AMANI 4 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) takorikabara@gmail.com MUKHTAR Har ya isa sassan Ummami yana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin sa da Amani yan mintunan da suka shige. Mukhtar yace a ran sa kenan gatan iyaye ma wani abu ne mai girma ga dan adam! Da Maimartaba bai bijiro da zancen bashi Sa-daka ba, da bai san ranar da Amani zata yi nadamar halayen ta har da abubuwan data yi masa irin haka ba, don shi har yanzu jikin sa bai karbi ikirarin Amani tana son shi yanzu ba, ya dai ji ta, and he was puzzled, ya dai fi yarda da cewa gudun kishiya ne ya ruda ta. Bai dawo gidan ba ma don baya son ta sake saka shi gaba da kukan ta da fitinar ta, sai lokacin da ya kintata cewa ta yi barci, don baya son ta kuma saka shi a kwana kada tayi saurin samun lagon sa, da raunin zuciya ya wuni yau, sabida kasalar da nadamar Amani da kukan ta suka saukar masa. Sai da ya dauke takun sawun sa kamar mara gaskiya da ya shigo falon da ya raba nashi da nata. Kuma yana shigewa dakin sa ya rufe a hankali har da key, ba tare da Amani ta san dawowar sa ba sam. So yake ta koyi son nasa da gasken gaske, har ta zo tana kewar ganin sa, mai yuwuwa in ta daina ganin sa ta yi kewar sa, don ya ga canji mai yawa ranar da ya dawo daga Burkina Fasso. Amani kamar tayi hauka, ganin har washegari Mukhy bai neme ta ba, ga dakin sa ya rufe da key, ta kasa gane a gidan ya kwana ko aah? Jikin ta ya bata kawai watakila an kawo sadakokin, a can wajen su Mukhtar ya kwana, to a ina aka sauke su bata da masaniya? Kafin garin Allah ya waye in ka ga yar Daddy bazaka gane ta ba, ta zama kamar kudin guzurin da kullum ake yafita yake karewa. Haka Mukhy ya dinga yi mata wannan batan dabon har kwana uku, ko sassan Ummami bata iya zuwa yanzu don ta san sai ta tambayeta me ke damun ta. don Amani bata saba da shiga damuwa ba a rayuwar ta, shi yasa yanzu data sameta ta kasa controlling din ta, gashi in zaa kashe ta idan an tambaye ta meye damuwar ta ta san ba abinda zata ce yana damun nata din sai kewar Mukhy. Tunda ta ajiye damuwar sadakokin sa aside, ta bar musu shi, amma hakika rashin ganin sa (for good three days) dinnan yana azabtar da ita yadda bata zato a zuci da ruhi. Da tunanin ta na yana can tare da sadakoki yana shan shagalin sa, shiyasa ta daina ganin sa a sassan ta kwata-kwata. Baba Sahura kuwa in ta zo bata ko bari su yi doguwar magana zata ce ta kyaleta ta, ta tafi gunUmmami don Allah, bata son dogon surutu irin na Baba Sahura. Hatta Sugra da Tahirah sun san uwardakin su ta shiga yanayi, ta ce kada ta kara ganin kowaccen su a gaban ta in ba ita ta neme ta ba. Baba Sahura sai dai ta yi dariya, ta ce, ai wato shi Allah haka yake alamarin sa, duniya rawar yammata wai na gaba ya koma baya. Amani ta zama daga kwanciya sai kwanciya bata umh bata umh umh, domin ta gama gayawa ran ta an kawo sadakokin nan, an basu wani gidan, Mukhy yana can tare da su. Da safe Baba Sahura ta shigo dakin ta don taga lafiyar ta yau da safe, ta same ta ta hada kai da guiwa tana kuka tamkar marainiya, haushi mai tsanani ya kama Baba Sahura, sai ta kada kai ta ce, lallai, aure mai ladabtar da mace, Uwa duk kin yi sanyi kamar ba Tafisun Alhaji ba, kin koma talalabuwa, yo idan ma Sadakan ne aka kawo ai ba ta haka zaki gabza da su ba, tsaf kina nan kina wannan doloncin zasu janye shi, ke kina nan kina cika bokiti da hawaye, ai ta shi tsaye zaki yi ki zama kamar Ummami wajen karawa da kishiyoyi komin yawan su, in ya so mai karfi da iya kissa da iya gado da iya kula da miji ta kwata. Ba miji irin Maina ake sakarwa kwarkwarori a koma gefe ana kuka ba, ni wallahi duk kin zama sullutuwa, wannan karfin ikon naki da izzar taki duk sun bar ki, a irin wannan lokacin kuma suna da amfani, ni nafi son Tafisu ta baya ba ta yanzu ba da namiji ke neman kassarawa. Sai ta ji tamkar Baba Sahura ta yi mata allurar sanya kuzari, da gaske kishi da soyayyar Mukhtar ke neman kashe ta a tsaye in tayi wasa, ya gama narka Tafisu ya gama kashe lagon ta da soyayyar sa, shi bai san ma tana yi ba, yana can yana murzar kuruciyara sa da kyawawan yammatan abzinawa har biyu. Shin da soyyar sa da ke cin ran ta, da kishin Mukhy da ke azabtar da ita zata ji ko da bakakaen maganganun Baba Sahura na yau daban na gobe daban? A wani bangaren, ga kuma kwadayin son ganin fusatattar kyakyawar fuskar sa da ke addabar ta a yanzu. Don haka yau Tafisu ta kwarara zuciyar ta, ta kuduri aniyar ko zata kwana a zaune zata hana idon ta barci zata yi hakan, don ta bincika ta ga inda Mukhtar ke kwana. Aka ce sa kai ya fi bauta ciwo. Kuma shima wani ikon Allah yau ya kasa yin daren da yake yi a gun Ummami don kan sa ciwo yake yi kadan-kadan, kuma shi kan sa ya gaji da boyon da yake yi mata don yana takura kan sa a daki ne, domin ya gane wahalar da yake baiwa zuciyar sa ba kadan bane, ko ya ki ko ya so, yayi kewar kyawawan idanun Tafisu, masu kama da kwan zabo, koko dan itacen nan na almond. Murmushin ta da bata fiya yi ba sai wuri ya kure, da takun tafiyar nan nata mai kama dana macen Dawisu don rangaji da iya takun tafiya mai daukar hankalin namiji. Mukhy ya sa hannu ya rike kan sa da ke sarawa tamkar zai rabe gida biyu. Ya ce. Wash! Ummami ta juyo tana tambayar shi lafiya kake rike kai? In barci kake ji ka tafi ka kwanta mana? Nima yanzu gun Mai zan wuce, kwana biyun nan na rasa gane kan ka, duk ka bi ka hanani sakat da binbini, duk inda nayi sai ka bi ni cikin gidan nan Maina kamar yaron goye? Ni ina matar ka ne ma kwana biyun? Itama na daina ganin gilmawar ta a sassa na sai kai uban yan binbini, bita zai-zai. Mukhy yayi murmushi bai ce komai ba yana kara dafe kan sa da ya kara sarawa. Na rasa dalilin da yasa kake yin dare yanzu a waje na ko wajen Mai, kai da aka ajiyewa amarya ko sati bata rufa ba, amma sam baka dokin ta, anya Maina? Lafiya?. Murmushi ya sake yi kadan, ya ce Ummami ai kanwa ta ce wane irin doki kuma? Ni kanwa nake yi da ita, ba amarya ba. Tun daga nan Ummami ta ke fahimtar wani abu is fishy a tsakanin su a kwana biyun. Ta fahimci tun ranar da aka yi zancen sadakoki ne Amani tayi mata batan dabo. Don itama Tafisun kwana biyu da ya tsiri shigowar ya jima mata a sassa har wani lokacin yayi barci ya farka, ita kuma ta daina shigowa kwata-kwata. Baba Sahura dai ta tabbatar mata Amani lafiya take, shakiyancin ta ne ya motsa ko kofar falo ta daina fitowa. Ta kori su Sugra ma. Ya shiga gidan sa ko in ce bangaren sa cikin jin ciwon kan na karuwa masa, shi kan sa ya san akwai matsala a tare da shi yau, don duk dauriyar sa ta kare, da gaske daurewa kawai yake amma tunanin Amani da yake kwana da shi yak e tashi da shi da son kasancewa da ita ko sau daya ne a rayuwar su, ya fara haifar masa da rashin sukuni a cikin jikin sa, zai ratsa ta falon karshe wanda a nan dakunan barcin su suke, ya ga Amani zaune firgai-firgai tana dakon jiran shigowar sa, ta ki shiga dakin ta balle ta kwanta, ta yi rantuwa yau sai ta ga gadon barcin Mukhy da sadakokin sa. Sai ya sa kai zai wuce ta ba tare da ya ce mata komai ba, but hes touched da ganin yadda ta rame ta yi zuru-zuru kamar ba yar gayun nan Amani Faskari ba, hakan ya taba zuciyar sa sosai, kuma hakan yasa nan take ya tuna Alhaji, da yadda yake lelen abar sa, sai ya ji kamar baya kyautawa abinda yake mata, kamar yana cin amanar Alhaji Usman, duk da haka har yau Amani bata yi hankalin da yake so ba, shi kuma in har ba ya tabbatar da canzawar ta da halayen ta da baya so, ko da ba duka ba, tunda ance hali zanen dutse ne, amma a kalla ta cire wanda Allah baya so (girman kai), izza da fariya da tunanin ta na ta fi kowa, yana so ya tabbatar da cewa tana mishi so na hakika na fisabilillah irin wanda zata sake da shi a shimfida da zuciyar ta da gangar jikin ta bakidaya, ba don shaawar gangar jikin ta na yar adam ba, sai don so da kauna na domin Allah, sannan ne zai iya sakin jiki da Amani su fara rayuwar da yake musu tanadi shi da ita. Makeken Gadon sa ya haye ya kudundune yana amsar zafin da jikin sa ya dauka, jikin sa har yana rawar dari, domin tuni zazzabi ya kawo masa hari, ya ja bargo ya kudunduna har kan sa. Amani duk da bai kula ta ba, ya wuce ta ne a zaune sai bata yi kasa a gwiwa ba wajen biyo shi dakin, ta yi saa bai saka key din ba yau, don bai san inda kansa yake bama, amma kuma bata ga wata sadaka a dakin ba sai shikadai. Amani har da sauke wata lafiyayyar ajiyar zuciya, rigimar da ta shigo da ita ta nema ta rasa, ko don irin kwanciyar da taga Mukhy yayi da kudunduna cikin duvet kullihin sa ko AC bai kunna ba. Sai jikin ta yayi dan sanyi, kuzarin balain data shigo da shi yayi kasa sosai, ko daga irin kwanciyar da Mukhy yayi yau zaka fahimci bashi da lafiya. Farar rigar barci ce a jikin ta iya guiwar ta mai santsi, amma ta daura zanin atamfa a kai, gashin kan ta ma duk ya susuce babu taza, babu kitso, tafi dacewa da a kira ta da birkitacciya Amani yanzu ba yar gaye Amani Faskari ba, sabida yadda ta koma sam ba nutsuwa da walwala da farin ciki a tare da ita, duk a dalilin rashin samun kan Mukhtar Issouffou Massaoudou. A lokacin da zuciyar ta ta afu a kan sa, da son ganin su a wani matsayi na cikakkun mata da miji cikin kauna da soyayya kamar kowadanne maaurata, ba wannan matsayin da suke kai a yanzu ba, kamar dai Mai Diffa da Ummami, kai bazaka ce sun tsufa ba, kullum cikin kaunar juna da tattalin juna suke, da ka zauna da dayan su sai ka ji ya ambaci dayan a cikin zancen sa na koyaushe, ta hanyar bada misali da kyautatawar da dayan su ke yi masa. Yadda son Mukhy da kishin sa suka taru suka sukurkuta Amani sai ta koma kamar ba yar gayun nan kuma yar kwalisa (wanke hannu kafin ka taba) da ya sani a gidan Hon. Usman mai suna Amani Usman Faskari ba. Amma yanzu kam fama yake da kan sa da ya tambaye ta dalilin wannan ramar haka, da dalilin susucewar ta, to ko magana baya son yi, ya rasa dalilin wannan masassara data same shi yanzun nan, jikin ta duk yayi sanyi da yanayin da ta gan shi a ciki na rawar dari don bata taba ganin sa cikin irin sa ba, sai ta zauna a gefen gadon jikin ta ya dau rawa itama, murya a sanyaye kuma tana yar rawa ta ce. Ya Mukhy are you alright? Why are you shivering?! Ya ce umh cikin karfin hali, sai ta zauna a daidai kan sa ta ce. Na ji dadi yau ka dawo da wuri, amma kamar baka da lafiya sai itama ta soma karkarwa, ta tambaye shi da me zan iya taimaka maka? Akwai magani a dakin? Ya sake cewa umh da murya irin ta mai jin zazzabi, Amani ta gama firgita, ta yi kwanciyar yan bori a kusa da Mukhy don ta gane ba kalau yake ba, ko ta hanyar saukar numfashin sa da ke sauka a kai-akai cikin hucin zafi, don haka ta ji ta kasa korafin ina yake kwana da ta so yi, ko tambayar sa an kawo masa kwarkwarorin ne ta daina ganin sa yana kwana a nan? Maimakon hakan, sai ta samu kan ta da cigaba da nacin tambayar sa Yaya Mukhy, don Allah da me zan iya taimaka maka? Kwarai a wannan yanayin yana bukatar taimakon nata, amma kuma... Im not well! Ya bata amsa da kyar, ta kara matsowa daidai kan sa, bakin ta tasa daidai kunnen sa ta ce me yake damun ka Ya Mukhy? A gajarce yace sanyi. Amani sanyi nake ji, wani irin sanyi har cikin bargo na, duk da na rufa, amma kamar ina ciki kankara still, ko dai mutuwa zan yi? Amani ta kara gigicewa ta mike a sukwane to bari in kashe maka A/Cn, ta mike da niyyar tafiya kashe AC sai taji Mukhtar ya riko ta da hannnun hagun sa da ya dauki dumi da karkarwa, ta juyo ta dube shi idanun ta sungama kwalalowa, cikin karkarwar jiki ta tsaya, domin gabadaya ta rude ta rasa abin yi, sai ta ji muryar Mukhtar a hankali yana fadin. “Amani sammin dumin jikin ki, it wil be absolutely okay for me. Ta so ta gane me yake nufi wato dumin jikin ta yake so, shi kadai zai taimaka masa ya samu rangwamen sanyin da yake ji, amma da ko kusa bata kawo hakan a ran ta ba kuma a rude take, sai bata gane me yake nufi din da dumin jikin ta ba, don haka ta tsaya tana dawurwura, sai ji ta yi Mukhy ya ja ta a hankali ya kwantar, ba tayi musu ba ta bi umarnin sa, sannan ya daga bigilar rigar jikin nata ya cire ta ta sama, ya warware zanin jikin ta da kyar cikin rawar hannu ya jefar da shi a kasa, da wata irin azama Mukhtar ya manna Amani a jikin sa, wuyansa da sajen fuskar sa cikin nata wuyan. Ya kuma kudundune su cikin bargon tare. Wato su sha zafin zazzabin tare. In ma mutuwa zai yi, yana fatan ya mutu manne ciki jikin ta.. Ko hakan ya sa su tashi tare ranar lahira a matsayin mata da miji, tunda a duniya Allah bai yi zasu rayu tare ba. Kusan zafin jikin Mukhy jikin Amani ya dinga komawa, irin yadda ya mannata a jikin sa ya sa komai nasa ya fara sauyawa, hatta saukar numfashin sa ya sauya, Amani ta samu kan ta da kara rungume Mukhtar, suna raba zazzabin nasa tare. Duk da cewa kuwa ba karamar wahala take sha ba, ga zafi kamar ya kashe ta. Sai tsakar dare suka samu zazzabin ya soma sauka, ta gane hakan ne da yadda ya soma yanka gumi yana jika ta, amma hakan bai sa Amani ta tashi ba, duk kuwa da cewa ba barcin take yi ba ita har tsayin lokacin. A yau ji take wata irin nutsuwa na shigar ta, kasancewar ta cikin wannan intimacy din na body contact tsakanin ta da mijin ta Mukhtar Diffa, soyayyyar Mukhtar da wata gigitacciyar kaunar sa na kara ratsa ta, yanayin jikin ta ya soma sauyawa itama ta kara kankame shi, shi kam zuwa lokacin ya samu barci mai nauyi, sai ta kara manna shi a cikin jikin ta, tana fatan su dawwama a haka. Tana fatan kada gari ya waye. A haka suka kwana, da asubah Mukhy ne ya fara tashi da kyar ya raba jikin sa da na Amani saboda yadda ta bi ta makale shi cikin jikin ta, wadda ya gama jikawa da gumin jikin sa jagab, ji tayi kamar ta rike shi ta hana shi tashin, don ta fi so su dawwama a haka. Mukhy ya je yayi wanka da ruwan sanyi kana ya dauro alwallah ya fito, yana mamakin abinda ya same shi jiya kamar farfadiya kamar bugun aljannu, ita sai a lokacin ma ta samu barcin ya zo mata. Mukhtar ya soma kokarin tuno abinda ya faru da shi a daren jiya da mamakin ganin Amani kwance a kan gadon sa, don ya manta ma yadda aka yi ta shigo tsabar yadda zazzabin ya buge shi jiya. Amani ta ji alamar tsayuwar Mukhy a kan ta don haka ta bude ido tana kallon Mukhtar a hankali da idanun ta da ke cike da barci, shima yana kallon ta da kyawawan idanun sa yana kara son komai nata, mace kamar ita tayi wa kanta halitta komai nata mai ban shaawa ne da daga hankalin da namiji. A hankali ta lumshe idanun ta cikin nasa, tana jin karin son sa a ran ta, sai hawayen suka dirgo marasa dalili bare madafa. Mukhtar ya dauke kai kamar bai ga hawayen ba, ya kada kai ya wuce ga sallayar da yake sallah a kai, ya ce mata. Tafisu ki tashi ki sallah haka!. Daga kwancen da take ta ce ciki raunin murya Ya Mukhy ka yafe min? Na yarda banida kirki, na yarda bani da hali, na yarda ban fi kowa ba, na yarda wanda yafi kowa shine wanda yafi kowa tsoron Allah, na tuba na bi Allah na bi ka! Kada ka sake tafiya ka bar ni, I promised to become a changed person. Muryar Mukhtar wannan karon cikin jin dadi da tausayi. Ya ce cikin kwantar da idanun sa a kan ta. Kiyi sallah Amani, sai ki zo mu yi magana ta fahimta, bana so wannan ramar da kike faman yi, kin ji? Gayun ma duk kin daina, haba Tafisu ni ina son gayun ki fa!” Dadi ne ya kama ta, tana son tashi amma ta kasa janye bargon daga jikin ta, sabida rigar ta da Mukhy ya cire cikin zazzabin da ya makanta shi jiya. Daga ita sai bra da panty din ta. Cigaba da kwanciyar tayi har sai da ya tada sallah, sanan ta yi maza ta dauki rigar barcin ta ta maida amma bata daura zanin atamfar ba, ta wuce nata dakin don ta shirya sosai. Sosai ta zauna ta cancada kwalliya, gayu iya gayu, cikin wani (swiss lace orange colour) da aka yi wa dinki riga sa da siket matsatstsu, ta fesa turaren ta na dindin watau Elizabeth Arden. Ta yi alkawarin yau ko kofar gida bazata bar Maina ya fita ba, jinyar sa zata yi da tarairayar abun ta, in an neme shi zata ce ai bai da lafiya, sai ta tabbatar ta wanke duk wata tsatsar ta dake ran sa, in dai ta amsa suna Amina-Amani, Aminatu Mamar Manzo, ba wai sauran mata ta rako duniya ba kamar yadda ake goran ta mata ta koina. Zata gwada nata diyaucin na ya mace da kissar da ake cewa da ita aka haife kowaccen mu. Amani ta yarda za ta bada hakuri yau, ta duk hanyar da zata iya da irin nata baiwar da Allah ya yiwa kowacce diya mace. Ta koma dakin nasa ta same shi ya idar da sallah ya koma ya kwanta don jikin sa ba karfi. Hidima sosai take ta yi da shi yana daga kwance yayi dai-dai wai bayan sa ke ciwo, hatta tea yau har kan gadon sa ta hada masa ta kuma bashi da cokali a baki, har sai da ya ture ya ce ya ishe shi. Amani ta koma taga an shirya musu kalaci kala-kala ta zubowa Mukhy farfesun koda da hanta ta kawo masa, ya ce na koshi fa, bani dai magani in sha, sai kiyi min tausa a bayan nan, duk jikina ciwo yake, akwai first aid box a cikin drawers din can, duba ki dauko min paracetamol, Ta yi yadda ya umarta, ta dauko maganin ta ballo biyu ta hado da gorar ruwan Faro mara sanyi ta kawo masa, a baki ta saka masa maganin, sannan ta kafa masa gorar ruwan a baki ya hadiye. Shi da kan sa bai yi marmarin fita ba yau, ganin yadda ake ta gatan ta shi, tuni zazzabin ya sake shi sai bin Tafisu da kasaitaccen kallo yake daga kwance, ga kwalliya ta fece ta fita tsara yadda yake son ganin ta, an yi daurin nan a kan goshi, irin dai yadda take yi a Katsina a lokacin da take kan ganiyar ta ta TAFISU! Yana hangota daga nesa yana hadiyar miyau yana faduwar gaba, domin babu karya Tafisu ta iya daukar wanka. Abin mamaki shi da baya kashe wayar sa sam, amma yau sai ya samu kan sa da kashewa. Duk wanda ya neme shi ta waya ya samu wayar Maina a kashe, yau har Ummami ya kasa fita gaishe ta sabida uwargida ta murda kambu. Ya Mukhy ka tashi muje na hada maka ruwan wanka ya kalle ta kasa-kasa yace ai na yi da asubahi, ko ke zaki cuda ni yanzun? Amani ta kai tafukan ta ta rufe fuska cikin jin kunya tana yar dariya, kuma sai ka tube a gaba na in hau cuda maka baya? Ai bazan iya ba kai ma bazaka iya ba. Mukhy ya ce wa ya gaya miki bazan iya ba? Sai kace nima irin ki ne dan kauyen Faskari? Yanzu dubi daurin da kika yi a kan goshi, yammatan yanzu basa yin irin sa, sai na acuci, wannan daurin naki fa tun na zamanin Maryam Babangida Amani me zata yi ba dariya ba! Bata san sanda ta tuntsire da dariya ba tayi ta yi, ta ce Ya Mukhy! A ina ka san a cuci da daurin Maryam Babangida kai ba dan Najeriya ba? Ya mika mata hannu ya ce zo in gaya miki ta rufe ido tana murmushi domin cinyar sa ya gyara mata yana nufin ta zo ta zauna kai. Amani ta rasa inda zata sa kan ta don kunya, sai ta bige da cewa. Ya Mukhy yau bazaka je fada bane? Wannan shine kora a fakaice. Kin taba sa ni zuwa fada? Inada fadar da ta wuce wannan? Mukhtar ya fada tare da mikewa ya nufe ta da azama don ya fahimci neman guduwa take yi don ta fara tsorata da idanun Mukhy yau, caraf! Ya ruko ta ta baya, ya kuma rungumota gabadaya, ya kwantar da kan sa a kafadun ta, ya kai hannu ya shafi kirjin ta da ke zagin sa tun dazu, ahe ko bra babu jikin su, yayi wata irin ajiyar zuciya yace. By Allah you will be the death of me AMANI!. Ya juyo ta suka fuskanci juna kafin ya sumbaci kirjin cikin lumshe idanu, sannan ya zuge zip din rigar gabadaya. Amani ta runtse idon ta tana kiran sunan sa kafin ta soma tirjiya cikin jin tsoron yanayin da Mukhtar ya koma mata yanzu, tuni ya balle bra din cikin dan lokaci da wayo da dibara, yana mata hira mara kan gado a cikin kunnuwan ta, Amani ta soma kokarin janyewa don ta soma tsorata, ya ce. Oh Amani, Oh! Tafisu, don Allah kada ki bar ni yau, in kika yi min haka, zaki kashe ni da rai na! Mukhtar ya gama saddaqarwa yau in Amani ta zuqe masa a wannan halin, ko ta yi amfani da damar ta ce zata rama abinda yake yi mata itama a kwanakin nan, babu shakka gawar sa zaa dauka. Tun tana neman zuqewa yana riko ta cikin lallashi da shafa gashin kan ta zuwa tsakiyar gadon bayan ta, don ita bata tsammaci wannan a yau ba, don ta san bai da cikakkiyar lafiya kuma, tsakanin ta da Allah jinyar sa ce tasa take yin duk abinda take yi, ba don ta ja hankalin sa ba. Shi kuwa Mukhtar a yau kam duk wasu EXPERIMENTS DA YA DORA AMANI A KAN SU, YA YARDA AMANI BATA FADI KO DAYA BA!!! Don haka ya yarda wannan safiyar ta zama first morning din su maimakon first night da ake cewa. Don ji yake kamar an kawo sabuwar lafiya an kara masa. Kafin kace meye wannan har Amani ta soma yin laushi, sumbar da Mukhy ya soma mata ta soma shigar ta, ta ratsa har cikin kwanyar ta. Saura kadan Amani ta sume sailin da Mukhtar ya susuce a sumbatar kirjin ta, sai zuba sambatu yake cikin hargitsa gashin kan ta, cikin rokon ta shima ya tuba. Ya daina muzanta mata. Can na jiyo Mukhy da wata yar murya tamkar ba tasa ba, yana fadi wa Amani cikin kunnen ta Ya bi Allah ya tuba, ya mayar da duka kalaman shashasha, ballagaza, rakiyar mata da yake kiran ta da su a baya, yayi rantsuwar cewa yau ya mayar dasu cikin cikin sa!. Hawayen farin ciki suka zubowa Amani, ta dora hannayen ta a kan kafadun sa ta ce MUKHY, I LOVE YOU YA MUKHY! Ta soma mayar masa da martanin sumbar kaunar da yake mata, Mukhy ya karasa rikicewa Amani, don bai zaci wannnan alfarmar daga gare ta ba, ya ce. Pls Tafisu hug me today, it is the beginning of our blessings, the truth which I. I must confess loudly. “ TAFISU KIN FI SAURAN MATA A ZUCIYA TA!. Sai hawayen farin ciki suka shiga tsere suna diga dis-dis, daga idanun Amina-Amani, zuwa kan kyakkyawar fuskar Mukhtar Issoufou Massaoudou, kawai sai Mukhy yasa halshesa yana dauke mata su, silla-silla, wannan ya kara rikita Amani, ta kara sakar masa jikin ta sosai, ya shiga yin yadda ya ga dama da komai nata, domin kalamai ne da bata taba zaton ji daga Mukhtar ba. Tunda shi kullum burin sa shine yayi kasa da ita, don ya rage mata jin izzar wannan perception din nata na tafi sauran mata!!! Sune kuma kalaman da suka fidda duk wani tsoro da fargabar abun da ke ran ta, ta mika wuya ta bashi damar da ya dade yana nema, wato ya tara da ita a lokacin da take son sa, so na hakika. Ta mallaka masa zuciya da ruhin ta da gangar jikin duka a tare. Ta kuma karbi kowane tayin sa da hannu bibbiyu. **** **** **** At last, bayan komai ya lafa Amani na jiran Mukhy ya lalace a tarairaya da lallashin ta, ta daga sabuwar shagwabar data kakalo, da kukan rakin da take sake babbakowa (bayan fa ta gama taya shi komai an mori kuruciyar tare), cikin taimakon juna da kaunar juna, wannan karon kukan nata na zallar shagwaba da raki ne, na azabar da ke ziyartar ta ne yanzu bayan kanwa ta kar tsami, kwannafin su duka ya kwanta in ji hausawa, kishin sadakoki bay a gaban ta yanzu sabida ita kan ta ta san a yanzu kam ta yi wa sauran mata zarrah tayi wa kowacce mace fintikau! A zuciyar Mukhtar. Ko da bai fada cikin nutsuwar sa ba, a yau ya fada cikin shidewar sa a soyayyah. Mukhtar ya fito daga toilet yana goge kan sa da towel, ya kalle ta tana kwance tana sharer hawayen da yaki tsayawa, ta kudundune jikin ta cikin duvet din sa, ta dauka zai lalace a lallashin ta ta cigaba da shagwabewa yadda take so, amma Mukhy sai cewa yayi, ragguwa kawai, sakaltatta, zaki tashi ki wanka ko bazaki tashi ba? Ko kina nufin daukan ki zan yi in kai ki toilet din? To tun farko ni nace a yi? Ba ke kika ce kin yarda ba? Ni da bani da lafiya ma, amma baki yi laakari da hakan kin tausaya min ba, ba saida kika yi disvirgining dina hankalin ki ya kwanta. Amani ta daga kai tana kallon sa baki bude, hawaye na zuba, Mukhtar ya ce eh mana. Kin sa yau na tashi daga suna na mai dadi Mukhy na koma Daddy (Baba). Besides, ni kam ai ban shirya sallama daga kuruciya ta a yau ba, so na yi sai kin yi hankali mai yawa, kin kara nutsuwa, kin tabbatar da Allah guda daya ne, amma yarinyar nan sai da kika san yadda kika yi kika seducing mara lafiya, kika kayar kasa warwas, saboda kin samu sarbadeden saurayi a bagas! Bayan duk cin mutuncin da kika gama yi masa, amma duka yau kin manta, kika saka shi a daki kika more. Ya yi mata murmushin sace zuciya, Anyway, AMANI you are a DARLING! Ko Sadaka sun zo a bayan ki suke. Ya sunkuya ya sumbaci goshin ta ya ce I love you with all my heart Amani, tun gani na da ke na farko kin sani, na fara son ki ne from the very first time I saw you, ranar da na dawo daga France ke kuma kika zo wani hutu, sai ya zamanto na fuskanci halayen ki sun saba da nawa, na gane bazamu taba daidaitawa ba da wadannan halayen naki, don na tsani mutum mai GIRMAN KAI, FARIYA, TAKAMA DA IZZA, a takaice halin ki ne kawai bana so Tafisu, tun daga wancan lokacin, amma ba ke ba. And today, Amani I love you more than any worthly earthly possessions, for the wonderful gift I received from you, for the love we shared, it will continue to linger in my memory. Ya sake kai mata wata warm sumbar a kasan cibin ta, wanda yasa Amani rufe idanu da hanzari, cikin kunya da kuma jin dadin kalaman sa. To amma me, duk ciwon nan da take ji a cikin jikin ta, Mukhtar ko ya sani ko kuma bai sani ba? Zata iya cewa Mukhy ya so kan sa da yawa, duk da ya taba cewa he will not be selfish a kan hakan, yau kam yayi son kai, don ta san bata yi healing from the first ba, lokacin da ta gane neman tafiya karo na biyu yake yi duk kuwa da yana lallashi, yana yana kuma bada hakuri ta hanyoyin nuna kauna da dama. Duk ta san kauna ce ta sa hakan, amma hakika ta tausayawa kan ta domin ta ji jiki ba na wasa ba. Tana so ta ce aa, tana so ta yi korafin ya bar ta ta samu hutu, at least ko zuwa gobe, amma da ta tuna ‘sadakoki masu zuwa da abinda Ummami ta ce mata a kan halittar su, ai sai ta gyagije, tare da bada sabuwar himma, wajen nuna rashin gajiyawar ta duk kuwa da cewa Amani ta jigata yau a hannun Mukhy, ya mori auren sa da yayi missing sama da watanni biyu a wunin ranar yau kadai. The whole day for Mukhy! ***** ***** **** Haka daren yau ma bakidaya Muktar ya hanata aikin komai sai nashi, bai bar Amani ta huta ba har washegari yana amarci, haka basu je koina ba wunin yau, sun bawa juna lokacin su gabadaya, ta yarda auren ibada ne da gaske, ibada mai zaman kan ta, ba wai zata ce jin dadi ne zallah a cikin sa ba, kamar yadda take tunani a baya, akwai takura musamman da bata saba ba. Amani ta yarda cikin kowacce ibada kuwa sai an saka juriya da sadaukarwa ga juna. **** **** **** D uk yadda ta so da safe Mukhy ya gaya mata ya fasa karbar Sadaka, ko don wannan aikin bajinta data kwana ta wuni yi masa, wuni guda da dare guda Mukhtar na shan amarci kamar bazai ragewa gobe ba yadda yake so, ba tare da ya yi laakari da cewa, itama kamar shi, shigar fari ce cikin situation din, kusan har ta ce ta samu tear, a yadda take jin radadi a tare da ita. Abun na Mukhy duk da cewa (is not by force, is so gentle, so soothing and so romantic), domin yana yi ne yana hadawa da lallashin ta a kowanne dakika, ta hanyar kwantar da gashin kan ta da hannun daman sa, kuma baya rushing, yana yin komai a sannu, sannan yana bari ta huta na wasu awanni yana bata labarin rayuwar sa a Paris da irin wahalhalun da ya sha wajen neman na kai da neman ilmi, to amma fa ita a wurin ta akwai mugunta da son ladabtar da ita duk da haka. A wurin Maina Mukhtar yadda ka tafiyar da matar ka a daren farko a haka zata mike, don haka Mukhtar bai yi da sauki ba, sosai ya baiwa Amani irin darussan soyayyar da yake so ta tashi dasu. Ta mika da su har karshen rayuwar su. In fact, sai da ya fanshe duka kwanakin auren nan nasu da aka kwange masa a daren jiya da wunin jiya kadai, ko yace ya sauke wahalar duka samartaka data tuzurancin sa within 24 hours only. Da asubahin ranar Amani ta kafa sabon kuka, musamman data ga bazata samu yadda ta ke so daga gare shi ba, wato so take Mukhtar ya lalace yayi ta lallashi da tarairayar ta, kamar Romeo kada ya je ko’ina, amma tuni shi ya tashi ma yayi wankan sa ya zuba farar shaddah Wagambari, kyale ta yayi tana ta yi riii-riiii-riii, wai don ya ce ta taka da kanta zuwa toilet, bazai iya barin lokacin sallah ya shige shi ba, shi baya son rakin nan nata, ya hau shirin tafiya masallaci, ta tabbatar fita zai yi, sai ta kara rushewa da kuka. Da ya rasa yadda zai yi da kukan nata don baya son jin sa ko kadan, zuciyar sa tabuwa take, tsinkewa take, sai ya yi wa Baba Sahura waya, yana tsoron kada yau ma Amani ta sa yayi missing jamI kamar yadda ta sa shi sallah a daki jiya, da wannan kukan nata mai bukatar ya lalace a lallashin ta. Sahura na shan barcin bayan asubahi wayar Maina ta tashe ta, da sauri ta tashi zaune ta amsa, sai ta ji gyaran muryar Mukhy yana cewa, yi hakuri Baba Safoorah, na tashe ki daga barci, Im so sorry. Nan da nan Sahura ta wartsake ta ce Babu komai Maina, Allah ya sa dai lafiya kuke, ran ka ya dade? Gabana ya fadi. Sai da ya kai zuciya nesa sannan ya iya cewa Yar ki ce bata ji dadi ba, ni kuma ban san taimakon da ya dace in bata ba, sannan inaso in samu sallah. Ya fada cikin dakewa, don ya gwammace ya kira ta akan dai ya kira Ummami, duk da itama Baba Sahuran yana jin kunyar ta, amma ya san gara wata kunyar a kan wata. Baba Sahura nan da nan ta je gano, ta soma murmushi ta ce ranka ya dade ai ba abun damuwa bane, ba sai na zo ba, hada mata ruwan zafi cikin abin wankannan ka saka ta a ciki kamar minti talatin, ka bata panadal ta sha tayi barci mai kyau shikenan zata samu karfin jikin ta in sha Allahu. Har ya je ya yi sallah ya dawo tana nan yadda ya bar ta amma barci na fizgar ta. Bayan sun aje wayar itada Mukhy Baba Sahura kasa rike wannan labarin ita kadai ta yi a ran ta, bakinta har kaikayi yake, ta kira Ummami ta sheka mata labari, Ummami ta ji kunya amma sai ta hau ta da fada tana fadin ita fa Uwa ce ta dinga kama kan ta, ta daina shiga shaanin su, ta kuma hau murmushi ita kadai, a lokacin tana tare da Mai a turakar sa, amma ya fita sallah bai dawo ba, tana ta murmushin ta na farin cikin yau Mukhy ya zama magidanci, sai ga Mai ya shigo, tana rike da wayar a hannun ta. Me ya faru ne Mowar Sarki? Irin wannan murmushi da sassafe ban yarda kalau ba. ke da wa kike waya da asubahin Allah?. Ta yi yar dariya ta ce labari Sahura ke bani wai yau Maina ya zama magidanci, shine nake mata fada na ce ta daina shiga shaanin su. Farin cikin Mai Diffa ya kasa boyuwa, Ummami ta kara da cewa kuma ta ce diya ta ta kawo mutunci fal, kamar yadda dai aka san gidan mu. Alhamdulillah. Mai Diffa ya daga hannu ya yi wa Allah godiya, yace ki shirya kyauta ta musamman ki bata in ji ni, amma kada ki gaya mata dalili, ko ta san mun sani, to ya maganar sadakokin da Sultan ya bashi? Tunda sai yanzu ya angwance ma? Anya basu yi wuri ba Ummami? Ummami ta ce gaskiya dai, a dan dakata kadan, a tsahirta ko zuwa ta yi haihuwar fari ne, su fahimci juna sosai tukunna, da koyon rayuwa tare a gidan sarauta, wanda basu tashi sun girma cikin sa ba. Don na lura akwai kuruciya har yanzu a tare da su su duka musamman ita. Mai Diffa ya yarda da shawarar Ummami. **** **** **** Ka ce wai nauyi, nauyi ne da ni, don haka bazaka iya daga ni ka kai ni toilet da kan ka ba Ya Mukhy? Amani ta fada cikin marairaicewa, kafin ya amsa ta sake cewa “to shin wa ya dauko ni ya kawo ni dakin nan? In ji dai na san ba da kafafuna na shigo ba? Amani ta bashi dariya sosai da wannan maganar, amma da yake ba gwanin yin ta bane murmushi yayi, haka ta cigaba da nacin sai ya dauketa ya kaita toilet yadda Romeo yake yi wa Juliet, dariyar ta subuce masa wannan karon, sannan ya ciccibeta ya dauka duk da nauyin nata da yake korafi ya nufi toilet da ita. Ke dai ki rufe min bakin tsiwar nan, kafin ki zaburo ni na kara dinke shi. An ce na hada ruwan zafi a Jacuzzi in saka ki a ciki na rabin awa, kada ki tashi. Amani ta fiddo ido Wane irin ruwan zafi kuma Ya Mukhy? Haihuwa nayi? Mukhtar ya ce To me marabar ki da mai haihuwar tunda na bude hanyar haihuwar? Mace sai tambayar tsaya tana fama da kan ta, amma ba ta tsayawa ta ci ribar zance. Mukhtar ya dire ta a toilet ya hada ruwan yasa hannu yaji shi da zafi cau, kamar na wankan jego, sai ya dauka haka Baba Sahura ke nufi, ya dauki Amani ya tsumbula ta a ciki, da ta yi wani zillo sai ga ta ta koma jikin sa ta shako shi, sai gashi shima tsudum ya biyo ta sun fada cikin ruwan tare, shima ya ji zafin yace, wash! Muguwa! Ta ce ai gara mu sha zafin tare Mukhy ya ce of course, tunda tare muka sha dadin ma! Amani ta rufe ido tana jin kunya, in wani ya gaya mata wannan Mukhyn Alhaji ne mai wannan daure fuskar da rashin walwala kamar malaikan daukar rai zata musa, tabbas (mace mai canza namiji a aure komai zafin sa). Amani ta boye kan ta a kirjin Mukhy cikin murya mai ban tausayi ta ce ni kam ban gane komai ba sai azabar da ka bani Ya Mukhy, muryar ta abin tausayi ta saka Mukhtar ya rungume ta sosai a cikin ruwan, ya sumbaci lips din ta affectionately sannan ya ce, kada ki damu kin ji ko Sweetheart, don na farko ne shi yasa, you will soon come begging for more! Amani ta rasa inda zata sa kan ta don kunyar da Mukhy ke bata yau, amma ta lura Mukhy ko a jikin sa. Yau cikin nishadin sa yake komai. Don haka tare aka yi wankan jinyar, Mukhtar da Amani. Aka zo maganar wankin zanin gado, yace ni kam bazaki saka ni aikin wahala ba bayan wanda na kwana yi, ki dauki abin ki ki wanke. Amani ta yi narai-narai da ido, ta ce ai ka san ko a gida ban taba yin wanki ba, balle na zanin gado, ni fa ko bras dina Rakiya ke wanke mun da azama ya bada amsa nan kuma ba gida bane wajen neman lahira ne, wallahi in bazaki wanke ba, Baba Sahura zan kaiwa ta wanke. Amani ta bare baki zata yi kukan nata na gado, Mukhy ya ce cikin kwafa, kina farawa ina karawa. Sai ta maida bakin ta ta rufe har da toshe shi da hannun ta, shi kuma ya yaye zanin gadon ya aje shi gefe ya ce ta shimfida sabo. Bata kula da sanda ya dauka ya jefa shi a kwandon kayan wankin su ba, ta shimfida sabon bedsheet ta lallaba ta koma ta kwanta, sai Mukhy ya baro magani ya kawo mata da kofin ruwa. Amani ta ce narka min shi a kan cokali, ban iya hadiyar kwayar magani ba Mukhtar ya ce Amani kina wahalar da ni ina wahalar da kai ko ka wahalar da ni? Ko dai mun wahalar da juna? Kema fa yarinyar nan na lura a matse kike, Allah ne yayi cewa ni din nine da kin hana sadakoki na masu shigowa samun sauran komai a tare da ni. Tun da ya fadi haka Amani bata sake kula shi ba, ta juya ta kwanta ba tare da ta karbi maganin ba. Mukhy ya ce. Gara ma ki karba ki sha, don ki warke kafin dare, this is your daily duty as a house wife, tunda ke kadai ce for now, gara ma ki sani tun yanzu ban fasa karbar sadakoki na ba, sai ranar dana karbi ta goma! Zan rufe kofa. Amma har a Aljannah ina fatan ki zamo shugabar mataye na. Amani ta tashi zaune, idon ta fal hawaye, duk da cewa ya karramata cikin maganar sa ta karshe amma ko kadan bata son zancen sadaka kamar yadda bata son mutuwar ta, ta ce a sanyaye. Yaya Mukhy, wanda ya sake cutar da wani tsakanin mu daga yau, koda da zazzafar magana ne, ko maganar da dayan mu ya nuna baya so, bayan mutual understanding din da muka samu yau, and forgiveness to each other, ina rokon Allah ya bi masa hakkin sa a kan dan uwan sa!. Sai kuka. Juyawa yayi bayan ya ajiye mata maganin akan bed-side din, jikin sa ya dan yi sanyi da jin kalaman ta, ya yarda da gaske Amani bata son maganar sadaka. Ai kuwa shi maganar yanzu ma ya fara domin ya samu makamin yakin sanya Amani ta yi masa abinda yake so a duk lokacin da ya ga dama da barazanar Sadaka, ba don wai ya yanke a ran sa zai karba ko ba zai karba ba. Ganin kukan da take bilhaqqi take yin sa, sai ya koma lallashi To shikenan, ki yi hakuri Sweetheart, idan na daina maganar Sa-daka, kullum sau nawa zaa yi mun alfarmar? Kafin in fita fada, da bayan na dawo? Kin ga ke din Sweetheart dina ce bana gajiya da rabar niimar da Allah ya yi miki, ga ki Sweet 16 Amanin Mukhy, Allah da ya halicce ki ba da kyawun sura kadai ya bar ki ba, daga sama har kasa har ciki Amani Tafisu ce, Tafisu ba dai abunnan ba. Ya karasa da rungumeta sosai yana kissing idon ta da suka yi narai narai da hawaye, ta ce ko sau nawa kake so Ya Mukhy, ko zan mutu zan amince, in dai zaka bar maganar sadaka. Sai Mukhtar yaji wani dadi a ran sa, ya riko hannayen Amani cikin tafukan sa, ya kai su ga fuskarsa suka tallafi lallausar sajen dake kwance a kowanne gefe na fuskar sa. Balle ma bazaki mutu ba, sai dai hakan ya kara min son ki, sannan ki yi ta suburbudo min yaya ina kara son ki da kaunar ki, ina kara kula da ke Tafisu. Ke din wata mutum ce mai daraja a waje na saboda ALHAJI! Wadda komai tsayin lokaci da canjin da zamani zai kawo, ko tsufa, ko canzawar halitta saboda shekaru ko girma da ya same mu, ko wani abu makamancin hakan, bazan taba iya wulakantawa ba. Daddyn ki mutum ne da bazan taba manta alkahirin sa a rayuwa ta ba. Don haka zan kula masa da tilon Tafisun sa, in adana masa ita a daki na ni kadai, in mayar da ita TAFISU TA GASKIYA, amma ba da komai tawa Tafisun zata fi sauran mata ba sai da nagarta, kyawun hali da rikon addini, kula da miji da iya soyayya ga mijin auren ta, da kuma iya kula da yayan ta da iyayen ta. Kalaman sa sun kashe Amani don dadin su a ran ta, Mukhy ya daina ce mata shashasha, ya yarda ita din, ba ballagaza bace. Idon ta fal hawaye ta dube shi da dukkan kauna da soyayya a kasan idanun nata, ta soma magana cikin rauni murya. Na san bazan ce ina son ka ka yarda ba yanzu Ya Mukhy, na san na makara, bazan ce maka tuntuni ba kin ka nake ba, kishin yadda Alhaji ya fifita son ka a kaina ne ya sa nake kyarar ka ka yarda ba, bazan ce maka a kasan raina ina yawan yaba surar ka da a fili nake kushewa ka yarda ba, don na bar baya da kura mai yawa, bani da say a yanzu da zai yi tasiri a zuciyar ka a kan SO, tunda baki shi ke yanka wuya, kuma maganganu zarar bunu ne. Na fadi maganganu cikin jahilci da yawa, wadanda da inada dama a yanzu, da na mayar da su na hadiye su a ciki na. Mukhtar ban fara son ka don na ga kai waye bane, ko don nasabar ka, ni dai kawai gani nan ne, zan iya cewa tun a Saliyo! Ranar nan. Na fara samun sauyi a zuciya ta a kan ka. Ka yi min rai Ya Mukhy kada ka karba Sadakoki, ba don ni ba! Ta cigaba da matsar kwallah tana cewa duk abinda kake so zan maka daga yau, ko da ya fi karfi na, zan aro karfin a duk inda yake, wani irin kishi ne da ni a kan ka, mai barazanar haukata ni, idan suka shigo. Mukhtar yama rasa me zai ce don dadi yau. Ya shirya tsaf cikin irin kayan gidan su, amma bai nada rawani a kan sa ba. Your actions will prove your words Hajjaju, babu bukatar rantsuwa anan Hajiya Amani, abun nufi, in gani a kasa kawai, Mukhy sama Mukhy kasa ana kula da ni, wato ki cigaba da yadda kika fara yau, saboda ke dinnan tsoro kike bani, sakamakon halin ki na hawainiya yau fari gobe baki, na rantse tuban ki na muzuru ne a yawancin lokuta, ba kya taba tuba don Allah! Sai kin ji wuya. Maganar sa ta so ta bata dariya don tasakanin sa da Allah ya fada. Iya karantar da yayi mata kenan sama da shekaru goma. Halin ta mai wuyar canzuwa ne don an ce hali zanen dutse ne, sai dai ma iya cewa zata rage wasu in aka cigaba da ankarar da ita a hankali cikin kauna da soyayya. Zani gun Mai, daga nan zamu je Dosso nadin sarautar dan sarkin Dosso, probably sai Maghriba zan dawo. Ya juya zai fita, Amani daga kwance ta kira sunan sa, muryar ta abun tausayi ta ce. Ya Mukhy! Ya dakata ba tare da ya juyo ba. Sai ji yayi Amani ta ce. Baka yi min goodbye kiss ba, you know I love your kisses! Mukhtar dai yau duk abubuwan da ke faruwa a mafarkai yake kallon su, amma gara ya zarce a cikin mafarkin nan da dai ya farka daga niimomin dake cikin sa. Murmushi yayi ya daga mata gira da kafada a tare, ya ce cikin dariya. Na ki din! Maana wato ba zai yi goodbye kiss din ba, har da make kafada alamar ya ki, sannan ya fita yana mata murmushin dake neman narka zuciyar ta. Idan wadannan canje-canjen da yake gani a tare da Amani cikin dan lokaci na gaskiya ne kuma zasu dore, baya jin zai yi maraba da wasu kwarori, kowacce mace kazama kuma dukun-dukun zai gan ta a kan Amanin sa. Sai dai ita din Zuma ce sai da wuta, amma hakika Amani ta sanya shi cikin madaukakin farin ciki yau, da yake fatan su dawwama a cikin sa har karshen rayuwar su. ***** **** ***** Fitar sa ba jimawa ta sha maganin da ya aje mata ta cigaba da kwanciya har ta ji kwarin jikin ta, sai ta ta shi ta shiga wanka, a gurguje ta shirya cikin sassaukar shiga ta wuce sassan Ummami. Tun a hanyar isar ta bangaren Ummami take shirya kalaman da zata doshi Ummami da su. Ummami na kitchen tana hada Karin kumallon Mai ta shigo kitchen din ta same ta, rabon ta da ita har ta manta tun daga zancen sadaka da aka gaya mata, amma Baba Sahura ta tabbatar mata lafiyar ta kalau ittikafin zuciya ta shiga a kan sadaka, kamar an jefo ta Ummami ta gan ta a bayan ta duk ta rame, amma tayi kyau sosai kamar ramar ta kara mata kyau ne. Tausayi mai tsanani ya kama Ummami, ta dube ta ta ce ke kam lafiya kika fito haka da sassafen nan? Ke da aka ce ba lafiya ce ta ishe ki ba? Yanzu nake shirin shiga in dubo ki, ina jiran abincin ki ya karasa ne. Ta samu kujerar zaman cin abinci a kitchen din ta zauna, cikin jin kunya sosai kamar ba Amani Faskari ba mai ido a tsakar ka, ta gaida Ummami, amma bata amsa maganar da Ummami ke yi ba, saboda yau surukuta sosai take ji da ita ba Uwa ba. Tunda itada Mukhy yau babu hijabi. Ummami da rawar jikin ta taje ta juyo farfesun Zabuwa data ke yi mata da hannun ta, ya ji kayan kamshi na gargajiya sai tiriri yake da tashin kamshi, ta zubo shi a wani tangaran mai fadi haka kamar bowl na sarauta ta kawo mata, tana cewa cikin kulawa ki ci maza yanzu, ki shanye romon duka, ko kya ji dadin jikin ki. Ta karba ta soma ci a yangace, cikin yaukin ta na halitta. Ummami ta lura cikin damuwa ta ke, ba nutsuwa a tare da ita, ga ba walwala, ga hawaye sun ciko a idon ta. Ummami ta ce cikin tausasawa ki yi hakuri kin ji? Wannan ita ce rayuwar kowacce diya mace a gidan aure, a hankali zaki saba, har ya daina zame miki takura sai armashi da nishadi, kuma ba zan bar ki haka ba In sha Allah, zan baki abubuwan da zaki dinga amfani da su, ki ci ki sha don karin niima da kuzari da koshin lafiya. Kowacce mace da kika gani da yayan ta gwanin shaawa an ce miki ta sauki ta same su? Soyayyar aure na da dadi, amma wani lokacin sai an jure, rayuwar da Allah ya tsara mana kenan mu mata, wadda muke fatan samun aljannah ta hanyar ta. Amani da ke neman rushewa da kuka ta ce to Ummami amma da wahala ai, gashi Ya Mukhy bai daina zancen sadaka ba har yanzu, da me zan ji? Da wannan matsawar tasa ko da damuwar maganar Sadaka da naji ana yi? Tun ranar ban yi barci ba Ummami, ido na bai runtsa ba ko na sakan, ko gyangyadi na yi in na tuno zancen sadakoki sai na farka, na yi duk kokarin da yake so amma duk da haka ya ce bai fasa karba ba. Ummami na so ta yi dariya, amma ta maze, Me zai karba ne ban gane ba? Ta ce Ummami mun daidaita kan mu ni da Ya Mukhy jiya, ba kallon juna muke da ido ba, don Allah a yi hakuri a fasa bashi sadaka. Ummami ta ji dariya na son bada ita, ta ce to ai baki sani ba, a halittar da Allah yayi musu ne mace daya bata isar su, da a kara masa mata uku na aure ba gara miki sadakokin ba? Tunda su ba matsayin ku daya ba dole suna kasan ki ne? Amani tasa hannu ta rufe ido ta runtse shi ta kauda kunya, ta ce. Ummami, da yardar Allah ni Amani na yi alkawari ni zan ma Ya Mukhy hidimar da mata hudu zasu yi masa, in sha Allahu. Yanzu kam Ummami ta kasa rike dariyar ta sai da ta sake ta kadan, ta ce Magana tana hannun Mai, ba ni na roka masa ba, an kawo masa kyautar su ne daga Sultanate of Damagaram (Zinder) sabida girmama wannnan masarauta da yi masa barka da dawowa gida, duk a cikin shirye-shiryen bashi sarauta ne. Amani ta daure ta hadiyi miyau da kyar, sannan ta ce Ummami kin ce ni da ke ba surukuta tsakanin mu ko? Uwa ce da yar ta ko? Kin ce in miki alkawarin kula da Mukhy zaki zame min garkuwa a kan sa, to nayi miki wannan alkawarin na kara yi, ina rokon ki, ki taimake ni! Ki yi min garkuwa da wadannan sadakoki. Zuwa yanzu Ummami ta gama fahimtar Amani irin masu zafin kishin nan ne na balaI, duk irin bayanin da zaka yi musu akan kishiya agidan sarauta bazasu fahimta ba, kuma akan kishi kusan rasa tunanin su da hankalin su suke yi, sai ta ce to shikenan Amani, zan gayawa Mai sakon ki, na zaki iya ma mijin ki abinda mata hudu zasu iya, kin yarda? Kunya ta kama Amani, ta rufe ido ta ce haba Ummami, ta yaya zaki gaya masa hakan? Ai rokon sa kawai zaki yi yayi min alfarma ya bar su, ki ce ya duba ya gani ban dade tare da Ya Mukhy cikin kwanciyar hankali ba sai yau, kuma shikenan sai a bashi yammata zabga-zabga har biyu, ni to meye amfani na? Sai ta saka kuka tana cewa, wallahi Ummami duk abinda nayi masa a baya na tuba, sharrin shaidan ne da rashin tarbiyyar UWA, ban taba sanin dan uwa na bane, ban taba sanin mutum na da darajar da babu halittar da ke da darajar sa ba sai a kan Ya Mukhy, ji nake in aka bashi sadakokin nan zan mutu Ummami! Ummami ta ga abun na Amani azimun ne, babu Sarki sai Allah, sai ta ce Amani! Amani saurare ni. Kullum ki tuna Moukhtar da kike aure Sarki ne, dan Sarki kuma jikan sarki mai jiran sarautar garin su, don haka in kina son zaman lafiya da zuciyar ki ki cire maganar son rayuwa da shi ke kadai daga ran ki, haka suke, haka Allah ya halicce su, haka kuma suka gada daga iyaye da kakannin su (polygamy). Makami daya zaki rike ya fishsheki a kan su; ke dai kiyi kokarin zama ta kwarai ga mijin ki wadda sauran mata bazasu iya shan gaban ta ba wajen kyawun hali da nagarta da iya tafiyar da shi a shimfida. Kin ganni nan ni Aisata kishiyoyi sun fi 20 na gani a gidan nan, wannan ta shigo wannan ta fita amma ni din dai kin ganni har yau zama daram! Maina uban shi ba zai kyale shi cikin kewar mace ba, alhalin ya san dan sa ne mai irin halittar sa. Kunya kuma ta zo ta lullube ta, ta ce Ummami ke mace ce yar uwa ta zaki fahimce ni, ban iyawa, wallahi ban iyawa. Ta mike tana kuka wurjanjan. Ummami ta janyo hannun ta ta maida ta zaune, tace shanye romon nan ki cinye zabuwar nan Im not in the mood of eating ta bata amsa a haka zaki daure ki ci, don lafiyar jikin ki ko ba kya so. Haka ta sa ta a gaba da lallashi sai da ta cinye, ta hado mata shayi mai zafi sannan ta ce to ki cire damuwar hakan a ran ki, zan yi magana da Mai, shima kuma har yanzu ba wai ya bayar da amsa bane, na san so yake ya tabbatar da daidaitawar ku da canzawar ki don yana korafin kina masa rashin kunya Amani. Ta kara zama abun tausayi ta ce da Ummami Wallahi Ummami daga yau na tuba! Na tuba na bi Allah na bishi, mun daidaita na bashi hakuri ta sake share hawaye ta ce ai yanzu na yi hankali, ko makaho ya shafa ya san wannan ba Tafisu ba ce, Bata-kai su ba ce. Ummami couldnt control her laughter, ta yi dariya ta ce shikenan zauna in baki abubuwan da ba sai kin tsaya kina masa wannan zubar da ajin ba, a kan kada ya karbi sadakoki, ki ci ki shanye kawai, ki zama kullum a jiraye da karbar bukatun sa duk yawan su, babu jimawa zaki saba, kada ki kara zubar da kimar ki akan zancen sadaka. Da haka Ummami ta samu ta lallashe ta ta kuma daddaka mata tsumin Damagaram, da kayan gyara nasu na hakika, sannan ta ce ta koma gidan ta ta kwanta ta samu barci, kada ta haukata kan ta a kan namiji. Da kyar ta iya komawa sassan ta. ta hana su Tahira zuwa inda take. Ta kwanta a main bedroom nata bayan dawowar ta daga sassan Ummami, amma barcin da Ummami ta ce ta yi don samun nutsuwa ya gagare ta har yanzu, hakika babu tashin hankalin da yafi kishiya a gurin diya mace, gata ita nata bama daya ba biyu a lokaci guda, Mukhtar gari banza ma cike yake da kasaita da izza balle ya mallaki wasu matan bayan ita, ai ita tata ta kare kenan. Tana ta wannan kukan Baba Sahura ta shigo, Ummami ce ta ce ta je ta zauna da ita har sai Maina ya dawo, tunda bata jin dadi, Baba Sahura na shigowa ta hau tattare dakin da aka hargitsa, ta shiga toilet don ta wanke mata bayin, tayi kamar bata san me take ciki ba, don Ummami ta hana bayi shiga dakin barcin su. Nan Sahura ta ga zanin gadon a dukunkune cikin kwandon kayan wanki, ta dauka tace bari ta wanke, gulma irin ta Baba Sahura ta ce bari dai ta bude ta samu abun tsokanar Tafisu. Ai kuwa nan ta ci karo da aikin Mukhy. Ta mayar ta dukunkune zanin gadon a hannun ta fito ta tsaya a kan Amani da ke kuka, ta ce. Uwa, Uwa ashe yau an kashe Boss? Haka da wurwuri? Daga kwance ta karyo ido ta dube ta don bata fahimci me take nufi ba, ta san dai in Baba Sahura ta gane me take ciki yau ta shiga uku! Wato shine Ran shi ya dade ya bani a kudundune? Yo ai ni na dauka ciwon tafiyar Alhaji kike yi da ya ce wai ba kya jin dadi, ashe-ashe! To ni kam wace jinya zan yi banda in tambaye ki ya aka yi haka? Kika bada kai daga shigowa daki? Ai ni na dauka gudun aure zaki dinga yi kullum dare zuwa gun Mowa, irin yadda ake yi a zamanin mu in baa son mijin, irin dai yadda ba kya son Maina, na dauka har sai ya gaji ya daure ki jikin karfen gado Kawai kuma sai in ga kwana daya da zuwa an kar Boss? Kuma da Mukhtar din da ba so ake ba, ake wulakantawa? Amani kamar ta rusa ihu da wannan habaici na Babar ta Sahura, amma bata yi ihun ba. Tsaki tayi, tayi banza da Sahura, ta juya kai ta cigaba da kwanciya. Sahura ta hau latsa wayar ta tana cewa ai dole Yaya ya bani goron albishir, har Jalan ba zaa bari a baya ba. Nan kuwa ta kira Mamma Jalan ta ce Jalan, kunnen ki nawa? Kunne na biyu kara biyu ki sha labari Mamma na dariya ta ce na kara takwas ma sun zama goma Yawwa to yau dai su Uwa an kai munzali, yanzu zan wanke zanin gadon nan, ke baki gan ta ba abun tausayi duk bakin rashin kunya ya mutu! Mamma ta kashe wayar ta tana cewa Sahura-Sahura ban san yaushe zaki girma ba. A lokacin Haj Jalan ta fadi ta yi wa Ubangiji sujjadar godiya, ta yarda sa idon iyaye yana taimakawa tarbiyar yara ne kawai, amma kiyayewa tana wajen Ubangiji, a yadda Amani ta taso, wa zai mata wannan kyakkyawan zaton? Har digirin zamani ta yi. Surutun Sahura ciwon kai yake kara mata, sai ta ce don Allah don Annabi Baba Sahura na yafe jinyar taki ki je, ni lafiya ta kalau ba abinda ya same ni. Sahura ta kara babbakaro dariya sannan ta ce oho dai, mun ga karshen rashin kunyar Tafisu, da karshen rashin So, kwana daya da zuwa an mannewa bawan Allah an tsotse shi tas!. Sai kuka ya kwacewa Amani, ga damuwar dake ran ta ga bakin cikin da Baba Sahura ke kumsa mata. Ba wata jinya data wuni yi mata sai shakiyanci, da yamma Ummami ta zo ta gan ta a zaune tana shan madarar rakumi data bata, ta daina kukan amma bata yi wata kwalliya ba don haushin Mukhtar take ji sosai. Ummami ta dan zauna suka yi hira da Baba Sahura sannan ta koma sassan ta. Da Mukhy ya dawo daga Dosso gun Ummami ya fara zuwa, yace yana son zai sha tea, ta ce ka je wajen matar ka ta baka mana? Yace Ummami pls, ai na san da ita na ce ki bani din, kada in soma ce mata ina son wani abu, ta ji dadin yi min zancen Sadaka Ummami ta ce to bazan bayar ba, sadaka kuma zan roki Mai kada a baka yanzu, yar mutane na neman zarewa. Yar dariya Mukhy ya yi, ya tashi zai fita, a ran sa ya ce Umh, Ummami bata san Amani ba ne shiyasa take tausaya mata, ai shi kam wannan Sadaka ko baa bashi ba, ya gode da tayin su da aka yi masa, ko babu komai sun sa jiya ya more iya morewa. Yanzu ma da barazanar su zai ci gaba da samun kan Amani ya cigaba da yin yadda yake so, lokacin sa ne. Itama sanda take gaban iyayen ta tana kan tsinin ta na Tafisu wane rashin mutunci ne bata tata masa ba? Ai shi nashi nafila ne, tunda bai hadawa da cin zarafi kuma bai taba alaqanta ta da kama da shegu ba wai don tana da kyau, wannan magana ta dade tana haunting din sa duk da cewa in kyau ne ai sai dai su yi kunnen doki shi da ita. Haske kawai ya fi ta. Ya isa sassan su yana wannan tunanin, ya isa har falon sa yana waya da Kamilu, wanda ya gaya masa su Alhaji sun sauka gida lafiya, yau ga Alhaji a kujerar ofishin sa ta FASKARI INVESTMET (Executive Director) wato Alhaji ya koma office yana dan dogara sanda amma, farin ciki mai tsanani ya kama Mukhy, ya ce da Kamilu duk da haka kada ya dinga barin sa yana ayyuka masu yawa, ya san halin Alhaji sarai, wajen neman kobo. Jin shigowar sa yasa Sahura yi mata sallama, ta ce to Uwa zan je na kwanta, maigida ya dawo ko kula ta bata yi ba don akaifa take ragewa da nail-cut a lokacin. Har dakin ya shigo bayan sun gaisa da`Baba Sahura da ke fita, sannan ya kashe wayar sa ya saka a aljihun sa. Ta daga kai a hankali ta dube shi, sai annuri, cikar zati da kwarjinin mulki ke fita daga fuskar sa maabociyar zati da kamala, ya ji dadin labarin da Kamilu ya bashi na samun lafiyar Alhaji da komawar sa office, Mukhy ya sha rawanin sa fari kal, ya fito a cikakken Diffa-Arab din sa, ya tsaya daga kan ta yana warware rawanin, ya ce, Sweetheart, na dawo me zan samu Maam Amani? Bata yi magana ba, ta cigaba da cutting farcen ta kwarjinin sa da kamshin turaren sa duk sun cika ido da hancin ta, sai ta tuna ta yi alkawarin zama macen kwarai, macen kwarai kuwa tana yi wa miji sannu da zuwa da adawo lafiya. A hankali ta daga sexy eyes din ta ta zube su a kan shi, ta ce, sannu da zuwa Ya Mukhy. Ta mike tana cewa bari in taya ka cire rawanin nan, na ga alama tsayi gare shi, ta shiga taya shi warware rawanin, sai ya ruko kwibin ta, ya rike ta cikin hannayen sa ya dube ta da idanun Rahma har cikin ido. Duk kin rame, a abinda bai fi sati guda ba kacal, me yake damun ki haka Tafisu? Mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki sai ta saki kukan dake cin ran ta a hankali, a sukwane ta fada jikin sa. Mukhy ya samu yadda yake so domin ta rike shi gam tana rawar jiki, tana fadin yau a gaban ka zan tube, ka kalle ni da kyau ka gani ba abinda bani da shi da sauran mata ke da shi, watakila nawa ma ya fi nasu cika, idan nayi hakan zaka fasa karbar sadaka? Mukhy me zai yi banda fashewa da dariya, ya ce By Allah you will be the death of me Amani.. Ya soma sumbatar ta ta koina, don ya samu ya mantar da ita zancen sadaka. Amma bata yi shiru ba, cigaba ta yi da fadin. Wallahi Ya Mukhy da gaske nake na tuba, na tuba na bi Allah na bi ka ba zan sake ba, to ni nace kin min laifine a bani sadaka a kan hakan? Ko shi Mai (Sarki), bai san ma me kika yi min ba, balle ya bani sadaka don ya rama min. Alada ce kawai kyakkyawa ta gidannan yake son ya cikasawa, alada ba addini bace Ya Mukhy, besides yanzu addini ya daina supporting concubinage, irin wannan auren wasu malaman ma yanzu suna fadin bai halatta ba a wannan zamanin, tun da baa yaki balle a samo ganimar bayi. Mukhtar ya kasa hadiye dariyar sa yace Ya Shaikh! Amani kenan, su bayin basu da yaya? Kuma yayan su ba bayi bane? Baki san ana gadar su ba daga iyayen su? Kuma in ban karbi Sadaka ba aure kike so in kara da kuruciya ta mata su cika min kwanya? Ai adalci ne aka yi miki, ta hanyar girmamaki, a baki su a matsayin ababen ikon kisai kin so zasu zo inda nake haka sai kin nemi hutawa zan bukace su. Mukhy ya cigaba sumbatar ta a dokance, yana cigaba cewa, In kina son mu zauna lafiya kada ki sake yi min zancen Sadaka, wallahi na gaji da jin zacen nan, na gaji Amani, ki bar ni in huta. Amani kawai nake so yanzu, amma kina neman haukata min ita, duk kin birkita min Amani ta koma kamar zararriya. Daga haka ya juya akalar hirar tasu zuwa wadda yafi so a yi, wadda ya dawo cikin dokin ta, Amani bata da zabi ban da bin umarnin sa, na barin zancen sadaka da baya so, ba don ta gamsu cewa Mukhtar ya fasa karba ba, tunda kuwa bai furta fasawar da yawun bakin sa ba har yanzu. Sai taji duk kokarin sa na faranta mata rai, ta hanyar nauikan soyayyar sa da sumbar sa mai shiga har kololuwar ran ta yanzu sun daina sanyata nishadi ko irin yanayin da yake saka ta a baya. Ta dai yi hakuri ne ta kyale shi amma yau bata yi kowacce hobbasa ta taya shi. Mukhtar a ran sa ya ce in haka mata ke kin kishiya da dukkan zuciyar su, willing to do everything ga mazajen su don su kada a yi musu ita, da ya baiwa duka maza shawara su kara aure, ko don mata fitinannu irin Amani su shiga taitayin su. Shi kam yau dan gata ne sai yadda ya juya abar sa.. madalla da iyaye masu son cikar farin cikin yayan su irin nasa iyayen. ko babu komai sun samo masa kan Amani yadda baya zato, daga jiya zuwa yau ya mori auren sa har fiye da kima, daga jin zancen sadaka. ***** ***** **** Ummami a bar maganar sadakokin nan, don Allah ni dai Mukhtar na yafe, ban san ba ko can gaba, amma (for now), a bar su, ina tsoron ta kamu da depression. Jiya ni kadai na ga abinda na gani, har cikin barcin ta sambatu take tana zancen sadaka, I was terriby scared a daren jiya, sannan ma dai Ummami ni (shes okay for me), kada ku tara min mata su tsofar da ni da tension din su tun da sauran kuruciya ta, kai Ummami jiya na ga boni! Umami ta yi ta dariya ta ce ka tabbata ta isa? Har tayi yawa Ummami, amma kada ki gaya mata na ce a bar su, bar ni in ta cin albarkacin su. Mukhtar zai kashe ta da dariya, don haka ta wuce toilet ta bar shi a wurin ta san ba komi bane gyaran da ta yi wa Amani ne jiya yake dawainiya da shi. Don haka a wadannan sati hudun, Maina Mukhtar, ya rakashe son ran sa, ya more kuruciyar sa iya morewa, yayin da yar Daddy duk ta zama kamar kazar mayu don rama da rashin nutsuwa, don har zuwa lokacin da bakin sa bai ce mata ya fasa ba. Abin ya zame mata kamar masifa, sabida yadda kullum son Mukhtar karuwa yake a ran ta, haka kishin sa na neman karar da numfashin ta. Duk bayin da aka bata ta kore su ta kawo tsofaffi. Tahirah da Sugrah kawai ta bari. Ta kasa nutsuwa duk da nasihun da Ummami ta ke yi mata kullum, a kan ta fitar da batun kishiyoyi ko sadakoki daga ran ta in tana so ta zauna lafiya da zuciyar ta, ta kuma tsira da lafiyar jiki da kwakwalwar ta. Kusan watan su uku kenan da tarewa a sassan su. Amani ta soma zazzabin dare. Ga wani tashin zuciya na babu gaira babu dalilli da ke uzzura mata. Sai kuma wani babban tashin hankalin da ya same ta yanzu, ba ta son Mukhtar ya kusance ta ko kusa ko alama, kai har kiss dinsa da take mararin ma, wani zubin har take rokon sa yanzu bata so kwata-kwata don dacin da take ji a cikin bakin ta. Komai daci yake yi mata, ta rasa appetite din ta gabadaya. Komai taci bata jin ainahin dandanon sa sai dai ta tura don kada yunwa ta yi mata illa. Allah sarki Amani, ga dai mulki, da jin dadi fiye da wanda ta baro a gida Katsina, ga soyayyar Mukhy ta gama samu yanzu, ga kulawar uwar miji data mahaifin sa, tana kwance ake mata komai sai dai ta wanke goma ta tsoma biyar, ta zama wanke hannu ka taba ko da can ma hakan take gareta, amma duka wannan bai hana a wannan dan tsukin kewar Daddy da Mamma ya dame ta ba, ta daina jin dadin komai, komai ya daina burge ta, amma haka ta yi shiru bata gayawa kowa abunda ke damun ta ba, tana ganin kamar nausea din yana zuwa ne kawai sabida Mukhtar ya uzzura mata. Ba ya bari ta huta yadda ya kamata ko ya bari har sai ta ji marmarin abun kafin ya bukata, duk sanda ya bushi iska kawai sabida yadda Uwar sa ta dage da yi masa gyara na manya ya gama haukata shi, gashi ya sa yanzu har abun ya fita kan ta, bata ko son ya zo kusa da ita. Tun tana jurewa don tana ganin zazzabin ta ne idan ta daina zazzabin zata koma daidai, amma ina! Abu ya ki barin ta, har a daren yau da komai ya fara kankama ta bangaren sa kawai sai ya ji Amani ta ture shi, ta mike ta dirgo kasa, ta hau kwarara amai, kamar zata amayar da yan hanjin ta, duk kyankyamin Mukhy da vomiting amma bai ji kyankyamin na Amani ba, ya dafa bayan ta yana mata sannu, ta koma gefe tana maida numfashi bayan ta gama kakarin aman bakidaya, ya rasa inda zai sa kan sa da damuwa, dama dai yana ta noticing canjin da take samu a kwanakin nan, daga na mood har na behavior, ya ce da safe zaa kira likita ya duba ta, ta ce atafau kada ya fara, ita bata son allura. Ita ta san matsalar ta daya kawai ya daina kusantar ta, in ta samu hakan zata koma daidai. Don haka ta kulla abinda take ganin zai fishshe ta cikin ran ta, don ko bayan ta huta da aman data gama, dan anacan nata bai bar ta ba a daren sai da ya samu yadda yake so. Garin Allah na wayewa Mukhtar na tafiya fada ta sa Sugra ta hau hada mata kayan ta da duk abubuwan da zata bukata, ta ce ta ai mata su dakin Ummamitana zuwa yanzu. Tahirah da wasu kuyangin suka tasa a gaba kaamr wasu body guards din ta sai dakin Ummami. Bazata zauna haka kawai Mukhy ya kashe ta kwanan ta bai kare ba. Ummami na cikin magana da kuyangin ta tana basu umarnin abinda zasu yi yau, don ita ce da girki, Amani ta shige su da sauri, cikin takun ta mai kama da na macen Dawisu, ta shige can kuryar dakin Ummami ta haye gadon ta ta kudunduna don sanyi take ji sosai yana shigar ta, ta cigaba da barcin ta cikin kwanciyar hankali, tana fadi a ran ta (at last she is safe). Ummami bata tashe ta ba har hantsi ya dubi ludayi, ta gaji da barcin ta tashi don kan ta, ta kuma tashi ne da wata azababbiyar yunwa kamar ta ci babu, aka yi saa Ummami na dakin lokacin da ta tashin, tana ta zabga hamma irin ta yashewar ciki, Ummami ta sa ta a gaba ta zuba mata ido tana mamakin kamannin su da Jalan, ita Ummami din da Jalan ba wani kama suke yi ba, sai na dirin jiki, amma Amani da Jalan kamar an tsaga kara, musamman in ta tuna kuruciyar Jalan din da yammatancin ta. Tuwo, Ummami Tuwo zan ci!. Ta fada tana hamma tana ture bargon jikin ta, sakamakon zufa da ke karyo mata. Alamar zazzabi-zazzabin data tashi da shi yau ya sauka. Dama kina cin Tuwo? Kika ce min ke sam ba kya son Tuwo Ummami ta tambaya cikin mamaki wallahi shi nake so yanzu, kuma na Dawa, miyar kuka, irin wanda Ya Mukhy ya saya min a Lagos da zamu wuce Saliyo Ummami ta yi dan jim, kafin ta ce to bari in sa a tuka yanzu, ai bazaa rasa Dawar a kitchen ba, ina yawan tukawa Mai ita. Pls Ummami, a saka daddawa da yawa tayi doyi sosai miyar. Ummami ta juyo tana kallon ta, kallo na kurullah sanan ta yimurmushi ta ce to bari a yi sauri, Allah ya sa akwai daddawar. Amma maimakon tasa kuyangin ta su yi mata da kan ta ta shiga kitchen ta yi mata kyakkyawan tukin tuwon dawa, miyar kuka ta zabga mata daddawa da naman Dawisu, tana yi tana adduar Allah yasa abinda take zargi ne, Allah yasa ita zata fara yi wa Mai Diffa wannan albishir din. Har yamma lis, tana kwance kamar ruwa a gadon Ummami, tayi dai-dai da kafafu an ware mata AC, sallah ce kawai ke tada ita. Ga aladar sa kullum sai ya fara zuwa gun Ummami kafin ya wuce part din su, in ya dawo daga fada, haka in zai shiga fada ma sai ya fara zuwa wajen ta sun gaisa da safe, sun yi hira ta da da mahaifi, sannan ya wuce fada. Yau ma da ya dawo sai ya zarce sassan Ummami, domin yayi mata sai da safe, sai ya tarar da ita tare da Hajiya Tarha watau kishiyar ta, suna magana, Saadiyya Yayar sa ce ta haihu, wato yar wajen Haj. Tarha, ana so a je Guinea da yawa don a yi mata barka, shine ta zo tambayar iznin Ummami ko zaa tafi har da matar Maina? A bisa rokon ita Saadiyya din, don Gimbiya Sayluba ma wato babbar Yayar su zata je. Ummami ta ce Eh toh, bana ce ba, amma bana jin Maina zai bar ta, don bata jin dadi kwana biyun nan. Sai da gaban Haj. Tarha yayi mugun faduwa, don dama abinda take son tabbatarwa kenan, don an kai mata gulmar matar Maina har ta samu rabo. Ta yi amai a kan hanyar ta ta wucewa sassanta kuyangin Tarha sun gani. In banda haka ina amaryar da ko shekara bata rufa ba a dakin ta ba ina tafiya wani barkar haihuwa har kasar Guinea? Ta dan sukurkuce tana fadin ai toh, abinda na ji gaskiya ne kenan? Har ta yi tuntube daga zuwa? Ummami sai da gaban ta ya fadi, wato baka taba raba gidan sarauta da gulma da daukar zance, ko ita da ke tare da su dare da rana zargi take, bata tabbatar ba, zargin ma yau ta fara shi, amma ashe har zance ya cika gida har je kunnen kishiyoyin ta? Tsoron ta Allah tsoron ta kada Sarki ya sa abinda Maina zai haifa yayi irin rayuwar da yasa Maina yayi, wato tashi ba tare da kulawar iyaye ba, wai don nema masa tsari daga magauta. Sai ta shiga adduar ita kam gara in ma cikin ne da Amani, to Allah yasa ta haife diya mace, da dai ta haifi namiji yayi irin rayuwar da mahaifin sa yayi. Menene tuntube kuma ni ya su? In ji Ummami, har addua take kada Amani ta fito ko tayi motsi daga kuryar daki don bata so ma Tarha ta gan ta. Sai ga Mukhtar ya shigo dakin da sallama, daidai Ummami ta rako Tarha zata tafi, tana gaya mata tuntube yana nufin an samo rabo. Sai Ummami ta kira kariyar Allah a zuciyar ta, ta hanyar cewa; UIzu bikalimatullahi tammah, nimal shaitanin wa hammah, wa min kulli ainin lammah. Sannan ta ce wa Tarha ni dai kin ganni ban sani ba!. Ya gaida Haj. Tarha dake fita, sannan ta wuce. Ya zauna a kujerar da Tarha ta tashi yana cewa, Ummami ki yi hankali da ita fa, ni bana son kirkin Haj. Tarha sam, duk kudin goro nake musu ita da Haj. Ummu Aymana, ban yarda da ita ba, na bi kirki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta. Ummami ta yi dariya ta ce lallai Maina ka ji Hausa a Katsina, kada ka damu, Tarha ba irin Ummu Aymana bace, akwai dai kishi wanda dole ne a tsakanin mataye da ke auren miji guda, amma bata da mugun nufi a kai na, sannan tsakani na da kowa a gidannan hasbunallahu waniimal wakeel. Bana tsoron kowa sai Allah, kai dai ka rike Allah, sannan ka rike sallah, ka kuma rike addinin ka da imanin ka, wallahi kai da kowa sai gani sai hange. Mukhtar ya gamsu da bayanin mahaifiyar sa, ya zauna dab da ita kamar zai shige cikin ta, yana fadin na gaji da yawa Ummami, mulkin alumma ba abu ne mai sauki ba, ina matukar ganin kokarin Mai, bawan Allah! Ni kuma yanzu ga matar gidan can kuma ba lafiya na kasa gane kan ta. Ummami ta sakar masa harara ta ce fita ka bani wuri kada surutun ka ya tashe ta, da kyar ta samu barci Mukhy ya ce wa kenan? Tace ita wadda kake zance barci take yi? Kuma a cikin dakin ki? Mukhy ya tambaya da mamaki. Ta ce eh mana, me ye da dakin nawa da bazaayi barci a cikin sa ba? Ba haka nake nufi ba Ummami? Ita bata da daki ko me? Ummami ta mike tsaye ganin ya fara fusata, ta kwantar da murya ta ce Ka kyaleta don Allah Maina, har kayan ta ta hado ta dawo nan, na lura bed rest take so ta yi, duk da dai batace min komai ba. Mukhtar sai ya mike tsaye yana cewa yau nake jin abinda ba zai yiwu ba Ummami ta ce ya yiwu ya gama, baka ganin bata da lafiya ne? Na tabbata matsanta mata kake Ummami ko suma take tana farfadowa bazan iya kwana ni kadai ba. Umami ta ga ran sa ya soma baci, sai ta ce to Tarha da take so a tafi Guinea da ita wajen Saadiya ashe bazaka bari ba? Ya ce what! irin yadda ya tsorata abun saida ya baiwa Ummami dariya. Kai tsaye ya wuce dakin Ummami ita kuma sai ta dauki mayafin ta ta bar musu dakin kada a yi abun kunya a gaban ta. Tana jin duk abinda suke fada domin lomomin tuwo take kaiwa bakin ta a lokacin, wani na bin wani, Mukhy ya bi abinda ta ke ci da kallo ya ga tuwon dawa ne da yaji kanwa da wata bakar miya, duk dakin ya cika da warin daddawa, yana toshe hanci ya ce. Halan AMANIE baki da lafiya? Halan something is fishy with you? Whats this annoying smell for? Amani ta ajiye kwanon tuwon, ta hau side hannu, sannan ta daga robar ruwa ta kai bakin ta ta shanye tas, kamar Giwa, ta daddage ta saki gyatsa mai ban haushi, Mukhy ya rasa inda zai sa kan sa da wannan sabuwar Amanin mai matukar ban haushi da takaici, yaushe rabon yayi magana ta yi masa banza! Tashi kiyi brush mu tafi muyi wanka mu kwanta haka don Allah, na debo gajiya tausa nake so kimin yanzun nan, kin ji Amani-Amani na? Ta russunar da idonta kasa ta ce ka yi hakuri Ya mukhy, ba inda zani gaskiya, na dawo nan kenan. Mukhtar ya soma shaqa, sai ya juya kawai yana cewa to babu laifi, bari in je in yi changing, sai in dawo da filo na nan, mu kwana tare a gadon nata. Ta dauka wasa yake yi, amma ba jimawa sai gashi ya dawo cikin fararen kayan barci riga da wando masu kauri a jikin sa samfurin Blooming Dales, yayi wanka ya kara yin fresh da shi, har da turaren sa da ya san yana jan hankalin ta da shi wato Azzaro Visit ya fesa, ya taje sumar kan sa tayi lub gwanin shaawa duk dan ya ja hankalin Hajiyar tasa ta ta yarda ta bi shi, yana shigowa ya jefa filon a gadon Ummami, ya haye yayi kwanciyar sa yana danne-danne a wayar hannun sa. Amma sabanin baya da hakan ke tasiri a tare da ita, ta isa gare shi da kan ta, ta ce Ya Mukhy me kake so? Shi kuma yace message ko Amani. Don a irin wannan yanayin ko Mukhy bai yi magana ba ta san yana gayyatar ta ne, daga messaging bata sanin sanda yake zarcewa. Amma sabanin sauran renakun na baya, yau matukar haushi Mukhy ya bata. Ta zaro idanun ta waje tana fadin. Ya Mukhy! Ka rufa min asiri ka tashi, gadon Ummami ne fa ya ce ko na Mamma Jalan ne, in baki tashi mun tafi ba nima a kai zan kwana, ta yaya karfi da yaji kin hana min karbar kwarkwara yanzu zaki bullo da wannan yaren da ban gane masa ba? Kunya da tsoron kada Ummami ta zo ta gan shi kwance a gadon ta duk ya addabe ta, ta shiga rokon sa Allah Annabi ya tashi, kada Ummami ta ce basu da sauran kwalli a idanun su. To ki tashi mu tafi, tunda ke kina da sauran kwallin a idon, sarkin masu kunyar suruka, ba kuma rokon ki nake ba umarni ne ki tashi mu tafi. Kamar ta fashe da kuka ta ce wallahi na gaji, Allah ya gani yanzu bana so, kai abinka babu hutu sam? Ko inji wani zubin ai yana bukatar hutu balle mutum, ni yanzu ba sadakoki biyu ba, in ma su goma da mata uku zaka karo, bisimillah, ga fili mai doki, don kaga bana so ne kake amfani da hakan kana uzzura min, to na baka dama yanzu Ya Mukhy ka karbi Sadakoki as much as you like. Mukhy yayi sakale! Daga kwance yana jin ta, yana mamakin ta, yarinya kamar mai hawainiya, rana daya daga yin amai duk tabi ta birkice tana masa tutsu, in ya ce gaban sa bai fadi ba da wadannan kalaman nata ba ya yi karya, don kamar ta daina son nasa kenan. Kenan ta daina damuwa da shi ko watanni biyar basu rufa suna amarcin ba. Shi kuma yanzu ne ma ya fara so da dokin Amani ta kasance tare da shi, sakamakon niima irin ta mace mai yaron ciki da ta fara saukar mata. Murya na dan rawa, Mukhy ya ce ki yarda mu tafi, I will not force you kin sani, I will never force a woman to sleep with me, ni ba wasu Sadakoki da nake so yanzu, ONLY AMANI- I LOVE! Ki tambayi Ummami ki ji tuntuni na ce ta gayawa Mai bana so, bana bukata, matata AMINA ta ishe ni rayuwar duniya, domin ta fi min goman su. Hawaye take yi sosai, amma kalaman sa na tasiri sosai a ran ta, sun sa ta jin kan ta ya kumbura, ta ji ta a Tafiun ta, kamar tana yawo a kan gajimare. Ni bana so ne kana zuwa inda nake yanzu, Kiss din ma dana ke cewa ina so, kana min yanga a kai to yanzu bana so, barci kawai nake so in yi ta yi, kada a tashe ni! Ta fada da iyakacin gaskiyar ta, tana kaucewa kaifin idanun sa. Yau Mukhtar yana ganin ikon Allah, da kyar ya ce Ni Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, na yi alkawarin bazan kasance da mata ta Amani a daren yau ba, sai bisa yarda da amincewar ta. Amma ai ina gani kana toshe hanci da ka shigo, wato doyi nake yi ko? Ta kara fashewa da sabon kuka. Ni ban ce kina doyi ba, dakin ne ina shigowa naji yana wani wari-wari da ban saba ji ba tuwo na ne fa, kuma ni yanzu shine abinci na, kada in je gidan ka ka ce kuma na kai maka wari gida kuma to yanzu saboda Allah Amani, me kike nufi? A wane dalili ina da mata ta a cikin gida na zan yi kwanan gwauranci? Ai ko ban ce ban yafe ba, Allah zai saka mini sau sabain, tun da na lallashe ki na kuma yi miki duk alkawarin da zan iya kin ki ji. Ya mike yana cewa. Since you insist, do as you wish. Ya dauka ganin bacin da ran sa ya yi muraran, zai saka ta biyo shi, amma har dare ya tsala bata ba alamar taita a lokacin ma ta kai Zaria a barcin ta har da minshari na kwanciyar hankali da hutu. Kwanan kadaici da damuwa yayi, sai yanzu ya san yayi mugun sabo da Amani yadda baya zato, kuma ta shiga ran sa yadda baya tsammani. Bai san yana son Amani har haka ba, bai san soyayyar da yake mata ta yi wannan zurfin ba, sai yau da duk inda ya mirgina babu ita sai filin ta a gadon barcin su, ya rasa kulawar ta a gefen sa, da nacin ta na son yayi kissing din ta, ko saukar numfashin ta a kunnen sa yau bai samu ba, wanda hakan yasa Mukhy yayi kwanan wahala ba yar kadan ba. Yayin da Amani tayi barcin ta cikin salama, don koda Ummami ta dawo dakin bata ko tashe ta ba, don ta gane da gaske tana bukatar hutun. **** **** **** Washegari da ya zo gaida Ummami, ya maka bakin glass don boye kumburin idanun sa da launi da suka canza irin na rashin barci, yana ta cin magani, kuma har suka gama hirar da zasu yi da Ummami bai yi korafi akan Amani ba, ya barwa ran sa, mai nufin ya yi fushi da ita. Ita Ummami ce da kanta ta fahimci hakan, don haka sai ita ce da kan ta ta dauko zancen Amani, inda ta ce masa cikin lallashi. Maina sai ka yi hakuri da Amani yanzu, a lokacin da mace ke da yaron ciki ta kan samu sauye-sauye a jikin ta, wani zubin har da na halaye da dabiu, sakamakon halittar da ubangiji ke yi a mahaifar ta. Wata kuma tsanar mijin take gabadaya, ta ji bata so ya zo inda take, wata kuma kamshin jikin sa ma bata so sam. Abun daban-daban ne (from one woman to another), ka yi fatan Allah ya raba su lafiya kawai, kai kuma ka jure na dan lokaci ne, in kuma a kawo sadakokin toh? Sai in yi wa Mai Diffa din magana. Mukhy ya rasa a yanayin da kwakwalwar sa ta karbi zancen Ummami, idan ya fahimta daidai, to Amani juna biyu gare ta kenan shiyasa take masa tutsu? Allah da girma yake. Wannan wane irin rantsatstsen rabo ne na gaggawa haka daga Allah! Burin Alhaji Usman zai cika, cikin dan lokaci kalilan na hada zuria tare da shi, Ummami da Mai zasu samu jikoki daga gare shi tun suna raye da sauran karfin su. Tsakanin Hon. Usman da Mai Diffa, bai san wa zai fi farin ciki da wannan kyakkyawan albishir din ba. allah abin godiya. A lokacin Maina ji ya yi son Amani na ninkuwa a ran sa, kamar yau ne ma ya fara koyon son nata. Bacin ran ta da ya kwana da shi yana tafiya daga makogaron sa yana narkewa. Mukhy, ya lumshe idanun sa a hankali, ya samu kan sa yana tambayar Ummami ko sai zuwa yaushe ne Amani zata iya koma masa daidai ta daina sababbin dabiun ta da ke ci masa rai haka? Dariya Ummami ta yi, ta ce ya danganta, mai yiyuwuwa in cikin ya cika watanni hudu ko biyar. Mukhy ya mike tsaye cikin daburcewa ya na cewa. Ummami, ko dai wata kasar zamu tafi ta ga kwararren likita? Ummami ta ce babu inda zaka dauke ta da karamin ciki jirgi ya jijjige shi, don babu wani likita da zai mata maganin wadannan abubuwan sai lokacin tafiyar su ya yi, babu inda zaku, har sai Allah ya sauketa lafiya don ga dukkan alamu, cikin Amani mai tsirfa ne, in ka dauke ta kuka tafi wani wurin ina zaka nemo mata ire-iren abubuwan da take son ci din nan? Suka saki wannan hirar suka cigaba da wata hirar daban, amma dai Mukhy ya saki fuska ba kamar sanda ya shigo ba. Daga bisani Amani ta fito falon, ya bita da kallo tana zama daga kasan kafafun Ummami, Mukhy ji yayi kamar ya ciro cikin daga jikin ta ya ajiye a nasa ko Amani ta samu lafiya su cigaba da rayuwar su mai nagarta yadda suka saba. Ummami sai ta tashi ta fita cikin gida ta bar su a falon. A sanyaye ta ce, Ya Mukhy ina kwana? An tashi lafiya? Ga dukkan mamakin sa sai ya ji baya jin haushin ta yanzu, sai tausayi, ya tausasa murya ya mika mata hannu, yana mata kallon rahma da kulawa, yace ta shi mu tafi kawai, duk abinda baki so na daina, in ma ya kama mu raba daki sai mu raba, amma (for now) ban iya zama a gidan nan ni kadai. Sakamakon yadda ya sa idanun sa cikin nata, ya kuma tausasa harshe sannan ya bata hannu, sai ta kasa tankwabe tasirin wannan soyayyar da sadaukarwar, tunda har ya yarda in ma daki zaa raba a raba, shi dai kawai ta kasance cikin gidan sa, don gani tayi ya fi ta zama maraya a kwana daya kacal, duk da gashi a dakin mahaifiyar sa. Sai kawai ta juya ta soma hado kayan ta da ta kwaso, ta fito da su rie da jakar tana kiran Tahirah, Tahira da dam aba wani nisa suka yi ba suna falon da suke zama su jira ta ta zo da sauri ta amsa ta yi gaba da su, Mukhy ya saka ta a gaba suka kama hanyar komawa gidan su. Baba Sahura ma yau sai komawa tayi sassan Ummami da zama, da ta zo ta tarar sun rufe sassan su da safiyar Allah. Su Sugrah ma duk sai wajen Ummami suka koma gabadayan su, wai Maina da kan sa ya ce musu su tafi sai ta neme su. **** ***** ***** Umami ta ce Allah ya taimaki Mai Diffa, na zo da kyakkyawan albishir. Sarki ya tattaro hankalin sa ya baiwa Mowa, ya ce ai ke fara ce mai farar aniya da farin albishir kullum, kullum alkhairi ake ji a bakin ki, fadi ina sauraron ki”. Ummami ta yi murmushi ta ce cikin ikon Allah ina kyautata zaton Maina ya samu rabo. Maana maidakin sa na da juna biyu. Sai Mai Diffa ya dan tsura mata ido, kafin kawai ta ga Sarkin Diffa Maimartaba Issouffou Massaoudou, ya kai goshin sa kasa ya yi sujjadah, dama a zaune yake a kan darduma. Sarki ya yi wa Allah godiya, ya ce zai sa a fara sadaqa da addua ta musamman a kan Allah ya sauke ta lafiya. Tun daga wannan ranar nan ake ririta Amani a gidan sarautar Diffa, aka kara mata hadimai a sassan ta, aka hana ta aikin komai sai dai ayi ta tuka mata tuwon dawa tana ci da naman zabuwa ko na dawisu a ciki, tayi wani irin bulbul tayi kumatu sumul irin na matan sarakai, Amani an samu mulkar mutane yadda ake so, amma ita da miji ko oho don ko daki sun daina hadawa. Iyakaci da safe ya zo ya duba ta sannan ya dan sumbace ta ya fita fada, yana fadawa ran sa duk in the process na zama Uba ne, har ramewa Mukhy yayi a kwanakin nan, don ta ce yana matsowa kusa da ita nausea din yake zuwa mata. In ka ga Maina wannan lokacin har duhu yayi, amma kwarai yana son ganin an haife jikan Ummami da Hon. Usman lafiya, shi yasa yake daurewa da tsirfar Amani, yake biye mata don dai ta zauna a sassan ta kusa da shi, amma me? Yau dai ta kawo shi makura, ta kawo shi bango, don ya lura abin nata har da mugunta kuma amma cike take da koshin lafiya da kuzari. Misalin karfe bakwai na safiyar ranar da ya fito daga wanka ya ganta a dakin sa yau, ta gyagije kamar ba itaba ta ci kwalliya da wani yadin karen miski na kasar Senegal da aka yi wa dinki Senegalese, rabon ta da shigowa turakar sa har ya manta, wai ta zo su gaisa kafin ya fita, ya fito wanka ya tadda ta zaune gefen gadon sa tana waya da Alhaji ne ko Maman ta bai gane ba, tana ta smiling, kai ga dukkan alamu dai da Mamma Jalan take wayar, saboda rashin kunya irin na Amani ji yayi tana gaya mata wai har ta fara jin motsi da mutsu-mutsu a cikin ta, bai ji me Mamma ta ce ba dai ya ga ta hau murna tana cewa don Allah a kawo ta da wuri. Tana ajiye wayar ta daga kai, sai ta ga Mukhy yana mata kallon nan nasa da ita kadai ta san fassarar sa, ya mika mata hannu daga tsayen da yake, Amani ta sunkuyar da kai ta rufe ido, Mukhtar ya janyo ta a hankali ya rungume ta ya cire wayar daga hannun ta, yana rada mata cikin kunnen ta isnt this punishment enough? Ki ji tausayi na Amani, na daina barazana da sadaka, nayi hakuri for quite this time amma Its a promise it will not be hurting, I will treat everything in a soothing and romantic manner, and I will make sure ban jigata baby na ba, Ive tried for you Amani, for your happiness I truly tried kin sani, wata daya ba kwana daya bane, kada abun ya koma da daukar hakki na kuma. Da wannan Mukhy ya samu ya kalallame Amani har y karbi duk abinda yake so. Ta ce a ran ta ashe dama can ya iya lallashi girman kan sa ne ke hana shi sai yanzu da ya aga kwal uwar daka. Duk ya bata tausayi ya. Ta yarda yayi hakurin kamar yadda bata zata ba for her own well-being. Amani ta daure yau ta amshi Mukhy din ta a safiyar yau da dukkan jaruntakar ta, suka jima suna farantawa juna rai, kuma yayi kokari ya cika alkawarin da ya daukar mata, ya biyar da ita cikin sassaukan yanayi na soyayya mai shiga rai. Yau gashi har cikin yayi watanni hudu amma Amani bata bar feleke na masu yaron ciki ba, tun bayan wancan encounter din nasu bata sake yarda da shi ba, kullum jiya I yau, cewa take kamshin jikin sa nausea yake saka mata. Yau ma dai Mukhtar tura ta kai bango, a daren yayi shirin barci ya shigo dakin ta ya tarar tana ta cin gyada dafaffiya, ga cikin ya fara bayyana sosai ta cikin rigar barcin ta ya mata kyau kuma, abin ki da doguwar mace, kan ta babu kallabi ta sha kananan kitson da Sugrah ta yi mata gwanin shaawa. Yayi sallama ta amsa, ya zauna gefen gadon ta ita kuma tana daga zaune a kan tumtum a kasa, ya ce ina Baba Sahura ko har ta kwanta? Yanzu ta wuce, bayan ta kawo min gyada to amma Amani cin komai hayau- hayau haka, ba kya tunanin zai lalata miki ciki? Komai kika samu sai kin ci, sai kace Kura, ni kam wannan Baby ya ya kake so in yi ne? Baka tausayi na sam. Gabadaya ka canza min my real Amani, daga yar gayun Tafisun ta zuwa typical, local, Amani. Anyway Alhamdullah alaa kulli haal, with your arrival to the esteemed royal family. You My dear. the incoming PRINCE of DIFFA!. Ta saki wani lallausar murmushi wanda ya taho from ear to ear, kafin ta ce cikin zolaya don tsaf ta gama gano shi, kana son wani abu ne Ya Mukhy? Ya Harare ta wata irin harara mai cike da soyayya sannan ya ce cikin gatse shima, Aah, sabon kitson nazo gani, zuciyar ta daya ta ce to jeka zan kwanta, yau bana son yawan tashi daga zaunen nan da nake, na dauka tea kake so dama. Haushi da takaici ya kama Mukhy, ya ce Yau Amani ni kike kora ko? Ko fa turare na ban shafa ba duk sabida ke? Na yi rantsuwa da Allah yau ko ki sallama ko gobe a kawo Sa-dakokin nan, ina dalili? A kan ki a ka fara ciki? Wannan izaya fa ta ishe ni. Yadda Mukhy ya fitittike yana fadan, ta san da gaske ta kawo shi bango, ta kuma san ya kwatanta mata adalci yadda bata zato, duka daga samun cikin ta zuwa yanzu sau nawa ta kasance dashi bai fi a kirga ba, ita ma kuma shakiyanci ne ta fara kewar sa sosai a kwanakin nan, duk wadancan abubuwan sun sake ta, don cikin har ya shiga watanni na biyar yanzu, duk abubuwan da take ji sun lafa tuntuni, don haka yana mika mata hannu ta kama ba musu, sai ya sa karfi ya ciccibe ta ya daga ta a kan hannayen sa zuwa main turakar sa. Amani ta amincewa ran ta in sha Allahu yau zata faranta ma Mukhy irin yadda bata taba yi masa ba a rayuwar auren su. You add weight, more weight, Oh! Koda yake ba dole ki kara nauyi ba, bayan girman Baby ina jin daga samun cikin nan zuwa yanzu kin ci buhun Dawa da bokitin daddawa, Zabbi hamsin, Dawisu hamsin, ni kuma na ci ukubar da bana yiwa kai na fatan sake afkuwar ta. The whole night for Mukhy!!! **** **** **** C ikin Amani na da watanni takwas yanzu, ba abinda Ummami take sai shirin tarbar haihuwar ta, duk abinda ya dace a tanada hatta feeder din jariri sun tanade shi, wasu kayan baby da yawa daga Guinea Saadiyya ta aikowa Ummami don tana shiri da Mukhy sosai. Sau biyu yana zuwa kasar Guinea duba ta da bata da lafiya. Haka Yayar shi Sayluba ma ya je Tahoa sabida sada zumunci da ita. A wannan hutun ne aka kawo mata Fajur, hutu, zata zauna har sai ta haihu, a bakin Fajur ta ji wani labari da ya gigitata, wai Mamma Jalan ma cikin ta ya tsufa. A gigice Amani ta kira Mamma tana son tabbbatar da abinda ta ji daga kanwar tata, Haj. Jalan ta rasa inda zata tsoma ran ta don kunya sai ta hau Amani da fada tana cewa ni abokiyar wasanki ce ko Amani? Don kin ga tsayin mu daya girman mu daya ko? Shikyasa kika maida ni saar ki. A shekaru na ai na wuce haihuwa yanzu, ki zauna Fajur tana gaya miki abinda bazai yiwu ba. Ita kuwa Fajur tayi rantsuwa ta maya cewa cikin Mamma yanzu yafi nata girma, kuma kusan kullum sai ta je asibiti awo. Amani sai ta kira Alhaji da kan sa. Daddy da gaske ne? mamma zata baima su Fajur kanne? Hawayen farin ciki suka tsirgowa Alhaji Usman Faskari na godiya ga Allah. Ya ce da gaske ne Tafisu, da gaske ne! Uwa sai ta saka kuka don dadi. A halin farin ciki dana bakin ciki duka, Uwar su Alhaji ta fi gane ta yi kuka. Amani har katon Sa da rago tasa aka kayar, ta rabar da shi sadaqa ga bayin gidan ta, tana mai taya Daddyn ta godiya ga Allah, da adduar ita da Mamma Jalan duka, Allah ya sauke su lafiya cikin koshin lafiya. **** **** **** EPILOGUE