya sameta hannunta d'aya dafe da kwankwaso d'ayar kuma ta dafe kai dashi, ta'be baki yayi a zuciyarshi yace yau kuma Ina wayan? Kallon jikinta yayi tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga me guntun hannu cikinta ya bayyana sossai, ba laifi kyakyawa ce ajin farko ga gashi Masha Allah, tana ganinshi tace; "Barrister!!" Chak ya tsaya da niyyar hawa sama da yake ya juyo ya kalleta fisha ya d'auke ido wadda hakan ba karamin rud'ata yayi ba har ta kasa furta wani kalman seda yace "ya akayi? Kina bukatar wani abu ne?" In ina ta fara "am uhmm wai nace kai ne ka fita da Sahar tun safe?" Ya san ta san ba me fita da ita tun sassafe haka se shi amma se yace "yeah tana chan gida". "Allah sarki" tana fad'an haka ya juya ya fara haurawa se ji yayi tace "am sorry" ba tare da ya juyo ba yace "wani abin kikayi ne?" Be jira amsanta ba ya haura abin shi, dafe kanta tayi tace "Anya kuwa zan iya Adda ramla?" Ta karashe da turo baki; Wuraren 9am yayarta Ramlah tazo kasancewar da tazara sossai tsakaninsu Sannan tana da matukar zafi wadda hakan yasa zaheerar ke shakkarta, a sadda ta zo d'inma tana haurawa d'akin zaheerar ta d'aka mata mari a cinya wadda ya sata zabura ta tashi a firgice tana kallonta, ganin itace yasa ta natsu ta kuma had'iye masifar da ta tashi dashi tare da yin kasa da kai tace "Adda Yaushe kika zo?". Cikin azalzala tace "ban sani ba! Nace ban sani ba!! Wai ke zaheera yaushe zakiyi hankali ne? Wani irin banzan d'abiya ne wannan? Baki kunyar a ganki a haka a ga gidanki a haka ace kuma ke d'iyar gomnan Adamawa ne? Ji fa zarnin da toilet d'inki ke fitarwa... na rantse kin yi dacen miji me hakuri amma fah Ina jiye miki randa zaki kaishi bango, tashi ki wanke toilet d'innan Ina nan Ina jiranki kuma ki tabbatar kin fito a wanke tsab kin kuma wanke kankin nan, wawiya kawai shashasha". Sumsum ta mike ta shige toilet, tsabar masifa Irin na Adda ramla har zaheera ta fito daga toilet bata zauna ba se diri take tana karkad'a kafa, kaman sabuwar munafuka haka ta karasa wardrobe d'inta ta d'auko riga doguwa turare kawai ta shafa ta sanya rigar tare da drying kanta da ya fita sossai wadda se yanzu na lura ashe tana da gashin, bayan ta gama ta tsaya tana kallon Adda ramla. Dakuwa ta mata tana furta "d'akin kuma uban wa ze gyara miki?" Har da hawayenta wurin gyaran d'akin Adda ramla na nan tsaye har ta gama, seda ta gama ta tattara kayan wankinta jibgi ta fitarwa me masu kan Adda ramla ta zauna bakin gado bayan ta bayar ta shigo, Adda ramla ta mika mata hannu "bani wayarki". Rau Rau tayi da ido seda ta daka mata tsawa kan ta mike ta d'auko ta mika mata tana rike bayanta da take ji kaman ze fita sbd ba saba motsa jikin tayi ba, Adda ramla cikin takaici tace "zaheera yaushe zaki zauna wai kiyawa kanki fad'a? Ashe kunnenki na kashi ne bazaki ta'ba jin magana ba? Allah ya baki miji nitsatse marar son tashin hankali amma ke gaki kazama fitsararriya, Toh karki yarda ki kaishi bango kaman yadda na gayamiki Don bazaki ji daad'i ba kuma da na sani ko... keya ce, wayanki na kar'ba se jibi zan kawoshi na rantse da Allah in shigo gidan nan jibi In ga d'igon datti kuma ban samu abinci akan dining ba se na fasfaskeki ba ruwana da cikin jikinki Sannan inji labarin kin saya wata wayar wallahi watan cin ubanki ya kama, wawiya ana nuna miki annabi ya faku kina runtse ido". Tana kai nan ta mike ta fice ko sauraran hakurinta batayi ba kan ta gama sauka ta juyo tace "Sannan ki tabbatar kin shirya da mijinki zan kirashi inji abinda ba haka Allah da Abba zan had'aki kin san halinshi", tana kai nan tayi gaba abinta. Shinefa abinda ya d'aga mata hankali ta gangaro take safa da marwa cikin tafkeken parlorn kasan cikin tunanin Anya zata iya rayuwa na kwana uku ba waya? Allah ya gani bazata iya rayuwa ba In ba Instagram, Twitter da Snapchat ba...... ** Yana haurawa ya samu magaani ya sha tare da fad'awa kan gado ya jima sossai kwance har be san sadda bacci ya kwashe shi ba, kiran sallahn azahar ya tasheshi ya mike ya karasa cire kayan jikinshi ya fad'a toilet, wanka ya tsala ya fito yana zabga kamshi d'aure da towel kugunshi wardrobe ya nufa ya fidda kayan da ze sa tare da gyara hair style d'inshi ya tashe had'add'iyar kasumbarshi tare da feshe jikinshi da body's pray ya saka kayanshi ya kuma feshe jikinshi da perfumes. Cikin azama ya fito yana d'aura had'addiyar agogon fatanshi a tsintsiyar hannunshi kafafunshi sanye da normal takalmi na maza, yana shirin fita yaji muryanta tana cewa "amm barrister ga abinci fa" kallon mamaki ya mata irin tooh yaushe rabo!! Ta'be baki yayi yace "Ohk se na dawo" yana kai nan ya fice abinshi da mota ya fita sbd ba dawowa ze yi ba se ya gama abinda ze yi. Seda yayi sallah kan ya wuce AUN nursery section inda ya samu baturen headmaster d'insu ya mishi bayanin yarinyarshi abunku da harkar kud'i a take aka mata komai da komai aka bada uniform d'inta zata fara zuwa monday, daga nan se da ya tsaya gidan Adda sumayya sbd suna kusa da Aptin sama sama suka gaisa ya wuto jimeta inda direct GRA ya nufa wato Dougirei, horn ya danna sau biyu lawalli ya zo ya bud'e mishi ya kutsa kan motanshi ciki. Ganin motan ummie yasa ya d'an ta'be baki a fili yace "kenan an sallamesu" fitowa yayi ya nufi cikin gidan kan ya karasa yaji wayanshi na ringing zarowa yayi tare da kai idanunshi kai, d'an wara zara zaran idanunshi yayi ganin sunan dake rubuce baro baro a kan screen d'in wayan, a ladabce ya d'aga cikin sanyi yace. "Abba tuba nake" murmushi Abba yayi daga d'ayan 'bangaren yace "barrister nawa, ka san kayi laifi kenan?" D'an zagayawa yayi yana tafiya a hankali yace "Abba aiki ne fa yake sha min kai" Abba yace "wadda har yake sa kake manta Abbanka a wani kasa ko? Da maaminka ne na tabbatar baza ka iya kwana ka yini baka kirata ba, amma ni yaushe rabon da muyi waya?". Idanunshi ne suka rine a take sbd maaminshi da ya ambata wadda har Abban ya gane baran baramar da yayi se waskewa yayi yace "Barrister ya ayyukan hope kana kan ganiyar nasararka kaman yadda na sanka?" Murmushi yayi yace "Abba ai nasara tana nan ne bayan me gaskiya a duk sadda wannan nasara ta kau to fa me gasakiyan ne ya sauya zuwa marar gaskiya". Abba yace "Toh Allah ya taimaka sede a dinga kula please Alhj Umar mubi ya kirani yana min barazanar In ja wa d'ana kunne, me ya had'aku?" Taune lip d'inshi yayi yace "Abba ba wani abu bane case ne ya had'a da building d'inshi da Yayi collapsing da talakawa dayawa sbd rashin Ingancin gini da saninshi kuma akayi hakan, Abba Allah bazan rabu dashi ba se an bi ma talakawan nan hakkinsu" ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "Allah ya baka nasara ya taimakeka a kan duk abinda ka sa a gaba" *** Rike da hannun Sahar suka fito ta mata wanka ta sauya mata kaya zuwa wadda mahaifinta ya kawo ta dashi riga doguwa fara iya kaurinta Don bata kai kasa ba an kawata rigar da adon manyan blue fulawowi. Sam bata kula dashi ba seda ta kusa iso inda yake daddad'ar kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta a wajen ya katse mata tunanin da take ciki, a natse ta d'ago kanta ta dubi me ita. Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu cikin aljihu wandonsa, hannun damansa kuma ya kasance wayace da ya kafa a kunnensa, farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a saman fuskan sa yayi lufluf, yana da tsawo ba laifi hakanan yana da fad'in fuska kad'an, idanunsa zara zara masu matsakaicin girma farare sol, hakanan tsiririn hancinsa da tsukakken lebbansa ruwan hoda ya kara taimakawa wurin fiddo da tsantsar kyaun da Allah ubangiji ya mishi. Sanye yake da shadda ruwan toka kansa babu hula agogon da ya d'aura a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyaun hannunsa wadda ke cike da ke cike da gargasa. A tsanake yake fidda kalmominsa cikin hausa da turanci, a daidai lokacin da yake sallaman wadda suke wayan suka had'a idanu, Ai babu shiri tayi gaggawar janye idanunta daga gareshi, waye wannan me matukar kama da Aadil sede ya d'ara Aadil nesa ba kusa ba kyau? Bata gama tunaninta ba taji Sahar ta fisge hannunta tare da kwala kiran "daddyyyy". Dukawa yayi fuskanshi cike da annuri ya warewa d'iyar tashi hannu taje da gudu ta fad'a tace "I miss you daddy" yace "miss you too babynah" d'agota yayi yana kallon gashin kanta yace "eyyeh wa ya miki kitso?" Juyawa tayi tana kallon bilkees tace "Antyn chan" shima kallonta yayi se suka kuma had'a idanu da sauri ta matso tace "Ina yini" bata jira amsanshi ba ta wuce da sauri. Dage kafad'a yayi yace "albishir!!" Tace "goro" tana dariya yace "zaki fara zuwa school monday" tsalle da ihu tayi ta dire tare da bashi hannu suka tafa yana sakan murmushin ganin farin cikinta Ai da gudu ta wuce tana cewa bari taje tayiwa Anty Albishir da su uncle fahad. Girgiza kai yayi tare da gimtse fuskanshi yabi bayanta cikin yanayin cin magani ya shiga parlorn da azama Yasmin da ta sauke hannunta kan fuskan Bilkees tayi saurin daka tsalle zuwa Baya tana zazzare ido, Sahar ce ta tsala ihu tana fashewa da kuka ita da ba ita aka mara ba, cikin kuka tace "daddy ba kaga Anty yasmin ta duki Anty me kirki ba, kuma ba abinda ta mata" zaro manyan idanunta tayi tana kallon daddyn da ake kai kaara a zuciyarta take furta na shiga uku zata kasheni da bala'in yasmin, kallonta yayi cike da son tabbatar da abinda idanunshi suka gane mishi se suka kuma had'a idanu.... πŸ–€GureenjoπŸ–€