*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI 08066726866 Mai mashin ɗin da ya ɗauki Mimi bai direta Ko ina ba sai ƙofar gidan marigayi Sulaiman Dabo da taimakon kwatancen da ta yi masa. Ta sauka ta ciro kuɗin sa a cikin jakar dake hannunsa ta bashi ya karɓa yana ta mata godiya ganin ta ba shi har dubu ɗaya sannan ba ta tsaya yin mganar karɓan chanjin ba har ta kai jikin get ɗin gidan ta fara bugawa.   Megadi na zaune ya ji ana ta buga gida sai ya taso zai buɗe amman yana tambayan waye?. Cikin Shaƙewar murya Mimi ta amsa masa da ita ce Binta ce, da sauri ya buɗe karamar Kofar sakamakon akwai hasken ƙwai wuta a wajen sai ya samu sararin ganin fuskarta tar da ta yi wani ja ja alamun ta sha kuka sannan Idanuwanta sun yi jajir sun kuma tasa. "Binta? Ke ce tafe da daddaaren nan?   Ya faɗa cikin mamakin ganinta. Domin har bayan ya leƙa bai ga motar ta ba sannan bai ganta tare da kowa ba, halin da take ciki ne ya sa ba ta tsaya ma sauraran megadin ba ta wuce shi da Sauri zuwa Kofar da za ta sadata da falon Hajiya, shi kuma sai ya bi ta da kallo domin wannan zuwan dai daga yanayin Bintar ma za ka fahimci ba Lafiya lau sai ya fara tunanin ko dai wani abu ne ya samu Hajiya? Gabansa ya faɗi a sarari ya furta" In sha Allahu khairan."   Kofar falon a rufe ta ke sai da ta buga, Baaba Uwani ɗakin na falo ne amman ba ta ji bugun kofa ba, ta yi aikace aikace ta gaji daman tana da nauyin barci, Mimi har ta ga ji da buga Kofa ta dakata tana ƙokarin lalubo wayarta ta kira lambar Hajiya. Sai ta ji kamar ta shin magana daga cikin falon, Ashe Hajiya ce ba ta yi barci ba ta ji bugun Kofa Daga ɗakin ta  shi ne ta fito ta leƙa ta na kiran Sunan Baaba Uwani sai da ta tashi Sannan ta ce ta ta je ta buɗe Kofa ta ji kamar ana bugawa. "Buga ƙofa kuma Hajiya?   Baaba Uwani ta faɗa da sigan tambaya ta na kallon Hajiya. Lokaci ɗaya kuma tana duba agogon dake cikin ɗakin da ya zama nata tun farkon zuwanta gidan. Karfe 11:04pm dai dai na dare a lokacin. Hajiya na tsaye a kofar ɗakin ta ce" Fito ki Saurara ki ji, ni dai tabbas na ji ana buga Kofar falo." A tare suka ɗumgumo zuwa falo dai dai lokacin Mimi ta ƙara buga ƙofar sai Baaba Uwani ta kalli Hajiya itama sai ta kalleta gabansu a tare ya faɗi, Hajiya ta yi Saurin cewa" Ko dai Hamza ne? Allah yasa lafiya hanzarta ki buɗe Uwani."   Baaba Uwani jikinta na ɗan rawa ta ƙarisa wajen Kofar ba ta buɗe ba sai da ta fara da tambaya. "Waye?.." "Ni ce Baaba Uwani!" "Ke ce wa? "Bintu ce Baaba Uwani.."   Mimi ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙokarin maida kwallar da ta taso mata, Hajiya na bayanta ta ji muryan Mimi, Baaba Uwani ma sai daga baya ta gane muryanta jiki da zuciya na rawa ta buɗe kofar dai dai Hajiya ta kariso wajen tana faɗin'" Bintu kuma? da wannan daren? Maganarta ta tsaya ne lokacin da Mimi ta shigo falon.Duk iya kokarinta na kar ta yi kuka ganin Hajiya sai da kuka ya kwace mata kawai sai ta tafi ga Hajiya ta faɗa Jikinta ta fashe da kukan da take ta riƙewa mai karfi yana kuma fitar da sauti, kukan zafin zuciya ne, kukan abin da kake tunanin kana so ashe shi tunanin shi ba shi a kan ka, kukan takaici da baƙin ciki wanda ka yi ma soyayya gaskiya shi kuma a na shi bangaren ba haka ba ne. "Innalillahi wa'inna alaihirraju'un! Hajiya ƙarama lafiya kuwa?   Baaba Uwani ta faɗa cikin tafa hannayenta, Hajiya kuwa daman tuni take ta salatin ta a cikin ranta,  ammam Mimi ba ta san suna yi ba ta kamkame Hajiya tana ta kuka nan tsayen ta saki jakar hannunta da mayafin jikinta kayan barcin dake jikinta suka bayyana Sai baaba Uwani ne ta duka ta ɗauke mata sai faman salallami take yi. Ita kuma Hajiya sai ta riƙe Mimi cikin Kwantar da murya ta ce" Binta Allah ya sa lafiya? Ko wani abu ne ya samu mijin naki? Sai ta girgiza mata kai alamun a'a Hajiya ta ƙara tambayanta ko wani abu ne ya samu Merin? Nan ma ta ce a a. Gaban Hajiya na faɗuwa ta ce" To me ya faru kika biyo wannan daren ke kaɗai kina kuka? Ko wani abu ya faru tsakanin ki da mijin naki ne? Jin haka ya sa Mimi ta ƙara sakin kukanta lokaci ɗaya kuma ta rabu da jikin Hajiya ta kama hanyar ɗakinta tana Cigaba da kukanta kamar wacce a ka ce mata an yi mutuwa.   Hajiya da Baaba Uwani suka bita da kallo, Baaba Uwani ta yi wani iri tana duban Hajiya kafin ta ce" Hajiya me ya ke faruwa? Hajiya ta yi shuru kafin ta sauke numfashi Tana faɗin" Ban sani ba Uwani, amman mu ba ta lokaci ta samu natsuwa zuwa da safe mu ji, in taki mgana sai na nemi ita Merin naji abin da ya faru." Baaba Uwani ta ce a sanyaye" Hakane Hajiya, To Allah ya ijeshemu alheri." Hajiya ta amsa da Amin Amin amman Jikinta na ba ta wani abu ne gagarumi ya faru haka nan Binta ba za ta zauna tana wannan uban kukan ba.   Karɓan kayan hannun Baaba Uwani ta yi ta bi bayan Mimi ta ɗauka tana ɗakin ta sai ta isketa nan saman gadon ta ta dunƙule tana faman kuka. Hajiya ta shigo ɗakin ta maida Kofa ta rufe sannan saman kujera ƙwara ɗayan da ke cikin bedroom ɗin ta ijiye mayafin Mimi tare da jakarta sannan ta karisa bakin gadon ta zauna tana faman kallonta amman kamar ba ta san tana ɗakin ba kuka kawai take yi mai karfi kamar ranta zai fita. "Fatima.."   Hajiya ta kira sunanta cikin taushi. Amman Mimi ba ta amsa mata ba, kuka kawai take yi. Sai kawai Hajiya ta miƙe kan madubin da ke ɗakin ta isa ta ɗauko wayarta lokaci ɗaya tana faɗin" Tun da ƙin ƙi mgana ballantana nasan abin da ke faruwa bari na kira Meri, ƙila ita s ta faɗamin abin da ya fito dake daga gidan mijin ki, kika zo  nan kina ta min koke koke" Ba ta san lokacin da Mimi ta sauko daga kan gadon ba sai ganinta ta yi a gabanta lokaci ɗaya ta warce wayar hannunta. Cikin mamaki Hajiya ke kallonta kafin ta samu zarafin magana Mimi ta riƙo duka hannayenta ta jimƙe cikin nata pokaci ɗaya tana ƙokarin danne abin da ke ranta amman hawayenta ba su tsaya ba. "Hajiya in roƙe ki wata alfarma? Na san tun tasowa ta a gabanki kike yi min duk wani abin da nake so, to ina so ki yi min na yau ko da zai zama shine wani abu na ƙarshe da za ki yi min"   Mimi ta ƙarishe faɗa cikin kuka. Ganin haka yasa Hajiya ta jinjina kai sannan ta riƙo Mimin zuwa saman Kujera suka zauna sannan ta saka yatsun hannunta tana share mata hawaye lokaci ɗaya tana faɗin" To shike nan daina kukan hakanan kin ji ko?. Sai Mimi ta gyaɗa mata kai, amman kukan na sake fito mata. Kanta na ƙasa ta ƙara rike hannayen Hajiya tana faɗin"Hajiya ki yi min alfarman ba za ki takuraman sai na faɗa abin da ya faru ba,  kuma ba za ki takuramin sai na koma gidan Mansoor ba." Hajiya ta ƙura mata ido lokaci ɗaya kafin ta ce" Saboda mene? Sai kawai Mimi ta kwanta a jikin Hajiya tana faɗin" Na hakura da AURAN nan Hajiya ba zan iya ba. Wallahi  ba zan iya ba."    Take faɗa tana kuka, Hajiya ta yi shuru kafin tace" An taɓa cewa an haƙura da Bautar Ubangijine ba tare da wani dalili ba Binta ba? Ta faɗa lokaci ɗaya  tana dafa kafaɗan Mimin alamun lallashi,  Mimi kuma sai kawai ta kara saka ma Hajiya kuka cikin kukan tana faɗin" Hajiya ina da dalilaina amman ba zan iya faɗa miki ba, ki bar ni a baya ni dai na ce ina so  yanzu kuma na ce ba na so Hajiya domin Allah kar ki takuramin." "Ya sake ki ne da kike faɗin haka?   Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce"Bai sakeni ba, amman zai sake ni dolen sa Hajiya." Sai lamarin ya fara ba ma Hajiya tsoro amman ba ta sake mgana ba, ganin irin kukan da Mimi take yi yasa ba ta sake jan ta da wata mgana ba sai ta rumgumeta tana lallashinta cikin taushin murya take faɗin" Shike nan ya isa daina kuka ya isa Binta ya isa." Take faɗa tana bubbuga bayan ta, Mimi tun tana kuka har ta koma sauke numfashi cikin dashewar murya, Hajiya ta lallaɓata ta koma kan gado ta kwanta ta rufa mata bargo kanta ta shafa kafin ta ce" Ki daina kuka. Da safe sai mu tatttauna kin ji ko? Sai Mimi ta gyaɗa mata kai lokaci ɗaya tana jin yar salama tana da tabbacin cewa Hajiya za ta mara mata baya.   Dukkansu daga Mimi har Hajiya ba wanda ya samu cikakken barci, Mimi damuwa da bakinciki ne suka hana ta kwanciya, Ita kuma Hajiya tunani da kuma damuwa suka hana ta samun barci da wuri. Ta yanke shawaran da safe za ta kira Hamza domin ya zo ya ji abin da ke faruwa ita a tunanin ta matsala ce tsakanin Binta da mijinta kuma shi aure yana da tsari da doka domin ta ce ta hqƙura ba za a barta a zura mata ido ba ya zama dole a yi binciken abin da ke faruwa. ******   Yadda Hajiya da Mimi suka yi kwanan damuwa da rashin barci. Haka Inna Meri ta kwana salla tana kai ma Allah kukanta Hibba da Walida ma sun kusa raba dare ba su yi barci ba, gwara ma Walida ta samu barci daga baya amman Hibba ta kasa saboda duk farkawan da ta yi sai ta leko Inna a falo sai ta ganta tana sallah tausayin Inna Meri ya gama cika mata zuciya. Domin hannu ta ɗaga sama tana hawaye  lokaci ɗaya  take faɗin" Ya Allah ga bawan ka nan Mansoor ka fi ni sanin abin da ke cikin zuciyarsa Ubangiji ka saka mishi salama da yafiya a cikin ransa, ka saussauta masa wannan baƙar zuciya dake damunsa, ka ba shi zuciyar yafiya da afuwa, Ya Allah ni ba zan iya ba ka dafamin ka shiryamin rayuwar wannan yaron."   Tana yi tana kuka, Hibba sai dai kawai ta koma ta kwanta har tana sharan kwalla, a daran ta kira wayar Mu'azzam ba ta samu ba. Sai da asuba sannan ya kira ta akan mganar tafiyar ta, sai kuma Hibba ta sanar da shi wani labari mara daɗin ji. Cikin tashin hankali ya ce" Subhanallah! Yanzu ina ita Anty Mamin? Hibba ta ce" Ta tafi gidan Hajiya tun a daran Jiyan." Da sauri ya ce" Me ya sa kuka barta ta tafi? Inna kuma ba ta hana ta tafiya ba? Hibba cikin sanyin murya ta ce" Inna ba ta hana ta ba, ni ce na hanata tafiya amman ta rantse sai ta tafi." Mu'azzam ya dafe kansa daga can bangaren kafin ya ce" Yanzu ina shi Yaya Mansoor ɗin? Hibba ta ce" Wlh ban sani ba, tun jiyan ya fita ya bar gidan."   Mu'azzam ya saki huci kafin yac e" Kin gane bari na neme shi a waya, Ina Inna take ? Hibba ta ce"Inna na tsakar gida,.Duk ta damu jiya kwana ta yi ba ta yi barci ba gaskiya abin da ɗan uwanka ya yi bai kyauta ba kuma ina tsoron haƙƙin Mimi da Inna ya kama shi." Mu'azzam ya jinjina kai kafin ya ce"Bari na neme sa a waya." Daga haka ya katse wayar cikin tashin hankali ya fara neman lambar Mansoor din amman wayar ta na kashe ne. Gabaɗaya sai ya rasa mafita. Sai ya sake kiran wayar Hibba ya ce ta ba ma Inna wayar, lokacin da aka kai mata ta karɓa suka gaisa sama sama. "Inna na ji abin da ya faru yanzu Hibba ke faɗamin, Inna me ya sa ba ki hana ta tafiya ba? Da sai a zauna a sulhuta mganar a nan gida ba sai ta je da mganar gidan su ba."   Inna Meri ta yi mirmishin taakaici kafin ta ce"A a Mu'azzamu in na yi haka kamar na danne ma yarinyar nan haƙƙinta ne, gwara da ta tafi gidansu danginta su nema mata haƙƙinta, in na ce ta zauna ai ba zan iya taƙwasa Mansoor ba,  ya fi karfina, tun da kuma har ya furta baya sonta to ko ƴata ce iyakar abin da zan yi mata kenan." Duk yadda Mu'azzam ya so ya fahimtar da Inna amma ta dake kan magana ɗaya wallahi ba za ta saka baki ba, Mansoor sai ya saki Mimi ita kuma da ya saka ta jin kunya ba za ta yi masa baki ba, ta yafe masa amman wallahi tallahi ta cire hannun ta a kan rayuwarsa za ta kira can kwami ta sanar da su halin da ake ciki ta yi iya nata ba za ta iya ba su zo su saka hannu suma tunda ɗan sune.   Dole ta saka Mu'azzam ya ce ma Hibba ta zauna zai shigo garin jibi jumma'a domin ya ga halin da ake ciki, amman zai dai cigaba da neman layin Mansoor ɗin ya ga ko zai same shi. Jikinsa a sanyaye ya shirya ya tafi wajen aiki, amman yana tunanin me ya sa Yayan na shi ya aikata abin da ya aikata? Yana masa tsoron kar haƙƙin Mimi da  na Inna ya kama shi kamar yadda Hibba ta faɗa. Har ya je office ɗinsa wayar Mansoor tana kashe ne ya rasa kuma hanyar da zai same shi su yi mgana.   Gama wayar Inna da Mu'azzam ba daɗewa, Inna na kofar ɗakin ta, ƙokarin dama kunu take yi. Ta ji tashin hayaniya daga Bangaren Magajiya ta ji muryan Baba Sani da na Baba Danlami, amman mganar da ta ja hankalinta har ta dakata  da abin da take yi ta saurara shivne muryan Baba Ɗanjuma da ta ji cikin fushi yana faɗin" Ba ruwan ku a wannan mganar. Ɗaki dai nawa ne, kuma ni ba ma Mansoor ɗakin nan da Kaina na ce ya zauna da matarsa har sai shi da kanshi  ne ya gaji ya ce zai tashi. Saboda haka kai Sani da Ɗanlami baku da iko kan abin da yake mallakina tunda ina raye ban mutu ba." Tunda Inna  ta ji wannan kalaman jikinta ya fara rawa shike nan ta faru ta ƙare, abin da ta daɗe tana gudu sai da Baban Inna ya ja ai ya kyauta.   Cikin wannan halin ta dama kunun saura kaɗan ma ta saki tukunyar ruwan zafin a kafarta saboda damuwa. Tunda sai tashin maganganu take ji daga bangaren Magajiya, Ta dama koko kenan ta ɗora ruwan zafi sai ga Magajiya ta faɗo shashen Inna Merin cikin hargowa tana faɗin" Malama ki faɗa ma ɗanki ya tashi ya bar ma masu gida waje, tunda dai ko bayan Ɗanjuma ya faɗi ya mutu ba shi da gadon ko filoti a cikin gidan nan." Take faɗa tana kallon Inna Meri cikin reni, sannan ta rike kugunta alamun yau da bala'i ta shigo   Kallonta kawai Inna Meri ta yi amman ba ta yi mgana ba, Baba Danjuma ne ya shigo ya na kwalama ta kira cikin tsawa" Magajiya ba na ce ki bar mganar nan ba ne? Baba Sani da Baba Ɗanlami su ka shigo har suna haɗa baki wajen faɗin" Me ya sa za ta bar maganar? Ai gwara ta faɗa mata domin ta ji  yadda ta bar agolan ɗan ta ya kame a gidan nan gwara a sake fahimtar da ita ba shi da gadon ko taku a cikin gidan nan." Abun mamaki har da Saddiqun shima yana bayansu amman bai yi mgana ba, Inna Meri ta kai kununta ɗaki. Sannan ta sake fitowa hayaniyar har ya fito da Walida da Hibba. Baba Ɗanjuma ke nufar Inna Meri yana faɗin" Meri kar ki tankasu yi shigewarki ɗaki domin Allah." Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" A'a kyale su gaskiya su ke faɗa, nan ai ba gidan uban shi ba ne ni kaina ban ga dalilin zaman shi ba."   Ta faɗa lokaci ɗaya tana haɗiye wani abu da ya taso mata daga ƙasan zuciyarta. Baba Ɗanjuma ya kalleta cikin mamaki amman ya kasa mgana Baba Sani ya ce" Kwarai ashe kema kin san gaskiya. Na rasa me yaron nan yake so a duniyar nan, yana da gidan shi amman nan dai haƙƙin wasu marayun ne ya tsole masa ido." Saddiqu na daga baya ya ce"To ni in baya son gidan ne ya ba ni na zauna, in kuma ba haka ba ya tashi ya ba ma magada wajen su." Baba Ɗanlami ya ce"Ahto in ya na son zama a gidan gado sai a koma ƙauye a zauna a gidan tsoho ba" Hibba ta kalli Walida itama ta kalleta domin dai kalaman sun yi girma. Magajiya haka take ta masifa tana faɗan maganganu tana zagin Inna Meri a fakaice sannan kuma Baba Ɗanjuma ya kasa tsawarta masu daman ko a baya Magajiya ba ta jin mganarsa ballantana su Baba Sanin. Ana cikin haka sai ga Bintu ta shigo gidan ita da su yara har da Junior.   Ta iske an tasa uwarta gaba ana gaggaya mata mganganu. Daman kuma tun da asuba Walida ta saci wayar Inna ta tura mata saƙon abin da ya faru, shi ne tun safe ta zo gidan amman ta iske ana ta cin ma Inna mutumci har magajiya na faɗin tana takama ɗanta na da arziƙi zaman me ya ke a gidan da ba shi da gado? Ina kuɗin? Baba Sani ya ce ko akwai kuɗin zuciyarsa ta mutu mganganu dai marasa daɗi. Inna Meri ta kasa mgana Baba Danjuma kuma na daka musu tsawa amman ba wanda ya saurareshi Sai abin da suka manta ba su faɗa ba.   Idon su ya rufe ba wanda yasan Bintu ta zo gidan sai da ta kwaɓe hijabi ta ci ɗamara ta sha gaban Inna tana nuna Magajiya da yatsan hannunta lokaci ɗaya tana faɗin" Ya ishe ki fa magajiya kul ɗin ki, Innar mu ta fi karfin reni daga gareki, yayanmu ya fi karfin ku kirashi yana hango wani abu me zai hanga? Me kuke da shi? Miye a wamnan gidan ban da tsiya? Na rantse da zatin Allah ban ga wani abun arzikin dake gidan da Yayanmu zai nace sai ya zauna ba sai dai can wani ra'ayi na shi ,kuma  dukkan nan kunsan ya fi karfin zaman a wannan a kurkin ɗakin da kuke rigima a kan shi." Ta faɗa cikin bacin rai, Magajiya sai ta saki baki ta na kallon Bintu, haka ma su Baba Sani Baba Ɗanjuma kuma sai ya yi mirmishi a kallah dai yasan yanzu za su saurara.   Baba Sani ya nuna kansu yana faɗin" ke ke, wai mu kike kira matsiyata don uban ki? mu sa'annin ki ne? Magajiya ta saki shewa tana faɗin" Lalle, to in har ana da arzikin a tashi a bar ma masu gado gida ehe." Saddiqu ya harzuka ya faɗo tsakiyar wajen kamar zai kai ma Bintu duka Inna Meri ta tare gabanshi tana faɗin" Kul kar ka  sake ta taɓa ta, matar aure ce kuma sannan ƴaƴanta na kallon ka." Sai Baba ɗanlami ya fara Kumffar bakin ta na kare mata amman tana gani tana yi musu rashin kunya. Saddiqu kuma yana haƙilon sai ya yi kasa kasa da Bintu ita kuma ta na bayan Inna ta na faɗin Uban da ya fasa wlh in ya taɓa ta sai ya yi kwanan cell.   Inna Meri ta kalleta kamar ta make ta tana faɗin" Rufe min baki me ya sa baki da kunya ne? Bintu ta tura baki tana faɗin" Inna to ba ki ji abin da yake cewa ba ne, ni zai da ka? To wallahi kar ya fasa." Inna Meri ta ja Bintu ta turata cikin ɗaki har su Hibba ta ce su shige da yaran kar wacce ta sake fitowa, itama sai Baba Danjuma ya riketa ya na neman tura ta cikin ɗakin yana yi mata magiyan ta yi shuru lokacin fa har su gaje sun jiyo hayaniya sun shigo gidan.   Amman Inna ta kafe ta ce ita ba faɗa za ta yi ba mgana za ta faɗa musu sai ya sake ta. Kallonsu ta yi dukkansu kafin ta ce" Ku kwantar da hankulanku zaman Binta a gidan nan tun jiya ya ƙare, ga ɗaki nan ku yi yadda kuke so da shi.Ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halin shi ba, in da ace Baban Inna mai jin mgana ne wallahi da yau ba ta zo ba, amman ku yi hakuri ga ɗaki nan in kuma nan ma bai isa ba, ni ma kuna son na tashi na bar ma shi Saddiqun shashen ne gabaɗaya sai in ta shi, miye a ciki? Ai ba wani damuwa tunda gidan ubansa ne, ni kuma matar babanshi nake  kuma ya fini iko da gidan gabaɗaya"   Da sauri Baba Ɗanjuma ya ce" Ki fita ki bar musu shashen? To ban animce ba, ba ke ba ko Manaoor ba in da zai je." Inna Meri ta ce"Magana ai ta kare kuma, ga ɗaki nan zan kira Hajiya su zo su kwashe kayan su, abin duk bai kai na faɗa ba." Sai mamaki ya kamasu Baba Ɗanjuma cikin mamaki ya ce"Ban gane ba, ina ita Bintar? "Ta na gidan su tun jiya.? "Me ya faru? Inna ta kalle shi lokaci ɗaya kafin ta yi mirmishi tace" Ina ga sun rabu ne." Gabaɗaya su Baba Sani suka zaro ido, ita Inna Meri ɗaki ta shige da sassarfa Baba Ɗanjuma ya bi bayanta cikin mamaki. A ka bar su Magajiya a tsakar gida suna ta magana ƙasa ƙasa. Magajiya ko har dariyan mugunta ta saka da karfi ta ce"To daman ina wannan auran zai yi karfo? An gama karyan arziki ya auro wacce ta fi karfin shi, ai daman hausawa sun ce kwarya ta bi kwarya in ta hau akushi sai ta fashe fasss." Ita dai tunda an ba da ɗaki ta yi wucewarta shashenta tana waƙe waƙe  Ta bar su Baba Sani na mganganun su, Gaje ta bi bayanta Harira dai duk ba ta ji daɗin abin da ya Faru ba,.Haka suka fito suna ta dariyan cewa Daman ai tun farko ya kai kansa in da aka fi karfinsa , Saddiqu ma sai dariyan mugunta yake yi domin ya ce ya na jin haushin Mansoor ya yi ta nuna yafi kowa sa'an rayuwa.   A can ɗaki kuwa Baba Danjuma ya tsare Inna Meri sai da ta maida masa abin da duk ya faru a daran jiya. Cikin tashin hankali y ace"Innalillahi! Ban san duk haka ya faru ba, jiya na gaji sai na kwanta da wuri amman Meri me ya sa kika barta ta tafi? Inna Meri ta bar gaban Baba Ɗanjuma sai ta koma gaban tibin dake ɗakin tana neman Sigan da za ta saka ma Kuni lokaci ɗaya tana  faɗin"me ya sa kuke tunanin zan hana ta tafiya? Shi wanda ya ijiyeta da kanshi muna ji ya ce ta tafi ɗin zai fi, ni kuma a wa da zan ce kar ta tafi,? wallahi  na ɗauki Binta a matsayin ƴata kamar Bintu ko itace Bashir ya yi mata wannan wulaƙanci sai na dawo da ƴata gabana sannan na saka ya sake ta tunda ba a zaman aure dole ko domin alfarma."   Baba Ɗanjuma da ya fahimci ranta ya ɓaci sai ya ce"Yanzu Shi Baban Inna yana ina? Inna Meri ta yi masa banza ta duka tana saka ma kuninta siga,  sai ya shiga ƙwalama Walida kira sai ga ta fito ita da Bintu su yake tambaya Mansoor walida ta ce tun jiya da ya fita bai dawo ba sannan Yaya Mu'azzam ya ce yana ta kiransa bai same shi ba. Baba Danjuma ya fice yana faɗin bari ya neme shi ya gani ko zai same shi. Ya na fita Bintu ta ce" Yaya Mansoor bai  kyauta ba, ga shi yanzu saboda shi  an zo Anci mutumcin Inna" Nan suka zauna suna mai da yadda akayi Inna ba ta saka musu baki ba tana dai ta hidima da yara abin ta, Bintu ce ta kira Yaya Amina da Yaya Halima ta ce su zo gida su dai sun ce in Inna ba za ta saka baki ba su za su saka, in ta kama sai su je su ba ma Mimin hakuri da kansu, tunda Hibba nata kiran wayarta ba ta ɗauka ba,daga baya ma sai su ka ji wayar a kashe. ****** *MANSOOR.!* Tun a daran jiya da ya bar gidan ya isa camp ɗin su domin a tunanin shi anan zai samu natsuwa. Sai dai Ina! wannan natsuwar da ya ke fata ya kasa samun shi, gaɓadaya ji ya yi kamar ya na cikin nadama wata zuciyarsa tana faɗa masa abin da ya aikata ma Mimi bai kyauta ba? A ƙasan ran shi ya ke jin radaɗin maganganun da ya gaggayamata sannan a cikin kunnuwansa ya ke jin sautin kukan ta, me ya sa? me ya aikata? Menene laifin Mimi da ya riƙeta a cikin ransa? In har zai yi adalci da ita da shi duk suna matsayi ɗaya ne a lokacin.   Amman sai wata zuciyarsa ke faɗa masa abin da ya aikata shi ne dai dai domin duk abin da ya faru Babanta ne sila, kuma ya san duk barazana ce ba za ta iya tafiya ko ina ba saboda ta na son shi, bai taɓa tunanin da gaske Mimi za ta iya tafiya ba in da ace yasan za ta suɓuce masa da bai tafi ba da ya tsaya ya bata hakuri. Ko ya yi tunanin kamar ya tashi ya koma gidan ya ba ta hakuri amman sai zuciyarsa mara kyan ta hana shi, sai yake ganin kamar shi za ta ba ma hakuri domin shi aka fi Saɓamawa da wannan tunanin ya sa ya kasa dawowa amman barcinsa rabi da rabi ne gabaɗaya sai yake jin sa kamar wani mai laifi, yana ji kamar ba shi da gaskiya sannan yana jinsan kamar wanda ya ɗauki wani irin nauyi mai girma a saman kansa.   Uwa uba ga kallon da Inna ta yi masa a jiya nan yasan ba shi da bakin kare kan shi, sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba ya fara nadama sai wannan baƙar zuciyar tasa ta rinjayeshi ya ji kamar abin da ya aikata daidai ne, amman kwana ya yi da ya runtse ido sai ya ga Mimi ta na wannan kukan. Da asuba ya kashe wayarsa saboda wata  zuciyarsa na zuga shi akan ya ɗaga waya ya kira wayar Mimi ya ji lafiyanta ita kuma wacce baƙar zuciyar nasa na nuna masa shi ne akan dai dai. Saboda kar ta  rinjayesa ya kira ne ya sa ya kashe wayar gaɓadaya.   Ranar morning traning gare su sai dai ya wakilta Zinder ya tsaya da su, ya ce ba ya jin daɗi ɗakinsa dake cikin camp ya koma ya kwanta saman ƙaramin gadon yana faman tunani ya yi juyi ya fi sau goma amman Mimi ce a cikin ransa! Ko ya koma gidan ne ya ga halin da take ciki? Ko kuma ya kira ta a waya ne? Haka yake ta wannan tunanin sai ya ji kamar ya amince ya ta shi ya je ya ganta sai wata zuciyar ta ce"Me kake shirin aikatawa? Ai ba ka yi mata laifi ba duk abin daka faɗamata gaskiya ka faɗa." "A'a na na yi mata ƙarya, na yi mata karyan cewa ba na sonta ahalin duk duniya duk wata macen bayan uwata da ƴan'uwana su biyo bayan Mimi a zuciyarsa duk saboda ita ne ya koma haka saboda tsananin kishinta da yake yi ne ya sa a tsawon shekarun zuciyarsa ta kasa zama cikin salama a baya yana da tabbacin in da ace Mimi wani ta aura ba shi ba, to ko bai mutu ba sai ya Ta ggayara.   Duk yadda da ya so ya manta da abin da ya faru ya ƙasa, sai ya yi tunani ya bari ta huce, amman a ransa yata ta addu'an Allah ya sa ta daina kuka, sai kuma gefen zuciyarsa ta faɗa masa Inna za ta lallasheta sannan ga Walida ga matar Mu'azzam ya tabbata ba za su barta ta yi ta kuka ba. Ya yi tunanin ko ya Kira Mu'azzam ne saboda halin da yake ciki a karon farko yana son ya tattauna da wani na kusa da shi Amman sai ya ji ba zai iya yin wannan maganar da Mu'azzam ba, har gobe ƙaninsa ne kuma shi a ƙarami na ƙasa da shi yake kallon sa. Duk wanda tunaninsa ya kawo masa sai ya ga ba haka ba ne. Daga karshe sai ya yi tunanin kiran Ahmad sai kuma ya fasa tuna ya yi nisa, kuma shi ba shi da wasu abokai bayan su, ko zamanin da ya yi karatu ban da gaisuwan nutumci har ya gama bai yarda ya yi aboki ba rayuwarsa kawai yake yi a bangaren kwallo ma sai da yaran dake ƙasan shi da Caach ɗin dake saman shi suma maganar aiki ce kawai a tsakaninsu ba shi da wani sakewa da nutane kuma a wannan halin yana son ya yi mgana da na kusa da shi wanda ya san shi sosai domin yana bukatar ya amsa masa wasu yan tambayoyi.   Ya yi tunanin Makama sai ya ga bai san gidan shi ba sai dai gidan Nasir shima tunda da daɗewa lokacin ana ginin gidan suka je gidan  yanzu ma baya tunanin zai  iya gane gida. Duk da ya san iskancin Nasir amman a yanzu ba shi da mafita tunda yana bukatar shi. Jaket ɗin sa ya ɗauka da wayarsa sannan ya ɗora saman riga da wandon jikinsa ya dora P. cap a saman kansa, ya dauki key ɗin motarsa ya fice yana fita can haraban Studio din su ya nufa in da suke traning suna ganin shi suka bar abinda suke  yi s ka taso zuwa gaban shi suna kiran sunan shi da "Captain" Cewa kawai ya yi su kula da kansu sannan in caach ya zo su faɗa masa ya ɗan fita amman ba zai daɗe ba. Yana ma tunanin za su ba su hutun sati biyu su je gida tun da ƙarshen shekara ba su yi hutu ba saboda wasannin da suka yi ta bugawa.   Bai yi tunanin zai ga ne gidan Nasir ba sai ga shi ya gane, a kofar gidan ya tsaya sannan ya kunna wayarsa ya lalubo lambar Nasir da ba zai iya tuna ranar karshe da ya kira shi da kansa ba ma ya doka masa kira. Nasir na tare da matarsa Nafisa da ƴaƴansu suna karyawa wayarsa na gefen nafisa ta fara kukan ana kira sai ya ce ta ɗauko masa wayar lokaci ɗaya yana faɗin" Waye ne hala? Ta kalli Screen din wayar lokaci ɗaya tana faɗin" Wai AJI..'" Nasir ya dakata da cin buredin dake hannunsa lokaci ɗaya yana maimaita sunan. "Aji.." Da sauri ya karɓi wayar lokaci ɗaya yana miƙewa. Shafa wayar ya yi ya ɗaga kiran ya na mai karawa a kunnensa bakinsa da alamun cikar buredin da ya tusa. "Nasir kana gida ne? "Eh ina gida,."   Nasir ya fada lokaci ɗaya bakinsa cike da abu, sai da ya ɗauki kofi ya kurbi tea ya wuce da shi dai dai lokacin da Aji ya ce" To ina kofar gidan ka." Nasir ya zaro ido kafin ya ce"Kai ɗin? wani gidan? Ka yi ɓatan kai ne? "Mallam ina jiran ka, kar  ka ɓatamin lokaci."   Daga haka ya katse wayarsa, Nasir na jin haka bai koma kan datarsa dake faman tambayan shi ina zai je, bai juyo ba ya ce nan waje zai fita yanzu zai dawo. Da sauri ya zura takalmi ya fita sai kofar guda mamakinsa ya kare da ya hangi motar Aji a fake sai ya riƙe baki a ranshi yana mai ɗimbin mamakin ganin Aji a fofar gidansa yau. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3002* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI 08066726866. Mamaki ya hana Nasir ƙarisawa kusa da motar Aji,  ya yi tsaye kawai yana kallon motar cikin tsananin mamakin ganin Aji  wai a ƙofar gidan shi yau. Shi kuma Aji yana daga cikin motarsa abin duniya duk ya dame shi, tagumi ya yi fa abin da ya daɗe bai yi sai ga shi yau ya jinginar da kansa a jikin Kujeren da yake zaune ta bangaren direba amman fa ya zabga uban tagumi kallo ɗaya za ka yi masa kasan ya na cikin damuwa. Bai ma san fitowar Nasir ba sai da ya sauke Ajiyar Zuciya ya waiwaya yana kallon kofar gidan Nasir ɗin sannan ne ya hango shi a tsaye ya harɗe hannayensa a kirjinsa yana bin motar na shi da kallo.   Ƙaramin tsaki Mansoor ya ja, sannan ya danna ma Nasir hon har sau uku sannan ya ga ya fara takowa zuwa wajen sa, yana zuwa ya buɗe masa bangaren mai zaman banza lokaci ɗaya ya na faɗin" Ka shigo ciki." Nasir ya leƙo yana faɗin" Na ɗauka za ka shiga cikin gida ne? Aji ya yamutsa fuska cikin yar damuwa kafin ya ce" Cikin Ina? Malam ka shigo mgana na zo mu yi, me kuma zai kai ni shiga gidan matan aure ina magidanci? Dariya ta kama Nasir domin a yadda Aji ya saka kalmar magidancin har yana wani gyara zama. Shiga motar ya yi ya zauna lokaci ɗaya yana rufewa, Aji yake kallo wanda ya yi shuru kawai hannunsa guda ɗaya ya tare bakin sa. "Ran Ajin Jihata ya daɗe wani abu ne ya faru?   Ya faɗa lokaci ɗaya yana nazarin Ajin domin zai iya cewa ya daɗe bai gansa cikin yanayin sanyin jiki irin na yau ba. Shi ya sa yake ta kallonsa Aji kuma ya rasa ta ina zai fara sai faman sakin huci yake yi shi kaɗai. Nasir ya gaji da zaman jiran shi sai kawai ya ce" Ni fa kaga zan koma cikin gida, karyawa nake yi da iyalai na lokacin da ka kirana ko wanka ban yi ba." Hararansa Aji ya yi kafin kai tsaye ya ce" Nasir ina fatan ba gorin Iyalai kake yi min ba ko? Nasir ya yi wata yar dariya kafin ya ce" Nayi maka gori mana. Domin har yanzu ba mu ji Mimi ta fara tafiyar nauyi ba, in kana so ka fara amsa sunan mai iyali sai ka fara yara Ƴaƴa daga ɗaya zuwa biyu amman yanzu dai kana matsayin magidanci Mata kawai." Aji ya yi shuru ya na kallon Nasir na yi masa dariya numfaahi ya shaƙa sannan ya fesar. "Nasir tambayan ka na zo na yi! In fatan za ka faɗa min gaskiya" Yadda ya faɗi mganar ne ya sa Nasir ya san ba wasa a maganarsa, tun ballantana ma shi Aji ba mai yawan wasa ba ne duk maganar da ya faɗa ya na kan gaskiyarsa ne. Sai shima ya gyara zama lokaci ɗaya yana faɗin" In sha Allahu zan faɗa maka iya gaskyan abin da na sani" "Game da kaina ne Nasir, ina son na san wani abu a game da abin da nake yi ne." Nasir ya kalle shi cikin mamaki kafin ya ce"Topha! Kamar na me kenan? Aji na shirin mgana wayarsa ta fara kiɗan alamun ana kiransa ya na ɗaukowa ya fuba sai yaga Mu'azzam ne, Sai bai ɗauka ba sannan bai katse kiran ba sai da ta katse ta katse kenan ya na shirin kashe wayar gabaɗaya Saboda ba ya so wani abu ya katse shi in ya fara sauraran Nasir. Sai dai bai kai ga kashe wayar ba sai ga wani kiran amman wannan karon daga Baba Ɗanjuma ne.   Shima bai ɗauka ba, sai da ta katse sannan ya yi saurin kashe wayar ya buɗe cikin ɗan bankin motar ya jefeta, Nasir na kallonsa ya ce" Ka ɗaga kiran mana, in ya zo mai muhimmanci ne fa? Aji ya ce"Kada ka damu, yanzu dai mu yi mganar da ta kawo ni." "Ina jin ka" Nasir ya faɗa ya kosa ya ji abinda Aji ke son sani kuma game da kansa shine har sai da ya zo wajensa. "Ina so ka faɗamin shin ina aikata wasu abubuwa ba dai dai ba ne? As in ina da wasu mugayen hallayan da ba'a jin daɗin zama da ni?  Sannan ina da hali mai kyau ko ba ni da shi? Kana ɗaya  daga cikin waɗanda suka sanni tun ba yau ina da tabbacin za ka iya sanin wasu abubuwan a kaina."   Ya faɗa ya na huro iskar bakin shi, Nasir ya yi kasaƙe kawai yana kallon Aji har sai da yaji shuru shima ya Juya ya na kallonsa kafin ya haɗe rai yana faɗin" Ba kallo na na ce ka yi ba  amsa za ka bani." Nasir ya sauke numfashi kafin ya gyara zama yana faɗin" Na ɗauka duk waɗanan tambayoyin naka za ka fini sanin amsar su." "Inda na sani zan zo har nan in tambaye ka? Aji ya faɗa cikin jin haushi. Nasir na danne dariyan shi ya ɗaga hannu yana faɗin" Shike nan mai da euƙar  kai ka girma ammman ba ka daina gitina ba." "Da gaske kenan ni fitinanne?   Ya faɗa ya na kallon Nasir wanda ya yi jim kafin ya ce" E,wannan ai jalittarka ce tun a baya, ka manta in dai mu ka zauna waje ɗaya kafin mu rabu sai mun yi faɗa kamar Sau uku ko sau huɗu, Ko da yaushe Makama da Ahmad na cikin raba tsakanin mu, kai fitina ni kuma rashin jaƙuri." Ya karishe faɗa yana yar dariya Aji kuma kansa ya kauda bai ce komai ba sai Nasir ya Cigaba da faɗin.   "Mansoor mutum ne mai kirki da sanin ya kamata, sannan kana da kyakyawan mu'amala da mutane a baya. Sai dai tun bayan abin da ya fru tsakanin ka da mahaifin Mimi ka sauya Aji. Rayuwarka ta yi Juyin waina daga sama zuwa ƙasa."   Aji ya juyo ya na kallonsa kafin ya ce" Daga sama zuwa ƙasa? Kamar ya? Ban gane ba." Ya faɗa cikim sigar tambaya sai kawai Nasir ya dafa kafaɗansa lokaci ɗaya yana faɗin" Yes ka sauya tun faruwar abin da ya faru a Lokacin, ka guji kowa naka ciki har da mu, ka yanke alaqa da kowa ka koma kana wata irin rayuwar kaɗaici wanda ya ba ma sheɗan Ddman kara hura wutar gushi da zafn zuciya a cikin ranka. Ka koma mai wata irin zuciya mara yafiya da afuwa,  ka koma abu kaɗan in aka yi maka sai ranka ya ɓaci, Sannan sai ka riƙa gayyato mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ka riƙa saka su cikin Fushin ka, mu ina Laifin mu a cikin abin da ya faru? Ko laifin waɗanda ka haɗa kana Jin haushi? Ita kanta Mimi ba ta da laifi har ga Allah Mahaifinta ne kuma ya rasu  Aji me ya sa ba za ka bar zuciyarka ta huta ba? Sai ka riƙa fushi da wanda ta shi rayuwar ma ta ƙare tuntuni, Allah ma fa muna yi masa Laifi ya yafe mana duk girmansa. To kai me ya sa ba za ka kasance mai afuwa da yafiya ba? Duk abubuwan nan da suka faru rashin Afuwarka ne da maida komai ba komai ba ne da a ce ka kasance mai barin abin da ya faru a matsayin kaddara da ka kasance mai sanyin zuciya da kyakyawan daɓia a cikin mu."   Ya karishe faɗa yana mai kallon Aji ido a cikin Ido kuma ya ga maganganunsa sun shige sa sosai, domin shuru ya yi na wani lokaci kafin ya fesar da numfashi ya ce" Yanzu kana ganin ni da a ka saɓawa in na nuna an ɓatamin sai ya zama Laifi? Nasir ya girgiza kai kafin ya ce"In ka nuna an yi maka ba dai dai ba, ba ka yi laifi ba amman riƙon nan ba shi da wani amfani Aji, mutumin nan daga baya ya yi nadama ya aiko har gida a ka zo a ka baka hakuri Saboda su wanke laifin su, suka ɗauki Mimi suka aura ma a bisa tsarin ka shin ko zaman da yarinyar ta yi da kai duk da ka yake mata wasu haƙoƙinta ba ta chanchanci saboda ita ka manta abin da ya faru ka Fuskanci gaba ba? Aji ya yi shuru domin ya san gaskiya Nasir yake faɗa masa sai ya kasa mgana domin nadaman abin da ya aikane ya zo ya ƙara lulluɓe sa.   Nasir na ganin haka ya cigaba da faɗin" Don Allah ka manta baya mansoor ka bar zuciyarka ta samu salama, ka ɗauka a ranka da duk abin da ya faru Ubangiji ne ya shirya sannan ka rika tuna lokaci, a can baya Allah ya rubuta a wancan lokaci ba za ka auri Mimi ba shi ya sa abin da ya faru ya faru a baya, sannan a lokacin da ka aureta a lokacin ne Ubangiji ya ce Kum fa yakun Mansoor shi ya sa kagl ga alokacin ka aureta, abin da kake nunawa dai dai yake da ka na ja da ƙaddaran Ubangiji akan rayuwarka Mansoor."   Kansa ya jinjina kafin ya ce" Haka ma Mimi ta ce min jiya, wai ina ja da kaddaran Allah a kan rayuwata." Nasir yace"Yes! Is Truth, duk abin da ta faɗa maka gaskiya ne, gwara ka buɗe zuciyarka." Aji ya yi shuru kafin ya sauke numfaahi lokaci ɗaya yana faɗin" Na ji, to yanzu in ina so na manta abin da ya faru ya zan yi? Ko ina so na manta sai na kasa saboda zuciyata ce ta kasa manta abin da ya faru a baya." "Sheɗan ne ke rinjayar ka, amman ka fara Koyon yaƙi da abin da ke cikin zuciyarka ka yi yakinin cewa na yafe ma duk wanda ya taɓa cutata, sannan sai ka fara kokarin manta baya ko da zuciyar taka tana dawo da kai acan baya sai ka yi saurin neman tsarin Ubangiji ina mai tabbatar maka cikin lokaci za ka manta komai sannan zuciyarka za ta samu salama da amincin da ta jima ba ta samu ba." Nasir ya gama faɗa hannunsa saman Kafaɗan Aji, wanda ya runtse ido lokaci ɗaya sannan ya buɗe yana faɗin" Shike nan zan yi kokarin na gwada haka." Nasir ya gyaɗa kai kafin ya ce"Allah ya sa, sannan don Allah ka rage kafiya da zafin zuciya, kuma ka daina jin cewa a cikin ranka sai abin da ka ga dama za ka yi, ka yi tunani da kanka ka gani ka girma yanzu  kana bukatar natauwa waje ɗaya da kyakyawan zamantakewa a wajen matarka." Kansa na ƙasa ya fitar da Iska ta bakinshi kafin ya ce" Na ɓata komai Nasir, jiya nan na gaggaya Mimi mganganu ni har Babanta ina ji na kira da azzalumi."   Nasir ya zaro ido lokaci ɗaya yana faɗin" Innalillahi, Aji garin ya ya ka yi wannan ɗanyen aikin?. Mansoor ya saka hannu ya shafo kansa sannan ya fara faɗa ma Nasir abin da ya Ffru tun na kan tafiyarta Abuja zuwa jiya daga karshe yac e" Inna ma ta ji komai Nasir kuma kasan halinta, Ni banjin Mimi saboda nasan ta na sona za ta gama fushinta ta hakura, kuma ni tun jiya na yi nadaman maganganun da na faɗamata,  Inna nake ji za ta ɗauki fushi da ni, ka gani ma Mu'azzam na ta kirana shi da Baba kuma nasan kan mganar ne." Nasir ya kalli Aji cikin matsanancin takaici kafin yac e" To da gaske ashe baka son Mimi? Ka daina sonta ne daga baya ko daman can tun farko ba  son ta kake yi ba? Wani sakaran kallo Aji ya yi masa kafin ya ce" Wannan wani irin tambaya ne Nasir? Kasam Mimi ita ce rayuwata."   "Ba ita ba ce rayuwarka, domin da ita ce rayuwarka da ba ka ci zarafinta tare da na iyayenta ba sannan da ba ka baro ta tana kuka ka yi tafiyarka ko a jikin ka ba Aji."   Nasir ya faɗa cikin ɓacin rai, Aji ya dafe kansa kafin ya ce"Oh! Na ce maka na yi nadama, kuma kar ka damu da ita tana sona ba za ta iya dogon Fushi da ni ba? "Haka kake gani ko?  yanzu kana da tabbacin ba ta tafin kamar yadda ta bukata ka amsa mata ba? Cikin ƙwarin gwiwa ya ce"Yes! Ina za ta je? Na faɗa maka ba za ta iya tafiya ba, ni ne rayuwarta kamar yadda nima take matsayin rayuwata" Sai da Nasir ya yi yar dariya a cikin ransa ya na fatan Mimi ta yi tafiyar ta domin har yanzu Aji bai yi laushi ba akwai jin kai a tare da shi.   Aji roƙansa ya yi akan ya zo ya raka shi gida ya t ba ma Inna hakuri, karo na farko da Mansoor yake jin tsoron haɗuwa da Inna, Sai Nasir ya ce bari ya shiga ya yi wanka wani harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Dilla mallam mu tafi, nima ai ba wanka na tsaya na yi ba." Nasir yace"Shike nan ba zan shiga na sallami Iyalai na ba? Kafin Nasir ya rufe baki sai gani ya yi kawai Aji ya ja mota sun bar ƙofar gidan sai Nasir kawai ya saki baki yana kallonsa shi kuma sai kawai ya ɗauke kansa har ya na wani ɗaga wuya lokaci ɗaya da tattare naman goshin sa.   Lokacin da suka isa gidan a kofar gida su ka haɗu da Baba Sani da Baba Ɗanlami suna ta kuskus sun haɗa kai, suna ganin Mansoor jikinsu na rawa suka tare shi,Irin gaisuwarshi ya yi musu, Nasir ne ya yi musu irin gaisuwar da suke so. Yana ƙokarin ya wuce cikin gidan amman Baba Sani ya tare shi da faɗin" A she kuma abin da ya faru kenan, To Allah ya kyauta na gaba kune yaran zamani in an gaya muku gaskiya sai kuka ga kamar ana muku bakin ciki ne, yanzu ina amfanin abin da ya faru? Baba Ɗanlami ya karɓe da faɗin" Ba amfani fa, shi ya sa a kace kowa ya tsaya matsayinsa, ina kai ina auran ƴar masu kuɗi? Da cikin yaranmu ka nema ai da ba'a ji kan ku ba, ina riba ace aure ko shekara bai yi ba ya ƙare, abun dai ba daɗi." Mansoor ya yi kasaƙe kawai yana kallonsu Nasir ma su yake kallo sannan ya koma ya na kallon Aji cikin mamaki. Domin shima yana so ya fahinmci mganarsu ne.   "Na ce ba, saki nawa ne ka yi mata? In ba uku ba ne sai a shiga a gyara lamarin saboda ko bakomai mu cece darajan wannan gidan kar a fara kirga ma ƴaƴan mu auri saki."   Hankalin Aji sai ya fara tashi da sauri ya ce"Saki?  wa aka saka kuma? Ya faɗa yana kallon fuskokinsu, Baba Ɗanlami da Baba Sani suka kalli juna kafin Su haɗa baki wajen faɗin" Toh ba ka son a sani ne? To ai Meri ce da safenan ta ce ka rabu da matarka tana ma gidansu tun jiya." Aji ya zaro ido lokaci ɗaya yana jin wani abu kamar zafi zafi na ratsa sassan jikinsa cikin mamaki ya ce"Mun rabu? tana gidansu? Sai kawai ya juya ya shiga gidan da sauri kamar zai kifa Nasir ya bi bayan shi. Domin in ya fahimta Mimi dai tun a jiya nan ta koma gidansu.   A tsakar gida suka ci karo da Magajiya tana Aikinta tana wake waƙenta cikin gara'a, abin da ya ba ta mamaki ganin yadda Mansoor ya wuce kamar zai ta shi sama, Duk da ba kasafai take amsa irin gaisuwar sa ba, ta san bai taɓa shigowa gidan nan ya ganta zaune bai mata irin ta shi gaisuwan ba ko da ba za ta amsa ba, amman sai ta ga yau ya wuce fuu kamar Iska sai Nasir ne ya bari da gaisheta ta amsa a ranta tana tunanin me ke faruwa? Wata zuciyar ta ce"Me ko ya faru, abin da ya faru da safe ne uwar ta kira duka ƴaƴanta ta sanar da su, sun zo sun cika gida, yau ko sai dai a yi fito na fito." Tuna haka yasa ta ja tsaki kawai ta cigaba da aikinta.   Ɗakin Inna cike da ƴayanta da jikokinta suna ta faman maida yadda aka yi tun bayan zuwan su Yaya Amiman, Inna Meri alwala ta yi ta koma cikin ɗakinta kawai ta zauna ta rasa mafita. Domin ta gama yarda Baban Inna baya son  farincikinta sannan Babban Burinsa ya ga ya ɓata mata rai ya saka ta a cikin wani hali, ina amfani wannan jin kunyar da ya jawo mata, kamar daga sama ta ji muryaansa a cikin falonta cikin kaushi yana faɗin" Ina Mimin take? Sai falon ya yi tsit, kowa na kallon kowa ciki  mamakin ganinsa ba su Bintu ba hatta su Yaya Amina sun kasa mgana domin suna ganin yanayinsa a fusace yake.   Kawai sai ya fita har yana bangaje Nasir ɗakinta yana buɗe ne sai dai an sakaya ne shiga cikin ɗakin ya yi yana kiran sunanta amman shuru shi ne har bedroom ɗinta har toilet ya leƙa ba kowa ya duba kayanta na cikin wardrope ya ga ba'a taɓa komai ba. Sai hankalinsa ya ɗan kwanta da sauri ya fito daga ɗakin ya sake dawowa ɗakin Inna sai ya iske Nasir na durkushe suna gaisawa da Inna. "Inna me ya sa kika bari Mimi ta tafi?   Ji wata tambayar renin wayau haka Hibba da Bintu suka ce acikin ransu, Inna kuma baƙin ciki ya sa ta kasa mgana kawai miƙewa ta yi ta shige ciki ta bar shi nan tsaye jiki a sanyaye, Yaya Amina ce ta yi gyaran murya kafin ta ce"Tun jiya Mimi ta tafi gida nima ina faɗan me ya sa suka barta ta tafi? Shi ne suka ce min Inna ta ce tafi,sannan sun yi sun yi su hana ta tafiya ta ce sai ta tafi." "Is ok! duk in da ta je ma ai za ta dawo, Nasir ta shi mu je."   Haka kawai ya faɗa cikin bacin rai sannan ya bar ɗakin sai ma ya fice daga gidan gabaɗaya. Nasir mamaki ya kama shi Aji yaushe zai yi laushi ne ya gane Annabi ya faƙu? A mota ya same shi yana cika yana batsewa sai da ya shiga motar ya rufe kawai sai ya ga Aji ya ja motarsa sun bar kofar gidan. Cikin mamaki ya juya yana kallonsa kafin ya ce" Ya haka?  mu da muka zo ban haƙuri? Kamar ba zai yi magana ba, hankalinsa na wajen tuki sai can ya ce"Inna ta yi fushi ba za ta sauraremu ba yanzu. Sai bayan kwana Biyu in ta huce." "Ita Mimin fa? Ba za mu je can gidan Hajiyar mu ba ta hakuri ba? Kallonsa Aji ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Itama ka ƙyaleta, duk in da ta je ai za ta dawo tunda da aurena a kanta." Nasir ya ce"Ina mganar da ka ce ta ce tana jiran takardanta in kaƙi, za ta kai ka Kotu.". Cikin mirmishi Aji ya ce"Kai ka yarda za ta iya kai ni kotun? To ta kaini kotun sai a ga ni shege ka fasa."   Nasir mamaki ne ma ya hana shi magana har Aji ya maida shi gida. Shi dai har cewa ya yi ya kira ta a waya.Aji ya ce ko ya kirata ta hau dokin zuciya ba za ta ɗauka ba shi kuma ba ya son ya kira ba'a ɗauka ba in ransa ya ɓaci abun ba zai yi mata daɗi ba. Yana ijiye Nasir a gidansa ya juya kan mota ya koma gidansa. Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan ya kunna wayarsa ya kira Mu'azzam. Shima dai duk mgana ɗaya ne bai kyauta ba Inna ta ce ta cire hannunta a kan shi, shi na Innar ya fi damun shi sai kawai ya ce"Mu'azzam kar ka damu kanka, ba sai ka taho ba komai zai dai dai ta in sha Allahu." Mu'azzam ya ce"Ta ya ya? Inna ta rantse da Allah ta baza ta saka baki ba. Na yi ta kuma Kiran wayar Mimi ba ta ɗauka ba, mun yi mgana da Baba zan shigo jibi sai mu dumguma mu je mu same ta mu ba ta hakuri."   Kai Tsaye ya ce"Ni ban aike ku ba, kowa ya cire bakinsa a mgana ta da Mimi, ba kuma wanda zai je ba ta haƙuri." Daga can bangaren haka Mu'azzam ya saki baki ya kasa mgana. "Ka da ka ce za ka bar aikinka ka taho, na gaya maka ka yi zaman ka, matar ka kuma za'a turo maka ita gobe, Inna na cikin damuwa ku yi min alfarman barin mata Junoir awajenta tunda an yaye shi." Mu'azzam kasa mgana ya yi sai da ya ji ya ƙara faɗin" Is an oder Mu'azzam." Shike nan kawai ya ce ya kashe wayarsa. Baba da ya kira shi daga baya abin da ya faɗamai kenan kar  ma wanda ya yi yunanin zuwa wajen Mimi su bar shi da ita, shi a tunanin shi Mimi ba za ta iya dogon Fushi da shi ba za ta dawo Saboda tana son shi sannan yana tunanin in aka bita kanta zai yi girman da za ta fahimci Aji na dai dai da ita zai tsaya ya ga iya gudun ruwan ta amman da gaske ne ya yi nadama sannan yana ta tunanin shawarwarin Nasir a gare shi yana kuma tunanin gaskya ya faɗa masa Kamar lokaci ya yi da zai daina ganin laifi wani a kan wasu. Saboda yadda ma bai saurari Mu'azzam ba, bai samu sanar dashi rigiman ɗaki ba. ******** *MIMI* Mimi yadda ta kwanta da Kuka haka ta tashi  da wannan kukan, Hajiya ce ke ta faman lallashinta dakyar ta yi shuru har ta samu ta yi wanka amman ta saka wani abu a cikin ta ta kasa, ji ta ke yi kamar ba ta da ɗandano a harshenta sai da Hajiya ta nuna ɓacin ranta sannan ta iya shan Tea shima kaɗan, ba ta da aiki sai kwanciya tana hawaye domin in ta tuna irin cin zarafin da Aji ya yi mata sai ta kasa tsaida kukanta. Hajiya duk ta damu ita da Baaba Uwani, ta kasa kiran kowa sai daga baya ta bi shawaran zuciyarta ta kira Alhaji Hamza ta ce ya zo gida in ya samu sarari yau tana neman shi ya ce sai zuwa dare domin baya gari ya shiga Bauchi.   Mimi ta riga ta fitar da auran Aji acikin ranta a yadda ta ke jin kanta ba ta tunanin za ta iya kara zaman aure da shi, Shi ya sa ta na gani su Bintu da Hibba na kira ba ta ɗauka ba ta ga har kiran Mu'azzam ba adadi ba ma su kaɗai bakwata kwata ba ta ɗauki wayar kowa ba. Daga karshe ma sai ta kashe wayar gabaɗaya tunda tana da tabbacin Shi uban gayyar ba zai kira ba, to wanda ya ce in ta tafin ma zai fi, kuma a mganganunsa babu so ko tausayi da gaske yake baya sonta kenan tuni ya daina sonta a tunanita yana sonta har yanzu ashe ashe bata sani ba shi baya wannan tunanin kanta ya aureta ne domin ya ɗauki fansa abin da ya faru a baya shi ya sa ya riƙa kuntata mata amman duk dai ta daure, Shi ya sa jauswaa suka ce IDAN AN CIZA a hura saboda kar a gaba a yi nadama ita dai ga ta cikin nadaman saurin amincewa da auran Aji da ta yi cikin gaggawa.   Yini ta yi kwance a ɗaki sallah kawai ke ta da ita. Bayan Tea ɗin da ta sha da safe ba abin da ya ƙara shiga cikin ta. Baba Uwani Saboda ita ta yi alalan manja da rana amman Mimi ba ta iya ci ba, Hajiya ta ce a dama mata kunin gyaɗa shi ne ma ta samu ya shiga cikinta a cikin kwana ɗaya ta rame Idanuwa sun Kumbura kamar ba Mimi yar gayu ba, Hajiya kuma har waya sun yi da Mommy amman ba ta iya gaya mata wani abu ba. Sannan da yamma Yaddiko ta zo duba ta amman har ta tafi ba ta gaya mata Mimi na gidan ba, ta bari dai Alhaji Hamza ya zo shine matsayin uba a wajenta in ya Kirata suka yi mgana ƙila ta iya gaya masa abin da ya faru. Ta yi niyar kiran Meri amman sai ta fasa,a tunanin ita kanta Merin ya kamata ta nemeta amman shuru, ita kuma Inna Meri kunya da nauyi suka saka ba ta yi tunanin kira ba har tunanin zuwa gidan ta yi amman Kunya take ji ya sa ta rasa mafita a lokacin.   Da daddaren bayan Mangariba Hajiya ta shiga ɗakin ta iske Mimi kan sallaya da hijabi fuskar nan ba fara'a amman tana shekin damuwa. Hajiya ta tsaya a kanta ta yi shuru ta kasa mgana sai da Mimi ta gama laziminta ta mike ta naɗe darduman ta maida shi ma'ajiyarsa sannan ta koma gefen gado ta zauna. Hajiya tasamu gefenta ta zauna lokaci ɗaya tana faɗin" Binta ba na son ganin ki cikin wannan damuwar, kuma ni tun jiya kin kasa yi min bayanin abin da ke faruwa." Ta gama faɗa cikin yar damuwa. Sai kawai Mimi ta murmusa kamar za ta yi kuka cikin sarƙewar murya ta ce", Hajiya ina bukatar kaya na, ki faɗa ma Mommy a kwasomin kayana daga gidan su Mansoor." Hajiya ta zaro ido kafin ta ce"Kaya fa kika ce Mimi? daman da gaske kike yi ba za ki koma ba?.   Ba ta ce koma ba sai kawai ta juya ta kwanta tana faɗin" Na faɗa miki tun jiya Hajiya, aure tsakanina da Aji ya ƙare." "Saboda mene?  Ba ki faɗa min dalili ba, kin kuma ce bai sake ki ba."   "Eh bai sake ni ba! Amman zai sake ni dolen shi ballantana ma shima yana ra'ayin haka." Hajiya ta yi zuru domin Mimi rufe Idanuwanta ta yi kamar mai barci duk sai ta kasa gane kanamari haka ta mike ta fita Jiki a sanyaye bayan fitan ta Mimi ta mike zaune ta na bin bayan Hajiya da kallo. Ba za ta iya faɗa musu abin da ya faru ba domin tama da tabbacin sai sun tsane shi ita kuma ba niyarta ta ɓata masa suna ba, su yi rabuwan Lafiya tun da baya sonta ba amfanin zaman aure domin alfarma. Ba ta san cewa Hajiya ta kira Daddy ba sai can wajajen tara na Dare har ta yi sallar Isha'i na tana kwance tana tunani Baaba Uwani ta zo ta kira ta ta ce Hajiya da Daddy suna jiran ta a falo. Sai  da gabanta ya faɗi, kenan ya zama dole ta faɗa ma Daddy dalilinta domin ta san shi da tsarin sanin abin da ya faru kafin ɗaukan mataki.   Jiki a sanyaye ta saka hijabin da ta yi sallah na Hajiya ne ma tunda kusan rabin da kwatan kayanta suna can gidan, jiki ba kwari ta ƙarisa falon shi kan shi Daddy ya ga yanayinta sai bai ji daɗi ba domin Hajiya ta gama yi masa bayanin abin da ya faru cikin wani yanayi ya ce"Haba Hajiya me ya sa tun a daran baki kirani kin faɗa min ba? Hajiya ta ce"Na ga dare ya yi, na ɗauka kuma za ta gaya min abin da ke faruwa amman taƙi ce min komai faɗi kawai take yi ita ta ce ta na so da farko yanzu kuma ta ce ba ta so a kyaleta ɗazu da mangariba tana min maganar a kwaso mata kayanta ne."   Daddy ya jinjina kai yana kallon Mimi da ta zauna a kasa saman cafet kanta yana ɗan nazarinta duk yadda aka yi ruwa ai baya tsami banza, duk inda ka ji mace ta ce ta gaji da auran da ta zaɓe shi da kanta to ba daɗi cikin yanayin mganarsa ya kira sunanta ta amsa sai ya umarceta da ta taso ta zo ta zauna a kusa da shi a saman Kujera, da ta taso sai ba ta zauna a sama ba sai ta zauna a kasa a kusa da kafafunsa lokaci ɗaya tana gaishe shi ya amsa cikin sakewa kafin ya ce" Me ya faru ne Mimi? Hajiya ta ce kina ta Kuka kuma kin ƙi yi mata bayani ina fatan za ki yi ma Daddyn ki bayanin abin da ke faruwa." Sai ya ga ta yi shuru kanta na ƙasa, da sauri ya ce" Kar  ki damu, matukar ke kike da gaskiya ba zan taɓa goyon bayan ki koma ba."   Kan Mimi na ƙasa ta ce"Daddy na haƙura da auren ne kawai." "Saboda  me ya sa  kika ce haka? An taɓa hakura da aure ne Mimi in dai ba wanda kike ke zaman shi ba ne ya ce ki je ya gaji da ke ba." A ranta ta ce kusan hakane amman gili sai ta ce" Saboda akwai tazara mai yawa tsakanina da shi Daddy, abaya na yi tunanin in na aure shi zan iya haɗe wannn  tazaran dake tsakanin mu. Amman daga baya sai na fahimci ba zan iya gyara abin da Allah bai so ya gyara ba. Don Allah kar ku matsamanin akan sai na koma na gaya masa ya aikomin da takardan sakina." Hajiya ta saka salati, Daddy kuma sai ya yi shuru ganin Mimi na matsan kwallah. Amman sai bai nuna wani abu tunda har Yanzu ba'a zo in da yake so ba. Cikin sigan lallashi ya ce"Duk naji, amman ba haka nale son ji ba, Kin dai  san ni a matsayin Major nake a wajen ka sai in da karfina ya kare wajen kwatar miki yanci in dai na tabbatar dake aka zalunta. Saboda haka ki natsu ki gayamin abin da ya faru." A cikin Lallashi ya gama maganar yana dafa mai kanta, Mimi kuma sai kuka kawai take yi ba ta yi mgana ba, shi kuma bai takura mata ba ya ce ta natsu ta yi masa bayani. Ganin ta yi shuru ya sa ya gyara zama yana faɗin" Mimi ba zan iya gane komai ba inkina wannan kukan shi aure ai ya na da dokokinsa da tsarin sa, ba zai yuyu ba wani ƙwaƙwaran dalili ba kawai na ce ki zauna a gida ki kashe auran ki ba. A'a dole sai mun san abinda ke faruwa, tunda kin ki mgana bari na kira shi Mijin naki sai ya zo mu tattauna kila shi ya yi mana bayanin abin da ke faru."   Ya faɗa kamar gaske har ya na ciro wayarsa kamar ya na da lambar Mansoor Ahalin ba shi da ita, Mimi na ganin haka ta ɗauka da gasken kira zai yi da sauri ta ce"Kar  ka kira shi Daddy, zan gaya maka abin da ya Faru." Sai ya yi mirmishi ya ijiye wayarsa a gefe yana faɗin'" Yauwa ina jin ki uwata." Kan Mimi na ƙasa ta ce" Daddy cewa ya yi baya so na, ba ya sona.." Ta karishe faɗa Cikin kuka, cikin mamaki Daddy ya ce"Baya son ki? To me ya sa ya aure ki? "Yace Saboda Hajiya da Mommy sun je sun roƙe shi. Sannan kuma Daddy kamar auran ɗaukan fansa ya yi dani tunda sai ya riƙa tafiyar da ni akan abin da ya faru ysakaninsa da Abi a shekarun baya." "Ka ji wani sakarci kuma?   Daddy ya faɗa ransa ba ce yana kallon Hajiya da ta kasa mgana, Mimi na kuka ta gyaɗa kanta tana faɗin" Shi ne na taho kawai daddy tunda babu amfanin zama da wanda baya somka sannan yake kokarin yin ramakon wani abin da ya faru a baya a kanka." "Yes! Kin yi dai dai abin da kika yi, wannan ai shirme ne, kuma ba ma bautar ubangiji ya maida auran ba sai wasan yara.vGaskiya ya bani kunya ina ganinsa kamar he is matual ashe sakarai ne mara wayau? Kuma yasan kin taho amman bai dakatar dake ba? Mimi ma sharan ƙwallah ta ce"Ya sani har cewa ma ya yi zai fi in da har na tafin." Daddy ya jinjina kai kafin ya yi wata yar dariyansu ta manya yana kallon Hajiya lokaci ɗaya ya na faɗin"U see ko Hajiya? A baya an ga laifin Major ne amman ta wani bangaren yana da ƴar gaskiyarsa. Sai da na so na hana Hajiya tado da wannan maganar ki duba duk alfarman da a ka yi masa muka aura masa ƴar mu kamar sadaka  amman ki ji fa irin wulakancin da ya biyo baya har yana fadin in ta tafin zai fim So is ok gwara da kika taho domin ki nuna masa kinsan me kike yi, Is Good,.."   Sai ya dakata yana dai dai ta kansa Hajiya kuma sai ta ce"Hamza a bi komai a sannu, Ina ta Merin duk tana nanabubuwan nan suka faru? Da sauri Mimi ta ce"Ba ta sani ba Hajiya, itama ba jin mganarta yake yi ba, ko ta hana shi ba ya hanuwa wani lokacin ma bata san ya aikata wani abun."   "Ashe yaron ba shi da tarbiya ban sani ba? Komai aka haɗa da jaki sai ya ci ƙara, Kuma daga jiya zuwa yau bai kira ki ba kuma bai bai turo kowaba? Mimi ta gyada kanta kafin ta ce"Eh! sai dai ƙannensa sunta kirana a waya ban ɗauka ba." Daddy ya ce"That Good! gwara da ba ki ɗauka ba, shi ba shi da baki ne sai kannensa ne za su ci masa albasa? Na fahimci ya na da jinkansa. To shike nan ki kwantar da hankali ba za ki koma ba sai in har ya yi nadaman abin da ya aikata ya kawo kansa in har ya na son ki kuma kina da daraja zai sauke kansa ya kawo kansa, ni kuma zan nuna masa cewa ba Isar sa ba ce ya sa na bashi auran ki,  ba  kuma chanchanta ba ne shima alfarman Hajiya da Murja ya ci, in kuma aka yi wata huɗu bai zo ba kuma bai yi wani abu da zai nuna kina da daraja a wajensa ba zan nema miki Saki,in ya nuna taurin kai sai alƙali ya karɓa miki takardan ki."   Hajiya ta ce"A'a Hamza abun bai dace ba ka yi hakuri a bi komai a sannu mana" Daddy ya mike ya na gyara  babban rigansa lokaci ɗaya yana faɗin" Hajiya kar ki hanani shiga wannan mganar, ki duba mganar yarinyar nan gabaɗaya gani yake ba ta da wani daraja a wajenza tunda mun bi umarninsa mun aura masa ita ai bai eahala ba tunda har ya ke fama da jin kai yana cewa gwara ta tafi ɗin zai gane a baya alfarman ki yaci yanzu ne zai gane shayi ruwa ne, Mimi ki daina kuka sha kurimin ki kin ji? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce" Daddy a kwaso min kayana." Kai tsaye ya ce"Dole ai akwai sabon zama, in har ya na son auran ku muma sai mun zuba masa namu sharuɗdan ciki har da gama zaman ki a wannan gidan nasu zan yi magana da Maman yara duk yadda ake ciki za ta kira ki zuwa gobe za'a dawo miki da komai naki gida in sha Allahu." Sai Mimi ta ji dadi acikin ranta domin gwara dai kowa yasan ita kan ta gama zaman aure da Aji.   Hajiya kuma sai cewa take yi a bi a sannu amnan Daddy ya ce wannan karon Hajiya ta cire bakinta gani ya yi kamar sun ba shi auran bai wahala ba. Mimi tana tunanin in da ta zauna ta faɗa nusu yadda ya tafiyar da ita tun farkon auran fa? Da mganganun da yake gayamata da zarafin iyayenta da yake ci? Ta tabbata sai sun ji sun tsane shi shi ya sa ta sakaya maganar. Bayan tafiyar Daddy Hajiya ta dawo tana nuna ma Mimi illar abin da za ta aikata amman ta ce ita fa tana kan bakanta, abun haushima shi fa bai ma san ya aikata ba dai dai ba sannan ita ba za ta cigaba da zama da mara afuwa ba, sannan ba za ta iya zama da wanda bai iya sarrafa zuciyarsa ba Sannan da bakinsa ya ce baya sonta ba ta ga amfanin zamanta ta da shi ba.   Zuwa da safe dai tuni mutanen dake kusa susan Mimi na gidan Hajiya, Mommy ma ta sani saboda Hajiya da kanta ta kirata ta sanar da ita abib da ke faruwa ta ce za ta shigo Gombe cikin satin, sannan bangaren Daddy kuma da ya koma ya tattauna da Mama itama ta ba da hoyan bayan haka, ta ce haba auren ai ya yi kaskanci ba Dole ya yi abin da yake so ba saboda an ba shi Mimi kamar sadaka. Ita ta kira Jaheed taa gaya masa abin da ke faruwa ya yi mamaki kwarai.Har Maman na zolayanshi da cewa ƙila in da rabo Mimi rabon shi ce nan da nan farinciki ya cika zuciyarsa.   Kuma Daddy ya ba da umarnin a nemo mota a je a kwaso duka kayan Mimi a kai mata gidan Hajiya, amman ko shi a cikin ranshi ba shi da niyar kashe ma Mimi aure ita kanta a mganganunta fushi ne kawai amman tana son mijinta kuma shima yana sonta amman girman kai ne ya hana shi zama ya fahimci yadda zai iya nuna ma mimin so. Shi ya sa ya zaɓi ya yi amfani da karatun siyasar sa ya gyara auran Mimi sannan ya cire wannan jin kan da fushi daga zuciyar Mansoor ba tare da ya bari ko Mimin ta san ga manufarsa ba. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3003* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Daddy na yi ma Mama maganan kwaso kaya ta kira ƙanwarta Hajiya Turai suka yi maganar ta nema musu mota, Har tana ƙyanƙyasa mata abin da ya faru Hajiya Turai ta ce"Haba ni fa daman na sani duk burgan banza ne, yarinyar nan ba za ta iya zama a wannan gidan ba." Mama na ƴar dariya ta ce"Uhm to ai komai ya ƙare" ita kamar har wani jin daɗi take yi ita da suka yi mgana da Daddy sai ga shi har Antyn yara sai da ta sanar mata da ga abin da ke faruwa kowa ya ji sai ya ce gaskiya daman wannan auran na Mimi sai a hankali.   Jaheed ya fi kowa murna da faruwar haka, Tun bayan auran Mimi yake cikin garari, sai dai kule kulen ƴanmatan zamanin nan da ba ka raba Mazan zamani da shi, bai san Yaddiko ba ta sani ba sai da ya kirata ya gaisheta kawai ya faɗa mata saboda ya san tana goyon bayansa ko a baya aiko nan da nan ta ce ba ta sani ba amman anjuma za ta leka gidan Hajiyan ta ga abin da ke faruwa, Lamarin ya daure mata kai, ita fa ba ta son ta ga mace da ƙuruciyarta tana bin ɗakuna in ya zama jiki bshike nan duk in da ta yi aure ba za ta zauna ba. Da daddare ta saka ƴaron makotan su ya kawo ta gidan Hajiya, Ta kuma gasgata abin da Jaheed ɗin ya faɗa mata tunda ta ga Mimi a gida sannan da ta yi mganar ba'asi Domin sai ta nuna Kamar ba ta san abin da ke faruwa ba.   Nan Hajiya ta yi mata bayani da zuwan Daddy jiya da maganar da ya yanke a kan Mimi ɗin, Yaddiko ta gyara zama lokaci ɗaya ta na faɗin" Haba Hajiya me ya sa za ku biye mata? Tun farko sai dai a ka nuna mata ga Ɗan'uwanta ta dage sai abin da take so an kuma yi auran nan amman kawai sai ta kamo kafa ta dawo ta ce ta hakura da zaman aure? Haba dai Hajiya ai ya kamata ku ma ku zauna ku yi tunani kar ta maida mi kananun mutane mana" Hajiya ta kalleta kafin ta ce" To yanzu tunda mu ba mu iya ba, ya kike son ayi? Kai tsaye Ta ce" A kira shi mijin nata Yaya ya zauna da shi sai a ji shima ta bakinsa." Hajiya ta gyaɗa kai kafin ta ce"To kuma har yanzu bai zo kuma bai kira waya ba, shi kuma Hamza ya ce ba wanda zai neme shi." Sai Yaddiko ta yi shuru ta kasa mgana Hajiya ta cigaba da faɗin" Ba na nufin Auran Binta ya ƙare har ga Allah Yaddiko.  Amman mu ba su lokaci mu gani ina ji a jikina ko ba yanzu ba nan gaba kaɗan za su daidaita in sha Allahu." Yaddiko dai ba ta kara mgana ba saboda ta ga Kamar wannan karon ma Hajiya tan goyon bayan Bintar ne.   Kuma ba ta hakura ba da za ta tafi, sai da ta leƙa har ɗakin Hajiya ta na ce ma Mimi" Binta rayuwar nan ta aure duka fa hakuri a ke yi, ke shaida ce irin hakurin da Murja ta yi da Yaya Allah ya jikansa da ba ta yi haƙuri ba,da ba ku ta shi kun ga iyayen ku waje ɗaya ba, kowa ki ka gani a gidan auran shi ya na zaune to karki so ki ji irin haƙurin da yake yi a zamantakewarsa, in ka ji na wani sai ka ce naka nafila ne, auran dai kika na ce kina so kuma a ka bi abin da kike so a ka baki shi sai kawai aure ko shekara bai yi ba sai ki dawo gida ki ce ba za ki koma ba? Kar  fa saboda kin ga ana bin abin a kike so ki riƙa zuwa mana da renin hankali aure ibada ne ba wajen wasa ba." Har Yaddiko ta gama maganarta Kan Mimi na ƙasa ta kasa mgana sai dai Idanuwanta sun tara ƙwalla ai ba ta da wani ikon kare kanta yanzu shiyasa ta yi shuru.   Yaddiko na fita ta koma ta kwanta tana kuka, Mommy ma da safe ta kira ta tana yi mata faɗa akan wannan abin da ta yi har ta na cewa ta shirya ta koma gidan Mijinta,  ita kuma ta saka mata kuka cewa ba za ta koma ba ta yi ma Daddy magana kuma shi yace ta zauna. Da Mommyn ta kira Daddy bai saurare ta ba ya ce in ta samu lokaci ta shigo Gombe su tattauna da haka suka rabu da juna, Mommy da kanta ta sanar ma Khadi, ita kuma khadi ta sanar ma da Dr . Sulaiman da Madiha a bakinta suka ji L labarin abin da ya faru tun daga lokacin suke rige rigen kiran wayarta amman ba ta ɗauka ba, Madiha ma ba ta kira ba cewa ta yi daman ta faɗa ma Mimin ba abun kunya ba ne in ta dawo gida ta nemi Saki, ita kuma Khadi kanun zencen ta ke so ji. Dr. sulaiman kaɗai ta daga kiransa suka yi magana shima dai bakinsu ɗaya da Mommy in ma wani abu take so ta yi mgana a yi mata amman ta bar mganar kashe auranta gwara ta koma zai fi mata alheri.   Shima kuka ta saka masa tana faɗin ita ba za ta koma ba. Saboda ai shi Ajin ya san tafiyarta kuma da kanshi ya ce ta tafin, kuma har yanzu bai zo kuma bai kirata ba kenan shima ya gaji da auran nata.  Jin haka yasa bakin Dr  ya mutu amman shima ya ce a cikin ranakun weekend in ya samu lokaci zai zo Gomben. Shima ya kira Daddy sun yi mgana  ya ɗan dai yi masa bayanin Mimi za ta koma matuƙar Mijinta ya zo biko a ka zauna a ka ji inda suke da ɓaraka a yi gyara amman matukar bai tako ba shi ba zai maida masa Mimi ba tunda ba ƴar sadaka ba ce. Ta nan kuma Dr ya ga gaskiyan Daddy ko ya ya ne a nuna masa Mimin tana da daraja, amman matarka ta biyo dare ta dawo gida amman baka kira ba, sannan ba ka zo ba, sannan ba ma tunanin ko wani abu ya faru da ita bayan fitar ta ba, shima ta wannan bangaren ya ga wawancin mijin na Mimi a haka kuma a fuska kamar mai hankali da Tunani.   Ita Hajiya sai fakewa take yi da ƙannensa suna kiran ta wayarta ba ta ɗauka Daddy ya ce ƙannensa dabam shi dabam, ba ƙannensa ke auranta ba shi ya ke auranta kenen bai ma san darajanta ba kenan. Kan kuma maganar kwaso kaya ne domin Maman ta zo a daran ta ce gobe da safe za su je tare da Turai su kwaso kata kayanta da umarnin babanta. Hajiya ba haka ta so ba, ta so a dakata ba ta san vaggawa amman Daddy ya ce sai an kwaso saboda shi kaɗai ya bar ma kansa Sanin dalilin shi na cewa a kwaso kayan da gaggawa.   Washegari misalin ƙarfe 10:20am na safiya ranar jumma'a Mama ta isa gidan Wanzamai, ita ta fara yo gaba Hajiya Turai za ta zo da mai motan ɗaukan kaya, Inna Meri na ayyukanta a tsakar gida Mama ta shigo ta gane ta sai ta karɓe ta hannu bibbiyu ta shigarta da ita har cikin ɗakinta ta saka Walida ta kawo mata ruwa, Inna Meri kunya duk ya kamata a tunanin ta ko Maman ba ta san Mimi ta koma gida ba ne, Tana shirin ce mata ai Bintar na gidan Hajiya sai kawai ta ji Mama tana faɗin" Key ɗin ɗakin Mimi nake so don Allah." Sai Inna Meri ta kasa magana saboda jikinta ya yi sanyi amman sai ta yi yaƙe kawai ta tashi sda kanta ta shiga ciki ta ɗauko daman ita da kanta ta rufe ɗakin ta riƙe key ɗin a hannunta. saboda jatsari ne barin ɗakin a buɗe tunda akwai kayan kudi a ciki.   Ba tare da ta tambayi ba'asin abin da Mama za ta yi a ɗakin ba ta damka mata makullayen ɗakunan, Ita kuma har ta amsa ta fita daga ɗakin ba ta ƙara cewa komai ba, Ta buɗe dakin ta shiga ciki Inna Meri ba ta taba tunanin za'a kwashe kayan Binta ba ne duk daman ko yau sai da Magajiya ta zo Kofar ɗakin ta ta tsaya ta na faɗin suna bukatar ɗaki domin Matar Saddiqu za ta dawo nan ne cikin gaggawa. Walida ta same Inna zqune kawai ta yi tagumi, Hibba ta je gidansu Jiya ba ta dawo ba sai ta kwana a can, Junior kuma ya ƙi zaman nan sai gidan Bintu saboda su Husaini.   "Inna ko dai an zo ɗaukan kayan sawan Anty Mimi ne?   Walida ta faɗa tana zama kusa da Inna Meri, ita kuma sai ta girgiza kanta kafin ta ce"Ban sani ba, makullin ɗakin kawai ta tambaya." Ita kanta Walida duk jikinta ya yi sanyi, Uban gayyar kuma tun ranar da suka zo da Nasir ba wanda ya ƙara ganin shi Baba Ɗanjuma har ya yi tunanin su je gidan Sanata Hamza shi da abokinsa Mallam Hashimu su ba da hakuri Inna ta hana ta ce shi wai mai auren bai damu ba sai su ne za su damu kansu? Ai abin da ya nuna ya nuna ma duniya shima hakan ya zaɓa. Cewa ma ta yi in dai ya je ita ba da yawunta ba, Shi ya sa sai ya dakata shi kuma gogan in an neme sa sai ya ce kar kowa ya saka baki yana tutiniyan duk in da Ma Mimin ta je a cewarsa za ta dawo ne ma. Har su Yaya Amina sun so su  zuwa har gidan Hajiya su Samu Mimi su ba ta haƙuri Inna Meri na ji ta ce kar wacce ta taka ta je, ba hurumin su ba ne.   Su dai suna zaune sai gani suka yi wata mata ta shigo Hajiya Turai, Mama ita ta leƙo ɗakin Inna ta ce a gaya ma matan gidan Maza za su shigo su fita da kaya shike nan ta faru ta kare. Daman Zuwan Mama kayan Sawan Mimi ta gama haɗa mata duka a cikin akwatinta da duka kayan kwalliyarta da takalmanta, Inna ko iya fita ba ta yi sai Walida ne ta je ta gayama magajiya Maza za su shigo ɗaukan kaya. Tana jin haka ta san Dalili a ranta ta ce abin dai ya tabbata kenan Daman itama duk ita da gayama yaƴanta har Maaeesha dake gidan Zuwaira ta je ta kai mata labari sai ta ji daɗi ko banza za ta zama tauraruwa a wannan gidan. Kuma ta ji daɗi da za ta koma ɗakin Mimi Saboda ya fi jin kayan gyara sannan ya fi kyau komai na fantin ɗakin da abubuwa Uniqui ne masu tsada da yarari. Walida hankalinta ya ta shi ganin da gaske fa tunda ana ta fita kaya. Sai ta Lallaɓa ta saci wayar Inna Meri ta Kira Bintu ta sanar da ita abunda ke faruwa sai ta ce ga ta nan zuwa ta kuma ƙara kiran Hibba ita sai ta ce ta na kan hanya tunda sun yi waya da Mu'aazzanm tun asuba ya ce ya ta so. Da Bintu da Hibba a kofar gida suka haɗu suka shigo gidan lokacin har gqdon Mimi an kwance an fita da shi Kujeru ne su kaƙi fita a na tunanin a haura da su ta garu kamar yadda dama suka shigo gidan tun farko.   Ɗakin Inna suka faɗa cikin wani yanayi Bintu ke faɗin" Inna ke kika ce su zo su kwashe kaya? Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai Walida ne ta maida musu abin da ya faru, Bintu ta ɗauko wayarta daga aljihun rigarta ta lalubo lambar Yayan na su ta kira shi amman wayarsa tana kashe ne so take yi ta sanar da shi abin da ke faruwa ƙila in ya ji ya zo ya dakatar da su. Hibba faɗi take yi" Inna domin Allah ki dakatar da su mana.". Inna Meri ta miƙe tana faɗin" Saboda wani Dalili Hibbatu? Ba ni da wannan hujjar." saboda ma kar su dameta fita ta yi ta zuba ruwa a buta ta zagaya ta kama ruwa tana fitowa ta ɗauro alwala ta zo ta shige ciki ta shimfiɗa sallaya ta kabbarta salla. Ganin ba mafita ya sa Bintu ta ja hannun Hibba suka fita lokaci ɗaya tana faɗin" Mu je mu yi musu mgana. Wlh makiyan gidan nan dariya suke yi mana." Sun shiga ɗakin sun iske Mama da Turai suna maida wasu kayan Kitchen ɗin a cikin kwalayensu bayan sun gaishe su sai kuma suka kasa mgana har sai da Mama ta ce"Lafiya ko? Bintu ta marairace kafin ta ce"Don Allah Mama ku yi hakuri da kwashe kayan nan, shi fa Yaya Mansoor bai ce ya saki Anty Mimi ba." Mama ta yi yar dariya tana kallon ƙanwarta Kafin ta ce" N ma yar aikace, umarnin Babanta ne ya ce Lalle lalle yau mu zo mu kwaso mata kayanta." Turai ta ce"To tunda har ya ce ba ya sonta zaman me za ta yi da shi? Mama ta ce" Babu kam, abin da yake so ne ta yi masa tunda ta ce za ta tafin ya ce gwara ta tafin."   Da sauri Hibba ta ce"Sharrin sheɗan ne, sannan faɗan ma'aurata ne, in da an ɗan dakata za su iya sulhunta kansu." Mama ta sake yin yar dariya kafin ta ce" To wannan kuma ban sani ba, amman ni dai yanzu Umarnin Babanta na ke aiwatarwa." Duk iya ƙokarinsu amman su Mama ba su saurare shi ba. Daga karshe ma suna mgana sai suka yi musu kunnen uwar shegu. Dole su ka fita jiki duk a sanyaye sannan sun koma suna ta kiran Mimi ba su sameta ba, abin da suka lura shi ne kamar ta rufe su ne ba za su ƙara samun ta a waya ba. Suna ji suna gani aka kwashe kayan Mimi gabaɗaya tas kayan abinci kaɗai suka bar musu a kitchen da za su tafi suka ba su makullin ɗakin ba su ko ga Inna Meri ba ta na cikin dakinta.   Makota ko sun cika ƙofar gida ana maida mgana, wanda ma bai sani ba duk ya san abin da ke faruwa Magajiya na tsakar gidan tana dariyan zuci burinta ya cika. Mariya ba ta cika zama a nan ba ita ce gidan Zuwaira ko gidan Auwalu, Saboda anan ba za ta sake ta riƙa yin taɗe taɗe yadda ta ga dama ba sannan magajiya na takura mata kuma ba sa shiri da matar Saddiqu. Sai ga ɗakin da Mimi ta yi rayuwa fayau ba komai a ciki haka su Hibba suka koma ɗakin inna suka yi jugum jugun abin haushi ma ba'a ɗade ba sai ga Saddiqu ya shigo Shashen shi da wani abokinsa ba sallama ba komai suka shige ɗakin suna dubawa baƙin ciki ya sa sai Bintu da ta yi kwallah ta ce ma Hibba bari ta je ta dawo ta fice daga gidan gabaɗaya tana jin magajiya na shewa ita da Gaje daman ai murna za su yi. Daga nan Binta mashin ta hau zuwa gidan Yaya Amina domin ta sanar da ita halin da ake ciki ya kamata su san matakin da za su ɗauka kafin su zama abun dariya a cikin gida da maƙota. ****** Duka kayan Mimi gidan Daddy a ka sauke su,. Sai dai kayan sawanta ne Mama ta aika mata da su gabadaya gidan Hajiya. Washegari Asabar Mommy ta biyo jirgi ta zo Gombe, can gidan Daddy ta je ta same shi suka tattauna bai fito ya nuna mata manufar shi ba amman ya ce sai ya nuna ma yaron nan Mimi yar gata ce, in yana sonta zai kawo kansa ya kuma ce kar ma wanda ya takuramata da Maganar komawa tukunna a ƙyaleta sai ta kara samun natsuwa da hutu.   Dole Momny ta bar mganar shi ya sa ma kwananta ɗaya ta juya, sun yi saɓani ba ta daɗe da tafiya Dr. sulaiman ya zo garin shima, Duka dai bayanan da Daddy ya yi ma Mommy shi ya yi mishi ya ce kuma su taimaka masa wajen dawoma da Mimi darajanta a idon mijinta su cire bakin su su bar shi da shi da Mimin gabaɗaya. Shima ɗin bai kwana ba a ranar ya bi jirgi ya koma kano amman ya je gidan Hajiya ya gaisheta sannan ya ga Mimi sun yi mgana shi dai ya ce ta kwantar da hankalinta komai zai wuce kamar bai faru ba. Khadi kuma aiki ya hana ta zuwa amman Kwazzaba yasa sai da Mimi ta amsa wayarta.   Har tambayan Mimi take yi wai daman ance baƙaƙen maza sun iya rashin mutumci tana so dai Mimi ta buɗe mata cikinta ita kuma sai taƙi, ce mata kawai ta yi i ta ta ce ta na so daga farko yanzu kuma ta ce ta haƙura ba dole sai an matsa mata anji dalilinta ba, itama tana da wayon ta san kowa na rufe siirin shi ita ba za ta bar na ta a buße ba, ko da ta zaɓi rabuwa da Aji har yau har gobe zuciyarta ba ta daina son shi ba. Kawai dai ta zaɓar ma kanta barin rayuwarsa ne saboda ƙimar iyayenta, Sannan kuma yana da hallaya masa kyau ɗin da ba za ta iya zama da shi ba, to wanda bai da kyakyawan zuciya ai zama da shi hadari ne. Mutumin da ba ya ganin ka da kai da Iyayenka a wata tsiya ai ba amfanin zama da shi.   Madiha kam da suka yi waya ce mata ta yi" Zan yi supporting ɗin ki karo na farko Sisto, In bai sake ki ta arziƙi ba to za mu maka shi a Kotu alkali ya karɓan miki yancin ki, kin fi sa komai shi ne zai yi asaran rasaaki, ke kuma sai dai ki samubwanda ya ninka sa. daman abin da Abi ya guda kenan tun farko amman at last dai Hajiya da Mommy sun kasa ganewa ke ma wawanci ya rufe miki Ido, amman kar ki damu ba ki makara ba abin da kuma kika yi kin yi dai dai i support your Decession."   Mimi dai ba ta ce mata komai ba. Daman ai madiha kowa yasan irin kalamanta kenan, ta kuma san za ta fi kowa jin daɗin abin da ya faru, amman ko da ita ba ta yarda ta furta mata wata mgana ba. Ita yanzu wa za ta zauna ta faɗa ma tun auran su ko hannunta sai bisa kuskure Aji ya taɓa kamawa? Sai maganar ta kara girma sai daga baya ma ta fahinci kamar ba ya sha'awarta ne tunda ba ya sonta amman ko ita ta san tana da sura mai jan hankali maza. Wata zuciyar ta ce" Ba yana kishin ki ba? Sai kuma a zuciyarta  ta ce kishin banza da wofi ba shi da amfani a wajenta yanzu.   Jin daɗin ma tana Annual Leave ne, shi ya sa ba ta aikin komai a gida sai kwanciya da tunanin. Tuni ta daɗe da blooking ɗin duka lambobin yan gidansu Mansoor domin ba ta so ma ta ɗauka a roketa abin da ba za ta iya ba, Ko Rukky ba su yi waya ba ballantana tasan abinda ke faruwa ra bon ta da mgana da ita tun ta na Abuja, kila za ta yi tunanin ba ta dawo ba ne. ita kuma ba ta so ma  ta sani saboda surutun Rukky ne ba ta so, daman itama tana daga cikin ƴan adawa da auran. ****** Bangaren Mu'azzam kuma tun da ya sauka garin yake lallashin Inna da ban baki da roƙon ta domin Allah ta shirya ta je gidan Hajiya ta ba ma Mimi hakuri ta dawo, haka duka yaran suka haɗe mata kai, ita kuma ta yi rantsuwan cewa ba in da za ta je suma kuma duk wanda ya je ba ta aike shi ba. Abin a ya fi bata musu rai ma shi ne a ranar asabar da safe aka fara kwaso kayan Maeesha zuwa ɗakin Mimi ba sanarwa ba komai maza na giftawa, bayan Inna Meri da kanta ta zo ta share ɗakin ta goge. Sannan ta fito da kayan abincin da aka bari a ɗakin ta watsar nan kofar ɗakin Inna Meri sai da Hibba da Walida suka kwashe suka shigo da su ɗakin Innar.   Ganin Inna ta cije, domin ita ɓacin ranta ɗaya, yadda shi uban gayyar bai ma san ana yi ba tunda washegarin ranar da ya yi tsiyar bai ƙara dawowa ba to sai ta ga ko an shiga mganar ba amfani zai iya maimaita abin da ya aikata tunda bai san darajan matar ba, Sannan ita da kanta ta kira Alhaji Kabiru babansa na  Bauchi tana gayamasa abin da ke faruwa a tunaninta zai zo garin ya same shi ya yi mishi faɗa tunda ita dai daman ya renata ba ya jin mganarta. Amman kawai sai ta ji ya ce"Haka aka yi kenan? Daman ai Gwaggon sa Yalwa ta faɗamin baya son yarinyar, kawai ya saketa sai ya zo gidana ya duba mata na aura masa ." Haushi ya kama Inna to ko ɗiyar Babansa ya aura zai iya yi mata abin da ya fika haka in dai wanna mai bakar zuciyar ne. Daga nan ba ta kara neman su ba, Domin ta na da tabbacin suma ya fi ƙarfin su.   Mu'azzam tare da su Yaya Amina suka yi shawara, shi yanzu su Nasir yake jira Ahmad ne yace a jira shi zai shigo garin tunda dukkansu sun ji labari, kuma cikinsu duk wamda ya kira Aji baya ɗaukan wayansa su sun ce za su yi masa ne bisa zaman tare da abokantaka bisa Amana, za su je su yi gamgami su samu Mimi su ba ta hakuri, Sai Mu'azzam yace kafin su je, su matan su shirya su je su gani. Ba tare da Inna ta sani ba suka haɗu a gidan Bintu domin Hibba cewa ta yi Walida za ta rakata gida ta ɗauko wasu kayan. Inna bqta sani ba suka haɗu gabaɗayansu Har da Yaya Halima sai gidan Hajiya amman abin da ya ƙara ba su tsoro Hajiya da kanta ta ce musu Mimi ta kwanta kanta na ciwo kuma ba zai yuyu a tashe ta ba. Zaman kusan awa huɗu suka yi tun la'asar anan ma suka yi sallar mangariba amman Mimi ba ta bari sun ganta ba. daga baya dai suka fahimci cewa Ita ce ba ta son su haɗu.   Yaya Amina ce ta yi ma Hajiya mganar a yi hakuri abun bai kai haka ba don Allah Mimi ta dawo ɗakinta su suna sonta, Inna ma kunya ce da nauyi suka hana ta zuwa. Amman sai Hajiya ta yi dariya kafin ta ce" Ayya ni kaina zan so hakan, amman kuma mganar ba ta hannuna tana wajen Binta da Babanta ne, abin da duk suka yanke shike nan." Fahimtar da suka yi lamarin ya wuce tunaninsu haka suka dawo gidan Inna jiki ba daɗi suka iske wani ƙarin abun haushi ƴan'uwan Maeesha sun dawo da ita sun yi kaca kaca da shashen suna ta shewar su, Inna dai ba ta gaya musu ba ne amman Ko darajan gaisuwa ba ta samu ba. Sai da suka dawo ne suka faɗa mata abin da ya faru da in da su ka je, Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Sun yi min dai dai, ku kuma Allah ya ƙara sai da na ce kar ku je, wanda ya ɓata bai san hanyar gyara ba sai ku?   Mu'azzam da ya zo ya ji labarin abin da ya faru sai jikinsa ya yi sanyi, yanzu haka Aji ya bar masa gida shi a Camp yake kwana in kuma ya je da niyyar su yi mgana sai ya ce suna da traning haka dai duk ya shanshantar da maganar Mimi, shi kuma Mansoor tunaninsa ya bi Mimi gidansu ya ba ta hakuri kamar ya sauko ne ya yi Arha, a tunaninsa auranta na hannunsa to zai tsaya ya ga iya gudun ruwanta shi bai ce ta tafi ba, ita ce ta zaɓi tafiya shi kuma ya goya ma zaɓinta baya, kuma ba ya son kowa ya shiga maganar kotun da ta ce za ta kaisa ya ke jira, ɗayan tunaninsa nasa kuma na gayamasa Mimi na son shi ba za ta iya rayuwa ba shi ba, tabbas duk in da ta je ma za ta dawo ko labarin an kwashe kaya bai samu ba balle ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci shirmen da ya tafka yana nan yana shirme da tunanin banza..   Ahamad ya shigo garin. A kuma daran suka ka haɗu su huɗu zuwa gidan su Mimi, suma ɗin dai Hajiyar kawai suka samu gani, a cewarta Mimi ba ta jin daɗi ta kwanta alhalin tana nan tunda Hajiya ta ce  mata abokan Mansoor ne da ƙaninsa ta roƙi Hajiya da ta ce ba ta garin ta tafi Abuja ita kuma Hajiyan ta ce ba za ta yi ƙarya ba. Sai da Mimin ta marairace tana faɗin" Don Allah Hajiya ki taimaka min, ko na je mun ga juna ba zan yi musu abin da suke so ba." Dole Hajiya ta fito ta sake ƙaryan Mimi ba ta jin daɗi ta kwanta, Suma sun ta rokon Hajiya suma kuma ta ce magana na hannun Mimi da babanta. Jin haka ya sa suka ce bari su karisa gidan tsohon Sanatan su gan shi, daga gidan Hajiya can suka nufa sun kuma ci sa'an yana na gidan nan da nan aka yi musu iso zuwa falon da yake ganawa da baƙin sa.   Shima dai bayan sun gama gaisawa, Nasir ne ke rattaba hawabin ban hakuri Alhaji Hamza ya gama karantarsu duka da jinsu sannan ya gyara zama yana faɗin" To duk na ji bayanan ku, abin da nake son sani shi Mansoor ɗin ne ya aiko ku, ko kuma kune ku ka aiko kan ku? Daga yanayin yadda suke magana ya sa ya fahimci ba shi ya turo su ba. Sai kawai ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Me ya hana shi zuwa da kansa ya yi bikon matarsa? mu'azzam ke faɗin saboda baya gari sun tafi buga wasa. Sai kawai Daddy ya ce"Shike nan kun gama naku bangaren a matsayin ku na abokan sa na amana kuma an gode muku, abin da nake  so daku shi ne ku cire bakin ku a wannan maganar shi dai shi ne mijin Mimi in har kuma yana sonta zai zo ya zauna a gabana kamar yadda kuma kuka zo kuka zauna a gaba na.". Sun san gaskiya Daddy ya faɗa shi ya sa su ka kasa masa musu hakanan jiki ba ƙwari su lka yi masa sallama su ka fito daga gidan a hanya Nasir nata faɗa yana faɗin" Wallahi ni na cire hannuna kuma abin da Baban Mimi ya faɗa mana gaskiya ne, akwai bangaren da mu ba mu isa mu gyara masa ba sai in har ya gyara da kansa." Ahmad ya ce" Wannan gaskiya ne, shima zuwa yanzu yakamata Aji ya san ya girma ya daina wannan taurin kai." Makama kuma ya karɓe da faɗin" To wai ba ya son ta ne? In bai son ta ya sake ta kawai kowa ya huta tun da shi girman kansa da jin kansa ya sa har yau bai gane annabi ya faƙu ba."   Suna tafe ne a motar Mu'azzam, suna wannan mganar shi dai Mu'azzam ya ma kasa mgana Ahmad ya ba da shawaran duk in da Aji ya k a neme shi cikin dare su gayamasa halin da ake ciki. Mu'azzam ya ce yana Camp ɗin su nan da nan suka juya mota zuwa cikin gari. Aji na cikin ɗakinsa aka sanar da shi yana da baƙi ya ɗauka Mu'azzam ne sai da ya fito kawai ya ga su Nasir bai yi mamakin ganinsu ba, Sanin halin da ake ciki. Waje ya samar musu suka zauna saman wasu fararen kujeru Da Ahmad kaɗai suka gaisa Nasir ya fara masa masifan ashe bai ji shawarwarin da ya basa ba. Kai tsaye Aji ya ce"Naji mana, amman sai zuwa gaba zan yi amfani da su" Cikin mamaki ya ce"Saboda mene ba yanzu ba? Aji kuma ba tare da tunanin komai ba ya ce"  To ba ka ga Mimin ba ta nan ba ne? Ka bari sai ta gaji da yajin da ta yi ta dawo tukunna." Gabaɗayansu baki suka saki suna kallonsa Makama ne ya daki kafarsa lokaci ɗaya yana faɗin" Kana tunanin za ta dawo ne ba tare da ka je ka ba ta hakuri ba? Cikin kwarin gwiwa Aji ya ce"Of course.". Sai kawai Makama ya yi wata dariya kafin ya ce" To in ma kana wannan tunanin tuntuni ya kamata ka daina, yanzu haka daga ganmu nan daga gidan su muke, mun je gidan hajiya Mimi ba ta bari mun ganta ba Hajiya ta turamu wajen Babanta tsohon Sanata, yanzu haka daga gidansa muke muka yo nan wajen ka."   Cikin mamaki Aji ya ce"Me ya sa kuka je? Na ce ku fita daga wannan mganar." Mu'azzam ya ce"Yaya me ya sa za ka ce mu fita daga mganar nan? Ko kasan har an kwashe kayan Anty Mami har matar Saddiqu ta tare a ɗakin ta tun jiya." Aji ya ƙurama Mu'azzam ido gabansa ya faɗi amman bai nuna ya razana ba sai ma kai da ya kauda kafin ya ce" Wannan duk ba matsala ba ne, in ta dawo ba za ta rasa wajen zama ba" Nasir baƙin ciki ya kusa kashe shi. Da ya sa kawai ya miƙe ya na faɗin"Ku kyale shi ku zo mu tafi, abin da muka yi maka ba saboda kai muka yi ba. Saboda hallacin zaman tare da kuma ƙaninka Mu'azzam, mun je babanta ya ce mun gama namu, in har kana son matarka sai ka shirya ka je da kanka ka ramkwafa ka roke shi, itama Mimin wlh ba za ka same ta sauki ba, in kana tunanin za ta dawo saboda tana sonka ne to ka yi ma kanka ƙarya. Gwara ma ka farka daga wannan mafarkin naka da ba ka da ranar farkawa, in ka tsaya wannan jinƙan kan naka na rantse da wanda raina ke hannunsa  za ka iya rasa ta rasawa na har Abada." "Nasir..!   Aji ya miƙe ya faɗa a fusace yana nuna Nasir  shi kuma ko a jikinsa sai ma juyawar da ya yi ya yi tafiyarsa, Makama ma ranshi ya ɓaci shima bayan Nasir ya bi sai Mu'azzam aka bari da Ahmad suna tausan Aji, wanda ransa ya ɓaci wai Nasir na gaya masa zai iya rasa Mimi na har abada. Cikin haushi ya ce"To sai me in ba ta dawo ba? Ai igiyar auran na hannuna ba sai na ga ta tsiya ba, Au  so suke sai na je na duka Ina veeging ɗin su sannan matata za ta dawo? Lalle ko sai dai ta cigaba da zama a gidansu da aurena a kanta ba in da zan je." Ya ƙarishe faɗa cikin tsawa sannan kamar Kabubuwa haka ya shige cikin Camp ɗin ɗakunansu ya bar su nan. Jikinsu suma a sanyaye suka fito, ba su ga su  Nasir ba sun yi gaba sun fara takawa da kafafasun kafin ma Mu'azzam da Ahmad su shiga mota su cin musu sun tare mashina sun hau kowa ya yi hanyar anguwar shi rai ɓace, Mu'azzam ya rasa yadda zai yi bai ji daɗin abin da ya faru kwata kwata ba. Daga abun alheri sai kuma ya koma haka. Yaya Mamsoor wani lokacin bai san abun arziƙi ba.   Sai da ya maida Ahmad gida, Sannan ya dawo nan gidan Mansoor ya kwana, amman sai da ya kira Hibba ya ce ta shirya da Asuba za su wuce. Haka ko aka yi ana Idar da sallah suka ɗauki hanya sai dai su bar ma Inna Juinor, saƙon test nassges ya turama Aji na cewa ya wuce tare da Ahmad suka tafi  ya sauke shi a kano daga nan ya hau motar Kaduna. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3004* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Tun da safen Aji ya ga saƙon ƙaninsa Mu'azzam amman bai kira shi ba sai can dare lokacin sun sauka gida suna Hlhuce Gajiya.  Bayan sun gaisa da tambayar hanya ba jiran komai kawai Aji ya kashe wayarsa, Daman lokacin suna zaune ne a falo suna cin abinci lokaci ɗaya suna kuma tattauna maganar shi da Hibba.   Da ya ga bai masa mganar ba ne ya sa sai shi ya ƙara kiran shi, kamar ba zai ɗauka ba sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga lokaci ɗaya yana faɗin" Ka yi mantuwan kuɗi ne a gidana? Sai da Mu'azzam ya yi yar dariya kafin yace"A'a daman zan gaya maka Junoir na wajen Inna muka bar shi." "Good.." Aji ya furta lokaci ɗaya kafin ya gyara kwanciyarsa yana gidansa ne a kwance amman kwanciyar ma ba ta yi masa daɗi a kwanaki nan baya samun ishashen barci sai dai ya kwanta ya yi ta Juye juye yana faman tunane tunane.   Shurun da ya ji Mu'azzam ya yi ne,  ya sa yasan cewa akwai mgana a bakinsa, to daman ai yasan akwai mgana a bakin Mu'azzam, shi ya sa ya ƙara gyara kwanciya yana faɗin" Me kake son faɗa ne Mu'azzam? Mu'azzam ya yi shuru yana tauna mganar, Hibba na gefensa tana masa inkinya da hannu akan ya yi masa mgana domin ta gaya masa shi kaɗai ne zai iya gaya ma Yayan na shi gaskiya ya ji, ya sanar da shi Inna tana fushi da shi, kuma fushin uwa bala'i ne gare shi gwara tun farko ya je ya neme ta gafara in yana so ya ga da kyau.   "Uhm! Ina sauraran ka, ko kunya ta kake ji ne? Aji ya faɗa cikin zolaya saboda Mu'azzam ya saki jikinsa, shi kansa ya san yana bukatar a yi masa faɗa. Saboda yana aikata wasu abubuwan da ya san mutane da dama ba sa jin daɗin sa, sannan Mu'azzam ƙaninsa ne duk duniya ba shi da wanda ya fisa kusa da shi irin shi. "Yaya Mansoor, kan maganar abin da ya faru ne, kasan dai ba ka kyauta ba ko? Inna na fushi da kai, sannan ka ɓata ma su Nasir rai ya kamata ka kira su ka ba su hakuri."   Aji ya yi shuru kafin ya ce"Zan dai iya zuwa na duƙa na ba ma Inna haƙuri tunda Ita ta haifeni, amman naganar na ba su Nasir haƙuri bai ta so ba, domin ba ni na aike su ba."   Mu'azzam bai yi mamaki ba sanin halin yayan na shi sai kawai ya ce"Ni na ba su  hakuri tunda ni na gayyace su a lokacin.' Aji ya yamutsa fuska kafin ya ce"Allah ya ƙara, kai ma rashin jin mgana ta ne, me na gaya maka? Sai kawai Mu'azzam ya ce" Maganar ita Anty Mami fa? Ya kamata ka je Yaya bai kamata wannan abin da da kake yi ba." Aji ya yi jim kafin ya ce" Itama za ta dawo in sha Allahu." "Yaushe? Ba fa za ta dawo ba sai ka je ya kamata ka darajata, sannan iyayenta su gane ka daraja ƴar su" Aji ya yi gajeren mirmishi kafin ya ce" Daman ai ta tafin ne saboda na je gidansu ina roƙo? To ku kyaleta ta yi ta zama mana waya damu? Mu'azzam na shirin ƙara mgana. Kawai ya ji Yayan na shi ya ce"Kai ni fa barci nake ji, Kai ba ka gaji ba ne? Maza ka je wajen matarka sai da safe." Bai ba shi zarafin mgana ba kawai ya katse  wayarsa ya bar shi nan sake da baki, Daman Hibba ta shiga ciki ne ta ba shi waje su yi mgana sai ga shi ta dawo yanayin da ta ganshi yasan ta san abin da ya faru. "Ba'a dace ba ko?   Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ja numfashi ya ce" Ya ce zai je ya ba ma Inna hakuri, amman ba zai ba ma su Nasir ba. Maganar Anty Mami kuma ya ce za ta dawo da kanta amman shi ba zai je gidansu yana roƙo ba." Hibba ta kaɗa kai kafin ta ce" Ina mamakin yadda yake da ƙwarin gwiwan a kan wai Mimi za ta dawo da kanta? Ina tsoron wannan jin kan na yayanka ya tashi a banza Mimi ta ja shi kasa warwas. Sannan in da ta na ɗaukan wayana sai na gayamata kada ta sake ta koma sai ya raina kansa." Wani kallo ya yi mata, kamar zai yi mgana sai kawai kuma ya fasa, ya ta shi ya shige ciki jikinsa a sanyaye Hibba ta bi shi da kallo gaskiya magana ce fa sai an faɗa Yaya Mansoor ɗin nan ya cika jinkai da Isa, shi wai ya na takama da cewa Mimi na son shi wato ba za ta iya rabuwa da shi ba. Daman illah ne babba mace ta nuna ma Namiji soyayya mai tsananin da za ta ya iya yin komai saboda shi kuskure ne babba ga Maza ma irin su Mansoor da ba su san darajan da ƙimar da Ubangiji ya ba ma mace ba. Tana tattara kwanukan da suka ɓata ne take wannan tunanin, haba ka yi laifi amman taurin kai da jinkai su saka mutum tunanin kai ne ma za'a ba ma hakuri haka ake yi tsakani ga Allah, gwara Mimin ta sha zamanta sai ta ga karyan tsiya ita dai tasan wlh shima yana sonta in ya ga zai iya rasa ta dole dai ƙanwar na ƙi. ******** *Bayan kwana uku.* Kimanin Mimi na da kwanaki takwas kenan a gidan Hajiya, Rukky ba ta sani ba saboda Bibi ba ta sani ba domin haushi ya sa Makama bai gaya mata ba, Sannan Mimi na cikin hutun ta ne, ba ta zuwa wajen aiki kuma ita ba ta dame ta a waya ba tunaninta yanzu ba da ba ne, Mimi na da aure ita ba ta san ta na yawan kiranta saboda wannan mara mutumcin mijin nata.   Ranar tana wajen aiki Na Misau na zencen Mimin sai ta ɗaga waya ta kirata amman Sai ba ta same ta a waya ba sai ta yi tunanin in ta tashi daga wajen aiki za ta biya ta dubata, la'asar ta baro ma'aikantarsu ta hau adaidaita zuwa Gidan Wanzamai a kofar gida ta haɗu da Baba Danjuma a lokacin su ka gaisa, shi kuma bai yi mata wani bayani ba sai da ta shiga gidan, abin da ya bata tsoro shi ne ganin wata a ɗakin Mimi, Saboda lokacin da ta shigo Inna na ɗakinta, Walida kuma ta tafi makarantar Islamiya. Shi ya sa ta shiga ɗakin Mimin kai tsaye sai kawai ta ga komai ya sauya har da mai ɗakin ma gabaɗaya.   Cikin mamaki ta ke kallon Maaesha kafin ta kara komawa baya a tunaninta ko ta yi makuwan shashen ne. Sai dai ta ƙara ganin tabbas nan ne. Cikin mamaki ta ce"Ko na yi makuwa ne? Ba nan ne ɗakin Mimi matar Mansoor ba? Maeesha na zaune ta na cin Aya ta yi waata yar dariya kafin ta ce" A da ba, amman yanzu ya zama ɗakin Maeesha matar Saddiqu." Rukky ta yi shuru tana kallon Maeesha cikin tarin mamaki, amman ba ta sake mgana ba gabanta na faɗuwa ta fita daga ɗakin rike da wayarta tana ƙara kiran layin Mimi sai kuma ta shiga dalilin da ya sa ko ɓarayin dakin Inna Meri bata kallah ba. Allah ya taimake tana fita sai ta ga mai adaidaitan da ya kawo ta bai tafi ba ya tsaya mgana ta waya sai kawai ta faɗa ciki dai dai lokacin da Mimi ta ɗaga kiran Rukky. "Baby Ruƙayya.."   Mimi ta faɗa cikin sanyin murya, Ita kuma Rukky Kamar zuciyar ta za ta fito waje ta ce"Fatima kina ina ne? Na zo gidan mijin ki a ɗakin ki na ga wata, ko kin ta shi ne ban sani ba? Mimi ta yi dariya daga bangarenta kafin ta ce"Eh! Ina gidan Hajiya ki zo ki same ni." Cikin faɗuwan Gaba Rukky ta ce"Mimi me ya faru ne? gaba na faɗuwa." "ke dai ki zo, ba komai sai alheri." Daga haka ta katse wayar,  Rukky gabaɗaya sai da jikinta ya yi sanyi, mai adaidatan na mganar Hajiya komawa za mu yi? Tace Eh amman yanzu anguwan Hashidu Estate za su je, nan da nan ya juya kan adaidata suka nufi gidan su Hajiya.   A Gaggauce Rukky ta shigo, gidan Hajiya na falo Baaba Uwani na kitse mata kanta da ya cika da farin ga shi. Tsabar ma ruɗewa da gaisuwan da tambayan Mimi duk a lokaci ɗaya ta yi su, Hajiya ta ce tana ciki ta shiga ta same ta ai ko har da gudunta ta wuce Hajiya da Baaba Uwani suka bi ta da Kallo Hajiya ta girgiza kanta kafin ta ce"Ina ga ta ji labarin Binta na gida" Baaba Uwani ta ce"Hajiya yanzu ba za'a gyara lamarin nan ba? Hajiya ta ce" To Hamza ne kan batun ya ce na cire bakina, sai in har Mijin Binta ya tako da kansa sannan za'a yi maganar gyara." Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" kuma bai zo ba ko? Ni fa kamar sau ɗaya ma na taɓa ganinsa tun bayan auran nan." Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Zuwan na shi bai wuce ɗayan ai zuwa biyun." Baaba Uwani na son cigaba da Magana amman Hajiya ta kauda mganar ta fara mata zencen mutanen can garin su na Akko sai su saki hiran Binta suka kama ta mutanen gida.   Mimi na kwance ta na latsa wayarta Rukky ta faɗo ɗakin cikin damuwa. Kamar ta faɗa kanta haka ta faɗa saman gado tana faɗin" Kar dai ki faɗa min kun rabu ne? Mimi ta miƙe da sauri ta na faɗin" Rukky me ye haka? Kin bani tsoro wlh." Ba ta damu ba sai ma gyara zama da ta yi ta na faɗin" Don Allah ki gayamin abin da ke faruwa ko zan samu natsuwa." Mimi ta yi shuru kafin ta ce" Eh mun rabu amman ba mu rabu ba." "Ban gane ba? Rukky ta tambaya cikin zullumi. Sai Mimi ta gyara zama tana faɗin"Rukky labarin na da tsawo amman takaice shi ne na dawo gida ne. "Saboda mene?   Ta tambaya tana mai tsare Mimi da ido, ita kuma ta kauda kanta saboda Idanuwanta sun fara tallah kwalla, babban baƙin cikinta yadda ta fahimci ba ta da wata faraja a wajen Aji kwananta takwas da dawowa Gida amman ko kiran ta bai yi ba, ba Saƙo ba zuwa kenan ya nuna ma kowa cewa bai Damu ba da zamanta da tafiyarta duk ɗaya ne a wajensa. Kawai sai ta saka ma Rukky kuka, ita kuma baki buɗe take kallonta kafin ta ce"Mimi me ya faru ne? Ki bar kukan nan ki yi min bayani domin Allah." Miƙewa Mimi ta yi zuwa gaban window ɗin da ke ɗakin lokaci ɗaya tana faɗin" Ruƙayya ban taɓa tunanin hukuncin da na yanke ma rayuwata na auran Aji kuskure ba ne sai yanzu, na yi gaggawa me ya sa bayan na ciza ban tsaya na hura ba? Rukky Aji ba ya sona iya wancan Soyayya na yarinta ta gushe a zuciyarsa ya aure ne kamar zai rama abin da Abi ya yi masa a shekarun baya, Rukky Aji baya sona tunda na aure shi bai taɓa kama hannuna da gangan ba sai dai bisa Kuskure." Ta yi shuru ta na sauke numfashi Saboda kuka ne ke cin zuciyarta.   Rukky ta yi kasaƙe tana sauraran Mimi cikin mamaki ta ce" What? Hoto kike a wajen sa? Mimi ta Juyo tana fuskantar Rukky kafin ta koma ta zauma kusa da ita, ita kaɗai ce aminiyarta sai ta ji tana son gayamata abin da ya faru tun farko har zuwa karshe.. Sai ta samu kanta da fara ba ma Rukky labarin auran da Aji har zuwa abin da ya Faru ta dawo gida amman ta sakaya yadda ya ke cin zarafin iyayenta ta dai nuna mata ba shi da zuciya mai kyau tunda bai san afuwa da yafiya ba sannan ya na amfani da abin da ya faru yana mu'amalanta da shi. Cikin Kuka Mimi ta ce"Rukky da kansa ya ce na tafi din ya nuna bai damu ba, yau kwana na takwas a gidan nan bai kirani ba sannan bai zo ba,  ƙannensa ma da suke zuwa da abokansa wah sun yi ne domin suna son aure da shi ba saboda shi ba. Na rasa wani irin miji nake aure? Wlh Ajj ya sauya a baya ba haka yake ba Rukky, ina son mijina amman ya zama dole na yi nesa da shi ko zai fahimci Muhimmancina a rayuwarsa."   Ta ƙarishe faɗa tana gunjin kuka, Tausayinta ya kama Rukky sai ta kama ta Rumgume tana bubbuga bayanta alamun lallashi, har sai da ta yi shuru sannan ta dago kanta suna fuskantar Juna Rukky ta fara faɗin" Na ji daɗin yadda kika nuna masa ke ma macece, sannan na ji daɗi da Daddy ya goya miki baya sannan na ji daɗin yadda baki saurari ƙannensa da abokansa ba, Ire iren mijin ki Fatima yan burauba ne hanyar Sauƙi ba ta bille musu sai an biyo musu ta bayan gida, Na fahinci wlh ƙarya yake yi yana sonki in baya sonki ba wata Hajiya ko Mommy da yake gani da mitumcin da saboda su zai aure ki. Sai dai tsabar bakar zuciya da Tunanin banza ya sa yake ta gasa miki aya a hannu kuma ya yi anfanin da cewa kina son shi duk kashin da zai yaɓa miki ba za ki iya ɗaga kai ba, To Wlh ya yi karya har shi ya isa? Mimin ce zai yi ma wannan cin zarafin? Kinga share hawayen ki na rantse da wanda raina ke hannunsa sai Aji ya zama a tafin hannun ki, sai Aji ya nuna ma duniya kece mace mafi daraja a wajensa, Wlh tallahi sai kin rama kwatakwacin abin da ya yi miki kila ma fiye da wanda ya yi miki. Sai ya wahala sai ya raina kansa sai ya yi laushi sai ya yi la'asar ba tun farko ya ki sharen masallaci ba, to ai yanzu ina baki tabbacin zai yi na kasuwa sai mun saka shi ya ƙasƙaatan da kanshi in da yake tunanin ya fi karfi sai Aji ya zo ya duka yana miki magiyan da roƙon ki dawo cikin rayuwarsa ke kuma a lokacin kike da damar rama duk abin da ya yi miki har ma fiye da hakan."   Har Rukky ta gama maganarta kallon ba ki da hankali Mimi take yi mata. Kafin ta girgiza kanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ba ki da hankali Rukky Ajin ne duk zai zauna na yi masa haka? Ke wai duk ba ki saurari labarin da na ba ki ba ne?  Nan matar ƙaninsa Hibba ba abin da ba ta ce na yi ba amman daga karshe me na samu? Bayan cin mutumci da wulaƙanci.? Rukky ta bigi Kafaɗan Mimi  lokaci ɗaya tana na faɗin" ke dilla gafara can, kina wani abu kamar  ba mace ba, wa ya gaya miki ba abin da kika samu? Kin samu mana ke ce ba ki fahinta ba amman tabbas Aji na sonki so kuma mai tsananin da shima ba zai iya rayuwa ba sai dake. To tunda ya yi kuskuran bari mu ka sani ya shiga uku, Ajin banza ajin wofi, ai sai dai ya cigaba da amsa wannan sunan a waje amman a gabanki sai dai shi ya zama Ajin waje ke ki zama ajin cikin gida, na yi rantsuwa ko Kaffara ba zan yi ba yana can cikin tunaninki ya tsaya ne yana tunanin za ki neme sa ku daidaita, yana tunanin kina son shi saboda haka ba za ki iya dogon fushi da shi ba to ya yi kuskure, tabbas sai kin rama tabbas sai ya gwammaci YA CIZA ya hura kafin ya ƙara aikata laifi mai kama da wanda ya aika miki a baya tabbas zai gane kuren shi duk wannan jin kan da bakar zuciyar da wani jin haushi sai ya sauke shi, shi ɗin banza da Wofi tunda dai yana son mu ai kuma ya tashi  aiki."   Irin yadda Rukky ke mgana cikin ƙwarin gwiwa ya sa Mimi sai da ta yi dariya kafin ta jinjina kai tana faɗin" Ruƙayya ba irin su Aji ake yi ma haka ba, Da bakin shi fa ya ce ba ya sona alfarman rokon su Hajiya ya sa ya aureni, to a haka ne kike tunanin wai zo ya na roƙo na? Rukky ba ki san Aji ba ne shi ya sa."   Rukky  ta kalli Miki cikin tausayawa kafin ta murmusa lokaci ɗaya tana cewa"Ƙarya fa yake yi, duk kalaman da ya faɗa miki karya ne, kuma zai ƙaryata kansa da kansa a gabanki nan ba da jimawa ba." Mimi ta karkace kai kafin ta ce"Rukky ba na tunanin haka, ni nasan wanda nake aure Rukky" Rukky ta ce" Ki yarda da ni, ni kuma na yarda da kaina, amman kafin nan ya kamata ke ma kinsan kuskuren ki a kan wannan lamarin gabaɗaya." Mimi ta kalli Rukky amman ba ta yi mgana ba sai Rukky ta kama hannuwanta ta rike lokaci ɗaya tana faɗin"In har kin yarda dani to ina ba ki tabbacin Aji zai zo da kafarsa, sannan zai ta bulayin neman ki, zai iya yin komai saboda ke Mimi." Mimi ta yi shuru ta na kallon Rukky itama ta na kallonta na wani lokaci kafin Mimi ta Sauke ajiyar zuciya tana faɗin" Shike nan na aminta dake, amman sai na k..   "Shii..., Ki yi shuru kawai, kawo kunnen ki ji."   Rukky ta faɗa dai dai tana jawo kunnen Mimi ta yi mata mgana na tsawon mintina goma sannan ta sake ta. Sannan lokaci ɗaya suka koma suna kallon juna, Mimi ta ɗage giranta sama kafin ta ce" Are u sure Ruƙayya? Rukky ta amsa mata da ceewa"very very sure.." Hannu Mimi ta ba ta suka tafa lokaci ɗaya tana  faɗin" Yoh have my word, zan yi gwargwadon abin da kika ce." Ita kuma Rukky sai ta aika mata da Jinjina tana dariya. Mimi ta sauke numfashi, kafin ta ce"Sai yanzu na ji na samu yar natsuwa, ina jin ki faɗamin kuskurena, ni kaina nasan ai na yi gaggawa." Rukky ta gyara zama L lokaci ɗaya tana faɗin" kuskuren ki guda ɗaya ne, na yadda ki ka nuna masa kina tsananin son shi, za ki iya komai saboda shi, kin nuna masa sai da shi za ki iya farinciki, r da wannan damar ya samu yana miki yadda ya ga dama, da wannan damar ya ke tunanin zai iya yi miki komai ki shanye, a tunaninsa saboda kina son shi zaki iya jure duk mganganun da zai ga ya miki, yana tunanin ko dukan ki yake yi  ba za ki iya ɗaga kai ba. Shi Namiji ba ka nuna masa ka mutu saboda Son shi, ko kana son shi sai ka koyi iya Sarrafa soyayyar ta yarda ba zai zama makamin da zai samu galaba a kan ki ba, amman ko a yanzu lokaci bai kure miki ba za ki iya gyara abin da ki ka ɓata tun farko." Mimi ta sauke numfashi kafin ta ce" Tabbas kin yi gaskiya,  da wannan damar ya samu galaba a kaina ya ke tunanin ko ni ce ya yi ma ba dai dai ba sai dai na yi hakuri na bi shi tunda Ina son shi, to ya yi kuskure daga yanzu zai fahimci hasashensa ba gaskiya ba ne." Rukky ta ba ta hannu suka tafa lokaci ɗaya tana faɗin" Thats my Girl."   Zuwan Rukky ba ƙaramin garinciki ya kawo ma Mimi ba har su Hajiya na Jiyo hiransu da shewan su. Sai bayan isha'i Rukky ta tafi bayan ta ci abinci ta yi sallah Sannan su ka yi sallama da Mimi akan sai sun yi mgana ta waya su kaɗai suka san irin muguntar da suka shiryama Bawan Allah Baban Inna. A baya ba ta cika barin wayarta na awa huɗu a kunne ba amman yanzu da shawaran Rukky da ta ce ta daina kashe wayarta tun ba karya ta yi ba. Ta riƙa barin wayarta a kunne amman kada ta amsa kiran yan koran Aji ta bari shi Ajin da kansa ya kawo kansa sannan. Shi ya sa har Mu'azzam da su Nasir ta rufe su ko sun kirata ba za su sameta ba a daran ma sai da su ka yi waya da Mommy itama abun ya ba ta haushi da Mimi ta ba ta tabbacin Mansoor bai kira ba kuma bai zo ba. Cikin ɓacin rai ta ce"Na fara yarda da Maganar Alhaji Hamza, in bai kira ba kada ki kira shi in bai zo ba, ba za mu bi shi ba sannan ba za ki koma ba in watanni uku suka cika kotu zan kaisa ya sauwaƙe miki tunda bai san hallaci da mutumci ba." Kenan itama Mommy ta fara Dawowa daga rakiyarsa Hajiya dai yar cewa a bi komai a sannu. ******* Har aka shafe wajen sati biyu da komawar Mimi gidan Hajiya, Ba Mansoor ba ƙeyarsa bai ƙara tako kafarsa gidan Inna Meri ba, ita kuma daman ta ce ta cire hannunta a kansa. Baba Ɗanjuma ne yaga rashin jankalin Mansoor ya yi yawa sai ya kira shi a waya yace duk abunda ya ke yi yau da daddare ya zo gida ya same shi. Sai ya amsa masa da toh, shi kuma daman Kunyar Inna meri yake ji, yana so sai ta fara hucewa sannan yana fargaba ya shigo gidan ba Mimi a cikin shi. Har gabansa faduwa yake yi in ya tuna bata nan bayan ganinta a cikin gidan ƙarƙashin Inuwarsa Kuzarinsa har karuwa yake yi in ya shigo gidan ya ganta, yana so ya kirata amnan kuma yana tunanin in ya kirata kenan ta yi nasara shi ya sa yake iya sarrafa damuwarsa amman shi duk a tunaninsa Mimi za ta dawo domin kanta bai taɓa tunanin za ta iya ba shi Wahala ba.   Wajajen karfe tara ya zo anguwan a mashin ɗin haya saboda motarsa sai an mata juye, mashin kuma duk ya yi kura tunda ya daɗe bai yi amfani da shi ba, Sai kawai ya hayo na haya ya zo a kofar gida ya iske Baban Danjuman na jiran shi, ya san akwai mgana aiko ya sha faɗa kamar zai dake shi yana kuma nuna masa illar abin da ya aikata Mahaifiyarsa na fushi da shi amman ya nuna bai damu ba. Kansa na ƙasa ya ce"Na damu mana Baba, kawai dai na ga ranta Inna  ya ɓaci sai na bari a ɗan kwana biyu in ta ƙara hucewa sai na zo na bata hakuri." Baba kamar ya kai masa duka cikin takaicinsa ya ce" Haba Baban inna ina tunaninka yake ne? Ita uwa in ta yi fushi ba ta bukatar a bata lokaci Mansoor, a lokacin za ka yi kokarin kaga ka nemi gafaranta yanzu adadin kwanakin da ka ƙara adadin ɓacin ranta a kanka, Maza mu je cikin gida ka duka ka nemi gafaranta." Kafa da kafa Baba Ɗanjuma ya tasa shi har falon Inna Meri ta na zaune tana kallon Tibi tunda akwai wutar nepa. Walida na kwance kan kujera tana game da wayar Inna. Sautin waƙa kuma na tashi daga ɗakin Matar Saddiqu haka take duk dare ta hana mutane sukuni. Bayan sun shigo Walida ta mike tana gaishe su Baba kaɗai ya amsa ban da uban gayyar, Inna Meri ko mijinta kaɗai ta yi ma sannu da zuwa Mansoor ko kallo bai isheta ba. Sun zauna kenan Shi Baba a saman kujera shi kuma Aji a ƙassn cafet.   "Daga ina wannan sautin ke fitowa?   Baba ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Inna Meri wacce ta yi kamar ba ta ji ba,Junoir ne kan jikinta ya yi barci shi kawai ta gyara masa kwanciya ta cigaba da kallon shirin gata nan gatan nan ku da ake haskawa a Karamchi tibi. Walida ce da ta kawo musu ruwa ta ce"Baba ɗakin Matar Yaya Saddiqu ce wlh tunda ta dawo wannan bangaren ba ta barin mu yi barci da saka kide kiɗe. Da Inna ta yi mgana sai cewa ta yi nan gidan Mijinta ne ba wanda ya isa ya takura mata." Mansoor ya ji ransa ya baçi sai dai bai yi mgana ba ganin Baba ya yi shuru kawai bai ce komai ba Domin magajiya ta fi karfinsa har barazana ya yi mata na saki amman ta nuna bata damu ba sannan Inna Meri ta ce kada ya hana natar Saddiqu tarewa domin Allah kar ya sake mgana shi kuma yana ganin darajan Inna shi ya sa ya yi shuru. "Je ki faɗa mata ta in ji ni na ce ta kashe sautin nan, ko ba ta san dare ya yi ba ne?   Baba ya faɗa cikin nuna ɓacin ransa, sai Walida ta amsa da toh,  har za ta fita Inna Meri ta dago tana faɗin" Walida dawo abun ki, kyaleta Mallam ai gaskiya ta faɗa nan din gidan mijinta ne, ni ban isa na takura mata ba." "To Inna ke sa'arta ne da za ta gaya miki haka? Ko ba ki isa ki ce ta daina abin da take yi ba ne?   Mansoor ya faɗa ransa bace, Inna Meri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce" ta isa ne shi ya sa ta faɗi haka, me ya sa zan damu?  duk wa ya ja min? Ɗan da na haifa ne da cikina ya sa na koma abun cin mutumcin acikin gidan nan tunda ko shima bai ɗauke ni wata aba mai daraja ba, to tunda ɗan da na haifa bai ganni  da daraja ba wa zai kake tunanin zai kalleni da daraja? Ta faɗa cikin jin ƙuna a cikin ranta. "Ki yi haƙuri Inna.."   Ta yi masa shuru kamar ba ta jisa ba. Sai da ya ƙara faɗin" Ki yi haƙuri inna don Allah ki yafe min." Sai a lokacin ta juyo tana kallon shi kafin ta ce" Haƙurin me kake ba ni? Ka min wani laifi ne? Ba ka min komai ba ta shi ka yi tafiyarka sabogiginka Allah ya yi albarka." Ta faɗa lokaci ɗaya tana kokarin ɗaukan Junoir da ke kwance saman jikinta, Da sauri Baba Danjuma ya ce"Ki yi haƙuri Meri ki tsaya ki saurare shi, tunda har ya gane kuskuren shi ya baki haƙuri domin Allah ki daina fushi da shi" Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba, Baban Inna na ta ban hakuri Baba Ɗanjuma na tayasa sai kawai ta ce"Ni fa ban riƙe shi ba. Har ga Allah na yafe masa Saboda ɓacin raina zai iya jefasa cikin bala'i, hannuna ne na ce na cire a kan rayuwarsa ya je ya yi duk rayuwar da ta yi masa dai dai." Baba Ɗanjuma ya ce"To baki hakuran ba kenan? " Wlh na yafe masa tuntuni a cikin raina." "To in har kin yafe masa ina nema masa alfarman ki shirya ki je gidan Hajiya ki yi masa bikon matarsa."   Dariyar nishaɗi inna ta saka kafin ta ce"Au an zo wajen kenan? Tana gama faɗin haka ta mike ta sunkunci Junior lokaci ɗaya tana faɗin" Ai ya ce ba ya sonta shi ya sa ya ce ta tafi gidansu, in ya ga dama ya sake ta duk ban damu ba ni abu ɗaya ya dame ni yadda ya ɓatamin suna ya sakani jin Kunyar yarinyar nan da Iyayenta, Amman ni ban damu da duk abin da ya aikata ba wannan rayuwarsa ce abin da ya fi masa daidai shi zai yi." "Ki yi hakuri Inna." Abunda Kawai Mansoor ya ce kenan, Baba Danjuma a ka bar shi da cewa" ba ki dai yafen ba kenan? Inna Meri ta ce"Na yafe masa, amman wallahi tallahi kafata ba za ta taka gidan su Binta da sunan yi masa biko ba. Shi ne ke auran nan in har ya na son natarsa yana da Kafa kuma ya san in da zai sameta amman in ni yake Jira to ya daina jirana na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, ba in da zan je" Tana gama faɗin haka ta shige cikin uwar ɗaka in da Walida ke kwance ta kasa kunne tana ganin Inna ta shigo sai ta yi barcin karya. A ranta ko daɗi ta ji wlh kada Inna ta je, shi da ya aikata barnansa ya je ya gyara da kansa.   Ganin Inna ta shige ya sa Baba ɗanjuma ya kallesa kafin ya ce"Tunda ta na ce to ba za ta je ba, ka shirya ka je ka yi bikon matarka ka ji ko? Cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu Baba., daman ai tsakanina da Mimi ba saki, amman za ta iya yin yaji wani lokacin in bukatar hakan ya ta so." Kai tsayen shi ya faɗi haka, kuma har acikin zuciyansa haka yake nufi. Sai Baba Danjuma ya ƙara faɗin" Ko kuma in za ka je ka min mgana sai mu tafi tare" Da sauri yac e"A'a Baba kada ka damu ba sai ka je ba." "Ka tabbata? Sai ya gyaɗa masa kai, shi kuma sai ya dafa kaffaɗansa kafin ya ce"Sannan ka yi hakuri akan abubuwan da suka faru, kasan halin magajiya ita ta saka rigimar dawowar Matar Saddiqu ɗakin Fatima, yanzu in za ta dawo a ina za ka ijiye ta? Mirmishi ya yi kafin ya ce"Wajen zaman ta ba matsala ba ne Baba, bakomai na gode ƙwarai Allah ya ƙara girma." Baba Danjuma ya amsa da Amin bai daɗe ba ya ce zai tafi 30k ya ba ma Baba ya ce Auwalu zai kawo kayan abinci na wannan Watan Baba Danjuma nata godiya har ya tafi Inna Meri ba ta fito ba, ga shi ya na jin yunwa amman kuma yasan yau Inna ba za ta basa abincin ta ba. Da ya fito ya tsaya jim ya na kallon ƙofar ɗakin Mimi, na wani lokaci sannan ya kaɗa kai ya fice, dole zai ɗauko mataki daga Saddiqun har matarsa ba su isa su raina masa uwa ba.   Bayan fitan sa ma Baba Ɗanjuma da kansa ya tsaya kofar ɗakin ya yi ma Maaeesha mganar ta kashe wannan Sautin ba ta da yadda za ta yi dole ta kashe, Saddiqun baya nan ya koma Lagos daga nan ya shiga ɗakin Magajiya ya ja mata kunne ya ce ta yi mata Surukarsa mgana wlh baya son diɓan albarka ta daina takura ma Meri da daddare da sautin banza in ba haka ba wlh za ta bar masa gida. Magajiya ta buga shewa ta ce saboda Meri zai kori matar ɗansa? To lalle kuwa sai dai itama Merin ta bar gidan. Shi dai bai biye mata ba ya fice zuwa ɗakin sa ya barta tana Kumfar baki ko kunyar Mariya dake ɗakin ba ta ji.   Mansoor Aji kuwa yunwa ta saka sai da ya biya ya siya nama da lemu sannan ya koma gidansa, rabonsa da  abinci tun eea ɗin da ya sha da safe. Sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci ya ɗora da lemu. Tunaninsa yadda zai tunkari Mimi ne, Dama tuni ya ke so  kiran ta amman ba shi da dalili amma tunda yanzu Baba ya yi mgana ya samu abun fakewa.   Yana kwance daga shi sai hajeren wando ba riga ya ɗauki wayarsa ya laluɓo Lambar Mimi da ya yi mata saving da LIFE PARTNER , Sunan ba iya rubuce ba ne har a gaske ma itace cikon rayuwarsa, ba wanda yasan ma sunan da ya saka mata wayarsa kenan hatta ko da ita kanta. Yana kiranta sau ɗaya ya dauka da rawan jiki za ta ɗauka sai ga shi sai da ya yi mata Missed call biyar ba ta ɗauka ba,  kuma shi ya san ba ta da ɗabi'an barcin wuri yana da tabbacin Idanuwanta biyu. Nan da nan wata zuciyar ta harzuƙa shi, kamar shi Mimi za ta yi ma wannan wulaƙancin? Sai kawai ya shareta bai ƙara kira ba amman kuma ya kasa sukuni har ya kwanta amman ya kasa barci yana ta juye Juye. Sai kawai ya sake ɗaukan  wayan ya ƙara kiranta har sau uku ba ta ɗauka ba. Saboda ɓacin rai har wani duhu duhu ya fara gani kawai sai ya shiga wajen saƙo ya rubuta mata haka.   "Ni ne za ki wulaƙanta Mimi? ni ko? To ya yi miki kyau."   Ya gwada ne domin ya samu tabbacin tana ganin nashi ko ba ta gani ba?   Hasaahen shi ya zama gaskiya domin ba daɗewa, sai ga martanin saƙon ta.   "Maganar saki ne? Kada ka damu za ka iya turomin ta text nassages, ko kuma ka aiko min da takardata gidan Hajiya ko wajen Daddy."   Idanuwansa har rawa suke yi da ya karanta ßakon Mimi, bai san lokacin da ya yi mirmishin takaici ba, lalle ma wannan yarinyar da shi za ta yi wasaa ko? "Ina jiran sammaci ne."   Abin da ya aika mata da shi kenan, amman ha wajen bayan awa ɗaya waya na hannunsa ya na gadi amman ba ta dawo masa da amsa ba. "Kin yi shuru? Ko kin fara karaya ne?   Haka ya sake turamata nan ma shuru. Sai ya koma ya sake kiranta kawai sai ya ji ta danna masa lamba busy. Wayar ya bi da kallo a fili ya furta" Kan uba can!" Haka ya faɗa, har ya na wani hararan wayarsa, wai shi ne Mimi ta kashe ma waya? Wasa wasa kasa sukuni ya yi yana kwance yana ta juye Juye ya kasa barci har cikin dare sai da ya tashi ya kara kiram Mimi ba ta ɗauka ba har asuba ma sai da ya kara kiranta ta kuma  ƙara danna masa busy Ransa ya kai kololuwar ɓaci. Yana kiranta yana Hargagi shi kaɗai. "Mimi ki ɗaga kiran kafin ranki ya ɓaci."   Amman ba ta ɗaga ba Daga karshe ma wayarta a kashe ya ji. Haka nan ya shirya ya tafi camp suna da morning traning, amman kowa ya gansa yasan ran maza a ɓace ne daga can gida ya wuce ya gaida Inna Meri amman tunda ta ce lafiya lau ba ta ƙara masa mgana ba haka ya gama zamansa Shuru kuma ga shi ya na jin yunwa amman Inna Meri ba ta bashi Koko da Kosan da ta yi ba,  har ya gaji ya yi mgana kaii tsaye Inna Meri ta ce ya kare kuma yana ganin shi ga shi a fulas tunda a gabansa ta juye. Daga nan yasan saamun Kwanciyar hankalinsa da kuma ganin farin cikin Inna shi ne ya je ya samu Mimi su yi mgana.   Yana durkushe a gaban ta ya ce"Inna yau zan je na samu Mimi mu yi mgana za ta dawo in sha Allahu."   In dutse na mgana to Inna Meri ta yi mgana haka ya kwashi sanyin jikinsa ya fice. A tsakar gida ya ga Maeesha kazama ce ta fito daga ɗaki ta na tsintar da yawu nan kofar ɗaki, kusan amai ya tashi yi kallo ɗaya ya yi mata ya fice ganinta ma ya sa ya tuna da Maganar da ya ce zai yi ma Auwalu. Yana hanyar komawa gida ya kira shi ya gayamsa cewa ya ja ma ƙaninsa kunni ya tsawatar ma matarsa domin Inna Meri ba sa'arta ba ne, in kuma bai iya ja mata ba to shi zai yi abin da rayuwaka za su ɓaci, Auwalu ya ba shi hakuri ya ce zai yi mgana da Saddiqun. Shi daman yasan wannan zaman ai ba za'a wanye lafiya ba.   A daran ya so zuwa gidan Hajiya da fakewar ba zuwan kanshi ba ne saboda Inna ne da Baba Ahalin zuwan kanshi ne, domin har a daran ya kirata a kashe, Bai samu zuwa ba saboda ya samu wayar Coach Team ɗin kwallon kafa na Anguwan Jeka da Fari suna bukatar a shirya musu wasan sada zumunci da Team ɗin Tudun wada, kuma a matsayin sa na Captain na Gombe united gabaɗaya yana kula da sauran kananun Team din dake Jiharsa, abin da ya ɗauke masa hankali kenan da zuwa Gidan Hajiya in ya fita tun safe sao dare ba ya samun zama.   Sai da aka shirya wasan da za a buga a Stadium ɗin  su na cikin gari, sannnan ya samu kansa, kwana huɗu tsakanina ya shirya da Daddare saboda har a lokacin Inna ba ta masa magana daga gaisuwa shike nan ko a waya ya kira suna gaisawa ta ke ce masa sai an juma, Mu'azzam ma yanzu ya fahimci ya daina goyon bayansa su Nasir daman an yi rabuwan ba daɗi shi zai neme su kuma bai neme su suma suka ce sai dai a dauwama a haka har gwarama Ahmad sun yi mgana sau biyu.   Shigar farar shidda ya yi har da hula, wani farinciki ya ke ji zai je ya ga Mimi amman sai ta raina kanta shi za ta yi ma wulakanci Saboda ta ga yana nin ta ko? To zai gaya mata ba saboda ta isa ba ne, Saboda Inna ne da Baba, Ya tuna har Babansa Kabiru na Bauchi ya kira shi kan maganar abin da ya ba shi mamaki ce masa ya yi ya zo gidansa ya zaɓi mata. Sai ya ce masa ai bai saki matar ta shi ba sai kawai ya ce"To ka sake ta mana, ba an ce ba ka son ta ba? Cikin mamaki ya ce"In ji waye ya ce ba na son matata?. Kai tsaye ya ce" In ji Gwaggon ka Yalwa ta ce ka ce ba ka son ta ko ƙarya ta yi maka? Baki ya riƙe ya na mamaki, kafin ya ce"A'a ba ta yi ƙarya ba. Sai dai in ba ta ji da kyau ba, Baba Na gode da yayin ka amman ba na jin bayan Mimi zan iya auran wata macen, matata na sona nina kuma  ina sonta, kawai dai akwai dalilin da ya sa abubuwa suka yi faruwa  ne, kuma ba laifi ba ne in ka ɓata ma mace rai ta yi yaji, in ta je gida ta huta nima na huta zamu daidaita daga baya.". Da haka ya samu ya kashe bakin Baban na shi, wai ya ba shi mata? Bai jin ma in ya yi wani auran zai iya yin adalci. Mace ɗaya ce a cikin zuciyarsa tun farko ita ya zaɓa a yanzu ma ita ya kara zaɓa.   Yana tafe ne a mota yana wannan tunanin, Sai ga shi a kofar gidan Hajiya ya yi jon megadi ya leko da ya ga shi ne suka gaisa ya buɗe masa get ya shiga da motarsa ciki,bai yi niyar shiga can ciki ba ba sai ya ɗauki waya ya Kira Mimi amman ba ta ɗauka ba sai ya cije baki ya tura mata saƙo.   "Ina haraban gidan Hajiya ki fito da kayan ki ina jiran ki.".   Shuru shuru sama da mintina ashirin ba Mimi, tun yana mota sai ga shi ya fito, ya jingina da motar ta shi. Haushin kanshi ya fara ji yadda ya tsaya Mimi na yi masa wulakanci ta manta hala har yanzu shi mijinta ne? Ya kamata ya nuna mata har yanzu tana ƙarkashinsa ne. Yana wannan tunanin sai ga sakonta ya shigo jiki na rawa ya buɗe. "Ka shigi cikin gida. Domin ba zan iya fitowa ba."   Ya yi jim yana tunanin wai ita a dole za ta rama ne? Sai kawai ya yi yar dariya ya kulle motar ya nufi hanyar falon Hajiya kofar na kulle sai da ya kwankwasa Baba Uwani ta zo ta buɗe masa tana ganin shi ne ta gaishe shi cikin girmamawa a bakin kofar ya tsaya yana faɗin" Mimi, ki yi mata mgana ki sanar  mata ina jiranta." Ya faɗa yana duba agogon fatan dake tsitsiyan  hannunsa na hagu. Baaba uwani ta yi shuru kafin ta ce"Binta ba ta nan ta yi tafiya. Sai dai Hajiya shigo ciki ka zauna bari na gaya mata zuwan ka." "Ba ta nan? Ta yi tafiya?   Haka ya riƙa nanatawa a cikin tansa Bai san ma Baba Uwani ta koma ciki ba yana tsaye ne yama jin zufa na keto masa Mimi ta maida shi wani cartoon ne ko kuwa wani sakarai ko sauna? Ba ta nan? To gidan iban wa ta je da auran sa a kanta? Yana wannan tunanin yaji muryan Hajiya na faɗin" Na yi fushi tunda sai yau nake ganin Megidan nawa." Dalilin da ya sa ya ɗan saki fuska kenan ya tako kafarsa zuwa cikin falon ya ysaya ya cire takalminsa sannan ya karisa kusa da Hajiya ya zauna a kasan cafet. Dai dai lokacin da Baaba Uwani ta kawo masa ruwa da lemu da ƙaramin kofi. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3005* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya, Ita kuma ta amsa masa cikin sakewa kamar wani abu ma bai faru ba. Har ta na masa irin zolayan da ta saba yi masa, tunda har ga Allah ba ta san da zuwan sa ba tunda Binta ba ta kira ta ba. Kallon sa ta yi kansa na duke lokaci ɗaya tana faɗin" Ka makara da zuwa biko, Binta ba ta na nan shekaran jiya can ta tafi can Abuja wajen Murja. Hala ba ku yi waya ba ne? Kansa na kass a cikin zuciyarsa ya maimaita" Abuja? Lalle ne ma Mimi ta maida shi wani sakarai ya ga alama akwai kasawa ma ya ce ma Hajiya sun yi magana a waya shi ya sa kawai sai ya ce mata ya kira wayar ta bai same ta ba. Hajiya ta muskuta kafin ta ce"Ai ko ba ta nan, amman tunda biko ka zo kuma ta karfe ta gudu, me zai hana ni mu daidaita? Ta fada cikin Sigar zolaya yar dariya ya yi yana shafa kansa kafin ya ce" Haka za'a yi Hajiya." Shuru na wani lokaci, Hajiya ce ma take ɗan Jansa da hira tana tambayan shi aiki da mutanen gida. Ya amsa mata da duk suna lafiya kai tsaye ta ce" Ka gaida min da Meri dakyau dakyau." Ya amsa da In sha Allahu, ko ruwan da aka kawo masa bai sha ba ya yi ma Hajiya Sallama da cewa zai koma. "To ko za ka ƙarisa gidan Babanta Hamza ne. Daman  yana neman ka." Hajiya ta ce tana kallonsa lokacin da ya miƙe shi kuma ba ya son wata doguwar mgana sai kawai yace mata Toh, amman shi ya san ba zai je ba wato ya kai kansa kenan tunda daman ana jiran shi. Kuɗi ya ijiye ma Hajiya a nan ƙasa ta saka hannu ta ɗauka tana faɗin" Ai shike nan kana bikon dani tunda ka fara toshi, Na gode kwarai Allah ya ƙara ma rayuwa albarka." Ya amsa mata da Amin Amin sannan ya yi mata sallama ya bar falon ta bi shi da kallo,  Binta ta cika taurin kai sai da ta hana ta tafiyar nan amman ta haɗa ta da ubanta ya ce a ƙyaleta ta je ta gaida mahaifyarta ga shi megidanta ya zo ba ta nan, Baaba Uwani Hajiya ta kira ta Umarce ta da ta Dauko mata Wayarta a cikin ɗakinta. Bayan ta kawo mata sai ta ce ta kira mata Binta tunda Baaba Uwani ta iya karatun Hausa ita ta nemo lambar Mimi ta kira ta sqnnan ta miƙa ma Hajiya tana ɗauka ta fara faɗin" Hajiya ta, kin yi kewata ne? Hajiya ta ce" Kin san cewa yanzu mijin ki ya bar gidan nan yana neman ki? Sai Mimi ta gyara kwanciyarta kafin ta ce" Wa? Aji? Ban sani ba saboda bai kirani ba." Ta yi ma Hajiya ƙarya. Sai ita kuma Hajiyar ta ce"To ya zo, na sanar da shi bakya nan amman na ce ya karisa wajen babanki  ke kuma sai ki yi kokari ki dawo a daidaita ki koma gidan Mijin ki." Ba gaddama ta amsa ma Hajiya  saboda ko ta ce za ta yi gaddama Hajiya ba za ta gane in da ta dosa ba ne. Bayan sun gama waya da Hajiya ita kaɗai take ta Mirmishi, Kaɗan ya gani yanzu ma aka fara wasan ba ɗaɗewa ko sai ga kiran shi ya sake shigo mata wannan karon ba ta kashe ba barin shi ta yi har sai da ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa ya katse har sau uku bayan mintina kaɗan sai ga saƙon sa. "Kin raina ni ko Mimi? Kina jin daɗin kin yi wasa da hankalina ko? to ya yi miki kyau amman ina so ki sani ki sauke wannan abin da da ki ka ɗauka na tunanin za ki wahalar da Aji ko ki yi ramako a kaina, Never zuwan ma da kika na yi saboda inna da Baba sun matsa sai na zo na dawo dake gida, in kin ga dama daga nan Abujan ki ci gaba kin ji ko." Daga ganin yanayin saƙon ta san ranshi ne ya ɓaci, tana yar dariya bayan ta karanta wato zai fake da Baba da Inna shi a dole kada a hango ya gaza,  a lokacin ba ta yi tunanin maida masa da martani ba sai bayan kamar awa ɗaya tun da barin ɗakin ta yi zuwa falo in da Asma'u ke kallo Mommy kuma tana ɗakin ta tana faman duba takardu sai wajen goma saura ta Daawo ɗakinta ta yi wanka ta kuma yi shirin kwanciya sai da ta kwanta sannan ta jawo wayarta ta tura masa saƙo. "To shike nan zan ci gaba kamar yadda ka ce." A lokacin da saƙonta ya shigo kamar tasan yana kwance ne yana kisima hukuncin da zai yanke Mata in ta bari suka haɗu, tsabar ma takaici ko abinci bai ci a daran kuma in ya je gidan Inna ba bashi za ta yi ba domin tun bayan barin Mimi gidan inna ta daina masa tayin abincin ko ya ce zai ci sai ta ce ya kare ko da ga shi nan ko yana gani shi ya sa yake rufa ma kansa a siri ko ya gani bai nuna yana bukata. Barcin sa rabi da rabi ne a baya ne da yasan Mimi na ƙarƙashinsa ya ke samun Ishasshen barci amman tunda ya fahimci kamar ta yi masa nisa ya daina samun barci cikin natsuwa. Shi fa a ransa sai da ya ga laifin Hajiya ta ya ya za a su bar matar aure tana yawo ba tare da sanin Mijinta ba shi fa tafiyarta Abuja ta fi masa raɗadi fiye da yadda take yi masa wannan renin wayau. Da farko ya yi alkwarin ba zai ƙara kiran ta ba amman ba shi da mafita saboda ya kasa sukuni ko da bai kirata ba yana bibiye da dukkkan wani motsinta. Haka kawai saboda ita zai hau facebook da WhaApps ya duba ta, a Facebook duka Account ɗin ta guda biyu na Fatima Kabir Dabo(Mimin karamchi) da kuma na wanda ta buɗe a ɓoye na MIAJ, duk ya san dasu kuma yana vibiyanta amman ba ta taɓa sani ba, to abubuwa da dama ma ba ta sani ba wani abun gwara ka bar shi a rufe saboda Sanin shi a lokacin ba shi da wani amfani. Yini yake duba ta sai ya ga ba ta saka komai ba kamar ma tun bayan auransu motsin Account ɗinta ya dakata. Sannan ya duba bangaren hidan tibin da take aiki, daman tun kwanaki ya ga ma kallata gidan Tibin suna ta cigiyarta sai suka ba da sanarwan ta na nan lafiya ta ɗauki hutu ne ma'ana Anaual leave ɗin ta, ƙaramin tsaki ya ja shi fa ya tsani aikin nan domin shi bai ga wani amfanin shi a Al'umma ba, Kuma zai bude data yana ganin tarin Groups da aka saka shi yawanci duk na ƙwallo ne tunda babu wani Team na nan Gombe da ba'a saka shi a ciki ba, akwai wani ma da tunda aka saka shi an tara saƙo sama da dubu bai taɓa buɗewa ba, kuma ko a Private ka yi masa mgana in ka ci sa'a ya buɗe ya karanta ba zai maida maka amsa ba sai dai in ta kama ya kira ka. Saboda gani yake ɓata lokaci ne ya tsayawa yana typing. Shi ya sa duk yadda su Nasir suke caccakan sa a group ɗin su na Brother's bai ko shiga ba, Ko mu'azzam ba ya chart da shi sai dai in ya ga ya yi masa mgana ya sauka ya kira shi, yawanci ma shima yasan hali yafi tura mishi hotuna ko wani abu mai muhimmanci,group ɗin su na jami'a ko tuni ya fice,an sake maida shi ya sake fita har sau uku, daga nan suka ƙyaleshi. Har ta goup ɗin su na Gombe United kowa na da amfani ban da shi hatta Coach na su yana mgana da sauran bayanai amman shi sai dai a waya ko ya je Camp ɗin ya tara su yi magana shi ya zauna ne wai ya ga yana rubutu ya ke ganin shi a ɓata lokaci ko kuma wai ya kunna voice note shi fa har mamakin ma su yi masa vioce yake yi, wani mai tsawon ma shi ai ba shi da wannan lokacin, wani lokaci yana buɗewa yake kashewa ba ya da lokacin saurara shi ya sa ga wanda yasan tayuwar Aji gwara ya kira shi a waya amman domin ya yi magana ta chart kamar ya zama aikin banza ne Gabatowar wasan da suka shirya ne ya sa ya rage Tunani da damuwar Mimi sai da aka buga wasa aka ta shi lafiya sannan ya dawo natsuwarsa, kuma shi abin da ke ba shi mamaki Inna ƙiri ƙiri ta nuna ta fi son Mimi a kansa tsakani ga Allah shi fa Ɗanta ne, Ita fa Iyayenta ba su juya mata baya ba sai shi? Haka zai je Inna Meri ta yi kamar ba ta gan shi ba da ya Kira Mu'azzam ya yi masa ƙorafin abin da inna ke yi masa kai tsaye ya ce"Ni fa ba ruwana tunda ka ce kowa ya cire bakin shi a ciki." Cikin haɗe rai Aji ya ce"A maganar Mimi ba,  maganar Inna fa dole za ka yi min amfani ka kira ta ka nuna mata ni fa Ɗan ta ne ai bai kamata tana banzarta da ni ba, ita kanta Mimin da take min haka saboda Ita iyayenta ai ba su nuna son fi sona da ita ba, Itama Inna ta gane mana kowa fa nashi ya sani." Mu'azzam na ta faman danne dariyansa, amman sai da ta fito Aji ya ji sa. Sai kawai ya yi kafci kafin ya ce" Au dariya na baka? Ya yi maka kyau." Daga nan ya kashe wayarsa, Mu'azzam ya biyo bayan kiran aka yi banza da shi ba'a ɗauka ba. Dole ya Kira inna Meri domin yi ma fan'uwansa biko, ya kuma maida mata abin da Mansoor ɗin ya ce kowa fa na shi ya Sani inna, ki yi masa hakuri in sha Allahu zai daidaita komai. Sai da ta gama jinsa sarai kafin ta ce"Mu'azzamu in kana son kanka da arziƙi a wajena kada ka ƙara kirana kan mganar ɗan'uwanka, ni na ce na yafe masa amman na tsame hannuna a kan rayuwarsa ya yi duk yadda ya ga dama." Mu'azzam ya ce"Inna to ai baki haƙuran ba kenan, cewar da ki ke yi kin tsame a hannun ki  a kansa kamar baki ne fa ki ka yi masa" Inna Meri ta ce"Ban yi masa baki ba, kuma na yafe masa saboda ɓacin raina ma kaɗai bala'I ne wajensa, amman ba zan ƙara bari Baban inna ya ɓatamin rai ba, tunda shi haka ya ke ba ya jin mgana sannan abin da ya ga dama shi yake yi to ba sai ya je ya yi ta yi ba, ai yanzu ba mai ce masa don me, ni ce kuma na tsame bakina da hannuna a kan sa." Mu'azzam na so ya ƙara mgana. Amman Inna Meri ta ƙi sauraran shi cewa ta yi in mganar da ya kirata su yi kenan za ta kashe wayarta dole ya bar maganar. Sai washegari ya samu Aji ya ɗauki wayarsa shi kuma ya gaya masa yadda suka yi da Inna numfashi ya furzar kafin ya ce" Ai shike nan." Mu'azzam ya ce"Mafi masalaha ka je ka Dawo da Anty Mami in har kana son Inna ta Daina fushi da kai." Cikin jin haushi ya ce"Wai ba na je ba. Tayi tafiyarta wai Abuja domin ta raina ni, da aurena a kanta amman iyayenta sun barta tana yawon tafiye tafiye." Yadda ya faɗi mganar ne ya sa Mu'azzam ya yi shuru yana danne dariya kada ta fito abin a ya shafe sa. "Gaskiya ba ta kyauta ba. To ka kira ta a waya mana? "To taba ɗauka ne? Wani irin kira ne ban yi mata ba ta ɗaga kirana ba." Mu'azzam ya yi tsai kafin ya ce"Topha! To ko za ka shirya ka je can Abujan ne ka same ta? Kasan mata fa yan Lallashi ne in ta ga ka Bbta za ta sauko sai ta Saurare ka." Kai tsaye ya ce"Amman ba ka da hankali Mu'azzam ni ne zan bi ta har Abujan? Lalle to ta shekara a can." Mu'azzam na shafa kansa daga can bangaren ya ce"Ba za a yi haka ba. Ya kamata ka samo mafita saboda Inna." "To ai daman saboda ita ne ya sa ka ga ina bin ta amman ni har Mimi ta isa ina kiran ta a waya tana min wulaƙanci? Sai ya yi kafci kuma shi kaɗai irin abun ya nan ya gama ɓata masa rai. Shi ko Mu'azzam wayar ya matsar gefe yana ta dariya shi kaɗai sai ji ya yi Aji na faɗin"Ni na ce ba zan kara kiranta ba  amman kai in za ka kirata ne ba zan hana ka ba tunda ka matsa" Mu'azzam ya yi ta dariya bayan sun gama waya da daddare ne lokacin Hibba na tiolet ta na wanka tun tana ciki ta ke jiyo dariyan Mijinta sanda ta fito ta iske shi ya na Dariya shi kaɗai cikin mamaki ta ce"Me ka samu ne kake ta dariyan nishaɗi? Yana dariya yana tuna amsar da ya bama Yayan na shi da cewa" Nima fa ba ta ɗaukan wayata. Sannan daga baya ma ina jin rufe ni ta yi ko na kira ta ba na samun ta, Ai ina ganin wannan faɗan ya fi karfin ƙanin miji sai dai mijin da kansa." Kawai sai Aji ya ce"Kai dai ka sani." Da haka ya katse wayarsa ya bar Mu'azzam na Kwasan dariya shi kaɗai. "Ina nan ina dariyan Yaya Mansoor, ina tunanin mu kusa mu ji shi a garin Abuja ya je biko." Hibba ta ƙariso gefensa da sauri tana faɗin" Ba ni in sha, me ya faru?. Nan ya labartamata abin da Yayan na shi ya gaya masa yaje gidan Hajiya Mimi ta tafi abuja sannan ya na kiran wayanta ba ta ɗauka. Hibba ta saka dariyan ƙeta kafin ta ce"Kai na gode ma Mimi, ai sannu sannu ba ta hana zuwa sai dai a ɗaɗe ba'a je ba." Mu'azzam ya ce"Ina tsausayin shi ni nasan duk ya damu amman ba ya son ya nuna ace ya damu da ita, kuma muna nan dake zai kirani ya ce zai je Abuja amman saboda Inna ne." Hibba na dariya ta ce"Nan gaba kaɗan zai ce saboda ke ce rayuwata. Sunan Inna tuni zai manta da shi." Dariya suka saka har suna tafawa, Mu'azzam ya san waye yayan shi fiye da kowa amman ya na tausaya masa Saboda ga duk alamu wannan karon Mimi sai ta Jijiiga yan maza. Daran shi da Hibba kusan raba dare suka yi suna ta tattauna batun Hibba na goyon bayan Mimi shi kuma Yana goyon bayan Yayan shi yana tausayin shi ita kuma Hibba ta ce ai gwara dai a jijjiga shi saboda duk abin a ya faru shi ya ja. Daman ance ai dama ɗaya take zuwa a rayuwa shi ya bar daman na shi tun a farko ga shi yanzu ya fara nadama dukda dai bai fito ya furta ba amman kowa ya san ya yi nadaman maganganun da ya faɗa Mimi a wannan daran. ****** Mansoor bai ƙara tsinkewa da lamarin ba sai daran ranar jumma'a da ya zo gidan, shima ɗin ya zo duba Baba ne da baya jin daɗi mura ta kwantar da shi.Shima sanin shi Yaya Amina ce ta kira shi take gayamasa Mu'azzam ma ya kira shi baya kusa da kuma ya zo ya gani bai kira ba. Baban ya ji sauƙi amman ranar bai fita ko'ina ba yana gida. Zuwan Mansoor ne ya Dauke sa zuwa wani ƙaramin cinic suka amso mganguna ya biya ya siya masa tsire da fura sannan ya dawo da shi gida ya kuma kaisa har ɗakinsa ya tsaya a kansa ya ci naman ya sha furan kaɗan ya balla masa magunguna ya sha ya kwanta. Inna Meri ta yi ta shigowa duba shi. Anan ne na yake ce mata ta ɗauki tuwon ta ya yi kwantai. Tsire Baban inna ya siya masa ya ci ya ƙoshi, ba musu Inna ta ɗauke kwanukanta Mansoor yana shirin ya ci ne ya ga Tuwo ne miyar Kuɓewa ɗanya amnan tunda Inna ta kwashe kayanta ya san sai dai ya haɗiye yunwarsa. Shigowar Magajiya ya sa ya bar ɗakin zuwa bangaren Inna ba wutar nepa amman akwai hasken farin wata sannan garin an fara zafi. Da ya sawo kanshi shashen ya ga mutun kwance gabda ƙofar ɗakin Inna Meri, ya ɗauka Walida ce bai kawo ma kansa matar Saddiqu ba ce shi ya sa yana karisowa ya fara faɗin" Ke Walida ƙofar ɗaki ne wajen kwanciya? Ba na son wawanci kwashe wannan shinfiɗar a wajen" Shuru ba magana sai ranshi ya ɓaci ya Daka mata tsawa ya na mai kiran sunanta amman Maeesha ko gizau daman tun fara zafi ta samu wannan iskancin sai ta zo ta simfiɗa abin shimfida ƙofar ɗakin Inna, ko innar ne sai da ta raɓa ta gefe ta wuce Walida ta yi mata magana ta ce ɗan cikinta ba ya son zafi ko za ta hana ta kwanciya ne Inna ta ce ta ƙyaleta kada ta kara mgana. "Yayanmu gani nan fa." Walida ta katse shi daga Kiran sunanta da yake yi, ya ɗaga kai yana kallonta cikin mamaki kafin  Ya yi mgana da sauri ta ce"Matar Yaya Saddiqu ce." Buɗe ido ya yi kafin ya ce"Oh iskancin nata nan kuma ya dawo? In iskar take son sha ta je Kofar ɗakin magajiya mana sai anan duk ta tare ma mutane hanya" Bai tsaya ba kawai ya nufeta gadan gadan kamar zai takata da sauri ta matsa baya da sauri da kwanciyar sarakai ta yi tana hararan shi tana ko matsawa ya saka takalminshi ya ture shimfiɗar yana faɗin"In ta sake kwanciya kada wanda ya kauce mata, ku taka ta ku wuce" "A taka ni fa ka ce? Saboda ba ka da asara.? Maeesha ta faɗa cikin hargowa shi ko kamar bai ji ta ba ya shige ɗakin Inna wacce ke salla ta kosa ta Idar kada Baban inna ya ƙara jawo mata wata masifar, Maeesha bakin ciki ya rufe ta sai kawai ta saka kuka tana faɗin an takura mata ita da gidan Mijinta ba ta da halin sararawa Walida na gefe tana yar eariya daman matar nan ta gama cika mata ciki da iskancin ta a cikin gidan nan saboda ita Bintu ta daina zuwa gidan in ta ga abun magana sai ta yi mgana Kuma tana mgana sai a fara hayaniya Ita kuma Inna yar zaman Lafiya ce ita ta ce in fitina ke kawo ta itama ta zauni gidanta. Maeesha ta yi ta kumfar baki tana tunanin Magajiya za ta fito amman shuru ita kuma Walida sai ta tafa hannu kafin ta ce"Sorry fa, ko shi Yaya Saddiqun ba zai iya da Yayanmu ba ballantana ke karamar alhaki." Da haka itama ta nufeta gadan gadan kamar za ta murje mata hannu ya sa da sauri ta mike tsaye Walida ta shige ɗakin Inna tana faɗin" Ashe karyan tsiya kike yi." Fuu Maeesha ta koma ɗaki tana kuka ta kira Saddiqu tana gaya masa karya da gaskiya har ta na faɗin Aji ya saka yakalmi ya taka ta kuma da gangan. Shi kuma cikin Kumfar baki ya ce mata ai ya Kusa dawowa zai yi sharia da wanda ya taɓa masa mata daman ai ya na jin hauahin warning ɗin da ya saka Auwalu ya kira shi ya yi masa to wai shi da me ya ke takama ne? A ɗakin Inna ko ta na sallame sallah cikin ɓacin rai ta kalli Mansoor kafin ta ce"Ba na son fitina. Ba na so ina zaune lafiya ba za ka jawomin wata fitinar ba, in kai ba ka san darajan matar ka ba, wasu sun sani kuma da gaskiyanta gidan mijinta ne a barta ta yi abin da ta ga dama mana." Lokacin ya na wasa da Junoir ne wanda tun shogiwarsa a she bai yi barci ba ya naɗe masa. Sai ya kasa mgana domin kamar gori ne Inna ta yi masa. Walida ce ta tura baki kafin ta ce"Shikenan Inna sai a barta ta rika mana abin da ta ga dama." A fusace Inna ta ce"Sai me? Ai wuri ta samu ɗan da ka haifa ma bai ji mganarka ba sai wani can ne za ka damu kanka domin ka yi masa mgana bai ji ba." Yadda Inna Meri ke mgana ne ya sa ya san ranta ya ɓaci kai tsaye ya ce"Ki yi hakuri inna." Sai kawai ya miƙe ya na faɗin"Inna ki ba ni Junior na tafi da shi wajena ya kwana." Wani kallo mai kama da harara Inna ta sakar masa kafin ta kalli Walida lokaci ɗaya tana faɗin"Ke karɓe shi, " Walida ta yi shuru kafin ta karisa za ta karɓeshi shi kuma ya makale masa sai ta Juya tana faɗin" Inna ko za ki bari ya tafi da shi ne, duba fa ki gani baya son zuwa." Inna ba ta sake mgana ba ta miƙe ta warce Junoir a hannun Babban Inna yaron ko ya fashe da kuka Inna ta mikama Walida shi tana faɗin ta kai shi ciki ya kwanta. Ta kalli Manaoor da ya yi kasaƙe kawai yana na kallon Inna komawa ta yi ta zauna lokaci ɗaya tana faɗin" Mu kwana lafiya." Takaici ya kume shi cikin ɗan jin haushi ya ce"Inna ɗan Ɗan uwane fa? Inna kai tsaye ta ce"E fa! Amman ai ba ɗanka ba ne ko ? In ka ji haushi ka haifi naka sai ka rika kwana da su." Har ya dawo gidansa in ya tuna kalaman Inna sai ya ji kamar ya yi kuka wai shi Inna ke yi ma gorin Mata da haihuwa, takaici ya sa a daran ya Kira Mu'azzam y na gayamasa shi kuma ya nuna bai ji daɗi ba. Sai kawai Aji ya ce" Amman ba komai, ta kwantar da hankalinta sai ta gaji da ɗaukan Ƴaƴa na" Mu'azzan sai ya ji ya ba shi tausayi ya kuma san Inna ta yi masa hakane Saboda ya ji haushi ya gyara abin da ya ɓata kuma kamar hakan ya yi tasiri daga baya shima ya zauna yana tunanin shekaru sun tura ya kamata ace shima yanzu ya wuce wannan matsayin tunda har Inna ta fara masa gorin mata da haihuwa to nan gaba bai kuma san wa zai masa gori ba, ya fi su fa bukatar matarsa akwai abubuwan da suka faru ne suke danne wannan bukatar ta shi amman cikin ikon Allah da shawarwarin Nasir tun kwanaki ya fara yaƙi da abin d ke ransa kuma Alhandulillah yana jin abun na raguwa. Duk iya yadda ya so ya share Mimi sai ta neme shi amman ba ta neme shi ba Sai ya ji ya kasa hakuri ana neman cin wajen wata ɗaya sai ya fara jin tsoro kada fa ya yi sakacin da zai ƙara jefa rayuwarsa cikin yarari a karo na biyu. Ba shi da wani abokin shawara sai Mu'azzam Shi ya kira ya na ce masa" Mu'azzam kana ganin na bi Mimi Abuja ba matsala.? Mu'azzam na mirmishi ya ce"Me zai hana? Ba wata matsala, ka kirata in ba ta ɗauka ba ka tura mata sakon za ka zo sai ku zauna ku yi mgana." Kamar wani yaro sai ya ce ma Mu'azzam Toh, Sai yayan na shi ya ba shi tausayi yasan yadda ya tsani garin nan amman ga shi yau zai koma kuma a kan dalilan nan guda ɗaya wanda saboda shi ya je a karon farko a wannan karon ma saboda shi zai koma. "Don Allah Yaya Mansoor kada ka ce za ka mata yi faɗa,  ka lallasheta tunda dai kai ne mai laifi." "Uhm! Kawai ya ce daga nan bai ƙara mgana ba Saboda a lokacin yana tunanin ya je ko kuma kar ya je,  amman ya bi shawaran Mu'azzam ya ƙara Sauke kai ya kira Mimi amman matar nan ba ta ɗauka ba sai ya tura mata sakon ta tura mishi adireshin gidansu zai zo su yi mgana. Lokacin da ta ga sakon shi matuka ta sha mamaki, wani gidan y ke nufi? gidan da ya ce Allah ya yi masa tsari ya ƙara takawa,  ba ta yi gaggawan tura masa sai da ta kira Rukky ta sanar da ita, ita kuma tana dariya ta ce" Na fahimci ba ma zai yi mana wahalan kamuwa ba, tura masa kada ki sake ki gaya masa wani abu." Kai tsayen ta tura mishi yadda zai gane, An yi wajen kwana biyu ba ta kara ji daga gare shi har Rukky ta kira ta na gayamata ta ji Aji shuru Rukky ta ce zai zo fa ki kwantar da hankalin ki, shi ko tunanin tafiyar ne amman haka nan dai ya sauke girman kansa da wannan rikon da ya yi a ranshi a ransa ya kudurta ba zai shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga haraba.. Bayan Mu'azzam ba wanda yasan zai je Abuja Jirgi ya bi zuwa can ranar wata Asabar da safe domin ko da sha ɗaya ta yi sun sauka a garin Abuja, a direshin ya nuna ma mai Taxi ɗin sai ga su har kofar gidan Marigayi Major Kabir Dabo dake anguwan Gwamrinpa. Tsawon shekaru goma anguwar ba ta sauya masa a i do ba. Sannan gidan kan shi bai sauya masa, sama da mintina talatin ya na bakin get ɗin gidan  yana kokuwa da yanayinsa domin ji ya ke kamar a wancan lokacin ne da suka sauka shi da Mu'azzam kawai sai komai yake dawo masa daki daki kamar a lokacin yake faruwa ya yi tunanin ba zai shiga gidan ba, in fa ana son a samu masalaha har gobe ba zai daina ganin baƙin wannan gidan da mutanen dake cikin sa ba. Wayarsa ya ɗauka ya kira Mimi abin mamaki wannan karon Mimi ta ɗaga wayarsa. "Hello, na iso gani a kofar gida amman ki fito ba zan shigo ba." Cikin yanayin maganarta tacce"Ni kuma ba zan iya fitowa ba, in ka na so in saurare ka sai ka shigo cikin gida." A ransa sai ya ji daɗi da ya ji muryanta amman kuma yana tsoron wani abu da sauri ya ce" Kada ki sake ki shirya wani abu, domin na ga alaman kin sakani cikin dangin ku bangaren abokan wasan ki." Dariya ta saki mai kayatarwa kafin ta ce"Kar ka damu, yi ma megadi mgana ka ce kai baƙo na ne." Daga haka ta katse wayar ba karamin jarumta ya yi ba. Har sai da ya kai zuciyarsa nesa sannan ya iya tun karan get ɗin ya buga megadi ya leko sai ya ga yau kam ba Soja, wani dattaijo ya gani bayan sun gaisa ya ce masa ya zo wajen Mimi ne sai ya buɗe masa kofa ya shiga amman sai ya ce ya jirasa bari ya shiga ya sanar musu. Yana bin haraban gidan da kallo, ba sojoji ba motoci ba iko ba komai sai haraban gidan wayam, Rayuwa kenan yana nan tsaye ya na kallon abun kamar yau yake faruwa Sanye yake da manyan kaya har da hula saboda Sumar kansa ta yi yawa kuma bai je ya rageta ba. Megadi ya dawo ya ce Hajiya ta ce ya shiga ciki, kamar yace a'a sai kuma ya bi shi a baya shi ya yi masa jagora har cikin falon Gidan da ba abin da ya sauya a sanin da ya yi masa a baya sai dai an samu sauyin abubuwan dake falon. Duk yadda ya so ya zauna kasa zama ya yi kawai ya yi tsaye hannayensa goye a bayansa ya na jinsa kamar akan ƙaya Ita kuma Mommy tana cikin ɗakinta tana fa waya da Mimi domin ita ta kira ta ta ce Aji na waje ta saka a shigo da shi. Mommy cikin faɗa ta ce"Au kin ma san zai zo shi ne ki ka saka kafa kika yi tafiyar ki? Mimi ta marairaice kafin ta ce"Ni fa ban sani ba, yau yake gaya min." Mommy ta san karya ne. Rana Tsaka shekaranjiya ta ce Kano za ta je gidan Dr da ta hanata sai ta yi mata karyan kwana biyu za ta yi ta dawo, kuma daman sun yi waya da Hajiya ta san da labarin zuwan shi can gidan da ta kira Alhaji Hamza ta yi masa mganar tun dai ya zo ya neme sa a sansanta lamarin shi kuma sai ya ce har yanzu bai zo gabar da nake so ba, in har yana son Sasanci tsakaninsa da Mimi ya san in da zai same shi. Mommy ba ta fito ba sai da ta kira Asmau a waya dake ɗakin ta ta ce ta fita falo ta kai ma mijin Mimi ruwa da lemu a falo. Da to ta amsa mata sannan ta saka lulluɓi ta fita falon ta ganshi tsaye kamar yana kan ƙaya ba ta taɓa ganinsa ba sai sau ɗaya a wajen Kwallon da aka yi amman ta gane shi. Cikin girmamawa ta gaishe shi ya amsa sau ɗaya kafin ya ce"Ina Mimin? Sai ta yi shuru cikin mamaki kafin ta kalle shi cikin mamakin shi bai san Anty Mimi na kano ba ne? "baka sa ni ba? Anty Mimi ba ta nan ta tafi kano." Mirmishin gefen baki ya yi kawai domin in yace zai ɓata ransa ya rantse ds Allah sai ta raina kanta ya yarda ma kansa Mimi tana masa wasa da tunani da hankali. Kitchen ta shiga ta haɗo masa lemu da ruwa da kofi saman faranti sannan ta kawo masa falon ta ja center table ta ijiye masa, Juya ya yi zai yi tafiyarsa sai ga Mommy ta fito Allah ba domin ta kira sunan shi ba so ya yi ya ficewarsa har shi za a yi ma Iskanci. Dole ya dawo amman tsabar kamar akan ƙaya yake bai ko cire sahu cikin takalmin da ke kafarsa ba, daga gefe ya tsugunna ya gaishe da Mommy kadahan Kadahan ta amsa itama cikin yar sakewa kaɗan. "Sannu da zuwa. Ba ku yi waya da Mimin ba ne? Ba ta nan tana Kano gidan Dr." Kawai sai ya samu kanshi da cewa ya kira ta bai same ta ba, kai tsaye Mommy ta ɗaga wayarta tana faɗin" Bari na kira ta, ka zauna a kan kujera mana nan ma ai duk gida ne." A ransa ya ce ban ga gida anan ba amman a fili sai ya yi shuru kansa na kasa ya ji Mommy na faɗin" Ya ce wayarki ba ta shiga, ga shi ku yi mgana amman ki tabbatar da kin dawo yau ko gobe." Daga haka ta miƙe ta isa har in da Aji yake ta miƙa msaa wayar hannunta ya amsa ita kuma sai ta koma ciki lokaci ɗaya tana kwalama Asma'u kira. "Wai ke a tunaninki wahala kike son ba ni? Uhm ba za ki iya ba ni wahala ba Fatima, sai dai mu wahalar da juna." Mimi ta yi yar dariya kafin ta ce"Sorry fa, na je duba matar ɗan'uwana ne." "Da izinin wa kika tafi? "Da izinin mijin da zai sake ni kwananan mana." Baki ya buɗe kafin ya yi mgana ta yi saurin cewa" Shi ya ce in na ga dama na wuce  Abuja ma shi ya sa na tafi." Kai ya jinjina ba tare da ya yi mgana ba Daga can bangaren ta ce"Ko za ka ƙariso kanon ne? Wlh ina gidan Dr." Kasa ma mgana ya yi, domin ba shi da abun cewa dakyar ya samun bakin cewa" Ki sani dai akwai nauyin igiya uku a kanki, duk wani abun da za ki yi na saɓa ma mijinki Mala'iku suna rubuta miki, gwara ma ki sani ba ni kika yi nawa ba kan ki kika yi ma wa." Daga haka ya kashe wayar kawai ya yi shuru ya na furzar da iska daga bakin shi,Da gaske ne Mimi ta fara bashi Wahala, da niyarsa ya yi tafiyarsa amman Mommy ta hana shi tafiya ta ce sai ya tsaya yq huta ya ci abinci sannan,  kuma kamar an rufe masa baki sai ya kasa yi mata Gaddama haka ya zauna a falon gidan su Mimi a ɗaɗare. Har Asma'u ta gama yi masa lafiyayyan fride rice da naman kaza an yi Pepe. Da farko ya so ne ko ruwa bai zai sha ba sai ga shi har abincin sai da yaci daman da yunwa ya fito ko karyawa bai yi ba. Ya kusa ma yin abun kunya kaɗan ya rage abincin sai daga baya ya riƙa jin haushin kansa. Karfe biyu da wani abu ya baro gidan, Mommy ta jaddada masa Mimi za ta dawo kuma da kanta za ta dawo da ita gombe,  duk da bai wani saki jiki ba amman shi kan shi ya yi mamakin kanshi ko a tarihi bai ɗauka kafarsa za ta kara taka wannan gidan ba, sai ga shi a karo na biyu ya dawo saboda Mimi. Airport ya je ba jirgin gombe dole ya nemi hotel ya kama ya kwana da safe ya samu jirgin Gombe zuwa sha biyu na rana yana gidansa kwance yana tunanin Yadda zai yi ma Mimi rashin Mutumci in ta dawo ba dai shi za ta wahalar ba jiya ba har tana tura masa sako. "Ya gajiyan tafiya? Mommy ta ce yau dai Aji ya ci abincin gidan Major Kabir Dabo. Na yi mamaki ƙwarai amman na ji daɗi. My ex husband." Ko ba Ex ba haka ya rika maimaitawa shi kaɗai, wata zuciyar ta ce ko dai ta samu wani da take yi masa haka? Zabura ya yi cikin ta shin hankali, saƙo ya tura mata tunda ba ta ɗaga wayarsa. "In na sake ki kina da tabbacin akwai wanda zai aure ki ne a bazawara? Tsakanin saƙon shi da nata mimtina huɗu ne ta turo masa da amsar da ya kusa barazanar yafiya da numfaahin sa. B"E, mun daidaita da shi,  kai kaɗai yake jira mganar shi ta je wajen Daddy. Ya na sona sosai domin tun kafin na aure ka ya so ni, sai na zaɓe ka a tunanina kana sona sai daga baya na gane cewa na yi rashin masoyin ƙwarai da kaina na neme shi na bashi hakuri. Saboda haka ka sani aurena da kai ya ƙare Mansoor. Ina jiran takardan saki na." Fatima Kabir Dabo. Wannan saƙon na Mimi kaɗan ya rage bai kashe shi da ranshi ba,Allah ne ma ya sa kwanan shi na gaba. Da gaske take yi ta nemi wani namijin? Lalle akwai ƴaƙin duniya na uku matukar akwai wanda ke ganin matarsa da sunan so. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3006* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *BAYAN KWANA HUƊU* A cikin kwana huɗun da suka shuɗe duk a daddafe Mansoor ya yi su, duk yadda ya so ya fushi da Mimi kamar yadda ya so a farko tun bayan dawowar shi daga Abuja saboda ta ba shi haushi. Sannan tunda ya fahimci wahala take son ba shi ko ta yi ramako dalilin haka ya so ya share ta ya fita batun ta ya ga dai ƙaryan tsiya sannan kuma ya ga iya gudun ruwanta, shi ba ita ta fi ba shi baushi ba sai Iyayenta da suka zama tsoffn kawai suna kallon ta tana yawo gari gari da auransa a kanta amman a ka rasa mai tsawarta mata, ko ma me ya faru ai bai ce ya sake ta ba, ita ta ga dama ta yi tafiyarta shi kuma lokacin ransa ya ɓaci ba zai iya tsayawa yana ba ta hakuri. Amman tunda ta tura masa saƙon wai ta samu wani. Ya ji kasa sukuni maganar ta ƙi barinsa ya zauna Lafiya barcin sa ma ragagge ne. Baƙin kishi gare shi shi fa a tsarin rayuwarsa in har ya riga matarsa mutuwa Allah zai bar wasiyyan in ta sake aure bai yafe mata ba, ba zai iya ɗaukan wannan kwamacalan ba a ce in da ya shiga ya yi nomansa wani ya shiga ya ba za ta shi hajar ba zai iya ɗaukan haka ba. Ballantana yana raye a duniya nan Mimi ta je tana kula wani, ya fara tunanin waye ta ke nufi? Ko dai wannan sakaran ɗan'uwan nata ne? domin ai ya san labarin shi a bakin Makama In ko hakane lalle daga Mimi har iyayenta zai ɗaga musu hankali. Sannan ko da ya ce ba zai ƙara nemanta ba ya kasa, ya sake kiranta amman wayarta a kashe amman bai haƙura ba, karin abun ma ko barci yake yi sai ya riƙa mafarkin ya ga Mimi da wani ta na ta masa dariya, a kwanaki nan barcinsa duk babu salama da sukuni a cikin sa. Duk yadda ya so ya nuna bai damu ba ya kasa damuwar har ta fara bayyana a saman fuskarsa baya samun cikakken barci haka za ka ganshi zuru zuru,  duk kauce kaucen sa na kada a fahimci Mimi ta ci nasara a kanshi ya kasa. Duk kuma tunaninsa na ya share ta shima ya kasa tuni zuciyarsa ke rinjayansa ya bi ta can kano, wata kuma zuciyar na hana shi, amman kuma wata na tunkuɗa shi saboda samun natsuwar shi, Ga shi har a Lokacin Inna sama sama take yi masa ya bata hakuri bai san adadi ba sai ta ce ita bai mata komai ba, ya yi mata maganar Mimi ya ce ta kwantar da hankalinta za ta dawo kai tsaye ta ce masa wannan kuma abin da ya shafi rayuwarsa ne ita nufinta ta fita a ciki, In ya neman masu mai faɗa ne ya nemi dangin ubansa ita kan ta gaji da bin bayansa ba shi kaɗai ta haifa ba. Har Baba Ɗanjuma ya gaji da yi mata mgana ta kafe ta ce ita wlh ta yafe masa ɓacin ran da ya saka ta amman kuma ta ƙi ta koma masa kamar baya. Yana ma dai zuwan gidan ne domin ya zame masa dole amman ba ya jin daɗin gidan kwata kwata. Sai dai saboda Junior in ya je gidan da ya gansa zai ɗane shi yana murnan ganinsa in ko ya ce zai fita da shi Inna ta fara faɗa kenan ta ce in nesa zai yi ka da ya fita da shi, Shi dai ai na shi ban hakuri ne sai dai ya je ya yi yawo da shi cikin Camp ɗin su, Ko kuma ya yi yawo da shi acikin mota ya na siya masa kayan kwalama da kuma kayan wasa. Ya so cikin satin da zai shiga ya je Kano duk da baya samun wayar Mimin amman hakan bai samu ba  baya samun shima lokacin kansa, wani girma ne Allah ya ba shi a sanadin wannan kwallon kafa. Matasa matasa dake Gombe da zagayenta suna yawan zuwa wajen sa neman karin bayani ko wani taimako,  duk da shima ya dan ƙwallo ba ra'ayinsa ba ne sannan ba burin shi ba ne, amman tunda abin da Allah ya zaɓa masa kenan sai ya rumgume shi hannun biyu, tunda shine komai na shi yanzu komai zai zama ko ya zama a wannan rayuwa sanadin wannan sana'ar ne a farko bai wani ɗaukesa da wani irin Muhimmanci ba amman daga baya sai ya rike abun ya san Allah ne ya yi masa kyakyawan zaɓi ta hanyar da bai za ta ko tsammani ba. Har satin ya ƙare. Bai samu yanke shawara ba, a satin kuma da ya shiga suna da traninng saboda watan gaba suna da buga wasa, to duk ba ya samun zama sannan Baba ma ya kira shi kan maganar Walida da Mariya ya ce zai shigo gidan su yi mgana. Abin da ya sa ma ya yi musu shuru ba su ci Jamb ba, ya na tunanin su jira wata shekara su sake rubutawa, sai su tafi jami'ar Gombe kamar yadda ya yi ra'ayi duk da ya san Baba aure yake so su yi saboda tsarin gidan wanzamai kenan ba'a dogon karatu a gida. Suna mgana da Mu'azzam shi dai ya damu ya zo kanon nan ya yi bikon Mimin sai ya riƙa nuna masa zai yi tunanin har a lokacin bai gama gaya masa ga abunda ya yanke ma ransa ba., daga baya kuma sai ya ce ko ya na son zuwa ba shi da mafita tunda wayar Mimin tana kashe ne ta ina zai iya sanin adireshin gidan yayan nata. Sai Mu'azzam ya ce ya na da lambar Dr. Sulaiman saboda tun a wajen ɗaurin auran shi suka karɓi lambar juna tun wata hira da ta shiga tsakaninsu ya gaya masa a kano ya ke aiki, to tun a lokacin ayyuka ya sa ba wanda ya neme wani a cikin su. Mamaki ya kama Aji cikin ɗan shan kunu ya ce"Me kuka haɗa da su da kake ijiyar lambobin su? Mu'azzam na dariya ya ce"Mun haɗa mana, tunda Yayana na auran ƙanwarsa ai an zama ɗaya in sha Allahu" Uhm kawai yace domin ya ga Mu'azzam ne da Kalan dangi,  har ya na cewa kada ya damu zai raka shi gidan in ya zo kanon,  shi kuma ya ce bai saka shi ba, kuma ya ƙi gaya masa ga lokacin da zai zo ya ce kuma in ya dame shi zai fasa zuwa daga nan Mu'azzam ya kama bakin shi. Bangaren su Nasir da Makama sun yi fushi sun ce in dai Aji bai ba su haƙuri ba to ba za su haƙura ba. Mu'azzam ya ba su haƙuri a madadin sa amman Nasir ya ce ya fita a wannan faɗan ba ruwan shi, shi ko gogan ya manta da abin da ya faru suna can sun ɗaukan ma kansu da Mu'azzam ya kara mgana sai cewa ya yi wani abu daman ya faru ne? Ya fahimci Nasir ya koya ma Makama banzan halinshi, shi yana da abubuwan da suka sha masa kai ba shi da Lokacin tunawa da abin da ya faru in kuma suna jiran ne shi ya Kira su ya ba su haƙuri alhalin shi dai bai san ya yi musu laifi gaskiya su yi ta jira. Suma ɗin fa su san halin shi kawai saka ma rai wahala ne amman Nasir na kira Mu'azzam ya ji ina aka kwana, saboda ya damu ko ya ya zai yi fushi da Aji abokatansu ba karya ba ne. Kimanin shuɗewar sati biyu Sannan ya samu natsuwar kansa. Ranar Asabar da Yamma ya shiga anguwan Arawa saboda maganar da za su yi da Baba, anan ya yi sallar Mangariba da Isha'i tare da su Baba A masallaci. Su Baba Sani har suna tara shi gefe suna mai faɗan zama haka ba amfani ya kamata ya ƙara aure, Baba Sani ya ce akwai yar abokinsa mallam mati in yana so yarinyar uwarta Jajir tunda Bafullatanace, kuma ta dauko kyan uwar ne, Baba Ɗanlami yace gwara dai ya zo ya duba a cikin anguwa in da ake ganin mutumcin ba inda ba'a ganin shi a wata tsiya ba. Duk bai katse su ba sai da su ka gama koro jawabinsu sannnan ya gyara tsayuwa yana faɗin" Na gode Baba da kulawa. Amman ni ban saki matata ba, ta je gida ta huta ne amman za ta dawo soon in sha Allahu." Yasan harda kuɗi suke bukata a hannun shi haka ya ba su 20k kowanne suka karɓa suna washe baki, duk da yana da abin da ya fi haka amman ba ya sakar musu kuɗi tunda yasan halinsu ba zuwa gidan suke yi su ba ma matansu a ji daɗi ba Sharholiyansu kawai su ke yi acikin gari shi ya sa ko kayan abinci ya gwammace ya ba ma Auwalu ya siya musu ya kai musu. A kofar gida suka samu keɓewa da Baba Ɗanjuma ya yi masa mganar Walida da Mariya ya ce zaman su ne ya ishe sa ba sun gama karatu ba? Mansoor ya ce" Eh sun gama matakin sakandiri ba, Ina so su cigaba har matakin jami'a in sha Allahu." Baba ya yi shuru kafin ya ce"A'a ni na fi son kowacce ta kama ɗakin ta kamar sauran ƴayana." Mansoor ya ce"To Baba, sun samu maneman ne? Baba Ɗanjuma ya gyara zama kafin ya ce" To ban sani ba, amman abin da ya sa na kira ka kenan, ka kira su dukkansu ka zauna da su ka ji in akwai waɗanda ke nenan su, in ka ji akwai sai a bincika in an aminta da nagartansu shikenan." Mansoor ya yi shuru kafin ya ce"In kuma babu fa? Baba Ɗanjuma ya ce shikenan sai ka ba su daman fara yin zence har Allah yasa a dace. Bai yi gaddama ba ya ce zai yi mgana da su in ya shiga cikin gida anan waje ya bar Baban wajen abokinsa Mallam Hashimu ya na ko shiga da Mariya ya fara cin karo tana wankin kayan da za ta saka gobe a dara nan shi bai ma ganeta ba sai da ya ji tana gaishe shi sannan ya tsaya ya na kallonta shi ya daɗe ma bai ganta ba. "Ke ina kike zuwa, ba na ganin ki a cikin gidan nan? Haka ya faɗa lokaci ɗaya yana kallonta da sauri ta ce" E. mm ina gidan Yaya Zuwaira ne." Kai tsaye ya ce"Me ya sa kika je can? Sai ta kasa mgana kanta na kasa dai dai lokacin da magajiya, ta ɗago labule ta Fito ta na kallon su, shi kuma ko kallo bata ishe sa ba kawai sai ya juya ya na faɗin" Barka da dare, ke Mariya ki same ni a ɗakin Inna zan yi mgana da ku." Yana gama faɗin haka ya yi wucewarsa Magajiya ta bi shi da harara. Bai ma san tana na yi ba tsaki ta yi lokaci ɗaya tana Kallon Mariya" Ko zai ce ki daina zuwa gidan Zuwairan ne tunda shi ne uban Ɗanjuma? Mariya ta kalleta kafin ta ce"Kai  Magajiya." hararanta ta yi kafin tac e" Dilla ta fi can sakara, kuma kije ki dawo ki gayamin abin da ya ce." Mariya ba ta kara mgana ba ta dai shanya kayanta daman ɗauraya take yi, ta wuce Bangaren Inna Meri ta samu ɗakin Maeesha a sakaye tunda Yaya Saddiqun na gari tun shekaranjiya ya shigo garin sai firita take yi tana shwagaɓa ita mai ciki, a falon Innar Daga Walida sai shi Junior ma ya yi barci Inna Meri kuma barci take ji bayan sun gaisa ta ce za ta shiga ta kwanta ta huta amman ba ta fara barcin ba ta ji yana tambayansu ko suna da ma su son su? Mariya da Walida suka kalli juna cikin mamaki, ita dai Mariya tana da samari ita kuma Walida ba ta da wani takammame, Tunda ba tsayawa take yi da samarin ba, Samnan ba ta da waya Inna ko yar ganin dama ce, in ta ga dama ko wayar ma walida sai ta yini ba ta gani ba Innar ta yi boyon kayanta mariya ko tana da waya wani Saurayin ta dake sonta ya siya mata. Ganin duk sun yi shuru ya sa ya yi gyaran murya yana faɗin" Baba na son ya aurar da ku, ni kuma ina son ku yi karatu wacce take ganin ta na da wanda ke sonta sai ta yi mgana." Walida ta yi shuru, kafin ta ce"Ni dai ba kowa, zan fi son na cigaba da karatuna Yar jarida nake son zama kamar Anty Mimi" Bai ce mata komai ba tunda hankalinsa na kan wayar hannunsa ne. "Ke fa? Ya faɗa ya na cigaba da duba wayarsa, murya can ƙasa mariya ta ce"Ni.. ni akwai wani." "Ina yake? Ya haka ya katseta da sauri ta ce" A tudum wada. Yaya Auwalu ma ya san ashi." Kai ya girgiza kafin ya ce"Ok zan yi mgana da Auwalu ɗin, ke kuma tunda ba ki ci Jamb ba  ba za ki zauna hakanan ba zan nema miki ko yar diploma ki je ki yi a kan na'ura mai ƙwalƙwala, kafin wata shekara sai ki sake rubuta Jamb ɗin mu ga Abin d Allah zai yi." Gabaɗayansu su ka yi masa godiya,  nan ya bar su ya fita bayan ya ce Walida ta gaya ma Inna ya tafi, ya so ya gaya mata gobe zai je kano amman kuma bai samu fuska ba, Ita ko Innar ta na jinsa mirmishi kawai ta yi, ko da ace shi ɗin yana da fitina amman kuma yana da kyakyawan hallayan da fole a ɗaga masa kafa. Tana jin su walida na kuskus a falo, Ko da ce ma Mariyan ba ta da saurayin Magajiya ba za ta bari ta cigaba da karatu ba, aure za ta ce ƴarta za ta yi, Walida kuma ta san ba ta da wani saurayi sai tarkace ita ba za ta saka baki ba tana da uba da Sauran yayyenta abin da su ka yanke a kanta ba za ta ja ba. Yana fita su ka kusa cin karo da Saddiqu da ya fito daga cikin ɗakin sa daga shi sai gajeran ƙaramin wando, Kallo kallo suka yi ma juna shi da Aji, kwarjini ya yi masa yasa ya ba shi hannu su ka yi musabaha duk da ya sha alwashin ba zai ƙara gaishe shi ba, sannan ga gulmar da Aishar ta kai masa amman ga shi ga Mansoor ɗin ya kasa masa wata mgana. Shi ko kallon kasa da sama ya yi masa kafin ya ce" ya kamata dai kasan a yanayin da za ka riƙa fitowa, nan gidan akwai iyayenmu akwai ƙannen mu bai kamata ka riƙa fitowa haka ba." Yana gama faɗin, ya saki hannun shi ya yi wucewarsa ya bar Saddiqu na bin shi da harara sai da ya tabbatar da ya bar shashensa sannan ya saki tsaki yana faɗin" ƴan ƴan, sarkin iyayi ai sai ka hanani ni da gidan ubana." Daga baya kenan. ******** *03rd Febuary 2023* Ba a motarsa ya shirya tafiyan ba. Sai ya shirya tafiyar tasa a motar haya. Takwas na safe yana tasha kafin tara motar kano ta ɗaga da Aji aciki kuma har a lokacin yana kiran wayar mimi amman amsar ɗaya ne tana kashe ne, Daman tun kwanaki ya saka Mu'azzam ya tura masa lambar Dr. sulaiman ɗin bai kuma kira shi ba sai da ya sauka tashawajen sha biyun saura na rana sannan ya kira shi. Wajen kira biyu ya yi masa ana uku ne ya ji an ɗaga kiran da sallama, shima sai ya amsa masa suka gaisa. "Ba ka gane wa ke mgana ba ko? Dagacan bangaren Dr. sulaiman dake haraban asibitin Aminu kano ya fito daga duba Patient ɗin da ya yi ma tiyata jiya ya samu Kiran Aji. "E wlh ban gane ba. Lambar ba bu suna.". "Sunana Mansoor Aji, mijin ƙanwar ka Fatima Mimi." Mirmishi ya suɓuce ma Dr. Sulaiman yana gyara zaman gilashin da ke idonsa ya ce" Allah sarki, kasan da ya ke ba mu taɓa waya ba shi ya sa ban ɗauki muryan ba." Aji ya jinjina kai kafin ya ce" Gani na sauka a tashar Kano. Adireshin gidanka nake so, na zo wajen matata ne." Ciki mamakin da har ya bayyana saman fuskar Dr Sulaiman ya ce"Ikon Allah, ok to yanzu na shigo asibiti ne na duba patient ka gaya min tashar da ka sauka sai na ƙariso  na ɗauke ka ko? Sai Aji ya waiwaya ya ga sunan Tashar ya faɗa masa sai Dr ya ce ga shi nan tafe in sha Allahu. Sannan suka yi sallama ya ƙarisa wajen motarsa ya buɗe ya shiga. Sai da ya hana Mimi tafiya amman Daddy ya ce a kyaleta tunda dai har ya ji labarin ya bita wajen Hajiiya kuma ya taka har Abuja saboda ita amman kuma ba ta bari sun haɗu ba, Ya yi mata faɗan ta koma Gombe amman Mimi taki jin mganarsa yanzu kuma bai san da wani yare zai faɗa masa Mimi ta bi Madiha da mijinta zuwa Umra ba. Yana wannan tunanin cikin lokaci ya isa ta shar Allah ya taimake shi bai haɗu da mugun Goslow ɗin kano ba, daga bakin tashar ya tsaya saboda in ya shiga wajen fitowa ne matsalan tunda tashar Kano Line ne sai ya kira layin da Aji ya kira shi da farko ya ce ya ɗan Fito daga tashar ya na nan a bakin tashar a wata mota mai ruwan toka. Ba su sha wahalan gane juna ba, Dr Sulaiman ya fara gane Aji tunda ya san shi, shi kuma Aji fuskar Mimi ya gani a fuskar shi sannan ya ɗaga masa hannu kuma ga shi a jikin mota mai ruwan toka. Aji ya na sanye da shadda mai ruwan toka ɗinki zamani ya dora bakar dara a kansa takalmin kafarsa sahu waje ne. Sai wayarsa kawai dake hannunsa. Bayan ya ƙariso suka yi musabaha sannan Dr Sulaiman ya buɗe mai gaban mota ya shiga suka ɗauki hanyar cikin gari. Gidan Dr na anguwan sharaɗa ne. Suna tafe Dr. Sulaiman na jan sa da hira shi kuma ya na amsa masa ɗaya da ɗaya, yawanci kan mganar wasa ne, Dr na zolayansa da cewa za su riƙe shi ya buga musu wasan kano Pillars da kuma Gombe United mirmishi kawai Aji ya yi amman bai yi mgana ba. Su ɗan ja lokaci kafin su isa gidan, tunda da nisa, sun isa gidan ɗan madaidaci mai kyau da shi har sai da ya burge Aji. A Haraban gidan ya faka motan suka firfito Aji bai yi niyyan shiga cikin gidan ba sai kawai ya ce"Ka yi mata mgana kawai." Sai Dr ya ce" Haba dai ka shigo mana bakomai nan ma gida ne." Sai Dr ya yi masa kwarjini ya sa ya bishi suka shiga ta falon ɓakin sa na kofar waje. Sai ya ce Aji ya zauna bari ya shiga ya fito sai ya jinjina masa kai, ya samu ɗaya daga cikin Kujerun falon ya zauna yana ɗauko wayarsa yana dubawa. Ya so ya kira Mu'azzam sai kuma ya fasa, yac e sai ya gama rigimarsa da Mimi sannan zai neme sa. Dr. Sulaiman kuma na shiga cikin gidansa ya iske Jawahir a falo turus tana zaune da tsininin cikinta a gaba. Yara duk ba sa nan suna Mandawari sun je gidan kakanin su..ta na ganin shi ta sakar mai mirmishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka dawo da wuri yau." Yana zama gefenta yac e"Kinsan ba aiki na je yi ba, duba Patient ne kawai." Sai ta gyaɗa kai ta yinkura ta mike dai dai lokacin yake faɗin" Kun yi mgana da Mimi tun bayan tafiyar su Umra? Jawahir ta ce"Sau ɗaya muka yi mgana lafiya dai ko? Sai kawai ya miƙe yana faɗin"Bako gare ta. Mijinta ne ya zo." Jawahir ta zaro ido kafin ta ce"Yana ina? Sai ya nuna mata falon baƙi yana kora mata jawabin yadda aka yi ya ƙarishe da faɗin", na rasa me zan ce masa." Jawahir ta ce"Gaskiya ba daɗi, tun zuwansa Abuja na yi ma Mimin faɗan ta yi hakuri ta koma gida ta saurare shi a kallah dai ai ya nemata, ina amfanin wannan abu kuma? Ai sai ya ɗauka kuma mutanen banza ne." Dr ya mike lokaci ɗaya yana fadin"Daddy ne duk ya ke biye mata, amman yanzu dai haɗo min ruwa da lemu akwai abinci? Sai ta ce sai da miya amman bari ta dafa ko shinkafa ne da Ssauri sai ya ce ta hanzarta, Ta wuce Kitchen duk da cikin ta ya girma amman matar likita ce motsa jiki a wajenta na da matukar amfani. Shi kuma Dr. Sulaiman sai ya kira Daddy bai dauka sai da ya ƙara gwada kiran shi sai ga shi ya ɗauka sai daga baya ya tuna yau oahadi ne, bayan sun gaisa sai ya ke gayamasa zuwan Aji tare da cewa"Daddy ina jin kunya me zan gaya masa? Kai ya ce"Ka gaya masa gaskiya mana, miye abun ɓoye ɓoye." Dr Ya yi kasaƙe bai yi mgana ba jin haka ya sa Daddy ya ce"Ka ga kada ka damu, in har yana da hankali ya san in da zai zo komai ya warware." Ya kashe wayarsa ya na yar dariya ɗan tselen uwa ashe dai ƴa na son fiyar ta shi har yanzu, in gaji da zagaye zagaye zai neme shi, a lokacin shi kuma zai gaya masa matsayarsa. Jiki a sanyaye Dr. ya kwashi farantin ruwa da Lemu ya kai ma Aji dake zaune a falo har ya fara auna Mimi ta shigo falon nan ya fara balbaleta da faɗan sa amman maimakon ita sai Yayanta ya kara gani. Da ya ce ba zai sha ruwan ba sai ya nuna bai ji daɗi ba shi ya sa sai ya tsiyaya ya sha kaɗan shi da Babban shan ruwan shi ya ga Mimi a gabansa. Amman sai ya ga ba ta zo ba,.Sannan Dr na zaune bai yi masa wata mgana ba sai ya gyara zama yana faɗin" Mimin ba ta nan ne? Dr ya sauke numfashi kafin ya ce"Eh. Ba ku yi waya ba ne? Aji ya maimaita E, cikin mamaki kafin ya ce" Ba ta nan?  To ta na ina? Ya faɗa cikin mamaki sannan lokaci ɗaya ya na ɓoye takaicin sa. Cikin ɗan jin nauyi Dr ya ce"Tana Umra. Ta je Lagos wajen Madiha to ita da mijinta za su je Umra sai ta bi su suka tafi tare daman tana tare da Internationl ɗin ta, na ɗauka ma ko kun yi waya ne ta sanar maka? "In ta sanar da ni ai da ba za ka ganni ba., Ni ba ta kirani ba asali ma na ɗaɗe ba na samun ta waya, kenan ka ga tafiyar da take yi ba da izinina ta ke yin su kuma, tunda har gobe ina matsayin mijinta ban ce na saketa ba, sannan ban ce ta yi yaji ba ganin damanta ne sai na kyaleta saboda ita mace haka t ke in ta gaji da abu sai ka bata iska, Amman ace da yau sakinta na yi da iddata ne akanta kuna Iyayenta za su  barta ta riƙa yawo gari gari? Yanzu ma wata kasar ta fi ba tare ni Mijinta na sani ba tsakanin ga Allah hakan da ta yi ya dace ko a bangaren zamantakewa kafin ma a shiga mganar Addini.? Aji ya karishe faɗa yama mai ƙura ma Dr Ido shi kuma sai ya jinjina kai kafin ya ce"Tabbas bai kyauta ba amman ka yi haƙuri, ni kaina ban san da tafiyar ba sai ana gobe tashin su amman zan kira wayar Madiha tunda kamar Mimin ta kashe wayarta zan gaya mata ta dawo akan lokaci." Mansoor Aji miƙewa kawai ya yi lokaci ɗaya ya na saka wayar a cikin aljihun gaban Rigarsa kafin ya ce"A'a ku ƙyaleta kawai." Takaici ne da ɓakin ciki suka hana shi mgana Dr na roƙomsa ya tsaya ya ci abinci ya ce ba zai tsaya ba. Cikin jin nauyi Dr.Sulaiman ya ce"To haka za ka koma baka ci komai ba? Sai kawai ya samu kanshi da Cewa"Ba wani damuwa, da yake ma kasan kanina SP ne a nan garin zan je gidansa mu haɗu." Haka nan kawai ya ji yana faɗin haka, Dr Sulaimam duk bai ji dadi ba hakanan suka yi sallama ya rako shi har waje yana kara bashi hakuri shi kuma ya ce bakomai Saboda ya raunana Allah Mimi ta kure hakurin shi zuwa yanzu ya rasa matakin ɗauka a kanta duka matakan ƴakinsa sun rushe da gaske take yi abij da ta faɗa ba za ta bari su yi mgana ba, kuma da gaske take yi ta hakura da auran shi. Sai yaji duk ya damu wata zuciyar na gaya masa duk laifinsa ne me ya sa a daran bai tsaya ya bata hakuri ba? Sai ya fara jin Tsoro kada Mimi ta suɓuce masa a karo na biyu in wancan karon ya sha wannan karon ba zai iya sha ba kam. Sai dai kawai Mu'azzam ya samu wayar Yayan na shi ya na tambayan shi yana ina? Shi kuma lokacin ya na Office ya zo saboda mganar Cases ɗin wani maraya da dangin babansa suka cinye ma gado. Sai ya ce masa yana Office abun mamaki Ranar da ta zama ranar tarihi ga Mu'azzam kawai sai ji ya yi Aji ya ce ya tura masa adireshi ga shi nan zuwa. Ko kafin ya kariso ya fito haraban Division ɗin na su ya na jiran shi,.Yana sanye da kakinsa ya fito a matsayin SP M.G ƊANJUMA, wato Mu'azzam Gaddafi Ɗanjuma. Bakin nan yaƙi rufuwa karon farko da Mansoor zai kawo masa ziyara wajen aikinsa,.Sannan a karon farko za su haɗu da kaki a jikinsa. Sun kuma haɗu, Mansoor sai da ya ji wani iri ganin ƙanin nasa cikin uniform Rumgume shi ya yi kamar ya samu karin girma zuwa DPO tsabar murna da zumuɗi. Sai ga Mansoor a kayattacen Office din ƙanin nasa gwanin burgewa. Ba wani takarce bayan wajen zama sai daga can haka wasu kananun kujeru. A kwai hotunan gwamma garin sai na Sarki  a saman teburin Mu'azzam kuma akwai hoton Junior sai a gefe hoton Mansoor ne da kayan kwallo a jikinsa ya yi ɗan mirmishin gefen baki. Mansoor sai da kwallah ya tarun masa a ido, ya yi saurin basarwa, Mu'azzam ya rasa ina zai saka shi ya ji daɗi, nan da nan ya saka aka haɗo masa shayi ya na kuma rawan jikin tambayansa abin da zai ci kawai sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Ka natsu, ai yanzu na zo ni da zan ƙarisa har gida in sha Allahu." Mu'azzam ya ji kamar an yi masa bushara da gidan aljannah jiki na rawa ya kira Hibba ya gayamata suna da babban bako a tanadi abinci bai gayamata ko waye ba amman yanayin murnan shi ya sa ta san baƙon mai muhimmanci ne. Ba su zauma ba sai da su ka yi sallar azahar Kowa kuma sai Mu'azzam ya nuna shi ya ce Yayansa ne daman ko da ya ƙariso mutanen da zai gani ba su kariso ba sai da Mansoor ɗin ya jira suka gama ya sallame su sannan suka natsu yaya da ƙaninsa domin tattaunawa. "Allah ya sa dai kun gama mgana da Anty Mamin? Aji ya yi shuru kafin ya ce"Ban ganta ba, bata nan wai ta je Umra? Mu'azzam ya zaro ido kafin ya ce"Umra? Topha? Ikon Allah." Shi kan shi lamarin ya ba shi mamaki kafin ya ce" To kuma ba ku yi mgana a waya ba? Aji ya girgiza kansa kafin ya ce"Na gaya ba na samun wayarta kwata kwata.". "To me take so ne? "Ƙure ni take son ta yi mana? Kuma kamar ta yi nasara, Mu'azzam na fara jin tasoro, ina jin wani tsoro na shiga na tsoron da ban taɓa jin irin sa ba" Ya faɗa cikin karyewan sauti, daga alamu kuma abin da ya ke faɗa daga karkashin ransa ne ganin yadda ya yi laushi lokaci ɗaya. Bai ma Mu'azzam damar mgana ba ya cigaba da faɗin. "Mu'azzam kana tunanin Mimi za ta dawo mu cigaba da zama? Ko kana tunanin abin da ta faɗa da gaske ne? Mu'azzam ya ji tausayin Yayan nashi cikin kwantar da murya ya ce"A'a ni fa ina ganin akwai abin da kake yi mata ne ba ta so, in za ku zauna ku samu daidaitu za ta dawo in sha Allahu." Aji ya dafe kansa lokaci ɗaya yana faɗin" To ta ƙi ba ni damar haka? Allah ba zan mata faɗa ba zan saurareta wannan karon, sannan ina ji a zuciyata zan iya mata abin da ta ke so, mganar gida kuma sai in da take so za ta zauna na janye duka sharuɗda na a kan ta." Ya faɗa lokaci ɗaya yana tagumi kafin ya cigaba da faɗin "Mu'azzam na taɓa ga ya maka ina son Mimi? Na taɓa ga ya maka itace rayuwata? Ya faɗa yana mai kallon ɗan uwan na shi Mu'azzam ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce" Na san kana sonta mana amman abin da ban gane ba me ya sa bayan ka same ta ka kasa nuna mata wanman son? Me ya sa kuma ka ga ya mata ba ka sonta? "Ba ni da wani dalili Sai na jin hauahin abin da ya faru a baya. Sannan Allah ni fa ba gaskiya na faɗa ba, kawai dai na faɗa saboda ta ji haushi, kuma ita ta ja na faɗi haka saboda ita ta riƙa ja na da maganganu." Haka ya faɗa yana rike fuskarsa yana sakin huci Saboda tsoro ne ya shigesa tsoron rasa Mimi a wannan karon. Har ga Allah tabon dake zuciyarsa ya fara raguwa ga shi har ya zo Office ɗin kaninsa ya zauna suna mgana kai, ka ba ma zuciyarka aminci ma wani salama ne zama cikin kunci ba shi da amfani. Yau ɗin ranar sakin duk abin da ke damunsa ne haka ya riƙa yi ma Mu'azzan zan tuka na fita hayyaci da nadama. Sai Kawai Mu'azzam ya ce"Ina da shawara me zai hana in ka koma ka nemi Babanta Alhaji Hamza? Tsohon Sanata tunda shine Waliyinta? Aji ya yi shuru kafin ya ce"Da na ce ba zan je ba, amman yanzu ai ba ni da zaɓi. Zan je in sha Allahu da zaran na koma." Sun ɗan tattauna Mu'azzam na kara gaya masa in ya je ya kwantar da kai tunda sulhu ya ke so, Bayan nan suka gangaro kan mganar gida Mu'azzam na faɗin Bintu ta gaya mai Inna wulakanci take kwasa tun bayan dawowar Matar Saddiqu bangarenta. Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ka san Allah na kusa ɗauke Inna daga gidan, kawai dai ba na so Baba ya ga na nuna masa shi ya gaza ne." Mu'azzam ya yi saurin cewa" Ni ma na yi wannan tunanin. Tunda Dai Magajiya ta fi ƙarfin  Baba ba ya iya tsawarta mata, Inna kuma kasan halinta ko dukanta za su yi ba za ta taɓa mgana ba." Mansoor ya koma ya jingina da Kujeren da ya ke zaune kafin ya ce" Kar dai a yi wani abin da zai ɓata min rai, zan ɗauke Inna gaskiya a wannan gidan." Mu'azzam ya ce"Ko Yaya Amina abin da ta ce kenan gidan duk ba daɗi." Sun cigaba da tattaunawa har kan batun su Walida Mu'azzam ya ce hakan ya yi dai dai, Aji yac e da zaran ya koma zai nemi Auwalu kan mganar ita Mariya. Nan su ka shantake sai bayan oa'asar sannan suka ɗumguma zuwa gidan Mu'azzam d ke BUK old site. Sai dai Hibba ta ga Yaya Mansoor kamar daga sama  itama bakinta kamar zai yage, faɗi take yi" Lalle muna da babba  baƙo, sannu da zuwa Yaya Mansoor" Ya amsa mata cikin sakewa abincin da ta yi sun fi kala huɗ nan suka baje suka ci suka sha suna ta hira kamar kada su rabu, Mu'azzam ya kira Inna ya sanar da ita ga shi ga Baban Inna itama kanta ta yi mamaki ta ce ya kyauta. Sun ɗauka ma ko kwana zai yi ya ce ba zai kwana ba. Sanin halin shi ya sa Mu'azzam bai matsa masa ba wajen shidda da rabi ya kai shi tasha ya hau mota sai da suka tashi ya dawo gida tafiyar dare suka yi sai wajen sha biyu ya iso Gombe, bai je gidansa ba a Camp ya kwana kuma evening Traning suke dashi shi ya sa tun bayan sallar asuba ya kwanta barci ya kwashe shi. Bai ta shi ba sai da ya ji ana ta kiran wayar sa yana tashi ya Duba sai ga inna ta kira shi Bintu ma haka. Sai ya bi bayan kiran yana duba Lokaci goma saura na safe, Wayar Inna ta na ƙara ba'a ɗauka ba, yana cikin neman Bintu sai ga kiranta sai ya ɗauƙa da sauti gabansa na faɗuwa yana tunanin ba lafiya. Kuka ya ji ta na yi masa, da sauri ya miƙe ya na laluban rigarsa. Cikin fargaba ya ce"Bintu me ya faru ne? "Faɗa ake yi a gida saboda Matar Saddiqu ta dagi junior har sai da ta ture shi ya fasa goshi, shi ne shi ne Walida ta yi magana Meesha ta ja ta da faɗa suka kama Kokuwa sai ta faɗi, Saddiqu na zuwa kawai ya rufe Walida da duka Inna ta zo ta hana ya tureta har sai da hannunta ya goce." Bintu ta faɗa ta na shesshekan kuka, Aji ya ji wani abu ya taso masa a ƙasan zuciyarsa. cikin maimaitawa ya ce"Ta goce? Ita Inna ce ya gotar don uban shi? Lalle ne ma." Haka kawai ya ce ya kashe wayar daman ya saka riga kawai sai ya zura takalmi ya ɗauki key ɗin mota tabbas yau Saddiqu zai fahimci yana cin darajan mai daraja ne amman tunda har tura ta kai bango yau za'a buga final ɗin. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3005* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Cikin girmamawa suka gaisa da Hajiya, Ita kuma ta amsa masa cikin sakewa kamar wani abu ma bai faru ba. Har ta na masa irin zolayan da ta saba yi masa, tunda har ga Allah ba ta san da zuwan sa ba tunda Binta ba ta kira ta ba. Kallon sa ta yi kansa na duke lokaci ɗaya tana faɗin" Ka makara da zuwa biko, Binta ba ta na nan shekaran jiya can ta tafi can Abuja wajen Murja. Hala ba ku yi waya ba ne? Kansa na kass a cikin zuciyarsa ya maimaita" Abuja? Lalle ne ma Mimi ta maida shi wani sakarai ya ga alama akwai kasawa ma ya ce ma Hajiya sun yi magana a waya shi ya sa kawai sai ya ce mata ya kira wayar ta bai same ta ba. Hajiya ta muskuta kafin ta ce"Ai ko ba ta nan, amman tunda biko ka zo kuma ta karfe ta gudu, me zai hana ni mu daidaita? Ta fada cikin Sigar zolaya yar dariya ya yi yana shafa kansa kafin ya ce" Haka za'a yi Hajiya." Shuru na wani lokaci, Hajiya ce ma take ɗan Jansa da hira tana tambayan shi aiki da mutanen gida. Ya amsa mata da duk suna lafiya kai tsaye ta ce" Ka gaida min da Meri dakyau dakyau." Ya amsa da In sha Allahu, ko ruwan da aka kawo masa bai sha ba ya yi ma Hajiya Sallama da cewa zai koma. "To ko za ka ƙarisa gidan Babanta Hamza ne. Daman  yana neman ka." Hajiya ta ce tana kallonsa lokacin da ya miƙe shi kuma ba ya son wata doguwar mgana sai kawai yace mata Toh, amman shi ya san ba zai je ba wato ya kai kansa kenan tunda daman ana jiran shi. Kuɗi ya ijiye ma Hajiya a nan ƙasa ta saka hannu ta ɗauka tana faɗin" Ai shike nan kana bikon dani tunda ka fara toshi, Na gode kwarai Allah ya ƙara ma rayuwa albarka." Ya amsa mata da Amin Amin sannan ya yi mata sallama ya bar falon ta bi shi da kallo,  Binta ta cika taurin kai sai da ta hana ta tafiyar nan amman ta haɗa ta da ubanta ya ce a ƙyaleta ta je ta gaida mahaifyarta ga shi megidanta ya zo ba ta nan, Baaba Uwani Hajiya ta kira ta Umarce ta da ta Dauko mata Wayarta a cikin ɗakinta. Bayan ta kawo mata sai ta ce ta kira mata Binta tunda Baaba Uwani ta iya karatun Hausa ita ta nemo lambar Mimi ta kira ta sqnnan ta miƙa ma Hajiya tana ɗauka ta fara faɗin" Hajiya ta, kin yi kewata ne? Hajiya ta ce" Kin san cewa yanzu mijin ki ya bar gidan nan yana neman ki? Sai Mimi ta gyara kwanciyarta kafin ta ce" Wa? Aji? Ban sani ba saboda bai kirani ba." Ta yi ma Hajiya ƙarya. Sai ita kuma Hajiyar ta ce"To ya zo, na sanar da shi bakya nan amman na ce ya karisa wajen babanki  ke kuma sai ki yi kokari ki dawo a daidaita ki koma gidan Mijin ki." Ba gaddama ta amsa ma Hajiya  saboda ko ta ce za ta yi gaddama Hajiya ba za ta gane in da ta dosa ba ne. Bayan sun gama waya da Hajiya ita kaɗai take ta Mirmishi, Kaɗan ya gani yanzu ma aka fara wasan ba ɗaɗewa ko sai ga kiran shi ya sake shigo mata wannan karon ba ta kashe ba barin shi ta yi har sai da ta katse, wani kiran ya ƙara shigowa ya katse har sau uku bayan mintina kaɗan sai ga saƙon sa. "Kin raina ni ko Mimi? Kina jin daɗin kin yi wasa da hankalina ko? to ya yi miki kyau amman ina so ki sani ki sauke wannan abin da da ki ka ɗauka na tunanin za ki wahalar da Aji ko ki yi ramako a kaina, Never zuwan ma da kika na yi saboda inna da Baba sun matsa sai na zo na dawo dake gida, in kin ga dama daga nan Abujan ki ci gaba kin ji ko." Daga ganin yanayin saƙon ta san ranshi ne ya ɓaci, tana yar dariya bayan ta karanta wato zai fake da Baba da Inna shi a dole kada a hango ya gaza,  a lokacin ba ta yi tunanin maida masa da martani ba sai bayan kamar awa ɗaya tun da barin ɗakin ta yi zuwa falo in da Asma'u ke kallo Mommy kuma tana ɗakin ta tana faman duba takardu sai wajen goma saura ta Daawo ɗakinta ta yi wanka ta kuma yi shirin kwanciya sai da ta kwanta sannan ta jawo wayarta ta tura masa saƙo. "To shike nan zan ci gaba kamar yadda ka ce." A lokacin da saƙonta ya shigo kamar tasan yana kwance ne yana kisima hukuncin da zai yanke Mata in ta bari suka haɗu, tsabar ma takaici ko abinci bai ci a daran kuma in ya je gidan Inna ba bashi za ta yi ba domin tun bayan barin Mimi gidan inna ta daina masa tayin abincin ko ya ce zai ci sai ta ce ya kare ko da ga shi nan ko yana gani shi ya sa yake rufa ma kansa a siri ko ya gani bai nuna yana bukata. Barcin sa rabi da rabi ne a baya ne da yasan Mimi na ƙarƙashinsa ya ke samun Ishasshen barci amman tunda ya fahimci kamar ta yi masa nisa ya daina samun barci cikin natsuwa. Shi fa a ransa sai da ya ga laifin Hajiya ta ya ya za a su bar matar aure tana yawo ba tare da sanin Mijinta ba shi fa tafiyarta Abuja ta fi masa raɗadi fiye da yadda take yi masa wannan renin wayau. Da farko ya yi alkwarin ba zai ƙara kiran ta ba amman ba shi da mafita saboda ya kasa sukuni ko da bai kirata ba yana bibiye da dukkkan wani motsinta. Haka kawai saboda ita zai hau facebook da WhaApps ya duba ta, a Facebook duka Account ɗin ta guda biyu na Fatima Kabir Dabo(Mimin karamchi) da kuma na wanda ta buɗe a ɓoye na MIAJ, duk ya san dasu kuma yana vibiyanta amman ba ta taɓa sani ba, to abubuwa da dama ma ba ta sani ba wani abun gwara ka bar shi a rufe saboda Sanin shi a lokacin ba shi da wani amfani. Yini yake duba ta sai ya ga ba ta saka komai ba kamar ma tun bayan auransu motsin Account ɗinta ya dakata. Sannan ya duba bangaren hidan tibin da take aiki, daman tun kwanaki ya ga ma kallata gidan Tibin suna ta cigiyarta sai suka ba da sanarwan ta na nan lafiya ta ɗauki hutu ne ma'ana Anaual leave ɗin ta, ƙaramin tsaki ya ja shi fa ya tsani aikin nan domin shi bai ga wani amfanin shi a Al'umma ba, Kuma zai bude data yana ganin tarin Groups da aka saka shi yawanci duk na ƙwallo ne tunda babu wani Team na nan Gombe da ba'a saka shi a ciki ba, akwai wani ma da tunda aka saka shi an tara saƙo sama da dubu bai taɓa buɗewa ba, kuma ko a Private ka yi masa mgana in ka ci sa'a ya buɗe ya karanta ba zai maida maka amsa ba sai dai in ta kama ya kira ka. Saboda gani yake ɓata lokaci ne ya tsayawa yana typing. Shi ya sa duk yadda su Nasir suke caccakan sa a group ɗin su na Brother's bai ko shiga ba, Ko mu'azzam ba ya chart da shi sai dai in ya ga ya yi masa mgana ya sauka ya kira shi, yawanci ma shima yasan hali yafi tura mishi hotuna ko wani abu mai muhimmanci,group ɗin su na jami'a ko tuni ya fice,an sake maida shi ya sake fita har sau uku, daga nan suka ƙyaleshi. Har ta goup ɗin su na Gombe United kowa na da amfani ban da shi hatta Coach na su yana mgana da sauran bayanai amman shi sai dai a waya ko ya je Camp ɗin ya tara su yi magana shi ya zauna ne wai ya ga yana rubutu ya ke ganin shi a ɓata lokaci ko kuma wai ya kunna voice note shi fa har mamakin ma su yi masa vioce yake yi, wani mai tsawon ma shi ai ba shi da wannan lokacin, wani lokaci yana buɗewa yake kashewa ba ya da lokacin saurara shi ya sa ga wanda yasan tayuwar Aji gwara ya kira shi a waya amman domin ya yi magana ta chart kamar ya zama aikin banza ne Gabatowar wasan da suka shirya ne ya sa ya rage Tunani da damuwar Mimi sai da aka buga wasa aka ta shi lafiya sannan ya dawo natsuwarsa, kuma shi abin da ke ba shi mamaki Inna ƙiri ƙiri ta nuna ta fi son Mimi a kansa tsakani ga Allah shi fa Ɗanta ne, Ita fa Iyayenta ba su juya mata baya ba sai shi? Haka zai je Inna Meri ta yi kamar ba ta gan shi ba da ya Kira Mu'azzam ya yi masa ƙorafin abin da inna ke yi masa kai tsaye ya ce"Ni fa ba ruwana tunda ka ce kowa ya cire bakin shi a ciki." Cikin haɗe rai Aji ya ce"A maganar Mimi ba,  maganar Inna fa dole za ka yi min amfani ka kira ta ka nuna mata ni fa Ɗan ta ne ai bai kamata tana banzarta da ni ba, ita kanta Mimin da take min haka saboda Ita iyayenta ai ba su nuna son fi sona da ita ba, Itama Inna ta gane mana kowa fa nashi ya sani." Mu'azzam na ta faman danne dariyansa, amman sai da ta fito Aji ya ji sa. Sai kawai ya yi kafci kafin ya ce" Au dariya na baka? Ya yi maka kyau." Daga nan ya kashe wayarsa, Mu'azzam ya biyo bayan kiran aka yi banza da shi ba'a ɗauka ba. Dole ya Kira inna Meri domin yi ma fan'uwansa biko, ya kuma maida mata abin da Mansoor ɗin ya ce kowa fa na shi ya Sani inna, ki yi masa hakuri in sha Allahu zai daidaita komai. Sai da ta gama jinsa sarai kafin ta ce"Mu'azzamu in kana son kanka da arziƙi a wajena kada ka ƙara kirana kan mganar ɗan'uwanka, ni na ce na yafe masa amman na tsame hannuna a kan rayuwarsa ya yi duk yadda ya ga dama." Mu'azzam ya ce"Inna to ai baki haƙuran ba kenan, cewar da ki ke yi kin tsame a hannun ki  a kansa kamar baki ne fa ki ka yi masa" Inna Meri ta ce"Ban yi masa baki ba, kuma na yafe masa saboda ɓacin raina ma kaɗai bala'I ne wajensa, amman ba zan ƙara bari Baban inna ya ɓatamin rai ba, tunda shi haka ya ke ba ya jin mgana sannan abin da ya ga dama shi yake yi to ba sai ya je ya yi ta yi ba, ai yanzu ba mai ce masa don me, ni ce kuma na tsame bakina da hannuna a kan sa." Mu'azzam na so ya ƙara mgana. Amman Inna Meri ta ƙi sauraran shi cewa ta yi in mganar da ya kirata su yi kenan za ta kashe wayarta dole ya bar maganar. Sai washegari ya samu Aji ya ɗauki wayarsa shi kuma ya gaya masa yadda suka yi da Inna numfashi ya furzar kafin ya ce" Ai shike nan." Mu'azzam ya ce"Mafi masalaha ka je ka Dawo da Anty Mami in har kana son Inna ta Daina fushi da kai." Cikin jin haushi ya ce"Wai ba na je ba. Tayi tafiyarta wai Abuja domin ta raina ni, da aurena a kanta amman iyayenta sun barta tana yawon tafiye tafiye." Yadda ya faɗi mganar ne ya sa Mu'azzam ya yi shuru yana danne dariya kada ta fito abin a ya shafe sa. "Gaskiya ba ta kyauta ba. To ka kira ta a waya mana? "To taba ɗauka ne? Wani irin kira ne ban yi mata ba ta ɗaga kirana ba." Mu'azzam ya yi tsai kafin ya ce"Topha! To ko za ka shirya ka je can Abujan ne ka same ta? Kasan mata fa yan Lallashi ne in ta ga ka Bbta za ta sauko sai ta Saurare ka." Kai tsaye ya ce"Amman ba ka da hankali Mu'azzam ni ne zan bi ta har Abujan? Lalle to ta shekara a can." Mu'azzam na shafa kansa daga can bangaren ya ce"Ba za a yi haka ba. Ya kamata ka samo mafita saboda Inna." "To ai daman saboda ita ne ya sa ka ga ina bin ta amman ni har Mimi ta isa ina kiran ta a waya tana min wulaƙanci? Sai ya yi kafci kuma shi kaɗai irin abun ya nan ya gama ɓata masa rai. Shi ko Mu'azzam wayar ya matsar gefe yana ta dariya shi kaɗai sai ji ya yi Aji na faɗin"Ni na ce ba zan kara kiranta ba  amman kai in za ka kirata ne ba zan hana ka ba tunda ka matsa" Mu'azzam ya yi ta dariya bayan sun gama waya da daddare ne lokacin Hibba na tiolet ta na wanka tun tana ciki ta ke jiyo dariyan Mijinta sanda ta fito ta iske shi ya na Dariya shi kaɗai cikin mamaki ta ce"Me ka samu ne kake ta dariyan nishaɗi? Yana dariya yana tuna amsar da ya bama Yayan na shi da cewa" Nima fa ba ta ɗaukan wayata. Sannan daga baya ma ina jin rufe ni ta yi ko na kira ta ba na samun ta, Ai ina ganin wannan faɗan ya fi karfin ƙanin miji sai dai mijin da kansa." Kawai sai Aji ya ce"Kai dai ka sani." Da haka ya katse wayarsa ya bar Mu'azzam na Kwasan dariya shi kaɗai. "Ina nan ina dariyan Yaya Mansoor, ina tunanin mu kusa mu ji shi a garin Abuja ya je biko." Hibba ta ƙariso gefensa da sauri tana faɗin" Ba ni in sha, me ya faru?. Nan ya labartamata abin da Yayan na shi ya gaya masa yaje gidan Hajiya Mimi ta tafi abuja sannan ya na kiran wayanta ba ta ɗauka. Hibba ta saka dariyan ƙeta kafin ta ce"Kai na gode ma Mimi, ai sannu sannu ba ta hana zuwa sai dai a ɗaɗe ba'a je ba." Mu'azzam ya ce"Ina tsausayin shi ni nasan duk ya damu amman ba ya son ya nuna ace ya damu da ita, kuma muna nan dake zai kirani ya ce zai je Abuja amman saboda Inna ne." Hibba na dariya ta ce"Nan gaba kaɗan zai ce saboda ke ce rayuwata. Sunan Inna tuni zai manta da shi." Dariya suka saka har suna tafawa, Mu'azzam ya san waye yayan shi fiye da kowa amman ya na tausaya masa Saboda ga duk alamu wannan karon Mimi sai ta Jijiiga yan maza. Daran shi da Hibba kusan raba dare suka yi suna ta tattauna batun Hibba na goyon bayan Mimi shi kuma Yana goyon bayan Yayan shi yana tausayin shi ita kuma Hibba ta ce ai gwara dai a jijjiga shi saboda duk abin a ya faru shi ya ja. Daman ance ai dama ɗaya take zuwa a rayuwa shi ya bar daman na shi tun a farko ga shi yanzu ya fara nadama dukda dai bai fito ya furta ba amman kowa ya san ya yi nadaman maganganun da ya faɗa Mimi a wannan daran. ****** Mansoor bai ƙara tsinkewa da lamarin ba sai daran ranar jumma'a da ya zo gidan, shima ɗin ya zo duba Baba ne da baya jin daɗi mura ta kwantar da shi.Shima sanin shi Yaya Amina ce ta kira shi take gayamasa Mu'azzam ma ya kira shi baya kusa da kuma ya zo ya gani bai kira ba. Baban ya ji sauƙi amman ranar bai fita ko'ina ba yana gida. Zuwan Mansoor ne ya Dauke sa zuwa wani ƙaramin cinic suka amso mganguna ya biya ya siya masa tsire da fura sannan ya dawo da shi gida ya kuma kaisa har ɗakinsa ya tsaya a kansa ya ci naman ya sha furan kaɗan ya balla masa magunguna ya sha ya kwanta. Inna Meri ta yi ta shigowa duba shi. Anan ne na yake ce mata ta ɗauki tuwon ta ya yi kwantai. Tsire Baban inna ya siya masa ya ci ya ƙoshi, ba musu Inna ta ɗauke kwanukanta Mansoor yana shirin ya ci ne ya ga Tuwo ne miyar Kuɓewa ɗanya amnan tunda Inna ta kwashe kayanta ya san sai dai ya haɗiye yunwarsa. Shigowar Magajiya ya sa ya bar ɗakin zuwa bangaren Inna ba wutar nepa amman akwai hasken farin wata sannan garin an fara zafi. Da ya sawo kanshi shashen ya ga mutun kwance gabda ƙofar ɗakin Inna Meri, ya ɗauka Walida ce bai kawo ma kansa matar Saddiqu ba ce shi ya sa yana karisowa ya fara faɗin" Ke Walida ƙofar ɗaki ne wajen kwanciya? Ba na son wawanci kwashe wannan shinfiɗar a wajen" Shuru ba magana sai ranshi ya ɓaci ya Daka mata tsawa ya na mai kiran sunanta amman Maeesha ko gizau daman tun fara zafi ta samu wannan iskancin sai ta zo ta simfiɗa abin shimfida ƙofar ɗakin Inna, ko innar ne sai da ta raɓa ta gefe ta wuce Walida ta yi mata magana ta ce ɗan cikinta ba ya son zafi ko za ta hana ta kwanciya ne Inna ta ce ta ƙyaleta kada ta kara mgana. "Yayanmu gani nan fa." Walida ta katse shi daga Kiran sunanta da yake yi, ya ɗaga kai yana kallonta cikin mamaki kafin  Ya yi mgana da sauri ta ce"Matar Yaya Saddiqu ce." Buɗe ido ya yi kafin ya ce"Oh iskancin nata nan kuma ya dawo? In iskar take son sha ta je Kofar ɗakin magajiya mana sai anan duk ta tare ma mutane hanya" Bai tsaya ba kawai ya nufeta gadan gadan kamar zai takata da sauri ta matsa baya da sauri da kwanciyar sarakai ta yi tana hararan shi tana ko matsawa ya saka takalminshi ya ture shimfiɗar yana faɗin"In ta sake kwanciya kada wanda ya kauce mata, ku taka ta ku wuce" "A taka ni fa ka ce? Saboda ba ka da asara.? Maeesha ta faɗa cikin hargowa shi ko kamar bai ji ta ba ya shige ɗakin Inna wacce ke salla ta kosa ta Idar kada Baban inna ya ƙara jawo mata wata masifar, Maeesha bakin ciki ya rufe ta sai kawai ta saka kuka tana faɗin an takura mata ita da gidan Mijinta ba ta da halin sararawa Walida na gefe tana yar eariya daman matar nan ta gama cika mata ciki da iskancin ta a cikin gidan nan saboda ita Bintu ta daina zuwa gidan in ta ga abun magana sai ta yi mgana Kuma tana mgana sai a fara hayaniya Ita kuma Inna yar zaman Lafiya ce ita ta ce in fitina ke kawo ta itama ta zauni gidanta. Maeesha ta yi ta kumfar baki tana tunanin Magajiya za ta fito amman shuru ita kuma Walida sai ta tafa hannu kafin ta ce"Sorry fa, ko shi Yaya Saddiqun ba zai iya da Yayanmu ba ballantana ke karamar alhaki." Da haka itama ta nufeta gadan gadan kamar za ta murje mata hannu ya sa da sauri ta mike tsaye Walida ta shige ɗakin Inna tana faɗin" Ashe karyan tsiya kike yi." Fuu Maeesha ta koma ɗaki tana kuka ta kira Saddiqu tana gaya masa karya da gaskiya har ta na faɗin Aji ya saka yakalmi ya taka ta kuma da gangan. Shi kuma cikin Kumfar baki ya ce mata ai ya Kusa dawowa zai yi sharia da wanda ya taɓa masa mata daman ai ya na jin hauahin warning ɗin da ya saka Auwalu ya kira shi ya yi masa to wai shi da me ya ke takama ne? A ɗakin Inna ko ta na sallame sallah cikin ɓacin rai ta kalli Mansoor kafin ta ce"Ba na son fitina. Ba na so ina zaune lafiya ba za ka jawomin wata fitinar ba, in kai ba ka san darajan matar ka ba, wasu sun sani kuma da gaskiyanta gidan mijinta ne a barta ta yi abin da ta ga dama mana." Lokacin ya na wasa da Junoir ne wanda tun shogiwarsa a she bai yi barci ba ya naɗe masa. Sai ya kasa mgana domin kamar gori ne Inna ta yi masa. Walida ce ta tura baki kafin ta ce"Shikenan Inna sai a barta ta rika mana abin da ta ga dama." A fusace Inna ta ce"Sai me? Ai wuri ta samu ɗan da ka haifa ma bai ji mganarka ba sai wani can ne za ka damu kanka domin ka yi masa mgana bai ji ba." Yadda Inna Meri ke mgana ne ya sa ya san ranta ya ɓaci kai tsaye ya ce"Ki yi hakuri inna." Sai kawai ya miƙe ya na faɗin"Inna ki ba ni Junior na tafi da shi wajena ya kwana." Wani kallo mai kama da harara Inna ta sakar masa kafin ta kalli Walida lokaci ɗaya tana faɗin"Ke karɓe shi, " Walida ta yi shuru kafin ta karisa za ta karɓeshi shi kuma ya makale masa sai ta Juya tana faɗin" Inna ko za ki bari ya tafi da shi ne, duba fa ki gani baya son zuwa." Inna ba ta sake mgana ba ta miƙe ta warce Junoir a hannun Babban Inna yaron ko ya fashe da kuka Inna ta mikama Walida shi tana faɗin ta kai shi ciki ya kwanta. Ta kalli Manaoor da ya yi kasaƙe kawai yana na kallon Inna komawa ta yi ta zauna lokaci ɗaya tana faɗin" Mu kwana lafiya." Takaici ya kume shi cikin ɗan jin haushi ya ce"Inna ɗan Ɗan uwane fa? Inna kai tsaye ta ce"E fa! Amman ai ba ɗanka ba ne ko ? In ka ji haushi ka haifi naka sai ka rika kwana da su." Har ya dawo gidansa in ya tuna kalaman Inna sai ya ji kamar ya yi kuka wai shi Inna ke yi ma gorin Mata da haihuwa, takaici ya sa a daran ya Kira Mu'azzam y na gayamasa shi kuma ya nuna bai ji daɗi ba. Sai kawai Aji ya ce" Amman ba komai, ta kwantar da hankalinta sai ta gaji da ɗaukan Ƴaƴa na" Mu'azzan sai ya ji ya ba shi tausayi ya kuma san Inna ta yi masa hakane Saboda ya ji haushi ya gyara abin da ya ɓata kuma kamar hakan ya yi tasiri daga baya shima ya zauna yana tunanin shekaru sun tura ya kamata ace shima yanzu ya wuce wannan matsayin tunda har Inna ta fara masa gorin mata da haihuwa to nan gaba bai kuma san wa zai masa gori ba, ya fi su fa bukatar matarsa akwai abubuwan da suka faru ne suke danne wannan bukatar ta shi amman cikin ikon Allah da shawarwarin Nasir tun kwanaki ya fara yaƙi da abin d ke ransa kuma Alhandulillah yana jin abun na raguwa. Duk iya yadda ya so ya share Mimi sai ta neme shi amman ba ta neme shi ba Sai ya ji ya kasa hakuri ana neman cin wajen wata ɗaya sai ya fara jin tsoro kada fa ya yi sakacin da zai ƙara jefa rayuwarsa cikin yarari a karo na biyu. Ba shi da wani abokin shawara sai Mu'azzam Shi ya kira ya na ce masa" Mu'azzam kana ganin na bi Mimi Abuja ba matsala.? Mu'azzam na mirmishi ya ce"Me zai hana? Ba wata matsala, ka kirata in ba ta ɗauka ba ka tura mata sakon za ka zo sai ku zauna ku yi mgana." Kamar wani yaro sai ya ce ma Mu'azzam Toh, Sai yayan na shi ya ba shi tausayi yasan yadda ya tsani garin nan amman ga shi yau zai koma kuma a kan dalilan nan guda ɗaya wanda saboda shi ya je a karon farko a wannan karon ma saboda shi zai koma. "Don Allah Yaya Mansoor kada ka ce za ka mata yi faɗa,  ka lallasheta tunda dai kai ne mai laifi." "Uhm! Kawai ya ce daga nan bai ƙara mgana ba Saboda a lokacin yana tunanin ya je ko kuma kar ya je,  amman ya bi shawaran Mu'azzam ya ƙara Sauke kai ya kira Mimi amman matar nan ba ta ɗauka ba sai ya tura mata sakon ta tura mishi adireshin gidansu zai zo su yi mgana. Lokacin da ta ga sakon shi matuka ta sha mamaki, wani gidan y ke nufi? gidan da ya ce Allah ya yi masa tsari ya ƙara takawa,  ba ta yi gaggawan tura masa sai da ta kira Rukky ta sanar da ita, ita kuma tana dariya ta ce" Na fahimci ba ma zai yi mana wahalan kamuwa ba, tura masa kada ki sake ki gaya masa wani abu." Kai tsayen ta tura mishi yadda zai gane, An yi wajen kwana biyu ba ta kara ji daga gare shi har Rukky ta kira ta na gayamata ta ji Aji shuru Rukky ta ce zai zo fa ki kwantar da hankalin ki, shi ko tunanin tafiyar ne amman haka nan dai ya sauke girman kansa da wannan rikon da ya yi a ranshi a ransa ya kudurta ba zai shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga haraba.. Bayan Mu'azzam ba wanda yasan zai je Abuja Jirgi ya bi zuwa can ranar wata Asabar da safe domin ko da sha ɗaya ta yi sun sauka a garin Abuja, a direshin ya nuna ma mai Taxi ɗin sai ga su har kofar gidan Marigayi Major Kabir Dabo dake anguwan Gwamrinpa. Tsawon shekaru goma anguwar ba ta sauya masa a i do ba. Sannan gidan kan shi bai sauya masa, sama da mintina talatin ya na bakin get ɗin gidan  yana kokuwa da yanayinsa domin ji ya ke kamar a wancan lokacin ne da suka sauka shi da Mu'azzam kawai sai komai yake dawo masa daki daki kamar a lokacin yake faruwa ya yi tunanin ba zai shiga gidan ba, in fa ana son a samu masalaha har gobe ba zai daina ganin baƙin wannan gidan da mutanen dake cikin sa ba. Wayarsa ya ɗauka ya kira Mimi abin mamaki wannan karon Mimi ta ɗaga wayarsa. "Hello, na iso gani a kofar gida amman ki fito ba zan shigo ba." Cikin yanayin maganarta tacce"Ni kuma ba zan iya fitowa ba, in ka na so in saurare ka sai ka shigo cikin gida." A ransa sai ya ji daɗi da ya ji muryanta amman kuma yana tsoron wani abu da sauri ya ce" Kada ki sake ki shirya wani abu, domin na ga alaman kin sakani cikin dangin ku bangaren abokan wasan ki." Dariya ta saki mai kayatarwa kafin ta ce"Kar ka damu, yi ma megadi mgana ka ce kai baƙo na ne." Daga haka ta katse wayar ba karamin jarumta ya yi ba. Har sai da ya kai zuciyarsa nesa sannan ya iya tun karan get ɗin ya buga megadi ya leko sai ya ga yau kam ba Soja, wani dattaijo ya gani bayan sun gaisa ya ce masa ya zo wajen Mimi ne sai ya buɗe masa kofa ya shiga amman sai ya ce ya jirasa bari ya shiga ya sanar musu. Yana bin haraban gidan da kallo, ba sojoji ba motoci ba iko ba komai sai haraban gidan wayam, Rayuwa kenan yana nan tsaye ya na kallon abun kamar yau yake faruwa Sanye yake da manyan kaya har da hula saboda Sumar kansa ta yi yawa kuma bai je ya rageta ba. Megadi ya dawo ya ce Hajiya ta ce ya shiga ciki, kamar yace a'a sai kuma ya bi shi a baya shi ya yi masa jagora har cikin falon Gidan da ba abin da ya sauya a sanin da ya yi masa a baya sai dai an samu sauyin abubuwan dake falon. Duk yadda ya so ya zauna kasa zama ya yi kawai ya yi tsaye hannayensa goye a bayansa ya na jinsa kamar akan ƙaya Ita kuma Mommy tana cikin ɗakinta tana fa waya da Mimi domin ita ta kira ta ta ce Aji na waje ta saka a shigo da shi. Mommy cikin faɗa ta ce"Au kin ma san zai zo shi ne ki ka saka kafa kika yi tafiyar ki? Mimi ta marairaice kafin ta ce"Ni fa ban sani ba, yau yake gaya min." Mommy ta san karya ne. Rana Tsaka shekaranjiya ta ce Kano za ta je gidan Dr da ta hanata sai ta yi mata karyan kwana biyu za ta yi ta dawo, kuma daman sun yi waya da Hajiya ta san da labarin zuwan shi can gidan da ta kira Alhaji Hamza ta yi masa mganar tun dai ya zo ya neme sa a sansanta lamarin shi kuma sai ya ce har yanzu bai zo gabar da nake so ba, in har yana son Sasanci tsakaninsa da Mimi ya san in da zai same shi. Mommy ba ta fito ba sai da ta kira Asmau a waya dake ɗakin ta ta ce ta fita falo ta kai ma mijin Mimi ruwa da lemu a falo. Da to ta amsa mata sannan ta saka lulluɓi ta fita falon ta ganshi tsaye kamar yana kan ƙaya ba ta taɓa ganinsa ba sai sau ɗaya a wajen Kwallon da aka yi amman ta gane shi. Cikin girmamawa ta gaishe shi ya amsa sau ɗaya kafin ya ce"Ina Mimin? Sai ta yi shuru cikin mamaki kafin ta kalle shi cikin mamakin shi bai san Anty Mimi na kano ba ne? "baka sa ni ba? Anty Mimi ba ta nan ta tafi kano." Mirmishin gefen baki ya yi kawai domin in yace zai ɓata ransa ya rantse ds Allah sai ta raina kanta ya yarda ma kansa Mimi tana masa wasa da tunani da hankali. Kitchen ta shiga ta haɗo masa lemu da ruwa da kofi saman faranti sannan ta kawo masa falon ta ja center table ta ijiye masa, Juya ya yi zai yi tafiyarsa sai ga Mommy ta fito Allah ba domin ta kira sunan shi ba so ya yi ya ficewarsa har shi za a yi ma Iskanci. Dole ya dawo amman tsabar kamar akan ƙaya yake bai ko cire sahu cikin takalmin da ke kafarsa ba, daga gefe ya tsugunna ya gaishe da Mommy kadahan Kadahan ta amsa itama cikin yar sakewa kaɗan. "Sannu da zuwa. Ba ku yi waya da Mimin ba ne? Ba ta nan tana Kano gidan Dr." Kawai sai ya samu kanshi da cewa ya kira ta bai same ta ba, kai tsaye Mommy ta ɗaga wayarta tana faɗin" Bari na kira ta, ka zauna a kan kujera mana nan ma ai duk gida ne." A ransa ya ce ban ga gida anan ba amman a fili sai ya yi shuru kansa na kasa ya ji Mommy na faɗin" Ya ce wayarki ba ta shiga, ga shi ku yi mgana amman ki tabbatar da kin dawo yau ko gobe." Daga haka ta miƙe ta isa har in da Aji yake ta miƙa msaa wayar hannunta ya amsa ita kuma sai ta koma ciki lokaci ɗaya tana kwalama Asma'u kira. "Wai ke a tunaninki wahala kike son ba ni? Uhm ba za ki iya ba ni wahala ba Fatima, sai dai mu wahalar da juna." Mimi ta yi yar dariya kafin ta ce"Sorry fa, na je duba matar ɗan'uwana ne." "Da izinin wa kika tafi? "Da izinin mijin da zai sake ni kwananan mana." Baki ya buɗe kafin ya yi mgana ta yi saurin cewa" Shi ya ce in na ga dama na wuce  Abuja ma shi ya sa na tafi." Kai ya jinjina ba tare da ya yi mgana ba Daga can bangaren ta ce"Ko za ka ƙariso kanon ne? Wlh ina gidan Dr." Kasa ma mgana ya yi, domin ba shi da abun cewa dakyar ya samun bakin cewa" Ki sani dai akwai nauyin igiya uku a kanki, duk wani abun da za ki yi na saɓa ma mijinki Mala'iku suna rubuta miki, gwara ma ki sani ba ni kika yi nawa ba kan ki kika yi ma wa." Daga haka ya kashe wayar kawai ya yi shuru ya na furzar da iska daga bakin shi,Da gaske ne Mimi ta fara bashi Wahala, da niyarsa ya yi tafiyarsa amman Mommy ta hana shi tafiya ta ce sai ya tsaya yq huta ya ci abinci sannan,  kuma kamar an rufe masa baki sai ya kasa yi mata Gaddama haka ya zauna a falon gidan su Mimi a ɗaɗare. Har Asma'u ta gama yi masa lafiyayyan fride rice da naman kaza an yi Pepe. Da farko ya so ne ko ruwa bai zai sha ba sai ga shi har abincin sai da yaci daman da yunwa ya fito ko karyawa bai yi ba. Ya kusa ma yin abun kunya kaɗan ya rage abincin sai daga baya ya riƙa jin haushin kansa. Karfe biyu da wani abu ya baro gidan, Mommy ta jaddada masa Mimi za ta dawo kuma da kanta za ta dawo da ita gombe,  duk da bai wani saki jiki ba amman shi kan shi ya yi mamakin kanshi ko a tarihi bai ɗauka kafarsa za ta kara taka wannan gidan ba, sai ga shi a karo na biyu ya dawo saboda Mimi. Airport ya je ba jirgin gombe dole ya nemi hotel ya kama ya kwana da safe ya samu jirgin Gombe zuwa sha biyu na rana yana gidansa kwance yana tunanin Yadda zai yi ma Mimi rashin Mutumci in ta dawo ba dai shi za ta wahalar ba jiya ba har tana tura masa sako. "Ya gajiyan tafiya? Mommy ta ce yau dai Aji ya ci abincin gidan Major Kabir Dabo. Na yi mamaki ƙwarai amman na ji daɗi. My ex husband." Ko ba Ex ba haka ya rika maimaitawa shi kaɗai, wata zuciyar ta ce ko dai ta samu wani da take yi masa haka? Zabura ya yi cikin ta shin hankali, saƙo ya tura mata tunda ba ta ɗaga wayarsa. "In na sake ki kina da tabbacin akwai wanda zai aure ki ne a bazawara? Tsakanin saƙon shi da nata mimtina huɗu ne ta turo masa da amsar da ya kusa barazanar yafiya da numfaahin sa. B"E, mun daidaita da shi,  kai kaɗai yake jira mganar shi ta je wajen Daddy. Ya na sona sosai domin tun kafin na aure ka ya so ni, sai na zaɓe ka a tunanina kana sona sai daga baya na gane cewa na yi rashin masoyin ƙwarai da kaina na neme shi na bashi hakuri. Saboda haka ka sani aurena da kai ya ƙare Mansoor. Ina jiran takardan saki na." Fatima Kabir Dabo. Wannan saƙon na Mimi kaɗan ya rage bai kashe shi da ranshi ba,Allah ne ma ya sa kwanan shi na gaba. Da gaske take yi ta nemi wani namijin? Lalle akwai ƴaƙin duniya na uku matukar akwai wanda ke ganin matarsa da sunan so. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3006* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *BAYAN KWANA HUƊU* A cikin kwana huɗun da suka shuɗe duk a daddafe Mansoor ya yi su, duk yadda ya so ya fushi da Mimi kamar yadda ya so a farko tun bayan dawowar shi daga Abuja saboda ta ba shi haushi. Sannan tunda ya fahimci wahala take son ba shi ko ta yi ramako dalilin haka ya so ya share ta ya fita batun ta ya ga dai ƙaryan tsiya sannan kuma ya ga iya gudun ruwanta, shi ba ita ta fi ba shi baushi ba sai Iyayenta da suka zama tsoffn kawai suna kallon ta tana yawo gari gari da auransa a kanta amman a ka rasa mai tsawarta mata, ko ma me ya faru ai bai ce ya sake ta ba, ita ta ga dama ta yi tafiyarta shi kuma lokacin ransa ya ɓaci ba zai iya tsayawa yana ba ta hakuri. Amman tunda ta tura masa saƙon wai ta samu wani. Ya ji kasa sukuni maganar ta ƙi barinsa ya zauna Lafiya barcin sa ma ragagge ne. Baƙin kishi gare shi shi fa a tsarin rayuwarsa in har ya riga matarsa mutuwa Allah zai bar wasiyyan in ta sake aure bai yafe mata ba, ba zai iya ɗaukan wannan kwamacalan ba a ce in da ya shiga ya yi nomansa wani ya shiga ya ba za ta shi hajar ba zai iya ɗaukan haka ba. Ballantana yana raye a duniya nan Mimi ta je tana kula wani, ya fara tunanin waye ta ke nufi? Ko dai wannan sakaran ɗan'uwan nata ne? domin ai ya san labarin shi a bakin Makama In ko hakane lalle daga Mimi har iyayenta zai ɗaga musu hankali. Sannan ko da ya ce ba zai ƙara nemanta ba ya kasa, ya sake kiranta amman wayarta a kashe amman bai haƙura ba, karin abun ma ko barci yake yi sai ya riƙa mafarkin ya ga Mimi da wani ta na ta masa dariya, a kwanaki nan barcinsa duk babu salama da sukuni a cikin sa. Duk yadda ya so ya nuna bai damu ba ya kasa damuwar har ta fara bayyana a saman fuskarsa baya samun cikakken barci haka za ka ganshi zuru zuru,  duk kauce kaucen sa na kada a fahimci Mimi ta ci nasara a kanshi ya kasa. Duk kuma tunaninsa na ya share ta shima ya kasa tuni zuciyarsa ke rinjayansa ya bi ta can kano, wata kuma zuciyar na hana shi, amman kuma wata na tunkuɗa shi saboda samun natsuwar shi, Ga shi har a Lokacin Inna sama sama take yi masa ya bata hakuri bai san adadi ba sai ta ce ita bai mata komai ba, ya yi mata maganar Mimi ya ce ta kwantar da hankalinta za ta dawo kai tsaye ta ce masa wannan kuma abin da ya shafi rayuwarsa ne ita nufinta ta fita a ciki, In ya neman masu mai faɗa ne ya nemi dangin ubansa ita kan ta gaji da bin bayansa ba shi kaɗai ta haifa ba. Har Baba Ɗanjuma ya gaji da yi mata mgana ta kafe ta ce ita wlh ta yafe masa ɓacin ran da ya saka ta amman kuma ta ƙi ta koma masa kamar baya. Yana ma dai zuwan gidan ne domin ya zame masa dole amman ba ya jin daɗin gidan kwata kwata. Sai dai saboda Junior in ya je gidan da ya gansa zai ɗane shi yana murnan ganinsa in ko ya ce zai fita da shi Inna ta fara faɗa kenan ta ce in nesa zai yi ka da ya fita da shi, Shi dai ai na shi ban hakuri ne sai dai ya je ya yi yawo da shi cikin Camp ɗin su, Ko kuma ya yi yawo da shi acikin mota ya na siya masa kayan kwalama da kuma kayan wasa. Ya so cikin satin da zai shiga ya je Kano duk da baya samun wayar Mimin amman hakan bai samu ba  baya samun shima lokacin kansa, wani girma ne Allah ya ba shi a sanadin wannan kwallon kafa. Matasa matasa dake Gombe da zagayenta suna yawan zuwa wajen sa neman karin bayani ko wani taimako,  duk da shima ya dan ƙwallo ba ra'ayinsa ba ne sannan ba burin shi ba ne, amman tunda abin da Allah ya zaɓa masa kenan sai ya rumgume shi hannun biyu, tunda shine komai na shi yanzu komai zai zama ko ya zama a wannan rayuwa sanadin wannan sana'ar ne a farko bai wani ɗaukesa da wani irin Muhimmanci ba amman daga baya sai ya rike abun ya san Allah ne ya yi masa kyakyawan zaɓi ta hanyar da bai za ta ko tsammani ba. Har satin ya ƙare. Bai samu yanke shawara ba, a satin kuma da ya shiga suna da traninng saboda watan gaba suna da buga wasa, to duk ba ya samun zama sannan Baba ma ya kira shi kan maganar Walida da Mariya ya ce zai shigo gidan su yi mgana. Abin da ya sa ma ya yi musu shuru ba su ci Jamb ba, ya na tunanin su jira wata shekara su sake rubutawa, sai su tafi jami'ar Gombe kamar yadda ya yi ra'ayi duk da ya san Baba aure yake so su yi saboda tsarin gidan wanzamai kenan ba'a dogon karatu a gida. Suna mgana da Mu'azzam shi dai ya damu ya zo kanon nan ya yi bikon Mimin sai ya riƙa nuna masa zai yi tunanin har a lokacin bai gama gaya masa ga abunda ya yanke ma ransa ba., daga baya kuma sai ya ce ko ya na son zuwa ba shi da mafita tunda wayar Mimin tana kashe ne ta ina zai iya sanin adireshin gidan yayan nata. Sai Mu'azzam ya ce ya na da lambar Dr. Sulaiman saboda tun a wajen ɗaurin auran shi suka karɓi lambar juna tun wata hira da ta shiga tsakaninsu ya gaya masa a kano ya ke aiki, to tun a lokacin ayyuka ya sa ba wanda ya neme wani a cikin su. Mamaki ya kama Aji cikin ɗan shan kunu ya ce"Me kuka haɗa da su da kake ijiyar lambobin su? Mu'azzam na dariya ya ce"Mun haɗa mana, tunda Yayana na auran ƙanwarsa ai an zama ɗaya in sha Allahu" Uhm kawai yace domin ya ga Mu'azzam ne da Kalan dangi,  har ya na cewa kada ya damu zai raka shi gidan in ya zo kanon,  shi kuma ya ce bai saka shi ba, kuma ya ƙi gaya masa ga lokacin da zai zo ya ce kuma in ya dame shi zai fasa zuwa daga nan Mu'azzam ya kama bakin shi. Bangaren su Nasir da Makama sun yi fushi sun ce in dai Aji bai ba su haƙuri ba to ba za su haƙura ba. Mu'azzam ya ba su haƙuri a madadin sa amman Nasir ya ce ya fita a wannan faɗan ba ruwan shi, shi ko gogan ya manta da abin da ya faru suna can sun ɗaukan ma kansu da Mu'azzam ya kara mgana sai cewa ya yi wani abu daman ya faru ne? Ya fahimci Nasir ya koya ma Makama banzan halinshi, shi yana da abubuwan da suka sha masa kai ba shi da Lokacin tunawa da abin da ya faru in kuma suna jiran ne shi ya Kira su ya ba su haƙuri alhalin shi dai bai san ya yi musu laifi gaskiya su yi ta jira. Suma ɗin fa su san halin shi kawai saka ma rai wahala ne amman Nasir na kira Mu'azzam ya ji ina aka kwana, saboda ya damu ko ya ya zai yi fushi da Aji abokatansu ba karya ba ne. Kimanin shuɗewar sati biyu Sannan ya samu natsuwar kansa. Ranar Asabar da Yamma ya shiga anguwan Arawa saboda maganar da za su yi da Baba, anan ya yi sallar Mangariba da Isha'i tare da su Baba A masallaci. Su Baba Sani har suna tara shi gefe suna mai faɗan zama haka ba amfani ya kamata ya ƙara aure, Baba Sani ya ce akwai yar abokinsa mallam mati in yana so yarinyar uwarta Jajir tunda Bafullatanace, kuma ta dauko kyan uwar ne, Baba Ɗanlami yace gwara dai ya zo ya duba a cikin anguwa in da ake ganin mutumcin ba inda ba'a ganin shi a wata tsiya ba. Duk bai katse su ba sai da su ka gama koro jawabinsu sannnan ya gyara tsayuwa yana faɗin" Na gode Baba da kulawa. Amman ni ban saki matata ba, ta je gida ta huta ne amman za ta dawo soon in sha Allahu." Yasan harda kuɗi suke bukata a hannun shi haka ya ba su 20k kowanne suka karɓa suna washe baki, duk da yana da abin da ya fi haka amman ba ya sakar musu kuɗi tunda yasan halinsu ba zuwa gidan suke yi su ba ma matansu a ji daɗi ba Sharholiyansu kawai su ke yi acikin gari shi ya sa ko kayan abinci ya gwammace ya ba ma Auwalu ya siya musu ya kai musu. A kofar gida suka samu keɓewa da Baba Ɗanjuma ya yi masa mganar Walida da Mariya ya ce zaman su ne ya ishe sa ba sun gama karatu ba? Mansoor ya ce" Eh sun gama matakin sakandiri ba, Ina so su cigaba har matakin jami'a in sha Allahu." Baba ya yi shuru kafin ya ce"A'a ni na fi son kowacce ta kama ɗakin ta kamar sauran ƴayana." Mansoor ya ce"To Baba, sun samu maneman ne? Baba Ɗanjuma ya gyara zama kafin ya ce" To ban sani ba, amman abin da ya sa na kira ka kenan, ka kira su dukkansu ka zauna da su ka ji in akwai waɗanda ke nenan su, in ka ji akwai sai a bincika in an aminta da nagartansu shikenan." Mansoor ya yi shuru kafin ya ce"In kuma babu fa? Baba Ɗanjuma ya ce shikenan sai ka ba su daman fara yin zence har Allah yasa a dace. Bai yi gaddama ba ya ce zai yi mgana da su in ya shiga cikin gida anan waje ya bar Baban wajen abokinsa Mallam Hashimu ya na ko shiga da Mariya ya fara cin karo tana wankin kayan da za ta saka gobe a dara nan shi bai ma ganeta ba sai da ya ji tana gaishe shi sannan ya tsaya ya na kallonta shi ya daɗe ma bai ganta ba. "Ke ina kike zuwa, ba na ganin ki a cikin gidan nan? Haka ya faɗa lokaci ɗaya yana kallonta da sauri ta ce" E. mm ina gidan Yaya Zuwaira ne." Kai tsaye ya ce"Me ya sa kika je can? Sai ta kasa mgana kanta na kasa dai dai lokacin da magajiya, ta ɗago labule ta Fito ta na kallon su, shi kuma ko kallo bata ishe sa ba kawai sai ya juya ya na faɗin" Barka da dare, ke Mariya ki same ni a ɗakin Inna zan yi mgana da ku." Yana gama faɗin haka ya yi wucewarsa Magajiya ta bi shi da harara. Bai ma san tana na yi ba tsaki ta yi lokaci ɗaya tana Kallon Mariya" Ko zai ce ki daina zuwa gidan Zuwairan ne tunda shi ne uban Ɗanjuma? Mariya ta kalleta kafin ta ce"Kai  Magajiya." hararanta ta yi kafin tac e" Dilla ta fi can sakara, kuma kije ki dawo ki gayamin abin da ya ce." Mariya ba ta kara mgana ba ta dai shanya kayanta daman ɗauraya take yi, ta wuce Bangaren Inna Meri ta samu ɗakin Maeesha a sakaye tunda Yaya Saddiqun na gari tun shekaranjiya ya shigo garin sai firita take yi tana shwagaɓa ita mai ciki, a falon Innar Daga Walida sai shi Junior ma ya yi barci Inna Meri kuma barci take ji bayan sun gaisa ta ce za ta shiga ta kwanta ta huta amman ba ta fara barcin ba ta ji yana tambayansu ko suna da ma su son su? Mariya da Walida suka kalli juna cikin mamaki, ita dai Mariya tana da samari ita kuma Walida ba ta da wani takammame, Tunda ba tsayawa take yi da samarin ba, Samnan ba ta da waya Inna ko yar ganin dama ce, in ta ga dama ko wayar ma walida sai ta yini ba ta gani ba Innar ta yi boyon kayanta mariya ko tana da waya wani Saurayin ta dake sonta ya siya mata. Ganin duk sun yi shuru ya sa ya yi gyaran murya yana faɗin" Baba na son ya aurar da ku, ni kuma ina son ku yi karatu wacce take ganin ta na da wanda ke sonta sai ta yi mgana." Walida ta yi shuru, kafin ta ce"Ni dai ba kowa, zan fi son na cigaba da karatuna Yar jarida nake son zama kamar Anty Mimi" Bai ce mata komai ba tunda hankalinsa na kan wayar hannunsa ne. "Ke fa? Ya faɗa ya na cigaba da duba wayarsa, murya can ƙasa mariya ta ce"Ni.. ni akwai wani." "Ina yake? Ya haka ya katseta da sauri ta ce" A tudum wada. Yaya Auwalu ma ya san ashi." Kai ya girgiza kafin ya ce"Ok zan yi mgana da Auwalu ɗin, ke kuma tunda ba ki ci Jamb ba  ba za ki zauna hakanan ba zan nema miki ko yar diploma ki je ki yi a kan na'ura mai ƙwalƙwala, kafin wata shekara sai ki sake rubuta Jamb ɗin mu ga Abin d Allah zai yi." Gabaɗayansu su ka yi masa godiya,  nan ya bar su ya fita bayan ya ce Walida ta gaya ma Inna ya tafi, ya so ya gaya mata gobe zai je kano amman kuma bai samu fuska ba, Ita ko Innar ta na jinsa mirmishi kawai ta yi, ko da ace shi ɗin yana da fitina amman kuma yana da kyakyawan hallayan da fole a ɗaga masa kafa. Tana jin su walida na kuskus a falo, Ko da ce ma Mariyan ba ta da saurayin Magajiya ba za ta bari ta cigaba da karatu ba, aure za ta ce ƴarta za ta yi, Walida kuma ta san ba ta da wani saurayi sai tarkace ita ba za ta saka baki ba tana da uba da Sauran yayyenta abin da su ka yanke a kanta ba za ta ja ba. Yana fita su ka kusa cin karo da Saddiqu da ya fito daga cikin ɗakin sa daga shi sai gajeran ƙaramin wando, Kallo kallo suka yi ma juna shi da Aji, kwarjini ya yi masa yasa ya ba shi hannu su ka yi musabaha duk da ya sha alwashin ba zai ƙara gaishe shi ba, sannan ga gulmar da Aishar ta kai masa amman ga shi ga Mansoor ɗin ya kasa masa wata mgana. Shi ko kallon kasa da sama ya yi masa kafin ya ce" ya kamata dai kasan a yanayin da za ka riƙa fitowa, nan gidan akwai iyayenmu akwai ƙannen mu bai kamata ka riƙa fitowa haka ba." Yana gama faɗin, ya saki hannun shi ya yi wucewarsa ya bar Saddiqu na bin shi da harara sai da ya tabbatar da ya bar shashensa sannan ya saki tsaki yana faɗin" ƴan ƴan, sarkin iyayi ai sai ka hanani ni da gidan ubana." Daga baya kenan. ******** *03rd Febuary 2023* Ba a motarsa ya shirya tafiyan ba. Sai ya shirya tafiyar tasa a motar haya. Takwas na safe yana tasha kafin tara motar kano ta ɗaga da Aji aciki kuma har a lokacin yana kiran wayar mimi amman amsar ɗaya ne tana kashe ne, Daman tun kwanaki ya saka Mu'azzam ya tura masa lambar Dr. sulaiman ɗin bai kuma kira shi ba sai da ya sauka tashawajen sha biyun saura na rana sannan ya kira shi. Wajen kira biyu ya yi masa ana uku ne ya ji an ɗaga kiran da sallama, shima sai ya amsa masa suka gaisa. "Ba ka gane wa ke mgana ba ko? Dagacan bangaren Dr. sulaiman dake haraban asibitin Aminu kano ya fito daga duba Patient ɗin da ya yi ma tiyata jiya ya samu Kiran Aji. "E wlh ban gane ba. Lambar ba bu suna.". "Sunana Mansoor Aji, mijin ƙanwar ka Fatima Mimi." Mirmishi ya suɓuce ma Dr. Sulaiman yana gyara zaman gilashin da ke idonsa ya ce" Allah sarki, kasan da ya ke ba mu taɓa waya ba shi ya sa ban ɗauki muryan ba." Aji ya jinjina kai kafin ya ce" Gani na sauka a tashar Kano. Adireshin gidanka nake so, na zo wajen matata ne." Ciki mamakin da har ya bayyana saman fuskar Dr Sulaiman ya ce"Ikon Allah, ok to yanzu na shigo asibiti ne na duba patient ka gaya min tashar da ka sauka sai na ƙariso  na ɗauke ka ko? Sai Aji ya waiwaya ya ga sunan Tashar ya faɗa masa sai Dr ya ce ga shi nan tafe in sha Allahu. Sannan suka yi sallama ya ƙarisa wajen motarsa ya buɗe ya shiga. Sai da ya hana Mimi tafiya amman Daddy ya ce a kyaleta tunda dai har ya ji labarin ya bita wajen Hajiiya kuma ya taka har Abuja saboda ita amman kuma ba ta bari sun haɗu ba, Ya yi mata faɗan ta koma Gombe amman Mimi taki jin mganarsa yanzu kuma bai san da wani yare zai faɗa masa Mimi ta bi Madiha da mijinta zuwa Umra ba. Yana wannan tunanin cikin lokaci ya isa ta shar Allah ya taimake shi bai haɗu da mugun Goslow ɗin kano ba, daga bakin tashar ya tsaya saboda in ya shiga wajen fitowa ne matsalan tunda tashar Kano Line ne sai ya kira layin da Aji ya kira shi da farko ya ce ya ɗan Fito daga tashar ya na nan a bakin tashar a wata mota mai ruwan toka. Ba su sha wahalan gane juna ba, Dr Sulaiman ya fara gane Aji tunda ya san shi, shi kuma Aji fuskar Mimi ya gani a fuskar shi sannan ya ɗaga masa hannu kuma ga shi a jikin mota mai ruwan toka. Aji ya na sanye da shadda mai ruwan toka ɗinki zamani ya dora bakar dara a kansa takalmin kafarsa sahu waje ne. Sai wayarsa kawai dake hannunsa. Bayan ya ƙariso suka yi musabaha sannan Dr Sulaiman ya buɗe mai gaban mota ya shiga suka ɗauki hanyar cikin gari. Gidan Dr na anguwan sharaɗa ne. Suna tafe Dr. Sulaiman na jan sa da hira shi kuma ya na amsa masa ɗaya da ɗaya, yawanci kan mganar wasa ne, Dr na zolayansa da cewa za su riƙe shi ya buga musu wasan kano Pillars da kuma Gombe United mirmishi kawai Aji ya yi amman bai yi mgana ba. Su ɗan ja lokaci kafin su isa gidan, tunda da nisa, sun isa gidan ɗan madaidaci mai kyau da shi har sai da ya burge Aji. A Haraban gidan ya faka motan suka firfito Aji bai yi niyyan shiga cikin gidan ba sai kawai ya ce"Ka yi mata mgana kawai." Sai Dr ya ce" Haba dai ka shigo mana bakomai nan ma gida ne." Sai Dr ya yi masa kwarjini ya sa ya bishi suka shiga ta falon ɓakin sa na kofar waje. Sai ya ce Aji ya zauna bari ya shiga ya fito sai ya jinjina masa kai, ya samu ɗaya daga cikin Kujerun falon ya zauna yana ɗauko wayarsa yana dubawa. Ya so ya kira Mu'azzam sai kuma ya fasa, yac e sai ya gama rigimarsa da Mimi sannan zai neme sa. Dr. Sulaiman kuma na shiga cikin gidansa ya iske Jawahir a falo turus tana zaune da tsininin cikinta a gaba. Yara duk ba sa nan suna Mandawari sun je gidan kakanin su..ta na ganin shi ta sakar mai mirmishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka dawo da wuri yau." Yana zama gefenta yac e"Kinsan ba aiki na je yi ba, duba Patient ne kawai." Sai ta gyaɗa kai ta yinkura ta mike dai dai lokacin yake faɗin" Kun yi mgana da Mimi tun bayan tafiyar su Umra? Jawahir ta ce"Sau ɗaya muka yi mgana lafiya dai ko? Sai kawai ya miƙe yana faɗin"Bako gare ta. Mijinta ne ya zo." Jawahir ta zaro ido kafin ta ce"Yana ina? Sai ya nuna mata falon baƙi yana kora mata jawabin yadda aka yi ya ƙarishe da faɗin", na rasa me zan ce masa." Jawahir ta ce"Gaskiya ba daɗi, tun zuwansa Abuja na yi ma Mimin faɗan ta yi hakuri ta koma gida ta saurare shi a kallah dai ai ya nemata, ina amfanin wannan abu kuma? Ai sai ya ɗauka kuma mutanen banza ne." Dr ya mike lokaci ɗaya yana fadin"Daddy ne duk ya ke biye mata, amman yanzu dai haɗo min ruwa da lemu akwai abinci? Sai ta ce sai da miya amman bari ta dafa ko shinkafa ne da Ssauri sai ya ce ta hanzarta, Ta wuce Kitchen duk da cikin ta ya girma amman matar likita ce motsa jiki a wajenta na da matukar amfani. Shi kuma Dr. Sulaiman sai ya kira Daddy bai dauka sai da ya ƙara gwada kiran shi sai ga shi ya ɗauka sai daga baya ya tuna yau oahadi ne, bayan sun gaisa sai ya ke gayamasa zuwan Aji tare da cewa"Daddy ina jin kunya me zan gaya masa? Kai ya ce"Ka gaya masa gaskiya mana, miye abun ɓoye ɓoye." Dr Ya yi kasaƙe bai yi mgana ba jin haka ya sa Daddy ya ce"Ka ga kada ka damu, in har yana da hankali ya san in da zai zo komai ya warware." Ya kashe wayarsa ya na yar dariya ɗan tselen uwa ashe dai ƴa na son fiyar ta shi har yanzu, in gaji da zagaye zagaye zai neme shi, a lokacin shi kuma zai gaya masa matsayarsa. Jiki a sanyaye Dr. ya kwashi farantin ruwa da Lemu ya kai ma Aji dake zaune a falo har ya fara auna Mimi ta shigo falon nan ya fara balbaleta da faɗan sa amman maimakon ita sai Yayanta ya kara gani. Da ya ce ba zai sha ruwan ba sai ya nuna bai ji daɗi ba shi ya sa sai ya tsiyaya ya sha kaɗan shi da Babban shan ruwan shi ya ga Mimi a gabansa. Amman sai ya ga ba ta zo ba,.Sannan Dr na zaune bai yi masa wata mgana ba sai ya gyara zama yana faɗin" Mimin ba ta nan ne? Dr ya sauke numfashi kafin ya ce"Eh. Ba ku yi waya ba ne? Aji ya maimaita E, cikin mamaki kafin ya ce" Ba ta nan?  To ta na ina? Ya faɗa cikin mamaki sannan lokaci ɗaya ya na ɓoye takaicin sa. Cikin ɗan jin nauyi Dr ya ce"Tana Umra. Ta je Lagos wajen Madiha to ita da mijinta za su je Umra sai ta bi su suka tafi tare daman tana tare da Internationl ɗin ta, na ɗauka ma ko kun yi waya ne ta sanar maka? "In ta sanar da ni ai da ba za ka ganni ba., Ni ba ta kirani ba asali ma na ɗaɗe ba na samun ta waya, kenan ka ga tafiyar da take yi ba da izinina ta ke yin su kuma, tunda har gobe ina matsayin mijinta ban ce na saketa ba, sannan ban ce ta yi yaji ba ganin damanta ne sai na kyaleta saboda ita mace haka t ke in ta gaji da abu sai ka bata iska, Amman ace da yau sakinta na yi da iddata ne akanta kuna Iyayenta za su  barta ta riƙa yawo gari gari? Yanzu ma wata kasar ta fi ba tare ni Mijinta na sani ba tsakanin ga Allah hakan da ta yi ya dace ko a bangaren zamantakewa kafin ma a shiga mganar Addini.? Aji ya karishe faɗa yama mai ƙura ma Dr Ido shi kuma sai ya jinjina kai kafin ya ce"Tabbas bai kyauta ba amman ka yi haƙuri, ni kaina ban san da tafiyar ba sai ana gobe tashin su amman zan kira wayar Madiha tunda kamar Mimin ta kashe wayarta zan gaya mata ta dawo akan lokaci." Mansoor Aji miƙewa kawai ya yi lokaci ɗaya ya na saka wayar a cikin aljihun gaban Rigarsa kafin ya ce"A'a ku ƙyaleta kawai." Takaici ne da ɓakin ciki suka hana shi mgana Dr na roƙomsa ya tsaya ya ci abinci ya ce ba zai tsaya ba. Cikin jin nauyi Dr.Sulaiman ya ce"To haka za ka koma baka ci komai ba? Sai kawai ya samu kanshi da Cewa"Ba wani damuwa, da yake ma kasan kanina SP ne a nan garin zan je gidansa mu haɗu." Haka nan kawai ya ji yana faɗin haka, Dr Sulaimam duk bai ji dadi ba hakanan suka yi sallama ya rako shi har waje yana kara bashi hakuri shi kuma ya ce bakomai Saboda ya raunana Allah Mimi ta kure hakurin shi zuwa yanzu ya rasa matakin ɗauka a kanta duka matakan ƴakinsa sun rushe da gaske take yi abij da ta faɗa ba za ta bari su yi mgana ba, kuma da gaske take yi ta hakura da auran shi. Sai yaji duk ya damu wata zuciyar na gaya masa duk laifinsa ne me ya sa a daran bai tsaya ya bata hakuri ba? Sai ya fara jin Tsoro kada Mimi ta suɓuce masa a karo na biyu in wancan karon ya sha wannan karon ba zai iya sha ba kam. Sai dai kawai Mu'azzam ya samu wayar Yayan na shi ya na tambayan shi yana ina? Shi kuma lokacin ya na Office ya zo saboda mganar Cases ɗin wani maraya da dangin babansa suka cinye ma gado. Sai ya ce masa yana Office abun mamaki Ranar da ta zama ranar tarihi ga Mu'azzam kawai sai ji ya yi Aji ya ce ya tura masa adireshi ga shi nan zuwa. Ko kafin ya kariso ya fito haraban Division ɗin na su ya na jiran shi,.Yana sanye da kakinsa ya fito a matsayin SP M.G ƊANJUMA, wato Mu'azzam Gaddafi Ɗanjuma. Bakin nan yaƙi rufuwa karon farko da Mansoor zai kawo masa ziyara wajen aikinsa,.Sannan a karon farko za su haɗu da kaki a jikinsa. Sun kuma haɗu, Mansoor sai da ya ji wani iri ganin ƙanin nasa cikin uniform Rumgume shi ya yi kamar ya samu karin girma zuwa DPO tsabar murna da zumuɗi. Sai ga Mansoor a kayattacen Office din ƙanin nasa gwanin burgewa. Ba wani takarce bayan wajen zama sai daga can haka wasu kananun kujeru. A kwai hotunan gwamma garin sai na Sarki  a saman teburin Mu'azzam kuma akwai hoton Junior sai a gefe hoton Mansoor ne da kayan kwallo a jikinsa ya yi ɗan mirmishin gefen baki. Mansoor sai da kwallah ya tarun masa a ido, ya yi saurin basarwa, Mu'azzam ya rasa ina zai saka shi ya ji daɗi, nan da nan ya saka aka haɗo masa shayi ya na kuma rawan jikin tambayansa abin da zai ci kawai sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Ka natsu, ai yanzu na zo ni da zan ƙarisa har gida in sha Allahu." Mu'azzam ya ji kamar an yi masa bushara da gidan aljannah jiki na rawa ya kira Hibba ya gayamata suna da babban bako a tanadi abinci bai gayamata ko waye ba amman yanayin murnan shi ya sa ta san baƙon mai muhimmanci ne. Ba su zauma ba sai da su ka yi sallar azahar Kowa kuma sai Mu'azzam ya nuna shi ya ce Yayansa ne daman ko da ya ƙariso mutanen da zai gani ba su kariso ba sai da Mansoor ɗin ya jira suka gama ya sallame su sannan suka natsu yaya da ƙaninsa domin tattaunawa. "Allah ya sa dai kun gama mgana da Anty Mamin? Aji ya yi shuru kafin ya ce"Ban ganta ba, bata nan wai ta je Umra? Mu'azzam ya zaro ido kafin ya ce"Umra? Topha? Ikon Allah." Shi kan shi lamarin ya ba shi mamaki kafin ya ce" To kuma ba ku yi mgana a waya ba? Aji ya girgiza kansa kafin ya ce"Na gaya ba na samun wayarta kwata kwata.". "To me take so ne? "Ƙure ni take son ta yi mana? Kuma kamar ta yi nasara, Mu'azzam na fara jin tasoro, ina jin wani tsoro na shiga na tsoron da ban taɓa jin irin sa ba" Ya faɗa cikin karyewan sauti, daga alamu kuma abin da ya ke faɗa daga karkashin ransa ne ganin yadda ya yi laushi lokaci ɗaya. Bai ma Mu'azzam damar mgana ba ya cigaba da faɗin. "Mu'azzam kana tunanin Mimi za ta dawo mu cigaba da zama? Ko kana tunanin abin da ta faɗa da gaske ne? Mu'azzam ya ji tausayin Yayan nashi cikin kwantar da murya ya ce"A'a ni fa ina ganin akwai abin da kake yi mata ne ba ta so, in za ku zauna ku samu daidaitu za ta dawo in sha Allahu." Aji ya dafe kansa lokaci ɗaya yana faɗin" To ta ƙi ba ni damar haka? Allah ba zan mata faɗa ba zan saurareta wannan karon, sannan ina ji a zuciyata zan iya mata abin da ta ke so, mganar gida kuma sai in da take so za ta zauna na janye duka sharuɗda na a kan ta." Ya faɗa lokaci ɗaya yana tagumi kafin ya cigaba da faɗin "Mu'azzam na taɓa ga ya maka ina son Mimi? Na taɓa ga ya maka itace rayuwata? Ya faɗa yana mai kallon ɗan uwan na shi Mu'azzam ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce" Na san kana sonta mana amman abin da ban gane ba me ya sa bayan ka same ta ka kasa nuna mata wanman son? Me ya sa kuma ka ga ya mata ba ka sonta? "Ba ni da wani dalili Sai na jin hauahin abin da ya faru a baya. Sannan Allah ni fa ba gaskiya na faɗa ba, kawai dai na faɗa saboda ta ji haushi, kuma ita ta ja na faɗi haka saboda ita ta riƙa ja na da maganganu." Haka ya faɗa yana rike fuskarsa yana sakin huci Saboda tsoro ne ya shigesa tsoron rasa Mimi a wannan karon. Har ga Allah tabon dake zuciyarsa ya fara raguwa ga shi har ya zo Office ɗin kaninsa ya zauna suna mgana kai, ka ba ma zuciyarka aminci ma wani salama ne zama cikin kunci ba shi da amfani. Yau ɗin ranar sakin duk abin da ke damunsa ne haka ya riƙa yi ma Mu'azzan zan tuka na fita hayyaci da nadama. Sai Kawai Mu'azzam ya ce"Ina da shawara me zai hana in ka koma ka nemi Babanta Alhaji Hamza? Tsohon Sanata tunda shine Waliyinta? Aji ya yi shuru kafin ya ce"Da na ce ba zan je ba, amman yanzu ai ba ni da zaɓi. Zan je in sha Allahu da zaran na koma." Sun ɗan tattauna Mu'azzam na kara gaya masa in ya je ya kwantar da kai tunda sulhu ya ke so, Bayan nan suka gangaro kan mganar gida Mu'azzam na faɗin Bintu ta gaya mai Inna wulakanci take kwasa tun bayan dawowar Matar Saddiqu bangarenta. Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ka san Allah na kusa ɗauke Inna daga gidan, kawai dai ba na so Baba ya ga na nuna masa shi ya gaza ne." Mu'azzam ya yi saurin cewa" Ni ma na yi wannan tunanin. Tunda Dai Magajiya ta fi ƙarfin  Baba ba ya iya tsawarta mata, Inna kuma kasan halinta ko dukanta za su yi ba za ta taɓa mgana ba." Mansoor ya koma ya jingina da Kujeren da ya ke zaune kafin ya ce" Kar dai a yi wani abin da zai ɓata min rai, zan ɗauke Inna gaskiya a wannan gidan." Mu'azzam ya ce"Ko Yaya Amina abin da ta ce kenan gidan duk ba daɗi." Sun cigaba da tattaunawa har kan batun su Walida Mu'azzam ya ce hakan ya yi dai dai, Aji yac e da zaran ya koma zai nemi Auwalu kan mganar ita Mariya. Nan su ka shantake sai bayan oa'asar sannan suka ɗumguma zuwa gidan Mu'azzam d ke BUK old site. Sai dai Hibba ta ga Yaya Mansoor kamar daga sama  itama bakinta kamar zai yage, faɗi take yi" Lalle muna da babba  baƙo, sannu da zuwa Yaya Mansoor" Ya amsa mata cikin sakewa abincin da ta yi sun fi kala huɗ nan suka baje suka ci suka sha suna ta hira kamar kada su rabu, Mu'azzam ya kira Inna ya sanar da ita ga shi ga Baban Inna itama kanta ta yi mamaki ta ce ya kyauta. Sun ɗauka ma ko kwana zai yi ya ce ba zai kwana ba. Sanin halin shi ya sa Mu'azzam bai matsa masa ba wajen shidda da rabi ya kai shi tasha ya hau mota sai da suka tashi ya dawo gida tafiyar dare suka yi sai wajen sha biyu ya iso Gombe, bai je gidansa ba a Camp ya kwana kuma evening Traning suke dashi shi ya sa tun bayan sallar asuba ya kwanta barci ya kwashe shi. Bai ta shi ba sai da ya ji ana ta kiran wayar sa yana tashi ya Duba sai ga inna ta kira shi Bintu ma haka. Sai ya bi bayan kiran yana duba Lokaci goma saura na safe, Wayar Inna ta na ƙara ba'a ɗauka ba, yana cikin neman Bintu sai ga kiranta sai ya ɗauƙa da sauti gabansa na faɗuwa yana tunanin ba lafiya. Kuka ya ji ta na yi masa, da sauri ya miƙe ya na laluban rigarsa. Cikin fargaba ya ce"Bintu me ya faru ne? "Faɗa ake yi a gida saboda Matar Saddiqu ta dagi junior har sai da ta ture shi ya fasa goshi, shi ne shi ne Walida ta yi magana Meesha ta ja ta da faɗa suka kama Kokuwa sai ta faɗi, Saddiqu na zuwa kawai ya rufe Walida da duka Inna ta zo ta hana ya tureta har sai da hannunta ya goce." Bintu ta faɗa ta na shesshekan kuka, Aji ya ji wani abu ya taso masa a ƙasan zuciyarsa. cikin maimaitawa ya ce"Ta goce? Ita Inna ce ya gotar don uban shi? Lalle ne ma." Haka kawai ya ce ya kashe wayar daman ya saka riga kawai sai ya zura takalmi ya ɗauki key ɗin mota tabbas yau Saddiqu zai fahimci yana cin darajan mai daraja ne amman tunda har tura ta kai bango yau za'a buga final ɗin. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3007* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Allah kaɗai ya kawo sa anguwan Arawa lafiya. Domin a yanayin yadda ya tuko motar nan a fusace ne yana kuma ganfala gudu kamar zai ta shi sama. Motar ma kusan a karkace ya iya faka ta a kofar gidan ko  key ɗin bai zare a jikin motar ba ya fito da sauri ya shiga cikin Glgidan abin mamaki har su Baba Sani da matan su suna gidan wai ace har Saddiqu ne zai ture Inna har sai da ta goce saboda rayuwa ta lalace gabaɗaya.   Bangaren Inna Meri ya cika da mitane, su Gaje ma duk suna wajen abinn mamaki Baba Ɗanjuma ma yana wajen ko da yake ba abun mamaki ba ne tunda kaf ƴaƴan Magajiya da ita kanta sun fi ƙarfinsu lokacin da ya shigo ya iske magajiya ta riƙo Maaesha wacce ke wani lamgwaɓe wa tana kuka kamar wacce haihuwan ce ta zo, Binta na Kofar ɗakin Inna tana harare harare, Inna Meri na zaune a kasa a kofar ɗakin ta kanta a kasa Walida na gefenta tana kuka kamar ranta zai fita junior kuma na raɓe jikin Bintu ga goshinsa sannan ya sunduma sauran kuma duk  suna tsaye suna kallon Magajiya na ta bala'i tana faɗin Saboda mugunta mata da ciki za ki ja ta da dambe? Lokacin da ya shigo Saddiqu ba ya gidan ya je ɗauko mai adadaita domin kai matar sa asibiti.   Yana tsaye daga bayan su ba wanda ma ya san ya shigo gidan ya goya duka hannuwansa a bayansa yana ƙokarin sarrafa ɓacin ransa domin ji ya ke yi kamar ya je ya hambare Magajiya a wajen nan,  kuma abun haushi har Baba na wajen amman ya kasa tsawarta mata sai Harira ce ta kalleta lokaci ɗaya tana faɗin" Gaskiya Magajiya kina faɗan rashin gaskiya ne, shi abin da Saddiqun ya aika ma Meri da Walida ya yi dai dai kenan? Sannan ita matar ta shi da ki ke faɗin ba ta da lafiya ita ce ta samu karfin ture wannan yaron har sai da goshin sa ya samu rauni? Ya kamata mu rika gayama junan mu gaskiya Magajiya bakya kallon abin da ƴaƴan suka yi a matsayin laifi sai dai ƴaƴan wasu."   Kafin ma ta dire maganarta Magajiya ta taso mata da cewa" Ba wani, yaro ya yi mata rashin kunya ba za ta dake shi ba? Ta ce ma mgana kawai ta yi masa ya daina zubar mata da ruwa a kofar ɗaki saboda sauro kawai sai ya shiga ɗaki yana kuka ita kuma wannan mara kunyan ta zo rama masa,  in tana da mutumci ai Saddiqu Yayanta ne amman ta yi ma matarsa rashin Kunya Aisha ta ce tana mgana ne ta ji ta cacumeta da dambe ko tausayin halin da ta ke ciki ba ta yi ba. Ban ga laifin Saddiqu domin ya kama ta da duka ba ai ta yi abun dukan ne sannan ita kuma Meri son kai ne da gulma miye na kokarin hana Saddiqu ɗaukan hukunci? Kuma ba da gangan ya tureta ba ita ta ja ma kanta, ai shi ne abin tausayi shi da yana zama zamansa an jawo masa wata laluran kashe kuɗi, in ma Allah ya takaita abun ya tsaya a iya kashe kuɗin kenan."    Baba Ɗanjuma cikin mamaki yake kallon Magajiya da wani irin bacin rai a fuskarsa da cikin zuciyarsa abib da ya faru yau ya sa ya kasa mgana, Allah ya sa ya iya gyaran targaɗe ko karaya shi ya samu ya ja ma Inna Meri hannunta,  abin da ya ba shi tsoro shi ne ganin hawaye a idanuwan Inna daganan sao jikinsa ya ƙara yin sanyi ya rasa matakin da zai ɗauka tunda ga ita makiran sai kuka take yi tana dafe cikinta a cewarta a ciki Walida ta dake ta. Yau hatta su Baba Sani sun kasa yin wani sharhi kamar yaadda suka saba har Baba Ɗanlami yau dai sau ɗaya ya ce Magajiya ta yi shuru Saddiqun ya dawo a je asibitin a gani Allah ya sa ba wata nabbar matsala ba ne.   Za ta ƙara mgana Baba Ɗanjuma ya daka mata tsawa ya ce ta yi ma mutane shuru ana cikin haka sai ga Mariya ta shigo tare da Yaya Zuwaira kusan lokaci ɗaya da Auwalu, Dalilin da ya sa a kasan Mansoor ashe tun ɗazu yana tsaye daga bayansu, ba su yake jira ba wanda ya ke son gani bai shigo ba so ya ke yi ya fara cin ubansa tukunna sannan ya ɗauka dai ya ci darajan mai daraja wlh da sai ya saka an kulle shi na tsawon wata ɗaya sakamakon abin dda ya aikata.   Baba Ɗanjuma da ya gansa sai da ya ji Kunya, kansa ya sunkuyar kasa ma ya kasa mgana Zuwaira da Mariya suka nufi magajiya suna taya ta rike Aisha da take kara narkewa kamar ranta zai fita , ita ko Magajiya faɗi kawai ta ke yi ina Saddiqun ne shima ya je ya yi zaman shi, Bintu kuma wajen walida ta nufa ta duka tana lallashinta Harira kuma ta ƙarisa kusa da Inma ta riƙo ta tana faɗin" Ki tashi daga kasan nan Innar Mu'azzam, ki koma cikin ɗaki." Amman Inna ta kasa tashi. Hawaye take yi amman tana saka hannunta guda ɗaya ta na gogewa,  Mansoor ji ya yi kamar ya mutu saboda Baƙin cikin dake cin ransa Inna suka saka kuka lalle nema. Shi fa kafin ya fara aiwatar da komai sai ya fara cin uban Saddiqu wlh, Auwalu ma lamarin bai yi mishi daɗi ba haka ya duka yana ba ma Inna da Walida haƙuri, Baba Sani ya juya ya na kallon Mansoor dake tsaye har lokacin hannunsa goye a bayansa yana cije leɓensa na ƙasa Ya ce"Kai kuma tsayuwar me kake yi, ka zo ka lallashi ita Merin ta koma ɗaki lamarin bai yi daɗi ba sai hakuri." "Akwai wanda na ke jira ne."   Amsar da Mansor ya bashi kenan a kausashe kafin kuma ya kalli Walida kukan ta ma ɓata masa rai ya ke tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ki yi min shuru anan wajen," haka ya faɗa yana kokarin saisaita fushinsa a lokacin ji yake yi kamar ya mutu sai wajen ya yi shuru har mai kukan ƙaryan ta natsu Bintu ya kallah daga baya yana faɗin"Bintu kama Inna ku koma ɗaki." Yana gama faɗin haka dai dai da shigowar Saddiqu da sauri yana faɗin" Magajiya ki kamota ga mai adaidaitan na samo." Gadan gadan kawai ya nufo bangaren shi kuma Mansoor daman shi yake jira Kawai sai suka haɗe. Ya saka hannu ya ture Saddiqu sai da ya kusa faɗuwa kasa ya dago cikin mamaki domin ya ga waye ya yi masa haka kawai Mansoor ya daddage iya karfinsa ya tsinke Saddiqu da lafiyayyan marin da sai da ya ga hasken taurari, bai gama dawowa hayyacinsa ba ya ƙara masa wani, da sai da ya faɗi kasa ya bi shi ya saka hannu ya damƙo ƙwalan rigan shi ya ɗago shi sannan ya ƙara masa wani marin mai shiga jiki sannan lokaci ɗaya ya ture shi da ƙarfin da sai da ya faɗi kasa. Kowa sai ya buɗe baki yana kallon ikon Allah Baba Ɗanjuma kuwa saboda jin daɗi da karfi ya ce"Na gode maka mansoor, kayi masa dukan tsiya."    Harira ma ta ji daɗin hukuncin Gaje dai ba wanda ya gane yanayin ta, Baba Sani da Baba Danlami sai faman subhanallahi suke faɗi kawai domin Saddiqu ya maru lokaci ɗaya har shacin hannu ya bayyana a dama da haunin fuskarsa sannan jini na bin hancinsa kenan haɓo ya yi. Zuwaira ta kira sunan Mansoor cikin tsawa tana faɗin kada ya kara taɓa mata kaninta Auwalu na gefe ya ce"Wlh ya yi min dai dai gwara ya kara masa tunda ba shi da mutumci." Bintu ko kamar an sakata a Ajannah har Walida mai kuka ta ji daɗi, yau kam Inna na zaune amman ba ta hana ba. Lalle tura ta kai vango magajiya kuma tsaabar ruɗewa ba ta san ma ta saki mai ciki ba tana mamakin wai Agola ne ya kama ɗanta da duka ita kuma Maeesha ba ta san ma ta tsaya da kafafunta ba jikinta ba inda bai rawa ganin Mijin nata da take taƙama da shi a gabanta ya maru, to ita fa? Tuni ta manta da an dake ta a ciki ta mike ga jikinta tana wani fiƙi fiƙi da idanuwa.   Saddiqu kuma cikin ɓorin kunya ya lakato jinin dake saman hancinsa ya gani. Sai kawai ya taso yana faɗun" Ni ka mara. Wallahi sai na rama." Ya nufi Mansoor gadan gadan sai Auwalu ya riƙe shi amman yana fizge fizge kamar zai iya wani abun, Mansoor ya kalle shi cikin fushi kafin ya nuna shi da yatsa lokaci ɗaya yana faɗin" Mari na farko na Junior ne, mari na biyu na Walida ne mari na uku saboda Inna ne. Kai har ka isa uwar tamu kake son ka kashe mana?. Wallahi ka ci darajan Baba da yau sai ka raina kanka banza kawai sakarai wanda ba namiji ba." Ya gama faɗa lokaci ɗaya har yana hambari sa shi da kafafunsa shi kuma Saddiqu tana hakilon nanza.    Juyawa mansoor ya yi ya isa ga Inna ya saka hannu ya ta da ta tsaye lokaci ɗaya yana faɗin" Ki yi hakuri Inna komai yau ya zo karshe." Bintu ya kallah kafin ya ce"Ɗauko ma Inna hijabi ta saka, ke ma ki shirya Walida ta ɗauko mayafinta mu je mota ki riko hannun Junior." Ya faɗa Lokaci ɗaya yana rumgume Inna ta gefren kafaɗanshi da sauri ko Bintu ta shiga ɗaki ta ɗauko masa hijabin Inna ya taimaka ya saka mata, Inna hawayenta sun ƙi tsayawa abin da ya faru yau ya ba ta tsoro matuka da mamaki. Walida ma ta sako hijabinta ita da Bintu, Inna Mero kuma Mansoor ya saka mata takalmi da kansa sannan ya Juya yana kallon Baba lokaci ɗaya yana faɗin" Baba ka yi hakuri amman Inna ba za ta cigaba da zama a gidan nan ba tunda har oamarin ya kai ga duka bamu san abib da zai faru a gaba ba kuma, kada ka ji a ranka kamar ka gaza kawai dai ba zan iya hakurin na barta ba ne gwara ta bar gidan sai waɗanda basu san zamanta a gidan su haɗa da ɗakinta suyi ta zama zauna." Baba Ɗanjuma ya jinjina kai kafin ya ce"Bakomai Mansoor, nima a yau ina goyan bayan ka, Mahaifiyarka ce kana da Ikon kare martabanta tunda ni na kasa, ku je duk inda ta koma ni a matsayina na mijinta zan bita ko'ina ne."   Sai a lokacin Magajiya ta samu bakin mgana sai ga ta, ta yi wani tsalle ta sha gaban Mansoor da Inna Meri lokaci ɗaya tana faɗin"Ina za ka?. Wallahi baka isa ka dokar min ɗa kuma ka juya ka yi tafiyarka kamar ba abin da ya faru ba. Ba ka isa ba domin ban taɓa ganin inda Agola ya daki ɗan ma su gida ba, Ko ka ɗauke ta daga baya kenan bayan kun gama zama kun gama more komai, nan gidan dai shi ya yi muku komai dangin uban naka me suka tsinana maka?  tunda ka shigo rayuwarmu kai da mahaifiyarka kuka rugumin gidana a da ina zaune da gani sai ƴa'yana da mijina amman zuwan wannan matan da zuwan wannan Agolan gidan nan komai ya sauya. Yanzu Danjuma ya fi fifita Agola sama da ƴayansa, in ba lalacewa ba a gaban idon ka a ɗaki ɗanka amman ka kasa mgana sai ma munawa da ka yi abin da aka yi dai dai ne to ni wallahi ban yarda ba sai an bi ma ɗana haƙƙinsa"   Take faɗa tana wani hura hanci, Mansoor ya yi niyar zagayeta su wuce ne amman Inna ta hana ta kalli Magajiya na wani lokaci kafin ta yi mirmishi ta ce" Kin ce wai dangin ubansa me suka yi masa ko? Ai ko sun yi masa komai tunda dai tun zuwan Baban Inna gidan nan abin naira biyar baki taɓa taimakon shi da shi ba kin ga baki da ikon faɗi wata mgana ba. Sannan na daɗe ina hakurin duk irin cin kashin da kike yi min a cikin gidan ki yi ta aibatana ɗana kina kiran shi da Agola Allah Sarki da ace Ibrahim ya yi tswon rai Magajiya na rantse ga Allah kila har ki koma ga Ubangiji ba za ki  haɗu da ni ba. Ba zan zo aure a wannan gidan har na zo da Baban Inna ba mutuwa ce ta yi ma shigar sauri ita ce ta maida shi mara uba amman ba Agolan da kake tunani ba, ni  ce nan na matsa sai na taho da shi saboda ba na son ya yi nesa dani amman ke kam shaida ce ba domin dangin Babansa sun gaza da ga riƙon sa ba. Na zauna da kowa bisa amana a wannan gidan ban taɓa tunanin cutar da kowa ba, ban sani ba ko tun zamana na taɓa yi miki wani abu na ɓacin rai da ya sa kika tsane ni. To yau ta kare ki yi hakuri ki yafe min Magajiya, Allah ya baki hakuri in dai laifina auran Mallam da kuma riƙon Yayan da ya bani to duk kiyi hakuri rayuwar nan duka duka nawa take? Wata rana ba ni ko ba ki a duniya nan? Ko kuma ba Mallam ko mu rasa wasu daga cikin yaran mu duka sanin gaibu sai Allah ki yafe min Allah ya kaddara saduwa."   Inna Meri ta gama faɗa tana mai fashewa da kuka sai jikin Magajiya ya yi sanyi duka masifanta ta kasa magana, Inna Meri na kuka ta kalli su Gaje tana faɗin" Saboda zama da rayuwa in na taɓa saɓa muku ku yafe min, ni dai wlh ban taɓa rike kowa a cikin ku ba na yafe muku duniya da lahira, Sani da Ɗanlami ku ma ku yafe min ƙila zama na tare da ku na yi muku wani abu ni dai ba ku min komai ba wlh, ina rokon ku da yafe min saboda rayuwa." Tana magana tana kuka  Gaje da Harira jikinsu duk a sanyaye su ka ce wlh ba ta yi musu komai ba ita ce ma suka yi ma laifi ta yafe musu ta ce bakomai su baba Sani sun kasa mgana Ɗanlami ne ya ce su kam ba ta yi musu komai ba. Magajiya na ji da gani Mansoor na rike da inna Meri su k fice daga gidan su Gaje suka raka su har da Baba Danjuma aka bar mata gidan gabaɗaya amman kuma ta kasa farinciki Har Auwalu da shi a masu rakiya,  tuni makota sun fara taruwa,  su Gaje ke faɗin Inna Meri ne za ta bar gidan sai ga shi an fara cika wajen tuni Dije matan Mallam Hashimu ta garzayo, ta lna kuka tana faɗin Ina Inna za ta tafi ta barta Inna ta ce ba inda za ta je, amman ta san duk in da Baban Imna zai kaita in da za ta samu natsuwa ne amman ba auranta ba ne ya mutu gidan ne kawai ta fahimci alheri ne ta bar shi.   Shi amfanin zama da mutane lafiya yana da kyau haka makota ke ta sharan hawayen barin Inna anguwar nan saboda kyawawan hallayanta wasu har suna faɗin ita ce Alherin gidan wanzamai wasu kuma su ka ce tunda Innar Mu'azzam ta bar gidan nan Sun daina shiga gidan daman saboda ita ce mace mai kirki da karamci mai zumunci duk abin da ya faru in dai ta ji sai ta je abun kaico kaico da abun Allah ya sanya alheri ga hannun kyauta ga son mutane da mutumci hatta da su Gaje sun koka wlh, Baba Danjuma duk jikinsa ya yi sanyi amman shima gwara haka ita kuma Magajiya ga ta ga gidan sai ta zauna.   A gaban mota Inna ta zauna su Walida har da Mariya da tana kuka ta ce za ta bi su ta ga in da za su koma suka shiga baya, Sai Baba Danjuma ya ja mansoor gefe yana tambayan shi in da zai kai Inna?. Kai tsaye ya ce" Gidana za ta koma Baba."  Cikin mamaki ya ce"Gidan ka? To kai fa? Mirmishi ya yi kafin ya ce" Kada ka damu Baba, zan iya siyan wani gidan ko na gina wani, Allah ya rubuta daman gidan zai zama na Inna nw wata rana.". Sai kawai Baba ya dafa kanshi yana ta saka masa albarka. Makota kuma ma su jajen tafiyar Inna ta ce duk su yi hakuri in har ta ga in da suka koma za ta sa Bintu ta zo ta gaya musu sai su zo su ga in da take amman zumunci ba zai yanke ba. Haka aka yi dafifi wajen motar Mansoor suna  ɗagama  makota hannu suma suna ɗaga musu, hatta su Baba Sani sun kasa motsi kamarin ya girgiza su, Magajiya na cikin gida ta kasa fitowa domin ta rasa me ke mata daɗi, Zuwaira na fadin daman ya san yana da in da za kai uwar tasa ya barta anan ta ce ma magajiya ai gida ya zama naki yanzu, Saddiqu kuma sai kumfar bakin sai ya ɗauko ma Mansoor yan daba sun yi masa dukan tsiya yake yi   Matarsa kuwa ta ja jikinta ɗaki ba ma wanda ya ƙara ganinta tuni aka manta da dukan ciki ballantana maganar zuwa asibiti.   Magajiya ɗaki ta shige, tana zaune Zuwaira da Saddiqu suna mganganu amman ba ta sauraransu ita kaɗai ta san hqlin da Zuciyarta ta ke ciki. Kamar ta ɗora hannu ta rusa ihu. Ga shi dai Meri ta bar mata gidan amman ta kasa farinciki sannan ji irin yadda Mutane suka taru suna kukan tafiyarta wai har da su Gaje, sannan ita me ya sa ta kasa farinciki? Ina za ta koma? Ko dai gidan shi zai kaita? Ta na hasaso wanman katon gidan domin lokacin da aka gama ginin Danjuma ya matsa sai da su ka je gidan suka saka albarka, in dai Meri ta koma wannan gidan ai ta ci gaba ita kuma ta bar ta a gidan gado? Kamar ta saka kuka haka take ji Kallon Zuwaira ta yi Idanuwanta sun kala sun jajir kafin ta ce"ina Mariya? Saddiqu ya ce"Kila ma ta bisu, tunda daman ba ta da kishi, duk irin su Auwalu ne." Sai Magajiya  ta yi  tagumi domin ta rasa kuma wani nazari za ta yi. Ga shi dai gida ya zama sai ita kaɗai amman kuma ba ta jin farinciki saboda tunanin in da Meri za ta koma ya fi in da ta ke sau ɗari da saba'in keman ita ta ci gaba ita kuma ta na nan a waje ɗaya. Duk mganganun da su Zuwaira ke yi ko ɗaya ba ta ji ba, ta yi nisa cikin tunanin makomar rayuwarta a wannan gidan ga shi dai burinta ya cika gida ya zama nata amman kuma a kasan ranta ta kasa farinciki. ***** Bangaren su Inna Meri kuwa daga nan ƙofar gidan Wanzamai sai gidan Mansoor, dake anguwan Tunfere, Ya nan a yadda yake kamar sabo tunda ba zama aka yi a gidan ba shi ne kuma regular ne wata rana ma ya na cinye satin shi a Camp. Bintu ya ba ma Key din gidan ta buɗe shi kuma ya riko Inna Meri har tsakiyar falon gidan da ba komai sai katon tibi da cafet, Inma sai kallon gidan take yi, Bintu da Walida kamar za su suma saboda daɗi. Gidan akwai kura saboda ba mutane a ciki amman komai sabo ne. Sannan gidan 4Bedroom ne, Sai daga waje haraban parking in da mashin ɗinsa take sai ɗakin megadi da wani ɗaki daga waje sai Fulaowin da ya shuka suka ƙarama gidan kyau a ciki akwai katon Kitchen sannan kowani ɗaki akwai Tiolet a ciki daman a cikin ɗaya yake zaune ɗaya kuma ya saka kayan motsa jiki. Sai ya ce ɗayan su share ma Inna ɗayan kuma Walida ta zauna a ciki kafin ya san in da zai kai kayan shi. Su kam ai suna can suna faman zagaya gidab suna murna daman sau ɗaya suka zo gidan tun bayan an gama shi tun lokaci suke  santin gidan. Mariya ma ji ta ke yi kamar ta dawo nan itama su zauna tare da Walida.   Inna Meri na tsaye ta kasa zama idanuwanta sun ciko da hqwaye, Mansoor ya zo ya riƙe ta yana faɗin"Inna ki zauna mana, an juma za'a kawo sabbin kujeru da sauram kayan amfani in sha Allahu." Inna kamar ta yi kuka ta ce"Baban Inna wamnan gidan ya yi mana girma da haya ka kama min" Cikin Mamaki ya ce"Haya kuma Inna? Wani irin haya kuma?  Ina da gida kuma sai ace mahaifiyata sai na ne man mata haya? Inna na rike hannunsa ta ce" Kai fa? Ina Binta za ta zauna in  ta dawo?. Mirmishi ya yi mata sannan ya kamata ta zauna saman Cafet shi kuma ya zauna a gabanta yana faɗin" Inna ina da kuɗin da zan iya siyama Mimi wani gidan ta zauna ko na gina mata wani, amman daga yau wannan gidan ya zama naki halas malak Inna." Inna Meri ta fashe da kuka tana faɗin" Allah Sarki haihuwa mai rana Na gode kwarai Allah ya yi maka albarka, don Allah Baban Inna zan roƙe ka wata alfarma." Ta faɗa tana riko Hannuwansa duka biyun da sauri ya ce"Faɗi koma menene ni kuma Zan yi miki  shi in har bai gagareni ba." Inna na hawaye ta ce"Kukan farimciki nake yi Baban Inma ba na baƙin ciki ba. domin haihuwa ta min rana Ubangiji ya gama min komai. Ni kamin komai wlh na gode amman ina so kaima  na ga ka samu Farinciki Don allah ka manta komai ka je ku daidaita da matarka ka dawo da ita ku zauna domin kaima ka samu farinciki ka tara zuru'an da za ka yi alfahari da su sannan ka samu rayuwa mai inganci Baban Inna"   Inna ta gama faɗa tana hawaye  Sai Mansoor ya share mata hawaye kafin ya ce"Ina sha Allahu Inna, ba saboda mganarki ba ni da kaina nake son na dawo da Mimi in sha Allahu." Haka Inna ta ji daɗi ta rika saka masa albarka tana hawaye. Su Bintu ya kira yac e ta bishi su je gida su kwaso kayan sawan su, Inna na zaune ta ce" Har da ma sauran kayan amfanin ai ba sai an siya wasu ba." Shi kuma ya ce a'a ta bar musu gidan da abib da ke ciki kayan sawan su kawai sai abin da suke so za su ɗauko Inna ba ta da abin cewa sai fatan alheri kawai.   Daman kuma tuni Bintu ta kira su Yaya Amina ta gaya musu abin da ya faru mamaki ya kama su suka ce ga su nan zuwa, Da Bintu kaɗai a ka koma can gidan ita ta haɗo duka kayan sawan su Inna da duk abib da za su bukata har da kayan amfanin gida su mopper da botikai da sauran su sannan ta saka key ta kulle ɗakin, daidai sai ga Yaya Halima daman sun yi waya ta ce tana gidan ta zo ɗaukan kaya gidan shuru ba motsin kowa kamar ba nutane. Bayan mota sai da ya cika da kaya da booth, sai Yaya Halima ta bi Mansoor ita kuma Bintu ta hau adaidata suka isa can gidan Yaya Halima ta samu Inna na ta sharan kwallah ta fara mgana sai ta ce ke ni kukan daɗi nake yi Halima sai dariya kuma gabadayan su nan da nan suka mike suka fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Yaya Amina ma ta ƙariso. Mansoor kuma ya ce bari ya je ya dawo Junior na ta murna ya ga irin gidansu na Kano.   Tun da mansoor ya tafi sai bayan la'asar ya dawo ya je ya yi wanka ne ya sauya kaya ko da ya dawo ma sun yi dubaran yin girki Tunda Bintu ta taho da kayan abinci da gas tunda daman Inna na da shi ita ce ba ta cika amfani da shi ba. Sai ya ji daɗi daman yana can ya na tunaninsu sun yi waya da Mu'azzam ne wanda ya ce Auwalu ya kira shi ya faɗa masa ga abib da ke faruwa sun yi mgana sabbin kayan gidan da za'a saka ma Inna suna gama waya Mu'azzam ya tura ma masa 100k yace a kara da shi ai ko ya sha faɗaa domin Mansoor ya ce shi bai ce ya kawo wani abu ba, shi kuma ya ce ai Inna mamansu ce gaɓadaya shima ya na neman albarka sai bakin Mansoor ɗin ya mutu.   Nan ya ce su Yaya Halima su zauna su rubuta duk abib da za su bukata na kayan amfani gida oabulai kayan gadaje da Kujeru kuma ya ce har da su duk su je su zaɓo Atm dinsa na babban bankin sa First  Bank ya damka musu su kuma su ka ce tunda yamma ta yi sai da safe za su yi sammakon fita  Gabda mangariba ya bar gidan shi kanshi ya samu natsuwa tunda nan yaci abincin rana Jallop ɗin shinkafar da suka dafa da daddare ma Bintu na dafa shinkafa da miya ya ce su ijiye masa zai dawo tuni sun gyara gidan gabaɗaya sun tsabtace komai kayan Inna sun samu matsugunni cikin wardrope Walida kuma tuni ta manta da duka ta ware tana murna ita abin daɗinta wannan kayattacen tiolet na cikin ɗakin da aka ce nan za ta zauna ga Wardrpoe ɗin bango daman tun lokacin ginin aka gina da shi sai dai aka saka masa Kofifi kawai.   Bintu a nan ta kwana tunda ta kira Bashher ta gaya masa Inna ta sauya gida za ta tsaya ta taya su gyare gyare. Da kan shi ma ta yi masa kwatance ya zo ya kawo ma ta su Hussaini tunda abokiyar zamanta ba ta nan ta na gidansu ana suna, ya zo ya ga gida shima ya yi mamaki, amman jin gidan Babban Yaya ne sai bai yi mamaki ba. Yaya Halima da Yaya Amima gidajen su suka koma su ka kwana sai washegari suka dawo da sassafe suka tafi kasuwa su uku tare da Bintu tun safe sai yamma a kamfanin da suka siya kayan su suka basu motar da ta ɗauko musu kayan da kuma ma'aikatan su Kafin dare duka an haɗa gadajen, falom ma tuni an zagaye shi da sabbin kujeru masu kyau da yarari, har da labulayan suka siya da karafan su ma'aikatan suka haɗa musu komai tunda an riga daman an ɗinka su a kirchen ma sun yi ma Inna ɗaki domin har kololi sabbi suka siya mata da sauran kayan amfani kitchen da na tiolet gida dai ya fito kamar gidan wata amarya yana kuma tashn shin kamshi tun da daman sun siyo turarukan tsinke da na rushi.   Gadon Inna shine 6by7,Na Walida kuma karami ne 6,by 6 ne. Gida ya fito ras da shi sai son barka, Inna Meri duk ta damu wai shi Baban Inna ina zai riƙa kwana? Ya na dariya ya ce"Inna ina da wajen kwana ga Camp ɗin mu, sannan ga ɗaki na nan in ina son kwana tare daku zan zo na yi kwanciyata sannan daga yau mun zama family daya ko da Mu'azzam ya zo da iyalansa waje ɗaya za mu rika kwana a matsayin Ahali ɗaya in sha Allahu." Sai Inna ta jinjina kai domin itama ta ji matukar ɗadi ganin iyalanta a waje ɗaya.   Maƙota na ta zuwa ganin gida suna murna Mariya kwananta biyu sannan ta koma gida ta labartama Magajiya gidan Inna da yadda aka saka komai sabo, Bintu ce da gayya ta ke yi ma jama'a kwatance ana zuwa ana ta yabo da cewa Inna Meri ta samu muhalli mai kyau in aka ce waya siya mata gidan? sai ace babban ɗanta mana sai dai ki ji ana tambayan shi ko aikin me ya ke yi haka? sai ace  ai Babba ne a ƙwallon kafa, Jummai ta zo itama ta ga waje ita da su Gaje Magajiya dai da zuwaira bakin ciki bai bar su ba hatta su Baba Sani sun zo gidan nan da Auwalu sai ga su zaune a falon Inna suna hira sun ci sun sha wai yau sune ke yi ma Inna hira suna dariya, hasken wuta ko'ina da yake ana barin wuta sannan kuma Mansoor ya kira an duba za'a saka ma Inna Sola a gidan, Baba Ɗanjuma kuma ya zo ya yi kwanaki biyun sa kamar kada ya koma gidan wajen Magajiya da aka barta daga ita sai halinta ba mai lekowa gidan daga nan ta gane duk jama'ar na Meri ne ita kuma Maeesha gida iyayenta suka ce a maidata ta haihu acan gida daga magajiya sai halinta Mariya ma guduwa take yi gidan Yaya Zuwaira ko gidan su Walida.   Kayan ɗakin Inna na da kuwa su Bintu suka raba a tsakaninau Kujerun da gadon Yaya Amina ta ɗauka tunda jinyar mijinta a lokacin ya sa duk ta saida kayan ɗakin ta Cafet kuma da sauran kayan amfani Yaya Halima ta ɗauka ta kuma ɗauki kula da sauran filet filet da yake komai na Inna sabbi ne Mansoor ya sauya mata sannan Mu'azzam haka, kamar kayan ɗakin wata Amarya sakin wawa Fridge ne kaɗai suka kaima Inna can gidan tunda daman ba su siya ba suka ce nata bai yi komai ba. Kaf suka kwashe koma ko roba ba su bari ba Sai ma datti da suka bari Bintu ce daman ta je ta rufe ɗakin ta leka ɗakin Magajiya ta ba ta key ɗin ta ce ta ba ma Baba in ya dawo ga shashen nan gabaɗaya Inna ta bar musu in ta ga dama ta koma ɗakin Innar gabaɗaya wannan dai ya rage nata. Sai ga Magajiya shuru ta kasa maida mgana da Baba Ɗanjuma ya dawo ya ba shi makullin shima cewa ya yi ta riƙe ta ba ma Saddiqu ya haɗa ma Matarsa duka ta zauna a ciki Meri ce kuma ta samu wani sauyim alheri, Ita dai ba ta je ba amman har Vadeo gidan Mariya ta ɗauko a waya ta numa mata tabbas Meri ta samu kyakyawan sauyi.   Duk saboda abib da ya faru ya sa maganar Mimi ta ɗan sarara a ran Aji, amman kuma bai manta da mganar Mariya da ya ce za su yi da Auwalu ba ya same shi sun yi mgana ya ce ya san yaron zai bincika ita kuma Walida aka sama mata wani shagon koyon Computer za ta yi na wata shidda 30k Mu'azzam ya biya kuɗin ya ce tunda yayan na shi ya yi hidima, kuma da yake an san mai shagon ba matsala a  anguwan su Yaya Amina ne, za ta rika ziwa monday to friday daga karfe goma zuwa huɗun yamma. Sai da ya ga ta fara zuwa sannan ya fara Samun natsuwa su Nasir har gidan sun zo gaida Inna shi tare da matarsa Nafisa ya zo Mu'azzam  ne ma yake gayamusu Makama ma yazo amman duk ba su samu Ajin ba sai daga baya Inna ke gaya masa zuwan su.   Sai da kimanin sati biyu ya shuɗe da zuwansa kano  sabgogi sun saka bai kara neman wayar Mimi ba itama ba ta neme shi ba, amman dai ya na akan bakan shi na zuwa gidan da aka ba shi auranta. Sai ya bari ranar lahadi da daddare saboda yadda zai same shi baban nata a gida. Shigar manyan kaya ya yi a ranar kuma ya je aka rage masa gashin kansa sai ya saka hula yana kamshin turare, bai je da mota ba sai mashin yana zuwa megadi ya gane shi, Shi kuma ya tambaye shi Alhaji na nan? Megadi yace ma sa Eh bai daɗe da dawowa ba sai ya ce ya shiga ya gaya masa Mansoor ne mijin Mimi.   Megadi ya tafi da sauri ya isar da saƙo Daddy na tare da matansa a lokacin sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce" Ɗan tselan uwa ashe dai ya san in da zai zo ya samu masalaha," Kai tsaye ya ce a shiga ada shi falon baƙi, Mama na zaune ta ga ya tashi ya na saka hula kai tsaye ta ce"Sai ka saurare shi?  watan Mimin nawa a gida bai nemeta ba sai yanzu? Ya na fita daga falon ya ce"In ji wa ya ce bai neme ta ba? Ke dai ba ki san komai ba, bari na je dai." Anty ce kaɗai ta bi shi da adawo lafiya, Mama kuma haushi ta ji tana ta ya ɗan ta kishi yana ta murna kuma murna za ta koma ciki. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3008* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Mansor na tsaye a tsakiyar falon gidan tsohon Sanata Alhaji Hamza sulaiman Dabo. Hannayensa harɗe a kirjinsa, lokaci ɗaya yana nazarin falon, ya taɓa shigowa falon kusan sau biyu wani lokacin a can baya Mimi ta matsa masa ya shiga suka gaisa na farko rashin lafiyan Hajiya na biyu ya manta falilin. A haka Daddy ya zo ya same shi yana tsaye bai zauna ba, yana ƙarisowa ya miƙa masa hannu suka yi masabaha. Sannan Daddy ya nuna masa kujera ya ce ya zauna amman sai bai zauna ba sai ya zauna a saman tattausan cafet ɗin da ya malale fallon gabaɗaya saboda ya tuna wayar su da Mu'azzam yana hanyar tahowa nan ya yi ta hadadda masa ya je neman sulhu ne kuma surukinsa ne ya kamata ya nuna masa girma da daraja. "Haba ka tashi ka zauna saman kujera mana." Kan Mansoor na ƙasa ya ce"A aa nan ma ya isa Alhaji." Sai Daddy bai ja ba kawai sai ya gyara zama suka gaisa yana tambayan shi wajen iyayanshi a sanyaye ya ce Alhamdulillah, shuru na wani lokaci ba daɗewa sai ga Anty ta shigo da farantin ruwa da lemu ta sauke nan saman center table ɗin dake falon, Itama Mansoor ya gaisheta ta amsa cikin sakewa kafin ta ce"Ah yallaɓai ya ka bar surukin namu ya zauna a ƙasa kuma? Daddy ya yi mirmishi kafin ya ce" Biko ya zo shi ya sa ya ninka biyayyarsa." Tare suka yi dariya shi da Anty sannan ta fice shi ko Mansoor kansa na ƙasa domin sai ya ji Daddy ya yi masa kwarjini ya kuma rasa ta ina zai fara ma mganar, In hr Mimi ta faɗa musu dukkan abin da ya aikata mata ai da Kunya, Shi kuma Daddy nazarinsa yake yi ta gefen ido amman bai nuna ba, wata Jarida ma ya ja anan gefe yana karantawa kamar yadda Daddy ya yi masa kwarjini haka shima Daddy ya ga ƙwarjinin Mansoor ya cika falon gabaɗaya. "Ka sha ruwan mana." Daddy ya katse shi lokaci ɗaya yana kallon sa, sai Mansoor ya muskuta ya ɗan mike ya isa ga wajen ruwa ya saka kofi ya tsiyaya Kaɗan ya sha sannan ya ijiye kofin sannan ya koma in da ya tashi ya zauna. Shuru ya sake wanzuwa na wani lokaci kafin Daddy ya sake katse shurun da cewa" Ya wajen aikin na ku? Kwanaki abokanka da ƙaninka suka zo sun ce wasa gare ku masu yawa baka samun lokaci." Sai ya samu kansa da amsawa da E, shi kuma Daddy sai ya jinjina kai kafin yac e"Good! Allah ya saka albarka," Aji ya amsa da Amin cikin yanayin maganarsa amman muryansa ta yi kasa sosai. Gani ya yi Daddy ya yi kamar bai san dalilin zuwanshi ba, ya ma cigaba da karatun Jaridarsa lokaci ɗaya kuma ya na amsa waya in an kira shi. Mansoor kuma na duke ya rasa ta in da zai fara dakyar ya iya kundunbalan ɗagowa ya na kallon Daddy kafin lokaci ɗaya ya fara da faɗin. "Alhaji dama kan mganar Fatima ne.." Sai ya dakata shi kuma Daddy sai ya kalle shi kafin ya ce"E, ina jin ka, Mimi ba ai ta dawo mana nan cikin kuka, ta ce ka ce ba ka sonta sannan ta ce za ta tafi ka ce is better da ta tafi ɗin, ni kuma da na ji haka sai na ce ai ba dole a cikin aure kuma in ka ga alaqa ta fara lalacewa gwara rabuwar shi ya fi alheri." Mansoor ya yi shuru kafin yac e" Alhaji ni ban ce ta tafin da gaske ba" "To me ya sa bayan ta taho a daran ko washegari ba ka biyo sahun ta ba, in ba ka nufin ta tafin ba? Kai tsaye Mansoor ya gyara zama yana faɗin" Ina da dalilina Alhaji, saboda ka san su mata wani lokacin in ransu ya ɓaci gwara ka yi nesa da su su huce, na ga ranta ya ɓaci a lokaci to ba laifi ba ne domin ta dawo gida ta huta amman ba na nufin wai ta tafi saboda ba na sonta, in ba na sonta ai ba zan yarda na aureta ba. Kawai na bata lokaci ne ta huta sannan ta huce daga ɓacin ran da take ciki." Magana ɗaya bayan Ɗlɗaya haka Manaoor ke fitar da ita, Daddy yana kallonsa amman yana mirmishi kafin ya gyaɗa kai ya ce"Na ji dalilin ka, ta wani fannin kana da ƴar gaskiyar ka ta wani fannin kuma ba ka da shi, amman duk ba wannan ba babban abin shi ne ga rashin ba ka sonta sannan ta ce ka kasa manta abin da ya faru a shekarun baya sai ka riƙa kallonta da abin, ka ga kuwa ai ba kyau irin haka riƙo ba shi da amfani sannan tunda har da bakin ka ka ce ba ka so ai ba wanda zai yi maka dole da sai ka zauna da ita ko ba haka ba? Kan Mansoor Aji na ƙasa ya ce"E, ta nan kam ina da laifi, amman na gane kuskurena Alhaji a yi hakuri in sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba." "Maganar rashin son fa? Ba zan ba ka bikon ƴata ba sai na ji gaskiyar mgana.* Ya faɗa ya na ɗan haɗe rai. Sai Mansoor ya sadda kansa ƙasa cikin jin nauyi kafin ya ce"Ita ce ko a da, a yanzun ma ita ce har gobe da jibi ma ita ce, ɓacin rai ne ya sa na yi mata mganganu cikin fushi amman in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba." Sai Daddy ya saki fuska yana faɗin" Alhamdulillah Allah ya sa na ji daɗin haka, ka burgeni yadda ka amshi laifukan ka sannan ka ce za ka gyara sannan na amince zan baka damar yin bikon matarka saboda dalilai guda biyu na farko ka yi laifi kuma ka amsa laifin ka, ka ba da hakuri sannan ka yi niyar gyara na biyu kuma na ji labarin ka je Abuja da kano ba ka samu ganinta ba hakam ma ya saka ni yarda da mganarka ta farko. Tabbas da farko da ta dawo gida da Koke koken cewa ita a raba auran ku in da ban yi zurfin tunani da duka rayuka sun ɓaci amman sai na bata lokaci kamar yadda ka ce itama ta sauka daga fushinta na tabbata a yanzu ba za ta so rabuwar auran ku ba sai dai daman an tauna aya ne domin tsakuwa ta ji tsoro. Sannan ina son na yi maka nasiha shi riƙo ba shi da amfani mu kasance ma su afuwa tunda Allah ma muma yi masa laifi, yana yafe mana kuma shi ya ce mu kasance masu afuwa, sannan shi kan shi Yaya Kabiru kafin rasuwarsa wallahi ya yi nadama kan abin da ya aikata maka kuma Hajiya da Brr. sun je sun yi mgana da kai sun kuma nema masa afuwarka sannan kafin rasuwarsa shi ya ce duk abin da Mimi take so a yi mata dalilin da ya saka aka yi auran ku bisa duk Sharaɗɗun da ka saka ka ga ba wanda ma ya maida kansa, To me ya sa kai ba za ka yi hakuri ka manta baya ba? Sai ka bar abu na shekaru ya hana ka sukuni da zaman lafiya? Shi kan shi Yayan ina yake yau ? Ai ba shi a duniya ya ma manta shi ya taɓa rayuwar duniya, ni ma ƙila ban sani ba nan kusa ne, wataƙila kaima nan kusa ne duk ba mu san gawan fari ba, sai fatan Allah yasa mu dace sannan ka sani Allah ya yi ma masu Afuwa wani babban tanadi, Ina ba ka shawaran ka manta baya don Allah domin samar ma kan ka da zuciyarka salama." Gabaɗaya jikin Mansoor ya yi sanyi mganganun sun shiga zuciyarsa sosai daman kuma shi tuni ya saki wannan abun Sai ya ji kamar ana rage masa nauyin zuciya cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu komai ya wuce. na gode Alhaji Allah ya ƙara girma." Sai Daddy ya ji daɗi har ya nuna a saman fuskarsa ya kalli Aji Lokaci ɗaya yana faɗin" Na ji daɗin yadda ka saurare ni, da duka amincewata Mimi za ta koma ɗakinta, zan kirata da kaina na ce ta dawo amman sai ka same ta ku tattauna wannan kuma tsakanin ku ne ba zan shiga ba." Aji ya rankwafar da kai yana godiya Daddy yace"Ba laifi. Na gode kwarai Allah ya yi ma rayuwa albarka Allah kuma ya kaɗe fitina a tsakanin ku." Aji ya amsa da Amin Amin kafin ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa ya zaro kuɗi bai san ko nawa ba ne ya ijiye a gaban Daddy sannan ya miƙe yana yi masa sallama Daddy duk da yana da rufin asirin sa amman ya girmama wannan alherin ya miƙe Lokaci ɗaya y na ɗaukan kuɗin kafin ya ce"Har da ɗawainiya? To yau dai zan ce na ci kuɗin ƙwallo kenan." Mirmishi kawai mansoor ya yi ba tare da ya yi mgana ba Har haraban gidan Daddy ya rako shi, suka kara yin sallama shi ya koma cikin gidan shi kuma sai ya hau mashin ɗinsa ya bar gidan, yana tafe iska na kaɗa shi yana jinsa kamar ya na shawagi a sararin samaniya, sannan nauyin da ke zuciyarsa ya ji ya yaye, wani irin nishaɗi da farinciki ke shigar sa bai sani ba, Yana tafe yana Faman mirmishi shi kaɗai. Daddy kuma yana komawa cikin gida Mama daman na falo tana jiran shi ya na shigowa ta miƙe tana faɗin" Har ya tafi? Shi kuma bai ba ma tambayarta wani muhimmamci ba ya ce" E." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na zama kan ɗaya daga cikin kujerun falon gefensa ta koma ta zauna tana faɗin" Allah sa dai ba ka ba shi fuska ba" Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce" wani fuskan kuma ? Na saurari bayaninsa na nuna masa Kuskuransa kuma ya karɓa ya ce zai gyara na kuma bashi izinin in Mimi ta dawo ya je su zauna su daidai ta." Mama ta yi wani iri wanda har sai da rashin jin daɗin ya bayyana saman fuskarta. Cikin mamakinta Alhaji Hamza ya kalleta kafin ya ce"Sai na ga kamar ba ki ji daɗin jin hakan ba ko? Da sauri ta ce"Ba wai ban ji daɗi ba gani na yi yarinyar nan ita ta ce ta na so daga farko amman yanzu kuma ta ce ba ta so, kana ganin a tsaya sauraran shi ba ɓata lokaci ba ne? Sannan sam ba su dace da juna ba ji irin gidan da ya kai Mimi domin Allah fa." Mirmishi ya yi domin shi ya gama gano in da ta dosa amman gudun ka ɗora ma mutun zargi ya sa yac e" To ba ki san tsakanin mata da miji sai Allah ba kenan? Itama a lokacin ɓacin rai ne amman tana son mijinta kuma ba za ta so rabuwarsu ba, mganar gida kuma ai ta san ra'ayin sa tun farko kuma ta ce ta ji ta gani, ba hurumun ba ne yanzu mu san abin da suka yanke ni dai na ce ya same ta su yi mgana abin d suka tattauna namu na saka albarka ne." "Amman ba dai wanman gidan na su za ta koma ba ko? Mama ta faɗa cikin yanayin damuwa a muryanta kai tsaye ya ce"Ban sani ba,ko ma can ne ko wani gidan ne can tsakanin su dai." Sai Mama ta sauke ajiyar zuciya ba tare da ta yi mgana ba sai Daddy ne ya kalleta na wani ookaci kafin ya ce"Na san damuwarki kan Jaheed ne." Da Sauri ta juya gare shi tana faɗin"Yallabai Yaron mu na son Mimi har yau ya kasa ba ma wata mace dama, bayan dawowan nan nata baka gq murnan da ya yi ba." Dariyansu na manya ya yi kafin ya ce"Shi ma dai sakarai ne, mace da mijinta bai sake ta ba ne yake murna a kanta? Ke ce kuma ba ki ga ya masa gaskiya ba gwara tun da wuri ya hakura da Mimi in da ace tana son shi da ta zaɓe shi amman tunda ba ta iya zaɓarsa a baya ba yanzu ma ba za ta zaɓe shi ba, ki zauna ki gaya masa gaskiya Mimi ta haramta gare shi gwara tun lokaci bai ƙure masa ba ya nemi wata domin ba zan barshi ya tsallake shekaran nan bai yi aure ba." Yana gama faɗin haka ya mike ya shige ciki ya barta zaune da tagumi, har Allah ta na jin haushin Hajiya domin ita taƙi ba ma Jaheed goyon baya in da tana so da Mimin ba ta isa ta yi gaddama ba, amman an na ce an ce sai abin da take so ga ta nan ga abin da ta ke so ɗin nan ya na wahalar da ita. Ranta ba daɗi itama ta bar falon zuwa ɗaakinta tana tunanin kiran ƙanwarta Hajiya Turai su tattauna mganar. ******* *MIMI* Lokacin da Daddy ya samu wayar Madiha wajen kwana uku da zuwan Aji wajensa ya na ta kiran wayar Mimi ba ya samu sai ya kira ta Madihan tunda suna tare, bayan sun gaisa ya ce ta haɗa shi da Mimi sai ta ce tana na ɗakinta in sun fito zuwa masallaci da yammah zata sanar da ita akan ta kira shi. Wannan saƙon Madiha ta gaya ma Mimi sai ita kuma ta kunna wayarta ta nemi Daddy a waya suka yi mgana ba tare da wani dogon mgana ba ya ce" An gaya miki mijin ki nata zuwa neman ki baya samun ki? Sai ta amsa masa bai ba ta samar mgana ba ya cigaba da faɗin" To daga ƙarshe dai ya zo ya same ni mun tattauna ya karɓi laifukansa ya ce zai gyara na ba shi damar ya same ki ku yi mgana kin ji ko? Gaddama ba halinta ba ne ya sa ta ce masa in sha Allahu sannan ya ƙara da cewa"Yaushe za ku dawo? Kai tsaye tace" Bansa ni ba amman ina tunanin cikin satin nan." Sai ya ba ta umarnin in ta dawo ta nemi mijinta su yi mgana har ya kara da cewa" kada ki damu na yi mgana da shi na fahimci fushin zuciya ne amman shima ya na sonki kuma ya faɗamin ma da bakin shi, kawai dai ki yi amfani da wannan damar ki sauyashi zuwa yadda kike son ya dawo kin ji ko? Cikin girmamawa ta amsa masa sannan su ka yi sallama sai ga ta rumgume da waya a kirjinta tana hamdala karfinta zuwanta umra akan Aji ne ta roƙi rabil samawati ya sausauta zuciyar bawansa Mansoor ya sanya masa salama da Aminci da natsuwa ya daidai ta masa rayuwarsa sannan ya Haɗe kansu shi da ita su zauna Lafiya su gina rayuwa mai kyau tare da zuru'a ɗayyiba, in da alheri a komawarta in kuma babu alheri ya cire mata son shi salin alim a cikin zuciyarta. Itama dai tuni duk wani fushi da take yi ta ji komai ya yaye mata ta ji ta yafe masa duk da cin zarafin iyayenta da ya yi in ta tuna ranta na ɓaci, sannan kuma sintirin da ya riƙa yi a kanta ya tabbatar mata da cewa tana da wata ƴar daraja a wajensa Sai yanzu ta ke ganin amfanin shawaran Rukky kuma a yanzu take da damar sauya rayuwarsa kamar yadda Daddy ya yi mata gugar zana. Daman tun da suka zo garin Ma'aiki ta kashe wayarta tana Ibadunta, wayar da suka yi da Daddy ya sa ta fara yi ma Madiha zencen komawa, ita kuma daman ta na siyayya shi ya sa a satin ba su samu dawowa ba sai da wani satin ya shiga sannan suka dawo lokacin suna da sati huɗu kenan a can. Sun dawo suka iske Jawahir ta sauka amman sai da aka yi mata C.S. Shi ya sa kwana uku kawai mimi ta yi ta huta sai ta bi jirgi daga lagos Jirgi zuwa Kano Ta kunna wayarta ta yi mgana da Hajiya da Rukky tana gaya mata halin da a ke ciki Rukky ta buga shewa kafin tac e"Dakyau. Lokacin mu yanzu ya fara, ki kira shi ki sanar da shi kin dawo amman za ki tsaya a kano saboda haihuwar Matar Dr" Haka ko ta yi amman ta kira shi har sau bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙo. "Na dawo, amman Ina kano Anty Jawahir ɗin Dr ta haihu, zan kai sati ina ga kafin na dawo Gombe." Amman har dare ba ta ga kiran shi ba har ta fara jin haushi shi kuma suna Jos a lokacin sun je buga wasa sai dare ya ga kiranta da saƙon ta a lokacin ya ga ji sai kawai ya tura mata da cewa " Allah ya raya abunda aka samu, in kin dawon ki sanar da ni, nima ba na gari ina Jos" Ta yi barci sai da safe ta ga saƙon sa. Sai ta yi masa uzuri tunda ta ji ya ce baya gari to sun je buga wasa ne tabbas. Sai kawai ta share kafa a gidan Dr, Jawahir kuma samar matar likita ne tuni cikin kwana uku ta fara motsa jikinta Shi y asa ba'a ɗaga suna ba.Dangin Mommy da suka zo barka su ga Mimi ba su kawo wani abu ba har Inna Zainaba tunda Mommy ba ta sanar da su an samu wata matsala ba, Sai da suka zo suma mata tsiyan sai dai ta zo ta tsaya gidan Dr sh ine fa ta ji kunya ta bi inna Zainaba gidanta ta kwana ra ɗan zaga yan'uwa tare da dangi na kusa kwananta biyu a Soron ɗinki ta tuno da Hibba sai ko ta ɗaga waya ta kirata bayan ta cire ta daga Kullenta da ta yi, Hibba kamar amafarki ta ga kiran Mimi ta ɗauka cikin mamaki tare da neman yi mata tsiya Mimi na dariya ta ce tana kano ta tura mata adireshi gidanta za ta zo sai su yi mgana jiki na rawa Hibba ta tura mata, Mu'azzam na Office ta kira shi ta na gaya masa suna da babban bakuwa Mimi za ta zo, shima cikin murna ya ce zai baro Office ya zo su gaisa. Tana tura mata ba daɗewa ta baro gidan Inna Zainaba, mai adaidaita ta nuna masa kwatance ya ce ya san Gidan ya na bakin hanya ne da ba ta gane ba ta kira Hibba Sai ta fito bakin gidan sannan ta hangeta, Bayan ta sallami mai adaidaita ta karisa suka rumgume juna da Hibba wacce ke yi mata tsiyan cewa" Anty Mimi idon ki kenan? Mu kan ba da laifi ba duk an haɗamu an hukunta." Ta na dariya ta ce" Shi ya sa na zo ban hakuri." Suna dariya suka karisa cikin gida Hibba ta rasa ina zata saka Mimi ta kawo mata Breakfast domin lokacin sha dayan safe ne Hibba ta ce ta karya sai dai na rana tunda nan za ta yi mata yini. Nan fa suka zauna suna ta hira Hibba ta ce" Mu dai me muka yi ne gabaɗaya a ka kulle mu Hajiyar Allah? Mimi na dariya ta ce" Ba fa abib da kuka yi kawai dai lokacin sai a hankali na kuma san roƙo na za ku yi ni kuma ba zan iya muku abin da ku kuke so lokacin ba shi ya sa." Hibba ta ce"Duk da haka dai, ni dai kinsan ba zan matsa miki kan abib da ba ki yi niyya ba, mu ka je har gida kika hanamu ganin ki sannan a wayar ma duk an rufe mu yanzu kin kyauta kenan? Laifin Babba Yaya sai ya shafe mu? Ta ƙarishe faɗa ta na yar dariya Mimi na dariyan take yi tana ba ta hakuri. Hibba ta ce"Ya muka iya? Dole mu hakura amman bayan an gama bamu wahala, Kawai sanadin ki sai ga Yaya Mansoor har gidan nan." Mimi na mamaki ta ce"Kai don Allah." Hibba ta ce" Wlh ai albarkacin kaza ma Kadangare kan sha ruwam kasko, kin ciru tuta tun dai ya na basarwa har dai ya fahimci ke ɗin ce, sai faman sintiri yake yi a saman hanya saboda ke fisabillahi mu dai a kyale mana Yaya haka anan ai dai ko a haka aka tsaya jikin ta ƙaura ya yi la'asar." Mimi na dariya t ace"Tabbas haka ne." Nan ta shiga ba ma Hibba labarin wayarsu da Daddy da abin da ya ce. Duk da Mu'azzam ya gaya mata Yaya Mansoor ya je can gidan kuma an samu daidato sai Mimi ta dawo amman bai buɗe mata ba, Hibba ta ce"Ma sha Allah haka ake so, Wlh Yayammu ya sauya kamar ba shi ba. Gida kuma ai sai dai ya siya miki wani tunda har Inna ma yanzu ba ta a gidan." Mimi ta zaro ido kafin ta ce" Innar? Me ya faru? Sai Hibba ta shiga warware mata abib da ya faru ta ƙare da cewa"To dai yanzu Inna ta samu cigaba tana gidan Yaya mansoor, ya kuma ce ya mallakaa mata har Abada." Mimi na jinjina kai ta ce"Allah Sarki. Na yi ma Inna Murna, daman ni tuni nasan wannan Maeesha makira ne, kai Allah ya kyauta dai." Hibba ta amsa da Amin lokaci ɗaya tana faɗin" Ke kam ai sai dai ki ba da izini kawai a fara ɗora miki gini." Mimi na dariya ba ta yi mgana ba, Hibba kuma ta kara da cewa" A yi hakuri in sha ba za mu ƙara ba, kuma muna da kuɗi za mu gina miki duk irin gidan da kike so.".! Nan ta bar Mimi da dariya. Haka suka cigaba da hiraran su, Mimi ba ta ɓoye ma Hibba komai ba kan shirin da suke yi ita da Rukky itama ta goyon baya da cewa"Dakyau, wlh ban ga laifin ki ba gwara ki gwara mana kansa irin su Yaya Mansoor sai da haka." Sallah kaɗai ya tada su bayan sun Idar suka shiga kitchen Mimi na taya Hibba da yanke yanke suna yi suna hira tare suka yi girkin su ka gama sannan suka zauna suka ci. Ana ta kiran Mimi a waya Khadi ce ta ce ta iso amman ba ta ganta ba an ce ta na soron ɗinki ki sai ta ce ga ta nan zuwa Mu'azzam ma ta tsaya jira sai bayan pa'asar ya shigo gidan Mimi ta tambayi Junior Hibba ta ce mata ya na can Gombe wajen Inna. Shima kamar Hibba Mu'azzam ciwon baki ya fara yi ma Mimi tana Mirmishi ta ce"Ku yi hakuri, a lokacin ba ni da abin da zan ce ne shi ya sa." Mu'azzam ya ce" Duk da haka dai da an Saurare mu." Mimi na yar dariya tac e"To shike nan ku yi hakuri yanzu za'a saurare ku." Saboda ganin Mimi na sauri bai tsaya cin abinci ba ya ce Hibba ta saka mayafi su maida Mimi gidan Dr daga nan su yi barka. Tana su bar shi amman ba su saurare ta ba, Suka ɗauketa tana musu kwatance har gidan Dr. Sulaiman sai dai a ka ga Mimi da baki tana dariya wajen cewa ƙanin mijinta ne da matarsa suka shiga har ciki suka yi ma Jawahir barka sannan ta raka su har haraban gidan suka tafi da alƙawarin Hibba na in sha Allahu za ta zo suna. Bayan tafiyarsu Khadi ta kalli Mimi lokaci ɗaya tana faɗin"Ke da aka ce kin buga yaji da kukan sai kin kashe aure, sai kuma a ganki kina bin gidajen dangin Miji? Mimi ta kalleta kawai amman ba ta yi mgana ba Sai Khadi ta fara dariya tana faɗin" Wai ni ki gaya min me ya yi miki ne da zafi haka? Aji ne fa Ajin nan da kike matukar so? Shege namiji ɗan Babansa ya kunsa miki kenan? Tashi kawai Mimi ta yi ta ba ta waje saboda ta san tana dukan ruwan cikinta ne ta ji labari nan ta barta da Jawahir tana ta mganganu ita kuma sai dai ta yi mata mirmishi. Har Dr. da ya dawo sai da Khadi ta ce masa" ƙanwarka an ce ta yi yaji amman kuma sai ga ta ta na bin gidan ƙanin mijinta.* Dariya ya yi kafin ya ce"Bacin rai ne amman yanzu mun huce za mu koma." Haka Khadi ta rika tsuntsura dariya tana Faɗin" To daman ita an gayamata soyayya ta na dauwamana, ku gaya mata kowa ma hakuri yake yi a gidan auran shi. Duk da ban so auran su ba amman daga baya na saki, duk lalacewar aure gwara auran da rabuwar wani lokacin, kawai ta cigaba da hakuri daman an ce baƙin mutum akwai faɗin rai sai kin ninka haƙurin ki." Ƙala Mimi ba ta ce mata ba. Sai Dr ne ke kare ma Mimi yana faɗin har nan Aji ya zo biko kuma dai shi kam ya ba shi bikon Mimi. Madiha ba ta zo ba sai ranar suna, Asma'u ma Mommy ta turo ta dag anan za ta tsaya gida ta yi hutu, Madiha ba ta san an daidaita har Mimi ta sauko ba sai da ta ga zuwan Hibba ana cewa matar ƙanin Mijin Mimi sai kuma da ta ganta sai ta tuna ta taɓa ganinta a wannan gidan da aka kai Mimi, Tun anan ta nuna ba ta ji daɗi ba Mimi ba ta ma san tana yi ba ta riƙa ina ta saka da bakuwarta Hibba ta na nan har dare har riga ta kawo ma Bby Girl da ta ci sunan Mahaifiyar Jawahir mai suna Hadiza, Sai bayan da Mu'azzam ya zo ya ɗauketa ne da daddare suna ɗakin Dr su huɗun gabaɗaya Madiha ta tada zencen da cewa"Ke Mimi me ya haɗa ki da dangi wancan matsiyacin? Ba Mimi kaɗai ba harta Khadi sai ta ji wani iri, Dr ya kalleta cikin ɓacin rai kafin ya ce" Haba Madiha, ko an rabu ai bai kamata ki kira shi da wannan sunan ba, Ballantana har gobe a matsayin mijin Mimi yake." Madiha cikin halin ko in kula, ta ce"To sai me? Ai sai ya sake ta wlh in ya yi taurin kai a maka shi a kotu," Khadi ta yi Saurin cewa"Ke, to tana son mijinta, yanzu hakama ya je ya samu Daddy kuma ya ce ya ba shi bikon ta, tana komawa Gombe sai shirin tarewa daman Yajin barazana ta yi ko Mimin Abi? Mimi ta kasa mgana Idanuwanta har sun kawo kwallah, Dr ne ya tsawarta ma Madiha da cewa" Ki daina shiga hurumin da ba na ki ba don Allah, Mimi ba za ta ji daɗi ba." Madiha ta kalle su cikin mamaki kafin ta ce" Mi ye illar mgana ta? Na ga ita da kanta ta ce ba ta son auran domin na taimaka mata komai ya kare laifi ne? Sai kawai Mmi ta miƙe tana kallon Dr kafin tace" Dr gobe ko jibi zam koma Gombe." Ta na gama faɗin haka ta bar musu ɗakin. Khadi ta kai duban ta kan Madiha kafin ta ce"Gaskiya Sisto ba ki kyauta ba, kamar ni ne fa ki zagi Muhammad" Madiha ta taɓe baki kafin ta ce"Muhammad dabam wannan talakan dabam, ki daina ma haɗa su." Khadi na dariya shi kuma Dr ya haɗe rai yana mata faɗan abin da ta yi na ta kyauta ba sai kawai ta ce"Au don nace matsiya ci? Karya na yi? To shike nan na cire bakina." Ba za ta daina ba halin su ɗaya da Abi shigen kafiya aiko har washegari Mimi ba ta ƙara yi ma Madiha mgana ba sai ta nemi ma jirgin Komawa Gombe ta samu na yamma. Dr bai hana ta tafiya ba, an kulla mata Naman suna da yaji na ta da na Hajiya, Jirgin karfe biyar ta bi zuwa Gombe Dr. da Khadi su ka kaita filin Jirgi sai da za ta tafi sannan ta yi ma Madiha sallama ta amsa a daƙune ita gani take yi ina laifi domin ta faɗi gaskiya. Sai dai Hajiya ta ga Mimi sarkin Ya ji kamar daga sama kuma ba domin mganar Daddy ba, hutun ta ya ƙare ya zama dole ta dawo. Hajiya ta yi murna Baaba Uwani ta ce daman gidan shuru da ba ta nan, ta kira Daddy ta ce masa ta dawo kila anan Mama taji ta gayama Jaheed daman tun da ya ji ta Dawo gida ya addabeta da waya yana gaya mata yana kan bakan shi ta ce ba shi ma da hankali da auranta ai ba ya mutu ba ne. Sai da ya ji ta dawo wai zai biyo jirgi gobe su yi mgana. Daman a gidan Madiha zuwan sa uku wajenta yana mata magiya ta faɗa masa Mijinta bai saketa ba amman ya na ce wai zai taya ta karɓan sakin daman ai ba su da ce da juna ba, shi a tunanin shi Madiha na goyon bayan shi, shike nan ya same ta ya gama. Tun da ya ce mata zai zo washegari ta ce masa ka da ya zo, domin ita ta san abin da take yi da auranta ba za ta zo tana haɗuwa da shi ba. Washegari hutawa ta yi a gida, shi kuma Jaheed bai samu dama a wajen aiki ba Shi ya sa bai zo ba, Aji kuma Daddy da kansa ya kira shi ya faɗa masa Mimi ta dawo daman ranar sun karɓi lambar wayar juna sai ya ce zai shigo gidan ko a ranar da daddare ko washegari da yammah. Bai samu zuwa a daran ba sai washegari bayan la'sar daga gida yake ya je ya gaida Inna sai da ta kara masa mganan Mimi ya ce daga nan wajen ta zai nufa. A motarsa ya je yana sanye da ƙananun kaya, megadi na buɗe masa get ya shiga motarsa Mimi na fitowa tare da Rukky da ta zo ta rakota sun tsaya suna mgana sai ganin Aji suka yi ya fito daga motarsa duk da ya saka hula P. cap ta rufe rabin fuskar shi ba zai hana taƙi gane shi ba. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3008* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Mansor na tsaye a tsakiyar falon gidan tsohon Sanata Alhaji Hamza sulaiman Dabo. Hannayensa harɗe a kirjinsa, lokaci ɗaya yana nazarin falon, ya taɓa shigowa falon kusan sau biyu wani lokacin a can baya Mimi ta matsa masa ya shiga suka gaisa na farko rashin lafiyan Hajiya na biyu ya manta falilin. A haka Daddy ya zo ya same shi yana tsaye bai zauna ba, yana ƙarisowa ya miƙa masa hannu suka yi masabaha. Sannan Daddy ya nuna masa kujera ya ce ya zauna amman sai bai zauna ba sai ya zauna a saman tattausan cafet ɗin da ya malale fallon gabaɗaya saboda ya tuna wayar su da Mu'azzam yana hanyar tahowa nan ya yi ta hadadda masa ya je neman sulhu ne kuma surukinsa ne ya kamata ya nuna masa girma da daraja. "Haba ka tashi ka zauna saman kujera mana." Kan Mansoor na ƙasa ya ce"A aa nan ma ya isa Alhaji." Sai Daddy bai ja ba kawai sai ya gyara zama suka gaisa yana tambayan shi wajen iyayanshi a sanyaye ya ce Alhamdulillah, shuru na wani lokaci ba daɗewa sai ga Anty ta shigo da farantin ruwa da lemu ta sauke nan saman center table ɗin dake falon, Itama Mansoor ya gaisheta ta amsa cikin sakewa kafin ta ce"Ah yallaɓai ya ka bar surukin namu ya zauna a ƙasa kuma? Daddy ya yi mirmishi kafin ya ce" Biko ya zo shi ya sa ya ninka biyayyarsa." Tare suka yi dariya shi da Anty sannan ta fice shi ko Mansoor kansa na ƙasa domin sai ya ji Daddy ya yi masa kwarjini ya kuma rasa ta ina zai fara ma mganar, In hr Mimi ta faɗa musu dukkan abin da ya aikata mata ai da Kunya, Shi kuma Daddy nazarinsa yake yi ta gefen ido amman bai nuna ba, wata Jarida ma ya ja anan gefe yana karantawa kamar yadda Daddy ya yi masa kwarjini haka shima Daddy ya ga ƙwarjinin Mansoor ya cika falon gabaɗaya. "Ka sha ruwan mana." Daddy ya katse shi lokaci ɗaya yana kallon sa, sai Mansoor ya muskuta ya ɗan mike ya isa ga wajen ruwa ya saka kofi ya tsiyaya Kaɗan ya sha sannan ya ijiye kofin sannan ya koma in da ya tashi ya zauna. Shuru ya sake wanzuwa na wani lokaci kafin Daddy ya sake katse shurun da cewa" Ya wajen aikin na ku? Kwanaki abokanka da ƙaninka suka zo sun ce wasa gare ku masu yawa baka samun lokaci." Sai ya samu kansa da amsawa da E, shi kuma Daddy sai ya jinjina kai kafin yac e"Good! Allah ya saka albarka," Aji ya amsa da Amin cikin yanayin maganarsa amman muryansa ta yi kasa sosai. Gani ya yi Daddy ya yi kamar bai san dalilin zuwanshi ba, ya ma cigaba da karatun Jaridarsa lokaci ɗaya kuma ya na amsa waya in an kira shi. Mansoor kuma na duke ya rasa ta in da zai fara dakyar ya iya kundunbalan ɗagowa ya na kallon Daddy kafin lokaci ɗaya ya fara da faɗin. "Alhaji dama kan mganar Fatima ne.." Sai ya dakata shi kuma Daddy sai ya kalle shi kafin ya ce"E, ina jin ka, Mimi ba ai ta dawo mana nan cikin kuka, ta ce ka ce ba ka sonta sannan ta ce za ta tafi ka ce is better da ta tafi ɗin, ni kuma da na ji haka sai na ce ai ba dole a cikin aure kuma in ka ga alaqa ta fara lalacewa gwara rabuwar shi ya fi alheri." Mansoor ya yi shuru kafin yac e" Alhaji ni ban ce ta tafin da gaske ba" "To me ya sa bayan ta taho a daran ko washegari ba ka biyo sahun ta ba, in ba ka nufin ta tafin ba? Kai tsaye Mansoor ya gyara zama yana faɗin" Ina da dalilina Alhaji, saboda ka san su mata wani lokacin in ransu ya ɓaci gwara ka yi nesa da su su huce, na ga ranta ya ɓaci a lokaci to ba laifi ba ne domin ta dawo gida ta huta amman ba na nufin wai ta tafi saboda ba na sonta, in ba na sonta ai ba zan yarda na aureta ba. Kawai na bata lokaci ne ta huta sannan ta huce daga ɓacin ran da take ciki." Magana ɗaya bayan Ɗlɗaya haka Manaoor ke fitar da ita, Daddy yana kallonsa amman yana mirmishi kafin ya gyaɗa kai ya ce"Na ji dalilin ka, ta wani fannin kana da ƴar gaskiyar ka ta wani fannin kuma ba ka da shi, amman duk ba wannan ba babban abin shi ne ga rashin ba ka sonta sannan ta ce ka kasa manta abin da ya faru a shekarun baya sai ka riƙa kallonta da abin, ka ga kuwa ai ba kyau irin haka riƙo ba shi da amfani sannan tunda har da bakin ka ka ce ba ka so ai ba wanda zai yi maka dole da sai ka zauna da ita ko ba haka ba? Kan Mansoor Aji na ƙasa ya ce"E, ta nan kam ina da laifi, amman na gane kuskurena Alhaji a yi hakuri in sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba." "Maganar rashin son fa? Ba zan ba ka bikon ƴata ba sai na ji gaskiyar mgana.* Ya faɗa ya na ɗan haɗe rai. Sai Mansoor ya sadda kansa ƙasa cikin jin nauyi kafin ya ce"Ita ce ko a da, a yanzun ma ita ce har gobe da jibi ma ita ce, ɓacin rai ne ya sa na yi mata mganganu cikin fushi amman in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba." Sai Daddy ya saki fuska yana faɗin" Alhamdulillah Allah ya sa na ji daɗin haka, ka burgeni yadda ka amshi laifukan ka sannan ka ce za ka gyara sannan na amince zan baka damar yin bikon matarka saboda dalilai guda biyu na farko ka yi laifi kuma ka amsa laifin ka, ka ba da hakuri sannan ka yi niyar gyara na biyu kuma na ji labarin ka je Abuja da kano ba ka samu ganinta ba hakam ma ya saka ni yarda da mganarka ta farko. Tabbas da farko da ta dawo gida da Koke koken cewa ita a raba auran ku in da ban yi zurfin tunani da duka rayuka sun ɓaci amman sai na bata lokaci kamar yadda ka ce itama ta sauka daga fushinta na tabbata a yanzu ba za ta so rabuwar auran ku ba sai dai daman an tauna aya ne domin tsakuwa ta ji tsoro. Sannan ina son na yi maka nasiha shi riƙo ba shi da amfani mu kasance ma su afuwa tunda Allah ma muma yi masa laifi, yana yafe mana kuma shi ya ce mu kasance masu afuwa, sannan shi kan shi Yaya Kabiru kafin rasuwarsa wallahi ya yi nadama kan abin da ya aikata maka kuma Hajiya da Brr. sun je sun yi mgana da kai sun kuma nema masa afuwarka sannan kafin rasuwarsa shi ya ce duk abin da Mimi take so a yi mata dalilin da ya saka aka yi auran ku bisa duk Sharaɗɗun da ka saka ka ga ba wanda ma ya maida kansa, To me ya sa kai ba za ka yi hakuri ka manta baya ba? Sai ka bar abu na shekaru ya hana ka sukuni da zaman lafiya? Shi kan shi Yayan ina yake yau ? Ai ba shi a duniya ya ma manta shi ya taɓa rayuwar duniya, ni ma ƙila ban sani ba nan kusa ne, wataƙila kaima nan kusa ne duk ba mu san gawan fari ba, sai fatan Allah yasa mu dace sannan ka sani Allah ya yi ma masu Afuwa wani babban tanadi, Ina ba ka shawaran ka manta baya don Allah domin samar ma kan ka da zuciyarka salama." Gabaɗaya jikin Mansoor ya yi sanyi mganganun sun shiga zuciyarsa sosai daman kuma shi tuni ya saki wannan abun Sai ya ji kamar ana rage masa nauyin zuciya cikin jinjina kai ya ce"In sha Allahu komai ya wuce. na gode Alhaji Allah ya ƙara girma." Sai Daddy ya ji daɗi har ya nuna a saman fuskarsa ya kalli Aji Lokaci ɗaya yana faɗin" Na ji daɗin yadda ka saurare ni, da duka amincewata Mimi za ta koma ɗakinta, zan kirata da kaina na ce ta dawo amman sai ka same ta ku tattauna wannan kuma tsakanin ku ne ba zan shiga ba." Aji ya rankwafar da kai yana godiya Daddy yace"Ba laifi. Na gode kwarai Allah ya yi ma rayuwa albarka Allah kuma ya kaɗe fitina a tsakanin ku." Aji ya amsa da Amin Amin kafin ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa ya zaro kuɗi bai san ko nawa ba ne ya ijiye a gaban Daddy sannan ya miƙe yana yi masa sallama Daddy duk da yana da rufin asirin sa amman ya girmama wannan alherin ya miƙe Lokaci ɗaya y na ɗaukan kuɗin kafin ya ce"Har da ɗawainiya? To yau dai zan ce na ci kuɗin ƙwallo kenan." Mirmishi kawai mansoor ya yi ba tare da ya yi mgana ba Har haraban gidan Daddy ya rako shi, suka kara yin sallama shi ya koma cikin gidan shi kuma sai ya hau mashin ɗinsa ya bar gidan, yana tafe iska na kaɗa shi yana jinsa kamar ya na shawagi a sararin samaniya, sannan nauyin da ke zuciyarsa ya ji ya yaye, wani irin nishaɗi da farinciki ke shigar sa bai sani ba, Yana tafe yana Faman mirmishi shi kaɗai. Daddy kuma yana komawa cikin gida Mama daman na falo tana jiran shi ya na shigowa ta miƙe tana faɗin" Har ya tafi? Shi kuma bai ba ma tambayarta wani muhimmamci ba ya ce" E." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na zama kan ɗaya daga cikin kujerun falon gefensa ta koma ta zauna tana faɗin" Allah sa dai ba ka ba shi fuska ba" Kai tsaye ya kalleta kafin ya ce" wani fuskan kuma ? Na saurari bayaninsa na nuna masa Kuskuransa kuma ya karɓa ya ce zai gyara na kuma bashi izinin in Mimi ta dawo ya je su zauna su daidai ta." Mama ta yi wani iri wanda har sai da rashin jin daɗin ya bayyana saman fuskarta. Cikin mamakinta Alhaji Hamza ya kalleta kafin ya ce"Sai na ga kamar ba ki ji daɗin jin hakan ba ko? Da sauri ta ce"Ba wai ban ji daɗi ba gani na yi yarinyar nan ita ta ce ta na so daga farko amman yanzu kuma ta ce ba ta so, kana ganin a tsaya sauraran shi ba ɓata lokaci ba ne? Sannan sam ba su dace da juna ba ji irin gidan da ya kai Mimi domin Allah fa." Mirmishi ya yi domin shi ya gama gano in da ta dosa amman gudun ka ɗora ma mutun zargi ya sa yac e" To ba ki san tsakanin mata da miji sai Allah ba kenan? Itama a lokacin ɓacin rai ne amman tana son mijinta kuma ba za ta so rabuwarsu ba, mganar gida kuma ai ta san ra'ayin sa tun farko kuma ta ce ta ji ta gani, ba hurumun ba ne yanzu mu san abin da suka yanke ni dai na ce ya same ta su yi mgana abin d suka tattauna namu na saka albarka ne." "Amman ba dai wanman gidan na su za ta koma ba ko? Mama ta faɗa cikin yanayin damuwa a muryanta kai tsaye ya ce"Ban sani ba,ko ma can ne ko wani gidan ne can tsakanin su dai." Sai Mama ta sauke ajiyar zuciya ba tare da ta yi mgana ba sai Daddy ne ya kalleta na wani ookaci kafin ya ce"Na san damuwarki kan Jaheed ne." Da Sauri ta juya gare shi tana faɗin"Yallabai Yaron mu na son Mimi har yau ya kasa ba ma wata mace dama, bayan dawowan nan nata baka gq murnan da ya yi ba." Dariyansu na manya ya yi kafin ya ce"Shi ma dai sakarai ne, mace da mijinta bai sake ta ba ne yake murna a kanta? Ke ce kuma ba ki ga ya masa gaskiya ba gwara tun da wuri ya hakura da Mimi in da ace tana son shi da ta zaɓe shi amman tunda ba ta iya zaɓarsa a baya ba yanzu ma ba za ta zaɓe shi ba, ki zauna ki gaya masa gaskiya Mimi ta haramta gare shi gwara tun lokaci bai ƙure masa ba ya nemi wata domin ba zan barshi ya tsallake shekaran nan bai yi aure ba." Yana gama faɗin haka ya mike ya shige ciki ya barta zaune da tagumi, har Allah ta na jin haushin Hajiya domin ita taƙi ba ma Jaheed goyon baya in da tana so da Mimin ba ta isa ta yi gaddama ba, amman an na ce an ce sai abin da take so ga ta nan ga abin da ta ke so ɗin nan ya na wahalar da ita. Ranta ba daɗi itama ta bar falon zuwa ɗaakinta tana tunanin kiran ƙanwarta Hajiya Turai su tattauna mganar. ******* *MIMI* Lokacin da Daddy ya samu wayar Madiha wajen kwana uku da zuwan Aji wajensa ya na ta kiran wayar Mimi ba ya samu sai ya kira ta Madihan tunda suna tare, bayan sun gaisa ya ce ta haɗa shi da Mimi sai ta ce tana na ɗakinta in sun fito zuwa masallaci da yammah zata sanar da ita akan ta kira shi. Wannan saƙon Madiha ta gaya ma Mimi sai ita kuma ta kunna wayarta ta nemi Daddy a waya suka yi mgana ba tare da wani dogon mgana ba ya ce" An gaya miki mijin ki nata zuwa neman ki baya samun ki? Sai ta amsa masa bai ba ta samar mgana ba ya cigaba da faɗin" To daga ƙarshe dai ya zo ya same ni mun tattauna ya karɓi laifukansa ya ce zai gyara na ba shi damar ya same ki ku yi mgana kin ji ko? Gaddama ba halinta ba ne ya sa ta ce masa in sha Allahu sannan ya ƙara da cewa"Yaushe za ku dawo? Kai tsaye tace" Bansa ni ba amman ina tunanin cikin satin nan." Sai ya ba ta umarnin in ta dawo ta nemi mijinta su yi mgana har ya kara da cewa" kada ki damu na yi mgana da shi na fahimci fushin zuciya ne amman shima ya na sonki kuma ya faɗamin ma da bakin shi, kawai dai ki yi amfani da wannan damar ki sauyashi zuwa yadda kike son ya dawo kin ji ko? Cikin girmamawa ta amsa masa sannan su ka yi sallama sai ga ta rumgume da waya a kirjinta tana hamdala karfinta zuwanta umra akan Aji ne ta roƙi rabil samawati ya sausauta zuciyar bawansa Mansoor ya sanya masa salama da Aminci da natsuwa ya daidai ta masa rayuwarsa sannan ya Haɗe kansu shi da ita su zauna Lafiya su gina rayuwa mai kyau tare da zuru'a ɗayyiba, in da alheri a komawarta in kuma babu alheri ya cire mata son shi salin alim a cikin zuciyarta. Itama dai tuni duk wani fushi da take yi ta ji komai ya yaye mata ta ji ta yafe masa duk da cin zarafin iyayenta da ya yi in ta tuna ranta na ɓaci, sannan kuma sintirin da ya riƙa yi a kanta ya tabbatar mata da cewa tana da wata ƴar daraja a wajensa Sai yanzu ta ke ganin amfanin shawaran Rukky kuma a yanzu take da damar sauya rayuwarsa kamar yadda Daddy ya yi mata gugar zana. Daman tun da suka zo garin Ma'aiki ta kashe wayarta tana Ibadunta, wayar da suka yi da Daddy ya sa ta fara yi ma Madiha zencen komawa, ita kuma daman ta na siyayya shi ya sa a satin ba su samu dawowa ba sai da wani satin ya shiga sannan suka dawo lokacin suna da sati huɗu kenan a can. Sun dawo suka iske Jawahir ta sauka amman sai da aka yi mata C.S. Shi ya sa kwana uku kawai mimi ta yi ta huta sai ta bi jirgi daga lagos Jirgi zuwa Kano Ta kunna wayarta ta yi mgana da Hajiya da Rukky tana gaya mata halin da a ke ciki Rukky ta buga shewa kafin tac e"Dakyau. Lokacin mu yanzu ya fara, ki kira shi ki sanar da shi kin dawo amman za ki tsaya a kano saboda haihuwar Matar Dr" Haka ko ta yi amman ta kira shi har sau bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙo. "Na dawo, amman Ina kano Anty Jawahir ɗin Dr ta haihu, zan kai sati ina ga kafin na dawo Gombe." Amman har dare ba ta ga kiran shi ba har ta fara jin haushi shi kuma suna Jos a lokacin sun je buga wasa sai dare ya ga kiranta da saƙon ta a lokacin ya ga ji sai kawai ya tura mata da cewa " Allah ya raya abunda aka samu, in kin dawon ki sanar da ni, nima ba na gari ina Jos" Ta yi barci sai da safe ta ga saƙon sa. Sai ta yi masa uzuri tunda ta ji ya ce baya gari to sun je buga wasa ne tabbas. Sai kawai ta share kafa a gidan Dr, Jawahir kuma samar matar likita ne tuni cikin kwana uku ta fara motsa jikinta Shi y asa ba'a ɗaga suna ba.Dangin Mommy da suka zo barka su ga Mimi ba su kawo wani abu ba har Inna Zainaba tunda Mommy ba ta sanar da su an samu wata matsala ba, Sai da suka zo suma mata tsiyan sai dai ta zo ta tsaya gidan Dr sh ine fa ta ji kunya ta bi inna Zainaba gidanta ta kwana ra ɗan zaga yan'uwa tare da dangi na kusa kwananta biyu a Soron ɗinki ta tuno da Hibba sai ko ta ɗaga waya ta kirata bayan ta cire ta daga Kullenta da ta yi, Hibba kamar amafarki ta ga kiran Mimi ta ɗauka cikin mamaki tare da neman yi mata tsiya Mimi na dariya ta ce tana kano ta tura mata adireshi gidanta za ta zo sai su yi mgana jiki na rawa Hibba ta tura mata, Mu'azzam na Office ta kira shi ta na gaya masa suna da babban bakuwa Mimi za ta zo, shima cikin murna ya ce zai baro Office ya zo su gaisa. Tana tura mata ba daɗewa ta baro gidan Inna Zainaba, mai adaidaita ta nuna masa kwatance ya ce ya san Gidan ya na bakin hanya ne da ba ta gane ba ta kira Hibba Sai ta fito bakin gidan sannan ta hangeta, Bayan ta sallami mai adaidaita ta karisa suka rumgume juna da Hibba wacce ke yi mata tsiyan cewa" Anty Mimi idon ki kenan? Mu kan ba da laifi ba duk an haɗamu an hukunta." Ta na dariya ta ce" Shi ya sa na zo ban hakuri." Suna dariya suka karisa cikin gida Hibba ta rasa ina zata saka Mimi ta kawo mata Breakfast domin lokacin sha dayan safe ne Hibba ta ce ta karya sai dai na rana tunda nan za ta yi mata yini. Nan fa suka zauna suna ta hira Hibba ta ce" Mu dai me muka yi ne gabaɗaya a ka kulle mu Hajiyar Allah? Mimi na dariya ta ce" Ba fa abib da kuka yi kawai dai lokacin sai a hankali na kuma san roƙo na za ku yi ni kuma ba zan iya muku abin da ku kuke so lokacin ba shi ya sa." Hibba ta ce"Duk da haka dai, ni dai kinsan ba zan matsa miki kan abib da ba ki yi niyya ba, mu ka je har gida kika hanamu ganin ki sannan a wayar ma duk an rufe mu yanzu kin kyauta kenan? Laifin Babba Yaya sai ya shafe mu? Ta ƙarishe faɗa ta na yar dariya Mimi na dariyan take yi tana ba ta hakuri. Hibba ta ce"Ya muka iya? Dole mu hakura amman bayan an gama bamu wahala, Kawai sanadin ki sai ga Yaya Mansoor har gidan nan." Mimi na mamaki ta ce"Kai don Allah." Hibba ta ce" Wlh ai albarkacin kaza ma Kadangare kan sha ruwam kasko, kin ciru tuta tun dai ya na basarwa har dai ya fahimci ke ɗin ce, sai faman sintiri yake yi a saman hanya saboda ke fisabillahi mu dai a kyale mana Yaya haka anan ai dai ko a haka aka tsaya jikin ta ƙaura ya yi la'asar." Mimi na dariya t ace"Tabbas haka ne." Nan ta shiga ba ma Hibba labarin wayarsu da Daddy da abin da ya ce. Duk da Mu'azzam ya gaya mata Yaya Mansoor ya je can gidan kuma an samu daidato sai Mimi ta dawo amman bai buɗe mata ba, Hibba ta ce"Ma sha Allah haka ake so, Wlh Yayammu ya sauya kamar ba shi ba. Gida kuma ai sai dai ya siya miki wani tunda har Inna ma yanzu ba ta a gidan." Mimi ta zaro ido kafin ta ce" Innar? Me ya faru? Sai Hibba ta shiga warware mata abib da ya faru ta ƙare da cewa"To dai yanzu Inna ta samu cigaba tana gidan Yaya mansoor, ya kuma ce ya mallakaa mata har Abada." Mimi na jinjina kai ta ce"Allah Sarki. Na yi ma Inna Murna, daman ni tuni nasan wannan Maeesha makira ne, kai Allah ya kyauta dai." Hibba ta amsa da Amin lokaci ɗaya tana faɗin" Ke kam ai sai dai ki ba da izini kawai a fara ɗora miki gini." Mimi na dariya ba ta yi mgana ba, Hibba kuma ta kara da cewa" A yi hakuri in sha ba za mu ƙara ba, kuma muna da kuɗi za mu gina miki duk irin gidan da kike so.".! Nan ta bar Mimi da dariya. Haka suka cigaba da hiraran su, Mimi ba ta ɓoye ma Hibba komai ba kan shirin da suke yi ita da Rukky itama ta goyon baya da cewa"Dakyau, wlh ban ga laifin ki ba gwara ki gwara mana kansa irin su Yaya Mansoor sai da haka." Sallah kaɗai ya tada su bayan sun Idar suka shiga kitchen Mimi na taya Hibba da yanke yanke suna yi suna hira tare suka yi girkin su ka gama sannan suka zauna suka ci. Ana ta kiran Mimi a waya Khadi ce ta ce ta iso amman ba ta ganta ba an ce ta na soron ɗinki ki sai ta ce ga ta nan zuwa Mu'azzam ma ta tsaya jira sai bayan pa'asar ya shigo gidan Mimi ta tambayi Junior Hibba ta ce mata ya na can Gombe wajen Inna. Shima kamar Hibba Mu'azzam ciwon baki ya fara yi ma Mimi tana Mirmishi ta ce"Ku yi hakuri, a lokacin ba ni da abin da zan ce ne shi ya sa." Mu'azzam ya ce" Duk da haka dai da an Saurare mu." Mimi na yar dariya tac e"To shike nan ku yi hakuri yanzu za'a saurare ku." Saboda ganin Mimi na sauri bai tsaya cin abinci ba ya ce Hibba ta saka mayafi su maida Mimi gidan Dr daga nan su yi barka. Tana su bar shi amman ba su saurare ta ba, Suka ɗauketa tana musu kwatance har gidan Dr. Sulaiman sai dai a ka ga Mimi da baki tana dariya wajen cewa ƙanin mijinta ne da matarsa suka shiga har ciki suka yi ma Jawahir barka sannan ta raka su har haraban gidan suka tafi da alƙawarin Hibba na in sha Allahu za ta zo suna. Bayan tafiyarsu Khadi ta kalli Mimi lokaci ɗaya tana faɗin"Ke da aka ce kin buga yaji da kukan sai kin kashe aure, sai kuma a ganki kina bin gidajen dangin Miji? Mimi ta kalleta kawai amman ba ta yi mgana ba Sai Khadi ta fara dariya tana faɗin" Wai ni ki gaya min me ya yi miki ne da zafi haka? Aji ne fa Ajin nan da kike matukar so? Shege namiji ɗan Babansa ya kunsa miki kenan? Tashi kawai Mimi ta yi ta ba ta waje saboda ta san tana dukan ruwan cikinta ne ta ji labari nan ta barta da Jawahir tana ta mganganu ita kuma sai dai ta yi mata mirmishi. Har Dr. da ya dawo sai da Khadi ta ce masa" ƙanwarka an ce ta yi yaji amman kuma sai ga ta ta na bin gidan ƙanin mijinta.* Dariya ya yi kafin ya ce"Bacin rai ne amman yanzu mun huce za mu koma." Haka Khadi ta rika tsuntsura dariya tana Faɗin" To daman ita an gayamata soyayya ta na dauwamana, ku gaya mata kowa ma hakuri yake yi a gidan auran shi. Duk da ban so auran su ba amman daga baya na saki, duk lalacewar aure gwara auran da rabuwar wani lokacin, kawai ta cigaba da hakuri daman an ce baƙin mutum akwai faɗin rai sai kin ninka haƙurin ki." Ƙala Mimi ba ta ce mata ba. Sai Dr ne ke kare ma Mimi yana faɗin har nan Aji ya zo biko kuma dai shi kam ya ba shi bikon Mimi. Madiha ba ta zo ba sai ranar suna, Asma'u ma Mommy ta turo ta dag anan za ta tsaya gida ta yi hutu, Madiha ba ta san an daidaita har Mimi ta sauko ba sai da ta ga zuwan Hibba ana cewa matar ƙanin Mijin Mimi sai kuma da ta ganta sai ta tuna ta taɓa ganinta a wannan gidan da aka kai Mimi, Tun anan ta nuna ba ta ji daɗi ba Mimi ba ta ma san tana yi ba ta riƙa ina ta saka da bakuwarta Hibba ta na nan har dare har riga ta kawo ma Bby Girl da ta ci sunan Mahaifiyar Jawahir mai suna Hadiza, Sai bayan da Mu'azzam ya zo ya ɗauketa ne da daddare suna ɗakin Dr su huɗun gabaɗaya Madiha ta tada zencen da cewa"Ke Mimi me ya haɗa ki da dangi wancan matsiyacin? Ba Mimi kaɗai ba harta Khadi sai ta ji wani iri, Dr ya kalleta cikin ɓacin rai kafin ya ce" Haba Madiha, ko an rabu ai bai kamata ki kira shi da wannan sunan ba, Ballantana har gobe a matsayin mijin Mimi yake." Madiha cikin halin ko in kula, ta ce"To sai me? Ai sai ya sake ta wlh in ya yi taurin kai a maka shi a kotu," Khadi ta yi Saurin cewa"Ke, to tana son mijinta, yanzu hakama ya je ya samu Daddy kuma ya ce ya ba shi bikon ta, tana komawa Gombe sai shirin tarewa daman Yajin barazana ta yi ko Mimin Abi? Mimi ta kasa mgana Idanuwanta har sun kawo kwallah, Dr ne ya tsawarta ma Madiha da cewa" Ki daina shiga hurumin da ba na ki ba don Allah, Mimi ba za ta ji daɗi ba." Madiha ta kalle su cikin mamaki kafin ta ce" Mi ye illar mgana ta? Na ga ita da kanta ta ce ba ta son auran domin na taimaka mata komai ya kare laifi ne? Sai kawai Mmi ta miƙe tana kallon Dr kafin tace" Dr gobe ko jibi zam koma Gombe." Ta na gama faɗin haka ta bar musu ɗakin. Khadi ta kai duban ta kan Madiha kafin ta ce"Gaskiya Sisto ba ki kyauta ba, kamar ni ne fa ki zagi Muhammad" Madiha ta taɓe baki kafin ta ce"Muhammad dabam wannan talakan dabam, ki daina ma haɗa su." Khadi na dariya shi kuma Dr ya haɗe rai yana mata faɗan abin da ta yi na ta kyauta ba sai kawai ta ce"Au don nace matsiya ci? Karya na yi? To shike nan na cire bakina." Ba za ta daina ba halin su ɗaya da Abi shigen kafiya aiko har washegari Mimi ba ta ƙara yi ma Madiha mgana ba sai ta nemi ma jirgin Komawa Gombe ta samu na yamma. Dr bai hana ta tafiya ba, an kulla mata Naman suna da yaji na ta da na Hajiya, Jirgin karfe biyar ta bi zuwa Gombe Dr. da Khadi su ka kaita filin Jirgi sai da za ta tafi sannan ta yi ma Madiha sallama ta amsa a daƙune ita gani take yi ina laifi domin ta faɗi gaskiya. Sai dai Hajiya ta ga Mimi sarkin Ya ji kamar daga sama kuma ba domin mganar Daddy ba, hutun ta ya ƙare ya zama dole ta dawo. Hajiya ta yi murna Baaba Uwani ta ce daman gidan shuru da ba ta nan, ta kira Daddy ta ce masa ta dawo kila anan Mama taji ta gayama Jaheed daman tun da ya ji ta Dawo gida ya addabeta da waya yana gaya mata yana kan bakan shi ta ce ba shi ma da hankali da auranta ai ba ya mutu ba ne. Sai da ya ji ta dawo wai zai biyo jirgi gobe su yi mgana. Daman a gidan Madiha zuwan sa uku wajenta yana mata magiya ta faɗa masa Mijinta bai saketa ba amman ya na ce wai zai taya ta karɓan sakin daman ai ba su da ce da juna ba, shi a tunanin shi Madiha na goyon bayan shi, shike nan ya same ta ya gama. Tun da ya ce mata zai zo washegari ta ce masa ka da ya zo, domin ita ta san abin da take yi da auranta ba za ta zo tana haɗuwa da shi ba. Washegari hutawa ta yi a gida, shi kuma Jaheed bai samu dama a wajen aiki ba Shi ya sa bai zo ba, Aji kuma Daddy da kansa ya kira shi ya faɗa masa Mimi ta dawo daman ranar sun karɓi lambar wayar juna sai ya ce zai shigo gidan ko a ranar da daddare ko washegari da yammah. Bai samu zuwa a daran ba sai washegari bayan la'sar daga gida yake ya je ya gaida Inna sai da ta kara masa mganan Mimi ya ce daga nan wajen ta zai nufa. A motarsa ya je yana sanye da ƙananun kaya, megadi na buɗe masa get ya shiga motarsa Mimi na fitowa tare da Rukky da ta zo ta rakota sun tsaya suna mgana sai ganin Aji suka yi ya fito daga motarsa duk da ya saka hula P. cap ta rufe rabin fuskar shi ba zai hana taƙi gane shi ba. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3009* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Mimi na sanye da wata doguwar riga amman rigar mai roba ce ta ɗan kama mata jiki kaɗan. Sai ta saka mayafin rigar a saman kanta Rukky ma baƙar Abaya ne a jikinta amman ita sai ta saka ƙaramin hijabi a sama sannan har da Igiyan ID card ɗin ta dake maƙale a saman wuyanta, Saboda daga wajen aiki ta biyo wajen Mimi.   Dukkansu yana fitowa daga mota suka zuba masa ido. Shi kuma ya fito kenan sai aka kira wayarsa sai ya tsaya yana amsa wayar, Mimi ta ƙura masa ido kamar yadda shima ya ƙe kare mata kallo daga kasan hulaarsa wato ita wani ja ma ta ƙara da haske da kiba shi kuma ya na nan ta barshi yana faman wahala, ita kuma sai ta ga ya ƙara mata tsawo saboda ta daɗe ba ta gan shi ba, har wani sanyi sanyi take ji a ƙasan ranta, ta shagala da kallonsa ba ta san Rukky na kiran sunanta ba sai da ta ji ta dafa kafaɗanta. "Mimi.."   Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta maida kallonta kan Rukky lokaci ɗaya tana faɗin" Sorry me kika ce? Rukky ta balla mata harara kafin ta juya ta na kallon Aji ya gama wayar yana tahowa wajensu da sauri ta matsa kusa da Mimi lokaci ɗaya tana faɗin" Dilla behave you self." Duk da bai ji abin da ta faɗa ba amman ai ya ga bakinta na motsi, yana jin sau ɗaya ya taɓa ganin Rukky amman yana ganinta sai ya ganeta ita ce wannan kawar ta Mimi wacce ba ta masa ba munafuka ce, illau ga shi yau ya ga shaida sai wani kyfta ido ta ke yi alamun ba ta da gaskiya. Shi kuma cikin yanayin takunsa na masu karfi da Kuzari ya ƙarisa gabansu duka hannayensa zube a cikin aljihun wandonsa.   Sai da ya zo gaban Mimi Sannan ya tsaya ya kuma saka hannu ya ɗan daga gularsa sama yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa ya juya yana kallon megadi na zaune a mazauninsa da radion sa ya na ji. Sannan ya juya ya na kallon Mimi Sai dai ba fara'a ko kaɗan a fuskarsa sannan Rukky dake wajen ko kallonta ma bai yi ba, sai ma ya yi kamar bai san da wanzuwar a wajen ba. "Haka kike fitowa waje ba hijabi ba mayafi Mimi.?   Haka ya fara faɗa lokaci ɗaya yana ƙara daƙune fuskarsa kamar wanda aka faɗa masa wani mummunan saƙo, Mimi ta kalli Rukky itama ta kalleta a ranta dai sai da ta ce mai hali baya fasa halinsa amman a fili sai ta haɗe rai itama ta juyar da fuska tana faɗin" Wa ya gaya maka na dawo? sannan me yasa ka zo ba Sanarwa? Ta faɗa tana wani masa jijjigan jiki lokaci ɗaya tana taɓo hannayen Rukky wacce ta dukar da kanta ta ƙasa ta kasa  ɗagowa saboda Aji ya yi mata ƙwarjini ba ta ɗauka za ta kasa haɗa ido da Ajin in suka haɗu gaba da gaba ba. "Alhaji ne ya gaya min kin dawo. Sannan domin zan zo wajen matata ai ba na bukatar ɗan saƙo."   Haka ya ce mata yana kallonta cikin ƙara nazarinta da sauri ta kallesa kafin ta ce" Wani Alhajin? Kafin ya samu damar magana ta zaro ido tana faɗin" Wai Daddy ne Alhaji? Ba za ka iya kiransa da sunan Daddy ba kenan? Ta faɗa cikin masa wani kallon kasa ƙasa, cikin mamakinta ya ce"Daddy kuma? To ai kinsan ni a gidan da aka haifeni da in da na taso, Inna da Baba muke cewa, in kin ji mun ce Alhaji alamamun girmamawa ne." Ita kanta ba ta san ta masa wannan kallon ba sai da ta ga ya yi mirmishi wanda tun zuwansa wajen bai yi ba sannan ya ce"To na bari, Daddy ba shike ban ba? Sai ta gyaɗa masa kai, kawai sai ya gyara tsayuwa a ransa ya na faɗin"Rigimammiya kawai." Rukky ce ta ga kamar Har Mimin ta manta da ita. Sai ta matsa gefe tana faɗin" Mimi zan tafi, yamma ta yi" Ta gama faɗa lokaci ɗaya tana duba agogon fatan dake tsitsiyan hannunta na hagu sai a lokacin Mimi ta tuna da ita domin har ga Allah in tana gaban Aji mantawa take yi da kowa da komai ciki har da ita kanta ma. "Aji ga ƙawata Rukkaya, Rukky ga Aji ku gaisa."   Mimi ta faɗa cikin Mirmishi tana kallon su duka, Aji ya yi shuru yi ya yi ma kamar bai ji ba sai can ya ce"OH na ganta." Daga haka ya juyar da kansa yana kallon wani ɓarayin Rukky ta watsa ma Mimi wani kallo ita kuma tana faman roƙonta da hannu a kan ta gaishe shi abin da ba su sani ba duk yana kallonsu ta gefen Ido, abin da ya bashi mamaki ita yanzu ƙawar Fatima Jira take yi ya gaisheta? Amman yarinyar ba ta da hankali ya fara tunanin haka. "ina yini"   Haka Rukky ta faɗa Kamar ba ta so. To daman dole Mimi ta saka ta, sai da ya nishaɗu sannan ya juya yana kallonta lokaci ɗaya yana faɗin" Barka da ƴamma" Sannan sai ya juya yana kallon Mimi kafin ya ce"Na ɗauka tana jiran na gaisheta ne." Sai Rukky ta ji kunya ya kamata da sauri ta ce"A'a na bari ku gama gaisawa ne." "Gaisawa? da wa? Ba gaisuwa muke yi ba ko kin ji sanda ta gaishe ni? Sai Rukky ta kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da faɗin" Ko ita ƙawar taki ba ta isa ta zauna in gaisheta ba, koda nake auranta ba ta isa ba."   Daga Rukky har Mimi kai suka jinjina, kafin Rukky ta ce"Ta cancanci ka gaisheta mana, ka fa ba ma ƙawata wahala." Ta faɗa tana yar dariya mirmishin gefen baki ya yi kafin ya ce" Ita kaɗai?  ba ta gaya miki nima ta ba ni wahala ba? Mun ba ma juna wahala shi ne gaskiyan magana." Ya faɗa yana kallon Mimi ita kuma sai ta harareshi ta na tura masa baki har sai da ya yi yar dariya Rukky na tsaye tana kallon Ikon Allah a tunaninta Mimi ba za ta sakar masa fuska a zuwan farko amman kalli abin da take yi. Shi kuma agogon hannunsa ya duba kafin ya kalli Mimi ya na faɗin" Kina  da mintina goma,ki sallami baƙuwar ki, ina son mgana dake." Yadda ya yi maganar cikin ba da umarni ya sa Mimi ba ta ga damar masa musu ba sai ta ce ya shiga falo ya jira ta bari ta taka ma Rukky kamar zai ce rakiyar ba ta isa haka nan ba sai ya fasa bai shiga cikin gidan ba ya tsaya nan yana jiranta daga in da yake suka matsa gaba kaɗan yana gani Rukky na ta magana Mimi na marairaicewa kamar hakuri take ba ta shi fa baya raba ɗayan biyu duk abin da Mimi ta aikata ba tunaninta ba ne tunanin wannan ƙawar ta ta ce, kuma daman tana da fuska da yanayi na munafukai.   Dole Mimi ta sallami Rukky ganin uban gayyar ya kasa ya tsare ta na fita daga get ɗin Mimi ta dawo wajensa tana faɗin" Ba ka ciki ba ? Kai tsaye ya ce"Ke nake jira, sannan kada ki ƙara fitowa a haka ba ki saka babban mayafi ko hijabi ba." Baki buɗe ta ce" A cikin gidan? Kansa ya ɗauke kafin ya ce"E na dai gaya miki." Yanayin yadda ya haɗe rai ne ya sa dole ta yi shuru tana gaba yana Binta a baya har zuwa falon gidan Hajiya ta ce ya zauna sai ya samu kujera mai zaman mutum biyu ya zauna ita kuma ta ce tana zuwa. Sai ta juya tana tafiya ya bi ta da kallo yana haɗiyan miyau har ta ɗauke ma ganinsa Ajiyar zuciya ya sauke dole ma ya ijiye duk makaman yaƙin sa matarsa yake bukata cikin lokaci.   Ɗakin Hajiya ta fara shiga ta isketa tare da Baaba Uwani suna mgana ta gaya mata zuwan Aji sai ta koma ɗakinta domin ta gyara fuskarta, ita kuma Hajiya ta fito tare da Baaba Uwani ta gaishe shi ya amsa cikin yanayinsa sannan ta shiga kitchen ta kawo masa ruwa da lemu, Hajiya kuma har kasa ya sauka ya gaisheta ta na masa tsiyan ba ta ce in Binta ba ta son auran ita a zo a yi da ita ba kansa na ƙasa ya ce shikeman in ta ƙi komawa sai ya zo kawai su daidaita Hajiya na ta dariya bayan tambayan su Meri ya ce tana gaisheta kai tsaye Hajiya ta ce"Ai ka gaya mata na ce na yi fushi, tunda abun nan ya faru ban ganta ba sannan ba ta kirani ba." Mirmishi kawai ya yi ba tare da yayi wata magana ba, nan Hajiya ta bar shi ta shige ciki ta je ta na yi ma Binta tsiyar ta shanya shi, ita kuma har kaya ta sauya daga baya sai ta fasa domin zai ɗauka ta hakura ne tunda har da kwalliya sai ta maida wanda ta cire har da saka uban hijabi sanda ta dawo falon yana zaune ya gama shan ruwa kenan kujeran dake kallonsa ta zauna shi kuma ya na kallonta daman tun shigowarta. Cikin mamaki ya ce"Wannan hijabin fa?  fita za ki yi ne?. Kai tsaye ta ce"A'a ba kai ka ce na riƙa saka hijabi ko a cikin gida ba ne?   Dariya ta ba shi har sai da ya dara sannan ya kaɗa kai kafin ya ce"Kin yi nesa da ni, ta ya ya za ki iya jin abin da zan faɗa? Ki matso nan domin ba zan ɗaga murya ba." Ya faɗa yana nuna mata kujeren dake gefensa mai zaman mutmn uku ba musu ta miƙe ta koma nan ta zauna sai da suka ɗauki wani lokaci kowa na sake saƙe sannan Aji ya yunƙura kaɗan yana faɗin"Ina fatan hutun da kika yi ya ishe ki?. Kallon bangane ba ta yi masa sai ya cigaba da faɗin" Na san ban kyauta ba. Mu manta abin da ya faru a baya Mimi ki dawo gare ni domin na nuna miki komai ya wuce." Kai tsaye ta kalle shi domin ta ga da gaske yake yi sai kawai ta kauda kai kafin ta ce"Ni fa na ɗauka takardan saki na ka kawo min." "Subhanallah, ki daina wannan zencen ni ban aureki domin na sake ki ba" "To ana dole ne? tun da  ka ce ba ka sona? Sannan ba za ka iya daraja iyayena ka manta abin da ya faru saboda ni ba, ni ma kuma ban ga laifina domin na ce ba zan cigaba da zama da kai ba."   Yadda take mganar da alamun abin na taso mata ne domin kamar za ta yi kuka,  huci ya fitar daga bakinsa kafin ya ce" ɓacin rai ne ya sa duk na faɗi wasu mganganun, ki yi hakuri." Mamakin yadda ya yi saurin laushi ta yi sai ta kalle shi shima ita yake kallon cikin irin kallon nan mai kassara oafiyan jikin ƴa mace, ita ta yi saurin kauda kanta kafin ta ce" Wasu mganganun?  kamar su wanne kenan? Bakinsa ya ciza leɓen kasa kafin ya ce"Na ƙaryata kaina Mimi, ke sai ki yarda cewa ba na son ki? Ya faɗa cikin wani sauti ba ta son kallonsa Saboda kada ya ga rauninta kanta na gefe ta ce" Na yarda tunda da bakin ka ka faɗamin alfarman Hajiya da Mommy nake ci."   Bai san ya aka yi ba shi dai kawai ya gansa zaune kusa da Mimi kafaɗanta na dukan Kafadansa haka itama taji mutum zaune gefenta kafin ta samu zarafin mgana ta ji kawai ya yi mata wani irin riƙo mai karfi lokaci ɗaya yana faɗin" Shike nan kuma sai ki yarda da duk abin da na ce? Ke ba ki san bacin rai ba? Raina ne ya ɓaci shi ya sa na faɗi haka." Ya faɗa cikin sanyin murya ta ɗago tana kallonsa shima ita ya ke kallo,ta buɗe baki za ta yi mgana kawai ya saka hannunsa samman bakin yana faɗin" Shiii." Sannan ya hura mata iskar hucin zafin ɓakinsa kusan suman zaune ta yi kafin ta dawo hayyacinta ya yi mata magana cikin raɗa raɗa kamar wanda ba ya so a ji. "Ke ce ta farko, ke ce ta biyu ke ce har ta uku da ta huɗu. Sannan ke ce a baya da shekaranjiya  yau da gobe  har da jibi da gata, ke na zaɓa ke ma kinsan ba zan iya daina son ki ba Fatima." Ya faɗa ya na kureta da kallonsa, kasa jurewa ta yi sai ta kwace kafaɗanta ta matsa baya tana sauke numfashi. "Allah da gaske nake yi, ba ki yarda ba ne?   Numfashi ta ja ta sauke kafin ta ce" In hakane kana sona? Me ya sa da na ce zan tafi ba ka hana ni ba? Cewa fa ka yi wai is better na tafin" Cikin dafe kansa ya ce"Mimi. Ke wai ba ki san gatse ba ne? Ni fa gatse na yi miki ban taɓa tunani  za ki yi fushi ki taho gida ba wallahi" Wata harara ta yi masa kafin ta ce"Ai dole na zauna tunda ni ba ni da zuciya sannan ban san ciwon kaina ba." Da sauri ya ɗaga hannayensa sama lokaci ɗaya yana faɗin"ba haka na ke nufi ba, ni dai ki yi hakuri ki saka ranar da za ki koma don Allah." Shuru ta yi masa ganin haka ya sa ya matso kusa da ita, ba ta sani ba sai jin maganarsa kawai ta yi a kusa da ita. "Kin ji My Mimi? Komai ya wuce ko?   Da Sauri ta matsa can karshen kujera kafin ta ce"A a. Cikin mamaki ya ce"To me ya rage? Na amsa duka laifukana na kuma ba da haƙuri." "Akwai saura? Haka ta faɗa ta na kallonsa shima kai Tsayen ya ce"Me ya yi saura kuma? Kai tsaye ta gyara zama tana faɗin" Matsayin Mahaifina a wajen ka nake son sani yanzu, domin ba zan cigaba da zama da kai kana kiransa da azz.." "Ya isa. Haba Mimi na ce fa na yi nadama ki yi hakuri mana."   Ya katseta da sauri domin yana jin kunyar sunan da ya kira mahaifinta da shi , ita kuma sai kuka cikin yar shagwaɓa ta ce" Kai fa ka kira shi da hakan" Da sauri ya ce"Ai ban yi gaddama ba, na tuba bazan kara ba kin ji ko? Sai ta ɗago tana kallonshi Idanuwanta duk hawaye kafin ta ce"Ka na nufin ka yafe duk abin da ya faru.? Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Eh na yafe masa, na gane riƙo ba shi da amfani, na yi miki alkwarin ba zan ƙara duban ki da wannan abun ba. Sannan zan ɗauke shi a matsayin kaddara in sha Allahu." Cikin jin daɗi ta ce"Da gaske kake yi? Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" In sha Allahu, Allah ya jiƙan Abi ya sa ya huta." Mamaki ya kama Mimi ba ta san lokacin da ta fara dariya ba ga hawaye lokaci ɗaya cikin girgiza kai ya ce"Kin ji daɗi? Ina fatan komai ya wuce? Ta na goge hawayenta ta ce" Eh, tunda ka yarda ka yi kuskuren  kuma ka amsa za ka gyara, shike nan nima na haƙura." Cikin jin daɗi ya ce"Nago de, to goge hawayen shagwaɓɓiya mai kuka da dariya kawai." Hararansa ta yi ba ta yi mgana dukkansu zukatansu ya cika da farinciki. "Yaushe za ki koma? Yau ko gobe?    Kallonsa ta yi a karkace kafin ta ce"Ko zan koma sai ka amince da wasu sharuɗɗai na nima, a baya kai ka saka naka nima a yanzu lokacina ne ma gindaya maka naka."   Baki sake ya ce"Topha, ka ji wata sabuwa." Tana murgaɗa masa baki ta ce"Ba dole, in ba ka amince ba sai n ace na fasa komawa." Da sauri ya ce" WANE AJI? shi ɗin banza zayyano su ki kaddara ma duka sun tabbata." Tana dariya ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Komawa na tare da wannan sharuɗɗan guda ɗaya in ka tsallake ba zan koma ba." Tagumi ya yi kafin ya ce"Ya na iya? Tun da ɓarawo ya shiga hannun mata ai ya shiga uku." Yadda ya yi mganar ne ya sa ta ƙyalkyalce da dariya  Shi kuma ya na kallonta da Mirmishi ta juya kenan sai ya kira sunanta. "Mimi.."   Sai ta juyo tana kallonsa sai kawai yace"Amman dai mganar kin samu ba da gaske ba ne ko? Tana ɗage masa gira ta ce" Da gaske ne mana, in baka amince da sharuɗdana ba da shi za'a yi." Nan da nan ya haɗe rai yana faɗin" Kin san dai kina da ma tarin laifi wajen Ubangiji, kin yi ta zuwa garuruwa ba tare da izinina ba, in kuma ban yafe ba Allah ba ki sha ba." Kugu ta riƙe lokaci ɗaya da  bakin tana faɗin "Ba ka yafe ba ka ce! To ai da izinin ka na je ko'ina tun da kai ka ce na je duk in da nake so." Zai yi mgana ta yi saurin cewa"Ka yafe ko ba ka yafe ba? Yanayin yadda ta tsare shi da ido ya sa ya koma ya jingina da kujera kafin ya ce"Wannan shi ne a dake ka, sannan a hana ka kuka, ya na iya?  Na yafe." Ya faɗa kamar ba ya so, Mimi ta saka masa dariya ta juya tana wani irin taku zuwa Koridin da zai sada ta da ɗakunan su. Shi kuma ta barshi da bin ta da kallo kamar wani sauna kira mana shashaaha.   Ta na shiga ɗakinta ta buɗe wata ƙaramar jakarta dake rataye ta ɗauko biro da takarda a cikin wani Memo ta yanka na bikin Biban su Dukky ne. Da farko ba wannan zencen sharuɗɗan amman yanzu ta ji ta na so shima ta jarabasa, kai tsaye ta fara rubutu bayan ta zauna a saman gado, wasa dai da ta kusa cika takardan nan da rubutu sannan ta ninke ta, ta koma falon ta miƙama Aji lokaçi ɗaya tana faɗin"Sai ka koma gida sannan ka buɗe ka karanta a tsanake, in ka amince sai ka yi ticking ɗin duka sannan ka saka hannu a ƙasa, nima sai ka dawo min da takardan na saka hannu, sannan saɓa alkwarin mu dai dai yake da sunan ba zan koma ba." Karɓan tarkadan ya yi lokaci ɗaya yana faɗin" Kamar Interviuw ɗin ɗaukan aiki? Hararansa ta yi da sauri ya ce"Sorry Matas" Ita kuma sai ta koma tana wani hura hanci bai daɗe ba ya ce zai tafi saboda bayan mangariba zai gana da Coach ɗin su ya ce yana son ganin shi, ko Hajiya bai tsaya ma sallama ba ya ce Mimi ta gaya mata da zai tafi ko rakiya ba ta yi masa ba sai da ya ce"Matas ba rakiya?. Kai tsaye ta ce"Sai ka cike sharudɗanmu tukkunna" Sai ya jinjima kai kawai ba tare da ya yi magana ba.   Shi dai yana mamakin me ta rubuta? Me kuma take so? Ya san dai ba za ta ce kuɗi ba, Saboda zaman da za su yi da Caach ya sa bai samu damar duba takardan lokacin da ya koma ba.Sai wajen ɗaya suka gama Meeting ɗin ga shi ya gaji ga shi ya na jin yunwa amman hakanan ya kwanta bai duba takardan ba, da Safe kuma yana cikin barci wayar Inna ya ta da shi ta ce ya fita bakin Camp ɗinsu Walida ma jiran shi. Ya yi ta mamakin lafiya riga ya saka ya fita ko da ya je ma ba kowa ya na shirin kiran Inna sai ga Walida ta sauka daga mashin, Da kwandon abinci riƙe rike sai da ya yi hawaye Allah sarki uwa. Cikin ɗan faɗa ya kalli Walida yana faɗin"Inna ta ba ki wahala?  ba shago za ki tafi ba? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce"Eh, ita ta ce na biya na kawo maka.". Sai ya karɓa yana yi ma Inna fatan Aljjana acikin ransa mai mashin ɗin bai tafi ba shi ya tsaya ta hau zai kai ta in da ta ke koyon Computer bai fito da ko wallet ɗinsa ba sannan ba kuɗi a hannunsa amman ya ce zai shiga gidan anjuma.   Yana komawa ɗakinsa na cikin Camp ɗin ana Sake kiran shi yana dubawa sai ya ga Baba, sai bai ɗauka ba sai da ta katse sannan ya bi bayan kiran bayan sun gaisa, daya ke sun kwana biyu ba su haɗu ba shi fa tun barowar Inna wannan gidan anguwam bai ƙara komawa ba, ko kan maganar Mariya a camp Auwalu ya zo ya same shi suka yi mganar, kiran Baban ma saboda haka ne yana gaya masa waliyyan yaron sun zo suna bukatar a saka musu Shekara mansoor ya ce a saka a hakan ai kamar gobe ne, kuma tunda an yi bincike yaron da sana'arsa ɗinkin maza da mata yake yi kuma ba shi da wata matsala. Sun tattauna kan maganar sannan suka yi sallama ya zauna ya ci wainar da Inna ta aiko masa sannan ya sha tea ya haɗa da soyayyen buredi da ƙwai.   Yana gama ci ya natsa kawai sai ya koma ya kwanta ya yi ta barci tun yau ba su da Traning sai gobe yana ta jin hayaniyarsu sun fita can haraba amman bai iya ta shi ba, wayarsa ma kashe ta ya yi sai gabda azahar ya ta shi ya yi wanka lokacin har sun yi sallah tunda suna da masallaci a cikin Camp ɗin sai ya yi na shi a cikin ɗaki sannan ya kunna wayarsa. Ya duba sakonni masu muhimmaci, har da sakon Mu'azzam daman ya faɗa masa zai je wajen Mimi a jiyan, sai a lokacin ya tuna da takardanta da sauri ya miƙe ya isa ga ma sagalan kayansa ya zura hannu a aljihun wandon da ya sa jiya ya ɗauko takardan ya zo ya zauna a saman ƙaramin gadon dake ɗakin ya warware ya fara karantawa.. *SHARUƊƊAN KOMAWA TA GIDAN AJI.* 1. BA ZAN KOMA BA SAI NA SAKE YIN WANI TARON BIKIN. 2. SAI KA HAƊAMIN LEFE, DOMIN BAN ƊAUKE MAKA BA. 3.SANNAN ZA KA RIƘA ZUWA TAƊI, DUK BAYAN BAYAN KWANA UKU, DA KUMA YAWAN TURAMIN SAƘONNIN SOYAYYA.. 4. NA ƘARSHE SHI NE SAI KA GYARA MU'AMALANKA DA KOWA CIKI HAR DA SASANTAWA DA ABOKAN KA, DA MAI DA DANGINKA DANGINA DA MAIDA DANGINA DANGINKA." "Amincewar ka ga sharuɗdana sune tikitin komawata gidan ka."   A ƙasa sai ta rubuta sunanta Fatima Kabir Dabo, shima daga gefe sai ta rubuta sunan shi Manaoor Ibrahim aji, sannan daga kasa ga wajen saka hannu da kawanan wata.   Ya maimaita takardan ya fi sau goma amman ya rasa wani yarinta ne ke damun Mimi? Wai sai ta sake sabon taro ? Shi na lefen ma bai dame shi ba, sannan wai ya riƙa zuwa taɗi sai kace mara aikin yi? Ga tura saƙonin soyayya wannan ai ga na masa azaba kawai za ta yi ina ga ya ga lokacin wannan shirmen tab, ko taɓa takardan bai yi ba ya ninke ta ya ijiye. Sauran wainarsa na safe ya ci ya sha ruwa sannan ya fita da kwando waje, Su Zinder ya gani ya ba su ya ce su cinye su wanke kwanon, suka karɓa suna mai faɗin" Thank you Captain." Shi kuma sai ya koma ɗaki yana duba takardun da Coach ya ba shi jiya sai wajen uku da Rabi ya ta shi ya yi wanka ya sauya kaya lokacin har sun wanko kwanukan sun dawo da shi,  azumi ke gabatowa akwai tunanin ba su hutu zuwa bayan sallah.   A masallacin cikin Camp ɗin ya yi sallar la'asar sannan ya kwashi kwandon da aka kawo masa abinci sai gidan Inna, nan kuma ya iske ba ta nan Bintu ce kawai da Walida a gidan wei ta je can anguwam Arawa matar Saddiqu ta haihu. Bai yi mamaki ba ya san halin Inna daman ba za ta zauna ba, bai tsaya ba ya ijiye kwadon abincin ya ce bari ya je ya dawo ya na fita suka fara gulmansa domin Hibba ta kyankyansa musu Su Yaya Mansoor ana ta zuwa biko. Har zuwan Mimi gidanta na kano sai da ta gaya musu.   Yana fita daga gidan Inna sai gidan Hajiya yana Hanya ya Kira Mimi ya ce ga shi nan zuwa, kafin ya kariso ta ci kwalliyarta cikin dogowar rigar atamfa ta kuma kashe ɗauri tana tashin kamshi yau kam ko mayafin ba ta saka ba. Sannan ta kawo masa abinci Jallop din shinkafa da nama ya ce ita ta dafa tace a'a sai ya ce sai ranar da ta yi masa girki sai ya ci kai tsaye ta ce"To in ka fara zuwa taɗi zam riƙa yi maka girki " Bai yi mgana ba yana kallonta kenan da gaske take yi, shima ya sha kwalliyarsa yau har da hula tunda manya kaya ya saka ta kalleshi tana dage masa gira lokaci ɗaya tana faɗin"Ehye, an sha kyau za'a zo taɗi wajen ƴar budurwa." Ta faɗa tana masa wani irin mirmishi, Kallonta  yake yi ko kiftawa ba ya yi, da gaske take yi kenan? Sai kawai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardan harda ma bironsa ya zo, a kasan Cafet ya sauko sannan ya kalli Mimi lokaci ɗaya yana faɗin" Matso ki gani." Ba nusu ta matso har kansu na haɗuwa waje ɗaya.   Lambar farko ta ga ya tsaya sannan ya kalleta kafin ya ce"Ke yanzu ban da rigima ina ke ina ƙara yin wani biki? Kiran bidi'a ko ɓata lokaci? Ko sake ɗaura mana aure za'ayi ba bikin da za mu yi ballantana haka kawai daga kin yi yaji kuma sai ki ce sai an yi biki. Gaskiya a'a ban yarda da wannan ba." Kawai sai ya saka biro ya soke ta kallesa cikin mamaki ba ta samu zarafin mgana ba ya je ga na biyu ya na faɗin" Nawa kike bukata? Ya faɗa sannan ya yi ticking lokaci ɗaya ya zura hannu a gaban aljihun rigarsa ya ɗauko Atm ɗinsa na bankin albashinsa, ya sauke a gabanta lokaci ɗaya yana faɗin" Daga naira ɗaya har milyan ɗari za ki iya amfani da shi wajen haɗa abin da kike so." Sai kawai ya gangara na uku ko ba ta damar magana bai yi ba.   Ya nuna rubutun ta kafin ya ɗago yana kallonta lokaci ɗaya yana faɗin"Haba Mimi yanzu da girman ki kike wani zencen taɗi? Haba ko yara kanana yanzu sun daina wannan ɓata lokacin mq? Me ye taɗi in ba a zo a samu fahintar juna ba? Ni kuma d ke tun muna yara zukatan mu suka samu. daidaito ba amfanin da aueren mu, mu zo muna wani abun ɓata lokaci. Sannan mganar wai saƙƙonin soyayya haba Fatima ni ina na ga wannan lokacin? Kin san fa yanayin aikina  ni fa mutun ne kamar kowa ba zan miki karyan abin da ba zan iya ba,  Mijin Novel ne ke tsara mace da kalaman Soyayya, ni kuma mijin zahiri ne, in Soyayya kike so tsantsan na gaskiya zan nuna miki ita a kan gadon mu na Sunna in sha Allahu" Ya faɗa ya na kallonta ƙasa ƙasa, nakwa nakwa ta yi da fuska kamar za ta yi kuka sai ya saka biron hannunsa ya lakace mata hanci kafin yana faɗin" Rigimammiya."   Cigaba da duba takardan ya yi zuwa lambar karshe sai ta ga ya yi ticking lokaci daya yana faɗin"Wannan ba matsala, Abokaina kada ki damu zan neme su mu sansanta duk da ni banga laifin da na yi musu ba, mganar dangina kuma daman ko Inna na ga alamun  ta fi son ki a kaina. Sai mganar naki dangin ki suma in sha Allahu zan saki da su mu zama ɗaya saboda ina son ki, kuma abin d mata take so shi miji ya ke so? Ko ba haka ba Mimin Aji?. Ya faɗa ya na kallonta, kawai sai ya ga ta koma ta zauna a gabansa ta harɗe hannayenta saman kirjinta tana wani ɓata rai sai shima ya miƙe ya zauna yana faɗin"To kuma yanzu menene laifina! Na yi miki fa duka bayani" Kawai sai ta fara mgana cikin shagwaɓa"Ni dai wlh ko ɗaya ba zan soke ba, kuma ai ba gayyata zan yi ba kawai dai kawayena da Yan'uwana mganar taɗi kuma ni ko? Ba za ka rika zuwa kana ganina ba ko? Yadda ta yi mganar ne ya sa bai san lokacin da ya ce"Na ji shike nan sai kuma me? Har ta na jan hanci kafin ta ce" Ni dai in ba ka amince ba, sai na ce na fasa komawa." Har da kukanta fa, gefe kawai ya koma ya na kallonta kafin ya ce"Da girman ki, Mimi ki yi ta shagwaɓa?   Sai ta ƙara narkewa tana matsan hawaye, Har ta na cewa shike nan tunda baya sonta ba zai mata abin da take so ba. Ya na jin haka ya ƙarisa gareta ya riƙo hannuwanta yana faɗin" Sorry, shike nan na ji ki daina kuka" Da sauri ta ce"To ka amince? kai ya gyaɗa kafin ya ce"To ya zan yi? Tunda na auri yar gata shagwaɓɓiya." Dariya ta yi masa sannan ta kwantar da kanta saman kirjinsa sannan ta jawo takardan ta saka hannu ta miƙa masa ya karɓa yana faɗin"Kamar auran coci, ni fa ba guduwa zan yi ba." Tana dariya ta ce"Eh na ji dai." Haka nan ta saka shi ya saka hannu sannan ta ɗauki takardan tana faɗin" In na fara zuwa aiki zan ba da a yi mana photocopy, na ba ka naka nima na ɗauki nawa." Sai ya yi fuska kafin ya ce"Ba na so, ki riƙe a hannun ki kawai"   Dariya ta fara ta na son kallon fuskarsa shi kuma ya haɗe rai ya kauda kai.Sai bin shi ta ke yi, daga karshe ma ture kanta ya yi daga kafaɗansa har ya na juya mata baya, ta shi ta yi ta koma gabansa ta na jan kumatunsa lokaci ɗaya tana faɗin"Ehem Ehem, kamo shi nan kamo shi nan." Har matse masa fuska ta yi sai da ya yi dariya kawai sai ji ta yi ya riƙe mata hannuwana sannan ya rumgumeta yana sauke numfaahi, itama sai ta yi lakwas tana shakan ƙamshin turarensa.   "In na zo taɗin me za ki riƙa bani?   Haka ya faɗa cikin dishewar murya itama a hankali ta ce"Duk abin da kake so? Ɗagota ya yi yana kallonta kafin ya ce"Komai fa kika ce? Sai ta ɗaga masa kai, sai kawai ta ji ya Sumbaci bakinta kafin ya ce"Har wannan? Sai ta fara waige waige tana zaro ido da sauri ta matsa daga jikinsa tana faɗin"No." Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ai ba ki isa ba kin yi alkwari yarinya." Tana tura baki ta ce"Ni ban yi ba, ba wannan a sharuɗdan mu." Kansa ya shafa kafin ya ce" Wa ya ga ya miki su Nasir na gaba da ni? Dariya ma ya bata cikin mamakinsa ta ce"Au su ke ma gaba da kai? Cikin basarwa yace"To ni me na yi musu? Suma dai da shisshigi ina ruwan su da shiga tsakanin mata da mijinta Ehe" Mimi ta dage masa gira kafin ta ce"Kai dai." Da sauri ya ce"Zan neme su amman ba hakuri zan ba su ba." Sai ta kaɗa kai tana mirmishi shi kuma sai ya duba agogon hannunsa ya ga an kusa mangariba da sauri ya ce" Maganar gida matso mu yi mgana." Ba musu ta matso kusa da shi, ya kalleta kafin ya ce"Ba ni da gida a ƙasa yanzu. Gini kike so a yi miki ko kuma a siya gidan kawai.? Kai tsaye ta ce"Ina gidan ka?. Sai ta nuna kamar ba ta sani ba hararanta ya yi kafin ya ce"Ban sani ba, shi wanda ya faɗa miki mun samu matsala da su Nasir bai faɗa miki Inna na ba ma gidan  ba?   Dariya tayi har tana rufe bak.  Mirmihi ya yi kafin yace" Kinga azumi na matsowa zuwa bayan sallah nake son ganin ki a gidana ya ya tsarin gidan ki, ya ki ke so ya kasance? Sai kawai ta lamgwaɓar da kai ta ce" Ni ba ni da wani zaɓi tsarin da kake so shi nake so." Kai tsaye ya ce"Shike nan daman ina da wani fili sai kawai a gina tunda ina da kuɗi ginin zai kamallah nan da  bayan sallah zan yi mgana da mai zane sannan zan nemi Auwalu." Da haka suka tsaya kan mganar. Ana gab da kiran sallah ya tafi ta yi ta yi ya karɓi Atm ɗin sa, ya ce ta riƙe a hannunta ita kuma ta ce ko ta riƙe tare za su riƙa fita siyayya ya fahimci dai ya kawo kansa. Shi ya sa Mimi ta ke gungurashi duk yadda ta so. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3010* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. *BAYAN KWANA BIYU.* Tun bayan sharuɗɗan da Mimi ta saka tsakaninta da Aji ya zama duk ya takura, ya fahimci Mimi so take yi ta maida shi kamar wani sharukhan ɗin Kasar India, to da girmansa da komai ace sai ya koma yana soyayya kamar wani yaro? Ya tabbata yanzu matasa na sun daina wannan soyayyar domin duk yaudara ce, masu yin ta ma yanzu mayaudaran sun fi yawa. Ko bai kirata ba sai ta kira shi ta ce bai turo mata kalaman soyayya ba. Sai ya ce zai tura mata ya rasa shi ina ma zai samu kalaman Soyayya ya manta da wannan tun a zamanin baya. Dole dai ƙanwar naƙi ya shiga Playstore ya ɗauko Application na lalaman soyayya In hausa da turanci, bai ma tsayawa karantawa da safe sai ya yi mata copying da forwarding ya tura mata haka da rana in ya tuna haka da daddare ma, amman duk da haka sai da ta gane domin ce masa ta yi. " Kalaman na ka ba emotion a ciki Aji, kamar dai wai da gasken ba ka sona." Ya rasa da wani yare zai mata wannan bayanin da fahimta ba ruwan ina son ki da wasu kalamai, kawai dai ta ga soyayya aikace ina ruwanta da wani wai sai ya riƙa yi mata kalamai?. Da ya ga ba za ta gane ba sai ya ƙyaleta da ta matsa masa sai ya ce"Mimi ni fa ban iya duk wannan karyan ba, to ƙarya mana soyayya yanzu ai duk ta zama shirme ki buga ma misali da kan mu, ina son ki kina sona muka yi aure amman ki duba yadda matsaloli suka zagayen mu da ya saka sai da kika yi Yaji, to duk ina wannan son da muke ma juna? Zaman aure zaman haƙuri ne kawai da sadaukarwa, ina son ki zan iya zama dake har abada sauyin fuska ko wani nakasu ba za su shafi soyayyata ba ko da Sauyin hallaya ne sai dai zan yi koƙarin cewa ki gyara amman wani ina sonki na yi kewarki duk magana ce ta fatar baki ya kamata ki gane wanman Fatima." A waya ne ya ke gaya mata haka sai da ta tura masa baki kamar ya na ganinta kafin ta ce" Wai na yi yaji? Haka fa ka ke cewa yaji" Kai tsaye ya ce" To ba yajin kuke cewa ba? Ko barkonu zan ce." Haushi ya sa ta kashe wayarta ta barshi ya na ta mirmishi, ya san ba za ta hakura ba da daddare da ya zo kwanciya ya kira ta nan ta ɗauka tana ta kumbure kumbure t sai ya nuna kamar bai gane ba sai ya ce"Gobe zan zo taɗi me za ki tanadar min? Ita kuma sai tace"Gobe zan koma aiki." Ɗan bata rai ya yi kafin ya ce"Tunda ba acan za ki kwana ba da sauƙi, zan zo bayan sallar Isha'i tunda sai na shiga na gaida inna." Ganin kamar bai gane tana fushi da shi ba ne ya sa ta ce"Ina fushi da kai. Amman sai na ga kamar ka basar ba ka gane ba" Ya na shafa kasan gemunsa ya ce" Au wai fushi kike yi? To wannan fushin na ki ba na komai ba ne sai na shagwaɓa kuma lallashin ki ai sai ina kusa, ki anada fushin har sai na zo kin ji ko matas? Har gobe dai Aji ba zai sauya ba in an yi gabas shi sai ya yi yamma. Dole ta saki ranta suka cigaba da waya sai da ta fara hamma sai ya ce ta je ta kwanta saboda fita aiki gobe. "Sai da safe Mijina, I love u." Mirmishi ya yi mata kamar ta na ganin shi kafin ya ce"Sai da safe Matas, ki yi shigar nutumci gobe, kada ki manta ke matar aure ce matar auran ma matar Mansoor Aji." Tana yar dariya ta ce"Yes Sir.." "I love u." Haka ya faɗa da sauri ta zaro ido kafin ta yi mgana ya yi saurin katse wayar ya barta da shauki. Ranar barcinta cikin natsuwa ta yi shi, har ta na makara sai shi ne ya ta she ta da asuba kamar ya sani ya ce ya ji a jikinsa barci ya kwasheta ta kasa tashi. A gurguje ta yi sallar asuba da azakar sannan ta yi wanka ta shirya ta yi shigar lafaya ta yi kyau sosai tunda daman can ita mai kyau ce. Motar ta tun shekaranjiya ta kira Bakanikenta ya zo ya tafi da ita da yake ta daɗe ba ta yi amfani da motar ta, ya yi ma ta juye da service sannan jiya ya dawo mata da shi tana so ma ta sauya mota da kuɗin gadon ta, amman kuma ba ta so Aji ya ga kamar ta na nuna masa kuɗi amman tuni Khadi ta sauya ta ta motar. Sannan an riga an gama ginin masallatan nan da bohol ɗin ruwa a wasu anguwannin dake cikin garin kano sai dai fatan Allah ya kai ladan Kabarin Abi, bayan ta shirya ta ɗauki kanta hoto ta tura ma Aji sannan ta fita zuwa ɗakin Hajiya su ka gaisa Hajiya ta ga sai faman nishaɗi take yi cikin zolaya ta ce"Binta dai za'ayi kome ko? Daman ance kome ai ya fi sabon aure daɗi ko? Mimi ta rufe fuska tana dariya kafin ta ce"Kai Hajiya ta" Hajiya na ƴar dariya ta ce"Ai na gano ki, tunda Mansoor ya zo ranar nan kike cikin nishaɗi, to gaya min yaushe ne komen na mu.? Mimi ta zauna kusa da ita lokaci ɗaya tana sagala hannunta saman Kafaɗan Hajiya tana faɗin" Saboda ginin da za'ayi ya ce sai bayan sallah lokacin duk na gama sauran shirye shiryena." Hajiya na Mirmishi ta ce"Ya yi kyau, To gidan shi da aka ce ya gina fa? Mimi ta ce"Ban gaya miki ba? Ai Inna Meri ta koma gidan da zama" Nan Mimi ta ba ta labarin da Hibba ta gaya mata ta ƙara da cewa" To shi ne ya ce yana da fili gwara a gina kawai." Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Ma sha Allah, na ji daɗin haka Allah ya sa albarka, ke kuma da ku ke mganar tsayawa wasu shirye shiryr? Me za ki shirya? Na ga dai komai kina da shi? Mimi ta mike tana dariya kafin ta ce"Ke fa kika ce kome ya fi sabon aure daɗi ko? To ai sabon biki zan yi da zai tabbatar da Komen da zan yi ya fi sabon aurana na farko." Kafin Hajiya ta samu bakin mgana Mimi ta fice da sauri tana faɗin" Sai na dawo Hajiya za mu yi mgana." Hajiya ta bi ta da Allah ya tsare tana Cigaba da jan casbahanta lokaci ɗaya tana wani mirmishin jin daɗi. Farincikinta ta ga Binta ta koma ɗakinta ta yi zamanta cikin Salama. **** KARAMCHI TV Ma'aikatan Karamchi kowa ya yi murna da dawowar Mimi, bakinta ita kuma ya ƙi rufuwa sai gaisawa take yi da mutanen arziƙi, wani farinciki na ratsata sun gaisa da Salim Bunza ya na zolayanta da cewa"Tunda kin dawo nima ya kamata na ɗauki hutuna nima." Cikin Magiya ta ce"Ka rufamin asiri mana Bunza, in ka tafi yanzu ai sai aiki ya nemi kashe ma mijina mata." Sai kawai ya yi mata dariya Na Misau na gefe ya ce" ƙila ma sai ya haɗa mana da zanga zanga." Suna ta raha da nishaɗi. Ta je Office ɗin Manaja suka gaisa shima sai da ya yi mata tsiya" Na ɗauka wannan rigimammen mijin naki ya hana ki dawowa aiki damu ne gabaɗaya.? Mimi na dariya ta ce"Ko ɗaya yallaɓai kawai dai ba na gari ne har Umra na je na dawo kuma matar Yayana ta haihu na tsaya sai da aka yi suna na dawo, nan ɗin sai da na zauna na huta tukunna." Ya na jinjina kai ya ce"To ai shinke nan muna yi miki barka da dawowa." Daga nan suka tattauna abin da ya shafi aiki kafin ta haɗu da editor ita ta karanta labaran safe na ranar oaraba. Jama'ar gari na ta nurnan ganinta domin wasu har sun gaji da tambayan Ina Mimi take a tunaninsu ta daina aiki da gidan talabijin na karamci ne ne sai kuma kwatsan a ka ganta ta yi kiba ta yi bul ɓul, kamar ba ita ba har wasu ma su kallon tashar suka ce kamar tana da shigar ƴaron ciki. A cikin waɗanda suka kalli labaranta na safiyar ranar har da Inna Meri da Walida da kuma Maeesha dake can gidansu tana jego, Tuni ta ji kishi ya kama tana ganin Mimi, ta tabbatar da kome za ta yi ba za ta kama kafar ta ba. Sannan ta ji a bakin matar Auwalu cewa ba sakinta ya yi ba, kenan auran su na nan za ta iya dawowa a kowani lokaci kila ma a katon gida na alfarma kamar yadda Inna ta koma katon gida na alfarma duk da ba ta je gidan ba amman ta ji labarin tsaruwan gidan a bakin Mariya ta kuma ji labarim komai sabo ne, ita a ganinta ita ya dace ta riƙa samun wannan abubuwan ba wasu ba. Sannan ita ya kamata ta zama a bar kwaten ce ba wata can ba. Bayan komawrarta gida ba daɗewa ta haihu samu mace kuma Saddiqu ya ce sunan Magajiya zai saka ma ƴarsa, asalin sunan Magajiya Mardiya ne da farko ita Maeeshan ta ɗauka Magajiyan ne sunan har ta fara bala'in ba mai sakan ma ƴarta suna Magajiya sai daga baya ta ji sunan ashe Mardiya ne sai ta koma ta yi laushi, An yi suna na karya da garari duk abin d Saddiqu ya ce ba shi da shi sai Maeesha ta ce bashi ne aka ci zai biya daga baya, Ita kanta Magajiya sai da ta raina kanta ta kuma gane amfanin Meri da uaƴanta a tare da su da ace suna gidan komai na sha'in taron suna da kuɗi ba zai yi mata wahala ba, itama ta yi taron suna a nan gidan amman dakyar aka samu a ka yi fate, Auwalu ne ma ta samu dubu goma a wajensa zuwaira biyar amman Jummai tana nema itama. Kuɗin da za ta haɗa ma a siya zannuwan suna ba ta da shi sai da ta ci bashin Atamfa da rigar yarinyar sai Inna Meri itama ta yo turmi, sai da Bintu ta hana ta amman ta ce ba ruwansu ta kuma matsa musu suma sai da suka leka sunan nan gidan Wanzamai daga nan suja wuce gidan su Maeshan. Har Gaje na yi musu tsiyan tunda Inna ta bar gidan suka daina ganinsu, Yaya Amina ce ma ke ba da hakuri amman Bintu cewa ta yi" To me za mu zo mu yi muku? Tunda daman wacce muke zayan domin ta kun kore ta daga gidan? Ai ita ce mu , mune ita dole ko ku daina ganin mu ai ga gidan nan mun bar ma masu gidan sai su haɗa duka su yi ta zama har ranar busa ƙaho." Saboda su Zuwaira ta yi mganar su ma dai ba su tanka ba. Sai ga shi ko Kunya Zuwaira ta ja Yaya Amina gefe ta na mata mganar, In sun zo da abun suna don Allah su kawo a haɗa anan ana haɗa na dangin uba ne daga bangaren su, sai Yaya Amina ta ce bari ta yi ma su Halima magana. Aiko dai Halima ce kaɗai ta ba da 5k, Daman ita Yaya Amina rigar ƴarinya ne da kuma pampers, Bintu kuma da Yaya Amina ta yi mgana sai ta ce ita kam ba ta da shi kuma ba za ta matsa ma kanta ba ashe sai yanzu aka san su ma ƴanuwan Saddiqun ne ƙiri ƙiri kuma su san tana da shi amman ta ce ba ta da shi dole suka ƙyaketa sana'ar saida ruwa take yi da zoɓo amman Bintu kafiya gare ta abin da ba ta yi nyya ba, ba mai sakata dole. Sai ga shi tafiya ma can gidan mai jegon Jummai ta ce su jira zuwa la'asar su tafi gabaɗayansu sai a tafi da kayan gabaɗaya shi ya sa suka jira, Inna Meri daman ba ta zo ba tana gida tare da yara. Su ne sai wajen biyar da wani abu suka isa gidan su Maeesha suka iske a na ta shan DJ. Mai jego ta ci gayu har da mai kwalliya ta ɗauko da mai hoto sannan sun yi abinci mai rai da lafiya har da Alala da zoɓo an tarbesu dai sama sama sai da ma suka buɗe kayan da suka kawo ne sannan suka ga ana ta duban juna ana taɓe baki, Atamfa biyu ce cotoon ɗaya ɗayar roba ce sai rigar ƴarinyar guda uku da sabulan wanka da Pampers ɗin Yaya Amina, kuɗin kuma ba su san ina a ka siya fallayan zannuwan guda biyu wai Mejego sai ta yi goyo da shi, Gaje ce ke kora wannan bayanin Amman ko alama ba su ji daɗin wannan kayan ba ko godiya nan in da suka sauke kayan nan aka bar su kamar sun kawo kashi Binta na ta dariya ƙasa ƙasa ga shi kuma Walida abokiyar gulmarta tana wajen koyon Computer, Mariya dai daman a gidan ta kwana tun jiya ta na can waje cikin ƴan rawa anman ta zo ta gaishe da su Yaya Amina har ta na zolayanta da Amarya tunda an saka ranar auranta Shekara. Ko Jaririyar ba'a ba su sun ɗauka ba sai da Yaya Halima ta yi mgana sannan Maeeshan ta kawo musu. Su kuma aka fi ma sakar ma fuska tunda an gan su sharr ba wahala a jikinsu barin ma Bintu da take ta wani shan ƙamshi ko gaishe da mejegon ma ba ta yi ba, ana ta gulma dai a gidan ana raɗan su waye su Bintu? Maeesha ta ce ƴayan Inna Meri ce ta bangare da ta koma matar da ta zo ta yi ma Jinjira wanka ta mata gashi, Domin Inna Meri ranar da ta zo barka har Maeesha sai da ta ji kunyar abin da ta aika mata nuna komai ba komai ta yi ba ta zage ana ta hidima da ita a lokacin yarinyar tana kuka ashe xibiya ce ba a yi gashi ta kume nan fa ta ce a saka ruwan zafi ta zauna tana ta ga shin cibiya sai ga Yarinyar ta yi shuru tana raba ido washegari kuma ta dawo ta kara yi mata ta shafa mata wani mgani a daran cibiyan ta faɗi. Sannan tunda aiki a ka yi ma Maeesha sai ta ba su shawaran kada ta yi wanka ganyen yanzu sai zuwa gaba amman a riƙa yi mata da towel kada jikinta ya ɗanyan ce amman ta ce a riƙa ba ta abinci sosai kuni da ruwan shayi tana sha saboda shi zai taimake ta. Uwar Aishan ta ji daɗi domin ita ce yar fari ba sanin haka ta yi ba. Kafin su bar gidan nan sun ga abu har hoto ma suna gani ana yin hotuna ba wanda ya gayyace su, Bintu ce ma da shegen neman mgana ta shiga hotunan bayan ta ɗauki Jaririyar ta rike su Zuwaira dai sai rakuɓewa a gefe kamar wasu almajira shi ya sa ana kiran sallar mangariba suka yi musu sallama daga gidan suka rabu, Yayan Inna Meri can suka koma gidan ta saboda ɗauko yaran su Zuwaira kuma suka yi gidan Wanzamai suna ta ƙananun mganganun wulakancin da aka yi musu suka koma ma da Magajiya abin da ya faru, To me za ta ce? Baba Danjuma ma ko sisi bai ba da ba ya ce ba shi da shi yanzu ta fahimci in ta cika ma matsa masa sai ya hau masifa yana maganganu, Kamar kada Inna Meri ta bar gidan shik enan ta koma ta yi sanyi kamar ba ita ba. Saddiqu daman ya gaya mata duk kuɗinsa sun kare wajen aikin nan da aka yi ma Aisha, Duk abin da ma za ta yi na suna ya ce ta ci ba shi abinci ma da sauran su duk iyayenta ne za su yi da kuɗin su. kudin aikin ma sai da ya Kira Mu'azzam ya taimaka masa da 100k tunda an ce za'a yi aikin amman ba shi da ko dubu 20 dole dai ƙanwar naki ƴaƴan Inna Merin da suka ci ma mutumci sune su ke tallafe da su, Shi kuma Baba Danjuma ya koma gefe kawai ya saka ma Magajiya ido daga ita har ƴayanta ya ga in da hassada za ta kai su. Shi har Allah Allah yake yi kwanakin girkin Inna su shiga in ya tafi can ya fi samun kwanciyar hankali da natsuwa, in ko yana wajen magajiya ko fara'a ba ya y. Saboda Magajiya tun da ya aureta bai taɓa samun kwanciyar hankali da ita ba ko da yaushe masifa da bala'i. **** Ana azumi saura kwana huɗu Mansoor ya koma gidan Hajiya Wajen Mimi, ya iske Yaddiko ta zo duba Hajiya da ta ganshi sai da ta ce ma Hajiya" Sun daidai ta kenan? Hajiya ta ce"Eh, tace bayan sallah za ta koma in sha Allahu." Yaddiko ta ce ya fi mata tunanin kashe auran da take yi,Hajiya tace daman ba da gaske ba ne duk shegentaka ne. Yau bai wani jima sosai ba. Ya dai kawo mata zanen da mai zane ya yi na tsarin gidan ta ce komai ya yi yana faɗa mata har an fara saka doundiom in sha Allahu za'a gama cikin wata ɗaya da wani abu tunda akwai kayan aiki, abincin ma da ta yi masa sai dai ta kwashe masa ya tafi da shi saboda ana jiransa ne za su yi meeting a Camp, Ita daman Mimi da Rukky kaɗai take shawara kuma itama ta ce duka tsarin Mimi ya yi dai gwwra dai yasan yanzu mai daraja zai ɗauka, bayan Rukkyan kuma ba ta gaya ma kowa ga abib da ke faruwa ba Hajiya dai ta yi mgana da Mommy ta kira ta itama ta gaya mata sai bayan Sallah Saboda ginin gida haka ma ta gaya ma Daddy da ya zo gidan sai ya ce ai Mansoor ɗin ya kira shi sun yi magana, sannan ya ƙara da cewa"Ki yi hakuri Mimi kin ji ko? Kin ga ribar hakuri ga shi yanzu gidanki ke kaɗai yake ƙokarin samar miki, shi ya sa akace komai mai wucewa ne" Hajiya ta amsa masa da wannan gaskiya ne sun rabu da cewa duk abin da take so, ta kirasa kawai shi uba yake gare su in sha Allahu komai zai yi musu in dai yana da shi, Har khadi ta kirata sun yi mgana shi ne Khadi ta ce"Ai sai ki zage da gyaran Headquater saboda ya san da, da kuma yanzu akwai bambamci." Dariya kawai ta yi, amman ta ce za ta yi har gyaran jiki tunda wancan lokaci duk a firgice take ba ta yi komai ba. Har Dr da Jawahir sun kirata amman ban da Madiha itama ko ba ta ko nemeta ba, saboda haka ta dai fahimci har abada suna da bambamcin rayuwa da ra'ayoyi ita da Madiha kuma dukkansu ba za su samu daidaito ba, kowa kawai ya tsaya kan ra'ayin sa. Maganar haɗa Lefe kuma Mimi ta dage ta ce tare za su riƙa shiga kasuwa da Aji. Ya yi kokarin zamewa amman ta ce in ba zai iya samaar mata lokaci ba sai a bar siyan kayan dole ya se su riƙa shiga da weekend tunda ba ya samun lokaci, ba ma haka ba shi kunya yake ji ba zai iya tuna ranar da ya shiga kasuwa da sunan siyayya ba, in kayansa ne Store yake zuwa yawanci kuma yaddika da Shaddodi Ahmad yake turama kuɗi ya siya ya ɗinka masa daga can Kaduna. Shi daman ta bangarensa daga Mu'azzam sai Inna kawai ya yi mgana da su, ko Baba bai samu sun haɗ ba, ballantana su yi mganar sai Auwalu da kwangilar ginin ke hannun shi, Inna meri ta yi ta saka albarka filin ya na can wata anguwa mai suna Dubai quaters anguwan ta masu hannu da shuni ne gaskiya shi ya sa tun a lokacin da ya siya filin ya na da daraja, Inna Merin ce ta gaya ma su Amina halin da ake ciki sai Bintu ta ce kwanaki ta kira Mimn ta ce mata in sha Allahu bayan sallah za ta dawo suma suna ta murna kada Mu'azzam da Hibba su ji labari ita da yanzu ta ke fama da oaulayi domin ana shirin maida Junior sai ga ciki ya ɓulla dole a ka rabu da shi sai Bayan Sallah tun da Mu'azzan ya ce anan za su yi sallah in za su koma sai su tafi tare da shi. Bangaren su Nasir kuwa ba kiran su ya yi ba, a group chart ɗin su ya shiga ya yi sallama sannan ya yi tagging ɗin Nasir da Makama sannan ya yi mgana." Ba dai kyau gaba a musulunci, ni na kwashe ladan Assalamu Alaikum" Sai da suka yi mamaki domin tunda aka buɗw group ɗin a ka saka shi ko kala bai taɓa cewa ba sai ranar. Makama dai ya tanka ya ce su ba gaba suke yi da shi ba, shi ne dai ya nuna ba su da wani matsayi a wajensa, shi kan Nasir ya gani sai ya yi kamar bai gani ba, Makama kuma sauka ya yi ya kira wayar Aji suka yi mgana Daman Sarkin zuciyan Aji ne da Nasir, Ya dai ba shi hakuri har kuma ya yi masa bayanin yadda a ke ciki, makama yace zai zo su haɗu domin ya je ya ga ginin. Nasir kuma sai da Aji ya dauke girman kai ya kira shi sannan suka daidai to. Ranar asabar ranar da aka tashi da azumin farko suka haɗu da yamma a can filin in da a ka fara ginin har ya kusa kaiwa linter. Nasir ya daki kafaɗan Aji lokaci ɗaya yana faɗin"Shege Ajin duniya wato shi kan shi Gidan Aji. ma na dabam ne." Makama ya ce"Tsarin ginin na turawa ne zaman gidan mace ɗaya, in da rabo Mimi ba ta cikin masu zama da kishiya." Aji ya ce"Wannan kuma na Allah ne, in yana cikin Kaddara na fa? Amman yanzu kam ita ce a baya ita ce kuma a gaba." Dariya suka saka har suna tafawa, suna taren Mimi ke ta kiranshi wai shi suke jira sai a lokacin ya tuna yau za su fara shiga kasuwa kawai sai ya Kalli su Nasir kafin ya ce"Nan zan bar ku? Saboda zan je na ɗauki Mimi za mu shiga kasuwa." Nasir ya buɗe baki Makama kuma na dariya tun kafin ma su yi mgana ya ce" Wlh ta matsa min wai tare za mu riƙa zuwa haɗa lefe, in na ce a a kusan ta tun a baya yar rigima ce" Nasir na kaɗa kai ya ce"Ƙwarai hanzarta ɗankwali yaja hula, lalle Mimi ta ciru tuta yau Aji za'a je kasuwa zaɓan kayan mata." Shi da Makama har suna tafawa dariya kawai ya yi musu suka ɗaga masa hannu ya shiga motarsa ya bar wajen su kuma suna wajen ginin suna ganin yanayin aikin har kusan mangariba sannan suka bar wajen. Aji kuma su ne har bayan mangariba a kasuwa suka sha ruwa, Mimi tare da Rukky shagon Atamfofi da lesuka suka fara zuwa Komai sai Mimi ta ce sai Aji ya zaɓar mata shi kuma ya gaji da azumi ga ciwon kai saboda hayaniyar kasuwa ya saka P.Cap ya rufe rabin fuskarsa saboda baya so mutane su gane shi, shi dai gaji ya yi komai sai Mimi ta ɗauka ta kara a jikinta tana ce masa ya yi mata kyau? Cikin kosawa ya ce"Ki ɗauki duk abin da ya yi miki saboda komai kiia saka yana miki kyau saboda ba kayan ba ne ma su kyau, ke ce mai kyan saboda haka ki ɗauki abin da kike so Aji ya na so shima" Sai Mimi ta fara mirmishin jin daɗi Rukky na gefe ta zama yar kallo ana musayan kallon Masoya. Kayan ma anan suka bar su, Sai gobe za su dawo su gama dubawa akwatina daman a online Mimi ta gani ta siya masu kyau guda huɗu huɗu takws kenan, da ta ce sha biyu amman Aji ya ce" Takwas ɗin dai Hajiya ta, ni fa talaka ne kada ki karar min da arzikina da zai kai ni shekaru uku nan gaba." Tana dariya ta ce"ba ka ce kai mai kuɗi ba ne? Kai tsaye ya ce" Duk da haka ban kai ki kuɗi ba, Malama ki yi abun hankali." Bayan shi ya ce ta siya duk abin da take so da ta ce shi ya ce haka sai ya sha mur ya na faɗin"Ni? To kila ba na cikin hayyacina ne, kin yi min farin yaudara, ko kuma dai ƙila gatse na yi miki, ke kuma kamar ƴar fari bakya gane baƙar mgana da gatse." Tana masa dariya ta ce"Ka manta ni Auta ce? Sorry sai na yi ma Atm ɗin kalmar nan ta ƙare dangi." Kai tsaye ya ce" Kya ci da kanki kuwa nan gaba." Haka dai suka yi rahan su, a hanyar dawowa daga gidansu Rukky tunda har gida suka maida ta, Rukky ta ce"Yallaɓai muna godiya sai Allah ya kaimu." Karon farko da ya yi mata mirmishi ya ce"To ƙawarmu asha ruwa lafiya, muma mun gode." Da ya kai Mimi gida sai ta hana shi tafiya dole ya tsaya anan ya yi sallah ya ci abinci, Kunin gyaɗa ne mai zafi ya sha da kosai, Abincin kuma ya ce ta ba shi kawai ya tafi da shi daman wasu kololinta suna can Camp bai dawo mata da shi ba. Haka nan ta kara zuba masa ya tafi da shi bayan ya ce ya na binta ba shi abincin shan ruwa da kanta yake so ta yi masa girki ta ce in sha Allahu, har mota ta rako shi ta na shafa kansa ta ce Ka yi tuki a sannu ka ji ko Mijin Mimi? Sai shima ya shafa hannunta kafin ya ce"In sha Allahu Matar Aji, ki kular min da kanki." Kawai sai ta duka ta sumbaci kuncinsa. "I miss u." "I love u." Shi kuma ya maida mata da martanin suka raka juna da mirmishi tana ɗaga masa hannu har ya fice daga gidan, bai wuce camp ba saboda a gidan Inna zai kwana saboda ya fi satin rabon shi da gidan. Sai dai ya yi musu sakon kayan azumi ta hannun Yaya Amina, ita ta ya ma kuɗin ta siya musu su dankali da kwai kayan abinci kuma Auwalu ne kamar yadda suka saba Kuma gabaɗaya ne har da can gidan har da su Baba Sani kamar yadda suka saba. Sannan sun siya gero da siga shi da Mu'azzam Inna ta ba ma gaje kwangilan ana kokon sadaka da kosai, sai kuma can gidan kakkanin Mu'azzam shima ya aika musu da sakon azumi kamar yadda ya saba. Matan kuma Aji ne yaa raba ma Yaya Amina da Yaya Halima dubu hamsin, Bintu kuma dubu goma ya ba ta, ta ce za ta kara jarin zoɓo ne. Ko da ya isa giden ya na yin hon Walida ta zo da gudu za ta buɗe masa get ya ce ta koma shi ya fito ya buɗe ma kansa bayan ya shiga da motar ciki ya koma ya ja get ɗin ya rufe. Sai dai suka gansa da kwandon abinci Kafin ma Inna ta yi mgana ya ce daga gidansu Mimi yake. Inna na mirmishi ta ce"Suna lafiya ko? Ya ce lafiya lau sannan ya yi ma Inna barka da shan ruwa Walida ma ta gaishe shi Junior kuma an samu carrton bai ma san ya shigo ba sai da ya ji an ɗaga sama sannan ya washe baki yana fadin"Daddy" Abinci ya ce Walida ta kai kitchen cikinsa ya cika sannan kafin ya shiga ciki Sai da ya ba ma Walida hakuri kan mganar wayar da ya ce zai siya mata zuwa bayan sallah ta ce bakomai. Sai ya ce ma Inna bari ya shiga ya yi wanka, Da Junior ya shiga ɗakin amman ya na shiga wanka ya fito ya dawo falon wajen kallon cartton ɗinsa. Aji so yake yi in an gama gidan can gabaɗaya sai ya kwashe kayan shi ya koma can gabadaya. Bayan ya yi wanka ya sauya kaya an kira sallar isha'i sai ya fita sallah da zai dawo ya biya ya siya ma su Inna tsire tana ta saka albarka, gabaɗaya ya gaji shi ya sa ya ce bari ya shiga ya kwanta. Ya na kuma kwanciyar sai barci sai cikin dare ya farka ya ga Mimi ta kira shi ma, bai samu kiranta ba sai da asuba. Ranar lahadi me yana gida ko da ma ba lahadi ba ne an ba da hutu matasan yan Gombe United ɗin duk sun tafi gida hutu sai yan nesa ne da kuma waɗanda ba sa son tafiya su suka rage kawai a camp ɗin suna sake bitan traning ɗin su. Da wuri ya je ya ɗauki Mimi suka biya ma'aikatarsu suka ɗauki Rukky tunda ita ta shiga duba wani abu, suna kasuwan nan har bayan la'asar bayan sun gama da bangaren Atamfa, leshi, abayoyo, material sai bangaren jakunkuna da takalma sai bangarem kayan kwalliya da bangaren Undies, su dai kam bai bi su ba ya ce su shiga su kaɗai, sai da aka je shagon mayafai y aga Mimi ta na jidan mayafi kala kala sai da ta gama zaɓa sannan ya kalleta yana daga gefe ya harɗe hannuwansa a saman ƙirjinsa sannan ya ce" Duk waɗanan mayafan na waye? Ta kannne ido ɗaya kafin ta ce" Ana mana." Sai kawai ya karkace kai kafin ya ce"Amman kinsan ba na son wannan abun ko? Kai tsaye ta marairace kafin ta ce"Naka ne fa, in za mu fita tare zan riƙa yi maka kwalliya." Ya kasa mgana yana ta kallonta kawai Rukky ma ta saka baki tana faɗin"Yallabai a yi hakuri duk saboda a yi maka kwalliya ne." Mai shago ma dake son ciniki sai da ya tanka kafin ya ce"Ango a yi hakuri, ka ji dai ta ce wannan na fita auting ɗin Amarya da ango ne." Kai tsaye Aji ya ce"Wani Ango? Ba fa Amarya ba ce, Yaji ta yi duk wannan abin daka gani domin za ta yi kome ne." Mimi ta ji kunya ba ta san lokacin ta ɗauki mayafi ɗaya ta sarke wuyan Aji da shi ba, shi kuma sai ya rike mata gefen hijabi yana faɗin" Yi hakuri na manta to kin daka barkonu a ke cewa ba Yaji ba ko?. Ya faɗa yana kallon Rukky da mai shago da suke ta musu dariya. Saboda haushi ledan mayafan gabaɗaya ta hana yaran shago ɗauka tac e shi zai ɗauka zuwa mota hakan ban ya rumguma yana faɗin" Allah dai na gani." Mimi ta taso masa da faɗin" Yana ganin mene? Da sauri ya ce"Irin son da nake yi miki mana." Sai aka bar Mimi da mirmishin jin daɗi, Mai shago da suka gama burgeshi ya ce"Allah ya sa ke da ƙara yin wani yajin har abada Hajiya." Sai aka bar Mimi da jin kunya Rukky na dariya ta amsa da Amin Aji ya amsa da cewa"Ai ba za ta ƙara ba saboda tana tsananin sona, na bayaa da ta yi duk burga ce na sani." Mimi ta ɗauki Jakarta ta maka masa a baya yana dariya ya ce", Shi fa illah ka yi yaji kenan har ƴaƴa da jikoki sai ya bika" Mai shagom mayafai ya sha nishaɗi, Rukky kuma haka take ta dariya tana ma Mimi raɗan daman haka Aji yake? Mimi na dariya ta ce Ya fi haka ma in ya yi niyar yin raha. Mimi ƙiri ƙiri ta ce ba zai kai mayafan nan Mlmota ba sai sun je shagon hijabai sannan haka nan da ledoji niƙi niƙi a hannu suka je shagon hijabi ta zaɓa amman anan suka bar masa sai an ɗinka yau ɗin ma sai mangariba suka fito daga kasuwa booth da bayan mota ciki da kaya Dakyar Rukky ta samu wajen zama. Suna hanyar maida Rukky gida, Mimi take gaya masa abin da Rukky ta ce sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba haka nake ba fa, duk ita ta maida ni haka." Mimi ta daki kafaɗansa tana faɗin" Wallahi ka daina gaya ma nutane na yi yaji ba na so" Ta faɗa ta na shan mur. Kai ya jinjina kafin ya ce"To ai shike nan na yi shuru da bakina." Rukky dai ta na shan kallo suka sauketa gida suna ta mata godiya yau bai tsaya shan ruwa ba. Sun rabu dai akan gobe ba zai zo ba sai jibi ta yi masa abin shan ruwa kuma ta ci kwalliya saboda zai mori kallon matarsa sa son ran shi. A gidan Inna Meri ya sha ruwa ranar. Washegari kuma gidan Nasir ne tunda shi ya gayyacesa tare da Makama, kamar ba zai je ba ba sai kuma ya tuna yanzu fa ya ce ya gyara sai ya shirya ya je,.Sai a ranar ma ya iya ganin Nafisa da ƴaƴan Nasir, Nasir na ta yi masa tsiyan ya ji kunya bai san ƴaƴan sa ba, shi kuma ya ce kada ya damu tunda dai shi ubansu ne ko da sun girma ne za su iya gane shi. Nafisa kuma sai da ta tambayi Mimi kai tsaye Aji ya ce" Nasir bai gaya miki ba? Ai ta yi yaji ne amman za ta dawo bayan sallah.' Me su Nasir za su yi in ba dariya ba, ita kanta Nafisan sai da ta yi dariya, da zai tafi 10k ya ba ma Nafisa da yaran da ya koma gida ya kira Mimi sai ya gaya mata Nafisa ta tambayesa shi kuma ya gaya mata ta yi yaji, Mimi ta riƙa dariya tana fadin ita kam ta shiga uku da wannan yajin. Shi kuma ya ce wlh kada ta ƙara. Domin yaji a aure yana da tambari, kawai miji bai sake ka ba sai ka dawo gida ka ce ka gaji da auran saboda samun waje, ta ce eh ta ji ai ta tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro, ya ce kuma da wannan don wannan. Ranar labara tunda sun yi anan zai sha ruwa a masallacin kusa da gidan Hajiya ya yi sallar mangariba dabino kawai ya ci ya karisa gidan. Da yake ya zama ɗan gida yanzu ya na zuwa kai tsaye falon yake shiga, Tabbas ya ga baƙuwar mota a haraban gidan amman tunaninsa bai kawo masa wani abu ba. Ƙananun kaya ne a jikinsa rigar mai ruwan kasa ce wandon kuma baki ne kafarsa takalmi ne mai buɗewa. Sai Kuma yau bai saka hula ba sumar kansa ta sha gyara tana ƙyalli, sallamar da ya yi ƙokarin yi ta makale ne a fatar bakinsa lokacin da ya yi mugun gani, to mugun gani mana, Mimi ce cikin kayatticiyar kwalliya na wani leshi fiteed gown, ta yi ɗaurin gashinta a waje daga baya, kuma ba mayafi ga kayan sun kamata tsam tana tsaye gaban wani namiji tana yi masa dariya. Wani irin Kolulin abu ne ya ji ya taso masa ya tokare masa kirji saboda Kishi har duhu duhu ya koma gani. Daga anan sai ya ga kamar Mimi rumgume da wannan mutumin tuni idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, jijiyon kansa suka ɗaga. Ya ma kasa yin wani motsi, Mimi ce ke facing kofar ita ta fara ganin shi daman roƙon Jaheed take yi ya tafi kafin Aji ya zo ya gan shi ya ja za mata wani bala'in ashe aikin gama ya riga ya gama. Ba ta san Jaheed ya zo garin ba sai kwatsam tana wanka ya zo gidan bayan ta gama yi ma Aji abincin shan ruwa ita ba ta ma san ya zo ba ta shirya ta fito ne Hajiya ke gaya maya Jaheed na falo yana jiranta. Da sauri ta bar gaban Jaheed ta fara takawa zuwa wajen Aji amman wani kallo da ya yi mata ya sa ta tsaya cak. Da ya sa Jaheed ya juya shima sai ya ga abin da ya sa Mimi rawan jiki ya gane shi saboda yadda Mimi ta so shi ya sa har hotonsa yana da shi a wayarsa sannan yana da duk wani labarinsa Ya yunkura domin ya bi bayan Mimi sai kawai Aji ya juya da sauri ya bar falon, Mimi ta mara mishi baya da sauri tana kiran sunan shi. "Aji.." "Mansoor" Amman ina ko juyowa bai yi ba, yana zuwa da sauri ya shiga motarsa ya kunna ta zo tana ƙwankwansa masa gillas ya yi banza da ita. Ribas zai taka yana ƙokarin taka ta sai ta yi tsalle ta koma gefe dai dai lokacin Jaheed ya kariso sai ya riƙe mata kugu yana tambayanta ko Lafiya take, wannan rikon a Idon Aji da sai da ya ji kamar ya mutu hon ɗin ma da karfi yake saki Megadi ya buɗe masa get ya fice da gudu kamar zai tashi sama. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB30011* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Hankalin Mimi ya yi bala'in ta shi. Jikinta sai rawa yake yi, ba ta ma san Jaheed ya riƙe ta ba sai bayan da Aji ya bar gidan sannan ta juya da sauri ta koma cikin falon tana rawan jiki da na zuciya saboda tsabar firgita da Irin kallon da ta ga Aji na yi mata Kamar za ta faɗi har da gudu take haɗawa Jaheed ya bi bayanta yana kiran sunanta amman ina ko jin sa ma ba ta yi, wayar ta na cikin ɗakinta a gaggauce ta shiga ta ɗauko wayar ta fara laluɓan lambar wayarsa ta fara kira amman tana ta ringing amman bai ɗauka ba, da wayar ta tsinke sai ta ƙara kira wajen kira a jere ya fi sau goma amman bai ɗaga ba. Haka ta fito falo a firgice sai suka ci karo da Hajiya da ta fito daga ɗakinta amman yanayin da ta ga Mimi ne ya sa ta san ba lafiya saboda ba ta ma tsaya ba sauri sauri ta wuce ta, Sai Hajiya ta bi bayanta tana kiran sunanta. A falo Jaheed na zaune Baaba Uwani na zaune a kasa a gefensa ta na ta yi masa surutu amman da alamu baya sauraranta mamakin irin tashin hankalin da ya gani a tare da Mimi ne kan wannan Mijin nata da ta ce ba ta son auran yanzu. Kawai yana zaune sai gani ya yi ta dawo falon kamar za ta fita saboda tsabar ruɗewa. Sai ya miƙe da sauri yana kiran sunanta daidai hajiya ta kawo cikin falon, ta tsaya kawai tana bin su da kallo cikin mamaki, Mimi ta rasa ina za ta je ta ji daɗi, ha waya a hannunta tana sake kiran Aji amman tana ta ringing amman ba ya ɗauka, Jaheed kuma ya ƙariso kusa da ita lokaci ɗaya yana faɗin" Mimi wai saboda ya ganmu ne kika ruɗe haka? To ba kin ce sakin ki zai yi ba? Tana jin shi sai ta yi kamar ba ta ji ba, Ta cigaba da kiran wayarsa tana matsawa daga gaba zuwa baya. Ganin ba ta tanka sa ba sai ya saka jannu ya riƙo hannunta lokaci ɗaya yana faɗin" Zo ki zauna..' "Kar ka ƙara taɓani.." Haka Mimi ta faɗa a fusace kamar za ta yi kuka tana yi ma Jaheed wani irin kallo, Hajiya ta karisowa tsakiyar falon lokaci ɗaya tana faɗin" Me ke faruwa ne? Ita kuma Baaba Uwani faɗi take yi. "Subhanallah Binta me ya faru" Jaheed kuma sai ya tsaya sororo yana kallon Mimi wacce ta cigaba da danna wayar ta. Sai Hajiya ta juya tana kallon Jaheed lokaci ɗaya tana faɗin" Jaheedu me ke faruwa ne? Shi ne ya ɗan yi bayanin ain da ke faruwa ya ƙarishe da faɗin" Ni ban san me ya faru ba kawai na ga duk ta ruɗe saboda ya zo ya ganmu tare ya fita a fusace ta bi shi tana masa magana ya yi banza da ita. Saura Kaɗan fa ya ture ta da mota Hajiya." Hajiya ta yi shuru ta na kallon Jaheed kafin ta ce"Dole za ta damu mana, mijinta ne fa kuma ba daɗi ya zo ya ganku tare." Cikin mamaki ya ce" Mijinta kuma? Ba ta ce ba ta son auran ba yanzu? Sai Hajiya ta kasa mgana Mimi kuma tana cikin tashin hankali amman sai da ta watsa ma Jaheed wani banzan kallo kafin ta ce"Da na ce zai sake ni ai ban ce maka ya sake ni ba. Wanda yake ma tunanin zai sake ni to ya daina bayan sallah zan koma gidan Mijina." Tana gama faɗin haka ta wuce fuu,Sai ya bita ya na ƙara kiran sunanta kawai sai ta juyo a fusace cikin tsawa tana faɗin" Don Allah ka kyaleni, wannan bala'in da me ya yi kama! Kai ba ka ga abin da ka ja min ba ne? In ba so kake yi ka kashemin aure ba ka fitar mana daga gida" Cikin mamakin kalamanta Jaheed ya nuna kansa yana faɗin" Ni yau kike kora daga gidan nan Mimi?. Kai tsaye ta ce"Eh In dai alheri zai kawo ka ba. Ni ce kuma na gaya maka ina da aure kaai na bibitayata Allah ya baka wata wacce ta fini." Daga haka ta yi wucewarta ta bar sa nan tsaye baki buɗe Baba Uwani ne ke ta jinjina kai, Hajiya kuma sai ta koma ta zauna ta yi shuru ba ta yi mgana ba. Jaheed ya kaɗa kai kamar ya yi kwallah kafin ya juya yana faɗin" Sai da safe Hajiya.". Ba ta ma amsa masa ba, Baaba Uwani ce ke ce masa bai ko ci wani abu ba ya tsaya mana ya sha ruwa anan ko sauraranta bai yi ba ya fice daga falon da sauri. Baaba Uwani ta kalli Hajiya kafin ta ce"Hajiya ba ki tsaida shi ba? Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" ƙyale shi kawai." Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" Shike nan Hajiya" daga haka ta wuce ta shiga Kitchen ita dai har ga Allah tana tausayin jaheed sannan ya fi mijin Binta fara'a da son mutane, kuma ga na gida ai gwara na gida da wani bare. Hajiya ta haɗo ma kayan shan ruwa ga abincin da a ka shiryama Aji nan a kamalle waje ɗaya, Mimi kuma na cikin ɗakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kira wayar Aji kamar ba gobe amman bai ɗaga ba. Gajiya ta yi ta hakura ta koma ta zauna Gefen gado kamar ta yi kuka, kanta ta dafe lokaci ɗaya tana fitar da huci daga bakinta. Wannan wani irin kishi ne. Wannan kishin na Aji ya na bata tsoro kada ya zame mata wata matsala anan gaba, tunanin kiran Mu'azzan ta yi, Sai ta ga ya na nesa ba amfanin kiran shi. Har Nasir ta yi tunanin kira sai ta fasa. Sai daga baya tunanin kiran wayar Inna Meri ya faɗo mata amman kuma ta na jin Kunya tun bayan barowanta gidan ba ta ƙara kiranta ba sai yanzu ta kira ta ce ta na neman ɗanta. Abun da kunya kamar ta fasa amman kuma ta kasa hakura ta riƙa Allah yasa wayar tana hannun Walida Allah kuma ya amshi addu'arta, tana kiran wayar Inna Walida ta ɗauka ita kuma damab wayar na hannunta, pokacin da ta ga Binta ta ɗauka Bintu ne ba ta ma tsayawa dubawa ba ta ɗauka sai ta ji muryan Mimi tana faɗin" Walida ce? Sai walida ta sake ɗago wayar tana ganin mai Kiran sai kawai ta daga tsalle tana faɗin" Anty Mimi". Ta faɗa cikin tsananin murna. Daman wayar na hannunta a cikin ɗakinta tana faman latse latse. "Walida Yayanki na gida? Haka kawai Mimi ta faɗa.Sai walida ta ce"Anya? Ba ya nan me ya faru? Sai kawai Mimi ta ce"Bakomai ki gaida Inna." Sai kawai ta katse kiran, abin ya ba ma Walida mamaki ta bi wayar da kallo, to kuma me ya faru? har ta shi ta yi ta fita falo ta iske Inna na zaune daga kallo ta fara gyangyaɗi haraban gidan ta leka ta ga motar ba sai mashin tabbacin Yaya Mansoor ba ya gidan kenan sai kawai ta koma ɗakinta, Ita da Junoir wanda tun ɗazu daman ya yi barci amman sai da ta kashe tibin dake ta yi shi kaɗai, domin Inna na zaune sai faman gyangyaɗi take yi. ***** Mimi na jin cewa Aji baya gida tunaninta ya ba ta yana Camp ɗin su, duk da ba ta taɓa zuwa ba amman tasan wajen yana cikin gari ne. Sai kawai ta ɗauki mayafi ta yafa ta zura wani saukakƙun takalma ta fita falo ta iske Hajiya na shan kayan marmari ita da Baba Uwani ba ta ma tsaya ta kansu ba ta faɗa Kitchen, ta kwashe abincin da ta yi ma Aji ta zuba acikin kwando mai zif ta zage sannan ta fito falon a gaggauce tana faɗin" Hajiya zan je na dawo." Cikin mamaki Hajiya ta ce" Ina kuma za ki Binta? dare fa ya yi kuma kin yi Azumi amman komai ba ki ci ba." Kawai wucewa ta yi tana faɗin" Hajiya sai na dawo zan iya cin wani abu." Kafin ma Hajiyar ta sake wata mgana ta fita, Sai da ta fita ta tuna ba ta ɗauko Key ɗin Mota ba sai ta dawo da gudu gudu ta koma ɗaki ta ɗauko Key ɗin motar ta fice ta na jin Hajiya na faɗin"Binta dare fa ya yi" Ita dai ta fice tana faɗin" Hajiya ba zan daɗe ba. In sha Allahu" Ko ba ta faɗa ba tunda Hajiya ta ga ta kwashi abinci ta san in da za ta je. Sai kawai ta kaɗa kai ta cigaba da shan kankanarta, Duk Binta ta jaa ma kanta da ba ta baro ɗakinta ta zo gida ba da duk haka bai faru ba, Baaba Uwani ko mgana ce a bakinta amman yadda Hajiya ta kame fuskarta ya sa ta kasa furta wani abu. Megadi ma ya yi mamakin fitar Binta da daddare abin da ba ta yi, duk tsiya ana mangariba take dawowa gida. Amman yau bayan mangariba wajen takwas saura ta shiga mota ta fita sai dai ya bi ta da fatan dawowa Lafiya, ita kuma tana tuki amman hankalinta na kan wayarta tana ƙara kiran lambar Aji anman bai ɗauka ba. Kusan ɓacen hanya ta yi ma sai da ta sake komawa tunda ta manta wajen daga karshe sai da ta tsaya a bakin hanya ta yi tambaya sannan a ka yi mata kwatance kai tsaye sai ga ta a bakin get ɗin Gombe United Camp. Akwai Security masu kula da shiga da fita domin tana zuwa sai suka hana ta shiga tun da ba su taɓa ganinta ba. Sun tambayeta wa take nema? "Mansoor Aji.." Kai tsaye Mimi ta faɗi sunansa. Security ɗin guda biyu ne suna sanye da uniform da kuma manyan fitilu suna haske motar Mimi da ita kanta tunda kamar cikin Camp ɗin ya yi duhu ba wuta. Dukkansu suka kalli juna kafin bahaushen ciki ya kalli Mimi lokaci ɗaya yana faɗin" Captain kike nufi?. Sai ta gyaɗa musu kai lokaci ɗaya tana faɗin" Yana ciki ko? Sai ya ce"Eh bai daɗe da shiga ba, amman ya san da zuwan ki? Sai Mimi ta girgiza kanta lokaci ɗaya tana ɗaukan wayanta a hannunta. "Bai sani ba, ina ta kiran shi bai ɗauka ba." Tana faɗa tana rubuta masa saƙo. "Ina bakin get ɗin Camp ɗinku.." Haka kawai ta rubuta masa. Dai dai lokacin taji wani cikinsu na faɗin" Bari mu kira wayar ɗakin sa, wa za'a ce masa? Tun da akwai telephones a cikin Camp wajen guda uku da na reception da na ɗakin Aji da na meeting room ɗin su. "Mimi.." Sunanta ta faɗa musu. Sai ta jira a cikin mota ta na ji suna mgana a Telephone amman ba ta jin me su ke faɗa ba.Ta ga dai ɗaya daga cikinsu ya zo ta gefen tagar motarta dake ke buɗe yana faɗin" Ki shiga ciki Hajiya.". Sai ta amsa masa da kai dai dai lokacin dayan ya buɗe mata get ɗin ta shiga ciki saboda ba ta san yanayin wajen ba sai ta rasa ina za ta yi fakin. Dole ta tsaya a bakin ginin wajen da aka sake rubuta GOMBE UNITED CAMP. Ta Fara waige waige kenan kamar suna jiranta sai kawai a ka kawo wuta wajen ya gauraye da haske, sai kawai ta fito daga cikin motar da wayarta a hannunta sai dai wajen tsit sai kukan tsuntsuye haka ta rika juya ido tana bin cikin wajen da kallo. Kai wajen fa ya haɗu dole Aji ya riƙa zuwa nan domin za ka ssmu cikakken natsuwa. Ba ta san daga ina ya fito ba kamar dai Kila ta bayanta ne ta ji dai mgana kawai a saman kanta. "Me ya sa kika zo nan? Da sauri ta juya yana tsaye daga bayanta yana sanye da riga da wando saukakku, fuskar nan tasa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba, tana ganinsa ta sauke Ajiyar zuciya sai kawai ta buɗe mota ta ɗauko kwandon abincin lokaci ɗaya tana faɗin" Ga abin da na kawo maka." Ta faɗa tana ƙarisawa gabanshi. Juyawa ya yi kawai ya fara tafiya yana mai faɗin" Me yasa ba ki ba ma saurayin na ki ya cinye ba? Ba ta yi fushi ba haka ta bi bayan shi da sauri tana faɗin" Aji mana. ka Saurare ni ne mana, Yayana ne fa" Bai juyo ba ya ce" Yayanki guda ɗaya na sani. Dr Sulaiman bayan shi ban san kina da wani Yaya ba." "Cousin Brother ɗina ne. Jaheed ne Son ɗin Daddy." Cak ya tsaya. Har ta kusa cin masa kafa fuskarta ta daki bayansa yana juyowa ya ga ga kwandon hannunta na neman faɗuwa da sauri ya saka hannu ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin "Oh muharraminki ne da zai riƙa taɓa jikin da ni kaɗai ne nake da ikon taɓa shi? Ko kuma ya dace ki tsaya da shi ba mayafi a jikin ki duka suran ki ya bayyana wanda ni kaɗai ne shari'a ta ba ni damar ganin ki a haka. Wato shi kin yarda ya ganki a haka ya kuma taɓa jikin ki ni kuma da shari'a ta ba ni wannan damar ba ki taɓa yarda wani abu ya shiga tsakanin mu ba ko? Me ki ka mai da kan ki ne Fatima? So kike yi ki kasheni lokaci nq bai yi ba ko? Kin san yadda zuciya take yin kuna? Kin san cewa hoton ku ya kasa ɓacewa daga tunanina? To in ma ya na tunanin zan rabu dake ne ya aura to ki gaya masa ya farka daga wannan nafarkin nasa domin ba zai taɓa zama gaskiya ba, ke ko mutuwa na yi ki ka sake aure Allah ya isa ban yafe ba." Haka ya faɗa cikin fusata Idanuwansa sun kada sun yi jajir, Mimi ta zaro ido tana kallon shi jin mamakin kalamansa a ina yasan cewa Jaheed na sonta.? Kuma wai Allah yas a ko bayan ransa in ta ƙara aure. Ba ta samun zarafin mgana ba ya kuma juya kawai ya fara tafiya zuwa wajen motar ta lokaci ɗaya yana faɗin"Ki koma gida dare ya yi" Tura baki ta yi kafin ta ce"Ni a'a sai ka ce ka haƙura." Banza da ita ya yi har suka karisa wajen motar ta ya buɗe baya y sakaa mata kwandon abincin lokaci ɗaya yana faɗin" "Ba na son gaddama, ki shiga mota." Yadda ya yi mganar ya sa ta san ba wasa Idanuwanta suka tara kwallah a sanyaye ta ce"Ka yi hakuri ba abin da kake tunani ba ne.' Wani kallo ya yi mata da yasa ta buɗe bangaren direba ta shiga ta zauna kafin ta kalle shi a marairaice tana faɗin" To ka yi hakuri ka ɗauki abincin" Kansa ya kauda da sauri kamar za ta yi kuka ta ce"Ni na girka fa da kaina don Allh kada ka ce a'a ka ji." Sai ya ɗan kalleta da sauri ta ƙara shagwabewa kafin tac e"Don Allah na ce fa" Tana gani ya sauke numfashi sannan ya buɗe bayan motar ya ɗauko kwandon abincin dai dai karisowam wani matashi ya na tafiya ne da alama dai ya fito shan iska ne sai Aji ya kira sunan shi. Da sauri ya ƙariso Cikin ladabi yana faɗin" Barka da dare Captain" Kwandon kawai ya mika masa lokaci ɗaya yana faɗin" Ka saka min a cikin ɗakina." Da sauri ya amsa amman yana leƙen Mimi a mota akwai haskem wuta ya gane ta tabbas Matar Captain ce ma'aikaciyar gidan tibi ya na tafe yana faman waige ya ƙosa ya je ya kai sakon ya shiga group chart ɗin su ya kai ma su Zinder labarin yau matar Captain ta kawo masa ziyara a cikin Camp. Shi ko sai da ya ga kabiru da suke ma laƙabi da pele ya wuce sannan ya zagaya ta bangaren Mimi kai tsaye ya ce"Fito.." Ba musu ta fito, shi kuma ya shiga mazaunin direba ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Sai na ce ki zagaya ki zauna? Da gudu Mimi ta zagaya tana mirmishi ta shiga bangaren mai zaman banza ta zauna "Seat belt" Da Sauri ta saka nata, shi daman ya zura na shi sannan ya ta da motar tunda daman key din na jiki. Tun da ta fahimci gida zai kaita ta ke ta faman mirmishi a sannu sannu har zuwa bakin get shi ya leka ya yi mgana da Security suna ganin shi ne suka buɗe mishi get suka fita suma suna gulmar kila madam ɗinsa ce domin tunda suka fara aiki a wannan wajen ba su taɓa ganin mace ta zo wajensa ba sai dai maza, suna tafe a hanya amman ba wanda ya yi ma wani mgana Mimi ce ta ga kamar ya na fushi da ita har lokacin ta kara narke murya tana ba shi hakiri kanzil bai ce mata ba har ya kai ta gida har cikin haraban gidan sai da ya yi parking Sannan suka fito a tare. Key ɗin motar ya mika mata ookaci ɗaya ya na faɗin" Kada ki ƙara cewa za ki tuka mota da daddare, in kika haɗu da miyagu fa? Kanta na kasa ta ce" To ba kai ba ne ka tafi kaba fushi da ni ba" Kamar za ta yi kuka. Kallonta ya yi kafin ya tura mata key din motarta ta saka hannu ta karba sannan ya juya kawai ya wuce ta bi shi da kallo, da sauri ta bi shi tana faɗin" Kana da kuɗi a hannunka ne? Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya nuna mata hqnnu cikin kaushinsa yana faɗin" Ki koma ciki gida Fatima." Yadda ya yi mganar ya sa dole ta juya tana tafiya a sannu har falon Hajiya amman sai da ta laɓe tana lekensa su ka yi mgana da Megadi sannan ya fita ya bar gidan. Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana juyowa ta ga Hajiya zaune taba gyanyadi ta kuma san zaman jiranta take yi. Sai ta yi mirmishi sannan ta ƙarisa wajenta tana tashinta Hajiya ta farka sai ta ga Mimi da sauri ta ce"Binta kin dawo? Sai ta riƙe Hannun Hajiya ta miƙar da ita tsaye lokaci ɗaya tana faɗin" Na dawo Hajiya, ki kwantar da Hankali Aji ne ya dawo da ni gida." Hajiya ta jinjina kai ba ta yi mgana ba. Sai Mimi ta riketa har zuwa cikin ɗakinta ta kwantar da ita kan gado Hajiya na faɗin, ki samu wani abi ki ci Binta kin yi azumi ba ki ci komai ba." Sai ta amsa mata. Nan ta bar Hajiya ta koma ɗakinta ta cire kaya ta yi wanka da sallar Isha'i sannan ta fita falo zuwa Kitchen ta diɓo abinci da kayan marmari Baaba Uwani ta jima da shiga ciki, sai da ta gama cika cikinta ta sha zobon da ta yi sannan ta koma ɗaki ta ɗauki waya ta kira Aji amnan bai ɗauka ba, so take ta ji ya koma gida lafiya? Sai ta kyale shi gajiya ne a jikinta saboda ta wahala yau ga azumi ga aiki, amman ɗazun nan ba ta ma jin yunwar. Sai yanzu da ta kwanta gajiyan ya taso mata, har ta fara barci ta ji karan wayanta tana dubawa ta ga Aji ne da sauri ta ɗaga kiran na shi tana tambayansa ya ya koma gida? Ya amsa mata a dakune lokacin fa ya gama cin abincin da ta yi masa ne farar shinkafa da miyar naman rago da cowslow, sai zoɓo da kunu, daman bai ci komai ba amman kishi ya hana shi ya nemi wani abu da ba ta kawo masa ba haka zai kwana kuma ya tashi da azumi. Haka dai su ka yi wayar yana ta wani cin mgani ta na dai bashi hakuri. Shi bai ce ya haƙura ba shi kuma bai ce bai haƙura ba, Karshe ma barci ne ya kama idanuwanta ya sa ta yi masa sallama tace za ta kwanta, da asuba ma wayarsa ne ya tashe ta ya ce ta tashi ta yi Sahur ita kuma sai da za ta tafi wajen aiki ta kira shi yana barci sai bayan ta je wajen aiki ya kira ta daga jin muryansa ma ta san yana barci ne sai suka gaisa sama samma sannan suka yi sallama har a lokacin dai bai gama Hucewa ba sai bayan wajen kwana huɗu sannan ya warware ya daina fushi fushi. Amman da ta ce ta ƙara gayyatansa shan ruwa cewaa ya yi ba zai zo ba kada ya ƙara zuwa ya ga ta gayyato saurayinta. Sai ta riƙe baki kafin ta ce"Ba ka hakura ba kenan? Kuma ni ai ba ni na gayyace sa ba." Banza ya yi mata. Sanda suke mganar ya kaita ne kasuwa ta amso ɗinkunan hijabanta a ranar ta ba shi Atm ɗin sa ya kalleta kafin ya ce"Kin gama komai? Domin kika sake na karɓa in ma da wani abin sai dai ki siya da kuɗin ki" Tana jin haka ta yi saurin maida shi jaka tana na faɗin" Ban cire na gyaran jiki ba." Taɓe baki ya yi bai yi mgana ba, da ta ga kamar ya ƙara shaƙa sai ta ce"Ka zo gobe don Allah zan jira ka." "Ba zan zo ba." Haka ya ce kuma yanayin mganarsa ya sa ta san da gaske yake yi sai ta kyale shi. Da ta gaya ma Rukky itama sai da ta ce Jaheed bai kyauta ba amman ta ba shi hakuri to sai ya nuna kamar ya hakura sai kuma ya nuna kamar bai haƙura ba. Ko da ya kai ta gida ma bai shiga ba ya yi tafiyarsa. Wajem sati fa ya na mata wannan halin sai ta yi masa mai gabaɗaya ranar da aka kai azumi goma ta shirya masa abun shan ruwa ta kira shi ta ce ya zo ya ce ba zai zo ya ga abin haushi ba ,sai kawai ta ce zan zo to na kawo maka" Da sauri ya ce"Ba ki da hankali ne? Ki tsaya gani nan zuwa wlh kada ki ce za ki taho." Daman ta shirya masa ne, ta san in ya ji ta ce za ta so sai ta shi hankalisa tunda daman ko ranar sai da ya ƙara mata fadan zuwan da ta yi, ko Minti talatin ba'a yi ba sai ga shi ya zo amman ya ce ba zai shiga ciki ba sai dai ta kawo masa ya tafii da shi, ita kuma sai ta shagwaɓe masa tana faɗin" Mu shiga ciki mana, ba sai ka ga abin da ka ce ina maka rowa ba? Ya kasa mata musu saboda ta rike hannunsa sannan ta ma masa fari dole ya bita cikin falon ya zauna ta haɗo masa kayan shan ruwa tun yana basarwa har ya saki jiki, Ita kuma tana cire mayafi ya ganta cikin wata riga mai roba ta kama ta. Kirjinta rabi duk a waje ssannan ba ta saka ɗankwali ba ta ɗaure gashinta kawai, Aji na cin abinci ya na kallonta ƙasa ƙasa, Sai bayan sun gama ta kwashe abin da suka yi amfani da shi sannan ta dawo gabansa ta juya masa dakyau sannan ta kashe masa ido ɗaya tana faɗin" Ga gama kallon ne? Haka ta faɗa tana masa dariya sai kawai ya kalleta cikin wani yanayi kafin ya ce"Kaɗan na kalla." Baki ta rufe tana dariya, ba ta san lokacin da ya ta so ba jinta kawai ta yi a jikinsa ya rumgumeta kamkam, itama sai ta lafe a kirjinsa tana shaƙan kamshin turarensa mai saka ta natsuwa. Rungumeta kawai ya yi sai ita ce ma da ya ɗago ta sumbaci bakinsa sai ya kalleta sai ta ji kunya ta juya baya sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce"Daran ranar ba ɗaga kafa wallahi." Haka ya faɗa sannan ya koma ya sha mur kamar ba shi ya faɗa ba da zai tafi ya ba ma Hajiya 5k, baba Uwani 3k, ita dai ya ce ko sisi ba zai ba ta ba, da ta ce tukwaicin girki fa? Sai ya ce to ai ladanta na wajen Allah Tun da ta ciyar da mijinta sannan shi ba shi da kuɗi ta gama talauta shi ma gaɓadaya shi ya yi mganar sai ya bar ta da dariya. Tun daga ranar ta samu ya huce, yabq zuwa a sati sau biyu su yi Buɗe baki, gefe daya tana ta shiryen shiryen tarewa gini kuma yana ta nisa sun yi mgana da Mommy dole kayan gida komai sabo za'a siya ita Mommy ta yi mgana da Daddy ya ce ba laifi in an gama gidan sai aje aka ga abib da ya kamata a siya, ita dai bangaren Mimi kayan ɗakinta da a ka kwaso daga gidan Wanzamai ta ce a bar mata sai ta saka shi a wani falo tun da ya ce falo biyu ne nata sai bedroom uku sai shi falo ɗaya Bedroom guda biyu, ga sallah na matsowa kuɗin da ya tara Mimi duk ta yi kasa da su, Hibba ya ba ma kwangilan kayan sallah na Inna da Walida Junoir, sai Mariya da Baba da magajiya, Bintu ma ya yi mata kala ɗaya. Inna kala uku, Magajiya biyu, Baba ma shadda da yadi guda biyu su Baba Sani Kuma Mu'azzam ya yi musu har da su mariya suma ya kara musu da kala ɗaya ɗaya. Magajiya sai dai ta ga Baba ya shigo da kaya Hatta Mariya kala uku ne Mu'azzam kuma ya haɗo musu da kuɗin dinki. Gaje da Harira ma ya yi musu Atamfofi kala daya daya, suna ta godiya Magajiya ta kasa mgana domin kaf a cikin ƴayanta ba wanda ya ke mata kayan sallah sai Mu'azzam da Mansoor, Auwalu na fama da kanshi Saddiqu kuma bai garin ina ya ga ta zama bashi kaɗai ya ishe shi, Dole kanwar ñaki zuru'an Innan dai sume suke taimakon su tunda ga sutura har bangaran abinci tunda in sun ci su ne, in kuma sun sha suma sune. Mariya sai murna take yi tana da kala huɗu, tunda saurayinta ya yi mata ɗaya sannan su ka haɗa kudi su biyar za su yanka sa Nasir Makama, Ahmad Mu'azzam da Aji domin su raba a tsakaninsu, Aji kuma ya ce zai ƙara da shiga tantan saboda Can gidan da su Baba Sani. Ana sallah saura kwana huɗu Hibba da Mu'azzam suka sauka a garin, da kaya niki niki na kayan fulawa duk ta siyo komai anan za su yi cincin da sauran cimar fulawa, Matan su Yaya Amina kuɗi yan'uwa suka ba su, Bintu dai an mata kaya ita da yayanta, Ana jibi sallah suka yanka san su, naman duka gidan Inna aka kawo sannan ga kaji Mu'azzam ya siya guda goma. Biyar nan gidan Inna uku Magajiya biyu Baba Sani da Baba Danjuma. Shi kuma Aji naman tantan na 50k ya shiga aka raba na Magajiya kashi Biyu su Baba Sani kashi ɗaya, sai ga shi karon darko Magajiya da aka kawo mata nama da kaji ta buɗe baki ta ce Allah ya yi albarka sannan Auwalu ma ya kawo musu Nama tunda a kwangilan aikin gidan Aji Alhamdulillah, ya na samu kuma haka ya gaya ma Magajiyar. Shuru kawai ta yi ta kasa magana ko Jummai ma da ta kira Mu'azzam dubu goma ya tura mata, Saddiqu kuma sai kiran babu, domin ya ce Maeesha ta matsa masa sai da ya tura mata wasu kudaɗe biyar ba'a samu ta hannunsa ba, in da ace ma dasu aka dogara da an mutu ba'a ci ba. Ana gobe sallah gabaɗayansu sun haɗu a gidan Aji da ake gini har an saka get da Kofifin cikin gida yanzu POP suke yi da plasta sannan masu saka tayil da Interlock na cikin gida na aikinsu Ahmad ya ce"Lalle Aji ka tara kuɗi." Aji ya ce"Duk sun ƙare, Mimi kaɗan ya rage ba ta maidani talaka ba." Nasir ya ce"Ta cancanta ne." Suna gidan har aka sha ruwa lokacin da Ma'aikatan su ka ta shi akwai wanda ke kwana a gidan saboda barayi. Dag nnan gidan Makama suka wuce nan suka shirya shan ruwa suna gidan Rukky ta zo kawo mata ɗinkunanta kawai sai ta gan su cikin mamaki ta kama baki tana faɗin" Yallaɓai na Mimi ashe kana nan? Aji na Mirmishi ya ce"Nan fa gidan abokina ne, za ki iya ganina ko wani lokaci." Nan fa aka gaggaisa, ta shiga ciki Nasir ya ce"Yayar matar ta ka akwai girman kai." Makama ya ce" Da alamu dai kana ciki da ita domin ina ganin ka, kana satan kallon ta.". Nasir ya fara rantsuwan ba haka ba ne, Makama na rantsuwan ya gano shi, Aji na gefe ya ce"To miye! In kana sonta ka shiga cikin Manema kawai kai namiji ne mijin mace huɗu" Me za su yi in ba dariya ba domin Nasir ne ya ce"Kwarai mutumina." Da alamu ya na so yana kaiwa kasuwa, da Rukky ta fito za ta tafi kawai sai Makama ya ce ga Nasir zai kaita gida, Aji ya dafa kafaɗansa yana faɗin" Sa'a dai Nasiruddeen Angon Nafisa da Rukayya." Dariya har su Mu'azzam na dafe ciki ganin Nasir ya miƙe ya jinjina ma Aji hannu lokaci daya yana faɗin"Na gode namijin duniya, Angon Mimi." Suna ta masa shakiyanci har ya fice. Shi kuma ya kaita gida amman hiran na su sama same ne ya dai karɓi lambar wayarta sai da ya dawo sannan suka watse Nasir da Ahmad tafiyar su ɗaya Mu'azzam da Aji ma haka. Sanda suka koma gida su Hibba na ta fama da suyan nama ga Walida da Mariya na ta fama da suyan dumblan ba su ci abinci ba domin cikinsu ya cika sai suka zauna a falo suna ta hira da Inna Meri, Inna na faɗin Yalwa ta kira ta tana godiya ta ce Mansoor ya tura mata 50k Aji ya ce ba shi da kuɗi ne ya so ya fi haka shina Mu'azzam Inna na ta saka albarka, sannan ta ɗauko musu wata farar keda da kaya ciki Mimi ta aiko da shi ta yi ma Inna Atamfa da hijabi da takalmi, sai kuma Walida Abaya da mayafi, Aji bai ma san da saƙon ba kwata kwata nan ma Inna ta yi ta saka albarka sai da suka koma ɗaki shi da Mu'azzam ya kira Mimi, yana ce mata ta ga kuɗi a hannunta baja baja tana ta hidima da shi a ciki ta yi ma su Inna kaya Ita kuma ta ce"Eh da yake kai kaɗai ke da Kuɗi ka manta nima aiki nake yi" Ya ce"To ma su aiki, ni ai kin san zaman banza nake yi." Dariya ta yi masa kafin ta ce"Kayan sallah ta fa? Ba ka aiko min da shi ba? Kai tsaye ya ce"Amman ba ki da tausayi, duk kuɗina ya kare ki ɗauka cikin na lefe ki ɗinka mana." Mimi ta shagwabe tana faɗin"Haƙƙin ka ne fa ka min sutura, da ci da ciyarwa." Aji ya yi shuru kafin ya ce"Ai zan ci kuma zan yi ciyarwan in sha Allahu. Sai daga baya ta gane maganarsa ai sai ta saka Ihu ta kashe wayarta ta bar shi ya na Mirmishi, Mu'azzam ya fito daga wanka ya tsaya kawai yana kallon Yayan na shi sai daga baya ya ganshi, ya ga yana kallonsa sai ya basarwa ya miƙe yana faɗin" Ka fito? Mu'azzam na yar dariya ya ɗaga masa kai har ya shiga tiolet ɗin yana bin sa da kallo ya na yar dariya. A daran aka faɗi an ga watan salla washegari a ka ta shi da shirin zuwa sallar Idi. gaɓadaya gidan har da su Inna, Mu'azzam zai je ya ɗauko su Baba Danjuma su uku tunda matan su ba sa zuwa. Hatta Magajiya kuwa Amman Inna sallar Idi ba ta taɓa wuce ta ba, Aji kuma zai ɗauki Inna da su Hibba. Masallacin takwas da rabi suke tada salla nan cikin gari ne Aji da Mu'azzam shigar fararen shadda suka yi harda babban riga da baƙaƙen takalma da huluna da agogo baƙaƙe, Ahmad ya ɗinka musu daga kaduna zuwa da shi kawai ya yi Mu'azzam ya biya komai da komai, in ka gansu kamar yan biyu, Inna na kallonsu tana mirmishi sai kwalla addu'a take yi a cikin ranta Allah ya kara haɗa kawunan su Hadda Junoir shima an ɗinkka masa shaddan matan kuma kowacce ta ci gayunta lalle ne kaɗai ba su yi ba sai sun dawo daga idi tun da ba lokaci. Rufe gidan a ka yi gabaɗaya, a masallacin Idi su ka haɗu da su Mu'azzam da kuma su Nasir tunda duk can suke zuwa. Bayan an idar da sallar idi kenan zaratan abokan suna ta hotuna daman Nasir da matarsa ya zo haka Ahmad da Makama, kawai sai kuma su ka haɗe da Mimi, ita ta kawo su sallar idi ita da Hajiya da Baaba Uwani. Kamar haɗin baki matan abokan suka haɗe gabaɗaya Mimi ta ji kunyar Inna ta duka ta na gaisheta Inna ta ta da ita tsaye ta na saka mata albarka, Hajiya kuma na ta yi ma Inna tsiyar Idonta kenan shike nan sai yara su raba zumunci inna na dariya ta ce tana nan zuwa. Mimi ta sha kyau cikin abaya mai ruwan kasa, ta naɗa mayafinta a kanta. Saboda su Inna da su baba ba su daɗe ba, Hibba da Mimi sun yi mganar sai sun yi waya sannan suka rabu kowa ya shiga motar da ya zo, Aji dai sai da ya jira Mimi saboda go slow, sai da ya samu suka fita sarari tare sannan suka tafi tare zuwa juction ɗin da suka rabu. Bayan duk an koma gida aka fara ciye ciye da cin nama, ranar Idi ce ranar zama cikin Iyaye da ƴan'uwa Aji da Mu'azzam a gida suka yini cikin yan'uwansu amman sun kira ƴan'uwansu sun yi musu barka da salla har Baba Yakubu ya kira bayan ya kira can Kwami ya yi musu barka da sallah Sannan sai ga shi ya kira Dr. sulaiman, ya yi masa barka da Sallah sannan ya kira Mommy itama ya yi mata barka da sallah har da Daddy kuma sun ji daɗi, Ita Mimi ma mommy ke gaya mata da farko sannan Dr ma ya faɗa mata Daddy sai da ya zo gidan ne ya ke ce mata mijinta ya kira shi sai ta ji daɗi kenan dai da gasken Ajinta ya sauya. Ranar ba su yi waya sosai ba saboda kowa na can cikin ahalinsa. Ranar yawon sallah na farko ma duk suna gida ranar na uku ne gidan Inna ya cika da su yaya Amina da jikoki ranar kuma aka yi abincin sallah su kuma su Mu'azzam da su Nasir gari suka shiga suna ta ziyarce ziyarce sune har gidan surukan Nasir da Makama. Rukky na gida itama tunda Bibi itama gidan ta je Nasir dai bai furta yana son Rukkaya ba amman ta fahimci haka. Daga nan suka je gidan surukan Ahmad bayan nan suka zagaya duka gidan iyayensu har gidan Wanzamai da wajen inna suka mata barka da sallah gidan Hajiya ne ƙarshe Mimi ba ta san ma da zuwan su ba gidan Hajiya cike da yaddiko da ƴaƴanta da jikokinta ta ji kiranta yana faɗa mata ga su sun yi ma Hajiya barka da sallah. Sai a ranar wasu cikin ƴaƴan Yadikko suka ga mijin Mimi lalle ya ci sunan shi Aji haka suke faɗa Hajiya ta ji dadi tana ta zolayansu Kowanne su sai dai ya bata goron sallah, Ba su wani tsaya ba suka ce za su karisa gidan Daddy naman da cake din sai package din shi Mimi ta yi musu, ta yi kyau cikin leshinta doguwar riga kamar ka sace ta ka gudu. Daga anan sai gidan Daddy shima ya na gida sun kuma samu harda Jaheed tunda shima yaran na shi duk sun zo gaisuwan sallah hakika ya ji daɗin wannan ziyaran duk da shima gidan cike da mutanensu yan Siyasa sai a ranar Aji suka taɓa musabaha da Jaheed kowa na kallon kowa. Sai bayan sun baro gidan ne Makama ya kalli Aji yana faɗin"Yau dai ka ga rival ɗin ka Aji." Tun da shinl ne daman ya kawo ma Aji labarin Jaheed ɗin da ya ji a wajen Bibi. A wajen ginin Aji suka yada zango aiki akwai ake yi ba dare ba rana domin nan da kwana goma Aji ke bukatwr matarsa daga can suka ka rabu kowa ya yi gidan shi. Washegari kuma Hibba ta tafi gidansu itama ta yi gaisiuwan sallah. Mimi kuma a ranar suka yi mgana da Aji ya jadadda mata kada abin da za ta yi ya wuce nan da kwana goma. Dole ta kira Rukky domin su fara shiri mganar gida daman ya yi mata vedio ta gani ta tura ma Mommy ta ce ba matsala tuni ta ba da oder komai da komai, mganar gyaran jiki suka fara yi, kayan gyara kuma Khadi ta haɗa ta da wata Surayya Dee mai saida kayan mata da gazar sababi tana kano ne aiko mata da shi kawai za'a yi, kayan surayya dee mai suna Bojuwa kaya ne masu inganci da daɗewa a jikin mace kafin su sake, ku yi amfani dashi domin zamowa tauraruwa kamar Mimi a gidan Ajin ta.+234 803 277 3332 Sannan ma yaddiko ta aiko mata ds su gumba, Mommy kuma ta siya wasu kayan daga wajen Surayya mai kazar sababi na Amare da uwayen gida +234 803 277 3332 ta siya mata babban Package har da kaza da matsalan ta yanzu wajen aiiki ne amman sun yi shawara da Rukky za ta samu manaja ko hutun sati ɗaya ya taimaka ya ba ta, duk shirin nan da ake yi Madiha ba ta saka kanta a ciki ba Khadi ta kira ta ta faɗa mata za ta je Gombe Mimi za ta koma sabon gida sai ta ce ba za ta samu zuwa ba, ita dai ta ce za ta je Dr kuma ya ce Jawahir za ta zo daman kuma ta yi arba'in za'a kawo ma Daddy Baby shi da Hajiya. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3012* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI *08089965176* *07084653262* Sallah da kwana uku mai gyaran jiki ta fara zuwa gida yi ma Mimi, kuma gashi in an fara ba'a san ana yawaita zirga zirga in da ma Allah ya taimake ta a satin sau uku take da karanta labarai, sai ta samu natsuwa amman duk ranar da za ta fita dogon hijabi da safa fuskarta ne kaɗai a waje kuma kowa ya ganta sai ya yi maganar ta ƙara kyau da fari har da su Aisha Farida iyayen gulma waɗanda Rukky daman ta gaya musu mijin Mimi yana nan yana danƙara mata wani katon gida, sai bakin su ya mutu daman can suna ta faman yawo da mganar ita ko Mimi har yanzu  tana nan a wannan gida kamar a kurki?    Tun da ba wanda ya san abin da ya faru ya sa daga Rukky sai na jiki jiki. Ba wanda Mimi ta yi maganar da shi, sai dai ma na faɗan cewa za ta koma sabon gida. An shirya daman za'a yi waliman sauka a gidan Aji kuma daman ya ce za'a yi Saukan Qur'ani a gidan kafin ta tare,  daga shi har ita ba su da sukuni ita tana ta fama da shirye shirye. Shi ma kanshi baya samun zama tun salla ba su ƙara haɗuwa ba sai dai su yi mgana ta waya. Tuni har ta karɓo ɗinkunan da ta ba da ɗinki. Maganar kayan gida kuma daga waje Mommy wannan karon ta yi mata Oder bayan sun yi mgana da Daddy, Cikin Satin nan ma kayan za su iso. Sai turarukan wuta na jiki da na ɗaki, duk da ta lna da su amman ta siya wasu ta ƙara domin wannan karon ba auran wasa za ta je yi ba, auran ne da gaske take kuma fatan har Abada ya zama mutuwa ce za ta raɓa.   Gyaran jikin sati ɗaya a ka yi mata. An yi mata dilka da halawa, masha Allah Mimi ta yi wani irin kyau, fatar ta ta yi wani irin silɓi da tsantsi. Ta ɗan dakata da zuwa wajen aiki tunda ta samu izinin Manaja da cewa za su tare a sabon gida akwai shirye shiryen da za su yi. Sai ya ba ta sati ɗaya shi ya sa suka samu lokacin zuwa kunshi da gyaran kai ita da Rukky. Wacce ba ta da zence sai na Nasir, Mimi ta gaji ta ce"Wai kuma kike ta yaɓon Nasir. Bayan kin gama zaginsa da cewa ɗan renin wayau ne." Sai Rukky ta harare ta kafin ta ce"Ba na son sharri, lokacin kafin mu fara mu'amala ne na san shi sosai." Mimi ta kalleta a karkace kafin ta ce" Ikon Allah! To Allah ya tabbatar mana da alheri." Rukky ta amsa da Amin tana murgaɗa baki, Tunda Nasir dai ya yaɗa manufarsa kuma ta amsa masa.   Gyaran kai Mimi ta fara yi sannan sai washegari tun safe suka tafi kunshi, ba da motar ta ta je ba ga shi kuma sun yi dare dole Aji ta kira ya zo ya ɗauke su. Tare da Nasir suka zo ita dai Rukky a hannanye a ka yi mata. Ba su bi su Mimi a daidaita Nasir ya tara zai raka Rukky gida, sai da suka hau kan titi ne Mimi ta kalli Aji lokaci ɗaya tana faɗin" Abun mamaki, Nasir wai aure zai ƙara? Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Ikon Allah me? Ai ba abun kunya ba ne, ko kawar ta ki ta fi karfinsa ne.? Mimi ta kama baki kafin ta ce"Ni ban ce ba, kawai dai ina mamaki ne.Duka duka fa na ga Yayansa biyu ne, kuma zai ƙara aure sai na ga kamar ya yi sauri da ya ƙara aure." A kaikace Aji ya kalli Mimi kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa. Sai ya kauda mganar da cewa" Yau masu aiki fenti suka yi , zuwa gobe za su ƙarisa." Mimi ta jinjina kai kafin ta ce" Aikin ya yi sauri gaskiya. Daman Gobe za'a kawo kaya, Mommy ta min mganar in da za'a ijiye kayan, na ce daman zan maka mgana in an gama gidan sai a je a gyara a sauke kayan a can kada ya zama wahala biyu."   Aji ya yi shuru kafin ya ce" A'a sai an gama daman na saka Baba ya samo waɗanda za su yi sauka ina so kafin a fara komai sai an gama saukan Qur'anin da na ce miki." Cikin gamsuwa Mimi ta ce"To ba matsala, Allah ya nuna mana." Sun ƙarisa gida kenan Aji ya kalli Mimi kafin ya ce" Ina Atm ɗina? gabana na ta faɗuwa na san gabaɗaya kin gama kwashe min tattalin arziƙina." Mimi na dariya ta buɗe karamar jakarta ta ɗauko ta mika masa ya karɓa lokaci ɗaya ita kuma tana faɗin" Na gode Mijina, Allah ya ƙara arziki da wadata." Ya amsa da Amin yana yi mata wani kallon ƙasa ƙasa kafin ya ce"Dole ki yi min addu'a mana tunda kin gama ƙwaçe min ƴan kudaɗe na."   Yana dariya tana taya shi, sun ɗan jima a Motar suna Hira kafin ya rakata har kofar falon Hajiya sai da ta shiga gida sannan ya koma ya shiga motarsa ya bar gidan ita kam Mimi wani abu ne ke ba ta mamaki duk irin rawan kafa nan na matasan zamanin nan Aj ba shi da shi, ko dai ba shi da lafiya ne? In ya zo fa daga rike mata hannu in ya yi abu mai nisa ne ya rumgumeta, ita ce ma take sumbatarsa wani lokacin, ba ya wuce gona da iri sannan yana da kiyayewa har tunanin Ko dai ba shi da lafiya ne duk ta yi shi, bayan ya koma gida ya kirata sai da ta yi masa mganar da cewa.   "Wai ba ka ga lalli na ba ne, ko ka ce ya yi kyau? Sannan na yi gyaran jiki kowa ya ganni sai ya yaba amman ban da kai." Kai tsaye ya ce"Kin nuna min ne? Baki ta buɗe kamar ya na kallonta kafin tace"Au ba ka gani ba,? Kai tsayen ya sake cewa" Ni ban gani ba." Sai Mimi ta kasa mgana ganin zai yi wasa da hankalinta cikin raɗa ta ce" In dai ko ba ka gani ba, ko dai ko dai.? "Ko dai mene ne? Sai ta kasa mgana ta koma tana dariya ya fahimci maganarta bai san lokacin da ya yi sariya mai sauti ba, kafin ya ce "Yaro yaro ne. Yaro man kaza, Uhmm" Haka kawai yace bai ƙara yi mata wani mgana ba suka cigaba da hiransu ita ba ta san yadda yake iya surving ɗin rayuwarsa in har ya zo su ka haɗu ba, ko muryanta wanka ta ke saka shi in ko ya je ya ganta in ya dawo sai  y yi wanka dauriya yake yi ba ya so ya wuce gona da iri, kuma shi yana da kiyayewa ba ya son ya watsar da darajan auransa a kan titi shi ya sa ba ya rawan kafa wajen taɓa jikinta shi ya sa take tunanin ko ba shi da lafiya ne? Lalle ko zai nuna mata kwanjinsa da lafiyansa ƙila har sai ta fara cewa ita ta gaji.   Kamar yadda ya faɗa washegari ma'aikata suka karisa fenti, sannan a daran masu sauka suka fara, wani malami ne mai almajirai shi ya wakilta babban Almajiransa da yara goma suka kwana a gidan suka kuma sauke Qur'ani zuwa wayewar gari tare da sauran addu'o'i, zuwa safe kuma a ka sallame su da abun sadaka.Mansoor ya yi mgana da Inna kan gyaran gidan tunda an gama aiki sai Inna Meri ta kira ƴan'uwansa mata su Yaya Amina daman Hibba tana nab  ba su koma ba,Mu'azzam hutun sallarsa na Sati uuɗu ne sai bayan tarewar Mimi za su koma, su suka hadu har da Walida da Mariya da matar Auwalu da ya ce itama ta je ta kama musu suka je gidan suka share suka goge amman fa kowa ya san wannan gidan ya kai makura wajen haɗuwa,  har yamma suna can sai gabda mangariba suka gama gyarawa suka koma gida suna zuzuta ma Inna kyan gidan da tsaruwarsa.   Bayan kuma barowansu gidan ba daɗewa kayan Mimi suka iso, Khadi daman ta zo garin a ranar ita da Baaba Uwani da Anty Mama cewa ta yi ba ta jin daɗi, Mimi ta kira Aji ta gaya masa sai ya ce su haɗu a ƙofar gidan da kwatance da komai suka isa. Shi ya ba su key ɗin gidan suka kuma gaisa da shi  cikin mutunci. Masu kayan daman tare da masu haɗa su suke tafe a daran aka gama haɗa komai sauran ɗakunan kuma sai gobe, Ita kanta Khadi sai da ta yi santin gidan nan haka ta koma tana ce ma Mimi" ke ashe dai mijin nan na ki kuɗi ne da shi, Hajiya kin ga gida? Ma sha Allah wlh gida ya yi kyau Allah ya sa a shiga a sa'a" Hajiya ta amsa a fili Mimi kuma ta amsa mata a ciki,.Washegari Jawahir ta iso itama duk ba wani taro ba ne Yayan Yaddiko sun zo da su aka haɗu a ka koma gidan da sauran kayan Mimi na gidan Daddy aka gama gyaran gidan gabaɗaya.   Hatta bangaren Aji an saka masa kujeru a falo bedroom kuma gado da wardrope, ɗayan ɗakin daman ya ce kada a taɓa shi akawai abib da zai yi da shi,  babban falon Mimi kujerun ta kalan browna mai haske haka ma kalan fentin yake sannan cafet da komai kalan shi kenan da labule, kowani falo Bedroom guda biyu ne. To duka gadajen guda biyu masu ruwan browan ne mai haske sai ƙaramin falon aka maida mata Kujerunta na farko, da gadon ta ɗayan  bedroom ɗin kuma aka siya masa wani gado shima amnan ƙarami ne. Kitchen ɗin ta kuma ga fali da fili. Nan aka cika mata da kaya, firizanta guda biyu, bayan akwai wani a ɗayan bedroom ɗinta amman shi ƙarami ne ga kuma again fridge a wajen dinning, gaskiya gida ya yi kyau ma sha Allah suka turare shi da turaren kamshi sannan suka yi ta Video Khadi jiki na rawa ta turama Mommy da Madiha, ita kanta Madiha tasan gidan da take ciki a lagos bai fi wanda Mimi za ta shiga ba yanzu duk kushenta sai da ta ce"Woww gidan ya yi kyau Khadi. Ko dai haya ne ba na shi ba ne? Khadi na dariya ta ce" Na shi ne to ko wata biyu ba'a yi  da fara gina shi, Kuɗi ne da bakin mijin nan na Mimi wallahi"   Madiha ta jinjina kai kafin ta ce"Na ga alama wato abun na shi ma mugunta ce." Ita dai Khadi na ta yi mata dariya, Mommy kuma da ta gani ta yi ta saka albarka da tarin addu'o'i, Rukky ta zo itama daga baya ta ga gida ya yi kyau ɗas da shi itama ta saka albarka washegari ya kama jumma'a a kuma ranar Mimi za ta tare. Daga nan bayan sun gama gyaran sun rufe gidan tunda akwai megadi suka koma gida suna ta ƙara Koɗa kyan gidan, Rukky kuma tana ciki tana na taya Mimi haɗa kayanta na gida a daran suka fito da akwatin da suka haɗa reras guda takwas cike da kaya, bayan waɗanda a ka dinka, kowa nata mamaki Hajiya ce kaɗai tasan da maganar kayan kefe. Sai Mommy amman ita ba ta gani ba Mimin dai ta sanar da ita.   Khadi na ɗaga kaya tana santi ta gaji dai ta ce"Ke wai a ina aka haɗa kayan nan ba mu da labari ne? Rukky ce ta ba ta amsa da Cewa" Anan garin mana cikin azumi muka yi ta shiga kasuwa har da shi, ina gaya miki Anty Khadi Atm ɗinsa ya bamu muka siya komai da komar bai karɓa sai kwanan bayan mun gama duka shirin mu." Khadi ta zaro ido kafin ta ce"Kai kaji rabo, kuma kuɗin ba su ƙare ba? Rukky ta ce"Ko girgiza kuma mun kashe kudi ya yi miliyan huɗu wlh," Sai kowa ya fara hinjina kai, ƴayan Yaddiko na ma juna gulman daman mai kuɗi ne, Rukky ke ta kora jawabi da cewa" Daman fa da kuɗinsa, kwai dai yana da dalilinsa ne tun fark. To ɗan kwallo ne fa kuma Babba wallahi an ce suna samun mahaukatan kudaɗe."   Khadi ta ce"Na ga alama. Muhammad ma ai ya faɗa min na ga kuma zahiri, ga gida ga lefe ina ga sama da miliyan talatin sai da ta yi kuka kai jama'a, amman ya shammace mu." A na ta mata dariya ba ta gaji ta kara gyarawa tana ɗaukan Video ɗin kayan nan da nan ta tura ma Dr da Madiha da Mommy ta ce lefen Mimi ne,.Daman Mommy ta san da maganar ta na gani ta saka albarka amman ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da darajarsu, Madiha kan sai ta kasa magana ta ce au har da lefe an yi ne? Khadi ta ce ga zahiri nan ta na gani lefe ne na gani  na faɗa. Dag anan bakin Madiha ya mutu ta ji daman ta zo domin ta ba ma idanuwanta abinci amman dai za ta yi koƙari ta zo ko da baya ne domin ta ga komai da Idanuwanta.   A daran suka gama haɗa komai, bangaren kayan gara ma Daddy ya aiko da shi komai buhu, itama Mimi ta kara siya ma kanta abin da take so, kamar irin su kayan kamshin girki da zannuwan gado na kamfanin FHB CLOTHING domin zamnuwan gadon su masu inganci ne, shi ya sa Mimi ke yaba kayan su, in kina so kema ki samu zannuwan gado masu kyau kamar irin na Mimin Aji nemi FHB CLOTHING Phone no 08034109622 Wtsapp no.08080266674    Sun yi mgana da Aji da asuba a kan mganar Walima ita Mimi ta so a bari sai ranar asabar amman Gogan yace a ranar Za'ayi komai a gama shi.Saboda haka ta yi duk abin da ya kamata kafin biyu tana gidanta sai a yi waliman daga lokacin zuwa dare, Da ta gayama Hajiya da su Khadi su ka ce hakan ya yi zaman me za'a yi dama tunda ba wani gagarumin taro ba ne, Rukky ta faɗa ma su Aisha Farida da su Glorin na wajen aikinsu amman direct can gidan za su sauka tun da a matsayin walimar gidan a ka gayyace su. Tun safe Mimi ta yi wamka mai kwalliya ta zo ta yi mata sannan sun kira mai hot. Wani leshi Mimi ta saka ɗinkin riga da sikat kayan sun karɓe ta matuka ta sha hotuna ma su kyau da yarari. Gidan ba kowa daga su Khadi sai Anty da ta zo da safe da Yaddiko da ƴayanta,  Rukky ma tun safe ta zo ita da Bibi, suma sun sha kwalliyar su gwanin burgewa, Mama ma ta zo ita da ƙannen Jahedd wanda dole dai ya hakura da Mimi tun da Har Daddy sai da ya kira shi ya yi masa fata fqta, sannan tun bayan abin da ya faru tsakaninshi da Mimi ya fara kokarin cire ta a ranshi tun kuma bayan sallah da ya tafi bai dawo ba amman ya yi ma iyayensa alƙwarin cire soyayyar Mimi a ranshi domin ya gina sabuwar rayuwa.   Rukky har video ta saka Mimi ta yi na waƙar kewa na mawaƙi, Auta waziri ta kuma tura ma Nasir. Shi kuma bayan ya gani sai ya tura cikin group ɗin su ya yi tagging ɗin Aji da cewa"To kai fa Aji ka ji, maganar gaskiya yau kada ka ɗaga kafa Amarya ta ce ta yi kewar ka." Su Ahmad suka fito suna ta dariya shima yana gari bai koma ba shi da matarsa,Aji kuma bai ma ga sakon ba sai daga baya yana gani ya yi delete for everyone, Nasir na ganin haka ya ƙara turawa Aji ya sake gogewa tun da dukkansu kowa admin ne, Har wajen sau uku, Aji na ganin haka ya danna ma Nasir kira yana ɗagawa ya ce. "Nasir miye haka?  Hoton matata ne zai sama abun wasan ka? Nasir na dariya yana kwaikwayon waƙan" Kewa. Kewa. Nayi kewar masoyiya." Aji ya ce"Mallam ka goge shi a wayarka tunda ko a shari'a ya haramta ka riƙa ganin hoton matata, to wai ma a ina ka samu wannan Vedio? Ni fa ban da shi" Nasir na dariya ya ce" Baby Rukky ta tura min." Aji ya girgiza kai kafin ya ce"Lalle ne ma,." Daga haka ya katse wayar ya kira Mimi, an ci ko sa'a Rukky ta ɗauki wayar Mimi na ɗakin Hajiya kai tsaye ko ya ce mata me ya sa ta tura ma Nasir video ɗin Mimi? Sai tacl ce saboda ba ta da lambarsa ne. A dakune ya ce" Ki goge shi haka kurum ni ban ga adon matata ba wani gardi na can na gane min hakan adalci ne?   Rukky na danne dariyanta ta ce ya yi hakuri za ta goge, sannan ya ce yauwa ya kashe wayar ya bar Rukky na dariya. Kamar haɗin baki sai ga Nasir ya kirata nan fa ta sabar da shi abij da Aji ya ce ya na dariyan mugunta ya ce"Kyale shi, nima ai ya kirani ya na min surutu." Rukky ke gaya ma Mimi abin da ya faru, Mimi ta harareta kafin ta ce" Ke ma da gulman tsiya, Mijina bai ga kwalliya ta ba sai saurayin ki.? Rukky ta ce"Na bani, ni da masu miji miji ko? Mimi ta yi mata fari kafin ta ce"Kwarai, masu miji ehe." Nan Jawahir ta zo ta same su Mimi ta gaya mata abin da ya faru tana dariya ta ce"Maganar gaskiya ba'a kyauta ma Ango ba dole ranshi ya ɓaci, ke kuma Rukky baki kyauta ba." Mimi ta fahimci suna mata shakiyanci ne sai ta bar musu wajen kawai.   A can gidan Inna Meri ma kamar tana sake sabon biki, makota sai zuwa suke yi daga can anguwan Arawa. Har da su Gaje domin Bintu ce ta shiga da gayya ta sanar da su Mimi za ta tare a sabon gida, ita kuma ta biya gidan Jummai ta gaya mata ta kuma san za ta gayama Zuwaira,. Sai ga shi har da Maeesha ta zo tunda ta dawo daga wankan gidan,  Zuwaira ma ta zo Magajiyar ce kawai ba ta zo ba Mariya daman tun jiya tana gidan Har da matan Auwalu da ta daina adawa itama tunda mijinta ai yana gaya mata irin taimakon da Yayan Inna Meri suke yi ma rayuwarsa. An ci abinci shinkafa da alala lemuka da ruwa kam duk na gora ne aka yi ta sha ana guzuri. Daman sun ce za su je gidan su Mimi bikon ta daga nan sai su ƙarisa gidan gabaɗayansu suka yi gungu suka tafi, Inna kaɗai suka bari a gida da Dije matar mallan Hashimu sai yara har da su Gaje sun tafi Maeesha kuma daman ganin kwakwaf ne ya kawota kuma ta ga irin daular da Inna ke ciki saura kuma in ta je gidan su Mimi ta sha kallo.   Sai da suka yi azahar wajen uku saura sannan suka hau adaidaita suka tafi, ba su ko jira kowa ba  Hibba ta kira Mu'azzam ya ce suna gidan Makama kafin ma su kariso sun yi nisa shi ya sa kawai ta ce bari su tafi, Suna shirin tafiya ne sai ga Nafisa matar Nasir da Fati matar Ahmad sun zo gidan yi ma Inna murna. Dalilin su ya sa ma suka kai har biyu a gidan Inna sannan suka tafi, sai dai Mimi ta gansu kwatsam tunda ba su gaya mata za su zo ba, Bintu ce uwar faɗin sun zo ɗaukan Amaryansu ne. Rukky ta ce"Kwa dai jira dai mu miƙa ta can gidan ko? Hibba ta ce"Ai ta mu ce tuntuni, saboda haka a bamu matar mu mu mikata gidan ta da kan mu." Ana ta raha ana dariya an kawo musu abinci su ka ce sun koshi amman irin su Jummai sai da suka ci, suna ta mamakin girman gidan sai ma su ka ji an ce nan ɗin gidan kakkaninta ne Gidan iyayenta na Abuja su Gaje sun sha kallo irin su Maeesha sai zaran ido ba baki ai tuni ta raina kanta. Mimi ta yi ma Rukky raɗa kunne da cewa" Ga kishiyar can" Ta na nuna mata Nafisa da ido wacce ke ba ma yarinyarta nono, Rukky ta ga ba ta da aibu kwata kwata ga ta doguwar mace sai dai kawai abun namiji amman mai mace har Nafisa ai ba shi ba sake kallon wata ua mace sai dai su daman maza haka Allah ya hallice su.   Duk saurin da a ka yi sai da suka kai la'asar a gidan Hajiya tun da sai bayan oa'asar ɗin su Mu'azzam suka zo da motociin, Ahmad ne ya tuka motar Aji a motar Mu'azzam a ka ɗauki Amarya da yake akwai motocin gidan Daddy wajen guda uku shi ya sa kowa ya samu har da su Hibba kuwa, Kuma daman su Anty sun yi gaba tun ɗazu sun kai Yaddiko ta ga gidan daga can za ta wuce gida ba ta jin daɗi tana ta fama da kafa, Sun iske su sun ƙara gyara gidan ma sha Allah ya na faman ta shin kamshi.   Guɗa kawai ke tashi Bintu ne da wannan aikin, Khadi da Mama suka riƙe Mimi ta yi addu'an sosai sanman suka shigar da ita tana nannaɗe cikin lafayanta ja. Gida fa ya yi kyau turbakallah masha Allah, Walima a ka ce za'ayi Mama ce ta gayyato wata malamar Islamiya an kawo Mimi ba daɗewa ta zo. Bayan ita sai ga yan wajen aikin su Mimi Rukky ta fita bakin hanya ta shigo da su ta bakin Aisha Farida ta ce aiko daga yanayin anguwan za ka san ta masu abin ne  Sai da suka ga gidan Mimi suka ruɗe, suna tambayan kuma gidan Sabo ne? Rukky ta ce"kwarai dal ma kuwa, kowata biyu ba'a yi da fara gina shi ba a ka gama sh." Haka suka riƙa zagayen gidan suna buga sqntin an raba cake da nama a  babban falon gidan aka taru malama ta yi nasiha sannan tare da addu'o'in sabon gida na awa ɗaya sannan a ka tashi kowa na saka albarka, Maeesha dai ban da yaƙe ba ta komai gassadan ma ta kasa samun muhalli domin daga gidan har kayan gidan kowa yasan na alfarma ne. Ta kuma ƙara yardan ma kanta Mimi ba sa'ar karawarta ba ne.   Ana gama walima ba wanda ya tsaya har su Khadi sun tafi.Su Hibba kawai a ka bari a gidan su Gaje ma sun tafi tare da su Maeesha,  daga Nafisan Nasir sai Fatin Ahmad ma ta koma gida ta yi girki. Su aka bari da ƙara gyaran gidan Rukky kuma na tare da Mimi nan suka yi sallar mangariba bayan sun gama gyara Ko'ina sannan suka yi shirin tafiya,  da wuri suka ce za su kawo Ango shi ya sa su Yaya Amina suka tasa su Mariya har da Bintu zuwa gida Hibba kawai a ka bari saboda mijinta da ita da Nafisa da Rukky, suna ƙara ɗan gyara gidan Mimi ta yi wanka ta sauya kaya anguwan ga su da ruwa ita Mimi Bahol gare ta ma ba ta da wata matsala. Ana idar da sallar Isha'i Angawayen suka shigo su biyar Ango dai ya yi shigar wata deep blue ɗin shadda tana yarari da maiko ga hula bakar dara da takalmi sau ciki sauran kuma kowa dai ya saka manyan kaya, Mu'azzam ne ɗauke da ledojin kaza, Sai kuma sun shigo da katan katan ɗin ruwa sai kayan tea da buredi siyayya fa da yawa, Rukky na yi ma Ajin tsiyan wato dai in ya fara cin amarci ko Kofar gida ba zai fita ba.   Yana shafa keyarsa ya ce"Ashe kin gane.". Sai ya bar su Nasir da yi masa tsiyan bai isa ba sai ya fito. Falo Mimi ta fito suka haɗu suka yi musu yan nasihohi daman a auran farko ba su aiwatar da wannan al'adan ba, Saboda Nafisa na wajen ya sa Nasir bai yi rawan kafa akan Rukky ba. Dukkansu sun kame kansu,  Aji ya duba agogon fatan hannunshi ya ga tara har ta gota kawai sai ya kalli Mu'azzam kafin ya ce" Lokacin ku ya kare fa, kwashi abokan ka da matanku ku je na gode sai Allah ya kai mu." Suka saka masa dariya gabaɗaya Nasir na masa raɗa a kunne shi kuma ya daki Kafaɗansa yana yar fariya, da za su tafi ko Rakiya bai yi mu su ba iyakarsa ƙofar falo suna fita ya rufe kofa. Makama a ka bari da kai Rukky gida roƙonsa Nasir ya yi, shi kuma ya ɗauki matarsa, Ahmad kuma ya bi Mu'azzam da Hibba za su sauke shi a gida. Hankula sun kwanta tunda Mimi dai ta tare a gidan Aji a karo na biyu.   Ajin na jin buɗe get da alamun fitan su ya sauke ajiyar zuciya ya ƙarisa kusa da Mimi ya ɗago ta daga zaunen da take cikin mayafinta tana tashin kamshi, kai tsaye ya rumgumeta cikin natsuwa suka yi luf a jikin juna suna shaƙan kamshin turaren Juna, sun ɗauki wajem minti goma a haka sannan ya ɗago ta ya yaye mata mayafinta suna kallon juna cikin wani irin murya ya kira sunanta "Fatima.." Da wani salo ya kirata da ya sa ta ji ta ƙara narkewa cikin sanyin murya ta ce"Na'am.." Kallonta kawai ya ke kamar ya ga ta sauya masa sai da ta shafa fuskarsa tana faɗin"Kallon fa? Na sauya maka ne? Numfashi ya fesar ta baki kafin ya ce"Eh mana, kin ƙara kyau, duk da daman ke ɗin mai kyau ce." Mirmishi ta sakar masa kafin ta ce"Ajin Mimi ma ya yi kyau sosai." Riƙo ta ya yi lokaci ɗaya yana sagala hannunsa ta wajen kugunta kafin ya ce"Kin yi sallar Isha'i? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ya cigaba da faɗin" Wannan tarewar ta sha bambam da auranmu na baya, wannan da niyar ingattaciyar zamantakewa ne a tsakanin mu saboda haka mu je ki yi alwala nima na yi domin mu yi sallar da Annabi ya umarce mu da yi a daran farko tare da roƙa mana Zuru'a mai albarka  da zaman lafiya." Tana Mirmishi ta ɗaga masa kai kafin ta ce"To mijina." Ya kalleta ta kalle shi sai kawai ya sumbaci goshinta suna rike da juna har zuwa cikin Bedroom ɗin, tare suka shiga tiolet ɗin daman diukkansu suna da alwala sun dai sake sabunta ta ne, sannan suka fito a tare ya shimfaɗa musu sabuwar sallayar da ya gani nan saman gado, yana gaba tana bin shi a baya sai da suka yi raka'a Takwas sannan suka zauna ya ɗaga hannuwansa sama itama ta ɗaga yana ta yi musu addu'an zaman lafiya sannan daga karshe yace Allah ya tsare su daga dukkan wani sharri. Daga karshen karshen ya ce Allaha ya jikan Iyayensu su kuma ya sa su tafi a sa'a cikin aminci.   Daga nan ya miƙe zuwa falo ya ɗauko ledan kazar amarcin sa yana faɗin"Amarya Fatima mai kazar amarci guda biyu." Mimi ta sunkunyar da kai tana faɗin"ɗaya dai wancan ai ban ci ba." Yana kallonta ya ce"Oh ni dai ai na kawo miki saboda haka ki shirya. Sau biyu zan fanshe kaza ta." Kunya ta ji ta kasa mgana, ita ta je kitchen ta ɗauko baban tire da kananun kofunan atangaran suka baje kajin da yan shilla ga madaran hollandia. A baki ya rika bata in ta ce a'a sai ya ce"Gwara ki ci ki samu energy domin Allah zan fanshe kaza ta dakyau ne." Ba ta ci da yawa ba ta dai sha madaran shi kuma kusan kaɗan ya rage ya ɗora da madaran ya kwashe komai ya maida kitchen sauran kazan da madaran ya saka a Fridge, yana dawowa ɗakin ya iske ta fesa turaren Air fressher. Sai ya ce ko za ta yi wanka sai ta ce ta yi wanka, shi kuma daman ya zubo wasu kaya kafin ya yi parking suna can ɗakinsa ya ce bari ya je shi ya yi wankan yana zuwa.   Fitan sa  ya sa gabanta ya ɗan daina faɗi amman ita kanta ta san yau mai kwatan ta sai Allah, kayan jikinta ta cire ta saka wata ta barci mai kauri amman doguwa ce, Sannan ta kuma maka mayafi amman sai ta yi ma jikinta wankan wata humra ce mai azaban kamshi. Sama da minti talatin sai ga shi ya dawo ɗakin da jallabiya yana tashin kamshi shima, yana shigowa kuma ta ga ya kwaɓe jallabiyar jikinsa daga shi sai ƙaramin wando ta juya baya gabanta na faɗuwa, ba ta san ma ya kariso gabanta ba sai da ta ji ya rumgumeta ta baya yana tusa kansa a tsakanin wuyanta lokaci ɗaya yana faɗin"Kina zargin ba ni da lafiya ne gwara na fara nuna miki lafiya ta ƙalau.". Ba ta samu zarafin mgana ba. Ta ji wani abu na yi mata yawo kamar sanda daga bayanta jikinta ya fara rawa, shi kuma yana ta shinshinanta, kafin ya juyo da ita suna kallon juna Idanuwansa a lumshe ya zare mata mayafin jikinta kafin y ace"Shekaru sama da goma ina jiran wannan daran, Fatima ki ba ni dama ni da ke mu zama abu ɗaya."   Jikinta sai rawa yake yi. Sai ya jawota ya rumgume yana faɗin" Ba zan miki da zafi ba, amman ka da ki yi min raki kin ji ko? Sai ta gyaɗa masa kai ta na ji tana gani ya Kashe hasken ɗakin sannan ya ja ta samman lafiyayyan gadonta suka kwanta, Ba za ta iya sanin duka abin da ya faru ta dai san sun rabu da duka abin da ya yi musu shamaki da fatar jikin juna.Sannan Aji ya yi ta lashe sassan jikinta cikin fitar hayyaci ta yi masa rawaj jiki sosai da rawan murya. Ta ɗauka abun iya romancig ne domin ya yi dogon wasa da ita har ta manta a inda take ta riƙa ƙamƙamesa tana jin kamar za ta shiɗe, ai sai ta ya kai ta makura sannan ya ɗauki hanya bayan ya karanta Addu'ar Saduwa da iyali da farko daman a sannu sannu ya riƙa bi da ita sai da ya isa bakin boda sannan ya kara ƙarfin gudunsa, Mimi ta dulmiya duniyar jin daɗi ai sai ta ji daga duniyar ɗaɗi ta koma zuwa na zafi zafi da raɗadi ƙoƙarinta na ture shi amman ina ya riga ya yi mata rumfa, ya shiga amman ya kasa kai da kawo saboda ji ya yi wani irin daɗi  na ratsa shi kamar zai mutu tun daga tafin kafar sa har cikin ƙansa, bai san ya ɗauki lokaci a waje ɗaya ba sai da ya ji ya ƙara rike Mimi gam, sannan ya fara motsawa daɗi kaɗan ya rage bai saka Aji ya zauje ba, ya yi alƙwarin bi a sannu amman ya saɓa kuma Mimi kan ta gurzu kuka ya kuma sha raki. Shi dai kam bayan mintina talatin sai ya ji kamar bai koshi ba, Mimi kuwa kuka har da majina shi dariya ma ta ba shi.   Ya jawota jikinsa ya rumgume yana faɗin" Daman ya ya lafiyan kura ballantana ta yi zawo." Hannu ta saka ta ture shi cikin jiniyan kuka tana faɗin"Wayyo Allah na zafi." Sai ya duka yana faɗin" Mu ga ni, ko kin yage ne? Saboda haushi kafa ta saka ta matse masa wuya shi kuma sai ya kai hannunsa wajen da ta ji zafi sai ta sakar masa ƙara. Da Sauri ya cire hannunsa yana faɗin"Da zafi ko? Sorry mu je mu yi gashi, nima na wahala Allah duk kin kurje ni." Kasa ma magana ta yi, Shi ya taimaka mata ta mike, ya rufa mata mayafinta a jikinta shi kuma sai ya saka ƙaramin wandon sa suka shiga tiolet suna da wajen ruwan zafi da na sanyi ya tara mata a Jucuzzi ta shiga tana ta kukan ya fita ya ba ta wuri za ta iya taimakon kanta, Aji na dariyan jin daɗi ya ce"Ikon Allah taimakon ki fa zan yi." A tsiwace tac e"Ban so, ni dai ka fita." Saboda ya na tsaye ya na kare mata kallo ne kamar wani maye. Sai kawai ta ga yana shirin cire wando lokaci ɗaya yana faɗin"Nima gashin zan yi ma kaina  tunda nima ai saurayi ne kin yi disvarging ɗina"   Mimi ba ta san ta yanka masa ihu mai ƙarfi ba tana runtse ido, ya na jin haka ya fita yana ntoshe kunne, ya koma ya kwanta kan gado ya na shafa kirjinsa. Wlh daɗin da ya ji kamar zai mutu haka yake ji. Kusan rabin awa Mimi ta yi bayi sannan ta fito tana tafiya sannu sannu ya taikmata ta zauna gefen gado sai ya ce shima bari ya je ya yi wanka ya na shiga ta juya ta ga zanin gadon jini kaɗan ne ya ɗiga sai kuma abib  da ya ɓata shi shi ya sa ta rarrafa ta cire shi ta nannade shi ta tura cikin wardrope tana ƙokarin shimfaɗa wani ne ya fito ɗaure tawel ganin ta na yi tana cije baki ya sa ya karɓa ya taya ta shinfiɗawa,  shi ya taimaka mata tasha fa mai ta sauya rigar barci shima kuma ya gyara jikinsa suka koma suka kwanta kamkame da juna har da makara sallar asuba.   Duk halin da Mimi ke ciki zazzabi na meman kamata amman sai da Aji ya lallaɓeta ya kara yi bayan asuba. Ai ko ya ga ɓarewan baki kuka ta rika yi masa shi kuma yana rufe mata baki lokaci ɗaya yana faɗin"Ɗan shiga fa kawai na yi na fito, ji yadda kike ihu kamar wacce na yanka." Gwiwan hanunta ta saka ta matse masa ciki, ya sake ta yana dafe wajen kawai ita kuma sai ta juya ta cigaba da kukanta haka nan ya sake biyota ya rumgumeta ta baya yana faɗin" Shike nan daina kuka. Bazan ƙara shiga ba sai kin neme ni." Ta na kuka amman sai da ya saka ta dariya, Haka nan ya saka ta kara yin wani wankan da kuma gasa ƙasanta, duk kanta ya jiƙe shi ya sa ta so ta yi kitso Rukky ta ce ta bari sai an kwana biyu.   Da gaske Aji ya gajiyar da ita haka ta kwanta ta a ta barci sai wajen goma saura ta ta hi lokacin har an aiko musu da abin kari daga gidan Inna da kuma gidan Hajiya, Sai da ya jirata ta yi wanka ta saka wata riga mara nauyi gajera iyakarta cinya suka fita falo suka karya shi ne ke ba ta a baki tana ɓare masa baki tana kuka hawaye shaɓe shaɓe, har dai ya gaji ya ce" Shekaran ki nawa ne wai? Tana sharan kwallah ta ce"31." Hararanta ya yi kafin ya ce"To ke yarinya ce, ji yadda kike ɓaremin baki kamar na yi ma ƴar shekara tara fyaɗe ? To sannu yar gata nima fa ya kamata na yi kukan nan domin tare muka y..." Bakinsa ta rufe masa da hannyenta tana faɗin"Don Allah fa" Ta faɗa cikin shgwaba sai ya koma yana faɗin"To na ga dai yara ma ƙanana basa wannan kukan, kuma ma Allah na tuba me na yi? Ban fa shiga duka ba sai an juma zan ƙara jarabawa na gani." Mimi bakinta ya mutu shuru kawai ta yi, Ranar ba wanda ya zo gidanan an bar su huta abinci kuma safe da rana da yamma duk daga gidan Hajiya da Inna sai da Mimi ta kira waya t ace a daina kawowa yana musu yawa Allah ya sa ma ga Maigadi.   Dakyar da magiya Aji ya ɗaga mata kafa na kwana biyu sannan ya cigaba da amarcinsa, Mimi na gurzuwa in ta yi kuka sai ya ce ita ai ba yarinya bace, kuma wai har ya na cewa zai rama zata neme shi, shima sai ya yi yanga.  Mamaki ya ke ba ta wannan azaban abun ne za ta nema Allah ya tsare ta. Baya barinta sukuni a dare a yi da asuba ma da rana ma haka ta gaji, Ko da yaushe cikin gasa kanta take yi. Baya ɗaga mata kafa sai ya ga tana kukan da gaske yake kyaleta, kwana huɗu suna gida ba su fita kuma ba wanda ya zo, domin shima sai a ranar ne da yamma ya je ya gaida su Inna sannan suka yi sallama da Mu'azzam za su tafi washegari da safe.   Itama a ranar Khadi ta zo gidan ta yi mata sallama ta ga Mimi duk ta faɗa ta fara mata dariya, ita da Jawahir Mimi ta marairace amman ba ta yi mgana Jahawahir ne ke bata shawaran ta riƙa cin abinci sosai tana kuma sakin jikinta, ta kuma kula da gyara kanta,  sai a kwana na shidda ne Rukky ta zo gidan da yamma itama daman ranar litini za ta koma aiki. Har dare tana gidan Nasir ya zo tare da Aji Mimi ta ce daman ba don Allah yazo ba don Rukky ne ya ce to hakan ma da ta ɗauka dai dai ne. Tare da suka fitan da Rukkyn zai kaita gida washegari asabar kuma tun safe suka tafi gidan Inna sai dai Inna ta gansu kwatsam tun da bai gaya mata nan ya barta ya je Camp ya dawo. Sannan ta taya shi ya tattara kayan shi tunda ya ce zuwa gobe zai saka a maida masa komai can har Injinan traning ɗinsa,  bayan azahar suka bar gidan Inna zuwa gidan Hajiya suka gaisheta ba su daɗe ba suka tafi gidan Daddy sai su Mama shi baya gida nan ma ba su daɗe ba Daga nan suka biya kasuwa Mimi ta yi musu Cefane suka dawo tunda ta ce ta yi sati ɗaya ya kamata ta fara yin girki.   Washegar lahadi jigilan kayansa ne da Injinan training ɗin sa ya kwaso zuwa gida nan a ka saka mai cikin ɗakin da ya ce zai yi amfani da shi kafitar kuma can ya bar ta saboda baƙin kwana.Sai sauran tarkacen kayan kwallon sa da kyaututukar da ya samu a cikin kwalaye aka sako su. Kayan sawan shi na gidan ya kwaso gabaɗaya na Camp ma haka sai abin da ba'a rasa ba.   Ranar kuma Mimi ta fara girki, ta yi ma Inna kula ita da Hajiya, Aji ya ce har da Baba kuma da kansu suka kai musu da shi kaɗai zai je Mimi ta saka rigiman ba zai barta a gida ita kaɗai ba. Dole suka tafi tare gidan Wanzamai ne karshe suna can har goman dare abun mamaki Magajiya na maraba da su a ɗakinta ma suka zauna suka jira Baban kafin ya dawo, ba harara ba bakar mgana sai ma sakin fuska har ɗakin Meesha Mimi ta shiga sun gaisa da Baban ya dawo yana ta saka albarka wajen goma da rabi suka koma gida a gajiye suke wanka kawai suka yi suka kwanta amman da Asuba Aji bai barta ta huta ba, ga shi ranar za ta koma aiki tunda ta tashi ba ta koma ba tana kitchen ta na aiki shi kuma yana can yana motsa jiki,   Kafin bakwai ta gama komai dukkansu sun yi wanka. Tare suke karyawa cikin soyayya kamar yadda suka saba Mimi ta ci hijabinta jalbab  har ƙasa Aji ya kaita tunda motarta na gidan Hajiya sai ta ta shi aiki za ta biya ta ɗauka bayan ya kaita ya dawo gida ya kwanta yana barcin gajiya, a can wajen aiki kuma ana ta ma Mimi  murnan sabon waje Rukky kuma da suka haɗu tana mata tsiyan amarci ya karɓeta ta yi wani irin kyau na ban mamaki. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3013* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI *08089965176* *07084653262* Haka suka sake cinye wannan satin cikin soyayya da ƙaunar junansu. A satin kaf saboda yana da free time shi ya kan kaita wajen aiki da safe sannan ya je ya ɗaukota in ta kira shi ta ce ta tashi aiki, duk da ta ɗauko motar ta amman ba ta fara fita da ita tukunna ba. Zaman su suke yi lafiya cike da kauna da muradi. Ba mai zuwan musu gida an ba su ookaci su mori lokacin su, kuma sun mora gani suke yi a lokacin sun fi kowasu ma'aurata fahimtar juna da son juna. Soyayyar su ta shekaru goma ta koma kamar sabuwa sun baje ta kawai suna jan harafin su. Kamar Yadda Aji ya faɗa haka ta ke gani domin ya ce daman in ta na son ganin soyayya sai a gidan auran su lalle ko tana ganin soyayya kala kala wajen Aji har mantar da ita kanta yake yi in suna tare, lalle ta yardan ma kanta shi dabam yake kamar yadda ya sha faɗa mata sunan mijinta Mansoor saboda haka ta bambamta da sauran wasu matan aure, ita dabam ce a wajen mijinta kamar yadda shima yake na dabam a wajenta. Wakeend ya ƙara zagayowa haka suka ƙara yini a gida suna jin daɗin su, ta taya shi suka gyara ɗakin sa. Ta jera masa kayansa a wardrope da sauran dai tarkacen sa, ɗayan ɗakin da ya saka injina motsa jiki kuwa ya koma na so su biyu. Saboda itama matsewa take yi cikin ƙananun kaya ta ce itama ta zo motsa jiki ranar farko da ta shiryo ta zo ya kalleta daga sama har kasa kafin ya ce" To ke wani jiki za ki motsa? Ki na da kitse ne? Mimi na lamgwaɓe kai lokaci ɗaya tana faɗin" Eh mana, ba na so na yi kiba ne kada na gagare ka ɗauka ka ƙaro min kishiya." Saboda dariyan da ta kama shi sai da ya sauke karfen dake hannunsa ya miƙe zufa na tsiyaya daga jikinsa ƙaramin towel ɗin da ta kawo masa ya ɗauka yana goge jikinsa sai ta yi saurin karɓa tana goge masa lokaci ɗaya tana faɗin" Eh mana ai gaskiya ne saboda maza yanzu ba ku san mata masu kiba." Ruwa ta ɗauko masa na gora ta buɗe masa ya karɓa ya kwankwaɗa kusan rabi sannan ya ba ta, ta karɓa lokaci ɗaya tana faɗin" Ba ka ce komai ba? Nuna min wanda ya dace da ni daga yau zan fara." Dariya ya yi har sai da sautin ta ya fito. Da dariya na yi masa wahalan yi amman tunda suka tare ta na yawan ganin dariyansa a kai a kai, yau ma shagala ta yi da kallonsa sai ji ta yi ya riƙo kugunta da hannunsa guda ɗaya yana faɗin" Yaushe za ki daina haɗa kan ki da wasu matan ne Mimi? Sannan sai zuwa yaushe ne za ki daina haɗani da sauran maza? Na sha gaya miki ke mijin ki sunan shi Mansoor bai zama lalle rayuwar auran ki ta zama dai dai da na wata ko na wasu ba." Sai ya ɗan dakata ya na kallonta kafin ya duka ya sumbaci bakinta lokaci ɗaya yana faɗin" Ni ba ruwana da kiɓar ki, ai ni ke na ke so ban damu da yanayin da za ki koma ba indai baki sauya da hallayan da na san ki da su tun farko ba. Sannan ba zan iya miki alƙwarin ba zan taɓa miki Kishiya ba, saboda in na yi hakan kamar na tsallake hurumina na faɗa bangaren Ubangiji, aure na Allah ne kamar yadda muka ga haka a zahirin auran mu, amman za ki iya yarda da ra'ayina? Wallahi tallahi ke kaɗai kin isheni rayuwar duniya Fatima amman in Allah ya nufeni da ƙara auran nan gaba to ki saka a ranki ba ki gaza ba, kuma ba ki kuskure ba sai domin sunnar ma'aiki da kuma abin da ya kaddaromin acikin kaddarata amman ke ce a jiya da yau da shekaranjiya har kuma gobe da jibin ma gabaɗaya." Ya gama faɗa yana rumgumota zuwa jikinsa. Sai ta kwanta saman ƙirjinsa kalamansa na saka ta mirmishi. Tana son Aji saboda hallayarsa ma su kyau yana da gaskiya da sanin ya kamata yana mgana cikin natsuwa ba ya nufin kuma ya yi mgana domin wani ya ji daɗi, iya gaskiyan yake faɗa, kanta ya ke shafawa lokaci ɗaya yana faɗin" Amman tun da kina som rage kitse ba zan hana ki ba, amman kada ki yi min raki, domin na ga kin ɗauka ɗaga Karafunan abun wasa ne." Dariya ta yi ya ja kunnenta yana faɗin" Bar dariya yarinya." Sai ta daina dariya ta sha mur ta sake shi lokaci ɗaya tana ɗaga power hannunta tana faɗin"Nima ina da karfi fa." Kallonta ya yi ta gefen ido kafin ya ce"To ai yanzu duk zamu ga ni." Wani ƙaramin Karfe ya ba ta ya ce ta ɗaga amman abun mamaki yana sakar mata kawai sai karfen ya bi ta zai danne ta da sauri Aji ya riƙe karfin ya maida shi mazauninsa ita kuma Mimi ta kai ƙasa da sauri ya saka hannu ya ɗagota yana kallonta itama shi take kallo cikin haƙi tana faɗin" Na shige su, daman haka abun yake da nauyi? Mirmishi ya yi lokaci ɗaya, yana faɗin" To daman mana? Kin ɗauka cin abinci ne ko aikin gidan tibin da kike zuwa ki zauna kawai ana ɗora miki camera? Ya faɗa lokaci ɗaya yana laƙuce mata hanci, Mimi sai numfashi take saki ta tsorata. Da sauri ta ce"Ba wani mai ßaukin ɗauka? Aji ya yi shuru kafin ya kai bakinsa saitin kunnenta yana faɗin" Akwai mana, gani ai ni ina da sauƙin ɗauka" Kallonsa ta yi kafin ta balla masa harara lokaci ɗaya tana faɗin" Ba wani sauƙi, duk kanwar ja ce" Ido ya zaro kafin ya ce"Au ni fa daman tausaya miki nake yi, amman tunda kika ce haka za ki gane baki da wayau yau. Sunan Hajiya da Mommy duk yau ba zai saka na ƙyale ki ba." Tana jin haka ta yi saurin faɗin" Daga wasa? Ya fara bin ta in da ta matsa yana faɗin" Ni kuma ga shi ban san wasa ba." Tana dariya ta ce"Haba Nawan. Haba mana ka ga fa ba mu ko ƙarya ba," Shi kuma ya ce za mu yi duk wannan daga baya. Ta kwasa da gudu za ta bar ɗakin ya tare ta cak ya ɗaga ta sama da nshi da komai ya ɗauketa yana faɗin" Duk anan karfina na yau zai ƙare." Ta fara yawo da kafafunta tana faɗin"Wayyo Hajiya, Mommy Inna ku zo ku taimake ni." Ya na tafiya da ita zuwa, ɗakinsu na barci yana fwaɗin" Su kaɗai? Ba ki kira Dr da Daddy ba, ki kuma ƙara Volume ba su ji ki ba." Tana ganin sun shiga bedroom ɗin su shike nan ta saduda ta miƙa wuya kuma kamar mugunta, sai da ta fara masa kuka sannan ya ƙyaleta shima dai ya ce saboda yana da tausayi ne amman yadda ta haɗa sa da wancan karfen haka zai yi mata. Sai bayan sun natsa sun yi wanka sannan suka yi zaman ƙaryawa. A lokacim Mimi ta yi masa mganar tana son zuwa ta ɗauko Hajiya ta zo ta ga gidansu, sai ya ce ta bari an juma sai su je su ɗaukota Inna ma yana son kawo ta itama ta ga gida ta saka albarka. Bayan La'asar suka sake wanka suka fita gari. Gidan Inna suka fara zuwa suka gaishe ta, ita kaɗai a gida suna gidan Walida ta dawo. Sun ɗan jima kamar awa ɗaya sannan suka tafi gidan Hajiya, ba su daɗe ba suka ɗaukota Baaba Uwani daman ita ta je ta ga gidan lokacin tarewan. Sun kawo Hajiya ta ga gida ta yi ta saka albarka har tana faɗin" Kai Mansoor ya mganar mu ne! Na fa ga ya maka na ji na gani ka zo mu daidaita ba zan bar ma Binta wannan gidan ba ya yi mata girma." Mimi na dariya ta ce"Hajiya na tare gaba na tare baya, ba ki da muhalli a wannan gidan" Shi kuma Aji ya ce"Kada ki damu Hajiya ke ma ai sai na gina miki wani gidan wanda ya ninka wannan kyau da tsaruwa." Hajiya ta ce"Shike nan kuwa an raba gardama." Haka suka zauna suna ta hira xuciyan hajiya kamar farar takarda saboda jin daɗin ganin Mimi na zaune lafiya da mijinta. Hana ta tafiya suka yi har dare sai da Mimi ta gama dinner suka ci sannan suka maida ta gida a tare Ranar litini Mimi ta fara fita aiki da motar ta in yana da morning traning wani lokacin ma ya na riganta fita, ko kuma su fita a tare, megadin su wani matashi ne daga can anguwan Arawa Auwalu ya samo shi, an san gidan su ba shi da matsala shi ya sa in Mimi ta yi abinci Aji ya ce ta riƙa zuba masa amman fa bai amince ta riƙa fita da kanta tana ba shi ba sai dai ta ijiye in ya dawo ya ɗauka ya kai masa. Kashedi iri iri Mimi ta sha shi da za ta koma wajen aiki.Kada ta riƙa mgana da maza ba ya son ta je ana haskata a gidan Tibi tana dariya kada ta manta ita matar aure ce, matar ma matar Aji. Ta san halin shi da mugun kishinsa na bala'i aikin ma ba domin Inna ta yi mgana ba da tuni ya rabata da shi, ita kuma saboda tana son aikinta ya sa take tsaka tsantaan. Tuni faman ta daina saka mayafi in za ta je wajen aiki sai dai hijabi, in kuma za ta saka mayafi sai in suna tare irin za su fita gidan Hajiya ko gidan Inna, shima sai ta masa yar shagwaɓa ta ce daga mota fa sai gida wane ne zai ganta ballantana ya ce wani abu, to in ta ce haka sai ya barta amman bayan haka sun zame mata kaya na ajiya kawai. Kimanin sati uku da tarewarsu. Ya ɗauko Inna ta zo itama ta ga gida ta yi ta saka albarka Baba Danjuma ya zo tare da su Baba Sani da suka ji zai zo su ka ce suma za su zo, Mimi kuma ta yi ta hidima da su sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Aji ya ɗauke su a mota ya maida su gida iyakarsa kuma daga Kofar gida shi tunda Inna ta bar gidan bai ƙara taka kafa cikin gidan ba Magajiyar ne baya son gani daman Inna ke kaawo shi kuma yanzu ba ta a gidan ba shi da abun ɗauka a gidan kuma, ya ɗauka sai ya shekara bai taka kafarsa a cikin gidan ba amman dalilin Magajiya ba ta da lafiya zazzabi da ulcer suka kwantar da ita har a gadon asibiti Inna Meri ta kira shi ta faɗa masa ya bar Mimi su je dubiya tare da su Bintu ya ce a'a, ta bari in zai je sai su tafi tare daman kuma Bintu ba ta matsa ma kanta ba sau ɗaya ta je ta duba ta gwara ma su Yaya Amina sun je sau biyu Inna kuma kullum sai ta je kuma ta yi abincin ta tafi da shi wazai hana ta? Ko an hana ta ba za ta ji ba shi ya sa yayan nata suka saka mata na mujiya. Kwanan ta uku a asibitin a ka sallamo ta, Kuma duk Aji ne ya yi hidima asibitin Ƴaƴanta nata da take ganin ba kamar su ba su da shi gwara ma kowa ma da Saddiqu duk ya wani susuce. Lagos ɗin ma tunda ya dawo bai koma ba, matan kuma daman duk a wahale suke Manssor din dai da Mu'azzam su ne nauyin gidan nan, Washegarin ranar da aka sallami Magajiya da daddare ya ɗauko Mimi suka zo gaisheta shima ko asibitin bai je ba amman dai ya tura ma Auwalu 20k, Sun iske har su Zuwaira a gidan da Saddiqu da matarsa, Mimi daman ta yo abincin ta zo da shi bai hana ta ba saboda ba zai iya hanata aikin alheri ba. Amman in da ba ta ce za ta zo da abincin ba, ba zai taɓa matsa mata ba, a hanya ta kuma saka shi ya siya kayan marmari ta ce ai ba za su je hannu rabbana ba. Ai ko duk sai suka yi tsuru tsuru sai ga Magajiya na amsa gaisuwan Aji da Mimi cikin rawan baki. Baba baya nan lokacin shi ya sa ba su wani daɗe ba. Mimi ta tura kyakyawan kulan abincin da ta zo da shi tare da ledan kayan marmarin gaban Magajiya, Saddiqu daman suna shigowa ya fice ko kallo bai ishi Aji ba. Tun bayan abin da ya faru ko ƙara ganinsa bai yi ba sai yau. Sai ga Zuwaira na godiya Magajiya ma na kwance tana faɗin" Na gode Allah ya jiƙan mahaifa." Mimi ta amsa da Amin Amin dama tun shigowarsu sun gaisa da su Zuwaira. Har Maeesha na ce mata hala aiki ne ya hana ta zuwa asibiti sai ta amsa mata da cewa wallahi, har yarinyar sai da ta ɗauka kafin su tafi, ta fahimci Maeeshan na so ta kara shige mata ne tunda har ƙofar gida suka rako su ita da zuwaira. Suna shirin tafiya sai ga su Baba Ɗanjuma da ƴan'uwasa Baba Ɗanlami ya ce ya kamata Mimi ta shiga ta gaida su Gaje ai Baba Baba Ɗanjuma ne kaɗai uban mijinta ba. Shi ya sa Mimin ta shiga gidan ta gaida su Gaje sun kuma ji daɗi kwarai duk da ba ta wani daɗe ba,.Suna hanyar komawa gida yaron Gwaggo Yalwa ya kira wayar Aji ya na gaya masa jikin Gwaggon ya ta shi kwana biyu, a tunanin Mansoor Inna ma ba ta sani ba saboda bai ji ta yi masa mganar ba sai kawai suka biya daga nan wajen Inna ya gaya mata halin da ake ciki sai ta ce daman ta kwana biyu ba ta je ba ya kamata ta shirya ta je ta duba ta, Aji dai ya ce ba zai samu halin zuwa ba amman ya na tunanin in ya samu sarari sai su tafi tare da Mimi tun da ba ta taɓa zuwa ba. Haka ko a ka yi, Inna ya yi ma shirin tafiya da kuɗin mota da abin da za ta je da shi, ita kaɗai ta tafi, Walida kaɗai aka bari a gida da farko har Mimi ta ce ta dawo gidansu ta zauna kafin Innar ta dawo. Gogan ya ce a'a bai gama cin amarcinsa ba. Ko ta koma gidan Bintu ko kuma a nemi wata mafitar to sai ga shi ma Mariya ta ce za ta zo ta ya ta zama har Inna ta dawo tunda jikin Magajiyar da sauki, shike nan sai a ka samu mafita Inna Meri kuma ta je ta iske jikin Yalwa sai a hankali daga kwana huɗu sai ga ta ta yi sati amman tana waya da ƴayanta suna jin halin da ake ciki. Ta ce za ta ɗan kwana biyu saboda ta kula da Yalwan an kaita asibitin Bauchi, Baba Yakubu ma ya taimaka, a gidansa suka sauka ana ta faman hidiman asibiti. Ganin Inna Meri sama da sati biyu ba ta nan ya sa suka yi magana da Mu'azzam gwara ya je Bauchin ya duba su, sun shirya tafiya tare da Mimi amman kuma sai zuwan su Mommy ya sa tafiyar da ita bai yu yu ba, shima a ranar bai tafin ba sun yi Meeting sai a washegari amman a daran sun je gidan Hajiya sun gaida Mommy da Inna Zainaba kano ta fara sauka shi ne suka ƙariso gamobe tare. Mimi ta yi mamakin ganin yadda Aji ya zauna suna ta hira da Mommy kamar ba shi ba daman Dr shima ya gaya mata suna waya sosai, balle Daddy da sai dai ta ji ya ce mun yi mgana da Daddy ya ce ya na gaishe ki. Washegari ya kama hanyar Bauchi tare da Yaya Halima da ta tambayi izini a ka barta sun je sun iske jikin yalwa da sauki amman duk ta rame Inna da matan Baba Yakubu ke kula da ita ciwon sugar ne bai kwana ba a ranar ya juyo amman nan ya bar Yaya Halima za su dawo da Inna nan da kwana uku, tun da nan gidan Baba yakubu za'a bar Yalwa saboda tana zuwa ganin likita sai zuwa gaba in ta ƙara murmurewa sai ta koma tunda can Karimu ma yana fama da kansa ne, ƴayan Gwaggo Yalwan ma kowa na ta kanshi da iyalansa ne. ***** Bayan wata ɗaya. 02:20AM. Suna ƙamkame da juna, ba su daɗe da samun natsuwa ba, sun yi wanka sun tsarkake jikinsu saboda babu kyau zama cikin najasa, sun lulluɓe jikinsu da bargo har zuwa cikin su, kansu na kan matashi guda ɗaya sun kuma juya suna fuskantar juna bayan sun kamkame juna kamar za'a raba su, Mimi nata wasa da suman kan Aji ba tare da ta yi mgana ba amman sun taru sun yi shuru suna jin bugun numfashin juna ɗakin ya yi duhu amman akwai iskar fanka kaɗan kaɗan yana hurasu lokaci ɗaya yana yawo da labulen window ɗin bedroom ɗin Aji. Kitso Mimi take yi masa sai ta yi sai ya warware duk ta yamutsa masa gashin kai, da ya gaji ya riƙe mata hannuwa lokaci ɗaya yana faɗin" Yarinya ta ga gashi ba irin na ta ba." Dariya ta yi masa ta na shafa kitson dake kanta a wajen aiki Aisha Farida ta yi mata da kuma ta ce a wajen aiki aka yi mata sai ta tuna diraman da suka kwasa tsakanin da Aji faɗa ya fara yi mata me ya sa ta je ta buɗe gashinta gaban maza, an taɓa yin wani kitso ne a wajen aiki ban da wulakancin? Ta yi masa bayanin a wani keɓantattacen waje ne maza ma basa shigowa amman ya kasa ganewa amman ya gargaɗeta kada ta sake yin irin haka baya so, dole ta koma tana ban hakuri domin ta manta waye take aure shi ya sa ta ba shi wannan labarin. Hannunsa ta kama ta ɗora bisa kanta tana faɗin" Ka ji bambamcin ko sai na yi maka bayani? Shafa kanta ya yi kafin ya ce"Tsawon gashi kawai za ki fi ni, amman santsi wane mutum? Ni fa da ina da barin shi ya taru da tuni na fiki gashi." "Me ya sa to ba ka bar shi ya tarun ba? Ai da yanzu sai ka fara kitso." Ta faɗa tana ƴar dariya kara jawo ta jikinsa ya yi lokaci ɗaya yana faɗin" Inna ba ta so ta ga na tara gashi, ni kuma ina so amman saboda ita na ke ragewa shi ya sa in dai zan je gida sai na saka huka saboda ba na son ta yi min faɗan na tara suma ban yi aski ba." Mimi ta kara tusa yatsunta a cikin sumar kansa da ya tara, sai kamshi take yi tunda ta na shan gyara kafin ta ce" Nima ina so zan dinga yi maka kitso ka ji." Sai ya tura mata kan yana cewa"Ki yi mana, Za ki tsefe shi da kanki ne yarinya." Ta fara curkuɗa masa kan amman kitson baya kamuwa da ta yi sai ya warware, gajiya ya yi ya janye kansa yana faɗin"Mu yi barci MIAJ." Galala ta yi ta na kallon shi a cikin duhun ɗakin saboda mamakin sunan da ya kirata, to a ina ya san tana amfani da wannan sunan? Tana cikin tunanin ya ɗago kanta ya ɗora saman kirjinsa ya kamkameta yana faɗin"Kina mamakin a ina na san wannan sunan ko? Bai ba ta damar mgana ya cigaba da faɗin" Na san ki, na san ke kike amfani da sunan Miaj da boyayyen account ɗin da kika buɗe saboda ni." Mimi ta zaro ido kafin tac e"Ka sani ka ce fa? To ta ya ya? Mirmishi ya yi kafin ya ce"Mun zama ɗaya lokaci ya yi da za ki san wasu abubuwan da yawa waɗanda ba ki sani ba Fatima." Goshinta ya sumbata kafin ya ce"Ina son ki, na yi miki wani irin so mai tsananin da na kusa mutuwa saboda soyayyarki Mimi, bayan dawowata daga gidanku da faruwar abin da ya faru kaɗan ya rage ban hqkura da rayuwa ta ba. Sanadin ki na sallama Komai ina tunanin in ba ki cikin rayuwata mafarkina bai cika ba, ciwon rasaki sama da shekaru goma ya ke damun zuciyata bayan ke ban ñara ganin wata mace da sunan so ko vurgewa ba. Shi ya sa na sha gaya miki ke ce a jiya da gobe da shekaranjya da jibi a cikin zuciyata ba ki da kishiya ke ɗin da na zaɓa tun farko na kuma ƙasa sauya ki Fatima. Soyayyarki ce duk ta wahalar da ni ta sakani na riƙa rayuwa dabam da na sauran mutane, gani nake yi duk abin da ya faru babanki ne ya yi sanadin faruwan shi da farko ba na bibiyanki saboda Ina so na manta dake amman daga lokacin dana fahimci ina sonki ba kuma zan taɓa daina sonki ba sai na fara bibiyan ki a lokacin kina Univesity of Ibadan har ranar graduation ɗin ku ina cikin makarantar ku, na ganki amman ke ba ki ganni ba." Mamaki ya kama Mimi cikin alj'abi ta ce"Ka je har ibadan? Aji ya gyaɗa kai kafin ya ce"E. mana, na je har hoton ki na ɗauka a lokacin zan nuna miki da safe, ina bibiyan duka motsin ki saboda ina so na gani ko kin manta dani sai na samu tabbacin ke ma ba ki manta da ni ba. Dawowarki Abuja ya sa na cire rai dake saboda na san mahaifinki ba zai bani auran ki ba,nima kuma na haramta ma kaina ke a lokacin na fita batun ki daga bibiyanki amman kin kasa fita daga rayuwata faɗawata harkan kwallon kafa ya sa lokacina ya zama ragagge. Sai ya riƙa ɗauke min hankali daga tunani da shiga damuwa amman na kasa mantawa dake, a cikin kirjina na ke jin kuna amman ina samun salama in nasan ke ma ba ki yi aure ba, kamar yadda nima ba wata ƴa mace a gaba na.Nasan ke ce mai accuout ɗin Miaj kuma ba wani ya gaya min ba a jikina na ji hakan ko daga yadda kike yawan bibiyata, amman ban tuna nuna miki na gane ki ba. Na dawo da sanin komai na rayuwarki ne daga fara aikin da gidan Tv hankalina ya tashi kin san ina da bala'in ki shi ba na so na ga wasu mazan suna yabon ki, ko suna ambaton kin birgesu, kuna nake ji in na tuna kina can kina birge wasu mazan, na kalli hiran da kika yi a gidan talabijin ɗin ku kina ba da labarin ki da yanayin yadda a ka riƙa comments na yabawa gare ki, kwana na yi ban yi barci ba sai na fahimci duk ɗauriyata ba zan iya ba Na fi ki farincikin haɗuwata dake a Dinner bikin Makama domin ganin ki ya sa na ji kamar zan iya samun ki. Sai dai na kasa ba ma zuciyata dama kan abin da take so saboda tunanin abin da mahaifinki ya yi min. Mimi wlh tallahi lokacin da Hajiya da Momny suka zo min da mganar auran ki kaɗan ya rage ban suma saboda daɗi ba na kwana farinciki da godiyar ubangiji na yi ta sadaka sannan bayan azumin Kaffara na yi azumi bakwai wanda na yi alƙwari tsakanina da ubangiji a kan duk ranar da na same ki zan yi wannan azumin. Na saka miki waɗannan sharuɗdan ne saboda ina tunanin zan iya rama kwatakwatancin zafin da na ji a zuciyata saboda rashin ki, Mimi saboda ke nake son shiga bangaren Inna in na ganki sai naji damuwata ta yaye, in na zo ban ganki ba sai na ji ni cikin kunci, ina tsokanarki Ssboda na ga fushin ki saboda kina yi mini kyau sannan ina so ki rika biyemin muna mgana a tsakanim mu, Mimi in na saka ki kuka ji na ke yi kamar zan mutu yadda na tsani kukan Inna haka ma tsani na ji kina kuka, lokacin da kika fara sakarmin fuska muka fara zama na fi kowa farinciki in da za ki tona zuciyata a Lokacin kamar farar takarda, ba a son raina na gayya miki mganganu ba Fatima har ga Allah zuciyata ne na ƙasa iya sarrafata ta manta baya shi ya sa na kasa ba ta haɗin kai ko dama kan abib da take so. Sai na yi yunkurin mu gyara zaman su sai wata zuciyar ta hana ni, sheɗan ya yi tasiri a kaina na so na yi ma kaina saken da zan ta nadama har na koma ga Allah. Har ga Allah ban ɗauka za ki tafi ba na ɗauka kamar yadda na ke sonki kina min son da ba za ki iya bari na ba bayan tafiyata ranar ban yi barci ba na yi ta nadaman abunda na aikata, a lokacin da baki nan na shiga tashin hankali kawai ina daurewa ne ina cikin zullumin da tunanin kada na rasaki a karo na biyu , ko ba ki zo min da wasu sharuɗɗan ba da addu'an iyaye da abokai na suka na gane gaskiya riko ba shi da amfani gwara na bar komai ya wuce domin nima na zauna lafiya cikin rayuwa mai kyau kamar kowa, abin da ya sa na gaya miki haka ina so yau ki sani tun bayan rabuwar mu da shekaru goma har yau har gobe matsayin ki bai taɓa sauyawa ba, I love u so much, ke ce mahaɗin farincikin rayuwata Fatima" Kafin ya gama magana Mimi har ta fara shessheƙan kuka. Saboda mganganun sun shige ta, ƙara wani kamkame shi ta yi kamar za ta maida shi ciki ta ƙara fashe masa da kuka lokaci ɗaya tana faɗin" Shi shi ne ka yi ta ba ni wahala haba mana." Haka ta ke faɗa ta na dukan sa a kirji shi kuma ya na jinta amman bai hanata ba haka ya ƙara rumgumeta kamar zai maida ta ciki lokaci ɗaya yana faɗin"Na sani, na sani amman yanzu komai ya wuce." Kuka mimi ta riƙa yi kafin cikin kukan ta ce"ka sa na kasa kallon wani ɗa namiji da sunan so, na kasa ganin kowa sai kai. Kowa ni yake kallo an ce naƙi aure kai na ke jira ba ni da tabbas a kaina kowa sei yace ka daina sona ni kuma ina da yakinin kana sona har gobe, aji ina barci da hotonka a saman kirjina, ina kuka a kan hoton ka saboda ina tunanin ka yi min nisa!. Me ya sa ka bani wahala!.? Ka bar ni ina zaman jiran ka shekaru sama da goma bayan kuma ma same ka ka yi ta ba ni wahala, me ya sa ka min haka? Kasan yadda n ke kwana kuka saboda kai? Ta faɗa tana kara fashewa da kuka lokaci ɗaya ta na dukansa da hannunta sai da ya bari ta yi har ta gaji sannan ya kamata ya sake rumgumeta ya haɗe bakinsu wake ɗaya na tsawon lokaci ɗaya sannan ya sake ta, ta lna haki ta ce"Da na rasa ka da bansan wani hali zan shiga ba, ina sonka, da ban same ka ba da na shi." Bai barta ta ƙarisa ba ya ƙara haɗe bakinsu waje ɗaya bayan ya maida ta kasa shi kuma ya zama yana samanta daga nan sai zencen ya sha bamban Mimi ta kamkame Aji tana sakin masa kukan farinciki shima ji ya yi kamar ya yi mata kukan saboda yanayin da yake ciki, ji ya ke yi kamar ya buɗe zuciyansa ya saka ta a ciki domin ta fahimci soyayyarta ta wahalar da shi. A Wannan daren masoyan sun raya shi ne wajen fallasa ma juna abin da ke cikin zukatan su, da safe Aji ya ɗauko hoton Mimi da ya ɗauka a ibadan a cikin wayarsa tabbas ko ya je, itama nan ta nuna masa Ajiyayun hotunansa na wayarta da kuma ma ajiyan sirrinshi in da hotunansa suke da ta saka a ka yi mata babban frame har da tsohuwarta wayar da tsoffin tasa tasan da suka riƙa yi ma juna a shekarun baya. Ya yi mamakin ganin har a lokacin ta na nan a jiye da duk abin da ya dangance sa. Ranar kasa fita ya yi itama haka sai kawai ta zama ranar tuna old momory ɗin su. Su yi dariya su ji haushin juna sannan su kuma koma su ƙamkame juna kowa na faɗin da ya rasa ɗan'uwansa bai san halin da zai shiga ba, tunda kowa ya san ba ma ɗan'uwansa wahala barin ma Aji sai ya yi alkwarin ba ta dukkan wani farinciki a zamantakewar su itama haka ta yi masa alkwarin ba shi dukkan wani jin ɗaɗin rayuwar aure. Amman ya faɗa mata ta kiyaye masa kanta da auransa yana da kishi, in ta kiyaye sai su zauna lafiya har abada ba mai jin kansu sai dai in sun samu matsala su zauna su sulhunta kansu a tare. Sun fara gudanar da kyakyawan rayuwa mai cike da abun sha'awa in Rukky ta zo gidan Mimi ta yi ta ba ta sha'awa tana tunanin Allah ya sa itama Nasir ya nuna mata so haka. Da gaske ne ta na son shi har ya shiga gida, Mimi ta fahimci mijinta mai son a yi masa biyayya ne sannan a bi ra'ayinsa sannan in ya ce abu to a yi masa cikin gaggawa sai ta zama mai danne bukatunsa a kan nata, sai a ka zauna lafiya tunda ya zama shugaba kuma wakilinta komai in za ta yi sai ta tambaye sa, ko shawaransa mota ma da za ta sauya sun yi magana sai ya ce ya so shi ya sauya mata mota amma ba yanzu ba. Ba zai tsaida ta ba in tana bukatar canjin yanzu ne shike nan jin abin da ya ce ne ya sa ta fasa siyan motan saboda ta girmama maganarsa kuma ya ji daɗin haka. Target ɗin shi na gaba Inna ta je ta sauke farali bayan nan komai wani irin buri ne zai cika shi daga baya, burin kai Mimi duk in da take so a faɗin duniya sannan ya yi mata komai take bukatan anan duniya domin shi take so ta kuma zauna da shi duk tsanani da wahala. Duk in da ya ce kada ta tsallaka ba ta tsallakawa, ko gidan Hajiya in ya ce ba za ta je ba ko ba ta so ba ta nuna damuwa shi ya sa da kansa in ya ga dama zai ce ta je in ta tashi aiki, ko gidan Inna ne in bai yi ra'ayi ba sai ya ce daga wajen aiki ta koma gida, cikin lokaci Mimi ta sauya ta fara Kiba da Kumatu ta nacin mai kyau ta sha mai kyau ta kuma kwanta a waje mai kyau sannan hankalinta ya na kwance, duk wanda ya ganta ko ya yi waya da ita zai san ba ta da wata matsala. Sau ɗaya ta taɓa shiga kasuwa ta yi cefane da kuɗin ta da ta dawo Aji ya yi mata faɗa kai tsaye yac e"Ni ban kasa a gidana ba Fatima, me ya sa za ki nemi ki kashemin Kokarina a kan ki? Ki bari duk ranar da na ce ba ni da shi ina bukatar taimakon ki sai ki taimakamin amman by now hqkkin ki na kaina naira biyar ban yarda ki kara kashe ma kanki da gidana a cikin kudin ki batare da kin gaya min ba." Da sauri ta ce masa ya yi hakuri ba za ta ƙara ba tun daga ranar ba ta ƙara ba in abu ne ya kare shi za ta gayamawa ya je ya siyo. Kitso ko da kunshi duk bayan sati uku wata makociyar Bintu ke zuwa tana yi mata ya biya ta. Maganar ma siya ma walida waya da ta zo wajenta ta ce ta ƙara tuna masa da ta yi masa mgana bai ce komai ba sai ta yi tunanin bari ta siya ma Walidan wayan amman da ta nemi izininsa sai ya ce a'a, sai dai ta masa kuka da cewa tunda haka ya ɗauka shike nan amman ita walida ƙanwarta ce ganin haka ne ya sa ya ce ba haka ba ne waya shi ya yi alƙwari amman ba zai hana ta ta siya mata wani abun ba. Ai ko dai Walida ta sha gwangwanja a lokaci ɗaya sai ga waya da sabuwar laptop, Shi ya siya waya Mimi ta siya mata laptop tunda ta kusa gama ma koyon computer, an kusa yaye su daman wattani shida ne Walida kamar ta suma saboda daɗi Inna na yi mata dariya. Haka ta riƙa kiran yan'uwanta ta na gaya musu abun arzikin da ya sa me ta, Hajiya kuma har gida ta zo ta ga gida ta yi ma Inna Meri murna sannan itama Innan ta na zuwa duba Hajiyan lokaci bayan lokaci. Gidajen yan'uwansa ko Mimi ta leka sau daya, gwara ma gidan Bintu da mijinta ya siya mota sun je Allah ya sanya alheri ta bi Walida sun tafi tare, gidan Yaya Amina sau ɗaya taje haka ma gidan Yaya Halim gwara ma can gidansu Hibba in aka yi wani abu Inna ta gaya masa sai ya ce ta shirya ta bi su, ita dai daga gidan Hajiya sai gidan Daddy shima tare su kan je sai gidan Rukky da yanzu ya ke barinta zuwa amman Rukkyn ma ta fita zuwa wajenta lokaci bayan lokaci. Sannan Meesaha ma ta zo wajenta ya fi sau biyar, ita dai ba ta sakar mata ta yi ta kawo mata mganganu Saddiqu yanzu babu komai ya daina zuwa Lagos ɗin sai zaman banza a gari, ita kuma Mimi sai ta ba ta shawaran tunda ta yi karatu ta nemi aiki domin ta taimaki mijinta. Mansoor bai hanata mu'amala da kowa ba domin ya ce ita ba yarinya bace ta san yadda za ta tafiyar da komai, ba ruwan shi da yana da matsala da wani shi dai matarsa kawai ya sani ita yafi kiyyewa fiye da kowa, in ta zo in ta na da abu za ta ɗauka cikin mallakinta ta yi mata taimako ba ta tasallake iyakarta, Tasan wanda take aure shi ya sa ba ta karambanin taɓa abin da yake na shi ne sai da izinin shi. Ya sanar da ita ya na so ya samu lokaci su je can kwami ta ga tushensa da ganan su shiga Bauchi in sun dawo kuma ya ba ta izinin za ta je Abuja ta ga Mommy ko na kwana biyu ne Mimi na ta murna, shi kuma ya yi mata kara ne ganin ba ta taɓa nuna masa ƙosawar ta ba, shi kuma farincikinta yake so, adalci ya ke son yi mata kamar yadda ta yi masa, kuma ba ya son yau ace Mimi ta ji ta na son wani a bu ya kasa yi mata shiyasa kafim ma ta tambaya yake kokarin yi mata shi, Har cewa ta yi ya kamata su je kano ya ce ita da kano sai Hibba ta haihu, ai ta je kafin tareewarsu ba ta gaji da zuwa ba. Dole ta kama bakinta, iya ma Abujan ta gode ma Allah da ya barta shima baya nan lokacin za su je kaduna. In ya na gida tana girki ya kan taya ta da niko wannan ɗauke wannan, baya takura kansa abin da zai iya shi yake yi, ya ce girki na mata ne amman ba shi zai hana ya ɗan taimake ta da abin da ba'a rasa ba. Rayuwa dai suke yi dai dai rayuwar mallam bahaushe. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3014* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. _28TH. MAY 2023_ *SUNDAY, 12:00PM* Tunda yau lahadi ana cikin hutun ƙarshen mako, da ga shi har ita suna gida ba su fita ba gwara shi caach ya kira shi da safe ya fita zuwa camp sun yi mgana a kan wani gagarumin taron da babban kungiyar ƙwallon Kafa ta ƙasa baki ɗaya za ta shirya a garin Abuja wato Super Eagles shi Aji baya son zuwa taron Caach ɗin su kuma ya matsa masa ya na so ya wakilci jaharsu tunda shi ne Captain tunda abin kamar dukk an gayyaci manya manya kungiyoyon ƙwallon kafa na Nageria ne gabaɗaya.   Shi kuma Aji ya ce Coach ya fi shi matsayi shi ya kamata yaje, shi kuma ya na nuna masa shi dai ɗin ya kamata ya je haka suka rabu ba su samu matsaya ba. Tunda Aji ya kafe har da cewa tafiya za su yi zuwa garin su shida Mimi amman Coach ya ce ya ma fara shirin tafiya Abuja ba fashi, da wannan haushin ya dawo gida Mimi na barci ba ta tashi ba daman sanda ma ya fitan ba ta sani suna kwance ne suna barci ya zare jikinsa ya fita, sanda kuma ya dawo sai ya yi zamansa a falo kawai yana wani lissafin. Shi fa ko da yake sanannen ɗan ƙwallo a jiharsa shi mutum ne mara son shigewa mutane kada ma ace yana neman wani abu ko kuma neman fada da wajen zama. Shi ya sa rayuwarsa yake yi kai tsaye baya neman kowa sai wanda ya neme shi Coach ɗin su ma ya yi ta son haɗa shi da sanannu manya a ƙwallon kafa na ƙasa gabaɗaya amman Aji sai ya riƙa noƙewa.   Gajiya ya yi da zama a falo yana ta saƙe sake bai isa ya gujema wannan tafiyar ba Coach kamar uba yake gare sa. Da dai ace sanda ya yi turjiyan ne ya amince shikenan amma  yanzu tsarinsa ya rushe, zuwan shi kwami da Bauchi ba zai samu ba sannan Mimi ma ba zai hana ta tafiya Abuja tunda ya riga ya yi mata alƙwari kuma ya san ta sanar da Mommy, sai dai yanzu su tafi tare shi ya je ya yi abin da ya kaisa ita kuma ta je gidansu ta zauna in ya gama abib da ya kai sa sai su dawo tare, ga kuma babbar salla ta ƙarato sai dai su ɗaga tafiyarsu Kwami zuwa bayan sallah. Gajiya ya yi da zama ya tashi ya kunna talabijin a tashar kwallon ƙafa daman su yake kallo ko tasoshin wa'azi Mimi kuma daman kallo bai dame ta ba barta da barci sai kuma waya,wayar ma ba sosai ta dame ta ba.   Bai san fitowarta ba sai ji kawai ya yi ta saƙalo hannayenta daga bayansa zuwa wuyansa lokaci ɗaya tana ɗora kanta a saman kansa cikin yar shagwaɓa ta ce"Shi ne ka tashi ni ba ka tashe ni ba ko? Ta faɗa ta na sosa kirjinsa da ɗayan hannunta ɗayan hannun nata kuma ta fara sosa masa kunninsa guda ɗaya, juyowa ya yi bayan ya riƙe mata duka hannayenta sannan ya zagayo da ita har gabansa ya zaunar da ita kan cinyarsa suna masu kallon juna ya ce"Kina ta sharan barci duk kin bugemin jiki, kina ta munshari, ga shi kin saki baki galala da miyan barci." Ya faɗa lokaci ɗaya har ya na kauda kansa yana ƴar dariya. Rufe baki ta yi tana kallonshi cikin mamaki kafin ta ce"Ni ne ke minshari da miyan barci? Ta faɗa har ta na zaro ido cikin tsoro domin har ga Allah ta ɗauka da gaske ne.   Rumgumeta ya yi yana faɗin" E, mana, ban taɓa faɗa miki ba ne, amman kada ki damu ke na ke so ba zan damu da minsharinki da miyan barcin ki ba" Yadda ya ƙarishe maganar da dariya ne ya sa ta gane abin da ya ke nufi, da sauri ta saka hannu ta mintsine shi a cikinsa har sau biyu kuma mintsinin da zafi da ya sa dole ya saketa ya yi gefe yana raɗin"Mimi ba na son mugunta fa daga faɗin gaskiya? Mikewa ta yi daga kan cinyarsa ta riƙe kugu daga ita sai rgar barci fara mai shara shara iyakarta gwiwamta sannan surar jikinta duka yana buɗe ne gashin kanta ma yana ɗaure ne kanta ba hula ba ɗankwali. "Waye mai miyan barci da minshari?   Haka ta faɗa ta na zare masa ido har da ɗaga hannu kamar za ta kai masa duka ya saka hqnnuwansa ya kare kansa yana faɗin" Allah ya baki hakuri Inna Fatima." Ya faɗa yana yar dariya sai kawai ta ja cution ɗin kujera ta mara dukanshi da shi ya na karewa da hannunshi yana dariya bai hana ta ba sai da ta gaji ta bari shi kuma daga kwancen ya saka hqnnu ya jawo ta ta faɗo jikinsa ya rumgumeta ita kuma tana neman ƙwace kanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ina miyan barci ko? Ya na yar dariya ya ce"Na tuba na janye mganata ina ga ni ne me miyan barcin da minshari ban sani ba" Hararansa ta yi kafin ta ce"Za ka ma sani ne." Ta faɗa ta na kokarin tashi ya sake riƙeta ya nannaɗeta a cikin jikimsa yana mata raɗa a kunne ba ta san lokacin da ta yi dariya ba. Bai bari ba sai ya fara yi mata cakulkuli ta fara dariya kamar za ta shiɗe tana faɗin" Cikina na ciwo don Allah ka bari." Sai da ya ga tana hawaye sannan ya kyaleta ya koma ya na sumbatan bakinta. Daga nan suka rike kan juna suna sumbatar bakin juna cikin shauƙi da soyayya.   Sun ɗauki lokaci suna farantama juna rai sannan suka saki juna suka koma su ka sake rumgume juna suna maida numfashi, kan Mimi na saman kirjin Aji shi kuma ya saka hannunahi ya na shafa gashin kanta,  Idanuwanta a lumshe tana jin wani irin farinciki na ratsa ta a nan duniya gani take yi kamar tafi kowa dacen samun abokin rayuwa nagari, shi ma a bangarensa addu'a yake yi Allah kada ya bashi ikon kuntata ma Mimi, Allah ya zaunar da su lafiya ya kaɗe fitina. "Me za mu yi breakfast da shi yau Aji?   Haka Mimi ta faɗa, tana ƙamƙame dashi, kai tsaye ya ce" Duk abin da Mimi ta shiryama Aji kinsan bai taɓa juya mata baya ba." Buɗe idanuwanta ta yi kafin ta ce" Ko mu soya kwai ne mu gasa buredi, mu sha Tea ko? Sai ya gyaɗa mata kai kafin ya ce" Ni fa ba ruwana da wannan bangaren, ke dai kawai ki ciyar da ni, ni kuma ina yin aikina na ci da ciyarwa." Ya faɗa lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, Sai kawai Mimi ta daki kirjinsa cikin sigar wasa tana masa mirmishi,  sannan ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Rana ta yi, bari mu karya karfina ya dawo jikina tukunna." Da kallo ya bita za ta shiga kitchen sai ya kwala mata kira ta juyo kai tsaye ya ce"Ba na hana ki shiga kitchen ba takalmi ba dankwali ba? Sai Mimi ta dafe kanta kafin ta shagwaɓe tana faɗin"Na manta ne Aji."   Miƙewa ya yi bayan yac e mata bari ya zo cikin bedroom ɗin su ya shiga ya ɗauko mata hula da silafas ɗinta na cikin hida ya zo har gabanta ya duka ta saka takalmin sannan ya kama kanta ya saka mata hular sannan ya kalleta kafin ya ɗan rankwasheta yana faɗin"Ba ki san saka Dankwali ko? Sai na yi miki aski" Baki ta tura kafin ta ce"Aski? To sai ka kalli gashin wa? Ya na juyawa zuwa kan kujeran da ya tashi ya ce" Aure zan ƙara, ba zan zauna da mai kai kamar na maza ba." Tsaye ta yi ta na buga kafa za ta fara masa kukan shagwaɓa, ya na jinta sai ma ya ɗauki romot ya ƙara ƙaran talabijin ɗin lokaci ɗaya ya na faɗin" Fatima ina jin yunwa fa. Ɗaya saura na rana ban karya ba fisabilillahi fa"   Haka ya faɗa ya sa ta faɗa kitchen ɗin lokaci ɗaya tana faɗin"Da laifin ka me ya sa baka tashe ni ba? Bai san ko ta ji ba ya ce"Mace tagari ba ta jira miji ya tada ta sai dai ta tada shi, amman ke sai barci kamar kasa, zan ga ranar da za ki haihu Fatima." Ita ba ta ji sa ba. Ta kunna gas ta fara ɗora ruwan tea ɗin bayan ta saka kayan ƙamshi da ganyen shayi, sannan ta fara koƙarin Kwaso ƙwan da za ta soya buredi ya na can saman dinning wanda za ta gasa ga shi kuma sai da ta fara fasa kwan ta tuna sai kawai ta fito bakin kitchen ɗin tana kiran sunan Aji bai jita ba sai da ta ƙwalaa masa kira da Karfi sannan ya juyo lokaci ɗaya yana na rage ƙaran talabijin ɗin. "Miye ne?   Haka ya ce mata yana haɗe rai, shi fa baya son mace ta riƙa saka shi aiki kuma ya lura halin Mimi ne ta riƙa saka shi aiki kamar wani ɗanta. "Buredi za ka ɗauko a saman dinning.." Ta faɗa cikin yar shagwaɓa, hararanta ya yi kafin ya ce"Ke fa? Kafar ki na ciwo ne? Wani kallon ƙasa ƙasa ta yi masa kafin ta ɗaga masa hannuwanta lokaci ɗaya tana faɗin" Na saka hannuna a kwai ne, don Allah ka kawo min." Kamar ba zai ta shi ba haka ya tashi yana tura baki kamar mace ita kuma tana danne dariya yana ganinta sai ya dakata yana faɗin" Dariya ma kike yi ko ? To Allah ba zan ɗauko ba." "Afuwan haba Nawan, Aji na ajin zuciyata." Haka ta faɗa har ta na masa fari Mirmishi ya yi kafin ya ce"Eh mana tunda kin sakani aiki ba, dole ki yaudare da kalamai mana." Haka ya je ya ɗauko mata shima ba ta karɓa ba, ta ce hannunta ba kyau ya kai mata kirchen, da sauri ya shiga ya sauke mata samman wani faranti har yana sauri ya fita ta bi shi tana Faɗin" Ka tayani mana,ko gasa buredin Aji" Ko juyowa bai yi ba ya fice yana faɗin"Yunwa nake ji, don Allah ki yi sauri." Daman ta san ba zai tsaya ba ba ta san me ya sa ba baya son ta yata aiki ba, aiki in dai ba shi ya yi niyya ba ita kuma tana so ta ga suna aiki tare cikin soyayya da ƙauna.   Bayan ta gama fasa kwan sai ta tuna bata yanka albasa da kayan miya ba, wanke hannayenta ta yi ta yanka buredin ta saka masa butter ta saka shi cikin oven yunda Aji ba ya son gasaahen buredi da ƙwai ya fi son shi da Butter ya yi taushi. Gani  ta yi aikin baya mata sauri tana yanka  su tattasai, ta ƙwalama gogan kira ya ƙi amsa mata sai ta da ƙara ɗaga murya sai ga shi a bakin kitchen ɗin lokaci ɗaya yana faɗin"Wai na ci miki bashi ne Mimi? Kada ki ce za ma ki ƙara aike na domin nima yunwa ta saka ba ni ma da kuzari." Ya faɗa yana harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa, har ya na wani kauda kai ganin haka ya sa da sauri ta marairaice tana faɗin" Aji to ka kama min na gama da wuri mana." Hararanta ya yi kafin ya yi mgana da tare shi da shagwaɓa tana faɗin" Don Allah haba mana." Ɗaure fuska ya yi kafin ya ce"Me kuma zan yi yanzu? "Albasa za ka yanka min don Allah."   Ido ya zaro kafin ya ce"Albasa? Mugunta ko? Kin san fa ranar haka ki ka sakani ina ta kukan dole."   Dariya takke so ta yi amman sai ta kanne ta lamgwabar da kai kamar za ta yi kuka kafin ta ce"Shike nan bar shi ma," Yadda ta yi mganar ne ya sa dole ya shiga Kitchen ɗin ya na faɗin" Ina albasan? Tana mirmishi ta nuna masa ya ɗauka sannan ya dauki wuƙa, ta nuna masa wani ƙaramin vol ya ɗauka ya fara yankawa a ciki yana ƙunƙuni ta na jin sa sai ta kanne ba ta yi magana ba sai da ta ga ya na ta yankawa manya manya sai ta kalle sa kafin Ta ce. "Haba Aji, sun yi girma yankan"   Hararanta ya yi har ya fara ƙanƙance ido kamar yajin ya fara tasowa. Haka nan ya gama yanka mata sannan ya tace ruwan tea ɗin ya juye cikin flaks ɗin ruwan zafi, ita kuma ta fara soya kwan shi kuma ta ce ya duba buredin a oven, ya cire ya nuna mata ta ce sun gasu ta karɓa ta ƙara sakaa wasu buredin da butter ta maida, ita kuma tana cigaba da soyan ƙwan suna hira sama sama.    A tare suka gama sannan Mimi ta gyara kitchen ɗin dakyar Aji ya taya ta ɗaukan Kayan karyawan nasu zuwa Dinning suka zauna saman karyawa, a lokacin ne yake ce mata mganar zuwan su kwami ba ta sai dai zuwa gaba. Cikin mamaki ta kalle shi lokacin tana tura Buredi da ƙwai bakinta sai da ta kurɓi Tea sannan ta ce"Me ya sa? Kai tsaye ya ce" Nima tafiya ce ta dole ta kamani zuwa Abuja." Sai Mimi ta washe baki kafin ta ce"Gaske? Me za ka je yi?. Nan ya ke gaya kata yadda suka yi da Coach ita kuma ta ce"Gaskiya bai kyautu kace ba za ka je ba. To ya kenan? Ya na kallonta kai tsaye ya ce" Tare za mu tafi Abujan sai ki je gida ki yi adadin kwanakin da zan yi, domin ba zan barki can ba tare za mu dawo." Cikin gamsuwa ta ce" To can Bauchin fa? Sai da ya kurbi Tea shima kafin ya ce"Sai dai zuwa bayan sallah tunda kinga yau sallah bai fi saura kwanaki goma ba." Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Allah ya kaimu da rai da lafiya." Ya amsa mata da Amin Amin, suka cigaba dahiiran su,  ba kasafai ya cika faɗa mata wasu abubuwan da suka danganci aikinsa ko iyayensa ba, sai in yan hiran na shi suna kusa. Kamar daga sama ta ji ya ce"Fatima kinsan burika na guda uku ne anan duniya? Sai ta girgiza kanta amman ta maida hankalinta a kansa  tunda dukkansu sun gama ƙaryawan. "Burina na farko shine Inna ta kasance cikin farincikin da kowacce uwa ke fata, Sannan burina shi ne na kai ta kasa mai tsarki ta sauke farali, na biyun kuma na mallakeki shi na cika wannan burin tunda na same ki, sannan na cika burin inganta rayuwar Inna abu ɗaya ya ragemin na kaita kasa mai tsarki ta sauke farali, ɗayan kuma zan faɗa miki daga baya."   Mimi ta yi shuru tana kallonsa kafin ta ce"In sha Allahu za ka cika burin ka, inna za ta je ta sauke fqrali ƙila ma ba sau ɗaya ba." Mirmishi ya yi kafin ya ce"Ba ni da kuɗi yanzu duk na yi amfani da su Wajen hidindimu, ga kuma sallah na matsowa akwai sauran hidima amman ina so a wannan shekaran Inna ta je ta sauke farali In sha Allahu." Mimi cikin jin daɗi ta ce"Allah ya amince,in kana bukatar kuɗi, akwai kuɗi a hannuna sai ka yi amfani dashi in ka samu sai ka maida min." Bai ce mata komai ba, sai ta cigaba da faɗin" Kuma ga shi ma za ka je wannan taron na ji ana ta zuzuta ka iya taka leda nasan za ka iya kaiwa matakin kaiwa A kungiyar kwallon kafa ta Nageria." Sai a lokacin ya ce"Ni fa ba ruwana da wannan, in da na ke ma ya isheni Fatima a baya ban taɓa tunanin zan kai haka ba, Shi ya sa ban cika son tusa kaina ba,  matsayin da na kai a yanzu ma Ubangiji ne ya kai ni, ina kuma gode masa ban sani ba ko nan gaba Ubangiji ya ƙara dagani amman yanzu ni dai ba zan tusa kaina ba. A hakan ma Alhamdulillah." Mimi ta na so ta kara mgana amman sai ya dakatar da ita miƙewa ya yi lokaci ɗaya yana na faɗin" Zan yi wanka Fatima." Sai ta miƙe suka jera zuwa cikin Bedroom ɗin su kowanne na sake sake a cikin ransa.   Yinin ranar yana gida bai fita ko'ina ba sai dai waya kawai.Sai bayan mangariba ya fita ya je gidan Inna suka gaisa, ta yi masa mganar zuwa Kwami nan ya ke gaya mata cewa sai dai bayan sallah tafiya Abuja ta kama shi daman kuma ya yi ma Mimi alƙwari za su tafi tare ita sai ta sauka a gida Inna tace hakan ma ba laifi,  yana gida har a ka yi sallar isha'i kuma sai da ya ci yuwo da miyar kuɓewa, da su ka yi waya da Mimi ya gaya mata ga shi ya na cin tuwo sai ta ce itama don Allah ya ce ma Inna za ta ci, kai tsaye ya ce"Ni ɗan aiken ki ne? Ba zan iya daukan tuwo ba." Ta san halin shi ya sa ta kira wayar Inna ta gaya mata tana son tuwo nan da nan inna ta ce a saka mata a Kula Baban Inna ya wuce mata da shi, ya na zaune kai tsaye ya ce"Ni kuma Inna? Daga nan ba gida zan je ba fa." Inna ta harareshi kafin ta ce"Ko ba gida za ka je ba sai ka ɗauka ba na son iyayin banza." Shuru ya yi bai kara mgana ba har Walida ta zubo tuwo da miya a kula sai yake mata mganar yaushe za ta gama Traning ɗin ta? Kai tsaye ta ce"Wata mai kamawa yayanmu., Amman mai shagon ya ce zai rikeni na riƙa zama masa kafin lokacin zana jamb ɗin ya yi." Da sauri ya ce"A'a ba za ki zauna ba, ki dawo gida ki cigaba da taya Inna zama." Inna ba ta yi mgana ba daman itama tunda ta gaya mata ta ce ba ta amince kuma daman tasan shima Baban inna bazai amince ba. Inna ce ta ga Walidan ta ɓata rai sai ta ce"Nima na ce mata ta yi hakuri ita mace ce, ko wannan ɗin ma da ta yi saboda Kun matsa ne. Ni da har shawaran ta fara zuwa can anguwan da muka taso wajen Bahijja yar wajen Dije ta fara koyon ɗinki kada ta yi ta zama ba ta wani abun."   Mansoor ya mike lokaci ɗaya yana faɗin" To gwara ma can ɗin, ki yi mata mgana Inna abin da a ke bukata sai a sanar da ni." Shike nan ma har ya zartar da Hukunci Dole Walida ta yi shuru, amman ita har ga Allah ba ta son koyon ɗinki yana da wahala, Inna kuma Daman shawara ce nata abin da Baban Inna ya ce shike nan ballantana Baba da duk abin da ya zartar sai ya ce mata ya yi, gwara Mariya auranta za ta yi, itama ta na da samarim amman kuma tunda ta ce karatu za ta yi ba ta da ikon sauya wata mgana daga baya. Tana ji ta na gani Baban Inna ya bar gida  bayan inna ta ce za ta kira Dijen su yi mgana ko ita Walidan ta je ta samu Bahijja su yi mgana.   Abu kamar wasa ƙaramar mgana ta zama Baba Inna ta kira Dije ta ce ai bakomai an zama ɗaya,  ta ce Walida ta fara zuwa gidan Bahijja ita a Tunferre take zaune kuma babbar Tela ce gidanta cike da yaran mata har da matan aure ma ba'a bar su a baya ba, Walida ba ta da ra'ayi amman tunda mai gayya mai aiki ya zartar shikenan Kuma duk abin da ake bukata Aji ya ba ma walida kuɗi ta siya, kenan ba ta da iko da ta ce ba za ta je ba, an gama mgana da cewa da zaran an yayeta a computer Traning za ta fara zuwa,  da ta gayama mariya abin da Yaya Mansoor ya ce itama ta ce ta na so za ta yi kafin auran ta ya zo, tunda wani Lokacin Walida na biyawa ta gidan Magajiya ta yi laushi kamar ba ita ba wani ookacin har cewa ta ke yi, Walida ta gai da Inna amman kunya ya hana ta zuwa gidan innar da kanta.   Mariya Auwalu ta yi ma mganar itama tana son koyon ɗinki tunda ga Walida ma za ta fara zuwa da ta ce za ta yi ma Yaya Mu'azzam magana sai ya ce ta bari shi zai ba ta kuɗin abin da za ta bukata, ba zai zama lalle sai komai Mu'azzam ko Mansoor sun yi musu ba, suma ya kamata su riƙa taimakawa da wani abun, Saddiqu dai lagos ɗin ta gagare shi ya koma yana zaman shago, gida duk ya lalace ga dai ɗakin nan Inna ta bar musu amman ba kowa ciki sai tara tarkace Maeesha ke yi, can ma bangaren da Maeeshan ta tashi shima Mariya ce ke tara tarkacenta a ciki, tabbas dai Inna ita ce gida ko shiga da fitan jama'a babu kamar baya. Shi kuma Baba  tunda bayan abin da ya fqru ya daina ɓata bakin shi, ya bar Magajiya da Ƴaƴanta duniya ta koya musu hankali daman an ce indan an ciza a hura Saboda gudun ranar nadama kuma ga dukkan alamu nadamar ta fara shigar su. *****   Ana sallah saura kwana shidda Mimi da Aji suka tafi a Abuja jirgi suka bi, ana gobe taron da Mansoor zai hallata. Har gida ya rakani Mimi sai da Mommy ma ta saka baki ya tsaya ya sauka nan ya yi sallah ya ci abimci kwana kuma ya ce ba zai kwana ba, Mimi ta san halin yan kayanta shi ya sa ba ta matsa masa ba, hotel ya kama ya kwana washegari kuma a ka yi taron a Eagless Squeare, An san da zuwan shi tunda ya na wakiltan Gombe United ne ya haɗu da shugabbanin Kungiyoyin kwallon kafa ta jihohin Nageria  waɗanda ya sani, da ma waɗanda ma bai sani ba su sun  san shi, ya haɗu da su Ahmad Musa shima sun gaisa sannan ya nuna masa sani da cewa yana kallon wassanin shi sannan hatta shuggaban Super Eegless ɗin sun yi mgana da Aji abin da bai sani ba Coach ɗin su ya daɗe yana kai mganarsa sama tare da video ɗin wasannin Aji fatan sa kafin Contart ɗin sa ya ƙare Allah ya ɗaga sa zuwa sama amman baya taɓa bari Ajin ya sani tunda yasan in ya sani zai ce shi baya bukata.   Kwana biyu a ka yi ana taron na ƙara ma juna sani ne kan abib da ya shafi ƙwallon Kafa ne, bai ƙara neman Mimi ba sai da suka gama taron gabaɗaya sannan ya memeta. Ranar da ya je gidan sun daɗe suna hira nan ya yi sallar mangariba da isha'i ya ci na rana da sare sai dare ya tafi washegari Mimi ta matsa masa sai da suka fita zaga gari, su ne wajajen shakatawa da kuma wajajen siyan kayan ƙwalama sun yi hotuna da Vedio sai dare ya maida ta gida. Washegari suka juya Gombe,sun koma saboda sallah saura kwana biyu ne. Tun yana Abujan sun yi mgana kan ragunan layya da zai siya. Daman duk salla Aji ke yi ma Inna layya Mu'azzam kuma sai ya yi ma Baba.   Akwai daman wani anan anguwansu mai safaran Rlraguna daga taraba daman wajensa suke siya, Mu'azzam ya turo kuɗin raguna biyu ya ce ɗaya na Baba ɗaya kuma Baba Sani tunda shi ne Babba in kuma shi ya yi layya naman gida biyu za'a raba Baba Danlami ya ja na shi, shi kuma sai ya siya guda biyu na shi ɗaya na Inna guda ɗaya, Mimi ma za ta yi amman ita Daddy ne yake siya mata ita da Hajiya. Ana gobe sallah a ka raba ma kowa ragon shi su Baba Sani suna ta godiya, Auwalu kuma ya siya ma Magajiya ɗan bunsuru ya ce ta yanka ta yi ta murna tana saka masa albarka, abin da ba ta yi a baya amman yanzu ta fahimci yadda duniya take. Ana goben sallah a daran sai ga wata ɗiyar  kanin Maman inna, suna matsayin yar mace da yar namiji ne, amman ubansu ɗaya ne da babanta. Lokacin da suka rasa mahaifinsu mahaifiyarsu ta kwashe yayanta sai bayan sun girma me suka nemi dangi, kuma shima ba'a nan sokoto ya ke zaune ba ya na tureta ne cikin garin Sokoto, Ita ce ta sauka a gidan wanzamai tunda wayar Baba Ɗanjuma ta kira.   An faɗa mata tana da wata uwa a garin Gombe shi Baban nata dake kwance ya na jinya ya ba ta lambar Baba Ɗanjuma da ita kaɗai gare shi ba shi da lambar Inna. Da ta fara biyawa ta can babban gidansu na Argugun ne ta samu tabbacin Inna Meri na aure a garim Gombe ne duk da ta kwana biyu ba ta je ba, shi ne ta shirya ta zo gombe sai ga ta a gidan Wamzamai ta sauka ɗakin Magajiya. Inna ta san Tanimu ne kaɗai ya rage mata acikin ƴan'uwanta duk sauran sun rasu amman shi ba shi da zumumci sau ɗaya ta taɓa zuwa cqn Tureta, ko argungun sai ya fi shekara goma bai je ba.shi ya sa itama ta manta da shi kawai. Ta san yana da ƴaƴa amman ba za ta san su da adadin su ba..   A Daran salla Inna meri na zaune a falo tana na casbaha,Walida na kitchen tana ta suyan kajin da Yaya Mamsoor ya kawo musu sai ga Baba Ɗanjuma tafe ba bakuwa tun kafin ma ta yi mgana Inna ta ga kamar su da Ahalnta. Safiya da goyom yaronta namiji ta zo sai guda biyu yan biyu  mata ma su takawa, Lokacin da ta ce ita ɗiyar Tanimu ce Inna ba ta yi mamaki ba domin taga kama bakinta yaƙi rufuwa Safiya ta ga tarba ɗakin mai katifa aka sauke ta a ciki Inna ta ce Walida ta ba ta duk abin da take bukata, a daran kwana suka yi hira nan ta ji ashe Tanimun na kwance ma ba lafiya shi ne ma yace ta je ta nemeta tana da wata Uwar a garim Gombe, Ita ma a can Tureta ta ke aure yayansu namiji ne amman ya rasu saura su mata biyar itace ta uku Inna Meri tana ta faɗan shi ya yarda zumumci, ga shi yanzu ko can gida ba wanda yasan halin da yake cikim Safiya ta ce an sani amman ba wanda ya bi ta kansa Inna ta ce To tunda bai ɗauki kowa da muhimmanci ba wanda shima domin yanzu Lalura ta same shi a tsaya ta kanshi. Nan da nan Inna tace ana fice sallah za ta bi Safiya ta je ta Duɓa Ɗan'uwanta,  Washegari sallah ko Sabom kayan inna Ta ɗauka ta ba ma Safiya ta saka tunda sai a hankali daga ita har yaran nata daga gani suna cikin wahala. Halima ce mai yaran mata sa'anin yan biyu Inna ta kirata ta ce in za ta zo ta zo mata da wasu daga cikin kayan su zainab, yaran kuma na goyo Inna ta ce Amina tunda ta na da ƙaramin goyo. Mansoor bai son da mganar zuwan wata bakuwa ba sai da ya zo ɗaukan Inna domin tafiya Idi ya ga bakuwar. Inna ta gabatar da ita a matsayin tubashiyarsa ita kuma ta sanar da shi Baban Inna kenan babban yaronta da ta haifa a can garin kwami Sauran yaran suna nan zuwa za ta gan su.   A mota Mansoor suka je sallar Idi, Inna sai Walida da Safiya sai Mimi a gaban mota can gida kuma Baba ya tafi a mashin ɗinsa tunda Aji ya ba shi mashin ɗinsa,  bayan sun dawo sallar idi a ka yanka yanka ragunan layya masu fili da gyara suna aikin su,  ita na Mimi a can gidan Hajiya za'a gyara a soya mata na shi kuma anan za'a gyara sai su tafi da shi can Mimi ta soya. Suna gidan har azahar Safiya na ta yi ma Aji wasan dake tsakanin su amman ba ta ga fuska ba sai bayan tafiyarsu ne Walida ta ce mata"Wanman fa da kika gani bai son wasa ba, dama yaya Mu'azzam ne." Ita ta zauna ta na yi ma Safiya bayanin iyalan Innar gabaɗaya.   Lokacin da Aji ya kira baba Yakubu domin gaisuwan sallah ne yake gaya masa bikin Yayansa guda uku bayan sallah da sati ɗaya, Inna ta sani domin ta taba gaya masa sannan Gwaggo Yalwa ta na can har yanzu ba ta koma gida ba sannan kuma da ya kira can kwami Sadi yaron baba karimu ke faɗa masa tautsuyi ya samu Babansu ya faɗi a mashi a hanyar gona ya samu karaya da raunika kenan bayan sallah tafiya kwami da Bauchi dole. Ranar sallah na biyu Mimi na gida ta lna aikin nama su cincin kuma aikatau ta ba da, Ranar salla ta uku kuma gidan Inna ta yini, Safiya ta yi ta mamakin ganin yadda su Halima ke yi da Inna ta sha mamaki da Walida ta ce ba ita ta haife su ba. Bintu ce sarkin baki tana cacankarta itama tana ramawa, ranar salla ta uku Mimi ta je gidan Hajiya dagacnan ta biya ta gaida Daddy,har suka haɗu da Jaheed suka gaisa kamar wani abu bai faru ba. A ranar ta je har gidan su Rukky daga nan ta rakata suka je gidan Bibi, gidan Nasir ne ba su je ba saboda Rukayya Ahmad kuma wannan sallar a kaduna suka yi. Sai Dare ta dawo gida Aji kuma ya ce ta gama fita,  ta yi zumumci gidan Nafisa bai samu ba sai dai ta kira wayarta suka gaisa Nasir din dai da makama sun zo gidan.   Mu'azzam da Hibba ba su zo sallah ba. Suna can kano amman suncji labarin zuwan bakuwar Inna, Safiya da tafiyar Inna, amman ba su tafi ba sai bayan sallah da kwana huɗu,.Tunda har gidan Wanzamai ta je ta yi ma Magajiya sallama abun mamaki har ta na ba ma Safiya 1k, ta yi ma Inna faram faram kamar ba ita ba. Mansoor ya kai Inna tasha sun rabu akan cewa ta gaya masa Bintu da Halima da Mimi za su je bauchi biki shi kuma ya je ya gaida Babansa sai ya bar su su karisa Bauchi sai an gama biki sannan za su dawo. Kai tsaye ya ce" Inna to ni fa? Da wa zan zauna? Inna ta masa dakuwa kafin ta ce"Ban sani ba, da dawa kake zaune? Sai ya sosa kai yana mirmishi. Safiya taga sha tara na arziki. Kaya na sawa haka su Bintu suka haɗa mata har da na yara sannan ga Atamfofi guda uku biyu Manoor ya siya ɗaya kuma Mu'azzam Innan ma ta ba ta kayanta sabbin ga Safiya sannan ga kuɗi ma su yawa da Mansoor ya ba su a hannun su wanda zai ishe su har da guziri. Inna ta tafi da kwana ɗaya Aji da Mimi da Bintu da yaya Halima suka sauka a garin kwami Walida na gida wajen Magajiya domin da taji Inna na mganar ta koma wajen Amina sai ta ce me zai hana tazo ta zauna tunda ga Mariya? To daman ai magajiyan ke nuna wani abu Inna na jin haka ta ce walida ta koma can sai ta dawo gidan kuma a ka rufe, Walida ba ta so amman ba ta da yarda za ta yi.   Sun je sun iske Baba Karimu har an ɗaura sa, Mimi ta ga gidan da aka haifi mijinta Mansoor nan ya bar su za su kwana da safe tare da sauran mutanen da za su je biki za su karisa Bauchi, ya ba da kuɗi a hannun Sadi babban yaron Baba karimu kuma ya ce in akwai wani abu a kira shi. Inna ta isa Tureta tun a daran da suka tafi, Kuma tun bayan da suka yi waya ba su ƙara ba sai da ya dawo daga Kwami suka yi mgana ta ce jikin Tanimu ya yi tsanani gobe za su kaisa asibitin sakkoto. A ɗakin Matar Sadi Mimi da Bintu suka kwana sun ga karamci,  Mimi garin ya gama burgeta da safe suka ɗauki hanyar Bauchi  har da matar Sadi, kowa ya ga matar Mansoor sai ya ce yar gayu mai kyau da ita, sun isa Bauchi da wuri tunda sun samu mota mai kyau. Can ma ana ta maraba maraba da baki daman an san da zuwan su. Gwaggo Yalwa jiki ya yi kyau kamar ba ita ba, nan fa aka shiga ina aka saka da iyalan Inna Meri. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3015* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* Ranar Jumma'a suka sauka a garin Bauchi, suka kwana asabar kuma a ka tashi da hidimar biki. Mimi sun yi waya da Aji amman bai gaya mata zai zo ɗaurin aure ba, Shi kan shi ba zuwa a cikin tsarinsa amman a safiyar ranar sun yi waya da Inna ta ce maza ya shirya ya je ɗaurin aure. Sai ya yi tunanin bari ya yi ma Nasir mgana sai ya raka shi su tafi tare.   Haka ko a ka yi daya ke ɗaurin auran na Rana ne ɗaya da rabi ne. Shi ya sa suka samu ishashen lokaci. A can Bauchi kuwa Mimi ta ga karramawa sosai wajen Maman Bauchi tare da sauran yaran gidan, ta yi mamakin yawan iyalan gidan daman Aji ya gaya mata duka ƴaƴa mata gare shi Allah bai taɓa ba shi haihuwan wani ɗa Namiji ba Sai mata amman kuma Allah na son shi da Rahama tunda da sun taso sai kuma Allah ya kawo musu mazajen da ya ke aurar da su zuwa gare su. Da safiyar ranar bikib an raka Mimi ta je ta gaishe da Baba Yakubu da yake shi  mutun ne mai faɗin mgana kai tsaye, Kai tsaye yace ma Mimi" Ke ce matar Mansoor ɗin? Ta ɗaga kanta sai ya yi mirmishi kafin ya ce"Ba shakka shi ya sa a baya ya yi ta cewa baya so da na ce ya zo gidana na bashi mata sai ya ce min shi bai ce baya son ki ba." Kan Mimi na ƙasa ba ta yi mgana ba shi kuma bai damu ba sai ya cigaba da faɗin" Duk da fa yaƙi amman ban janye maganata ba,  har yanzu ina da sauran yara in ya na so bazan hana shi ba."   Ya karishe faɗa da sigar zolaya Maman Bauchi na wajen Sai ta yi saurin cewa" Alhaji mganar nan ai ta wuce ko? Kai dai a matsayinka na uba ka saka ma auran su albarka." Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" Haka ne to Allah ya yi ma auran ku albarka" Mimi ta amsa da Amin acikin ranta maman Bauchi ne ta amsa a Fili. Sai ya gyara zama lokaci ɗaya ya na faɗin" Meri ashe ta na can garin su ko? Jiya ta kirani mun gaisa ta ce min ɗan'uwanta ne ba shi da lafiya." Sai Mimi ta ɗaga kanta gefe ɗaya kuma Maman Bauchi sai ta kwace hian suna cikin mganar sai ga Bintu da Anty Halima sun shigo sai a ka haɗu ana ta tattauna mganar kan  Baba karimu da ya samu hatsari Mimi na gefe ba Kasafai ta kan saka musu baki ba.   Bayan sun baro falon megidan suna komawa ɗakin maman Bauchi da suka sauka suka ƙarya. Sannan suka leka ɗakin da Yalwa ke ciki itama jiki ya yi saukí Sai hamdala. Daga nan sai suka yi wanka suka shirya tunda babu wani aiki duk aikatau su ka kai, ko wanke wanke da shara akwai masu aiki balle su baki da sun ce za su yi wani abu sai Mama ta hana ta ce ga masu aiki sannan ga ƴan'uwanta nan sun zo z su yi komai.  Amaren kuma suna gidan da ke kallon na Baba Kabiru can su ka kwana Bayan sun yi wanka sun shirya Bintu ta ja ta suka koma can gida suna ganin shiryawan Amarya da ƙawayenta. Mimi ta yi shigar wani leshi ne  jikinsa baki aamman kwalliyarsa ja ne sai ta yi amfani da jan mayafi da takalmi da jaka ja, ba wani kwalliya ta yi ba amman kayan sun karɓeta ta yi wani irin fresh fatar ta na wani irin santsi kamar wata baturiya sannan ɗinkinta mai flenting ne ta baya ya yi mata wani irin cif a jikinta.   A wajen sai ta zama abun kallo, ga ta yar gayu ga kyau ga kwarjini sannan ga Ilimi da kamala ga turanci domin tana gidan ta samu wayar wani ma'aikacin gidan radion Jamus ba ta yi mamakin in da ya samu labarta ba sun yi mgana da harshen turanci a kan suna son su yi aiki da ita, ba wannan ne na farko ba. Har NTA na ƙasa ma sun kirata D.W ma haka har da BBC, Sai dai ba ta da ra'ayi zuwa ko'ina ta fi kaunar zama a jiharta tun a baya ma balle yanzu da ta yi aure ta auri miji irin Aji ba zai taba barinta ta je wani gari ko ƙasa da sunan aiki ba. To ta sha turanci fa sai ta zama kawai abun kallo in an tambayi Amare wace ce Mimi? Sai su ce matar yayansu ne yaron yayan Abbansu da ya rasu ɗan ƙwallon nan da suke ba su labari saboda suma suna yawan faɗa mana ƙawayen na su suna da wani yaya a Gombe ɗan kwallon kafa ne, to daman mai mata irin Mimi me kuma zai ƙara neman wajen wasu matan? Ai ya gama samun dukkan jin daɗin nan duniya.   Suna tare da Amaren har a ka ɗaura aure, Tana ma cin alalan da a ka yi ne ta gama cin waina kena  ta samu kiran Aji, yana tambayan ta  tana ina? Sai ta ce suna makota tare da Amare sai ya ce ta fito ga su a waje abun sai ya ba ta mamaki ta tsame hannunta kan abin da take ci ta fita ta wanke hannu ta lulluɓa mayafinta a saman kanta ta fita, ba sa waje ashe suna cikin gida suna gaisawa da mutane ciki ta shiga sai gamu da Yaya Halima sai ta nuna mata ɗakin da Gwaggonsa Yalwa ke ciki tace suna ciki,  ta yi mamakin ganin shi tare da Nasir ko alama bai sanar da ita zuwan shi ba, har da Mommy da Hajiya sun yi waya da safe su ka ce ko mijin nata zai zo ɗaurin aure ne? Sai ta ce musu a'a saboda ba su yi mganar zuwan na shi ba.   Ta ji daɗin ganinsa kwana biyu kawai sai da ta yi wani irin kewarsa ta na masa mirmishi ya na yi mata, ya sha shadda fara dinkin zamani tqzarce har da hula sai ya yi wani irin kyau kamar ba shi ba. sun gaisa da Nasir da tambayan yara, Sai kawai ta ce"Da na san za ka zo, da na ce ka zo min da ƙawata." Nasir na dariya ya ce" Tafiyar ba tawa ba ce, ni kaina sai da safen nan na sani, kin san halin mijin nan naki akwai yi ma mutane karfa karfa." Wani kallo Aji ya yi ma Nasir shi kuma sai ya na dariya, Yalwa na gefe itama tana mirmishi, nan ɗakin a ka kawo musu abinci suka ci, suna gama ci wajen uku da rabi su ka ce za su tafi lokacin Baba Kabirun ma bai dawo ba ya na can yana sallaman bakin da suka zo daga nesa. Kawai sai Aji ya kira wayar Mimi kai tsaye yacl ce ta shirya ta fito suna jiran ta, Sai mamaki ya kamata saboda ita dai sun yi da shi sai gobe za su koma gida. Cikin mamaki ta fito ta same su nan ƙofar gida baki a buɗe ta ce" Na ji kace na zo mu tafi ka manta sai gobe za mu koma tare da su Bintu? Kai tsaye ya ce"Su dai za su dawo gobe amman ke yau za ki koma gida."   Mimi ta ɓata rai kafin ma ta yi mgana ya ce"Gobe kaɗai gareni jibi za mu tafi katsina wasa sai mun yi sati, kinga ni ba zan je na zauna a gida ni kaɗai ba." Mimi ta yi kamar za ta yi kuka har ga Allah ita ba ta saka ran komawa a ranar ba, Kawai sai ta ji ya na rage murya har ya na faɗin" kin manta ma jibi za ki koma wajen aiki? Gwara ki zo mu tafi kin ji ko? Cikin shagwaba ta ce"Su Bintu fa da Anty Halima? Kai tsaye ya ce" Ina ruwan ki da su? Sun fi ki sanin hanya in sun gama bikinsu za su dawo ke dai ki je ki ɗauko jakarki mu ta fi kada mu yi dare a hanya."   Mimi ba ta da wata mafita dole, ta juya za ta koma cikin gida amman kuma sai ta rasa abin da za ta ce musu kawai sai ta ce za ta bi miji su koma gida? Sai ta dawo ta na ce masa" To ni me zan ce musu? kawai sai nace musu zan bika? Kallon sama da ƙasa ya yi mata kafin ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya yana faɗin" To shike nan sai ki zauna." Ya faɗa a fusace dole ya sa ta koma cikin gida ta samu Yaya Halima ta gaya mata ita kuma sai ta yi dariya kafin ta ce"Ki bi mijin ki Mimi ai an gama biki, mu za mu zauna har zuwa jibi kada ki damu." Yaya Haliman ce ta sanar ma mutane tafiyar Mimi ba wanda ya damu da tafiyarta Maman Bauchi har waje ta raka Mimi da abun arziƙi na jaka da kofunan biki da za su raba, ko Bintu ba ta samu komawa ta yi ma sallama ba suka ɗauki hanya. Aji ke tuki Nasir na gefen bangaren mai zaman banza, ita kuma Mimi tana baya ta na ɓata rai. Shi ko Aji sai ya basar da ita ya koma suna ta hiran su shi da Nasir.   Suna hanyar Rukky ta kirata cikin damuwa tana tambayanta ina ta je ta zo gidan ta bata nan? Mimi tace ba ta nan ta je Bauchi amman yanzu tana kan hanyar dawowa. Yadda ta ji muryan Rukky a sanyaye ne ya sa ta ji jikinta itama ya yi sanyi har sai da ta ce" Me ya faru Rukky? Daga can bangaren Rukky ta ce"Bakomai sai dai kin dawo ɗin." Daga haka sai ta katse wayar sai abun ya ba ma Mimi mamaki kamar  ta yi ma Nasir mgana sai kuma ta fasa  ta bari gwara sai ta koma sai ta kira Rukkyn su yi mgana. Wajen mangariba suka isa Gombe sun biya gida sun sauke Nasir, wani abun mamaki ita dai Mimi ba ta ga ko sau ɗaya sun yi waya da Rukky ba ahalin kuma ta san a baya ba haka suke ba dole ta fara zargin akwai wani abu a ƙasa.   Haka suka isa gidansu Mimi na shan kamshi, Aji kuma sai ya nuna kamar bai gane ba ya na ta ɗiban ta da mgana ita kuma ta na basar da shi, kuma duk gajiyan nan haka ya saka ta sai da ta yi musu girkin dare ya je ya siyo amman ya ce shi wlh ya daina siyan abinci yana magidanci har da cewa zai taya ta amman kuma ban da ɗauko miko ba abin da ya yi mata. Sai juya kayan miya kawai ko greeting cewa ya yi baya son hannunsa ya taɓa ya ji, ganin da ta yi duk fushin da ta ke yi bai gane ba dole ta saki fuska kamar komai bai faru ba. Daman ya gaya mata ranar litini zai yi tafiya shi ya sa a daran dai kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Da kuma safiyar ranar suka tashi da wayar Inna da labarin rasuwar ƙaninta Tanimu, saboda haka za ta jima tunda yanzu sai bayan an yi bakawai, duka dai yaran sun kirata sun yi mata gaisuwa ya yi nisa ba lalle ace sun tashi daganan zuwa can shiyar sakoto ba.   Ranar lahadin a gida suka yini washegari litini kuma tun safe su Aji suka kama hanyar katsina tare da sauran team ɗin su, Mimi dai ta sha dokoki kada ki yi kaza kada ki yi kaza, har sai da ta gaji da amsawa da To, shi dai ta kular masa da kanta da gidansa,  itama ranar a wajen aiki ta yini ba kuma su haɗu da Rukky ba an ce ta zo ta fi daga baya ta kuma kira wayarta ba ta same ta ba, Bintu ta kirata ta na masa tsiyan shike nan sai ta gudu ta bi mji tana ta dariya nan take gaya mata suma ba su daɗe da shigowa garin ba, an ba su kayan fulawanta gobe Bintun ta ce za ta zo ta kawo mata. Suna cikin wayar ne ra ga madiha na ta kiranta  bayan sun gama sai ta kira ta wanda tun bayan tarewanta sau ɗaya suka yi mgana nan ta ke gaya mata ta shigo garin tana gidan Hajiya ta na so ta zo ta ga gidanta amman Hajiya tace ta yi tafiya sai ta ce mata ta dawo tun shekaranjiya tana wajen aiki amman in ta ta shi za ta biyo ta gidan Hajiya.   Haka ko a ka yi da gidan su Rukky ta so ta wuce amman zuwan Madiha ya sa ta fasa,  saƙo ta turama Aji kan cewa Anty Madiha ta zo za ta biya ta gidan Hajiya, da yamma ta je ta iske ta ko a gidan hajiya kamar ita kaɗai ta zo ba yara ba mijin ta ce wasu kaya ne suka kawota za ta ƙarisa Abuja ta ga kayan da ganan ta ga Mommy, sun gaisa sama sama kamar yadda suka saba Madiha sai wani ƙare mata kallo ta ke yi ƙasa ƙasa ita dai a dole sai ta samun abun kushewa sai kuma ga shi ta kasa samu. Duk Mimi na kallonta a ranta tace mai hali dai baya fasa halinsa, amman saboda ta kure Madihan ya sa ta ce mata ta zo su je gidanta ta kwana. Cikin mamaki ta ce"Gidan ki kuma? Shi mijin na ki fa? Mimi ta ce"Ko ya na nan akwai ɗakuna, balle ma baya nan sun tafi katsina buga wasa." Hajiya na gefe ta ce" Ai ko dai ki je ki kwana gidan ƴar'uwan ki Madiha." Sai ba ta yi gaddama ba. Bayan sallar Isha'i Mimi ta ɗauke ta a motar ta zuwa gidanta Madiha ta sha mamaki domin duk kyan gidan a hoto a fili ya zarce tunaninta. Acikin bedroom ɗinta ta sauke Madiha ta kuma tuɓe tana ta hidima da ita abincin ta yi musu mai rai da lafiya suka ci suka sha ruwa. Vduk kushe irin na Madiha ta rasa abun kushewa sai bin ko'ina ta ke yi da kallo, ta na gani Mimi na waya da Aji bayan ya sanar da ita sun sauka lafiya, ita kuma sai take gaya masa ga Yayarta ta zo. Kai tsaye ya ce"Wacce daga ciki? Ta kaduna ko ta Lagos? Sai tace masa da ta Lagos abin mamaki sai ya ce ta  bata wayar su gaisa, a karon farko Madiha da Mansoor Aji suka gaisa cikin girmama juna sannan suka yi sallamam Da dai Madiha ta rasa abun cewa sai ta bige da faɗin" Ina fatan dai kuna nan zaune lafiya ko? Mimi ta ce mata suna nan lafiya kalau. Sai Madiha ta gyara zama lokaci ɗaya tana faɗin" To gwara dai haka, kar dai ki zauna soyayya ɗa namiji ta rufe miki ido, duk da kina aiki ya kamata ki fara tunanin fara wani kasuwancin da kuɗin ki." Kai tsaye Mimi ta ce"To zan yi magana da mijina in sha Allahu." A karkace Madiha tace"Mijin ki? Au daman kuɗin shi ne? Mimi ta ce"Kuɗina ai kuɗin shi ne tunda ina ƙarkashinsa, ko Mommy ma ta ce duk abin da na gada nawa ne, kada na kuma zartan da wani abu ba tare da na shawarci  mijina ba ko a addinmun hakan ba laifi ba ne, kada kuma ki manta ko yau na faɗi na mutu abin da na tara rabi na shi ne." Sai Madiha ta kasa mgana saboda ta ga kamar Mimin ta fi ta gaskiya.   Da yake ba wata sakewa tsakanin su ya sa ba su jima suna hira ba suka kwanta sai da eafe Khadi ta kira Mimin ita ke gaya mata Madiha a gidanta ta kwana kai tsaye Khadi ta ce"Mimi na ji kun fara yawon honneymoom ke da mijin ki, Kaduna ba ta zo muku a layi ba ne? Mimi na dariya ta ce"Ta kusa zuwa layi in sha Allahu." Khadi na dariya ta ce" Yauwa, don Allah ku zo mun nima muna da wajen kwana ko wata ne ma za ku iya yi." Da haka suka rabu bayan ta ce ta miƙa ma Madiha wayar nan ta bar su suna waya ita kuma ta fita zuwa kitchen.   Tare suka fita Mimin ta sauke Madiha a gidan Daddy za ta gaishe shi itama ba ta tsaya ba ta wuce wajen aiki, tana zuwa bayan ta gama karanta labaran safe ta karisa bangaren su Rukky ta same ta ta zo aiki amman duk ta faɗa ta yi wani iri kamar Rukky ba, Mimi ta damu ta kalli Rukayya lokaci ɗaya tana faɗin"Me ke faruwa ne? Kin ga yadda kika wani lalace? Kuma kin ce za ki zo gida ki same ni kuma ban gan ki ba." Sai Rukky ta furzar da numfashi kafin ta ce" Ki bari in muka tashi mu je gidanki mu yi magana, nan ba wajen mganar nan ba ne." Da haka Rukky ta samu kan Mimi ta yarda sai sun ta shi aiki za su tafi gidanta su yi zauna su yi mgana.   Da wuri suka baro ma'aikatan na su ita da Rukky suna tafe ne amman ba wani mganar da ke shiga tsakanin su, Rukky ta yi tagumi daga ganinta tana cikin dqmuwa Mimi dai ba ta ce mata komai ba amman tana tuki tana kallon Rukky cikin tausaya ba ƙaramin abu ne zai saka Rukky ta zama haka ba, ta ma fita surutu fa amman ji ta ko mgana mai karfi ba ta son yi. Sun isa gidan amman ko ruwan da ta kawo ma Rukky ba ta sha  ba zaune kawai ta yi , kamar mara lafiya, Mimi ta kariso ta zauna kusa da Rukky lokaci ɗaya tana dafa Kafaɗanta cikin wani yanayi ta ce"Me ke damun ki ne Rukayya? Na damu da ganin ki cikin wannan halin don Allah ki gaya min abin da ke damun ki.? Rukky ta furzan da numfashi kawai sai ta sakar ma Mimi kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Ta ɗora kanta  a saman kafaɗan Mimi tana shesshekan kuka daga gani kukan na fitowa daga ƙasan ranta ne wanda ya daɗe yana cin ta a cikin zuciya ta kasa furtama kowa.   Mimi ta riƙa lallashinta ta hanyar ɗan bubhuga bayanta da sigar lallashi. Har sai da Rukky ta daina kuka sannan Mimi ta ɗago kanta ta saka hannu tana share mata hawaye lokaci ɗaya tana faɗin" Ki daina kuka ki natsu ki gaya min abin da ke faruwa." Rukky ta ja numnfashi kafin ta ce"Nasir ne." Mimi daman ta tsammaci haka amman kuma sai da ta nuna mamakinta kafin ta ce"Me ya faru da Nasir ɗin? Ko kun yi faɗa ne?   Rukky ta girgiza kanta kafin ta ce" Ba faɗa muka yi ba matsala ce daga wajen mahaifiyarsa ta ce ba ta amince Nasir ya aureni ba." Cike da wani karin mamaki Mimi ta ce"To Saboda mene kuma? Ba an gama mganar cewa tura magabatansa kawai zai yi gidan ku ba.? Rukky na sharan ƙwallah ta ce" Eh mana, mun gama mgana da shi kawai daga baya yake gaya min maman shi ba ta amince ba." "To saboda mene? Mimi ta je fa mata tambaya, Rukky ta gyara zama lokaci ɗaya ta na faɗin" Saboda hujjarta na fi karfin Nasir idanuwana sun buɗe na yi karatu mai zurfi sannan ina aiki zan zo na fi karfin shi, zan raina shi zan kuma raina yan'uwansa da matansa Shi ya sa ta ce ya bar mganata ba ta amince ba." Sai kawai Rukky ta kara fashewa da kuka ta na cigaba da fqɗin" Ina son Nasir Mimi shi ya sa na shiga tashin hankali, yana ta ce min zai samu mafita amman har yanzu ba mafita ko mgana ta waya ma mun rage baya zuwa wajena saboda maman shi ta hana shi, ya a ke so na yi?  wlh ina son shi ina jin wani zafi a cikin zuciyata Mimi" Haka ta ke faɗa tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya, Mimi ma ta shiga tashin hankali cikin damuwa ta ce"Subhanallah to shi daman ya san ba ta amince ba ya tusa kansa? wallahi ban sani ba kuma ina jin ko Aji bai san abin da ke faruwa ba." "Ba wanda ya sani, ba na tunanin ya faɗa ma wani" Sai Mimi ta kaɗa kai kafin ta ce"Abin bai yi daɗi ba, ki yi hakuri ki daina kuka bari na kira Aji na gaya masa kila akwai abin da zai iya yi a kai."   Da haka Mimi ta ɗauki waya ta kira shi, amman bai ɗauka ba daman sun fi mgana da daddare ko da asuba sai Mimi ta cigaba da lallashin Rukkaya da kalaman kwantar da hankali.Har ta samu ta daina kuka ita dai Mimi ta ce ta yi ta addu'a abin da ya ke alheri ne Allah ya zaɓa mata amman kuka da damuwa ba nata ba ne, Rukky na gidan har mangariba tare suka yi girki da Mimi ta na shirin tafiya sai ga wayar Aji nan fa Mimi ke gaya masa abin da ke faruwa kai tsaye ya ce"Topha, Shi kuma Nasir ya zai yi haka? Ya san ba amincewar iyayensa kuma ya zo ya bata ma ƴar mutane lokaci? Mimi ta ce"Ka ji fa, ita ta damu ne na ce ko za ka shiga mganar ne? Da sauri Aji ya ce"A'a ni bai gaya min ba kin ga kenan bai so na sani ba. Kawai ta koma gida ta cigaba da addu'a, mgana in ta haɗa da iyaye tana da karfi in mijinte ne kaddara za ta  sake haɗa su." Tunda Mimi ta ji haka ta san cewa Aji ba zai yi wani abu ba  Sai ta fara wani tunani acikin zuciyarta. Rukayya ƙawarta ce da kowa ya santa tare da ita abokiyar kuka abokiyar dariya ba za ta iya barinta cikin damuwa ba. Har ta Rukky ta tafi tana tunanin yuyuwar abin da take tunani. Ta so ta yi mgana da Aji ta neme shawaransa sai kuma ta fasa a tunaninta sai ya dawo sai ta nemi shawaransa.   Ba tare da wani tunani ba ta kira Jaheed a waya shima dai ya yi mamakin kiran nata tunda ba kiran shi take yi ba. Sai dai maganar da ta zo masa da shi ne ya ba shi mamaki,  kai tsaye ta tambaye shi" Jaheed ka na da wata dudurwan da kake nema ne yanzu? Cikin mamaki ya ce"Eh a'a kinsan dai bazan rasa masu sona ba amman ni ba kowa a raina." Da sauri ta ce" In ka yarda da ni zan haɗaka da ƙawata Rukayya na san ka santa kuma ina mai baka tabbacin za ka so ta." Sai ta shiga ba shi labarin soyayyarta da Nasir da halin da a ke ciki. Amman ba ta gaya masa abokin mijinta ba ne ta roki Jaheed domin Allah ya fara mgana da Rukkaya domin ya yi mata gwaji ya tabbata dai, ba za ta kawo masa wani abu mara kyau ba. Bai yi mata gaddama ya ce"Ki turomin da lambata da ni da ita za mu iya daidaita wa tunda duka zukatanmu suna fama da ciwo iri ɗaya." Ko Rukkyn ba ta gayamawa ba ta turama Jaheed lambar Rukayya a daran, amman ta turama Rukkyn sakon cewa Jaheed zai kirata sauran mgana sai sun haɗu.   Sai washegari suka haɗu a wajen aiki Rukky ta tsareta da tambayan ba ta gane manufar ba ma Jaheed lambarta, Mimi kuma ta warware mata niyyarta na alheri Rukky ta ce"Ina son Nasir fa kin sani Mimi." Mimi ta ce"Ki cire sa a ranki domin mganarsa sai dai in kaddara ki buɗe zuciyarki ku fahimci juna da ke da Jaheed kin san dai ba shi da wata matsala" Ita dai Rukky kamar ba ta yarda ba amman ta kasa yi ma Mimin gardama bi sa ga abin alherin da ta yi masa. Cikin ikon Allah kuma sai ga shi da Jaheed ɗin ya kirata ta saurare shi har ta ke jin za ta iya manejj da shi a yanzu ko hakan zai rage mata damuwa a kan Nasir da har yanzu ba wata mgana mai daɗi daga bangarensa.   Kwanansu Aji takwas suka dawo Mimi ta shirya masa tarba amman kuma sai ya Dawo a fusace kamar ya na jiranta.Faɗa kan faɗa ya na cewa shi ba zai iya ba ana kallonsa da mutumcinsa amman daga gefe ana masa kallon sakarai. Abun ya ɗaurea Mimi kai ta ga dai ko da safen nan suna hanya sun yi mgana lafiya lau amman ya dawo kamar ya na jiranta ko an gaya masa wani abu ne a kanta mara daɗi ko an ce masa ta yin wanin abin ne? Cikin mamaki Mimi ta ce" Me kuma na yi? Ko wani abu ne ya faru? Kai tsaye ya ce"Komai ma ai ya faru, aikin nan na ki Allah za mu samu matsala da ke in har haka za'a cigaba da yin sa" Kenan mganar aikinta ne sai ta kasa mgana amman tana mamakin abin kuma ya faru. Wayarsa ya danna ya nuna mata Sreenshoot ɗin da ya yi.   Ashe wai shirin labaran da sukan ɗora a shafin su ta facebook wani ya yi comment da cewa" Na ga Hajiya Mimi na ta kumatu ne ko dai an samu ƙaruwa ne? Aji to ya shiga kuma ya ga wannan Comment ɗin a hanyarsa ta dawowa shi ne fa ya dawo a fusace. "Ba ta yuyuwa kina matata amman daga gefe kina burge wasu banzayen ba,ki ji fa wannan wulaƙanci? Ina ruwan sa in kin yi kumatun? In ma kina da cikin ina ruwan sa? Matarsa ce? Ko ƙanwarsa ne ya dace ya Faɗi haka? Mimi ta kasa mgana kanta na kasa ta ce"Ka yi hakuri zan musu magana su rufe comments section ɗin" Tashi ya yi a fusace ya shige ciki ya bar Mimi da dafe kai, gabaɗaya tarban da ta shirya masa duk ya rushe saboda kishi baya ya juya mata duk son harka irin ta Aji  bai laluɓeta ba, ga shi ta sha kayan gyara daga Kwararriyar mai gyaran amare da uwargidaye daga Surayya Dee Bojuwa da kanta. Kayan gyaranta suna da kyau da inganci tun da Mimi fa fahimci nagartansu shikenan ta riƙe su, kema in kina son zama tauraruwar mata a wajen mijinta irin Mimin Aji nemi Surayya dee Bojuwa domin ki zama kasaittaciyar mace a gidan auranki.+234 803 277 3332. Tuni yanzu Mimi ke da lambarta suna waya duk abin da take so, in ta siya za'a saka a mota a kawo mata har gida, wani lokacin daga gidan yadikko ta kan saka makocinsu ɗin nan ya karɓo mata a tasha ya kawo mata har gida.   Sai da mganar nan ta fi sati sanman Aji ya bar ta ta wuce, shima bayan Mimi ta yi ma Manaja mganar a rufe comments section mutane ba sa sanin abin da suke faɗa. Kada mutane su kashe mata aure saboda mijinta na da kishi, maganganun na su ya na harzuƙa shi, kowa ya aminta da ita sai kawai a ka rufe  comments section ɗin gabaɗaya.. Aji kuma ko yana zaune ne in ya tuna da abin  sai ya yi ta tsaki shi kaɗai har ce ma Mimi Ya yi" Malama wai ba za ki iya komawa wani shashen da ba mai ganin fuskar ki ba ne? Kawarki ai tare kuke aiki amman ai ba'a ganinta ko? Mimi shuru ta yi ba ta ce komai ba, saboda lamarin Aji ya daina bata mamaki neman fin karfinta ma yake yi. Kishin sa a kanta mai yawa ne, ba ƙaramin hakuri yake yi da aikin nan nata ba amman in abun ya kunna shi ya riƙa cewa"Kai da matarka amman ba kai kaɗai take Burgewa ba, har da kowani kare da doki." Ita dai bakin Mimi daga ka yi hakuri sai kuma shuru kada ta furta wami abu na ta ya yi zafi.   Inna Meri daga Tureta. Argungun ta wuce ta na can ba ta ma saka ranar dawowa ba, ba ta nan a ka yaye su Walida, a ka ba su certificate  Tana kuma wajen Mqgajiya har a lkacin kuma lafiya kalau ba nuna bambamci tsakaninta da Mariya. Sai dai ta leƙa gidan Bintu ita da Mariya, kwana biyu da yayesu suka fara zuwa gidan Bahijja ita da Mariya saboda darajan Inna yasa Bahijjan kyauta za ta koya musu, duk da tana karɓan 20k na mutum ɗaya a wata shidda shekara 40k kenan. Sai da inna meri ta shafe sati shidda da kwanaki samman ta dawo gidanta, yaranta duk sun yi kewarta Mu'azzam ya zo mata sannu da zuwa tare da gaisuwa Hibba ba ta zo ba cikinta ya yi girma ba ta iya doguwar tafiya, Inna ta raba tsarabanta hida uku ne, ka shi ɗaya na ƴayanta ɗayan kuma ta aika ma Magajiya ta ce ta diɓar ma su gaje ɗayan kuma ta rabama makota da abokan arziki Har Hajiya ta zo ma Inna gaisuwa ta ɗiɓan mata tsaraban gujiya da gyaɗa da yawa da ta zo da shi. Daman washegarin ranar da ta dawo Mimi Daga wajen aiki nan ta yini sai dare Aji ya zo ya ɗauketa suka koma gida suma ta tarin tsaraban su, Walida tana murna Inna ta dawo gida daman ta yi kewar Inna. Abin mamaki kaf yaran Magajiya sun zo ma Inna gaisuwa. Sannan kwananta huɗu da dawowa a daran Magajiya ta zo ita da Gaje Maeesha tare da Matar Auwlu suka zo.   Karon farko da Magajiya ta tako kafarta gidan inna, ta kuma ta karbesu hannu biyu, sun jima sai wajem goma na dare suka tafi, Magajiya dai ta kasa sakin jiki kunya da Nauyin sun isheta ta gama ganin ishara, Innar dai da take yi ma hassada da kyashi ta ga in da Ubangiji ya yi da rayuwarta ita kuma hassadarta da kyashinta ya cinyeta, Ƴaƴan inma Merin sune gatan su ita da na ta iyalan gaba da naya, ita Inna Meri ko a fuska ba ta nuna wai daman ba su shiri da Magajiya ba suna ta hira da Gaje tana kuma sako magajiya a cikin zencen na su. Daman haka rayuwa ta gada, hassada mugun ciwo ne mai hassada sai ta ci sa, in ka zauna da kowa lafiya da zuciya ɗaya sai Ubangiji ya turama masu hassada da kyashi a aniyarsu.   Bangaren Rukky da Jaheed kuma soyayya ta mika har Jaheed ya zo garin saboda Rukayya. Maganar Nasir kuma ta sha ruwa tun da mahaifiyarsa ba ta amince ba.  Nasir ya yi ma Aji mgana shi dai ya ba shi shawaran ya fara daidaitawa da iyayensa tukunna, haka su Ahmad suka ce da ya fito group ya yi mganar, ita kuma Rukky Jaheed ya fara ɗauke mata hankali ya zo gida sun yi magana da alamu za su daidaita nan da lokaci kaɗan Mimi ta fi kowa murna. Tana so ta yi mganar da Aji sai kuma ta sha'afa yasa har lokacin bai san abin da ke faruwa ba. ****** _Monday_ Tun da ta tashi take jin jikinta ba daɗi amman ba ta nuna ba, Aji da wuri ya fita suna da morning traning tare suka fita ya sauke ta wajen aiki da cewa za ta kira shi in ta tashi domin ya je ya ɗauko ta. Kanta ke sara mata da safen kuma ta sha paracetamol, amman kamar ya sauka ashe bai sauka ba dakyar ta gama karanta L Labaran safe ta koma Setting Room ta kwanta.   Cikin lokaci kaɗan sai zazzabi ya rufeta ta fara rawan sanyin Aisha Farida ce ta je ta kira mata Rukky ta ga halin da take ciki. Sai ta yi amfani da wayar Mimi ta kira Aji amman har kira uku bai ɗauka ba, itama kuma tunanin abun na gaggawa ne ya sa ta kira Jaheed ta ce ya zo ma'aikata ya same su Mimi ba ta da lafiya  jin haka ya sa a ruɗe ya taho daman bai koma ba a ranar yake tunanin bin jirgi zuwa Lagos. Ba jimawa sai ga shi ya zo, zafin zazzabi yasa Mimi ta kasa ma mgana Rukky ta riketa suka fita ana bin su da Allah ya sauwake ganin ko iya buɗe ido ba ta yi ya sa Jaheed yace su tafi asibitin da suke zuwa itama a can Mimi ke da katin ta. Wani asibitin kuɗi ne suna zuwa a ka karɓi Mimi aka dibi jininta, sai a ka saka mata drip da allurai. Jaheed da Rukky suna tare da ita, Ita Rukky ta manta da wayar Mimi a cikin jakarta kuma sun barota a motar Jaheed, Aji na ta kira ba'a ɗauka ba daga Camp ma'aikatansu ya biya Na misau ke gaya masa Mimi ba ta da lafiya Rukayya da wani namiji sun zo sun ɗauketa.   Da farko ya ɗauka Nasir ne sai da ya kira shi sai yace masa yana wajen aiki. Sai ya fara tunanin to waye? Shi kuma ba shi da L lambar Rukayyan ballantana ya kira sai ya yi tunanin ya je gida ya gani, nan ma ba ta nan  kuma ya na cigaba da kiran wayarta amman ba'a ɗauka ba har bayan la'asar. Ba tunanin da sheɗan bai sakaa masa ba Har hassowa ya yi wai Mimi ta bi wani namijim Ransa in ya yi dubu ya ɓaci, kirjinsa na sama da kasa idanuwansa sun yi jajirce, Zagaye kawai ya ke yi a falo ko zama ya kasa yi ya kira wayar Mimi bai san iyaka ba amman ba ta iya ɗauka ba.   Su kuma suna asibitin har la'asar sai da a ka cire ma Mimi ƙarin ruwa sannan eesult ya fito, Mimi ciki gare ta na tsawon sati shidda da kwanaki, ita kanta ba ta san da shi ba amman dai ta san watan da ya gabata ta yi ɓatan wata, Ita likitar ma ya ba ma tarkadan sakamakon Rukayya da Jaheed suna waje kuma ko da ta fito ba ta faɗa musu ba sai kawai ta ce maleria ce,  da tare da Rukky za'a kaita gida amman sai mamansu ta kira waya hankali ta she ta ce Rukayya ta zo mijin Bibi ya kirata ya ce tana asibiti za ta haihu., Don ma ta yi ɓarin cikin ta na farko da ta jima da haihuwa. Dalilin da ya sa suka rabu a nan kenan ta hau abin hawa zuwa asibitin da a kace Bibi na can ta na naguda shi kuma Jaheed ya ɗauko Mimi zuwa gidanta.   Aji na jin ƙaran bude get ya yi zaraf ya fito haraban gidan a kan idanuwanshi Jaheed ya shigo da motarsa ya yi parkimg sannan ya fito ya zagaya ya buɗe ma Mimi ta fito. Jikinta ba karfi yasa ta yi kamar za ta faɗi sai ya riketa sannan ya karbi jakar hannunta, takardan Result ɗin cikin kuma na cikin aljihun rigan jikinta ta saka. Aji na ƙofar falon gidan yana kare musu kallo a ƙankance, Ba abin da sheɗan ke gaya masa sai Mimi ta bi tsohon saurayinta sun je sun gama yawon iskancin su shi ne ya kawota gida saboda dukkansu ba su da kunya. Saboda kishi da ɓacin rai har wani huci mai zafi yake fitarwa ta baki Mimi ta na tafe a hankali jaheed na riƙe da hannunta tana dagowa suka haɗa ido da Aji sai da ta ji ta warke gabaɗaya da sauri ta kwace hannunta a na Jaheed ta na jin gabanta na faɗuwa. Aji a fusace ya juya ya koma cikin falon yana tsaye ya na zagayen falon yana huci hannayensa goye a bayansa. Suna shigowa Mimi ce a kan gaba sai Jaheed ya na tafe da jakar Mimi da ledan mganganinta na karin jini da na saka cin abinci, tunda an rubuta magani suka tsaya phamarcy suka siya.    Mimi ce ta yi sallama amman ko ƙarisa sallaman ba ta yi ba Aji ya daka mata wata razananiyar tsawar da sai da ta yi baya kaman za ta faɗi, Jaheed dake bayanta ya tare ta yana faɗin" Subhanallah ki yi a hankali kin san jikin ki ba karfi." Aji ya kallesu tuni sheɗan ya haska masa zargi a cikin zuciyarsa idanuwansa ya rufe bai yi tunanin da ya ciza ya hura ba. Cikin nuna su da yatsa ya ce"Me kuma ya kawo ku gidana? Wato saboda ba ku da kunya kun gama watsewar ta ku a waje shi ne sai kun zo har gabana kun nuna min ku ƴan ta zubar ne? Mamaki ya hana daga Mimi har Jaheed magana, kawai sai Aji ya cigaba da faɗin"Ashe kina can tare da tsohon saurayin ki shi ya sa nake ta kiran wayarki ba ki ɗauka ba ko? To me ya dawo da ke gidana,? Me ya sa ba ki bi shi can gidan na su ku cigaba da barbaɗan naku ba." "MANSOOR...!"   Mimi ta ƙwala sunan shi cikin karfi da karkarwa ba in da jikinta ba ya rawa, Idanuwanta har sun fara zubar kwallah ta nuna kanta Lokaci ɗaya tana faɗin"Me ka ke nufi? Kana nufin kana zargina ne da Jaheed? Kai tsaye ya ce"Ba zargi ba ne tabbaci ne, saboda ga shi nan tare kuka dawo kuma Saboda ba ku da kunya a gaban idanuwana yake taɓaki ai dai kwaji kunyar aikata son ranku a gaban idanuwana amman da yake damman an ce mara kunya ya aikata duk abin da ya ke so. Ya yi miki kyau." Ya karishe faɗa cikin fusata Jaheed ya buɗe baki zai yi mgana Mimi ta hana shi. Kukan bakinciki take yi da har gobe Aji bai yarda da ita ba, da zai yi tunanin za ta iya cin amnarsa da wani namijin? Ko ya yi nadaman kalamansa saboda Idanuwansa ya rufe yasa ya ce ta juya su koma in da suka fito, ba musu ta juya za ta fita Jaheed ya ce"A'a Mimi ki tsaya na yi masa bayani." A Fusace ta ce" Sai ka tsaya ko ba ka ji abin da yace ba ne? Tunda ya na zargina babu amfani zama da wanda ba zai iya shedar ka ko a bayan idonka ba." Daga haka ta fice Jaheed da Aji suka kalli juna kafin Jaheed kaɗa kai yana faɗin" Ina jin tsoron wannan kishin naka kada ya lalata muku aure, ya kamata in rai ya ɓaci hankali ya nemosa, sannan ka sani in an ciza a hura saboda kada rashin hurawar ya taho da nadama." Ya na gama faɗin haka ya juya ya bi bayan Mimi da sassarfa, Aji sai ya tsaya yana kallon in da suka bi a cikin zuciyarsa yana faɗin"Sai kuma ta bi shii ɗin suka fita? Bai ƙara dawowa hayyacinsa ba sai da ya ji ƙaran buɗw get yana leƙawa ta window ya ga motar Jaheed ta fice daga gidan. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3016* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Sheɗan ya shiga hasko masa su cikin yanayin da bai kamata ba, kenan ta zaɓe shi a kan shi,? Sun koma su cigaba da abin da suke yi kenan? Wani irin tururi ya ji yana fitowa daga cikin zuciyarsa har ya na jin hucin zafin a cikin fatar jikinsa, bakinsa ya saki iskar na fita yana ta kuma sakin hucin da sauri sauri ga sanyin A.C ga na fanka amman gumi na ke tsattsatso masa kamar wanda a ka watsa ma ruwa. Bai san lokacin da ya dungule hannanunsa guda ɗaya ya daki bangon ɗakin  da shi ba.   Ya ji radaɗin har a tsakar kansa daga. Har sai da ya yarfe hannu nasa saboda azaba. Cije baki ya yi kafin ya kalli hannun nasa ganin ya sale har ya fara jini kan kujera ya koma ya zauna ya na ƙokarin daidaita numfashinsa da ke fita da zafi sannan a kai a kai kamar wanda ya yi gudun tsere, yana nan a zaune nan ba abin da sheɗen bai saka masa ba har tunani ya yi daman raba musu jiki Mimi take yi shi da wannan tsohon saurayin nata? Ya kasa tuna waye Fatima a wajensa? Ya kasa tuna matsayinta a ransa ya kasa tuna shi ya karɓi ƴan matancinta, ya kasa yi mata kyakyawan sheda saboda kishinsa na banza da wofi ya saka zargi a cikin auransa.   Duk da haka ya kasa samun natsuwa. Har waya ya ɗauka zai sake kiranta amman ya fasa ya kuma kasa fita ko'ina ya na gida ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunaninsa bai hasaso masa me zai faru ba, a tunanin shi duk in da ta je za ta dawo, in tana kunya ba za ta bari wani ya san abin da ta aikata ba. Yana gidan a zaune a saman kujera a cikin falon yana kallon ƙofar falon, motsi kaɗan zai ji zai ta shi ya leƙa ta window amman Har mangariba ba Mimi ba dalilinta sai ya fara tunanin ina ta bi shi suka tafi? Gidan Hajiya? An ya za ta je can kuwa?   A lokacin idanuwansa sun rufe ya kasa sarrafa zuciyarsa har sai da ya ga an yi isha'i tara ta kusa na dare sannan  nadama ya fara shigarsa ya fara tambayar kansa da me na aikata kenan? Cikin Rawam jiki ya ɗauki waya ya kirata amman sai ya samu wayarta ta na kashe, kansa ya dafe da ke sara masa a karon farko ya furta" Hasbunallahi wa'imal wakel." Ya aikata kuskure babba. Zafin zuciya da kishi sun saka Mimi ta zaɓi wani namiji sama da shi, hankalinsa ya dawo jikinsa ya na tuna kalaman da ya je fa mata, Ya san Mimi mai tarbiyace duk abin da ya ke tuhumanta a kasan ranshi yasan ba za ta aikata ba amman sheɗan ne da bakar zuciyarsa suka kaisa suka baro sa. Tunanin kiran Hajiya ya yi, amman kuma sai ya fasa saboda kunya me zai gaya mata in Har Mimi ta je ta faɗa mata mganganun da ya yi a kanta? Kansa ya dafe ya na faɗin"Aji me ya sa ka yi haka? Sai yau ya fara jin haushin kansa da haushin wannan zuciyar tasa, sannan ya fara tunanin kishinsa zai saka wata rana ya aikata wani abun da zai dawo yana kuka da idanuwanshi saboda nadama.  Ko abinci ya kasa ci, ruwa ma bai iya saka ma cikinsa ba, barci kuma sai dai ɓarawo amman kusan raba dare ya yi a falo idonsa biyu wayar Mimi kuma ya kira bai san adadi ba har ya gaji ya tura mata saƙo. _Don Allah Mimi ki yi hakuri ki faɗa min in da kike sai na zo mu yi mgana. Ki tausayamin sharrin sheɗan ne_   Tunaninsa Allah ya sa ba gidan Hajiya ta je ba. Sannan Fatansa ya sa ko kila gidan kawarta Rukayya ta je, amman in har ta je gidan Daddy ta faɗa masa, to shi fa ba shi da bakin kuma da zai iya kare kansa wannan karon. ***** MIMI. Bangaren Mimi kuwa tana zaune a bangaren mai zaman banza a motar Jaheed amman ban da kuka babu abin da take yi, kuka sosai mai Sauti fuskarta ta yi chaɓa chaɓa da hawaye har da majina Jaheed na bata hakuri amman kamar yana ma ƙara zuga ta ne. "Mimi don Allah ki daina kuka, kin ga fa halin da kike ciki, ba ki da lafiya na ce miki mu koma ki ba shi hakuri mu yi masa bayanin abin da ya faru."   Mimi ta dago fuskarta duk hawaye cikin Kuka ta ce"Ba ya bukatar wani bayani Jaheed da kunnen ka  ka ji ya ce ba zargi ya ke yi ba, tabbaci gare shi a kan ina cin mmanarsa tare da kai, abin da ya fi min baƙin ciki ace yau mijin da kake so kuma ka ke aure shi ne ba zai iya shedar ka ba. Yau ni Aji ke kira da lalattaciya ina lalacewa da wani namijin Alhalin nasan ina da aure wannan abun ya fi komai baƙan tamin rai."   Tana gama faɗin haka sai ta ƙara rushewa da kuka Jaheed ya girgiza kansa cikin damuwa kafin ya ce" Gaskiya bai kyauta ba, bai kamata ya yi haka ba." Daga haka sai ya yi shuru saboda shi ya ma rasa abun faɗamSuna tafe Mimi na cigaba da kuka Rukayya ta kira wayar Jaheed bai ɗauka ba saboda kukan Mimi sai ya maida wayar a silent. Kuka take yi ta manta ma da in da take  sai dai kawai ta ga Jaheed na hon a bakin get ɗin gidan Hajiya sannan ta dawo cikin hayyacinta. Da sauri ta kalli Jaheed hankalinta a tashe lokaci ɗaya tana faɗin" A'a mu juya Jaheed ba zan je ma Hajiya cikin wannan yanayin ba." "To ina za ki je? Ta yi shuru kafin ta ce" Mu je gidan su, wajen mahaifiyarsa."   Jaheed ya kalli Mimi kafin ya ce"Me ya sa sai can? Kai tsaye Mimi ta ce"Ba na so wani acikin dangina ya san abin da ya faru, kowani aure ya na da nashi ƙalubalen Jaheed. Gwara na je wajen mahaifiyarsa a kan na je ma Hajiya ina koke koke." Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa har Megadi ya leko ganin motar Jaheed ya buɗe get amman sai ya ga ya juya kawai ya mike bai shiga gidan ba cikin mamaki ya bi motar da kallo kafin ya koma ya rufe get ɗin bai lura ma da Mimi da ke gaban mota ba a tunaninsa ƙila wani uzirin ne ya sa bai shiga gidan ba.   Suna ta fe Mimi na masa ƙwatance har ƙofar gidan Inna Meri, Jaheed ya bi gidan da kallo kafin ya ce"Nan ne gidan? Sai ta kaɗa masa kai ta na share hawayen fuskarta da mayafinta lokaci ɗaya tana faɗin" Eh nan ne Mahaifiyarsa ke zaune." Sai suka yi shuru gabaɗaya. Jaheed ya mika mata jakarta da ledar mganinta kafin ya ce"Ki kula da kanki, kinsan dai ba ki da lafiya." Ta buɗe baki za ta yi mgana da sauri ya tare ta da faɗin" Na sani ba zan gaya ma kowa ba. Ciki ko har da  Rukayya, ba na fatan na zama silar samun matsala ga auran ki, ki yi masa bayani in ma bai yarda ba akwai Rukayya ita za ta zama shedarmu." Wani mirmishin takaici Mimi ta yi kafin ta ce"Kada ka damu ba abin da zai faru. Na gode kwarai ka gaida su Daddy." Da ga haka ta buɗe mota ta fita. Ta ɗaga masa hannu shima ya ɗaga mata sannan ta juya tana tafe a hankali jiri ma take gani, mamakin ta wai tana ciki? Bayan ɓatan watan nan ba ta fahimci wani alamun tana da shigar ciki ba sai yau da zazzaɓi ya rufe ta.   Gidan ya na buɗe sakayawa kawai a hankali ta tura kanta ta shiga  yamma ta yi tunda shidda saura ne, Inna Meri na tsakar gida tana kwashe shanyar zogalan da ta zo da ita daga can gida ɗanya shi ne take shanyawa tare yakuwa, ganin mangariba ta kusa yasa ta fito tana kwashewa. Tana duke ta na tsince na kasan da ya zube lokaci ɗaya tana sakawa cikin farantin gabanta,  ba ta ji sallamar Mimi na farko ba sai da ta ƙara yi sannan ta ji ta, da sauri kuma ta ɗago kanta tana kallon Mimi take tafiya dakyar kamar za ta faɗi, Cikin mamaki Inna Meri ta miƙe lokaci ɗaya tana faɗin" Binta?  ke ce da yamman nan? Kalamanta sun tsaya sanda ta ga Mimi ta dafe kanta. Jakar hannunta ta sulale tare da ledan mganinta wani irin juwa ce ta kwashe ta za ta kai ƙasa cikin zafin nama Inna Meri ta tare ta lokaci ɗaya tana faɗin" Subhanallah Binta ba ki da lafiya ne?   Ba mgana sai kawai Mimi ta saka mata kuka, Inna ta ruɗe ga shi ita kaɗai ce a gidan Walida ba ta dawo daga wajen koyon ɗinki ba. Sai ta rike Mimi ta taimaka mata zuwa cikin falo ta zaunar da ita a kan Kujera, amman sai ta koma ta kwanta Inna Meri ta yi mata zuru tana kallonta lokaci ɗaya da nazarinta ba ta raba ɗayan biyu Fitinannen yaron nan ne ya yi wata tsiyar, Sake fita ta yi ta je ta kwaso jakan da ledan mganin ta duba daman ai daga ganin Binta ba ta da lafiya duk ta wani ɗashe, Inna ba maganin ta gani ta fahimta ba ita fa uwace tun lokacin da ta dawo Mimin ta zo mata sannu da zuwa ta ga yadda ta yi wani fari ta ga alamun Bintar na da shigar ciki, kuma a tunaninta daman dukkansu da ga ita har Baban Inna ba su san dashi ba.   Falon ta koma ta iske Mimi na rawan sanyi sai ta shiga ɗakin walida ta ijiye mata jakar da kedan ta ɗauko mata blanket bargo ta rufa mata sai faman jera mata sannu take yi, ta koma ta kashe fanka  falon sannan tunda mangriba ta kusa. Sai ta saki labulayen falon ta kuma rufe ƙofar falon da Window saboda ɗakin dai ya yi ɗumi, kitchen ta shiga ta kunna gas tunda ta iya sai ta ɗora ma Mimi ruwan zafi ta samu ta yi wanka ta gasa jikinta sai taci wani abu ta sha mgani ruwan na tafasa ta fito falon sai ta isken Mimin na barci sai ta kyaleta. Har a ka kira mangariba tana barci Inna Meri kuma ba ta tashe ta ba. Ta shiga ciki ta ɗauro alwala ta zo nan falo ta shimfiɗa sallaya tana cikin sallar ne Walida ta shigo gidan Inna ma jin ta tana faɗin"Laa Anty Mimi' Sai kuma ta leƙa ta kafin ta ɗago tana kallon Inna, goshinta ta taɓa ta ji da zafi kaɗan sannan ta ga tana zufa. "Inna Anty Mimi ba ta da lafiya ne?   Innar na sallah ya sa ta san ba za ta samu amsarta ba. Sai ta kwashi hijabinta da jakarta zuwa cikin ɗakinta ta na shiga ta ji ana ta kiran waya a jakar Mimi ta gani yasan ta san wayarta ce ta buɗe kenan ta ɗauko wayar ta ga an saka Baby kafin ma ta yi wani abu wayar ta ɗauke da alamu ƙila ba chaji ne, ba ta yi tunanin saka mata chajin ba sai dai ta maida mata wayarta cikin jaka, ledan maganin ta ɗauka ta duba abun ya ba ta mamaki Yaya Mansoor ya yi tafiya ne? In ba haka ba me Anty mimi ke yi a gidan nan a dai dai wannan lokacin? Ba ta da mai ba ta amsa ba ya sa ita ma ta sauke kayan hannunta ta faɗa tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallah tana cikin tahiyar karshe ta ji Inna na ƙwalamata kira shi ya sa tana sallamewa ta fice zuwa falo tana ce ma Inna ta na sallah ne lokacin da take kiranta.   Inna Meri ta kalli Mimi da ta farka ta janyen bargo daga jikinta saboda zazzabin ya sauka zafi ma take ji, cikin tausayawa Inna ta ce" Sannu Binta ya jikin? Mimi kamar mai ciwon baki ta amsa ma Inna da sauƙi, Walida ma ta karisa kusa da ita ta zauna lokaci ɗaya ta na faɗin"Anty Mimi Allah ya baki Lafiya.". Ta amsa da Amin idanuwanta sun tasa abun ka ga farar fata duk fuskarta ta bayyana halin da take ciki. Walida Inna Meri ta kallah kafin ta ce"ki je kicthen na saka mata ruwan zafi ki sake ki kai mata bayi ta samu ta yi wanka ko jikin nata zai saki." Daman abin da Mimi take bukata kenan wanka, da sauri ko Walida ta mike ga aikin da Inna ta sakata. Sai falon ya yi shuru Inna sai ta maida hankalinta kan laziminta amman tana ganin Bintar na share ƙwalla, tausayinta ya kamata wai har yaushe ne Baban Inna zai bar rayuwar ƴar mutane ta zauna cikin salama ne? Ta san wlh tsiyar shi ce amman bari Bintar ta natsa ta ji abin d kuma ya sake aikatawa wannan karon.   Bayan Walida ta kai mata ruwan zafi saboda jikinta ba karfi, ta mike Walida ta riketa hannun da a ka yi mata karin ruwa har ya kumbura da walida ta taɓa wajen sai da Mimi ta yi wash, cikin sauri walida ta saki hannu kafin ta ce"Sannu ƙarin ruwa a ka yi miki? Mimi ta gyaɗa kanta kafin ta ce"Daga wajen aiki ne na fara ciwom sai Rukayya ta kaini asibiti can na yini aka sakamin ruwa da Allurai." Inna Meri da Walida suka haɗa baki wajen faɗin Allah ya ƙara lafiya.   Cikin kayan Walida. Walidar ta zaɓo mata wata doguwar riga, da yake daman rigar ta mata yawa ta kuma san za ta yi ma Mimin,Ai ko ta ji daɗin gasa jikinta sosai sannan ta ɗauro alwala salla tun ta asuba rabon ta da yi, rigar ta saka ta yi mata sai dai tsawon ne ya yi mata kaɗan sai ta ce Walida ta bata zani ta ɗora saman rigar ta yi salla kuma Alhamudulillah a tsaye ta yi sallar tunda ta samu sauƙi tana idarwa Walida ta kawo mata Tea mai ƙauri da buredi ta sha, sai ta fara dawowa daidai, bayan tea ta  dafa mata Indomie da ƙwai taci ta yi kat sannan ta sha ruwa, ba ta da alwala ya sa ta koma Tiolet ta yi alwala ta zo ta yi sallar Isha'i ta sha mganinta sannan Walida ta gyara mata gado ta hau ta kwanta, Inna Meri ta zo ta dubata ganin har ta kwanta ya sa ta kyaleta ta huta zuwa da safe.   Walida ce ta kasa hakuri ta koma falo tana faɗin" Inna wai anan Anty Mimi za ta kwana? Inna ta amsa mata da eh, cikin ƙarim mamaki ta ce"To ko Yaya Mansoor ya yi tafiya ne? Inna ta kalleta kafin ta ce"Ban sani ba, ba na son tambaye tambaye mara amfani, ki je ki kwanta ki kula da ita tunda ba ta da lafiya." Ganin Inna ta haɗe rai ya sa Walida ta kama bakinta ta yi shuru, ta yi ma Inna sai da safe ta koma ɗakin ta shimfiɗa bargo a kasan cafet ta yi shirin kwanciya sannan ta kwanta ta ɗauki wayarta tana danne danne. Ba su farka ba sai asuba Mimi ta ji daɗin barcin nan ta kuma ta shi kamar ba ita ba. Bayan sun idar da sallah Walida ta fita gyaran gida tunda da wuri take fita, Mimi ba ta san wayarta ta mutu ba sai da ta ɗauko domin kiran Rukayya ta gaya mata ta cike mata takarda za ta ɗauki hutu ba ta da lafiya sai ta samu wayar a kashe, da chazar Walida ta saka chaji sannan ta koma ta zauna a wajen har ta ɗan farfaɗo ta kunna wayar ta na gama saituwa sannan saƙo ya shigo wayar daga Aji tana gani ko dubawa ba ta yi ba, tana shirin kiran Rukky sai ga kiran jaheed ta san yana ta neman lambarta bai samu ba.   Ta ɗauka a sanyaye suka gaisa ya ce ya jikinta ta ce masa ta ji sauƙi. Kai tsaye ya ce"Ina fatan ba matsala? Kai tsaye itama ta ce"Da Sauki dai, za mu yi mgana daga baya." Da ga haka suka yi sallama bayan ya ce ta kira Rukky tana ta neman wayarta itama a kashe. Suna gama waya Rukkyn ta kira nan take gaya mata Bibi ta haihu aiki a ka yi mata ta samu mace suma asibiti, Mimi ta yi mata Allah ya raya sannan ta ce in ta shiga ma'aikata ta rubuta mata takarda sai ta ce mata eh za ta je. Daman Manaja ya san ba ta jin daɗi amman za ta je ta yi rubutun ta ba da, ko alama Mimi ba ta nuna ma Rukayya wani abu ba itama ba ta sani ba tunda Jahedd ya rike alƙwari bai faɗa ma kowa ba .   Tana gama abunda za ta yi da wayar ta sannan ta kashe wayar ta maida ta chaji, ta na shirin komawa ta kwanta Inna Meri ta shigo cikin ɗakin sanye da hijabin da ta yi salla. Mimi na ganin ta da sauri ta duka ta na gaisheta Inna Meri ta zauna gefen gado lokaci ɗaya tana faɗin" Tashi ki zauna Binta ke da ba ki da lafiya? Sannu ya karfin jikin na ki? Ta amsa mata da sauƙi kanta na ƙasa, Inna Meri ta yi mata fatan Allah ya kawo afuwa, shuru na wani lokaci sannan Inna Meri ta gyara zama lokaci ɗaya tana kiran sunan Mimin. "Fatima.." Mimi ta ɗago tana kallon Inna Meri bayan itama ta daidaita zaman ta a nan gefen gadon na Walida ta amsa mata cikin ƙanƙantar da kai. "Kin ɗauke ni a matsayin uwa Ko Fatima? Mimi ta gyaɗa kanta sannan Inna Meri ta cigaba da faɗin"Na kuma ga haka, tunda ki ka zo wajena ba tare da kin tafi ga Hajiya ko Mahaifiyarki ba  na ji daɗi da kika mutumtani Binta, ki faɗamin abin da ya faru kika zo gidan nan cikin wani yanayi kuma har kika kwana ban ga megidan ki ya zo bin bayan ki ba? Me ya faru? Ki faɗa min kada ki ɓoyemin komai domin Allah Fatima."   Inna Meri ta ƙarishe faɗa tana kallonta Mimi kuma sai ta ji idanuwanta sun cika kwallah, ta kasa mgana jikinta har ya fara rawa Da sauri Inna ta matsa kusa da ita ta na mai dafa kafaɗanta kafin ta ce"Kada ki damu ni uwace, mai jin damuwar ƴaƴanta ta kuma taya su addu'a ko kuma in tana da hanyar mangancewa ta yi musu mganin damuwarsu, ki sanar da ni abin da ke faruwa nayi miki alƙwarin yi ma duk abin da ya faru adalci in sha Allahu." Mimi sai kawai ta fashe da kuka har da shessheƙa Inna kuma na faman lallashinta da kalamai ma su sanyaya zuciya lokaci ɗaya tana bubbuga kafaɗan ta da hannayenta.   Sai da Mimi ta samu natsuwa sannan ta iya warware ma Inna Meri abin da ya faru, wannan karon ba za ta iya rufa masa asiri tun da har ya saka zargi a zaman auran su, ta karishe da faɗin" Inna abu ɗaya ya fi min zafi yadda Mansoor ya kasa shaidata ya ce tabbaci gare shi ina cin amanarsa da ɗan'uwana, ya saka zargi a cikin ransa kinga kenan ya na so ya ɓata auran mu, sannan da bakinsa ya ce na fitar masa daga gida na koma in da na fito daga yawon iskancin nawa." Ta faɗa ta na kuka da karfi saboda yadda in ta tuna abun ta ke jin kamar bakin ciki zai kasheta.   Inna Meri ranta ya yi mummunan ɓaci ba ta san lokacin da ta ja wani dogon salati ba" Innalillahi wa'inna alaihirraju'un na shiga uku ni Meri, a she Baban Inna dabba ne jaki ne kuma ni ban sani ba? Haka ta faɗa saboda ranta ya ɓaci ta rasa ma wani suna za ta kira Baban Inna da shi. Cikin harzuƙa ta cigaba da faɗin"Sakarai ne ashe mara tunani ya na abu kamar jahili wanda bai je makaranta ba? Da kansa zai lalata auran shi? da kansa zai kalle ki ya ce ya na zargin ki? Ashe shi jaki ne ban sani ba.? Inna Meri ta ƙarishe faɗa itama baƙin cikin duniya ya ishe ta. Me ya sa Mansoor ba shi da hankali ne ba ya tunani in zai aikata abu? Shi ya sa ta sha faɗa masa in dan an ciza a hura saboda gudun nadama wata rana. Kafaɗan Mimi ta dafa lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi hakuri don Allah Binta ki daina kuka, na kuma gode ma Allah da kika yi tunanin zuwa wajena, ni kuma zan ɗauki matakin da ya dace kuma sai ya raina kansa zan saita masa tunani tunda na lira shi ɗin dabba ne mara hankali ai ko Mu'azzamu da yake ƙaninsa wlh ba zai yi abin da ya yi ba. Shashasha kawai ki yi kwanciyarki kada ki sake ki ɗaga wayarsa balle ki faɗa masa kina nan barsa zai zo da kafarsa tunda yana zargin ki kenan ba amfanin zaman ku tare sai ya zo ya sake ki ya auri wacce zai riƙa saka ta a riga yana yawo."   Dole Mimi ta yi shuru ganin Inna Meri ta fita ɗaukan zafi amman ba ta bar ɗakin ba sai da ta tattabar da Mimin ta daina kuka ta kuma share hawayenta sannan ta koma ɗakin ta  sai faɗa take yi ita kaɗai wannan karon sai ta ci ma Baban Inna mutumci tunda ba shi da tunani. Walida ta gama gyaran gida sannan ta yi musu abin karyawa itama ta karya sannan ta yi wanka ta ta fi wajen koyon ɗinkinta, Mimi kuma sai da ta yi wanka sannan ta karya ta sha mgani ta kwanta Inna kuma na zaune a falo tana jiran ta ga idon mara mutumcin. ****** *MANSOOR* Barcin kirki ma bai samu ba. Shi ya sa har ya na makara sallar asuba sai dai a gida ya yi ta shi, ga yunwa yana ji amman ya kasa ma kansa wani ƙokari har kuma da wayewar garin yana ta kiran wayar Mimi a kashe shi ya sa karfe bakwai ya bar gidan zuwa Camp sun yi morning traning bayan sun gama Daga nan ko gida bai je ba ya tafi gidan hajiya. Sai dai daga yanayin tarban da kuma zolayan Hajiya ya san Mimi ba ta zo ba domin Har Hajiya sai da ta ce"Yau kai kaɗai ka zo kenan? Ina ga ka zo dai mu sansanta ne shi ya sa ka baro ta a gida." Daga nan ya san Mimi ba ta zo ba sai kawai ya fake da ya zo gaida Hajiya ne  ya ijiye mata kuɗi bai daɗe ba ya bar gida.   Yana fitowa daga gidan ya kira Mommy a waya itama dai suna gaisawa ya ji ta ce" Ya wajen Mimi? Fatan duk kuna lafiya? Daga nan ya tsuke bakin shi suka gaisa ya katse wayarsa shine har Dr. Sulaiman ya kira shima ɗin dai ba wani bayani alamun dai Mimi ba ta je can ba, sai kawai ya saka ma ransa tana gidan su Rukayya daman ya san gidan sai ya kaɗa kan mota sai gidan su Rukayya, ya iske ba ta a gida sai ƙanwarsu karama ita ke gaya masa Anty Bibi ce ta haihun Mama na wajenta a sibiti Anty Baby kuma ta dawo amman ta shirya ta tafi wajen aiki. Sai a lokacin ya tuna ya ga kiran Makama jiya da daddare bai ɗauka ba kuma bai bi baya ba, kenan haihuwar matarsa yake son gaya masa.   Daga gidansu Ruƙayya ma'aikatansu na Karamchi Tv ya wuce, Rukky na can ma bangaren su Mimi ne suna mgana da Manaja, a ka ce tana da baƙo a waje ta yi mamakin ganin Aji,sai da gabanta ya faɗi ta ɗauka wani abun ne ya faru da ƙawar ta ta. Cikin ruɗewa ta ƙarisa gabansa cikin ruɗewa take faɗin" Me ya samu Mimin? Ko dai jikin ne ya tashi, na shiga uku ni Ruƙayya" Haka ta faɗa tana dafe ƙirjinta  Cikin mamaki Aji ya kalleta kafin ya ce"Ban gane ba. Daman ba ta da lafiya ne? "Ba ka sani ba? Itama Rukky ta maida masa martanin tambayansa cikin mamaki.   Sai ya ji kunya ta kamashi cikin wani yanayi yacce"Rukayya me ya faru? Don Allah ki gaya min ina Mimin ta je jiya? Rukayya cikin mamaki ta ce"Jiya ta zo wajen aiki ba ta da lafiya na kira wayarka baka ɗauka ban Sai na kira Jaheed ya zo ya kaimu asibiti a ka yi mata allurai da karin ruwa bayan an sallamo ta, za mu kai ta gida na samu waya cewa Bibi na asibiti. Sai na bar Jaheed ya kai ta gida ni kuma na wuce asibiti, ban gane duk ba ka san abin da ya faru ba? Yana kallon Rukayya cikin wani yanayi ya ce" Ina Fatiman take yanzu? Rukky fa ta fara tunanin akwai wani abu cikin karin mamaki ta ce" Ah ikon Allah kai zan tambaya ba tana gidanka ba l? Mun yi waya da ita da safen nan har ta ce min na zo cike mata takarda, za ta zauna a gida na kwana biyu sai ta ƙara warwarewa." Aji ya yi shuru kawai kamar ruwa ya ci sa, innalillahi kawai ya ke maimaita a cikin ransa. Me ya aikata? wani irin shirme ya tafka? Me ya yi ma kansa ne? Kawai sai ya juya zai shiga mota da sauri Rukayya ta ce"Mimin ba ta kwana a gida ba ne?Sai kawai ya kaɗa kai kafin yace" Kada ki damu ba matsala." Daga haka ya koma mota ya kunna ya bar haraban ma'aikatan.   Rukayya mamaki ya kamata sai kawai ta ɗaga waya ta kira Jaheed tana gaya masa abin da ya faru da kuma tambayan ko wani abu ya faru ne jiya? Bai gaya mata sai kawai ya ce"Ban sani ba, a waje na sauketa jiya nan." Da sauri Rukky tace"An ya? Ina zargin da wani abu. Mimi ba ta kwana a gida ba, Bari na sake kiranta." Da sauri ya ce" A'a Ruƙayya kyaleta. Shi aure daman ya gaji haka tunda ba ta faɗa miki ba to ba ta son ki sani ne, ki yi musu addu'an Allah ya daidaita su kawai." Shi ya hana Rukky sake kiran Mimi amman abun ya dameta tana tunanin me ne ya faru haka,? Jaheed kuma bai ba ta damar da za ta gane ya san wani abu ba, yana  ma faɗa mata Jirgin karfe uku zai bi zuwa lagos su haɗu a asibitin da a ka yi ma ƙanwarta aiki su yi sallama.   Shi kuma Aji daga ma'aikan su Mimi bulayi ya fara yi a gari duk in da ya yi tunanin Mimi na can ba ta je ba, to ta na ina? Ko dai tana gidan Bintu ne? Ya kira wayar Bintu ta ɗauka suka gaisa sai ya ji hayaniya sai yake tambayanta ta na ina ne? Sai ta ce masa tana  gidan su Bashir Hajiyarsa ba lafiya tunda ya ji haka ya san ba ta je bam Bayan Bintu har su Yaya Amina ya kira nan ma shuru suna ta tunanin yau Aji na jin zumunci duk ya kira su sun gaisa bai taɓa kawo tunanin tana wajen Inna ba  ganin ba shi da mafita ne ya sa ya yanke shawaran zuwa gaban Inna ya faɗi ya gaya mata duk abin da ya aikata ta taimake shi kada ya rasa Mimi in ya rasa ta ya shiga uku. Yana tafe a Mota kamar mara lafiya duk ya faɗa saboda bai ci komai ba tun jiya da rana.   A kofar gida ya bar motar, ya shiga gidan shima yana layi kamar zai faɗi, a tsakar gida ya ga Inna ta na shanya zogalanta ya yi sallama ta amsa masa a ciki ko kallonsa ba ta yi ba, tun bayan kallo ɗayan da ta yi masa bayan ya shigo ba ta kara ba. "Ina kwana Inna.."   Haka ya faɗa yana kokarin zama kan damdalin ƙofar ɗakin,  kamar ba ta jisa ba haka ta yi masa banza sai ya ƙara gaisheta sai ya ga kamar ma ba ta san yana wajen ba  Da ace ba ta amsa sallar masa ba sai ya ce ba ta san da zuwan sa ba, amman ta amsa kuma ta kallesa, tabbas wani abu na faruwa, Kafin ma ya samu bakin ƙara mgana ya ga Inna Meri ta wuce su zuwa cikin falon ta barsa nan kamar ma ba ta  gansa ba, baki sake ya bi ta da kallo kafin a ranshi ya ce" Me kuma na yi? Ko dai Mimin nan ta zo?  tuna haka ya sa dai gabansa ya faɗi da sauri ya tashi ya bi Inna cikin falon lokaci ɗaya yana faɗin" Inna wai baki..."   Sauran mganar ta sa ta maƙale ne a fatar bakinsa, ganin Mimi zaune a saman kujeran falon inna, sun kuma haɗa ido ta ganshi ya ganta, kafin ma ya samu zarafin mgana Inna Meri da ta fito daga kitchen ta kalleta lokaci ɗaya tana faɗin" Binta shiga ciki." Ba musu Mimi ta mike tana tafiya a sannu sannu ta shige ɗakin Walida ta rufo kofa. Amman an ce tsakanin miji da mata sai Allah sai ta tsaya jikin kofar kawai har ga Allah ta ji tausayinsa ganin rana ɗaya duk ya faɗa, jikinta a sanyaye ta karisa gefen gado ta zauna ta yi tagumi. Inna Meri kuma Mimi na shiga ciki ta koma saman kujera ta zauna har t na jawo Radionta tana kunnawa kamar ma ba ta san da wanzuwarsa a falon ba.   Ƙafafunsa suka yi sanyin da suka kasa ɗaukansa ba shi da mafita  Inna ba za ta saurareshi ba. Gwara ya bi ta hanyar Mimin kila ya samu ragowa tunda ta na son sh. Salau salau haka ya wuce zai nufi hanyar ɗakin da Mimi ta shiga. Cikin mamakin rashin kunyar sa Inna ta bi sa da kallo,gani ta yi zai shiga tana zaune bai ji kunya ba. Sai kawai ta juya tana faɗin" Kai.." Haka ta faɗa sai ya juyo yana kallon Inna cikin rashin madafa   Inna ta nuna masa hannu kafin ta ce" Ina kuma za ka je? Haka ta faɗa tana hararanshi kansa a ƙasa ya ce" Zan zan je wajen Mimi ne Inna." Wani sakaran kallo Inna ta yi masa kafin ta ce"To mara kunya, sai yanzu ka san da ita ? Ba cewa ka yi ta bar maka gidanka tun da tana cin amanar ka ba  miye za ka zo kana wani sanyin jiki? Fita ka ba ni waje kafin na tashi na yi maka dukan mahaukaciya wlh." Ido ya zaro ya na kallon Inna, wai ta yi masa dukan nahaukaciya. Ganin yadda ranta ya baci yasa jiki ba kwari ya yi kamar zai bar falon sai kuma ya dawo ya duka a gabanta muryansa na rawa ya ce"Don Allah Inma ki yi hakuri wlh sharrin sheɗan ne." Banza Inna ta yi masa har tana ƙara volume ɗin radion ta, tana jin sa yana ta ban hakuri yana ta kuma faɗin sharrin sheɗan ne.   Haushi ya kamata kamar ta watsa masa mari, ba ta san lokacin da ta kashe radion hannunta ba a fusace ta ce"Rufe min baki, in ƙara jin kace sharrin sheɗan ne ka ga ni in ban watsa maka marin ɓarin makauniya ba." Haka ta faɗa ta na hararanshi. Kallon Inna ya yi cikin mamaki kafin ya ce"Inna kin ce za ki dakeni yanzu kuma kin ce za ki mareni? Baban inna ne fa? Inna ta ce"Eh  Mansoor ba ɗan ibrahim na gane ka, ka wuce dukan ne? Ka ƙara cewa sharrin sheɗan ne ka gani in ba wanke fuskar ka da mari ba." Sai Aji ya yi gum kansa na ƙasa. Domin ya san in kuma ya sske ya sake mgama tabbas Inna za ta iya wanke sa da mari. "Ki yi hakuri inna, na tuba.."   Haka ya ke ta faɗa, Inna sai da ta ga dama  sannan ta kalleshi kafin ta ce"Sheɗan din ne ya sake ka da sauri haka? Ƙaryan banza Ka raina ma kanka wayau, waye sheɗan din in ba kai ba, in ba sheɗan ba waye zai aikata abin da ka aikata, kana zargin matar auran ka Mansoor? Kai kam wani irin jaki ne? Baki ya buɗe yana maimaita kalmar jaki a ransa a she a fili ne a fusace Inna Meri ta ce"Eh mana jaki mana, wani mutum ne mai tunani zai aikata abin da ka aikata? Ka kore ta ba ka tsaya ka ji bayanin ta ba. Yanzu da ta je wajen iyayenta ta sanar da su fa? Wallahi da sun daina ganin ka da daraja, sai ta yi wayon zuwa wajena ni kuma wlh zan bi mata kadin abib da ka yi mata ne. Tun da har kana zarginta ya tabbata auran ku ba zai zauna lafiya ba gwara ka sake ta na maida ta hannun Iyayenta ka fin ka aikata abin da za ka hanani shiga mutane."   Haka ta faɗa tana kallonsa cikin ɓacin rai. Cikin zaro ido ya ce"Saki kuma Inna? "Eh haka na ce" Ta faɗa tana haɗe rai. Sai kawai ya yi zaman dirshan gaban Inna lokaci ɗaya yana faɗIn" Ki yi min rai Inna don girman Allah ki yi hakuri." "Rai ai na Ubangiji ne, ba ka yi tunanin haka za ta faru ba ka aikata abin da ka aikata? Da sauri ya ce"Inna kishi ne, kinsan ina da kishi, kuma ina takiran wayarta ba ta ɗauka ba sannan na ga sun dawo tare ya na riƙe da ita, kuma Inna tsohon saurayinta ne fa me kike tunani? Inna tac e"Ba komai sai alheri, zuciyarka ce ba ta da kyau kishi halas ne ga matar ka amman naka ya yi yawa ya zama na jahilci da daƙikanci tunda kake zargin matarka da cin Amanarka? Kai ba ka da lura ne? Ina tunaninka yake? Na sha gaya maka in ka ciza ka hura Mansoor, in rai ya ɓaci hankali ke nemosa. Hadisi ne fa Annabi(SAW) yace ma wani sahabinsa Kada ya yi fushi har sau uku sannan a matsayin ka na musulmi mumini in ranka ya baci sai ka lallashi zuciyarka ka yi hakuri ka jira in ka huce sai ka yanke hukunci amman yanke hukunci cikin fushin shi ke haifar da dana sani Mansoor."   Duk abin sa Inna ta faɗa gaskiya ne, Kai tsaye ya ce"Inna sheɗan ne, amman wallahi gar ga Allah ba na zargin Mimi ki yi hakuri." A kufule Inna ta ce"In sheɗan ne me ya sa ba za ka nemi tsari da shi ba? In ka ji zuciyarka na zafi ka kira sunan Allah mana  ka nemi tsari daga sharrin sheɗan din mana ka gani in abubuwa ba su yi maka sauki ba." Shi dai sai hakuri ya ke ba ta amman Inna ta fusata ta ce tunda yana zarginta shike nan ya ba ta takardan sakin Binta ta fahimci bai san darajan mace ba. Daga karshe ma banza da shi ta yi yana mgana shi kaɗai, ta shi ma ta yi ta shigewarta ɗaki, sai kuma ta dawo falon kada barinta falon ya sa ya shiga wajen Binta so take yi sai ya gane kuranshi wanda nan gaba ba zai ƙara gigin aikata haka ba.. Yana zaune in da ta barshi sai ta shige Kitchen ta barsa gajiya ya yi da zaman ya ɗauko wayarsa ya kira Mu'azzam kamar an saka masa batir ya shiga gaya masa duk abin da ya faru. Mu'azzam ya saka salati ya saukewa kafin ya ce"Haba Yaya Mansoor me ya sa ka yi haka?  Gaskiya ba ka kyauta ba." Shi dai Mansoor faɗi ya ke yi Mu'azzam ya taimaka masa ya kira Inna ya ba ta hakuri sai ya ce bari ya kirata.   Inna na kitchen Mu'azzam nata kiran wayan ta anan falo Manaoor ne ya ɗauka ya kai mata tunda ta ga Mansoor ta san kan zencen, bayan ta ɗaga kiran sun gaisa tunda ya fara rage murya ta sakatar da shi da cewa"Ka fita daga mganar nan Mu'azzamu ai tunda shi Yayan naka Babban kwabo ne ka fi shi sanin darajan mace shike nan ya sake ta sai ya zauna shi kaɗai tunda yana da kishi baya son a ga matarsa amman shi zai fita ya na kallon  matan wasu, in dai saboda shi ka kirani ni ina aiki ne." Daga haka ta kashe wayar, Mansoor tsaye a Kitchen kamar ya kurma ihu, Inna Meri tuwo ta ɗora abunta ga shi yunwa yake ji anman ya kasa mgana jiki ba kwari ya fita falo ya sake kiran Mu'azzam kawai sai ya ce masa"kawai ka zauna kada ka tafi sai ta baka matarka." Shawaran Mu'azzam ya bi ya yi zamansa a falo ga shi ba halin ya shiga ɗakin Mimi Inna Meri na kai da kawo, yana zaune ya fara barci sai da Inna ta zo ta tashe shi ta ce bai ji ana sallah ba ne sannan yafita masallaci ya yi sallah ya sake dawowa. Allah ya bashi sa'a Inna na ɗakinta sai ya yi wuf ya shige ɗakin Walida har da rufo kofa Mimi na kan darduma ta idar da sallah itama duk ta faɗa ga laulayi. Ba ta san ma ya shigo ba ta na can tana tunanisa. Sama sama ta ji faɗan Inna ta ɗauka ma ya tafi ne. Sai ji ta yi kawai ya duka ya rumgumeta ta baya ƙamƙam cikin wani yanayi kamar zai yi kuka. " kiyi hakuri Mimi don Allah, wlh na tuba ba zan ƙara ba." Haka ya ke ta faɗa ya riketa gam. Ta fara kokarin kwace kanta amman kuma yaƙi ba ta damar haka,  wata zuciyar ta ce ya ce tabbaci gare shi Mimi kada soyayyarsa ta rufe miki ido, kawai sai ta saka ƙarfi ta tureshi da sauri ta mike tana kallonsa kafin ta ce"Ka manta ne, ni ce wacce kake zargin ina cin amanarka! Ko da yake kace tabbaci gare ka ba zargi ba ne." Kawai sai ta saka masa kuka . Da sauri ya miƙe yana koƙarin nufarta da sauri ta ja baya tana faɗin"Wlh ka da ta ƙara taɓani, ai jikina najasa ne tunda ina tarayya da wani bayan kai." Shi kokarinsa ya riketa kada Inna ta ji ta, ita kuma Kuka take yi yavsa ba ta san inda ta kai kanta ba sai ji ta yi ta buge kafarta da gefen gado azaba ya isheta sai da ta yi yar ƙara. Ta yi kasa tana rike kafarta shi kuma ya nufeta yana faɗin" Mu gani me ya same ki? Ƙwace kafarta ta yi, ta matsa baya tana kuka.   Kofar ɗakin suka ji ana bugawa, da kuma Kiran sunan Mansoor da inna take yi lokaci ɗaya ta na Faɗin" Baban inna ka zo ka buɗe nin kofar nan ko na saɓa maka." Ba shi da mafita illah zuwa ya buɗe kofar ya na buɗewa Inna Meri ta shigo da muciya a hannunta daman ta ɗauko ne za ta yi talge ta ji Kukan Binta, ba ta yi wata wata ba ta maka masa muciyan a gadon baya ya duke yana faɗin"Inna.." Ƙoƙarin ƙara maka masa take yi sai Mimi ta riƙe muciyan lokaci ɗaya tana faɗin"Don Allah inna, kada ki yi masa lahani." Sai Jikin Inna ya yi sanyi ta sauke muciyan tana hararan Mansoor da ya sadda kai kamar mutumin kwarai. "Fita ka ba ni waje, kaji kunya ita tana tausayinka amman kai ba ka tausayin ta, Yaron ciki gareta ita da ke bukatar kulawa amman kai kake saka ta a damuwa."   Sai ya kalli inna cikin mamaki sannan ya kalli Mimi da kanta ke kasa kunya ya kamata ya a ka yi Inna ta san tana da ciki? "Inna yaron ciki? Wai mimi ke da ciki? Muciyan ta ɗaga za ta kara buga masa ya sa ya fice da gudu da rakashi har falo tana faɗin" Zan maka rubiti da abin hannuna In baka fita daga idona ba. Takardanta za ka kawomin ka ji ma na gaya maka." Kawai sai ta ga yana mirmishi kafin ya ce"Inna ba kyau sakin aure da ciki, ki yi hakuri kawai ki ba ni matata mu koma gida mu daidai ta." Sai Inna Meri ta kasa mgana. Wani kallo ta yi masa sannan ta shige kitchen ta barsa nan farinciki ya cika sa, shima zai haihu Allah sarki rayuwa. Wata zuciyar ta ce da sanadinka cikin ya zube fa? A fili ya furta" da ba zan yafe ma kaina ba."   Mansoor ya ki tafiya ko'ina Inna kawai ya ke ma magiya har ta gama tuwonta kuma ba ta saka masa ba, ya ce rabon sa da abinci tun jiya Inna Meri ta ce ina ruwanta ai tunda bai san baiwar da Allah ya yi masa yanzu ya fara zama da yunwa kiri kiri Inna Meri tahana shi, ruwa kawai ta bar shi ya sha sai faɗa take yi tana fadin ya fita ya bar mata gida in kuma yana takaman gidan shi ne sai su su fita su bar masa gidan. Yana jin haka ya mike ya dau key ɗin motarsa ya fice yana faɗin" Inna gidan nan fa naki ne, me ya sa za ki ce haka?. Inna ta ce"To ba zan ce ba, ka zo ka min zaune kamar wani ɗan kaciya"   Ai da gudu ya bar gidan kafin Inna ta saka a yi masa a tare, gida ya koma ya yi wanka ya sauya kaya sai ya kira Mu'azzam yana faɗa masa yadda suka ƙare da Inna. Mu'azzam ya ce"Ga shawara ka je ka samu Baba na san shi ne kaɗai zai sauko da fushin Inna." Sai a lokacin Aji ya tuna da Baba ai nan da nan ya kirasa a waya sai ya ce baya gida zuwa anjuma in ya dawo Mansoor ɗin ya zo ya same shi. Shi ya sa bai sake fita ba. Dakyar ya iya dafa ruwan zafi ya sha tea Rana ɗaya kawai ya fara raina kansa, amman da ya tuna Mimi na da ciki sai ya ji kamar an saka sa a cikin Aljannah. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3017* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Bai fita ba sai bayan mangariba bayan ya sake kiran Baba ya gaya masa ya dawo gida ya zo ya same shi. Shigar manyan kaya ya yi harda hula sannan ya hau motarsa ya nufi anguwan Arawa, yana hanya ya ji ana ta kiran sallar Isha'i ya iso kofar gidan na su ya iske Baba na alwala shi da amininsa Mallam Hashimu sai shima ya bi a yarin su ya ɗauro alwala suka karisa masallacin suka yi sallah. Bayan sun idar ma sun ɗan dade a waje matasan anguwan nan suna ganin Aji suka dafe masa sai da ya ji da su sannan ya samu ya sulale. Ya samu Bab da su Baba Sani suna mgana.  Bayan sun gaisa sai suka yi musu sallama suka shiga gida, tunda yanzu sun gane karatun sun rage roƙo sun fahimci ko ba su roƙa ba Meri ta riga ta yi tarbiyan Ƴaƴan ta da alheri gabaɗayan su. Baba Ɗanjuma ya so su shiga ciki amman Mansoor ya ce su dai tsaya daga wajen zai fi. "Me ke faruwa ne Baban Inna? Na gan ka kamar a gaggauce ne?   Mansoor ya yi shuru kansa a ƙasa. Da kunya ya fadi abin da ya aikata amman kuma ba shi da wata mafita  dole ya buɗe baki ya warware ma Baba Danjuma duk abin da ke faruwa har zuwan shi gidan Inna da matsayar ta ya ƙarishe faɗa cikin bayyana nadamarsa lokaci ɗaya yana faɗin" Wlh Baba sharrin sheɗan ne ban san abin da ya shiga kaina ba ne a lokacin, na tuba na kuma gane kuskurena in sha Allahu ba zan kara ba, ka shigemin gaba mu je ka ba ma Inna baki ta taimaka ta ba ni matata Baba." Baba Ɗanjuma ya kalli Mansoor cikin wani yanayi kafin ya ce" Innalillahi wa'inna Ilaihirraju'un haba Mansoor haba. Sau nawa na sha faɗa maka ka riƙa tausasa zuciyarka sannan ka daina yanke hukunci cikin fushi, itama mahaifiyar taka ko da yaushe nasihan ta kenan ka rika haƙuri sannan ka san yadda za ka yi ka sarrafa fushinka saboda gudun faruwan abin da ke faruwa yanzu. "Ka yi hakuri Baba, na yi nadama kuma in sha Allahu zan iya bakin ƙoƙarina wajen sarrafa fushina in sha Allahu." Mansoor ya faɗa kamar zai yi kuka har ya na marairaicewa.   "Amman ka san wannan abin da  ka aikata ba mai kyau ba ne Ko? Sannan kana sane da cewa zargi na daga cikin abin da ke ɓata aure ko? Baba Ɗanjuma ya faɗa yana kallon Mansoor ɗin wanda ya sadda kai ƙasa kamar bashi ya aikata ba, ya yi nadama shima ba laifin sa ba ne laifin soyayyar Mimi ne da ya yi masa yawa shi ya sa yake kishinta kishi mai zafi amman yanzu ya fahimci komai sai ka bi shi a sannu ya sani zai fara sarrafa fushinsa amman ba zai iya daina kishin matarsa ba har abada. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Na sani Baba, in sha Allahu hakan ba zai ƙara faruwa ba."   Sai Baba ya kaɗa kai kafin ya ce"To bari na shiga ciki na sanar da Magajiya sai mu je tare na yi mata mgana." Tare suka shiga cikin gida, Mansoor ya ce bari ya gaida magajiya, suna shiga suna ma tsakar gida ne ita da Mariya suka shigo ya rankwafa ya gaida Magajiya da irin salon gaisuwarsa ta amsa cikin sakewa kamar yadda ta saba yanzu ta daina ɗaure musu fuska, ko da ma da sauran wani abu a cikin ranta ta boye ma zuciyarta Mariya na gefe ta gaishe shi ya amsa lokaci ɗaya ya na faɗin"Ke kina nan?  yaushe rabon da na ganki? Kanta na ƙasa ta ce"Kwanaki mun je gidanka ba ka nan Anty Mimi kawai muka samu a gida." Sai ya jinjina kai Magajiya ta ce" Ranar lahadi tunda tana gida sai ku je ke da Walida ku gaishe su." Sai ta amsa dai dai lokacin da Saddiqu ya shigo gidan fakan fakan kamar mahaukaci, daman ya samu labarin yanzu sai yawon gari can lagos ɗin dama yar buga buga ce kuma jari ya suɓuce. Har da Auwalu sun yi mganar ya ce ya zo ya fara harkan gini ya ce ba zai iya ba ya koma sai zaman shagon wani abokinsa. Dole Maeeshan ta nemi aikin koyarwa tana zuwa domin ta rufa ma kanta asiri.   Ko Magajiya bai gaisar ba. Sai ita ce ta ga zai wuce zuwa bangaren matarsa ya sa ta ce" Kai Saddiqu ba ka ga Yayan ka ba ne? Sai ya juyo ya na kallonta ya na kuma kallon Mansoor tunda akwai wuta haske ya gauraye tsakar gidan. Sai ya kasa mgana Yana mamakin yadda Magajiya ta koma ruwan sanyi shi fa jin su kawai yake yi, ba bu wani abin da mutum zai yi maka wanda Allah bai maka ba. ƙaramin tsaki kawai ya ja ya yi wucewarsa mirmishin gefen baki Mansoor ya yi domin wanda bai daraja uwarsa ba har yaushe kake tunanin kai zai iya daraja ta ka mahaifiyar? Magajiya kunyar duniya ya kamata saboda abin da Saddiqu ya yi mata.   Dai dai lokacin da Baba ya fito cikin shirinsa yau kwanan Magajiya ne sai gobe ne  yake gidan Inna shi ya sa yana fitowa ya kalli Magajiya lokaci ɗaya yana faɗin" Magajiya Mansor zai ɗauke ni zuwa gidan Meri zan dawo zuwa anjuma in sha Allahu.". Sai Magajiya ta kallesa a sanyaye kafin ta ce"Ina fatan dai ba wata matsala? Da Sauri yace"Lafiya lau, wata yar matsala ce amman kada ki damu." Ganin bai faɗa mata ba ya sa ta kaɗa kai kafin tace to Allah ya sa a dawo lafiya. Mansoor ya yi mata sallama suka fita tare da Baban ta bi su da kallo tana girgiza kanta, Ko ta ƙi ko ta so Ƴayan Meri da agolan da ta raina su ne su, yaran nata kuma da ta nuna sun fi kowa ga shi nan su ne rayuwarsu ke wulaƙanta gwara gwara ma Auwalu da shi yanzu ya zama Enginer ba ya gini sai dai karɓan kwangilan gini kuma ba laifi yana samu sannan ya na yi mata tunda ba halinsu ɗaya da Saddiqu ba, Jummai sai dai ta zo ta ƙarbe na ta, har gwara ma Zuwaira to yanzu haka shi kan shi Saddiqun kusan ci da shi na wajen su ne tunda ba shi da komai yanzu sai bakin rai. Mariya kuma ba domin su ba da tuni itama rayuwarta ba ta inganta ba, tana da tabbacin da bikin ta in ya zo su ne za su yi komai da abunda uwa za ta yi da abin da ubq zai yi ta na da tabbacin suna yi domin Allah ne ba domin komai ba  in da ace suna yi domin ganin ido ne da tuni sun daina tun baya da take nuna hassadatan a fili, yanzu kan ta saduda tunda ta ga jama'a ma suna gudunta har su Gaje yanzu sai su yi wata ba su leƙo ta ba, ko wani abu ya faru a anguwa sai dai in ta biya musu su ce sun shiga jaje ko Allah ya kyauta, amman ba sa nemanta Ta dai fahimci duniyar ce gabaɗaya ta sauya gwara ka aikata alheri yanzu in da mutuwa ta yi fa? Haka mutanen da ta zauna da su za su yi mata?  ta kuma fahimci lalle ka zauna da mutane lafiya shima wani abu ne, Sannan ka aikata alheri tun kana duniya za ka ga amfanin haka, ga shi Meri ta bar mata gidan amman  kamar ta tafi da duk wani albarkan gidan  gabaɗaya. ****** Tunda Inna Meri ta ga Baba Ɗanjuma da Mansoor ta san ƙaranta ya kai. Shi ya sa tunda suka shigo ta haɗe rai, ta ga fa zuwan su suna zaune a falo suna jiranta Baba Ɗanjuma ke saman kujera Mansoor kuma yana zaune a ƙasa. Walida ce ta kawo musu ruwa Aji sai faman waige waige yake yi ko zai ga Mimi amman ba ta fito ba. Inna Meri ko kamar da gayya ta shiga aikace aikacenta wai wanke wanke da daddare saboda dai kada ta sauraresu. Mansoor yunwa ya ke ji bai ci wani abun kirki ba, sai ya tambayi Walida abin da suka dafa kai tsaye ta ce"Tuwo Inna ta yi da rana na zubo maka ne? Sai ta amsa mata da eh, ai kam tana zuwa Kitchen ɗin Inna ta ga za ta zuba abinci ta tambayeta wa zai ci? Ta ce yayanmu ne. Kai tsaye Inna Meri ta ce"ba zai ci tuwon ba, rufemin kular nan" Cikin mamaki Walida ta ce"Saboda mene Inna? Inna ta mata wani kallo kafin ta ce"Sai na ji shaƙa sannan." Walida na jin haka ta yi sum sum ta fita daga Kitchen ta koma ta gaya ma Mansoor abin da Inna ta ce sai ya yi mirmishi kawai ba tare da ya yi mgana ba Baba Ɗanjuma ya ce" Me ya sa Meri take hakane? Ban san ta da wannan fushin ba." Kawai sai ya miƙe yana faɗin bari ya je ya sameta a cikin madafin.   Yana ta shi, Mansoor ya kalli Walida yana faɗin" Ina Antyn ki? Sai da ta kalli ɗakin sannan ta ce"Tana ciki, kila ta kwanta ne" Kai ya jinjina mata sai kawai ta wuce ta shiga ɗakin nata, ta iske Mimi kwance amman ba barci take yi ba, ta na shiga ta yi saurin miƙewa zaune lokaci ɗaya tana faɗin" Aji ne ya zo? Sai Walida ta ce"Eh shi da Baba, wai me ya yi ma Inna ne? Abinci ma fa hana shi ta yi.". Mimi ta zaro ido kafin ta ce"Kai.! Walida ta zauna gefenta tana faɗin" Wlh Allah, kuma fa ta ga har da Baba amman ta na kitchen tana wanke wanke." Sai Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba, to ita me za ta ce?  duk da ya yi mata ba dai dai ba amman bai kamata Inna ta hora sa da rashin abinci ba, gabaɗaya tausayin shi ta ke ji, Kamar ta ta shi ta je ta roki Inna kuma tana da tabbacin bai ci wani abinci ba tun jiya nan, amman ba za ta iya ba sai Inna ta ga kamar ta yi rashin kunya kuma duk abin da take yi ta na yi ne saboda ta ƙwatan mata ƴancinta. Suna ciki suna jin tashin maganar Baba da Innar a talon,  kenan Baba ya samu nasaran Fito da Inna Meri daga cikin kitchen.   Inna Meri na saman kujera Baba Ɗanjuma na gefenta Mansoor na gefen Baban kansa a ƙasa. Shi kuma Baba Ɗanjuma sai faman kallashi inna yaoe yi da kalaman ban hakuri faɗi yake yi" Haba maryamu ban san ki da dogon fushi ba, ina miki shedar ke macece mai afuwa, tunda har ya san ya yi laifin kuma ya ce ya yi nadama ya ba da hakuri to me zai hana ba za ki yi hakuri ki ba shi matarsa su koma gida su daidaita ba?. Inna Meri ta yi shuru kafin ta muskuta lokaci ɗaya tana faɗin" Ya gaya maka zargin matarsa yake yi? Ya sanar da kai shi da kansa ya ce ta fitar masa a gida, shi isheshe mai gida ba."   Ta faɗa tana hararanshi lokaci ɗaya tana cigaba da faɗin" Ya yi sum sum da kai kamar mutumin ƙwarai. Ahalin ya iya aikata tsiya kala kala, ace a shekaran Baban Inna talatin da ɗoriya bai san ciwon kansa ba? Ƙanin sa Mu'azzamu wlh ban taɓa jin kansu shi da matarsa ba. Amman shi kamar wani ƙaramin yaro daga wannan sai wannan., ni kuma na gaji da wata rana ya yi abin da za mu kasa shiga mutane gwara ya sauwaƙe mata cikin girma da arziƙi na maida ma Hajiyar jikarta na ba ta hakuri." Inna Meri ta gama faɗa tana ƙara haɗe rai shi dai Mansoor sai faman ba da hakuri ya ke yi,  Baba Ɗanjuma ma haka. "Duk ya faɗa min wlh, na kuma yi masa faɗa tunda dai ya yi nadama ki duba girman Allah ki yi hakuri Maryama.."   Baba ya kirata da mafi soyuwan sunan da ya ke kiranta da shi  wani lokacin, ta ɗago ta kalle shi daga shi har ɗan na shi sun maraiiraice sai ta ji wani abu a ƙasan ranta, Da sauri ta kauda kai tana faɗin"Shi mai uba ko? Ya je ya ɗauko ka, kun yi min taron dangi saboda ni kunga nawa uban ya mutu ko? Da Sauri Baba ya ce"Ko ɗaya, ke yanzu kin fi wata mai uban, Allah ya ba ki ƴaya sanyin Idanuwanki waɗanda suka lulluɓeki da alheri sannan kina da ni, ina da tabbacin kin gama samun komai a nan duniya sai fatan cikawa da Imani kawai Maryama Inna Meri kauda kanta ta yi tana share ƙwallah kafin ta ce"Shike nan amman ya sani wannan ne na farko kuma na ƙarshe wallah tallahi in ya sake aikata wani kuskuren sai ya rasa Binta." Da sauri Mansoor ya ce"Ba zan ƙara ba Inna, ki yarda da ni." Kallonsa ta yi kafin ta ce"In ka ji irin haka ya shige ka, ka kira sunan Allah domin ka samu natsuwa ina ƙara yi maka nasihan cewa ka koyi sarrafa wannan zuciyar taka saboda watan wata rana za ta kai ka ga aikata abin da ko kaso ka gyara ba zai taɓa gyarun maka ba." Kansa na ƙasa ya ce"In sha Allahu."   Baba Ɗanjuma na Mirmishi ya ce"Mun gode, Sai ki yi mata mgana ta fito su tafi, In sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba." Inna Meri ta gyara zama kafin ta ce"A'a.." A tare suka kalleta cikin mamaki kafin ta cigaba da faɗin" Itama macece mai ƴanci ita kuma ya yi ma wannan laifin zan kirata a gabanka a gaban shi, in ta amince ta masa afuwa ba zan hana ta bin sa ba amman in har ta ce ba ta hakura ba, ba zan iya hana kaina goyon bayanta ba." Baba Ɗanjuma ya ce"Ba ma za'a yi haka ba, Kirata ta zo nima na ba ta hakuri." Inna Ta mike lokaci ɗaya tana faɗin"Ba ma  ta da lafiya, gwara ta zauna waje na har sai ta warware wannan mara tunanin magana kawai zai iya gasa mata da zai ɗaga mata hankali wani abu mara kyau ma ya faru. "Me ke damun ta?   Baba Ɗanjuma ya tambaya kafin Inna ta yi mgana da sauri Mansoor ya ce"Baba Inna ce ta ce Mimi na da ciki, tsakani ga Allah kula da mai ciki ai sai uban cikin ko? Inna ta ji kunyar duniya ya kamata Baba ma kai ya kauda kafin ya ce"Wannan gaskiya ne. To to Allah ya raba lafiya." Inna meri kuma daƙuwa ta maka ma Mansoor kafin ta ce" Ba ka da kunya ko? Sai a lokacin ya tuna tabargazan da ya yi da sauri ya maida kai ƙasa yana sosa keyarsa ya na yar dariya. Walida Inna ta kwalama kira bayan ta fito sai ta ce ta kira mata Binta. Mimi daman tana zaune nem Jin Inna na kirata ya sa ta mike ta zura hijabin Walida zuwa Falo tun da kuma ta fito gogan ya kafe ta da ido kuma maganar gaskiya ta rame ta yi wano fayau to wai daman haka alamun cikin yake? Me yas a shi bai gane ba?   Kusa da Inna ta zauna kanta na ƙasa ta gaida Baba ya amsa cikin sakewa lokaci ɗaya yana faɗin"Ya jikin Fatima? Kanta na ƙasa ta amsa da sauki ya ce Allah ya ƙara lafiya Mansoor a ka bari da amsawa Inna ta wurgeshi da maficin Hhnunta sai da ya same shi shi ya sa ya kama bakin shi. Bayan tattaro duka bayanan Baba Ɗanjuma ya sake ba ta hakuri da cewa"Ki yi hakuri kin ji ko Fatima? Itama uwar taki mun ba ta hakuri kuma ta ce ta hakura amman mu tambayi izinin ki, ina so ki cire komai a ranki ko domin lafiyan abib da ke cikin ki, ki tashi ki bi mijin ki kin ji ko? Bai kyauta ba mun masa faɗa ya kuma ya ce ba zai ƙara ba,  mu abin da kika yi mana na ɗauƙan mu iyayen ki ya fi komai yi mana aɗi Allah ya yi muku albarka Allah ya zaunar daku lafiya tare da zuru'a mai albarka." Wannan karon gogan a cikin ransa ya amsa sai Inna ce ta amsa a fili. Mimin kanta na ƙasa ta kasa mgana. "Kin yi shuru Fatima? Ki ce wani abu mana."   Baba Ɗanjuma ya tambayeta. Sai ta ƙara sadda kanta ƙasa kafin ta ce" Na hakura Baba, ni daman saboda zargin yake yi min ne ya sa na kawo muku wannan mganar." Da sauri Baba ya ce"Eh wlh, kuma kin kyauta mganar zargi ai babban mgana ce, an yi masa mgana ba zai ƙara ba." Sai Mimi ta jinjina kai kafin tac ce"Shike nan zan bi sa mu koma." Baba ya ce Alhandulillah Allah ya yi miki albarka Mansoor kuma har da sauke Ajiyar zuciya. "Amman kuma ina da sharaɗi. Sharaɗin nawa kuma ina so ku zama shaida Baba da Inna.."   Haka ta faɗa kai tsaye tana kallon Aji da ke kallonta, Inna ta yi mirmishi kafin ta ce" Faɗi sharadin ki, muna goyon bayan duka hukuncin ki Binta." Sai ta kauda kanta kafin ta ce"Na yi hakurin zargin da ya jefeni da shi, amman ku zama shaidata wlh tallahi in har ya ƙara maimaita wani abu makamcin haka zan tafi, kuma in na tafi bazan dawo ba, domin ba zan iya zama da wanda bai yarda da ni ba sannan ba zai iya shaida na ko da a bayan idanuwana ba ne." Baba ya jinjina kai kafin ya ce"Gaskiya ne, In sha Allahu ma haka ba zai ƙara faruwa ba." Inna Meri kuma ta ce"Kin yi min dai dai, ni da kaina wlh in ka ƙara sai na tursasa maka ka saketa, in dai kai ba ka san baiwar da Allah ya yi maka ba to ka in ka yi sakaci Binta ta bar ka sai dai ka mutu ba ka yi aure domin ban ga macen da za ta yi hakuri ta zauna da kai  da mummunan hallayarka na rashin lissafi ba. kishi ai ba hauka ba ne sai ka hana yarinya walwala kawai saboda kishin ka na banza? To wlh ka shiga hankalin ka tun kafin wata rana ka yi ta kuka ba mai share maka hawaye."   Baba Ɗanjuma ya ce"Gaskiya ne, amman duk hakan ba zai kai ga faruwa ba in sha Allahu" inna Meri ta harari bangaren Mansoor kafin ta ce"Shi dai ya sani,damar ta karshe gare shi, ki je ciki ki shirya sai ku tafi." Mimi ta miƙe a sanyaye ta wuce Mansoor ya bi ta da kallo, shi yanzu ai yana cikin TSAKA MAI WUYA. Ya san yana da kishi amman kuma dole ya koyi sarrafa kishin sa matukar yana son zaman lafiya. Bayan tashin Mimi nasiha faɗa haka Inna da Baba suka tasa shi suna yi har sai da Mimi ta fito Walida ta rakota da jakarta da kayanta da Walidan ta wanke mata. Inna ta kalli Mimi lokaci ɗaya tana fadin"In kina bukatar wani abu ki gaya min sai na saka Walida ta kawo miki kin ji ko?. Sau ta gyaɗa kanta, so take yi ta ce a zuba mata tuwo amman ta kasa mgana sai Walida ta yi ma raɗa ita kuma ta gaya ma Inna. Mirmishin su na manya ta yi domin ta na da tabbacin domin Mansoor za ta ɗauki tuwon nan sai ta ce Walida ta zuba musu a kula su ta fi  da shi.   Mansoor ya ce Baba ya zo su fara sauke shi a gida yace a'a zai samu mai mashin su dai su tafi. Har bakin mota Walida ta rakata ta saka musu tuwon a bayan mota da jakar Mimi da kayanta tare da magungunta. Har su ka bar anguwan nan kallo Aji bai ishi Mimi ba shi kuma sai ya rasa abun cewa, ya kalleta sai ya ga ta na kallon gefe ne ba ta ma son kallon shi, sai ya rasa abun cewa sai da ya ji ta na tari sannan ya ce"Sannu, ko a rage A.c ne? Ta yi masa banza da kansa ya rage iskar motar sannan ya koma yana faɗin" Har da mura ke damun ki ko? Kamar ba ta motar haka ta yi masa, Ya yi ta taƙalan mgana amman Mimi ko uffan ba ta ce masa ba, har suka isa gida yana hon megadi ya buɗe musu get suka shiga gidan yana gyara parking ta yi saurin buɗe motar ta fito, baya ta buɗe baya ta ɗauko jakarta da ledan mganinta da sauri ya zagayo ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin"Ke da ba ki da lafiya ina ke ina ɗaukan kaya Mimi? A sanyaye ya yi mganar, sai kawai ya ga ta ƙara kauda kai ta sakar masa kayan hannunta ta juya a hankali ta nufi cikin gida shi a ka bari da kwaso kayan har da kwandon da Walida ta zuba musu tuwon ko da ya shiga falon har ta shige ciki ya duba ba ta a bedroom ɗinsu a she ɗakinta ta shige a bin ta yana shiga kuma ya ganta ta tuɓe za ta shiga wanka, bai yi mgana ba ganin kallonsa ma ba ta san yi, dole ya koma falo ya zauna yana shafa kansa.   Mu'azzam ne ya kira shi suka yi mgana ya ce masa Inna ta hakura, shima sai da ya ƙara yi masa faɗa sannan suka yi sallama Hibba na gefensa da katon cikinta ta ce"Kai ni dai na kasa gane halin yaya Mansoor." Mu'azzam ya ce"Ya dai kusa zama uba watarana sai labari." Hibba ta zaro ido kafin ta ce"Mimi na da ciki? Sai ya gyaɗa mata kai, sai kawai ta saka shewa har suna tafawa da Mu'azzam a fili ta ce wa ya ga Yaya Mansoor da ɗa akwai shan kallo, Aji baya jin kunyar faɗan Mimi da na ciki shi a ganinsa abun alheri ne miye kuma na ɓoye ɓoye.   Ya na nan zaune ya na ɗuba saƙonnin sa na kan WhatSApp da ya kwana biyu bai duba ba, har da na Makama ya tura masa hoton jaririyar, tun ranar da a ka yi haihuwar bai ma duba ba kuma ko barka ma bai kirasa ya yi masa shima yana cikin wani hali alokacin. Sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa tunda Mimi ta dawo gare shi, a kasan hoton jaririyar da Makama ya turo masa ya yi tagging ya rubuta" Allah ya raya, nima nan da lokaci kaɗan za'a haifa min irin ta ko irin shi a gidana." Ya gama rubutawa kenan ya ji buɗe kofa, Ya juyo sai ya ga Mimi ce ta yi wanka ta saka rigar barci riga da wando masu taushi, ba ta kalle shi ba ta nufi jakarta da ledan mganinta ta ɗauka ta juya kenan ta ji ya ce"Tuwon fa? Ko ba za ki ci ba ne? Ba ta juyo ba a sanyaye ta ce" Na ƙoshi." Daga haka ta yi shigewarta ɗaki, yana jinta tana saka key sai kawai ya yi zaune yana bin ɗakin da kallo, tun bayan auransu ba su taɓa raba ɗaki ba, ko da sun samu matsala ba ta kai su ga raba makwanci amman yanzu kan ya san bashi da gaskiya shi ya sa ya kasa wani motsi. Zai jure har sai ta sauko ya godema Allah tunda Inna ta ba shi matarsa.   Haka ya zauna ya ci tuwon nan sosai leda ɗaya ya rage kawai sannan ya tattara komai ya maida kitchen miyar ya saka ta acikin Fridge ya kashe komai na falon sannan ya shiga ɗakinsa ya yi wanka ya yi shirin kwanciya sai ranar ya samu yin barci sosai da safe shi ya tashi ya buga ma Mimi ƙofa sai ya ji ta na tashi tunda ta yi masa gyaran murya, Mimi gasan ƙuma ta ke yi ma Mansoor ba ta masa mgana ko zai yi mganan duniyan nan daga eh sai a a ne, Tunda ta dawo za ta yi masa abun karyawa da na rana da na dare, a baya in ta ce ya zo ya taya ta aiki sai ya ce shi ta na bashi wahala amman yanzu haka ya ke zagewa ya na shige mata da faman nacin da me zai taya ta sai ta ce bakomai, har girkin ya ce ta daina yi tunda ta na da  juna biyu, itama fa haushi yake ba ta tunda har bai yarda da ita to ba ta ga amfamin soyayyar dake tsakanin su ba.   Sannan duk shi ya haɗa mganar cikinta har Mommy sai da ta ji,Hajiya da Baaba uwani sun zo dubata, ta ji sauki sai dai kasala da jiri take fama da shi da tsinkewar miyau sai zazzabin dare, ba ta koma aiki ba amman Rukayya ta zo dubata, kuma daga can ma'aikatansu ana ta kiranta ana gaisheta. Jaheed ya kira ta sau biyu shima bai samu natsuwa ba sai da ta ce masa ta koma gidanta sannan ya samu salama har ya na cewa"Kina ganin kiran ma da nake yi miki ba matsala? Kai tsaye ta ce"Kada ka damu ba zai kara kuskuran da ya aikata ba, ko ba soyayya kai shakikina ne saboda haka bai isa ya hanani mu'amala da kai ba." To ai bai ma ga fuska ba,Mimi ko da yaushe fuskarta a kirne kuma ba ta son ma kallon shi in zai fita ta ce masa a dawo lafiya in ya dawo sannu da zuwa ta yi masa duk abin da yake bukata ta shige ɗaki ta kwanta.   Ko zai yi ta mgana ba ta amsa masa, Saboda dai ya saka su fita ya ce ta shirya su je barkan matar makama. Jin gidan Bibi ne ya sa ta shirya suka je da daddare suka yi mata barka an dawo da ita gidan su wajen mamanta tun bayan sallamota daga asibiti ba ma za'a yi taron suna ba saboda yanayin rayuwar da ake ciki, bayan sun baro gidan suna hanya ya yi mata surutun ba ta ga yadda jaririyar ta mata kyau ba kamar ce ta ta ce, sannan ya koma mata magiyan me ta ke so ya biya ya siya mata. Sai a lokacin ta kalle shi kafin ta ce" Abu ɗaya nake so shi ne ka ƙyaleni." Daga haka ta kauda kanta muryanta kamar za ta yi kuka dole ya kyaleta amman tsakani ga Allah ya gaji da wannan horon bayan fagen.   Fiye da sati biyu suna cikin wannan rayuwar, ya gaji ya fara bin ta da ban hakurin ta yafe masa ,ita kuma ta ce ta yafe kawai dai ta kasa sakin jiki ne tunda har shi bai yarda da ita ba, in ta tuna haka har kuka ta ke yi saboda bakin ciki. Tana mamakin yanayin cikinta baya sakata amai sai dai tashin zuciya wani lokacin, ita dai sai dai kasala da jiri sai zazzabin dare ba ta kuma zaban abinci amman dai ta na cin goro, saboda sauƙin tashin zuciya ta na iya kula da kanta da gidan aikin ma za ta koma ranar Monday tun da ta samu sauƙi. Ranar da Allah ya nufi su shirya. Ranar asabar ne Walida da Mariya a gidan suka yini suka girka shinkafa da miyar kifi. Kifin ma tun Tsaraban Inna ne na Argungu, ba ta ma sani ba suka saka shi a miyar sai kuma ta yi mata daɗi taci sosai a daran ma ta ƙara ci ta dora da maltina ta kwanta ai misalin sha biyun dare cikinta ya hana ta barci sai tashin zuciya, haka ta rarrafa ta shiga Tiolet ta rika kwara amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta.   Da jan jiki ta dawo gefen gado ta ɗauki waya ta kira Aji, daman bai yi barci ba yana duba wani tsare tsaren wassanin su na gaba me ya ga kiranta, kuma sai da gabansa ya faɗi ya san ba lafiya. Sanda ya zo har ta fara galabaita tana son yin aman amman ba komai a cikinta, ganin yanayinta ya sa kawai ya saka mata hijabi ya taimakamata suka fita falo,da gudu ya ɗauko key ɗin mota jallabiyansa a juye ya saka ya rike Mimi zuwa wajen mota megadi ya taso  ga gudu ya na jera mata sannu, kawai sai Mansoor yace a buɗe masa get.   Wani asibitin kuɗi ya kaita mafi kusa,  suna zuwa a ka karɓe ta saboda emergency ne  Mimi ta sha wahala duka sai da ta amayar da abin da ke cikinta sannan a ka mata allurai bayan an saka mata drip anan asibitin suka kwama ita an ba ta gado shi kuma ya na zaune da ita,.Sai bayan ya je sallar asuba ne ya dawo ya kira Inna ya faɗa mata hankali tashe ta ce gata nan zuwa, likitan da ya karɓe su ya kira shi ya yi masa bayani Mimi ta daina cin kifi domin cikin ta ba ya son shi, ta na daina cin wani abun da cikinta ba ya so. Allah ya sa abun ya zo da sauƙi Inna Meri ta zo ta yini da ita a ranar sai Hajiya da Mansoor ɗin ya je ya gaya mata, kwananta viyu a ka sallameta ta koma gida duka yan'uwanta sun kirata a waya kuma kowa ya san ta na da ciki Khadi har da mata tsiyan cewa Oho su Mimi da ciki an kusa zama uwa.   Mommy ba ta zo ba amman suna mgana ta waya, Mama da Anty har Daddy ya zo gida dubata shi ya ce a bar mata Baaba Uwani ta zauna da ita Hajiya ta ce itama me ta ke yi a gidan? Mansoor kuma ya ce har Hajiyan don Allah su zauna tunda Walida ba ta da lokaci yanzu. Yadikko ma ta zo ita da iyalanta su Anty Amina da su Bintu ma duk sun zo. Su jummai da su Zuwaira har Maeesha da matar Auwalu. Magajiya da su gaje sun zo duba ta, kuma taji daɗi kwarai yadda suka nuna mata kulawa shima kanshi gogan rawan jiki kawai yake yi, Nasir da su Makama duk sun zo dubata Rukayyan kusan kullum tana gidan. Zaman Hajiya da Baaba Uwani ya daidai ta Mimi da Aji, tunda dole ta bar musu ɗakin ta koma ɗakin Aji tana kwana kuma suna gidan ai ba za ta masa horon da ta saba a gabansu sai ta ke nuna komai lafiya sai sun shiga ɗakin ta yi masa gum  Ranar dai ya gaji cikin dare ya miƙe ya kunna hasken ɗakin ya ta da Mimi, ta tashi tana sosa idanuwanta cikin sanyin ta ta ce"Me ya faru? Gurfana ya yi daga saman gadon a gabanta ya ba ta kanshi lokaci ɗaya yana daɗin"Gani ki yi min duk abin da kike ganin za ki wuce, na gaji Fatima kina horani wlh na tuba ba zan ƙara ba." Ya faɗa kamar zai yi kuka idanuwansa sun kala yana bukatar matarsa amman sama da wata ɗaya Mimi na masa kisan munmuƙe. Kallonsa ta yi kafin ta kauda kai tana kokarin komawa ta kwanta da sauri ya rikota ya jawota jikinsa ya kamkameta ya na Faɗin"Kin ce kin yafe min amman ki duba abin da kike yi min? Ba ki yi min mgana ba na ganin dariyan ki.  Ni fa bayan ganin ki a tare da ni ina bukatar ganin ki cikin farincikin ba na jin daɗin ganin ki haka don Allahi ki yi hakuri mu koma kamar baya." Mimi kwallah suka cika mata ido cikin rawan murya ta ce"Me zan maka? Na kasa manta maganganunka ne Aji, da bakin ka kace tabbaci gare ka  a kaina ba zargi ba ne. Ni wai na ke cin amanarka? Ni wai haba don Allah ban yi lalacewa tun ban da aure ba sai da na yi aure zan lalace? Me ya sa ba ka za kamin uziri ba? Ni ba ka yarda da ni ba? Kai ne fa ka taɓa sanina  a ƴa mace amma har kake so ka saka zargi a zaman aure  mu  Saboda ina sonka ina kiyayema duka dokokinka komai ka ce in yi shi nake yi saboda mu zauna lafiya amman duk ban tsira ba, ka ce wai kana da tabbacin ina cin amanarka.. Aji ni ce fa Mimin ka ni? Abunda ya fi min baƙin ciki shi ne yadda ba ka yarda da ni ba, sannan kana mijina wanda ya fi kowa sanina ka kasa iya shaidata to waye zai yi shaida ta?.   Tana mgana ta na kuka saboda abun in ta tuna sukan ranta yake yi, Aji gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi haka ya kara kamkame Mimi shima kamar zai yi kuka yana faɗin" Wlh sharrin sheɗan ne da kuma sonki, ina sonki Fatima shi ya sa nake kishin ki." Cikin kuka ta ce"In kana kishi na sai ka bari ka kasa yarda da ni? Haba don Allah shekara nawa muna tare? Ka rika sarrafa zucyarka sannan  ka rage kishin ka, ka tuna sanda ka ɗauke ranga ranga zuwa asibiti ka manta likitan namiji ne ya dubani a lokacin ba ka damu ba saboda lafiyata kake nema, To haka za ka rika hakuri da rayuwa dole zan fita wasu za su ganni kai ma za ka fita za ka ga wasu abunda kawai za ka saka a ranka shine ka yarda da ni, ko bayan ba idanuwanka ni mai tsare maka amana ne amman wlh abunda ka yi min yasa min bakinciki a zuciyata sannan kuma yasa na rage ganin ka yadda nake ganin kaa cikin Idanuwana." Haka ta faɗa tana kuka, Aji ya ruɗé yana faɗin"Don Allah kada ki daina sona Fatima, in kika gujeni wa zai so ni? Zan gyara halina zan riƙa sarrafa zuciyata da kishina amman kada abunda ya faru ya sa ki ji kin tsaneni." Mimi ba mgana sai kuka shi kuma ya na ta ban hakuri kamar zai mata kuka. Tabbas ya yi nadama kuma ba zai yarda ya ƙara aikata abin da ya aikata ba. Itama tana son mijinta duk da wasu hallayan na shi ba su da kyau.Sai dai ai daman ɗan adam tara yake bai cika goma ba, a komai ba za ka ce ka samu abu ɗari bisa ɗari ba. Ko 50% ka samu sai ka yi hakuri da shi, tunda har ya Ffhimci bai kyauta ba ta na da tabbacin gaba ba zai kara yarda ya aikata abin da ya aikata a baya ba.   Sai ta rumgumeshi cikin shesshekan kuka ta ce" Shi mgana zarar bunu ce, kuma wata mganar ta fi kaifin takobo kaifi, in ka caka ma mutum zata huda cikinsa har ta fita ta waje, ka daina barin ranka na ɓaci kana faɗin mganganu mara kyau a kan abin da ka ke so, wata rana za ka cutar da ni cutar da bazan iya yafe maka ba." "In sha Allahu ba zan kara ba." Da haka ta yafe masa ta kuma yi alkwarin manta abin da ya faru amman ta ce ba yanzu ba sai a hankali za ta iya manta abin da ya faru. Shike nan ma'auranta suka shirya, amman duk da haka Mimi ba ta sakin jiki da Aji, in ta tuna kalamansa a kanta sai gwiwanta ta yi sanyi shi dai ko da yaushe ban hakuri ne. Satin Hajiya biyu suka koma gida tunda Jikin na Mimi ya yi kwari, ta na yin amai amman ba sosai ba. Kasala ne dai da jiwa shima ba sosai ba. Sai zazzabin dare shima ya yi sauki sai dai ta yi fari fayau ta kuma rame. Sama da wata ɗaya sannan Mimi ta koma aiki. Gogan ya yi sanyi yanzu yana gani za ta saka mayafi ta fita sai dai ya kauda kai tunda ya yi alƙwarin yarda da matarsa kafin kishin sa a gaba, itama kuma tana yi domin ta ga ko da gasken ya daina abunda yake yi. Da gangan take saka abaya ta sha rolling ta wuce, baya mgana amman dai ya kan ce" Abaya tana nuna sufar jiki ko za ki saka hijabi ne Mimi? Sai ta kalle shi ta ce"Sai in saka ɗin in kana tunanin har yanzu ba ka yarda da ni ba." Da ta ce haka sai ya ce Allah ya ba ta hakuri,  In sheɗan ya saka masa wani tunani sai ya yi saurin yin ta'awizi ya kuma tuna cewa ba yadda zai hana Mimu fita to saboda haka sai ya yi hakuri da wasu abubuwam   Mimi kuma sai harabasa take yi ta ga ko zai kara yin wani abun amman sai ta ga da gasken ya gyara halinsa. Kuma har a lokacin ba ta gaya masa Alaqar Jaheed da Rukayya ba har manya sun shiga mgana abu ne daman me za'a jira? Har an saka rana wattani shida amman dole Rukky za ta bar aiki da karamci Jaheed ya ce a can zai nema mata aiki. Sai dai Mimi ta ba ma Aji mintin saka ranar Rukayya da Jaheed Baki sake y ace"Mimi abokin nawa fa?. Kai tsaye ta ce"Ya tsaya wasa. Ga ɗan gaske nan ya zo ya ɗauka." Nasir kam da kanta Rukayya ta gaya masa, Ya damu tunda shi a tunaninsa ta na jiransa ya daidaita da iyayensa ne. Jin ga wanda za ta aura ya sa Nasir ya ce"Ni miye laifina da zai huce a kaina ya kwace min dudurwa." Aji ya yi masa rantsuwan Mimi ba  ta faɗa masa. Kuma saboda ta kure shi har gidan ta sake gayyato Jaheed, tare da Rukayya ba tare da ta gaya masa ba domin ta ƙara jaraba nadamarsa.   Ko da ya dawo ya gansu bai nuna mata wani abu ko a fuska ba, sun yi masabaha da Jaheed har ya bashi hakuri kan abunda ya faru a baya shi kuma ya ce komai ya wuce shima ya na mai bashi hakuri. Rukayya sai a lokacin ma ta san an samu rashin fahimta ba ta yi mamaki ba, ita kawar Mimi ce ta san kishin Aji a kanta. Ita kam har ya na zolayanta da cewa ta yaudare su ta ce su ne suka yaudare ta. Sai yamma suka tafi, Aji bai yi ma Mimi mgana sai da daddare bayan sun kwanta ya kalleta yana faɗin"Fatima, wai ke nan har gobe ba ki yarda da nadama ba! Ba ki amince da na ce bazan ƙara ba? Sai ta yi shuru ba ta yi mgana Mirmishi ya yi ya na rumgumeta lokaci ɗaya yana Faɗin"Abin da nake so ki gane har abada ba zan daina kishin ki ba Fatima, ina sonki ba na so kuma ki kasance abun burgewa a idanuwan wasu mazan, gwajin ki a kaina ba shi zai saka ki gane nadamata ba, in na ce zan bar abu to kokari na ke yi na yi yaƙi da zuciyata a kan haka, na fahimci yarda shi ne kan gaba akan kishi shi ya sa na aminta da ke, ina son ki kuma ba zan daina kishin ki ba kema ina rokon ki aminta da ni kin san ina sonki ina kishin ki. Don Allah ki kiyayewar motsawar zuciyata Mimi" Ƙara shigewa jikinsa ta yi lokaci ɗaya tana faɗin" In sha Allahu Merapyaar.." Ya na mirmishi ya ce"Sunan Indiya kuma a ka saka min?   A kunnensa ta msa raɗa da cewa"Eh My love(Merapayaar) da yaren hindi." Sunan ya yi masa daɗi ya sa ya yi kyakyawan mirmishi kafin ya ce"Ke kuma kin koma My jan, domin ke ce rayuwata amman Ina son sunan ki, ina jin ɗaɗin kiran ki FATIMA.." Suka kara ƙamkame juna cikin soyayya da muradi, shike nan zaman lafiya ya ɗore musu kamar yadda ya roketa ta manta baya sannan ta na kiyayewa motsawar zuciyarsa. Tana masa abin a yake so, tana kiyaye abin da baya so,shima kuma ya daina takura mata amman fa mganar kishi, sai da ya rage shi duk da kuma hakan in ya ga abunda baya so zai yi mgana kuma za ta gyara,. Da gaske ne ya yarda da ita, itama ta aminta da shi sai suka samu kyakyawan fahimtar juna, Hankalin Inna ya kwanta tana fatan daga yanzu su rika fahimtar matsalan junansu suna magancewa da kansu.   Cikin Mimi na da wata huɗu Hibba ta haihu, kuma lafiya lau a gida ta haihu a hannun mijinta.Sai washegari ne suka je asibiti a ka duba ta an samu mace tun a daran Mu'azzamu ya raɗa mata suna MARYAMA." *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3018* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* Tunda Mimi ta ji labarin haihuwan Hibba shike nan ta fara murnan tafiya kano suna. Ba ma ita kaɗai ba hatta su Bintu kowa na ta shiri saboda haihuwanta na fari a gida nan Gombe ta zo ta haihu. Wannan karon ne za'a sha shagalin suna a gidansu da ke kano, Kuma uwa uba kuma Maryama sunan yarinya Inna Meri a ka yi ma takwara sai ya kasance sunan ma na musamman ne.   Tun sanda labarin haihuwan ya zo Gombe Ƙanwar mamanta ta shirya ta tafi wajen Maijego su kuma nan duk suna shirin tafiya ana gobe suna ne gabaɗayan su. In da Allah ya taimaki Mimi haihuwan ranar Jumma'a ce kenan tana da lokaci a weekend sannan kuma daman tana so in ta je ta leƙa har kofar Soro ta gaida dangin Mommy sannan ta leƙa har gidan Dr ma so take yi Mera ya bar ta ta yi ko da sati ne sannan ta dawo. Ita kaɗai take shirin yin sati ba tare da ta yi mgana da megidan ba. Bangaren Inna kuma tace an yi mata takwara ba za ta zauna ba ta saka a ka yi ma Hibba yajin Jego da kuma garin kuni mai yawa wanda zai taimaka wajen ciko mata da ruwan mamanta. Sannan kuma ta saka su Halima kowa ya kawo abin da yake da shi, a haɗa na kayan suna, su ma suka ce za su yi kan jiki kan karfin su in dai a kan Mu'azzam ne.   Anty Halima turmi biyu ta kawo da kayan jaririya da sabulai, Yaya Amina ma haka Bintu kuma wani less ne mai tsada wanda ta siye shi da kuɗin adashen da ta yi, Inna Meri kuma da ƴan kudaɗen dake hannunta itama ta sa ka aka siya turmin Atamfa da kayan jaririya masu kyau guda biyu. Ba ta yi ma Mansoor mgana ba sanin ko ba ta yi masa ba zai iya bakin ƙokarinsa. Maganar kawai ma su zuwa suna suka yi tunda akwai masu zuwa da yawa sai yace gwara a ɗauki tashar mota kawai tunda da Magajiya ta zo mata barka ta ma ta mganar zuwa sai ta ce baza'a bar gida ba kowa ba ga Zuwaira ta ce za ta je, to fa tunda a ka ji Mansoor zai yi tashan mota sai kowa ya miƙe yace zai je Harda Jummai da matar Auwalu ga matar Saddiqu ma Walida da Mariya ma sun ce za su je. Sannan a gidan su Baba Ɗanlami Inna ta ce ko Gaje ko Harira ga kuma can gidansu Hibba ko mutame biyu ne za'a ɗauka.   Ranar Alhamis daga camp Mansoor gidan Inna ya sauka kan mganar motar, dama sun yi mgana da ƴaron Baba Ɗanlami mai jan motar sharon, shi zai kai su sannan ya koma in an gama suna ya ɗauko su tunda daman yana zuwa kano kaduna ne daga nan Gombe. Mansoor ya sha mamaki da Inna ke yi masa lissafin masu zuwa cikin nuna mamakin sa ya ce"To ai motar ma ta cika Inna? Haba abu sai kace biki? Sun yi yawa ya kamata komai a yi shi da tsari ne. Inna ta gyara zama ta na faɗin"  Bakomai arziƙi ne, kuma dukkansu ba su san gidan ba. In ba domin haihuwan ba wa zai ta shi yace zai je Baban Inna? Kuma wa kake ganin a cikin su bai cancanci zuwa ba? Daga ƴan'uwanss sai yan uwan matarsa sai ƙannensa a ciki wa kake ganin za'a ce ba zai je ba?. Tun da ya ji Inna ta fara magana ya yi shuru ya san daman karatun za ta ɗora masa kenan amman sai da ya kaɗa kai kafin ya ce" Duk da haka dai Inna a yi abin hankali mana, shima Mu'azzam ɗin wata ɗawainiyar za a ƙara ɗora masa kada ki manta haihuwa a ka yi masa ya yi hidima Inna." Inna ta na mirmishi ta ce"To duka duka kwana nawa ne? In sun daɗe fa kwana huɗu."   Da sauri ya ce"A'a kwana biyu za su yi Inna, zan ma gaya ma su Yaya Halima kada wacce ta fi haka." Inna sai kawai ta kaɗa kafin ta ce"Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya." Ya amsa mata da Amin, suna zaune ne daman dukkansu a saman kujerun falon, ita ta na daga gefe shi kuma ya na zaune saman kujera mai zaman mutum biyu yana danna wayarsa suke wannan mganar da Inna.. "To ita Bintar za ta samu zuwa ko?   Kai tsaye ya ce" Eh za ta je, amman Inna kina ganin ya kamata Walida ta tafi? Sai a bar ki ke kaɗai? Inna ta balla masa harara kafin ta ce" Yarinya ce ni da za ka ce a barni ni kaɗai? Ta je abun ta Allah ya dawo su lafiya kafin na haife ku ai ni kaɗai nake zaune miye a ciki? Sai kawai ya kaɗa kai kafin ya mike yana mata sallama sai ta ce ya tsaya ya ga kayan da suka tara dole ya koma ya zauna Walida ta kwaso masa kayan, bai ko ɗaga ba amman ya kallah kafin ya yi mgana Inna Meri ta yi masa bayanin abin da suka hada sannan ta ce ɗazu da yamma Matar Auwalu ta kawo turmi da omo da sabulai ta ce na ta da na Magajiya Auwalu kuma dubi biyar ya ba da gasu a hannu.   Kai tsaye ya ce Allah ya saka albarka. Sai a lokacin ya tuna da ana ma fa wani abun in an haihu duk da ya turama Mu'azzam ɗin 100k ya kara amman sam hankalinsa bai kawo masa Mimi ma ba haka ya kamata ta je ba. Amman ganin kayan da Inna ta nuna masa sai ya farga daga nan gidan Inna sallar isha'i ya tsaya ya yi a hanya sannan ya shiga gida ya iske gida sai ta shin kamshin turaren wuta, ga kamshin girki ga kanshin matar gidan da ta chaɓa ado ta ci kwalliya domin farincikin mijinta. Tarba ta yi masa kamar yadda ta saba, suka makale juna kamar wani zai raba su. Bayan ya yi wanka suka zauna saman dining suna cin abinci jefi jefi suna hira.   "My Jan me za mu siya na sunan mai sunan Inna?   Kamar daga sama ta ji tambayar na shi, lokacin ma nama ne a bakinta sai da ta hadiye ta sha ruwa sannan ta kallesa kafin ta ce"Kamar me kenan? Sai kawai ya ce"Kaya mana, ba na ga wai ana siyan atamfa ko kayan jarirai ba." Sai Mimi ta saka dariya kafin ta ce"Ashe ka sani, ko gaya maka a ka yi? Kai tsaye ya sanar da ita a gidan Inna ya gaani mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Ni ai ban jira ka ba, mu gamaccin abinci mu shiga ciki ka gani." Sai da su ka gama cin abincin ta kwashe komai ta kai kitchen. Sannan ta gyara wurin ta rike masa hannu zuwa ɗakinta a saman gado ya ga akwatinta ƙarama. Gefen gado ta zaunar da shi sannan ta buɗe wardrpe ta ɗauko wata katuwar leda, ta sauke a gabanshi shi kuma dai dai lokacin ne ya kalli akwatin nata kafin ya ce"Wannan akwatin fa? Ko shima kayan sunan ne a ciki? Mimi na dariya ta ce" Kayan dai mai zuwa suna, kasan sati fa zan yi ina so ka bar ni zan je kofar soro na gaishe su sai kuma na leƙa gidan Dr." CBai samu ma bakin mgana ba, ya ga kawai ta zazzage ledan hannunta kaya sun faɗo, Atamfa da less sai rigunan Jarirai masu kyau guda uku sai katon pampers guda ɗaya sai wifer, sai wasu huluna na jarirai da safa a kalayensu masu kyau sai over roll shima na kwali masu kyau guda uku sai saitin man shafawan yara mai haɗe da hoda da olive. Ta gama ɗaga masa kayan ya gani sannan ta maida a leda lokaci ɗaya tana faɗin" Ni na gama mawa saura naka uban Maryama." Mirmishi ya yi kafin ya ce"Duk yaushe kika yi wannan siyayyar ban sani ba?. Gira ta ɗaga masa kafin ta ce" Zauna nan, kasuwa na je ni da Rukkayya." "Da izinin waye kika je kasuwan?   Haka ya faɗa yana tsare ta da Idanuwansa sai kawai ta saka masa dariya kafin ta ce"Da izinin mijina mana, ka manta ranar na ce maka Rukky za ta rakani anguwa? Ka ce sai na dawo kada na yi dare? To ai kasuwan ne anguwan" Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Na ji kin yi naki, ni me ya kamata na yi? Sai da maida ledar in da ta ɗauko sannan ta zauna gefensa kafin ta ce" To me ya kama ta ka yi? Tunda ni na siya waɗanan kayan me zai hana kai sai ka ɗora mata da Kuɗi? Kai tsaye kuma ta cigaba da cewe" Kuɗin zai fi, tunda ka ga ni na siya kayan sai mu ɗora da kuɗin zai fi." Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shike nan amman kamar nawa ki kke ganin zan ɗora na kuɗin? Kai tsaye ta ce"  Duk abin da Allah ya hore maka Merapyaarr" Sai ya gyaɗa kai kafin yace bari da safe in Allah ya kaimu.   A daran bai mata mganar satin da ta ce za ta yi ba sai da safe tunda tun asuba ta tashi tana aiki. Daman tun a daran jiya ta yi masa miya saboda tasan shi ba ya son aiki. Sannan ta saka an yi masa snak cake da cincin da samosa ya riƙa shan Tea da shi kafin ta dawo duk kuma ta kaisa kitchen ta nuna masa, har tana cewa ya riƙa dafa farar shinkafa ko taliya ya na ci da miya. Kallonta ya yi a karkace kafin ya ce"Wai wata za ki yi ne a can? Mimi ba ta ba ma tambayansa muhimmanci ba ta ce"Ka manta, na ce maka zan yi sati ɗaya."   Bai ƙara mgana ba. Sai da suka karya har Mimi ta yi wanka tunda Bintu ta kira ta ce suna gidan Inna ita a ke jira mai motar ya ce karfe tara na safe za su tafi, Aji ya riga ya biya kuɗin motan na zuwa da na dawowa. Sai da suka zo sallama duk da shi zai kaita gidan Inna a motarsa, ya rumgumeta yana shafa cikinta da ya fara tasawa lokaci ɗaya kafin ya ce"My jan.." "Uhm Merapayaar." "Bai kamata ki je ki yi sati ba. Saboda kina da juna biyu ni ya kamata na riƙa kula da lafiyarki, don Allah ki yi kwana biyu ki biyo su Yaya Halima ku dawo" Da sigar lallashi ta faɗa, da yasa ta yi shuru ta lafe a jikinsa. Ganin ta yi shuru yasa ya ƙara sausauta murya kafin ya ce" Na saba dake, ba zan ji daɗin zama ni kaɗai ba, ba ki tausayina? Wa zai rika ba ni abinci yana min hira? Ki bari daga baya ko bayan kin haihu ne sai ki je ki gaishesu. Ni sai ma mu tafi tare na rakaki amman na roke ƙi da Allaj ki dawo tare da su Yaya Halima.". Nan ma shuru ba amsa, Idanuwanta ya ciko da kwallah. Domin har ta faɗa ma Mommy za ta je soron ɗinki, sannan kuma yanzu sai ta ce ba za ta samu zuwa ba? Ganin yadda ta nuna ne ya sa sai ya raba ta da jikinsa lokaci ɗaya yana faɗin"Amman kin kin ga da takura ba zan hana ki ba, ki yi satin sai ki dawo daga baya." Sai kawai ya juya zai fita daga ɗakin da sauri ta riƙo hannunsa kafin ta rumgumeshi ta baya lokaci ɗaya tana faɗin" Umarni kawai za ka ba ni ba alfarmana za ka roƙa ba, ai zaman ka nake yi, Kada ka damu zan dawo in sha Allahu tare da su."   Kamar zai yi kuka  ya juyo yana faɗin "Kwana biyun za ki yi ko? Sai ta gyaɗa masa kai, rungumeta ya yi cikin farinciki lokaci ɗaya yana faɗin" Allah ya miki albarka My Jan, na yi miki izinin ko Walida ko Bintu su raka ki ki je ki gaishe su kin ji ko? Sai ta gyaɗa masa kai, Ita da kanta ta yi ɗage ta sumbaci kumatunsa. Shi kuma ya yi saurin damƙe kanta ya rankwafa yana sumbatar bakinsa, ita kuma sai ta zagaye hannayenta daga bayansa ta rumgumosa sun daɗe a haka kamar ka da su rabu gani ta yi zai ɓata mata kwalliyarta yasa ta ƙwace jikinta lokaci ɗaya tana faɗin" Suna jira na fa." Ƙara riƙota ya yi lokaci ɗaya yana faɗin"Minti biyar to."   Dole ta kyaleshi ya rumgumeta kawai ya na shakan kamshinta. Sannan ya sake ta lokaci ɗaya  yana riƙe mata hannu ɗayan hannun kuma ya rike akwatinta, sai ta karɓa Lokaci ɗaya tana cewa"Sai na sauya shiri." Shi taya ta ta rage wasu kayan, kayan sunan ma da za ta kai ma Hibba duk a ciki ta tusa kafin su fito har Yaya Amina sai da ta kira shima Kuma Mansoor Auwal na ta kiran shi Mu'azzan tun asuba ya kira baki ya ƙi rufuwa yan'uwansa suna hanya. Shi ya rike mata akwatin har jakarta sannan ya saka mata mayafinta a saman kanta ya rike mata hannu ya kai ta har mota, sannan shima ya zagaya ya shiga a hanya suka tsaya ya cire kuɗi 50k yace ta haɗa ta kai ma Hibba ta amsa lokaci ɗaya tana faɗin. "Mungode Baban Maryam Allah yasa ka ma nema albarka." Yana mirmishi ya ce"Amin Amin Ummu Maryam." Suka haɗa ido suka yi ma juna mirmishi, ya rike mata hannu da hannunsa guda ɗaya, ɗayan kuma ya na tuki dashi, kewarta yake yi tun kafin ta tafi, ganin yadda ya matse mata hannu yasa ta rike hannayensa da hannunta guda biyu ta jimke kafin ta kallesa cikin shagwaɓa Ta ce. "Ina sonka, ina matukar kaunar ka.."   Wani kayattacen mirmishi ya saki kafin ya ce" Kin san dai na fi ki son ki ko?  Ina sonki, ke ce komai nawa Fatima." Sai suka ƙurama juna ido, ganin kamar hankalinsa na kanta yasa da sauri ta ce"Tuki kake yi, ka kula Merapayaar" Sai ya maida hankalinsa kan hanya Allah yasa ma titin ba motoci sosai. Suna tafe amman suna ƙanƙame da hannuwan juna "Ki kula da kanki, kin ɗauko magungunan ki?  Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa"Ka da ki ci wani abun da cikin ki ba ya so, ina son cikin nan Mimi nima na ƙosa ki haifamin wata Maryama ɗin"  mirmishi ta yi masa kafin ta ce" In sha Allahu kada ka damu." Sai ya jinjina kansa, sun shigo anguwan Tunfere kenan ta ji yana faɗin" Na ma gayama Mu'azzam ya kula da ke, kina da juna biyu." Mimi ta kalleshi cikin jin kunya ta ce"Kai, wai kai baka jin kunyar gayama mutane ina da juna biyu? Suna tsayawa ƙofar gidan Inna dai dai lokacin da ya kalleta yana faɗin" To miye a ciki? Ai ba abun kunya ba ne na ga abin farinciki ne kowa kuma na son matarsa ta samu ciki."   Mimi ta ce"Duk da haka dai ba a faɗa sai dai a gan shi ya fito, haka fa da muka je gaida Daddy ka faɗa masa wai ina da juna biyu." Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce"Kin ji ki da wata mgana? Abun kunya ne?  Na ga dai abun alhafari ne, kuma ke ba ki san masu shege ma suna nuna ma duniya ba? Ballantana ni da ɗan sunna zan haifa" Dai dai yana buɗe mota ya fito sannan ya zo ya buɗe mata ya rike hannunta ta fito daidai lokacin da ta ce"Amman ai da kunya tun da kowa ya san abin da muka yi a ka samu cikin ko? Aji ya kalli Mimi ganin har ta na wani ɓata fuska. Dariya ta kamashi ya kama yi tun da Mimi take da Aji a sanin da ta yi masa a baya da yanzu ba ta taɓa ganin shi yana dariya haka ba. "Shekaran ki nawa wai? Ai daman kowa ya san sai da muka haɗu a ka samar da saduwa sannan kika samu ciki, tunda ba a ruwa za ki sha ba."   Haka yake faɗa yana mata dariya, kamar za ta yi kuka ta dake shi a kirji shi kuma ya na riketa yana dariya dai dai lokacin sai ga mai motar tare da Auwalu da Gaje a ciki ita ce za ta je. Sai matar Auwalun da Maeesha da Mariya, da Jummai da Zuwaira kowa cikin shirinta, Auwalu ne ya sauko suka gaisa yana gaya masa yaron mai motar ne zai kai su kanon shi yana gida baya jin daɗi, Aji ya kalli direban kafin ya ce"Ka tabbata ya iya mota?  matata ciki gare ta ban shirya ɗaukan wannan kaddaran ba yanzu." Ai Mmi na jin haka ta ja jikinta zuwa wajen su Yaya zuwaira tana gaishesu domin in ta cigaba da tsayawa saita ji abin da zai saka ta ba za ta ƙara kallon Yaya Auwaln ba.   Tare suka shiga gidan suka iske su Yaya Amina tun ɗazu suna nan suna jiran su, nan a ka gaggaisa sannan sai ga su Auwalun sun shigo gidan tare da Mansoor suka gaida Inna sun shirya daman motan kawai suke jira, Yaya Halima ce ta kalli Aji kafin ta ce"Na ji ana zencen kwana biyu na ce mu fa huɗu za mu yi." Kai tsaye ya ce"A'a kwana biyu za ku yi gaskiya." Haɗe rai ya yi kada ma ta kara mgana, Ita daman zolayanshi take yi, Bintu ce ta ce a hankali ita sati mijinta ya barta ta yi. Hararanta Mansoor ya yi kafin ya ce" Duk wacce ta ga kwana biyu ya yi mata kaɗan za ta iya ƙarawa amman litini da safe mota za ta koma wanda ya ga zai dawo shike nan. Haka ya faɗa lokaci ɗaya yana ficewa Bintu ta tura baki ta ce" An ya in Anty Mimi ta haihu za mu je mu yi sati muna suna kuwa? Yaya Amina ta ce" Kina da koƙari, in ma ya bari an yi sunan kenan tsab zai ce ba taron suna in dai Baban Inna ne."   Mimi na gefe ta na jin su tana yar dariya, ba ta ce komai ba, Yaya Halima ta ce"Duk fa wannan muzurin saboda matarsa ne, kada mu kara kwana a barshi a gauro." Gabaɗaya suka saka dariya Bintu har suna tafawa da Yaya Amina. Mimi ta harare ta kafin ta ce" Har da ke ko? Zan gaya masa." Bintu ta tsuke baki tana faɗin" Ni ban ce komai ba, ba ruwana." Suna cikin mganan ne Auwalu ya leko ya ce su fito su Yaya Zuwaira daman suna tsakar gida Maeesha ne kawai tare da su, Mariya da Walida yan zumuɗi suna kofar gida wajen mota su Auwalu suka fiffita da kayan a ka saka a booth, sannan a ka tsara tafiyan Aji shi ya saka Mimi a gaban mota ita da Mariya tunda ba ta da jiki, Yaya Jummai ta kaɗa baki tana faɗin"To ai da baya ta dawo,  ko ka saka Bintu madadin Mariya." Kai tsaye ya ce"A'a Bintu za ta matse ta, kuma ni ina so ku kula da ita ne, juna biyu gare ta fa"   Kunya kamar Mimi ta nutse kanta ta sunkuyar Yaya Auwalu ne a ka bari da faɗin" ƙwarai kuwa, ku kula da matar yallaɓai dakyau." Gaje ce ta ce" Kada ka damu Baban inna  zamu kular maka da matarka da abin da ke cikinta in sha Allahu." Suna ta masa dariya shi kuma ya haɗe rai, Mimi ko kunya ta rufe ta wai har ya na ma direba warning cewa kada ya yi gudu ya bi a sannu matarsa juna biyu gare ta har yana cewa"Ita ce komai nawa, ka bi su a hankali don Allah ban da gudu.". Direba na dariya yace"In sha Allahu Yallaɓai " Inna Meri ma har kofar gida ta rakosu,  tana musu fatan Allah ya tsare, baya mutum huɗu Gaje da Jummai da Zuwaira, sai Maeesha. Kujeran tsakiya kuma Yaya Amina da Yaya Halima sai Bintu, sai Walida da a ka gyara ma inji sauran kujeran za'a biya Tudun wada a ɗauki mutum ɗaya daga gidansu Hibba.   Suna ɗaga musu hannu tare da fatan su isa lafiya, Tudun suka biya su ka ɗauko Zaliha ɗiyar ƙanwar Maman Hibba ne sai bayan sun dau hanyar kano Nafisan Nasir ta kira Mimi ta ce ba ta san sun shirya tafiya ba, Nasir ya barta da ta zo. Sai mimin ta bata hakurin itama ta sha'afa ne ba ta mata magana ba, amman wai Nasir ɗin ya yi ma Aji mgana shi kuma wannan tuni ya manta ma.   Direban ya ji mganar Oga Aji bai yi gudu ba amman sun isa wajajen uku ne na rana. Shi kan shi Aji ya yi mamakin saurin su haka yace ma Mimi da suka yi waya. Murna wajen Hibba da Mu'azzam ba'a mgana, suka rasa ina za su saka su saboda murna sun iske wasu daga cikin ƙanen Hibba da yayenta sun riga su zuwa tun jiya suke. A ka rasa ina za'a saka su kawo wannan miko wannan Sun rasa bakin godiya ga zuwa ga abun alheri Mu'azzam sai da ya yi ƙwallah domin Yayan nasa ya gana mishi komai bayan kudin da ya tura masa ya biya kuɗin mota sannan ga ɗawaniyar kayan suna da kuɗi, ya kira shi zai masa godiya ya kashe wayarsa. Ba su zauna ba da yamma a ka fara aikin suna raguna biyu a ka yanka ma Maryama da safiyar suna. Sannan sun dafa shinkafa sun yi alale da Zoɓo an kuma soya kayan ciki bayan haka kuma ga nama ya siya ɗanyen an yi girki da shi, a ranar Mimi ba ta samu fita ba sai washegari ranar lahadi Bintu da Walida tare da mariya suka rakata gidan Dr ta fara zuwa baya nan ma yana asibiti sai dai Jawahir nan suka yi sallar la'asar sannan suka wuce soron ɗinki, Inna Zainaba sai da ta mata tsiyan ta ɗauka za ta kwana ne amman sai ta ce washegari za su koma gabaɗaya, suna can har dare sannan a ka saka direba ya dawo da su gida.   A ranar daman su Yaya Amina suka soya Nama a ka diɓar musu na su a daran. Na Inna daban haka na Baba sai sauran kuma a ka haɗa su gabaɗaya. Amman na Baban inna roba guda cike da nama in ji ɗan'uwansa, misalin sha biyun rana direban yazo amman sai da suka yi azahar suka ci abinci shima yaci sannan suka ɗauki hanya nan suka bar ƴan'uwan Hibba su sai jibi za su koma anman ƙanwar mamanta na nan sai ta yi arba'in. Sai mangariba suka iso gida, gidan Inna su ka yada zango, nan suka raba naman kowa ya ɗauka na shi, sannan Mu'azzam ya ba su kwalin omo da sabulu yace su raba gabaɗaya.   An raba amman Mimi ba ta amsa ba, Naman ma cewa ta yi su haɗa ma Inna sabulun kuma ta ba ma Jummai omon kuma ta ba ma Yaya Zuwaira su sun fita bukata. Yaji jegon ma an ba su wanda ƴan'uwanta su ka mata sun raba gabaɗaya. Zuwa bayan isha'i kowa ya yi gidanshi inna ta diɓar ma Magajiya naman da Yaji ta ba Mariya ta kai mata, Gaje ma har na Harira an ɗiba mata ita daman Inna an san rabar da shi za ta yi kila ma ko a bakinta sai an yi da gaske za ta ɗanɗana.   Mimi dai nan ta jira Aji ya zo ya ɗaukota da daddare suka tafi gidansu, daman a daddafe ya yi kwana biyun nan. Washegari ma ba ta samu zuwa wajen aiki ba sai ranar laraba ta koma.Miyan ma da ta yi masa ko sau ɗaya bai yi amfani da ita ba. Ya dai ci cake da samosa, itama ya ce domin ya na so ne yasa ya soya ya ci, da tace ina ya ke cin abinci ya ce gidan Inna da ta gama za ta kira shi ya je ya cika cikinsa, ina zai iya wani Dafa shinkafa bayan ta gama sangarta shi.. In da Allah ya so ta da rahama ba ta yi mugun laulayin da zai hana ta aikace aikacen da kuma biya ma mijinta bukata ba ko amai ba sosai take yi ba bar ta dai da cin goro sai kayan kwalama suma ba kasafai ba. Cikin fari ne amman Alhandulillah ta same shi da sauki fiye da tunaninta, fatan ta Allah yasa yadda ta samu laulayi da sauki ta samu haihuwan ma cikin sauƙi. ****** *BAYAN WATTANI BIYU..* Har Hibba ta yi arba'in ta zo gombe ta yi sati ta kawo ma Inna takwaranta wacce suke kira Ammi. Mu'azzam ya zo ya ɗauke ta suka koma gida, cikin Mimi kuma watannin shi shida ne, har ta fara zuwa awo a wani asibitin kuɗi a cikin gari tana kuma cigaba da zuwa aikinta. Cikin ya bi jikinta tunda tana da tsawo sai da ya saka ta buɗe daga kasanta saman ta kuma mamanta sun yi manya kumatunta ya kumbura sannan hancinta ya ƙara girma tuni dai halittar ya sauya. Hajiya ce ta gaya mata cikin jikinta ya bi shi ya sa ba'a ganin girmansa, shi kuma Aji ya ce ta zauna a haka ta fi masa kyau a koda yaushe ya kalleta ya na jin farincikin yau ita ce ke ɗauke da cikinsa wannan ma abun alfahari ne.   Zaman su suke yi lafiya cike da kauna sai ɗan abun da ba'a rasa ba. Tun da daman shi zamantakewa zo mu zauna ne zo mu saɓa ne, sai dai suna ƙokarin Fahimtar juna domin samun daidaito. Shi yanzu babban Blburin shi shi ne ya samu ya biya ma Inna ta je makka ta sauke farali, ga shi Contart ɗin shi saura shekara biyu ya ƙare a Gombe United amman bai yi tunanin yi ma kansa wani tanadi anan gaba, ya samu kuɗi tunda a wata ɗaya sun je kano da kaduna sun buga wasa bayan albashinsa akwai allowense. Sannan kuma mganar Contrart din Captain din Team an saba daga waje akan ɗauko wani a ba shi horo amman wannan karon sai ya samu Coach ɗin su da maganar ga Musa pele a cikin su yake yana da ƙokari tunda shi ne kamar matsayin Assitancen ɗin Aji, yace me zai hana shi a ba shi horon.?   A lokacin kallonsa Coach ɗin na su ya yi kafin ya ce"In contart din mu ya ƙare, ka shirya in da za ka koma ne? Sai Aji ya ce"Tukunna dai Coach." Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Ba na so ka bar mu, kuma ina son cigaban ka ina inan ina yi maka wani ƙokari in ya tabbata zan neme ka, in kuma bai tabbata ba sai dai mu ƙara singing ɗin contart ɗin da kai amman ba zan bari Gombe United ta yi rashin zaƙwaƙuru irin ka ba." Ya daɗe daman ya na jin Coach na yawan faɗin ya na masa jokari bai taɓa maida kansa ba, ballantana ya yi tunanin makomarsa anan gaba, shi kam me ya ke nema? Komai ya samu sai dai godiyar Ubangiji kawai mutum ne shi da ba shi da hange hange, saukaƙƙiyar rayuwa ce a gabansa ya yi ma iyalansa sannan ya farantama Iyayensa..   Shi kaɗai yake da burin biya ma Inna saudiya ko da Mu'azzam bai taɓa yin zencen da shi ba, Saboda baya son taimakon kowa  yanzu dai haihuwan Mimi ne a gabansa sai Jamb ɗin da Walida za ta sake yi, ga bikin Mariya na matsowa duk da shi sai bayan ƙaramar salla gabda nabban sallah sannan za'a yi bikin. Ya dai fara ba ma Mimi kuɗi ta rike na siyan kayan haihuwa, itama a ɓoye tana siyan ma kanta saboda in megidan ya gani zai yi mata faɗan cewa shi ya gaza ne? Ko ya sakata ne? Shi ya sa ma ta ke ɓoyewa ba ta bari ya gani ba saboda dai a samu zaman lafiya, duk da tana da kuɗi amman bai yarda da ta kashe ma kanta naira biyar ba, sai dai komai take so ta yi masa mgana, in bai da shi a lokacin sai ya ce ta ba shi lokaci, in ya samu sai ya ba ta, ba ya taɓa duba aikinta ko gadon da ta tara shi dai ya sauke nauyin shi, sai kuma yake ganin kamar gazawa ce da ci baya ya zauna mace na masa hidima da kuɗinta amman za ta iya siyan kayan ado domin kanta ko ta yi wani sha'anin a bangarenta ko kyauta ga wanda ta ga dama ba zai hanata ba. Ya sake biya ma Walida Jamb bayan ya gama ja mata kunnen saura ta je ta faɗi, sannan ya saka ta jamb class, sai faɗa yake yi in aure take so ta yi mgana kada ta saka shi kashe kudi, Mimi ke tausan shi da cewa Jamb fa sa'a ne da rabo shi kuma ya ce har dakewa kuma da gaskiyansa duk abin da aka yi ma dakiya za ka iya cin ma nasara, itama Walidan ai ta sani dole ta dake da ƙoƙari. Sannan BUK ya cike mata saboda Mu'azzam ya ce za ta zauna a gidansa ta yi karatun ta, bai yi mata katsalanta kan ra'ayinta ba ya ce ta zaɓi Course ɗin da take so sai ta saka Microbiology.   Rayuwar dai haka ta cigaba tafiya  a kwana a tashi ba wuya ga cikin Mimi na wattani takwas, Mommy ta yi mganar za ta koma gaban Hajiya ta haihu, Mimi na gaya ma Aji yace bai amince ba a tsarin shi ba tsarin matarsa ta je gida wanka a nan gidan za ta zauna ta yi wankanta da jegonta. Tunda kuma ya ce haka ta san yana kan matsayarsa sai ba ta matsa ba, ta ce ma Mommy za ta yi jegonta a gidanta ai suna kusa ba matsala,  A watan ta je kaduna Khadi ce ta samu ɓari ta yi ta zubar da jini kamar ba za ta rayu ba.   Ba tafiyar mota suka yi ba Jirgi ne ita da Hajiya da Mama suka kwana biyu suka dawo. Amman ta je gidan Ahmad sun gaisa da Matarsa  ta na kuma dawowa Rukayya ta taso ta gaba kan shiryen shiryen biki tunda saura wata ɗaya da an yi ma sai dai an ƙara ma wata ɗaya ne a sama. Ga cikinta ya tsufa ba ta iya wannan zaryan Aji ma ya ce Rukayya ta ɗaga mata kafa, ita kuma ta ce sai sun rama ma kura aniyarta itama haka ta wahala da na su bikin Aji ya ce dama ba don Allah ta yi ba kenan? Rukky ta na dariya tace eh sai an rama biki ba.   Karamchi Tibi ta yi rashin ma'aikaciya Irin Rukayya domin tun saura wata ɗaya da wani ta ijye aiki, duka ma'aikatan sun yi kewarta musamman ma Na Misau,itama Mimin ta na so ta ɗauki hutu amman sai ta haihu saboda ta samu ishashen ookaci a gida tana kula kanta da abin da ta haifa tare da mijinta.Saboda shi ya na son kulawa ba zai mata uzirin domin ta haihu ta yi masa banza ba, nauyi ne zai haɗu mata dole sai ta samu lokaci da hutu. Zuwa Lokacin sun gama siyan kayan haihuwa har na fitar suna, Itama ta ƙara ta siya ma kanta abin da take so da kuɗin ta. Zirga zirgan bikin Rukayya ma ya sa ta sassaɓe. Ga shi biki gida biyu ga gidan su Rukayya ga gidan Daddy ana saura sati biyu biki a kai kai lefe akwati takwas kuma kaya sai wanda ya gani. Nan gidan za'a kawota ta yi sati ɗaya sannan mijinta ya ɗauketa zuwa lagos gidan da Jaheed ya siya fili ya na ginawa ba'a gama ba, sai an gama za'a yi ma amarya jere anan Gombe.   An shiga satin biki zirga zirga da hidima ya ƙaru, Mimi da katon ciki a gaba ta ce ma ita ba wani kyau za ta yi ba tunda duk hallita ya sauya, sannan Gogan bai hana ta amman duk dare zai je ya ɗauko ta ta kwana a gida da safe ya maida ta, ba ta zama a gida ga zuwa aiki ga hidiman biki, shi yavsa ba ta san Mu'azzam da yayan na shi sun samu matsala har sai Baba ya yi musu sulhu ba, kan mganar biyama Inna aikin hajji ne, an ta biya sannan ga Walida ta samu Jamb har Buk sun ba ta admmission shi ne ya kira Mu'azzam kam hidimar makarantar anan ne ma ya ke faɗa masa kuɗinsa kaf zai haɗa ya biya ma Inna saudiya, shi kuma Mu'azzam ya na jin haka sai ya ji haushi ya ce ai tare suka ce za su haɗa kudi su kai Inna Saudiya me yavsa ya zare shi a ciki? wato ya nuna masa shi Inna ba ta haife shi ba kenan?, shi ta haifa Mansoor ya so ya fahimtar da Mu'azzam cewa ba haka ba ne. Amman ya yi fushi Ya riƙa kiran shi a waya bai ɗauka ba sai da Mansoor ya je ya gayama Baba  shi ya kira Mu'azzam ya yi musu sulhu, amman sai dai a ka yi yarjejeniyar Mansoor zai biya miliyan shida shi Mu'azzam ya cika sauran, dole a ka tsaya a haka sai dai Inna ta ji kawai ƴayanta za su biya mata ta je ta sauke farali ai sai ta saka kuka ta yi sujudaan godiya ga Allah ta na kuka ta na yi musu addu'an Allah yasa su gama da duniya lafiya.   Ko kafin a gama bokin Rukayya har an kai Inna an mata pasport, an biya mata hajji ƙarkashin jihar Gombe.Kowa na ta zuwan ma inna murna baki ya ki rufuwa, ita kuma Walida sai bayan salla za ta wuce kano makaranta tunda azumi ya kusa. Gefe ɗaya kuma su Inna sun fara zuwa bita. Rukayya Amarya suna gama satin su suka yi sallama da ƴan'uwa suka ɗaga sai garin Ikko Mimi ta ba ta lambar Madiha tacce ga Yaya nan ta yi mata ba za ta yi kaɗaici ba.   Bikin Mariya zai kama gabda babban sallah ne, Magajiya ta ce a ɗaga shi sai bayan babbar sallah Uwar amarya ba ta nan lokacin ta dawo Inna kenan, tunda yanzu Magajiya ta saduda ta nemi gafaran Inna suna zaune lafiya sannan ƴa'yan gabaɗaya sun haɗe kansu, Maeesha da Mimi ma sun haɗe kansu waje ɗaya kamar wani abu bai faru ba Saddiqun ma harkan gini Auwali ya saka shi tunda shi yanzu sai godiyar Allah ya samu ɗaukaka.   Ana azumi saura sati ɗaya Mimi ta sauka, cikin dare gab da asuba Naguda ya kamata Aji ya ɗauke ta zuwa asibiti daman tuni ta shirya akwatin kayan hqihiwanta cikin ikon Allah ko awa ba ta kai tana nqguda ba, ta haifi ƴarta mace jajir da ita idanuwan da bakin da hancin na Aji ne fatar da suman kan  kuma duk na Mimi ne. Turbarakallah mssha Allah sanda ta haihu Inna na asibitin da Yaya Amina sai Baaba Uwani da Mama tunda ya kira su a waya ya sanar da su. Kafin gari ya waye labarin haihuwan Mimi ya karaɗe Gombe da kewayenta. Kuma kai tsaye uban ƙarnin ke fadin an samu wata MARYAMA ta biyu. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3019* *INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,* *09069067488* https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba. Mimi ba ta kwana a asibiti ba, ta dai yini zuwa dare bayan an tabbatar da lafiyanta da na abin da ta haifa a ka rubuta musu takardan sallama amman fa asibitin nan ta ga gayya kashi kashi kama daga ƴan'uwanta zuwa ƴan'uwan Abu Maryam ɗin. Gidanta a ka maidata, saboda daman Aji ya ce ba ya son wankan gida matarsa a gidanta za ta zauna ta yi jegonta sai dai a samu mai zama da ita, Mommy tuni daman ta yi ma Inna Zainaba mgana ta na jin an haihu a ranar ta iso, amman a gida ta same su tunda ba ta taso a kan lokaci ba. Hajiya bakinta yaƙi rufuwa har da ita a asibiti har kuma suka dawo gida, ta ɗauki Jaririyan ta saka albarka sannan ta kalli Mimi dake zaune gefen gado a cikin bedroom ɗin ta, wani katon Jug ne a hannunta Inna Zainaba ta haɗa mata tea bayan sun yi wanka ita da jaririyar. Sai ta ji kwallah ta tarun mata a cikin ƙwayar ido, Allahu akbar yau ga shi Binta ta yi aure har ta kai ga ganin ƴarta a duniya. Sai dai Kabiru baya raye. Burin shi kenan ya ga Binta ta samu kyakyawan rayuwa irin na kowa ta mace. Hawayen nata sai da suka zubo ta share lokaci ɗaya tana faɗin"Allah ya jiƙan kabiru. Allah ya cika maka burin ka Binta ta samu kyakyawan rayuwa mai cike da farinciki da kake yi mata fata." Mimi ba sai hawaye ta tuna da Abin ta amman a cikin ranta ta na yi masa addu'an rahama da dacewa. Su Mama da Anty duk suna gidan har da Mamansu Rukky da Bibi da Nafisan Nasir, Sai su Bintu da Walida da Mariya su Yaya Amina sun tafi kafin mangariba, Inna kuma daman tun a asibiti bayan an haihu lafiya isowar su Mama ta koma gida. Sai can bayan isha'i gidan ya watse a ka bar Inna Zainaba kaɗai sai mai Jego ta kasa zama sai kai da kawo take yi domin kula da Mimin wacce ta samu ƙari sai da a ka yi mata ɗinki tana bukatar shiga ruwan ɗumi lokaci bayan lokaci, Aji bai shigo gidan ba sai wajen goma suna tare da Nasir da makama yau kam bakinsa ya ƙi rufuwa bai taɓa tunanin haka a ke jin farinciki in a ka zama uba ba sai yau wayar da ya amsa na barka bai san adadi ba, Mu'azzam daman shi ya fara kiran shi ya sanar da shi Fatima ta sauka an samu wata maryama Mu'azzam ɗin ne ya rika gayama sauran mutane, har su Baba Ɗanjuma da rana sun je asibiti sun Duba Mimi da abin da ta haifa. Itama ta bangarenta har sai da ta gaji ta amsa wayoyin mutane, bayan ta dawo hayyacinta na natsu daga gumurzun Naguda ita ai sai dai ta yi ma Allah godiya domin ta samu ciki cikin sauki ba ta yi wahalan laulayi ba sannan wajen haihuwa ma Ubangiji ya saukaƙa mata, in a ka cire ƙarin da ta samu suka yi mata ɗinki sannan ba ta yi doguwar naguda ba, ko da yake Inna Zainaba tace irin Mommy ce itama haihuwan ta cikin sauƙi ne kafin ma a tafi asibiti wani lokacin ta haihu, har ita kanta Mimin a gida ta haifeta sai daga baya suka je asibiti a ka duba su. Rukky ce ta fara kiranta lokacin da ta fara amsa waya suka yi mgana bayan kuma sauran wayoyin da ta rasa ba ta amsa ba, ta yi mgana da duka ƴan'uwanta har Mommy suna yi mata barka da arziki har da Madiha da megidanta domin ita kai tsaye ta ce"Congratulation Fatima Kabir Dabo, Za mo wa uwa ba abu ba ne mai sauƙi. Allah ya raya abin da kika samu ke kuma ya baki lafiya da ƙwarin jiki wajen shayarwa tare da tarbiya." Sai ta ji daɗi da abin da ya kai ɗan'uwa daɗi a wannan duniya ko da kuwa kuna da tarin bambamcin hallaya ne a tsakanin ku. Haka ma Dr ya ce ya yi ta mata addu'a sannan da faɗan ta kula da kanta, shi da Jawahir sau biyu suna kiranta haka ma Hibba da Mu'azzam ta samu wayarasu ita dai ba ma za ta iya kirga waɗanda suka kirata ba amman dai abu mafi soyuwa shine babban kyauta ne na Ubangiji ace yau ka na amsa sunan uwa wani farinciki na dabam ne. Farincikin da take ciki ya sa ta kasa daina kallon jaririyar da Aji ya yi mata huɗuba da Maryama ba. Mamaki take yi yau itace ta haihu? Haihuwan ma tare da Aji abin da ba ta taɓa tsammani ba, har ta cire tsammani kuma sai Ubangiji ya kaddara za su zamo abu ɗaya. Sanda ya shigo gidan ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya sauya ya tsaya ya amsa wayar Coach na su in da ya ke yi masa barka, ya kira shi da safe suna asibiti sai ya tura masa saƙon ba zai shigo Camp ba saboda mai ɗakinsa ta sauka shi kuma Coach na jin haka ya gayama sauran ƴan Team da cewa matar Capatin ɗin su ce ta haihu so ranar shi ya jwgoranci morning traning ɗin, abinci da komai da zai bukata Mimi ta faɗa ma Inna Zainaba a ka tanadar mishi a saman Dining bai duba abincin ba sai da ya leƙa ɗakin Mimi ya gaida da Inna Zainaba sannan ta fice falo ta ba su waje, gefen gado ya zauna lokaci ɗaya ya na faɗin"Me jego." Mimi na mirmishi ta ƙara kishingiɗa lokaci ɗaya tana faɗin"Na'am Angon ƙarni." Mirmishi suka yi ma juna, sannan ya leƙa jaririyar dake kwance gefenta tana tasharan barcinta na wani lokaci sannan ya dawo ya daidaita zaman shi. "Sannu da koƙari Matar Aji.." Mimi na mirmishi ta ce"Yauwa Mijin Mimi.". Hannunta ya kama ya riƙe yana kallonta kafin ya ce"kin ƙara kyau, yau kaɗai jego nan ya karɓe ki." Dariya ta yi amman ba ta yi mgana ba sumbatar hannun nata ya yi kafin ya ce"Ina fatan komai lafiya ko? Ta fara shan nono? Haka ta faɗa ya na rike da hannuwanta. Sai Mimi ta girgiza kanta kafin ta ce" Ruwan zamzam kaɗai a ka bata, ruwan Nono dai kaɗan ya fara zuwa kila sai da zuwa gobe haka." "To ba matsala zuwa goben? Ba za ta ji yunwa ba? Mimi na dariya ta ce"Yunwa kuma? Ba za ta ji ba kada ka damu, na sha tea,kuma Inna Zainaba ta damamin kuni na sha zuwa Gobe ruwan nonon zai zo in sha Allahu " Sai ya jinjina kansa alamun gamsuwa, sai kallon Mimi yake yi itama ta na kallonsa ta na nasa mrmishi, ita ta ɗauko yarinyar ta ɗora ta saman jikinsu dukkansu biyun a tare suka rike ta, sannan ɗayan hannun Mimi ta saka ta sakalo bayan Aji da shi, sun haɗe yarsu waje ɗaya sun rike. Ya riƙe hannun jaririyar ya haɗa da na Mimi ya damke kawai ya na mirmishi ya kasa mgana. "Ka ga Kyautar da ubangiji ya yi mana ko? Yau mun zamo iyaye ma'ana mun zamo uwa da uba daga yau, nauyi ya same mu mun zama iyaye akwai haƙƙin ƴarmu a kan mu na tarbiya da kula da ita." Ƙura ma jaririyar ido ya yi ta na ta barcinta sai kawai ya yi mirmishi kafin ya ce" Allah ya raya ki Inna ta, " Haka kawai ya faɗa ya na cigaba da kallonta In Mimi ta na mgana sai dai ya ɗaga kai ya kalleta ya yi mirmishi kamar yau sauran kalaman bakinsa nasa sun ɗauke. Ya dai kalleta cikin wani yanayi ya ce" Na gode sosai, na gode da kika yi dalilin jin wannan farinciki a matsayina na Uba na gode kwarai da kika kasance a cikin rayuwata Fatima kika kuma bani dukkan farincikin da gata a zamantakewar mu na aure. Na gode miki bisa yardan ki, haƙurin ki, Koƙarin ki a kaina Allah ya shirya mana Maryama ya ba mu ikon yi mata tarbiya ita da sauran ƴan'uwanta da suke tafe nan gaba." Kanta ta ɗora saman kafaɗansa lokaci ɗaya tana faɗin"Amin Amin Mera. Nima na gode da ka yi sillar zamowa ta Uwa. Allah ya bar mu tare Amin." Shima kansa ya jinginar saman kanta yana amsa mata da Amin Amin, sun ɗauki lokaci a haka sannan Mimi ta ɗago da kanta tana faɗin" Na manta ka ci abinci kuwa?. Sai ya girgiza mata kai da sauri ta karɓi Jaririyar daga hannunsa lokaci ɗaya tana faɗin"Yana can saman dinning." "Me kuk dafa ne? "Jallop rice ne Bintu ta dafa ɗazun nan kafin su tafi, sai na ce su saka maka Food Flaks kada ya yi sanyi kafin ka dawo" Kai ya jinjina kafin ya miƙe lokaci ɗaya yana faɗin"Kuma sai da kika yi mgana na tuna ina jin yunwa tun tea da na sha da safe ban kara cin wani abu ba." Mimi na mirmishi ta ce"Na sani, na ga duk ka fara rama ne." "Zo ki rakani mana, ni kaɗai za ki bari naci abincin? Ta na yar dariya ta ce"Jego fa na ke yi Mera, ba'a son na zauna wajen sanyi Inna ma ba za ta barni na fita falo na bar yarinyar nan ita kaɗai ba. Da sauri ya ce"Tare da ita za ki taho, ina cin abinci ina kallon ku ina jin ɗadi." Mirmishi ta yi masa kafin ta ce"Haihuwa fa na yi jego nake yi, in na fita Inna za ta min faɗa sai ka yi hakuri fa." Dakuna fuska ya yi kafin ya ce"To shi ne me? Jegon dai ba a haihu a taru a yi suna aci abinci ba ne? Ina ce shike nan an gama jegon.? Ta na dariya ta ce"A'a sai na yi kwana arba"in ina jego a na kula da ni tare da mai sunan Inna, akwai dokoki ciki har da zama a ɗaki mai ɗumi." Sai ta faɗa ya ji zafin ɗakin tunda ba fanka sannan an kashe Ac. Har gumi ya fara ma bai sani ba abun sai ya ba shi mamaki har sai da yace Topha, ya na koƙarin sake mgana ne Inna Zainaba ta yi sallama a Kofar ɗakin suka amsa mata sai ta shigo Kai tsaye ta kalli Aji ta ce"To Baban Maryam mu kwana lafiya ko? Kallonta ya yi cikin mamaki bai yi mgana ba,a gabansa ta kalli Mimi ta na faɗin"Za ki kara shiga ruwan ɗumi kafin ki kwanta.". Sai ta gyaɗa mata sai kuma ta ƙara cewa"Ga Kunin ki nan a fulas anjuma ki ƙara sha, Sannan wankan towel ɗin nan zuwa sati zai tsaya, ganye za'a samo min na daki jikin ki da shi." Mimi ta zaro Ido haka ma Aji da bai bar ɗakin ba. Inna Zainaba ko a jikinta ta shige toilet domin haɗa ma Mimi ruwan dumi ba ta ciki da iskacin yaran zamani na fahimci Mijin nan na Mimi ɗan gadara ne, ta gama masa kara in ta masa lamunin ganin matarsa da ƴarsa minti goma ne za ta riƙa shigowa tana ganin abin da ke faruwa. Aji ya kalli Mimi kafin ya samu damar magana ta masa alama da hannu alamun ya yi shuru sannan ta ce ya fita amman bai fita ba sai da ya dawo ya sumbaci yarsa da matarsa sannan ya fice yana faɗin"Sai da safe Ummu Maryam." Amman har ya gama cin abinci ya na mamaki shi fa ya ɗauka wani ɗaki mai kula da Mimi za ta kwana shi kuma ya kwana tare da matarsa amman kuma sai yake jin wani karatu na dabam, da ya koma ɗaki ya saka kayan barci ya kwanta ya kira Mu'azzam ya na masa ƙorafi Mu'azzam na danne dariyan sa ya ce"Ai hakuri za ka yi Yaya sai in Anty Mami ta yi kwana arba'in sannan komai zai dawo dai dai.". Aji ya ce" Haka ta ce, wai daman da gaske take yi? Ni kaɗai zan rika kwana kamar wani mara gata, addini ne ya ce a yi haka ne? Mu'azzam ya ce A'a nan take Aji ya yi tsaki kafin ya ce"To saboda wata al'ada sai a ware ni, ana gama taron suna zan ce kowa ya tafi a barni zan iya kula da matata da ƴa ta." Mu'azzam na ta danne dariyansa amman ya san tunda yayansa ya faɗa zai aikata shi ya sa da asuba yakira Inna da shawaran Hibba saboda ta ce gwara a kwabe sa tun yanzu kada ya aikata ya bar mutane da jin kunya. Inna na jin abin da Baban inna yake shirin aikatawa ta yi yar dariya kafin ta ce"Bar ni da shi, shi ya sa ya ce ba za ta je gida ba saboda ya yi wannan diɓar albarkar ko? To zan ce bayan suna ta koma gaban Hajiya sai naga karyan tsiya fitinannen yaro kawai sai kace a kansa a ka fara haihuwa." Mu'azzam na jin haka da sauri ya ce"Kada ki yi haka Inna ki dai yi masa mganar don Allah kada ya yi wata mgana ya bar ƙanwar mamanta da kika ce tana wajen ta ta zauna ta kula da ita kin ji ko Inna? In ta koma gidan Hajiya an ƙwari yayana tunda shi baya ra'ayin ta koma can in kika matsa masa kamar an shiga haƙƙin sa ne." Da waɗanan kalaman ya lallashi Inna Meri ta bar mganar cewa bayan suna Binta ta koma gida, amman da safiyar ta je can gidan duba Binta da takwaranta ta iske tuni sun sha wakan har sun karya ta samu Mimi na cin ferfesun kayan ciki ta iske su Mama a gidan su suka taho mata da shi. Ta iske suna ta maganar yau da safe an samu ruwan nono har yarinyar ta samu ta sha, amman sai barci ta ke yi Mama ta ce" Daga gani rigiman dare za ta riƙa yi." Inna Meri ta ce"Shima ai haka ya yi, na fi wata takwas da haihuwa Baban Inna bai daina kukan dare ba." Ana ta dai raha ana dariya. Baya gidan tun safe ya fita zuwa Camp, dawowarsa kenan ya shigo yana gaishesu sai ya ga Inna bai ma san ta zo ba. Daga nesa ya kalli Mimi ta kalleshi suka yi ma juna mirmishi, Sai a ka bar shi da tambayan Inna Zainaba yana faɗin" Ba wata matsala ko inna? Ko akwai wani abu da kuke bukata? Cikin mirmishi ta ce"Ba ma bukatar komai, ai komai ai akwai shi sai godiya Allah ya ƙara buɗi na alheri." Ya amsa da Amin kansa a kasa sannan ya miƙe ya fita sai Inna Zainaba ta ce Mimi ta ɗauki yarinya ta je su gaisa jikinta na rawa ta mike ta sunkunci yar amman sai da Inna Zainaba ta saka ta ta saka mayafi da takalmi daman kafar nan da safa tun da ta haihu ko'ina na jikinta ya na rufe Inna Zainaba jegon mutanen da take yi mata.. Aji har ya fara ƙorafin mutum da matarsa an barshi da kallo daga nesa sai ga Mimi farinciki yasa sai da ya rumgumeta yana sauke ajiyar zuciya. Ba ta daɗe ba tunda tasan halin Inna Zainaba amman sai da ta ɗauko masa abun ƙaryawansa ta jera mai sanan cafet a cikin Bedroom sannan ta koma ɗaki har magiya ya yi mata ta tsaya ya gama ƙaryawa tace a'a in ta daɗe za ta yi mata faɗa, daman bayan fitan ta sai da Mama ta ce" Yaran zamani jikinsu na rawa za'a je wajen miji." Inna Zainaba ta ce"Su ko tausayin kansu ba sa ji." Inna na gefe ba ta ce komai ba, ta san halin Baban Inna bai son kara ba. Sai da ya yi wanka ya sauya kaya sannan yace Inna Meri ta fito ya kaita gida, Itama daman tana son mgana da shi, ta yi musu sallama akan anjuma Walida za ta kawo garin kuni, a hanya ne ta yi masa mganar ya rika kawaici sannan kada ta ji ya yi mganar bayan suna a watse in an barshi da matar da yarinyar zai iya kula da su ne? Ya na jin haka yasan Mu'azzam ne ya kai mgana wajen Inna bai ce komai ba, illah tura baki kafin ya ce" To Inna mutun da matarsa sai a hana shi ganinta." Inna ta yi masa wani kallo kafin ta ce" Ka dai ji abin da na gaya maka, in ka ce ba za ka yi kawaici ba wlh zan ce a maida Binta gaban Hajiya sai bayan wata biyu sai ta dawo " Yana jin haka da sauri yavce"Allah ya baki hakuri Inna, In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba" Amma bayan ya sauke Inna, bai shigan ba ya juya a hanya ya kira Mu'azzam yana ce masa"Kai ba'a sirri da kai ko? Ban ƙara gaya maka wata mgana." Tunda yaji haka ya san kan mganar yana koƙarin mgana yayan nashi ya katse kiran sannan ya kira shi daga baya bai ɗaga ba sai kawai ya ƙyaleshi za su daidaita daga baya. A cikin satin da Mimi ta haihu kafin suna ko da yaushe gida cike da baƙi. Ba yan'uwanta ba na megidan ba, Khadi tun ana saura kwana biyu suna ta iso Madiha ma ta ce sai ranar suna za ta zo har da ƴan'uwan Mommy daga kano. Jawahir ma ana gobe suna ta iso ita da yara Rukky dai tana lagos ba za ta samu zuwa ba, amman har abokan aikinta mata sun zo mata barka sannan za su zo suna, mazan ma har gida suka zo su ka yi mata barka. Daman hutun haihuwanta sai bayan ta haihu zai fara aiki wattani uku kafin ta koma, kullum sai Magajiya da Gaje sun leka in da wani aiki su kama sannan Yaya Amina da Yaya Halima suna zuwa Bintu da ma Maeesha gwarama su Yaya Junmai suna fashin rana amman suma kan sun yi kokari Inna Zainaba sai yabawa take yi, ga uban gayyar kafin ma a bukace wani abun ya kawo shi. Inna Zainaaba tana waya da ƴar'uwata lokacin da Mommy ta ce"Ina fatan ba wata matsala ko? Inna Zainaba ta ce"Wlh babu Murja, Mimi ta yi dacen miji da danginsa masu karamci da mutunci komai da kika sani wlh sai dai ma mu yi kyautarsa. Mimi da Maryama ba abunda suka nema suka rasa waɗanan mutanen akwai karamci da kirki " Mommy ta ji daɗi kwarai hakama khadi ta dinga faɗa, domin kayan Mimi da na jaririya duk safe Magajiya da Bintu ke zuwa su wanke sannan su dafa ruwan zafi su yi ma jaririyar wanka Mimi kuma Inna Zainaba ta yi mata. Bintu kuma da Maeesha suke gyara gidan su turarashi da kamshi.Su Yaya Amina kuma su zo su yi girkin rana da dare su Mama suna zaune suna hira ba abin da suke yi, duka yayyen Angon karni ne da ƙañensa ke yin komai yaddiko ma da ta zo sai da ta yaba musu, sannan Inna ma ta kan leko da safe, garin kuni haka ta yo shi da yawa ana damama Mimi har ruwan nono ga shi ya samu sosai. Hajiya ma ta na gida labari ya zo mata Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Meri basakkawata ce mai kirki, sanna yayanta sun samu tarbiya daga bangarenta, babu nadama ga haɗa zuru'a da ita." duk da sunan ya zo ranar farkon azumi amman ba abin da aka fasa, komai an yi waina ce daman su Mimi suka yi da Sinasir aikatau a ka kai. Sai raguna biyu ɗaya na ta ɗaya kuma Aji ya raba abun ya ce a bama ƴan'uwansa, ya ba su komai na su a gidan Inna danginsa za su yi nasu taron tita kuma Mimi da na ta dangin a gidan ta. Sannan sun haɗa ma Mimi kayan Atamfofi sama da guda biyar ga kayan Baby, Hibba ma ana gobe suna ta zo ita da Mu'azzam da Atamofi guda biyu sai na Bby sai 30k daga Mu'azzam. Ranar azumin farko a ka yi shagalin suna duk da azumi ne Mimi ta ga taron mutane kaf yan'uwanta sun zo har da Madiha gida cike kuma isu isu tunda su Bintu suna can gidan Inna suna na su taron. Mimi ta sha kunshi da kitso. Sannan ta shiga ta fita ita da Maryama wacce Mimi ta ce za su riƙa ma lakabi da Ummi tunda yar wajen Mu'azzam Ammi suke kiranta. Sannan har Makeup an yi mata sannan sun sha hotuna, an yi tsire ga wanda ba za su tsaya a sha ruwa ba, a wata yar jeka sai a saka sinasir ko waina sai naman kaza ko na rago sai a saka maka cake ko samosa sai lemu da ruwa, duk sun yi zobo mai rai da lafiya da kunin aya amman zobon wannan na uban gayya ne za su yi walima da daddare a can Camp ɗin su. Sinasir ɗin da waina Mimi ta ɗibar masa kula ɗaya sai fride rice da yasa Binta da su Yaya Amina za su yi masa, sai soyayyen Naman kaza pepe sai kayan Snaak ɗin da Mimi ta ba da a ka yi gabaɗaya bayan an kawo ta diɓar masa tsire kuma daman na Aji ne sai aka raba uku ɗaya Mimi da danginta ɗaya kuma na su Inna da yan'uwansa ɗayan kuma nashi. Matan su Nasir duk suna gidan Mimi har da matar Ahmad.Tun da ya ce shi zai koma amman ita sai bayan salla anan za ta yi azumi sannan cikinsu ba wacce ta zo hannu rabbana. Daddy kuma turmi biyar ya yi mata da kudi 100k Ƴaƴan yaddiko ma haka kowace da zaninta har Rukky da Jaheed sun tura mata kuɗi sannan ƴan ma'aiikatansu suma ba su zo hannun rabbana ba. sun haɗa mata kudi sun siya mata zannuwa da kayan jarirai tunda lokacin bikinta ya zo a kurewar lokaci ba su samu sun yi mata ba. A ji dai suna gidan Makama gabaɗayansu ya sha farar shadda tana kyalli.Nasir ya so har wasa a buga Aji ya ce a'a Walima dai ya shirya domin a taya shi murnan samun ƙaruwa. Bayan an sha ruwa Walida da Mariya suka kawo musu abun buɗe baki anan gidan Makama suka ci suka sha.Sallar mangriba ma sai Ahmad ne ya yi musu limanci, suma ɗin duk sun haɗa masa kudi ya ce ba zai amsa ba su kace ya raina ne sai ya karɓa ya saka albarka dagan gida ya koma saboda ya yi wanka walimar karfe takwas na dare abunci kuma da ababen shan su Mu'azzam za su ɗauka zuwa can Camp ɗin su.Gayyar da ya yi kaɗan ne daga yan Tream ɗin su sai abokan shi sai kuma yan nasaran Team Tudun Wada team da sauran Clubs ɗin ƙwallon kafa na Gombe manyan ciki. Sai Coach din su na gombe United da sauran shugabbanin ƙananun kungiyoyinsu. Ko da ya koma gida, ba'a wani ragu ba yawanci duk nan za su kwana sai illa yan Kano ne suka koma gidan Hajiya. Yana shigowa falon su khadi ne da su Bibi sai su Yayan Yaddiko. Khadi tana ganinshi ta fara sakin guɗa tana masa kirarin Angon karni baban Maryama mjin Fatima. Karon farko da ta ga dariyansa hayaniyarsa ya fito da sauran da ke ciki, ana cikin haka sai ga su Yaya Amina da kaya niki niki na suna shi yas a ya sulala zuwa ɗakinsa ya ɗaga waya ya kira Mimi sai gata, ta zo ita da Ummi sun sha kwalliya ya kama su ya rumgume sannan ya sake ta ya ce zai shiga wanka ta zaɓa masa kayan da zai saka kafin ya fito ta fito masa har da takalmi shadda mai ruwan sararin samaniya har da babban riga ya fara korafin babban rigan tana damin shi ta shagwaɓe mass lokaci ɗaya tana faɗin" Don Allah ka saka, kai fa yanzu ka girma sunan ka Baban Maryam." Da kalaman ta samu ya saka ta saka masa hula da agogo baƙaƙe ta fesa masa turare, Ya yi kyau har sai da ta ɗauki wayarsa ta yi musu hoto.Nasir sai faman kiran shi yake yi ya ce su na can ga su ma za su yi sallar sai yace shi zai tsaya a hanya ya yi sallah sannan ya ƙariso. Zuwan su Yaya Amina ya sa har ya fice ba ba a lura ba ana kallon kaya ana saka albarka, yana hanya Daddy ya kirashi ya na masa tsiyan haka ake yi shike nan tunda yana uba baza'a gayyace shi waliman ba ne? Sai Aji ya ji kunya kwarai ya ba shi hakuri da cewa bai san ya na son zuwa ba. Nan Daddy ya ce ya bashi address in ya tashi daga in da ya je zai biyo ko da bai daɗe ba nan da nan ya tura masa adireshin Camp ɗin su dake cikin gari. Ko da ya isa hall ɗin cikin Camp ɗin su da suka yin meeting ko wani taro ya cika da jama'a. Yana zuwa a ka fara gaisawa da shi ana masa fatan alheri ji kawai kake yi ana faɗin" Congratulation Captain Allah ya raya mana mai sunan mama Maryama." Walima ce daman an ci an sha an yi badali da nama da Kaji, an ci tsire an sha lemuka an sha zoɓo da kunin Aya har da masu guzuru su Musa Zinder sun fi kowa murna da wannan walima domin sun ci sun sha sai hqmdala, ana gabda tashi sai ga Daddy ya zo ya dai gaggaisa da mutane bai tsaya ba sai a mota aka saka masa tsiren da Sank ɗin sa zuwa goma na dare kowa ya watse bayan an gama yi ma Maryama(Ummi) addu'an rayuwa cikin aminci, bayan an gama taron yana wajen tawagan ƴan Team ɗin shi suka same shi da roƙonsu suna son zuwa gidanshi su ga Maryama(ummi) sai ya ce su bari zuwa jibi sai mota ta kwashe ta kaisu su ganta Coach ma har gida ya je ya yi barka ya ba ma Mimi wani abu ya ce ta siya ma Ummi abun wasa. Ranar ba'a gida ya kwana ba shi da Mu'azzam suka kama hotel, a daran ne Aji ya ce dole suna bukatar wani gida in dan irin haka ya faru su samu wajen sauka. Zuwa washegari taron suna ya tashi saboda azumi daga Khadi har Madiha a ranar suka koma Jawahir daman tun 12 yan kano suka mika hanya. Gida daga Mimi sai Inna Zainaba, naman suna kuma daman yan kano kawai a ka dibarmawa da yaji sai gidan Daddy sai Hajiya su khadi duk ba su tafi da shi ba gwarama Jawahir an ce ta kai ma Dr, Hibba da Mu'azzam kuma ba su koma ba sai washegari duka duka kwanan su huɗu ne saboda azumi a ranar kuma doguwar motar Team Gombe United ta kwaso su Zinder gabaɗaya dai yan Team din zuwa gidan Aji karo na farko suka yi ma Mimi barka. Kowanne sanye da kayan suna Bluee ɗin riga da wando, daga ma morning Training suke Aji ya ce a kawo su. Ummi ta sha ɗauka Kb har kallon Aji ya yi yana faɗin"Captain ina kamu in ta girma." Suka fashe masa da dariya Aji ya yi mirmishi bai yi mgana ba ,Inna zainaba da suka ba ta sha'awa ta ce" Haba ina za ka jira ta? Kai da ko yanzu ka isa aure." Da sauri Kb ya ce"Ko ta uku ko ta huɗu don Allah Captain." Ya fada har yana magiya harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Kun ganta ko? Maza back to camp now." A tare suka amsa da" Yes Captain." Ba Inna Zainaba ba har Mimi sun matukar burgeta, ta ji da a ce namiji ta haifa ba abin da zai hana bai gaje ubansa ba. Mimi ta cigaba da jegonta cikin gata ko sati uku ba ta yi ba ɗinkinta ya warke tunda ta na samun kulawa ta koma asibiti an ce komai lafiya, Inna Zainaba ne ke kula da ita sai Hajiya da kan leko itama hakama Inna, an yi salla karama duk tana cikin Jego amman fa gaskyan Aji ne jegon nan ya yi mata matukar kyau kamar ba ita ba, Sannan Ummi ta yi wani irin kiba. Daman Aji bai yarda an yi wannan exculation ɗin nan ba ruwnta a ke ba ta ya ce ba zai iya daukan hakki ba, bayan sallah da wasu kwanaki Mimi ta yi arba'in sai kuma ta fara gyara kanta daman kuma Inna Zainaba ta ma ta kokarin shiga cikin ruwan bagaruwa sannan Yadikko ta aiko mata da Gumba ta na sha da Madara ita kuma sai ta siya haɗin kazan Uwargida na Surayya Dee, Bojuwa saboda ita dai Mimi ta amince da kuma yarda da haɗin kazan Surayya Dee saboda ta na daɗewa a jikin ta kafin ta gama aiki sannan uban gayyar yana ruɗewa in ta samu gyara daga surayya dee bojuwa mai kayan gyara.+234 803 277 3332 kuma har ta aiko mata da shi har ta fara amfani da shi. Inna Zainaba kuma ta fara shirin komawa Kano, ta sha tara arziki kuɗi kawai 30k Aji ya ba ta bayan zannuwan da Mimi ta haɗa mata Inna ma da omonta da sabulanta da yaji da ta saka a ka daka mata.Kwanansu Hamsn Inna Zainaba ta koma kano da sha tara na arziƙi. Mimi ba ta je ko'ina ba bayan ta gama jego, Sai da Aji ya gama famshe kwanakin da ya yi kewarta ta ma kusa arba'in biyu sannan ya bar ta taje gidan Hajiya ta yini sai dare yaje ya dawo da ita gida.bWashegari gidan Daddy ta yini, ba ta kara fita ba sai bayan kwana biyu ta je gidan Yaddiko daga nan ta lelleka gidan yayanta dake kusa. Washegari kuma gidan Inna ta yi yinin ta, Inna ko Ummi na bayanta tun da suka zo, sai dare ya zo su ka koma gida daga nan jefi jefi tanq fita ta je can gidan wajen Magajiya daga can ta leƙa su Gaje Yaya Jummai da Yaya Zuwaira sai gidan natar Auwalu da gidan bintu tun da Aji ya ce ta yi su a rana ɗaya ba zai iya da yau a fita gobe ma a fita da sunan yawon arba'in ba har gidan Mallam Hashimu inna ta saka sun shiga. Gidajen su Yaya Amina ba sai daga baya ya kaita ta gaishe su. Ta rasa wannan kulle na Aji sai ya ce shi dai ba ya so ta fita daga gidan, abunda ya sa ba ta damu ba, ba iya danginta ba ne har da na shi Abuja kaɗai yace za su je tare su kai ma Mommy Ummi ta ganta, amman sai Inna sun ɗaga saudiya tunda an biya mata da wuri jirginsu zai ɗaga a farko farko. Amman sai kafin nan shirye shiryen tafiyar walida makaranta a ke yi. Ta je ma kanon ta dawo ta yi Rigistration ta dawo ta haɗa kayanta, Aji ya yi mata provition da sauran bukatu ya kara mata hijabai da takalma Mimi kuna ta siya mata dogayen riguna da mayafi kowa dai ya kawo wani abu ya bata daɗin abun ma a gida za ta zauna Ta sha dai faɗa da nasihan ta kula da kanta Allah ya masa ga Mu'azzam ga Hibba, Ita da dawowa sai bikin mariya Tafiyar Inna ma saudiya tana kano ba za ta ga tafiyar ta ba. Inna an daga kasa mai tsarki. Har Mu'azzam sai da ya zo suka yi sallama gabaɗaya ya'yanta suka rakata sansanin Alhazai na gombe har da su Magajiya da Gaje su Baba Ɗanjuma ana gaba gaba, gida kuma Saffiya ta zo daga Tureta za ta zauna har sai Inna ta dawo kada gidan ya zauna ba kowa. Aji ya sauya ma Inna waya da za ta tafi saboda a rika jinta an yi waya da ita bayan tafiyarta da kwana hudu suna madina ana can ana ta ibada kuma Inna duk ta haɗu da mutanen kwarai ƴan Jihar gombe da suke tare a can Madina sai abun ya zo da sauƙi, salla babba ke kan gaba sannan ga bikin Mariya. Shi ya sa tafiyarta Abuja ya kasance ita kaɗai ta samu tafiya ta je ta kai ma Mommy Ummi ta ganta can a ka yi ta koke koken tunawa da Abi kwananta huɗu Aji ya kirata ya ce shima ga shi zai zo Abuja ya samu waya daga shugaban kungiyar kwallon kafa na kasa gabaɗaya wato Super Eaglees Yusuf Tijjani yana nemansa da gaggawa. Da a ranar za ta dawo sai ya ce ta jira shi ya zo garin amman sai yamma ya ƙariso gidan suka gaisa da Mommy nan ya sauka tunda akwai bangare bangare ya yi wanka ya ci abinci har washegari suka hau jirgi suka koma gida Aji bai gayamata dalilin shi na zuwa Abuja kuma ita ba ta tambaya ba sanin halinshi amman koma menene ya damu kwarai ta na ganinshi yana ta shiga tunani. Sai a ranta ta yi masa fatan koma Menene Allah yasa ya zo masa da sauƙi. Bsai ana babbar sallah saura kwana biyar da ya sake komawa Abuja ne ya dawo mata da takardan ya zama cikakken ɗan kungiyar kwallon kafa ta kasa gabaɗaya. Ba kuma kokarin kowa ba ne sai na Coach ɗin su, Wanda har gida shi da Mimi suka je masa Godiya yace ba komai shi Mansor kamar ɗa ya daukesa zai yi komai domin cigabansa, Ya je har gida ya sanar ma da Baba Ɗanjuma shina tare da su Baba Ɗanlami sun je yi ma Coach godiya duk da Aji ya iya buga wasa amman lamarin sai da hanya, Sai Agent ya cinna kai kuma ba kyauta sai ka biya shi, ya gaya Mu'azzam shi kuma ya gaya ma su Nasir sai kiran shi a ke yi ana mishi murna duk da ya san ya samu cigaba amman har ga Allah ya na kewar Team dinsa na Gombe suma da suka ji labari har da masu kuka karahenta dai Pele ne zai samu horo zai maye kujeran Captain ɗin wanda Bayan sallah zai koma Abuja tunda can Camp ɗin su na kasa gabaɗaya yake. Inna na Saudiya ya kirata ya faɗa mata ta yi addu'a ta ce tunda ta sauka garin ma'aiki take ma ƴa'yanta da zuru'anta addu'an samun albarka, da kuma yi ma kasarta da waɗanda suka rasu addu'a. An fara shirin bikin Mariya tunda bayan sallah ne da wata ɗaya sun raba abun, Mu'azzam zai ji da kayan wuta, tibi da Fridge gas, da su cafet shi kuma Aji zai yi abunda uba ke yi gado da kujeru Matan kuma sun haɗa kansu za su yi kitchen, Mimi kuma tace za ta yi labulayan da zannuwan gado, tunda ga ta ga FHB CLOTHING Phone no 08034109622 Wtsapp no.08080266674, domin zannuwan gadon su masu kyau ne da inganci. Auwalu kuma ya ce zai ji da kayan gara da abunda za'a ci da biki. Saddiqu kuma da ke da ƙaramin karfi ya ce zai taimaka da abin da ya samu, Magajiya sai kuka ganin Yayan dai Inna su ne za su rufa mata asiri a bikin yarta, kuma kowa ya fara ba da kuɗi domin bangaren da ya ɗauka bayan an sallaci babbar salla a ka fara shirin biki tuni Aji ya ba da rabin kuɗin aikin gado da kujeru bayan an gama zai cika kuɗi sannan shi zai yi har kafita kowa dai ya na ta kokari kan bangaren shi. Bayan sallah da kwana goma ya je Abuja, Kuma daman ya yi bankwana da Gombe United komai na shi ya kwaso zuwa gida, Sai da ya yi kwallah domin an ce sabo shi a ke yi ma kuka ya shaku da yaran nan sosai amman duk da haka ba'a rabu ba. A can Abuja Camp ɗin su na Super Eagless ya samu wajen zama tunda nan Horo ne zai samu na tsawon wattani uku, ya kuma ga bambamci domin akwai ƙwararru sosai a buga wasa duk da shima ya yarda da ƙwarewansa.Sai dai su yi waya da Mimi duk son shi da kada ya yi nesa da gida Allah bai so ba ya na ji ya na gani ya koma Abuja da zama. Ba ya fita ko'ina ko da yaushe yana cikin Camp, sai dai ya yi waya da ƴan'uwa. Mimi ko ta haddace da lukatan da ya ke free suna makale da waya da Ummi ta ƙara wayau, ta kuma zama burtuka. Sannan ta koma aiki tunda itama zaman shurun ya yi mata yawa. Su Inna ne wajen jirgi na biyu a dawowa tunda daman suna cikin yan farko farko a masu tarbanta babu Baban Inna ba Mu'azzam kowanne aiki ya yi masa yawa sai dai sauran yayan nata gida ya cika da masu sannu da zuwa Inna ta sauya kamar ba ita ba kai Allah mu ma ya kai mu Saudiya domin Alfarman ma'aiki (SAW) Amin. Sai da suka kira wayarta suka mata barka da dawowa, Inna Meri ta yi mamakin grman Ummi saboda ta zama kamar yar turawa. Safiya na nan ba ta koma ba sai bayan bikin Mariya, a satin bikin kayan Inna suka iso na Tsaraba ba kuma wanda ba ta ma tsaraba ba, makota kuma sun sha tsaraban dabino da ruwan zamzam karshe ita ta kare ba ta samu komai ba. Baba Danjuma jallabiya da sallaya hakama su Baba Danlami sallaya matan su kuma ɗankwali, Magajiya ta samu doguwar riga Mariya ma haka, Walida dai ta sha tsarabarsa su Bintu ma haka Mimi kuma an siya mata sarka da kuma kayan wasa na Ummi sannan ta siya zannuwan gado ta ce na Mariya ne. Bintu dai har da kukan ta Inna ba ta siyo mata hakurin makka ta saka ba,Inna ta ce a raba ta da shegenka ita baitar ubangiji ta je, da tsufanta ina ruwanta da wani haƙorin makka. ƴaayansu dai ai sun sha taraba suma sai son barka. Ta ijiyeme Baban Inna da Mu'azzam Jallabiya da darduna sai ruwan zamzam da dabino.Sannan ta ji daɗin yadda suka haɗa kai aka rufa asiri tunda Magajiya da bakinta take faɗa mata an gama gadaje da kujeru. Har katifa Aji ya turo kuɗi an siya Mu'azzam ya siya kayan wuta daga can za su zo da shi su matan kuma sun ta siya kayan kitchen. Kafin dai zuwa ranar jere komai ya kamallah har gara Baba Ɗanjuma ya rika saka mausu albarka gabaɗaya. Biki saura kwana huɗu Mu'azzam da Hibba da Walida suka iso, daman tuni dangin Magajiya sun fara cika gida Mariya kuma ta na gidan Bintu ana ta mata dilka da gyaran jiki Yaya Amina ba ta yi mata wasa da kayan gyara ba, Mimi ma ta siya mata kayan gyara wajen Surayya Dee ta siya mata kazar haɗin Amarya da mganin sanyin sadidan na Bojuwa. Ita fa Mimi saboda aminta da kayan Surayya dee, duk in da ta ga ana neman kayan gyara sai ta yi ma mutane maganar kayanta, domin suna da inganci ƙwarai ta gwada kuma ta na ganin nasibin kayan gyara daga surayya dee bojuwa.+234 803 277 3332, ke ma ki gwada domin dacewa da ingamcin da Mimin Aji ta dace dashi, sannan mijin ki ya zamo sahu maza masu rabo irin Mansoor Aji. Maeesha ma ta kawo mata gumba mai kyau ta na sha da madara. Mariya na ta nurna ganin Walida duk da tana da ƙawaye amman ai Walida ta dabam ce kuma ƴar'uwanta ce. An je jere ana saura biyu daurin aure angon Mariya ya yi gidansa ɗan daidai an danka mata shi da kaya ko wata yar gatan sai haka gado biyu ga tibinta ga firiza ga gas ga Tv stand ga center table ga cafet ga labulayan masu kyau da zannuwan gado kitchen ma koma ya ji ga kayan garanta an yi daidai gwargwardo har dake dake ma yan'uwan Magajiya sun yo sannan su Gaje ma sun ƙara mata. Inna ce uwar Amarya da su Gaje da su ake shawara. Aji sai ana gobe ɗaurin aure ya dawo daga Abuja ya yi kiba ya ƙara haske. Murnansa ya ga Inna da matarsa da Ummi ai ko shima ya yi mamakin girman Ummi yana dariya ya ce yar lukuta. Ranar a gida Mimi ta kwana ana sabunta amarci sai can rana ya kawota gidan wanzamai inda ake sha'anin bikin,Inna ta bashi tsarabanta ya karɓa da godiya a ranar ma da yamma jallabiyan ya saka haka kuma ya ga Mu'azzam ma ya saka naahi, sai suka kalli juna suna mirmishi suma suna ta shiryen shiryen wajen daurin aure a masallacim kusa da su ne amman sun saka an share kofar gida an gyara shi saboda mutane. Har saddiqu da shi ake komai ya ga ba sarki sai Allah ya saduda. Yaya Mansoor sama Yaya Mu'azzam domin ya fahinci in ya yi tawaye ba riba hakama Magajiya ta faɗa masa. Gida cike da baki ana ta hada hada Matan sun yi ankon Atamfa na biki,sannan ko walima ba'a yi ba sai ranar lahadi a gidan Amarya. Mariya a gidan Bintu za su yi zaman su tunda kusa ne sai ya kasance su Mimi duk suna can har da su Nafisa da Bibi matar Ahmad dai sun koma kaduna. Har da Yan'uwansu Hibba duka da su ake sha'anin ƙannen mahaifansu Yaya Amina kuwa, daman duk wani sha'ani da su keyin shi kuma duk saboda Inna Meri ne a ka zo a ka yi ma Magajiya karan. Ana jibi bikin nan suka kawo lefe akwati shidda kuma da kayansu ma sha Allah daidai karfin talaka mai nema. Ranar asabar aka tashi da shagalin biki sha daya na safe aka ɗaura auren Mariya da angon ta Aminu, Baba Ɗanlami me waliyin Amarya anan wajen ya ce ya wakilta Aji ya yi ma Mariya wallici shi ya ba da auranta ga waliyan Aliyu sannan bayan ɗaurin auran ana rawan jikin gaisawa da shi wanda bai ma san shi ba an gaya masa sunan shi. Ango da tawagansa sun sha fararen kaya suma su Mu'azzan kowa da kalan kayanshi amman sun saka babban riga har da Saddiqu da ya saka ta bikin shi, Baba ma sabuwa Mu'azzam ya ɗinka masa da Sabon takalmi a cikin gida kuwa ana ta hada hada an dafa ahinkafa da alala sannan an yi waina Amarya da ƙaawayenta sun yi firaidi rice din shinkafa da Alala sai nama da Mimi ta bada kuɗi aka siya kilo uku saboda baki Walida yan jami'an an sha kwallya tunda sun yi makeup, nan aka bar wasu ƙawayen su Mimi suka tafi da Amarya can gidan ana ta hotuna duk rashin son hoton Aji su Yaya Amina suka rike shi sai da ya shiga amman ya na rike da Ummi a kafaɗansa ɗayan hannun kuma ya na rike da Junior da damam ɗan gidanshi ne. Ammi dai tana wajen uwarta Mu'azzam dai daman ba shi da wani nane ma yara. Gabaɗaya ahalin gidan Wanzamai a ka haɗu a ka yi family picture su Gaje da Harira da yayansu maza da mata da su Baba Ɗanlami Inna meri da Magajiya da Baba Danjuma da su Aji da yayansu da matansu gabaɗaya a ka dauki joton kowa ya gansu sai ya ji sun ba shi sha'awa babu abunda yafi haɗin kai daɗi. Bayan La'asar Mansoor da Auwalu suka dauki amarya zuwa ɗakinta daga umarmin Baba Ɗanjuma, tare da Inna su ka je da wata ƙanwar Magajiya sauran daga baya su ka zo bayan ango ya kawo motoci, Mariya na ta kuka domin yayyenta sun mata faɗa ta zauna lafiya kowaani aure da ta gani yanzu na da shi kalubalen gwara ma ta zauna lafiya, Walida ne da sauran ƙawaye suka kwana a gidan sauran kuma suka koma gidajemsu suka kwana su Hibba dai a gidan Inna daman suke kwana Mimi kuma Aji ba barinta daman zai yi ba. Sai washegari suka koma kai kayan da ake ba ma dangin ango bayan sun ɗauki Mariya zuwa gidan iyayen mijin, su Mimi da su Yaya Amina sai Inna da su Gaje,an gama komai cikin girma da arziki sun mika amanarta ga dangin mijinta suka baro ta acan tana kuka. Wasu suka sauka gidan Magajiya wasu kuma gidan Inna irin su Mimi da sai dare Mansoor ya zo suka koma gida. Wasahegari litini Mimi ta tafi aiki shi kuma sai ya leka Camp ɗin su na Gombe United su ka gaggaisa da su Kb suna ta cewa sun yi kewarsa ya ga pele sosai daman yake da kokari shima auransa ya kusa sun zauna da Caach suna ta hira kan sabon horon da yake samu anan Abuja sai can rana ya baro wajen ya isa ma'aikatansu Mimi ya ɗaukota suka dawo gida. Ranar talata ya bi jirgi ya koma Abuja Mu'azzam kuma washegari shima suka koma kano, amman ba su tafi sai da suka sallami Safiya da kuɗin mota za ta koma An yi cincin da dublan na Amarya an yi kuma na rabo an dibar ma su Mu'azzam sai Mansoor da Mimi ta haɗa masa cikin kayan snkas din ta yi masa , har da dambun kaza da miya ta yi masa saboda ya gaya mata wancan tafiyan ba karamin wahala ya yi ba, shiyasa wannan karon ta shirya ma tafiyar nashi sannan sun yi mgana da Mommy ta ce za tariƙa ba ma direba abinci da lambar wayarsa sai ya riƙa kai masa can Camp ɗin su. Amman kuma ta san halin Aji ba lalle ya amince ba amman duk da haka sai ta ce za ta gaya masa, ta na ko yi masa mgana ya ce a'a ba ya son ya saka Mommy wahala da ɗawaniya. *Janafty* [9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3020* Duk da yace ba ya son saka Mommy ɗawaniya amman duk weekend Asma'u kan yi abinci a saka direba ya kai masa har Camp ɗin su fitowa kawai ya ke yi ya karɓa. Daman abinci ya fi ba shi wahala saboda Camp ɗin Abuja ba ɗaya yake da Camp ɗinsu na Gombe karami ba wannan babban waje ne da ya tattara manyan yan wasan kwallo na ƙasa gabaɗaya duk wanda ka gani a cikin wannan kungiyar fitattace ne sannan ya kwarewarsa ce ta kaisa. Shi ya sa ko yanayin traning ɗin su ba ɗaya ba ne, duk da akwai manyan ƴan wasa da ƙasa ta jima da sheda fuskarsa dama duniya gabaɗaya wasu yanzu suke cin zarafin su wasu kuma suna cin zarafin nasu har kuma wa'adin da za su yi ritaya ya cimma musu shi ya sa a ka ɗauki ire iren su Aji masu ƙokari domin maye gurbin su. A baya ba shi da burin zama a wani gari face jiharsa saboda Inna da kuma yanzu ya zama uba kuma mai mata, ko a yanzu da ya samu sauyin wajen aiki bai ji ko a ranshi wata rana zamansu gabaɗaya zai dawo Abuja ba, ya saka a ranshi duk matakin da zai taka a rayuwa jihar Gomb uwace a gare shi ba da Mama. Ya kan yi sama da wata a Abuja wani lokacin ma sai ya raba wani watan ya ke zuwa Gombe ya ga Mimi da Ummi da Inna tare da sauran ƴan'uwansa sannan in ya dawo in ya daɗe ne kwana huɗu zai koma Shi ya sa sai zaman kaɗaicin ya yi ma Mimi yawa sai ta ke roƙon shi bayan ta tashi daga wajen aiki ko ta biya gidan Hajiya ko wajen Inna to shima ɗin ba kullum ba ranar da bai ga dama ba sai ya ce ta koma gidanta ta zauna in ta ce ba kowa sai yace ga Ummi nan, kada ta damu ita uwace yanzu kuma yanzu suka fara gina rayuwarsu a kwai lukatan da za su yi nesa da juna ba domin suna so ba, sai domin neman halas da kuma inganta zamantakewarsu ta nan gaba, ta maaa uzuri sanin halin shi ya na da Kulafacin gida amman tunda ta ga Aji ya hakura da zaman Gombe ya koma Abuja ta san ya ƙarbi canji da Ubangiji ya yi masa da hannaye bibbiyu. Wani lokacin sai su yini ba su yi mgana ba, ya fi kiranta da asuba ko can wajen sha biyun dare lukatan da ya ke samun sukuni kenan itama sanin ba shi da lokaci ba ta takura masa da kira sai in har tana da mgana da shi mai muhimmanci da ta shafeta ko ta shafi Ummi ko inna, sai ta kira shi in ya zo ya ga kiranta zai kirata daga baya. Hakan ce ta faru yau ma tunda tun kwanaki a wajen aiki sun yi mgana da Manaja kan wani sabon shiri da Ma'aikatansu za ta ƙirkira shirin kuma na mata ne, mai suna matsalolin mu Ayau shirin da zai riƙa gayyato mata dabam dabam domin jin irin matsaloli da challages ɗin da suka fuskanta a rayuwa kuma ana so ita ta kasance presenter ta shirin gabaɗaya ba, ba ta amsa ba sanin halin mijinta ta ce sai sun yi mgana da shi, to ba ta samu sun yi mgana ba saboda karancin lokaci, yau ɗin ma ba su yi mgana a daran ba ta kira shi wayarsa a kashe sai da Asuba ya kirata ya ce sun shiga Meeting ne shi ya sa ya kashe wayarsa sannan ba gama da wuri ba shiyasa bai kirata ba a tunaninshi ta yi barci kada ya tashe ta ita da Ummi. Bayan gaisuwan da tambayar yadda take ita da Ummi su ka ɗan yi zantukan soyayyarsu na kewar da su ka yi da juna. Sannan Mimi ta shigar masa da maganar Manaja nan ta ke Aji ya fara faɗa ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba,Mimi ta jawo Ummi da ke barci ta rumgumeta a sanyaye ta ce" Kayi hakuri Baban Ummi." Haka kawai ta ke faɗa amman ya ma ƙi sauraranta sai faman faɗa yake yi yana faɗin" Ba fa mganar hakuri ba ne Fatima renin wayan ne na ga ya yi yawa. Me ya sa sai ke? Ke kaɗai ce ma'ikaciya mace a wannan wajen na ku? Haba sai ace ke dole fuskarki ce za ta riƙa yawo a akwatin Talabijin ɗin kowani gida? Haba ba ta yuyuwa kina matata ina son ki, in na kalle ki kina burgeki sha'awan ki na kamani, amman ace abun hauahi da baƙin ciki ni a matsayina na wanda Ubangiji ya yarje min ba ni da ikon kallon ki ni kaɗai na yaba, da wanda ya dace da wanda bai dace ba, kowa kallon fuskarki yake yi ya na yabawa. Wallahi Tallahi ko aikin nan da kika ga na barki kina yi ba a son raina ba ne Fatima , ina da kishi kishin da ni kaɗai na ke son na yi ta kallon ki ina yabawa. Amman ya zan yi? Yanzu ina hanaki wannan aiki sai ace ni mugu ne ba ni da adalci na ganki da aikin ki na aure ki kuma na rabaki da shi Ƴan'uwanki su zageni ke ma a ranki ko ba ki furta ba sai kin ce ni mugu ne ba ni da adalci." Cikin Mamakin kalamansa Mimi ta ce"Ni? Me ya sa zan kira mijina da suna mugu? Ka isa ne shi ya sa ka hanani saboda kai ɗin mijina ne kuma shugabana, yan'uwana kuma ba su da abun cewa tunda ba suke aure na ba, na su sai dai shawara ne ko jin ta baki" Aji ya ciji leben bakinsa na ƙasa kafin yacce"Ina son na hanaki, amman kuma gwara na yi miki adalci kema ki yi min,in na dawo za mu sake yin mgana" Ta san cewa akwai mgana tunda ya ce sai ya dawo za su ƙarisa mgana, tun kafin ma ya ce bai amince ba mganganunsa sun nuna in da ya dosa yasa ta faɗa mana Manaja Megidanta bai amince ba sannan ta ba da Shawaran tun da a shekaran a ɗauki sabbin ma'aikata me zai hana su jaraba wata sabuwar fuska! Nan da nan ko a ka karɓi shawaranta a ka fara shirye shiryen kaddamar da shirn tare da zaɓo cikin sabbin ma'aikatan da a ka ɗauka domin cire wacce ta fi chanchanta a ciki. Ko da suka yi waya da Rukky ta yi mata zencen itama sai da ta ce"Ke ma Mimi da son jan ma kanki faɗa kike yi, wannan mijin naki mai shigen kishi ne zai amince? Aikin ma ai ba ason ranshi kike yi ba, da kin sani tun da Manaja ya tuntuɓeki kin datse abun da ba ta kawo ku da gabar haka ba." Mimi ta ce"Haka ne Rukky, ai na ce su nemi wata sabuwar fuskar mijina bai amince ba." Ruƙayya tace shike nan kuwa sai ki zauna lafiya. Saboda maganar na ranshi sati biyu tsakani ya dawo gida, amman sai da ya zaunar da ita yana gaya mata ba dole sai an riƙa ganin fuskarta ba akwai ma'aikata da dama da suke aiki ta bayan fage fa ba'a son su ba, me zai hana itama a maida ta wannan bangaren? Mimi ta ce"Ba ni da zaɓin bangaren da zan yi aiki, zaɓi na kenan bangaren da na fi ƙwarewa broadcating, Kuma ni ban isa in ce ga in da za su ijiyeni ba sai dai in zan ijiye aikin gabaɗaya na dawo gida na zauna tunda haka kake so." Jin haka yasa bai ƙara mgana ba tunda ya ga idanuwanta sun ciko, ya san tana son aikinta kuma yanzu ya ce ta bari kamar bai yi mata adalci ba, ita ba wata sana'a take yi ba sannan shi kuma ba mazaunin gari ba sannan In har Inna ta ji labari sai ya raina kanshi shiyasa ya danne ma zuciyarsa bai ƙara mgana kan aikinta ba har ya gama kwanakin shi ya koma Abuja. Ya koma ba Daɗewa Mimi ta samu wayar Mommy ta ce tana neman ta a Abuja, a she ba ita kaɗai ba gabaɗaya yayan nata har da Dr tunda shi ne babba, kiran ya ba su mamaki amman su a tunanun ko maganar gidane, kuma dukkansu ta ƙi ce musu komai a waya ta dai ce su nemi izini wajen mazajensu weekend ɗin da zai shiga tana son ganin su gabaɗaya, Aji ma da ta gaya masa sai da ya ce" Topha! Allah ya sa lafiya." Mimi ta ce"Ina tunanin ba lafiya, dukkan mu fa ta kira har Dr, ni ba ka ce min ka je wancan satin ba? Ko ka fahinci wani abu ne? Aji ya ce"A'a lafiya lau take ba wata matsala, mun daɗe muna hira da ita, ba na jin ko akwai wani abu na damuwa sai dai in wata mganar ce ta dabam, ki kwantar da hankali hairan in sha Allahu." Da haka ya samu ta natsu amman ita duk ta damu, Abun da ya ƙara ba ta mamaki da ta je gida gaida Hajiya nan ta ke gaya mata ta saka Daddy ya nema musu jirgi gaɓadayansu har da shi za su tafi Murja na neman su. Sai Mimi ta saka a ranta ƙila kan mganar gida ne tunda ba'a raba gidan ba har yansu su sun ce sun barshi Mommy ta zauna har karshen rayuwanrta ne. Daga gidan Hajiya gidan Inna ta biya ta na gaya mata za su tafi Abuja tare da Hajiya da Daddy, Inna ma kanta sai da ta ce"Lafiya kuwa? Ko wani abun ne ya faru? Mimi ta ce"Lafiya ƙalau Inna za mu je dai mu gaishe ta ne." Haka ta faɗa ma Inna, saboda itama ba ta san dalilin kiran ba. Nan ta kai har mangariba saboda Aji baya nan ya sa ta koma da wuri kuma a motar ta ta zo, washegari kafin ta je aiki sai da ta kai Ummi asibiti ta kwana kuka ashe kunnenta ke ciwo a ka bata mgani. Daga asibitin ne ta wuce wajen aiki amman ba ta daɗe ba ta koma gida saboda Ummi, amman Alhamdulillah mganin da a ka bata ta ɗiga mata sau uku shike nan ta samu sauƙi ta cigaba da walwalanta irin na su na yara. Tun ranar Jumma'a Khadi da Madiha suna Abuja, su Mimi kuma jirgin safe suka bi, wajen sha ɗaya suna falon gidansu a Abuja, abun da ya ƙara ninka mamakinsu ganin har da Inna zainaba suka iske a gidan kenan mganar babba ce, a yinin dai ba'a yi wata nagana ba an haɗu ana ta hira kowa sai mamakin kiɓan Ummi yake yi khadi ta dauketa ta na nishi lokaci ɗaya tana faɗin"Ka ga min burtuka, ke ubanki ɗan firit uwar taki kuma ba kiɓa ba, to ina kika ɗauko wannan jikin? Hajiya na dariya ta ce"Ƙibar yara ce, taba fara girma za ta ragu, sannan ita kanta Binta haka Murja ta yo goyonta sai da ta fara girma sannan ta fara raguwa." Mommy na wajen ta ce kwarai haka ta yo goyon Mimi da wannan kibar kamar kazar turawa jiki suɓu suɓu kamar Ummi, Dr ya ce to ga in da ta yi gado nan wajen uwarta ana ta dariya har Madiha ta na saka baki ta ce Yarinyar na burgeta ta na son ganin yaro da kibarsa sannan da ƙarsashinsa har ɗaukanta ta yi, Allah ya haɗa jininta da na Ummi duk ba ta damu da ɗaukan yara ba, nata ma a hannun masu aiki suka yi wayau Har dare Mommy ba ta ce musu komai ba, Sun dai ga sun shige ciki ita da Daddy da Hajiya sun jima suna mgana sannan ya fito, shi a ranar ya koma daman ba kwana ya ce zai yi ba. Hankalinsu ya kwanta ganin Mommy lafiyanta ƙalau ta na ta zirga zirganta suna da tabbacin ba ita ce wani abu ya same ta ba. Har Asma'u sun ma mgana ta ce itama ba ta sani ba, sannan sun yi ma Inna Zainaba mgana ta kalli Khadi da ita ce ta tsarete da tambayan abunda ya sa Mommy tace ta na son ganinsu." Inna Zainaba ta ce"Ban sani ba,ko jira ita uwar taku ai tunda ta kira ku za ku ji abin da ke faruwa." Sai suka yi shuru ba su kara mgana ba ko Dr da yake namiji bai damu ba. Harkan gabansa kawai yake yi sai su ne duk suka damu barin ma Khadi da Madiha. Madiha ba ta hakura bq sai da ta je har ɗakin Mommy a daran ta ga ta na waya amman ta na ganinta sai ta ce"Zan kira, yanzu zan yi mgana da yaran nawa." Daga nan ta juya tana kallon Madiha cikin Mirmishi kafin ta ce" Madiha Kabir Dabo,." Haka ta kira sunanta sai itama ta yi mirmishi kafin ta ce" Barrister me ke faruwa ne? Kin kiramu kuma kin ƙi ce mana komai? Kin san gobe zan koma ga Dr ma ya na da Tiyata jibi ya ce." Sai Mommy ta dafa kafaɗanta kafin ta ce"Ina sane da abin da nake yi, mu je ɗakin da Hajiya ta sauka sai mu yi mganar gabaɗaya. Tare suka fito da Mommyn da Madiha Dr ya na ɗakin da yake sauka Mommy ta kira shi a waya ta ce ya shigo cikin gida. Mimi kuma tana ɗakinta suna waya da Aji, yana gaya mata gobe zai zo su haɗu daman ya yi kewarta sosai, itama Khadi ta zo ta kira ta Ummi dqman tana goyo bayan Inna Zainaba ta na barci bayan mangariba ta fara rigima ana yi mata mata wanka sai ga shi ta yi barci bayan ta goyata. Gabaɗayansu sun haɗu a ɗakin da Hajiya ta sauka amman kafin nan inna Zainaba ta faɗi wata mgana da ya jefa su a duhu domin kallon Mommy ta yi kafin ta ce" Murja kina ba ni mamaki sai wani tare tare kike da yara? Ba fa saɓon Allah za ki yi ba sannan ke ce wwarsu ba su ba, ballantana ki ce yardan su kike nema ai ya kamata daman tuntuni ki yi ma kanki faɗa tunda zaman haka gare ki da sauran kuruciyarki ba zai miki kyau ba." Ga shi dai ba ta faɗa kai tsaye ba amman dukkansu sun sha jinin jikinsu, ai ba su ƙara firgita ba sai da Mommy ta warware musu mgana ce ta aurenta ya ta so, wani Alkali a ya ganta ya na so tun daɗewa amman dai ba ta bashi fuska ba, yana ta bin ta sai yanzu ne ta bashi daman a takaice tana so ta yi aure kuma ba har ya je kano ya ga ƴan'uwanta yanzu ma haka gobe a ke son a je can kano a ɗaura auran amman ta ce a dakata mata sai ta yi magana da janin mijinta da wwar mijinta da kuma Yayanta, to ɗazu ta yi mgana da Daddy ya ce abu ne mai kyau daman zamanta haka ba daɗi, Hajiya ma ta ba ta dukkan goyon baya, ita ta ma yi garaje ne tana ganin kamar in ta kawo maganar Murja ba za ta amince ba, amman har ga Allah taso Hamza ya auri murja amman tunda har ta daidaita da wani sai ba ta kawo mganar Hamza ba, ta ba ta dukkan goyon baya. Ita yanzu tana son jin ta bakinsu ba, su ɗin ƴaƴanta ne suna da haƙƙin ta sanar da su kafin auran ita ta ce ma adakata amman in ta waliyyanta ne da tun zuwan farko an ɗaura mata aure da Alƙali Mustapha Tafida, matarsa ɗaya yayansa biyar amman duka sun yi aure kawai shi dai ya na son Barrister Murja ne amman ƙarin aure ba shi cikin tsarinsa matarsa likita ce tana aiki a wani babba asibiti anan garin Abuja. Gabaɗaya sun kasa mgana saboda lamarin ne ya zo musu a bazata. Ban da Dr da ya yi mirmishi kafin ya ce"Haba Mommy don za ki yi aure sai ki ce sai kin nemi yardan mu? Mun san cewa tunda Abi ya rasu wata rana za ki yi aure tunda ke ma kina bukatar Kyakyawan rayuwa anan gaba, mu ma a matsayin mu na ƴaƴanki hankali mu zai kwanta sanin kina ƙarƙashin wanda zai kular mana da ke, sannan a kallah bayan Abi ƙin kara samar mana gurɓin ƙara kiran wani da sunan uba." Mommy sai kawai ta fashe da kuka, Hajiya ma sai da ta share kwallah tana fqɗin"Allah ya yi maka albarka Sulaimanu, ban taɓa ganin mai hankali kamar ka, kaf cikin Ƴayan Murja ba kamar ka, Allah ya raya maka zuru'a shi kuma babanku Allah ya jiƙansa da rahama." Ya amsa da Amin ya na mirmishi kafin ya tashi ya ƙarisa kusa da Mommy ya zauna ya na lallashinta, Mimi ta ji abun a ranta domin Abi kawai ta tuna amman ba ta jin za ta iya cewa kada Mommy ta yi aure, amman har ga zuciyanta sai ta ji zafin auran da Mommy za ta yi. Bangaren su Khadi kuwa ba wanda ya san abin da ke ransu sai da Hajiya ta kalle su kafin tace" Ku ba ku ce komai ba? Ba yardan ku ta ke nema ba, kawai dai ta gaya muku ne saboda kuna da haƙƙin ku sani ku saka mata albarka mahaifiyarku ce ba ku da kamarta, kun dai ji kalaman yayan ku? To kuma ku yi ko yi da shi." Madiha ce ta girgiza kanta kafin ta ce"Tsaya tsaya Hajiya ni fa ban gane ba, shin Mommy za ta yi aure gobe? To menene amfanin gaya mana ba yardan mu take nema ba, tunda ko mun ce a'a ba abin da za'a fqsa. Maganar gaskiya ni ban goyo bayan wannan auran na Mommy ba, me ta nema ta rasa? Me take bukata? Abi ya rasu ko shekara biyar bai yi ba Mommy kin manta da shi za ki je ki auri wani, kuma ki sakamu mu kira shi da sunan Baba, gaskiya Mommy ba zan iya miki wannan biyayyar ba, ba da yawun bakina a wannan auran na ki ba sannan ni uba na ɗaya ne ya rasu bayan shi ba ni da wani uban kuma." Daga haka ta mike ta fice t na kuka, Khadi ma ta na sharan kwallah ta ce" Gaskiya ba ki kyauta ba, wani irin aure kuma? Da girman ki gotai gotai da ke kice za ki yi wani aure? duka duka yaushe Abi ya rasu da har kin manta da shi za ki yi wani auren? Ni ma gaskiya ban yarda ba kuma ban amince da wannan auren ba." Itama tashi ta yi ta fice ta na kuka Sulaiman na kiranta amman ta ƙi sauraran shi, Hajiya ta girgiza kai ba ta ce komai ba, daman ta san haka zai faru, Momny kuma tana ta kuka Mimi kuma ta kasa mgana kanta na ƙasa amman a cikin ranta itama ba ta son auran da Mommy za ta yi amman ta kasa mgana, Hajiya ta kalli Mommy lokaci ɗaya tana faɗin" Murja ki daina kuka, su ai ba su isa su hanaki aure ba, in kika biye ma yaran nan marasa jin mgana sai dai ki ƙare a haka, su ba'a aure suke zaune a gidan mazajasun? Ba na son iskanci da wawanci." Mommy ta ɗago ta na kallon Mimi kafin ta ce" Mimi ba ki ce komai ba? Ke ma kina ganin na manta da babanku ko na ci Amanar sa ne? Ganin yadda Mommy ke hawaye ya sa Mimi ta girgiza kanta kafin tace"A'a Mommy. Ni ban san me zan ce ba. Amman dai ba zan hanaki aure ba tunda kina so Allah ya sanya alheri, amman ina so ki ba ma su Khadi lokaci za su sauko daga baya.." Ta na gama faɗin haka itama ta fita Mommy ta ta shi za ta bisu Sulaiman ya hana ta ya ce shi zai je ya same su, nan ya ta shi ya fita ya bar ta da Hajiya tana ba ta baki. A ɗakin da Madiha ta sauke ya iske su sun haɗa kai suna kuka har da Mimi nan ya zauna ya na jawo hankalinsu da nuna musu falalan auran da Mommy za ta yi amman Madiha cikin ƙaraji ta ce" Ban amince ba, domin ban ga wata falala a auran Mommy ba, da girmanta ne sai ta yi wani auren? a she ba ta son Abi tunda har da mutuwansa ba daɗewa take tunanin sake auran wani Nlnamijin." Tana faɗa khadi na faɗa. Sun ƙi sauraran sulaaiman, Allah ya kawo Inna ZAINABA ta yi musu wankan tsarki ta karishe da cewa"Wato ita ba mace ba ne sai kada ta yi aure, ta zauna ta cigaba da takaban uban ku yana kabari ta ƙare rayuwanta a lalace ko? To ba ku isa ba tunda Allah ya ba ta wannan damar wlh sai Murja sai ta yi aure ta samu natsuwa, ku na gidan auran ku ina ruwan ku da auranta? In ba'a aure ku me ya sa kuka yi? Ai mace ba ta wuce aure in ba mutuwa ta yi haka namiji, ina laifi ta zauna tsweon shekara uku ba aure, in da ace yau ita ce ta raau na tabbata in uban ku ya yi mata hallaci ta yi shekara a ƙasa tuni zai ƙara aure sai mace ce a ke ganin laifinta bayan ta rasa miji ta ce za ta yi aure sai ace gotai gotai da ita ko? Shi amman namiji ko ɗan shekara ɗari ne ba mai damuwa da shekarunsa sai ma a aura masa budurwa ba wanda zai ce wani abu, to bari ku ji na gaya mu ku, ko da yardan ku ko ba yardan ku wlh Murja ta gama zama matar aure a gobe in sha Allahu wanda ya ji haushi ya yanke ta kada ya sake nemanta, ku ne za ku taɓe domin ita sha kudum ce tunda kuka bari ta haifeku ta zama uwarku." Haka ta ke ta faɗa da Dr ya ba ta hakuri ne ta sassauta amman sai da ta ce"Raina ne yaɓaci Sulaiman, ku ba yara ba kowace da mijinta da yayanta amman kuma ku ce murja kada ta yi aure? To ta zauna zaman ubanku a cikin gida? Wlh ba ku da tsausayi, daman na san ko kowa bai ce wani abu ba sai kin ce baki yarda ba, tunda daman ba ki da zuciya mai kyau, To mu zuba mu gani shege ka fasa." Ta tafa hannu bayan ta gama nuna Madiha da yatsa, sannan ta yi tsaki ta fice Sulaiman kuma kalaman bakinsa sun ƙare sai tashi ya yi shima kawai ya fita. Mimi ce mai sauƙi sauƙi itama haka su Madihan suka gama saka mata na su tunanin a ranta har ta ji itama tana jin haushin Mommy, A ɗakin nan suka kwana ko Ummi sai da asuba Inna Zainaba ta kawo ta, ta ce ta ba ta Nono kafin ta yi mata wanka. Suna cikin ɗakin nan ko karyawa ba su yi ba. Sai da Dr ya sake dawowa ya lallashe su amman ba su ji ba gwara Mimi ta sha tea sannan ta ci dankalin da Asmauu ta soya ko saboda goyo. Sannan ta saki fuska har ta je ta gaida Hajiya da Mommy da duk idanuwanta sun kumbura saboda kuka Hajiya ta kalli Mimi kafin tabce"Binta ka da na ji ko na gani kin biye ma sakarkarun yayyenki kin saɓa ma Murja, kin ji ko?. Sai ta gyaɗa mata Hajiya sai faɗa take yi Inna Zainaba na wajen ta ce"Hajiya kyalesu sai dai su mutu aure kamar an yi an gama." Mommy daman a jiyan ta ce ita ta fasa Inna Zainanba ta dira kanta da faɗa da cewa"Sai zauna ki koma baya kina bin ƴaƴa sai abunda suka ce aure fa ba mai tada shi na ce duk wanda ya ji haushi kada ya ƙara neman ki." Khadi da Madiha suka fara shirin tafiya, Sai dai misalin goma sha ɗaya safe suka ji Inna Zainaba na sakin guɗan an daura auran Mommy da wani, gabaɗaya sai hankalinsu ya ƙara ta shi, ba yadda sulaiman bai yi da su su tsaya kada su tafi ba suka ƙi ba da asuba kafin ya wuce tunda shi ma jirgin karfe bakwai ya bi ya koma kano ya samu ɗaurin auran Mommy. ita madiha ta samu jirgi amman Khadi motar haya ta bi zuwa Kaduna kuma ko sallama ba su yi ma Mommy ba ballantana Hajiya, Mommy ta damu Inna Zainaba ta ce kada ma ta saka a ranta su je, ma ji ma gani in sun isa su sauya ma tuwo suna. Mimi ce kaɗai a gidan itama sun yi da Aji zai zo bai kuma zo ba sai bayan azahar shima da labarin Mommy ta tare shi sai ya washe baki yana riƙe da Ummi lokaci ɗaya yana faɗin"Ma sha Allahu abun alheri madallah. Na yi ma Mommy murna Allah ya ba su zaman lafiya." Kawai sai ta saka masa,kukan me ya sa zai yi murna saboda Momny ta yi aure? Ba ya kishin Abi ne me ya sa Mommy za ta ƙara aure? Cikin Mamaki ya kalli Mimi kafin ya ce"Ban gane ba? Saboda addini ya ba ta wannan damar gwara da ta yi auranta sai mutumcinta ya fi fitowa a idanuwan waɗanda suka santa, sannan kuma kwanciyar hankalinku ne ku tuna yau tana da miji kuma sannan kun kara samun wani abu a karo na biyu." Kawai sai Mimi ta saki baki ta kasa mgana, Aji ba zai gane ba ne shi ya sa ba ta ma samu damar gaya masa abunda ya faru da su khadi ba sai da ya shiga suka gaisa da Hajiya ita ke gaya masa har ta na cewa" Ga ta nan duk da itama ba ta ce komai ba amman zuciyarta ba daɗi ka sake yi mata faɗa don Allah kada su saka ma Murja hawan jini." Aji ya kalli Mimi da ke gefen sa kafin ya ce"Haba Hajiya, suma ɗin yarinta ne amman in su san ciwon kansu ai ba za su yi haka ba, sannan su mata tunanin su a karkace yake, shi Dr da yake namiji ne ai ya fahimta kada ki damu Mommy auran da ki ka yi masalaha ne ga rayuwarki da ta su gabaɗaya ba za kuma su fahimta ba sai nan gaba kaɗan." Inna Zainaba ta ce" Ka ji maaganar masu hankali, itama sai ɓata rai take yi tunda ƴan'uwan sun yi fushi sun tafi." Kuma da gaske nan ko fara'a Mimi ba ta yi Mommy ma duk ranta a jagule ga shi sai kiranta a ke yi masu yi mata murna, tunda acan kano aka ɗaura auran shi kan shi Alƙali bai je ba. Sai dai waliyyansa kuma da kan shi ya faɗa mata an ce babban ɗanta ne ya ƙarbi sadakinta wato Dr Sulaiman farinciki ya cika Mommy har sai da ta yi kuka a ranta ta yi ma Sulaiman fatan ya gama da duniya lafiya shi da iyalansa yadda ya ke faranta mata shima Allah ya faranta masa haka. Aji bai tsaya wani lallashin Mimi ba saboda ya ga kamar abun na su har da iskanci, bai nuna ma ya gane ta na jin haushi ba bai daɗe ba ya tafi sun rabu akan itama gobe za ta koma, cikin zolaya ya ce" Ki tsaya mana ko zuwa laraba ku gaisa da sabon Abin naku mana." Hararansa ta yi sai ya yi shuru ya na dariya , har ya ci abinci ta tafi raka shi tana kumbure kumbure shine ma ya sa ta saki fuska tunda cakulkuli ya riƙa yi mata tana dariya. Yana kuma tafiya ta koma yadda take, Mommy ba ta yi gayya ba amman ta gayyaci abokan aikinta sun zo mata murna tunda da ɗaurin auren da tariyan duk ɗaya ne ita a gidanta za ta zauna shi ne zai rika zuwa wajenta in ranar girkinta ya shiga, bai zo a daran ba sai washegari da safe da ta ce ya zo su gaisa da Hajiya da Mimi za su koma Gombe. Gaskiya a ido mutum ne mai kamala da dattako ba yaro ba ne domin zai iya yin sa'an Abin ma, sun gaisa cikin girmamawa da Hajiya, Mimi kuma tana gaisheshi ya kama sunanta da cewa"Mimi auta ko? Yau dai navga auta." Ya faɗa ya na mirmishi ya miƙa hannu ya karɓi Ummi yana faɗin"Ga kuma Ummi maryama ko? Sai Mimi ta gyaɗa masa kai a ranta tana faɗin su Mommy manya, ta sha kwaliyarta suna ta yi ma juna wani kallo. Ba ta gama mamaki ba sai da ta ji ya na tambayan su Madiha tunda Mommny ta gaya ma sa dukkansu sun zo. Da sauri ta ce Madiha za ta koma saboda yara ita kuma Khadi saboda aikinta sai ya ce bakomai wata rana ai za su haɗu Dr dai yana kano sun haɗu tunda shi ya ba da auran Mommyn tashi ya faɗa har ya na kashe ma Mommy ido, Mimi ta ji kamar ta make shi saboda haushi. 10k ya saka ma Ummi a jikinta sannan ta yi masa sallama ta bar falon zuciyanta na ɗaci saboda haka ta matsama Hajiya suka koma Gombe a ranar domin ba za ta iya zaman ganin wannan bakincikin ba Aji ma ya yi da ita ta zauna da Mommy ko na sati ne sai su koma tare amman ta ki sai ta fake da aiki shi kuma ya san dalili amman sai ya ƙyaleta. Kuma da ta dawo ko a zencen ba ta taɓa faɗan cewa Mommy ce ta yi aure ba. Ko Inna ba ta gaya mawa ba ta kuma san Aji ba shi da surutu daman dai Mu'azzam ne, Rukky dai ta samu labari ta bangaren Jaheed da ta kira ta ta na tambayanta ashe kuma Mommy ta yi aure sai kawai ta ce"Uhm" daga nan ta sauya mganar har Rukky dai ta gano Mimi ba ta son mganar. sannan da kanta ta kira su khadi ta na gaya musu abin da ya faru sanda Alƙali ya zo tana gaya musu Mommy ta ba shi labarin kowa ya san shi ya sunan sunan shi. Madiha bakin ciki kamar ta mutu sai ta ce" Wai mommy yarinya ce? Ji fa wannan aikin da take yi mtswww.." Ta yi tsaki duk suka ƙara saka Mimi a tafiyarsu na ba su amince da auran ba shi ya sa ko da ta dawo ko sau ɗaya ba ta kira Mommyn ba sai ita ce ta kirata tana cewa ba ta kira ta ba kada bakin Mimi sai ta ce"Ina zan kira na takura miki Mommy, na baki lokaci ne ki ci amarcin ki.' Mommy sai ta kasa mgana jiki a sanyaye ta ce"Ke ma kin kasa fahimtata ko Fatima.? Da Sauri Mimi ta ce"Na fahimta kina son aure kuma kin yi, Allah ya ba da zaman lafiya. Daga nan ta kashe wayarta daga ranar ba ta ƙara nemanta ba, itama Mommy sai ta ba ma zuciyarta haƙuri ta tsaya ganin in da suka dosa. Matar alƙali da yayansa sun karɓeta sosai sai ita ce ke da yayan da ke yi mata barazana in ka cire Sulaiman Asma'u sai murna take yi ta samu Abba amman ban da su Madiha da suke kishin Abi sannan suna ganin kamar abun kunya ne. Hibba ta saamu labarin auran da Mommy ta yi ta bakin Jawahir tunda sanadin Mimin suna zumunci ta je gidan shi ne ana hira labari ya kawo ta faɗa mata, tana komawa kuma ta faɗama mijinta shi kuma sai ya xe bai ji ba, bayan ya kira yayanshi ya tambayeshi sai ya ce eh da gaske ne. Ke Hibba sai ki ka ga Mimi a chart sai kika ce mata" Matar Yaya ashe kuma Mommy ta yi aure? Allah ya sanya alheri." Sai ta tura emojin dariya har da na rawa, wannan abun Mimi ta gani sai ranta ya ɓaci kawai sai ta yi ma Hibba vioce da cewa miye take mata dariya saboda Mommy ta yi aure? Abun dariya ne ya faru da za ta riƙa mata dariya? Tun Hibba na ganin wasa har Mimi ta maida mgana faɗa ta kira Hibba a waya tana gaya mata mganganu marasa daɗi har tana faɗin in abun dariya ne to ta bari in nata Baban ya rasu mamanta ta sake wani auren za ta yi mata dariya ta ji in da daɗi. Ran Hibba ya ɓaci sukavyi ta gayama juna mgana ita da Mimi a ka rabu ba daɗi har da su blocking ɗin juna. Hibba ta nata kuka haka Mu'azzam ya dawo ya ssme ta da ya tambayi ba'asi sai ta gaya masa abin da ya faru tun farko sannan ta kunna masa Vioce ɗin Mimi da wayar da su ka yi domin ta yi recording abun dai duk ba daɗi ya yi ma Hibba faɗa me ya sa ba ta ba ta hakuri ba? Ita kuma sai ta ce ita fatan alheri ta yi ba na tsiya ba, saboda dai a kashe mgana ya sa ya kira Mimi da kansa domin ya ba ta hakuri shima ta shafe su ba ta ɗaga wayarsa ba sai ya kira Inna Meri ya gaya mata abin da ya faru, ta ce itama ba ta ma san Mommyn ta sake aure ba tun da daga Binta har Mansoor ba wanda ya faɗa mata sai ta ce ya bar mganar a hannunta Mansoor shi zai kashe wannan fitinar. Ta fahimci Binta dai tana kishin Babanta ba ta so auran Mommy ba. Shi ya sa duk rayuwaka suka ɓaci itama kuma Hibba ta na ganin ba wani abu ta faɗa ba sai a ka kasa samun fahimtar juna gabaɗaya. Inna Meri da kanta ta kira Mansoor ta faɗa masa abin da ke faruwa ta ƙara da cewa" Ba ina goyon bayan Hibbatu ba ne, amman zencen gaskiya ta fi matarka gaskiya saboda ita ba ta san abin da ke faruwa ta yi mata fatan alheri, daga karshe sun kasa fahintar juna har abubuwa suka lalace, na so na je na bata hakuri amman sai na yi tunanin ba hurumina ba ne tunda ba ta gaya min ba, ba na so a fara samun baraka daga matayenku saboda in hakan tana faruwa wata rana kuma ɓaraka za ta iya bayyana daga bangaren ku, kai ka yi ma Binta mgana ka fahimtar da ita shima Mu'azzamu na gaya masa ya fahimtar da matarsa in an samu daidaito sai su kira juna Hibba ta ba ma Binta hakuri magana ta wuce." Sai Aji ya ce cikin satin nan zai zo gida zai yi mgana da Mimin shi ya ɗauka Fatima na da tunani ashe dai da sauranta. Mu'azzam suna waya amman bai gaya masa ba. Sannan ko Walida da ke gidan ta kwana ta tashi ba ta san wani abu ya faru, sai ya bari kawai sai ya dawo gidan ya samu lokacin da zai yi ma Mimin faɗa sosai ko ta dawo cikin hayyacinta ya je ma ya kara ganin Mommy tana hawaye ta na gaya masa duka yaran sun juya mata baya harda Mimi sannan ta hada shi da Alƙali har ga Allah bai ga illan shi ba, kamili mai mutumci sun samu uba amman suna haukan banza. Ranar jumma'a ya dira gombe, ko a fuska bai nuna ma Mimi wani abu sai da ta gama bikin tarbansa bayan ya yi wanka ya ci abinci ya so ya yi mata mgana amman sai kewarta ta hana shi a ka kwana ba ma juna Soyayya da asuba ya tafi masallaci bayan ya dawo ya koma barci asabar ne ba ta fita aiki bai tashi ba sai goma na safe yana fita falo ya iske ta, tana goge goge ga Ummi saman kujera an jinginar da ita alamun an fara Koya mata zama. Ita kuma matar gidan tana ta gogen tibi wayarta na saman kujera ta saka speaker suna mgana da Madiha abun da kunnuwansa suka jiye masa shi ne Madihan na cewa" Ni fa na gayama Khadi in har Mommy na son mu sai dai ta zaɓa ko auran ta ko mu." Mimi ta ce",Wlh nima fa ko kiranta ban sake yi ba, in har tana son mu sai ta zaɓa ko wannan mijin ko mu ƴayanta." Yana tsaye ya ji Madiha na zuga Mimi da kada ta ƙara kiranta ta bar ta in suna da amfani za ta neme su. Saboda haushi ko Mimi ba ta san ya shigo falon sai da ta ji muryansa yana faɗin" Ko shekara ɗari ta yi ba ta neme ku ba, ba abin da zai sameta amman ku sami ko wata uku kuka yi ba ku neme ba ta tsinuwan Allah da ta mala'iku sai ta tabbata a kan ku, sannan ku sani ita ce ta haifeku ba ku ne kuka haifeta ba, aure ta yi ba zaman zina take yi ba, ko da saka albarkan ku ko babu za ta zauna lafiya.Ku ne in ba ta yafe muku ba ku ke cikin bala'i da masifa, sannan zan miki gargaɗi na karshe in har ba alheri za ki kira matata ki gaya mata ba, to don Allah kada ki sake kiranta ina son ta samu rabauta a duniya sennan ta samu lahira ke da kika juya ma Albarka baya je ki ki yi ta fushin ki ki jira ranar da mahaifiyarki za ta zabi sunnar ma'aiki a kan ki, ga ki kamar mai hankali maimakon ki zama jagoran ƙannen ki wajen faɗa musu gaskiya sai ke ce ke ƙara zugasu kuna kauce hanya, girman banza gareki sannan takmar ilimin ki bai yi miki wani amfani ba, ki je can ki yi ta sakarcin ki amman na gaya miki wlh tallahi ka da ki kara kiran matata kina zugata." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar, Mimi ta dankare a tsaye tana kallon Aji cikin mamakin manya manyan kalaman da mijinta ya sauke ma yayarta, ta buɗe baki za ta yi mgana itama ya ɗaga mata hannu ya fara zazaga mata nata faɗan tas ya yi mata sai ta fara kuka tana faɗin" To koma menene sai ka gaya ma yayata mganganu haka? Kai tsaye yavce" An gaya mata in kuma za ki rama mata ne, bismillah ina ruwana da girmanta tunda girmanta bai mata amfani ba,.Mahaifiyarku ce fa amman saboda rashin tunani kuna neman saɓa mata saboda haukan banza in ba'a aure za'a haifeta? Ita ba tana gidan Mijinta ba ne? Sai ta hana ta auren ita? Ba ku da adalci ba ku ba yara ƙanana ba amman kuma kuna yin abin da ko yara suka yi sai an yi mamaki, har saboda haka Hibba ta yi miki murna ki ka bi ta da zagi saboda ke kin isa ina laifin wanda abun alheri ya same ka yace maka Allah ya sanya alheri? Sai ki zage ta? Mimi na kuka wiwi ta ce" Ni fa ban zageta ba, ita ce ta min dariya to abun dariya ne? Shima ya taso mata da cewa to abin kuka ne, ko so take yi ta ta ya ta haukan da take yi na faɗa da mahaifiyanta saboda ta yi aure. Mimi duk yadda ta so kare kanta Aji bai ba ta dama ba, ya yi mata faɗa sosai ya kuma bar ta, tana kuka ya ɗauki Ummi suka shige ɗaki ranar gidan yini ya yi ba daɗi ko abun kari ba ta yi ba ta shige ɗaki tana kuka shi kuma ya ɗauki ƴarsa suka fita zuwa gidan Inna ya karya ita kuma Inna ta yi ma Ummi wanka tunda Aji cewa ya yi Mimin ba ta jin daɗi. Saboda nono ne ya sa ya maida Ummi gidan a mamakinsa sai ya ga Mimin ta tashi har ta yi abinci ta gyara gidan,ganin haka ya sa bai sake fita ba ya zauna ya na ƙara mata da nasiha, ita kuma ta baahi hakuri ta ce za ta,kira Mommy ta ba ta hakuri ita da Hibba. A gabansa ta kira Mommy ta ba ta hakuri, Mommy kamar ta yi kuka farinciki ya cika ta, ta yi ta sakama Mimin albarka tana faɗin" Wlh Allah saboda ku na yi wanman auran saboda na kare muku mutumcin ku da na ƴayan ku." Mimi na hawaye tace"Hakane mommy ki yi hakuri, In sha Allahu ba zan kara ba suma su khadi duk za su daina." Mommy tace bakomai ita ba ta rike su ba ta yafe musu tun kafin ma su roke ta Haka ta kira wayar Hibba bayan ta cire ta a blaklist ta ba ta hakuri itama ta ba ta hakuri shike nan sai mgana ta wuce. Amman fa Madiha sako ta turama Mimin da cewa ta gode tunda ta ba da damar da Mijinta ya zage ta har Dr ta kira ta gaya mawa shi kuma ya ce abunda Mansoor ɗin ya yi daidai nw in ita ba ta da hankali sai ta yi ta yi,Khadi ma ta kira Mimin ta mata surutun ta zaɓi namiji a kan su ƴan'uwanta tunda a gabanta ya zagi Madiha ta kasa mgana ita dai sai hakuri ta ba su, tunda ko ita ba ta tsira da faɗan ba kuma suna nan a kan bakansu na ba su som auren. Sai ga shi wata ɗaya da wani abu da auran mommy Khadi ta samu matsala da dangin mijinta sai ga ta gaban Mommy tana kuka, Mommy ita ta kira mijin khadi ya zo har gida suka yi mgan matsalace ta gida yayyensa ne suke son ya kara aure, karshen dai Alkalin da suka raina suke jin haushi ya tsaya mata tare da Mommy dashi suka maida ta kaduna suka kuma nuna ma mijinta ba ruwan Khadi da auransa amman ya kare mutumcin matarsa tunda yayyen nasa har gida suke zuwa su ci zarafinta, tun daga nan Khadi ta saduda itama Madihan ganin ba ta da abokin adawa yavsa ta fara saki amman ba duka ba. To ta na da wacce tafi Mommyn ne? itama Madihan kuɗi ya hado su da Mijinta tunda Kuɗin na su a waje ɗaya ne suna kasuwanci ti shekara ta yi kuma an zauna ana ta lissafi an gano dai shima yana karkatar da wasu kuɗi rigima har Abuja wajen Mommy. Sai ga shi Alkali Mustapha shi ya warware matsalan a ka samu sulhu, itama daga nan ta fahimci aure ga mace sutura ne komai tsufanta kuwa, ta saki suka rumgume alƙali a matsayin uba sannan akwai yarsa Batula dake aure a lagos Lakcara ce a Legal ya haɗa su suna zumumci itama Khadi akwai namiji a kaduna yana aiki da NNPC Shima tare da iyalansa sun zama ƴan'uwa tare da Khadija akwai wacce ke kano, sunanta Badiyya likitan yara ce ashe ma asibiti ɗaya suke aiki da Sulaiman ya san ta ta san shi sai wannan dalilin ne zumuncin su ya ƙara zama na sosai Iyalanta na zuwa gidansa shima iyalansa na zuwa, ɗayan namijin Soja ne yana Abiya tare da iyalansa amman suna mgana a waya dukkansu. Bayan wannan ya wuce an samu daidaito zukata kuma sun samu natsuwa sai Mimi ta kara bijiro da mganar ta na son siya wata sabuwar Motar, Aji dai da ta nemi shawaransa cewa ya yi" Ni tun a baya na baki shawara,sannan na yi miki alƙwarin in na samu kuɗi da gumina zan siya miki mota amman na ga kamar kina sauri ne bazan hana ki siya ba tunda kuɗin ki ne amman da kin hakura da siyan wata motan ki cigaba da lallaba taki, ga tawa ma duk ki haɗa ki riƙa amfani da ita, in har Allah ya hore mana ko Jirgi ki ke so zan iya siya miki Mimi ba ma mota, gwara ki fara ko wani kasuwanci ne da kudin kamar zai fi,amman in ba ki ji shawarata ba shike nan ba zan hanaki yin yadda kike so da kuɗin ki ba." Da ta yi mgana da Mommy da Hajiya suma dai shawaran da suka bata kenan sai ta amince da shawaran ta fara kasuwanci amman ta rasa ina zata fara tunda ba ta da Ra'ayi ko ido a kan kasuwanci da ta yi mgana da Aji sai ya ba ta shawaran ta yi mgana da Yayarta Madiha ai yar kasuwa ce za ta ba ta shawarwari amman shi da ita sun tsaida shawaran ta fara kasuwancin saida Abayoyo da jaka da takalmi in ta karɓu har shago za ta iya buɗewa. Ta yi mgana da Madiha kuma ta yi na'am da shawaran Mimi ta ce za'a riƙa mata Oder jakunkuna wasu daga Lagos wasu kuma daga China ko India ko Italia,dogayen rigunan kuma daga daga Dubai, tunda ita tana harka da yan kasuwa daga kasashen waje tuni ta haɗa Mimi da su har ta tura kuɗi za'a fara kawo mata kaya kaɗan ta jaraba ta gani. Tunda tana aiki tallatawa ba zai mata wahala ba In ji mijinta Mansoor Ibrahim Aji. ****** "Maryama(Ummi) na da wattani goma sha ɗaya a duniya Mimi ta samu wani cikin, kuma har ya yi wajen wattani biyu da kwanaki a jikinta ba ta sani ba, kamar na Ummi ne, shima bai zo da laulayi ba in da ma ta fahimta ta na yawan ganin jiri da tashin zuciya sannan aiki kaɗan sai ta ji ta gaji kasala duk ya rufeta sannan sai ta fara,kwana da zazzabi mai zafi lokacin Mansoor Aji ba sa nan ya fita wasan shi na farko a kasar Ghana, amman ya bubbuga wasu anan Nageria ƙaananun wasanni wannan ne dai suka tafi wata kasa buga wasan. Ba ta gaya mai ba ta da lafiya ba ta shirya ta je asibiti domin tafara zargin ciki gare ta sai ga shi gwajin farko a ka gani ciki ɗan wattani biyu da kwanaki a cikin jininta. Hankalinta ya yi bala'in ta shi Ummi ba ta shekara ba amman ta yi yawo tana tafiyanta da kafarta ko'ina amman ita ba ta shirya kara haihuwa ba shirye shiryen komawa makaranta ma take domin yin Phd ɗinta tunda yanzu alhandulillah komai na duniyan ta samu, miji nagari sannan ta samu kuɗi tunda Allah ya saka ma kasuwancinta albarka Odar kusan na goma kenan kuma tana samun ciniki da sun iso da sun ƙare. Sannan Hibba na sara acan kano kuma ta na aikawa da shi Abuja Asma'u na tallata mata ta Online anan ma Gombe sai gqmdala tunda gidan Talabijin ɗinsu ta ba ta dama ta tallata kayanta Shike nan da ta kawo oder suke ƙarewa musamman ma abayoyin. Sannan Rukkya ma ta na saran Abayoyin ta na siyarwa tunda zaman ko me ka taka ba zai yuyu ba ita mace da sana'a a ka santa domin cigabanta. Duk da ta koma can lagos ɗin tana aikinta a wani gidan Talabijin amman duk da haka ta ce itama za ta fara kasuwancinta amman sai ta samu jari mai ƙarfi. Duk da ba ta yi mgana da gogan nata kan maganar cigaban karatun nata ba amman ta saka a ranta za ta matsa masa sai ya barta tunda dai ba mazauni ba ne,sai ya yi wata biyu ba shi a Gombe ballantana yanzu da aka fara haskashi a duniya ba ma ƙasa ba, shiyasa ta yi tunanin ijiye aiki ta koma makaranta duk da tana da tabbacin mijinta ba shi da ra'ayin ya maida ta Abuja da zama a kusa da shi ya sha faɗa mata a Gombe za ta cigaba da zama ba wai don baya bukatar ta acan ba a'a sai saboda Inna in ya koma Abuja da zama zai zama sai bayan wasu wattani za ta ganshi kamar Mu'azzan kenan. Shi kuma baya son haka ba ta da kowa sai su ba zai yuyu in har Mu'azzam na kano shi kuma ya bar Gombe ba, saboda Iyalansa ya san a kai a kai zai riƙa zuwa Gombe ba kuma ita saboda aikinta ba sai saboda wannan dalilin na shi, da kuma dalilin ba ya son barin garin Gombe saboda yana son garin kamar yadda itama Gombe ta zame mata wani jigo a rayuwarta ba tun yanzu ba tun tana ƙarama take ƙaunar garin. Bta dawo gida cikin tashin hankali, ko wasan su Aji da aka haska a tashar Rt Tv ta dai kallah ne amman hankalinta baya wajen sai daga baya ta fahimci Nageria ita taci ghana da ci biyu da ɗaya. A Daran Khadi ta kira ta tana mata murna ta ce suna ma kallo ne sannan Rukky ma sun yi mgana ta ce sun kallah jar da Daddy shima da Mommy sun kalli wasan na shi,a gida kuma Inna ma ta kalla tunda Walida na gari ta zo gida hutu, ita duk ba wannan ne damuwanta ba ya za ta yi da cikin jikinta? Sun kuma kasa samun lokacin su yi mgana ta waya sai dole ta yi hakuri suka dawo daga Ghana ya zo Gombe sannan ta gaya masa ga halin da take ciki ya fara murna kamar zai goyata cikin taruwan hawaye ta ce" Ummi fa ko shekara ba ta yi ba Baban Maryam? Sai ya kalleta kafin ya ce"Shi ne me? Ummi ai ta girma ta na tafiyanta ko'ina ina waɗanda ke samun ciki bayan sun yi arba'in ma? Amman ke nan da kafin ki sauka Ummi ta kusa shekara biyu ba na son wannan koke koken naki, daga Allah ya baki kyauta sai kuma ki fara min kuka? Cikin hawaye ta ce"Ni ina tsoron haihuwan ne kai da kai ne sai ka ga ba lokacin ma da za ka iya ma yaranka tarbiya." Kai tsaye yvace"Ba ruwanki da wannan tarbiya ta Allah ce duk da ke ma da naki kokarin amman ni nasan tarbiyan ƴayan da zamu haifa ba za su gagaremu ba, Sannan in mganar halin rayuwa ce daman ita kan saka a guji haihuwa ma gabaɗaya Fatima Allah ya rufamin asiri ba ma ke da yayan da Allah zai bani ba, ina ɗaukan nauyin mahaifiyata da ƴan'uwana saboda haka duk abin da kike tunanin ma ba zai faru ba ba zai faru ba, in sha Allahu. Abun damuwar kawai lafiyan ki da ta Ummi za mu je asibiti mu yi mgana da likita sai ya bamu shawara ko? Mimi dai ta kasa mgana sai kuka, shi ya share mata hawaye ya rumgumeta yana lallashinta ga shi ta na so ta ce so take ta koma makaranta amman ba ta samu wannan damar ba. Washegari tun safe suka tafi asibitin da ta ke zuwa, suka samu likitan da mganar Ummi da lafiyan Mimi nan da nan ya ba su shawara ya ce bakomai. Za ta cigaba da shayar da Ummi har sai cikinta ya kai wattani biyar sai ta yaye ta tunda dai akwai rufin asiri Ummi ba za ta wani samu matsala in dai za ta samu abinci mai rai da lafiya da zai gina mata jiki ita da Mimin gabaɗaya, nan ta ke Aji ya ce ya yi alƙawarin sai in da karfin sa ya kare sun baro asibitin bayan ya rubuta ma Mimi maganganun karin jini saboda cikin jikinta tare dan ƴan dokokin daza ta kiyaye kaɗan ba ma su yawa ba, suna hanyar komawa gida Mimi ta roƙi Aji da Allah da Annabi kada ya yi tallar ta na da ciki kamar yadda ya yi da ita a cikin Ummi ganin ta damu ya sa ya ce ba zai gaya ba amman in har aka tambaye shi zai faɗi gaskiyansa ta ce ta ji kuma ta amince. Har ya koma Abuja yana lallaɓa Mimi ganin duk ta damu,amman har ya koma sai a hankali ba ta wani saki ba fahimtar haka yasa ya ce in ta samu sarari ta ziyarci Hajiya da gidan yaddiko da duk in da take son zuwa kila ko shiga mutane zai rage mata damuwa kamar ko ya sani fita mutanen da ta yi yasa sai damuwanta ta ragu sannan iya bakin ƙokarinta Mimi ta ɓoye cikin jikinta. Ita ce har gidan Nasir da Makama su rana ɗaya ta je musu ranar lahadi tunda ba ta da shiga wajen aiki ranar, kuma in ta dawo daga wajen aiki ta kan sauka gidan Hajiya ko Inna, ko sun gane tana da ciki ko ba su gane ba Oho ba dai wanda ya yi mata wata mgana, amman abin da ba ta sani ba daga Hajiya har Inna Meri sun fahimci Bintar ciki gare ta. Sannan yaddiko ma ta gane lokacin da ta je gaisheta sai da ta ce"Ai yanzu kya yaye wannan katuwar yarinya ko kina so ko bakya so." Ita ba ta gane ba, saboda Yaddiko ta sha mata tsiyan girman jikin Ummi ya yi yawa ya kamata ta yayeta in ta shekara ko da wattani ne ita kuma ta ce sai ta kai wa'adi, ko da ta yi mata mganar har a cikin ranta ba ta kawo ta fahimci wani abu ba ne. Ita a tunaninta ba wanda ya sani sai dai in ya fito a ganshi. Cikin ta na shiga wata biyar ta cire Ummi a Nono, saboda ma kada kowa ya fahimci wani abu ta kasa kaita gidan kowa da sunan ya ye,sai babanta ne da ya dawo ya kwashi kayanta ya kai ma Inna da ya dawo ta tambayesa me Inna ta ce? Kai tsaye ya ce"Ta tambayeni dalilin yaye Ummi ni kuma nace ciki gare ki." Ai sai Mimi ta saka masa kuka kamar ya daketa ya fara fahimtar wannan cikin mai son rigima ne mgana kaɗan ko a waya ne sai ta fashe masa da kuka, tunda ya fahimci yanayinta sai ya koma lallashinta har suka rabu lafiya. Cikin uan'uwa Mimi ba wanda ya san tana da ciki sai yan Gombe ne da ya fito suka gani, Ita Mommy ta zo garin ta ga Mimi da ciki a gaba ta kama baki, suma yan'uwan Aji haka suka ganta da shi abun Allah kuma lokaci ɗaya ita da Bintu suna da tsohon ciki sannan itama Mariya na da ciki irin wanda ana zuwa a ke tutuɓe da shi a kofar ɗaki, kuma shima wannan cikin tun da wuri suka gama siyan komai Bintu ta rigata haihuwa An yi suna da kwana uku Mimi ta haihu, ta na fara jin naguda ta haɗa kayan haihuwa zuwa asibitin da take awon ta sannan ta kira inna ta faɗa mata sannan ta kira Hajiya kafin ma su zo ta na ɗakin haihuwa , wannan haihuwar dai ta ɗan sha wahala sai la'asar ta sauka wannan karon Namiji ta haifa baki mai kama da uban sak. Kwana ɗaya ta yi a asibitin suka maida ta gida, Aji sai dai ya ga hoton Baby boy da Mimi ta ɗauki hoto ta tura masa, Ya yi farinciki sannan ya yi godiya ga Allah jin Mimin tana lafiya tun da aka faɗa masa namiji a ka haifa Ya raɗa masa suna IBRAHIM, ita kuma Mimi ta na murnan a saka mata sunan Abi sai da ya dawo ta ji yana faɗin ya yi ma Jariri huɗuba da Ibrahiim,abun na ranta ya sa sai da ta furta masa shi kuma ya ce ai haihuwa yanzu suka fara ta yi kokari nan da wattani kaɗan ta kara samun ciki sai ta haifi Baban nata, Murgaɗa masa baki ta yi ba tare da ta yi masa mgana ba ganin kamar da gayya yake mata mganar, su khadi sai dai suka zo suna suna mai cike da mamakin daman Mimi ciki ne da ita? Shi ne ba su taɓa sani ba Mommy ce kuma da Hajiya su kuma ba su yi mganar da kowa ba, ko Rukky a bakin Aisha Ta Karamchi ta ji Mimi na da ciki ta kirata tana mata tsiya ta samu zuwa suna tunda daman wannan shi ne karon farkonta na zuwa ganin gida. Shima a sunan Ibrahim wanda za'a riƙa ma alkunya da Babangida, an yi abubuwa sosai kamar na sunan Ummi ma sha Allah, a haihuwan Babangida Aji ya siyama Mimi danƙareriyar sarka gold mai tsada a matsayin tukwaicinta. Sannan ya ce itama mota za ta biyo baya da yardan Allah. Mimi ta ji daɗin wannan kyautar sosai haka ta riƙa nuna ma mutane cikin jin daɗi. Haka dai mimi ta cigaba da jegonta wannan karon Baba uwani ne ta zauna da ita na sati biyu sai ta koma gidan Hajiya ita kuma daman ta iya ta cigaba da Kula da kanta da ƴayanta. Miji kuma sai dai su yi mgana ta waya Aji na neman ya ɓace ma ganinta saboda yanzu duniya ce ta san shi ba jiha ko ƙasa ba. Mimi na kula da yayanta gefe ɗaya kuma ta na kula da kasuwancin ta da yanzu sai habaka yake yi, Aji kuma na can Abuja sai ya samu lokaci zai zo ya ganta amman fa komai na bukatar rayuwa ya tanadar musu ba abunda take nema ta rasa kuɗin ta kuma suna account ɗin ta. Ba abunda ta ke siya in ba kyauta za ta yi ba,ko ta ga wani abun ta ke so za ta siya ko za ta siya ma yayanta. Rayuwrta take yi cikin kwanciyar hankali tun tana damuwa na rashin Aji a kusa da su ne har ta fara sabawa tunda ga ƴanuwa lulluɓe da su, ta gama arba'in ɗin Babangida Mariya ta haihu suka sha suna, Ta samu namiji an saka sunan baban mijinta Ahmad, Walida kuma tana kano sai sun samu hutu ta kan zo gida, Inna kuma daman ta saba zama ita kaɗai in kuma tafiya ta kamata ta rufe gida ta je ta yi zumuncinta, ko kuma wani lokacin yaran su Bintu na gidan suna ɗeɓeta mata kewa. Amman Ummi kan sai dai in tare da Mimin suka je gidan Aji ba mutum ba ne da kan bar yaransa su je wani waje hutu ba, ko da gidan Inna kwana in ya wuce ɗaya zuwa biyu sanda ta fi sati ma lokacin da ta yaye sati biyu ta yi da kansa bayan ya dawo ya je ya ɗaukota zuwa gida. Shi ba shi da ra'ayin irin haka ba wai domin yana da wani dalili ba ne. ****** *BAYAN SHEKARU SHIDDA* Bayan shuɗewar wasu shekaru kamar shidda. A ya yinda Mimi da Aji suke da shekaru goma da aure ƴaƴan su biyar Tunda Mimi haihuwan kusa kusa take yi bayan Babangida ta kara samun mace sai taci sunan Mommy, suna kiran ta da Batul,sannan ta kara yin mace mai sunanta sunan Hajiya kuma wato Fatima suna kiranta Fati ba sa mata alkunya, sai ƙaramin su mai sunan Mu'azzam shima ba sa masa alkunya, duka cikin shekaru goma Mimi ta haifi waɗanan Zzaratan ƴayan nata, tare da gwarzon mijinta Best Nigerian player Mansoor ibrahim Aji wanda ya shahara ya samu ɗaukaka ba iya kasar mu ta Nageria ba, ya kutsa kasaahen ketare sun buga wasa manyan kasaahen duniya ma sun kutsa sun buga cikin kwararun manyan yan wasan kwallon kafa, kama daga manyan manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasashen ketare sun yi wasa da su. Sannan sun ta kawo masa hari domin hayarsa ya koma turai buga wasa ya ce har Abada shi sunan shi Aji Ajin kasar ne shi ba Ajin turawa ba, shiyasa an kasa siyan shi ballantana ya bar kasar sa ya koma wata ƙasa. Sun buga easa tun daga Nation Cup da sauran manyan mamyan wasanin FIFA, a yanzu a kungiyar kwallon kafa ta ƙasa mai suna Super Ealges ba kamar ɗan wasa irin Mansoor Aji, tunda sannanun duk sun yi ritaya su Ahmad Musa, shi ne kuma ke rike da muƙamin Captain da ya samu wannan matsayin saboda shin ɗin Dodo ne a Filin wasa sannan ƙwararra ne wanda ya samu kyakyaawan ƙwarewa. A yanzu a Nageria Mansoor Ibrahim Aji ne fitattacen ɗan wasan kwallon kafa da ke kan gaba da kowa cikin shekaru kusan ashirin da ya kwashe ya na buga ƙwallo ya na da shekaru arba'in da huɗu a yanzu amman sai kace ɗan shekara talatin ne saboda hutu da jin daɗi da kuɗin da suka zauna masa, Mansoor Aji ya na da kuɗi da bai san iyaka ba, kwallo yake yi kuma ita ta raa masa. Duniya ce ta san shi ta dalilin kwallo ya taka kasaahen da bai taɓa tunani ba sannan ya buga wasanni da ƴan kwallon da a baya sai dai ya gansu a hoto. Bya samu cigaba sosai acikin shekara shiddan nan da ta gabata ya kai Baba Makka har da Magajiya ta je ta sauke farali, Sannan gidan wanzamai a garin gombe da ke anguwan arawa in kasan gidan a baya a yanzu in ka so ba za ka gane gidan ba, an buge shi an gyara shi zuwa na zamani har da katon get. bangaren Magajiya an haɗe mata har da in da Maeesha ta tashi a ka mata flat mai girma sannan itama Maeeshan can bangaren an haɗe mata na in da Inna ta tashi ya zama Flat mai girma sannan kuna bangaren su Gaje man an maida shi na zamani sai wanda ya gani, gidan ya fita dabam a anguwa saboda kyan shi sannan ya gyara masallacin kusa da su an yi masa bene ya koma na zamani, sannan matasa anguwa da sauran jama'a ya na taimakon su daidai gwargwardo ba ma iya anguwansu ba kaf kafatin Gombe da kewayenta suna alfahari da samun zaƙwaƙuri daga jihar su. Har can gidansu na mallam Sidi ya gyara ya maida shi na zamani Yalwa dai an gama jinya an koma ga Allah ya ba ma Baba karimu jari mai kauri yana kasuwanci. Inna kuma ta je saudiya sau biyu sannan ta je Umra, Mu'azzam ya samu karin girma an sake cilla shi kaduna shima yayansa uku, su Bintu kuma dukkansu suna cikin rayuwa mai kyau, Aji ya ba ma kowacce jari suna kasuwanci, Auwalu kuma ya zama babban Enginer har gidan kansa ya yi shi kuma Saddiqu na zama a shagon da Mimi ta buɗe na Abaya da Takalma da Jaka mai suna MIAJ STORE shima yana saida jallabiyan maza da huluna ba ta masa mugunta yana samu sosai ya na rufa ma kansa asiri. Aji ya siya mata sabuwar motar ya yi mai kyau sannan ya siya ta yara wacce ake kai su makaranta har Inna ya siya mata mota ya kuma ɗaukan mata direban da zai riƙa zirga zirga da ita, tsohuwar motarsa kuma ya ba ma Baba ita, mashin ɗin kuma aka siyar sai a siya ma baba Danlami da Baba Sani sabbi suna hawan su, babu wanda Aji bai taimaka ba adanginsu ba, Mu'azzam ma yana iya bakin ƙokarin shi. Tunda bai kai Aji samu ba shi da a wata yana samun sama da Miliyan albashinsa( ba ƙarya ba yan kwallo suna samun mahaukata kuɗi balle shi Aji da kasa ke alfahari da shi). Gidan gwammatin Gombe ba ya da shamakin shiga haka ma can Villa a garin Abuja, sannan ya zo ya na taimakon Gombe United camp din su, su zinder suma duk sun samu cigaba sai wasu ne eake cigaba da rain sannan har Coach ɗin su bai manta da shi ba alheri daidai gwardo yana yi masa. Shi dai burinsa matasa su cika burinsu, har Team na shi na musamman ya kirkira daga anguwan Arawa mai suna M.I AJI ARAWA TEAM, jaririya ce horar da matasa ake yi masu sha'awan ƙwallon kafa. Kaf ƴayan nan huɗu a gombe Mimi ta haife su, sai karamin su ne Mu'azzam ta haife shi a garin Abuja ko da yaushe Aji na kan hanyar zuwa ya gansu ko kuma in sun samu hutu su je ita da yara, Inna ta gaji da zirga zirga ta zaunar da shi ta ce ta yafe masa ya ɗauki iyalansa zuwa in da ya e zaune domin Mu'azzam ne ya gaya mata abunda ya sa Ajin ya ƙi maida Mimin can Abuja gaɓadaya, lokacin daman an maida ta Editer a ma'aikatansu na karamchi ta daina karanta labarai Office gare ta duk ta dalilin Aji domin kishinsa bai ragu ba, sai ma abin da ya karu, dole ta ijiye aikinta ta tattara ita da yara suka koma Abuja gida kuma sai megadi tunda in suka zo garin nan suke sauka har Mu'azzam ma yanzu ya mallaki gida an garin Gombe. Su Nasir ma duk sun samu cigaban rayuwa, amman duk da haka Aji bai manta da su ba ana tare har yanzu kamar baya sun zama manyan mutane sun girma sun yi 6aƴa girma ya kama su shekaru sun ja, A shekaran da ta Mimi ta koma Abuja suka je suka yi aikin Hajji tare da Aji a kuma wannan lokacin tana karatunta na Phd ta online a wata jami'a a america sannan gefe ɗaya ga kasuwaancinta yanzu kai tsaye take oder kaya daga India ko Dubai. Da kyakyawan takardunta da ƙwarewanta wajen aiki ta samu aiki a NTA Abuja matsayin News Editer again, burin Aji ya cika an daina nuno fuskarta ta daina karaɗe duniya ya zama shi kaɗai yake kallonta ya na jin daɗi, ya na nan faɗacin sa amman kuma rayuwa tasa ya rage wasu abubuwan sai mai hali baya fasa halinsa, kuma hausawa sun ce hali zanen dutse. sannan itama Mimi ta nan a yadda take yar gayu mai kyau domin ba ta amince ta bar jikinta ya lalace ko da yaushe cikin gyara take, tunda ta rike surayya dee mai gyaran amarya da uwargida ta zama tauraruwar mata a zuciyar Ajin ta.+234 803 277 3332 Nemi Surayya dee Bojuwa domin dacewa da sahihin kayan gyara. Sannan bayan haihuwan Mu'azzam ta so yin tsarin Iyali Aji ya ce bai amince ba dole ta haƙura, saboda in ma ta je ta yi wani abu ya faru ita ta sani. ƙaton gida Aji ya siya musu mai kyau da tsari duk da suna ɗan nesa tsakaninsu da Mommy ba ta damu ba tunda ai suna gari ɗaya a kallah dai ba za ta yi zaman kaɗaici ba. Khadi ma ta na can an zama uwar garke itama yayanta biyar Madiha ce yan boko ƴaƴanta uku ba ta kara ba, mataimakiyar shugaba ce ta kanfaminsu kuɗi sun zauna musu, Rukky ma yayanta biyu suna Lagos suna aikin su ita da mijinta Jaheed. Mommy sun aurar da Asma'au a garin Jigawa ita da Baba Alƙali, Walida dai ba ta yi aure ba ta samu jinkiri amman tana cigaba da Masters ɗin ta a kaduna state University KASU, ta na kuma zaune tare da su Mu'azzam har lokacin. amman ta samu miji anan kaduna tare suke masters ɗin su har yazo gida manyan sun shiga mganar. Hajiya kuma ta na nan da ranta tsohuwa ce mai ran ƙarfe. Daddy ma rayuwa ta inganta hankula sun kwanta duk da ba dari bisa dari ake samu ba amman an gode ma Allah tunda daman ba lalle sai ka samu abin da kake so ba. Mimi sun shekara a Abuja Gombe sai dai sallah ko wani abu ya faru. zuwan su na karshe sun je sallah sun dawo saboda makaranta yara, fati ne kawai da Mu'azzam basa makaranta Ummi yar primary 2 ce sai Babangida 1, sai batul ta na Nursery sectiion ne, itama bayan sun dawo Abuja ne a ka saka ta tare da su Ummi a makaranta mai tsada ta ƴaƴan gata. A shekaran da ta shiga ne za'a buga World Cup kuma Nageria tana ciki ana ta shirye shirye wannan shekaran a Agentina za'a buga ƙwallon duniyan gabaɗaya. ****** *MURFI.* _ABUJA, 99POBOX MAITAMA._ *202....* Gidan na su Mimi cike da baki mutanen Gombe da mutanen kaduna har da ma Abujan gabaɗaya.Saboda ta ya murna ga ɗan wasan kwallon kafa ta kasa wato MANSOOR IBRAHIM AJI bisa nasaran da suka samu na hayewa matakin karshen na cin kofin duniya sai dai sun ci ɗaya kodubuwa suka cire su amman duk da haka Nageria take murna da alfaharin wannan nasara da suka samu, tun suna can Argentina murna ya zagye kasa baki ɗaya yau jirgin su zai sauka, kuma walima ce Mimi ce ta shirya Aji bai ma san da ita ba. Mu'azzam da matarsa Hibba da Yayansu sai Nasir da Makama da Ahmad duka da matansu da yayansu, su Binti su Yaya Amina Inna ce kaɗai ba ta zo ba su Auwalu da matan su har da Saddiqu, Khadi ita da Mijinta da yayanta har da Dr tare da Jawahir suma da yayansu su Madiha ne kaɗai da Rukky suna can Lagos ba su taho ba amman suna ganin komai a waya. Gida ya cika manyan mata suna gefe suna hira mazan ma suna yin na su na dabam yara kuma suna ta wasannin su duk abin da za'a ci a sha duk Oder su suka yi an riga ma an kawo an gabaɗaya gidan an cika shi da Bloon da fulawas da kuma wani katon Allo an rubuta WELCOME BACK CAPTAIN MANSOOR AJI. Wani kuma an rubuta CONGRALATULATION OUR NIGERIAN CHAMPION. Wani kum an rubuta ISSE GOAL AJIN FROM NAGERIA. Kuma a tsarin nasu da yara ne su Ummi da Junoir za su jere a layi da symboll ɗin in ya iso so zuwa tarbansa amman kuma sai ya ce sai sun fara biyawa ta gidan Shugaban kasa tunda shugaban kasan da kansa da wakilan gwammati za su tarbesu sai suka hakura amman suna gida suna ganin komai a kafafa sada zumumta suka ga saukan su ga Aji nan sanye da riga fara mai ratsin green da fari haka wandon ma mai ruwan ganye sun sauko suna rike da tutar Nageria bakinsu har kunne amman ban da angon Fatima fuskar nan ko da yaushe dai kamar yadda kowa ya sani,suna tashan yabo da addu'o'i kuma ma abun alfahari kwallo ɗaya nan ma da suka ci Aji ne ya samu nasaran je fa ta a raga. Sai ki ka ga kasa ta ruɗe da kirarin AJI IS A GOAL ko Mimi ma haka ta saka a status ɗin ta bayan ta saka hoton shi da ya tura mata a can Argentina ɗin tunda Nageria ita ce ta yi na uku sun dawo tare da kambun girmamawa . Tun suna saka ran ganin shi da wuri har su ka cire tunda har dare bai iso gida ba. Hatta Mommy da Baba Alƙali suna gidan suna jiran dawowarsa Amman sai bayan sallar isha'i a ka rakosa gida da jama'a da Security, ya na shigowa get sai Abu ya fara tashi da farko duhu ne ya mamaye ganinsa Yana shigowa suka kunna wutar gidan gabaɗaya a ka fara waƙan AJI IS A GOAL NAGERIA IS A GOAL NAGERIA IS THE GREAT AGAIN." Gabaɗaya bakinsa ya ki rufuwa kayan ƙwallon nagerian ne ko a jikinsa, bai sauya ba abun da ya ba shi mamakin ganin duka yan'uwansa a waje ɗaya suna masa tafi, sai ga su Ummi sun jere a gabansa su Fati kuma suna jan wata igiya Bloons suka cika haraban gidan gabaɗaya. Aji ya na dariya da mirmishi lokaci ɗaya bai sani ba ya tsaya kawai ya kasa motsi. Yana ta saka ido ko zai ga Mimi maman Maryama da Ibrahim, amman bai ganta ba sai da suka gama wakarsu sannan suka haɗa bakin wajen faɗin" Congratulatoon Aji In sha Allahu nan gaba kai za ka ɗaukan ma Nageria kambun nasara." Ya na ta mirmishi ya kasa mgana Mu'azzam ya je gare shi suka rumgume juna shi sannan ya dago ya na dukan kafaɗansa Lokaci ɗaya yana fadin" Thanks Bro." Haka ma su Nasir ke rumgumansa ɗaya bayan daya suna gaisawa, har da Baba Alƙali ya na neman ya ramkwafa ya gaishe shi ya hana shi ta hanyar kai masa rumguma yana faɗin"Congratulation Son in low" ya amsa ya na mirmishi Dr ma ya kariso shi da Muhammad duka rumgume juma matan kuma ya karisa ya na kiran sunayensu su kuma suna gaishe shi, Mommy kuma ya duka ya gaisheta ta amsa tana faɗin"Sannu Allah ya sa albarka muna alfahari da kai." Shi dai har lokacin bai ga Mimi ba kuma ya kasa mgana sai ya koma yana ɗaukan yara bayan ɗaya ya na dire su, Ummi ta maƙale sa tana faɗin"Abba.." Shima ya ɗaga ta sama yana faɗin"Uwata ta fi ta kowa." Ammin ɗin Mu'azzam ta tura baki kafin ta ce"Abba har da ni m maman taka ta fi ni? Ta faɗa cikin shagwaba gabaɗaya a ka saka dariya ya juya ya na kallonta sauke Ummi ya yi ya ɗaga ta sama yana faɗin"Haba Mamana ai ba wata sai ke? Sai ta washe baki kafin ta ce"Yauwa ka daina ce ma Ummi ta fi kowa." Yana dariya yac e an gama Inna, Babangida kuma sai ya fara jan kafarsa yana faɗin"Abba ni ba ka ɗauke ni ba? Ya faɗa ya na wani haɗe fuska, domin kamar yadda ya ke kama da Aji a hallita haka ya diɓo hallayansa na zuciya da baƙin rai tun yana karaminsa. Dole ya sauke Ammi ya ɗauke shi yana fadin"My photocopy, My Baaba.." Haka ya faɗa ya na jan kumatun Babangidan domin ya saki fuska, amman kuma ya ƙi sakin fuskar, sai ma wani ƙara dakuna fuska da ya yi, Nasir na dariya yace"Kamar uban kamar ɗan." sai abun ya koma gasa ga gajiya a tare da shi sai da Mu'azzam da su Nasir suka zo suka raba shi da yaran sannan suka dumguma cikin gida Zuciyarsa na son sanin inda matarsa ta shiga .ya dai san ta tura masa wani gigitacen sakon da ya ke jiranta da safen nan, ta san haknee ta ɓoya ma ganinsa Ahalin da kishin ruwanta ya dawo? Suna zuwa falo nan ma wani Decoratoin ɗin ne Aji na dariya ya ce"Lalle yau rana ta ce." Sai ya juya yana kallon su Nasir kafin ya ce"Ni na ga kowa amman ban ga matata ba, ina ta ke ne? A hankali ya yi mganar, shi kuma Nasir da karfi ya ce" kana da rawan jiki ai za ta fito kuma za ka ganta" Kunya yaji ganin har da su Mommy a wajen,sun zazzauna kenan Junior ya ƙi zama ya koma gefe ya harɗe alamun kamar ya yi fushi Bintu ta kira shi amman ya ki jin ta, sai Aji ya kalle sa kafin ya ce"Junior ta ho ka zauna mana" Ya wani ƙara bata rai kafin ya ce"Abba ni ka ga kowa amman kamar ma ka manta da ni Alhallin kuma ni nre zan ga je ka na zama ɗankwallo." Ya faɗa ya na nuna rigan jiknsa, ta Jc na ƴan kwallo gabadaya falon a ka ɗau dariya shi kuma sai ya kara fusata dole dai Aji ya mike ya je lallashi har ya hakura,.Shi ya yi masa raɗa a kunne ina Anty Mimi sai ya ja hannunsa ya ce bari ya kaisa wajenta afalon ba wanda ya bi ta kansu suna ta hiransu har suka shige ciki kowa ya bi su da kwallo suna kunshe dariya. Junoir na shigar da shi Bedroom ɗin ya kulle kofar kamar yadda a ka basa umarni ya dawo falo yana dariya .Bedroom ɗin duhu ne amman sai tashin kamshin turare, ba ya iya ganin ko tafin hannun shi amman ya na jin Nlnumfashin Mimi a ɗakin.. "My jan kina ina ne? Kinsan idanuwana ke kaɗai suke mararin gani don Allah ki fito na ganki kafin na suma saboda zullumi." Wal hasken ɗakin ya kawo. Yanaa juyawa baya ya ga kyakyawan matarsa da ba ta tsufa a idanuwansa ta ci riga da wando na White an Green bai taɓa mantawa shi ya kawo mata kayan ta tsuke har da p. Cap ta yi wani irin tsayuwan gayu har da farin takalmi covrer mai igiyoyi, galala ya tsaya yana kallonta ta ɗauro ga shinta ta baya har tsayuwan da ta yi abun kallo ne da sha'awa. Mirmishi ta sakar masa sannan ta ɗaga Hannunta sama ta zana love da hannunta duka biyu, sannan ta hura masa iskar Love ɗin zuwa gare shi lokaci ɗaya tana faɗin" WELCOME BACK AJIN MIMI." Jikinsa har wani rawa yake yi wajen nufarta, kafin ya matso ita ta yi gudu ta faɗa jikimsa suka wani irin rumgume juna kamar za su maida junansu ciki, yana faɗin na yi kewarki Mimi ta na faɗin na yi kewarka Aji na, shinshinta ya ke yi saboda kamshin Turarenta ita kuma sai raɗa masa wasu zantuka take yi da suka susatar da shi ya nemi ya birkice mata dakyar ta kwace jikinta ta tura shi Tiolet ta tuɓe sa ta yi masa wanka karshenta itama cikin shower ya jawo ta, dole kafin a yi wannan wankan sai da a ka yi ta shagali da love sannan suka sake wanka suka fito suka kuma shirya a tare shi ya yi shigar shadda mai ruwan kasa har da Babban riga ita kuma ta saka lafaya a saman atamfar da ta saka, shi a koƙarinsa ya na son kaɗaicewa da ita, ita kuma tana gaya masa suna da baki a falo haka nan ya hakura suka fito falo sai tafi ya tashi khadi da Bntu suka rangaɗa guda, Hibba ta ce"Barka da fitowa Mr and Mrs Ibrahim Aji." Suna ta fama mirmishi nan fa aka ba za manyan dardumai a tsakiyar falo a ka zauna nan fa su Bintu suka fara kai da kawo da abincin da snaks da nama, kaza tsire da sauran a baben sha ci, Walima ce ta Family domin taya sa murna Mimi ta haɗa a ka ci a ka sha ana ta hira da raha,bayan an gama an yi hotuna duk da dai dare ne da vedio bayan an gyara in da aka ɓata suka yi shirin tafiya gidan Mommy gabaɗayan su matan mazan kuma a Hotels za su kwana sai ga shi Aji na ba da umarnin har yaran gabaɗaya a tafi da su wajen Mommy yana bukatar hutu ne. Nasir ya kallesa kafin ya ce"To Allah ya sa hutawar da gaske za ka yi? Hararansa ya yi har yana ta ka masa kafa, Su Bintu suna dariya suka tarkata yaran har da Mu'azzan ƙarami, Akwai motoci ga direban yara har da shi a ka kira ya zo duk ya kwashe su sai gidan ya yi shuru. Suna tafiya tun a falo Aji ya rike Mimi yana faɗin"Ki cika alkwari Mimi, ke fa kika ce min kin cika makil da ruwan ni'ima ni kawai kike jira." Gira ta ɗaga masa lokaci ɗaya tana kai hannunta wani wajen ai sai ya ƙara gigicewa dakyar ya bari suka isa bedroom suka faɗa kan gado, sai ka ce daran amarci sannan suka yi watsi da kayan juna. Kowa na nuna yadda ya yi kewar ɗan'uwansa. Sai da suka samu natsuwa sannan suka yi wanka, suka koma suka kwanta akwai gajiya a tare da shi ya sa ta zauna tana masa tausa yana jin daɗi idanuwansa a rufe ya ce"Allah ya yi miki albarka Fatima Fatima mai zogale." Ya faɗa cikin sigar waƙa ita kuma tana dariya, bakin ta har kunne farincikinta anan duniya ya gama samuwa. Auranta na shekara goma ta fuskanci ƙalubale ma su yawa da za ta ba da labari, ta kuma samu cigaban da za ta iya faɗa, tunda ga shi ma anan Abuja ma tana shirye shiryen buɗe wani shagon kaya take yi,sannan a bangaren sanin menene aure duka za ta iya mgana a haka sannan a bangaren sanin hallaya maza ma za ta ce wani abu, Ita za ta iya dukan kirji ta ce aure na da daɗi sannan in ka yi dace aure rahama ne sannan farinciki ne abin da ya fi daɗi irin ka ga mijinka tare da yayan da Allah ya baku tare, bayan duka gwagwarmayan da a ka sha a baya an fahimci juna ana zaune cikin farinciki in akasasin sa ya samu sai a yi hakuri da juna, ta fahimce shi ya fahimce ta sai kuma suka gina zaman su cikin yarda da Amana, duk da zamantakewa daman zo mu zauna ne zo mu saɓa, balle ita irin mijinta amman Alhamdulillah, Aji ya canza a cikin kaso mai yawa na hallayarsa ya sauya wasu saboda samun daidato da Miminsa. "Tunanin me kike yi? Aji ne ya katse mata tunani, kuma kafin ma ta ce wani abu ya saka hannu ya jawota jikinsa lokaci ɗaya yana faɗin" In har ina kusa da ke, har abada baki ba tunani in dai ni ne kin samu har gangan jiki ba ma kan ba." Mimi sai mirmishi take yi cikin kunya shi kuma yana sake mata raɗa a kunne ta na zillewa, blanket ya ja ya rufe su gabaɗaya lokaci ɗaya yana faɗin"Mu shiga cikin nan Fatima ta ba ni zogalen ta mai ɗan karan daɗi." Suna ta kyatatan dariya, Mimi ta ƙamkame Aji a cikin zuciyarta tana faɗin"Bismillahi da Alhamdulillahi duka a lokaci ɗaya." *Tammat bihamadulillah* *Nima na fara da Bismillahi zan ƙarƙare da Alhamdulillah. Nan na sauke alƙalamina daga rubuta labarin IDAN AN CIZA. Abin da na rubuta dai dai Allah ya haɗamu a ladan gabaɗaya, kuskuren dake ciki Allah ya yafe min, wataƙila akwai abin da bai yi muku ba, to ku yi hakuri akwai ajizanci na ɗan adam duk yadda naso na yi komai ɗari bisa ɗari ba zan iya ba, dole za a samu kuskure ta wani bangaren. Na gode kwarai bisa soyayyar ku gare ni, na gode bisa yadda kuka yi tururuwa wajen siyan wannan labarin Na gode kwarai Ubangiji ya yi albarka Amin.