AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 41. 📖🖋️ ________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala. Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa suke kinyi dai-dai wallahi". Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci takeyi" . Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala. Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda zanyi" . Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita Yana kokarin Kiran waya. Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa". Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa mutum suna". Ta taso tana karbar tabarmin. "Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da sanyin jiki". Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji kamshin yayi min Dadi". "Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita". Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar. A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki. Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?. Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki da izinin Allah". Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita. "Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi". Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron. "Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa" 'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi". "Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin kauda Kai zakiçi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba". Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba. Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata". "Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida". Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata". Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata. "Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi". "Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba" Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi idan Kaya ne". Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin. Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka ringa shigowa. Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta ta saka ta fice daga gidan. Ba Bata lokaci tana fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka Kaini". "Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa". "Muje Zan baka kudin drop din". Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwanta ba sai da taga sunyi nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yasa na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba ta Zama Masai" Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi. Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin sunyi over dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?" Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare". "Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka". Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin". Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin dinsa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na sallami gidan sai na Kara fitowa". *********** Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkuna uku har da adudu biyu. Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da Nan Rukayya ta Fara share hawaye. Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun shigo?" "Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake ganinta ba". "Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota". "To mommy". Ta fada sukayi waje su uku. Hajiyar makwarari kuwa cewa take "Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka tafi". Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da zatabi wasu mutane". "Ungo Nan". Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken babu it's Babu dalilinta komai Kama da Zahra Babu. Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa. Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma harya Gama secondary school dinsa. A tsakar gida ya samu su mommy anyi cirko-cirko. "Gani mommy lafiya na ganku haka?". Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko alamarta". Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?" "Allahu A'alam, da farko abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace Bari na Kira ka". "Ok, Bari naje Nan Ina zuwa" Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?. Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi, har ya juya sai wani Mai sayar da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar nan ya nuna hanyar gidan shatema. Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya hankali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa Haseena waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane" Jiki ba kwari ya koma ciki.. ***** ***** ***** Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa". Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki. "Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?" "Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin". "Allah sarki ko kawu Musa?" "Shine Ashe kin sanshi". Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne".. "Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin". Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida. Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa. Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH Page 42. _______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice. Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga". "Yanzu ya za'ayi kenan?" Rukayya ta tambaya. "Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba. Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take. Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?" Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta. Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare. A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere yasa Fateeha ta gane da matsala. "Wai menene?" Ta fada cikin damuwa. "Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan". Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce". Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta". Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta. "Ka Kira ka fada masa?" Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba". *** *** *** *** Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?" Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya". "Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya". Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo" Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan". "Eh zamuzo Aunty zahra". Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana cike da tunani barkatai a zuciyar ta. Tana shiga jakar hannunta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi. Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata dasu ne. Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar tare da sallama. "Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". "Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba". "Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta fita ba tare suke da amininsa da kanwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare". Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan. "Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta nasan ba lafiya ba Ashe garin sukazo ta kawo min ziyara". Jim Ammah tayi tana jinjina lamarin. "Anya kuwa ki dai saka Mata Ido zuwa safe kome ke nan sai ki fada min idan anzo daukarta to da sanin mijin tazo idan Kuma tace zata tafi ki hanata ki fada min na gode kwarai Allah yayi Mana jagora ya Raya Mana zuri'a". "Allahumma Amin". Sukayi sallama. Zuciyar Ammah sai bugawa takeyi a hankali ta furta "meke Nan Kuma? Ni Asma'u Allah ka taimaki 'yar marainiyar Allah, matsaloli daga an toshe wannan sai waccen ta bulle Allah yayi Mana maganin wannan matsaloli yanzu kuma ko menene damuwar datasa ta tsallake tabar inda suke gashi ta Kama wayar ta rufe Dan ma kada a San inda take,ai kuwa zamu gauraya bazan dauki shashanci ba". Ta hada duk kayan ta zuba a ledar da aka kawosu ta fice daga dakin ta nufi dakin Abban Yara tunda ita keda girki. Saida Umman sajida tayi wanka tayi sallah sannan ta fito har lokacin suna falon da yaran direct dining ta nufa taci abinci sannan ta dawo falon. Gaisheta zahra ta Karayi tana tambayar ya Mai jikin, Dasu Baffa. Sun dauki lokaci suna hira kafin Ummar tace "Wai daga Ina kikazo ne daga can Azaren ne ko Kuma kinzo nan garin ne?" Shiru zahrar tayi kafin tace "ganin likita nazo akan wannan ciwon marar da bakeyi duk wata". "Ikon Allah kuma ke kadai Kika taho ganin likitan kamar marar gata". "A'a bani kadai nazo ba tare da Aunty Zilai Mai aikin Ammah mukazo tana can a Nasarawa G.R.A". "Ok, to mryasa baku taho tare ba Nan din". Shiru tayi Bata ce komai ba, ganin da Yara yasa itama ummar tabar zancen. Kafin kowa ya tashi Zahra ta tashi tana fadin "Umma Bari naje ba kwanta barci nakeji" "To Allah ya tashemu lafiya. Basu Dade ba Suma suka shige daki Daman duk sun gaji. Lokacin da Ammah ta shiga dakin Abban samun Mama tayi kane -kane tana ta zuba zance da kudi a hannunta masu Dan yawa da gani a gurin Abban ta Karba, cikin alamun rashin gaskiya mamar ta Fara fadin. "Aina leka parlourn ki naji Shiru nayi zaton kina Nan wallahi Ashe Baki shigo ba" Fuska ba annuri Ammah tace. "Eh ban shigo ba idan kin gama na dawo ta juya har Takai kofar ficewa Abban yayi gyaran murya Yana fadin "dawo ki zauna Ina Kuma Zaki ita ta tashi ta tafi tunda ta gama abinda ya kawo ta" Jiki ba kwari Mama ta tashi tana fadin "ai Kam na Gama Allah ya tashemu lafiya nagode Allah ya Kara arziki". Ta nufi inda Ammah ke tsaye tana fadin "mu kwana lafiya ki tayani yiwa Abban yara godiyar abin arzikin Daya bawa Najjahi na kudin registration". "Masha Allah! An gode Allah ya bada sa'a". Ta fada fuskar ta Babu walwala ko alama, da gaske ta kule Abun Yana so ya Zama rainin hankali tayi noticing dinta duk ranar girkinta sai ta dunga Karakaina a part din Abban Amma idan tasan wata ai Bata San wata ba. Dawowa tayi ta zauna kusa dashi "meya Bata Miki Rai ne Kika juya Zaki bar dakin?" "Ba komai". Ta Bashi amsar in short. Haka Nan yabar zancen badan ya gamsu da abinda ya fada ba. "Neman izinika na shigo zanje Kano gobe in Sha Allah".. Saida ya Kare Mata kallo tsab sannan yace. "me akeyi a kanon da zakije?" Kai ta girgiza ba komai zanje barka ne na yaron nan Sameer ranar da yazo daukar su Zahra yake fadawa magaji anyi Masa haihuwa an samu takwaran mijin Zahra". "Kai Masha Allah, ai ban sani ba da nayi Masa barka ranar da yazo". Tashi tayi zata fice Abban ya mayar da ita "Wai me yake faruwa ne Naga ranki a bace tun shigowar ki". "Ba komai zanje na dawo ne yanzu in Sha Allah". Ta Mike ta nufi kifar ficewa, haka Nan yayi Shiru badan ya yarda da ba yasan da abinda yake damunta taqi fada Masa ne kawai". Ammah na shiga part dinta ta Kirawo Abdul Hakeem, lokacin Yana kofar masallaci tare da Habib. A parlour ya samu Ammar ta zuba tagumi. Saida yayi sallama biyu sannan taji. "Wa'alaika Salam". Ta fada tana kallon Abdul Hakeem din, kusa da ita ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah Ina sallama bakya jina?" Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "yanzu ba dadewa Umman Sajida ta kirani waiga zahra taje Mata zata kwana a can Kuma ita kadai ba tare da zilai ba, na Kira zilan tace min tun fitar safe Basu dawo ba har dazun, ka Kira Sameer kaji shin yasan da tafiyar ko Kuma wani Abu ya faru tayi musu yqji nasan halin kayana zatayi abinda yafi haka ma in dai zahra ce, Dan haka ka kwana da Shirin Kano sakko zamuyi ko Abban KU ban fada Masa wannan maganar ba ina tsoron ta fito duk da nasan ba lallai ta fito din ba amma sha'anin mace da miji sai Allah" "Allah ya rufa asiri". Abdul Hakeem ya fada Yana Kiran Sameer duk da lokacin ya ja Sha Daya ta gota. Ringing Daya saneer ya daga kafin Abdul Hakeem ya Fara magana Sameer ya rigashi Dan ko sallama Babu ya Fara fadin "Abdul Hakeem zahrar tazo Nan ne?. "Easy my man! Tana Nan Kanon a Janbulu gidansu Sajida, yanzu Umman su sajidar ta Kira Ammah ta fada Mata saboda hankalin ta be kwanta da ganin zahrar ba duka yaushe akayi Abu da zata wani zo yawon ziyara tasan da wata a kasa, shine ta Kira zilai ta fada Mata tun fitar safe baku dawo ba". Ajiyar zuciya ya sauke, sai Yanzu ya samu nutsuwa dan Yanzu suka gama wayar da mommy akan ko akwai wani cigaba? Yace Mata Babu Kuma tun lokacin da abun ya faru yake ta kokarin ya Sami Mahmud Abun ya faskara. "Na gode kwarai Abdul wallahi muna nan hankalin mu a tashe tun bayan Azzahar muke Abu Daya, Dan Allah kayi min godiya gurin Ammah, kace Kuma tayi hakuri ba sai tazo ba Dan Allah ga mommy ta Isa tayi komai ka fada Mata laifi akayi mata amma in Sha Allah hakan baze Kara faruwa ba wannan ma tsautsayi ne". Kai kawai Ammar ta gyadawa Abdul Hakeem ya gane me take nufi tunda handsfree ya saka wayar". "To ba damuwa tace ayi maka godiya da kwaramniya" "Ba komai yiwa Kaine ka turo min da address din gidan Yanzu na gode". Sukayi sallama ta kashe Kiran Yana Maida hankalinsa a Kan Ammah. "Ammah lokaci yayi daya kamata a zauna da Mahmud asan who's he? Aure ba Abun Wasa bane asan asalinsa Kinga muna tare sosai wallahi be taba fada min asalinsa ba kawai dai nasan he's educated fiye da tunanin mu badai ya nunwa ne kawai anyway kome Kenan dai kiyi abinda ya kamata kawai". *** **** *** Suna Gama waya Sameer ya lalubo Number Rukayya tana dauka yace ki fadawa mommy gani Nan zamuje mu taho da Zahra tana janbulo gidansu friend dinta". Bai jira tayi abinda zata fada ba ya katse Kiran ya saka jallabiya ya dauki key din motar yayi waje. A kofar parlour ya tarar da Rukayya da Mommy. Fitowa yayi yana fadawa mommy Yanda sukayi da Abdul Hakeem da Ammah. "Dan Allah ki zauna mommy muje da ya Sameer kawai ana ganin mu dake za'a San ba lafiya ba Kinga ai itama zato takeyi kawai muce Mata ya Mahmud ne ya dawo yace muzo mu taho da ita tinda da saura lokaci". "To shigo mu tafi tsari mistress". Saida suka dauki titin rijiyar zakin sannan Sameer ya mikawa Rukayya wayar da address din da aka turo Yana fadin " duba ki gani ko kinsan laying kune masu yawo lungu da sako na garin nan". Dubawa tayi tana fadin " Nasan gurin layin gidan su saliha sani Musa ne tare mukayi Excel da ita". Cikin ikon Allah suna tsayawa a kofar gate din motar ya Abba ta shigo shida Abie dinsu sun dawo daga kwangwalam bodar NIGER inda sukaje gaisuwar mahaifar amininsa data rasu jiya, sun biya ta kazaure gurin wani abokin aikinsa daya kwanta a Asibiti Shima a Nan sukayi dare. Ganin mota a kofar gidan yasa Abie yace Abba ya tsaya yaje yaji ko lafiya Yana fita Mai gadi ma ya fito Yana ganin Abba ya karasa gurin da sauri, fitowa Sameer yayi ya tarbesu Yana Mika musu hannu sukayi musabaha Yana fadin "Ayi hakuri munzo cikin dare ba sanarwa,Daman munzo mu tafi da zahra ne tun Rana tazo Bata Fadi zata kwana ba sai Yanzu mijinta ya dawo gashi ba waya a hannunta, ganin da sauran daren yasa muka biyo samunta". ,"Ok. Ba damuwa muma Yanzu shigowar kenan munje unguwa tare muke da Abie". "To mu karasa Mana na gaishe shi ya juya yabi bayansu suka nufi gurin Abie din, Rukayya gani tayi kamar akwai rashin kyautawa ace tana kallo aje a gaishe da babban mutum tana zaune sai kawai ta fito ta rufa musu baya. Cikin girmamawa Sameer ya gaishe da Abie din sai Jin muryar Rukayya sukayi daga baya tana gaishe da Abie din, hankalin Ya Abba biyu ya kasu ga wata murya data fizgeshi lokaci Daya ga Kuma bayanin da yake yiwa Abie. ""Ba wani Abu Bari a Kirawo Umman tasu saita fada Mata ta fito wannan ai shashanci ne ya za'a bar yarinya ta nemi gurin kwana da mijinta da komai". Sameer ne ya Dan shafa Kai. "Ayi hakuri Abie mijin ne baya Nan sai yanzu ba dadewa ya shigo kasar". Mazaunin direba Abban ya koma suka nufi ciki tunda Daman Mai gadi ya bude gate Yana jiran su shigo. A waya Abie ya Kira Umma har lokacin idanunta biyu da wuya tayi barci matukar tasan mijinta baya Nan da sauri ta dauki wayar tana Masa sannu da zuwa. "Yauwa ya amsa a takaice Yana fadin. "ki taso bakuwar da kikayi a gidan mijinta ya dawo gasu Nan a gate". Ya kashe Yana nufar part dinsa. Shiru tayi waye ya fada masa da bakuwar a gidan jiki ba kwari ta nufi dakin sajida, barci ta Samu tanayi sadidan kamar Nan duniya Bata da damuwa Kota sisi dakin ta shigo tazo bakin gadon ta tsaya tana Kiran sunan ta a hankali, tana fadin "tashi ki kimtsa ki fito ga Mai gidanki can zaku tafi gida". Idanun tadan zaro tana fadin "wallahi bazani ba Umma kice musu bana nan sai hawaye".. AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 43. _______ kuka zahra keyi ba kakkautawa a hankali Umman ta zauna kusa da ita, ki daina kukan Nan kiyi hakuri ki tashi ku tafi, kiyi ta addu'a Allah ya kawo Miki saukin ko menene damuwar, kada ki Kara tunanin yin irin haka idan Abu ya dameki ki tafi kibar gida ba shine maslaha ba kinji, tashi ki cire Rigar barcin ki canza suna jiranki Kinga dare ya farayi inaga tun Rana suke bulayin nemanki sai Yanzu suka samu inda kike". Kai ta gyada tana goge hawayenta, Bata taba tunanin yau zata koma gidan Nan ba Dan ita a budget dinta daga Nan gaba zatayi Dan kasar tayi niyyar tsallakewa tayi gaba abunta tunda passport dinta yana jaka, to Wai ta Yaya suka gano tana gidan Nan Wama yasan gidan a cikinsu, to shi yaushe ya dawo? Haka zuciyarta ta dunga sake-sake. Fita Umma tayi ta Bata guri ta canza Kayan, jiki a mace ta fito ta iske Umma da Ya Abba a parlourn, gaishe da Ya Abban tayi ya amsa Yana fadin "wallahi kin wahalar da mutane da wannan Daren Kika sakasu fitowa har da mace Ina jinma mijinta ne" .ita dai zahra Shiru tayi Masa ta nufi Hanyar fita daga parlourn tana fadin "ummah na tafi Saida safe". Ta fada tana yin gaba "to Allah ya tashemu lafiya kiyi hakuri da safe idan Allah ya kaimu ki bude wayar zamuyi magana". "To Ummah in Sha Allah Zan bude". Suka fice daga Fallon. Ya Abban Yana biye da ita tun kafin ta karaso Rukayya ta taho cikin sassarfa ta ringume Zahra tana fadin "wallahi kin dauki alhakina da Hajiyar makwarari Kinga kukan da muka Sha yau? Tambayi Ya Sameer kiji duk kin tashi hankalin mu". Wani sanyi ya ratsa Ya Abban Jin Rukayya ta ambaci Sameer da yayanta, daman Kuma yaga Kama ta zahiri duk da dare ne Bai Hana shi ganin kamannin nasu ba. Shiru zahrar tayi Mata ita sai Yanzu taji wata kunya duk ta rufeta, me kenan tayi? Shike Nan zasu dauka fa tayi yaji ne dole ta magantu. "Wai Dan Allah Aunty Rukayya ku kasa barina nayi kwana ko Daya ne a gurin Ummata nifa bada wata manufa ba na taho kawai dai nasan idan nace zanzo ba Bari Oga sameer zeyi ba zece saina nemi izinin....." Sai tayi Shiru. "Izinin wa za'ace ki nema?". Gaba tayi kawai ta nufi gurin da Sameer yake tsaye jikin kofar driver, da wannan damar Ya Abba yayi amfani ya matso kusa da Rukayya yana fadin "Ashe Aunty tasha kuka zanso Naga kina matse hawaye". Kallonsa tayi haka nan taji yayi Mata kwarjini. 'yar dariya tayi tana fadin "Ina yini?" "Lafiya kalau beauty, ki saka min number ki Zan kira naji ya kukaje gida tunda sister Zahra har wayar tayiwa tawaye". Ya karasa Yana murmushi itama murmusawar tayi tana karbar wayar, number ta saka Masa ta Mika Masa wayar tana fadin "bari na wuce ya Sameer Yana jirana" Tayi gaba. "Ok saina kira shima gurin Sameer din ya nufa sukayi sallama, ya leka ta window Yana yiwa Zahra magana. Tunda suka dauki hanya ba Wanda ya Kara magana sai ajiyar zuciyar Zahra ke sauka kadan- kadan. A hankali zahra ta bude Baki tace "Dan Allah oga sameer kayi hakuri na Bata maka Rai bada niyya nayi ba kawai dai Ina son Naga Ummah ne Naga kuma kamar bazaka yarda naje na kwana ba". "Ba komai kawai, Daman Yanda su mommy suka tada hankalin su ne ya daga min hankali nasan ba Bata zakiyi ba tunda da kafarki Kika fice". Shiru tayi tasan magana ce ya fada Mata a kaikaice, tasan a kule yake da ita kawai dai Batasan dalilin Daya hana yayi Mata buyaji ba, Dan taga alama ya iya tijara Yanda ya karewa Rukayya dazu ko shi yasa taja bakinta tayi shiru Yanzu. Sha biyu da minti goma yayiwa Mai gadin gidan horn Saida ya leko shima Sameer din ya fito Yana ko waye sannan ya bude. Yana shiga da motar Maimakon yaje kofar main parlourn sai taga yabi ta baya ya nufi wani gani Mai azabar kyau ko Ina tar kamar dauko ginin akayi aka aje ga wata 'yar baranda data hade ginin biyu an saka glass anyi kamar katanga da wasu irin flowers masu kyau a jere ana ganinsu gurin yayi matukar kyau da burgewa a kusa da steps din da ze sadaka da Main parlour, Zahra ba tayi kokarin bude side din da take zaune ba, dan juyowa Sameer yayi "Dan Allah kada maganar nan ta fita kawai da safe ki fada musu mun Dade a Asibitin ne yasa Kika bamu dawo da wuri ba sun kulle, kiyi using da Nan kawai ki barsu su a can, Rukayya zata kawo Miki kayanki da safe kiyi idan Allah ya kaimu". "To nagode". Abinda ta iya fada kenan, ta bude ta fita Rukayya man ta fito tana fadin " Bismillah kizo muje na rakaki". Tare suka jera suka hau zuwa kofar, ita Kanta kofar abin kallo ce ita Yanzu zahra abin har ya daina Bata mamaki so take taga iya gudun ruwan bayin Allah nan Kullum lamarin su ba baya yake ba gaba yakeyi daga Nan sai can suna shiga ta Kara jinjina girman lamarin Wai shi wannan abokin nasu wane irin kusancin ne a tsakanin su da za'a dunga sauke ta a duk inda akayi ra'ayi. Wannan part din yafi wancan komai parlour sun Kai hudu, a cikin parlour na uku ne suka taka steps ya Kai shida sannan suka shige want korido ko Ina tadal sai wani special kamshi ke tashi bedrooms ne guda biyu a jere, Rukayyar ce ta Dan juyo tana murmushi "to madam gasu Nan saiki shiga Wanda kike so ki kwanta, tunda kin samu muna yawon dare kamar marasa gaskiya, Zan Baki shawara sai kin Zama jaruma fa a gidanki Dan Ya Mahmud wallahi Mata rubibinsa suke, idan kikace Abu kadan Zaki fece kece ki tafi kece a kwana Dan idan yayi wata tafiyar sai ki kwana hamsin Baki saka shi a idonki ba, pls you have to be very strong gaskiya kada ki yarda a gano Ina kike da lapse akwai damuwa kwarai ki rike mijinki da kyau ki mutunta shi ki girmama iyayensa zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah, zabi na rakaki dakin na wuce barci Kuma nakeji tunda Allah yayi Mana gyadar dogo ya rabamu da kwanan zaune to matar big bro ta Bata Ina Ni Ina barci ai sai kwana sallah". Ta fada tana 'yar dariya. "Ki sakani kowanne Wanda za'a sanwa ya taba cewa way gutsiri nan? Duka zaman na yau zuwa gobe ne Dan gida zamu koma bana son wani surgery a Nan idan ma yimin din za'ayi ba wannan Mai fuska kamar Jan karas din zatayi min ba muma muna da qualified a can Dan dai kada nayi musu dashi ne kawai". "Kinga mu Shiga na koma dare Karayi yakeyi gara naje na kishingida". Dakin da yake facing dinsu ta bude MashaAllah" ta fada Tana karewa dakin kallo sannan ta juyo tana fadin mu kwana lafiya" Kallonta Zahra keyi tana son tayi Mata tambaya Amma ta rasa ta Ina zata Fara, Dan Yanda tasan gudan Nan da Yanda take fadar wasu abubuwan akan Mahmud ga Kuma abinda Hajiya kakarsu ta fada Mata dazu maganganun suna kamanceceniya da juna amma Bari ta Adana tambayoyinta da sauran lokaci. "Nagode Aunty sai da safe, Amma fa Ina Jin tsoron gurin nan fiye da can din wallahi, Kinga Nan ba kowa. Allah mu kwana tare ko kin tafi bazan iya barci ba". Dan Jim tayi tana tunani ita Kanta Bata San dalilin Ya sameer na kawota Nan ba, amma tasan dole da dalilinsa nayin hakan. "Ok ba damuwa Bari naje na dauko sleeping dress Dina da naki saina dawo" "Ok, yauwa Aunty ki taho min da phone Dina tana cikin bedside". Ta nufi Hanyar fita, wayarta ce ta dauki ringing number ce tasan Wanda ya Karba ne dazu a ta daga da sallama suka Kara gaisawa ya tambaye ta ya suka zo gida ta fada masa lafiya kalau sukayi sallama ta fice. Kofar ta rufe ta farko tayi gaba tana fadin "kamar wata Rukayyar mahaukata na shigo wannan part din na kwanta a can ma naki kwana ballentana a Nan yarinya Allah ya kawo mijinki ki tarairayi kayanki kuna gefe Naga alama sai nayi Mata budedden karatu sannan zata gane mace har Mace ta fita kunya Amma ki tsaya kina Wasa da damarki". Ta wannan barandar Mai glass ta Shiga Daya part din da yake tasan wanancin lambobin kofofin tunda duk sati suke zuwa da sauran yaran gidansu suna gyara bedrooms din kawai sauran Kuma da masu aikin da sukeyi dakunan kwanan ne dai Batasan dalili ba masu aiki basa shiga. Ko Ina tsit a gidan baka Jin komai sai kukan kananun kwari da dai daikun tsuntsaye ta gefen inda zahrar ta kwana ta wuce da gaske ko ita data Saba da Shiga gidan wani lokacin tsoron Yana kamata bare a irin Nan da sauri ta shige parlourn na uku ta wuce corridor da za sadata da dakunan. Tana bude dakin zilai ta bude ta fito tana fadin "sannunku da dawowa, Dan Allah lafiya kuwa tun rana sai Yanzu sha biyu ta wuce?'. "Lah ba wani damuwa munje unguwa ne motar ta samu matsala sai dazu muka shigo garin muka biya gidan mommy a can muka Shantake Sai Yanzu ya Sameer ya kawo mu". Wani sanyi zilai taji a ranta, "to ai shikenan Allah huta gajiya da ko barci na kasayi ina ta tunani barkatai". "Kai haba ba komai Allah ya tashe mu lafiya ta bude kofar ta shige itama Zilan ta Koma ciki. Tun bayan fitar Rukayya zahra ta dosana gefen ta zauna ta zabga uban tagumi, da sauri tashi ta fito ta dauko handbag dinta ta biyo Hanyar da suka shigo kofar fitar ta murda tajita bam ko motsi batayi, tayi tayi taji kamar tana taba dutse, hakuri tayi ta juya sai lokacin tsoron ya rufeta da gudu ta shige dakin tana turo kofar, dube-duben makulli kofar ta Farayi ita dai bataga gurin wani key ba har zata hakura taga wasu numbers a jikin wani Abu kamar switch din kunna wuta numbers din ta Danna Yanda suke a jere taba taba ta karshe taji want Dan sound daga jikin kofar handle din ta Kama zata bude taji ta rufe gam, sai lokacin ta Dan samu peace of mind, ta nufi gadon ta aje jakar a gefe ta nufi toilet dole saita sake gyara jikinta. Tana Shiga ta cire rogar material din sajida data sako ta taho da ita ruwan zafi ta hada tayi wanka ta fito da towel a jikinta sanin ba wasu kayan sakawa a Nan yasa ta Haye gadon daga ita sai towel ta rage hasken dakin ta janyo lallausan bargo ta rufe jikinta sai fuskar kawai ta Bari a hankali ta Fara Addu'oin kwanciya barci, kafin ta Gama barcin yayi awon gaba da ita. Karfe Daya da rabi daidai jirgin Max air ya sauka da duban jama'a daga kasahe daban daban na duniya, cikinsu harda Muhmud Muhammad Dange, a hankali yake tako stairs din jirgin sanye yake da kananun Kaya Ash T- shirt da black jeans a jikinsa sai jakar laptop dinsa a kafadarsa. Yana karasa saukowa wani matashi fari marar jiki ya nufe shi Yana fadin "barka da sauka yallabai, ga key din motar Nan a hannunta oga yace na kaika gida, sai Balarabe ya bimu da wata motar sai mu dawo tare dashi". Hannu ya mikawa Mai bayanin Yana fadin "bani key din kawai kace masa na gode kwarai da kulawasa, zanyi driving da kaina". Mika masa Yana fadin "Allah ya tashemu lafiya kayi min godiya sosai ya Ciro kudin America ya mika Masa sannan ya bar gurin. Lokacin Daya fito daga airport din Daya da minti ashirin da bakwai, tuki yake cikin nutsuwa sau biyu kawai ma'aikata suka tsayar dashi, har yazo gate din gidan ba Wanda ya Kara tsayar dashi, sau Daya yayi Horn Mai gadin ya falfalo da gudu yana leken waye a Nan baisan motar ba Dan haka ya koma ya dauko abinda ze Bashi kariya. Kafin ya bude ya fito, Mahmud ya fito ya harde hannusa a kirjinsa ai Mai gadin Yana ganinsa yayi sauri ya koma da gudu Yana Fadin "barka da sauka fari Mai farar Aniya Allah ya Kare gabanka da bayanka baya Mai goya marayu" Dan murmusawar Mahmud yayi Yana fadin "wani Abu sai Malam Musa shi Babu ruwansa da dare". Ya fada Yana kunna Kai harabar gidan wadda take kamar rana, mutane hudu ne suka bullo daga mabambantan gurare. Parking lot suka nufa sun San Mai gidan ne tunda suka jiyo hargagin Malam Musa. Shima da gudu ya karaso gurinsa Yana cigaba da Yi Masa kirari. Sun gaisa sosai dasu har kusan minti biyar sannan yayi musu sallama Saida safe ya nufi babban part din, Murtala ne yayi sauri ya sameshi "yallabai Ina ganin madam din kamar tana can sabon gurin can Dan Nan Naga Sameer ya ajesu dazu ita da Rukayya kanwarsa, can ya nufa Yana mamakin me yasa Sameer ya kaita can alhalin yace a barta a tsohon part din. AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 44 _________ kamshinta ya Faraji Yana shigowa parlourn, wani limshe idanu yayi Yana ayyana abubuwa da yawa a ransa, direct ya wuce bangaren bedrooms din Yana jinsa cikin nishadi, wato Sameer Yana expecting dinsa ne a kasar shi yasa ya bude Mata nan kenan, a hankali ya taba handle din kofar farko ya jita a bude Shiga yayi komai tsab, iska ya huro daga Bakinsa ya aje jakar laptop dinsa a Kan sofa da take dakin, ya zauna a gefe Yana cire takalman kafarsa, wanka yake son ya Fara kafin ya Shiga gurin waccen danger girl din "yar yarinya ta Hana shi sakat duk ta birkita Masa Lissafi" ya fada a fili Yana rage kayan jikinsa. Wanka ya shiga bai wani dauki dogon lokaci ba ya fito saboda dare ya Fara nisa ga gajiyar zaman guri daya, pyjamas ya saka masu kalar sky-blue ya fesa turarensa ya dauki wayoyinsa ya fice daga dakin ya nufi dakin da zahrar take, wani Abu ya taba mai Kama da socket din electric na kunna wuta sai kofar ta bude,a hankali ya shige Yana Jin kamshinta yanda ya cika dakin, shi dai yawanci duk matan da suka zamar Masa dolensa suna bala'in son kamshi, yana ida shigowa kofar ta rufe Kanta Wai Abu ya taba ba Wanda zahra ta taba ba, yayi gaba Yana nufar gadon inda ya hangeta ta kudundune cikin bargo, da gani a tsorace tayi barcin, wayoyinsa ya aje a Kan bed side ya zauna a gefen gadon Yana Kare Mata kallo, shifa duk hankalinsa ba a kwance yake ba tunda aka fada masa matsalar dake damunta yaji ba shida sauran nutsuwa idan ba zuwa yayi ya ganta ba, Kuma Dole ma yasan abinyi akan ciwon Nan ko ana Wasa da wasu lamuran Banda lafiya baik'i tasan kowaye shiha a wannan lokacin dole ya dauketa ya kaita inda za'a dubata Masa ita duba na gaske. Remote din AC ya dauka ya rage gudunta dakin yayi sanyi da yawa duk da Yana son sanyi amma wannan yayi yawa, a hankali ya saka hannu ya janye bargon daga fuskar ta barcinta takeyi shower cap din dake Kanta ta cire sai gashi Baki sidik Yana ta walqiya a cikin Dan hasken data Bari a dakin, Kara zame rufar yayi har zuwa kirjinta jikin sai wani glowing yakeyi Jin sanyi Yana shigarta yasa ya juyo da fuskar ta inda yake zaune "ya Salam". Ya fad'a a hankali, gani yayi ta Kara yi Masa wani kyau na musamman, Kare mata kallo yayi yaga daga ita sai towel a jikinta, murmushi yayi da gani Batasan da Kaya a dakin ba. Kayan jikinsa ya cire ya Zama daga shi sai boxer short ya shige jikinta ya janyo lallausan bargon ya rufesu Yana sauke ajiyar zuciya, a cikin barci taji an rungumeta gaba dayanta jikinta ne ya dauki rawa shikenan tasan tata ta Kare shi yasa suka nemota da tsohon dare suka kawota Nan Yan ko wane irin ihu zatayi ba Mai jinta, cikin murya Mai rauni tana cracking ta Fara farin "innalilllahi na Shiga uku wayyo Allah na.... Bata katasa fadin abinda tayi niyyar fada ba taji yace "shittt...Ni ne fa cool down precious ba abinda ze sameki a cikin gidan Nan sai ikon Allah, akwai kyakykyawan tsaro". sansanyan kamshin turarensa ne ya shiga hancinta, kokarin kwace jikinta takeyi Dan yayi Mata kane-kane so take taga zahirinsa Amma ya Hana hakan, ita mamakinta Daya yaushe yazo garin kuma ta Ina ya shigo Dan ita dai tasan ta rufe kofar nan. Dai dai kunnenta ya saka Bakinsa "ki kwanta muyi barci na gaji da yawa kin hana duniyata kwanciyar hankali kina min kisan mummuqe ko wayar ma kin haramta Mana yinta, tunda Naga alama Nima Mai laifi ne". Ya fada yana shafa gashin kanta zuwa bayanta, hannu Daya yasa Yana zare towel din data daura a jikinta da sauri ta rike tana girgiza Masa Kai. "Dan Allah ka Bari bafa kyau muyi barcin to". Wani guri ya taba a jikin gadon wasu irin fitilu suka Kama kamar star masu haske sosai, Bata ankara ba ya fizge towel din gaba Daya daga jikinta Yana Mata wani mayen kallo hannu tasa ta kare kirjinta cikin matsananciyar kunya tace Masa "Dan Allah ka kashe hasken Nan wallahi kunyarka nakeji". "Ni kike Jin kunya?" Kai ta gyada Masa, 'Well done Yanzu kuwa Zan cire kunyar nan daga idonki". Wani bed sheet data gani a gefen gadon ta janyo da sauri ta lullube jikinta dashi tana Kara sadda Kai kasa Dan da gaske ya saka taji kunya sosai. Wutar ya kashe ya matso sai Jin mutum tayi ya shigo cikin Bedsheet din data rufa dashi ya hanye shi ya maye gurbinsa da lallausan bargon. "Ki hanani Zama a gurin neman abincina sannan na dawo ki Kama guduna, ai impossible wallahi muyi barcin da safe mayi bayanin". Ya Kara mannata a jikinsa suka samu body contact da kusancin zahiri. Sun jima yana sarrafata.Tayi laushi iya laushi dan da gaske da kishirwarta ya shigo garin tamkar mayunwacin Zaki badan tana cikin rashin tsarki ba da Babu abinda ze Hana labarin sauya salo, dan tuni ya wani manta da Alkawarin da ya daukarwa Kansa, Saida tafiya tayi nisa ya ji abinda yayi Masa cikas Dole ya saurara Mata, sun kai kusan karfe uku da rabi a haka shi Mai fad'ar barci ya keji sai gashi ya bige da Hana Mai barcin yin Bata barcin. Sai sauke ajiyar zuciya suke su duka har lokacin hannunsa Bai daina shafe shafe ba, wani irin yanayi jikinta keyi har mararta ciwo ta Dan Fara Mata cikin dashashshiyar murya mai dauke da salon shagwabar da Batasan iya ba,ta kankame Shi jikinta na wata irin tsuma muryarta ta dishe tamkar me yin mura ta Fara magana. "Dan Allah ka bari wallahi marata ciwo takeyi...". Baiyi magana ba sai kakkameta da yayi kamar ze shige jikinta shima ya hade bakinsu Yanda ba Yanda za'ayi ta iya furta wata maganar ba, hannunsa ya tura Yana shafar marar ji yayi tadan tasa kamar ta Dan kumboro, hannun ta rike tana girgiza Masa Kai. Zare hannun yayi ya dawo dashi sama yaci gaba da sabgarsa ya Kuma ki sakin bakin da zatayi korafin, suna haka har wayarsa ta Fara rera kiran sallah. A hankali cikin muguwar kasala ya saki bakinta yana Maida numfashi da sauri da sauri gefe ya margina Yana dafe da tasa marar idanunsa a rufe, Zahra naji ya raba jikinsu ta Kara takurewa a cikin bargon wani irin tsoro ne ya lullube ta da gaske yazo Mata da wani lamari Mai girma, ita ai ko idanu bazata yarda su hada ba ai da kunya wallahi duk yabi ya tsorata tas ya lalube ko Ina na jikinta, Ashe can baya Wasa ne kawai yayi Mata yanzu ne ya nuna Mata true colour dinsa tana ganinsa salihi Dan bawan Allah Ashe shima guda ne ba gyale ba, kirjinta sai zogi da ciwo sukeyi mata yayi son ransa da jikinta. Tana jinsa ya tashi ya shige toilet ya jima tana jiyo motsinsa, sannan taji ya fito alamun tsayuwarsa taji a Kanta,a hankali ya saka hannu ya janye bargon kankame jikinta tayi Dan daga ita sai pant Kare Mata kallo yakeyi take yaji alwalarsa na neman warwarewa, laimar hannunsa ya Dan yarfa Mata a jikinta "wash...Allah na!". Mayar Mata bargon yayi ya shige clothset din dakin jallabiya ya sako Fara tas da hula mahadinta raka'atanul fajri yayi, jikin gadon ya matso ya Dan zauna "zanje masallaci". A dawo lafiya tayi Masa tana kudundune Yanda take, tanaji ya fice daga dakin. Sai ta tabbata ya Kai masallacin sannan ta yunkura ta tashi ta nufi toilet, tsabtace jikinta tayi sannan tayi wanka ta fito,lotion din data gani ta shafa sai body mist na itacen sandal wood Dana oud ta hada ta fesa kayan da zata saka ne ya zama cikas Dan bazata iya mayar da Wanda ta cire ba Kuma bazata Kuma Zama da towel ba tunda taga abinda hakan ya janyo Mata, Shawarar duba clothset din tayi idan taga Kaya sabo Kona waye zata saka, tana mamakin ace Mai gidan Nan bashi da Mata Kuma ya sakarwa abokai irin haka baya gudun a ring aikata fasadi a cikinsa, were Dan wannan sai ka shekara a ciki ba'asan kana nan ba. Ba karamin mamaki tayi ba ganin kayan Mata masu yawa har Sunfi na wancen apartment din ba wani d'ar undies ta saka ta saka doguwar Rigar material Bata daura Dan kwalinba wasu hulina na Mata ta gani da yawa ta duba kalar ash irin flowers din jikin material din ta saka a Kanta, barci takeji sosai Dan tunda Allah yasa ya tasheta da aalonsa Bata Kara rintsawa ba shiko gogan Allah besa an raba barcin jiya dashi ba. Harta juyo zata bar gurin taji tana son ta bude dayan side din, kayan make up ne dasu turarika shoe and bags turaren ta dauka tana dubawa duk yawanci irin nata ne sai wasu irin nasa ga Kuma kayan maza nan Lodi Lodi dasu underwears tana tsayen tana dubawa taji kawai an rungumota ta baya, ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido Sam bataji alamun bude kofa ba ko takun tafiyarsa, Kansa ya Dora a kafadarta Yana Dan hura Mata iskar Bakinsa a kunne "Good morning my previous". "Morning Yayana". Ta fada da wani salo, juyo da ita yayi suna facing din juna. "Bude idonki ki kalleni ki fada min waye yayan naki? Wato har yanzu da sauran Rina a kaba kenan ko? Nifa bazaki tauyeni ba Ni ba wani Yayanki bane a bani special name Dina, kodan kinga mu 'yan gargajiya ne "ya'yan Alarammomi Malam soro, bamu da wayewa irin taku ko?" Batasan lokacin data sauke ifanunta a Kan nasa ba, tana jinjina maganarsa. "Wayewar saita kasheku". Tayi subul da baka ta fada harga Allah a zuciyar ta tayi niyyar fada bakinta ya subuce ya fada. "Kai! Nine wayewar saita kashemu to nida waye zata kashe din?" Kauda Kai tayi tana Jin kunyar maganar. *Ni ba haka nake son fada ba Bakina ne ya furta hakan". *Ok, zomu kwanta barci nakeji tunda kin hanani barci da fitinarki". Rigar ya zuge zif din ya cire mata ita ya barta daga ita sai undies kawai ya dauketa can ya nufi bed din da ita tana mutsulmutsultun ya sauketa ya kiya Saida ya dangana ta da saman bed din, shima jallabiyar ya zare ya janyota ya lullubesu da gaske barcin za'ayi Dan tunda ya sakata a jikinsa Bai Kara yi Mata komai ba. *** *** *** Tunda Ammi tayi sallah Bata Koma barci lazimi ta zauna tana yi amma zuciyar ta Babu dadi kwanan nan kusan Kullum sai tayi mafarkin Mahmud da wata yarinya budurwa Yana rike da ita da hannu Daya dayan Kuma Yana ta faman fada da wasu irin halittu mara kyawun gani, to yau ma shita Karayi Saida taga wasu mutane dattijai guda biyu sunzo sun Taya Shi kashe wadannan halittun sun tasa su shida yarinyar har wani gida sai da suka shige sannan suka juyo suka tafi. A haka Mai gidan ya sameta Saida ya zauna ya Kare Mata kallo yasan da akwai damuwa a tare da ita sai dai tana kokarin biyewa. "Ammin Yara me yake damunki duk kwanakin Nan Baki da walwala Sam ko kula dani ma tayi baya ko Baki huce bane har yanzu?". Kai ta girgiza "A'a kawai dai lamari Hussain ne yake damuna kofa da Rana Daya Bai taba kirana ba ko sako ta email Bai taba Yi min ba, gashi a kwanakin nan sai wasu irin mafarkai nakeyi dashi marasa dadi abinda yafi tsaya min a Rai Kullum da wata yarinya budurwa kamar 'yar India nake ganinsa da ita Ina tsoron wani Abu wallahi na rasa yanda zanyi Dan Allah kayi wani Abu akai". Sai hawaye sharrrr. "Subahaballahi! Haba zainab ya Zaki ringa yi Masa kuka kinsan masifar zubarwa da d'a hawaye kuwa ko wani abun yake aikatawa ai saiya karu idan kina Masa kuka, addu'a zamuci gaba da Yi Masa nifa jikina Yana bani Yana Dubai Dan last week na samu leakage akan Yana can din Dan yayi wasu ziyarorin bazata a can harya dakatar da wasu ma'aikatansa sai dai duk kokarin a gano min masaukinsa sabo hakan yaci tura Dan ba'a inda yake sauka ya sauka ba tunda gudun hijira yayi". Hawayen ta goge ta tashi tana ninke sallayar ta zauna kusa dashi. "Shikenan Allah ya shiga cikin lamarin ya kureshi daga sharrin zinace zinacen zamani wallahi badan komai nufin Allah bane Wanda yaso yake bawa kyautarsa danace dama bashi ya samu wannan budin ba da kananun shekaru to yanda yaso haka yake tsara kayansa, Amma ga yayunsa Nan ba Wanda ya takura musu Suma ai suna da wadatar,tunda Allah yayi muku karfin arziki waye talaka a cikin family din nan?". Dan murmushi general yayi Yana kallon yanda take fadin magana abinda ba halinta ba inda akan twins ne sai dai wani yayi magana Amma ta zage tana fadin son ranta. "To ya zamuyi da hukuncin Allah shi yaso ya daukaka a cikin zuri'ar da Wanda ya Isa yace a'a Ina cewa Alhaji Ishaq ne ya bashi jarin Daya Fara sana'a dasu tun Yana hannun Hajja, Amma yanzu zaki hada arzikinsu ko kusa ko alama Babu Hadi,.koni Dana haifeshi ya mallaki abinda bani da kwatqnkwacinsa, Keda Kika haifeshi kin mallaki abinda yake dashi? To kiyi istigifari ga Allah tunda shine yace Yana azurta Wanda yaso ba tare da hisabi ba,ai kin gane?". "Na gane Allah ya Zama gatansa a duk inda yake,Amma fa yarinyar Nan ta tsaya min a rai idan Yana kusa da wannan ai zai manta da kowa ne tunda cikin bacin rai yabar gida ga Kuma kudi a tare dashi kaga sai Allah kadai ze kare shi". Dariya ta bashi sai da yayi sosai kafin yace. *In Sha Allah in dai Zina gado ce to Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w zuri'ar mu bazasuyi ba Ni ba mazunaci bane haka kema ba ita bace in Sha Allah.Allah baze jarabcemu da ita ba, Kika sani ko bushara ake Miki ke uwa kin samu sirika". "Haba dai har abun ya Kai haka yayi aure ba sanin iyayensa ai kuwa da lamarin ya lalace". 'yar dariya yayi. "Kedai kije ki shirya min breakfast daurin Aure zamuje kabba na Dan gidan sanata Abdul Aziz" "Ok.bari na shiga kitchen din" Ta tashi ta fice tana baza kamshinta as usual. ****** Tun idar da sallar Rukayya ta taso ta nufo part din da zahra ta kwana,abin mamaki an canza pin kofar dan ta kwada yafi sau goma Amma taki budewa. Nan da Nan taji hankalin ta ya tashi me Kenan badai wani bane ya shigewa 'yar mutane ba gashi jiya Taki Kai Mata wayarta da ba saita kirata ba, gudun kada tace sai sun kwana ya hata ta Kai mata. Number ya Sameer ta lalubo lokacin Yana barci, Yana dauka ko gaishe shi bata tsaya yi ba ta Fara fadin "Ya Sameer ka taimakeni wallahi tun sassafe bake kokarin shiga part din da zahra take Amma kofar kofar kamar an canza pin din na saka yafi sau goma Amma yaki budewa". Tsaki yayi "Waike Dan Allah Ruky yaushe Zaki girma ne? to oga ne ya shigo cikin dare Nima da asuba naga text message dinsa Dan haka ki Zama ready idan na shigo saimu wuce tare Amma yanzu kada kuyi komai za'a kawo abinci". "To ai su Iya Rahane har sun kusa gamawa baka fada min ba tun dazu". Ok, ba komai sai a hada tunda gidan da jama'a, yauwa zuwa an Jima ki bude musu part din Nan na kusa da parking lot sai su zauna a nan tunda shima ogan Bai san ze shigo kanon ba harsu Gama su koma to matsalar madam din ce inaga ta caza Masa Kai Wai cewa fa yayi daina amsa Masa waya tayi". "Kamar ya Bata amsa masa waya? Batasan kowaye bane da zata ringa yi masa haka?" "Eh kusan hakan ne gaskiya" "Allah ya rufa asiri" ta fada. Sukayi sallama ta kashe Kiran tana dariya "su oga anzo hannu ana walagigi da rayuwar 'yan Mata gashi kaima kazo hannun yarinya tana juyaka son ranta, nasan bana raba Daya biyu saboda shi ta rufe wayarta jiya, taki magana dashi a wayar Ya Sameer karshe ma ta sakata jirgi, yes! Haka nake son irin matansu su kasance, idan suka samu wadda ta mace a kansu ta Zama sorry Amma wannan ta shuka mulkinta yanda takeso tunda Batasan waye shi ba". Ya juya ta koma kitchen inda tabar su zilai suna aiki, tana shiga zilan tace Wai ni lafiya yarinyar Nan? naji shirun yayi yawa ko dai rakani zakiyi na gano lafiyarta kada na Zama babbar kwabo an hadoni da yarinya nayi wasarere da lamarinta". 'yar dariya. Rukayya tayi "gaskiya kinaji da matar big bro irin wannan shiga damuwa jiya fa ko barcin kirki bakiyi ba kina zaman jiranmu yau ma tun Asuba kike ta nemanta, ki kwantar da hankalin ki Aunty sirikinki ne ya taho ba Shirin wannan 'yar taki tsaye ce taki saurarensa ko a waya dole ya tsallake hidimominsa ya nufo Nigeria". Iya Rahane ce ta aje Wukar hannunta tana duban Rukayya "kikace uban gidan mu ya shigo garin?" "Kwarai kuwa iya jiya cikin dare ya shigo Kinga kuwa sai ki fadawa Aunty ta kauda Kai kawai gurin son ganin 'yarta ba yanzu ba gaskiya, Dan haka da an gama aikin Nan zamu bar Nan Bangaren mu koma wancan". "Wannan gaskiya ne inba tayi dalili ba yaushe zamu shigo wannan guri harda kwana a cikinsa, Amma dalilin uwar dakinmu mun dangwali arziki ai wannan ba komai bane akan gidan da aka sauke mu a sokoto, Kai Naga inda arziki ya amsa sunansa wannan yaro uwarsa tayi farar haihuwa wallahi Nan kusa Banga mutane masu karamcin su ba, uwarsa yarinya karama sai halin girma". Ita dai zilai sai ta rasa Wai wannan maganar dawa ake ne waye suke zance a kansa ne ita fa maganar Zahra take musu su Kuma sun kamo wata tashar Ina hadin zahra ba Wanda suke magana a kansa ko dai Mai gidan ne ya dawo Basu gane me take nufi ba, ita Zahra matar Almajirin Malam Bukar Wanda gidan zaman ma na Baba Malam ne mutanen da yaje yiwa aiki turawa suka gyara Masa shi, to Ina shi Ina wannan Aljqnnar duniyar suda aka kawosu zaman 'yan kwanaki na ganin likita. Cikin nuna mamaki zilan tace "ikon Allah ai ban sani ba kice da anyi uwar banza gara da Kika fada min kada naje nakai kaina girma ta Fadi". "Ai Koda kin shiga basa Nan ba a nan suka kwana ba". Wayar Rukayya ce tayi qara ta dauka ta fice daga kitchen din shine abinda ya Hana zilai fadar abinda tayi niyyar tambayarki Rukayyar. Hira iya rahane taci gaba da yiwa zilai a Kan Mahmud amma ko Daya zilan Bata gano ainishin waye take magana a kansa ba. .[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨ AUREN HUCE HAUSHI. ✨✨ MAMAN FATEEMAH. Page 45. ________Sai kusa karfe Sha Daya da rabi Mahmud ya farka shima yunwa ce ta tashe shi, ido ya tsura Mata barcinta take hankali kwance tayi pillow da gefen kafadarsa, hannu yasa ya shafi gefen fuskarta da gashi ya kwanta lambam, hancinta ya dan ja kadan, dan yamutsa fuska tayi tana bude idanunta a hankali, Ido cikin ido sukayi dashi da sauri ta Maida nata ta rufe. "Ki tashi muyi wanka ki bani abinci Naga alama ke barci baya isarki". Zare jikinta tayi still dai idanun a rufe, tana Jan bargon zuwa kirjinta. "Kaje ka Fara Yi sai nayi nima". Ta fada tana juya Masa baya, Dan murmushi yayi ya Dan rankwafa dai dai fuskarta. "Ok, ba damuwa jeki hada min ruwan saina Farayi kafin na fito, saiki hada min abinda zanci". Yunkurawa tayi ta tashi zaune, tana mutsumutsun yanda zata tashi haka a gabansa. "Ka Miko min Riga na saka saina shiga na hada maka". Ba musu ya dauko Mata Rigar ta Karba ta saka ta Mike ta nufi toilet din. Saida ya tabbatar da ta shagala gurin abinda takeyi ya tashi ya nufi toilet din, tana zuba turaren wanka cikin ruwan data hada ya shigo ciki ba zato ba tsammani sai ganin mutum tayi ya shigo daga shi sai boxer a jikinsa, gurin da take tsaye ya nufo, da sauri ta matsa gefe kanta a kasa Bata yarda sun sake hada Ido ba tace Masa. "An Gama hadawa". Tana aje robar dake hannunta ta juya da zummar barin gurin. Taku biyu tayi taji anyi sama da ita cak sai cikin ruwan daga ita har kayan jikinta, wata ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "Dan Allah ka Bari wallahi nayi wanka fa". "I know, tayani zakiyi Dan rashin kirki ai ni bakonki ne ya kamata ki tarairayeni har wankan ma kiyi min tunda kin hanani sukuni Saida Kika gargadoni na dawo gurinki Kinga kuwa ai duk lokacinki yanzu nawa ne". Har ta bude Baki zatayi magana ya Dora Dan yatsansa a Kan lips dinta "kin manta ba'a magana a cikinki toilet? Muyi wankan later munyi maganar". Janyota yayi jikinsa ya Fara cire Mata jikakkun kayan jikinta, a tsorace da Kuma wata azababbiyar kunyarsa da takeji ta Kara ninkuwa, dan wani Abu ne da be taba faruwa da ita ba a tarihin rayuwarta irin wannan kebewar da namiji baligi da uwar tana irin wannan Bata taba yiba shi yasa Daya hade jikinsu ta shiga tsuma kamar wadda Zazzabi ya rufe, wankan sukayi tare duk da shi dai kadai yake sha'aninsa Dan ita dai kam sai hankali. Saida ya Gama son ransa sannan ya karasa wankan ya fito ya barta a ciki,Saida ta kimtsa kanta sannan ta fito, lokacin har ya shirya cikin wasu kananan Kaya Yana daura agogo, tsaye tayi a kofar toilet din ita Bata koma ba ita Bata karaso inda yake ba, kallon kasa kasa take masa gani tayi gaba Daya ya canza Mata kamar anyi musanyarsa da wani ya Kara zaman wani handsome dashi jikinsa ya Kara Zama fresh dashi. Inda take tsayen ya nufa "pls ki shirya Ina son fita ne wurin after zuhur". Kofa ya nufa ita Kuma ta nufi gurin mirror tana goge jikinta, hand dryer data gani a gefen mirror ta dauka ta jona ta busar da kanta, cikin kankanin lokaci ta shirya gurin kayan ta nufa tsaye tayi tana kallonsu. To Wai ita Nan din Ina ne gidan waye taga ya shigo ya barrarraje Yana tsula sha'aninsa ga kayan Mata birjik Kuma ance mamallakinsa ko aure beyi ba to Ina ba"asin kayan nan na can part din Aunty Rukayya tace nata ne to wannan fa na waye su kuma? Qundunbala tayi ta dauko wasu English wears, ta saka masu kalar brown dark sai veil milk colour tayi rolling ta fesa turarenta dake cikin handbag dinta sai lokacin taga maganin da Hajiyar makwarari ta bata, Dan murmushi tayi a zuciyarta ta ayyana "zanzo na Baki hakuri Hajiya nasan ban kyauta Miki ba dole ce tasa na aikata hakan". Dakin ta Fara gyarawa ta cire bedsheet din ta duba gurin da take tunanin zata iya ganinsu ta duba. Very luckily ta gansu ta Ciro Daya ta baza zata Fara shimfidawa ke Nan ya shigo dakin Yana waya, da hannu ya nuna Mata ta taso, ba musu ta taso ya nufo inda yake hannunta ya kama ya nufi kofa wani Abu kawai ya taba daga can kasa kofar ta bude, da kallo ta bishi tana mamakinsa gaba Daya ya canza Mata Kuma yanda yake mu'amala da gidan Yana Bata mamaki, har suka fito parlour na biyu Yana ta wayarsa wadda ta fuskanci kamar suna maganar kasuwanci ne sabo da aka Riga aka fara, direct dining ya nufa da ita Saida ya zaunar da ita sannan ya zauna. Wani Dan guri ya danna jikin table din, ba'a Jima ba saiga wani saurayi ya shigo ta wata kofa. Baiyi magana ba tun bayan sallamar da yayi Zahra ta amsa masa, wayar ya kashe ya juyo Yana duban Wanda ya shigo din. " Safwan Kada naji labarin Ina garin nan a bakin kowa, kaje inda na turaka jiya?" "Naje oga komai ya Zama normal, harma sun Fara aiki saidai Zayyan yace wannan Matar tana yawan zuwa kusa da gidan amma dai Bata karasowa take komawa". "Ok ba damuwa kaje kawai idan ka dawo ka taho da fresh milk da fruits a saka a kitchen din nan". "Ok sir, na gode ya juya ya nufi inda ya fito har ya danyi nisa yaji maganar Mahmud. "Safwan banji ka gaishe da madam ba, bahaushiya ce ba wani yaren zatayi makaba, Naga alama saina miqaka makarantar koyon turanci tunda Naga shi kadai ne kake da matsalarsa". Dan Sosa Kai yayi yana dawowa baya. "Afuwan Auntyn mu wallahi na dauka bakijin yaren mu, Ina kwana?" "Lafiya kalau ya aiki?". "Alhamdulillahi Auntyn mu, Allah ya Kara sutura ya bar Mana ke a gidan oga Dan isar Annabin Rahama". "Amin ya Hayyu Ya Qayyum". Muhmud ya fada. Hanya ya nuna Masa alamar ya wuce bai Kara tofa wata maganar ba ya juya yabar gurin. Ita Zahra kallon ikon Allah takeyi wallahi wannan ba Wanda suka zauna a Azare bane da banbanci nesa ba kusa ba. Iskar Bakinsa ya hura Mata a fuska saitin idanunta, "kallon na menene Kona canza Miki ne? Kika tsareni da wadannan eyes din naki masu hanani sakat idan Ina kallonsu Dan Allah ki barni naci abinci kome kike bukata saina Baki badai kin hanani zaman can ba, to aini gaba ta Kaini gobarar Titi a jos, haka ake fada ko?" Ya tambaya Yana bude abincin. Dan kwabe fuska tayi tana Dan turza kafa a kasa. "Ni wallahi bani nace ka dawo ba kawai Kaine kayi niyya da kanka ka dawo Ni ba ruwana to na kiraki nayi maka me?". "Au haka Zaki ce shike Nan yanzu dai bani abinci daga baya sai kiyi min bayanin yanda aka haihu a ragaya". Bata gane hausar tasa ba tayi Shiru dai kawai. Abinci ne kusan kala biyar Banda pepper soup na turkey. Kasa hakuri zahra yayi Wai daga Ina wannan abincin irin haka?" "Daga jama'ar Annabi, kinsan mu 'ya'yan malamai ko Ina muka sauka gida ne". Shiru tayi ta zuba Masa abincin zata Zuba nata ya dauke plate din. "Kin manta ai ba raba Abinci a tsakaninmu muci kawai". Tare sukaci abincin suka Gama, tana Dan kallonsa lokaci-lokaci, da gaske yazo Mata da abubuwan mamaki da yawa Amma azarbabi ba nata bane. Dole tabi kamai a hankali saida ya tabbatar ta koshi sannan ya saurara mata, Nan cikin parlourn suka dawo suka zauna ya dorata a cinyarsa yasa hannunsa ya zagayo cikinta yana ta faman amsa wayayoyi, sai ya amsa way kamar uku, sannan ya aje ya fuskance ta. Wasu irin wayoyine guda uku Wanda ita dai sai a T.V take ganinsu amma sai gasu a hannunsa kuma ya wani ci magani Dan kada ta Tama Fara masa wasu tambayoyi. ' "Bani labari ya akayi ciwo Bai tashi kamaki ba Saida nayi Nissan Zango, naji doctor tace Wai rashin samun biyan bukata ne yake kawo miki yawan ciwon marar saboda sha'awarki tana motsawa Baki samun biyan bukata". Waro Idanu tayi Baki bude tana Masa wani kallo.."Ni kuma? Wane irin magana ce wannan bayan fibroid din Kuma harda bita da kullin sharri? ta Nan Kuma ta bullo? To ai sai tazo ta ta cire min sha'awar tunda ita ta ganta, kawai ta Fadi gaskiya tanaso tayi amfani da aikinta ta cuceni,tunda da hadin bakinka Ashe ni aka mayar sakarya aka tasoni tunda daga kauyen mu aka kawoni gurin budurwaka ta dubani,ta ganeni ciki da bai kaga ko idan ta aureka bani da wata fuffuka da zanyi Mata, wata Kila da Allah baisa ta fito da maitarta fili ba da Allah kadai yasan illar da zatayi min.Da Jin saita cire min mahaifa gaba daya, ka fada Mata wallahi da gatana Ina da gatan da wallahi ta cutar da lafiyata Saida ta kare rayuwarta a life in prison, kuma indai Kaine nabar Mata taje ta hadiyeka kada wata ta Kara ganinka tace tana so, an fada Mata Ni Ina da damuwa ne da zata ringa wulakantani in dai saina Kara zuwa ta dubani ciwon yayi min abinda Zeyi min Kuma yau in Sha Allah gida Zan koma bazan iya Zama a Nan ba Ni duk kanon ma ta fice min daga Rai, ka mayar Dani inda nafi wayo". Ta karasa fada tana juyar da fuskar ta gefe. Kwanto da kansa yayi gefen wuyanta. "Cewa fa nayi ki bani labari ba cewa nayi meye damuwar ki ba, Ni meye laifina daga na turoki a duba min lafiyarki". Ai fadar hakan saiya tunzurata nan da nan sai hawaye. "Oh! My God!, Mena fada Kuma? pls tell me". "Kwace Kanta ta shiga yi tana fadin. Daman nasan ba Sona kakeyi ba tunda Ni matar shige ce Bata da daraja kuma wallahi duk Wanda ya Zama sanadin da wannan gararin rayuwar ya sameni ban yafe Masa ba, da qimata da mutuncina an mayar Dani wata shakatafi kowa saiya takani yanda yaso bani da wata qima". Ta sunkuyar da kanta tana wani kuka Mai cin zuciya. Iya dagula lissafi tayi Masa Dan kasa cewa komai yayi sai sakata da yayi a jikinsa ya kwantar da ita shi kadai yasan abinda yakeji, suna haka yaji wayar Daya Bari a kunne wadda yake amfanin yau da gobe ta dauki kida Mai Dadi. A hankali ya Kai duba gurin wayar, Sameer ne. Dauka yayi baice komai ba "Ina kofar part din Nan kana da bakuwa". "Dude ka shigo sai muyi maganar". Ya kashe ya aje wayar, Jin ya ambaci Sameer ya shigo yasa zahra yayi kokarin zare jikinta amma Dan bawan Allah nan kememe yaki sakinta saiya gyara Mata Zama kawai. Dago Kai tayi da niyyar yi Masa magiyar ta saketa ta tashi dai dai lokacin Sameer ya karaso gurin, be taba tunanin tana jikinsa ba tunda shi kadai ake hangowa Saida ya kure musu yanda ba yanda za'ayi ya koma, tsaye yayi shi Bai Kona ba shi Kuma be karasa gurinsu ba ita kuma Zahra kunya kamar ta nutse wallahi Bata taba tunanin rashin ta idonsa ta Kai har haka ba. "Have a seat, kazo ka tsaya Wai kuka take min na kawota an Mata wulakanci na Maida ta gida ita ko sunan Kano Bata sonji". Sameer 'yar dariya yayi "Ni ba ruwana a ciki Dan aikene ni kasan Mata Dan Abu kadan saiya tada musu hankali, Daman bakuwar tata ce Hajiyar makwarari ce ta kirani bayan nabar Nan Ina gidan mommy na mayar da Rukayya saiga kiranta Wai lallai saina daukota tazo taga madam shine mommy tace na kawo ta indan ba haka ba zata iya rikita lissafin kasan halinta dai". "Ok ba damuwa ku shigo tare ai Hajiyarmu ce ba inda bazata shiga ba". "Ok sir". Ya juya ya fice daga parlourn da sauri,mamakin Mahmud ne ya kamashi sosai ya rasa wane irin so yake yiwa yarinyar Nan ne haka? Yana tare da wannan mezeyci da wata Haseena ai saidai tayi hakuri da can Bata you tasiri ba gurinsa ba bare yanzu daya Sami abinda ya kwallafa rain a kansa. Zahra Jin Sameer ya fice yasa ta dago da kanta daga kijinsa tana ajiyar zuciya, Dan just tayi kukan ta Kama nasa guri sai mamakin furucin oga Sameer daya cika Mata zuciya wai sir to me hakan ke nufi itafa kada su manna Mata Dan karamin hauka gaskiya. Dan Allah ka barni na tashi kaji fa Hajiya ce yace fa Zata shigo, Kuma Dan Allah bakaji kunya ba ka wani sakani a jikinta salon yace bani da tarbiyya". Wani kallo ya watsa Mata "ai yau ko waye ze shigo gurin Nan a haka ze samemu gara asan Ina sonki tunda kina ganin ba sonki nake ba har kina kallona kina fadin Wai matar shige ce ke idan aka sameni rungume da kayana Ina lallashi kuwa koya saiya sheda ina son abuna, nine dai ba Sona ake ba anfi son wannan Mai jan kamar karas tunda saboda shi aka yarfeni da bakaken maganganu". Har ta bude Baki zata bashi amasa taji rangada sallamar Hajiyar makwarari, ai ita kanta Bata San yanda akayi ba ta tsinci kanta a tsaye ballentana shi da ake zaune a jikinsa, shi dai Sameer Bai San lokacin da dariya ta kubce Masa ba ganin yanda Zahra tayi wani wuk'i-wuk'i da ita shima gogan dariyar yake Amma a ciki. Da sauri ta nufi Hajiyar tana fadin. Oyoyo -oyoyo ga Hajiyata ga Hajiyata". "Ke tafi can Ashe duk abinda na fada Miki ta bayan kunnenki ya wuce Saida Kika fice Kika barmu da tashin hankali, jiya kukan da nayi rabona da yin irinsa tun rasuwar mijina. Amma Kika sakani maimaitwa Dan Allah ke kuwa 'yar Nan Ina Kika tafi jiya". "Haba Hajiya Dan Allah haka mukayi da ke a gida kafin mu taho wato kin karya Alkawarin kenan? To a kazarki ta juma'a wallahi" Ita dai Zahra borin kunya ta Fara "Allah ya Baki hakuri nifa na fada Miki kawai dai yawan mutane ya Hana ki gane waye yake Miki magana, Amma yaushe zanyi Miki haka Allah naji maganar ki kinga yanzu ma Zan Sha maganin fa". Mahmud ne ya taso Yana fadin "Hajiyar mu ki shigo ciki ki fada min abinda ba'a so na sani Zan Baki abinda yafi kazar ma". "Yauwa nasan kafi da haka, kanaji jiya ne wata daukakkiya ta tadawa yarinyar Nan hankali Wai kome gareta a mahaifa bansan dai sunansa ba da yaren Nasara Amma dai da hausa muna ce Masa tsiron mahaifa Wai sai tayi Mata tiyata,haka kawai ta ragewa zukekiyar 'yar Nan kwaliti yo an yanka mutum tun baiyi haihuwar fari ba Ina labari, shine nace baza'a yanka ta ba ga magani Nan Tasha na wata Daya in Sha Allah ze narke, ai sai daga baya Rakiya ke fada min ita waccan din ta Dade tana sonka tun Kuna turai koba haka bane? Ja'ira taga yarinya danya Sharab zata zauce tayi Mata illah to Banda abunka yaushe zaka ce buduwarka ta duba matarka ai wauta ce babba, wallahi kada a Kara kwatantawa, shine fa yarinyar nan tayi Mana batan dabo tun azzahar muka nemi 'yar Nan muka rasa nayi kuka kamar Zan yada idona to me zamu fada maka daga kawo yarinya ace ta Bata a gidana wallahi in takaice maka labari sai goma Sha biyun dare aka ganota ta Janbulo gidansu kawarta, itama uwar da yake ta kirki ce sai tayi tunani ta Nemo uwarta a waya take tambayarta duk da tana gurinta ta haka akasan guduwa tayi daga gurina cikin dare suka daukota to kaji yanda magana dai take". Wani kallo ya yiwa Zahra Mai ma'anoni da yawa, sannan ya juya Yana kallon Sameer Wanda tunda Hajiyar makwarari ta Fara zuba ya sadda kansa kasa yayi Dana sanin kawota tafi cikin cikin masaki. "To shike Nan in Sha Allah za'a kiyaye yanzu kiyi hakuri bata kyauta ba za'a duba korafin, nima ita ta tasoni na dawo ba Shiri wallahi hajiya yarinyar nan rikicinta yayi yawa". "To ai tayi mini dai-dai ashe jikar tawa tasan kanta zo Nan Yar albarka". Gurinta tazo ta zauna a kasa kusa da kafarata tana fadin "Hajiya Ina kwana?". "Lafiya kalau ya jikin naki?" "Nifa yanzu lafiya ta kalau ba damuwar komai". Shima Muhmud Zama yayi kusa da ita da gani da shakuwa Mai yawa a tsakaninsu. "Hajiyarmu kwana biyu Shiru ko nemana bakyayi ko?". "Kaji kinibibi ta Ina Zan nemeka bayan kayi gudun hijira". Dariya ya kamayi har ya bawa Zahra mamaki Daman Yana dariya haka. Tashi tayi duk da Batasan Kan gurin ba Amma tana tunanin kitchen ne a cikin corridor din dake jikin dining area. Babban tray ta dauko ta sako ruwa da lemo da Madara da plates ta dauko warmer din da aka zuba pepper soup din turkey din ta nufo parlourn ta dire cener table dake gaban Hajiyar tana fadin gashi Hajiyata ki Sha ruwa kafin nayi Miki girki yau fa a Nan Zaki wuni tunda oga ya dauke min Aunty Rukayya ko sallama bamuyi ba". Inda Sameer din yake Hajiyar ta kalla "baka kyauta ba ai sai suyi sallama Mana kaga bataji Dadi ba". "Ai zata dawo tunda zamuje Azare Nan da jibi". Zahra na son taji ba'asin za'a tafi a barta Amma ba hali Dan tunda suka shigo ta kasa had'a Ido da Sameer da gaske ba karamar kunyarsa takeji ba. Fita sukayi dare suka bar hajiya da zahrar. Hira Hajiya ke Mata sosai tamkar sun shekara da sanin juna, taci Naman sosai Tasha madarar tana fadin "irinta muke Sha a makka laban kuke cewa ko tunda Sameer yace min mamarki balarabiyar Jordan ce ko?" "Eh 'yar can ce". "Ikon Allah ke Kuma Allah ya kaddaro naki mahaifin a wannan nashiya tamu, ai Sameer ya bani labarinki batun yanzu ba tun lokacin da mijinki ya kaini jidda akayi min aikin Ido da yaga wata yarinya diyar larabawa yake bani labarin ya ganki a jirgi keda wani mutum ko mahaifin ne ko Kuma dai mariki ne basu ba, Saida za'a daura Aurenki yazo yake dauko min tsohon zancen harna gane nace nasa a Ina suka laluboki yace min ikon Allah ne ya hada ku, daga Nan ban Kara ce masa komai ba, Fadima ki rik'e mijinki da kyau Yana sonki yanda Baki zato tun Baki San meye so ba yake Miki shi, kingan shi nan tun suna makarantar sakandire suke tare da Sameer Bai yadda shi ba, da Allah ya daukaka shi saiya Kara janyo shi jikin shi duk inda ya saka kafa Sameer yake aje tashi, duk abinda Sameer ya mallaka mijinki ne sila komu iyayensa da kakanni muna cikin cin arzikin". Zahra abin jinsa take wani bai-bai me hakan yake nufi ne wai? Ana nufin Mahmud ne ubangidan Sameer ko me ake nufi? Lallai biri yayi kama da mutum duba da yanda suke rayuwa a Nan daga lokacin da sukazo garin zuwa yanzu kusan umarni ne oga Sameer yake karba kawai kasa hakuri tayi Saida ta tofa tata tambayar. "Wai ni Hajiya waye Mai gidan nan ne? na Ya Sameer ne? ko kuma na wani abokin nasu ne? Naga ya sakar musu ragamar ko Ina na gidan Baya tsoron abinda zeje yazo,nifa tsoro ma yake bani kamar baza'a mutu ba gaskiya ya mayar Dani gida inda nafi wayo, anan mutum saiya shagala da duniya wallahi". Baki Hajiyar ta rike tana yiwa zahra wani kallo. "Amma yarinyar nan lamarin ki da sauran gyara, gidanwa ze daukoki ya kawo idan ba gidansa ba, yo wannan ai Bai kama kafar gidajensa na sokoto da Abuja ba, ni duk naje Kinga na Abujan,? ganin likita naje lokacin Ina ciwon kafa, na sokoton Kuma bikin kanwarsa wadda take a can Germany mukaje, wannan mutane da karamci suke, gashi kinyi sa'ar suruka Hajiya zainab Bata da damuwa ko kankani" . Tsai Zahra tayi da ranta Kenan da gaske shi Dan Sokoto ne kamar yanda ya fada Mata sannan da gaske sunan Babar tasa zainab din Kennan lokacin da take fadar iya Abu yace ta daina fada gatsal sunan surukarta ne ta dauka Wasa yake Mata wallahi kenan duk abinda ya fada ba joking a ciki. "To ai shike nan nayi zaton ko gidan na wani ne muka Mike kafa a cikinsa".. 'Ko alama ranar dasu Hajiya Inna sukazo ai nayi zaton fa a Nan zasu kwana gurinki sai Kuma suka juya surukar Taki ce Bata samu zuwa ba sai ita kakarsa da matar kanin mahaifinsa, ki yiwa Allah ki taushi zuciyarsa yayi hakuri ya koma gida tunda Naga alamar kece Zaki iya wannan jahadin, wani irin fushi yayi da kowa har Amminsa abin ya shafa ranar da nace Miki su Hajiya innar sunzo Saida Tasha kukanta a dakina, wallahi Banda idan na Fadi ga inda yake abin ze iya shafar tarensu da Sameer da saina fada musu kodan samun kwanciyar hankalin Ammin tasa tafi kwanan watanni Bata gidan ubansa saboda rikicin da akayi a gidan yanda mijinki ya fice yabar gidan itama ta fice ta bar musu gidan, abunfa Babu dadi kiyi wannan aikin ladan Dan Allah ko an samu kwanciyar hankali a zuri'ar su. Ita dai zahra Banda gyada Kai babu abinda takeyi, Dan ji tayi abin yafi karfin dan karamin tunaninta. [2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH Page 46. _______Sun Jima a gurin suna hira da Hajiyar tana Kara Bata labarin taren Sameer da Mahmud, anan tasan mamansa 'yar Niger ce Kuma cewa shi din da gaske twins ne su kamar na Ammah mace da namiji. Suna nan suna hira har aka Kira sallah, da sauri Zahra ta tashi tana fadar "Hajiya Kinga guri Yana neman kurewa ban Dora miki abinci ba ko". "Kinga dawo ki kaini inda zanyi alwala nayi sallah Banda kinibibi ki wani ce Zaki dafa min abinci, to Wanda Rahane da wannan yarinyar Dana gani akace tare kuka taho da ita Wanda suke faman aikinsa kuma ayi iri dashi? Ina fada Miki ki nutsu mijinki yawa ke garesu Kuma duk cikinsu mijinki daban ne sai kin koyi kamewa da gaske sannan Zaki fuskanci yanayin kowa Ina ke Ina wani dorawa Baki abinci banqiba dai in mijinki Zaki ringa yiwa wannan ba laifi,amma ba kowanne karabiti ba kice Zaki wani kama rawar jikin yi Masa, mujeni ki nuna min nayi dahara kafin a shiga sallah". 'yar Jakarta ta hannu ta daukar Mata suka nufi bedroom din da suka kwana. Saida ta rakata har cikin toilet din ta nuna Mata duk abinda ya kamata sannan ta fito, sallaya ta shimfida Mata sannan ta karasa gyaran gadon da Bata Ida ba dazu ta saka freshner ta Daki ta rage karfin A/C din dakin. Hajiyar ce ta fito tana fadin "Ina dalili komai ya Zama na tab'e tab'e sai mutum yasha wahala kafin ya tantance yanda za'ayi" Dan murmushi Zahra tayi "Haba Hajiya me yake da wahala saboda Allah?" "Babu Miko min gyalena nayi sallah naji kamar an tada sallar" Hijabin ta Mika Mata tana fadin "Bari naje na dawo ta nufi kofa ta fice. Gaba Daya ta fice daga part din, ta cikin barandar Nan tabi ta shiga babban part din, ko Ina tadal sai sanyi da sansanyan kamshi ke tashi Nan ma wani bangaren ne daban da gyar ta gano inda ta kwana saboda duk gurin shine parlourn da yafi kankanta Amma yafi sauran tsaruwa, a hankali ta bude dakin ta shiga yana nan yanda tabar Shi direct bedside din ta janyo wayar na Nan yanda ta ajeta Saida kudin America dollars data gani a ciki shiya Bata mamaki Daman dasu a ciki ta saka ko Kuma daga baya aka aje Dan tab'e Baki tayi tunda ba matsalarta bace, gurin mirror taje ta dauko kayan da Aunty Rukayya ta saya Mata ta dauko luggage dinta ta zuba kayan ta duka ta fito daga ciki, a nan parlourn ta aje luggage din ta wuce ta ratsa duk parlours din Shiru ba motsin kowa, ta nufi inda su Aunty zilai suke Nan ma shiru, ta dawo kitchen Nan ma shiru abin ya Bata mamaki to suna Ina ne? Hanyar fita ta nufa sai Kara jinjina maganganun da sukayi da Hajiya takeyi abin yayi matukar daure Mata Kai shin abinda Hajiyar makwarari ta fada haka yake ko Kuma rudun tsufa ne kawai. Cikin sa'a tana fitowa ta hango iya Rahane ta bullo ta bayan wani gini da wani babban basket a hannunta, ganin zahra yasa ya tsaya tana fadin "ai Daga can nake nayi zaton ko tare kuka fita Maida Hajiyar makwarari da shiga naji Shiru a gurin naku". "A'a Iya Ina nan Hajiyar ma tana nan sallah takeyi Ina wuni? Wallahi tun dazu naso fitowa to saiga Hajiya ita ta zaunar dani sai data shiga sallah na fito". 'yar dariya Iya Rahanen tayi "Lafiya kalau ya jikin naki? Sai Kuma ga Uban gidan mu yayi Mana zuwan bazata ko? Masha Allah, ai Hajiyar sai ku kai almuru Bata gaji ba kin Sha labari dai Kam". "Lallai kam nasha hira, Wai Kuna Ina ne? Na duba banganku ba a can". Rike Baki tayi kamar yarinya " ke! 'yar Nan ki rufa Mana asiri, Banda dalilin wadalilatan Ina mu Ina kwana a bangaren yallabai, tun sassafe muka dawo nan kafin Rukayya ta tafi, Bari na yiwa zilan magana ko?". "A'a mu shiga kawai". Tare suka karasa shiga cikin bangaren. Masha Allah guri ne Mai kyau tamkar gidansu na Azare abinda ya banbanta su kalilan ne tunda wancan Renovation ne,wannan Kuma haka aka tsara shi sai banbancin furnitures kawai, nan ma question mark tayiwa abun. Jin sallamar zahra yasa zilai fitowa daga kitchen din tana fadin "Masha Allah, wallahi jiya ban samu kwanciyar hankali ba Saida Rukayya ta shigo tace min kin wuce Daki kin kwanta har Ammah na Kira na fada Mata Baku dawo ba, tace min na kwantar da hankalina ba komai tunda bake kadai Kika fita ba, Kuma sai muka wayi gari da zuwan yallabai? Ai ya shigo shida oga Sameer mun gaisa". "Eh wallahi muna cikin gari gidan Hajiyar makwarari kakar oga har dare, kunyi waya da Ammah kuwa yau?" Saita share zancen Mahmud din. "Eh mun gaisa tun wurin karfe shida na safe har take tambayar ya jikin naki tunda wayarki Bata shiga, nace mata da sauki amma dai kun wuni a Asibiti Dan sai wurin Sha biyun dare kuka dawo". "Ok.ba damuwa Bari na bude wayar na kirata sai yanzu na dauko wayar, Bari na koma na baro Hajiya tana sallah inaga yanzu ta Gama kada ta jini Shiru amma dai Zaki zo can din ko?". Ta fada tana mik'ewa tsaye. Zaro Ido tayi Kamar wadda taga abin tsoro. "A'a wannan fa Daya ai jiya ba yau ba, sai dai In da abinda za'ayi Miki ki fada min ta waya sai nazo nayi Miki". Sallama ta yiwa Iya Rahane suka fito tare da Zilan, Saida sukayi nisa sannan zahra ta tsaya itama Zilan tsayawa tayi. "Aunty zilai me Kika fashimta daga lokacin da mukazo zuwa yanzu?" Zahra ta jefa Mata tambaya. "To abin ne da yawa gaskiya, Dan ni lissafina ya kwance gaba daya wallahi na rasa tudun dafawa Amma dai komai rintsin mijinki shine ke Jan ragamar gidan nan Dan dazu lokacin da oga Sameer ya kawo Hajiya naji suna magana da wasu ma'aikatan gidan Nan akan oga yayi zuwan bazata, sai Kuma lokacin Daya fito a can gurin Naga ya Tara su yana magana dasu oga Sameer Yana gefe harya gama oga Sameer ya rarraba musu kudi muma har ya aiki wani Wanda Naga ya shigo da waccen babbar motar ya kawo Mana dubu ashirin ashirin nida iya Rahane". Ajiyar zuciya zahra tayi tana duban bangaren motocin hango motarta tayi a cikin parking lot din, kenan a Nan ya ajeta ko kuma jiyan yazo da ita Nan Dan kamar Bata ganta ba jiya, rausayar da Kai tayi tana wani tunani kafin tace. "Muje kawai Aunty zilai mu zuba idanu a hankali gaskiya zatayi halinta, nifa duk hankalina ya koma gida Amma naji yana fadin zasuje Azare jibi za'a dawo min da Aunty Rukayya, Kinga ba zancen komawar mu kenan, ni Kuma abinda bazan yarda ba kenan ya ajeni a wannan gjdan da bansan asalinsa ba gashi Nan Kashi-kashi kamar gidan marasa gaskiya". "A'a kada kiyi haka ki Bari kiga iya gudun ruwansa Mana nasan dai baze cutar dake ba, to kiyi Masa biyayya a duk abina ze umarceki matukar Bai sabawa shari'a ba,kiyi hakuri wata rana ma garinsu ze koma sai kice bazaki bishi ba? ai shi aure ba inda baya Kai mace, ki duba Maman Akwanga kin taba cewa tayi rayuwar Azare". Haka zilai ta dunga tausar zahra har suka shiga part din da suka zauna Zahra ta dauki luggage dinta Zilan ta karba suka shiga ta ciki suka fito barandar nan zilai sai mamakin abin take Bata taba tunanin da wani ginin a bayan wannan ba, Bata Gama sarewa da lamarin ba Saida suka shiga ciki, a parlourn farko suka tarar da Hajiya ta rabsa uban tagumi ta zubawa kofa idon suna shigowa ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Haba 'yar Nan daga Bari na dawo Kika nemi gurin Zama Kika manta Dani saboda Allah kin kyauta min kenan? duk sanyi ya game min jiki har attishawa na Fara nasan mura Kuma sai abinda hali yayi kawai". Da sauri zahra ta karasa kusa da Hajiyar tana fadin "Ayya wallahi nayi tunanin ko zakiyi nafilfili ne fa shi yasa na fita dauko wayata da kayana Dana Bari a wancen dakin, taso muje kici abinci kinji Hajiyarmu insha Allah bazakiyi mura ba, Aunty zilai Naga da kaji a can bangaren inda muka fito kiyi Mata irin pepper soup din da Naga kin yiwa Inna maimuna lokacin tana mura, ko a soya Mata ta tafi gida dashi". "To in Sha Allah Bari naje ai kayan dazu wani mutum ya debesu ya mayar kitchen din part din da muka koma harma an karo wasu kayan masu yawa mun shafa'a mu nuna Miki su". Ta fada tana mik'ewa ta nufi kofa ita Kuma zahra ta nufi dining ta daukowa Hajiyar abinci. *** *** *** Tunda garin Allah ya waye Mama ke faman Kai kawo a cikin Daki ta Kai gwaro ta Kai mari, tun bayan wayar da sukayi da Aunty larai hankalinta Bai kwanta ba sai yarfe gumi takeyi baji ba gani, ta Kira wayar Asabe yafi Shurin masaki amsar Daya ce switch off. Wannan wane irin Abu ne Kullum tana tubkar gaba baya na warwarewa, Wai ita wannan Matar meta taka ne, duk abinda takeyi ya tashi a banza Kenan? Tun bayan kaiwa Mai gadi sakon Nan Basu Kara samun damar shiga gidan Nan ba ko kofar ma tafi karfin zuwansu gashi yanzu Kuma aunty larai tazo Mata da wani Abun d'aga hankalin ga sako Amma isar dashi shine aiki ga wayar Asabe Bata shiga da sai ta Kai ko ta bayan gidan ne ta jefa abin bukatar dai ya shiga gidan ga sakon ya taho daga Jos din Kuma ance ba'a son ya kwana ba'a aiwatar dashi ba, akwai matsala Dan ze iya warware duk ayyukan baya, kuma wani aikin ze iya yin kome a Kanta ko 'ya'yan ta shine ta tada hankalin ta, tunda tasan idan tayi sake kwabarta ce zatayi ruwa, tayi tunanin ko sahura zata aika Tasha ta karbo sakon idan yaso sai tayi Mata bayanin yanda zatayi da sakon idan ta Kai can gidan zahrar, tayi tunanin ko zilai zata Kira tace Mata ta fadawa Zahra sahura zata je tayi musu share-share kafin su dawo, Nan ma taga abun ba lallai ya yuwu ba. Kara Kiran Asaben ta gwada still dai a rufe, dangwarar da wayar tayi duk abin duniya ya taru yayi Mata yawa. Duk iya tunanin ta ya Kare ta rasa Ina ne mafita dole ta tashi ta fice daga dakin tana tunanin dole ta tura sahura taje ta Kirawo Mata Asaben in ba haka ba tasan watan Jin kunya ne yake neman Kama Mata. Wannan kenan. Tunda Ammah ta fita daga bangaren Abban take kokarin neman zahra Amma Shiru har bayan Azzahar inda taji Dadi da zilai tace Mata zahrar a gidan ta kwana Kuma Mai gidan ma yazo, tasan kome ne ne zezo da sauki. Banda kada yaron Nan Sameer yaga Kamar ta raina abinda yakeyi da yanzu ta tsufa a Kano, sakon text ta turawa zahrar ta tashi ya nufi bedroom dinta. **** **** **** Tun bayan fitar zilai zahra ta wuce bedroom tabar Hajiya nacin abincin ta, a gurguje ta sake wanka ta gyara jikinta Bata wani Bata lokaci ba ta shirya cikin wata doguwar Rigar lace cotton Mai kalar blue black, anyi touching dinsa da silver ash yayi Mata kyau sosai.Bata daura dankwalin ba rolling tayi da ash din gyalen ta feshe jikinta da turenta ita abin har mamaki yake bata, ta rasa yanda akayi duk inda take sai taga turaren da take amfani dashi a gurin. Dan watsa hannu tayi irin baka gane Abu ba din nan. Parlourn ta koma gurin Hajiya dai dai lokacin da su Sameer da Mahmud suka shigo. "Bakin Hajiya ne yaki rufuwa data hango zahra ta nufo ta Fadi take "Masha Allah! Haka ake so wwnnan 'ya naga alama bazakiyi saken da za'a karbe miki miji ba, ki Kama abinki ki rike wallahi sonsa akeyi kamar goron hannun sarki ki matse kayanki tunda Allah kadai yasan gwagwarmayar da yasha kafin ki shigo hannunsa..." Sameer ne ta katse Mata hanzarin zancen data dauko ya Fara fadin "ki tashi na mayar dake gida garin Zan Bari yanzu Banda kina Nan da nayi nisa a Hanya". Shi kuwa Mahmud Banda kallon zahra ba abinda yakeyi gani yayi ta Kare Masa wani sanyin kyau a idanunsa, Kuma fir Taki yarda su hada Ido dasu duk kowa da kalar kunyar da takeji tasa. "Hajiyarmu ya zaman guri Daya nasan kin gaji sosai ko". "Mahmud din ta kalla Wanda ya nufo ta. "A'a ban gaji ba ai wannan yarinyar da Abun gari take, jiya ma dai an Bata Mata Rai ne yasa na ganta Kamar marar wayo Amma yau ai ka gani sai Ina taka saka Dani takeyi". "Dan Allah ki taso bana son nayi dare a hanya ke Kuma kin tsaya sai maimaita zance kikeyi, abinda ya wuce ai ya wuce". Da sauri Zahra ta juya ta koma ciki ta barsu Sameer nata yiwa Hajiyar Dan zance, turarika da sabulai ta daukowa Hajiyar ta fito, lokacin Hajiyar na gyara lullubin gyalenta tana fadin "ai Zan dawo ne tunda ban karbo Mata dawa'in Dana saka ayi Mata ba a sanka, Kasan duk wannan jidaliyar ta jiya Bata Hana da almuru Saida Tofeek ya kaini Sanka naje na fadawa Malam karami ya taimawa jikata da maganin tsarin jiki Dana Baki, yo anyi sake Baki ya Kamata dubi fa yanda take tubarkalla, yo tunda ya fito da ita Nan ai magana kuma ta gare haka ze dunga reto da ita,to kasan wani idon da bakin ba masu kyau bane, shi yasa gara a dafata daga Nan" shi dai mahmud ban kunshe dariya ba abinda yakeyi yasan kadan da aikin Hajjaju ne hakan, shi Kuwa Sameer ya cika yayi fam shi yayi Dana sanin kawota gidan nan Dan Allah kadai yasan abinda ta fada Mata tunda kanwa Bata jiqa a bakinta. "Wallahi Zan tafi na barki a gidan nan haba saboda Allah kin kama zance kamar an saka Miki batir". Dakuwa tayi Masa ungo Nan. Dan nema kake wani zaro min Ido to tsoron ka zanji kome? wato gaskiyar ce baza'a fada ba". Juyawa yayi ya nufi kofa da hanzari Hajiyar tabi bayansa itama zahrar da sauri tabi bayan Hajiyar, ji tayi an riko ledar da hannunta gaba daya ya dawo da ita jikinsa. "Precious ba irin huge din Nan na welcome saiki wani shareni" Ya fada Yana Dan goga Mata sajensa a gefen kumatunta cikin wani irin low voice. Wani yar taji a jikinta. Cikin shagwaba tace "Dan Allah ya Bari na rakata kada su tafi ban Bata komai ba, Kuma na saka Aunty zilai ta dafa Mata nama". Juyota yayi suna facing din juna. "Baze tafi ba kawai ya gaji da surutun Hajiya ne itafa Bata gajiya da magana, kawo na gani dame-dame za'a bawa kakar tamu?" Ya fada Yana duba cikin ledar. "Inye ashe dai da wayonki irin wannan Abu haka? jazakumullahu khairan. Bari na Kara gyara Miki kudi ya Ciro daga aljihun wandonsa ya saka a ledar Yana fadin sai kice ta sayi man shafawa ko kice ta sayi goro, bari mu dawo ki bani abida ya samu, Kuma idan anjima Zaki rakani gidan su Sameer na gaishe da mommy sannan muje muga Mai sunana" . Bai saki hannun nata ba, a haka suka nufi kofar fita. Taso ta zame hannunsa daga cikin nata tasan ba Karamin aikinsa bane su fita harabar a haka, kuma taga alama gidan da mutane da yawa ga kuma Hqjiya da Sameer. Ganin kada ya Bata kunya yasa ya saki hannun ya rike ledar kawai kafin taje gurin motar ta shiga gurin su Aunty zilai ta gani ko angama. Cikin ikon Allah ta samu an Gama soya Mata cikin roba, Ashe Daman tun safe suka dafa aka saka a fridge yanzu soyawa kawai sukayi, a ciki babban warmer aka zuba zilai ce ta dauko suka fito suka nufi gurin da suke tsaye suna jiran zuwansu. Saida Motar tabar harabar gidan sannan suka juya suka koma, Saida suka wuce idanun jama'a ya janyota jikinsa Yana shagar kamshin jikinta, a haka suka shige ciki zame jikinta tayi tana Dan dubansa. "ga abinci Nan na kawo maka nan ko can table Amuje". Dan bakinta ya shafa kadan ka Yana kwaikwayon maganarta.. "Bari nayi wanka sai muzo muci abincin nasan kema bakici ba ko?". "Kai ta gyada masa. Gurin da Hajiyar taci abincin ta gyara sannan ta dauko wata table mat da shimfida a kasa ta jera abincin, gurin kayan kallo taje da gani ko hadasu ba'ayi ba, ta tsuguna tana hadawa ya shigo, yayi wanka ya saka Riga armless da wando three quarter blue black na kamfanin Adidas sai fitar da wannan kanshin nashi yakeyi wanda har ya Zama constant a jikinsa, direct inda take ya nufa dago ta yayi "oya taso kibar wannan ba aikin ki bane akwai Wanda zaya hadasu". Kai ta gyada masa ta bishi suka koma, abincin ta zuba musu sukaci Saida suka koshi, sannan ta tattara gurin ta dauke komai ta dawo ta zauna a gefensa. Jikinta ya Dan kwanto Yana Dan matsa kafadar ta. "Precious". Ya Kira sunan sunanta. "Na'am". "Fada min me Haseenar ta fada Miki Kika yi yaji Zaki Kira min Ruwa? Banda Allah yasa Ammah tana yina da kin tayar min da zaune tsaye, ni na taho Ina mararin ki ke kuma kina gudun Zama dani ko?". Sakin kafadar yayi ya kwantar da ita a cinyarsa suna facing na juna. "Nifa na fada maka ba guduwa nayi ba to a cikinsu ai ba Wanda yayi min laifin da zanyi yaji? Kuma Dan lalacewa na tsaya Ina yiwa wannan Mai saffar mazan yaji,kawai dai Naga bazan iya tolerating na nonsense dinta ba,wato zatayi amfani da damarta tayi min illah tunda Nina hanata cikar muradinta ki? Ai naji ance tare kukayi karatu ba a UK? Dan Allah ka fada min waye Kai wallahi zuciyarta taki samun nutsuwa, abubuwan da nake gani a Nan sun girmewa tunanina, pls tell me, Me amor". Tsuru yayi da Ido Yana kallonta Dan kalmar ta bashi mamaki data fito daga bakinta. "A ina Kika iya yaren Portuguese?". Ai Yana fadar haka ta bude Baki alamar mamaki da sauri ta yunkura zata fece ya mayar da ita jikinsa. "Ya haka Zaki gudu daga tambaya". "Nima bansan ko wane yare bane na fada sunan ne naji yayi min Dadi shi yasa na fada maka Ni ko ma'anarsa ban sani ba". Ta fada tana Kara sunne Kai a kirjinsa. "A'a idan ba Rami meya kawo zancen Rami? Meye na Jin kunya tinda kince Baki San ma'nar sunan ba duk da haka yau ranar Nan special ce a gurina badan da dutse tsakanin mu ba da Saina bada special gift Nima". . [2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI. ✨✨✨ MAMAN FATEEMAH. Page. 47 📖🖋️ ________Duk yanda Mahmud yaso zahra ta bashi amsa abun yaci tura da gaske take kunyarsa Bata taba zaton Yana Jin yaren ba, shima kyaleta yayi dan bashi da amsar tambayarta a yanzu dai sai hakan yayi Masa dadi, wata hirar ya dauko Mata ta tafiyar da yayi da ire-iren cigaban da yake ganin makarantun mu zasu samu, har aka Kira sallar la'asar suna gurin tashi yayi suka shiga ciki yayi Shirin masallaci. Misalin karfe takwas da kwata suka fito zuwa unguwar da zata raka shi, sunyi wata irin dacewa dole idan ka kallesu ka Kara, Dan kallonsa tayi "Zan leka na yiwa su Aunty zilai sallama". Daka ya amsa Mata saboda Yana amsa waya. A parlour ta iskesu suna Hira, a gurguje suka gaisa ta fada musu zasu fita, a dawo lafiya sukayi Mata ta juya ta nufi kofa har ta kusa fita ta ji maganar Aunty zilai bayanta. "Uwar dakina Ammah tace a fada Miki ki bude wayarki tana son magana dake, yanzu ba dadewa ta kirani tace na Kai Miki tawa, na fada Mata Mai gidan Yana Nan shine tace to idan kin fito na fada Miki lallai ki bude zakuyi magana". Dan rausayar da Kai zahra tayi da alamun damuwa a fuskarta. "Ni wallahi na kasa bude wayar ne laifi nayi Mata fa". "Laifi Kuma kina Nan tana can akayi laifin?" Kai ta gyada Mata alamar Eh. "Dan Allah ki bude wayar kuyi magana ko hankalinta ya kwanta,Allah a cikin damuwa take". "To shikenan sai mun dawo din". Ta fice tana amsa a dawo lafiyar Aunty zilan. Motarta daya kawo ta gani, Wanda ya Kira da safwan dazu ya fito daga ciki da alamar shiya kawota nan seat din kusa da driver Mahmud ya budewa Zahra Yana fadin "Bismillah" Saida ta zauna sannan ya nufo gurin safwan din yayi Masa magana sannan ya shigo ya tayar da motar suka nufi gate din fita, a dawo lafiya masu gadin sakayi musu Dan ba mutum Daya zahra ta gani ba. Sunyi tafiya Mai Dan nisa kafin ya riko hannunta Bai kalleta ba gabansa yake kallo yace. "Kina tambaya ta wannan gidan na wanene ko?" Ya Dan juyo Yana kallonta. "Eh" ta fada a takaice. "Gidan a hannuna yake, kusan Kuma ni aka wakilta a Kan ma'aikatan cikinsa to Yana yin rayuwa ne yasa nayi nesa dashi Amma yanzu bani da sabgogi da yawa Ina ga ma anan zamu Dan Zauna na wani lokacin kafin muga yanda za'ayi akan matsalarki ta fibroid din nan dan tunda aka fada min hankalina kasa kwanciya yayi Saida na Kira likitan dana fada Miki, shine yace ya kamata muje suyi nasu binciken su tabbar da abinda Nan din suka fada". Dan marairaice Masa tayi. "Nifa wallahi na warke na fada maka ba wani ciwo fa yanzu Dan Allah ka hakura, kaga su Ammah Basu San zamu Dade ba, kaga harda Mai aikinta ta bani aro fa Kuma kusan itace ma'aminciyarta a fannin abincin bangaren ta". "Kin warke kamar Yaya? Ai abinda ze Hana a duba min lafiyarki sai ikon Allah kinaji fa Yana Hana Mata haihuwa Ni Kuma da nake son duk shekara ki aje Mana baby koma babies, idan Allah yasa nafi ki karfin jini ki dinga bamu twins, kawai lokaci kadan ki ciki gidan da 'ya'yan mu". Ya fada Yana Kai hannunsa akan cikinta Yana kashe Mata Ido daya. "Oya talk Mana kinyi shiru". "To me kakeso nace ai ka Gama Yanke hukunci". Saita share maganarsa ta biyu. Gidan Sameer suka Fara nufa Sam Sameer din besan da zuwansu ba Saida ya kusa da shiga kuntau din sannan ya kirashi ya fada Masa gasu Nan zuwa. "Masha Allah gida ne shima Babba Mai kyau sosai Amma baiko Kama kafar inda sukayi masauki ba, da fara'a sosai Fateeha ta tarbi zahra wannan shine haduwarsu ta farko face to face ba karamin mamaki Fateeha tayi ba, duk da Sameer ya nuna Mata wani hoton zahra amma sai taga hoton Wasa ne akan zahirin gaskiya ba karya oga Mahmud yayi mace dai dai da level dinsa Dole 'yan bani na iya su dauki na wuta Dana gashi da ita, me wannan mezeci da irinsu Haseena. Da sauri ta garasa gurin zahrar tana fadin "maraba da babbar bakuwa irin wannan zuwan bazata? Ta mika Mata yaron da yake hannunta tana murmushi, itama zahrar murmushin ta mayar Mata. Cikin parlourn suka shiga gaba daya, gaishe da Muhmud din Fateeha tayi, yayi Mata barka, sannan zahrar ma suka Kara gaisawa da oga Sameer, taje ta Mikawa Mahmud Babyn. "Ki rikeshi a haka na ganshi, wallahi bana iya daukar Yara a haka tausayi suke bani, Sai naga kamar Zan karya su ne idan na dauke su".Ya fada Yana jifanta da wani kallo. Itama kallon nasa Zahra tayi da yi Masa alamar zakayi bayani da hausar garinku, tana Dan kada Masa sexy eyes dinta. A haka yayi masa addu'a ya shafa kansa, cheque ya Dora Masa a jikinsa abinda ta gani jikin cheque din ba Karamin mamaki ya Bata ba, shi Kuma Dan gogan Saiya fuske yayi kamar baiga kallon tuhumar data bishi dashi ba. Godiya sosai Fateeha tayiwa Mahmud ta dauki cheque din ta kaiwa Sameer, ba karamin mamaki yayi ba yana Kara duba cheque din Yana kallon Mahmud. Kai ya girgiza Masa "don't say anything pls shi yasa ban baka ba na madam ne wadda tayi nakudar haifar min takwara" Shiru yayi kawai Dan wata kyautar tafi gaban godiyar fatar Baki, a haka Fateeha ta wuce ta barsu tana kakabin abun a zuciyarta Wai shi wane irin kudi wannan bawan Allah ya mallaka Wanda baya Jin ciwon kashe da kyautar su irin haka?. Abubuwa motsa Baki Fateehar ta kawowa Mahmud, sannan taja zahra suka shige bedroom dinta. Kan sofa zahra tayi masauki tana rike da Ayyan sunan da ake fadawa yaron kenan, Fateeha na fadin " Masha Allah, Amarya kin Sha kamshi sai yau Allah yayi haduwarmu?". "Wallahi kuwa Aunty, barka Allah ya Raya Mana". "Amin ya Rabbi, nifa na dauka da Rana zakizo mu yini muna hira Amma sai naji sweetheart Yana fadar Wai gaku Nan a harya". Da gyarawa Ayyan riko tayi tana zame rolling din kanta. "nima bansan da fitar ba sai dazu da yamma yace zamuzo nifa naso ya barni nazo suna lokacin Amma yace a'a saiya dawo zamuzo". Har Fateeha ta bude Baki zatayi magana ta tuna gargadin Sameer akan sakin bakin magana yace ta iya bakinta akan abida Zata fadawa zahrar. "Kinsan komai nufin Allah ne sai yau ne ya kaddari mu hadu,munga sako Allah ya saka da Alkhairi yabar zumunci, Kaya irin haka kamar za'a bude Masa Boutique dasu, wasu ai har ya shekara biyar sannan yayi amfani dasu, Kinga wannan material din da Kika sako min me kalar peach wata sister dina da za'a yiwa biki ta kwallafa rai a kansa tana son tasa ranar dinner da taje kasuwa kasa sayensa tayi 350k 4yrd, saita gano na sayar Mata da nawa tunda suna gidan safwan ya kawo kayan". Ita dai Zahra Shiru tayi Dan ji tayi wani bambarakwai tunda ita dai bataga wasu Kaya ba, amma saita wayance da fadar "lah ba komai ai dan "komai nayiwa d'ana ban fad'i ba, Allah dai ya Raya Mana yayi musu Albarka". "Allahumma Amin". Knocking akayi daga waje, umarni Fateeha ta bayar wata yarinya 'yar matashiya ta shigo da babban tray da kayayyakin motsa Baki a Kai ta aje ta gaishe da zahra ta juya ta fice. Suna cikin hira Sameer ya Kira yace zahra ta fito zasu wuce. Har gurin mota suka rakosu suna ta godiya, jikin window din da zahra take ta Dan leka tana "Fadin zamu mu shigo in Sha Allah mu yini a gurinki tunda ni bakizo Mana da rana ba". "To ai ba laifina bane Kinga niba sanin garin naku nayi sosai ba sai a yanda akayi Dani". Dariya Fateeha tayi "to ai kin Zama 'yar kanon kema tunda gaki a cikinta Baki San ranar barinta ba". Sameer ne ya yiwa Fateeha magana ta yiwa zahra sallama, ta bude back seat ta saka ledar dake hannunta. Direct gandun Albasa suka nufa gidan mommy, zahra Bata tashi Jin abinda tayi da Bata kyauta ba Saida suka shigo harabar gidan mommy din. Dan marairaice Masa tayi da fuska a Karon farko ta riko hannunsa. "Please me amor ka shiga Kai kadai wallahi kunyar mommy nakeji bazan iya shiga ba". Ta fada a shagwabe kamar zatayi Masa kuka. Saida ya gyara parking sannan ya maido hankalinsa gaba Daya gurinta. Meya hadaki da mommy Kuma da kike Jin kunyar haduwa da ita?". "Jiya fa harda ita a gidan Hajiyar oga Sameer". Mai gadi ne ya karaso Yana gaishe da Mahmud tare da jera masa godiya wadda zahra Bata Dan isalinta ba, fitowa Mahmud yayi suka gaisa da Mai gadin,abinda ya tilastawa Zahra fitowa, gaishe da Mai gadin tayi ta Dan Fara tafiya duk da Batasan inda kofar shigar take ba. Gurin wasu kujeru data gani ta nufa ta zauna da alamar Kamar Baki ne suka tashi daga gurin. A Nan ya sameta ya Mika Mata hannunsa ta kama ya mikar da ita tsaye, "zo muje ciki dare Yana karayi kin zaunar damu a gurin Fateeha kome kuje fada ma oho Allah yasa dai ba gulma kujeyi ba". Kafin tayi yunkurin bashi amsa daga bayansu sukaji maganar Rukayya "lah wa nake gani kamar Ya Mahmud da Auntyn mu?" Da sauri zahra ta zame hannunta ta juya baya tana Fadin "wallahi Aunty Rukayya nayi fushi saboda Allah saiki taho bako sallama". "Ayya sorry wallahi Nima karfina akafi dole tasa na taho kinsan Ya Sameer ba sauki shine ya tattaroni ko wanka fa sai a gidan Nan nayi". Ta juya ya Mahmud Ina yini an dawo lafiya?". "Lafiya kalau Ruky ya kikaji da 'yar rigima Ashe Kuma yaji tayi muku ta gudu". "Wallahi kuwa ya Mahmud ai jiya nayi kuka kamar ba gobe tashin hankalina Daya idan ta B'ata me za'a fada maka idan ka dawo Ashe kana hanya". Baki zahra ta zubura tana kiftawa Rukayya Ido. Kafin yayi magana sukaji magana daga bayansu. "Waye nake gani kamar DANGEN SHUNI!?" Da sauri Mahmud ya juya itama zahra juyawar tayi Jin kamar muryar data sani ce take Fadin hakan. "Lah! Lah! Lah! Wa nake gani haka? Zakariyya Daman ana ganinku, rabon da mu hadu tun zuwana na karshen kontagora". Zahra ce ta Matso tana Fadin Lah Ya Abba, Kaine ina yini?" "Lafiya kalau ya kukaje gida? ai da safe na Kira Rukayya take fada min bakwa tare ta dawo gida". "Eh wallahi, yasu Umma?" "Suna lafiya daga Ina haka?" Dan kallon Mahmud tayi kafin tace Masa "daga gida muke Mommy mukazo gaishewa". Kusa da Mahmud ya matso Yana Fadin "DANGEN SHUNI! Allah ya taimaki manyan kasa. Daman ana ganinku haka available? Gaskiya na zama lucky. Daman wallahi neman number ka nakeyi nayi interview da kamfanin ku na Nan Kano last two weeks Amma har yau ban samu number ba, kasan lamarin kasar Saida wakasani,to ya akaji da jama'a?" . "Lafiya kalau Alhamdulillahi, Rukayya ki bashi number ta zamuyi maganar later, ko kana Shirin Zama sirikina ne?". 'yar dariya yayi "Hakan nake fata ai zuwan zahra jiya Ni Alkhairi ya zamar min". Dan Jim Mahmud yayi, me kenan zakariyya kenan brother din sajida ne? "Anyway we'll talk later in Sha Allah, madam let's go". Sukayi sallama da Ya Abba suka nufi ciki zuciyar zahra fal murna wato duk abinda Allah yayi akwai hikima a cikinsa, wannan dalilin ne yasa ta tattara ta nufi Janbulo Ashe ita zata Zama dalilin haduwarsu. Saida suka gulewa ganinsu sannan Ya Abba ya kalli Rukayya, "Daman Kuna da relation da DANGE?". "Eh aminin Ya Sameer ne tun suna secondary School, yanzu haka shine P.A dinsa ai jiya zahra da muka dauko daga can wife dinsa ce an samu wani incidence ne tayi tafiyar ta can Janbulo din". Baki sake yake kallon Rukayya abin jinsa yake kamar Almara badan ya gansu tare ba baze taba gaskata zance Rukayya ba, gaskiya he's surprised to ai shi ba haka maganar tazo Masa ba daga bakin sajida. "Wai kina nufin DANGE ne mijin zahra?" "Eh Mana shine, Wai Daman Kasan Ya Mahmud din ne?" "So sai kuwa farin sani, muna haduwa da a kwantagora a unguwa Daya ma kuwa, ai kakarsa ta wurin Babansa 'yar can ce Nima kakata 'yar can ce Ummar mu kadai ta Haifa a Rimin sumaila Aurenta ya mutu ta koma gida, duk 'yan uwan Umma suna can kwantagoran na Niger state da Abuja, kinsa meya daure min Kai kuwa?" Girgiza Masa Kai tayi alamar A'a. "Cewa fa akayi ita zahrar an aura Mata Almajirin wani malami da yake a unguwarsu saboda duk Wanda yazo ze aureta sai an fasa Auren" "Nima naji kadan daga labarinta gurin ya Sameer to ga dai mijinta Nan sauran bayanin Kuma ban San yanda akayi ya faru ba, tunda ya Sameer ba fada mana zeyi ba". A parlour suka Sami mommy da kannan Rukayya Mata Bilkisu da Husna sai karamar yarinya 'yar Auntyn su Sameer Afra. Tunda suka shigo zahra ke sadda Kai kasa da gaske nauyin mommy take ji, gaisuwar yaran suka ringa amsawa da gudu Afta ta nufo zahra tana Fadin "welcome Aunty" ta shige jikinta tana tattabata. Hannunta zahra ta riqe suka karasa gurin da mommy ke zaune yayin da su Husna suka koma dayan parlourn. A kasa Kan carpet suka zauna, a tare suka gaishe da mommy din, ta yiwa Mahmud sannu da dawowa sannan ta Dora da godiya, hidima da akeyi da Sameer. Zahra ta kalla ganin sai sadda Kai tajeyi yasa tace. " 'ya ta ko jikin ne Naga bakya walwala sosai?". Yana ji yayi fuska Bai tankaba ba dai iya shegen da tayi ba kenan jiyan saita magantu da bakinta. Bata yarda sun hada Ido ba tace. "A'a ba komai mommy lafiya ta kalau". "To Masha Allah haka nake son ji, kina jina ki saki jikinki Dani ki daina Jin nauyi na kinji, ni uwace idan kina da damuwa duk da bama fatan hakan ki sameni ki fada min ki daina yanke hukunci da kanki". "To in Sha Allah bazan qara ba na gode". Ta fada tana Wasa kitson Afra kanana Yar dasu. Tashi mommy tayi tana fadin "Bari na fadawa Alhaji kunzo sai ku shuga ki gaisa yaga 'yar tasa wadda bai sani ba". Ta nufi nufi wani corridor dake hannun dama. Bata dade ba ta dawo tana fad'in "Mahmud kuje Yana parlourn kasa". Saida aka yiwa Afra wayo da chocolates sannan ta yards tabi mommy dakinta ita Kuma zahra suka nufi bangaren Abban su Sameer din. A Nan suka same shi a parlourn Wanda yaji kayan more rayuwa dai-dai da shekarunsa, babban mutum mai cikar Kamala, fari sosai kamar irin buzayen nan, a Nan zahra ta gano inda Aunty Rukayya ta samo farin ta dan mommy dai irin wankan tarwada din nan ce shi yasa tayi mamakin Jin Rukayya kanwarsa ce uwa Daya uba Daya. Da madaukakiyar fara'a ta taresu Yana fadin "Masha Allah sannunku da zuwa, ka kyauta Mahmud daka kawo min yarinyar nan kaga na Riga Alhaji Muhammad ganinta ko? masha Allah ku zauna". Ya fada Yana nuna musu seat din Zama, basu zauna ba a kasa suka zauna suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska, da gani shi mutun ne Mai yawan fara'a. "Allah yayi muku Albarka ya kade fitina a tsakaninku naji Dadi kwarai daka kawo min ita, yarinya ayi hakuri da juna kinji, mijinki na jama'a ne Saida hakuri kiyi Masa biyayya gwargwadon iyawarki, Kai Kuma ka kula da lamarin ta kada ka yarda wani ya wulakanta maka ita amana ce suka baka, a yanda kaje musu ba kowa ne ze dauki yarinya kamar wannan ya baka ba, to ka kula da ita sosai ka Bata dukkan farin ciki tayi rawar gani, daga karshe Ina rokonka abinda ban taba saka Baki a cikin duk kwaramniyar da akayi a baya ba sai yau, kayi hakuri ka koma gida ba girmanka da mutuncinka bane haka ai ba'a fushi da iyaye duk rintsi albarkarsu ake nema kome ka Zama indai kana da iyaye yaro ne Kai, nasan an bata maka Amma idan ka duba ko tukwicin wannan yarinyar da Allah yayi Maka ai sai ka huce ka nuna godiyarka ga Allah Daya baka ita, Kai ba karamin mutum bane a kasar Nan Koda kuwa a shekaru kake da karancin girma, kaje gida ka hada hankalin ka guri daya, Allah yayi Albarka ya Kara daukaka numa ganin sakonni mun gode kwarai da gaske, idan Kuma naji Shiru baka koma ba da kaina zanyi abinda baka so ayi din, Dan ko shekaranjiya Saida Hajiya Inna Tasha kukanta a dakin Nan Ina amfanin irin haka ai musulmin kwarai da yafiya aka San Shi kaji Mahmud ayi hakuri ayi afuwa Allah yasa son masu yafiya". Tunda Alhajin ya Fara magana jikin Mahmud yayi sanyi da gaske duk badak'alar da akayi ko uffan Bai tofa ba sai yanzu Kuma yasan baya raba Daya biyu damuwar da yaga hajiya Inna a ciki ta Dame shi. Cikin ladabi Mahmud ya Fara magana. "Nagode Abba in Sha Allah Zan koma, Nima nayi wannan tunanin ba fushi nayi dasu ba sune dai sukayi fushi dani, Ina son su huce ne tukunna kada na koma a maido hannun agogo baya". "Kai haba wannan maganar ai babu ita to ai itama zahara'u ta zamar maka garkuwa, ki tashi ku tafi dare ya Farayi ga yanayin sanyi Allah yayi Albarka ayi kokari ayi yanda nace". "In Sha Allah Abba". 'yar karamar Leda Fara Alhajin ya mikowa Mahmud Yana fadin "ungo rikewa 'yata". Godiya sukayi Masa Sosai suka nufi kofa Yana saka musu Albarka. Lokacin da suka fito Rukayya ta shigo suna tare da mommy. "Aunty Rukayya har Ya Abban ya tafi?". Zahrar ta fada tana nufar inda Rukayyar take. "Eh ya wuce tun dazu". "Ok shikenan da sako Zan bashi gurin Ummah Amma na Kirata a waya". Sallama sukayiwa Mommy Rukayya ta rakosu har gurin mota da ledar da mommy ta bawa zahra kyautar dangin turaren wuta dasu humra. Da sukazo fita kudi masu yawa taga ya bawa Mai gadin gidan sannan suka wuce, tunda suka fito daga parlourn Alhaji Abban su Sameer Mahmud yayi dif da alamar anyi Masa famin wani Miki a zuciyarsa. Ganin haka yasa zahra ta Kama kanta itama. Titin gidan Bashir tofa suka fito gasu can sun fita gidan Buhari, sahad store taga ya shigo ya nemi guri yayi parking sannan ya bude Yana Fadi ki jirani ina zuwa ya wuce ciki. Bai Dade da shiga ba wata mota tayi parking kusa da tasu, gurin akwai wadatar hasken da yasa kana iya ganin Wanda yake cikin mota. Ba zato ba tsammani kawai idanun Zahra suka sarke Dana Musbahu Wanda ya fito daga gurin driver suna tare da wani Guy da alamar dayan irin ya'yan hutun Nan ne, da gani Suma sayyayar sukazo, da sauri ya nufo gurinta jikinsa har rawa yakeyi Yana fadin "Zahra!" dai-dai lokacin Kuma Mahmud ya fito tare da ma'aikatan gurin sun dauko Masa Kaya sun nufo motar, shi Kuma wannan gayen Yana ganin Mahmud yayi wata irin zabura ya nufeshi ya rungume shi jikinsa na wata irin tsuma Yana fadin "Ya Mahmud Ina ka shiga ka barmu". [2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI MAMAN FATEEMAH. Page 48. ___ Rungume juna sukayi sosai, kuka ya saka Masa kamar karamin yaro da gani ba karamin missing dinsa yayi ba , Shima Mahmud Jin wani Abu yake yi a zuciyarsa badan namijin duniya bane da Babu abinda ze hana shi zubda hawayen shima, yayi kewar Faruq sosai saboda sunyi wata irin shaquwa dashi ta ban mamaki,duk da ba uwa daya ta haifesu ba Kuma kusan sa'anni ne Dan baifi wata hudu Mahmud ya bashi ba, Amma Yana bashi girma sosai,duk abinda yakeyi hankalinsa dari bisa dari Yana Kan musbahu Wanda yayi mutuwar tsaye shi Bai karasa gurin zahrar ba, shi kima bai dawo baya ba, me yake Shirin faruwa ne? wannan din meye dinta yasan dai tayi aure ance wani k'olo aka aura mata, to Ina auren kada dai gudowa tayi ta shigo yawon duniya?. Ita ma zahrar ji tayi komai ya tsaya mata, har wata zufa taji tana tsatstsafo Mata a jikinta abun kamar a mafarki, gurin da su Mahmud suke ta kara kallo still suna yanda suke Saidai gaba Daya hankalinsa Yana gurinsu fuskarsa ba annuri ko misqala zarratin kamar dade duniya be taba dariya ba, sadda Kai zahra tayi dan ji tayi wani irin tsoronsa na shigarta tuna karonsu tayi wanda ya kusan cinye mata lebe, kasa tayi da kanta jiran taji ya zata kaya. Bayansa ya Mahmud ya ringa Dan bubbugawa da tafin hannunsa Yana fadin. "Haba Faruq meye na kuka da girmanka da komai Kai ba mace ba, ka nutsu ka share wannan hawayen, akwai mace fa a kusa damu tana kallonka, wallahi wata Rana sai tayi maka gorin ragon maza" Ya fada Yana sakinsa da sauri yama duban masu rike da kayan daya saya a hannu "sorry na barku da Kaya kuyi hakuri Dan Allah mu karasa ku saka a mota" Yayi gaba yana yiwa Mushahu wani shegen kallo, Faruq na rike dashi ram Kamar Yana gudun ya bace Masa. Back seat Faruq ya bude suka zuba kayan,Faruq din ne ya curo kudin da baisan yawansu ba ya Mika musu sukayi godiya suka wuce bakin aikinsu. Jikin motar Mahmud ya tsaya Yana facing din musbahu da fuskar shanu. "Dan Allah Ya Mahmud kana Ina ne duk tsawon wannan lokacin? Kuma wacece wannan da kuke tare?" Fuska Babu annuri Kona sisin kwabo ya Maida dubansa Kan Faruq din "Idan ka Gama abinda kazoyi ka sameni a Bawo road komai dare Ina jiranka". Ganin yanda mahmud ya daure fuska yasa yaja bakinsa yayi shiru be kara tambayarsa komai ba. "Ok. Zan shigo yanzu ma in Sha Allah, Nima yau na shigo around four thirty, yanzu ma uncle mushahu na rako, dan yayar Mamee ne gashi nan,bari nayi masa magana ku gaisa be ganeka bane". Da hanzari Mahmud ya daga masa hannu "pls Faruq no need". Ya fada yana dhugewa motar, abinda ya daurewa Faruq kai kenan, wai Ya Mahmud ne yake driving da kansa, sai yake ganin kamar an canza masa Ya Mahmud dinsa da wani. Saida ya fice daga harabar gurin sannan Faruq ya karaso gurin Uncle dinsa yana fadar "Yanzu fa a hanya muke maganar Ya mahmud da kai ashe yana kusa damu wallahi ba wanda ya zaci yana kasar nan, abinda ya bani mamaki wannan Babyn da suke tare a sanina da Ya Mahmud baya harkar mata gaskiya, sai dai ban sani ba ko bacin rai ya saka shi yin hulda irin wannan dasu". Faruq be ankare da shi kadai yake zubarsa ba sai da ya kai aya yaji Musbahu be tofa masa ko A ba sannan ya dan taba shi. Firgigit yayi alamun yayi zurfi a cikin dogon tunani. Dogon numfashi yaja yana yiwa Faruq duban tsanaki, kafin yace. "Faruq waye wannan nake gani kamar Mahmud?". "Shine mana baka ganeshi bane?". Wani gumi yaji nan da nan ya rufe shi tabbas Shiya gani a cikin hotunan da Najib ya turo masa na daurin Auren zahra, ya dade yana hasaso inda yasan face din amma ya kasa tantancewa ke nan DANGE shine mijin da aka aurawa zahra a matsayin Almajirin Alaramma? take a nan yaji wata irin karaya ta mamaye masa zuciya yasan ya rasa zahra har abada, shi dinwa da ze iya ja da wannan dan tahaliki, ko manyan manajojinsa bai isa yayi takara dasu ba kafin ma a kai ga P.A dinsa. Cikin nuna tsantsar karaya ya cewa Faruq. "Ban gane shi ba sai bayan ya wuce, ina labarin dana baka dazu akan fasa aurena da akayi?" Kai Faruq ya gyada masa yana fadin "Na gane bana yarinar nan 'yar Azare ba?. "Eh to ai wannan ta cikin motar itace yarinyar da nake fada maka kuma tabbas shine aka aura mata a matsayin Almajiri kolo, bari na nuna maka hotunan daurin auren, dan wani yaro nasa ya turo min hotunan na dade ina tunanin inda nasan fuskar Amma ban taba ko hasashen shine ba, tunda nasan meze kawo shi Azare harda zaman Almajiranci". "What!!! Almajiranci kuma? "Yes of course, bari na nuna maka pictures din ka gani". Ya fada da kyarin gwiwa duk da karfin hali kawai yakeyi hankalinsa idan yayi dubu a tashe take. Ya ciro wayarsa daga cikin aljihun wando ya shiga gallary ya nemo hotunan, cikin sauri da zaquwa Faruq ya karbi wayar, da Sameer ya fara cin karo a hoton yana kusa da Ya Mahmud sai kuma wadanda be sansu ba, a hankali ya ringa duba hotunan tabbas Ya Mahmud ne tunda ga P.A dinsa nan wato duk tunanin da akeyi yana turai ashe yana Bauchi state saboda tsabar iya bada kafa. Dago da kai yayi yana kallon Uncle din nasa da mamaki fal fuskarsa. "Na gani tabbasa wlh shine, to amma ta yaya hakan ta faru? nayi mamakin auren daka fada min yayi, bafa wanda yasan inda yake ya yanke hulda da kowa fa, yanzu na gama fada maka irin badaqalar da aka sha a family din wanda yasa ya tsallake yayi tafiyarsa, uncle sorry bari na bishi hankalina baze kwanta gani nake kamar dabara yayi min ya gudu". Kai kawai Musbahu ya iya jinjina masa, yayi hanyar ficewa da sauri, yana fita Allah ya kawo adaidaita ba kowa ya tare ya shiga saida suka fara tafiya ya fada masa Hausawa Bawo road. Tunda Mahmud ya fice daga harabar sahad store ya saki motar yana wani irin tuki, ko iskar data aje zahra be duba ba itama takurewa tayi jikin kofa da gaske shakkarsa takeji dan ya hade gabas da yamma kudu da Arewa, ya doki sitiyari yafi sau shurin masaki. Ita dai zahra sai addu'a take Allah ya sauke su lafiya, gaban wani gida taga ya tsaya Mai shegen kyau haske ya cika ko Ina da karfi ya danna Horn din kamar ance masa Mai gadin sabon kurma ne, da sauri ya fito ya nufo motar banban mutum ne ba yaro ba, ganin baisan motar ba yasa ya karaso da sauri ganin Wanda yake wannan mahaukacin horn din. Bazato yayi arba da Mahmud, da sauri ya zube Yana kwasar gaisuwa, hannu kawai ya iya d'aga Masa da sauri ya koma har Yana hadawa da gudu yaje ya bude gate din, da gudun dai ya shige har kofar ya nufi ba parking space ba, kofar da zata sadaka da main parlourn ya tsaya ko motar be tsaya kashewa ba ya zagayo ya bude side din zahrar take zaune yasa hannu ya fisgota waje, be saurari komai ba ya nufi steps din shiga ciki da ita, ganinsa kamar mahaukacin Zaki ya saka zahra cikin tashin hankali, da hannu Daya ya zura katin ya bude kofar, be tsaya a parlourn ba direct upstairs ya nufa da ita tana turjewa tare da fasa masa kuka Dan wani irin riko ya yiwa hannun Kamar ze tsinke Mata tsintsiyar hannu, be saurareta ba Saida ya dangana da inda yayi niyya bedroom din da suke sama guda uku, ya nufi na kusa dashi da karfi ya tura kofar da suka shiga yasa kafa ya Maida kofar,Kan wani lafiyayyan Turkish bed yayi musu masauki, yana zuwa Bai bi takan kukan da takeyi ba ya saka hannu ya fisge Rolling din da tayi yana huci.Dan magana ma ya kasayi saboda wani Abu da yake taso Masa, baya tayi da sauri ganin Yana neman cakumo rigarta, Kan gadon ya hauro Shima ko takalmin kafarsa be cire ba, Rigar jikinsa ya cire yayi jifa da ita, ya kamota tata Rigar ms yasa hannunsa ya karketa tun daga sama har kasa, take jikinta ya bayyana, ya kasance daga ita sai farar bra tas da farin pant a jikinta,jikin Nan sai wani glowing yake kamar kifi tarwad'a, cikin tashin hankali da matsananciyar kunya ga kuka take fadar "Dan Allah kayi hakuri me nayi maka wallahi bani na kirasa ba, shine ya ganoni ya taho ko magana banyi Masa ba,ai kana kallon mu, wallahi bansa zasuzo ba ba Kaine ka kaini gurin ba?". Ta fada tana kankame jikinta. Duk abinda ke jikinsa ya cire ya jefar, Shima Dan ganinta a haka ba karamin bijiro Masa da tsohon tsimi yayi ba Rabon da yaji haka tun karonsu a Azare lokacin data farfada Masa maganganu Hannu yasa ya fisgota jikinsa ya fisge brezier da karfi ya jefar, Yana fadin. "Daman kun shirya had'uwa dashi shine yasa Kika gudu d'aga gidan Hajiyar ko? saboda ki samu damar sheke ayarki tare dashi tunda be aureki ba ai sai kije yayi abinda yaga dama dake ko? Niga sakarai Wanda besan inda yake masa ciwo ba, yau basai gobe ba zamu raba wannan rainin ni dake, ganin na daga Miki kafa Ina tausayinki yasa raini ya Fara shiga tsakaninmu ko? abun har ya Kai a gabana ake neman rungumarki wlh da yayi wannan gangancin Daya gane maza suna suka tara, idan kina cikin matsuwa saiki fada min ba kije kina kyarkyara ba a waje na isa nayi satisfied din duk fitinarki yarinya, sarauki ne ni Zan iya da duk bukatarki, ya Kamo hannunta ba zato taji ya Dora shi a......." Cikin wata irin zabura tayi wani juyi kafin ta Kai ga sauka ya cakumota gaba dayanta ya dawo da ita jikinsa, jikinta sai tsuma takeyi kamar ana kada Mata gangi. Dai dai kunnan ta ya saka Bakinsa. "Ina Zaki ai yau no way out, badai abinda kike muradi ba kenan?Baki da matsalarsa na fiki finita Dan haka kizo mu kwada daga Nan zuwa wayewar gari". Yana gama fada ya hade bakinsu guri daya Dan kukan ta nema yake ya karya Masa zuciya. Da zafi- zafi yake tafiyar da ita Dan da gaske duk wani Alkawari ya jingine shi a gefe yau jinsa yake kamar mayunwacin zakin da ya kwana uku baici nama ba ko yaron Daya wuni baisha Mama ba Saida tafiya tayi nisa yaji labarin ya canza salo dan shi harga Allah ya wani manta tani wani period. Kankameta yayi Yana wani irin numfashi har Saida tsoron da tajeji ya ninku ta dauka ko somewa zeyi cikin wata dasheshshiyar murya yace Mata "marata ciwo take min duba dakin tsakiya ki dauko min wani magani a cikin kwalba a bed side din jikin gwdin " ya Kamo hannunta ya Dora akai taji wani dumi a marar tasa, matse hannun nata yayi Yana sakin wani Nishi cikin galabaita, take ta Kara rudewa da sauri ta tashi ta daura gyalen ta tunda Riga ta tashi daga aiki da sauri ta fita tana waiwayensa ya rintse idonsa hannunsa Yana Kan mararsa. A bude dakin yake Bata tsaya kallon dakin ba, bedside din ta nufa direct cikin ikon Allah wadda ta Fara dubawa a Nan taga kwalbar da kananun tables a ciki, har zata fito taga irin karamin fridge a dakin, budewa tayi da sauri cikin sa'a ta samu ruwa a ciki ta dauki Daya ta fice da sauri tana shiga ta nufe shi da sauri tana Fadi tashi kasha ga maganin, taji Shiru Kara matsawa tayi tana Masa magana Nan ma shiru taji da sauri ta hau gadon tana girgiza shi cikin tashin hankali. . .. [2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨ AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. P. 49 ______ Duk budirin da take Yana jinta tana ta faman jijjiga shi Sai da yaga da gaske hankalinta ya tashi sannan ya dago kansa Yana kallonta da hargitsatstsun idanunsa, wata ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta kauda idanunta da gasken gaske wani irin nauyinsa takeji, matsowa jikijnta yayi a hankali ya sakata a jikinsa Yana fitar da numfashi a jikin wuyanta, wata irin kasala ta kara saukar mata gashi ba halin kwacewa ya kanainayeta ta ko ina. Cikin kunnenta yayi maganar da wani yanayi Mai wuyar fassarawa. "bani maganin na Sha". Da sauri ta Mika masa 'yar kwalbar, jikinta ta janye da sauri ta dauko robar ruwan data Dan gangara wurin karshen gadon. Kwara biyu ya Ciro maganin ya karbi ruwan ya watsa maganin a bakinsa yabi da ruwan, Saida ya shanye shi tas sannan ta karbi robar. Zanewa yayi ya kwanta rigingine, hannunsa Yana dafe da goshinsa Dan ji yayi kansa Yana wani irin Sara masa, ganin haka yasa zahra janyo blanket din ta rufe jikinta dan itama har lokacin jikinta Dan karkarwa yake mata daga ciki. Sun jima a haka kowa da abinda yake sakawa a tasa Zuciyar, Amma ita zahra Hamdala take ga Allah Daya tarfawa garinta nono, tab da yanzu ba wannan batun akeyi ba, tsikar jikinta ce ta tashi sharrrrrr.. jikinta ta kankame guri Daya tana ayyana wani Abu a cikin ranta, Jin motsin tashinsa tayi, dan waiwaya inda yake kwance tayi taga ya tashi ya nufi toilet Yana hada hanya. Har ranta taji tausayinsa sai dai tafi tausayin kanta a kan halin da yake ciki. Ya jima tsakiyar ruwan sanyi Yana dukan jikinsa,sai ajiyar Zuciya yake saki ba kakkautawa tamkar yaron Daya wuni kuka baiga uwarsa ba, Saida ya samu nutsuwa sosai sannan yayi wanka ya fito har lokacin tana kudundune a cikin blanket din. * Har gate din gidan Mai adaidaita sahun ya kawo Faruq yana fadin "Yallabai kayi muhalli Mai kyau Allah ya kawo abokiyar Zama ta gari Masha Allah". Shi dai Faruq hankalinsa in yayi dubu to Yana Kan ya shiga yayi arba da Ya Mahmud dinsa badan yaso ba ya taho ya barosa, yaso kafarsa kafarsa su taho dan gani yake kamar guduwa zeyi ya rasa inda ya shiga, kudin da baisan adadinsu ba ya Ciro ya mikawa Mai Dan sahun yayi gaba. Yana Jin Mai Dan sahun na fadin " Yallabai kudin fa sunyi yawa ka duba kuwa?" Bai waiwayo ba ya dago masa hannu Yana fadin "kaje ka Kara petrol da sauran". Yayi gaba abinsa, yana jiyo yanda yake kwararo Masa addu'a kamar ba gobe, da yake irin mutanen Nan ne masu kaifin harshe kamar jikan maroki. Sau biyu Faruq yayi knocking din gate din,malam Musa ya leko ta kofofin dake jikin gate din, ganin shine yasa da sauri ya bude Faruq din ya shigo, sun yiwa juna farin sani tunda sun Sha zuwa da Mahmud suna kwana idan wani Abu ya kawo su kanon, sauda yawa anan gurin malam musan yake zama idan baya son fita ko Ina. Cikin mutunta juna suka gaisa malam Musan yake fadar "Ashe tare kuke da yallaban Amma kunyi shigowar dare gaskiya, kaga motar can ma a kunne ya barta Naga kamar Matar tasa Bata Jin Dadi, dan da sauri suka wuce ciki ko motar Bai samu damar rufewa ba, nayi mamaki da naga yau yallabai da kansa ma yake tukin motar". 'yar dariya Faruq yayi, Bai tofa ko kalma Daya ba akan maganar tasa da yayi akan Ya Mahmud din, gurin da motar take Ya nufa Yana fadin. "Ina zuwa Baba Musa Bari na gyara parking din". Zuciyarsa fari tasss, Daya samu Mahmud a gidan ba kafa ya bashi ya gujewa haduwarsu ba kamar yanda ya yanke hulda da kowa, bai San Yana da irin wanna Zuciyar ba Saida aka samu matsalar, Amma Abu mafi daure Kai yanda Baba Musa yasan matarsa ce har yake fada Masa, ko a Ina ya samu labarin dasu Family dinsa Basu sani ba?. Saida ya Kai motar parking lot sannan ya dawo gurin Baba Musa ya zauna suka Fara Hira, tunda mutuminsa ne sosai, sai da sukayi nisa a hirar sannan Faruq ya tambayi Baba Musan ko da sabuwar lambar Ya Mahmud a gurinsa shi ya baro wayarsa Mai sabuwar lambar a gida, tunda ya fada Masa ba tafiyar su Daya ba, shi biki yazo garin, shine ya shigo tunda ya fada masa Yana garin. Ba musu ya Miko masa wayar yana fad'in. "Duba ka gani Nima jiya jiya nan ya kirani da ita yake fada min za'a kawo kayan gyaran wancen sabon ginin da aka Gama". Ya fada Yana nuna Masa inda su Mahmud din suka shiga. Number ya saka a wayarsa ya maida Masa wayar Yana fadin "dauko min keys din wancan part din na shiga na kwanta na gaji sosai". Dakinsa ya shiga ya fito Yana fadin gasu ka duba niba banbancewa nakeyi ba. Amsa yayi yayi masa sallama ya nufi part din Zuciyar sa fal da tambayoyin Daya Kamata ace ya yiwa Baba Musan Amma gudun bada wata kofa da za'a Sami wata kofar sanin wani abun yasa yaja bakinsa yayi shiru. Har Mahmud ya shirya cikin pyjamas dinsa sky blue tana kudundune a cikin blanket din, duk Kai kawon da yake tana jinsa amma ko motsin kirki batayi ba, sai ya Gama komai ya nufi kofar ficewa daga dakin ya juyo kadan Yana Kare Mata kallo da gaske ita ce rauninsa yaga alama, a hankali ya koma cikin dakin yaje har inda tayi wurgi da hand bag dinta ya tsuguna ya dauka ya koma gefen gadon ya zauna ya bude jakar, wayarta ce da sauran tarkace irin na Mata sai ATM cards dinta da 'yar robar maganinta a ciki na wajen Hajiyar makwarari, ATM'S din ya dauke da wayar da sauran kudin data Ciro jiya a Hanyar Janbulo, harya mayar da jakar ya ajiye sai kuma yayi saurin Kara daukota kamar Wanda aka tsikara ya Kara budeta cikin wani zip na gefe ya bude takardu ya gani ya cirosu duka passport dinta ya gani da wasu magungunan da aka Bata na Asibiti sai takardun tests da akayi Mata na Azare Dana Nan kanon. Passport din ya dauke ya hade da abubuwan daya dauka ya Mike ya fice daga dakin yana saka Mata alamar tambayoyi masu yawa. Saida taji ya fice daga dakin da kusan minti goma sannan ta samu zarafin tashi zaune tana Dan turo Baki tana 'yan matanganunta a ciki Wanda ita kadai tasan me take fada. Sai lokacin ta shiga bin jikinta da kallo ita fa duk ya dagula Mata Lissafi. Banda taimakon Allah da yanzu ba wannan batun akeyi ba, tsikar jikinta ce ta kara tashi yarrrr kankame jikinta tayi tana sauki wani malalacin numfashi, tare da furta "Narrow escape". Ta Kai dubanta inda yayi Mata wurgi da kayan jikinta, ita har zuwa lokacin ta rasa meya tunzura shi haka daga ganin Musbahu ita ba ita takai kanta ba, ba ita tace ajeba ballentana yayi tunanin setup ne. Itama wankan ta shiga yi tana zuwa ta duba jikinta cikin ikon Allah period din ya dauke Daman tun safe taga alamun hakan duk pad din data saka a yinin haka nan take cirewa, ta yanzu ma hakan ce ta kasance, tayi hamdala ga Allah tafi a qirga wato ba karamar kariya wannan pad din ta Bata ba. Wankan tsarki tayi tare da wankan sabulu ta fito daure da towel, yanzu ta Zama 'yar gari gurin suturar sakawa, gurin kawai ta nufa ta Ciro Riga da wando sleeping dress masu rawa ta saka ta dauko hijabi ta shimfida sallaya ta tayar da sallar magariba da insha'i. Mahmud Yana fitowa dakin Daya tura zahra dauko Masa magani ya shiga, direct wurin wasu lokoki ya nufa a ta tsakiya ya bude ya zuba duk kayan daya dauko a Jakarta, wayar kadai ya rike a hannunsa. Kira ne ya shigo wayarsa yana dubawa ya gane number Faruq ce. "Ya Salam". Ya furta a hankali wallahi ya manta da batun Faruq kwata kwata Saida yaga kiransa ya tuna Daya hadu dashi ma, to Ina ya samu wannan number din shidai yasan be Kira wasu mutane da yawa ba da layin Dan sabo ne jiya ya Fara amfani dashi, sai Kuma ya tuna ya Kira malam Musa dashi jiya yasan a gurinsa ya karba, tasowa yayi ya nufo parlourn farko Yana dealing number din Faruq din. Yana dagawa yace Masa "ka shigo sabon part din nan ka sameni a parlour". Ya yanke Kiran.. Cikin kujera two seaters ya zauna a kasalance badan Shima Yana Jin kishirwar haduwa da Faruq din ba da Babu abinda ze fito dashi ba. Fitowa yayi da zummar dauke motar Daya Bari a gurin, ga mamakinsa Bata gurin a parking space ya hango ta, Dan murmushi yayi yasan aikin Faruq ne. A Nan ya tsaya ya Zuba hannunsa a cikin aljihun rigar Yana shaqar iskar dare da take kadawa a hankali Mai dadi, malam Musa ne ya hango shi a tsaye a gurin da sauri ya nufo gurin Yana fadin "barka da dare yallabai anzo lafiya?". Hannu ya Mika masa duk da nokewar da malam Musan yakeyi sai da sukayi musibaha. Mahmud din na fadin "lafiya kalau Alhamdulillahi, nagode kwarai, ya iyalin naka da jikin". "Wallahi Alhamdulillahi kamar ma batayi lalurar ba, Allah yaja da Rai ya Kara daukaka yaja da ran mahaifa ya baka zuri'a d'ayyiba". "Allahumma Amin". Faruq ya amsa addu'ar lokacin da yake karasowa. Komawa bakin aikinsa Malam Musa yayi su Kuma su Mahmud Maimakon su koma Daki sai suka gangaro kasa gurin irin hut (bukka) din Nan ta zamani an wadatata da isashshen haske Mai wani daukar hankali Wanda ya Kara kawata gurin. Zama sukayi a tare kusa da kusa tamkar Muhmud din ze gudu cikin murye me rauni Dan har idanunsa sun cicciko da hawaye Faruq ya Fara fadin "why me yasa kayi haka Ya Mahmud? Kasan yanda kabar baya da kusa kuwa? Rayuka da yawa sun baci Kasan Ammi ma zazzagewa tayi tayi tafiyarta Niger, sai fa a wancan satin ta dawo sokoto. Lamarin babu Dadi ko kadan ga Hajiya Inna ma ta tashi hankalinta Wai itace tayi silar barinka gida tunda ita ta kara tunzuraka da maganganunta, ga Abie ya Kori Aunty Samira da Safna har da masu aikin part dinta Dan sai daga baya maganganu suka dunga fitowa har da asiri fa sukayi maka akan kabar Sokoto har abada ko sunanta kada kara tunawa, Kuma Duk abinda kake dashi ya lalace,kasan wani abun mamakin Wai a cikin masu tayata wannan shirkar harda uncle Saminu". Sai lokacin Mahmud ya dago da Kansa ya kalli Faruq dan tunda ya Fara maganar yaji kamar a lokacin abin yake faruwa. Cikin cikakkiyar kamalarsa yayi wani murmushi kafin ya bude bakinsa cikin Jin Kai Dan maganar ma kamar baya son yinta Dan har lokacin jikinsa ba daidai yake jinsa ba yace "Na sani mana sosai ma kuwa, ai kome akace yayi ba zanyi mamakinsa ba, kasan ya tareni gaba da gaba yace min ba dai Ina takama da nafi 'ya'yan su rufin asiri ba shi yasa nace bazan auri 'yarsa Asma'u ba, shima ai ba matsiyaci bane to sai yayi min sanadin da sai zaman sokoto dama kasar Baki Daya yayi min wahala, Sam ban kawo komai ba akan furucinsa Dan nasan ba abinda ya Isa yayi min Saida Izinin Allah, Kasan Abu mafi yi min ciwo a duk cikin jumurdar da akayi tayi?" Kai Faruq ya girgiza Masa. "sharrin zina da akayi min Wai harda Cikin shege, ko Ina Zina me zaci da Safna kazama kawai yarinyar data Zama karya ko wane kare binta yakeyi har ayi kokarin hadani aure da ita, wallahi Dana auri yarinyar nan gara na mutu a gwauro babu aure, sannan Abu mafi ciwo babu Wanda ya ji view dina an dauki abin da zafi kowa bakinsa yana kaina har Ammi Taki yarda Dani, tana ganin D'an yanzu babu abinda baze iya aikatawa ba, shi yasa na nufi gurin Hajiya Inna Nan ma gurinta babu sauki shi yasa naji gara nayi nesa da gida tunda kowa ganin mutumin banza yake mini. kasan kuwa duk abinda yake faruwa Ina da masaniyarsa? har barin Ammi sakoto, kawai dai na Kai zuciyata nesa ne sau uku Ina zuwa Yamai amma sai naji bazan iya tunkararta ba saboda tana ganina wannan badakalar zata sake dawo mata a zuciya duk da gaskiya tayi halinta, so nake kowa ya ji yanda naji lokacin da akeyi min nak'i aka juya min baya! Kamar bani da gata, wallahi nayi Dana sanin Fara business dina da kananun shekaru Dana San idan na Fara haka Zan Zama yanda na Zama da ban yarda uncle Ishaq ya dorani akan kasuwanci ba, Allah swa yayi gaskiya Daya ce dukiya da 'ya'ya fitina ne, da Ina level irin na kowa a family din ba Wanda ze dameni tunda duk familyn wanda baya da rufin asiri da nasa wadatar? To ni abin ne yayi min waya wallahi ga kananun shekaru, kasan uncle Saminun dai ya taba fada min ko kungiyoyin matsafa dai na shiga, shi yasa na Zama abunda ba Zama cikin kankanin lokaci, a gaban Hajiya Inna da uncle Mustapha akayi har Saida suka samu mugun sabani da uncle Mustaphan Dan ma Hajiya Inna ta tsawatar kasan Bata da Wasa a gurin 'ya'yanta, sosai ta ciwa Uncle Saminun mutunci tace ze Bata Mata zuri'ar ta, na rasa mena tsare masa haka da zafi Sam baya kaunata ko alama, haka Sam baya ko shiga part din Ammina sai dai idan guri ya kure su gaisa Dan dole". Ya fada cikin bacin Rai sosai Dan idanunsa sun kada sunyi jajir, kwantar da Kansa yayi jikin kujerar yana sauke ajiyar Zuciya, da ganinsa kasan yayi famun ciwon da yake Zuciyarsa. Dan muskutawa Faruq din yayi shima abin saiya dawo Masa sabo. "Kayi hakuri Dan Allah Ya Mahmud kasan idan Allah yayi maka daukaka zaka gamu da kalubale kala-kala ba cikin family ba ba cikin jama'ar gari ba ba cikin abokai ba dole hakan ta faru yanzu dai ka koma gida, ayi duk wacce za'ayi duk da gaskiya tayi halinta an banbance tsakanin aya da tsakuwa, wallahi rayuwa lami ta zamar min da baka Nan, kofa a email na turo maka sako baka bani amsa nayi magiyar har naba uku lada, amma baka kulani Nima fushin ya shafeni ko? Wallahi yanzu ma nasan addu'ar da nakeyi ce ba dare ba Rana Allah ya amsa min ya kawo dalilin zuwana kanon Nan dafa harna cewa mamee ba, Kuma wallahi Allah kenan harna kwanta naji uncle musbahu ze fito sayan wasu abubuwan na amfani da mamee ta bashi ya list ya sawo Mata shine fa nace Bari na rakashi na Jima ban shigo garin ba na Dan Zagaya tunda ba dadewa zanyi ba, Ashe farin gani zanyi Dan Allah Ina ka shiga a kasar nan? Wallahi babu Wanda ya taba kawo kana kasar Nan ko alama Dan anfi maida hankalin nemanka a European countries da Asia wallahi ba Wanda ya kawo zaka zauna a 9ja". Girarsa Daya ta gefen dama ya Dan dage Yana yiwa Faruq wani kallo. "Au kunyi zaton Ina waje kenan ko? To Ina gida Bauchi state, cikin garin Azare katagum local government, nasan ba sai nayi maka bayanin komai akan Zahra ba, an fada maka wacece ita tunda Wanda na ganku yasan komai a Kanta watakila Abu Daya ze bashi mamaki ganin mu tare a Nan tunda ya sanni ko ba sosai ba a can tunda time to time Yana shiga gurin malamina suna gaisawa idan ya shiga garin, sai albishir Daya Zan maka itace yarinyar da nake fada maka mun taba haduwa da ita a cikin jirgi ita da Babanta wadda na tura Sameer ya bisu Zuwa Jordan,ai ka gane bayanin ko?" Kai Faruq din ya jinjina Yana fadin "Yes". Ya fada yana mamakin abun sosai wato shi Mahmud komai ya sake a gaba saiya cimma burinsa. "Sai yanzu ya gane ka har hotunan daurin auren ya nuna min a phone dinsa, Shima ya Dade Yana tunanin a Ina yasan fuskar ka tunda ba farin sani yayi maka ba sai dai a hoto, shi yasa Sam be ganeka ba tunda ta Ina za'ayi tunanin zakayi irin wannan rayuwar, Dan Allah fada min ta Yaya hakan ya faru harda Auren irin wannan yarinyar haka wato ribar kafa kenan ko?" "To abubuwan da yawa Dan Ni dai nasan na baro gidan Hajiya Inna cikin fushi kofa takalmana ban iya tsayawa na saka ba kawai dai nasan duk phones dina suna jikina na kamo hanya a kafata Amma Abu Daya nayi noticing kamar jama'ar da nake wucewa basa ganina sam, nayi tafiyar da bansan iyakarta ba daga Nan Kuma ban Kara sanin abubuwan da suka faru ba na dai tsinceni ne a gadon Asbiti bana magana ko kadan amma Ina Jin abinda ake fada mayarwar ce Bana iyawa, Wanda suka shinceni wani babban malami ne da marikin zahra da d'an Kanwar Malam din, shifa Malam din ya dage min da Addu'oi a kaina Dan har Taraba Saida yaje akan matsalata gurin wani tsoho malaminsa, a haka har Allah ya bani lafiya, sai Kuma nayi arba da Zahra a garin duk da Daman a bincken Sameer ya gano mazauna Bauchi state ne, sai naji Naga gurin Zama na dage da Addu'a da sadaka amma fa ban fadawa kowa ba ko Sameer saboda a lokacin maganar aurenta akeyi na shiga wani Hali a lokacin sai dai nayi Alkawari sai halarci daurin aurenta Kuma sai nayi Mata kyauta ta ban mamaki kafin nabar garin, sai kuma ubangijin da yake amsa addu'ar bayinsa ya juya lamarin cikin kankanin lokaci, aka bani aurenta lokacin Dana yanke kauna da samunta a matsayin matar aure uwar 'ya'yana". Ba karamin mamaki Faruq yayi ba ya Kuma Kara jinjinawa girman Allah swa, wato duk gwagwarmayar da aka Sha Rabon wannan yarinyar ne ya rantse Kuma ya kaddaro shine ze taka da kafarsa ya karbi aurensa ba tare da wakilcin iyayensa ba sai iyayen Amana. "Wato Ni duk lamarin ya juye min wallahi". Dan murmushi Mahmud yayi Yana fadin. "Kaima kenan da ba a kanka hakan ya faru ba, sometimes idan na zauna sai naga kamar Almara wasu abubuwan da suka faru, kasan abinda zakayi min". Kai Faruq ya girgiza alamar "A'a. Fuska ya hade Sosai Yana kallonsa Ido cikin ido. "Kada naji labarin ka hadu Dani a Sokoto Koda wasa, Nina fita da kafata Kuma ida kafata Zan koma Amma ba yanzu ba, Kuma kada naji labarin nayi aure a gurin kowa koda nazo da Zahra kada ka nuna kasanta ko a fuska, Nina taro match din ni zanji da kayana". Kai kuwai Faruq ke gyadawa tunda ya Fara maganar yasan ba Wasa a cikinta. "In sha Allah hakan bazata faru ba". Sun Kai kusan karfe uku suna tattaunawa akan abubuwan da suka ringa faruwa bayan bayanan, kafin kowa ya nufi NASA gurin kafin lokacin sallar asuba. Ba karamin mamaki Faruq yakeyi ba idan yaji Mahmud Yana fada masa wani abun Dan shi sai gurinsa yaji wasu abubuwan duk da Yana cikin gidan. Itama zahra Bata kwanta ba sai kusan biyu da rabi bayan ta gama karatun Alqur'ani ta Fara nafifili sannan ta kwanta, harta gama addu'ar kwanciyar barci sai Kuma ta canza Shawara ta tashi ta dauko Jakarta tana fadin "Bari na kunna wayar nan ba turawa Ammah text na ban hakuri tayi breakfast dashi sai Kuma da Dan hantsi na kirata nasan zata huce ta saurareni lokacin, sannan na Kira bestie musha hurar yau she gamo". Jakar ta dauko ta koma saman gadon Tana gyara Zama, duk iya binciken ta tayi Babu duk wani Abu Mai mahimmanci data saka a ciki, zazzage jakar tayi wayam kamar ba'a taba ajewa a cikinta ba. Tagumi ta buga tana tunanin, to a Ina suka zube wadannan kayan? Kuma me yasa sauran Basu zube ba? ko jiya lokacin da suka fito daga gidan mommy komai Yana ciki Kuma ai ko daga motar Bata fito ba lokacin da sukaje sahad din. Jiki ba kwari ta matsa tsakiyar gadon ta kwanta ita duk lamarin ya tsinke Mata wa zata tambaya Ina kayanta na jaka suke da wannan tunanin barci yayi gaba da ita. Hudu da rabi Mahmud ya tashi as usual, duk da Daren da suka raba da Faruq besa shi ya makara ba, nafila yayi sannan yayi raka'atanul fajri ya fito Jin an Fara Kiran sallar na biyu, harya nufi Hanyar fita daga corridorn sai ya dawo baya ya tura kofar dakin da take, a kwace ya ganta tsakiyar gadon hular data saka ta cire gefe guda Ribom din shima yayi nasa gurin blanket din ya sauka har saman cikinta ga rigar ita da Babu duk Daya, a hankali yake shigowa cikin dakin kamar Mai tsoron kada ya tasheta, Yana Kare Mata kallo yanda tayi wani mahaukacin kyau a cikin dinligh din dakin, har ze tasheta saiya tuna condition din da take ciki ya juya ta fice daga dakin, yaso ya gyara Mata gashin Amma yasan matukar ya tabata sai ya sake alwalasa, a waya ya Kira Faruq ya fito su wuce masallaci. A cikin barci taji kamar an bude kofa dakin, fargigit ta tashi tana addu'ar tashi daga barci, kamshin turarensa da taji ya hade dakin shiya tabbatar Mata daya shigo cikin dakin. A gurguje ta nufi toilet jin har an Fara sallah a masallatai, fatan ta Allah yasa har ta Idar Bai dawo daga masallacin ba Dan ita fa wallahi tsoronsa takeji Bata shuryawa abinda yake muradi ba... [2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 50. _______Tun idar da sallar Zahra ta shiga kakkabe gadon Tana dubawa ko Allah zesa tayi arba da tarkacen ta na cikin jaka amma ko alamarsu Babu dole ta hakura ta linke sallayar da hijabin Adana saboda tsaro. Bata koma barci ba gyara dakin tayi duk da ba wani datti Dan da gani sabon guri ne da alama ma kamar a jiyan aka Fara amfani dashi Dan ko toilet din shima haka ne, Bata dauki dogon lokaci ba ta gama komai ta bazawa dakin kamshi Dan ga Room freshners Nan kamar anyi gorinsu, wanka ta shige, ta Jima tana gasa jikinta da ruwan dumi sannan tayi wanka ta fito haka nan taji tana son tayi kwalliya Sosai. Zama tayi ta tsara light makeup tabi jikinta ta Sanya turaren gabobi Dana bayan kunne duk ta saka tunda gasu nan kamar ba da kudi ake sayensu ba, ita dai ta zubawa sarautar Allah Ido taga inda wasan ze Kare, clothset din ta nufa ta bude dayan bangaren, English wears ta saka riga da siket blue black masu ratsin fari a jikin coat din,rolling tayi da farin veil ta fito Shar da ita gefe gadon ta zauna tana karanta addu'ar Azkar din safe. Su Mahmud Basu shigo gidan ba sai wurin bakwai tun bayan idar da sallar sukayi zaman karatun alqur'ani da Azkar din Suma a masallacin. Faruq yaso ya wuce gida amma Mahmud ya Hana shi yace yayi zamansa a Nan ze fiye Masa shi yau ze koma Nasarawa Daman akwai abinda yazo yi Nan din zuwa anjima Idan ya gama zasu wuce Kuma ma Basu gaisa da madam ba, part din Daya kwana ya wuce shi kumq Mahmud ya nufi sabon part din har ya Fara hawan steps din ya dawo Yana Kiran Faruq. Shima gangarowa yayi Yana nufo Mahmud din Saida ya Karaso yace masa. "Ina key din waccen car din akwai Kaya a baya za'a fito dasu". "Oh! Sorry, wallahi na manta Yana ciki trouser din Dana sake jiya, harna na fito dashi na manta ban baka ba, daman ni ka barwa ita Naga tayi maka kadan motar five millions ai sai mu Kuma ma motar Mata ce" "Nima ba tawa bace ta madam ce idan kana so ka tafi da ita kawai". Baki ya rike alamar mamaki Yana 'yar dariya. "Haba dai yaushe za'ayi haka da Wasa nake gani nayi dai tayi kankanta a gurinka harma ita din gaskiya". "To Yaya kake son ayi kenan?kaga dai bani na Bata ita ba Babanta ya saya Mata Kuma saina ce batayi ba, Ina laifi da ake bani aro da ita fa nazo airport lokacin da zanyi tafiya,Kuma anan na aje ta harna dawo sannan na dauko Mata abarta, Kuma kawai saina ce Mata tayi kadan to ina wadda tafitan da Zan bata?". Ya fada Yana kallonsa, shima kallon nasa yake yi, shi wani zance yake masa me Kama da zaurance me yake nufi da hakan Yana nufin a baibai ya ninketa kenan kome?. "Pls jeka dauko min we will discuss later". Da sauri ya nufi ciki ya dauko key din suka nufi gurin da motar take. Kayan ciki suka dauko, da gudu malam ya taho ya karbe kayan hannun Mahmud Yana fadin "Haba yallabai meye amfanin na a gidan da har zaka dauki kaya". Ya karba yayi gaba da sauri Faruq ba biye dashi suka nufi parlourn kowa da dauke da ledojin a hannau. Har gurin dining table ya Kai kayan ya Dora kayan Faruq ma a Nan ya dora na hannunsa, Malam musa ne ya koma ya dauko sauran da suka rage a cikin motar. Maimakon Mahmud ya shigo saiya Koma dayan part din bai jima ba ya fito rike da laptop da wayoyi tablet guda biyu. A parlourn ya iske Faruq Yana tsaye kusa da wani freme Mai hoton wani tsibiri a tsakiyar teku gurin yayi matukar kyau sosai. Jin shigowar Mahmud yasa ya baro gurin Yana fadin "gaskiya tsarin gurin Nan yayi kyau sosai banyi zaton ze kai haka ba kafin a gama". Wani kallo Mahmud din yayi masa Yana aje abubuwan dake hannuwansa. "Amma Faruq ka fiye gulma, Ina cewa Kaine ka zana ginin Nan da hannunka zakazo kana wani zance daban a Kai Kuma, ni zonan ka shigar min da wasu sakonni cikin laptop din nan jiya naso yin aikin ka hanani". Ya fada Yana kokarin kunna wayoyin dake hannuwansa. Saida ya nuna masa komai sannan ya nufi upstairs. Tunda ya doso saman yaji wani kanshin Dadi Wanda ya kasa tantance Kona menene, direct dakin Daya kwana ya shige Yana son ya sake wanka yana son ya fita wasu sabgogin nasa wanda yaken son yayi da Kansa. Ya shiga ciki ba dadewa Zahra ta fito ta nufi kasa tana ayyana bari ta duba Koda kayan amfanin kitchen Dana abinci tasan abinda ya kamata tayi kada ta Zama sakarya wadda ta rako Mata. Plat shoes ta saka fari tas dashi ta nufo down stairs din cikin takunta mai daukar hankali, Bata ankara da mutum a zaune ba Saida ta ahigo tsakiyar falon taja ta tsaya tana rarraba idanu tana son tantance ya fasalin ginin yake da inda ya Kamata ta dosa,. Carab suka hada Ido dashi ya aje abinda yakeyi ya Zuba Mata idanu irin kallon Nan na wuce shari'a Yana tsarkake ubangijin da ya yi wannan halittar da take gabansa. Dan zabura zahrar tayi ganin mutum ba zato ba tsammani. Aje abinda yakeyi yayi ya taso har lokacin Yana kallonta Dan ja baya tayi ganin ya nufo ta. "Ina Zaki Kuma nida na taso na gaishe da Aunty na". Ya fada Yana murmushi, saida ya matso ta Dan gane shi, shine jiya ya rungume Mahmud a kofar store din da yayi sayayya. Sai lokacin ta Dan nutsu amma da tana tunanin ta Ina zata fece ta Koma saman tasan ko banza tana da mafaka a can. Dan murmushi tayi itama tana fadin "Yaya sunan bakon da babu sallama? Kawai na wayi gari da ganin mutun ai dole na rasana". Dariya yayi Yana fadin "Good morning Aunty". "Morning". Ta amsa masa a dan darare din nan ba wani sakewa, tana kallonsa. "I am Faruq Dange". Ya fada Yana juyawa zuwa inda yake aikinsa. A hankali ta bude bakinta tace Masa. "Sunana Fatima Zahra Muhammad Sani, Ina maka.barka da zuwa". Tana Gama fada ta wuce can inda ta hango Kaya akan dining table. Sakato yayi Yana kallonta Bai taba tunanin tana Jin yaren ba, Kai kawai ya girgiza Yana dan murmushi Yana fadin "wato Ya Mahmud sai a barshi kawai sannin inda ya dosa sai Allah, shi yasa kenan duk yayi d'iban Karan mahaukaciya da matan daketa rashin hankali a Kansa yayi tafiyarsa ya kyale kowa da nata salon rashin hankalin". Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy ta Bata ta cire ta aje a gefe sai Kuma Wanda ya sawo jiya ta cire na kitchen, kofar data gani a tufe taje tadan tura ga mamakinta a bude ta ganta shiga tayi kitchen ne modern sosai babu abinda babu a cikinsa tsayawa tayi tana nazarinsa kafin ta juya ta koma dauko Kayan. Saida ta aje komai a muhallinsa sannan ta bude freezer data gani ta kwance, nama ne dasu kifa da kayan miya a Nike cikin manyan bikitin roba, kaji biyu ta Ciro da Zuba a roba ta tarasu a famfo saboda kankarar ta saki. Filawa ta diba ta kwaba da yeast da barking powder ta rufe ta koma ta gyara Naman ta Dora a wuta. Wani ruwan ta Dora daban ta dauko Madara ta bude ta diba Mai yawa ta dama Zuba akan ruwa data Dora ta Dan zame murfin sannan ta ciro hollandia custard ta fasa ta dibi yanda take ganin zata ishesu ta dama ta aje a gefe. Plates da cups da duk abinda tasan za'a bukata ta dauko ta wanke ta aje a muhallin Daya dace. Filawar data kwaba ta dauko taga ya tashi ta ringa murzawa round sai ta Gama ta shafa Mai a frying pan ta rage wuta ta shiga gasawa tanayi tana juyawa. Biyu ta raba Naman ta dattaka rabi tayi source Rabin Kuma tayi pepper soup dashi ta dama custard din ta dafa coffee Kuma. Tun daga sama Mahmud ke jiyo wani irin kanshi girki yayi tunanin ko da wani sabon restaurant a Nan kusa dasu, Saida ya fito yana saukowa yaji kamshin ya cika gidan. Shigar kananun Kaya yayi yayi masifar kyau, yau shigar da yayi ta fito da ainihin ko waye shi Dan ba karya kana kallonsa kasan matashi ne Mai cike da Jin Dadi da wadatar arziki Dan agogon dake hannunsa kadai na millions of naira ne, shigar da ya Jima da daina yinta Nan gida Nigeria rabon da ya fito haka tun kafin ya shiga rubibi. Hannu Faruq ya shiga tafawa Yana fadin "perfect match, wallahi kun Dace Ashe haka Auntyn tawa take? Haba shi yasa baka sauraren masu yi maka rawar Kai, ya Mahmud Ashe da abinda ka taka shiyasa kayi shuru ka kyale kowa, Mai irin wannan matar mezeci da tarkace irinsu Safna, wallahi na Dade Banga ma'auratan da suka tafi da imanina kamar kai da Aunty na ba, Dan Allah ka tsaya min na auri kanwarta pls🙏". Ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo lokaci Daya faruq ya gigice masa wato yaga zahrar kenan tunda ya sauko yaji gidan ya hade da kamshin girki yasa itace a kitchen, ko ba komai yasan Allah yayi Mata baiwar iya abinci a Dan zaman da sukayi ya fashimci hakan. Shi rasa abin cewa ma yayi a Kan kalaman Faruq, Dan uwansa ne na jini, amma ya gigice da ganin matarsa, tab lallai da matsala Babba. Bai nuna Masa komai ba sai Dan murmushi da yayi Yana fadin. "Ai mata ta ita kadai ce Bata da Kani ko kanwa, nine wanta nine komai nata Sai dai ka duba ko a Ina ne Zan shige maka gaba in Sha Allah". "Dan Allah nidai ka taimaka ko cikin family dinta ne ayi min wanna alfarmar ka shige min gaba". Kyale shi yayi ya nufi kitchen din lokacin ta Gama hada komai ta juyawa kofar baya tana cire jan bayan kwakwa zatayi amfani da ita in anjima. Kamshinsa ya Fara fada Mata ya shigo gurin a hankali ta juyo, Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa ya zubawa bayanta Ido,yanda ta juyo din nan shi Kansa da take halalinasa Saida yaji wani yarrr a jikinsa Dan gani yayi gaba Daya ta canza Masa ga wani irin cikowa da kirjinta yayi sosai. Lumshe Ido yayi Yana tunanin lallai dole addinin musuluci da yayi Hani ga mutum baligi ya shiga gurin macen daba muharramarsa gaskiya. Yana can Yana tunani ya tsinkayi muryarta tana fadin "Ina kwana" batare data Kara kallon inda yake ba. Bai amsa ba ya danyi gyaran murya. "Meye Kuma Ina kwana? Na fada Miki ki iya tarairaya ta wallahi, kada garin kallon ruwa kwado yayi Miki Qafa, kina da kishiya fa kinsan idan ta fiki iya lafazi da tarairayata can Zan tare a gurinta". Warrr tayi masa da sexy eyes dinta tana Masa wani kallo. "Yes ko Baki yarda ba? yanzu na Kira Miki ita ku gaisa". Kai ta girgiza Masa alamar A'a. "Come on, zo Nan ki fada min bakya son kishiyar?" Ya bude Mata hannuwansa alamar ta shigo, kafada ta make ta aje kwakwar ta nufi famfon cikin sink ta Fara wanke hannunta. Cikin takunsa na nazantaka ya shigo ciki directly gurinta ya nufa Yana fadin "Ni gani na shigo sai nazo ki bani hot one tunda ni ba'a son nawa". Bai jira tace komai ba ya saka hannunsa ya rungumeta ta baya Yana shafa cikinta. Shiru tayi Masa kamar ruwa ya cinyeta, Jin hannun nasa ya nufi wata jihar yasa tayi saurin rike Masa hannu tasan idan ya karasa akwai damuwa sosai. "Pls Dan Allah ka Bari kaga da bako a gidan kada ya jiyo mu fa". Ta fada tana kokarin kwace kanta. "Ok saboda shi Zaki hanani na sake kenan? To Bari na sender shi inda yafi wayo". Dayan hannun ya saka ya ciro wayarsa yayi dialing din number Faruq, Sam batayi zaton kiransa zeyi ba, Saida taji Yana fadar "Faruq kaje wancen part din ka qarasa aikin gani Nan zuwa". Bai jira yaji abinda yake kokarin fada ba ya kashe wayar ya Dora a gefen cabinet din kitchen yana fadin "to saiki sake ki bani hakkina tunda sirikinki yabar gurin". Juyota yayi ya hade bakinsu ya cire rolling din, yana shafar gashin da yaji gyara ga qamshin hair spray sai tashi yakeyi ya jima Yana yamutsata kafin ya janye Dan Kansa yana Maida numfashi. Tsugunnawa yayi ya dauko Mata veil din ya rufa Mata a Kanta Yana fadin "dauko wasu flask din ki zubawa Faruq nasa ki saka a basket na Kai Masa can idan ya gama ya tattara ya tafi gurin bikin da yazo". "Me yasa? ba yace min shi qaninka bane". "Ok. Dan Yana qanena saina zauna dashi gida Daya Yana kalle min Mata ko? Ai ya tafi shine mafita Dan akanki zamu iya batawa da kowa to maganin Kar ayi kada a fara, Dan Allah ki ringa saka hijab idan munyi Bak'i ba kowa ne ze iya kawar da Kai a kanki ba Kinga kuwa yanda Faruq ya gigice min na Nemo masa sister dinki, na fada masa babu Amma ya kasa fahimta sai rokona yake na samo Masa mace ko cikin family dinku ne" Ya fada a Dan zafafe. Shiru tayi ta nufi abinda ya sakatayi Saida ta Zuba Masa komai ta saka basket din ta aje a gefe ta dauko Wanda ta zubawa Mai gadi ta aje a kusa Dana Faruq din. Malam Musa ya Kira yace yazo kofar parlourn su hadu, dauka yayi ya fice daga kitchen din yabar zahra da dogon tunanin akan abinda yace Faruq din yayi. ___ Tunda garin Allah ya waye Ammah ke faman neman number zahra abin yaci tura, a yau dai hakurinta ya Gaza Dan tun Daren jiya da zilai ta Kira Ammah tana fada Mata yanda fasalin gidan da suke yake da kuma kudin da tace an Basu dubu ashirin da safe da yamma ma an kawo musu wasu kudin dubu dari-dari ita da iya Rahane ga turamen atamfofi guda hudu hudu da lace bibiyu, Kuma ta fada Mata tunda su zahrar suka fice Bata Kara ganin giccinsu ba ga wayar ta ma a rufe. Akalar Kiran Ammah ta canza ta shiga lalubo Number Abdul Hakeem. Ringing din farko ya dauka yana Fadi "barka da Asuba Ammah, an tashi lfy?. "Alhamdulillahi, idan ka tashi ka shigo Ina son ganinka" ta fada cikin damuwa. "To in Sha Allah, gani nan shigowa".. Ta kashe wayar, ta ajiye a gefe tana fadin "kazo ka nemomin wannan yaron ya fada min waye shi Ina Kuma ya Kai min 'yata ko waya ya Hana muyi da ita inji meye dalilni Daya hana ta amfani da wayar, tunda Naga Abban ba wani Abu zeyi ba, ga wannan kinibabbiyar matar tasa da koma sai taji Masa kwakwaf". Tsaki tayi tana Jin duk Zuciyar ta ba dadi ko kadan, tana Nan zaune Abdul Hakeem din ya shigo sanye da jallabiya coffee colour a jikinsa ya gaishe da Ammah ya nemi guri ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah?". "Da sauki, Nemo min mijin Zahra a wayarka naji dalilinsa na yanke ma'amalarta Dani tunda suka bar garin Nan ban Kara Jin duriyarta ba". Shiru Abdul Hakeem din yayi kafin yace "ba haka za'ayi ba, Zan kirasa na saka handsfree sai kiji yanda zamuyi dashi idan munji da alamun rashin gaskiya sai a San abunda ya Kamata tunda ba'asan dalilinsa. Ba na hanata amfani da wayar, ke uwace kiyi hakuri babu abinda ze Samar Miki 'ya da izinin Allah, in Sha Allah sai kinyi alfahari da Auren Nan Muhmud mutumin kirki ne bashi da wata alama ta rashin gaskiya, kinsan ya fada min shi Dan Sokoto ne,.har unguwar su da iyayensa duk ya fada min lokacin da zeyi tafiyar nan, yace saboda halin Rai Koda be dawo ba na nemi Sameer ko sabon mai gadin Daya kawo a can gidansu na hayin banki, ko Binya na gidan Baba malam duk mutanensa ne. Bari na kirasa Dan hankalinki ya kwanta". Ya Fara dialing din number sa. Sun Gama break fast din kenan wayarsa ta dauki slow music daga kitchen inda ya barota tsam ya tashi ya nufi kitchen din kafin yaje Kiran ya yanke, sunan Abdul Hakeem ya gani, kafin ya Kira wani Kiran ya shigo. Saida ya zauna daf da ita ya daga kiran. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu babban yayan mu, barka da Asuba". Ya fada Yana murmushi. "Wa'alaika Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu kadai, ya iyalin?" Dariya abin ya bashi "Gasu Nan muna ta basu hakuri kasan Mata sai a hankali". Ya fada Yana Dan Jan tsunin hancinta, Batasan dawa yake wayar ba. "Wai meya samu wayarta ne Bata shiga kwata-kwata duk hankakii Ammah fa ya tashi, Jin kwana biyu shiru ba suyi magana ba idan tana kusa ka Bata suyi magana Dan hankalinta ya kwanta". "Ya salam Dan Allah ka bawa Amman mu hakuri laifi tayi min na karbe wayar, amma Zan Bata ita yau in Sha Allah, ai Zan shigo garin gobe ko jibi". Tunda ta fashinci da Ya Abdul Hakeem yake wayar taji hankalinta gaba Daya yayi gida Jin cewa zeje Azaren bada ita ba sai taji duk ta shiga tashin hankali da gaske gida take son komawa, ta dauka da Wasa yake Mata lokacin da yace ze dauko Mata Rukayya idan zasuje Azare. Wayar ya Mika Mata ya Mike ya fice daga parlourn gaba Daya. Sallama tayiwa ya Abdul Hakeem din sannan ta gaishe shi. Sannan ya dora da fadin "ga Ammah nason magana dake". "Dan Allah Ya Abdul Hakeem ka Bata hakuri wallahi saboda bansan abinda Zan fada Mata ba na kashe wayar Allah ba yaji nayi ba, kaina ne yayi zafi gurin fa buduwarsa ta turoni Asibiti ita Kuma ta shiga wulakantani, Dan Allah ka rokarmin shi ya maidoni gida wallahi na gaji Ni tsoro nakeji bakaga irin gidajen da yake kawoni ba kamar baza'a mutu ba fa". Ta ida fada tana kuka. Duk abunda ke wakana Ammah na zaune tayi tagumi tana Jin wani sanyi da tausayinta a Zuciyar ta, amman koba komai ta samu nutsuwa taji lafiyar ta sauran Kuma tasan shegantake ce kawai. Wayar Abdul Hakeem ya mikawa Ammah ya tashi ya fice shima gara ya Basu guri su tattauna. "Wai kukan Kuma na menene haka? ai kowa ya gyara ya sani kowa ya Bata ya sani, kiji tsoron Allah ki rike sirrin mijinki kinsan baqi kinsan fari keba karamar yarinya bace,saboda me Zaki tafi wani guri har ki nemi kwana bada izinin mijinki ba, haka kawai kin tashi hankakin jama'ar da suka daukeki da mutumci kin kyauta kenan? To wallahi kada na sake Jin wani Abu makamancin haka daga gareki ki nutsu ki rike aurenki kada na Kara Jin kin ambaci ya dawo dake nan, kinsan dai ba'a nan zaku dawwama ba ina cewa ya fada Miki garinsu wata Rana dole ze koma gida sai kice bazaki bishi ba? Akul na karajin magana makamanciyar wannan daga bakinki". Tunda Ammah ta Fara magana Zahra ke shashsheka a hankali. "Kiyi hakuri wallahi na daina bazan Kara ba, wallahi bansan laifin da nayi Masa ba ya dauke min wayar da passport dina har da kudi da ATM duka". Salati Ammah ta dauka tana fadin "Ni Asma'u yanzu harda passport dinki Kika dauka dole ya kwashe wato guduwa kuka shirya zakiyi kibar kasar ko?" Cikin gigita Zahra ta fashe Mata da kuka sosai tana Fadi "wallahi ba guduwa zanyi ba Daman suna cikin jakar fa". Ji tayi an zare wayar daga hannunta Batasan lokacin daya taso ta shige jikinsa ba tana fadin "Dan Allah ka fadawa Ammah abinda take zargina dashi ba haka bane". Ai Jin wannan furucin na Zahra yasa Ammah yanke Kiran cikin gaggawa. Jin alamun yanke Kiran yasa shi Kara sakata a jikinsa baya son kukanta ko misqalazarratin. [2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: 💞 * AUREN HUCE HAUSHI * Maman Fateemah Page 63. ............ cikin sa'a zahra ta Sami magajin a wayar, tsokanar ta ya fara. "Dan Allah ka tsaya ka isheni da magana, kanaji Wai sahura ce zata tambaye ka Ina na koma kada ka fada Mata kace Mata bana garin kawai". "An Gama yallabiya, kinsan bazata Fara ma tunkarata da wannan maganar ba, ba sakar Mata fuska nakeyi ba tunda na gane ita munafuka ce" Tsaki zahra tayi. "Can ta matse musu duk munafurcin mutum sai dai ya koma Kansa babu abinda ze sameni sai abinda Allah ya hukunta min, Wai sako to sakon me? har wani abun arziki Mama zata taso mutum ya kawo min wadda ko kallon arziki baya hadani da ita saboda tsabar kin jinina da tayi". "Share kawai bakin ciki ne taga Allah yayi halitta a Nan take hasaada saboda nata 'ya'yan Kamar ka yanka ka boye wukar, Ni bansan wace kaddara ta Kai Abba Aurenta ba, duk matan jihar Nan Saida ya tsallake ya dauko ta Dan ma Allah yasa Basu da yawa da ansha kwantai". Ya fada Yana wata dariyar rainin wayo. Zahra ce ta katse shi tana fadin. "Amma wallahi baka da kirki magaji 'yan uwanka nefa kake fada musu haka". "Kema dai ai kinsan gaskiya na fada duba fa ki gani, kawai dai abar kaza cikin gashinta". "Allah ya shiryeka wataran sai ka fada a gabanta, ta sauke maka ajja". Tana Gama fada Masa ta yanke Kiran tasan sai su Kai minti goma shi ba gajiya zeyi ba. Zahra Bata koma gurin Aunty zilan ba a Nan daki ta zauna, karatun Qur'an tayi sosai Dan Saida tayi surori da yawa, sannan ta shafa Addu'a ta tashi. * Sahura ce ta shiga dakin Mama Jiki ba kwari, ganin ta shigo yasa Mama tashi zaune tana fadin. "Meya faru Kika dawo? na dauka yanzu kinje can din?" "Eh naje Amma gidan babu alamun da mutane a cikinsa gaskiya. Dan idan ba idona ne bega dai dai ba babu wata alama data nuna giccin mutane ma a nan kusa a cikinsa, sai na Kirawo zilai nace ta fada min suna Ina ne, sai cewa tayi Wai ita Bata San sunan unguwar da suke ba tunda ba fitowa tayi ba tunda ta shiga gidan, Dan tsabar munafurci". Ta fada tana aje kunshin kayan da za'a Kaiwa zahra. Wata shariya Mama ta lafta tana fadin. "Har yaushe raini irin wannan ya shiga tsakanina da zilai? Har ta Isa ta nuna min wuyanta ya Isa yanka, wallahi idan tayi Wasa saina yi mata sanadin barin aikin kwata-kwata, ai dama matsiyaci be iya cin arziki ba". Hakuri sahurar ta ringa ringa bawa Mama ganin Nan da Nan ta ture sai masifa takeyi bakinta har kumfa yake fitarwa saboda bala'in da take kwasa . Ita dai sahura sai abin ya daure Mata Kai, to menene najin zafi haka, dan zanyi maka Alkhairi anje ba'a sameka ba, ba sai nabar abuna ba ko na bawa wani tunda Inda nayi niyya ba rabonsu bane. Cikin bacin Rai tace kije ko magaji ne ya rakaki Mana Zaki zo kiyi tsaye Kamar baki da wayo da dabara Dan Allah wuce a gurin". Kayan ta dauka ta nufi kofa tana fadin. "Bari naje na gani ko Yana nan din". Ta wuce ta fita. Zugum Mama tayi tana nazarin yanda abubuwa suketa lalace Mata, Wai yarinyar Nan me take takama da shine? duk abinda za'ayi da sunanta sai ya lalace,ko da tsiya-tsiya yau sai sakon Nan ya shiga gidanta duk Inda ta koma ma saina lalubo shi Dan wallahi bazanga bakin cikin da ze hanani barci ba. Duk iya kokarin sahura na taga magaji abun ya gagara wayar zilan ma an rufe ta, ko Kuma network yaki bada hadin Kai. Wata dabara ta fadowa sahura, da sauri ta nufi gurin Bala driver tana fatan samun mafita a gurinsa saboda Bata fatan ta rasa abinda Mama ta kwadaita Mata zata Bata. Yana aikin goge mota da alama fita zasuyi da Abba, sallama tayi Masa suka gaisa sannna tace Masa. "Dan Allah malam Bala ko zaka taimaka ka kwatanta min gidan da yarinyar Nan zahra suka koma naji ance sun tashi daga Nan hayin banki,Kuma na nemi duka lambobinsu ban samu ba". Ta fada tana fatan samun abinda take so. Tunda ta fara Kora bayani malam Bala ya dakata da aikin da yakeyi Yana kallon ta Saida ta Kai aya sannan yace Mata. "Haba sahura yaushe Zan dunga bin diddigin yarinyar da take gidan mijinta, ai wannan rashin lissafi nema ma wallahi ai da kunya ki fito neman gidan Zahra a Nan gurin mu alhalin ga uwarta can a cikin gida, to ke me zakiyi a can Wanda Baki son uwarta ta sani". Cikin rashin yarda da Kai ta Fara fadin. " A'a wallahi kasan wani abun alherin idan mutum zeyi baya son a gani sai dai shi yaron ya fadawa uwar tasa daga baya". "To shiga ciki ki nemi bayani dole" Ya juya yaci gaba da aikinsa ya bawa banza ajiyar ta, it's Kuma ta koma ciki da ledarta a hannu, mita yake shi kadai. "Haba mutane sai halin tsiya, Nan gaba kadan wallahi wannan mijin nata ze shayar da mutane mamaki Dan naji Alhaji Yana wani furuci jiya bansan dai dawa yake waya ba Amma Ina ganin da bincken da yake yi akan yaron Nan Kuma jiya Wanda ya saka shi ya dawo Masa da amsa". Shi kadai yaci Baga da Yan maganganunsa. Duk iya dabara Mama tayi Amma babu wani cigaba dole ta nufi bangaren Ammah. Cikin iya makirci Mama tayi knocking a kofar falon Ammah. Autane ya taso ya bude mata kofar, parlourn yasha gyara sosai sai kamshi ke tashi da sallama ta shiga, duk sai ta Raina nata dakin Dan babu karya ko yanayin gyaran da banbanci. "Mama Ina yini". ba zato Mama taji muryar magaji yana gaisheta daga bayanta. Da sauri ta juya tana fadin. " A'a Magaji! Daman kana gidan Nan tun dazu nake nemanka na rasa, Dan Allah tashi ka taimaka ka raka sahura gidan Zahra akwai wasu Kaya Dana saka a kawo Mata Amma shiru basuzo ba sai yau da safe shine nake son a Kai Mata su banso ko Ammah ma ta sani ba, sai dai zahrar ta Bata labari, to anje ance Wai basa gidan". Zama magajin ya gyara, Yana kallon Mama Ido cikin Ido. "Wai Mama kina maganar zahra ne?". "A'a to da maganar wa nake maka". "To ai Bata garin nan tun jiya suka wuce Kano, kinsa mijin nata baya kasar suna tare da Baba malam a India, to yafi son ta zauna a ca gaskiya, kin San manya Basu fiye son zaman gefe ba gara gurin da yake da kyakykyawan tsaro" Rasa abin fada tayi, ta rasa zancen wa zata Kama na magaji Kona zilai data ce Bata San unguwar da suke ba, kenan ba'a garin Nan ba kenan take nufi,ai da mamaki Daman Ace Wai zilai Bata San sunan unguwa a garin Nan ba, to Wai waye ma babban da taji magaji ya fada shi yaron ko Kuma waye?. Tunda magaji ya Gama fada Mata abinda zahra ta fada masa ya koma yayi kwanciyarsa, yaci gaba da latsa wayarsa. Fita tayi daga parlourn ta koma nata part din duk dabara takwance mata Kuma Bata taba zaton wankin hula ze kaita dare ba sai yanzu, tana fita Ammah na shigowa. Magaji Ammah ta kalla tana fadin. "Waye ya fita yanzu?" Tashi zaune sosai magaji yayi haka Musaddiq ma matsowa yayi tana fadin. "Ammah Wai Ya magaji yaje ya raka sahura gidan Adda Zahra". Gyara Zama magaji yayi sosai Yana fuskantar Ammah. Kinsan wani Abu Ammah Anya zahra Bata San wani abu ba game da maganar zuwan da sahura ba zatayi ba? saboda ina zaune Zahra ta kirani ta kada min warning akan kada na kuskura na kawo sahura inda take, tace min na fada mata Bata Nan sun koma Kano, to yanzu magamar ce ta kawo ta wai na dauki sahura na kaita gidan zahra zata kai Mata sako shine nace Mata ai sun koma Kano". Jinjina Kai kawai Ammah tayi tace. "Allah ya kyautata". A binda ta iya fada Kenan tayi gaba abin ta, ita lamarin Mama har ya daina ma Bata mamaki tausayi take Bata hassada ai mugun ciwo ce. * Sai kusan Sha biyu na agogn kasar India Habib ya tashi, yayi mamakin yanda lokaci yayi gudu haka, da sauri ya nufi toilet Yana yiwa Kansa fadan me kenan yayi shida ya biyo marar lafiya Amma ya bige da dogon barci irin haka, "ko Yaya Baba malam din yake?" Ya yiwa Kansa da Kansa tambaya. A gaggauce yayi wanka ya fito, Bai wani Bata lokaci ba ya shirya ya fito yana ayyana Allah yasa Mahmud ya dawo Dan jiya sun Dade suna dakon zuwansa Amma shiru dole suka hakura suka kwanta. A parlour ya iske mahmud Yana ta faman aiki a cikin computer desktop wadda take girke a parlourn, daga gefe Kuma wasu indiyawa ne su biyu Yana musu magana da harahen indianci suna amsa masa, da alama Kamar Umarnin wani Abu yake basu, har Inda yake zaune Habib ya Karasa yayi Masa sallama ga mamakinsa sai yaji gaba Daya sun amsa masa, Shima Mahmud barin abinda yake yayi ya juyo Yana sakin murmushi ya mikawa mahmud hannu sukayi musabaha, sannan ya mikawa bakin mahmud suka gaisa, ganin Kamar Habib na dari-dari dashi dan Yana kula da yanda yake tsare shi da ido, sai idan yaga zasu hada Ido yayi saurin janye nashi, tashi muhmud yayi daga Kan computer ya riko hannun Habib Suma sauran biyun suka rufo musu baya. "Bakon india, nasan ka gajine shi yasa na Hana Abubakar tashinka nace ya barka kayi barcin gajiya tunda ka gaji da yawa". Ya fada suna Zama a kujera two seater, "Bari kawai ni kaina nayi mamakin barcin da nayi, Ina Abubakar ne?". "Sun fita da Mr Ajey kasuwa, inaga sun kusa dawowa ma yanzu, ga abinci nan kaci idan ka gama zaku fita dasu Mr Salman zasu rakaka kuje a Sami kayan sakawa tun dazu suke jiran ka fito ku tafi baka tashi ba, ga abincin can ka duba Wanda zaka iyaci sai ku wuce, nima Zan shiga naga doctors din dake kula da Baba malam yanzu suka nemi ganina tunda tun jiya suka shiga dashi dakin bincike na musamman sai gobe za'a fito dashi, kasan tsare-tsaren Asibitocin su da banbanci da namu na Nigeria".. ATM mahmud ya mikowa Habib na bankiya juya Kuma yayiwa su Mr Salman maganar da Habib besan me aka fada ba, ya wuce ciki Yana fadin. "Kada ka dauko kaya kadan Dan bamu San how long samu zauna a Nan ba sai yanda Hali yayi". Shi dai Habib kasa cewa komai yayi Dan ya gama Shan ruwan mamaki ba kadan ba, Mahmud din da suke kwana su tashi tare ne wannan? ko a mafarki be taba kawo haka ba". Cikin abinda be wuce minti latatin ba Mahmud ya fito cikin kananun Kaya yayi fresh dashi ya fice daga gidan, har lokacin su Abubakar Basu dawo ba, da kanshi yake driving din, da Dan hanzari yake tafiya saboda gaba Daya hankalinsa yayi Asibiti. Lokacin Daya shiga direct office din consultant din ya nufa, be same shi a office ba Yana cikin ward inda yake duba patient dinsa, baifi zaman minti goma ba doctor din ya dawo da zugar wasu dalibai a bayansa Yana ganin mahmud ya gane shi, tunda yaji yana Jin yaransu yake Nan Nan dashi. A cikin office din wasu hotuna ya dauko ya aje a Kan table dinsa yace mahmud da sauran daliban su matso.Dalla Dalla ya shiga Yi musu bayanin yanda ciwon yake da yanda yake yiwa mutum illah idan har ba'a Farga an kawo mutum Inda za'ayi Masa aikin gaggawa ba saboda yanda spinal cord din ta matse to komai ze iya faruwa za'a iya rasa kafa da amfanin kasan Jiki na har abada, Dan haka daga Nan zuwa Kwana uku za'ayi wannan aikin, Amma dole charges zasu karu tunda sun Kara gani karaya a kashin hakarkarinsa na hagu guda biyu sai kashin mukamikinsa Daya goce". Take a Nan mahmud ya nemi a bashi bill na Karin charges din da aka samu, yaje ya biya komai ba damar ganin Baba malam haka dokar take,yana tafiya a Kan barandar Asibitin Yana sauri ya Karasa gurin Daya aje mota yaji daga bayansa ance. "Waye nake gani Kamar Mahmud Dange". Da sauri ya juya Yana mamakin waye wannan yayi Masa farin sani haka. Faisal ya gani kanin Aunty Surayya matar uncle Mustaphan zasuyi sa'anni da mahmud din, cikin fara'a Mahmud ya Fara fadin. "Faisal bungudu Long time, Daman talaka Yana ganinku?". "Kaji ka da wani magana Kai ganin ku ai sai Mai sa'ar gaske, Nigeria kun Mata tawaye ma kwata-kwata yaushe ake ganinku, meya kawo ka Nan ne haka ko patient gareka". "Eh wallahi wani Babana ne ya samu spinal cord injury muka kawo shi Nan, Kai Kuma meya kawoka?" "Wallahi Alhajin mu ne ya samu accident tun kusan wata hudu da suka wuce, karaya ya samu a cinya, anyi gyara har sau uku abun yaki shine, wani doctor da muke gani a wani private orthopedic hospital a Sokoto yayi Mana hanya mukazo nan, kaga jiya uncle Mustapha ya bar Nan kasar tunda shine ya kawo mu sai da ya Gama Mana koma". Jinjina Kai Mahmud yake kafin yace. "Allah ya bashi lafiya, ga jikin girma ga lalura muje na ganshi na duba shi". Tare suka juya Faisal din Yana fadin. "Wallahi Rabon mu hadu ne nace Bari na koma masaukina nayi wanka na huta tunda ba wata damuwa a tare dashi sunce sai Nan da sati uku zasuyi Masa aiki sai sunyi treating din gurin da infection ya Kama sannan zasu sake Masa aiki" "Allah yasa ayi aikin cikin sa'a yasa da nasara yasa a dace. "Allahumma Amin" Faisal ya fada. Lokacin da suka shiga Alhajin Yana zaune a gadonsa Yana lazimi da casbaha dinsa. Ganin Faisal ya dawo da wani yasa ya maida hanklinsa a Kansu, har suka karaso yana kallonsu. Sallama Mahmud yayi masa ya amsa sannan Mahmud din ya gaishe shi da jiki. Faisal ne ya yiwa mahaifansa bayanin Mahmud, cikin nuna Jin Dadi mahaifan na Faisal ya shiga jorowa mahmud godiyar abinda akayi masa, Basu jima ba Mahmud ya aje Masa Dala dubu yayi masa sallama, Mahmud yasha shi Albarka Kamar ze Bari Baki gurin godiya. Shima Faisal godiyar ya dunga jerawa Mahmud Kamar me, shiya dauki Faisal ya Kai shi har masaukinsu sannan Shima ya hada shi da dala dari biyar yayi gaba, wani irin shauki ke dibarsa akan yaje gidanta tunda gari ya waye yaji ba abinda yakeso irin yaje ya ganta ita da yaran, amma wata zuciyar na fada Masa kada kaje akwai k'ura Kuma wannan match din bazaka iya playing dinsa yanzu ba, kwabarka ce zatayi ruwa, dole ya karkata Kan motar ya dauke daga direction din da ze Kai shi gidanta, Amma fa dole yaje gareta duk rintsi Dan yanzu ma yasan Yana zuwa wani labarin za'ayi ba wannan ba Dan dole ballin ya tashi. __ Har dare Zahra Bata Jin dadin jikinta Sam da mahmud ma ya Kira Basu Dade ba yace Yana da wani uzurin da zeyi sukayi sallama. Wurin karfe biyu da rabi ta farka sai taji Kamar an Zuba Mata ruwa, da sauri ta yunkura ta tashi zaune abunda ta gani ya sakata tashin hankali ta sauko a zabure tana sallallami jikinta sai rawa yakeyi, period ne yazo abinda Bata taba yiba kenan ai sai kowa yasan da zuwansa Amma wannan sai ganin Abu tayi da wata irin Zuba ta tashin hankali. "Na shiga Tara mezan gani haka?". Toilet ta nufa tana cikin rudu ba kadan ba data shiga ta cire nighty din ta sakarwa kanta Ruwa ta wanka Yana bin kafarta Zuba yake sosai har da guda guda, ganin abin bana hankali bane yasa ta fashe da kuka, da kyar ta samu ya Dan tsagaita da Zuba ta hada pad biyu ta saka ta fito ta kunna wutar dakin yanda taga Kan bed din sai hankalinta ya Kara tashi cire bedsheet din tayi tana share hawaye. Cikin washing machine ta saka bedsheet din ta fito da towel a bucket da detergent ta Fara aikin gurin tana cikin aikin tayi wata irin Zuba wadda har Saida ya biyo kafarta saboda yawa hannu ta Dora a ka ta fasa kuka tana fadin. "Na shigesu shikenan mutuwa zanyi". Wayarta da dauko ta lalubo number Muhmud ta Kira ba tayi tunanin ko karfe nawa bane a can. Yana zaune yana aiki a laptop dinsa yaji Kiran ta ya shigo agogon dake parlourn ya duba yasan yanzu a Nigeria tsakar dare ne to lafiya yasan ba gwanar chart din dare bace bare yayi tunanin kiransa tayi suyi Hira. Yana dauka yaji shashshekar kukanta. Cikin kidima ya tambayeta. "Menene? Meya faru? Keda waye a dakin?" Kiyi min magana Mana ". Duk ya jero Mata wadannan tambayoyin, Bata bashi amsa ba sai faman fadin ta shigesu take. "Wai precious so kike Nima na fasa kukan ne? na tambaye ki kinyi min banza kina ta kuka, ko wani ne ya mutu aka fada Miki kike wannan kukan ko wani Abu yake damunki ne?" Ya fada Yana kwantar da murya Dan so yake tadan samu nutsuwar da zatayi masa bayanin damuwar data saka tayi masa Kiran tsakar dare. "Pls precious tall me menene Mana?". Cikin karaya da sallamawa ta bude bakinta da kyar tana shashsheka. "Wallahi me Amor jinane ze Kare bleeding nake kagan shi Nan sai Zuba yake duk na Bata bedroom din Nan Ni dai ka yafe min nasan mutuwa zanyi ta fada wani kukan Yana kwace mata. Jin abinda take fada ya daga Masa hankali sosai, saima ya rasa Yaya zeyi Mata wani tunani yayi, saiya aro jarunta ya yafa yace mata. " Pls haba my angel ki nutsu babu abinda ze sameki kinji maza kirawo Matar nan tazo ki hadani da ita. Kai kawai ta gyada Kamar Yana kallonta, Kiran number Aunty zilan tayi, tana cikin barci taji Kira figigit ta tashi ta dauka sunan Zahra ta gani da sauri ta dauka cikin kuka Zahra tace Mata. "Kizo Aunty zilai zan mutu". "Innailaihi wa innailaihi raji'un! Na zilai na shiga uku meya sameki?". Shiru tayi mata, da gudu-gudu zilan ta karasa bedroom din Zahra abinda ta gani ya daga Mata hankali. "Na shiga uku Ni zalaihatu meya sameki wannan ai Bari ne, tun yaushe Kika Fara zubar da jinin nan? Bari na fadawa Mai gadi ya kaimu Asibiti wannan ai ba abun Wasa bane, Kiran Mahmud ne ya shigo Aunty zilai ta mikawa wayar. Jin muryar Mahmud yasa Aunty zilai Kara risunawa tamkar yana gabanta, magana ya Fara Dan ko gaisuwar da take masa Sam beji ba. "Dan Allah ki taimaka Mata ta gyara jikinta ga zayyan can Yana jiranku zaku wuca Asibiti. A&E sukaje anyi Mata tambayi daga karshe sukace sai nayi scanning da safe zasu tantance Dan Zahra ta kafe ita ba miscarriage tayi ba su Kuma sunce babu abinda ze kawo Mata irin wannan heavy bleeding din Sai shi, suna Asibitin mahmud ya sake Kiran zayyan ya tambaye shi me sukace ya sameta. Yace Masa ance miscarriage tayi Amma da safe zasuyi hoto su duba. Jim Mahmud yayi Yana tunanin meya hada zahra da barin ciki Kuma? Sai dai wani abun na daban gaskiya. Sunyi mata duk abinda ya kamata Kuma Alhamdulillahi zubar tayi sauki, wurin karfe hudu da rabi suka dawo gida sai da safe zasu koma za'a Mata scanning a ga menene mu"assasa na kawo zubar jini kuma ayi Mata pcv. Bayan daqowarsu mahmud ya kirata yafi sau biyar Yana tambayarta ya jikin? Ba wata matsala? Meke mata ciwo?. Haka yayi tayi ita har Saida ya koma Bata tausayi ma ya fita shiga damuwa ita keda Matsalar Amma ya fita shiga tashin hankali nesa ba kusa ba, ya fada Mata yayi Dana sanin tahowa ya barta,Amma dole yasan abinyi tunda akwai matsala. [2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: *AUREN HUCE HAUSHI* 08055362975 Or 09061432330 My WhatsApp number. AISHAT ISAH MUSA (Aunty Uwani) Naman Fateemah. Page 64. .............Sun koma asibitin sunga consultant g Gynecology doctor sabuwar ce tazo daga federal medical center Birnin kudu, Dr Hajara yqrinya ce karama Amma tasan aikinta, so sai ta duba zahra ta turata ayi Mata special scanning saboda taga history na ciwonta a cikin file dinta. Basu Dade a gurin scanning din ba suka dawo, tunda doctor din ta bude take jinjina Kai abun yayi matukar Bata mamaki, Saida ta aje result na scanning din sannan ta cire eye glasses din idonta. "Dan Allah sister me ki kayi amfani dashi akan matsalarki ta fibroid? Ma'ana kin Sha wani magani na hausa Kona Islamic chemist haka akan matsalarki?". Kai zahra ta gyada mata alamar eh. "Pls my friend talk to me". Ta fada tana murmushi. "Eh nayi amfani da wani magani Amma Ina ganin black pepper ne kawai da kakata ta bani tace na ringa Sha da ruwan zafi Amma sai yayi twenty minutes Zan tace na Sha safe da yamma tace ze narke basai an yanka an cire ba, tace ma Yana maganin haihuwa Wanda baya haihuwa idan Yana amfani dashi eggs dinsa zeyi producing a samu haihuwa, tace min Yana magani sosai a bangaren ciwuwwukan Mata da suka shafi mahaifa, ko macen da bata haihuwa shima idan tana amfani dashi In Sha Allah zata Samu haihuwa, abinda ta fada min kenan". Zahra ta fada tana kallon Dr din. "Masha Allah, batayi karya ba Babu komai a cikin mahaifarki yayi dissolving ya wuce a cikin jinin da Kika zubar, Naga sun rubuta miscarriage irin haka ne yake kawo a batawa yarinya suna alhalin ba haka bane". Ta fada tana kallon Aunty zilai. "Kinga sister dina budurwa ce dal babu wata alaka data taba hadata da wani namiji na gani Dan haka ku bani number din Mama nayi Mata bayani nasan ba Karamin tashin hankali ta shiga ba a jiya nasan har yanzu Bata da nutsuwa da wata ce ma tana Nan tare damu ayi komai a gabanta". Kallan kallo ake tsakanin Aunty zilai da zahra. Me maganar likitan ke nufi da tace zahra budurwa ce? Tsatstsare Aunty zilai zahra tayi da Ido kafin ta juya ta kalli doctor Hajara kamar yanda ta gani a jikin Dan siririn freme a Kan table dinta. "Nagode doctor Amma ba sai kin Kira Ammatah ba Bata kasar taje ganin likita tana da hawan jini ne Batasan ma bani da lafiya ba, ya pcv din Naga 48% ya Isa kenan?. Murmushi tayi doctor din. "Sister zahra ai yanzu haka sai ki bada jini,me 27% ma is ok basai an Kara masa jini ba sai dai a bashi maganin Karin jini". "Ok tom shike Nan nagode kwarai sai an Jima" zahra ta fada tana tashi tsaye, har sun Kai Bakin kofar fita taji doctor din na fadin. "Sister zahra bazaki bani number wayarki ba idan an tashi bikinki nazo Miki, bansan kowa ba a garin Nan daga Jigawa mukayi transfer nida mijina shima doctor ne pediatric banu Dade da Aure ba Ina son nayi kawa a nan". Dawowa zahra tayi tana fadin. "Ai kuwa na gode kwarai da gaske kawo na saka Miki number dina sai ki kirani Naga taki". Ita dai Aunty zilai mamakin duniyar Nan ya cikata, har gurin mota doctor Hajara ta raka zahra saboda Bata da patient a ranar zata shiga ante-natal zasuyi awo. Address din gidan Ammah ta bawa doctor din, sukayi sallama suka wuce, suna hanya mahmud ya Kara Kira yanda yaji muryar ta cikin nutsuwa yasan lamarin yayi kyau. "I will call you later, we are on the way". Ta fada Masa a hankali. "Ok" Kawai yace ya yanke Kiran. Tunda suka shigo motar zahra ta hade gabas da yamma yanda Aunty zilai ma ba zatayi Mata wata magana ba, don taga yanda ta zaro Ido lokacin da doctor ke bayani. Har kofar parlour zayyan ya kawo su ya sauke Yana fadin. "Ranki shi dade Allah ya Kara lafiya". "Allahumma Amin" Zilai ta fada. Ita ta bude kofar Zahra ta shiga, suna shiga ciki zahra ta juyo tana fuskantar zilan. "Aunty zilai wannan maganar ta Zama sirri yarda da Aminci yasa nake yin abubuwana a gabanki tunda bamu taba samunki da wani abun ashsha ba, ko Ammah bana son taji labarin wannan abun Daya sameni Kinga dai ance babu ya wuce to zancen ya tsaya ya junan mu". "In Sha Allah babu Mai ji uwar dakina, Amma wani hanzarin ba gudu ba, ko kuma dai a fadawa Ammah mijin naki bashi da lafiya sai a nemar Masa magani ai irin wannan ba'ayin shiru kada karamar matsala ta Zama Babba, yaro har yaro Amma babu lafiya". Ta fada tana Jimamin abun. Dariya maganganun ta suka bata ita bilhaqqi da gaske take maganar ta. "Ki daina dariya wallahi ba abun dariya bane, yanzu saboda Allah kuja Baki kuyi shiru Dan yarinta, ai wannan ba Karamar matsala bace ba fa". "Wai Aunty zilai waye yace Miki bashi da lafiya? Lafiyarsa kalau wallahi". "Eh Daman lafiyar kalau Mana azahiri Amma a badini kuma ai Mai tsananin ciwo ne". "Allah Ina fada Miki ba abinda ya sameshi fa". Wani kallon Amma Baki da lissafi zilan tayi mata. "Eh Naga lafiya a tare dashi tinda akace har yanzu kina nan a buduwarki Kinga kuwa ai lafiya ta tabbata a gare shi, yo ko waliyi ne aka aje Masa danyar yarinya kamar ki ya aje walittakar ya Raya sunna Amma shi yaro sharaf dashi ace ya Zuba Miki Ido tsawon watanni ai kinsan da matsala". Ganin ba zata fahimce ta ba yasa Zahra fadin. "Kinga Aunty zilai babu ruwan ki da shiga sangarsa ki Zuba Masa ido idan ma bashi da lafiyar ai ya sani ze nemarwa Kansa magani". "Gaskiyarki Kuma fa babu ruwanw kada na dauko ruwan dafa kaina da kaina". "Da dai yafi". Bedroom Zahra ta wuce barci takeji sosai. Tana shiga ta cire rigar jikinta wani wankan ta sake, fitowa tayi daure da towel sky blue a jikinta, jinta take wani iri Bata taba samun irin wannan bleeding din ba shi yasa duk ta takura. Zama tayi tana shafa lotion na razac tana sonsa sosai, tana cikin shafawa taji ringing din wayarta a Kan bedside tashi tayi tsam ta nufi gurin sunansa ta gani Yana yawo Kan screen din, wallahi tausayi yake Bata ya kasa samun nutsuwa Kota sisin kwabo. Video call ne, dauka tayi tana Masa sallama. Tsura Mata Ido yayi yana tasbihi ga ubangijin da yayi wannan surar, wani yawu ya hadiye ba shiri, kashe mata Ido Daya yayi Yana dage girarsa ta hagu. "Precious..," Ya kirawo sunanta in a deep voice, lumshe Ido tayi Dan sai taji yau sunan ya zamar Mata wani so special. Gefen bed ta zauna ta Dan jingina da pillow a jikin gadon, sexy eyes dinta ta Zuba Masu kamar Zaiba a ciki kafin ta amsa Masa gently. "Na'am.. meu Amor....". Saida ya lashe lips dinsa saboda wani abu ya tsirga Masa cikin mararsa har Saida ya rufe Idanunsa, a hankali ya sauke su a kanta fal fitina Yana Mata wani kallon kasa-kasa. "Kin tashi hankalina fa ba kadan ba, na rasa nutsuwa ta, hakurin zamanki nesa Dani ya Kare gaskiya bazan iya wannan jarumtar ba, gangar jina ke Nan Amma zuciyar tana Nan Kinga kuwa mutum ba zuciya ai babu mutum, ya jikin naki? Me suka fada da sukayi scanning din? naji zayyan na fada min wai sun ce miscarriage kikayi, nace a'a sai dai wani abun badai shi ba". Gyara kwaciyarta tayi. "Nima da farko haka suka fada Aunty zilai ma haka tace data gani, na fada musu bashi bane Amma Basu yarda ba, sai doctor din data dubani da safen Nan tace fibroid din ne yayi dissolving ya biyo period shine ya kawo heavy bleeding din, Kuma fa da har number din Ammah ta nemi na Bata Wai zatayi Mata bayanin abinda ya faru Dani tasan hankalinta ba a kwance yake ba ance 'yarta budurwa tana dauke da ciki tayi bari, gara ta fada Mata Babu wani Daya taba sanin yarta a matsayin mace lalura ce kawai, kasan muna dawowa Aunty zilai ta tsareni da maganar bamu da wayo Ashe baka da lafiya muke zaune bamu fadawa kowa ba ita zata fadawa Ammah a nemar maka magani tunda Amana ta turota gurina, da kyar fa na fashimtar da ita nace babu ruwanta ta barka ka nemi maganinka". Dan cute pink lips din ta yake bi da kallo harta Gama bashi statement din. Kankance Idanunsa yayi Yana Mata wani kallo. "Gaskiya Kam maganar doctor gaskiya ce, Ni nasan har yanzu rainon a Bata nake yi koba haka bane? Kice da Auntyn ki ta Kira Mana Ruwa? da bazan Kara yarda mu hada ido da Ammah ba ai tonon sillil ne wannan shikenan na Zama ragon maza a idanunta". Ai zahra Bata gane ta saki layi ba Sai daga baya, kunya taji ta rufeta. "Nifa labari na baka ba Wai wani Abu ba". "A'a gara na saka shimma kada a zaci da gaske ne, yanzu ita ta yarda bani da kuzari fa sai dai tayi ta kallona a haka koba haka bane?. "Pls dan Allah mubar zancen Nan yafi karfina". Murmushin nan nasa yayi mata yana fadin. "Bayani zakiyi da yaren garinku yarinya gashi nan kin jamin ana min kallon wani lusari ko?". Kira ne ya shigo Masa daga Asibiti, da sauri ya yanke Kiran Yana fadin. "Bari na daga kirane daga Asibiti. Yana sauka daga online tayi ajiyar zuciya Allah ya taimaketa, da Allah kadai yasan meze baro Mata taga alamar kamar hakurinsa Yana neman karewa, Dan wannan idanun nasa abinda suke fitarwa Yana Bata tsoro. ______ Maganar canza lokacin aiki sukayi masa saboda wasu dalilai da suka saka za'ayi Masa aikin gobe Dan haka suna iya shigowa sun fito da Baba Malam din daga investigation room din. Yana aje wayar Abubakar da Habib suka shigo, tashi yayi Yana fada musu su shirya zasu wuce Asibiti gurin baba Malam Wai sun canza ranar aikin gobe zasuyi Masa Ina ganin sun gano wani Abu daya zama dole aikin ya Zama emergency. Cikin abinda Bai wuce minti talatin ba suka shiga Asibitin office din doctor suka nufa tunda ya bukaci ganin mahmud saboda ze cike wasu forms ze Kuma yi signing a takardun da za'ayi aikin. Basu Dade ba suka Gama da office din doctor suka nufi dakin da Baba Malam din yake. Suna tafiya kawai Habib kallon mahmud yake ya rikide ya juye daga mahmud din Baba Malam ya koma wani na daban Mai wani irin kwarjini da cikar Kamala ko Zama sukayi Hira irin ta da yanzu sai Habib yaji baze iyaba sai fa mahmud ya matsa Masa sannan yake Dan sakewa, ga Abubakar wanda shine babban guard dinsa Amma sukayi basaja ba Wanda ya gane, ga wani Karin abin mamakin Wai Bilyaminu ma yaran mahmud ne. Har suka karasa dakin yana ta faman tunanin abun. Masha Allah ba karamin Dadi sukaji ba da ganin yanda jikin Baban yake. Sallamar su ya amsa Yana sakin murmushi tamkar ba Mai lalura ba, gani ma sukayi har wani haske ya Karayi duk da Daman farin mutum ne Shi, Yana kwance sandam da sauri mahmud ya Karasa kusa dashi Yana fadin. "Masha Allah! Baba jiki ya Fara kyau Alhamdulillahi, ya kaje jin jikin naka?". "Alhamdulillahi Mahmud jiki ya Fara kyau ko yanda nakeji da banbanci akan kwana ukun baya, sannunku da kokari Allah yayi Albarka yasa afi haka". "Allahumma Amin". Suka amsa su duka, Abubakar da Habib ne suka matso suna gaishe da shi da tambayar ya jikin nasa. Ya amsa musu da sauki suma yayi musu godiyar dawainiyar da suketa faman yi dashi. A Nan suka zauna har dare suna dauke Masa kewa mahmud ya cika Alkawari ya kirawo Bilyaminu video call yace ya Kaiwa iya Abu zasuyi magana da Malam, taji dadin yanda taga jikin nasa Dan sun Jima suna Hira har su mahmud sukaje suka Kara dubo Alhajin su Faisal. Sai wurin goman dare na agogon kasar suka wuce daga asibitin, ba gida suka nufa ba, Abubakar ke driving sai Habib dake zaune a gefensa sai Kuma oga kwata-kwata dake baya yana ta cinkunar wayarsa. "Sir ina zamu Fara zuwa?" Abubakar ya tambaya cikin ladabi. Saida ya Gama duba results din club dinsa real Madrid, sunyi Wasa lokacin suna Asibiti shine yanzu yake duba results din wasan. "Wuce Africa Avenue kawai na gama ganawa dasu sai mu shiga Taj idan lokacin be Qure ba". "Ok sir Leela palace kenan?". "Eh a can nace musu zamu zauna" "Ok." Akalar motar ya canza daga hanyar da yake bi, shi dai Habib nasa ido ne Dan fadan da yafi karfinka sai ka mayar dashi Wasa. Ganawa ce mahmud din zeyi da managers na different companies dinsa ya Dade Basu hadu ba sai dai ta Internet kawai, shine yayi amfani da wannan damar ya tarasu duk da yaso sai Nan gaba to wata kura ce ke neman tasowa shine yayi musu Kiran gaggawa. Habib yaso fita mahmud ya Hana shi, ba karamin abin al'jabi Habib ya gani ba yanda yaga manyan mutane daga different countries suna Masa aiki a Nan Indian shifa har tsoro ya Fara kamashi waye Mahmud ne Wai? Yanda yaji managers da Accountant suna bada lissafi saida jikinsa ya dauki tsuma, basu suka baro Leela palace ba sai kusan Daya da rabi na dare. Suna shiga gidan Mahmud ya wuce bedroom, requesting coffee kawai daga gurin Mr Ajey. Su Habib dai sunci Abinci sannan suka wuce, kowa ya shige nasa, tun jiya aka hada dayan dakin Habib ya koma ya barwa Abubakar wanda suka Fara sauka. A gajiye mahmud ya shiga bedroom dinsa wayar da eyeglass din ya aje a Kan bedside ya wuce toilet. Lokacin Daya fito Mr Ajey ya kawo masa coffee dinsa. Saida ya saka pyjamas dinsa milk colour mai haske sannan ya zauna Yana sipping din coffee a hankali yana Jin dadin yanda yake ratsa Masa makogwaro Yana gangarawa. Kira ne ya shigo wayarsa yasan ba previous bace har ze share sai ya dauka ya duba Sameer ya gani. "Sameer" ya ambaci sunan a fili sannan ya daga Kiran. Daga can Sameer din ya Fara magana. "Sir Naga sakonka, wallahi da kyar na samu visar madam yau Amma sai Monday zata taho in Sha Allah gara nima dai na huta". Ya fada Yana dariya. "Au dariya ma kakeyi ko? wallahi idan tace na mayar dakai China da Zama Allah saika koma can,Kuma Banda madam zaka tafi, sai bayan wata shida zaka ringa zuwa Kuna gaisawa shima sai ta amince, idan Bata amince ba sai dai once in year". "Tuba nakeyi gani nayi ka kasa hakurin rashinta a kusa da Kai tun yanzu to Yaya idan labarin yasha banban"?". Ya fada Yana dariya irin ta shakakikan friends. "Allah ya shiryeka badai abinda zakaji Dan saka Ido kawai, ka aje komai jibi ka wuce Nigeria Kai da kanka zaka kawota min ita Kano". "Ok. In Sha Allah". Sukayi sallama,wayar ya aje yana tunanin ko ya kirata ko Kuma ya kwanta ya huta. ** *** ** Barci sosai Zahra tayi Bata tashi ba sai kusan la'asar toilet ta shiga ta sake gyara jikinta. Alhamdulillahi Abun ya Fara sauki sosai, amma dai ha lrokacin Yana Zuba over, Saida ta shirya ta nufo parlour tana rike da wayarta, ba kowa a ciki sai kamshin turaren daki da tureren wuta. A hankali ta ratsa ta nufi dining Abinci ta gani kala biyu coconut rice ce sai danbun shinkafa da yaji vegetable a ciki, dambun ta Zuba kadan taci kadan ta tashi ta dawo parlour ta zauna. Aunty Hasana ta kiya har sau biyu ba'a dauka ba saita tura mata text, Aunty Safiya ta Kirawo lokacin suna makaranta dalibai na Exams, dauka tayi tana amsa sallamar zahra tana fadin. "Kaga Mrs Dange, ya kanon?". 'yar dariya zahra tayi. "Kaji dai Aunty Safiya, to Ina Azare Kuma kusa dake ma". "Ahhh haba Dan Allah....!" "Wallahi Ina layi na biyu bayan layinku". Dan Jim Aunty Safiyar tayi tana tuna wani gida data gani lokacin da taje barka layin Wanda "yan layin suke ce masa gidan Dan America, masu aikin ginin ne da wani ya tqmbayesu gidan waye sukace Mai gidan Yana America shikenan suka sakawa Masa gidan Dan America. "Kamar nasan gidan naje barkar haihuwa kwanaki baya Naga wani sabon gida akace mai shi baya kasar Ina shine gamu Nan zamu shigo da Amatu in Sha Allah". "A'a kice na tashi na shirya abin tarba, Ina jira, Dan Allah kuzo da wuri". Aunty zilai ce ta shigo fadin. "Wallahi daga na Dan kwanta na huta barci ya daukeni". "Ai Rai dangin goro ne hutu yakeso, Ina laifinki sannu kema ai jiyan yanke Miki barci akayi shi Kuma ba'a cin bashinsa sai an biya" "Haka ne Kam ai anyi ta barka dai tunda na rabu da wannan kaddararren ciwon cikin gaskiya duniya da magani waye ze taba kawo masoro zeyi irin wanna aikin?". "Gaskiya dai Kam". Zahra ta fada. "Amma dai uwar dakina kin Kira Hajiyar makwarari kiyi Mata albishir ko?". Kai zahra ta girgiza alamar bazata kirata ba. "A'a ba'a haka,ki kirata ki gaisheta ki fada Mata magani yayi aiki kiyi Mata godiya ai zataji dadi'. "To shikenan na kirata anjima saina fada mata, yanzu me za'a Karayi Mai sauri zanyi Baki ne abokan aikina da muka zauna a Inda nayi service". "Akwai samosa da nayi dazu na saka a fridge sai a soya Musa tunda da abinci da drinks ina ga ai ya Isa ko?". "Eh hakan yayi". Kitchen Aunty zilan ta koma ita Kuma zahra tabi lafiyar kujerar. Aunty Rukayya ta kirawo. Bata kusa sai mommy ta dauka cikin ladabi zahra ta gaisheta mommyn ce tace Mata. "Ai kuwa Rukayya na gidan Hajiyar makwarari dazu ta tafi ta manta wayar a gida garin sauri". "To mommy Baki na Kira da layin Hajiyar na gode". "To nagode Allah yayi Albarka, ya wajen Mai jikin Kuma Sameer yace sun wuce indai ko". "Eh suna can da sauki". "Allah ya bashi lafiya yasa ayi aikin a sa'a". "Allahumma Amin nagode". Sukayi sallama. Akalar Kiran ta juya ga Hajiyar makwarari cikin sa'a wayar na hannunta ta Gama amsa wani Dan uwanta Malam na Dala Kiran zahra ya shigo. Dauka tayi tana fadin, "Salamu Alaikum, waye yake Kira?". "W/slm, Hajiya nice zahra". Dan Jim tayi tana tuna Ina tasan muryar Nan. "Zahra wace ce kenan? Ko Zahara,un Hajiya Fateen lalloki?". "A'a ba ita bace". Sai zahra ta rasa me zata ce Mata ne, tace zahrar mahmud abokon Sameer, sai taji da nauyi ta fada Mata haka. Rukayya ce ta shigo da cup din kunun tsamiya data damawa Hajiyar a hannunta. "Wa Kika Sami haka naji kina ambatar zahrar lalloki". "Ungo kiji ko wacece tayi shiru batayi min bayani ba ke kiji ko zata fada Miki". Wayar Rukayya ta karba tana mikawa Hajiyar kunun a cup. "Aunty Rukayya". Zahra ta Kira sunanta. Take ta dauki muryar zahrar. "Au kice min amaryar big bro ce ai bayani Zaki yiwa Hajjaju, kince zahra Ina zata gane". "Hajiya matar Ya Mahmud ce mutuniyar ki da Kika Gama maganarta dazu to gata 'yar halak ta kiraki". "Ga Hajiyar ku Gama gaisawa Dan ba barina zatayi muyi hirar kirki ba idan Baku gaisa ba tunda nazo take you min zancenki". Wayar ta mayar Mata ta nemi guri ta zauna. " 'yar Nan Daman kece ki kak'i yi min bayani dan Ashatta". Gaishe da Hajiyar tayi tana fadin. "Cewa nake Zaki ganeni fa, Daman kiranki nayi na gaisheki Kuma na fada Miki ciwon Nan na cikina ya narke yanzu babu shi". Wata zabura Hajiya tayi kamar yarinya tana fadin. "Kai Masha Allah kice nayo shiri na taho Azare na kawo Mik wani maganin saboda bibiko da Kuma aasske- sassake saboda sanyin dake Hana Yara haihuwa kinsan yanzu kuma sai a Fara shirye-shiyen haihuwa Kwana kadan ai sai laulayi, Dan ma naji labari mijin naki ya Kara yin halin nasa ya fice daga kasar wallahi sai kin jajirce kin zamar masa karfen kafa sannan zakiji dadin aure, Amma Kika zauna sanyin Nan sai kinyi tsa-tsa a banza Naga shi matan ma basa gabansa ta Neman kudinsa kawai yake, Kullum mutum na sama kamar tsuntsu to kinji dai na fada Miki". Baki bude Rukayya ke kallon Hajiyar. [2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: * AUREN HUCE HAUSHI* MAMAN FATEEMAH. Page 65 ---------- Wayar hannun Hajiyar makwararin Rukayya ta karbe tana fadin. "Dan Allah ki daina fadin wata maganar ba girman ki bane". "To uwata saiki hanani na saita yarinya, ai gobe in Sha Allah Mahfuz ze dangana Dani Azare, yo duk abinda aka yiwa matar Mahmud ai bazamu iya biyansa abinda yayi Mana ba, Banda rashin lissafi irin naki Rakiya ke kome nace zanyiwa iyalin yaron Nan ai naki idone,kina zaune ya daukeni ya kaini wata uwa duniya aka gyara min ido da yanzu kina Nan kina min jagora ko bakya so kuwa. Tashi ki kimtsa ni ki rakani kurmi na Sami abinda bani dashi, muje agadasawa a Sami kilishi da dambun nama na tsaraba mu shiga madatai a samo gireba da su bakilawa to kinji" Ta yunkura ta tashi Tana daukar sauran kununta, ita dai Rukayya bakinta mutuwa yayi da kalaman Hajiya, tunda ta furta tafiyar nan Allah ne kadai ze kawo abinda ze hanata zuwa Amma badai Dan mutum ba, tun su Sameer na secondary tasu tazo Daya da mahmud tun Batasan Allah ze daga shi haka ba. A nutse Amatullah ke driving dinsu, taso ta wuce gida saboda ta gaji sosai Amma jin zahra na garin Kuma babu nisa da gidan yayar mamanta da take zaune a hannunta sai kawai tayi waya ta fada Mata zasuje unguwa. Tunda suka shigo layin Amatu ke Kakabin gidan tana fadin. "Kambala'i wannan Kuma waye yayi one in town din Nan? lallai Aunty Safiya unguwar taku ta masu ido da kwalli ce". Murmushi tayi mata tana kokarin Kiran waya. "Mun shigo ki turo a shiga damu". Dan saurare tayi kafin tace. "Ok muna jira". Ta sauke wayar daga kunnenta. "Kika ce menene?". "Cewa nayi unguwar taku ta Zama ta masu Ido da kwalli". "Bakiji ranar nan muna maganar layin Dan America ba? To ai gidan ne ake cewa gidan dan America". Labarin yanda gidan ya Sami suna ta Bata. Dai dai suna zuwa kofar katafaren gate din gidan. "Dan tsaya a Nan mu jira muga ta Ina zata bullo Mai kaimu gidan". Amma ita Safiyar ta hakikance matukar da gaske MAHMUD DANGEN ne da gaske mijin Zahra to babu ko tantamar wannan gidansa ne. Saka aya a tunaninta da bude Karamar kofar gate din ya Zama lokaci Daya. Zilai Mai aikin gidansu zahra Amatu ta gani ta fito, zaro Ido tayi tana kallon Aunty Safiya. Gyada Mata Kai tayi kawai, sannan ta bude kofar ta fito. Gaisawa sukayi da Aunty zilan, sannan tace Mata. "Ko kune Bakin Uwar dakina Zahra". "Eh mune". Aunty zilan juyawa tayi da sauri ta koma ta fadawa zayyan zahra tayi Baki. Jim yayi Yana kallonta kafin ya samu zarafin fadin. "Yallabai fa ya kafa dokar kada nabar kowa ya shigo gidan nan, Amma Bari na fada Masa duk da nasan ba wadanda yake nufi bane. Tana tsaye ya Kira Mahmud cikin sa'a ya sameshi, tun kafin ya fada masa wani Abu yace masa. "I sw everything, just open the door". Kawai ya katse Kiran Dan yana bibiyar gidan ne tun lokacin da yaga ta saka ayi wani girkin, Dan har a kitchen Saida aka saka CCTV. Gate din zayyan ya bude musu suka shigo, parking lot Amatu ta aje motar suka fito zilai tayi musu jagaba. Amatu sai raba Ido take Dan wallahi gidan ya tafi da imaninta ba kadan ba. Suna shiga zahra tayo wani tsalle tana fadin . *Wayyo Allah oyoyo! oyoyo!! Sannu da zuwan ku Amatu, Aunty safiya nagode da Kika kawo min Amah wallahi Daman Ina nemanta. Dan ja Baya Amatun rayi tana fadin. "Ni ba gurinki nazo ba Aunty safiya na rako". Hannunta zahra ta riko tana fadin. "Haba my bestie kiyi hakuri Dan Allah na tuba kowane laifi nayj kada a tona".. . dariya sukayi su duka, Ammatu dai 'yar kauye ta zama Dan Saida ta tada Kai taga yanda saman dakin yake kamar sararin samaniya Dan harda taurari da wata. Dauko wancan kawo wannan zahra da Aunty suka shiga yi, sai murna zahra keyi na ganinsu, sunci sun Sha sannan suka Dora da hira har aka Kira sallar magariba hirar yaushe gamo akeyi, cikin hirar ne Zahra ke fadin "Wai da gaske kinsan Mahmud?" Zama ta gyara tana fadin. "Wallahi ba karya har gidansu na sani sai dai shi nasan be sanni ba". Daga Nan ta tsaya itama Zahra Bata zafafa ba taja bakinta tayi shiru. Dakin kusa dana Aunty zilai zahra ta kaisu sukayi alwala, har Amatu zata Fara sallah ta tsaya ta dubi zahra. "Ya Naga ke Baki tashi kinyo alwalar ba". "To sa'i'dawa Ina ruwanki". Gurin zahra Amatun dawo ta zauna a gefen gadon in da zahra ke zaune. "Zahra Wai ya haka, ko dai planning kikeyi ne? Amma ace har yanzu babu wani labari, Ni da naganki kinyi wani sirrin kyau nayi zaton ko an Mana ajiya ne? Kuma kice Wai bakya sallah". Dariya zahra tayi tana Fadin. "Cikin lafiya? Ai ni ban isa haihuwa ba". Wata malalaciyar dariya Amatullah tayi. "Kice min 'yar yaye aka kawo masa, Wai Ina yallaban? Ko yana ciki kin Hana shi fita Dan Naga yanda Kika cika din Nan nasan baya Wasa gurin zagaya gonarsa tunda ga yabanya Nan tayi kyau da gani ana samun ban Ruwa akai akai". Ta fada tana Kara wata dariyar. "Wallahi Amah ki daina wannan dabi'ar Baki da magana saita wannan sabgar Kinga fita ta, Ni idona da sauran kunya a cikinsa Banda tsabar jaraba a gaban Aunty safiyar kike fadar irin wanna magana, Dan tsabar gulma da kinibibi kinyi alwala Amma Kika zauna Zaki Fara zancen da ze karya Miki ita, wallahi mijinki yaga ta Kansa irin ku ne maza suke guduwa daga gida saboda halinku". Tana Gama fada ta Mike ta fice, wayar ta aje a Kan gadon. Daukan wayar Amatullah tayi tana juyawa, ba karamin mamaki tayi ba da ganin wayar dake hannun Zahra. "Wai ba zakiyi sallar ba kema Naga da alama ma kin Manta zakiyi sallar in dai lamarin gidan Nan ne bakiga kamai ba, I'm telling you in dai 'yan wannan family din ne, kinsan Allah duk wannan Wasa ne ko ita kanta Mai gayya Mai aikin Batasan wa take Aure ba, kin manta na fada Miki indai shine baze iya rayuwa da matarsa a wancen gidan ba?". Kai Amatullah ta gyada alamar haka ne, Bata iya tofa wata maganar ba saboda shigowar zahra. "Au bakiyi sallar ba kenan? Gaskiya kina Wasa da sallah". "Kema dai Kya fada Mata, gashi na baro baby na Dan ma tana cin Abinci shi yasa Honey Bai takura min da Kira ba, suna cikin gari duka gidan Baba Dan lawan". Tashi Amatullah tayi ta tayar da sallah. Basu suka bar gidan ba sai bayan insha'i Shima Saida mijin Aunty safiyar ya Kira Dan bayan sunyi sallar babin karatu Aunty safiyar ta budewa zahrar Dan idan ta Fadi wani abun rufe Ido zahrar takeyi Amah na Mata tsinyar Wai muna furcine idan suka shige other room wata Kila ita ke Jan sitiyarin motar ai tasan ba'a banza ba tayi irin wannan cikowar tasan ta gane garin. Sai a Nan Zahrar ke fada musu mahmud din ma baya kasar Yana India an Kai malaminsu Asibiti ya samu matsala a bayansa. Sun jajanta sosai, mayuka da turaruka Zahra ta basu, Aunty safiyar tayi mata Alkawarin kawo Mata wasu kayan Mata dasu tureren mara Mai fitar da oga daga hayyacinsa duk iya yanda ya Kai ga kame bakinsa, Amma Bata fada Mata hakan ba tasan halin kayanta sai taki amfani dashi. Har gurin mota zahra da Aunty zilai suka rakosu, bayqn sun tafi ciki Zahra ta wuce wanka takeso Dan ki take kamar ya Bata Mata jiki. Basu Dade suna Hira ba Zahra taga Aunty zilai tana hamma sai tace Mata taje ta kwanta kawai tasan har yanzu da sauran ramuwar barcin a idonta. ********* Tun karfe shida na safe Mahmud ya wuce asibitin shida Mr salahuddeen, Saida ya jira doctor din yafi son ya Gama da doctor din kafin yaje gurin Baba malam misalin bakwai da rabi doctor ya shigo office dinsa be Jima da shiga ba mahmud ya shiga suka gaisa da yarensu na indianci, sannan yayi Masa bayanin yanzu takwas dai-dai zasu shiga dashi suna tunanin zasu dauki awa goma Sha biyu suna aikin Dan ma lakkar Bata tsinke ba. sallama sukayi ya nufi dakin da Baba malam din yake. Lokacin da suka shiga har an shirya Baba malam cikin Kayan aiki. Murmushi ya fara yi da yaga mahmud ya shigo. Da sauri Shima ya nufe shi Bai taba jin karaya ba irin ta yau daya ganshi kwance sandam babu inda yake motsawa daga kugunsa zuwa kafarsa. "Sannunka jarimin namiji, ubangiji yayi Albarka Mahmud ko yanzu Allah ya bani abunda bani dashi da namiji, kayi min komai Babu abinda zance maka sai godiya, idan Allah yasa na tashi falillahil hamdu idan Kuma lokacin komawar yayi to muna rokon Allah yasa mu cika da imani, ga Zainabu Nan Dan Allah a kula da ita, ga Kuma makaranta Nan Daman yanzu ni suna ne kawai na me makaranta, Amma kune ke dawainiya da ita, to kada a kasa ko bayan Mana Nan bamu San abinda ubangiji ke nufi da kawoka gurinmu ba shiya barwa Kansa sani, a kula da ibada da Kuma riko da gaskiya, Mai gaskiya baya tab'ewa kayi duk Mai yuwuwa ka koma mahaifarka Dan girman Allah a rage fushi kaji mahmud bashi da kyau ko alama ka Zama Mai yafiya kaima Allah ya yqfe maka kaji, Nima ka yafe min Zaman da mukayi Kona saba maka, Kuma ka rokarmin sauran jama'ar da muka zauna dasu Suma a fada musu na yafewa kowa Nima su yafe min, Abu na karshen da Zan fada maka ga yarinyar nan kaji tsoron Allah a Cikin lamarin ta nasha yin istikhara Ina ganinka a Cikin wata irin wadata Wadda na kan samu kaina da tunanin abun to duk yanda rayuwa ta juya ka kula da Amana ta Fadima marainiyar Allah ce". Tunda Baba malam ya Fara Masa wannan magqngaun masu Kama da wasiyya jikinsa ke tsuma daga ciki Yana ta faman rokon Allah akan ya rufa Masa asiri kada bawan Allahn nan aikin ya Zama sanadinsa. "Idon jajur da gani kukan zuci yake ya Kara rike hannun Malam. "Baba in Sha Allah lafiya za'ayi aikin nan a Gama Kuma ka warke in Sha Allah saika taka da kafarka ka zagaya Asibitin Nan Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w, Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne ya bada nasarar aikin da za'ayi, ai sunce babu wata matsala Mai yawa dama mun zauna a Nigeria anyi aikin". Kafin Baba malam ya fadi abinda yayi niyya ma'aikatan da zasu tafi dashi sun shigo da gadon da zasu tura shi zuwa theater room din, lokacin da zasu canza Masa gado ya ringa fadin. "Wash!!! Allah kuyi a hankali bayana bana son ana motsani" . Da sauri Mahmud ya karaso Yana musu magana da yarensu, da sauri suka mayar dashi suka fita. Sannu kawai mahmud ke jerawa Baba malam Nan da Nan jibi ya rufe shi. Kusan mutum bakwai suka shigo suka hadu aka Dora shi a gadon sannan suka tura shi a hankali suka fice daga dakin mahmud na biye dasu, har kofar karshe mahmud ya raka baba Malam Bai tsaya ba saboda dauriya kawai yakeyi Amma Yana Daf da zubar da hawaye. Guri ya nema ya zauna Yana kallon yanda manyan doctors manya da kananu suke Kai kawo kafin time ya cika suka rufe kofar. Yana Nan zaune har kusan one hour sannan Kiran Habib ya shigo Masa. Cikin dari dari Habib ya Fara fadin. "Yallabai ya maganar zuwa Asibitin ne munji shiru baka fito ba tun bayan da muka dawo daga sallar Asuba". Tsaki mahmud yayi dama duk ransa ba dadi ga wani sabon salon da Habib ta tarka Wai yallabai. "Wallahi ka Kara kirana da wani yallabai sai munyi uwar watsi a kasar nan da Kai,ba dai ba barci kuzoyi ba sai kuyi tayi, yanzu Baba malam ya samu good one hour a dakin tiyata, zaka wani ce min maganar Asibiti,kaima wallahi inaga saina kaika Inda zaka Kwana a tsaye kana aiki ko Abinci sai dai kaci a tsaitsaye sannan zaka fashinci namiji Allah yayi ka, ka fadawa dayan ya kawo ku yanzu Ni tun shida Ina nan". Ya yanke Kiran ya dafe goshinsa da yake Sara Masa. * * Karfe bakwai da rabi dai dai Mai a dai daita ya sauke Salma a kofar katafaren gate din gidansu,kudin dake hannunta ta Mika Masa ta wuce da sauri ta shige ciki, ba kowa a harabar gidan ko Mai gadi ma ya shiga sallar insha'i. Wuf tayi ta shige part din Mama cikin sa'a babu kowa a cikin parlourn directly master bedroom dinta ta wuce, can ta hango Mama ta Zuba tagumi tana zaune duk tayi zumu ba wannan gayun da kwalisa, tunda ta rasa tudun dafawa a Kan sakon da za'a kaiwa Zahra ta shiga halin ha'ula'i tunda Saida aka gindaya mata sharadi ta amince gashi kuma kwabarta na neman yin Ruwa. Ganin shigowar Salma ko sallama babu yasa Mama ta wani zabura ta taso tana fadin. " Ke!!! Salma lafiya? Daga Ina kike da wannan tsohon daren? Ina Hameeda Kuma?". Zama tayi a gefen gado tana sadda Kai kasa tayi shiru. "Wai ba magana nake Miki ba Dan ubanki kin mayar Dani banza". Kuka ta fasa Mata Mai cin Rai, Wanda ya firgita 'yar sauran nutsuwar Mama. [16/02, 8:31 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI* 08055362975 09061432330 MAMAN FATEEMAH. Page 70. .........….. Luggage din da Zahra ta aje matar ta dauka tana fadin "taso mu shiga,wallahi nayi loosing control dina ne wallahj abun ne da mamaki ban taba tunanin Zan ganshi a irin wannan lokacin dana hakura na sallama". Jiki ba kwari Zahrar tabi bayanta suka shige ciki, a zaune suka same shi, yaron yana lik'e a jikinsa ya lafe sai Karamar da yake yiwa wasa tana balbala dariya Kamar ba yanzu ta Gama tsandara kuka ba. Suna shiga matar ta karasa inda ya zauna tana fadin. "Yanzu ina alkwarin mu? Haka mukayi alkawari da Kai, ka bace bat a cikin duniya ka manta da kowa? Ba waya ba sakon Email? Wallahi ka dauki Alhakin Ammi ba kadan ba, kasan yanda Hajiya Inna ta rude kuwa? Abbie ma ba karamin tashin hankalin ya shiga ba, da farko ya dauka fushin 'yan kwanaki ne Saida yaga tafiyar ta mik"a yasan da gaske ne, har nan ko ya taso takanas ta kano, Wai yasan ko baka fadawa kowa in da kake ba yasan ni dole nasan inda kake". Hannu ya daga Mata. "Pls Aisha Dan Allah ki rage surutu, kin bar yarinya a tsaye ki kaita daki ta huta kinsan long journey din da tayo? Ki tayata shiga da kayanta zata nuna Miki abinku na Mata da bakwa iya tafiya Saida tsaraba". Wata harara ta wurga masa. "Ai duk Kai ka jawo na manta da ita, sorry sister kinsan abin ne da al'jabi wallahi twins dina ne yayi batan dabo a duniyar nan, nayi kukan rashinsa har naba uku Lada, zo muje". Wata ni'ima Zahra taji tana shiga jikinta, sai lokacin ta Kare Mata kallo kamarsu Daya Dan dai shi namiji ita mace. "I am coming". Ta fada tana haura stairs da sauri. Tana bacewa ganinsu ya juyo Yana kallon Zahra. "Precious". Bata amsa ba Amma ta dago tana kallonsa kafin tayi magana Aishat ta sauko da sauri da keys a hannunta. "Muje ko bakuwa ni ko introducing dinki Bros Bai yi min ba". "Kije ki rakata Mana tunda na kawo Miki ita ai magana ta Kare, diyar uban gidana ce Bata da lafiya ne zataga likita, sannan malamina ma Yana Nan anyi Masa aikin spinal cord ne da sauran fractures Daya samu. Ya fada Yana fuskewa. Daki ne comfortable yaji komai, na bayan more rayuwa. Aisha Bata fita ba Saida ta Taya Zahra saka komai a muhallinsa sannan ta fito. Zama Zahra tayi a gefen gadon tana nazarin maganganunsa, me yake nufi da diyar uban gidansa, Amma zata raka shi taga iya gudun ruwansa Shima namiji ya iya danne abunda ke ransa bare ita mace. Aishar ce ta Kara shigowa da tray an dora snacks da Ruwa da drinks. Da murmushinta ta karaso tana fadin. "Ashe Fateemah ce, sannu da hanya zahra, ya jikin naki nagi Bros yace Baki da lafiya, Ni Sunana Aishat Muhammad Dange, twins din Al-husasain". "Masha Allah, Aunty nagode kwarai sannu da kokari". "Lah ba komai, ki Sha ruwan kiyi sallah saiki fito lokacin an shiya muku abinci" Sallar zahra tayi ta Jima tana addu'ar neman mafita daga wata sabuwar rigimar da take hangowa. Nan Kan sallayar ta Dan kwanta barci yayi awon gaba da ita. **** Zaune suke Yana cin abinci ita Kuma tana duba sakonni whatApps har zata wuce salon Faisal saita dawo saboda Basu fi minti goma da Gama ways dashi ba Yana Mata magiyar ta turo da kudi suyi sarin Kaya, ta nuna masa ya jirata zasu shigo ganin jikin Abban nasu sai ayi abinda ya kamata, sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta akan ta duba ita me majiyyaci ai share sako ba nata bane. Ta maimaita karanta sakon ya Kai sau biyar tana ganin kamar ba gaskiya bane. Dialing din number Faisal Aunty Surayya tayi, Yana dauka Bata jira komai ba ta jefa Masa tambaya. "Shin text din daka turo min gaskiya ne". "Eh wallahi Aunty ko jiya ma yazo gurin Abba mantawa nayi na fada Miki bakiga yanda yake kula da Abba ba kinsan har daki ya canza Mana mantawa nayi na fada Miki ayi Mana godiya gurin Auncle Mustapha". "Ok shi kenan ina zuwa". Ta fada tana yanke Kiran. Auncle Mustapha ta juya tana kallo Wanda Shima ita ya zubawa idanu, batace Masa komai ba sakon ta bude ta Mika Masa. Yana Gama karantawa ya dago da sauri yana neman Karin bayani. "Nima shine na Kira Faisal din ya bani tabbacin haka ne, Wai ya Kai wani Babansa ne". Spoon din ya aje ya mike ya zari hularsa da key din mota ya fice, Surayya na Masa magana hannu kawai ya daga Mata yayi gaba. Duk yanda Aishat taso mahmud ya Bata hadin Kai suyi magana ya Kiya yace ta Bari sai dare zasu zauna suyi magana sosai. Abincin ta shirya a table ta nufi dakin da zahra take, samu tayi barci ya dauketa a saman sallar da tayi sallah, Bata tasheta ba dawowa tayi tana fada Masa tayi barci da alama ta gaji. Shida Abulkhairi sukaci abincin, yayin da Aishat ta dauki Afnan Wadda tayi barci ta haya da ita sama. Kamar jira ake ta shiga bedroom dinta Kiran sweet heart ya shigo. Tana dauka ya Fara fadin. "Sweetie Ina Mahmud din yake Dan Allah?" Saida taja fasali sannan tace Masa. "Yana down stairs, wallahi sweet heart kamar Almara nake ganin abin duk na rude Dan Allah kazo kada ya Kara tafiya... Yace matukar na fadawa Abbie ko Ammi Bazan Kara ganinsa ba". Ta fada tana share hawaye. "Cool down your temper my sweetie Babu inda zaya, ban tsoro ne kawai yake miki yasan idan yayi Miki haka bazaki fadawa kowa ba, ki jirani zuwa gobe da safe in Sha Allah, ki daina yi min asarar hawayenki a banza, a gurina suna da mahimmanci , ki kyaleni dashi yanzu basai an Jima ba zanyi informing din Abbie gara ayita ta Kare tunda shi Abu baya wucewa a gurinsa". "Gaskiya dai Kam ki shiga cikin Lamarin kuyi Masa taron dangi, kasan da wata yarinya yazo Wai 'yar gidan uban gidansa ce ya kawota Asibiti, nifa I doubt much akan yarinyar Nan kasan dai halinsa baya sabga da macen daba muharramarsa ba ya kake ganin ze dauko yarinya mace kamar wanna ka ganta kuwa? Allah Ina Jin ta hada iri da Larabawa Dan she is very young and beautiful". "Just ka bishi a yanda yake so idan na shigo zamu Yara da yaren garinmu rabu dashi". Basu wani Dade ba yayi Mata sallama Yana Kara kwantar Mata da hankali akan tunda ya kawo kafarsa har gida in Sha Allah komai yazo karshe. A mota uncle Mustaphan ta karaso gidan duk da babu nisa Amma sai yaga idan yace ze tako a kafa kamar baze zo ba. Directly part din Ammah ya nufa Don baya son maganar ta fita tun kafin su tabbatar da abunda aka fada, very lucky ya samu yayan nasa general a part din. Batool ya bude Masa kofa ya shigo tana gaishe shi. Ya amsa Yana fadin. "Ina Abbie Amminku take?". "Tana part din Abbie na cikin nan". Ok, Bari na kira shi" Ringing Daya ya dauka Yana fadin. "Ko Ina kake Mustapha maza kazo Ina son ganinka ina kokarin kiranka naka Kiran ya shigo". I "To ai gani a part din Ammi Nima neman ka nakeyi". Ya fada yana nufar kofar baya yabi corridorn da ze sada shi da part din General din". Yana shiga da sallama a bakinsa yayi turus ganin Ammi tana shafe hawaye, a sanyaye ya karasa cikin parlourn. "Lafiya! meya faru?". "Zauna Mustapha yanzu ne Abbas ya kirani daga Jamaica inda yaje aikin da nake fada maka, wai Aishat ta kiwo shi ga Dan uwansa yazo Yana tare da ita". Neman guri uncle Mustaphan yayi Yana tabbatar da gaskiyar maganar Faisal. "To ai Nima abinda ya tasoni kenan na taho, kasan Alhajin su Surayya Yana can Indian an sake Masa gyaran kafa shine suka hadu da mahmud din yaketa dawainiya dasu shine ya fadawa surayyar tayi min godiya kasan ba kowa ne yasan case din da ya faru ba kawai dai an wayi gari ba'a ganinsa duk da zancen duniya baya buya nasar Surayya Bata fada musu komai ba gaskiya, Ammin Yara ki daina kuka ko lokacin da ake cikin tashin hankali ba Wanda yaga hawayenki sai yanzu da asking ya I gaban gashi". Share hawayen tayi tana fadin " dole nayi kuka ni kadai nasan dacin Dana ci a lokutan baya da dararen Dana Raya akan ubangijina ya dubi Lamarin yaron nan ya juyo min da hankalinsa gida". "To godiya ya kamata ki yiwa Allah Daya amshi addu'ar ki ba kuka ba". Wani murmushi general yayi yana duban Mustapha. "Ni bansan lokacin data aje karar 'ya'yan fari ba da ko me zakayi musu Bata daga Kai ta dubeka amma yanzu dibi yanda take Kora bayani Kamar ba ita na". "Kan barta tayi Yaya ai taking jarunta ma ba uwa duka ba, yanzu Yaya kenan za'ayi? Da nida madam zamuje next week amma dole mu raba tafiyar a yau Zan shiga neman visa ko nawa Zan bayar saina samu nan da jibi in Sha Allah Zan tafi Indian Zan kadi shi mu taho gida da izinin Allah. Amma dan Allah kada a fadawa Hajiya Inna wallahi idan taji cewa zatayi kafarta kafa ta". "Kaje kayi shiri zanyi magana akan visar taka, ka Zama cikin shiri kawai". Tashi Ammi tayi ta shiga ciki ta barsu suna tattaunawa akan Lamarin. ***** Saida zahta tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, wanka ta shiga tana fitowa lokacin magariba ta kusa kawo jiki, tayi mamakin dogon barcin da tayi. Lotion kawai ta shafa sai roll-on da tasa sure sai body midt da normal turaruka da take amfani dasu designers na kamfanin Alharamaini, rigar atamfa ta saka simple style A shape ta yafa Karamin gyale sai tayi wani sansanyan kyau, a hankali ta bude kofar ta fito tana takunta gentle ta shigo parlourn Aishat ta gani a zaune da Abulkhairi a gefenta tana koya masa homework, kafin tayi sallama har sansanyan kqmshinta ya jewa Aishat. Dago Kai tayi tana amsa sallamar da Zahra tayi. "Masha Allah!" Abinda Aishat ta fada kenan Dan babu karya yarinyar ta hadu ta ko Ina macece ga asalin kyau Dan gaske, murmushinta Mai kayatarwa zahra tayi Mata tana fadin. "Sannu da hutawa Aunty". Hannu Hanan ke dagowa Zahra tana zillo daga cinyar mamanta. Daukarta tayi tana Zama daga dayan gefe Kan wata kujerar. "Yauwa sannu, Zahra ko?" Kaita gyada Mata alamar eh. "Kinsha barcin gajiya, ga abincinki can Kan table muje kici kin kwanta da yunwa, bro yace na fada Miki yaje Asibiti sai dare ze dawo". "Ok, nagode kiyk zamanki Bari muje da 'yar gidana Aunty ki bani ita Dan Allah Ina sonta". Dan murmushi tayi idan mijin da Zaki aura ya amince ki dauka Ni tawa Mai sauki ne na Baki". Gaba tayi tana dariya kasa-kasa ta nufi dining din save da Afnan. Sun Dade suna Hira da Aunty Aishat har barci ya Fara Kama Zahra sannan tayi Mata sallama ta nufi inda akayi Mata masauki, bayan ta wuce Aishat da Dade tana auna Lamarin Zahra a zahiri Sam batayi Kama da yarinya marar tarbiyya ba ko masu budedden idanu Amma tayiwa tafiyarsu da Dan uwanta Question mark, idan ta tuna da irin warning din da yayi Mata kafin ya bar gidan. "Gata Nan amanace a gurinsa shi yasa na kawo ta Nan inda zata zauna safe, ki kula sosai nasan halin sayyid a Kan mata duk da kince yayi tafiya to Koda za'a samu akasi yazo bana nan, to ki fada masa yarinyar nan da mijinta Dan muna komawa za'ayi bikinta ya dauke idonsa daga kanta idan Kuma ba haka ba za'a iya samun matsala. "Maji ma ganj, an binne tsohuwa da Rai" Ta fada a fili. A Nan taci gaba da Zama tana jiran ta inda Dan uwanta ze bullo, wurin Sha Daya da minti goma ya bude ya shigo gidan, ya yi mamakin ganin Aisha Ido biyu. "Ashe dai Hali yana nan, yanzu Dan Allah bakiyi barci ba". "Naka wasa ne kana tunanin Zan iya barci banji komai daga gareka ba Nima ban Amayar maka da abinda ya faru bayan baka nan ba". "To ai shikenan Bari nayi wanka na fito inaga kwanan zaune zamuyi yau". Ya shige ainihin dakin da yake sauka idan yazo wani aiki kasar bata yarda ya sauka a hotel ko Daya daga cikin gidajensa, inda Allah ya taimakesu Abbas Dan kanwar Abbie ne Kuma sa'anni suke da yayunsa gashi tasu tazo Daya da mahmud sosai Dan kusan tare suke aiwatar da ayyukan kamfanonin Abbie. Bai Dade ba ya fit Yana baza natural kamshinsa ya zauna yana fadin hada min coffee sai zance yafi tafiya dai dai". Ta tashi ta nufi kitchen tana fadin. "Bari na hada coffee maker yanzu na kawo maka". Tashi yayi ya nufi dakin da Zahra take, a hankali ya tura kofar a kwance a tsakiyar bed din ya hangota da wayar ta a yashe a gefe da gani batasan lokacin da barci yayi awon gaba da ita ba. A hankali ya tako har gaban gadon Yana Kare Mata kallo a cikin dim light din dake dakin, Dan sunkuyawa yayi daidai lips din ta ya Bata light kiss ya shafa gashin kanta a hankali, wayar ya dauke ya Dora Kan bed side ya gyara Mata blanket din ya rage karfin A/Cn ya tofa Mata Addu'oi ya ja Mata kofar ya fice yana Jin wata irin kewarta. A tsaye ya samu Aisha da kallon tuhama ta bishi, yana kallonta Sarai yayi Mata fuska. "Bani idan ya Zama ready". Ya fada yana Mika Mata hannu. Kada hakuri tayi ta kalleshi idi cikin ido. "Wai wacece wannan yarinyar a gurinka? Kuma meye dangantakarka da ita Naga ka shiga inda take alhalin ba muharraminta bane Kai?". Ta fada tana tsare shi da Ido amma zuciyarta sai dokawa take Bata fatan abinda take sak'a Mata ya kasance gaskiya. "Ple Aisha zauna ki nutsu ki tambayeni duk abinda ya shige Miki duhu". Bataki tasa ba zaman tayi tana Kara jaddada Masa tambayarta akan dangantakarsa da Zahra. "Wai meye damuwar ki da ita ne na fada Miki 'yar uban gidana ce, daga haka me kike son ji Kuma?" Lokacin da suke wannan maganganun ita Kuma Zahra kishirwa ta tasheta Karamin fridge din cikin dakin ta duba Babu ruwa a ciki Wanda Kuma Auntyn ta shigo Mata dashi dazu ya huce bazeyi Mata dadin Sha ba. Kofa ta bude ta fito da niyyar zuwa kitchen ta dauko ruwan ta saka ma a fridge din dakin, maganganu ta rinka jiyowa kasa kasa da farko har tsoro ya kamata sai daga baya ta ringa jiyo maganar Mahmud ne da 'yar uwarsa. Abinda taji ya masifar daga hankalinta. "Na fada miki babu komai a tsakanina da yarinyar nan kina ganin Zan iyayin gaban kaina nayi Aure ba tare da sanin iyayena ba? ki rubuta ki aje duk abinda Ammi ta yanke a kaina na karba ita zata nemar min matar aure da kanta, idan kin tuna ta taba fada tayi min Mata a Niger,Wadda har aka kawota tayi sati biyu a lokacin Abbie ya Hana maganar to yanzu zanje natsuguna a gabanta na nemi yafiyar abinda nayi Mata Kuma ta zabar min duk wadda tayi Mata Zan karba da hannu biyu tunda ni dai babu Wadda na gani ta kwanta min da sunan Aure, Kinga gara ita ta zabar min da kanta".. Ai jikin Zahra karkarwa ya fara me yake nufi duk abinda yake Mata pretending ne ba gaskiya ba kenan? Da kyar ta Kai kanta dakin Dan tana shiga ta zube a kasa tana fadin . Naga ta kaina Ni Zahra Ashe ni kadai nake kidin girbina bani da wata kima da daraja a idanun Dan tahalikin nan?. [19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI* MAMAN FATEEMAH. 09061432330 Or 09055362975 Page 71 ..….... Sai da Zahra tayi kukanta ta bawa uku Lada sannan ta share hawayenta tana hakurkurtar da kanta, lallai irin wannan cin fuskar da ciwo ita meta rasa da yake gudun nunata a matsayin matarsa? Wai 'yar ubangidansa, To ita Kuma zata Kama Kanta in Sha Allah ba Kuma zata nuna taji hirar nan tasu ba. "Ya ubangiji ka shiga cikin lamarinta ka Bani hakuri da dangana bisa jarabawar da kake jarantata da it's Dan isar fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.". Ta fada a fili tana tashi daga inda ta zauna tana kissima abubuwa da yawa a wannan karo. Amma dole ta nemi tudun dafawa dole ta iya Kanta tunda abun yazo da cin fuska har ze ringa gudun hada kansa da ita. Ranar barci dai sai barawo, kwana tayi tana nafilfili da rokon ubangiji mafita. Bayan tayi sallar Asuba ta koma ta kwanta lamo batajin zata iya fadawa kowa wannan maganar zatayi hiding din kayanta taci gaba da addu'ar samun mafita a gurin lillahil wahidul Qahhar ya shiga duk lamuranta. Da safe kin fitowa tayi har Aunty Aishat ta biyota daki, Tana ganinta Zahra ta tashi zaune tana fadin. "Ina kwana Aunty, Ina Afnan da Abul?" "Lafiya kalau, ya bakunta Kuma? Afnan Kuma Bata tashi ba sai takai twelve tana barci in dai ta farka da Asuba, shi kuma Babana ya tafi school" "Ok. Allah sarki". Zahra ta fada tana Dan Jan blanket din zuwa jikinta saboda yanda rigar barcin take sai a hankali. Dan zama Aunty Aishat din tayi gefen gadon. "Ki tashi ki shirya kiyi break yau zamu shiga Asibiti a duba ki,tun jiya nayi Mana booking na ganin doctor din, kinsan Hussein sai a hankali idan yaso Abu to babu sauki bare Naga ya dauki lamarinki ba Nan kusa ba". "Nifa Aunty ki fada masa na warke tun a Nigeria fa,na biyoshi ne kawai saboda na duba jikin Baba Malam,Kuma wallahi azumi nakeyi yau". Tsare Zahra tayi da Ido sai taga yanayin yarinyar ya canza ba kamar jiya ba, Amma dai batace komai ba ta tashi tana fadin. "Bari na fada masa". Ta fice duk zuciyarta babu Dadi da gaske yarinyar tayi wani irin collapse Wanda Bata San dalilnsa ba. Tunda Aishat ta wuce yace duba tsadedden agogo Rolex dake hannunsa, shifa jiya da kyar ta iya barci ba tare da ita ba a jikinsa sau uku Yana zuwa kofar yana jinta bam da key a rufe. Sai Zuba Ido yake yaga ta bullo, Maimakon ya gansu su biyu sai yaga Aishat ita kadai ta dawo. Kasa hakurin ta karaso yayi ya tashi ya nufi inda take. "Tana Ina Kuma? Lokaci fa Yana tafiya nifa tun seven thirty na shirya". Wani kallo tayi masa ganin duk ya wani rude. "Tace ita babu inda zata ita ta warke, kuma da azumi ta tashi bazatayi break ba". "What!! Bata da hankali ne? wane irin ta warke duka last week fa tayi ta fama da bleeding duk ta daga min hankali, shine yanzu zata fadi haka, salon mu koma Kuma wata matsalar ta taso, tasan halin Dana shiga a wancan lokaci Bari naje na sameta". Ikon Allah Aishat ta tsaya tana kallo, lokaci Daya ya daga hankalinsa ya wani birkice, Wai me taji Yana fada ne? Me kalamansa suke nufi idan ba Rami me ya kawo zancen Rami. Da sauri ta rufa Masa baya duk ya wani susuce lokaci Daya ita ba taga abin daga hankali ba tace Bata so Amma lafazinsa sun sakata a kokonto ba Dan kadan ba. Da zafinsa ya Kama handle din kofar sai dai tayi locking dinta, a zafafe ya Fara dukan kofar Yana fadin. "Precious me kike nufi da baza kije Asibitin ba? kina son ki tayar min da hankali ne ko? maza bude ki fito mu tafi tun jiya aka Gama komai". Tsayawa Aishat tayi turus Jin kalaman da yake fada Wai ko ya manta a Ina yake ne?. "Previousss...." Ta fada a hankali tana girgiza Kai komawa tayi tunda Allah baisa ya ganta ba. Ita Kuma Zahra tana jinsa yanda ya ambaci precious sai taji wani irin bacin Rai ya lullibeta wata harara ta zabgawa kofar tana gunguni a ciki. "Saina shayar da Kai ruwan mamaki saika karyata kanka da kanka Wallahil Azim, Ni Zahra nafi qarfin cin fuska gurin 'yan uwanka saina saiwa kaina kimar daka Zubar min sai ka nunawa duniya ni wani bqngare ce ta rayuwarka". Toilet ta shige taba iska ajiyarsa. Kasa hakuri Aishat ta dawo, Bata karasa inda yake ba daga dan nesa dashi ta tsaya tamkar a yanzu ne ta biyo shi. " "Wai menene na tada jijiyar wuya, tace bataso ka qyaleta Mana ba lafiyar jikinta bace, ka wuce kawai Nima Ina son na shiga kasuwa saboda wasu Abubuwan amfanin sunyi kasa". Wani duban Baki da lissafi yayi mata. "Wai kinsan wahalar da Tasha kuwa, Kinga yanda ta daga min hankali kuwa? Kin..." Ai baisan lokacin Daya ci wani burki ba shaf ya manta Aishat fa Bata San komai dake tsakaninsu ba. Tahowa yayi ransa a hade ta rufo Masa baya, Zama yayi ya dafe Kansa. Daga sama ya tsinkayo maganar Aishat. "Wai meya jawo dacin rai haka daga fadin Bata zuwa Asibiti,Kuma sai sakin magana kake kamar da wani Abu a tsakaninka da wannan yarinyar ni ka fada min kamanta bama rufewa juna damuwa ko farin ciki tare fa muke sharing". Bai dago ba Bai Kuma tanka Mata ba. "Miskili kawai". Ta fada a zuciyarta. Itama Bata Kara tofa tata ba tayi wucewar ta sama. Da Ido ya rakata Yana ayyana subul da bakan da yayi. Lokacin da Zahra ta fito daga wanka Bataji motsinsa ba, ta kuduri aniyar sai dai wani tsautsayin idan ya gotta ya ganta Amma ta haramtawa kanta haduwa dashi. Yafi zaman awa Daya da rabi ko motsinta Bai Kara jiba ya koma kusan sau uku, amma babu canji dakin dai a rufe. Dole da yaga Babu sarki sai Allah ya hakura ya wuce Asibitin gurin Baba malam. Yana ficewa Aishat ta sauko kasa ta nufi dakin da Zahra take knocking tayi Tana Kiran sunanta. Lokacin tana chart da sajida tana fada Mata next week zasuyi graduation, taji kiran da Aunty Aishat din ke Mata, tsam ta taso ta bude kofar arba tayi da Afnan wadda akayi Mata gayu sosai sai kamshin Bom-bon tajeyi zallo ta Fara tana dariya, hannu Zahra ta Mika ta amsheta tana matsawa daga hanya. "Sannu Aunty,ko fita zakiyi ne?" Zahra ta fada tana Zama a gefen gado ita Kuma Auntyn ta zauna a Kan sofar dake dakin, kallon Zahra tayi Ido Cikin Ido. "Me yasa Kika rufe daki kina Jin bro Yana Miki magana kikayi kunnen uwar shegu dashi ko da wani Abu a tsakaninku dashi?". Girgiza Kai tayi. "Ba komai Aunty Ina wankane Kuma na rufe jacuzzi din shi yasa ban jiba, Kuma maganar asibiti mijina ne yace na Bari ba sai naje ba tunda an tabbatar da narkewar ciwon kada a jogalo min wani Abu daban, lokacin da muka taho Baya nan sai Abbana ya hadoni da Ya Mahmud tunda Shima zezo India din, sai a dubani sosai to jiya bayan na shigo ya kirani yace sunyi magana da doctor Hajara tace babu komai kawai dai nazo yawo ne, shine yace to kada naje wani asibiti zeyi magana da Ya mahmud din Ina ganin ya manta ne ko sai yau ze fada Masa". Ta karasa maganar kamar Dade duniya haka akayi ta. Kallonta Aishat keyi tunda ta ambaci mijinta ita fa nema suke su caza Mata Kai kowa da nasa salon, shi yana wani furuci dake nuni da ita din kamar suna da wata alaka da daf da daf Dan yanda ya ture dazu ita ya saka Mata shakku a cikn furucin nasa, itama kuma gashi tayi wata magana wadda tayi karo da zarginta kuma. Nisawa tayi tana fadin "Allah ya rufa asiri". "To Zaki zauna a gida ne keda Afnan ko kuma Zaki bini muje kasuwa? To ai Kuma kina azumi kada ki kwaso kishirwa". Zubut Zahra ta Mike da Afnan a hannu tana fadin. "Muje Aunty Nima Ina son nayi sayyaya Naga gari Kuma". "To kin fadawa mijinki zakiyi yawo ko?" Dan murmushi tayi tana wasa hannun Afnan. "Ai ban tare ba, Kuma yace duk inda ya Kama naje yasan bazanyi rashin gaskiya ba". "A'a Kice aikin gyaran amare ya sameni kinzo inda ake bidi'ar gyaran aure". Dariya tayi tana fadin. "kaji Aunty Ni wane gyara za'ayi min kawai ki Bari". Ta fice daga dakin bayanta Aunty Aishar ta biyo. Ita ke driving din motar Zahra na gefenta rike da Afnan. Basu Dade a kasuwar ba suka dawo Zahra laffaya ta dauko tsaraddu masu kyau da tsada a gurin biya Aunty Aishar ta hanata ta biya ta biya Mata. Ba zato suka tarar da mahmud a parlour Yana ibadar kallon ball ana Asian cup, Zahra you tayi kamar Bata San Allah yayi ruwan tsirarsa a gurin ba ta wuce da Afnan a kafadarta Wanda tayi barci, har ta kule ganinsa Yana kallonta a zuciyarsa ya Fara tunanin Wai to meya shiga Kan yarinyar Nan ne haka totally ta canza Masa yanda ta nuna tamkar Bata taba saninsa ba ko gaisuwar Daya Raina ta Hausawan baici arzikinta ba. Remote ya dauka ya kashe kallon Yana fuskantar Aishat. "Shatu Wai me yake damun yarinyar Nan ne ko magana fa batayi min ba ta wuce, kota fada Miki wani Abu da nayi Mata, wato Naga alamar raini ya Fara shiga tsaninmu. Zama tayi daura dashi tana fad'in. "Toni Ina Zan sani ne dazu dai ta fada min mijinta ne ya hanata zuwa Asibitin Wai yace kada a jankwalo Mata wani Abu tunda a Nigeria sun Basu tabbacin babu sauran ciwon". A zabure ya gyara Zama Yana wani kankance idanu. "Kikace menene ? Mijinta kome?" Gyada Kai tayi tana bashi assurance na abinda ta fada. "Mijinta fa kikace? Haka ta fada Miki?". "Eh haka ta fada min dazu kafin mu fita kasuwa, harma tace min Bata tare ba sai ta komai gida, gaskiya mijin yarinyar Nan yayi Dace da mace ta gari Naga alama tana jida mijin nata...." Bai jira yaji abinda zata fada ba ya nufi dakin data ke. Yanzu ma ta b'ame dakin Yana zuwa yaji shi a rufe, baiyi knocking ba dawowa yayi ya zauna Yana huci, Nan da Nan Yana yinsa ya canza har abun yaso yaba Aishat tsoro. Ita ta rasa wane irin lamari ne haka idan ma da wani Abu a tsakaninsu to a Cikin gidan Nan ya faru Dan jiya harta kwanta lafiya kalau suka rabu da ita, Amma wayewar garin yau aka tashi da wannan sabon canjin daga gareta. Har tausayi ya Bata da gani Yana Cikin damuwa.. "Dan Allah Dan sonka da Manzon Allah ka fada min meke tsakaninku da wannan yarinyar dazu naji kana fadar maganganun da suke nuna kamar Kaine ke Jan ragamar rayuwarta wacece ita? Wace irin alaka ce a tsakaninku? Yarinyar Kace? Ko matarka ce? Ka fada min Kona samu nutsuwar zuciyarta,wallahi duk duniya babu Mai Jin wannan maganar". Bai dago ba harta Gama fadar abinda ke bakinta, yasan Dole ya fuskanci tuhuma daga Aisha dan ya kasa controlling Kansa tun lokacin Daya fuskanci tana fushin da baisan Kona menene ba da Kuma ma'assasar yinsa ba. Motsin bude kofa yasa mahmud dagowa yaga waye, yasan dole ya kasance ahalin gidan ne. Abbas ne ya shigo rataye da jakar laptop dinsa, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su Mahmud yasan ko rantsuwa yayi babu kaffara Aishat ce ta gargado shi tunda jiya tace masa aikin wata biyu zeyi a Jamaica kafin ya dawo duka jiya kuma satinsa uku a can, inda yake ya tsaya Yana warewa Aishat hannu idan da sabo mahmud ya Saba ganin wannan sabgar tasu. Hannunta ya riko suka shigo ciki Yana kallon mahmud Wanda ya yi fuska. "A'a sweetie wa nake gani kamar 'yan gudun hijira?" "To gashi Nan dau". "Ammah bansan lokacin da kika Zama Mai fuska biyu ba, shine kika zagaye Mika gayyato min mijinki ko?" Hannun Aishat Abbas ya saki Yana nifar gurin mahmud, dariyar farin ciki Yana Dan doka kafadarsa. "My man kace mun ciri tuta tunda mune masaukin bakin, dan duniya wallahi Mahmud baka da dama,kayi masifar bamu kafa Wai ashe kana Bauchi state, Bari na watsa Ruwa na fito nayi welcoming dinka sosai". Harara mahmud ya Kara zubawa Aishat ita Kuma ta wani dauke Kai ai dai ta samu mataimaki tunda ita ya rainata Yana it's shata Mata layin da bazata iya tsallakewa ba gara maza su shiga. Suf ta wuce tana fad'in Bari Fara maka preparing na kayan wanka". Saida ta wuce Mahmud yace. "Ya Abbas yaushe matarka ta koyi 'yar kasa ta iya fuska biyu, nace Mata fa kada naji kada nagi shine ita Mai mijin ta tattago ka babu shiri kuzo koyi mini taron dangi, dama kayi zamanka daga Nan Sokoto nayi ayita ta Kare". Ya fada Yana huci, Abbas na ganin haka yasan da abunda ya tunzura shi. "Koma dai menene Abbie yace mu kaika sokoto dead or alive". Ya wuce shi yayi strais da sauri. Har Abbas suka sauko Yana inda suka barshi,.bayan Abbas yaci abinci ya dawo kusa da mahmud ya zauna. "Wai me yake damunka ne ko baka da lafiya mu wuce asibiti? Ko Kuma malantar ce tasa ka zama haka? Kasan ku alarammomin nan da izza kuke". Ya fada Yana dariya, shima mahmud din dariyar yayi. "Kai Amma Aishat kin kware gurin kinibibi yanzu har kin fada masa wannan maganar gaskiya min Dena sirri dake tinda yanzu babu Aminci a tsakaninmu kina da naki ma'amincin". Itama dariyar tayi tana nufar corridor din dakin Zahra, tana tunanin wayon yarinyar da gani akwai abinda suke boyewa su duka Dan da alama horo ne take Masa a Cikin ruwan sanyi Dan ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba da wata a kasa. Cikin ikon Allah tana kokarin knocking taga Zahra ta bude kofar tana sabe da Yar gidanta Wanda ta tashi daga barci. "Sannu Aunty, gata ta tashi tun dazu batayi dai kuka ba na Bata fresh milk dai sai Naga gara Tasha natural nata dai". Ta fada tana Mika Mata Afnan din, abun mamaki sai yarinyar taki zuwa gurin uwar. "Huta roro Nima na huta da tsotsa, amma kuzo muje ki gaisa da sweet heart ya dawo shine ma yake tambayar Afnan din tunda yau Abulkhairi baya Nan yaje week end gidan Dr Suraj abokin Daddynsa". "Allah sarki shi yasa banganshi ba Ashe baya gidan". Bata bukatar komai Dan ta yafa wani veil Amma karamine ta saka abaya Dubai maroon Mai adon stones kanana saita haskata sosai yarintarta ta Kara fitowa da wani sirrin kyau Dan asali ga kanshin turarenta da Kuma irin Wanda Hajiya Amina ta hada Mata masu janyo Hankalin oga duk irin kamewarsa kuwa. Tare suka Jero suna magana wadda tasa Zahra yin wani tsadedden murmushi sai akayi dace duk su biyun suna facing din hanyar. "Tabarakallahu ahasanil kaliqin". Abbas ya fada. Shi Kuma Dan gogan ya kasa dauke idanunsa daga kanta sai yaga murmushin kamar da gayya take yinsa. Cikin takunsu na matan da suka San takan gayu suka karaso parlourn, sallama Zahra tayi. Abbas ne ya samu zarafin amsawa shi kuwa mahmud tamkar an rufe Masa Baki, ai shi Abbas Bai zaci haka zahrar take ba yanda sweetie ke bashi labarin ta Sai yaga ai Sam Bata iya fasalta mutum ba. Afnan na ganin Daddy ta shiga irin rawar murnar kaga abinda kake so din nan da Yara sukeyi tana zillo gurinsa zahrar ta nufa da nufin ta kaita. Ita da duk saura ba Wanda yaga lokacin da mahmud ya diro gabanta Dan ja da baya tayi da sauri tana fad'in. "Subhanallahi! Lafiya meye faru?". Baiyi wata wata ba ya rungumosu ita da Afnan din dake hannunta. Kici kicin kwacewa take Dan Bata taba tunanin zeyi irin wannan danyan aikin ba. "Na shiga uku! Aunty ku taimaka min Dan Allah ku janye shi inaga bashi da lafiya kada yayi Mana illah Ni da yarinyar nan". Ta fada tana kuka. "Wallahi bazaki sakamin ciwon zuciya ba kin hanani sakat tun safe kin Hana ko fuskarki na gani,kinki yarda muje asibiti, me nayi Miki Mai zafi haka har kike ikirarin Wai mijinki ya Hana kije Asibiti, waye mijin naki bayan ni? Fada mini!!!..????" Ya fada Yana hargagi abinda Bata taba gani ba kenan a iya zamanta dashi,kuka Afnan ta kwallah saboda yanda ya matsesu ga Kuma hayaniya da yake musu. Da sauri Abbas ya taso yaga mahmud din kamar baya cikin nutsuwarsa. Hannunsa Daya ya kamo sai yaji jikin nasa na tsuma. Daidai kunnensa Abbas yayi magana. "Pls sakarta kaga ka saka yarinya kuka, ka nutsu ta fada maka me yasa tayi hakan kowa ai yasan taka ce Ina ga da abinda kayi Mata Mai ciwo". Da kyar ya yarda ya saketa ita da yarinyar. Zaunar dashi Abbas yayi ai Zahra na Dora yarinyar a cinyar uwarta lokacin Abbas na can Yana bashi Baki ta fice. Tana shiga tayi locking din door tana sauke numfashi tare da goge 'yan hawayenta na karya data kakarosu. "Wallahi saina rama zakayi bayani da bakinka guy ni zaka yiwa cin fuskar da ze Zubar min da daraja da kimata sai zuciyarta da Bakinka sun Fadi gaskiyar da kake boyewa, Kuma Wallahil Azim addu'ar tsamiya yanzu na Fara har FAHAZAMUHUM BI'IZIMILLAHI YA WADUDU YA JAMI'U MALIKIN NASI MALIKI YAUMIDDIN zanta zabga maka sai ka Raina kanka kasan Dan an baka kyautar zahra ba Yana nufi Zan Zama matar shige ba, sai duniya ta shaida zahrar Zahra ce, tayi kwafa ko yanzu na rage tension ko ya yake tunda kaima kaji a jikina ka Kuma karyata maganar daka fadawa 'yar uwarka jiya, Wai bakaga wadda tayi maka ba, sai kasan bayanin da zakayi musu Kuma tunda magana zarar bunu ce bata komawa. Lokacin da Abbas ya juyo da zummar yiwa Zahra magana yaga sai filin gurin kallon Ina take ya yiwa Aishat.. "Ta gudu Ina zata tsaya ya nakasa ta yayiwa mijinta asara,kuma saboda Allah sai ka kakume Matar mutane da yammacin gari yaushe ka Zama haka yarinya da aurenta da komai wannan kasan haramun ne basai an fada maka ba, Ina cewa gida Daya kuka zauna ba diyar malaminka bace me yasa kasan kana sonta kayi shiru har wani ya aura ni Naga kokarinsa Daya amince ka taho Masa da irin wannan diamond baby din wata uwa duniya baya tsoron sharri shaidan ya gitta tunda gashi a gaban mutane ka iya rungumeta yaya idan daga Kai sai ita ne ai labarin ba irin wannan bane ki.." "Stop!!!..... Aisha, ni kike fadawa abunda yazo bakinki? to Zahra halaliyata ce matata ce ta sunna". Ya fada a zafafe tashi yayi ze fice da sauri Abbas ya riko shi. " Dawo magana zamuyi ta fashimta". Baiyi gardama ba ya dawo ya zauna, ita dai Aisha rasa ta cewa tayi wai barawo a hannun Mata. Very close dashi Abbas ya zauna ya riko hannun mahmud Yana fadin. "Munji matarka ce amma yanda sweetie ta fada min kace matar ubangidanka ce me yasa ka boye mata Bata cancanci haka ba, kasan irin wahalar Dana Sha da ita lokacin da case din Nan ya taso? yanda kasan zata zautu wallahi Amma sai ka dawo Mata da wata fuskar daba taka ba duk rintsi bakwa rufewa junanku komai, kasan ta fada min cewar wallahi matarka ce Dan ta shaida bazaka taba yarda kayi tafiya da mace irin wannan da mace kamar wannan babu alaka Mai karfi a tsakaninku". Mahmud ji yayi duk ruwa ya cinye shi yarinya karama ta dagula masa lissafin da tasa ya saki layi duk yanda yake shirya nasa planning din ta rusa a lokaci daya yayi amansa ya lashe. "To tayi hakuri ni kaina bansan me yasa na kasa fada Mata ba Ina Jin nauyin yanda Zan tunkari Ammi da Abbie da wannan maganar ba wallahi, sai Naga nayi wani Abu Daya sabawa al'adar mu ta Malam bahaushe, Kuma ita na rasa abinda nayi mata lafiya kalau mukazo gidan Nan Amma ta sauya min na rasa abinda yake min dadi wallahi Ya Abbas yarinyar nan itace weakness dina a rayuwa ni kaina nasan hakan, itace fa wadda nake fada maka na gani da dadewa a jirgi ita da Abbanta ka tuna?". "Off cause anyi haka,Amma how comes hakan ta faru?". Furzar da iska yayi daga bakinsa. "It's long story, idan ka huta zamu tattauna akai, yanzu dai ki tashi like kiyi min Biko tunda Naga alamar kina da masaniyar laifina". Baki Aishat ta dafe da hannu Wallahil Azim ban sani ba, nifa duk abin Nan hasashe nake yi ban tabbatar ba sai yanzu, ni wannan aikin ba nawa bane Kai zaka gyaro kayanka da abinda kayi Mata tunda Naga Bata da kwaramniya Sam, Kuma ya zakayi da ita kenan? Zakaje kace ga matata nan tsaraba fushin da nayi ko Yaya za'a kayi?". "Ki Bari kawai alkawarin da nakeso kuyi min mu rufe maganar nan a nan duk da Faruq ma ya sani amma nasan tunda na kada Masa warning bazeyi karambanin fadawa kowa ba, nina taro match dina Ni zanyi playing din kayana kawai kuyi min addu'ar samun nasara kada Ammah tayi min nak'i". Ya fada Cikin raunin murya. [19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: *AUREN HUCE HAUSHI* MAMAN FATEEMAH 09062432330 Or O8055362975. Page 72 ........... Cikin kankanin lokaci mahmud yaji ya Dan samu nutsuwar Daya rasa, yarinya karama ta saka shi sakin layi a gaban mutane, ita dai Aishat sai jijjiga Afnan takeyi wadda har lokacin take 'yar mita, tashi Mahmud yayi da nufin barin gurin, Ya Abbas ne ya riko Masa hannu Yana girgiza masa Kai. "Dawo magana zamuyi ta fashimta, baiyi gaddama ba. "Kana ji yanzu ka Bata sarari ta huta ta Kuma Huce daga fushin da tayi da kai, idan so Samu ne ka koma gidanka ka kame kanka, kada ka Bari ta Kara ganinka Nan kusa har sai an Kai wani limit da zata nemeka ruwa a jallo ta rasa yanda ko kun hadu babu saura fishi sai dokin ganinka dole ba Zama very strong a fannin soyayya Kaine namiji kada ka yarda ta gane itace rauninka, sannan dole ka koyi takatsantsan kasan inda na dosa idan ba haka ba za"ayi amfani da wannan damar a cutar maka da ita Koda ta furucin Baki ne". Shiru mahmud yayi Yana saurarensa wato shi kansa zaman takewar auren sai an shirya mata, Dan rausayar da Kai yayai yana fad'in. "Anyway shike nan,Amma da so nake ta yarda muje asibiti su dubata tukunna sai na wuce din". Wani kallon me yake damunka Ya Abbas yayi Masa. "For God sake! Ashe bazaka Zama Mai karfin ba kenan? Tunda nace ka kame kanka ai sai kayi yanda nace ko, tashi mu fita ja rakani na dubo patient din namu ma ida discussion din a hanya tunda Naga alama ka rifta da yawa". Ya fada Yana Masa dariya, sumar kansa ya shafa shima Yana murmushi. Bayan fitarsu Aishar Goya Afnan tayi so take tayi barci, Bata Kara bi takan Zahra ba ta shige kitchen ta Dora ruwa ta dauko kaza ta Fara gyarawa ta Dora a wuta ta debo fresh fruits ta wanke ta Fara hada fruits salad ta saka a fridge tayi lemon kankana da Madara pepper chicken tayi da chicken rice sai coslow data hada ta dafa ruwan tea Mai hadin spices masu Dadi na dafa tea kafin magariba ta Gama komai, Babban tray ta hadawa zahra kayan bude Baki ta aje a gefe sannan ta ringa fita da nasu zuwa dinning tana jerawa Saida ta Gama komai ta dauki na zahra lokacin har duhun magariba yayi, knocking Daya tayi Zahra ta bude Mata ta matsa gefe tana fad'in. "Sannu Aunty da aiki Aunty". Ta fada tana karbar kayan Amma taki yarda su hada Ido. "Zanje nayi sallah idan na Gama zamu zauna dake Ina so mu tattauna wasu abubuwa". Aishat ta fada tana juyawa. "To Aunty zanzo basai kin dawo ba". Dan dakatawa tayi da tafiya ta waiwayo. "Kiyi zamanki ai Amare 'yan lalashi ne, ni zanzo on behalf of my beloved brother". Ta fada tana dariya, itama zahra murmusawa tayi. ******Daga gida direct Asibiti su Mahmud suka nufa, sun samu Habib da Abubakar, Ya Abbas yayi mamakin ganin Abubakar a gurin sosai Amma baice komai ba kenan da wadanda mahmud yayi hijirar dasu. Lokacin Baba malam Yana zaune suna Hira, har gabansa su mahmud suka karasa suka gaishe shi da Kara suba shi, sannan su Habib suka gaishe dasu mahmud, Ya Abbas ne ya kalli Abubakar Yana fadar. "Wato har Kai gurin kufe Mana gaskiya ko? Kana ji ana ta Fadi tashin nemansa kayi fumfurus kana kallon kowa daga karshe ma akace ka canza gurin aikine". Sadda Kai yayi yana Dan sosa gefen wuyansa, gyaran murya Baba malam yayi Dan duk da bayanin matsayin Ya Abbas da mahmud yake basa baisa ya dauke hankalinsa daga maganar da Abbas din fada ba. Jin gyaran muryar Malam yasa suka juyo gaba Daya suna kallonsa. "Ayi Masa Afuwa shima Mai bin umarni ne,sai yanda akayi dashi kada aga laifinsa amanar kenan da baya da Amana baze yarda dashi irin haka ba. Allah yayi albarka ya kiyaye gaba, ai karfin addu'a ne yasa komai ya Zama tarihi naji dadin ganinka sosai Malam Abbas Dan Allah kayi min aikin Dana kasa ka maida min Dana gida tare da iyalinsa ka bawa mahaifinku hakurin karambanin da mukayi musu wallahi nagarta muka duba ba komai ba tunda Bamu San gaibu ba, in Sha Allah idan lafiya ta Samu Ina Nan zuwa sokoton da kaina". Waje su Habib suka fice, ya Zama daga Malam din sai su Ya Abbas. "Babu komai Malam Allah ya baka lafiya, muke da godiya ya fada min duk dawainiya da kayi dashi tunda kuka tsince shi har kawo yanzu ai kaima ubane ka Isa kayi yanda kaga dama dashi, Allah ya Kara lafiya da sutura yasa kaffara akeyi in Sha Allah amanarka Zan idata, ai mu bamu da Bakin godiya sai dai ubangiji ne ze biyaka". Sun Jima suna tattaunawa anan Malam yake farawa Abbas yanda kayiwa mahmud makaru abinda Bai taba fada Masa ba sai yanzu yakeji, har wasu hawayen gefen Ido Mahmud yaji sun taro Ashe haka akaso a kassara Masa rayuwa Allah yayi Masa gada da Rahama ya kawo Habib ya gashi a gurin da yake a yashe a kasa. Anan sukayi magariba sukayi insha'i sannan sukayiwa Baba malam sallama, mahmud ne yace suje su duba jikin Alhajin su Aunty surayyar uncle Mustaphan Shima Yana nan. Shima sun samu 'ya'yansa maza biyu sunzo duba jikin nasa, sun gaisa tare da jajanta musu, shima Alhajin jikin da sauki sosai Dan har Yana takawa shima da karfe. Gida suka koma mahmud yayi dinner tare dasu, haka Nan yayi ta maza bai nemi zahra ba Suma babu Wanda yayi maganar ta har suka gama, Mahmud Bai wani zauna ya shiga dakin da ya mayar nasa tun ba yanzu ba ya dauko laptop din da wayoyinsa ya fito. "Ka Bari na saukeka Nima Ina son fita ne". Ya Abbas ya fada. "No, ka barshi kawai nayi waya da Mr salahuddeen Yana kusa da isowa, kawai dai Alfarma za'ayi min twins zasu shiga Nigeria a tsakanin kwanakin nan harna Fara musu processing na visa harda yaran duka". "Ba damuwa Nima Ina son suje Nigeria din to saboda makarantar Abulkhairi ne, Amma yanzu dole suje tunda ta Kama amma naji kana fadar kana nemar musu visa Kai kana Nan kenan?". Kai ya girgiza Yana fadar "A'a akwai dalilin raba tafiyar ne jikina Yana bani wani Abu da bansan ko menene ba". "To Allah ya rufa asiri, Zan fadawa sweetie ka wuce tana can gurin 'yar daru ita da dare take tata rigimar amma da Rana lafiya kalau za'a wuni da ita". Dan murmushi Mahmud yayi Yana ayyana Wai babyn su ce da zahra suna tarairayarta. Yana fitowa harabar gidan motar sayyid tana shigowa, dai dai gurin Mahmud ya tsaya ya kashe motar ya fito da sauri ya rungime Mahmud Yana fad'in . "Ina ka shiga a duniyar nan ka barmu da tashin hankali? Munyi nema har mun godewa Allah kasan Umma cewa tayi a saka nemanka a jaridu da mujallu da kafafen sada zumunta na zamani,Su uncle Mustaphan ne suka Hana sukace abun ze zama tonon sillil Wanda Bai sani bama ze sani". Dan zare shi daga jikinsa mahmud din yayi Yana fad'in . "Ai gashi Nan dawo sayyid ya karatu ace ka koma PhD ko?" "Wallahi kuwa". "To Masha Allah. Allah ya taimaka, Nima Zan wuce ne matar abokina na kawowa Aishat su zauna a Nan asibiti sukazo zataga likita". Ya mika Masa hannu yayi gaba, sayyid Yana da kirki amma fa gurin lamarin Mata sai a hankali, ko baya Zina ta zahiri akwai 'yan tabe -tabe. Yana fita ya turawa Aishat text message a waya. Amma fa karfin Hali kawai yakeyi Sam zuciyarsa Bata nutsu ya tafi yabar zahra da wannan Karen farautar a gidan ba, amma dole ya kauda Kansa yayi kawaici da Kara kada Ya Abbas yaga Bai dauki maganarsa ba. Koda ya koma su Habib suna gida Suma sun baro asibitin, coffee ya bukac Mr Ajey ya kawo Masa ta wuce ciki Saida yayi wanka ya bude laptop dinsa Yana aiki Yana sipping din coffeen, ya Kai kusan biyun dare Yana Abu Daya Saida ya tabbatar da komai ya dai daita sannan ya kwanta zuciyarsa da gangar jikinsa suna mararinta, filo ya rungime a haka barci yayi awon gaba dashi. Bayan sun sallar Asuba barci mahmud ya koma knocking din da ake a kofar bedroom dinsa ya tashe shi daga barcin da yake Mai Dadi Wanda ya saka shi nishadi. Umarnin budewa ya bada Yana daga Cikin blanket dinsa. Mr sunny ne Mai yin share share da goge goge. " Good morning Sir" Ya fada Cikin ladabi daga Bakin kofa sannan ya Dora da fadin. "Akwai Baki daga Nigeria". Wani smile yayi Yana tashi zaune yasan za'a Rina sai yanzu ya gane hikimar ya Abbas na cewa ya dawo nan shi kansa baze so zahra taga dabin da za'ayi ba". "Kaje ayi musu duk abinda ya kamata, Mr Ajey ya Basu abinci kafin na fito". Toilet ya shige yayi suk abinda zeyi sannan ya fito Yana tsane sumar kansa da Karamin towel a nutse ya Gama shirinsa ya fito a Mahmud dinsa, ya riko wayoyinsa hannu ya nufo main parlour. Da uncle Mustaphan ya Fara yin tozali kafin ya sauke idanunsa a Kan uncle saminu, nan da nan ya hade girar sama data kasa tamkar yaki ya rigshi kofar gari. A ciki ya gaishe su duk da shafi ce ta shafi uncle Mustapha sai yayi musu kudin goro, neman guri yayi ya zauna Bai Kara cewa komai ba, uncle saminu ne yazo iya wuya Dan ba haka yayi zaton zega Mahmud ba l,Dan an Bashi assurance na ya Gama lalacewa,dan a yanda a kayi Masa aikin rigar sawa ma sai tafi karfinsa, bare wani arzikinsa sai dai komai ya lalace masa, sai ya Zama abinda zeci ma saiya fi karfinsa, sai Kuma yaga sabanin haka Dan yanda yake da kyawun gani a yanzu ko kafin faruwar matsalar da suka Zama asasin fatuwarta Bai Kai haka kyaun gani ba. A zuciye ya taso yana fad'in. "Kai din banza har yaushe kayi arzikin da zamu tako har inda kake ka wulakantamu eyeh? Ka maida mu 'yan iska Wanda Basu San ciwon Kansu ba ko a Nan ma halin akuyancin kake tabawa shi yasa ka makale kana gyallin goshi?' Uncle Mustapha ne ya taso da sauri yana fadin. "Meye haka kakeyi saminu? Daman abinda ka shirya kayi kenan? Amma kaji kunya wallahi Dan zumunka? ko abinda kuka kitsa kaida munafukarka kuka lankaya Masa sharrin da gaske Yana yinsa ai ka rufa Masa asiri ba kazo kana wannan shirmen ba Wanda Allah ya daga ya daga shi sai dai mahassada suyi kuka, dai dai gwargwado meka nema ka rasa da yawa ta taka suke nema Basu samu ba wace irin sutura ce Ubangiji baiyi Mana ba Amma ka tsaya kana yiwa dan Dan uwanka hassada saboda Allah ya daukaka shi a cikin family din kace ya auri 'yarka yace baya so to nuna kin jini na me Kuma wani ya taba auren matar daba tasa ba ka ragewa kanka wannan walahar Dan babu inda zata kaika sai fagen Dana sani, Ashe 'yar burumburum kayi min ka nuna komai ya wuce muzo mu tafi dashi gida". Sadda Kai saminu yayi baiyi zatom Mustapha zeyi masa haka ba Dan Saida ya shirya ya taho da zummar duk abinda yayi babu Mai iya tanka Masa. Maganar Mahmud uncle Mustapha ya tsinkayo daga bayansa. "Ka daina Bata Bakinka uncle Wanda yayi nisa baya Jin kira,ni Mahmud ta zamar Masa kadan garen bakin tulu ya barni na Bata ruwa a karni a Kar tulu, babu abinda ya Isa yayi min tinda bashi ne ya halicceni ba Kare ya canza min kaddarata kuma har abada Bazan taba auren wannan karyar 'yar tasa ba, yaje yayi bincken wacece ita kafin ya samu bakin fadawa mutane maganar suna Zina aje asibitin tugar barau ka nemi solomon kaji sau nawa ya zubarwa da 'yar taka ciki? Ko an fada maka bamu San haka ba Dan anyi shiru an kyaleta ba' a fasa maganar a family ba idan kace karya ne yanzu na nuna maka hujjata Mai karfi, kaci gaba da abinda kake kada ka fasa Dan Allah mu Zuba sharri dai Dan aike ne kada ka rufe kofa ze dawo Komai Daren dadewa, uncle Mustapha kayi hakuri wallahil azim Bazan bika ba yanda na fito ni kadai haka Zan koma indai da wannan mutumin zamu tafi Saida na mutu ban koma ba, bani da wani Hadi dashi Wanda ze shige min gaba a dukkan lamurana. Uncle Mustapha baiyi yunkurin Hana shi ba saboda yasan irin bakin Cikin da yaron ya kunsa a wancan lokacin. Juyawa mahmud yayi ze fice daga parlourn, uncle Mustapha ya riko hannunsa. "Ina zaka tafi?". Idunu jajur ya kalli uncle din, yana girgiza masa Kai, wallahi bazan zauna dashi ba idan ka matsa min za'ayi Dana sani, yanzu babu abinda ze hanani nayi abinda banyi a wancan lokacin ba, uncle kana da daraja da qima a idanuna to ka fada masa ya fita faga sabgata idan Yana so ya tsira da Dan sauran mutumcin Daya yage Mana to ya kiyaye shiga duk abinda ya shafeni, mu hadu a Sokoto two thirty flight dina ze tashi duk abin bukata a kwai shi a nan, idan ka shiga asibiti Faisal ze rakaka gurin malamina ka duba shi anyi Masa aikin spinal cord ne".. Ya kada ya fice abinsa. "Yanzu irin wannan Ina ranar ta ka zubarwa da kanka qima da girma saboda sakawa Rai hassada a banza, shima ya juya ya fice daga gurin zuciyarsa babu Dadi Dan ko kadan baiga laifin yaron ba an Bata Masa fiye da kima. ya bar uncle saminu ya kasa ko kwakwjwaran motsi. [19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI* AISHAT ISAH MUSAH. (Maman Fateemah) Bismillahir Rahamanir Rahim. P. 73 ........... Tunda Zahra ta farka daga barci taji Sam Bata Jin Dadi jikinta ita ba Mai zazzabi ba duk jijinta ciwo yake Mata, ta Kuma kasa fita Dan Bata son su hadu da Dan gidanta kada ya Kara Bata kunya Dan taga alama tasa tayi kaura daga idanunsa sai ya iya yi Mata abinda yafi hugging ma ga Kuma uwa uba tana Jin bala'in nauyi Ya Abbas tunda ko banza yayan mijinta ne ya wani kwakumeta ko kunya babu, agogon waya ta duba karfe Tara saura kwata na agogon kasar, tattaunawrsu da Aunty Aisha ta ringa dawo Mata tiryan-tiryan. Tasha mamakin halin da aka saka mahmud Ciki yaga masifa da tashin hankali ace kowa yayi maka naqi, kuma dadin dadawa kowa ya kasa fashimtarsa, ta yarda kamar yanda Aunty Aishat din ta fada abun an Dade ana shirya shi Saida aka Sha Kan kowa sannan aka fasa maganar, kuma tayi wani irin tasiri Banda taimakon Allah da wani labarin akeyi ba wannan ba. Yunkurawa tayi ta tashi sai taji tana bukatar kasancewa kusa dashi ta lallashe shi, abin tausayi be kuma abunda ya fada gaskiya ne, sai yanzu ta gane gundarin me maganarsa take nufi duk da na gari dole yabi iyayensa, kawai shedan ne ya tunzura ta ta hau dokin zuciya Mai mmakon ta Zuba Ido taga yanda abun ze kasance sai ta kasa ta hau fushin fari, ai dole ma hakan ce zata kasance tunda Yana da magabatansa, idan sun amince da auren da akayi Masa laba'asa idan Basu amince ba shikenan. Tana zuwa wannan gab'ar taji wata irin faduwar gaba, kada fa iyayensa Suki yarda da ita a matsayin mararsa. "No!!!. In Sha Allah mutu ka raba takalmin kaza.". Ta sauko daga gadon gara ta fita ko tayi arba dashi tayi yanda tayi ta Shawo Kan kayanta. Wanka ta shiga shaf-shaf ta fito ta shirya ta saka rigar cotton lace marar nauyi tana baza kamshinta, bata daura dankwalin lace din ba karamin gyale ta Dan rufe gashinta dashi ta sako plat shoes ta fito zata shiga kitchen tayi musu abin break fast kada ta Zama cima zaune sai dai ayi a Bata. Parlourn ba kowa shiru sai karar a/c kakeji kawai sai Kuma sansanyan kamshin turarukan daki tunda gidansu akazo, kitchen ta nufa Kai tsaye saboda tana da yakinin masu gidan Basu tashi ba, da sauri tayo baya ganin mutum tsaye Cikin kitchen din daga shi sai boxer short da singlet, shima Jin motsi daga bayansa ga wani scent Mai shegen Dadi ya bakunci hancinsa yasa shi juyowa babu shiri. "Ya subhanallahi!". Ya fada lokacin daya Dora idanunsa Kan fuskar Zahra, da wani mahaukacin sauri ta juya fit ta fice daga Cikin kitchen din, shima sayyid da sauri ya aje cup din Daya dauko ze Zuba coffee din daya dafa. Ko duriyarta sayyid Bai gani ba sai dai kamshin da tabar Masa. Zahra na shiga daki ta Danna Masa key tana maida numfashi. "Waye wannan Kuma da yake da irin wannan freedom din a cikin gidan matar aure irin haka? Gaskiya wannan rayuwar da sake, dole meu amor yazo su bar shi ai da matsala sosai gidan musulmi Kuma matar gidan Matashiyar mace Mai jini a jika, shaidan ake gudu gaskiya. Wayarta ta dauka tana neman Aunty Hassana su gaisa. ______ Mahmud yana fita kofar baya ya koma ya shiga bedroom dinsa ya dauko abokiyar tafiyarsa jakar laptop ya shiga mota sai tashin motar uncle Mustapha yaji Dan ya fita har waje baiga mahmud din ba Bai Kuma kawo Yana Cikin gidan ba. Da sallama ya shiga dakina da aka kwantar da Baba Malam din Yana zaune shi kadai Yana lazimi ga kayan break fast Nan an kawo Masa Bai Kai ga cinsa ba. Sallamar Baba malam ya amsa Yana fadin. "Sannu da zuwa mahmudu, Amma yau kayi sakko, ya Naga ran naka babu Dadi lafiya dai ko?" Dan murmushi yayi duk da iyakarsa fuska. "Babu komai kawai dai bana Jin dadin jikina ne". Ya fada Yana karasawa kusa dashi ya gaishe shi ya Kara duba Jikin nasa, abinci ya dauko ya hada Masa yaci sosai sannan ya fada masa Yana son yaje Nigeria a yau in Sha Allah, addu'a yayi Masa sosai tare da Kara bashi Baki yayi hakuri ta koma ga iyayensa, sadda Kai kasa yayi kafin yace. "A karayi Mana addu'a can na nufa idan Allah ya amince Mana". "Kai! Masha Allah kazo min da abinda ya faranta min Raina mahmudu ubangiji yayi maka albarka ya Kara Kare ka daga dukkan sharri abin halitta Dan isar Manzon Allah s a w.w, kaje babu abinda ze faru da yardar ubangiji,Ina Kuma Fadimar ko ba tare zaku tafi ba?". "Eh su sai jibi zasu taho da Hasanata wadda Dan uwana da mukazo dashi ya dawo ya kawota ta duba ka". "Ikon Allah ai Bai min bayani ba yace dai ga iyalinsa tazo ta gaisheni, yanzu mahmudu daman takwayene Kai? Koda Wai ban taba sani ba, ko danma Kai ai saidai hamdala Amma me kake fada". Murmushi yayi Yana Dan shafa sumar Kansa wadda Tasha gyara. "Ayi hakuri yanayin ne yazo a haka". "Babu komai hakan shine dai dai Allah yayi yagora ya Kara arziki Mai dorewa". "Allahumma Amin". Nurses ne Wanda suke bada maganj suka shigo, suka gaisa da malam Cikin harshen turanci sannan suka gaisa da mahmud da yarensu, magunguna suka bashi ya Sha sannan suka fice,Hira sukaci gaba dayi inda Baba malam ya dinga bawa mahmud Addu'oi masu karfi na tsarin jiki sanan ya Kara bashi wata yace ya dunga karantawa duk bayan sallar farilla in Sha Allah badai sihirin Dan mutum ba. BISMILLAHI WA BILLAHI BISMILLAHI MASHA ALLAHU BISMILLAHI WALA HAULA WALAQUWWATA ILLABILLAH ÷ QALA MUSA MAJI'ITUM BIHISSIHIR INNALLAHA SAYUBDULUHU INNALLAHA LAYUSLUHU AMALAL MUBSIDIN FAWAQA'QAL HAQQU WA BADALA MA KANU YA'AMALUN FAGULIBU HUNALIKA WQNQALQBU AAGIRIN. Godiya sosai mahmud ya yiwa Malam yace masa ze tafi Amma baze wuce sati daya ba ko biyu ze dawo tunda ya fadawa doctor kada a sallamar masa patient sai tafiyarsa ta nuna kukunna. Yana fita ya Kira Mr salahuddeen yace su hadu a Airport ze dauko mota. Karfe biyu da mintuna flights din su Mahmud ya dago Nigeria text kawai ya turawa Ya Abbas, itama Aishar ya tura Mata nata da bayanin komai. Sayyid ya Jima a tsaye a parlour ko zaga ta inda Zahra zata bullo Amma yaga Shiru dole ya koma ya dauko coffee dinsa ya wuce dakinsa. Bai Jima da barin parlourn ba Aunty Aishar ta sakko Cikin gayunta kitchen ta shiga ta Fara aiki tana tunanin irin yanda Hussein ya gindaya Mata dokoki akan matarsa tana ganin soyayya Amma sai take ganin Dan uwan nata yayi zurfi da yawa. Tana Cikin aiki Sayyid ya shigo yayi Shirin fita school. "Aunty Ina kwanq?" Ya fada Yana shigowa ciki. "Lafiya kalau Sayyid har an fito yau da wuri haka? Gashi ko break ban Gama hadawa ba". "No Aunty I am ok, Nasha coffee tun dazu, Wai Ni Aunty bakuwa kikayi a gidan Nan ne ko Kuma gamo nayi da safiyar Allah wata"Ala?". Dariya tambayar ta bawa Aunty Aishar,duk yanda akayi yaga Zahra kenan, Amma sai tace masa. "Meta faru Kuma kake wata magana irin haka?" "Wallahi Aunty ba maganar jocking Naga yarinyar India ko larabawa a gidan Nan har fa Cikin kitchen din nan ta shigo muna had a Ido ta fice kamar walkiya ko dana fita ko Mai kama da ita bangani ba wallahi". "Eh bakuwa ce nayi Baku San juna bane shi yasa ita ma Bata San da zamanka a gidan bane shi yasa inaga itama tsorata tayi gaskiya". "Wow! Amma daga Ina Kika samo irin wannan Mai zafin haka? Gaskiya za'a da ita Dan Allah Ina kamu wallahi daga wannan Kuma kallo ya Kare ki Fara min campaign Dan Allah". Ya fada Yana hade hannu irin ba 'yan kabilar Hindi na nan Indian din🙏🙏. Anzo gurin tab Allah kiyaye da mijinta baya nan da a gabansa zeyi wannan kwabar da kuwa sun kwashi 'yan kallo. "Wai kana nufi sonta jakeyi kenan?" "Kwarai kuwa". Ya fada da tabbatarwa. "To ai matar Aure ce". Dafe Kai yayi Yana fadin. "Oh my God! Waye wannan Mai sa'ar da yayi min shigar sauri Dan Allah?". "Wanda ya fika sonta ne ya dauke abarsa". Langabar da Kai yayi Yana fadin. "Shikenan na wuce school, Amma fa I really loved her". "Matar Auren?" Baice komai ba ya saka Kai ya fice daga kitchen din ransa babu Dadi. "Allah ya kyauta, wato mahmud ya yiwa Sayyid wani irin farin sani kenan, yasan matukar zeyi arba da ita sai an samu matsala gashi kuwa ya kasa ba marad'a kunya". Sai da ta Gama komai ta dauko abincin data Zuba musu ita da zahrar a wani guri ta aje basket din ta koma ta dauko wani Abu kaman story mat da table mat ya shinfida sannan ta koma sama lokacin sweet heart din ya fito daga wanka, taimaka Masa tayi ya shirya tunda shi azumin litinin da alhamis yakeyi itama Aishar lalurar mu ta Mata ta hanata dauka, fita zeyi Yana da wasu ayyuka da Mahmud ya turo Masa Wanda zeyi masa su, tare suka gangaro Aishar ke fadar . "Bari na kirawo Zahra ki gaisa tunda ba lallai yau ku hadu ba naji kace sai dare sosai zaka dawo aikin da yawa". Dan janyota yayi jikinsa. "Kyaleta ai Dan uwanki ya dasa Mana 'yar kunya a tsakaninmu tunda yayi mata irin wannan wawar rungumar a gabana kamar ze bude aiki kinji yanda jikinsa yake tsuma kuwa a lokacin?" "Kai sweet heart Banda fa... Dan kaga baya kusa, shida abarsa har zakace Wai jikinsa Yana tsuma Kamar wani sabon shiga". "Ni dai abinda naji nake fada Miki bawai Qage nayi masa ba, Kika sani ko farin shigar ne koma Bai shigan ba". Ya fada yana dage Mata girar idonsa Daya. "Wallahi Kai dai Yaya Babba ne, Banda irin haka da gani kasan ai Yana shanawa dubi fa yanda ya damu daga Dan turza shi da tayi yanzu ma kaji yanda yake jaddada min na kular masa da ita kamar wata jaririya". "Ke dai mubar maganar lokaci ne ze nuna". Har gurin mota tayi masa Rakiya tana fada Masa zasu fita fa. Sama ta koma ta dauko Afnan wadda ta koma barci tun da akayi Mata wanka Dan kada ta tashi suna can bazajiyo kukanta ba. Dakin Zahra ta Dan buga kadan tana fadin. "Pls open the door" . Jim muryar Aunty Aishar yasa Zahra tasowa da sauri ta bude kofar tana sakin murmushinta Mai kayatarwa. "Ina kwana Aunty?" Ta fada tana karbar Afnan dake barci, can tsakiyar gado Zahra ta kaita ta kwantar. " Ki fito muyi break fast tun dazu na kawo na koma na sallami sweet heart ne shi yasa". Tare suka jera zuwa gurin da tayi musu shinfida, abincin gargajiyar ba bahaushe tayi musu kunun tsamiya ne da kosai sai pepper soup din cow legs. Suna gamawa Zahra ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta wanke su ta aje komai a muhallinsa, taso ta yiwa Aunty Aishar magamar guy dai data gani sai wata Zuciyar ta kwabeta, Bata sani ba ko kaninta ne shaqiqi muharraminta. A gurin ta dawo ta Sami Aunty Aishar tana amsa waya daga ganin yanda take amsawa kasan ba wayar sawa bace Mai wayar Yana da girma da kima a idanunta. Zahra Bata zauna ba ciki ta shige tana shiga taga Afnan tana daddaga kafa tana Wasa ta tashi, daukarta tayi tana fadin. "My Afee Babyyy.." Yarinyar na ganinta ta Fara dariya shaidar ta ganeta kenan. Saida Aunty Aishar ta Gama wayar ta shigo tana fadin. "Au Kice mutuniyar ce ta tashi? Sai ki shirya fita zamuyi yanzu guri ya kure sosai kinsan Hussein shi komai nasa baya fada sai guri ya kure, sosai jibi fa zamu wuce Nigeria shine yace muje kasuwa kiyi tsaraba shi ya wuce Nigeria". Da madaukakin mamaki Zahra ta dago ta kalli Aunty. "Ya wuce Nigeria?" Sai idonta yayi kwal-kwal ta tabbata abinda ya fada gaskiya ne, shikenan ita Kuma haka tata kaddarar take. Girgiza Mata Kai Aunty Aishar tayi. "Haba Banda shagwaba Mana, keda kike fushi dashi, yasan ko yazo bazaki saurarasa ba shi yasa ya tafi tunda baisan laifin da yayi Miki ba kike dafa shi da naki salon, Dan Allah a rangwanta Masa shi bako ne a cikin soyayya Bai taba yinta ba ke Kuma Naga taki da zafi ta kamashi batayi Masa da Wasa ba". Da kyar ta iya mayar da hawayen, da suka so zubowa ta rasa dalili itama tata zuciyar Bata da wani karfi a Kan lamarinsa. "Shike nan Aunty inda sabo na Saba yayi tafiyarsa Bai fada min ba". Aunty Aishat ji tayi yarinyar ta Bata tausayi, kenan shima Yana gwada Mata halin miskilancin nasa, nata ne baya iya jurewa. "Ki rabu dashi tafiyar ce tazo masa ba zato kiyi hakuri dole zamu zauna ya daina Miki irin haka tunda ke ba sanin halin yawonsa kikayi ba, inaga duk duniya Amminsa kadai yake bude Baki ya fada Mata duk inda zaya a cikin duniyar nan kafin yayi fushi kenan". A hanya ma sosai Aunty Aishar ta dinga bawa Zahra Baki harta Dan ware, sun shiaga manayan shagununan kayan sakawa Ganin Zahra taki daukar komai yasa Aunty Aishar lodar kayan da take ganin sun dace, sunje bangaren jewelry's ma ta dauka Kamar me shoes and bags ta dauka kamar Gori ita Zahra Abu har tsoro ya Fara Bata kashe kudi ake kamar yayi daurin cargo aka yiwa kayan Aunty Aishar ta cike komai sannan suka bar gurin, sun shiga kasuwa nan ma ba kananun kudi ta kashe ba suma awon cargo din tayi musu daga karshe suka nufi gurin gyaran gashi da jiki Aunty Aishat ta saki kudi ba kadan ba anyi Mata gyara iya gyara, suna Cikin Yi Mata gyaran jiki matar Mai gurin tazo tana tambayar Aunty Aishar cikin yaren indianci, tunda su dai basa Jin turanci duk da India suma suna English. Zaru Aishat din tayi domin ta rasa yanda zata tunkari Zahra da tambayar domin wani Abu matar ta sakawa Zahra a hannu taga yaki Zama kuma a ka'idarsa na matan aure ne kuma an fada Mata matar Auren ce gyara kawai za'a Kara yi mata, magana matar tayi Mata akan taje ta tambayar Mata ita saboda tasan wane iri abubuwan zata yi Mata. Aunty Aishar ji tayi abun yayi Mata nauyi gaskiya, ai da kunya taje tana titsiye yarinya da irin wannan tambayar,cewa tayi suyi Mata na 'yan matan kawai mantawa tayi tace musu haka ashe Bata tare ba. Zahra har Saida ta gaji da Shan abubuwa, Miko Mata ake tana shanyewa Saida taji tana neman yin amansu sannan aka saurara Mata aka dosa tureren jiki, kunshi ne tace bata son irin nasu Mai yawan Nan sai akayi Mata Dan kadan Mai azabar kyau, lokacin da aka Gama Mata komai ta fito Saida Aunty Aishar ta shiga wani shock Dan yes matar bros ta wanku iya wankuwa Ina ma Yana Nan da yau dai saiya maida yawu kenan maganar sweet heart da kamshin gaskiya kenan tunda idan ba Rami meya kawo zancen Rami ance an saka Mata abun matan aure yaqi Zama kenan budurwa ce, ita kwamacalarsu nema take tafi karfin tunaninta. Sun dauki hanya sosai Afnan na jikin Zahra duk tayi laushi da gani ta gaji, sai 'yar mita take Auntyn ce da Dan kallo inda suka tana ci gaba da driving din ta, tamabaya ta jefowa Zahra Wai dazu kun hadu da Sayyid ne da safe?". Dan Jim Zahra tayi sai Kuma tace "ko wani Dana gani a kitchen daga shi sai boxer short da singlet Yana tsaye a gurin coffee maker?" "Eh shi nake nufi". "Na ganshi lokacin Dana fito da zummar na Dora abin break sai na gashi ba yanda ya kamata ba tunda baligi ne shi Kuma ba gidansa bane, Kinga ai Bai kamata Yana fitowa a haka ba,ko Dan bansan ya kuke dashi ba ko mamanku daya". Wata kwana ta shiga kafin ta danyi tsaki.. "Wallahi kanin sweet heart ne, ni kaina bana son zamansa a gidan tunda idan Yana nan bana sakewa nayi duk irin shigar da nakeso tunda Allah yasa shi Mutum ne Mai shegen son Mata dan haka yau a sama Zaki kwana bana son samun matsala Daman abunda yasa na baki daki a kasa Ina muku wani zato ne ashae hasashena gaskiya ne, yanzu kuwa da baya kasar saina shige dake ciki gudun samun matsalar da yaketa jamin kunne a kanta". Nisawa Zahra tayi tana fadin Allah ya kyauta. Koda suka shigo Basu huta ba abin bude Baki suka yiwa masa. A tsakanin kwana biyun nan Zahra ta gaji iya gajiya Kuma Basu Kara haduwa da Sayyid ba,dan duk wata kafa Aishat din ta toshe ta yayi nacin har yayi zuciya Dan ko kasa Bata saukowa. Ranar da zasu tafi Mr salahuddeen yazo ya daukesu da kayansu sai a ranar Abulkhairi ya dawo gida, har dashi za'ayi tafiyar. [23/02, 12:00 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHIN* . AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah. 09061432330 Or 08055362975. Page 75 ......... Tunda jirgin su zahra ya sauka a filin jirgin sultan saddiq Abubakar dake Sokoto gabanta ke faduwa,tasan a Nan ne komai fa ze iya tabbata ko ayi ko a fasa gata a Sokoto sai Kuma abinda Rabbi Izzati ya hukunta shi ne ze tabbata, Afnan ce a sabe a kafadarta tana takawa a hankali tamkar Bata son taka kasar Dan da gaske ta Gama yin giving up a cikin Lamarinsu da mahmud. Aunty Aishat ce tsaye a Kan kayan da sukazo dasu Saida komai ya kammala sannan ta nufo inda Zahra suke ita da Afnan yayin da Abulkhairi yake biye da ita kafa ya kafa. Kamar tare Aishat din suke da Sameer Dan tana karasowa shima Sameer Yana karasowa da waya a kunne da alama doguwar waya yakeyi, saida ya Gama sannan su zahra suka gaishe dashi har Aunty Aishat na fadin. "Nayi fushi kaje har India amma ka kasa zuwa mu gaisa". "Kiyi hakuri kinsan halin kayanki bashi da lokacina a lokacin Kuma infact ma dai bai barni na zauna ba". "Ai shikenan Daman ku Ina kuke Zama guri Daya tamkar marasa gaskiya Baku da standard gurin Zama dole ku canza yanzu kun aje iyali suna da hakki a kanku baze yuwu ki ringa Abu babu lisafi ba Daman kasan tun farko Ammi Bata son wannan dabi'ar taku ko misqalazarratin Sai dai da yake Abbie ya tsaya muku ne yasa dole ta hakura". "Wannan gaskiya ne Auntyn mu za'a gyara in Sha Allah ko Baki fada ba zakiga canji ke dai kisa Ido kawai zakice na fada Miki". "Allah yasa hakan ta kasance". "In Sha Allah". Sameer ya fada yana Dan kallon zahra ta gefen Ido tana ta yiwa Afnan Wasa. "Madam barka da sauka sokoto Allah yasa mun shigo kenan, yasa Albarka a cikin rayuwar da zakiyi a cikinta". Dan murmushi tayi, yayin da Aunty Aishat ta amsa da. "Allahumma Amin, ni jikina ya Gama bani zahra Alkhairin mu ce". Kayansu aka dunga jida ana kaiwa mota Sameer sai mita yake yiwa Aunty Aishat akan sun lodo Kaya bayan Wanda suka turo jiya sukazo yauma ga wasu. Kunnen uwar shegu tayi masa sufa sunfi son daga su sai kayan jikinsu, tunda suka dauko hanya zahra ke kallon garin, yayi matukar burgeta ba kadan ba tayi santinsa duk da hankalinta ba a kwance yake ba Amma ba karya sokoto tayi Mata 💯% sai dai Bata San meze biyo bayan zuwan nata ba, wata zuciyar ta fada Mata. "Khairan in Sha Allah" Take ta Fara addu'ar sauka a sabon garin da kaje ba garinku ba, Dan harga Allah ta manta. "RABBI ANZILNI MUNZILAN MUBARAKAN WA ANTA KHAIRUN MUNZILIN". Ta fada a zuciyarta tana rokon ubangiji ya dafa Mata a cikin lamuranta gata ta shigo garin da babu uwa ba uba ba dangin iya babu na Baba sai wannan bawan Allahn shi kadai ta sani, kallon garin taci gaba dayi daga kasan Zuciyar ta Kuma abubuwa ne rututu gasu Nan. Wani katafaren gida taga Sameer ya dosa tamkar fadar shugaban kasa, Zahra hankalinta ta tattaro ta nutsu taga Nan kuma Ina ne Sameer ya kawo su Yana tsayawa a kofar katafaren gate din Mai Kama Dana kofar gari saboda girmansa wasu masu uniform suka taso su uku suka Karaso gurinsu Sameer kafin su Karaso sameer ya sauke glasses dan bada da baya,suna sameer ne suka gaisa sannan suka gaisa da Aunty Aishat da suke zaune a baya. Katafaren gata din aka bude musu suka shige, " masha Allah". Abinda zahra ta fada kenan a zuciyarta, wasu gine-gine take ganowa kamar a cikin film, an kawa gefen titin da flowes masu kyau da fitilu compound din ba mutane sosai sai 'yan tsiraru masu banruwan flowers har kofar part din Ammi na baya sameer ya kaisu ita dai zahra ba baka sai kunne Dan ba karya gidan gida ne tamkar dauko ginin akayi aka Dora a gurin a zuciyarta take tunanin meya yi zafi da har Wanda yake rayuwa a nan ze tsallake ya bar shi yaje yana rayuwar kwanan shago, ita dai saida Aunty Aishat ta Dan tabata ta dawo hayyacinta. "Mu shiga ciki?" Fitowa tayi dauke da Afnan a kafadarta tabi bayan Aunty Aishar wadda me rike da hannun Abulkhairi, numbers Auntyn ta saka ta bude kofar Dan juyowa tayi kadan tana fadin "Bismillah". A hankali zahra tabi bayan wasu parlours suka ringa ratsawa na garari sai da suka wuce parlour biyar sannan Aunty Aishar ta cewa zahra ta Dan jirata tana zuwa ta nufi upstairs tana rike da Abulkhairin. A kan center carpet zahra ta zauna tana wasa da Afnan wadda duk tayi laushi ta gaji danma yarinya ce mai hakuri, dogon tunani zahra ta shiga bata taba tunanin maganganun Hajiyar makwarari gaskiya bane sai Yau wallahi duk a lokacin shirbtun tsufa ta dauki zancenta Ashe batama fada mata gaskiyar zancen ba. A sama direct bedroom din Ammi Aunty Aisha ta nufa knocking tayi daga ciki taji Ammin na fadin "shigo mana batool kinsan bana son yawan damu da safe" A hankali tura kofar ta shiga da sallama, ai Abulkhairi na ganin Ammi ya Zane hannusa daga na mamansa ya ruga ya rungume Ammi wadda tayi tsaye kawai tana duban Aishar Dan ba karamin mamaki ta bata ba."surprise ko Ammina?" Ta fada tana shgewa jikin Ammin tana dariya. "Kin kyauta kenan ki dauko jiki daga uwa duniya Amma bazaki fada ba ko Addu'a ayi muku sai dai ba ganku ba zato ba tsammani". " Afuwan my Ammi nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya waccan, kinsa dan gidanki baya jira". "Ina kika ganshi ko kuma daman yana tare dake kika ki fada? Ina kuma Afnan din take?". " suna master parlour da bakuwa mukazo fa". "Bakuwa kuma?". " Eh shigowa nayi na fada miki, to sannunku da hanya muje kasan a Samar muku abun break fast". Suka nufo kasan takun takalmansu das das ya saka zahra dago kanta daga wasan da take yiwa Afnan tana bulbula dariya, caraf suka hada ido da Ammi nan da nan taji gabanta ya fadi, itama Ammi wani shock ta shiga babu ko tantama wannan fuskar take gani tare da Hussein dinta a mafarki yau gata a zahiri, tayi mafarkin yarinyar nan yafi sau shurin masaki me hakan ke nufi kenan. Suna shigowa kamshin Ammin ya hade parlourn. Zahra ba tayi tunanin haka zataga Ammin ba, babu Wanda zece ita ta haifi su Aunty Aisha sai dai ace yayarsu ce, 'yar gayu ce ta ajin karshe ga jindadin daya hana shekarunta nuna Kansu,a hankali take takowa idanunta na kan zahra wadda taji wata irin kunya ta rufeta, gurin da suke zaune Ammin ta karasa tana fadin. "Sannunku da hanya, a kunya ce zahra ta bude bakinta tace. " yauwa Ammy, ina kwana".. "Lafiya kalau ya gajiyar hanya?". Ta fada tana mika hannu zata dauki Afnan, makalewa tayi a jikin zahra alamar bazata zo ba. Gaba Ammin tayi ta zauna tana fadin huta roro waken gizo yaqi 'ya'ya". Aunty Aisha ce dubi Ammi tana fadin. " Ammi ga zahra nan 'yar Amanar Hussein diyar mai gidansa ce bata da lafiya aka kaita India ganin likita shine yace na taho da ita Nigeria kafin yazo su 'yan jihar bauchi ne katagum local government sunanta Fateemah zahra". Dan gyara zama Ammin tayi tana kara kallon zahrar from head to toe, haka nan taji wani Abu yana mata kai kawo a kasan zuciyarta. "Sannu fateemah ya jikin naki?". Kanta na kasa bata yarda ta dago ba ta amsa. " Da sauki Sosai". "Masha Allah, Hasana rakata sama dakin fake opposite da bedroom din ki bude Mata tayi wanka kafin a hada muku breakfast". " To Ammi bari muje,ko kuma muje can gurina saita zauna tunda duk cikin part din nan ne". Kaita girgiza "kaita sama inda sauran 'yan uwanta yara suka can gurinki ba zataji fadi ba nan kuwa gasu Batool nan kuma ba kince bata jin dadi ba sai saida babba a kusa maza kuje lokaci yana tafiya gara taci abinci ta kwanta ta huta tunda ba irin ujilarku ta iya ba". A kunya ce zahra ta mike tana sabe da Afnan. Saida suka bacewa ganin Ammi sannan ta dauke idonta daga kallon zahra. " ya rabb kai kasan abinda ke boye da make nuna min yarinyar nan tare da Dana sauran sirrin kuma bani da masaniyarsa, ubangiji ka tsareni jin abinda ze zamar min tashin hankali". Ya fada a cikin murya mai rauni. Suna shiga dakin Aunty Aishat din tace "wow! Lallai matarmu you are special ai bansan haka Ammi ta hada wannan bedroom din ba, bari na sauka da wannan 'yar taki makale matar kawai" Ta dauko ta tana kuka ta fice da ita, tana jin Zahra na magiyar ta dawo da ita tayi mata wanka Amma ta wuce kawai. Lokacin da Aishat din ta sauko bata samu Ammi da Abulkhairi ba itama wata hanya ta nufa tana dan jijjiga Afnan. Kafin minti arba'in an hadawa su Aishat breakfast mai rai da lafiya, zahra tana fitowa daga wanka tayi tsaye a gaban mirror tana kallon kanta yanda tayi wani irin kyau na ban mamaki wato Inda ake gyaran jiki anayi dan tamkar anyi mata wankan inji,lotion din data gani ta Shafa tunda nata da take shafawa yana can cikin kayansu ba'a shigo dasu ba saida ta gama shafawa tayi turus Ashe bata da kayan sakawa kuma gashi towel din jikinta ma karami ne kusan Rabin cinyoyinta duk a waje suke, gefen gado ta koma ta zauna ita dai bazata iya mayar da kayan data cire ba, dan kwanciya tayi a jikin pillow dan tunda tayi wanka wata irin kasala ta saukar mata ba, tayi minti biyu ba barci yayi awon gaba da ita. Jin shirun zahrar yayi yawa yasa Ammi tacewa Aishat ta bita ta kirata ko nauyin saukowa takeji tunda taga yarinyar akwaita da kunya. Sau biyu tana knocking Amma shiru, kamar ba mutum a dakin a hankali ta murda handle din ta tura kofar ganinta tayi tana barci,komawa tayi a hankali dan bazata so ta gashi taga ta ganta a haka ba, haba dole bros ya rikice musu Ashe shi yasan sirrin kayansa Ashe a fuska wasa ne, tasan Allah ne yayi mass tukuicin kazafin da akayi masa ya bashi irin wannan yarinyar. Sai data fara gangarowa ta tuna Ashe bata da kayan sakawa a tare da ita. "Ya salam! Wallahi shaf ta manta tunda su basa dauko kayan sakawa suna dasu a nan. ****** Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa ta buga masa daki tana jinsa a rufe, wanka yayi ya fito cikin yadin filtex mai laushi fari tas, a parlour ya samu Hajiyar da Aminiyarta Innoni suna hira, kusa da Hajiya Innar ya zauna yana gaishe da innonin, kama haba tayi. " kai kuma yaushe ka dawo garin namu?". Tabe baki Inna tayi "kin gashi nan saida malamai suka gama karbar nasu rabon ya mula ya Mile ya dauko jiki sinkin fakiti ya dawo, yazo kuma ya zaune min yaki ko leka kofar gidan nan, kofa gidan iyayen yaki zuwa ni naga ta kaina kasan da irin wannan ranar amma ka tsallake kayi naka guri sai yanzu zaka zo kana daddofar na kaika gidan". Wata dariyar da bai shirya ba ta kubce masa. " Amma wallahi matar nan kin gama dani ni zaki cewa ina kamun kafa fake ki kaini gida,ni kadai na fito ni kadai zan koma kuma kinyi da dan halak idan na fice sai kin shekara baki sakani a idanunki ba". Ya mike ya nufi kofa, nan da nan Hajiya inna ta rude. "Idan ka bawa Annabi daraja ka dawo wallahi wasa nake maka ga abincinka can kazo kaci". Ya tsaya Amma bai juyo ba. "A aje min idan na dawo zanci lokacin magariba ya karato masallaci zani". Yana gama fada ya bude kofa ya fice. " miskili kawai idan ba haka nayi masa ba ko gidan baze leka yau ba duk kuwa yanda yake da kawa zucin uwa". "Ai mutumin naki sai ke". Saida ya gaisa da masu gadi sannan ya shiga motar da yazo a ciki ya nufi unguwarsu tunda babu nisa daga unguwar su Hajiyar, yana shiga ana kokarin tayar da sallah da sauri ya shiga cikin masallacin gidan nasu tunda da alwalarsa. Sahun bayan su Abbie dinsa yayi sallah da aka idar masu fita suka fita shi daman a dabi'arsu yawanci basa fita sai sunyi insha'i zirillahi yaci gaba dayi Abbie din bai juyo ba shima bai matsa ba sai Babban yayansu Ibrahim da yake daga jikin ginin masallacin ta kudu yake mamakin yaushe Mahmud din ya dawo kuma uncle saminu ya dawo dazu yace Mahmud ya gudu daga India, uncle mustapha ya bazu nemansa to ga Mahmud kuma a sokoto ga uncle mustapha ya sauka a abuja ze biyo jirgin karfe bakwai na dare zuwa sokoto to me kenan hakan ke nufi? Shifa daman ya dade yana zargin uncle saminu da wasu abubuwa marasa kyau a tsakaninsu. Ana idar da insha'i Mahmud ya tashi ya fice kafin Abbie din su ya tashi, hannu kawai ya dagawa securities din ya wucesu suna faman murna dan sunsan kakarsu ta yanke saka mai yiwa dawa ruwa bare gashi a karkara,koda bayanan sakonsa yana iskesu to bare gashi ya dawo. Ya dan jima a parking lot na gurin Ammi yana Karewa harabar gidan kallo ko ina haske ne tar ga wata iska mai dadi da take busowa cikin motar tare da kamshin furanni mabanbanta, abubuwan da suka faru suka dunga dawo masa daki-daki lumshe idanu yayi baiyi aune ba yaji ruwan hawaye suna bin kumatunsa abinda baiyi ba kenan duk badaqalar da aka sha a gidan nan a lokacin, kansa ya kifa jikin sitiyarin motar baiji alamun tafiya ko wani Abu sai dai jin hannun mutum yayi a bayansa bai dago ba, bubbuga kafadarsa yaji an fara kafin ya tsinkayi muryar Abbie dinsa yana fadin. "Haba! namiji baya kuka tunda ka iya jure kwaramniyar baya baka nuna rauni ba yanzu lokacin fuskantar gaba ne taso mu shiga ciki kada kannanka suga kana kuka, su raina min kai". Da Saudi ya dago jin furucin da bai zata ba daga bakin Abbie idan yayi la'akari da lokacin da guguwar abun ta tashi tsine masa ne kawai baiyi ba Amma yayi masa wata irin tujara ta Ala tsine uwar mai karya. Jikinsa ya fada yana fadin. " wallahi Abbie ban aikata ba! Ban taba zina ba, ka bani Qur'ani zan rantse da Wanda ya halicceni idan na taba zina a rayuwata Allah yayi min abinda yaso na azaba, ka yarda dani ka fadawa Ammi banyi ba sharri ne akayi min na fada Amma Baku yarda ba...kum..." Sai jikinsa ya langabe ya saki. Da sauri Ya Ibrahim dake tsaye a gefe Wanda shima hawayen yakeyi ya zaburo yana fadin . "Suma yayi Abbie bari na samo ruwa" Ya tafi da gudu ya haura steps din part din Ammi, suna zaune ya bude kofar afujajun baiko kalli su Ammi ba da saura yaran yayi kitchen da gudu ya dauko ruwan sanyi da sauri Ammi da Aishat da Batool suka rufa masa baya Ammi na tambayarsa menene? Bai ko juyo ba yayi gaba,suma gurin daya nufa suka nufa turus sukayi ganin Abbie a tsaye rungume da mutum Ya Ibrahim yana bulbula masa ruwan sanyi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da shashsheka abinya yake fada yaci gaba da fada. Ka fadawa Ammi ni ba nazinaci bane ban aikata ba". "Pls kayi shiru mana ta sani ka kwantar da hankalinka bama zarginka kaga Amminka tana jinka fa". Da sauri ya juyo sai kuma jiri ya kwashe shi ze zubar Ya Ibrahim yayi saurin rike shi suna faman jera masa sannu, juyawa Ammi tayi idanunta fal hawayen tausayin dan nata kenan duk tsawon lokacin nan yana fama da wannan damuwar wadda sai yau ya fasata gashi zata janyo masa matsala a lafiyarsa. " Allah ka biwa yaron nan haqqinsa". "Allahumma Amin". Taji su Batool sun fada sai lokacin tasan a fili tayi addu'ar. Su zahra na tsaye tana dauke da Afnan tun shigowar Wanda ya dauki ruwa ya fita su Ammy suka bishi taji gabanta yayi wata irin faduwa, ta mike tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kuma taga an shigo da Mahmud din a rirrike yana layi kamar Wanda ya bugu da kayan maye. Ai bata San yanda akayi ba ta dira a gabansa jikinta yana wata irin tsuma cikin rufewar idanu da manta a ina ma take ne ta fara fadar " Na shiga uku meya sameka meu amor...? Me akayi maka fada min dan Allah..." Hannu Aunty Aishat da Dora a bakinta data bude tana fadin. " kai? Wonderful...! the game is over". [23/02, 11:59 am] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI * AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah. Page 76. .............. Aunty Aishat ce tayi sauri tazo gurin zahrar saboda kowa a gurin wutarsa daukewa tayi barema Abbie da Ya Ibrahim da Basu da masaniyar da wata bakuwar fuska a gidan, itama zahrar sai data fada ta dawo Cikin hayyacinta, wata irin kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta tsage ta shige Dan kunya, me tayi kenan shike Nan tayi abun kunyar da zata Dade Bata hada Ido da Amm bai wallahi. Kan kujerar dake kusa dasu su aje Mahmud Wanda tun dirowar Zahra gabansa yaji wata irin Rahama ta saukar Masa a zuciyarsa badan a gaban iyayensa bane saiya Bata hot kisses na nuna godiyar nauyin data sauke Masa Cikin kankanin lokaci ta isar da sakon Daya Dade Yana tunanin ta Ina ze bullo musu Sai gashi in some minutes tayi musu aikin. Aunty Aishat na rike da hannun zahra suka shige Cikin wani parlourn har lokacin jikinta Bai dawo normal ba, Afnan Auntyn ta karbe daga hannunta suka zauna. "Ki nutsu babu fa abinda ya same shi inaga farin ciki ne ya sakashi sumewa, kinsan mutumin naki da kwakawar son iyaye kinsan kuwa haduwar ai Daman za'a iya samun irin haka". Ita dai Zahra kasa daga Ido tayi ta kalli Aunty Aishar wannan abun kunya har Ina da farawa da iyawa ranar data sauka a ranar ta baza abin fada to Wai ita meye ya shiga kanta ne ta kasa controlling kanta a gaban mutane?. Itama Aunty Aishat Bata dameta da yawan magana tasan tana Cikin Jimamin abunda tayi Wanda ya bude wwani murfin da suka kasa budewa sai gashi wadda aketa kunbi kunbiyar bayyana wacece ita tayi ta bude aiki da kanta ba tare da itama ta sani ba, ta Kara girmamawa girman Allah buwayi gagara misali Dan wani connection din idan aka hada shi sai dai kayi kallo kawai, tashi tayi fice ta koma can main parlour din. Da Ido Ya Ibrahim yabi su Aishat har suka fice daga parlourn Yana kissima abubuwa masu yawa a cikin Zuciyarsa "kafa fa a gudu ba'a tsira ba". Yayin da Ammi da Abbie suka dubi juna da alamar tambaya a fuskarsu, Ammi nayi masa wani duba na Mena fada maka?. Aishat na shigowa Hajiya Inna na shigowa atfujajan uncle Mustapha na biye da Auncle Autan Hajiya Inna. " Muhammadu Rasulullahi! Ni Hadiza Naga abunda ya isheni Ashe haka ka dunga gararamba yaron Nan a cikin kasar nan kamar marar gata? saida ubangiji ya tallafeka da mutanan kirki bayin Allah masuyi Dan Allah yanzu Nan Mustapha yazo min da wannan labarin daya jiyo gurin bawan Allahn Daya tsinceshi a yashe a kasa ko takalmi babu a kafarsa ko magana fa yace baya iya yinta a lokacin, wannan Dan taliki Ubangiji yayi Masa sakayya da gidan Aljanna, duk Kuma Wanda yake da hannu gurin neman tagayyara min rayuwar jika Allah ya wulakantashi tun anan duniya Kuma wannan yaron KAINUWA ne dashen Allah ba dashen mutane ne ba, ita Kuma sameera mun barta da Allah suje suji da abun kunyarsu munafukarkar banza da Ido kamar an rutsa mazuru a dakin tantabaru na godewa Allah da 'ya'yan da take haihuwa basa Zama da yanzu ta tafi tabar mana mugun irin". Ammi CE ta matsa kusa da Hajiya Innar tana fadin. "Ayi hakuri Hajiya ai komai ya wuce ki daina tada hankalinki saboda lalurarki Bata son yawan bacin rai". "Yo bacin rai na nawa Kuma zainab ai saidai kada a Kuma". Shi dai Abbie ya yayi shiru Yana jujjuya Lamarin a zuci. Gurin Zama Ammi ta raka Hajiya Inna ta zauna kusa da inda mahmud yake zaune idanunsa a rufe. "Kai Kuma menene haka ta wani kike Riga sharaf ka kuma Kama ido ka rufe sai qif-qif kake dasu kamar wani sabon makaho". "Trouble woman". Ya fada a zuciyarsa. Abbie ne ya matso Yana gaishe da Hajiyar Yana fadin. "Haba Mustapha saboda me zaka dauko ta da Daren Nan ku taho basai a barwa safiya ba". "A'a nice nace baze taho ya barni ba kada ku taru ku nakasa shi a banza yanzu ma zuwa nayi mu tafi ko abinci baici ba, gashi ya laimin kuwa nazo na tarar kunyi ira-ira da gani wani Abu kukayi masa. Kai bude idonka ka fada min waye yayi maka wannan dibar albarkar ya jikeka sharaf haka?". Abbie ne ya zauna daga gefenta Yana fadin. "Babu Wanda yayi Masa komai murnar yaga Amminsa ce tasa ya sume Saida aka Zuba Masa ruwa sannnan ya dawo hayyacinsa". Tabe Baki tayi tana kallon Ammi wadda ta zauna daura da kafafuwan Hajiyar tana saurarenta. "To Daman zuwa nayi na jawa kowa layi akan rayuawar yaron nan kada naji kada Kuma na gani, anyi Daya babu Kari, Kuma na nazo Kan maganar waccen matar Mai idanu Yana gwarawa wallahi ko bayan raina ka mayar da aurenta ban yafe ba sai Allah yayi Mana hisabi akan,haka me akeyi da wannan matar Mai bakar aniya aini har abada bazan taba yafe Mata ba". Ta fada tana kallon Abbie fuskarta a hade alamar ranta a bace yake. Hakuri suka dunga Bata mahmud najinsu Kuma yayi mirsisi ya bude idanunsa. "Saika tashi mu tafi ka Gama zaman gidan nan gara ma kayi aure inga ta karyar sharri Kuma haka kawai an takura maka kowa neman lika maka 'yarsa yakeyi an mayar da Kai na mamajo, kazo muje Ina da yaran dana zabar maka har hudu idan ma duka kake so saina shige maka gaba a aura makasu Rana Daya inga ta tsiyar kawo maka rida Kuma". Su dai hakurin dai suke Bata, shi kuwa da goyan tana ambatar ya tashi su tafi yayi wani Dan murmushi a cikin Zuciyarsa. "Tab ba inda zani yanzu dai da precious ke cikin gigita Sai taji dumina na kwantar Mata da hankali Nima bana son mu zauna guri Daya matsla za'a samu gara muna Dan nesa". "Wai bazaka tashin bane kayi min kunnen uwar shegu kana wani farfar da Idanu?". Uncle Mustapha ne yace mata. "Kiyi hakuri idan ya warware zuwa safe sai ya shigo ai Daman mahmud naki ne, bakiga a gurinki yayi masauki ba daze tafi ma kece ta katshen daya gani kafin yabar gidan, kefa Dan gata har sakawa yake azo takanas a kirashi video call Yana ganinki kofa tsiren da kikace Na Maru yana badawa a kawo Miki saboda Alkawari tunda a gurinsa Mahmud yake sawo Miki Bai daina kawawa ba, da naje nasameshi ya bani bill da adadin kudin tsiren Daya kawo Miki cewa yayi Wai an turo Masa kudin tsirenki na shekara ne, Yana fadin haka nasan aikinsa ne, Dan haka tashi muje na mayar dake gida idan Allah ya kaimu gone saina kawo Miki shi har gida" . Yunkurawa tayi ta tashi sai lokacin idonta ya Kai Kan Aishat. "Ke Kuma saukar yaushe Hasana? Ko Kuma ke Kika kawo shi kasar ne?". "A'a bani na kawo shi ba arashi kawai akayi nazo shima yazo". Mahmud naji suka wuce ita da uncle Mustaphan da uncle Aliyu. Abbie da Ammi da Ya Ibrahim suka bisu a baya. Saida yaji fitarsu sannan ya bude idanu Aishat da Batool kawai ya gani a parlourn duk sauran yaran sun wuce ciki. "Sannu Ya mahmud". Batool ta fada tana Dan matsowa kusa dashi. "Yauwa Batool" ya fada Yana kallonta, Aishat din ya kalla Yana Mata inkiyar tana Ina?. 'yar dariya tayi tana fadin. "Saboda Allah ka saka yarinya ta gigice irin haka har ta saki layi irin haka nasan saina amsa tuhuma a gurin Ammi Dan Naga wani irin kallo da tayi min". Batool ce ta Kara motsowa sosai ta kwantar da murya. "Ya mahmud Wai da Allah wacece wannan? tunda na ganta naji Ina sonta ina sonta wallahi gata very wise da ita, tana da kirki gashi duk abinda zata fada a Dan zaman da mukayi dazu zakiga da hikima a cikin maganarta, hikimarta ta girmi shekarunta gaskiya, gashi Bata da Jin Kai Sam idan wata ce yanda Allah yayi halitta a gurin ai sai yanda Hali yayi kawai". "Kice kin zurma dai batool irin wannan kodawa haka?" "Gaskiyar kenan Aunty wallahi tayi, ji nake kamar jinin mu ce ita" Lumshe ido dan gogan yayi jin yanda ake Koda Masa precious tun Bata kwana a garinba har ta Fara shiga ran kannensa haka. "Matarsa ce fa bakiga ta rude ba da aka shigo dashi a rirrke ba?" "Yehhh... Yessss... Wallahi Ko yanzu Ya mahmud ka nuna kai jarimi ne ka dauko matar da babu irinta a dukkan Family ai gara da akayi yunwa halin kowa ya fito". Ta fada tana tsallen murna kamar Karamar yarinya. A haka su Abbie suka shigo Amma ba Ya Ibrahim ya wuce parta dinsa da yake a Cikin estate din suke shida saura yayunsa. "Ke Kuma wane irin sakarci ne wannan da tshon dare kike yiwa mutane ihu haka?". Jikin Ammi ta fada tana fadin. "Wayyo Dadi Ammi Wai ashe Aunty Zahra matar ya Mahmud ce,". Shi dai Abbie gurin mahmud ya nufa ya zauna kusa dashi ya Dan taba gefen wuyansa. "Sannu me yake damunka yanzu?". "Ba komai kawai kaina ne yake ciwon kadan". "Ok.ai na yiwa doctor Hashim waya yace gashi Nan zuwa". Jin abinda Abbie ya fada yasa Aunty Aishar da Batool suka nufi parlourn da Zahra ke zaune Basu tarar da ita a gurin ba sama suka nufa Batool nata kakabin abin tana faman magiyar Auntyn ta fada Mata ita ce ta hada Ya mahmud da Aunty Zahrar? Amsar Daya ce dai take fada Mata yanda ta ganta itama haka ta ganta. Knocking biyu sukayi Zahra tace su shigo a kan sofa suka sameta ta Zuba tagumi tana aikin tunani Afnan ta karba daga kafadar Auntyn wadda tayi barci kwantar da ita Zahra tayi. "Kuma saiki gudo Baku gaisa da Abbie ba". Sadda Kai tayi dan ji tayi Auntyn ma kunyar hada Ido takeyi da ita. "Zamu gaisa ne ai yanzu bazan iya zuwa ba wallahi kunya nakeji, ji nake kamar nayi tsuntsuwa na gudu". "Kaji Aunty meye abun kunyar a ciki keda ba rungumarsa kiyayi ba "Dan kin nuna damuwa a Kan halin da yake ciki ai Kara kankarowa kanki mutunci kikayi su iyayensa, ai Dadi sukaji ko Basu fada ba irin wannan rudewa da antayo soyyaya a gabansu sun San idan aka shiga other room Kuma sai yanda Hali yayi kenan,gaskiya a gurinki zanyi degree harda masters ma akan soyyaya Naga alamar kina Dora Ya mahmud a network". Riqe Baki Aunty Aishat tayi tana kallon Batool. "Yaushe Kika lalace haka? Wallahi Zan sami Ammi ayi gaggawar saka Miki Rana kece Mai fadar irin wannan maganganun a gaban idanuna gara a yiwa tubkar hanci kinyi service din a gidan mijinki". "Kai Aunty Mena fada Ina ce kece ya kamata ki zaunar dani kiyi min Karatun yanda Zan Kama mijin nawa, Amma bakiyi ba sai kuma Kice Zaki hadani da Ammi Wai ayi bikin ko service banyi ba salon laulayin ciki ya hanani yinsa cikin dadin rai". "Allah ya shiryeki wannan yarinyar da Baki samu miji ba wallahi cewa zanyi Ammi ta fadawa Abbie ya badaki sadaka Naga alamar idan Kika Kara watanni za'a iya samun matsala gaskiya". Dr Hashim Bai Bata lokaci ba yazo bedroom din dake kasa wanda mahmud din ya mayar dakinsa suka shiga Dr ya duba shi, ya auna B.p normal yace ya rage saka damuwa a zuciyarsa saboda kada ta shafi lafiyarsa a irin wannan shekarun, tea yasa Ammi ta hado Masa ya Sha yayi Masa Allura ya bashi magunguna Yasha sannan ya tafi. Ba'afi minti biyar dayi Masa allurar ba ya Fara hamma zuwa minti goma yayi barci. Karfin A/C Abbie ya rage masa sannan suka fice daga dakin. Suna fitowa Ammi taja ta tsaya tana duban General. "Kaga abinda naketa fada maka ko? Game da mafarkin wannan yarinyar wallahi itace zahiri ake nuna mini a Cikin mafarkina suna tare dashi". Hannunta ya kamo suka zauna. "Ki kwantar da hankalinki lallai Allah ya nuna Miki wani sirrine da yaso ki fara gani kafin zahiri yazo Miki, tun ranar talata Mustapha ya turo min hirarsa da malamin Daya ya rike Miki yaro lokacin da baya Cikin hayyacinsa da yanda Sukayi ta fadi tashi akan nemar Masa magani da yanda ya fada anyi Masa asirin barin garin na har abada da yanda akayi auka bashi wannan yarinyar yanzu haka dai in takaice Miki labari matatmrsa ce ta sunnan wadda marikinta yayi Mata AUREN HUCE HAUSHI, saboda itama anata samun matsaloli ne a dukkan lokacin da auernta ya tashi, shine markinta Kuma Aminin malamin ya yaba da hankalinsa ya bashi aurenta ba tare da la'akari da irin matsayinsa na bako kuma Almajiri ya bashi ita, babu irin surutun da ba'ayi Masa ba ya toshe kunnensa ana ta fadar Dan ba 'yarsa bace ya Bata marar gata. To shi malamin ne ya gamu da jarabawar matsalar Spinal cord injury shi mahmud din ya fita dashi India lokacin dashi malamin yake kokarin dawo dashi gida sai kuma ya gamu da wannan lalurar yace a bamu hakuri sunyi kuskuren yi Masa Aure Amma mu dauka haka kaddarar take a rubuce gurin Ubangiji shiya kawo aka samu matsalar da tasa mahmud ya tsallake yabar gida har hakan ta faru da ba'a samu wannan matsalar ba da ta Ina zeje Azare ya zauna har a bashi auren yarinyar? Kinga Koda matarsa ce sai dai su hadu ta wata fuskar badai wannan ba tunda Allah ya hukunta matarsa ce". Jinjina Kai kawai Ammi keyi Tana Kara girmamawa girman Allah s.w.a idan yayi wani abun sai dai bawa ya kalla da Ido kawai. "Na fashimta bazan ja da hukuncin Allah ba, duk yanda yayi da bawa shine daidai naji Dadi da Allah yasa Dan uwanka yazo da maganar nan bashi Hussein ya fada ba da kuma abinda ita yarinyar tayi yanzu a gaban Dan uwansa Dan haka saika tarasu kasa Mustaphan ya kunna musu suji da kunnensu bazan dauki abinda na dauka a baya ba, Kuma sabon biki za'ayi kamar yanda ake yiwa kowa a gidan Nan maganin tsegumi Dan haka da safe Zan Kira Ya I Ishaq ya bani aron Aunty Badi'a zata rakata har Azare ta yiwa mamanta bayanin sabon biki za'ayi kosu can Basu sake ba su hada jama'arsu za'a zo a dauketa kamar ko wace Amarya da dangin mijinta suke zuwa su daukota, zatafi kima da daraja a Cikin family fiye da a wayi gari ace wai yazo da Mata ai wani ma abin magana ze Zama ko Yaya kake gani? kasan tunanin mace da namji ba Daya bane". "A maganarki babu gyara hakan yayi Amma idan har hakan za'ayi no need a ce sai kowa ya San gaskiyar maganar kawai Mustaphan yace an daura aure ne yanzu bikin za'ayi kawai Daman suna Shirin dawo dashi gida ubangidan nasa ya samu matsala Yana asibiti a India inda aka kawo labarin ganin mahmud din Ashe jiyya sukeyi a can". "Hakan yayi Allah ya Kara sutura" "Allahumma Amin" Abbie ya fada, muje ki bani wani Abu marar nauyi naci tunda Naga Alamar murna ta hanamu yin dinner a gidan nan, ki kawo min can part dina". "Kaiiii Yallabai ayi min afuwa yau Daya dai Ina da bakuwa ai nayi entertaining dinta". "Babu wannan kizo Ina jiranki ki bar musu Nan din kinsan dai zasu iya abinda zesa ki kusa nutsewa a kasa Dan kunya kuma ma ke Ina ruwanki dasu ba tare Kika gansu ba kinsa auren nasu ya dauki watannin da yinsa?". Dan murmushi Ammin tayi. "Ni fa Banga alamar yarinyar nan an mayar da ita mace ba gaskiya budurwa ce". "Kamar yaya, yarinya da mijinta ki ringa fadar haka?" Shiru tayi masa ita dai taga abinda ta gani tun ganinta da tayi dazu kafin ta sauki daga steps ta kiduri duba abinda Hajjo ta fada Mata da yake nuna yarinya budurwa ce ko tana ma'amala da maza, da niyya taje da niyyar daukar Afnan Saida ta gani sannan taji ta Samu nutsuwa. Lokacin da Ammi ta haura saman shiru da alamar sun kwanta,Saida ta Gama duk abinda zatayi ta rufo kofarta kamar zata shiga gurin zahrar saita juya ta nufi downstairs kawai tasan idan ta shiga kinya zata Bata gara ta Bari abun ya Dan bi jiki tunnna, downstairs ta nufa tana ayyana sai ta Dan yamutsa musu lissafi ko Yaya ya ne Dan su Kara sanin darajarta itafa tana kishin mace ganin an bashi yarinyar Nan a sama saiy Zahra ta Dade tana tunanin makomar aurenta baran barama dai tariga tayi sai Kuma yanda ta yuwu Wai Dan daudu a lahira. "Koyaya jikin nasa?" Ta fada a zuciyarta, ta Jima tana sakawa da kwancewa, gashi duk yanda taso ta Kira Aunty Hasana abun ya faskara haka Ammah duk network yaki bada hadin kai. Sai wurin Daya saura tayi barci, can a Cikin barcinta taji Kamar ana tabata, kwanciyarta ta gyara ba tare data bude Ido ba sai tajita a jikin mutum da wata irin zabura ta yunkura zata Mike taji an mayar da ita Baki ta bude zata zabga ihu taji carab ya hade bakinsu sai lokaci taji kanshin turarensa a hancinta, wata ajiyar zuciya ta sauke, tayi lif a jikinsa da gaske sunyi missing din juna Saida yayi Mai isarsa sannan ya dan saurara Mata ya yanye bakinsa suna maida numfashi. "Previous kin azabtar Dani whyyy... Me nayi Miki Kika haramta min ganinki kwata-kwata? Fada min kinsan halin Dana shiga kuwa? Kikasa na kasa controlling kaina a gaban elder brother dina kin kyauta min kenan?". Ita dai mukus tayi to me zata fada masa tace labewa tayi taji shirarsu da Aunty Aishat ko tace Masa me shirun shi yafi Alkhairi. Juyin duniyar Nan taki magana dole ya kyaleta ya koma wata shirar da ban. "Wai dazu da rungumeni zakiyi a gaban su Ammi?". Saka kanta tayi a kirjinsa Cikin kunya tana gigiza Masa Kai. "Kin dauka Zan tafi na barkine ko? To muna Nan sai kin haifo Mana fine babies masu Kama dake". Ya fada Yana Kai hannu akan cikinta Yana Dan shafawa. "Ka Bari Dan Allah Ammi fa tana Nan ka tashi ka tafi Dan Allah kada wani ya ganka ka shigo yayi zaton wani Abu fa". "Kwantar da hankalinki ai kin Gama Mana aikin Dana kasa yinsa a Cikin kankanin lokaci meya rage kuma? sai mu tattara mu tafi inda mukafi wayo Nima nasan nayi aure na huta da ragaita mu fuskanci rayuwa kuma, badan nayi alkawarin kawowa Ammi ke a yarinyarki ba Aida yanzu muna Shirin tarbar babyn mu ko ba haka ba?" Wannan furucin nasa shi ya ankarar da ita akwai fa sauran Rina a kaba, Nan da Nan wani tsoro ya kamata Nan ne fa karshen maganar, a Nan ne me afkuwa fa zata afku,tunda gata a sokoto har dakin mahaifiyarsa saura da me ya rage kuma?. Cikin shagwaba ta Fara fadar "Ni dai ka daina wannan maganar gaskiya wallahi ni Ina Nan kusa da Ammina ai ba muyi haka da kaiba nifa tsoro nakejiiii..." Wani special smile ya sakar Mata duk da dakin dimmer light ce Bata hanata ganin yanda dimple dinsa ya lotsa ba. "Wani abu nace zanyi Miki ne da zaki Fara tsorona? Ki zana feel free Dani har abada babu cutarwa a tsakanin mu, kin manta Abba da Baba Malam Amanarki suka bani?". Kai gyada Masa alamar eh. Cikin jikinsa ya sakata Yana fadar muyi barci da sauran lokaci duka yanzu one thirty five am". Kafada ta make tana kallonsa ta gefen ido ita fa da abinda yake figitata gaskiya. "Dan Allah ka tafi kada kaja mini Ammi fa tana Nan kada ta ganka nidai babu ruwana wallahi". "Nace Miki ki kwantar da hankalinki Amma Bata Nan fa tana gurin mijinta itama to Kinga Kota ganni ai ba wata damuwa ko?". Ita dai barci rabi da rabi tayi a kunnenta aka Kira sallar farko data biyu tana jinsa ta tashi ya shiga toilet ya fito ya zura jallabiya Daya zo da ita Cikin ledarta ya Dan shafi gefen fuskarta wadda tayi fayau a Cikin Dan hasken dake dakin. "Tashi lokacin sallah yayi, Zan wuce masallacin daga can zanje gurin Hajiya inna, jiya Baki ganta ba ko lokacin kin gudo tazo gidan Nan Wai zata tasani a gaba mu tafi Wai na daina zaman nan. Kin amince nayi nesa dake?". Jin za'a tada sallah yasa yayi sauri ya fice daga dakin, Karan rufe kofa yasa Ammi dawowa ta bude kofarta wadda shigarta dakin kenan Dan yallabai na tafiya masallaci ta nufo part dinta, bayansa kawai ta iya gani saboda saurin da yakeyi na kada ya rasa raka'ar farko, jinjina Kai tayi tana fadar. "Dole ayi yanda za'ayi ku tattara ku Kama gabanku badani za'ayi wannan dibar Albarkar ba, wato abinda general ke nufi kenan Daya tilastani zuwa gurinsa" Sallah ta tayar ta zauna zaman azkar da lazimi Ala ala take shida da rabi tayi ta Mira Niger, Saida ya dai daici lokacin dawowa daga masallacin yayan nata sannan ta Kira shi. Yana ganin Kiran yasan ba lafiya ba Dan Yana dagawa ya Bai saurari gaisuwar da take masa ba ya Fara fadin. "Zainab lafiya? Meya faru kuma?". "Wallahi ba komai Yaya sai Alkhairi". "To Alhamdulillahi, lfy kalau ya yaran da Mai gida" "Kowa lafiya, daman Mira nayi na fada maka danka ya dawo harda tsarabar Mata aka Mata aka bashi tana nan sunzo ita da 'yar uwarsa can ya Kai Mata ita" Sai kuma ta dauko masa Asalin dalilin kiran nasa shima supporting dinta yayi harma ya Kara da fadin dole a hada da babbar mace su tafi tare kamar zefi girma da daraja a gurin Iyayen nata, sunyi sallama akan idan an samu tickets dinsu damagaram to sokoton zasuyi waya wata irin nutswa taji ta saukar mata, gara ayi a wuce gurin. Da gari ya Fara haske zahra ta tashi daga Kan sallayar da tayi sallah ta ninke ta kintsa gurin wanna tayi ta shirya Cikin rigar material Mai budedden dinki San rigar Bata Kama Mata jiki ba tayi rolling da gyalen material din Nan da Nan ta gyara dakin ta fesa roomfreshner ta fito Cikin so take ta gaishe da Ammi Amma Bata San takamaimai Ina ne dakinta ba sannan kuma Batasan da wane Ido zata dubeta ba, tana kokarin juyawa ta koma kenan kofar dakin Ammi ta bude ta fito Shar da ita tana baza kanshinta da mamaki a fuskaerta ta fito tana fadin. "Masha Allah, harkin tashi kenan?" Ta tambayi Zahra. Da sauri Zahra ta tsuguna tana fadin. "Ina kwana Ammy". "Lafiya kalau ya bakunta?". "Lfy kalau". Ta fada tana Wasa da gefen gyalen da tayi rolling, ta kasa hada Ido da Ammi din. Ciki Ammi ta koma tana fadin "Shigo nan magana zamuyi dake" Zahra ji tayi gabanta ta yanke ya fad'i, jiki ba kwari tabi bayan Ammi ta shiga gefen gado Ammin ta nuna Mata ta zauna amma ta Kiya ta zauna a Kan carpet din dake gaban gadon tana jiran taji abinda za'a fada Mata. Zama Ammin tayi tana karewa zahra kallo yarinyar tana wani irin kyau Mai daukar hankali. "Kina jina Fateemah number mamanki Zaki bani ina son nayi magana da ita". "To Ammy gata" Ta Fara karanto Mata harta cika. "Tashi kije zuwa anjima Ina Jim zakuje unguwan insha Allah Amma Bari nazo muje ku gaisa da Abbie dinku". Ammi na gaba zahra na binta a baya suka nufi katafaren part din Abbie compound din ba kowa silent da alamar gidan bashi da yawan hayani kowa Yana gurinsa a kame sai munafurci fall a cikinsa a parlour suka sameshi tunda suka shigo zahra ta sadda Kai kasa har kusa da inda yake zaune zahra ta karasa ta tsuguna har kasa ta gaishe shi, Cikin muryarta Mai nutsuwa, albarka dai zahra Tasha ta gurin Abbie da godiyar abinda iyayenta suka yiwa gudan jininsa, cewa yayi ta zauna sosai ta zauna ya ringa yi Mata tambayoyin tun tana dari dari dashi harta dan sake dashi, lokacin da zasu dollars din America ya Bata raffer biyu ya Bata a Leda. Ammi ta karbar Mata Tama godiya. Har suka dawo Basu hadu da kowa ba ba Karamin Dadi Ammi taking da faruwar hakan ba, suna shiga suka samu masu aikin girki da share -share. Zahra Bata koma sama ba gurin Aunty Aishat ta wuce yayinda Ammi ta nufi kitchen. Auntyn kawai ta Sami ta tashi yaran duk Basu tashi ba, waya takeyi saida taji tace gata Nan ma Bari na Bata, wayar ta mikawa Zahra tana fadin "Bari nayi wanka tunda Allah ya kawo min ke bana son na shiga wanka ba kowa a Musa dasu* Wayar ta Kara a kunne tana sallama, amsawa yayi Yana fadin. "Pls My preccious Kina jina, dan Allah anjima da yamma ki biyo Sister Aishat kuzo tare ki gaishe da Hajiya inna Kuma na cika wani alkawarin Dana dauka tun ranar Dana bar gida nayi shi to shine nakeson cika shi ai asan zaki tayani mu cika alkawarina ko?". Ya fada da sigar rarrashi. [25/02, 7:40 pm] Abu Saleh: I *AUREN HUCE HAUSHI* 09061432330 Or 08055362975 AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah Page 77 .............karfe bakwai dai dai mahmud ya baro gidan Hajiya Inna, bayan yayi wanka,dole tasa yazo gidan tunda a gidan Ammi baya da kayan sakawa ya duba baiga komai ba be sani ba ko canza musu guri akayi ko bayarwa tayi abinda be bi ba'asi ba kenan yaga gara ya taho Nan ya shirya kawai, shigar kananun Kaya yayi ya fito Shar dashi, Bai koma gurin Hajiya Inna ba duk da albishir din da tayi Masa na sinasir da tasa ayi Masa da pepper soup din kafafuwan shanu. Yaso ya shiga gurin Abbie Amma gurin Amminsa zaya har yanzu bakinsu Bai Saba ba jiya da zummar suyi kwanan zaune ya shigo sai kuma aka samu akasi ya bige da allurar barci. Ta kofar baya ya shigo part din Ammin har ya Haye sama Bai hadu da kowa ba dakin da Zahra ta kwana ya bude ba kowa sai kamshinta Wanda har ya Fara kama dakin, komai tsab ba tamkar ba'a kwanta gadon ba, kofar ya janyo ya nufi dakin Ammi yasan a irin wannan time din Bata ciki turo kofar yayi da sallama shiru sai kamshi kawai ke tashi a dakin. Wani sanyin dadi ya ratsa shi jinsa yake kamar an sauke Masa wani katon dutse daga kansa, a tsakiyar dakin ya tsaya Yana tuno wasu lokutan baya da shigo cikinsa tamkar mahaukaci Yana magiya Amma ko gezau Ammi Batayi ba Saima tsallakewa da tayi ta wuce ta barahi a durkushe, Amma yau gashi ya shigo cikinsa da walwala da Aminci ba bacin Rai ba tashin hankali. Kwanciyarsa yayi a Kan sofa Yana fashi "Alhamdulillahi Ala kulli halin". Yayi zaman kusan minti talatin kafin yaji alamun bude kofar a Hankali ya cira Kansa daga wayarsa da yake duba sakonnin whatapps, Ammi ce ta shigo tunda ta shigo master parlourn ta tasan ya shigo gurin Bata Kara tabbatarwa ba Saida ta hauro saman Dan kamshinsa na daban ne. Tsayawa tayi a gurin tana Kare Masa kallo, Masha Allah gani tayi ya Zama Babba ya cika Ido kenan jiya ganin tsoro tayi masa gashi ya Kara yin wani fresh dashi da gani ya samu nutsuwa ba kadan ba. Aje wayar yayi ya taso ya nufota inda take tsaya murmushi yaki barin Bakinta ta Kuma kasa dauke idanunta daga kansa. Ba wata wata mahmud na zuwa ya shige jikinta Yana fadin. "Ammina fushi kike Dani ko? Nasan zakiyi fishi dani, gani Nazo kiyi min duk hukuncin Daya Dace Dani in dai Zaki yafe min, Dan Allah kiyi hakuri Nima bansan me yake faruwa Dani ba, Sam bana kaunar ko sunan garin nan naji an fada bana Kuma son naji ko sunan Wanda na sani in dai Yana Cikin family wallahi". Zamewa Yayi ya tsuguna ya rike kafafunta sai hawaye. Dan duk'awa tayi ta kamo hannunsa ya taso jansa tayi kamar Karamin yaro har gefen katafaren gadonta ta zaunar dashi itama ta zauna. "Waya fada Mata Ina fushi da Kai? Ko alama dama ma banyi fushi da Kai ba sai yanzu da Ubangiji ya amshi rokona ya share min hawayena, bakayi min komai ba ko kayi ma na yafe maka duniya da lahira, Allah yayi maka albarka ya baka kariya daga sharrin dukkan wani abunqi, yanzu Ashe kana Bauchi state kayi zamanka akayi ta nemanka a turai da kasashen larabawa?". "Ammi Nima fa wayar gari kawai nayi na ganni a garin bansan ta Yaya naje ba, Saida Habib Wanda ya ganni a yashe a kasa karkashin bishiyar gamji ya fada min a halin daya ganni nayi mamakin to ta Ina nabi naje can? da kafata naje ko kaini akayi? duk ban sani ba, Ammi Ina jinfa na rasa hankalina na wasu kwanaki ko watanni, Ammi hatta magana fa daina yinta nayi sai dai Ido Ina Jin abinda ake fada Amma bana iya bude bakina na mayar mutanen Nan ba Karamin jihadi sukayi ba gurin ceto rayuwata, Idan malam dawo har Azare Zan kaiki ki yiwa Baba malam godiyar abinda sukayi min kudi dai bazasu iya biyansu ba sai dai Allah mutane ne su masu karamci". Nan ya zazzage mass Mata duk irin rayuwar da yayi a Azaren har ya zauna a dakin waje na amajirai. Baiyi zato ba yaji shashshekar Ammi. "Subhanallahi ! Haba Ammi me yasa Zaki Bata hawayenki abin fa ya Riga ya wuce, Ina fada Miki ne kawai saboda ki Kara yi min addu'a saboda bamu San me goben zatayi ba". Knocking din kofa akeyi mahmud ya bada izinin shigowa. Aishat ce da suhailat suka shigo itace Mai bin batool. Da murnarta ta Karaso sai Kuma tayi turus tana kallon Ammi dake share hawaye Aishat ma jikinta sanyi yayi. "Meya sameta take share hawaye? Aishat din ta jefawa mahmud din tambayar. Ammin ce ta Bata amsa "Ba komai Hussein ne yake fada min halin rayuwar Daya shiga tamkar marara gata harfa so akayi a haukata min d'a a banza wallahi Ina istigifari ga Ubangiji kafin na fada, dama wani Allah ya bawa dukiyar Nan bashi ba da yake da kananun shekaru irin haka, wallahi da nasan wannan condense milk din itace sila Dana yiwa jama'a unguwa rabonta an wuce gurin,to ba haka zanen kaddarar take ba sai hakuri". Suhailat ce ta dan matso kusa da mahmud tana fadin. "Sannu Ya Mahmud ya jikin naka?" "Jiki da sauki suhailat ya karatun kin Gama ko?". "A'a da saura sai next year in Sha Allah". "Allah ya taimaka". "Amin" Suka fada gaba daya. Aishat ce tacewa mahmud "kaje Abbie Yana nemanka a parlournsa na part din nan, Ammi kema yace a Kai masu abin break fast can kamar na mutun bakwai". Mikewa yayi yana fadin "Bari naje Ammi". "Jeki ki fara hada abinda za'a shigar part din Abbie din keda sauda da Batool Kice iya Halima ta Zuba pepper soup din kayan Cikin Nan a babban warmer sauran ta saka a fridge". "To Ammi" Waje suhailat din tayi da sauri. Saida suhailat din ta fice shima ya nufi kofar Yana Daf da ficewa Aishat tace masa. "Ka fada Mata wacece zahra a gurinka Naga alamar ba iya playing match din zakayi ba". Tsaye yayi shi Bai fice ba shi kuma bai juyo ba, sai Kuma ya juyo ya dawo a Hankali ya zauna a gabanta ya sadda Kai da gaske wani irin nauyinta yakeji Wanda Bai taba tunanin zeji kwatankwacinsa ba a tare da ita, a Hankali kamar baya son yin magana ya furta. "Ammi ga zahra Nan an bani aurenta a Azare, tun watannin baya nace saina kawo Miki ita idan ta kwanta Miki a matasyin suruka ki saka Mata albaka ki kaita dakinta da kanki idan Bata yiiki ba ki saka a mayarwa da iyayenta ita a Basu hakuri, duk hukuncin da Kika yanke na karba da hannu bibiyu". Yana gama fada Bai jira yaji abinda zata fada ba ya tashi ya fice da sauri Dan ba Karamin kokari yayi ba gurin kinar bakin waken fada Mata ba. "Eh to da dai hakan yafi a mayar musu da yarnyarsu tunda akwai alkawarin da nayiwa fulani, Ina ga sai dai suyi hakurin gaskiya" Abinfa ya iya jiyowa kenan daga bakin Ammin tasa bai it's cewa komai ba ya fice. Daga shi sai Wanda ya halicce shi suka San abinda yake ji a kasan Zuciyarsa. Aishat zatayi magana Ammi ta daga Mata hannu dole ta kame bakinta daga abinda tayi niyyar fada. "Kuje kiyi serving din ku kafin na fito, idan kun Gama ki hadawa yarinyar Nan kayanta Wanda kikece min tsaraba yasa akayi Mata nafi son tabar gidan Nan kafin wani tsegumin ya fito". Sororo Aishat tayi tana duban Ammi wadda ta tashi ya shige toilet kirjinta na bugawa da sauri da sauri. "Allahumma Ajirniy fiymusibati, wannan wane irin tashin hankali ne Kuma? Allah ka kawo sauki". Fita itama Aishat din tayi jikinta a mugun sanyaye, bedroom dinta ta nufa ta yiwa Zahra magana suka fito tare, da kyar Aishat tayi ta maza ta danne zuciyarta sukaci abincin tare da su suhailat duk da basa cin abinci da wuri Amma dole tasa tunda Umarnin Ammi ne. ** Ammi najin fitar Aishat ta fito daga toilet din ta dauki wayar ta Kira number data karba a gurin zahra, Bata so Kira a irin wannan lokacin na safiya ba amma dole tasa hakan. Lokacin Ammah na kitchen Musaddiq ya kawo Mata wayar yace kiranta akeyi, tana wanke hannunta wani Kiran ya shigo Saida ta goge hannunta ta karbi wayar, bakuwar number ce. Dauka tayi tana amsa sallamar tana ficewa daga kitchen din ta barwa Alawiyya aikin, gaisawa sukayi da Ammi kafin Ammin tace. "Ko Hajiya Asma'u ce maman Fateemah Zahra?". Sai Ammah taji gabanta ya Fadi ana ambatar sunan zahra. "Eh nice, Allah yasa lafiya?". Dan murmushin da Bata shirya ba ya kwacewa Ammi. "Lafiya kalau sai Alkhairi,sunan Hajiya zainab daga Nan sokoto mahaifiyarsa Mahmud mijin Fateemah". Cikin nuna jin Dadi da tsantsar fari ciki Ammah ta Fara fadin. "Masha Allah! Hajiya ya gida ya akaji da jama'a ai jiya ta fada min suna Nan naso na karbi number ki mu gaisa sai tace min wai bazata iya tambayar mi ba, to yau naso na karba a gurin shi mijin nata mu gaisa". "Kai haba babu komai muya Kamata mu tako muzo muyi godiya yanzu ma bamu fasa ba wata dai Alfarma nake nema akan 'yata yau komai dare suna Nan bisa hanya zasuzo tare da 'yan uwa na sai anzo daga Nan an daukar min ita an kaita dakinta kamar kowace Amarya ba Wai a wayi gari a ganta a matsayin matarsa ba bana son ayi Mata wani duba na daban kinsan Yana yin kowa ne family da irin nasu matsalolin,duban irin kalubalen da aka fuskanta a Nan din kafin barinsa gida, naso ace wani nawa yayi Miki wannan bayanin to basa kusa kiyi hakuri nayi rashin kunya akan Dan Fara". Ta fada tana 'yar dariya irin gentle din Nan. Itama Ammar yin tata tayi, tana fadin. "Na fashimta kina dai son kankarowa diyar taki mutunci ne ko?" "Gaskiya dai Kam Allah dai ya saka Miki da Alkhairi kinyi abinda duk uwa ta gari zata yiwa yarinya mace Hussein ya fada min komai, mun gode da Karamancin ku garemu kin dauki yarinya kamar wannan kin bashi ba tare da kunsan asalinsa ba, sai nazo har gida nayi godiya in Sha Allah". Sukayi sallama kasake Ammah tayi tana lissafo maganganun su da mahaifiyarsa Mahmud daga ji ba wata Babbar bace sosai sai dai tasan kanta da alamar Allah ya karbi Addu'oin ta Wanda take ba dare ba Rana akan Zahra na neman dace da kwanciyar hankali a gidan Aure, sai Kuma tayi murmushi wannan sirikar ta Zahra za'a da ita tasan ta Kan duniya wato sai ansan yayi aure ba Wai yazo da Matar ba kamar Auren bariki. Part din Abban ta nufa na bangaren ta, tana shiga Yana aje wayarsa da ya gama. Ganin fuskarsa da wani irin annuri yasa ta fasa fada Masa abinda tazo dashi gara ta Fara Jin nasa tukunna. "Wane irin albishir akayi maka haka Mai Dadi Daya saka Zuciyarka a irin wannan Nishadin haka?". "Zoki zauna yanzu muka Gama waya da sirikin uwata Wai ashe yaron Nan mahmud Dan wajen General Muhammad Dange ne, Saida ya kirani yanzu na gano inda nasan fuskarsa Kullum na kalleshi sai Naga nasan fuskarsa ko a wani gurin ne daban Ashe fuskar mahaifiyarsa nake gani a tasa fuskar, kinsan kuwa waye General Dange? To babu abinda zewa Ubangiji sai godiya ya sakawa uwata da abinda hankali da tunanin mu Bai taba kawowa ba mijinta fa shine Dan general din Wanda ake hasashen Yana Daya daga Cikin matasan masu kudin Africa sahun farko duk fa yanda family dinsu sukayi popular a kasar nan ta fuskar arziki yaron yayi musu wata irin tazara, Abu Daya yake bani mamaki yanda ya iya jure rayuwa irin ta Cikin Almajirai ba kyamata ko kadan Abu Daya ne dai kawai ya ringa sani a tunani yanda tun bayan samun lafiyar yaron komai na makarantar ya canza akace NGOs sun shigo suna wannan mahaukatan ayyukan Wanda ba'a yinsu a sauran makarantu Dan ma daga baya sun canza salo sun shigo da wasu makarantu harma Dana Karkara". Jinnina Kai kawai Ammah takeyi tasan wannan ba tsuminta ba ba Kuma dabararta ba Rahamar Allah ce ga bawa kawai da yake yinta ga wanda yaso a lokacin da yaso, lallai sun kunshi takaici da yawa a baya Amma Cikin Rahamaniyya ta Ubangiji sai gashi abun ya zamo wani haske daga karshe abinda babu Wanda ya zata Koda kuwa a Cikin mafarki ne. "Abban Yara Nima abinda ya shigo Dani kenan na fada maka munyi communicating da mamansa yanzu". Nan ta fede Masa daga biri har wutsiyar yanda Sukayi da Ammin mahmud. Dariya Abban yayi yana fadin "Nima ya fada min har Yana bani hakuri da halin Mata na bidi'a Wai ita uwar sai tayi bikin danta kowa yasan yayi aure" Sun Dade sun tattaunawa na Suma dole su nuna Mata gata tunda inda Allah ya kaita ba gurin Wasa bane na take Abban ya turawa Ammi makudan kudi ayi abinda ya Kamata Dan ma da furnitures a aje Wanda Ummee suka turo ba'a sakaba saboda babu guri Kuma Kaya ne na garari. ******** Tunda su zahra suka Gama Break fast suka koma parlour na uku suka zauna suhailat ta kunna musu tv ana yin wani series na 'yan Lebanon, manyan jakunkuna taga masu aikin Ammi suna fita dasu daga dakin da aka aje kayan da suka zo dasu ba dadewa Kuma taji maganar mutane daga dayan parlourn, sai kuma taga suhailat ta tashi da sauri tana fadin. "Kai su mummy Badi'a ne yanzu da safen Nan haka kamar Wanda suke daga wata unguwar" Ta wuce ta nufi inda suke. Da gudu suhailat ta fada Kan mummy Badi'a tana fadin. "Sannunku da zuwa mummy keda Hajji zuwaira, ina kwanan ku Ya hanya? Amma zuwan Cikin dare kukayi ko? Naga duka yanzu Sha Daya fa". Gaisuwar suka amsa sannan mummy Badi'ar tace "ko kadan dazu muka zo wurin karfe Tara da rabi ta baya muka shigo muna sama ne gurin Ammi itama yanzu zata sakko". Aishat ce ta shigo daga wata kofa wadda zahra Bata San ko Ina bane, ranta a hade ta cewa Zahra ta taso suka nufi gurinsu su suhailat. Suna shiga bakin suka fara fadin. "Masha Allah, wannan ce Fateemar? Matso mu gaisa Hajja zuwaira na fadin "nice dai ta karfen keta katako ce" mummy Badi'a na tare mata, cikin Jin nauyi zahra ta tsuguna ta gaisheni su Cike kunya da girmamawa. Aishat sai taji tana jin haushin maganar Hajja ita ana ga yaki tana ga k'ura, Ammi na maganar a mayar da Zahra gurin iyayenta a Basu hakuri ita Kuma tana maganar wani itace ta karfe. Ammi ce ta shigo rungume da wani Abu anyi rapping dinsa tazo ta zauna kusa da mummy Badi'ar tana fadin gara ku tashi komai ya Zama ready kada kuyi dare tunda tafiyar mota ce". Tashi tayi tana fadin . "Hasana kuje kofar baya gamu Nan zuwa". "Taso sister muje" Ta fada tana taba kafadar zahra. Ita fa Bata gane ba an sakata a duhu Ina zata kuma taji ana fadin kada ayi dare to suwa zasuyi Daren? Ita Kuma meya hadata da bakin Ammin da taji kamar da ita zasu tafi. Ita dai bin Aunty Aishar takeyi wadda taji kicin kicin da rai kamar ta fasa kuka. Wata lafceciyar GLK Mercedes-Benz 2024 model Parke a kofar baya sai daukar Ido takeyi Baba Habu drivern Ammi na Amana Yana gefe Yana jiran Umarnin Ammi. Da saurinsa ya matso Yana gaishe dasu zahra, fa sauri zahra ta Dan duqa ta fadin. Lafiya kalau Baba".. Su Ammi ne suka fito har inda su Zahra suke tsaye Ammi ta Karaso, ta Kamo hannun Zahra ta dankata a hannun Hajja zuwaira tana fad'in. Gata Nan Hajja na Baku Amana ku damkata hannun mahaifiyarta Dan Allah, Allah ya tsare hanya". Kunshin abinda ke hannunta da wani gidan sarka White gold Mai azabar kyau sarkar kudinta sun tasarwa milion hamsin ta mikawa Zahra tana fadin "Allah ya tsare hanya ki gaishe min da mamanki". Ta bude motar ta sakata ta juya ta koma Bata Kara kallonsu ba saboda ji tayi kamar rabuawar kenan. Wasu hawaye Aishat taji sun cika Mata ido da gudu tabi bayan Ammi tana fadin . "Why! Why! Why! Ammai kin kashe min farin Cikin bros wallahi". Mahmud ne ya fito daga part din Abbie yaji wannan kalaman daga bakin twin sister dinsa. Yayin da a waje itama Zahra data Gama fuskantar inda aka dosa ta kifa kanta a gefen kafadar mummy Badi'a tana sakin wani marayan kuka tana ayyana shikenan ta faru ta Kare wata sabuwar matsalar kuma. A Hankali zahra ta bude idanunta sharaf da hawaye Jin motar ta harba da wani irin speed ta nufi main gate, ta juya ta yiwa gidan kallon karshe gidan data kwana Daya Tak a cikinsa da sunan matar dansu wadda a yau kuma bata San wane suna zata Zama ba, wata Kika sunanta ya tashi ya koma bazawa kuma, Dan rashin 'yanci ko Jakarta ta hannu ba'a Bata dama ta shiga ta dauko ba. [27/02, 11:13 am] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI* AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah 99061432330 Or 08056362975 Page 78 ............. Cikin wani irin karsashi mahmud ya riko Aishat Yana fadin. "Meye haka kikeyi? Kinfi Ammin sannin abinda ya Kamata tayi ne, Ni ne nace Mata idan zahra Bata kwanta Mata ba tayi abinda ya Kamata, ina cewa a gabanki komai ya faru? to meye kuma na daga hankali Allah yasa hakan yafi Alkhairin". Ya juya ya fice daga part din gaba daya, mota ya shiga yabar gidan gaba daya, isolation yake bukata a yanzu Dan Kansa babu abunda yake sai Sara Masa besan me yasa Ammi tayi hakan ba amma jikinsa be bashi Wai an rabashi da precious bane har abada, akwai wata manufar yin hakan duba da zuwan gaggawa da yaga su mummy Badi'a da Hajja zuwaira matar kawu yusufu sunyi yasan da magana a kasa Kuma ga tafiarma a sirrance akayita ta kofar baya motarma Mai duhun glass ce, Duk abinda mahmud ya fada Ammi taji shi sarai Amma tayi gaba dole ta nemarwa matarsa uwar 'ya'yansa Qima da mutumci bazata biyewa yarintarsu ba a haifi Dan da babu idanu. Sama ta Haye tana lalubo number Aunty Surayya matar uncle Mustapha. Daki Aishat ta koma ta dubo ko Afnan ta tashi tunda Abulkhairi Yana gurin Batool, Amma fa hankalinta yaki kwanciya so take taji daga bakin Ammi din dole su zauna. Kwanciya tayi tana lalubo number sweet heart dinta dole su ta fada Masa halin da ake ciki saboda a gabanshi Komai ya faru akan yanda ya gigice daga yi masa fushin d'an lokaci to Ina ga anyi Mai dungurungun kuma, ai sai yanda Hali yayi tasan abinda ya fada kawai dauriya ce bawai har Zuciyarsa haka abin yake ba. *******Tunda su zahra suka dauki hanya tayi shiru mummy Badi'a ke yiwa Zahra Hira da hannunka Mai sanda akan abubuwan da suka danganci zamantakewar aure da irin 'yan dabarun rike miji yaji ba wata sai Kai, ita dai zahra daga eh sai a'a take fada ko hanyar Bata lura da inda suke nufa,ita dai Hajja zuwaira barcinta take Sharawa tunda suka dauki hanyar dodar, tafiya Malam Habu yakeyi iya tafiya ga kuma lafiyayar mota, a Kano sukayi sallar azzuhur da la'asar suka dauki hanya zahra tayi mamakin yanda wannan bawan Allah yasan hanya haka gashi dai ya fara manyanta. Karfe shida da rabi suka shigo Cikin garin Azaren katagum, dan rage tafiya Malam Habu yayi ya Dan juyo Yana fadin 'ranki shi dade Ina muka nufa gamu Allah ya kawo mu Azare". Hanya ta ringa nuna Masa Yana bi har kofar gidan Abba. "Masha Allah". Mummy Badi'a ta fada a ranta ganin gidan da suka zo da gani Suma ba kashin yadawa bane da nasu rufin asirin daidai gwargwado dan ko makaho ya Shafa yasan da abun. Horn biyu malam Habu yayi Baba sani ya leko ganin Bai sheda motar ba ya fito ya nufo su dai dai gurin window din driver ya leko gaisawa sukayi kafin Zahra tace Masa. "Baba sani nice zahra ka bude Mana". Da sauri ya juya Yana fadin "sannunku da zuwa ai bangane ba sai yanzu". Suna sako Kai Cikin harabar gidan magaji na fitowa da sauri da alama wani uzirin ne ya taso masa ganin bakuwar mota Mata na fitowa yaja ya tsaya yaga su waye ganin Bai sheda su ya nufi hanyar ficewa yayi taku kadan yaji maganar Zahra daga bayansa tana fadin. "Sulaimanu". Da sauri ya juyo yana dariya. "Kai Kice cere Bina ce ta shigo garin". Mummy Badi'a bata san lokacin da dariya ta kubce Mata ba, tana kallon magaji Daya nufosu da sauri. Gaishe dasu mummy Badi'ar yayi Yana fad'in. "Sannunku da hanya Bismillah ku shigo, yayi gaba da sauri don ya isarwa da Ammah sako, haba Ashe da dalili shi dai yaga anata faman dafe-dafe Daya tambaya ba Wanda ya bashi amsa, Zahra na gaba su mummy Badi'a suna bayanta cikin gidan shiru ba kowa sai su zilai da sahura suna gyaran kitchen din waje daga nesa sahura ta hango su zahra zasu shige part din Ammah. "Kai zilai Kinga kamar uwar dakinki sa wasu mata sun shiga part din Ammah". Banza zilan tayi Mata tana ganin tsabar gulmace kawai irinta sahura wace zahrar kuma wadda bata kasar ma gaba daya, jin tayi banza da ita yasa ta hakura taci gaba da abinda takeyi. Su zahra na shigowa Ammah da magaji suna fitowa daga kofar baya wadda aka Samar da ita saboda part din Abba. Cikin farin ciki Wanda har ya bawa zahra mamaki, Ammah ta taresu tamkar tasan da zuwansu, Fadi take "sannunku da hanya kunsha doguwar tafiya nayi ta neman zahra dazu network ba kyau sai hakuri nayi". Zahra taso ta shige jikin Ammah kamar yanda ta Saba Amman sai taji nauyin yin hakan a gaban bakin Ido sai dai dan kwantar da kanta tayi a jikin Ammah nan da nan taji wata karaya da tausayin Ammah ya kamata tunda ta Zama budurwa Ammah Bata huta da kwaramniyarta ba yanzu ma gashi ana murna anyi auren ga Kuma wata sabuwa ta bullo In "yan caca. "Bismillah ku zauna Hajiya sannu sannunku fa" Alawiyya ce ta shigo da katon tray dauke da abubuwan sanyi ta aje tana gaishe da bakin nasu. Mummy Badi'a ce tacewa Ammah. "Yauwa sannu Hajiya ya muka sameku". "Lafiya kalau Alhamdulillahi" Ammah ta gaishe da Hajja zuwaira. Ruwa kawai suka Sha kafin a rakasu dakin da akayi musu masauki a Nan part din Ammah din Amma Yana daga can gefe daban ba'a fiye amfani dashi ba tunda da wadatar dakuna. Magaji ma fita yayi da ruwa da kwalin exotic da Coke na gwangwani yaje ya budewa Baba Habu dakin Baki na waje lokacin Yana gurin Mai gadi suna Hira. Kayan dake Cikin motar malam Habu ya Fara fitowa da magaji yana fadin. "Dan Allah shigar musu da kayan nan". Zahra dakin da take Zama ta shige tana mamakin yanda Ammah Bata nuna tsahin hankalinta ba duk da Batasan dalilin zuwansu ba ita da 'yan uwan Ammi. Cikin Kan kanin lokaci magaji ya Gama shigo da kayan ya zube su a parlour ya shiga ya fadawa Ammah. *** Su zahra basu fi minti ashirin da tafiya ba Part din Ammi ya fara karbar Baki matar Aliyu Halimatu ita ta fara zuwa Ammi batayi mamaki ba tasan karshen maganar kenan duk wanda ya samu labarin mahmud ya dawo zaiyi kokarin zuwa ya gani da idonsa ballantana tasan maganar zahra zata karade dangi shi yasa tayi wannan Kandagarkin ta turata gida duk masifar mutum da iya gulmarsa Saida ya koma da gwiwa a sage Dan Mai Kama da itama baze gani ba, kafin azzuhur part din ya dinke da jama'a 'yan taya murna, na gida Wanda suka Isa sai yan leke-leke sukeyi basa sama basa kasa, irinsu Habiba matar uncle saminu har gidan Hajiya Inna sukaje ita da Matar Ya Abdallah first born din Abbie, tasu tazo Daya da Habiba itama 'yar adawar mahmud ce ta gaske sai dai ita ta iya takunta ba lallai ne lokaci Daya ka ganeta ba,haka suka dawo ba wani labari sai Kuma suka shiga kokonton gaskiyar maganar yarinyar da aka fada yazo da ita. Aishat na kwance Kiran Aunty Surayya ya shigo. "Wai kina Ina ne tun Dan hantsi nake gidan Nan sai yaran nake gani Amma ke ko duriyarki Babu". Yunkurawa tayi ta tashi zaune tana fadin. "Ina masaukina a kasa bana Jin Dadi ne shi yasa, Aunty Ina wuni". Dariya Ammi tayi saboda wayar a speaker take, tana ayyana kina min dacin Rai dai na tura muku Mata gida,Baku San nemar muku daraja nake yi ba duk wannan taruruwar murnar da ake zuwa ba domin Allah ake yinta ba saboda aga yarinyar da aka Kai musu labarin ta. " Lafiya kalau, kizo sama yanzu Ina bedroom din Ammi". Ta kashe wayar, saukowa Aishar tayi ta zura takalma ta fice tana hawan strains taji Kira ya shigo Mata tana dubawa Sameer ne. Ta daga da sallama suka gaisa sannna ya Dora da fadin. "Dake da waye zakuzo gidan oga na arkilla zaku duba wani Abu kuga Koda abinda za'a gyara". "Ok Bari na fadawa Aunty Surayya sai muzo tare". Ta fada tana tura handle din kofar bedroom din Ammin. A zaune ta samesu su Aunty Surayya nata faman rubutu a Cikin wata jotter. Da sallama a bakinta ta shiga ta gaishe dasu Ammin ta nemi guri ta zauna, Saida Aunty Surayya ta Gama rubutun ta dago tana kallon Aishat din. "Ungo duba kin gani Koda gyaran da za'ayi". Jotter ta karba ai Bata San lokacin da tayi super ta Haye jikin Ammin su ba. "Allah ya Kara sutura Ammi, ya jikan mahaifi yanda Kika faranta Mana Allah ya haskaka qabarin Alhaji Haroona ya yalwata Masa, mun gode Amminmu sai yanzu na samu kwanciyar hankali wallahi". Murmushi Ammin tayi. "Allahumma Amin, da kin dauki fushi Dani Dan Ina nemar muku daraja da kima kinsa yau har sama Hajiya Babba ta hauro saboda taga kwakwaf tunda nasan yayan ki Ibrahim ya fada Mata komai har dakun Nan ta shiga Wai sau Daya ta taba shigarsu Ina jinta dasu Batool Suma da Taya bera Bari har kciki suke shiga Kuma jikin ba kwari ta sauka da kyar fa take taka kafar Amma gulma ta hauro da ita saman Ina jiyo wash wash dinta tana sauka". "Allah ya kyauta ai ba Karamin Basu kafa mikayi ba Ammi sai yanzu na gane plan dinki na gaggawar ficewa da zahrar daga gidan Kinga kin kashe bakin tsanya babu batun mutum ya bugi kirji yace ya ganta da idanunsa, yanzu Sameer ya kirawo ni yace muje gidan bros na Arkilla muga wani Abu ko da abunda za'a gyara". "To Kuma da boutique dina zakuje a hado lefen da za'a Kai musu can nasan ba wani abun azo a gani akayi Mata ba duba da yanda abun ya faru kinsan halin kayanki Kuma". "To Bari mu Fara zuwa Arkillar in yaso sai mu wuce can din ko Aunty Surayya?". A gidan suka Sami mahmud da wasu abokansa biyu sai sameer. Suka gaishe da Aunty Surayya har tana zolayar mahmud. Sameer ne ya shiga ya bude musu inda kayan da suka zo dasu daga Dubai da Kuma akwatunan. "Auntyn mu gasu Nan ku duba idan da abinda babu ko za'a canza ko karawa sai a fada".. Ya ja musu kofar, kayan suka Fara dubawa ba karya komai yayi harda abinda ma ba'a sakawa an saka sunyi santin kayan kamar me Dan naira da taci gidansu a gurin ba Bata lokaci suka shiga zubawa a Cikin akwatunan abinda ya daukesu kusan awa hudu suna Abu Daya. Saida suka Gama komai sannan Aunty Surayya ta Kira Ammi video call lokacin Ammin tana gurin Hajiya Inna Dan ana shiga magariba ta fice ita da suhailat wadda ke driving dinsu suka nufi mabera gidan Hajiya Inna taje ta fada Mata komai ake ciki ta Kuma Bata hakurin yanke hukuncin da tayi ba tare da ta nemi Shawarar ta ba,nuna Mata Hajiyar tayi ba komai idan akace sai an tsaya ciccira maganar abin baze Zama sirrin ba hakan da tayi shine dai dai. To Kuma saiga Kiran WhatsApp tunda duk gidajensu da wifi suke amfani. Akwatunan Ammi ta Fara gani gasu Nan birjik sai da suka Kai karshe sannan Aunty Surayyar ta dago da wayar tana fadin . "Ammi kin gani? To Dana ya Gama aikinsa Kaiwa kadai ya rage ba'a bukatar komai Ina za'a kawo Kayan? Can ko kuma a barsu a nan kawai?". "Masha Allah, Kice kun hutar dani? Ki fada musu su kawosu gidan Hajiya kawai sai a fadawa Wanda ya kamata suzo su gani a Nan kawai". Sukayi sallama Hajiyar ke tambayar. "Me za'a kawo Mini Nan kuma?". A kunyace Ammi ta fada mata". "A'a kirawo su azo a kaini Arkillar na gani yaushe za'a wani kawo min Kaya da wani kiran jama'a su ringa dodon gani Abu guri yana neman kurewa ga Azumi Yana karatowa gara ayi a Mika Masa matarsa ai yayi rawar gani ma wallahi a 'ya 'yan zamani ba kowa ne zeyi abinda dan Albarkar Nan yayi ba, shi yasa yaki zuwa gidan kenan yayi min zaune a Nan yake min wasu maganganun a bai-bai". Ita dai Ammi Dan murmushi kawai takeyi. Daga Arkilla gidan Ammi su Sameer da Tajuddeen suka nufa da lefen har lokacin Su Habiba suna nan Wai suna neman Ammi suyi Mata sallama da momin kano Maman su Faruq wadda ta dawo da gefin magariba daga Dubai inda takeyo oder din Kaya, tana zuwa yaran ta suka fada Mata dawowar Ya mahmud din shine bayan tayi sallah ta shigo sai Kuma Bata Sami Ammin ba sun dauka ko tana part din Abbie ne. Suna zaune aka Fara shigowa da akwatuna ana ajewa Saida aka shigo dasu gaba daya Nan kallo ya koma sama suna mamakin daga Ina kuma wannan su Aunty surayya ne suk shigo daga karshe Nan suke fada musu lefen mahmud ne, Akayi caaaa kowa na fadar Albarkacin bakinssa aka Fara daddagawa, ana wannan rarumar Ammi ta wuce ciki. **** Saida su Aunty Badi'a sukayi salllolinsu Alawiyya da zilai wadda tayi suf ta baro sahura ta shigo, dazu Sarai ta gane zahra ta gwasale sahurar ne Dan kada tayi halin nata na kinibibi tunda Bata San menene dalilin zuwan ba ga Kuma Bakin fuska suna tare tana gani zata shiga gurin Mama ta Kai tsegumu Dan ma kwanan nan ta rasa me yake damun Mamar duk ta fada sai idanu gashi ta rage wannan izzar da wulakancin nan na ganin kowa a banza. Sai da suka Gama suka kimtsa wannan Ammah ta shiga suka gaisa sosai tayi musu sannu da zuwa. Aunty Badi'a ce ta Fara Kora bayanin dangantakarsu da Ammi sannan ta Dora da fadin dalilin zuwansu duk da Ammi ta yiwa Ammah a takaice. "Hajiya ga yarinyar mu Nan mun kawo ta badon mun Raina iyawarku ba a'a bisa wasu dalilai na abinda ya faru da yaron muke son azo a daukar Masa matarsa a Cikin mutuncinta da kimarta kamar ko wace yarinya budurwa da ake aurarwa a gaban iyayenta,kinsan ko wane family akwai tasu matsalar da fatan bamu Bata muku ba". "Kai haba wannan ai gyara kayanka ne kuma kun nuna Mana yanda kuke kaunar zahra da gaskiya mun gode sosai, ku huta kafin Abban nasu ya shigo ku gaisa". Har Ammah taje baking kofa ta dawo tana fadin. "Na shafa'a ga waya Hajiya zainab zata Kira tace min layinku baya shiga a nan kasar". "Wallahi kuwa haka ake fama idan Suma suka shiga sai dai su sayi sabon sim na can wallahi". Tunda zahra ta shige Bata ko leko waje ba, kwanciya tayi duk abun duniya ya taru yayi Mata yawa, ga Ammah ma bata ko leko ta ba tana ta bakinta shima meu amor shiru Bai nemeta ba haka Aunty Aishar itama shiru Sai taji Zuciyarta ta tsinke tasan shikenan sai yanda Hali yayi tunda har zuwa lokacin Bai kirata ba tasan Amminsa Bata sonta gashi harda mutane ta hadota a bawa iyayenta hakuri. Aunty zilai ce ta shigo taga zahra ta rabsa uban tagumi ko daga inda take Bata tashi ba, ga abincin da aka kawo mata ko taba shi batayi ba. Matsowa tayi tana fadin. "Haba uwar dakina tagumi ai ba naki bane, wane gata ne Ubangiji baiyi Miki ba ai ke sai hamdala ta kamace ki". Dago aexy eyes dinta tayi ta watsasu akan Aunty zilan tana fadin. "Kayya Aunty zilai idan ana cin baure ba'a tona cikinsa Kuma daudar gora ciki ka shata, gida fa Ammimsa tace a rakoni a bawa Ammah hakuri Kinga abinda ma ta bani da zamu taho tace min sai wata rana". Sai kukan da take rikewa ya kubce Mata. Hakuri Aunty zilan ta Riga bata, tana Cikin kukan ne wayarta ta dauki Kira harta tsinke Bata daga ba da gaske abin yayi Mata ciwo da tasan karshen abun haka ze Zama da Bata yarda tayi irin wannan sabon dashi ba. Wani Kiran ne ya shigo Aunty zilai ce ta dauka da sallama muryar yallaban taji duk sai ta daburce ta rasa abun fada, Cikin in Ina ta furta."yal..labai Ina wuni". "Lafiya". Ya amsa mata in short. "Ina zahrar take ne?". Da sauri tace "gata Nan yallabai bansan meye ya sameta ba sai kuka takeyi" "What! Kuka kuma?". "Wallahi kuwa yallabai nayi lallashin nayi lallashin taki ta saurareni". "Pls Bata wayar". Duk abinda suke zahra na jinsu ita fa wani Haushinsa takeji su baro wannan garin nasu Mai shegen nisa tun Dan hantsi Amma ya kasa kiranta sai da ya mula ya mule da tsohon Daren Nan ze wani kama kiranta tayi masa me. Kin karbar wayar tayi ai ba bakuwa bace Aunty zilan da zataji nauyi ta dauka ko Dan kunyarta. "Ta tashi ta fita yallabai Sai hakuri kasan da yarinta a Cikin Lamarin ta". "Ok shikenan" Wayar ya dangwarar a Kan bed side yana lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. "Haba uwar dakina yallabai baici irin wannan hukuncin ba, kiyi hakuri kome yayi Miki ki daga wayar kiji meye ze fada miki". Autane ya leko Yana fad'in. Aunty zilai kizo inji Ammah tana bedroom dinta". Ya juya ya fice daga dakin. ** S.K.T Saida kowa ya Gama iya nasa iya yin gurin ganin lefen Amma dai mutum ko shine hasidin Iza hasada Bai Isa ya mushe kayan Nan ba, Saima korafin sunyi yawa yarinya Kamar wata diyar sarki, ba dai Wanda ya tanka tsakanin Aishat da Aunty Surayya, ba'a daukesu daga parlourn ba sai da Abbie ya shigo shida uncle Mustapha sukaga kayan Aishat taso ta bude musu uncle ya Hana Yana fadin. "Haba Hasana sai kace Mata zamu zauna muna bude kayan sakawa muna kallo, Allah ya Sanya Albarka ya hada kawunansu ya kare fitina". "Allahumma Amin" Suka fada gaba daya, Aunty Surayya bata bar gidan ba Saida suka Gama duk abinda ya kamata suyi na shirye-shiyen Baki Dan Ammi taci alwashin sai ansan danta yayi Aure. Saida Aunty Surayya ta taya su Aishat shiga da kayan wani daki kusa da Wanda Mahmud ya kwana a ciki, Amma Dan Karamin kit din da sarkokin gold ke ciki dakin Ammi aka kaisu. Washe gari aka tashi da rabon IV na dinner da yini abinda ya girgiza duk wata yarinya data kwana ta wuni a family din dake kokarin cusa kansu gurin mahmud Kota halin Yaya ne. **** Su Aunty Badi'a basu samu gaisawa da Abbansu Zahra ba sai da safe, yaji dadin abinda Ammin tayi sosai yayi godiya. Bayan sun dawo sunyi break fast ne Ammah tazo musu da bayanin Abba ya sallami drivern tun dare sukayi sallama ana yin sallar Asuba ya dauki hanya yace Bauchi za'a kaiku kubi flight zuwa sokoton. Godiya suka yiwa Ammah kamar wasu kayan duniya aka Basu, sai da zasu tafi Mama ta shigo shima Abba ne ya turota su gaisa da bakin Ammah, Amma batayi niyya ba duk da sahura ta kaimata tsegumin bakin ita abinda ya dameta shine a gabanta Lamarin salma wadda da kyar aka Zubar da Cikin tamkar bazata rayu ba Dan ta Suma yafi sau goma da kyar aka samu ta farfado, jini kuwa an Kara Mata shi yafi Leda bakwai Dan Zuba yake tamkar lalataccen famfo. Ammah ce tayiwa su Aunty Badi'a bayanin wacece mama a gidan da kuma Matsayin su na iyayen mijin zahra. Har dakin da zahrar take Aunty Badi'ar taje ta samu zahrar tana karatun Alqur'ani mai girma. Tana Kai aya zahra ta rufe Qur'an din. Shigowa tayi tana kallon Zahra wadda ta saka rigar wani material da Aunty Fateeha ta bawa tele ya dinka Mata sai tayi wani mahaukacin kyau, gefen gadon Mummy badai'a ta zauna ta nuna mata kusa da ita, Bata zauna kusa da ita ba saita zauna a Kan carpet din dake kusa da kafarta. "Zamu tafi diyata me Zaki bamu mu kaiwa Dana kafin ki isko shi?". Sadda Kai zahra tayi,duk kunya ta rufeta. "Kina jina". Kai zahrar ta gyada Mata alamar eh. "Ki kwantar da hankalinki kada ki jewa yarona da rama, babu abinda ze rabaku in Sha Allah,mun kawo ki ne Dan Kara nema miki mutumci a idanun 'yan uwan mijinki idan aka wayi gari kawai suka ganki bazakiyi daraja da kima ba a idanunsu sai ayi muku wata fassara ta daban kinji, ki yiwa Amminku biyayya yana sonki sosai wallahi tun kafin ta ganki Allah ya nuna Mata ke a Cikin mafarkanta sau babu adadi tare da mahmud Kuma a zahiri ma Kuma ke dince dai ba wata ba, zata turo matanenta suzo har Cikin gidan Nan su daukeki su danka ki Amana a hannunta gadan dangin mahaifinsa da nata dangin, kuma duk jarabawar da tayi Miki a zaman kwana Daya daikayi da ita ba'a samu matsala ba haka muma a namu bangaren babu kuskuren da aka samu Sai ma abinda babu shi da muka samu Karin haske a cikinsa,Dan haka ki fadawa kawayenki na kusa zasu rakaki dakinki na dindidin duk sauran Wasa ne ai ya fada min yanda kukayi ta gantali kamar mararsa mafadi,Dan Allah kiyi Masa biyayya ki kula dashi jariri ne a gurin soyayya ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kece mace ta farko Daya taba so a tarihin rayuwarsa da bakinsa ya fada min wannan yace min ya fara sonki tun Yana dan shekarar farko a university lokacin ya Dan Fara business Sameer Yana raka shi, Bai dai bude min maganar ba to kinji dai da sonki ya rayu Dan haka ki Zama jaruma a dukkan al'amuransa kinji diyata". Kai ta gyada Mata alamar to. Bayan tafiyar bakin ne Ammah ta dawo Cikin a parlour Ammah ta Sami zahra tana fada Mata yanda ta yaba da halin surukarta ba kadan ba. Ba jimawa Hajiya Kaltum ta shigo suka kule da Ammah bed room din. Zahra ma Bata koma ciki ba zamanta tayi a parlourn ita kadai tana kallon girkin larabawa. Wurin Sha biyu da rabi Ya Abdul Hakeem ya shigo Yana fadin. Ina Zahrar tazo tayi bako". *AUREN HUCE HAUSHI* AISHAT ISAH MUSAH (Maman Fateemah) 09061432330 Or 08055362975 Page 79. ........... Maganar data sauka a kunnen Ammah kenan, wani kallo Ammar ta yiwa Abdul Hakeem na ina tunaninka yake da lissafinka yake. "Me naji kana fada tayi bako Kuma kamar yaya?". Dawo yayi daga fitar da yayi niyya. "Ammah bafa wani bane da ban Sameer ne abokin mijinta Ina ganin sako ne ze Bata fa, ya za'ayi nazo kiranta idan bansan waye ba tubda da aurenta shima ganin na hannun Daman mijinta ne Kuma ga bayanin da Kika yi min nasan da abinda ya kawo shi girinta". "Ah to yanzu naji magana, turo min magaji ya bude Masa falon baki. "Haba basai na turosa ba bani kawai na bude masa". Gurin dinning Ammah ta nufa ta dauko Masa keys din ta bashi ya fice, Alawiyya Ammah tasa ta Zuba abinci da drinks ta Kai Masa. Sai da Zahrar ta bashi a kalla minti talatin tasa dai zuwa lokacin ya Gama komai sannan ta leqa ta fadawa Ammah zataje gurinsa. Lokacin da tayi sallama ta shiga Sameer Yana tsaye da waya a kunne Yana fadin. "Dan Allah ka koyi hakuri Mana haba kamar a kanka aka Fara Aure duk ka tashi hankalina nace maka Ina Cikin gidan abincin tarba aka kawo min kafin ita madam din ta fito.....yauwa gata Nan ta fito". Ya fada Yana mikowa Zahra wayar wadda ke fadin. "Barka da sauka oga Sameer". "Yauwa sannu amarya, ungo mijinki ya hanani sakat Saida ya tasoni daga aikin daya sakani a garin nan Wai nazo na gani da abinda yake damunki". Dan murmusawa tayi. "Ni lafiya ta kalau kawai dai baya son ka huta ne, Ina baby na?". "Baby sun dauki hanyar sokoto acan zaku hadu, harda su Rukayya da mommy da mutuniyar ki ai Rukayya na fada Mata tayi tsallen albarka tace tafiya ta tashi". Ya fada yana nufar kofa. Wayar ta duba Yana Kan layin Yana jinsu. "Karawa tayi a kunne tana fadin. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". A zuciyarsa ya amsa sallamar Amma a zahiri sai yace Mata "Haba precious kunyi min adalci kenan? me yasa Zaki yarda a maida Mana hannun agogo baya, Wai Dan kada mutane suyi surutu sai a dauke min ke? Nifa nayi zaton koma menene a iya sokoto Nan ze tsayaKema na kiraki Dan na samu relief sai kik'i daga wayar sai ace min wai kuka kikeyi wato so kike na nuna musu raunina a kanki ko? Shiru tayi ita ta rasa mema zata ce Masa Umarnin mahaifiyarsa zata tsallake, da kunnanta fa taji Yana fadar Ammi ze bawa zabi ta zabar Masa Mata, to Kuma tace ta tashi tabi yan uwanta su tafi to musu zatayi Mata tace bazata ba ko Yaya?shi me yasa ya Bata zabin tayi abinda ya dace, ita Bata kullace shi ba sai ita zega laifin ta taho wato shi yayi biyayya ita kuma ta nuna ba haka ba ace kwadayin dukiyar su take yi kenan,duk da itama a Cikin wadatar ta tashi gaba da baya Amma ai ba kowa ne ya san hakan ba. "Kinyi shiru precious". "Me kake son na fada bayan biyayya na yiwa Ammi cewa fa tayi na tashi mu tafi kawai lokacin banma San inda zamu ba Saida mukazo Kano Naga mun dauki hanyar Azare na gane Ina zamu,ai Ina ganin kawai mu hakura mu yiwa Iyayen mu biyayya kaga Nima biyayyar nayi lokacin da aka bani Kai bansan Koda waye aka daura min aure ba,Amma na hakura nayi biyyyar iyaye kaima kayi biyyyar idan Ammi bani bace zabinta muyi hakuri haka Allah ya nufa zaman takaitaccene kabi abinda takeso bazaka tabe ba in Sha Allah". Cikin tashin hankali ya Fara magana. "Me kike fada haka preciousss? Kina son heart attack ya sameni? Waya fada Miki Ammi Bata Sonki? Soyayyar tasa ta raboki da gidanta badan Bata sonki ba Kinga yanda ta kasa zaune ta kasa tsaye duk fa kunyar Dan fari Ammi ta aje a gefe hidimarta takeyi babu Kama hannun yaro, Ina gama da sakon data bawa Sameer ya kawo Miki, na Ammah Ina Jin sai gobe za'a taho dashi, ki shirya dake za'a taho min fa a Mika min kayana daga cikin daki Nima naji abinda 'yan uwan sukeji na gaji da gararamba gara na tsuguna Nima na Fara hada nawa family din, in sha Allah da biyu Zaki Fara min ko 'yar gidana". Runtse idanu tayi ita fa idan yana ambatar irin wadannan kalaman na haihuwa tuno yanda sabgar take kafin samun abun haihuwar shine damuwar ta da gasken gaske tana hasaso ranar da alama Kuma an dauki hanyar zuwanta. "Dan Allah ya mahmud ka Bari ba kyau fa irin wannan maganar" "Kam bala'in waye yayan naki Allah ki iya bakinki babu hadin Zuma da guna,ki nemi yayanki tun dare be Miki ba,Ni ki barni a your love dinki kawai ko kin manta meu amor dinki ne...? Pls Dan fada min irin tanadin da aka yiwa meu amor a wannan special day din?". "Wayyo.... Dan Allah ka rufa min asiri.. ni wallahi wannan zancen yafi karfina pls Kan bariiii..? Ta fada da sigar data yamutsa Masa jam'iyya nan da nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa. "Ya salam! Previousss Anya Zan iya hakurin kwana uku nan gaskiya tahowa zanyi na daukeki mu wuce Dubai inda a tanadar Miki Dan amarcinki alkawarin nayi azumi uku kawai bazan iya ba" Ya fada Yana Mata wani irin numfashi a kunne, da sauri ta cire wayar daga kunnenta tana fadin "nashiga Tara me kuma nayi Masa? Da sauri ta mayar da wayar tana Masa magiyar ya rufa Mata asiri kada ya jawowa mahaifiyarsa abun fada Cikin kishiyoyi. Ba Karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin ya hakura, da gaske tuburewa yayi shi baya son bidi'a ansan tun yaushe suke tare da za'a wani tarki bikin babu gaira babu dalili, tana samu ya Dan sauka tayi Masa sallama tace Ammah tana kiranta anyi Baki,yasan neman guduwa takeyi kawai Bai barta ba saida ya jaddada Mata ze Kira da dare. Lokacin data fito Sameer baya kusa tasan suna tare da ya Abdul Hakeem part dinsu ta nufa Ya imam ta gani ta tambaye shi ko su Ya Abdul Hakeem suna nan? Tabbacin hakan ya Bata Kira shi a wayar ta tace tana jiran oga Sameer. Ba jimawa suka fito ya Mika Masa wayarsa, tana fadin . "Gashi nagode". Karba yayi yana fadin.. "Bari na dauko Miki sakon Ammi Wanda ta bayar a kawo Miki".. Wata Leda Yar madaidaiciya ya Miko Mata Yana fadin. "Gashi Aunty Aishat tace zakuyi waya". "Ok Nagode, bazaka shiga ku gaisa da Ammah ba?" Yar dariya yayi. "Na nawa kuma? Na shiga mun gaisa". Dan murmushi tayi ta nufi Cikin gida. Ba zato tayi arba da Aunty Hasana da gudu ta shige jikinta tana fadin. "Aunty kin manta Dani wallahi, laifin me nayi Dan Allah". "Kuji mun yarinya ! Sai Kuma nayi ta kiranki a waya har mijinki ya Raina ni ya daina Jin 'yar kunyar tawa da yakeji ai yawan damun kani ko d'a da Kira a waya bini-bini Yana kawo raini da rashin ganin kima a tsakani gara a ringa daukar lokaci yanda duk lokacin daka Kira ya Zama ana marmarinka ku rabu ana kewarka da Jin ba'a gaji da Hira da Kai ba". "Wannan maganar taki bisa hanya take, haka ake son Babba yaja girmansa". Hajiya kaltume ta fada. "Ah to Mamma fada Mata dai so take girma ya Fadi a gurin kanin nawa yanzu kuwa Aunty sama Aunty kasa duk bayan kwana biyu saiya kirani ya gaisheni". "Aunty Ina zuwa". Zahra ta fad'a tana nufar bedroom din data yiwa kanta masauki, Bata Jima ba ta fito da abinda Ammi ta Bata ta mikawa Aunty Hasana tana fadin. "Gasu Nan na manta dasu Ammi ce ta bani jiya da zamu taho". Bata zauna ba daki ta jiya tana rike da hannun Autar Aunty. Aunty Hasana ce ta cire rapping sheet din na madaidaicin, white gold din ne yayi musu maraba, da sauri Hajiya kaltume ta matso tana fadin. "Masha Allah girma sai Dan girma wani kayan sai amale wane jaki,lallai babban goro sai magogin karfe, irin wannan kyautar girma haka, 'yan biting bude sauran muga abinda ke ciki". Wata ubansun Alkyabba ce baka da ratsin zare golden sai turarika masu azabar kamshi a ciki. Jim maganar Hajiya kaltume yasa Ammah fitowa daga daki taga menene ake dagawa murya haka? Sarkar Hajiyar ta mikawa Ammah. "Duba kiga Karamar arziki irin wannan daga uwar mahmud, Ashe dasu tazo gidan ta aje ta shiga tata sabgar, inga fa sarkar Nan ta tasamma wajen fifty millions wallahi Dan kwanaki mun siyar da wata Bata Kai wannan ba wurin forty seven milion aka sayar". Ammah rasa abin fada tayi saboda abin ya Bata mamaki to su wane irin dukiya garesu mutanen nan?. Nan suka zauna suna ta maida yanda akayi har kusan la'asar duk abinda ya kamata sunyi yi an bada aikin kayan garar da za'a Kaiwa Zahra Dana Iyayen mijin duk wata al'ada da ake a sokoton Ammah ta tambaya an fada mata, da yammaci suna zaune Abba ya shigo Yana fadin. "Asma'u ku tanadi abun tarbar Baki gobe in sha Allah bakin sokoto na Nan tafe yanzu ba dadewa Kanin Alhaji Muhammad ya kirani yake fada min zasuzo naso na hanasu duba da nisan dake tsakanin Bauchi da sokoto Amma ya nuna min a'a idan ma yafi haka zasuzo godiya ce zasu zo tunda ba aure za'a sake daurawa ba inaga ko maza ne ko kuma Mata da maza ne ban sani ba dai sai ayi dai abinda ya kamata nace Abdul Hakeem suje da magaji a debo zabi sai a Kara Dana gidan idan yaso sai a kawo sabo Naman na gida. "To Allah ya kaimu, ya Kuma maganar furniture's din da za'a tafi dasu daga nan?". Sai goben insha Allah za'a had a da kayan da kikace za'a kawo daga Bauchi Sai a tafi dasu gaba daya ai inaga hakan yayi ko?" "Eh hakan yayi Allah ya saka da Alkhairi ya jikan mahaifa". Ameen su Hajiya da Aunty Hasana suka fada ciki ya shige Aunty Hasana ya tashi tabi bayansa. Aiki su Ammah suka Fara babu kama hannun yaro auta Ammah ta turo makota tace ya fada musu su shigo gobe za'a karbi Kaya Kuma ya fadawa mamansu mujiba idan Abbansu yana gidan ta tambaye should ta shigo zasuyi aiki. Hajiya kaltume Bata bar gidan ba sai kusan Tara na dare, taso a Kara yiwa Zahra gyara Amma Aunty Hasana tace a karba a tafar Mata dashi tunda Hasanarsa ta kaita gurin masu gyaran Amare a India a barta haka Nan tunda Abu ne a duhu ba'asan yanda abun yake ba". "Eh to kema da gaskiyar ki Naga 'yar tawa har yanzu zubin 'yan Mata gareta babu kamar cikakkiyar mace a tare da ita". Da haka suka rabu haka Nan taji Bata son a Kara Bata komai idan ba fruits ba gaskiya Bata son wannan tonon sililin duk da bata da tabbas na wani Abu be shiga tsakani ba duba da tun lokacin da akayi bikin to sai dai a yanda zilai ta fada Mata bayanin da likitar Nan tayi Mata Lamarin abun dubawa ne kwarai, ita fa tausayin Zahra takeji yanda taga anyi Mata wannan gyaran tasan sai yanda Hali yayi kawai Amma da Qura a gaba. Washe gari da sakkon aiki suka tashi Dan tun shida Maman mujiba ta shigo ita da Aina'u makociyar itama suna gaisawa sosai da Ammah din, duk bidirin da akeyi Mama Bata fito ba ko kuma tace me akeyi babu Daya,itama Ammah ta bawa banza ajiyarta. Karfe Tara Mai kyau su Inna maimuna sun shigo gidan a Bauchi suka kwana saboda sunyi dare bana Wasa ba dole suka hakura suka kwana a can. Wasu dunkuna ne aka kawo wanda Aunty Hasana ta bayar aka dinkawa Zahra express laces ne na manyan Mata Wanda suke ji da Kansu na manyan kudi ta saya saboda yau masu kawo Kayan walau maza ne ko Mata ya Zama dai babu raini duk da babu inda makusa take ta ko ina kawai dai idan kana da kyau ka Kara da wanka ne. Karfe sha biyu ta gota wasu lafta laftan motoci suka tsaya a kofar gidan Alhaji Jafar Mai yadi wa Bata lokaci Mai gadi ya bude musu tunda Alhaji ya fada Masa za'ayi Baki a gidan to Yana ganinsu yasan bakinne. Gate baba sani ya bude musu suka Sanya Mai cikn harabar gidan. A can Kuma Zahra ce tayi make up simple ta saka fitted gown na rigar lace sai ta fito da ainihin structure din jikinta yake. Su dai su Hajiya kaltume dasu Inna mainuna suna zaune Basu yi aune ba sukaga an Fara shigowa da Kaya, tun suna girgawa har suka zubawa sarautar Allah Saida aka zube set goma Sha biyu, sai kuma mata suka shigo bisa jagorancin magaji su kuma mazan suna gurin su Abba da jama'arsa. Sannu da zuwa aka Fara jera musu mutanen Cikin parlour din tare da Basu girin zama, Aina'u ce ta ware murya ta zankada guda uku a jere abinda ya fito da su zilai da sahura daga Ina suke zaune a gidan, Mama ma fitowa tayi da Dan sauri tana fadin. "Menene akeyi a gidan nan haka da uwar Rana ake ta rafsa guda. Part din Ammah ta nufa da sauri su zilai duna biye da ita a baya, turus tayi ganin Iyayen akwatuna a zube a parlourn,kasa daurewa tayi. "Wannan kayan fa na waye haka?" Inna Maimuna ce ta Bata Amsa "na Amarya Zahra ne kin san mijin nata ya koma gida shine iyayensa suma zasuyi nasu bikin". Taku biyu tayi sai ganin ta akayi a kasa ta fadi jikinta na wata irin karkawa Nan da Nan aka yo kanta da sauri Dan Bata taimakon gaggawa. ********************** ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** ************************* ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ************************** . , .