BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM KURKUKUN ƘADDARA TAKUN ƘARSHE 🔥 LABARI DA RUBUTAWA HAFSAT BATURE MUHAMMAD 🌹✍️ Kada ku manta da ni, Ina barar addu'ar ku, Aduk lokacin da ku ka buɗe document ɗin nan, ku taya ni da addu'a, Ko wace kalace indai ta fatan Alkhairi ce Inaso, Sannan Littafin nan Na kuɗine, da gumina na rubuta shi, Kada ki ɗauki haƙƙin wani akanki/ka, In kasan baka Biya ba, Ka hanzarta biya ka karanta halal din ka👍 Gargaɗi da jan Kunne kar a kuskura A canzamun wani abu na Littafin nan, ko da harafi ne ta kowace siga ban amince Ayi amfani da shi ba, ina da lawyer na da kuma wadanda zasu kwatar min haƙƙina, ku ji tsoron Allah, kuma kuji ta6a hakkin da bana ku ba 👍 GA ME BUKATAR MALLAKAR KURKUKUN ƘADDARA COMPLETE 1,2,3,4, ZAI BIYA NEW PRICE DIN SHI NA YANZU 700 NE VIA FIRST BANK, ACCOUNT NUMBER 3196407426 ACCOUNT NAME BATURE HAFSAT MUHAMMAD, ZA'A TURO SHAIDAR BIYA TA WHATSAPP A TUNTU6I NUMBOBIN NAN KAITSAYE👇 08103884440 KO 08169856268. 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~<><><><><><><><><><><><><><>< DAGA ALKALAMIN HAFSAT BATURE MUHAAD✍️~ ~___________________________________~ Sheikh Imam Malik Shahararren malamin addinin musulunci ne, kuma babban alkalin Kotun Musulunci, Haifaffen jihar jos ne, wayayyen malamin addinin musulun ci ne kuma dan boko maiji da kanshi, ga wadatar arziki da Allah ya yi mashi, sheikh Imam ya yi suna wajen yin adalci, rukon amana tausayi da jinƙai, yana da ƙwarewa ta fannin shari'ar musulunci, mutunne shi mai tsastsauran ra'ayi akan addininsa, kuma kaifi ɗaya ne In ya furta magana baya canza ta, da dama mutane masu aikata mugayen laifuka suna jin tsoron shari'ar sheikh Imam Malik saboda sun san Halinsa baya kar6ar Cin hanci, dole mutun Ya kar6i hukunci dai dai da abunda ya shuka ko ɗan uban wanene, sannan yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, sai dai duk da hakan Yana da sauƙin kai ga wanda ya iya zama da shi. Matarsa Ta farko Malama Fatima Batool wadda ta kasance Yar uwarsa diyar wan mahaifinsa mazaunin Sudan, Auren zumunci iyayensu suka haɗa su, Kuma cikin Ikon Allah jininsu ya haɗu soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu har takai su ga yin aure, Sunyi zama Na amana saboda Ra'ayinsu yazo ɗaya, Yaji dadin zama da ita saboda kyawawan halayenta, tanayi mashi biyayya sau da kafa, A lokacin data samu ciki yayi murnar da bazata misaltu ba, baya gajiya dayi mata addu'a akan Allah ya sauke ta Lafiya, bayan data haihu ne ta koma ga Mahaliccinta yayin da tabar masa Yar jinjiran da ta haifa masa, Shiekh Imam Yaji rasuwar ta, duk irin juriyarshi da tawakkalinsa sai da ya zubda ƙwalla saboda babban rashin da yayi. Rainon yarsa ya koma hannun gwaggwansa kanwar Mahaifiyarsa, A lokacin iyayensa duk basa araye, itace ta kula masa da Yarsa Har ta dan fara tasawa. daga bisani Kawunsa na sudan ya bashi auren kanwar Matarsa Aunty Laura, a wani zuwa da yai sudan kai masu ziraya, A lokacin sheikh imam baida niyar ƙara aure saboda bai warke daga radadin rasa matarsa da yayi ba, amma saboda aunty laura ta kasance Jinin Malama Batool yasa shi amincewa da aurenta. Bayan auransu da wata daya Rainon Aisha ya dawo hannun Aunty laura, ta rike ta da amana kamar yar cikinta, tana bala'en Son Aisha, saboda jininta ce ita uwa uba kamanninta sak dana Yayarta Malama Batool, saboda yadda take bata kulawa ba zaka taba gane ba yarta bace sai an fada maka. hakika sheikh imam malik yayi namijin kokarin gurin tarbiyantar da rayuwar yarsa, ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, gaba daya halayanta da dabi'unta irin nashi ne, abu daya da bata ɗauko na shi ba shine Zuciya, tana da tsantsar hakuri kamar Mahaifiyarta Malama Batool, hausawa sukace kyan ɗa ya gaji ubansa itama hakan ta ke Aisha tagaji mahaifinta da kuma mahaifiyarta malama Batool. Sheikh Imam ya ɗaura mata burin duniya, Bai taba son wata aba kamar yarda yaso Aisha ba, ita kadai ce ƴa daya tilo da Allah ya albarkace shi da ita, Babu irin gatan da sheikh Imam bai yi mata ba. Aishatu macace mai cikar kamala, mai tsantsar kamun kai, samun matashiya mai irin baiwar ilmin da Allah ya bata zaiyi wuya a fadin duniyar nan, ta haddace alkur'ani mai girma tun tana da shekara goma sha uku a duniya, mutane dayawa suna yabonta saboda kyautatawarta a gare su, kyawawan dabi'unta da halayanta abin koyi ne ga duk wata ya mace, kuma burin kowani namiji ne ya mallaki mace kamarta. duk wani abu da zai sabama Mahaliccinta gudun shi takeyi, tana da jinƙai da son taimako bata gajiya da hidimtawa addininta. Abun burgewa iyaye mata da matan aure suna karuwa da ita, also she's a role model for young women. tun tana yar matashiyarta take koyawa a islamiyar Mahaifinta mai suna madarasatul Fatima Batool dake a kusa da gidan su, tana yin wa'azi ta kuma yi da'awa ga waɗanda basuyi imani ga Allah ba, ta dalilin Aisha, Sheikh imam malik Ya samu daukaka fiye da zaton shi, ta kare mashi martabarshi da kirmarshi ta kuma daukaka darajar shi a idon duniya, sau dayawan lokutta baya sanin tayi wani abun, sai dai akira shi awaya ko azo har gida ayi mashi godiya akan alkhairin da Aisha tayi, yai ta mamaki farin ciki ya cika shi, sai ya kirata ya tambayeta me tayi tukunna take fada masa Alherin da take samu a gurin Gasar karatul al'qur'ani da wadanda mutane suke bata kyauta saboda dadin wa'azinta da suke ji, dama A duk lokacin da ta kawo mashi kudin don ya dauki wani abu baya kar6a, kudinne take tarawa in suka taru dayawa da su take amfani gurin tallafawa marasa karfi, tana yawan ziyartar asibitoci, gidajen yari, da gidajen marayu ta basu tallafin kayan abinci da suturu in kuma bata da kudin da zata basu zatayi masu wa'azine da nasiha mai ratsa zuciya, shiyasa sheikh imam ya ke bala'en ji da Aisha, yana matukar son Yar shi, itama bata da abu mafi soyuwa dayawuce Mahaifinta, tana yi mashi biyayya sau da kafa, batason bacin ran mahaifinta, tana kokarin yin duk wani abu da zai faranta ran shi. Dangantar da ke a tsakanin Benazir da Ayshah da Dr shureim ta samo asali ne tun daga kan Iyayen su Maza, Sheikh Imam malik baida amini daya wuce Alhaji ubaid Wadata sun kasance makwabtan junane, Gidansu Yana a jikin na juna, Akwai zumunci mai karfi a tsakanin Iyalansu, atare suka taso tun kuruciya, kasantuwar Alhaji ubaid Dalibin Mahaifin sheikh Imam ne agurinsa yake ɗaukar karatun addini kafin Allah yayi masa rasuwa, Alhaji Ubaid dan babban Gidane, Family dinsu yayi shura A jihar, saboda Arzikin Mahaifin su marigayi Alhaji mu'azzam wanda akeyiwa lakabi da wadata babban dan kasuwane a zamaninsa. Benazir da Aisha Ƙawayen junane kuma aminnai tun kuruciya, atare suka taso kuma atare su ka yi primary da secondry a makarantar Sheikh Imam Malik wadda Har Islamiya ake koyawa a cikin ta, abun da zai ɗaure ma kai, kwata kwata halin Aisha dana Benazir baizo daya ba, sun sha banban, Benazir tana da girman kai, rashin kunya kuma bata iya shigar mutunci ba, duk suturar da zata sanya sai ta matse jikin ta. Sarai Sheikh Imam yasan da Halin Benazir Ya kuma san Gado tayi agurin Hajiya layla, mutane suna yawan kawo mashi tsegumi akan ya raba yar shi da Benazir In ba haka ba zata bata masa tarbiyar ƴa, Bai ta6a ɗaukar maganarsu ba, saboda Shi ya yarda da tarbiyar daya ba Aisha yasan bazata ta6a bari Benazir ta rinjaye ta ba, sai dai ita ta rinjayi Benazir gurin karkato da hankalin ta don ta shiryu, bayan hakan Yayi Wa Benazir farin sani, Yasan Bata Jin magana kuma bata da kunya sai dai ita din ba Yar iska bace, bata shaye shaye, bata bin maza, Rashin ɗa'arta abaki ne da kuma yanayin Shigarta, sai kuma yawon gantali da take fita a kowani dare ne sai taje Night club, gata yar hana biki maraici, kuma zabaya ce a fagen rawa, amma Sheikh bai ta6a gigin raba ƙawancen su ba, saboda yana son duk wani abu da Aisha ke so. bayan haka baya son abunda zai raba zumuncinsu da makwabtan shi. Wadannan dalilan ne suka sa Shiekh imam Ya amince ma ƙawancen Aisha da Benazir, Amma sai da ya gindaya mata sharudda akan bai lamunta tadinga fita yawo ba, kulle ya ke mata daga makaranta sai gida, In har zasu hadu da Benazir sai dai tazo gidan su, Ko kuma In Aunty laura zataje gidan gurin Hajiya layla ta tafi da ita, sai kuma in sun haɗu a school, amma sam bai yarda ta dinga bin Benazir suna fita yawon gantali ba bayan haka ya hanata kula kowani saurayi saboda akwai wanda yake burin ta aura har sa'insa su ke yi da Aunty laura akan ya hana Aisha kula samari ita ta rasa gane ma manufarsa akan Aisha kamar ba yar cikinsa ba, maganganu marasa dadi take fada masa bai ta6a biye mata ba. Aunty laura wayayyiyar macace Yar boko kwararriya ta fannin business, ta inda suka sha banban da Imam ita tana da karancin addini akai, kwata kwata halinta ba irin na yayarta mariganya Batool bane, shiyasa basu jituwa da sheikh imam malik, sa'insa suke da junansu saboda ta tsani yadda yake zafafawa akan addini kuma A ganinta kullan da ya ke yi ma Aisha takura ce. shi kuma yanayi ne saboda Farin jinin da Allah yayi mata, Babban abunda Ke ci mashi tuwo a ƙwarya yadda wasu mazan basa iya kau da maitarsu akan Aisha, saboda Dirin da Allah yayi mata, tun tana ƙanƙanuwarta wani irin dirin jiki ne da ita mai jan hankali, duk taku daya idan tayi sai jikin ya girgiza koda kuwa ta sanya dogon hijabi ajikinta ne sai shatun dirinta Ya bayyana wani irin farin jinin samari gare ta kuma mafi akasarinsu ba don Allah suke son ta ba sai don kwaɗayin Surar ta. wannan dalilinne yasa shi tsananta mata tsaro ko fita za ta yi dole ta sanya dogon hijab da niƙab, daga makaranta sai gida makarantar ma shi ke kai su da kanshi In an tashi ya dauko su ita da Benazir, wani sa'in In aikin yayi mashi yawa ko zaiyi zaman shari'a Aunty Laura ce ke dawainiyar kaisu wani lokaci in ta samu damar dauko su daga school in an tashe su sai ta saci hanya takai su Shopping mall tayi masu siyayyar kayan amfanin su na mata. Awata rana ne Aisha tana a zaune kan darduma sai ga Benazir ta shigo gidan da rawar jiki ta shigo har dakinta ta ruko hannunta da farin ciki take fada mata tazo taga Uncle musa da Yaya shureim sun dawo Nigeria, kasantuwar su dukansu A lokaci ba mazauna Nigera bane, Shi Alhaji musa harkar kasuwancin shi yakeyi a kasashen ketare yayin da Shureim ke karatu a kasar egypt can gurin ammin su ya ke da zama. da fara'a Aisha tace meyasa bata fata mata ba, Benazir tace kawai tana son tayi suprising dinta ne, cike da farin ciki tace ta jira ta a falo zata shirya, Benazir na fita daga dakin Aisha ta soma shirya kanta cikin abaya, sai ga Aunty laura ta fito daga daki ta iske Benazir zaune kan sofa, da fara'a suka gaisa da juna har ta tambaye ta meya sanyata farin ciki nan take fada mata yaya shureim da Uncle musa ne suka dawo Nigeria shine ta zo don ta fada ma Aisha, washe baki aunty laura tayi tana fadin Ah lallai manya manyan baki, shine ba'a fada min ba? tana cikin magana sai ga Aisha ta fito sanye da dogon hijab hada nikab akan fuskarta. fuska adaure Aunty laura tace kefa matsalata dake kenan, kamar kinfi kowa tsoron Allah, kullum cikin nikab, yanzu nan da gidan makwabtan namu sai kin saka hijab da nika..." a karshe ta korata daki tace taje ta sako Mayafi..da damuwa tace ita bazata iya ba, saboda hijab mutuncin ya mace ne, bayan haka baba ya hanata fita ba hijabi har ta soma janyo mata aya, aunty Laura ta mike rai a6ace taja hannunta suka koma daki, adole saida ta tursasa ma Aisha ta saka Wani guntun veil a kafadarta, baiwar Allah duk sai taji ba dadi ganin yadda abaya din ta ɗame jikinta, dirinta nan nata mai jan hankali ya bayyana muraran musamman ta gurin mazaunanta sun fito rudu rudu.. ahaka Banezir taja hannunta suka tafi gidansu, shigarsu keda wuya ta gate din adai dai Lokacin Alhaji musa Yana atsaye gaban dankareriyar motarsa ya dauki wankan shadda hannunsa ruke da waya, kallo daya da Aisha tayi mashi saida gabanta ya fadi saboda ƙwarjinin dake gare shi, wata irin kirar jiki gare shi irin ta yan dambe. Benazir ce ta gabatar mata da Uncle dinta, duk irin izzar Alhaji musa da yayi tozali da Aisha saida Ya rasa nutsuwarsa saboda shi irin mazan nan ne masu kwadayin mace mai kyawun sura, sanin da yayi mata tuntana karamarta yanzu kuma ta girma, wani irin kallo yadinga binta da shi harya kasa amsa gaisuwar da ta ke yi mashi, A lokacin rudewa Aisha tayi saboda bai kwanta mata arai ba, musamman da ta ga hakoransa ya sanya masu Gold-plated teeth.. ita kanta Benazir ta lura da yanayin da ya shiga. Hakan yasa taja hannun Aysha suka nufi cikin gidan, Uncle musa yabi bayanta ta da kallo yanayin yadda take tafiya jikinta na girgiza ba karamin tayar masa da maitar sha'awarsa tayi ba, kuma tun daga lokacin ya kudiri aniyar saiya mallake ta. Bayan sun shiga babban falon gidan, anan suka iske Hajiya layla tare da Alhaji ubaid suna zantawa tsakaninsu, bayan sun gaishe dasu hajiya layla tace su shiga ciki su gaida shureim.. Tun da Allah Ya Halicci Aishatu Bintu Imam bata ta6a ganin mutumin daya kwanta mata aranta ba, da kallo ɗaya ta fada tarkon son shi sai akan dr shureim yanayin da suka same shi adakin shi yana zaune kan darduma Ya buɗe al'kurni yana karatu cikin nutsastsiyar Muryarsa ba karamin jan hankalin ta yayi ba, tayi mamakin girman daya ƙara tsawon shekaru a lokacin rabon shi da Nigeria. Sai da yakai aya, cikin sanyin murya yace masu su shigo yaga sun yi tsaye bakin kofar dakinsa, Jan hannunta Benazir tayi suka zukunna agaban dardumarsa ta gabatar masa da aminiyarta yar makwabtansu diyar sheikh Imam, ganin kamar bai gane ba don tun suna kanana Yabar Nigeria, Aisha ta gaishe da shi tare da yi mashi bangajiyar tafiya, da murmushi akan fuskarshi ya amsa mata, abunda bata sani ba Dr shureim yasan da zamanta, Yana yawan sauraron kira'arta da take yawanyi a taron musabaka, wanda mutane ke yaɗa videon a social media amma saboda miskilancinshi sai ya nuna kamar bai gane ta ba. sun ɗan jima Yana jan su da fira, lokacin da ta tashi tafiya dr shureim ne ya yi mata rakiya tare da Benazir har kofar gidansu, saida suka ga shigarta kafin suka koma gidan su. a daren ranar Alhaji musa Ya kira Benazir ya soma tambayarta dangane da Aisha, ko tana da tsayayyan da zata aura"? Benazir tayi mamakin tambayoyinsa saboda tasan Uncle din nata mugun miskiline bai cika shiga sabgar da bata shi ba, In fact mata basa agaban shi bata kawo komai aranta ba ta fada masa komai dangane da Aisha, Hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba jin cewa bata kula samari, fargabansa daya Sheikh Imam malik saboda basa ga maciji. A bangaren Aisha tun bayan data koma gida tunanin dr shureim Ya hana zuciyarta sukuni, Kwana take da shi aranta, haka zalika in tana koyama dalibanta karatu wasu lokuttan shagala take da tunaninsa har sai daliban su ankarar da ita. ta bayan fage Uncle musa ya fara ba Banezir makudan kudi masu auki don suje yin siyayya da Aisha, kuma yace mata baya son Aishar ta sani, Benazir bata ta6a fada mata Uncle musa ne ke bata kudi ba, Sai ma in ta tambayeta ina take samun kudi sai tace dr shureim ne ya bata, hakan ya sa ta saki jiki duk da bata da kwadayin abun duniya tayi azan yaya shureim yana son ta ne shiyasa yake ba Benazir kudi don suyi siyayya. kusan kullum sai Aunty laura tayi masu hanyar fita daga gidan batare da sanin Shiekh Imam ba, don suje Mall suyi siyayya harma da yawon buɗe ido koda Aisha ta nuna bata son fita Aunty laurace ka tursasa mata in ta turje sai ta fashe mata da kuka tana fadin bata mata biyayya saboda ba ta ɗauketa uwa, don taga ita bata haihuwa, in ta fadi hakan jiki na rawa Aisha take bin Umarninta. Tun bata sake ma Uncle musa in suka haɗu harta fara sabawa da shi, tana matukar girmama shi tanayi mashi kallon Uncle dinta. Haka zalika shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da dr shureim, Benazir tayi mamaki saboda sanin da tayi ma Aisha bata Kula maza sai gashi dr shureim ya ciri tuta, sun saba da juna, Benazir ta sanya masu ido sosai, Ta fahimci dukansu suna son juna, ita Aisha Kunya ce ta hana ta furta mashi Kalmar so, yayin da shi kuma miskilanci ne Ya hana shi bayyana mata, bayan haka Yana jin nauyin yayi soyayya da Aisha saboda yanayi mata kallon Kanwarsa. A duk lokacin da Benazir taso Ta bugi cikin shureim don ya fada mata In yana son Aisha sai yace mata shi babu soyayya atsakaninsu kallon kanwa ya ke yi mata, haka In ta bugi cikin Aisha don taji in tana son ya shureim sai tace mata ita fa ba son shi ta ke yi ba, kawai tana yi mashi kallon yayanta ne saboda zumuncin dake a tsakaninsu, In Benazir zata shekara tana tambayarsu amsa daya suke bata. Bayan da suka kammala Secondry School, Alhaji Ubaid ya sama masu admission a wata Jami'a dake a birnin hagen na kasar Jamus batare da sanin sheikh Imam Malik ba sai daga bisani ya same shi har gida ya sanar da shi. shiekah Imam bai nuna amincewarshi ba, Yace shi bazai bari yarsa ta tafi uwa duniya karatu ba, duk Universities din dake a Kasar har sai an fita waje neman ilmi? Alhaji ubaid ya ce yayi hakuri da bai nemi shawarar shi ba ya tashi ya yanke hukunci dama yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah. A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam yace mata ya gama magana bata isa tasa shi canza ra'ayin shi ba. Ganin da gaske Shiekh Imam zaiyi mata bukulun kudin da take samu agurin Alhaji musa yasa ta kwashi kafa taje gidan kakarsu ta bangaren Uba da ta rage masu mai Suna Hajjo, ta tsara mata karya da gaskiya akan kullan da Sheikh imam ya ke yi ma yarsa, ta ce ita bakin cikinta gorin da ya ke yi mata akan Aisha sai kace ba diyar yayarta ba, In da kara aisha ai yar ta ce tana da ikon juyata son ranta, bayan haka ta fada mata Alhaji Ubaid Ya sama ma Aisha gurbin karatu a kasar germany ita da Benazir amma Ya hana bai dubi zumuncin dake a tsakanin su ba, Hajjo da ranta ya 6aci ta sa Aunty laura ta kira mata imam a waya tace yazo tana son ganin shi, koda yazo ta balbaleshi da fada kamar zata rufe shi da bugu kasancewar shi mai biyayya yadinga bata hakuri kamar zai durkusa mata kasa tace mashi in har yana son farin cikin ta yabar Aisha ta tafi karatu kasar germany, Shiekah imam yayi kokarin ankarar da ita illar dake akwai na tura ɗa karatu kasar waje balle ita da take mace amma Hajjo ta rufe ido tace itafa ta gama magana, kawai yabi abunda tace mashi, ta ko'ina ta matsa mashi lamba ba dan yaso ba ya amince zai barta, don yasan halin Hajjo rikicin tsufa ne ke damunta. bayan komawarsu gida baibi takan Aunty Laura ba Ya kira Aisha ya tambayeta da son ranta zataje kasar waje karatu? Aisha tace aa bata so saboda batason tayi nesa da shi, amma benazir ta nuna tana so suje suyi karatun atare acan tun da ba wasu shekaru ne masu yawa ba" a maganarta shiekh ya fahimci bada son ranta ba amma tana son ta bi aminiyarta ba yadda ya iya hakanan ya amince. Bayan Alhaji Ubaid Ya kammala yi masu travel arrangement, ana i gobe zasu tafiya sheikh imam bai iya runtsawa ba, saboda zazza6in tafiyar da Aisha za ta yi, wannan ne karo na farko da zatayi nesa da shi, bawan Allah akan dardumarsa Ya raba dare yana yin nightprayers duk akanta, washe garin ranar aunty laura ta shirya ta tsaf, a motar sheikh imam suka tafi, acan airport suka hadu da Benazir tare da family dinta da su ka yi mata rakiya, Aisha tasha kuka na rabuwa da Baba imam, har nasiha yayi mata akan ta ji tsoron Allah, kada ta canza a yadda yasan ta, sannan ta kare mutuncin kanta, karatu yakaita daga shi bai amince tayi wani abu da zai sa6awa mahaliccinta ba. Baba imam bai ƙyale Aisha hakanan ba saida Ya hadasu da Benazir ya karayi masu nasiha mai tsuma zuciya sannan ya damƙa ma Benazir amanar Aisha yace ya yarda da ita bai ta6a barin Aisha ta kula wata kawa in ba ita ba don haka ya bata amanar yar shi, ta kula mashi da ita. Benazir jikin ta ba karamin sanyi yayi ba, har kuka saida tayi saboda tausayin baba Imam, Alhaji ubaid ma yayi masu nasiha, bayan ya gama dr shureim Ya kirasu agaban shi Yayi masu addu'o'i tare da yar nasiha A lokacin Aisha ta dinga kallon shi, tayi fatan Ya furta yana sonta kafin su tafi amma sai baiyi ba saboda shi kallon kanwa ya ke yi mata, bawai don baya sonta ba sai don kasancewarsa miskili da zurfin ciki ko kallonta bai cika yi ba, bayan Aunty laura da hajiya layla sun sanya masu albarka tare da fatan alkhairi a karatun su, daga nan suka yi masu bankwana. Silar hawan su jirgi Allah Ya ƙaddara haduwarsu Da Aneelerh Muhammad falgore itama a lokacin za ta je yin karatu kasar germany, ta zauna a seat daya da Benazir taga ta burgeta ta ɗan fara janta da fira har Benazir ta dan saki jiki da ita, A lokacin Aneelerh batasan da zaman Aisha a cikin jirgin ba tana a seat din bayansu ta rufe fuskarta da mayafinta zuciyarta cike fal da tunanin mahaifinta data bari da kuma muradin ranta. Bayan jirginsu yayi Landing a airport na birnin hagen, Alhaji Musa Ya turo wani escord ɗinsa Yazo daukarsu a hadaddiyar mota, sukayi sallama da Aneelerh suka shiga mota, a zaton su kaitsaye escord din zai wuce da su Jami'ar da zasuyi karatu acan, amma sai suka ga akasin hakan, a wani katafaren gida da Alhaji musa Ya kama masu haya a kusa da Jami'ar, Anan Escord din yakai su a matsayin gidan da zasu zauna, Aisha tayi mamakin haduwar katafaren Gidan, tayi azan a hostel zasu zauna amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci hada masu aiki Ya aje masu agidan, kamar ba karatu suka je yi ba Aisha ta ɗanji shakkun ta zauna agidan saboda gudun kada ta shagala ta kasa ta6uka abunda ya kawota amma saboda Benazir yasa ta amince ta zauna, rana ta farko da suka fara shiga jami'ar, ba zato ba tsammani sukayi arba da Aneelerh ashe itama a nan zatayi karatu, Sunyi farin ciki da ganinta duk da ba'a department ɗaya suke da ita ba, rayuwarsu a jami'ar gwanin ban sha'awa shiga class kadai ke rabasu amma da zarar sunfito zasu hadu da Aneelerh a karshe ma da kawancensu yayi karfi da Aneelerh sai suka yi mata tayin ta baro hostel ta dawo gidansu da zama, Aneelerh bata musa ba ta amince masu toh ita kanta data ga inda suke rayuwa saida ta girgiza da mamaki saboda haduwar Gidan. Uncle musa ba karamin gatanci yayi masu ba, shi ke daukar dawainiyar komai nasu, tun daga cinsu shansu suturarsu masu kyau da tsada har account ya sanya yaronsa ya bude masu na kasar germany, baya gajiya da tura masu dollars kamar baison zafin neman su ba, lamarin shi ya fara daurewa Aneelerh da Aisha kai ganin yadda ya ke ji dasu yana tarairayarsu, wani abun daure kai Duk weekend sai yazo kasar germany daga America, kuma agidansu Yake sauka anan zai kwana su yi breakfast lunch dinner duk tare da shi, har yawon buɗe ido Yake zagayawa dasu a motar shi, da abun ya fara damun aisha ta dai gaza hakuri ta fada ma Benazir itafa zata koma hostel da zama saboda tana jin tsoron baba Imam Yaji labarin ba a jam'ar take zaune ba zai iya yi mata fada bayan haka bata son yadda Alhaji musa ke kashe masu kudi abun yayi yawa, sannan meyasa yake zarya duk week end sai yazo ya kwana agidansu? A ganinta hakan bai dace ba, a matsayinsu na musulmai kuma mata su dinga barin Namiji yana kwana a gidan su, Benazir ta nuna kin amincewarta da komawar Aisha Hostel, ta dinga lallashinta akan tayi hakuri ta zauna, na dan wani lokaci ne, kada ta damu da Alhaji musa halinsa ne shi mutum ne mai son yin alheri yana da wayewa don haka kada ta dauka da wata manufa ya ke zuwa kawo masu ziyara, sannan kuma kada ta damu sheikh Imam bazai ta6a sani ba. dakyar Benazir ta shawo kanta har ta hakura da komawa hostel ɗin, kusan kullum ne saita kira babanta a waya hakan ba karamin kwantar masa da hankalinsa ya ke yi ba, kuma duk in ya kira sai yayi mata nasihar daya saba yi mata, haka aunty laura ma suna yawan yin waya da ita, wasu lokuttan da dama tana son ta kira Yaya shureim amma idan ta tuna bai ta6a nemanta ba sai ta fasa saboda bata son ta zubda ajinta Sai dai taji labarinsa awurin Benazir idan tayi waya da shi wani lokacin Benazir tana bata wayar don ta gaisa da shi hakan ba karamin dadi yakeyi mata, haka itama Aneelerh silar Benazir ta san Yaya shureim har suka saba da shi, itama Aneelerh duk in zatayi waya da mami da Abie sai ta hadasu da aminnanta donsu gaisa ta haka suka ƙarfafa zumuncin su. har whatsapp group suka buɗe na sada zumunci da family dinsu harta baba Imam saida Aisha ta sanya shi aciki, Aneelerh ta saka abie da mami, itama Benazir ta sanya Alhaji ubaid da hajiya layla tare da dr shureim Wani irin zumunci mai karfi ne ya shiga tsakanin family din su duk time da suka hadu online fira suke sha ba kadan ba, har hotunansu suke tuttura masu. Duk idan suka samu hutun School Nigeria suke dawowa tun a airport family dinsu zasu harhadu domin tarbarsu har party Uncle musa Yake hada masu, idan hutu ya kare zasu koma germany har kuka sukeyi saboda basu son rabuwa da family din su. Akwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin sa'a suka kammala degree dinsu, duk da Benazir da Ummi sun riga Aneelerh kammalawa saboda ita nata course din almost 6 years ne medicine and surgery su kuma Business Administration ne shekaru uku ne, Amma saboda shakuwar da tayi da su yasa ta matsa lamba akan zata ajiye karatun saboda bata jin zata iya cigaba da zama a germany batare da su ba, tasan in suka gama tafiya zasuyi su barta, suma sun damu da hakan, a wani zuwa da Uncle musa yayi gidansu, Benazir ta same shi da maganar Aneeleerh, Sai cewa ya yi karsu damu, zai sa arage mata shekarun karatun ta ya koma daidai da nasu, sunyi matukar yin mamakin hakan, aikuwa sai gashi Ya yi mata hanyar da zasu kammala a shekara daya da ita, Amma duk da haka In ta dawo Nigeria sai ta kara karatu akan wanda tayi. Uncle musa yayi masu halaccin da bazasu taba mantawa da shi ba, Kyautatawarshi agare su bata misaltuwa, da Ayshah tana kokwanton dukiyar shi ganin yadda yake masu barin kudi kamar baisan wahalar nemansu ba, Benazir ce tayi brainwashing dinta, ta fayyace mata cewa kudinsa na Halal ne, babban Dan kasuwane kamar dai mahaifinta Alhaji Ubaid. ranar da zasu yi graduation celebration (bikin yaye dalibar) wanda shuwagabannin jami'ar ne suke daukar nauyin yin shi a cikin makarantar, gaba daya family din kowan nan su saida Ya hallara hatta sheikh Imam saida Yaje masu aiko Aisha tayi murnar ganin baba Imam, Ranar sunyi farin cikin da basu ta6a yin makamancinsa ba saboda Yadda yan uwa da abokan arziki suka dinga basu kyaututtuka da yi masu fatan Alkhairi arayuwa, aranar ne sukayi hotuna sosai, abunda yafi basu sha'awa Yadda Family dinsu suka hada kai kamar yan uwan juna, musamman Aisha tayi murna da ganin yadda ya yadda Shikeh Imam ya yarda da Abie din Aneelerh sun zama abokai, haka iyayen su mata sun hada kai sai zumunci suke sadawa a tsakanin su. (Bayan dawowarsu Nigeria, da sati biyu kacal) A yammacin wata rana Sheikh Imam Yana zaune akan Sofa dake a cikin katafaren Sitting room din gidansa, yana tsaka da karanta Jarida, daya daga Cikin security Officer na gidansa yayi masa sallama bayan ya amsa Ya isar da sakon Ana sallama da shi, bai motsa daga Inda yake ba ya tambaye sa wanene ke nemansa? Officer din yace Kanin makwabcin su ne Alhaji Musa, Shiru ya danyi jim aransa yana mai mamakin karfin Halin Alhaji musa da har ya iya takowa yazo gidansa neman shi, daga bisani yace ma Officer din ya shigo da shi. sallamar Alhaji musa ce ta katse zancen zucin nashi, dakyar ya sakar mashi fuska suka gaisa har ya taya shi murnar kammala karatun su Aisha, bayan sun yi shiru na dan lokaci kowa da abunda yake sakawa aranshi, daga bisani Alhaji musa yai gyaran murya ya ce"dama nazo ne don in nemi alfarma agurinka" bai jira jin ta bakin sheikh imam ba ya cigaba da cewa"Ina son ka bani auren Aisha, saboda ta kwanta min araina" wani kallo shiekh Imam ya watsa masa mai kama da harara. Tashin farko Yace"sai yau na tabbatar da baka da Hankali Musa, kai baka ji kunyar tunkarata ido da ido ka fadamin wannan maganar ba? an gaya maka ni mahaukacine da zan dauki ƴata mai daraja in hada ta da fasiƙin mutun, irin ka"? Maganar imam Ta sosa zuciyar Alhaji musa amma dayake shike nema agurinsa sai ya shanye bacin ransa, yace"bai kamata ka gaya min maganganun nan ba, wanda yace yana son naka ai masoyinka ne, saboda nasan mutuncinta shiyasa na tako nazo da kaina don in nemi aurenta agurin ka..." murmushin takaici Sheikh Imam yayi"Haba Musa, ko kayi zaton namanta wanene kai"? Ya fada tare da miƙewa daga kan kujerar da yake ya juya ya nufi bookshelves din dakin mai ɗauke da kundin dokoki dana tarihi, da sauransu. A cikin kundaddakin Ya curo Criminal record Na Alhaji Musa, Ya wurga masa akan kirjinsa, Kafin Ya dafe table din gabansa da tafukansa Ya soma magana Yana kallon Cikin idanunsa.. "Mara Kunya fitsararre, Sau nawa Muna yanke maka hukunci a kotu akan mugayen laifukan ka, amma da zarar kaje prison sai dai muji labarin ka fita, saboda kasan me ka taka kana da manyan mutanen da suke daure maka gindi, sune suke sama maka mafaka a kasar waje, shiyasa kake sheke ayarka" ya faɗa yana kallon Cikin idanun shi. "Tayaya har kake tunanin Ni Imam malik zan iya baka auren yata aisha bayan nasan Halinka ciki da bai? Musa kaine Dealer mai fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan, kai ne Cin zarafin mata masu rauni gurin tilasta masu don suyi karuwanci a kasashen waje, baka gajiya da keta haddin mata, last shari'ar da nayi akanka, yara masu talla kayi ma fyade sannan ka binne su da ransu don kada asirinka Ya tonu, cikin rashin sa'a aka samu wani bawan Allah dayaga lokacin da kake aikatan hakan harya kaika kara police station bayan sun gama bincike akanka suka mika ka kotu abun takaici bayan mun yanke maka hukuncin daya dace dakai mun tura ka prison sai dai muka ji labarin babu kai a kurkuku harma Ka gudu ka koma America da zama, saboda bakin zalincin ku, kai da ubayen gidan ka kuna amfani da haramtacciyar dukiyar da ku ka tara gurin toshe bakin shaidu da bawa jami'ae cin hanci...." Ya karashen maganar yana huci tamkar zai doke sa. Alhaji Musa ya sunkuyar da kansa kasa, ya dunkule yatsunsa, ransa ya baci matuka da jin maganganun da Sheikh Imam ke gaya masa saboda kawai ya nemi auren yarsa. "ka yi haƙuri ka nemi wata, amma sam ba ka cancanci ka mallaki aisha ba, nafi sha'awar ta auri mutun mai tsantsar ilmin addini musulunci, mai jin tsoron Allah, mai kuma kyawawan halaye da dabi'u wanda zai ruke min ita amana, Wallahi idan har na aura ma Aisha kai banyi mata adalci ba, Allah ma bazai barni ba saboda ita din amana ce agare ni"! yanayin fuskar Alhaji musane Ya canza ganin wahalar shi na niyar ta tashi abanza. Cikin kankai dakai yace"kada kayi min haka, wallahi inason Aisha itace mace ta farko da nayi burin in mallaka don mu raya sunnah, idan har don saboda halayena ne, nayi maka alkawarin zan shiryu in har zaka bani auren ta" cike da takaici Sheikh imam Yace"Oh har saina baka aurenta zaka shiryu! Ba zaka shiru don Tsoron mahaliccinka ba"? "Naji zan shiru saboda Allah, Kawai ni ka amince min in aure ta, komi ka ke so zan baka ina da tarin dukiya wanda zai ishemu muyi rayuwar mu" Da gadara yakeyi masa magana, Dariya sheikh imam yayi"Musa kenan, Kai abun duniya ya dama, ni dukiya bata agaba na, ban damu da kyalekyalen duniyar nan ba, wanda wata rana zaka mutu kabarsu ne, daga kai sai halinka za'a binne ka, sannan ka duba kaga gidan da nake rayuwa cikin rufin asirin Allah, babu abunda na nema na rasa don haka kadaina yi min bagu da dukiyar daka tara ta hanyar Haram.."! hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, abunka ga mutumin da bai ta6a neman abu ya rasa ba, babban takaicin shi yadda ya aje girman kansa da komai yazo don ya nemi auren ta amma Sheikh imam Ya watsa mashi kasa a ido. "Amma ai ka bari ita yar taka ta furta bata sona ko"? Ya fada tare da ɗage masa gira... Shiekh Imam Yace"Wallahi koda Aisha tana sonka ba zata aure ka ba! Balle ma nasan Jinina bazai ta6a kaunar fasiki irin ka ba, in sha Allah kaida Aisha sai dai hange daga nesa amma aure har abada, nayi fatan ma ace shureim ne yazo min da maganar auren ta, wallahi jiki na 6ari zan aura mata shi, saboda Ya cika duk wasu sharuddan da zan Iya mallaka masa Aisha..." cikin rauni na murya Uncle musa yace"da me shureim yafi ni? wasu sharuddane ya cika wanda ni ban cika su ba" Sheikh Imam Yace"ko ban fada maka ba, kai ka sani, shureim hafizi ne mai dumbin tarin ilmin addini, mutum mai tsoron Allah, mai koyi da sunnar manzon Allah SAW, ba kamar kai ba, daka sa duniya agaba...." wani irin zafin kishine Ya rufe idon Uncle musa, Yaji zafin maganar Shiekh Imam Ko sallama bai yi mashi ba Ya mike azafafe Ya fuce daga sitting room din. Bayan Uncle musa Ya koma gidan yayansa damuwa ta hana shi sukuni, Yana ji aransa in har bai mallaki aishaba har ransa zai iya rasawa, bakomai yake hadama ba face surar jikin ta.. Dayaga bashi da wata manufa sai ya yanke shawarar tunkarar Aisha don ya nemi soyayyarta, yasan in har ta amince mashi Shiekh imam bai isa Ya raba su ba, Har court zai iya kai shi ƙara. Da taimakon Aunty laura ta shirya mashi ranar da zaizo gidan donsu gana da aisha aranar shiekh Ya tafi gurin aikinsa. . Agarden suka zauna, tana asanye cikin dogon hijab dinta cikin girmamawa ta gaishe da Alhaji musa ta kara yi mashi godiya bisa ga kokarin da yayi akan karatunsu, yaji dadin tarbar da tayi masa har yaji aransa ba zata ta6a ƙin amsa bukatarsa ba. Cikin nutsuwa Uncle musa ya fayyace mata irin kaunar da yakeyi mata, tashin farko Aisha tace"kayi hakuri da amsar da zan baka, wallahi bawai bana sonka bane, kawai ban ta6a yi maka so daya shafi aure ba, Ina jinka kamar Uncle dina saboda zumuncin dake atsakanina da Benazir, amma ni inada wanda nakeso..." bata kare maganar ba Yai saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga nata hannu har saida tadan sha jinin jikin ta. "Karya kike kice bakisona, babu macen dana ta6a nuna inaso tayi rejecting dina, don haka kema akwai soyayyata acikin zuciyarki, idan ma kina jin kunyata ne to ki daina, ni ba Uncle dinki bane, ashirye nake da in aure ki, Aisha kiyi tunani akaina kafin ki yanke shawara, zan jira naji daga gare ki" yana fadan hakan yayi tafiyarsa, gaba daya tashiga halin damuwa kuma ta kasa sanarma kowa, hatta Benazir da Aneelerh basu san da maganar ba, kusan sau biyar Alhaji musa yana tuntubarta a waya don yaji in ta canza ra'ayi amma ta nace akan ita bazata iya auren shi ba, tana da wanda takeso, daya matsa mata akan ta fada masa wanene takeso sai tace mashi yaya shureim ne, a lokacin ji yayi kamar ya binne ta da ranta saboda bakin kishine da shi, ya ji zafin furta sunan shureim da tayi, zuciyarshi ta raya mashi cewar ba ra'ayinta bane Shiekh imam ne ya cusa mata nasa ra'ayin dama ya nuna yafi sha'awar ta auri shureim daga nan ne ya kuduri aniyar saiya shiga tsakanin su. Har gida yaje ya samu shureim Ya tambayesa meke a tsakaninsa da Aisha, dr shureim yace babu komai face mutunci, shi ya dauke ta kamar kanwarsa. Uncle musa yace bai yarda ba, in har yana son ta ya fada mashi zaiyi mashi hanyar auren ta, daya matsa mashi da tambaya kawai sai yace mishi eh yana sonta amma bai ta6a sanar da ita ba. Hankalin Uncle musa ba karamin tashi yayi ba, saboda ya fahimci dukan su suna son juna, kuma In har Shureim Ya furta yana son Aisha tofa babu makawa sai Sheikh imam Ya bashi ita. hakan yasa shi yanke shawarar komawa gurin imam malik don ya kara rokonsa akan ya bashi ita, kusan sau biyar yana zuwa gurin imam amma ya rufe ido akan bazai ta6a aura masa aisha ba, ta ko'ina babu sauki, har aunty laura yaba cin hanci na makudan kudi donta karkato da hankalin sheikh imam akansa amma duk abanza, itama aishar ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta amince da soyayyar shi akarshe sai tayi blocking duk wata hanya da zata haɗa ta da shi, hatta gidansu Benazir ta daina zuwa sai dai Benazir tazo gidansu ta same ta, ranshi ba karamin baci yayi ba, shi a ganin shi bata yi mashi halacci ba, kodan saboda dawainiyar da yayi dasu yaci ace ta saka mashi amma saita butulce dama shi baya abu dan Allah sai idan yasan zai samu riba. bayan wasu kwanaki Uncle musa ya ɗauke ƙafa da zuwa Gidan yayansa kwata kwata suka daina jin duriyarshi, da Benazir ta sanar da Aisha baya kasar Ba karamin dadi taji ba, kuma ta saki jiki ta cigaba da zuwa gidan, wani lokaci atare suke zuwa gidansu Aneelerh wani sa'in kuma Anila ce ke zuwa gidajen su ta kawo masu ziyara, har takaiga iyayen su na ziyartar junan su. Daga baya da soyayyar Aisha ta fara addabar Dr shureim har takaiga dakyar yake runtsawa saboda tunaninta, baya da burin daya wuce ya aureta, aranar daya shirya tunkararta don Ya fada mata irin kaunar da yake yi mata, A lokacin Aysha da Aneelerh sunzo Gidan su suna a dakin Benazir Suna fira, A bakin kofar dakin ya tsaya yana tunanin taya zai tunkareta da maganar? Zata kar6i tayin soyayyar shi ko kuwa? yana jin fargaban Aisha taki amincewa da shi shiyasama tuntuni yaki sanar da ita saboda fargaban amsar da zata ba shi. Har ya zaro waya daga Aljihu da niyar Ya kirata don ta fito su ke6e, kwatsam kunnuwansu suka jiyo mashi firar da su ke yi.. "Yanzu tun da mun kammala karatu me ya rage mana"? Benazir ce tayi tambayar. Aneelerh tace"Aiki da kuma Aure, amma Abie yace bazai bari in fara aiki a private hospital din daya buɗe min ba har sai na tsayar da miji" Benazir tace"Why not Ki ba Uzair damar ya turo da magabatansa? Tun da naga Jininku Ya haɗu da shi" Murmushi Anila tayi"Wai da Ke nake Jira, Idan Kinba Taj damar Ya tura da nasa magatan Gidan ku nima sai in ba Uzair Damar Ya tura gidan mu..." wani kallo mai kama da harara Benazir tayi mata.. "Pls mana ki amince masa nasan fa Kin mutu akan kaunarsa amma sai ki ta wani Ja mashi Aji" "hmmm nifa ba aji nake ja masa ba, Ina tunanin ta yadda zan tunkari mommy da wannan maganar, daddy baida matsala nasan zai amince min, amma mommy bansan ya zata dauki abunba kinsan Mommy bata son dan jarida sannan shi ba dan wani Hamshakin mai kudi bane..." Tun da suka fara magana Aisha bata tsoma baki ba, tayi shiru kamar hankalin ta baya akansu, har saida Benazir ta ɗan dafa kafadarta tukunna ta mai da hankali akansu. "Meke damunkine? Tun dazu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko baki ji abunda muke magana akai bane" Murmushi tayi"Naji mana, mamakine ya kamani, Naji kuna maganar Taj da Uzair su wanene su din? Yanzu duk kawancen mu daku ashe har akwai wani sirri naku da bansani ba"? Dariya su ka yi, Anila tace"Ay mana afwa Ustatha, ba haka bane, wlh mu ma bamu dade da sanin su ba, kin tuna ranar da muka fada maki zamuje shopping mall? One week da dawowarmu"? "Hakane na tuna, Ay ranar na fadamaku Uzirin daya hana ni fita" Benazir tace"toh A ranar muka hadu da su, kyawawan Samari kuma sun kwanta mana arai" Taya su murna tayi Allah ya sa su zama Alkhairi agare ku Suka amsa mata da ameen. Anila tace"pls muna so muji ra'ayinki, Donni bana so mu riga ki yin aure, nafi so yadda muke aminnan juna, Muyi aure atare ya'yan mu su taso a tare" Benazir tace"Aisha fa bata da matsala, Kinsan Allah yayi ta da farin jinin samari iri iri, attajiran masu kudi, Manyan Malamai sai ta zaba ta darje, Ko yau ta fidda miji baba Imam aurar da ita zaiyi Allah" ta fada tana dariya, Murmushin takaici malama Aisha tayi Cikin raunanniyar murya tace"Bazan boye maku ba, dani daku mun riga da mun zama daya, Munsan sirrin Juna, Wallahi bana alfahari da farin jinin da nake da shi, saboda mafi akasarin mazan da suke sona ba dan Allah bane sai don Surar Jikina, Wlh Benazir da wuya namiji yazo gurina da sunan soyayya batare daya neme ni ba, Ina jin bakin ciki da taikacin hakan, ni nasan zaiyi wuya asamu wanda zai soni dan Allah..." dakyar ta kare maganar saboda kukan daya ciyota, Kalamanta sun karya masu zuciya. Cikin shesshekar kuka tace"Inason Aure fiye da tunaninku, inaso in raya sunnar manzon Allah SAW amma taya zan samu wanda zai soni dan Allah"? Gaba daya tausayinta ne ya kamasu. Lallashinta suka somayi tare da kwantar mata da Hankali, su ka ce In sha Allah zasu tayata da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zaiso ta tsakani da Allah. Dr shureim dake a labe yana sauraronsu tun dayaji maganganun Aisha sai jikinsa yayi sanyi zuciyar shi ta karaya, Har Yaji shakkar furta Yana sonta saboda gudun kada tayi tunanin shima surar jikinta ya ke so. Bayan wani Lokaci, Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa kuma cikin sa'a ya shiga da kafar Dama, Arziƙin shi ya habbaka sosai, Rawar kai a wurin Hajiya layla har ba'a fada, dama ta jima tana cusa mashi ra'ayin ta akan ya shiga siyasa saboda taga yadda Alhaji musa ke fantama da dukiya abunda take ma kwadayi kenan, dama arayuwarta ta tsani taga Alhaji musa yafi Alhaji Ubaid Arziƙi tana jin haushin hakan sosai. Dr shureim ya so ya kalubalanci siyasar da mahaifinsa ya shiga, Amma Hajiya layla ta take mashi burki ta hana shi magana adole yaja baki yayi shiru. Alhaji musane yayi mashi hanyar da ya shiga Jam'iyarsu, a Karon farkon da Jam'iyar JDP ta tsayar da shi a matsayin Dan takararsu Na Gomna sunyi murnar da bazata Misaltu ba. Saboda Farin Cikin hakan yasa Hajiya Layla ta shirya masu gagarumin Party don taya Alhaji Ubaid murnar takarar da aka tsayar da shi da kumayi mashi fatan Alkhairi. Kafin Shigarshi siyasa saida ya fara tuntubar Shiekh Imam don ya bashi shawara, Sheikh yace shi bazai hana shi yin siyasa ba amma da zai bashi shawara yacigaba da kasuwancinshi sai yafi zama alkhairi a gare shi, saboda yawancin yan siyasa sai sun kauce hanya suke samun mulki, Nasiha sosai yayi mashi har yace ya dauki shawarar shi amma daga baya sheikh imam sai dai yaji labari agurin mutane cewa Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa yayi mamaki sosai saboda bai ta6a bashi shawara bai dauka ba sai a wannan karan, abun daya kara ɗaure mashi kai, ɗauke kafa da Alhaji Ubaid yai kwata kwata ya daina shigowa donsu gaisa sai in sun hadu a masallaci, daya fahimci kaukaucewar da yakeyi masa sai ya kyale shi don ya gano baya son ya hana shi yin siyasa shiyasa ya janye jiki da shi. Lokacin da Celebration din Ya matso, Hajiya Layla ta gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayasu Murna, daga cikin wadanda ta gayyata hada Aunty Laura, Benazir kuma ta gayyaci Anila da malama Aisha, koda Aisha ta nemi izni agurin baba Imam yace bai amince taje party ba saboda yahudancine babu shi a addinance, bata ta6a musa masa ba sai akan maganar Party din nan, ta dinga rokonshi akan yabarta taje saboda ta yi ma Benazir alkawarin za ta je, In har ba ta je ba Benazir ba za ta ji dadi ba, Shiekh imam Yace tayi hakuri kawai, don bazai ta6a bari taje ba, wunin ranar kwata kwata babu walwala akan fuskarta, Har Aunty laura ta roka akan ta nema mata alfarma agurinsa aunty laura tace ita bazata sanya masu baki ba, saboda an nuna mata iyakarta don haka suje can su karata ita da uban nata, abunda yasa tace haka saboda taji haushin bukulun da shiekh imam yayi mata akan kudin da Alhaji musa yayi mata alkawarin zai bata intaja hankalin imam da Aisha suka amince da auranshi amma gaba daya suka watsa mata ƙasa a ido abun ya kona ranta. Ana i gobe za'ayi partyn, Tafiya ta kama sheikh Imam malik, manyan abokansa wadanda suka kasance shahararrun malaman addinin Islam yan kasar sudan dayake acan yayi karatu lokacin daya zauna gurin Kawunsa, abokanne suka gayyace shi wani taron karrama malamai da za'a gabatar a kasar sudan, kafin tafiyarshi saida ya kira Aisha ya kara gargadinta akan bai lamunta taje partyn nan ba, tace mashi toh in sha Allah bazata je ba, bayan tafiyarsa Aunty laura tace ma Aisha ay yanzu tunda mai gadin nata bayanan, sai ta shirya ta tafi tace ta fasa zuwa saboda batason ta sa6ama mahaifinta, bata matsa mata ba amma da Alhaji musa Ya kira ta waya yace mata yana son Aisha ta halarci Partyn in har tasa tazo zai bata Dala dubu goma sha biyar, Jiki na 6ari Aunty laura taje har dakin Aisha ta tunzurata akan ta shirya su tafi, baiwar Allah duk yadda taso ta hana zuciyarta bijirema mahaifinta saida takasa saboda tana son zuwa itama. Wuraren ƙarfe biyar na marece dai dai, suka shigo gidan Alhaji Ubaid, Aunty Laura ta dauki wankan shadda, Ta coge daurin dan kwalin ture kaga tsira, Ita dai Aisha Abayane a jikin ta doguwa har kasa, sai nikab din da ta sanya. Anan suka iske manyan bakin su Hajiya layla, babu masaka tsinke, Yan uwa da abokan arziki duk sun hallara a katafaren garden din gidan da aka kawata shi da kayan ado da kujerun da baki zasu zauna an tanadi duk wani abu da baki zasu bukata don jin dadin su, Ga mawaka da Maroka sun Cika gidan sai kaɗe kaɗe sukeyi da yan raye raye. Tunda suka shigo gidan gaban Aisha keta faduwa rass rass, kwata kwata hankalinta ba akwance yake ba, duk sai taji ba dadi saboda ta sabawa mahaifinta. Lokacin da ta lula duniyar tunani Yayin da Aunty laura ta shige Cikin mutane tabarta. Sam bata ji takun mutun ba, sai dai taji an rungumeta, har firgita saida tayi amma da taga Benazir ce sai ta sauke ajiyar zuciya, cike da farin Ciki suke kallon juna, Banezir ta ɗauki wankan tsadadden leshi ko arzikin dan kwali babu akanta.. "Amma wallahi naji dadin zuwanki Aminiyar, har na fara fidda rai, ashe zakizo, ya ki ke ya baba imam? Cikin sanyin murya tace"baba bayanan ya tafi sudan, atare da aunty laura mukazo" ruko hannun ta Benazir tayi "mu shiga ciki, ki gaishe da Uncle Musa, tun Shekaran Jiya ya dawo Nigeria, tare da matar daya aura baturiya, amma baizo da ita nan ba, acan gidansa na Abuja yabarta, bai sanar da kowa game da auransa ba sai dai muka ji abakinsa jiya daya zo" tun da Benazir ta fara surutu Hankalinta ba akwance yake ba, wani irin faduwar gaba taji jin ta ambaci sunan Uncle musa fuskarta babu walwala tace"kina nufin Uncle musa yana acikin gidan nan"? Jinjina mata kai tay"eh," tace toh tabari da anjima in an gama partyn sai suje su gaida shi, Benazir ta amsa da toh, damuwace karara Akan fuskarta, Benazir bata lura da halin da take a ciki ba. bayan sun shiga falo ta iska kawayen Benazir Hada Anila kowaccen su ta dauki wanka na mutunci Aneelerh na ganinta cikin sauri taje ta rungumota, Sauran kawayan Benazir sai murna suke yi Aisha bintu imam tazo, har rige rigen daukar hotuna sukeyi da ita, baiwar Allah tadinga kakkauce masu saboda gudun kada baba Imam yaga hotanta agurin partyn daya hana ta zuwa, Aneelerh ce ta lura da yanayinta hakan yasa taja ta gefe daya ta tambayeta meke damunta? Bata boye mata komai ba ta sanar da ita, ta kara da cewa ita kawai hankalinta bai kwanta ba, tana ji aranta kamar wani abu zai faru, cikin sigar lallashi Aneelerh ta soma kwantar mata da hankalinta har saida taga ta saki jiki... tun da aka fara gabatar da shagalin hankalin Aisha ba kwance Yake ba, ga kawayen Benazir sai cashewa suke yi suna tikar rawa ga abinci kala kala ko kadan batay sha'awar ci ba. Tana zaune kan kujera Wayarta ta fara ringing, tayi picking tare da karawa kan kunnanta Muryar shureim Taji yana fadin ta same shi a upstairs yana son yin magana da ita" Bata kawo komai aranta ba, ta yi azan zai bayyana mata soyayyar shi ne Hakan yasa ta mike batare da sanin kowaba Ta nufi upstairs, abakin kofar dakin dataga takalmansa tayi knocking ana bude kofar dakin aka janyota ta fado ciki, a firgice ta dago don taga wanene rass taji gabanta Ya fadi ganin Alhaji musa atsaye fuskarsa babu annuri daga shi sai short a jikin shi, wani irin faduwar gaba taji, da tsantsar mamaki ta furta"uncle kaine"? Daga mata gira yayi"nine Aisha.."arude tace"amma yaya shureim ne Ya kira ni, yana ina" "Ni ne nayi muryarsa, saboda nasan idan kikaji ni ke kiranki ba zuwa zaki yi ba" matsawa yayi dab da ita tayi saurin ja da baya cikin sanyin murya yace"aisha, inaso ki dubeni daga kasa har sama ki fadamin me Allah ya rageni da shi"? Kawar da kanta gefe tayi muryarta na rawa tace"bakomai" "In har hakane meyasa baki sona?.. "Saboda bakai nake so ba,"runtse idanun shi yayi saboda jin zafin maganar shi "Aisha idan kikai min hakan baki min adalci ba, kin hana zuciyata sukuni saboda ke na kashe makudan kudi donki samu rayuwa mai kyau, Harta karatun da kukayi a germany nine na dauki nauyin shi ba Alhaji Ubaid ba, kawai nayi amfani da shi ne saboda nasan Halin mahaifinki da tsautsauran ra'ayi ba lallai in yaji nine nayi hakan Ya amince kije ba, kuma nayi hakanne saboda in dinga samun ganinki akai akai, saboda Imam bazai bari ina zuwa zance gurin ki ba, amma da kuna karatu a germany ba karamin morewa nayi ba saboda ina ganinki a duk lokacin dana so" Hankali atashe tace"Dama duk dawainiyar da kayi mana a germany ba dan Allah kayi ba? saboda son da kake min ne" jinjina mata kai yayi... "Wallahi da ace nasan kaine ka dauki nauyin karatunmu a kasar germany, da ba abunda zaisa inje" tana fada ta juya zata fuce yayi saurin ruƙo qugunta da tafin hannun shi ya janyota da karfi ta faɗo kan kirjin shi, ya soma matsa mazaunanta yana sakin nishi, For the first da ta fara hada jikinta da namijin daba muharramin ta ba, rai a6ace ta banbare jikinta daga nashi ta daddage ta wanka mashi zazzafan mari ji kake fasss!. dafe kuncinsa yayi da tafinsa, idanunsa suka kada jawur cike da bacin rai yace"ni kika mara"? Tana haki tace kadan ka gani, Nan gaba idan ka kara gigin ta6a jikina wallahi saina yi maka abunda har abada ba zaka manta ba, dama ba don Allah kakeso na ba, sai don wata mummunar manufa taka" tana fada ta buɗe kofa ta fuce... Tun da yake wani dan adam bai ta6a daga hannu ya maresa ba sai akan Aisha, yaji zafin marin nan adaddafe Ya fada kan gadon shi yana juyi, ransa ya baci matuƙa jikin shi har gumi yake zubdawa. abangaren malama Aisha bayan fitarta daga dakin a jikin bango ta Jingina bayanta, fuskarta sharkaf da hawaye taji takaicin rungumar da Uncle musa yayi mata, kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta ke ji, Ya dasa mata kiyayyarsa a cikin zuciyarta. Tana cikin tafiya wani irin ciwon mara Ya turnuke ta, da sauri ta dafe cikinta da tafin hannunta, sam takasa cigaba da tafiya a nan ta durkushe tana faman fitar da huci... Adai dai lokacin dr shureim Ya hauro Upstairs din domin amsa kiran da Uncle Musa yayi ma shi, Yana ganinta Jikinshi na rawa ya karaso gurinta Yana tambayarta meke damunta? muryarta na rawa ta furta"cikina yaya shureim ciwo yake min, ka taimaka ka maida ni gida" ganin halin da take a ciki yasa shi ruko hannunta, ya taimaka mata ta miƙe suka sauko down, A lokacin babu kowa a falon gaba daya sun Koma garden can inda akeyin shagalin. Har suka fito harabar gidan basu ci karo da kowa ba. Sai nishi takeyi tana jan numfashi, dr shureim sai sannu yakeyi mata har suka karaso Cikin Gidan Imam, Ya tambayeta tana da maganin ciwon cikinne ko yaje ya siyo mata ne? Dakyar ta bude baki tace mashi bata da shi ya kare" Cikin sauri Dr shureim Ya fita Ya nufi chemist din dake a kusa da su don ya siyo mata maganin, tausayinta duk ya kama shi.. Lokacin daya dawo gidan hannun shi ruke da leda ta maganin daya siyo mata, a bakin kofar falo yai ta ƙwala sallama shiru bata amsa mashi ba, Kuma Yan aikin gidan duk basa a kusa, wayar sa ya zaro ya danna mata call tana fara ringing, tayi picking yanayin yadda yaji Muryarta ba karamin ɗaga masa hankali tayi ba. Cikin shesshekar kuka take fadin"ya shureim mutuwa zanyi, ka taimaka min, " adabarbarce ya furta"Aisha kina ina ne? Ga maganin na kawo maki" shiru yaji bata amsa mashi ba, a rude Ya mike Ya soma neman bedroom dinta saboda bai taba shiga dakinta ba, duk zuwan da zaiyi gidan A falo ya ke tsayawa. Dakyar ya gano bedroom dinta, saboda tsabar rudu ya afka Ciki, a kwance ya taras da ita tsakiyar gadonta, sai juyi takeyi tana murkususu, tafukan hannayenta adaddafe da mararta, sam babu abaya ajikinta zafin daya taso matane yasa ta cireta cikin fitar hayyaci batare da saninta ba, sai Camisole data rage a jikinta shara shara gaba daya surar jikinta ta bayyana muraran. Bai kula ba saboda hankalinsa ba akwance yake ba burinsa kawai ya taimake ta, Aje maganin yai akan bedside drawer Ya fito da sauri jim kadan ya dawo hannun shi ruke da bottle water Ya zauna daga gefen gadon.. Sai da Ya ballo kwayar maganin Ya juyo don ya taimaka mata tasha, kwatsam Idanun shi suka sauka akan Santala santalan Cinyoyinta lokaci ɗaya tunanin shi ya gushe, ya fara jin wata irin matsananciyar sha'awa na taso mashi kamar ransa zai fita, Zuciyarshi ta dinga azalzalarshi kanshi ya fara juya mashi kamar hankalinshi na barin jikinshi, Bawan Allah a lokacin yaita kokari kaucewa sharrin shaidan amma abun Yaci tura saboda yadda surar ummi ke fusgarsa har baisan sa'adda Ya afka mata ba, ga zafin ciwo tana fama da shi a haka dr shureim ya keta mata haddi, taji radadin da bazai misaltu ba, cikin fitar hayyaci ta dinga Sakin kukan azaba, tana yi masa magiya akan ya kyale ta, kada ya kashe ta, kada ya rabata da mutuncinta, amma duk abanza saboda a lokacin shureim yayi nisan da baya jin kira. Ya Ilahi! *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~<><><><><><><><><><><><><><>✍️~ ~___________________________________~ Bata tashi farkawa ba, sai Bayan sallar Magrib, bakinta dauke da sunan Allah, tana kokarin motsawa don ta miƙe taji wani azababben zafi agabanta, ga wata kasala data baibaye sassan jikinta, tunani to soma yi meya faru da ita? A ina take"? jin iska na ratsa jikinta yasa tay saurin shafa jikin nata, lokaci daya gabanta Ya soma faduwa jin babu sutura a jikinta cikin sauri ta yunkura ta miƙe zaune, tana kallon kanta kafin ta yi saurin kallon gefenta, shureim ta gani a kwance kan gadon batare da sutura a jikin shi ba, sai dan bargon daya lullu6e ass dinsa, sam ta kasa tuna komai amma tabbas taji a jikinta raping ɗinta yayi Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, Koken da ta ke yi ne ya farkar da shi, a firgice ya bude idanun shi da suka kada jawur ya dube ta da su, baiyi aune ba yaji saukar zazzafan mari kan kuncinsa ta shaƙe wuyanshi tana kuka ta furta"nashiga uku! yaya shureim ka kashe min rayuwata, ka gama dani! Ka wulakanta martabar jikina ka goga min ƙazantar Zina, Allah Ya isa tsakanina da kai, bazan ta6a yafe maka ba..." zafafan hawayene suka wanke fuskarshi kwata kwata baiji zafin marin da tayi mashi ba saboda ruɗun da kwakwalwarsa ta shiga gaba daya yabi ya rikice yana kokarin tariyo abunda ya aikata mata, saboda baya a cikin hayyacinsa komai ya faru, wlh ko a mafarki bai ta6a sha'awar ya kusanci macen da ba muharramarsa ta aure ba, balle Aisha da yake yi mata kallon kanwarsa, tana kuka Yana kuka Yace"Aisha bayin kaina bane, ba halina bane aisha, ke shaidace akaina, wlh ni ba mazinaci bane..." bai ƙare maganarba ta Fasa tsawa tana huci tace "babu abunda zaka fada min ya shureim, wlh sai Allah yayi min sakayya, da kasan irin burin da nake dashi akanka da ba kai yi min haka ba, da tunfarko ka fadamin kana son Jikina, Ni mai iya aurenka ce don in dinga biya maka bukatarka saboda son da nake maka, amma ka rasa ta hanyar da zaka neme ni sai ta hanyar Zina"? Tana magana Jikinta na kerma, Idanunta sun kada jawur kamar an watsa mata barkono. Cikin disasshiyar murya tace "ka karyamin zuciyata yaya shureim, ka cuceni, ka zalunce ni, Inayi maka kallon mutun mai tsoron Allah, ashe kaima fasiki ne, kana daya daga cikin mazan da basa son mace don Allah sai don surar jikin ta, kaja mun aikata zunubi, Yanzu da wani ido kakeso In kalli Babana, da mutanan da sukeyi min kallon mutuniyar kirki! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." duk yadda yaso ya shawo kanta ya kasa, taki ta saurareshi balle ta fahimce shi, saukowa tayi daga kan gadon jikinta duk ba kwari dakyar ta mayar da rigarta da gudu ta shuge toilet tana kuka ta kulle kofar, tabar shureim a zaune kan gadonta yana ta kuka kamar karamin yaro, sau uku yana marin kanshi saboda bakin ciki da takaicin abunda ya aikata ma Aisha, Matar da yayi burin ya aura. "Ya Allah ba halina bane, Kafi kowa sanin bawan nan naka, Ni maijin tsoronka ne mai gudun saba maka ne, kullum ina rokonka akan ka kareni daga sharrin zuciya da sharrin shedan amma meyasa Hakan ta faru dani? Meyasa na aikata ma Aisha haka"?... Cikin shesshekar kuka yajiyo muryarta daga cikin toilet tana fadin"Yaya shureim ka tashi ka tafi tunkafin Aunty laura ta dawo".. Jiki asanyaye Ya sauko daga kan gadon Cike da danasani Ya mayar da suturarsa, Wlh Yaji kunya mara misaltuwa, Yaji radadin da har yau In ya tuna sai yaji ɗaci aran shi. ______________________________________✍️ Lokacin da su Benazir suka lura babu malama Aysha a gurin partyn nanfa hankalinsu ya tashi suka dinga nemanta sako da lungu na gidan, har layin wayarta suka kira akashe. Hankalin su atashe suka tuntu6i Aunty Laura da maganar, tace kada su damu, ta koma gida dama bada son ranta tazo ba, bayan Kammala partyn suka biyo Aunty Laura gidan don suga idan ta dawo, bayan sun shigo gidan suka Nufi dakinta, adatse suka iske kofar, Knocking su ka yi tare da ambaton sunanta, Tana jinsu tayi shiru bata amsa masu ba, har saida suka fara gajiya da bubbuga kofar su ka fara tunanin ko bata nan ne. A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga kiran ta ya shigo layin Benazir, cikin sauri Benazir tayi picking up tana tambayar ina ta shiga ne? Suna ta neman ta. Cikin raunanniyar murya Aysha tace kada su damu, tana acikin dakin, ta kwanta ne saboda bata jin dadin jikinta amma da sauki. Cike da tausayinta Benazir tayi mata sannu da jiki kafin ta mika ma Anila itama tayi mata sannu. Daga bisani su ka yi wa Aunty Laura sallama suka tafi, zuciyoyinsu cike fal da tunanin yanayin da sukaji Muryar Aisha. Tun daga Ranar Aisha ta ɗauke Kafa da zuwa gidan aminnanta, Babu wanda yasan abunda ya faru tsakaninta da dr shureim, ita kadai tayi ta nukunuku ta ki yarda Aunty laura ta gane halin da take a ciki, saboda bata son kowa ya sani ta fiso ta rufawa kanta asiri. Tsawon kwana uku bata bude wayarta ba, baci ba sha, ba bacci, ta killace kanta adaki, wani irin depression ne Ya kamata ga ciwon rabin kai da take fama da shi, In ta fara kuka har sai hawayenta sun kafe tukunna take dakatawa, kusan kwana ta ke yi tana yin istigfari tare da kai kukanta gurin Allah. Saboda tayi imanin shi kadai ne zai kawo mata mafita, Hankalin Aunty laura ba karamin tashi yayi ba, ganin Aisha na neman ta halaka kanta, Ta rasa gane meke damunta gaba daya ta hana kanta sukuni, ta rame tayi duhu, idanunta kullum a kumbure suke saboda kukan da take sha, ba irin magiyar da batayi mata ba akan ta faɗa mata meke damunta amma taki sanar da ita, sai dai tace ta tayata da addu'a Allah ya yaye mata abunda ke damunta, tace toh In sha Allah zatayi mata addu'a. Idan muka koma bangaren Dr shureim tun washe garin ranar da abun Ya faru, Yabar Kasar, Ya tafi Egypt saboda bazai Iya cigaba da jurar zama yana ganin Aisha da abun kunyar daya aikata mata ba. Bayan makonni da afkuwar Lamarin, Sheikh Imam Ya dawo Nigeria, Bayan ya huce Gajiya a dakinsa, Aunty laura ta jera mashi abincin shi akan rug din dakinsa, Kasa cin abincin yayi saboda faduwar da gaban shi keyi, kuma yaji shiru Aisha bata leko ta yi mashi sannu da zuwa ba, kamar yadda ta saba yi mashi. "Ina mamana? Ko taje islamiya ne, Aunty laura tace aa tana adaki Yace ta kira ma shi ita. Fitowa tayi daga dakin ta shiga dakin Aisha, tayi mamakin ganinta a kudundune cikin bargo jikinta sai kerma yakeyi kamar wadda sanyi ya kama. Hankali atashe Aunty Laura ta haye kan gadon tare da yaye bargon, gabanta ne ya fadi rass, ganin yadda idanun Aisha suka juye, tsabar zafin da jikinta ya dauka tamkar naman da aka gasa da wuta, arude Aunty laura ta zabga salati Ta watso aguje ta nufi dakin sheikh Imam Ta sanar da shi halin da Aisha take aciki, abincin da bai ci ba kenan, jikinshi na 6ari yabiyo bayan Aunty laura suka nufi dakin Aisha, Suna shiga suka taras da Amai na fita daga bakinta. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" arude Sheikh Imam Ya furta, baiyi wata wata ba, Ya sungumi Aisha Ya fuce da ita da gudu Laura tabi bayanshi, Suka shiga mota. Kaitsaye Suka Nufi Asibiti da ita, aranar saida aka kwantar da ita saboda jikinta yayi tsauri. A asibitin suka kwana, Sheikh Imam bai runtsa ba, Yadda Ya ga rana haka yaga dare, har fada saida yayi ma Aunty Laura akan sakacinta na rashin kula da Aisha, gaya nan har ciwo yakamata batare da ita ta sani ba, Aunty laura dai sai hakuri take bashi tace ba laifin ta bane, nan ta fayyace masa halin da Aisha ta shiga bayan tafiyarsa, ta kara da cewa ba irin magiyar da banyi mata ba akan ta fadamin meke damunta amma takiya sai dai tace Intaya da addu'a, Sheikh Imam ya damu sosai, Babban abunda ya kara daga masa hankali ramewar da tayi, kamar ba Aisharsa ba. Basu sanar da kowa game da ciwonta ba, a duk lokacin da su Benazir suka kira Aunty Laura su kai mata korafin sun kira layin Aisha basa samu sai tace masu su yi hakuri ayyuka ne su ka yi mata yawa, kwanansu ɗaya a asibitin baci ba sha saboda damuwar Halin da Aisha take a ciki, Bayan dr din dake kula da Aisha ta gama bincikenta akan lafiyarta, ta kira Sheikh imam don suyi magana acikin Office din ta. Bayan sun shigane Dr din Ta dube shi dakyau fuskarta da damuwa tace"Sheikh, naji dadi da Ya kasance Ni Ce amintacciyar Likitar dake duba Iyalanka, Saboda kai malamina ne, ni kuma dalibarka ce, ni me rufa maka asiri ce don kare martabarka" Cike da gamsuwa sheikh Imam Ya jinjina mata kai da alamun rudu akan fuskarsa. Takardar dake a hannunta ta miƙa masa jiki asanyaye ya kar6a har zai buɗe muryar Dr din ta katse shi. "Sakamakon gwajin da mukayi ma Aisha ne" A hankali Ya soma karanta sakamakon, abun mamaki sai taga yana dariya maimakon taga tashin hankali akan Fuskarshi don ta san muddin Ya karanta sai Hankalinsa ya tashi ba kadan ba. "Sheikh Lafiya naga kana dariya" mika mata takardar yayi"Ki duba dakyau, wannan sakamakon bana Aisha bane, watakil kunyi mistake ne, Aisha da bata da aure, Ina ita Ina ciki"? Ya fada da murmushi akan fuskarta, Idanun Dr dinne suka cicciko tab da kwalla saboda tsananin tausayin shi daya kamata. "Dan Allah, Ki bani na Aishana inaso in san meke damunta, wannan kuma ku nemo mai shi ku bata, kada asamu matsala..." girgiza kai Dr din tayi cikin rauni na murya tace"Kayi hakuri Sheikh, kai malamine nasan kayi imani da Allah ka kuma yi imani da kaddara, wlh result din Aisha ne, Tana dauke da juna biyu, Nima dana ga sakamakon saida na karyata kaina saboda nasan Aisha bata da aure, sannan Aisha kamilar macace, amma dana zurfafa bincike na sai na gano dagaske Cikine a jikin ta...." bata ƙare maganarba sakamakon Tsawar da Sheikh Imam Ya doka mata tamkar zai fasa dodon kunnanta, Tuni tasha jinin jikin ta. Yana Huci Ya furta"Kin bani mamaki dr Husaina, kin kuma ji kunya wlh, baki taba yi min karya ba sai yau, wannan sakamakon da kika nuna min bana Aishana bane, mamana bazata taba aikata zina Ba, Ƴata kamila ce, mai jin tsoron Allah bazata taba aikata abunda zai sabawa Mahaliccin ta ba, Na yarda da ƴata Aisha bazata ta6a ruke koda hannun Namijin daba muharraminta bane, don haka ki gaggauta janye kazafin da kike kokarin yi mata, watakil biyanki akayi don kiyi mata ƙazafi, dama akwai masu jin haushin daukakar da Allah yayi mata watakil kema kina daga cikin su...' kwata kwata Dr husaina bataji haushin kalaman Shiekh Imam ba, sai ma tausayin shi daya ƙara kamata. Kekketa Takardar yayi, Tare da watsa pieces din saman table din gabanta, Ya juya afusa ce Yabar Office. Yana tafiya Visitors dake zarya acikin asibitin sai kallon shi sukeyi ganin Sheikh Imam wasu har gaishe da shi sukeyi amma bai kula su ba, Yana shiga dakin da aka kwantar da Aisha Ya iske Aunty laura zaune kan kujerar dake a gefen gadon ta zabga uban tagumi.. Tana jin motsin shigowarshi ta mike tana tambayarshi me dr tace. Rai a6ace yace"ba zamu cigaba da zama acikin asibitin nan ba, Gida zamu tafi inyaso sai muyi jinyarta acan" "Amma ba'a sallame mu ba, kuma jikin nata har yanzu da sauranshi..." bata ƙare maganar ba, Ya daka Mata tsawa"Ki ruko Aisha mu tafi" jikinta na bari ta taimaka ma Aisha ta mike baiwar Allah ko tafiya bata iyayi sai layi take kamar zata kife ƙasa a haka suka shiga mota da ita. Bayan sun dawo gida Aunty Laura Ta matsa mashi akan ya faɗa mata me doc Husaina tace akan ciwon Aisha Nan ya kwashe komai da suka tattauna ya sanar da ita, itama a lokacin biye mashi tayi suka karyata maganar Dr husaina. Cikin da laulayi ya zo ma Aisha, bakar wahala take sha, wani sa'in tana a kwance kan gado take fara kwarara amai ta sauko da gudu ta fada toilet ta karasa shi acan. Gashi kullum Cikin yin zazzabi takeyi, daga bayane Aunty Laura ta gano Ciki ne da ita, Bazan Iya misalta tashin hankalin da Aunty Laura ta shiga ba, a daki ta same ta kwance kan gado tace taji tsoron Allah ta fada mata gaskiya! Akwai ciki jikinta ko babu? saboda ta fara kokwanto akan yanayin ta, Kafin ta sanar da ita saida ta fara rokonta akan karta fada ma baba Imam tabarshi a matsayin sirri atsakaninsu duk da tasan watarana dole ne Yaji, Aunty laura tace tayi mata alkawarin bazai taba ji abakinta ba. Anan ta labarta mata komai daya faru tsakaninta da shureim, a lokacin Aunty Laura ta zabga salati tana sallallami, Jikinta Ya kama bari Saboda razanar da tayi, ta girgiza ba kadan ba, musamman dataji cewa Shureim ne yayi mata aika aikar, Babban tashin hankalinta Idan Sheikh Imam Ya gano Cikin ne dagaske, to fa itace mutun tafarko da zai fara tuhuma saboda ita ta matsa ma Aisha akan suje Partyn. Aunty Laura tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda tausayin Aisha daya kamata, Yarinya Kamila da ita an zubar mata da mutuncin ta, dr shureim Yasha tsinuwa agurin Aunty laura, tace dan iska munafuki mai fuska biyu, kamar Na Allah, In sha Allahu sai yaga sakayyar abunda yayi mata, daga bisani ta lallashi Aisha taja ta ajiki sosai, ta dinga bata hakuri hadi dayi mata nasiha har hakuri ta bata akan Tursasa matan da tayi akan taje, gani take ma kamar itace Silar komai daya faru da Aisha. A haka aka cigaba da rayuwa, Har Ila Yau sheikh Imam yaki yarda cewa Aisha ciki gare ta, wani'sa'in agaban shi zatayi amai amma ko kadan bai yarda ya zargeta da ciki ba, Iya bakin gwargwado tana samun kyakkyawar kulawa agurin Baba Imam, baya barinta cikin damuwa, Ya hana a kaita asibiti kuma Ya hana dr Husaina zuwa agidan, Ko tazo da niyar duba Aisha tun daga bakin gate security Officers ke korarta. lamarin ya daure mata kai, ita burinta kawai ta taimaka ma sheikh Imam su nemi mafita gudun kada kimarshi ta zube sai dai Yaki bata damar ganawa da shi, Har court taje ta same shi a office dinshi Amma Yaki sauraronta, badan taso ba tahakura da bibiyar shi. Saboda zullumi da fargaban abunda zai biyo baya In sheikh Ya san Aisha tana da ciki, yasa Aunty Laura ta rame, kamar mai fama da zazzabi har saida sheikh Imam Ya lura da canjin da tayi, ko da ya tambayeta meke damunta sai tace mashi Ciwon aisha shine silar damuwarta, hakuri kawai yake ba. Dubarace ta fado mata arai, ta sami Aisha da zancen su zubda Cikin kawai, Aisha tace bazata iya ba, bata son ta kuma aikata wani zunubin na kisan kai bayan wanda suka aikata, ita bazata iya kashe rai ba, laifin da shureim ya aikata mata bazai shafi abun dake a Cikin ta ba. Aunty laura taita kokarin tunzurata don ta amince asamu arufawa kai asiri amma Aisha ta yi kunnan Uwar shegu da maganarta, ganin tasa kafiya yasa Aunty laura ta dinga zuba mata maganin zubar da ciki aboye take barbada mata shi cikin abinci ko cikin abun sha, sai dai wani Iko Na Allah tun da tasoma yunkurin 6arar mata da ciki Allah bai nufa ba, saima kara lafiya da ta ke yi. Lokacin Da Cikin Yakai wata Biyar, Ya fara bayyana a jikinta, daga ka kalle ta zaka gane tana da ciki Amma sheikh Imam Ya kasa Yarda Ciki ne saima yace ture akai mata, Ajiyar Aljanu ce, haka ya dinga banka mata ruwan addu'o'i tana sha, In zataci abinci sai ya tofe shi da addu'a in zata kwanta bacci sai ya shigo har daki gaban gadonta yayi mata addu'a, Zuciyar Aisha ta karaya da ganin irin Yardar da mahaifinta yayi da ita, shiyasa ta kasa buɗe baki ta furta mashi Ciki ne a jikin ta, sai dai in suna atare yanayi mata addu'a ko yana bata abinci abaki, tayi ta zubar da hawaye tana kallon shi, ya dinga lallashinta yana fadin mamana kiyi hakuri Allah yana tare da bayinsa masu Hakuri, ki jure ki cinye jarabawar nan, In sha Allah koma wanene yake nemanki da sharri kanshi zai koma, mutanene ba Allah aransu bakin ciki da hassada sunyi yawa azukatan mutane. Wani sa'in in yanayi mata maganar sai ta dinga Yunkurin buɗe baki don ta fada mashi gaskiya amma sai ta kasa, In Aunty laura na akusa taga tana kokarin fada masa sai tayi saurin janye hankalin shi da tunanin wani abun. Saboda Lalurar Aisha Yasa Sheikh Imam Ya hana ta fita ko kofar falo bata leƙawa, saboda baison wani yaga Aljiyar da aljanu sukayi mata a zargi ciki ne, duk wanda yazo nemanta gida sai dai suce mashi bata nan tayi Tafiya Sudan gidan Kawunta, babu wanda yasan Aisha tana agida har su Benazir. Daliban Aisha na islamiya, Da abokananta malamai da duk wani mai sauraren wa'azinta sai da ya damu da rashin ganin Aisha, saboda Allah yayi ta da farin jinin mutane suna son Aisha. A kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin Aisha Ya Cika wata tara Cuf, tashi dakyar zama dakyar haka ta ke fama, a daren wata ranar Juma'a ne nakuda ta kamata, Aunty Laura ta matsa akai ta Asibiti ganin yadda take shan wahala, amma Sheikh Imam Ya hana yace ciwonta bana asibiti bane, sai dai ya bata ruwan addu'a tasha, a lokacin Aunty Laura, har yunkurin fada mashi gaskiya tayi amma saboda tsoron Kada ya saketa Yasa taja baki tayi shiru, ta bar shi ya gani da idon shi. A falo ya zauna yana jan cazbaha, Ya baro Aunty laura adakin Aisha. Bayan wani Lokaci, Kukan Jariri Ya cika kunnen shi, Wani irin Bugu Zuciyar shi tayi tamkar zata fasa kirjin shi, Tsantsar tashin hankali da rudanine Ya bayyana akan fuskarshi, cikin sauri Ya miƙe Ya shiga dakin Aisha, dira kafarshi keda wuya ba zato ba tsammani idanun shi suka sauka akan Jinjirin da Aunty Laura ta ruƙe a hannunta. Lokaci daya yanayin fuskarshi ya sauya, A lokacin Ayshah tana a kudundune Cikin bargo Aunty laurace ta taimaka mata tayi wanka bayan ta kar6i haihuwarta. Jikinshi na kakkarwa ya karasa shiga dakin a gaban Laura ya tsaya yana ƙarewa Jinjirar kallo idanunshi azazzare. Babyn Fara Sol da ita, Idanunta dara dara farare kamar an diga zaiba, ga wata yalwatacciyar sumar kai har gaban goshinta gashin ne a nannaɗe, kallo daya zakai mata kagane Ba jinsin bakar fata bace. A lokacin Jikin Aunty Laura kerma yake kamar mazari, Ga wani bugu da kirjinta keyi mata saboda tsoron Hukuncin da Shiekh Imam zai yanke mata. Numfashi yaja tare da miƙa hannu Ya kar6i jinjirar daga Hannun Laura, Ya kura mata idanu Yana kallon ta. Ya kasa yarda da abun da Zuciyarshi ke raya mashi, ya yi fatan ace mafarki ya ke yi ba gaskiya ba, wani kululun bakin cikine da takaici Ya tokare makoshin shi.. Muryarshi na rawa ya furta"Shegiya agidana? Gidan Alkali sheikh Imam? Sanannan malamin addinin islama! Me yi ma wasu fada da nasiha akan aikata Barna"? Yau agidana aka aikata barna? Ni sheikh? yata Aisha ce ta haifi Shegiya acikin gidana? Batare da Aure ba? inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." wani makokon bakin cikine ya mamaye zuciyarshi, hannayenshi na kerma Ya mika ma Laura yarinyar da sauri tasa hannu ta kar6a, jikinshi na kerma ya zauna Gefen gadon Aisha Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya ya furta"mamana, tayaya kika samu Ciki? Wanene yayi maki aika aikar nan"? Kunya da bakin cikine suka sa Aisha tagaza furta kalma, taki fitowa daga cikin bargon jikinta sai kerma ya ke yi. Shurun da tayi ne ya bata masa rai, Ya doka mata tsawar data firgitar da su, Har Jaririyar saida ta fashe da kuka Yana Huci Yace"Ba zaki bani amsar tambayar da nayi maki ba"? Aunty laura tana kuka tace"Abien Aisha tsautsayine da kaddara..." Bata kare maganar ba, Ya zabura ya miƙe ya nufe ta gadan gadan, batai aune ba Taji safkar maruka zafafa kan kuncinta, Har saida shatun hannayensa suka fito rudu rudu akan kuncin ta, gefen bakinta ya fashe jini ya fara ɗiɗɗiga. "Allah Ya isa tsakanina dake Laura, Kin cuce ni kin cuci kanki kin kuma Cuci Aisha, sannan kin Cuci malama Batool! Kin ci amanata, nasan komai ya faru da Aisha kece Sila, kece kika ja komai, shashasha mara hankali" Fashewa tayi da kuka Jinjirar hannunta sai kuka takeyi. "Kunyi tunanin bansan komai bane? Duk abunda ke faru agidan nan an fada min, Kece Kika matsa ma Aisha kuka tafi partyn dana hanata zuwa, kina amfani da biyayyar da takeyi maki gurin Cutar da rayuwarta.." Cikin shesshekar kuka tace"wallahi Allah shine shaidana, Ni ban ta6a Cutar da Aishaba, na ruke amanar da ka bani, Kai ka sani in ba ni ba wa kake tunanin zata kula maka da yarka kamar yadda na kula maka da ita"? Bai kula ta ba, Ya koma ga Aisha Ya sanya Hannu Ya yaye bargon data lulluba da shi wata irin zabura tayi ta mike zaune jikinta na kerma ta dinga girgiza kai batare data iya furta kalma ba. "Ki gaya min wani fasikin ne yayi maki ciki"? Cikin rawar murya ta zayyana mashi komai daya faru. "Dan Allah ka yafe min baba, Ba laifina bane, bayin kaina bane, Na rantse maka da wanda raina yake a hannunsa Bada son raina komai ya faru ba, dr shureim shine Ya yi min fyaɗe, baba kayi hakuri kayi hakuri, nasan nakarya maka zuciya, Naji kunya baba, nayi abun kunya, har rokon Allah nayi ya dauki raina in huta saboda bakin cikin abunda yaya shureim yayi min..." sambatu tadinyi yi mashi... Bai san sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba. Cikin raunanniyar Murya yace"Aishana, meyasa lokacin dana hanaki fita partyn bakiji maganata ba? Meyasa? Har ni zansa maki doka ki karya saboda Wannan shashashar ta tursasa maki" ya fada yana nuna Aunty laura da yatsa. "Aishana baki taba yi min gardama ba, ban taba hanaki abu kika ƙiyi ba sai akan Paryn nan! Kika bijiremin, Ni dama saida raina ya bani wani abu zai iya faruwa shiyasa Na hanaki zuwa, da ace kinbi maganata da duk hakan bata faru ba, Kinga illar Kin bin Umarnin Iyaye ko"? jinjina mashi kai ta yi Jikinta nata kerma. "Aisha, Kinbiyewa Son zuciyarki, Kin cuce ni Kin Cuci kanki, Kin kuma Cuci mutanan da suka yarda da mu, sannan Kin zubarmin da mutucina kema kuma Kin zubar da naki mutunci, kinja mana abun kunyar da shiga cikin mutane zai gagaremu, Kin karya alkawarin da kikayi min na kare mun mutuncina da kimata a idon duniya, masuyi maki kallon mutuniyar kirki da zarar sunsan abun kunyar da kika aikata zasu fara yi maki kallon fasika mai fuska biyu, da Ina alfahari dake amma A yanzu babu wannan Aishana, Kin lalata komai, farin Cikin da kika sama min tun ranar haihuwarki a yau kin bata shi, Kin dasa min bakin cikin da har abada bazan ta6a warkewa daga radadin da naji ba, Aisha Ina da makiya wadanda suke son ganin bayana, Idan har sukaji abun kunyar da kika aikata zasuyi min dariya, kuma zasu yi amfani da hakan gurin ganin raunina..." fashewa tayi da kuka tana fadin"baba kadaina fadin maganganun nan bana jin dadi baba, Kaifa malamine, kafi ni sani baba, Abunda ya faru dani Kaddara ce, wata irin addu'ar neman tsari ce bakai min ba? Nima haka inayi ma kaina amma hakan bai hana kaddara ta afkamin ba, saboda Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, babu wanda Allah baya jarabta baba, Annabawan Allah sun fuskanci jarabobin rayuwa basu taba gazawa ba, ya kamata kaima kayi koyi da su, baba wannan ne karo na farko daka fara fuskantar jarabawa mafi muni arayuwarka sau ɗaya tak yarka tayi ciki batare da aure ba, Dan Allah baba Mu dauki Hakan amatsayin Kaddararmu, muyi hakuri mu jure, baba Kafi jin kunyar duniya akan ta lahira? Mutane bazasu amfane mu da komai ba saboda basune zasuyi mana hisabi ba"! Maganganun Aisha sun karya Zuciyarshi, har ya gaza yanke mata hukuncin da yayi niyar yi mata. Mikewa yayi da sauri Ya fuce daga dakin, Yana fita Aunty laura ta mika mata Jinjirar dake ta kuka"ki bata nono Tasha yunwa take ji" Kar6ar jinjirar Aisha tayi, ta fara shayar da ita idanunta akan fuskar Jinjirar yayin da take tsotsar nono sai kallon fuskar mamanta takeyi, hawayen Aisha dake gangarowa ta cikin idanunta kaitsaye yake sauka saman fuskarta, tayi azan In ta haifi yarinyar zataji tsanar ta saboda bata sameta ta hanyar aure ba, amma sai ta ji tsantsar kaunar yarinyar fiye da komai na duniyar nan. Aunty laura ta kara lallashin Aisha har saida ta kwantar mata da hankali. "Aisha nayi danasani da nayita kokarin zubda maki Ciki saboda inajiye maki bakin mutane da kuma abunda zai biyo baya idan mahaifinki Yaji, wlh yanzu da kika tunasar damu sai naji jikina yayi sanyi, da na kashe yarinyar nan da nayi danasani na har abada, baiwar Allah gata kyakkyawa kamanninta sak dana Ubanta, Allah ya raya mana ke bisa tafarkin addinin islam, Allah yasa ki gaji Kyawawan halayan Mamanki" aisha na murmushi ta amsa mata da ameen. "Bari naje na shirya maki Abinci nasan kina jin yunwa" "Aunty Laura, Baki gaji ba? Naga kin raunata" murmushi tayi kada ki damu Aisha, duk raunin da zan ji bai kai wanda kika ji ba. Ta fada tare da fucewa ta shiga kitchen da kanta Ta hada mata farfesu bayan ta gama ta kawo mata adaki. A bangaren Sheikh Imam bayan daya Koma dakinsa safa da marwa ya cigaba dayi, Zuciyarshi cike fal da tunanin ta yadda zai bullowa lamarin saboda bayason asirin abun da ya faru da yarshi aisha ya tonu a idon duniya, yana jiye masu tsoron tozarcin da zasu fuskanta agurin mutane.. A bangaren Dr shureim tun bayan daya Koma Egypt gurin aminsa, Bai kara samun kwanciyar hankali ba, saboda damuwar abunda yayi ma Aisha, Sai da ya shafe sati daya cur bai runtsa ba, abinci sai anyi dakyar ake samu yaci, ya yi duhu ya rame saboda tunanin A wani hali aisha take aciki, ga wani irin azababben sonta daya kara nunkuwa acikin Zuciyar shi, har takaiga baya iya bacci batare da yayi mafarkinta ba, Sometimes sai yayi tunaninta ya ke samun nutsuwa a cikin zuciyar shi, kusan kwana yakeyi akan darduma yana istigfar tare dayi ma Aisha addu'ar Allah yaye mata damuwarta ya kawo mata sauki acikin rayuwarta, saboda yasan zunubin daya aikata mata bazai barta ta zauna lafiya ba, dole su fuskanci kalubale ita da Mahaifinta. tun yana boye abunda ke damunshi har amminsu ta lura da rashin walwalar shi ta dinga tambayarshi meke damunshi yaki fada mata, ta kasa jurewa ta kira iyayen shi ta sanar da su halin da Dan su ke a ciki, da jin hakan Hajiya layla ta bashi Umarnin ya dawo Nigeria, saboda ammi tace ta rasa gane kanshi, baya bacci baya son cin abinci, wanka ma saita matsa mashi ya ke yi kamar karamin yaro. Bayan ya dawo Nigeria, Iyayenshi suka tasa shi agaba da tambayar meke damunshi? yaƙi ya sanar dasu, Ba irin lallashin da basuyi mashi ba amma duk abanza. Saida Ya samu nutsuwa ya kira Benazir a dakinsa ta same shi ya tambayeta Ina Aisha? Tace mashi rabon ta da Aisha kusan wata tara da kwanaki, Aunty Laura tace masu ta tafi sudan gurin kawunta, Ko sun kira layinta basa samu kuma koda zata tafi ba ta yi masu sallama ba" Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, Zuciyarshi ta karaya sosai. Ana haka saiga kiran Sheikh Imam Ya shigo wayar shi, wata irin kunyace ta kama shi kamar bazai daga kiran ba sai kuma Ya daga, Ko sallamar shi sheikh Imam bai amsa ba Yace shureim Inason ganinka, Ka same ni agidana, Ya amsa mashi da toh. Bai bata Lokaci ba, Ya shirya kanshi cikin shadda Ya nufi gidan Sheikh Imam A garden Ya taras da shi zaune kan kujera fuskarshi babu walwala kamar bai taba dariya ba, tuni Shureim Yasha Jinin jikin shi. Bayan daya zauna kan kujerar dake fuskantar sheikh Imam Malik Ya yi shiru Yana sauraron shi.. Kallo ɗaya sheikh Imam yayi mashi Ya lura da irin ramar da yayi daga gani yana acikin damuwa. "Akwai wata rana, dana farka tsakar dare, na fito daga daki Ina zagaye Gidana, dama Ina yawan yin hakan sometimes bana iya bacci batare dana tofe ko'ina da addu'a ba, ina gab da zan gifta dakin aisha Najiyo shesshekar kukan ta, Kasan me naji tana fadi"? ya tambaya da tsantsar bacin rai Yana kallon fuskar Shureim daya gama rudewa, Girgiza kai yayi"aa baba' "Addu'a takeyi Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri yaron makwabtana data mutu akan kaunarsa batare da sanin shi ba.." wata irin karaya Zuciyar dr shureim tayi. "Nayi mamaki a wannan lokacin, saboda Aisha bata taba bude baki ta fadamin ga wanda takeso ba, amma a lokacin danaji tayi addu'ar nan ni kuma sai nayi alkawarin zan aura mata yaron nan da take so saboda in cika mata burin ta.." zafafan hawayene suka wanke fuskar Dr shureim. "Yarinyar da tayi dakon soyayyarka acikin zuciyarta na tsawon shekaru, ta hana idonta bacci don ta roki Allah ya mallaka mata kai ita ka wulakanta rayuwarta Shureim? Ya faɗa rai abace. "Inayi maka kallon mutumin kirki kamili, mai jin tsoron Allah, ashe na yaudari kaina! shureim ka sani ka take sani? Da yata ka aikata zina? Sannan baka taba waiwayonta ba, Ka haura kafa kabar kasar, Sai jiya na samu labarin ka dawo! Baka damu da halin da ka jefata ba shureim! Har yabonka nakeyi saboda na yaba da kyawawan halayenka amma ka tashi ka watsa min kasa a ido" Fashewa da kuka dr shureim yayi kamar karamun yaro, shima sheikh Imam din hawaye ne ke zarya kan kuncinsa. Cikin karyayyar murya mai tattare da danasani dr shureim Shureim Ya soma bashi hakuri Yace ya amsa laifinsa amma wlh baisan Ya akaita ba, Allah shine shaidarshi bai ta6a kusantar zina ba, bai ta6a sha'awar Ya kusanci Aisha batare da aure ba, Amma ya karbi laifinsa kuma Yana neman alfarmar ya bashi aurenta saboda su rufawa kansu asiri. Sheikh Imam yace yaji amma yana so yaje gida Ya fada ma iyayensa abunda Ya aikata sannan Ya sanar da su zai auri Aisha, Duk abunda su ka ce Yazo ya sanar da shi, Jikinshi na 6ari ya mike har tambayar sheikh yai Aisha tana nan cikin gidan? Yace mashi eh, ya sake cewa zai iya ganinta? Imam Yace aa bai amince Yaganta ba, har sai bayan an daura auransu. Bayan komawar Dr shureim gida ya kira Alhaji ubaid da Hajiya layla a falo Benazir ce kadai ke babu a cikinsu. Bayan sun nutsu, Dr shureim Ya fayyace masu komai daya faru tsakanin shi da Aisha Sannan Yace Ya yanke shawarar zai aureta.. Tunkan Ya kare maganar Hajiya layla ta fara zazzaga masifa tana fadin wallahi bada yawunta ba, bai isa Ya bata masu suna agari ba, sai dayaga zabe ya kusa zai zo masu da wannan maganar mara dadin ji? Salon yaja masu zagi agurin Jama'a? ta inda take shiga bata nan take shiga ba. Da farko Alhaji Ubaid yaso Ya fahimci dr shureim Har fada yayi masa akan abunda yayi ma Aisha, sannan yace ya amince masa zaije suyi maganar aurensu da sheikh Imam din, Shureim Yaji dadin maganar Mahaifinsa hajiya layla sai banbamin bala'i takeyi, Ita damuwarta ba akan abun kunyar da shureim yayi ma aisha bane, face Takarar da Alhaji ubaid Ya tsaya ga zabe ya kusa In har abokan adawarsu suka Ji abun nan zasu nemi bata masu sunane, a karshe su rasa kujerar da suke nema. Bayan kwana daya da afkuwar Lamarin, Alhaji Ubaid Ya canza magana, ya kira shureim Ya fada masa yayi hakuri amma gaskiya bazai bari ya auri Aisha ba, saboda yayi bincike ya gano aisha ba mutuniyar kirki bace, dama can ta saba bin maza, har videos dinta na batsa wanda tayi tare da maza an tura masa awaya, sannan abun da ya faru tsakanin shi da ita ya yarda bayin kanshi bane, laifin Aishar ne itace shaidaniyar dataja Hankalin shi donta biya bukatar kanta. Hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba, ya dinga salati Yana karanto duk wata addu'a da zata sanyaya zuciyarshi, ranshi ya 6aci matuka da jin kazafin da mahaifinsa yayi ma Aisha, Yace wlh daddy karyane, wannan maganar ba gaskiya bace, kaji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da zaka koma gare shi, Aisha ba fasika bace, mutuniyar kirkice ita, abunda aka fada maka akanta karyane, kai kasan wacece aisha tuntana karamarta kamilar macace mai kamun kai, daddy kada ka biyewa son zuciyarka! Nasan siyasa ce ke nema ta rufe maku ido shiyasa kuke gudun in auri Aisha kuma maganar nan har yanzu ma ba Wanda yasan da ita daga gidansu sai nan, dan Allah kubarni in aureta in rufa mata asiri, Nine fa nayi silar jefasu a halin da suke aciki ita da mahaifinta, meyasa ni ba za ku ga laifina ba sai laifinta ta? Ita da nayiwa fyade"? hajiya layla Ta balbale shi da masifa tace"ko yaki ko yaso aisha ba mutuniyar kirki bace, abunda mahaifinsa ya fada akanta gaskiya ne, dama ita can bata yarda da ita ba, munafukar kullum tana yawo cikin hijabi kamar ta Allah, ashe maza take bi, gashinan zata bata mata tarbiyar ɗa, don haka ta yanke duk wata alakarsu da sheikh Imam malik, zumuncinsu Ya kare. Gaba daya suka juya ma Dr shureim baya, duk wannan abun dake faruwa Benazir bata sani ba, Saboda bata agidan ta tafi Abuja gidan Uncle Musa. Shiekh Imam malik ya yi ta Jiran zuwan Alhaji Ubaid Ko shureim don Yaji daga garesu amma Yaji shiru wai malam yaci shirwa. Har dai ya yanke shawarar zuwa gidan da kanshi don yaji ya ake ciki. Bayan ya isa Security Officer din dake tsaron Gidan Ya shiga yayi mashi sallama da Alhaji Ubaid. Sai ga Jam'in ya dawo yace mashi Ya shiga daga ciki. A falon gidan Shiekh Imam Ya zauna kan Sofa Yana Jiran fitowarsu, Tsawon mintuna Sai ga Alhaji ubaid da Hajiya layla sun fito daga part dinsu, akan sofa suka zauna suna fuskarshi, tun daga yanayin fuskarsu Ya fahimci babu lafiya, kamar basu taba yin dariya ba, Koma arzikin gaisuwa bai samu ba. ya yi tsammanin zasu bashi hakuri kan abun kunyar da dansu yayi ma yarsa, amma sai yaga akasin hakan, bayan da ya kora masu jawabin abunda ya kawo shi Alhaji Ubaid Yace Yayi hakuri ya rungumi kaddara, Amma shureim bazai auri Aisha ba, saboda sun yi bincike akanta sun gano ba mutuniyar kirki bace ta saba bin maza.." bai dire maganar ba Sheikh Imam Ya doka masa tsawa Rai amatukar bace Yace"amma baka da Mutunci Alhaji Ubaid, ka bani mamaki, mutumin banza mutumin wofi, yau da kanka kake yiwa aishana kazafi? Yarinyar data taso agabanka tuntana karama kasanta farin sani, har alfahari kakeyi da ita saboda kyawawan halayanta, ba kamar yarka Benazir ba da kowa yasan bakin halinta data gada awurin jatumarta, Ni ban ta6a aibata yayanka ba saini zaka aibata nawa Ubaid? Akwai dan iskan dayawuce danka daya keta mata haddi? Nayi zaton in masifa ta same ni kaine mutun na farko da zaka fara rufa min asiri ka sharemin hawayena ashe na yaudari kaina!!...." Dakyar ya ƙare maganar hawaye wasu nabin wasu akan kuncinsa Yaji zafin maganar Alhaji Ubaid. Hajiya layla ranta Ya 6aci matuka da jin yadda sheikh Imam Ke gaya magana akan ya'yanta, dama ba mutunci gareta ba, tana da sonkai, nata kadai ta sani, ko da take zumunci da su Albarkacin Alhaji ubaid suke Ci. Nan ta shiga surfa mashi ruwan masifa zagi ta uwa ta uba kamar zata dokesa, saboda rashin kunya, kwata kwata sheikh Imam bai damu da maganganunta ba saboda yasan halinta, Bata da kunya fitsararriya ce, kuma dama ita tabarmar kunya da bori ake naɗeta. Alhaji Ubaid kasa magana yayi, saboda Zuciyarshi da tayi rauni saboda maganar Sheikh Imam malik ta karya Zuciyar shi, Ya danji tausayin shi amma da ya tonu hudubar da shaidan yayi mashi saiya canza ra'ayin shi. Ya mike Ya fara gaya ma sheikh Imam magana Yace"ya jira ya ga abunda aka tura masa, zaisan ba kazafi yayi ma Aisha ba" Ya juya ya nufi dakinsa sheikh Imam Yana atsaye jikinshi na kerma zuciyarshi cike fal da tunanin menene Alhaji Ubaid zai nuna masa"? Bai karashe zancen zucin ba, sai Ga Alhaji Ubaid Ya fito hannun shi ruke da wayarsa Ya miƙa ma Sheikh Imam"gayanan ka gani da idonka" Yatsun hannunsa na kerma Ya kar6i wayar lokacin daya daura idanunsa akan Screen din wayar saida Zuciyar shi takusa dakatawa da bugawa saboda tsabar firgitar da yayi, a lokacin Jikin shi yadinga tsuma idanunshi suka kada jawur, baisan sa'adda Ya saki wayar Ta fadi kasa Ya juya cikin fitar hayyaci ya fuce daga gidan Yana tafiya kafafuwanshi na hardewa kamar zai kife kasa. Bayan fitarshi Zainab mai aikinsu Taje ta fada na Dr shureum abunda Iyayensa sukayi na sheikh Imam Malik, Ransa ya 6aci a zuciye yaje ya same su ya dinga yi masu fada kamar zai doke su, Yace basu kyauta ba, meyasa zasuyi ma sheikh Imam haka? Shifa makwabcinsu bayan haka sunyi zama na amana, amma saboda rashin adalci da son zuciya sun rufe ido akan rashin gaskiya suka ci mutuncin shi, babban abunda yafi kona mashi rai abunda suka nuna ma Sheikh Imam ya gani, yaji zafi sosai, amma su ko a jikinsu. Aisha tana zaune cikin dakinta a kan gado, tana tsaka da shayar da babynta, Baba Imam ya fado dakin Afujajan ko sallama baiyi mata ba, Jikin shi na zubda Gumi Yakai hannu Ya damƙi ƙeyar Aisha da ita da yar duka Ya wurgo su tsakar falo Ta kife kasa Yarinyar ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Da gudu masu aikin gidan suka fito sakamakon Kukan Aisha da suka jiyo, Aunty Laura dake a cikin dakinta tana tsaka dayin waya tajiyo kukan Aisha dana jinjirarta, batasan sa'adda ta jefar da wayar kasa ta watsa da gudu Ta shigo falon tana haki, Gabantane ya yanke ya fadi ganin Sheikh Imam tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki ga Aisha da jinjirarta yashe a kasa suna kuka. Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ta faɗa tare da nufar Aisha donta taimaka mata ta mike sai dai kafin Ta karasa Sheikh Imam Ya doka mata tsawa Yace"karki kuskura ki taba ta! Idan ba haka ba, abakin aurenki" cak ta tsaya jikinta na kerma. "Allah Ya isa tsakanina dake Aisha, Allah Tsine maki Albarka, In sha Allah sai kinga sakayyar abunda kikai min" waro idanu waje Aunty laura tayi, Hankalinta amatukar tashe, gashi ba halin tayi magana balle ta dakatar da shi, maids din suka daura hannayensu asaman kansu cike da tashin hankalin jin furucin sheikh Imam ga yarsa, ba su taba zaton zai yi mata haka ba, su din amintattunsu ne, koda asiri Ya tonu agidan suka gane Aisha tana da ciki basu ta6a nuna sun sani ba saboda basa son abunda zai zubar da martabar sheikh Imam da ita Aisha. "Kin cutar da rayuwata kin yaudareni Aisha, Idan aure Kikeso Meyasa ba zaki fada min ba inyi maki!? Sai kika zabi ki zubarmin da mutunci na, inayi maki kallon mutuniyar kirki ashe ke din fasika ce, mara tsoron Allah, Dama tun farko banso Kika je Germany karatu ba saboda hankalina bai kwanta ba, ashe bayan da kika je karuwanci ki ke yi acan, naga komai Aisha an nuna min videos dinki da hotunanki tare da kato, Yau silarki An zageni anci mutuncina Aisha wlh nayi danasanin haihuwarki da akayi"❗ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️* *Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~___________________________________~ fashewa tayi da matsanancin kuka sam ta kasa buɗe baki ta yi magana saboda bakin cikin tsinuwar da mahaifinta yayi mata, bata taba zaton zaiyi mata haka ba ko da kuwa ta aikata abunda ya ke zargin ta da shi, ta rasa gane wanene yayi mata kazafi? Laifin me tayi masa"? A lokacin Aunty Laura kasa jurewa tayi, tana jin koda zai sake ta ne sai tayi magana, Cikin fushi da nuna bacin rai tace"wallahi ka bani mamaki baban Aisha! Idan rai ya baci ai hankali bai kamata ya gushe ba, shin Ina ilminka ya ke da har zaka bari shaidan da zuciya su rinjaye ka! Kai fa ba mahaukaci bane, Da hankalin ka amma tayaya za'ay wa yarka kazafi ka yarda harka dauki mummunan mataki akanta...." bata kare maganar ba, sakamakon Marin daya kifa mata akan kuncinta, tuni hawaye sun cuccuko tab da idanunta, taji zafin marin da yai mata. Ganin hakan Yasa Maids din gidan suka sha jinin jikinsu, daya bayan daya suka bar falon zuciyarsu cike fal da tausayin Aisha da babynta. Murmushi Aunty laura tayi tana kallon cikin idanunshi da suka kada jawur sai tsuma yakeyi yana huci.. "Bazan fasa magana ba wlh, ko da zaka kashe ni ne! Wlh ka bani kunya kuma ka bani mamaki, sannan kaji kunya wlh, Tun wuri kayi gaggawar janye hukuncin da kayi ma Aisha tunkafin kayi danasani! Abune da ka sani na sani, kai da Aisha kuna da makiya masu jin haushin daukakar da Allah yayi maku kai baka tunanin sune suke kokarin 6ata maku suna? Bayan haka videos din da kake ikirarin an nuna maka ka ganta da ƙato Ka duba dakyau ba fuskarta aka dauka akayi editing ba"? Ta jefa mashi tambayar tana akai masa harara sam baya fahimtarta, ya riga daya hau kan dokin zuciya.. Sassauta muryarta tayi"yakamata ka dinga amfani da kwakwalwarka da kuma saninka, idan Aisha batayi abun kunya ba, to kai ne zakayi babban abun kunya, haba Imam ko da ace Aisha ta aikata laifin da kake zargin ta, kai ba maiyi mata uziri bane kaja ta ajiki don ta shiryu, korarta da za ki yi shi ne mafita? Hmm duk dai inda Aisha zataje Yarka ce, Kuma kowa yaganta zai ce diyar imam malik ce, Kaga kuwa babu ribar korarta! bana so kayi danasani mara amfani ...." Kalaman Aunty Laura sunso suyi tasiri acikin Zuciyarshi, Amma duk idan Ya tuna abun da idanunsa suka gane masa sai yaji wani irin kunci a cikin zuciyar shi, saboda shi yasan wacece Aisha, yana da tabbacin videos din da aka nuna mashi ba editing bane itace da kanta" Sheikh Imam bai dauki hudubar Aunty laura ba, ya ce ma Aisha ta tashi Tabar mashi gidan shi! baya bukatar ganinta, yana karashe maganar ya fuce yabar gidan. Maids din da Aunty Laura suka kewata sunata aikin lallashinta da bata hakuri, bata taba ganin bakar rana irin ta yau ba, har addu'a tayi Allah ya dauki ranta ta huta amma dayake Lokacin mutuwar nata baiyi ba sai bata mutun ba. Kasa tafiya tayi saboda bata son ta tafi, mahaifinta Yana fushi da ita, ga tsinuwar da yayi mata, tafi son Ta roki yafiyarsa inyaso saita tafi. Tsawon kwana uku tana zuwa dakinsa donta bashi hakuri bai ta6a sauraronta ba, Ko gaisuwarta baya amsawa, gaba daya ya ɗauke ƙafa da yi mata magana, ko kallon ta bai son yi. Aunty laura ta yi kokarin ta tunbi Hajjonsu don ta sanar da ita abunda ke faruwa don tasan ita kadaice zata iya take mashi burki A lokacin da take kokarin kiran layin Hajjo batasan sheikh Imam Ya shigo dakin nata ba, aiko batai aune ba, taji ya fusge wayar ya Maka ta da kasa ya take ta da kafarsa, yana huci ya gargadeta akan in ta kuskura ta fada ma wani wlh abakin auren ta, ba arziki taja bakinta tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido. Aisha ta shiga tsaka mai wuya, damuwa takusa tayi mata illa ko ma ince tayi mata illa, da abun ya ishe ta, ta kunna wayarta sakonni sukai ta tururuwar shigowa, ko ɗaya batayi sha'awar budewa ba ta lulubo layin Anila ta danna mata kira, don bata jin zata iya fadama Benazir saboda sun fita aranta batason komai daya shafe su. Lokacin da Anila taga kiran malama Aisha tayi mamaki bayan tsawon watannin data dauka bata neme su ba. Bayan ta daga kiran tayi ta tambayarta meyasa ta yada su? In sun kira basu samun layinta, kuma tayi tafiya ko sallama ba ta yi masu ba. Cikin shesshekar Kuka Aisha ta kwashe komai daya faru ta sanar da Aneelerh, Aneelerh Tayi kuka taji bakin ciki da takaicin abunda dr shureim yayi mata, Duk da tasan ba halinsa bane, kuma taji zafin Hukuncin da baba Imam yayi ma Aisha, sannan taji tausayinta sosai, Aisha tace mata tayi danasanin zuwanta germany karatu saboda anyi mata kazafi an daura mata laifin da bata aikata ba, Hankalin Aneelerh ya tashi sosai har tace mata zatazo gidan tare da Abie da Mami donsu tayata bashi hakuri ya yafe mata. Cikin sauri Aisha tace karta kuskura ta fada masu halin da take a ciki, Baba Imam yana da bad temper idan ransa ya 6aci baya ji baya gani sai daga baya ya ke yin danasani, Idan har yasan ta fada mata abunda ke faruwa da ita, to kuwa zai kara hukuntata ne, amma ta roke ta akan ta tayata da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai. badan Aneelerh taso ba tace mata toh amma dan Allah kar ta tafi ta zauna agidan, idan ma ya matsa mata akan ta bar masa gidan toh toh tazo gidan su ta zauna, Aisha tace mata toh. Bayan sun kammala waya Aneelerh bata ƙara samun kwanciya hankali ba, saboda zullumi da fargaban kada Aisha ta tafi, gashi ta hana ta faɗa ma Benazir halin da take a ciki ta kuma hana itama tazo gidan saboda gudun kada laifinta ya shafe su. Tayi azan Baba Imam zai sassauta hukuncin daya yanke mata, Ganin har anyi kwana biyu bai kara yi mata maganar ba, haka Aunty Laura ma tayi tunanin yaji nasihar ta ne shiyasa ya ƙyale Aisha, Hankalin su har ya dan kwanta. a daren wata ranar Alhamis, tana tsaka da yin bacci, ta rungume babynta da ke bacci akan kirjinta, Sai ga sheikh Imam Ya fado dakin Yana huci Ya tashe ta daga bacci Yace ta tashi tabar gidan bai son ganinta, Ta yi nesa da shi idan ba haka ba zai kashe yarta, Ya tsaneta baya son ganinta kuma wlh in har ta bari wani yasan tayi cikin shege ta haihu Sai Ya lahantata, tace mashi baba kada kayi min haka! Idan ka kore ni a cikin daren nan ina kake tunanin zan tafi? Bayan ka hana in nemi taimakon dangin mu, nifa yarka ce baba, amana ce agare ka, nasan da mahaifiya ta, tana araye wlh koda ace ni karuwace ba zata kore ni ba, saima taja ni a jikin ta don in shiryu, balle kai da ka taso tare dani ka sanni ciki da bai, ka tarbiyantar dani, kuma ka yarda dani amma a yau kaine kake korata? Saboda kaddara ta afka min? Bai Saurareta ba, Tana kuka ta sauko daga kan gadon, ko Aunty laura bata sani ba adaren ranar shekh imam Ya kori aisha daga gidan Har bakin gate Ya rakata Bata dauki komai nata ba sai yar wayar data tsira da ita. a bakin gate din gidan Alhaji Ubaid ta tsaya hannayenta rungume da jinjirarta dake ta sharar baccinta. Tana kuka Ta kalli sararin samaniya taga hadari ya hadu bakikkirin Babban tashin hankalinta kada a barke da ruwa sama batasan Ina zata sanya yarta ba. Anan ta yanke shawarar kiran dr shureim duk da bata da tabbacin yana nan ko bai nan don tunda abun nan ya faru bata kara jin duriyarshi ba tun da ba fita ta ke yi ba, wayarta kuma akashe take, ko ya kira ba sani zatayi ba. sau uku tana Kira baya Picking, sai ana hudune taci sa'a yai picking tace"shureim ina a kofar gidanku, Baba Imam ya kore ni daga gida, Ka zo ka kar6i yarka, idan ba haka ba zaka rasata ne"! Tana karasa maganar, ta kashe kiran. Ko mintuna biyar ba ayi ba sai ga dr shureim Ya fito jikin shi sanye da jallabiya, kallo daya da yayi ma Aisha saida gaban shi ya fadi ganin yadda ta rame idanunta sun kaɗa jawur sun kumbura, A lokacin yaji kunyar hada ido da ita kamar ya haƙa ƙasa ya binne kanshi, tsantsar tausayintane ya kama shi sam bai ma lura da babyn hannunta ba. Karasawa yayi kusa da ita, harya bude baki zaiyi mata magana ta dakatar da shi"ban kiraka don muyi magana ba, Yaya shureim nagode da abunda ka saka min da shi," ta fada tare da manna mashi yarinyar da ke a nannaɗe cikin towel dinta a kirjin shi yai sauri rungumeta wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyar shi. "Gatanan Itace abunda muka samu, nabar maka ita amana, badan bana sonta ba na baka ita, sai don bana so tasha wahala tunda ni yanzu bani da kowa banma san inda zan tafi ba, wata rana zan dawo in kar6i abuna, Inaso kayi mata huɗuba da sunan mahaifiyata FATIMA BATOOL, Idan har kabari rayuwarta ta cutu ka sani Allah yana sama yana Kallonka, Nima kuma bazan yafe maka ba, akwai ranar hisabi" maganganun Aisha sun karya mashi zuciya, baisan sa'adda ya fashe mata da kuka ya dinga yi mata magiya akan kada ta tafi tabarshi wlh yana sonta ashirye yake da ya aureta yayi mata alkawarin zai wanke laifinsa zai share mata hawayenta, zai kula da rayuwarta, tace mashi ya makaro, Lokacin daya kamata ya furta mata hakan ya riga daya wuce, sai bayan daya 6ata komai, sannan ita bazata taba auren namijin daya santa ba. Ba yadda baiyi da ita ba amma ta kafe, har cewa yayi ta shigo ta kwana agidansu amma takiya, ta juya zata tafi yabi bayanta yace sai dai su tafi atare saboda bazai iya rayuwa batare da ita ba, sannan Yar da tabar masa, shi baida abunda zai shayar da ita ta taimaka ta dawo suyi aure su rufawa kansu asiri da kuma yarsu. Aisha bata saurare shi ba, da taga dagaske Dr shureim binta zaiyi sai ta watsa da gudu Shima yabita aguje a karshe ta bace ma ganin shi... 😭 Tun daga wannan Lokacin dr shureim bai kara ganin Aisha ba, babu wanda yasan Ina ta dosa, Anila saidai taga sakon data tura mata. _Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu."_ A daren ranar bayan Dr shureim Ya koma da baby cikin gidan, batare da sanin kowa ba, Ya nufi daki da ita Ya kwanta kan gadonshi yayin daya rungume Yarshi a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da bakin cikin abunda yayi ma Aisha shine silar komai, yaji takaicin tafiyarta, yaji kunci da radadin rasata da yayi. Dakyar ya samu nutsuwa, ya buɗe fuskar babyn ya zuba mata idanunshi da suka kada jawur yadinga kallonta kamar zai hadiyeta, A hankali ya sumbace ta a saman forehead dinta da cheeks dinta, wani irin tsantsar sonta ne ya lullu6eshi kamar ya mayar da ita cikin shi, a kalla ya shafe rabin awa yana kallonta, aranshi ya ayyana inama ace ta hanyar aure suka same ta da sai yafi kowa farin cikin zuwanta duniya, amma ahakanma Ya gode ma Allah daya bashi ita, addu'o'i sosai yayi mata har yai mata huduba da sunan*FATIMA BATOOL* Bai tashi sanin yana a cikin musibaba, Saida Ta farka tsakar dare ta fara tsala kukan Yunwa, A firgice ya farka ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi duk yabi ya Ruɗe, ya sungumeta akan kafadarshi ya sauko daga kan gadon ya dinga zarya da ita a tsakar dakin yana lallashinta haɗi da jijjigata. Sakamakon kukan data dinga tsalawane Yaja har mutanan gidan suka farka daga bacci, Cike da mamakin jin kukan jinjira a cikin gidansu. Da gudu Suka nufo Dakin Dr shureim Alhaji ubaid da hajiya layla sai Mai aikinsu zainab, suna shigowa suka iske shureim ya rungume baby a kirjin shi. Cike da mamaki suka tambaye shi yar wacece? Donsu kwata kwata basu san Aisha ta haihu ba, sun dai san abunda ya faru tsakaninta da shureim. Jin yayi shiru bai basu amsa ba yasa hajiya Layla ta doka mashi tsawa tace shureim ba kaji ina magana ba? Yar uban wacece wannan"? Cikin sanyin murya yace"ƴata ce, babyn da Aisha ta haifa mince, Baba Imam ya koreta daga gidansa, shine ta kawo min ita jiya da daddare" Bai ƙare maganar ba Hajiya layla tayi tsalle ta dire tace"Wlh bazata sa6u ba! Shegiyar zaka kawo mana acikin gida? So kake kaja mana surutu agurin mutane? Wato shi uban nata ya koreta saboda gudun abun kunya sai mu zaka jajubo mana annoba ka kawo mana agida? Saboda baka da hankali"? Ta inda take shiga bata nan take fita ba, Kamar zata rufesa da bugu, Kalamanta sun Kona ransa, musamman data kira yarsa da sunan shegiya, bai kula ta ba hankalinsa na akan fatima dake ta kuka surutunsu Ya kara hargitsa kwakwalwarta duk tabi ta rude ga yunwa tana ji. Alhaji Ubaid Yace"shureim, kayi hakuri da abunda zance, badan bana son jininka ba, sai don gudun abun kunya, kuma kaga an kusa fara zabe in har maganar nan ta fita wlh za ka ja min asara ne, don Allah ka dauki yarinyar nan ka kaita gidan marayu su kula maka da ita, Inyaso sai ka dinga zuwa kana dubata..." sai a lokaci Ya fuskance su da wata irin fusatacciyar murya yace"ɗan ku ne shegen da yayi wa uwarta ciki ta haifeta, wallahi ba inda zan kaita! Ban taba sanin baku da imani ba sai yau da kuka nuna min, Yarinyar nan koba dan kasancewarta jinina ba Yakamata ku tausayamata, Jaririya ce fa? Ta rasa mahaifiyarta, ni kadai na rage mata, ya kuke so tayi da rayuwarta ne"? Idanunsa cike tab da kwalla yai maganar. Aunty Zainab tayi kokarin tayashi fadan amma Hajiya layla ta koreta daga dakin ta fuce tana kuka saboda sun bata tausayi. Kusan dare suka raba ana abu daya, kowa yana akan bakanshi. Hakika dr shureim Yaci wahalar Iyayenshi, kullum sai sunyi barazanar kashe mashi ƴa in har bai fitar masu da ita daga gidan ba amma Yakiya. wulakancin yau daban na gobe daban Sun daura mata karan tsana ba gyaira ba dalili, Aunty zainab ce ke shayar mashi da ita a boye batare da sanin su ba. Hajiya layla har ɗaukar babyn tayi batare da sanin shi ba, ta fuce da ita daga cikin gidan, a lokacin yaje masallaci yin sallah sai da ya dawo ya duba dakin shi bai ganta akan gado ba, ya fito arude yana nemanta, Aunty zainab ce ta fada mashi taga hajiya layla ta shiga dakin shi, tana da tabbacin itace ta ɗauke ta, hankalinsa ya tashi, ya dinga kiran layinta bata picking, time data dawo cikin motarta ta shigo gidan ya nufeta yana huci yace ina yarshi tace tabada ita sadaka. Ji yayi kamar ya dauketa da mari, ya dinga rokonta akan ta dawo mashi da yarshi tayi banza ta kyale shi, yai hakuri Ya jira time da Alhaji ubaid ya shigo gidan, ya tuntube shi da maganar ya dinga rokonsa akan ya yi ma mommynsu magana ta dawo masa da yarsa, Alhaji ubaid bai kulasa ba saima yace tayi abunda ya dace. rai a6ace Ya nufi Kitchen Zainab tana a ciki tana yin girki taga yashigo ya dauki wuka Ya fita da ita aguje tabi bayanshi. A lokacin Hajiya layla tana a zaune kan kujera tana danna waya batai aune ba, taji ya ɗaura mata wuka a akan wuyanta, ta zare ido gabanta na faduwa, shureim yana huci yace"kodai ta fada mashi inda takai mashi baby, ko kuma ya kasheta" adabarbarce tace"nashiga uku shureim ni zaka kashe? Mahaifiyarka? Saboda kawai na kawar da ƙazantar zina daga cikin gidan mu"? Ihunta da Alhaji Ubaid ya ji yo ne yasa shi watso wa da gudu Yafito daga dakin shi ganin abun da Shureim ke kokarin yi ne Ya tada hankalinsa kafin Ya karaso Shureim Yace"kana karasowa zan hada dakai in kashe!" ba arziki Alhaji ubaid Yaci burki yana lallashin shi akan ya aje wukar zasu dawo mashi da yar shi, Zainab tana kallon komai dake faruwa, ko kadan bata sa baki ba, saboda taji dadin barazanar da Shureim yayi masu, tun da su ba Allah aran su. Hajiya layla data gama tsorata cikin shakakkar murya ta fada mashi sunan gidan marayun data kai Batool. Sakin wukar yayi da gudu Ya fuce daga gidan Cikin motar shi Ya tafi. Kafin marecen ranar sai gashi ya dawo da babynsa, ya rungume abunsa a kirjin shi, baiwar Allah tayi kuka har ta gaji idanunta sun kada jawur dakyarma ya samu Caregivers din dake rainon yaran suka bashi ita, saida ya basu cin hanci harna Dubu dari shidda kafin suka damka mashi ita. Abun da ya ɗaurewa shureim kai, Mugayen halayan da iyayensa suka sauya wanda ada ba haka suke ba, har kwara hajiya layla yasan tunfil azal bata da mutunci, batason talaka, ta tsani talauci, ga girman kai, amma mahaifinsu Alhaji ubaid ba halinsa bane, Shi shaidane babansu mutumin kirkine amma tunda ya faɗa harkar siyasa ya canza shima, Ya rasa gane meke faruwa ne? Duk wannan badakalar da aka sha Benazir bata sani ba, ko awaya inta kira su don su gaisa ko suka kira donsu gaisa da ita babu wanda ya taba gigin faɗa mata. don wlh da ace ta sani zasu sha ruwan mamaki saboda masifarta, har hajiya layla data gado shakkarta take ji, zata tsayama shureim ne kuma babu wanda ya isa ya ɗaga ma yarsa yatsa agidan. Shureim harya fara tunanin sun hakura, ganin kwana biyu basu bi takanshi ba, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba, ashe wata wutar bala'en ce zasu kunna mashi. Alhaji Ubaid yasa aka kulle mashi bank account dinsa, Ya hana shi abincin gidan shi, duk wani abu da yayi mashi a matsayin uba saida ya kwace shi, hada key din motarsa ya kwace ya kasance baida ko sisi, ita kuma zainab da hajiya layla ta gano tana shayar da yarsa kuma tana satar abinci aboye takai ma shureim aikuwa tayi mata shegen duka da girmanta da komai ta kuma koreta daga gidan gashi bata da kowa a nigeria danginta da komai suna a egypt haka tayi ta gagari cikin gari. Dr shureim ya shiga matsananciyar damuwa, da shi da yarshi suna a tsaka mai wuya, Ya rame yayi duhu, Itama jinjirar ba lafiya, ga yunwa da rashin bacci, kwana su ke yi idon su biyu har rokon su yayi kan su taimake shi kada ya rasa yarshi suka kiya saima su ka ce In har yana so su mayar masa da komai nashi da suka kar6a to ya mayar da Batool gidan marayu, kusan kullum sai ya jaraba kiran layin Uncle musa don ya fada masa halin da ya ke a ciki saboda yasan shi kadai ne zai goyi bayansa sannan ya taimaka masa amma ko ya kira layin a kashe ya ke samun shi, baisan ya zaiyi ba, ga Hajiya layla tace in har ya kuskura ya kira wani nata don ya taimaka mashi Allah ya isa bata yafe ba shiyasa ya kasa kiran Ammin su. Baida wata mafita daya wuce ya gaya ma Allah, A karshe ya dauki yarsa yabar masu gidan. Ko a jikinsu damuwarsu daya kada su rasa dan su amma donta yarinyar basu damu ta mutu ko tayi rai ba. Baisan Ina zai nufa da ita ba, a wannan zamanin bakowane zai kula maka da dan ka tsakani da Allah ba, gashi bakowa ya sani a joss ba, saboda rabi da kwata na rayuwarsa a gurin amminsu yayita can Kasar egypt. Tafiya ya ke yi Jikin shi ba kuzari, ya rungume babynsa a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da tunanin makomar rayuwar yarsa. Tuntana kuka har ta gaji tayi shiru bacci ya ɗauketa, kwatsam aka fara ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ya rasa ina zai sama masu mafakar da zasu zauna, Baiwar Allah tana tsaka da baccinta ruwa ya farkar da ita, Ta dinga tsala kuka ya rasa ina zai kaita don kada ruwan yai mata illa. a karshe dai ruwan gaba daya akansu ya ƙare, Har dare ba adaina ruwan ba, saida daren Ya tsala ruwan Ya dauke a lokacin Ya ma fidda rai da ita saboda Zuciyarta ta daina bugawa Jikinta ya saki. Anan ne ya yanke shawarar binneta, Saboda yaga baida wata mafita, in har ya barta wahala zata cigaba da sha, mutane ma ba zasu kyale ta ba za'acigaba da tsangwamarta ne tunda har iyayensa sun shegantata sun kirata da kazanta inaga mutanan waje? Kowa ma zai samu kwarin gwiwar cuzguna mata ne idan ta girma, kwara ya saukaka mata ta huta itama, yasan in ta mutu Allah zaiji kanta. A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacin shi kamar ya fara zaucewa, Da hannayenshi Ya haƙa rami, Ya sakata a ciki ya kwantar da ita yayi mata addu'a, Yana kallon yatsun kafafunta dake motsi alamar bata mutuba, amma Ya rufe ido saboda bayason taci gaba da shan wahala Ya rufe mata kasa a jikinta ya daddale gurin da kafafuwan shi, anan ya zauna kamar mahaukaci yaci gaba da sambatu shi ka ɗai daga bisani ya suma akan kabarin ta. Bayan sati Biyu da afkuwar lamarin, Dr shureim Ya farka a gadon asibiti, ya fara lalubar Yarsa Yaji shiru babu ita a jikin shi, Yabi ya rude hankalin shi Ya tashi, ya sauko daga kan gadon Yana fadin Ina yarsa! Ina fatimarsa! Ina batool dinsa! Tana Ina"? Likitan dake dubashi Ya rurruke shi Yana kokarin kwantar masa da hankali, aikuwa ya bangaje shi da karfi har saida doc din Ya kife kasa. Hajiya layla Da Alhaji Ubaid da ke a waje suna jiran tsammani, muryarsa da suka jiyo daga cikin dakin yana kwala ma batool kira yasa suka yi saurin shigo cikin dakin, yana ganin su ya nufe su yana tambayar su Ina yarsa take? Ta na ina? Hajiya Layla tace suma basu san Inda ya kai ta ba, abun da ya faru bayan ya bar gida suka baza jami'ae don su nemo shi, cikin sa'a jami'an suka tsintoshi a sume a gaban wata bishiya, amma basu ga yar shi ba, shine suka garzaya da shi asibiti, Yau sati biyu kenan baya a cikin hayyacin shi.." sai da tayi wannan maganar ya tuna da abunda ya aikata ma Batool, wani irin jiri jirin tashin hankali Ya gani acikin idanun shi, ya dinga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un kamar maganarsa zata kare! wai mike faruwa da rayuwarshi kamar wanda akayima jifa? bala'i daga wannan sai wannan. Bai karasa jin zancen ba, Ya watsa da gudu Ya fito daga asibitin, suka biyoshi a cikin motar su, Ya dinga gudu kamar zai fadi kasa, har titi Ya hau mota ta kusa bankade shi Allah ne dai Ya tsare shi dakyar Ya gano gurin da ya binne ta, Ya zube kan gwiwowinsa, Jikinshi na kerma Ya haƙa ramin wani irin faduwar gaba Yaji ganin kasusuwanta, Harta mutu ta rube kashinta kadai ya rage, daddafe kanshi yai da tafukan hannayen shi saboda matsanancin ciwon kan da yaji, nan Take Ya yanke jiki ya fadi a sume. A lokacin motorsu Alhaji Ubaid ta karaso gurin da yake, bayan sun fito suka taras da shureim rai hannun Allah, ga ramin daya haƙa abude sai kasusuwa birjik a cikin sa. Basu tsaya bata lokaci ba, Alhaji ubaid Ya dauke shi ya shigarshi da shi cikin motar, suka koma asibiti da shi. Tun daga wannan Lokacin shureim bai kara hankali ba, ya zama mahaukacin karfi da yaji, bayagajiya da sambatu yana fadin wayyo Allahana, na kashe Batool, da hannuna na binne ta acikin rami, Batool ta mutu ta zama kashi, Naci amanar da aisha ta bani, Allah bazai barni ba" sai da takai ga ko sallah shureim bai iyayinta cikin nutsuwa, A lokacin Hajiya layla da Alhaji Ubaid sun ji tausayin shi sun kumayi danasanin tilasta mashin da sukayi akan yarinyar gayanan sun ja ya binneta ta mutu, shi kuma Ya haukace. saida ya shafe wata daya bai dawo daidaiba, A lokacin Hajiya layla ta dawo da zainab mai aikinsu gidan tana daya daga cikin masu bashi kulawa duk da baya acikin hayyacin shi tayi kokarin tambayarshi meya faru? A haukan nashi Ya fayyace mata komai, tayi bakinci sosai sai dai bata ga laifin shi ba, saboda tasan me yaja mashi ya aikata hakan, haka ta dinga kokarin kwantar mashi da Hankali. Ganin za6e ya kusa ga mutane sun fara yi masu surutu akan Halin da shureim ya shiga duk da kullan da sukeyi mashi amma an asamu wasu daga cikin ma'aikatan gidan sun fitar da sirrin su a boye, Hakan Yasa suka yanke shawarar tura shi Egypt, to a lokacin ya ɗan fara dawowa hayyacin shi tunkafin ma suje mashi da maganar ya tattara yanashi yanashi batare da saninsu ba ya tafi egypt saboda bayason zama tare da su sun fita aranshi, bayan ya isa ne ammin su ta kira hajiya layla ta sanar da su shureim yazo sai dai bata gane meke damun shi ba, ko magana ba ya iya yi mata. Hajiya layla tace ta taimaka ta lallashe shi sannan ta bashi kulawa, ya samu tabin hankali ne sakamakon buguwar da kanshi yayi garin tukin mota ya yi accident har jinya yayi a asibiti. Karya da gaskiya ta dinga fada mata har ammi ta yarda da maganarta tace in sha Allah zatayi kokarin bashi kulawa, hakan ba karamin dadi yayiwa hajiya layla ba. Bayan komawarsa egypt ya gaza jure radadin da zuciyarshi keyi mashi kullumne sai yayi mafarkin Batool a cikin rami tana kuka, Hakan ya ƙara dagula mashi lissafi har takaishi ga fadawa harkar shaye shaye ya zama cikakken dan kwaya. _(Kunji alakar dake atsakanin Ummi da su Benazir da kuma shiekh Imam malik, da kuma kaddarar datayi silar rabuwar su da ita, Bayan haka duk wata sa'insa da dr shureim yakeyi da iyayenshi bayan dawowarshi daga egypt a lokacin dayaji sauƙi ya dawo hayyacin shi ya kuma daina shaye shaye, wannan rashin jituwar ta samo asaline daga abunda sukayi mashi, yana yawan furtawa hajiya layla sune silar masifar daya shiga, ita kuma tace basu bane saboda lokacin da zai aikata bai yi shawara da su ba, bayan haka Hotunan da yake yawan kallo acikin wayarshi hoton mutun biyune! Hoton Aisha da kuma hoton Yarsa Batool daya ta6a dauka a wayarsa, ko bayan dawowarsa Nigeria bai yarda yarsa batool ta mutu ba, saboda a lokacin duk in zaiyi mafarki da ita araye yake ganinta ba amace ba, sannan kasusuwan daya gani a cikin kabarinta yana kokwanton bana mutun bane kamar na kare ne, bayan haka yana mamakin yarda tayi saurin zama kashi in two week da binne ta❗ shiyasa yake zargin akwai wata makarkashiya, amma daga baya ya hakura da tuhumar iyayensa Ya dauki dangana, Benazir bata tashi sanin abunda Ya faruwa ba saida ta baro gidan Uncle musa aranar ma tare da shi suka zo joss din da iyalinsa Sara da kanwarsa Hajiya laura dake zaune agidansa, anan sukaji komai daya faru abakin Alhaji ubaid sai dai bai bayyana masu ukubar da su ka yiwa shureim da yarsa ba, sun dai fadi laifin shureim na binne Batool da yayi, Uncle musa ya nuna rashin jin dadin shi har fada saida yayi masu akan sakacin da sukayi har suka bari shureim ya binne yarsa, Benazir kuwa saboda bakin cikin abunda shureim yayi ma Aisha da kuma yar daya binne saida tayi jinya gadon asibiti saboda tana da fusatacciyar Zuciya, bayan da aka sallame ta daga asibitin ne, ta taka taje har gidansu anila ta rufe ta da fada akan boye matan da tayi, anila tay ta kokarin fahimtar da ita cewa ba laifinta bane, Aisha ce ta hana ta sanar da ita saboda gudun abun da zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu faɗa, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya ɗaure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany, bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji👍)_ Gaba ɗaya suka bita da kallo yayin da take ƙarasa saukowa daga kan stairs ɗin ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta. cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"! Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir. Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."? Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita. Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta. Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu, a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."! Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwaɗaita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana ƙarasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka haɗa kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su. "Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya faɗa yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna. Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi. Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi .. Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba. Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ƙara girma ya kuma ƙara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da. Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya faɗa idanunsa cike tab da kwalla. "Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu. Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers" Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji "Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla. Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?" Gabansu ne Ya faɗi rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta. Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga! Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba. "Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...." bata ƙare maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aruɗe ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru. "Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take? Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla. Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata.. "Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ƴata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"? Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani. Gaba daya maganganun Aisha sun ruɗa Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan ɗaya, ya rasa gane inda suka dosa. Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan meya hada ku ba" "Daddyn Angel, kace suyi min magana Ina babyna take? Sunyi banza sun kyale ni suna ji ina magana"! Tausayin ta ne ya kama Taj, yace"dan Allah ku fada mata Ina babynta ta ke"! In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....." kasa ƙarasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un.. "Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi, amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..." Benazir bata ƙarasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu. "Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.." Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse ƙofar. *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 ~___________________________________~ A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu ɗauke da damuwa. "Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki faɗa ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi ƙona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......" daƙyar Benazir ta ƙare maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa. Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin. "Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda baƙin cikin da na ji, wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan" Aneelerh ta ɗaura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki faɗa min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu? Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike? Kina raye ko kin mutu? Meke faruwa a cikin rayuwar ki.... " Aneelerh bata ƙarasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba ɗaya ɗokin ganinki mu ke yi" Babu alamun zata tanka masu. "Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita" Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun kaɗa jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake saƙawa a cikin Zuciyar shi. Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su. "Pls ina son insan meye alaƙarku da Aisha ne? A nan take zaune?" Murmushi Taj ya ɗan yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar. A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya ƙara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..." Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita. A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina! Meke damunki? Meyasa ki ke kuka? Waya 6ata maki rai!" Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so! Ki faɗa min meke damun ki?" dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini! Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi! Baki ji radadin da nake ji ba..." sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ruɗewa ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa. "Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake ba?" ta faɗi hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi. Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta miƙar da ita zaune saboda karfin hali irin nata.. Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest ɗinta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta haɗu data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya ɗauka har a jikinta tana jin shi. Ruɗewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki.. " ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta faɗa ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi taƙi bari ta motsa. Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta. Kafin Ta ɗaura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke ɗan bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya. Ji ta yi inama ace Batool ce ɗiyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran daɗewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne. Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta ƙara tabbatar da hasashen ta. "Aunty Ummi da sauki?" Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh . Time da aka fara kiran sallar la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu ɗaya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da ƙafarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arziƙi ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar ƙafa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sauƙi, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya faɗa tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota ta dawo ta gaban shi, ya yi ta ƙoƙarin miƙewa yana kasawa har saida Dr. Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi. __________________________________✍️ Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta ƙurawa ceilling idanunta da suka kaɗa jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita? Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi ƙona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka? In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta? Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai maƙura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara. _______________________________🌹✍️ Around ƙarfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari ɗaya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit. With respect Security Officers din suka sara mashi, har zai juya muryar driver dinsa ya katse shi "Sir, should I bring in the suitcases?" He nodded, then turned away, ya nufi falo. Cikin sauri SA ɗin ya buɗe tanƙameman boot din motar Chief, ya soma fiddo wasu hadaddun akwatina, guda biyu bayan ya gama ya rufe boot din, ya ruƙo handles dinsu ya bi bayan Chief da su. Chief bai taras da kowa a falon ba, Kaitsaye Ya nufi Upstairs saboda a gajiye ya dawo he needs some rest, duk da yafi bukatar ya gana da su. Bayan shigar shi dakin, SA din Ya shigo mashi da akwatinnan ya ajiye su kafin ya fuce. Shaf shaf ya rage kayan jikin shi Ya shiga bathroom don ya yi wanka. Bayan wani Lokaci ya fito daga part dinsa ya dauki wankan blue sky voile, sai kamshi ke tashi a jikin shi, walking magestically ya nufo down. tun kafin ya ƙaraso takun tafiyarsa yaja hankulansu ga duban shi, a lokacin sun dawo falo suna jiran shi. A hanzarce suka mimmiƙe tsaye, kaitsaye ya nufi Dr Shureim, side hug ya yi masa tare da ruko hannunsa sukayi musabaha, Dr shurem ya ɗan yi mamakin saukin kan Chief yadda ya tarbe shi kamar sun saba da juna. With respect Aneelerh da Benazir suka gaishe da shi tare da yi mashi sannu da dawowa, fuskarsa da fara'a ya amsa masu. Gaba ɗaya Ya lura da yanayin fuskokin su kamar ba walwala akai. Sarah mashi Taj ya yi daga zaunen da ya ke bai motsa ba ya yi mashi sannu da dawowa, mayar masa da martanin sarawar ya yi kafin ya amsa gaisuwar da ya yi masa tare da miƙa masa hannu suka gaisa da juna. Daga bisani ya zauna gefen Taj, ya kasance suna fuskantar su Dr shureim.. "A yi mini afwa, na barku kunata jirana." Ɗan murmushi suka yi gaba dayansu. Dr shureim ya ce, "bakomai wlh, Allah yasa dai bamu katse maka aiki ba" Fuskarshi a sake ya ɗan jinjina kan shi, Tunkafin ya tambayi wani abu Taj ya yi hanzarin daukar wayar Ana dake ajiye gefensa ya kunna masa videon tare da miƙa masa ya sa hannu ya kar6a tare da daura idanunsa akan Screen din wayar ya nutsu yana kallon videon, bayan ya gama kallo shiru ya yi yana ɗan jinjina kan shi. Lamarin ya ɗaure mashi kai tamau, kuma tunanin su ya zo ɗaya dana Taj. Gyaran murya ya yi masu a hankali suka mayar da dubansu gare shi. Tambayoyi ya fara yi ma Anila dangane da Ana da kuma Uncle din ta, bata boye masa komai ba duk abunda ya tambaya sai ta bashi amsa. Bayan Ya kammala yi mata tambayoyin, Taj ya ce, "Benazir, ki yi masa bayanin abun da ke damun ki" cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh, A tsanake ta kwashe komai da ya faru da ita a gidan Uncle musa ta sanar da Chief, ta ƙara da cewa, "Ban sanar ma kowa ba, Yaya Shureim ne kaɗai ya sani, bayan haka yanzu an ɗaga ƙafa da kawo min harin." Yanayin fuskar Chief ya nuna tsantsar ruɗani da al'ajabi, kallon Dr Shureim ya yi wanda gaba daya hankalin sa baya akan su, duba da yadda ya sadda kan shi ƙasa. "Za ki iya suffanta mini mutumin da ya kawo maki hari a cikin toilet?" Ta amsa da eh, kafin ta fara siffanta mashi mutumin. Kallon kallo suka jefawa juna tsakanin shi da Taj, lamarin ya daure masu kai, saboda gaba ɗaya yadda Benazir ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant ɗin kurkukun Ƙaddara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya ɗago ya dubi Benazir suka haɗa ido cikin na juna. "A lokacin baya, kafin ƙaddara ta rabaki da gidan mijin ki, babu wanda ki ka ta6a yi ma laifi kuka samu sa6ani a tsakanin ku har ta kai ya ci wani alwashi a kan ki?" Girgiza kai ta yi,"Gaskiya ni ba wanda wani abu ya taba haɗa ni da shi..." Bata ƙare maganar ba, ganin irin kallon da Taj ya yi mata, nan take ta fahimci me yake nufi wato yasan halinta ciki da bai. Gyaran murya ta dan yi, "A lokacin baya nasan bana jin magana, idan nace ban taba samun sabani da wani ba to na yi ƙarya, amma bana tunanin na yi laifin da har za'ayi yunƙurin kashe ni" "Bakya tunanin wanda ya yi maki kurciya shine yake nema ya kashe ki saboda ya ga kin dawo a raye, may be akwai wani abu da ya haɗa ku ko sanin sirrin wani wanda baya son asirin shi ya tonu ta silar bayyanar ki shiyasa yake nema ya halaka ki..." Maganar Chief tasa ta jin faduwar gaba, zurfin tunani ta shiga yayin da ƙwaƙwalwarta ke kokarin tariyo mata abubuwan da suka faru a lokacin baya kafin ta gudu daga gidanta, sai dai ta kasa tuna komai kamar an wanke mata brain dinta. "Ki yi kokari ki tuna Benazir, ba ƙaramin taimako zaiyi mana ba" Taj ne ya yi mata maganar cikin kwantar da murya, har kallon shi saida tayi kamar wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Chief yana lura da duk wani motsin su haɗi da karantar yanayinsu ta fuskarsu. Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Aneelerh dake yi mata magana cikin raɗa, "Please ki tuna Benazir, ni nasan baza a rasa wadanda kuka taba samun sabani da su ba, ko ya ya ne ki yi tunani pls" Wani abu da Chief ya lura da shi shine satar kallon Dr shureim da take yi, hakan yasa shi zargin akwai abun da ta sani, kuma tana so ta fada sai dai bata son Dr Shureim ya ji shiyasa take satar kallon shi a fakaice. Fahimtar hakan yasa shi cewa, "Kada ki damu, zan baki lokaci, bayan kin koma gida kiyi kokari ki tuna in ya so sai ki kira Taj a waya ki sanar da shi" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da ɗin murmushi ta ce, "In sha Allah idan na tuna zan kira in sanar da ku" Shiru suka dan yi na wani lokaci. "Meke damun shi ne?" Chief ne ya fada idanunsa akan fuskar Dr Shureim ƴan hawayen da suka cika idanun shi sai kokarin sauka kan kuncinsa suke yi. Taj ya ce, "Yawwa Sir, namanta ban fada maka ba...." A hankali Chief ya mayar da hankalinsa akan Taj, komai da ya faru bayan fitowar Ummi Ya sanar da shi, jinjina kai ya yi tare da kallon su Anila, "Zan iya sanin menene alaƙar ku da ita?"? Har suna haɗa baki gurin furta eh saboda suna son ya taimaka masu tunda agidanshi take da zama. "Yaya Shureim," Benazir ce ta kira sunan shi, cike da damuwa ya ɗago ya kalle ta, a kunne ta yi masa raɗa, "Suna son sanin menene alakar mu da Aisha, zan iya faɗa masu komai da ya faru? tun da ka ga agurinsu take da zama may be idan su ka ji su taimaka mana" Ya ɗan ji nauyin maganar, amma a halin yanzu baida za6i, Cikin sanyin murya ya ce, "Idan kina ganin zasu sama mana mafita, ki fada masu komai," Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta maida dubanta akan Taj da Chief. Nan ta fara basu labarin rayuwarsu, da alakar su da Aisha, da kaddarar data raba su da juna, bata 6oye masu komai ba, da yake ta iya bada labari ko mistake bata yi. Lokacin data ƙarasa basu labarin idanunta cike tab da ƙwalla, yayin da su kuma tsantsar mamaki da al'jabine ya kamasu, A sanin su da Ummi tantiriyar Karuwace da ta yi ƙaurin suna a America, ashe kaddara ce ta canza mata rayuwa, sun ji tausayinta sosai, har ta kai ga sun yi shiru jimm suna ɗan jinjina heads din su, shi dama Taj ya daɗe yana yi mata kallon sani, sai yanzu da Benazir ta bada labarinsu, Ya tabbatar ma kansa Bintu Imam ce. "Dan Allah ku taimaka mana, kada ku bari Aisha ta koma America, ku ruke mana ita har sai mun sansanta tsakaninta da mahaifinta da kuma mu, muna so ta koma kamar yadda take a da, sauyin da muka gani atare da ita ya tada mana hankali, wlh kallo ɗaya da nayi mata na fahimci ta canza rayuwarta" Chief ne ya ce,"Na yi maku alkawari In sha Allah, Aisha ba zata koma America ba, zan cigaba da ruke ta anan har sai na cika maku burukan ku, saboda nima na damu da ita na tausayama rayuwarta sosai, na ji zafin abun da ya yi silar rabata da mahaifinta da kuma halin da ta jefa rayuwarta, wanda nayi imanin tsinuwar da mahaifinta ya yi mata ce ke bibiyarta, bayan haka Dr Shureim..." Ya amsa mashi da na'am idanunsu acikin na juna. "Kaima na tausaya maka sosai, labarinku ya ta6a zuciyata, kun bani tausayi, please ka cigaba da hakurin da ka saba yi, in sha Allah ni Chief na yi maka alƙawarin Ummi won't leave this house until everything is settled" Maganar Chief ta kwantar masa da hankalinsa, wani dadine ya ji ya lullu6e zuciyar shi, Anila Da Benazir basu san sa'adda suka saki murmushin jin dadi ba, har suna hada baki gurin yi mashi godiya. "Ina fata mun gama magana, ko akwai sauran wani abu?" Cikin kulawa Chief Ya faɗa yana duban su, "Unaisah, ta ƙi kula ni...." gaba daya ta fada mashi abunda ya faru tsakaninta da Unaisah, har cikin ranshi bai ji dadi ba, amma ya fahimci Unaisah, baiga laifinta ba, dole ne dama ta ƙi accepting din ta saboda ta ƙullace ta aranta. "Kada Ki damu, Ni zan yi mata bayanin da zata fahimta, In sha Allah" Ita dai Anila tunaninta ya fara komawa gida fargabanta kada Junaid ya saki baki ya furta dodon da ya kashe Anah a gaban Uncle. "Akwai gargadin da nake so na yi maku gaba dayanku, daga rana irin ta yau inaso ku dauki kanku a matsayin jami'an sirri, kada ku kuskura ku faɗa ma wani damuwarku, sannan kada ku bari yanayin ku ya nuna! Duk wani abu da muka tattauna anan to mu binne shi anan!" Ya faɗa yana nuna floor da index finger ɗinsa. "Sirrinku a cikin zuciyarku, In zai yiwu ma, ku daina tunanin abun cos kuskure kaɗan zai iya jefa rayuwar ku cikin hadari. Tun da har kun fada mana komai, from now on Case din yabar hannun ku, yanzu yana a hannunmu, kuma in sha Allah zamu cigaba da yin bincike akai" Gaba ɗaya sun yi amanna da maganar shi, kuma sun daukar mashi alƙawari zasu kiyaye. "Yakamata mu tafi, na ga an kusa fara kiran Magrib" Aneelerh ce ta faɗa tana duba wrist watch din hannunta. Taj ya ce, "Zamu ruƙe wayar Ana a hannun mu, har zuwa time da zamu kammala bincike. Mungode sosai, Allah ya maida ku gida Lafiya" Atare suka hada baki gurin furta Ameen muna godiya muma da aka kar6e mu hannu bibbiyu tare da fatan nasara. Dakyar Dr shureim ya mike fuskarsa sam ba walwala, ya so ace zai iya ganin Aisha kafin su tafi. Daƙyar ya iya furta,"Please zan iya samun phone number din Aisha?" Taj ya ce, "Mi zai hana." ya ɗauko wayarsa ya lalubo layin Ummi ya mika masa, yatsun hannunsa har kerma suke saboda zumudin ya kar6a, shaf shaf yayi copying dinta bayan ya gama ya mika ma Taj tare da yi mashi godiya. Benazir dake kallon shi ta kasa gane me ya hana shi mikewa? A ganinta ko rakiya ne yakamata ya yi masu. "Muje nayi maku rakiya" Chief ne ya fada tare da mikewa, ya ruko hannun Dr shureim a cikin nashi suka yi gaba, Aneelerh da Benazir suna a biye da bayan su. Bin su da kallo ya yi har saida suka 6ace ma ganinsa, lumshe idanun shi yayi a hankali yake tariyo komai da ya faru tun farkon zuwan su Benazir. Unexpectedly ya ji an sumbaci forehead dinsa, a firgice ya buɗe idanun shi, har saida gaban shi ya fadi da ya yi tozali da Benazir ta sunkuyo da kanta saitin fuskarshi, nan da nan ya haɗe rai, "Baki tafi ba?" "Taya zan tafi kana fushi dani" Ɗaure mata fuska ya yi. "Pls abunda ya faru ɗazu ka yafe mini, raina ne ya 6aci," Ta fada tana kashe mashi murya. "Na ji, ya wuce." "Yaushe zaka maida ni ne? Na gaji da jira." Wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce, "Toh rasa kunya 6eran tanka, ke baki ji kunyar furta in maida ki ba? Hauka nake da zan dauki macen da take ruƙe kwalar rigana kamar zata doke ni!" Ya fada babu wasa akan fuskarsa. Marairaice fuska ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce, "Pls ay na baka hakuri, wlh na gane kuskure na, don Allah ka daina wahalar da ni mana, nafa san kana sona har yanzu." ta faɗa tana yi mashi farfari da idanunta. Hakan da tayi ba ƙaramin sace zuciyar shi ta yi ba. "Ka yi shiru bakace komai ba," Ta fada da yar shagwa6arta. Ɗagowa ya yi suka hada ido cikin na juna wani kallon so da kauna suke jefawa junan su, bakomai take tuna mashi ba face Unaisah. "Wallahi wannan karon idan ka mayar dani, zan yi maka biyayya sau da ƙafa, zan tarairayeka kamar jinjiri, yanzu fa na canza ba Benazir din da ka sani ada bace, ka ga yanzu na iya girki, na iya gyara gado, na iya wanki, wlh har wanka zan dinga yi maka...." Duk yadda ya kai ga hana kanshi sakar mata fuska baisan sa'adda ya tuntsire da dariya ba, saboda kalamanta sun bashi dariya, kuma dagaske take fada masa babu wasa akan fuskarta. "Oh, kina nufin yanzu kin gane an halicci hannayenki don ki girka ma ƙato abinci?" Ya fada tare da ɗage mata gira, dariya ta saki har dimples dinta ya lotsa. "Bama iya girki ba, komai zanyi masa." Tabe bakinsa ya dan yi. "Yakamata ki tafi suna jiranki." Ɗan bubbuga kafafunta ta yi kan floor, "Taya zan tafi baka bani amsa na ba?" "Zamu yi magana a waya" Ba don ta so ba tace, "ka yi mini alƙawari?" Jinjina mata kai ya yi. "Okay, ka rama min kiss da na yi maka." Zare idon shi ya ɗan yi bata jira amsar shi ba ta manna mashi peck ta juya tana dariya ta nufi Kofa, bin bayanta ya yi da kallo har ta bace ma ganin shi. ________________________________________✍️ Around ƙarfe tara na dare, Benazir ta fito daga bedroom dinsu, hannunta a ruƙe da wayarta, har ta sanya kayan bacci a jikin ta, sai dai baccin ya ƙauracewa idanunta, a hankali take tafiya yayin da zuciyarta ke ta azalzalarta akan ta kira Taj ta faɗa masa abunda ta kasa sanar da su ɗazu, sai dai tana matuƙar jin shakkar ta fitar da sirrin gani take kamar zai koma masa ne, amma in ta tuna halin da Aisha ta shiga, da irin uƙubar da Dr Shureim Ya sha akan yarinyar sai kawai ta ji ƙwara ta fada kawai ko da hakan zai yi silar rasa rayuwarta ne, ta ma san ko bata fada ba, hakan bazai hana a cigaba da yunƙurin kashe ta ba. Tana Ƙoƙarin juyawa ta koma ɗaki ta ji motsin shigowar mutun Falon, da sauri ta kai idanunta ga duban shi, Alhaji Musa ne ya shigo cikin takun nan nasa na izza yake tafiya fuskarsa ba annuri, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon shaddar Jikin shi, hakanan ta tsinci kanta da jin faduwar gaba, cikin sauri ta juya da sauri ta faɗa bedroom din ta, kamar munafuka ta dinga leƙen shi, waro ido ta yi ganin ya dan dakata da yin tafiyar, alamun ya ji ajikin shi ana kallon shi, jikinta na kerma ta datse kofar ɗakin. A hankali yake bin ko'ina da kallo, ganin ba abunda ya yi zata bane yasa shi gyaɗa kai ya cigaba da tafiya Ya nufi part dinsa. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hadiyar yawu, tunani ta soma yi a ina yakamata tayi wayar cos bata so wani ya ji koda kalma ɗaya da zata furta ne. Ɗaura idanunta ta yi akan Zeenatu da ke a kwance kan bedmatress tayi nisa acikin baccin ta, Cikin tafiyar sanɗa ta nufi gadon ta janyo duvet ta lullu6e mata jikinta gaba daya. har ta nufi toilet zata shiga sai kuma ta fasa, tunawa da babu kyau yin magana acikin toilet. Gaba daya kanta ya ɗaure, tsoro take ji, ga shi abun ya dameta so take kawai ta fallasa sirrin da ta daɗe da shi a cikin zuciyarta, ba zata iya jira gobe ta yi ba. Akan Mirror Chair ta zauna, ta fara danna wayar ta kira layin Taj ta kurawa screen din wayar idanunta tana jiran ya yi picking. Lokacin da kiran ya shigo layin Taj, yana a kwance kan gadonsa har ya fara bacci kiran ya katse shi. Kasantuwar ya aje wayar a kusa da kunnansa, ransa a ɗan 6aci ya janyo wayar ko da ganin kiran Benazir cikin sauri ya daidaita nutsuwar shi. Bayan yayi picking ya kara wayar a kunnansa. Ko sallama bata yi mashi ba ta ce, "shine ko ka kira ka tambayi mun isa lafiya ko?" Cikin disasshiyar muryarshi ta wanda bacci bai ishe shi ba yace, "I'm sorry Ummu Unaisah, wlh kuna araina, tun dazu nake ta zucci zuccin in kira ku.." Da shagwa6a ta ce, "Hankalinka kwance ma bacci kake yi, Ni gani nan damuwar rashin ka a kusa dani ta hanani runtsawa sai faman tunanin ka nake yi" Har cikin ranshi ya ji dadin kalamanta, murmushi ya yi, "Waya fada maki ni ban damu dake ba? Nima kin tafi kin barni da tunanin ki, da zarar na rufe idanuna ke nake gani," Sautin dariyarta ne ya cika kunnan shi. ( Allah sarki tsohuwar Zuma😂 har wani ƙara kankame pillow yake yi a kirjin shi, da alama Benazir tayi winning heart din Taj.) "Ina babynmu?" "Tana a bedroom din su, may be ta yi bacci" "Okay," shiru su ka dan yi jimm har saida ya furta, "Akwai wani abu da kike son fada mini ne?" Cikin sauri ta ce, "Eh dama dazu akwai tambayar da ku ka yi mini ban samu na amsa maku ba, saboda Yaya Shureim yana a wurin bana so yaji..." Cike da zumudi Taj ya ce,"Okay, Ina sauraron ki Ummu Unaisah" Calmly Ta soma ba shi labari. "Kafin dawowar mu Jos, A lokacin ina a gidan Uncle Musa, ban kai ga sanin komai da ya faru tsakanin Yaya Shureim da Aisha ba, na ta6a kama Uncle yana yin wata waya ta sirri, wuraren karfe ɗaya na dare ban runtsa ba, dama dabi'atace idan ina yin Chatting bana yin bacci da wuri, to adaren ranar na fito daga ɗakina dake a cikin gidan sa, hannuna ruke da wayata ina tafiya ina yin chat da niyyar daukko ruwa, gaba daya na shagala har na sauko down batare dana ankara ba, Na shiga zagaye falon gidan kafin na nufi walkway din da zai sadani da backyard din gidan na tsaya, kwatsam kunnuwana suka soma jiyo mun muryar mutum yanayin waya ƙasa kasa kamar baya son wani ya ji shi, a firgice na kalli saitin inda nake jin maganar sa a hankali cikin sanda na karsa bakin kopar da zata 6ula da kai bayan gidan, a zaune na hango shi kan ɗaya daga cikin kujerun shaƙatawar dake a wurin, a lokacin na dan ji tsoro saboda ban tsammaci zanga mutun a irin wannan lokacin ba, amma sai na dake saboda ina son in san wanene kuma ina son jin wayar mecece ya ke yi a tsakar dare! Ni abunda yafi daure mun kai duk rooms din dake acikin gidan da falo ya rasa inda zaiyi waya sai a backyard, hakan yasa na dasa masa alamar tambaya, aikuwa cikin sanɗa na matsa gaban tukwanan furannin da ke a bayanshi na zukunna tare da kasa kunnena ina sauraron shi. "Kada ku bari ta yi 30 Mins a cikin ramin, zamu iya rasata ne, ku kasance a ankare, da zarar kun ga jami'an sun tafi da shi, kuyi hanzarin haƙa ramin ku ɗauko Jinjirar, Sannan bayan kun cire ta daga ciki, Ku kashe daya daga cikin karnukan ku, Ku je ku zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin" Lokacin da naji wannan maganar wani irin faduwar gaba na ji duk da ban fahimci inda zancen nashi ya dosa ba, gaba daya nabi na rude amma a haka na toshe bakina na cigaba da sauraron shi saboda ina son inji karashen zancen na shi. "Bana so a samu matsala, dole sai kun yi taka tsantsan! ka da ku yi gangancin da wani zai gan ku, idan ba haka ba kun sauran sauran," Ya faɗa tare da yin rejecting call din ganin ya miƙe yasa na yi saurin zuƙunnawa ƙasa da rarrafe na dinga tafiya cikin sanɗa sai da na ga nayi nisa da backyard din, tukunna na mike da sauri na koma dakina na ja kofa na datse. Aranar na kwana da tunanin wacece naji Uncle Musa yana bada umarnin a haƙa ramin da take a ciki a curo ta? Kuma yace a kashe kare a zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin? Menene manufarsa ta yin hakan?" A lokacin gaba daya na ruɗe, na kasa gane komai, dakyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ni, tun daga ranar ban kara samun kwanciyar hankali ba, saboda tunanin wayar dana kama Uncle musa yanayi atsakar dare, zuciyata ta dinga azalzalata akan in tunkare shi in tambaye shi game da wayar da na ji yanayi, sai dai tsoro da fargaba sun hanani yin hakan, bayan haka bansawa raina wani mugun abun ya ke yi ba saboda na yarda da Uncle Musa, daga baya ma sai na watsar da zancen na cigaba da yin harkokin gabana. Taj da ya kasa kunne yana sauraronta, tuni ya mike zaune saboda mamakin daya daure zuciyar shi. Benazir ta ɗaura da cewa, "Lokacin da na kudiri Aniyar saina gano koma wanene ya shiga tsakanin Ya shurem da Aisha, da kuma munafukin da ya ƙulla mata makirci a ƙasar Germany, Lokacin da na saci hanya na shiga dakin Aunty Zainab na tambaye ta meya faru a tsakanin Dr Shureim da iyayen mu saboda ina zargin bakomai suka faɗa mana ba, bayan zainab ta fayyace mini komai, Hankalina atashe na koma ɗaki na, inata wasi wasi akan wayar nan dana ta6a kama Uncle Musa yana yi a bayan gidan sa, sai da na zurfafa tunanina nayi dogon nazari kafin na gano wayar nan fa da Uncle musa yake yi akan babyn Ya Shureim ce. Amma abun da ya ɗaure min kai shine Meyasa Uncle Musa zai yi haka? A raina na ayyana ko dai yana son ya yi mashi hankaline saboda rashin hankalin da ya yi na binne ƴarsa, amma kuma dana kara yin tunani sai na gano wannan fa yafi karfin abunda nake hasashe, ganin an dauki kwanaki Uncle Musa baida niyar fallasa shi ya dauki yarinyar, bayan da kunnanshi ya ji irin bakar wahalar da Ya Shureim yasha bayan ya binneta kuma ya yi danasani, to amma meyasa da farko Uncle Musa ya nuna baisan komai ba? Bayan mun yi waya da Ya Shureim har ya fada mini yasha jaraba kiran layin wayar Uncle don ya nemi taimakon sa, amma baya samun shi, tun daga nan ne na fara zargin da akwai wata mummunar manufa atare da shi. Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya zama gwamnan jihar wanda tun da ya hau mulkin bai ƙara lafiya ba, saboda ciwon ƙafa da ya matsa mashi, ba irin maganin da ba'ayi mashi ba amma ciwon yaki ci yaƙi cinye wa. Wani iko na Allah da zarar an fita da shi kasar waje don a nema masa lafiya sai ciwon nashi ya warke, amma da zarar an dawo da shi Nigeria ciwon na shi yake komawa sabo, a karshe da yan jam"iyarsu suka fahimci ciwon nashi bame ƙarewa bane, sai suka shawarce shi da ya aje mulkin yaje ya nemi lafiyarsa, Shekara daya yayi kafin ya sauka, zaman Jahar ya gagare shi silar hakan iyayenmu suka koma Dubai da zama, Ni kuma saboda auren da na yi ne yasa suka barni a Jos. A lokacin Uncle Musa ya zama Shahararran dan siyasa, ganin sa yayi mini wuya saboda bai cika zuwa Jos ba tun da iyayen mu suka koma Dubai, ya ɗaga ƙafa da zuwa Jos daga Abuja sai ƙasashen waje, Kuma duk in na kira phone numbers dinsa bana samu. A ƙarshe na yanke shawarar tura mashi text message, na rubuta mashi komai dana ji ya fadi a cikin wayarsa, sannan na yi mashi barazanar ko dai ya dawo da babyn Shureim, Ko kuma in tona masa asiri a gurin Daddy da Mommy har da ma Ya Shureim din. Da tura mashi saƙon ko minti biyar ba'ayi ba, sai ga kiran Uncle Musa ya shigo wayata, na yi mamaki sosai saboda tunda nake kira ba'a picking. Bayan na ɗaga ko sallamata bai amsa ba ya ce, "Benazir! Ni za ki yi ma kazafi? Yaushe kika ji ina yin wannan maganar? Bayan haka ni miye haɗina da yarinyar Shureim da har zansa a binno ta daga rami? Me zanyi da gawa..."? Bai ƙare maganar ba na ce, "Haba Uncle, wlh baka isa ka raina mini hankali ba! Da kunnena na ji ba gaya min a ka yi ba, Wlh babyn Shureim tana araye kuma ta na a gurin ka, Kai kasan inda ka kaita, kuma na rantse idan har baka dawo masa da ƴar sa ba, saina tona maka asiri.." Ina ƙarashe maganar na kashe wayar, cike da saran zai neme ni. Aikuwa ba zato ba tsammani a yammacin ranar da na yi waya da shi sai ga kiran shi ya shigo waya ta, a lokacin baka a gida, bayan na ɗaga kiran na ji yace in fito wajen gidana ya turo da escort dinsa yana jirana a cikin Mota. Na ɗan ji fargaba amma da ya ke lokacin ina jin tashen rashin ji, bana jin fargaba kuma bana jin tsoron tunkarar koma uban wanene. Batare da saninka ba, na bi Escort dinsa acikin mota ya kawo ni guest house din Uncle Musa dake anan Joss. Bayan na fito daga motar, escort din ya rakani har cikin falon gidan, Ina shiga na taras da shi a zaune saman Sofa ya ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, fuskarsa kwata kwata babu annuri kamar bai taba dariya ba, Nima na haɗe rai fiye da yadda ya haɗe ta shi fuskar, tunkafin ya bani iznin in zauna na samu guri kan sofa din dake fuskantar shi, na zauna tare da ɗaura ƙafata ɗaya kan ɗaya hakan ba karamin daure mashi kai ya yi ba. Tambayar farko da ya yi min shine in fada masa gurin wa na ji maganar dana fada masa?" Na ce in har yana so in fada masa to ya fara kawo min Babyn Shureim. Lallashina ya fara yi duk dan in faɗa masa, na sanya kaifi nace wallahi ya daina wahalar da kanshi saboda bazan faɗa ba, dole sai ya fara kawo mini yarinyar. Shu'umin murmushi ya saki tare da cewa bai damu ba in je in fada ma duk wanda zan fadamawa, saboda bani da hujjar da zan iya tuhumar shi, balle har in tona masa asiri, kuma in bi a hankali in ban iya kama barawo ba sai barawon ya kama ni.." na yi dariya hada shewata na ce, "Ka bani mamaki Uncle, ina yi maka kallon mutumin kirki ashe kai din mutumin banza ne! Ka yi zaton bansan komai ba?" Na faɗa ina zare mashi idanuna, a lokacin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa tsantsar al'ajabi da rudani. "Benazir Ni kike kira mutumin banza? Ido cikin ido batare da jin shakkata ba? Kin manta matsayina agurin ki?" Harara na galla masa, "Na je na fada Uncle, Wallahi Hakkin Aisha bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba, Ka cuce ta Ka cuci Yaya shureim ka kuma cuci Babyn da suka haifa"! Ina magana hawaye na shararowa kan kuncina. "Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake taƙama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a ƙungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka haɗa Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka ke shiga ɗakin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...." Tun kafin in ƙarasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma ɗaga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake ƙullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun kaɗa jawur. Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fyaɗe ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan leƙen asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka ƙyalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita faɗa masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...". Ban kai ga ƙarasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai. "Benazir! Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari! Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum? Na faɗa ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba, ƙazafi nake yi masa. raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce. "Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi. "Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan! Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai, "Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne? Yakamata ki iya bakinki Benazir! Har yanzu bakisan wanene ni ba! Sabo da kaza bai hana in yankata! Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kashe banza." A lokacin gabana ya faɗi na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama" Maganar da na yi ta ɗaga hankalinsa matuƙa, Zuciyarshi ta hasala kamar ya rufe ni da bugu haka yake ji. Har na ɗaga kafa zan fuce na sake tsinkayar muryarsa a cikin kunne na, "Ko don saboda abun da ke a cikin ki, Yakamata ki yi takatsantsan idan ba haka ba, zaki jefa rayuwarsa a cikin haɗari ne..." Wani irin faduwar gaba na ji, saboda a lokacin bansan ina ɗauke da juna biyu ba, cikin sauri na dafe cikina tare da zare idanuna akan fuskar shi, gaba daya na bi na ruɗe, Murmushin mugunta ya sakar mun saboda ya gano lago na.. "Benazir, nafi karfin ki nesa ba kusa ba, wlh baki isa ki ja dani ba, ƙaramar yar iska mai kwana da wando, saboda baki da hankali ki rasa wa zaki tuhuma sai ni? Kinsan wanene ni kuwa?? Ki fara sanin wanene ni kafin ki yi ja in ja dani, Sannan zan ƙara tuna maki, kina da miji, kina da juna biyu, kina da iyaye, kuma kina da ya ya mafi soyuwa a gare ki, Ina fata Kin fahimci abunda nake nufi???" Yana karasa maganar ya juya ya nufi up batare da ya sake waiwaye na ba, har saida ya 6ace ma ganina kafin na kawar da idanuna daga barin kallon sa. Har na dawo gida ban daina tariyo maganarsa a cikin kunnena ba, Saboda hankalina ya tashi sosai, Lamarin Uncle Musa ya fara bani tsoro, na riga da na gane mugun mutunne shi, mara imani, kuma tantirin shaidani nasan zai iya aiwatar da komai don ya rufawa kansa asiri.. Bayan sati biyu na je ganin likita batare da saninka ba, bayan doc yayi mini gwaje-gwaje sakamakon ya nuna ina dauke da ciki na sati biyu, nan fa hankalina ya ƙara tashi kwata kwata ban yi farin ciki da cikin ba a lokacin saboda zai zama rauni na, kuma ina jin tsoron in haife shi saboda fargaban kada Uncle Musa ya salwantar da rayuwarsa, Ko ya ɗauke sa kamar yadda ya dauke ɗiyar Ya Shureim, wannan dalilinne yasa nayita yunkurin in zubar da cikin Angel, wlh Allah shine shaidata badan bana son shi ba, Kawai a lokacin muna yawan samun sabani da kai saboda bani da kwanciyar hankali, Damuwa tayi mini katutu, kullum cikin zullumi da fargaba nake yi saboda nasan Uncle Musa bazai ƙyale ni ba, kamar yadda ya fada dole ya dauki mataki akaina, kuskuren da na yi shine ƙin sanar da kai, Na ƙi faɗama kowa nabar abun a matsayin sirri, saboda gudun kada na faɗa ya koma mashi karshe inja ma kaina da kuma dangina don har lokacin ban saduda na kyaleshi kan fito da yarinyar Yaya Shureim ba, ka ji dalilin da yasa a duk lokacin daka kamani ina yunkurin zubar da cikinta ka tuhume ni dalili, sai ince maka bana son ya'ya, kuma bana son cikin saboda zai bata mini shape ɗin jikina, Amma a zahirin gaskiya bada son raina ni ke yin hakan ba, gaba daya rayuwar aurena da kai wani abun sai daga baya na gane bayin kaina bane, nasan bana jin magana, amma wlh Taj na so mu yi zaman lafiya sai dai na kasa faranta maka, saima cuzguna makan da nake yi hakanan bakai mini komai ba, kawai sai inji haushin ka, da tsanarka acikin Zuciyata, hatta mai aikin gidanmu Janet na ji na tsane ta, laifin da bai kai ya kawo ba idan ta yi mini bana ƙyale ta, saina azabtar da ita...." Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan da ya ƙwace mata, Haƙiƙa Zuciyar Taj ta karaya, tsantsar mamaki da al'jabi sun ruke zuciyar shi tamau, duk da sanyin A.c din dake a dakin hakan bai hana shi fitar da zufa ba, jikin shi har tsuma yake yi, wani irin tausayin Benazir ne ya kama shi ya yi danasanin zarginta da ya dinga yi, ashe bayin kanta bane, makircine aka shirya mata. Numfasawa ta yi, cikin shesshekar kuka ta ci gaba da cewa, "Bayan wani lokaci, ban ƙara jin ɗuriyar Uncle musa ba, har lokacin da cikin Unaisah Ya cika wata tara cuf, nima kuma ban ƙara tuntubarsa ba ko in yi tunanin sanar da wani game da sirrin, a tunanina saboda bana son in jefa rayuwar ahalina Cikin hadari ne, a daren ranar da naƙuda ta kama ni, da ni da kai muna a kwance kan gadonmu mun yi nisa a cikin baccinmu, kwatsam ba zato ba tsammani, na fara jin naƙuda na taso mun, a firgice na farka daga baccin hannayena daddafe da cikina, ina ta faman cizon le6e saboda radadin da nake ji a jikina. Zufa duk ta wanke jikina, naita kokarin kai hannu don in tashe ka daga bacci amma nakasa, na yi kokarin in yi koda addu'a ne nan ma abun ya ci tura saboda haƙorana sun game gam, Taj ban ƙara sanin me ya faru dani ba, nadaisan bana a cikin hayyacina na sauko daga kan gado ina jan ƙafa na tura ƙofar toilet na shiga. Wlh Taj haihuwar Unaisah ikon Allah ne, kwata kwata bana a cikin hayyacina a haka na kar6i haihuwana da kaina amma bansan na yi ba, bansan dame na yi amfani gurin yanke cibin ba, a lokacin dana haifeta saida na kalleta cikin jini, na rungume abuna ina kuka tana kuka, abun da nake ta gudun in haifa sai gashi na haifeta, kuma sai na ji na kamu da ƙaunarta fiye da komai na duniyar nan, ina tsaka da kallonta, Kwatsam na fara jin ana ambaton sunana da wata iriyar murya mai matuƙar tsoratarwa, kuma nan take na dinga jin bakin ciki a cikin zuciyata, na ji na tsani komai in har ban je na amsa kiran da bakuwar muryar ke yi mini ba zan iya rasa raina ne, saboda yadda tsigar jikina ke tashi kamar ana tunzurani, yadda kasan ana zare raina ban ma san sa'adda na kwantar da Unaisah cikin bathtube ba, cikin hanzari duk da rashin ƙwarin jiki na fuce daga cikin toilet din, ko waiwaye ban yi ba na nufi gate, baba mai gadi yana adakinsa yana bacci baisan na fita ba, saboda wani ƙarfine ya zo mini bangaza ɗaya na yi wa kofar jikin gate din mu dake a kulle nan take ta buɗe nasa kai na fuce da gudu na bi santar mu. Ban ƙara sanin meya faru ba, sai dai na wayi gari na ganni a kwance kan gadon asibiti magashiyan rai a hannun Allah, bayan dana dawo hayyacina na tambayi nurses din dake kula dani akan meya faru da ni? anan suke faɗamin wani matashi ne ya bankaɗe ni da motarsa akan titi shine ya kawo ni asibitin, abun da ya ɗaure mini kai, ni da na ke a Jos meya kawo ni Abuja? Ban sanya damuwa araina ba saboda lokacin burina kawai in yi nesa da dangina saboda bana son su a kusa da ni.💔 Tun kan ta ƙarasa bashi labarin ya soma ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! cikin karyayyar Murya ya ce, "Benazir! Dama haka komai ya faru baki ta6a sanar da ni ba? Kika sa nayi ta zargin ki, Ya Salam!! Pls ki yafe mini"! In a cool voice ta ce, "Ba laifin ka bane, rashin sanine ya jawo hakan, Nima ka yafe mini 6ata maka rai da na yi a zaman mu na aure.." "Ki manta da komai ya wuce, saboda ke ma bayin kanki bane, Ina tunanin Uncle dinki shine Ummul aba'isin komai da ya faru, yanzu ina so ki faɗa mini kece kika tura min sakon In sake ki!" "Bani bace Taj, saboda ni ban tafi da waya ba, ni bansan wanene yayi mini hakan ba amma ina zargin Uncle Musa, saboda bayan na dawo gida Daddy da Mami sun faɗa min ana tura masu sakonni ta layin wayata, wai hada sakon da nace ni na gudu da son raina kuma na shiga duniya kada suyi tunanin zan dawo gare su kuma kada su sha wahalar nema na..." Dafe kai Taj ya yi da tafin hannunsa, Idanunsa sun kaɗa jawur da su. "Benazir, Ni kuma saƙon da aka tura mini da bakuwar number ne, Idan bazan manta ba, abun da aka rubuta a cikin sakon shi ne ka sake ni Taj, kuma kada ka yi tunanin zan dawo na tafi kenan har abada, har kiran layin na yi amma saina ji shi a kashe kuma daga ranar ba'a ƙara tura min saƙo ba, tun ina sa ran dawowarki har dai na fidda rai" Fashewa ta yi da kuka tana fadin, "Shiyasa kowa ya ƙullace ni aranshi saboda ana zargin da son raina na tafi, Koma wanene ya yi min hakan bazan ta6a yafe masa ba, Allah ya isa wlh sai Allah ya yi min sakayya, lallashinta ya shiga ya har ya samu ta yi shiru, shima ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sai sautin Numfashin junan su da suke ji ta cikin wayar, so yake ya bata labarin rayuwar Unaisah a gidan Kurkukun ƙaddara saboda Yana zargin dasa hannun Uncle dinta sai dai ya kasa saboda baya son ya ƙara ɗaga hankalinta, ganin halin damuwar da ta shiga, gaba daya ya fahimci bibiyar rayuwar su ake yi, tun daga kan Benazir, da Aisha da Dr Shureim, da kuma Iyayensu suma ba'a ƙyale su hakanan ba. Jin shirun ya yi yawa ne yasa shi tunanin ko ta yi bacci ne . "Benazir?" In a low voice ta ce, "Na'am' "Pls, Ki kwantar da hankalinki, nasan ba zaki rasa ciwon kai ba saboda kukan da kika sha, dan Allah kada ki sanya damuwa a ranki, maganar Uncle din ki zan faɗa ma Chief in sha Allah, duk yadda mu ka yi da shi zamu tuntu6e ku, yanzu ki kwanta ki yi bacci..." Bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa, "Don Allah Taj, ku taimaka mana, har yanzu ina ji araina Babyn Shureim tana a raye, kuma tana a gurin Uncle, shi kadai yasan inda ya aje ta, amma nasan in har kuka yi bincike akan shi zaku gano komai..." Kwantar mata da hankali ya cigaba da yi saida suka raba dare suna yin waya kafin suka yi sallama, A daren ranar Taj bai iya runtsawa ba, saboda maganganun da suka tattauna da Benazir sun hana shi sukuni, har dai ya gaza jurewa ya kira layin Chief saboda yasan ba lallai bane idan ya yi bacci ba saboda a irin lokacin yana yawan tashi yin nafila, Cikin sa'a Chief ya yi picking call dinsa, a nan ya sanar da shi sun yi waya da Benazir, ya ce ya duba whatsapp dinsa ya tura mashi recording din da ya ɗauka na tattaunawar da suka yi, Chief ya amsa mashi da toh. Bayan Chief ya kammala sauraron audio din da Taj ya tura masa, har sujjada saida yayi saboda nuna godiyarsa ga Allah da ya fara kawo masa sauƙi a cikin lamuransa ya kuma ƙara yin addu'ar neman nasara akan abun da suka sa a gaba. After Two days, ana gobe za'a yi family meeting, kiran sallar asubahin farko Private jet din Prime minister ya yi landing a Airport, Mai girma Sharafuddeen tare da Security details dinsa ne suka je dauko su acikin dankara dankaran motocin su, wannan karon daga shi sai Escorts dinsa suka zo Nigeria batare da iyalinsa ba, kuma bakowa ne yasan da zuwan nashi ba sai family dinsa, ko yan jarida ba a bari sun san da zancen zuwan na shi ba. Kaitsaye suka wuce Vila da shi, Sai da ya fara huce gajiyar da ya kwaso, Har bacci ya yi a dakin ɗan uwansa Sharafudden kafin zuwa marece suka shigo Estate. Gaba daya yan'uwansa suka hallara a main falo din baba Obie don su tarbe shi, Yana shigowa falon suka nufe shi cike da tsantsar farin cikin ganin shi, ɗaya bayan daya suka dinga yin hugging dinsa, burinsa ya ƙarasa ga mahaifinsa sun hana shi motsawa kowa ɗokin ganinsa yake yi. Daƙyar ya samu suka kyale shi ya nufi Baba Obie dake ta sakar mashi murmushi ya rungume shi kamar zai maida shi cikin jikin shi, su Hajiya Saratu baki yaƙi rufuwa saboda murnar ganin Yaya Hateem, kowa ya buɗe baki sai ya tambaye shi ina iyalinsa? Meyasa bai zo da su ba? Ya ce masu su kwantar da hankalinsu suma zasu zo ne, amma a halin yanzu gimbiya da su Yazrin sun tafi Dubai gurin danginta hidima ce gare su, ita kuma Faryat bata samu hutun makaranta ba, shiyasa bata samu damar zuwa ba. Lokacin da marece ya nutsa, sai ga kiran his excellency Abdul razak ya shigo wayar Baba Obie ya sanar da shi sun ƙaraso Abuja yana a aiport, Batare da 6ata lokaci ba Baba Obie ya tura da motocin Escorts suka dauko shi, bai jima da ƙarasowa ba sai ga motocin His excellency Deen na Kaduna sun iso cikin Estate din. Sun yi farin cikin sake haduwa da yan uwansu saboda sun yi kewar juna, Baba Obie sai haba haba yake da su, saboda murna bakinsa ya ƙi rufuwa. A daren ranar saida suka raba dare suna hira da mahaifinsu kamar ba zasu yi bacci ba har saida Baba Obie ya ce suje su kwanta su huta tukunna suka yi sallama da shi, Hateem dai ruƙe shi ya yi a ɗakinsa yace tare zasu kwana saboda ya yi kewarsa, hakan ba ƙaramin dadi ya yi ma Prime minister ba, a kan gadon Baba Obie suka kwanta, zai kwana da tunanin mutumin da ya kwallafa rai da son ganinshi, ɗazu da Chief ya zo gaishe da shi har tambayar shi ya yi ina baby boy dinsa? Yana lafiya? A lokacin hankalin Chief ba karamin tashi ya yi ba, amma saboda baya son ya ɗaga masa hankali yasa shi cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya, amma baya a gidansa yanzu, yana a camp din su na isod, yana kar6ar training. Dakyar ya samu ya shawo kan Hateem har ya haƙura da maganar Danish amma fa yace duk yadda za'a yi kafin ya koma yana son ganin sa. ~________________________________🍁~ *_🔥🔥🔥The Chief Owais Birthday Celebration and Family Gathering🔥🔥🔥_* *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 _*~....................................................................~*_ ~___________________________________🌹✍️~ Around Ƙarfe 10 na safe, Kiran Chief Ya shigo wayar ta, a lokacin tana a zaune kan prayer mat ta nutsu tana yin karatun alkur'anin da ta buɗe akan qur'anic stand, bayan da ta kai aya miƙewa tayi daga kan Prayer mat din, ta ɗauko wayarta da ɗaura kan Pillow ta yi picking Call din tare da kara wayar a kunnanta. "My babe, how're you? i hope you slept well "? Sa'ilin da muryarsa ta ratsa kunnanta wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta. "I'm doing well, thanks hubby, "Okay, Idan baki komai ki same Ni a part ɗina" "Okay Sir" rejecting call din ta yi. da sauri taje gaban prayer mat din ta rufe qur'anin, Bayan ta saka High heels dinta ta fuce ta nufi part dinsa. yana a kishingiɗe kan bedmattress dinsa, single da short ne a jikin shi Ya mike kafafunsa yayin da idanunsa ke a lumshe kamar na mai jin bacci, yau tun da ya farka daga bacci Omar ke ta faɗo masa arai, saboda a duk ranar birthday dinsa Omar ne mutun na farko da ya ke fara turo ma shi happy Birthday greetings tare da Birthday gift, Omar baya so wani ya riga shi taya Chief murnar birthday dinsa, wannan karan Allah bai nufa za'ayi da shi ba. Lokacin da ta karaso bakin Door room din, sau ɗaya tayi knocking kofar ta buɗe, sallama tayi mashi daga ciki tajiyo voice dinsa ya furta"Come In babe" Walking slowly ta nufe shi ta dan tsaya daga gaban Gadon, idanunta akan fuskar shi still bai buɗe eyes dinsa ba suna a lumshe. sumar kan shi tabi da kallo ganin hadadden ducktail haircut din da akayi masa, ya ƙara ƙawata kyawun fuskar shi, ya yi mata kyau daga gani yau akayi masa shi. Sau uku tana gaida shi bai amsa mata ba, tayi azan bacci yakeyi amma sai ta tuna before ta shigo saida ya bata izni. "My Chief, ko ka yi bacci ne? Nayi magana naji ka yi shiru, pls kayi min magana" bata ƙarashe maganar ba, taji ya furta"kin bata min rai Unaisah, fushi nake da ke" Ya faɗa tare da buɗe idanunsa akan fuskarta. Gabanta ne ya fadi adabarbace tace"I'm sorry ban fahimce ka ba, Meyasa ka ke fushi da ni? Laifin me nayi maka"? Saukowa yayi daga kan gadon, hannun sa ruke da wayar sa, ya juya ya nufi tattausan rug din dakin sa, a ruɗe tabi bayan shi da kallo, gently ya zauna akan rug din tare da nuna mata gabansa da yatsan shi"sit here Babe" jiki asanyaye ta zauna tana fuskantar shi, jikinta duk yayi sanyi ganin mood dinsa ba walwala. Kasa jure kallon da ya ke yi mata tayi, slowly ta kawar da idanun ta gefe daya.. "Meyasa kika tsani mahaifiyar ki? Laifin me ta yi maki? nan take bacin rai ya wanzu akan fuskar ta, her voice barely above a whisper tace"Because she doesn't love me, she hates me, That's why lokacin da ta haife ni ta jefa ni a cikin bathtub, sannan ta gudu ta tafi batare da ta sake waiwaye na ba...." tun da ta fara magana ya nutsu yana kallon smooth pinkin lips dinta har saida ta kai aya tayi shiru tana jiran amsar shi.. "You were rude to her, banji dadin maganganun da kika gaggayawa mahaifiyar ki ba!" ya fada yana mai nuna bacin ran shi "uwa uwa ce koda ta banza ce It's not acceptable to disrespect her!" "Amma bata sona meyasa tayi watsi da ni"? "Ki daina cewa bata sonki Unaisah"! Da yar tsawa ya fada, har saida ta zare mashi gray eyes dinta hakan yasa shi sassauta muryarsa saboda baison ya daga mata hankali "I know you're intelligent and thoughtful, Don't you think there's a reason your mother ran away from you? pls kiyi tunani ta haife ki a tsakar dare a cikin toilet ta kar6i haihuwarta da kanta, ta saka ki a cikin bathtub ta gudu daga gidan ba tare da sanin mahaifin ki ba..." arude ta dube shi gabanta na faɗuwa "Nasan bakomai kika sani dangane da tafiyarta ba, kamar yadda shima mahaifinki bakomai ya sani ba, rashin sani ne yasa kuke fushi da ita saboda kunyi tunani ta gudu ne saboda bata son zama da ku bayan ba haka bane....." gaba daya Unaisah ta rude da jin maganar shi. Audio Recording din da ya ɗauka na Labarin Ummi da Benazir ya kunna mata a wayarsa, ashe ya yi recording batare da sanin su ba. Tun da ta fara sauraran shi yanayin fuskarta ya canza zuwa rudani da tashin hankali, aranta ta ayyana dama Aunty Ummin su Malama ce? Bata taba jin mace mai tausayi da kamun kai da tsantsar ilmin addinin islama irin ta ba, baiwar Allah ashe kaddara ce ta yi silar canza rayuwar ta. Hawaye ne suka cika idanunta tab, tsananin tausayin Aunty ummin su ya kamata, ga wani kaunarta daya shiga zuciyarta, abun daya yafi ta6a zuciyarta a cikin labarin Hukuncin da sheikh Imam ya yanke ma ta, da kuma binne yarinyar da wan mahaifiyar yayi, Abun ya ta6a Zuciyarta sosai, muryarta na rawa tace"ban ta6a jin labarin daya taba zuciyata ba, irin wannan, kuma banyi zaton sheikh Imam zai iya yin hakan ba, a matsayin shi na malami, Aunty ummi ta bani tausayi ita da ya ya shureim, amma banji dadin binne yarinyar da yayi ba" muryarta na rawa ta ƙarashe maganar. "Yanzu inaso ki fadamin, Kafin ki saurari wannan labarin Wani irin kallo ki ke yi ma Aunty Ummin ku"? tamkar zata fashe da kuka tace"tun kafin na santa, Dr. Laura ta america ce ta fara bani labarin ta, tace min karuwace ita, bata da kamun kai, kuma tayi kaurin suna a america, kawai dai ba mutuniyar kirki bace, amma da zama ya hada mu da ita sai na gane tana da sauƙin kai, ba kamar yadda na zata ba, a ranar da ta fara yin karatun al'qur'ani agabana, na razana sosai, har nayi tunanin meya sa bata amfani da saninta take aikata sabon Allah ashe ba halin ta bane, kaddara ce ta afka mata...." ta karasa maganar cikin sanyin murya. "Yanzu fada min meyasa ki ke yi mata kallon mutuniyar banza"! "Rashin sani ne," Gyaɗa kai Chief yayi"haka zalika, itama mahaifiyarki rashin sanine yasa ki ke tunanin ta gudu ta bar ki saboda bata sonki, bayan ba haka bane, itama bada son ranta ba" waro idanu waje tayi, jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, ni na hana mahaifinki yayi maki magana, saboda na daukarwa mommynki alkawarin zan sasanta tsakanin ki da ita, tun shekaran jiya da su ka zo bayan sun tafi, a daren ranar mommyn ki ta kira dad din ki, ta fada masa komai da ya faru da ita, har ma sunsasanta tsakanin su saboda ya gane ba laifin ta bane, may be bai fada maki ba, saboda nace yabar komai a hannu na" ya ƙarasa maganar tare da kunna mata audio din da Taj ya tura masa ya mika mata wayar "Calm down and listen, zaki samu amsoshin tambayoyin da kike nema a gurin mommyn ki..." yatsun hannunta na kerma ta kar6i wayar daga hannunsa tare da kangata saitin kunnanta don ta samu damar ji da kyau. A hankali Chief ke kallon fuskarta yadda take zazzare gray eye balls dinta tare da moving lips dinta ba ƙaramin tafiya yake da shi ba. Bai aune ba Yaga ta zabura ta miƙe, Jikinta na kerma yadda kasan wadda Electric shock Ya kama, wayarsa dake a hannunta sai kerma take saboda jikinta dake kakarwa, Dafe kanta tayi da tafin hannunta, Labbanta na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"! Ganin ta juya arude yasa shi sauri kiran sunanta"Unaisah Ina zaki je ne"? Yarfa hannun ta ɗaya tayi, ta kamo gaban hijab din jikinta ta soma fifita da shi saboda zafin daya taso mata gaba daya ta rude. "Calm down babe, dawo ki zauna muyi magana mana" Calmly ya faɗa idanunsa akan fuskarta dake fitar da gumi kamar babu A.c a dakin. Lokaci daya ta fashe da kuka tana fadin wayyo Allah na, na shiga uku, ina son naga momnyna, Ina son in nemi ya fiyarta, Inaso na bata hakuri! i love her, i really wanna see her..." ganin yadda ta daga hankalinta yasa Chief Ya miƙe tare da kar6ar phone din gudun kada ta kayar da ita kasa, Cikin boxer pocket dinsa Ya zura phone din, kafin ya tallabo fuskarta da tafukansa. "Kalli cikin idanuna Unaisah" dakyar ta iya buɗe idanunta da suka cika da hawaye, cheeks dinta sunyi jawur da su. "Ki daina kuka, Ba laifin ki bane Unaisah, rashin sanine yajawo hakan, nasan yanzu kinyi danasani, saboda kin gane gaskiya" Jinjina mashi kai tayi alamar Eh. "Ki gode ma Allah Unaisah, mommyn ki jaruma ce, I've wondered who gave birth to this remarkable child, cos you're different, with a sharp mind and loving, Ina alfahari da mommynki, saboda tayi bajinta, tayi abunda ya cancanta a jinjina mata..." tun daya fara magana ta ɗan sassauta da kukan sai shessheka da ta ke yi, Kalaman Chief Sun ƙara sa ta jin wani irin masifaffan son mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan. "Uncle din mommynki Shine silar komai daya faru, shine munafukin dake ƙulla makirci atsakanin su, bayan haka muna zargin yana da sa hannu a kungiyar matsafan kurkukun kaddara, yanzu haka mun fara bin diddiginsa nan bada jimawa ba zai shigo Hannu" In a low voice tace" I think he's the one who sacrificed me, kuma ina zargin yarinyar Aunty Ummi daya dauka in dai basu kashe ta ba, zai iya yiwuwa tana a cikin fursinonin kurkukun kaddara, watakil ma tana atare da mu" "Tunanin mu yazo ɗaya Unaisah ..." "Amma, Ina jin fargaban mommy na taƙi kula ni" "Zata kula ki Unaisah, a yanzu haka jiran ki ta ke yi, na fada mata zaki neme ta da kanki, ki kira ta awaya ki bata hakuri sannan ki nemi yafiyarta hakan zaisa taji dadi acikin zuciyarta" cike da zumudi ta juya zata tafi yai saurin dakatar da ita"ina zaki je" Fuskarta a yamutse tace"i wanna call her" kayataccen murmushi Chief ya dan saki"Okay, ga kayanan ki tafi da su" ya fada tare da nuna mata suitcases din dake ajiye gaban Couch, arude take kallon su a lokacin harya juya ya nufi ƙofar da zata kai shi gym room dinsa Ya shige ciki. Kasancewar akagare take da ta kira mommynta, bata tsaya yin wani dogon tunani akan akwatinan ba, cikin sauri ta nufe su, taja handle din daya ta fuce da shi. ______________________________🍁✍️ Tana shiga Bedroom dinsu, ta ɗaura akwatin saman gadon su, Ta dauko wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta danna ma layin da tayi saving da Aunty Benazir kira, saboda zumuɗi sam ta kasa zama sai zarya ta ke yi a tsakar dakin, almost 3 times tana kira ba'a picking, jikinta ne yayi sanyi saboda ta yi zaton fushi take yi da ita shiyasa bata daga ba. _Message ta tura mata mommy, dan Allah ki daga kirana akwai abun da nakeso In fada maki_ Ba'afi minti biyu data tura sakon ba, sai ga kiran Aunty Pretty ya shigo wayar ta, kwata kwata batayi farin ciki da ganin kiran ba, saboda a halin yanzu bata son ganin kiran kowa in ba na Aunty Benazir ba, har ya katse batayi picking ba, sai da aka ƙara kira, ta haɗe rai ba annuri ta ɗaga kiran tayi shiru batayi mata sallama ba. On the Other hand jin tayi Shiru yasa Benazir tace"daughter, kin bukaci kina son yin magana dani, kuma na kira kinyi shiru"? Waro idanu waje ta yi saboda rudanin da ta shiga, sai da ta fara janye wayar daga kunnanta ta duba number ɗin da kyau taga ta aunty pretty ce da sauri ta shiga messages ta duba number ɗin data tura ma saƙon, taga ba kuskure tayi ba Aunty Benazir ne ta turamawa amma ya akai Aunty Pretty ta kira ta sannan tace taga sakon ta? Nan take zuciyarta ta bata amsa da cewa zai iya yiwuwa mutun ɗayane ke amfani da layi biyu, Ras taji gabanta Ya dan faɗi, labban na kerma ta furta"Aun.. Aunty pretty, dama kece Mommyna Aunty Benazir"? Sautin Dariyar Benazir ce ta ratsa kunnanta, cike da nishadi tace"ni ce mana, layin da kika turama sako na Uncle din ki ne da nake amfani da shi, bayan na kar6i contact dinki agurin Aneelerh, ina saka number din Unexpected naga sunan da nayi maki saving ya bayyana akan screen din wayata nayita mamaki nace ashe da daughter dina nake waya batare da sanina ba, daga nan na yanke shawarar kiran ki da layin ya shureim saboda bana so ki gane ni ce...." wata irin kunyace ta kama Unaisah, tayi shiru tana zare idanun ta. "Kin daina fushi dani..."? Benazir ce ta tambaya akagare da son jin amsar ta. Kwatsam taji ta fashe mata da kuka kamar ranta zai fita, Hankalin ta ba karamin ta shi yayi ba, muryarta na rawa tace"Unaisah lafiya kike kuka? Meke damunki ne? Waya taba min ke"? Cikin shesshekar Kuka tace"Forgive me, Mommy I realize my mistake I apologize for hurting you, I love you more than anything in this world, I want Daddy to remarry you and bring you back to me, cos I need you in my life...." tana jiyo muryar Benazir dake ambaton Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mini ranar da nake ta jiran zuwanta Unaisah dagaske Kina sona yanzu? Kina son mommynki ta dawo kusa dake"? Jinjina kai tayi kamar tana agabanta tace"seriously, I love you so much, i want you to take care of me, I thought since Daddy had done everything for me, bazan bukace ki ba amma ayanzu na gane ke ce cika makon farin cikin rayuwata, bani da tamkar ki har abada..." Bata karasa maganar ba sautin kukan Benazir ya cika kunnan ta, hankalinta ne ya tashi da rawar murya tace"dan Allah ki daina kuka, bana son ji, pls, Allah zaiyi fushi dani idan kina kuka akaina..." cikin shesshekar murya Benazir tace"ba kukan bakin ciki bane Unaisah, kukan Farin Ciki ne, kin faranta raina, Kin sani jin kamar nafi kowa farin ciki a duniyar nan, yanzu bani da sauran damuwa, Mijina ya daina fushi dani, yata ma ta daina guduna, Alhamdulillah..." "Ba ki ce kin yafe min ba"? Benazir bata bata amsar tambayarta ba, sai taga ta canza call din zuwa Video Call, picking tayi lokacin da idanunta suka sauka akan fuskar Benazir wata irin kunyace ta lullube ta, fadawa tayi kan gado wayar na a hannunta tayi saurin janyo pillow da dayan hannun ta lullu6e fuskarta tana dariya, itama Benazir din dariya take ma yi. Cike da zolaya tace"rasa kunyan 6eran taka, Lemme see your face, kin tuna karyar da kikai min, Kina zuwa school sannan a kano kike da zama uhum"? Ƙyalƙyalewa tayi da dariya ba tare data furta kalma ba. "Oh ni Benazir, mamaki nake wai ni ce na haifi zankaɗeɗiyar balarabiyar nan tubarkalla kamar hurul ain" fashewa ta kumayi da dariya, Hakan ba karamin faranta ran Benazir ya yi ba, dama tayi ne donta saka ta farin ciki ganin ta damu sosai. "Aneelerh ta bani labarin kuruciyarki, yadda kasan ni agari, nima haka nayi kuruciyata amma fa ban kaiki rashin ji ba, gaskiya ni ban taba sa an kai daddyna cell ba" ta fada tana kallon Unaisah data kare fuskarta da pillow sai dariya ta ke yi. "Taya zamuyi magana bayan kinki bari inga fuskarki uhm? Pls let me see your face, " A hankali ta zame pillow din, ta matso da screen din wayar saitin fuskarta suka zubawa juna ido gwanin ban sha'awa. "Wow, ƴata tafi ta kowa kyau, launin idanunki irin na Ammin mu ne ta eygpt, kinsan me har yanzu tana araye ta tsufa tukuf..."murmushi Unaisah ta yi tana faman sauke ajiyar Zuciya. "Fadamin waya sa ki kirani awaya"? "Chief ne, shine ya fada min komai daya faru da ke" "Mutumin kirki, ya taimake ni, Allah ya saka sa masa da mafificin Alkhairin sa" Ta amsa mata da ameen.. "Kina da saurayi" cike da jin kunyarta tace"shine ai" "Wa"? "Zan fada maki ba yanzu ba" "Okay, abun da nakeso dake, Ki manta da komai daya faru, na yafe maki Unaisah, kuma ba laifin ki bane, rashin sanina yasa kika ƙulla ce ni aranki, amma ni ban ruke ki a cikin zuciyana ba, in ma akwai mai laifi to ni ce Unaisah, duk da nima bada son raina na tafi nabarki ba, amma naji dadi da ban tafi dake ba, watakil da yanzu baki araye tunda bana acikin hayyacina zan iya jefar dake akan titi...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan dake kokarin balle mata, cikin karyayyar murya Unaisah tace"pls kada kiyi kuka mommy, bana son ganin hawayen ki,..." jinjina mata kai tayi"bazan yi ba tun da bakya so....." sun dade sunayin waya akalla sun shafe awa daya da rabi a hakan ma basu gaji da yin wayarba, sai da Benazir tayi mata alkawarin zata zo gidan tukunna ta hakura su ka yi sallama da junansu. miƙewa tayi tsaye kan gadon, ta dinga tsalle kan matress din fuskarta dauke da murmushin Farin ciki. Shigowa dakin Batool tayi, jikinta asanye da kayan bacci riga da wando ko mayafi babu akanta. burki ta ci ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda Unaisah ke daka Tsalle tana dariya kamar karamar yarinya. Baki asake da mamaki tace"Sis Meke damunki ne? Meyasa kike yin tsalle akan katifa sai kace karamar yarinya"? Bata amsa mata ba, ta duro daga kan gadon ta nufe ta, tare da rungume sosai, Batool duk ta rude ta rasa gane kanta fatanta Allah yasa ba tabin hankali ta samu ba. "Sis meyasa ki farin ciki ne uhm"? Ta fada tare da raba jikinta daga na Unaisah Fuskarta dauke da annurin farin ciki tace"Batool ki tayani farin ciki, na gano wacece mommyna wadda ta haife ni" waro idanu Batool tayi"are you serious? Ta ina? Wacece"? Murmushi tayi"Aunty Benazir, mai kama dake, Itace Mommyna, kuma itace Aunty pretty da mukeyin waya da ita.." farin ciki ne ya lullu6e Batool"ina tayaki murna sis, Kinji dadin rayuwarki, Mommynki da daddynki suna nan, Baki rasa kowa naki ba..." maganar Batool ta taba zuciyarta, jikin ta ne ya yi sanyi sosai, tsananin tausayinta ne ya kama ta, su da basu taba sanin dangin su ba. "Sis amma kin yafe mata laifin da tayi maki ne? Kuma taya akai kika gane itace mommynki uhum"? Ta fada akagare da son amsar ta. "Shekaran jiya bana baki labarin Aunty Benazir da Aunty Aneeleeh sunzo ba"? "Eh na tuna, ay time din na fada maki aunty ummi bata jin dadi, atare ma bacci ya dauke mu adakin ta.." ɗan girgiza kai Unaisah tayi"baiwar Allah, Aunty Ummi, ta bani tausayi, naji labarin rayuwarta ashe kawaye ne su, da ita da mommyna da Aunty Anila, kaddara ce tayi silar raba su, nima mommyna bada son ranta ta gudu tabar ni ba" ta fada fuskarta. amarairaice. "Waya fada miki pls, nima ina son ji"? "Zan baki labarin komai daya faru amma ba yanzu ba, saboda nasha kuka wlh har zazzabi nake ji a jikina, amma da nayi waya da mommyna sai naji sauki acikin zuciyana.." badan taso ba tace"Toh sis zan jira ki, wlh har na kagara naji, kuma ina ƙara tayaki murna Unaisah" "Nagode my own sis," "Lah! Akwatin wanene wannan"? Ta faɗa tana nuna suitcase din da Unaisah ta aje, bata jira amsarta ba ta nufi akwatin dake ajiye, ta zauna daga gefen gadon ta soma kokarin bude shi tana fadin"wallahi yayi kyau sosai..." sai da tayi maganar Unaisah ta tuna da akwatin, da sauri ta dawo gaba gadon ta zauna, suka saka akwatin a tsakiyar su.. Kasa bude akwatin tayi, dakyar Unaisah ta buɗe shi waro Idanu waje su kayi ganin jigunanun Laces dinkakku tare da Materials da atampopi hada shaddoji, ɗaɗɗaga kayan suka somayi bakunansu sun ki rufuwa saboda mamaki. "Dan Allah waya baki su" "Ɗazu da chief ya kirani naje dakinsa shine yace min in dauka, dama ya kar6i awona ran nan, amma naji dadi wlh dama bamu da kayan hausawa acikin kayan mu..." sai murna ta ke yi tana yaba kayan, Batool dai jikinta yayi sanyi ganin kamar kayan na Unaisah ne kadai banda nata a ciki. "Bai ce hadani ba"? Da budar bakin Unaisah sai cewa tayi"Anya, kamar nawa ne ni kadai, amma kada ki damu zamu dinga sanyawa atare, ai abuna naki ne" mood din fuskarta kamar bataji dadi ba, in a cool voice tace"a'a ni bazanyi amfani da su ba, naki ne saboda ke ya siye su, kada ki damu..." ta fada tare da saukowa daga kan gadon, ruko hannun ta Unaisah tayi"meya faru ne naga kamar bakya farin ciki"? Murmushi ta kakalo kan fuskarta"don't mind your self, Am ok, inaso zan je dakin Aunty Ummi" tana ƙarasa maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, Unaisah bata kawo komai aranta ba, ta maida kayan cikin akwatin kafin ta datse shi tare da ruko handle dinsa, ta sauko ta fito daga dakin ta nufi dakin Aunty Ummi. _💘UMMIN AMERICA💘_ Fitowa tayi daga Toilet jikinta sanye da bathrobe, wayar ta dake akan gado sai ringing takeyi, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa. Hararar wayar tayi bata da niyar daukarta. Sai da ta gama shirya kanta cikin Jallabiya, kafin ta dauki wayar tare da yin picking ta kara a kunne. Kakkausar muryarsa ce ta ratsa kunnanta " Ummi, why haven't you been answering my calls for two days? I've even sent you messages, but you didn't respond." Batasan ya akai ta tsanci kanta da jin haushin shi ba. "Bana jin dadi ne, wayar ma ban san inda na jefa ta ba, sai yau na dauko ta" "Okay, ya jikin naki" "Da sauki" "Inason ganin ki, zanzo da anjima.." bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa"Sorry, basai ka zo ba, ka bari idan na samu time zanzo gidan ka" muryarsa da mamaki yace"Ummi kin canza min, wani abu ya faru ne"? "A'a ba abunda ya faru, kawai bana so kazo nan dinne," "Okay.." ya na faɗa yai rejecting call ɗin. nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata aje wayar saiga kiran dr shureim ya shigo wayar, tun shekaran jiya da suka zo yake ta kiran ta, sau daya ta taba picking tana jin muryar shi ta katse kiran amma tayi saving contact dinsa. A kalla tana da missed calls dinsa kusan dari da hamsin, daga shekaran jiya izuwa yau, ga messages da ya ta turo mata na ban hakuri da rarrashin ta akan rashin da su ka yi na yar su. Wi-pi din wayar ta kunna kafin ta shiga whatsapp, ta bude chat din shi, A hankali ta zauna daga gefen gadon ta soma karanta last message da ya tura mata. _Aisha ba zaki yafe ma yayanki ba? Pls bani baki tausayi, tsawon shekara sha takwas ina dakon soyayyarki a cikin zuciyata, dan Allah ki taimaki bawan Allahn nan, gani da ƙoƙon barata agare ki, ko bacci bana iyayi saboda tunanin ki, nasan da babynmu tana araye watakil inci albarkacin ta, saboda kina son ta, amma baki son mu sake samun wata atare? Kiyi tunani Aisha ni kadai ne zan iya baki irin ta_ A hankali ta furta"nasani ya shureim, kai kadai ne zaka iya bani irin ta, tabbas ina so na sake haihuwar mai kama da ita, but I can't marry you! I've already told you I won't marry the man who raped me, I can forgive you, but I can't marry you, even though I still love you amma meyasa kayi mini haka? jefar da wayar tayi kan gado kafin ta kifa kanta jikin pillow, kuka take ji sai dai hawayen sunƙi zubowa, sai dai takama yin kukan zuci. "Aunty Ummi" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah, Da sauri ta shanye damuwarta ta mike zaune tana kallon Unaisah dake shigowa ciki hannunta ruke da akwatin ta. "Ina Batool din? Tace min zatazo gurin ki, " "Batool bata shigo nan ba, akwatin wanene wannan"? Ta fada tana nuna akwatin hannun ta "Kayan da Chief ya siya minne" ta fada tana murmushi, Ummi tace"Masha Allah, amma na taya ki murna, gaskiya Chief yana ji dake.." ta fada yayin da take buɗe akwatin data kar6a a hannun ta, tayi mamakin kayan masu kyau da tsada. ______________________________✍️ bayan ya kammala motsa jikin shi, ya fito daga Gym room din ya nufo dakin sa, hannun shi ruke da bottle water me sanyi, ya rataya farin towal akan shoulder dinsa, kwata kwata babu riga a jikin shi sai Boxer short dinsa, gaba daya jikin shi gumi yake fitarwa.. Harya bude murfin robar zai kai baki da niyar yasha ruwan, wayarsa ta doka alert, dan dakatawa yayi ya nufi wayar dake akan couch, ya danna unclock button, bai jira yaga wanene zai shigo ba ya juya baya ya kanga bottle din abakinsa ya fara shan ruwa. can cikin kunnansa yajiyo takun tafiyar mutun, abun ya daure kansa aransa ya ayyana wanene ya shigo masa daki batare da sallama ba? A sukwane ya juyo don yaga wani isasshen ne, da dan mamaki akan face din sa ya ke kallon ta, tayi tsaye idanunta na kallon floor, kamar mara gaskiya sai wasa takeyi da yatsun hannunta.. *~_____________________________////////////////////🔥🌹~* *Daga Alkalamin Boss Bature🔥🫰* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 _ *The Unexpected Guest *_ ~___________________________________🌹✍️~ Da ace wani ne ya shigo masa daki haka zai tuhumesa ne amma da yake yasan wacece ita, da irin rayuwar da tayi sai bai damu ba. "Me ke damun ki"? Ya fada ganin kayan baccin jikinta sunyi squeezing, ga sumar kan nan nata a haukace ba gyara. Sam ta kasa bashi amsa, wani irin shakkarshi take ji, batasan ma ta shigo dakin ba, saboda bata a hayyacin ta, Nufo ta yayi jikinta na bari ta juya zata fuce, tana ruke handle din kofar taji ta adatse, wani irin faduwar gaba taji, ta dinga jan handle din amma taki buɗewa kamar zata saka kuka. Mamakine ya kama shi, ya rasa gane kan ta, aransa ya ayyana ko dai tana da tabin hankali? If not why zata shigo dakinsa ba sallama kuma yayi magana tayi shiru, sannan ya nufo ta tana kokarin guduwa"? Daga bayanta ya tsaya yana kallon yalwatacciyar suman kanta data cika bayanta. "Fada min meke damun ki? Baki da lafiya ne? Ai ko ki akayi guri na? Ko kinzo ne don ki gaishe dani'? Cikin rawar murya tace"am sorry, bansan na shigo ba, ba wanda ya aiko ni, " "Look, ni nasan ba hakanan ki ka zo ba, dole akwai abunda ya kawo ki daki na, just Calm down and tell me " Batare data juyo ta dube shi ba tace"ka ba Unaisah akwati, ni baka bani ba kuma inaso" Murmushin gefen fuska ya saki"Akwati biyu nace ta dauka, daya nata daya naki" "Ai daya ne tazo da shi, kuma tace nata, ita kadai ka ba mawa" juyawa yayi tare da kallon inda ya ajiye akwatinan daya ya gani. "Oh, ina tunanin ta manta bata ji ni dakyau ba..." ya juya ya nufi akwatin ya janyo handle dinshi ya mika mata"ga naki kema" maimakon ta juyo ta kar6a sai ta mika mashi hannun ta ta baya don ya bata. "It's improper ki juya mun baya ina magana, if you wanna me to give it to you, Turn around and face me" sarai ya fahimci shakkar shi take ji, kuma tana da kunya. Dakyar ta juyo ta fuskance shi idanunta na kallon floor. dayasan haka zai ganta inya matso kusa dabai ce ta juyowa ba, saboda gaba daya shatun nipples dinsa sun fito sosai ta jikin rigar baccin ta, bata saka bra ba, da sauri ya kawar da idanunsa gefe ɗaya, Ya mika mata akwatin hannunta na kerma ta ruƙe handle dinta cike da zumudi ta juya zata fuce ya dakatar da ita. "Kar in kuskura in ƙara ganin kina yawo babu mayafi akanki! Ki dinga suturta jikinki dakyau" gabanta na faduwa ta amsa mashi da toh, Ya raba ta gefenta Ya danna code din kofar ta buɗe da sauri ta fuce, tsayawa ya yi yana kallonta yayin da take jan akwatin ta nufi stairs, sai dadi take ji har zukunnawa tayi kan stairs ta shasshafa jikin akwatin batasan yana kallonta ba, sai da tagama kalle shi ta mike cike da zumudi ta karasa sauka down ta nufi dakinsu don taje ta gwado ma Unaisah itama ya bata suitcase. Sakin kofar yayi ta yi locking kanta, har zai juya idanun shi suka sauka akan siraran gashin kanta da ya kakkaba a kan floor, wasu irin dogaye masu kanannaɗa. juyawa yayi ya nufi tissu box dinsa dake ajiye gaban mirror ya yago tissue ɗin ya dawo ya zukunna gaban gashin Ya daura tissue din Ya nannaɗo su aciki, Kafin ya mike ya nufi drawer, ya bude Ya sanya Tissue din a ciki. ______________________________🔥🔥🔥 Bayan Kammala Sallar Juma'a around ƙarfe biyu da yan mintuna, Hamshakan Motoci Suka fara tururuwar shigowa Obie Estate, bakowane a cikin su ba face yan uwa da Abokanan Chief Owais yan team dinsa na isod tare da U.s Armies. Raba hanya motocin su kayi wasu suka nufi Gidan Baba Obie yayin da wasu suka nufi Gidan Chief Owais.. *CHIEF OWAIS🔥💪* Yana atsaye Cikin Lift, ya dauki wankan tuxedo suit, anyi masu adon Gold Gem stone dark blue, sai kyalli su ke yi, kayan sunyi fitting dinsa, ga wannan hadadden ducktail hair style din da yayi ma sumarsa. idanunsa na akan wrist watch dinsa kirar patek philippe wanda sai dan wane da wane suke sanyata. Time yake kallo, Yana karasa saukowa down Lift din ta buɗe Ya fito Ya nufi Dining area Tun kan ya karasa fragrance dinsa Ya daki kofofin Hanci nan su kusan atare suka dago suna kallon shi, ya yin da su ke a zaune kan Dining Chairs suna cin lunch din su. kasa haɗiye kingin abincin dake a bakunan su sukayi saboda rudewar da sukayi na ganinsa, Ya tafi da imanin su, Ba ummi ba ba taj ba har Unaisah da Batool sun shagala da kallon shi.. Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka gyara nutsuwar su.. Cikin girmamawa Ummi da Taj suka gaishe da shi, fuskar shi asake ya amsa masu kafin ya mayar da dubansa akan Unaisah dake ta kallon shi a fakaice Ya kashe mata ido ɗaya, gaba daya ya ƙara dagula mata lissafi, sai ta dinga ganin kamar Danish ne. "Happy birthday Chief namu, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka, Allah ya kara girma da daukaka, Allah ya kare mana kai daga sharrin makiya da mahassada" "Ameen, Thanks, Allah yabar zumunci atsakanin mu" "Bangane ba, Yau ne birthday din Chief, shine ba'a fada mana ba"? Ummi ce ta faɗa tana duban Taj "Am sorry, Laifi na ne da ban fada maku ba, yau ne Birthday dinsa, ya ƙara shekara daya, saura kaɗan ya cike 40yrs" ya fada da zolaya yana murmushi. "Amma dai banji dadi ba, da an fada mana da wuri ay da mun shirya muma anyi celebration din da mu"! ta faɗa tana kallon Chief, tattausar murmushi ya sakar mata. "ay min afwa, Idan na dawo da anjima zamuyi wani celebration din agida.." "Allah yakaimu anjima lafiya, sannan nima ina tayaka murnar birthday dinka, Allah ya cika maka burikanka na rayuwa, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya mara yankewa arayuwarka, Allah ya ƙara maka lafiya, Allah kuma ya baka mata tagari wadda zata zama cika makon jin dadin rayuwar ka..." a hankali yake amsa mata da ameen ameen, Unaisah tun da taji an ambaci mata tagari kuma taga ya kalle, ta dan saki murmushin gefen fuska tare da kawar da idanun ta gefe ɗaya. "Happy Birthday Chief, Allah ya faranta maka rai kamar yadda kake faranta mana" Batool ce ta faɗa da murmushi akan fuskarta, kallonta yayi ganin ta yi rolling mayafi akanta hakan ya tabbatar masa da taji warning din da ya yi mata. "Thank You," Wani kallo Taj yai ma Unaisah hakan yasa tace"happy birthday My husband to be, Allah ya baka nasara akan abunda kake nema, Allah kuma ya cika maka burikan ka" Waro idanu Ummi tayi"What"? cike da jin kunya ta sunnar da kanta ƙasa, Batool ce kadai bata fahimci me tace ba, shi kuwa Chief ƙayataccen murmushi Ya saki idanun shi akan fuskarta, Taj sai faman sakin murmushi yakeyi Yaji dadin abun nan. "Amen, shukran laki wife to be, Allah ya cika mana burin mu" cike da jin kunyar daddynta ta amsa mashi da ameen. "Zan kai karfe shida, pls kafin na dawo Ku shirya kanku, zan ma Chefs magana su hada maku Cake..." haɗa ba ki su ka yi gurin yi mashi godiya, tare da fatan Alkhairi. har ya juya baya basu daina kallon shi ba, yadda yake tafiya cike da aji ba karamin kayatar da su yayi ba, kafin taj ya dawo da duban shi gare su tuni Unaisah ta gudu zuwa daki saboda kunyar kada ta hada ido da shi. Yana fitowa Falo Yayi Arba da motocin da ke shigowa Villa Dinsa, a jere suka tsaya a parking Space. Ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga Cikin motocin, Kowan nan su Ya ɗauki wankan expensive Suits na kece raini, tun daga kan CO, CI, Agent zahra and Osman, tare da U.s Armies, fuskokinsu dauke da farin ciki suka nufe shi, aransu sai yaba kyawun shi su ke yi su kansu wankan shi ya tafi da imanin su, Gaba daya sai yaji bakin Ciki Ya mamaye zuciyar shi saboda rashin Ganin Omar atare da su, Farin cikin shi ragagge ne, suna karasowa suka sara mashi, shima Ya sara masu, tare da mika masu hannu daya bayan daya sai da ya yi Musabaha da su, a mutunce suka gaisa da junansu, bayan sun yi mashi happy birthday, Saida suka fara shigowa Cikin gidan suka duba jikin Taj kafin suka fito, ahanzarce security officers suka bude masu Cardoor suka shiga cikin motocin a jere suka nufi Cikin Obie Estate. Daidai Lokacin da za'a fara gudanar da Shagalin, gaba daya Hall din a kewaye yake Da sojoji harma da Isod Soldiers, baka jin komai sai sautin kidan Isod Anthem dake ta shi. A gaban Hall din motoci suka dinga yin parking. Ahanzarce Jami'an suka soma bude masu cardoors... Yana ƙoƙarin fitowa daga Cikin motar, Idanunsa suka sauka akan Daddynsa dake fitowa daga cikin motar shi, Karaf idanunsu suka shiga cikin na juna, nan da nan Ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi gefe ɗaya. Girgiza kai sharafuddeen yayi duk sai yaji ba dadi, badan ya damu da shi ba, da ba abunda zai sa shi zuwa birthday dinsa sai dai shi bazai biye mashi ba. gaba ɗaya Uncle dinsa sun fito daga cikin motocin su hada Baba Obie, jikokin family din bakowane Ya samu damar halarta ba, wasu uzuri ne ya ruke su, kowan nan su Ya dauki wankan shadda geztner blue sky, sai ya zamana kamar sunyi anko da Chief ne. Akan Idon shi Chief Ya nufi Baba Obie yayi hugging dinsa tighly tare da manna masa peck a cheeks dinsa, bayan sun gama gaisawa ya nufi Hateem Yayi hugging dinsa kafin Yabi sauran Uncle dinsa da Yan uwansa duk yayi hugging dinsu, amma shi ko arzkin gaisuwa bai samu ba, hakan ba karamin taba zuciyarshi yayi ba. babu wanda ya lura da hakan sai Hateem dama tunda yazo ya fahimci akwai wani abu dake damun Dan uwansa, bai dai tambaye shi ba, sai yanzu yaga amsar tambayar shi lamarin ya daure mashi kai sosai. Gaba ɗaya suka dunguma izuwa Cikin Hall din da aka kawata shi da decoration, makada da mawaka da akayi inviting Sun hada kai sai kirari suke yi ma Chief. basu dade da shiga Ciki ba, Saiga Mommynsa gimbiya malik tare da hajiya laura da kanwarsa hindu sun shigo, gaba dayansu Laces ne a jikin su, yana ganinsu ya nufe su, tun kafin Ya karaso hindu ta riga shi isa tayi hugging dinsa tighty tana fadin"happy birthday Big bro, we're so proud of you" fuskarshi dauke da murmushi Ya dan bubbuga bayanta da tafin sa. Kafin ya dago ya rungume mommynsa, shafa sumar kan shi tayi"happy birthday, my beloved son, You're the light of our family, and I'm so grateful for your kindness, compassion, and leadership, May this year bring you happiness and success." "Ameen mommy, I can't thank you enought, kin gama min komai, kece silar daukakana" ya fada tare da raba jikin shi daga nata, murmushi suka sakar ma Juna. Kafin ya dubi Hajiya laura, suka gaisa a mutunce itama ta yi mashi fatan Alkhari. Shigowa Hall din Hajiya Saratu tayi, jikinta sanye da pakistan na manyan mata riga da wando, tayi rolling veil akanta, ga wani hadadden shade fari data saka, ta wanku iya wankuwa, pravin Yana a gefen ta, yayin da su twins ke abiye da bayansu, gaba dayansu Indian outfits ne a jikinsu, sunyi bala'en kyau, sun fito da ainihin suffar su ta indiyawa. Hajiya laura na ganinta ta nufe ta da fara'a suka yi hugging din Juna sai yaba kyanta Hajiya laura take yi, bayan su twins suna gaishe da ita suka wuce Gurin Chief, suna karasowa Ya yi hugging dinsu atare sukayi mashi happy birthday. Pravin ma Yaje yayi mashi, kafin Hajiya saratu itama ta matso kusa tayi hugging dinsa tare da yi mashi fatan Alkhairi, Kafin kace me tuni Hall din ya cika da yan uwa da abokan arziki, Sai yan gaishe gaishe suke yi atsakanin su, Hatta U.s Armies da Senior agents saida Chief ya kai su gurin baba Obie suka gaishe da shi, ya kuma kaisu gurin Mommynsa suka gaishe da ita cikin girmamawa, haka sauran Uncles dinsa duk saida su ka gaisa da abokan aikin sa mahaifinsa ne kadai bai kai su wurin shi ba. daga bisani Mc ya hau kan Stage, hannun shi ruke da mic, ya farayi ma Baki maraba da zuwa, tare da gabatar masu da kan shi, dayawa sun gane fuskarshi shine yayi mc A farewell dinner na hateem, Baba Obie ne ya yi inviting dinsa a wannan karo ma. Bayani ya soma korawa, Hankulan Kowa Ya dawo kan shi. _"Ladies and gentlemen, esteemed guests, family, and friends, welcome to Chief Owais's birthday celebration!"_ _Today, we gather to honor a remarkable leader and an extraordinary individual"_ ya fada yana nuna Chief Owais. gaba daya suka fara tafa mashi, bayan ya kammala Speech dinsa Yayi inving Iyayen Chief don suyi speech dinsu, bayan Gimbiya Malikat Ta kammala nata mutane sunata tafa mata, Mai girma sharafuddeen ma yayi nashi Speech din mai ratsa zuciya, sai dai ko kadan Chief bai nuna Yaji dadin yabon da yayi mashi ba, saima yaki dagowa su hada idanun su, hakan ba karamin bata ran Mai girma shafuden ya yi ba_ Time da Mc yayi inviting Chief don yayi speach dinsa, Hankalin Kowa na hall din ya dawo kan shi... Cikin nutsastsiyar muryar shi mai Jan hankali Ya kora jawabi mai matuƙar taba zuciya, abun da ya kara daurewa Uncles dinsa Kai Jin ya yabi mahaifiyarsa tare da su, amma bai sanya sunan mahaifinsa ba, basu kawo komai aran su ba, saboda sun yi tunanin ba dagangan ya yi ba. Bayan Ya kammala speech dinsa Mc yace"I'm inviting his wife to give a speech on stage" Tunkan Ya kare maganar Hajiya saratu ta ɗaga murya tace"ai har yanzu bashi da aure, tazuru ne" gaba daya hall din suka kama dariya cikin nishadi, sun sa shi jin kunya. Cike da zolaya Mc Yace"Chief what are you waiting for? Me ka nema ka rasa? Zankadedan saurayi kamar ka, burin kowace ya mace uhm? Ya faɗa yana kallon sa, kamar baisan yanayi ba, idanunsa na akan wayarsa da yake dannawa.. "Cikin yan matan nan da suke hauka akanka ya kamata aba daya dama mana" dariya suka sanya, Hajiya saratu tace"He has a fiancee, Insha'Allah, we will soon invite you to his wedding celebration" Gaba daya jama'ar dake acikin Hall din suka sanya shewar murna. Daga Bisani Labulan daya Lullube ke6ataccen gurin da aka tanada saboda Chief ya soma ɗagewa sama a hankali gaba daya hankulan mutane ya koma kan shi Wata katafariyar throne Chair ce da aka kawatata saboda shi, daga gaban kujerar wani hadadden table ne anan aka daura katon cake din da akayi domin sa, mai hawa 10 hada sunan shi a jikin Cake din da wani salon rubutu me jan hankali akayi shi, daga saman silin din gurin an kawata shi da navy blue balloons da steamers, wurin Ya burge mutane, friends dinsa ne suka yi mashi rakiya Ya hau kan kujerar Ya zauna tare da daura kafarsa ɗaya kan ɗaya like a King on his Throne. Minti 30 aka ware saboda baki su samu damar Cin abinci, bayan kowa yaci yasha anyi kullu wash rabu hani'an Mc Ya sa Mawaka suka fara wake Cheif Owais, wakar tayi mashi dadi hatta yan uwansa sunji dadin wakar birthday din da akayi masa. Lokacin da Mc Yayi inviting Yan uwa da abokan arziki donsu fito tsakiyar filin su taka rawa, nan fa suka fara hawa kan dancer floor din cike da nishadi suke taka rawar girma, kowa saida Ya taka In ka cire Mutun daya Mai girma sharafudden da ransa yagama 6aci, Jira yake kawai agama shagalin su shiga family meeting don Ya fallasa abun da ke faruwa tsakaninsa da owais, saboda hakurinsa ya ƙare ya ƙwammace kowa ya ji. Lokacin da aka kusa kammala shagalin, Yan uwa da abokansa suka taya shi Yanka cake, ya 6allo cake din Yaba momynsa abaki, bayan taci itama ta debo ta saka mashi abaki yaci. ya bi Uncle ɗin sa daya bayan daya ya gutsuro cake ɗin ya sanya masu abaki suka ci, ko da yazo kan sharafudeen Saida Ya fara aika masa da harara kafin Ya bashi cake din, badan idon mutane ba da ba abun da zaisa ya ci cake din nan, hakanan ya jure ya bude baki Ya sanya mashi cake din kamar anyi masa dole. Bayan ya gama basu Hindu ta debo cake din ta bashi abaki, shima ya bata abaki, Baba Obie Ya ballo Ya tura masa abaki, kowa ka kalla fuskarsa dauke da farin Ciki banda mahaifinsa. Mintuna talatin da suka rage kafin A kammala Birthday din, photographers suka fara daukar su Hotuna da videos, sai da Chief Ya dauki hoto da kowa daya halarta amma banda mahaifin sa, Ko kusa da shi Yaƙi bari Yazo, balle yasa ran zai yi hoto da shi. Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, Yan uwa da abokan arziƙi sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, bayan kammala addu'ar tashi daga taro da Mc ya gabatar tare da yi ma Baki fatan sauka gida lafiya. *HAJJATY🍁* Tana akwance kan gadonta, Ta lullube kanta cikin bargo, Jikinta sai makekketa yakeyi saboda zazzabin daya lullu6eta, duk yadda taci burin ta halarci birthday din Owais, Allah bai nufa ba, Tun safe take fama da zazzabin har magani tasha amma yaƙi sauka, har kiran layin Pravin ta yi don ta fada mashi halin da take aciki amma bai yi picking call din ba, rabon ta da shi tun bayan kammala sallar asubahi daya leko dakin ta bata ƙara ganin ƙeyarsa ba. Yan aikin gidanne kadai suka san bata da lafiya, Har abinci suka kawo mata amma takasa cin shi, burin ta kawai taga pravin saboda shi kadai ne zai iya kwantar mata da hankali. ________________FAMILY MEETING🔥 "Owais meya haɗa ka da Mahaifinka? Meyasa kake zarginsa? wani laifine kake tuhumarsa da shi Ya fada min ba yadda bai yi dakai ba akan ka fada masa amma ka ƙi sanar da shi why pls"? Hateem ne Ya faɗa Idanunsa a kan Chief owais dake a tsaye yana fuskantarsa, Suna a cikin dakin Baba Obie. Fuskarsa babu walwala ya furta"zanyi maka bayani anjima" girgiza kai Hateem yayi ransa abace yace"No, Yanzu nake son ji Owais, Dole ka amsa min tambayata idan har ba so kake raina Ya baci ba"! Shiru yayi saboda ya rasa ta ina zai fara kora masa jawabi. "Hateem meke faruwa ne? Har an fara shirin Family meeting bangan ku ba, yanzu nake tambayar kuna ina, auta take fadamin taga shigowarku dakin baba " Sir mubarak ne ya yi maganar yayin da ya ke shigowa dakin idanun shi akan su. Kafin wani daga cikin su Ya furta Kalma suka ji an banko kofar dakin gaba daya suka kai dubansu ga mai shigowa. Mai girma sharafuddeen ne Ya shigo dakin fuskarsa kwata kwata babu annuri, sai huci Yake yi kamar mayunwacin zaki, kaitsaye ya nufi Owais yana karasawa gaban shi, Ya damƙo Arm dinsa da ƙarfi Ya fusgoshi Ya nufi kofar dakin da shi... Hankali atashe Hateem da Sir Mubarak suka bi bayanshi suna kokarin dakatar da shi. Bai nufi ko'ina ba sai falon, A lokacin Baba Obie tare da sauran Uncles dinsa da Hajiya saratu duk suna a Falon kowan nan su yana azaune kan sofa, shigowar Shafudden ne Ya ɗaga hankulan su a razane suka mimmike tsaye , cike da rudu suke kallon su.. "Dad.. let go of arm" yana huci ya fada sharufudeen Yace"bazan saki ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..." "meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"? Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza miƙewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife ƙasa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa. Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya faɗa maka" ya faɗa yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya ɗaura min karan tsana, yau wata ɗaya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya faɗa...." Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta.. Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa. Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"? "Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla. Gaba daya basu ji dadin abun da Owais ya yi masa ba. Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"? Ya faɗa yana kallon chief wanda har lokacin bai ɗago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa. "Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar.. His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"! Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, " ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka," Pravin da ke ƙoƙarin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su. A fusace Owais Ya miƙe tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi. Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba. Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci. Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi. Dakyar ya haɗiyi ƙululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi.. Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"? Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..." Gyaɗa kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana ɗaya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ƘADDARA❗...." Aruɗe Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"? Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya faɗa! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa? Hateem har ya buɗe baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba. Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji. "ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..." bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya damƙi kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..." "Haba yaya Sharafudeen pls Owais.." Hajiya saratu da ta ɗauko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba. Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!" fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, ɗan sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da ɗa suna faɗa atsakanin su.." fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace. Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba. "Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba.. Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa.. Lokaci ɗaya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi. bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa. wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin "zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...." girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa. "Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa. Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma. Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. "Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..." His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa. "Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"? Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba, "Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba, kunsan dai ba zai yi maku karya ba....." Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..." dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...." juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi. Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne. Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi. Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais.. Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa.. "Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"? Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya. "ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"? his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar. Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba. A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba.. Hannayen shi dake kerma ya ɗaga sama cikin karyayyar murya ya ce _"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...." bai kaiga ƙarasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data karaɗe kunnuwan su *_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_ ~*_________________________________*~ *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹 _ * *_ ~___________________________________🌹✍️~ A matuƙar ruɗe suka juya tare da kallon mai shigowa... Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, daƙyar ta ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma. Cike da tsantsar ruɗani suke kallon ta daga ƙasa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ƙahon zuciya. A sukwane Sharafudeen Ya miƙe yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba. Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani.. Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta ƙi aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi, kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ruɗani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo... "Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji dame ta zo musu. "Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate ɗin?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke. Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah.. Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka miƙe daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo... "Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq... "Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faɗa yana zare idanun sa.. "Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..." Senate Lateef ne ya ɗauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ƙoƙari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin. Tana gab da zata ƙarasa gaban Sofas ta ɗan dakata tana mayar da numfashi. Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ƙaraso tsakiyar Sofas ɗin, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...." Bai ƙarasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma. Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate ɗinsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!' Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzuƙa za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta. Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike taƙama ne?" Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!" Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaɗo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..." Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruɗu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?" "Ba zaku ɗauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da baƙaƙen aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..." Pravin ne Ya faɗa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru. Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ƙarasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta damƙi mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya zaƙinta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.." Balbaleta da faɗa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Sai da suka gama harzuƙa kowa zuciyarshi ta zo a wuya. Pravin yana ƙoƙarin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faɗo ƙasa ta bi tasa ƙafarta ta take shi ya faffashe. Ɗagowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta ɗaga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba ɗaya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya ɗarsu acikin zukatansu, Sun ruɗe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita. Sai lokacin ta yi ƙarfin halin buɗe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!" Ta faɗa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya miƙe tsaye a kiɗime yana zazzare idanunsa! lokaci ɗaya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matuƙar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ruƙe shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa.. Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike taƙama ne, wace ce ke wai..."! Bata ƙare maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruɗe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaɗunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ƙoƙarin gano wacece ita.. Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!" Ta faɗa tana ƙoƙarin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ƙwalla. Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya ɗauke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku ƙaryar na mutu bayan ina a raye...." Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da ƙwaƙwalwarsu ke ƙoƙarin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki. Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya jiƙe sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi. Pretending ya yi duk don ya ƙara dagula masu lissafin ƙwaƙwalwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!" Ya faɗa a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce. "Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..." Ta faɗa tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ruɗani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu ɗaya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin ƙwayar idanun ta. In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya faɗa yana girgiza kansa. Bai ƙare maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ruɗani! gaba daya mun ruɗe, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya faɗa fuskarsa sharkaf da hawaye. Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi. "Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku ƙaryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..." La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! Ƙarya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya faɗa yana nunata da yatsansa dake kerma.. "Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ruƙiya zaku tabbatar da abunda nake faɗa maku..." Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ƙululun bakin ciki da ya tokare maƙogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shaiɗani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasiƙi ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...." bata ƙare maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ruɗar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu ɗauka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu. Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ƙame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa. Damƙar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana faɗin, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son haɗa uba da yayansa, ni nasan maƙiya ne suka turo ki don ki yi mini ƙazafi..." Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata ɗauki. "A'uzu billahi minasshaiɗanir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma baƙar munahika" Ya faɗa yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu. Tana kuka haɗi da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana miƙa masu hannu, "Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ƙara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni kaɗai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta faɗa idanunta cike tab da ƙwalla, tana ta ƙoƙarin ƙwace hannunta daga mugun ruƙon da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita. Hankalin Pravin Idan yayi dubu toh ya tashi, murnar da yake yi tuni ta koma ciki, ya murtuke fuska, hannayenshi biyu ya ɗaura a saman kanshi alamar ya shiga uku, ƙirjin shi kamar ana luguden ta6are, kafin ka ce me tuni ya haɗa uban gumi, jikinshi ya kama makyarkyata kamar wanda farfaɗiya ta kama. Har ya kusa fucewa da ita daga falon Sharafudeen ya yi kukan kura ya watsa da gudu ya nufe su, yana ƙarasowa ya bangaje baba Obie gaba daya ya kife ƙasa kafin ya ɗago Sharafudeen ya damƙo hannun Khala ya juyo da ita suka dawo Falon. Da sauri Hateem ya nufe su ya kar6e hannun Khala dake acikin na Sharafuddeen ya yi hugging ɗin ta akan broad chest dinsa, ya ƙanƙameta sosai kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta kamar yadda shima ya ji sanyi a ranshi, rungumar da ya yi mata tasa ya ƙara yarda mahaifiyarsu ce saboda wani yanayi da ya tsinci kan shi wanda uwa da ɗa kadai ke jin irin shi idan jikinsu ya haɗu da na juna. "Yaya kun yarda da ita? Kun yarda cewa momma ce?" Hajiya saratu ce ta faɗa a ruɗe "Ta yaya bazamu yarda da ita ba, koda kowa bazai yarda ba mu mun yarda mahaifiyarmu ce, ni tun lokacin da idanuna suka shiga cikin nata, raina ya bani momma ce..." A cewar Sharafuddeen. "In hakane taya akai ta rayu bayan ta mutu? kuma mun ga gawarta da idanunmu?" Ta jefa ma su tambayar . Sharafuddeen ya ce, "Shi yakamata ku tuhuma.." Ya faɗa tare da nuna baba Obie "Saboda na fara kokwanto akan shi! kuma dama shi borin kunya da hauka ake naɗe shi, in ba haka ba meyasa zai ɗaga hankalinshi don kawai ya ganta? Bayan haka a gabanku baba ya juyamin baya ya hana kowa ya yi magana akan tuhumar da Owais ke yi mi ni, wai har ni zai ce in kare kaina agurin Owais!....." Ya faɗa yana jifar shi da kallon tuhuma. Bai ƙarasa maganar ba Baba Obie Ya nufo su cike da rashin kuzari, yana fitar da huci kamar mayunwacin zaki ya nufi Khala da Hateem ya rungume, har ya miƙa hannu da niyyar ya damƙo ta, Sharafuddeen ya yi saurin damƙo hannunsa ya jefar da shi gefe ɗaya baima san sa'adda ya daka mashi tsawa ba, dama da haushinshi a cikin zuciyar shi. Gabansa ne ya yanke ya faɗi jin yadda Sharafudeen ɗan cikinsa ya daka masa tsawa kuma ya jefar da hannunsa, hankali a tashe ya furta, "Na shiga uku..!!!" "Baba, don't dare touch our momma! Don't touch her! Let her talk, Idan har kana da gaskiya meyasa zaka ɗaga hankali akanta huh? Ka barta ta yi magana mana!" rai abace Sharaudeen ya faɗa yana kallon cikin idanun shi. Zare idanu baba Obie ya yi with pure confusion on his face, Tsantsar mamaki ya hana su Sir mubarak furta magana sai binsu da idanu su ke yi. nuna kanshi ya yi da yatsan shi, "Sharafuddeen ni kake yi ma tsawa? Ka na cikin hayyacinka kuwa? Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.." ya faɗa yana dafe kanshi da tafukan hannayensa.. "Baka ga komai ba Obinna...." Tsohuwar ce ta faɗa tare da raba jikinta daga na Hateem ta dubi baba Obie da wani ƙasƙantaccen kallo mai cike da tsana.. "Dama bana faɗa maka ba akwai ranar ƙin dillanci? Shin ban fada maka duk min daran daɗewa asirinka zai tonu ba? Dama hausawa sun ce rana dubu ta 6arawo rana ɗaya ta me kaya, yau dubun taka zata cika...." Girgiza mata kai ya dinga yi idanunsa sun kaɗa jawur tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, ya rasa ya zai yi ya dakatar da ita.." Cikin raunanniyar murya ya furta, "Kada ki yi min haka! Na roƙe ki, kada ki tona mini asiri, Kada ki raba ni da ƴaƴa na, kada ki raba ni da mutuncina, Ki rufe mini asiri ki agazama rayuwata, ki taimake ni kodan saboda darajar ya'yan mu, In kika fallasa asirina kamar kin fallasa asirin ahalinmu ne, zaki ja mana tozarci a idon duniya...." Zubewa ya yi akan gwiwowinsa yana ci gaba da girgiza mata kai hadi da marairaice mata fuska don ta tausaya mashi. Kallo Ya koma sama, kalaman Baba Obie sun ɗaga hankulansu, sun jefa zuciyoyinsu acikin rudani tunma kafin su ji wani asiri ne nashi da baya son ta tona. "Lokacin da na dinga roƙonka akan kada ka kashe ni ka barni da raina baka yi hakan ba saboda zuciyarka ta ƙeƙashe babu ɗigon imani a ranka, zalunci kadai kasa a gaba, ba irin magiyar da ban yi maka ba amma ka toshe kunnuwanka kuma ahaka kake tunanin ni zan rufa maka asiri bayan Allah ya tseratar da ni uhm?" Ta faɗa tana kallonshi da raunatattun idanunta. Ruƙe ƙafafunta ya yi da hannayenshi ,"Dan Allah ki rufa mun asiri, kiyi min rai, kada ki kashe min rayuwata, na yi maki alƙawarin zan shiryu..." cikin jin ƙunar rai ta haɗiyi yawu mai ɗaci tare da kawar da idanunta daga barin kallon shi ta dubi sama hawaye na cigaba da zarya kan kuncinta, ranar da ta daɗe tana gargadinsa akan zuwanta, ba irin jan hankalin da bata yi mashi ba amma yaƙi ji yanzu wa gari ya waya? "Dan Allah ki faɗa mana dagaske momma ce ke? Dama baki mutu ba kina a raye? Kuma me ya faru dake? Me babanmu ya akaita? Dan Allah ki faɗa mana, kun ɗaga mana hankali, Kun ruɗar damu..." Hajiya Saratu ce ta fada fuskarta a yamutse, Sir Mubarak ya ce,"Momma ki faɗa mana gaskiya, muna son mu ji taya akai kika rayu bayan kin mutu? Kuma me mahaifinmu ya akaita maki? Sannan wani asiri ne nashi da baya son ki faɗa?" Tsantsar tausayinsu ne ya kamata, saboda tasan in ta faɗa su da farin ciki har abada, watakil ma baƙin cikin mahaifin nasu zai yi silar rasa ran wasu daga cikin su. Amma ya zata yi bata da mafita da ya wuce wannan, saboda alwashine ta daukarwa kanta, Allah ne ya amsa addu'arta shiyasa har ta rayu don ta tona masa asiri don haka bazata butulce ba, mutun azzalumi irin sa bai cancanci a rufa masa asiri ba. Cikin karyayyar murya tana kuka ta ce, "Ku yi haƙuri! ku yi haƙuri!! ku yi hakuri!!! da abun da zan faɗa, nasan abun da ciwo amma ya zaku yi ubanku ne ya ja maku, shine silar komai...." Ta faɗa da tsawa tana kuka jikinta har jijjiga ya ke yi, Chief Owais ya kasa furta kalma, sai rarraba idanunsa ya ke yi akan fuskar Obie da Khala haƙika sun jefa shi a ruɗani. "MAHAIFINKU OBINNA SHINE ELDER NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, SHI DIN MUGUN MATSAFI NE, BAIDA IMANI, MUGUNTA DA ZALUNCI YASA A GABA, TUN FIL AZAL, DUKIYARSA BATA HALAL BACE, KUMA SHI BA MUSULMI BANE, ARNE NE, IDAN BAKU SAN KURKUKUN KADDARA BA, ZAN FAYYACE MAKU KOMAI, GIDAN KURKUKUN KADDARA GIDAN MATSAFA NE, YA KAFA SHI TSAWON SHEKARU TALATIN DA DAURIYA, ME AKE AIKATAWA A GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? ƘANANUN YARAN DA BASU JI BA BASU GANI BA SUKE KULLEWA A CIKINSHI, BA FUCE BA SHIGE, TUN SUNA JARIRAI SUKE RAINONSU HAR SU GIRMA, ZASU TASO BATARE da addini ba, ba salla ba sallati, sai tsantsagwaran jahilci cike da kansu, basu san wanene mahaliccinsu ba, gaba daya sun tauye masu hakkinsu na rayuwa, abu mafi muni suna azabtar dasu azaba mai radadi, su yi lalata da su, su sha jininsu, su kwanta da gawa, su cire sassan jikin su, kai har jarirai basu bari ba da mata masu ciki suna kwanciya dasu, matasan yan mata da suke tsaka da shan azabar Jinin al'ada a haka suke saduwa dasu duk watan Allah idan ya kama, Ni kaina bazan iya misalta rayukan da suka salwantar ba, Nima ina ɗaya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, saboda tsautsayi yasa na yi masu leƙen asiri nasan sirrinsu shiyasa ya shirya makirci ya dauke ni daga gare ku,....." Bata ƙarasa maganar ba Sir mubarak ya doka mata tsawar da ta yi silar firgicewarta, Yana huci ya ce, "Ƙaryane! Bazai ta6a zama gaskiya ba, kazafi ki ke yi masa, mahaifinmu bazai ta6a iya aikata munanan zunubban nan ba, mahaifinmu mutumin kirki ne, Mai jin tsoron Allah, mutun ne mai zuciyar imani da tausayi, bazai taba aikata abunda kike zarginsa da shi ba...." Bai ƙare maganar ba senate Lateef da ya gama harzuka zuciyarshi a wuya yai kukan kura zai shaƙe wuyanta, Sharafuddeen ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar damƙe wuyan hannunsa, yana huci ya ce, "Ka sake ni Sharafudeen!! Wannan mahaukaciyar matar ta rasa wa zata yi ma ƙazafi sai mahaifinmu? Baka ji munanan kalaman da ta jefe shi da su ba? Wai mahaifinmu ne matsafi? Ɗan kungiyar asiri???" Ya faɗa yana zare idanunsa da suka kaɗa jawur. Cikin jin ƙunar rai His excellency Abdul Razak ya girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya ce, "Wlh kodai ku fitar da tsohuwar nan ko kuma in kashe ta a gurin nan, ta ya zaku bar mahaukaciya tana cin zarafin mahaifinmu a gaban idanunmu, wannan ai zancen banza ne, wlh sai munyi shari'a dake dole ki fuskanci hukunci mai tsanani...." Deen ya amshe, "Ai ga irinta nan! tun farkon shugowarta yakamata a kore ta, ni bansan uban waye ya bata iznin shigowa ciki ba! Ku kuma kun yi tsaye kamar wasu sakarkaru a gabanku ake yi wa mahaifinmu ƙazafi, daga gani abokan adawarmu ne suka turota don ta tarwatsa zaman lafiyar mu...." Ya faɗa yana nuna su Hateem. Kalamansu sun cika kunnan baba Obie, wata irin karaya mai haɗe da faɗuwar gaba ce ta ɗarsu acikin zuciyarshi dake yi mashi wani irin mahaukacin bugun barazana, wani kallo yake binsu da shi mai wuyar fassaruwa ganin yadda suka haƙikance akan kazafi ne ake yi masa saboda yardar da su ka yi da shi. Cikin raunanniyar murya Khala ta ce, "Koda zaku kashe ni bazan fasa faɗar gaskiya ba, na yi maku uzuri saboda nasan irin yardar da ku ka yi wa mahaifinku, hakika ya cutar da rayuwarku, ya zalunce ku, tsawon shekaru kuna tare da mugun iri acikin ku batare da kun sani ba, Ya daɗe yana munafurtarku...." Ta ɗan dakata tana jan numfashi, sai ƙoƙarin kai mata bugu suke yi amma Hateem da Sharafudeen sun hana, sai ma suka katangeta ta yadda bazasu iya ta6ata ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana a tsakiyar su taci gaba da magana. "Dukiyarsa bata halal bace, Haramun ce tsantsa, ya ciyar daku da haram! Ya tufatar daku da haram!! Ya gina ku da haram!!! Mahaifinku mutunne mai neman duniya ido rufe, baidamu da lahirarsa ba, koda ya ke baiyi imani da Allah ba, burinshi ya shahara, darajarsa ta ɗaukaka duniya tasan da zaman shi, shiyasa ya jefa kanshi cikin halaka da ku kanku saboda kuma bai barku hakanan ba, duk wata nasara da kuka samu, da duk wata ɗaukaka da kuka samu, sun samo asali ne daga abunda mahaifinku ya ke yi maku, shiyasa baku ta6a faɗuwa ba a rayuwarku, ya sanya maku farin jinin da in har kuka shiga mutane sai kun shahara acikin su, haka zalika in kuka ta6a abu zai yi albarka......" Wannan karon bakinsu ya mutu bawai don sun yarda da maganar ba, sun dai fara wasiwasi acikin zuciyoyin su. Yanayin fuskokinsu ya nuna tsantsar tashin hankali da damuwa haɗi da rudanin al'ajabin maganarta. Baba Obie dake a zuƙunne kan gwiwowinsa ya kasa motsawa ji yake kamar an rufa masa bargon azaba a bayanshi saboda tashin hankalin da ya shiga, da wani ido zai dubesu a wannan baƙar ranar, gaba daya ya ɗimauce ji yake kamar ya haƙa rami ya binne kansa, babban abun takaicin sihirinsa ya ƙi tasiri a kanta, ya so tun farko ya dakatar da ita sai dai Allah bai yarda ba, this time around jikinta akwai kariyar ubangiji. Tsohuwa Khala bata dakata da yin magana ba taci gaba da cewa, "Sau nawa matayenku suna haihuwar ya'ya su zo babu rai a jikinsu ko bayan sun haihu jariran su mutu?" Ta faɗa tamkar tana yi masu tambaya, Ta ɗaura da cewa, "To waɗannan yaran ba mutuwa su ka yi ba, ku tambayi ubanku Obinna ina yaran ku suke! Ta faɗa a tsawace tare da nuna shi da yatsan ta. Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!, Wlh alƙalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyarsu ta karaya da ganin yadda ya yi shiru ya kasa kare kanshi daga abunda tsohuwar ke tuhumarsa." Cikin shesshekar kuka Hajiya Saratu take fadin, "Nashiga Uku! Na bani na lalace! Baba dan Allah ka yi magana! Baba ka ƙaryata tsohuwar nan! Baba ka agazamana zuciyarmu ta raunata! al'amarin nan ya fi karfin zukatanmu! Baba mu mun yarda da kai munsan bazaka iya aikata abunda take jefanka da shi ba, wlh kazafi ta ke yi maka, Mahaifinmu ba fasiƙi bane, mahaifinmu ba matsafi bane, mahaifinmu bazai taba iya aikata rashin imanin da kike tuhumarsa da shi ba, dan Allah baba ka tashi ka ƙaryata tsohuwar nan....!" Tana cigaba da kuka ta nufe shi ta dafa kafaɗunsa tana kokarin mikar da shi tsaye don ya yi magana sai dai ya ƙi bata haɗin kai, wasu irin narka narkan shatun jijiyoyine suka fito saman fatar goshinsa.. "Baba ka taimaka min, Ka agazama rayuwarmu, baba ka yi magana, na roƙe ka, dan Allah dan soyayyarka da manzon Allah SAW......" Murmushin takaici khala ta yi, "Hmmmm Saratu dama kin daina wahalar da yawun bakin ki, saboda a halin yanzu mahaifinku baida bakin magana, wannan kaɗai ya isa yasa ku gasgata magana ta..." Ta faɗa tana kallon fuskar baba Obie dake fitar da gumin zufa, shatun jijiyoyin wuyansa sun fito ruɗu ruɗu, jikinshi ya ɗauki wani irin mahaukacin zafi. "Duk wani jariri da matayenku suka haifa ya zo ba a raye ba sune suke ɗauke shi daga gare ku, da haɗin bakin munafukan likitocin asibitinsa, Ku tambayi munafuki MD Dr Jidanna, da Dr Adam da kuma Dr chisom, da sa hannunsu ake yi maku wannan aika aikar...." "Zaku haifi ɗa ku ganshi a mace alhalin ba shi bane rufa ido su ke yi maku su yi musayar shi da aljani su ɗauke na gaskiyar su tafi da shi gidan kurkukun kaddara, ku kuma ku dauki aljanin ku yi jana'izarsa ku rufe a ƙabari da sunan jinjirinku ku ka rufe...." ta faɗa cike da takaici, "Haƙiƙa Obie ya zalunce ku wlh wata shari'ar sai dai a lahira, amma fasiƙin mutumin nan ya daɗe yana aikata luwaɗi da zina da jikokinsa da ya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, ya sha jininsu, ya kashe su saboda neman duniya, bashi kaɗai ba harda sauran fasiƙan da suke aikata fasadi a bayan ƙasa, Elders din suna da yawa sune miyagun dake sadaukar da jininsu matsayin fursinoni, da yawa ma ƴa'ƴan naku azaba ce ke kashe su, cikin ka so ɗari baifi ka so goma ne ya rage daga cikin su ba...." Numfashinta ne ya fara tsaitsayawa, jini ya fara bleeding daga cikin hancinta hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Sharafudeen da Hateem ya yi ba.. Daurewa ta yi duk da azabar da ta ke ji a jikinta a haka ta cije ta ci gaba da cewa, "Na rantse da wanda raina ya ke a hannunshi duk abunda na faɗa maku ba ƙarya bane, idan baku yarda ba, gayanan agabanku ku turkeshi ya fada maku gaskiya...." Tsayawa ta yi tana haki fuskarta ta jiƙe sharkaf da gumi, ta dafe saitin zuciyarta da tafin hannunta... "Kamar yadda na faɗa maku, bashi kaɗai bane Elder, akwai muƙarrabansa da suke take masa baya, Amininsa Ifeanyichukwu inkiya Jan kunne amma a gidan kurkukun kaddara jan harshe shine nickname dinsa, shine Mataimakinsa a tare suke aikata fasadi, abun takaici sun auri junansu tun da daɗewa saboda tsantsagwaran jahilci da tumasanci...." Kutumar U! Zaro idanu suka yi kamar ƙwayar zasu faɗo ƙasa, sun shiga matsanancin tashin hankali, maganarta ta ƙara dagula masu lissafi, jin abun suke kamar wasan kwaikwayo. "Bayan haka, surukinku mijin Saratu, shine Jan kunne na gidan kurkukun ƙaddara..." Tunkan ta ƙarasa maganar hajiya Saratu ta daddafe kanta da tafukan hannayenta, ta dinga girgiza kanta, tsabar kiɗimar da ta yi ne yasa ta dinga sambatu kowace addu'a ta zo bakinta furta ta kawai ta ke yi.. Runtse idanunta ta yi ruɗu yama hana ta iya tantance me Khala take nufi, buɗe idanunta keda wuya Unexpected ta hango Pravin da ya arta a guje ya nufi sashen yan aikin gidan, aikuwa jikinta na 6ari tabi bayan shi... Khala bata dakata ba, ta ci gaba da cewa, "Sir Benjamin baturen amuruka, abokin mahaifinku wanda suka yi tashen yawon duniyarsu atare da obie da amininsa, shine jan le6e na gidan kurkukun ƙaddara, mugun fasiƙi ne....." "Bayan shi sai baƙin shaidanin da taƙadarancin sa yafi na fir'auna, zan iya cewa tun da Allah ya halicce ni ban ta6a ganin mugun bawa irinsa ba, bazan iya misalta mugayen zunubban da yake aikatawa ba, shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon giants ɗin kurkukun ƙaddara, baida imani ko misƙala zarratin, asalin shi bawan Obie ne daga baya da likafa ta ci gaba sai ya bashi muƙamin Elder...shish.. Shish..... Kasa ƙarasawa ta yi saboda abun da ya sarƙe maƙoshinta, dama ba koshin lafiya ne da ita ba, jiri ne ya kwasheta a galabaice ta yanke jiki zata faɗi, cikin sauri Sharafudden ya sungumeta ya kwantar da ita akan doguwar kujera, sai kokarin ƙarasa maganar take yi amma ta kasa... Wai shin Ina Chief Owais? bawan Allah Komai dake faruwa akan idanunsa kuma kunnuwansa na sauraro, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, zufar dake tsastsafowa ta saman fatarsa ta jiƙe jikin shi sharkaf, kwata kwata ya gaza yarda da abunda Khala ta faɗa, Gani yake kamar mafarki yake yi ba gaske bane, duk da ya gama raunana zuciyarshi ta karaya da ganin yadda baba Obie ya yi shiru bai tanka ba! Hakan na nufin da gaske ne ba kazafi aka yi masa ba tun da ya kasa kare kan shi, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'haula wala quwata illa billah, da wannan ranar ƙwara mutuwarsa, addu'o'i yake ta nanatawa acikin zuciyar shi.. Jiki a mace Sir mubarak ya zauna kan Sofa, zafi ne ya taso mashi har ta kai ga ya tu6e rigar shi ya jefar da ita ƙasa, ya ɗaura gwiwar hannunsa akan hand sofa ya zagba uban tagumi, kamar wanda ya rasa gata a duniya. "Deen! kana jin abun da nake ji kuwa? Deen Ka tsunƙule ni dan Allah inaso na tabbatar in ba mafarki nake yi ba..." Cikin raunanniyar murya His excellency Abdul Razak ya faɗa yana kallon His excellency Deen da ya haɗa uban gumi a jikin shi, girgiza kai ya yi cikin karyayyar murya ya ce, "Ba mafarki bane, kada mu yaudari kanmu! Da gaske ne komai ke faruwa, baba da muke sa ran zai kare kansa daga ƙazafin da tsohuwar nan ta yi masa ya kasa, gashi nan yana ji ya yi shiru..." Ya faɗa yana nuna Obie.. Muryar Sharafuddeen ce ta katse shi da cewa, "Abun da momma ta faɗa akansa ba ƙarya bane, ya aikata ne shiyasa ya kasa kare kansa....." "In kuwa hakan ya tabbata gaskiya ne, Baba ka kashe mana rayuwa, ka gama da mu, mun mutu, mun bani mun shiga Uku! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un......" Senate Lateef da ya ɗauko maganar bai kaita karshe ba Ya yanke jiki ya faɗi a sume, a firgice Deen da Abdul Razak suka rufa akan shi suna ambaton sunan shi haɗi da bubbuga jikin shi don ya tashi.. "Ruwa, tana buƙatar ruwa..." Hateem ne ya yi maganar, cikin sauri Sharafuddeen ya je ya dauko bottle water me sanyi yana gab da zai ƙaraso Ya lura da Owais dake a tsaye baya motsi da alama suman tsaye ya yi, wuce shi yayi ya nufi Hateem ya miƙa masa robar ruwan Ya kar6a yatsun hannunsa na kerma ya kanga ma tsohuwa Khala a baki, kusan rabin ruwan ta shanye sam ta kasa magana idanunta ma sun rufe gam bata iya buɗe su. Kar6ar robar Sharafuden ya yi daga hannun Hateem cike da rashin kuzari ya nufi su Deen Ya mika masu bayan sun yayyafa ma Senate Lateef ya farfado yana sambatu kamar mai tabin hankali har yana fadin Allah yasa mafarkine abunda ya ji. Kar6ar robar ruwan ya yi daga hannun Deen ya je gaban Owais ya daddage ya watsa mashi ruwan a saman fuskar shi, lokaci ɗaya yaja dogon numfashi ya furzar da shi da wani irin zafi. Kamar mahaukaci haka ya damƙi gaban rigar Sharafudeen hawaye na zarya akan kuncinsa da wata irin karyayyar murya ya ce,"Ka faɗa min kaima kana ɗaya daga cikinsu?" Ya fahimci ba ya acikin hayyacinshi, tsigar jikinshi duk ta tashi haiƙam zuciya ta riga da ta tsinke. Tsananin tausayin shine ya kama shi, Cikin sanyin murya ya ce, "Bana ɗaya daga cikin su Owais..." "Meyasa ka kasa kare kanka lokacin dana tambayeka?" Girgiza kanshi ya yi, "Saboda na daukarwa baba alƙawarin bazan faɗa ma kowa ba..." Katse shi ya yi, "Wani alƙawari ne ka daukar masa?" "Shine ya kira ni a waya ya faɗamin zaku je kai farmaki gurin matsafa masu haɗarin gaske, ya gargade ni akan kada in kuskura in barka ka je, nace mashi ai yafi kusa da kai kafi jin ma maganarshi, me zai hana ya yi maka magana, sai ya ce min ba ya son bacin ranka ne yasan idan ya hana ka zuwa baza ka ji daɗi ba, shiyasa ya kasa amma yasan ni idan na yi maka magana bazaka ji komai ba, kawai in baka umarnin kada ka je, nace mashi baba ban ta6a hana Owais ya je kai farmaki ba, hasalima ni nake ƙarfafa masa gwiwa akan aikinsa idan na hana sa wannan karan dole zai ji ba daɗi ne, sai ya fara min faɗa yana fadin har shi zai bani umarni in ƙi bi! Yana magana ina magana, da ni da owais din duka ba a ƙarƙashin ikon shi muke ba? Na dinga bashi haƙuri har saida na amince zan yi maka magana tukunna ya haƙura, Sannan ya ce zai turo da ɗan saƙo da maganin bacci in saka maka a cikin Coffee, saboda in kasa kafiya ka turje akan ba zaka bi umarnina ba, sai in baka kasha coffee din, kuma baya son kasan shi ya sakani, nayi masa alkawarin bazan bari ka sani ba, kaji dalilin da yasa lokacin da na kira ka a resting home dina ka ƙi bani hadin kai ni kuma na baka coffeen dana zuba maganin baccin ka sha...." Gaba ɗaya maganganun Sharafudden a cikin kunnuwansu sun ji komai, hankulansu sun ƙara tashi, cikin rawar murya Owais ya ce, "Kana nufin baba shine ya hanani kai farmaki, kuma shine ya sa ka bani maganin bacci, amma a daren ranar ina ka je saboda an faɗa min ba a gan ka ba?" Ya fada a ƙagare da son jin amsar shi.. "Owais ni ban je ko'ina ba, ina a villa, adakin mommynka na kwana zaka iya tambayarta ka ji, bayan haka sanin kowannanku ne Villa tana da tsaro, ba yadda za'a yi shugaban ƙasa ya yi fitar sirri in the midst of the night batare da wani daga cikin security ya bi shi ba, Allah shine shaida ta..." Ya fada fuskarsa a yamutse. "Hakan na nufin Baba shine ya ƙulla maka makirci saboda ya ɗaura maka laifin sa? Ko don ya shiga tsakanina da kai?" Jinjina kai Sharafudden ya yi,"Babu tantama Owais, baba shine Master planner ɗin da ke shirya maƙarƙashiya atsakaninmu, bansan meyasa ya yi hakan ba..." Cikin shesshekar kuka ya ƙarashe maganar, wata irin juwa ce ta ɗibi Chief ya yi taga taga zai kife ƙasa cikin zafin nama Sharafudeen ya janyoshi ya rungume abunsa akan kirjinshi, atare suka fashe da matsanancin kuka tamkar ransu zai fita. Haƙiƙa baba Obie ya muzanta, kunyar duniya ta kama shi, ya shiga matsananciyar damuwa, bai ta6a zaton wannan ranar zata zo ba, Wani irin azababben ƙunci da bakin ciki da takaici ne suka turnuke zuciyar shi, jin kanshi yake kamar ba mutun ba saboda tashin hankali. A zabure ya miƙe kamar mahaukaci ya juya jikinsa na 6ari zai bar wurin sai dai kafin ya kai ga tafiya Owais ya hango shi, a zuciye ya 6an6are jikinsa daga na daddynsa ya nufi baba Obie cikin zafin nama ya damƙi damtsen hannunsa ya juyo da shi suka fuskanci juna gaba da gaba, kunya ta hana baba Obie ya haɗa ido da Owais saidai ya sadda kanshi ƙasa. Cikin raunanniyar murya ya ce, "Baba kai kaɗai ne zaka share min shakku na, Ina so na ji daga bakin ka, da gaske kaine Elder na gidan kurkukun ƙaddara? Kuma kaine mutumin da ya fitar da ni daga fagen yaƙi ya jefa ni a daki uhum??" Ya faɗa cike da fargaban amsar da zai bashi, wlh ya yi fatan ace zai iya kare kansa sai dai ya kasa saboda asirinsa ya riga da ya tonu. Gaba ɗaya idanunsu na a kan fuskarshi amsar shi kawai suke jira su ji, batare da ya ɗago da idanunshi ya dube shi ba ya jinjina mashi kai alamar Eh, a lokaci ji ya yi kamar ya haƙa ƙasa ya binne kansa saboda baƙin cikin da ya ziyarci zuciyarshi, raɗaɗin da suka ji yafi na ƙunar wuta zafi..Ya Ilahi! Zuciya ce ta ɗibi Owais baisan sa'adda ya ci kwalar rigarshi ba, da hannu biyu ya damƙe shi sosai jikinshi na 6ari. Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, duk irin jarumtakar namiji hakan bai hana sun fashe da kuka ba kamar ƙananun yara, gaba ɗaya sautin koke kokensu ya cika falon, wasu suka dafe kawunansu da tafukan hannayensu saboda azabar radadin da zuciyarsu ke yi musu, wlh sun yi danasanin zuwansu duniya a lokacin, sun ji ɗaci a ransu, ranar ta zame masu mafi muni a rayuwarsu. Gaba daya suka kewaye shi suna tambayar shi don me zai yi musu haka? Meyasa ya ci amanarsu ya ha'ince su? Wannan wani irin neman duniya ne? Me yasa ya aikata musu hakan? Wlh Hankalinsu ya tashi matuƙa, duk sun fita hayyacin su, kuka kawai suke yi kamar ransu zai fita.. Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, bai ta6a danasanin irin rayuwar da ya daukarwa kansa ba irin yau, saboda Allah ya jarabce shi da masifar son ya'yan shi, Koda ya ke sadaukar da jikokin shi bai ta6a sadaukar da ya'yan shi ba. daƙyar ya iya haɗiye baƙin cikin shi, da wata irin karyayyar murya ya furta, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN!!! Na shiga Uku! wlh na daɗe ina fargaban zuwan wannan ranar, dama nasan duk mun daran daɗewa asirina zai tonu ne sai dai ban ta6a zaton zai tonu ta wannan hanyar ba! Ranar da nake jin zullumi da fargaban zuwanta, ranar da nake jiye ma kaina tsoron zuwanta, ya zan yi da rayuwana? ya zan yi da rayuwarku? Nasan na cutar da rayuwarku cuta mafi muni, na zalunce ku, na kuma zalunci kaina, Amma koma dai menene bakin alƙalami ya riga da ya bushe, na riga dana tabka babban kuskure, ban kuma san da wasu kalmomi zan roƙe ku gafara ba, banma cancanci in nemi yafiya agurinku ba, wlh na muzanta, na tozarta, na ji kunyar haɗa idanuna da ku, kaicona!...." Bai ƙarasa maganar ba ya fashe da kuka, hawaye suka wanke fuskar shi, mutumin da sun manta when last suka ga hawaye ya zuba daga cikin idanunsa saboda jarumtakarsa ashe tsantsagwaran matsafine, Yana kuka suna kuka an rasa me lallashin wani, daƙyar yake kallon fuskokinsu cike da jin nauyin abun kunyar da ya aikata musu. "Nasan na biyewa son zuciya, amma wallahi ba laifina bane, Nima gado na yi, tun kakanninmu da iyayenmu na taso acikin matsafa, shine hanyar samunmu, na yaudare ku da musulunci amma ni ba musulmi bane, arne ne ni kamar yadda ta faɗa muku, tun da na taso rayuwata bansan mai kyau da mara kyau ba haka iyayena suka tarbiyantar da ni, duk abubuwan da suka faru son zuciya ne da son ɗaukaka, buri na in tara dukiya, in ɗaukaka in zama shahararre a duniya, ƴa'ƴana ma su ɗaukaka a idon duniya, wannan dalilinne yasa gaba ɗaya kuka ɗaukaka kowannanku na nema masa duniya kuma ya same ta..." Bai ƙare maganar ba HATEEM ya katse shi ta hanyar cakumar shi cikin tsananin tashin hankali ya furta, "Baba! Baba!! baba!!!...." Idanuwansu cikin na juna a marairaice yake kallon shi.. "Meyasa ka za6i ka ciyar da mu haram? Baba duk irin ƙaunar da muke yi maka, kullum burinmu mu kare maka mutuncinka sai gashi kai ka zubar mana da namu mutuncin, ɗaukakar daka sama mana ta tashi a banza wlh! Saboda da zarar mutane sun ji abunda kake aikatawa wlh mun zama abun gudu, za'a juya mana baya ne a tsangwamemu zamu zama abun ƙyama, makiya zasu samu damar cuzguna mana, Baba ka bar mana mummunan tabon da mutane zasu dinga cin zarafin mu da shi! Haba baba! Wlh ka bamu mamaki baba, wai mahaifinmu ne yake aikata munanan zunubban nan?" Ya faɗa yana haɗiyar yawu mai tsananin ɗaci cikin mutuwar jiki ya sake shi.. Sharafudeen ya ɗaura da cewa, "Baba yanzu ina amfanin irin wannan? Wace riba ka samu baba? Ina hankalinka yake? Tayaya ka bari shaidan da zuciya suka rinjaye ka? Kamanta da wata rana zaka mutu ka koma ga Allah, baba Idan ka nema mana duniya lahirarmu fa? Ya kake so mu yi baba? Muna alfahari da kai, kaine abun tunƙahon mu, kaine silar ɗaukakarmu ashe mun yaudari kanmu baba, A yau mutuncinka ya zube acikin idanunmu baka da sauran daraja baba, wlh da wannan bakin cikin daka ƙunsa mana da kashe mu ka yi kamar yadda ka saba kashe ya'yan mutane...!" Kuka ne ya ci ƙarfinsa har ya kasa karasa maganar.. Baba Obie sai kuka yake yi babu ƙaƙƙautawa.. Senate Lateef ya ce, "Baba wace shafewar basira ce ta same ka? Ni abun da ya dauremin kai yadda har ka iya kashe mutun ka sha jinin shi, ka kuma lalata rayuwar yaran da basu ji ba basu gani ba, baba wa ya koya maka zaluncin nan? Har yanzu na gaza yarda kaine kake aikata hakan Baba, Tsawon shekara nawa kana aikata fasadi a doron ƙasa! Wallah baba da ace ka yi hakuri tun fil azal ka yi rayuwarka cikin talaucinka da sai ya fiye mana kwanciyar hankali, shi arziki da daukaka na Allah ne, sai wanda ya so yake bawa, watakil ma kana ɗaya daga cikin wadanda Allah ya tsaga da rabonsu kaine baka sani ba, ka biyewa son zuciyar ka baba, gayanan ka jefa rayuwarmu a halaka, bayan haka jin dadin duniya ƙalilan ne baba, gaba dayanmu mutuwa zamu yi, komai muka mallaka anan gidan duniya zamu barshi, lahiri itace dawwamammiya, wlh da wannan masifar daka jefa mu a ciki wlh gara ace mun taso rayuwarmu a matsayin musakai marasa gata a duniya da dai irin wannan rayuwar, baba yanzu da ka ɗaukakamu ya zaka yi da mu? sai da ka bari duniyar tasan da zamanmu ana yi mana kallon mutane masu daraja da ƙima, masu martaba a idon duniya, yanzu idan suka ji miyagun laifukan da kake aikatawa me kake tunanin zai biyo baya?" Ya jefa mashi tambayar yana kuka yana girgiza kai. kafafunsa ne suka gaza ɗaukarsa ya zube kan gwiwowinsa, idanunsa sun rune jawur, kumatunsa sun yi jajir, duk ya faffasa labbansa da haƙoransa, gemunsa ya jiƙe sharkaf da ruwan hawayensa, Ko'ina na jikinsa zufa ce take tsattsafo masa kamar babu A.c a falon. Wlh ya sadaƙas bai ta6a zaton zai ji kunyar zunubban da yake aikatawa ba sai yau da Khala ta fallasa asirin sa a gaban ya'yansa mafi soyuwa a gare shi. Dukkan ilahirin jikinsa kerma ya ke yi, ga wani irin azababben zazzabi da ya lulllu6esa, mutumin da sai ya yi shekara da shekaru bai yi ciwo ba saboda ƙoshin lafiyar dake gare shi to yau dai hada matsanancin ciwon kai, bazama a raza ciwon zuciya na farat daya ba saboda depression din da ya kama shi, gaba ɗaya suka zauna kewaye da shi kamar malami da almajiransa kuka hada majina, sun kasa tsayar da kan su. 😭 Daƙyar ya iya furta, "Idan na ce ku yi hakuri ban yi maku adalci ba, iya cutarwa na cutar da rayuwarku, ban cancanta na ci gaba da rayuwa ba, nasan a halin yanzu da kuka gano wanene ni kun tsane ni fiye da komai na duniyar nan, don haka na miƙa wuyana a gare ku, nasan na aikata maku ba dai dai ba, Ku yanke mini duk wani hukunci da kuka ga ya dace dani, ku azabtar da ni, sannan ku kashe ni, idan ba haka ba, Ni zan kashe kaina, saboda bazan iya cigaba da rayuwa da abun kunyar da na aikata muku ba..." Yana faɗa yana kuka haɗi da tari. Sama sama khala dake a kwance kan Sofa take jiyo maganganunsu, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, ta tona masa asiri burinta ya cika sai dai bata yi farin ciki ba, saboda halin da ya'yan shi suka shiga shiyasa kafin ka fara aikata wani abu mara kyau ka fara tunanin makomarka da kuma halin da zaka jefa wanda ya yarda da kai abun yana da ciwo. "Ku kashe ni, in har baku kashe ni ba mutane bazasu ƙyale ni ba, ku kashe ni kawai nafi so na mutu a hannunku, ko dan saboda ku dauki fansar abun dana aikata maku, ku kashe ni na ce, in ba haka ba zan kashe kaina..." Zumbur ya miƙe jikinshi na kerma, Lokaci daya gabansu ya fadi ganin jinin da ya wanke gaban wandon shi. Har suna haɗa baki gurin ambaton sunanshi, Allah sarki duk da abun da ya aikata hakan bai hana su ɗaga hankalinsu a kanshi ba, "Mu kai shi asibiti kada ya rasa ranshi!" Sharafuddeen ne ya yi maganar a ruɗe. Har sai da baba Obie ya dube shi da raunatattun idanunsa, ƙasa ƙasa da murya ya ce, "Duk abunda na yi maka baisa ka daina damuwa da ni ba Sharafuddeen....?" Girgiza kai ya yi, "Ku yi hakuri bazan je asibiti ba, ku barni a gida, in ma mutuwace ta riske ni a cikin ku...." Yana ƙarasa maganar ya shallake su ya juya a hanzarce ya nufi part ɗinsa, da gudu suka bi bayanshi kafin su ƙaraso tuni ya shige ɗakin ya ja ƙofa ya datseta ta yadda ba zasu iya buɗeta ba. 😭 Yanke jiki ya yi ya faɗi kan floor ya dinga birgima yana bubbuga goshinsa kan floor har saida ya fashe jini ya 6alle masa, daga waje suna juyo kururuwar azabar da yake fitarwa mai kuwar gaske kamar zai fasa dodon kunnuwansu. Da iya ƙarfinsu na karshe suka dinga bubbuga ƙofar hadi da ambaton sunan shi da karfi. Chief kamar zai 6alle ƙofar da kafaɗarsa ya dinga bangazarta duk da raɗadin da ya ke ji. "Baba ka buɗe mana ƙofa, bamu gama magana da kai ba, baba kada ka mutu kabar mu, baba dan Allah ka buɗe bamu gaji da ganin ka ba, akwai tambayoyin da baka bamu amsoshinsu ba, baba! baba!!, zamu iya yafe maka amma ka buɗe mana kofar, baba pls, baba pls, idan ka tafi ka barmu a cikin wannan mawuyacin halin daka jefa mu ya kake so mu yi da rayuwarmu! Ka taimaka mana baba, ka fitar damu baba.. " Ba irin bugun da ba su yi ma kofar ba amma ta ƙi 6allewa, a karshe da suka galabaita a gaban kofar ɗakin nashi suka zazzauna suna cigaba da yin kuka kamar masu zaman makoki. Gaba ɗaya abun da ke faruwa ƴan aikin gidan basu sani ba, saboda anyi masu iyaka da shiga falon dama ƙa'ida idan za'ayi family meeting ba'a buƙatar bare agurin shiyasa kwata kwata basu leƙo ba kuma basu ji sautin koke koken da ake yi ba, saboda akwai tazara tsakanin sashen su da main falo. _____________________PRAVIN 🥵 Tun lokacin da khala ta fara fallasa asirin su, cikin rawar jiki ya bar falon batare da sanin kowan nan su ba, bai nufi ko'ina ba sai sashen yan aikin gidan. A lokacin Hajjaty tana a ƙudundune cikin bargo har ta samu bacci ya ɗan dauke ta, kwatsam ba zato ba tsammani kamar daga sama ta ji an cakumeta, ta fasa ƙara tana kokarin kwache kanta cikin ruɗu da tashin hankali, kwata kwata batasan wanene ba saboda bargon da ya lullu6e fuskarta, a saman kafaɗarshi ya sa6e ta, tana kuka tana ihu tare da ambaton sunan pravin don ya kawo mata ɗauki, juyawar da zai yi keda wuya ya yi arba da hajiya Saratu dake shugowa ɗakin afujajan nan take gabanshi ya yanke ya faɗi ya zazzare idanunshi yana kallon ta kamar yadda take kallonshi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta.. Numfashinta na fita da hucin bacin rai ta ce,"Munafiki, Gidan ubanwa zaka kai ta eye? Yan iska maciya amana, wato Kun daɗe kuna cin amanata, yanzu da ka ga asirinka ya tonu shine ka lalla6o ka saci jiki ka shugo don ka dauki kwartuwarka don ku gudu ko?" Ta faɗa tana zare idanunta. Tsawa ya daka mata har saida ta razana, muryarsa na rawa ya ce, "Ki matsa ki bani wuri in wuce tunkafin in yi maki illah!" Cikin fusatacciyar murya ta ce, "Illah kuma ta nawa? Ka bani mamaki pravin, Ka karya min zuciyata, munafuki dama na daɗe ina zargin Hajjaty ashe tare kuke aikata fasiƙanci, wai a haka na aure ka na haifa maka ƴa'ƴa, Ka cutar da rayuwata pravin, hakkina da na ya'yanka bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba wlh, kuma na rantse babu gidan ubanda zaku je, mayaudaran banza, dole ku gurbi abun da kuka shuka..." Bata ƙarasa maganar ba, sakamakon naushin da ya sakar mata akan kuncinta, nan take gefen bakinta ya fashe ta fara bleeding, azabar zafin da ta ji ne yasa ta dafe gefen bakin, da mamaki ta furta,"Pravin! yau da hannunka ka dake ni? Inna lillahi..! " Rai a 6ace ta yi kukan kura ta haɗa su duka biyun da shi da Hajjaty ta hankaɗa su gaba ɗaya suka kife ƙasa, bargon jikin Hajjaty ya warware baiwar Allah tuni ta jima da sumewa sakamakon buguwar da kanta yayi dama ya lafiyar gwiwa. Ransa ya 6aci matuƙa, a harzuƙe ya yunƙura ya mike Ya nufi hajiya Saratu batai aune ba, ya damƙi ƙeyarta da hannunshi ya jata ta karfi ya nufi mirror tana ta kokarin ta kwace kanta sai dai ta kasa saboda raunin da zuciyarta ta yi yasa ta kasa ta6uka komai. Yana isa gaban madubin ya buga kanta jikin shi nan take madubin ya fashe, duk ya sossoke fuskarta, tuni ta fara bleeding, kukan ma ta kasa yi saboda zogin azabar da ya ratsa sassan jikin ta, ya ɗago da kan nata ya wurgar da da ita a galabaice ta kife kan floor ta mirgina numfashinta yana ta kokawar ɗaukewa. Hakan bai masa ba sai da ya take yatsun hannayen ta da tafin ƙafarsa duk ya murjesu suka faffashe jini ya soma tsastsafowa. kwata kwata babu imani a zuciyarsa, ga idanun nan nasa sun kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, Ya na huci ya furta, "Allah ya isa tsakanina da ku, Dangin matsafa masu arziƙin jini, Duk ubanku ne ya ja min shiga halin da nake a ciki, shine mugun da ya sa na jefa rayuwata cikin halaka ina zaman zamana lafiya, dama ni ban ta6a son ki ba, dukiyarki ce tasa na aureki da kuma kwaɗayin surar jikin ki, Kin daɗe kina baƙanta min rai ke ga mai arziki ɗiyar ƙaruna, ki yi ta min gorin arziƙi don ina zaune a gidan ku, to ai ga irinta nan, yanzu ai kin gane arzikin naku bana halal bane ko? Ya faɗa yana tottafa mata yawu a kan fuskarta. "Kuɗin jini ne kuke tunƙaho da su, wlh badan ƴa'yan dake tsakanina dake ba da ba abun da zai hana in huce haushina a kanki, zan bar ki da ranki ne ba don na so ba.." Ya faɗa yana kallon fuskarta da ta jiƙe sharkaf da jini kamanninta har sun sauya saboda azaba ta gama fita hayyacinta, juyawa ya yi da sauri ya nufi bargon Hajjaty ya janyo shi ya rufa mata a jikinta tare da nannaɗeta a cikin bargon ya mayar da ita kan kafaɗarsa, Ya tsallake hajiya Saratu dake a kwance rai hannun Allah cikin sauri ya fuce daga ɗakin, batare da sanin kowa ba ya gudu daga Estate ɗin......💔 ___________________________________✍️ *_(SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN AHLIN FAMILYN SUKA KARASO SUKA JI ABUN DA KE FARUWA❓GA HAJIYA SARATU AKWANCE RAI HANNUN ALLAH! WA ZAI KAI MATA DAUKI❓ YA RAYUWAR BABA OBIE ZATA KAYA ZAI KASHE KANSHI NE KO KUWA❓ ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN ELDERS SUKA JI LABARIN ASIRIN ELDER YA TONU❓YA LABARIN PRAVIN DAYA GUDU DA HAJJATY GIDAN UBAN WA ZAIJE❓ DA WANI IDO YA'YAN BABA OBIE ZASU FUSKANCI DUNIYA? KUNA TUNANIN BA ZASU FUSKANCI KALUBALE BA AKAN MUKAMAN SU❓ TAYA ZA'A HADA KOWANI PRISONERS DA IYAYENSA❓ TAYA ZA'A KAMA SAURAN ELDER❓ TO WAINI TAYAYA MA AKAI TSOHUWA KHALA TA RAYU?😳 YANZU NE LOKACIN DA ZAKU ƊAURA ƊAMARARKU TAMAU DON JIN YADDA ZATA KAYA🔥💪_* *Gani ga wane Ya ishi wane Jin tsoron Allah😭 page din nan ya taba zuciyata)* *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥🔥😭* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*~___________________________________🌹💋🫀☠️💗🔥✍️~ Ɗayan bayan ɗaya suka soma shigowa cikin main falo, twins ne a gaba daga bayan su Captain Yaseer ne sanye cikin pilot suit dinsa da bai kai ga cirewa ba, bai jima da ƙarasowa ƙasar ba, su twins ne suka je ɗauko shi a airpot. Justice Nadeem da Ziyad sun saka shi a tsakiyar su, shigar su keda wuya saiga Mommy Turai tare da Jazz sun shigo suma, fuskokinsu da fara'a, a mutunce suke gaisawa da junansu, hayaniyar hirar da suke yi ce ta cika falon yayin da suke tafiya atsanake suna tunkarar interior din sa. "Mommy Zaki bai zo bane?" Ziyad ne ya tambaya yana kallon Turai, ta ce, "Bai zo ba wlh, daddynsa ya faɗa mun sunyi waya yace bazai samu damar halarta ba saboda ayyuka da su ka yi mashi yawa, amma yace a kira shi video call idan aka fara don ya samu jin abun da za a tattauna..." Ziyad ya ce, "Na so ace ya zo wlh, munyi missing nashi, amma bakomai zamu yi magana idan an kira shi video call din.." Turai ta ce, "Ai wannan karon naga bakowa ya samu damar halarta ba, kowa ya shiga busy, wasu suna school wasu kuma aiki ne ya ruƙe su.." "Mutumina ya gajiyar aiki? Na ga ko kakin baka samu ka cire ba.." Justice ne ya faɗa yana dafa kafaɗar Yaseer, yamutsa fuska ya yi tamkar baison furta maganar ya ce, "Alhamdulillah, bana so a fara meeting din batare dani ba, bayan haka na yi missing naku sosai, bazan iya jure rashin ganin ku ba, tun da jirginmu ya yi landing nake ta zumudin in ƙaraso don inga yan uwana..." Murmushi suka saki, gaba ɗayan su sun ji dadin maganar shi. Zayn ya ce, "Muma mun yi kewarka Bro, kuma mun yi murnar ganinka..." Sumar kan Zayn ya shafa da yatsunsa da zolaya ya ce, "Nima na yi kewarku, dangin lord shiva, ay na ga yau indiyancin ne ya motsa, kun yi gayu abun ku" Dariya suka saki. Zaid Ya ce, "Aikin daddy ne, shine ya matsa mana sai mun saka kayan india..." Jazz dake sauraronsu murmushi ne dauke akan fuskar shi, yana jin dadin yadda suke fira da junan su burge shi su ke yi, ba halin ya saka musu baki saboda shakkar Captain Yaseer ya ke ji, Ya tsani bare yana da girman kai sosai, haka zalika Zayn halin shi kusan ɗaya dana Yaseer bambancin su kaɗan ne. Lokaci ɗaya suka Ci burki ganin babu kowa A falon, ko gifcin mutun babu, kallon juna suka yi..Justice ya ce,"Bangane ba! Ina mutanan gidan nan ne? Ba dai har sun kammala meeting din ba?" Ya faɗa a ɗan rude. Captain Yaseer ya ce, "In kuwa hakane basu kyauta mana ba Allah, duk saurin da na yi ace har an gama, ai dana sani ban zo ba ke nan.." Ya faɗa fuskarsa a haɗe ya ɗago da wuyan hannunsa yana duban diamond wrist watch dinsa. "Wataƙil mun makaro ne, amma ni abun da bangane ba Ina mutanan gidan ne? Babu kowa kodai sun bar gidan ne?" Zaid ne ya tambaya, Zayn ya ce, "Ko dai sun canza gurin da za a yi meeting dinne?" "Nafi tunanin haka, cos duka baifi karfe hudu da rabi ba akwai sauran time" A cewar Captain. Mommy Turai ta ce, "Gaskiya bana tunanin sun canza wurin yin meeting din, ko a wurin birthday din Owais sai da Baba Obie ya ƙara jaddada mana a nan za'a yi, kuma ina ji a raina ba'a gama meeting din ba sai dai idan wani abunne na daban..." "Bari na kira daddy na ji ina su ke ne..." Jazz ne ya faɗa tare da zaro wayarsa daga aljihu, har ya fara danna wayar kwatsam Idanunsa suka sauka akan rigar shaddar dake yashe kan floor.. Cikin sauri ya nufi rigar duk suka bi shi da ido, Ya zukunna tare da ɗaukar rigar ya kanga ta a hancinsa. Dubansu ya yi fuskarsa da ruɗu ya ce, "Rigar daddy ce, na ji ƙamshin turarensa.." Maganar da ya yi ta jefa su a a ruɗani, Turai ta ce, "Hakan na nufin yana acikin gidan nan kenan! To amma ina suka shiga? Sannan meyasa ya cire rigarsa ya bar ta akan floor"? Ta faɗa a rude, ɗan dafe kai Captain Yaseer ya yi, cike da rashin walwala ya dan ja da baya, juyawar da zai yi keda wuya idanunsa suka sauka akan dattijuwar dake a kwance kan doguwar sofa rai hannun Allah. A firgice ya daka tsalle ya ja baya yana faman zare hazel eyes dinsa, labbansa na kerma ya furta, "Wa'inna hu min sulaiman wa innahu bismillah!Kuna ganin abunda nake gani kuwa? Wacece tsohuwar nan?" Gaba ɗaya ya bi ya ruɗe yayi zaton ba mutun bace. Hankulansu a tashe suke kallon tsohuwar gaba ɗaya basu lura da ita a kan kujerar ba saboda sun bata baya shiyasa basu ganta ba, kuma Sofas din suna da yawa two sets ne. gaba ɗaya sun razana da ganin ta, basu san wacece ita ba. Ziyad ya ce, "Ko dai baƙuwa ce muka yi?" Girgiza kai Yaseer ya yi, "Bazai yiwu ba, bana tunanin mutunce, sai dai idan Aljana ce, ni hankalina bai kwanta da ita ba, jibarta fa ka ga ni.." ya faɗa yana nunata da yatsan sa dake ɗan kerma. "Duk ƙasusuwa a jikin ta, kamar mai fama da cutar ƙanjamau..." ya faɗa yana yamutsa fuskarsa.. Ta6e baki Zayn ya yi, "Na fi tunanin mutum ce, amma waya kawo mana bare a family dinmu? Bai kamata aga wannan halittar a gidan mu ba." A wulaƙance ya faɗa, kwata kwata basu damu da halin da take a ciki ba, har gwara justice da bai tanka ba shida Ziyad. Jiki a sanyaye Turai ta nufe ta duk da tana jin fargaba, zukunnawa ta yi daga gaban sofa din ta ƙura mata idanunta, tsantsar tausayinta ne ya kamata ganin jinin dake ɗan ɗiga daga hancin ta, gashi a wahalce take jan numfashi, ta fahimci bata acikin hayyacinta sai sambatu ta ke yi ƙasa ƙasa. A hankali ta shafa forehead ɗinta da tafin hannunta ganin fatar wurin ta yi tamoji tamoji ta yi duhu kamar ta ta6a ƙonewa. "Ina tunanin bata da lafiya, amma wacece ita? Wa ya kwantar da ita anan? Ta ya za'abar majinyaciya ita kaɗai batare da likitan da zai duba ta ba.." Ta faɗa cikin nuna tausayawa. Yaseer dai tsoronta Yake ji sai faman zazzare eyes ɗinsa ya ke yi. Twins ma duk sun sha jinin jikin su. "Jazz zo ka dubata pls, mu taimaka mata kada ta rasa ranta.." Matsawa Jazz ya yi gaban kujerar ya zauna saman hand sofa din, kafin Ya daura tafin hannunsa saman kan Khala a hankali ya kamo tafin hannunta ya ƙura mashi ido yana nazari akan ta, har wuyanta ya shafa. "Jazz baka da hankaline! Kasan wacece ita da zaka ta6ata, salon ka kwaso mana cuta?" Zayn ne ya faɗa da tsawa, Ko kula sa Jazz bai yi ba hankalinsa na akan Khala da tausayin ta ya fara kama shi. Ziyad ya ce, "Koma wacece ita ina ji araina mutunce ita, dole akwai wanda ya kawota gidan nan, abunda yakamata mu yi shine mu tuntu6i baba a waya muji ina suke, in ya so sai mu tambayeshi game da ita..." Ya ƙarasa maganar tare da zaro wayarsa daga aljihu ya shiga kiran layin Baba Obie. Almost 5 times tana ringing ba'a yi picking ba (rashin sani yafi dare duhu) "Wayar na shiga amma ba a ɗauka ba" ya faɗa yana dubansu. Cikin sauri Captain Yaseer Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kira layin daddynsa His excellency Abdul Razak.. Shima Almost 5 times tana ringing ba'ayi picking ba.. "Me zai hana mu je part din baba? Nasan ba su wuce can" Zaid ne ya faɗa, basu tsaya 6ata lokaci ba suka dunguma izuwa sashen baba Obie ya rage saura Turai tare da Jazz dake duba momma. Tunkan su ƙarasa suka hangosu zazzaune bakin door room din baba Obie sun raku6e jikin ƙofar, kwata kwata basu motsi sai numfashin su dake fita da ƙarfi, ga wani bugun barazana da zuciyoyin su ke yi, fuskokin su sunyi sharkaf da jirwayen hawayen su, idanun su sun kaɗa jawur sun kumbura tamkar yaji ya shiga cikin su. Wani irin faduwar gaba suka ji, lokaci ɗaya yanayinsu ya sauya zuwa tsantsar tashin hankali da fargaba, a hanzarce suka ƙarasa gabansu kusan atare suka zube kan gwiwowinsu suna fuskantar su. Cike da tashin hankali suke tambayar su meya faru da su? Meya sanya su yin kuka? Meke damun su?" Hakika sun razana da ganin halin da iyayensu suke a ciki, basu ta6a ganin rauninsu irin na wannan ranar ba, ko magana basa iya yi sai dai suka dinga bin su da raunatattun idanunsu da suka galabaita. gaba daya gumi ya wanke jikin su kamar babu iska a wurin. Magiya suka dinga yi masu akan suyi masu magana su fada musu meke faruwa amma babu alamun zasu tanka musu. Labbansu duk sun faffashe sakamakon cizon su da suka dinga yi cikin fitar hayyaci, sunyi zugudum kamar hotuna, daga wanda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, sai wanda ya langwa6e kansa jikin door room din baba Obie, Sir Mubarak ya dage sai tauna farcensa ya ke yi da hakoransa baima san yana yi ba, tsabar damuwa ne da fusatar zuciya ke addabarsa.. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku! Daddy! Uncles! Meke damunku? Meya saka ku zubar da hawayenku? Baba Ya mutu ne?" Ziyad ne ya faɗa arude tare da tallabo fuskar Senate da tafukansa yana kokarin tursasa masa don yayi maganar. "Dan Allah ku faɗa mana abunda ke faruwa? Hankalinmu ya tashi da ganin halin da kuke aciki, pls daddy ka faɗa min! Me ya jefa ku a halin da kuke aciki ? Ina baba Ya ke? Me kuke yi a kofar dakin sa, ko dai ya mutu ne?" Cikin shesshekar murya Captain Yaseer Ya fada tare da dafa kafadun daddynsa da tafukan hannayensa. "Uncles pls, kuyi mana magana, dan Allah kuce wani abu! Gaba ɗaya bakwa acikin hayyacin ku, yanayin ku ya nuna kuna acikin mawuyacin hali na damuwa, idanunku sun kumbura alamar kunsha kuka, wai meya faru ne??" Zayn ne ya fada yana rarraba idanunsa akan fuskar Hateem da Sharafudden, kusan atare suka sadda kawunansu ƙasa batare da sun tanka ma shi ba! Zaid Ya ruƙo hannayen mai girma Sharafudden acikin nashi cikin raunanniyar murya ya furta, "Mun shiga uku, pls Uncle ku yi mana magana ko hankalinmu ya kwanta, wai meke damunku ne? Gaba ɗaya kun raunata babu wani mai walwala acikin ku? Idan baba Ya mutu ne ku fada mana..." Cikin sanyin jiki Justice Ya tallabo fuskar mahaifinsa, "Dad ka yi min bayani pls, meke damunku ne huh? Meya faru? Ni ban taba ganin ku a mawuyacin hali irin na yau ba, dan Allah daddy ka fadamin kada zuciyata ta buga don bazan juri ganinku acikin wannan halin ba.." ba irin magiyar da basuyi musu ba amma shiru basu tanka musu ba." hakan ya ƙara jefasu cikin damuwa har ta kaiga sun fashe da kuka, suma ubannin nasu wani sabon kukan ne ya 6alle musu, aka rasa me lallashin wani, suna kuka suma suna kuka yayin da suke fuskantar junansu, Hakika zuciya ta karaya, tayaya zasu yi ma ƴa'ƴanasu bayanin abun da kakan su yake aikatawa? Wani hali zasu shiga idan suka ji? Ya zasuyi da rayuwar su? Yaran da basu san wani abu wai shi tashin hankali a rayuwarsu ba, tun da suka taso nasara da gatanci suka sani basu taba neman wani abu sun rasa ba, wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa mai wuyar gaske, amma duk bama wannan ba tunanin da yafi tsaya musu a ƙahon zuciya ya'yansu da suka rayu tsawon shekara da shekaru cikin uƙubar rayuwa har suka mutu basu san su wanene iyayen su ba? Ba don addu'o'in da suke ta nanatawa a cikin zukatansu ba, da tuni zuciyarsu ta daina bugawa saboda depresssion din dake barazanar yi musu illah. A lokacin baba Obie Ya daɗe da yin shiru, shiyasa suka ƙara rikicewa basu san awani hali ya ke a ciki ba yana a raye ko ya kashe kan shi! _______________________________✍️ "Jazz meke damun ta? Ko ta suma ne uhm? Mom Turai ce ta faɗa tana duban shi, yayin da ya ke tsoma mayafin khala da ya cire a cikin bucket mai ɗauke da ruwan sanyin daya ɗebo, A hankali ya ke matsa mata shi a saman kanta da wuyanta har izuwa kafafun ta. Girgiza mata kai ya yi, "Bata suma ba, but she needs medical attention, da bukatar a yi gaggawar kai ta asibiti..." Har ta buɗe baki zata yi magana kenan, Unexpected suka jiyo sautin koke koke da sallallamin da ake yi.. A sukwane suka miƙe tsaye suna duban hanyar da suke tsammanin daga nan koke koken ke fitowa kafin suyi wani motsi, ƴan aikin gidan suka shigo agurguje cike da tashin hankali suke ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Sai faman yarfa hannayensu su ke yi sautin muryoyin su ma daƙyar su ke fita saboda tashin hankalin da suke a ciki.. Har suna haɗa baki ita da Jazz gurin tambayar su meya faru? "Wayyo Allah! Inna lillahi! Aunty Saratu! Tana a ɗakin Hajjaty rai hannun Allah kwance cikin jini, dan Allah ataimaka kada ta rasa ranta, wlh bamu san meya faru da ita ba, fuskarta duk ta 6aci da raunuka.." Kaitsaye maganganun ƴan aikin suka dira acikin kunnuwan kowa dake a bangaren kasantuwar da ƙaraji suke yin maganar. Lokaci ɗaya hankulansu da ya gushe suka dawo jikin su, arude suke nanata sunan Saratu da suka jiyo a cikin kunnuwan su. Especially twins wadanda tuni sun jima da barin gurin, duk da rashin kuzarin Jikinsu hakan bai hanasu miƙewa ba gaba dayansu suka baro part din baba Obie tsabar saurin su ƙarasa har suna bangaje junan su, kafin su iso falon tuni Jazz da Turai da yan aikin sun nufi ɗakin Hajjaty aguje. Tunkan su karasa ga dakin suka soma jiyo koke kokensu, Lokacin da suka shiga dakin kusan suman tsaye suka yi, sa'ilin da idanun su suka sauka akan fuskar hajiya Saratu, Turai ce ta kwantar da kanta saman cinyoyinta sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita twins ma kukanne ya balle musu.. Cikin raunanniyar murya Hateem ya furta. "Who's she?" Ya fadi hakanne saboda bai gane fuskar wacece ba, sakamakon jinin da ya wanke fuskarta. Cikin shesshekar kuka abla tace"Aunty Saratu ce, bamusan me ya faru da ita ba, ni ce ɗazu na zo duba jikin hajjaty da bata da lafiya, ina shigowa na taras da mutun kwance a ƙasa cikin jini ga glass ya sossoke fuskar ta, wlh na yi zaton hajjaty ce amma dana duba ta dakyau sai nagane aunty Saratu ce saboda launin fatarsu ba ɗaya ba, na yi mamakin ganinta adakin hajjaty saboda bata ta6a takowa sashen yan aiki ba...." Ta karasa maganar tana matse kwallar ta, hankalinsu idan ya yi dubu toh ya tashi, abin da ya ruɗar dasu shine meya kawota dakin yar aiki? Meya faru da ita?" Wa kuma yayi mata wannan ɗanyan aikin? Saboda sun gane buga kanta aka yi a jikin mirror tun da gayanan sunga madubin ya zube ƙasa.. "Ina ita wadda ke ɗakin??" Zayn ne ya tambaya a fusace fuskarshi sharkaf da hawaye, amsa mashi suka yi da basu ganta ba. Sharafuddeen bai tsaya bata lokaci ba, ya yi hanzarin matsawa ya sanya hannayenshi biyu ya ciccibi hajiya saratu ya daura akan kafadarsa ya juya a gaggauce ya fuce daga dakin su twins dake ta kuka kamar ransu zai fita gani suke kamar hajjaty ce ta yi mata haka, dama sun tsaneta basu kaunarta, bayin Allah sai bin bayan sharafuddeen suke yi kamar jela. Sune har bakin Entry Hall, Yana fitowa da ita ya nufi Escorts dinsa dake sintiri agaban motocinsu, tunkan ya karasa ya daka musu tsawa a rude suka dube shi da hannu ya yi masu alamar su buɗe mashi mota, a hanzarce suke bude backseat na daya daga cikin motocin su, jiki na bari zayn ya fara shiga ya zauna yana ta kuka, bayan daddy Sharafudden ya shigar da ita cikin motar, zaid ya shiga suka saka ta atsakiyar su. gaba daya suka kankameta suna cigaba da kuka.' In weak Voice Prime minister Ya ce, "Twins ku daina kuka, baku ga halin da take a ciki bane? Addu'arku take bukata, kuyi hakuri In sha Allah zata ji sauƙi, kuma koma wanene yayi mata aika aikar nan zamu kama sa ne sannan ya karbi hukuncin abun da ya aikata" ya fada yayin da yake datse murfin motar, kalaman shi sun ɗan tausasa zuciyar su.. Umarni yaba escort din da zaiyi driving dinsu da ya kai su Asibitin Villa, batare da 6ata lokaci ba escort din ya shiga driver's seat ya zauna tare da yiwa motar key ya ja ta da matsakaicin gudu ya bi titin da zai fitar da shi daga estate din.. Motar su bata kaiga fita daga estate ɗin ba, sai ga Jazz ya fito kafadarsa dauke da Khala, gaba daya hankulansu suka ƙara tashi ganin ta, sam sun manta da ita saboda gushewar da hankalinsu ya yi, umarni Sharafudeen yaba wani Escort din da ya buɗe wata motar, bayan Escort din ya buɗe, Sharafudeen ya kar6i khala daga hannun Jazz, a mazaunin baya na motar ya shigar da ita cikin kulawa ya zaunar da ita tare da jingine kanta jikin seat, basu barta ita kadai ba jazz ne ya shiga cikin motar ya zauna daga gefen ta Hajiya Turai ma ta shige ta zauna cike da fargaba, Jazz ya daddafe ta a jikin shi duk da baisanta ba ya ji ajikin shi tana da alaka da baba Obie..' Akan Idonsu Motar ta fuce daga eatate din tabi bayan motar da aka dauki hajiya Saratu tare da wasu motocin na securities.. Acikin Mota Twins sai magiya suke yi ma mommynsu, akan kada ta mutu ta barsu ta taimaki rayuwarsu, Idan suka rasa ta basu san ina zasu sa ransu ba, kwata kwata bata acikin hayyacin ta, bata san ma wake akanta ba.. Kafin su karasa Villa, Mai girma Sharafudeen ya kira gimbiya malika a waya bayan tayi picking ya sanar da ita game da zuwan su Hajiya Saratu ta ce ai su har sun shirya zasu dawo nan saboda baƙin da suka yi sun tafi. Ya ce mata ba wannan ba yanzu, Su aje maganar dawowa Estate, so yake ashirya medical team din da zasu duba lafiyarsu kafin su ƙaraso, Jin wannan maganar ya ɗaga hankalin ta dama tunda suka fara wayar ta ji muryarsa kamar babu walwala, a ruɗe ta ce, "Meke damun ta ne? Ko bata lafiya ne? Amma ba ɗazu muka rabu da ita lafiya agurin celebration ba?" Bata kare maganar ba yace"Eh amma ba ita kadai bace, tana atare da yar'uwar mu, ki yi abunda na ce pls, a tabbatar an duba su yadda ya dace su, zamu yi magana anjima." badan ta so ba, muryarta da damuwa tace, "Toh shikebnan, Allah ya kawo su lafiya, ka kula min da kanka." da ga haka su ka yi sallama. Gaba dayan su suka koma falo, anan suka zauna kan carpet din da ke atsakiyar kujerun falon, bayin Allah daga wannan sai wannan, kuma ransu ya 6aci da abunda aka yiwa Saratu, sunyi mamaki suna a mawuyacin halin nan a haka aka samu wani mara imanin ya zagaya ta baya yaje ya cutar da ita, damuwarsu ta ƙara ninkuwa. Har lokacin sunƙi sanar da ya'yan nasu meya faru! Sunyi magiyar har sun gaji sunyi shiru sun zubawa sarautar Allah ido. Yan aikin gidan kuwa bayan da aka tafi da hajiya Saratu, jiki asanyaye suka koma part dinsu, suna taya juna alhinin abun da ya faru da ita, su abunda da ya daure musu kai me ya kawo hajiya Saratu dakin Hajjaty? Bayan basu jituwa ko kaɗan! Ina kuma hajjatyn take? Tayaya akai madubin dakinta ya fashe har ya sossoke fuskar Aunty saratu? Sun rasa wa zasu zarga akan lamarin nan! Sun san da wuya in Hajjaty zata iya yin hakan, Gaba ɗaya suna zargin wani mummunan abun ne ke faruwa da ahalin gidan cos sun lura ma gaba daya mutanan dake gidan babu kwanciyar hankali atare da su. Shin Ya labarin Chief Owais? Bawan Allah Tun lokacin da suka daina jiyo kururuwar da baba Obie ke yi jikin shi na 6ari ya zame jiki daga cikin su ya kewaya ta bayan part dinsa koda ya ga ɗayar kofar a kulle take, sai ya matsa daga gaban katafariyar glass window din dakin baba Obin dake a bayan, nan ma ya taras da ita a garƙame ya yi ta kokarin balle glass din cikin shesshekar kuka yake kwala masa kira yana fadin baba ka buɗe min kofa, kada ka kashe kanka baba, idan ma kana tunanin mutuwa ce mafita agare ka, to kadaina, kada ka mutu ka bar ni, in ka yi min haka baka yi min adalci ba baba..." Shiru bai amsa mashi ba, dunkule hannayensa ya yi yasa karfi yai ta dukan glass din duk ya raunata yatsunsa amma windown bata buɗe ba saboda quality dinta, dole sai idan ta ciki aka buɗe ta, ko aka yi amfani da remote control din ta, da takaici Ya ishe shi ya dinga bubbuga goshinsa jikin glass din dama akwai tsohon rauni a gurin nan take ya fama sa wani azababben ciwon 6arin kai ne ya fara addabarsa, lokaci ɗaya ya fara ganin biji-biji juwa ta ɗebesa nan take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa, bai ƙara sanin inda kan shi ya ke ba, bai mutu ba kuma bai suma ba, sai dai bai san inda kan shi ya ke ba, komai dake faruwa a cikin gidan bai sani ba haka zalika babu wanda ya yi tunanin ina ya ke saboda hankalinsu ba a kwance ya ke ba... (🥺) ___________________________________ Damuwa ce ƙarara akan fuskar Unaisah, ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, tayi jiran dawowarshi har ta fara gajiya da jiran shi, tana ta kiran layin sa baya picking. Bayin Allah har sun kammala shiryawa tun da rana da ya ce su shirya zasu yi celebration na birthday dinsa a gida, bayan tafiyar sa Aunty Ummi ta shiga da su home beauty saloon dinsu tayi masu hadadden gyaran gashi da gyaran jiki, after sallar la'asar suka yi wanka, kowaccensu ta ɗauki wanka na mutunci, Shi kadai suke jiran dawowarshi, Chefs har sun kawo masu ƙaton Cake mai hawa bakwai komai ya kammalu sai dai babu Chief babu alamarsa. Hakan ya jefa su acikin damuwa, fitowa tayi daga bedroom dinsu jikinta a sanye da fitted gown ta swiss cord lace, gown din tabi shape din jikinta kayan sunyi mata kyau sun fito da kyakkyawar surarta, tana tafiya jikinta na girgiza sautin chunky heels din kafafuwanta ya cika kunnuwansu, kwas! kwas!! Hannunta ɗaya ruke da head din kayan yayin da dayan hannun yake a ruƙe da wayar ta, idanunta na akan screen din wayar, da take pressing, light make up ne akan fuskarta. Gyaran gashin da ummi tayi mata fishtail braids ne ya ƙara fito da kyawunta, kitsone masu gwa6i guda biyu wutsiyarsu ta sauko ta gaban kirjinta har kan stomach dinta, ga wani daddan fragrance dake busowa ta jikin ta, fuskarta a yamutse ta nufi cikin falon. "Unaisah har yanzu bai ɗaga kiran ba?" Ɗagowa tayi tare da kallon ummi da tayi maganar, suna a tsaye gaban table din da aka ɗaura Cake. Ummi tana sanye da atampa Chiganvy gold riga da skirt sun kama jikin ta, tudun hips dinta ko cup aka ɗaura sai ya zauna, ta kashe daurin kallabi, Batool kuma kalar kayan Unaisah ne a jikin ta, hatta takalmansu iri ɗaya, Ummi taso ta bambanta musu hair style din amma ta nace ta ce itama irin na Unaisah take so saboda bata son Unaisah tafi ta kyau, amma fa sunyi kyau su dukan su, sun wanku kamar ya'yan Minister of finance.. Girgiza kai ta yi da damuwa ta ce, "Har yanzu bai ɗaga kiran ba, ni dai hankalina bai kwanta ba, ina ji araina kamar ba lafiya, saboda bai saba min haka ba, har message na tura mashi bai mayar min da reply ba.." tana magana tana yamutsa fuska.. Ummi ta ce, "Anya lafiya kuwa? a sanina da chief bai sa6a alkawari, amma ko ya akai shiru bai dawo ba, har an kusa fara kiran sallar magrib?" Ta tambaya da damuwa akan fuskarta, Batool duk tafi su shiga damuwa duk ta yi sukuku da ita.. "Har daddy na yiwa magana yace shima ya kira shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma bai daga ba, wlh ji nake kamar in bi shi cikin estate din.." ta faɗa tana zum6ura ƙaramin bakin ta.. Murmushi Ummi ta yi, "Allah ya huci zuciyarki gimbiyar Chief Owais, da girman kujerar ki, mu yi hakuri mu jira shi, may be kafin mu kammala sallar magrib ki ga ya dawo gidan..." Bubbuga kafafunta ta yi akan floor da dan murmushi akan fuskar ta, alamar ta ji dadin kalaman Ummi, "Haba Aunty Ummi, in har sai lokacin zai dawo ni dai bai kyauta min ba Allah.." Ta faɗa tare da goya hannayenta akan kirjin ta. "Calm down your mind his princess, nasan me kike yi mawa, wato kada kije yin alwala make up ɗinki ya goge, toh kada ki damu kina da ni, zan canza maki wani make up din ne.." ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Batool da ta yi shiru idanunta sun ciko da ƙwalla, kwata kwata hankalinta ba ya akan su. "Sis are you okay?" In a cool voice ta ce, "bana jin dadin zuciyata, ji nake kamar wani abu na faruwa da Chief din mu.." Dafa kafadarta Ummi ta yi, "Na fahimci kun damu sosai, nima na damu da shi, but pls ku kwantar da hankulanku, in sha Allah ba abunda ya faru da shi, zai dawo gida lafiya har ma mu yanka cake atare da shi, wataƙil wani uzurin ne ya ruke shi." murmushi suka ɗan saki badan hankalinsu ya kwanta ba.. A fakaice Ummi take satar kallonsu daga ƙasa har sama, ta daɗe bata ga kyawawan matasan ƴan mata irin su ba, tana yaba kyawun su sosai, Allah yayi halitta masha Allah tabarakallahu ahsanul khalikin, A ranta take fada, kamar yadda take mamakin kyawunsu suke burgeta suma haka take burgesu, burinsu suma suyi irin body dinta, especially Unaisah in dai zata kalli Aunty Ummi sai tayi fatan dama ita ke da dirinta. "Ku matso mu yi hotuna kafin ya karaso" Matsawa su ka yi gefe da gefenta suka tsaya, yayin da cake table din ke agabansu ta saita su da camera wayarta ta fara ɗaukar su zafafan hotuna style kala kala ta dinga nuna masu yadda za su yi, bayan sun gama ta nuna masu hotunan, koda suka gani ihu suka sanya suna santin su saboda kyawun da su ka yi a pics din.. "Aunty Ummi ki turamin hotunan In turama Mommy da Aunty Aneeleeh su gani.." Ta faɗa tana kallon fuskar Ummi, walwalarta ce ta dauke kamar bata taba yin dariya ba. Ta fahimci indai zata yi mata maganar Benazir ko Anila bata farin ciki, shiyasa ta kasa faɗa mata tasan tarihin rayuwarsu. "Sai dai ki ɗauki wasu hotunan keda Batool ki tura masu amma banda nawa.." ta fada fuskarta a ɗaure ba annuri.. "Meyasa Aunty Ummi?" Batool ce ta tambaya, "baku ga babu mayafi a jikina ba? Bai dace a ganni haka ba koda a hotone" Ta ƙarashe maganar tare da miƙewa ta juya ta nufi Up, bin ta da kallo Unaisah tayi harta hau kan stairs ta ɗan dakata da yin tafiyar, ta rasa meyasa take ji aranta kamar sakacin su Benazir ne ya ja ta rasa babynta, Zuciyarta ce ke tunzurata akan manufarta shiyasa ko sun kira bata ɗaga kiran su, saƙonnin da suka tura mata sun kai ɗari amman ko ɗaya bata buɗe ba balle tasan me suka rubuta a ciki, Shureim ne kaɗai idan ya yi mata sako take dubawa saboda har yanzu akwai ƙaunarsa a cikin zuciyarta. Har bayan sallar Isha'i ba Chief ba labarin sa, hankalinsu ya tashi matuƙa, saboda damuwar rashin dawowar shi da tayi masu katutu acikin zuciya, hakan yasa bacci ya ƙauracewa idanunsu, hankalinsu ya ƙi kwanciya, gani suke kamar wani abunne ke faruwa da shi, a falo suka raba dare gaba ɗayan su harda Taj, ko cake din da aka kawo masu basu ci ba. Lokacin da bacci ya fara cin karfin su, Ummi da Batool har sun fara gyangyaɗi, Unaisah dai ba alamun bacci atattare da ita, ta kasa ta tsare sai Chief ya dawo. "Ummi ku tashi kuje ku kwanta, dare yayi sosai" Taj ne ya fada yana duban su.. Sun langwa6e kansu jikin Sofa, girgiza kai Ummi ta yi, "Bana tunanin zan iya runtsawa in har Chief bai dawo ba, wlh na damu Boss, ace ko waya baya picking?" Ta faɗa fuskarta a yamutse. Da damuwa akan fuskarshi ya ce, "Ku yi hakuri kuje ku kwanta, in sha Allah ba abun da zai faru da shi, bafa wata uwa duniya ya tafi ba, yana agidan grandpa dinsa dake a cikin estate din nan, may be yan uwansa ne suka ruƙe shi, amma nasan in sha Allah da asuba zai dawo nan din.." "Amma in har lafiya, meyasa munata kiran sa baya picking? bayan shi da kan shi yace mu shirya idan ya dawo zamuyi celebration a gida.." "At least in ma bazai dawo ba, yakamata ya kira a waya ya faɗa mana.." "Ummi, kuyi masa uziri, Allah kadai yasan me ya tsayar da shi, a sanina da Chief bai cika mantuwa ba, mutunne mai son cika alkawari, sai dai bansan meyasa bai dawo ba, kuma bansan abinda ya hana shi kiran mu ba, amma mu yi hakuri mu jira zuwa gobe.." Ummi ta ce, "Ni ba rashin dawowar shi bane ya ɗaga min hankalina, kawai muna so muji in yana lafiya sai hankalin mu ya kwanta.." Dakyar Taj ya samu ya lallashe su har suka hakura da jiran na shi kowa ya nufi bedroom dinsa don ya kwanta. ~______________________________~ ELDERS🔥 Duhu ne ya mamaye ko'ina, ba zaka iya ganin komai dake a kewayen wurin ba. Yayin da yake a tsaye cikin shiga ta doguwar riga baƙa ta sauka har ƙasan kafafunsa dake a sanye cikin bakaken takalma na fata, Ya lullu6e sumar kansa da hular rigar tasa, baka iya ganin komai na jikinsa in ba ƙwayar idanunsa ba, hatta fuskarsa a lullu6e take da baƙin takunkumi, yayin da ya ruƙe sandar sa a hannun shi na dama. Tun daga yanayin tsayuwarsa zaka fahimci babu ƙoshin lafiya atare da shi, akwai rauni da karayar zuciya atattare da shi.. Unexpected hasken wutar candles dake a kewayen wurin ya soma kunna kansa, hakan ya bani damar ganin sauran bil'adaman dake a cikin katafaren ɗakin, har saida na firgita da ganin wasu irin dogayen mutane masu ƙirar ƙarfi a jikin su, gaba dayansu suna a zaune kan armchairs din dake a kewaye da shi. Shigar jikinsu bata da bambanci da tashi, bakaken dogayen riguna ne a jikinsu, sun rufe kansu da hulunan rigunan, kowannansu yana a ruke da sandar shi ta alfarma, gaba daya sun sadda kansu ƙasa. Hankalinsu ya dugunzuma ainun, basu ta6a shiga mawuyacin hali na farga irin wannan ranar ba, tun da Elder ya fada musu abun da ya faru da shi hankulansu sun tashi matuƙa, wlh sun kaɗu da jin asirin Elder ya tonu, dole su razana saboda basu taba tsammanin asirin shi zai tonu cikin sauƙi ba, shi da yake shugaban su, ina ga su na ƙasa da shi. Abun da ya daure musu kai ta yadda har sihirin shi yaƙi tasiri a lokacin da khala take tona mishi asiri, bayan haka sun yi mamakin tabya akai ta rayu bayan Elder ya tabbatar musu da mutuwar ta❓ A ƙalla Elders din dake a dakin sun kai su goma sha ɗaya, gaba daya sun tattara nutsuwarsu sun mayar da hankulansu akan Elder da ke kora musu jawabi cikin harshen su na matsafa.. "Haƙiƙa yau na ji kunyar da ban ta6a jin taba a rayuwata, nasan da zuwan wannan ranar amma ban ta6a zaton zata yi silar da zan ji danasani atare da ni ba, hankalina ya tashi, zuciyata ta karaya, fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata, bawai don asirina ya tonu ba, sai don halin da na jefa rayuwar ya'yana da suka aminta da ni, nine silar ɗaukakarsu, nine ƙashin bayansu kuma jigo sannan jagora na rayuwar su, kuma nine abu mafi soyuwa agare su, kamar yadda nima na ɗauke su dangina, bugun zuciyata, sune nake gani in ji dadi a raina, sune farin cikina kuma jin dadin rayuwana, amma a yau da asirina ya tonu a gaban idanunsu, na muzanta na ji kunyar da banta6a jin ta ba a rayuwana, na karaya da ganin yadda suke kukan bakin ciki saboda zaluncin dana aikata ma ya'yan su da kuma ha'intar su da na yi a matsayina na uba a gare su, na cuce su na cuci kaina, na kuma cuci ya'yan su dana sadaukar......." Tun da Elder ya fara maganar sauran Elders din suka kafe shi da idanunsu da suka cika da tsantsar al'ajabi da rudanin maganarsa, gani suke kamar mafarki ne ba gaske ba, jin maganganun da suke fitowa daga bakin shi, asanin su da Elder mutunne mai taurin zuciya, bai ta6a karaya ba, kuma bai ta6a danasanin abunda ya ke aikatawa ba sai yau? Abun ya ɗaure musu kai tamau har sun fara kokwanton anya Elder din su ne? Ko dai musayarsa aka yi musu? Taya ya karaya cikin sauki ya ajiye makaman yaƙinsa?" Gaba daya sun ruɗe matuƙa. "Harshe na bazai iya misalta muku irin kuncin da na ji a cikin zuciyata ba, naji bakin ciki da takaici mara misaltuwa, na ji radadin da yafi na ƙunar wuta zafi acikin zuciyata, nayi fatan ace na mutu kafin zuwan wannan baƙar ranar" Ya faɗa cikin raunanniyar muryarsa, a hankali ya dafe saitin zuciyar shi da tafin hannunsa. Kafin ya ɗaura da cewa, "Jikana dana fi kauna yau da kansa ya shaƙi wuyan rigata kamar zai doke ni, mutuncina ya zube a idanunsu, na yi musu mummunan tabon da har bayan ransu bazai ta6a goguwa ba, na yi zaton tsafina da dukiyata zasu sama min komai na duniyar nan, ban ta6a zaton akwai ranar da tsafina bazai amfane ni ba, a yau na raina karfin sirihina saboda na gane cewa shima tsafin ba gaskiya bane yaudarar kaine, akwai wanda yake da iko da masu tsafin da shi kanshi tsafin wanda idan ya so cikin daƙiƙa zai kar6e sihirin daga gare mu, kamar yadda dangina suka mutu a fagen fama, lokacin da maƙiya suka kawo mana farmakin bazata, mu tsafi gare mu sukuma basu da wannan tsafin amma a haka suka ci galaba akan dangina suka kashe kowa baifi mu shida muka rage ba a lokacin, In har tsafi bazai hana matsafi fuskantar mummunar kaddara ba, kuma bazai hana matsafi mutuwa ba, me hakan ke nufi....."? Ya karashe maganar cikin raunanniyar murya yana duban Elders din dake sauraron shi ..❗ "Bamu gane abunda kake nufi ba Elder! Kalaman ka suna nema su rikita tunaninmu, mun rasa gane ina ka dosa! maganganunka sun jefa mu a ruɗani..." Jan le6e ne ya yi maganar.. "Ka gafarce ni Elder, amma na yi mamakin yadda kayi saurin karaya saboda kawai asirinka ya tonu a gaban ya'yanka? Kada ka bamu kunya mana, Faduwa ba taka bace Elder! Ba'asan Elder da rauni ba, kuma ba'a san su da saurin karaya ba, a sanin mu da kai jarumin namiji ne, wanda ba'a halicci zuciyarsa da imani ko tausayi ba, kaine kake ƙarfafa mana gwiwa akan karmu kuskura mu bari zuciyar mu tayi raunin da zamu ji tausayin wani ko mu karaya.." A cewar Jan Ido... Da kakkausar murya Jan Wuya ya ce, "Ni kuma baka ta6a bani kunya irin na yau ba Elder! Ina hankalinka da tunaninka suke? Ina dakakkar zuciyar ka take? Ina izzarka da zaluncinka suke! Kaine fa dodon dake tsoratar da wasu Yau kuma kaida kanka ka tsorata saboda asirin ka ya tonu a gaban ya'yanka uhum?" Ya fada rai a 6ace, "kada ka bari son ya'ya ya rufe maka ido har ka yi abin da zaka yi danasani Elder! Idan ma kana tunanin ajiye kambun zalunci ka ne to ka daina! Saboda ka riga da ka makaro Elder! Tubanka bazai kar6u ba Elder saboda tarin ɗumbun zunuban da ka aikata, Koda ka shiryu hukuma da al'ummar duniya bazasu kyale ka ba, mutuncin nan naka da ƙimarka zasu ruguje za'a cigaba da tsangwamarka kaida ahalinka har sai baƙin ciki ya yi silar barin ku duniya, ka tuna kana da maƙiya kaida ya'yan ka, me kake tunanin zai biyo baya idan suka ji abunda ka aikata? Zasu yi amfani da wannan damar ne gurin cuzguna muku!" Ya faɗa da kakkausar murya hadi da dunƙule yatsunsa, "Kuma idan hukuma ta damƙe ka sai ka yi danasanin zuwanka duniya saboda azabtarwar da zasu yi maka, bayan haka idan mutuncin ka ya zube, zaka tashi daga dattijon arziki ka koma ƙasƙantacce, mugu, kuma tantirin ɗan ta'adda a idon jama'a, za'a cigaba da aibata ka ne..." Ya faɗa yana sakin dariyar shaƙiyanci da alama shi ko a jikin shi bai damu da halin da Elder ya ke a ciki ba, shiru Elder ya yi bai tanka masa ba, hakan ya bashi damar cigaba da yin maganarsa, "Yanzu ya rage naka Elder, ka zauna kayi tunani kafin ka yanke shawara, har yanzu muna da damar da zamu farfaɗo da gidan kurkukun ƙaddara, ka kashe kowa naka da ya san sirrinka, mu cika sharuɗɗan allon tsafin mu, a ganina ba dole saida Iyalanka zaka cigaba da rayuwa ba, kabar kowa naka, mu canza sheƙa...." "Aminina, ni ina ganin mu ɗauki shawarar Jan Wuya, ita kaɗai ce mafitar dake gare mu, Ba zan so ɗaya daga cikin abunda ya faɗa ya faru da mu ba, ina jiye mana tsoron kalubalen da zamu fuskanta, ni bazan baka shawarar ka kashe ya'yanka ba, amma mu yi nesa da duniyar mutane, inda babu wani mahalukin da ya isa ya tunkare mu koda ba zamu cigaba da yin tsafin ba.." Jan Harshe ne ya yi maganar cikin tausasa murya... "Har yanzu baku fahimce ni ba, Na lura wasu daga cikin ku basu damu da halin da nake a ciki ba..." ya faɗa yana jan numfashi gami da furzar da shi.. "Ba haka bane Elder, Mun fahimce ka, sai dai mu ba zamu miƙa wuya ba, koda kai zaka yi murabus daga kan muƙamin ka na Elder, Mu muna akan bakanmu, tsafi da rainon yara yanzu muka fara, babu wani mahalukin daya isa yasa mu ajiye makaman yakin mu..." Wani Elder ne daga cikin su yayi maganar.. Jan Ido ya ce,"Fatan mu shine, ko da ka ji ka gani kana son yin murabus, Ka rufa mana asiri tun da mu bata kaiga faɗin sunayen mu, ko a cikin Elders ba kowa ta sani ba! na gidan kurkukun ƙaddara kaɗai ne ta sani, don haka muna rokanka alfarma ta ƙarshe, a matsayinka na shugabanmu wanda ya yi silar ɗaukakarmu, kuma ƙashin bayan Elders na gidan kurkukun ƙaddara, wanda har abada ba zamu manta da kai ba, saboda kayi mana halaccin da har abada ba zamu iya biyanka ba, mu a wurinmu ka fiye mana kowa na duniyar nan, bauta maka ne kaɗai bamu yi ba, amma ka cancanta har bautar ma mu yi maka..." Elder din da ya ɗauko maganar bai kaiga dire ta ba, sakamakon buga sandar da Elder ya yi da ƙarfi akan floor, tuni kowannansu yasha jinin jikin shi, magana yake son yi saidai ya kasa furta ta saboda raunin da zuciyar shi ta yi.. Daƙyar ya tattara ƙwarin gwiwarsa ya ƙarfafa zuciyar shi gurin furta, "Ni bazan ɗauki huɗubar ku ba, na riga da na gane kuskure na, na yi danasani kuma zan miƙa wuya a gare su, saboda inason su dauki fansar abunda na aikata ma ya'yan su, wataƙil ta silar hakan su yafe mini, kuma a shirye nake da in fuskanci ƙalubale in dai akan su ne..." Ya ɗan dakata yana jan numfashi kafin ya ɗaura da cewa, " Kuma ina baku umarni! tun wuri ku ajiye makaman yaƙin ku, zaku iya guduwa ku nemi mafaka don ku kare kanku, amma kada ku cigaba da aikata miyagun ayyukan da kuke yi, yakamata ku dauki darasi a kaina, kuna gani dai sihirina bai amfane ni da komai ba...." Bai ƙare maganar ba, Jan Wuya ya katse shi abun da bai ta6a yi masa ba, yana huci ya ce, "Ya isah haka Elder! Yakamata ka san mi zaka faɗi! Bai kamata kana tursasa mana akan mu bi ra'ayin ka ba, bayan kaine ka janyo mu cikin harkar, ka lasa mana zuma a baki, don haka mu ba zamu fasa ba, ba gudu ba ja da baya, kawai abunda muke so kayi mana shine karka kuskura ka tona mana asiri, tun da mu asirinmu a rufe ya ke, bata fallasa mu ba, kai tun da ka ji zaka iya haƙura saboda zuciyarka ta mutu akan son ya'yanka to ka je ka mika wuya, wanda ya ƙi ji ba zai ki gani ba....!" Bai karasa maganar ba, Elders suka dakatar da shi ta hanyar daka mashi tsawa, yana huci ya ja baki yayi shiru badan ya so ba.. Cikin fusatacciyar murya Jan Harshe ya ce, "Ka fara wuce gona da iri Jan Wuya! Ka iya bakin ka! in ba so kake in canza maka kamanni a gurin nan ba, tun kan aje ko'ina har ka fara yi mashi magana da tsawa! Wanene kai? Bana tunanin ko darajar takalman ƙafarsa ka kai, kai din ba bawansa bane da ya ɗaukaka ya baka muƙami? Zaka iya biyansa abunda ya yi maka ne?" Ya faɗa a tsawace yana kallonshi, Maganar Jan Harshe ta ƙona masa rai, Zuciyarsa ta zo wuya, har wani gurnani yake fitarwa saboda 6acin rai.. "Koda Elder ya aje muƙaminsa hakan ba yana nufin ya zama abun wulaƙantawa a gurin mu ba, har abada shine Elder na kurkukun ƙaddara, da izininsa komai ke faruwa, idan ya so cikin daƙiƙa zai ƙwace sihirin dake a jikin kowannanku! Ya kamata ku san da wannan, gargadi ne na yi maku, idan ma akwai wanda ke da wani mummunan kudiri a cikin ku...." Ya fada yana nuna su da sandar hannunsa. Gaba daya suka sha jinin jikinsu hatta Jan wuya da yake ta tada jijiyoyin wuya saida ya sha jinin jikin shi saboda baida wani ƙarfi in har Elder ya kwace sihirin jikin sa, dama da shi ya ke taƙama, lokaci ɗaya suka sauko daga kan kujerunsu suka zube kan gwiwowinsu, kamar zasu yi mashi sujjada ƙiris ya rage goshinansu su ta6a ƙasa... Atare suka hada baki gurin furta, "dodon tsafi ya huci zuciyarka Elder, a gafarce mu Elder, tuba muke Elder, kanmu bisa wuyan mu, zamu yi biyayya agare ka, ka rufa mana asiri kada ka rabamu da sihirin da ke a jikin mu" Mutum ɗaya ne bai zuƙunna ba a cikin su, Miƙewa ya yi daga kan kujararsa ya nufi Elder da ya sadda kanshi ƙasa, hannunshi da ya ruƙe sandar shi da ita sai kerma yake yi.. Dafa kafaɗunsa Jan Harshe ya yi da tafukansa, tun kafin ya yi magana Elder ya riga shi cewa, "Kada ka ce min komai, ka barni kawai, bazan canza ra'ayina ba, zan bar maka komai har muƙamina, amma ni bazan bar ƴa'ƴana ba, dame za su ji idan na gudu? Ya faɗa cikin rawar murya.... "Rashin ganina zai ƙara jefa su cikin mawuyacin hali, ni dai koda zasu tsane ni ne na ƙwammace in zauna atare da su..." Kasa ƙarasa maganar ya yi saboda kukan da ya sarƙe makoshin shi.." Cikin raunaniyar murya Jan Harshe ya ce, "Bazan misalta maka tashin hankalin dana shiga ba, naji kwatankwacin raɗaɗin da ka ji acikin zuciyarka, kamar yadda kayi danasani nima na yi danasani aminina, kuskure ne mun riga da mun tabka shi!" Ya fada cike da takaici.... "Amma na ɗaurawa kaina alhakin kowani laifi da ka aikata saboda nine sila, lokacin da ka ƙyamaci abun a zuciyarka, ka nuna cewa ba dole saida tsafi zamu cimma burinmu ba, akwai wasu sana'o'in da zamu iya yi, ni ne na tunzuraka da cewa ba zamu ta6a samun abunda muke so ta cikin sauƙi ba sai ta wannan hanyar, kuma gadonka ne da iyayenka suka bar maka, bai kamata ka yi watsi da shi ba, a lokacin na matsa maka har saida ka dauki shawarata ka haƙa sihirin ka maida shi a jikin ka, wanda nayi imanin da ace babu Evils a jikinka ba zaka ta6a iya kashe rai ba...." Kifa kan shi ya yi akan kafaɗar amininsa sosai ya fashe da kuka mai tsuma zuciya.. Hakan ba ƙaramin ɗaga hankulan Elders ya yi ba, jin kukan Elder, tun da suke da shi ba su taba ganin ko da ɗigo na hawayen shi ba, tabbas sun razana sosai, faɗuwar gaba ta darsu a zukatansu.. "Ka yi hakuri na cutar da rayuwarka, na jefa ka a tsaka mai wuya, amma ka jure ka dauki shawarar Jan wuya, mu yi nesa da duniyar mutane, saboda ina jiye mana tsoron azabtarwar da zamu fuskanta agurin hukuma da kuma tozartar da zamu yi a idon duniya, in ya so idan muka gudu sai mu bar harkar tsafin mu tuba..." A hankali ya ɗago da kanshi, idanunshi sun kaɗa jawur hawaye wasu na bin wasu akan kuncinsa. Cikin shesshekar kuka ya ce, "Babu inda zan tafi, wannan karon, babu wanda ya isa yasa in canza ra'ayina, na riga da na yanke ma kaina hukuncin da na ga ya dace dani, zan miƙa wuya, kuma zan tuba, zan kuma kar6i kowani hukunci da za'a yanke min..." Gaba ɗaya Elders din dake a dakin suka hau yi mashi magiya wasu jahilan cikin su har sujjada suke yi mashi duk don ya ji ƙan su ya canza ra'ayin shi.. "Dama kun daina wahalar da kanku.." ya faɗa yana girgiza kansa. Cike da sanyin jiki Jan Harshe ya rungumeshi sosai kamar zasu koma mutun ɗaya, cikin karyayyar murya ya ce, "Koda kowa zai juya maka baya a cikin Elders, ka sani kana da ni, alƙawari ne muka daukarwa kanmu tun yarintar mu, duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, a kowane hali na rayuwa, don haka nima na ajiye makaman yaƙi na, ra'ayinka shine nawa, ba gudu ba ja da baya, zamu miƙa wuya a tare, kuma zamu kar6i hukuncin da za'a yanke mana, a tare zamu girbi abunda muka shuka." Ya faɗa jikinshi na kerma. "Ka faɗa musu ba sai sun sha wahalar nemana ba, zan kawo kaina har abujan, cikin estate dinka, saboda in sauƙaƙa musu..." Cikin shesshekar kuka ya ce, "A'a bazai yiwu ba, bazan jure ganinka cikin mawuyacin hali ba, ka bi sauran Elders din ku nemi mafaka, na yi maku alkawarin bazan tona muku asiri ba, koda za'a azabtar dani ne akan in fada, shi kaɗai ne gatan da zanyi muku na karshe, kamar yadda kowan nan ku ya sani dokar kurkukun kaddara ne kuma alkawari ne muka daukarwa junanmu wani bazai tona asirin wani ba, don haka ni ma bazan tona asirinku ba, amma ku sani idan har wani daga cikin ku ya yi gigin cin amanata, wallahi! na rantse da izzar mulkina baza ku sha ba, zanyi maku abunda baku ta6a zato ba.." ya faɗa da kakkausar muryarsa mai firgitarwa. Har saida Elders din suka razana da jin maganar shi... Ƙara ƙanƙame shi Jan Harshe ya yi, "Kaima kasan abu ne da bazai ta6a yiwu ba, ni bazan barka ba, ka so kanka da yawa, idan na barka kai kadai a cikin kuncin rayuwa ban yi maka adalci ba, kamar yadda bazaka sauya ra'ayinka ba, nima bazan ta6a canza nawa ra'ayin ba, ba inda zan je Obinna, ƙafarka ƙafata, har mutuwarmu..." Ya faɗa yana ƙara jaddada mashi... "Tun da har kun yarda zaku miƙa wuya, me zai hana ku bamu sihirin dake a tare da ku? In ya so sai mu ƙara da namu, in har dagaske kun tuba to kamata yayi ku bar komai da ya shafi tsafi..." Jan Wuya ne ya yi maganar, sauran Elders ɗin suka goyi bayansa akan su basu sihirinsu, nan take suka fahimci basu damu da halin da suke a ciki ba, tun da gashi har sun fito da haɗamarsu a fili, wato muƙaman su suke so su basu don su samu damar cigaba da aikata fasadi...💔 Babu wanda ya tanka musu a tsakanin Elder da Jan Harshe sarai sun ji me suka ce a cikin kunnuwansu. lokaci ɗaya wani hayaƙi mai kama da guguwa ya karaɗe dakin da suke a ciki, kafin wani lokaci kowannansu ya 6ace, dama ba a guri ɗaya suke ba, dabarun sihiri ne da suke kira magician's dream, a mafarki suke haɗuwa da tsakar dare su yi magana da junansu, kowani Elder dake a kasashen ƙetare dana gida Nigeria in har suka yi mafarkin nan to kowannansu zai bayyana ne a cikin sa..🔥✍️ Dare mahutar bawa, sai dai bakowani rai bane yake samun damar da zai huta a cikin sa, haka ta ke a bangaren Obie family, bayin Allahn nan Yadda suka ga rana haka suka ga dare, babu wanda ya runtsa daga su har ya'yansu, a zaune suka kwana saboda depression din da ya yi musu katutu a zuciya... _______________________________🔥✍️ *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*~___________________________________🌹💋🫀☠️💗🔥✍️~ A washe garin ranar, ba zato ba tsammani Sheikh Imam malik yayi musu zuwan bazata, batare da wani daga cikin su ya gayyace shi ba. Babu wanda yasan da batun zuwanshi saboda bai sanarma kowa ba. tun jiya da yaje masallaci yin sallar Magrib bai ga kowa na family din Obie ya halarci sallar ba. kuma a sanin da yayi musu basu da wani masallaci da sukeyin sallah in ba masallacin shi ba, tun nan abun ya fara da mun shi, ya yi ta tunanin anya lafiya, mutanan da duk in lokacin sallah yayi sune zaka gani a sahun farko. Zuciya da saƙe saƙe har ya fara tunanin ko dai sun canza masallaci ne? lokacin da aka kira sallar isha'i mutane sunata taruwa domin yin sallah yaita baza idanu cike da sa ran ko zai ga gifcin su sai dai har aka ƙare sallar babu su babu alamarsu, abun ya dame shi matuka, ba shi kadai ya lura ba, har jama'ar dake yin sallah a masallacin saida sukayi ta tambayar ina ahlin Obie? Meyasa basu zo masallaci ba? kodai ba lafiya ne"? Wadanda suke zumunci da dattijon arziki har jaraba kiran layin shi sukayi bai daga ba, suka kira layin ya'yansa ba wanda yayi picking, haka shima sheikah imam ba irin kiran da bai yi ma baba Obie ba awaya amma baya shiga kwata kwata. sai da takaiga ya kira ya'yan shi dukansu babu wanda wayarsa ke shiga, Hakan Ya kara jefa shi a hali na damuwa, daren jiya dakyar ya runtsa saboda tunaninsu da yayi mashi katutu a cikin zuciyar shi. lokacin sallar asuba nayi bayan ya farka daga bacci, yayi shirin zuwa masallaci cike da sa ran zaiga ahlin Obie sun halarta. bayan ya isa masallacin ya yi ta sa ran ganinsu har masallata suka kammala hallara ya tada sallah, bayan ya gama sallar, yayi nasihar daya saba yi abayan kowace sallar asuba, anan ne mutane sukai ta tambayarshi meye hana Ahlin Obie halartar masallaci tun jiya? Ko an kira su awaya ba'a samu, ko dai sun canza masallacin da suke yin sallah ne ko sun yi tafiya ne "? abun daya sa suke tambayarshi Imam saboda sun san yafi su kusancin da baba Obie, cike da damuwa yace musu baida masaniyar akan abunda ya hanasu zuwa masallaci amma in sha Allah zaije Estate din ya dubo a wani hali suke a ciki, gaba daya sunji dadin maganar shi, har suka ce idan ya isa, komai ake ciki kada ya manta ya kira ya sanar da su ko hankalinsu zai kwanta, Yace musu in sha Allah zasu ji daga gare shi. Ko masaukinsa bai wuce ba, daga masallaci Ya shiga motarshi yana driving yana tunanin su, kaitsaye Ya nufi Obie Estate.. 💔 Tun da Motarshi ta shigo estate din Ya tsinci kanshi da jin matsanancin faduwar gaba da bai taba jin irin ta ba. Da sunan Allah abakinsa, ya tsayar da motar a parking space yana fitowa securities dake zarka suka dinga gaishe da shi cikin girmamawa, fuskarsa da fara'a yake amsa masu kafin yayi hanzarin wuce hannunsa ruke da cazbaharsa Ya nufi Katafaren falon gidan bai kaiga shiga ba, ya tsaya daga bakin kofar yayi sallama, shiru ba'a amsa mashi ba, kusan sau bakwai yana doka sallama shiru kamar yayi magana da bango, lamarin Ya daure mashi kai, da har zai tafi sai kuma Ya fasa saboda baya jin zai iya tafiya batare dayasan awani hali suke a ciki ba.. Da zuciya ɗaya ya kutsa kai cikin falon, Yana shiga yaci burki yana kallon abun da yayi matuƙar daure masa kai aransa ya furta dama suna nan, ina tayi musu sallama basu amsa min ba"? Wlh tun daga yanayin da ya riske su ya fahimci babu lafiya atare da su, akace labarin zuciya a tambayi fuska, karasa shiga ciki yayi, kwata kwata basu san da zaman shi a falon ba, babu alamun sunji motsin tafiyar shi, yadda kasan gangar jikinsu ce kadai zazzaune kan Sofa, ruhinsu baya atare da su, damuwa ta ƙara gusar da hankalin su, saboda rashin baccin da basuyi ba jiya, idanunsu sun kara kumbura, sunyi jawur kamar garwashin wuta, gaba ɗayan su babu riguna a jikinsu sai gajerun wandunan da suka bari.. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un...." Shiekh iman ne Ya furta Yana lekan fuskokinsu, ya razana da ganin Halin da suke a ciki, har yatsunsa ya fifita saitin fuskokin su don yaga ko akwai rai a jikin su amma babu alamun zasu kyafta idanun su, Ya rasa gane suma sukayi ko kuwa wani abunne? Amma fa hankalinsa Ya dungunzuma ainin. "Hateem! Sharafudeen! " ya fada yana kallon faces dinsu, kamar hotuna, saboda rudu Ya kasa gane suna numfashi ko basayi, juyawa yayi kan sauran"Abdul Razak! Deeni! Wai baku ji ina magana? Meke damunku ne? Meya faru daku? Kuna acikin hayyacin ku kuwa eye"? Juyawa yayi kan Sir mubarak arude Yace"Mubarak! Wai dan Allah meke damunkune uhum? Mayesa bakwa motsi? Suma ku ka yi ne ko kuwa wani abunne ya faru da ku.." fuskarsa ya mutse da damuwa bai ƙare maganar ba, ya tsinkayi muryar mutun abayansa Yana karanta addu'ar tashi daga bacci. a hanzarce ya juya dan ganin wanene! Wani faduwar gaba yaji ganin wasu daga cikin matasan familyn kwance akan floor suna bacci, kamar marasa galihu, hankalinsa ya kara tashi matuka. a hankali Ya mike zaune yana miƙa hadi da yin hamma, Cikin sauri Imam Ya nufe shi cike da sa ran zai samu amsar tambayarsa agurin sa.. Zukunnawa yayi agabansa cikin rawar murya yace"Nadeem, meke damun iyayenku ne? Meke faru wa da ku ne"? "Gaba daya na rude hankalina ya tashi, kamar babu lafiya atare da ku.." ya kare maganar cike da sa ran zai samu amsoshin tambayoyin shi agurin Justice. yamutsa fuskarsa yayi cike da damuwa ya fayyace masa halin da suka risƙe su a jiya. tamkar zai fashe da kuka ya kara da cewa"shiekh ka taimaka mana, mun rasa gane kansu, ba mu san meke damun su ba, babu magana sai kuka, jiya daga mu har su babu wanda ya runtsa, ko ruwa bai gifta makoshin mu ba, bayan haka bamu ga baba ba, Kofar dakinsa a kulle take, ko da muka same su abakin kofar dakinsa, munyi tsammanin ya mutune, saboda mawuyacin halin da muka taras da su yafi kama dana wanda ya rasa abu mafi soyuwa agare shi, amma koda muka tambaye su ya mutune basu tanka mana ba, ko magana basa iyayi..." araunace ya karasa maganar, ta ko'ina kan shiekh imam ya kulle ya ce"dama sun taba yin irin hakan"? Arude justice ya dubi Uncles din nashi, don kwata kwata bai san abun ya munana har haka ba, har kwara jiya sun motsa lokacin da yan aiki suka fara koken abun daya faru da Saratu... Girgiza kai Justice yayi"ban taba ganin sunyi ba, amma ina tunanin Zuciya ce, saboda grandpa ya ta6a yi sau biyu daɗewa tun kafin na mallaki hankali na, lokacin da Senior mom ta rasu da kuma lokacin da Kanwarsa ta rasu.." sheikh Imam bai ƙarasa sauraran maganar Justice ba, Ya juya jikinshi na 6ari ya samu guri daga tsakiyar Sofas din da suke, afujajen Ya zauna dirshan tare da tankwashe kafafunsa yayin zaman cin tuwo.. "A'uzubillahi minasshaidanirrajim, Bismillahirrahmanirrahim..." ƙira'ar alkur'ani mai girma Ya cigaba da yi musu tun yanayi kasa kasa har ya ɗaga muryarsa da karfi idan yaja aya saiya dire ta yake jan numfashi kafin ya daura da wata, kankace me tuni ya haɗa gumi akan fuskarsa yanayi yana duban su. justice daya langwa6e kansa, Yayi shiru yana jin yadda kira'ar shiekh ke ratsa zuciyar sa.. Kaitsaye Sautin ƙira'arsa ya ratsa dodon kunnuwansu, har izuwa sassan jikin su, Unexpected zuciyoyin su suka fara bugawa da matsanancin karfi, Numfashin su ya fara fita da sauri da sauri Gaba daya bai lura ba, saboda ya sadda kan shi ƙasa, Yana tsaka da karatun kwatam ba zato ba tsammani suka fara dawowa hayyacinsu, wata irin nannauyar ajiyar zuciya gami da atishawa da tari suka dinga saki a jere a jere. "Ruwa.. Ruwa.. " cikin disasshiyar murya Hateem Ya firta.. Jikim Justice na bari ya mike garin sauri hada tuntube ya nufi kitchen area, jim kadan Ya dawo da gudu, ya rugume bottle waters masu sanyi a kirjin shi. bayan ya cire masu murafan robunan ruwan Yabi su daya bayan daya ya mika musu ruwan yatsun hannayensu na kerma suka kakkarba tare da kaiwa baki suka fara sha, makoshin su har sauti ya ke fitarwa kwat kwat!! Kamar zai ballo.. At same time ziyad da captain Yaseer dake kwance kasa suna bacci suka farka sakamakon kira'ar imam data cika kunnan su kamar wadanda suka sha kayan maye a kasalance suka miƙe zaune tare da jingina bayansu jikin Sofas. Kowan nan su saida ya shanye ruwan dake acikin robar sa, kafin suka jefar da robobin... Sai lokacin ƙwaƙwalan su su ka dawo bakin aikinsu, sunyi mamakin ganin gari ya waye, ko da suka ga shiekh Imam dake a zaune Yana kira'ar alkur'ani, kusan atare suka sauko daga kan sofas din ko mikewa sun gaza yi saboda rashin kuzarin jikin su, da rarrafe suka ƙarasa gaban shi, gaba daya suka kewaye shi kamar zasu lullu6e shi da karajen su, babu wanda bai jigata ba a cikin su, jiya izuwa yau saboda tashin hankali Har faɗawa sunyi, kwarin idanunsu sunyi ja musamman masu hasken cikinsu cheeks dinsu sun yi ja. shesshekar kukan su ce ta cika kunnuwan shiekh imam malik, baisan sa'adda ya dakata dayin karatun alkur'anin ba yabisu da kallo mai cike da ruɗani, hankalinsa ya tashi da jin yadda juraman maza kamar su suke kuka da idanunsu.. hankalinsa atashe ya fara tambayarsu meke damunsu? Me yasa suka fita hayyacinsu. rurruƙe hannayen shi sukayi cikin raunanniyar murya su suka soma fadin . "Baba Imam mun shiga uku, mun bani shiekh, muna a cikin musiba, baba yaja mana bala'e, zuciyoyin mu sunyi rauni, hankalinmu ya tashi, anyi mana bakin tabon da bazai taba goguwa ba..." gaba daya sun ruɗa Imam malik Ya rasa gane ina maganganunsu suka dosa. Tun da suka fara yin magana su Captain suka shiga rudani, sun rasa gane ina zancen su ya dosa? Shin me baba ya akai ta ne? "baba ya kunsa mana bakin cikin da har abada bazai taba barin Zuciyoyin mu ba, Ya ha'ince mu, Ya zalunce mu, ya kashe mana rayuwa, kuma ya cuci kan shi, sheikh tun jiya gobara ta kama ci acikin zuciyoyinmu bamu iya kashe wutar dake konata ba sai da kayi mana karatun alkur'ani mai girma tukunna muka samu sassaucin radadin da muke ji" wani irin faɗuwar gaba Imam malik yaji adabarbarce yake rarraba idanunsa akan fuskokin su.. "Baba Imam ka tayamu rokon Allah ya dauki ranmu mu huta, watakil hakan ya zama sauki agare mu, saboda bazamu iya cigaba da rayuwa ba, da wani ido zamu dubi duniya? kowa zai juya mana baya, zamu zama abun gudu, baba imam bakin ciki zai kashe mu,...." ya fahimci wani mummunan abune ya faru da su kuma daga maganganunsu ya gane baban su ne ya jefa su a halin da suke a ciki.. Jikinsa ne yayi sanyi tamkar babu laka, tsantsar tausayinsu ne Ya kama shi, tun kafin ma yaji abun da zasu fada masa.. A hankali ya soma ɗaura tafukan hannayensa asman kawunansu kamar kamun ciwon kai ya ke yi masu, addu'oi ya soma karantowa yana shafe masu kai.. cikin ikon Allah nutsuwa ta fara shigar su, numfashin su dake fita a hargitse ya fara daidaita, wani irin gumi ne ya soma wanke goshinsu alamar zazzabin jikinsu ya fara sauka.. "Ba sai kun fada min abunda ke damun ku ba, na riga dana sani, sai dai karin bayani da zan nema..." arude suke kallon shi da tsantsar al'ajabi . "Shiekh, taya akai ka sani? Mun shiga uku, shikenan kowa ya riga daya san miyagun ayyukan da baba ya ke aikatawa, kowa ya sani, tamu ta kare, mun bani .." Senate Lateef ne ya fada tare da daura hannayensa asaman kansa.. Cikin sanyin murya Imam yace"Lateef, babu wanda Ya sani, daga Allah, sai ku sai kuma ni, nima din bakomai na sani ba.." "Kwana daya da banganku a masallaci ba, Hankalina Ya tashi, bani kadai ba, hatta jama'ar dake halartar masallacin sun damu da rashin ganin ku, kowa muka kira layinsa a cikin ku bama samu, shiyasa na yanke shawarar zuwa nan din dan in duba ku, saboda naji araina ba hakanan ku ka ki zuwa masallaci ba..." ya dan dakata tare da jan numfashi kafin ya kuma cewa" Ba jiya bane ku ka yi family meeting ba? Ina Owais ina kuma sauran ahlin naku"? Sai lokacin suka tuna da shi, Kowa Yana ta kan shi, cike da rashin ƙwarin jiki sharafudeen Ya mike tare da juyawa a hanzarce ya nufi cikin gidan ya bazama neman sa, saboda yaji aransa bai fita ba, watakil ya fada wani gurin daban.. "Bakowane Ya samu damar halarta ba..." His excellency deen ne ya fada yana sharce kwallarsa, da yatsan hannunsa Ya nuna su Justice yace "su kadai ne, suka zo, sauran Uzirurrukane suka ruƙe su..." kwata kwata bai nemi su faɗa masa ainihin abun da ke faruwa da su ba. Takun tafiyar su ne Yaja hankulansu ga duban inda sautin ke fitowa, Sharafudden ne ya 6ullo Hannunsa ruke da damtsen Owais dake ta layi kamar wanda yasha kwaya.. Gwanin ban tausayi suke kallon shi, Hankali atashe su justice suka mike tare da nufar shi, kwata kwata basu san yana a gidan ba, sakar musu shi Sharafudeen yayi, cikin sauri suka tallabesa tare da rungumesa suna tambayar shi meke damun shi? Meke faruwa da shi? A ina ya kwana? "Can na tsinto shi a back room din baba, Ina tunanin tun jiya acan ya kwana..." Hankalinsu Ya kara tashi basu taba ganin Owais a mawuyacin hali irin wannan ba, ko magana bai iyayi, fuskarsa duk jirwayen hawayen sa.. "Ku miko min shi nan" sheikh Imam ne Ya fada Tare da mika musu hannu, Ruko shi Captain yayi ya taimaka masa Ya karasa ga imam, Jikin nasa ne babu kuzari gaba daya ya durkushe saman gwiwowinsa agaban Imam Malik. tallabo keyarsa yayi tare da janyoshi Ya fado kan kirjinsa, cikin sigar lallashi Yake dan bubbuga tafin hannayensa akan bayansa, a hankali ya fara karanto addu'o'i yana tottofa masa asaman sumar kan shi.. "tun da yanzu kun riga da kunsan komai babu batun boye boye a tsakanina da ku, maganar gaskiya daliline yasa na shiga jikin ku don in samu kusanci daku saboda in tabbatar da abun da nake zargi akan family din ku..." da rudu suke kallon Imam, maganarsa ta daga hankulan su, owais daya fara dawowa hayyacin sa, cikin kunnansa ya tsinkayi maganar Sheikh Imam da mamaki ya dago da kansa yana dubansa.. yadan numfasa kafin ya daura cewa"ni Allah yayi min wata baiwa In har zan zauna tare da mutum mai bakin sihiri a jikin shi wlh sai naji a jikina, Mahaifinku da surukinku pravin na dade da sanin suna da sihiri a jikin su amma ban taba bayyana maku ba, saboda bani da isassun hujjojin da zan tunkare ku da maganar, lokacin dana fara kutsa kaina ga mahaifinku har na samu ya yarda dani rana ta farko daya gayyaceni don inzo in gana daku, sai da gabana ya fadi ganin yadda kukeyi masa biyayya sau da ƙafa, kun yarda da mahaifinku kuna son shi, jikina yayi sanyi dama tun kafin na gane ma idona, sai da naji abakin mutane amma dana gani da ido abun ya karya zuciyata, nayi al'ajabi yadda kuka kasance masu kyawawan halaye da dabi'u kun fita daban, samun irinku zaiyi wuya, Allah bai rageku da komai ba, sai dai kash mahaifinku yayi muku cikas, 6atacce ne ku kuma tsarkakakku ne, wallahi a lokacin koda na fadamaku ba zaku yarda dani ba, zama ku iya tunanin turo ni akayi don inyi masu kazafi, watakil ma kusa a daure ni, shiyasa naja bakina nayi shiru, amma duk da haka ban hakura ba, saboda Allah ya jarabceni da kaunarku, naji inason in taimake ku shiyasa nabiyo ta bayan fage batare da sanin kowa ba, na fara kiran Owais ta boyayyiyar number, na fada masa ya bincika family dinsa akwai bara gurbi a cikin su...." dafe kai Chief Owais yayi da tafin hannunsa bakinsa abude da tsantsar mamaki yake kallon Imam wai ashe shine boyayyan mutumin dake kiransa awaya.. "Sheikh dama kaine boyayyan mutumin dake kirana awaya? Ya fada arude, murmushi Imam malik ya sakar masa"Nine Owais, nasan za ka yi mamaki, kamar yadda kake amfani da brain dinka nima haka nake amfani da kwakwalwata, ban taba bari ka gane nine ba, na toshe duk wata hanya da zaka iya bin diddigin layin da nake kiran ka da shi, bayan haka duk idan zamuyi waya ina canza murya saboda bana so ka gane nine..." dafe kansa yayi da tafukansa Shiekh Imam Ya basa mamaki, yayi zaton malamin addinin islama ne ashe bayan kasancewar shi alkali har ilmin computer gare shi saboda ba karamin wahala ya bashi ba, yasha ya zauna ya baje basirar sa gurin gano wanene boyayyan mutumin dake kiransa amma ya kasa kamar Aljani haka ya koma masa, kowa dake awurin yayi mamaki sosai.. Ruƙe hannayensa Chief yayi"meyasa tuntuni baka fito fili ka fada min kaine ba? Why pls? Da ka fadamin ay da tuni na dauki mataki akai" Shafa sumar kanshi imam yayi"Owais, koda na fada maka ba zaka yarda ba...." "Dan Allah ku fada mana meke faruwane? Tun jiya kunbarmu a duhu, ku sanar damu mana! Kunce baba Ya kulle kansa adaki, meyasa yayi hakan? Wani laifine ya aikata da da yaja har kuka shiga mawuyacin halin nan.."? Cike da damuwa Ziyad ya tambaya yana binsu da kallo gaba daya fargaba ta hana su bude baki su furta.. Captain yaseer daya gama Fusata zuciyarsa tazo wuya rai a6ace yace"nagaji da jiran ku fada mana, gaba daya kun tada mana hankalinmu, kuma kunki ku sanar damu meke faruwa, wlh da nasani da banzo ba.." ya fada yana girgiza kansa.. Marairaice fuska justice yayi tare da kallon sheikh Imam tamkar zaisa kuka yace"Dan Allah baba Imam ka fada mana tunda su sunƙi su sanar damu, pls ku taimaka ku fada mana meke faruwane mun kasa gane inda zancenku ya dosa...." bai ƙarasa maganar ba, Chief Owais Cikin raunaniyar muryarsa da ta disashe ya fara zayyana musu abunda ya faru jiya kafin a fara family meeting, tiryan tiryan ya fayyace musu tun daga biri har wutsiyarsa.. Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, tun kan ya karasa suka fara jefawa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar al'ajabi da rudani hadi da tsantsar tashin hankali, ga wani irin faduwar gaba da suka fara ji, Lokaci daya suka zazzare idanunsu jin abun da basu taba zata ba, murya na rawa Justice ya furta"ba zai ta6a yiwuwa ba Owais, wannan wani irin labarine mai kama da almara? Bazai ta6a zama gaskiya ba wlh, Owais ka sake bincike watakil kunyi kuskure, Baba bazai ta6a zama daya daga cikin azzaluman mutanan ba, ka bani mamaki Owais ka rasa wa zakai wa kazafi sai baba? sai kace bakasan halin shi ba"? Cikin fusatacciyar murya ya fada tsabar bacin rai shatun jiyoyon wuyansa sun fito rudu rudu kan fatarsa.. "Tayaya zaku yarda da abunda wata tsohuwa bare ta fada? Wallahi karya takeyi maku, ba momma bace, wanda ya mutu baya dawowa ba, ni batai min kama da mai hankalin ba, makiya ne suka turota don tayi ma grandpa kazafi, Ai wlh da nasan abunda makirar matar nan ta aikata, da tun lokacin dana ganta kwance kan sofa, zan danne hancinta da fillow har sai ta bakunci lahira...." Captain yaseer daya gama rikicewa jikinshi na 6ari ya dubi Imam malik daya sadda kanshi ƙasa "shekh pls kayi masa rukiya, Owais Ya haukace, He needs a psychiatrist to examine his brain, he's not well, Owais would never say this in his right mind, saboda wlh bayin kansa bane, Owais ba zai taba fadin maganar nan da hankalinsa ba, zai iya yiwuwa aljanunne suka shige shi, dad...Uncles pls kuce mana karyane abunda Owais ya fada akan grandpa, ni nasan ba acikin hayyacinsa ya fada ba, Baba ko kiyashi bazai iya kashewa ba, balle rai..." tashin hankali Ya hana Ziyad furta kalma, kunnuwansa sunjiye mashi abunda ya fi karfin jin shi, baima san sa'adda ya fara unbottoning din rigarsa ba, saboda wani zafi daya taso mashi, still basu gasgata maganar owais ba, amma fa sun kaɗu ba kadan ba saboda sunsan mawuyacin abune Owais yayi masu karya saboda ba halinsa bane, kawai suna jin tsoron su gaskata abunda ya fada musu ne.. Gaba daya ubannin nasu sun kasa magana saboda sun razana da ganin yadda suka ɗaga hankulansu, ta wani bangaren zuciyarsu ta karaya da jin kalaman dake futowa daga bakunansu, bayin Allah saboda yardar da sukayiwa kakansu sun kasa yarda da maganar da aka fada musu akansa.. runtse idanu shi yayi gam a hankali wasu zafafen hawaye suka fara shararowa kan kuncin sa, cikin shesshekar muryarsa mai rauni ya furta"sheikh ni dama nasan za'a rina, baba ya karya mana zuciya, wlh ba kazafi nayi masa ba, shine Elder na gidan kurkukun kaddara kamar yadda kukaji, zaku Iya tuna yaran da nake ruko agurina? Wanda nace maku sojojin america ne suka tsince su a dajin Evil forest kuma suka damƙa case din mu a hannun hukumarmu? To wadannan yaran suna daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, A Lokacin sun ku6uta daga gidan kurkukun ne, ai kowa daga cikinku ya gansu a ranar farewell dinner din Uncle Hateem.." nan fa kwakwalensu suka fara tariyo masu fuskoki yaran masu bala'en kama da wasu daga cikin su, still basu gasgata maganar shi ba, amma fa sun fara shan jinin jikinsu, maganarsa ta haifar musu da kowanto.. "Bayan mun kai farmaki, Munyi nasarar ceto wasu daga cikin yaran, A yanzu haka suna akwance gadon asibiti karkashin kulawar likitoci, Aminina omar shima an kwantar da shi tare da dan uwan yaran Salsabeel, har yau basu farfado daga Coma ba, Idan har yanzu baku yarda ba zan iya nuna maku videos din yaran da muka kubutar..." Wayarsa ya zaro daga cikin front pocket din aljihunsa ya kunna masu video din fursinonin ya nuna masu gaba daya suka leƙa suna kallon su, gasu nan a kwankwance saman gadajen asibiti jikinsu sanye da patient uniform, har sheikh imam saida ya kalla, ya kuma kunna masu videos din su Unaisah daya dauka yayin tattaunawarsu a questioning room, wlh sun girgiza gaba dayansu ashe basu ji komai ba agurin khala, sai yanzu da suka ji ainihin labarin azabtarwar da akeyi masu agidan kurkukun ƙaddara, abun ya taba zuciyarsu sosai, kamar zasuyi hauka saboda tausayin su daya kama su, su Captain duk sun yarda dagaske ne abunda owais ya fada musu sai dai basu yarda kakansu Obie yana daga cikin azzaluman da suka azabtar da su ba, saima cewa sukayi koda zasu yarda labarin na zahirine amma bazai taba yiwuwa baba ya aikata ba, saboda su sun yarda da shi sun kuma san halin shi, sheikh Imam Ya kasa furta kalma, saboda raunin da zuciyarshi tayi, baiyi zaton abun ya munana har haka ba, sai ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihurraji'un yakeyi Bai ma san sa'adda ya zabura ya mike tsaye jikinsa na 6ari Ya kama zarya a tsakar falon ba, Cazbahar hannunsa tuni ta jima da barin yatsunsa ta faɗa kan floor, har kwalla saida ta zubar masa bai bari sun gani ba yayi saurin sanya tafin hannunsa ya goge ta, hakika Baba Obie ya karya Zuciyar Imam malik, bai taba zaton zai iya aikata makamancin rashin imanin nan ba, abu biyu dayafi kona masa rai ya karairaya zuciyarsa irin yadda suka shafe shekaru suna aikata fasadi a doron ƙasa batare da an kama su ba, Yaji takaicin irin azabtarwar da sukayiwa yaran da basu ji ba basu gani ba, abun takaici yaran jininsu ne, babu imani ba tausayi suke azabtar da su, labarin da owais ya basu ya fama masa tsohon raunin da ke a cikin zuciyarsa, Bazai ta6a mantawa ba, yaso ya fada musu ainihin dalilin dayasa ya fara zargin ahlinsu sai dai ya kasa ganin halin da suke a ciki, abun dayafi damunsa makomar Ahlin Obie, ya'yansa masu daraja da kima a idon duniya, babu na banza acikinsu, kowa yabonsu yakeyi saboda kyawawan halayensu da dabi'unsu, amma fasikin mutumin nan saida ya zubar masu da mutuncinsu! Bai kyauta ma kanshi ba, da alama abun ya taba zuciyar imam so yake yayi kuka don ya fitar da abunda ke ransa sai dai ya kasa saboda bai son suga rauninsa hakan zai iya ƙara jefasu a mawuyacin hali.. a karo na biyu ya share kwallarsa yayin daya basu baya, saida ya daidaitsa nutsuwarsa ya daure ya cije cike da karfin hali ya juyo ya fuskance su a lokacin sun kasa yin kukan na zuci sukeyi mai radadin gaske... Cikin sanyin murya ya tambaye su tun da suke arayuwarsu sun taba fuskantar mummunar kaddara ko wata jarabawar rayuwa irin wannan"? har suna hada baki gurin furta aa sukace su tun da suka taso rayuwarsu basu ta6a fuskantar kaddara mara kyau ko wata jarabawar rayuwa ba, nasara da jin dadin rayuwa kadai suka sani, idan ma akwai abun daya taba sanyasu kuka da idanunsu to bai wuci ranar da suka rasa mahaifiyarsu ba, acewar su His excellency, gyada kai sheikh imam yayi idanubsa cike tab da kwalla yace"wannan ne karo na farko da zasu fara fuskantar mummunar jarabawar rayuwa, yace shi tunda ya taso rayuwarshi yana jin labarai iri iri na irin jarabawowin da mutane suke fuskanta wasu su daga hankalinsa wasu su sashi zubar da kwalla saboda tausayi, amma bai taba jin kaddarar data girgiza shi irin tasu ba, yajiye masu bakin ciki da takaicin abunda mahaifinsu ya aikata musu, ya tausayawa rayuwarsu, amma kada su karaya, nan ya fara yi musu nasiha mai tsuma zuciya... _Abun da akeso a yayin da Allah ya jarabce bawa da wata mummunar kaddara, Ana kwadaitar da su da su amsa jarabawan da hakuri da godiya suyi biyayya ga Allah, domin hakan yana tabbatar da gafara da lada daga Allah, kuma Allah yana tare da masu hakuri, sannan dukkan tsanani yana a tare da sauki_ _Wani lokaci Allah yakan jarrabi bayinsa da musibu domin ya daukaka su, kuma ya kankare zunubansu, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake cewa_ _(For every misfortune, illness, anxiety, grief, or hurt that afflicts a Muslim, even the hurt caused by the pricking of a thorn, Allah removes some of his sins.")_ _“Duk wata musiba, ko rashin lafiya, ko damuwa, ko bakin ciki, ko cutarwa da ke damun musulmi, ko da wata ƙaya ce da ta same shi, Allah yana kankare masa wasu daga cikin zunubbansa"_ A cikin suratul Ankabut ayata 2 _Allah buwayi yace"Ashe Mutane Suna Tsammanin Cewa Za'a Barsu, (Don Kawai) Sunce Munyi Imani, Alhalin Kuma Su Baza'a Jarabcesu / Baza'a Fitinesu Ba?_ _Acikin suratul Surah Al-Baqarah Allah yana cewa_ _Wa lanablu wannakum bishai’im minal khawfi waljoo’i wa naqsim minal amwaali wal anfusi was samaraat, wa bashshiris saabiroon._ _"Kuma lalle ne, zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace, kuma ku yi bushara ga masu hakuri."_ _"Ku tuna cewa hikimar Allah da iliminsa sun wuce fahimtar mutum, Maimakon tambayar dalilin da ya sa Allah ya jarrabe mu, ya kamata mu mai da hankali ga amsa jarabawowin da imani, da hakuri, da godiya_ _Annabi Muhammad (SAW) ya ce, "Babban lada yana tare da fitintinu masu girma, idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su, kuma wanda ya yarda da shi ya samu yardarsa"_ _Kaffarar Zunubai Allah yana iya jarraba mutane domin ya tsarkake su daga zunubansu, kuma idan suka yi haquri za a gafarta musu zunubansu._ _And sometimes Allah tests us with calamities and sometimes with blessings, to show who will be thankful and who will be ungrateful, and who will obey and who will disobey, then He will reward or punish them on the Day of Resurrection _ _Kullum ka ɗauka cewa kana cikin jarabawa ne, domin dukkanin rayuwarka jarabawa ce, Allah zai jarabceka da abubuwa daban daban, waɗanda ka sani da waɗanda baka sani ba, tsammaninka kayi juriya kayi haƙuri_ _Ba kullum ne zaka samu rayuwarka ta kasance maka yadda kake so ba, akwai ranar farin ciki, sannan kuma akwai ranar baƙin ciki, akwai ranar samun riba, sannan kuma akwai ranar (faɗuwa) yin asara"_ _Haka jarabawar rayuwa take, amma babu makawa duk abinda ya faru gareka, idan kayi biyayya ga Allah, sannan kuma kabi manzonsa, haƙiƙa zaka kasance daga cikin masu cin nasara a duniyarsu da kuma lahira"_ Tunda Imam Ya fara yi musu nasiha jikin su yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu, nasihar shi ta ratsa zuciyarsu sosai, musamman daya tunasar da su irin yadda annabawa suka fuskanci jarabawowin rayuwa masu tsanani kuma sukayi hakuri sukai biyayya ga Allah, sai suka ga tasu jarabawar bakomai bace somun ta6i ne, sannan yace yasan basu fara ganin komai ba, sai lokacin da abun ya fallasa duniya ta sani a wannan lokacinne zasu fara fuskantar kalubalen rayuwa amma baya son su karaya, kuma su daina jin fargaban mutane su sani, laifin nan basu suka aikata ba, Allah ya sani, kuma yana atare da su, don haka su mika lamuransu gare sa, sannan su dage da yiwa kansu addu'a akan halin da suke a ciki, shima zai tayasu, In sha Allah wata rana sai labari, zai zama kamar ba'ayi ba, sai dai tashin zance, kuma kada su kuskura duk runtsi duk wuya su jefa kansu a mawuyacin hali saboda maganganun da mutane zasu fada akansu, koda zasu rasa mukamansu ne kada su karaya, mutane basu da wuta basu da Aljanna ba zasuyi masu hisabi ba, kada su ji kunyar laifin da basu suka aikata ba, koda za'a cuzguna masu ne, ayi musu kazafi, ko azage su aci zarafin su, kada su kuskura su canza daga yadda suke, saboda sau dayawa mutane suke jaza ma mutun bakin cikin da zai zaiyi silar da zai tsani kansa ya kuntata har yayi tunanin kashe kanshi bayan yin hakan kuskure ne babba ba...💔 Yayin da yake yi masu nasihar ya haɗa gumi akan fuskarsa kamar babu A.c a falon, har lokaci bai zauna ba, yana daga tsaye yana fuskantar su batare da gajiyawa ba, wlh ji sukayi kamar ana wanke damuwar dake a cikin zuciyarsu, ga wani sanyi dake ratsa jikinsu, imam ya karfafa masu gwiwarsu, Ya farfado da jarumtakarsu, aransu har sunji zasu iya fuskantar kowani irin kalubale da zasu fuskantar... "Kuma ku sani, Nima ina atare daku, zan tayaku yaƙi atare zamu cinye jarabawar nan da take tunkaro mu, in sha Allah, zan tsaya maku tsayin daka don ganin baku tozarta a idon duniya ba" ya faɗa yana kara jaddada musu da murmushi akan fuskarshi, wannan maganar da yayi ta faranta ransu, har basu san sa'adda suka saki murmushi akan fuskokinsu ba, kusan atare suka mike tare da nufar shi, atare suka hada baki gurin yi mashi godiya kamar zasu durkusa kasa, sun ma rasa bakin magana, sukace su basu san dame zasu iya biyanshi ba, saboda basu da abun da zasu biyashi da shi Allahne kadai zai iya biyan shi, Bazan iya misalta dadin da imam malik yaji ba, daya bayan daya yabisu ya rungume su a kirjinshi.. Daga bisani Ya umarce su da suje suyi wanka kuma in akwai sallar da basuyi ba toh suyi gaggawar ramata dama so yake ya samu su samu natsuwa sannan yayi masu magnar sallar, babu musu suka amsa mashi da toh..💔 Gaba dayansu a part din iyayen su mata da ke a cikin gidan Suka shiga, wanda tun bayan rasuwar su, basu daina amfani da shi ba, masu aikin gidan suna shiga su gyara shi akai akai, kullum zaka taras da part din a atsaftace kamar akwai me rayuwa acikin sa, aduk time da suka ji kewar iyayen su mata, idan suka zo gidan a part din suke huce gajiyar su. Bayan sun yi wanka sukayi sallah, daga bisani suka fito falo, kamar yadda suka bar sheikh Imam haka suka taras da shi, a kewaye da shi suka zazzauna, ya tambayi ina yan aikin gidan suka ce tun jiya suka hana wani daga cikin su shigowa main falo.. Sheikh Imam yace a kira su, don su girka musu abinci, bai kare maganar ba, Prime minister ya tari da numfashin shi da cewa"basai an kirasu ba, daga rana irin ta yau, ko ruwan gidan ba zasu ƙara sha ba..." sauran ma suka goyi bayan maganarsa, sheikh imam bai musa masu ba, sai dai yace shi bazai barsu da yunwa ba, yana ji kamar Allah ne ya kaddara zuwansa gare su don ya taimaka musu don haka suyi hakuri su bar shi yayi aikin shi Yana kwadayin ladar da zai samu ta silar taimakon su da zaiyi. Badan sunso ba, suka amince masa amma fa bisa sharadin ba zasu ci abincin gidan ba. A karshe shi ya basu shawarar tunda matayensu suna da restaurant na hadin gwiwa kuma bada dukiyar mahaifinsu suka gina shi ba, halal din su ne, me zai hana su kira manager ayi musu order na kayan abinci da duk wani abu da zasu bukata naci.. Shawarar shi suka ɗauka, batare da bata lokaci ba, Mai girma sharafuddeen ya dauko wayarsa bayan ya kunnata ya kira hajiya laura, lokacin data daga kiran nashi kuka yaji tanayi tare da tambayarsa meke faruwa ne? Jiya taga an kawo hajiya saratu asibitin su rai hannun Allah, fuskarta duk ta baci da raunuka garin ya ya hakan ta faru da ita? har su twins ta tambaya suka ce mata hajjaty suke zargin tayi mata haka! Shin dagaske ne? Kuma wacece dattijuwar da aka kawo su a tare? Sannan suna ta kiran layinsa basa samu tun jiya bai dawo villa ba" kamar yar jarida ta tsare shi da tambayoyi ga kukanta daya cika kunnansa. bai bata amsar tambayarta ba, sai dai ya kwantar mata da hankalinta, yace tayi hakuri su jira shi idan ya dawo villa zaiyi masu bayanin komai, dakyar ya samu ya shawo kanta kafin daga bisani ya bata umarnin tayi musu order na kayan abincin dana sha daga restauranta dinsu akawo masu anan estate dinsu..." maganarsa ta jefa ta a rudani tana kokarin ƙara tambayar shi ya katse kiran.. Cikin abunda baifi mintuna ba, Delivery Vans (motocin daukar kaya) biyu suka fara shigowa estate din, masu dauke da tambarin Royal Courtyard Restaurant. bayan sun tsayar da motocin a parking space, Delivery staffs suka fara fitowa daga cikin motocin kafin suka fara jigilar ɗauko Containers na kayan abinci da kayan sha daga cikin motar suna kaiwa Cikin Store din gidan.. Lokacin da suke shigowa, Maids din gidan dake lekensu daga sashen su, Sunyi mamakin ganin restaurant staffs suna shigowa ciki da kayan abinci, bayin Allah har sun fara tunanin ko dai wa'adin aikin su ne Ya kare, nan fa hankalin su Ya tashi, dama jiya sun kwana da fargaban abun daya faru da hajiya saratu, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana musu Hajjaty ce ta yi silar abun daya faru da ita, shiyasa ta gudu daga gidan, gayanan zata ja musu ba'la'e idan laifin ta ya shafe su basu san ina zasu sa kansu ba, har saida ma'aikatan gidan suka kammala aikinsu, tukunna maids din suka koma cikin part dinsu cike da zullumi. Dakyar Sheikh Imam ya samu suka ci abincin kadan badan suna jin dadin shi ba. Kasa tafiya yayi, saboda ya damu da su, gani yake idan ya haura kafa ya bar gidan zasu kara shiga mawuyacin hali ne, Hakan yasa bai je ko'ina ba, afalon gidan ya zauna atare da su Yana ƙara kwantar musu da hankali.. Su ka ce su yanzu damuwarsu suna son su san awani hali baban nasu Yake a ciki? Yana araye koya mutu, don tun daya gama kururuwarsa adaki basu kara jin koda tarin sa ba, ganin yadda suka nuna damuwarsu Yasa shi ce musu su taso su tafi part dinsa, gaba daya suka mimmike tsaye Yace Ma Chief ya ɗauko mashi abincin da zai ci, store Ya shiga ya hado masa lunch a madaidaicin tray, Ya fito suka dunguma Izuwa Part din baba Obie. kwankwasa kofar dakin Sheikh Imam yayi tare da ambaton sunansa kusan sau biyar bai amsa ba, cike da damuwa Chief yace bazai bude ba, amma su zagaya ta bayan dakinsa, akwai glass windown da ya fara kokarin fasawa jiya ya kasa, yasan zuwa yanzu quality din glass din Ya ragu zai kara jaraba fasa shi.. In a weak voice Justice Yace nima zan taimaka abude tagar, captain da ziyad ma sukace zasu taimaka gurin balle tagar... Batare da bata lokaci ba, suka zagaya ta bayan dakinsa cike da sa ran zasu iya balle kofar.. Bayan sun Isa gaban Window din, suka fara kokarin fasa glass din, abunka ga majiya karfi sun haɗu, Naushi suka dinga sakar ma glass din har saida Ya fara barazanar fashewa. Kubi a hankali kada ku raunata kanku, shiekh Imam ne yayi maganar.. Dakyar da sidin goshi suka samu faskeken glass din Ya fara Tsastsagewa, naushi daya Hateem Ya sakar mashi gaba daya ya zube kasa har saida suka dan ja da baya.. Lokacin da suka dago da idanunsu ba zato ba tsammani suka hango sa a zaune Tsakiyar gadonsa sanye cikin doguwar riga baka mai hula, basu iya ganin fuskarsa ba saboda ya basu baya. duk da haushin shi da suke ji hakan bai hana sunji sanyi aransu ba, ganin shi araye ba kamar yadda suka zata ba.. labbansu na kerma suka hada baki gurin ambaton sunan shi Baba. Shiru bai amsa musu ba, kuma da alama yana jin muryoyin su acikin kunnanshi. Ba irin magiyar da basu yi mashi ba, akan Ya juyo ya fuskance su amma yayi shiru ba alamun zai yi abunda suke so kuma bai tanka musu ba, hakan yayi matuƙar taba zuciyarsu, su ziyad da basu gasgata abunda owais ya labarta musu ba ayanzu sun fara kokwanto akan kakan nasu l. wani sabon kukan suka kuma fashewa da shi ganin yadda lokaci daya mahaifinsu ya jefa kanshi a mawuyacin hali ya kuma jefa su suma... Shiekh Imam Yayi kokarin sanya shi yayi magana kodan saboda ya'yanshi da suka damu da shi, amma yayi shiru bai tanka masa ba.. badan sun so ba suka hakura dayi mashi magana, Jikin asanyaye suka fara zame jiki suna barin bayan dakin nasa saboda ganin sa da su ke yi yana kara fama raunin da ke a cikin zuciyar su. Imam malik yaso yayi magana da shi saboda akwai wani abu dayake so ya fada masa sai dai ya ƙyalesa zuwa lokacin da zasu ke6a saboda idon ya'yansa dake a gurin. Chief ne kadai Ya rage a bakin tagar yanata kallon bayansa, ba dan akwai makarin daya toshe tagar da dakin ba, da ba abunda zai hana ya dira. tray din abincin daya zo masa da shi ya fara kokarin turawa ta cikin tagar yaki shiga, dakyar yayi dibarar aje tray din kasa ya dauki warmers din ya dinga jefa su ta tagar ta yadda abincin ciki bazai 6are ba, saboda ya datse murfinsu sosai, hada drinks din Ya jejjefa cikin dakin bayan ya kammala ya sauke ajiyar zuciya.. Cikin raunanniyar muryar shi Ya furta"baba kana jina, jiya ina ta kiran sunanka baka amsa min ba, anan na kwana, wai meyasa kayi min haka baba? Kaga halin da ka jefa kanka damu kanmu ko? Muna zaman mu lafiya, gaba daya ka lalata farin cikin mu, Jiya babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali baba, ka kuntata kanka muma ka kuntata mu, ina kaunar da mukeyiwa juna baba? Yanzu ka sanya katanga atsakanina dakai..." kasa karasa maganar yayi, kumburarrun idanunsa sun cicciko tab da kwalla, Sai kallon bayan shi yakeyi yayi tunanin zai motsa sai dai ko gizau baiyi ba, kamar gunki. In a broken Voice Ya furta"shikenan, ni zan tafi, ga abinci nan na kawo maka, dan Allah, ka taimake ni kaci, kada ka zauna da yunwa, kuma bana so kaje wani wuri, dan Allah kada ka tafi kabar mu, nasan zaka iya 6acewa idan ka so, amma pls kada ka tafi pls.." Harya juya zai bar bakin tagar, kwatsam Ya tsinkayi muryarsa wlh bai taba jin muryar data daga hankalinsa irin tashi ba, kamar ba muryar kakansa ba muryar tayi rauni ta kuma disashe.. "Owais, nasan meyasa ka roke ni akan kada in tafi, ba dan kana sona bane, sai dai baka son in gudu batare da ka mika ni ga hukuma an yanke min hukunci ba ko"? Kamar ba shi yayi maganar ba, dan ko kadan bai motsa daga yadda yake ba. Shiru owais yayi batare daya iya furta kalma ba, tabbas babu karya a maganarsa, "Hakane, Inaso ka tsaya ka kar6i hukuncin da za'ayi maka, ta hakane zaka samu yafiyarmu, kuma ta hakane zaka samu sassauci, In har ka mika wuya batare daka bamu wahala ba, amma maganar nadaina sonka, ka daina, tabbas na tsaneka baba, ka karya min zuciyata, ka ci amanar yardar da nayi maka, amma ya zanyi? Inason ka wlh, har yanzu ina kaunar ka, amma ba kamar da da nake ma kallon dattijon arziki mutumin mai mutunci, kuma wlh kaunar da nakeyi maka bazata hana in hukuntaka ba, dole hukuma tayi aiki akanka baba, dole ka girbi abunda ka shuka baba, tabbas idan nabiyewa son zuciyata, zance ka gudu ne saboda kaunar da nake maka, amma in na tuna hakkin rayukan dake akanka, da zaluncin da ka aikata, sai inji bazan iya kyale ka ba, saboda koda na kyaleka wlh Allah bazai barka ba, dole ka ga sakayya tun agidan duniya, nima kuma in ban dauki mataki akanka ba, Allah zai kamani ne wlh..." cikin shesshekar kuka ya kare maganar.. "Jikallena, kada ka damu, kakanka ba inda zaije, nayi maka alkawarin ina nan, kuma zan mika wuya saboda inason ku dauki fansar abunda nayi maku, in har hakan zaisa ku yafe min, duk da nasan ban cancanci ayafe min ba, Owais bazan iya misalta maka halin da nake a ciki ba, danasani bata da dadi ko kadan, gayanan naja ma kaina..." a hankali ya kifa kansa saman bedmatress din sa, duk akan idon Chief owais, baisan ya akai ya ke jin kamar tausayinsa na shigar shi ba.. "Kai kenan, Inaga wadanda suka yarda dakai, wadanda sukeyi maka kallon jagoran rayuwarsu, kasan kuwa halin da muka shiga jiya izuwa yau? Bai amsa mashi ba yayi shiru kamar ma kuka yakeyi.. "Ka taimaka ka bude min kofar dakinka, Inaji ajikina baka da koshin lafiya, zan kira doctor ya dubaka" In a low voice ya furta"wata irin zuciyar imani gare ka Owais uhum? Meyasa zaka damu dani? Ko da yake nasan kanayi ne don kada inyi rashin lafiyar da zatayi silar mutuwana batare daka hukuntani ba...." katse shi yayi"ba haka bane baba, na damu dakai .." bai kare maganar ba ya katse shi"bana bukatar likita Owais, Azzalumin mutun irina bai cancanta aduba lafiyarsa ba, Yaran da muka azabtar agidan kurkukun kaddara, da yawansu idan suka fara ciwo, likitocin mu basa duba lafiyarsu, illa iyaka idan muka ga zasu gaza sai musa Surgeons su farke cikin su su debi sassan jikin su, shine ni zaka ce ka kira doctor ya dubani? Na cancanci hakan Owais..." bai kare maganarba, Zuciya ta debi Chief Ya daki karfen jikin tagar, Yana faman cizon lips dinsa Ya furta"Ya isa haka baba! Bana son ji! Kabarni inji da abunda ke damuna..." ya fada yana jan numfashi.. Dakyar ya tausasa zuciyarsa, Yai karfin halin Furta"Ina so ka fada min, su wanene sauran Elders..." "Kaje ka tambayi Aurora ta fada maka"! "Tace bakowa ta sani a cikin su ba, kuma a halin yanzu tana a kwance gadon asitibi batasan inda kanta yake ba, Kai kadaine zaka Iya fada min su.." cikin karyayyar murya ya furta"aurora bata da lafiya? Meke damun ta"? Bai amsa masa ba Yace"ba wannan na tambayeka ba, baka cancanki ka sani ba, kaida kaso ka kashe ta Allah bai nufa ba, kawai ka fadamin su wanene sauran Elders saboda tace min kun kai ku goma sha biyu, shida suna jagorantar gidan kurkukun kaddara, sauran shiddan kuma ba'a kasar nan suke ba, sune suke safarar yara daga kasashen waje suna shugo maku da su gidan kurkukun ƙaddara.." "Owais, naso ace zan iya fada maka su wanene su amman ba zan iya ba, dokar aikin mu ce, amana ne kuma alkawari ne a tsakanin mu, wani bazai tona asirin wani ba, don haka kayi hakuri ba zaka taba ji abakina ba, nidai na mika wuya, Aminina basai kun sha wahalar kama shi ba, shima ya mika wuya zai kawo kan shi, su kuma sauran ba zasu taba canza ra'ayin su ba, tun da har kun ceci rayuwar sauran yaran da suka rage, kuyi ƙoƙari ku sanya musu tsaro, sannan taimakon da zanyi maku shine ku yi gaggawar gano su wanene sauran Elders din ku kama su, idan ba haka ba, kama ni da kukayi kamar kun kashe maciji ne baku sare kan shi ba, ko dai ku kamo sauran Elders din, ko kuma ran kurkukun kaddara ya dawo fiye dana da..." wani irin faduwar gaba Chief yaji, Cikin rawar murya ya fara yi masa magiya akan ya fada masa su wanene in ba haka ba taya zai iya gano su? su da suke matsafa kama su zaiyi masa wuya. Baba Obie yace"Owais, Kai fa musulmi ne, meyasa zaka nemi taimakon matsafi uhum? Shiru yayi bai tanka masa ba. "Ka nemi taimakon Allah Owais, shi kadaine zai kawo maka mafita, duk da banyi Imani da Allah ba, amma bayan da asirina ya tonu na zauna nayi nazari na gane cewa Allah yana da karfin ikon da babu wani mahalukin da yake da shi, zai iya mayar da abu mara yiwuwa ya zama mai yiwuwa tabbas naga ishara akaina Owais, Dan Haka inaso ka mika lamuranka gare sa, kuma bana so damuwar abun da na aikata yasa kayi rauni Owais, bana so kayi sanya, bana so ka karaya, jarumtakar nan taka da kwazon ka, da kaifin basirarka su nake so ka farfado da su gurin bada himma akan aikin ka..." hakika yayi mamakin kalaman baba Obie, Har cikin ransa yaji dadi daya fara gane Allah daya ne, kuma Yaji dadin karfafa masa gwiwa da yayi duk da bai samu abunda yakeso agurin sa ba.. "Danish Yana araye ko ya mutu"? Kamar daga sama yaji ya tambaya.. "Bani da masaniya akan hakan, tun ranar da muka je kai farmaki ya fada cikin rijiya tare da sabon garkuwar ku amma meyasa ka tambaye ni bayan nasan kasan komai"? "Hmmm, kawai Ina mamakin wani abu ne, amma ina kokwanto owais.." "Zan iya sani"? "Kawai kayi abun da nace maka owais, shi kadaine taimakon da zan iya yi maka ayanzu, sannan idan har aka kawo maku farmakin bazata, Kayi gaggawar sanar dani Owais..." yaso ya kara yi mashi wasu tambayoyin amma saiya hakura ya bari zuwa wani lokacin yanzu hankalinsa ya karkata akan gano su wanene sauran Elders din.. _"kaddara da bugun zuciyar kurkuku, Ku sanya musu tsaro, rayuwarsu tana a cikin hatsari, da su ka ɗaine za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara a halin Yanzu"_ Lokacin da Obie ya furta maganar shi ta karshe, Chief owais bai jiyo shi ba. baisan Ya tafi ba saida yaji shiru babu motsin mutun tukunna ya sauko daga kan gadon Ya nufi kayan abincin da Owais ya jefo masa ya zukunna yana tattara warmers din guri guda.. *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*~___________________________________🌹💋🫀☠️💗🔥✍️~ Lokacin da sheikh Imam zai tafi rokonsa suka dinga akan kada ya tafi yabarsu, ya zauna atare da su, ya fahimci kamar suna jin tsoron ya tafi yabar su, gani suke kamar idan ya tafi zasu kara shiga cikin damuwa ne, lallashinsu yayi tare da basu hakuri yace in sha Allah kullum zai dinga kawo masu ziraya sannan su jure su danne damuwarsu kada su bari tun yanzu agane halin da suke a ciki, yakamata su cigaba da zuwa masallaci yin sallah saboda mutane sun damu da rashin zuwansu, su cigaba da gudanar da komai kamar yadda sukeyi ada, cike da ladabi suka amsa mashi da toh har bakin motarsa suka rako shi, har zai shiga ciki ya juyo ya fuskance su, idanunsa cike tab da kwalla, suma idanun nasu kwallarce ta cika su, bayin Allah sun koma abun ban tausayi, kafin tafiyarsa yace ma Owais ya jira kiransa, sannan yace ma sharafuddeen next zuwan da zaiyi zasu raka shi asibiti ya dubo jikin Hajiya saratu da momma daga bisani ya yi musu sallama ya tafi har saida sukaga motar shi ta bace ma ganin su tukunna suka koma ciki jikinsu asanyaye... 🥺 Sheikh Imam yana driving yana share kwallar dake kokarin gangaro masa kan kuncin sa, bakomai ya ke tunawa ba face labarin rayuwar prisoners daya ta6a Zuciyar shi, ga tausayin Ahlin Obie daya mamaye zuciyar shi, shiyasa ya za6i ya tafi yabar su saboda ya samu damar da zai huce radadin da ya ke ji a zuciyar shi.. _____________________________🔥✍️ Da marece💔 a lokacin gaba ɗayan su suna a falo zazzaune kan Sofas zun zabga tagumi kamar masu zaman makoki, damuwar rashin dawowar chief ne ya hana su sukuni, Unexpected suka jiyo motsin shigowar mutun falon, ransu ne ya basu shi ne ya dawo, Kusan atare suka mike cike da zumudin ganin shi, kwata kwata basu lura da halin da ya ke a ciki ba, jikin su na bari suka nufe shi don suyi mashi sannu da zuwa, sai dai ko kallo basu ishe shi ba, bai kula kowannansu ba hatta Taj Da Unaisah, kaitsaye ya juya ya nufi part dinsa batare daya waiwaye su ba, Ya Ilahi, jikinsu ba karamin sanyi yayi ba, ganin yadda Chief ya sauya babu annuri ko walwala akan fuskarsa, abun dayafi daga hankulansu share sun da yayi, Batool har kuka saida ta yi.. Kasa jurewa su ka yi hakan yasa suka wanki kafa suka nufi part dinsa, a bakin kofar dakin suka tsaya gaba dayansu, suka soma yin knocking din kofar hadi dayi mashi magiya akan ya taimaka ya bude musu kofar amma yayi shiru bai tanka musu ba, babu alamun zai bude masu kofar. Lamarin Ya ɗaure musu kai, sunyi matuƙar damuwa da shi, Yadda ya wuni a cikin ɗaki ba ci ba sha, haka suma suka wuni abakin kofar dakinsa baci ba sha, lokacin salla ne kadai ke tayar da su, haka zasuje suyi sallar ko sun dawo bakin kofar a datse suke taras da ita, da suka matsa da rokonsa akan ya fada musu mai ke damunsa dakyar yace su taya shi da addu'a Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi, Ya kuma kawo masa mafita acikin lamuransa, badan sun so ba, suka amsa ma shi da toh, kuma su ka daukar mashi alkawarin zasuyi mashi addu'a, yayi wannan maganar ne acikin dakinsa yayin da suke awaje suna sauraron shi, Zuciyar su ta karaya ba kaɗan ba. Almost hours, Chief bai leƙo daga part dinsa ba. Wuni su ka yi kamar marasa lafiya, saboda damuwar da su ka yi da shi. Ko sun kira layin shi baya yin picking. __________________________________ELDERS🔥 gaba ɗayan su suna a kwakkwance kan wasu hadaddun Plush poolside loungers dake a cikin Katafaren Gidan Gonar su, aljanar duniya an kawata shi da kayan alatu kamar ba za'a mutu a barshi ba, kwata kwata babu riguna a jikinsu sai short, kirjinsu da bayansu a zane yake da tattoo na tambarin kurkukun ƙaddara, sun rufe rabin fuskokin su da gold mask su shida ne gefe da gefen su matasan yan mata ne masu jini a jiki sanye da short gown a jikin su, launin ja, sun saki gashin kansu ta baya, hannayen su ruke da madaidaicin tray mai dauke da expensive bottles na whisky wanda a kalla farashin kowace kwalba yakai 1.5 million dollars, cikin kulawa su ke yi serving dinsu a cikin wasu hadaddun crystal glasses yayin da wasu daga cikin yan matan suke yi masu tausar kafadun su. daga gabansu wani tankameman Swimming pool ne makil da ruwa launin pure blue sky, ga wasu haɗaɗɗun Floating bean bags da ke shawagi saman ruwan, tantiran karuwai ne kwance asaman su masu dirarran jiki, sanye da swim suit da suka bayyana tsiraicin su, kowaccensu ta manna Sunglasses a idanun ta, saboda haduwar su idan ka kallesu saika sake kallon, sukai su goma sha biyar, daga ganinsu ba jinsi da ya bane, hankalinsu kwance suke shakatawarsu ga iska dake ratsa fatar su.. A hankali ya ke zukar cigarettes din dake a hannunsa idan ya shaƙa har ta hanci yake buso hayakin ta tsabar kwarewa... "Maganar da Jan harshe ya faɗa ta kona min rai, na kwana da ita acikin zuciyata, arayuwata na tsani mutumin da zai yi min magana da tsawa, bayan haka ya kira ni da kaskantacce, har ni zaice wai ban kai darajar takalmin Elder ba? Kawai saboda sun taba taimakona arayuwa nayi aiki a karkashinsu shine har suka samu damar da zasu yi min gori...." rai abace ya faɗa. Jan le6e yace"ni banga abun damuwa ba, yanzu fa tasu ta ƙare, kabarsu suji da kunyar duniya, ai sun tabka babban kuskure da suka amince zasu mika wuya, ban taba sanin elder maloho bane sai wannan karon da ya karaya, saboda son ya'ya ya rufe mashi ido, har shawara ka basu basu dauka ba, saboda dakikanci da shafewar basira, ka jira ka gani da kansu zasuyi danasani...." gaba ɗaya suka bushe da dariya da wannan budaddiyar muryar tasu mara dadin ji... Jan Ido yace"ni abun daya bata min rai, meyasa suka ki bamu sihirinsu bayan sunce sun tuba? Anya ba tuban muzuru su ka yi ba? saboda nayi mamaki wallahi, Mutanan da suka gaji sihiri suka san dadin shi zaiyi wuya su tuba ta cikin sauƙi" Ya ƙarashe maganar yayin da yake miƙa ma matashiyar dake a gafensa hannu cikin sauri ta tsiyaya masa whisky a glass ta miƙa masa ya kar6a tare da kaiwa baki yana kur6a. "Bakin ciki ne da hassada don kada mu samu cigaba, Watakil kuma saboda suna jin fargaban mu farfado da ran kurkukun kaddara, ko kuma suna jin tsoron mu ci amanar su..." acewar jan le6e, wata yar iskar dariya suka sanya.. A hankali jan wuya ya kur6i whisky din dake a hannunsa kafin yace"yakamata mu san abunyi, ni hankalina bai kwanta da alkawarin da Elder ya ɗaukar mana ba na cewa bazai tona mana asiri ba, yadda ya mutu akan kaunar jikan nan nashi kuna tunanin ba zai iya fada masa komai ba idan ya matsa masa? kuma ina kokwanto dakyar in ba makirar tsohuwar nan tasan ni ba, Kada sai mun saki jiki su fallasa mu..." maganarsa ta dan daga hankalin Sauran Elders din.. Jan Le6e yace"bana tunanin Elder zai iya cin amanar mu, mun riga da munsan halin shi mutunne mai rukon amana, ko da zasu azabtar da shi, bazai faɗi sunayen mu ba,...." bai Ƙare maganar ba, Jan wuya yace"hmmm dan adam ba abun yarda bane, ni ban yarda da kowa ba, kawai mu nema ma kanmu mafita..." bai kare maganar ba, jan ido yace"me kake nufi"? Wani makirin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon su, sai da Ya zuki tabar hannunsa kafin yace"ku yi amfani da brain dinku mana, idan har muna so mu zauna lafiya batare da fargabar wani abu ba, to fa dole sai mun kawar da Obie family, saboda sun san komai game da kurkukun kaddara da kuma sirrinmu, tun kafin labarin ya fita duniya ta sani, muyi gaggawar tura masu Evil giants under cover of night, su kashe su duka batare da sanin kowa ba, and no one will suspect a thing, kunga daga nan zamu ci gaba da cin karen mu babu babbaka...." har ya Ƙare maganar tashi elders din basu tanka mashi ba, kamar shawarar tashi ba ta kwanta masu arai ba.. Jan le6e yace"wannan shawarar daka bamu bamai 6ullewa bace, ko kamanta gargadin da jan harshe yayi mana"? ya tambaya yana kallonsa bai jira amsar shi ba ya dasa da cewa"Idan ka manta bari na tuna maka, Har yanzu Elder shi ke a ruke da masarrafinmu, idan muka kuskura muka ce zamu ci amanar shi wallahi zai yi mana tsiya ne! elder zai iya rufa mana asiri amma abu dayane zaisa ya tona mana asiri ya kuma ƙwace sirihin jikinmu shine idan muka ci amanarsa, Saboda shi baya yafewa wanda ya ci amanarsa, Kuma kai kana tunanin Evil giants zasu Iya farmakar Ahlin Obie bayan Elder Yana araye..."? Ya jefa masa tambayar, nan da nan annurin fuskarsa ya ɗauke ɗuff.. Jan ido yace"kayi tunani mai kyau Jan le6e, ba zamu iya cin galaba akan ahlin Obie ba har sai bayan ransa.." Shiru su ka yi na ɗan wani lokaci, young ladies din da ke a kewaye da su sun yi zururu da idanun su, ga gajiyar da suka farayi da tsayuwa ba halin su ce zasu zukunna.. "Abun da ya kamata mu maida hankali akai yanzu, shi ne Mu nemo Jan kunne duk inda ya shiga acikin garin nan, saboda shine mai rauni a cikin mu, Idan mukayi kuskuren da Jami'an isod suka riga mu kama shi zai tona mana asiri ne da zarar sun fara azabtar da shi saboda ba shi da juriya ko kaɗan...." acewar jan le6e, kusan atare suke mike daga kishingiden da suke sam sun manta da batun wani jan kunne dama bawani mahimmanci suke bashi ba, saboda Obie yasa suke tarayya da shi... "jan kunne baida amfani agurinmu, ko da mun kama shi sai dai mu kashe shi, tun da asirin shi ya riga daya tonu..." jan wuya ne ya faɗa da kakkausar muryarsa. Jan ido yace"wayarsa a kashe take, wataƙil ya jefar da ita wani gurin don kada jami'ae su bi diddiginsa, duk da sakarcin shi wani lokacin yana da wayau, amma hakan bashi zai hana mu ƙyale shi ba, dole mu kashe shi..." ya karashe maganar tare da kur6ar giyar dake a hannun sa... "Ranar da muka yi zaman tattaunawa a mafarki, shi kadai ne bai halarta ba, zai iya yiwuwa ya gudu yabar kasar ne.." ya faɗa yana kur6ar whisky dinsa.. "ba zai yi mana saukin kamawa ba, saboda karfin sihirinsa Ɗayane da namu"! Jan le6e ne ya fada rai a6ace.. Jan wuya yace"kubar komai a hannuna, zan nemo shi da kaina, Kuma zan kashe shi..." tuntsirewa sukayi da dariya hahahaha... "Ya batun dawo da ran gidan kurkukun ƙaddara? Kada ku manta Har yanzu muna da sauran dama fa, idan har muka cika sharuɗɗan da ake buƙata zamu jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, na farko zamu iya canza location din gidan kurkukun ƙaddara, abu na biyu in har mukayi nasarar cika sharuddan karfin sihirinmu zai ƙaru, ta yadda ko Elder bazai Iya ja da mu ba, ..." wani irin annurin farin cikine Ya cika su, jin abun da Jan le6e ya fada, Jan ido yace"tayaya hakan zai yiwu"? Shu'umun murmushi jan le6e yayi"kada ku manta, tun kafin ku san Elder na riga ku sanin shi, atare mukayi yawan duniyancin mu, duk wani sirrin shi na sani, wannan maganar dana faɗa naganta ne a rubuce cikin tarik sijnil ƙadar wanda mahaifin Elder ne ya rubuta littafin da alƙalamin shi tun da dadewa..." wata irin shewa suka sanya har saida suka tsorata matasan yan matan dake yi masu hidima. "Amma fa wanda ya riga cike sharuddan a cikin mu, shine zai maye gurbin Elder, shi kuma Elder zai rasa karfin sihirin sa ta yadda bazai iya sarrafa evils din jikin mu ba" Wannan maganar da jan le6e ya faɗa ta faranta ran Jan wuya, sai faman sakin shu'umun murmushi yakeyi aransa harya fara tunanin yadda zai riga su aiwatarwa saboda ya samu karfin ikon Elder, tsabar hadamarsa yafi so yafi kowan nan su karfin sihiri, ta hakane kadai zai iya mayar da su karkashin ikon shi, don ya cigaba da juyasu son ran shi 😳 *💘UNAISA ANGEL💋* A cikin kunnanta ta jiyo sautin dirar Mota a gidan, baiwar Allah a lokaci bacci ne ke kokarin ɗaukarta, tana a kudundune cikin duvet dinta ta kasa runtsawa saboda tunaninsa, ranta ne ya bata shi ne ya shigo gidan.. Jikinta na 6ari ta sauko daga kan gadon, Batool tana akwance gefe daya tayi nisa a baccinta, ta kudundune kanta cikin duvet din ta, Night gown ce a jikin ta Ja, Mayafi ta dauka ta yafa ma kanta, ko takalma bata saka ba, garin saurin ta fita daga dakin har tuntube tayi amma hakan bai dame ta ba, burinta kawai ta je ta dubo in shi ne. Tana fitowa daga dakinsu ta nufi main falo unexpected Ta hango shi yayin da yake tafiya akan stairs, aranta ta ayyana dama yana fita a irin wannan lokacin idan sunyi bacci? tayi kewarsa cikin kwanakin nan daya juya masu baya, daga yanayin yadda yake tafiya ta fahimci babu kuzari atare da shi kamar wanda yasha ƙwaya, Cikin sauri tabi bayanshi sai dai kafin ta karasa tuni Ya shige bedroom dinsa, tana isowa bakin kofar room din tayi knocking shiru babu alamun zai bude mata, cigaba da bubbuga kofar tayi tana ambaton sunan shi tare da yi mashi magiya akan ya bude mata kofar. abun daya ɗaga hankalinta sautin nishin da ya ke saki har cikin kunnanta take jin shi, ganin baida niyar bude mata kuma bai bata iznin shiga ba, hakan yasa batai wata wata ba, ta fara kokarin danna code din kofar da ya ke ya taba nuna mata tun farkon da suka fara shakuwa da junan su, abun daya sa bata taba gigin yi mashi katsadan din ta shiga batare da izninsa ba, saboda ba muharraminta bane, kuma bai dace ta fada masa daki batare da izninsa ba, batasan awani yanayi zata taras da shi ba. Nishin da taji yanayi ne yasa ta razana har bata san sa'adda ta saka code din kofar ta bude ta, a fujajen ta dira kafafunta cikin dakin, wani irin burki taci, lokacin da idanunta suka hango mata shi, har ya cire kayan jikin shi, yana daga tsaye gaban gadonsa ya bata baya, boxer short ne kadai a jikin shi, Ya ruƙe Syringe mai dauke da ruwan allura a cikin shi, yana kokarin caka ta a upper arm din sa.. "My hubby...." dakatawa yayi jin muryarta a cikin kunnan shi, kwata kwata baisan da zamanta adakin ba, hatta knocking din da ta dinga yi baiji ba saboda hankalin sa baya a tare da shi, kawai so yake yayi ma kansa allurar ko ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa, kwana biyu rabon da yayi bacci saboda pressure din daya daura wa kansa na gano su wanene Elders, bai da wani kwanciyar hankali idan har ba gano su yayi ba. A hankali take tafiya tana tunkarar shi, daga bayan shi ta tsaya tana duban gefen fuskarsa daya jike sharkaf da gumi.. "Me ke damun ka? Meyasa ka juya mana baya? Ka hana zuciyata sukuni, saboda kai ko bacci bana iyayi, na rasa gane kanka acikin kwanakin nan! ..." ta fada tana dan girgiza kanta idanunta sun cika da kwalla.. "Why would you inject yourself? Aren't you well?” Ta fada araunace. da wata irin kakkausar murya ya furta“I don't want to see anyone close to me! Don't you dare take one step closer to me! ki fuce min daga daki..." gabanta ne ya faɗi a rude take kallon bayansa, kamar ba daga bakinsa kalaman ke fitowa ba. Ta razana sosai, Cikin rawar murya tace"Husband to be, yau ni kake kora daga dakin ka? Me yake damunka ne? A tunani na damuwarka tawa ce, bai kamata ka boye min ba, Pls ka fadamin zan taimaka maka mu shawo kan matsalar..." numfashi Yaja tare da furzar da shi, ganin taki tafiya yasa shi daka mata tsawar da ta tsoratar da ita “Don’t you dare make me repeat what I said! Get out of my room before I do something bad.” gyada kai tayi, idanun ta cike tab da kwalla ta soma ja da baya tana cigaba da kallon bayansa, ta lura ko kallon ta baison yi, abu kamar aikin asiri in a short time ya canza musu. A hankali ta juya takai hannu zata buɗe ƙofar, sai kuma ta fasa saboda zuciyarta dake azalzalarta akan kada ta tafi, ta tsaya taji meke damun sa. Sakin handle din kofar tayi da tunanin tayi ko karta aikata abunda zuciyarta ke saqa mata, ga tunanin nasihar dadynta amma bata jin zata iya barin shi a halin da yake ciki, juyawa tayi slowly ta nufe shi tana karasawa batay wata wata ba, ta faɗa kan bayansa, she slowly wrapped her arms around his waist, ta daura tafukanta a saman shafaffen cikinsa, lokaci ɗaya ya tsinci kanshi awani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, har baisan sa'adda Ya saki sirinjin hannun sa ba, wata irin kasala ta haifar masa, lumshe idanun shi yayi a hankali yana jin bugun zuciyarta da hucin numfashinta on his neck. Yatsunsa taji akan hannunta yana kokarin banbareta don ya rabata daga jikin shi, cikin sauri ta furta"na roke ka, dan Allah, dan soyayyar da kake yiwa manzon Allah SAW kada ka kore ni, ka barni atare dakai, inaso naji meke damunka, ko ban sama maka mafita ba, zan tayaka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, baka taba barin mu cikin damuwa ba, taya kake tunanin ni zan iya barin ka a mayuwacin hali irin wannan"? Kalamanta sun sanyaya zuciyarshi, sai dai baya jin zai iya fada mata abunda ke damunsa, baisan ya zasu dauki abun ba idan suka ji cewa kakansa ne Elder mamallakin gidan kurkukun kaddara, mutumin daya azabtar da rayuwarsu, Ya Ilahi, Ji yake kamar kowa zai juya masa bayane.. wata irin kara mai tattare da bakin Ciki Ya fasa, tuni shatun jijiyoyin goshinsa dana wuyansa suka fito ruɗu ruɗu saman fatarsa, tun da ya yi tsawar gaban ta ya faɗi rass hankalin ta ya ƙara ta shi duk tabi ta ruɗe.. Nauyin jikin shi daya sakar mata ne yasa ta gaza jurewa saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, aikuwa gaba daya suka faɗa saman bedmattress dinsa. a rubda ciki ya faɗa yayin da take akwance saman bayansa, sam sun kasa motsawa har na tsawon mintuna, dakyar ta yi kokarin raba jikin ta daga na shi, da wata irin kasala ta mike zaune tare da zuba mashi idanunta da suka cicciko da kwalla. Duk da batasan meke damunsa ba, amma hankalinta ya tashi ta kuma ji tsantsar tausayin sa acikin zuciyar ta, jikinta harya fara daukar ɗumi saboda zafin jikin shi da ta goga silar haɗuwar da fatarsu tayi. ya kasa jure radadin da yake ji ne, baiso ya bayyana rauninsa a fili ba, duk yadda yaso ya danne damuwarsa ya kasa bawan Allah. Cikin shesshekar kuka ta dinga tambayar shi meke damunshi har ta haƙura ta yi shiru saboda yaƙi furta kalma, daidaita nutsuwarta tayi cikin sanyin murya ta fara zuba mashi kira'ar alqur'ani mai tsuma zuciya, lokaci ɗaya ya fara jin tamkar ana wanke damuwar da ke acikin zuciyarsa, bacci ne ya ziyar ce shi a hankali ya fara lumshe idanun.. bata kaiga dire ayar data janyo ba, kwatsam ta fara jin gyangyaɗin bacci har bata san lokacin da ta sulale gefen sa ta kwanta ba, Kafin wani lokaci, wani wahalallan Bacci yayi awon gaba da su, ikon Allah kenan bai kaiga yin sedative injection din da ya so yayi ba, sai gashi silar karatun qur'anin da Unaisah tayi masa yasa shi yin bacci...💔 sai da suka shafe tsawon awanni bakwai suna yin baccin, tun karfe ɗaya da rabi na dare, har karfe bakwai na safe basu farka ba kamar wadanda suka sha sleeping pills. Tun da garin Allah ya waye Batool taga babu Unaisah a dakin, har toilet ta duba bata ganta ba, hankali atashe ta nufi dakin aunty ummi don ta dubo ko taje can, tana zuwa taga babu unaisah nan ta fada ma Aunty ummi bata ganta adaki ba, hankalinsu atashe suka fito neman ta, sako da lungu na gidan sun duba basu ganta ba, kuma basu kawo ma ransu tana adakin Chief ba, har dakin Taj suka shiga a lokacin yana a zaune kan darduma Yana jan cazbaha bayan sun gaishe da shi, Ummi ta tambaye shi Unaisah batazo nan ba, yace musu ko gifcin ta bai gani ba amma kada su damu yasan duk inda taje ba zata wuce cikin gidan ba, ya fada tare da dauko wayarsa ya danna mata kira tana ta ringing ba'ay picking ba.. __________________________________🔥💋 A hankali ya soma kokarin bude idanunsa da sukayi mashi nauyi ga wata kasala data baibaiye jikin shi, jin hucin numfashin mutun a gefen shi kasa kasa cikin natsuwa ya ke fita, yasa shi saurin karasa bude idanun nasa. tamkar wanda ya yi loosing memory dinsa, ya ɗan razana da ganin mace a kwance saman gadon shi tana bacci, kuma suna fuskantar juna, kitson kanta yabi da kwallo, dan mayafin da ta yafa ma kanta tuni ya bar jikin ta, kwakwalwarsa ce ke kokarin tariyo masa abun daya faru! Nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke, tunawa da komai daya faru tun farkon shigowarta, yayi mamakin baccin daya sha, wani iko na Allah kwata kwata babu inda keyi masa ciwo, saima wata lafiya dayaji a jikin shi, kamar ana dawo masa da kuzarinsa, yana ji aransa silar kira'ar qur'nin da Unaisah tayi mashi ne, kuma dama shi qur'ani waraka ne. Slowly ya zame hannayensa daga kan gefen fuskarshi, Ya daura tafinsa saman lallausar sumar kanta da aka kitsa, A hankali Yake shafa gashin nata har na tsawon mintuna, kafin ya dan dago da face din tata, hakan ne ya bashi damar kallon fuskarta dakyau, wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, yayi fatan ace bai farka daga baccin daya dauke shi ba, saboda kwanciyar hankalin daya samu.. Tunawa da sallar asubahi da bai yi bane yasa shi saurin mikewa ya sauka daga kan gadon, shaf shaf ya fada toilet yayi wanka kafin Ya dauro alwala, Ya fito waist dinsa daure da towel, Ya nufi walk in closet dinsa Ya shirya kansa cikin jallabiya, kafin ya nufi prayer corner dinsa after Ya gama sallar, yayi addu'o'i har da hawayensa, kafin daga bisani Ya mike Ya nufi gadon, a hankali ya kwanta yana fuskantarta, yaso ya tashe ta tayi sallah sai dai ya kasa yin hakan saboda bai son ya katse mata baccin ta, ya lura kamar ba ta samu isasshen bacci, ya fahimci hakanne saboda alamar daya gani saman kwarin idanunta da sukayi ja, kuma yasan shine silar shigarta halin da take a ciki, tsantsar tausayinta da kaunartane suka mamaye zuciyarsa ko gajiya da kallon ta ba ya yi, mutumin da saboda kamun kansa da gujewa abun da zai sabawa mahaliccinsa bai ta6a bari ya ke6anta kan shi da macen da ba muharramarsa ba, balle har su hada shimfida, amma yau saboda halin da yake a ciki ya kasa ankarar da kanshi kuskuren yin hakan saboda a buqace yake da son samun wanda zai kwantar masa da hankali.. Akan idonsa ta fara yamutsa pinkish lips dinta da suka bushe ƙamas. ziraran eye lashes dinta sai kerma suke yi, Tunawa yayi da ranar farko daya fara ganin fuskarta lokacin data kira sa video call da kuruciyarta, a ranar kasa runtsawa yayi saboda tunanin yar tahalikar nan.. Da alama baccin nata ya ƙare, ƙoƙari take ta bude idanun ta da suka kumbura saboda kukan da ta sha, daura tafin hannunsa ya yi a saman gefen fuskarta, a ɗan firgice ta zare idanun ta. kaitsaye suka shiga cikin nashi wani irin shock taji ganin Chief agabanta, ganin yadda ta ruɗe ne yasa shi sakin tsadaddan murmushin nan na shi, baisan ya ƙara jefa ta a rudu ba, duk tabi ta dabarbace sam takasa ci gaba da kallonshi, saboda yanayin data tsinci kan ta.. "Na samu bacci silar karatun alkurnin da ki ka yi min, I can't thank you enough baby..." ya faɗa tare da dan shafa sajen gefen fuskarta da ya kwanta luff, shiru tayi tana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa saboda kusancin da suke da juna.. “I’m so sorry, I made you cry, nima bada son raina ba, banso kika ga raunina ba, na kasa jure abunda ke damuna ne.." ya fada yana kare mata kallo. In a cool voice tace"ba laifin ka bane, daga zuciyarka ne, I understand that something bad happened that put you in this difficult situation of worry, but I want you to know that I will never leave you in such a situation, It is my duty to calm you down, and I will help you find a solution after that, I will remind you, no matter what, kada ka bari hankalinka ya gushe, jarumtakar nan taka da nutsuwarka su nakeso na gani atare da kai, komai ya same mu arayuwa muyi hakuri mu mika lamuran mu ga Allah shine zai nema mana mafita". har cikin ranshi yaji dadin kalamanta masu sanyaya zuciya, harya fara tunanin irin rayuwar farin cikin da zasuyi idan sukayi aure, zai more rayuwarsa saboda samun mace tagari kamar ta. "Ka fada min meke damunka pls, amma idan sirrinka ne da bai kamata in sani ba, to kada ka sanar dani, kuma koda baka fadamin ba, nayi maka alkawarin zan tayaka da addu'a Allah yaye maka damuwarka ya kuma kawo maka mafita acikin lamuranka" bai san sa'adda ya saki murmushi ba wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana, saboda dadin kalamin ta, ita kanta batasan ya akai ta samu kwarin gwiwar furta masa su ba, kamar ancire mata jin nauyin sa hada karin tausayinshi daya mamayeta. “My secret is yours, Unaisah, Even if no one understands me, I’m sure you will understand me, sai dai bana jin zan iya fada maki abunda ke damuna a halin yanzu saboda banaso na daga hankalin ki, amma nasan zaki ji agurin daddynki idan na fada masa" cike da kasala ta dago da kanta, ta fuskance shi idanunsu suka shiga cikin na juna, hakan yasa numfashinsu ya dinga gaurayewa dana juna saboda qarin kusancin da suka samu da junansu.. Tsananin tausayinsa ne ya kara kamata, ganin yadda cheeks dinsa su kayi suntum, reddish eyes dinsa sun kara ciza launinsu hasken ya rune zuwa ja, bakomai take hangowa cikin idanun nasa ba face tsantsar damuwa da tashin hankali. Cikin muryar raɗa ya furta “Thank you for taking care of me, I can't wait to have you as my wife…” kunyar shi ce ta kama ta, dama dakyar take jure kallansa saboda nauyinsa da take ji.. "Ku yi hakuri, jiya na bar ku kuna ta jirana, ban kuma kira na fada maku bazan dawowa ba, banji dadi ba" "Kada ka damu, komai ya wuce.." "Kin lura da time..." ya fada tare da nuna mata katafariyar agogon dake manna jikin bangon dakinsa .. ' kallo daya tayi mata tare da jinjina kanta.. "Ki shiga toilet dina ki yi alwala... Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet dinsa, tana tafiya kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai, gabanta nata faduwa, kwata kwata bata son shiga toilet dinsa saboda glass wall din dake gare sa wanda ke a waje na iya ganin komai na cikinsa, batasan ya zatayi amfani da shi ba, abun da take ma zullumi kada Chief ya gane mata budurcin ta anata wautar 😂 Agaban kofar toilet din ta tsaya tana dan zazzare idanunta kamar wadda tayi ma sarki karya fadawa suka turketa. ita a wurin ta kauyacine ta tambaye shi ya ake amfani da toilet din, kanta ya kwance, ranta ne ya bata ta juya baya taga idan yana kallon ta, juyowar da za ta yi keda wuya, idanunta suka sauka akan nashi yayin da yake gyara kwanciyar shi. Idanunta ne suka dinga nuna mata kamar murmushi ya ke sakar mata, zuciya da sake sake saita dinga ayyana mata da gangan yace ta shiga toilet dinsa don ya ganta.. lumshe idanun shi ya danyi, lokaci daya ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo masa maganganun da suka tattauna tare da grandpa dinsa. "Wife to be...." can kasan makoshi ya furta.. Kamar jira take ya kira sunanta, jikinta na bari ta baro bakin toilet din, don batajin zata iya shiga. Daga gaban gadon ta tsaya tare da amsa mashi "Naam ..." "Idan ba zaki manta ba, last time mun yi magana akan hotunan dake a cikin diary din yarinyar nan, har yanzu baki tuna komai dangane da su ba..."? Ya tambaya akagare da son jin amsar ta, shiru tayi jim tana kokarin tunanowa, bakomai ya fado mata arai ba face hotunan nan na dakin su da suka tsin ta, dama tana ta kokwanton kamar a cikin diary din suke. Cikin sauri ta furta"Na tuna, bari naje na dauko maka" Calmly ya furta okay, cikin sauri ta fuce daga dakin har wani ajiyar zuciya take saukewa. Mikewa zaune yayi tare da jingina bayansa jikin head board dinsa, dawowarta kaɗai ya ke jira.. Bayan ta koma dakin bata iske kowa ba, sai da tafara shiga toilet ta watsa ruwa tayi alwala sannan ta fito ta dauko hijabi tayi sallah a tsanake, bayan ta gama ta dauko hotunan data ajiye a cikin drawer chest, cikin sanda ta wuce part dinsa batare da wani yaganta ba. After some minutes Yaji motsin shigowarta, da sauri ya kalle ta, karasowa tayi tare da samun wuri gefen gadon ta zauna, hannun ta ruke da hotunan ta miƙa masa"tun da jimawa na tsince su a karkashin gadon mu, a lokacin ina tsaka da neman wayata, bansan su wanene akan hoton ba, kuma ban san waya kai hotunan dakin mu ba.." kar6ar hutunan yayi daga hannunta, ya shimfida su akan tafinsa tare da daura idanunsa akansu, lokaci daya yanayin fuskarsa Ya nuna tsantsar radani da mamaki.. "A daren ranar da muka baro part din daddyna, mun dawo nan saboda wayata da nake nema, ni da Batool muna tsaka da neman wayar acikin dakinmu, kawai sai naji Batool tace min a ina kika samu wadannan hotunan? Nan nake fada mata inda nagansu, sai tace To ay mutumin aunty Ummi ne wannan, Ita kuma wannan kin tuna ƙawarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue, da tayi wannan maganar nan take sai na tuna ta, itace kawar aunty Ummi mai suna NATASHA, sai nace mata Amma taya akai tasan Mutumin aunty ummi ne wannan, shine tace Zata faɗa mini, amma dan Allah kada in fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a gargadin ta, akan bata son ta ta6a mata waya, sai nace mata naji ba zan fada ma Aunty ummin ba..." tun da tafara Kora masa jawabi, Chief owais ya kafe ta da idanunsa da suka cika da al'ajabi "Shine tace min wai ranar aunty ummi ta shiga toilet aka kira wayarta, garin ta dauka kawai tayi picking call din, nan tagan shi kwance acikin kwamin wanka, kumfa ta lullu6e jikinsa sai fuskarsa kadai ta iya gani, a fahimtana shi baiga fuskar Batool ba, ita kadai ce ta gan shi watakil ta kare front camera din wayar da yatsan ta tun da ba sanin takan waya tayi ba, koda ta fada mini hakan, mamaki ne ya kamani, har na fara kokwanton maganarta, saboda nayi mamakin ta yadda har ta iya ruke kamannin fuskar mutumin da tagani farat ɗaya a video call bayan haka waye ya kawo hotunan adakin mu"? Ta fada tamkar tana tambayarsa.. "A tunanina Aunty Ummi ba zata taba yin gangancin da zata kawo hotunan dakinmu ba, tun da har ta ta6a gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bata so tasan sirrin ta" tunkan ta karasa maganar ta lura da yanayinsa da Ya sauya, shiru tayi tana jiran jin me zaice.. Miƙa mata hoton Alhajin yayi"me zan yi da shi" ta faɗa tare da ruke hoton a hannun ta. "Kin san wanene wannan mutumin"? Girgiza mashi kai tayi.. Murmushin takaici ya dan saki tare da cewa“He is your mom's uncle, Alhaji Musa Wadata, former president of our country After that, his sister Hajiya Laura is my daddy's second wife" Bai karasa maganar ba, ganin yadda ta zabura ta mike tsaye tana zazzare idanun ta cike da rudu akan fuskarta.. Labbanta na kerma tace"tayaya hakan zai yiwu? Me ya kawo hotonsa a dakin mu"! "Ina zargin mutumin nan yana ɗaya daga cikin Elders na gidan kurkukun kaddara, in har ya zamana dagaske hotunan nan sune acikin diary din yarinyar, a labarin da kika bani, ta ta6a fada maki nickname din mahaifinta ne Jan wuya, sannan a shafin farko na diary din ta akwai nickname din sa a rubuce, jan wuya kuma yana ɗaya daga cikin Elders kamar yadda Danish ya faɗa mun nicknames dinsu da suke amfani da su a gidan kurkukun, bayan haka kawar ummin nan, zai iya yiwuwa mahaifiyarta ce ko marikiyar ta ..." tashin hankalin da ba'a saka mashi date, da tsantsar rudani suke kallon kallo atsakanin su, cikin rawar murya tace" In kuwa hasashenmu ya zama gaskiya, to kenan bai rabu da Aunty Ummi ba? Yana atare da ita, Sannan shine ya sadaukar damu! Ni da babyn Uncle shureim..."? Dakatawa tayi da yin maganar kamar an tsikare ta, lokaci daya takuma zare idanunta alamar ta tuna wani abu "Are you okay," ya faɗa yana dubanta, Jinjina mashi kai tayi adabarbarce tace"shine.. ! wallahi shine.. mutumin nan shine Jan wuya mahaifin Unaizah, saboda Ina zargin Yarinyar Wurinsa yar uwar Unaizah ce saboda kamannin su ya 6aci, kamar twin sister din ta ce, a ranar dana fara ganin ta sai da na razana..." Nan ta labarta masa farkon haduwar su da Zeenatu, wlh sai yanzu ya gane dalilin dayasa farko daya daura idanunsa akan hoton unaizah yai tajin kamar yasanta aran shi, ashe saboda kamanninta da zeenatu ne, Ya San ta, tun da kuruciyarta, lokacin da Hajiya sarah take zumunci da hajiya saratu tana yawan zuwa da ita estate ɗinsu kafin daga baya ta ɗauke kafa da zuwa.. gaba daya sun rude da lamarin, Cikin sauri ta kuma cewa"bayan haka, rannan ina tsaka da neman Sim card din da daddyna ya saka min acikin backpack din Unaizah, aranar ne ma Na curo texbooks din ina dudduba su, ina da tabbacin silar neman sim dinne yaja har hotunan suka faɗo daga cikin diary din batare dana ankara ba, wani abu daya daure min kai, ina a zaune tsakiyar gadonmu Ina tsaka da neman sim din saiga sajeed Ya shigo dakin mu kamar baya a cikin hayyacin shi..." nutsuwa Chief yayi yana sauraranta yayin da take basa labarin, idan tana bada labari tiryan tiryan babu kuskure kamar yar jarida sai ya dinga tuna mommynta, ya faminci halayenta da dabi'unta sunfi karfi ta bangaren mommyn ta. "Da ya sake jaraba Kiran layin wayarsa, kwatsam sai muka ga kiran ya shiga sai dai ba'a daga ba, daga baya munyi waya da me lambar har na bata hakuri nace wrong number ne na kira, amma sai na nemi alfarmar inaso mu dinga zumunci da ita saboda ta kwanta min arai na, toh daga nan ne muka shaku da junan mu, kusan kullum sai ta kirani, ko bata kira ba, to ni zan kirata ne, wlh bantaba sanin mommyna bace, sai a ranar dana kira layin ta, bayan ka fayyace min komai daya faru da ita, nayi al'ajabin taya akai sajeed yayi guessing number din zeenatu"? Dafe kansa yayi da tafin hannunsa, gaba daya suka zurfafa tunanin su. "A labarin da kika bani, kince Sajeed Ya fada maki zai iya gane fuskar mahaifinsa Idan ya gansa ko"? Jinjina mashi kai tayi"Eh, haka ya faɗa mini, kuma wani abun daure kan nidai dana kalli hoton akaro na farko sai naga sunyi kama da Sajeed kamar yayi kakinsa.." baisan ya akai ya kara jin ƙarfin gwiwa atare da shi ba. "Babe abun da nakeso dake, komai da muka tattauna a tsakaninmu mubar shi a matsayin sirri, kija baki ki yi shiru, har yanzu bamu kai ga tabbatar da abun da muke zargi ba tukunna, masu iya magana sunce idan baka iya kama 6arawo ba, shi barawon sai ya kama ka, ina fata baki fada ma auntynku Ummi kinsan labarin su ba"! Jinjina mashi kai tayi"ban fada mata ba" "Good Girl, kibarni da ita, ni zan tuntubeta dakaina, agurin ta zan samu karin bayani dangane da shi, in har ta bamu hadin kai, zamu yi amfani da ita gurin kama sa, don ba ƙaramin shaidani bane, mutunne mai hadarin gaske, tunkararsa abune mai wuya, kamasa bazaiyi mana sauki ba, dole saida dabara sai kuma mun hada da addu'a..." Har ya ƙare maganar bata farfado daga duniyar tunanin data lula ba, maganganun Unaizah ne suka fara dawo mana acikin kwakwalwarta, tabbas za ta yi farin ciki kuma zatayi bakin ciki idan hasashen su ya zamana gaskiya akan Uncle din mommynta, hakan na nufin Unaizah yar uwarta ce ta jini! ya ilah, wlh Alwashine ta daukarwa kanta, sai ta kashe shi da hannun ta.. Cikin sanyin murya tace“idan har muka tabbatar da zarginmu akansa, nima zan bada gudummuwata gurin hukunta shi, saboda nayi ma Unaizah alƙawarin abu biyu, kafin mutuwarta, ta rubuta min wasika don in ba Mommynta da daddynta su karanta, abun da yasa ban baka wasikar ba, saboda amana ce ta bani, sannan ta roke ni akan in daukar mata fansar cin zalun da mahaifinta yayi mata, tana so in kashe shi da hannu na..." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sarke makoshin ta, sakamakon tunawa da Unaizah, ta fama raunin da ke kwance a cikin zuciyarta. Sauko wa yayi daga kan gadon, ya tsaya daga gabanta suka fuskanci juna, tuni ta jima da sakin hoton hannun ta Ya fadi kasa. cikin shesshekar kuka tace"Ka taimaka min dan Allah, nasan bani da karfin da zan iya kama shi, amma in har kuka kama min shi zan iya kashe shi, wlh na tsani mutumin nan fiye da yadda na tsani mutuwa ta, ban taba ganin mutun mara imani, tantirin fasiki kuma azzalumi irinsa ba, inaso yaji radadin da Unaizah taji a lokacin da take akan gabar mutuwa, zan hada masa jini da majina akan fuskarsa, fiye da yadda Unaizah tayi kukan bakin cikin daya kunsa mata, Ka taimaka min hubby, ku barni in kashe shi na roke ka..." hawayen dake sauka kan kuncin ta ya soma sharewa da tafin hannunsa. "Kukan ya isa haka Unaisah, in har ya zamana shi ne mutumin da muke zargi, ni Chief nayi maki alkawarin zan taimaka maki gurin cimma burin ki akansa, koda hakan zai saba ma doka ne, Ni zan yi maki hanyar aiwatar da hakan ta cikin sauƙi, a hannun ki zai mutu Unaisah, sai kin azabtar da shi kafin ki kashe dan iskan..." batasan sa'adda ta soma sakin murmushin farin ciki ba, gani take kamar har ma sun riga da sun kama shi saboda zumudin ta aika shege lahira, ada fansar mutun daya tayi niyar dauka akansa amma ayanzu da take zargin Uncle din mommyntane, Sai ta kara fansar mutun biyar akansa, Fansar auntyn Ummi da fansar abun da yayi ma mommynta, da kuma fansar prisoners, Cikon fansar mutun na biyar da zata dauka shine Uncle Uzair in har akayi bincike aka gano sune suka kashe shi 🔥 Batai aune ba taji ya manna mata peck on her Cheeks, cike da jin kunyar shi ta sunnar da kanta kasa.. Bata bar bedroom dinsa ba, har saida suka yi breakfast atare, suka ciyar da junansu kafin daga bisani tay mishi sallama bayan ta roke shi ya taimaka ya sauko down ya gaisa da su aunty ummi da batool saboda sun damu da shi yace mata karta damu zai zo su gaisa.. *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️* *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* ~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Daga Alƙalamin Boss Bature💋✍️* ZEENATU💗 Tana a zaune saman swing chair dake a cikin katafaren garden din gidan, fuskarta sam babu walwala sai tarin damuwar da tayi mata katutu acikin zuciyarta, ta yi zurfi cikin tunaninta idanunta suna akan Peacocks din da ke shawagi cikin garden din.. Da matsakaicin gudu motar Alhaji Musa ta kunno kai ta cikin main gate din gidan ta nufo parking space, yana hakimce a backseat din motar idanunsa suka hango mashi ita ta cikin glass window, umarni ya ba drivernsa ya tsaya kusa da ita. Horn ɗin motar ne ya razanar da ita, a firgice ta ɗago da idanunta da suka kaɗa sukai ja ta dubi motar da a daidai lokacin tayi parking, fitowa yayi daga cikin motar, like always fuskarsa a murtuke ya ɗauki wankan suit. Ya saba idan ta ganshi da gudu zata nufe shi tayi hugging dinsa amma yau ya sha bamban, tunda ta kalle shi sau ɗaya ta kawar da idanunta gefe ɗaya, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin sa ya yi ba. Daga gefenta ya zauna tare da ɗaura tafin hannunsa saman kanta ya janyota a hankali ya kwantar da kanta saman kirjin shi, sai lokacin ta samu damar fitar da abunda ke ranta, fashe mashi tayi da kuka. A ruɗe ya soma shafa bayanta da tafinsa, tare da tambayar ta meke damunta? Wa ya ta6a mashi babynshi? Ko bata jin dadi ne. Lokaci ɗaya duk yabi ya rude saboda ko kaɗan baya son damuwar Zeenatu. Cikin shesshekar kuka ta ce, "Daddy, Yaya Shureim.." "Meya yi maki?" "Daddy, he stopped paying attention to me bana jin dadin share ni da ya ke yi, I don't know what I did to him, he's completely changed towards me" tun da ta fara magana ya haɗe rai kamar bai ta6a yin dariya ba "Aunty Benazir ma ta rage kula ni, ni gaba daya zaman gidan bai yi min daɗi daddy, mommy ma bata da lokaci na, in ta dawo daga office agajiye bata kulani sai ta shige daki ta kama bacci, da anjima kuma in ta farka bata fira da ni, sai dai ta je gurin mommy Layla su yi fira, shima ya Shureim din baya fira da ni da aunty Benazir ya ke yi kullum suna a tare, kaima idan ka tafi sai tsakar dare kake dawowa lokacin na riga da na yi bacci, ni gani nake kamar baku sona, baku damu da ni ba, baku bani kulawa yadda ya kamata..." Ta ƙarashe maganar cikin shesshekar kuka. Bai ji dadin halin da take a ciki ba, ya fahimci kaɗaici ne ke damun ta, har cikin ranshi bai ji dadi ba. Shafa sumar kanta yayi cikin sigar lallashi ya ce "Stop thinking that way, my princess, bana so kina sanya damuwa a ranki, you're more important to us than anything, please ki daina fadin ba'a sonki ko ba a damu da ke ba, sanin kan ki ne bani da abu mafi soyuwa da ya wuce ke, ko da kowa zai juya maki baya ki tuna ni ina atare dake, koda bana nan kina a cikin zuciyata..." kalamai masu tausasa zuciya ya dinga faɗa mata har ya samu ta ɗan lafa da kukan. Tighting dinta ya yi a kirjinshi ta yi lamo fuskarta sharkaf da hawaye sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi. "Daddy yaushe zan cigaba da karatu? Ka ce sai nayi aure zaka barni in cigaba, dan Allah daddy ka yi mini auren, saboda inaso in dinga zuwa makaranta harma in haɗu da ƙawayen da zamu dinga zumunci atsakanin mu, saboda na fahimci babu tsara na agidan nan shiyasa ba'a zama a yi fira dani...." Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, ya lura da akwai abun da ya 6ata mata rai shiyasa take fadin ta cikin ta. "Kada ki damu, Nayi maki alkawari ƙarshen shekarar nan, zan aurar dake, kuma zaki cigaba da zuwa makaranta" Murmushi ta saki saboda taji dadin maganar sa, ba karamin ɗebe mata kewa yayi ba, ya bata lokacin shi sosai sun daɗe suna fira kafin suka sauko daga kan kujerar, hannunsu cikin na juna suka nufi falo. Lokacin da suka shigo falon, A dining Suka hango mutanan gidan sun hallara suna cin lunch din su, ran Alhaji Musa Ya 6aci ganin yadda su ke yin walwala, hakan yasa shi yarda da maganar Zeenatu, wato basu damu da Zeenatu ta ci abinci ko bata ci ba. Fusgar hannunta ya yi ya ja ta suka nufi dining din, takun tafiyarsa ne ya ja hankulansu ga duban shi, har saida gabansu ya fadi ganin yadda ya murtuke fuska. Yana ƙarasowa ya sanya hannu ya damƙi table cloth din da aka shimfiɗa kayan lunch din saman shi, ya hankade shi gaba daya kayan abincin suka 6are kan floor, a sukwane suka miƙe suna kallon shi cikin ruɗu. A tsorace Zeenatu ta la6e bayansa jikinta na kerma.. Hajiya layla da ranta ya 6aci ta watsa mashi harara tare da cewa, "Wannan wani irin wulakanci ne? Ta ya muna cin abinci zaka 6arar da shi kamar wani ƙaramin yaro.." Bata ƙare maganar ba ya daka matsa tsawa tare da nuna ta da yatsan shi, "Karki kuskura ki sake min magana idan baso kike in 6ata maki rai ba..." sakin baki ta yi sototo tana kallon sa, hankalin hajiya Sarah ba karamin tashi ya yi ba, sai yarfa hannayenta take yi tare da marairaice masa fuska don yayi haƙuri. "Haba Musa, wani irin almubazzaranci ne wannan? Yanzu abun da kayi ka kyauta fisabilillah? Laifin me mu ka yi maka? Meya sa zaka zubar mana da abinci?" Alhaji Ubaid ne ya faɗa cikin fushi, Harara ya watsa mashi rai a 6ace ya ce, "In har Zeenatu ba zata ji dadi a gidan Ubanta ba, to kuwa babu wanda zai zauna lafiya a cikinku! Saboda rashin hankali kuna nan hankalinku kwance, kun bar min yarinya a waje cikin kaɗaici? Wato baku damu da ita ba, babu ruwanku cikinku kaɗai kuka sani ko!" Da tsawa ya ƙare maganar kamar zai doke su, Benazir da Shureim sun saki baki suna kallon ikon Allah, sam sun kasa magana.. "Babe, wllh ba haka bane, bansan me Zeenatu ta faɗa maka ba, amma wlh bamu manta da ita ba, ka tambaye su ka ji saida na aika Tani bedroom dinta don ta kira ta tazo ta ci abinci, bayan Tani ta dawo ta ce min Zeenatu tace ba zata ci abinci ba, wai bata jin yunwa, dama kwanan nan fama na ke yi da ita, na rasa gane kanta, da kaina na je ɗakin na matsa mata akan ta zo mu ci abinci amma taƙiya shiyasa na ƙyaleta, na jira saika dawo in sanar da kai..." Harara ya watsa musu, tare da jan dogon tsoki, ya juya yana cika yana batsewa ya nufi part dinsa.. Hajiya layla ji take kamar tabi bayan shi ta shaƙe shi, saboda haushinshi da ya cikata, "Wlh Musa bai da mutunci, ni wlh na gaji da wulaƙancin da ya ke yi mana, don kawai muna zaune agidansa...? Bata ƙare maganar ba, Hajiya Sara ta juya tabi bayan shi, bayan tafiyar ta Shureim da Benazir suka haɗu suna rarrashin mommynsu, Zeenatu dake kallonsu duk tasha jinin jikinta ganin abun da ta ja musu... Fashewa ta yi da kuka tare da juyawa jikinta na kerma ta nufi hanyar ɗakin ta, bata kaiga ƙarasawa ba Dr. Shureim ya bi bayan ta da sauri ya taso ƙeyarta ya dawo da ita dining din, zaunar da ita ya yi kan kujera ya tsareta da tambayar me ta faɗa ma uncle Musa, cikin shesshekar kuka ta zayyana musu komai, cike da takaici Benazir ta ce, "Haba Zeenatu, me yasa zaki mana haka? Idan mu muka 6ata maki rai why ba zaki faɗa mana ba uhum? Kinsan halin uban naki, yanzu gashi kin ja ya zubar mana da abinci hankalinki ya kwanta ko? Kin shiga tsakanin mu da shi..." Fashewa ta kuma yi da kuka, Alhaji Ubaid ya ce, "Ya isa haka pls, ni banga laifin Zeenatu ba, gaskiya bakwa kyautawa, ku yakamata ace kuna jan ta a jiki, tunda ku kaɗaine ƴan uwa dake a kusa da ita, bayan haka yarinya ce sai kuna haƙuri da ita.." Ta6e baki hajiya Layla ta yi, "Ni Zeenatu bata yi mini komai ba, in ita bata da cikakken hankali ai shi uban nata da hankalinshi ko? In ba rashin wayau ba meye na ɗaukar maganar yaro? Ta ƙare maganar tare da jan tsoki ta juya ta bar dining din, da sauri Alhaji Ubaid yabi bayanta don ya lallashe ta. Cikin shesshekar kuka ta ce, "Am really sorry, idan na 6ata maku rai, ni ban faɗa masa don yayi maku faɗa ba, Aunty benazir am sorry, yaya Shureim kaima ka yafe min.." Tausayinta ne ya kama su, har su ka ji basu kyauta mata ba, lallashinta su ka koma yi. "Nasan nine na 6ata maki rai ko?" Ya tambaya yana kallon ta, yamutsa fuska ta yi tare da sunnar da kanta ƙasa, Kallon Benazir ya yi suka haɗa ido, tashin hankali! gaba ɗaya sun gane inda Zeenatu ta dosa, gashi a halin yanzu Dr Shureim baya jin sonta, tun ranar da Allah ya haɗa shi da Aisha, ya gane ba son aure yake ma Zeenatu ba, rashin Aisha ne yasa har ya kula ta da sunan soyayya, amma a zahirin gaskiya baya jin zai iya haɗa Aisha da wata mace a duniyar nan, bai ma ta6a lura da Zeenatu tayi masa ƙaranta ba sai ranar da idanunsa suka yi mashi tozali da Juliet ɗinsa. Ƙumshe dariya Benazir tayi, don ta riga da ta gane me ya Shureim ke tunani aransa, ɗan ja gefe ya yi yadda zai kauce ma Zeenatu kada ta ji mi zai ce don yasan zata iya fahimta, cikin harshen larabci ya ce, "Ya zanyi Benazir? Wlh tun da na ga Ummi na ji kamar ancire mini son Zeenatu, yanzu soyayyar da nake mata ta ƴan'uwantaka ce bata aure ba." Itama cikin harshen larabci ta ce, "Ya shureim sau nawa ina kokarin ankarar da kai akan Zeenatu uhum? Saida na ce maka tayi maka ƙanƙanta, ba sa'ar auranka bace, duk da ba haramun bane don ka yi soyayya da ita, amma ni dama nasan mace ɗaya ce a cikin zuciyarka, ka so zeenatu saboda rashin Aisha, yanzu kuma Aisha ta bayyana, in ka ji zaka iya haɗawa biyun tau, ka dai san Zeenatu da kishi, kuma tsakani da Allah da raini ka haɗa Aisha da Zeenatu yar cikin ta.." Ta faɗa tana dariya, gaba ɗaya maganganun da suke yi Zeenatun bata fahimtar abun da suke fadi saboda basu ɗaga murya ta sadda kanta ƙasa. "Ka daure ya Shureim, kada ka karya mata zuciya, ko da ba za ka aureta ba, ka taimaka ka kwantar mata da hankali, wlh tana sonka, kaga ta fara shiga damuwa, in ya so daga baya zamu san abun yi..." Jinjina mata kai yayi tare da mayar da hankalinsa kan Zeenatu ya matsa wurinta, cikin sanyayyar muryar nan tashi ya ce, "Am really sorry rabin raina, na gane kuskurena, ke ce baki fahimce ni ba Zeenatu, taya zan daina kula abar kaunata uhum?" Murmushi ta ɗan fara saki.. Ruƙo hannunta Benazir tayi a cikin nata, "Pls Zeenatu, ki daina biyewa zuciyarki, wallahi babu abun da ya canza na daga kaunar da mu ke yi maki, mun damu dake, muna son ki rabin ranmu, daga yanzu komai a tare zamu dinga yi in sha Allah, mu ci abinci atare, muyi fira atare, muyi kallo atare, mu yi gym atare, kai har tilawar alqur'ani zamu dinga yi kullum tare da ya Shureim." Murmushin farin ciki ta saki ga wani dadi da ta ji. "Yanzu ma ba zamu barki da yunwa ba.." ta faɗa tare da kwala ma Tani kira, jim kaɗan sai gata ta nufo su, tana ganin kayan abincin da aka 6arar a ƙasa ta daura hannu akai tana tambayar meya faru.. "Pls ki kwashe kayan abincin da ya zube ki canza mana wani, sannan ki turo wata maid din ta goge floor din, muna jiran ki." Benazir ce ta fada, jikin Tani na 6ari ta amsa da toh ta zuƙunna tana tattara kayan abincin, bayan ta gama jera su a tray ta nufi kitchen.... ______________UNCLE MUSA Bayan ya shiga bedroom dinsa yana ƙoƙarin fara rage kayan jikinsa, wayarsa ta ɗau ruri. zaro ta yayi daga cikin aljihun wandonsa yayi picking tare da kara wayar a kunnansa... "Sir, har yanzu bamu gano shi ba, a binciken da mu ka yi, ba shi kaɗai ya gudu daga estate din ba, hada yar uwarsa ba'indiyar nan.." Tsoki ya ja cike da takaici ya ce, "Na raina kokarin ku, tayaya har sakaran mutumin nan ya gagare ku ganowa um!" Ya fada a fusace.. "Sorry Sir, we'll do our best to locate..." Bai ƙare maganar ba ya daka mashi tsawa yana faman cije le6e ya ce, "Idan har baku gano inda ya 6uya ba nan da one week, ku kuka da kanku! sannan bana buƙatar shi araye da shi da yar uwar ta shi, just kill them all and bury them where no one can find their bodies!" "An gama sir," Rejecting call din ya yi, sai faman fitar da numfashi mai ɗumi ya ke yi, ran manya ya 6aci... Wani layin ya kira tare da kara wayar a kunnansa, "Mark, how's his condition? Has he recovered from the coma?" On the other hand Dr. Mark ya ce "He still hasn't regained consciousness, amma ka kwantar da hankalin ka, yana samun kulawar likitoci, nan bada jimawa ba zai farfado, kasan aminin nasa baya wasa da lafiyar sa" cije le6ensa yayi tare da jan numfashi ya furzar da shi. "Ko da zai cire ran shi yaba Omar don ya rayu, bazai ta6a burge ni ba, bana son alaƙar su kwata kwata, sai kace shi na haifa ma shi, Omar ya jima yana baƙanta min rai saboda Owais, shi ya raba ni da shi, ya mallake min ɗa, amma nasan maganinsa dole in shiga tsakaninsu wlh..!" Bai ƙare maganar ba, ya tsinkayi muryar Hajiya Sarah, "Babe..." Nan da nan ya haɗe rai, da sauri ya katse kiran tare da jefa wayar saman mattress, afusace ya juyo yana kallonta tana daga tsaye bakin kofar ɗakin, "Ban hana ki yi min la6e ba idan ina waya?" Marairaice masa fuska ta yi, "Am sorry, ba la6e nake yi maka ba, dama na biyo kane don inji meyasa ka yi mana haka pls?" "Oh! kin biyoni ne don kiyi min faɗa kan abunda na yi halan? Ya fada yana ɗage mata gira.. Ƙwarjini yayi mata hakan yasa ta kasa faɗan ta cikinta.. "In har zaku cigaba da 6ata ma zeenatu rai, nima bazan daina 6ata maku rai ba, yarinya da gidan ubanta ace kowa ya juya mata baya babu mai kula da ita!" "Bai kamata kana ɗaukar maganar Zeenatu ba, har yanzu fa yarinyace, babu abunda aka yi mata fa, ita ce ta ƙuntata kanta.." Bata ƙare maganar ba ya katse ta, "Pls, fuce ki bani guri, bana son takura.." gyaɗa kai tayi maganarsa ta 6ata mata rai. Dama da haushinshi aranta, kwanakin nan kwata kwata baya bata hakkinta yadda ya kamata, in ya fita sai cikin dare ya ke dawowa gidan kamar aljani, tayi ta jiranshi baiwar Allah, har sai bacci ya dauke ta, kuma in ta farka ta gansa ta nemi ya kulata sai ya kama yi mata faɗa yana faɗin ya gaji ita bata da hakuri ne, bata ga a gajiye ya dawo ba, kawai ta kyalesa bacci zaiyi, baiwar Allah zaman hakuri kawai ta ke yi da shi. "Abincin naka fa?" "Bazanci ba" Cike da 6acin rai ta ce, "Kada Allah yasa ka ci Musa, ka cigaba da yi min abun da kaga dama, ni da kai in har akwai wanda ke cutar wani Allah zai saka masa ne ka jira ka gani, don kawai ina haƙuri da kai sai ka yi ta min abunda kaga dama..." A ruɗe yake kallonta cike da mamakin ina ta samu kwarin gwiwar gaya masa magana ido cikin ido batare da jin shakkar shi ba.. "Ƙaddara ce tasa na aure ka, amma wlh nafi ƙarfin ka, koda yake ba laifin ka bane, nina ja ma kaina, shiyasa har ka samu damar wulaƙantani son ranka..." Juyawa ta yi a fusace ta nufi room door din, batai aune ba taji ya damƙi wuyanta, a tsorace ta kware baki zata fasa ƙara, ya yi hanzarin sanya tafin hannunsa ya toshe bakin nata. Saitin kunnnanta ya kai bakinsa da wata irin murya mai cike da shu'umanci ya furta, "Matsoraciya..." Ajiyar zuciya ta sauke tana faman haɗiyar yawu... "Faɗa min a ina kika samu kwarin gwiwar nan ne?" Ya faɗa yana leƙen fuskarta.. "Ka 6ata min rai ne, ni kawai bana jin dadin abun da ka ke yi min ne, basai na fito fili na faɗa maka ba ka riga da ka sani .." "Am sorry my queen, mother of my princess, na kar6i laifina, bazan ƙara ba, nima bada son raina hakan ke faruwa ba, ayyukane su ke yi min yawa amma zan gyara in sha Allah." ta ɗan yi mamakin yadda yayi mata magana cikin tausasa harshe. "Muje ki taimaka min in yi wanka, mun kwana biyu bamu yi wanka atare ba.." Bai jira amsarta ba, cikin sigar yaudara da jan hankali ya ɗauketa kamar jinjira ya nufi bathroom da ita. _______________________________ Lokacin da Taj ya je ma Ummi da zancen neman ta da Chief ya ke yi, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, zullumi da fargaba suka cika zuciyarta, ta yi ta tunanin meyasa ya ke nemanta? Kasa fita tayi daga dakinta, har saida Taj ya kirata a waya ya ƙara tunasar da ita game da kiran da Chief ya ke yi mata yace ta same shi yanzun nan a sitting room dinsa tukunna, ta zumbula dogon hijabi ta fito cike da ɗar-ɗar ta nufi sitting room dinsa, saida ta tsaya bakin door din ta daidaita nutsuwarta, kafin tayi sallama cikin nutsastsiyar muryarta. Daga ciki ya amsa mata sallamar, ya na daga zaune kan sofa ya ɗaura kafarsa ɗaya kan ɗaya yayin da idanunsa ke akan Apple ipad dinsa da ya ke daddanawa, shiga ciki ta yi, tunkan ta ƙaraso ya nuna mata kujerar dake fuskantar sa, table ne ya raba tsakanin su. Bayan ta zauna ta sunnar da kanta ƙasa cike da jin nauyin sa gaba ɗaya ya yi mata kwarjini. "Ina fata kin wuni lafiya." Da ƙyar ta furta, "lafiyalou, ya kake, ya aiki, ya family ɗin ku" "Alhamdulillah ina lafiya, suma family ɗina suna cikin ƙoshin lafiya," Shiru suka ɗan yi na wani lokaci, daga bisani ta tsinkayi muryarsa a cikin kunnanta, "Na kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarki.." Zare idanu ta yi, har ta fara tunanin ko dai ya ji komai agurin su Benazir ne. Bai damu da yanayin ta ba ya ci gaba da maganarsa, still bai ɗago ya kalle ta ba, idanunsa na akan apple ipad dinsa da yake cigaba da dannawa, "A ranar da ƙawayenki suka zo gidan nan, Taj ya faɗa min halin da kuka shiga lokacin da kuka ga juna, kuma ya ji a bakin Ex-wife din sa cewa ke aminiyarsu ce..." Har ya ƙarashe maganar bai ɗago ba, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa tsantsar 6acin rai da damuwa, kwata-kwata bata son kowa yasan labarinta, saboda tana jin kunyar a sani, bayan haka bata son ta fama tsohon raunin dake a cikin zuciyarta, abun da ya ɗaure mata kai meyasa Chief ya ke son jin labarin ta? Ko Taj da suka fi shaƙuwa da shi bai nemi ya sani ba sai shi da bai ta6a shiga shirgin ta ba hakan yasa ta dan ji shakkun ta faɗa masa.. "Kin yi shiru ba ki ce komai ba," Kamar mara gaskiya ta kama yi mashi yan kame kame, muryarta kamar ta mai in'ina ta ce, "Sir, I'm sorry to say why do you want to hear about my life?" "Saboda ina son in sasanta tsakaninki da ƙawayenki, cos a fahimtana kun samu sa6ani ne, kuma akwai wani abu da ya faru wanda yayi silar raba ku. " Yamusa fuska tayi kwata kwata babu walwala ta furta, "Ina ganin girmanka yallabai, bana fata Allah ya nuna min ranar da zaka nemi wani abu agurina in kasa yi maka shi, amma ina mai baka haƙuri, ni bazan iya baka labarina ba..." Gently ya ɗago da reddish eyes dinsa ya ɗaurasu akan fuskarta, tuni ta ji wata nutsuwa ta shige ta, wani irin kwarjini yayi mata wanda hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar tata. "Pls ki faɗamin, In har kin yarda da ni, amma idan kina ganin da takura ki bar shi..." Yanayin yadda yake yi mata magana cikin kwantar da murya yasa ta dinga jin kamar yaya Shureim ne ke yi mata magana, hatta fuskarsa sai ta dinga koma mata irin ta Shureim, batasan sa'adda ta fara bashi labarin rayuwarta ba, tiryan tiryan ta labarta masa komai daya faru da ita har izuwa lokacin data bar gidan mahaifin ta. Idanunta cike tab da ƙwalla ta ƙare maganar, lallashin ta ya yi cikin nuna tausayawarshi gareta har ya samu ya shawo kanta. "Tayaya akai kika bar ƙasar nan? Ki ka koma America da zama, bayan kin canza rayuwarki?" Sunnar da kanta ƙasa tayi cike da jin nauyin ta fada. "Zan fahimce ki Ummi, tun kafin ki fara yi mana aiki mun riga da mun san komai game da rayuwarki a America, don haka kada ki ji komai, abun da ya faru da ke jarabta ce daga Allah..." Kalamai masu dadi ya faɗa mata har sai da ta ji zata iya fada masa komai saboda ta yaba da hankalinsa ta kuma aminta da shi, a tsanake ta fayyace masa komai da ya faru bayan rabuwarta da mahaifin ta. Daƙyar ta ƙarasa labarin ganin yadda hankalinsa ya tashi matuƙar sosai, jikinshi har kerma ya ke yi saboda tsabar bacin rai da fusata, bai ta6a jin tsanar mutun kamar yadda ya ji ya tsane sa ba, zaluncin sa yayi yawa, bayan ya rabata da kowa nata, ya kuma maida ta karuwa, cikin fushi ya daki gaban table dinsa da hannunsa. Hankalinta a tashe ta ce, "Sir meke damunka? Ko labarin dana baka ne baiyi maka dadi ba..!" "Har yanzu kina atare da Uncle din nata?" girgiza kai ta yi, "Mun rabu da daɗewa," Wani kallo yayi mata da ya sa tasha jinin jikin ta, batasan ya san komai ba. "Ki ji tsoron Allah, Ki faɗa min gaskiya!" Tamkar zata fashe da kuka ta ce, "Pls kada ka tilasta mini, bazan iya faɗa maka amsar tambayarka ba, ka yi haƙuri kawai.." Murmushin takaici ya yi tare da cewa, "Okay, Kin taba haihuwa da shi?" Aruɗe take kallonsa jin wata tambaya mara ma'ana, ba dan tana ganin girmansa ba da ba abun da zai sa ta zauna yana mata tambayoyi kamar ɗan jarida, "A'a, amma na ta6a samun cikin shi, wanda silar zubar da cikin da na yi yasa muka samu sa6ani da shi, har ya ɗauke ƙafa da kawo min ziyara, abun da yasa nayi hakan saboda bana so in 6ata shape din jikina sannan bani bukatar in ƙara haihuwa, ƴata dana bari ta ishe ni in ƙarasa rayuwata, ashe ma ƴar da nake ta hauka akanta ta mutu batare da na sani ba...." Fashewa tayi da kuka ya dinga lallashinta har ya samu ta yi shiru.. "Amma meyasa baki taba kar6ar tayinsa na aure ba?" Tana cikin share ƙwalla ta ce, "Saboda ban ta6a son shi da aure ba, bayan haka a duk lokacin da yayi mini magiya akan in amince in auresa, da zarar na amince muka fara shirye shiryen auranmu toh bazai ƙara lafiya ba, har sai ya fasa zancen auren, wannan dalilinne yasa har ila yau bai aure ni ba." Duƙar da kanta kasa ta yi jikinta yayi sanyi da ganin yanayinsa, duk sai taji ta muzanta, saboda tayi zaton haushin rayuwarta ya ke ji, tuni idanunta sun cicciko da ƙwalla, "Kayi hakuri, idan labarin dana baka ya 6ata maka rai, shiyasa tun farko banso ka matsa min akan in fada maka ba.." A hankali ya buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur ya girgiza mata kai, "Ba abunda kike tunani bane Ummi, labarin ki ya karya min zuciyana, na ji tausayin rayuwar ki..." hankalinta ne ya kwanta jin ba abun da ta zata ba ne. "Nagode da kika aminta da ni har kika faɗa min sirrinki" Ɗan murmushi ta yi. "Amma kai ma kamar kana da damuwa, kada ka ce na sanya maka ido, wlh ka rame, babu karsashi a jikin ka" Murmushin yaƙe ya ƙaƙaro akan fuskarsa, "Kada ki damu da ni, zazzabine ke damuna amma na ji sauƙi..." Girgiza kai ta yi, "Yallabai, halin da ka shiga yafi ƙarfin zazzabi, kada ka boye min pls, tun da har na aminta da kai na baka labarina dayake sirrina kaima ya kamata ka sanar dani taka damuwar, ko da bazan iya sama maka mafita ba, zan tayaka da addu'a." marairaice masa fuska ta yi. Shiru yayi jim yana tunanin ya zata ɗauki abun in ya fada mata, Cikin sanyin murya ya ce, "Ummi mun fara gano su wanene Elders na gidan Kurkukun ƙaddara! Kuma muna zargin uncle din ƙawarki Benazir yana ɗaya daga cikin su..." Bai ƙare maganar ba ganin yadda ta zare idanunta, walwalar fuskarta ta ɗauke tamkar bata ta6a yin dariya ba. A dabarbarce ta ce, "Sir ka san me ka ke faɗa kuwa? Wallahi ba dan ina ganin girmanka ba da ba abun da zai hana..." Kasa ƙarasawa ta yi, can kuma ta ce, "Bazai yiwu ba, big boss baya ɗaya daga cikin su, saboda shi ba matsafi bane kuma ba mugu bane, ni nasan wanene big boss! Nasan halinsa ciki da bai, pls ku sake bincike akan shi zaka tabbatar da abun da nake faɗa maka!" Rai a ɗan 6ace ta faɗa, ta haƙiƙance akan gaskiyarta. "Ke baki tunanin mutumin nan da wata mummunar manufa yake atare dake Ummi? Ke fa malama ce, kina da tarin ilimi akan ki, kinsan mai kyau da mara kyau, taya zaki yi tarayya da fasiƙi kuma har kina kare sa daga laifin da ake tuhumarsa...?" "Baki tunanin saboda kin nuna baki son shi dr. Shureim kikeso shiyasa ya ƙulla makircin da ya shiga tsakanin ki da shureim ya kuma raba ki da mahaifinki saboda yasan bazai bari ki aure shi ba tunda baki son shi, sannan bayan kin gudu da tsakar dare tayaya akai har kika haɗu da shi a wannan lokacin? Shi Aljanine baya bacci ne? Ba yadda za'ayi ya fito in the midst of the night batare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, gaba ɗaya plan dinsa ne Ummi..." Shiru tayi jim ba tare data furta kalma ba, bata san tayaya zata fahimtar da Chief ba, gani take kamar ya fara zarewa. "Kiyi amfani da hankalinki Ummi, meyasa ya ɗauki nauyin karatunku a ƙasar germany? ya kuma kama maku hayar gida, bayan haka duk weekend sai ya kawo maku ziyara har ya kwana agidan ku," ya faɗa yana kallon cikin idanunta. Gaba ɗaya tabi ta ruɗe, sai dai kwata kwata bata gasgata maganarsa ba, saboda ta yarda da Uncle Musa fiye da kowa tun da ita ya yi mata hallacci, ya so ta a lokacin da kowa ke gudunta, ya zama danginta a lokacin data rasa dangin da zata jingina da su. Murmushin takaici ya dan saki, saboda ya fahimci ta cikin sauƙi bazata yarda da shi ba, Zura hannunshi ya yi cikin front pocket na jallabiyarsa ya zaro hotuna, Kamar daga sama ta ji ya ce, "Nasan har yanzu kuna a tare Ummi, saboda akwai ranar da ya kira ki a waya kin shiga toilet, Batool ta gani ta ɗauka batare da sanin ki ba, a yanzu haka ina da hujjojin da za ki gasgata magana ta.." She was utterly perplexed, but she didn't believe his words at all. Ya ƙarashe maganar tare da ɗaura mata hotunan akan table dinsa, lokacin da ta daura idanunta akan hotunan wata irin firgita ta yi, gaba daya tabi ta rude, muryarta da mamaki ta ce, "Sas.. Sir ina ka samu waɗannan hotunan?" Ta tambaya aƙagare da son jin amsar shi, bai tanka mata ba, har saida ya zaro ɗayan hoton ya jera shi da sauran hotunan.. Lokaci ɗaya ta ƙara ruɗewa, labbanta na kerma ta furta, "Baby preety, Sir Ina ka samu hotunan su um??" Numfasawa yayi kafin ya ce, "zan faɗa maki inda na samu hotunan amma ki fara faɗa mini miye alaƙar dake atsakanin mutanan dake a cikin hotunan nan?" Jinjina mashi kai tayi kafin ta fara kora masa bayani, "A tare na san shi da Natasha, sun daɗe a tare, karuwarsa ce kuma baturiyar england ce, ita kuma baby preety rainon ta ya kawo mata tun tana jaririya, amma lokacin da ta kai shekara sha shidda ta ce min ya kar6e ta, ya mayar da ita gurin mamanta da ke anan Nigeria.." Runtse ido chief Owais yayi saboda takaicin da ya turnuke zuciyarsa, aransa ya ayyana hakan na nufin ƴan biyu ne ita da ƴar wurinsa! Kamar yadda su ka yi tsammani, Ya sadaukar da ɗaya, ita kuma ɗayar tana agurin mamanta. "Sir meya faru um? Dan Allah tun da na amsa maka tambayarka, nima ka fadamin a ina ka samu hotunan su! Na ƙosa na ji." Miƙa hannu yayi cikin table drawer din gabansa ya curo diary ɗin Unaizah ya ɗaura mata akan table din, "kinga inda na samu hotunan, Kuma diary din nan mallakin ɗaya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara ne, nasan ba zaki manta yarinyar da Unaisah ta bada labarin mahaifinta da ya yaudareta ya sadaukar ita gidan kurkukun kaddara a matsayin Korean School...?" Wani irin faduwar gaba taji daram dararam kamar ana buga gangunan yaƙi a ƙirjin ta. Yatsun hannunta na kerma ta buɗe diary din ta soma karanta shi, Wa'iyazubilla! tana karantawa yayin da brain dinta ke tariyo mata fuskar yarinyar, tabbas ta yarda diary din mallakin baby preety ne babu tantama saboda yawanci duk abunda ta rubuta a cikinsa ta ta6a jin labarin a bakin Natasha. Bata ƙarasa karantawa ba, ta rufe diary din tare da kifa kanta saman shi, wlh bazan iya misalta tashin hankalin da ta shiga ba, She was completely bewildered and shocked, unable to believe it, Aranta tana jin ba zai yiwu uncle Musa ya iya aikata rashin imanin nan ba, mutun mai tsoron Allah da tausayi irin sa would never do such terrible thing, amma kuma ta fara kokwanto saboda in har ba a diary din baby preety ba, to kuwa babu inda za'a samu hotunan Big boss da Natasha da kuma na baby preetyn, sai dai bata so ma zargin su akanshi ya zamana gaskiya. "Yanzu kin yarda da maganata ko kuwa kina akan bakanki" Jinjina mashi kai ta yi, "Bani da matsaya, amma na yarda da big boss, kuma na yarda da kai, sai dai bazan iya yarda da abun da ka fada akansa ba, wadannan hotunan na yarda a cikin diary din baby preety aka same su amma bana tunanin itace yarinyar da Unaisah ta bamu labarin ta, please na roƙe ka ku sake bincike akan shi.." Duk yadda Chief ya so ya kwatanta mata cewa ba mutumin kirki bane taƙi yarda, tana akan bakanta saboda ta aminta da mutuminta, yadda kasan wadda aka asirce, kwata kwata bai ji haushinta ba saima tausayinta da ya mamaye zuciyar shi saboda ya lura ta ruɗe ne sosai kuma bata son zargin da suke yi ya tabbata akan shi saboda halin da zata shiga, shiyasa tun farko baima yi tunanin faɗa mata komai game da babynta ba saboda gudun halin da zata shiga. "Ummi, Zan baki lokaci kije ki yi tunani akan abun da na faɗa maki, sannan ko da baki yarda ba, Inaso ki bamu hadin kai please..." Girgiza kai ta yi, "Ka yi haƙuri ba zan iya ba, nayi masa alkawarin bazan ta6a bari wani ya san muna a tare ba, in har ya ji na karya masa alkawari bazai ji dadi ba, zaiga kamar na ci amanarsa ne, ni ko maganarsa bana son yi da wani." Zuciyarsa ta sosu ransa yaso ya 6aci, sai dai bai nuna mata a fuska ba.. "Zaki iya tafiya..." Har zata miƙe ya tsayar da ita, "Zan gargaɗe ki, Kada ki kuskura ki bari mutumin nan ya gane abunda muke zargi akansa! bama shi ba, ko da ƙawar nan taki ce, idan har na ji maganar nan agurin wani, hmm, ba abun da zai hana in garƙame ki a cell kuma kema zaki shiga cikin zargin da muke akan sa, sannan kada ki canza masa ku cigaba kamar yadda kuka sa6a." Maganarsa ta ɗaga hankalinta, dama da biyu ya yi mata barazana, fuskarta ta jiƙe sharkaf da gumi, kwata kwata babu walwala atare da ita, Ya rudar da ita ba kaɗan ba, Ya kuma tsoratar da ita. Hanky ya miƙa mata, "Share zufar dake akan fuskarki, don bana so wani ya gane halin da kike a ciki." Cikin rawar hannu ta kar6i hanky din ta soma share gumin fuskarta, har ce mata yake yi, "Ki share da kyau fa.." tace toh, bayan ta gama ta juya zata tafi da hanky ɗin ya dakatar da ita, "Bani abuna.." miƙa masa hanky din ta yi, ko waiwayensa bata yi ba saboda a ƙagare take da ta bar sitting room din nasa.. Lumshe idanunshi yayi tare da jingina bayan shi jikin kujarar, bawan Allah abun duniya ya ishe shi, saboda gujewa tunanin da zai haifar masa damuwa yasa baya barin zuciyarsa hakanan batare da yayi tasbihi ba 💔 Bayan fitar Ummi daga dakin, jikin bango ta jingina bayanta, yayin da zuciyarta ke tariyo mata wasu abubuwa da suka haifar mata da kokwanto akan mutuminta! bakomai ta fi tunawa ba face ranar data fara ganin Danish babu shirt a jikinsa! zanen tattoo dinsa ya tsaya mata a rai, har yau bata manta ba, saboda sak irin na big boss ne, kamar anyi photo copy dinsa an ɗaura masa abayansa, kuma tun da take mu'amala da americans bata ta6a ganin mai irin tattoo dinshi ba, sai akan Danish shiyasa ranar data ganshi al'ajabi ya kamata, bayan haka maganganun da Chief ya faɗa a game da shi sun tsaya mata a ƙahon zuciya, tabbas diary din baby preety ne, agurin ta kaɗai za'a samu hotunansu, wani abu da ya ƙara ruɗar da ita nickname dinsa da ta gani a rubuce cikin diary din Preety, kuma a labarin da Unaisah ta basu ta fadi sunan mahaifin Unaizah yar gidan daddy, gaba ɗaya dai kanta ya ɗaure tamau, kwakwalwarta ta rikice sai tufka da warwara ta ke yi.🍁 "Ummi, kun gama magana da Chief dinne?" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Taj, a firgice ta dube shi yana zaune kan wheelchair dinsa, danne damuwarta ta yi ta kakaro murmushi kan fuskarta, "Eh mun gama magana da shi, shine ma ya ce min in tafi. Sarai ya lura akwai damuwa atattare da ita sai dai kawai ya basar. "Yakamata ka ajiye wheelchair din nan, tun da ka fara samun sauƙi, idan ba haka ba zaka manta yadda ake yin tafiya da kafafu," Ta faɗa da zolaya. Murmushi ya sakar mata, "wlh iya yine irin nawa, kinsan ance sabo turken wawa, ɗan hawan ta da nake yi yasa har na saba da ita.." ya faɗa yana ƙoƙarin mikewa, A hankali ya samu ya tsaya kan kafafunsa, murmushi ta yi mashi, "in shigar maka da kujerar ciki?" "No, bana so Unaisah tasan na samu lafiya, tafi ji da ni Allah, duk in zata ganni ina gungura kujerar jikinta na 6ari take kamamin ta tura ni.." Duk da halin damuwar da take aciki hakan bai hana tayi dariya ba, maganarsa ta bata nishadi ashe lambon ciwo yake ma Unaisah. Bayan ya shiga sitting room din Chief, Jiki asanyaye ta wuce bedroom dinta, tana kallon Unaisah da Batool zaune kan rug, sun baza textbooks dinsu da alama karatu take koyawa Batool, bata bi takansu ba, cikin sanɗa ta wuce don kada su ganta saboda a halin yanzu tafi bukatar kadaici.. Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki *Daga Alkalamin Boss Bature💋✍️* Sallamar Taj ce ta katse tasbihin da ya ke yi, A hankali ya buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai ja ya dube shi bayan ya amsa mashi sallamar.. Fuskar Taj da damuwa ya zauna kan sofa yana fuskantar sa.. "Haba Owais, har sai yaushe ne zaka fadamin abunda ke damunka? Ko kafi son in yi ta zama cikin damuwa ne? Unaisah ta ce min ka ce za ta ji a gurina kuma nima din ka ƙi sanar dani ba yadda banyi da kai ba..." ya faɗa yana mai nuna 6acin ransa . Cikin sanyin murya Chief ya ce, "Am sorry, nasan ban kyauta ba, amma ka ƙara hakuri zuwa gobe idan muka shiga meeting zaka ji komai..." Gyaɗa kan shi ya yi, "Allah ya kaimu da rai da lafiya" ya amsa da ameen Shiru suka ɗanyi Jimm kowa da abun da yake saƙawa a ran shi.. "Please Owais, duk da bansan meya faru ba, amma tun ranar daka dawo daga yanayin ka na lura babu kwanciyar hankali atare dakai, da akwai wani mummunan abu daya faru, saboda ba karamin abune zaisa ka ki kulamu ba, kuma ka kulle kanka adaki, sannan baka son cin abinci, ka rame, even the chefs have complained about your lack of appetite, pls ka yi hakuri kada ka bari damuwa ta yi maka illa, nasan kai mutunne mai tawakkali, har burgeni ka ke yi saboda jarumtarka, da wuya mutun ya iya gane kana a halin damuwa, sai in tura ta kai bango ne ake iya gane me kake a ciki..." Murmushi ya yi yana sauraron future in-in law ɗinsa, yana ƙara jin ƙaunar sa a zuciyarsa, da duk wani wanda suke rayuwa a gidan saboda yadda suke nuna damuwa akan shi, suna son shi suna son farin cikin shi, ranar da ya kulle kanshi a ɗaki abun da ya karya mashi zuciya yadda suka dinga zarya a ƙofar ɗakin suna masa magiya don ya buɗe masu, ta ya bazai gode da ni'imar da Allah yayi masa ba? Sosai Taj yake lallashinsa tare da kwantar masa da hankali, "Ni bansan da wasu kalmomi zan yi amfani gurin yi maka godiya ba, sai dai ince Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta mini, Allah ya ƙara dankon zumunci da kauna atsakaninmu.." Ya amsa masa da Ameen, fira Taj ya fara jan shi da ita duk dan ya kawar mashi da damuwa ya saka shi nishadi.. "Wa zaka fara aura a cikin su? Ina son in san matsayin ƴata," Ƴar dariya chief ya yi tare da kai hannu ya shafa sajen fuskarshi, cike da jin nauyin shi ya ce, "A rana ɗaya zan aure su." Taj ya ce, "Ban yarda ba, wayo zaka yi mini, kawai ka faɗamin wacece amarya wacece kuma uwargida." Ƴar dariya Chief yayi, "Nazli ce uwargida saboda ta girmi Unaisah, ina so Unaisah ta ɗauke ta a matsayin yayarta, ta haka ne zasu mutunta juna.." Murmushi Taj ya yi. "That's a good idea, amma yakamata ka sanar ma Unaisah ba ita kaɗai zaka aura ba." "I couldn't tell her I left it until the time comes, In sha Allah..." Kafin Taj ya ƙara magana wayar Chief ta fara ruri, idonsa ya kai kan screen din wayar tasa dake saman table, sunan sheikh Imam Malik ne ya bayyana, janyo wayar ya yi tare da yin picking ya kara a kunnansa... Bayan sun gaisa Sheikh Imam ya ce mashi ya yi haƙuri ya ji shiru bai neme sa ba, yanzu yana son yin magana da shi in yana free, Cike da ladabi ya ce toh a ina zai same shi? Bayan ya faɗa masa address din suka yi sallama ya mayar da duban sa kan Taj "Sheikh Imam yana nema na." Taj ya ce, "Ok, ko zamu iya tafiya tare?" Ya amsa. "Eh." Duk da baisan ko shi kaɗai sheikh Imam yake son gani ba amma yasan Taj bazai bada matsala ba.. A motar Taj suka tafi, bayan sun ƙaraso apartment building din da Imam Malik yake a parking space suka aje motar, lokacin da suka fito sai ga sheikh Imam ya fito sanye da Jallabiya, fuskarsa da fara'a ya nufe su, cikin girmamawa suka gaisa da shi. "Bismillah, mu shiga daga ciki..." A apartment living room dinsa suka tsaya, bayan kowannansu ya zauna kan sofa ya miƙe ya nufi ciki, jim kaɗan ya dawo hannunshi ruƙe da ƙaramin tray mai dauke da drinks ya ajiye masu akan table da fara'arsa ya ce, "Sai fa kun yi hakuri, kun zo gidan gwauro, ni nake komai nawa, don ma bana jin dadi ai da har girki zan yi maku." Murmushi suka saki gaba dayan su. Chief ya ce, "Da nasan baka da iyali tuntuni dana sa an kawo maka house helpers wadanda za su taimaka maka da ayyukan gidan.." Ƴar dariya ya yi. "Daka kyauta Owais, amma fa kada ku damu na saba, bana jin wahalar ayyukan gida, tun da safe nake tashi inyi share share da goge goge, idan na gama in kuma girka abun da zan ci.." Waro idanu suka yi Taj ya ce, "Gaskiya ba zamu bari ka ci gaba da zama babu iyali ba, waɗannan ayyukan bana maza bane, a shekarun nan naka hutu kake bukata..." Murmushi sheikh ya yi, ya ji dadin yadda suka nuna damuwa akan shi. "Bismillanku," Ya faɗa yana nuna masu drinks din, har zai zuba masu, chief ya yi saurin kai hannu ya ɗauki juice ɗin ya tsiyaya masu a cups, kowannan su ya ɗauka ya sha. "Na ga ku biyu kuka zo, shima yasan komai ne"? A ruɗe Taj yake kallon sheikh da ya yi tambayar... Chief ya ce, "A'a na bari sai mun haɗu gurin meeting zan sanar da su komai tun da atare muke gudanar da binciken case din, kuma Taj da iyalinsa sun bamu gudummuwa sosai..." murmushi sheikh Imam ya yi. "Ma sha Allah.." Shiru suka ɗan yi, da Taj ya lura kamar akwai abun da sheikh ke son ya tattauna da Chief a sirrance sai ya yi dubarar miƙewa tare da curo waya ya ce, "Ina so zan yi waya." amsa mashi suka yi da toh, Ya nufi ƙofa yana ɗangyasa kafa Sheikh ya yi mashi addu'ar ƙara samun lafiya, bayan ya fuce cikin mota ya koma, Benazir ya danna ma kira bayan ta ɗaga suka fara shan soyayya.. "Ya mutanan gidan naku Owais?" "Suna nan lafiya, Alhamdulillah." "Baban naku fa?" "Har yanzu bai buɗe ɗakin ba, Kuma ya ce baya son mu buɗe shi, mu bar shi har zuwa lokacin da muka kama sauran Elders din zai fito da kan shi.." "Kun yi magana da shi ne?" Jinjina mashi kai ya yi, kafin ya labarta masa abun da suka tattauna da shi, ya ƙara da cewa, "Yana cin abinci idan muka kai ma shi..." Shiru sheikh imam ya yi a can kasan zuciyarshi wani irin tausayin rayuwar ahalin Obie ne, dama saida ranshi ya bashi Obie bazai iya guduwa yabar ƴa'yanshi ba koda za'a kashe shi ne da azabtarwa, saboda yasan yadda yake tsananin son su, ta wani bangaren hankalinsa ya kwanta saboda baya son baba Obie ya gudu ya fi son ya tsaya ya kar6i hukuncin da za'a yi masa koya samu sassauci agurin hukuma. "Owais, Ni ba mazaunin Abuja bane, Idan har ka ganni a abuja to gayyatata aka yi wani muhimmin taro ko wani aiki ya kawo ni, a ranar da abun ya faru na 6oye maku gaskiyar abun da yasa na shiga jikinku, saboda na ga hankalinku ba akwance yake ba, kuma nasan muddin na faɗa zaku ƙara shiga damuwa, shiyasa na ce zan neme ka a waya tun da kai ne jagoran binciken case din nasu.." Ya ɗan dakata yana duban Owais da ya nutsu yana sauraron shi "Ban ji daɗi da ya ƙi faɗa maka su wanene sauran ba, amma karka damu in sha Allah zamu dage da addu'a har sai asirinsu ya tonu...." Numfasawa ya ɗan yi, kafin ya ɗaura da cewa, "Shekara kusan takwas da suka gabata, mun yi babban rashi na abokin mu ɗan kungiyarmu ta malaman ahlussuna, mai suna Malam Jazuli shi da ƴa'yanshi guda biyu. Ya ta6a kira na awaya kafin afkuwar lamarin a lokacin bana a ƙasar, ina a gidan Uncle dina dake a Sudan, a lokacin da ya kira muryarsa babu nutsuwa ya ce shiekh Imam Allah abun tsoro ɗan adam abun tsoro, na ce masa meya faru? Ya amsa min da cewa ya ga abun da ya ɗaga hankalinsa akan hanyar dawowar shi daga Kano, Uziri ya kama shi har ya yi parking motarsa a gefen titi, ya fito daga motar hannunsa ruke da robar ruwa ya ratsa cikin daji don yayi uzirinsa, bayan ya kammala yana kokarin miƙewa ya jiyo kukan jarirai can nesa da inda yake, lamarin ya ɗaure masa kai, ya yi ta mamakin meya kawo kukan jarirai a cikin dajin Allah? Har zai tafi sai kuma ya ji bazai iya tafiya batare da ya ga a ina kukan nan ke fitowa ba, saboda zuciyarsa ta shiga raya mashi zai iya yiwuwa yada su aka yi ko kuma mace ce me ciki wata ƙaddarar ta afka mata da har ta haife su a cikin daji. Bai yi ƙasa a gwiwa ba, Ya ratsa cikin dajin yana ta mamakin yadda ya iya jiyo kukan tun daga inda yake bayan akwai tazara mai nisa tsakaninsa da inda yake jiyo kukan jariran, ba ƙaramar wahala ya sha ba har ya fara tunanin kodai kukan jariran bana mutane bane, saidai kuma ya kasa haƙura ya koma, yana cikin tafiyar kwatsam ya ƙaraso wani guri mai manya manyan bishiyoyi, duk da marece ya nutsa duhu ya fara bayyana hakan bai hana shi ganin meke wakana ba da taimakon hasken wutar dake ci jikin firewood... La6ewa ya yi bayan bishiya yana leƙen su ganin manyan mutane zaune saman buzu, kwata kwata babu sutura a jikinsu sai jan ƙyallen da suka ɗaure ƙugunsu da shi, daga tsakiyar shimfiɗar ta su jarirai ne sabuwar haihuwa su biyu kwance saman jan ƙyalle sai tsanyara kuka suke yi kamar ran su zai fita. Gaba ɗaya ya ruɗe ya rasa gane meke faruwa? Su wanene waɗannan mutanen masu kama da bokaye? Me zasu yi da jariran nan... Bai ƙarasa zancen zucin nashi ba maganar wani daga cikinsu ta ratsa kunnanshi. "Me kake nema? Daukaka ko arziƙi ko wani kake so a yi ma sihiri? Muryar dattijo ya jiyo yana faɗin, "Arziƙi ranka shi daɗe, na gaji da talauci, shekara saba'in a duniya har yau ban mallaki gidan kaina ba, ba ci, ba sha, ba suturar sanyawa ta kirki, mutane har tsangwamarmu suke yi suna kiran iyalina da iyalan faƙiri, so nake ku azurtani ta yadda zan zama hamshaƙin mai kuɗi, shiyasa na kawo maku jariran nan ƴan biyu ne, Jikata ce ta haife su bata san na ɗauko su ba" Mahaukaciyar dariya suka saka gaba dayansu kafin daga bisani suka ce ma shi ya tashi ya tafi daga rana irin ta yau ya gama talauci a rayuwarsa, duk wanda zai rabesa sai ya yi arziƙi, sannan in akwai wanda ke buƙatar taimakon su, ya haɗa shi da wanda ya yi masa hanya har ya samu ganawa da su." yana faman washe baki ya amsa da toh, Wani daga cikin dattawan ya ce Sadaukarwar da ya yi ta mallaka ce, In har mutun ya mallaka masu ɗa, koda yana a cikin uwarsa ba a kai ga haihuwarsa ba zasu iya biya masa buƙatarsa, amma fa a bisa sharaɗin koda bayan wanda ya yi sadaukar ya mutu ne sai sun kar6i jinjirin in aka haife sa, kuma basu yarda da asara ba, in suka baka bashi sai ka biya su, dattijon ya amsa da toh.. Hankalin malam Jazuli ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin abun yake kamar a mafarki, bayan tafiyar dattijon ya ci gaba da yi masu labe, anan ya ji suna maganar zasu kai yaran kurkukunsu don a raine su. Ya ce min a lokacin bai ƙarasa jin maganganun nasu ba jikinsa na bari ya baro cikin dajin ya shige motarshi, ya bata wuta... Abun ya tsaya mashi a rai, sai dai baisan su wanene suke aika aikar nan ba, amma ya ƙudiri aniyar sai ya gano su saboda bazai bari ana aikata fasadi a doron ƙasa ba. Baisan ya zai yi ba, kullum da tunanin bayin Allahnnan yake kwana. Bayan wata biyu da dawowarshi Jos, Kwatsam a wata ranar juma'a ya je masallaci yin salla, bayan an kammala yana akan hanyar dawowarsa gida yanata tunani har baisan ya hau titi ba, mota tayi masa horn a ɗan firgice ya ja baya, Mai motar ya zuge glass ya fara zazzaga mashi masifa yana faɗin bai da hankali ne zai hau kan titi ko shi makaho ne? A lokacin da ya dubi fuskar mutumin wani irin faɗuwar gaba ya ji ganin tsohon nan fakiri da ya ta6a gani a daji wanda yaje sadaukar da jikokinsa, lamarin ya daure masa kai har ya kasa tanka masa, mamakinsa yadda yayi arziƙi in a short time, saboda motar da yake a cikinta ta kai ta miliyan ɗaya da rabi lokacin. Haƙuri ya bashi bayan ya tada motar ya tafi, ya ce na yi saurin tsayar da mai abun hawa na ce ya bi mani bayan motar, mai abun hawan ya kawoni unguwar da yake har layin gidan mutumin, nan fa na ga abun da ya kara daure mini kai ganin gidan da motar ta shiga ya haɗu. Bayan na dawo gida na yi ta tunanin tayaya zan shiga jikin dattijon nan don in gano su wanene waɗannan mutanan? Dubara ce ta faɗo min tunawa da maganganun da su ka yi da mutanen, nan na shirya kaina cikin yagaggun kaya da suka jikata, na sanya takalma ware daban daban, na yi shigar talaka futuk. Na je har gidan dattijon nan faƙiri da ya dawo mai arziƙi, na yi masa sallama bayan ya fito na zuƙunna ƙasa na fashe da kuka na dinga rokonsa akan ya taimaka min da abun da zamu ci, Iyalina bata da lafiya ga ciki a jikinta, tun safe nake bin gidajen masu hali don su taimaka mini amma babu wanda ya kula ni don Allah ya taimake ni kamar yadda Allah ya taimake sa..." Daɗin baki na shiga yi masa, da farko ya ɗaure min fuska kamar bazai taimaka min ba, sai kuma ya zaro kudi bendir ɗaya ya bani ya ce ya taimake nine saboda Allah saboda kuma shima ya taba shiga irin halin da nake a ciki. Ƙin kar6ar kudin na yi nace masa idan ya bani yau wa zai bani gobe? Na nuna masa bawai don na raina abin da ya bani bane sai don bana so zuciyata ta mutu in koma ina bara da maula, nafi son ya taimaka mini da jari mai ƙarfi, ko ya sama mini aikin da zan dinga yi har in samu wadatar da zan iya ɗaukar nauyin iyalina. Bai kawo komai aransa ba ya ce nayi tunani mai kyau, In bashi number ta zai neme ni idan ya sama min aikin." Jikina na kerma na curo ƴar karamar wayata da ta ji jiki na miƙa masa, da ya kar6i wayar har jujjuyata yayi ganin yadda ta rakwarkwa6e, bayan ya saka min number ya ce in tafi, na yi masa godiya na nufi gidana. Bayan kwanaki uku ina ta jiran kiransa shiru shiru har na fara fidda ran zai neme ni, kwatsam a cikin kwana na huɗu saiga kiran tsohon ya ce min yana taya ni murna ya sama min hanyar da zan samu jari, na ce Alhamdulillah ya tambayi ina da kudin abun hawa ko kuwa ya zo ya ɗauke ni? Na ce mashi zan ranci kudi in zo, ya ce mini a'a yafi so ya zo da kanshi saboda ya ga iyalina" Da jin hakan sai gabana ya fadi na fara tunanin tayaya zan samu iyalin ƙarya wadanda suka jigata? A gurguje nabar gidana na nufi bakin titi, da akwai wasu almajirai da suke bara agurin, mata ce mai jiki tare da ƴa'ya guda biyu, da matar na haɗa baki bayan na yi mata alƙawarin zan biya ta kudi masu yawa in har tayi abun da nake so ta ce mini ta amince. Bayan nayi shigar basajan da nike yi, na kwashe su a abun hawa ita da yaran nata muka nufi wani kango na ginin da na fara yi. Anan muka zauna ni da su, kafin ƙarasowar shi nabi mutanan dake rayuwa a layin na basu cin hanci saboda koda ya tambaye su dangane damu su faɗa mashi sun san mu da kuma halin talaucin da muke a ciki. Haka kuwa aka yi bayan ya ƙaraso bai kira ni a waya ba saboda wayau sai ya fara tambayar matasan unguwar ina ne gidan Barau matalauci, suka nuna masa kangon suka ce anan muke da zama, kuma kongon ma ba namu bane, wani bawan Allah ne ya bamu shi don mu zauna ganin yadda muke ta garari muna neman matsugunni. Da jin wannan maganar sai ya ji tausayinmu ya mamaye zuciyarsa, kusan duk wanda ya tambaya amsa ɗaya ya ke bashi hakan yasa ya yarda da ni. Bayan ya shigo cikin kangon ya taras damu a zaune kan tabarma, yaran matar suna ta kuka suna fadin baba yunwa muke ji, ita kuma almajirar sai faɗa take min tana faɗin, "wai ba zaka tashi ka nema mana abun da zamu ci ba? Jiya haka muka wuni ba ci ba sha, ko so kake mu mutu ne?" Sallamar mutumin ce ta katse mu, dama mun san da zuwanshi da gangan muka nuna kamar bamu lura da ya shigo ba, jiki na 6ari na miƙe na je gaban shi ina kuka na ruƙe kafafunsa na yi masa magiya akan ya taimake mu ya dubi halin da muke a ciki, tun jiya rabon mu da abinci, na yi fafutuka amma ban samu komai ba. Cike da tausayawa ya ke duba na, bayan ya gaisa da iyalin nawa yace in same shi a mota. Yana fita nabi bayan shi, bayan mun zauna ya ce da ni kamar yadda ya faɗamin na samu jari sai dai baisan ko zan iya bin sharuɗdan ba, saboda sai an kauce hanya..." na ce mashi koma wani irin aiki ne zan yi, in dai bai sa6a ma mahaliccina ba, Ya ce min, "baka ji me na ce bane? Dole sai an kauce hanya, in har kana son ka zama attajirin mai kudi cikin kankanin lokaci.." Na ce masa toh ya faɗamin inji in zan iya. Yana murmushi ya ce, "Sadaukarwa ce, in har kana so zaka bada ya'yanka ko jaririn dake a cikin matarka, idan har ka yi hakan ta zaka samu abun da kake so." Hankali a tashe na ce Alhaji bangane me kake nufi ba? Ya'yana fa ka ce, wace irin sadaukarwa ce wannan? me kuma za'a yi da ƴa'ya na?" Kwantar min da hankali yayi tare da cewa ba wani abu za'ayi masu ba, Uban gidansa ne Allah bai basu haihuwa ba, shine yake neman yaran da zai raina a matsayin nasa, In har na bashi ƴa'yana zan samu abunda nake so kuma yaran nawa zasu taso cikin wadatar arziki, amma fa in har na bada su, ya zama dole in manta da su kwata kwata, don ba za su taba dawowa gurina ba. Nuna mashi na yi ban amince ba, ya dinga tausata yana kokarin shawo kaina har dai na ce mashi na amince zan bada jaririn dake a cikin matana in ta sauka. Nan ya ce min toh zai haɗani da ubangidansa don mu yi magana, anan ya kira sa har ya bani muka yi magana, tun daga kan muryarsa na shiga ruɗu saboda sai na ji kamar na ta6a jin ta. Bayan wasu kwanaki ubangidan nasa ya kira ni a waya ya ce in same shi a gidan gonar shi yayi min kwatance. Kafin in tafi saida na sallami almajiran nan da ƴa'yanta na ce su nisanta kansu da garin saboda bana so in jefa rayuwarsu cikin haɗari, sai da na haɗa musu sha tara na arziƙi kafin tafiyar su. Bayan dana zo gidan gonar da yayi mini kwatance, cikin shigar basajan da na saba yi, A garden na iske shi zaune kan kujera, ya rufe fuskarsa da takunkumi ya kuma sanya baƙin tabarau a idanunshi. Hakan ya hana in gane wanene, bayan mun yi musabaha ya ce in zauna, na samu guri na zauna kan kujerar dake fuskantar shi, wani kallo na ga yana bina da shi tun daga ƙafafuna har izuwa hular dake a kaina, duk saina sha jinin jikina.. Yace min kada in damu da kallon da yake yi min, na ce masa toh. "Saura wata nawa matar taka ta sauƙa?" ya tambaya, cikin faɗuwar gaba na ce masa biyar. Ya ce, "Toh yanzu kamar nawa kake buƙata mu fara baka bashi kafin zuwa lokacin da zata sauka.. ?" Na ce Miliyan ɗaya.. Miƙa hannu ya yi tare da buɗe jakar dake akan table ɗin gabansa ya zaro bandir bandir na ƴan dubu dubu ya ajiye min a gabana, ya ce in ɗauka in tafi zasu neme ni. Na yi masa godiya da fara'ata ta ƙarfin hali, bayan ya gargaɗeni akan kar in kuskura wani ya ji maganar na ce masa toh kafin na tafi. Bayan na koma gida, na fara tunanin komawa gidan gonar saboda in yi masu leƙen asiri tun da na ga hanya.. A cikin kwanakin matata ta rasa gane kaina, hatta ƴa'yana basu samun kulawata, saboda hankalina ba zai kwanta ba in har ban ƙarasa aikin dana ɗaukarwa kaina ba. In ta fara min korafi, sai in ce suyi hakuri su taya ni da addu'a Allah ya bani sa'a akan abun da nasa a gaba, da yake tana da hakuri sai ta ce min toh in sha Allah zasu cigaba da tayani addu'a.. Tsautsayi ne da ƙaddara ya maida ni gidan gonar nan, Allahne ma ya nufa zan iya gane hanyar komawa saboda ruɗun dake akwai ina tafiya ina karanta addu'o'i a cikin zuciyata.. Ban taras da kowa a ƙofar shiga ba hakan ba ƙaramin dadi yayi min ba, cikin sanɗa na shige ciki kaitsaye, koda na shiga falo ban iske kowa ba, na fara bin ɗakunan dake a cikinsa ina leƙe ta window nan ma banga kowa ba, ni ne har hawa na ukun gidan gonar still nan ma babu mutane kwata kwata, raina ya bani ko dai babu kowa ne? Wataƙil kuma dalili ne ke kawo su gidan gonar, wata kofa na gani kamar wadda zata fitar da mutun bayan gidan, banyi ƙasa a gwiwa ba na bi kofar, ina leƙawa idona ya sauka akan dattawan dake a zaune kan kujerun shan iska...., Sheikh na shiga rudu sosai saboda ganin fuskokin mutanan dana sani, na ga ɗan iya, na ga dattijon arziki da surukinsa ba'indiyan nan, na kuma ga Musa, a raina na ayyana me ya kawo mutumin kirki dattijon arziƙi a gidan gonar nan? Ko dai nayi makuwa ne? Kasa kunne na yi ina sauraron firar da suke yi, "Kai saura sadaukarwa ɗaya ta rage maka, kai kuma sadaukarwa biyu ya rage maka, idan har kuka yi zan ƙara maku muƙami, ta yadda zaku samu ƙarfin sihiri a jikin ku da kuma ɗaukaka ta har abada.." dattijon arziƙine ya faɗa yana nuna surikinsa ba'indiyan nan da Musa. Ruɗewa na yi jin abun da ya girgiza tunani na, ganin abun nake kamar a mafarki. Ban gama dawowa hayyaci na ba na ji Ɗan Iya ya ce, "Bansan me kuke jira ba, yin ciki ne naku, muna da karuwan da zasu haifa maku ƴa'ya ba dole sai ƴa'yanku na sunna zaku sadaukar ba, amma idan kuka bada na sunna ɗin sai kun fi samun ƙarfin sihiri..." Dattijon arziki ya ce, "Na yi magana da abokan huldarmu na kasashen waje, karshen shekarar nan zasu kawo mana yaran mutanan da suka sadaukar, gaba ɗaya a gidan kurkuku zamu zuba su domin biyan buƙatar kanmu...." Dafe kai na yi da hannayena, a ruɗe na shiga ambaton Inna lillahi Wa'inna Ilaihirraji'un..! Kwatsam na ji muryar ɗan iya ya na fadin, "Na ji ƙamshin mutun a kusa damu, ina ji araina akwai wanda ya shigo gidan gonar nan..." Da jin wannan maganar, na arta aguje na nufi hanyar barin gidan gonar, cikin tashin hankali da fargaba. Sheikh Allah ne ya taimake ni harna samu na ƙaraso gida.. Ban iya bacci ba saboda zullumi da fargaban kada asirina ya tonu agurinsu su gano ni saboda nasan irin mutanan nan basu da imani indai akan sirrinsu ne zasu iya yin komai koda kuwa kashe mutunne. Amma fa dattijon arziki ya karya min zuciyata, kwana na yi ina kukan zuci, duk in na tuna yadda mutane suka yarda da shi, kowa nayi masa kallon jagora nagari ashe mutumin banza ne mai fuska biyu..." Chief Owais da ke sauraron sheikh Imam Malik, damuwa ce ƙarara akan fuskarsa, bai san sa'adda ya saukko daga kan sofa ya dawo kan carpet ya zauna tare da dafe kansa dake sara masa. Dakatawa sheikh Imam yayi idanunsa cike da ƙwalla ya ce, "Owais, tun bayan da muka yi waya da shi ya sanar dani komai ban ƙara jin ɗuriyar shi ba, saƙo na karshe da ya tura min shine. "Sheikh nifa tawa ta ƙare asirina ya tonu, sun gane nine nake yi masu leƙen asiri, nasan bazasu ƙyale ni ba. Don Allah ko bayan ba raina kada ku kyale su, kuyi kokarin damƙa su ga hukuma in ba haka ba zasu cigaba da aikata fasadi ne, nasan abu ne mai wuya saboda manyan mutana ne masu faɗa aji a ƙasar nan, bakowa ne zai yarda da labarin nan ba, dole sai kun yi takatsantsan gurin tona masu asiri, in ba haka ba zasu iya salwantar da rayuwarku." Numfasawa sheikh Imam ya yi kafin ya ɗaura da cewa, "Owais, da na ji shiru bai ƙara tuntu6a naba, kona kira wayarsa baya ɗagawa sai hankalina ya tashi, duk wani abokinmu da na tuntuba sai ya ce mini shima ya kwana biyu bai ji daga gare sa ba. Na damu sosai, a karshe na baro Sudan na shigo Nigeria ban nufi ko'ina ba sai gidansa ina zuwa na iske gidan a garƙame da kwaɗo, na tura yaro ya kira min makwabcinsa, bayan ya fito muka gaisa na tambaye shi ina malam Jazuli kwana biyu ban ji duriyarsa ba.." Makwabcin nasa ya ce, "Ai yau wata ɗaya kenan babu shi babu ƴa'yan shi an neme su an rasa, matarsa ma tuni ta tattara kayanta ta koma gidan iyayenta..." Hankalina ya tashi da jin maganar, ban 6ata lokaci ba na nemo address din gidansu matar tashi na je, bayan nasa anyi min sallama da ita, ta fito muka gaisa na ce mata na ji abin da ya faru meyasa bata sanar damu ba, kuma ina son in san haƙiƙanin abun da ya faru. Tana kuka ta ce min wallahi batasan komai da ya faru ba, a daren ranar da abun ya faru bata a gidan, tana a gidan ƙanwarta da ta haihu acan ta kwana saida safe ta dawo gidan, ta taras babu kowa daga shi har yaransu biyu, sun miƙa case din gurin ƴan sanda amma har yanzu ba wani labari. Lallashin ta na yi na ce ta yi haƙuri in sha Allah mu ma zamu bada gudummuwar mu gurin nemo su, ta yi min godiya bayan mun yi sallama na baro gidan nasu cike da damuwa. Owais ban iya ta6uka komai ba saboda bana so nima in jefa rayuwata cikin haɗari batare dana cika burin malam Jazuli ba na ganin na tona masu asiri, saboda raina ya bani su ne suka ɗauke shi watakil ma sun kashe su, saboda ba irin neman da ba'a yi masu ba amma ba'a gansu ba, har tsawon shekara jami'ai suna bibiyar case ɗinsu, daga baya ma suka watsar da batunsu. Ni da yan kungiyar mu, mun yi neman har mun gaji, ban ta6a gigin tunkarar mutanan da ya faɗamin sunayensu ba, saboda duniyar nan ta 6aci da marasa gaskiya Owais, kuma suna da karfin da ni bazan iya ja da su ba, babu wanda zai goyi bayana don ko abokanmu dana faɗa masu basu yarda da maganar ba nan take suka ƙaryata labarin da malam Jazuli ya bani, tun daga nan gwuiwata ta sage amma ban sare ba, sai na fara tunanin ta wace hanya zan shiga jikin waɗannan bayin Allahn don in samu hujjojin da zan maka su ga hukuma.. A ƙarshe na yanke shawarar dawowa Abuja da zama don in samu kusanci da su, saboda nasan dukansu mazauna Abuja ne, a lokacin bani da iyali. Da taimakon wani abokina mazaunin nan dana tuntu6a na faɗa masa zan dawo nan da zama, shi ya taimaka min gurin sama min apartment din nan da nake haya, bayan na saida wasu kadarorina na tattara yanawa yanawa na baro Jos na dawo Abuja. Ban jima da dawowa ba na fara tunanin ta wace hanya zan samu kusanci da Obinna? saina fara bibiyar mutane ina neman sani akan halayanshi anan nake jin mutane suna yabon shi suna cewa mutunne shi na jama'a, yana da mutunci, ga tausayi da jin ƙai kuma yana da yawan kyauta da sadaka. Dana bincika saina gano babu masallacin dake a kusa da Obie estate, sai kun baro arean ku ku ke zuwa masallaci, ni kuma dana tashi sena nemi dillallin wani fili dake a kusa da Obie estate, bayan mun yi ciniki da tsada da komai na siye shi, saida kuɗina suka ƙare gurin gina masallacin. Bayan da ya kammalu na gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayani murnar masallacin da zan buɗe, daga cikin wadanda na gayyata harda family ɗinku, da manyan mutanan da muke ma hidima da ta shafi bangaren addini da sauransu, araina inata zumudin zuwan ranar walimar saboda inga ko wani daga cikin family dinku zai halarta ko kuwa ba zaku zo ba, don nasan mawuyacin abu ne saboda an faɗa min ba kowani taro kuke halarta ba. Da ranar walimar ta zo, dubban jama'a suka hallara a masallacin domin taya ni murna tare da yi min fatan alkhairi, har na fidda rai da zan ga wani daga ahalin ku, sai da aka kusa gama walimar, ba zato ba tsammani sai ga motocin escorts na obie estate suna shigowa cikin masallacin, nan fa mutane suka fara zancen su, wani irin farin ciki ne ya lullu6e ni, dama abokina ya faɗa min in har aka gayyace shi taro da wuya yayi fashin zuwa. Lokacin da escorts suka bubbuɗe masu motar, jiki na rawa na ga mutane suna kewaye su, nayi ta mamaki na ce wannan wani irin farin jini ne da ɗaukaka? Mutane kamar zasu durƙusa ƙasa saboda tsabar girmamawar da suke yi mashi kuma daga cikin mutanan harda manyan ƴan siyasa na gomnatin dake ci a lokacin da hamshakan yan kasuwa, nima saina bi bayan mutanan, da ƙyar na samu aka bani hanya na miƙa masa hannu muka yi musabaha ina ta faman washe baki na gaishe da shi cikin girmamawa, da fara'arsa yake amsa min. Wlh Owais a lokacin ban ta6a ganinsa ido da ido ba, a tv nake ganinsa in ana labarai sai kuma a social media saboda kullum labarin family dinku trending ya ke yi, tun anan zuciyata ta karaya ban san ya akai na ji ya kwanta min arai ba, komai nasan cikin dattako ya ke yin sa, mutum ne wayayye baya ƙyamar kowa, ko maƙiyansa burgesu yake yi, wlh har kokwanto na yi a raina na ce anya malam Jazuli ya gano dakyau hada mutumin nan? Ko dai bai gani da kyau ba ne? saboda na ruɗe da ganin yadda yake kyautatawa mutane, ban zaci mutun mai daraja irinsa zai iya aikata abun da aka faɗa min ba. A ranar muka haɗu kuma duk a ranar muka fara shaƙuwa, tare da shi muka ci abincin walimar har muka ta6a fira da shi, shi kanshi saida ya faɗa min yayi mamakin yadda ya saki jiki da ni. Lokacin da aka kira sallah bayan kammala walimar ni na jamu sallar muka yi, bayan mun kammala mutane suka fara watsewa kamar karmu rabu da shi kafin tafiyarsa saida mukayi musayar numbers... Dakatawa ya ɗan yi yana mayar da numfashi, Chief Owais ya zabga tagumi yana sauraron shi jikinshi duk yayi sanyi laƙwas.. "Cikin ƙanƙanin lokaci zumunci mai karfi ya shiga tsakaninmu da shi har na koma babban malaminsa dake yi masa hidima da ta shafi addini, idan zai fidda zakka ko sadaka ni yake tuntuba, wani lokaci idan yana neman shawara baya tuntubar kowa in bani ba, toh a kullum in muka zauna muna yin fira da shi bashi da maganar data wuce ta jikanshi Owais, abakinsa na ji cewa kai jami'in bincike ne na sirri, kuma hukumarku tana da ƙarfi gurin yin yaƙi da ta'addanci. Koda na ji hakan saina nemi da ya bani number ɗinka don mu dinga gaisawa saboda nima na ji ka kwanta mun a rai, bai kawo komai aransa ba ya bani number ɗinka, idan ba zaka manta ba har waya ya ta6a ba ni muka gaisa da kai.." jinjina kai Owais ya yi. Bayan na dawo gidana, na shiga social media na fara bincike akan shafukanka, ta hanyar comment din da mutane su ke yi maka yasa na fahimci irin ƙwazon dake gare ka, abun da ya fi burgeni yadda mutane suke yabonka da jinjina maka akan gaskiyarka da son adalci, duk wanda zai yi magana akan ka sai ya kurantaka, bayan haka mutane marasa gaskiya suna jin tsoron case dinsu ya shiga hukumarku saboda baku yi masu da sauƙi. Bayan na gama bincike na akan ka, abu ɗaya da nake tunanin zai yi min wahala shine ta yadda zan tunkare ka, nasan kaitsaye idan na faɗa maka komai ba zaka taba yarda ba tun da kakanka ne mafi soyuwa agare ka, har kulle ni zaka iya yi, shiyasa na yanke shawarar kiran ka asirrance, kafin na yi hakan saida na nemi ilimi akan ta yadda zan yi hakan batare daka bi diddigin layina ba saboda na gano you're a cyber expert.. Lokacin da ya ƙarasa masa labarin, kwata kwata hankalinsa bai tashi ba, saboda a halin yanzu babu abun da zai ƙara bashi mamaki a duniyar nan tun daga kan kakansa.. "Owais, yanzu tun da na faɗa maka komai, pls ka yi ƙoƙarin yin magana da kakan naka, tun da yana kula ka, ina so ka tambayesa game da malam Jazuli nasan ba zai rasa sanin sa ba, duk da ina ji araina kamar basa a raye, amma duk da haka ka tambayesa, ƙwara mu san meya faru da su, wlh har yau danginshi nemansu suke yi musamman matar shi. Jiki asanyaye Chief Owais ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce, "Baba Imam thank you for sharing everything, na ji dadi, kuma in sha Allah zanyi magana da grandpa, duk yadda muka yi da shi zan sanar maka." Hugging ɗin juna suka yi, kafin ya ruƙo hannunsa har bakin motar Taj ya rako shi. Har ya buɗe motar zai shiga sheikh Imam ya ce ya ɗan jira akwai saƙo da zai bashi, ya amsa mashi da toh. Cikin sauri Imam ya koma Cikin apartment nasa, jim kaɗan ya dawo hannun shi ruƙe da date boxes (kwalayen dabino) Ya miƙa ma Owais ya sa hannu ya kar6a, "Idan ka koma gida, ka ba su Unaisah da Ummi, ka gaishe min da su.." Tsananin tausayin shi ne ya kama Chief Owais, saboda ya fahimci saƙon na Ummi ne yake son ya bata, amma sai ya fake da sunan su Unaisah kafin nata saboda baya son ya gane komai baisan ya riga da ya sani ba. "In sha Allah zan kai masu, ina ƙara godiya baba Imam, you have done so much for us, we can't repay you, Allah yasaka maka da alkhairinsa..." Murmushi sheikh Imam yayi masa tare da amsawa da Amin, bayan sun yi sallama ya shige cikin motar tare da kai hannu ya ɗan dafa kafaɗar Taj dake sharar bacci, firgigit ya farka yana tambayar waye ne.. "Daga yin waya na ji ka shiru baka dawo ba." Murmushi ya yi."Na kira ummu Unaisah ne mun daɗe muna waya bayan mun gama kuma bacci yai awon gaba dani, " Ya ƙarashe maganar tare da tambayar ina sheikh Imam ya ce ai har sun yi sallama da shi ya koma ciki su tafi kawai. Amsa mashi yayi da toh kafin suka tafi... Kafin su karaso Taj ya lura da yanayin fuskar chief kwata kwata babu walwala kamar an ƙara ninka masa damuwarsa.. "My in-law, meya faru ne? Na ga kamar babu walwala atare da kai." Yamutsa fuskarsa ya yi ya furta, "Kada ka damu pls.." gyaɗa kai Taj ya yi tare da kallon date boxes din dake akan laps dinsa bai dai tanka ba.... Can ya tsinkayi muryarsa a kunnansa, "Zaka iya tuna sunan malamin nan da matsafa suka handame shi da ƴa'yan shi a lokacin da ku ka yi ma su leken asiri?" Ya tambaya yana duban shi.. shiru ya ɗan yi jim yana kokarin tunanowa. "Am.. kamar Jazuli ne amma ban ji da kyau ba saboda a lokacin sun yi nesa damu, bamu iya jin me su ke cewa sosai..." Murmushin takaici Chief yayi jin abun da yake tunani ya tabbata, amsa mashi ya yi da okay, daga haka bai ƙara tambayar shi ba, shima kuma bai nemi sanin meyasa ya tambaye shi ba har suka koma gida. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ *daga Alkamin Boss Bature💋✍️* Bari mu koma baya mu ji meya faru bayan kwana ɗaya da afkuwar lamarin❓ Bayan sun koma cikin main falo kowan nan su ya samu wuri saman Sofa ya zauna, yanzu da suka ɗan samu nutsuwa damuwar su da tunaninsu ya karkata akan halin da Hajiya saratu da momma suke a ciki, sun so da suka fita raka imam daga can su wuce Villa, amma sai basu yi hakan ba saboda akwai buƙatuwar su fara yin nazari akan wani muhimmin abu.. Kafin su fara tattaunawar, Sharafudeen ya zaro waya ya kira layin sarauta, bayan ta ɗaga kiran muryarta cike da damuwa ta soma tambayar shi. "Why babe ka barni cikin damuwa, ko bacci ban yi ba jiya saboda rashin kwanciyar hankali, pls ka fada min menene ya faru da hajiya Saratu? how did she get the shards that hurt her face, na tambayi su twins sun ce suma basu sani ba, amma suna zargin faɗa ne ya haɗata da hajjaty, shin da gaske ne? kuma meyasa ina ta kiran ka baya shiga, baka dawo ba kuma baka faɗamin zaka kwana a gida ba, kodai wani abu ya faru ne?" "Ki yi hakuri da ban samu ɗaga kiran ki ba, ban kuma kira na ji a wani hali kuke ciki ba, am really sorry, in sha Allah nan da 30 mins, zamu shigo villa din, and we can discuss then" Ta amsa mashi da toh, "Ya jikin marasa lafiyan namu?" "Babe the doctors gave me some information about Sarah's condition since yesterday, they've cleaned and treated her facial lacerations, and she's receiving antibiotics to prevent infection, they assured me she'll feel better in a few days, in sha Allah" Da yake handsfree ya sanya wayar gaba ɗaya suna sauraron maganar Sarauta. "What about Momma? Ita ya jikinnata? Is she getting better?" "Who's Momma?" Ta tambaya saboda bata gane wa yake nufi ba. "I mean the old lady" Ya amsa mata. "Oh, she's getting better, according to the doctor's explanation, Her brain injury has caused short-term memory loss, and they can't restore her memory, If she doesn't remember herself." Da damuwa a fuskarsa ya dubi ƴan'uwan nasa dake sauraron bayanin sarauta.. "Babe, zan iya sanin wacece? tayi min kama da momma, amma tafi momma tsufa, ba dan momma ta mutu ba da sai in ce ita ce, and One thing puzzled me when I sat next to her she was mentioning Honeyboy and Superstar, who are they? Bai san sa'adda murmushi ya kubce mashi ba ya ɗago suka haɗa ido da prime minister, wanda idanunsa suka cicciko tab da kwalla. "Nagode da kulawarki agare su, idan na shigo zamu yi magana, Saratu tana magana?" "Bata farka ba, allurar da su ka yi mata ne bata sake ta ba, amma muna sa ran zata farfado nan bada jimawa ba." Sallama su ka yi da juna, Ya aje wayar tare da maida hankalinsa akan yan uwansa dake kallonsa. "Menene mafita? Bai kamata mu ja baki mu yi shiru ba, batare da mun ɗauki mataki akan abunda aka yi wa Auta ba" His excellency Deen ya ce, "Ni so nake insan wani mugunne yayi mata haka? Meyasa? Me kuma ya kai ta ɗakin Hajjaty?" Abdul Razak ya ce, "Wallahi raina ya 6aci abun ya ƙona mini rai, muna a cikin mawuyacin halin nan aka samu wani mara imanin ya zagaya ta baya yaje ya cutar da ita, so yayi ma ya kashe ta badan Allah ya kaddara maids sun je ɗakin ba har suka gani ai da tuni ta jima da mutuwa." Chief Owais da sauran matasan dake agurin sunyi shiru suna sauraron su. Deen ya sake cewa, "Baku zargin faɗa ne ya haɗa ta da hajjatyn har tayi mata bugun kawo wuƙa?" Girgiza kai Abdul razak yayi. "Bana tunanin hajjaty zata iya cutar da Saratu, tsawon shekaru bata ta6a cutar da wanin mu ba, bawai don na yarda da ita ba, ni yanzu na yi hankali, mugu bashi da kama, kowa zai iya rayuwa da kai da fuska biyu na tsawon lokaci yana kyautata maka saboda wata muguwar manufa ta shi, tun da har mahaifinmu ya ci amanar mu balle ita da take bare, kawai abun ya ɗaure min kai ne na rasa wa zan zarga..." Ya ƙare maganar fuskarsa a yamutse. "Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya, kada mu yi saurin yanke ma hajjaty hukunci saboda ganin hajiya Saratu da aka yi adakinta, ba dole ya kasance ita ne ta cutar da ita ba..." Sharafuddeen da ya ɗauko maganar bai kaiga direta ba, Sir mubarak ya dan yi gyaran murya, gaba ɗaya suka maida dubansu a gare shi, tun da suka fara magana bai saka baki ba sai yanzu. "Tun ɗazu da ku ka ga na yi shiru, nazari nake yi akan abubuwan da suka faru abaya, maganar gaskiya bana zargin hajjaty ce ta cutar da auta, sai dai idan Pravin ne ya yi mata hakan.." Da ɗan ruɗu akan fuskarsu suke kallon shi, sam sun shafa'a sun manta da Pravin basu lura ma babu shi agidan ba. "Meyasa ka ce haka?" Deen ya tambaya. "Abun da yasa nake zargin pravin, Idan ba zaku manta ba aranar dinner din Hateem, Pravin ya yi wani abu da ya ja hankulan mutanan dake agurin, a bainar jama'a ya damƙi hannun Hajjaty ya tursasa mata akan tabar hall din, tun anan na sanya masu alamar tambaya..." Da yayi wannan maganar nan take suka tunano lokacin da abun ya faru babu wanda bai zargi akwai boyayyiyar alaka a tsakaninsu ba, a lokacin har mataki suka ce zasu ɗauka akan shi, amma daga bisani suka yi watsi da maganar. Sir mubarak ya ɗaura da cewa, "May be sun daɗe suna kulla makirci a bayan idon mu, bayan haka komi ya faru da Saratu baba ne ya ja mata, lokacin da ta zo da shi daga ƙasar India ta nuna shi take so ta aura gaba ɗayan mu babu wanda ya amince saboda bai kwanta mana a rai ba, saida muka musa akan mu bamu yarda Saratu ta auri bare wanda ba jinsin mu ba, mutumin da ko asali baida shi, ba mu san kowa nashi ba in ba ita ƴar uwar ta shi ba da ya zo da ita daga baya, amma Saratu ta ƙi sauraron mu saboda baba ya goya mata bayan ta auri za6in ranta" ya faɗa ransa a matuƙar 6ace. "Bayan haka ina zargin baba shine ya janyo pravin cikin harkar tsafinsa, watakil sunyi yarjejeniyar zai bashi auranta idan ya amince zai yi masa abun da yake so shi kuma da ya ke dama kwaɗayin dukiyar Saratu ce ta ruɗe sa shiyasa ya biyo ta don ya kwashi rabon shi, shine ya amince zai masa biyayya..." Maganar Sir Mubarak ta ɗaga hankulansu saboda suma sun hasaso abun da ya ke zargin. Hateem ya ce, "In kuwa hakane Baba ya zalunci Saratu, ni dama na yi mamakin yadda ya yi saurin amince ma auranta da shi, saboda kwata kwata ba ajinta bane, a matsayinsa na mutun mai girmama darajarsa da ƙimarsa amma ya rufe ido ya nace akan abar Saratu ta auri za6in ta, abun ya tsaya min araina, a lokacin har kwatanta masa muka yi ya rufa mana asiri kada ya zubar mana da mutuncinmu Saratu ta fi karfin Pravin, ba sa'an aurenta bane, mutane zasu yi mana surutu amma duk bai duba wannan ba, thats mean dama can da wata a ƙasa a tsakanin su..." Chief Owais dake sauraronsu zuciyarshi ta zo wuya saboda tsabar 6acin rai da tsanar hali irin na grandpa dinsa da kuma haushin Pravin. Jikinsu Ziyad ya yi sanyi lakwas, jin abun suke kamar a mafarki saboda al'ajabi. "Lokacin da momma ta fara tona masu asiri, munafukin batare da sanin mu ba ya zame jiki ya fuce daga falon, ina tunanin a lokacin da zai gudu Auta ta gan shi, shine ta bishi don ta tuhume shi akan abunda momma ta faɗa, watakil ta riske shi a ɗakin hajjaty suna kokarin guduwa shine su ka yi mata haka don kada ta tona masu asirin abun da suke kokarin yi..." Da ruɗu akan fuskokin su suke kallon shi, gaba daya sun yarda da maganar shi. "Mayaudaran banza, na dade banga mugun miji irin pravin ba, tsawon shekara da shekaru yana auran Saratu ashe bada zuciya ɗaya yake tare da ita ba, ni takaici na ƴa'yan dake atsakanin su, ya za su ji idan su ka ji mugun halin uban su? Da kuma abun da ya aikata, dama ya lafiyar gwiwa! Suma ba hankaline ya ishe su ba, uban nasu ya 6ata su, badan mun tsaya masu tsayin daka ba akan tarbiyarsu, da Allah kadai yasan lalacewar da zasu yi...." Senate Lateef ne ya faɗa cikin fushi. "Kuma wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa, ɗaya daga cikinsu ba zai sha ba, ko da zasu gudu daga ƙasar nan ne su tafi birnin sin saina sa an kamo min su an dawo dasu nan, dole su gir6i abun da suka shuka..." Ya faɗa tare da kai hannu ya daki hand sofa. "Dole Saratu ta shiga mawuyacin hali, nafi jin tausayinta, ba ta yi dacen uba ba, ba kuma ta yi dacen miji ba.." a cewar Deen "Owais, su wanene sauran Elders din?" Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da duban daddyn nasa, "Elders goma sha biyu ne, shidda suna jagorantar kurkukun ƙaddara, sauran shiddan ba a ƙasar nan suke da zama ba, mutun huɗu da momma ta fada su kaɗai muka sani a cikin su, amma akwai mutun biyu da muke zargin suma elders ne, anan Abuja suke da zama, nan bada jimawa ba zamu kammala bincike akan su, na tambayi baba amma ya ki ya sanar da ni..." ya faɗa cikin raunannan murya. Har suna haɗa baki gurin furta, "ka yi magana da baba? Yaushe?" Numfasawa yayi kafin ya zayyana masu komai da suka tattauna tare da baba Obie. Gaba ɗaya basu ji dadin ƙin faɗa masan da bai yi ba, duk da sun riga da sun san halin uban nasu, duk da mugun halinsa yana da amana da kuma rukon alkawari, tun da har ya ƙi sanar da shi to kuwa bazai ta6a faɗa ba. Kwantar masa da hankali su ka yi, su ka ce kada ya damu tun da har ya ce ya nemi taimakon Allah, toh ya dage da addu'a suma zasu taya shi da addu'a, kada ya kuskura ya bari maganar baban ta sagar ma shi da gwiwa, in sha Allah babu abun da zai gagare shi, su basu ma so ya nemi taimakon sa ba, da ya yi shawara da su da ba zasu bari ba, saboda haushin shi da suke ji, kuma suna so ya sani a yanzu binciken bana hukumarsu bane kaɗai suma sun shiga ciki, zasu taya shi faɗan har zuwa lokacin da zasu kawo ƙarshen su, sannan komai ake ciki ya sanar da su, zasu taimaka mashi da iyakar iyawarsu, su kuma wadanda momma ta fadi sunayen su a cikin elders din za su yi kokarin kama su don ba zasu bari a ci gaba da aikata fasadi a doron kasa ba...." Maganganunsu sun karfafa zuciyar Chief, musamman da suka bashi shawarwarin da zasu amfane shi akan binciken shi, sun bashi goyan bayansu dari bisa dari, prime minister ya ce zai ƙara mashi da Canadian Police, Sir mubarak ma ya ce zai bada gudummuwar sojoji, kwata kwata basu yi magana akan inmates ba, ba don basu damu da su ba, sai don sun fi so su fara kawo karshen elders amma abun yana aran su, suna son suga duka inmates watakil su samu sauran yaransu da ke a raye🔥 Har maganar Jan kunne suka yi sir Mubarak ya ce, "Abun haushi abun takaici wai aure! haba ni dama abun na daure min kai, amintarsu ta jima tana burgeni, basu taba samun sabani ba, basu gajiya da ziyartar juna, musamman shi jan kunnan, ashe akwai wata a ƙasa, wama yasan me suke aikatawa idan suka shige ɗaki, bamu taba kawo komai a ranmu ba, saboda yardar da mu ka yi da su, munafuki shiyasa ya ƙi ajiye iyali ashe yasan me ya taka, wato uban namu ne iyalinsa ko..." Maganar shi ta so basu dariya ba don halin da suke a ciki ba. Lokacin da marece ya kunno kai, gaba daya suka shirya tafiya Villa, Chief ne kadai bai bi su ba saboda ya damu da ya dawo gidansa, a cikin motocin security details din Sharafuddeen su ka tafi, ba zan iya misalta maku haduwar presidential resident ba, abun sai wanda ya gani. Daya bayan daya motocin suka shiga cikin Villa, da matsakaicin gudu suka nufi presidencial medical center, a gaban hospital din suka yi parking, a hanzarce security officers din dake tsaron asibitin suka yi hanzarin karasowa tare da buɗe masu cardoors din, suna fitowa suka fara sara masu.. Cikin sauri suka shiga cikin katafaren asibitin duk inda suka gifta jiki na 6ari hospital staff suke gaishe da su with respect kamar zasu durkusa kasa, wasu daga cikin staffs din ne suka yi masu jagora zuwa Private room din da aka kwantar da Momma, suna shiga ciki idanunsu suka sauka akanta tana a kwance saman medical bed sanye da patient uniform, wuyan hannunta na dama asanye yake da canula, da alama tayi nisa a cikin baccinta, hankalinsu ba karamin kwanciya ya yi ba ganin yadda take bacci cikin kwanciyar hankali, daga gani tana samun kyakkyawar kulawa. Docs din dake kula da ita ne suka shigo dakin jin zuwan Mr president da yan uwansa bayan sun gaisa da su, suka fara kora masu jawabi game da cigaban da suke samu akan lafiyarta, bayan sun gama sauraronsu suka yi masu godiya bisa ga kokarinsu, kafin su bar dakin momma saida suka je har gaban gadonta suka kura mata ido kamar za su haɗiye ta musamman Hateem da Sharafuddeen wani irin kaunar mahaifiyarsu ne ya ƙara shigarsu ba dan basu son su katse mata baccinta ba da ba abun da zai hana su tada ta, a hankali suka ruko hannayenta kowan nan su ya manna mata kiss, hatta su Sir mubarak saida suka sumbaci hannunta, kafin daga bisani suka bar dakin nata. Docs su ka yi masu jagora zuwa private room din da aka kwantar da hajiya Saratu suna shiga ciki suka taras da su twins a zazzaune kan kujerun dake agaban gadon, jiya izuwa yau har yar rama suka yi, idanunsu sun kumbura sunyi jajur daga gani sun sha kuka, suna jin takun tafiyarsu suka mike da sauri suka nufe su, cikin sauri suka rungumesu, wani sabon kukan suka kuma fashewa da shi, lallashin su suka dinga yi, cikin shesshekar kuka Zaid ya ke tambayarsu ina dadynsu? Me yasa bai zo ya duba halin da mommynsu take a ciki ba? Ko har yanzu bai dawo gidan bane? Tun jiya suke kiran wayarsa a kashe.." Zayn dake ta cizon le6ensa saboda zuciya cikin bacin rai ya ce, "Uncles ku fada mana meke faruwa ne? and Where's Hajjaty? Did she return home or run away? Wallahi we must take revenge for what she did to our mom, She must feel the pain our mom felt, jiya daga mu har ita babu wanda ya runtsa, muna jiyo sambatun da ta dinga yi tana ambaton sunan hajjaty da na daddyn mu..." Maganar Zayn ta ƙara karfafa zargin su akan Pravin da Hajjaty tun da har Saratu tayi sambatun sunayen su, hakan na nufin sune suka yi mata aika aika, senate Lateef ne ya ce su yi hakuri yanzu haka su kansu basu san inda daddynsu yake ba, amma suna sa ran zai dawo nan bada jimawa ba, ita kuma hajjaty sun yanke shawarar zasu baza jami'ai cikin gari su nemo ta.." Dakyar suka shawo kan su, bayan kamai ya lafa suka karasa shiga dakin, a kwance suka hango hajiya Saratu sanye da patient gown, fuskarta a naɗe take da bandage, idanunta da lips dinta ne kadai abude, baiwar Allah ta galabita sosai ko idanunta bata iya buɗewa, jikinta sai kerma ya ke yi musamman yatsun hannayenta da suka raunata har ɗauri aka yi masu saboda gocewar da su ka yi. cike da tausayawa suke kallon ta, biyu daga cikinsu ne suka ruke hannayen ta, yayin da docs din dake a tare da su suka fara kora masu jawabi akan abun da ke damunta, abun da ya ƙara daga hankulansu jinin ta da ya hau, tun jiya ya ƙi sauƙa. Duk da doc din sun ce zasu yi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya, kuma tafi bukatar duk wani abu da zai kwantar mata da hankali saboda akwai depression atare da ita. Koda jin wannan maganar nan fa suka hada baki gurin lallashinta da bata baki kuma suka tabbatar mata cewa sun gano wadanda suka jefata a halin da take a ciki kuma soon zasu kama su don su hukunta su, da kanta ma suke so ta dauki fansar abun da su ka yi mata. Lokacin da suke fada mata maganganun nan, ta yi ta kokarin bude idanunta don ta samu ganinsu sai dai ta kasa saboda raunin da su ka yi mata, la66anta na kerma ta furta, "babb..pur, hahaj" Bata ƙare maganar ba, Sharafudeen ya yi saurin tarar numfashin ta da cewa, "Don't force yourself to talk, you'll hurt your wound, I know what you want to tell us, As we told you, we've already found out everything, and we'll take action So, please calm down, we don't want you to worry, and we don't want to lose you. In sha' Allah, you'll feel better soon" Kalamai masu daɗi mr. president ya gaggaya mata duk da halin jinyar da take a ciki saida ta ji sanyi aranta, musamman da ta ga yadda suka nuna damuwa akanta, kowa lallashinta ya ke yi da bata baki, kamar kar su tafi su barta saida su ka shafe rabin awa adakin anan ma har sharafudden ya kira p.a dinta ya sanar da ita cewa bata da lafiya an kwantar da ita asibiti, don haka ya dakatar da ita zuwa aiki, har zuwa lokacin da zata ji sauƙi, p.a din ta nuna damuwarta bayan ta yi addu'ar Allah ya bata lafiya, ta ce zasu zo tare da sauran health staffs don su duba lafiyarta, bayan sunyi sallama kafin su bar room din saida kowan nan su ya yi mata addu'a, duk tana jin su sai dai ta kasa buɗe idanu ta dube su. Lokacin da suka fito daga dakin yayi dai dai da zuwan Sarauta tare da hajiya Laura, da Turai tare da Jazz daga cikin villa suka nufo asibitin don su ƙara duba patient din nasu, kowan nan su ka kalla babu walwala akan fuskarsa. Gaba ɗaya suka nufe su, Jazz da sauri ya nufi Sir Mubarak ya yi hugging dinsa, bayan sun gaggaisa da junan su, Hajiya laura ta ja hannun Sharafuddeen suka koma gefe daya, Hajiya Malikat ma ta bi bayansu, tunkafin ma su fara magana ya labarta masu abun da ya faru da Saratu ya ce suma basu san me ya kaita dakin Hajjaty ba, amma suna zargin fada ne ya kaure atsakanin su, ita kuma tsohuwar da suke magana akan ta ƴar uwar baba ce..." Kwata kwata bai bayyana masu abun da ya faru na tonuwar asirin babansu ba saboda ba ya son su sani. Cizon yatsa Hajiya Laura ta yi rai a 6ace ta ce, "Ni dama nasan za'a rina, hajjaty makira ce, ba dan Allah take a tare da ku ba, na jima ina zargin akwai wata makarkashiya da take yi maku, munafuka yar tsibbu, ba irin gargadin da banyi ma Saratu ba akan ta kore ta daga gidan, tama bar ƙasar ta koma India amma ta ƙi jin maganata ai ga irinta nan, kun kawo mugun abu kun aje a gida gashi nan tana neman ta halaka Saratu, dama ita take haƙo, tana bakin cikin ganin hajiya Saratu tafi ta komai, da yake bata san halacci ba, ni ban san ma tayaya akai har tafi ƙarfin Saratu ba, koda yake ai matsafiya ce da rauhanai take amfani, watakil ta asirceta ne shiyasa ta kasa tabuka komai har ta yi mata jahilin bugun nan, kuma wlh koma gidan uban wa hajjaty ta shiga dole a nemo ta.." tun da ta fara maganar bai katse ta ba, ya fahimci ranta ya matukar 6aci, da zata ga hajjaty ba abinda zai hana ta binne ta da ranta. Hajiya Malika kuwa tsabar al'ajabin abun da Sharafudden ya fada ya hana ta furta kalma, ta gaza yarda cewa Hajjaty ce tayi ma Saratu haka duk da bata mu'amala da ita, ko magana bata haɗa su in ba ta zo gaishe ta ba idan suka je gidan baba, amma tana kyautata mata zato, bata tunanin zata iya aikata abunda suke zarginta. Sai da ta bari hajiya Laura ta gama magana da shi tabar gurin, sannan ta fuskance shi tare da marairaice fuska ta ce ya fada mata gaskiyar abun dake faruwa, saboda tun da ta gansu ta lura da akwai damuwa atare da su, kuma ta ga alamun kamar sun yi kuka, sannan abun da ya faru da hajiya Saratu tana kokwanton in hajjaty ce ta yi mata hakan duk da ba agabanta komai ya faru ba, amma sun yi bincike dakyau? Shiru ya yi batare da ya iya furta kalma ba, saboda ya rasa amsar da zai bata, yasan halin kayansa dama saida ya yi fargaban ta tuhume shi, babu mai iya karantar halinsa bayan shakikinsa sai kuma ita. Jin yayi shiru bai bata amsa ba yasa ta ce, "kada ka boye min pls, damuwarka tawa ce, ban ta6a boye maka damuwana ba, saboda babu sirri atsakaninmu, abun daya shafe ku nima ya shafe ni tun da nima yar uwa ce, bawai iya matsayin matarka nake ba, ka taimaka ka fadamin in ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, kuma matar da ka ce dangin baba ce, kayi hakuri amma ni ban yarda ba, nafi tunanin dangin momma ce saboda tayi kama da ita..." Duk yadda ya so ya canza mata tunaninta ta ƙi bari, a karshe da ta kafe ya lallabata ya ce ta yi hakuri, tabbas akwai abun da ya faru da su, amma bazai iya sanar da ita ba, kada ta matsa mashi akan ya fada mata, ta yi hakuri har zuwa lokacin da ya ji zai iya sanar da ita.." tace mashi in sha Allah zata jira har zuwa time da ya ji zai iya sanar da ita. A bangaren Sir Mubarak, tuni shima Turai ta ja hannunshi suka ke6e, ta tambaye shi menene makasudin abun da ke faruwa? ta tambayi su twins sun ce mata hajjaty ce ta lahantata, sai dai ita bata yarda hajjaty zata iyayin hakan ba saboda ta yarda da ita, aminiyarta ce, tasan halinta ciki da bai, hajjaty ko kiyashi ba zata iya kashewa ba saboda tausayinta balle har ta iya yiwa hajiya Saratu haka, ita a saninta ma Hajjaty tsoron hajiya Saratu take ji saboda rashin jituwar dake a tsakaninsu" Sir Mubarak ya ce, "Su kansu basu tabbatar da abun da suke zargi ba akanta, amma abun da yasa suke zarginta saboda guduwar da ta yi tun jiya har yau bata dawo ba.." Hankalin Turai ba karamin tashi ya yi ba, cike da rashin jin dadi ta ce, "Pls duk da haka ku yi mata uziri, kada ku zarge ta, zai iya yiwuwa wani ne ya ke son ƙalla mata sharri, saboda a jiya kafin ta zo birthday celebration din Owais ta kira ni a waya har ta faɗa min bata da lafiya tana fama da zazzabi, bayan na yi mata sannu da jiki na ce mata zan shigo in duba ta, mutumin da baida koshin lafiya, ina ya ga karfin da zai iya faɗa da babbar mace irin hajiya Saratu?" Yakamata kuyi bincike da kyau, Hajjaty matsoraciya ce bata da karfi, wallahi bata iya fada ba ko na baki..." Maganar Turai ta dan sanya shi kokwanto acikin zuciyar shi, ya ce mata in sha Allah za su yi bincike idan ma bata da sa hannu za su gano ne. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kuma tambayar shi ina pravin? Ya akai bai zo ba? Ko dai baisan me ya faru da Saratu bane?" Ya ce mata pravin tun jiya bai dawo gidan ba, sun kikkira layinsa a kashe, amma suna sa ran zai neme su ne! " Shiru ta yi jimm kafin ta ce Allah ya sa ya yi tunanin dawowa ko dan saboda twins din sa, watakil in suka gan shi hankalinsu ya kwanta, saboda sun bata tausayi jiya, ko ruwa basu sha ba, a zaune suka kwana, shiru kawai ya yi bai tanka mata ba. Kafin tafiyar su, saida suka sa kitchen staff suka shiryama su twins abinci kuma suka tursasa masu dole su ka ci abincin, sannan su ka yi wanka, kowan nan su ya sauya kayan jikin shi da wanda Hajiya malika tasa aka kawo masu. Babu wanda bai tambayi ina baba ya ke ba a cikin su, da suka rasa amsar da zasu basu a a karshe sai dai suka ce masu baba bayanan jiya bayan an gama celebration din Owais, likitan amininsa ya kira sa a waya ya fada masa baya da lafiya, basu san ma ya tafi ba, abun da ya sa ma basu sanar da shi abun da ke faruwa ba saboda basu san su ɗaga hankalin shi. Lokacin da suka tashi tafiya saida suka koma ɗakunan marasa lafiyansu suka kara duba jikin nasu, still momma bata farka ba, sun so su gana da mahaifiyarsu a ƙarshe dole suka hakura, su twins ba su bar asibitin ba suna a tare da mommynsu, Sharafuddeen ma bai bi su ba. Jazz da mom Turai ne kadai suka bi sauran suka dawo estate din su.. CIGABA🔥 ____________________________✍️ Zaune su ke saman gadon Aunty Ummi, su biyu suna fuskantarta, yau gaba ɗaya sun rasa gane kan ta, duk ta bi ta kuntata kanta. "Aunty Ummina meke damun ki ne? babu walwala atare dake, ko murmushi baki yi.." Batool ce ta fada tana marairaice mata fuska. "Pls aunty Ummi, Ki faɗa mana damuwarki mana ko baki da lafiya ne..?" Kallon Unaisah ta yi, "Kada ku damu, Lafiyana lou, kawai hankalina ba a kwance yake ba, tun dazu gabana ke faduwa, Ina jin ba dadi a cikin zuciyana." ta faɗa fuskarta a yamutse.. "Ki daina sanya damuwa aranki pls, zata iya haifar maki da wani ciwon, kinsan mun damu dake bamu san mu ganki a wani yanayi mara dadi..." Murmushi ta saki har cikin ranta ta ji dadin maganar Unaisah.. "Shiyasa nake bala'en son ku wlh, kuna da hankali, kuma kun damu da duk wanda ke tare da ku, nima ba zan so in sanya ku a damuwa ba don haka na daina, tun da baku so, but pls ku ta ya ni da addu'a." murmushi suka saki atare suka hada baki gurin furta, "In sha Allah zamu yi maki addu'a, muma muna son ki sosai, Allah ya bar mana ke aunty Umminmu.." "Ameen." ta faɗa da fara'arta, "Me yakamata mu yi yanzu? Yoga or what"? Ta tambaya don ta ji ra'ayinsu.. "Ai bamu iya ba" "Zan koya maku yanzu, in muka gama sai mu yi wanka." Saukowa suka yi daga kan gadon, gaba dayansu riga da wando ne a jikinsu na shan iska, akan tattausan rug din dakin suka fara motsa jikin su, da kanta take koya musu yadda zasu yi yoga din, tuni suka fara haɗa gumi suna sakin nishi.. Wayar Ummi ce ta soma yin ringing, mikewa ta yi daga kwancen da take a ƙasa ta dube su duk sun baje sun ɗage kafafunsu sama doguwar sumar kansu ta lullube fuskokin su.. "Ku cigaba da yi, zan amsa kira.." tana fada ta mike ta dauko wayar, mood din fuskarta ne ya canza ganin sunan me kiran ta, nan take ta fara tariyo maganganun da suka tattauna da Chief ta rasa gane meyasa take kokwanto akansa? Kamar mara gaskiya ta dubi su Unaisah dake ta aikin motsa jiki, ganin hankalinsu baya akanta ne yasa ta lallaba ta shige toilet ta yi picking call din sam ta kasa magana sai mayar da numfashi take yi kamar wadda ta sha gudu. Husky voice dinsa ce ta ratsa kunnanta, "Ummi ya muka yi da ke? shiru ta yi bata amsa masa ba.. "Nace zan zo kin hana ni, kema kin ce zaki zo amma baki zo ba, ina ta jiran ki, meyasa kika fara canza minne?.." Ya faɗa cike da rashin jin dadi. Dakyar ta daidaita nutsuwarta kafin ta ce,"Me zan yi maka idan nazo uhm?" "Abun da kika saba yi min, Ummi a buƙace nake da ke, tsawon wata baki bani hakkina ba.." Murmushin gefen fuska ta saki ta so ta bijire masa amma tunawa da maganar Chief ya sa ta kashe masa murya, "I need you too my big boss, fiye da yadda kake bukatana, ba canza ma na yi ba, ba a bani iznin fita bane, kuma ina yin taka tsantsan ne saboda sharadin da ka gindaya mini." tana iya jiyo sautin ajiyar zuciyarshi alamar ya ji dadin kalamin ta. "Yanzu da yaushe za ki zo guest house ɗina?" "Zaka iya haƙura har zuwa weekend?" "Zan iya amma bisa sharadin idan ki ka zo kwana za ki yi.." "Ba damuwa big boss, your command is my wish, kasan kai nawa ne ni kadai.." Shu'umar dariyarsa ya saki, idan na damƙe ki this time, ba zan raga maki ba,.." Wani iri ta ji aranta kamar kalamansa basu yi mata daɗi ba, sai ta ji inama dr Shureim ne yake furta mata su bayan sun yi aure, mafarkin da ta daɗe tana yi. har su ka yi sallama babu walwala akan fuskarta. Dafe wayar ta yi akan kirjinta ta lumshe idanunta, tana tariyo maganganun chief Owais a cikin kunnanta sun tsaya mata a ƙahon zuciya, ta kasa yarda, big boss bazai iya rashin imanin nan ba, ita ba ta yi masa kallon mutumin banza, Saboda komai ya faru game da haramtacciyar mu'amalarsu tare da hadin kanta ne ba dole yayi mata ba, shiyasa bata ganin laifinsa, kawai abu biyu ne ya jefa ta a ruɗu, me ya kai diary din Unaizah da hotunansu a ciki❓Yarinyar da bata taba barin Uk ba❓ abu na biyu zanen tattoo din sa dana Danish❓ bazata ta6a yarda ba in har bashi Uncle Musa dinne ya bayyana mata komai da kansa ba, amma ta fara tunanin zata basu hadin kai saboda dalili biyu! Na farko don ta wanke Uncle Musa daga zargin da suke yi akan shi! Dalili na biyu saboda bata so tayi disrespecting din Chief Owais, tana ganin girmansa bazata iya ƙin bashi hadin kai ba🔥 Fitowa ta yi daga cikin toilet din, turus ta tsaya tana kallon su Unaisah dake sharar bacci, daga motsa jiki suka zarce yin bacci.. Tattausan Murmushi ta yi tare da dan girgiza kanta. "Babes anji jiki, kun yi tunanin yin yoga abu ne mai sauƙi.." ta faɗa tana yin yar dariya.. Batare da saninsu ba ta dauke su hotuna har kala goma, ta koma gefen gadonta tana kallon hotunan nasu, ba karamin burgeta su ka yi ba, duk in ta kallesu sai ta tuna da babynta, ƴar kyakkyawar jinjira, jinin arab, _Wanda ya fi ni sonki ya ɗauki abunsa, laifina ne dana tafi na barki, watakil kuma hakan shi ya fi zama alkhairi, I luv u little Batool dina.." Idanunta cike tab da kwalla ta fada_ Aminnanta ne suka faɗo mata aranta, nan da nan ta haɗe rai, tana kewarsu tana son su zauna su yi firar yaushe rabo sai dai ba ta jin zata iya yin hakan saboda fushin da take yi da su.. "Sun haifi ƴa'yansu sun basu kulawa, amma ni basu kula min da ƴata ba, har ta mutu.." kifa kanta ta yi saman pillow, tana kuka ƙasa ƙasa don kada sautin ya farkar da su Unaisah. Bayan sallar magrib suka hallara a tv room din gidan kamar ƙaramar cinema, su hudu ne zaune kan kujeru, sun nutsu suna kallon indian drama a cikin faskekiyar plasma tv din dakin. Unaisah tana a kusa da daddynta ta langwa6e kanta saman kafadarsa, yayin da Batool take a gefen Ummi hannayensu ruke cikin na juna, cikin nishadi suke kallo. Wani romantic scene da aka zo, jaruman suna kokarin yin kisss kusan atare Taj da Ummi suka rufe masu idanunsu da tafukan su, aikuwa gaba daya suka tuntsire da dariya, su kansu basu tsammaci zasu ga abun da zaisa su ji kunya ba. Saida aka wuce gurin, tukunna su ka buɗe masu idanunsu. Da yar shagwa6a Batool ta ce, "Aunty Ummi, why did you cover my eyes? "It's not appropriate for you to see" dariya su ka kuma yi.. "Daddyn Unaisah ya batun sauran yaran fa? Ina ta so inyi maka magana, ko har yanzu baku yanke shawara ba ne? Wlh sun takura, kullum na yi waya da su sai sun roke ni akan in yi ma Chief magana a dawo da su nan.." Ta fada tana kallon Taj. Unaisah ta ce, "Wallahi munyi missing dinsu, nima duk idan mu ka yi video call da su har kuka suke yi min, pls daddy, kayi wani abu mana, ko mu mu koma can gurin su ko su dawo nan zai fi masu kwanciyar hankali.." Taj ya ce, "Nima suna a raina, ko ɗazu saida na yi ma Chief maganarsu, na ce masa gwara a dawo da su nan din su san cewa mun dawo ga kuma abun da ya faru, in ya so sai mu lallashe su su yi hakuri su rungumi kaddara, sai Chief ɗin ya ce shima yayi tunanin yin hakan amma da akwai dalilin da ya sa ya za6i su cigaba da zama acan din har zuwa time da zamu kammala kama Elders, yana so ya basu mamaki nima kuma na goyi bayan hakan, ko dan saboda Sajeed ya ƙwallafa rai akan yar uwarsa, bamu san ko hada ita cikin yaran da muka ku6utar ba, mun bari sai zuwa time da lafiyarsu ta inganta saboda akwai majinyata a cikin su, wasu ma har surgery aka yi masu," Tsananin tausayinsu ne ya kama su, nan da nan walwalarsu ta ragu. "Daddy, when will we go to the hospital to see them? Batool ce ta tambaya, Unaisah ta ce, "I even asked the Chief about it, but he said no for now because the hospital is far from the city.." Bata ƙare maganar ba Taj ya ce, "Kuyi hakuri zuwa lokacin da za su ji sauki, cikin gari za'a dawo da su, a hada ku gaba ɗayanku" murmushi suka yi, Ummi ta ce, "I can't wait to see wallahi, har walima zamu haɗa don taya su murnar samun yan'ci ..." murmushi suka saki gaba ɗayansu.. "Amma daddyn Unaisah, taya za'a iya gano iyayen su da suka sadaukar da su? Kuma har su nawa ne pls"? "Da bincike In sha Allah zamu gano duk wanda ya sadaukar da su, saura kuma da bamu samu iyayensu ba, zamu ruke su a gurin mu, duka fursinonin dake a asibitin dari uku da wani abu ne." Cike da tausayawa ta ce, "Allah Sarki, Ubangiji Allah Ya raya su, Allah ya kare su, Allah Yas a karshen wahalar su kenan, Allah basu lafiya. Su kuma fursinonin da suka mutu Allah Ya jikansu da rahamarsa..." Amsa mata suka dinga yi da Ameen ameen. "Allah Ya saka masu cin zalunsu da aka yi, Ubangiji Allah ya toni asirin Elders din nan, Allah Ya wulakantasu a idon duniya, Allah Ya hana su kwanciyar hankali, Allah ya jarabce su da masifu iri iri..." Da ƙarfi su Unaisah suka furta Ameeen. Kafin suka mayar da hankali akan Kallon da sukeyi har saida Chef ya shigo ya sanar da su su fito their dinner is ready, sannan suka baro Tv room din suka nufi Dining area. Kafin su karasa saiga Chief ya sauko down jikin shi sanye da Thobe ya nufe su, hannunsa ruƙe da date boxes din da Sheikh Imam ya bashi. Suna niyyar zama kan dining chairs, sallamarsa ta dakatar da su, juyawa sukai tare da kallon shi. Lokaci ɗaya walwalar dake akan fuskar Ummi ta dauke duff tunawa da abunda suka tattauna, kawar da fuskarta gefe ɗaya tayi zuciyarta na bugawa da sauri, kallo ɗaya ya yi mata ya mayar da idanunsa kan su Batool dake gaishe da shi, yana murmushi ya amsa masu. Bayan ya gaisa da Taj, Ummi ta yi karfin halin gaishe da shi, ya masa mata tare da miƙa mata kwalin dabino. Kin kar6a ta yi saboda tana kokwanton ko ba ita ya ke miƙo mawa ba. "Sako ne daga sheikh Imam malik, ke da su Unaisah," Tsantsar mamaki ne akan fuskarta, cike da zumudi ta kar6i kwalin ta soma jujjuya shi a hannun ta, gaba ɗaya sun lura da farin cikin da ya mamaye ta, sai daɗi take ji mahaifinta ya fara nuna kulawa agare ta, sam ta manta da su agabanta, sai kallonta su ke yi, tausayinta ne ya cika zuciyoyinsu, in ka cire Batool da batasan komai ba game da labarinta. Tunawa ta yi da lokacin baya, duk in sheikh Imam ya fita ƙasashen larabawa sai ya dawo mata da tsarabar dabino da ruwan zamzam tare da irin suturunsu, tana ji aranta ya bata dabinon ne don ya tuna mata da wannan lokacin, me hakan ke nufi? Ko mahaifinta yana son yin sulhu da ita ne? Kuka take so ta yi sai dai ta kasa yi agaban su, bata ɗago ta dube su ba ta juya da sauri ta nufi Up, Duk akan idanunsu, Batool har ta zabura zata bita Taj ya ruƙo hannun ta, "Ku zauna ku ci abinci, zata dawo ne" "Ga wannan naku ne." Ya faɗa tare da miƙa ma Batool ɗayan box din ta kar6a tare da yi masa godiya. A fakaice suke satar kallon Juna shi da Unaisah, kamar zasu haɗiye juna. Kasa tafiya ya yi, saboda kewarta da ta mamayesa, sai dai baya son Taj ya gane saboda ita ya tsaya, hakan yasa shi juyawa zai tafi, muryar Taj ce ta katse shi, "Bismilla, ka zo mu ci a tare mana, zaka fi jin dadi." Juyowa ya yi, "Ban ƙi tayinka ba, amma..." bai karasa maganar ba ya dan dakata yana kallon Unaisah da ke yi masa mimi da baki, da hannu take nuna masa kujerar dake fuskantarta don ya zauna. Batasan Taj ya ga abun da take yi ba, girgiza kai ya yi tare da yin murmushi, ita dai Batool hankalinta na akan chief sai kallon shi take yi kamar ta samu tv. "Okay, " Ya faɗa tare da jan kujera ya zauna, da kanta tayi serving na shi, abincin suke ci amma hankalinsu na akan juna, tun batool bata lura ba, har ta fara lura da irin kallon love din da suke ma juna. Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin ƙunci ba, gaba daya abincin ya kundureta, ta rasa gane meke damunta. A bangaren Ummi bayan shigar ta ɗaki saman gado ta fada cike da kewar mahaifinta, komai na rayuwarsu take tunowa, har yau tana tambayar kanta meyasa yayi mata haka a matsayinsa na ubanta, wanda ya fi kowa sanin wacece ita, meyasa tsawon shekarun nan bai ta6a nemanta ba? Nan da nan ta ji baƙin ciki ya cikata, Dabinon ma kasa bude shi ta yi, ta tura kwalin ƙarƙashin gadon ta. __________________________________________ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3k Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *daga Alkalamin Boss Bature* ISOD HEAD QUARTER AT MEETING ROOM..🔥 Meeting Room ba lafiya, tun da suka hallara, Chief ya zabga tagumi da tafukansa biyu, hakan ba ƙaramin daure musu kai ya yi ba, kiran gaggawa ya sa aka yi musu don su yi meeting, kuma sun zo ya kasa magana ko kallonsu bai yi ba, cike da ruɗu suke ta kallon fuskar sa, daga yanayinsa suka fahimci baya jin dadi ganin yadda ya faɗa, kuma akwai wani abu dake damunsa, duk da sanyin A.c ɗin ɗakin wani irin gumi ne ke keto mashi....Cikin kunnuwanshi ya tsinkayi muryoyinsu sama sama suna yi mashi magana cikin harshen turanci tamkar raɗa, "Sir Are you Okay?" "Sir meke damunka? Baka da lafiya ne"? "Sir pls, gaba ɗaya mun damu da kai, ka faɗa mana in akwai abun da ke damunka.." Dafa Kafadarsa Commender James yayi, "Owais, meke faruwa da kai ne uhum?" Sai lokacin ya ja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya zame tafukansa daga kan kuncinsa, ya zube hannayensa saman laptop keyboard din gabansa, a hankali ya ɗago da raunannun idanunsa da suka kaɗa juwar ya bi su da kallo. Na hannun damansa ne zazzaune kan kujerun dake a gefensa na hagu, daga bangarensa na dama U.s Armies ne tare da General Noah da Taj, wannan karon hada shi Chief ya yi inviting.. "Owais, mun fahimci akwai damuwa atare da kai, daga yanayin ka muka fahimci baka da kwanciyar hankali, Pls, in ba damuwa ka faɗa mana mu nema mafita a tare, mun riga da mun zama ɗaya..." Cikin kulawa General Noah ya yi maganar yana dubansa. Bawan Allah, kallonsu kawai ya ke yi shi kaɗai yasan meke damunsa, baisan ma tayaya zai fara yi musu bayani ba! Ya za su ɗauki abun idan suka ji cewa kakansa ne Elder! Ya Ilahi, fargaban da ya ke yi kenan shiyasa yake ta jin zullumin ya faɗa abun da ya tara su, abun da takaici. Numfasawa yayi a hankali ya soma magana, "Abun da ya sa na tara mu anan, saboda in taya mu murnar cigaban da muka samu a binciken da mu ke yi akan Elders na gidan kurkukun ƙaddara, ina yi maku albishir na gano wanene shugaban kurkukun ƙaddara..." Zare idanu suka yi cike da tsantsar al'ajabi jin abun da ya ce, ya basu mamaki matuka don basu taba zaton nesa zata so musu kusa ba... "Chef ta yaya akai ka gano Elder? Abun da muke tunanin ba zai samu cikin sauki ba....?" Commender ne ya faɗa da mamaki akan fuskarsa.. General Noah ya ce, "Amma dai ka shammace mu Chief, ka yi matukar bamu mamaki..." Ya faɗa da murmushi akan fuskar. kwata kwata basu lura da yanayin sa ba, Taj ne kaɗai ya fahimci babu lafiya, aransa ya ayyana zai yi wuya in ba wani nashi ba ne Elder, duba da yadda ya rame ga damuwa tsantsa akan fuskarsa, hakan yasa bai nuna farin cikin sa ba.. "Sir, ba dan daga bakinka na ji maganar nan ba, da sai na ce ba gaskiya bane, saboda na razana da jin ka gano mana tantirin dan ta'addan nan, amma tayaya ka gano sa? Kaina ya kulle, banyi zaton zamu iya gano sa ta cikin sauki ba.." CI ne ya fada.. COO ya ce, "Allah yasa ba mafarki nake ba, Chief pls ka fada mana wanene ɗan iskan mutumin nan uhum? Wani shegen ne? Wlh na ƙosa na ji harna fara tunanin azabtarwar da zamu yi masa, kai mutumin nan ko kotu ba zamu kai shi ba, saboda bana tunanin zasu iya yanke mishi hukuncin da ya dace, mu zamu haɗa baki mu murkushe ɗan iska a cikin cell, But, sir sauran Elders din fa?" Wani raunannan kallo ya ke binsu da shi, sai farin ciki suke yi suna ɗurawa Elder ashariya basu san grandpa din sa ba ne, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji wanene Elder din sai tambayar shi suke yi yayi shiru yana kallonsu, Agent Zahra ya ce, "Zan so inga idon azzalumin mutumin nan, ƙarya ta ƙare masa, ko ya zaiji idan muka ɗamke sa, amma kuna tunanin kamasa zaiyi mana sauƙi kuwa? Tun da basa jin makamin mu, zai iya amfani da tsafi ya 6ace..." Ya faɗa da damuwa akan fuskarsa.. A hankali Chief ya dubi Taj dake ta kallonsa, ruwan hawayen da ya gani kwance a cikin idanun Chief ya ɗaga hankalinsa, girgiza mashi kai ya ɗan yi alamar kada ya karaya, cike da damuwa ya yamutsa pink lips dinsa tare da cizon lower lip din da hakoransa. Cike da rashin kuzari ya miƙe daga kan kujerar da yake ya fuskance su tare da zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa, gaba daya suka bi shi da kallo a ƙagare da son jin me zai ce. Nauyin haɗa idanu da su ya ji, a hankali ya fito daga gaban kujerar ya juya masu baya lamarin ya ɗaure musu kai, Ya ji zafi aranshi fiye da zafin ƙunar wuta, surutan da suka yi akan kakansa sun ta6a zuciyarsa, ina ga kuma sauran al'umma idan komai ya fallasu, Allah kaɗai yasan cin zarafin da za a yi musu. Haƙiƙa Baba Obie ya cutar da su, ya ja musu zagi da cin mutunci a idon duniya, sai da ya yi silar ɗaukakar su tukunna ya tarwatsa darajar su.. Gwauran numfashi ya ja, cikin karyayyar murya, mai matukar rauni da ƙarfin hali ya furta, "Ina baku haƙuri da abun da zaku ji daga gare ni, I'm really disappointed, an karya min zuciyata, zallumi da fargaba ne suka hana in sanar da ku tuntuni..." A ruɗe suke kallon kallon a tsakaninsu, nan take ransu ya fara basu kodai na jininsa ne Elder ɗin? Wataƙil cikin uncles ɗinsa ne, kwata kwata ba su kawo ma ransu zai zama kakansa ko mahaifinsa ba. "Kada ka ji komai Owais, ka faɗa mana zamu fahimce ka.." Commender james ne ya faɗa.. Cikin rawar murya ya ce, "Ba mahaifina bane, Ba kuma cikin Uncles ɗina bane, amma wanda ya yi silar zuwan su duniya shine Elder shugaban Kurkukun ƙaddara...." Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, Tunkan ya ƙarasa maganar A kiɗime suka zabura tare da miƙewa tsaye, a lokaci ɗaya suka ɗaura hannayensu saman kawunansu, Idanunsu azazzare cike da tashin hankali haɗi da al'ajabin da ya kamasu! Lamarin ya gigita su. Duk da sanyin A.c din dake ratsa fatar jikinsu hakan bai hana gumi wanke gaban goshin su ba, wlh sun karaya matuka, Hankalin maza ya tashi. A sukwane General Noah ya zame hular kakinsa dake a kansa ya kifa ta saman table dinsa.. A dabarbarce Commender James ya furta, "Owais, kana cikin hayyacinka kuwa? Kasan me kake faɗa? Ko ka sha giya ne uhum? Kakanka fa ke nan, Kana nufin Obinna, anya ka yi bincike da kyau? Ta ya ma hakan zai yiwu?" Girgiza kai CI yayi cike da takaici ya ce, "Sir am sorry to say da wani ne ya faɗamin maganar nan Allah sai ya ci na jaki, Hakan ba zai ta6a yiwuwa ba, ba gaskiya bane, Baba Obie bazai aikata munanan ayyukan nan ba, Owais ka bani mamaki, ban taba zaton zaka iya furta wannan maganar akan kakan ba, kafi mu sanin wanene shi, amma ko mu kanmu da muke abokanka mun yi imanin baba Obie bashi bane Elder, Mutumin mai kyawawan halaye da tausayi irinsa bazai iya aikata abun da Elders suke yi ba... "Ni dai danasan zaka fada mana wannan almaran da ba abun da zaisa in halarci meeting ɗin nan, sai dai ka yi hakuri Chief amma yau ka 6ata min rai, ka ce Elder ne kakan ka, Wanda ya haifi baba, gaskiya sir kwakwalwarka bata aiki yadda ya dace kana bukatar a duba ka.." Coo ne ya fada tare da zame glass din kan fuskarsa ya zaro hanky yana sharce gumin dake tsastsafo masa. Kasa juyowa ya yi ya fuskance su, baisan taya zai yi musu bayani ba, baba Obie ya cuci kansa ya yaudari mutanan da suka yarda da shi, gayanan duk wanda aka faɗamawa sai anyi da gaske kafin ya yarda.. Taj Tuni hawaye sun wanke fuskarsa, dama saida ranshi ya bashi hakan, wata irin karaya ya ji, baba Obie ya bashi mamaki, ba tun yanzu ba ya jima yana al'ajabin dukiyarsa da ɗaukakar ahlinsa ashe bana Allah da Annabi bane, haƙiƙa bai kyauta ma rayuwarsu ba, ya zalunce su wata shari'ar sai A lahira... "Tun da nake daku na taba yi maku ƙarya? Mutumin nan kakana ne nafi ku sanin wanene shi! Miye ribana in na mashi kazafi? Tun da na ce maku shi ne ku yarda kawai, kakana ne Elder!" Ya faɗa cikin shesshekar murya ba tare da ya juya ya fuskance su ba, Wannan karon kusan suman tsaye suka yi saboda sun fara karaya da maganarsa jin kamar yana shesshekar kuka... "Ba shaye shaye na yi ba, da hankalina da tunanina, Ni ba mahaukaci bane, ba kuma kazafi na yi masa ba, zan sake maimaita maku, Kakana Obinna shine Elder, azzalumin da ya ke azabtar da rayuwar yaran da ba su ji ba basu gani ba a gidan kurkukunsa, mutumin da muke nema ruwa a jallo, ashe daga tsatsonsa na fito, ban ga laifinku ba da kuka kasa yarda da maganata saboda muma lokacin da muka ji hauka ne kaɗai bamu yi ba, na yi fatan ace ban kai wannan lokacin a raye ba, gaba ɗaya mun yi danasanin kasantuwar mu jininsa, amma ba yadda zamu yi haka Allah ya ƙaddara mana, Allah yana fitar da rayyayye daga jikin matacce, Ga misali nan akan mu, Kakanmu gurbatacce ne, mai fuska biyu, mu kuma ba haka muke ba, gaba ɗaya uncles dina da mahaifina babu sa hannunsu a ciki, hasalima basu taba jin wani abu mai suna kurkukun kaddara ba, a ranar da asirin ya tonu, abun ya daure mun kaina, sai na ga kamar ban ma taba sanin shi ba saboda na ji abubuwa game da kakana wanda ni ko iyayenmu babu wanda ya taba sani..." Jikin taƙaura fa ya yi la'asar, tuni annurin fuskokinsu ya ɗauke duff kamar basu taba dariya ba, zuciyarsu ta karaya, ga baƙin cikin da ya mamaye su, hankalinsu ya tashi, har basu san sa'adda suka cire hulunan kakin da ke akansu suka ɗaɗɗaura su gaban table ba, a ɗimauce suka koma kan kujerun suka zauna tare da sadda kansu ƙasa.. Har tsawon mintuna ashirin cuf babu wanda ya furta kalma daga cikin su saboda matsananciyar damuwar da suka shiga, kwata kwata meeting din yau bai yi musu dadi ba, saboda jin abun da basu taba zata ba, basu ji dadin maganganun da suka faɗa akan kakansa ba, wannan ne karo na biyu da suka ga raunin Chief, ranar da Danish ya faɗa rijiya da kuma yau, wlh sun tausaya masa sosai, sun ma ga kokarinsa da ya iya jurewa in wani ne tuni zuciyarsa zata buga ya mutu ko ya halaka kansa saboda baƙin ciki..💔 Miƙewa Commender ya yi ya nufe shi tare da ruƙo hannunsa ya juyo da shi, hankalinsu ya tashi da ganin siraran hawayen dake zarya kan kuncin sa. _Zaunar da shi kan kujera Commender ya yi, tare da zaro Hanky ya share mashi ƙwallar shi, mikewa sauran suka yi gaba ɗaya suka kewaye sa duk da raunin da suka yi hakan bai hana su ƙarfafa zuciyarsu gurin lallashin shi da bashi baki akan ƙaddarar data same su, babu wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba gurin kwantar masa da hankali, su ka ce ya yi hakuri ya jure radaɗin da ya ke ji, sun san abun da ciwo, dole zai shiga mawuyacin hali amma ya yi hakuri, kada ya ji komai su masu fahimtar shi ne, tabbas su kansu sun karaya sun kuma razana da jin cewa kakansa ne, amma ya zasu yi babu wanda ya isa ya canza abun da Allah ya riga ya kaddara faruwarsa, wlh saboda tausayin da ya basu da suna da halin da zasu cire mashi damuwar shi da ba abun da zai hana su yi hakan kodan su sauƙaƙa mashi radadin da yake ji, amma ba zasu bar shi ba, zasu kasance a tare da shi, No matter what, shi Chief dinsu ne na har abada, su sun yarda da shi fiye da yadda suka yarda da kansu, don haka kada ya ji komai, laifin kakansa ba zai taba shafarsa da ahlinsa ba, zasu tsaya masu tsayin daka don ganin basu tozarta a idon duniya ba, bashi kadai zai yi fadan ba, ya sani yana da su zasu taya shi yin fighting ɗin duk wani wanda yayi yunkurin cin zarafin ahlinsa ta hanyar amfani da abun da kakansa ya aikata! Bayan haka basu san rauninsa, yana ɗaga masu hankali, abun da suke so da shi ya yi ƙoƙarin cire damuwar da ke aransa, saboda zata iya haifar masa da rauni wanda kuma hakan faduwa ne a gare su, sun san Chief ɗinsu jarumin namiji ne, mai dakakkar zuciya, kuma mai tawakkali, basu so ya canza daga yadda ya ke a da, ya sawa ransa cewa zai iya, ya manta da cewa kakansa ne Elder, ta haka ne zai kore damuwarsa har su samu su ƙarasa aikin su."_ Maganganu masu daɗi da ƙarfafa gwiwa suka gaggaya masa har saida ya ji karfi a jikin shi, sun faranta ranshi, kuma dama abun da ya kamata kenan idan mutun ya shiga wani hali a tausaya masa, a ja shi a jiki, bawai a dinga cuzguna masa ba saboda wata ƙaddara ta same shi, wasu har daɗi suke ji su dinga bullying ɗinka don su baƙanta maka rai, su ja depression ya kama mutun daga haka har ya lahanta kan shi, wa'iyazubilla..💔 Tun suna share mashi ƙwallar da ke gangarowa kan kuncinsa har ta kai ga sun fara tsokanar shi, baisan sa'adda ya fara sakin murmushi ba, saboda dadin da ya ji har godiya ya yi musu, su ka ce kada ya damu hakkinsu ne su bashi kulawa, yanzu tunda sun fahimci ba ya jin dadi yana bukatar ya ga likita saboda lafiyarsa, don haka zasu ɗaga meeting din, zuwa lokacin da zai ji sauƙi. Ya ce masu bai ƙi shawarar su ba, amma bazai yiwu a ɗage meeting ba, akwai muhimman abubuwan da yakamata su tattauna akai idan ba haka ba zasu iya fuskantar matsala, hankalinsu ya tashi da jin hakan, suka ce tun da haka ne, zasu tafi hutun awa uku saboda sun damu da lafiyarsa suna so ya huta... A cikin yan mintuna suka kira Isod docs suka bincika lafiyarsa anan cikin medical room ɗin su, bayan sun tabbatar da ciwon dake damunsa ya gargaɗe su akan kada su faɗa musu sakamakon saboda baya son kowa ya sani... Lokacin da suka koma zaman meeting din, ba laifi sun ga ya ɗan saki jikinshi da walwala akan fuskarsa, A tsanake ya fayyace musu komai da ya faru bayan zuwan Khala.. Sun yi matukar mamakin jin cewa kakarsa ce, kuma Obie ne ya yi ƙaryar mutuwarta ya kai ta kurkukun kaddara, duk ba wannan ba, abun da ya basu haushi da takaici abun da Pravin ya aikata, ashe shima Elder ne na gidan kurkukun kaddara, lallai Obie Family sun haɗa giggan ƴan ta'adda acikin su. Bayan sun taya shi murnar ganin grandma ɗinsa, da jimamin abun da ya faru da familyn sa Commender James ya ce, "Yanzu ta ya za'ai mu iya gano sauran Elders? Kana ganin grandma ɗinka zata iya samun sauƙi nan kusa!" Girgiza kai ya yi, "Bakowa ta sani a cikin su ba, yanzu haka da ita da aunt ɗin nawa an kwantar da su asibiti basu san inda kansu yake ba, amma suna samun kulawar likita.." "Me zai hana mu tuntubi shi Elde...Au, afwan sir grandpa nake so na ce,..." murmushi chief ya yi tare da kallon CI da ya yi maganar. "Duk yadda ma ka faɗa daidai ne CI, already na yi masa magana akan ya fada mun sauran Elders din amma ya ƙi sanar da ni...." Nan ya labarta musu abun da suka tattauna tsakaninshi da baba Obie. Kallon kallo suka jefawa junan su cike da tashin hankali, Agent Jabeer Osman ya ce, "Akwai sauran rina a kaba kenan, In har bamu yi gaggawar kamasu ba zasu iya mayar da hannun agogo baya, nasan iwar haka suna nan suna shirin kawo mana farmaki." Gaba ɗaya sunyi amanna da maganarsa, Agent Zahra ya ce, "Ni damuwana ina zasu farmaka? ya tambaya yana duban su, "Hankalina ya fi karkata akan fursinonin da muka baro a Csh." Taj ya ce,"Asibitin yana da tsaro tunda na sojoji ne, amma fa kada mu dogara da hakan, mun riga da mun san su wanene Evil Giants, in har suka farmake mu da su, toh Allah ne kaɗai zai iya ƙwatar mu, za su iya amfani da sihiri su kashe sojojin dake tsaron su, su kwashe yaran abunda ba a fata, amma menene mafita...?" gaba ɗaya suka zurfafa tunaninsu kowa na tunanin abun da yakamata a yi. "Kuskuren da muka yi tun farko shine barin makaman da grandma ta bamu, da mun sani mun taho da su, saboda da su kaɗai ne za'a iya yaƙar su.." A cewar Captain.. Cike da takaici Canal ya daki gaban table dinsa yama rasa abun cewa.. Jackson ya ce,"Akwai gagarumar matsala, dole fa mu fara kai masu farmaki kafin su kawo mana idan ba haka ba, ba zasu yi mana da dadi ba, bamu san ina zasu farmaka ba!" Lieutenant Thompson ya ce, "Ni dai a nawa ganin shawara ɗaya ce, Chief grandpa shine mafita, shi kaɗaine makamin da muke da shi a yanzu, tun da ya ce zai mika wuya toh ya taimaka ya faɗa mana komai idan ba haka ba, ba zamu iya cin galaba a kansu ba, a kowani lokaci zasu iya kawo mana farmakin bazata..." Girgiza kai Chief Owais ya yi, "mu yi hakuri mu nemi wata mafitar, saboda ba irin magiyar da ban yi masa ba amma ya ƙi fada mun, ya ce a dokar aikinsu wani baya tona asirin wani, alkawari ne suka ɗaukarwa junansu, kuma shi ba zai ci amanarsu ba, tun da har ya fadi hakan bai duba ƙaunar da yake yi mini ba, toh wlh ba zai ta6a bamu hadin kai ba, koda zamu azabtar da shi ne, amma a maganarsa ya ce in har aka kawo mana farmaki mu sanar da shi, amma wannan ba mafita bane, tayaya za a yi mu san za'a kawo mana farmakin?" Da damuwa ya jefa musu tambayar, gaba daya sun shiga tashin hankali.. "Ni a ganina mu fara nemo wadanda grandma ta fadi sunayen su? In ya so sai muci ubansu mu azabtar da su har sai sun faɗa mana su wanene sauran Elders din..." Taj ne ya fada yana huci zuciya ta kai wuya..! General Noah ya ce, "No ba zamu iya kama su ba, har yanzu bamu da isassun hujjojin yin hakan!" "Sir, muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su..." Gaba ɗaya suka maida hankali akan Taj da ya yi maganar har suna haɗa baki gurin tambayar wata hujja ce? Bai jira Chief ya bashi umarnin ya faɗa ba, ya fara zayyana musu komai da ya faru tun daga kan labarin Ummi har izuwa labarin da Benazir ta bashi akan Alhaji Musa. Lamarin ya ɗaure musu kai, basu gama shan mamaki ba, sai da Chief ya samu ƙwarin giwar tunawa da wata hujjar da yake da ita, nan shima ya labarta musu komai da ya gano game da shi tun daga kan hotansa dake a cikin diary din Unaizah, ya ƙara da cewa, "Har yanzu bai rabu da Ummi ba, bayan ya rabata da kowa nata ya maidata karuwarsa, shine ya tafi da ita America..." A rude U.s armies suke jefawa junansu kallo mai cike da tsantsar al'jabi, Ummi dai da suka sani tantiriyar karuwa yau sun ji asalin labarinta da kuma azzulumin da ya yi silar canza rayuwarta, gaba ɗaya basu ji daɗin abun daya faru da ita ba, tausayinta ne tsantsa a kan fuskokinsu, ba su kaɗai ba hatta General Noah dana hannun daman Chief sun nuna tausayawar su a gare ta, labarinta ya taba zukatansu, kuma basu taba ganin mugun mutun irin Musa ba, labarin yarinyar da ya sa su zubda ƙwalla ashe shine Ubanta, sun ma riga da sun yanke ma kansu shine JAN WUYA mutumin da suke nema ruwa a jallo.. Chief Owais bai dakata ba, ya ɗaura da basu labarin da Sheikh Imam ya ba shi ... Taj ya ce, "dama sai da raina ya bani, sune suka kashe Uzair..." Ya faɗa cikin ƙunci da baƙin ciki. General Noah ya ce, "Wai ni Musan nan bashi bane former president ba? Mahaifin Ddg? Kuma ƙanwarsa tana auran daddynka ko?" Jinjina mashi kai Taj ya yi. Cikin fushi Noah ya buga saman table rai a 6ace ya ce, "Babu tantama zai aika, Ni dama bai ta6a burgeni ba, mutun sai girman kai da izza ashe dukiyar tasa ta kungiyar asiri ce, shi dama karen yan siyasar nan na daɗe ina zargin sa saboda mugun munafuki ne.." CI ya ce, "Zai yi wuya in ba daga tsatson fir'auna ya fito ba, mutun ba imani ba tausayi! Zalunci da mugunta kaɗai yasa gaba, aikuwa dubunsa ta cika, daƙiƙin kwata kwata baya amfani da kwakwalwarsa, gashi nan cikin rashin sani ya tabka kuskuren da ya yi silar tonuwar asirin sa..." Coo ya ce, "Wlh ikon Allah ne, ka duba yadda ya daɗe yana sheƙe ayarsa tsawon lokaci batare da an iya kamasa ba, wai a haka har matsayin president ya taka, ko da yake ya samu ɗaurin gindi ne..." Bai ƙare maganar ba, Taj ya yi masa gyaran murya tare da furta "Hattara dai.." Cike da jin kunyar Chief CI ya sunnar da kansa, bawan Allah Chief ɗan murmushi ya saki tare da ɗan girgiza kan kanshi. "Sir, Yanzu meye abun yi tunda muna da isassun hujjojin da zamu iya kama su? Taj ne ya faɗa yana dubansu.. Commender James ya ce, "Babu bukatar 6ata lokaci, mu kama su kawai su fara kar6ar sakamakon zunubin da suka aikata..." General Noah ya ce, "da shi ɗan iyan, da Musan, da pravin da aminnan grandpa, da likitocin da momma ta faɗa suna da sanya hannu suma a kama su, sannan kada a kuskura abar pravin ya ƙetare kasar nan, nasan iwarhaka yana neman hanyar da zai gudu, watakil ma ya gudun, shiyasa banso kuka ɗauki lokaci baku sanar damu ba, wlh da kun faɗa mana tun ranar da abun ya faru zamu bi diddiginsa mu kama ɗan iskan, amma na yi maka uziri nasan alhinine ya hana ka sanar mana..." Chief ya ce, "Mun tattauna da Uncles dina, suma zasu bada gudummuwarsu..." Nan ya labarta masu abunda suka tattauna da Uncles ɗinsu, sunji dadi kuma sun ƙara jin kwarin gwiwa a tare da su.. "Bayan haka tun ranar da ya gudu nake ta trying layinsa a kashe yake, har jaraba bin diddiginsa na yi amma ban iya gano komai ba, ina tunanin ya jefar da wayar ne don kada mu bi diddiginsa." Agent Zahra ya ce, "Zai iya yiwuwa ya canza layi, in kuwa yayi kuskuren zuwa yin register zamu iya samun bayanansa." "Ita yar'uwar tashi ka kira layinta ne?" James ne ya tambaya.. "A ɗaki tabar wayar, na kar6i number dinta a hannun yan uwanta maids, dana kira sai na gano location din wayar a cikin gidan ya ke, da kaina na shiga na dudduba dakin har na gano wayar nata." Taj ya ce, "Za mu iya haɗa baki da abokan aikin nata, ita Hajjatyn zata iya yin kuskuren kiran wani daga cikin su tun da ta yarda da su atare suke aiki, ko basu ba mu nemi aminiyarta ta ƙut da ƙut, wadda muke da tabbacin zata iya kiran ta, sannan mu haɗa baki da ita, da zarar ta kira ta tayi hanzarin sanar damu, mu kuma sai muyi kokarin bin diddigin su..." Shawarar da Taj ya kawo ta yi masu daɗi.. Ya kuma cewa, "Amma ni abun da ya ɗaure mun kai, Ita hajjatyn tasan abun da ya aikata kuma ta bi shi suka gudu? Ko dai dama a tare suke aikata 6arna ta bayan fage..." Amma da kamar wuya saboda Hajjaty mutuniyar kirki ce .." Wani marayan kallo Chief ya yi masa.. "Mugu bashi da kama Taj, abun da ya faru da ni ya isa yasa ka dauki darasi, ba kowani nagari bane mutumin kirki, akwai masu fuska biyu, a fili Musa a zuci fir'auna, ni bana zargin ta, amma ta aikata babban kuskure da ta haura ƙafa ta bi shi suka gudu, in har muka gano da sa hannunta akan abun da ya faru da auntyna, kuma tasan abunda yake aikatawa wlh na lahira sai ya fi ta jin daɗi, dole mu hukuntata daidai da abun da ta aikata, babu wanda zamu ragamawa kamar yadda bazan raga ma kakana ba, dole kowan nan su ya gir6i abun da ya shuka..." Ya faɗa tare da bugun kan table din gaban su, gaba daya idanunsu akan fuskarsa, maganarsa ta burge su, suna alfahari da shi, ya cancanci su yaba mashi saboda jajircewar shi akan gaskiya, a dai yadda duniyar nan ta baci da rashin son gaskiya, da wani mai son kan ne idan yasan nashi ne yake aikatawa 6oyewa zai yi, ko ya bashi hadin kai ya gudu don kada a kama sa, ko kada su kunyata a idon duniya, gaskiya samun mutun mai irin zuciyar chief zai yi wuya a fadin duniyar nan, he's a true leader, ba karamun mai tsoron Allah bane zai yi hakan💘💋... Almost one hour suna tattauna yadda zasu kama Elders, kowa yana kawo idea dinsa, a karshe suka yanke shawarar zasu tuntubi Ummi saboda ta hanyar ta ne suke sa ran za su damƙi Musa ta cikin sauƙi. Chief ya ce su bar komai a hannunshi ya riga da ya yi mata magana amincewarta ya ke jira, zai ƙara yin magana da ita duk yadda su kai zai sanar da su..🔥 *PRAVIN❗* Aje Motarsa yayi a haraban wani gida, fitowa yayi jikinsa sanye da suit ya rufe fuskarsa da mask, hatta hannayensa da ƙafafunsa ya saka musu safa, sai yan waige waige ya ke yi daga gani yana a cikin fargaba, zagayawa yayi ta baya ya buɗe boot din motar, ya janyo ƙaton buhun dake a ciki ya aje ƙasa, kafin ya bude backseat ya sungumo baƙar jakarsa ya rataya ta kan kafaɗarsa, da sauri ya ja buhun ya shige da shi ciki, kulle door din ya yi da code kafin ya nufi Ciki. Shigarshi falo keda wuya ya soma jiyo kakarin aman da ta ke yi, hankalinsa a tashe ya zame jakar ya jefar kan sofa ya saki buhun cikin sauri ya nufi bedrom din da take. Yana shiga ciki bai same ta a saman gadon ba, sai dai bargonta dake a yashe ƙasa, cike da fargaba ya bangaje kofar toilet ya shiga yana haki saboda gudun da ya yi, lokacin idanunsa suka sauka akan ta yayin da take a gaban sink tana kwarara amai tamkar yan hanjin cikinta zasu zazzago, ta daddafe bakin sink din da hannayen ta. Ƙarasawa ya yi da sauri ya dafe kafadarta yana yi mata sannu. Bata ko kula shi ba sai da ta gama amayar da komai da ta ci, ta kunna faucet ruwa ya wanke aman. Kokarin daukarta ya yi don ya sauwaƙe mata tafiyar, cikin bacin rai ta bangaje shi ya yi taga taga zai faɗi yai saurin tsayar da kansa yana kallon ta. Tsantsar bacin rai ne akan fuskarta, idanunta sun kumbura sun kaɗa jawur saboda kukan da take sha, gown din dake a jikin ta tayi squeezing kamar an ƙwatoto daga bakin kura, doguwar sumar kanta ta cukuikuye kamar ta mahaukaciya, mace mai tsafta ta zama ƙazamar karfi da yaji saboda rashin lafiya da damuwa.. A hankali zafafan hawaye suka soma zarya kan kuncin ta, labbanta sun bushe ƙamas sun ɗan faffashe ga jikin nata har yanzu ba sauƙi.. Cike da bacin rai ta furta, "Karka kuskura ka ƙara matsowa kusa da ni, i don't want to see you Pravin, ka nisanta kanka dani, idan ba haka ba zan yi ma kaina illa!" Bai ta6a ganin Hajjaty a cikin fushi irin na yau ba.. A hankali ya sanya hannu ya cire mask din dake akan fuskarsa, cikin yan kwanakin nan saboda zullumi da fargaba har rama ya yi, tun ranar da ya gudo da Hajjaty, bai nufi ko'ina ba sai guest house dinsa da ya daɗe da mallakarsa, babu wanda yasan yana da gidan. "Ba halin ki bane, bansan ki da fushi ba, na rasa gane kanki cikin kwanakin nan, duk abun da kika ga ina yi saboda in kare ki ne, amma kin kasa fahimta na.." Harara ta watsa mashi, cikin bacin rai ta ce, "Idan ba halina bane to kai ne ka sauyani Pravin, ni bazan cigaba da yarda da munafuki ba, na gaji da sauraran ƙarairayin ka! ka faɗa min gaskiyar abun da ya faru, ka raba ni da mutanan da nake rayuwa da su ka kawo ni wani gida ka boye ni a cikin sa! Kullum na tambaye ka sai ka yi shiru, wai me ka ɗauke ni ne? Don ina da hakuri ba hakan yana nufin bani da hankali ba! Zan iya jure komai amma wallahi bazan jure rainin wayon ka ba...." Tuni ya sha jinin jikinshi jin yadda Hajjaty ke masa faɗa kamar uwarsa, tana magana tana ciccije le6enta saboda radadin da take ji.. "Tayaya kake tunanin zan cigaba da zama da kai? Bayan baka ɗauki iyalinka da muhimmanci ba sai ni Pravin? Wani laifi ka aikata ne da yasa har ka gudo da ni? A ranar kafin in fita hayyacina na ji muryar Hajiya Saratu a cikin kunnena, ta shigo daki na, duk da ban ji abun da ku ka tattauna ba amma raina ya bani ta gano abun da muke yi shiyasa har ta shigo ɗakina, kuma na ji lokacin da ta bangaje mu muka faɗi daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba..." Dakatawa ta dan yi tana jan numfashi idanunta a cikin na shi, ya yi zuru zuru ya rasa ta ya zai shawo kanta, kwanakin nan basu jituwa saboda yaƙi faɗa mata laifin da ya aikata, ta ƙi kwantar da hankalinta balle har ta ji sauƙin abun da ke damunta.. Girgiza kai ta yi idanunta suka cicciko da ƙwalla... "Ka kasa kare kanka saboda baka da gaskiya shiyasa ka yi shiru ko? Ni ina ji araina wani laifi ka aikata musu shiyasa ka gudu da ni, saboda hujjar daka bani bata gamsar da ni ba.." Sunnar da kanshi kasa ya yi, jikin shi ya yi sanyi lakwas, baisan ya zai yi ba, ya jefa rayuwarsu a cikin bala'e da masifa, ya yi danasani tafi sau a ƙirga, yana matukar jin kunyar Hajjaty, yana jin nauyin tasan miyagun laifukan da ya aikata wa'iyazubillah!! Bata ƙara yin magana ba, ta juya ta nufi kofar fita da sauri ya bi bayanta, shigowa cikin dakin ta yi, jikinta na kerma ta nufi bedside drawer ta soma kwashe magungunanta tana jefa su cikin dustbin din dakin, shigowa ya yi da sauri ya damƙi hannayenta, kokoyi suka kama yi.. "Pls ki saurare ni, zanyi maki bayani, ki daina zubar da maganinki, da tsada na siye su saboda lafiyarki..." Wani kallo ta wurga masa, "Ban damu ba Pravin, bana son lafiyar tawa, nafi son na mutu, saboda wanda na yarda da shi yana neman ya karya min zuciyata..." Bai san sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, duk yadda ya so ya dakatar da ita abun ya ci tura, ƙarfi yasa gurin ɗaukarta ɗungurugum ya kwantar da ita kan gadon, ta dinga kuka tana bubbuga mattress da hannayenta, bin ta ya yi saman gadon ya janyota jikinshi tana turjewa, ya rungume ta kan ƙirjin shi, duk yadda ta kai ga jin haushin shi da ya yi mata hakan sai da ta ji sassaucin damuwarta. Cikin sanyin murya ta ce, "Pravin dan Allah ka fadamin meyasa ka gudu da ni? Meyasa ka bar Obie estate? Wani laifi ka aikata? Kada ka yi min karya Pravin, babu sirri atsakanin mu, kasan bani da kowa in ba kai ba, kaine majinginata, ƙashin bayana, bana so ka ci amanar yardar da na yi maka Pravin, dan Allah ka faɗamin na yi maka alkawarin zan rufa maka asiri kuma zan taya ka neman mafita.." wani irin tsantsar sonta da tausayinta ne ya mamaye zuciyar shi, tsoma yatsun hannayensa ya yi a cikin sumar ta yadinga cakuɗa gashinta kamar yana mata susa, Cikin sanyin murya ya ce, "Ki yi hakuri na boye maki ne saboda bana so na ɗaga maki hankali, amma gaskiyar abun da ya faru, Hajiya Saratu ta gano ina zuwa dakin ki, harma in kwana, bayan mun dawo an fara shirye shiryen family meeting, sai na shiga ɗakinta don in canza kayan dake a jikina, ina kokarin cire riga na jiyo muryarta a cikin toilet tana yin waya ƙasa ƙasa kamar bata so aji, saina lallaba na je bakin ƙofar dakin na yi mata la6e a nan na ji tana faɗin wallahi bazata sa6u ba, dama ta jima tana zargin kin asirce mata miji saboda yadda kike gayu, wallahi ba zata ƙyale ki ba, sai ta kashe ki da poison..." Zare ido Hajjaty ta yi, Pravin ya sha mur ya ci gaba da zabga mata ƙarya, "Da na ji haka gabana na faduwa na fara tunanin me yakamata in yi saboda nasan mugun halinta na kishi wlh tsaf zata kashe ki, ni banma san wani munafukin bane ya kulla maki makirci, na so inji da wa ta ke yin wayar, ina jin alamun ta gama yin wayar na ma fasa canza kayan, jiki na na kerma na baro dakin nata, na nufo ɗakin ki don in faɗa maki abunda ke faruwa, shigowata keda wuya ina kokarin in tashe ki na ganki a kudundune cikin bargo, kwatsam na jiyo muryar hajiya Saratu daga waje tana tambayar maids ina ne ɗakin ki? da sauri na la6e bayan labule ina jira inga me za ta yi maki, tana shigowa ɗakin ta nufi gadonki hannunta ruƙe da poison..." Dafe kirji Hajjaty ta yi jikinta ya hau 6ari, daɗi ya ji acikin ranshi ganin ta fara yarda da maganarshi.. "Ji nayi bazan iya bari ta cutar dake ba saboda nasan ba imani gare ta ba, saboda tashin hankali banma san lokacin dana yi wuff na fito daga bayan labulen ba tana jin motsi na ta juyo mu ka yi ido biyu, ta ware baki zata fasa ƙara na shaƙeta tana ta sambatu tana faɗin maciya amana, zarginta ya tabbata akanmu, wlh saita kashe mu, da na ga ta turje ta ƙi saurarena kawai saina sumar da ita, na sungumeki na bar estate ɗin da ke, don nasan muddin ta farka kwanan mu ya ƙare..." Cike da damuwa Hajjaty ta ce, "Banji dadi ba, amma koma wanene ya ƙulla mana makirci Allah ya isa tsakanin mu da shi, mutane basu tsaron Allah. Amma hajiya Saratu bai kamata tana daukar zigar wani ba, ko da ya ke dama ta tsaneni, tasha faɗamin saita raba ni da gidan ubanta, amma bansan tsanar da ta yi mini ta kai har haka ba, kuma dama kwanaki ko hanya bata son haɗawa da ni, abinci ma indai ni na dafa bata cin shi.." Pravin ya ce, "Hmmm, ɗan adam fa ba abun yarda bane, indai ka biyewa mutane zasu kaika su baro ka, kuma dama bata sonki ta sha saka ki kuka, ta ƙuntata maki saboda tana jin haushin zaman da kike yi agidansu, ni kaina da nake mijinta bata ƙyaleni ba, kullum saita goranta mini saboda ina zaune gidan ubanta. Saratu bata da wayau, sakarya ce, kwata kwata bata da halin kirki, zaman hakuri kawai nake yi da ita, amma ni kaina ba sona ta ke yi ba, wahalar da ni ta ke yi, taita juyani son ranta." Yana magana yana yamutsa fuska, "Amma pravin meya kamata mu yi yanzu? Ni ina ga kawai mu je mu basu haƙuri mu faɗa masu gaskiya, In ba haka ba za su mana kallon mutanan banza kuma maciya amana.." Waro idanunsa ya yi, "Ke! Kina hauka? Tab lallai, ay wlh muddin muka koma estate din nan sai sun hukunta mu, sai ka ce kin manta irin yadda baba Obie da yayyanta suke ji da ita? "Pravin, koma me zai faru mu ne masu laifi, mutanan nan sun yi mana hallaci, sun yarda da mu, tsawon shekara da shekaru muna rayuwa acikin su basu ta6a gudun mu ba, amma mu muka ƙi fada masu alaƙar dake atsakaninmu, bamu kyauta ba, kuma nasan zasu fahimce mu in har mu ka je muka basu haƙuri muka kuma faɗa masu akwai aure a tsakanin mu za su yafe mana, koda hajiya Saratun bata yarda ba nasan za su yi ƙoƙarin sasanta mu da ita, tun da su din mutanan kirki ne suna da hankali da kuma tausayi...." Bata ƙare maganar ba ya tari numfashinta da cewa, "Hmmm, na lura har yanzu baki san halin hajiya Saratu ba, nasan mutanan kirki ne amma wlh akan Saratu zasu iya komai, kin manta labarin dana baki lokacin da ta zo da ni don inga danginta? Ƙiri ƙiri suka nuna basu sona sun tsaneni saboda ni ba jinsin su bane, kuma bani da asali da arziki irin nasu, a lokacin ba don baba Obie ya goya mini baya ba ai da basu bani auranta ba..." Dafe kai ta yi da hannu ɗaya, "Me zai hana mu tuntu6i baban toh? nasan zai taimaka." "Har yanzu kin ƙi fahimtata, nifa bazan ci gaba da zama ƙasar nan ba, saboda hajiya Saratu ba zata raga mana ba, ƙwara mu tattara yanamu yanamu mu tafi, don yanzu haka nemanmu suke yi ruwa ajallo don su hukunta mu.." Maganarsa ta ɗaga hankalinta, da damuwa ta ce, "Pravin meya kawo maganar barin ƙasa? Ka san me kake faɗa kuwa? Ina zaka kai ƴa'ƴan naka da matarka? kaima kasan wannan bamai yiwu bane, kawai saboda asirinmu ya tonu sai mu gudu kamar waɗanda suka aikata wani mugun laifi...?" dafe kanshi yayi da hannu ɗaya baisan tayaya zai shawo kanta ba.. "Pravin ka daina wannan maganar, ba zan ta6a baka shawarar ka tafi ka bar iyalinka ba, bamu aikata laifin daya kai har mu gudu ba, kawai kuskuren mu shine ƙarya da muka yi masu tun farko muka boye masu gaskiya, in har muka nemi yafiyarsu bayan mun faɗa musu komai wlh zasu yafe mana Pravin, mun shaƙu da mutanan nan, mun saba da zama cikinsu, sun zama kamar danginmu da muka rasa! Sun ɗauki nauyin komai namu Pravin, wlh idan muka gudu baza su ji dadi ba, zasu ga kamar dama da wata manufa muke atare da su shiyasa bayan mun samu abun da muke so muka tafi, kai baka tunanin halin da ƴa'ƴanka da matarka za su shiga? Wai kuwa Pravin anya kana jin kanka amatsayin ubansu..." bata ƙare magabar ba ya toshe mata bakinta da yatsan shi.. Ta rasa meyasa take ji aranta kamar pravin ba gaskiya ya fada mata ba! Saboda yanayinsa da kuma maganganunsa abun tuhuma ne! Kawai saboda ƙaramin laifin da bai kai ya kawo ba sai ya gudu ya bar iyalinsa? Ganin kamar ta fara ɗago shi ya sa shi saurin daidaita nutsuwarshi cikin sanyin murya ya ce, "Na gane kuskurena, kawai bana so ta cutar dake ne shiyasa na yi wannan maganar, amma ba har cikin raina ba, ni ba zan iya tafiya na bar iyalina ba, banma san na fada ba, ki yi haƙuri idan na 6ata maki rai.." Ajiyar zuciya ta sauke, "Yanzu da yaushe zamu je estate din mu nemi yafiyarsu?" "Me zai hana mu bari sai an kwana biyu, lokacin da suka yi kewarmu, koma suka neme mu da kansu don su ji ba'asi sai mu je mu faɗa masu gaskiya,..." ta aminta da maganarsa saboda a halin yanzu tasan jiran su suke yi. "Na yarda, amma tayaya zasu neme mu? Bayan babu waya gaba ɗaya mun barsu agidan.." Yamutsa fuska ya yi, "Kash, sam na manta, amma akwai waya da na siya, nama yi mana hada siyayyar kayan abinci, da duk wani abu da zamu bukata.." "Pravin basu da layin da zasu tuntubemu a yanzu." "Karki damu, ki bari da kaina zan je estate din, in faɗa masu komai in sun hakura suka yafe mana zan sanar da ke komai." Ta ce, "Toh Pravin, yaushe zaka je ne?" A takure ya yamutsa fuska, kwata kwata bai son tana yi masa maganar Obie estate, da tasan masifar da suke a ciki da bata ƙara marmarin ambaton ko da sunan estate din ba. "Ƙarshen satin nan." Ajiyar zuciya ta sauke, "Toh Allah ya kai mu, amma dan Allah ka kwantar da hankalinka, bana so in gan ka a cikin damuwa, addu'a yakamata mu yi Allah ya sa abun ya zo da sauki su yafe mana." Jinjina mata kai ya yi batare da ya furta kalma ba. Ta yi tunanin hajiya Saratu ce damuwar shi batasan mugun abun da ya aikata ba. Ruƙo hannunta ya yi, "Mu je in taimaka maki ki yi wanka, yau kwana huɗu jikinki baiga ruwa ba." Bata musa mashi ba ya ɗauke ta kamar jinjira ya nufi toilet da ita, after mins ya futo dauke da ita, ta yi ɗaurin ƙirji da towel, ya kwantar da ita kan gadon shi. Juyawa ya yi ya nufi closet tabi bayanshi da kallo tana mai ƙara jin kaunarsa saboda kulawar da ya ke bata. Dawowa ya yi hannunsa ruke da riga da wando na shan iska, tun ranar da ya kawota nan ya siya masu kaya kala uku uku.. "Za ki iya sakawa ko in taimaka maki?" Murmushi ta sakar mashi, "Bana so kana wahala, na lura hada damuwar ciwona ke damunka, kada ka damu zan ji sauki in sha Allah..." Murmushin yaƙe ya yi mata.. Bayan ta kar6i kayan ya fuce daga ɗakin, shiru bai dawo ba, saukowa ta yi daga kan gadon, bayan ta kammala zura kayan a jikin ta, ta je gaban mirror tana kallon kanta. Zuciyarta cike fal da kewar Ahlin Obie, ita dai ta kamu da ƙaunarsu tun farko, kuma ba ta jin zata iya rabuwa da su ko da hajiya Saratu zata hukunta su ne, ta ji zata zuƙunna kan gwiwowinta ta roƙeta akan tayi hakuri ta yafe su. Bakomai tafi ji ba face halin da ƴa'ƴansu za su shiga idan suka rabu. Can kuma ta canza akalar tunanin nata, ta fi jin kewar aminiyarta akan komai, ta so ace akwai waya a hannunta da ba abun da zai hana ta kira Turai ta faɗa mata halin da suke a ciki tasan zata fahimce su kuma zata taimaka masu.. Body oil ta shafa ma skin dinta ta dauko comb ta sharce gashin kanta dakyar dakyar saboda yawanshi ga tauri da ya yi ga kuma jikinta ba ƙwari.. Jin shiru pravin bai leƙo ba ya sa tayi tunanin ko ya fita daga gidan ne. Hakan ya sa ta miƙe daga gaban madubin ta fito ta shiga falo, ɗan madaidaici ne ya haɗu sosai, Pravin ya daɗe yana kokarin jan hankalinta da ta dawo gidansa da zama ta ƙiya saboda bata son rabuwa da obie estate... Idanunta ne suka hango mata bag ɗinsa da ya ajiye kan sofa, sakamakon jefar da ita da ya yi lokacin da ya shigo har ta buɗe abubuwan dake a ciki sun zubo waje.. Buhun ta nufa ta soma buɗe shi, ba komai ne a ciki ba face kayan abinci, komai da zasu buƙata ya siya masu, murmushi ta yi tare da miƙewa har zata juya idanunta suka sauka akan passports dake ajiye kan hannun kujera. Zuwa ta yi gaban kujerar, ta kai hannu ta curo Passport din da ta gani, shiru ta yi jim tana duddubasu aranta ta ayyana me Pravin zai yi da passports dinsu? Bata kawo komai ba a ranta ta mayar da su cikin jakar ta yi zipping dinta, ƙamshin suya ta fara juyowa a cikin hancinta, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta jin motsin shi Direction din da take jiyo motsin ta nufa, dadi kamar zai kashe ta ganin pravin yana girka mata abinci, daga shi sai short a jikin shi, ya haɗa gumi sai aikin motsa suya yake yi... Kamshin naman ne ya daki hancin ta, cikin sanda ta shiga ciki ba tare da sanin shi ba saboda ya bata baya. Hugging dinsa tayi ta baya, wata firgita da ya yi saida ta yi noticing wani abu, "Waw.. waye...! " Ya faɗa tare da ɗaga ƙaton spoon din hannunsa da niyyar ya kwaɗe wanda ya ruke sa.. Ajiyar zuciya ya sauke ganin Hajjaty ce, "meyasa baki yi min sallama ba?" "Saboda in baka tsoro." Ta faɗa da murmushi.. "Hmm, zan rama ne Allah." "Ki koma daki pls, har yanzu babu ƙoshin lafiya atare dake, idan na gama zan kawo maki a daki." Maƙe mashi kafaɗa ta yi, "Kaima kasan bazan bari kana yin aikin da ya kamata ace ni zanyi ba, in har ba zaka bari in taya ka ba, to ka bani in ƙarasa tun da jikin nawa da sauki." Dakyar ya lallabata har ya samu ta koma falon ta zauna. Bada jimawa ba ya fito hannunshi ruke da tray, daga saman shi plates ne na chicken pepper soup, da na shinkafa, ga juice a glasses.." Tunkan ya karasa ta fara haɗiyar yawu.. A saman rug ya a je tray ɗin ta sauko ta zauna shima ya zauna suka tasa tray din a tsakiyar su.. A tare suke ciyar da juna, idan ta bashi a baki shima sai ya bata... Suna ci suna fira, duk ta ishe shi da santi.. "Da ka yi mini girkin nan har ka tuna min lokacin da muke a gida, kafin mu yi aure, ni dai na yi dacen ɗan uwa kuma yayana sannan mijina, tun ina ƙaramata kake kula da ni baka ta6a gajiyawa ba, ci na, suturata, da duk wata ɗawainiyana kaine, baka ta6a bari na da yunwa ba, koda kai zaka rasa toh zaka nema min ni in ci..." Idanunta cike tab da ƙwalla ta yi maganar. Jikinsa ya yi sanyi lakwas. _"Dan Allah Pravin no matter what, kada ka canza daga yadda na sanka, ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye sa6a masa, da ka zalunci wani ƙwara kai azalunce ka saboda Allah baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, ka kau da ido ga abun da ba halal dinka ba, ka yi haƙuri da abun da Allah ya baka. Duk abun da ka samu shine rabonka, ita duniyar nan ba matabbata bace, wata rana zamu mutu mu barta ne, lahira ita ce matabbata kuma dawwamammiya, mu ruƙa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari, daga kai sai halinka za a binne ka, komai da muka tara anan zamu bar shi, kowa zai girbi abun da ya shuka, walau na alkhairi ko na sharri...."_ Tun da ta fara yi masa nasihar jikinsa ya soma 6ari, zuciyarsa ta ƙuntata sosai. Bai ƙarasa sauraronta ba ya miƙe kamar zararre ya nufi daki, yana shiga ya faɗa kan gadonsa ta rubda ciki ya kwanta.. Da gudu ta bi bayan shi, ta hau kan gadon tana tambayar shi me ya faru? Meke damun shi? Ko nasihar da ta yi masa ne bata yi mashi dadi ba... Cikin karyayyar murya ya ce baya jin daɗin zuciyar shi bacci yake so ya yi, saukkowa ta yi daga kan gadon taje gaban mirror ta dauko tissue box, yago tissue din ta yi, ta koma kan gadon ta soma goge masa hannayensa da bai wanke ba, bayan ta gama ta daura box din saman drawer.. Rungume kanshi a ƙirjinta ta yi, tana jin yadda zuciyarsa ke harbawa fat fat kamar zata tsaga ƙirjinshi. Ta ruɗe da ganin yadda ya razana daga kawai ta yi masa nasiha, sai dai bata kawo komai aranta ba, a haka bacci ya yi awon gaba da su. Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. .~________________________________🌹☠️💗🔥~ A bangaren Ummi ta riga ta gama yanke shawarar zata basu haɗin kai, kamar yadda ta kudirta aranta saboda ta wanke big boss daga tuhumar da su ke yi ma shi ba dan ta yarda da tuhumar da suke yi ma shi ba. bayan da ta taje ma Owais da maganar, yayi farin ciki sosai, ta kuma fada masa game da zuwan da zatayi gurin Alhaji musa, Hakan yayi masa dadi sosai, cos wannan dama ce babba agurin su, yace mata idan weekend din yazo zai faɗa mata plan din su, sannan Yace yana son ganin kawarta Natasha, in zai yiwu ta kirata awaya ta fada mata tana son ganin ta cikin week din nan, babu musu ta amsa mashi da toh, tun aranar da sukayi maganar ta kira Natasha awaya, ta faɗa mata tana son tazo Nigeria, tayi missing dinta, tana son ganin ta, Natasha taji dadin jin hakan dama neman hanyar da zato nigeri ta ke yi, har tambayarta ta yi dg zai barta tazo gidansa? Ummi ta gano abunda take ma hari, tace mata karta damu zai barta, kawai ta taho, tace mata toh in ta gama shiri zata sanar da ita. *~_______________________________HAJJATY🌹~* A firgice ta farka sakamakon knocking din daya katse baccin ta, idanunta biji biji cike da kasalar bacci ta soma kokarin mikewa, shafa gefen ta tayi jin wayam babu pravin yasa tayi tunanin ko shi ne ya fita, tun da babu wanda yasan da wannan gidan nasa.. Saukowa tayi daga kan gadon, tana mika hadi da yin Hamma, Yar rigar bacci ce a jikin ta dai dai gwiwarta, ga dukkan alamu ta dan ji saukin zazza6in jikin ta.. Bude kofar dakin tayi, Ta nufi kofar shigowa falon don anan ne takejiyo sautin kwankwasa kofar da akeyi. har ta ruƙe handle din Kofar zata buɗe, Unexpected Tasoma jin sautin durowar wani abu mai nauyi abayanta.. Ta jikin bangon da take fuskanta Ta hango Idanuwar su, wani irin faduwar gaba taji, Kirjinta ya fara mata dakan uku uku, Tuni tasha jinin jikin ta, tsoro Ya hana ta juya, jikinta ya soma 6ari, sai faman zare na mujiya takeyi ganin inuwar mutane Motsin da suka somayi suna tunkararta ne Yasa ta fasa ƙara, tare da juyawa ta manne ma kofar muryar na rawa ta shiga ambaton sunan Pravin Pravin... Watsawa tayi da gudu ta fada bedroon dinsu, adai dai lokacin Pravin Ya fito daga wanka waist dinsa daure da towel tana ganinsa ta boye bayansa, Tana nuna masa kofar shigowa dakin da yatsanta dake kerma sam takasa magana sai haki takeyi... "Mun shiga uku, pravin dodanni ne masu bakaken kaya suna a falo zasu shigo su kashe mu" dakyar ta furta, da farko ya razana amma da ya ji hakan sai ya gane ture akayi masa daga gurin Elders, da kafarsa Ya bangaje kofar toilet Ya jefar da hajjaty ciki Yaja kofar ya kulle ta a ciki. Ya gyara ɗaurin towel dinsa don ya zauna dakyau, da gudun gaske ya fito daga dakin Ya dira atsakiyar su, suna ganin shi suka girgiza jikinsu nan take suka rikiɗa suka koma dodanni, shima Ya rikida ya koma irin siffarsu, faɗane ya kaure atsakanin su, sautin buge bugensu da gurnaninsu ya cike falon, wata irin ƙura ce ta buɗe su.. shi ɗaya su biyar amma saboda yafi su karfin sihiri ko ƙwarzane basu yi mashi ba, sai dai yaji jiki ba kaɗan ba, daya bayan daya saida yayi masu jahilin bugun daya salwantar da rayuwarsu gaba daya ya zubar da gawarwakinsa saman floor, nan take Ya rikiɗa ya dawo suffarsa ta mutane, a zukunne Yana huci tare da haki kamar mayunwacin zaki, ransa yayi mugun baci, bai ta6a zaton Elders zasuyi masa haka ba, dama yasan ba zasu kyaleshi ba saboda sun tsane shi, suna bakin ciki yadda Elder Ya shigar da shi cikinsu ya bashi mukami daidai dana su.. Akan idanun shi gawarwarkin giants din suka 6ace, dama ka'ida ne Idan giant Ya mutu Evils basu barin gawar shi gaba daya suke 6acewa da shi. Tunawa da Hajjaty yasa yayi saurin mikewa ya gyara falon ta yadda bazata gane komai ba. Bubbuga Kofar takeyi da karfi cikin gunjin kuka take fadin"Pravin ka bude min kofa! Meyasa ka kulle ni Pravin? Dan Allah kada ka je gurin su, banaso su kashe min kai, zasu iya cutar dakai, dan Allah pravin ka shigo mu boye anan.." ita kadai take ta sambatun ta. Jin motsin buɗe kofar yasa tay wuff ta fito atsaye ta taras da shi Yana haki, shassshafa jikin shi ta hau yi tana duddubawa don taga ko akwai rauni a jikin shi. Adabarbar ce ta furta"pr.. Pra..vin meya faru? Suna ina? Sun tafi? Ba suyi ma ka komai ba"? Murmushi ya ɗan saki ganin yadda take zare idanun ta a tsorace.. Hugging dinta yayi a kirjin shi tare da dan bubbuga bayanta Cikin sigar lallashi Yace"ture akayi mana, amma na kona su da ayar Allah, ba ki jiyo sautin karatun qur'anin da nayi ba a falo"? "Banji ba" murmushi ya saki "Ayatul kursiyo tayi aiki dana fara karantota saida suka dinga bani hakuri akan indaina zasu tafi, nace bazan daina ba sai sun fada min waya turo su.." dagowa tayi daga kan kirjin shi ta zuba mashi ido tana kallon shi.. "Pravin sun fada maka wanene ya turo su"? Yamutsa fuskarsa yayi"hmmm basai dana fada maki mu bar kasar nan ba kika nace akan mu zauna, toh wlh hajiya saratu ce ta turo su don su kashe mu nima daga bakin daya daga cikin aljanun naji..." ya wani sha mur don karta karto shi. rudani ne tsantsa kan Fuskarta, aranta ta ayyana hakan na nufin hajiya saratu tana bin bokaye? Dama itace kenan tayi asirin data gano akwai aure tsakaninta da pravin shine ta hada baki da marwa donsu 6ata shi agurin ta watakil ma itace ta daurawa marwa cutar Kuturta.." gaba daya ta tsorata da al'amarin nan, daya lura ta yarda da shi sai yace"yakamata musan abunyi tun da har ta gano inda muke, in ba haka ba kashe mu zatayi.." zugata ya dinga yi har saida ta dauki zugarsa tace"pravin jiya naga passports dinmu acikin jakarka, pls ka nema mana hanya mubar kasar nan inyaso daga baya in komai ya lafa sai mu dawo saboda ya'yan ka, ko in suka neme mu, saboda ni wlh hankalina ya tashi, Hajiya saratu bata da imani, ashe har rai zata iya kashe wa? Pravin yace"hmm ke kike mata kallon mutuniyar kirki fiye da haka zata iya aikatawa.." Ruko hannunta yayi suka zauna daga gefen gadon su. "Dama saboda kin nuna bakiso mu tafi shiyasa na fasa, amma tun shekaran jiya nayi mana booking flight a online, na gama mana komai, ko yau kika amince ko gobe sai mu tafi" Cikin sanyin murya tace"na amince pravin, mu tafi kawai, amma ina zamuje? Ko delhi zamu koma"? "A'a, Idan muka koma delhi wa muke da shi? Ticket din dana siya mana bana india bane, na china ne, kinsan muna zuwa idan aka tura mu daga Companynmu yin semina ko wani abu, har gida ina da shi, zamu fi samun kwanciyar hankali acan" Ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta saman kafadar shi"koma ina zamuje mu tafi Pravin, duk inda zakaje zan bika, amma zanyi kewar Ahlin Obie, da Aminiyata.." ta karashe maganar da kuka.. Ajiyar zuciya ya sauke yaji dadin amincewarta, ƙwara ya gudu da ita tun da har an fara kawo mashi hari, Elders suna neman shi ga jami'an isod da ke neman shi ruwa ajallo...💔 *NATASHA'S ARRIVAL🔥* Tana a cikin Toilet ta jiyo ringing din wayarta daga cikin ɗaki, saboda kira ne mai mahimmanci yasa ta dakata da abun da takeyi, ta fito da sauri, waist dinta daure da towel, bayan ta dauko wayar tayi picking ta kara a kunne.. Muryar Natasha tajiyo a cikin kunnanta "Hey, guess what?" "Your location shows you're in Nigeria, at the airport," Ummi ta faɗa da murmushi akan fuskarta "Hehehe, you guessed right, Send someone to pick me up, you knw I've never been to Nigeria." "Okay, wait a bit, I'll arrange for someone to pick you up." "Okay." Bayan ta aje wayar kan gado, shaf shaf ta nufi closet dinta, ta shirya kanta cikin abaya, Ta na kokarin fitowa daga bedroom din su ka yi kici6us da Batool wadda ke shiowa hannun ruke da plate mai dauke da coconut buns "Aunty ummina, have a bite" Murmushi tayi tana zura hannu cikin plate din ta ɗauki coconut bun ta tura abakin ta, tana tauna hadi da dan jinjina kanta tace"wow ya yi dadi sosai, Ki aje min a cikin ɗaki, yanzu zan dawo.." ta faɗa tare da manna mata peck a forehead dinta. Saukowa down tayi cikin sauri ta nufi part din Chief Owais tana zuwa ta taras bayanan. down ta dawo ta fito daga main falo, adaidai Lokacin Motar Chief Owais ta kunno kai ta gate. Akan idonta motar tayi parking, officer ya buɗe mashi motar Gently ya fito sanye da kakinsa "Sir, sunnu da dawowa.." juyowa yai tare da kallon ta, murmushi yayi" yawwa Ummi hope kina lafiya" "Lafiyalou ya gajiyar aiki" "Alhamdulillah" "Am Natasha called me, She's in Nigeria, at the airport pickup area, I told her to wait for me to pick her up." "Bani contact nata, tare da hotonta, zan tura Officer ya ɗauko ta" Nan take ta tura mashi, ta juya ta koma ciki. Bayan Owais ya turama Officer bayanan Natasha, da sauri yabi bayan Ummi, a main falo Ya taras da ita, tana ganin shi ta nufe shi ganin ya nufo ta, a tsakanake ya tsara mata yadda zata tarbeta batare data zargi wani abu ba. Lokacin da officern daya tafi dauko Natasha ya karaso Pickup area din tun kan yayi parking din Motar, Idanunsa suka hango mashi ita ta cikin glass din motar, da kallo ɗaya ya gane aka turo sa ya dauko. Ta fita daban ko acikin mutanan dake a arean gurin, sanye take da button front robe, daga ciki tasaka Cami top. Sai wani trouser da tasaka kallar robe din hot pink, gefen cikinta da wuyanta har saman kirjinta zanen tattoo ne na tantiran yan iska, hancinta na sanye da nose ring, saman le6enta ma wani hujan ne mai ɗauke da ring, ga wasu zako zakon Nails masu ƙyalli da tasaka. Hannunta daya ruƙe da wayarta yayin da dayan hannun ke a dafe da hannun suitcase dinta. Ta rufe idanunta da shades, ga wani hadadden kitso dake akanta wutsiyarsa jan gashin ta ta sauko har tsakiyar bayanta.. Agabanta ya tsayar da motar, ya fito ya nufe ta tare da mika mata hannu"welcome to Nigeria.." yamutsa fuska ta yi, tana yatsina baki tace"Who are you? Or Are you the one ummi sent to pick me up"? Ta faɗa tana nunasa da yatsan ta. Jinjina mata kai yayi"yeah, it's me" Ƙin yarda tayi har saida ta kira ummi ta tabbatar mata da shi ne, sannan ta mika masa hannu suka gaisa, Ya kar6i suitcase dinta ya shigar mata da shi cikin boot, Ya buɗe mata front seat ta shiga ciki ta zauna tare da jan belt ta ɗaura. Motarsu tana karasawo cikin Gidan, Ummi ta fito da sauri ta nufe ta, fuskarta dauke da murmushi. Tana fitowa suka rungume juna. "Welcome to Nigeria My gurl, I'm happy to see you, I miss you," ta fada tana sumbatar cheeks din ta "I miss you too, Ummi, I'm glad to see you.." dakatawa ta danyi da yin maganar, mood din fuskarta ya sauya.. A rude tace"You changed, Ummi I didn't expect that, Why are you covering your body?" ("ummi, kin canza min! Ba haka na zata ba, meyasa kika lullu6e jikinki") "Natasha, zanyi maki bayani, kinsan a gidan dg ne, dole inbi dokarsa, shiya hana ni yin shigar da zata bayyana tsiraici na" ta fada tare da ruko hannunta"mu shiga daga Ciki" "Ciki zan shigo maki da akwatin"? Drivern ne ya fada cikin hershen turanci Da hannu tayi mashi alamar A'a.. "Kabarmin shi a boot, ba'a nan zan kwana ba.." "Why"? Ummi ne ta tambaya, yayin da suka shiga main falo.. "Gidan dg ne fa, i can't stay long, He won't let me hang out or enjoy myself, I'll be confined like a prisoner, Ƙwara in kira big boss ya turo a ɗauke ni" dariya Ummi tayi aranta ta furta"am sorry Natasha, nayi ma ki laifi, nima bada son raina ba..." tun da suka shigo take ta zuzuta kyawun Gidan Dj A main Falo suka zauna kan sofas suna fuskantar Juna. "kin gudu kin barni da mutananki, kullum tambayana sukeyi Ina Ummi Ina Ummi? Ina taje ne, Yaushe zata dawo, Sunyi kewarki ummi, nima nayi kewarki, yakamata ki aje aikin nan mu koma america.." Murmushi tayi mata"Natasha, zamuyi wannan maganar, amma ba yanzu ba, Kina bukatar ki huta, nasan kin kwaso gajiyar tafiya"... Girgiza kai tayi"No, babu gajiya a tare dani" "Zakiyi wanka ko zaki ci abinci"? "Zan fara da abincin, but You know I'm allergic to meat" "Karki damu, nasan me zansa akawo maki" ta fada tare da kiran landline din kitchen, ta sanar da Chefs abun da take buƙata.. "Big boss ya san da zuwanki kuwa? "Ban faɗa masa ba, kinsan halinsa baya son mu san identity din shi, in har na fada masa zai hanani ne, ni kuma bana so ya sani saboda wannan zuwan da nayi, nayi shi ne saboda kin neme ni, kuma saboda inaso naga baby preety na..." yanayin fuskar Ummi ne ya sauya zuwa damuwa da faɗuwar gaba, tunawa da abun da suka tattauna da Chief game da big boss, batasan ya Natasha zata ɗauki abun ba, tasan halinta tana da kafiya da rashin kunya ba kowane zai iya juya ta ba.. "Ummi me kike tunani ne"? Ta tambaya tana kallon fuskarta"kamar akwai abun da ke damunki" Girgiza kai tayi"ba abun da ke damuna Natasha..." bata kare maganar ba, Chef Ya shigo falon bayan yayi ma Natasha barka da zuwa yace sun kammala shirya masu lunch a dining room Godiya ummi tayi masa, kafin ta dubi Natasha mu tafi" mikewa tayi suka nufi dining, bayan sun zauna kan kujera suna fuskantar Juna, chef ya yi serving na su.. Suna cin abinci suna firar yaushe rabo. "Ina taso in tambayeki Ina handsome boy din nan"? Shiru ta ɗanyi jimm kafin tace"Yana a isod camp, gurin training" ta faɗi hakanne saboda tasan ko ta fada ma Natasha ya rasu ba yarda zatayi ba. "Wow, i can't wait to see him in isod uniform, he will look hotter, but ina sauran yaran? Banji motsin kowa ba, ko ke ka ɗai ce a gidan" "Bani kadai bace, yaran basa nan, suna agidan Kawun dg, Biyu ne suke a tare dani, bari na kira maki su ku gaisa.. Tana niyar ɗaukar waya muryar Unaisah ta katse su"aunty Ummi, baƙuwa mu ka yi ne"? ta fada tana nufo su, sanye take da long gown. Lokacin da Natasha ta jiyo suka fuskanci juna wani irin faduwar gaba taji, ganin matar da take ha6o, batayi tsammanin ganin ta ba.. miƙewa Natasha tayi ta mika mata hannu"nasan baki sanni ba, amma nasan ummi ta fada maku dangane dani, ina fata na same ku Lafiya..." da ido Ummi tayi mata alamar ta saki jikin ta, cos ta lura da yadda ta haɗe rai kamar bata ta6a yin dariya ba Murmushi tayi tare da nufarta, suka yi hugging din juna, cike da kyankyaminta Unaisah tayi saurin raba jikin su. Wani irin kallon tsana Unaisah take jifar ta da shi, yayin da Zuciyarta ke tariyo mata fuskar Unaizah, hatta Kitson kan Natasha shigen irin kitson da ke akan Unaizah. Daƙyar ta haɗiye abun da ke aranta ta ɗan saki fara'a tace "I welcome you, I'm happy to see you, Natasha." Washe baki Natasha tayi tana faɗin"I'm glad to meet you too, What's your name?" "Unaisah," "Wow, you impress me" .ta faɗa tana ƙare mata kallon, haushi duk ya cika Unaisah ganin yadda take kallon hips dinta da kirjinta tana kashe mata ido har wani zuro harshe take yi tana lashe lips din ta kamar karya.. Ummi bata lura ba saboda ta bata baya. _Heartless monster, kin gama yawo tun da kika kawo kanki Nigeria_ ta faɗa a cikin ranta. Juyowa ta yi rai a6ace tabar dinning area din tana gab da zata shiga bedroom dinsu tayi kici6us da Batool dake fitowa"Ina zakije" "Gurin Aunty Ummi" Wani kallo tayi mata, aranta ta ayyana bazan bari karyar can ta ganki ba sis.. "Aunty Ummi ta yi Bakuwa, kuma bata son kowa Yaje kusa da su, mu koma Ciki, zan kunna mana korean drama mu kalla....." ta faɗa tare da jan hannunta suka shige ciki, taja kofa ta kulle duk don kada ta ƙara ganin Natasha. "Ummi, this girl has grown I know she's mature now, naga hips dinta sun buɗe, ƙirjinta sun ciko, ta tada min jarabata, dana kalli nipples dinta sai da naji..." bata ƙare magabar ba, Ummi ta daka mata tsawa a firgice ta zare idanunta tana tambayar meya faru? Bama tasan me tayi ba, saboda jakkanci.. "Am sorry Natasha, nan gidan dg ne, yakamata kisan irin maganganun da zaki faɗa, yaran nan ko kallon banza ki ka yi ma su ba ƙyale ki za'ayi ba.." zare blue eyes din ta tayi"saboda me"? Banza tayi da ita, duk taji komai ya fita ranta saboda kalaman da ta furta akan Unaisah, har ga Allah ta daɗe tana jin tsanar halin Natasha mace ba kamun kai kamar balamar tinkiya. Bayan sun kammala Cin abincin, Ummi tace ta tashi su tafi akwai dakin hotel da ta kama mata, Natasha tace ita fa taga wurin zama, ta fasa tafiya anan zata kwana. Tun da taji hakan ta gane me take mawa aikuwa ta dinga lalla6ata don ta tashi su tafi, saboda batason taja mata abun kunya, Natasha ta kafe akan maganarta, har tana fadin ko dai korarta takeyi ne? In ba haka ba why zata gayyace ta kuma ta matsa mata akan ga inda takeson ta kwana"? Badan taso ba ta ƙyaleta.. Around ƙarfe shabiyu na dare, natasha ta farka daga bacci, ta sauko daga kan gadon, Camisole ce a jikinta shara shara kana iya hangen Inners din ta. Mika tayi tare da yin hamma, ko da ta hango ummi kwance kan couch tana bacci wani shu'umin murmushi tayi ganin ta samu damar da zata aiwatar da kudurinta. Cikin sanɗa ta fuce daga ɗakin, ta sauko down, ta fara neman bedroom din su Unaisah, ko tsoro bataji, bedrooms din dake a down stairs taita buɗewa tana leka cikin su Batasan Cctv tana tana ɗaukar duk wani motsin ta ba. Dakyar ta gano kofar dakin, tana shiga ta hangosu kwance kan gadon sunyi nisa a baccin su, kowannansu da inda yake fuskanta, lashe le6enta tayi, kura taga nama, Cikin sanɗa ta nufi gadon ta tsaya tana bin su da mayataccen kallo, kasantuwar bargon da suka lullu6e ya zame daga kan jikin su. Shantala shantalan cinyoyinsu da dukiyar fulanin su ne suka tsone mata idanun ta. Tayi zaton irin yaran da ta saba yima wayou ne ta lalata su. A hankali ta hau saman gadon, ta fara shafa laps din Unaisah tana lashe harshe, kamar mayya, har wani sautin jaraba take fitarwa, tana kokarin zame mata pant. Kwatsam batai aune ba taji an duma mata zazzafan dundu a saman bayanta, ji kake durum! A firgice ta furta"what the f...?!" bata ƙarasa ba, Ya toshe bakinta da tafinsa, Ya janyota ya sauko da ita daga kan gadon, yajata ta karfin tsiya ya fitar da ita daga dakin, ya nufi can ciki da ita, a wani daki da ke a hanyar backyard din gidan, Ya jefar da ita Ciki ya kulle kofar, ta dinga bubbuga kofar tana zage zage, batasan ɗakin Soudproof bane, in mutun yana a ciki ko zaiyi ihu babu wanda zai jiyo shi daga waje. Batasan dama dakonta yakeyi ba, lokacin da take neman bedroom din su Unaisah yana atsaye kan stairs, Yana kallon duk wani motsin ta. Dama Yaji a labarin Unaizah ta bada gudummuwa gurin lalata yarinyar hakan na nufin yar les ce ita kuma tana bin maza, tayaya zai iya bacci da mugun abu agidansa? Komawa yayi bedroom din su Unaisah, don ya gyara masu duvet din su Yana ruko bargon unexpected ta cafke hannun shi, har saida gabanshi ya faɗi, farkawarta kenan, a hankali ta mike da rudu kan fuskarta take duban shi Ganin shi a bedroom dinsu, daga shi sai short da shirt.. Cikin sauri Taja rigar baccinta ta lullu6e laps dinta. Wani kallon tuhuma take jifarsa da shi, kasa magana yayi saboda ya rasa amsar da zai basa, abun da kunya baisan tayaya zai kare kanshi ba, Natasha taja ma shi Ya taka sahun 6arawo, Girgiza mata kai yayi cikin nutsatstsiyar muryarsa ya furta" zanyi maki bayani Unaisah, ki saurare ni, kinsan ba hali bane.. " "Yaya Owais, wani irin bayani zakayi min bayan wanda nagani da idanuna? Me ya kawo ka dakinmu? Me kuma yasa ka ta6a jikina har ka yi yunkurin cire min rigana? ..." bata kare maganar ba, yai saurin toshe mata baki da tafinsa, zama yayi daga gefenta" idanunsu cikin na juna. Kafin ya dan saci kallon Batool dake a kwance tana bacci, fargabansa kada ta tashi abun zaiyi masa yawa.. "Bani bane nayi maki haka ba, Natasha ce kawar Ummi, Na kamata ne tana kokarin... " kasa karasawa yayi, ta zare idanunta cike da bacin rai, dama saida ranta ya bata bazata ƙyaleta ba, wannan wata irin dakikiya ce"? "Ki kwantar da hankalin ki, yanzu haka na kulleta a daki, ba zata kara fitowa ba, har sai mun gama bincike akan ta.." ajiyar zuciya ta sauke ta re da cire hannunsa daga kan bakinta"am sorry hubby, rashin sani ne, bansan haka abin ya faru ba.." Murmushi yayi"na fahimce ki, ki koma ki kwanta.." ya fada tare da mikewa Ya juya har ya kusa fucewa daga bedroom din ya dan dakata tare da kallon ta yace _"kisa ma ranki, Ni chief bazan ta6a gigin ta6a jikinki ba, har sai munyi aure lokacinne nake da damar da zanyi komai nakeso dake.."_ yana karasa fada ya fuce, murmushi tasaki tare da janyo pillow ta rungume shi a kirjinta. ~______________________________~ Motsin bude kofar da taji ne yasa tayi saurin mikewa cikin bacin rai da fusatacciyar murya tace"Who the hell are you? And why did you lock me in this room?" Kunna switch din dakin yayi haske ya kawo, tana ganin Chief Owais ta washe baki ta nufe shi da ƙwarƙwasa don taja hankalinsa, batasan kallon ƙato ya ke mata ba. "Abun daya faru kuskure ne, ni ban shiga don na cutar da su ba.. " ta faɗa tana kokarin kai hannu donta shafa kirjinshi aikuwa ya damƙi wuyan hannun Ya murɗe shi kamar zai 6ulle shi. fasa ƙara tayi radadin da tajine yasa ta fitar da gumi, saida ta galabaita ta dinga sambatu tukunna Ya wurgar da ita kasa kamar kayan wanki ta kife kan floor "Ki shiga taitayin ki idan kinason mu rabu lafiya idan ba haka ba, Jikinki ne zai gaya maki.." ya fada tare da zama kan kujera Ya daura kafarsa daya kan daya.. Ranta a6ace ta dube shi"bakasan wacece ni ba, sai na rama abun da kayi min.." mikewa tayi ta nufi kofar dakin tana rukewa tajita a kulle.. "Ni kuwa nasan wacece ke, fasikar data lalata rayuwar matashiyar da aka bata rainonta tun tana jaririya, mace mara imani mara tausayi, wadda bata san zafin haihuwa ba"! Kalamansa sun daga hankalinta, tayaya akai yasan wannan labarin? A rude ta juyo ta fuskance shi, a ranta ta ayyana badai ummi ce taci amanarta ba? Ko dai dama ta kira ta ne da wata manufa... "Abun da kike tunani aranki gaskiya ne" "Ni nasa Ummi ta kira min ke.." Cikin rudu da fusata tace"saboda me? dama tarko ne ku ka ɗana min kai da Ita ko? Bazan kyaleku ba, zan kira big boss, you'll all pay for it" "Taya zaki iya kiran shi? Sai lokacin ta tuna bata da waya a hannunta ga kuma kofar a kulle. "Open this door! Let me out, Ka bude min kofa in fita in har ba kidnapping dina ku ka yi ba.." duk tabi ta ruɗe.. "Akwai tambayoyi da nakeso in yi maki, idan kika amsa minsu ta lalama zan barki ki fita . ." bai kare magabar ba, ta kwatsa mashi tsawa"I won't answer your questions, ba mu da wata alaka da juna, bakasan ni ba nima bansan ka ba, don haka ka kyaleni in tafi, ita kuma Ummi bazan ƙyaleta ba, tun da har taci amanata saina tona mata asiri agurin Big boss, dakai da ita duka zaku gane kurenku" duk yadda yaso ya shawo kanta taki bashi hadin kai, har saida ta fusata shi ya zuciya rai a6ace ya mike daga kan kujerar da ya ke, ya nufeta tana zare idanu ta shiga fadin kar ya taba ta, karya kuskura ya matso kusa da ita. Ƙokarin kai mashi bugu tayi, yayi saurin kaucewa ya damƙi ƙeyarta ya buga kanta jikin bango ta fasa ƙara. "Gargadi zanyi maki na karshe, karki kuskura ki kara yi min magana da tsawa ko kice zaki yi min rashin kunya, I'm easy-going, but don't test me.." ya faɗa da kakkausar murya. sakin ta yayi, ta juya ta fuskance shi, hannun ta dafe da gefen bakin ta daya fashe. ya zaro bindiga yayi tare da saita ta da ita, gabanta na faduwa ta zazzare idanun ta, duk tabi tasha jinin jikinta... "Idan na kashe ki na kashe banza, Kinsan da hakan ko" a firgice ta jinjina mashi kai "Wa kike da shi a Nigeria? Shi kanshi wanda kike taƙama da shi bazai iya ku6utar dake ba, saboda shima mai laifi ne, idan ke yafi karfinki, baifi karfin doka ba, mahaifina shine shugaban kasar nan, ni kuma dg din Isod ne" dabarbarcewa tayi muryarta na rawa ta furta"I won't repeat my mistake, Please don't kill me" "bazan kara maimaita kuskuren da nayi ba, kada ka ka kashe ni..." ta faɗa tana zama kan kujera "Ka fadamin meyasa kuka kira ni? Wani laifi big boss ya aikata? Meyasa kuma ni zaku sanyani a ciki bayan ban hada alakar komai da shi ba..." murmushin gefen fuska Chief yayi jin ta sauya magana yanzu dataga bata da mafita.. "Naji komai daga bakin Ummi, game da alakar dake a tsakaninki da big boss, sai dai ina neman karin bayani, ki fada min komai idan ba haka ba kema zaki shiga cikin wadanda muke zargi .." a tsorace ta ɗan zare blue eyes din ta. Tana faman share zufa tace"bansan komai dangane da shi ba, ka tambayi ummi, ni ban taba zuwa nigeria ba, wannan ne karo na farko, kuma da nasan tarko kuka dana min da banzo ba, big boss baya bari insan identity dinshi, farkon haduwana da shi a beach ne, ni nafara shisshige mashi har saida ya bani hadin kai, ya kuma nuna yana son in zama karuwarsa zai dauki nauyin komai da zan bukata arayuwata, na amince masa saboda a lokacin ya kwanta min a rai, bayan haka ina cikin bukatar kudi. Silar haɗuwana da shi, Ya mallaka min gida da mota, ya bani black card dinsa, komai da nakeso yi min yakeyi.." "Bai ta6a nuna yana son ya aureki ba"? Girgiza kai tayi"ni nake son shi, Inason na aure shi amma bai taba bani dama ba, ya riga daya fadamin ba da aure yake sona ba, bazai aureni ba, but he will keep coming and having sex with me, ba yadda banyi da shi ba, har na hakura nabiye ma shi" Lokacin da muka shaku sosai shine ya kawomin jinjira a cikin towel yace min ya bani ita dana tambayesa yar wacece sai yace min yar matar yayansa da ya rasu ne, bayan da ta haifeta ta samu matsalar shayarwa shine ya kawomin ita don in raineta, ya fadamin sunanta Unaizah, yarinyar ta kwantamin araina, ni na shayar da ita na raine ta har ta girma.." "Meyasa bakiyi bincike ba kika kar6i yarinyar da baki taba ganin wani nata ba? Kawai don ya kawo mi ita, yace miki yar yayansa ce sai ki kar6a? Baki yi tunanin meyasa bai ba wani danginsa ya kula da ita ba sai ke? Bayan kinsan cewa tushen shi daga Nigeria ne, bayan haka saboda rashin hankali kika bada gudummuwa gurin gurbata ta ko? Baki dauketa ya ba, baki bata tarbiya ba, dake da shi ku ka hadu kuna amfani da ita saboda rashin hankali" "Ai ba laifi bane, abun da takeso ne mukeyi mata..." baisan sa'adda ya wanka mata mari ba, har saida fuskarta ta kalli gefe daya, dafe kuncinta tayi, taji zafin marin sosai, cike da bacin rai yace"kinji kunya, banza dakikiya, saboda kinga ya wukalantata shine kema kika bada goyan bayan a wulakantata ko? baki yi tunanin ya mahaifiyarta zataji ba, baki taba tambayarsa ya maida ma uwa yarta ba, saboda son zuciya ko? Idanunsa sun ciko da kwalla.. Hankalinta ya tashi da ganin bacin ran dake a cikin idanunsa "You never asked him to return the daughter to her mother because of selfishness." "Why should I worry about asking him after he never discussed returning her with me? Why do you keep accusing me when I'm not guilty? Everything I did was with his support, I treated her well, with morals, I never hurt her, I took care of her, made her happy" (Tayaya ni zan damu da tambayarsa bayan shi bai ta6a yi min magana akan zai maida ta ba? Meyasa zaka dinga tuhumata bayan ni bani bace mai laifi ba? komai da nayi shi ya bayani goyan baya, kuma ni haka na taso rayuwata, azamana da baby pretty ban ta6a cutar da ita ba, na bata kulawa, na bata tarbiya na kuma bata farin ciki, komai takeso inayi mata shi) "duk da bani na haifeta ba, bata ta6a sanin bani na haifeta ba, saboda ya gargaɗeni akan bayason ta sani kuma nayi hakan saboda yarjejeniyace a tsakanin mu, Kuɗi ya ke biyana.." _cike da takaici Chief ya dafe kansa bakin cikine ya cika zuciyar shi, komai daya faru ubanta ne yaja mata, maganar Natasha gaskiya ne, da ace bai kai mata ita ba da duk hakan bai faru ba, kuma da ace ya kwa6e ta akanta da bata 6atata ba, amma dayake dama da biyu ya kai ta saboda ya riga daya sadaukar da ita bata da amfani a gare sa, bayan haka Natasha baturiya ce baturiyarma mai yanci kuma karuwa, dama wasunsu ba hankali gare su ba, gani suke indai jin dadin rayuwane komai da zasuyi don su faranta ransu mai kyau ko mara kyau ba laifi bane, suna da right din da zasuyi amma duk da haka bazai kyaleta ba, yadda Unaizah ta dandani zafin cin amanar da su kayi mata haka ya ke son kowan nan su ya danɗani kwatankwacin raɗadin da taji a cikin zuciyarta_ "Since last year, ya raba ni da ita, ya maidata gurin mamanta, yanzu haka wannan zuwan da nayi hada don inason naganta, in kuma rokesu su bani ita saboda bazan iya rayuwa batare da ita ba..." bata kare maganarba ya kwatsa mata tsawar da data razana ta "Su baki ita don kicigaba da biyan bukatarki da ita ko"? Ya fada kamar zai rufeta da bugu. Girgiza kai tayi"ba saboda haka nakeso ta dawo gurina ba, inason ta, ina jinta kamar yar dana haifa a ciki na, After that, I had a problem, I'll never give birth" "Kina daukarta kamar ƴa? Kina nufin har yarki ta cikin ki zaki iya kwanciya da ita.."? Cike da jin shakkar shi ta ɗaga mashi kai alamar eh A zuciye ya ɗaga hannu zai mareta tayi saurin kare fuskatarta da hannun ta "Ya isa haka! Nagaji! Ka daina mari na! Ko dan saboda girmana ya kamata ka girmama ni, na fahimci haushina kake ji, ka tsaneni, amma yakamata ka gane ni bani da laifi..." "Ke kike ganin girma a tare dake, Ni kaskanci da jahilci nake gani a tare dake, baki da mutunci ko kima a idanuna, saboda ke din mara imani ce, dabba mara hankali.." taji zafin kalamanshi sai dai kwata kwata bata nuna hakan ba. "Yau ki ka zo nigeria, Kuma a yau kika shiga dakin yaran da baki hada alakar komai da su ba, ki kai yunkurin taba jikinsu saboda jaraba kuma a haka kike kiran kanki mara laifi? shiru tayi bata musu ma shi ba. Jinjina kanshi yayi ji yake kamar ya binneta da ranta saboda haushinta da yake ji "Kin ta6a haihuwa da shi"? cikin fushi tace"I don't know, I'm tired of your questions, kamar nayi maka laifi saboda kawai nazo gidanka zaka tsareni da bugu kamar jaka.." rufe shi da fada tayi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Sam ta manta da gun din hannunsa sai da taji ya har6i vase tayi kara taja baki tayi shiru a firgice. "Zaki amsa min tambayata ko kuwa"? Harara ta watsa mashi tana yatsina fuska tace"Na ta6a sau ɗaya, amma ba araye na haife su ba" a takure ta amsa tambayar.. "Mata ne ko maza"? "No, they are mixed twins" jinjina kan shi yayi da alama akwai abun da ya ke tunani aran shi. Yanzu ya gane itama Ya ci amanarta batare da sanin ta ba, hakan yayi mashi dadi, saboda itama taji abun da uwa take ji idan wani ya cutar mata da, kuma zatayi danasanin komai da tayiwa Unaizah. "Pls kada ka kara tambayana nagaji.." ta fada tana yatsina masa baki, fuskarta sai naso ta ke yi kamar ɗanyen nama. Jinjina kan shi yayi"Okay" "Tunda na amsa maka tambayoyin ka, nima ka amsa mun nawa, wani laifi big boss ya aikata? Me kuma yasa ku ka kira ni? Sannan meyasa kake tambayana akan Unaizah? Kana da alaƙa da ita ne? "Zaki sani amma ba yanzu ba" Juyawa yayi zai tafi tayi saurin bin bayanshi Juyowa yayi"ina zuwa"? "Zan koma ciki mana, in ba baka son ganina tafiya zanyi yanzun nan don ko mintuna banso in ƙara a gidan nan" Murmushi Chief yayi"nan ne masaukinki a gidan nan, babu ke babu fita, za'a dinga kawo maki abinci, da kuma suturar sanyawa, akwai toilet in bukata ta kamaki .." arude tace"bangane ba? Me kake nufi? Garkuwa kukayi dani ko kuwa na aikata laifin daya cancanta ku kulle ni ne? ..." bai tsaya sauraranta ba, ya fuce tana kokari fita kofar ta datse kanta. Bugun kofar ta din ga yi da kafarta da hannunta, kamar zata balleta, a karshe data galabaita, agajiye ta sulale kasa ta jingine kanta jikin kofar, zuciyarta a cunkushe take da bakin cikin cin amanarta da ummi tayi, gayanan taja mata bala'e da ta sani da bata zo ba 🔐 (🔥UNEXPECTED CALL OF HAJJATY🔥) Around ƙarfe 2 da rabi na dare suna akwance kan gadonsu, rabin jikinsu lullu6e yake da duvet, babu wadataccen haske a dakin nasu, kasantuwar sun kashe light din before su kwanta sai dai hasken Bedside lap da su ka bari a kunne.. Ringing din waya ne ya takura baccin nasu.. Wayar sai ruri take daga kiran ya katse wani ke shigowa. Farkawa tayi bakin ta dauke da addu'ar ta shi daga bacci, a hankali ta buɗe idanunta da suka kada ja saboda bacci ta dube shi da su.. Murmushi tayi, ganin ya samu bacci yau. Tana tsaka da kallon fuskar shi, Ringing din wayar ya katse ta. Sam ta manta me ya tayar da ita daga bacci sai da taji ringing din Gabanta ne ya fadi da rudu akan fuskarta ta furta wanene ke kira na da tsakar daren nan? Kasa motsawa tayi saboda tsoro ne da ita, tayi lamo a kirjin Mijin nata. Sai da taji anƙi daina kiran wayar nata ne yasa ta fara tunanin ko dai wani muhimmin abu ne yasa aka kira ta? Wata kil ma na cikin gidan ne ke kira. A hankali ta raba jikinta da ga nashi, ta sauko daga kan gadon cikin sanda ta ɗau wayar, duk don kada ta tada shi daga bacci. Juya ta nufi can cikin dakin daga bangaren walk-in closet din su. Screen din wayar ta duba, missed calls ta gani daga new number Hakanan ta dinga jin fargaba, kamar karta daga kiran, amma zuciyarta ta matsa mata akan ta daga taji wanene.. Adaidai lokacin an sake kira, yatsun hannunta na kerma ta yi picking ta kara wayar a kunne unexpected taji yo muryar Hajjaty tana yin magana cikin muryar raɗa "Kina jina? Taji ta ambata. Wata ajiyar zuciya ta sauke dadi ya lullu6eta kamar zata saka kuka tace"hajjaty ina kika shiga? Meyasa zaki gudu batare da kin neme ni ba? Kin kuwa san halin dana shiga? Kullum tunanina wani hali kike ciki..." bata kare maganar ba ta katse ta.. "Pls, bana so wani yasan na kira ki, ke ka ɗai ce ko kina a tare da Oga" "Ni kadaice hajjaty, babu kowa a kusa dani" tana jiyo ajiyar zuciyarta. "Ki fada min meyasa kika gudu? Ta tambaya kamar batasan komai ba. Fashe mata tayi da kuka"kina nufin baki ji komai ba"? "Banji ba, nadai ji labarin kin gudu" Saboda ta aminta da ita yasa ta faɗa mata komai da Pravin ya sanar da ita, turai ta ruɗe da jin labarin yasha banban da wanda ita ta sani. "Ki yi hakuri ban ta6a sanar dake ba, yanzun ma tura ce takai bango, bani da mafita daya wu ce in sanar dake gaskiya, Pravin ya matsa mu bar kasar saboda yana jin tsoron hukuncin da zamu fuskanta agurin Hajiya saratu da yayyanta, ni kuma banaso mu tafi saboda ya'yan shi da matar shi, ni ma kuma na saba da ahlin obie, nayi nayi da Pravin ya bari muzo mu nemi yafiyar su amma yaƙiya, kwat kwata baison wani yasan inda muke, ko fita zaiyi da mask a fuska ya ke fita, na rasa ya zanyi in shawo kanshi, yanzu haka da nake maki magana baisan na saci wayar shi na kira ba, Yana adaki yana bacci.." "Hajjaty, ki kwantar da hankalin ki, Naji komai tabbas baku kyauta ba, da kuka zauna tsawon shekaru kuna boye musu alakar dake atsakanin ku, da tun farko kun fada masu komai da duk hakan bata faru ba, amma yanzu abun da nakeso dake, Karki bari Pravin yasan kin dauki wayarsa, ko kinyi waya dani, tun da na fahimci tsoro ya ke ji, kawai idan mun gama magana ki goge number ta, kada ki kara kira kuma kada ki ta6a ta, ni duk zanji da komai, In sha Allah zan yi kokarin sulhunta tsakanin ku da su.." "Nagode Aminiyana, dama nasan ke kadaice zaki iya share min hawaye na, amma taya zaki tuntu6e mu idan sun yafe mana? gobe fa zamu tafi" "Kin san sunan anguwan da kuke ne? "Bansan komai ba, lokacin daya kawo ni bana a hayyacina" "Okay, Kiyi yadda nace maki, ki ajiye wayar" zan sake kira amma ki kwanta kinji"? Amsawa tayi da toh"amma pls kiyi sauri ki kira kafin ya farka, wlh idan yaga na kira ransa zai baci" "Toh" daga haka su ka yi sallama. Juyawa tayi cikin sauri ta koma kan gadon su. "Babe, ka tashi, Hajjaty, ta kira ni, ka tashi pls! Gobe zasu bar kasar" dakyar ta samu ya farka yana yamitsa fuska idanunsa a rufe yace"pls kada ki takura min, Ki kyaleni.." saitin kunnanshi takai bakinta"hajjaty ta kira yanzun nan.." bata kare maganar ba, taga ya ware idanunsa tare da mikewa yana tambayar ta wace hajjatyn? "Hajjaty dai daka sani, ba ka ce nemanta ku ke yi ba, To ta kirani da bakuwar number yanzun nan" Bai tsaya sauraron karashen zancen ba Yace Ina number din data kira da ita, Wayar ta mika masa yasa hannu ya kar6a, ya na dubawa.. Me kuka tattauna da ita.. Zayyana masa tayi, ta dan marairaice fuska tace"babe, na rasa gane kan zancen, a maganar hajjaty bata nuna tasan wani abu game da ciwon hajiya saratu ba, ku kuma kunce kuna zargin faɗane ya haɗa su! Ban dai tambayeta komai ba ban kuma fada mata meya faru da hajiya saratu ba, gudun kada in daga hankalin ta, amma tayaya akai hajiya saratu tasan da aure atsakanin su? anya Praveen yana da gaskiya kuwa? Na fara zargin shi, meyasa zai matsa akan su bar kasar nan? Bayan ga matar shi nan rai hannun Allah, ga kuma ya'yansa kuma meyasa pravin yakeso su bar kasar akan abunda bai kai ya kawo ba? Tun da ta fara maganar bai kula ta ba, yana ta danna wayarta. "Dan Allah kayi kokari ka taimaka masu nasan sun tsoratane shiyasa zasu gudu, tun da sun gane kuskurensu a kira su aji meya faru, ni bana zargin su, pls muyi wani abu, kafin gobe" Wani kallo Sir mubarak yai mata, tuni taja baki tayi shiru "Kin cikani da surutu kamar aku, zaki kwanta ko saina matseki" ya fada da zolaya, dariya tayi tare da kwantar da kanta, yaja mata bargo ya lullu6eta duka har kanta Daga cikin bargon taci gaba yi masa magiya akan ya taimaka ya dawo mata da yar kawarta gida.. " Saukowa yayi daga Kan gadon, daga shi sai dan short, ya nufi walk-in closet nasu jim kadan ya dawo, sanye da jallabiya a jikin shi, har ya fuce daga dakin bata sani ba sai bayan tafiyar shi ta ɗan leko daga cikin bargon tayi mamakin ganin babu shi kuma bai aje mata wayar ba, fatan ta Allah yasa za su je su dawo da su hajjaty ne. ________________________🔥 *ANEELERH🔥* Around ƙarfe sha biyu na safe ta farka daga guntun baccin daya dauke ta tun bayan da suka kammala breakfast, Miƙa ta yi tare da yin hamma kafin ta sauko daga kan gadon jikinta sanye da jallabiya, ta lullu6e kanta da hula, doguwar sumar kanta ta sauka gefe da gefen kafaɗarta, bata damu da rashin ganin junaid a bedroom din ba, tasan bazai wuce dakin mami ba ko na zahra, cos yau ba school weekend ne, har ta juya zata fuce daga dakin wayar ta dake ajiye kan bedside drawer ta fara ruri juyawa tayi cikin nutsuwa takai hannu ta ɗauki wayar ganin sunan Benazir ya bayyana akan screen din yasa ta sakin murmushi cike da zumuɗi tayi picking call din tare da kara wayar a kunnanta. "Amarya kuma uwar gida agurin Taj, ya kike? Ya su mami? fatan kuna lafiya..." On the other hand sautin dariyar Benazir ya cika kunnanta"har kinsa naji wani sanyi araina da kika ambaci Taj, da ace muna a kusa har tukuici zan baki saboda faranta min rai da ki kayi..." murmushi Anila ta saki, bayan sun gama gaisawa Anila tace"yaushe zamu sake komawa gidan Dj ne? Nayi missing din Aisha, Inaso na sake ganinta, kullum da tunanin ta nake wuni, gashi har yanzu bata ɗaga kirana ...." Benazir tace"wallahi nima har yanzu bata ɗaga kirana, bansan me mukayi mata ba, shima ya shureim bata ɗaga kiran shi, saboda yadda na damu da ita har mafarkinta nakeyi..." bata ƙare maganar ba Anila ta katse ta da cewa"bakya tunanin akwai wani dalili dayasa take fushi da mu? In ba haka ba me mukayi mata"? Ta faɗa fuskarta a yamutse kamar tana a kusa da Benazir din. "Anila ni kaina saida nayi wannan tunanin, amma na rasa gane laifin me mukayi mata? In ma saboda abunda ya shureim yayi mata ne yakamata ace komai ya wuce yanzu, bawan Allah nan har hakuri ya bata, mu ma mun bata hakuri, abu fin shekaru tana rukon shi a zuciyarta..." Anila tace"har yanzu bana ganin laifinta, kinsan zuciya bata da ƙashi, Aisha tasha wahalar rayuwa, in har zata dinga tuna bakin cikin data kunsa silar abun daya shiga tsakaninta da ya shureim ba lallai ta yafe masa ba, ni wallahi abun daya daga hankalina game da ita, canzawar da tayi, bansan wata irin rayuwa Aisha tayi a america ba, amma kallo daya zaki mata ki gane ba ustatha bace, zato zunubi amma kammanninta kamar irin na tantiran yan barikin nan, idanunta sun buɗe, dai dai da tafiyarta bata uztazai bace..." bata kare maganar ba jin shesshekar kukan Benazir "Koma meya faru da Aisha mune ne sila" lallashin ta Anila tayi har saida ta samu tayi shiru na ɗan wani lokaci kafin Anila ta ce"sun ce zasu neme mu, amma naji shiru har yau basu kira mu ba, nifa kawai ina rayuwa a cikin gidan nan ne saboda iyayena suna a cikin sa, amma wallahi kullum cikin fargaba nake saboda Uncle dan iya, ko haɗa hanya da shi bansan yi, mutumin ya fita araina na tsane shi, shiyasa na kosa su gama binciken su akan videon ana, suzo su kama shi kawai kowa ya huta" Cikin sanyin murya Benazir tace"nima din hankalina ba a kwance ya ke ba, koda yaushe cikin fargaba nake, tun da na fitar da sirrin abun da na sani game da Uncle musa, dama ina zargin shine ke yunkurin kashe ni, shiyasa time da nayi ciwo nai ta pretending kamar bana acikin hayyacinta saboda na fahimci bai hakura ba, har yanzu yana akan bakansa na daukar mataki akai na, Anila bansan ya zanyi ba, banaso wani abu ya samu iyayena da ya shureim, gashi duk muna a karkashin ikon shi, in har ya gane na fitar da sirrin wlh zai iya binne mu da ranmu tun da ba imani ne da shi ba.." gaba daya sun shiga damuwa. "Benazir, mu dai bamu yi dacen kawunnai ba, wallahi ban taba zaton Uncle dan iya zai iya aikata rashin imanin nan ba, mutumin banza me fuska biyu, Allah kadai yasan ina yakai Ana, na rasa gane kashe ta yayi ne ko kuwa wani gurin ya kulleta, daurewa kawai nakeyi amma duk idan na ganshi ji nake kamar in kama gemun shege in tsistsinka shi,...." ƙyalƙyalewa da dariya Benazir tayi jin abun da Anila tace. "ni wallahi abun dayafi damuna Su zahra, yara masu kirki sai dai kash ba su yi dacen uba ba.." "Hmm ke dai bari, Idan suka san mugun abun da fasikin ubansu ke aikatawa ay wlh sai sun kusa zaucewa..." Benazir ce ta fada can kuma tace "Anila, kin tuna abun da Dj ya gargademu akai? Ki daina daga murya kada wani ya ji yo ki, Ina fata ke kaɗaice a dakin nan don na ji kamar motsin wani a cikin kunne na.." Zaro idanu Anila tayi cike da fargaba, can kuma ta saki dariya"wlh kin tsoratar dani, har kinsa gabana ya faɗi, idan Uncle dan iya ya kamani ina yin wayar wlh na mutu" dariya Benazir tayi"yaya shureim yana kira na sai anjima zamuyi magana.." sallama su ka yi, fuskarta ɗauke da murmushi ta ɗaura wayar saman mirror tare da sauke ajiyar zuciya, ta ɗan lumshe idanunta, kwatsam ta tsinkayi motsin mutum adakin ta, tayi azan junaid ne hakan yasa ta furta "my baby boy, ina ka shiga na farka daga bacci bangan ka a kusa ba"? Ta faɗa ba tare data buɗe idanunta ba, ga kuma motsin yana cigaba da tunkarota. "Babyn mommy ka yi min magana mana, nayi missing dinka, zo nan kusa da ni..." ta faɗa tana miƙa hannunta. shiru taji ba'a tanka mata ba, In har junaid ne tasan bazai ta6a share ta ba, tunawa tayi da maganar Benazir _ina fata ke kadaice a dakin nan don naji kamar motsin wani_ Cikin sauri ta buɗe idanunta kaitsaye suka sauka acikin na shi ta cikin madubi, wata irin zabura tayi kamar wadda taga dodo, ta zazzare idanun ta cike da tashin hankali, kwata kwata bata tsammaci zata ga mutun adakin ba, me ya kawo shi dakin ta? abun da take ma fargaba kada ace yaji wayar da tayi da Benazir, kirjinta kamar ana luguden ta6are, da wata irin faduwar gaba ta zabura jikinta na kerma ta miƙe tsaye tana ƙare masa kallo daga ƙasa har sama ta cikin madubin batare data waiwayo ta fuskance shi ba. Yana a tsaye ya ruke qugunsa da hannunsa na dama, yar shara da gajeran wando ne a jikin shi, kwata kwata fuskarsa ba walwala ko miskala zarratin, fuskarsa sai naso take ga wani uban shade fari daya ƙwama a idanun shi ya sauko har ta kan karan bajajjen hancin shi, uban goshin nan nashi kamar jirgi yayi asubanci, bakomai ne akan fuskarsa ba face tashin hankali da ruɗanin abun da bai ta6a zata ba... Kafin kace me daga shi har Anila tuni wani azababben gumi ya tsatsafo ta saman goshin su. aranta ta ayyana Na shiga Uku, Wayyo Allahna, La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu munazzalim, wa'inna hu min sulaiman wa innasu bismillah.... duk tabi ta rude ta rikice duk wata addu'a data zo mata arai cikin hanzari take ambaton ta. Har murza idanunta tayi don taga ko gizau ya ke yi mata amma koda ta gama goge idanun still babu abunda ya canza. Cikin rawar murya ya furta"babu abun da zaki 6oye min Anila, Naji komai da kika faɗa a cikin wayarki, inaso ki faɗa min wani video ne na ana kuka gani? A ina kuka gansa? Naji kuma kin ambaci kin kosa su gama bincike su zo su kama ni su wanene? Me kuma nayiwa Ana da naji kina fada mata"? Ya jefa mata tambayoyin a jere.. zazzare idanu tayi tare da haɗiyar yawu ba tare data iya furta kalma ba, jin ta share shi yasa shi daka mata tsawar data razanar da ita a ruɗe ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Uncle wayar da kaji inayi ba dakai nakeyi ba, firar wani drama muke yi watakil kunnuwanka ne suka jiyo maka badaidai ba..." bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"Karya kikeyi Anila, ko dai ki fada min gaskiya ko kuma inyi maki abun da baki ta6a zata ba..." afusace ta juyo ta fuskance shi idanunta suka shiga cikin nashi, duk da shakkarshi da takeji hakan bai hana ta furta"ai ba tsoronka nake ji ba, maganar girma ta kare Uncle, mutuncinka ya zube kasa wanwar, wayar da ka ji inayi dagaske ne, nasan komai Uncle, kar nake kallonka, Allah ya tonu asirinka, Naga komai da idanuna balle kace zaka karyata magana ta, wallahi kasan Inda Ana take kawai ka fadamin Ina ka 6oye ta Idan ba haka ba hmmm" babu alamun ya fahimci inda zancenta Ya dosa sai ma ruɗu daya mamaye zuciyarshi cike da tashin hankali Yace"wannan wani irin zancen banza ne Anila? Kina hauka ne? Meya haɗina da Ana? Kin bani ajiyarta ne da zaki tuhume ni akan 6atanta, anya kina a cikin hayyacin ki kuwa, Ko kin fara shaye shaye ne"? "Ɗan Iya ba shaye shaye nayi ba, Ina Cikin hayyacina, Idan ma akwai wanda ya fara shaye shayen to kaine mutumin banza, mai fuska biyu..."waro idanu waje yayi cikin rudu ya ke kallon ta. Dakyar yayi karfin halin furta"Har ni zakiyiwa kazafi Anila? Saboda tsabar rashin kunya da ta6ara ki kalli tsabar idanuna ki gaggayamin magana batare da jin shakkata ba? Wani video ne kike ikirari akai"? ta fahimci yafi damuwa dayasan videon menene suke magana akai. Harara ta watsa mashi kafin tace"videon komai daka aikatawa Ana, kawai ka fada min Ina Ana take? Tana araye ne ko ka kashe ta"? aruɗe ya daura hannu saman kan shi ya shafo Sanƙon kanshi tare da jan gemun shi yana faman zare idanunshi kamar na kwarton mazuru. tsantsar al'ajabi ne akan fuskar shi, tayaya akai har Anila ta samu videon abun da yake aikatawa ana? Tayaya? Anya ba burga ta ke yi masa ba? A sanin shi babu cctv a gidansa. "Ashe tun bayan da muka dawo gidan nan kake lalata da ana aduk lokacin da takeyin jinin Al'ada, kana amfani da sihirinka ka gusar mata da hankalin ta, sa'ilin da ta gane Allah ya fahimtar da ita komai tace zata tona maka asiri shine ka fara neman hanyar da zaka kawar da ita gudun kada ta jaza maka matsala" bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Uncle ɗan Iya ya daka mata wadda tayi silar faduwar gaban ta. Idanunsa sun kaɗa jawur kamar garwashin wuta, Uban goshin nan nashi sai naso yakeyi ya hada gumi kamar ba A.c adakin.. a hankali Ya cire glass din dake akan idanunsa Ya jefar da shi ƙasa, tare da sanya tafin hannunsa ya shafo ƙeyarsa har izuwa rantalin sa, gaba daya kansa ya ruɗe Anila ta rikita ƙwaƙwalwarsa.. Dakyar ya shanye mamakin shi ya furta"Anila zaki tabka babban kuskure na zargina batare da kina da ƙwaƙƙwarar hujja ba, Ni fa Uncle dinki ne kinsan wanene ni kinsan halina bansan wani shaidani bane Ya yi maki hudubar da har kika gasgata maganar shi ba, Ni bazan iya aikata rashin imanin nan ba, Ƙazafi ne kawai ake nema ay min..." bai ƙare maganar ba Anila tayi wata irin dariyar takaici "Bayan kasancewarka Matsafi, Fasiƙi kai ɗin babban makaryaci ne...." ta faɗa cikin fusatacciyar murya tare da nuna masa kofar dakin da yatsan ta. "ka fuce min daga ɗakina, Bana son ganin ka.." "Ba zan fita ba Anila, ki zauna muyi magana ta fahimta, kada ki manta ni Uncle dinki ne, duk inda za'aje adawo, dole ki amsa min amsoshin tambayoyin da nayi maki! Wani video ne Ana tayi? A ina kika same shi, ke kika dauke shi da kanki ko kuwa itace ta bar abunda ta dauki videon, sannan bayan ke su wanene suka ka kalli videon.." bai kare maganar ba, ta zare mashi idanunta da suka kaɗa jawur cike da tsanar shi ta furta"bazan faɗa ba, Ka jira ka gani, wallahi dole ka girbi abunda ka shuka, har kana wani fadin kai uncle dina ne, to ai ko ubanane ya aikata abunda kayi wlh saina damƙa shi ga hukuma ta hukunta shi, balle kai karen kaɗa miya, karere a danginsu Abie, ai nasan komai, baku da wata alaƙa ta jini, tsintarka su kayi, wallahi jinin abie ɗina bazai ta6a aikata fasikanci da ka aikata ba..." maganar Anila ta fusata shi, har baisan sa'adda Ya cije gefen tafin hannunsa ba. "Cikin lalama ka fita kabar dakin nan, Idan ba haka ba zanyi maka ihun da kowa na gidan nan zai ji, Kuma idan suka tambayeni meke faruwa zan fada musu abun da ka aikata ne..." harara ya watsa mata, ya juya ransa a 6ace Ya nufi kofar fita daga ɗakin, har ya daga kafa zai fuce sai kuma ya fasa ya tsaya cak, kwakwalwarsa na tariyo masa abun daya faru. cike da takaici Ya daki jikin ƙofar, evil heart dinsa ta motsa ji yayi bazai iya ƙyale ta ba, tun da har tasan sirrinsa kuma ga dukkan alamu ta kai shi ƙara gurin hukuma, kwara kawai ya aikata abun daya dace. Anila dake a tsaye tana kallon sa, wani irin faduwar gaba taji, ganin ya datse ƙofar dakinta, murya na rawa ta furta"me.. me.. me zakayi min..? Ba zaka fita ka bar min ɗakina ba? Wallahi zan yi maka ihu.. " "kada ka kuskura ka tabani, bani kadai na kalli videon ba, zan iya rufa maka asiri amma idan ka cutar dani asirinka zai tonu kowa ya sani..." jikinta na karkarwa ta soma laluban makamin da zata kwaɗe shi da shi. juyowa yayi yana huci kamar mayunwacin zaki ya durfafe ta, har wani gurnani ya ke fitarwa kamar mazuru. Da kakkausar murya yace"kinjama kanki bala'e da masifa Anila, tun da har kika shiga gona ta, bazan ƙyale ki ba, zanyi maki abun na ke yi wa Ana sannan In kashe ki, In kuma binne gawarki a cikin ɗakin nan! Su kuma wadanda kika turawa videon suka gani zan gano su ne daya bayan daya in kashe su..." hankalinta idan yai dubu to ya tashi, duk tabi ta rude ta razana, sai faman girgiza kanta takeyi kamar yar kadangaruwa, sai zagaye dakin sukeyi taki bari ya damke ta, gaban mirror ta nufa takai hanninta da ke kerma ta rarumi kwalaben turarurrukanta ta dinga jifar shi da su ko gizau baiyi ba,.. "Kada ka matso kusa dani, kada ka ta6ani Uncle, zakayi danasani...." ta faɗa tana zare mashi idanun ta cikin tsoro har ta kware baki da niyar ta fasa ihu don mutanan gidan suji, sai dai kash bata kaiga yin hakan ba, ɗan iya yayi kukan kura Ya damƙi keyarta da hannu ɗaya, yakai ɗayan hannun saman bakinta ya toshe shi, Ƙyanƙyami da ƙyamar shi ne ya kama ta, Idanunta suka kaɗa jawur, tadinga kokarin kwace kanta daga rukan da yayi mata ta kasa, tafin hannunsa daya toshe bakinta da shi ta dinga cizo hadi da yakushin shi da akaifunta, amma yaki ya sake ta, tana jiyo knocking daga wajen dakin kamar tayi hauka saboda ta kasa iya furta kalma.. Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___✍️~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. 💔~______________________________~🌹💘🔥💋~ "Aunty Anila, lafiya kika kulle room door din ki? pls ki buɗe min, baby junaid yana son ganin ki gayanan abayana na goya shi sai faman turbune min fuska ya ke yi...." daga wajen dakin Zahra tayi maganar batasan halin da Anileerh ta ke a ciki ba Muryar junaid ta jiyo yana fadin"mommy ki buɗe mana kofa, mu shigo..." idanunta sun kaɗa jawur hawayen da suka cika su a hankali suke zarya kan kuncin ta, Uncle dan iya dake kallanta wata yar iskar dariya ya saki kasa kasa, Cikin muryar raɗa ya furta"ina ta ya ki bakin ciki Anila, daga rana irin ta yau ba zaki ƙara jin ko da muryar su ba, zaki rasa kowa naki za kuma ki rasa kanki saboda shegen bin ƙwaƙƙwafin ki da kafiyarki..." iza ƙeyarta yayi, tana turjewa yasa karfi gurin ingizata suka shiga toilet, Ya datse ƙofar, ba tare daya saki bakinta daya toshe ba, Yajata har izuwa gaban bathtube faucet Ya kunna tafasasshen ruwan zafi Ya fara kwararowa da gudun gaske Tiririnsa Ya cika toilet din.. hankalinta ya ƙara tashi ta zazzare idanunta kamar ƙwayar zasu faɗo kasa, Hular data rufe kanta tuni ta jima da barin kan nata. lokacin da bathtube din Ya cika da ruwan zafin, ya ƙara da sihiri gurin tafasa shi, sannan ya kamo wutsiyar Sumar kanta Ya zura a cikinsa nan take gashin Ya kone akan idanun ta.. wata irin razana tayi ta dinga ƙoƙari ƙwace kanta daga gare shi, tana ta gunjun kuka ta rasa ina zata tsoma ranta, tsoro da fargaba ya kamata. "Zaki fada min Inda kika samu video din ko kuwa kin za6i in zabka ki a cikin ruwan nan kamar yadda ake zabka kaza..." ya faɗa tare da buɗe mata baki don tayi magana..."ko da kinyi ihu ba zasu ji ki ba.." Haki ta dinga yi dakyar ta iya furta"koda na fada maka, ba za ka fasa kashe ni ba, ba zaka yi min wayou ba, mutum mugu irinka ba ya yafe wa wanda yasan sirrinsa..." bata kare maganar ba, Ya damƙi kanta ta tsiya ya tura sa gab da ruwan zafi, Hucin da ta shaka ne Ya haifar mata da karancin numfashi, ta fashe da kuka saboda azabar da taji, wata irin azababbiyar mura ce ta farat ɗaya ta kamata hancin ta yadinga sakin wata irin tsinkakkiyar majina mara kauri. Cikin shesshekar murya ta furta"zan.. Zan faɗa! Zan faɗa maka! Kada ka kashe ni dan Allah..." saida ya bari ta galabaita ta fara fita hayyacin ta, kana ya ɗago da kanta, ya kura mata kwartayen idanun nan nasa marasa kyan gani, abunka ga farar fata fuskarta tayi jawur kamar ka ta6a jini ya ɗigo. "Ina sauraronki..." kasa magana tayi sai haki take yi. Tsawa ya daka mata"zaki fada ko kuwa"? Cikin disasshiyar murya ta furta"ka riga ka makaro Uncle, kona fada maka ba abun da zaka iyayi saboda na riga dana turawa Jami'an isod videon A yanzu haka sun fara bincike akanka..." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya tsantsar tashin hankali da fargaba ne a cikin idanun shi, cikin shi ya duri ruwa.. bai gama shiga tashin hankali ba, Unexpected jiniyar motocin da ke shigowa gidan ta karaɗe kunnuwan kowannansu.. Su Uncle dan iya ido Ya raina fata, Jikinshi ya hau kerma kamar mazari.. Anila dake ta sakin numfashi sama sama ga raɗaɗi tana ji amma ahaka take sakin murmushi"bakaga komai ba Uncle, nasan za ka yi mamaki, lokacin da ka juya baya kana kokarin kulle kofar dakina, a tsakanin wannan lokacinne na dauki wayata nayi hanzarin tura ma su sakon su kawo min agaji.." bata kare maganar ba, sakamakon shaƙar da yayiwa wuyanta, ranshi yayi makura agurin baci, kumatunsa har kerma su ke yi. kasa furta magana yayi saboda 6acin rai da zullumin kada su riske shi, da karfi Ya wurgar da ita tayi gadan gadan zata fada cikin kwamin wankan kafin ya 6ace daga cikin toilet ɗin bat babu shi babu burbushin shi...😳 _(Shin menene dalilin da ya kawo Uncle ɗan Iya ɗakin Ana? Bakomai bane face yazo ya sanar da ita game da aikin daya sama mata don ta shirya ta tafi interview, sai kuma Ya risketa tana waya harya tsaya yana sauraron firar su)_ Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un...." mami ce ta fada yayin da take fitowa daga kitchen, da gudu ummi ta biyo bayanta, koda idanun ta su ka yi arba da abun da mami ke wa sallallami nan ta ke ta ɗaura hannayenta biyu asaman kanta tana ambaton la'haula walaquwata illa billah sojoji agidan nan? Bayin Allah kodai 6atan hanya ku ka yi ne"? Hankalinta atashe ta ƙarashe maganar tana kallon Isod agents din da ke shigowa Falon, sanye cikin kakin su, hannayen su ruƙe da bindigogi.. Watsowa zahra tayi da gudu bayanta agoye da junaid ta nufo falon Jin jiniyar motoci tun kan ta ƙaraso idanun ta suka yi mata tozali da isod soldiers ja da baya ta soma yi a tsananin tsorace ta zazzare idanunta, numfashinta kamar zai ɗauke saboda tashin hankali da ta shiga. Mahboob dake a cikin toilet Yana wanka, ko da jin jiniyar motoci a cikin gidansu, aguje ya fito daga toilet din jikin shi duk kumfar da bai kaiga ɗauraye wa ba, Ya dafe guntun towel din daya daurawa qugunsa, jikinsa na 6ari ya nufi window din dakinsa ya zuge ta tare da leƙe kansa, dafe kirjin sa yayi da tafin hannunsa cikin rawar murya ya furta"Allahumma Ajirni Fi Musibati wa akhluf Li Khairan Minha....". 😳 Komawa Cikin Toilet din yayi ya ɗaurayo jikinsa da ruwa, Jikinsa na bari Ya dawo dakin Ya ɗauko Jallabiya Cikin closet dinsa ya zura a jikin shi. Da ɗan gudunsa Ya fito daga dakin "Wayyo Allah Mommy, Ni sauke ni in tafi gurin mommy, bana shon ganin su.." baby junaid ne ya fashe da kuka yana ta duma ma zahra dundu abayanta don ta sauke shi sai dai hankalin nata gaba daya ba akan shi ya ke ba.. Mami kamar zata saka kuka tace Dan Allah ku fada mana meya kawo ku gidan nan? Ni nama rasa ganewa yan sanda ne ko yan fanshi ne" ba su iya ganin fuskokin su saboda mask din da suka saka. Wani mai budaddiyar Murya ne daga Cikin su yace"Ina mai gidan? Kallon juna su ka yi, murya na rawa Mahboob daya karaso Yace"su biyu ne, Abie da Uncle din mu wa kuke nema a ciki" ummi tace"mun shiga Uku, ganin mutanan nan ba alkhairi bane, Ni dai Allah yasa ba wani bane ya tsokano mana su ba" "Ɗan iya muke nema! idan yana a cikin gidan ku yi mana sallama da shi" "Mahboob ka shiga ɗakin shi ka duba" har mahboob Ya juya zai tafi muryar Anila ta katse su"Baya agidan Ya 6ace akan idanuna" gaba daya suka juya suna kallon ta, fuskarta tayi jawur saboda hucin ruwan zafin daya dake ta ga hawayen da suka cike idanunta, tunkan ta karaso Junaid ya sauko daga bayan zahra Ya nufe ta yana kuka, daukar shi tayi tare da rungume shi a kirjin ta, mami da ummi har suna hada baki gurin furta"anila! Wata irin 6acewa kike magana akai"? Daga tsakiyar su ta tsaya tare da kallon su Mami, a halin yanzu tasan komai yazo karshe bata jin fargabar ta sanar da kowa tun da ita kanta rayuwarta na acikin hatsari. Nan take ta labarta masu abun daya faru tsakanin ta da Uncle dan Iya, Tashin hankali tsantsa akan fuskokin su, adai dai Lokaci Abie da baba Mai gadi sun nufo falo shigowar shi kenan tunkan yayi parking mota, baba mai gadi ya sanar da shi zuwan jami'ai, Hankali atashe suka nufo ciki, Komai da Anila ta fada akan kunnan su. "Duk da ya gudu ba zamu fasa abun da ya kawo mu ba, dg Ya bada Umarnin Mu bincike gidan gaba daya, don haka kubar hukuma tayi aikinta, naku kallo ne kawai..." wanda yai maganar daga gani shine led team ɗin su Kallon mahboob yayi wanda komai jinsa yake yi kamar a mafarki"muje ka nuna mana dakin mai aikin ku Ana, da dakin mahaifinku" dakyar ya iya amsawa da toh. "Ina mai gadin gidan nan" jikin Baba mai gadi na bari Ya ce gani yalla6ai.. "Ka tabbata a ranar da abun ya faru baka ga gifcin kowa ba? "Ƙwara ka fada mana gaskiya idan ba haka ba, doka zatayi aiki akan ka" kamar zai fashe da kuka ya hau yi masu rantse rantse akan shi baiga kowa ba tun bayan da mutanan gidan suka tafi unguwa.. Ruko Hannun Mahboob Agent zahra yayi, suka bar sojoji agents biyar, a falon tare da su Anila, hudu suka nufi dakin Ana.. "Bayin Allah daga Ina? Tayaya zaku fadowa mutane gida? Wa kuke nema? Abie ne ya tambaya arude sai lokacin ya samu damar bude bakin sa. Anila ce tay saurin Tarar numfashin shi da cewa"Abie zan fada maku komai,..." gaba daya suka kura mata idanu. Nan ta soma zayyana masu komai daya faru tun daga ranar data shiga dakin Ana har ta gano wayarta. "Ni da Benazir munyi maku karyar zamuje gidan Hajiya adama, toh ba can muka je ba, Gidan Dj mu ka je kai kara akan Uncle..." Ɗaura hannu biyu Ummi tayi akai tana zabga salati, zahra ta zazzare idanunta saboda tashin hankali, mami duk tabi ta rude Abie yace"Anila meyasa tun lokacin baki sanar dani ba? "Saboda banaso In jefa rayuwarku cikin hadari, kuma koda na fada maku wallahi ba zaku yarda dani ba, shiyasa na yanke shawarar sanar da Benazir don mu nemi mafita" "Amma Anila kinyi gaggawar sanar da jami'ai, meyasa zaki yarda da maganar Ana da tayi maki a video? Ki ka san ko ƙazafi tayi ma shi saboda wata manufa tata? Sai kace bakisan halin Uncle din naki ba? Me zaiyi da yar aiki kafira! Kuma taya akai ita tasan yana da sihiri dudu yaushe kuka dawo gidan? Ummi ce ta faɗa cikin rudu da bacin rai. Abie Yace"baki kyauta ba Anila, Maganar nan acikin gida yakamata Mu yi ta atsakanin mu mu binne ta, amma sai kika fitar da ita waje gashi yanzu kinja mana, kuma wallahi in har abun da kika faɗa ba gaskiya bane saina sa6amaki..." kowa da abunda yake faɗa. Agents suna atsaye suna sauraron tattaunawar su, Kamar zasu rufe Anila da bugu sai faɗa sukeyi mata saboda basu yarda da abun da ta fada ba. "Ba a shaidar dan Adam, tun da har kuka ga na kai karar Uncle dina da kaina, Yakamata Ku yarda dani, Ni ban aikata laifi ba, Ummi Itama Ana yar adam ce, ko da kasancewarta me aiki, na rayu da ita tsawon shekaru, nasan halinta Ciki da bai, fiye da yadda nasan halin Uncle, Ana ba zata ta6a yi masa kazafi ba tun da har ta fada toh Ya aikata ne.." ba ƙare maganar ba Abie Ya daka mata tsawa"kar in kuskura In kara jin bakin ki mara kunya, wallahi in har suka gama binciken nan basu gano komai ba ki kuka da kanki.." cikin shesshekar Kuka tace"nima zanyi fatan hakan Abie, amma mawuyacin abune.." "Aunty Aneelerh dan Allah kiyi shiru, Ki rufa mana asiri ki daina magana, ni nasan daddy bazai aikata abunda kike zarginsa ba, In sha Allah bazai ta6a zama gaskiya ba" Zahra ce ta fada tana kuka. Wani kallon tausayi Anila tayi mata, Junaid Sai kara kankameta yakeyi kamar zai koma cikin ta. A bangaren Agent zahra, bayan Mahboob Ya buɗe masu dakin Ana, suka shuga daga Ciki suka fara gudanar da bincikensu Har suka kare basu gano komai ba. Suka tasa ƙeyar shi Yakaisu dakin Uncle dan iya bayan sun shiga nan ma suka fara binciken ko'ina na cikin dakin, Mahboob duk yana kallonsu gabansa nata faɗuwa. A karkashin gadon shi sojoji suka zaro wasu akwatina Guda hudu, Balle murfin sukayi, bakomai bane a ciki ba face kudi bendir bendir sabbi fitigill mahboob har saida Ya dafe kirjinsa saboda razanar da yayi, Kallon saman ceilling din dakinsa sukayi Agent zahra Ya ba sauran agents din Umarnin su babbake ceiling din, Mahboob ne ya dauko masu katuwar guduma suka taka drawer, har suka cimma ceilling din, da guduma suka yi nasarar 6alle wani sashe na ceilling din dakyar da sidin goshi tunkan su karasa Kudi suka fara faɗowa ƙasa yan dubu dubu, wlh tsabar kidima yasa mahboob ya firgita cikin rudu, saboda yasan daddynsu baida wannan kudin, mutumin da shegen makonshi bai bari ya biya masu bukatunsu kanshi kadai ya sani, hakkinsu daya yake basu shine abincin da zasu shi, amma suturarsu da abun hawa da sauransu su suke siyawa kan su bai damu da lafiyar su ba sai ummi ke fafutuka. Kudin sai fadowa kasa sukeyi kamar ana zuba yashi sun taru akan pillow tili gudu. Bayan sun gama da Ceilling din, Suka bude fankaceciyar wardrobe dinsa suka fara zazzago kayan Jikin ta, daga kasa cikin drawer chest dinta suka ga wasu makudan kudaɗen sai faman jinjina kai su ke yi. Kurama bangon da wardrobe din take yayi da ido tare da nazarin yadda take "ku dauke min wardrobe dinnan daga jikin bango" agent zahra ne ya bada Umarni, Hada karfi agents din sukayi gurin ture wardrobe din tun daga tushenta suka 6a66ako ta tare da jingine ta gefe ɗaya. Ƙurawa bangon idanu sukayi basu ga komai ba, can Agent Yace su fasa bangon, aikuwa suka fara ƙwanƙwashe shi da gudu ma, har saida Marbles Ya zube kasa, nan take wata boyayyiyar kofa ta bayyana a jikin bangon, ashe zahra yaga abun daya gani. "Ku bude ta," ya basu Umarni, bayan sun cire kofar, duhu suka gani, tunkan suyi ma mahboob magana yayi saurin ɗauko masu fitilar saman drawer Ya mika ma agent, ya kar6a tare da masa godiya kafin suka shige ciki. Da farko yaji tsoron Yabi bayan su amma kuma yana so Yaga karashen al'amarin na ubansu hakan Yasa yabi bayan su. Lokacin da suka shigo munafukin dakin, mai ruke da fitilar ne Ya haska masu Cikin sa, bakomai bane a cikinsa face Kayan tsafi, hada kwarangwal din mutune da layoyi, zare idanu Mahboob yayi Jikin shi Ya hau yin kerma, Yana kokarin Ja da baya atsorace cikin rashin sani Ya taka wani guri mai kamar danshin ruwa nan take kafarsa ta zurma ya fasa kara, cikin zafin nama wani agent ya damƙi hannunsa, dakyar Ya fito da kafar shi, bawan Allah duk yabi ya rikice, lallashin shi sojojin sukayi har suka samu Ya dan dawo hayyacin sa.. Agent zahra dake bin dakin da kallo karaf idanunsa suka hango mashi digger da shabir, a wata kusurwa hada busasshen jini a jikin su. Da hannu ya nuna ma sojoji su Yace"Ku dauko mun su" Cikin sauri suka kwaso su tare da kawo mashi a kasa suke zube su, Zukunna wa yayi tare da daukar digar yakaita gaban hancin shi, Yamitsa fuskarsa yayi tare da kallon Inda kafar Mahboob ta zurma nan take ranshi ya bashi wani abu aka binne a gurin. Umarni yaba agents din su haƙa inda kafar Mahboob Ta zurma. Da sauri biyu daga cikinsu suka dauki digger da shebir, suka nufi gurin suka hada karfi gurin tone kasar gurin. Mahboob dake ta zare idanunsa Sai ja da baya yake yi. Ƙananun ƙwari ne suka soma gangarowa ta cikin ramin. Ganin yadda suke ta sara kasan da karfi ne yasa Zahra ce masu Su bi a hankali saboda su samu damar ganin me aka binne a gurin. Kwatsam! Suka fara hango Hannayen mutun barbade da kasa. Aje kayan aikin sukayi sai sukayi amfani da hannayensu gurin Janyo da gawar suka fito da ita waje gaba daya ƙasa ta barbade jikin ta, wani iko na Allah batay komai ba, babu alamun ru6ewa a jikin ta, daga gani bata jima da mutuwa ba, Allah dai ya nufa sai anganta, wata kara Mahboob Ya fasa tare da fashewa da kuka Ya zube kan gwiwonsa Yana ambaton"ana ! Ana! Ana! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..wallahi itace! Ana ce, ta mutu, Wayyo Allahana na bani na lalace.." da rarrafe ya nufi gawar, Ya ruko yatsanta dake asanye da zoben daya bata da shi Ya gane ta. Gaba daya Jikin agents ɗin yayi sanyi lakwas zuciyarsu ta karaya, ransu kuma ya 6aci sosai. "Yaro, wacece wannan din? Wani agent ne ya tambaya. Cikin kuka Yace"mai aikin gidanmu Ana da muke ta nema itace" kallon kallo suka jefawa juna, hasashen su Ya zama gaskiya.. Duk wannan abun dake faru su mami dake a falon basu son komai ba, saboda sun yi nesa da su basu iya jiyo sautin komai.. Kwatsam suna zazzaune a saman sofas na falo, suka soma jiyo kukan Mahboob kamar ana zare ransa, Hankali atashe suka zabura tare da mikewa kafin su motsa sai ga shi ya watso da gudu hawaye jaga jaga da fuskar shi yana karasowa bai iya furta kalma ba Ya yanke jiki ya faɗi asume, har suna hada baki gurin ambaton sunan shi basu kaiga karasawa gare shi ba, kwatsam saiga agents sun biyo bayan shi, biyu daga cikinsu sun dauko gawar Ana asaman wani buhu, wa'iyazubillah tsabar tashin hankali kasa motsi sukayi, saboda al'ajabin daya rikirkita su, har agents din suka ajiye gawar a tsakiyar su basu motsa ba. Anila bata san sa'adda ta saki Junaid ya fadi kasa yana kuka, zubewa tayi kan gwiwowinta akan gawar ana da hannu ta dinga kakka6e kasar dake akan fuskarta har saida ta goge ta sosai ainihin kamannin fuskarta ya fito. Cikin shesshekar kuka ta dubi agents din"A.. a ina kuk.. Ka samu gawarta"? Agent zahra yace"a wani dakin sirri dake a jikin dakinsa wanda kofarsa bayan wardrobe dinsa take.." fashewa tayi da kuka, Zahra tuni ta jima da sumewa, ummi ma nan take ta yanke jiki ta faɗi. Anila ta dubi abie daya kame atsaye shida mami tana kuka tace"yanzu kun gasgata abunda na fada maku ko? Gayanan kun gani da idonku, Ana ba sharri tayi masa ba, bayan ya gama lalata rayuwarta shine Ya kasheta Ya binne don kada asirinshi Ya tonu.." baba Mai gadi daya gama rudewa yama raɗa ina zai sa kansa. Agent zahra ya fayyace masu komai da suka gani adakin Dan Iya. Yace sun dauki bayanan da suke so Saura su kama shi, kuma suna neman goyan bayansu In har ya taka kafarsa a cikin gidan su yi hanzarin sanar da su sannan zasu tafi da gawar ana don su karasa binciken su akanta, idan suka gama zasu yi mata jana'iza, bayan haka sun kulle dakin dan iya dana Ana, kada wanda yayi kuskuren bude shi. Kafin su tafi da ita Anila da abie da Mami suka zuzzukunna agaban gawar suka dinga yi mata addu'o'i. Abie yace Idan zasu yi jana'izar su sanar da shi yanaso ya halarta suka amsa mashi da toh. Bayan tafiyar su, Abie Ya dauko ruwa Ya yayyafa ma wadanda suka suma, koda suka farfado cike da damuwa suke tambayar mafarki sukayi ko gaske ne abun da su ka gani? Abie ya faɗa masu abunda sojoji su ka ce, ya kuma ce suyi hakuri su rungumi kaddara, dan iya bai kyauta ma kanshi ba Ya ha'ince su Ya karya masu zuciya, bai ta6a zaton zai iya aikata rashin imanin na ba, ummi tana kuka tace Allah ya isa tsakaninta da shi, in sha Allah sai yaga sakayyar cin amanarsu da yayi da kuma abunda yayi ma Ana, anan har Ta labarta masu lokacin da take zuwa gyara masa badroom dinsa duk in taci karo da makudan kudi Sai yace mata bana shi bane, kudin Campaign ne da yan siyasa ke bashi, a karshe dayaga tacika sanya mashi ido saiya hana ta shiga dakin Kwata kwata, yace ta daina zuwar masa daki, a duk lokacin daya bukace ta zai shigo nata dakin, akan wannan maganar har fada sukayi batare da sanin kowa ba, kuma tun daya buga mata warning bata kara shiga dakinsa ba in bashi ya kirata ba, har yanzu abun yana ƙona mata rai amma bata taba faɗa ma kowa ba sai yau da Asirin shi ya tonu. Akalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, sunyi kuka tamkar ba gobe, Zahra da mahboob Har saida zazza6i ya lullu6e su bayin Allah, basu ji ba basu gani ba Ubansu Yaja masu. Sai da takaiga Mami da Abie ne suke lallashin su su kansu karfin haline kawai sukeyi saboda matsanancin halin da suke a ciki. Ahaka basu Ji komai ba, dan wannan introduction ne na abunda ya ke aikatawa. Kamar masu zaman makoki, haka sukai ta alhini, baci ba sha kamar masu azumi.. Batare da sanin su ba, baba mai gadi ya tattara yanashi yanashi ya gudu daga gidan, saboda tsoron kada laifin ubangidan sa Ya shafe shi. Wuraren Karfe ɗaya da rabi na rana, saiga Isod soldiers din sunzo gidan, gaba daya suka kewaye gidan bisa Umarnin Dg, sune zasu cigaba da gadin gidan har zuwa lokacin da zasu kama ɗan Iya🔥 ~_______________________________🌹~ Dr Jidenna Yana a zaune kan Kujerar Officers dinsa ya ɗaura Ƙafa daya kan ɗaya, as usual asanye yake da Ankara riga da wando, ya daura lapcoat fara akai, ga karkatacciyar hular nan tasa ta inyamurai daya kifawa kansa kamar kujera yar tsugunno, wuyansa yana a rataye da statescope, a tsanake Ya ke yin Operating Laptop dinsa dake akan desk din gaban shi, sanyin A.c na ratsa shi, Hankalin shi kwance bai da wata damuwa, yana aiki yana shan coffee din sa dake a cikin cup din gabansa. Wayarsa ce tayi ringing, saida ya mula ya sha iska tukunna yayi picking tare da karawa a kunnansa.. "Dr.adam ya akai? Ina aiki ka katse ni, ba nace nayi cancelling meeting din da zamuyi ba.." bai ƙare maganar ba, muryar dr. Adam ta katse shi"sir ba wannan ba, akwai matsala, Idan kana a office kayi gaggawar guduwa idan ba haka ba, ka mutu..." cikin rudu yace"bansan zancan banza Adam! In gudu sai kace wani 6arawo? Ka manta da wa kake magana? Md ne fa, ka duba layin da ka kira ko kayi mistake ne..." katse shi dr Adam yayi cikin rawar murya yace"kutmar Uban md din! don ubanka ka gudu nace! Asirin mu ya tonu, sun san komai, sun san cewa da sa hannunmu ake sadaukar da jariran su In har ka bari suka ritsa dakai ka mutu, Ni ma ganin nan zan gudu in bar ƙasar" Tuntsirewa yayi da dariya"bana son shirme da shiririta, yanzu ba lokacin yin tsokana bane" Dr adam yace"ba tsokanarka ka na keyi ba, dagaske nake maka, ka gudu yanzun nan ko ka kwana a ƙabarin ka" "Ka fahimce ni, rayuwar mu tana a cikin haɗari, yanzu haka da nakeyi maka magana, gidan dan iya, a kewaye ya ke da Sojoji ni ma kaina ya ɗaure na rasa gane tayaya akai hakan ta faru? Taya suka san komai..." "Bari na kira obinnan muji, Ni nasan labarin nan ba gaskiya bane, waya isa ma ya tona asirin dattijon arziƙi balle har a kama shi, bayan suke rike da kasar da iznin su ake komai..." katse kiran yayi ya dannawa Layin baba Obie kira, tana shiga ba'ayi picking ba, kira ya dinyi baya picking.. "Kai ko ka daga mana! Nasan a bakin ka ne zanji gaskiyar zance" Knocking Kofa Yaji daga waje, rai a6ace yace"pls bana bukatar ganin kowa, na ce na fasa meeting din.." bai kaiga ƙarasa maganar ba, suka bankaɗo kofar, da karfi, a zuciye ya dubi mai shigowa da niyar ya tsawatar ma su, A fadace yai pointing din su, da indext finger dinsa, cak ya tsaya kamar andasa mashi aya, ya shiga zare jajayen idanun shi kamar na mujiya, cikin shi ya duri ruwa duk yabi yasha jinin jikin shi.. Isod Agents ne suka shigo su huɗu sanye da black suits Ɗaya daga Cikin su ne Ya nuna masa Id Card dinsa"sunana Agent Jabeer Osman daga hukumar Isod, muna gayyatarka zuwa headquarter din mu, ka biyo mu mu tafi salin alin, batare da kayi kuskuren da zaisa wani ya gane meke faruwa ba, Idan kuma kace za ka yi mana gaddama..." bai ƙare maganar ba, ya ɗage masa gira tare da kai hannu ya shafa bindigar dake soke a qugunsa, tsantsar tsoro ne da tashin hankali akan fuskar dr jidenna, jikinsa ya kama kerma kamar mazari, zufa ta wanke goshinshi, sai faman sharceta yakeyi da yatsunsa, Agent Jabeer ya kara da cewa"bayan haka, Iyalinka suna a karkashin kulawar sojojin mu, kasan me zai biyu baya idan ka bijire ma na" Agent din dake a gefen Jabeer da hannu ya nuna masa kofa"this way please" cikin rawar jiki ya bi su suka sanya shi a tsakiyar su, gaba daya hospital staffs din babu wanda yasan meke faruwa, sun ga dai Md jidenna a tsakiyar bakinsa masu bakaken suit sai washe bakiyi yake yi suna fira, wasu daga cikin visitors har gaishe da shi su ke yi yana amsa masu dakyar dakyar. Shi ka ɗai yasan musibar da ya ke a ciki, marassa Ta cika da fitsari.. _______________________________🔥 Horn din Mota ne Ya karade kunnuwan mai gadin wani katafaren gida, mikewa yayi daga kan bencin da yake a zaune, cikin sauri ya karasa tare da zuge gate din gidan, ta shigo da motarta a parking space ta ajiye, da sauri mai gadin gidan Ya nufi motar, Ya buɗe mata Car door, fitowa tayi daga ciki, babbar macace jawur, daga ganinta inyamura ce yar gayu da ita, sanye da lace, tayi rolling mayafi akanta.. "Sannu da dawowa Hajiya, ya gajiyar aiki" sama sama ta amsa mashi, kafin ta nufi gidan, tun a falo ta fara cin karo da high heels ƙafa biyu, ga handbags saman sofa" Nan take ta fahimci tayi baƙi, Girgiza kai tayi cike da bakin ciki ta nufi bedroom din mijin nata, nishi da gurnani ta dinga jiyowa. Acikin kunnanta, ko knocking batayi ba, ta ture kofar ta shige, a kwance ta same su turmi da tabarya, shi daya mata biyu akan shi.. Wa'iyazubulla, kwata kwata basu san ta shigo ba, saboda sun fita hayyacin su, Ba yau ta saba kama shi da karuwai a cikin gidan su ba, idan ta ce zata tanka sai ya rufeta da fada hada bugu. Wannan karan batajin zata iya kyaleshi hakurinta ya kare, zuciyarta a wuya take, juyawa tayi cikin sauri ta nufi kitchen, jim kadan ta dawo hannunta ruke da bowl mai dauke da jajjagen attarugu, bayan ta shiga saida ta kulle kofar dakin, Ta yadda babu wanda zai iya fita, gadan gadan ta nufi gadon, ta daddage Ta watsa attagurin a gabansa da saman bakin shaidaniyar karuwarsa, ita ma dayar bata kyaleta ba, a cikin idanunta ta watsa mata sauran daya rage, Azabar zafin dayajine yasa shi mikewa daga zaune ya fara dura mata ashiriya, Karuwan nasa suna ta iface iface. Saukowa yayi daga kan gadon, Yana ta kakkabe gabansa, cikin bacin rai ya nufe ta, da gudu ta fuce yabi bayanta, ga radadi yanaji amma dayake zuciyarsa a bace take, yafi so ya fara azabtar da ita kamar yadda ya saba, fucewa tayi daga falon, Yana kokarim zura kan shi don ya fito, bai aune ba, Yaji An damƙi keyarsa"You"re Under arrest dr chisom" wani irin faduwar gaba yaji mai hade da razana, a rikice ya dubesu, Isod agents ne kewaye da shi, matar tasa tana a bayansu sai haki ta ke yi.. "Uban wanene Ya turoku ku kama ni? Laifin me na aikata? Kuna da hankali kuwa, ku shigo har gidana ku kama ni? Mai gadi da iznin ubanwa suka shigowa"? Balbalesu da masifa yayi, shi dama borin kunya da hauka ake naɗe shi. "Ba neman izni muka zo nema ba, umarnine daga dg, bamu bukatar 6ata lokaci.." babu ruwansu da tsiraicin shi, da yayi yunkurin yin fada da su don ya gudu aikuwa suka hadu su biyar suka nakaɗa masa dukan tsiya, fuskarsa tayi rudu rudu da shatun marukansu. Tasa ƙeyarshi sukayi, Matar tasa dayake wulakantawa, Ita ta taimaka mashi da mayafinta, ta daure mashi qugunshi saboda ta kare mashi mutuncin shi, ko tambayar jami'an laifin da yayi batayi ba, saboda tasan mijin nata criminal ne, kuma ita taimakonta su ka yi don tasan badan zuwansu ba, da wallahi har kasheta zai iyayi saboda bakar zuciyarsa, akan idonta suka tura shi cikin motarsu, sai da taga tafiyarsu, ta koma cikin falon, ta kulle kofar, a lokacin karuwan nasa sun fito daga dakin zir haihuwar uwarsu, akan floor suka zauna suna jiran ya dawo, sai jinyar wurin da ta zuba masu attaguri su ke yi. Zagayawa tayi cikin sanɗa ta nufi kitchen ta dauko tabaryar karfe, ta dira akansu kamar Allah ya aikota ta dinga jibgarsu kamar ta samu jakuna, duk saida ta raunata gabban jikinsu, suka dinga ihu suna kuka tare da yi mata magiya suna rokonta tayi masu rai, a karshe da suka ga bata da niyar kyalesu, da gudu suka fuce daga gidan tana ta kiransu don su kar6i suturar su ko waiwayon ta ba su yi ba. Lokacin da dr Adam Ya kira md Ya sanar da shi abun da ke faruwa, Yana a cikin Motarsa sai baza gudu ya ke yi zai tafi airport, don Ya gudu yabar ƙasar kafin su ritsa da shi, Yana driving zufa tana ta tsatstsafo ma shi saman fuskar shi, kwata kwata baida kwanciyar hankali, zullumi da fargaba sun cika zuciyar shi, Allah Allah ya ke yabar kasar. Yana karasowa Airport din Ya suri akwatinsa da jakarsa Ya nufi ciki sai sauri yakeyi, sai daya kammala duk wani clearance harya shiga Jirgi Ya zauna a seat dinsa, jirgin yana gab da zai tashi Unfortunately, Isod soldiers suka ritsa da shi a cikin jirgin, suka fito da shi sai mazurai yakeyi yana rawar jiki, hatta suitcase dinsa da Jakarsa saida aka fiddo mashi da su, wato ya yi gudun gara ya faɗa gidan zago... _______________________________🔥 *NATASHA* Yadda taga rana haka taga dare, Ta kasa runtsawa, damuwa da bakin ciki sun mata katutu a cikin zuciyar ta, a kan idonta ƙarfe 6 na suba tayi.. Tana tsaka da yin safa da marwa cikin dakin da Owais Ya kulleta, cikin kunci da bacin rai take jan tsoki tare da ƙwafa, ranta yakai makura agurin Baci, Ummi kawai takeso ta gani don taji meyasa taci amanarta? Meyasa zata matsa mata tazo Nigeria don a wulakanta rayuwarta? Tabbas bazata kyale ta ba, Alwashi ta daukarwa kanta saita Faɗawa big boss komai da su ka yi mata.. Kwatsam tajiyo motsin bude ƙofa, afusace ta nufi kofar, kafin ta karasa suka shigo su biyu, Ummi ce sanye da dogon hijab, Chief Owais yana abiye da bayanta bayan da ya shigo ya kulle ƙofar, kukan Kura Natasha tayi ta dira agaban Ummi ta shaƙe gaban hijabin ta... "Kin yaudare ni ummi, Meyasa zakiyi min haka? Meyasa? Dama kin kirani ne don inzo Nigeria a wulakanta rayuwa ta? Tun jiya nake a kulle kamar dabba?"? In a calm Voice Ummi tace"Natasha, Ki kwantar da hankalin ki, Kinsan wacece ni kin kuma san halina, ba canzawa wa nayi ba, Ba yaudararki nayi ba, kuma ban kiraki don a wulakanta ki ba...." bata kare maganar ba Natasha ta katse ta cikin fushi tace "Bazan taba yarda da ke ba Ummi, bayan haka ki sani bazan ƙyaleki ba, saina fadama big boss abunda kikayi min keda wannan mutumin..." ta faɗa tana nuna Owais da Yatsan ta.. Da sauri Ummi ta buge hannunta"karki kuskura ki ƙara nunasa da yatsa idan ba so kike ki rasa yatsanki ba, meke damunki ne? Ki nutsu ki saurare ni mana! Zan yi maki bayanin da zaki fahimce ni! Ni bazan cutar dake ba, ba kuma zan bari a cutar dake ba.." girgiza kai tayi"ba zan taba fahimtarki ba Ummi, na gama yarda dake..." "Kin fiye taurin kai Natasha, In har ba zaki saurareni ba zaki dawwama a kulle cikin dakin nan, ba zan iya taimakon ki ba ba"! Ta fada tare da duban Chief Owais"am really sorry da halin Natasha, tana da wuyar sha'ani ba kowa ke iya zama da ita ba sai wanda ya saba da ita..." jinjina mata kai yai"karki damu Ummi, na saba mu'amala da mutane masu taurin kai da kafiya irin ta, dama na kawo ta ne saboda kin damu da rashin ganin ta.." Natasha dake kallonsu sai rarraba kwartayen idanun ta ke yi akan su, cikin rudu da rashin fahimtar manufarsu akanta. "Ba zaku fadamin dalilin ku na kulle ni ba? Laifin me na aikata? Ko ina da alaka da ku ne? Idan big boss ne yayi maku laifi ni meye ruwana a ciki? Bani da akaka da shi! yarinya kuma da kake tuhuma ta akai na fada maka kudi ya biya don raine ta, kuma ni bansan yar wacece ba, bayan haka na fada maka ya kar6i abunsa! Meyasa kuke so ku haukata ni ne eyeeh? Ku barni in koma ƙasata! Idan ba haka ba zan tona maku asirin kunyi garkuwa dani idan na ku6uta daga tarkon ku, Idan kuma big boss Yaji ku kuka da kanku..." ta faɗa tana nuna su da yatsan ta. Basu saurareta ba, Suka fuce tana kokarin biyosu kofar ta datse. "Har yanzu baku tabbatar da abunda kuke zargi akan Big boss ba, ni nasan bai da sanya hannu, pls bana son tuhumar da kuke yi masa ya shafi Natasha, Ba ta da laifi, batason kowa a Nigeria ba, gashi har ta fara yi min kallon naci amanarta, Pls ka sassauta mata, Ku barta ta tafi koda ba zata zauna anan ba" "Kinsan meta aikata"? Aɗan ruɗe ta dube shi"Sir bangane me kake nufi ba? Ji ya tazo kasar nan, wani laifi ne tayi"? Atakaice Ya labarta mata abun daya faru jiya da daddare bayan ya ritsa ta a dakin su Unaisah. Dafe kai tay da hannu daya, Kunya da takaici Ya hana ta saka idanun ta Cikin na Owais.. Da tasan Natasha zata aikata abun kunyar nan da bata amsa bukatarshi na kiranta ba. "Am sorry sir, ban sani ba, bansan Natasha zatayi masu haka ba, da ban bari ba, ni banma san lokacin da ta fuce daga ɗaki na ba, na riga nayi bacci..." "Karki damu, Na fahimce ki, amma Natasha zata kasance a kulle cikin ɗakin nan, har zuwa lokacin da zamu kammala binciken mu a kanta, sannan bana son kowa ya san tana anan, daga ni saike, sai kuma chef din da zai din ga kawo mata abinci, ina fata bata fada ma musan game da zuwanta ba..." jinjina mashi kai tayi. "But pls, Ku kula da ita, abun da ta aikata ma Unaisah banji dadin shi ba, Tasa naji kunya wlh, amma ka yi hakuri, kasan dabi'ar turawa basu gudun abun kunya" Da sakin fuska yace"na sani, Nima cikinsu nataso, asalima kakata baturiyace amma ba irin natasha ba.." ya faɗa da zolaya duk don ya kwantar mata da hankali, murmushi ta yi ta ɗan ji sanyi aran ta.. ~_______________________________🌹🔥~ around karfe biyu na rana suka kammala shirin tafiya Airport, fitowa su kayi daga bedroom dinsu, yana sanye da suit ya lullu6e fuskarshi da mask, ya kuma saka shade baki a idanunsa. hannunsa daya ruke yake da suitcase dinsa, yayin da ɗayan hannunsa ke a ruke da passports din su. A falo ya tsaya yana jiran ta "Kiyi sauri mu tafi, kada lokaci ya ƙure mana.." tana daga ciki ta amsa mashi da toh.. gabansa sai faduwa ya ke yi rass rass, in har ba barin kasar nan yayi ba baida sauran kwanciyar hankali, Allah Allah yake ta fito su tafi.. Har ya bude baki zai kara yi mata magana, sai gata ta fito daga dakin, sanye da Black abaya, ta saka nikab kamar yadda Ya umarce ta da tayi, ko idanunta baka iya gani. "Pravin ni ban saba da nikab ba, bana jin dadin shi, duk a takure nake".. "Hakuri zakiyi mu tafi" A lokaci ji take kamar ta fasa ihu saboda damuwar rashin taimakon da Turai batayi mata ba, Yanzu tana ji tana gani zata tafi tabar Ahlin Obie, tun dazu da ya ke ta mata faɗan tayi sauri ta shirya tana sane ta tsaya yin nawa duk don saboda ta sanya rai zasu neme su. Pravin kwata kwata baisan ta yi waya ba, ta ki fada masa ne saboda tasan zai hana, kuma jiya turai ta ce karta faɗa masa. "Kawo na ruƙe maka trolley din" "A'a ke da baki da koshin lafiya" ya faɗa tare da sakin Suitcase din gefe, ya saka code din ƙofar bayan ta bude ya janyo trolley din, Tabiyo bayan shi suka nufi parking space. "Pravin kai baka jin kewar kasar nan"? "Ina ko kaɗan, Ni dama batai min, ba don naso ba nake zaune a cikin ta" "Matar ka da ya'yanka fa? Baka jin komai zaka tafi kabar su"? Banza yayi bai tanka mata ba. Buɗe backseat motar yayi yana kokarin tura a kwatin ciki ya tsinkayi muryar mutun a kunnansa. "Hijra zakuyi ne"? Wani irin faduwar gaba Yaji daram dararam, A firgice ya dago da idanunsa ya dubi mutumin da ke a zaune saman seat din motar, Ya daura kafarsa daya kan daya, fuskarsa a murtuƙa babu annuri. Kamar wanda yaga malakul maut ido da ido, gaba daya yabi ya rikice jikinshi yakama kerma bai san sa'adda ya saki suitcase din, Ya damko hannun Hajjaty da ke abayansa kwata kwata bata lura da komai ba saboda zurfin tunanin da ta shiga. Batai aune ba taji ya fusge ta, da gudu yajata suka nufi gate din din gidan arude take tambayar shi pravin meye faru? Menene ya tsoratar dakai? Ina kuma zamuje, bayan ga motar can mun barota Pravin? Kwata kwata bai saurareta ba, hankalinsa ba akwance ya ke ba, ya razana da ganin Sir mubarak, tayaya akai yasan inda suke kuma har ya buɗe gate din gidan ya shigo batare da sanin shi ba. Buɗe kofar jikin gate din yayi, zufa sai keto mashi takeyi akan goshinta. Yana zura kai bai aune ba Yaji safkar Naushi a saman kumatunsa nan take gefen bakin shi Ya fashe arude ya furta"na shiga Uku"! Gaban Hajjaty ne ya fadi ganin Prime minister Hateem, Ga canadian Polices da sojoji kewaye da gidan su. "Allahumma Ajirni fil musibati" damƙar kwalar rigarsa prime Minister yayi"dan iska, Kai ka janyo ma kanka musiba, Kana tunanin zaka gudu ta lamama kabar kasar nan? Bayan 6arnar da kayi mana"! "Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un..." cikin rawar murya hajjaty ta faɗa... Fitowa Sir mubarak yayi daga motar Pravin Ya nufe su, Yana karasowa ya damƙi keyar Pravin Ya fara sakar mashi naushi a tsakiyar cikin shi, idan ya jigba sai ya ingixa shi gurin hateem shima ya jibga kamar sun samu jaki saida suka haɗa mashi jini da majina akan fuskar shi, kwata kwata ya kasa ta6uka komai, sun shammace shi, hatta sihirinsa yaƙi tasihiri wanda hakan na nufin alkadarinsa ya karye. Hajjaty ta dinga kuka tana rokon su su daina bugun shi, kada su kashe mata dan uwanta, su kyale shi, ita su bugeta amadadin shi.. "Dan Allah ku kyaleshi yaya mubarak wlh mun tuba munbi Allah da manzon sa, mun gane kuskuren mu, ba zamu kara yi maku karya ba, zamu nisanta kanmu da ku..." cikin shesshekar murya take faɗa. A lokacin sun gama raunata kowace gaba ta jikin shi, ko tsayuwa bai iyayi, suna sakin shi Ya sulale kasa wanwar.. Zukunnawa tayi a gaban shi, tadinga kuka ranta ya 6aci da ganin irin bugun da sukayi mashi saboda karamin kuskuren da sukayi. Cikin fushi ta mike ta nufi sir mubarak, Ta damƙi kwalar rigarshi ta jijjiga shi tana fadin"ban ta6a sanin baku da imani ba sai yau, wai ku wasu irin mutanene? Na baku hakuri bakuji ba, Ko Allah muna masa laifi ya yafe mana balle ku da kuke yan adam" gaba daya ta rufe su da fada, ta inda take shiga bata nan take fita ba, fuskarta sharkaf da hawaye, Cheeks dinta sunyi ja, idanunta sai tsiyayar da kwalla suke. Gaba daya ta kashe masu baki, kallon ta kawai sukeyi batare da sun tanka mata ba "saboda kawai munyi kuskuren yi maku karya bamu fada maku da aure tsakanin mu ba? Indai ahlinku ne zamu rabu daku na har abada, amma karku kuskura ku kara bugun Pravin..." bata dire maganarba zuciya ta ɗibi Sir mubarak, ganin yadda ta ci kwalar rigarshi, aikuwa Ya kwasa mata marin daya razanar da ita, har saida tayi taga taga zata kife, ta dafe kuncinta, Idanunta suka juye fari fat.. Nan take suka lura da jinin dake gangarowa ta cikin jikinta yana bin kafafunta.. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." tana furta kalmar ta sulale zata faɗi, sir mubarak yai sauri tarota ta fado kan Chest din shi. shigowa Ciki Polices din su ka yi, suka kewaye su, biyu da ga cikinsu suka sanya handcuff a hannun pravin, yayin da sauran suka daure kafafun shi da igiya. Daukar shi sukayi tare da fuce wa da shi, Suka saka shi a cikin boot din motar Sir mubarak kamar yadda ya umarta. A saman kafadarshi ya sungumi hajjaty, prime minister yabi bayan shi suka fito daga gida bayan sun shiga cikin motocin su, a jere suka fuce daga arean (Finally Pravin Ya shiga hannu)~______________________________________🔥💔☠️💓~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___✍️~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168. *UMMIN AMERICA💋* Motar su tana karya kwana kan titi, wata dankareriyar Mota zungureriya baƙa mai black tunted ta nufo su gadan gadan tasha gaban su, cikin sauri officer din da ke driving din ta Ya taka burki ƙiiii!!! motar ta bada sauti tare da tsayawa. Ummi da ke a zaune cikin backseat na motar, kwata kwata babu alamun damuwa akan fuskarta, ta riga da tasan Big boss ne ya turo a ɗauke. "Kada ka damu, shine ya turo a dauke ni, zan tafi, idan zan dawo zan kira ka, nagode" ta faɗa yayin da ta ke ƙoƙarin Buɗe cardoor din. Agent din yace"baki da damuwa ma'am, Ki kula da kan ki" "Thanks" ta furta. Ƙarasa fitowa tayi daga cikin motar, ta tsaya tana ƙarewa dankareriyar Motar nan Kallo, babu alamun na cikin ta zai fito, kwata kwata ba'a iya ganin wanda ke a ciki. A cikin kunnanta tajiyo tashin motar officer din da ya sauke ta, kamar jira suke motar tabar titin Unexpected Cardoor na backseat din Motar ya soma sliding slowly har ya buɗe gaba ɗaya Da wata irin tafiya ta jan hankali da dattako Ummi ta nufi Motar, tana ƙarasawa gaban cardoor din ta ɗan russina tare da leƙa cikin ta, har saida ta lumshe idanunta saboda yadda shu'umin kamshin turaren sa da Sanyin A.c din motar suka ratsa hancin ta, A hankali ta buɗe idanun ta akan shi, Yana a zaune ya hakimce cikin backseat din motar, sanye da tailored suit, rabin fuskarsa a rufe ya ke da gold mask, sumar kan nan tashi ya yi wani ɗan iskan hair cut irin na tantiran da suka kai matakin masters atashanci. Ya ɗaura kafarsa ɗaya bisa daya, kamar wani basarake asaman karagarsa haka ya zauna, daga gefensa Console table ne mai dauke da Drinks, tsabar haduwar motar sai ka rantse da Allah dakin wani basaraken ne. Bai tanka mata ba, kamar baisan da zamanta ba, a hankali ta shiga daga ciki ta zauna, Cardoor din tayi locking, daga inda take ko drivern da ke driving dinsu bata iya gani saboda curtain din daya shiga tsakanin backseat da front seat na motar, kamar yadda ya share ta haka itama ta share shi, jira take ya sauke girman kan shi da izzar tukunnna sai suyi magana.. Kasa jurewa yayi saboda kasalar da kamshin turaren ta ya haifar ma shi, satar kallon ta yayi ta wutsiyar idanun shi, tun daga kan head scarf da tayi rolling har zuwa wuyanta dake sanye da ziririyar sarƙa, mayar da idanun sa yayi kan kirjin ta wani mayataccen kallo yabisu da shi kamar zai kai mata hari, fitted gown din da ta sanya kamar a jikinta aka dinka ta saboda yadda tayi tighting inta ta fito da shape din jikin ta, sauke idanunsa yayi akan dirarran Qugunta daya cika fam kamar zai daɗe. Ya dan jima yana ƙare mata kallo kafin ya kawar da idanunsa gefe ɗaya, kwata kwata bata nuna tasan yana kallon ta ba, da gangan ta yi banza da shi, wayar ta ta curo daga cikin Purse ta Soma dannata a hankali.. Komai nata da yanga takeyin shi wanda hakan ba karamin jan hankalin shi ya ke yi ba. Ya daɗe yana tunanin meyasa baya gaji da ita? yana sonta fiye da kowace mace a duniyar nan, baya jin zai iya rabuwa da ita, shiyasa yake takaicin gaza mallakarta da baiyi, duk da a yanzun ma yana samun abunda ya ke so agurinta hakan bai ishe shi ba, yafi so ta zama mallakinsa, matarsa, uwar ya'yansa, sai dai kash ta nan Allah ya rage shi da ita, yasha fada mata in har bai aureta ba, babu wani mahalukin da ya isa ya aure ta, sai dai ta mutu ba aure, bazai ta6a barin wani ya mallake ta ba, in ba shi ba. A hankali hamshakiyar Motar ta kunno kai Cikin wani katafaren Gate na wani tanƙameman Villa, Aljannar duniya, me karfin imani ne kadai zai iya rayuwa acikin sa batare daya shagala da yin ibada ba, saboda an zuba kayan alatu, an kuma yi almubazzarancin dukiya gurin ƙera ginin, ga wasu Giant Security Officers dake sintiri sanye cikin kakin su mai kama da na Jami'an Isod. Har Motar tasu tayi parking daga gefen Entry Hall bata juyo ta dube shi ba, A hankali Cardoors din motar suka zamiye, ta fito daga ciki, ta ɗan tsaya tana gyaggyara veil din ta, gently ya fito daga motar ya zagayo ta bayanta ya dan jingina bayansa jikin motar ya harɗe hannayensa akan kirjinsa.. "Jira kike inyi maki magana"? Sai da ta mula ta sha iska, ta juya ta dube shi tare da ɗage gira tace"gashi kuma kayi min maganar, saboda ka damu dani, ka gaza jure ƙishin dake damun ka" tana ƙarashe magabar, ta juya ta nufi katafaren main door din falo. smirking yayi tare da bin bayanta yana kallon yadda take tafiya butt dinta na jujjuyawa aransa ya furta _"ita kaɗai ce macen da zata iya juya ni son ranta..."_ tana isowa bakin Kofar, ta daura babban yatsanta akan finger print din kofar, bayan computer tayi scanning dinta nan take kofar ta bude, tana shiga ciki, ta tsinkayi Ai assistant's voice a cikin kunnanta _"welcome Ummi, the lights, and temperature have been adjusted for your comfort"_ Murmushi tayi da alama taji dadin hakan sosai, komai na furniture din falon masu kyau da tsadane, a hankali ta nufi cikin falon tana tafiya sautin takunta Yana fita kwas kwas. Tsayawa tayi daga tsaye tana bin ko'ina da kallo da alama Falon Ya burgeta. batai aune ba taji ya damƙi hips dinta da faffadan tafin hannun sa, sai taji wani iri kamar bataji dadi. kwanto da kansa yayi saman wuyanta cikin wani irin salo na jan hankali ya dinga goga tsinin hancinsa akan wuyanta tana jin hucin numfashinsa, da sauri da sauri yake fita kamar zai rasa ransa sai faman kara narke mata ya ke yi, ta fahimci jarabarsa ce ta fara motsawa. tana a tsaye tana jin duk wani motsinsa a jikinta, bata san ya akai ta daina jin sha'awar son kasancewa da shi ba, gangar jikinta ce kadai a tare da shi amma ruhinta yana atare da ya shureim. duk ta6awar da big boss zaiyi mata sai ta dinga jin kamar shureim ne, shiyasa har ta ɗan saki jiki tabar shi saboda yanayin shaukin da ta shiga, bakomai take tunanowa ba face lokaci na farko da ta fara kasancewa da ya shureim dinta, duk da radadin da taji hakan bai hanata jin ni'imar dake a tare da shi ba, har yau bata samu namijin da ya yi satisfying din ta kamar yayi ba. yana kokarin 6alle zip din rigarta, kwatsam brain dinta ta soma tariyo mata maganganun da suka tattauna da Chief Owais, lokaci ɗaya ta yi saurin buge hannayen big boss daga jikin ta, ta ja baya tana haki tare da juyowa ta fuskance shi. walwalar fuskarsa ce ta ɗauke ɗuff, rudani ya bayyana akan fuskarsa. "Meke damunki ne? gaba daya kin canza min Ummi, ba haka kika saba min ba, kina ji ina ta6aki amma baki wani nuna kinji dadin abunda nake maki ba, yanzu kuma kin buge hannayena kamar wani mugun abu ya taba ki why"? Ya faɗa cikin bacin rai. tunawa da gargadin da Chief yayi mata ne yasa tayi saurin shiga tai tayinta, shafa cikinta tayi da tafin hannunta tare da yamutsa fuska tace"yunwa nake ji, banci komai ba na tafo saboda zumudin naganka, nafi so mu ci atare..." ta faɗa tare da matsawa kusa da shi ta ɗaura hannayenta saman shoulders dinsa. Lumshe idanun shi yayi, hancinsa na shaƙar mashi shu'umin turarenta, gaba dayansa acikin shauƙinta ya ke, "Get lunch ready for my babe, within minutes" ya furta yana kallon ta, daga inda yake bai motsa ba, bai kuma kira kowa ba yayi maganar, da ya ke computer ce ke isar da sakon. Tallabo waist dinta yayi da tafin hannuna suka nufi Dining, tunkan su karasa ta hango kitchen staff sanye da uniform dinsu sun kewaye katafaren Dining table din da suke jera kayan abinci akan shi, suna ƙarasowa chefs din suka gaishe da ita with respect, kafin suka juya tare da barin gurin. Har zata zauna sai kuma ta fasa tunawa da ba haka suka saba cin abinci ba, zai iya zargin wani abu idan ta canza mashi. Zagayawa tayi ta gefen da yake a zaune ta shafo shoulder din shi da ziraran yatsunta kafin slowly ta zauna saman laps dinsa, har wani lumshe idanun shi ya ke yi kwantar da kanta tayi saman shoulder dinshi cikin kashe murya ta furta"babe ka bani abaki naci.." ta fada tare da tallabo keyarsa ta shafa ta a hankali tana dan liliyata har iyazuwa sumar kan shi, daurewa kawai yakeyi amma gaba daya ummi ta tayar masa da jarabarsa, tasan duk wani salo da zata gigita gogan nata. Abaki ya fara ciyar da ita, cikin abinci kala shida da aka jera mata abu ɗaya taci ta dan sha juice kadan, ta dauki spoon da niyar ta bashi baki yai sauri damƙar hannun ta duban shi tayi"ba zaka ci ba"? "Yunwar da nake ji abinci bazai iya gamsar dani ba ummi.. " ya faɗa tare da tallabe butt dinta da hannayensa Ya miƙe ɗauke da ita, duk nauyin jikin Ummi baya jin shi, bedroom dinsa ya nufa da ita gabanta sai faɗuwa ya ke yi, batasan ya zatayi ba, wallahi bata so wani abu ya kara shiga tsakaninta da Uncle Musa, saboda tana jin tsoran zargin da su Chief su ke yi akan shi ya zamana gaskiya, da kuwa ya kashe ta da bakin ciki, wannan karon ba zata bari ya kusance ta ba, dole ta nema ma kanta mafita aranta take ta yin tufka da warwara. Wani katafaren bedroom ya shiga da ita, alkalamina bazai iya misalta haduwar shi ba, agaban hamshakin gadonsa Ya jefar da ummi ta lumbutse cikin lallausar bedmattress din, har saida headscarf din ta ya warware, gyaran gashin kanta ya bayyana. numfashi taja tare da dagowa tana kallon shi yayin da yake a tsaye gaban gadon yana tu6e suit jacket dinsa. Jefar da kayan jikin sa yayi, ya rage saura short, kamar mayunwacin zaki ya fada kan gadon, for the first time da ta fara jin shakkar Uncle Musa, Yana matsowa tana ja da baya, har saida suka ƙurewa gadon yadda kasan muzuru ya kama 6eta, ta zazzare idanunta cikin tsoro. Muryarsa tamkar ta wanda ya sha giya ya furta"ummi, tsoro na kike ji? Meyasa kike ja da baya kamar kinga dodo..." murmushin yaƙe tayi"ba abun da ka ke tunani bane, ka yi hakuri bana son na bata maka rai shiyasa ban faɗa maka ba, amma bazan iya kwanciya dakai ba.." ta faɗa idanunta a cikin na shi, still bai cire gold mask din shi ba. "Meyasa"? "Sorry, I'm having my cycle" ta fada cike da fargaban kar yaƙi yarda. 6acin rai ne ya bayyana acikin idanunsa, ya tsani yaji tana period saboda baya samun abun da ya ke so a gurin ta. "Ummi meyasa baki fadamin ba tun kafin kizo? Sai da kika tada min jaraba na sannan zaki fadamin labarin nan mara dadin ji"? In a weak voice ya fada.. "Am sorry big boss, nima bada son raina ba, ban san ya akai date din da yake zuwa min ya sauyawa ba, sai da na shiga toilet zanyi wanka kwatsam naga jinin...." ta fada tana marairai ce masa fuska. "Kuma kaga yau ne kaɗai na samu damar da zanzo.. " sanyayyar muryarta nema take ta zautar da kunnuwansa da dadinta.. "Ummi akwai hanyoyi da zaki iya gamsar dani, ba dole saina shige ki ba, bazan iya hakura ba..." zare idanunta tayi tana Ƙyafƙyaftasu akan fuskarsa. ya kashe mata ido tare da ɗage girarsa daya. yana kokarin kai hannu don ya damƙe ta ta yi sauri kubce mashi ta sauko daga kan gadon, arude yabita da kallo da alama ya fara ɗago ta.. "Giya nake so na sha" da mamaki yace"yaushe kika fara shan giya" ya fada tare da kishingiɗe kansa saman pillow. "Yau zan fara, saboda inaso na bugu na manta kaina" wata yar iskar dariya ya saki tare da saukowa daga kan gadon ya nufi wine cabinet din dakinsa Ya dauko bottle ɗaya tare da cup daya, ya dawo gaban gadon Ya zauna tare da tsiyaya mata a cup ya miƙa mata yana faɗin "ki komo kan gadon ki zauna kada ki faɗi" komawa tayi gefen gadon ta zauna har zata kai baki ta dan dakata tare da kallon shi ya tsareta da idanunshi da suka kada jawur tarasa gane kallon menene ya ke yi mata . "Kai ba zaka sha ba.." girgiza mata kai yayi"no, ke dai ki sha.." maƙe kafada tayi"in har ba zaka sha ba, nima bazan sha ba" smirking yayi tare da kai kwalbar abakinsa Ya soma ɗaɗɗakarta har saida ya shanye giyar duka. sannan ya janye kwallar daga kan bakinsa ya daura ta kan bedside drawer, girgiza kanshi yayi yana faman jan numfashi, da alama giyar ta fara bugar da shi, idanunsa na kokarin lumshewa ya dube ta"ki sha" kaiwa tayi saitin bakin ta, ta kur6a batare data hadiyeta ba, batai aune ba taji ya janyota jikin shi ba arziƙi ta saki cup din hannun ta. hugging dinta yayi ya soma undressing din ta, tana ta kokarin kubce mashi takasa saboda karfin daya sa mata, sai da rage daga ita sai pant da bra, sannan ya ƙyaleta, ya janyo duvet cikin maye ya rufa musu, ya zuro hannunsa daga cikin dubet din ya danna wani button jikin gadonsa nan take duhu ya mamaye dakin, romancing dinta ya farayi kamar zai haukatar da ita, short dinsa daya cire ya cillo shi wajen bargon. gurnanin shi da nishin shi ya cika dakin kamar zai fasa dodon kunnanta, kamar zata fasa ihu saboda kyama da kyankyamin daya kamata tarasa ya akai bata jin dadin hada jikinta da nashi ba kamar da ba, komai da yakeyi mata baya mata dadi yanzu, ta bashi giya don ta gusar mashi da hankalin shi, amma kamar giyar bata aiki akan shi, kokari ya ke ya shige ta, data turje ya yi forcing dinta akan tayi ma shi abun dayake so, duk fa yana a cikin mayen na shi, addu'oi ta dinga karantowa acikin zuciyarta tana rokon Allah yasa bacci ya dauke shi, cikin sa'a giyar dayasha ta ƙarasa bugar da shi, ya dinga sambatu na batsa marasa dadin ji har saida bacci yayi awon gaba da shi. Kasa mikewa tayi saboda ya matseta a kirjin shi, motsi kadan idan tayi zai iya farkawa in har ba baccin nasa yayi nisa ba, hakan yasa ta jinkirta tashin nata, har batasan sa'adda bacci yayi awon gaba da ita ba ~________HeartBeat🫀Destiny💫____~ A hankali ta fito daga toilet jikin ta sanye da bathrobe ga dukkan alamu wanka tayi duba da danshin ruwan dake a jikin ta, unexpected ta tsinkayi shesshekar kukan Unaisah a cikin kunnanta, gabantane Ya faɗi, da sauri ta nufi couch din da take a kwance ta kudundune jikin ta cikin bargo sai kerma ta ke yi.. "Ukhty! sisterna! Meke damunki ne? meyasa kike ku ka um? Ta faɗa cikin nuna kulawa tare da zama gefen ta.. Shiru tayi bata tanka mata ba, bubbuga kafadarta Batool tayi"kina jina kinyi shiru ba zaki fada min abun da ke damun ki ba"? Cikin shesshekar Kuka tace"dan Allah ki rabu dani inji da abun da ke damuna"! "Unaisah, please Ki fadamin zan taimaka maki mu nemi mafita". Wannan karan da tsawa ta furta"nace ki rabu dani! Ko da na fada maki babu abun da zaki iyayi min"! mikewa ta yi sukuku ta juya ta nufi toilet harta kusa isa ta dan dakata"bansan meyasa kike yi min haka ba, kawai daga tambaya sai ki rufeni da faɗa hada tsawa"? Ta faɗa cikin 6acin rai cos taji haushin tsawar da Unaisah ta yi mata. "Kawai saboda na nuna damuwa akanki? Batun yau kike min haka ba, duk in zanganki awani hali na tambayeki meke damunki baki faɗamin! Na sha farkawa tsakar dare in ganki kan darduma kina kuka, amma baki ta6a fadamin abunda ke damun ki ba why? Me kika ɗauke ni ne?wani sa'in kamar kina min kallon mara wayau, saboda bani da ilmi yasa kika raina ni Unaisah, Nafa girmeki, shekara biyu da watanni na baki! Ni ba tsararki bace! yakamata kina girmamani amma meyasa ki ke min haka"? Ta ƙarashe maganar tare da juyowa ta dubeta da idanunta wadanda suka cuko da kwalla.. Unaisah data yaye bargonta fuskarta sha6a sha6a da hawaye, Kasa furta kalma tayi saboda bata tsammaci Batool zata iya mayar mata da martani ba, ashe abun na damunta, amma saboda tana da hakuri yasa ta ke dannewa ayanzu kuma taji bazata iya ba. "Baki ɗauke ni kamar yadda na dauke ki ba, na tabbata da ace ina da ilmi ba zaki ta6a yi min haka ba, a tunanina damuwarki tawa ce! Babu sirri a tsakanin mu" jikinta ne yayi sanyi lakwas, duk sai taji ba dadi saboda maganar da Batool ta faɗa gaskiya ne. "Na tsani in tambaye ki meke damunki ki ce min baki sani ba, ko ki nemi raina min hankali, sometimes kin kwammace kiyi shawara da aunty ummi akan ki yi dani, ni kuma burina kullum in fi kowa kusanci dake, in fada maki damuwata, in nemi shawararki, amma ke ba haka ba.." juyawa tayi da gudu ta shige toilet taja kofa ta datse, bata ta6a ganin Batool a hali na 6acin rai irin na yau ba, kamar mai aljanu. Saukowa tayi daga kan kujerar ta nufi Toilet door tare da yin knocking, tana jiyo shesshekar kukan ta"Batool ki yi hakuri bansan abun yana bata maki rai ba, bansan nayi maki badaidai ba sai da kika fada min, tabbas nayi kuskure amma inaso ki sani wallahi ba abunda kike tunani bane, kada ki bari shaidan da zuciya su shiga tsakanin mu, Batool ban raina ki ba, wallahi bana maki kallon mara ilmi, ni da nake kokarin inga kun samu ilmi kun waye Batool? Ni ce fa Unaisah me son cigaban ku da farin cikin ku.."? Dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya su6uce mata, abun ya ta6a ta, abun ka ga mai zuciya. "Meyasa kike tunanin haka Batool? Kin bata mun raina, meyasa zaki bar abu yana cinki a zuciya baki sanar dani ba? Kin ƙullace ni aranki, ba halinki bane Batool, kamar yadda kike burin ki fi kowa kusanci da ni nima haka nake buri Batool, inasonki fiye da sauran yan uwan mu, saboda halaccin da kikayi min arayuwa bazan ta6a mantawa ba, dan Allah ki buɗe mun kofa, inason yin magana dake, zan fada maki abun da kikeson ji sannan ki daina kuka bana jin dadi." ta faɗa cikin shesshekar Kuka, Kamar marasa galihu sun dage sai kuka su ke yi. "Ba zaki fito ba? Kuma ki daina kuka acikin toilet babu kyau" "Ki ƙyaleni, bazan fito ba, saboda kona fito babu amfanin da zanyi maki" bubbuga kofar Tayi kamar zata balle ta tace"ki daina wannan maganar Batool bana son ji"! "Naje nayi ay gaskiya na fada.." ji take kamar ba Batool dinta ba, ta burkice mata lokaci ɗaya.. "Ki yi mun ko wani irin hukunci zakiyi min in har hakan zaisa ki huce, Ko ki fada min me zanyi in gyara kuskure na"? Ta fada tare da jogana kunnanta jikin kofar.. Sai da ta mula ta sha iska tukunna tace"kin makaro Unaisah, sai da na fada sannan zaki gyara? Hmmm, kawai ki rabu da ni, ko ganinki bana son yi" "Bazan iya rabuwa dake ba, bana jin dadin maganarki, Batool jinki nake kamar twin sister dina.." "Daɗin bakin ki bazaisa in hakura ba" murmushi Unaisah tayi still da hawaye akan fuskarta"ba daɗin baki nake maki ba, wallahi dagaske nake maki my heartbeat, Ki fito in nuna maki irin kaunar da nake maki" banza tayi da ita, tunani ta shiga yi meya kamata tayi don ta shawo kanta? da sauri ta nufi wadrobe Shelves inda ta ajiye sauran kayan da suka siyo a shopping mall, Batool ta dade tana kwakwar ta bata wayar nan taki bata a lokacin saboda ta raba gaddama tsakaninta da sajeed da shima ya kwallafa rai akan wayar, sai yau da take son faranta mata. Phone box din ta ruke a hannunta ta dawo bakin toilet door din"Ukhty na, come and see something special" banza tayi da ita, magiya ta dinga yi mata amma tayi shiru, still batayi fushi ba, saboda ta fahimci halin da yar uwar tata take a ciki, tasan Batool tana da hakuri baiwar Allah. a lokacin Batool tana a zukunne gaban kofar toilet din ta ciki ta jingina bayanta, kunnuwanta suka jiyo mata sautin wakar da Unaisah ta ke raira mata daga cikin dakin. _Ƙawata kina jina? In har kika barni sai na sha wuya_ _Sai na zam tamkar tsokar da babu jijiya_ _In ba dake ba sai dai rijiya_ _Rijiyar ma mai dauke da ƙugiya_ _Wacce zata caki rai na, ban kara kwana_ _Mai zai sa in kwana? Ban gano masoyiya ba_ _Kece aljannata duniya ta_ _Masoyiya ta, aminiya ta_ yayin da take sauraron wakar batasan sa'adda murmushi ya su6uce mata ba, wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta, kamar ana wanke mata damuwarta. "Please idan kinji dadin wakar da nayi maki, Ki fito mu fuskanci juna, Inason na ganki, wallahi har nayi missing ɗinki Batool dina, pls ki fito zan baki kyauta ta musamman, da zata faranta ranki" shiru tayi bata tanka mata ba, kamar zata saka ihu, Bubbuga kafafunta tayi"wai me kikeso nayi maki ne wanda zaisa ki yafe min" _"Ki ɗauke ni kamar yadda na ɗauke ki, shi kaɗai ne zai sa ni farin ciki"_ ta fada a cikin ran ta "Ina ta maki magiya ki fito amma kin ƙiya, ai ko Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu yan adam, Kada Allah yasa ki yafe kinji ko, Ki ta zama a cikin toilet, madaddalar shaiɗanu.." still bata tanka mata ba, yamitsa fuska tayi tare da hararar kofar toilet din, dabara ce ta fado mata, da gudu ta fuce daga dakin tana fadin"oyoyo Aunty Ummi, welcome back home, we really missed you, Muna ta jira ki dawo har munyi fushi.." A zabure Batool ta mike jikinta na 6ari ta bude toilet door din, ta watso a guje ta nufi kofar tana lekowa taga wayam babu kowa nan take ta gane set up din Unaisah ne don ta fito, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke duff, kamar bata taba dariya ba, tana niyar ta fucewa daga dakin harta daga kafa Unexpected taji an damƙi wuyan kafarta, atsorace ta zare idanun ta tare da kallon ta, ajiyar zuciya ta dauke ganin Unaisah.. "Am sorry Aunty Batool, Kaina bisa wuyana, na tuba bazan ƙara ba, bansan ki da fushi ba, pls, ki tausayawa yar kanwarki Unaisah, Zan gyara kuskurena, nasan bana jin magana amma ki min uziri hada yarinta ke damuna.." ta karasa maganar tare da kama kunnuwanta. Batool dake kallon ta, kiris ya rage ta fashe da dariya, saboda ta bata nishadi musamman da ta kama kunnuwanta kamar zomanya, ta wani marairaice mata fuska. "Bai kamata ki biyemin ba, kiyi fushi dani, kefa babba ce ni kuma ƙanwarki, idan nayi badai dai ba, nasiha yakamata kiyi min sai in gyara bawai kiyi fushi dani ba.." idanunta cike tab da kwalla tayi maganar, ita kanta batool din wasu hawayen ne suka cika idanunta, ta rasa gane meyasa take jin Unaisah fiye da sauran yan uwanta da ta fara sani kafin ita. Bazata iya jure fushi da ita ba, A hankali ta cire hannu ta miƙa mata, Jikin ta har kerma yakeyi gurin Zura hannunta a cikin na Batool, ta janyo ta, ta mike tsaye suka yi hugging din juna. Lallashin juna sukayi tare da ba juna hakurin sabanin da suka samu. "Zan fada maki abun ki ke son ji, daga yanzu babu boye boye atsakanina da ke, sirrina naki ne.." ta faɗa yayin da suke raba jikinsu daga juna, cheeks dinsu sunyi ja saboda kukan da suka sha. Ruko hannun Batool tayi suka zauna kan tattausan rug din dakinsu suna fuskantar juna, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin kunyar Batool, tayi mata ƙwarjini ko dan yau tayi gaba da gaba da ita. Lumshe idanunta tayi a hankali In a cool voice tace"a duk lokacin da kika ganni ina kuka, to na tuna da shi ne, wallahi shine silar halin da nake shiga! nayi iyakar ƙoƙarina dan ganin na daina tunaninsa sai dai nakasa, Ya mutu amma babu abun daya sauya na daga son da nake masa"! Nan ta ke Batool ta gane wa take nufi. "akwai wasu kalmomi daya furta min kafin su tafi kai farmaki sun tsaya min araina! da su nake kwana da su nake ta shi araina, nayi nayi in cire gur6ataccen tunaninsa da nake yi amma nakasa, zuciyata takasa mantawa da cewa shi fa yanzu mamaci ne ba rayayye ba, meyasa take tsananta min akan shi.." wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta.. Ruko hannayenta Batool tayi a cikin nata, wani irin tausayin ta ne ya mamaye zuciyarta, tayi zaton Unaisah ta daina son shi tun da baya araye ashe har yanzu da son shi sosai a cikin zuciyarta. shiru tayi tana tariyo kalaman daya faɗa mata a cikin brain dinta, a ranar da zasu tafi kai farmaki lokacin daya yi mata raɗa a cikin kunnanta.. _Unaisaah, my desire for you burns fiercely,Taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_ _I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_ _When I return, grant me my heart's desire, Unaisah. Fulfill my wish, And let's create a memory that will last a lifetime_ kifa kanta tayi saman kafaɗar Batool, cikin karyayyar murya ta furta"a lokacin daya furta mun kalaman nan, duk da bakomai na fahimta ba, amma naji wani bakon abu da ban ta6a jin shi ba a tare da ni..." ta fada tana jan numfashi, gaba daya tausayinta ya kama Batool _"Daga baya, na zauna nayita yin nazari akan kalamansa, na yi bincike ta hanyar wayana akan abun da ban fahimta ba, har saida na gano komai dayake nufi, i was shocked, Danish da baisan komai ba, tayaya ya samu ilmi kan abun da ni bansani ba, ko Aunty ummi bakomai take fayyace mana ba, saboda tana jin kunyar mu. shafa bayanta Batool tayi da tafin ta"mutuwa tayi min yankan kauna, naso ace na cika mashi burin shi akaina, sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ina daurewa ne idan kewarshi ta addabe ni, bana bari kowa ya sani, saboda abu biyu, bana so na fama ciwon Zuciyata saboda inason na rayu ko dan na ga ƙarshen Elders, sannan bana so in ɗaga hankalin ku, gaba daya na hana kaina kallon hotunansa da vidoes din da nayi masa wasu ma batare da sanin shi ba, saboda yanayin da nake shiga idan ina kallon su, da ace idan na bishi zamu rayu a kabari daya ne da ba abun da zai hana in roki Allah ya dauki raina nima, amma bana fatan hakan saboda a duk lokacin da na farka yin nafilfili nayi masa addu'a inajin wani dadi a cikin zuciyata"_ Lallashinta Batool ta cigaba da yi gwanin ban tausayi, a yanzu ta fahimci wasu abubuwan tanayi ne saboda ta kawar da damuwar rashin Danish. "Yanzu da na faɗa maki sirrina sai naji kamar an yaye min damuwana, musamman da kika kwantar min da hankali, pls amana ne atsakanin mu, daga ni sai ke, kema idan akwai abunda ke damunki ki fada min.." murmushi suka sakar ma Juna. "Kada ki damu, zan fada maki nima, amma ayanzu bani da wani sirri daya wuce in taimaka maki gurin ganin mun shawo kan matsalar da ke damun ki" ta fada tana shafa sumar kan ta. sun jima suna tattaunawa, fira tayi dadi, har saida cook yayi knocking Ya sanar da su su fito su ci lunch din su tukunna suka tsagaita. Phone box din ta dauko ta mika ma Batool, Wani uban tsallan farin ciki ta daka, hada yin sujudusshukr saboda dadin da taji, hakan ba karamin nishadi ya ba Unaisah ba, ganin ta sanyata farin ciki. "Ki yi hakuri tuntuni Yakamata in baki ita, sai dai banyi hakan ba saboda Sajeed ya nuna yanaso yanzu da baya nan gayanan na baki, kiyi ma daddy magana ya siya maki sim" tana faman washe baki tace thank you sis, you're special, kin faranta min rai atare suka buɗe kwalin wayar, sabuwa gal da ita ƙirar Samsung galaxy, "Nasan yau dakyar zaki Iya runtsawa" tana dariya tace "kamar kin sani" "Kije ki sanya kaya, zan jira ki" Ta fada tare da ruke mata wayar, da sauri ta nufi closet dinsu, shaf shaf ta zura gown a jikinta, ta dawo. "muje muyi lunch daga nan sai mu kira yan uwan mu mu gaisa da su ko" "Yeah" da farin ciki suka fito daga dakin. A dining room suka taras da Cooks dake jera masu kayan lunch din su, bayan sun zauna kan kujera suna fuskantar Juna, a tsanake suka soma cin abincin su. "Har yanzu shiru, aunty Ummi bata dawo ba, gidan duk ba dadi, babu Aunty Ummi, Chief tun safe bai dawo ba, daddy ma ya fita anguwa, sai mu kadai, nayi kewar su" Batool ce ta fada yayin da take tura Steak kebab abakinta tana taunawa. "Idan muka kammala Cin abincin zan sake jaraba kiran su, Inji yaushe zasu dawo gida" Unaisah ce ta faɗa tana tsoma hannunta cikin plate din gabanta dake a shake da farfesun ganda mai zafi da tafshi, daukowa tayi tare da turawa abaki tana taunar gandar. "Kwanakin baya kin yi min alkwarin zaki bani labarin aunty Ummi, har yanzu ban manta ba, Inaso naji..." dakatawa tayi da sharbar farfesun ta danyi shiru tana yanke shawara da zuciyarta, Chief ya hana ta fada amma kafin ya gargaɗeta akan kada ta faɗa ta riga tayi wa Batool alƙawarin zata bata labari, kuma tasan in har bata fada mata ba, zataji ba dadi. Dagowa tayi suka hada ido cikin na juna, ta kura mata idanun ta.. "Ki bari mu gama cin abincin mana" Girgiza kai tayi"haka kullin kike kawo uzirin da zaisa ki manta, kawai ki fada min a yanzu.." Saboda gudun 6acin ranta yasa tace "Okay, zan fada maki amma pls, amana, daga ni sai ke my sis" murmushi Batool ta saki taji dadin maganarta.. "In sha Allah.." a tsanake Unaisah ta fara labarta mata tiryan tiryan kamar yadda ta saurara a audio din da Chief ya kunna mata. tunkan takai karashen labarin Idanun Batool suka cicciko tab da ƙwalla cikin sanyin murya tace"sai yanzu na gane meyasa aunty ummi kuka rannan, nayi zaton ni Batool din take fadin ta rasa na mutu ashe bani bace, sunan babynta ce data rasu, na tausayawa aunty Ummi da uncle Shureim, labarinsu ya taba zuciya ta, ashe sheikh Imam ne mahaifinta amma meyasa ya yanke mata hukunci cikin fushi? Ta faɗa fuskarta babu walwala.. "ko dai ni da bani da ilmi bazan iya aikata abun daya aikata ba, abun daya faru tsakanin Aunty Ummi da Uncle shureim sharrin shaiɗanne, bayin kansu bane, duk da ba agabana komai ya faru ba, amma ni ina kyautata masu zato, kuma duk wata kaddara da ta faru da bawa, da akwai wata hikma ta ubangiji wanda mu ba zamu iya gani ba, kamar yadda bamu taba sanin ta arayuwar mu ba sai gashi silar taimakon mu da sojojin America su ka yi mun hadu da ita, kuma mune silar da ta dawo Nigeria harta sake haduwa da mahaifinta, da aminnanta, da kuma ya shureim.." muryarta na rawa ta karashe maganar, Unaisah tace"kinyi magana mai ma'ana, pls ki share hawayenki, nasan labarin akwai taba zuciya, amma ni ban fada maki donna sanyaki a damuwa ba, tsakanin mu da su aunty Ummi da babynta Addu'a ne da ita kadai zamu iya taimaka masu..." ta fada tana kur6ur juice da ta zuba a cup. "Chief yayi alkawarin zai sasanta tsakaninta da kawayenta, da kuma Mahaifinta, in sha Allah.." ta karashe maganar tare da zaro tissue cikin box ta mika mata, yatsun hannayenta na kerma ta kar6a tana share hawayen ta, Unaisah dake satar kallonta, batai mamakin ganin yadda jikinta ke kerma ba saboda tasan irin kaunar da take ma aunty ummi, dole labarinta ya karya zuciyarta, shiyasa ba komai ta sanar da ita ba, ta boye mata batun Uncle musa da kuma binne jinjirar da Uncle shureim ya yi. "Inama ace babyn aunty Ummi tana araye, da yanzu muna a tare da ita, Ni dai na kamu da son ta, Inason aunty ummi da ya shareim harma da mommynki da Aunty Anila" dariyar farin ciki Unaisah tayi"kuma kinsan wani abu, dana ji labarin nan sai na ji araina kamar ke ce babyn Uncle shureim saboda bala'en kama da ki ke yi da shi, don dai ta rasu ita bata araye.." murmushi Batool tasaki aranta tana tariyo farkon haduwarta da Uncle shureim har yau takasa manta lokacin daya cire mata errings dinta daya sargafe veil dinta. Ganin ta shagala da tunani yasa ta katse ta"mu karasa cin abincin kada ya huce" sai da suka ci suka koshi tukunna suka koma falo a saman sofas suka zauna. Sai jaraba kiran layin Ummi ta ke yi baya shiga, Har kiran daddyn ta ƙarayi shima baya picking, ta damu sosai, a karshe ta kira layin Danejo kamar dama jiran kiranta su ke yi, suna ɗagawa muryoyinsu suka cika kunnuwansu dayake handsfree ta saka kiran "Angel, Kun manta damu, almost one month and weeks An kulle mu a part din daddy taj, Pls mun gaji, wallahi, Muna so mu dawo inda kuke.. "Unaisah wai har yanzu su Chief basu dawo daga kai farmakin bane? Muna jira shiru ba labari, Ko mun kira bakya daga kiran mu, Hankalinmu ba akwance ya ke ba ku fada mana in wani abu ya faru pls" Angel, Ina danish dinmu? Ina yaya Salsabeel da Chief? Ina daddy taj, babu mai leko mu, kowa ya manta damu. "Ni abinci ma yanzu ya daina min daɗi, ki6ar har tayi min yawa, baku ga yadda na koma ba, pls Unaisah ku fada ma Chief abude mu, kullen Ya isa haka, mun takura sosai, Muna so mu sakata mu wahala.." muryar Parveen ce tuntsirewa su ka yi da dariya ita da Batool kamar zasu shake . "Pls ku kira mu video call mana" maida kiran Unaisah tayi video call, sai gasu reras su goma shabiyar, waro idanu sukayi ganin yadda hutu ya zauna masu, sunyi kiba kamar rainon turai, fatarsu tayi jajir yadda kasan ya'yan larabawa hatta masu duhun fatar cikinsu sun yi fresh fatarsu tayi kyau. fashe masu da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, ji suke kamar su yi tsalle su shige ta cikin screen din wayar. Haris sai tambayar Danish Ya ke yi, yana ina? Ya yake? Sun dawo daga kai farmaki ko har yanzu basu kaiga zuwa ba, Kasa amsa mashi su ka yi, shiyasa suke fargaban su kirasu saboda tsoron su tambayesu ina Danish gashi kuma duk sun damu da shi sai tambayar shi sukeyi. "Pls Sis, Ku fada mana gaskiya, ina ji araina kamar wani abu ya faru, sunje kai farmakin ko basu je bane"? Sajeed ne ya tambaya, fuskarsa amarairaice dakyar Unaisah tayi karfin halin furta"har sun dawo" waro idanu waje suka yi cikin mamaki da rudu, atare suka hada baki gurin firta"suna ina? Sunyi nasara? Meya faru da suka je? Sun kashe su um? Sun taimaki sauran prisoners din um? Kamar yan jarida suka tsare su da tambayoyi. Numfasawa tayi cikin karyayyar murya tace"sunyi nasarar taimakon fursinoni, yanzu haka suna a asibiti karkashin kulawar likitoci.." tunkan ta kare maganar Suka fara shewar Farin ciki.. "Yar uwata fa? Hada ita cikin su? Cike da zumudi Sajeed ya tambaya. Bata san amsar da zata bashi ba, Batool ce tay saurin cewa"hada ita, wata mai bala'en kama da kai, ai munje asibitin mun gansu, tana nan cikin koshin lafiya, sai tambayar dan uwanta Gabriel ta ke yi" bai ƙarasa sauraran Batool ba ya shiga furta Alhamdulillah, Alhamdulillah... " "Mu damuwar mu, ina bugun zuciyar mu? Murmushin yaƙe Unaisah ta saki"ku kwantar da hankulan ku, Danish, Yana nan Cikin koshin lafiya, ya ɗan samu rauni ne shi da ya Omar da salsabeel, shiyasa aka kwantar da su asibiti amma jikin nasu da sauki, har tambayar ku ya ke yi kuna ina muka ce mashi kuna nan lami lafiya.." jikinsu yayi sanyi lakwas, duk basu ji daɗin jin cewa baida lafiya ba, don basu san baya araye ba da ba karamin hauka zasuyi ba "Ku sanyasu a addu'a pls, ita suka fi bukata" amsa mata sukayi da toh.." "Amma da su ka je kai farmakin sun kashe Giants da mugayen da suka azabtar da rayuwar mu"? Mubeen ne ya tambaya "Sunyi nasarar kashe giant sosai, amma basu kashe elders ba, amma kada hakan ya dame ku, ita nasara ba'a samun ta cikin sauki, sai ansha wahala, cikin ikon Allah yanzu sun fara gano su wanene Elders kuma nan bada jimawa ba, cikin ma kwanakin nan zasu kamosu, gaba daya zamu gansu da idanun mu..." daɗine ya lullu6e su. "Yanzu mu sai yaushe za'a bude mu daga kurkukun nan? Muna so mu ganku, ko ku dawo nan, sannan dan Allah ki roki Chief yasa akai mu asibitin da aka kwantar da su danish mu ganshi ko hankalinmu ya kwanta" acewar haris"Kada ka damu zamuyi masa magana"! "Nima pls, ku rokarmin Chief, ya taimaka ya hadani da sister dina" Batool tace"kada ka damu zaka hadu da ita, yanzu bayanan in ya dawo zamu fada masa" Haris bai yarda da maganganun su unaisah ba, yana kokwanton in gaskiya suka fada musu ya dai bar abun aransa, tun da ba yadda zai yi. "Ina Aunty Danejo na"? Jemimah tace"tana can dakin ta kan gado ta hangame baki tana bacci, Ni na sato mana wayarta, don mu kiraki, Kuma munata kira ma bata shiga.." ƙyalkyalewa su ka yi da dariya.. "Munyi missing dinku, kuna aran mu, idan akwai abunda ke damunku bayan wanda kuka fada mana ku sanar damu" cikin kulawa batool tayi maganar . Har suna hada baki gurin furta bamu da damuwar komai, akwai abinci available ga kayan more rayuwa kawai mudai so muke abude mu mu dawo gurinku sannan akaimu mu gano su danish din mu.." murmushi suka sakar masu.. "Okay zamu fada ma Chief idan ya dawo, duk yadda mukayi da shi zakuji daga gare mu".. "Dan Allah kada ku manta, babu kyau jan rai, kullum haka kuke ce mana kuma sai muji shiru ko mun kira bakwa dagawa akai akai" acewar rubina.. "Wannan karon ba zamu manta ba, in sha Allah" amsawa sukayi da toh. "Kunyi kyau, kun ƙara haske, wasu sunyi ƙiba, tubarkalla masha Allah.." dadine ya lulu6e su jin abunda Unaisah tace.. Sarah tace"kuma haka, kun kara kyau,.." "Mungode, Ku more lokacinku, soon zamu zo maku da abun ban mamakin da zai girgiza ku" "We can't wait to see" Cikin nishadi suka cigaba dayin fira da yan uwan su sun debe masu kewa, baka jin sautin komai a falon sai sautin dariyarsu da surutun su, kamar wadanda suka shekara basu gana da juna ba.. ~_____________________________🔥~ Around Ƙarfe karfe shida na marece, ta farka da wata irin kasala a jikinta, tana kokarin motsawa taji ta a jikin mutun, buɗe idanunta tayi a disashe take kallon fuskar shi, tunawa tayi da abun daya kawo ta, a ruɗe tayi dabarar raba jikin ta daga nashi ganin baccin nashi ya yi nisan kiwo farkawarsa ba yanzu ba, ta karance shi tun da jimawa, In ya fara bacci da wuya ya farka ko da za'a buga ganga ne a kusa da kunnansa. zanan tattoo din bayansa ta ƙura wa idanu ya fito sosai, cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta janyo rigarta daya cire mata, ta saka a jikinta, gabanta na faɗuwa ta ɗauko wayar ta daga cikin yar purse dinta data jefar ƙasa, gabanta na faduwa ga tsoro da fargaba da suka mamaye zuciyarta ahaka ta nufe shi, bayan ta kashe camera sound din wayar ta saita bayan shi da camera ta ɗauki hoton tottoo din shi. Cikin sanɗa ta juya ta nufi toilet dinsa, ta bude ta shiga daga ciki, taja ƙofar tare da yin locking dinta, ajiyar zuciya ta ɗan sauke, Yatsun hannunta na kerma ta tura ma Chief hoton tattoo dinsa ta whatsapp chat dinsa. Unexpected taji anyi knocking toilet door din, waro idanu waje tayi tare da hadiyar yawu.. Daga waje tajiyo voice dinsa da alamun bacci bai ishe shi ba ya furta"Ummi, na farka ban ganki ba, kina a ciki'? Wani irin faduwar gaba taji, da rudu ta zare idanu aranta ta ayyana tayaya akai ya farka da wuri? Mutumin dake da nauyin bacci, Dakyar ta furta"yeah am in wanka zan yi" "Okay, open the door for me, nima zanyi wankan" dafe kirji tayi da hannu ɗaya, ta rasa ina zata saka phone dinta, Idan har yaganta da waya a cikin toilet zai zargi wani abu, kuma idan ta hana shi zai iya zarginta tun da sun saba yin wanka atare wani lokacin. Jin tayi shiru bata tanka mashi ba, yasa shi furta"Ummi, meyasa ki ka yi shiru uhum"? Cikin sauri ta tura wayar cikin bra dinta, ta gyara headscarf din kanta, kafin ta yi unlocking door din. Har saida gabanta ya fadi ganin yadda ya murtuke fuskarsa kamar bai ta6a dariya ba. Adabarbarce ta furta"am.. um.. ai na fada maka period nakeyi, bazan iya yin wanka atare dakai ba, bana so kaga abun da zai tada maka zuciya, nasan kana da ƙyanƙyami, ka jira in gama sai ka shigo" ta karashe maganar tare da ruko kofar da niyar ta rufe, batai aune ba taji ya bangaje kofar, ya shigo ciki tare da kulle ƙofar, aruɗe tace"big boss why? Na faɗa maka bazan iya wanka tare da kai ba ina period, yakamata ka jira ni awaje.." bata ƙare maganar ba, Ya janyota ta faɗo kan kirjinsa, hugging dinta yayi tightly, kirjinshi ya hadu da nata sosai, har saida nunfashin ta ya dinga fita dakyar. A hankali Ya tallabe ass dinta da palms dinsa.. In a low voice kamar yana mata raɗa ya furta"kada ki damu, ba zanji ƙyanƙyamin ki ba saboda kina jini, inason komai naki ummi, saboda ke din mai tsaftace, duk abun da zai fito daga jikinki tsaftatacce ne, babu kazanta a jiki mai tsarki irin naki.." ji take kamar ta fasa ihu, saboda fargaban kada Ya gano wayar data saƙa a cikin bra dinta, gashi sai yawo yake mata da hannayensa a jikin ta "Pls big boss, bana jin dadi, cikina ciwo ya ke yi min, wankan ma na fasa, kasa a kawo min magani in sha.." ta faɗa tana kokarin raba jikinta daga nashi, sa6arta yayi kamar diyar roba Ya nufi bathtube Yana fadin"ba sai kin sha magani ba ummi, zansa kiji sauƙin radadin ciwon cikin ki.." waro idanu ta danyi ganin ya nufo bathtube da ita, tuni tasha jinin jikin ta, abun da take jima tsoro kada ya yi attempting undressing dinta zai iya ganin wayar data 6oye Bubbuga kafadunsa tayi da tafukanta"pls, ka maidani bedroom, bazan yi wanka ba, na fasa, bana son ruwa ya ta6a jiki na, zazza6i nake ji.." Wata yar iskar dariya ya saki"da ruwan zafi zamuyi wankan, zaki ji dadin jikin ki" kukan shagwa6a ta sanya ma shi, bai ko kulata ba. da iya karfinta na karshe ta fusge hannayensa daya tallabe ta da su, ta bangaje shi da gudu ta nufi toilet door din tana isa ta bude kofar ta fuce. Tana ƙarasowa gaban gadon tana haki tayi saurin tura hannu cikin bra da niyar ta ɗauko wayar ta maida a purse sai dai me? Tana zura hannu ta laluba bra taji wayam babu wayar a jikin ta, gaba daya tabi ta rude ta zuge zip din rigar, ta 6alle hannun bra din ta cire ta duka ta zazzaga ta kwata kwata babu wayar, ruɗewa tayi gaba daya kanta ya daure ta rasa tayaya akai har wayar tabar jikin ta? Tunani tayi ko dai gudun da tayi ne yaja har wayar ta fado daga jikin ta? Girgiza kai tayi kamar ta6a66a, ta furta ba zai yiwu ba, anan na aje wayar, babu space din da wayar zata iya zamewa daga cikin bra dina saboda ta matse ni, ko dai na barta a toilet"? Yanke shawarar komawa toilet din tayi don ta dubo ko a nan wayar ta fadi. Juyawar da zatayi keda wuya kwatsam ba zato ba tsammani, Idanunta suka sauka akan wayarta dake a ruƙe a hannunsa. Yana a tsaye bakin kofar toilet din, yawu ta haɗiya cikin rudu ta furta"a ina ka ganta"? Shu'umin murmushin nan nashi ya sakar mata"a inda kika 6oye ta, Ummi me kike yi da waya a cikin toilet? Bayan asanina dake bakya shiga toiler da waya a hannun ki. murmushin yaƙe ta sakar mashi tana inda inda tace"am..um..dama Natasha ne ta kira ni, tana kara tuna min akan inyi maka maganar babyn pretty..." tsoki yaja"Ummi banason maganar nan, ki fiɗa mata ta fidda rai akan ta, saboda ba yar ta bace, na maida ma mommynta ita" Ajiyar zuciya ta sauke ganin bai dago ta ba"babe saida na fada mata haka, nace tayi hakuri, amma takasa saboda ta kwallafa rai akanta, shakuwace ke dawainiya da ita, dole tayi kewanta, ta fada tare da matsawa kusa da shi, cikin salon jan hankali take shafa kirjin shi, har takusa zame wayar daga hannun shi, kwatsam sai ga sako ya shigo wayarta akan idanunsa. _thank amma ba zamu iya bin diddiginsa ba ummi, Ki kula da kanki zamu nemi wata hanyar da zamu kama shi_ Yanayin fuskarsa ne Ya canza zuwa tsantsar al'ajabi da tashin hankali, cikin rudu da faduwar gaba ya dubeta, duk da batasan sakon menene ba sai da taji ƴan hanjin cikinta sun kaɗa ganin yadda walwalar fuskarsa ta dauke Cikin ruɗu ya furta"ummi, diddigin wanene za'abi don a kama shi, Kuma ta hanyar ki" ❓ Waro idanu waje tayi tamkar kwayar zasu faɗo kasa, adabarbarce ta furta"Um..kada ka damu, kasan nasaba irin wannan aikin na taimaka ma jami'ae donsu kama 6ata gari tun a america, yanzun ma wani ɗan ta'addane suke so su kama shine suka nemi in taimaka masu..." shiru yayi jim kamar zuciyarshi tana so ta musa mashi akan abun da ta fada. sai dai me rawar da jikinta keyi kamar mazari yasa shi zargin bata da gaskiya, saboda gaba daya babu nutsuwa a tare da ita. "Ina kokwanto akanki Ummi, ban yarda da maganarki ba, ki fada min gaskiya, tun kafin in gano da kaina, Idan ba haka ba, wallahi na lahira sai yafi ki jin dadi..." yawu ta haɗiya ƙutt tana faman zare idanu tace"meyasa ba zaka yarda dani ba? Na ta6a yi maka karya ne? Shekara nawa ina atare dakai big boss? Ban ta6a hada baki da wani don a cutar dakai ba babu wanda yasan ma muna atare dakai, pls ka yarda dani.." wani kallo yayi mata yana sakin wani shu'umin murmushi ya furta"ummi dan adam ba abun yarda bane, mutun ya sa6a wa mahaliccinsa balle ni, kawai idan kinaso In yarda dake ki cire min security din wayarki In bincika ta..." " Na shiga uku..." yarfa hannu tayi kamar zata fasa ihu saboda tashin hankali bawai don tana jin tsoron nuna masa ba sai don tana jin fargaban maganar Chief ya zamana gaskiya in kuwa hakane kashin ta ya bushe. Mika mata wayar yayi"bude min ummi na" yatsun hannun ta na kar6a ta kar6i wayar idanunsu a cikin na juna, tunawa tayi da maganar Chief, dole kiyi taka tsantsan idan ba haka ba, in har ya tabbata shine Jan wuya na gidan kurkukun kaddara ya kuma gano kin bamu hadin kai, har kashe ki zai yi, kada kiyi tunanin shakuwar dake a tsakaninku zaisa ya raga maki.." da gangan ta saki wayar ta kife kasa har wani sauti ta bada saboda tiles din data daka Pretending tayi a rude ta zukunna tare da daukar wayar tana fadin"Ya salam, screen din wayar ya fashe" mikewar da zatayi keda wuya, taga yana matsowa kusa da ita, ja da baya tayi a tsoroce ganin yadda Jikinshi ke kerma .. Yanayinsa kamar na wanda zuciyarsa ke nema ta karye... Kwatsam Ya shaƙe wuyanta da hannunsa Ya kure ta jikin bango, da wata irin buɗaɗɗiyar murya ya furta"sabo da kaza bai hana In yankata Ummi, muddin ta ci amanata, Ki fada min menene kike boye min? Tun kwanaki kika sauya min, abun da baki taba min ba, yau tun zuwanki ina lura da duk wani motsinki, baki shan giya ummi amma kikasa na kawo mana giya, saboda kina so hankalina Ya gushe donki samu damar aiwatar da abun da kike so, bayan da bacci ya dauke ni, sai kika dauki hoton tattoo dina, Ummi wanene ya saki huh?..." Tashin hankalin da ba'a saka mashi date, tuni ido Ya raina fata, wani irin faduwar gaba ta soma ji a kirjinta kamar ana buga war drum, Muryarta ashake ta furta"big boss, bazan iya cin amanarka ba, ka yarda dani..." katse ta yayi"kada ki min karya, ba halin ki bane, Idan kinaso In yarda dake ki fada min komai.. " rintse idanunta tayi tare da cizon le6enta muryarta na rawa ta furt"sus.. Sune suka sanyani, saboda suna zarginka, wallahi bada son raina ba, saida nace masu ba zaka taba iya aikata miyagun laifukan da suke zarginka dasu ba, amma suka matsa min akan cewa kana da sa hannu, koda suka rokeni akan in basu hadin kai gurin ka ma ka nace ni bazan yi ba, shine suka matsa min, ni kuma saboda na yarda dakai nasan baka da laifi shiyasa na amince masu saboda nasan ta silar bincike zasu gane sunyi kuskuren zargin ka" Aruɗe ya furta"wani irin zargi su ke yi akaina um"? zazzare idanunta tayi, wani kwarjini yayi mata har bata san sa'adda ta furta"dg yana zargin kana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun kaddara, wai kaine Jan wuya, mahaifin Unaizah yar gidan daddy, saboda sun ga hotunanka kai da Natasha acikin Diary dinta data bari a hannun yan uwanta prisoners din kurkukun kaddara, Dan Allah ka fada min gaskiya kaina ya kulle, na shiga rudani, zuciyata ta tsorata, naji fargaba da tashin hankalin da ban ta6a ji ba a lokacin da naji labarin kurkukun kaddara, da irin izayar da wasu azzulaman mutane su ke yi wa yaran da basu ji ba basu gani ba, big boss tayaya zan yarda da abunda suka fada akanka"? Ta faɗa tana kallansa.. "Bayan ni nasan wanene mutumina, saida na fada masa mutun mai zuciyar imani da tausayi, bazai iya aikata abun da suke zarginka da shi ba.." Bata ƙare maganar ba, sakamakon tsawar daya daka mata wadda tayi silar ruɗewarta, kamar zai fasa dodon kunnanta, Dafe kanshi yayi da tafukansa kamar mai faɗa da ciwon kai, Cike da tsantsar tashin hankali da rudu ya shiga furta"How is that possible? How do they know everything? How did they get Unaizah's diary? Who told them? Who is behind this? This is a lie! It's not true, it will never be true" Yana magana zufa tana wanke fuskarshi, Ummi dake kallon shi gaba daya tabi tasha jinin jikinta ganin yadda lokaci daya big boss ya nemi zaucewa, yama rasa ina zai sa kanshi kamar mahaukacin, kanshi ya daure da Jin abun da bai ta6a zata ba, ko a mafarki, mamakin shi taya akai Unaizah ta tafi da diary din ta batare daya ankara ba? Yana nan sake da baki Yana ganin cewa wayonsa da dubararsa ba zasu taba bari asirin shi ya tonu ba sai gashi ƙaramin kuskure yana nema yaja masa matsala. wata irin ƙara ya fasa tare da nufar maidaidaicin glass table din dake a seating area din dakin Ya kinkime shi, da sauri Ummi tabi bayanshi, Kafin Ta karaso Ya buga table din kasa nan take Ya tarwatse, ruko hannayensa tayi a cikin nata, cikin shesshekar murya ta furta"big bosa kada ka lahanta kanka, na fada maka ni ban yarda da su ba, dama nasan idan na fada maka zargin da su ke yi maka dole kaji ba dadi, pls kazo muyi magana, nayi maka alkawarin in har baka da laifi zan yi iya ƙoƙarina don wanke ka daga zargin da ake yi maka" bangajeta yayi da hannun shi tayi taga taga zata fadi, da sauri Ya damki arm dinta yana huci ya furta"har yanzu baki fadamin tayaya akai suka san ina atare da ke ba"? Tamkar zata fashe mashi da kuka tace"wallahi bani na fada masu ba, ka yarda dani, ban ta6a fitar da sirrinka ba.." muryarsa da tsawa yace"karya ki ke yi Ummi, ba zasu taba neman ku hada baki ba gurin kamani batare da sunsan muna a tare ba, saboda ganina ba abune mai sauƙi ba.." cike da jin shakkar shi tace"hakane, ay na fada maka, hotonka dana Natasha suka gani a cikin diary din, aranar da mu ka je airport a america tare da Natasha sun ganta, babu wanda baisan ƙawata bace, bayan haka akwai ranar daka kira video call, bana akusa na shiga toilet, ɗaya daga cikin yaran da nake kula da su ta shigo dakina da karanbani ta dauki wayar ta ɗaga kiran anan taga fuskarka, wallahi big boss yarinyar ko waya bata iya ba, babu komai akanta bansan ya akai ta ɗaga kiran ba...." bata boye masa komai ba.., Sakin arm dinta yayi tare da dafe kanshi da tafin hannunsa. Ita kanta ta tsorata da yanayinsa karfin hali tayi gurin firta"tunda na fada maka abun da ka ke son ji, Nima inaso ka amsa min tambayana big boss, tayaya akai Unaizah ta zama daya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara? Waya kaita bayan a labarin da naji mahaifinta ne Ya sadaukar da ita,...." tiryan tiryan ta zayyana mashi labarin Unaizah, ta kara da cewa"Abun ya dameni, tun da naji labarin ta, saboda nasan Unaizah ƴarka ce, kuma kaine mahaifinta, amma na ruɗe da naji yadda suka bada labarin cin amanar da mahaifinta yayi mata, ya yaudare ta ya kai ta kurkukun kaddara da sunan High school na korea, Big boss Ina Unaizah? Kuma wacece Zeenatu diyarka mai bala'en kama da Unaizah... bata kare maganarba Ya balbaleta da masifa, yana fadin meyasa take yi mashi tambayoyi kamar tana tuhumarsa? Ko itama ta yarda da abunda ake zargi akansa? Bayan bai ma taba sanin ina ne gidan kurkukun da take magana akai ba, balle wasu elders, shi bazai iya aikata munanan laifukan da ake tuhumarsa ba, tafi kowa sanin halin shi don haka ta rabu da shi, Yarinyar da take magana akai ba Yar shi bace, shi ƴa ɗaya gare shi Zeenatu, Kuma itace baby preetyn da take magana akai.." Yana magana yana huci kamar zai rufe da bugu, baima kare maganar ba Ya fuce daga dakin tabi bayan shi sai dai kafin ta karasa taji ya datse kofar, bubbugawa tayi taji ta a datse. Wani irin matsanancin ciwon kaine Ya taso mata, a daddafe ta nufi gefen gadonsa ta zauna, Zuciyarta ta karaya, saboda ta ga tsantsar rashin gaskiya atare da big boss din ta, abunda take jiyema fargaban Ya zamana gaskiya, Ya zatayi da rayuwarta? Ina zata sa ranta taji dadi?meyasa big boss Zai daga hankalinsa akan abunda Yake ikirarin bai aikata ba? Meyasa ya canza mata a lokaci? Meyasa ba zai kare kansa ba? Ya salam Kifa kanta tayi saman pillow, hawaye suka cika idanun ta, ga wani bugun barazanar da zuciyarta keyi mata, tana jin tsoron abin da zai biyo baya, wayarta ta ɗauko don tayi Kira sai dai koda ta duba screen din wayar ya tsastsage bata iya ganin komai, gashi ya kulle ta adaki no way out.. ~_______________________________🔥~ Bacci ya ƙaurace wa idanunsu ganin shiru Aunty Ummi bata dawo ba, kuma har time din Chief da daddynta basu dawo ba, sun yi jiran har sun gaji. Suna akwance kan gadonsu sanye cikin pyjamas, sun hada kai suna kallon wani korean drama a wayar Unaisah, ba laifi kallon Ya ɗebe masu kewa duk da hankalin su ba akwance ya ke ba. Kiran wayar Taj ne ya shigo wayar Unaisah, a hanzarce tayi picking ta kara a kunne. "Unaisah har yanzu bakuyi bacci ba"? Muryarta da shagwa6a tace"daddy ba zamu iya bacci in har baku dawo gida ba" "Kuyi hakuri ku kwanta, Ku huta pls, nan bada jimawa ba zan dawo gidan" "Toh daddy, Ina mommyna ba zata zo taga babynta ba" yar dariya yayi"gatanan a gefena, tana sauraronki.." bai kare maganar ba, Muryar Benazir ta katse shi"Babe barka da dare Ya kuke Ina fata Kuna lafiya"? "Lafiyalou mommy, nayi missing naki, inason ganinki, Kin ki zuwa kiga babynki" dariya Benazir tayi"Sorry, Kina araina, Gidan naku ne sai da izni ake shigar shi, ni da anila munata jira, sun ce zasu tuntu6emu in sha Allah zamu zo" bata kaiga furta kalma ma, Batool ta kwanto da kanta saman wuyan ta,"Mommy, barka da dare, Batool ce, Ina uncle Shureim din mu, munyi missing nashi.." "My baby Batool, Uncle shureim yana lafiya, shima yayi missing naku, kullum sai ya tambayeni ina babyn nan mai kama da shi" dariya batool tayi saboda dadin da taji"please mommy, ki gaishe min da shi, ki fada mashi ina kaunar shi" "In sha Allah zai ji, don ma baya akusa da mu ai dana bashi kun gaisa, amma zan sa ya kiraku ku gaisa" washe baki tayi"mungode mommy" "Okay, babes, ku kula mana da kanku, Ku kwanta kuyi bacci, yanzun nan daddynku zai dawo.." amsa mata sukayi da toh bayan sun katse kiran, Unaisah ta daura phone dinta akan ta batool dake akan Nightstand, hugging din juna sukayi babu alamun zasu runtsa saboda tunanin Aunty Ummin su da bata dawo ba. A hankali wata dankareriyar Mota baka, ta shararo izuwa main entrance gate Na villa din owais, ko da ganin baƙuwar Mota, Security Officers suka yi saurin nufo motar, tare da yiwa mata ƙawanya, knocking Glass din motar sukayi tare da bashi Umarnin Ya sauke glass don suga wanene shi, banza akayi da su har saida suka fusata kamar zasu 6a66ake window glass din motar tsabar yadda suke kwankwasa shi. sai da na cikin motar ya mula yasha iska tukunna ya zuge masu window glass, Tare da sauke Shade din dake akan fuskar shi, Waro idanu waje su ka yi cike da mamaki, a hanzarce suka buga kafa tare da sir mashi kusan atare suka furta"Sorry Sir.." Ƙayataccen murmushin gefen fuska ya dan saki, yayin da yake a zaune saman Driver's seat. "Ina fata na same ku lafiya"? "Lafiyalou Sir, munyi mamakin ganinka, bamu san ka samu lafiya ba,Ya jikin naka" still da murmushi yace"Alhamdulillah, naji sauƙi, Owais bai fada maku bane? Ya tambaya da mamaki kan fuskarsa su ka ce wallahi bai sanar da su ba, basu san komai ba game da samun lafiyar shi ba, ko sun tambaye shi sai dai yace masu da sauƙi jikin shi. "Ku yi masa uziri, Kunsan yanayin aikin namu, Yana a ciki"? "A'a sir, tun safe daya yabar Gidan har yanzu bai dawo ba" Okay, ya faɗa tare da yiwa motar key, Ya shige cikin gidan. Fitowa yayi daga Ciki, Jikin shi sanye da Kaftan, ya fito fess abun shi ko tabo babu akan skin insa, kamar bai taba jin rauni ba. Lokacin daya shiga Falon gidan bai Iska kowa ba, zama yayi a falon tare da daura kafarsa daya kan ɗaya. Chef ne ya shugo falon daga kitchen, yana hangosa da sarsarfa Ya nufe shi bayan sun gaisa yayi mashi ya jiki. daga bisani chef din ya tambaye sa ko yana bukatar abinci ya kawo masa? Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"ina Unaisah da Batool"? "Suna a cikin dakin su" "Ka kira mun su, Inason ganin su" Amsa mashi yayi da toh, kafin ya juya ya nufi ɗakin su Unaisah Bayin Allah har sun fara bacci, suka farka jin knocking, Batool ce ta bude kofar tana mika da hamma ta dubi Chef din "Big guy, yazo, yana a falo yana son ganin ku" waro idanu waje ta yi cike da mamaki tace"big guy Yaji sauki! Da kanshi yazo, Wayyo Allahna, Alhamdulillah ka faɗa masa, gamu nan zuwa.." juyawa tayi ta nufi Unaisah dake ta juyi kan gado, ta bubbuga kafafunta"sis Ki tashi, Big guy ne ya zo, ya samu lafiya yana a falo, yanzu chef ya fadamin yana son ganin mu" dakyar ta samu Unaisah ta sauko daga kan gadon tana mika tace"Dagaske Ya omar ne Ya yazo? Shi ka ɗai yazo ko tare da wani"? "Kinga ki zo mu je mu gaishe shi daganan sai muyi mashi ya jiki" Mayafi kowaccen su Ta yafa ma kanta, suka fito da sauri suka nufi falo, tunkan su karasa suka hango shi zaune kan sofa mai mazaunin mutun uku ya daura kafarsa daya kan daya, Yayin da yake danna wayarsa a hankali Jin motsin tafiyar su ne yasa shi ɗagowa da lumsassun idanunsa da suka kada jawur ya dube su. Cikin girmamawa suka zauna suna fuskantar shi. "Ya omar dagaske kaine? Munyi kewarka! Ya jikin naka? Ina ya salsabeel"? Yamutsa fuskarsa yayi"fushi nake daku, kun manta dani, kuna nuna kamar kun damu dani bayan tun da na kwanta jinya baku taba zuwa kun dubani ba" Ya faɗa yana kare masu wani kallo wanda yasa Unaisah tayi noticing wani abu a tare da shi. Batool tace"ba haka bane ya Omar, wallahi kana aranmu, chief ne bai sa akawo mu ba amma muna taso muzo mu duba ku.." Murmushi yasaki"ina Ummi ne? "Ta tafi anguwa, har yanzu bata dawo ba, daddy da Chief duk sun fita basu dawo ba" Agogon hannunsa ya duba "ku tashi mu tafi in kaiku asibitin da aka kwantar da sauran yan uwanku prisoners ku duba jikin su" cike da zumudi Batool tace"Toh," Unaisah ta maƙe kafaɗa alamar bazata je ba "ya omar, dare ne yanzu, bai kamata mu fita ba, why not zuwa gobe da safe sai muje, kaga kafin nan Daddyna da Chief harma da aunty Ummi sun dawo sai muje ba ki daya mu duba jikin nasu.." tunkan Ta kare maganar ya katse ta da cewa"kada ku bari damar nan ta wuce ku, Chief bazai bari ku fita ba, Ya cika tsananta maku tsaro, ku tashi kawai mu tafi in kai ku, cikin yan mintina zamu dawo" duk yadda Unaisah taso ta ƙi amincewa da fitarsu takasa saboda ya matsa lamba akan su shirya ya kai su. har dai tace"shikenan, bari mu shiga ciki mu sauya akaya" ta fada tare da jan hannun Batool suka nufi bedroom dinsu, suna shiga ta datse kofar, ta fuskanci Batool da ke fadin"muyi sauri mu shirya, kafin chief ya dawo, in ba haka ba zai hana mu fita ne" cikin muryar rada Unaisah tace"batool nifa ban yarda da ya Omar ba, wallahi kamar bashi ba ya sauya min, ke baki lura ba? Idanunsa kamar na mashayin giya, muryarsa katuwa ba irin ta ya omar ba mai sanyi, sannan Ya omar bai kai wannan duhun fata ba, duk da bawani sanin fuskarshi nayi ba saboda yana yawan saka mask amma wallahi akwai banbanci tsakanin Ya omar da wannan Omar din, kuma tayaya mara lafiyan da ya farfaɗo daga coma ya iya samun ƙarfin da zai yi driving? Shi kaɗai batare da likita ko wani security ba! nidai hankalina bai kwanta da shi ba..." Cike da matsuwa Batool ta bubbuga ƙafafunta akan floor. "haba sis, ki daina wannan tunanin, wallahi ya Omar ne, kodai kin samu matsalar gani ne? Yamutsa fuska tayi"ba zaki gane ba Batool, kawai daga zuwan shi sai yace mu tafi ya kai mu asibiti? Batare da iznin Chief ba, kawai sai mu kwashi kafa mu bi shi kamar wasu sakarkaru, bayan haka Mutumin da ya ke a coma yaushe ya farfaɗo? Kuma babu tabo ko kadan akan fatarsa.." dafa kafarta Batool tayi"ki kwantar da hankalinki, wannan ba wani abu bane may be yaji sauki tuntuni mune bamu sani ba, kuma in ban da abunki gidan nan atsare yake da jami'ai da kuma cctv, In bada iznin su ba tayaya zai iya shigowa? Tunzura ta Batool tayi harta shawo kanta ta amince zataje saboda itama tana son taga yan uwansu fursinoni da aka ku6utar da kuma Ya salsabeel. Shaf shaf suka sanya wide leg jumpsuit ajikin su masu kyan gaske, ta Unaisah Ja ta Batool yellow, daga sama suka daura Wrap coat, sai sukayi rolling veil asaman kansu, Bayan sun saka takalma suka ɗauki phones dinsu. Kafin su fito daga dakin saida Unaisah Tayi ta kiran Taj baya picking, ta kira chief shima baya picking, ta kira mommynta still itama bata yi picking ba, taso ta same su don ta fada masu batun zuwan big guy da kuma fitar da zaiyi da su amma bata samu halin yin hakan ba, feshe jikinsu sukayi da turare, suna fitowa suka iske big guy atsaye yana jiran su. "Mu tafi" ya fada tare da nuna masu hanya, ya yi gaba suka bi bayan shi, Har gaban motar shi tun fitowar su Unaisah ta lura da security officers din gidan sun yi tsaye kamar gumaka kwata kwata basu sintiri kamar yadda suka saba, lamarin ya jefata a ruɗani. Da kan shi ya buɗe masu mazaunin baya na motar, ya dafe murfin motar da hannunsa. Batool ce ta fara shiga ciki ta zauna, Unaisah tana niyar kutsa kanta ciki kamar ance ta saci kallon shi karaf idanunta suka sauka akan zanen tattoo din daya dan leko ta kirjin sa sak kalar na Danish, wanda hakan na nufin giant din kurkukun kaddara ne ❗ ruɗewa tayi ta shiga zare idanunta a tsananin tsorace. ganin ta toge taki shiga yasa shi lura da abun da idanunta ke kallo. "Sis ki shigo mu tafi" Batool ce ta faɗa daga cikin Motar batai aune ba taji ya ingizata cikin Motar, Ya datse Murfin, a hanzarce Ya bude front seat ya shiga ciki, da gudu Ya fusgi motar, ya miki hanyar fita daga estate din~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___❗~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 ____________________________🫀🌹💋~ Tun lokacin daya wurgo Unaisah ta faɗo jikin Batool arude ta shiga tambayarta meke faruwa? Tana lafiya? kasa magana ta yi saboda rikicewar da tayi, ɗagowa tayi tare da kallon madubin Motar, hankalinsa a kwance ya ke driving din su, haɗa idanu su ka yi, Ya sakar mata wani shu'umin murmushi, faɗuwar gaba taji kamar ana luguden ta6are a ƙirjin ta, ganin yadda kamannin big guy suka 6ace daga kan fuskarshi, ainihin suffar shi ta bayyana, wani mummuna da shi. gaba ɗaya tabi ta ruɗe ta rasa gane meke shirin faruwa da su, Batool fa kwata kwata batasan wainar da ake toyawa ba, wayarta take ta dannawa. da karfin Hali ta furta"Who are you"? sai lokacin Batool ta dakata da danna wayar ta ɗago tana kallon Unaisah. Bai kula ta ba ya cigaba da yin driving dinsa, Rai a6ace tayi kukan kura ta tsallake backseat ta dawo front seat din motar Ta rurruƙe hannayensa da ya ke yin driving din da su, ta soma kokarin dakatar da shi, ta ƙwammace su yi accident su mutu akan ta bari ya tafi da su saboda ta ji aranta daga kurkukun ƙaddara aka turo shi ya ɗauke su. kokoyi su ka kama yi, out of control motar ta dinga girgiza tana kaukacewa hanya akan titi. Karfin halin ta ya ɗaure mashi kai tamau, kuma still yaki tanka mata. Batool ta yi matuƙar razana da ganin abun da ke faruwa, sam takasa magana saboda razanar da tayi ganin big guy ya sauya kamannin fuskarsa. Tuni wayar hannunta ta fadi ƙasa sakamakon girgizar da motar ke yi har saida kanta Ya da ki window glass, kafin tayi wani yunƙuri, Ya Naushi cikin Unaisah da gwiwar hannunsa nan take wani azababben radaɗi mai kama dana ciwon mara ya ratsa sassan jikin ta. Cikin ɗimuwa ta shiga furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Batool ki gudu! Saida na fada maki ba ya Omar ba ne wannan, ki gudu Batool, ki buɗe murfin motar ki gudu, kashe mu zai yi.. " fashewa da kuka Batool tayi, cikin rawar murya take fadin dan Allah kada ka cutar da mu, ka ƙyalemu mu tafi, ka ƙyale mun yar uwata.." ta mirror ya ke kallon fuskar Batool dake ta kuka, ga Unaisah dake a gefensa ta daddafe cikinta dake mata zogin azaba. dakyar take fitar da numfashi mai haɗe da nishi, da hannu ta dinga yima Batool alamar ta buɗe murfin motar ta gudu saboda ita a halin yanzu yayi mata illar da bazata iya ta6uka komai ba.. Sakin sitiyarin motar yayi, Ta cigaba da driving din kanta, ya damaƙar keyar Unaisah ya yi tare da ɗaɗɗago da ita Ya jefar da ita backseat, jikin batool na bari ta janyota tare da rungumeta a kirjin ta"sis ta ki tashi dan Allah ki tashi, na shiga ukuna wayyo Allahna dan Allah ka maida mu gida, kada ka cutar da mu, Chief bazai ƙyale ka ba" cike da izza ya jingina bayansa jikin seat, yayin da yake kallonsu ta mirror din motar har wani lumshe idanun shi ya ke yi kamar mai jin bacci. Zura hannunsa ya yi cikin door pocket din motar, ya zaro sirinji biyu masu ɗauke da ruwan allura a cikin su, ya haura backseat, Ya caka ma Batool allurar a cikin jijiyar wuyanta nan da nan ta fara jin wani irin matsanancin bacci yana fusgarta har bata san sa'adda ta 6ingire kanta jikin seat, ya tallabo kan Unaisah da ta fita hayyacinta, ta langwa6e kanta saman laps din Batool, itama yayi mata allurar gaba daya suka fita hayyacin su, basu ƙara sanin meke faruwa ba. ~__________________________________💔~ ~UMMIN AMERICA~ Motsin buɗe ƙofar data jiyo ne Yasa tayi wuff ta miƙe tsaye tana kallon room door din, shigowa ciki yayi fuskarsa a murtuƙe ya nufe ta. "Big boss! Meyasa ka kulle ni adaki? Ina ka tafi ka barni, Ko ka manta dani ne.." bai ko ɗaga idanunsa ya kalle ta ba, ya damƙi arm din ta yana ƙoƙarin janta ta turje, tana kallon fuskarsa dake fitar da gumi tace"me zaka min? Ina zaka kaini" A hankali ya ɗago da raunannun idanunsa Ya dube ta da su"ɗazu kin tambayeni ban baki amsa ba, saboda ban samu abun da na ke so ba, amma yanzu inaso ki zo muje zan fayyace maku komai da ki ke son ji" bai jira amsarta ba, Yaja Hannun ta suka fuce daga dakin kaitsaye Ya nufo falo da ita. Juyo da ita ya yi Suka fuskanci juna, da ainihin suffarsa ta JAN WUYA, Idanunsu cikin na juna, ba ta ta6a jin faɗuwar gaba irin na wannan lokaci ba, tsantsar rudani ne akan fuskarta. "Ummi, Lokaci ya yi da za ki san ko ni wanene! Maganar 6oye 6oye ta ƙare a tsakanin mu, zan faɗa maki komai da ki ke son ji" kalamansa sun rikirkita tunaninta. "Dama nasan duk mun daran daɗewa dole gaskiya ta bayyana, kuma naji dadi da Allah ya nuna min wannan ranar, saboda nima jiran zuwan ta na ke yi" ya ɗan dakata tare da sakin shu'umin murmushin nan nashi Kafin ya ɗaura da cewa"ɗaukar fansa yasa nake atare dake, Ba dan Allah ba, duk wani abu daya faru atsakanin ku Nine nake kulla maku makirci, Ni na raba ki da mahaifin ki, Na shiga tsakanin ki da shureim, Na kuma lalata martabarki, na maida ki karuwa..." ta kasa yarda da abunda kunnuwanta ke jiyo mata daga bakin Uncle musa, jin abun take kamar a mafarki saboda ruɗu da tashin hankali. "bazan ta6a yarda da abun da ka faɗa ba, bazai ta6a yiwuwa ba, Uncle musa kana cikin hayyacin ka kuwa? Kasan me ka ke faɗa? ko dai giyar da ka sha ce bata sake ka ba"? Tallabo fuskarta yayi da tafukansa"ko kin ƙi ko kin so dole Ki yarda Ummi, Ki buɗe idanunki ki saurareni, Ni ba mutumin kirki ba ne, tantirin shaiɗani ne, bani da mutunci ko miskila zarratin, Mugunta da zalunci kadai nasa gaba..." bai ƙare maganar ba ta katse shi cikin rawar murya ta shiga fadin ya daina batason ji, ba yin kansa bane! Giyar daya sha ce.." "Ummi, Ki daina yaudarar kanki, mutumin kirki bazai ta6a mayar da kamilar mace karuwarsa ba"! "Komai daya faru mahaifin ki ne Yaja maki, nayi amfani da ke saboda in sanya mashi bakin cikin da har abada bazai ta6a mantawa dani ba, na daɗe ina neman hanyar da zan koya masa hankali ban ta6a cin galaba akansa ba, saboda kariyar dake gare sa, amma Ranar dana fara ɗaura idanuna akan ki sai na ji maitar sha'awarki ta kamani, Musamman da na ji cewa ke din ɗiyar imam malik ce, naji dadi a wannan lokacin saboda na samu hanyar da zan lalata farin cikin rayuwarsa, saboda ni ba'a shiga gona ta a zauna lafiya, bana yafiya, nasan bakisan komai daya faru ba a tsakanina da shi, may be bai fada maki ba a lokacin, shiyasa kika aminta da ni, saboda ke bakisan wanene Musa ba, kafin na bayyana maki soyayyata saida na fara zuwa gurin mahaifinki saboda in nemi auran ki, duk da nasan mawuyacin abu ne ya bani ke saboda yasan mugayen halaye na ciki da bai... .." labari Ya fara mata na abin daya faru tsakaninsa da sheikh Imam. wasu zafafan hawaye ne suka fara Dora kan kuncin ta masu ɗumi. "Ya san ni mugu ne meyasa bai bini ta lamama ba mun rabu lafiya? Sai ya dinga gaggaya min maganganu marasa dadi da suka tsaya min arai na, ya kalli tsabar ido ne yace wai ni ban cancanci in mallake ki ba, saboda yafi sha'awar Ki auri mutun mai tsantsar ilmin addini, mai jin tsoron Allah, Mai kuma kyawawan halaye, kuma koda zaki ce kina sona ba zai bari ki aure ni ba, ballema yasan jininsa bazai ta6a ƙaunar fasiki irin na ba, ni da ke sai dai hange daga nesa amma aure har abada ba zai yiwu tsakanin mu ba, abun da yafi baƙanta min rai daya ce ya yi fatan ace shureim ne yazo neman auranki, jiki na 6ari zai bashi ke, wallahi Ummi badan ni ke nema awurinsa ba a lokacin da har kashe shi zanyi, Kuma idan na kashe shi na kashe banza amma sai banyi hakan ba saboda ni so nake in mallake ki gaba ɗaya, arayuwata bana wasa da abu mai daraja da mutane suke rububi akan shi, sannan kuma bana neman abu ban samu ba, kuma bana yin alheri sai idan nasan zanci riba, naga nasara atare dake shiyasa na nace akan saina mallake ki, amma daga ke har mahaifinki Kuka ƙi amincewa da bukatana duk irin wahalar da nayi akan ki, ba irin magiyar da banyi maku ba gaba daya kuka ƙi jinina, Ni ban neme ki da fasikanci ba, sunna naso na raya dake amma mahaifinki ya yi min bakin da har yau na gaza cimma burina akan ki ummi, idan ma saboda mugun halina na ne yasa yaƙi ba ni ne in aura, to ai naga ko fir'auna mace ta gari ya aura ko"? Cikin fushi da 6acin rai ya ƙare maganar Yana kallon Cikin idanunta da suka kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, she was completely shocked and confused, unable to speak, Gaba d'aya ta gigice ta ruɗe ta kasa magana, ba ta ta6a sanin Musa ya nemi auranta agurin baba Imam ba sai da ya fayyace mata da bakinsa, kuma anan taji irin yadda Aunty laura taci amanarta saboda abun duniya. Numfasawa yayi kafin Ya ɗaura da cewa"ke da mahaifin ki ne Kuka cusa min tsanar Shureim a cikin Zuciyata, dama na kuɗuri aniyar saina mayar dake karuwa saboda wadannan maganganun daya gaggayamin, Yana wani alfahari yarsa mai tsoron Allah, mai kamun kai, mai ilmin addini wato ni mutumin banza ban dace na mallake ki ba sai shureim! Shiyasa Ni kuma Na mayar dake fasika don in bakanta masa, Kuma nayi amfani da shureim saboda in shiga tsakanin ku, nasan ba zaki manta da ranar da shureim Ya kawar maki da budurcinki ba, bayan na kira ki awaya nayi maki muryar shureim ki ka zo daki har muka samu sabani, Bayan kin fita daga dakin, Na dauki waya nakira shureim Nace yazo ina nemansa, saboda nasan zai haɗu dake, Ciwon cikin da kikayi a wannan lokacin bana al'ada bane nine na assasa maki shi, hatta lokacin da shureim Ya taimaka maki kika mike tsaye duk ina atsaye a bakin kofar dakin ina kallon ku. Akan idona Ya fito daga gidanku Yaje chemist ya siya maki maganin ciwon ciki... Ba'agabana komai ya faru ba amma nasan dole Ya faru kamar yadda na tsara, Shureim bai san yayi raping dinki ba, kuskuren da yayi shine kusanta kan shi da ke, anan ne nayi masa sihirin daya tayar masa da matsananciyar sha'awar da in har bai sadu dake ba, zai iya mutuwa, shiyasa ya keta maki haddi Cikin fitar hayyaci...." Ya ƙarashe maganar yana sakin wata yar iskar dariya. Girgiza kai ta shiga yi hawaye wasu nabin wasu kan kuncinta wani kululun bakin cikine ya turnuke zuciyarta, sam takasa furta kalma still idanunta a cikin nashi. Bai damu da halin da take a ciki ba Ya cigaba da yin maganarsa. "Komai dake faruwa Ina samun information gurin Yan leken asirina, daga cikinsu hada officers din dake gadin gidan ku..." ya faɗa yana ɗage mata gira. "Hatta kullan da ki ka yi wa kanki da zuwa asibitin da ku ka yi saida naji komai, naji dadi saboda haka ta ta cimma ruwa, na dasa bakin ciki a zuciyar mahaifinki, na jefa ku a tsaka mai wuya, na sanya maku fargaba da zullumi a zukatanku, amma hakan bai gamsar dani ba, saboda nafison In ga yana kuka da idanunsa, nafison in bar masa tabon da zaiyi silar da zuciyarsa zata buga ya mutu..." wani kallo take binshi da shi me wuyar fassaruwa. "Lokacin da Mahaifinki Ya kira shureim Har ya faɗa masa Ya gaya ma Iyayensa abun daya aikata ma yarsa sannan Su zo neman auranta" "Bai san cewa Alhaji Ubaid baida Iko da kansa ba, na riga da na asirce shi ni nake juya shi son raina, sai abun da na ke so ya ke yi, ko shawara bai Isa yayi da wani ba in ba dani ba, bayan ya kira ni awaya ya sanar dani komai da ke faruwa, naji daɗin yadda hajiya layla taki amincewa, shi kuma da naga yana goyan bayan ya aure ki, saina tunzura shi akan karya kuskara Ya amince shureim Ya aure ki saboda ba mutuniyar kirki bace ke, kin saba min maza, Kina amfani da fuska biyu, ko da naga zai musa min sai nace mashi ina da hujja akan maganata dama najima ina bin diddiginki saboda ina jin labarin fasikancin da kike aikatawa tare da Abokanaina hamshakan masu kudi, Kina jan hankalinsu da surarki, nace masa abun dayasa ma nake bibiyarki saboda bana so ki bata tarbiyar Benazir" Kallonsa kawai ta ke yi saboda ya kashe mata bakin magana. "Bayan mun gama yin waya da shi, Na tura mashi hotunanki da video, nasan za ki yi mamakin a ina na same su ko"? Ya faɗa yana yin wata dariyar izgilanci. Babu alamun zata firta kalma. "Lokacin da nake kawo maku ziyara a gidan dana kama maku haya a germany, kin tuna lokacin da nake zuwa duk weekend in kwana? Bai jira amsarta ba ya cigaba da maganarsa"tsakar dare nake farkawa a lokacin da na saisaici kinyi bacci, batare da sanin kowa ba nake shiga dakin ki, in hau har saman gadonki, saina na tabbatar da sihirina yayi tasiri akan ki tukunna nake rabaki da kayan jikin shi, in shafeki tass in kuma dauki videos dinmu da hotunan mu, Ummi ta haka nake kawar da sha'awarki dake addabata, Bani da abin kallo daya wuce wadannan hotanan na surar jikin ki, da su nayi amfani bayan na yi editing na canza wasu abubuwan da zaisa a gane fuskata a ciki, sai na tura ma Alhaji Ubaid da hajiya Layla a woyoyin su na tunzurasu akan cewa in har suka bari shureim Ya aureki zasu rasa takarar su sannan kuma mutuncin su zai zube a idon duniya...." labari Ya shiga bata tun daga lokacin da ta kai ma Shureim babynsa da irin gallaza masun da iyayensa su ka yi. jikinta har tsuma ya ke yi saboda baƙin cikin daya tokare Zuciyarta, ta karaya da jin irin Bakar izayar da iyayen shureim su ka yi masa shida babynsu. "komai da suke aikatawa ni nake basu shawara ta bayan fage, Kuma Ina sane na kashe layin wayata saboda nasan shureim zai kira ya nemi taimakona, bayan haka ni ne nayi masa asirin da yaja har hankalinsa ya gushe ya binne Yarinyar da hannayensa...." tiryan tiryan Musa ya zayyana mata komai babu abun daya boye mata na daga makircin daya daɗe yana kulla mata. Kamar numfashinta zai ɗauke saboda tsantsar 6acin rai da fusata, har batasan sa'adda ta wanka masa zafafan maruka akan kuncinsa na hagu dana dama. har saida wuyan Shi ya nemi jirkicewa amma ko kadan Biji zafin marinta ba. Damƙe hannayenta yayi a cikin nashi Cikin shaƙaƙƙar murya mai tattare da bakin ciki ta furta"meyasa kayi min haka? Me nayi maka dana cancanci wannan ɗanyan hukuncin daga gareka? Duk irin halaccin da nayi maka ka rasa da me zaka saka min sai da wannan? Tsawon shekara goma sha takwas Ka ra bani da kowa nawa, ka shiga tsakanina da mahaifina, ka kuma raba ni da masoyina sannan Ka ɗauke min ƴata? Fusge hannayen ta tayi daga cikin nashi, Ta damƙi Kwalar rigarshi Kamar zata doke shi, Ta jijjigashi da karfi, hawaye na cigaba da wanke fuskarta tace"kai wani irin azzalumin mutunne? Mugu mara tausayi mara Imani! Kai mutunne Ko Aljan? Kana da zuciya a kirjin ka kuwa? Wallahi da bakin cikin da ka ƙunsa min da ka sani tun farko ka kashe ni" ta faɗa tana bubbuga kirjin shi da hannayen ta. Dukkan Ilahirin jikinta kerma ya ke yi "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, ka kashe ni musa! Ka gama dani! Na mutu! ta faɗa tare da dafe Kirjinta da yayi mata zafi. wani irin jirin tashin hankali ne Ya ɗe6e ta tayi taga taga zata kife ƙasa yai saurin miƙa hannu zai ruƙo ta, ta bangaje shi gefe ɗaya, ta dafe handsofa tana jan numfashi sama sama, duk wata addu'a da tazo bakinta karantata ta ke yi duk don ta samu sassaucin radadin da zuciyarta keyi mata wanda zafinsa yafi na ƙunar wuta. "Zargin da su ke yi akaina ba karya ba ne, Ni ne Jan wuya na gidan Kurkukun ƙaddara, kuma Ni ne na sadaukar da ƴata Unaiza, da ita da yarinyar gurina Twins ne, ko mahaifiyarsu bata sani ba, a ranar data haifesu aranar na sa likitana Ya dauke Unaizah, na kaima Natasha ita don ta raineta, ban taba bari Unaizah tasan wani abu game da dangina ba, Ko sunana na asali, saboda Ina yi mata kallon sadaukarwar da na riga nayi, ni na hana Natasha ta fada bata ba ita ta haife ta ba, na gargaɗeta akan karta kuskura koda gigin wasa Unaizah ta gane ba ita bace mamanta ba, nayi mata kulle saboda bana son ma tafita harta ga abun da zaisa tasan wani abu game dani, hatta wayarta da laptop dinta sai abun da naso take gani a cikin su" bai ƙare maganar ba, ta katse shi cikin karyayyar murya mai rauni tace "nayi danasanin sanin ka da nayi arayuwata, ban taba ganin fasikin mutun, mara imani, azzalumi irinka ba, ka cuci rayuwar mu, Ka zalunce mu, yar cikin ka ma baka ƙyaleta ba, wallahi kaji kunya Musa, jahilin addini jahilin rayuwa, dabba ma tafika Hankali, kwata kwata baka tsoron Allah. ...." bata kare maganarba Ya daka mata tsawa Ko gizau batay ba saboda zuciyarta awuya take komai zata iya aikatawa. "Ki iya bakin ki In har ba so kike In kashe ki ba.." murmushin takaici tayi"ay ni ka riga da ka kashe ni, me kuma ya rage? kuma bazan fasa Magana ba, ka bugeni sannan ka hanani kuka? Bazai yiyu ba, Allah Ya isa tsakanina dakai, Na tsane ka fiye da yadda na tsani mutuwa ta, sannan inaso ka sani, ba mu ka cuta ba, kanka ka cuta, ka daina farin ciki, wlh rayuwarka ce take acikin bala'e da musifa, saboda Allah baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, ka dade kana sa6awa mahaliccinka, ina zaka kai ɗumbin zunubban dake akanka, ko ka yi tunanin wayon ka da dubarar ka ne zaisa ka zauna lafiya ko? Sai gashi Yarinyar daka kafurtar ta mutu a musulma, kuma tayi silar tonuwar asirinka, kuma in sha Allah tun agidan duniya zaka fara gir6ar abun da ka shuka....." Ƙyalƙyalewa yayi da wata shu'umar dariyar izgilanci, ko kadan baiji zafin kalamanta ba saboda yasan ya riga daya gama da ita. Matsowa yayi dab da ita yakai bakinsa saitin Kunnanta"kome zaki faɗa akaina, bazan ji haushi ba, ke baki isa ki 6ata min rai na ba, kuma maganganunki baza su sa in karaya ba, saboda nayi nisan da bana jin kira, kiyi tunanin me zai biyo baya Idan mahaifinki Yaji irin rayuwar sharholiyar da kikayi a america tare dani? A cikin shekaru goma sha takwas sau nawa Ina kwanciya dake, Ina biya bukatata da ke son raina" runtse idanunta tayi cikin bakinci da ƙunci kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu. "Na sanya maki jarabar da ba za ki Iya jure sha'awarki ba, shiyasa kowani namiji yazo maki da buƙatarsa, kike bashi haɗin kai, ko ya baba Imam zaiji idan yaji wannan? Ga hotunanki da videos dinki da na ajiye awayata! baki tsoron In tura mashi yaga kayan takaici? Watakil ma zuciyarsa ta buga Ya mutu..." fashewa tayi da kuka mai cin rai... Cikin halin Ko in Kula Yace"ba yadda za ki yi da ni Ummi, Na riga dana gama morarki, duk da haryan zu banji na koshi dake ba, zan hakura da ke amma ba zan haƙura da abu biyu ba! Zan barki da ranki sai dai ba zan taba bari Ki auri wani da namiji ba har ki koma ga mahaliccinki, abu na biyu zan barki da ranki saboda na samu abinda na ke so..." wani sabon kukan Ta 6alle da shi tamkar ranta zai fita "Ya Allah kafi kowa sanin wacece ni, ni baiwarka ce mai tsananin tsoronka, Mai jin tsoron sa6a maka, mai gudun duk wani abu daka haramta, me yi maka biyayya, Ya Allah ban ta6a nufin wani da cutarwa ba, amma ni anyi min cutarwar da bazan iya jure raɗaɗin ta ba, Amma ba zan tambayi meyasa ka jarabce ni da wannan mugun bawan naka ba, saboda nasan duk wata kaddara data same mu arayu mai kyau ko mara kyau, daga gare ka ne, kuma ba dan baka son mu ba ne, face don ka jaraba imanin mu, kuma kai kaɗai kasan hikmar dake a cikin kowace jarabawa da ka yi mana, Ya Allah ina roƙon ka da tsarkakan sunayen ka, Ya Allah ina roƙonka don son da kake ma fiyayyen halitta Annabi muhammad SAW ka bani hakuri da juriyar cinye jarabawar nan" yayin da ta ke yin maganganun nan yana atsaye gaban ta, ya goye hannayensa Kan kirjinsa, Ba yabo ba fallasa ya ke dubanta. "Ka fadamin Ina ƴata take? Ina son ganin ta, ina son in san Tana araye ko ka kashe ta"? "Tana a tare da ke, Komai da muka tattauna akan kunnan su, Sun ji komai..." aruɗe ta soma ƴan waige waige tana bin falon da kallo don ta a ina ta ke. "Ku shigo da su" kamar daga sama Taji ya Umarta.. Nan take ƙofar Falon ta buɗe, Ta ƙura idanunta akan ƙofar, tana jira taga su wanene za su shigo, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin matsananciyar faɗuwar gaba. Tun daga kasa ta soma kallon kafafuwansu da ke a ɗaɗɗaure da Leg irons, aruɗe ta ɗago da idanunta tana kallon masu shigowa, Giants biyu ne suka taso so agaba, sun rurruke damtsen hannayen su. Bayin Allah Kwata kwata babu kuzari a jikin su. Idanun su sai lumshewa su ke yi sun kasa tsayar da su abude, gaba daya sun haɗa gumi akan fuskokin su, ɗoguwar sumar kansu ta yarfo harta saman fuskar su ta rufe idon su ɗaya. Ido ta zaro a firgice lokacin da taga fuskokin su, tsantsar al'ajabi da ruɗani ne Ya kamata, abun daya ɗaure mata kai tayaya har suka iya shiga gidan Dj suka sato su? Amma da ta tuna matsafi ne, kuma ya saba zuwa gidan dj, batare da wani ya gan shi ba, ta dade tana mamakin hakan sai yau ta samu amsar tambayarta. Wurgar da su Giants din suka yi, gaba ɗaya suka tafi zasu kifa kasa, tayi hanzarin bangaje Musa Ta nufe su, sai dai kafin ta karasa tuni sun jima da kifewa saman floor, a galabaice, ba su iya taimakon kan su ba saboda hannayen su ma a ɗaɗɗaure suke da sarƙa. Durƙushewa tayi kan gwiwowinta agaban su jikinta na 6ari take kallon su. Fuskokin su tabi da kallo ga dai idanunsu abuɗe sai lumshewa su ke yi, sai dai basu Iya motsa koda yatsan su saboda kasalar data kashe musu jiki. Labbanta na kerma ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! U.. Unaisah... bab... batool.. Ku nake gani dagaske ko idanuna ne suke nuna min badaidai ba? Ku faɗa min tayaya har suka ɗauko ku daga gida"? Adabarbar ce ta dubi musa, da wata irin fusatacciyar murya ta furta"don me zaka sa a dauko maka su? Saboda me? Meye haɗinka da su? Laifin me suka maka? shu'umin murmushin nan nashi ya saki, da hannu yai ma giants din Alamar su tafi, a hanzarce suka bar falon. Zukunnawa yayi daga gaban ta "wannan matashiyar balarabiyar, itace ƴar ku ke da shureim, na faɗa maki ne saboda shine hallacin da zan iya yi maki na ƙarshe kafin rabuwar mu" wani irin faɗuwar gaba taji kamar saukar aradu a sukwane take duban fuskar Batool da tsantsar al'ajabi tace "kana nufin itace Ƴata"? Jinjina mata kai yayi"itace..." ta rasa farin ciki zatayi ko bakin ciki? Yatsun hannayenta na kerma Ta tallabo kan Batool ta daura saman Laps dinta, ashe ba banza ta ke ganin kamannin ta da shureim ba, ashe yar su ce, lallai rashin sani yafi dare duhu, yarinyar data mutu akan sonta, ta kwallafa rai akanta, ashe tana atare da ita batare da ta sani ba. Cikin raunanniyar murya ta ce "na kasa yarda cewa kece Ƴata Batool, Jinjirar dana bari a cikin tsumma, jinjirar da aka fadamin ta mutu! Ashe tana araye kuma itace yarinyar da nake atare da ita? na daɗe ina Mamakin kamannin ki da ya shureim, Tun kan nasan wacece ke Allah ya jarabce ni da ƙaunarki, kuma kema haka, ashe ke din gudan jinina ce"! ta faɗa tana shafa fuskarta, wata kerma da jikin Batool ke yi kamar wadda sanyi ya kama, siraran hawayen da ta gani suna sintiri kan kuncin ta ne ya tabbatar mata da taji komai da ta ke faɗa. A hankali ta ɗago da kannata, ta kwantar da shi kan kirjinta, ta rungumeta sosai, wani irin yanayi suka ji a tare da su. soyayyar da suke ma juna ta ƙara nunkuwa fiye da ta. Komai dake faruwa akan Idon Musa, Unaisah dai batasan meke mata daɗi ba, ta kasa juyar da kanta balle taga meke faruwa, sai dai komai da suke fadi a cikin kunnanta, idanunta sun cicciko tab da ƙwalla, gata ga mutumin da take nema ruwa ajallo sai dai ba za ta iya ta6uka komai ba. "Ka faɗamin me ku ka yi masu dayaja har suka rasa ƙarfin jikin su" idanunta jawur ta fada tana kallon shi. "Allurar maye ce nasa akayi ma su.." Cike da takaici ta watsa mashi harara, kafin ta mayar da idanunta akan Batool. "Nasan Kin ji komai daya faru, ba yin kaina bane, Ki yafe min, na tafi na barki ban kula da rayuwarki ba, kiyi hakuri, kada ki tsane ni, wallahi Inasonki fiye da komai na duniyar nan, har raina zan iya sadaukarwa saboda ki rayu" Kalamanta sun karya zuciyar Batool da Unaisah. "Ko ban faɗa ma ki ba, kin san na so ki tun kafin nasan cewa ke jinina ce" Batool tana ta Ƙoƙarin ta buɗe baki don tayi mata magana sai dai takasa, kamar za ta yi hauka. Unexpected Taji Musa Ya damƙi hannun Batool da karfi ya soma ƙoƙarin rabata da ita, a firgice ta ƙanƙameta ajikinta, ji tayi kamar ranta zai zare daga gangar jikin ta. "Kada ka rabi da ita, Ka barmin diyata, Ni na haifi abuna.." ta fada tana kara matseta a kirjinta. "Haihuwarta ka ɗai ki ka yi amma ni ne na yi silar samuwar cikin ta, daga ita har yar uwartata, saboda itama saida na amince tukunna kakanta Ya amince uwarta ta auri ubanta har suka same ta, don haka dama can su nawa ne halak malak, ni ne na sadaukar da su kuma Yanzu Ina buƙatar su, don Haka ki cire rai da su, karma Kisa ran zaki sake ganin su..". maganarsa ta ɗaga hankalinta. Kokawa suka kama yi, Yana jan Batool tana jan ta kamar zasu rabata biyu, batai aune ba, taji An rurruke hannayenta ta baya da karfi suka janyeta, a razane ta dubesu tana haki, Giants ne Guda biyu karfafa. Numfashinta kamar zai ɗauke, Zuciyarta sai tafarfasa takeyi saboda kunar da take ji.. Ta naji tana gani giant dinnan suka dinga janta, tana ta kokarin ƙwace kan ta amma takasa saboda sun fi ƙarfinta. Musa da ke kallonta, murmushin mugunta ya ke sakar mata, ya rurruƙe Batool da hannayensa.. Akan Idonta ta motsa dry lips dinta dakyar da wahala ta furta"mom.. Myyyy..." Duk da sauti bai fito ba, amma ta fahimci me tace, fashewa tayi da kuka tadinga yakunshin su da kai masu bugu amma duk abanza ahaka har suka fitar da ita daga cikin falin. Suna jiyo sautin kukan Ummi acikin kunnuwan su. Jefar Da Batool yayi ta faɗa kan Unaisah. baisan meyasa ya kasa cire Ummi aran shi ba, Kukanta yana Illata Zuciyarshi sai dai baya jin zai iya hakura da burinsa akan Yaran, dole Ya salwantar da su don Ya Cika burin shi, bama zai ta6a bari Ta rayu da yar shureim ba, tun da har taki ɗaukar cikin sa, dama da haushin zubar da cikinsa da tayi abaya. Wayarsa Ya zaro Ya kira wani layi, bayan anyi picking ya furta"Mark, Kasa driver Ya kaita Obie Estate, kada ya ƙarasa da ita ciki, ya aje ta akan titin estate din" "kai kuma ka shigo Ciki, bana so mu 6ata lokaci, zasu iya farmakar mu a kowani lokaci, nafiso mu hanzarta kai su Gidan Kurkukun ƙaddara, kafin su ritsa damu" "Okay Sir," rejecting call din yayi, tare da mayar da hankalinsa akan Su Unaisah dake a yashe kasa kamar matattu wata mahaukaciya ya saki hahhhahahaha... _babu wani mahalukin daya isa Ya dakatar dani!_ ya faɗa yana yiwa kansa kirari. Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168. *DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE✍️💋* Around ƙarfe Goma na dare Motar Taj ta ƙaraso layin gidan Alhaji Musa, baka jiyo sautin komai saina dariyar su da firar da su ke yi cikin nishadi. Officer ne ke yin driving dinsu, yayin da su ke a mazaunin baya na motar, dawowar su kenan daga Sightseen, a hankali officern ya tsayar da motar kusa da gidan. "Kin faranta min rai, gaskiya dana rasa ki danayi danasani Ummu Unaisah" farfari tayi mashi da idanun ta.. "Ni yakamata nace haka babe, kwanakin nan dakyar nake bacci saboda tunaninka, jurewa kawai na ke yi amma wallahi nakosa ka maidani ɗakina.." ta fada tana zumbura mashi ƙaramin bakin ta. Har wani lumshe idanun shi ya ke yi idan suna kallon juna, cike da shauki, da alama Taj ya manta data gida daya baro, ko maganarta bai son yi agaban Benazir, bai ta6a gigin sanar da ita yayi aure ba saboda yasan halin ta da kishin tsiya. "Ki sauka zamu juya, na bar yara suna jira na, nasan ba lallai suyi bacci ba" ya faɗi hakan ne ba dan ya gaji da ganin ta ba, sai dan saboda yanayin da take jefa shi. Maƙe kafaɗa tayi da shagwa6a tace"ai wallahi idan kana so in sauka sai ka yi min kiss" yadda tayi maganar kamar karamar yarinya. ga dukkan alamu sun manta basu kaɗai bane a motar, Officer yayi zuru yana satar kallon su ta mirror gwanin burgewa. "Pls, dare yana ƙara yi, nasan su mommy suna ta jiran dawowarki" rigima tasaka mashi har sai da tasaka shi dariya. Saida ta bari ya shagala yana ta tikar dariya tay wuff ta manna mashi kiss on his lips, zare idanu yayi kafin ya farfaɗo daga duniyar shaukin da ta jefa shi, tayi saurin buɗe murfin motar ta fuce da dan gudunta ta nufi Gate din gidan tana dariya benazir kenan hali na nan ya fada a xuciyarshi tare da girgiza kai. Gaba daya takashe mashi jiki, langwa6ar da kansa yayi jikin seat dinsa, tare da lumshe idanun shi, kamshin turarenta ya cika hancin shi, komai daya faru yau a tsakaninsu yake tariyowa, murmushin gefen fuska ya saki a hankali ya furta"I love you my Benazir, my hero wife, mother of my precious daughter..." Har Officern ya tada motar yayi reverse taj bai sani ba, gaba daya ya shagala da tunanin Benazir kamar ba yanzu suka rabu ba. Adaidai Lokacin da motar shi Ta ƙaraso main gate, sai ga Motar Chief Owais ta nufo bayan tashi, A jere suka ƙarasa shiga Gidan at same time su ka yi parking. Taj ne ya fara fitowa ya na ɗangyasa ƙafar shi, ya nufi Motar Chief Owais tare da buɗe masa Cardoor, fitowa yayi jikin shi sanye da jallabiya Ya mika ma Taj Hannu su ka gaisa. Har sun juya zasu nufi main falo, muryar Security Officer ta katse su da ɗan saurin shi Ya nufo su tare da sara masu kafin Yace"barka da dawowa Sir, ɗazu bayan sallar magrib, Big guy yazo.." bai kare maganar ba ganin wani kallon kallon da suke jefawa juna shida taj kallo mai cike da tsantsar rudani.. Har suna hada baki gurin furta"Big guy? Wani big guy din.." washe baki security Officer din yayi"big guy namu, ddg, Omar, da kanshi yazo a cikin motar shi.." aruɗe Taj yace"ban gane me kake nufi ba? Omar wanda yake a kwance gadon asibiti Yana a coma ko kuwa wani Omar din ka ke nufi..." da jin wannan maganar yasa Officer din ya ɗan ruɗe. "sir, kana nufin bakusan komai game da samun lafiyar sa ba? Amma ya fada mana kun sani har yace may be saboda sirrin aikinku yasa baka sanar damu ba.." Tsantsar Al'ajabi Ya hana Chief furta kalma.. Adabarbar ce Taj yace"da yazo ya shiga ciki, ko kuwa a bakin gate ya tsaya.." arude officer din Yace"sir, ya shiga Ciki..." ba su karasa sauraron shi ba, cikin sauri suka nufi main falo, Taj tuni ya manta da ciwon kafarsa, saboda tashin hankali. Abun daya daure masu kai, sunsan Omar bai farfado daga Coma ba, don da ace ya samu lafiya sune mutun na biyu da zasu sani bayan docs din dake kula da shi. Suna shiga falon suka nufi dakin Su Unaisah tsabar sauri da rawar jiki har bangazar juna su ke yi a sukwane suka ci burki lokacin da suka dira kofar su cikin daki basu taras da kowa ba.. Wani irin matsanancin faduwar gaba su ka ji a lokacin daya suka zaro wayoyin su daga cikin aljihu.. Miss calls suka gani na Unaisah Sakon data turawa Chief ne ya bayyana akan screen din wayarsa. _"Husband to be, yaya omar yazo zai tafi da mu asibitin da aka kwantar da yan uwan mu inmates, don mu duba lafiyar su, Ni dai hankali na bai kwanta da shi ba, ya matsa mana sai mun bi shi, kuma kamar ba ya omar ba wallahi, Muryarsa ƙatuwa, idanunsa jajaye, kuma ko tabon ciwo babu ajikin shi, kasan da zuwan shi? Mu bi shi ko mu tsaya"?_ A razane suka kalli juna, bayan da suka gama karanta sakon Unaisah. "Sir, Ko dai Umar din ne? Tun da in bashi bane Security Officer ba zasu taba bari ya shigo ba, sannan kofar falo tana da tsaro dole sai na'ura ta tantance shi zai iya shigowa ciki, in har ba umar bane bazai taba iya shigowa ba.." girgiza kai Chief owais yayi"Taj, ba Omar bane, ka yi tunani mana, in omar ne meyasa ba akira an faɗa mana ya farfado ba? Omar koda ace ya farfado daga Coma Ina yaga karfin da zai iya tuƙo mota yazo estate din nan? Motar wacece? Gaba daya motocin Omar suna A parking space, Taj bana fata abun da nake tunani ya tabbata .." Yana ƙarashe maganar, ya juya da sauri Taj yabi bayanshi kaitsaye suka nufi security Officers tunkan su karaso Officers din suka nufo su cike da fargaba saboda Officer din daya fara tarar su da maganar ya sanar da sauran akwai matsala. "Sir meke faruwa"? Cikin 6acin rai yace "tayaya akai kuka bari Ya shigo batare da iznina ba huh? Har suna haɗa baki gurin furta"Sir, Omar ne, tayaya zamu hana shi shigowa? Bayan yana da ikon yin komai a cikin gidan ka, kaine kace babu banbanci atsakanin ka da shi..." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya"baku da hankaline? Ba mun fada maku Omar baya acikin hayyacinsa yana a gadon asibiti har yau bai farfaɗo daga coma ba.." faɗa ya balbale su da shi ta inda yake shiga batanan Yake fita ba, Taj sai kokarin Shawo kanshi ya ke yi Yaƙi sauraron shi. Hankalin su ba karamin tashi ya yi ba, tun da suke da dg basu taba ganin bacin ransa irin na yau ba. "Wallahi Sir Omar ne, idan har ba Omar bane tayaya zamu barshi Ya shiga ciki, kuma tayama zai iya shiga batare da na'ura ta tantance shi ba? Sir ba yau muka fara maka aiki ba, mu fa amintattunka ne, bamu taba maka karya ba, kuma bamu ta6a cin amanarka ba, muna yin iya kokarin mu don ganin mun ba ku tsaro, tsakani da Allah muke atare dakai da zuciya daya, Omar ko a mafarki muka ganshi zamu gane shi balle kuma a zahiri"_ "In har Omar din ne meyasa ku ka bari Ya tafi da su Unaisah batare da kun kira kun sanar dani ba"? Zazzare ido su ka yi cikin rudu da tashin hankali kwata kwata basu san ya tafi da yara ba. "Sir ya tafi da su? Amma tayaya akai ba mu gani ba"? "Ni kuke tambaya? Saboda ganganci da rashin kula irin na naku Har wani bare Ya shigo min gida, Ya tafi da yara har biyu duk baku sani ba, baku da amfani, Gidan Dg da aka sani da tsaro..." Taj sai kokarin lallashin shi ya ke yi Yaki ma Ya dube shi. Yana magana Huci na fita"tsawon wani lokaci ya dauka kafin tafiyarsa"? Cike da jin shakkarshi wani Officer Yace"ya yi mintuna shabiyar a ciki, bamu san lokacin daya fito ba, sai dai muka ga babu motarsa a inda ya yi parking ɗin ta, kuma da tafiyarsa yanzu awa ɗaya da rabi" Runtse idanunshi yayi tare da ɗaura hannunsa ɗaya saman kan shi.. "Wallahi, Idan har wani abu ya faru da su, ku kuka da kanku.." yana faɗa ya juya cikin zafin nama Taj yabi bayan shi.. Cikin rudu da tashin hankali wasu daga Cikin officers din suka shiga motocinsu da wata irin jiniya suka fice don suje neman Omar. Daga gaban Motar shi ya tsaya tare da kiran layin doc din dake kula da Omar, bayan ya daga cike da fargaba ya tambayi ya jikin Omar"? Doc din yace"har yanzu bai farfaɗo ba, amma muna ganin cigaba a lafiyarsa, kuma muna sa ran zai iya farfaɗowa a kowani lokaci..." da jin maganar da doc din ya faɗa nan fa hankalinsu Ya ƙara tashi.. Jikin Taj ya hau yin kerma "in kuwa hakane, Koma wanene ya ɗauke su zai iya yiyu wa daga Elders ne, tun da har ya iya sauya kamannin shi, hakan na nufin matsafi ne, amma tayaya za'ay mu san wanene Ya ɗauke su? chief ne ya jefa ma kanshi tambayar da bashi da amsarta. Damuwace tsantsa akan fuskar taj "inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un bana fata hakan Ya kasance saboda nasan ba zasu masu dakyau ba, da nasani ban tafi nabar su ba, laifina ne, da duk hakan bata faru, rashin sani yasa dukan mu bamu ga kiran Unaisah ba, ni nasan tayi iyakar kokarinta donta same mu awaya, kuma inaji raina ba hakanan aka tafi da su ba, saboda Unaisah tana wayou dole akwai wani abu da akayi masu..." zafafan hawaye ne suka wanke Fuskar shi, ga wani zazzabi da ya rufa sa. Sum ma rasa ta ina zasu fara binciken wannan al'amari? Wanene Ya dauke su? Meyasa aka sace su? Da wata manufa akayi hakan? Me kuma zai biyo baya!. Babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sam sun manta da batun Ummi. Taj Ne ya kawo shawarar Su jaraba Bin diddigin Layin Unaisah, yana tunanin Ta tafi da wayarta tun da basu ganta a dakin su ba. A hanzar ce Chief Ya fara ƙoƙarin yin tricking din layin ta ta hanyar wayar sa, sai dai bai Iya gano komai ba duk ƙwarewar sa. Har Number dinta Ya turama wasu Cyber Experts daga Cikin jami'an su, amma daga baya suka kira tare da sanar da shi sunyi iyakar bakin kokarinsu don ganin sunyi hacking layinta, amma sun kasa gano taƙamaimai location din da wayar ta ke, suna tunanin tana a gurin da babu network ko kuma an jefar da wayar wurin da baza a iya tracking ba. bakin Ciki ne Ya cika Zuciyoyin su. Daga shi har Taj an rasa me lallashin wani kowa Ya shiga damuwa. Tunanin komawa Cikin gidan su ka yi don su kara bincikawa su tabbatar babu su din don jin abun su ke kamar ba gaske ba. Babu inda basu duba ba, suma officers din gidan sun tayasu neman su, babu su babu alamar su, Kowan nan su sai da ya haɗa gumi akan fuskarsa. Falo suka koma su biyu shida Taj suka zauna saman Sofas kowan nan su ya zabga Uban tagumi kamar marasa galihu. Unexpected suka tsinkayi sautin tafiya, kusan atare suka kalli Mai shigowa cike da sa ran su Unaisah ne. Kamar mahaukaciya ta faɗo Falon, Ko takalma babu a kafafunta, fuskarta jaga jaga da hawaye, idanunta sun kumbura suntum, gyalenta ma A hannu Ta ruke shi, har suna haɗa baki gurin ambaton Sunanta UMMI.. Kusan atare suka mike suna Kallonta ganin Yadda ta sauya lokaci ɗaya kamar wadda tasha bugu. Kaitsaye Ta nufi Chief Tana karasawa gaban shi, Ta zube kan gwiwowinta, kamar zata haukace masu, Cikin Kuka da wata irin raunanniyar murya ta furta"zai.. Zai kashe su! Shine Ya ɗauke su! Suna a wurin shi, Kashe su zai yi..." gaba daya ta ruɗar da su sun kasa gane kan maganarta. Faduwar gaba suka ji, daram dararam, a razane suka kalli juna. "Ummi ki yi mana bayani meke faruwa? Su wanene zai kashe? Kuma wanane kike magana akai"? Cikin shasshake murya tace"U..U..Unaisah, da Bab.. Ba tool, Ya faɗa min komai, Ya cuce ni, ya yaudare ni, shiya rabani da mahaifina Ya kuma rabani da kowa nawa, Batool diya ta ce, Ita ce babyn dana bari, bata mutu ba, tana araye, shiya sadaukar da su yanzu kuma Ya kara ɗauke su ....." Tsantsar tashin hankali ne ƙarara akan fuskokin su, Sun riga da sun gane wanene Ya ɗauki su Unaisah, dama sunata hasashen zasu kawo masu farmakin bazata, ba zasu ta6a kawo ma ransu ta kansu Unaisah zasu biyo ba, Wlh sun shammace su, ga kuma Mamakin kasantuwar Batool diyarta. "Ummi Ki natsu ki fada mana komai da kuka tattauna da shi, watakin mu samu ta hanyar da zamu iya ceto rayuwar su, mu kan mu bamusan tayaya akai suka dauke su ba, saboda ba mu a cikin gidan" Dakyar ta iya fayyace masu komai da Alhaji Musa ya faɗa mata. Ba su yi mamaki ba saboda sun riga da sun san komai itace bata sani ba, abun da yafi bakanta ransu ta yadda ya bayyana mata komai da yayi mata batare da tunanin wani hali zata shiga ba. Kwata kwata basu tambayeta meyasa tayi gangancin daya gano ta ba, duba da halin da take a ciki ba. Haɗuwa sukayi atare suna Lallashinta tare da yi mata alkawarin zasu yi iyakar bakin ƙoƙarin su don ganin sun Ceto rayuwar su. Dakyar suka shawo kanta, Taj Yace Ta shiga ta kwanta, ta huta. Tace mashi ita da hutu Har abada, bata tunanin zata iya rayuwa batare da Yar ta ba, don basu san me take ji a cikin zuciyarta ba. Tsananin tausayinta ne Ya kamasu, kamar zasu zubda mata ƙwalla. Tace ma Taj ya ara mata wayar shi, Tana son tayi kira. Ya tambayeta wa zata kira? Tace Ya shureim tana son Ta fada masa komai. chief Yace tayi hakuri ka da ta daga mashi hankali, Ta bari su fara samun mafita tukunna Kuka tasaka masu tare dayi masu magiya tana rokonsu akan su bata ta kira shureim tana son ganin shi tana son ta nemi yafiyar shi, sannan tana so ta faɗa mashi game da babyn su. Ƙin amincewa su kayi, gaba daya ta rikice masu kamar ta fara fita hayyacinta sai sambatu ta ke yi masu, can Kuma data galabaita wani matsanancin ciwon 6arin kai Ya taso mata, ta fara ganin jiri jiri tun tana karanta addu'o'i harta kasa, ta fada masu kanta ciwo yake mata, kirjinta zafi, numfashinta zai ɗauke. da sauri chief ya juya yaje medical room din gidansa ya ɗauko mata sedative, ya dawo falon tare da Glass of water a hannunsa ya mika ma Taj ya kar6a tare da miƙa mata maganin hannunta na kerma ta kar6a ta tura abaki, ya kanga mata ruwan ta sha, har saida takusa ƙwarewa kamar za ta yi amai ta kama kakari. sun bata maganin da nufin ta samu tayi bacci amma sai ya zamana kamar sun ƙara ninka mata azabar radadin da take ji, baiwar Allah kamar ƙaramar yarinya ta dinga rusa masu kuka tana ambaton sunan Baba imam, shureim, Babynta. Har tambayar ta su ka yi ta fada masu address din Guest house din sa, tace bata sani ba, sau biyu ta ta6a zuwa, kuma duk zuwan da zatayi shi ya ke zuwa ɗaukarta da motar shi, baya bari drivern daya ɗaukota ya karasa da ita, ba zata iya gane komai ba, ko sunan anguwar bata sani ba. Gudun kada ta hadiyi Zuciya ta mutu Yasa suka yanke shawarar bata wayar donta kira su, bayan Taj Ya nuna mata Contact din su a wayarta yace ta kira su ta ce su zo amma kada ta fada masu meke faruwa ta bari sai sun zo. dama Suna da burin Su sasanta tsakaninta da Mahaifinta, kuma a wannan ga6ar tana bukatar su saboda su kadai ne zasu lallasheta taji don wlh gab ta ke da ta zare. Chief bai ga ta zama ba, yace ma Taj Ya kula da ummi, shi zai tafi tare da jami'ai su nemo su, Taj yace bazai iya zama ba, ƙwara su tafi a tare, saboda Hankalinsa ba akwance yake ba, in har ba dawo da su Unaisah akayi ba. Chief yace ya kwantar da hankalinsa in sha Allah ba abun da zai faru da su, amma ba yadda za'ay su tafi da shi saboda har yanzu ƙafarsa bata daidaita ba, kuma gurine mai hadari zasu je, Taj yana sharar kwalla yace"bazai gane ba, tayaya ma zai iya kwantar da hankalinsa bayan yaransu suna a hannun fasiƙin mutumin da babu imani a zuciyarsa? Wa yasan me zai yi musu? Dakyar Chief ya lalla6a shi harya amince zai zauna badan yaso ba. *Dr. Shureim💔* Bayan ya kammala Yin Nafila Ya buɗe kur'ani yana karantawa, wayarsa ce ta soma yin ringing, saida yakai aya, Ya dubi wall Clock Karfe shabiyu, Aransa ya ayyana wanene ke nemansa a irin wannan Lokacin? Ko dai na cikin gida ne"? Mikewa yayi daga kan prayer mat din, Ya nufi wayar dake aje kan gadon nasa. Daukar wayar yayi da rudu Yake kallon bakuwar Number din da aka kirasa da ita. Baisan wanene ba, Kuma ba ya jin zai iya picking call at this time duk da wani sashe na zuciyarsa yana shawartarsa dayabi bayan kiran. Har zai aje wayar wani Kiran ya kuma shigowa. Picking Yai tare da kara wayar Yana kokarin Yin sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sheshshekar kukan mace ta cikin wayar, gabansa ne ya fadi Bai gane wacece ba, addu'ar neman tsari Ya karanta a cikin zuciyarsa kafin Ya yi sallama tare da tambayar wacece? "Ya shureim ni ce, Aishatu bintu imam ce.." sa'ilin da muryarta ta ratsa dodon Kunnansa wani sanyi mai haɗe da dadi yaji a cikin Zuciyar shi, kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna Adabarbarce Ya furta"Aisha dagaske kece? Ba mafarki nake ba? Ke da kanki kika kira ni"? "Ni ce Ya shureim, Ba mafarki bane..." bai karasa jin zancen nata ba Ya zube kan gwiwowinsa Ya fuskanci alkibla yayi sujudusshukr.. Time din da ya dago Hawaye farin ciki ne a kwance saman fuskarsa ga wani tsantsar annurin farin Ciki daya bayyana a tare da shi. "Aisha, har yanzu Ina kokwanto.." "Ya shureim, Inason ganinka! pls ka zo, idan ba kazo ba zan iya rasa raina, kai kawai nake son gani.." muryarsa da zumuɗi ya firta"basai kin rokeni ba, Zanzo yanzu, Karki damu, ki kwantar da hankalin ki.." Katse kiran yayi, jikinsa na 6ari Ya dauki Car key nasa, cike da zumuɗi ya fito Jikinsa na bari cikin sauri Ya nufi Hanyar fita daga Main falo.. Kafin Ya ƙarasa Ya tsinkayi Muryar Benazir a cikin kunnansa. "Ya shureim!..." ba dan Benazir ce ta kirasa ba da ba abun da zai hana Yaki waiwayonta.. Juyowa yayi fuskarsa da fara'a ya ke duban ta, sanye take da kayan bacci riga da wando maroon tayi rolling headscarf, sai da ta matso kusa da shi Ya lura da wayar dake a hannunta, Fuskarta duk a yamutse. Car key din hannunsa Ta kalla"ya shureim Ina za ka je da daren nan? Ka duba lokaci kuwa? Murmushi ya yi"Ki taya ni Murna Ukhtyna, Aisha ta kira ni yanzun nan awaya, tace tana son ganina, Inzo gidan dg" aruɗe ta furta"Aisha kuma? Ya shureim yaushe aisha ta sauko daga kan dokin zuciyar da ta hau da har zata kira ka? Ka kuwa duba kaga ita dince ta kira ka dagaske? "Bakuwar Number ce amma Tabbas Aisha ne, Ni naji muryarta.." "Muga number din" ta fada tare da mika masa hannu bayan Ya bata wayar ta dubi contact din nan take ta gane Number Taj ce. "Yanzu Can zan tafi, tana jira na" "Yaya shureim dagaske Aisha ce, number data kiraka da ita, ta Daddyn Unaisah ne amma meyasa take son ganinka a irin wannan lokacin? Ta faɗa da rudu akan fuskarta. "Kada ki tsayar Dani Benazir, ki bani kawai in tafi.." ya fada yana mika mata hannu.. Tana kokarin mika masa wayar, suka tsinkayi Muryar Mami a cikin kunnuwan su.. "Su wanene nan"? Ta fada tana nufo su, atare suka dube ta, Damuwace ta bayyana akan fuskar Shureim har saida Ya harari Benazir ganin taja masa har mami tagansu yasan ba lallai tabar shi Ya fita ba. Ƙarasowa tayi daga gaban su ta tsaya"meya ke faruwane? Ina kuma zuwa? Ta fada tana nuna key din hannun dr shureim.. Kamar marasa gaskiya sukayi shiru suna kallon kallon atsakanin su.. Hakan Yasa ta fahimci da akwai wani abu dake faruwa kuma basa son sanar da ita.. Har ta buɗe baki zata kuma yin magana phone ringing din Dr shureim Ya katse mata hanzarin ta, ganin number da Aisha ta kira ne yasa shi saurin yin picking.. "Ya shureim ka taimaka min ka zo, naji komai daya faru, bayin kanka ba ne, akwai abun da nakeso in fada maka dan Allah kazo, magana ce mai muhimmanci" Waro idanu waje su ka yi gaba ɗayan su sun ruɗe sosai, daga mamin har Benazir din sunji komai, basu karasa jin ƙarashen zancen ba kiran ya katse.. Arude Mami Ta kar6e wayar shureim tadinga kiran layin ba'a dagawa, kallon su tayi cikin rudani tace"ku fadamin wacece wannan ɗin? Meyasa take neman ka? Akan me take yin magana? nasan kun sani, kada ku 6oye min ku fada mun kawai in ba haka ba zan sa6a maku.." Ta karashe maganar kamar zata doke su.. Ran mami Ya 6aci jin sunyi shiru basu Bata amsa yasa ta daka masu tsawa"wai don ubanku ba zaku bani amsar tambayar da nayi maku ba? So kuke ku haukatani ne..." cikin rawar murya Benazir ta ce"aisha ce mami, kiyi hakuri mun boye maki, amma Aisha ce, tana agidan Dg, Kuma Yarinyar nan Azeezaty, bakowa bace face Unaisah ƴata Angel, mahaifinta kuma shine Taj mijina...." wani faduwar gaba Mami taji, sai zare idanu takeyi saboda al'ajabi.. Ruƙe Hannunta Benazir tayi"mami zanyi maki bayanin komai, mu ma bada son ranmu muka 6oye maki ba, Dg ne yayi mana warning akan karmu sanar da kowa game da su saboda Rayuwarsu tana acikin hadari, bazai yiwu a yanzu in fayyace maki komai ba, amma dan Allah mami kuzo mu tafi can gidan, zaifi mu hadu mu duka kowa yaji komai dake faruwa, Saboda Inaji araina Akwai wani abu dake faruwa shiyasa Aisha takira shureim ta nemi da ya je, kuma dama suna bincike akan case din daya shafe mu da kuma shi Taj din..." Cike da zumuɗi Mami Tace toh, bari in ɗauko hijabi Cikin sauri Ta nufi daki, tana shiga ta taras da Alhaji Ubaid Yana kokarin fitowa daga toilet, koda ya tambayi daga ina take? Tace mashi Ya biyota kawai su tafi, akwai wani babban al'amari" Badajimawa ba, sai gasu sun fito tare da Alhaji Ubaid din, sai tambayarta yake ina za su je cikin daren nan? tace mashi Yabi su kawai in sunje zai gani, da yaga Benazir da shureim Hankalinsa Sai ya kara tashi, bai dai tambaye su ba, yabi bayan su Suka fito daga Falon, Cikin sauri suka nufi Parking space, gaba dayansu a motar Dr shureim suka zauna, Hajiya Layla da Alhaji Ubaid suna a backseat, Benazir tana a front seats tare da Dr shureim. Key ya yi ma motar, tare dayin riverse Ya nufi Gate, sam Sun manta da Security Officers, aikuwa suna hango motarsu suka Tunkareta gadan gadan.. Hajiya layla tace karya kuskura ya tsayar da motar zasu 6ata masu lokaci ƙarshe su hanasu fita, tun da gate din a buɗe yake da alama wasu ne suka fita aka bude ba a kaiga rufewa ba ya fuce da su kawai. Alhaji ubaid yace kada ay haka su bi komai a sannu. Dr shureim dayafi su zumudi ya kure speed din Motar, Gadan gadan Ya nufi Security Officers din kiris Ya rage Yabi takansu da mota Hakan yasa suka dare tare da bashi hanya, Ya ba motarshi Wuta Ya kara gaba. Wasu daga Cikin Security Officers din Har bin Motar shi su ka yi sai dai tuni sunyi musu nisa. Sai da ya tabbatar da sun 6ace masu sannan Ya rage gudun Motar. Wayar Benazir ce ta soma ruri cikin sauri Ta duba Mai kira ganin Anila yasa ta yi picking tare da kara wayar a kunne Tana niyar yi mata sallama kukan Anila Ya katse ta, Arude Ta furta"Anila? Meya faru? Meyasa kike kuka"? Maganar da tayi ne ta karkato da hankulan su Hajiya layla ga kallon su. da wata irin raunanniyar Murya ta furta"Benazir, Muna cikin tashin hankali, Uncle Ya kashe ta, mun ga gawarta, yanzu haka da na ke yi maki magana gidan mu a kewaye ya ke da sojoji" Dafe kirji Benazir tayi"Inna Lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." "Menene? Meya faru? Benazir meke damun ta ne? Me ta fada maki"? Su mami ne Suke ta tambayarta Cikin rudu.. "Bani kadai bace Anila, Ina atare da su mami, Yanzu haka Muna akan hanyar zuwa gidan Dg, Aisha ce ta kira ya shureim tana kuka ta bukaci tana son ganin shi ina tunanin wani abu yana faruwa acan, in ba damuwa mu haɗe acan.." Ta amsa mata da toh Bayan tayi rejecting Call din ta dubi Dr shureim da ke kallon ta kafin ta mayar da dubanta ga su mami da ke abaya. "Anila ce, ta fada min wani abu ya faru agidansu, bana iya jin me take cewa kamar kuka takeyi, Amma nace mata mu hadu a gidan Dj nasan zata zo" Cike da fargaba suka amsa mata da toh kowa da abunda ya ke saƙawa A cikin ran su.. Lokacin da motar su ta haura kan Titin Obie Estate, Cikin sauri Benazir ta kira layin taj, bayan yayi picking ta fada mashi game da zuwan su, tace ya taimaka yayi masu hanyar da zasu shigo cikin sauki, ya ce mata kada su biyo ta gate din gaba, su shigo ta gate din baya na estate din, zai sanar da securies din. sallama su ka yi da shi, bayan ta fada ma dr shureim abun da ya ce, Ta yi shiru zuciyarta cike fal da fargaba, Muryar Taj da taji ta daga hankalinta kamar baya a cikin nutsuwar shi. ta gate din baya suka shiga Estate din basu sha wahala ba, saboda already Taj Ya sanar da securities din game da zuwansu.. A parking Space dr shurem ya yi Parking din Motarsa. Bayan sun fito, Hajiya layla ta dinga jinjina kanta, ganin haduwar tamfatsetsan Gidan dg, tayi zaton daga gidan Alhaji musa an gama Gini mai kyau a Abuja sai yau da Allah Ya kawota gidan Chief. Shi Kanshi Alhaji Ubaid Ya jinjinama haduwar Villa din.. dr shureim ne ya fara yin gaba jikinsa sai tsuma yakeyi saboda zumuɗi, da sauri suka Bi bayan shi. Basu kaiga ƙarasawa ga Kofar Ba, Horn din mota Ya katse masu hanzarin su, sunyi tunanin su Anila ne Hakan Yasa suka dakata tare da juyawa suna kallon Motar da ke shigowa da matsakaicin gudu ta nufo Entry Hall sai da takusa ƙarasowa inda suke suka ga gudun nata Ya ragu slowly ta yi Parking daga gefen su. Gaba ɗaya suka kura idanu suna jiran ganin wanene zai fito daga cikin Motar. Lokacin daya bude cardoor din Ya zuro kofarsa basu gane wanene ba amma daya karasa fitowa gaba daya suka Zare idanun su, Har suna hada baki gurin furta"Sheikh Imam Malik..." kwata kwata baisan da zamansu ba, Har saida suka ambaci sunanshi tukunna ya lura da su. A hankali ya ɗaura idanunshi akan fuskokinsu, Mutanan da har abada bazai ta6a mantawa da irin Butulcin da su ka yi masa ba, Tsantsar mamaki ne akan fuskokin kowan nan su daga shi har su din sun kasa motsawa. Tun Lokacin da suka samu sa6ani Yau kimanin shekara goma sha takwas da zumuncin su Ya yanke basu kara haduwa ba kuma babu wanda ya nemi wani, sai yau da su ka yi haɗuwar bazata cikin ikon Allah agidan dg. Wani irin nauyin shi da kunyarshi ne Ya lullu6e su, Hajiya layla ji tayi kamar ta haƙa kasa ta binne kanta saboda kunyar Imam malik, duk tasha jinin jikinta, Saboda Kunya yasa ta dinga kare fuskarta da kasan hijab din ta. Alhaji Ubaid kuwa Kasa jure hada idanunsa yayi dana sheikh Imam, wani irin kwarjini yayi masu. A hankali Yake binsu da kallo mai wuyar fassaruwa.. Kamar yadda suke mamakin ganin shi haka shima Yake mamakin ganin su, komai daya faru arayuwar su suka soma tunanowa kamar a yanzu yake faruwa, ba zai ta6a mantawa da rashin mutuncin da sukayi mashi ba, ganin su da ya yi sai ya zamana kamar sun fama raunin dake a acikin zuciyarsa ne. Kallon kallo su ke jefawa junan su, dr shureim da Benazir sun yi zuru da idanu kamar wadanda suka ma sarki Karya fadawa suka turke su. Shureim ne yayi karfin halin tunkarar sa duk da shakkarshi da yake ji, zuƙunnawa ya yi daga gabansa cikin sanyin Murya ya gaishe da shi cike da fargaban martanin da zai mayar masa. Kallonshi yayi kawai tare da juyawa ya haura kafarsa Ya nufi Ciki, Ransa Ya 6aci da ganinsu, Dayasan zai hadu da su da ba abunda zaisa Ya tako kafarsa Yazo gidan. Kasa mikewa Dr shureim yayi, saboda karayar da zuciyarsa tayi, kwata kwata baiji haushin abun da baba Imam yayi masa ba, duk da baiji dadi ba, amma kome ya faru yafi ganin laifin iyayensa, saboda sune suka dasa masa ƙiyayyarsu a zuciyarshi.. "Ya shureim, ka yi haƙuri, Ka tashi mu shiga ciki" cikin sanyin Murya Benazir ta faɗa, yayin da take tunkararshi, Ta ruko hannunsa acikin nata, lokacin daya ɗago hawaye ne kwance a saman fuskarsa. "Ba zan Iya shiga ciki ba, har yanzu baba Imam fushi yake damu, Nasan kona shiga bazai bari mu gana da Aisha ba, ku shiga zan jira ku a mota" ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka. Tsananin tausayinsa ne Ya kama su, iyayen nasa da yake sa ran zasu lallashe shi su taimaka masa ahalin da yake a ciki sam sun kasa magana saboda su kan su sun muzanta agaban Imam Malik, Gaba ɗaya sun sare har sun fara tunanin komawa Gida. Basu Gama Yanke shawara ba, sai ga Motar Abie Ta kunno kai, daga Inda su ke suna iya hango su a cikin motar, mutum biyu ne agaban motar Abie da isod soldier. Security Officers ne suka tsayar da su, amma daga baya suka ga Motar ta nufo ciki alamar sun samu iznin shigowa.. Yana tsayar da Motar, Anila ta fito daga back seat, fuskarta sharkaf da hawaye, ta goyo junaid abayanta, cikin sauri Ta nufi Benazir suka rungume Juna.. Daga Bisani Abie Da Mami suka fito Daga motar, kwata kwata babu walwala akan fuskokin su daga gani suna a cikin matsanancin Hali na damuwa. Bayan sun gaggaysa da juna, Kafin daga bisani suka dunguma Izuwa Cikin gidan, Gaban kowan nan su na faduwa rass rass daram dararam saboda zullumin me zai biyo baya, gasu dai dukan su sun haɗu. Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___✍️~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168. ~____________________________________🍁🍁🍁~ *Me ya Faru Bayan shigar Sheikh Imam Malik*? Ko sallama bai yi ba saboda 6acin ran da ya ke ciki, dakatawa ya yi yana tunanin meyasa Taj ya kira shi a irin wannan lokacin? Menene dalilin kiran nasa? Me kuma ya kawo Alhaji Ubaid da iyalinsa gidan?" Yasan dai ba su da wata alaƙa da Chief Owais, zuciyarsa ce ta raya mashi ko dai sun kira sa ne saboda sun ji komai da ya faru tsakaninsa da ƴarsa, shiyasa suka kira su Alhaji Ubaid don su sasanta su. Ƙunci ne ya mamaye shi, har ya juya zai fuce ya tsinkayi muryarta mai tattare da sautin kuka a cikin kunnanshi.. "Baba! Dan Allah kada ka tafi, ni nasa ya kira mini kai saboda ina son ganin ka, ina bukatarka a kusa da ni, ina so na yi magana da kai..." Jin muryar gudan jininsa ya sa shi dakatawa da yin tafiya, ya manta when last ya ji muryar ƴarsa yayin da take kiran shi da sunan babanta. Ganin bai da niyar juyowa ne yasa ta nufe shi tana kuka ta zube saman gwiwowinta a bayan shi, ta rurruƙe ƙafafunsa da hannayenta da ke kerma. Ba zai iya misalta yanayin da ya shiga ba, ya ji wani irin abu da ba zai iya kwatanta shi ba, sam ya kasa magana. Shesshekar kukan Aisha ya kashe mashi jiki, ya kuma fama masa raunin dake a cikin zuciyar shi, shekara goma sha takwas rabon da jikinsa ya haɗu dana gudan jininsa, ƴarsa ɗaya tilo da ya kora daga gidansa tare da jinjira a tsakar dare ba tare da ya yi tunanin wani hannu zasu faɗa ba, akan laifin da bata ji ba bata gani ba, wanda har yau idan ya tuna yana jin baƙin ciki mara misaltuwa. Dakyar ta iya miƙewa ta rungume shi ta baya, tare da kwantar da kanta saman kafadarsa ta zagayo da hannayenta saman cikin shi. Duk yadda zuciyarta ta kai ga tafarfasa da baƙin ciki sai da ta ji sanyi ya ratsa ta, jin ɗumin mahaifinta a jikin ta. Hannayenta da ta ƙanƙame cikinsa da su ya bi da kallo, sai ya rinka tuna ranar da mahaifiyarta ta haife masa ita, ta damƙa masa amanarta tana atsaka da fuskantar ajalinta, hakika ya ci amanar malama Batool. Hawayen da suka cika idanunsa ne suka fara zarya kan kuncinsa. "Baba! meyasa baka ta6a nemana ba, tsawon shekara goma sha takwas, bakasan irin rayuwar da na yi ba, hankalinka a kwance ka ke gudanar da rayuwar ka, baka ta6a tunanin wani hali nake a ciki ba, ina lafiya ko bana lafiya, ina raye ko bana raye, duk da abun da ka yi min hakan bai hana zuciyata tunanin ka ba, kullum ina sa ran zaka neme ni, amma shiru har sai da na fidda rai da ina da uba a duniyar nan, ka yi min iyaka da kowa nawa, baba hankalinka a kwance kake rayuwarka bayan ƴarka ɗaya tilo da kake da ita tana rayuwa a wani wurin, ko har yanzu fushi ka ke da ni? Baba ka ta6a danasanin abun da ka yi mini? Ka kuwa san halin da kasa na jefa rayuwata?" Maganganunta sun karya zuciyar shi, duk yadda ya kaiga jurewa saida kuka ya kubce masa, jikinsa na kerma ya ruko hannunta tare da zagayo da ita, ya rungume ta akan ƙirjinsa da hannayensa biyu ya tallabe bayanta. Komai dake faruwa akan idanun Alhaji Ubaid da iyalinsa, haka zalika akan idanun Abie da iyalinsa, da kuma Taj wanda ke a tsaye gefe ɗaya. Idanun kowan nan su ya cika tab da ƙwalla saboda tsantsar tausayin Aisha da mahaifinta, kamar sun samu tv haka suke ta kallon su. Cikin shesshekar kuka da rauni ya furta, "Ki yafe mini Aisha, hakkinki ne ke bibiyar rayuwata, na ci amanar mahaifiyarki, na cuce ki na kuma cuci kaina..." ya ɗan dakata yana mayar da numfashi, fuskarsa har kerma ta ke yi. Daƙyar ya ɗaura da cewa, "Taya zan guji gudan jinina kuma in zauna lafiya? Allah shine shaidata, wallahi na yi danasani tun a daren ranar dana kore ki na gane kuskure na, bansan meyasa nayi maki haka ba Aisha! Bana a cikin hayyacina Aisha, bayin kaina bane, ina tsaka da bacci na farka da tsanarki a zuciyata, na ji kin fita araina, kawai bana son ganin ki, kamar ana tunzura ni, a lokacin ji nake in har ban kore ki ba zan iya rasa raina, na daɗe ina tambayar kaina meyasa na yanke maki ɗanyen hukunci! Bayan nafi kowa sanin wacece ƴata, Aisha, bazan iya misalta maki mawuyacin halin da na shiga ba bayan dana neme ki na rasa, na yi kukan da ban ta6a ƴinsa ba arayuwata, na tsani kaina, na ƙuntata rayuwata, na ji rayuwar duniyar ma ta sire mini, mutuwa nakes o kawai na yi, Aisha gidan mahaukata ne kawai ban je ba, amma na yi haukan rashin ki, har kulle kaina na yi tsawon kwanaki ba asan inda nake ba ba ci ba sha, na yi rashin lafiyar data yi silar kwantar da ni asibiti, na yi jinya kamar bazan rayu ba, bansan wa ke akaina ba, saida ta kai ga sunanki kaɗai nake fada a cikin sambatuna, Aisha yanzu haka da nake maki magana ina da ciwon zuciya, Allah ne bai ƙaddara zan mutu ba, shiyasa na kawo har wannan lokacin a raye..." Shesshekar kukan Benazir da Anila ne ya cika kunnuwan kowan nan su. "Aisha ban manta dake ba, da ke nake kwana da ke na ke tashi araina, addu'ar da nake maki kullum a cikin sallata ban daina ba, kamar yadda ki ke sa ran zan neme ki nima haka nayi ta sa ran wata rana zaki dawo ki neme ni, amma baki ta6a tunanin kiyi hakan ba, shiyasa zuciyata ta karaya na yi tunanin ko kin mutu ne ko kuwa abun da na yi maki ne yasa baki ta6a nema ba..." Ya ɗan dakata yana mayar da numfashi. "Bani da kwanciyar hankali saboda zullumi da fargaban a wani hali kike a ciki, kullum saina kira layinki amma ban ta6a samun shi a kunne ba, kuma ban fidda rai ba, kullum addu'ata idan kina a raye keda jinjirarki Allah ya kare mun ku a duk inda ku ke, Ya zama gatan ku, Ya kuma haɗa ni da ku, idan kuma baku a raye Allah Ya jikanku da rahamarsa, ban ta6a gajiyawa ba da neman ku, saboda ku na sha zuwa aikin hajji don in yi maku addu'a..." Kasa karasa maganar ya yi saboda raunin da zuciyarshi ta yi, baiwar Allah ta yi kuka kamar ranta zai fita, bata taba tunanin ya damu da ita har hakan ba, ta yi zaton yana sane ya yi watsi da ita shiyasa bata ta6a tunanin ta dawo gida ba tun da bai neme ta ba, ta yi zaton har yanzu fushi ya ke yi da ita. Tallabo fuskarta ya yi da tafukan sa, idanunsu da ke tsiyayar da kwalla suka haɗu cikin na juna. "Aisha, saboda ke na ajiye aikina na rabu da kowa nawa, a karshe ma da na yi jiran shiru baki dawo ba, sai na bar ƙasar ba tare da sanin kowa ba." Numfasawa ya yi tare da girgiza kansa cike da danasani ya daura da cewa, "A ranar dana fara ganin ki a gidan nan, wani irin farin ciki mara misaltuwa na ji, kamar anyi min albishir da gidan aljanna, saboda na ji daɗin ganinki da ranki da lafiyarki, duk da na shiga tashin hankali saboda sauyin da na gani a tare dake, daga yanayin shigarki, na gane kin canza hali, har saida na yi kokwanton anya Aisha nane?" Amma saboda jinina dake yawo a jikinki yasa ban musa ba, a lokacin dalilin da yasa ban yi ma ki magana ba, saboda ina jin kunyarki, kema kuma sai kika nuna kamar baki taba sanina ba, shiyasa jikina ya yi sanyi, amma bayan na koma gida saboda farin ciki ban iya runtsawa ba, kwana na yi ina nafilfili don nuna godiyata ga Allah da ya bayyanar min da ke, har so nake Chief ya gayyace ni don in zo gidan nan saboda kawai zumudin in ganki.. " komai saida Imam ya fayyace mata na daga halin da ya shiga bayan rabuwar shi da ita. Bai ƙare maganar ba, Ya saki fuskarta da ya tallabe, ya tattare ƙasan jallabiyar Jikin shi da niyar ya zuƙunna kan gwiwowinsa don ya nemi yafiyar ta. Lura da hakan yasa ta yi saurin ƙanƙame shi tana rokonshi akan kada ya zuƙunna mata, ya bari, kada ya yi, idan ma akwai wanda ya cancanta ya nemi yafiyar wani atsakanin su toh ita yakamata ta nemi yafiyar sa, yana kuka ya ce mata ta barshi ya zukunna, idan har baiyi hakan ba bazai ta6a yafe ma kansa ba, koda ta yafe masa, saboda ya dade yana yi ma kanshi kallon mugun Uba, mara imani, saboda rashin adalcin da bai yi mata ba. Ta fashe da wani sabon kukan ta ce, "Baba babu yafiya atsakanin mu, abun da ya faru bayin kanka bane, haka zalika abun da ya faru tsakanina da yaya Shureim bayin kan shi bane, a yau na ji komai baba. Na ji abun da ya ɗaga hankalina ya kuma karya zuciyata, Baba ashe dama makirci ne aka kulla min saboda a ɗauki fansa akanka?" Kaitsaye maganar ta ratsa kunnuwansu, a ruɗe suke kallonta. Muryarsa na rawa ya furta, "Bangane me kike nufi ba? ki yi min bayani yadda zan fahimta!" Gajiya ta yi da tsayuwa, hakan yasa ta zauna shima ya zauna yana fuskantarta, yayin da sauran mutanan dake a falon suke atsaitsaye babu alamun gajiya a tare da su. "Ke nake sauraro Aisha.." A ƙagare da son ji duk da yana fargaban abun da ya daɗe yana zargi ya zamana gaskiya. "Baba, zan faɗa maka, amma zan roke ka, dan Allah ka yi min alkawarin zaka jure komai da za ka ji daga gare ni, kuma duk abun da zan faɗa maka ya riga da ya wuce, kuma anyi ne don a cusa maka baƙin cikin da zai yi silar mutuwarka, sannan kuma a lalata martabarka da ƙimarka, in har ka tada hankalinka akan abun da za ka ji toh zai yi nasara ne, shiyasa bana so ka sanya damuwa a ranka, nasan za ka ji raɗaɗin da yafi na ƙunar wuta zafi a cikin zuciyarka amma ina so ka tuna komai ya faru a rayuwar mu mukaddari ne daga Allah, ka ɗauki hakan a matsayin jarabawa da Allah ke yiwa bayinSa muminai, mu yi hakuri da cutarwar da aka yi mana, In sha Allah zamu ga ribar hakurin da muka yi, kuma Allah zai yi mana sakayya" Cikin sanyin murya ta ƙarasa maganar tana kallon fuskar mahaifin nata dake kallonta da rinannun idanunsa. Unexpectected ta ji ya furta, "Musa!" kowa da ke a falon sai da gabansa ya faɗi da jin sunan da ya ambata. Ba ta yi mamakin Jin ya canki sunan shi ba, dama tasan dole ya zo masa a rai tun da shine babban maƙiyinsa a duniyar nan. "Ki faɗamin shine ko? Shine ya shiga tsakanina da ke ko?" Cike da damuwa ya tambaya, Fargaban amsa mashi ta ke yi saboda zullum halin da zai shiga, tasan mahaifin nata da zuciya komai zai iya faruwa. Daƙyar ta jinjina mashi kai cikin raunanniyar murya ta ce, "Shine baba, uncle Musa, ya daɗe yana ƙulla makirci atsakanin mu, ban ta6a ganin azzalumin mutun irinsa ba, ya karya mini zuciyata, ya ha'ince mu, wata shari'ar sai a lahira, amma ya cutar da rayuwar mu..." kamar a mafarki suke sauraron maganar Aisha, gaba daya sun kasa tantance wani Musan take magana akan shi, Taj ne kaɗai ya san komai, sai kuma Benazir da Anila. Sauran da ke a falon sun ruɗe sosai, sun rasa gane inda ta dosa. "Aisha kada ki ji komai, ki fadamin kawai, bazan karaya ba, nasan zai aikata saboda ya kullace ni a ranshi, dama ni saida na yi zargin dasa hannunsa a cikin abun da ya faru, kawai don bani da hujjar da zan tuhume sa ne.." ya faɗa cikin karfin hali kamar zai iya jurewa. Ƙarasa shiga cikin falon suka yi, saboda su samu damar jin komai, a saman sofas kowan nan su ya samu wuri ya zauna suka nutsu suna kallon Aisha da baba Imam, kwata kwata basu san da zaman su ba, saboda hankalinsu ba akansu yake ba, basu san ma sun shigo falon ba. Numfasawa tayi cikin karyayyar murya ta soma zayyana masa komai da Uncle Musa ya faɗa mata, tiryan tiryan abu ɗaya da ta boye masa saboda gudun halin da zai shiga, shine karuwancin da ta yi a America da kuma haramtacciyar alaƙarta da Musa tasan in ya ji wannan komai zai iya faruwa ita kuma ba ta so Musa yayi nasara akan mahaifinta, ta dai sakaya ta ce shi ya kaita America ya ɗauki nauyin komai nata saboda ya kawar da tunaninta akan dawowa gida. Tunkan ta ƙarasa labarta mashi Hajiya Layla ta miƙe tsaye tana tafa hannayenta a kiɗime take zabga salati, Alhaji Ubaid dake a zaune sai jinjina kansa ya ke yi yama kasa furta komai saboda ƙuncin da zuciyarshi ta yi mashi, ina ga Dr shureim dake neman zaucewa saboda tashin hankalin da ya haifar masa da raɗaɗi mara misaltuwa a zuciyarsa, bai ta6a zaton Uncle musa zai iya yi masa haka ba, saboda yasan shi ya cutar da rayuwarshi shiyasa ya dawo da shi gidan shi da zama, haka lokacin da ya ke neman taimako yaita kiransa baya shiga ashe blocking ɗinsa ya yi, kowa dake falon sai da ya razana ba kaɗan ba, Musa ya karya zuciyoyinsu, basu ta6a tunanin shine munafukin da ke ƙulla musu makirci ba. Saboda bacin rai da fusata yasa shekh Imam zubda gumi akan fuskarsa, ba a ta6a cin galaba akanshi ba sai wannan karon, Musa ya cuce shi, wani laifi ya yi masa da yasa shi yanke masa mummunan hukuncin nan?" Kawai saboda ya hana shi auran Aisha? Saboda baƙin zalunci da rashin imani ya shiga tsakaninta da shi, yayi mata kazafi bayan ya shiga tsakaninta da Shureim, abun da yafi bakanta ransa tsawon shekarun da ya raba shi da ƴarshi, ashe yana a tare da ita, saboda zalunci irin na shi, yanzu ya gane komai da ya faru da Aisha shi ya ja mata, tun da akan shi yake ɗaukar fansa, bata ji ba bata gani ba. Ruƙo hannayenta ya yi a cikin nashi, saboda kerma da jikinshi ke yi itama nata jikin ya kama kerma idanunsu a cikin na juna yana kuka tana kuka ya ce, "Allah Ya yi maki sakayya Aisha, Allah ya bi maki hakkin ki. Wlh bamu ya cuta ba kanshi ya cuta, la'ananne, In sha Allah sai rayuwarsa ta wulaƙanta tun a gidan duniya, na yi danasanin sanin shi a rayuwata, dama wasu mutanan Allah yana hadamu da su ne don ya jarabcemu da su, wasu kuma don su zama alkhairi a cikin rayuwarmu.." kasa ƙarasa maganar ya yi saboda kululun bakin cikin da ya tokare makoshin shi, ya ji zafi a ranshi, bakin ciki ya cika shi kamar zai haɗiyi zuciya ya mutu. Kwantar da kansa ya yi saman kafaɗar Ummi, ya ɗaura hannayensa a saman bayanta. Cikin sigar lallashi yake dan bubbuga bayan nata, tsananin tausayinta ne ya kama shi, saboda gaba daya rayuwarta a cikin jarabta ta ke, kowa dake a falon sai da ya tausaya masu, Hajiya Laila ta yi danasani, sai cizon yatsa take yi, gani take kamar hada laifinta komai ya faru, idan har Musa yana sarrafa Alhaji Ubaid da sihirinsa toh ita da hankalinta take yin komai. A fakaice ta dinga share kwalla tana satar kallon Aisha da mahaifinta.. Cikin ruɗu Alhaji Ubaid ya ce, "Har yanzu na kasa yarda da abunda kunnuwana suke jiye min! Dan Allah ku fahimtar da ni! Kaina ya ɗaure, Wani musan kuke nufi? Ƙanina musa ko wani musan ne daban?" Hajiya Layla ta yi saurin cewa, "Wallahi zai aika! Fiye da haka ma, ai baida mutunci ko kaɗan, mutun sai bakar zuciya kamar ta kafuran farko, na daɗe ina zargin ba mutumin kirki bane Musa, kuma dukiyarsa bata Allah da Annabi ba ce, Ai ni bazan ma Musa ba...".. Benazir ta kar6e da cewa, "Abun da Aisha ta faɗa gaskiya ne daddy, na dade ina jiran wannan ranar da zan fadi ta cikina, ku yi hakuri da ban ta6a sanar da ku ba, na boye maku ne saboda nasan zai yi wuya ku yarda da ni a wannan lokacin, saboda ku kan ku sai yadda ya yi da ku...." mayar da hankalinsu su ka yi akan Benazir.. A tsanake ta labarta masu komai da ya faru tun daga lokacin data ta kama shi yana yin waya agidan shi, har izuwa kan asirin da ya yi mata.. Daura hannu biyu Hajiya Layla ta yi akanta. Mami ta zabga salati, Dr Shureim ya zabura ya mike a kidime jin ƴarsa da ya binne Uncle Musa ne ya dauke ta, yama kasa magana sai zazzare idanunsa ya ke yi gaba ɗaya ya ruɗe, nan ta ke ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru a baya, lokacin da ya je ya tone ƙabarinta ya ga ƙasusuwa saida ya yi zargin wani abu, just in two weeks da ya binne ta har ta zama ƙashi, bayan haka ya daɗe yana ji aranshi tana a raye saboda bai ta6a mafarki da ita a mace ba, Ya Ilahi! Yanzu ya gane komai. Jirin tashin hankali ne ya ɗebesa yayi taga taga zai kife, Alhaji ubaid ya yi saurin miƙewa ya tallabo shi, tare da rungume shi kan kirjinshi, kukan baƙin ciki ya fashe da shi kamar ranshi zai fita, tuni zazzabi da ciwon kai sun kama shi. Sheikh Imam ya ƙara shiga damuwa daga shi har Aisha jin rashin imanin da Uncle musa yayi ma Benazir saboda kawai ta nemi ta tona masa asiri don ta ƙwatarwa Aisha hakkin ta. Cikin shesshekar Kuka Hajiya layla ta dinga ɗura mashi ashariya tana tsine masa albarka, dama da ƙiyayyarsa aranta, bata ta6a son shi ba, kwata kwata baya burgeta saboda izzarshi, ta tsane shi ta tsani komai nasa. Ƙwallar bakin ciki ce ta cika idanun Alhaji Ubaid, cikin rawar murya yake ambaton duk wata addu'a da ta zo bakinsa don ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa. Abie da ke zaune a gefensa dafa kafadarsa ya yi batare da ya iya furta kalma ba, kowa ya razana da jin abun da Musa ya aika ta. Babu wanda zuciyar sa bata karaya ba.. "Har yanzu baku fayyace mana komai ba, Ina so in san wace irin sadaukarwa ce Musa ya yi da yarinyar Shureim da kuma yarinyar Benazir? suna a raye ko sun mutu?" Cike da fargaba Abie ya yi tambayar, saboda yana son yasan in duk a tare suke da ɗan Iya. Shiru su ka yi saboda basu da amsar tambayar da zasu ba Abie. _Taj Ka faɗa masu komai, yanzu lokaci ne da kowa yakamata yasan gaskiya, Illa iyaka kowa ya yi hakuri da abun da zai ji_ Zuciyarsa ce ta raya ma shi. Gyaran murya ya yi hankalin kowa ya dawo kan shi. falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, baka jin sautin komai sai na muyar Taj dake basu labari.. Ya fara ne daga kan labarin leƙen asirin da suka yi wa matsafa shi da Uzair, rabuwarsa da Unaisah da hannun da kowan nan su ya faɗa, Alherin da Chief Owais ya yi masa da kuma haɗuwarsa da ƴarsa bayan shekaru.. Lokacin da ya fara basu labarin gidan kurkukun Ƙaddara, saida suka yi danasanin jin labarin shi, saboda matsanancin tashin hankalin da suka shiga, sun ruɗe sosai, sun razana, zuciyarsu ta tsinke da jin irin azabtarwar da ake yi wa yaran da basu ji ba basu gani ba. Babu wanda bai share ƙwalla ba acikin su, kuka ne ya kubcewa Benazir da Anila kamar ransu zai fita, Hatta Hajiya Layla da Mami saida suka yi kuka na fitar hayyaci, shi Alhaji Ubaid ma kukan zuciya mai radadi ya kama yi, shi da Abie, musamman da ya zo kan labarin Unaizah abin ya ta6a zuciyoyin su. Jin abun suke kamar ba a gaske ya ke faruwa ba saboda ruɗun da suka shiga. Bayan ya ƙarasa basu labarin, ya juya ya nufi sitting room din Chief ya ɗauko diary din Unaizah wanda tun shekaran jiya da ya shiga ɗakin ya gan shi akan table. Bayan da ya dawo hannunsa ruƙe da diary din, ya Miƙa masu ya ce yana so kowan nan su ya dubi hotunan dake a cikin diary din da kyau. Alhaji Ubaid ya fara mika mawa hannunsa na kerma ya kar6a tare da bude shafin farko, wata zabura ya yi ya mike a firgice yake tambayar diary din wanene? Mai ya kawo hoton Musa da na ƴarsa Zeenatu a cikinsa.." Da jin wannan maganar yasa Benazir ta mike cike da rashin kuzari ta nufe shi, hajiya Layla ma tuni ta mike tana leƙa hoton ta furta, "Kai! Ai Zeenatu ce wannan! Da Musan! Me ya kawo hotunansu anan? Wace ce kuma wannan baturiyar?" Ta tambaya a ruɗe. Kowa sai da ya duba hotunan, bayan da suka gama kallo, Taj ya fayyace masu komai game da diary din, ya ce yarinyar da suka gani ba Zeenatu bace sunan ta Unaizah, twin sister din yarinyar wurinsa ce da ya sadaukar tun tana jaririya ya rabata da mamanta ya kaita England gurin karuwarsa ta raine ta. A bayanin da Taj ya yi masu suka fahimci yarinyar da yake yin magana akai itace ta kurkukun nan wadda ubanta ya yaudare ta. Kansu ya daure tamau, lamarin ya girmi tunanin su! Hajiya layla ta ce, "Anya Musa mutunne ba shaiɗan ba?" Ta ce ta na kokwanto, saboda rashin imaninsa ya yi over, kamar babu zuciya a kirjinsa, abun da ya fi basu takaici cin amanar da yayi ma hajiya Sarah, baiwar Allah batasan twins ne ta haifa ba, Har yar cikinsa bai bari ba, ya zata ji idan ta ji abin da ya yi ma ƴarta? "Kakan Chief Owais Shine shugaban Kurkukun ƙaddara, Kamar yadda Musa ya ha'ince ku, shima haka kakansu ya ha'ince su, ya dade yana sadaukar da jikokin family dinsu agidan kurkuku batare da sanin su ba. Musa Yana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun ƙaddara, Shine Jan wuya, kawun Anila shima yana ɗaya daga cikin Elders..." Duk da sanyin A.c din dake falon hakan bai hana su fitar da gumi ba, saboda tsantsar tashin hankalin da suke a ciki, gaba daya sun razana da jin maganarsa, rudu yasa suka shiga tambayar shi wani Owais din yake nufi kuma wani kakan nasa?" "Obinna," ya faɗa masu ne saboda su kwantar da hankalinsu, su san cewa basu kaɗai ta shafa ba, hakika sun razana fiye da yadda suka razana da jin munanan laifukan da Musa ke aikatawa, kamar an kashe masu bakunansu gaba daya suka yi shiru kamar masu zaman makoki. Abie ya ce, "Inama ace mafarki ne komai ke faruwa? Wannan wace irin musiba ce ta kunno mana kai? Wani irin neman duniya ne wannan da zaisa ka dinga azabtar da rayuwar bayin Allah waɗanda ba su ji ba ba su gani ba? ka manta da lahirar ka, Ka dauki rai ba a bakin komai ba? Hakanan bawa ya jefa kansa cikin bala'e ya kuma jefa ahalinsa, ina amfanin irin wannan rayuwar da suka ɗaukarwa kansu? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Ya fada yayin da hawaye ke zarya kan kuncinsa. Jikina ya yi sanyi wai an jefi kaza da gishiri, wlh komai na duniyar nan ya sire min, ɗan adam ba abun yarda bane, In har uba zai iya kwanciya da ƴar cikinsa meye kuwa bazai faru ba? Da yawa wasu fitintinun da ke faruwa da mu daga laifukanmu ne, bawa shi ke ja ma kanshi, tayaya zamu ga daidai bayan irin zunubban da muke aikatawa, tayaya zamu zauna lafiya bayan irin fasadin da ake aikatawa a doron kasa? A kashe wanda bai ji ba bai gani ba, ko a azabtar da shi, A tauye masa hakkinsa na rayuwa! Meyasa wasu basa tunawa da cewa kamar yadda suka kashe wata rana suma mutuwar zata riske su kuma basu isa su dakatar da ita ba?Ina zaka je da hakkin rayukan dake akanka? A ranar daka farka ka ganka a cikin ƙabari batare da komai na duniya da kake taƙama da shi ba ya za ka yi? kafin ka aikata ba daidai ba ka fara tunanin menene makomarka? Bakasan ranar mutuwarka ba, a wace rana, a wani lokaci? Don haka mu ji tsoron Allah! Duk a wannan zaman Taj ya faɗa masu game da sace su Unaisah da Musa ya yi, kuma ya bayyana masu ɗiyar Shureim ita ce Batool yarinyar nan dake a tare da Unaisah. Sun shiga damuwa sosai, duk da halin da sheikh Imam ya ke a ciki saida ya taimaka da yi masu nasiha ganin yadda su Benazir suke kuka, ya ce su daina kuka bazai ta6a yi masu maganin damuwarsu ba, in har sun dogara da Allah, kuma sun yi imanin shi kadai ne zai iya nema masu mafita toh su tashi a cikin daren su yi nafilfili In sha Allah babu abun da zai same su, Bi'iznillah... Sun ji daɗin shawarar da Baba Imam ya basu. Ba tare da 6ata lokaci ba, Taj Ya nuna masu ɗakunan da zasu shiga su yi alwala.. kafin su gama yin alwalar Taj ya yi ma ma'aikatan gidan magana suka shimfiɗa masu prayer mats a nan main falo, darduma ce mai faɗi da tsawo, Ummi ce ta ɗauko hijabs taba Benazir da Anila. Sheikh Imam Malik ne ya ja su sallar da kyakkyawar niyyarsu, mazan suna a sahun gaba, yayin da matan su ke a sahun karshe na bayansu gwanin ban sha'awa kamar a masallaci Yadda suka ga rana haka suka ga dare, nafilfili suka dinga yi batare da gajiyawa ba, har saida kafafunsu suka fara zogi tukunna suka kammala sallar, kowan nan su ya ɗaga hannayensa sama, Sheikh Imam ya dinga karanto addu'oi cikin harshen larabci suna amsa mashi da Ameen Ameen. Sun yi ma su Unaisah addu'o'in tsari da kariyar Ubangiji, suka yi ma su Chief addu'o'in nasara da kariya, sun kuma la'anci su Musa da sauran Elders na kurkukun ƙaddara.. Akan kunnuwansu aka fara kiraye kirayen sallar asubahi, nan ma suka kuma miƙewa su ka yi Salatul fajri. babu wani mai kwanciyar hankali a cikin su, sun damu sosai, zukatansu sun cika fal da fargaban a wani hali yaransu suke a ciki? Suna a raye ko ya kashe su?" Meya faru bayan tafiyar Chief Owais? Tun a daren ranar ya kira CI ya sanar da shi abunda ke faruwa ya kuma umarce shi da ya tattara Senior Agents dinsu da Isod soldiers dukansu Su bazama neman Alhaji Musa, ya kuma Kira Commender James ya Fada masa akwai matsala, Yana son ganin shi tare da sauran yan team ɗinsa. Daga bisani ya kira Taj ya ce ya ba Alhaji Ubaid waya yana son yin magana da shi, bayan Taj ya ba Alhaji Ubaid wayar, chief ya yi masa tambayoyi game da wuraren da yasan Alhaji Musa yana yawan zuwa. Alhaji Ubaid ya bayyana masa guest houses dinsa da location din da suke, Cos yana yawan zuwa da shi wasu lokutta in zai yi baki daga kasar waje. godiya chief ya yi masa daga bisani su ka yi sallama. Cikin ƙanƙanin lokaci jiniyar motocin jami'ai ta karaɗe ilahirin birnin Abuja, wiwi wiwi, ga sautin bikes din Isod soldiers dake sintiri kan titituna, duk wani rai da ke bacci saida ta girgiza saboda yadda ƙarar jiniyar ta cika kunnuwan mutane kamar za'a tada garin, saƙo da lungu na garin da kowani titi maƙil yake da sojoji harma da ƴan sanda. Hankulan jama'an gari ya tashi haikam, ganin yadda Jami'ae ke sintiri, Kowa so Yake ya ji meke faruwa? Musamman ƴan jarida tun safe suke ta sintiri jami'ai sun hana su yi aikin su, ko kusa da su basu isa su ƙaraso ba. Ba a ta6a fuskantar tsaro irin na yau ba a garin, kan al'umma ya ɗaure tamau, ko ina zancen ake yi, wasu ma ƴan jaridan har sun fara buga labaran ƙarya suna yaɗawa don su karkato hankalin al'umma. Idan muka koma Isod Headquater, wasu gungun cyber expert ne masu fikra a cikin katafaren Surveillance room din su, na'urorine ƴan bala'i cike da ɗakin, Kowani agent ya tasa computer dinsa a gaba sun baza basirar su da ƙwarewar su gurin yin binciken su. Ta cikin na'urorinsu suna kallon komai dake wakana a cikin garin abuja, sun sanya ido sosai akan motsin komai da ke gudana. Agent Ethan Kim ne yake jagorantar su, a bisa Umarnin Chief Owais, duk bayan ƴan mintuna sai ya leƙo ɗakin ya duba su don ya ga in ana samun cigaba. Duk bayanin da suka bashi batare da bata lokaci ba yake kiran Dg a waya ya sanar da shi halin da ake a ciki. ~_________________________________🍁~ Shin Meke Faruwa A gidan Alhaji Musa❓ Sakamakon jiniyar da ta karaɗe cikin gidan ne ya yi silar farkawar wadanda ke bacci. Da gudu Zeenatu ta fito daga bedroom dinta hannayenta rungume da pillow, hada duvet ɗinta da ya nannaɗe jikinta, tsabar rudu ne yasa ta rikice ta rasa ina zata dosa. "Mommy! Daddy! Ya Shureim! Aunty Benazir! Mommy Layla! Uncle! wai kuna ina ne? Babu mai jina ne?" Da sauri maids din gidan suka fito daga part dinsu daga gani bacci bai ishe su ba, hankulansu a tashe jin Jiniya. "Meke faruwa ne? Su wanene ke shigowa gidan? Daga Ina nake jin jiniyar nan? Kai jama'a kamar za'a fasa dodon kunnan mutane? Wannan ƙara haka ta lafiya ce kuwa?" Maids din ne suke ta suratai... A lokacin Hajiya Sarah tana a kishingiɗe kan gadonta, ta daura kanta saman pillow idanunta suna a lumshe, jiniyar ce ta farkar da ita sai dai har yanzu baccin bai sake ta ba, sam ta kasa tashi saboda kasalar da ta mamaye gabbanta. "Mom!mommy, where are you? Mommy, ki tashi ki gani! Wani abu na faruwa!" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu dake tunkaro dakin. Batai aune ba ta ji abu ya fado kanta, a firgice ta zare blue eyes dinta, ta yi zaton wani mugun abunne ashe Zeenatu ce ta faɗo kanta, ta ƙanƙameta kamar zata shige cikin ta. Jikinta sai kerma yake yi hakan ba karamin ɗaga hankalinta ya yi ba. "Zeenat! Meke damunki? Meke faruwa iye?" Cikin rawar murya take fadin, "Mommy, sojoji a cikin gidan nan, sun zagaye ko'ina, hannayensu ruƙe da bindigogi, kuma shugowa za su yi..." sai da Zeenatu ta yi wannan maganar ta tuna da abun da ya yi silar farkawarta daga bacci. Jikinta na 6ari ta banbare Zeenatu daga jikinta ta sauko daga kan gadon ta ɗauko mayafi ta lullu6e sumar kanta. Fitowa tayi daga dakin da sauri Zeenatu ta biyo bayanta. Tun kan su karasa suka hango maids din gidan a gaban kofar shigowa falon suna ta leƙen waje. Suna ganinta suka dare tare da bata hanya don ta wuce. Gaishe da ita su ka yi, bata amsa masu ba ta ce, "Meke faruwa ne?" Ta tambaya tana duban su. Tani ta ce,"Hajiya wallahi mu kanmu bamu sani ba, muna tsaka da yin bacci jiniya ta farkar da mu!" Bata ƙarasa sauraronsu ba, ta leƙa waje kaitsaye idanunta suka sauka akan soldiers din da suka kewaye gidan ta ko'ina sune. Kwata kwata babu securities din da ke tsaron gidan. Gabanta na faɗuwa ta furta, "Inna lillahi...."! Zeenatu dake la6e a bayanta sai leƙa kai take tana kallon sojojin. Bari mu koma baya mu ji tayaya akai soldiers suka shigo gidan? Kuma Ina Security officers din gidan su ke?" Abun da ya faru jiya bayan barin su Dr shureim gidan, kwatsam Security Officers din dake tsaron gidan suka soma jiyo ƙarar mashina, aikuwa suka mimmiƙe hannayensu ruƙe da bindigogi suka kewaye gaban main gate din suna jiran su ga daga ina jiniyar ke fitowa. Unexpected suka ga bike yana ƙoƙarin Shugowa ciki, Officer din da ya yi kokarin tare mashin din, buge shi ya yi ya fadi gefe ɗaya, hankali a tashe sauran officers din suka saita jami'in dake akan bike din da guns, sun yi tunanin farmaki suka kawo masu. Basu kaiga harba bindigar ba, mai mashin ɗin ya ɗaga hannayensa sama alamar yayi surrender, "Ku dakata! Ba dan fashi bane, jami'i ne daga hukumar Isod!" "Wata shaida gare ka? Me Kuma ya kawo ka?" Ɗaya daga cikin security officer ɗinne ya tambaya Yana tunkararsa da bindiga. Zura hannunsa ya yi cikin aljihun wandonsa ya zaro Id Card dinsa ya miƙa ma Officer din, Bayan ya kar6a ya dudduba ya tabbatar da gaske agent ne. "Agent Jabeer Osman." Ya furta tare da kallon shi, "Ka cire helmet din dake a kanka, muna so mu ga fuskarka." Bai musa ma su ba ya zame helmet din.. Kasantuwar akwai hasken electricity tamkar da rana hakan yasa suka ga fuskarsa dakyau. "Kaida su wanene kuma meya kawo ku?" Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma. "Megidan muke nema, idan kuma bayanan mun zo ne don mu yi bincike" Dariyar rainin wayau officer ɗin ya yi, "Bawan Allah ko dai 6atan hanya ku ka yi ne? Baku ga gidan wanene ku ka shugo ba? Ai baku da hurumun da zaku iya shiga gidan nan idan har megidan bai bada izini ba, don haka tun wuri ina shawartarku da ku koma inda kuka fito idan ba so kuke ku rasa aikin ku ba." Wata tsawa Agent Jabeer ya kwatsa masa yana huci ya ce, "Kai zan yi ma warning ka shiga taitayinka idan ba so kake ka rasa aikin ka ba, kasan su wanene jami'an isod kuma kasan wanene Dg din mu, bisa umarninsa mu ka zo nan, kuma ba mu zo don muyi jayayya da ku ba, saboda baku ne agaban mu ba, ubangidan ku muke nema, zai fi ku bar doka ta yi aikin ta, idan ba haka ba jikinku ne zai gaya maku." "Ko kuma ku jikinku ya gaya maku, don na lura kamar kuna da ta6in hankali, kun san wanene Alhaji Musa, a ƙarkashin ikonsa muke, dole saida umarninsa zaku samu iznin shiga, kuma idan kuka nemi ku wuce gona da iri, hmm, wanda ke a lahira sai ya fi ku jin dadi." wani tantirin officer ne ya faɗa da muryarsa ta ƴan ƙwaya.. Wani Officern ya ce, "Ni ban yarda ma daga hukumar Isod kuke ba, kun fi kama da yan ta'adda, kawai kun yi basaja ne..." "Ku bamu hanya mu wuce" Agent jabeer ne ya faɗa babu wasa akan fuskarsa.. "Ka ga malam karfa ka cika zaƙewa, don na lura kana da gadara da ji da kai, to ai ko shi uban gidan naku bai isa ya ƙetare gate din gidan Alhaji Musa batare da izininsa ba.." Bai ƙare maganar ba, Agent Jabeer ya yi fito mai sautin gaske.. Unexpected suka fara ganin bikes suna shigowa ɗauke da sojoji rutu rutu kamar a filin daga, hannayen su ruƙe da bindigu. Hakan bai saka sun sadudu ba, suka fara yunƙurin harbinsu aikuwa sojojin suka fusata, zuciya ta de6e su, basu san sa'adda suka afka masu ba faɗa ya kaure atsakanin su, har saida suka ci ƙarfinsu, suka yi masu shegen dukan da yasa wasu daga cikin su suka fita hayyacin su.. Ba su zo don su ta6a lafiyarsu ba ta lalama suka fara binsu, amma da suka sa kafiya kuma suka yi yunƙurin harbin jami'ai wanda yin hakan ya sa6a ma doka shiyasa suka basu ɗan banzan kashi, dakyar suka iya guduwa da ƙafafunsu kowan nan su ya kama gaban shi. Hankalin Sarah idan ya yi dubu ya tashi, juyawa ta yi da sauri Zeenatu tabi bayanta kamar jela, bedroom dinta ta shiga ta dauko wayarta data bari saman gado, hannunta na kerma ta soma kokarin kiran layin Alhaji Musa, kwata kwata kiran baya shiga, duka layukansa da ta kira a kashe ta same su. Hakan ba karamin ƙara daga hankalinta yayi ba, cike da fargaba ta juya ta dubi Zeenatu data zazzare idanunta, har yanzu jikinta ya ƙi daina yin kerma kamar mazari. "Mommy, daddy ba ya picking?" "Yaushe ma kiran ya shiga balle har ya yi picking, duka layukansa a kashe suke.." Tunawa da sauran mutanan gidan yasa ta yanke shawarar ta je ta sanar da su abun da ke faruwa, tayi zaton basu farka daga bacci ba ne. gudu gudu sauri sauri suka nufi dakin Hajiya Layla, knocking suka yi almost 5 times ba'a bude ba, ko da Sarah ta tura kofar dakin suka shiga basu ga kowa a cikin sa ba, nan fa damuwarsu ta ƙara ninkuwa.. Juyawa suka yi da sauri suka nufi ɗakin Dr Shureim nan ma suka taras babu shi a ciki. Har dakin Alhaji Ubaid dana Benazir saida suka shiga basu ga kowa ba. Gaba daya kansu ya daure sun rasa gane meke faruwa ne? Zeenatu ce ta kawo shawarar su kira layikan su! Kwata kwata tunanin yin hakan bai zo mata arai ba. Cikin sauri ta kira layin hajiya Layla, kiran ya shiga saidai babu alamun za'a ɗaga. Tana ƙoƙarin kiran layin Dr shureim sai ga kiran Benazir ya shigo wayarta, cikin sauri ta yi picking ta kara a kunnanta ko sallama bata yi ba ta ce, "Benazir meke faruwa ne? Ina kuka je? Muna ta neman ku, ga sojoji cike da gidan, gaba ɗaya mun rude hankalinmu ya tashi.." On the other hand Benazir ta ce, "Aunty Sarah mun fita anguwa, zamu dawo nan bada jimawa ba In sha Allah, and pls ku kwantar da hankalin ku, babu abun da zai faru da ku. Sojojin da kuka gani a cikin gidan daga hukumar Isod ne, bincike ne ya kawo su, dan Allah ku basu haɗin kai, ko mai suka tambaya ko suka buƙata ku yi masu ta cikin lalama don ku rabu lafiya.." Bata ƙare maganar ba ta katse ta, "Benazir kaina ya daure, na rasa gane inda kika dosa! Meya kawo jami'ai yin bincike agidan nan? wani ne ya aikata laifi ne uhym? Pls kada ki boye min komai kawai ki faɗa min! Saboda hankalina ba kwance ya ke ba, ina ji araina wani abu na shirin faruwa da mu, tun jiya uncle din ku bai dawo gida ba, kuma duka layukansa a kashe suke, a haka kike so in kwantar da hankalina..." ta faɗa cikin karyayyar murya mai tattare da fargaba. "Akan me zasu yi bincike? Kuma kin ce kun je anguwa, wace unguwa ne? Meyasa baku sanar da ni ba? Da yaushe kuka tafi...?" Ta faɗa fuskarta a yamutse.. Benazir dake sauraronta jikinta ya yi sanyi saboda tausayinta da ya kamata.. "Aunty Sarah, ki yi hakuri dan Allah, kada ki saka damuwa a ranki, na yi maki alkawari idan muka dawo zamu fada maki komai, amma yanzu ki kwantar da hankalinki, ki yi abinda na ce please." Cike da damuwa ta ce, "Toh, Allah ya dawo da ku lafiya." "Ameen, ina Zeenatu? Ta farka?" Ta tambaya. Kallon Zeenatu ta yi dake tsaye hannunta a cikin nata.. "Gata nan tana sauraronki." "Pls Ki bata wayar." Miƙa ma Zeenatu wayar ta yi ta kar6a ta sa a kunne. "Pls Zeenatu, nasan ki da tsoro, dan Allah ki nutsu, ki kwantar da hankalinki, babu abun da za su yi maku, da ga sun gama binciken su zasu tafi, mu ma zamu dawo gidan in sha Allah." Cikin sanyin murya ta ce, "Toh aunty Benazir, Allah ya dawo mana da ku lafiya." Ta amsa mata da Ameen. Zama suka yi kan sofa, ta janyo Zeenatu ta rungumeta akan ƙirjinta, gabansu sai faɗuwa yake yi, zuciya da saƙe saƙe taita ayyana mata Musa ya mutu wataƙil jami'ai ne suka kira Alhaji ubaid don ya ga gawar ɗan uwansa shiyasa suka tafi batare da sun sanar da ita ba don kada hankalinta ya tashi, wata zuciyar kuma ta ce ba mutu ya yi ba, ya aikata wani laifin ne da ya ja hukuma ke nemansa shiyasa ya kashe layukan wayarsa tun jiya ba a samun shi. Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, fatanta kada Allah yasa abun da zuciyarta ke saƙa mata ya zamana gaskiya. Akan idonsu senior agents suka shigo falon kusan su biyar, Maids din gidan na ganinsu suka watsa da gudu kowa ta nufi ɗakinta. Ko kaɗan ba su ji fargaba ba tun da Benazir ta kwantar masu da hankalinsu. Tambayarsu agents ɗin suka yi ina ɗakin maigidan, Sarah ta miƙe suka bi bayanta ta kai su har part ɗin uncle Musa suka shiga ciki, wasu jami'an suka fara zagaye gidan suna bincika ko'ina, wani abun al'ajabi dukiyar da suka tono agidan Alhaji Musa ta yi ninkin ba ninkin ta gidan ɗan Iya, bedmattress dinsa da suka cire dollars suka gani a shimfiɗe. Da suka 6alle drawers na gadonsa nan ma maƙudan kuɗi su ka gani a ciki. Ashe basu ga komai ba, wannan somun ta6i ne, da bincike ya yi bincike suka gano wata ƙofar sirri dake a cikin dressing room dinsa a bayan wani mirror, daƙyar ma suka iya gano da akwai ƙofa a bayan madubin. Security gareta, dole saida finger print ɗinsa zata iya budewa, da harsashin bindiga suka yi nasarar lalata murfinta daƙyar da sidin goshi.. Lokacin da suka buɗe kofar, tsani suka gani wanda mutun zai hau ya dira cikin ɗakin, su kansu Agent din sun yi al'ajabi, masu ɗaukar video din cikinsu sai jinjina kai su ke yi.. Bayan sun shiga ciki, nan fa suka fara cin karo da tuluna da akwatinan ƙarfe sunkai hamsin hada buhunhuna, ga wata faskekiyar wardrobe manne da bangon ɗakin ta mamaye ko'ina, floor lamp ɗaya ce take haskaka ko'ina na cikinsa.. Rarraba kansu suka yi wasu suka fara 6alle makullan akwatinan yayin da wasu suka dinga faffashe tulunan, bakomai ne a cikinsu ba face zinarai, wata irin razana suka yi cikin ruɗu suke kallon Ikon Allah, dukiya kamar baza a mutu a barta ba, sunyi zaton tulunan ruwa ne ashe na zinaraine, gaba ɗaya saida suka mamaye floor din dakin. Komawa suka yi kan wardrobe din nan, suka fara faffasa doors din jikinta har saida suka yi nasarar buɗe ta gaba daya, ja da baya suka yi cike da al'jabi suke kallon golds din dake a jere cikin kowani shelves nata, ga wasu bendir bendir din kuɗi na kasashe daban daban daga ciki hada Gbp da Dirham, baya ga daloli da naira, duk wani abu mai daraja daya mallaka yana a cikin wardrobe din nan, da wannan dukiyar tsaf za'a rabawa kowani ɗan kasa gida da mota, hada jarin da zai yi kasuwanci, amma saboda haɗama mutun ɗaya yayi babakere akan ta, dukiyar da har danginsu su ƙare ba zasu iya cinyeta ba, duk mun haɗamar mutun sai dai ya mutu ya barta. Saboda haɗama irin na wasu mutanan! Ka handame dukiyar al'umma da wadda ka samu ta haramtacciyar hanya, kai kanka kasan tafi ƙarfinka amma saboda rashin godiyar Allah da haɗama kokari kake ka tara wadda tafi ta kamar ba za a mutu a barta ba. Komai dake faruwa akan idanun Hajiya Sarah da Zeenatu, wlh sun razana da ganin yadda agents suke tono dukiyar Alhaji Musa, su kansu da suke atare da shi tsawon shekaru basu ta6a sanin yana da wuraren sirri acikin gidansa ba, Hajiya Sarah duk tabi ta ruɗe, sai zare idanunta ta ke yi duk inda jami'ae suka yi suna abiye da su. Bayin Allah duk sun sha jinin jikinsu. Tun safe agents suke tono dukiyarsa da ya boye har wuraren karfe 1 da rabi tukunna suka dakata, badan sun gama ba, saboda suna ji aransu gaba ɗaya ginin gidansa da aka yi bana Allah da Annabi bane da akwai wani sirrin a cikinsa da basu gama da shi ba, sun bari sai zuwa lokacin da za a basu umarnin su ruguje ginin gaba ɗaya tukunna. ~_________________________________🍁~ Duk wani guest house na Alhaji Musa dake a garin Abuja sai da agents suka ziyar ce shi, kuma duk gidansa da suka je saida suka bankaɗo dukiyar da ke a cikinsa abin harya fara basu tsoro, kaf ƙadarorinsa dake a Nigeria, sai da suka kullesu, tun daga kan kamfanoninsa, private jets dinsa motocin sa, hotels ne, malls ne, park ne, kowace kaddara tasa dake a garin Abuja saida suka kulle su duk a ranar, hatta accounts dinsa na bank, sun sa an daƙilesu, bai isa ya ciri kudi ba, haka shima ɗan iya sunyi nasarar gano 6oyayyun kadarorinsa sun kulle su, a halin yanzu basu isa su ratsa cikin gari batare da an kama su ba. Lokacin da sojoji suka je gidan gonarsu da ke a cikin wani daji kan hanyar shiga garin Jos, anan suka taras da tantiran karuwansu, da matasan ƴan mata yan shekara sha zuwa ashirin, ashe yaran nan fursinoni ne sun kai hamsin, bayin Allah suna azabtar da rayuwarsu, ba shige ba fuce, su suke yi ma karuwan hidima, da kuma su kan su Elders din, kullum cikin cin zarafinsu suke yi, lokacin da suka farmaki gidan gonar, giant officers din dake tsaron su suka hana su shiga, da suka bisu ta lalama suka ƙiya sai suka bi su ta tsiya, duk suka kashe su.. Gaba ɗaya young ladies ɗin suka razana da ganin su, saboda basu ta6a ganin sojoji ba, da gudu suka dinga shigewa ɗakunansu suna boyewa, wasu a karkashin gado, wasu a kitchen, hada wadanda suka boye cikin toilet.. Ko da karuwan suka ga an kawo masu farmaki da yake hatsabibai ne, sai suka ɗauko bindigoginsu suka fara harbin sojojin, dama can an horas da su yadda zasu kare kansu idan an farmake su, aikuwa sojojin suka ci ƙarfinsu, da ransu ya 6aci ganin ƙarfin halinsu na ɗaukar bindiga har sun raunata sojoji biyar, nan suka rufe su da bugu saida suka haɗa masu jini da majina tukunna suka iza ƙeyarsu har cikin bayan motocinsu, daga su sai pant da bra kamar tumakai. Young ladies din da suke tunanin inmates ne basu ta6a su ba, ɗaya bayan daya suka nemo su a inda suka 6uya, suka kwantar masu da hankali suka ce su basu zo don su cutar da su ba, sun zo ne don su taimaki rayuwarsu, da jin hakan suka kama murna hada kukan su, batare da 6ata lokaci ba, sojojin suka taimaka masu suka shigar da su cikin motocinsu suka tafi da su.. Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ ~*THE FINAL ATTACK*~ Tun da asuba bayan sun kammala sallar asubahi, Hajiya layla da Alhaji ubaid suka je har gaban Shiekh Imam cike da nadama suka roki ya yafe masu butulcin da suka yi mashi, sharrin shaiɗan ne da son zuciya, sun yi danasani kuma suna bashi hakuri akan abun da Musa yayi mashi shi da ƴarsa, sun kuma ji bakin ciki mara misaltuwa.." Akan idon kowa dake a gurin, har zasu zuƙunna kan gwiwowin su Sheikh imam yayi saurin dakatar da su, yace su manta da komai, ya yafe masu, duk abun da ya faru arayuwar shi da ƴarshi ya dauke shi a matsayin jarabtace daga Allah, bayan haka suma ai ba laifin su bane, Musa shi ne musabbabin komai da ya faru." Farin ciki ne ya lullu6e su, suka dinga yi masa godiya kamar zasu durkusa ƙasa. Daga bisani suka roki yafiyar Aisha akan abun da ya faru na rashin adalcin da basu yi mata ba, itama ta ce ta yafe masu, Allah kuma ya yafe masu gaba ɗaya suka amsa da Ameen.. Bayan komai ya ɗan lafa, kowa ya nemi yafiyar wanda ya 6ata ma rai, Abie da Mami su ka yi masu sallama suka tafi gida saboda halin da suka baro iyalin ɗan iya, suna bukatar su a kusa da su bayin Allah, Anila dai bata bisu ba tana a gidan Chief Owais, saboda aminnanta da suke a hali na jimamin ƙaddarar da ta same su, yanzu haka tana a ɗakin Aisha tare da Benazir. "Aisha, duk da komai da ya faru ba laifin kowan nan mu bane amma hakan bazai hana mu baki hakuri ba. Ki yafe mana dan Allah, mun san kin cutu, amma komai ya wuce dan Allah mu koma kamar yadda muke a da..." Benazir da Anila ne suka hada baki gurin yin maganar yayin da suke a zagaye da Aisha. Suna a zazzaune kan rug fuskokinsu sharkaf da hawaye, idanunsu sun kumbura sunyi ja sakamakon kukan da suka sha jiya ga rashin baccin da basu yi ba. da tafukan hannayensu suke share mata hawayenta dake sauka kuncinta. "Ni yakamata in nemi yafiyar ku, ku yafe mini, na yi kuskure da na tafi batare dana faɗa maku ba, nasan da duk hakan bata faru ba. Bayan haka na yi maku laifi, ranar da muka hadu tabbas na ji dadin da ba zai misaltu ba dana sake ganin ku, amma zuciyata sai ta dinga zuga ni akan kada in kula ku, sakacin ku ne yasa kuka bar ƴata ta mutu, baku bata kulawa ba, shiyasa ko kun kira bana picking..." idanunsu cikin na juna suke sauraronta. "Amma daga baya da na ji komai a bakin Musa, na yi danasani,.." Kifa kanta ta yi saman kafadar Benazir, "Kin yi abun da bazan iya biyanki ba Benazir, saboda kaunar da kike min yasa kika jefa rayuwar ki cikin hadari..." Ɗagowa ta yi da kanta, ta ruƙo hannayesu a cikin nata tana murza su. "Aisha, baki mana laifin komai ba, mu manta da komai da ya faru, mun yi imani da Allah, kuma mun yi imani da kaddara, kuma komai ya faru da mu jarabtace daga gare shi, tabbas uncle Musa ya zalunce mu amma ba mu ya zalunta ba kanshi ya zalunta, in sha Allah zai ga mummunar sakayya.." In a broken voice Benazir ta yi maganar. In a cool voice Anila ta ce, "Dukkan mu mu yi hakuri mu rungumi kaddara, tuna abun da ya faru baya ba zai amfanar da mu komai ba, illa iyaka ya fama raunin da ke a zuciyoyinmu..." nasiha mai dadi suke yiwa junan su. "Yanzu ni damuwata ƴaƴan mu har yanzu ba wani labari, sun gano su ko ba su gano su ba, bana so ya cutar da su bana so ya kashe min su.." Aisha ce ta fada cikin ƙunci. "Na fi jin Batool, yarinyar nan tun tana cikin mahaifiyarta take fuskantar jarabawa, ita ma kuma ta zo duniya ta dasa da fuskantar tata jarabawar..." cikin raunin murya Benazir ta ƙarashe maganar... Aisha ta ce, "Haka itama Unaisah, tun tana a cikin mahaifiyarta take fuskantar jarabawa, itama kuma da ta zo duniya ta dasa da fuskantar tata jarabawar, na daɗe ina nanata labarin Unaisah a zuciyata ban taba kawowa raina ke ce mahaifiyarta ba, amma Unaisah ta yi bajinta, gaba daya sun cancanta su yi rayuwar farin ciki a tare da mu..." Anila da ke sauraronsu sai share ƙwalla ta ke yi. "Pls ku kwantar da hankulanku in sha Allah babu abun da zai same su, kada ku manta addu'ar iyaye akan ƴa'ƴan su kar6a66iya ce, Kuma addu'ar wanda aka zalunta akan wanda ya zalunce shi itama kar6a66iyace, daren jiya mun kwana muna yi masu addu'a, bi'iznillahi addu'oin da muka yi masu zasu isa gare su ne, In sha Allah ina ji a raina zasu dawo da ransu da lafiyarsu.." Cikin kwantar da murya take lallashin su.. Knocking Kofar dakin aka yi.. "Wanene"? Aisha ce ta tambaya, "Shureim ne..." Daga waje suka ji ya ambata.. Kallon Aisha suka yi, ganin ta sadda kanta ƙasa.. "Nasan da ke yake son yin magana, tun jiya ya ke neman hanyar da zaku ke6e, dan Allah ki je ku gana." Benazir ce ta faɗa. Share hawayen fuskarta ta yi tare da mikewa ta nufi kofar ta ɗan buɗe tare da leƙa kanta, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin kwarjini ya yi mata ta yi saurin kawar da idanunta daga kallon shi, mutuncinsa da ya zube a idanunta ada yanzu ya dawo sabo, tun da ta ji komai a bakin Musa. Ya kafe ta da idanun shi yanata kallonta kamar zai haɗiyeta.. "Zamu iya magana"? Kamar jira take ya tambayeta, da sauri ta ce, "Eh." Juyawa ya yi tabi bayan shi suka nufi back yard din gidan, a saman park chair suka zauna wata irin ni'imtacciyar iska ce ke ratsa fatarsu Ta yi shiru tana jira ta ji me zai ce mata, Idanunta na akan yatsun hannunta da take wasa da su. Yayin da ya kafe ta da idanunshi, sai kallonta ya ke yi. "Aisha am..." Katse shi ta yi, "Nasan me zaka ce, komai ya wuce ya Shureim, kada ka yi min magana akan abun da ya faru baya, idan ma akwai wanda ya cancanci ya nemi yafiyar to ni ce, ka yi hakuri ya Shureim na munana maka zato bisa rashin sani, idan na tuna marin da na yi maka a ranar sai in ji bakin ciki ya turnuƙe zuciyata, ashe ba yin kanka bane, meyasa banyi maka uziri ba? Meyasa ban saurareka ba? Meyasa lokacin da ka ce na tsaya zaka aure ni mu rufawa juna asiri ban yi ba...?" Bata ƙare maganar ba ya yi saurin toshe mata baki da yatsan shi, suka ƙurawa junan su ido yayin da hawaye ke zarya kan kuncinsu, wani irin kallon so da kauna suke ma junan su..😍 "Aisha bana so kina magana akan abun da ya wuce, mu manta kawai, ina mai baki hakuri akan zaluncin da Uncle Musa ya yi maki, na ji bakin cikin da bazai misaltu ba. jinjina mashi kai ta yi alamar ta yi... "Ki yafe min Aisha, na yi kuskure tun farko da ban bayyana maki soyayyata ba, zurfin cikin da na yi shi ya ja min, ban tashi sanin kina sona ba sai da na ji a bakin mahaifinki, a ranar da ya kira ni don ya tuhumeni akan abun da na yi maki...." labarta mata tattaunawar da suka yi da imam malik ya yi.. "Lokacin da Benazir ta zo dake ɗakina don ta nuna min ke a ranar dana dawo daga Egypt, na nuna kamar bansan ki ba, amma wallahi Allah shine shaidata Aisha, na yi maki son da ban ta6a ma wata ƴa mace ba, tunkafin in mallaki hankalina nake son ki, da soyayyarki na girma a cikin zuciyata, lokacin da ina Egypt, bani da abun kallo a wayata da ya wuce hotunanki da videos din da ake yi maki a gurin musabaƙa, da zarar an saki videos dinki jiki na 6ari nake zuwa in kalla, dake nake kwana dake nake tashi a raina, kamar yadda kike addu'a a kaina nima haka nake yin addu'a akan ki, kin sha hanani bacci Aisha ..." Kalamansa sun karya zuciyarta, yanzu ta gane ba ita kadai ta yi dakon soyayyar shi ba, ashe shima ya so ta kamar ran shi.. "A ranar da na gaji da azabtuwa da sonki, na yanke shawarar zan tunkare ki in faɗa maki halin nake a ciki, a ranar ne na jiyo firar da ku ke yi ke da su Benazir a ɗakinta, na ji kina fadin kinsan babu namijin da zaiso ki tsakani da Allah sai don surar jikin ki, da na ji wannan maganar nan take gwiwata ta sage, na ji tsoron ma in tunkare ki da maganar saboda nasan nima zaki iya tunanin saboda surar jikin ki na ke son ki, dama tun farko abun da ya hana in faɗa maki saboda ina jin tsoron amsar da zaki bani, shiyasa na kasa tunkarar ki da maganar, saboda ina jiye ma kaina tsoron ki ce baki sona, zan shiga mawuyacin hali, haka na ci gaba da tunanin ta wace hanya zan tunkare ki da maganar batare da kin zargi jikinki nake so ba, ban kaiga samun mafita ba, wannan mummunan al'amarin ya faru..." bata san sa'adda ta kife kanta saman kafaɗarshi ba, wani irin son shi ne ke ninkuwa a cikin zuciyarta. "Yaya Shureim, gaba daya mun yi kuskure da bamu bayyana son da muke ma junan mu ba, nima abun da ya sa na kasa fada maka ina son ka, saboda ina jin tsoron ka ga kamar na zubda ƙimata, duk da ba haramun bane don mace ta ce tana son namiji, amma wasu mazan na zamanin nan ba su daraja macen da ta ce tana son su, hada kuma ƙarin nima ina zallumin ka ce baka sona..." gaba ɗaya jikin su kerma ya ke yi, sun kasa tsayar da hawayen dake sintiri kan kuncinsu. "Amma yanzu daka bayyana min soyayyarka, hankalina ya kwanta, sai na ji kamar an yaye min wani sashe na damuwata, ka yi haƙuri ya Shureim na ji kunya, na kuma ji tausayinka da na ji irin izayar da iyayenka suka yi maka kai da babynmu, ashe haka kake son jinina?" Ta tambaya batare da ta ɗaga kanta ba.. "Tayaya ba zan so jininmu ba Aisha? har raina zan iya badawa a kanta, a lokacin da nasan tana a raye wlh har raina zan iya sadaukarwa saboda in ceto rayuwarta. Ina son ta kamar yadda na ke son ki." "Ya Shureim ko bayan da abun ya faru ban tsaneka ba, saima sonka da ya ƙara ninkuwa a zuciyana, kawai dai na yi baƙin cikin ta yadda abun ya faru, amma ya wuce..." murmushi ya yi, still idanunsa akan ta, ko kyaftasu bai son yi "Ya Shureim ka ta6a ganin ta?" Ta tambaya tare da ɗago kanta ta dube shi. "Eh, a ranar dana kawo su Benazir gidan nan na ganta, har na taimaka mata gurin cire mata mayafinta da ya sargafe kunnanta.." Murmushi ta yi. "Ya ka ganta?" "Kamar na yi kakinta." Ya fada tare da jan hancin ta, murmushi suka sakar ma juna.. (Allah sarki Soyayya ruwan zuma, su boss ko yaushe romeo zai zo😂 Oh ni, inata aikin jiran baby Junaid.) "Tun a ranar farko da na fara ganinta nake ta kokarin in tuna dawa ta ke yi min kama, ban tashi tunawa ba sai ranar da na sake ganin ka. Ina son ta Ya Shureim, ina son jininka sai dai..." Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda ƙululun bakin cikin da ya tokare makoshinta, sakamakon tunawa da ta yi a yanzu yarinyar bata a tare da su, tana can hannun azzalumin mutumin da ya cutar da rayuwarta. Gefen fuskarta ya shafa,"Aisha nasan me ke damunki, nima ina jin raɗaɗin da kike ji a zuciyarki, but pls, mu yi hakuri mu jure, in sha Allah ba abun da zai faru da su, Allah ba zai bari ya cutar da su ba, tun da mun yi masu addu'oi toh mu jira muga abun da Allah zai yi akai tun da mun yi imanin shine mafitarmu.." Kalamai masu dadi da kwantar da hankali ya ci gaba da furta mata har saida ya samu ya shawo kanta.. Mayar da kanta ta yi saman kafaɗarshi ta dan lumshe idanunta. ~________________Benazir & Anila~ Suna tsaka da yin firar abun da ya faru da su jiya, knocking din kofar da aka yi ne ya katse su. "May be Aisha ce ta dawo, bari na duba. " Anila ce ta fada tare da miƙewa.. Benazir ta ce, "Anya Aisha ne? Ke kina tunanin ya Shureim zai kyaleta yanzu? Tun fa jiya da muna yin salla na lura daga an sallame sai ki ga ya juyo da kai ya dube ta.." Duk da halin da suke a ciki na zullumi da fargaba sai da suka dara. Buɗe kofar ɗakin Anila tal yi, Taj ta gani a tsaye ya rungume Junaid dake ta yin kuka a ƙirjin shi.. "Anila tayaya akai Junaid ya ga gawar Ana? Gashi nan tun da ya farka yake ta kuka yana ambaton sunanta, wlh na yi mamaki, inata lallashin shi ya ƙi yin shiru." Tausayin shi ne ya rufe Anila, da sauri ta kar6e shi ta rungume a kirjinta tana dan jijjiga shi, fuskarsa ta jiƙe sharkaf da hawaye, ta yi mamakin yadda har Junaid ya iya ruƙe abun da ya faru bayan baccin da ya sha. "Ka yi shiru my baby boy, ka daina kuka, ba abun da ya faru da Ana, tana nan.." Cikin shessheka ya ce, "Mom.. mommy ai na ga Ana, ta mutu, dodo ne ya kashe ta, ba na faɗa maki ba, kuma na ganta bata motsi, Ana ta mutu, ta tafi lahira gidan Allah..." ɗan zaro ido Anila ta yi ta ɗan kalli Taj suka hada ido, murmushi suka yi.. "Kana so Ana ta shiga aljanna?" Jinjina mata kai ya yi yana faman mutsustsuke idanunshi.. "To ka yi mata addu'a, amma in ka ci gaba da kuka Ana bazata shiga aljanna ba, ka ga ko mun je wata rana ba zamu ganta ba." da sauri ya soma share hawayen shi, "Bazan ƙara ba, na daina, ina so Ana ta shiga aljanna." Shafa sumar kanshi ta yi. "that's my boy." "Anila, ke da waye ne? Na ji kamar kukan Junaid." "Wlh shine Taj ya kawo min, Yaro ya burkice yana ta sambatu kan Ana.." Fitowa Benazir ta yi daga dakin. hada ido suka yi da aj, gaba daya sun fahimci damuwar da kowan nan su yake a ciki.. "Daddyn Unaisah, ka tashi lafiya? Ka ci abinci? Ka yi bacci kuwa?" Da damuwa ya ce, "In har kin yi duk abun da kika tambaye ni toh nima na yi, in kuma baki yi ba, nima ban yi ba.." Murmushi ta yi, "In har ba su Unaisah ne suka dawo ba, bana jin zan iya cin abinci ko in yi bacci." Bata ƙare maganar ba ya katse ta, "Inason magana da ke." Kallon Anila ta yi a lokacin har ta juya ta shige ɗaki da Junaid.. Bin bayan shi ta yi, suna gab da zasu gifta ta falo Alhaji Ubaid ya yi masu gyaran murya, sam basu lura da su ba. Shi da Hajiya Layla ne zaune kan kujera.. Cikin nutsuwa Taj ya nufe su, with respect ya gaishe da su.. Cike da jin nauyin shi hajiya Layla ta ce, "Taj kaima mun yi maka laifi, tun jiya nake ta so in nemi yafiyarka amma kunya ta hana ni Taj." Ta faɗa idanunta cike tab da ƙwalla tana ɗan girgiza kanta cike da danasani. "Tun da ka auri Benazir ban ta6a nemanku ba, lokacin da kuka 6ace, na ji labari amman ban nuna damuwa ba ko kaɗan, saboda banso Alhaji ubaid ya baka auren ta ba, shiyasa na zame hannuna a cikin rayuwarku tun da kai ba za6ina bane, na yi maka wulakanci saboda kasantuwarka ɗan jarida mai rufin asiri, a lokacin da idanuna suka rufe da son siyasa, a ganina zaka jaza mana matsala ne, ashe ba haka bane, kai din Alkhairi ne a cikin rayuwar mu, samun suruki irinka zai yi wuya a duniyar nan, gashi ta silar haɗa zuri'a da kai mun samu lu'u lu'un da kowa ke alfahari da shi. Murmushi suka yi shi da Benazir, har ga Allah bai ta6a ruƙe su aran shi ba, tabbas bai ji dadin halin ko in kulan da Hajiya layla take nuna masu ba, Amma saboda Alhaji ubaid yana son Unaisah yasa bai ta6a ruketa aran shi ba.. "Kada ki damu, komai ya wuce, na yafe maki, Allah ya yafe mana baki ɗaya." Ta amsa da Ameen. Alhaji Ubaid yana murmushi ya ce, "Gaskiya ni ban yafe mata ba, tsakani da Allah bata kyauta ba, ko fa fuskar jikarta bata ta6a sani ba, sannan kuma ka ce ka yafe mata ta cikin sauki, lalala, sai ta ji jiki tukunna." Dariya suka saka, kamar babu damuwa a tare da su. "Baba, ayi hakuri dai a yafe mata tun da ta gane kuskurenta, mu ma muna so in munyi laifi Allah ya yafe mana." Alhaji ubaid ya ce, "Toh mun yafe mata, ba don halin ta ba." Tana murmushi ta dubi Benazir, "Yanzu hankali ya kwanta ko? No more pretending, and no more tashin hankali akan mijina, ƴata, duk kika bi kika hana mutane bacci. murmushi suka saki gaba dayan su. "Daddy, mommy, pls, tun da mun haɗu gaba ɗaya kuma ga Taj shima, ku saka baki ya maidani..." buɗe baki suka yi da mamaki, kunya ta kama Taj ya sunnar da kai ƙasa. Alhaji ubaid ya ce, "Koda yake, ay da yake jinin ki ce, fiye ma da haka zata iya." Hajiya Layla ta yi saurin cewa, "Dan Allah ka daina mana, a gaban surukin namu." Ta faɗa tana nuna Taj, dariya suka yi.. Harara ta galla ma Benazar. "Ke ko irin alkunyar nan baki da ita, ay kya bari jikokin namu su dawo lafiya ko." Walwalar fuskarta ce ta ɗauke, ji ta yi kamar ta fama mata raunin zuciyarta. Lura da yadda jikinsu ya yi sanyi yasa Alhaji Ubaid da hajiya Laylan suka haɗu gurin kwantar masu da hankali. Daga bisani suka ce su tafi inda zasu je, miƙewa suka yi a tare suka nufi garden, a kan kujerun shaƙatawa suka zauna.. "Pls ki daina zubar da hawayenki, In sha Allah ba abun da zai faru da su, zasu dawo lafiya".. Jinjina kai tayi, "Zan daina amma kasan ba yadda za'ay hankalina ya kwanta bayan ƴa'ƴanmu suna a hannun fasiki, wlh baka ji yadda zuciyata ke bugawa ba, tun ɗazu nake jin fargaba, gabana yana ta faduwa..." "Ummu Unaisah, duk abunda kike ji nima ina jin shi, amma ya zamu yi? Tun da munyi masu addu'a kamata yayi mu bar ma Allah sauran, in sha Allah zai duba kokenmu kuma zai kawo mana mafita.." Kwantar mata da hankali ya yi har saida ya samu ya shawo kanta. Shiru suka yi, idanunsu akan fararen agwagin dake yawo cikin garden pool din gaban su. "Akwai abun da ban faɗa maki ba, saboda bana so kiji ba daɗi..." bai ƙare maganar ba, ta katse shi da cewa, "Ka auri yarinyar da ta ceci rayuwar Angel ɗina?" Da mamaki ya dubeta, "Tayaya akai kika sani?" murmushi ta yi, "Jiya bayan mun fita yawon shaƙatawa, lokacin da zamu dawo, da aka kira magrib ka shiga masallaci yin sallah ka barni a mota, an kira wayarka, dana duba screen din sai na ga suna ya bayyana My Danejo, na yi picking call din anan na ji tana faɗin ta ji shiru shiru har yau baka dawo gida ba, bayan ka faɗa mata kun dawo daga kai farmakin, dan Allah ka dawo ta yi missing ɗinka. Ban ƙarasa sauraronta ba na yi rejecting call din saboda kishin da ya turnuke zuciyata, amma ko bayan daka dawo ban bari ka gane halin da nake a ciki ba. Bayan na dawo gida, ko dinner ɗina ban ci ba, na ƙumshe a ɗaki na ci kuka na, saboda raina ya bani kana da aure ka boye min ne, jiyan nan kasa bacci na yi, ina jira washe gari ta yi don in kiraka in tuhume ka akanta, da damuwa ta ishe ni na fito daga ɗaki, kwatsam na ga Yaya Shureim yana ta sauri zai fuce daga falo na je na tare shi anan yake faɗa min Aisha ta kira tana neman shi..." tun da ta fara magana yake kallon cikin idanunta, a jiya daka bamu labarin abun da ya faru da kai, anan ne na ji irin taimakon da bafullatanar dajin nan ta yi ma Unaisah, kuma na ji ka ambaci sunanta Danejo, duk da baka bamu labarin da ita ka dawo ba, ko kun yi aure amma ni na gane itace wadda ta kira ka a waya, saboda hausarta bata ƙware ba, ina ji na gane bafullatana ce, nan take na gane kuna a tare. "Ummu Unaisah am sorry idan baki ji dadi ba, na aureta ne saboda ta so ni, kuma iyayenta ne suka damƙa mani amanarta saboda ta nuna bazata iya rayuwa batare da ni ba, bayan haka a lokacin bani da zabi, nima ina sonta saboda kyautatawar da ta yi ma ƴata da kuma ni, kuma nasa ma raina ba zaki ta6a dawowa cikin rayuwata ba..." A taƙaice ya labarta mata komai da ya faru tun daga farkon haɗuwarsa da Danejo... Ajiyar zuciya ta sauke, kwata kwata bata ji kishi ba tun da ta gane ita ce bafullatanar da ta taimaki Unaisah. "Taj, ka yi abun da ya dace, in ma baka aureta ba ni zansa ka aureta ne, saboda ta hakane kaɗai zamu iya rama mata halaccin da ta yi mana, da ba don Allah ya ƙaddara faɗawarta cikin ruwa ba, da yanzu babu Unaisah. Inason me son ƴata, don haka, bazan yi kishi da Danejo ba, zan dauke ta kamar ƙanwata." Kalamanta sun faranta ran shi.. "Allah ya yi maki Albarka Ummu Unaisah, Allah ya bayyanar mana da ya'yan mu." "Ameen..." "Idan Allah Ya maido mana su Unaisah lafiya, ka kaini part din ka in ganta." "In sha Allah" Daga haka suka yi shiru.. Yanzu dai gaba daya kowa jiran tsammani ya ke yi! Kusan sau hamsin Taj yana kiran Chief wayar bata shiga, ya ƙagara ya ji meke faruwa? Sun yi nasarar gano su ko kuwa har yanzu❓ Gaba ɗaya ko wani ahali daga cikin su haka suka wuni da fargaban a wani hali yaran nan suke a ciki, tun jiya da dare ba ci ba sha, ruwan tea din da suka sha lokacin da suka yi nafilfili ne kaɗai ya rage a cikin su.. Abu kamar wasa, har dare ya yi babu labari dangane da su, Hajiya Layla da Alhaji Ubaid da marece suka bar gidan Owais, sakamakon kiran da Hajiya Sarah take ta yi masu game da rashin dawowarsu gida, kuma sun barsu cikin fargaba. Kusan gaba ɗayansu suna a falo cikin damuwa, kowa ka kalli fuskarshi babu annuri bacci suke ji amma damuwa ta hana baccin ya ɗauke su, sun kasa sun tsare sai sunga dawowar ya'yansu, sheikh Imam ne ke tausarsu da nasiha mai ratsa zuciya, Taj ne kaɗai baya a falon bai daɗe da fita ba ya je ya kwantar da baby Junaid. Benazir da Aisha da Anila suna a zazzaune kan rug sun zabga tagumi suna sauraron Sheikh Imam, yayin da Dr Shureim ya ke a gefen shi, shi kanshi Imam malik din ba ƙoshin lafiya ne da shi ba, har yanzu yana jin ɗacin abun da Musa ya yi mashi a ranshi, ya yi masa abun da har abada ba zai manta da baƙin cikin nan ba, amma ya fawwalawa Allah, kuma baya son rauninsa yasa suma su shiga damuwa ko dan saboda alkawarin da ya yi ma Aisharsa. ~______________________________~ A bangaren gidan ɗan iya, bayan komawar su Abie, a falo suka iske mutanan gidan sun zabga tagumi, sunyi kukan har sun gaji sun godema Allah, baƙin ciki da damuwa sun hana su sukuni. Zahra ma bata da lafiya, tun bayan da lamarin ya afku zazza6i ya lullu6eta, ta dinga amai har daga kwance.. Mahboob ma kamar baya a cikin hayyacinsa, firgita ya ke ta yi, haɗi da sambatu yana ambaton Ana ta mutu, daddynsu ya kashe Ana, shima mutuwa zai yi,. Baiwar Allah Mami duk da halin bakin cikin da take a ciki ita ke ƙoƙarin lallashin su, sai dai duk da hakan ta gaza shawo kansu, sun ƙi cin abinci tun jiya har yau. Lokacin sallamar Abie ta katse su, Mami ta shiga faɗa masu halin da suke a ciki, ta ce su taimaka mata ta shawo kansu, bata son ta rasa ƴa'ƴanta, abun zai yi mata yawa..." Wlh kasa magana suka yi saboda tausayin su, fargabansu ma kada su ji sauran miyagun ayyukan da ɗan iya yake aikatawa, watakil zaucewa za su yi.. Daƙyar suka lallashe su, Abie ya taimaka ma Mahboob ya yi wanka, itama Mami ta shiga da Zahra ɗaki tasa ta yi wanka, daga bisani ummi ta shiga kitchen ta girka masu wani abincin, don wanda suka bari na jiya tuni ya lalace. A tray ta shirya abincin ta kawo masu a falo, gaba ɗaya suka kasa cin shi, suka dinga tausarsu suna lallashinsu akan su yi hakuri da abun da ya faru don ya riga da ya faru, basu isa su canza abun da Allah ya ƙaddara faruwarsa ba, tsakaninsu da Ana addu'a ne Allah Ya jikanta da rahama, Allah Ya bi mata hakkinta. Cikin kuka Zahra ta ce da wannan baƙin cikin da ya ƙunsa masu ƙwara mutuwarsu, wai mahaifinsu ne yake aikata fasikancin nan? har ya iya kashe rai? Anya shi ya haife su? Ko dai musayar uba aka yi masu? basu ta6a ganin 6acin ran Zahra irin na wannan lokacin ba, zuciyarta a wuya take. Ummi ta ce,"Zahra, mu daina yaudarar kan mu, ni na dawo daga rakiyar ɗan-iya, wlh shi ya aikata, zai iya komai don ya samu duniya, Allah ya isa tsakaninmu da shi, wannan abun kunya har ina! Allah ya sa jami'ae su kama shi, su hukunta shi daidai da abun da ya aikata." Da ƙyar suka shawo kanta har suka samu ta yi shiru, abincin ma basu iya cin shi da yawa ba, kaɗan suka ɗan tsaƙura. Bayan sun gama Mami ta ɗauko mata maganin zazza6i ta sha, cikin sa'a bacci ya ɗauke su daga ita har mahboob din da ke ta sambatu.. 🥺 *SHIN INA ALHAJI MUSA YA GUDU DA UNAISAH DA BATOOL, SUNA INA❓* ~______🔥_______🔥_____🔥______~ A hankali ta soma dawowa cikin hayyacinta bayan gushewar da hankalinta ya yi na wucin gadi, bata san inda kanta yake ba sai yanzu da Allah ya farfaɗo da ita. Wani irin zafi ne ya taso mata, zufa ta soma tsattsafowa ta saman fatarta, a wahalarce take jan numfashi saboda ƙarancin iskar da zata shaƙa, dukkan ilahin jikinta rawa yake yi ga wata irin matsananciyar kasala da ta haifar mata da rashin kuzari, tana ta ƙoƙarin buɗe idanunta sai dai ta kasa tsayar da su a buɗe saboda kasalar da take ji, cikin raunanniyar murya take sambatu tana ambaton sunan Batool, Batool saboda ita ce aranta. Kwata kwata batasan a ina take ba, saboda bata iya tuna komai da ya faru a baya, kamar ta yi loosing memory ɗinta. Ƙarar sarƙoƙi sun cika kunnuwanta, Kacacau! kacacau!! babu daɗin ji, ta rasa daga ina sautin ke fitowa, gaba ɗayanta a takure take cikin matsi, ta kasa motsawa. "A ina nake ne? Meyasa bana iya ganin komai sai duhu? Waya kashe hasken ɗakin?" Sautin muryarta daƙyar yake fita a wahalce, kaɗan take iya buɗe idanunta tana gani biji biji. ta shiga ruɗani sosai ga tsoro da ya mamaye zuciyarta, kwata kwata bata kawo ma ranta cewa ba a gida take ba.. "Ko mafarki nake yi? Ko na mutu ne ina a cikin ƙabari?" A cikin zuciyarta ta furta.. "Ya Allah ka kawo min dauki! Ka fiddani daga cikin duhun nan!" Har saida ta fidda rai da za a tanka mata, ta yi shiru tana jan numfashi. Kwatsam a lokacin da ba ta yi tsammani ba, sai ga wani siririn haske yana ƙoƙarin mamaye gurin da take, cikin ƙanƙanin lokaci hasken ya karaɗe ilahirin gurin, tamkar da rana, runtse idonta ta yi saboda hasken da ya kashe mata ganin ta. Lokacin da ganinta ya washe ta buɗe idanun a hankali, kaitsaye suka sauka akan bangon da take fuskanta, wa'iyazubillah! Wata irin firgita ta yi jikinta ya hau yin kerma kamar wadda sanyi ya kama, ta yi matuƙar razana, tsigar jikinta ta dinga tashi, gabanta ya shiga faɗuwa kamar ana buga gangunan yaƙi.. A wani babban ɗaki take mai kama da mayanka, koma in ce mayankan ce, gaba ɗaya bangwayen ɗakin ƙugiyoyine na ƙarfe sargafe da sassan jiki, kamar na mutun kamar na dabba, kuma daga gani sabuwar yanka ce duba da yadda jinin ya wanke ƙasan ɗakin da jikin bangon jawur, kaitsaye yake bin wasu siraran hanyoyi izuwa cikin magudajinsa, wani abun tashin hankali da firgitarwa wasu gungun ƙosassun ƙwari ta gani dadda6e da naman sunata tsotse jinin da ke a jiki, ta ƙara zazzare idanunta cikin ruɗu da tashin hankali. Daga tsaƙiyar ɗakin dogon teburin yanka ne na karfe duk jini a jikin shi har ɗiɗɗiga ya ke yi a ƙasa.. Bakomai bane a saman table din fa ce kayan aikin yanka, wuƙaƙe, gatari, adda da tsinken ƙarfe jikin su duk jini.. fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, ta tsorata sosai, hankalinta ya tashi matuƙa, ta rasa gane mafarki ne take yi ko a gaske ya ke faruwa. Kwakwalwarta nema take ta zauce, cikin shesshekar kuka take ambaton sunayen su.. "My man, Chief, daddy! Aunty Ummi, Batool, wayyo Allahna na shiga uku, Meke shirin faruwa da ni? Wani zunubi na aikata dana tsinci kaina a cikin wannan mummunan mafarkin, idan bacci nake yi ya Allah ka farkar da ni! Bazan iya jure ganin tashin hankalin nan ba, mutuwa zan yi..." bata ƙare maganar ba, ta tsinkayi kakkausar muryarsa a cikin kunnanta. "Welcome back to the Prison of Destiny." Wani irin bugun barazana zuciyarta ta yi, ta shiga rarraba idanu tana jiran ganin wanene ya yi magana? ta ina zai 6ullo, sunan kurkukun ƙaddara da aka furta ya fi komai ɗaga hankalinta, Hasbunallah! ƙwaƙwalwarta ce ta fara kokarin tariyo mata komai da ya faru... _"Ki yi bankwana da su, wannan ita ce ƴarku ke da Shureim, shine hallacin da zan iya yi maki na ƙarshe kafin rabuwar mu..." bata ƙarashe tunanin nata ba, kwatsam ta ga mutun ya bayyana a tsakiyar ɗakin jikin shi sanye da alkyabba ja mai hula, bata iya ganin fuskarsa ba saboda ya bata baya. "Wanene Kai?" Ta tambaya a tsananin tsorace. "Mutuwar ki ce!" Cikin ƙarfin hali ta ce, "Ba'a ganin mutuwa, ka faɗa min wanene kai, meyasa kuma ka kawo ni nan?" Juyowa ya yi tare da fuskantarta, rabin fuskarsa a rufe yake da mask, jajayen idanunsa kaɗai take iya gani. Bai tanka mata ba, har sai da ya matsa gaban ta, tukunna ya zuƙunna. Cike da fargaba take duban shi, kwata kwata bata ji tsoron shi ba ta dai sha jinin jikin ta. A hankali ya sanya hannu ya zame mask ɗin fuskarsa, wata zabura ta yi a gigice kamar zata shige ma bangon bayanta, ganin fuskar mutumin da take nema ruwa a jallo sai gashi yau Allah ya haɗa su, gata ga shi, face to face eyes to eyes nan take ta tuna da komai da ya faru, Ya Ilahi! nan take ta gane a cikin gidan kurkukun ƙaddara ta ke. Cikin rawar murya ta shiga furta, "Allaziina iza asabat'hum museebatun ƙalu 'Inna lillahi Wa'inna ilaihirraji'un, A'uzu Billahi Minasshaidanin Rajim. La'haula Wala quwwata Illah billah, Ƙarfin halinta ya bashi mamaki, baisan ya a kai ya tsinci kan shi da yin shu'umin murmushin nan nashi ba, ta ɗaure masa kai, ido cikin ido take furta addu'oin nan batare da jin shakkar shi ba. "Ko ɗan jarida bai kai ki haɗari ba, yar mitsila dake kamar in matseki a hammatata, da nasan zaki zamar mana annoba da tun lokacin da Ubanki ya zo neman auran Uwarki ban goyi bayan kakan ki ya bashi auranta ba, komai da ya faru kece sila, fitinanniya..." Ya faɗa ransa a 6ace kamar zai rufe ta da bugu. "Ya Allah, Ka raba ni da mugun ji da mugun gani, Ya Allah bazan tambayi meyasa ka jarabce ni da haduwa da wannan fasikin mutumin ba, wanda zuciyarsa babu imani da tausayi a cikin ta, sai zallar mugunta da zalunci, mutumin da ko maƙiyina bana masa fatan ya yi mafarkin haɗuwa da shi, bayyanarsa kamar bayyanar shaiɗan ce, kuma dodo, saboda baida bambanci da su, mutumin da idan ka ganshi a mafarki ka yi gaggawar tuba ka kuma kama yin istigfari don ba ƙaramin zunubi ka aikata ba..." Kwata kwata babu alamun ya ji haushin kalamanta, sai dai akwai mamakin ta akan fuskarsa dake a murtuke, ya yi zaton jinta ya fi ganinta ashe ganinta ya fi jinta, shi ya sadaukar da ita amma bai ta6a haɗuwa da ita a zahiri ba, ya dai san komai game da rayuwarta ta hanyar ƴan leƙen asirinsa masu bibiyar rayuwarta, saninta da ya yi a madubin tsafin su ne inda suke ganin komai da ke faruwa a sashen fursinoni. "Ina kokwanton kina da ta6in hankali, saboda mutum mai cikakken hankali ba zai ganni ido da ido ba, batare da ya tsorata ba saboda ƙwarjinin dake gare ni, yakamata ki shiga taitayin ki, ko baki ga inda kike ba ne..." ya faɗa yana nuna mata ƙugiyoyin naman dake a sargafe jikin bango. Gabanta ne ya fadi rass, sai dai bata bari ya gane ta tsorata ba. "Na ji daɗi da Allah Ya haɗani da kai, Allah Ya amsa addu'ata, kawo ni da ka yi nan ba yin kanka bane, Allah ne ya kaddara haduwar mu saboda nemanka nake ruwa a jallo.." Out of confusion ya ke kallon ta.. "Kamar yadda kake kokwanton ko ina da hankali? Nima haka nake kokwanton anya kana da zuciya a ƙirjinka? Kai mutunne ko dabba...!" Bata ƙare maganar ba, ya kifa mata zazzafan marin da ya kusa sumar da ita, har saida kanta ya juye ta bugi bango. "Ba a yi mini magana da tsawa.." Ya faɗa da gadara. Juyowa ta yi tana huci, sumar kanta ta rufe gefe da gefen fuskarta, gefen lower lips dinta ya fashe har ya fara bleeding, ga shatun marinsa akan kuncin ta ya fito.. "Na je na yi Musa, ka maida gabana gabas ka yanka ni, na tsane ka fiye da yadda na tsani mutuwa, ƙyamarka nake ji, saboda kai ɗin najasa ne.." ta faɗa muryarta na rawa tana zare mashi gray eyes dinta, tsantsar ruɗu ne akan fuskarsa. "Tayaya zan ji tsoron mutum irin ka? Pls ka dinga tuna wanda ya halicce ka mana, na lura kana da izza da jiji da kai, halan ka manta tushen hallitarka daga ɗigon maniyi ne? Ko ka manta ta kofar da aka curo ka lokacin da za'a haifo ka ne? daga jikin mace mai rauni ka fito!" Fuskarsa a ɗaure ya ke kallon ta. "Wanda mutuwa ta riske shi bai isa ya hana kanshi tafiya ba, Ni Allah kaɗai nake tsoro, bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, kuma baya bacci, da shi kuma na dogara, wanene kai? Um? Ta faɗa tana ɗage masa gira. "Mutanan da ka asirce ne suke jin shakkarka, amma ni baka isa ka sarrafa ni ba, na fi ƙarfinka wallahi, da Allah na dogara bada wani mahaukacin kare ba, mai taƙama da ƙarfin sihiri!" Ta faɗa kamar zata doke sa, sarƙoƙin jikinta sai ƙara suke yi kacacau kacacau saboda girgiza jikinta da take yi, yanayin fuskarsa bai nuna damuwa ko kaɗan ba. "Ki bini ta lalama mu rabu lafiya..." "Ai bana so mu rabu lafiya, nafi so tsiya ta raba mu da kai, saboda nasan ba zaka ƙyale ni ba, ka kawo ni nan ne don ka azabtar da ni ko ka kashe ni, saboda kana baƙin cikin yadda na yi silar lalata komai naku, na ja maku bala'e da musiba, na sanya tsoro a cikin zukatanku shiyasa zama cikin gari ya gagare ka, shiyasa ka sato ni ka ka kawo ni nan! Maimakon ka farmake ni gaba da gaba a inda nake!" bata ƙare maganar ba ya daka mata tsawa tare da sa hannu ya damƙi wuyanta ya matse shi kamar zai kasheta, nishi ta dinga saki numfashinta na fita a wahalce, tuni idanunta sun rune zuwa ja, har saida ta shaƙi ƙamshin mutuwa saboda tsabar raɗaɗin da ya ziyarci sassan jikinta. "Ƙaramar yar iska mai kwana da wando, idan na kashe ki na kashe banza, na fahimci bakisan wanene Jan Wuya ba!.." Ya faɗa tare da sakin wuyanta, fatar gurin ta yi jawur kamar wadda hucin ruwan zafi ya daka, ta dinga tari tana nishi Da ƙyar ta iya furta, "Ni kuwa nasan wanene kai, mugun uban da ya sadaukar da ƴarsa saboda neman abun duniyan da bazai amfanesa ba a ranar gobe alqiyama, kuma mugun mijin da ya raba ƴa da mahaifiyarta tuntana jinjira batare da sanin ta ba, ka raine ta batare daka bata tarbiya ba, da kai da fasiƙar uwarta ta bogi kuka hadu gurin lalata rayuwarta, duk hakan baiyi maka ba, ka hanata sanin komai game da addininka ka barta a matsayin arniya saboda kada Allah Ya tuhumeka a ranar gobe ƙiyama, shiyasa duk ƴa'ƴanka daka sadaukar babu musulmi a cikin su, saboda jakkanci da daƙiƙanci, da kuma shafewar basira irin naka..." bata ƙarasa maganar ba, ya kwasa mata wani marin da ya ja har hancinta ya fara bleeding.. Idanunta suka cicciko da kwalla, ta ji zafin marin nan, radadin sa ya ratsa ta, kuma bata fasa maganar ba, "Ai koda hakkin rai ɗaya aka barka wlh makomarka ba zata yi kyau ba, saboda Allah baya barin hakkin wani akan wani, kuma baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, balle kaida ka daɗe kana zaluntar rayukan da basu ji ba basu gani ba, rai nawa ka kashe? Rai nawa ka zalunta? Rai nawa ka lalata uhym? Ko an gaya maka Allah baya gani ne?" Ta faɗa tana ciccije la66anta tsabar masifa duk ta faffasa su, gaba daya ta kashe mashi baki, ko kaɗan bai girgiza ba bai kuma dakatar da ita ba ya bari ne ya ga iya gudun ruwanta, don shi har yanzu baya mata kallon mai hankali saboda ƙarfin halinta.. Tana jan numfashi cikin fushi ta ɗaura da cewa, "Bayan haka kaine mugun da ya raba mahaifiyata da danginta, kuma kaine shaidanin da ya shiga tsakanin Aunty Ummi da mahaifinta, sannan kuma kaine makirin mutumin da ya hada Aunty Ummi da Uncle Shureim, ka kuma raba su da ƴar su, bayan haka, kaine fasikin da ya mayar da aunty Umminmu karuwa ka rabata da kowa nata ka mayar da ita America, saboda wani dalili naka mara amfani.." ta6e la66ansa ya yi batare da ya furta kalma ba.. "Jahilin addini jahilin rayuwa, wallahi ka ji haushin rayuwarka, ka daina farin ciki don ka daɗe kana zalunci wlh kanka ka zalunta, ka gur6ata duniyarka da lahirar ka da kanka, shi zalunci ƙaiƙayi ne dake komawa kan mai shiƙa, kuma guba ne dake cin wanda yayi da wanda aka yi mawa, sannan ƙarshen zalunci nadama ne, kuma duhu ne aranar gobe ƙiyama! Wata riba ka ci yanzu? ni Ban ta6a ganin rai mara buri asararre tambaɗaɗɗe irinka ba.." Ransa ya yi mugun 6aci da jin maganganun da ta gaggaya masa, a rayuwarsa ya tsani mutumin da baya jin shakkar shi, abun da ya fi bashi takaici ƴar ƙaramar yarinyar dake gaya masa magana.. Yana fitar da numfashin bacin rai mai huci ya ce, "Ni ba asararre bane, ni ne mai buri, ban ta6a yin asara ba, komai na nema saina same shi, tun da nata so rayuwata ni mai nasara ne, mai faukaka kuma shahararre mai arziƙi, har matsayin shubagan ƙasa na taka, me yafi wannan?" Ya faɗa yana ɗage mata gira. "Kuma na ci riba, tun da na dade ina sheƙe ayata batare da asirina ya tonu ba, ina da karfin ikon da babu wanda ya isa ya ja da ni, ko mutuwa tsorona take ji.." Ya fada cike da alfahiri, Girgiza kai ta yi, "Wanda ya 6ace ya 6ace, lokacin mutuwar ka ne bai yi ba, ka daina alfahari saboda har yanzu baka yi nasara ba, Allah baya mantuwa, kuma shi mai ji ne kuma mai gani. Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Haƙiƙa ALLAH Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi bazai kuɓuce masa ba.” "Na fi ki ilimin addini ki daina kokarin yi min wa'azi.." "Banga alama ba, kuma koda kana da ilmin toh baka aiki da shi sannan baka fahimce shi ba, ka dai yi asara, kuma ka ji kunya. Unaizah ta mutu tana ambaton kalmatusshahada, abun da kake ma baƙin cikin ta samu, kuma ta gane wanene mugun ubanta, mun fayyace mata komai kafin mutuwarta, idan ma kana tunanin ƙarya na ke yi maka, da akwai wasiyyar da ta bar min in baka kai da kwartuwar karuwarka, sannan tasa na yi mata alƙawarin ɗaukar fansa akanka, kana ganin kanka mai wayou da dabara bakasan komai kake yi Allah yana a sane da kai ba, baya mantuwa, dama ce ta ɗan lokaci, Unaizah ita ce silar tonuwar asirinka, nasan ka girgiza da jin hakan lokacin da aka faɗa maka, ƙaramin kuskure ya yi silar tonuwar asirin ka..." da tsantsar ruɗani akan fuskarsa ya furta, "Unaizah ta musulunta? Kuma kun faɗa mata komai! Ta yaya hakan zai yiwu? ba gaskiya kike fadamin ba, karya ki ke yi..." Ya fada cikin 6acin rai.. Murmushin takaici ta yi. "Ka yarda ko kada ka yarda matsalarka ce, sannan twin ɗinka ya musulunta, nasan ka gane wa nake nufi, duk da bansan ko su kaɗai ne twins din da kake da su ba, tun da na ga kai din bunsurune baka da aikin yi sai zazzaga ya'ya kamar kashin awaki, kai ta sadaukar da su.." Maganganunta sun ƙona masa rai, cikin ruɗu ya furta, "Wanene twin din da kike magana akai? ƙyalƙyacewa ta yi da dariya ganin yadda ya 6ata fuska. "Ina magana akan Sajeed, ko da ya ke bari na yi maka ta yadda zaka gane, Gabriel nake nufi." "Tayaya akai kika san ɗana ne?" Ya tambaya a ƙagare da son ji. A takaice ta fayyaca masa komai.. Runtse idanunsa ya yi cikin bakin ciki ya ke tariyo lokacin da ya sadaukar da su, ƙa'ida idan ya sadaukar da yaro zai ƙone komai nasa da yake amfani da shi, amma a lokacin da ya sadaukar da twins dinsa, sai bai ƙone wayar Gabriel ba, sabuwa ce bai jima da siya masa ita ba, sai ya yi restore din wayar, sham ya manta bai cire sim card ɗinta ba, ya dawo da ita gidansa na Abuja, ya ba Hajiya Sarah ya ce taba Zeenatu ta dinga karatu da ita kafin ya mayar da ita school, bai ta6a zaton ƙananun kuskuren da ya yi zasu iya zamar masa matsala ba, lamarin ya ɗaga hankalinsa, ta yadda kwakwalwarsa ta toshe a lokacin da ya kawo wayar batare da ya tuna da sim card ba! Abun da ya fi daure masa kai meyasa bai tuna ba? Meyasa kuma bai yi tunanin siya mata wata wayar ba sai ya kai mata ta Gabriel ( Ga dukkan alamu Musa baisan ƙarfin Ikon Allah ba, idan Allah ya so ya tona maka asiri, wallahi da kanka zaka aikata ƙaramin kuskuren da zai yi silar tonuwar asirinka, dubararka ko wayonka baza su ta6a amfanar da kai ba, dole ne ka aikata ta hanyar da ya so) Yayi zurfi a tunaninsa muryar Unaisah ta katse shi, "Dukiyar da ka ke taƙama da ita ay bada guminka ka same ta ba, haka itama ɗaukakar taka bata Allah bace, daga gani kai din irin faƙiran talakawan nan ne marasa galihu marasa godiyar Allah masu kwaɗayin abun duniya, wadanda zuciyarsu ta mutu, ai ba a tunƙaho da dukiyar da aka tara ta haramtacciyar hanya. Tausayi ka ke bani saboda na fahimci har yanzu baka san musibar da kake a ciki ba, kaifa yanzu taka ta ƙare, asirinka ya riga da ya gama tonuwa, yanzu ne zaka gane komai daka tara baida amfani, zaka rasa darajar ka! mutuncinka da ƙimarka zasu lalace, al'ummar duniya zasu fara yi maka kallon ƙasƙantaccen ɗan ta'adda, ƴan jam'iyarka da yan uwanka da abokananka kowa zai juya maka baya, zaka zama abun gudu, zaka rasa su na har abada, lalacewa ta same ta, daga inda duniya tasan me ka aikata zaka tashi daga Alhaji Musa richest former president ka koma gur6ataccen ɗan ta'adda, mutane zasu fara aibata ka, za a dinga zagin ka da tsine maka albarka kuma ko bayan ranka ba za a daina sukar ka ba, waɗanda ma basu san da tarihinka ba, idan sun zo duniya zasu ji, amma ba a matsayin mutun mai daraja ba, a matsayin fasiƙi, azzalumin ɗan ta'adda. Kuma ina taya ka murna bayan tozarcin da zaka fuskanta, da kuma azabtarwar hukuma, zaka fara ganin sakayyar mutanan da ka zalunta, ka aikata sin jariya, zunubi mai wanzuwa, idan mutun ya mutu halinsa ne ke cetonsa, Musa da wani hali zaka ceci kanka? tun wurin zare ranka zaka fara shan azaba, ka yi tunanin makomar wanda ya sani ya take sanin, ai kai kana a can cikin ƙwarin azaba, ƙasa da kafiri, a halin yanzu ko titi baka isa ka ƙetare ba matsoraci, rundunar sojoji tana jiranka, ga al'ummar gari, kana dira kafarka zasu fara jifarka... ." Ta ƙarashe maganar tana sakin dariya kamar zautatta. Ransa yayi mugun 6aci, daga yanayin fuskarsa zaga gane ya ji zafin kalamanta kuma ya girgiza, tsabar yadda zuciyarsa ke tafarfasa har wani gurnani gurnani ya ke yi.. Shaƙe wuyanta ya kuma yi, kamar zai tsinka shi, numfashinta ya dinga kokawar daukewa tana ta nishi, yadda zufa ke tsattsafo mashi kan goshin shi itama haka gumi ke tsattsafo mata, tana ta kokarin kwatar kanta sai dai ta kasa saboda a ɗaɗɗaure ta ke da sarƙa. "Dole in yi maki azaba mai radadi, tun da nake wani ɗan adam bai ta6a gaya min bakaken maganganu ba sai a kan ki, duk da ba na yi maki kallon mai hankali hakan bazai hana in hukunta ki ba, daga yau ba zaki ƙara shaƙar numfashi ba, kashe ki zan yi mahaukaciya, laifi ɗaya da nake danasani a rayuwata shine barin ki da na yi a raye, duk abun da kika faɗa akaina ba zai ta6a faruwa ba, ina da sihirin da zan kare kaina da shi..." Yana fada yana fitar da numfashi mai huci, baiwar Allah ta gaza taimakon kanta, idanunta kamar zasu zazzago ƙasa sunyi luhu luhu. "Ni fa Uncle din Uwarki ne, kamar kaka nake a gurinki, ko dan haka yakamata ki girmamani don ubanki, ba zan kashe ki cikin sauƙi ba, ina so na saka tsorona a cikin zuciyarki, ta yadda ko haɗa idanu da ni ba zaki iya ba, ko kin manta da ƴar uwarki dana ɗaukko ku a tare? Baki tunanin a ina take? Tana a raye ko ta mutu? Ya tambaya cike da izgilanci yake ɗage mata gira, sakin wuyanta ya yi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita. Daƙyar ta iya furta, "Allah yana a tare da ita a duk inda take." "Ki daina ambaton sunan Allah, kina wahalar da kanki ne, Allah bazai ta6a taimakonki ba, ko kin taba ganin inda ka nemi taimakon Allah ya amsa maka nan ta ke?" "Tunaninka irin na marasa hankali ne, masu gajan hakuri, addu'a ita ce ta kare mutanan da ka so ka wulakanta rayuwarsu, Addu'a ita ce ta yi silar barin mu gidan kurkukun ƙaddara batare da saninku ba, baku iya yi mana komai ba har muka kawo wannan lokacin a raye.." "Ki daina tutiya, ba addu'arku ba ce ta cece ku, Danish ne ya zama garkuwar ku, badan yana a tare da ku ba, ko gidan kurkukun nan baku isa ku ƙetare ba.." sunan Danish da ya ambata ba ƙaramin karya mata zuciya ya yi ba. "Idan muka nemi taimakon Allah, ba kaitsaye ya ke taimakon mu ba, ba ganinsa muke da ido ba, sai dai ya yi mana hanyar da taimakonsa zai isa gare mu, Danish ya taimake mune saboda Allah ya kaddara shi ne zai zama garkuwar mu..." Shu'umar dariyarsa ya saki... "Meyasa na ga kamar jikinki ya yi sanyi? Saboda na ambaci sunan shi?" Harara ta watsa mashi batare da ta furta kalma ba. "Ko har yanzu kina son shi? Ya faɗa yana ɗage mata gira. Ta6e bakinsa ya yi, "Ni ban ga abun da ya gani a jikinki da ya ja hankalinsa ba har ya fada tarkon son ki, ko da ya ke ba yin kansa bane, Danish bai ta6a sonki ba, nasan ba a ta6a faɗa maki hakan ba, amma Danish bashi ne ya ke sonki ba, Evils din jikin shi ne suke son ki...." Wani irin faduwar gaba ta ji, maganarsa ta razanar da ita, saboda tunawa da maganar Salsabeel da ya ta6a cewa wasu abubuwan da Danish ya ke yi bayin kansa bane, kenan maganar Musa zata iya zama gaskiya. Shu'umin murmushi ya yi ganin ya fara baƙanta mata rai. "Tayaya ki ke tunanin zankaɗeɗan saurayi kamar shi zai so kucaka irin ki? Shi ba ajinki bane, Danish ya fi karfinki nesa ba kusa ba, ba abun da zai yi da ke, abun da baki sani ba, Danish ɗan homo ne shi, baisan daɗin mace ba sai na namiji, he's my guy, na daɗe ina kwanciya da shi, tun kafin ya mallaki hankalinsa, yana da dad..." Bai ƙare maganar ba ta kwatsa mashi tsawa, tsigar jikinta na tashi ta furta, "Bana son ji, ka daina faɗa min, ƙarya ka ke yi mini, Danish dina ba ɗan homo bane, meyasa ka ke min magana akan shi? Bayan Danish ya mutu, ka barsa ya kwanta a ƙabarinsa lafiya..." wata yar iskar dariya ya tuntsire da ita yana kallon baƙin cikin dake a cikin idanunta "Na ga kishi tsantsa a cikin idanunki, har yanzu bakisan wanene Danish ba, bakisan reality dinsa ba, he's really a bad guy, da kinsan adadin fursinonin da muka sa ya kwanta da su da baki 6ata ma kanki lokaci ba, kuma ba don baya haihuwa ba, da yanzu an samu ƴa'yansa a cikin fursinoni. " Fashewa ta yi da kukan baƙin ciki duk da tana kokwanto akan abun da ya fada, amma kalamansa sun rikita tunaninta, jikinta har kerma yake yi, "Ni ban damu da komai Danish zai aikata ba, idan ma kana faɗamin ne don ka baƙanta raina to ka sani ba zaka ta6a yin nasara ba, har yanzu ina son Danish fiye da yadda nake son raina, kuma na yi masa uziri saboda nasan komai da ya aikata ba yin kansa bane, tursasa masa ku ka yi, don haka ka daina 6ata shi a gurina, kuma ka daina yi min magana akan shi, saboda a yanzu shi ba rayayye bane..." Bata ƙare maganar ba ya katse ta, "Waya fada maki Danish ya mutu um? Kin ga gawarsa ne?" A ruɗe ta ke kallon cikin idanun sa. Makirin murmushi ya saki. "Danish yana a raye, kuma yana a tare da ni, bayan da ya faɗa rijiya, batare da sanin kowa ba, na taimaka masa ya fito sannan na kashe Jeremiah..." tsantsar ruɗani ne akan fuskarta, ta kasa yarda da maganar shi, "ƙarya ka ke yi, Danish ya mutu, baya a raye, saboda in har yana a raye bazai iya rayuwa batare da ni a kusa da shi ba..." dariya ya saki tare da buga tafin hannunsa ga ƙasa, nan take wani madubi ya bayyana a saman iska.. "Ki kalla ki gani wanene wannan?" Kura idanu ta yi akan madubin, su biyu ta gani a kwance saman gado, sun rungume junansu sunata aikata alfasha, kwata kwata babu sutura a jikin su...." runtse idanunta ta yi gam ta cicccije la66anta, saboda kishi har saida ta fasa lower lip ɗinta jini ya shiga daddigowa, nan take wani zazza6i mai zafi ya lullu6e jikinta. Cike da nishaɗi ya ke kallon ta. Cikin karyayyar murya ta ce,"Ba Danish ɗina bane, Danish ba zai iya aikata fasiƙancin nan ba, kawai ka yi amfani da tsafin ka ne don ka baƙanta raina, kamar yadda ka yi editing hotunan Aunty Ummi don ka cutar da mahaifinta..." haushi ya ji ganin ta ƙi yarda da gaske ne, sumar kanta ya damƙa kamar zai tsige gashin ta. "Dole ki yarda da abun da idanunki suka gane maki, Danish yana a raye, kuma yana a tare da ni ." "Ban damu ba ko kaɗan, saboda nasan cewa Danish ya mutu.." "Bansan meyasa ka matsa saina yarda da ƙarairayin ka ba, dan Allah ka tafi ka bani guri, ka rabu da ni, idan kuma kashe ni zaka yi ka kasheni kawai zai fi min kwanciyar hankali saboda na gaji da ganin ka, na tsani ganin mummunar fuskarka wallahi..." Girgiza kanshi ya yi cike da takaici yake rarraba idanunsa akan fuskarta.. "Nasan bakisan dalilin da yasa na dauko ku ba ko?" Banza ta yi da shi. "Saboda in dawo da ran kurkukun ƙaddara, saboda in samu ƙarfin sihirin da babu wanda zai iya ja da ni, zan gagari kowa, zan zama mai power, zan juya kowa, zan kuma sake gina kurkukun kaddara, bazan iya yin hakan ba dole saina cire zuciyar ƴar uwarki Batool na ba dodon tsafin mu ya haɗiyeta, sannan kuma in kashe ki, idan na yi hakan zan samu karfin iko fiye da na Elder." Abun da ya ɗaga hankalinta jin zai cire zuciyar Batool yaba dodon tsafi don ya cika mugun nufinsa, kwata kwata bata damu da ta mutu ba amma bata jin zata iya bari Batool ta salwanta, no matter what.. A ruɗe ta furta, "Ni bazan iya maye gurbinta ba? Ka cire zuciyata, ka bar batool a raye, kada ka kashe ta, ko da baka da imani amma yakamata ka tausayawa Aunty Ummi, wani irin bauta ne bata yi maka ba? Ka rasa dame zaka saka mata saida hakan? Dan Allah ka da ka kashe mata babynta, gaba daya rayuwarta a cikin jarabawa take, tun tana jaririya kasa daddynta ya binne ta da ranta, sannan ka bi ta bayan fage kasa aka ɗauko maka ita, sannan ka sadaukar da ita, meyasa wai ba zaka rabu da ita ba ne? Ka hana ta rayu da iyayenta, gaba daya ta ko'ina ka tauye mata hakkin rayuwarta, wai wata irin shaiɗaniyar zuciya gare ka??" Ta faɗa cikin kuka. Cikin halin ko in kula ya ce, "Ba shawararki nake nema ba, babu wanda ya isa ya dakatar da ni, dole in cika burina ko ta halin ƙaƙa, yanzu haka suna can zasu cire mini zuciyarta, ko zaki iya taimakonta ne?" Tana kuka tace bazan iya ba amma Allah zai taimaketa, kuma in sha Allah ba zaka ta6a cika burinka ba, ina ji araina zasu farmake ku a yau din nan, ka jira ka gani, ƙarshenka ne ya zo, tun da har ka yi kuskuren daukko mu, In sha Allahu daga yau ka gama yawo. Bushewa yayi da dariya, "Tayaya Allah zai taimake ta? Kefa da kanki ki ka ce Allah baya taimakon mutun kaitsaye sai dai yayi masa hanyar da taimakonsa zai iso gare shi? tayaya Allah da ya ke jinkirta amsa addu'ar bayinsa zai iya taimakon ku cikin sauri a irin wannan lokacin? Ki daina saka rai, saboda babu wanda zai taimake ku, babu wanda yasan a inda ku ke, babu network din da ma za'a iya bin diddigin ku, babu wanda zai iya tunkarar kurkukun nan a halin yanzu, saboda a kewaye yake da Evil Giants, sun ci nasara a karo na farko amma wannan karon babu wanda zai ƙara farmakar mu ya zauna lafiya.." girgiza kai ta yi, "In sha Allah zaka ga yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri akan wanda ya zalunce shi, zan kuma gwada maka yadda addu'ar mai imani wanda ya dogara da Allah take tasiri, ka jira ka gani, ni da kai wa zai yi nasara" Ido cikin ido suke kallon juna, fuskarsa a murtuke ya ce, "Mafarkinki ba zai ta6a zama gaskiya ba, baki isa inyi jayayya dake ba, nasara tawa ce, ke da zaki mutu ...." Ya faɗa tare da miƙewa tsaye yana kallonta.. "Waliyiya Unaisah, zan jira in gani idan addu'ar taki zata yi tasiri, sannan ki taimaki kanki da kuma yar uwarki." Ya faɗa tare da nuna mata ƙwarin dake daddabe jikin nama. "Ba irin ƙwarin da kika saba gani bane, wadannan na gidan kurkukun ƙaddara ne, mun tsaface su, jinin jikin mutun suke tsotsewa, su sanya mashi dafin da zai lalata yan hanjin jikin shi, ya ru6e." Wani irin tsoro ne ya mamaye ta. "Da zarar sun gama tsotse jinin da ke a jikin naman zasu dawo kanki ne." Hankalinta a tashe ta zazzare idanunta cike da fargaba ta wurga idanunta kan su, yawu ta haɗiya ilahirin jikinta ya kama kerma. "Na barki lafiya.." Juyawa ya yi taku ɗaya biyu ya 6ace ma ganin ta.. Fitar sa ke da wuya, ta lura ƙwarin sun kusa gama tsotse jinin naman, kafin kyaftawar ido har sun gama tsotse gaba ɗaya jinin dake a ɗakin sun fara bin bango suna tunkarota da saurin su, ga kukansu mai tsiwar gaske.. Cike da tashin hankali ta zazzare idanunta akan su, gwanin ban ƙyama, cikin rawar murya ta shiga furta duk wata addu'a da ta zo bakinta, batasan ya zata yi ba, ga hannayenta a ɗaɗɗaure kafafuwanta ma, kuma ba halin ta motsa saboda inda suka ɗaure ta jikin taga, lokacin da ƙwarin suka fara gangarowa kan floor gungu guda suka nufo ta sai sauri suke yi, ƙararsu ta cika kunnanta.. Tana ta tunanin wata dubara zata yi me yakamata ta yi? Saboda bata son ta mutu batare da ta ceci rayuwar Batool ba.. Juyawa ta yi da sauri ta dubi tagar da suka ɗaure sarƙar hannayenta a jikin iron bars ɗinta (sandunan baƙin ƙarfe) mai gida gida, yunƙurawa ta yi a tsorace tana nishi ta soma ƙoƙarin tura kanta a tsakankanin ƙarfen, daƙyar ta samu ya shiga ta dinga ingiza jikinta ya ƙi wucewa, fashewa ta yi da kuka jin kukan ƙwarin dab da ita, bata yi aune ba, ta ji sun fara hawa kan kafafunta suka soma caccaka mata tsinin bakinsu suna tsotsar jinin ta,Ya salam! wani maganaɗisun raɗaɗi ne ya ziyarce ta, ta fasa ƙara kamar ana zare ranta, ta dinga kuka tana bubbuga kafafunta har ta samu ta kakka6e su. Karkata jikinta ta yi ta fuskanci hannun damanta, a haka ta ci gaba da tura jikinta, daƙyar da siɗin goshi ta samu qugunta ya wuce, gaba ɗaya ta kundumo ta bayan tagar ta fado cikin wani ɗaki, still bata tsira ba saboda sarƙar da aka ɗaure hannayenta da su tana a jikin tagar, kuma a buɗe take zasu iya faɗowa ciki, kwata kwata bata lura da inda ta faɗo ba, Saboda hankalinta ba a kwance ya ke ba, karfen jikin tagar ta lura da tsatsa a jikin shi alamun ya daɗe ba a musanya shi ba, daddagewa ta yi da iya karfinta na karshe ta dinga jan hannunta tana nishi, gumi ya wanke jikinta, kukan ƙwarinne ya cika kunnanta kamar zai fasa dodon kunnanta. Saida ta galabaita, wuyan hannunta ya yi jawur kamar zai fashe saboda sarkar da ta takure gurin ga kuma jan gurin da take yi, dai dai lokacin da ƙwarin suka fara hawa jikin ƙarafunan tagar, a gigice ta fasa wata irin ƙara mai sauti tare da rufe idanunta, buɗe idanun da zata yi keda wuya, ta ga abun da bata yi zato ba, ƙarfen da aka daure sarƙar hannunta da shi ya 6alle biyu sakamakon jan da ta dinga yi, jikinta na 6ari ta buga murfin tagar da hannunta, ta danne da bayanta, tana jiyo kwarin dake ta bugun tagar kamar zasu fasa ta yadda kasan wata ƙatuwar halitta, lumshe idanunta ta yi gabanta na ci gaba da faɗuwa. Buɗe idanun da zata yi keda wuya, ta yi arba da tarin kawunan ƙwarangwal cike da dakin da ta faɗo, kwata kwata bata tsorata ba, saboda mawuyacin halin da take a ciki. Shiru ta ji ƙwarin sun daina fitar da sautin su, miƙewa ta yi tsaye kan kafafunta da ke a ɗaure, ta ɗan buɗe tagar kaɗan ta leƙa kanta, ruɗewa ta yi ganin ƙwarin kwakkwance a ƙasa basa motsi kamar sun mutu, lamarin ya daure mata kai, har ƙara zare idanunta take yi don ta tabbatar da sun mutun ko lambo ne suka yi mata, dabara ce ta faɗo mata a rai, da sauri ta tsotsi jinin dake akan le6anta, ta watsa shi cikin ɗakin don ta ga idan za su tsotse shi, still ba su motsa ba, shiru ta yi jim tana yanke shawara da zuciyarta, so take ta koma cikin ɗakin don ta kwance leg irons ɗin ƙafarta, shahada ta yi duk da shakkar da take ji, ta daddake ta ruke sandunan kofar da hannayenta ta kutsa kanta ciki, wannan karan bata sha wahala ba, ta burma cikin ɗakin gaba ɗaya ta faɗo kan ƙwarin dake yashe a ƙasa, anan ta ƙara tabbatarwa kanta sun mutu. daƙyar ta iya miƙewa, kamar yar tsana ta dinga yin tsalle tana tunkarar teburin ɗakin dama shi take hari, har kifewa ta yi ƙasa ta kuma miƙewa daƙyar ta ƙaraso gaban shi, ta zube kan gwiwowinta, jikin ƙarfen table din ta dinga buga sarƙar hannayenta da ƙarfi, duk ta hada gumi akan fuskarta, sai nishi take tana jan numfashi, dakyar da sidin goshi ta samu sarkar ta saki daga tamkewar da ta yi, 6an6areta ta yi daga hannayenta ta jefar da ita ƙasa, ta kai hannunta da ke kerma ta ɗauki zarto ta kunna shi tare da saita shi daidai saitin leg irons din kafafunta, duk da fargaban kada ta datse ƙafar saboda jikinta dake kerma a haka ta daddage ta dadara zarton da ƙarfi kamar ranta zai fita har fitsari saida tayi a cikin wandonta saboda wahala, dakyar ta yi nasarar 6alle irons din ta zame ƙafafunta daga cikin shi ta miƙe tana haki, tsayuwarma daƙyar ta yi ta saboda raunin da legs dinta suka yi, saida ta dan sarara tukunna ta miƙa hannu ta sungumi zarton ta rataya shi akan kafaɗarta, hakan bai isheta ba saida ta ƙara da tsinken ƙarfe ta soke shi a cikin aljihu, duk don ta kare kanta kamar wata mai ƙarfi, duk da ta zuciya, jinin ta akan akaifa ya ke, ƙwara ayi ta ta ƙare, ko a mutu ko ai rai. Gaba ɗaya ta sauya kamar ba Unaisah ba, ta zama kamar ƴar daba, Overroll ɗin jikinta duk ta 6aci da jininta, haka fuskarta ma a 6ace take da jini, sumar kanta kuwa bata da maraba da ta mahaukaciya, tana ɗangyasa ƙafarta ta nufi tagar nan ganin babu ƙofar da zata bi ta fita daga dakin duk a kulle suke, bayan da ta dira cikin ɗayan ɗakin ta shiga rarraba idanunta tana neman ta wace hanya zata fita daga ɗakin, ganin shima duka tagoginsa a kulle suke haka ƙofofin ɗakin ma. Da zarton ta soma kokarin 6alle ƙofa ɗaya, sai dai ta kasa saboda rashin kuzarin dake a tare da ita, gaba ɗayanta a raunace take... Langwa6e kanta ta yi jikin kofar, tana nishi yayin da zuciyarta ke tariyo mata wasu abubuwa da suka faru atsakaninta da Batool, nan take ta ji karfi ya zo mata, tunawa da kalamansa.. Bugu ɗaya ta kara yi ma kofar nan ta ke ta buɗe. Cike da fargaban me zata taras ta leƙo waje, bata ga kowa ba, wasu hanyoyi ne da babu kowa. Sama ta kalla don taga ko akwai cctv can kuma ta tuna da inma suna ganinta bai wuci ta madubin zafin su ba, komai zai faru sai dai ya faru amma fa ta ci alwashin ko zata rasa ranta saita ku6utar da Batool, cikin sanɗa take tafiya, duk dakin da ta gani sai ta leƙa tagar shi don ta ga idan nan suka kulle Batool. Cikin zullumi da fargaba, tana ƙoƙarin karya kwana kwatsam ta hango gungun Giants sun nufo gurin da take, ruɗewa ta yi cikin sauri ta koma da gudu batasan sa'adda ta dura wata windown ɗaya daga cikin ɗakunan dake a gurin ba, sai haki ta ke yi, ajiyar zuciya ta sauke jin alamun sun wuce, bin ɗakin ta yi da kallo, tsofaffin metal bed ne aka jibge ɗaya kan ɗaya a cikinsa, wata dabara ce ta faɗo mata, lokacin da ta dubi ceilling ɗin ɗakin da akwai access panel a jikin shi, duk da a kulle yake amma ta na jin zata iya tsaga shi, kama jikin gadajen tayi ta dinga bin jikinsu tanayin sama dakyar ta haura ta saman su, ta zauna tana mayar da numfashi. Tunawa da tarin ƙalubalen da ke agabanta yasa ta zaro tsinken karfen da ta soke, ta shiga caccaka ma panel din, kasantuwar yana da quality, ta ci wahala kafin ta 6alle murfin, ta leƙa kanta cikin ceilling din, ba laifi yana da space din da bawa zai iya ratsa cikinsa, tura kanta ta yi, a hankali ta shige dukanta, zafi ya doka mata sallama, ta fara zubda gumi, kwata kwata babu tsoro ko fargaba atattare da ita, jan ciki ta dinga yi tana yin gaba, har wata kwana kwana gare shi, bata tashi sanin ta yi wauta ba sai da ta rasa hanyar da zata 6ula, nan fa ta fara rarraba idanu, kwata kwata ba ta yi tunanin ta kalli ƙasa ba, kawai jan jiki ta ke yi tana yin gaba, sai daga baya tunanin hakan ya zo mata, cikin sauri ta soma bin celling din tana ƙare masa kallo cikin tsantsar ruɗu.. ~_____________________JAN WUYA🔥~ A tsaye ya ke gaban dakin fiɗa, zuciyar sa fari fat yau zai cika burin da ya daɗe yana mafarkinsa. Buɗe kofar ɗakin aka yi, babban yaronsa Dr. Mark ne ya fito, sanye da uniform din tiyata. "Mark, ka gama tiyatar ne? Ko har yanzu ba ka cire zuciyar ba ne?" Jinjina mashi kai ya yi, "Ban kaiga farawa ba, ina jira allurar kashe zafin da na yi mata ta fara aiki a jikin ta" Bai ƙarasa ba ya dakatar da shi. "Ba wannan na ke son ji ba, bana bukatar ka bi ta lalama, ka saka ƙumbunanka ka faffarke kirjin ta, bafa ta da wani amfani zuciyarta kaɗai nake so, in ba zaka iya ba ni ka bani guri in yi!" "Allah ya huci zuciyarka sir, in har mu ka ce zamu bi ta tsiya zamu iya lalata shirin mu, dole mu bi a sannu don mu cire zuciyar batare da an samu matsala ba." Tsoki ya ja, "Na baka nan da mintuna biyar ka cire ta kota halin ƙaƙa, don mu yi saurin lunƙumata a bakin dodon tsafi, bana bukatar bata lokaci." Cike da ladabi ya amsa mashi da toh ya juya ya koma dakin.. Bai motsa daga inda ya ke ba, jira kawai yake yi ya gama tiyatar, abun da ya faru tun jiya da daddare da suka zo kurkukun da su, ya so yayi amfani da sihirinsa gurin farke kirjin Batool don ya cire zuciyarta, sai dai matsalar, da aka samu, sihirin sa ya yi ma jikinta ƙarfi, in har ya kuskura yasa ƙarfi don ya cire zuciyar toh gaba ɗaya zata dagargaje, shiyasa dole su bi tsarin tiyatar asibiti. Gajiya ya yi da tsayuwa, ya fito daga sashen da tiyata room din ya ke, ya koma cikin wani katafaren falo mai kyan gaske komai na cikinsa launin ja ne, zama ya yi kan wata doguwar kujera ya ɗaura ƙafar sa daya kan ɗaya kamar wani basarake, kwata kwata baya tunanin a wani hali iyalinsa suke a ciki, ta kansa ya ke, already an riga da an fada masa sojojin isod sun kewaye gidansa da gidan ɗan iya, hakan bai dame sa ba. "Musa ya za kai mana haka? Wasa tare ci bambam? Me hakan Ke nufi?" Unexpected ya tsinkayi muryar Jan Ido a cikin kunnan sa, a sukwane ya miƙe yana duban su. ɗaya bayan ɗaya suke ratsa bango suna shigowa falon, cikin shigarsu ta dogayen riguna baƙaƙe masu huluna, hannayensu ruƙe da sandunan su, rabin fuskokinsu rufe da mask, idanunsu ne kaɗai a bayyane. Kansa ya ɗaure da ganinsu saboda bai sanar da kowa shirin shi ba, saboda baya son su sani, shi kadai ya ke so yayi. "Don me zaka yi komai a sirrin ce batare daka faɗa mana ba? me hakan ke nufi? Wani daga cikin Elders dinne ya faɗa.. Banza yayi da su bai tanka masu ba, sai ma wani shu'umin murmushin shaƙiyanci da yake saki. "Ka yi shiru baka ce komai ba? Ko hakan na nufin dagaske ne abun da aka fada mana? Kana so ka ci amanar mu ko? Shiyasa ka shirya komai a boye batare daka fada mana ba bayan mu yakamata a ce ka fara sanarmawa.." A cewar wani elder, wani kallon tuhuma suke jifarshi da su. Tafa hannayensa ya yi tare da bushewa da dariya cikin takun izza ya nufe su yana fadin, "Sannunku da zuwa! Tayaya akai kuka san ina anan? Wanene ya fada maku um?" Ya fada yana ɗage masu gira. Wani tsoho daga cikinsu cikin fushi ya ce, "Jan wuya baka isa ka ci amanar mu ba, mune a gaba da kai, baka isa ka yi gaban kanka ba, dama ni ban yarda da kai ba, saboda nasan halin ka ba ƙaramin shaiɗani bane kai, ka ƙware gurin iya haɗama da kulla makirci, wato shine yanzu da ka ga Elder ya yi murabus kuma asirinka ya tonu shine ka kware mana baya, ka sato yaran da kowan nan mu ya ke burin ya ɗauko su, don ka riga mu cika sharuddan allon tsafi saboda ka samu karfin ikon da za ka juya mu..." Ƙyalƙyacewa ya yi da dariya, tare da nuna su da yatsan shi da izgilanci ya ce, "har kuna da bakin faɗin ban isa in ci amanar ku ba? Dama akwai amana a tsakanin mugu da mugu? To ni ban yarda da kowannan ku ba, babu wani mai iko da ni a cikinku, saboda na fi karfinku nesa ba kusa ba, .." Ya fada yana huci. "Buri ne da na daɗe da shi a zuciyata tun farkon dana fara yi ma Elder bauta, duk wani ci gaba da aka samu a gidan kurkukun kaddara nine sila, don haka yanzu lokaci ya yi da zan fanshe wahalata, ni na cancanta in hau karagar Elder Obinna..." Ransu ya 6aci, yanzu sun gasgata abun da aka faɗa masu game da maƙarƙashiyar da ya ke shirin ƙulla masu. "You son of a bitch, Musa, you'll never become an Elder over my dead body, You're not worthy, If anyone deserves it, it's one of us, who've been with the Elder for a long time before he even knew you existed." (ba zaka ta6a zama Elder ba, baka cancanka ka zama ba, idan ma akwai wanda ya cancanta to daya daga cikin mu ne, mu da muka daɗe tare da Elder tunkafin yasan da zamanka a duniya,..." ) jan le6e ne ya faɗa rai a 6ace. Wani Elder din ya ce, "Ba zamu ta6a lamunta ka zama shugaban mu ba, saboda mun ji maƙarƙashiyan da kake son kulla mana, kana so ka samu ƙarfin sihirin Elder don ka ƙwace sihirinmu sannan ka kashe mu ko?" tun da suka fara magana hankalinsa kwance babu damuwa a ransa, amma da wannan Elder ɗin ya yi magana sai ya fahimci kamar wani ne ya yi brainwashing ɗin su. "Na fahimci wani ne ya zugo ku ya faɗa maku karya da gaskiya akaina don ya shiga tsakanin mu! nasan ban kyauta ba da ban sanar da ku ba amma banyi hakan don bana so ku sani ba, kuma ni bani da mummunan nufi akan ku, sai don nafi so in sawwaƙe maku wahala, amma maganar nan ba gaskiya bane, ni bana nufin kowannanku da sharri, burina dukanmu mu gudu tare mu tsira tare, saboda mun riga mun zama ɗaya, yakamata ku fahimce ni..." Ya faɗa cikin lalama, wani kallo suke yi mashi na rashin yarda duk da kokwanton da zuciyarsu ke yi sai dai ba zasu iya ƙaryata abun da aka faɗa musu akan shi ba, saboda daga majiya mai ƙarfi suka ji. "Koda zamu yarda da maganarka, ba zamu ta6a bari ka zama Elder ba, saboda baka cancanta ba..." Elder din da ya ɗauko maganar bai kaiga direta ba, Jan wuya ya daka masa tsawa yana huci ya furta, "Saboda me ba zaku bari in zama shugaban ku ba? Ko ina da wani aibu ne? Ko baku yarda da ni bane? Ko kuwa shi Elder Obinnan yana da wani magaji ne ehe? Meyasa ni ban cancanci in hau karagar mulkinsa ba?" "Bamu yarda da kai ba Musa, saboda ka yi abun da yasa mana zargin ka a cikin zukatan mu, kwata kwata babu gaskiya a tare da kai, kuma kai in ban da abun ka, ka yi tunanin hawa kujerar Elder abu ne mai sauƙi? To bari ka ji in faɗa maka gaskiyar zance, bare baya hawa kan karagar Elder, dole sai idan jinin Elder ne kadai zai iya hawa kan karagarsa, su da suka gaji abun ba kai da ka ke bare ba" Jan dasashi ne ya furta, ran Musa ya 6aci zuciyar shi ta zo wuya, sun fara harzuƙa shi. Sauran Elders din da suke haɗamar samun kujerar Elder a ruɗe suke kallon jan dasashi da ya yi maganar. "Kana nufin babu wanda zai gaje shi a cikin mu? Waya faɗa maka hakan? A ina ka ji eye?" A cewar Jan Gemu. Jan le6e ya ce, "Ko ni da nasan sirrin Elder Obinna ciki da bai ban ta6a jin wannan maganar ba, na gani da idona a rubuce ya ke a cikin littafin Sijnil ƙadar, babu inda aka rubuta jinin Elder ne kaɗai zai iya gadonsa, don haka maganarka babu ƙamshin gaskiya a cikin ta." "Jan le6e baka karanta da kyau ba, kai da baka jin inyamuranci?" Ya faɗa yana dubansa. "Na fahimci masu haɗamar kujerar Elder suna da yawa, sai dai babu wanda zai mallake ta, dole sai jininsa, ku yarda ko karku yarda, wannan maganar dana faɗa tana a cikin littafin tarik sijnil Qadri..." Cike da ruɗu suke kallon shi .... "Babu ƙamshin gaskiya a maganarka, Elder bashi da wani dangi nasa, idan ma kana nufin ya'yansa to kuwa ba zasu kar6i karagar tsafi ba, saboda sun ƙyamaci abun a zuciyar su, dole sai ɗaya daga cikin mu zai gaje shi.." Jan ƙeya ne ya faɗa.. Gaba ɗaya sautin maganganun su ya cika ɗakin da suke kowa yana tofa albarkacin bakinsa duk dai akan kujerar Elder Obinna. Musa ransa ya 6aci zuciyarsa ta zo wuya, gani yake rainin wayau ne yasa suka zo don su dakatar da shi, gashi suna ta 6ata mashi lokaci..~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ *~THE FINAL ATTACK 2~* Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *~THE FINAL ATTACK~* Cikin fusatacciyar murya ya ce, "Na fahimci idan na bi ku ta lalama ba za ku bari in samu abun da nake so ba, na rantse dole In hau karagar Obinna! kota halin ƙaƙa, babu ruwana da ni bare ne, ko ban cancanta ba! Ni ba amincewar ku nake nema ba! In kuwa kuka yi yunkurin dakatar da ni zan yi maku abun da baku ta6a tsammani ba, hmmmmm." Ya faɗa yana mai yi masu kashedi. "Ka shiga taitayinka Musa, karka cika zaƙewa, hawa karagar Obinna saida amincewar mu, don haka bamu amince maka ba, saboda baka cancanta ba, kuma ba jininsa bane kai, don haka ka yi gaggawar ba mu zuciyar yarinyar mu tafi da ita..." Elder din da ya ɗauko maganar bai kai ga direta ba Musa ya tari numfashin shi da cewa, "In har ni bazan gaji Elder ba, to kuwa babu wanda zai gaje shi a cikinku, idan kuma kuna da ja, mu kara da juna wanda ya yi nasara shi ne zai gaje shi..." Ya faɗa yana sakin shu'umar dariya. Kallon kallo suka shiga jefawa junan su, yadda ya yi maganar a gadarance da izza yasa suka fahimci da akwai shirin da ya yi masu ta bayan fage. Takun tafiyar da su ka ji ne ya ja hankulansu ga kallon mai shigowa. Dr Mark ne ya shigo hannunshi ruƙe da kwalba fara mai ɗauke da zuciyar mutun a ciki duk jini a jikin ta. kamar baiga sauran Elders din ba, ya nufi ubangidansa yana sakar masa murmushin nasara "Sir, na yi nasarar cire zuciyarta, batare da na samu wata matsala ba." Washe baki Musa ya yi kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna, farin ciki ya cika shi. Miƙa ma Mark hannu ya yi yana kokarin kar6ar kwalbar, Jan Le6e ya buge hannun shi da sandar shi, ya kai hannu Zai kar6i kwalbar, Dr mark ya janye ta. "Ka yi kuskure Jan le6e, ba a shiga hurumina..." wani azababen naushi ya kai ma Jan le6e a mummuƙensa. Rai a 6ace Jan ƙeya ya 6ace ya dira a gaban Mark ya damki kwalbar zai ƙwace, Musa ya shaƙe wuyan shi ya wujijjiga shi tare da ture shi gefe ɗaya. Jan gemu ya yi kukan kuka ya dira a gaban Dr. Mark, har ya miƙa hannu da niyar ya kar6e kwalbar, Musa ya sa ƙafarsa ya taɗiye shi, gaba ɗaya sun fito da maitarsu a fili, hankalinsu ya tashi haiƙam kowa burinsa ya kar6e kwalbar zuciyar. (Ina ma a ce zuciyata ce suke rububi akanta, ai dana basu sun bani kuɗi😂 just for fun) "Baku so zaman lafiya ba, wallahi babu wanda ya isa ya ta6a kwalbar nan batare da na ɗauke masa kai ba..." Ƙawanya suka yi ma su gaba ɗayan su suna huci kamar mayunwatan zakuna! Da ganin haka sai Musa ya yi ma Mark alama da hannunsa, shu'umin murmushi Dr Mark ya saki tare da yin fito mai sautin gaske, a ruɗe suke kallon Evil Giants din da ke ratso bango suna shigowa ciki, wasu ta sama suke durowa wasu ma bayyana suke yi a tsakar ɗakin. "Nasan za ku yi mamakin tayaya akai Giants suka koma suna bin umarnina..." Ya faɗa a gadarance. "Su kan su sun miƙa wuya saboda sun ga cancantata da in zama ubangidansu, nafi ku jarumta da komai tun da har na kawo ƙaddara da bugun zuciyar kurkuku..." Kwata kwata basu ji tsoro ba, kuma basu karaya ba, duk da sun sha jinin jikinsu saboda masu iya magana na cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. "Ku farmake su, bana so kubar ɗaya daga Cikin su a raye!" "Ma ci amana! Dama burinka ka ga bayan mu butulu, ka jira ka gani idan muka gama da su zamu dawo kanka ne." A cewar Jan Gashi. Bushewa ya yi da dariya cike da izza ya ce, "Wanda ya ke goyon bayana ya zo mu tafi." Yana faɗa ya juya cike da izza ya yi ma Mark alamar ya biyo bayan shi "Ku gafarce ni, bazan iya ci gaba da zama tare da ku ba, bazan iya ja da Evil Giants ba, bayan haka nima asirina ya tonu, ina buƙatar wanda zai ƙara mini karfin sihirina don in kare kaina." Jan ido ne ya faɗa tare da juyawa da sauri ya bi bayan Jan wuya suka tafi. Jan le6e ma ya ce, "Kada in yi biyun babu, jami'ai nema na suke yi ruwa ajallo, don haka zan bi bayan Jan Wuya, ba don ina goyan bayansa ba, sai don ina so inyi amfani da damar da nake da ita kafin in salwantar da rayuwarsa..." yana ƙarashe maganar shi bai jira amsar su ba ya juya ya bar gurin. "Matsoratan banza! Sun bani kunya, ba zamu raga musu ba, dole mu kashe su, sannan mu kuma ƙwace zuciyar yarinyar." Jan dasashi ne ya faɗa, gaba ɗaya ransu ya gama 6aci, zuciyar su sai tafarfasa ta ke yi da baƙin ciki. Girman kai ba zai bari su bi bayan shi ba, saboda sun tsani izzar shi batun yau ba ya saba shiga hancinsu da ƙudundune.. Kewaye su Giants suka yi kowan nan su ya ɗaura ɗamarar yaƙi, nan ta ke faɗa ya kaure a tsakanin su da Evil Giants, wata irin ƙura ta buɗe falon, haɗuwa suka yi su shidda suka haɗa ƙarfin sihirin su cikin sa'a suka kashe Evil Giants din dukansu. Sai haki suke yi saboda wuyar da suka sha. _Kar mu tsaya 6ata lokaci, nasan i yanzu sun kusa isa Temple of Evils, don kai ma dodon tsafi zuciyar, mu hanzarta bin bayan su mu kashe su, kafin Musa ya aiwatar da mugun nufinsa"_ Suna ƙoƙarin ɗaga kafafunsu don su bi bayansu, Kwatsam! babu zato ba tsammani suka tsinkayi muryar mutun a cikin kunnuwansu, "You're under arrest!" Tsantsar ruɗani ne ya hana su juya baya su fuskanci wanda ya yi maganar. Sunyi matuƙar razana da jin baƙuwar murya, nan take suka fahimci hari aka kawo masu! "Tayaya hakan zai yiwu? Wayasan da zuwan mu? Ko dai Musa ne ya yi mana cinne?" Tambayoyin da suka cika zuciyoyin su kenan. "Wanene kai?"? Jan Gemu ne ya tambaya. "Director General Of Isod." Ya bashi amsa kaitsaye. Zazzare idanu suka yi a matuƙar ruɗe suka juyo suna kallon shi, yana a tsaye sanye da kakinsa ya goya hannayensa akan broad chest dinsa. Basu gama razana ba saida suka ga Isod Soldiers da U.s armies suna shigowa falon hannayen su ruƙe da bindigu ƙirar dragon breath. "Tayaya hakan zai yiwu? Mafarki ne ko gaske? Waya faɗa maku inda mu ke? Kuma Tayaya akai kuka iya shigowa kurkukun nan?" "Ba zuwa muka yi don muyi fira da ku ba, ku miƙa wuya cikin lalama mu tafi, Idan kuma kuka yi yunƙurin guduwa, jikinku ne zai gaya maku!" Commender James ne ya fada yana mai yi masu kashedi da kakkausar murya. "Kar wanda ya kuskura ya matso kusa da mu, idan ba haka ba, zamu salwantar da rayukan ku, baku isa ku kama mu ba, makaminku bazai yi tasiri akan mu ba. An gaya maku ja da mu abu ne mai sauki!" Jan Dasashi ne ya fada cikin fushi da 6acin rai. Jan Gashi ya ce, "Musa ne ya yi mana cinne, maci amana, ya yaudare mu, ya zama dole mu 6ace ......" A lokaci ɗaya suka buga sandunansu ƙasa da niyyar su 6ace, sai dai me, babu abun da ya sauya suna nan a inda suke, a ruɗe suka kalli sandunan nasu, cikin zafin nama suka ƙara buga su da ƙarfi, still basu bace ba, firgici da karayar zuciya ce ta same su, sam sun gaza yarda da abun da ke shirin faruwa da su, cikin ɗimuwa suka ci gaba da bubbuga sandunansu ƙasa kamar mahaukata duk sun bi sun ruɗe. Sojojin dake a kewaye da su sun yi tsaye suna kallon su, kamar masu kallon wasan ƙwaiƙwayo. "Idan kun gama buga wasan naku, muna jiran ku." A cewar Chief Owais. Ba su yi aune ba, kwatsam! Wani baƙin hayaki ya soma kurɗaɗowa ta cikin ƙofofin hancinsu akan idanun su, wata irin razana suka yi ganin Evils din jikinsu suna fita wanda hakan na nufin sihirin su ya bar jikin su yanzu saura ƙarfin da Allah Ya halicce su da shi, Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana! Rikicewa suka yi, sun rasa gane wanene ya yi masu wannan aika aikar? "Arrest them!" Chief ne ya faɗa, da sandunan hannayensu suka soma kokarin kaima sojoji bugu, aikuwa suka rufe su da bugu saida suka raunata kowace ga6a ta jikinsu, suka yi masu bugun mutuwa, suka wanke jikinsu da jini, daga wanda ya rasa hakoransa sai wanda ya rasa idonsa ɗaya, duk saida suka rarrabasu da kayan jikinsu ya rage daga su sai gajerun wanduna, jikin nasu ma babu kyan gani duk gashi cunkushe wasu ƙazamai da su, gaba ɗayan su farar fata ne, basu ta6a muzanta da shiga tashin hankali ba irin na yau, kafin sojoji su tafi da su, ɗaya daga cikin su ya fakaici idanunsu ya yi saurin zare bindiga daga ƙugun soja batare da sojan ya ankara ba, ya harbe maƙoshin shi nan take ya faɗi a mace, ɗaya kuma Zuciyarsa ce ta buga da bakin ciki nan take ya faɗi shima a mace, sun ƙwammace su kashe kansu akan a tafi da su saboda sunsan ba zasu yi masu da kyau ba, a tunaninsu mutuwa ce mafita a gare su, basu san cewa sun ƙara jefa kansu cikin musiba bane don har ƙwara su ji kunyar duniya. Sojojin basu ji dadin wadanda suka mutu ba, saboda ba su son su mutu batare da sun fallasa ma duniya abun da suka aikata ba, sun fi so su ji kunyar duniya, su kuma gir6i abun da suka shuka. Ukun da suka rage basu a cikin hayyacin su shiyasa basu iya ta6uka komai ba, dama da igiyoyinsu suka zo, aikuwa suka ɗaɗɗaure su kamar dabbobi, shidda daga cikin sojojin suka fuce da su daga kurkukun ta ainihin babbar ƙofar fita daga kurkukun ƙaddara wadda a ƙalla tayi shekaru sama da ashirin batare da an buɗe ta ba sai yau da dubunsu ta cika! Ko tayaya akai hakan ya faru? Nima na ruɗe amma bari dai mubi alƙalamin Boss ! Shin Ina Jan Wuya ne 😳? Ransa fari fat, ya ƙaƙa6e kwalbar zuciyar a ƙirjin shi, shine a gaba gaba, Dr Mark yana a gefen shi, Jan ido da Jan le6e suna a biye da bayansu kamar bindi, sai zumbula uban sauri suke yi don su ƙarasa ga temple of evils. Inda mazaunin dodon tsafin su ya ke, tsabar yadda suke sauri kamar zasu tashi sama.. Lokacin da suka kusa ƙarasawa daga inda suke suna iya hango Temple of Evils da ke a kewaye da wasu samudawan Evil Giants, dogaye ne masu fadin kirji, tun da uwata ta haife ni ban ta6a ganin mutane masu irin ƙwanjin su ba, kallon su kaɗai zai iya sa gaban mutun ya fadi, ga mutum mai tsoro har suma zai iya yi idan ya gansu saboda firgitarwar da ke gare su, zai yi wuya in mutane ne ba zallar evils ba, hatta sautin takunsu kamar na dawakan yaƙi, gaba ɗayansu a sanye suke da jajayen dogayen riguna masu huluna, baka iya ganin komai nasu daidai da idanuwansu sai dai su su ganka, wadannan Evils din daban suke ko a gidan Kurkukun Ƙaddara, sune masu tsaron temple dinsu wato mazaunin dodon tsafin su. Suna da ƙarfin iko, basu san wani abu wai shi tausayi ko imani ba, saboda babu wannan a cikin zuciyar su, kuma suna da sharuɗɗansu, kafin ka tunkare su ka tabbatar babu tsarki a tare da kai! Ba'a ambaton sunan Allah gurinsu ko wani abu da ya shafi addini! Suna da girman kai da izza, basu magana sai dai suyi kwatance da hannayensu, suna dariya amma basu kuka, ba su ɗaukar raini, kuma ba a yi masu ƙarya, uwa uba ba su son maci amana, ba su yarda da kowa in ba Elder Obinna ba da aminin sa Jan Harshe, su kaɗai ne suke basu umarni su bi batare da an samu matsala ba, amma bayansu babu wani mahalukin da ya isa ya kawo masu wargi batare da sun azabtar da shi ba. Kuma idan zaka shekara kana zarya a gidan kurkukun ƙaddara ba zaka ta6a ganinsu suna sintiri ba, basu wuce iyakarsu, aikin su a temple yake nan kaɗai zaka iya ganin su, bakowa ke iya ganin mazaunin dodon tsafi ba sai mai sihiri a jikin shi, ko lokacin da sojoji suka kawo farmaki sun shiga ko'ina amma idanunsu basu gane masu mazaunin dodo ba, idan masu karatu ba zasu manta ba, Unaisah tamu tagargajiya ta ta6a yi masu leƙen asiri har suka yi mata wankan jini, itama a lokacin Allah ne ya nufa zata ga temple din da idanunta sai dai bata ga ainihin mazaunin dodon ba, da kuwa ta gama gani a duniya. Yayin da suke tunkarar su, Wani mayaudarin kallo Mark ya ke bin Musa da shi mai wuyar fassaruwa, batare da shi Musan ya lura ba, da alama akwai wata a ƙasa. Jan ido da Jan le6e dai sai bin su suke yi kamar jela, kowannansu da muguwar manufarsa a rai. Lokacin da suka ƙaraso gaban ƙofar Temple din, dakatawa suka yi da yin tafiya ganin yadda temple Evils din suka kare kofar shiga. Cike da gadara Musa ya soma yi masu magana cikin harshen su na matsafa, "Na cika sharuɗɗan da aka buƙata, na kashe Kaddarar Kurkuku, na kuma cire Zuciyar Kurkuku." Ya faɗa yana nuna masu kwalbar zuciyar cike da alfahari. Sannan ya ɗaura da cewa, "Don haka ku bani hanya in wuce ciki, yanzu ni ne shugaban ku..." Ya ƙarasa maganar cikin izza yana cika yana batsewa. Da hannu, ɗaya daga cikinsu ya yi mashi kashedi mai nuni da gargaɗi. Ƙyalƙyacewa ya yi da ƴar iskar dariyarsa cike da izza ya ce, "Kada ku ce za ku yi min taurin kai, ni ne uban gidanku a yanzu, dole ku miƙa wuya ku yi mini biyayya sau da ƙafa, idan ba haka ba da zarar na hau karagar Elder zan shafe babinku, ku bani hanya in wuce..." Ya faɗa yana dariya. A hankali Dr Mark ya soma ja da baya da baya, cikin takun sanɗa ya arta a guje batare da sanin su ba, ya rage saura su uku. "Ba ku ji abun da ya ce bane? Ku bamu hanya mu wuce, mu ƙarasa aiwatar da abun da ya kawo mu." Jan ido ne ya faɗa a tsawace... "Anya kuwa ba a yi kuskuren wani abu ba? Meyasa suka ƙi bamu hanya mu wuce? Idan har da gaske sharuɗɗan sun cika kamata ya yi tunkan mu ƙaraso zasu dare su bamu hanya..." Jan le6e ne ya faɗa zuciyarsa cike da kokwanto. Cikin sauri ya dubi kwalbar zuciyar da Musa ya rungume a ƙirjinsa. Nan take gabansa ya faɗi ganin wani abu. Cike da tashin hankali ya ce, "Musa mun mutu! Ka ja mana bala'e, wannan ba zuciyar yarinyar bace...!" Kai tsaye maganar Jan le6e ta dira a kunnanshi, kusan a tare Jan ido da jan wuya suka dubi zuciyar dake a cikin kwalbar nan take suka ga tayi duhu baƙiƙƙirin sa6anin ɗazu da jini ne a jikin ta, tsantsar ruɗani ne da tashin hankali ya bayyana akan fuskokin su, wallahi an shammace shi, gaba ɗaya ya razana ya bi ya ruɗe ya rasa gane meke shirin faruwa da shi? Wanene ya ci amanarshi ya yaudare shi, tunawa da Mark yasa shi saurin furta sunan shi, "Mark!! Mark..!!!" Gabansa ne ya fadi ganin babu Mark babu alamarsa nan take ya fahimci Mark ne ya ci amanar shi ya bashi zuciyar evil giant a matsayin zuciyar Batool! Bai ta6a zaton hakan daga gare shi ba! Mark Ya shammace shi. Wata irin kururuwa ya fasa ta baƙin ciki, ya rufe idanunsa gam, baisan sa'adda ya saki Kwalbar ta fadi ƙasa ta fashe, sai huci ya ke yi yana gurnani kamar mayunwacin zaki.. Batare da sanin shi ba, Jan ido da jan le6e suka zame jiki da gudu suka bar gurin ya rage saura shi kaɗai, saida ya gama haukan nashi ya juyo ya ga babu su.. Cikin fusatacciyar murya ya ce, "Ka tabka babban kuskure Mark! Har ni zaka ci amanata! Na rantse bazan ƙyale ka ba, sai na yi maka azaba, Mark ka gama yawo, dole in kashe ka!!!" Sai sambatu ya ke yi kamar mahaukacin kare, yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarsa Temple Evils suka yi mashi ƙawanya, Tashin hankali! dara ta ci gida! A dabarbarce ya furta, "Don ubanku ba zaku bani hanya in wuce ba eye! Kar ku kuskura ku bari in buɗe idanuna in ganku a gabana!" Ya ƙarashe maganar a tsiwace kamar zai doke su, ya runtse idanun shi yana fitar da numfashi mai huci, niyyar shi ya yi masu sihiri ya kashe su idan su kai masa gaddama. Bai aune ba ya ji kamar wani abu na fita ta hancin shi, a hanzarce ya buɗe jajayen idanunsa kaitsaye suka sauka akan baƙin hayaƙin dake fita ta kofofin hancin sa, wani irin mummunar faduwar gaba ya ji, ɗimuwa ta same shi, a kiɗime yake kallon hayakin, ya yi matuƙar razana cikin ruɗu ya dinga sanya hannu yana kokarin tattara baƙin hayaƙin don ya dawo jikin shi. Da alama dai dubun Jan wuya ta cika, sai sambatu yake yi yana fadin, "Ba zai yiwu ba! Bazai yiwu ba, don ubanku ku dawo jikina! Gidan Ubanwa zaku je! Ya kuke so in yi da raina? Wanene ke son ya haukatar da ni ne! Ya Allah ya zaka yi min haka? Waye ke son ganin bayana! Bazan ƙyale shi ba...." Yana magana zufar tashin hankali tana tsattsafowa kan goshinshi, jikinsa sai 6ari ya ke kamar mazari.. Bai gama sanin yana a cikin musiba ba, saida Temple evils suka yi mashi rubdugu suka ɗaga shi sama suka nufi cikin temple din da shi, ya dinga hauka yana kokarin kwace kanshi ya kasa, dama ba wani ƙarfi ne da shi ba, karfinsa na sihiri ne yanzu kuwa babu shi a jikin shi. Musa bai ta6a jin yadda radadin azaba ke ratsa jikin mutun ba, sai yau da temple evils suka shigar da shi ƙurya, sha tara na azaba suka haɗa mashi, saida suka tu6e kayansa suka yi masa zindir haihuwar Uwarsa sannan suka kwantar da shi ta rubda ciki, da zaƙo zaƙon ƙumbunansu suka yi masa 6alli 6alli a mazaunansa, kafin suka ɗauko bulalan su shar6a shar6a da suka tsaface su, Kusan su goma suka shiga zane shi kamar sun samu jaki, sha tara na azaba suka haɗa masa, saida suka haɗa mashi jini da majina, tun yana kokawar kwace kansa yana kokarin kai musu bugu har saida suka ƙarar da duk wani ƙarfi na jikinshi ya zamana bashi da kuzari ko kaɗan, gaba daya suka wanke jikinshi da jinin shi, wani sa'in in suka shafɗa mashi bulalar jini har tsalle Yake yi Ya ɗiga a jikin bango, duk suka faffasa bayanshi da bulalansu tun yana jurewa har ta kaiga Ya fara fasa ihu yana shure shuren ƙafa, ya aje girman kansa da komai ya dinga roƙonsu akan su barshi da ranshi Ya tuba ba zai ƙara ba, ya bi Allah ya bi manzonSa..." Wannan maganar da ya furta cikin sambatunshi ce ta ƙara ja mashi bala'e saboda ya furta sunan Allah a temple dinsu, aikuwa ransu ya 6aci, suka aje bulalan suka ɗebo ruwan dake a cikin tafkin dake agefen temple din a cikin ƙwarya, suka mayar da shi gishiri a saman bayanshi suka watsa gishirin, Ya fasa wata irin kururuwar azaba kamar ransa zai fita, ya dinga burgima yana fadin ya shiga uku, ya bani, ya lalace, ya mutu! Tun yana iya magana har ta kaiga ko yatsanshi baya iya motsawa daga ƙarshe ya sume. ɗauko shi suka yi wasu suka kama ƙafafuwansa wasu suka kama hannayensa suka fito da shi daga temple din suka jefar da shi a cikin tafkin ruwan. *(Jan wuya yau ya sha jar azaba 😂 ashe ba daɗi shiyasa kafin ka zalunci wani ka fara tunanin idan kai akai mawa ya zaka ji? Bawan Allahn nan ya saba ya kashe rai, ko ya ƙona rai yau ya ɗanɗani kwatankwacin radadin a jikin shi)* A bangare su Ɗan iya da suka arta a guje, suna ƙoƙarin saukowa down daga kan bene, ba zato ba tsammani sojoji suka ritsa da su, ƙofar raggo suka yi masu, burki suka ci a matuƙar ruɗe, wato sun yi gudun gara sun faɗa gidan zago. A tsawace Sojoji suka ce karsu kuskura su motsa, su miƙa wuya kawai su zo su tafi.. Ja da baya da baya suka yi gaba daya sun ruɗe kansu ya daure da ganin yadda aka farmake su batare da saninsu ba, wannan wata irin baƙar rana ce? Gaba ɗaya sun fahimci makirci aka ƙulla masu ta bayan fage tun akan zuciyar bogin da aka ba Musa. Wata irin zufa ce ta wanke fuskokin su, fargaba da tsoro ya cika su. "Ya zamu yi? Mu gudu kawai ko mu 6ace, idan ba haka ba kama mu zasu yi.." Jan le6e ne ya faɗa, sojojin suna a tsaitsaye suna kallonsu sun saita su da bindigu, Chief Owais ne a gaba tare da Commender James sun zubawa sarautar Allah Ido. Zuƙunnawa suka yi ƙasa kamar zasu miƙa wuya, cikin sauri suka buga ƙasa da tafukan su don su 6ace.. Saboda shafewar basira da ruɗu yasa su sakin dariya a tunaninsu sun 6ace sojojin basu ganinsu su kaɗai suke ganin su.. Cike da tunƙaho suke taka matakalar benen suna tunkarar sojojin da suka yi kasaƙe suna jira su ga iya gudun ruwansu don su fahimci rashin wayon su.. Saida suka shiga tsakiyar sojojin da niyyar su ra6a su wuce.. Sai kallon su kawai suke yi, ganin sun ƙi motsawa kuma sun ƙi tafiya kuma kallonsu suke yi yasa suka shiga ruɗu a ransu suka ayyana tsayuwar me suke yi basu tafi ba bayan basu ganin su? (😂) "Gidan Ubanwa za ku je??" Da kakkausar murya Chief Owais ya furta, wata irin firgita suka yi a razane suka kalle shi... Cikin rawar murya Jan ido yake tambayar shi wai da wa yake magana? Da sojojin da yake a tare da su ko kuwa da su yake...?" Bai ƙare maganar ba, Chief Owais ya sakar mashi zazzafan naushi akan kuncinsa.. "Da ku nake magana don Ubanku, Marasa hankali..." Zazzare idanunsu suka yi ganin da gaske fa babu garkuwar sihiri a jikinsu, abun da basu sani ba lokacin da suka gudo daga gurin Jan wuya suna tsaka da yin gudun baƙin hayaƙin ya dinga fita ta hancinsu ba tare da sun ankara ba.. Ɗaura hannu biyu Jan ido ya yi asaman kanshi alamar ya shiga Uku. A kiɗime ya shiga ambaton, "la'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin, Allahumma innee a'uzu bika minal khubthi wal-khaba-ith..." Ƙiris ya rage musulman da ke a cikin sojojin su fashe da dariya, Chief Owais ya ce, "Ka ji jakki, tayaya kaida kake azzulumi zaka nemi tsari daga azzalumai? Bayan Allah baya a tare da azzulamai, bayan haka saboda daƙiƙanci addu'ar shiga bandaƙi ce zata taimake ka?" Ya tambaya yana jifarsu da kallo mai cike da tsana. Jan le6e da ya gama rikicewa nan take ya saki fitsari a wandon shi... "Wa'inna hu min Sulaimanu Wa'innahu Bismillah, Ɗan iya mu gudu mu bar gurin nan...!" Jan Le6e ne ya faɗa a dabarbarce. "Tayaya wanda yake rayuwa da aljanu a jikinsa zai nemi tsarin su?" Chief Owais ne ya fada.. Ganin basu da wata mafita, yasa Jan ido ya damƙi rigar Jan le6e suka watsa a guje kamar zasu tashi sama, basu san ma a ina suka jefar da takalmansu ba, sai da suka gama gudun ceton ran nasu suna kokarin shan kwana suka yi kici6us da wasu gungun sojojin, aikuwa a firgice suka juya suka nufi wata hanyar daban, duk inda suka shiga sojoji ne a ciki, no way out, ƙarasowa bakin kofar wani hall suka yi, a guje suka shige tare da saka sakata suka kulle kansu a ciki. A wahalce suka ranƙwafa tare da dafe gwiwowinsu da tafukansu suna ta haki kamar jakuna. "Ganin komai nake kamar a mafarki! Tayaya hakan zai yiwu? Wanene Ya ƙulla mana makircin da aka farmake mu? Ina ji a raina dole na jikin mu, tun da shi kanshi Musan sun shammace shi, hakan na nufin bashi bane ya ci amanarmu ba..." Jan le6e ne ya yi maganar daƙyar saboda haki... Cike da takaici Jan ido ya ce, "Nima kamar a mafarki nake ganin komai, na kasa yarda dagaske komai ke faruwa? Benjamin rayuwar mu tana a cikin musiba, nifa tun da jami'ai suka zo gida nemana nasan cewa tawa ta ƙare, wlh dana san da zuwan wannan ranar da ban jefa kaina cikin bala'e ba, yanzu wa gari ya waya? Sai da Elder Obinna ya ce mu aje mukaman yaƙin mu mu gudu mu yi nesa da kowa amma muka yi kunnan uwar shegu da maganar shi yanzu ai ga irinta nan..." Benjamin ya ce, "Ɗan iya, kai baka tunanin su Jan ƙeya ne suka tona mana asiri? Saboda mun juya masu baya, watakil shiyasa suka yi mana cinne, in ba su ba wanene zai iya yi mana haka?" Jan ido ya ce, "Bana tunanin ko su sunsan da zuwan sojojin nan, ka yi tunani mana wanene ya kwance sihirin jikinmu? Ko shi Musa da ya fi mu shaiɗanci yaudararsa aka yi, an bashi zuciyar bogi a matsayin zuciyar yarinyar...." Zurfin tunani suka shiga kowa da abun da ya ke saƙawa a ranshi, kusan a lokaci ɗaya suka furta, "Elder Obinna!" Tare da kallon juna idanunsu a zazzare. "Shi kaɗai ne zai iya yi mana haka? Amma meyasa ya ci amanar mu?" Cike da 6acin rai Jan le6e ya faɗa.. Jan ido ya ce, "Ja mana akai, Elder bazai ta6a iya cin amanar mu ba, in har ba wani daga cikin mu bane ya ci amanarsa, yana da ruƙon amana amma kuma shi baya yafe ma wanda ya ci amanarsa ....." Tsoki Jan le6e ya yi fuskokinsu sai naso suke yi ga idanuwannan nasu a zare kamar na kwartayen mazurai sun yi jawur. "Musa nake zargin shine ya ja mana, in ba zaka manta ba, shine ya kawo shawarar mu tura evil giants su farmaki Estate dinsa, Musa daƙiƙine, baida wayou, gashi nan ya ja mana gaba ɗayan mu. Wayyo Allah mun shiga uku! ..." Cike da baƙin ciki Jan ido ya faɗa.. Jan le6e ya ce, "Haɗamamman banza, dama haushinshi nake ji, ya cika izza da ji da kai, gani yake kamar ya fi kowa a cikinmu, komai shine kan gaba, in har bashi ya bada shawara ba babu wanda ya isa ya faɗi ra'ayinsa a bi.." Jan ido ya ce, "Inda na gode ma Allah bamu kaɗai abun ya shafa ba, shi da ya ja mana yafi mu shiga cikin bala'e nasan i warhaka yana can hannun evils yana kar6ar tsumagiya...." Duk da halin da suke a ciki hakan bai hana su ƙyalkyacewa da dariya ba. "Dukkan mu mun yi asarar iyalanmu, dukiyoyinmu da kuma mutuncinmu, yanzu me ya kamata mu yi kafin su ritsa da mu?" Jan le6e ne ya tambaya tare da zuƙunnawa ƙasa ya dafe goshin shi dake sara mashi.. *"Babu wata mafita da ya wuce mu haƙa ƙasa mu binne kanmu, idan ba haka ba tayaya zamu fita, bayan sojoji sun yiwa kurkukun ƙawanya!"* "Wannan wace irin banzar shawara ce muna da makamin da zamu haƙa ƙasar ne? Ko kamanta bamu da sihiri a yanzu...?" Ya faɗa tare da juyowa ya dubi Jan ido dake ta zazzare idanunsa... Cikin rawar murya ya ce, "Don ubanka bani ne na yi magana ba!" Gabansu ne ya yanke ya fadi, zuciyarsu ta shiga harbawa fat fat kamar zata tsaga kirjinsu, tsoro ya hana su juya su ga wanene a cikin hall din bayan sun kulle ƙofa kafin su shigo. Kuskuren da suka yi shine kwata kwata basu lura da inda suka shigo ba, kawai sun ja kofa sun datse sun juya baya suna ta sambatunsu... "Congratulations, You're Under arrest!" Muryar Chief Owais ce ta ratsa kunnuwansu, A razane suka juya suna kallonsu, su biyu ne shi da Commender James, abun da ya faru lokacin da suka shiga hall ɗin sun gan su saboda sun biyo su, sai dai basu bi ta ƙofar da su suka shiga ba, saboda sun ga akwai wata kofar ta bayan hall din. Su biyu suka yi masu rubdugu, wani irin bugun mutuwa suka yi masu, idan Chief ya jibga sai ya tilla ma Commender James shi kuma ya jefa masa na hannunshi, haka suka dinga musayar su, saida suka haɗa musu jini da majina akan fuskokin su, Chief bai iya bugu cikin fushi ba, lahanta sassan jikin mutun yake yi, sai da suka faffasa fatar jikinsu, wani naushi da Chief ya sakarma Ɗan Iya a bakinsa nan take haƙoransa biyu na gaba suka babbako jaga jaga da jini suka faɗo ƙasa, ya dinga buga kanshi jikin bango, ɗan iya ya dinga fasa ihu da azaba ta ishe shi, ya rasa meke masa daɗi gaba ɗaya ya fita hayyacinsa . James da ya lura Chief ya kusa kashe shi.. Cikin sauri ya jefar da Jan ido gefe ɗaya ya nufe shi ya na kokarin raba shi da shi.. Cikin fushi yake fadin ka barni james! Ka ƙyale ni! ka barni in kashe fasiƙin mutumin nan..." yana magana muryarsa na rawa saboda 6acin rai, shatun jijiyoyinsa sun fito ruɗu ruɗu. "Owais, ka dawo hayyacinka mana, kashe shi ya sa6a ma doka!" Da ƙyar ya 6am6are Chief Owais daga jikin Ɗan iya, aikuwa ya koma kan Jan le6e abokin kakansa ya shaƙi wuyansa kamar zai tsinka shi, cikin harshen turanci yake fadin, "Owais ka sakar min wuyana ni fa ne Benjamin abokin kakanka, ka yi mini rai, kada ka kashe ni, na tuba Owais ka ƙyale ni..." Yana fitar da huci ya ce, "In ƙyaleka ka ce! To ai ko shi kakanka nawa ba ƙyalesa na yi ba balle kai da ban haɗa alaƙar komai da kai ba, banza daƙiƙi.." Ya faɗa tare da watsa masa yawu akan fuskarsa, kafin ya shiga kai mashi naushi a tsakiyar cikinsa, jini har ta baki yake amansa, ya dinga kurma ihu yana ambaton Jesus, Commender james ya ce, "Baka da hankali! ai ko shi jesus din bai ce a aikata zalunci ba, banza dakiki..." Sai da suka raunata duk wata ga6a ta jikin su, suka haɗa masu jini da majina akan fuskokinsu, Jan le6e tuni ya sume, Ɗan iya da ya kasa tsayuwa akan ƙafafunsa aikuwa ya yi taga taga cikin rashin sa'a da rashin sani ya faɗa cikin kaskon wutar da ke a bayan shi ya yi zaman yan bori a kanshi, wutar dake ci balala ta kama mazaunansa ya shiga kwarma ihu, raɗaɗi ta ko'ina a jikin shi, da sauri Owais ya damƙo gaban rigarshi ya fusgo shi daga kan kaskon wutar ya maka shi da ƙasa, ya yi saurin janyo wani madaidaicin carpet dake a ƙasan hall din ya shiga kakka6e masa wutar da ta kama rigarsa. Saboda bai son ya mutu yanzu batare da ya gir6i abun da ya shuka ba, tsabar radadi yasa har zawo ɗan iya ya saki a cikin gajeran wondon shi, daƙyar ya samu ya kashe mashi wutar, nama dai ya soyu (😂) Fito Owais ya yi, Nan take sojojin da suka kewaye hall ɗin suka shigo da igiyoyi a hannunsu, biyu daga cikin su suka ɗaɗɗaure su kamar mushen dabbobi gaba ɗaya sun sume, a haka suka cuccu6esu tare da fucewa da su. Yanzu mutun ɗaya ne ya rage su kama wato Jan Wuya da basu san inda ya boye kanshi ba... Bakomai ne yafi damun Owais ba fa ce rashin ganin su Unaisah da bai yi ba, har sojoji ya tura su dudduba ko'ina na kurkukun su gano su amma har yanzu ba labari, Ya Salam! Daurewa kawai ya ke yi. Fucewa suka yi da sauri suka nufi Cikin kurkukun, bayan sun raba kansu kaso uku, wasu suka bi straight, wasu sukai dama wasu suka bi hagu.. *JAN WUYA, Alhaji Musa, ƙaramin su babban su, Big boss, duk shi kaɗai🔥* Tun lokacin da Evils suka wurgo shi cikin tafki ya nutse can ciki, kuma nan take ya farfaɗo saboda taurin rai irin nasa bayan azabar da ya sha, da yake dai lokacin mutuwarsa bai yi ba shiyasa ya rayu, zuciyar nan tasa ta yi baƙiƙƙirin saboda 6acin rai da fusata, ya ji baƙin cikin da bazai iya misalta shi ba, duk irin izzar dake gare shi wai shine yau Evils suka tu6e ma kaya, suka zane shi da bulala kamar jaki? kamar ba su san shi ba? Ya Ilahi! Ya gaza yarda da komai da ya faru, kamar a mafarki yake jin kan shi, bai ta6a muzanta irin na yau ba, duk da mawuyacin halin da yake a ciki hakan bai saka ya saduda ba, shaiɗaniyar zuciyar nan tashi sai tunzura shi take yi akan ya nemo wadanda suka ci amanarshi ya kashe su don ba zai ƙyale su ba. Abun ya matukar ƙona masa rai, wutar baƙin cikin dake ci a cikin zuciyarshi sai ƙara ruruwa take yi. Bakomai ne ya fi karya masa zuciya ba face cin amanarsa da Mark ya yi, duk irin yardar da ya yi da shi, Ko p.a ɗinsa bai yarda da shi kamar yadda ya yarda da Mark ba, ya yi danasanin sanin shi a rayuwar shi, kuma ya ci alwashin sai ya azabtar da shi, kuma ba zai fasa mummunan kudirin nan nasa ba. Bai damu da raunatar da jikinsa ya yi ba, cin amanar da aka yi masa yafi radadin raunukan da ke a jikinsa.. Yayin da yake wannan zancen zucin yana a bakin tafkin ruwan, rabin jikinsa a cikin ruwa, da ƙyar fa ya samu ya yi iyo har ya fiddo da kanshi. Sai nishi ya ke saki kamar mai jin kashi. Fuskarsa duk shatun bulalan evils. Da ƙyar ya tattara sauran karfin da ya rage mashi ya fito daga cikin ruwan tun6ur, rashin kuzari ya hana ya yi tafiya, saida ya dafe bango, kwata kwata bai damu da babu sutura a jikin shi ba, saboda ƙarfin hali irin nashi ya dinga jan ƙafar shi yana tafiya zuciyar shi na ci gaba da tunzura shi, yadda kasan zai iya ta6uka abun kirki. Kwatsam, ya soma jiyo harbin bindigu a cikin kurkukun, ruɗewa ya yi ya soma tunanin ko dai ba daidai kunnansa suke jiyo mashi ba, kamar ta6a66e ya sanya hannu yana bubbuga kunnansa, bai gama farfaɗowa daga ruɗun da ya shiga ba a dai dai zai karya kwana, unexpected ya hango gungun sojoji suna ta aikin dasa bomb a kowace kusurwa ta gidan Kurkukun Ƙaddara. Ga kuma muryar Chief Owais da ke basu umarnin su shiga saƙo da lungu su gano Jan Wuya da su Unaisah. Gaba ɗaya ya shiga rudani, ya rasa gane meke faruwa da shi? Wannan wata irin bakar rana ce da bai ta6a zaton zuwanta ba? Abun da ya ɗaure mashi kai tayaya akai sojoji suka san suna anan har suka kawo masu farmaki! Lallai ba karamin tuggu aka shirya mashi ba, dole ya nemi mafita kafin su rutsa da shi. Mantawa ya yi da raunukan jikinsa, ya Juya da sauri yana ɗangyashi ya koma hawa na biyu na bene ya dinga neman inda zai 6oye kan shi, faɗawa ya yi cikin pharmacy ɗinsu wanda bayan ƙofar gaba da akwai kofar shiga tiyata room a cikinsa, jikinsa na 6ari ya kulle kofar yana haki. Zuciyarsa ce ta raya masa bai tsira ba anan ma, Idan kuma Bomb ya tashi da shi fa? Cike da 6acin rai ya naushi ƙofar tare da kifa goshin shi a jikin ta. _"Idan muka roƙi Allah ya taimake mu, ba kaitsaye yake taimakonmu ba, ba ganinsa muke ido da ido ba, sai dai ya yi mana hanyar da taimakonsa zai iso gare mu, ba na ce zan gwada maka yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri akan wanda ya zalunce shi ba? Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Haƙiƙa ALLAH Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi bazai kuɓuce masa ba.”_ _Kuma in sha Allah ba zaka ta6a cika burinka ba, ina ji araina zasu farmake ku a yau din nan, ka jira ka gani, ƙarshenka ne ya zo, In sha Allahu daga yau ka gama yawo..."_ Maganganun Unaisah ne suka dinga dawo masa a cikin kansa, wani irin baƙin ciki ne ya taso mashi kamar ya haɗiya zuciya ya mutu, baisan ya akai ya tsinci kan shi da jin tsoro da fargaba a cikin zuciyar shi, abun da bai ta6a ji ba, saboda ƙarfin zuciyar shi, wani irin bugun barazana zuciyar shi ke yi.. A ransa ya ayyana, _Meyasa maganganun yarinyar suke shirin zama gaskiya?" Tayaya akai tasan zasu farmake su? Ƙululun bakin Ciki ne ya tokare zuciyarsa, ya dinga bubbuga kanshi jikin ƙofar_ Unexpected ya soma jiyo motsin mutun a cikin kunnansa kuma a cikin ɗakin da ya ke. A firgice ya juya yana faɗin wanene? Kaitsaye idanunsa suka sauka akan ƙafafunta, yayin da take kokarin la6ewa a ƙarƙashin table, ransa ne ya bashi cikin yaran ne, aikuwa da mugunta ya durfafeta, ya damƙo kafarta ya janyo ta waje, ta fasa ƙara a tsananin tsorace ya juyo da fuskarta, tana haɗa ido da shi ta kuma fasa wata ƙarar kamar bakinta zai 6are. Matse bakinta ya yi da tafin hannunsa, fuskarsa ɗauke da shu'umin murmushi ya furta, "Wannan karon ba zaki kubce mini ba don Ubanki, sai na cire zuciyar ki..." Zazzare idanu ta yi cike da faragaba take kokarin ƙwace kanta, gaba ɗaya jikinta rawa ya ke kamar mazari, ga tashin zuciyar da ta fara ji saboda ƙyanƙyamin mummunar halittar gabansa da bai suturta ba.. Sakin bakinta ya yi, ya damƙi gaban rigarta da ƙarfi ya rabata biyu ya cireta, ya barta daga ita sai ɗan pant da bra a jikinta, ya ɗaure ƙugunsa da rigar. Kafin ya damƙi gashin kanta, fashewa ta yi da kuka saboda radadin da ta ji, cikin shassheƙar muryarta take ambaton sunan Unaisah, sam ta kasa taimakon kanta, ɗago da ita yayi ya buga kanta jikin table din, nan take kanta ya kama ciwo, ta zube kan gwiwowinta kanta na a kife jikin table ɗin, cuccu6arta ya yi tare da kwantar da ita saman table din, ga dukkan alamu ta sume. Juyawa ya yi yana huci ya nufi ƙaton pharmacy shelves din dake a jikin dakin, medicines ne jere a cikinsa, robobi da kwalaben magani da sauran abubuwa, da ƙyar ya nemo surgical knife din da yake nema ya dawo gaban table din kamar mahaukaci ya ɗaga wukar zai caccaka mata a kirjinta, kwatsam! ya ji dirar wani abu a bayansa mai sautin gaske. Juyowar da zai yi keda wuya, ta daddage ta sauke masa kafaɗa da zarton hannunta, wata azababbiyar ƙara ya fasa saboda yadda radadin ya ratsa sassan jikinshi, tuni jini ya wanke kafaɗarsa, da ƙarfi ta zare zarton da jinin ya wanke shi.. Buɗe idanunsa ya yi sun kaɗa jawur kamar garwashin wuta, ya saukesu akan fuskarta har saida gaban shi ya faɗi da ya yi arba da ita, ya razana da ganin ta a raye! Tayaya akai ta rayu har ta ku6utar da kanta? Kwata kwata babu tsoro ko fargaba a tare da ita, zuciyarta ta bushe, cike da ƙyanƙyami ta ke kallon shi, kanta ya ɗaure da ganin yadda ya sauya lokaci guda, ga shatun bulalai da raunuka a jikin shi, uwa uba babu sutura a jikin shi, ta lura rigar da ya ɗaure ƙugu da ita ta Batool ce abun kunya. Tuntsirewa ta yi da dariya cike da shaƙiyanci, ta soma kwaikwayon maganar da ya faɗa mata ɗazu.. "Ni ba asararre bane, ni mai buri ne, ban ta6a yin asara ba, komai na nema saina same shi, tun da na taso rayuwata, ni mai nasara ne, mai ɗaukaka kuma shahararren mai arziƙi, har matsayin shubagan ƙasa na taka, me ya fi wannan? Kuma na ci riba, tun da na dade ina sheƙe ayata batare da asirina ya tonu ba, ina da ƙarfin ikon da babu wanda ya isa ya ja da ni, ko mutuwa tsorona take ji.." Tsabar yadda take dariya har bubbuga ƙafafunta take yi ƙasa. "Musa mai izza, da jiji da kai, former richest president ina suturarka? Wanene ya zane ka da bulalai?" Wani irin ƙululun bakin ciki ne ya tokare makoshin shi, in har bai kashe yarinyar nan ba to bai haifu ba, baima san ta ya akai ta rayu ba? Wai ta ina ta shigo ɗakin? Sai da ya yi wannan tunanin ya lura da access panel na ceiling din da ta bude don bala'e ta ciki ta dinga tafiya da jan ciki har ta kawo nan! Takaicin duniya ya ishe shi cikin bakin rai ya furta, "Tayaya akai kika rayu don ubanki?" "Ba saida na faɗa maka babu hijabi tsakanin addu'ar wanda aka zalunta ba akan wanda ya zalunce shi ba..?" Bata ƙare maganar ba, ya durfafeta yana huci tare da sakin nishin azaba yana fadin, "Kin yi kuskure da kika kawo kanki, saina kashe ki, dake da ƴar uwar taki, kashe ku zan yi..." Duk da tasha jinin jikinta hakan bai hana ta dake ba, da zarton hannunta ta dinga kakkare kanta, daga ta ɗaga zata buga mashi sai ya kauce, cikin rashin sa'a ya fusge zarton daga hannunta, ya ɗaga zai buga mata a tsakiyar kanta tayi saurin zuƙunnewa ƙasa ta bi ta tsakankanin ƙafafunshi ta koma bayanshi, kafin ya juyo ta damƙi ƙafarsa ɗaya ta jata da karfi har saida tayi nasarar kayar da shi a ƙasa ya faɗi ƙasa timmmm kamar bakure. Tuni zarton hannunsa ya kubce ya koma gefe ɗaya, kafin ya ɗago ta soma tunanin mafita duk ta bi ta rude, tana kokarin juyawa da niyyar ta dauki Batool su gudu, batai aune ba, ya sanya ƙafarshi ya taɗiyeta, ta kife ƙasa kanta ya daku, kafin ta ɗago ya soma jan jikinshi ya nufi zarton, burin shi kawai ya farke ta da shi. Cikin hanzari ta daddage cike da ƙarfin hali ta miƙe, jikinta na bari ta bi shelves din dake a ɗakin. A lokacin har ya samu ya ɗauko zarton cike da rashin ƙuzari ya miƙe yana nishi, fuskarsa a murtuƙe sai gumi yake fitarwa, kwata kwata babu ƙarfi a jikin shi saboda jinin da ya zubar, ga raunukan jikinsa dake ta azabtar da shi da raɗaɗin su. Juyowar da zai yi keda wuya, Unexpected ta daddage ta watsa mashi acid saman fuskar shi, Wa'iyazubillah! ji ya yi kamar ta watsa mashi wuta, in a short time rabin fuskarshi ya zagwanye gwanin ban ƙyama, lokacin da zafin ratsa sassan jikinsa har izuwa kwakwalwarsa wata irin kururuwar azaba ya fasa ta fitar hayyaci jikin shi ya hau yin 6ari baisan sa'adda ya saki zarton hannunsa ba, gaba ɗaya ya yanke jiki ya faɗi kasa wanwar rai hannun Allah. Bata san ya akai take jin kamar ta aikata mummunan zunubi ba, jikinta sai kerma ya ke yi, sai zazzare gray eyes dinta take yi tana ƙare masa kallo ta rasa gane ya mutu ne ko suma ya yi. Gabanta na faɗuwa ta jefar da kwalbar acid din dake a hannunta, dama a cikin pharmacy shelves din ta zaƙulo ta. Bugun kofar da aka yi ne yasa ta fashe da kuka a firgice ta shiga fadin wayyo Allahna! Wallahi bani na kashe shi ba, bani bace, bansan na yi ba...." Gaba ɗaya ta runtse idanunta sai hauka hauka take yi.. "Unaisah..." Sanyayyar muryarsa ce ta ratsa kunnanta, a rude ta dube shi, kwata kwata bata san da zuwansu ba. "Ya Owais..." Ta furta cikin rawar murya, watsawa ta yi da gudu ta nufe shi, ya yi hugging dinta tare da ɗaura hands dinsa a bayanta, nutsuwa ta ji ta shigeta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi.. A ruɗe yake tambayarta me ya faru da ita meyasa take kuka? Wani ya cutar da ita ne? Ina Batool take...?" Cikin rawar murya ta ce, "Na ƙona masa fuska da acid, na kashe shi, gaya can a kwance.." Raba ta ya yi da jikinshi cikin hanzari ya nufi cikin ɗakin, tunkan ya ƙarasa ya hango Jan wuya dake a baje ƙasa babu sutura a jikinsa, al'ajabi ne ya kama shi, mutumin da suke nema ruwa a jallo ashe yana nan rai hannun Allah? Abun da ya daure masa kai tayaya akai Unaisah ta ci ubansa har ta yi nasara akan shi? Al'amarin akwai ɗaure kai! Lura da Batool dake sume kan table yasa shi saurin zame coat dinsa, ya cire vest ɗin ciki ya nufeta, da sauri Unaisah ta matso kusa da shi, da taimakonta ya saka mata vest dinsa, ya kuma ɗaure mata ƙugunta da coat din. Tactical raɗio dinsa ya zaro daga aljihun wondonsa ya kanga a bakinsa .. "Mun samu jan wuya a pharmacy room na gidan kurkukun ƙaddara, tare da yaran da muke nema, Ku hanzarta zuwa ku tafi da shi..." Ya ƙarashe maganar yana kallon Unaisah da ta dafe waist dinsa da hannunta, ta ɗan langwa6e kanta a jikinshi ya fahimci gaba ɗayanta a tsorace take, bai ji dadin ganin yadda ta raunata ba, fuskarta duk busasshen jini a kai daga gani ta ci baƙar wahala. "Ki kwantar da hankalin ki, ba laifi kika yi ba, kin yi abun da ya cancanta a jinjina maki Unaisah"! Lumshe idanunta ta yi, still jikinta bai daina kerma ba.. Suna a tsaye saiga sojoji sun soma shigowa dakin hannayensu ruƙe da bindugu... Wasu sun rike igiyoyin kaca... Babu wanda bai yi al'ajabin ganin shi baje a ƙasa ba, sun ruɗe da hakan, Ɗaɗɗaure shi suka yi da igiyoyin kaca kamar giwa, haka suka kama kafafunsa da hannuwansa suka ɗaga shi tare da fucewa da shi.. "Owais na ruɗe, meya faru? Tayaya akai ka yi nasara kan shi?" Cikin harshen turanci james ke tambayar shi. da hannu ya nuna masa Unaisah, sunnar da kanta kasa ta yi... "Ihu na jiyo a dakin shiyasa na shigo don inga wanene ashe shine da su a dakin.." A ruɗe U.s armies suka kalleta, murya na rawa ta labarta masu komai da ya faru tun daga farko da ta farka ta ganta a mayanka. Sun jinjina mata, amma abun da ya ɗaure masu kai, meya faru da Jan Wuya da yasa shi rasa suturarshi ga kuma shatun bulali da suka faffasa fatarshi saboda tace masu batasan meya faru da shi ba, itama ta yi mamakin ganinsa haka, ita kawai ta duro ta ganshi yana ƙoƙarin farke ƙirjin Batool... Basu tsaya 6ata lokaci ba, Owais ya ce ma U.s Armies su tafi da su Unaisah cikin jirgi, suka amsa da toh, a saman kafaɗa Canal Herry ya sa6i Batool.. Unaisah ta bi bayansu, ganin tana ɗangyasa kafarta ne yasa thompson Ya sa6e ta a kafadarshi, ta yi lamo saboda bata a hayyacinta.. Muyi sauri mu fita, nan da ɗan lokaci bamabamai zasu fashe.." Chief Owais ne ya faɗa, fitowa suka yi su uku da shi da James sai Jackson.. Cikin sauri suke tafiya har sun kusa karya kwana kwatsam chief yayi tuntu6e da wani abu agabansa, kusan atare suka dube shi, Evil giant ne kwance a kasa sai nishi yakeyi, yana birgima kamar mai fama da ciwon mara. Kallon juna suka yi a rude, Commender har ya zare bindingar ƙugunsa da niyyar ya harbe shi, Unexpected suka ga ya sanya hannayensa bibbiyu ya 6a66ake mask din dake akan fuskar shi. Wani kyakkyawan matashi ne, reddish long hair dinshi ya lullu6e gefen fuskar shi.. Miƙa ma Chief Owais hannu ya yi yana nishi ya furta, "Ka taimaka mini, bana jin daɗi, bana iya tafiya..." "Kada ka yarda da shi, tarko ne aka ɗana mana, mu kashe shi kawai mu tafi." Jackson ne ya fada tare da zare bindiga ya saita kan shi. Yana kokarin harbin shi Chief ya yi wuff ya buge bindigar ta faɗi ƙasa. Muryarsa a ruɗe ya furta, "Kuna ganin abun da nake gani kuwa?" A rude suka kalli inda idanunsa ke kallo, giants ne ta ko'ina suke 6ullowa gaban su da bayansu, gaba daya babu kuzari a jikin su, ko tafiya basu iya yi, sai jan ciki suke yi, masu ɗan saurin karfin cikin su ne suke iya rarrafe, sai nishi suke suna neman agaji. A rude Commender James ya furta, "What on earth..!" Tunawa ya yi da kalaman baba Obie, "Kafin ku isa taimakona zai riga ku isa can." Nan ya yi Nazari ya gano cewa baba Obie ya lalata sihirin dake a jikin kowani mutum na kurkukun kaddara, wanda hakan na nufin kowani giant zai koma ainihin wanene shi, babu sihiri, babu evils, kuma babu mugayen ɗabi'unsu, yanzu halinsu ne da ubangiji ya halicce su da shi, kuma nan take ya tuna da labarin da Danish ya bashi na yadda suke nuna masu fin karfi su maida su Giant, La'haula wala ƙuwata Illah billah! Wata shari'ar sai a lahira, Allah shi kadai zai iya saka ma wanda aka zalunta. Idanunsa ne suka cuccuko da ƙwalla, saboda ya gane bayin kansu bane. Dafa kafadarsa Jackson ya yi, "Yakamata muyi wani abu, kada su farmake mu, mu kashe su kawai." Girgiza kai ya yi, "In har muka kashe su, ba mu yi masu adalci ba, abun da suka aikata bayin kan su bane, sarrafa su ake yi, suma fursinoni ne irin Danish.." A rude suke kallon shi jin abun da ya ce. Sai lokacin ya fada masu komai da ya tattauna da baba Obie ya ƙara da cewa, "Idan kuka lura, tun da muka fara farmakar Elders basu iya amfani da sihiri ba, ina ji a raina garkuwar sihirinsu ce ta karye, to waɗannan Giants dinma babu sihiri a jikin su, suma yan adam ne, yanzu halin su ne wanda Allah ya halicce su da shi.." Yana karasa maganar ya miƙa ma matashin hannu ya ruko shi tare da janyo shi da karfi gaba daya ya fada jikin shi, hugging dinshi ya yi cike da jin tausayin shi. Gaba daya sojojin dake a gurin jikinsu ya yi sanyi lakwas, zuciyarsu ta karaya.. Jiki a sanyaye Commender James ya zaro tactical radio dinsa ya kanga a baki, ya umarci sojojin da suke a cikin kurkukun da su bi saƙo da lungu, duk inda suka ga giant kada su kashe su, su taimaka masu su fitar da su daga kurkukun a tare da su zasu tafi. yayin da yake wannan maganar gaba daya sojojin da ake a kurkukun sun ji sanarwar shi ta cikin tactical radio dinsu. Batare da bata lokaci ba, suka fara cika umarnin Commender, in a short time suka fitar da kowani giant da ke a cikin kurkukun. Ya rage saura matashin nan da Chief Owais ya rungume, a tare da shi suka kama hanyar barin kurkukun ƙaddara Finally sun yi nasarar barin gidan kurkukun kaddara bayan sun yi nasara🥳🥳🥳 Jiragen su da motocinsu na barin yankin gaba ɗaya gidan kurkukun kaddara ya rushe kamar bai ta6a wanzuwa ba ya shafe gaba dayan shi, saboda yadda ginin yake rushewa yana girgiza yasa dajin evil forest ya dinga girgiza kamar za a yi girgizar ƙasa, duk wata dabba dake a cikin dajin saida ta razana saboda rushewar kurkukun ƙaddara 🔥 (Rayuwa kenan, yanzu babu gidan Kurkukun Kaddara, sai dai tashin zance 🔥🔥🔥) Bari mu koma baya mu ji wanene ya ƙullawa Elders makircin da ya ja aka yi nasarar kama su? Meyasa Mark na hannun daman Musa ya ci amanarsa? Duk ba wannan ba, tayaya akai ma sojoji suka san suna a gidan Kurkukun ƙaddara? Da har suka kai masu farmakin bazata❓ Ku biyo ni don jin Amsar tambayoyin ku. Da tura ta kai bango, sun kai gauro sun kai mari a neman Musa da yaran da ya sace basu gano ba, babu inda basu duba ba sama ko ƙasa babu shi babu alamar shi. Hankalin Chief Owais ya kasu gida biyu, ga tashin hankalin rashin su Unaisah ga damuwar ahalin yaran da aka sace yasan suna a can cikin mawuyacin hali baisan ya zai yi da ranshi ba... Uncles ɗinsa da daddynsa sai kiran wayar shi suke yi batare da sanin shi ba, saboda hankalinsa ba a kwance yake ba ya saka wayar silent.. Sai da tura ta kai bango, ya ga baida wata mafita da ya wuce ya koma gurin Baba Obie ya roƙe sa akan ya taimaka masu.. Lokacin da ya je gidan baban, a main falo ya taras da wasu daga Cikin Uncles dinsa, tun da ya yi sallama suka nufe shi suna tambayar ina ya shiga suna ta neman shi tun jiya da jiniya ta cika garin, meya faru? Suna ta kira baya picking meyasa? Cikin rashin nutsuwa ya zayyana masu komai, basu yi mamakin jin Ɗan iya da Alhaji Musa suna a cikin Elders ba, saboda dama can mutane suna zargin dukiyar Musa bata halal bace, musamman yadda yake almubazzaranci, ga girman kan tsiya da izza ashe yasan meya taka.. Ɗan iya kuwa duk sun san halin shi na maitar son abun duniya, ya cika haɗama ga ƙarya a bakinsa, bayan kasantuwarsa munafuki ya kuma ƙware gurin haɗa yan siyasa faɗa, ya ƙulla masu makircin da zai raba kansu, in har aka biya shi kuɗi babu abun da bazai iya yi ba, shi dama baki gare shi, ko dan jarida bai kai shi haɗari ba, ya iya tsara kalaman ƙarya, idan yayi wa ɗan siyasa campaign zai yi wuya ka ga dan takarar bai yi nasara ba, shiyasa ya siye zuciyar politicians da ta al'umma, in ya so abu kamar zawo yake baida hakuri, ya iya shisshigewa masu hannu da shuni wadanda suka shahara, kuma baya gajiya da bauta masu don ya samu abin duniya. A tare suka haɗu da shi da Uncles din nashi, suka fara shawarar ta yadda zasu shawo kan baba Obie don ya taimaka masu su gano inda Musa ya je da yaran nan, sun san zai iya, a wannan ga6ar sun yarda ko sihirin ne ya yi saboda a taimaki rayuwar yaran kafin ya cimma manufarsa akan su, don suna ji a ransu ba hakanan ya za6e su su biyu ba, bayan ga fursinonin da suka killace a asibiti, amma duk ya tsallake su ya ɗauki yara biyu kacal dake a gidan Dg! Meyasa? Dama yana bibiyar rayuwarsu kenan? Wadannan tambayoyin ne suka tsaya masu a kahon zuciya, sun kasa samun amsoshin su, amma fa suna a cikin rudu da fargaban me zai biyo baya don sunsan ba alkhairi bane da akwai sauran rina a kaba...🔥 Da farko har sun yanke shawarar zasu tunkari Baba Obie gaba ɗayansu don su roƙe shi, prime minister ya ce kada su wahalar da kansu, sun manta wanene baban nasu, ba zai ta6a sa6a alƙawari ba, amma akwai wata hanya da ya ke ganin in suka bi za su yi nasara akan shi.. A kagare suka tambaye shi wace hanya ce. Ya ce nazarin da ya yi cikin tattaunawar da Owais ya yi da Baba Obin, ya fahimci wani abu, tabbas bazai karya masu alkawari ba amma in har suka ci amanar shi zai tona masu asirin su ne, dalili kuwa a maganar shi ya ce in har suka kawo masu farmakin bazata, su yi saurin sanar da shi, shawarar da zai bada su yi amfani da Saratu dake jinya, su faɗa masa an kawo masu farmaki kuma an raunata wasu daga cikinsu ga kuma shaida nan. Gaba ɗaya sun yi amanna da maganar Prime minister, sun kuma jinjina ma hikimarsa. A daren ranar Hateeem ya kira Sharafuddeen ya fada masa komai dake faruwa har set up din da zasu yi, ya kuma ce yana son ya tura ma Owais video din Auta. Cikin abun da bai fi mintuna biyar ba, Sharafuddeen ya tura ma Owais video din hajiya Saratu kwance akan gadon asibiti tana ta sambatu. Prime minister ne ya tsara mashi komai da zai fada ma baban, bayan sun gama shirya komai.. Chief Owais ya nufi back room dinsa, A gaban tagar ya tsaya tare da fashewa da kuka yana ambaton sunan shi baba baba baba, yadda kasan ƙaramin yaro. Kwata kwata baya iya hangensa saboda ya kashe light din dakin, duhu ne ko'ina. Sautin kukansa da baba Obie ya jiyo yayi matuƙar ɗaga hankalinshi, cikin raunanniyar muryarsa ya shiga ambaton sunan shi Owais Owais, jikallena? Meya faru? Kukan ka nake ji ko kunnena ne su ke jiyo min ba daidai ba?" Cikin shesshekar kuka ya ce, "Baba muna a cikin tashin hankali, jiya da daddare baka ji jiniyar motoci ba?" "Owais na ji, wani abu ya faru ne?" "Eh baba, jiya an kawo mana farmaki, muna tsaka da bacci, wasu miyagu suka ritsa da mu, kafin mu ɗauki mataki sun raunatar da wasu daga cikin mu..." Bai ƙare maganar ba, ya ji baba Obie yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, cikin ruɗu da tashin hankali, "Owais dawa dawa suka farmaka..." "Gidana, harma sun ɗauki yara biyu daga cikin yaran da nake kula, bayan haka sun farmaki auta, baba muna zargin da sa hannun Elders. Muryarsa da tashin hankali ya ce, "Owais me suka yi mata? Sun cutar min da ita? Tana raye? Owais ka fadamin! Ina Saratu take?" "Tana a kwance rai hannun Allah, gaba daya sun faffasa mata fuskarta da glass, kwata kwata bata a hayyacinta sunan ka kaɗai take fada, ba don munyi saurin kaita asibiti ba da tuni rai ya yi halinsa, ga shi ka kalli videon ta da na ɗauko maka." Ya fada tare da tura wayar ta cikin tagar. Baisan sa'adda ya sanya hannu ya kar6a ba sai dai ya ji babu wayar a hannunsa alamar ya ɗauka, cike da zumudi yake jiran ya gama ya ji me zai ce fatansa Allah yasa ya taimaka masa. "Owais, ku yi hakuri, komai ya faru ni ne na ja maku, laifina ne! Da nasan zasu ci amanata da ban boye maka su wanene sauran ba, gashi nan har sun fara farmakar ahalina, dama nasan za'a rina tun da ba Allah ne a ransu ba, wallahi tun da har suka ta6a jinina bazan ƙyalesu ba, sun ja ma kansu bala'e da musiba..." Farin ciki ne ya lullu6e zuciyar Owais. Aje masa wayar yayi kan tagar ya zura hannu ya ɗauka. "Baba kada ka damu dan Allah, ni ban nuna maka don na ɗaga maka hankali ba face don ka taimaka mana mu nemi mafita, in ba haka ba zasu iya ƙara farmakar mu..." Bai kare maganar ba, ya katse shi cikin fushi ya ce, "Owais, yaran da suka ɗauke meye sunayen su?" "Unaisah yarinyar da zan aura, ɗayar kuma sunan ta Batool, mun neme su sama ko ƙasa mun rasa baba! Na manta ma ban faɗa maka ba, na gano mutun biyu cikin Elders, Musa da Ɗan iya, kuma muna zargin Musa ne ya shirya komai. Da jin wannan maganar yasa baba Obie ya gano me suke shirin ƙullawa wato basu daddara ba bayan gargadin da ya yi masu akan su aje makaman yaƙinsu su gudu su nemi mafaka, amma saboda haɗama ƙarfin ikon shi suke so su ƙwace shiyasa suka ɗauke yaran don su cika sharuddan, kuma yafi zargin musa ne kamar yarda ya faɗa, saboda yasan mugun halin shi zai iya komai don ya cika burin sa. "Baba ka yi shiru ba ka ce komai ba, meya kamata muyi yanzu? Yaran tun jiya suka sace su bayan isha'e suka tafi da su, bana so su cutar da rayuwar su, gaba daya komai ya kwance mana!" "Owais, you have my word babu abun da zai faru da su, in har ba sun riga da sun cutar da su ba saboda jinkirin da kuka yi baku sanar da ni ba, amma ku shirya rundunar sojoji ku tafi kurkukun ƙaddara yanzun nan, suna a can tare da yaran, kafin ku isa taimakona zai riga ku isa." Godiya ya yi masa cike da zumudi ya juya cikin sauri ya tafi. Kafin ya bar gidan saida ya fara zuwa falo ya sanar da Uncles dinsa yadda suka yi da baban, sun ji dadi bayan sunyi masa fatan alkhairi ya fito daga gidan ya shige motar shi, Ya ce da driver dinsa ya kaishi Headquarter ɗinsu, kafin su isa ya kira layukan senior agents dinsu ya ce su yi gaggawar shirya rundunar sojojinsu daga ya ƙaraso zasu tafi kai farmaki gidan Kurkukun Ƙaddara🔥 (Kunji Yadda aka yi Suka yi Nasarar Kama Elders) Wani taimako baba Obie ya yi masu? Bayan tafiyar Owais, cikin duhu ya zauna kan kujerar gaban madubin dakin sa, da tsafi ya yi amfani, Duk Elder din da ya kira sunan shi zai bayyana ta cikin madubin, gaba daya saida ya kira Elders din kurkuku mazauna kasashen waje, ya ce sun kuwa san da makircin da Musa ke shirin ƙulla masu? A rude suka ce basu gane me yake nufi fa? ya yi murmushi saboda ya gane Musa bai sanar da su ba, shi kadai ya ke shirin shi, Ya ce dama ya san bazai sanar da su ba, saboda baya son su sani, amma zai fada masu yanzu haka Musa ya dauke ƙaddarar kurkuku, da bugun zuciyar kurkuku, Kuma ya tafi da su gidan Kurkukun don ya aiwatar da sharuddan dodon tsafinsu, in har suka bari Musa ya cimma burinshi, babu tantama zai ƙwace sihirin jikinsu ne sannan ya kashe su, ya ce abun da ya sa ya faɗa masu saboda ya tsiratar da su daga kaidinsa saboda shi ma Musa bai ƙyale shi ba, jiya ya turo da giants sun farmaki ahalinsa, tun da har shi da ya yi mashi halacci ya butulce masa su su wanene da suke tunanin ba zai ci amanar su ba?" Maganar da Obie ya fada masu tayi matuƙar daga hankulansu, da ya ga sun yarda da shi ya kuma cewa, "Ni ban damu wani daga cikin ku ya samu karfin ikona ba, amma ku yi tunani idan Musa ya hau karagar mulkin Elder me zai biyo baya? Kun dai san halinsa ba sai na fada maku ba, kun kuma san me zai iya da wanda ba zai iya ba, " Abun da ya harzuƙa su ta yadda Musa ya 6oye masu abun da yake shiryawa, shi yasa suka yi amanna da maganar baba Obie.. Daga karshe ya ce masu yanzu ya rage nasu! Ko dai su yi gaggawar zuwa gidan kurkukun kaddara kafin rana ta fadi ko kuma su yi dana sani na har bada, yana ƙare maganar, ya rufe madubin nashi da sihiri. Ya ɗauko wayarsa ya kira layukan sirri na Jan ido da Jan le6e bayan sun ɗaga suma ya faɗa masu abun da Musa ke shirin aikatawa. Jan Ido ya ce shi bai damu ba don hankalinsa ba a kwance yake ba, asirin shi ya riga da ya tonu, neman mafaka ya ke yi, Baba Obie ya ce mafaka ɗaya ta rage masa, ya gaggauta zuwa gidan kurkukun ƙaddara, Musa yana a can zai cika sharuddan dodon tsafi, idan suka samu ƙarfin ikon shi zasu fi ƙarfin kowa, in ma suka so zasu iya shafe memory ɗin mutanan da suka san sirrin su.." Da jin wannan maganar yasa suka amince zasu je gidan Kurkukun ƙaddara... (Kun ji yadda a kai Obie ya haɗa Elders gaba daya a gidan kurkukun kaddara saboda ya sawwaƙawa su Chief Owais don su kama su duka, da yake ƙwararrun matsafa ne har wadanda ke a nesa da zarar sun so zasu 6ace su dira a inda suke son su kasance, shiyasa suka haɗu cikin ƙanƙanin lokaci.) Sannan kuma ya tura Evils din jikinshi zuwa Prison Temple don su hukunta Musa, waɗannan Evils din da suka zane Musa da bulalai ba asalin Temple Evils bane, ba mutane bane, shaiɗanun aljanu ne masu haɗarin gaske, su ɗin amintattun Obie ne babu mai iya sarrafa su sai shi a cikin mutane, umarnin shi kaɗai suke ji, tushen su daga jikin mahifiyarsa ne a ranar da aka haifeshi a ranar suka koma jikin shi, tun yana jariri suke a tare da shi. Duk fa yana a cikin ɗakinsa ya aiwatar da komai, hatta Mark da ya butulcewa Musa Obie ne ya yi silar komai.. Yasan cewa shine amintaccen likitansa kuma yana tunanin shi zaisa ya cire masa zuciyar yarinyar saboda yasan jikinta bazai jure sihirin su ba. Aikuwa da ya tashi kawai daga inda yake ya tura Evil ɗaya na jikinshi ya umarce shi da ya shiga jikin Mark, ya faɗa ma evils din jikinshi shine ya turo shi don su sarrafa tunanin Mark, su hana shi cire zuciyar yarinyar su kuma taimaki rayuwar yaran.. Gaba ɗaya komai da ya faru bada sanin Mark ba, gangar jikinsa ce kawai, amma bashi ke sarrafa kanshi ba, aikin Evils ne. Obie ba ƙaramar tsiya ya yi masu ba, lokacin da hayaƙin nan ke fita daga hancinansu shine ya umarci kowani Evil da ya bar jikin Elders harma da Giants ya kuma ƙwace garkuwar sihirin jikinsu ya lalata komai ya barsu da halin su.. Sun daɗe suna sheƙe ayarsu sai gashi rana ɗaya a lokaci ɗaya Allah ya nuna masu iyakarsu, yanzu kuma saura su gir6i abun da suka shuka🔥 Ta yadda akai Batool ta ku6uta, lokacin da ta farfaɗo daga suman da ta yi, ta tsinci kanta a cikin ɗakin fiɗa saman gado, cikin ruɗu da razana ta soma kiciniyar kwance sarƙoƙin jikinta, tana ta kuka kamar ranta zai fita, adaidai lokacin Musa da Mark suka shigo ɗakin tiyatar, wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyarta ko magana bata iya yi sai zazzare idanu ta ke, akan kunnanta suka tattauna game da yadda zasu cire zuciyarta, gabanta ya shiga faɗuwa ta rasa ya zata yi, gashi babu Unaisah a kusa, a cikin zuciyarta ta dinga karanto La'ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin. Bayan da Musa ya fuce daga ɗakin, Dr. Mark ya nufe ta ta dinga masa magiya tana roƙonsa ya taimaka mata kar ya kashe ta, ya barta da ranta, tana son ganin mommynta, tana son ta ga daddynta, tana son ta ga ƴar uwarta Unaisah..." Unexpected ta ji ya ce, "Ki yi shiru, ba kashe ki zan yi ba, taimakon ki zan yi amma karki kuskura ki fitar da sautin da zaisa ya gane wani abu.." Zare idanu ta yi a ruɗe take kallon shi cike da mamaki. Nan take ya 6alle sarkokin jikinta da sihirinsa, ya sungumeta akan kafaɗar shi ya nufi kofar shiga pharmacy da ita, anan ya sauketa ya ce kar ta kuskura ta fito, duk abun da zata ji ta yi shiru ta jira shi zai nemo mata yar uwarta, farin ciki ne ya lullu6eta duk da akwai fargaba a tare da ita, cikin sauri ta samu guri ta zauna tana jiran shi, akan idanunta ya 6ace ma ganin ta. Wannan zuciyar da Mark ya ba Musa a cikin kwalba, ta giant ce da ya kashe batare da sanin shi ba. ~(Kun ji yadda akai Batool ta ku6uta)~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. )~_____🌹______🌹______🌹______🌹_______🌹~ Gaba ɗaya kowani ahali daga cikin su haka suka wuni da fargaban a wani hali yaran nan suke a ciki, tun jiya da dare ba ci ba sha, ruwan tea din da suka sha lokacin da suka yi nafilfili ne kaɗai ya rage a cikin su.. Abu kamar wasa har dare ya yi, babu labari dangane da su. Hajiya layla da Alhaji Ubaid da mare ce suka bar gidan Owais sakamakon kiran da Hajiya Sarah take tayi masu game da rashin dawowarsu gida, kuma sun bar su cikin fargaba. Kusan gaba ɗayansu suna a falo cikin damuwa, kowa ka kalli fuskarshi babu annuri bacci su ke ji amma damuwa ta hana baccin ya ɗauke su, sun kasa sun tsare suna jiran dawowar ƴa'yan su, Sheikh imam ne ke tausarsu da nasiha mai ratsa zuciya, Taj ne kadai baya a falo bai jima da fita ba, ya je ya kwantar da baby Junaid da ya yi bacci, Benazir da Aisha da Anila Suna a zazzaune kan Sofas sun zabga tagumi suna sauraron Sheikh Imam, yayin da Dr shureim yake a gefen shi, shi kanshi Imam malik din ba ƙoshin lafiya ne da shi ba, sosai yake jin ɗacin abun da Musa ya yi mashi a ranshi, ya yi masa abun da har abada ba zai manta da baƙin cikin nan ba, amma ya ɗauki dangana, kuma baya son rauninsa yasa suma su shiga damuwa ko dan Saboda alƙawarin da ya ɗaukarwa Aisharsa. *TAJ🌹* Yana a zaune gefen gadonshi. Idanunshi akan baby Junaid dake ta sharar bacci, bakomai ne ya fado masa aran shi ba face wasu maganganun da suka ta6a yi da Uzair, Allah sarki ba rabon Uzair yaga gudan jininsa.. Tunawa ya yi da lokacin da Unaisah take yar jinjirarta, murmushi ya yi, yayin da hawaye suka cicciko idanunshi, baya jin zai iya rayuwa batare da ƴar shi Unaisah ba. Shafa fuskar Junaid ya yi da tafin hannunsa, bai aune ba ya ji ya ka6e masa hannu cikin magagin bacci ya soma yin sambatu yana fadin, "Ni ka daina kallona, duk ka takura ni, ka tashi ka tafi tun da ka kwantar da ni." baisan sa'adda ya yi dariya ba. Ashe idanunshi buɗe suke, sun yi ja sai cika yake yana batsewa. "Baby Junaid, Ni ne fa? Daddy Taj." Zum6ura masa pink lips dinsa ya yi, "Ni ba wani nan, kawai ma ka takura ni, Allah saina faɗe mata abun da kake mini.." ya faɗa yana kokarin miƙewa zaune da sauri Taj ya mayar da shi ya kwantar, ya janyo duvet ya lullu6e shi dukan shi. "Pls ka yi hakuri ka yi bacci, ba zan ƙara damun ka ba" "Toh ka tashi ka tafi." Murmushi ya yi tare da miƙewa cikin sanɗa ya fuce daga dakin. Leƙowa Junaid ya yi daga cikin bargo, ganin babu Taj yasa shi mayar da kansa ciki ya ci gaba da yin baccinsa. Unexpected wayar Taj ta soma ruri, a lokacin yana gab da zai shiga falo, cikin sauri ya zaro wayar, ko da ganin sunan my in-law ya bayyana yasa shi saurin picking yatsunsa har kerma suke saboda zumuɗin ya ji ya ake ciki, duk da yana fargaban me zai ji daga gare sa. "In-law, Guess what? Muryar Chief ce ta katse shi. Ɗan zaro idanunsa ya yi cikin rudu ya ce, "Chief, bangane me ka ke nufi ba? Kun samo su um?" Sautin dariyar Chief Owais ya jiyo, "Ka fara yin sujudusshukr kafin in sanar da kai." Cikin sauri ya fuskanci alkibla ya yi sujjada, kafin ya miƙe yana tambayar shi meya faru?" Nan take Chief ya zayyana mashi komai da ya faru a gidan Kurkukun kaddara! Ya Ilahi ji ya yi kamar a mafarki. Ya ƙara da cewa, "Yanzu haka Elders suna a CSH ana yi masu treatment saboda raunukan da suka ji, Unaisah da Batool kuma suna a cikin asibitin Headquarter din mu, lafiyarsu kalou, amma ana ƙara bincika lafiyarsu, saboda kwakwalwar Unaisah ta ɗan ta6u sakamakon razanar da ta yi..." Bai ƙare sauraran Chief Owais ba ya arta a guje ya nufi main door zai fuce. Gaba daya suka bi shi da kallo, muryar Benazir ce ta katse shi, "Taj, meya faru? Ina zaka je?" Ya juyo fuskarsa ɗauke da murmushin farin ciki ya ce, "Sun dawo. Sus.. Suna a headquarter ɗin mu! Unaisah da Batool..." kusan a tare suka miƙe tsaye tare da bin bayan shi, tsabar ƙaguwa kamar zasu bangaje juna. Sheikh Imam da Aisha motar Dr Shureim suka shiga., Benazir da Anila suka shiga motar Taj, tare da Motocin Securities gaba da bayan nasu motocin. A lokaci ɗaya motocin suka fuce daga villa din sai baza gudu suke yi saman titi kamar zasu tashi sama.. *ISOD HEADQUARTER🔥* Lokacin da motocin su suka ƙaraso Headquarter basu sha wahalar shiga ba, suna yin parking dinsu, cikin sauri suka fito daga ciki, Taj da Benazir ne a gaba, Ummi da Shureim suna a biye da bayansu, yayin da Sheikh Imam da Anila suke biye da su. Isod Soldiers din dake zarya a tsakar headquarter din sai kallonsu suke yi, sai dai kwata kwata babu alamun sun ma san da zaman su saboda hankalinsu na akan abun da ke gaban su. Da yake sun san da zuwansu kuma ga Taj a tare da su hakan yasa duk inda suka bi a hanzarce agents din dake a ciki suke darewa su basu hanya don su wuce. Lokacin da suka karya kwanar da zata sada su da inda suke unexpected suka soma jiyo ihun Unaisah tana faɗin, "Acid na watsa mashi akan fuska! Na ƙona masa fuska, ya mutu! Bazai ƙyale ni ba, gayanan ina ganin shi, fatalwarsa ce, kashe ni zai yi..." Tsantsar farin ciki da rudani ne akan fuskokinsu, cikin sauri suka faɗa Private room din, Doc suka gani a bakin gadon da take, Chief Owais yana a zaune daga gefen gadon ya rurruƙeta, sai ihu take tana firgita kamar mai aljanu. "Babyna..." Benazir ce ta faɗa, da gudu ta nufi gadon, Chief Owais ya miƙe ya bata guri, zama ta yi tare da janyota ta rungumeta akan kirjinta, batasan sa'adda ta saki kukan farin ciki ba. Ta dinga shafa bayanta tana fadin, "Unaisah ki daina kuka, mommyki tana a tare da ke! Ina fata basu cutar min da ke ba.." Jajayen idanunta ta ɗaura akan benazir, tana magana yawu na fita ta bakinta ga majina dake zalalowa ta hancin ta, "Acid na watsa mashi a saman fuskar shi, na ƙona shi, ina ganin shi da idanuna yana a cikin ɗakin nan ya ce sai ya kashe ni, gashi nan zai ta6a ni...!" da karfi ta faɗa a rikice, shatun jijiyoyin wuyanta sun fito rudu rudu. Ƙanƙameta Benazir ta yi kamar zata mayar da ita cikin cikinta.. Babu wanda bai tausaya mata ba! "A ina aka gan su? Ina Batool? Ina Musan? Bai cutar da su ba? Meke damun Unaisah ne?" Chief suke ma tambayoyin, Shureim sai baza idanunshi ya ke yi burinshi ya ga Batool dinsa haka itama Ummi ta kasa samun sukuni. "Pls, ku kwantar da hankalinku, ba a cutar da su ba, Unaisah ta yi faɗa da Musa harta yi nasarar watsa mashi acid a saman fuskarshi, shiyasa ta razana, kamar gizau ya ke yi mata tun ɗazu muke ta kokarin mu shawo kanta mun kasa, ga docs nan ta ƙi bari su duba ta, kowa ya kawo hannu zai ta6a ta sai ta fashe da ihu tana faɗin gayanan zai kashe ta.." Tsantsar mamaki ne da rudani akan fuskokinsu, akwai tambayoyi da dama da suke son yi mashi sai dai sun lura ba a cikin nutsuwar shi ya ke ba. "Ina Batool? Itama hada ita kuka dawo?" Dr Shureim ne ya tambaya cike da damuwa.. "Harda ita muka dawo, amma sai dai ku yi haƙuri..." Gaban su ne ya fadi, cikin rawar murya Ummi ta ce, "Pls ba sai ka fada ba, in dai ba alkhairi bane ka yi shiru, zuciyata zata iya bugawa in mutu!" Fuskar Owais babu annuri ya ce, "Tun da baku buƙaci in fada ba ku biyo ni mu je ku gani da idanunku, amma pls komai zaku gani ku yi haƙuri." gaba daya sun sha jinin jikinsu. Bayan fitarsu daga ɗakin ya rage saura Unaisah dake rungume a kirjin mommynta, Taj yana a zaune kan kujerar dake fuskantar su, addu'oi suke ta tottofa mata akan ta. Doctor din da ya zo duba ta yana a tsaye yana jira su kammala shawo kanta don ya samu ya yi mata allura. A gaban dakin da take suka tsaitsaya cirko cirko, saboda zullumi da farbagan abun da zasu taras ya sa kowannan su yake jin tsoron ya shiga ciki. "Bismilla, mu shiga daga Ciki." Chief ne ya faɗa tare da bude masu ƙofar ɗakin. "Dan Allah sir, ka fara faɗa mana a wani hali take ciki? Ina jin tsoron na ga abun da zai yi silar mutuwa ta!" "Ummi, ke da kan ki kika ce inna san ba alkhairi bane kada na faɗa, why zaki canza magana, kawai ki shiga ciki." Yanayin yadda yayi mata magana da walwala akan fuskarsa kamar ba Chief Owais ba. Sheikh Imam ne kadai hankalinsa bai tashi ba saboda yasan Chief Owais ba zai ta6a bari su zo ganinta ba in har wani mummunan abun ya faru da ita.. Tura kofar sheikh Imam ya yi, ya shiga da bismillah a bakinsa, yana dira ƙafarsa ya hango ta a kwance saman gado ta yi ɗai ɗai tana ta sharar baccin ta. Wani irin annurin farin ciki ne ya lullu6esa da ƙarfi ya furta, "Alhamdulillah, ku shigo ku ga jikata da ranta da lafiyarta ba abun da ya sameta..." A hanzarce suka bankaɗo cikin dakin, Ummi da Shureim suna ɗaura idanunsu akanta, wani irin daɗine mai tattare da farin ciki ya cika zukatansu, kamar wadanda aka yi wa albishiri da gidan Aljanna, bakinsu ya ƙi rufuwa, idanunsu sun cicciko tab da kwalla. Kewaye gadon suka yi, jikin Ummi na 6ari ta zauna daga gefe, ba zata iya jira ta farka ba, tallabo kanta ta yi tare da rungumeta a ƙirjinta, batasan sa'adda kukan farin ciki ya 6alle mata ba, wallahi sai ta ji gaba daya kamar an yaye mata baƙin cikin da ke a cikin Zuciyarta. Cusa yatsun hannayenta ta yi a cikin gashin Batool ta na yamutsawa kamar tana yi mata susa ta ƙanƙameta, ta fara manna mata sumbata tun daga kan kuncinta har izuwa goshinta, kamar zata lashe ta, ta ma manta da sauran mutanan dake a ɗakin, kowan nan su murmushin farin ciki ne ɗauke akan fuskarshi, Dr Shureim sai washe baki ya ke yi, har sujudusshukr ya yi a dakin, lokacin da ya ɗago hawaye ne sharkaf akan kuncinsa, sai kallonsu ya ke yi kamar zai haɗiye su. Matsewar da Ummi ta yi mata ne yasa ta farka daga bacci, tunkan ta buɗe idanunta hancinta suka shakar mata ƙamshin turaren Aunty Umminta wanda koda yaushe in kana a kusa da ita sai ka ji shi a jikin ta. Cikin rawar murya ta shiga furta, "Aunty Ummi? Ke ce? Kece a kusa da ni? Aunty Ummi kamshin turarenki nake ji? Dan Allah in bacci nake yi kada ku farkar da ni, mommyna kawai nake so na kasance da ita har ƙarshen rayuwata, dan Allah kada ku bari ya raba ni da ita, ina so na rayu saboda ita, ina so na sanya ta farin ciki..." Sambatun da ta ke yi ba karamin karya musu zuciya yayi ba. Shiekh Imam a fakaice yake sharce ƙwalla, bakomai yake tunawa ba, fa ce ranar da ya kar6eta cikin tsumma daga hannun Aunty Laura, ya jinjina ta ya kira ta da sunan shegiya a gidansa, Ya Ilahi! Ya yi danasanin furta kalmar nan. Tallabo fuskarta Ummi ta yi da tafukan hannayenta, hawayen dake zarya kan kuncinta kaitsaye suke sauka akan kuncin Batool hakan ya tuna mata da ranar da ta haifeta irin hakan ta faru. "Batool, ki saka idanunki a cikin nawa, ni ce a tare da ke, ba abun da zai faru da ke, kuma babu wanda zai ƙara raba ni da ke, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba Batool, bazan ƙara tafiya na barki ba, ina sonki fiye da raina..." A hankali ta soma buɗe idanunta da suka yi mata nauyi saboda baccin da ta sha, har yanzu allurar da doc sukai mata bata sake ta ba, wata irin malalaciyar kasala take ji. Dakyar ta iya tsayar da idanunta a cikin na ummi. Cikin disasshiyar murya ta furta, "Aunty ummi na.. " jinjina mata kai ta yi da murmushi ta ce, "Daga yau ba sunana aunty ummi ba, ni ba gwaggonki bace, kuma ba yayyarki bace, Mahaifiyarki ce, ki kira ni da Mommy, ko kira ni da Ummi" gaba daya suka saka dariya cikin raha. Sam ta kasa kawar da idanunta daga kallon fuskarta, gani take kamar mafarki ne. Cike da so da ƙauna suke kallon juna. "Batool, ni baki ganni ba?" Dr shureim ne ya yi maganar cikin karyayyar murya, a hankali ta mayar da idanunta akan fuskar shi, lokaci ɗaya ta shiga tariyo maganganun Musa a cikin kunnanta, ta ji komai, ta ji irin baƙar izayar da mahaifinta ya sha saboda ita. Fashewa ta yi da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya hankalinsu ya tashi matuƙa, a tunaninsu wani abunne ya 6ata mata rai, lallashinta suka dinga yi, Dr Shureim har ya karaya, ya yi zaton saboda ta ji shine silar abun da ya faru da mommynta shiyasa ta ke kuka, kallon da take masa ya yi masa kama da kallon tsana. Jiki a sanyaye ya juya zai bar ɗakin batare da kowa ya lura ba, baisan idanunta a kan shi suke ba, ƙwacewa ta yi daga jikin Ummi, duk da rashin kwarin jikinta a haka ta duro daga kan gadon, suna ta tambayarta ina zata je, Anila na kokari ruƙota ta ka6e hannunta, da gudu ta bi bayan shi, yana gab da zai fuce ya ji ta rungume shi ta baya ta zagayo da hannayenta kan cikin shi, sosai ta ƙanƙameshi, wani sanyi ne ya ratsa zuciyar shi kamar kamar me. cikin shesshekar kuka ta furta, "Daddy, ina zaka tafi ka barni? Bakasan na fi bukatar ku akan komai ba? Daddy ina son ka wllh, kaine bugun zuciyata, jagoran rayuwata, wanda ya tsaya mini tsayin daka don ganin ban yi maraicin uwa a tare da ni ba, uban da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda ƴarsa ta rayu, idan babu kai babu ni daddy..." Yayin da take furta masa kalaman nan, ji yayi kamar anyi mashi albishir da gidan Aljanna, farin ciki kamar zai kashe shi, gaba daya mutanan dake a dakin saida suka yaba da iya tsara kalaminta, ta burge su, ta kuma sace zuciyar su, especially Sheikh Imam da Chief Owais sun kasa dauke idanunsu daga kallon su. A hankali ya ruƙo yatsun hannayenta, yayin da yake tunawa da ranar da ya fara ganinta tana jinjirarta, a lokacin da Ummi ta kawo mashi ita cikin tsummanta. Janyota ya yi ya dawo da ita ta gabanshi, ya sanya hannayenshi biyu ya yi hugging dinta tighly kamar zai mayar da ita cikinsa, a hankali yake shafa sumar kanta har izuwa saman kanta, so yake ya yi magana shesshekar kuka ta hana shi. "Kun ga yadda Allah ke ikonsa ko? An raba ku saboda zalunci, Allah kuma ya sake haɗaku ta yadda ku kanku baku ta6a tsammani ba, ribar hakuri da tawakkali kenan, mu runƙa hakuri da kowace kaddara ko jarabawa da ta same mu, duk abun da Allah ya yi a rayuwarmu mai kyau ne, amma sai mun yi hakuri zamu gane hakan, kawai mu yi hakuri mu ci gaba da addu'a, mu kuma yi masa biyayya kada mu sare ko mu butulce masa, mu dinga tunawa da ni'imomin da ya yi mana kafin jarabawarsa ta riske mu..." Anila ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi, hawaye sun ciko idanunta abun ya ta6a zuciyarta. "Zan iya cewa, yau ce rana ta huɗu da na yi farin ciki mara misaltuwa a rayuwata, ranar dana ga su Taj a raye, da ranar dana ga Aisha da Benazir da ransu da lafiyarsu, sai kuma yau da Allah ya nuna mini abun da ya fi komai faranta raina.." murmushi suka yi gaba ɗayansu. Miƙewa Aisha ta yi daga kan gadon ta je gaban Dr Shureim ta tsaya tana kallon su.. Ita shaida ce akan irin kaunar da yake ma Batool dinta. Da kyar ya iya furta, "Ki yi hakuri Batool, bada son raina komai ya faru ba, bansan na binne ki ba, bana a hayyacina, kuma bansan kina a raye ba, da wlh har raina zan iya badawa don in ceto rayuwarki.." Ɗagowa ta yi da fuskarta dake a jiƙe da hawaye, "Abba, zan roƙe ka alfarma ɗaya a duniyar nan." Cikin sauri ya ce, "Zan yi maki, komai kike so ki faɗi." Kowa ya nutsu yana jiran ya ji me zata ce. "Pls, mu manta da abun da ya wuce, bana ganin kowan nan ku da laifi, komai da ya faru na sani bayin ku bane, na ji komai da kunnena, idan kuna yin magana akan abun da ya faru a baya baku tunanin zai haifar min da damuwa?" Batool ba karamin kashe su ta yi da dadi ba, tun yanzu sun san wacece yar tasu, yarinya mai tawakkali, mai hankali da tunani jikar Imam Malik kenan, ɗiya ga Ustatha Aisha bintu Imam da d Dr.Shureim, lallai ta fito daga tushe mai daraja. "Na yi maki wannan alfarmar Batool, mun daina, ba zamu ƙara ba." Ya fada yana share mata hawayenta. Murmushi ta yi, "Nima yanzu ina da iyayen da zanyi alfahari da su, ina da gata, sannan daga yanzu za'a dinga kira na Batool Shureim kamar yadda ake kiran yar uwata da Unaisah Zaheer Tajudeen." gaba ɗaya suka sanya tafi. "Ina taya ku murna gaba ɗayan ku, Allah raya mana Batool dinmu Allah kuma ya kare mana ita." Anila ce ta fada tana nufar su, janyo batool ta yi ta rungumeta sosai. "Nima ina taya ku murnar ganin ƴar ku, kuma in sha Allah, ba za ku sake rabuwa da ita ba." Chief Owais ne ya faɗa cikin sanyin murya. Godiya suka yi ma shi, kafin ummi ta ja hannun Batool ta kaita gaban sheikh Imam malik, "Kin gane shi ko sai na yi maki bayani?" Murmushi ta yi, "Kakana ne, Baba Imam." Rungumeta ya yi a kirjinshi ya fara saka mata albarka da yi mata addu'o'i yana jin sonta da ƙaunarta na ratsa shi, ita ce jikar shi ta farko kuma ɗaya ƙwallin ƙwal daga gurin ƴar sa abun alfaharin sa. Allah kaɗai yasan ɗumbin farin cikin da Batool ta ji a yau, wallah baya misaltuwa. A hankali ta raba jikin ta daga na sheikh Imam Malik, Ummi ta ruƙo hannunta ta kuma ruƙo hannun sheikh Imam, ta ja su har gaban Chief Owais, ta yi ma Shureim da Anila alamar su matso kusa da su, duk yana a tsaye yana kallonsu ya harɗe hannayen shi kan ƙirjin shi ya rasa gane me zata yi. "Assalamu alaikum." Muryar Taj ce ta katse hanzarin ta, kusan a tare suka juya baya suna kallonsu yayin da suke shigowa, shi da Benazir ne sun saka Unaisah tsakiyar su, jikinta lullu6e da bargo kamar wadda sanyi ya kama. "Ku yi hakuri, kun ji mu shiru, Unaisah ta ƙi daina firgita, sai yanzu muka samu ta dawo daidai, tana ta neman ƴar uwarta..." murmushi kowan nan su ya saki, da sauri Batool ta nufeta suka rungume juna, kamar zasu koma mutun ɗaya, yau dai ta zama ranar tunawa a rayuwar su. (Ni boss hada ƴar ƙwallata 😥) "Sis kina lafiya? Meke damun ki? Ya cutar da ke ne um?" adabarbarce take tambayarta.. Da kyar ta iya buɗe baki muryarta ƙasa ƙasa ta ce, "Ba abun da ke damuna, lafiyana lou, bai yi mini komai, ina fata kema kina lafiya..." jinjina mata kai Batool ta yi, "Nima ina lafiya sister, na ji dadi babu abun da ya faru da mu, Allah ya kare mu, bai cimma manufarsa ba." Ta fada tana dan sauke ajiyar zuciya. "Sai dai ban iya tuna komai da ya faru ba." "Batool, tunawar baida amfani, tun da ba alkhairi bane, idan ma akwai abun da ya kamata ki ji zaki ji, amma ba yanzu ba.." Murmushi ta yi, "Na ji, amma kin yi min laifi, daga yanzu karki ƙara kira na Batool, ni ƴar uwarki ce, cousin dinki ce, kuma yayarki, sannan aminiyarki..." Gaba ɗaya suka sanya dariyar farin ciki, musamman iyayensu farin ciki ne tsantsa tare da su . "Kina nufin, ke ɗiyar Uncle ɗina ce Shureim? Jinin da ke yawo a jikina shine a jikin ki?" Ta tambaya kamar irin batasani ba.. Cike da jin dadi Batool ta jinjina mata kai, "Ba mamaki, shiyasa farko da kika fara ganina a gidan kurkukun kaddara kika manne min kamar ciki ɗaya muka fito ashe jinina ce ke." Dariya suka yi.. "Ina taya ki murna Batool, Aunty Ummi, Uncle Shureim kuma ina taya ku murna, kamar yadda Batool ta yi dacen iyaye nagari, kuma haka kun yi dacen ƴa ta gari, saboda Batool ta dabance, samun irinta zai yi wuya, ni ta yi min hallacin da bazan iya biyanta ba, saboda ta ja ni a jiki a lokacin da sauran yan uwanmu suke guduna, a lokacin da nake tsaka da maraicin rashin wani nawa a kusa da ni, a kuma lokacin da na tsinci kaina a baƙon guri mai rikitarwa, duk yadda zan misalta maku ba lallai ku fahimta ba.." ta fada tare da janyo Batool ta rungumeta. kukan farin ciki suka kama yi. gaba daya kowa dake a gurin saida ya zubda masu ƙwalla saboda sun ta6a zukatan su. Saida suka gama koke koken farin cikin nasu, daga bisani Ummi ta janyo hannayensu, ta kawo su gaban Chief Owais wanda komai dake faruwa a kan idanun shi, ta kuma ruƙo hannun Benazir ta ce ma Taj ya matso kusa da ita, gaba daya suka kewaye Chief Owais. "Bani da abun da zan iya saka maka da shi, bazan iya biyanka ba! illa iyaka in sanyaka a cikin addu'o'ina, Allah yasa silar kyautata mana da ka yi ya zama sanadin shigar ka Aljanna, Allah ya wanzar da farin ciki da lafiya mara yankewa a cikin rayuwarka, Allah ya yaye maka dukkan damuwarka, Allah ya lullu6eka da rahamominsa, Ya kare mana kai daga sharrin duk wani abun cutarwa da kai da ahalinka, Allah ya ci gaba da daukaku, Allah ya baku hakuri da juriyar cinye jarabawar da kuke fuskanta, Allah kuma ya baka mata tagari wadda zata zama cikamakon farin cikin rayuwarka..." Tun da ta fara yi masa addu'oin ya lumshe idanunsa yana ɗan jinjina kanshi, gaba ɗayansu suke amsawa da Ameen Ameen, Chief ya yaba da addu'oin ta sun faranta ran shi. "Abun da yasa na tara ku a gabansa, saboda ina so ku taya ni yi mashi godiya, saboda ba zan iya yi ni kadai ba." ta fada tana duban kowan nansu, aikuwa gaba daya suka haɗu suna yi mashi godiya da addu'o'i duk da ya nuna basai sunyi ba, ya ce su gode ma Allah shine abun godiya, suka ce sun yi wannan amma yabon gwani ya zama dole. Gaba ɗayan su suka fito daga headquarter din, suka nufi inda suka bar Motocin su, bayan kowan nan su ya shiga ciki, at same time motocin suka soma tafiya a hankali, har suka bar headquarter ɗin. "Baby, ina kika samu waɗannan kayan na jikin ki? Tun dazu nake ta so in yi magana." Ummi ce ta faɗa tana kallon Batool, da sauri ta dubi kayan, shirt ce fara, da coat din da aka daure mata qugunta da shi, daga gaban rigar an rubuta Dg. Zare idanu ta yi kafin ta yi magana Ummi ta riga ta cewa, "Kamar kayan Chief ne ko? Na ga sunan rank dinsa a jiki." "Bansan lokacin da ya sanya min rigar ba, bazan iya tunawa ba.." ta fada tana dan girgiza kan ta. Dr shureim da ke driving dinsu, a hankali yake satar kallon su ta mirror, sai faman sakin murmushi ya ke yi yana kallon family ɗinsa. "Wani kaya ne last a jikin ki?" "Overroll ce, irin ta jikin Unaisah, sai coat da muka ɗaura a sama, bansan ya akai na rasa kayana ba." Kwanto mata da kai Ummi tayi kan kafadarta, ta lumshe idanunta tana sauke a jiyar zuciya.. Wow 😍😂 _______________________Ex-Prisoners🔥🔥🔥🔥🔥🔥 "Naufal! ! Haris! Javed! Mubeen! Ku tashi na samo mana hanyar da zamu fita" can cikin bacci suka tsinkayi muryar Sajeed dake ta kiran sunayensu cikin muryar raɗa. Bubbuga kafafunsu ya yi, "Dalla ku tashi, idan ba haka ba zan tafi in barku." At same time suka farka tare da yaye bargunan su, idanunsu biji biji suke ganin shi, sai miƙa suke yi da hamma alamar bacci bai ishe su ba, a saman wata ƙatuwar mattress suke a kwance lallausar gaske, mai tudu kamar gado. Hasken dakin ya kunna hakan yasa suka samu damar ganin shi da kyau, yana a tsaye gaban katifar hannun shi ruƙe da nannaɗaɗɗiyar igiya mai kauri, zaro idanu waje suka yi a ruɗe har suna hada baki gurin furta, "Sajeed me zaka yi da igiya?" Harara ya watsa masu, "Bana ce maku ina ta nema mana hanyar da zamu fita ba? Ko baku so ku koma sashen Chief?" Haris da ya fi su hankali ya ce, "Sajeed kana da gajan hakuri, kuskure ne wannan mu yi gaban kanmu ba tare da izinin daddy Taj ko Chief ba! Ransu zai baci idan suka ji, tun da sun ce mu ƙara hakuri why ba zaka hakura ba?" Harara Sajeed Ya watsa mashi tare da tamke fuskarsa. Naufal ya ce, "Ni abun da bangane ba, ta wani kofa ne zamu fitan? Me kuma zamu yi da igiya?" "Haƙurina ya ƙare, ni bazan ci gaba da jira ba, wallahi babu wanda ya isa ya hanani in fita, na gaji na gaji, ku baku gaji bane da zama a kulle? Baku tunanin akwai wani abu da ya faru wanda ba aso mu sani shiyasa aka garƙame mu anan?" Kallon juna suka yi, kowan nan su da wannan tunanin a ranshi. "Idan nan zamu ci gaba da zama meyasa ba za a dawo da su Unaisah nan din ba? Me kuma yasa mu ba za a mayar damu can ba? Meye amfanin kulle mu?" "Sajeed, amma ai muna yin waya da su Unaisah ko? Kuma sun faɗa mana komai lafiya lou, sun je farmaki sun dawo lafiya." Javed ne ya fada fuskarsa a yamutse.. "Baku tunanin sun faɗa mana hakanne don su kwantar mana da hankali? Ku yi tunani mana! Wani abu yana faruwa! Har yanzu ban yarda Danish yana lafiya ba, kawai suna boye mana ne, ƙwara mu je mu gane ma idon mu." Kallon kallo suke jefawa junan su. Tunzura su ya dinga yi har saida ya shawo kansu suka amince zasu bishi, saukowa suka yi daga kan latifar, gaba dayansu pyjamas ne a jikin su, kowa da kalar nasa. Sajeed ne jagoran su wato Master Planner, yana a gaba suna a biye da bayan shi cikin sanɗa suke yin tafiya, kamar 6arayi duk don kar a kama su. Cikin muryar raɗa Naufal ya ce, "Mu kadai zamu tafi? Su parveen fa? Idan suka farka suka ga babu mu zasu shiga damuwa." "Ƙwara karmu tafi da su, kasan halin Jemimah tsiwarta kaɗai ta isa ta tona mana asiri, in aunty Danejo tasan me muke ƙullawa zata kira ne ta fada.." Javed ne ya fada. "Ku daina ɗaga murya, ku yi shiru." A cewar Sajeed. A hankali suke tafiya suna yan waige waige sun jera layi, sai da suka kusan ƙarasawa ga stairs unexpected suka ji muryar mutane a cikin kunnan su.. "Banza ki sha a hankali kada ki ƙware, matsalata dake kin cika haɗama, wlh zan tona mana asiri muna satar abinci uban kowa ya ji." "Wai ke ina ruwanki da ni, ba cewa ta yi mu ci komai muke so ba..." Gabansu ne ya faɗi kusan a tare suka kai dubansu gare su, suna a zaune kan matakalar benen da suke tunkara, su biyu ne, Praveen ta tasa plate din chicken pepper soup, da duka hannayenta biyu ta ke duma loma, bakinta duk maiƙon mai. Jemimah tana zaune a gefenta, saman cinyoyinta gwangwanin madara ne daga gani sabo ne ta fasa, ta buɗe shi sai sha take yi, duk ta yi buɗu buɗu da kumatunta, har saman gaban rigar baccin ta madararce ta 6are kamar farar kura. "Mun masu wayo sunata bacci, mu kuma kullum sai mun farka tsakar dare mun saci abinci, da safe aita neman wanda ya kwashe ragowar abinci, mu yi shiru da bakinmu, wai Aunty Danejo sai tace 6era ne batasan mune 6erayen ba.." Jemima ce ta fada. Parveen ta ce, "Ai ran nan ina jin ta tana tambayar waya sace naman miya, nasan kece munafuka." ƙyalƙyacewa suka yi da dariya, su kadai a tsakar dare ko tsoro basa ji. "Ya zamu yi? Haris ne ya tambaya. "Wallahi idan suka ganmu ba zasu bari mu fita ba," Naufal ne ya faɗa.. "Ku yi shiru, a hankali zamu bi ta ɗayan benan, kada ku yi wani motsi da zaisa su lura da mu!" Sajeed ne ya faɗa cikin raɗa.. Cikin sanɗa suka fara hawa stairs din, suna tafiya suna waiwayon su Parveen... Sai da ya rage saura Mubeen dake a bayansu yana gab da zai haura second floor tari ya kubce mashi. Aikuwa a rikice Parveen da Jemimah suka zabura tare da mikewa tsaye gaba ɗaya suka saki abun da ke hannunsu ya 6are ƙasa, kafin su kai idanunsu tuni Haris ya ja wuyan rigar Mubeen sun karya kwana. Kallon juna Jemimah da Parveen suka yi idanunsu azazzare.. "Jemimah kinji sautin tari?" Jinjina mata kai ta yi, "ƙwara mu koma ɗaki, ni tsoro ya kama ni, dama Aunty Danejo ta ta6a bamu labarin fatalwar dare dake zuwa ma mutun in bai yi bacci ba ta cinye kurwarshi..." A tsorace ta faɗa tana zare green eyes din ta. "Dallah ƙarya take maki, babu wani fatalwa, tatsuniya ba gaskiya bace ƙirƙirarran labari ne.." bata ƙare maganar ba idanunta suka sauka akan warin takalmin dake akan ɗayan stairs din gefen su. Cikin sauri ta nufi takalmin, Jamimah na gani ta gargaɗe ta akan kada ta ɗauka na ɗan aljani ne, ta yi banza da ita. Daukar takalmin tayi ta jujjuya shi nan take ta gane warin slippers din yan uwansu maza ne. "Wani ya wuce ta wurin nan, Jemimah ki jira ni, bari na je na leƙa." Ruƙe rigarta Jemimah ta yi"Ai wallahi ƙafata kafarki, Yo kawai ki barni fatalwa ta cinye kurwata." Dungurin goshinta Parveen ta yi, "Shashasha, mu je." Upstars suka hau, duk inda Parveen tayi Jemimah tana a biye da bayanta kamar bindi, har suka 6ullo ta hanyar da su Sajeed suka bi, suna ƙarasowa suka hango ƙatuwar glass window dake a buɗe, ta cikinta suka dira ta baya akan wani floor, anan suka hango igiyar da suka ƙulla jikin ƙarfen da ke a kewaye da gurin da tagar take. "Hakan na nufin su Sajeed sun fita!" Ta fada tana dan jinjina kanta, murmushin gefen fuska ta saki.. Ta soma kiciniyar kama igiyar don ta dira, ruƙo ƙafar wandonta Jemimah ta yi a tsorace ta ce, "Dan Allah kada ki tafi ki barni, bazan iya hawa ba." Harara Parveen ta watsa mata, "Ya zan yi dake? Karki kuskura ma ki ce zaki hau, faɗowa zaki yi kanki ya fashe ki mutu.." Kuka ta saka mata, bata saurareta ba ta buge hannunta, ta ruƙe igiyar ta bi jikinta, ko leƙenta Jemimah bata iya yi saboda gajartarta. Watsawa ta yi da gudu ta koma cikin gidan ta nufi dakin sauran yan uwan nasu. A lokacin suna a kwance kan mattress dinsu kusan su shida sun kudundune cikin duvet ɗinsu. Abun ka ga mai ƙarancin hankali tana shiga ta daka suka ta dira a samansu, aikuwa a firgice suka farka tare da yaye bargon, suna ganinta suka fasa ƙara saboda razanar da suka yi. Ganin yadda suka ruɗe ne yasa ta yi saurin cewa, "Ni ne fa Jemimah.." Ta faɗa tana goge garin madarar dake akan fuskarta, lokaci ɗaya suka sauke ajiyar zuciya. "Uban me ya kawo ki dakinmu?" "Kawai muna baccinmu kin wani zo kin tada mu! Me ma ya farkar dake a irin wannan lokacin.." Idanunta cike tab da ƙwalla ta ce, "Pravin ta fita, nayi nayi da ita ta tafi da ni ta ƙi." waro idanu waje suka yi cike da mamaki jin abun da ta ce, "Ina ta je?" "Ku zo in nuna maku, har takalmin su Mubeen muka tsinta suma sun fita, na je ɗakinsu ban gansu ba." Da shagwa6a ta ƙare maganar,.. Kusan a tare suka sauko daga kan katifar, in ka cire mutun ɗaya da bata farka ba, saboda nauyin bacci ne da ita sai sharar baccinta ta ke yi. Gaba Jemima ta yi suka bi bayanta, bayan da suka ƙarasa gaba ɗaya sun yi mamakin ganin igiyar da aka ɗaura. "Abun da za'ai, tun da mun samu hanyar fita, mu bi su kawai." A cewar Sarah. "Ɗaya bayan ɗaya zamu hau." "Ni fa wa zai goya ni?" Wani kallon rainin wayou su ka yi mata, "Ki koma ki kwanta, ba za ki iya hawa ba, zaki iya faɗuwa ki mutu." Fashewa ta yi da kuka, "Wlh saina tona maku asiri gurin aunty Danejo, tun da ba zaku hau da ni ba." Da jin hakan suka fara lallashinta, Hawwa ta ce, "Abun da za'ai yanzu, Jemimah ki je ki kira Azeeza da Deeja, su zo mu tafi, kada mu barsu Su kadai," Amsawa tayi da toh, sai bayan da ta tafi Sarah ta ce, "Meyasa zaki aike ta ta kira su?" "Saboda mu samu mu tafi, in ba haka ba ba zata ƙyale mu ba." Hannah ta ce,"Deeja bata da hankali, akwai matsala idan Jemimah ta gaya mata, Azeeza kuma bazata iya fitowa ba saboda tsoro." Hibba ta ce, "Yanzu ya zamu yi? Ga samu ga rashi, don wlh idan muka tafi risky ne su zo gurin nan," ta faɗa da damuwa.. Hanna ta ce, "Idan kuma muka dira muka je can, baku tunanin zamu ja ma kanmu wata matsalar?" "Yanzu me kuke nufi mu hakura mu koma?" Yasmin ce ta fada tana dubansu.. Rubina ta ce, "Kun manta nauyin baccin Deeja? Wlh ba zata farka ba ko Jemimah zata watsa mata ruwa ne a jikinta, ita kuma Azeeza tsoro gareta, ba zata iya hawa igiya ba, dole su haƙura da bin mu..." da jin wannan maganar ta Rubina nan fa suka samu kwarin gwiwar aiwatar da abun da ke ransu. Sarah ce ta fara hawan igiyar saida ta dira ƙasa, sannan Hawwa ta haura itama.. Ɗaya bayan daya suka dira gaba daya. Baiwar Allah Jemimah sun mata wayou, a gajiye ta koma dakin su ta je ta taso Deeja, ta dinga bubbuga kafadarta, cikin magagin bacci Deeja ta dinga zaginta, da ta saka naci aikuwa ta sanya ƙafa ta ingizata, gaba daya ta kundumo ƙasa daga kan katifar, cikin shesshekar kuka ta ce, "Allah Ya isa banza, don kin samu na zo tada ki, kuma wlh tafiya zamu yi mu barki, kuma saina rama." Ta faɗa tare da mikewa ta hau kan gadon, ta saita cinyar Deeja ta gartsa mata cizon da ya yi silar farkawarta ta fasa ƙara, kafin ta dawo hayyacin ta, Jemimah ta watsa a guje ta nufi ɗakin Danejo dake a upstairs, ta buɗe ƙofa ta shiga cike da zullumin kar Deeja ta biyo bayan ta. Cikin sanɗa take tafiya, ɗan hasken bedside lamps ne kadai ya haskaka dakin. Hawa ta yi kan gadon ta rarrafa ta nufi Azeeza dake a kwance gefen Danejo, saitin kunnanta takai bakinta, "Azeeza! Azeeza! Ki tashi ki ji wani abu." Takura mata ta yi da ƙyar ta farka, toshe mata baki Jemimah ta yi da tafinta, abun ka da matsoraciya ta zazzare eyes dinta kwata kwata bata iya ganin wanene ya toshe mata bakinta, saboda ƙarancin hasken ɗakin duk da ta samu lafiyar idanunta amma har yanzu in haske bai wadatu ba bata iya gani da kyau, sa6anin da ko da akwai haske sosai in dai dare ne bata gani. "Ni ce fa, Jemimah, ki taso mu tafi, su Parveen sun samu wata kofa a baya sun fuce daga gidan nan..." Ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Jemimah dake mata raɗa. Buge hannunta ta yi, "Ba inda zan je, ki kyale ni in ci gaba da yin baccina pls," "Dan Allah ki taso mu tafi, suna jiranmu, su suka ce in kira ki mu tafi." Da jin wannan maganar yasa ta miƙe, ruƙo hannunta Jemimah ta yi, ko mayafi babu akanta sai zallar sumar kanta da ta rufe bayanta. da taimakon Jemimah take iya ganin hanya, cikin sanɗa suka fuce daga ɗakin. ~________________________________🌹💋~ A bangaren su Owais, bayan da suka fito daga motocin su suka nufi main falo, fuskokin su ɗauke da murmushi. Officers suna ganin Unaisah da Batool suka fara sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah da ya dawo da su lafiya.. Chief yana jiyo muryar wani officer yana fadin, "Allah ya ku6utar da mu da ya dawo masa da hurul aininsa, don wlh ba raga mana zai yi ba, yadda yake ji da yaran nan kamar ransa akan su har kurkuku zai iya sawa a kulle mu." Murmushi Chief Owais ya yi tare da ɗan girgiza kan shi. Ummi da Shureim ne a gaba sun saka Batool a tsakiyarsu, yadda kasan wadanda suka ɗauko kwai a cokali sai tattalinta suke, ko tari ta yi sai sun tambayi is she okay. Haka Unaisah ma tana a tsakiyar Taj da Benazir, sun saka ta tsakiya, hannayensu tallabe da bayanta, Anila tana a gefen su. Sheikh Imam da Chief Owais suna a biye da bayan su. A hankali Ƙofar falon ta zuge, suna shiga Unexpected suka yi arba da Chefs kewaye da ƙofar, a tare suka hada baki gurin furta, "Muna yi maku barka da dawowa gida lafiya, Unaisah and Batool, mun yi murnar ganinku gaba ɗaya, shiyasa ma muka shirya maku dinner, Please ku biyo mu mu je..." Kallon juna suka yi bakin su a buɗe da mamaki akan fuskokin su. Basu yi ƙasa a gwiwa ba, suka bi bayan Chefs din, kaitsaye suka nufi garden din gidan. Suna shiga suka fara yin arba da sparkling light din dake haskaka arean gurin, shimfiɗa aka yi masu ta alfarma, wata hadaddiyar carpet mai faɗi da laushi, daga saman ta kayan dinner ne.. Gaba daya farin Ciki ya hana su furta kalma, sai dai suka dinga bin Chief da kallo saboda sun san shine ya shirya komai don ya faranta masu. "Chefs sun faɗa min tun safe baku ci komai ba, shiyasa na umarce su da su shirya maku dinner, tun da yanzu mun samu kwanciyar hankali, nasan akwai yunwa a tare da ku, Pls ku zauna ku ci..." sun nuna farin cikinsu sun kuma yi mashi godiya, a zagaye da dinner din suka zazzauna. Kowan nan su ya fara ɗaukar abunda ya ke son ci, a baki Ummi da Shureim suke ba Batool ta na ci, itama saita ɗebo ta sanya ma kowannansu a baki, sheikh Imam dake kallonsu ya rasa ina zaisa ranshi don farin ciki, Benazir ma a baki ta dinga ba Unaisah tana ci. "Sir, kai ba zaka ci bane?" Aneelerh ce ta tambaya tana duban Owais da ya yi tsaye yana ɗan daddana wayarsa. Da fara'a akan fuskarsa ya dago ya dubeta, kafin ya bata amsa wayarsa ta yi ringing, ganin kiran daga CSH ne yasa shi saurin ɗagawa yasan kira ne me muhimman ci. Ji suka yi ya furta, "Alhamdulillah, Alhamdulillah! Meyasa tun da suka farfaɗo baku kira kun sanar da ni bane?" "Okay, pls karku barshi ya taho, ku ruƙe min shi, nasan shi da kafiyar tsiya.." Ya fada yana dariya. Bayan ya yi rejecting call din ya dube su, "Kira ne daga Combat Support Hospital, Omar da Salsalbeel sun farfado daga coma, sun samu lafiya tun jiya da daddare.. Hada baki suka yi gurin furta Alhamdulillah.. Juyawa ya yi da sauri ya nufi hanyar komawa parking space, yana 6ullowa ta gaba ya hango Security Officers sunyi gungu guda suna magana baisan me suke tattaunawa ba. Nufar su yayi da ɗan saurin shi, suna ganin shi suka dare, a rude yake kallon yaran da yake ta ajiya a part ɗin Taj, daga kallon da yake yi masu yasa duk suka sha jinin jikin su. "Tayaya akai kuka buɗe kofar kuka fito?" Tambayar da ya fara jefa masu kenan, Da sauri suka nuna Sajeed da yatsan su, "Wallahi babu ruwanmu, Sajeed ne ya ƙulla mana igiya ta baya, da ita muka kama muka sauko ƙasa" Abun da ya faru bayan da mazan suka gudo, suna ƙarasowa gaban kofar shiga falon Chief security Officers suka ritsa da su, suka fara tambayarsu daga ina suke? Waya buɗe masu kofa suka fito. Suka yi shiru basu amsa masu ba, kwatsam suka jiyo takun tafiya suna juyawa suka hango ƴan matan dake 6ullowa ta bayan sashen Taj ɗayan bayan ɗaya, hankalin Officers din ya ɗan tashi a rude suke kallon su har suka ƙaraso, mazan na ganinsu suka ɗaura hannayensu a saman kansu alamar sun shiga uku, saboda rashin gaskiya sai suka rufe matan da faɗa akan don me za su biyo su. Aikuwa Parveen ta tona masu asirin ta yadda suka samu hanyar fitowa daga part din Taj, ran officers din ya 6aci suka rufe su da faɗa kamar za su buge su, duk sun tsoratar da su. Suna tsaka da korawa chief bayanin abun da ke faruwa suka jiyo ihu daga can nesa da su. Gaban kowan nan su ne ya fadi, a ruɗe Sarah ta ce, "Mun shiga Uku, Azeeza ce, wallahi ita ce, Kuma bata gani sosai idan dare ya yi, kada ta faɗo ta ji rauni..." bata ƙarashe maganar ba, da gudu suka dunguma izuwa bayan sashen, tunkan su isa suka hango Azeeza da ta maƙale a igiya jikinta nata kerma. Ga Jemimah ta biyo bayanta, ba dan Allah Ya sa sun ji ihun su sun zo ba da tuni sun salwanta saboda igiyar tana gab da kwancewa. Cikin zafin nama Chief Owais ya taimaka masu suka ƙarasa saukowa. Ransa a matukar bace ya rufe su da fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, abun da ya 6ata masa rai, igiyar da suka ƙulla yanzu da ta kwance sa'ilin da suke hawa ko ta subuce ma wanin su har rai zasu iya rasawa. Kuka suka kama yi mashi suna bashi hakuri, bai sauraresu ba, ya damƙi damtsen hannun Sajeed ya wurga ma Officers shi ya ce "Ku sanya min shi a boot din mota dina, ba abun da zai hana in hukunta ka, saboda ka yi yunkuri aikata kisan kai.." gaban Sajeed ne ya fadi rass! A tsorace ya dinga masa magiya yana fadin ya tuba bazai ƙara ba, ƴan uwansa ma suka dinga kuka suna rokon Chief ya yafe masa kada ya hukunta shi. Bai saurare su ba, akan idon su Officers suka ciccibi Sajeed dake ta turjewa, su kansu sun yi mamakin ƙarfin shi, da kyar suka ɗaga shi sama suka nufi parking space, ƴan uwanshi suka bisu a guje, kafin ma su karaso tuni Officers sun jefa shi cikin boot din motar Chief suka kulle shi. Bayin Allah ba yadda suka iya, dole suka haƙura, basu ta6a ganin fushin Chief irin na yau ba. Ko da suka matsa mashi akan ya yi hakuri ya yafe ma Sajeed, nuna su ya yi da yatsa ya ce duk wanda ya kuskura ya ƙara ko da tari ne sai ya sanya shi a boot an tafi da shi, da jin hakan nan fa kowan nan su ya shiga taitayin shi. Kafin tafiyar shi saida ya mayar da su part din Taj ya kuma kulle su. A saman floor suka zazzauna suna ta kuka, sautin koke koken da suke yi ne ya farkar da Danejo da Deeja, kusan a tare suka fito daga dakunansu suka nufo su. Hankalin Danejo ya tashi da ganin halin da suke a ciki, da damuwa akan fuskarta ta tambaye su meya faru? Meyasa suke kuka? Dakyar ta samu suka labarta mata abun da ya faru. Ta ce Allah shi ƙara in ma da ƙari ya kara, Chief ya yi daidai da ya tafi da Sajeed saboda baya jin magana, dama ta na lura da take takensa na son guduwa daga part din. Cikin shesshekar kuka su ka ce in bazata lallashe su ba, ta yi shiru ta barsu da abun da ke damunsu. Tana murmushi ta ce ai basu ga komai ba, su jira Chief ya gama hukunta Sajeed zai dawo kansu ne, saboda suma sun bada gudummuwa gurin aikata laifin. wani sabon kukan suka fashe da shi jin abun da ta ce. Deeja da ke sauraron su kuwa bushewa ta yi da dariya hada dafe cikin ta, tana fadin, "Allah ya ƙara maku, masu kunnan ƙashi, maganinku kenan. Ni dai Allah ya so babu ruwana, bansan anyi ba." Ta ƙarashe maganar tana yi masu gwalo, haushin ta duk ya cika su kamar su rufe ta da bugu. Daga bisani Danejo ta soma lallashin su ta ce su yi hakuri ita wasa ta ke yi masu tasan shima Sajeed din ba lallai ya hukunta shi ba. ~________________________________💫~ CSH (Combat Support Hospital) Katafaren Military Hospital ne masu jinyar majinyatan sojojin da suka samu rauni a gurin yaƙi, asibitin ba a cikin garin Abuja ya ke ba, a kusa da sansanin su yake. Yana da matuƙar tsaro, cikin shi da wajen shi soldiers ne ke tsaron shi, ga na'urorin dake sanya ido ga duk wani mai motsi ciki da wajen asibitin. Lokacin da Motar Chief Owais ta ƙaraso cikin asibitin, drivern dake driving nasa yana yin parking sojoji suka bude mashi motar ya fito, a hanzarce suka buga ƙafa tare da sarah ma shi. Zagayawa ya yi ta bayan motar ya buɗe boot dinta, lokacin da ya ɗaura idanunsa akan Sajeed da ya duƙunƙune a ciki kamar musaki saida ya ji tausayin shi ya kama shi, ganin yadda idanunsa suka yi jawur saboda kukan da ya sha. Ruƙo hannunsa ya yi tare da taimaka mashi ya fito daga motar, koda ya ga sojoji ta ko'ina suna sintiri ruke da bindigu a hannunsu sai ya kuma fashewa da wani kukan yana roƙon chief ya yafe masa kada ya hukunta shi bazai ƙara ba, ya taimaka ya maida sa gurin ƴan uwansa. Wani baƙin soja mummuna mara fara'a dake tsaye a gaban su ya ce, "Sir wannan ɗan shilan fa? Karairaya maka shi kake so mu yi ko tsallan kwadi zamu sanya shi?" Da jin wannan maganar, yasa jikin Sajeed ya kama kerma kamar mazari, a tsorace ya la6e bayan Chief Owais ya rurruƙesa yana roƙonsa, dariya sosai sojojin suka yi. Da yasan yadda Chief ke ƙaunarsu da bai ɗaga hankalinsa ba, ko sauro baison ya ta6a lafiyarsu balle shi ya hukunta su da hannun shi never. Ruko hannunsa ya yi suka nufi cikin asibitin yana ta zare idanunsa cike da zullumin Ina Chief Owais zai kai shi. Duk inda suka gifta military doctors din dake zarya tare da nurses with respect suke sara mashi tare da gaishe da su.. Sajeed dake ta ƴan kalle kalle idanunsa suka dinga hango masa patient din dake a ɗakunan da aka kwantar da su, ta glass din jikin ƙofofin yake hangosu, wasu ma sai yawon su suke yi a ciki, ƴan matasan mata da samari irin shi. A gaban wani medical room suka tsaya da tafiya, wani doc ne ya fito da fara'arsa ya sara ma chief shima ya sara masa bayan sun gaisa. D.r din har ya buɗe baki zai yi magana ya katse shi tare da kashe mashi ido ɗaya sannan ya nuna masa Sajeed. "Me laifi ne! Baya jin magana, ina so ka shiga da shi cikin dakin, ku cire masa kunnansa daya, sannan ku yanke harshen sa.." Sajeed ya fasa ƙara yana fadin, "Nashiga uku, wayyo Inna lillahi! Yaya Owais na tuba bazan kara ba, na roƙe ka dan Allah ka yi hakuri, ka yafe min, wlh mutuwa zan yi idan suka cire min harshe na.." a gigice ya zu6e kan gwiwowinsa ya rurruke kafafun Owais, ya dinga rokonsa yana kuka.. Murtuke fuska Owais ya yi, "Ku yi abun da na ce! Kar ku saurare shi." Rushewa ya yi da wani kukan, Docs din suka ce, "An gama sir," Da ya ga dagaske suke, jikinsa na bari ya mike tare da watsawa da gudu, sai dai kafin ya fuce, sojojin dake sintiri suka cafkoshi suka dawo da shi gaban Chief Owais, Docs din suka rurruke shi yana turjewa tare da waiwayen Owais da ya kawar da kansa gefe, docs din suka tura shi cikin dakin.. "Ku sake ni, ku kyale ni in tafi, wallahi kada ku ta6a ni.." Bai ƙarasa maganar ba, sakamakon abun da idanunsa suka nuna mashi wanda yake ganin kamar ba gaskiya ba ne.. Tana a kwance kan medical bed sanye da patient gown, sai sharar baccinta take yi, daga kan table din gefenta kayan marmarine a cikin plate data fara sha ta rage sauran. Murza idanunsa ya yi da hannayensa don ya ga ko gizau take yi mashi amma still ita ya gani. Gaba ɗaya ya ruɗe ya rasa gasgata abun da yake gani. "Kamar twin sister dina? Ni kaɗai nake ganinta! Ko mafarki ne..?" Fusge kanshi ya yi daga hannun docs din a rude ya nufi gadon ya ɗan zauna daga gefe ya ƙura idanunshi akan fuskarta. Jini ɗaya ba wasa ba, ko a mafarki ya ganta zai shaidata, duk min canzawar da za ta yi, saboda warinsa ce. A hankali ya ɗaura yatsunsa dake kerma saman fuskarta, ya ɗan shafa ta har izuwa kan curly hair ɗinta, komai nasu iri ɗaya, jinsi ne kaɗai ya bambanta su. Muryarsa na rawa ya furta, " GAB.. riella! Da gaske ke ce? Ke nake gani? Ba mafarki nake ba.?" Sambatunsa ne suka katse mata baccinta, a hankali ta buɗe idanunta, tana ɗaura su kanshi ta zabura ta miƙe zaune, wani irin tsantsar farin ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu. "My twin Bro! Kai ne da gaske nake gani a gabana? Ashe da rabon zamu gana da juna, na yi zaton bazan ƙara ganinka a rayuwana ba.." wata irin ruguma suka yi wa junansu kamar zasu koma mutun daya, a lokaci ɗaya suka fashe da kukan farin ciki. "Kasan irin uƙubar dana sha? Baka ta6a nemana ba, Ka manta da ni! Ba ka damu ina a raye kona mutu ba, ni kadai nake hauka na akan ka, ganin ka da na yi ya tabbatar min da ka riga ni barin kurkukun ƙaddara.." cikin kunci ta furta tana kallon shi. Duk sai ya ji ba dadi, cikin karyayyar murya ya ce, "Ba haka bane, kina a raina, na damu da ke, kamar yadda kike nema na nima haka nake neman ki, ki yi hakuri nasan ban kyauta maki ba, ba yadda zan yi ne..." Bai ƙare maganar ba ta daka mashi tsawa, "Ƙarya kake yi Gabriel, na tsani kaina dana damu da kai. Dama na sani na kashe kaina tuntuni, kalli yadda ka sauya kana cikin kwanciyar hankali, ni ina a can cikin azabar rayuwa, ban taba mantawa da kai ba, in ni ce wallahi bazan iya barin ka ba, koda zan rasa raina ne .." Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda bakin cikin da ta ji, jikinshi duk ya yi sanyi zuciyarshi ta karaya, yasan sister din nashi da zuciya, sai anyi da gaske zata sauko daga kan dokin zuciya.. "Dan Allah ki daina kuka zanyi maki bayani.." Bai ƙare maganar ba ta rufe shi da bugu kamar ta samu jaki, ta dunkule hannu ta shiga kai mashi naushi. saboda yasan bai kyauta mata ba yasa shi kasa dakatar da ita. Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da Docs din dake a ɗakin, tsantsar tausayin su ne ya kama su. "Gabriellah, ki daina bugunsa, i will explain to you.. " Owais ne ya faɗa, cikin shesshekar kuka ta ce, "Ka barni in ci ubansa, baisona banza shasha, wa nake da shi in bashi ba? Ni fa ƙanwarsa ce, twin sister ɗinsa, ciki ɗaya muka fito, don me zai barni cikin wahala ya tafi? Kunsan irin cin zarafin da aka yi min? Wannan mahaukaciyar karyar ta sa giant ya yi raping ɗina, ni kaɗai nasan azabar dana sha, mutuwa kadai ne ban yi ba..." gaba ɗaya ta labarta musu abun da ya faru da ita, Gabriel ya yi kukan bakin ciki kamar ransa zai fita. Docs din dake a dakin duk saida idanunsu suka ciko da ƙwalla saboda tausayinta. Chief Owais ya karaya da jin abun da ya faru da ita. Haɗuwa suka yi su duka suka dinga lallashinta har saida suka samu ta tsagaita da kuka. Chief Owais ya ce ta yi hakuri, sun san an cutar da rayuwarta amma ta sani Gabriel bada son ranshi ya tafi ya barta ba, bashi da mafita ne saboda ba a guri ɗaya suke ba, bayan haka sune silar da har suka san labarin kurkukun ƙaddara, da labarin ita kanta, saboda Sajeed shine ya dinga yi masa maganar ƴar uwarsa dake a kurkukun kaddara akan ya taimaka ya ɗaukko ma shi ita, bayan haka mahaukaciyar karyar da take magana akanta ta riga da ta mutu tun ranar da suka kai farmaki! Maganganun Chief Owais sun yi tasiri a cikin zuciyarta, jikinta ya yi sanyi har ta nemi yafiyar Gabriel akan faɗan da ta yi masa ya ce mata kada ta damu komai ta yi shi baiga laifinta ba, shi yakamata ya nemi yafiyarta, ta ce ta yafe masa amma kar ya ƙara tafiya ya barta, ya yi murmushi ya ce bazai ƙara maimaita wannan kuskuran ba, hugging din juna suka ƙara yi cike da farinciki. Daga bisani Sajeed ya dubi Chief Owais da hawaye akan fuskarsa ya ce shi baisan tayaya zai gode masa ba, yau ya shammace shi, ya yi mashi surprise din da bai ta6a zato ba, da farko ya yi zaton hukunta shi zai yi, ashe yar uwarsa zai nuna masa, ya ce, " Chief kai wani irin mutunne mai kyakkyawar zuciya? Na yi imanin zuciyarka ta daban ce, samun irin ka zai yi wuya a duniyar nan. Ka kyautata mana a rayuwa, ka yi mana abun da baza mu ta6a mantawa da kai ba, Allah ne kadai zai iya biyan ka..." Yayin da Sajeed ke furta masa kalmomin nan murmushi ne dauke akan fuskarsa. Itama Gabriella ta yi masa godiya, ya ce su godewa Allah, saboda shine ya kaddara zai zama silar taimakon su. Da sauri Sajeed ya sauko daga kan gadon ya yi sujjada don godiya ga Allah, da ya ga shiru Gabreilla bata sauko ta yi ba, ya miƙe ya ruko hannunta ya ce ta zo suyi sujjada su gode ma Allah, a rude ta ce, "Bansan me kake nufi ba, bazan yi sujjada ba, ni ba musulma bane, ko ka manta?". "Har kina da za6in addini a yanzu? baki ga wadanda suka taimake mu musulmai bane! Nima yanzu musulmi ne, Ki daina kira na Gabriel, bana so sunana Sajeed, kema na musuluntar dake, sunanki Sajeeda daga yanzu." maganar shi taba su nishadi. A nan take ya biya mata shahada ta musulunta ya kuma raɗa mata suna SAJEEDA, dama tuntuni ya ke ta tanadin sunan da zai sanya mata kalar na shi idan Allah ya haɗa su, bayan da ya samu sai ya adana sa a cikin zuciyarsa. Chief ya ce su jira shi zai shiga cikin asibitin gurin su Omar, suka amsa mashi da toh. Bayan fitarsu daga dakin ya rage saura su biyu. Sai dadi suke ji kamar yau suka fara sanin juna. Ta tambayeshi ya bata labarin ta yadda suka ku6uta daga kurkukun ƙaddara kuma a ina yake da zama? Bayan da ya labarta mata, ta ji dadi sosai har ta ƙosa ta ga sauran prisoners ɗin da yake a tare da su, sai ta ji dama tun farkon kai su kurkukun ba a raba masu ɗaki ba, saboda ta ji sun fi su samun gata ba kamar su ba da aka maida dabbobi. "Ina son nasan meya faru da khala, itama ta ku6uta ko bata ku6uta ba, na ga babu ita cikin wadanda sojoji suka ceto, ina son ta, itama tana sona, ba don ita ba da yanzu babu ni..." Ta fada idanunta cike da ƙwalla. "Ban so wani abu ya sameta, ina so ta rayu saboda in taimaka mata, ta faɗamin bata da kowa, itama cutar ta aka yi aka kaita kurkukun ƙaddara." Tambayar ta Sajeed ya yi wacece Khala? Nan take ta labarta masa irin taimakon da ta yi mata, duk da baisan wacece ita ba ya ji ta kwanta masa a rai, kuma yana son ya ganta saboda taimakon da ta yi ma yar uwarsa. Kwantar mata da hankali ya yi ya ce zai tambayi Chief game da ita don su ji in tana a raye. Bayan fitar Chief Owais daga ɗakin bai nufi ko'ina ba sai ɗakin da aka kwantar da amininsa, shigar sa dakin ya yi daidai da fitowar Omar daga toilet, yana tafiya daƙyar daƙyar, jikinsa sanye da kayan mara lafiya, kwata kwata bai lura da mutun a ɗakinsa ba, gadon sa ya nufa yana niyyar haurawa don ya kwanta unexpected muryar Owais ta katse shi, "Alhamdulillah, Ya Allah na gode maka da ka farfaɗomin da aminina! Na gode Ya Allah..." Cike da farin ciki Big Guy ya waiwayo tare da kallonsa. Bazai iya jira ya ƙaraso ba, da sauri ya nufesa suka rungume juna, irin sosai ɗin nan. "Na yi kewarka Omar, kullum da tunaninka nake kwana, ina ta zullumin kada na rasa aminina, bansan ina zan samu madadinka ba." Cikin shesshekar murya ya furta kamar zai fashe da kuka. Daɗi da farin ciki suka lullu6e Omar, in a cool voice ya ce, "Nima na yi kewarka bugun zuciyana, na so a ce kaine mutun na farko da idanuna suka fara yin tozali da shi a lokacin da na farfado amma sai na ga akasin hakan, baka ji yadda na ji ba, bansan meya faru ba tun bayan dana fita hayyacina a gidan kurkukun kaddara, amma da docs suka faɗa mini kana nan da ranka da lafiyarka sai na ji farin ciki ya cika ni, saboda ni damuwana akanka ne, ina son ka aminina." Ya faɗa yana ƙara hugging dinsa, daga gani sun yi kewar juna sosai, farin ciki duk ya cika su. "Omar, ina fata babu inda ke yi maka ciwo a yanzu? Ka ci abinci? Ka yi wanka?" Dariya ya yi, "Ka kwantar da hankalinka, doctor ya tabbatar min da na samu lafiya, raunin da na ji a brain ɗina ya warke.." Leƙa kansa Chief ya yi ya dudduba daidai inda aka yi masa ɗinki, ya ji daɗin ganin yadda gurin ya warke sosai. "Allah ya ƙara maka lafiya da tsawancin kwana aminina.." Da fara'arsa ya amsa masa da, "Ameen, kaima haka mutumina." "Am sorry Omar, na yi maka laifi, kwana biyu ban leƙo na duba ka ba, bani da kwanciyar hankali, abubuwa da dama sun faru masu daɗi da marasa daɗi..." Damuwa ce ta bayyana akan fuskar Big Guy, "Don Allah ka faɗa min meya faru? Me ake ciki? Dame dame ya faru bayan doguwar sumar da na yi? Ina Danish? Ina Salsabeel da Taj? Ina U.s armies? Ya labarin kurkukun kaddara da Elders da su na farka a raina? Har yanzu baku gano su wanene ba?" Kamar ɗan jarida ya tsare shi da tambayoyi. Girgiza kai Chief ya yi cike da takaici ya ce, "Omar, zan fada maka amma ba yanzu ba, na fi so lafiyarka ta inganta, bana so kaji abun da zai ɗaga maka hankali..." Bai kare maganar ba, Omar ya ce, "Kada ka damu da lafiyata na ji sauƙi, kawai ka fada min! In ba haka ba hankalina ba zai ta6a kwanciya ba wallahi.." Matsa mashi ya yi akan ya fada mashi saboda ya kagara da ya ji me ya faru.. Ba don ya so ba, cikin karyayyar murya ya fara zayyana masa abubuwan da suka faru, wa'iyazubullah! Lokaci ɗaya idanun Big Guy suka rikiɗa suka koma jajir, zufa ta fara tsattsafo masa saman fuskarsa, tsantsar tashin hankali da ruɗani ne akan fuskarsa, al'ajabi ya kama sa, damuwa da baƙin ciki suka mamaye zuciyarsa duk a lokaci ɗaya.. Cikin shesshekar murya ya furta, "Owais, jin komai nake kamar ba a gaske ba, kamar a mafarki ya faru, ina ma ace ban farfaɗo daga coma din nan ba, in mutu kawai!" Ya faɗa hawaye masu ɗumi suna sauka kan kuncinsa.. Wani irin kunci da baƙin ciki ne suka tarar masa a cikin zuciyarshi, idanunsa sun kaɗa jajir.. "Ban yi mamakin jin mahaifina ne Jan Wuya ba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya, amma wallahi, rantsuwar ɗan musulmi tun da labarin kurkukun kaddara ya riske mu na ji a raina mahaifina yana ɗaya daga cikin azzaluman da suke da sa hannu a cikin sa, na yi shiru ne saboda bani da hujjar da zan tabbatar da zargina akan shi shiyasa ban ta6a faɗa maka ba. Amma zuciyata ta karaya da jin cewa baba Obie shine Shugaban kurkukun ƙaddara! Hankalina ya tashi Owais, ban ta6a jin tsanar rayuwar duniya irin na yau ba. Owais meke damun su ne? Wani irin neman duniya ne wannan? Da zalunci da mugunta? Me suke nema ne wai? Wani irin tushewar basira ne haka? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!.." "Baba Obie bai kyauta ma rayuwarsa ba bai kuma kyauta maku ba, wallahi nafi jin zafin halin da kuka shiga akan wanda ni na shiga, saboda baba Ya zalunce ku, Ya dade Yana ha'intarku da fuska biyu, Owais, wai dan Allah da gaske ne? Ba mafarki ba? Wannan wata irin baƙar kaddara ce Allah ya jarabce mu da ita?" Ɗaura kansa ya yi akan kafadar Chief Owais ya fashe da kuka tamkar ana zare ransa. Cikin sanyin murya Owais ya ce,"Shiyasa ban so ka matsa min akan in fada maka ba Omar! Saboda nasan ba zaka ji dadi ba.." "Allah Ya isa tsakanina da shi, Allah ya wulaƙanta rayuwarsa tun a gidan duniya, Allah ya haɗa shi da dukkan musiba da fitintunun duniya, Allah ya saukar masa da cututtukan da zasu hana sa kwanciyar hankali, ko na minti ɗaya ban son ya ƙara jin dadin duniya. Lalacewar sa kawai nake son na gani, ban ta6a tsanar wani mutun kamar yadda na tsani mahaifina ba, shaiɗanin mutun azzalumi, fasiƙi mai kafurar zuciya, mutumin da tun da ƙuruciyata yake nema na, ni wai! Ɗansa na cikinsa! Shine Ya 6ata min rayuwata ya jefa ni a harkar safarar miyagun ƙwayoyinsa, ya hana rayuwata sukuni, ya ƙi bari mahaifiyata ta bani tarbiya, ya raba ni da danginsa, ya dinga sarrafa ni son ranshi. Owais ina da ciwon baƙin cikin da ya ƙunsa min, wallahi Owais ba don Allah ya ƙaddara zuwan ka cikin rayuwata ba, da yanzu nima ina ɗaya daga cikin giant din kurkukun kaddara, Allah ne ya tsare ni, wataƙil addu'ar mahaifiyata ce ke bibiyar rayuwa na, shiyasa bai yi nasara akaina ba..." Kasa ƙarasa maganar ya yi wani kalulun baƙin ciki mai tattare da radadi ya sarƙe muryarsa, ya kuma fashewa da kuka yana tari. Cikin sigar lallashi Owais ya daura tafukansa a saman bayansa a hankali yake dan bubbuga sa yana lallashinsa. "Omar, ka yi hakuri, ka yi hakuri, kuka bashi bane mafita ba, muma mun shiga mawuyacin hali, wanda na yi imanin dukkanmu in aka bincika lafiyarmu babu wanda za a samu batare da ciwon zuciya ko hawan jini ba, saboda depression din da ya kama mu, amma ba yadda muka iya, dole muka yi hakuri saboda bamu isa mu sauya abin da Allah ya kaddara faruwarsa a cikin rayuwar mu ba, bawa bai isa ya gujewa kaddararsa ba, iya cuta dai an cuce mu, an yi mana bakin ta6o, amma ba komai akwai Allah, su ke tunanin sun zalunce mu, wallahi bamu suka zalunta ba, kan su suka zalunta, sun kashe rayuwarsu da kansu, sun yi asarar duniyarsu da lahirarsu!" "Na fi jin tausayin ku Owais, ni bana jina a matsayin kowa, na rayu batare da dangina ba, bakowa ya sanni ba ko a family ɗinmu, ku kuwa duniya ce ta san ku, ina jiye mana halin da zamu shiga idan asiri ya fallasu mutane suka sani, bana so ahalinmu su muzanta a idon duniya, bana son laifin da bamu muka aikata ba ya shafe mu, mutane bakowa keda fahimta ba, wasu dama jiran mu suke yi, mun tara maƙiya da mahassada nasan da zarar sun ji abun da ke faruwa zasu yi farin cikin samun hanyar da zasu baƙanta mana rai don su ga raunin mu. Owais ya zamu yi? Meye mafita Owais um?" "Omar mafita ɗaya ce! Shine mu yi hakuri mu rungumi kaddara! Mu dogara ga Allah, mu miƙa lamuranmu gare shi, mu aje batun mutane gefe ɗaya, addu'a ita ce takobin da zamu kare kanmu daga dukkan me nemanmu da sharri." Gaba ɗaya komai da suke tattaunawa a cikin kunnan Salsabeel yana gani kuma yana sauraron su, tun da suka fara magana. Bawan Allah ashe ya ji labarin zuwan Chief a bakin docs din dake kula da su, shiyasa ya yanke shawarar zuwa ya gan shi ya ji shiru bai leƙo shi ba. Unfortunately ya iske shi a dakin Omar suna tattaunawa, kunnuwansa sun jiyo masa abun da ya karya masa zuciyarsa, yana daga tsaye bakin kofar ɗakin, hannunsa ɗaya ya ɗan karkace da ɗauri a jikin shi, fuskarsa ta jiƙe sharkaf da hawayenshi, so yake ya yi kuka sosai amma ya kasa, saboda bai son su san ya ji bai san ya zasu ɗauki abun ba, duk da shi bai zo da niyyar ya yi masu la6e ba. Ba zai iya jurewa ba, ya gaza yarda Danish babu shi a doron duniya, yaron da ya kwallafa rai akan son ganin ya haɗu da iyayensa ya kuma samu farin ciki mai ɗorewa a rayuwarsa, ga kuma tausayin Owais da Omar da ya kamasa, da farko ya yi farin cikin jin sun gano su wanene elders saboda shi kanshi ya ci burin ya gansu da ainihin suffarsu, amma da ya ji akwai kakan Owais da mahaifin Omar sai ya ji zuciyarsa ta karaya, jikinsa ya yi sanyi lakwas, damuwa da tashin hankali suka baƙunci zuciyarsa. Wlh ya ji ɗacin jin cewa dasa hannunsu a ciki sune ma giggan kurkukun, bayin Allah gwanin ban tausayi yake kallon su.. Jikin sa a sanyaye ya juya zai bar dakin, har ya kusa fucewa muryar Omar ta katse shi, "Salsabeel! Kai ma ka ji komai ko?" Baisan ya ganshi ba, lokacin da zai ɗago da kansa daga kan kafadar chief Owais ya hango shi. A hankali ya juyo ya fuskance su, "Ku yi hakuri, ba labe nake yi maku ba, na ji zuwan Chief shi na zo nema, sai kuma na taras da shi a dakin ka.." "Kana nufin baka ji komai da muke tattaunawa ba?" Umar ne ya tambaya fuskarsa a marairaice, "Ku yi hakuri, amma na ji komai da kuka tattauna, haƙiƙa zuciyata ta karaya, tsigar jikina ta tashi, na ji abun da ya ɗaga hankalina, ya kuma jefa ni a hali na damuwa, wallahi ban ta6a zaton za a samu Elders a family din da ya daga cikin ku ba, saboda kyawawan halayanku, amma idan na tuna faɗar Allah wannan bakomai bane..." Ya faɗa yana tafiya a hankali yake tunkarar su. "Na tausaya ma rayuwar ku, da ahalinku, bansan tayaya zan misalta maku ba, amma na razana sosai..." Daga gaban gadon ya tsaya tare da goya hannayensa akan ƙirjinsa.. "Sai yanzu na gane dalilin da ya sa lokacin da Danish ya rikiɗa ya zama maciji bai nufi ko'ina ba sai gidan kakanka.." A ruɗe suka dube shi. "Kiranye ne ya yi mashi saboda yana son ya mayar da shi gidan kurkukun ƙaddara, ni nasan ba za a rasa gurin da ya ke6ance a cikin ɗakinsa ba, wanda da zarar Danish ya faɗa ciki zai mayar da shi kurkukun ƙaddara ta ƙarfi ta tsiya..." Cike da takaici suka girgaza kawunansu. ɗakin yayi tsit na ɗan lokaci kowa da abun da yake saƙawa a zuciyarsa. Akwai tarin tambayoyin da suka cika zukatansu wadanda suke so su yi ma Owais sai dai damuwa ta hana su furta 💔 A daren ranar suka baro asibitin su dukan su, tare da twins bayan da docs suka tabbatar da lafiyarsu ta inganta ba abun da za su bukata.. Ba sai na bayyana maku irin farin cikin da su Unaisah suka yi ba na ganin Sajeed da twin sister din shi, duk a daren ranar Owais ya dawo da sauran yaran gidansa. Murna a gurinsu kamar waɗanda akaiwa albishir da gidan Aljanna... Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168 *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168. Idan muka koma bangaren jikokin Baba Obie mazauna ƙasar waje, da matayen ƴa'ƴansa da basu samu halartar family meeting ba, saboda uzururrukan da suka ruƙe su, kwata kwata basu da masaniya game da abun da ke faruwa da ahalinsu na Nigeria saboda ba a sanar da su ba, sai dai kowan nan su ya damu da rashin samun iyayen nasu a waya, sun saba akai akai suna kiran su su ji lafiyarsu, ko su yi fira a family groups din su amma wannan karon komai ya sauya ba kamar yadda suka saba ba, ko sun kira basa samun su, hakan yasa suka fara tunanin su dawo gida don su duba meke faruwa da ahalin nasu. Mazauna ƙasar wajen ne suka tattauna maganar a wani video call da suka yi tsakaninsu kuma suka yanke shawarar zuwa, batare da iyayensu sun sani ba, haka matayensu ma sun yi deciding biyo sahun mazajen su da suka ji shiru basu dawo ba kuma sun daina picking calls ɗin su. ~_____________________________💔✍️~ Sheikh Iman ne ya shawarce su da su kira sauran ahlin nasu su fada masu komai, tun kafin duniya ta ji, gudun halin da zasu shiga idan suka tsinci labarin a waje. Batare da 6ata lokaci ba suka ɗauki shawarar shi kowannansu ya kira matar shi da ya'yan shi ya umarce su da su bar komai da suke yi su zo gida zuwa gobe, sa'ilin da suke kiran su a waya yanayin muryoyinsu sun ɗaga masu hankali, hakan yasa wasu daga cikin su suka gaza hakura sai gobe su taho. A yammacin ranar flight din su gimbiya Her Excellency Jamila ya yi landing from Kaduna to Abuja, tare da Autanta Dr. Nawaz ta zo shima ba mazaunin ƙasar bane a Uk yake aikin likitancinsa, an ci sa a da safe ya dawo Nigeria sai kuma ga kiran da ya riske su na gaggawa hakan yasa bai yi ƙasa a gwiwa ba ya biyo mommynsa suka taho.... Washe garin ranar kiran sallar asubahin farko, business jet din da ya ɗauko su Zaki Mubarak Obinna ya yi landing a airport, tun jiya jirginsu ya taso su uku ne suka zo tare da Faryat da Ibad, bayan Zaki ya kira daddynsu ya sanar da shi sun ƙaraso, ba tare da 6ata lokaci ba ya tura da motocin escorts suka ɗauko su. Basu jima da ƙarasowa ba, sai ga kiran hajiya Her Excellency ya shigo wayar Deen bayan ya daga ta sanar da shi gasu a airport sun karaso, bai tsaya bata lokaci ba ya tura da motocin securities suka tafi dauko su, su biyu ne suka zo tare da last born ɗinta Dr. Yusrah. Wuraren goma sha biyu na safe, mai girma Sharafudeen tare da Iyalansa suka ƙaraso Estate din. Ba a fi ƴan mintuna da zuwansu ba, sai ga iyalan Senate Lateef sun shigo gidan baban suma.. A hankali ahalin suka fara taruwa a gidan Baba Obie, duk wanda ya zo da walwalarsa da zarar ya ga halin da ƴan gidan suke a ciki sai kaga yanayin fuskarsu ya sauya zuwa tsantsar damuwa da ruɗani, iyayensu mata suka dinga tambayar mazajensu meya faru da su? Meyasa suka rame? Meke faruwa ne babu walwala kan fuskokinsu, ga rashin kuzari, haka ƴa'ƴanma sun tsare su da tambayoyi kamar ƴan jarida, amsar da suke basu shine su jira Shiekh Imam ya ƙaraso. Hakan ba ƙaramin jefa su a rudani ya yi ba, hankalin Faryat ya ƙi kwanciya tun da ta je ɗakin mommynta ta ga babu ita babu dadynta, duk wanda ta tambaya ina suka je sai ya ce mata ta jira shiekh Imam ya ƙaraso zata ji komai a bakinsa, abun ya 6ata mata rai, dama bata so zuwa ƙasar ba Zaki ne ya taso ƙeyar su ita da Ibad bisa umarnin mahaifinsa. Around ƙarfe biyu agogon Nigeria ya buga, a daidai wannan lokacin Private jet din da ya ɗauko iyalan Hateem ya yi landing a airport from Dubai. Tun kafin ƙarasowar su, already prime minister ya tura da motocin canadian polices da zasu ɗauko su tunkafin ma flight din nasu yayi landing, kafin ka ce me gaba daya jikokin Obinna da surukansa sun hallara a gidan sa ƙwansu da kwarkwatar su, tun daga kan iyayensu har izuwa jikokinsa kaf ɗinsu, kowa da kowa, suna ta tambayar ina baba Obie da Hajiya Saratu ganin babu gifcinsu, nan ma ce masu akai su jira Shikeh Imam ya zo zai basu amsar tambayar su, lamarin ya ɗaure musu kai har ta kaiga ransu ya fara 6aci ganin sun ki faɗa musu meke faruwa, sun barsu cikin zullumi da fargaba, gaba ɗaya suka ƙagara da zuwan Sheikh Imam Malik...💔 Gaba ɗaya duk wani motsinsu akan idanun Baba Obie, haka zalika hayaniyar da suke ta yi duk yana jinsu, daga dakinsa yana kallon komai dake faruwa a gidan saƙo da lungu ko sauro ya gifta sai ya ganshi ta cikin laptop dinsa, farin cikinsa ragagge ne, a da in ya ga ahalinsa sun taru daɗi yake ji amma a yanzu kunya da fargaba ya ke ji saboda yasan tonan asiri za a yi masa kuma da zarar sun ji abun da yake aikatawa zasu tsane shi su shiga halin baƙin ciki da danasanin kasancewar su wani bangare nasa. Sir Mubarak ne ya kira shiekh Imam ya sanar da shi cewa kowa ya hallara na family dinsu suna son su bayyana masu komai, ya taimaka ya zo don ya yi masu nasiha gudun halin da zasu shiga, Sheikh Imam ya ce yanzu haka yana akan hanyar zuwa estate din nasu. Before ya ƙaraso gaba ɗayan su suka hallara a main falo, iyayen suna a zazzaune saman Sofas yayin da ƴan mata da samarin family din suka zazzauna kan rug, babu mai walwala akan fuskarsa.. Bayan ya iso ya shigo da sallama a bakinsa, cikin girmamawa suka gaishe da shi in ka cire Faryat da ta ɗage kai sama tana hura hanci, kamar bata gansa ba, ko arzikin mayafi babu a jikin ta, wata ƴar iskar short gown ce a jikinta ta marasa ɗa'a wadanda suka gaji rashin mutunci, ta kifa facing cap a saman kanta ta saki gashin ta a gadon baya, ga wani ɗan iskan shade data mannawa idanunta daga ka ganta dai ka ga ƴar duniya, a tsiya ce ta ke tauna gum a bakinta, sautin har fita ya ke yi ƙas ƙas, ba don iyayensu basa a cikin nutsuwarsu ba da tuni Sir Mubarak ya korata ta ɗauko mayafi, su twins da suka saka ta tsakiyar su, sun raku6e ko kaɗan ba annuri akan fuskarsu sai zallar damuwar halin da suka baro mommynsu a asibiti. A hankali Shikeh Imam yake ƙare musu kallon da ya sa duk suka sha jinin jikinsu ga waɗanda basu san meke faruwa ba. Ɗaura idanunsa ya yi akan iyalin Hateem dake a zaune kan doguwar sofa, sheikha Mujeedat tana a gefen Hateem, ta ɗauki wankan royal abaya ta alfarma, as usual ta saka chain mask akan fuskarta, kyawawan idanun nan nata suna akan Hateem da ya sadda kansa ƙasa yama kasa ɗagowa saboda zullumin abun da zai biyo baya idan suka ji abun da ya tara su, yana jin tsoron ya rasa gimbiyarsa fiye da yadda yake jin tsoron tozarcin da zasu fuskanta a gurin al'umma, saboda yasan koda ta haƙura zata ci gaba da zama da shi da baƙin tabon family dinsu ba lallai Royal Family ɗinta su yarda a zubar musu da mutunci ba, dama kafin auranta saida ya fuskanci ƙalubale ya sha wahala kafin aka bashi ita duk da tarin dukiyarsu saboda tsada ne da su, basu cika auren bare wanda ba jinin su ba, kuma ba royal family ba. Ruƙe hannunsa ta yi a cikin nata gam ta harɗe yatsunsu hakan yasa shi jin wata irin nutsuwa na shigar shi.. Gimbiyar izza Nazli da Yazrin suna a zaune daga gaban Sofa din da iyayensu suke akai, gaba ɗayansu royal gown ne a jikinsu sun yi rolling, tun da ta sadda kanta ƙasa bata ƙara ɗagowa ba saboda tsabar izza. Mai girma Sharafuddeen shima ya haɗa nasa matan guri guda, yana a tsakiyar su saman doguwar Sofa, su Hajiya Laura anyi zugudum ta zabga tagumi da alama ba kwanciyar hankali a tare da su, daga ita har kishiyar tata, Gimbiya Malika dama tuntuni suke zargin da akwai abunda ke faruwa a family din, tun kan abun da ya faru da hajiya Saratu, mijinta Pravin da Baba basu zo duba ta ba, kuma mijin nasu ya ƙi basu amsar tambayoyin su. Idan muka koma bangaren Iyalin His excellency Abdul Razak, Hajiya Muhibbat dake a zaune gefensa ta daura ƙafarfa ɗaya kan ɗaya, kowa ya shiga damuwa amma ita da alama ko a jikin ta, hasalima wayarta take daddanawa tana yi tana taunar gum a bakinta, gashi ta zuba uban ado kamar amarya.. Turai tafi kowa rashin sakewa, ta damu baiwar Allah, gabanta sai faɗuwa ya ke yi, tun da Sir Mubarak ya faɗa mata maganar meeting din da zasu yi, ran ta ya bata akan Hajjaty da Pravin ne amma da ta ga an kira kowa na family din sai ta ruɗe saboda ta fahimci ba abun da take hasashe bane, wannan yafi karfin laifin da su Hajjaty suka aikata. Sir Mubarak dake a gefen ta kwata kwata hankalinsa baya akan kowa ya lula duniyar tunanin makomar rayuwar family ɗin su. Ƴa'yansa suna a zaune gaban Sofas din da suke akai, Zaki da ya lumshe idanunsa kwata kwata bai so ya zo Nigeria ba, saboda baya son ma kusanta kanshi da abun da ya yi silar barin shi, sai gashi mahaifinsa ya dawo da shi. Ibad dake zaune gefensa na hagu abun ka ga mai kuruciya a kai, game yake bugawa a Ipad dinsa. Daga ɗayan bangaren Dr. Jazz ne ya langwa6e kansa jikin sofa, bawan Allah har rama ya yi cikin ƴan kwanakin nan saboda damuwar rashin ganin baba Obie baya picking calls dinsa, kullum wayarsa a kashe, ba kamar yadda suka saba ada ba, a rana sau uku yake kiransa kuma baya missing picking call nasa, dama tun lokacin da baba Mubarak ya faɗa masa baba ya yi tafiya bai yarda ba sai da ya zargi wani abu daban, ga kuma abun da ya faru da hajiya Saratu, yau da aka tara su ya shiga ruɗu sosai, gabansa sai faɗuwa yake yi. A bangaren Deen kuwa, shima yana zaune kan sofa tare da uwargidansa Jamila, batasan matsayar ta ba, kanta ya ƙulle, ta rasa gane meke shirin faruwa? Amma tana jin babu lafiya a family din.. Chief Owais yana a zaune dirshan kamar mai neman gafara, ba zaka ta6a gane halin da yake a ciki ba, gefe da gefensa Ziyad ne da Captain Yaseer sun saka shi a tsakiyar su, Dr Nadeem yana a gefen Captain, damuwa ce ƙarara akan fuskokin su, da ya ke su sun san komai. Filin dake a tsakiyar Sofas din wasu jikokinne zaune saman Carpet, Dr.Nawaz sai Yusra ƙanwar Yaseer tare da Hindu ƙanwar Owais, da kuma Zulaihat ƙanwar Ziyad, sun jera layi kowannan su ya yi zaman cin tuwo, babu wanda gabansa baya faɗuwa, tun ma kafin su ji me za a faɗa musu. Haka zalika Hajiya Madina tana a zaune gefen Senate Lateef, hannunta ruƙe cikin nashi sai tausar shi take yi ganin yadda ya yi sukuku kamar ba laka a jikin shi..💔 Sai da Shikeh Imam ya kammala kallace su tsaf kafin ya samu guri ya zauna kan Sofa din da ke fuskantar su, duk suka bi shi da ido gaba ɗaya sun ƙagara da son jin me zai ce.. "Ana ta ja mana rai, ni banga amfanin ɗauko mana malami ba, sai ka ce dai masu iskokai balle ace za'a mana rukiya.." faryart ce take gunaguni bata kai ga ƙarasawa ba, Zayn ya make bakinta da tafin hannunsa ya buga mata warning, harara ta watsa mashi da yake ba kunya ce ta ishe ta ba.. "Nifa na rasa ganewa, kaina ya kulle, meke faruwa ne? Meke damun kowa ne? Nifa bana son tashin hankali, kowa ka tambaya sai ya ce a jira sheikh a jira sheikh ga sheikh din ya zo amma ya yi shiru yana ta kallon mu kamar ya samu tashar bollywood..." Rai a ɗan bace Dr.Nawaz ya yi maganar shima da yake ba kunya ta ishe shi ba, tsagera ne.. "Karka kuskura ka ƙara magana!" A ɗan tsawace Nadeem ya faɗa, kallonsa ya yi tare da yamutsa fuskarsa batare da ya furta kalma ba. "Mijin mace ɗaya, yau ahalin namu ba lafiya, kamar masu zaman makoki, ni bansan meyasa ka matsamin akan in zo ba, ina tsaka da hidimar biki kasa na baro dangina, nayi nayi ka faɗamin meke damunka ka ƙiya, ga sheikh din ya ƙaraso ya wani tsare mutane da idanunsa kamar wasu masu laifi, wlh zan tafi ne idan na gaji da zama, kuma dai kasan bana zaman jin wa'azi ehe..." Her excellency Muhibbat ce ta fada tana kallon Abdul razak hada murguɗa ƙaramin bakin ta, tana karkaɗa ƙafarta.. Da yake yasan halin kayansa bai biye mata ba.. "Nifa Allah na gani, malaman sunnar nan ba burgeni suke yi ba, wlh da nasan tara mu za'a yi don a yi mana wa'azi ba abun da zai sa in wanko ƙafa in biyo mommy mu zo nan.." Cike da takaici Yusra ta yi maganar tana jifar Imam da harara a fakaice. In a cool voice Hindu ta ce, "Pls, Yusra, mu ƙara haƙuri, bai kamata kina fadin maganganun nan ba.." cuno baki ta yi ita ala dole an takura mata.. Gyaran muryar da sheikh Imam ya yi musu ne ya ja hankulansu ga dubansa, gaba daya suka tattara nutsuwarsu da hankalinsu a kansa, a hankali ya zauna kan Sofa din dake fuskantar kowannan su. "Innalhamdu lillahee, nahmaduhu wa nasta'eenuhu wa nastaghfiruhu, wa na'oodhu billaahi min shuroori anfusinaa wa min sayyiaati a'maalinaa. Wa man yahdillahu fala mudillilahu, wa man yudlil falaa haadiya lah "Alhumdulillah. Indeed, all praise is due to Allah....' ya ɗan dakata yana dubansu kafin ya ce, "Sallu Alal nabiyyul Kareem, Sallallahu Alaihi Wasallam..." atare suka haɗa baki gurin karasa ambaton Sallallahu Alaihi Wasallam kafin suka fara yin salatin annabi, Faryat dai ta ƙi tsayar da hankalinta guri guda, bayan sun kammala ya soma magana cikin harshen turanci saboda yana son kowan nan su ya ji me ya ke faɗa, "Nasan gaba ɗayan ku kun ƙagara ku ji dalilin da yasa aka umarce ku da ku baro komai da kuke yi ku zo nan, wataƙil an takura maku amma abu ne na gaggawa wanda da bukatar ku haɗu domin mu nemawa kanmu mafita a tare game da musibar da ta kunna kai a family din nan.. " Cike da tsantsar ruɗani suke jefawa junansu kallon kallon ga waɗanda basu san meya faru ba. Numfasawa sheikh Imam ya yi kafin ya daura da cewa, "Kafin mu fara sanar da ku, ina so in fara tunasar da ku da nasiha, saboda gudun halin da zaku shiga..." Maganganun sheikh Imam sun rikita lissafin kwakwalan su, sai zare idanunsu suke yi cike da fargaba. Tun da ya fara yi masu nasihar suka yi shiru suna sauraran shi, ko tari babu wanda ya yi a cikin su, da alama nasihar ta ratsa zukatansu, jikinsu ya yi sanyi lakwas saboda tsoron Allah da ya ƙara shigar su, duk da akwai tarin fargaba da zullumin abun da zai biyo bayan nasihar tashi don sun san dole akwai maƙasudin yin ta. "Jazakallahu Khairan Malam, mungode da nasiha, Allah ne kadai zai iya biyan ka.." Hajiya Madina ce ta yi maganar cikin sanyin murya, "Sai dai gaba daya hankalin mu ba a kwance ya ke ba, mun damu da ganin halin da mazajen mu suke a ciki, sannan babu Baba, Saratu ma bamu san ina take ba, munyi munyi su faɗa mana gaskiyar abun da ke faruwa sun ƙi sanar da mu, sun ce mu jira ka ƙaraso za mu ji komai a bakinka, don Allah malam ka faɗa mana, koma menene in wani ya rasu ne in kuma wani abun ne a fada mana, we're all muslim mun yi imani da kaddara mai kyau da mara kyau,.." Ta karasa maganar fuskarta a yamutse, gaba daya sauran suka tsoma bakinsu akan a fada musu meke faruwa. Shiru Sheikh Imam ya yi, shi kanshi yana jin fargaban sanar da su, saboda ya lura akwai masu ƙarancin tawakkali a cikin su. "Bismillah Owais, ka fada masu komai dake faruwa..." Ya faɗa idanunsa akan Chief Owais da ya raku6e kansa jikin Sofa, gaba daya suka mayar da dubansu gare shi. Tunani ya ke yi taya zai fara sanar da su? ya zasu dauki abun? Me zai biyo baya? Ba kaitsaye ya fara sanar da su ba, saboda harshen sa yayi rauni, ba zai iya ɗaga muryarsa ya yi magana mai tsayi ba. A hanakali ya zaro wayarsa daga cikin trouser pocket dinsa, ya mike cike da rashin kuzari a jikinshi ya ɗaura wayar saman c-table din dake a gaban Imam Malik, bayan ya kunna masu video din dake ɗauke da duk wani bayani game da gidan Kurkukun ƙaddara da miyagun ayyukan da ake aikatawa a cikin sa..." Ya ƙure musu volume yadda kowa zai ji dakyau, zama yayi dirshan gaban table ɗin tare da sadda kan shi ƙasa.. Da ya ke cikin harshen turanci ya yi audio din kowannansu yana sauraro kuma yana fahimtar me ake cewa, tun suna jin abun kamar shirin wasan kwaikwayo har suka fara ruɗewa da jin irin azabtarwar da ake yiwa matasan yaran da basu ji ba basu gani ba. Lokaci ɗaya suka ruɗe, suka fara tambayar Owais wai dagaske ne abun da suke sauraro yana faruwa ko dai ƙagaggen labari ne na almara? Gaba daya sun kasa yarda da gaske ne saboda aganinsu ba zai ta6a yiwuwa a rayuwar zahiri ba, don ko a tarihi basu ta6a jin makamancin labarin kurkukun ƙaddara ba, sai dai abun da ya ɗaure musu kai chief Owais ne ya ke yin magana a cikin audio din, sun gane voice dinsa ne. Hajiya Laura ta ce yaushe Owais ya zama ɗan jarida mai karanta hausa novel? Abun da daure kai.." Her excellency Muhibbat ta ce, "Ni na rasa ganewa, mu da muka zo don mu ji meke faruwa da mazajen mu why za'a kama bamu labarin ƙanzon kurege..." Lokacin da audio din ya yi nisa hankalin wasu daga cikin su ya tashi matuƙa, ƴan matasan cikinsu har sun fara zubda ƙwalla saboda yadda labarin ya ta6a zuciyar su har suna fadin wannan rashin imanin ya yi yawa, yaran nan ana zabtar da su wlh, saboda baƙin zalunci na wasu mutanan da babu Allah a ransu, kowa dai yana ta tofa albarkacin bakinsa, wadanda suka fi tausayi a cikin su irin su Jazz da Hindu da Zulaihat da Turai tuni sun fashe da kuka saboda tausayin yaran da ya kama su tsigar jikinsu har tashi take yi, musamman da aka zo kan labarin Unaizah da Majnoon wa'iyazubilla! Kuka sosai suke yi abun ya ta6a zuciyar su, hatta Gimbiya Mujeedat saida ta matse ƙwallarta, itama Hajiya malika zuciyarta ta yi rauni ta dinga fadin Owais ku yi mana bayani mana, wani darasi ne ake so mu ɗauka acikin labarin nan? Meyasa kuka kunna mana shi? Ko dan mu ƙara imani ne um?" Cikin sanyin murya Owais ya ce mommy ki yi hakuri ki ƙarasa sauraran shi, ta ce toh Owais Allah yasa mu ji Alkhairi, duk rashin tausayin su twins saida jikinsu ya yi sanyi lakwas dama zuciyarsu a raunace take duk sunyi sukuku da su a ransu suna ayyana in da gaske labarin kurkukun kaddara ke faruwa ya wadanda abun ya faru da su zasu ji? Dr. Nawaz da Faryart da Yusra ko gizau basu yi ba, tabbas labarin ya ta6a zuciyoyinsu sai dai ba kamar sauran ba, saboda su a tunaninsu bazai ta6a zama gaskiya ba, ƙagaggen labari ne kawai, jin abun suke yi wani iri. Ibad sarkin tsoro ga tausayi da ya addabe shi, tuni ya aje game din da yake bugawa, jikinsa sai kerma ya ke yi kamar mazari hakan yasa Sir Mubarak ya rungumo shi a jikin shi. A hankali Zaki ya zaro hanky daga aljihu ya soma share ƙwallar dake gangaro masa saman kuncin sa, zuciyarsa ta karaya. Shiekh Imam dake kallon fuskokinsu a hankali yake karantar yanayin su, tun anan ya fahimci masu rauni da marasa raunin cikin su.. Hatta Yazrin so take ta fashe da kuka ta kasa sai dai ta sadda kanta ƙasa, gimbiyar izza kuwa tun da ta fara sauraron Audio din bata motsa ba, dama ita haka take da wuya mutun ya iya karantar abun da ke a ranta ta yanayin fuskarta, saboda tsabar izza, Amma fa da alama ta razana da jin labarin kurkukun kaddara, duba da yadda yatsu ta suke ta kerma, cheeks dinta sun yi jawur saboda kaɗuwar da ta yi, haka zalika Hajiya Jamila tausayi yasa ta kasa jurewa, sai faman sharce ƙwalla take yi da yatsun ta. Cikin rauni na murya Jazz ya ce, "Tun da uwata ta haife ni a duniyar nan ban ta6a jin labari mai ban al'ajabi ba irin wannan! rashin imanin ya yi yawa, wasu mutane ba tsoron Allah, zalunci da mugunta kadai suka sa a gaba, na rasa gane me yasa idon wasu mutane ke rufewa akan neman duniyar da zamu mutu mu barta, basu tuna cewa suma fa halittar su aka yi kuma zasu mutu su koma ga Allah ne, amma dai yaran nan sun bani tausayi wlh, an azabtar da rayuwar su..." Bai ƙare maganar ba, cikin karyayyar murya Ziyad ya ce, "Wlh tun da na fara aikin jarida inje in ɗauko rahoto da sauransu, har kawo yau da nake ruƙe da matsayin director, ban taba jin makamancin wannan labarin da muke sauraro ba.." Ya faɗa kamar baisan komai ba. Kafin audio din ya kare gaba daya fuskokin wasu daga cikin su sun jiƙe sharkaf da hawaye.. Shiru suka yi yayin da zuciyoyinsu ke a cike fal da tunanin kurkukun kaddara da prisoners.. Kwatsam ba zato ba tsammani suka tsinkayi muryar Owais acikin kunnuwansu yana fadin, "Sheikh Imam ya yi maku nasiha don haka ku yi haƙuri da abun da zaku ji daga gare ni..." shiru ya ɗan yi kafin ya numfasa yana mai jin shakkar furtawa.. In a breaking voice ya ce, "Nasan kun yi tunanin labarin almara ne, to ba haka bane, da gaske ne ya faru, kuma bakowa bane shugaban KURKUKUN ƘADDARA FA CE KAKANMU OBINNA, PRISONERS DIN DA KU KA JI LABARINSU AKWAI JIKOKINSA A CIKIN SU...." Bai ƙare maganar ba, sakamakon wani abu da ya katse masa hanzarinsa, a ruɗe yake kallonsu ganin yadda iyayen su mata da grandchilds ɗin suka zabura gaba daya suka miƙe daga zaunan da suke, fuskokinsu ɗauke da tsantsar ruɗani, cikin 6acin rai hajiya Malika ta ce, "Owais kana hauka ne? Kasan me kake faɗa kuwa? Meke damunka ne??" A faɗace ta fada.. Hajiya Muhibbat ta ce, "Wannan wani irin zancen banza ne Owais? Ko ka fara shaye shaye ne? In ba haka ba ka rasa wa zaka hada da fasiƙan mutanan nan sai baba Obie? Uban da ya haifi Ubanka..!" Rai a 6ace ta faɗa kamar zata doke sa.. A firgice Jazz yake girgiza kanshi yana fadin wlh ba gaskiya bane Yaya Owais dan Allah ka daina fada, bazai ta6a yiwuwa ba, Baba ko ƙiyashi ba zai iya kashewa ba, balle rai, wlh ba haka bane ba gaskiya bane, ni nasan wanene Baba..." Kuka ya kama yi musu kamar ƙaramin yaro. Huyawa Hajiya Jamila ta yi akan iyayen su maza ta soma tambayar su,"Dama Owais ya samu ta6in hankali shine baku taba faɗa mana ba? Me yasa ba za ku kaishi asibiti likitan mahaukata ya duba shi ba uhum? Dan Allah ku yi magana mana! Kun yi shiru kuna jin kalamil ƙabihin da Owais ke faɗa akan kakansa...!" Ta faɗa cike da tashin hankali, Matsawa Hajiya Madina ta yi kusa da Owais, ta damki damtsen hannunshi ta fusgo shi har saida ya miƙe ta tasa ƙeyarsa gaban Sheikh Imam ta ce, "Don Allah ka yi masa rukiya, Owais ya haukace, wlh bayin kansa bane, Owais ba zai ta6a fadin maganar nan da hankalinsa ba, zai iya yiwuwa aljanu ne suka shige shi.." tsananin tausayinsu ne ya kama mazajensu da shi kanshi sheikh Imam ɗin da Chief Owais, wlh sun ƙara karya musu zuciya, ganin yadda suka yarda da surukinsu. Cikin fushi Malika ta nufi Owais ta fusgo shi kamar zata doke shi ta ce, "Owais ban ji dadin furucin da ka yi akan Baba ba, dan ubanka meke damunka ne? Baka da hankali? Maza ka zuƙunna ka ba kowa hakuri kuma ka je ka nemi yafiyarsa saboda ƙazafin da ka yi masa!" Runtse idanun shi ya yi gam, a hankali wasu zafafan hawaye suka fara shararowa kan kuncinsa, cikin shesshekar muryarsa mai rauni ya furta, "Sheikh bazan iya da su ba, ni dama nasan za a rina, ka taimaka ka yi musu bayanin da zasu fahimta, wlh ba ƙazafi na yi masa ba, shine Elder na gidan kurkukun ƙaddara kamar yadda ku ka ji. Zaku ya tuna yaran da nake ruƙo a gurina? Waɗanda na ce maku sojojin America ne suka tsince su a dajin Evil Forest kuma suka damƙa case din su a hannun hukumar mu? A ranar farewell dinner na Uncle Hateem na zo da su kuma nasan kowan nan ku ya gansu, to wadannan yaran suna daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, kuma akwai jininku a ciki..." nan fa ƙwaƙwalensu suka fara tariyo masu fuskokin yaran masu bala'en kama da wasu daga cikin su. still basu gasgata maganar shi ba, amma fa sun fara shan jinin jikinsu, maganarsa ta haifar musu da kokwanto.. "Idan har yanzu baku yarda ba zan iya nuna maku videos din yaran da muka kubutar..." wayarsa ya ɗauko ya kunna masu videos din su Unaisah a questioning room. Sun ɗan fara yarda amma still basu gasgata ba, saima cewa suka yi koda za su yarda labarin na gaske ne amma ba zai ta6a yiwuwa Baba ya aikata ba, saboda su sun yarda da shi sun kuma san halin shi. "Daddy ku yi musu bayani, watakil ku su yarda da ku..." Hajiya Laura ta ce karma su wahalar da kansu, ai wlh ko shi Obie din ya faɗa da bakinsa ba zasu yarda ba.. Cikin raunanniyar murya mai girma Sharafudeen ya basu labarin abun da ya faru a ranar da momma ta bayyana, gaba ɗaya ya fayyace musu komai da ya faru. Wlh Sunyi matuƙar razana, sun firgita sun shiga matsanancin ruɗani da tashin hankali, musamman da suka ji Momma tana a raye bata mutu ba, lamarin ya rikirkita tunaninsu har suna haɗa baki gurin tambayar tayaya hakan zai yiwu mutumin da ya mutu tsawon shekaru ashirin ya dawo a raye? Bayan su da idanunsu sun shaida mutuwarta, sai dai idan fatalwarta ce ta bayyana. Duk ta inda Owais ya taro su sai sun nemi abun da zasu fake da shi akan ba gaskiya bane, har mazajen su sunyi kokarin fahimtar da su akan gaskiyar zancen amma sun ƙi yarda. Sheikh imam ma ya yi kokarin fahimtar da su amma sun ƙi ma sauraron su. Cikin sanyin murya Hateem ya ce, "Banga laifin ku ba, mu ma lokacin da mu ka ji labarin, mun ƙaryata da farko, amma baba ya karya mana zuciya, saboda ya kasa kare kanshi kuma ya amsa laifinsa, yanzu haka baba yana a ɗaki ya kulle kansa tun ranar da asirin shi ya tonu..." Maganar Hateem ta ƙara ɗaga hankulansu. "Bayan haka cikin sunayen elders din da Momma ta faɗa ta kira sunan Pravin yana ɗaya daga cikin su, saboda rashin gaskiya Pravin ya gudu daga gidan nan tare da Hajjaty tun ranar da abun ya faru, kuma shine ya yi silar kwanciyar hajiya Saratu jinya, saboda ta kama su suna yunƙurin guduwa daga gidan nan, yanzu haka tana a kwance gadon asibiti ita da momma." Kamar a mafarki su twins su ke sauraron abunda Sir Mubarak ya ke faɗi, Bayin Allah a tare suka ɗaura hannayensu a saman kawunansu alamar sun shiga uku, kafin ka ce me tuni sautin koke kokensu ya cika wurin, Faryat ma batare da sun ankara ba ta yanke jiki ta faɗi a sume babu wanda ya lura saboda ɗimaucewar da suka yi. "Momma ba fatalwa bace, da gaske ita ce, bata mutu ba, tana a raye, Baba shi ya ƙulla makircin mutuwarta, lokacin da aka kawo gawarta da sunan sun yi accident din mota bamu ga fuskarta ba saboda ta ca6e da raunuka, ashe ba gawarta bace, Allah kaɗai yasan a ina baba ya samo gawar da ta yi kama da gawarta watakil ma rufa ido ya yi mana muka dinga ganin kamar ita ce..." Deen ne ya faɗa a raunace yana dubansu. Dafe kawunansu suka yi, kusan a tare suka shiga ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun daga iyaye mata har ƴa'yan nasu, cikin shesshekar Kuka Malika ta ce, "Wlh da gaske ne! Na yarda da maganarku, sai yanzu na gane wacece tsohuwar da aka kawo asibitinmu villa, dama tun da suka zo da ita nake ta yi mata kallon sani, amma saboda canzawar da ta yi shiyasa na kasa ganeta ashe momma ce bata mutu ba.." "La'haula walaquwwata Illa billah! Kai jama'a! In kuwa haka ne Baba ya gama da mu, ya yaudari yardar da muka yi masa, ya zalunce mu ya cuce mu, tsawon shekara nawa muna haihuwar yara su zo ba a raye ba, ashe sadaukar da su yake yi gidan matsafa, arzikinsa na jinin ƴa'ƴanmu ne jama'a, mun shiga ukun mu! Da wani ido zamu dubi duniya! Wlh baba ya karya mana zuciya, muna yi masa kallon mumini nagari ashe mutumin banza ne matsafi, mutuncinsa ya zube a idanunmu, wallahi ba zamu ƙyale sa ba, mu dai an cuce mu an goga mana mummunan tabo wlh..." Hajiya Muhibbat ce ta ke ta sambatun rashin ɗa'a "Wlh dana san haka, ba abun da zaisa in auri jininsa, yanzu gayanan mu da ba ƴa'yansa ba daga surukantaka an jaza mana musiba da bala'e, ana yi mana kallon mutane masu daraja saboda mun auri jinin dattijon arziki ashe dattijon banza ne tsohon najadu, wannan fasikanci har ina! Kawai an zubar mana da mutuncin mu wlh!" "Yadda muke alfahari da shi na kasancewar shi mutun nagari da ya haifa mana mazajen da muke alfahari da su, ashe ba mutumin kirki bane azzalumi ne, wlh sai Allah ya saka mana cin zalun da ya yi mana, ya ja mana abun kunya, ai wlh mutane suka ji wannan abun kunyar mun shiga uku! Shiga cikin jama'a sai ya gagare mu..." Kamar mahaukaciya sai 6a6atu take yi, babu wanda ya fahimci me take cewa saboda koke koken da ya cika falon, kuma ta yi maganganun ne cikin harshen shuwa. Maids din gidan dake leƙen su sun ji komai, bayin Allah sun yi kuka da idanunsu kamar ba gobe, su kansu Baba Obie ya karya musu zuciya, sun kuma ji tausayin halin da ya jefa ahalinsa, sai yanzu suka gane dalilin da yasa cikin kwanakin nan mutanan gidan suka shiga mawuyacin hali da kuma dalilin da yasa suke sa ake kawo masu abinci daga restaurant, ashe gujewa cin haram suke yi. Alƙalamina shima ya yi rauni, bazan iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyoyinsu sun karye, ga wata matsananciyar damuwa mai tattare da faɗuwar gaba da ta cika zukatansu, sun yi kuka kamar ransu zai fita, babu babba ba yaro, babu mai lallashin wani kowa ta kansa yake yi, duk da sanyin A.c din dake ratsa fatar su hakan bai hana su fitar da gumi ba, gaba ɗayan su babu wanda zazza6i bai kama sa ba, harda masu ciwon kai. Nan take suka fara yanke jiki suna faɗuwa ƙasa a sume, kusan mutun goma suka sume, Zaid da ya gama haukacewa cikin ɗimuwa ya nufi c-table ya ɗauki glass vase din dake akai ya ɗaga sama yana kokarin buga ma kansa, bai aune ba yaji an cafki hannunsa idanunsa jawur ya dubi Chief da ya ruke sa, fashewa ya yi da kuka yana fadin ya ƙyalesa ya kashe kanshi ko ya samu sassaucin raɗadin da zuciyar shi take yi mashi, mutuwa ya ke so ya yi wlh sai ya kashe kan shi. Chief baisan sa'adda ya dauke shi da mari ba saboda zafin kalmar kashe kan shi da ya furta aikuwa nan take ya faɗi a sume, hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba ya yi zaton zuciyarsa ce ta buga ya mutu, hankalinsa ya rabu gida biyu, kwata kwata kowa ya rikice, jikokin sai kokarin illata kansu suke yi, iyayensu ne ke ta kokarin hanasu aikatawa wlh duk sun haukace, daga sun taro wannan sai wannan ya 6alle gida ya rikice, hauka tuburan, Zayn da ƙunci ya mamaye shi babu wanda yasan ya zame jiki ya nufi kitchen ya ɗauko wuƙa yana kokarin dadarata akan wuyanshi, maids din gidan dake kallon komai dake faruwa aka samu wata ta ganshi aikuwa ta fasa ƙara tana fadin zayn zai kashe kanshi a kitchen, da gudu Sir Mubarak ya nufi kitchen din a lokacin har ya fara yanka gefen wuyan shi jini duk ya wanke shi, a zafafe Sir Mubarak ya fusge wuƙar ya jefar da ita, ya dinga kifa masa maruka har saida ya sumar da shi. Ya salam! sun yi tunanin mafita ne da suka fara sanar da su kafin su ji a bakin duniya gudun kar a ci zarafin su, ashe kiran nasu da suka yi a gida suka faɗa masu basu tsira ba, yaran nasu ne wasu ba tawakkali, suna da ƙarancin ilimin addini akai, ba kowan nan su bane zai iya ɗaukar ƙaddara, bayin Allah tun da suka taso rayuwarsu basu san wahala ba, basu san tashin hankali ba, basu san rashi ba, Allah ya basu komai, nasara da gatanci, wayewa ta yi masu yawa, rayuwarsu da dabi'unsu duk na turawa ne, dama irinsu basu cika ɗaukar ƙaddara ba, in mummunan abu ya faru da su sukan kamu da depression daga nan sai su kashe kan su toh abun da ke kokarin faruwa da su kenan. Ba don Allah ma yasa sunyi dabarar kiran su gida suka fara faɗa masu ba, watakil sai dai su ji labarin duk sun kashe kan su. Da abun ya ci ƙarfin su, a karshe sai dai suka kira docs, suka dinga rurruƙe su suna yi masu sedative injection tun da nasihar ta ƙi shigar su, basu ganewa depression ne na farat ɗaya ya kama su. Kowa ya fi jin tausayin ƴa'yan pravin, bayin Allahn nan suna a tsaka mai wuya, da ƙyar ma su dawo hayyacinsu batare da sun samu ta6in hankali ba. Al'amarin ya ɗaga hankalin Imam Malik da iyayen su, har nasiha aka yi musu don su dauki dangana, amma sai gashi suna abu kamar ma basu ji nasihar ba, ba irin kokarin da basu yi ba amma sun kasa tanƙwara wasu daga cikinsu, addu'o'i Sheikh Imam ya dinga karanto musu da kyar suka samu suka fara maimaita addu'o'in a cikin zukatansu, ta haka ne suka fara samun sassauci daga baƙin cikin da ke damun su, abun da ya fi karya zukatan iyayensu ganin tun yanzu sunata kokarin kashe kansu to ina ga idan aka fallasa sirrin mutane suka ji? Aka fara tsangwamar su! Akwai sauran Rina a kaba.. Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08093772168. ~________________________________🌹~ *HAJJATY💫* Bari mu koma baya muji meya faru da Hajjaty bayan su Sir Mubarak sun yi nasarar cafke su.. Tun bayan da ta suma, bata kara sanin inda kanta ya ke ba, lokacin da ta tashi farfaɗowa a wani ɗaki ta tsinci kanta a ƙwance saman gado, ga ƙarin ruwa sanye a hannunta, cikin disasshiyar murya take ambaton sunan Praveen! Sam ta manta da abun da ya faru. Da kyar ta tattara sauran karfin da ya rage mata ta samu ta dan motsa jikinta ta miƙe zaune, tana bin ko'ina da kallo, Tanata tunanin a ina take? Meye faru? Ina Praveen. Unexpected ta tsinkayi Muryar Sir Mubarak a cikin kunnanta. "Ina fata kin tashi lafiya? gabanta ne ya faɗi, a rude ta kalleshi, yana a tsaye bakin kofar dakin jikin shi sanye da kakinsa, nan take ta tuna da komai da ya faru. Cikin shesshekar murya ta ce,"Yaya Mubarak, dan Allah ku yafe mana laifin da mu ka yi maku, wallahi mu ba mazinata bane, da auran mu, munsan bamu kyauta ba da muka 6oye maku, amma ku yafe mana, mun tuba ba zamu ƙara ba, koda ba zaku maida mu cikin ku ba, ku yafe mana zamu tafi mu bar maku ƙasar gaba ɗaya amma dan Allah ku duba zumuncin dake a tsakanin mu, ko dan saboda iyalin Praveen ku taimaka ku ƙyale shi, kada ku kashe min ɗan uwana, shi kaɗai ne dangina da ya rage mini a duniya, na roƙe ka Ya Mubarak.." A hankali hawayen da suka taru cikin idanunta suka soma dira kan kuncin ta. A tsanake ya ke bin ta da kallo, kwata kwata babu alamun zai furta kalma saida ta ƙarashe maganartata, ya matso ya zauna kan kujerar dake a agaban gadon nata. "Baki bani amsa ta ba! Ya jikinki kin tashi lafiya?" Cikin shessheka ta ce, "Ban tashi lafiya ba, jikina babu sauƙi, in har ba ƙyale Praveen ku ka yi ba, ban ji daɗin yadda kuka buge shi ba, ban yi zaton haka daga gare ku ba." "Ina so nasan taƙaitaccen tarihin rayuwarki da ɗan uwanki Praveen." "Idan na fada maka za ku yafe mana?" ta yi narainare da idanunta. murmushi ya yi batare da ya furta mata kalma ba. "Ni ɗiyar uncle dinsa ce, Mun taso a gidan marayu, bamu da asali bamu da dangi, a bakin Praveen na ji labarin abun da ya faru da danginmu, saboda ni a lokacin yarinya ce ban mallaki hankalina ba, sanadin zuwa biki danginmu suka yi hatsarin jirgin ƙasa gobara ta kama, mutane da yawa suka rasa rayukansu, a lokacin Praveen shi ya goya ni a bayansa ya daka tsalle ya duro daga cikin jirgin, muka faɗi ƙasa duk mu ka ji munanan raunuka har muka fita hayyacin mu, ƴan sanda ne suka kai mu asibiti, bayan da muka samu lafiya, sun tambayi Praveen meya faru? Bayan daya fada masu, sun tausaya mana sun kuma jinjinama Praveen da ya iya ku6utar da mu daga cikin jirgin ƙasan. Bayan da muka samu lafiya suka mika mu gidan marayu. A rayuwana bani da gatan da ya wuce Praveen, shine uwata shine ubana, shine dangina, kuma shine komai nawa, bamu samun kulawa a gidan marayun, ba abinci mai kyau, ba sutura mai kyau, Idan gwammanati ko masu kuɗi suka kawo mana tallafi, bamu sani, masu kula da gidan marayun ne suke cinyewa sai su bamu kaɗan wanda ba zai ishe mu ba, Praveen shi yake fita ya yi aikin ƙarfi don ya sama mana abincin da zamu ci, da suturar da zamu sanya, idan bani da lafiya Pravin shi yake nemo kudin da zai kaini asibiti.." Sir Mubarak dake sauraronta zuciyarsa ta karaya tun kan ya ji ƙarashen labarin su. "Kwatsam muna zaman mu lafiya a gidan marayun, sai ga wani attajiri ya zo zai yi adopting, tun da ya ɗaura idanun shi akaina ya kwallafa rai ya ce ni yake so a bashi, masu kula damu su ka shawarce shi ya dauke mu mu biyu ni da ɗan uwana ya nuna kin amincewarsa. A lokacin Praveen baya kusa ya fita neman kudi. Haka suka bashi ni, na dinga kuka ina kiran sunan dan uwana Praveen. Basu saurare ni ba, suka nuna min fin ƙarfi gurin ɗaukana ina turjewa suka tura ni cikin motar mutumin. A dai dai lokacin da motar zata tafi sai ga Praveen ya dawo, ta window glass din motar mutumin na hango sa, na dinga kwala masa kira cikin sa'a ya hango ni, hankalinsa ya tashi ya bi bayan motar mu a guje. Tafiya muka yi mai tsayi, Praveen bai daina bin motar ba. Har muka ƙaraso gidan mutumin, ya fito daga mota ya ɗauke ni ya shiga dani ciki, na yi zaton ya yi adopting ɗina ne don ya raine ni tare da iyalinsa, ashe mutumin banza ne, ya dauke ni ne don biyan buƙatar kansa, a lokacin da yake kokarin keta min haddi, Praveen ya ritsa da shi, da ya ke yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, cikin fushi ya dauki kwalbar giyar da mutumin ya sha ya aje akan table, ya kwaɗa masa a saman kansa tare da caccaka masa a cikinsa har saida ya kashe shi. Hankalinshi ya tashi da ganin abun da ya aikata, cikin sauri ya goya ni a bayanshi, inata kuka ya gudu da ni, da kuɗin hannunsa ya yi amfani muka koma Delhi da zama, gudun kada asirin mu ya tonu a gane mu muka kashe shi. Bamu da kowa a Delhi, babu wurin kwana, sai dai mu ra6a a wani gidan abinci, anan muke kwana, idan gari ya waye masu kuɗi suka zo cin abinci, Praveen ya kan goge masu motocinsu su biya shi kudi, da waɗannan kuɗin ya ke yin amfani gurin biya mana buƙatunmu, wani lokacin har bara yake yi amma ni bai ta6a bari na fita nema mana kudi ba, shi ya ke fafatuka ni sai dai in ga ya siyo abinci mai rai da lafiya da suturar sanyawa, daga baya madam mai restaurant din ta ɗauke shi aiki, har ta bamu ɗakin da zamu dinga kwana a ciki." lokacin da ta ƙarasa masa labarin sai ta fashe da kuka. Sir Mubarak ya tausayama rayuwar su, musamman ita, saboda ya fahimci batasan komai da Praveen ya aikata ba. "Me kika sani game da auran shi da Saratu?" "Mun fara soyayya ni da shi tun yana da shekara ashirin, ni kuma ina da shekara goma sha biyu, soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu, amma saboda bamu da halin da zamu yi aure yasa muka jinkirta, to a lokacin da ya ƙara girma ya kai shekara ashirin da biyar, yana da abokai da manyan mutanan da yake yi ma aiki suna biyan shi kuɗi, akwai lokacin da ya zo min da maganar zasu tafi neman kudi shida abokansa, na saka rigima akan kar ya tafi ya bar ni, ya dinga lallashina, har ya samu na amince ya kai ni gurin madam me restaurant, ya bata kudi masu yawa ya ce ta kula masa da ni. Tun bayan da Praveen ya tafi ban ƙara jin ɗuriyar shi ba, kullum sai na yi kukan rashin shi, bana jin dadin rayuwata, da shi nake kwana da shi nake tashi, kullum cikin sa ran ganin shi na ke yi, madam din dake kula da ni ita ke lallashina idan na fara kukan rashin shi. Unexpected wata rana sai gashi ya kira madam a waya ya ce a bani mu yi magana, na yi murna da jin muryarshi ya lallashe ni ya ce in ƙara haƙuri zai dawo mini da abun mamaki, har ya ce zai dinga turo min kudi in sayi duk abunda nake so, tun daga ranar da ya kira kullum sai ya kira ni a wayarta mun gaisa, inta tambayar shi yaushe zai dawo na gaji da jiran shi, still hakurin ya ke bani Lokaci ɗaya rayuwata ta sauya tun da Praveen ya fara tura ma madam kudi, ta sanyani a makaranta, ta siya min surutu masu kyau, komai da zan buƙata siya min take yi, na dinga jin dadi Praveen ya yi kudi zamu daina shan wahala. Wallahi Yaya Mubarak ni bansan Praveen ya yi aure ba, bai fada min ba, ban ma san baya a ƙasar India ba, tsawon lokaci bai waiwayi Delhi ba. Ranar da ya dawo na yi murnar da bazata misaltuba, nayi mamakin sauyawar shi, yayi min kyaun da bai ta6a yi mini ba, ya zama ɗan gayu mai arziƙi, madam kanta tasha mamakin arzikinsa, har biyayya take masa sau da ƙafa saboda kudinshi. Koda na tambayesa tayaya akai ya samu arziƙi? Nan ya fara bani hakuri na ce masa meyasa zai bani hakuri kawai ya bani amsar tambayana. A nan yake faɗa min, ya yi mini ƙaryar sun je neman kudi shi da abokansa, gaskiyar magana ba haka bane, tafiyar da ya yi batare da abokansa ya yi ta ba, Allah ne ya haɗa shi da wani mutun mai arziƙi ɗan kasar Nigeria ya zo ganin ƴarsa ne dake karatun Medicine anan Delhi, shi kuma ya ta6a taimakon yarinyarsa har ta ji dadi ta nuna tana son su ƙulla abota, lokacin da baban yarinyar ya zo kawo mata ziyara saita haɗa shi da mahaifinta don su gaisa, bayan da suka gana da mahaifinta ya tambayesa su wanene danginsa? Yana karatu? Ko ya fara aiki? Sai ya faɗa masa baida kowa, har ya bashi labarinmu, mutumin ya tausaya masa ya ce zai taimakesa da aikin yi, da shi da ƴar uwarshi amma sai in har ya amince zai auri ƴarsa da ke son shi. Ya ce mini saboda baya son ya rasa damar da ya samu, kuma yana son rayuwar mu ta inganta, shiyasa ya amince ya bi mutumin da ƴarsa Nigeria, a can aka ɗaura musu aure. A lokacin da ya bani labarin na ji kishi mara misaltuwa, zuciyata ta karaya amma da ya lallasheni ya faɗamin baya sonta, ya aure ta ne saboda mu samu dangin da zamu jingina da su, mu kuma samu arzikin da zamu wadata kanmu, na ce na amince amma bana so ya yaudare ta, saboda na ji ya ce baya son ta ya aureta, kuma ya taimaki rayuwata da tashi, kada ya nemi kudi ta haramtacciyar hanya, kada ya aikata laifin da zai jefa rayuwarmu cikin wahala, komai zai yi a rayuwa kada ya zalunci wani, nasihar da nake yawan yi masa kenan. To daga baya ne ya zo zai tafi da ni Nigeria, a lokacin mun yi aure har ma na haifi yarona Naufal da baifi shekaru goma sha ɗaya ba a lokacin, ita kuma matar tasa ta Nigeria tana da ƴa'ya uku a lokacin, duk da ban ta6a ganinsu ba amma ina ganin hotunan su da videos dinsu a wayar shi duk idan ya zo. Ina son ƴa'yanshi sosai saboda ina yi masu kallon yan uwana kuma danginmu.... "Lokacin da Praveen ya zo da ni Nigeria, bai fara kaimu estate ɗinku ba, sai ya kaimu wani gida ya ce in fara zama a ciki, satin mu ɗaya a gidan Naufal ya yi rashin lafiyar da ta yi silar mutuwarshi, a lokacin har mun kai shi asibiti amma ya riga da ya mutu, na yi kuka kamar raina zai fita, har yau bazan manta raɗaɗin da na ji ba, na rasa Naufal.." Ta faɗa tana share hawayen ta. Sir Mubarak ya ce, "Bamu san komai game da yaron ki ba, bayan da ya rasu su wanene su ka yi jana'izar sa?" Cikin shesshekar kuka ta ce, "Bayan da muka je asibitin suka tabbatar mana da mutuwar sa, na dinga kuka kamar raina zai fita, docs da nurses suka dinga lallashina a lokacin ma bana jin harshen hausa ban san me suke cewa ba, sai idan Praveen ya fassara min da indiyanci nake fahimtar me suke faɗi, a ƙarshe na fita hayyacina na yanke jiki na faɗi a sume, ban ƙara sanin meke faruwa ba, lokacin dana farfaɗo na ganni a gadon asibiti kwance ga Praveen a gefe, cikin ruɗu na tambayesa da gaske Naufal ya mutu ko mafarki na yi? Ya ce min inyi hakuri ba mafarki bane, da gaske Naufal ya rasu, yau sati ɗaya kenan bana a hayyacina, harma sunyi jana'izarsa, sun ƙone gawarsa a crematorium kamar yadda muke wa mamaci a al'adarmu ta hindu, bazan iya misalta maka halin da na shiga ba a lokacin. Bayan rasuwar Naufal da wata ɗaya, ya ce zai kawo ni gurin dangin matarsa, amma yana so ya gargaɗe ni kar in kuskura in faɗa ma wani akwai aure a tsakanin mu, idan ba haka ba, zai rasa auran shi, kuma zasu kai ƙarar mu kotu.." Ya yi min barazana sosai, ya ce duk abun da ya faɗa akaina in amsa da haka ne na amince masa, ranar dana fara tsintar kaina a cikin estate ɗinku bazan misalta farin cikin da na ji ba, duk da wasu basu kar6e ni da hannu bibbiyu ba, waɗanda nake ta zumuɗin gani saida na yi danasanin haɗuwa na da su saboda ƙyarar da suke mini. Hajiya Saratu ta tsane ni, ƴa'ƴanta ma sun tsane ni, basu san ni auntyn su bace, kuma ni kaɗai ce dangin ubansu da ya rage a duniya, amma na yi masu uziri komai da ya faru Praveen ne sila, da tun farko ya faɗa masu matsayina a gurin su ya kuma daraja ni da ba su tsane ni ba, kuma hada ƙarin muna zaune a gidanku shi ya ja min ƙasƙanci a gurinsu. Kuma wlh ya so ya maida ni gidansa amma ni na nuna bana so saboda na saba da ku, ina son ahlinku, na ɗaukeku kamar dangina da na rasa..." Bata ƙarashe maganar ba, ta ji ya saka hanky kan fuskarta, a hankali yake share mata hawayenta, idanunsu a cikin na juna, duk sai ya ji ba daɗi, ya yi danasanin marin da ya yi mata, kuma da ya san bata da sanya hannu da ba abun da zaisa ya tuhume ta. "Ya Mubarak, ka taimaka ma rayuwarmu, ku yafe mana, ku bar mu mu ci gaba da zama tare da ku, zamu gyara kuskuren mu" Murmushin takaici Sir Mubarak ya yi. "Ki faɗa min meyasa kika bi Praveen kuka gudu? Kinsan laifin da ya aikata..?" Gabanta ne ya faɗi rass! Cikin rashin nutsuwa ta fayyace masa komai da ya faru. Girgiza kai ya yi cike da takaicin ƙaryar da Praveen ya yi mata. "Hmmmm, Praveen ba gaskiya ya faɗa maki ba, ba Hajiya Saratu bace me laifi, batasan da aure a tsakanin ku ba, kuma ba ita bace ta tura maku aljanu ba, hasila ma tsoron hulɗa da mai aljanu take yi balle har ta yi mu'amala da su, bayan haka yanzu haka da nake maki magana, Hajiya Saratu tana a kwance gadon asibiti.." Cikin ruɗu da tashin hankali ta furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un! Meya faru da ita? Meke damunta? Meyasa praveen ya yi min ƙarya ne? Ni dai Allah Ya sa bashi bane ya yi silar kwanciyarta gadon asibiti ba..!" Ta faɗa da damuwa akan fuskarta. "Ya Mubarak ka fadamin meke faruwa? Wani laifi Praveen ya aikata ma ku? Shiru ya yi yana sauraron muryar Owais dake yi masa magana ta cikin earbuds din dake a maƙale da kunnansa, komai da suke tattaunawa yana sauraron su, Sir Mubarak ne ya kira shi don ya ji komai. Cikin harshen yarbanci ya ce, "Owais, ina fata ka ji komai?" On the Other hand Owais ya ce, "Na ji Uncle, Hajjaty bata da laifi, bata san komai da Praveen ya aikata ba.." "Ta nemi in faɗa mata meke faruwa kana ganin yakamata mu sanar da ita?" "Uncle, ka fadamin ta yi 6arin ciki, nasan i war haka jikinta babu lafiya, jininta zai iya hawa, a yadda na ji shaƙuwarta da Praveen, idan ta ji abun da ya aikata zata shiga mawuyacin hali ne, amma me zai hana mu bari sai ta ji sauƙi sosai?" "Owais, ka yi magana mai ma'ana, na gode da shawararka." Daga haka suka yi sallama ya mayar da dubansa ga hajjaty, dama jiran shi take yi ya gama wayar, "Pls ka faɗamin wani laifi ya aikata? Dan Allah kada ka ce zaka 6oye min, na fada maka bani da kowa in ba Praveen ba, shine gata na, bana so na rasa shi! kuma me ke damun Hajiya Saratu?" Numfasawa ya yi kafin ya ce, "Allah shine gatan bawansa Hajjaty, zan faɗa maki amma ba yanzu ba, ki fara samun lafiya tukunna, sannan karki damu da maganar hajiya Saratu, ta ji saukin jikin ta yanzu." In a cool voice ta ce, "Shike nan zan jira har zuwa lokacin da zaka fadamin! Amma dan Allah ina Praveen ya ke?" "Karki damu, Praveen yana a wurin mu, kuma mun sanya doc sun yi masa treatment na rauninsa." "Zan iya ganin shi?" "A'a, ba yanzu ba." Gyaɗa kai tayi, "Shikenan..." "Amma yana inane? Kuma ni a ina nake?" Bai amsa mata ba sallamar Nurse ta katse su, mikewa ya yi ya nufi nurse din, "Pls, ki ci gaba da bata kulawa, duk abun da take bukata ki yi mata shi, ina so ta samu cikakkar lafiya." "Okay sir, zan yi iyakar bakin kokarina.." Juyawa ya yi tare da kallon Hajjaty da ke kallon shi. "Zata kula da ke, ko me kike bukatar ci ko sha ki tambaye ta zata yi maki, idan kika zauna salin alin, Praveen zai kasance cikin ƙoshin lafiya.. " tana kokarin yi masa magana ya sa kai ya fuce daga ɗakin, kamar ta fasa ihu.. "Pls, baiwar Allah, ki fadamin ina ne nan? Meyasa ya kawo ni? Kuma meke damuna ne?" "Am sorry ma'am, bai bani izinin in faɗa maki inda kike ba, bansan komai ba, abun danasani ya kira ni ne don in duba lafiyar ki.." Shiru ta yi zuciyarta duk ba dadi. ~_________________________________~ To fa manema labarai sun fara dandazo a layin Obie Estate sun haɗa uban cunkuso, burin su kawai su samu damar ganawa da ahalin Obie don su samu na ɗaukar rahoto, ba dan dakarun sojojin da ke a kewaye da Estate din ba da tuni sun 6urma ciki saboda tsabar zaƙuwa, masu ruwa da tsaki a mulkin ƙasar, sun kasa sun tsare suna jiran jin meke faruwa? Haka zalika ƴan jami'iyar Jdp da App sun ƙagu da su san meke faruwa, saboda duk sun ji labarin kewaye gidajen ƴan jam'iyarsu da soldiers suka yi, dama cikin yan kwanakin nan mutane sun fara tsegumin rashin jin ɗuriyar baba Obie, basu ji labarin yana a ƙasar ne ko ya yi tafiya ba, haka Alhaji Musa ma sun ji shiru babu duriyar shi, Ɗan-iya da ya fi kowa baki kusan kullum suna samun labaran yan siyasa a bakinshi ta gidajen radio da shafukansa na social media shima sun ji shiru ba labarinsa. Saboda yadda mutane ke kiran layukan su a waya yasa suka kashe wayoyin su. Alhamdulillah Hajiya Saratu ta samu lafiya, har an sallame ta, amma momma har yanzu memory ɗinta bai dawo ba. A main Falo na gidan baban suka haɗu gaba ɗayan su domin tattaunawa game da shawarar ya zasu yi da jama'ar da ke jiran su ji daga bakin su? Kowan nan su yana fargaban asirin mahaifinsu ya tonu, saboda gudun tozartar da zai yi da kuma su kansu, suna zullumin mutuncinsu da zai zube a idon duniya. Gaba ɗaya sun nuna basu san a fallasa sirrin, saboda basu son asirin shi ya tonu a bainar jama'a, suna jin fargaban abun da zai biyo baya, da kuma halin da uban nasu zai shiga, kuma basu son a gurfanar da shi gaban kotu, sun ƙwammace su bashi poison ya sha ya mutu, saboda basu son ma su ga tashin hankalin da zai fuskanta, ƙwara ya mutu su san babu shi a duniyar, duk da mutuwar ba hutu bace a gare shi, amma su a wurinsu ƙwara tun da ba a gabansu zai fuskanci abun da ya shuka cikin kabarinsa ba, amma in yana a raye sun san ba ƙyale shi za'a yi ba, dole ya fuskanci mummunan hukunci mai tsanani, ba zasu iya jure ganin halin da zai shiga ba, kuma ba zasu iya kashe shi da kan su ba, sannan basu son ya kashe kan shi, sun rasa ya za su yi da shi? Duk da fushin da suke yi da shi hakan baisa sun daina jin ƙaunar shi ba, kwata kwata ba su son ya wulakanta a idon duniya, duk da sun san ko sun rufa mashi asiri hakan ba zai hana asirin shi ya tonu ba, sannan Allah yana sane da komai, ko sun rufa masa asiri wallahi ba zai tsira ba tun a gidan duniya sai ya ga sakayyar abun da ya aikata, sai Allah ya kamasa, tayaya ma zasu goyi bayan rufawa azzalumi asiri? Bayan sun san Allah baya a tare da azzalumai, sun kuma san hakan ba daidai bane zama su ja ma kansu ne, bayan haka idan har suka nuna son kai, suka nemi su rufa masa asiri ko su 6oye shi, Allah ba zai bar su ba su kansu. Hajiya Saratu ta yi kuka tamkar ranta zai fita, ta dinga magiya tana roƙon yayyan nata akan kar su tona asirin Baba, kada su miƙa shi ga hukuma, su taimaketa su taimaki rayuwarta, idan ta rasa baba ina zata saka ranta? Su bar shi in har ba so suke zuciyarta ta buga ta mutu ba, lallashinta suka dinga yi suna bata hakuri tare da tunasar da ita akan kuskuren rufa masa asiri, aya da hadisi suka dinga janyo mata inda Allah da manzonSa suka yi magana akan azzalumai amma Hajiya Saratu ta burkice masu, kwata kwata bata ganewa ita kawai mahaifinta take so, ta kasa ganin laifinsa, tama ƙi yarda cewa ya aikata, idanunta sun rufe akan son baban nata, tausayin shi ta ke ji, bata son ya tozarta kuma batason a ta6a lafiyar shi, har faɗi take ita ta yafe mashi abun da ya yi mata suma su taimaka su yafe mashi, sannan kada su bari a raba ta da shi, tun da yana da sihiri ya 6ace kawai ya nisanta kanshi da duniyar mutane ya je can ya yi rayuwarshi, lokacin da take faɗin maganganun nan tana kuka mai tsuma zuciya, ba ƙaramin karya masu zuciya ta yi ba, tsananin tausayinta da kaunarta ne ya kama su. Sun ga juriyarta da haƙurinta, ta basu mamaki baiwar Allah, duk irin zaluncin da baban ya yi mata ita bata gani ba, tama riga su furta ta yafe mashi duniya da lahiri, babu wanda bai zubar mata da ƙwalla ba a cikin su. Ta fama masu raunin dake a zuciyoyinsu, in har zasu biyewa son zuciyarsu da halin da Hajiya Saratu take a ciki to kuwa ba zasu bari baban nasu ya fuskanci hukuncin da ya dace ba. A ƙarshe dai gaba ɗaya basu da wata mafita da ya wuce su miƙa shi ga hukuma, ba yadda suka iya. Sheikh Imam da ya kawo mazu ziyara ya ji komai da ya faru shi ya gargaɗesu ya ja masu kunne akan kar su kuskura su biyewa son zuciyarsu, su yi hakuri su rungumi ƙaddara, su manta cewa shi mahaifinsu ne, su dinga tuna zaluncin da ya yi masu da al'umma ta hakane zasu samu kwarin gwiwar fallasa shi, amma idan suka yi kokarin rufa masa asiri don gudun kada duniya ta ji toh su sani Allah yana a sama yana kallon su, bazai taba barin azzalumi da wanda ya taimaki azzalumai ba, har da nasiha sheikh Imam ya yi masu. A ƙarshe ba yadda suka iya, don dole suka miƙa wuya, a halin yanzu basu da burin da ya wuce babansu ya mutu kafin lokacin da za'a gurfanar da su a gaban kotu 😭 Chief Owais ne ya fara sakin videos din da suka ɗauka na Prisoners a shafukan hukumarsu na Instagram, Facebook da Youtube channel dinsu, wanɗanda ke da mabiya miliyan dubu ɗaruruwa daga kowani sassa na duniya. Yayin da Director Ziyad ya tutturawa manajojin Obie News Network labarin kurkukun ƙaddara da ya rubuta shi a wayar shi tun daga farko har ƙarshe, komai da ya faru a gidan kurkukun kaddara daki daki ya rubuta, ya basu umarnin su fara buga labarin a jaridarsu, sannan su kuma yaɗa shi ya shiga ko'ina na duniya. Yana a gidan radion nasu kiran Chief Owais ya shigo wayarshi, bayan ya ɗaga ya ce yana gayyatar gaba daya Press corps na ONN, da ƙarfe ɗaya su halarta a Isod Headquarter zasu tattauna da su.. Lokaci na cika motocin shahararrun ƴan jarida suka fara tururuwar shigowa isod headquarter. Wasu ruƙe da Camrecorders, wasu sun ruƙe Michrophones.. A katafaren Comference Room na headquarter din suka gudanar da taron.. Gaba daya senior agent suka hallara, tun daga DG, CI, Coo, Senior Agents, U.s armies, General Noah, kusan duk mai ruwa da tsaki a binciken Kurkukun Ƙaddara sai da ya hallara a comference room din Taj ne kadai bai samu zuwa ba. A saman kujeru kowan nan su ya zauna yayin da manema labarai suka kewaye su. Bayan sun gabatar da junansu, U.s Armies ne na farko da suka fara bada labarin farkon haɗuwar su da Prisoners din da suka ku6uta daga kurkukun kaddara har suka haɗu da su a dajin evil forest. Bayan sun gama, Chief Owais ya daura da nashi tun daga farkon ta yadda U.s Armies suka tuntu6e shi da case din yaran, ya bayyana masu yadda ya ji farkon da abun ya riske shi, bayan ya ɗan dakata team members din shi suka ɗaura da nasu bayanin game da Kurkukun kaddara.. Daga bisani Chief Owais ya bayyana masu ta yadda suka fara gano su wanene Elders, Ya ilahi! Ilahirin press corps din dake agurin saida suka razana matuƙa, jin abun da basu ta6a zata ba, hankalinsu ya fi karkata akan Chief Owais, saboda kansu ya ɗaure sosai, mamakin su ta yadda har ya iya tonawa kakansa asiri da kan shi!!! Gaskiyarshi ta yi matuƙar razana su. Lokacin da yake lissafa sunayen Elders, tsantsar rudani ne da razana suka bayyana ƙarara a cikin idanun manema labaran dake a kewaye da su, zan iya cewa tun da suke daukar rahoto basu ta6a daukar labari mai girma da razanarwa da kuma karya zuciya irin wannan ba! Abun ya ta6a su matuƙa. Duk wani abu da suke tattaunawa kaitsaye mutanan duniya suke kallon shi, wasu ta tv dinsu, wasu ta radio, wasu ta facebook live, wasu a instagram live, kai ko'ina fa labari ya bazama. Bayan da suka gama fallasa komai da ya kamata mutane su sani, manema labaran suka fara yi masu tambayoyi suna amsa masu ba tare da jin shakka ba. "Yallabai, ya kuka ji kaida ahlinku lokacin da asirin kakan ka ya tonu?" "Yallabai, wani hali kuka shiga da kuka ji kakan ku shine Shugaban kurkukun kaddara?" "Yallabai zamu iya sanin ina Elders suke a halin yanzu? "Yalla6ai, ba ku tunanin fallasa asirin kakanka da ka yi zai shafi ahlinku da muƙaman su?" "Yalla6ai gaba ɗayan mu mun kasa yarda da bun da kunnuwanmu suka jiyo mana, saboda rudanin da muka shiga, shin da gaske kakanka dattijon arziƙi yana da sa hannu? Mutum mai ƙima da daraja a duniya, wanda kowa ke girmamawa? "Yallabai ko zamu iya sanin ina fursinonin kurkukun ƙaddara suke? Mun dai ga video dinsu amma bamu san a wani hali suke ba, da buƙatar a bamu damar tattaunawa da su." "Sir, ina Zaheer Tajuddeen da Uzair? Zamu iya ganawa da su? Saboda ƴan jaridar mune ta jihar Joss da muka nema muka rasa tsawon shekaru, muna ta neman su ruwa ajallo!" Tambayoyi iri iri ƴan jarida ke yi mashi. A lokacin Owais ya yi rauni, idanunshi sun kaɗa jawur, yana mai jin baƙin cikin fallasa asirin Grandpa dinsa da ya yi, amma ya zai yi? Baya da mafita da ya wuce wannan! Ya zama dole mutane su ji miyagun laifukan da ake aikatawa a doron ƙasa ko dan su ɗauki darasi, su kuma ƙara imani da tsoron Allah su kuma kiyaye kan su. Gaba ɗaya kowa dake a gurin saida ya fahimci halin da yake a ciki, da ido abokansa suka dinga kwantar masa da hankali tare da dafa kafaɗunsa suna ɗan ƙarfafa mashi gwiwa don ya jure. Ji yake kamar an ɗaura masa nauyin duniya akansa, dauriya kawai ya ke yi. Cikin sanyi murya mai rauni ya soma magana cikin harshen turanci, _"Bazan iya misalta halin da family din mu suka shiga ba a lokacin da muka gano dasa hannun jagoran family dinmu, ko ban fada maku ba, kun sani, kowan nan ku zai iya ƙiyastawa a ranshi ya radadin abun yake idan wanda ka yarda da shi ya karya maka zuciyarka? Mun shiga mawuyacin halin da ba zai musaltuba! Ina fata mutane zasu yi mana adalci, kada su tuhume mu ko su zarge mu akan laifi da kakanmu ya aikata, kuma kada a juya mana baya ko a tsangwami ahlinmu saboda bamu da laifi, bamu san komai ba saida asirinsa ya tonu, in har aka daura mana laifin kakanmu zamu shiga mawuyacin hali fiye da wanda muka shiga. Ina roƙon mutane da su agaza mana, su tausaya ma rayuwar ahlinmu, kada wannan abun ya zama silar da za'a dinga cin zarafin mu! Komai da ya faru da mu, muƙaddari ne daga Allah, dama can rubutacce ne, kamar yadda bamusan komai ba, toh haka kowa ma zai iya faruwa da shi. Dalilin da yasa na fito bainar jama'a tare da abokan aikina na fallasa komai saboda hakkinku ne ku sani, bamu 6oye maku komai ba, saboda muna so ku ji kuma, don ku ƙara imani ku kuma ɗauki darussa daga labarin kurkukun ƙaddara, duk kuma wani mai aikata wani laifi a 6oye ya ji tsoron Allah ya daina tun kafin asirin shi ya tonu"_ "Akwai wanda ya tambaye ni, ba mu tsoron fallasa asirin kakanmu da muka yi ya shafi ahlinmu da muƙaman su?" Ya faɗa da murmushi akan fuskarshi, girgiza kai ya yi ya ce, "babu tsoro ko fargaba a tare da mu, kafin mu fallasa asirin saida muka yi wannan tunanin, amma bashi ne damuwar mu ba, saboda ba duniya muka zo nema ba, komai da muka mallaka a gidan duniya zamu bar shi, in har za'a yi mana adalci, bai kamata a tuhume mu ko a ɗaura mana laifin da bamu muka aikata ba, laifin wani baya shafar wani, bayan haka koda wasu sun zarge mu akan abun da ya aikata ina so su sani koda zai shafi muƙamanmu ba zamu damu ba, saboda idan muka mutu daga mu sai halin mu za a binne mu, muƙaman mu baza su cece mu ba, halinmu shi zai cece mu. Mun yi imani da Allah, kuma mun yi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, kuma mun san abun da ya faru da mu jarabawa ce daga gare shi, Allah shine shaidar mu, koda wannan abu zai shafe mu ba zamu damu ba, mun san dole akwai waɗanda ba zasu fahimce mu ba, akwai waɗanda kuma jiran rauninmu suke yi don su muzguna mana, to ina so su sani babu gudu babu ja da baya, ba zamu ta6a karaya ba, saboda Allah shi zai yi mana hisabi ba su ba, duk wanda yayi yunƙurin yin amfani da wannan damar don ya 6ata mana suna ko dan ya 6ata mana rai toh ya sani Allah yana kallonsa zai yi mana sakayya, akwai kuma ranar ƙin dillanci. Bayan haka, duk abun da kasan in akai maka ba zaka ji daɗi ba toh kada ka yi ma wani, kuma ka guji 6ata ran wanda baida abun dogaro da ya wuce Allah, ko don saboda fursinonin kurkukun ƙaddara yakamata mutane su san irin kalaman da zasu furta idan ba haka ba wani hali kuke tunanin zasu shiga? Idan ana fama masu raunin dake a zuciyar su? Da yawa waɗanda suka sadaukar da su iyayensu ne, wasu kawunnansu, wasu danginsu, na sani a cikin masu kallo na da sauraro na, akwai iyaye, akwai kawunnai, akwai yayye da ƙanne, kunsan ƙuncin da ake ji idan aka ta6a naka ko aka ci zarafinsa, da wannan nake roƙon kowan nan mu da mu kiyaye harshen mu, gaba ɗayanmu bamu ke da iko da kawunanmu ba, abun da ya faru da wani mara daɗi ka ji dadi ko ka yi dariya kaima baka wuce ya faru da kai ba, don haka idan har ba zamu faɗi alkhairi ba, ya fi mu ja baki mu yi shiru..." Kalaman Chief Owais ya ta6a zuciyoyin miliyoyin jama'a dake kallon su, ta ko'ina comments ɗin mutane ne ke ta yawo a social media.. "A halin yanzu, gaba ɗaya fursinonin da muka ku6utar suna a ƙarƙashin kulawar mu, in sha Allah zamu duba yiyuwar baku damar tattaunawa da su kaitsaye, bayan mun gama shari'ar Elders, bayan haka zamu buɗe shafukan da zamu dinga kawo maku duk wani abu da ya shafe su" CI ne ya amsa ma ɗan jaridar da ya yi tambayar.. "Elders suna a tsare hannun hukumar mu, ba zaku samu damar ganawa da su ba, har sai zuwa lokacin da za'a yi shari'ar su, zamu ci gaba da kawo maku bayanai game da su, ku ci gaba da bibiyar shafukan hukumar mu ta ISOD" Coo ne ya faɗa yana mai tabbatar masu da maganar shi. A ƙalla saida suka shafe awa suna tattaunawa da manema labarai tun suna amsa masu tambayoyi da marmari har saida suka fara galabaita. In a short time, labarin Kurkukun Ƙaddara ya bazu kamar wutar daji, ƴan jarida, gidajen talabijin, gidajen yaɗa labarai na duniya, da kuma shafukan sada zumunta sun cika da labarin kurkukun ƙaddara, BBC ne, Fox news channel, Cnn, msnbc, Newsmax, ko'ina zancen Kurkukun kaddara ake yi, labarin ya zama ruwan dare, Elders suna ta shan tsinuwar jama'a, DG da hukumarsu tana ta shan yabo daga bakunan al'ummar duniya, kowa ya jinjinawa kokarinsu musamman Dg da ya iya fallasa asirin kakansa, ya burge jama'a ya kuma siye zuciyoyin mutane, ta ko'ina yabonsa ake yi, mutane suna ta nuna tausayawarsu ga Prisoners, ba a ta6a samun labarin da cikin rana ɗaya ya samu billions of audience daga sassan duniya ba irin shi🔥 Ta ko'ina shafukan sada zumunta sun cika da hashtag # JusticeForTheVictims#justicefortheprisonersoftheprison ofdestiny #RemoveThemFromPower#punishthem#justicemustbeserved# Hada masu zanga-zanga ta online, wasu ma fitowa suka yi daga gidajen su, suka bazama kan tituna, inda suka buƙaci a yiwa fursinonin kurkukun ƙaddara adalci, a ƙwace wa Elders muƙamansu, a kuma gurfanar da su gaban kotu don su kar6i sakamakon laifukan da suka aikata. Hukumomin Human Right na ƙasashe daban daban kama daga Uk, America, Saudi arab da sauran ƙasashe sun buɗe wuta akan a hukunta Elders daidai da abun da suka aikatawa yaran da ba su ji ba basu gani ba. Haka zalika shuwagabannin ƙasashen ƙetare da aka samu ƴan ƙasar su cikin Elders da Prisoners suma sun buɗe wuta akan ba zasu lamunta ba, sun yi gargaɗi akan a gaggauta yankewa Elders tsattsauran hukunci a kuma mayar masu da yaran ƙasarsu da aka fitar, bayan haka zasu bibiyi shari'ar har sai sun tabbatar da anyi adalci, idan ba haka ba zasu ɗauki tsattsauran mataki. Gaba ɗaya hankalin duniya ya dawo kan Elders da Prisoners, abun ba iya Nigeria ya shafa ba, saboda Elders ɗin da fursinonin akwai jinsin wasu nahiyoyin.. Waɗanda suka fi shiga tashin hankali dangin Elders, Mutane sun fusata hakan ya sa jinin su akan akaifa ya ke, neman su suke ruwa a jallo don su fanshe abin da aka yiwa fursinonin kurkukun ƙaddara, ba dan sojojin dake kewaye da gidajansu ba, da tuni mutane sun sanya musu fetur sun ƙone su, ko su saka masu bomb saboda yadda suka zuciya, burinsu su yi arba da ɗaya daga cikin su don su ƙone shi. Lokacin da labarin abun da ke faruwa ya riski jam'iyar su Alhaji Musa, a lokacin ma suna tsaka da yin party meeting a conference room na headquarter dinsu, kwatsam sai ga kira ya shigo layin party leader ɗinsu Alhaji Bukar mai Guduma, bayan da ya ɗaga kawunsa ya ce su duba abun da ke faruwa a labarai. Nan fa suka kunna news, hankalinsu ya tashi matuƙa sun razana da jin labarin kurkukun kaddara, babban tashin hankalinsu hada ɗan jam'iyarsu Alhaji Musa, shine abun da ya fi razanar da su ya kuma jefa su a ruɗani sosai, sun yi baƙin cikin kasantuwarshi ɗan jam'iyar su, ya ja masu tozarci da tsana daga al'umma dama basu da farin jini, wannan abun kunya da firgici har ina, gaba ɗaya sun yi Allah wadai da Elders, duk da baƙin cikin da Musa ya ƙunsa masu hakan bai hana sunyi farin cikin jin cewa hada Baba Obie a ciki ba, dama da haushin shi a cikin zuciyarsu, tun lokacin da ya bar jam'iyarsu ya kafa tashi jam'iyar suke ta neman hanyar da zasu 6ata mashi suna su kuma lalata jam'iyar tashi, sai gashi cikin sauƙi yanzu sun samu damar da zasu 6ata ahlin Obie da jam'iyar su. Haka zalika ƴan jam'iyar APP ta su baba Obie, sun tashi da mummunan labarin da ya karya zuciyoyinsu, ya haifar masu da matsanancin tashin hankali da damuwa.. Haƙiƙa baba Obie ya karya zukatan mutanan da suka yarda da shi, kowa idan ya ji labarin da farko sai ya sanya kokwanto akan ba zai iya aikatawa ba, amma daga sun ga videos ɗin Chief Owais da yake kora jawabi sai jikinsu ya yi sanyi lakwas, saboda sun san jikanshi ba zai yi mashi ƙarya ba. Bangaren masu ruwa da tsaki a mulkin ƙasar sun razana da jin labarin kurkukun kaddara, sun kuma ɗimauce da jin cewa dattijon arziki uban maza, mutun mai daraja da ƙima a idon duniya shine shugaban kurkukun kaddara, kan wannan al'amarin har zaman tattaunawa suka yi a majalissa kowa ya tofa albarkacin bakinsa kan al'amarin, wasu suna goyan bayan a tsige ƴa'ƴansa daga muƙamansu yayin da wasu suka ƙi goyan bayan a yi hakan saboda basu yi wani laifi da zai sa a sauke su daga kan power ba, majority ɗinsu suna goyan bayan ahalin Obie ɗari bisa ɗari, kaɗanne suke nema su dangana su da laifin uban su. Har ƙuri'a suka jefa cikin kaso ukku kaso biyu suna goyan bayan ƴa'ƴan Obinna. Bari mu koma bangaren Iyalin Alhaji Musa mu ji meke faruwa da su? Da farko sun 6oyewa Hajiya Sarah abun da ke faruwa, kwata kwata suka ƙi sanar da ita, tayi tayi da su su faɗa mata meke faruwa sun ƙiya, kowa fargaban sanar da ita yake yi saboda suna jin fargaban halin da zata shiga, ba irin magiyar da bata yi masu ba, har kuka ta yi masu akan su faɗa mata abun da suke 6oye mata, idan ma mutuwa Musan ya yi kada su ji shakkun sanar da ita, zata fahimce su kuma zata rungumi kaddara, still suka ki sanar da ita, tsawon kwanaki sun barta a duhu, damuwa ta hanata sukuni, ta riga da ta sa ma ranta cewa wani mummunan abu ne ya faru shiyasa suke shakkun su sanar da ita, tun lokacin da sojoji suka kewaye gidan da kuma fitar da suka yi da daddare batare da saninta ba, abun da ya fi damun ta rashin dawowar Alhaji Musa gidan, tsawon kwanaki bata ji ɗuriyarshi ba, layukan wayoyinsa duk a kashe kum baya nemanta, duk wanda ta kira cikin abokan huldarsa da ta sani don ta ji ko su ya tuntu6e su sai suce mata a'a basu ji daga gare shi ba. Daga ita har Zeenatu sun damu, sai da ta kaiga ko abinci basu ci sosai, basu bacci, ko office ta daina zuwa komai nata ya tsaya cak.. Tsananin tausayin su ne kullum ya ke ƙaruwa a cikin zukatan su hajiya Layla, musamman da ta dinga bin su ɗaki ɗaya bayan ɗaya tana roƙon su akan su sanar da ita meke faruwa? Ta je ɗakin Benazir tana kuka ta roƙe ta ta faɗa mata amma ta ce ta yi hakuri ba zata iya ba, saboda bata son ta zama silar da zata shiga mawuyacin hali. Bayan ta fito daga dakin Benazir ta je dakin Dr Shureim shima ta roƙe shi akan ya faɗa mata, amsar da Benazir ta bata irinta shima ya bata, kamar sun haɗa baki. Zuciyarta ta sosu, still bata yi fushi da su ba, ta je ɗakin hajiya Layla ta roke ta itama ta ce ta yi haƙuri sanin bashi da amfani, bazata iya fada mata ba.. Kowa ta tambaya amsa ɗaya suke bata. Lokacin da haƙurinta ya ƙare, ta kira su dukan su a main falo ta ce kodai su faɗa mata abun da suke 6oye mata ko kuma ta tafi tabar ƙasar tare da Zeenatu, ba zasu sake ganinta ba har abada, zata koma gurin family ɗinta. Hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda sun san muddin ta koma gurin danginta, daga ita har Zeenatun zasu iya canza addini su koma nasu, dama ta ta6a faɗa masu iyayenta sun yafe ta daga family dinsu saboda auran za6inta da ta yi, tun farko sun nuna basu son ta auri baƙar fata wanda ba ɗan addininsu ba amma ta bijire masu ta auri Musa ta baro kowa nata. Wannan maganar da ta yi ne yasa suka yanke shawarar sanar da ita komai dake faruwa. Gaba ɗaya suka haɗu wurin fayyace mata komai tun daga kan cin amanar da Musa ya yi mata ya rabata da jinjirarta da kuma munanan ayyukan da yake aikatawa. Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." Kalmar ƙarshe da suka ji ta furta nan take ta yanke jiki ta faɗi, gaba daya suka rufa akanta suna ambaton sunanta haɗi da bubbuga jikinta don ta farka. Cikin sauri Dr. Shureim ya dauko ruwa suka yayafa mata shiru bata farfado ba, a ƙarshe suka yanke shawarar kaita asibiti, suna a wannan halin sai ga motar hajiya Laura ta shigo gidan, a haukace ta fito daga motar jikinta na 6ari ta nufi ciki don ta faɗa ma yayanta abun da ke faruwa, lokacin da ta shigo sun yi mamakin ganinta, matar da kwata kwata babu ruwanta da su saboda rashin jituwar ta da hajiya Layla yasa ta ɗauke ƙafarta da zuwa gidan, suna ganinta suka fara tambayarta meke damunta? Ganin babu takalma a ƙafafunta, ɗan kwalinta ma a hannu ta ruƙe shi, cikin shesshekar murya ta ce ina yaya Musa? Tana son ganin shi! akwai abun da zata faɗa masa.." Kwata kwata bata a nutsuwarta, ilahirin jikinta kerma yake yi, bata ƙare maganar ba, ta hango Hajiya Sarah dake a kwance kan floor ba numfashi Benazir ta rungume kanta a saman laps dinta sai yayyafa mata ruwa ta ke yi tana ambaton sunanta ta ƙi ta farka. A ruɗe Laura ta tambayi me ke faruwa, kamar jira hajiya Layla take yi ta tambayi ba'asi aikuwa ta shiga zayyana mata komai dake faruwa, Alhaji Ubaid yanata ƙoƙarin dakatar da ita amma ta ƙi sauraron shi. Tashin hankali ne tsantsa kan fuskar Laura, ita da ta zo kawo ma yayanta labarin abun da Obinna ya aikata, ashe shima yana daga cikin Elders ɗin wa'iyazubillah! Ta gaza yarda da abun da kunnuwanta suke jiyo mata, cikin ruɗu da gushewar hankali ta watsa da gudu ta nufi part ɗin yayanta tana fadin ba zai ta6a yiwu ba, hajiya Layla ƙarya ta ke yi mata, yayanta baya da sa hannu! Baisan komai ba, ƙazafi take yi masa dama tasan ta tsane shi.." bayan ta shiga part ɗinsa bata taras da kowa ba. Ta zaro wayarta ta dinga kiran layukan wayarsa gaba ɗaya a kashe take samun su, nan fa jikin taƙaura ya yi la'asar saboda bata ta6a kiran sa ta ji wayarsa a kashe ba sai idan da dalili, zama tayi akan couch ɗin dakin, duk ta bi tasha jinin jikinta, gabanta ya shiga faɗuwa rass rass, tsoro da firgici suka cika zuciyarta. Bakomai take ji ba fa ce tsoron kada maganar da hajiya Layla ta faɗa mata akan yayanta ta tabbata gaskiya ne, ya za ta yi? Bata da wani gata da ya wuce shi, da shi ta dogara, shine shaƙiƙinta abun tunƙahonta, bata tunanin zata jure tozarci da kunyar duniya. A ƙalla ta shafe awanni tana jiran dawowar yayanta don bata fidda ran zai shigo gidan ba.. Jin shiru bai dawo ba ya sa ta fito daga ɗakin, bata iske kowa ba, a bakin maids din gidan ta ji cewa sun tafi kai Hajiya Sarah asibiti. Kwata kwata bata damu da halin da ta riski matar yayannata ba, ita kawai damuwar ta yayanta ya zo ta ji daga bakin shi in gaskiya ne abun da ta ji a bakin hajiya Layla. Har dare ya yi Musa bai dawo ba, ƙarshe a gidan ta kwana washe gari ta dasa zaman jiran shi, ba ci ba sha tun jiya rabon da abinci ya gifta ta makoshinta. Kwana ɗaya da wuni mutanan gidan basu dawo ba, a lokacin Hajiya Laura ta sare da jiran yayan nata, kwatsam ta risƙi labarin kurkukun ƙaddara dake ta trending a social media, a nan ta ji cewa hada Alhaji Musa cikin Elders, kuma shine Jan Wuya mugun uban da ya yaudari ɗiyarsa, har labarin Unaizah ta karanta ta kuma ga hotonta da ke yawo a social media. Batasan sa'adda ta saki wayar ta fadi ƙasa ta fashe ba, ƙunci da baƙin ciki suka cika zuciyarta, ta dinga kuka tana tsine ma yayan nata da ya jefa su a cikin musiba, a ƙarshe komawa ta yi cikin part ɗinsa ta kulle kanta, ta hargitsa ɗakin ta dinga zaƙulo kayayyakinsa tana watsarwa a ƙasa tare da tattake su da kafafunta, kamar mahaukaciya sai sambatu ta ke yi tana ɗura masa ashariya, tana cikin halin kwatsam ta ji wani abu ya tokare ƙirjinta me raɗaɗin gaske, a gigice ta daddafe ƙirjinta da tafukanta, jikinta ya dinga kerma, cikin fitar hayyaci ta dinga zubda gumi nan take ta yanke jiki ta faɗi tana kakari still hannuwanta na dafe da kirjin nata, ga shi ba wani a kusa balle a yi gaggawar taimaka mata, bayan dan lokaci gaba daya ta daina motsi hannuwanta suka faɗi gefe 😳 A bangaren Hajiya Sarah tun ranar da suka kaita asibiti aka kwantar da ita, bayan gwaje gwajen da docs suka yi mata a ƙarshe sun gano abun da ke damunta, sakamakon mummunan labarin da suka gaya mata ne ya yi silar kamuwarta da anxiety attack, wanda silar hakan hawan jini da ciwon zuciya suka yi mata mugun kamu, wanda idan har likitoci basu iya ceton ta ba za su iya rasa ta ne. Hankalinsu ya tashi matuƙa har sai da suka yi danasanin faɗa mata ganin mawuyacin halin da suka jefa rayuwarta, kwata kwata bata a hayyacin ta. Basu tashi sanin suna a cikin tsaka mai wuya ba, sai da Tani ta kira Dr Shureim a waya ta faɗa masa sunga Laura a ɗakin Musa babu numfashi a jikinta, sun kuma je kiran Zeenatu don ta ci abinci, itama sun isketa kwance a ƙasa bata motsi, sai lokacin ne suka tuna da babu Zeenatu a tare da su sun barta a gida, tsawon kwana ɗaya suna asibiti gurin jinyar Hajiya Sarah. A asibiti suka baro hajiya Sarah karkashin kulawar likitoci, Lokacin da suka dawo gidan cikin sauri Alhaji Ubaid da Hajiya layla suka nufi ɗakin Musa, Dr Shureim da Benazir suka nufi up ɗakin Zeenatu. Shigar su ke da wuya, kwatsam suka hangota a kwance saman gadonta, maids ɗinne suka kwantar da ita bayan da suka taras da ita a ƙasa bata motsi. Kallon juna suka yi cikin rudu da tashin hankali, sam sun kasa ta6a ta sun rasa gane meya faru? Tani da ta biyo bayansu tana kuka ta miƙa masu wasiƙar data gani akan gadon Zeenatu. Yatsun hannun Dr Shureim na kerma ya kar6a tare da buɗe ta, suka haɗu shi da Benazir suna karantawa. _Na ji komai da ya faru, daddyna ɗan kungiyar asiri ne, ya raba ni da twin sister ɗina, ya zalunce ta, ba zan ta6a yafe masa ba. Kamar yadda ya sadaukar da ita ya yi silar mutuwarta, nima ya rasa ni na har abada, bazan ci gaba da rayuwa ba, zan bi ƴar uwata Unaizah, mommy ki yi hakuri da hukuncin da zan yankewa kaina, Yaya Shureim, Aunty Benazir ku yafe min, bazan iya jure baƙin cikin da daddyna ya ƙunsa mini ba, ya yaudare mu. Yanzu na gane dalilin da yasa ya ke yi min kulle saboda baya son ina fita don kada wanda yasan Unaizah ya ganni asirinsa ya tonu, kuma na gane dalilin da ya sa Azeezaty ta ruɗe a ranar da ta fara ganina har ta kira ni da sunan Unaizah ashe yar uwata ce da su ka yi rayuwa da ita a gidan kurkukun ƙaddara, Allah Ya isa daddy! Bamu yafe maka ba, Allah Ya wulaƙanta rayuwarka, in sha Allah hakkin Unaizah ba zai barka ba!_ Abun da ya faru lokacin da suke ba Hajiya Sarah labari, ashe Zeenatu ta fito daga bedroom dinta, tana kokarin shiga falon ta tsinkayi maganganunsu a cikin kunnanta, ta ji komai da ya faru hakan yasa ta ɗimauce, dama mai haƙuri bai iya zuciyata ba, hankalinta ya tashi zuciyarta ta karaya da jin labarin twin sister ɗinta da bata san da ita ba, hakan yasa ta juya da gudu ta nufi ɗakinta, tana shiga ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, babu wanda ya san me ya faru, har ta gama kukan ta rubuta wasiƙar da Tani ta tsinta a ɗakin. Lokacin da suka kammala karanta wasikar, zubewa suka yi agabanta saman gwiwowinsu suka fashe da kuka suna fadin meyasa zata kashe kanta bayan tasan babu kyau! Meyasa zata yi masu haka?" Idan muka koma bangaren Hajiya Layla da Alhaji Ubaid lokacin da suka shiga bedroom din Musa, a kan floor suka hango hajiya Laura a kwance babu numfashi. Da suka tatta6a jikinta a sandare suka ji shi, sun rasa gane ta mutu ko tana a raye saboda ruɗu, Lami ce ta kawo masu ruwa suka yayyafa mata a jikinta, ko gizau bata yi ba, nan fa hankalinsu ya tashi gaban su ya shiga faɗuwa. Suna a wannan halin suka soma jiyo muryoyin Benazir da Dr Shureim cikin tashin hankali suke ƙwala masu kira suna fadin, "Daddy, Mommy! Kuna ina! Ku zo ku gani! Zeenatu ta kashe kanta, ta mutu, babu zeenatu..." Basu san sa'adda suka saki Laura ba, Jikinsu na 6ari suka nufi falon har suna bangazar juna ita da Alhaji Ubaid, a daidai Lokacin sun nufo su Dr Shureim ne ya ɗauko gawar Zeenatu a saman kafadar shi. Wa'iyazubilla! bazan iya misalta maku tashin hankalin da iyalan Elders suka shiga ba, ƙuncin rayuwa da baƙin ciki ne ke addabarsu ta ko'ina ba sauƙi gaba daya sun sare da rayuwar duniya. A bangaren iyalan Ɗan iya, suma sun fuskanci nasu ƙalubalen bayan da asirin mahaifinsu ya tonu, suma sun ji komai game da kurkukun kaddara sun kuma ji hadda mahaifin su cikin Elders.. Gaba ɗaya saida shiga mutane ya gagare su saboda tsangwamar su da ake yi, dole suka killace kansu a gida. Duk wani mai hulɗa da su saida ya ja baya da su, kyara da tsangwama ba wanda basu fuskanta ba a gurin mutane, hatta shiga social media saida ya gagare su, saboda munanan maganganun da mutane suke yi akansu, ubanninsu sun ja masu abun kunya, bayin Allah, su da ba laifin su ba. Jarabta ce daga Allah kuma da suka yi haƙuri suka jure, cikin ikon Allah sun fara samun maslaha, manyan malaman addini na ƙungiyar sheikh Imam Malik dama wasu manyan malaman duniya sun tsawatarwa mutanen dake cin zarafin su akan laifin da bana su ba, sun yi nasiha sun yi wa'azi akan halin da iyalan elders suke a ciki, kuma cikin ikon Allah sai gashi sun fara samun sassauci, mutane sun gane kuskuren su na ƙuntata masu da suke yi, musamman da suka ji labarin abun da ya faru da twin sister ɗin yarinyar da labarinta ya ta6a zuciyarsu, hankalin kowa ya tashi da jin Zeenatu ta kashe kanta, mahaifiyarsu kuma tana a kwance rai hannun Allah sakamakon abun da mijinta ya yi ma ƴarta, su kansu ƴan'uwan nata basu san ya akai labarin Zeenatu ya fita ba, hasalima basu son asani saboda abu biyu, na farko basu tabbatar da mutuwar Zeenatu ba! Bayan da suka kaita asibiti doc ya faɗa masu da yiyuwar doguwar suma ta yi saboda babu alamun ta sha poison ko lahani na ciki ko na waje a jikinta, abu na biyu saboda tsoron surutun mutane, amma sai dai suka ji labarin yana yawo a social media tare da hotunan Zeenatu. Sai daga baya suka gano cikin ƴan aikin gidanne suka fitar da labarin, aikuwa ransu ya 6aci matuƙa, har mataki suka ɗauka akan ƴar aikin da ta yaɗa labarin duk da ta janyo masu tausayar al'umma.💔 Aslm barkanmu da wannan lokaci Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini Maganin matsiMaganin mata Maganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki Set na amarya Tabaje tsumin Gomba Xuma kiba ta hips and Brest Magungunan gyran Brest Magungunan Karin hips Maganin sliming Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291 Idan maganin mata kikeso akwai Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻 Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500 Garin bata gaban kishiya 500 Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500 Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500 Za a bakisu akan 4k Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki. *Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~___________________________________💔🔥~ Luxury-incense By Sapnah Borno. Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku. Wardrobe balls Kabbasa spray Chadian khumra Hawee Halud Gabgab Sandal sukkariya Kajinguru Dilka soap Ready to use dilka Karkar oil Turaren tsuguno Habil Dorut Dorot after period Brown khumra Dufr khumra Body milk Sudanese kuleccam Chadian dufr kuleccam Musk khumrah. Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take Our Chadian aphrodisiacs are. Beejay fire Sata jagab honey Wetness and sweetness combo Daka Great A sabaya Breast engagement powder Ciccibi Gumbar madara Gumbar dabino Bita Zaizai 08164570032. ~____________________________________Daga alƙalamin Hafsat Bature Boss✍️~ Kowan nan su yana a zaune kan kujera cikin Cell ɗin Isod, A hankali Chief Owais ke duban fuskar Praveen da ya sadda kanshi ƙasa cikin tsananin tashin hankali da fargaba, gaba ɗaya babu nutsuwa a tare da shi ga rashin koshin lafiya, la66ansa sun kumbura suntum, gefen idonshi na dama ya kumbura harda kwantsa a cikin su, gaba ɗaya jikinshi a kumbure yake ga tarin raunukan da ya ji sakamakon bugun da su Sir mubarak suka yi ma shi, har yau bai dawo daidai ba. Bakomai chief yake kallo a cikin idanun shi ba face tsantsar tsoro, firgici, da damuwa mai haɗe da ƙunci da baƙin ciki, saboda nauyin Chief Owais da ya ji ya sa shi kasa jure kallon shi. Girgiza kai Chief Owais ya yi, "Praveen, Allah ba azzalumin bawanSa bane sai dai bawa ya zalunci kan shi. Me ya ja maka Praveen? Ma ya kai ka aikata miyagun laifukan nan? Meyasa ka biyewa son zuciyarka da son abun duniya wanda zamu mutu mu barshi duk min daren daɗewa?" Girgiza kai ya yi cike da danasani ya ce, "Bada son raina ba, ba halina bane, sharrin shaiɗan ne da sharrin zuciya, nasan ina da son kuɗi sosai, zan iya komai don in samu kuɗin da zan rufa mana asiri ni da ƴar uwata, amma wallahi ban ta6a kisan kai ba, sai da na haɗu da Obinna..." Bai ƙare maganar ba ya dakatar da shi, "Ka iya kuma cin zarafin mata ko? Ko ka yi tunanin bamu ji abun da kake ma ƴan aikin gidanmu ba? Ka dinga masu barazanar za ka sa a kore su daga aiki duk don ka samu su baka haɗin kai, bayan haka kaine ka yi silar ciwon marwa..." Cike da tsana ya ke kallon shi. "Dama can babu imani a zuciyarka Praveen, baka da tausayi kuma kai ɗin mugu ne, ƴar uwarka kaɗai kake tausayi, grandpa ya faɗa min duk wanda suka saka a kungiyar kurkukun ƙaddara da son ran shi...." Sunnar da kan shi ƙasa ya yi. "Ka faɗa min tayaya akai ka haɗu da Saratu? Da kuma yadda akai baba ya sanyaka a ƙungiyar kurkukun ƙaddara? Karka ce zaka yi min ƙarya ko ka 6oye min wani abu, ƴar uwarka tana a hannunmu, idan ka yi laifi ba kai zamu hukunta ba, ita zamu hukunta.." Faɗuwar gaba ya ji, a ruɗe yake duban Owais da jajayen idanunsa.. "Na roƙe ka, kada ku ta6a Hajjaty, bata da laifi, batasan komai ba, na ji zan amsa maka tambayoyin ka.." Murmushin gefen fuska Owais ya saki, ya fahimci Hajjaty ce lagwon shi. dakyar ya ke magana yana sakin nishi. "Farkon haɗuwa na da hajiya Saratu a restaurant ɗinmu ta zo cin abinci, ni na je kai mata abincin, kawai saboda na goge cokali da rigata ta falla min mari, ta sanya hannu ta 6arar da kayan abincin ƙasa, ta soma zazzaga min masifa tana faɗin shiyasa bata cika son cin abincin indiya ba ƙazamai ne mu, ƙasƙantattu marasa hankali.." A lokacin na ji zafin marin da ta yi min, raina ya 6aci da kalamanta amma ban nuna ba, saboda na hango agogon hannunta ta zinari ce, bayan haka ni ina girmama masu kuɗi koda zasu wulaƙanta ni ne indai zan samu abun da nake so. Har zata tafi na ce mata ta 6arar da abinci bata biya kuɗin ba, cikin fushi ta tura hannu cikin handbag ɗinta, ta zaro dala ɗari ɗari bama na kuɗinmu rupee ba ta watsa mini kan ƙirjina ta juya ta fuce, na shiga washe baki ina tattara kudin da suka zube a ƙasa, wanda a ƙalla a kudinmu na indiya sun kai dubu ɗari biyar, nan fa na fara tunanin ta wace hanya zan ƙulla alaƙa da ita? Tun da na fahimci tana da arziƙi kuma ƴar masu kudi ce. Daga nan saina fara bin diddiginta, tun a ranar da ta shige motarta na bi bayanta da mai abun hawa, na ga ta shiga Medical University, a nan na fahimci ɗaliba ce ta zo karatu daga wata ƙasa, saboda na lura ba jinsinmu ba ce. Da na ci gaba da yin bincike akanta saina na gano ƴar Nigeria ce, kuma ta fito daga babban gida na masu arziƙi, a jami'ar babu wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya, tun daga ɗalibai har malaman shakkar 6ata mata rai suke, ita kuma bata da mutunci, ta ƙware gurin bullying ɗin mutane. Na ɗauki lokaci ina shawarar ta yadda zan shiga jikinta, a ƙarshe dubara ta faɗo mini a rai, na haɗa baki da abokaina na sa su farmaketa akan hanyarta ta dawowa daga makaranta zuwa gidanta da take zama don na gano ba a hostel take ba, katafaren gida gare ta harda masu aiki da masu tsaron gidan amma bata da driver ita ke driving da kanta saboda bata son ana sanya mata ido idan zata fita, a yadda na ji.." Ya ɗan dakata yana mayar da numfashi. Dg ya nutsu yana sauraron shi. "A ranar da ta fito daga school cikin motarta, batasan muna a biye da bayanta ba saman baburan mu, idan ba zan manta ba wuraren ƙarfe biyar na yamma ne, akan idon mu ta shiga gym, har lokacin da ta fito ta shige motarta, ta kuma nufi mall ta shiga, duk muna biye da ita, har sai wuraren ƙarfe takwas na dare sannan ta nufi hanyar komawa gidanta, kasantuwar ba jama'a layin da ta shigo, nan muka samu damar farmakarta, abokaina suka fara tarar motarta, suka tsoratar da ita da addunan hannayen su, dama plan ne muka shirya mata, suka yi mata barazanar zasu yi mata fyaɗe sannan su kashe ta, cikin ruɗu da tashin hankali ta ce su kyaleta ta tafi kar su kuskura su ta6a ta, idan ba so suke su rasa rayukan su ba, idan ma kuɗi ne suke so tana da su zata basu ko nawa suke so, amma kar su ta6a lafiyar jikin ta, saida na bari sun fara ƙoƙarin raba ta da kayan jikinta tukunna ni kuma na fito daga inda na la6e na nufe su da tsawa na ce, 'Kar ku kuskura ku ta6a ta, idan ba so kuke ku rasa rayukanku ba!' Ina ƙarasawa muka cuɗanya da su faɗa ya kaure a tsakanin mu, ta yi ta mamakin yadda na dinga bugun su, ni ɗaya na bubbuge su, har sai da suka arta a guje suka bar arean wurin. Kwata kwata bata gane fuskata ba, dama ranar da muka haɗu a restaurant bata yi min kallon arziki ba, a lokacin ban wani nuna zaƙewa ba, ina haki ina gyara hannun riga ta na dube ta na ce, 'Ki kiyaye fita a irin wannan lokacin, idan ba haka ba, 6ata gari zasu lalata maki rayuwa' Kamar dai yadda jaruman film ɗin indiya suke yin acting, na juya zan tafi ta yi saurin shan gabana, duk da girman kanta saida na burgeta still wani kallon ƙasƙanci ta ke bina da shi ganin suturar jikina irin ta marasa galihu ce, cikin sanyin murya ta ce min ta gode da taimakon da na yi mata, ba don ni ba da tuni sun yi nasarar cutar da ita. Na yi murmushin gefen fuska ganin plan ɗin mu na aiki, na ce mata kar ta damu na saba taimakon mutane, kawai ta bi shawarata. Ta ce min meye sunana? Kuma a ina nake da zama.. Na ce mata Praveen, ina a layin dake a gaban nasu. Ta ce ta yi mamakin ƙarfina, ta yi zaton abun da take gani a indian movies ƙarya ne, amma yau ta ga zahiri.." Na yi dariya, daga nan ta ce min in ba damuwa mu yi musayar number, idan tana buƙatar taimako zata dinga kira na, jikina na 6ari na bata number wayata, bayan mun yi rabu na je muka haɗu da abokaina mu kai ta murna kowa ya fara hasasho kuɗin da zai samu. Sai da na jera kwanaki ukku ina tura mata abokaina su farmake ta, kuma a duk lokacin da suke zuwa ni ke taimakonta, bata ta6a gane cewa nike turo mata su ba, idan ta tambaye ni ya akai a duk lokacin da miyagu suka farmaketa nake zuwa kamar aljani? Na ce mata saboda na damu da ita shiyasa nake bin diddiginta. Daga haka shaƙuwa ta fara shiga tsakanina da hajiya Saratu, ko da ta nemi sanin dangina na ce mata bani da kowa sai ƴar uwata ɗaya mu marayu ne, asalin danginmu masu arziƙi ne, silar hatsarin jirgin ƙasa muka rasa kowa namu, wanda kuma maƙiya ne suka farmake mu a cikin jirgin ƙasan suka kashe kowa sai ni da ƴar uwata kaɗai muka rayu, tun daga nan rayuwa ta sauya mana muka koma marasa galihu. A lokacin ta tausaya min sosai, har ta ce min zata taimaka mana. Sannu a hankali soyayya ta fara shiga tsakanin mu, muka shaƙu da juna, bata ta6a tambaya ta game da ƴar uwata ba, kuma bata ta6a zuwa inda nake ba, sai dai ni in je gidanta, sai da ta kaiga nine drivern dake tuƙata duk inda zata je saboda in dinga bata kariya. Lokacin da ta kammala karatu, makaranta ta shirya masu graduation celebration, mahaifinta ya zo delhi, a gidanta ya sauka, ta kira ni a waya tana murna ta faɗamin daddynta ya zo daga Nigeria tana so in zo mu haɗu, amma bata so in sanya kayan yan jagaliya, in nemi kaya masu kyau cikin waɗanda take siya mun in saka saboda mahaifinta babban mutunne mai arziƙi da duniya tasan da zaman shi, idan har ya gano wanene ni zai raba mu ne, na ce mata toh. A ranar da zan je, na ɗauki wanka na mutunci na je gidanta, a falo na zauna, masu aiki suka kawo min lafiyayyan abinci, daga bisani ta fito tare da daddynta, kallo ɗaya da na yi masa saida gabana ya faɗi saboda kwarjinin da ke gare sa, da kallo ɗayan na fahimci hamshaƙin mutunne. Jiki na a sanyaye na miƙe muka gaisa da shi cikin harshen turanci. Mun yi fira da shi kaɗan, bayan Saratu ta gabatar mashi da ni, ta kuma faɗa masa abun da ya faru da danginmu da kuma taimakon da na ke yi mata, ya nuna jin daɗinsa sosai, da zan tafi har kyautar agogo ya bani mai tsada. Bayan dana dawo ni da abokaina muka je kasuwa muka siyar da agogon, mun samu kudi sosai, muka raba kuɗin ni da su, nawa kason na je kasuwa nayi ma Divya siyayyar kayan sawa. Lokacin da Hajiya Saratu zata koma Nigeria, ta ce min in har ina so mu auri juna dole in biyota mu tafi Nigeria in ga danginta, sannan koda zata aure ni, sai dai ni in zauna a ƙasarta amma ita bazata iya zama a india ba. Abu ɗaya ne damuwata, ƙanwata da zan tafi in barta, kuma ina son in tafi saboda nasan idan na bi Saratu zan yi arziƙi sosai, hakan yasa na yanke shawarar bin ta. Bayan da mu ka zo Nigeria, kawunnanka sun nuna ƙin amincewarsu da auren mu, ƙiri ƙiri suka nuna min tsana da tsangwama saboda ni ba jinsinsu bane kuma bani da asali, bayan haka basu yarda da ni ba, duk na bi na tsargu amma saboda mahaifinku ya tarbe ni da hannu bibbiyu ya nuna min ƙauna yasa na saki jikina na ba banza a jiyar su, bayan kwanaki da zuwa na gidan ku, baba Obie ya kira ni a part ɗinsa mu biyu muka zauna muna fuskantar juna. Ya ce min yasan komai game da ni da kuma rayuwata.. A ruɗe na kallesa na ce bangane me yake nufi ba, ya yi murmushi ya soma zayyana min tarihin rayuwata tiryan tiryan, gabana ya faɗi na bi na ruɗe jin ya gano komai game da ni. Ya kuma cewa yasan ni nake saka abokai na su farmaki Saratu don in kawo mata taimako, meyasa na ke yin haka? Da mamaki na ce masa tayaya akai yasan duk wannan? Ya ce min Saratu autar shi ce, yana sonta fiye da komai, kuma duk wanda ya ra6e ta yana bibiyar rayuwarsa saboda baya son abun da zai cutar da ita, ta yadda akai yasan komai game da ni da kuma manufata, abokaina yasa yaransa suka kama, ya basu za6i kodai su faɗa masa komai game da ni ya biya su kuɗi, ko kuma ya basu kashi kuma su faɗa ta tsiya, sai suka za6i su faɗa masa komai don ya basu kudi. Bayan da ya kai min ƙarshen maganar tashi ya tambaye ni meyasa na yi haka? Ganin ya gano komai yasa na bayyana masa manufa ta, na ce saboda ina son in yi arzikin da zan kula da rayuwar ƴar uwata, saboda ita na ke yin komai. Anan ne yake faɗa mun zai yi min hanyar arziƙi mara yankewa, kuma zai bani auran Saratu harma da gurin da zamu zauna ni da ƴar uwata, zai ɗauki ɗawainiyar cin mu da suturar mu, sannan zai sama min aiki a kamfaninsa amma bisa sharaɗin zan yi komai ya ke so! Na yi murna mara misaltuwa na ce masa na amince koma menene zan yi ya faɗamin kawai, ya ce min na tabbata zan yi? baya son na yi danasani daga baya, ko in nuna bazan iya ba, na ce masa aini in dai akan kuɗi ne zan iya komai amma banda kisa, ya saki shu'umin murmushinsa. Bayan da ya faɗamin komai game da kurkukun ƙaddara, na razana, hankalina ya tashi, na bi na ruɗe na ce bazan iya ba rashin imanina bai kai nan ba, ina jin tsoron in jefa rayuwata da ta ƴar uwata cikin haɗari, ni dai ya yi hakuri ya barni in koma India zai fi min kwanciyar hankali. Dariya ya yi ya ce ai nama riga dana shiga ƙungiyar kurkukun ƙaddara tun da har na matsa ya faɗa min, kuma nasan sirrin su, kodai in amince ta lalama ko kuma ya kashe ni sannan ya kashe ƴar uwata Divya, za6i ya rage nawa. Ba yadda na iya, da na zauna na yi tunani, zuciyata ta raya min in amince masa ko don saboda alƙawarukan da ya ce zai yi min. Hakan yasa na amince, nima na zama member na kurkukun ƙaddara, daga bisani da likafa ta ci gaba, ya mayar da ni cikin Elders saboda yana so na, kuma yana nema na. Runtse ido Chief Owais ya yi wata kibiyar baƙin ciki ce ta soke shi, cikin rawar murya ya furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Praveen duk ya sha jinin jikin shi ganin irin fusatar da Owais ya yi. "Daga baya, shine ya bani iznin in kawo ƴar uwata gidan bayan da na faɗa masa na aureta hada yaron mu ɗaya, ya ce min idan ta zo baya son kowa yasan komai tsakanin mu, zata kasance yar aiki saboda baya son Saratu tasan tana da kishiya, kuma baya son asan alaƙar dake a tsakanin mu, shi kuma yaron mu baison kowa yasan da shi, saboda sadaukar da shi zan yi..." Kasa ƙarasa maganar ya yi idanunsa na tsiyayar da ƙwalla. "Ka zalunci kanka Praveen, meyasa lokacin da ya nemi ya jefa ka a gur6atacciyar harkarsa baka ƙi amincewa ba? Meyasa baka faɗa ma wani ba ko ka kaishi ƙara gurin hukuma? Kai wlh da dai irin wannan musibar ƙwara ka bari ya kashe ka kai da ƴar uwar taka sai ya fi maku kwanciyar hankali!" Cikin fushi ya ƙare maganar. "Kaima ka sani Owais, kakanka ya fi ƙarfina, wlh babu wanda zai yarda da ni koda na faɗa, kuma ban isa in gudu ba, bayan haka hada son abun duniya ne ya rufe min idona, amma ko a cikin Elders ni kaɗai ne mai rauni, ban ta6a kisan kai da son raina ba..." cikin ƙunci ya ƙare maganar tasa. "Owais ku taimaka mini, ku rufa min asiri, wlh na tuba, na yi danasanin hali irin nawa, na kuma yi danasanin sanin hajiya Saratu a rayuwata, saboda mahaifinta ne silar komai, Hajjaty bata da kowa in ba ni ba, ina jin kunyar tasan abun da na aikata.." Ya ƙarashe maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro.. Ko kaɗan Owais bai ji tausayin shi ba, amma ta wani wurin ya ɗan tausaya mashi saboda kakansa ne ummul aba'isin komai amma shima mai laifi ne. "Bayan kasan kai mai laifi ne, maimakon ka miƙa wuya cikin lalama, sai ka zagaya ta bayan fage, kaje ka ɗauki yar uwarka don ku gudu, da hajiya Saratu ta ritsa ku shine ka huce haushinka akanta, ka yi mata bugun kawo wuƙa, in ban da kai ɗin mugu ne, mara hankali, ba kai tunanin ƴa'ƴanka ba? Ita wadda ka cutar ba uwar ƴa'ƴanka ba ce? Koda ba don Allah ka aureta ba, baka tunanin wani hali ya'yanku zasu shiga? Wani irin uba ne kai mai son kai da zon zuciya?" Duƙar da kansa ƙasa ya yi, hawaye nata sintiri kan kuncinsa. "Ko kakanmu da ya kasance azzulami bai gudu ya bar ahlinsa ba, saboda soyayyar mu yasa shi miƙa wuya, kai fa?" Ya faɗa cikin 6acin rai. "Ka so ka kashe ta Allah bai nufa ba ta rayu.. " Gabansa ne ya faɗi a razane ya ke duban Owais.. "Bayan da ta ji sauƙi, mun faɗa mata mun kama ka zamu kawo ta gurinka don ta ɗauki fansar abun da ka yi mata, kasan me ta ce?" Jikinsa a sanyaye yake duban Owais.. Ipad ɗin hannunsa ya daddana, kafin ya juyo masa da screen ɗin ta, wata irin kunya ce ta lullu6esa ganin Hajiya Saratu a zaune kan gadonta, fuskarta duk tabo, video call ne Owais ya kira ta, tana kallon Pravin da ya muzanta ya kasa haɗa idanun shi da nata. Murmushi ta sakar ma shi, "Ka aure ni saboda dukiyata, da kuma sura ta ko? Dama masu iya magana sunce kwaɗayi mabuɗin wahala ne, yanzu wa gari ya waya Pravin? Kana tunanin makomarka kuwa? Mutum mai tarin zunubi irin ka, wlh ka mutu Praveen, ka kashe kanka da kanka, kana cikin musiba. Zafin cin amanar da ka yi mini, ya fi bugun da ka yi min raɗaɗi a gurina, na yi danasanin auranka, na kuma yi danasanin haifa maka ya'ya da har ka samu damar sadaukar da wasu azzalumi, kaima ka sani, nima ban ta6a sonka ba, na aureka ne, saboda makircin da ka ƙulla min don ka ci arziƙi, kuma ba zan rama ba, na yafe maka, ka ji da hukuncin da kotu zata yanke maka, da kuma abun da zaka taras a cikin kabarinka na sakamakon zunubin da ka aikata. Na tsaneka, kai ba abun a tausayamawa bane, mahaifin mu bashi ya jefa ka a halin da kake a ciki ba, saboda shi ba Allah ba ne da in ya ce ka yi abu ya zama dole ka yi, bayan haka, meyasa lokacin da ya yi maka ta yi baka fallasa asirinsa ba, ko da zai kashe ka ne ka ƙi amince masa, yanzu bala'en da kake a ciki ko mutuwa ba zata zama hutu a gare ka ba wlh. Praveen ka shiga uku! kana cikin musiba dumu dumu, ina taya ka murna sai mun haɗu a kotu. Ta ƙarashe maganar idanunta cike tab da ƙwalla tare da murmushin takaici akan fuskarta. Bai ta6a jin karayar zuciya da danasani irin na wannan lokacin ba, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba kamar ransa zai fita "Praveen yanzu ba lokacin kuka bane, lokaci ne da zaka fara tunanin menene makomarka! Ai ba ka ga komai ba, shawarar da zan baka shine, ka daure ka tanadi hawayenka, zuwa lokacin da alƙali zai yanke maku hukunci..." Yana kuka hadda majina ya ce, "Ki taimaka min Saratu! Ki taimaki rayuwana, in har da gaske kin yafe min ki sa baki, su yafe min su fitar da ni daga ciki, ko don albarkacin ƴa'ƴan mu, wlh na tuba, na bi Allah, na yi danasani zan sauya rayuwata, zan ma nisanta kaina da kowa..." Girgiza kai hajiya Saratu ta yi, "Praveen babu mafita, babu taimakon da zan iya yi maka, ka riga da ka jagula komai, kai koda zan iya fitar da kai Allah ba zai ƙyale ka ba, dole ka ga sakayyar rayukan da kuka zalunta, don haka ka yi haƙuri kawai ka girbi abun da ka shuka. Taimako ɗaya da zan iya yi maka shine zan roƙi yayyena, su bar Hajjaty ta ci gaba da zama cikin mu, saboda na tausaya mata bayan da na ji tarihin rayuwar ku, in sha Allah Hajjaty ba zata wulaƙanta ba, zamu zama danginta daga nan har ƙarshen rayuwarta, ba zata yi maraicin rashin wani nata ba.." ta ɗan dakata da yin maganar tana ɗan girgiza kan ta kafin ta ɗaura da cewa, "Ƴa'ƴan mu zasu kasance ƙarƙashin kulawar yayyena da kuma ni! Ba za su yi maraici ba, bayan da suka san komai da ka aikata sun tsaneka fiye da yadda suka tsani mutuwarsu, wlh da zasu ganka ido da ido da sai sun kashe ka har lahira, amma karka da mu, zan sama musu uba na gari wanda zasu yi alfahari da shi!" tana ƙarashe maganar ta katse video call din. Komai da suke tattaunawa, observers suna kallon su ta Computer ɗin su. Wata irin ƙara mai cike da baƙinci ya fasa, ya kama kuka kamar ransa zai fita, ya dinga yi ma Owais magiya akan su yafe masa kar su hukunta shi, ba laifinsa bane, baba Obie ne ya ja ma shi. Owais bai saurare shi ba, ya miƙe ya fuce daga cell ɗin, Har ya fita yana jiyo ihun da Praveen ke yi kamar zai fasa dodon kunnan sa. *On the previous days (kwanakin baya)* *HAJIYA ADAMA💔* Tana a zaune kan darduma jikinta sanye da hijab, wayarta dake ajiye kan gado ta fara ringing, saida ta kammala addu'o'in da ta ke yi ta miƙe cike da sa ran surukanta ne ke kira saboda ta yi kewar su. Ɗaukar wayar ta yi tare da duba sunan me kiranta, ƙanwarta ce Fatima, picking call ɗin ta yi, tana kara wayar a kunne ko sallama ba ta yi ba, muryar fatima ta katse ta da tashin hankali ta ce, "Aunty kin ji abun da ke faruwa?" "Wani abu ne kike magana akai fatima?" "Wai kina nufin bakisan badaƙalar da ake yi a cikin ƙasar nan ba?" Yamutsa fuska ta yi, "Look, kada ki ɗaga min hankali, kawai ki faɗa min menene?" "Hmmm, Aunty labari da ɗumi ɗuminsa, baya faɗuwa da baki, ki yi maza maza ki shiga social media ki gane wa idonki." Cikin sauri ta katse kiran, tana kunna wi-fi ta fara cin karo da labarai iri iri na Kurkukun ƙaddara, tun tana daga tsaye har ta fara ganin jiri jiri jikinta na 6ari ta zauna tana ci gaba da bibiyar labaran. Tiryan tiryan ta karance shi tsaf, hankalinta ya tashi matuƙa, ta razana ta kuma kiɗima, hotunan fursinonin ta buɗo tana duddubawa unexpected ta fara cin karo da video din Angel da Batool, zumbur ta miƙe tana zare idanunta, muryarta na rawa ta furta, "Bab...baby Angel! Angel!! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. !" Ruɗu ne yasa ta saki wayar ƙasa ta futo a guje ta nufi falo don ta faɗa ma Abdalla, tana shigowa ta iske shi zaune kan kujera sai kuka yake yi kamar ƙaramin yaro, zufa duk ta wanke jikin shi, ya tasa plasma tv a gaba yana ta kallon tattaunawar su Dg da manema labarai. Yama fita shiga tashin hankali, nufar shi ta yi, cikin rawar murya ta ce, "Mijina kaima ka gani ko? Yanzu nake ganin labarin da ya tada hankalina! Ka ga Unaisah da Taj suna a raye, kuma ka ji mummunar ƙaddarar da ta faɗa masu..?" Idanunta suka cicciko tab da ƙwalla ta zauna gefen shi, tare da dafa kafaɗar shi, sai kuka yake yana kallon labaran, jikin shi har wani jijjiga ya ke yi. Cikin shesshekar kuka ta ce, "Tun da har Taj da Unaisah suna a raye, wataƙil shima Uzair yana a raye, ya kamata mu tashi mu tafi gurin su..." Girgiza mata kai ya yi hawaye na sauka kan kuncin shi ya dubeta da idanunshi waɗanda suka kaɗa jawur, "Akwai abun da na daɗe ina 6oye maki, amma yanzu tun da asirin su ya tonu gaskiya ta yi halinta, nima zan bayyana maki komai..." Wani irin faɗuwar gaba ta ji, a dabarbarce ta furta, "Bana son ji, pls kada ka faɗamin in dai kasan ba alkhairi bane, ka barni kawai in ji da abun da ke damuna" Miƙewa ya yi tsaye. "Ya zama dole ki sani Adama.." miƙewa ta yi tsaye itama tana zare idanunta cike da fargaban abun da zai sanar da ita. "Kada kace min kana ɗaya daga cikin su!" Wani irin kallo ya ke yi mata "Bana ɗaya daga cikin su, amma akwai wani abu da ya ta6a haɗa ni da ɗaya daga cikin su, wanda ya yi silar samuwar arziƙi na!" Da tsawa ta katse shi, "Are you out of your mind! Abdallah me ka aikata? Waye ka sani a cikin su? Tayaya ya zama silar samuwar arziƙin ka ? Ko hakan na nufin kaima ka ta6a sadaukar da wani naka??" Sam ya kasa cigaba da magana saboda fargaban yadda zata ɗauki abun. "Kada ka ce min kaine ka yi silar 6acewar su Uzair!" Ta faɗa tare da kama kwalar rigar shi da hannayen ta dake ta kerma.. "Assalamu Alaikum." A kunnansu suka tsinkayi muyarsa, hakan yasa suka dakata da maganar da suke yi, Kusan atare suka dubi kofar falon jin muryar mutumin da suka daɗe basu ji ta ba, wani irin annurin farin ciki ne ya cika su duk da halin da suke ciki, har suna haɗa baki gurin furta "TAJUDDEEN." Yana a tsaye bakin kofar falo fuskarsa ɗauke da murmushin farin ciki ya amsa da na'am mommy Adama and My Only Uncle. Cikin sauri ta nufe shi, suka yi hugging din juna, ta ɗago tana shafa fuskarshi ta ce, "Taj, dama kuna a raye baku ta6a neman mu ba Taj?" Tsawon shekara bakwai! kasan irin neman da muka yi maku kuwa? Meyasa baka tuntu6e mu ba?" Ta faɗa fuskarta a yamutse, hawaye sai sintiri suke kan kuncinta, daga yanayin su ya fahimci sun ji komai. Matsowa kusa da Uncle Abdallah ya yi, da sauri ya rungume Taj kamar zai mayar da shi cikin shi.. Sai ya ji kamar ya haɗa jikin shi dana mahaifin shi Zaheer, saboda Uncle Abdallah madadinsa ne, shi kaɗaibne shakikin mahaifinsa kuma ɗan uwansa na kusa da ya rage masa a duniya. Haka Uncle Abdallah shima ya ji kamar ya rungume mahaifinsa Zaheer, sun yi kewar juna. "Alhamdulillah! Taj, ashe da rabon zamu gana da juna? bayan tsawon lokaci da muka neme ku muka rasa? Taj ka ga yarda ka manyanta? Ka ƙara girma ka yi kyau.." Ya faɗa bayan ya raba jikinshi daga na Taj ya dafe kafaɗunsa da tafukansa, idanunsu a cikin na juna, kamar yadda yake mamakin sauyawarshi shima haka yake mamakin tsufan da Uncle ɗin nasa ya fara. "Na yi kewarka Taj. Na ji komai da ya faru da ku, yanzu muka gama kallo a news." "Taj Ina Uzair? Ina Angel? Nasan suna a tare da kai." Hajiya Adama ce ta faɗa cike da ƙaguwa. Numfasawa ya yi tare da cewa, "Ku yi haƙuri na yi laifi da ban faɗa maku ba, amma nima bada son raina na ba, ya zama wajibi mu 6oye kanmu idan ba haka ba masu farautar rayuwar mu za su kashe mu ne, amma bamu manta da ku ba, kuna aran mu ko yaushe, mu ma mun yi kewar ku sosai." "Amma Taj, ko a waya ai ka kira ka sanar da mu kuna nan, kasan halin damuwar dana shiga na rashin ku?" "Uncle, Dg shine ya hana kowa yasan muna a raye, kuma shi ne ya taimaki rayuwar mu.." Jinjina kai Abdallah ya yi, "Allah ya saka masa da alkhairi, na ji dadin ganinka Taj, mu shiga ciki mu zauna, amma tayaya akai kasan inda muke?" Ya faɗa tare da ruƙe hannunsa ya nufi Sofa da shi, hajiya Adama tabi bayansu baiwar Allah duk ta ƙagu da ta ji ina Uzair ɗin ta.. Bayan sun zauna, Hajiya Adama ta shiga kitchen don ta hada mashi abun da zai ci, sai zumudi take yi.. Duk in ya kalli Uncle ɗin nasa sai ya ga kamar Uzair saboda kamannin shi dake a kan fuskarsa. "Taj, ka yi haƙuri ban baka kulawar da ya dace ba, gani nake kamar komai da ya faru laifina ne Taj, zamana Korea bai amfanar da ni komai ba, da a ce ina kusa da ku wataƙil da hakan bai faru ba.." Ya faɗa tamkar zai fashe da kuka. A hankali Taj ya ɗaura tafin hannunsa kan kuncinsa ya soma share masa ƙwallarsa. "Pls Uncle mu manta da komai da ya faru, tunawar baida amfani.." "Taj, ba zaka gane ba, akwai damuwa a tare da ni, ina jin ciwon abun a raina.." Ruƙo hannayensa Taj ya yi, "Uncle, nima na fahimci halin da ka ke a ciki, nasan bai wuci akan ɗan uwana uzair bane ko?" Maimakon ya amsa mashi tambayar shi sai cewa ya yi. "Baka bani amsa ta ba, tayaya kasan inda muke da zama?" Ya kuma tambaya. Murmushi Taj ya yi, "Anila ce ta tura min da address naku." "Masha Allah, ashe kun haɗu da ita" Jinjina kai ya yi, "Eh..." Bai ƙare maganar ba, Hajiya Adama ta shigo falon hannayenta ruƙe da tray na kayan abinci ta ɗaura akan c-table. "Nagode mommy, har yanzu kina nan yadda na sanki." Murmushi ta yi kawai. "Bari na ɗanɗana girkin mommyna na yi missing na shi." Murmushi suka saki suna kallon shi yayin da ya soma cin abincin sai santi yake yi masu, in ya yi wani abun sai ya dinga tuna masu da Uzair, ɗabi'unsu iri ɗaya sak.. Bayan da ya kammala ci, ya maida hankalinshi akan su. "Taj, har yanzu baka amsa min tambayana ba? Ina Uzair?" Haɗa ido suka yi da Abdallah, da kai ya yi masa alamar kar ya faɗa mata, dubanta ya yi in a cool voice ya ce, "Mommy, lokacin da abun ya faru ba a tare da Uzair muka bar gida ba..." A taƙaice ya labarta mata komai da ya faru bai dai faɗa mata game da irin mutuwar da uzair ya yi ba. Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, sun shiga damuwa sosai, kwantar masu da hankali ya shiga yi. "Yanzu haka Angel tana a tare da mommynta a gidan dg.." "Taj, komai da muka ji game da kurkukun kaddara da gaske ne? Don ni wlh ji na yi kamar shirin film ne ko irin hausa novel, saboda yadda kaina ya ɗaure, ko a tarihi ban ta6a jin labarin da ya ta6a zuciyata irin shi ba." hajiya Adama ce ta tambaya tana kallon shi, Jinjina masu kai ya yi cike da tabbaci ya ce, "da gaske ne komai da kuka ji" "Meyasa ba ka zo mana da Unaisah ba?" "Zuwa nan gaba in sha Allah zan zo maku da ita har ma da mommynta" Tun da suka fara magana Uncle Abdalla bai sanya baki ba, gaba ɗayansa babu walwala a tattare da shi, Taj ya lura da yanayin shi. Firar yaushe rabo suka yi cikin raha da annushuwa.. Kiran sallar azhar da aka fara yi ne ya katse masu firar ta su.. A tare da Uncle Abdallah suka tafi Masallaci.. Hajiya Adama ta zauna tana ta jiran su dawo, burinta ta ji menene Abdallah yake son sanar da ita? duk da tana jin zullumi da fargaban abun da zata ji. Bayan da suka dawo daga masallaci, Uncle Abdallah ya ruƙe hannun Taj ya ja shi suka zagaya daga bayan gidan, kan kujerun shaƙatawa suka zauna suna fuskantar juna.. "Taj, na ji dadi da Allah ya bayyana mun kai da ranka da lafiyarka, tsawon lokaci ina addu'a akan Allah ya bayyana min ku cikin ƙoshin lafiya.." Murmushi taj ya yi, ya ji daɗin maganarsa. "Nima haka Uncle, na ji dadi dana same ku da ranku da lafiyarku, na yi farin ciki mara misaltuwa.." Shuru suka ɗan yi na wani lokaci Taj ya lura da yanayin fuskar Uncle din nasa.. "Uncle, na fahimci akwai abun da ke damunka, kuma akwai abun da ka ke son faɗamin tun zuwa na na lura da hakan, don Allah ka sanar dani.." Shuru ya ɗan yi jimm kamar yana jin shakkun ya faɗa "Tajo, ina so ka fara fadamin gaskiyar meya faru da ku! Uzair yana a raye ko ya mutu? Pls kada ka 6oye min, ni ba yaro bane, kafin wannan anyi min rasuwa, na rasa iyayena da yayana mafi soyuwa a gare ni, a yanzu babu abun da bazan iya jurewa ba, saboda na yi imani da ƙaddara" Jinjina kai Taj ya yi, kalamansa sun sa shi jin zai iya faɗa masa.. A tsanake ya labarta masa komai da ya faru lokacin da Uzair ya kira sa a waya cikin tashin hankali ya sanar da shi abun da ke faruwa da shi, bai dai ce sun ƙona Uzair ba, amma ya ce mishi su yi haƙuri su fidda rai da Uzair saboda babu shi a raye, shekara bakwai da rasuwarsa yanzu." Girgiza kai Uncle Abdallah ya yi idanunsa sun ciko tab da ƙwalla, ya ji zafin mutuwar Uzair dama saida ran shi ya bashi baya a raye, wani baƙin ciki ne ya mamaye zuciyarsa, dafe kansa ya yi da tafin hannunsa yana tariyo rayuwar sa da ɗansa mafi soyuwa agare sa, yanzu shike nan ya rasa Uzair babu shi a doron duniya? Uzair ya mutu? Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Ya faɗa a cikin ran shi. Taj da ke kallonsa jikinsa ya yi sanyi da ganin halin da Uncle din nasa ya shiga. "Ka yi haƙuri Uncle, nasan dole ka ji zafin mutuwar Uzair.." Bai ƙare maganar ba, Uncle abdallah ya katse shi cikin raunanniyar murya ya furta, "Bakomai Taj, dukkan mai rai mamaci ne, nagode daka faɗa min. Allah Ya jiƙan Uzair, Allah ya gafarta masa, Allah ya kai rahama ƙabarinsa." Amsa masa ya yi da ameen ameen, "Su kuma waɗanda suka yi silar mutuwar shi Ubangiji Allah Ya wulaƙanta rayuwar su, in sha Allah zasu ga sakayyar abun da suka yi masa.." Shiru suka yi jigum kowa da damuwa a cikin ran shi. Har na tsawon mintuna babu wanda ya tanka a cikin su. "Taj, dagaske kun kama Elders kamar yadda na ji a labarai?" Jinjina mashi kai ya yi, "Hakane Uncle, mun kama su, yanzu haka suna a cikin cell na headquarter ɗin mu." "Alhamdulillah, na ji daɗi da Allah ya fallasa asirin su. Don Allah Taj kada ku raga musu, ku azabtar da su har sai sun tsani rayuwar su..." Murmushi Taj ya yi, "kar ka damu Uncle, yanzu haka idan ka gansu saika tausaya musu saboda raunukan dake a jikin su.." Ya faɗa da zolaya, wani kallo Uncle Abdallah ya yi masa. "Allah Ya kiyaye inji tausayin su, ai sai dai ma inyi masu Allah shi ƙara.." Ƴar dariya Taj ya yi. "Idan muna fira da kai, sai in ji kamar yayana ne Zahir saboda komai naku iri ɗaya, na yi rashi Taj, Allah ya jiƙan shi da rahama." Zuciyar Taj ce ta karaya tunawa da mahaifin nasa, "Ameen" ya amsa.. "Allah Ya jiƙan Yahanasu da mama, Allah Ya kyautata makwancinsu." hawaye ne ya ji sun ciko idanunsa. Amsawa ya yi da, "Ameen don son Annabi." Shiru suka yi na wani lokaci, still ya lura da akwai abun da Uncle ɗin nasa yake son sanar da shi, kamar yana jin shakkar fitarwa ne. "Uncle, idan akwai abun da kake son faɗa min pls kada ka ji komai ka sanar da ni, a yanzu bani da tamkarka kaima haka." jinjina kai Uncle Abdallah ya yi, "Ka faɗi gaskiya Taj, da akwai abun da nake son sanar da kai, duk da ina jin fargaban yadda zaka ji abun a ranka, amma zan sanar da kai saboda inaso ka taimaka min, ita kaɗai ce damar da nake da ita." ya ɗan numfashi kafin ya ɗaura da cewa, "Shekarun baya da suka gabata, Hajiya Adama ta ta6a yin matsananciyar rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da likitoci suka duba ta sai suka gano ta samu matsalar da sai anyi mata tiyata zata samu lafiya, kuma in har ba ayi saurin yi mata ba zata iya rasa ranta, ni kuma a lokacin bani da halin da zan iya biyan kuɗin da suka buƙata, bani da wani wanda zai tallafa min saboda iyayen mu ba hali gare su ba, yayana ma baida kudin da zai iya taimaka mun da su, shima fama yake yi da iyalin sa, ita ma haka iyayenta ba masu ƙarfi bane, hasalima talakawa ne sosai, ko kafin in aureta nasha wahala saboda basa bama talaka auren ya'yan su sai masu arziƙi, sun mayar da su kamar jarin su saboda Allah ya yi su da kyau. Taj ba irin wahalar da ban sha ba gurin fafutukar neman kuɗin da zan biya a yi mata aiki, amma na kasa tara adadin kuɗin da suke buƙata, ranar da na koma asibitin don duba lafiyarta, sai na tarar babu ita a ɗakin da suka kwantar da ita, ko da na tambayi nurses sai suka ce kuɗin gadon da muka biya sun ƙare, in har ina so su mayar da ita dole saina biya wasu kudin. Hankalina ya tashi matuƙa, na shiga nemanta, da ƙyar na ganota a bakin wata bishiya ta asibitin kwance a ƙasa, sai kuka take yi ta daddafe cikinta, wasu bayin Allah ne suka kewayeta suna tambayarta ina ƴan uwanta? Wa ya kawo ta asibitin? Bata da kowa ne.? Cikin sauri na je na daukota na koma da ita asibitin, na dinga roƙon su akan su taimaka mini su mayar da ita zan biya kudin zuwa gobe, da ƙyar na samu suka amince zasu mayar da ita, amma suka gargaɗe ni akan in har ban kawo ba zuwa gobe, babu wani uziri da zasu kar6a daga gare ni, bayan da suka mayar da ita kan gado, na baro asibitin na fara tunanin me zan siyar dan in biya kuɗin aikin nata? Na duba na hango bani da komai, a lokacin ko gidan kaina ban mallaka ba, a gidan haya nake da zama, kadara ɗaya da nake da ita, mashin ɗina, a ranar da nake shirin zuwa in siyar da shi, kwatsam sai ga kira ya shigo wayata da baƙuwar number. Da farko ƙin ɗagawa na yi, anata kira sai daga baya na yi picking na kara a kunne tare da yin sallama. Mutumin ya amsa min bayan mun gaisa na tambaye shi wanene saboda bangane me magana ba, na ga baƙuwar number. Yace min eh dama yasan bazan gane shi ba, saboda ban san shi ba, amma shi ya sanni, maganar gaskiya ya ganni a asibiti ne, shima a lokacin ya je duba marasa lafiya, dama ya saba zuwa bada tallafi a asibitin, toh ya ji komai dake faruwa hatta matata da suka sauke daga kan gado duk yana a wurin yana bibiyar mu saboda mun bashi tausayi, shiyasa ma har ya kar6i contact ɗina agurin nurse. Na ce Allah sarki, na gode sosai da nuna damuwa akan mu. Ya tambaye ni na samu kuɗin da zan biya kudin aikin nata ne? Nace masa a'a, ban samu ba, yanzu nake shirin zuwa in siyar da mashin ɗina duk da kona siyarma ba isa zasu yi ba, amma inason in fara biyan rabi don suyi mata aikin daga baya na cika. Yace min kar a yi haka, idan na siyar da mashin dina ni kuma da me zan dinga yawo? Ina ma amfanin siyarwar bayan kuɗin ba isa za su yi ba, abun da za'a yi shi zai biya kudin komai harma da jari zai bani." Na yi ƴar dariya na ce nasan ma wasa yake yi min, saboda nasan babu mai iya yi min wannan taimakon, duba da yadda taimako ya yi ƙaranci." Yace min wallahi da gaske yake yi, idan ina so in tabbatar da abun da yake faɗa zai bani address dinsa in neme sa.." Bayan mun yi sallama da shi, sai ga saƙon address ya shigo wayata, a lokacin hankalina bai kwanta da shi ba saina ƙi neman shi, bayan da na tafi kasuwa don siyar da mashin ɗina aka rasa samun wanda zai siye shi da daraja, sai tayin wulakanci da ake yi min, ga shi lokaci yana ta gudu har marece ya yi ina ta neman wanda zai siya da kirki ban samu ba, a ƙarshe na sha wahalar banza na dawo gida, da na ga bani da mafita saina yanke shawarar kiran mutumin don in faɗa masa zan zo. Bayan mun yi waya, na shirya na tafi gidan da ya yi min kwatance. A falo muka zauna ni da shi, ban iya ganin fuskarsa ba saboda ya saka mask, ya kuma sanya glass a idanunsa, bayan mun gaisa na gabatar masa da kaina. Ya ce min ai ya gane ni, kar inji komai in saki jikina, ba kaina ya fara tallafawa marasa ƙarfi ba, ya saba zuwa asibiti duba marasa lafiya har ma ya biya kuɗin jinyar su, da ya faɗi hakan saina ji hankali na ya kwanta sosai, ya ce min sai dai ya ji kuɗin da za'a yi mata aikin suna da yawa, zai biya rabi kyauta amma rabin zai bani a matsayin bashi, cikin sauri na ce na amince amma idan har yana da aikin da zan yi masa ya faɗa min in ya so cikin kuɗin aikin sai ya dinga zare bashin da ya ke bina. Ya yi murmushi ya ce min bashi da aikin da zai bani amma in har na amince zan bashi duk abun da ya ke so a matsayin biyan bashin toh zai bani. Na ce masa bangane me yake nufi ba? Ya ce min kar in damu ba wani abu bane, kawai yana son mu yi yarjejeniya in har ya bani kuɗin komai ya buƙata zan bashi. Da ya ke a buƙace nake na amsa mashi da na amince in dai ina da abun, nan take ya shiga ɗaki ya dauko jaka ya miƙa min tare da cewa in ɗauka miliyan biyar ne a ciki, na ruɗe a lokacin na ce masa sun yi yawa bazan iya kar6a ba, kuma bani da hanyar da zan iya biyan shi, sai dai ya rage ya bani daidai kuɗin da nake buƙata, ya ce dama ce a gare ni, in yi amfani da ita tun kafin in rasa, da jin haka sai na yi masa godiya , daga bisani muka yi sallama na tafi. Washe garin ranar, bayan da na je asibitin na biya kudin aikin ta. Cikin sa'a bayan an yi mata aiki ta ji sauƙi kamar bata ta6a yin ciwo ba, bayan da suka sallame mu muka dawo gida, ban ta6a faɗa mata game da yarjejeniyar kudin dana kar6a bashi ba. Taj wlh sai da nayi danasani, ni bansan da mugun nufi ya shiga rayuwata ba, ban yi bincike akanshi ba, saboda kuɗin nake cikin buƙata bani da yadda zan yi Taj, tun bayan da ya ban kuɗin ban ƙara jin ɗuriyar shi ba, nama manta da batun bashin da na ci, da kudin na fara neman na kaina ina ɗan ta6a kasuwanci harma na samu aiki a companyn kasuwanci. Lokaci ɗaya Allah ya buɗe min kofofin samu, na mallaki gidan kaina, na sayi mota, a lokacin Uzair ya zama matashi na dawo da kai gidana, kwatsam! wata rana sai ga kiran mutumin nan ya zo yasa akai masa sallama da ni, bayan na fito na yi mamakin ganinsa still fuskarsa da takunkumi, bayan mun gaisa na yi masa iso muka shiga ciki, a bayan gidana muka zauna ya ce ya ji shiru kona manta da bashin shine, nace masa ban ta6a mantawa ba, da abun nake kwana a raina, saboda ina son in sauke hakkinsa dake a kaina, don haka yanzu tun da mun haɗu ya faɗamin da me zan biya shi? Da buɗar bakinsa sai cewa ya yi, "Ƴa'ƴa yake so in biya shi da su." Na yi zaton zolaya ta yake yi, na yi dariya na ce don Allah ya daina zolaya ta, mu yi magana ta gaskiya, da me zan biya shi bashin, ya kuma ce min rai yake so, dana fahimci dagaske yake sai na ce masa ai ba a biyan bashi da rai, ban ta6a ji ba, kuma ni ban da ran da zan biya da shi, bama zai ta6a yiwuwa ba, in dai zan biya sa sai dai in biyasa da abun da ya bani ko ya fadi wani abun daban! Girgiza kai ya yi da kakkausar murya ya ce, "Na manta yarjejeniyar mu ne? Idan nasan ba zan iya bashi abun da yake so ba meyasa na kar6i kuɗinsa?" Raina a 6ace na ce, "Amma dai malam baka da hankali ko? Kawai saboda ka bani bashin kudi sai ka ce in baka rai? Kamar wani ran kaza? To wallahi bazan bayar ba, komai zai faru sai dai ya faru, a ina aka ta6a haka? Kudi sun isa su sayi darajar rai ne.. !" Na gaggaya masa maganganu cikin bacin rai saboda naga rainin wayon nasa ya yi yawa, cikin fushi ya ce oh shi zan ma butulci? Bayan halaccin da ya yi min? dama ba a gane halin talaka sai ya yi kuɗi, wato yanzu na samu bakin gaya masa magana ko? Ba don shi ɗin ba ai da yanzu na rasa matata, amma shike nan zai tafi amma fa in sani zan biya abun da na yi masa. Bayan fitarsa, abun ya dame ni, na yi ta tunanin meyasa yake son in biya shi bashi da rai? Me zai yi da ƴa'ƴa? Gashi dai da hankalinsa ba mahaukaci bane balle in ce ko ya samu ta6in hankali ne, can kuma raina ya bani ko dai irin waɗanda basa haihuwa ne waɗanda Allah ke jarabtarsu da son ƴa'ƴa. Da sauri na bi bayan shi, a lokacin yana kokarin shiga motarshi na dakatar da shi na tambayesa meyasa ya ke son ya'ya? Cikin karyayyar murya ya ce, Saboda rashin da ya yi, a lokacin baya yana da mata ɗaya da ƴa'ƴa biyar, sanadin haɗarin jirgin sama ya rasa su, shi kuma a lokacin ya samu matsalar haihuwa yanzu haka yana da aure amma bai ta6a samun haihuwa ba, yana son ya'ya sosai. Na tausaya mishi na ce mashi indai haka ne meyasa ba zai je gidan marayu ba ya yi adopting, sai ya ce min baya son ruƙon maraya yana da wuya, kuma yawancin su basu jin magana, shi yasa ya fi son waɗanda suke da iyaye, jarirai da zasu raina shi da matar shi, in yaso daga baya idan Allah Ya sa ya samu warakar lalurarsa zai mayarwa mai su, shiyasa ya bani bashin nan saboda yana so in taimaka masa in share masa hawayensa, har kuka sai da ya yi min. Taj tausayin sa ne ya cika zuciyana, har bansan sa'adda na ce masa na amince da yarjejeniyar mu, a lokacin ban san meke damuna ba, idanuna sun makance burina kawai in taimake shi, ji nake in har ban taimaka masa ba, zan iya rasa raina.. " Taj da ke sauraron sa tsantsar ruɗani ne akan fuskar sa. _"A lokacin nasan idan na faɗa ma hajiya Adama ko wani daga dangina ba zasu yarda ba shiyasa na yi shiru da baki na, a lokacin baku cika zama gida ba kuna zuwa makaranta. Sau biyu Adama tana haihuwa ina sace jariran tare da haɗin bakin mutumin da likitansa, bata ta6a sani ba, sai dai ta ga ta haifi jariri ya zo babu rai, likitansa ne ke yi masu allurar da zasu yi kamar sun mutu, babu wanda yasan lokacin da muke aiwatar da hakan..."_ To fa!Kallo ya koma sama, hankalin Taj idan ya yi dubu toh ya tashi, tsantsar al'ajabi ne ya kama sa! A ransa ya ayyana ashe kurkukun ƙaddara bai bar kowa ba! Abun ya zo har takan Uncle dinsa!" "Ƴa'ƴa biyu na bashi, mace da namiji, a lissafina yanzu namijin zai kai shekara ashirin, macen kuma ba zata wuce shekara sha takwas ba idan suna a raye, Taj kamar bani da hankali, ban ta6a sanin gidansa ko wani nasa ba, yadda kasan an rufe min bakina na kasa tambayarsa hakan, wallahi ko fuskarsa bansani ba, kullum da takunkumi nake ganin sa, a duk lokacin da na yi yunƙurin tambayarsa game da hakan sai in ji kamar an kulle min baki na..." "kuma tun bayan da na bashi ya'yan ban ƙara marmarin in waiwaye su ba ko in tuntu6i mutumin in ji wani hali suke a ciki, gaba ɗaya namanta da babinsu, har tsawon shekaru, sai daga baya ne a lokacin kun 6ace babu ku, muka shiga mawuyacin hali na buƙatar ƴa'ƴa, ga hajiya Adama ta daina haihuwa ko 6ari bata yi har asibiti muke ja docs suka ce matsala ta samu a mahaifarta ba lallai ta sake haihuwa ba, daga ni har ita mun shiga matsananciyar damuwa, na fi jin tausayinta saboda ni na cuce ta, na bayar da ya'yanta batare da sanin ta ba, ina jin fargaban ta ji maganar nan, nasan har rabuwa zata iya yi da ni, ni kuma banason duk wani abu da zai raba ni da ita. Taj lokacin da tunanin mutumin ya dawo min akaina, a lokacin na yi arzikin da zan iya biyansa kaf kuɗinsa harma da ƙari batare dana girgiza ba, na sha kiran layinsa baya ɗagawa, har saƙonni na tura masa baya min reply, har na fidda rai da zai ɗaga kira na, unexpected wata rana ina ƙara jaraba kiran shi ya ɗaga, (Idan masu karatu zasu iya tunawa, a kwai lokacin da Hajiya Adama ta yi ma Abdallah la6e yana waya a ɗakinsa har ta jiyo shi yana yin waya da wani mutumi, bari mu tariyo wayar da ya yi a wannan lokacin👇) "Ka yi haƙuri nasan ba haka mukai da kai ba, na sa6a alkawari amma ka dubi halin da nake a ciki, lokaci ɗaya na rasa ɗana bayan haka na rasa ɗan yayana tare da ƴarsa, na rasa yayana da kakata, kai kaɗai ne zaka iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kuɗin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su in dai suna a raye na ƙwammace na ƙare rayuwata a talauci akan in ci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..." Muryarsa a marairaice ya yi maganar kamar zai yiwa mutumin da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya. *Cigaban labari* "Na rasa ya zan yi Taj, nasan na cuci kaina, na kuma cuci yaran dana basa, bansan me ya yi da su ba, saboda ina zargin komai da ya faɗamin game da labarinsa ƙarya yake yi min, damfarata ya yi, kuma ba hakanan ya ƙyale ni ba. Ban tashi gane hakan ba, sai yau da na kalli news na ji labarin kurkukun ƙaddara da fursinonin cikinsa sai na dinga ji araina da wuya in mutumin nan ba yana a cikin matsafan ba, duk da bani da tabbaci, amma in har ya tabbata za'a iya samun yaran in suna raye.." ya karashe labarin da hawaye a cikin idanunsa. Numfasawa Taj ya yi cike da tausayinsa a cikin zuciyarsa ya ce, "Uncle na fahimci damfararka ya yi, kuma ya gusar maka da hankalinka daga tunaninsa da ya'yanka, babu tantama zai iya zama cikin matsafan.." Cikin sanyin murya ya ce, "Taj, tayaya zamu iya sanin idan yana a cikin su? Tayaya ma za a iya gane yaran nawa idan suna a raye, bayan koni bansan kamannin su ba?" "A labarin daka bani baka faɗamin sunan mutumin ba"? Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya ce, "Sunansa dana sani wanda ya ta6a faɗa min Alhaji Ja'afar Dila." Jinjina kai Taj ya yi tare da kwantar masa da hankali ya ce in sha Allah zai yi magana da Dj, idan ma yana a cikin su za su gano shi, zai yi iya ƙoƙarinsa saboda shima yana son yaran ko dan ya samu cousins ɗin da zasu maye mashi gurbin Uzair" Abdallah ya ce yana son su bar maganar nan a matsayin sirri tsakanin su, ko mutuwar Uzair baya son hajiya Adama ta sani, yafi son sai sun samu mutumin nan da ƴa'ƴansa sai su faɗa mata komai, yasan koda zata ji zafi ba za ta yi fushi da shi ba, zata yafe masa saboda tana da haƙuri kuma tana son shi sosai. Abun da basu sani ba, gaba ɗaya firar da suka tattauna a kan kunnan Hajiya Adama da ke yi musu la6e, kuka mai cin rai ta ke yi, ta toshe bakinta da tafukanta duk don kada sauti ya fito su jiyo ta, sai da taga sun miƙe ta watsa da gudu ta koma cikin gidan ta shiga toilet, ta wanke fuskarta don kar su gano ta, baiwar Allah ta ji zafin mutuwar Uzair sosai, ƙunci da baƙin ciki suka mamaye zuciyarta, ta dinga karanta addu'o'in neman sassauci a cikin zuciyarta, kwata kwata bata ji haushin abun da Abdallah ya yi mata ba, duk da bai kyauta mata ba da ya 6oye mata ya'yanta da ya bayar, kamar baisan irin yadda mata ke shan wahalar naƙuda kafin su haihu ba, wata tara ta raini ciki, ya dauka ya ba wani? Batare da sanin ta ba? Kamar ta ce masa batason ƴa'ƴan! Amma ta yi masa uziri saboda ta fahimci mutumin yaudararsa ya yi kuma hada asiri ya yi ma shi, bayan haka komai ya yi saboda son da yake yi mata ne, fatanta Allah yasa su gano mutumin nan don ya basu ƴa'ƴan su, Allah yasa suna a raye shi kaɗai ne hope ɗin da take da shi a yanzu. Kafin tafiyar Taj saida suka shigo ciki, ta fito suka ƙara ɗan ta6a hira cike da ƙarfin hali, kafin suka rako shi har bakin motar shi ya yi masu sallama, suna ta ƙara tuna mashi suna son ganin Unaisah ya ce zai kawo masu ita in sha Allah. Bayan da ya tafi ko bayan da suka koma cikin gidan hajiya Adama bata bari Abdallah ya gane ta ji komai ba, a 6oye take shan kukanta, tsoffin hotunan Uzair ta dinga ɗaukowa tana kallonsu, da su take kwana da su take ta shi.. ~__________________________________🔥💫~ A bangaren Natasha kowa ya manta da batun ta saboda halin da suka shiga, amma kullum ne sai chef ɗin da dg ya ba ɗawainiyar kula da ita ya je kai mata abinci sau uku a rana, daga bisani dg ya kira Ummi ya damƙa mata wasiƙar Unaizah da ya kar6a a hannun Unaisah, ya ce ta kai ma Natasha sannan ta faɗa mata wanene Musa, da kuma miyagun ayyukan da yake aikatawa. Bayan da Ummi ta je ɗakin bata saurari haukan Natasha ba, ta zauna ta fyaɗe mata komai game da Musa tun daga biri har wutsiyar sa, Ya salam! Natasha ta razana sosai, hankalinta ya tashi matuƙa, ta ji baƙin ciki da takaicin cin amanar da Musa ya yi mata, sai yanzu ta gane dalilin da yasa baya son ta san kowa nashi, ta daɗe tana mamakin dukiyar shi, saboda baya gajiya da basu kuɗi ita da Unaizah, ashe ba mutumin kirki bane ɗan blood cults ne, ba komai ya fi karya mata zuciya ba, face sadaukar da Unaizah da ya yi, ashe kwata kwata Natasha batasan inda ya kai Unaizah ba, ya 6oye mata komai, ita a yadda ya faɗa mata gurin mommynta zai mayar da ita, ita kuma Unaizah ya yaudare ta da sunan zai kaita korean school. Abun da ya faru a lokacin da zai sadaukar da Unaizah, Natasha bata a ƙasar, batasan komai ba, sai dai ta dawo ta taras da babu Unaizah agidan ta. Natasha ta yi kukan baƙin cikin da bazan iya misalta shi ba, a lokacin da Ummi ke bata labarin yadda Unaizah ta ƙare a gidan kurkukun ƙaddara, ta yi danasanin ƙulla alaƙa da Musa, ta tsane mashi sau ba adadi, gaba ɗaya ta ji rayuwar duniya ta sire mata, musamman da ta karanta wasiƙar Unaizah da Ummi ta bata, baƙin cikinta Unaizah ta mutu da tunanin harda ita Musa ya ci amanarta, bayan ita batasan komai ba. A ranar saida Ummi ta yi tunanin Natasha bazata rayu ba, saboda yadda ta dinga fasa ƙara tana fitar da gumi akan fuskarta, ta dinga lallashinta tana roƙonta akan ta yi haƙuri abun da ya faru ya riga da ya faru, yanzu haka Musa yana a hannun hukumar Isod zasu kai shi kotu, amma ina Natasha ba ta fahimtar komai... ~___________________________________🔥💫~ *ISOD HEADQUARTER* *DG OWAIS💪🔥* Yana a tsaye gaban ƙofar shiga Cell, a hankali yake danna code ɗin ƙofar, bayan da ta buɗe ya shiga daga ciki, Wa zan gani idan ba Ɗan iya ba, Yana a kwance kan floor kamar mushen jaki, warinsa ya cika cell din, 6arin mazaunansa ya ƙone fatar duk ta sa6ule jawur ba ƙyan gani, sakamakon ƙonewar da ya yi, badan ana yi mashi treatment ba da tuni naman wurin ya ru6e, amma da yake basu son su mutu sun fi so su fara girbar abun da suka shuka tun a gidan duniya shiyasa suke duba lafiyar shi, kwata kwata babu gashin gemunsa ya ƙone ƙurmus, yatsunsa duk sun lankwashe sun ƙone, ko sutura babu a jikin shi sai ɗan pant ƙarami irin na mata, sai nishin azaba ya ke saki, daga gani yana jin raɗaɗi ba kaɗan ba, cikin fitar hayyaci ya ke yin sambatu yana fadin, "Wayyyo Allah na, Wayyo na shiga uku na baniiiii, na baniiii, na baniiiiii na lalace, jikina zafi, ku sosa min bayana, ku sosa min ɗuwawuna ƙaiƙayi nake ji, ku cire min ciwon jikina, zan mutu..." Girgiza kai Owais ya yi ko kaɗan bai ji tausayin shi ba. A hankali ya zauna kan kujera tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana kallon shi. "Baka ga komai ba Dan Iya, wannan somun ta6i ne na daga azabar dake tunkaro ka, ko ka manta rayukan da kuke ƙonawa da fetur? Ya ka ji raɗaɗin na raunin jikin ka?" Da ƙyar ya iya juyo da kansa ya dubi Owais da idanunsa da suka kaɗa jawur kamar jan gauta, hancinsa sai tsiyayar da tsinkakkar majina yake yi gwanin ban ƙyama. Ƙaton le6en nan nasa ya ƙonu da wuta ya yi sumtum kamar ganda. Daga gani yana jin azabar radadi ta ko'ina a jikin shi. Muryarsa ma bata fita, guragura ya ke magana.. "Ba dati, na tuba, ku min rai, na gane kushkurena, Ku kai ni asibiti su cire min ciwon jikina, su canza min wata fatar, don Allah..." Ƙyalƙyacewa da dariya Owais ya yi, duk da ƙyanƙyaminsa da yake ji, maganarsa ta bashi dariya. "Sai da Lokaci ya ƙure maka, ka ga asirinka ya tonu baka da mafita tukunna zaka tuba? La'anannen Allah, azzalumi mai safarar ƴa'ƴan mutane ya kai su inda za'a azabtar da rayuwarsu, tayaya kake tunanin mu zamu yafe maka? In banda ma kai ɗin wawa ne jaki, kamar yadda baku da imani baku da tausayi, kuma baku iya yafiya ba, muma haka jami'ai muke akan mugaye irin ku, bamu da tausayi, idan muka fara azabtar da su sai sun ɗanɗani kuɗar su.." ya ƙarashe maganar cikin fushi tare da bugun gaban table ɗinsa. Fashewa da kuka Ɗan iya ya yi, nan take ya fara 6urkuta tusa da fitsari daga kwance, DG ya yi saurin zaro hanky daga aljihunsa ya toshe hancin shi, cike da jin ƙyanƙyami ya furta, "Abun ƙyama, yanzu ina tsafin nan naka? Da bakin ka? Suna ina? Ko zasu iya taimakon ka?" Ya faɗa yana ɗage masa gira. Fashewa ya kuma yi da wani kukan, bakinsa har ya fara fitar da jini, "Ka daina bana son ji, ka rabu da ni inji da abun da ke damuna, ka kira min matata da ya'yana su zo suga halin da nake a ciki..." "Su yi maka uban me idan sun zo? Ka yi tunanin kana da wani dangi ne da ya rage maka? Matarka da ya'yanka sun ji komai da ya faru, sun tsanake saboda ka ja masu abun kunya, ka bar masu mummunan tabo a matsayin gadonsu, wulaƙantacce! ....." Alkalamina bazai misalta tashin hankalin da Ɗan iya yake a ciki ba, wata irin wutar baƙin ciki ce ke ci a cikin zuciyar shi. "Ban zo don na sawwaƙe maka radadin da kake ji ba, na zo ne don in tambayeka menene alaƙarka da Abdallah Muhammad Buzu, kuma su wanene ƴa'ƴansa daka sadaukar a kurkukun ƙaddara? Kada ka ce zaka yi min ƙarya! na riga dana san komai, kaine mugun da ya damfare sa ya kar6e masa jarirai har biyu!" (Abun ka ga jami'i mai kaifin basira, bai nuna hasashe yake yi akan shi ba, saboda yasan ɗan iya shine leader na bangaren safarar ya'yan mutane na nan Nigeria zuwa kurkukun ƙaddara. Bayan haka salon yadda yake damfarar mutane ya 6oye fuskarsa da mask ya yi shige da mutumin da malam Jazuli ya bada labarinsa, uwa uba sunan da Abdallah ya faɗa a matsayin sunan sa wato Ja'afar Dila, toh Ja'afar din asalin sunan shi ne da ba kowa ya sanshi da shi ba, saboda nickname ɗinsa ya boye asalin sunan sa, ta haka Owais ya gane shine ya damfari Uncle Abdallah, bayan da Taj ya labarta masa komai." Mugu da yake shaiɗaniyar zuciyar na nan, yana huci yace, "Banshan wa kake magana akai ba, ni banshan wani Abdallah Muhamamd buzu ba, babu wasu ya'ya nashi dana sadaukar, duka ƴa'yan nawa ne." "Kada ka yi min ƙarya, ka duba halin da kake a ciki, wlh in baka faɗamin gaskiya ba zansa a shafa maka ruwan attarugu a jikin ka.." Yawu ya haɗiya yana faman zare na mazurai ya ce, "Na san shi, shima member ne na kurkukun ƙaddara, shi ya sadaukar da ya'yan shi da kan shi, bani na sadaukar mashi da ya'ya ba, na rantse maka da Allah ban damfare sa ba..." Cikin fushi Owais ya ce, "Ba zaka daina yi min karya ba? Ko so kake in aiwatar da abun da na fada?" Ya ƙarashe maganar tare da kanga wayarsa a kunne, "Ku shigo min da ruwan attarugu cikin cell din Ɗan Iya..." Tunkan ya ƙarashe maganar ɗan iya ya dabarbarce cikin razana ya shiga zayyana mashi komai. "Ka sadaukar da ya'ya talatin, na ga sunayen su, amma tayaya zan iya gane su wanene ya'yan Abdallah Buzu a cikin su? Ya ce min su biyu ne ya baka? Suna a raye ko sun mutu?" Yana faman sakin tusa ya ce, "Haris da Deeja..." Ajiyar zuciya Chief Owais ya sauke, dama saida ranshi ya bashi sune saboda akwai kamannin Abdallah a tare da su. "Ka taimaki kanka Ɗan Iya.." Yana faɗa ya miƙe ya fuce daga Cell din. *~_______________________________~Flashback 🥺* *BARI MU KOMA BAYA MU JI MEYA FARU A TSAKANIN DAN IYA DA ANA A RANAR DA AKA NEME TA AKA RASA❗❓* Bayan tafiyar su gidan hajiya Adama, ya rage saura Ana kaɗai a cikin gidan, gyara gidan ta fara yi goge goge da share share, bayan da ta kammala bata huta ba, gashi ta gaji sosai, amma a haka ta koma kitchen ta ɗaurawa Baby Junaid Cherie don tasan da ya dawo zai fara neman abinci.. Ta kuma ɗaura girkin abincin rana, tsawon awanni tana zarya zuwa kitchen gurin duba girkin da ta ɗaura.. Idan ta ga komai daidai saita koma falo ta ɗan huta, dama da wayarta a hannunta da take chatting da sisters din ta, hakan yasa kaɗaicinta ya ragu. Hankalinta ya fi kwanciya ganin babu mai takura mata a gidan, mutumin da ta tsana fiye da mutuwarta, ko gifcinsa bata son gani saboda cin zarafin da yake yi mata, ya addabeta, shine silar damuwarta, kullum cikin fargaban shi ta ke.. A lokacin bata kawo komai a ranta ba, bayan da ta gama girkin lunch din ta kashe gas ta nufi bedroom din ta, ganin ɗaya ta yi yasa ta shiga toilet ta ɗauro alwala, ta ɗauko hijab dinta da take ta 6oyonta don kar a ganta a gane ta musulunta ta zura ta a jikinta, kafin ta kabbara sallar a tsanake, da ta kammala ta zauna ta fara kai kokenta gurin Allah. Cikin ƙanƙan da kai take cewa, "Ya Allah, Ka fidda ni a halin da nake a ciki! Ka fi kowa sanin halin da baiwar nan taka take a ciki, ni bazan iya da shi ba, amma nasan kai zaka iya da shi, Ya Allah, ka kare ni daga sharrin Ɗan Iya, na tsani abun da yake yi mini, na tsane sa, ina jin zafin najasar da yake goga min a jikina! Ya Allah Ka raba ni da shi, Ya Allah ka tona masa asiri..." Kuka ne ya 6alle mata, tana jin ciwon abun, yadda yake nuna mata fin ƙarfi, ya ci zarafinta, kuma ta kasa tona masa asiri, saboda tasan kota faɗa ba yarda za'a yi da ita ba, bayan haka a duk lokacin da ta yi gigin tona masa asiri sai ta ji kamar an shaƙe makoshinta, bayan haka ya yi mata barazanar zai kasheta in har ta faɗa ma wani abun da yake yi mata.. Addu'o'inta duka akan ɗan iya ne.. Ciwon kai ta fara ji, A hankali ta kwantar da kanta saman darduma, bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita.. Almost 1 hour tana sharar baccinta, kwatsam knocking din kofa ya farkar da ita, a dan firgice ta farka, gabanta na faɗuwa ta miƙe, ta yi zaton ɗan iya ne shiyasa duk ta sha jinin jikin ta, cike da zullumi ta furta, "Wanene?" "Your husband to be..." Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Mahboob.. Da sauri ta cire hijab din jikinta ta daura kan gado, kafin ta je ta buɗe masa ƙofar.. Idanunsu na shiga cikin na juna, ta yi saurin sakar mashi murmushi, tare da mayar da idanunta akan j Junaid da ya goyo a bayansa ya yi nisa a baccinsa. "Me ya ke damunki ki ne? Na ga idanunki sun yi ja?" "Wataƙil don na yi bacci ne" Ta bashi amsa da fara'arta. "Ina mutanan gidan suke ne ko har sun tafi ne?" "Sun tafi tun ɗazu, ni kaɗai ce a gidan... " .. "Okay, ya faɗa tare da janyo Junaid daga bayan shi ya miƙa mata, "Take care of his excellency, ki kwantar da shi, idan ya tashi daga bacci pls ki yi mashi wanka, ki bashi abinci..." Murmushi ta yi shima ya yi mata murmushin. wani kallon ƙauna suke jefawa junansu. Bayan ta kar6i Junaid ta rungume shi a ƙirjin ta.. "Your command is my wish, amma kai ba zaka ci abincin ba? Ko baka jin yunwa..." Girgiza kai ya yi, "Sauri nake yi zan tafi kallon match, bana so na yi missing, idan na fita zan biya gidan abokina zan ci abincin acan..." Har ta buɗe baki zata ƙara furta kalma, ya yi saurin ruƙo yatsanta me sanye da zoben da ya bata ya manna mata kiss, ta saki baki cike da mamaki, ya ɗago tare da kashe mata ido ɗaya, "Take care of your self." Ya faɗa tare da juyawa cikin sauri, har ya kusa fucewa daga falon ya ji ta ƙwala masa kira, "MAHBOOB" Faɗuwar gaba ya ji, a hankali ya waiwayo tare da daura idanunsa akanta, murmushi ya ga tana sakar mashi, "Lafiya ? Ya tambaya"ko akwai wani abu da ki ke son faɗa min"? Ya faɗa yanayi mata murmushi. Girgiza kai tayi, "No, ka yi min kyau ne." Bai furta kalma ba, ya ɗaga mata hannu tare da sakar mata murmushi ya fuce. Ji ta yi kamar tabi shi ko ta roƙe shi ya dawo ya zauna saboda faɗuwar gaban da take ji. Fitowa ta yi daga dakin, ta nufi ɗakin Anila, tana kokarin kwantar da Junaid kan gado ya farka da rigimarsa yana ambaton sunan Mommy, koda ya ji muryar Ana sa'ilin da take lallashinsa nan fa ya fara kuka yana fadin shi mommy yake son gani, gurinta zai je,. Lallashin shi ta yi da wayou da dubara ta ce, "In har kana son ganin mommy, ka yi shiru ka daina kuka, zan kawo maka abinci ka ci ka ƙoshi, idan na yi maka wanka sai mu bi su anguwa.." Yana faman yamutsa fuska da shagwaba ya ce, "To ina suka je, shine ma ta tafi ta barni.." "Suna a gidan mommy Adama" tur6une baki ya yi.. Dakyar ta shawo kanshi ya yi shiru, Ta miƙe da sauri ta je kitchen ta zubo masa cherie a plate, ta haɗo masa da juice ta kawo masa, da kanta ta zauna tana bashi yana ci, bayan da ya gama ta mayar da kayan abincin kitchen.. Ta dawo dakin, cire masa uniform dinsa ta yi, ta ɗauke sa suka shiga toilet, bayan ta gama masa wankan, ta fito da shi, jikinshi ɗaure da towel, tana ta tunanin ya zata yi da shi? Gudun kar ya saka mata kuka in ya ga ta ƙi kai shi gurin mommynsa. cikin sa'a taga ya kama bacci, murmushi ta yi tare da kwantar da shi kan gado. "Baby Junaid, asha bacci lafiya, ni ma bari na je na yi wanka, don nasan idan ka farka ba zaka barni in yi ba.." Juyawa ta yi da sauri ta fuce daga ɗakin ta koma nata ɗakin ta shiga bathroom don ta yi wanka. Bayan da ta shiga ciki, fara tu6e kayan jikinta ta yi ta ɗaura towel ta kunna shower, har zata zame towel din ta tuna da mahboob, murmushi ta yi tana tuna murmushin da ya yi mata kafin ya tafi, shagala ta yi da tunaninsa, har ta manta da abun da ya kawota toilet ɗin. Kwatsam! Yanayin bugun zuciyarta ya sauya, ta dinga jin kamar wani abu zai faru da ita, fasa wankan ta yi ta mayar da kayanta ta fito da sauri don ta dubo baby Junaid, cikin sauri take tafiya, har ta kusa ƙarasawa ga bedroom din Anila kwatsam ta ji motsin mutun a cikin kunnanta, kwata kwata bata ga lokacin da ya shigo ba, ga dukkan alamu bata ƙofa ya shigo ba, ya yi tsafinsa ne, wata razana ta yi gabanta ya shiga faɗuwa, kwata kwata Allah bai nuna masa ita ba, ya wuce ya nufi bedroom ɗinta, Hankalinta idan ya yi dubu toh ya tashi, tun da ta ga ya nufi bedroom dinta tasan cewa ita yake nema, akan idon ta ya fito ya nufi kitchen ya ga babu ita, ya shige can ciki yana bin ɗakuna tare da kwaɗa mata kira da buɗaɗɗiyar muryarsa Ana, Ana cikin sanɗa ta lalla6a ta shige ɗakinta ta datse kofar, ta ɗauko wayarta jikinta na kerma kaf kaf ta shiga camera, ta saita fuskarta. Daurewa ta yi cikin ƙarfin hali ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tasan ba lallai ta rayu ba. _Na yi maku wannan video don in bayyana maku halin da nake a ciki, ina ji araina kamar wannan ce dama ta ƙarshe, nasan kun kyautata mun a rayuwa, kuna so na, mun shaƙu da juna, amma ba lallai kowan nan ku ya yarda da abun da zan faɗa ba, nima bada son raina ba, bazan jure fasiƙanci da yake aikatawa da ni ba, in har ban tona masa asiri ba, zan haɗiyi zuciya ne na mutu saboda baƙin cikin shi, bakowa nake magana akai ba face Uncle Ɗan Iya, ya kasance yana kwanciya da ni a duk lokacin da nake tsaka da yin jinin al'ada, ban ta6a sani ba, sai dai in farka inji raɗaɗi a gabana, abun yana damuna amma saboda ban san meke faruwa da ni ba shiyasa ban kawo ma raina mutunne ke saduwa da ni ba, ina ganin abun kamar a mafarki ya ke faruwa, nama yi zaton aljanu ne, shiyasa a lokacin da damuwa ta mamaye zuciya ta, na yi duhu na rame, duk kuka nuna damuwa akaina na kasa fayyace maku komai saboda bansan amsar da zan baku ba. A ranar dana musulunta, a ranar na gano wanene ke yi min hakan, ina a kwance ya afka min da tsakar dare kamar yadda na saba gani a mafarkina, da ya ga na ganshi zan fasa ihu sai ya toshe min bakina ya hana ni yin magana, na yi kukan baƙin cikin da ba zai misaltu ba, ban ta6a zaton zai yi min haka ba. Ina ganin girmansa ina ganin mutuncin ahlinsa da suka zama majinginata, a lokacin na yi kokarin in fasa ihu ko in bangaje shi don in gudu amma ya sanya min ƙarfi, ya yi min sihirin da jikina ya mutu na kasa motsawa ya kwantar da ni kamar matatta ya biya buƙatarsa da ni, ban tashi farkawa ba, sai washe garin Allah, cikin mawuyacin hali na yi wanka na yi sallah, na kasa tunkararshi saboda ina kokwanton in shine ya yi min hakan a zatona jinni ne ya bayyana da suffarsa, amma daga baya na gano shine shaiɗanin da kan shi, batare da sanin kowa ba na je har ɗakinshi da niyar in zazzaga mashi masifa in kuma yi masa iyaka da kaina, amma koda na je na gama 6a6atun bakina na kuma ce zanto na masa asiri sai cewa ya yi, ina tunanin zan iya tona masa asiri? Idan ma na faɗa ma mutanan gidan wa nake ganin zai yarda da ni? Bayan ni ɗin bakowa bace, bare ce ƴar aiki ƙasƙantacciya mara galihu, zai fi in shiga taitayina shi mutunne mai haɗarin gaske yana da tsafi a jikin shi, komai nake yi yana kallona, in har na ƙara furta zan tona masa asiri, ko na yi gigin faɗama wani abun da ya ke yi min, da ni da wanda na faɗamawa zai haɗamu ya kashe. Bani da mafita, sarrafa ni yake yi da sihirinsa, ba irin magiyar da ban yi masa ba akan ya tausayawa rayuwata, ya daina aikata fasiƙanci da ni, shi fa musulmi ne kuma yasan babu kyau, namiji ya kusanci macen da ba muharramarsa ba! Haramun ne, ko don saboda mutuncinsa da na iyalinsa ya rufawa kansa asiri ya ƙyale ni, in ba haka ba zan gudu in bar masa gidan, bayan na tona masa asiri... Ba irin barazanar da ban yi masa ba, amma ya ƙi saurare na. Bai da imani bai da tausayi, mugu ne..." ta ɗan dakata tana share ƙwallarta, fuskarta akan Camera.. *"_watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda ya ce ba zai kyale ni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kun ga ni kaɗai ce a gidan, yanzun nan na ga shigowar shi shiyasa na gudo ɗaki don in samu damar yi maku video. Don Allah don son ku da manzon Allah saw a duk lokacin da kuka kalli videon nan ku yi gaggawar kaishi ƙara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku 6ata lokaci, saboda shi ɗin mutum ne mai haɗarin gaske, ya sha yi min barazana akan in har na kuskura na faɗa ma wani abun da ya ke mini wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na faɗamawa shi yasa na kasa sanar da ku..."_* Bata ƙarashe maganar ba ta yi saurin katsewa, bugun zuciyarta ya tsananta jin takun tafiyarsa gab da ɗakinta. Cikin sauri ta janyo pillow ta zuge zip ɗinsa ta fasa soson ciki ta tura wayar a ciki ta maida ta rufe, juyowar da zata yi keda wuya kwatsam ya banko ƙofar dakin ya shigo. Cikin rawar murya ta furta, "La'ila ha illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin!" *Daga Alƙalamin Boss Bature💗🔥* ƙyalƙyacewa ya yi da tantiriyar dariyarsa ta shaiɗanu tare da ɗaura kwartayen idanunsa akan fuskarta ya shiga washe jajayen haƙoransa... "Dama saida raina ya bani zaka dawo don ka cutar da ni! Wai kai wani irin shaiɗanin mutunne? Mara imani da tausayi? Meyasa ba zaka rabu da ni ba? "Saboda kinsan sirrina! Ba zan ƙyale ki ba, ke barazana ce a gare ni..." Bai ƙare maganar ba ta katse shi cikin fargaba ta ce, "In har baka fara bibiyar rayuwata ba, tayaya ni zan san sirrinka? Meyasa kake aikata fasiƙanci da ni? Laifin me na yi maka? Kawai don ka azabtar da ni? Wallahi ƙwara na mutu da in ci gaba da haɗa jikina da naka! Kasa na tsani kaina, saboda ƙazantar da kake goga min!..." Cikin shesshekar kuka take yin maganar idanunta a cikin na shi, "Ba zan ƙara bari ka kusance ni ba, ko dai ka fita daga rayuwana ko kuma in tona maka asiri uban kowa yasan me kake aikatawa..." Ko gizau bai yi ba, sai ma wani shu'umin murmushi da yake saki, "Tun da har kin san komai, kuma kina barazanar zaki fallasa sirrina, ba zan ƙyale ki ba Ana, dama na faɗa maki dama nake jira da zan salwantar da rayuwarki kuma na samu...!" Gaba ɗaya ta ruɗe da jin maganarsa, gumin tashin hankaline ya fara tsattsafowa ta ko'ina a jikinta, kafin ka ce me tuni tsigar jikinta ta fara tashi haiƙam, la66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ja da baya ta soma yi tana neman hanyar da zata ku6uta daga gare shi, duk inda ta yi sai ya taro ta, gaba ɗaya suka hargitsa ɗakin nata, ta dinga ɗaukar abubuwa tana jifar shi da su, ba yadda bata yi ba don ta ku6uta amma ta kasa saboda ya toshe duk wata hanya da zata iya guduwa, a ƙarshe ya damƙi wuyanta ya maka da bango ya matse ta, idanunta suka firfito waje, numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa, ta dinga fitar da nishi tana harba ƙafafunta.. Cikin shakakkar murya ta furta, "A.. Al... Allah bab ba zai ta6a barin ka ba, Allah sa...ssai ya saka min cutarwar da kayi min, idan kana tunanin kashe ni shine mafita ka jira ka gani, ni zanyi silar tonuwar asirinka, kaima zaka mutu ne... " Akan idanunta ya girgiza jikinshi ya riƙiɗa ya sauya suffar shi ya zama dodo, tsantsar tsoro da tashin hankali mara misaltuwa suka ziyarci zuciyarta, duk da tashin hankalin da take a ciki bakomai take tunanowa ba face ƴan uwanta da Aunty Anila sune damuwarta, babban baƙin cikinta zata mutu batare da ta fallasa asirin shi ba. Bata da mafita da ya wuce Allah, yana kallonta da idanunsa da babu ɗigon imani a cikin su, A haka da ya shaƙeta jikin bangon kokarin keta mata haddi yake yi. Tana a cikin mawuyacin halin nan kwatsam idanunta suka hango mata Baby Junaid dake kokarin buɗe ƙofar dakin ta, ya zuro hannunsa ta ciki. Wani irin faɗuwar gaba ta ji, kamar ta fasa ihu, saboda tsoron kar Ɗan Iya ya gansa don tasan muddin ya gansa sai ya kashe shi. Da ƙarfi ta dinga yin kuka tana fasa ƙara, duk don ta hana shi jiyo sautin muryar Junaid dake kiran sunanta. Junaid da ya ji kukanta, ya fago da idanunsa kaitsaye suka sauka akan bayan ɗan iya, a firgice ya razana tare da kware bakinsa ya fasa gigitacciyar ƙara ya bi ya ruɗe tsigar jikinsa ta shiga tashi ganin dodo. Wani iko na Allah kwata kwata dan iya bai jiyo shi ba, kuma ya bashi baya, kuma harda ihun da Ana ke saki ya hana ya jiyo kukan Junaid. Girgiza kanta ta dinga yi, da hannu ta dinga yi masa alamar ya gudu ya gudu. Nan take ɗan iya ya ji aransa akwai mai kallonsa, yana kokarin juyawa, Junaid da ya gama razana cikin ikon Allah tsoro yasa ya juya a guje ya nufi ɗakin mommynsa, yana gudu towel dinsa na ƙwancewa, har tuntu6e ya yi ya faɗi ya miƙe da ƙyar yana kuka ya shige ɗakin su. Yana shiga ya fara neman gurin da zai 6oye kansa. Jikinsa na kerma ya buɗe wardrobe, ya taka gidan farko ya ruƙe na biyu da hannayensa ya haye sama ya kutsa cikin kaya ya 6oye, adai dai lokaci ɗan iya ya saki Ana ta yanke jiki ta fadi ƙasa bata mutu ba sai dai ta fita hayyacin ta. Ya juya cikin sauri ya fito daga dakin ya soma neman wanda ya shigo gidan ya dudduba ko'ina bai ga kowa ba, har ɗakin Anila ya shiga a lokacin Baby Junaid ya daɗe da sumewa, bai ji wani sauti ko alama da zai bayyana masa akwai mutun ba. Hankalinsa ne ya kwanta da ya tabbatar babu kowa kuma ya tuna basu dawo ba, ya baro su acan gidan Abdallah babu wanda yasan ma ya dawo gida. Lokacin da ya koma ɗakin ya taras da Ana, sungumarta ya yi a saman kafaɗarshi ya 6ace daga inda yake ya dira a ɗakin sirrinsa, ya ajiyeta anan bayan da ya kafeta da sihiri ta yadda bazata iya ta6uka komai ba in ba da izininsa ba, ko magana ba zata iya yi ba, balle ta motsa jikin ta, kwata kwata bata a hayyacin ta. Ashe tsawon lokacin da suke ta neman Ana tana a ɗakin sirrinsa, shi kaɗai ya san inda ya 6oyeta, ba ci ba sha, bata iya komai, ta zama mutun mutumi, babu rabon Ana ta rayu, ya riga da ya gama da ita. Daga baya ne da ya tabbatar ta mutu sai ya haƙa rami ya binneta a ciki, sati ɗaya kafin zuwan Isod Agents, shiyasa lokacin da suka haƙa ramin suka taras da gawarta bata yi komai ba saboda bata daɗe da mutuwa ba da kuma ikon Ubangiji.. 🥹 RIJF (ANAH) (Kunji komai da ya faru a tsakanin Ɗan iya da Ana) ~__________________________________🔥🌹~ "Cau cau, gafara dai, namiji Uban maza, The mastermind behind the conspiracy da girman kujerarka Uban munafukan duniya, sarkin mugaye, an buga da kai an barka Jan wuya Alhaji Musa. Ƙaramin su babbansu, ko ku ce big boss, duk nine. Mai izza, mai arziƙi, mai jiji da kai, shugaban azzaluman duniya, wanda mutuwa ke tsoronsa, dodon dodonni, wanda ya fi ƙarfin kowa saboda sihirin sa..." Kirari ya ke yi ma Alhaji Musa yayin da ya ke shiga cikin Cell ɗin da ya ke. (😂) Abun al'ajabi ba ya ƙarewa duniya, ni kaina da nake rubutawa saida na razana da ganin ɗan tahalikin nan, garƙame a cikin Cell, wato ruwa ne ya daki babban Zakara. Ba ka jin komai sai sautin nishinsa da gurnaninsa kamar wani namun dawa, yana a zaune dirshan a ƙasa kamar mabaraci, ko suturar kirki babu a jikin shi, sai gajeran wando baƙi, ƙafafunsa a ɗaure suke da leg irons. Dana kallesa sai da gabana ya faɗi ganin yadda halittarsa ta sauya, rabin fuskarsa ya lalace sakamakon Acid din da Unaisah ta watsa masa, fatar gurin ta zagwanye gwanin ban ƙyama, da ido ɗaya yake gani Sakamakon ruwan acid din da ya shiga idonsa ɗaya ya lahanta shi, gaba daya fatarshi ta lalace da raunukan bulalan da Evils suka yi ma shi har yau bai daina jin raɗaɗin azabar su ba, idan suka fara masa zogi ba halin ya sosa saboda da zarar ya sosa sai fatar ta ɗuri ruwa ta fashe ta dinga fitar da gur6ataccen ruwa mai ɗoyi, kafaɗarsa ta hagu da Unaisah ta yanka da zarto ta kumbura suntum har surgery aka yi masa a gurin amma still bai warke ba, ciwon har ya shafi hannunsa na dama ya kumbura suntum ya zamar masa jalli joga. Gaskiya Unaisah ta lahanta bawan Allahn nan ba kaɗan ba, da zai samu damar da zai ku6uta wallahi ita ce mutun ta farko da zai fara kashewa har lahira, a yanzu haka da yake zaune wutar baƙin ciki ce ke ruruwa a cikin zuciyar shi. idonsa ya kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin sa, ga wani jan ruwa da ya kwanta a ciki. Yana jin kirarin da DG ke yi ma shi, ya murtuƙe fuska kamar gwaggon biri saboda muni, ƙyanƙyami da ƙyamarsa ne suka cika Owais ya kasa zama sai dai ya tsaya a tsaye, ya toshe hancinsa da hanky. "Allah ya yafe maka Musa, tun a duniya kenan ka fara ganin sakamakon zunuban daka aikata, ina ga idan aka binne ka inda dukiyarka ko wani abu da kake taƙama da shi ba zai cece ka ba sai mugun halin ka? Ko da yake ba zuwa na yi don in yi fira mai tsayi da kai ba, nasan yanzu ka gane Allah ɗaya ne! Da juyi ɗaya Allah ya rikito da kai, ya kar6e komai da kake taƙama da shi, ya ɗebe albarkar rayuwarka, ya raba ka da kyawun suffarka! Ya kar6e dukiyarka da ƙarfin sihirinka! Ya raba ka da kowa naka, ya kuma zubar maka da mutuncinka, ya bar maka ranka da baƙar zuciyarka don ka ga ishara da idanunka, kai hatta ƴan jami'iyarka sun soke ka daga member ɗin su, sun ma ce a ƙaddara cewa basu taba saninka ba, saboda kowa gudu yake ya ra6eka ta shafe shi. Matarka tana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, tun lokacin da ta ji abun da ka yiwa jinjirarta daka raba ta da ita, nan take ta yanke jiki ta faɗi, yayanka Alhaji Ubaid ya yafe ka daga zuri'arsu, ya ce a daina ma kiran ka da Musa Wadata, saboda Alhaji Mu'azzam Wadata ba ubanka bane, ya fayyace ma kowa dangantarku, mahaifiyarku ƴar aiki ce a gidan su, halinta sak irin naka, bayan da mai gadin gidansu ya yi mata ciki, ta ƙulla makirci ta ce cikin Alhaji Mu'azzam ne, sai da tasa ya aureta bayan ta yi silar mutuwar mahaifiyar su Alhaji Ubaid, ta asirce Alhaji Mu'azzam, da ta haifo ka, ta ci gaba da mu'amala da mai gadin gidan, harta samu wani cikin ta haifi ƙanwarka, saboda Mu'azzam ya samu matsalar haihuwa, ƴa'ƴanta duk ba nashi bane, ta yi ne don ta ci gadon shi. Abun da na fahimta, shaiɗaniya ce ta haifi shaiɗan, mugun halinka a nono ka tsotse shi..." Tunkan Owais ya ƙarashe maganarshi Musa ya fasa wata irin kururuwar baƙin ciki, har saida gefen bakinsa ya fashe jini ya dinga ɗiɗɗigowa, dama a raunace bakin yake, abun da ya fi tsana a rayuwar sa shine tushen shi, wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarsa, ya ji zafi da Alhaji Ubaid ya fallasa sirrinsa wlh da zai gansa a gabansa ba abun da zai hana ya binnesa da ran shi. Yana gurnani cikin fushi ya furta, "Idan ma kana faɗamin ne don in saduda, to ka daina, ba a halicci zuciyata da rauni ba, ba zan ta6a karaya ba, ba abun da zaisa na yi nadamar abun da na aikata!" Ƙyalƙyacewa da dariya Owais ya yi hakan ya 6ata masa rai.. "Ina mamaki ne mutumin da rabin fuskarsa ya lalace, ba hannu ɗaya, ba ido ɗaya, wai shine ya ke da audacity din da zai iya furta wannan maganar? Me ya rage maka da bazaisa ka yi nadama ba? Bayan ga tsoro nan da tashin hankali kwance cikin idonka...." wata shu'umar dariya ya saki kamar jaki na haniniya. "Na ci dubu sai ceto, ba yadda kuka iya da ni, na riga dana ci riba, babu hukuncin da za ku yi min wanda zai kai wanda na yiwa rayukan dana azabtar, raina ɗaya ne tak, da shi na kashe ɗaruruwan rayuka, da shi na azabtar da rayuka, da shi na 6ata zukatan rayuka, wanda har abada ba za a ta6a mantawa da ni ba.." ya faɗa yana damula mummunan bakinsa. Owais ya ji zafin maganarshi, ganin kamar babu alamun karaya a tare da shi, a ransa ya furta wannan wani irin shaiɗanin mutunne? Anya mutun ne Musa? Gaba daya Elders sun saduda banda shi, in wani ne yake a halin da yake a ciki wlh ko kalmar alifun bazai iya furtawa ba, amma da ya tuna wanene Musa gurin girman kai da izza sai ya fahimci koda ya karaya ba zai bari ya gane ba ko dan ya baƙanta masa rai. Hakan yasa shi sakin murmushin gefen fuska. Kafin ya soma yin magana cikin nutsuwa yana kallon cikin idanunsa. "Waɗannan rayukan daka azabtar yanzu suna a cikin rahamar Ubangiji, sun barka da tarin hakkinsu akan ka, idan kana farin ciki saboda ka zalunce su to ka daina, kanka ka zalunta Musa! Ai kai musulmi ne, kuma ka san Allah baya yafe hakkin dake atsakanin bayinSa. Me ya ja ma shiga halin da kake a ciki?" Ya faɗa yana nuna sa cike da ƙyanƙyami. "Hakkin waɗannan rayukan, sune zasu baibaiyeka da fitintinu iri iri har abada, bayan haka bari na yi maka fashin baƙi tun da na fahimci kai dabba ne, jahili, kuma daƙiƙi.." cikin fushi ya ke jifar Owais da harara da idonsa ɗaya kamar ƙwayarsa zata faɗo ƙasa. "Yanzu na ƙara yarda cewa zalunci ƙaiƙayi ne da ke komawa kan me shiƙa, abun da baka sani ba, silar tonuwar asirin ka, ƴar ka Zeenatu ta kashe kanta saboda jin wanene Ubanta da kuma zaluncin da ya yi ma ƴar uwarta Unaizah..." bai ƙare maganar ba Musa ya yi wata irin zabura kamar zai miƙe, ya zaro idonsa waje cikin tashin hankali da baƙin cikin jin abun da kunnuwansa suka jiye ma shi. "Meyasa na ga tun yanzu ka fara karaya, ai ban kai ka in da na ke son ka je ba, bayan haka rayukan daka ƙullawa makirci cikin kankanin lokaci sun warke daga raɗaɗin da ka ƙunsa musu, Shureim da Ummi suna atare da ƴar su Batool, da zarar mun gama shari'arku, zamu shafa fatihar auren su..." cikin ƙunci da damuwa ya ƙara murtuke fuskarsa, ji yake kamar ya binne kansa don bakin ciki, zuciyarsa sai tafarfasa take yi.. "Sheikh Imam malik, da ka ƙullata a ranka, ka daɗe kana zaluntarsa don ka ƙunsa masa bakin cikin da zai yi silar mutuwar sa, a yanzu haka yana nan da ransa da lafiyarsa, harma ya je gano matarka Sarah da ke a kwance gadon asibiti, ka duba ka ga fa duk irin cutarwar da ka daɗe kana yi masa bai ji komai ba.." Wata wutar baƙin ciki ce ta taso mashi ya dinga buga kansa jikin bangon bayansa, jikinsa ya ɗau zafi rau, ya Ilahi, Ya rasa ina zaisa ranshi ya ji dadi? Duk tsawon lokacin da ya ɗauka yana wahalar ƙulla masu makirci don ya baƙanta masu rai kenan yanzu komai ya tashi a banza? Hakan na nufin haƙarsa bata cimma ruwa ba? Kwata kwata Imam bai ji zafin komai ba a ransa? Shifa duk a zaton shi imam malik yana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, ciwon zuciya ya kama shi ashe wai har yana da kuzarin da zai iya taka ƙafar sa! Chief Owais da ya lura ya haɗa masa sha tara na baƙin ciki wani sanyi ya ji yana ratsa zuciyarsa.. "Ka kwantar da hankalinka mana ai ban ƙarasa maka labarin ba, ƙanwarka Laura..." Zare idanunsa ya yi cikin damuwa. "Sakamakon razanar da ta yi lokacin da ta ji komai game da kai, ta haɗiyi zuciya ta mutu." gigicewa ya yi gaba ɗaya ya rikice har baisan sa'adda ya fara cizge akaifunsa ba, duk ya faffasa su, jini ya dinga tsattsafowa. "Sannan, na ji abun da ya faru da kai, na taya ka baƙin ciki, ashe shatun bulalin jikinka, Evils ne suka zane ka, bayan sun tu6e maka suturarka ka dinga ihu kana kuka, suka shafe maka jikin ka da gishiri suka jefa ka cikin ruwa, na ce dama tsakanin shaiɗan da ɗan uwansa shaiɗanu ana samun sa6ani? Sai kuma na ji wai na hannun damanka Mark ne ya ci amanarka, ya musanya maka zuciyar Batool da ta giant, abin takaici! A ƙarshe burinka bai cika ba, kuma zaka mutu baka cika shi ba...." Wani nishin baƙin ciki da Alhaji Musa ya saki nan take ya burkuta zawo a cikin wandonsa, wari ya cika cell ɗin. Chief Owais ya toshe hancinsa da bakinsa da hanky, har sai da ya yi kakarin mai. Da ƙyar ya iya furta, "Ƙato da kai kana sakin kashin zaune, ko ka yi zaton ni kaɗai nake tare da kai..." Ya faɗa tare da nuna masa surveillance cameras ɗin dake a kowace kusurwa, "Ba wai iya jami'an isod ke kallon ka ba, duniya ce take kallonka..." Wata zabura Alhaji Musa ya yi jikinsa ya hau kerma kamar mazari, tashin hankali tsantsa ne akan fuskarsa, kunyar duniya ta kama shi. 6a66akewa da dariya Owais ya yi, "Haba ranka shi daɗe, meyasa tun yanzu zaka razana? Ba zaka bari mu shiga kotu ba.." Ya faɗa tare da juya masa Screen ɗin Ipad ɗin hannunsa, wai ashe tun zaman shi live video ya ke ɗauka. Alhaji Musa ji ya yi kamar ya haka ƙasa ya binne kansa saboda wutar bakin cikin dake azabtar da zuciyarsa, Owais ya gama da shi, ya kashe shi da ranshi, ya ruguza duk wani mutuncinsa a idon duniya, yanzu kowa ya ga mummunar suffarsa da halin da ya ke a ciki. "Da zaka ga sharhin da mutane suke yi akan ka, sai ka ji ka tsani kanka, tsinuwa ce da la'anta ta ko'ina, sai kuma dariya da yi maka Allah shi ƙara." buga kansa ya yi jikin bango da ƙarfi. So yake ya mutu sai dai ba halin mutuwa, da biyu suka ɗaure mashi ƙafarshi da ɗayan hannunsa marar ciwon, don sun san zai iya amfani da su gurin kashe kan shi, ga zuciyar tashi da ke ta ƙonuwa da bakin ciki ta ƙi bugawa bare ya ware, lokacinsa bai yi ba. Tun a duniya ya fara ganin sakamakon zunuban da ya aikata, da ya ke jaki ne yafi jin kunyar duniya baisan tun awurin zare ransa zai gane kuskuren sa. "Unaisah ta yi maka ta'asa Musa, ka ga kuwa mummunar halittar jikinka? Kamar gwaggon biri, so ta yi ta kashe ka, amma mahaifinta ya hana abata damar da za ta yi hakan saboda ba ya son ƴarsa ta zama silar mutuwar wani, bayan haka mun fi so ka fara gir6ar abun da ka shuka anan kafin ka baƙunci ƙabarinka. zufa ta wanke fuskarsa, sai faman gurnani ya ke yi da nishi. "Na ga duk abubuwan da nake so na gani a tare da kai, amma banga nadama ba, sai dai itama nadamar za ta zo maka ne a yayin da ka ga wannan..." Ya ƙarashe yin maganar tare da zura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya zaro wasika, "Ka nemi duniya ido rufe, ka biyewa son zuciyarka, ka dinga yima mata ciki suna haifa maka ƴa'ƴa, ba kai tunanin iyayen ya'yan da su kansu yaran wani hali zasu shiga ba idan su ka ji irin cin amanar da ka yi masu, ka kasance me son kai Musa, burinka ka faranta ranka, ka nakasa waninka in har zaka samu abun da kake so, nasan Unaisah ta faɗa maka game da wasikar da ƴarka Unaizah ta bada a baka, to gata nan ta bani in baka, ya rage naka, in ma ka karantata ko ka ketata, matsalarka ce, amma zai fi ka karantata, ita ta rubuta da kanta.." a hankali ya ɗaura masa wasiƙar daga gabansa. Tun kafin ma ya buɗe wasiƙar ya karanta abun da ke a cikinta, wasu tagwayen hawaye suka fara zarya kan kuncinsa. Har Owais ya fuce daga cell din bai lura ba, ya kafe idanunsa akan wasikar da ya gaza buɗewa, yana jin fargaban ya ga me Unaizah ta rubuta masa! Lokaci ɗaya ya fara tariyo komai nata, gaba ɗaya ƴa'ƴansa da ya sadaukar bai ta6a yi ma wani son da ya yi ma twins ɗinsa mata ba, Zeenatu da Unaizah kuma su kaɗai ne ya samu ta hanyar Aure cikin waɗanda ya sadaukar, son duniya ne da ya rufe masa ido ya ja ya sadaukar da su gashi nan yanzu ya ja dukan su basa a raye saboda zaluncin shi. Da yatsun hannunsa mai ciwon ya samu ya buɗe wasiƙar da ƙyar, yana ganin handwritting ɗinta ya shaida ita ta rubutata, ta yi rubutunne cikin harshen da ta fi ji british english, da ƙyar ya samu nutsuwar karantata. ~________________________________________🥺🌹~ _Idan wani ya zalunci yaro, iyayensa ne na farko da yake fara kai kukansa wajen su, amma idan iyayen nasa ne suka zalunce sa, wurin wa zai kai kukansa? Ni da bansan akwai wanda ya halicce ni ba? Laifin me na yi maka daddy? Me na yi maka dana cancanci wannan hukuncin daga gare ka? Ka sani kokwanton anya kai ubana ne? Anya kana da zuciya a ƙirjin ka? Uba koda azzalumi ne shi zaka same shi da son ya'yan shi sai dai ya zalunci na wasu, me na yi maka? Yanzu na gane dalilin da yasa ka hana in san kowa naka, ka 6oye min real identity ɗinka, ni ina kokwanton ma zai yi wuya idan ba sato ni ka yi ba. Ka yaudare ni, ka ci amanata, ka ha'ince ni, ashe wasan da kake yi min da dariya da gatancin da kake bani duk kana yi ne saboda ka riga da ka sadaukar da ni saboda biyan buƙatarka, ina farin ciki daddyna yana sona, yana gatanta ni, baya son 6acin rai na, ya fi sona fiye da komai ashe na yi kuskure, ka ci amanar yardar da na yi maka, baka ta6a sona ba, ka karya zuciyata. Daddy na rasa wani zunubi na yi maka! Ubangijin da ya halicce ni ma ka hana in san shi, ka yi min ƙaryar babu wani addini, idan na ga kana yin sallah sai ka ce motsa jiki kake yi, kawai saboda ba ka son in ra6i rahamar ubangiji na, ka hanani duniyata ka kuma hana in nemi lahirata daddy, kun haɗu kai da mommy kun gur6ata rayuwata, ka yaudare ni, ka ce korean school zaka kaini, ashe gidan matsafa ka sadaukar da ni. Burinka ya cika, sun wulaƙanta ni, kamar karya suka maida ni, mutun shidda a kaina, manya waɗanda suka fi ƙarfin shekaruna, ni ɗaya, shekarata sha shidda, ka fi kowa sani. Abun da suka yi min ban ji zafinsa ba fiye da yadda na ji zafin cin amanar da ubana ya yi min, meyasa baka kashe ni ba tun farko? Wallahi na yi danasanin kasantuwarka ubana, mugu, azzalumi, mara imani, alade mai kwanciya da ƴar cikinsa. In sha Allah sai rayuwarka ta wulaƙanta, kukan baƙin ciki da na yi sai ka yi ninkin baninkinsa, radadin azabar da na ji sai ka ji mafiyinsa. Na tsanake! Na tsanake ka!! Ka kawo ni kurkukun ƙaddara don matsafa su amfana, nima na amfana, addinin daka hana in sani, ka ke boyemin don kar Allah ya tuhume ka, ƴar uwata Unaisah ta fayyace min komai, ita ce ta ganar da ni wanene mahaliccina, bayan haka silar zuwa na kurkukun kaddara, Allah ya haɗa ni da yan uwa masu sona tsakani da Allah, sun bani tarbiyar da baku bani ba, sun bani kulawar da baku bani ba, ku kuma ku je ku da Allah, ga duniyar nan, ita da kuke nema Allah ya bar ku da ita daddy, ku ga idan zata amfane ku, kuma duk min daran daɗewa kuma zaku zo inda nake. Allah ya isa ban yafe maka ba! Allah ya saka min cutarwar da ka yi min_. Bai ƙare karanta wasikar ba ya fashe da kukan baƙin ciki, wani irin ƙunci mara misaltuwa ne ya baibaye zuciyar sa, kuka har da majina, ya jibge guri guda kamar bijimin sa, haƙiƙa kalaman Unaizah sun karya zuciyar shi, sun sa shi jin raɗaɗin da ba zai misaltu ba, gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi, cikin shesshekar kuka ya ke ambaton sunanta Unaizah Unaizah, kwatsam! Ta soma yi masa gizau a cikin idanunsa, ya zama kamar mahaukacin kare, ya dinga haushi yana kai hannu zai kamo ta sai dai ya ji ya cafki iska.. A ranar da Isod agents suka zo tafiya da baba Obie, kowa da kowa na family dinsa saida Ya hallara a babban falon gidan sa, tun daga kan ƴa'ƴansa, jikokinsa, hada Sheikh Imam malik shima ya zo, momma ma tana nan, jiya jiya aka sallame ta daga asibiti, ta samu lafiya, memory ɗin ta ya dawo. family din matayensa da suke a tare da su duk suna anan, wasu suna a zaune kasa suna jimami, wasu suna a zaune kan kujera sun zagba tagumi, wasu ma kasa zaman su kayi, kowa ya shiga tashin hankali da damuwa. A gaban Kofar dakinsa Agents din suka tsaitsaya Chief Owais ne agaba, dama Ya faɗa masa idan suka kammala binciken su suka kama Elders zai buɗe ƙofar, bayan da yayi knocking ƙofar cikin karyayyar Murya yace"baba mun zo mu tafi da kai headquarter din mu, jibi za'ayi zaman shari'ar ku" kowa Jiran fitowarsa ya ke yi wasu Allah Allah suke Ya mutu adakin karya fito da ransa. Lokacin da suka fara jiyo alamun zai buɗe ƙofar dakin, Hajiya saratu tayi kukan kura ta dira agaban kofar dakin, Ta daddafeta da hannayenta, tana kuka ta dinga rokonsa tana fadin baba dan Allah kada ka fito, baba na roke ka, baba ka 6ace ka tafi wani guri kayi rayuwarku, in ba haka ba zasu azabtar da kai, su kashe mana kai, dan Allah baba ka taimaki rayuwana, banason ka tozarta a idon duniya, bana son su ta6a lafiyar jikin ka, .... " lokacin da ta ke yin wannan maganar a cikin harshen Igbo tayi, Bakowa ya fahimci me take cewa ba, Yayyenta ne kadai suke jin harshen mahaifin na su. Kowa dake agurin saida ya tausaya mata, baiwar Allah duk tabi ta haukace ta dinga kuka kamar karamar yarinya babu wanda bai zubda mata kwalla ba. Ƙiri ƙiri taƙi bari ya fito, taƙi kaucewa taba Agents din hanyar da zasu kama shi. A lokacin yana sauraron maganganunta acikin kunnansa, harya buɗe ƙofar, ya kasa motsawa saboda yaji saratu ta daddafeta ta hanasa ya karasa fitowa, kuma kowa ya kasa kawar da ita saboda karya masu zuciya da ta yi. Ya yi kukan zuci mai radadi, Ya kara jin danasani fiye dana ranar da asirin shi ya tonu, ganin irin halin daya jefa ya'yan shi, kuma still basu daina jin shi a amtsayin Ubansu ba, saratu ta bashi tausayi ta karya mashi zuciya. Dakyar Sharafudden da sir mubarak suka rabata da kofar dakinsa, tana turjewa suna janta, ta dinga kokarin ƙwacewa. Lokacin daya fito babu wanda gabansa bai fadi ba, sun razana da ganin yadda ya sauya cikin ƙanƙanin lokaci, Ya rame sosai, tsufansa ya fito, dakyar yake iya ɗaga kafarsa, bakar jallabiya ce a jikinsa mai hula, Ya rufe rabin fuskarsa da takunkumi, saboda kunyar hada ido da su yasa bai iya dagowa ya dubi kowan nan su ba, har saida suka hada baki gurin furta Baba. Tukunna a hankali ya ɗan dinga satar kallon fuskokin su ɗaya bayan daya tun daga kan ya'yan shi ya fara, har izuwa kan jikokinsa, akan fuskar kowan nan su ya karancin halin da suke a ciki, bai taba jin kunyar kansa irin na yau ba, jikinsa yadinga kerma kamar mazari, kukan saratu Ya cika kunnansa akan idon shi yaga Sir mubarak da Sharafudeen sun nufi daki da ita, tana ta kiran sunan shi tana fada masa ya 6ace kada ya bari su tafi da shi, a karshe ma hada zagi tadinga hada masa baba tana cewa ya 6ace, wallahi in ka bari suka tafi dakai Allah ya isa ban ya fe maka ba. Bai ƙara tabbatar da raunin mace da tausayinta ba sai yau, Duk irin abun da yayi wa saratu ya aura mata mijin da shi yasan ba son ta ya ke yi ba, Ya kuma gur6ata shi, amma ahaka take nema ta cece shi saboda bata son ataba lafiyarsa. A daki suka sanya saratu, tare da twins din ta, suka umarce su da su zauna tare da ita, gudun kada ta lahanta kanta, daga bisani su ka kulle dakin, ta yadda ba zata iya fitowa ba. Tadinga bubbuga kofar, twins suna rurruketa tana bangaje su, su fadi ahaka zasu mike su cigaba da ruƙe ta. Babu wanda ya ƙara furta kalma, tun bayan da suka ambaci sunan shi. Ko handcuff agents din basu sanya ma shi ba, saboda nauyin yin hakan agaban Dg sukeji. Lokacin da ya ke tafiya agents din na biye da shi, yayin da yake kallon kowa dake a kewaye da shi, karaf idanunsa suka sauka akan Jazz dake ta kuka kamar ransa zai fita, mommynsa turai ta rungume kansa a kirjinta, ita ta hana ya motsa da ba abun da zai hana yayi irin haukan da saratu ta yi, saboda kaunar da ya ke ma baba Obie, bakomai ne ya fado masa aranshi ba face maganganun da suka ta6a shi da baba Obie. _baba, Bana jin daɗin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba_ _Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buɗi baki sai yace ni ɗan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba_ _Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family ɗinka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina ɗaya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa_ A cikin ransa yake tariyo komai yayin da yake kallon Jazz, at same time jazz daya ga irin kallon da baba obie yake masa shima saiya tuna da ranar da sukayi maganar.. _ Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani ɗan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ƙaddarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ƙaddararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita" _Jazz baka ɗauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance_ Fashe wa ya kuma yi da wani kukan Aransa ya shiga furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Baba meyasa ka kasance azzalumi? baba me yaja maka? Meyasa ka sauya daga yadda nasanka? Ka karya zuciyata baba..." Aransa yayi maganar, adaidai lokacin baba obie ya ɗauke idanunsa da daga kan Jazz, ya dan girgiza kan shi, hawaye na sauka kan kuncinsa.. Sau ɗaya ya haɗa idanunsa dana Momma ya yi saurin kawar da su gefe cike da jin kunyar ta data kamashi, itama ta zubda kwalla kamar ruwan hawayen ta za su ƙare. Bayan da suka fito gaba ɗayan su, Chief Owais ya buɗe mashi backseat na Motar shi.. Bai kaiga shiga ba, Sai ga Mota ta kunno kai cikin estate din kaitsaye ta nufo gurinsu da matsakaicin gudu tana gab da zata karaso gudunta ya ragu slowly tayi parking a gefen su. Gaba ɗaya suka ƙura idanunsu akan Motar suna jiran ganin wanene zai fito. Amininsa ne Jan kunne Ya fito daga motar, fuskarsa jaga jaga da hawaye, kayan jikinsa sun yi squeezing kamar mahaukaci, ko takalma babu a kafarsa. Tsantsar tashin hankali da damuwa ne akan fuskarsa. Sunyi mamakin ganin shi, bayan yasan neman shi akeyi don a kama shi, Owais ne kaɗai yasan da maganar zuwan shi, saboda tuntuni baba Obie ya faɗa masa ya ce zai mika wuya saboda baba Obie kuma ya cika alkawarinsa ya kawo kan shi, don a hukunta su a tare.. Gaba ɗaya haushin shi da tsanar shi su ke ji, gani suke kamar shine ya jefa mahaifinsu a halin da ya ke a ciki, Ko arzikin kallon mutunci bai samu agurin su ba, kwata kwata baya a cikin nutsuwar shi, kamar ya fara samun tabin hankali. tun da ya fito bai nufi kowa ba sai baba Obie, Bai kaiga karasowa ba, Ya'yan baba Obie Suka kare ubansu cikin fushi suka daka mashi tsawa, su ka ce babu shi babu ubansu, tsakanin su sai dai hange daga nesa, amma ya gama kusantar inda mahaifin su ya ke. Baba Obie Yana kallon aminin nasa da ke ta ambaton sunan shi yana roƙon su akan su bar shi ya gana da amininsa shi kaɗaine zai iya kwantar masa da hankali. Baba Obie yaso su barshi suyi magana amma suka ki basu dama. Akan idon shi, agents suka sanya mashi handcuff a hannayenshi, suka tura shi cikin motar su. Owais Yace ya shiga daga ciki, cikin sanyi jiki ya shiga ya zauna, ya rufe masa cardoor din. Ta gilashin motar yake ta kallon ya'yansa da jikokinsa dake ta kuka kamar ransu zai fita. Chief owais da kan shi yayi driving din baba Obie. Duk suna atsaitsaye motocin suka fuce daga Obie estate, gaba da bayan su motocin sojoji ne dana yan sanda saboda su ba su tsaro.. Lokacin da ya ke yin driving dinsa yana satar kallonsa ta mirror, zuciyarsa ta karaya da ganin yadda baba Obie ke ta kuka hada magina a hancin sa. Cikin shesshekar murya yaji yana fadin kaicona, na zalunce kaina, na zalunci ya'yana da jikokina, na zubda mutuncina, na kashe rayuwar ya'yana da kaina, na kashe rayuwata, bani da hankali, dabbane ni, bazan taba yafewa kaina ba ya dinga zagin kansa yana aibata kansa. Kasa magana Owais yayi saboda baida abun da zai iya furta masa, amma daya tuna taimakon da yayi masu sai yaji zai iya masa wani abu. "Baba bani da abun da zan iyayi maka, ka riga da katabka babban kuskure, shawara ɗaya da zan baka shine, Ka tuba ka musulunta ka komama Allah kafin mutuwarka, ko dan ka samu sassauci" ya faɗa ne kawai don ya kwantar masa da hankali amma shi kanshi yasan ina! "Owais, Allah ba zai ta6a kar6ar tubana ba, koda na kar6i musulunci, babu abun da zai sauya Owais, ayyukana gaba daya irin na yan wuta ne, tun a duniya owais nasan menene makoma ta, duk wanda ya aikata mai kyau ya sani owais, na aika zunubbai masu yawa munana, hakkin rayukan dake akaina basu kirguwa, ina jin kunyar mahaliccina, ina jin fargaban ranar da zan farka in ganni a cikin ƙabarina daga ni sai mugun halina Owais, wallahi na kasa kashe kaina ne saboda tsoron abun da zan taras a cikin ƙabarina, wallahi na zalunci kaina saboda neman duniyar da zamu mutu mu barta, gayanan naja ma kaina da ahlina. maganganunsa sun jefa chief owais a hali na damuwa. "Duk da haka baba, ka musulunta in har dagaske ka tuba, kuma ka ji tsoron haɗuwarka da Allah, bansan hukuncin da kotu zata yanke maku ba, amma nasan zaku yi zaman gidan yari, kaga in hasashe na ya tabbata zaku samu sauran lokacin da yarage maku a duniya, hakan na nufin kana da sauran damar da za kayi ta yin istigfari", Girgiza kai yayi cikin kunci yace"owais, koda Allah zai yafe ma kowa zunubinsa banda irin mu, fir'auna ma daya nemi ya musulunta kasa karasa furta shahada yayi ruwa ya haɗe da shi, dafa hankalin mu mun sani muka take sani Owais.." "Baba Ka fahimta, kai ba musulmi bane, atlease in ka musulunta da imani a zuciyarka ko yayane zaka iya samun sassauci.." magiya owais yadinga yi masa yana driving a hankali saboda baison suyi saurin karasawa Headquarter din su, sarai baba Obie Ya lura da yadda ya ke yin driving din ya kuma fahimci dalilin dayasa ya ke yin hakan. "Owais, zanyi tunani akan maganar ka.." "Baba baka da lokaci daya wuce wannan! Dama ce agareka, daga jibi zamu shiga kotu za'a yanke maku hukunci, ba lallai mu sake haduwa ba, musuluntar da zakayi ita zata bamu kwarin gwiwar yi maka addu'a ko bayan ba ranka.." maganar Owais ta kayar masa da gaba. Duk yadda yaso ya shawo kanshi abun ya gagara, ya fahimci yana son ya musulunta sai dai yana jin fargaban koya musulunta Allah bazai kar6i tubansa ba, kawai ya cire rai ne da komai. Har suka ƙaraso Headquarter din baba Obie bai kar6i tayin Owais ba. da shi da amininsa agents suka tasa su agaba Owais Yana a ruke da hannun kakansa Ya kasa sakinsa yana ta nanata masa kalmatusshahada don ya kar6a amma yaƙi ya furta abakin sa. Gaba ɗaya Isod agents din dake a head quarter din da sojojin tun shigowar su, suka cire hulunansu tare da sadda kansu ƙasa, alama ce ta nuna girmamawa ga kakan dg. A inda cells dinsu suke suka nufa da su, suna jiyo kururuwar sauran Elders din da su ka kulle a ciki, sai dai basu Iya ganin su, saboda kofar cells dinsu ta dabance, na waje bazai iya ganin na ciki ba, haka shima na ciki bazai iya ganin na waje ba, amma jami'an dake kula da bangaren cctv suna kallon komai da su ke yi a cikin cells din. Bayan da suka saka kowan nan su, A cikin cell, suka kulle su. DG bai iya barin headquarter din ba, saboda bayason Ya tafi yabar kakansa. Bawan Allah Har dare Yana a nan, a karshe ma Cikin cell din Ya shiga, Ya zauna tare da shi, ya dinga kwantar masa da hankalinsa. Har ya samu ya ɗan nutsu Ya dakata da yin kuka, sannan Ya soma tambayarsa yayin da suke a zaune kan kujera suna fuskantar Juna daga tsakiyarsu table ne mai ɗan tsayi. "Owais, Idan akwai abun da kake son sani game dani ko kurkukun kaddara ka tambayeni na baka dama, nasan daga yau ba lallai Mu sake samun damar da zamu gana da juna ba... " cikin sanyin murya yace"ka fara fada min idan akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka, zansa docs dinmu su duba ka" Yace a'a baya bukata, saboda a halin yanzu babu likitan da zai iya shawo kan abun da ke damunsa.." gwiwarsa ta sare da jin maganar sa. "Tayaya zamu iya gano dangin fursinonin kurkukun ƙaddara da suka rage? Nasan mawuyacin abune mu iya ganowa da kan mu, bamusan ma ta ina zamu fara ba" "Owais, baku da matsala da wannan, akwai bayanin da zan yi maka wanda zai amfane ku, sadaukarwar kurkukun ƙaddara kala biyu ce! Sadaukarwar jini da sadaukarwar mallaka, duka dai dole sai na jini ake sadaukarwa, amma akwai banbanci, ita sadaukarwar mallaka wanda zai yi ta, ba zai taba zama member na kurkukun kaddara ba, zamu yi yarjejeniya da shi ne, zai bamu abunda muke so, shima zamu bashi abun da ya ke so, da ga zarar ya sadaukar mun bashi abun daya keso to shikenan, mun raba jaha da shi, babu mu babu shi, ba member ɗin mu ba ne, Elders su kaɗai ne members na kurkukun ƙaddara, da sauran ma'aikatan ciki, tun lokacin da salon tsafin mu ya sauya muka gano cewa in muka sadaukar da jinin mu munfi samun karfin sihiri da iko, daga nan salon tsafin ya sauya wanda ada, ba sadaukarwar jini mu ke yi ba, mutun zai kawo ko ba jininsa ba mu kar6a mu biya masa buƙatarsa daga bayane komai ya sauya.." ya ɗan dakata yana mayar da numfashi kafin ya dasa da cewa "Littafin rijister na fursinoni wannan litattin da alƙalamin sirihi na rubuta shi, tun shekarar dana gurfanar da gidan kurkukun ƙaddara, ni ne mutun na farko dana fara sadaukar da jikokina na farko da yan ukuna suka haifa (Yana nufin Senate lafeef, Abdul razak, da sir mubarak) bayan na aurar da su tun suna da shekara ashirin da biyar a duniya, a lokacin basu shirya yin aureba amma saboda manufata akan abin da nake hari, ni na matsa masu har saida suka amince akayi aurensu da matayensu, kusan atare matayen su suka fara haihuwa, jariran suna zuwa ba araye ba, har sau biyar a shekara biyar, tukunna na barsu suka samu ya'ya bibbiyu daga nan naci gaba da sadaukar da jariran su, ko sun nemi su hana matayensu haihuwa ganin sunata wahalar daukar ciki yara suna zuwa ba'araye ba, ni nake canza masu ra'ayi, in nuna ina son inga jikokina da yawa saboda bani da dangi suyi haƙuri zan cigaba da nema masu maganin matsalar su, in sha Allah idan suka cigaba da jarabawa za su haifi masu rai, da haka na dinga samu suna haifamin ya'ya ina sadaukarwa" Shi wannan Littafin rijistar na fursinoni yana ɗauke da sunan wanda yayi sadaukarwa da bayanansa, da kuma sunan waɗanda ya sadaukar, amma banda mutanan farko da suka fara sadaukarwa saboda lokacin ba cigaba, amma fursinonin da aka sadaukar daga baya duk na rubuta wadanda suka sadaukar da su, kuma babu wanda yasan inayin recording din nan sai Aurora, itace mutun ta farko data fara sani, tasan sirrina fiye da kowa, kuma da iznina tasani saboda kundin Yana da makulli a jikin shi, mai karfin shirine kadai zai iya buɗe shi, owais in har ku ka duba littafin zaku samu saukin gano duk wanda ya sadaukar da jininsa, bayan haka nima za ku ga adadin jikokina dana sadaukar da sunayen su har ma da sunayen mahaifan su, da kuma sauran Elders kowa akwai bayanansa a ciki fiye ma da haka za ku samu a cikin littafin sai dai bansan ko za'a iya samun littafin ba tun da nasan yanzu babu Kurkukun ƙaddara" Bayan daya ƙarashe maganar su ka yi shiru kowa da abun da ya ke sakawa aranshi, ta wani bangaren Owais yaji dadin bayanin daya basa game da littafin saboda zai taimaka masu sosai. "Baba a tsawon shekarun da ka ke sadaukar da jikokin ka, baka taba jin nadama ko rashin jin dadin irin azabtar da su da ka ke yi ba? Ko dan su ba kai ne ka haife su ba? Bakasan ciwon su ba"? Murmushin takaici yayi"Owais, ba lallai ka fahimceni ba, Wallahi mugune ni, zuciyata ta ƙeƙashe, ba ɗigon imani ko tausayi araina, tun lokacin da aminina ya bani shawara akan in kar6i gadon iyayena da suka barmin saboda muna a hali na talauci da matsin rayuwa, gashi ana farautar rayuwar mu, bayan haka muna da burin muyi arziƙi mu daukaka a fadin duniya, a lokacin dana mayar da sihirin jikina daga nan ne, Zuciyata ta rikiɗa ta koma irin ta shaidanu, sai nayi mugunta ko na zalunci wani nake jin dadi.." owais da ke sauraron shi, jikin shi yayi sanyi lakwas. "Ina son Ya'yana fiye da kaina, fiye da kuma komai na duniyar nan, amma Jikokina da nake sadaukarwa ban taba danasani ba, Sai akan Yaro ɗaya wanda banyi niyar sadaukar da shi ba, na kuma yi danasanin sadaukar da shi, saboda bada son raina ba, tsantsar son da nakeyi masa ne Yaja mashi! Kowa yasan cewa kaine jikan da na fi so, a zahirin rayuwa, amma a baɗini, son da nake masa yafi na sauran jikokina harya zarce son da nake ma ya'yan cikina, tunkafin a haifesa nake jiran zuwan shi duniya saboda Allah ya jarabceni da son shi, kuma tunkafin a haifesa nasan cewa shi ne magajin kurkukun kaddara, Nasan za ka yi mamaki, amma ni kowani ɗa da ya'yana zasu haifa sai nayi duba akan shi don insan menene acikin matayen su, a canada aka haifesa, a asibitin Family din aurora, lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi, for the first time da nayi tozali da shi sai da na razana, ganin ya ma wuce yadda nake tsammanin shi..." "Wanene"? Ya tambaya yana duban shi. "Hmmm, ko ban fada ba, nasan ka san wa nake magana akan shi, auraro ta fada maka ko ba haka ba" jinjina mashi kai ya yi. "Amma naji kace shi kaɗaine zai iya gadonka sihirinka meyasa? Kuma me hakan ke nufi" "Owais, ilmin mu ne na matsa fa, abun bin jini ya ke yi, tun da ga kaka da kakanni, bakowa ne zai iya hawa karagar mulkin Elder ba, dole sai wanda kaddarar ta fadamawa ba.." "Ina neman ƙarin bayani akan Sauran yaran, ƙaddarar Kurkuku da Bugun Zuciyar Kurkuku? Tayaya akai kuka za6e su a cikin fursinoni, kuka basu mukaman nan, Kuma kuka dauƙaƙa darajar su fiye da sauran prisoners din, sannan kuma saida Zuciyar Batool za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara abun ya ɗaure mun kai na"! Murmushi Elder yayi"tun kafin a haifesu muke jiran su suma.." ɗan zaro ido Owais yayi. "Nasan za ka yi mamaki, mu matsafan kurkukun kaddara munsan da akwai yara da za'a haifa wadanda zasu zo da wata baiwa wadda zai yi wuya asamu mai irin ta a duniya, amma bamusan ta ina zasu 6ullo ba, abu ɗaya da muka iya ganowa a duban mu, shine za'a haife su a ɗaya daga cikin family din Elders" "Kuma cikin ikon Allah hasashen mu Ya zamana gaskiya, ni aka samu ɗaya a family dina, musa Kuma aka samu biyu daga family dinsa.. " asannu Baba Obie ya fayyace masa komai. Yaji dadin bayanin nan sosai. "Zaka iya tuna wani ɗan Jarida da kuka kashe a lokacin baya, shekara bakwai da suka gabata"? "Meye sunan shi? "Uzair Abdallah buzu, ɗan uwan Zaheer Tajuddeen wanda ayanzu ina tare da shi kuma nasan kasan shi..." A taƙaice Chief Owais ya maimaita masa labarin don ya tuna masa. Ƙyalƙyacewa baba Obie yayi da dariya kamar fa ya fara zaucewa "Owais ƙwaƙwalwata bata mantuwa, tun da ka fadi sunan shi na tuna shi, nasan mahaifin Unaisah, da ɗan uwansa Uzair, Yan jarida mazauna garin Jos, ya'yan wa da kani, Taj yana zaune a gidan Uncle dinsa abdallah mahaifin Uzair..." da mamaki ya ke kallonsa jin yadda ya iya ruke komai. "Inaso nasan ainihin abun daya faru? Tayaya kuka gane Uzair Yana yi maku leƙen asiri har kuka kona shi a cikin motar shi? Numfasawa yayi kafin a tsanake Ya soma labarta masa.. "Doka ce duk wanda yayi mana leƙen asiri ko yasan sirrinmu sai mun kashe, idan bazan manta ba, Mun kama Uzair Yana yi mana leƙen asiri agidan gonar mu dake a joss, a lokacin Muna tsaka da tattaunawa game da kurkukun ƙaddara, karfe wani abu na dare, Yaje da camera Yana daukar mu batare da sanin mu ba, kuma a lokacin bamu boye fuskokin mu ba, Yagan mu kuma yaji komai da muke aikatawa, kwatsam Musa ya hango hasken camera din shi. ya fada mana akwai wanda keyi mana leken asiri, kuma ya dauki video din mu. Dayaji mun gane akwai mutun sai yayi saurin shigewa motar shi, Ya bata wuta, muka bishi a cikin motocin mu tare da bodyguards din mu. Da muka ga zai iya tsere mana, sai nayi amfani da sihirina gurin sarrafa motarshi, burki ya ƙwace mashi, motar ta bugi bishiya ta tsaya cak ta kashe kanta, yana ta ƙoƙarin Ya tada motar taƙi ta shi. Cikin sauri Ya buɗe motar ya fito da niyar ya gudu sai dai kash tuni mun kewaye Motar shi, yabi ya rude, hankalinsa Ya tashi Ya dinga rokonmu akan mu kyalesa Ya tafi zai fita a harkar mu, bazai tona mana asiri ba, a lokacin munyi mamakin ta yadda haryasan sirrin mu, muka tambaye shi meyasa yake mana leƙen asiri? Kuma tayaya akai yasan inda muke har yazo? Bayan haka dame dame ya sani agame da mu? Cikin rawar murya yace ya kai ziyara gidan gonar babansa da marece har dare yayi masa acan, yana akan hanyar dawowarsa ne yaga motocin mu suna shiga cikin dajin dake a kusa da gidan gonar, al'ajabi ya kamasa yayi ta tunanin su wanene a cikin motocin? Me zamuyi da tsakar dare a cikin daji a irin wannan lokacin, shine sai yabi mu don ya gane ma idonsa, yayi ta bin mu har yaga lokacin da muka shiga gidan gonar mu, Yabi bayan mu har yaga abun da muke aikatawa a sirrin ce, a lokacin daya bamu labarin bai bayyana mana cewa bashi kadai ne yasan sirrin mu ba, sai ya boye mana. Na miƙa masa hannu nace ya bani Wayarsa, bai musa mun ba, jikinsa na 6ari Ya bani, dana duba sai naga babu abun da ya dauka, na tambayesa ina videon daya dauka namu, yace min bai yi saving ba, nace masa kada ya yi mana karya, in har yanason ya tsira da ranshi, Ya faɗa mana gaskiya, Amma ya kafe akan bakansa, mun fahimci yana da kafiya da taurin kai, musa daya zuciya yace"mu kashe shi kawai" dan iya yace"a'a kada mu kashe shi, saboda idan muka kashe shi, ba zamu iya sanin sirrinmu daya sani ba, zai iya yiwuwa bashi ka ɗai ya sani ba, wataƙil ya tura ma wani. Daya ki faɗa mana gaskiya, Musa ya dauko galon din fetur abayan motar mu, ya fara masa barazanar zai kona sa in har bai sanar damu ba. Bawan Allan nan, ya razana jikinsa ya kama kerma. Unexpected muka ga ya yanke jiki ya faɗi. Da muka dudduba shi sai muka gane firgicine yayi silar da zuciyarshi ta buga ya mutu, bamu ji dadi ba, mun so Ya fara fada mana kafin mu kashe shi da kan mu, musa da yafi mu zuciya ransa ya baci, Ya ɗauƙi gawar Uzair ya zaunar da shi a mazaunin driver, Ya rufe motar, kafin Ya soma zazzaga mata fetur, kwatsam sai ga kira ya shigo wayar Uzair dake a hannuna, dana duba screen din wayar sai naga sunan dan uwana, aminina ya bayyana, Musa ya kar6e wayar daga hannuna ya ɗaga kiran da yaji muryar wani yana kira sunan shi, shine yace mishi idan yana son sanin meke faruwa ya maida kiran video call. Bayan da suka maida video call, daya tabbatar dan uwan nasa na kallon komai ta screen din wayar, sai Ya karasa zazzagawa motar fetur, Ya cinna mata wuta. Daga bisani bayan ya katse kiran, muka binciki wayar Uzair din anan ne muka ga firar da su ka yi ta whatsapp chat din su, akan leken asirin da su ka yi mana lokacin da muka handame wani malamin ahlis sunna da ya'yansa, Taj ya nuna kin amincewarsa akan bin diddigin mu, amma Uzair Ya matsa number akan saiya gano su wanene mu don ya fallasa asirin mu. Da muka ga haka, sai muka yanke shawarar zuwa gidan Taj, Don mu kashe shi, tunda mun fahimci shima yasan sirrin mu. Bamu tsaya bata lokaci ba, muka garzaya unguwar da taj Yake, adaidai Lokacin da motocin mu suka shiga layin muka hango motarsa yayin da ya ke kokarin guduwa, aguje muka bi bayansa..." girgiza kai chief owais yayi, idanunsa suka cuccuko da kwalla. "Kaji yadda komai ya faru, mu bamu san Taj yana araye ba, ai da tuni mun kashe shi, mun dai san Yarsa tana araye, bayan da muka cinna masa wuta, bamusan tare da yar sa ya ke ba, sai daga baya muka gano cewa tare da yarsa Ya gudu, hankalin mu ya tashi, muka fara nemanta, cikin sa'a muka gano tana araye, hannun Fulanin daji, muka cigaba da bibiyar rayuwarta, har zuwa lokacin da muka ɗauke ta.." ya ƙarashe labarin tare da sadda kan shi ƙasa cikin nadama da takaici. Shiru su ka yi na wani lokaci, babu mai magana a cikin su. Owais ya zaro wayarsa Ya kira cook ɗinsu Ya umarci a kawo mashi lunch a cell din kakansa. Jim kaɗan Jenior agent Ya shigo da madaidaicin tray mai dauke da kayan abinci ya ajiye a tsakankanin su. "Nasan kana jin yunwa" girgiza kai yayi"a halin yanzu owais, babu abun da nake jin daɗinsa, ko naci ɗaci zanji" "Ka daure ka ci, dan Allah" "In har zaka bani abaki kamar yadda ka sabamin lokacin da kana yaro zanci ." bai musa mashi ba, da ya ke yaji dadin hadin kan daya basu, komai ya tambaya yana amsa mashi, hakan Yasa shima Ya ɗan faranta masa. Abaki ya soma bashi yana ci suna fira. "Malaman Jazuli, tayaya akai kuka kama sa yana maku leken asiri? Naji ka ambaci sunan shi, nasan komai game da labarinsa, sheikh imam ne Ya fadamin.." a takaice ya fayyace masa komai. Murmushi baba Obie yayi"Allah sarki sheikh imam malik, ashe dama da biyu ya shiga jikina ban ta6a ganewa ba, Allah ya taimakesa da tuni shima mun kashe shi.." ya faɗa yana dan girgiza kansa. "Malam Jazuli, tun ranar da yaje suka hadu da dan iya agidan gonar mu, akan maganar sadaukarwar da zaiyi, kallo daya dan iya yayi masa ya gane basaja yayi don ya shiga jikin mu, amma sai bai nuna masa ya gane komai ba, har sukayi sallama Ya tafi, arana ta biyu dayazo yi mana leken asiri cikin rashin sa'a dan iya yajiyo kanshin mutun bare a gurin da muke, anan ya gane akwai mai bibiyar mu yana mana leken asiri, amma bamu iya kama shi ba, Harya tsere mana, sai dai abun da baisani ba, mu matsafa ne, idan muka so da sihiri zamu iya ganin komai daya faru abaya ta madubin tsafin mu, ta haka muka gane wanene shi. Da farko bamu yi niyar kashe shi ba, Na kirasa awaya na gargaɗesa akan karya kuskura Ya fitar da sirrin mu, Ya manta da abun daya gani, ya fita sabgarmu, In ba haka ba, zamu dauki mataki akansa.." da budar bakinsa sai cewa yayi"ta Allah ba tamu ba, bai fara don ya tsaya ba, mu bamu isa mu sa yaji tsoron mu ba, Da Allah ya dogara, mu zaija ma kunne muji tsoron Allah mu daina ta'addancin da mu ke yi, Idan ba haka ba zai tona mana asiri.." A lokacin nayi ƙoƙarin shawo kansa Yaki saurarena saima Ya kashe min waya, yayi zaton ja damu abune mai sauki, Dan tahalikin nan sau biyu ina masa gargadi akan Ya fita sabgar mu, amma sai Ya nace akan kudirinsa na fallasa mana asiri. Kaji dalilin dayasa muka farmakesa a tsakar dare muka daukesa da ya'yansa. Ya karashe labarin tare dakai hannu Ya dauki juice mai sanyi ya kur6a, Chief Owais sai kallonsa ya ke yi, jin komai yake kamar amafarki wai kakansa? Har yanzu yana jin zafin abun aransa. "Baba, Baka taba jin tausayi ko irin danasani, a lokacin da ka raba uwa da danta, ko ka kona mutun da ransa, ko ka keta haddin kananun Yara..." dakyar ya iya ƙarashe maganar saboda nauyin furtawa da ya ji. "bana jin komai, na fada maka, duniya nasa agaba, evils din jikina babu Allah aransu, bansan tausayi ko imani ba.." "Amma yanzu ina fata babu evils a jikinka da sauran Elders dama kowa dake da sihiri ta 6angaren ka" Yar dariya baba Obie yayi"kana tambayata ne saboda bakason in an tashi hukuntamu mu 6ace ko evils su taimake mu"? Girgiza kai Owais yayi"a'a kawai inaso na sani ne" "Babu Owais, Evils sun koma mazaunin su, na kuma binne sihirina babu wanda zai iya tono shi, In ba magajina ba" "In sha Allah shima magajin naka bazai ta6a binno shi ba har abada, mun rabu da annoba" dariya baba Obie yayi yadda kasan baida wata damuwa. "karka damu Owais, ai magajin nawa ya ƙyamaci abun a zuciyarsa tun farko shiyasa ko evils suka gaza yin tasiri akan shi, gadai shi amatsayin Evil giant amma bamu isa mu juya shi son ran mu ba, duk da nasan Allah ne ke tsare shi, akwai kariyarsa atare da shi, bayan haka sai gashi Kaddarar da muke tunanin killace ta zai zamar mana mafita, tazo ta sace Zuciyarsa har ma da evils dinsa, ni kaina nagaza sarrafa shi son raina, wannan yarinyar ba ƙaramar ta'asa tayi mana ba, yar mitsila da ita, owais nifa ban ta6a ganinta ido da ido ba, sai dai a madubin tsafina, sai kuma ranar dinner din Hateem, amma ina jin labarin taƙadarancin ta..." baisan ya akai maganar baba Obie taso bashi dariya ba. "Kana jin haushin tayi silar lalata komai naku"? "Bana jin haushinta Owais, hasalima burge ni ta ke yi, Ina son yaro masifaffe mara tsoro, mai ƙwarin gwiwa, kuma kaga tayi silar da kuka kawo karshen kurkukun ƙaddara, gaskiya na jinjina mata,..." ya fada da murmushi akan fuskarsa. "owais nifa lamarin Ubangiji Ya razana ni wlh, yadda komai ya sauya, duk wani munafunci da makircin da muka daɗe mu na yi a boye, tsawon shekaru bamu ta6a yin Kuskuren da wani zaisan koda suffar mu ta asali ba, amma wani abun daure kai, Cikin yan watanni komai ya warware, asirin mu Ya tonu, gamu a cikin cell, mu da muka saba garƙame ya'yan mutane kamar dabbobi, Yau mune a garƙame? Kurkukun da muke ƙuntata rayuwar mutane, mu azabtar da su a cikin sa, yanzu babu shi, muma nan da ƴan kwanaki ka ɗan zamu shige shi, Owais Allah abun tsoro duniya abun tsoro! owais komai dana mallaka ayanzu babu shi, na rasa dukiyata, ya'yana, yancina, mutuncina, gidana, farin cikina, komai owais, ban taba zaton ma rana irin wannan zata zo ba, owais inaga idan na mutu? Aka binne ni daga ni sai mugun halina? Meyasa ban fara tunanin menene makomata ba kafin na aikata badaidai ba? Meyasa banyi tunanin dole fa wata rana in mutu ba? Kuma komai dana mallaka a gidan duniya zan bar shi? kuma ita duniya ba madawwama bace, zama ne na dan lokaci, Kodai kayi ayyuka nagari ka ceci kanka duniya da lahira ko kuma ka dawwama cikin nadama da bakin ciki.." ya faɗa da damuwa akan fuskarsa. "Owais na shiga Uku, na bani na lalace! Ya zanyi Owais! Na riga na 6ata komai! Koda zan tuba Allah bazai yafe hakkin wadanda na zalunta ba, shine zunubi mafi muni da haɗari arayuwa, basa araye balle in nemi yafiyarsu, da zan curo maka zuciyata kaga yadda bakin ciki ke konata da raɗaɗi wlh zakayi mamakin meyasa bata dakata da bugawa ba" Tausayin sa ne ya kama Owais, har baisan sa'adda ya mike ya zagaya ta bangarensa ya zauna kan table din gaban sa ya rungumo shi a kirjin shi, kukan ma kasa zuwa masu yayi sai dai suka kama yin kukan zuciya, wata irin soyayyar shi Allah ya jarabceshi da ita, bamashi ba duk Wanda yake rayuwa da Obie zaiji irin ta a zuciyarshi saboda yadda yake kyautata ma ahlinshi dama wadanda ba ahlinsa ba kowa nashi ne ga jin kan na kasa dashi da son taimakon wanda baida shi, in badan haka ba karamar tsanarshi zaiyi ba baba Obie ya cici kanshi suma ya cucesu .. Kwana su ka yi a rungume da juna, ba bacci, sai zullumi da fargaban hukuncin da kotu zata yan ke mashi. Kamar yadda suma can Ahlin nasa basu iya runtsawa ba, kwana sukayi a zaune, sun yi kuka har sun gaji damuwa taci tacinye su, saura jiran tsammani *Daga Alƙalamin Boss Bature🔥🌹* ~_______________________________🔥~ *COURTROOM, FEDERAL HIGH COURT* *BABBAR KOTUN TARAYYA* A ranar da za'a yi zaman shiri'ar Elders kar ku so ku ga yadda jama'a suka dadda6e babbar kotun tarayya, ta ko'ina zauren kotun ya cika maƙil da ƴan jarida, da kuma human rights activists) masu fafutukar kare hakkin ɗan adam) ƴan majalissa da ministoci, gwamnoni da sauran manyan ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki a ƙasa. Wasu daga cikin iyalan Elders sun hallara, kuma abun ƙayatarwar, gaba ɗaya an buƙaci a zo da fursinonin kurkukun ƙaddara da suka rage. Ba'a ta6a yin shari'ar da ta ja hankalin duniya ba irin wannan, saboda kowa jiran ta yake yi, idon duniya ne akan kotun tarayyar Abuja, kowa ya ƙagara da ya ji hukuncin da za a yanke masu, sa'ilin da Isod Agents suke shigowa cikin zauren kotu tare da Elders sun yi masu ƙawanya, baka iya ganin fuskokinsu saboda an yi masu alfarmar rufe fuskar su da mask, amma idanunsu a buɗe suke. Alƙalin da zai yi shari'ar babban mutunne dattijo, Justice Salahuddeen Muhammad tsohon abokin baba Obie ne, yana a zaune kan kujerarsa, cikin shigar sa ta alƙalai, idanunsa sanye da farin glass. Bangaren Prosecutors gaba ɗaya sun hallara kowan nan su yana zaune kan kujerar sa, ga uban case files na kurkukun ƙaddara a gaban su suna duddubawa. Dangin baba Obie sun fi kowa shiga tashin hankali da damuwa. Lokacin da Justice Salahuddeen ya fara magana kotun ta yi tsit kamar mutuwa ta gifta, ko sautin tari baka ji saboda kowa burinsa ya ji me alƙalin ya ke cewa.. "This court is now in session..." Ya faɗa a nutse tare da kallon al'ummar dake cikin kotun, umarni ya ba court registrar na ya yi announcing shari'ar da za a saurara, bayan ya miƙe ya soma karantowa kamar haka, "The case before us today is that of the Federal Republic of Nigeria and Mr. Obinna Chimaobi wanda kowa ya fi sani da dattijon arziƙi, Alhaji Musa Wadata former president of our country, Ifeanyichukwu Lucas, Ja'afar Falgore wanda aka fi sani da Ɗan Iya......" Gaba ɗaya saida ya zayyana sunayen su, kafin alƙali ya buƙaci da a fiddo su gaban kotu, gaba ɗaya idanu suka koma kan su, kunyar duniya ta kama su, sun muzanta sosai, duk suka kasa haɗa idanunsu da na kowa bayan da aka buɗe fuskokinsu, hannayensu da ƙafafuwansu gaba ɗaya ɗaure suke da sarƙa, kamar dabbobi da ƙyar suke ɗangyasa ƙafafunsu. Har suka ƙarasa da su inda za su tsaya wato cikin dock, ba su ɗago da ido sun dubi al'umar da ke a cikin kotun ba, iyalin baba Obie sun shiga matsananciyar damuwa, hankalinsu na kan mahaifinsu tun lokacin da aka shigo da su suke ta kallon shi idanunsu cike da ƙwallar baƙin ciki, gaba ɗaya zuciyoyinsu a cike suke da zullumi da fargaba, haka ma sauran iyalan elders da suke a cikin kotun baƙin ciki ne ƙumshe cikin zukatansu. A duniya kenan ina ga ranar tonan asiri ta lahira. Bayan an fiddo su aka fara announcing of appearance, in da prosecutor ya miƙe cikin natsuwa, bayan ya yi kalamin girmamawa ga alƙali ya soma bayyana kan shi tare da sunan shi, ya ɗaura da faɗin, "...On my humble appearance is for the prosecution." Bayan ya gama ya koma ya zauna, wani ma ya miƙe bayan ya gyara rigar shi ta lauyoyi ya fara bayanin kan shi kamar yadda wanccan ya yi, ya ɗaura shima da faɗin, "...My humble appearance is for the defendants. (lauyan waɗanda ake ƙara) Haka duk suka rinƙa tashi suna gabatar da kawunan su. Bayan sun kammala prosecution counsel (Lauyan da ya yi filing case ɗin daga hukumar Isod) ya sake miƙewa ya bayyana charges da ke gare su tare da ranar da aka shigar, ya ɗaura da faɗin, "...The defendants are accused of dark magic cult, human sacrifices, kidnapping, torture, murder, and human trafficking." ("Waɗanda ake tuhuma, ana tuhumar su da laifin baƙin sihiri, sadaukarwar mutane, garkuwa da mutane, azabtarwa, kisan kai, da fataucin mutane.") Bayan ya gama zayyana laifukan da ake tuhumar su da su ya buƙaci da a karanta ma masu laifin charges ɗin don su amsa, bayan alƙali ya bada damar hakan court registrar ya miƙe idonshi akan elders ya ce masu ga abubuwan da ake ƙarar su akai su saurara don su ji, he reads the charges to them openly, da turanci ya zayyana masu kamar yadda ake magana a cikin kotun, amman duk da haka bayan ya gama sai da ya tambaye su sun ji abun da ya karanta ko akwai wanda bai fahimta ba bai jin yaren da aka faɗi da shi, wasu daga ciki ne suka jinjina kai alamar sun fahimta, yayin da wasu sukai shiru ba tare da sun ɗago kai ba, sanin su su waye kuma an san suna fahimtar yaren da ake magana da shi ya sa aka ci gaba, Prosecution Counsel ya sake miƙewa cikin nutsuwa ya soma kora jawabi dangane da kurkukun ƙaddara, bai yi kuskuren ko da harafi ɗaya ba, komai da Elders suke aikatawa a gidan kurkukun ƙaddara da irin azabtarwar da suke yi wa fursinoni saida ya zayyana su tiryan tiryan...." Kowa da ke a kotun ya nutsu yana sauraron shi, idanun mutane suka cuccuko da ƙwalla saboda tausayin prisoners da ya kama zuciyoyinsu, shi kan shi alƙalin farin ruwa ne kwance a cikin idanun shi. Kowa ya shiga tashin hankali da firgici, mutane sai girgiza kai suke wasu har da matse ƙwalla. Elders kuwa cikinsu ya ɗuri ruwa, sai zazzare idanu suke yi, cikin tashin hankali da kunyar duniya.. Bayan da me gabatar da ƙara ya ƙarasa zayyana komai da kuma hujjoji da shaidu.. A ƙarshe ya ce, "We urge the court to impose the maximum penalty for these heinous crimes." (Muna roƙon kotu da ta zartar da mafi girman hukunci kan waɗannan munanan laifukun) Ya koma ya zauna a mazauninsa. Jinjina kai Alƙali Salahudeen ya yi tare da numfasawa cikin murya mai kaushi ya furta, "Thank you, Br. Nawaz." Maida duban shi ya yi kan elders ya ce sun ji laifukan da ake tuhumar su da aikatawa sun amince? Farko duk shiru suka yi idanun mutanen kotun na akan su, kowa na su ya ji mi za su ce, Baba Obie ne ya fara jinjina kan shi tare da furta ya amince, duk sauran ma suka yi hakan, amman abun mamaki Musa nunawa ya yi bai amince ba, fuska a murtuke rabinta an rufe da bandeji ya ce yasan ya ta6a yin sadaukarwa don biyan buƙatun shi, kuma duk yaran da ya sadaukar jinin shi ne, don haka ƙazafi ne aka yi mashi shi bai aikata sauran laifukan ba kuma shi baya a cikin elders, jin abun da ya ce yasa Pravin a ruɗe shima ya ce sadaukarwa kawai ya ta6a yi bai aikata sauran laifukan ba baya a cikin elders, bayan da farko ya jinjina kai alamar ya amince, Ɗan-iya na so shima ya musa tuhumar da ake mashi amman ba dama don yasan iya gawar Anah da aka tono ta isa hujja akan shi, duk da halin damuwa da Chief Owais yake a ciki sai da ya ɗan yi murmushin takaici ganin yadda suke son naɗe tabarmar kunya da hauka, Jin haka ya sa alƙalin maida duban shi kan lauya masu ƙara ya ce mashi ya ji abun da suka ce na basu amince ba, miƙewa ya yi ya ce in an bashi dama zai gabatar da hujjoji alƙalin ya ce an bashi, lauyan ya buƙaci a fiddo da prisoners gaban kotu, bayan sun fito gaba ɗaya sun tsaya a cikin witness stand lauyan ya je gaban su a nutse ya fara yi masu tambayoyi game da kurkukun kaddara da abubuwan da ake aikatawa, gaba ɗaya sai da suka faɗi komai da ake aikatawa, bayan ya gama yi masu tambayoyi ya gabatar ma da kotun hotunan kurkukun ƙaddara da aka ɗauka lokacin da su Owais suka kai farmaki na biyu, bayan su ya ƙara gabatar ma kotun da wasu shaidu wanda suka samu daga wurin Baba Obie ciki harda vediotape na elders da su kan su basu san da shi ba da kuma list na sunayen su da bayanan su, harda hotunan abubuwan da aka samu a gidajensu da aka je bincike. Bayan ya gama gabatar ma da kotu duk hujjojin, alƙali ya maida duban shi kan lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma ya ce, "Defenses, do you have any statements to make?" Farko duk shiru suka yi kafin wani ya miƙe ya gabatar da kan shi a matsayin lauya mai kare Alhaji Musa (Dama kafin a zauna zaman shari'a, waɗanda ake tuhuma da laifi suna da hakkin ɗaukar lauyoyi da za su kare su), Ya fara bayani da cewa sam bai gamsu da hujjojin da aka gabatar akan alhaji Musa ba saboda za a iya yi mashi ƙazafi tun da shi babban mutum ne ɗan siyasa dole bai rasa maƙiya masu son ganin bayan shi, kuma duk hujjojin da aka bayar basu isa su gamsar da ya aikata sauran laifukan da ya ce bai aikata ba tun da yanzu muna a lokacin technology duk za a iya ƙagar su, har prisoners ya tambaya kan ko lokacin da suke a kurkukun sun san su waye elders duk suka amsa da basu sani ba, ya ce ko wannan ma hujja ce da zata sa kotu ta yarda ba lalle yana cikin su ba, bayan ya gama jawabin shi ya roƙi kotu da ta yi nazari sosai kada ta amince da hujjojin da aka bayar kafin ya koma ya zauna, hannu chief Owais ya kai ya ruƙe ha6ar shi, a ranshi yana mai mamakin wani alƙawari Alhaji Musa ya yi ma lauyan da har ya iya yin wannan ƙarfin halin. Bayan lauyan masu ƙara ya sake miƙewa ya buƙaci da a bashi dama zai ƙara gabatar da wasu hujjojin alƙali ya bashi, Unaisah ya buƙaci ta fito, bayan ta tsaya a wurin da aka tanada ya fara yi mata tambayoyi kan ko tasan alhaji Musa, aikuwa kaman tana jira nan ta shiga kora jawabi tun daga kan zuwan Unaizah kurkukun ƙaddara da yadda ta mutu da wasiƙar da ta bata da diary ɗinta mai ɗauke da hotunan su har da shi, daga ƙarshe ta yi bayanin yadda ya sace su ita da Batool ya sake maida su kurkukun kaddara don cika ƙudirin shi na zamowa shugaba inda har ta yi nasarar watsa mashi acid ta kuma buga mashi zarto a kafaɗa, bayan ta gama lauyan ya yi ƙarin bayani tare da nuna ma alƙali ciwukan da Unaisah ta ji ma alhaji Musa, daga baya ya gabatar ma kotu da wasiƙar tare da diary ɗin Unaizah. Bayan alƙali ya gama duba su ya tambayi lauya mai kare Alhaji Musa ko akwai abun da zai ce, miƙewa ya yi ya ce duk abun da Unaisah ta faɗa zasu iya zamowa ba gaskiya ba shirya mata aka yi amman yana son a bashi dama ya yi mata tambayoyi alƙali ya ce an bashi, tun da ya tsaya a gabanta ta wani murtuke fuska, tambayoyi ya fara yi mata kan yadda ta ce alhaji Musa ya sace su ya maida su kurkuku, duk tambayar da ya yi mata sai ta bashi amsa, "Kin ce bayan ya maida ku kurkukun, ya sanar da ke kudirin shi na son kashe ki sannan kuma ya cire zuciyar ƴar'uwarki, a ƙarshe kuma kika yi nasarar watsa mashi acid kika kuma raunata mashi kafaɗa, duk yana mi har kika samu damar da ke kika aiwatar masa da hakan ba tare da shi ya aiwatar da ƙudirin na shi a kan ki ba?" Wani kallo ta jefa mashi tana tura baki tare da hura hanci ta ce, "Allah ne bai nufa zai cutar da ni ba duk da ya samu damar hakan, kuma dama Allah Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi ba zai iya ku6uce masa ba, haka na sanar da shi a lokacin, to a ranar dama Allah ya ƙaddara dubun shi zata cika, dama na sanar da shi idan muka roƙi Allah ba kai tsaye yake taimakon mu ba don shi ba a ganin shi sai dai ya yi mana hanyar da taimakon shi zai iso gare mu, a lokacin na ce mashi in sha Allah zai ga yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri har ya yi nasara akan wanda ya zalunce shi, amman sai ya ƙalubalanci hakan da na faɗa ya ce wai zai jira ya ga ta yadda taimakon Allah zai iso gare mu, nasan Allah ne ya nuna masa ishara shine dalilin da ya sa ya jinkirta aikata abun da ya yi niyya a gare mu." Ba ƙaramin burge mutane ta yi ba yadda ta kora mashi jawabin, mutane suka shiga jinjina kai wasu da murmushi akan fuskokin su. Ƙarshe lauyan ya ƙaryata cewa Alhaji Musa ya aikata masu hakan ya ce duk sashi faɗi ne, ba yadda za ai ya samu dama irin haka amman ya kasa aiwatar masu da kudirin shi har ita ta yi nasara akan shi, in ma da gaske ne hakan ya faru da su to akwai yuwuwar bata a cikin hayyacinta ne ta ruɗe har ta kasa tantance wanda ya aikata masu hakan, yana rufe baki a tsiwace ta ce, "Ina a cikin hayyacina! Na yi rayuwa a cikin kurkukun ƙaddara na tsawon lokaci, tun ina da shekara 11 na tsinci kaina a kurkukun, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, an yanka mutum an feɗe gaba na, an yi mani wankan jini! Na ga abubuwan tashin hankalin da sun isa su saka ni in haukace amman hakan bai faru da ni ba, sai wannan ne zai sa in fita hayyacina har in kasa gane wanda ya aikata mini? Wannan azzalumin shine ya sadaukar da ni a kurkukun, kuma shine ya yi ma mahaifiyata asiri a ranar da ta haife ni ta tafi ta bar ni tsawon shekaru ba a san in da take ba saboda tasan wani sirrin shi da ya danganci kurkukun ƙaddara, shine kuma ya yi ma Uncle ɗina Shureim tare da makwabciyar su asiri saboda ta ce bata son shi Uncle ɗina take so sannan kuma yana jin haushin mahaifinta Sheikh Imam. Shi Elder ne! Duk abun da aka zayyana yana aikatawa wallahi..." Kuka ne ya ƙwace mata ta duƙar da kanta, duk da yadda ta yi maganar da tsawa har tana nuna Alhaji Musan da hannu ya sa6a ma dokar kotun amma alƙalin ya kasa dakatar da ita, gaba ɗaya kotun ta karaɗe da hayaniyar mutane, ƙarfin halinta ya matuƙar burge mutane, kuma ta ba mutane tausayi, hatta alƙalin ma ta bashi tausayi, umarnin a mayar da ita wurin zamanta alƙalin ya bada, kusan a tare Benazir da Owais da Shureim harda kakanninta da ƴan uwanta prisoners duk suka miƙe don su tarbe ta, kotu fa ta harmutse da hayaniya, har saida alƙalin ya bubbuga gavel ɗinsa tare da ambaton, "Order, order!" Sannan kotun ta daidaita, daga haka alƙalin ya sanar da kotu zata tafi hutu na ɗan wani lokacin kafin a dawo a ci gaba da sauraran shari'ar. Bayan wa'adin da alƙalin ya ɗauka ya ƙare aka dawo zaman ci gaba da sauraran shari'ar. A lokacin lauyan masu ƙara ya buƙaci Benazir, Batool, Shuraim, Ummi da kuma Sheikh Imam duk suka fito ya yi masu tambayoyi, duk suka amsa mashi saidai ba komai da ya faru da su suka faɗi ba sun bar wasu abubuwan matsayin sirri, haka shima lauyan dake kare Alhaji Musa ya yi masu tambayoyin ba kamar Batool ya fi yi mata tambayoyi game da komawar su kurkuku, a lokacin har saida alƙali ya buƙaci a gabatar masa Dr Mark, Chief Owais ne ya yi ma kotu bayanin cewa ya gudu amman suna akan binciko shi za su samo shi su kawo shi kotu shima da sauran likitocin dake da sa hannu a case ɗin. Ƙarshe dai sai da aka ƙure lauyan alhaji Musa saboda tarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu waɗanda ke nuna yana aikata duk laifukan kuma yana cikin elders, tun kan a dawo kan Pravin ya tabbatar ma kotu yana cikin elders don yasan shima za a samu hujjojin da zasu tabbatar da shi ba kamar da ya ga harda vedio recording ɗin alhaji Musa na cikin Cell ɗin hukumar Isod aka kunna ma alƙalin in da wasu maganganun da ya yi suka tabbatar da laifukan da ake tuhumar shi, ya san shima sun yi maganganun da Owais shiyasa ya saduda, amma ya ce ma alƙalin wllh Baba Obie ne ya yaudare shi ya saka shi cikin su ba da son ran shi ba. Bayan sauraran tarin hujjojin lauya mai ƙara, alƙali ya tambayi lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma kan ko suna da sauran abun da za su ce, Gaba ɗaya wutar su ta ɗauke, saboda basu da wani ƙwarin gwiwa ko hujjar da zasu iya kare su, gashi akwai masu son su nemawa dattijon arziƙi sassauci saboda da yawansu mutanan da suke mutunci da shi ne, da ƙyar wani bayerabe daga cikin su ya yi ƙarfin halin miƙewa ya ce, "Your Honor, while we acknowledge the severity of the crimes committed, we urge the court to consider the defendants ages, health, and social status. We request leniency in sentencing." (Ya mai girma mai shari'a, yayin da muka amince da girman laifuffukan da suka aikata, muna roƙon kotu da ta yi la'akari da shekarun waɗanda ake tuhuma, da lafiyar su, da kuma matsayin su na zamantakewa. Muna neman a sassauta hukunci) Ya faɗa tare da komawa ya zauna. Bayan nazarin da Alƙali ya yi, ya ɗan numfasa na wani lokaci, kafin ya ɗago ya dubi ilahirin mutanen dake a kotun. Cikin kakkausar murya ya furta. "I have reviewed the evidences presented in this case, and I find the defendants guilty on all counts, The crimes committed are among the most heinous and reprehensible imaginable..." Karanto hukuncin da kundin tsarin dokokin ƙasa ya tanada ga dukkan laifukan ya yi kafin ya dunƙule hukuncin da kotu ta yanke masu ya ce,"The court hereby, sentences each of the defendants to, Life Imprisonment without the possibility of parole (ɗaurin rai da rai batare da sakin layi ba) a cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa." Sallallamin da jikokin Obie ke yi ne ya cika kotun, ba ka jin sautin komai sai na, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.! Gaban Elders ya shiga faɗuwa cikin firgici da kiɗima suke ƙara zazzare jajayen idanunsu, ganin yadda reshe ya juye da mujiya, abun da suke yi ma wasu yau sune za a yi mawa, kurkukun ƙarƙashin ƙasa da alƙali ya faɗa wani kurman kurkuku ne saboda tsaronsa da uƙubarsa ya sa mutane suke yi masa laƙabi da kurkukun azaba, saboda mawuyacin abu ne mutun ya zarce watanni batare da zafin jail ɗin ya lahanta fatar sa ba, ƙuntatarsa kamar ƙabari, baka ganin kowa babu haske cikin duhu, ɗan hasken da za'a iya samu na wasu hudoji ne guda uku da ke a saman jail ɗin, dai dai da wanda zai kawo maka abinci ba zaka gansa ba, ta wata ƙaramar ƙofa da ke a jikin ƙofar jail ɗin su ke zuro maka kwanan abinci, kai kanka ba zaka san an kawo maka abinci ba, in har ba ka jiyo motsin buɗe ƙaramar ƙofar ba, daga kai sai halin ka a cikin jail ɗin nan, ba shige ba fuce, da yawa waɗanda ake kaiwa cikin kurkukun miyagun ƴan ta'adda ne masu haɗarin gaske, kamar Elders ɗin dai. Alƙali bai dakata ba ya ɗaura da cewa, "Dukiyar su da suka mallaka ta haramtacciyar hanya, Kotu ta mallakawa waɗanda abin ya shafa.." Ya faɗa yana kallon bangaren da fursinonin Kurkukun Ƙaddara suke a zazzaune kan kujeru sun yi shiru sun nabba'a, fuskokinsu ɗauke da murmushin farin ciki, kamar su zuba ruwa ƙasa su sha, sun ji daɗin hukuncin da aka yankewa Elders, ransu fari tass, ba don Dg ya gargaɗe su akan su nutsu ba in an shiga zaman shari'ar, da ba abun da zai hana su fasa ihun murna. "Ƙadarorinsu da suka mallaka ba bisa ƙa'ida ba, za a yi gwanjon su, abun da aka samu gwamnati zata yiwa ƙasa amfani da su..." Alƙali Salahudeen bai dakata ba, ya ci gaba da cewa, "Bayan haka kotu ta soke duk wata daraja da muƙami na su, bugu da ƙari, kotu ta bayar da umarnin a saka sunayen su a cikin rajistar masu aikata laifuka ta ƙasa!" Alƙali Salahudeen yana kai ƙarshen maganar shi, ya damƙi gavel ɗin gefensa mai kama da metal hammer ya buga da ƙarfi saman table ɗin gabansa, (shari'a ta ƙare) Zauren kotu ya harmutse da hayaniyar al'umma, masu kuka suna yi, masu murna suna yi, masu 6acin rai suna yi, kowa da abun da ya dame sa. Prison Officers tare da Soldiers ne suka tasa ƙeyar Elders suka fito da su harabar kotun, mutane daddabe da su, ƴan Jarida sai neman tattaunawa suke yi da iyalansu sun ƙi basu haɗin kai saboda tashin hankalin da suke a ciki. A wata ƙatuwar Prison Van za a shiga da su, wasu har sun fara shiga, Musa yana ta gurnani yana tirjewa kamar 6auna, bai aune ba, ya tsinkayi muryar hajiya Sarah a kunnansa. "Ba na ta6a faɗa maka ba? In har akwai mai cutar wani tsakanin ni da kai Allah zai yi masa sakayya..." A firgice ya waigo yana fitar da hucin 6acin rai. Tana a tsaye ta sanya baƙar abaya da niƙab. A hankali ta zame niƙab ɗinta, ta watsa mashi kallon ƙasƙanci. "Hakkin Unaizah ne ke bibiyarka, la'ananne... " Ta faɗa tare da tofa mashi kakin majina saman fuskar shi, ya yi wata zabura kamar zai cafkota sojoji suka rurruƙe shi, tare da ingiza shi cikin motar kamar dabba sai waiwayonta yake yi cikin ƙunci da baƙin ciki. Yana tsaka da waiwayon ta, ya hango hajiya Layla a bayanta bakinta washe kamar wadda ta tsinci haƙori, ɗaga mashi hannu ta yi, "Allah ya raka taki gona Musa, Allah ya ƙara nauyin ƙasa, sai mun haɗu a filin hisabi na lahira.." Ta ƙyalƙyace da dariya, wani irin baƙin ciki ne ya ziyarce shi kamar ya haɗiyi zuciya. "Ina maka fatan sauka ƙabari lafiya, kar ka wani damu zan ci gaba da kula da mommyna.." A ɗimauce ya kai idonsa ga Omar, yana tsaye bayan Chief Owais, wlh kwata kwata bai lura da su ba a kotun saboda bai ɗaga idonsa ya dubi kowa ba ashe duk sun hallara. Unexpected ya tsinkayi muryar Sheikh Imam Malik a cikin kunnansa. "Musa ina tayaka murnar kar6ar sakamakon zunubin ka na duniya.. " Cikin 6acin rai ya wurga idanunsa gurin da Imam Malik ya ke, gabansa ne ya faɗi ganin Ummi da Shureim sun saka Imam Malik tsakiya, daga gefen su Batool da Unaisah ne tare da Benazir, sai faman washe baki suke yi. Ya Ilahi! Kamar ya fasa ihu yake ji saboda baƙin cikin da ya turnuƙe zuciyarsa, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi magana Isod soldiers suka turmuƙa kan shege bayan motar, suna juyo kururuwar baƙin cikin da ya ke saki. Daidai Lokacin da Isod soldiers suka fito da baba Obie suna ƙoƙarin shigar da shi bayan motar, ƴa'ƴansa da jikokinsa suka kewaye shi, suna ta kuka kamar ran su zai fita. Ya dinga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, cikin karyewar zuciya, kallon bankwana yake musu, saboda ya san ba zai sake ganinsu ba, wannan tafiyar bata dawowa bace ta mutuwa ce. Babu Saratu a cikinsu, a gida suka kulle ta a ɗaki, Momma ma bata halarci kotun ba, da wasu daga cikin jokokinsa. Da raunannun idanunsa ya dubi ƴa'ƴansa cikin sanyin murya ya ce, "Ku yafe min, yawancin yaran da nake sadaukarwa na ku ne, wataƙil idan kuka yafe mini in samu salama a cikin Zuciyata" A tare suka haɗa baki gurin furta, "Zamu yafe maka, amma ka fara amsa buƙatar mu, ka musulunta baba, muma shi kaɗai ne fatan mu, ko mun samu mu dinga saka ka a addu'ar mu." Girgiza kanshi ya yi zafafan hawaye na sintiri kan fuskarshi ya ce, "Kuma kun sani, tuba na ba zai kar6u ba a wurin Allah, ban tuba ba saida asirina ya tonu? Bayan na sani na take sani?" Roƙonsa suka dinga yi suna masa magiya kamar zasu haɗiyi zuciya, Sheikh imam Malik ya sanya baki ya ce ya taimaka ya amsa buƙatar ƴa'yansa shine abu na ƙarshe da zai yi musu a duniya, da ya san halin da ya jefa su da bai musa akan buƙatarsu ba, har yanzu suna son shi, kuma musuluncin da zai kar6a kan shi zai yi mawa, shi ba zai ce kar ya musulunta ba, babu wanda ke shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa, in Allah ya so shi da rahama sai ya ga ya samu sassauci.." Kalamai masu tausasa zuciya Imam Malik ya furta masa, amma baba Obie ya kafe akan bakansa. Sojoji suna ƙoƙarin su shigar da shi, kwatsam! Muryar Hajiya Saratu ta karaɗe kunnuwan kowa. "Baba! Baba...!" A ruɗe ya shiga wurga idanunsa yana ƙoƙarin ya hango ta, kamar mahaukaciya, babu kallabi ko takalma a ƙafafunta, twins suna a biye da ita, hannayen kowan nan su ruƙe da mayafinta da takalmanta, ganin halin da take a ciki ne yasa mutane suka dinga darewa suna bata hanya don ta wuce, kowa ya razana da ganin Minister of Health cikin wannan halin. Hankulan Yayyenta ya tashi, basu san tayaya ta buɗe ƙofar ɗakin da suka kulle ta ba, wallahi da gudu ta nufi baba Obie tana ƙarasowa ta rungume ubanta tana kuka, shima kukan ya 6alle masa, hankulan kowa dake a gurin ya dawo kan su, gwanin ban tausayi, baiwar Allah mace mai rauni, a lokacin ta fidda rai da shi, cikin shesshekar kuka ta ce, "Baba ka yi haƙuri, kulle ni suka yi a cikin ɗaki shiyasa ban zo ba, meyasa zasu hanani ganinka bayan wannan ne gani na ƙarshe tsakanina da ubana. Baba ka yi haƙuri ni dai na yafe maka duniya da lahira, Ubangiji Allah Ya yafe maka, kuma zan dawwama ina yi maka addu'a akan Allah ya yafe maka zunubbanka..." Kalaman Saratu sun karya zuciyarshi, rungumar da ta yi mashi tasa ya ji sanyi a cikin zuciyarshi. "Saratu, mahaifin ku ya ƙi kar6ar musulunci..." Sheikh Imam ne ya faɗa yana daga bayanta. Baiwar Allah ita sam ta manta baban nasu ba musulmi bane, hada guzurin cazbaha ta kawo mashi wadda zai dinga yin tasbihi da ita a cikin jail. Maganar Sheikh Imam Malik ce ta tunasar da ita, nan fa ta fara roƙon shi tare da damƙa mashi casbahar a cikin tafin hannunsa ta dunƙule masa yatsunsa don kar ya yada ta. "Baba na roƙe ka ka musulunta saboda tsoron Allah baba, ba don saboda mu ba, don Allah ka taimaka ma rayuwana..." Tana kuka hada majina, har lokacin bata raba jikin ta daga na shi ba. Tunkan ta ji amincewar shi ta shiga karanto mashi kalmatusshahada, cikin karyayyar murya ya dinga amsa mata har ƙarshe. Gaba ɗaya suka haɗa baki gurin furta, "Alhamdulillah, Allahu Akhbar..." kwata kwata ba su yi zaton zai iya furta Kalmatusshahada ba. Suna kuka suka ce, "Mun yafe maka baba, duniya da lahira, Ubangiji Allah ya yafe maka." At lease ya samu sassaucin radadin da yake ji a cikin zuciyar shi ganin ya faranta masu. Sheikh Imam Malik ya tausaya masu bai san sa'ar da hawaye suka fara zarya kan kuncin shi ba. "Baba na canza maka suna, daga yanzu Imam zamu dinga kiran ka ba Obinna ba..." Cikin kuka ta faɗa, murmushi ya yi, idanunsa akan fuskarta a lokacin ta ɗago da kanta. Ya sumbaci goshin ta, ya miƙa ma Hateem hannu ya matso kusa da shi yana share ƙwallarsa, shima ya sumbaci goshin shi tare da hugging nasa, Sharafudeen ya matsa ya rungume shi, tare da sumbatar goshinshi, da sauri Deen da Lateef suka rungume shi, suma ya sumbaci goshin su, Abdul Razak ya matsa ya sumbace shi, Sir Mubarak ma ya je ya rungume shi sosai. Owais dake kallon komai shima ya zo ya yi hugging nasa tare da sumbatar goshinsa, ƴan jarida da ke kallon komai sun ma kasa mayar da hankalinsu kan aikinsu, sai aikin share hawaye suke yi, basu ta6a ganin soyayya tsakanin Uba da Ƴa'ya irin wannan ba, kowa al'ajabi ya ke yi, duk irin cutarwar da ya yi masu amma basu daina son shi ba, wannan bakomai bane face Ikon Allah. Cikin raunanniyar murya ya furta, "Allah Ya yi maku Albarka..." Ya mayar da dubansa kan Imam Malik ya ce, "A matsayina na mahaifinsu, na baka amanar su, na mallaka maka ƴa'ƴana, ka maye musu gurbina, ga autana duka na baku amanarta, ita kaɗai ce mace a cikin ku tana da rauni, don Allah Imam ka amshi tayi na ba don mugun halina ba... " Cikin sanyin murya sheikh Imam yace, "Na kar6a hannu bibbiyu Imam, zan ruƙe maka amanar su, In sha Allah bazan bari su yi maraicin Uba ba..." Murmushin ƙarshe Baba Obie ya sakar musu, daga haka sojoji suka shigar da shi cikin motar. Wani irin kuka hajiya Saratu ta fashe da shi, ta zube kan gwiwowinta tana ambaton, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..!" Cikin sauri yayyenta suka rurruƙeta tare da miƙar da ita tsaye, Hateem ya rungumeta a ƙirjin shi, suka haɗu suna lallashin ta cike da ƙarfin hali. Suna a wannan halin, suka jiyo kukan Praveen kamar ƙaramin yaro, yana ta sambatu yana ambaton sunan Hajjaty da ƴa'ƴanshi, kusan a tare suka kai duban su kan shi, yayin da Prison Officers suka nufi ɗayar motar kurkukun, sai tirjewa yake yi, idanunsa jawur ya ke duban twins ɗinsa da Saratu da ta ɗago da kanta daga ƙirjin Hateem tana duban shi. Haushin shi da tsanar shi ne ya cika zuciyar su, babu alamun sun ji tausayin shi. Zaid ne kaɗai ya ɗan tausaya mashi har ya je gaban shi ya ɗan rungume shi, Sir Mubarak ya nufe shi yana zura hannu cikin trouser pocket ɗinsa ya zaro wasiƙar da Hajjaty ta bayar a bashi, ya zura mashi a cikin aljihun gaban rigar shi sannan ya ce, "Hajjaty ce ta bayar a baka, bata samu damar zuwa ba, tana a kwance gadon asibiti tana jinyar zuciyarta, idan ka samu halin karantawa ko a cikin jail ne ka daure ka karanta..." Wata irin karayar zuciya mai haɗe da nadama ce ta riske shi, bai ƙara samun damar furta kalma ba, Prison Officers suka tura ƙeyarsa cikin Motar. Iyalan Ɗan Iya ne kaɗai ba a samu wanda ya halarta ba, sun fi kowa fusata, dama can ba son uban nasu suke yi ba. A kan idon kowan nan su motocin suka fuce daga arean kotun. Kafin mutane su watse, Alƙali Salahudeen sai da ya nemi ganawa da ahalin Obinna, musamman ya zauna da su a office ɗinsa bayan ya bayyana musu irin halin da ya shiga na jin abun da Obie ya aikata, ya kuma jajanta musu sannan ya jinjinawa Owais da ƴan team ɗinsa bisa ƙoƙarin su na kamanta adalci da gaskiya. Kafin barin su kotun, chef na gidan Owais wanda ke kula da ɗakin Natasha ya kira Owais a waya cikin tashin hankali ya faɗa masa cewa ya je kai mata abinci, ya iske ta kwance ƙasa rai hannun Allah, tana yin bleeding ta hanci da baki, yanzu haka sun garzaya da ita Obie Hospital. Hankalin Owais ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hanzarce ya faɗa ma su Ummi abun da ke faruwa da Natasha, ya ce ma Sajeed da Sajeeda su shiga motarshi, a gaggauce suka shige cikin motocin su, a lokacin Sarah ta ji komai itama ta shiga motar Omar saboda ta ƙudiri aniyar sai ta ɗanɗana mata raɗaɗin da ta ji na abun da ta yi ma ƴarta Unaizah. Lokacin da suka ƙaraso Asibitin bayan da suka fito daga motocin su cikin sauri suka nufi ciki. Kaitsaye suka wuce ICU, suna ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin, sai ga Docs din dake dubata sun fito fuskokinsu babu annuri. Gaba ɗaya suka ruɗe fargaba ta cika su. Owais ya tambayi Doc din meke damunta? Ya jikin nata?" Cikin karyayyar murya doc ɗin ya ce "Unfortunately, the patient's condition has taken a turn for the worse, Her blood cancer, specifically Leukemia has progressed rapidly, and we're seeing signs of severe bone marrow failure...." Salati Ummi ta zabga tare da ɗaura hannayenta saman kanta, Hajiya Sarah da ta zo da niyyar ta ɗauki fansar abun da ta yiwa ƴarta koda jin bayanin likita sai ta ji jikinta ya yi sanyi. A ruɗe Chief Owais ya dubi ummi yana tambayarta dama tana da blood cancer? Cike da damuwa ta ce batasan komai game da ciwonta ba, in ma ta daɗe a jikinta bata ta6a faɗa mata ba, bata ma tunanin Natasha tasan tana da leukemia. Doc ya katse maganar Ummi da cewa, "We're doing everything possible to manage her symptoms and stabilize her condition, but I must be honest with you the prognosis is grim she's at high risk of sepsis, organ failure, and even cardiac arrest." We're monitoring her closely and adjusting her treatment plan accordingly, but I want to prepare you for the worst, It's possible that we may lose her at any moment...." Gaba ɗaya damuwa ta ƙara mamaye zuciyar su, Owais kamar yasan ba zata rayu ba ya yi dubarar zuwa da ƴa'ƴanta, kwata kwata ba su san gurin wa aka kawo su ba. Shi ya ruƙo hannayensu a cikin nashi, ya shigar da su ɗakin, sauran ma duk suka shigo, Ummi ta zauna kan chair din gaban gadon, ta ruƙo hannun Natasha dake a kwance cikin mawuyacin hali, fuskarta asanye da oxygen mask da wasu na'urorin dake taimaka mata, Hajiya Sarah tana a tsaye daga bayan Ummi ta ƙura idanunta akan Fuskar Natasha tana tuna abubuwan da aka faɗa mata ta yiwa ƴarta, amma da ta tuna cewa Mahaifin Unaizah ne ya ja mata, hakan yasa ta ji zata iya yafe mata, musamman da ta ga halin da ta ke a ciki. Da hannu Owais ya nuna mata Hajiya Sarah ya ce, "Matar Jan Wuya ce, Mahaifiyar Unaiza." Zare blue eyes dinta ta yi, cikin ruɗu da razanar jin maganar shi take kallon Sarah. Hawaye ne suka ciko idanunta, jikinta na kerma ta soma ƙoƙarin cire Oxygen mask ɗin fuskanta, da sauri Ummi ta dan ɗage mata shi kaɗan ta yadda zata iya yin magana. Cikin shesshekar murya da gajarcewar numfashi Natasha taita kokarin furta ta yafe mata, ta yi nadama, ta yi danasanin abun da ta yi ma Unaizah, Musa ne sanadi, kuma hada ƙarin bata san wanene shi ba, da tun farko tasan manufar shi akan ta, da ba abun da zai hana ta kar6e ta, bata ta6a cutar da Unaizah ba, tana son ta, tana jin ta kamar ƴar da ta haifa, duk da tasan bata ba ta tarbiya ba, amma ta yi haƙuri tasan ta biyewa son zuciya, bata raini Unaizah yadda ya kamata ba..." dakyar ta ke iya magana saboda raɗaɗin da jikinta ke yi mata. "Who's she"? Gabriel ne ya tambaya. A hankali Owais ya dube su, suna tsaitsaye bakin gadon hannunsu ruƙe cikin na juna. "Mahaifiyar ku ce Sajeed, kamar yadda mahaifinku ya raba Sarah da ƴarta batare da saninta ba, itama haka ya rabata da ku bayan da ta haife ku, batasan kuna a raye ba..." kallon juna suka yi cikin ruɗu da al'ajabi. Sajeeda da ta gama ruɗewa ta ce, " Idan wannan ce mahaifiyar mu toh wacece ɗayar wadda ta raine mu?" Girgiza kai ta yi. "She'll never be our mom, I don't like her, she has no morals." yayin da ta ke yin maganar Natasha tana kallonsu idanunta cike tab da ƙwallar baƙin ciki da takaici. Sajeed ya ce, "Kunsa na ruɗe, tayaya wannan zata zama mommynmu? Bayan mommynmu tana nan, wadda ta haife mu ta kuma raine mu!" Cikin rawar murya ta ce, "I know I don't deserve for you to call me Mother, Redneck betrayed me, separated you from me, I never knew I had you, but I want you to know it's not my fault Please forgive me, Forgive me..." Ta faɗa tana kuka. "..Ku duba halin da nake a ciki, I'm not going to live, I want you to call me Mommy, just once, and hug me, I love you like my soul, I really wanna feel the warmth of your bodies against mine.." ta ƙarashe maganar tana kuka ta dubi ummi, "Ku sanya baki, ku taimaka min, ina son su kamar raina, ina so na ji ɗumin jikin su.." Cikin karyayyar murya Ummi ta dube su. "I'm sorry, As she said, it's not her fault, your father cheated on her and lied to her she didn't know you were alive, all she knew was that you died at birth, No one will love you as much as your mom, she carried you for nine months in her womb and labored, The one you're talking about is not your mother, she's his mistress" Maganar Ummi ta yi tasiri a cikin zukatan su. Owais ya ce, "Ku duba halin da ta ke a ciki, mu tausaya mata, bana so ku yi danasani daga baya.." Cikin sanyin jiki suka matsa kusa da ita, Ummi ta miƙe tare da taimaka mata ta miƙe zaune, Sajeeda ta rungumo ta sosai cikin shesshekar kuka ta furta. "Forgive me, Mommy, but I love you, I don't want you to die, ina sonki, bana son ki mutu, Ina so mu rayu da ke, kada ki tafi ki bar mu..." tsantsar ƙaunar su da son su ne ya mamaye zuciyarta, suma haka su ka ji son ta. Bayan da Sajeeda ta raba jikinta daga na Natasha, ta matsa ma Sajeed shima ya rungumota tighly kamar zasu koma mutun ɗaya, "Tun da na ganki raina ya bani muna da alaƙa saboda na ji tsantsar ƙaunar ki a zuciyata, ban so muka haɗu a ƙurarren lokaci ba, amma za mu yi maki addu'a, Allah ya baki lafiya mommy, muna son ki fiye da yadda muke son kan mu, zamu baki kulawa mommy, zamu kasance a tare dake har sai kin ji sauƙi.." Kukan farin ciki ne ya kubce mata, ta ƙara ƙanƙame shi, ta miƙa hannunta dake kerma ta tallabo Sajeeda ta haɗa su ta rungume a ƙirjinta, sautin koke koken su ya cika ɗakin. Kowa da ke a gurin ya tausaya musu. Sun daɗe a manne da juna babu mai lallashin wani sai daga bisani Ummi ta lallashe su ta samu ta shawo kan su. A hankali Natasha ta mayar da dubanta ga hajiya Sarah dake ta share hawayen ta. In a broken voice ta ce, "I didn't do you justice, I had the opportunity to meet my children, and you never saw your daughter until she died, I wish I could go down on my knees and ask you to forgive me, but I can't, my body is weak..." Tana magana twins ɗinta suna share mata hawayenta. "Amma a madadin Unaizah da kika rasa, ga twins ɗina, na bar maki su har abada, ban cancanta na zama mahaifiyar su ba, na san ma bazan rayu ba, ki ruƙe su a gurin ki, na bar maki su.." Cikin shesshekar kuka Sarah ta ce, "Na yafe maki Natasha, ba laifinki bane, laifin Musa ne, kuma shima yanzu haka yana a prison, Bazan kar6i ƴa'yanki ba bayan kina a raye, ki ruƙe abunki, babu wanda zai iya maye gurbin ki a gurin su..." Girgiza kai Natasha ta yi tana ƙoƙarin buɗe baki da niyyar ta furta kalma, kwatsam suka ga ta fara jijjiga, numfashinta ya dinga kokawar ɗaukewa, ta dinga zubda gumi. Cike da fargaba suke kallon ta cikin tashin hankali, Sajeed ne kaɗai ya yi tunanin biya mata shahada, gaba ɗaya suka shiga maimaita mata don sun fahimci ba rayuwa za ta yi ba. Cikin kuka twins ɗinta suke faɗin kada ki mutu mommy, muna sonki, muna son mu rayu da ke, kar ki mutu ki bar mu a lokacin da muke cikin buƙatar ki!" Sajeed da ya cire rai da ita bai daina furta mata shahada ba yana faɗin Mommy ki biya don Allah idan kika musulunta Allah zai yafe maki zunubanki, kuma muma zamu sa mu yi maki addu'ar samun rahama..." Da ƙyar da siɗin goshi suka samu Natasha ta biya shahada da numfashinta na ƙarshe. Alƙalamina bazai iya misalta muku raɗaɗin da twins ɗin Natasha suka ji ba na rashin mahaifiyar su, bayin Allah sun zama abun ban tausayi a ranar da suka fara ganin mahaifiyar su a ranar ta mutu, Musa ya cuce su, wata shari'ar sai a lahira. Ummi ta yi kukan rashin Natasha, Chief Owais ya yi danasani da tun farko bai yi saurin haɗa ta da ƴa'yanta ba, hatta hajiya Sarah saida ta zubda mata ƙwalla saboda tausayin ƴa'yanta da ta bari. A ƙarshe Hajiya Sarah ce ta kar6i twins ɗinta da hannu bibbiyu. 😭😭😭 ~_________________________________💔~ Haƙiƙa dangin baba Obie sun fuskanci jarabawa mafi tsanani a rayuwar su. Mutane saida suka hana Ahlin Obie sukuni, har ta kai ga basu iya buɗe wayoyinsu ko su fita waje batare da ƴan jarida da mutane sun farmake su ba, gaba ɗaya fita ta gagare su, suka killace kansu a cikin Estate ɗin su, saboda surutun mutane da masu barazanar lahanta su. Sun fuskanci barazana da tozarci daga gurin abokan hamayyar su na jam'iyoyin da ke adawa da su. Duk wanda ya ra6e su sai laifin baba Obie ya shafe shi, hakan yasa abokan su ƴan siyasa suka dinga zame jiki daga gare su, kowa tsoro ya ke kada su shafa mashi baƙin tabo, babu irin 6atancin da ba a yi masu ba, cin mutunci da ƙazafi iri iri ba wanda ba a yi masu. Surukansu suka fara ƙoƙarin yanke alaƙar su da su, waɗanda suka fi ɗaukar zafi, mahaifin Her Excellency Muhibbat da yake jan wuya ne babban mutum ne, bai son duk wani abu da zai ta6a mutuncinsa, tun a ranar da Muhibbat ta kira sa tana kuka ta bayyana masa komai da ke faruwa ya ce ta dawo gida babu ita ba Abdul Razak, ya yanke alaƙar su, da yake halinta ɗaya da na Ubanta bata musa mashi ba, duk da tana son mijin nata amma ta biyewa mahaifinta, batare da sanin kowa ba ta gudu daga Obie estate ta tafi gidan Ubanta da ke a nan Abuja. Her excellency Jameela ma a ranar da suka ji komai, ta koma gidan ubanta mai martaba sarkin Adamawa saboda tsoron kada abun ya shafe ta duk da itama bada son ranta ba, su dukansu ma babu wadda ta yi hakan don son ranta, saboda suna son mazajensu da ƴa'yansu, amma ba yadda suka iya, baba Obie ya karya zukatan su, ya ha'ince su ya kuma ci amanar su, ya yaudari yardar da suka yi ma shi, da suna alfahari da kasantuwar su surukan shi yanzu ya 6ata komai, abun da ya fi ƙona masu rai, jariran su da ya dinga sadaukarwar, shi yasa ransu ya 6aci suka zuciya. A yanzu ƴa'ƴan Obie sun gane waɗanda suke tare da su saboda Allah, da waɗanda suke tare da su saboda arziƙinsu da kuma ɗaukakarsu. _Ba zaka ta6a gane me sonka tsakani da Allah ba har sai musiba ta afka maka a sannu zasu dinga guduwa suna barinka_ Senate Lateef bai samu matsala da Hajiya Madina ba, mahaifinta malamin addini ne koda ya ji komai da ya faru daga jiharsa ya zo har Abuja ya ziyarce su don ya yi masu jajen abun da ya faru da su, ya kuma haɗa da yi masu nasiha akan su yi haƙuri kada su sare Allah yana a tare da su a sannu komai zai zama labari.. Hakan ba ƙaramin faranta ransu ya yi ba. Baiwar Allah Turai bata bari ta karya zuciyar mijin nata ba, sai ma lallashin shi da ta dinga yi tana kwantar masa da hankali saboda ganin halin damuwar da ya shiga. Sharafudeen bai samu matsala da Gimbiyarsa ba saboda ita ɗin jininsa ce, abun da ya shafi family ɗinsa ya shafe ta. A bangaren Prime minister Hateem tabbas iyalinsa sun girgiza da jin abun da baba Obie ya aikata amma basu bari sun baiyana damuwar su ta yadda zai karya zuciyar Hateem ba, Gimbiya Mujeedat ta yi jarumta gurin danne damuwarta da kwantar masa da hankali, wallahi kowa ya yi tunanin Sheikha Mujeedat ce ta farko da zata fara neman yanke alaƙa da su saboda martabar royal family ɗinta amma sai ta basu mamaki, ta ja mijinta a jiki, ta nuna ta ƙara jin ƙaunarsa da tausayinsa, kuma ta ce in ma yana tunanin zata juya masa baya to ya daina, bata aure shi don su rabu ba face don su rayu na har iya rayuwar su, don haka laifin babansa bai shafe shi ba, kuma ba zata bari mijinta da ahlinsa su tozarta a idon duniya ba, zata bada gudummuwarta don ganin mutuncinsu bai zube ba. Gimbiya Mujeedat ta ƙarfafa masu ta kuma basu mamaki sosai, sai dai Hateem bai samu nutsuwar zuciya ba, saboda yasan yadda royal family suke, sun ƙi jinin abun kunyar da zai zubar masu da mutuncin su a idon duniya. Yana ta jin fargaban kada iyayenta su neme shi, Unexpected sai ga kiran mahaifin Mujeedat, Emir Khalid ya shigo wayar Hateem da kan shi ya kira shi ya ce ya ji abun da ke faruwa a family ɗin su, ya zo ya same shi a fadar shi yana son ganin shi. Tun da suka yi wayar nan kwanciyar hankali ya ƙarewa Prime minister saboda zullumin me zai biyo bayan kiran nasa, don wlh ji yake zai iya barin komai har muƙaminsa amma ba zai iya rabuwa da Mujeedat ba, koda za a kashe shi ne, saboda tsantsar son da yake mata. Abu biyu ya haɗe mashi, ga gwamnatin ƙasar Canada suna jiran dawowar shi, don har ya zarce kwanakin da ya ɗiba, sun ji shiru ko sun kira baya picking kuma ba ya basu response na saƙonninsu. A lokacin duniya ta ji komai da ke faruwa da ahalinsa, amma gwamnatin kasar Canada da ƴan ƙasar sun fi so su ji daga bakin shugaban ƙasar nasu. Da ya ga bashi da wata mafita, ƴan uwansa suka bashi shawarar ya yi magana da Deputy ɗinsa in ma mulkin zai ajiye sun goyi bayan shi don sun san a halin yanzu ba lallai gwamnatin Canada ta bar shi ya ci gaba da yin mulki ba saboda abun kunyar da mahaifinsu ya aikata. Live video ya yi a presidencial page ɗinsa tare da press, ya bayyana masu halin da ya ke a ciki ya ce su yi haƙuri da abun da zai faɗa, yasan ba lallai hukuncin da zai yanke ya yi masu daɗi ba, amma a yanzu ya yi raunin da ba zai iya ci gaba da shuwagabancinsa ba, kuma ba zai iya dawowa Canada ba, saboda ba zai iya tafiya ya bar ƴan uwansa a cikin mawuyacin hali ba, don haka su yi masa afuwa, su nemi wani adalin shugaban da zai maye gurbin sa... " Wannan Live video ɗin da prime minister ya yi da manema labarai cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar Canada ta dauka, labarin murabus ɗin sa ya tayar da tarzoma a duk faɗin kasar Canada, kuma mutane da dama sun yi baƙin ciki da matakin da ya ɗauka kuma sun nuna ƙin amincewar su, haka zalika mutanen da ke kula da shi a tsawon wa’adin mulkinsa sun ƙuduri aniyar shawo kan shi don ya koma Canada ya ci gaba da aikinsa saboda su basu gaji da shi ba, bayan haka bai yi laifin da doka zata amince da yin murabus ɗinsa ba, laifin mahaifinsa bai shafe shi ba, har yanzu suna son shugaban ƙasar su. Bayan da yayi wannan Live video ɗinne, ƴan uwansa suka ƙarfafa masa gwiwa akan ya amsa kiran surukinsa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya bar ƙasar tare da iyalinsa, tafiyar sirri suka yi saboda jama'a dake neman su farmake su ruwa a jallo. Abun da ya ƙara sagar masu da gwiwa rashin tuntu6ar su da Familyn mahaifiyarsu ba su yi ba, a zaton su sune mutane na farko da ya cancanta su ja su a jiki su lallashe su akan mummunar ƙaddarar da suke fuskanta amma sai suka ji shiru daga 6angaren su, hakan ba ƙaramin karya masu zuciya ya yi ba, duk sai su ka ji ba daɗi, suna ganin kamar suna gudun su ne saboda kada martabar family ɗinsu ya rushe, gashi kuma su ne kaɗai dangin da suke da shi a duniya. Saida damuwa ta kusa illata su, gaba ɗaya suka yi murabus daga kan muƙaman su saboda depression da suke fama. A lokacin da gwiwarsu ta sage, suka raunata, basu da madogara da ya wuce Allah da Sheikh Imam dake zaryar zuwa yana ƙarfafa masu gwiwa, sai da suka fidda rai da komai, a wannan Lokacin ne kuma Allah ya juye al'amarin yadda basu ta6a zata ba. Dangin da suke ta jira su ji daga gare su suka yi masu zuwan bazata, gaba ɗayansu, tun daga kan kakanninsu na 6angaren Uwa, tsohon sarkin ƴarbawa, har izuwa kawunnan su, da yayan mahaifiyarsu mai martaba sarkin ƴarbawan jihar Lagos mai ci a yanzu gaba ɗayan su, suka zo Abuja a cikin family private jet ɗin su tare da royal guards ɗin da ke basu kariya. Tun a airport ƴan jarida suka dinga dandazo gurin neman ƙarin bayani daga gare su, sai dai ko kusa da su basu isa su ƙarasa ba, saboda royal guards ɗin da ke a kewaye da su. Kuma duk a rana ɗaya Edward's family na bangaren mahaifiyarsu Hateem suma suka zo Nigeria, kowa yasan irin power ɗin da ke gare su, sune ake ma laƙabi da jinin siyasa, they are famous politicians tun kaka da kakanni. Sun ji komai da ya faru daga bakin Momma da ta kira yayanta ta sanar da shi, family ɗinta sun girgiza da jin tana a raye, sun kuma fusata da jin zaluncin da mijinta ya yi mata, basu ta6a zaton haka daga gare shi ba, hakan yasa suka yi takakkiya tun daga Canada suka zo Nigeria a family jet ɗin su. Silar zuwan su abubuwa da dama sun faru, haƙiƙa Ahlin Obie sun yi farin ciki da zuwan dangin iyayensu mata, sun zo a lokacin da suke a mawuyacin hali, a kuma lokacin da suka yanke ƙauna da komai na duniya, waɗannan powerful families ɗin guda biyu suka haɗa kansu, suka tsaya masu tsayin daka, suka zama ƙashin bayansu, ɗari bisa ɗari suke goyan bayan su. A Obie Estate suka zauna tare da su, saboda sun yi alƙawarin ba zasu ta6a bari ƴa'yan Obinna su tozarta ba, kuma za su yi adawa da duk wani wanda ke kokarin 6ata masu suna da masu sukar su, akan abun da mahaifinsu ya aikata, sannan suka ce basu yarda da maganar murabus ɗinsu ba, dole su koma kan muƙaman su tun da ba mutane ne suka cire su ba, kuma ba mahukunta bane suka yanke masu hukuncin sauka daga kan mulkinsu ba, bayan haka ba su yi laifin da za a tsige su daga power ba. Wannan maganar da suka yi, sun yi ta ne a gaban manema labarai kafin ka ce me tuni maganar ta yaɗu ta ko'ina zancen ake yi a faɗin duniya. Abokan hamayyar su da suka matsa masu lamba, ta hanyar ƙulla masu makirci don su 6ata masu suna su kuma sa a tsige su daga kan muƙamansu, yanzu faɗan ya koma tsakanin Powerful families ɗinnan biyu da abokan hamayyar su, Har ƙara suka kai ahalin Obie kotu akan a yi adalci akan cin amanar ƙasa da mahaifinsu ya yi da kuma zaluncin da ya yi, ƙarshe haƙar su bata cimma ruwa ba, cikin rashin sa'a, kotu ta yi watsi da ƙarar, inda ta ce bata gamsu da hujjojin da suka gabatar ba, ƴa'yan Obinna basu da alhakin laifin da baban su ya aikata!" Da suka fusata da hukuncin kotun, ƙungiyar maƙiyansu suka shirya ɗaukar mataki da kansu, suka fara ɗaukar hayar gidajen talabijin da ƴan jarida da kuma mutane karnukan ƴan siyasa don yaɗa mummunar manufar su ga ahlin Obie, Amma duk a banza, haƙar su bata cimma ruwa ba, babu abun da suka rage su da shi, sai ma farin jinin da suka ƙara masu, mutane sun ƙi basu goyan baya.. Basu daddara ba koda suka ga ba su yi nasara ba, sai suka ɗauki hayar protestors suka bazu kan titunan Abuja suna ta nuna adawar su akan basu yarda abar ƴa'yan Obinna su ci gaba da mulki ba, dole a yi masu adalci a sauke su daga kan muƙamansu, a kuma hukunta su akan abun da babansu ya aikata saboda suma suna sane da sa hannunsu, in ban da raunin wayou tayaya za'a ce tsawon shekarun da suke a tare da shi basu ta6a sanin abun da yake aikatawa ba! su basu yarda ba, a bincike su dukiyar su bata halal bace, suna da sanya hannu! Maganganu iri iri marasa daɗi na 6atanci suke faɗa a kansu, ƙoƙari suke su ɗaura masu laifin baba Obie. Ma su adawa da su ba irin cin hancin da basu ba alƙalai ba, da masu zanga zanga amma gaba ɗaya basu yi nasara ba, Allah ya nuna masu iyakar su, ƴa'yan baba Obie kainuwa ne dashen Allah, sai ya zamana kamar suna ƙara masu farin jini da tausayawar al'umma, dama an ce hassada game rabo taki ce. Al'umma suka dinga yin zanga zanga akan tituna da ta yanar gizo hannayensu ruƙe da alluna mai ɗauke da taken zanga zangar da suke yi. Suka cika kunnuwan al'umma suna faɗin, _Justice for Obinna's sons! Justice for Hajiya Saratu, Minister of Health! Justice for President Sharafudeen! Justice for Senate President Lateef! Justice for Hateem Obinna! Justice for Sir Mubarak, Chief of Army Staff! Justice for Lagos State Governor Abdul Razak! Justice for the Governor of Kaduna, Deen Obinna! They are not criminals, their father's crimes do not affect them, They are innocent, We will not allow them to be removed from power, We support them and will oppose anyone who challenges their positions!_ Wannan zanga zangar ta yi silar dawo masu da farin cikin rayuwar su, ganin yadda mutane suke nuna ƙauna da goyan bayansu A can Canada suma sun fara zanga zanga a online suna nuna ƙin amincewar su da murabus ɗin Hateeem, _"We don't have a leader other than Hateem! We love Hateem! We want him to come back and continue to protect our country! Grant him justice! We do not want to remove the president of our country! Let justice be served to him, his father's guilt will not affect him, He is a good person and a just leader, We accept him and we support him_ _We will not stop! We will do our best to bring back our president_ Farin ciki kamar zai kashe su, koken da mutane suke yi akan su gwamnati ta amsa buƙatar su, tare da cewa su dama basu tsige su daga muƙamansu ba, sune suka nuna basu so amma yanzu tunda mutane sun nuna ƙin amincewar su don haka zasu dawo kan muƙamansu sannan sun basu hutu har zuwa lokacin da suka ji zasu iya ci gaba da ruƙe muƙaman nasu, yanzu mataimakan su ne ke ci gaba da gudanar masu da mulkin nasu. Yayin da su kuma suke a estate ɗinsu, a ƙarƙashin kulawar families ɗinsu Abokan hamayya sun ji kunya, don dole suka ajiye makaman yaƙin su saboda ba yadda zasu yi da dangin Obinna sun yi masu fintinkau, Allah ya kare abunSa, ba yadda suka so su wulaƙanta ba. Ɗaukakar su ta nunku, arziƙin su ya bunƙasa, ko'ina zancen su ake yi, abokanan hulɗar su da suka juya masu baya tuni sun fara yin nadama, daga baya suka dinga zuwa neman yafiyar su tare da jajanta masu abun da ya faru da su. Haka zalika surukansu da suka yanke alaƙa da su, kunyar duniya ta ishe su, tuni sun gane kuskuren su na yanke alaƙar su da su, ganin ba yadda suka zata ba, hakan yasa suka zo har estate ɗinsu don su jajanta musu da kuma neman sasanci tsakanin su da matayansu. yanzu fa duk wanda ya ra6i ahalin Obie sai ya yi farin jini a gurin al'umma Ƴan uwa da abokan arziki sai zuwa suke yi suna jajanta masu. Duk wannan abun da ya faru bayan zuwan danginsu, Hateem baya a Nigeria, tun lokacin da aka kammala shari'ar Elders yana a Dubai tare da iyalinsa domin amsa kiran da His highness ya yi mashi, tun bayan tafiyar su babu wanda yasan me ya faru? Me ya sa surukin nasa ya nemi ganinsa? Kwata kwata basu ji daga gare shi ba, kuma sun damu da su san a wani hali ɗan uwan nasu ya ke a ciki, saboda bai neme su a waya ba, ko sun kira wayarsa bata shiga, haka matarsa da ƴa'yansa duk basa samun su a waya, ko meya faru ta bangaren prime minister ❓ Isod agents basu ƙyale kowa ba, sun bada himma, duk wani mai sa hannu a kurkukun ƙaddara saida suka kama shi, da waɗanda ke a Nigeria da waɗanda ma ba a Nigeria suke da zama ba, sai da suka bi diddigin su, suka dinga yi masu ɗauki ɗai ɗai suna damƙa su ga hukumar ƙasashen su. Da bincike ya yi bincike saida suka gano mutane sama da ɗari biyar waɗanda suka ta6a sadaukar da jininsu don biyan buƙatar kan su, gaba ɗaya suka gurfanar da waɗanda suka ta6a yin sadaukarwar a kotun ƙasashen su, bayan haka suka mayar wa dangin su da ƴa'yan su, sai gashi gaba ɗaya sun yi nasarar gano dangin fursinonin hannun su, wasu turawa ne, wasu larabawa, wasu ƴan yankin Asia ne, wasu kuma ƴan Africa ne. haka suka dinga bankaɗo sirrin masu sadaukarwa ta hanyar amfani da littafin rijistar fursinoni🔥 Idan muka koma bangaren ƴa'yan baba Obie suma Owais ya mayar masu da ƴa'yan family din su da suka rage. Daga cikin jikokinsa na kurkukun ƙaddara, da suke a raye, akwai Parveen ɗiyar Hajiya Saratu wadda Praveen ya sadaukar da ita, Azeeza da Jemimah ƴa'yan Sir Mubarak da Hajiya Turai ne, asalin sunan Jemaimah Naja'at ne sunan mariganya matar Sir Mubarak, bayan su sai ɗan gidan Prime Minister, Last born ɗin shi Omair, wanda aka fi sani da Danish wanda a yanzu baya a raye. A bangaren Deen da matarsa Hajiya Jameela suma sun samu triplets cikin ƴa'ƴan su da suka rage wanda Obie ya sadaukar. Hanna, Hibba, Hawwa, babu wanda yasan ƴan uku ne saida Owais ya gano a cikin littafin rijistar. A bangaren Abdul Razak da Her excellency Muhibba, suma Allah ya azurta su da samun twins cikin waɗanda Obie ya sadaukar, su ne Rubina da Mubeen, wani iko na Allah Hajiya Muhibbat kamar ta yi kaki Rubeena kamanninsu ya 6aci. Senate Lateef shima ya samu ƴayansa biyu daga cikin prisoners Yasmin da Sarah. A bangaren Mr. President shima Allah Ya azurta shi da samun last born ɗinsa, bakowa bane face Javed wanda asalin sunan sa shine Hateem, kamanninsa sak da na ƙanwar Owais Hindu, launin fata ne ya bambanta su. Abun da ya fi ɗaurewa Unaisah kai, jin cewa Deeja da Haris ƴa'yan kawun daddynta ne Abdallah Buzu da Hajiya Adama hakan na nufin ƙannan Uzair ne, in ba zaku manta ba, Haris ya ɗare Deeja da shekaru kusan biyu, ko a prison Haris ne tsaran Danish, kowa ya yi mamaki ashe ƙaunar da ke a tsakanin Deeja da Haris ta ƴan uwantakar jini ce. Ita ma Hajjaty, Owais ya mayar mata da yaronta Naufal, gaba ɗaya lokacin da ya mayar masu da ƴa'yan a ranar da ya shirya musu walima a gidansa suka haɗu gaba ɗayan su, ya buɗe littafin rijistar a gaban kowan nan su ya zayyana musu sunayen ƴa'yansu da Obie ya sadaukar da kuma waɗanda suka rage a raye, ya kira sunan su ya nuna masu iyayen su, murnar da suka yi a wannan lokacin bata misaltuwa, daɗi kamar zai kashe su, daga su har iyayen nasu tsantsar farin ciki ne ya mamaye zukatansu, wata irin ƙauna mara maisaltuwa ta shiga tsakaninsu a ƙanƙanin lokaci. kwata kwata basu nuna ƙin amincewar su ga iyayen su ba saboda Owais ya riga da ya bayyana musu wanda ya sadaukar da su kuma sun halarci kotu sun gan su sun kuma ji hukuncin da aka yanke musu. A ranar da U.S Armies suka yi masu bankwana zasu koma America, sun yi kukan rabuwa da su, gaba ɗaya prisoners tare da senior agents suka raka su Airport, U.s Armies sun ji zafin rabuwa da su saboda shaƙuwar da suka yi da juna, ba zasu ta6a mantawa da su ba a rayuwar su, ta silar aikin da suka yi sun samu awards daga ƙasashe daban daban, tun kafin ma su koma America har president ɗinsu ya yi masu alƙawarin za a ƙara masu matsayi idan suka dawo, Prisoners sun ji kewar rabuwa da su, suma baza su ta6a manta taimakon da suka yi masu ba, sune na farko da suka fara tsamo su daga dajin Evil Forest, ƙaddara ce ta haɗa kuma ta raba. Har bayan tafiyar U.s armies basu daina jimamin rabuwa da su ba. *game Bukatar Kurkukun ƙaddara Ya tuntu6i number din nan 08103884440* *DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥* BAYAN WANI LOKACI 🔥 Kasantuwar gwamnati ta kar6e ƙadarorin Elders yasa suka fara tunanin barin Obie Estate kafin wa'adin da aka basu ya cika, sai da suka fara yin shawarar game da inda zasu mayar da iyalin su, da har sun fara shawarar zasu mayar da su ƙasar Canada su zauna a family House ɗin su, a ganin su zai fi masu kwanciyar hankali. Momma ta ce shawarar su bata yi ba, tayaya zasu mayar da iyalan su Canada su kuma suna a Nigeria, duk da suna da halin da zasu iya zuwa duk ƙarshen mako su dubo su, amma ya za su yi da matasan ƴa'yansu da ke buƙatar kulawar su? Suma kuma suna son su a kusa da su, ta ce amma su bata lokaci zata yi shawara da family ɗinta dana mahaifiyar su Sir Mubarak tun da sun ce su faɗa musu kome ake ciki za su taimaka musu. Batare da sanin su ba, Momma ta yi shawara da families ɗin, ta bayan fage suka fara nema masu gidajen da zasu zauna, cikin Ikon Allah, suka gano wani sabon katafaren housing Estate da ba a jima da kammala shi ba, a nan cikin garin Abuja ya ke, da suka yi bincike sai suka gano mamallakin Estate ɗin bakowa bane face Deputy President Ahmad Musa. Momma ce ta nemi alfarmar haɗuwa da shi, a ranar da ta je guest house ɗinsa tare da Imam Malik suka ziyarce shi, da yake yanzu Imam Malik shine na hannun damanta, da shi ake komai. ya yi masu kyakkyawar tarba cikin mutunta juna, bayan sun tattauna game da sabon Estate ɗinsa, da yake yasan komai da ya faru kuma yasan su wa zata siya mawa, hakan yasa ya ce zai yi musu ragi saboda Allah saboda kuma zumuncin dake a tsakaninsa da Sharafuddeen, hasalima ba siyar da shi zai yi ba, ya yi sa ne saboda ya zuba ƴan haya a cikin sa amma dai zai bar musu shi. A ƙalla Estate ɗin yana ɗauke da gida je sama da arba'in a cikin shi, tare da private facilities, bai kai Obie Estate ba, amma yana da girma ya haɗu saboda amenities ɗin dake cikin sa, komai da mutun zai buƙata akwai a cikin estate ɗin, darajar sa ba ta kananun kudi ba ce amman duk da haka ya ce zai yi masu sauƙi. Da yake harka ce ta arziƙi, basu nemi ragin yadda ya faɗa musu ba, nan take momma ta kira Elder Brother ɗinta ta faɗa mashi, ta kuma kira sarkin ƴarbawa ta sanar da shi, ba tare da 6ata lokaci ba dangin biyu suka haɗa masu kudin saidai wanda bangaren dangin momma suka bada sun fi yawa. Bayan da suka gama ciniki, suka biya shi kuɗin, ya damƙa musu takardun shaida da yarjejeniyar mallaka musu Estate ɗinsa a gaban lauyoyin su. Lokacin da ta kai musu takardun Estate din, sun yi murnar da ni kaina bazan iya misalta muku ita ba, ko sisin su babu a ciki. dangin su sun faranta masu rai, sun gatanta su, sun nuna masu soyayya mara iyaka. Abu ɗaya da ya rage musu kafin su koma shine kayan furniture ɗin gidajen, batare da 6ata lokaci ba Prime minister ya ce su bar komai a hannunshi, ba ya buƙatar su haɗa kuɗin su zai ji da wannan. Daga shahararren Companyn furnitures na kasar Canada ya yi musu Order na komai da za su buƙata a cikin gidajen dama estate ɗin gaba ɗaya, kaya masu kyau da tsada, Cikin sati guda, ma'aikatan companyn suka gama yi masu jere, abun sai wanda ya gani. Bayan da su sheikh Imam Malik da ƴan kungiyar su ta malaman ahlussuna suka yi masu safkar alqur'ani a cikin Estate ɗin, a rana ɗaya suka koma tare da iyalansu, Har walima saida suka yi. Chief Owais bai bar Taj ya koma Jos ba kamar yadda Taj ya so ya tafi da ƴarsa tun da basu da mazauni a Abuja, Unexpected Chief ya gwangwaje shi da kyautar gida a cikin sabon Estate ɗinsu, wayyo Allahna saboda farin ciki har ƙwalla saida ya zubar, Unaisah ma ta yi murna saboda bata so ta tafi ta bar ƴan uwanta fursinoni. Haka zalika Imam Malik da Dr Shureim sun samu kyautar gidaje a cikin estate ɗin daga momma, ita ta basu saboda bata son su rabu da su, ta ji daɗin kyautatawar Imam Malik ga ahalinta, shiyasa ta janyo su kusa don a ci gaba da rayuwa a tare, sun yi murna sosai, zaman apartment ya ƙarewa Imam Malik dama hayar sa yake biya yanzu sauƙi ya samu ya yi gidan kan shi, Shureim ma ya mallaki gidansa yanzu burin sa ɗaya da ya rage shi ne auran Aisha. Chief Owais da kan shi ya nemi alfarma a gurin momma ya ce yana son gidaje biyu a estate din su a sayar masa, ta tambayesa me zai yi da su? Ya ce mata zai siyawa Salsabeel da Matar Alhaji Musa, saboda ya ji a bakin Alhaji Ubaid cewa Hajiya Sarah tana shirin komawa America kuma baya son ta tafi da ƴa'ƴanta saboda zumuncin dake a tsakaninsu da cousins ɗin sa. Momma ta ce ya kwantar da hankalinsa, itama tana goyan bayan shi, ba zata bari jinin tsohuwa Tamira ya tagayyara ba, Salsabeel nata ne, tana jin shi kamar ɗanta, don haka tana son Salsabeel ya dawo gidanta da zama, zata ware masa part ɗinsa, in kuma ya tashi yin aure zata bashi kyautar gida, bayan haka Hajiya Sarah ta ci albarkacin marayun da take ruƙo, suma ta mallaka musu katafaren gida a cikin Estate ɗin, Owais ya yi murna sosai, duk da haka bai gamsu ba saida ya ƙara neman alfarma agurinta akan ta siyar mashi wasu gidajen akwai waɗanda zai bamawa, ta fahimci Owais so yake ya dawo da duka iyalan Elders a estate ɗin su, koda ta tambaye sa meyasa yake son ya dawo da iyalan elders estate ɗinsu, ya ce mata saboda zumuncin su ya ƙulle, yana son prisoners, ya shaƙu da yaran baya son ya raba kansu da ƴan uwansa, yana nufin cousins ɗin sa su Parveen, Bayan haka a ganinsa ta haka ne zasu samu ƙwarin gwiwar gudanar da rayuwar su cikin farin ciki da annashuwa ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba saboda sun san juna, babu wani bare a cikin su. Ta yi farin ciki da jin kyakkyawar niyyar shi, ta ce mashi kar ya damu, ba zasu siyar masa da gidajen ba, zasu basu kyauta saboda Allah, a ƙarshe Uncle Abdallah da Abie sun samu kyautar gidaje a sabon estate ɗin Ahlin Obinna. Yayin da Hajjaty da ɗanta Naufal, suke a ƙarƙashin kulawar Sir Mubarak, part ɗinsu yana a cikin gidan sa. Alhaji Ubaid da Hajiya Layla suna shirin komawa Joss tun da ƙura ta lafa, Hajiya Sarah ta hana su tafiya, ta dinga roƙon su akan su taimaka su zauna a kusa da ita, tun da sun riga da sun zama ɗaya, ko don su taimaka mata gurin kula da ruƙon marayun da aka bar mata, har ta ce in sun amince sai su koma gidan da Owais ya bata kyautar shi a estate ɗin su tun da wannan gidan da suke a ciki na Alhaji Musa gwammanti ta kar6e shi, da zarar wa'adin da aka basu ya cika zasu kar6e ginin ne.. Sun ji daɗin yadda ta nuna bata son su tafi, dama ba son tafiya suke yi ba, kawai don ba yadda zasu yi ne tunda ba gida gare su a Abuja ba. A ƙarshe gaba ɗayan su suka koma gidan Hajiya Sarah na Imam Estate, yana da girma da faɗi, side by side duplex ne, bangare ɗaya na Hajiya Sarah da ƴa'yanta, ɗayan bangaren na su Hajiya Layla ne, babu abun da suka nema suka rasa a gidan, sun ji daɗi sosai tsakanin su da ahalin Obie sai godiya da addu'a. Alhaji Ubaid gaba ɗaya ya siyar da kadarorinsa na Jos, da kuɗaɗen yake amfani gurin tafiyar da iyalinsa da na Alhaji Musa, yanzu shi ke ɗawainiya da su, don ma Hajiya Sarah tana da arziƙinta, dama can mace ce mai zafin nema babbar ƴar kasuwa ce, daga baya ne ma da gwamnati ta ƙwace kadarorin Alhaji Musa itama ta rasa aikin da take yi a companyn sa. Amma Alhamdulillah yanzu gaba ɗaya waɗanda suka rasa ayyukan su cikin family ɗin Elders sakamakon abun da ya faru Sharafudeen ya ɗauke su aiki a babban companynsa, babu mai zaman banza, Kowa ya na ƙoƙarin neman na kansa. Gaba ɗaya dai Ahlin Elders sun zama tsintsiya ɗaya maɗaurinta ɗaya, wata irin shaƙuwa da zumunci mai ƙarfi ne atsakanin su. Shin ya labarin Zeenatu? tun bayan da tayi doguwar suma sai da ta shafe makonni bata dawo hayyacinta ba, tana a ƙarƙashin kulawar docs, bayan shari'ar Elders da sati ɗaya, Zeenatu ta farfaɗo cikin hayyacinta, mommynta da ƴan uwanta sun yi murna sosai, har kukan farin ciki suka yi duk da a lokacin bata magana sai dai idanunta da ke tsiyayar da hawaye, sun fahimci har yanzu da damuwar abun a ranta, bayan doc ya sallame ta suka dawo gida da ita, tsantsar kulawa suke bata, kwata kwata bata tambayi ina daddynta ba, saboda tsanar da ta yi mashi ko sunan shi bata son ji, kuma wani iko na Allah Zeenatu ta daina son Yaya Shureim da aure, babu soyayya a ranta, da suna ta zullumin tayaya zasu faɗa mata game da soyayyar Shureim da Aisha amma da suka lura babu son shi a ranta, yanzu kallon ɗan uwa kuma Yaya take yi masa sai suka godewa Allah da ya kawo masu mafita, bakomai ne ya faranta ran Zeenatu ba, face ganin tagwayen da mommynta ke ruƙo, har tambayarta ta yi su wanene? Nan Hajiya Sarah ta labarta mata komai game da su, ta tausaya ma rayuwarsu, ta kuma ji daɗi da ya kasance mommynta ne zata ci gaba da ruƙon su, da kallo ɗaya ta ji ta kamu da ƙaunar su, suma haka suka ji, yanzu ta samu tsararrakinta a gidan duk da sun girme ta da shekara ɗaya. Batare da 6ata lokaci ba, Alhaji Ubaid ya mayar da su school, daga jami'a suka fara shi ya yi masu ƙoƙari gurin sama masu takardun secondary da kuma admission na shiga jami'a da taimakon Owais. A baya kafin zuwan su twins kurkukun ƙaddara sun yi karatu harma sun kammala secondary, shiyasa karatun su ya zo musu da sauƙi, gaba ɗayan su yanzu suna a jami'a, sajeed Yana karantar Cybersecurity, yayin da Zeenatu da Sajeeda suke karantar Human Rights, su suka za6a da kansu saboda suna da burin su bada gudummuwa gurin kare hakkin ɗan adam. bayan haka kuma suna zuwa islamiya wadda ke a cikin estate ɗin neman ilimin addini sun bada himma sosai. Hajiya Sarah ta yi namijin ƙoƙari gurin tafiyar da rayuwar su, babu abun da suka nema suka rasa da arziƙinta ta ke kula da su, ba zaka ta6a gane ba ita ta haifi twins ba sai in an faɗa maka, haka zalika Alhaji Ubaid da Hajiya Layla suna bada gudummuwa gurin tallafa mata akan kula da yaran, Shureim da Benazir da Omar ma ba abar su a baya ba, suna ƙoƙari gurin koya masu abun da basu iya ba, sun zama yayye nagari a gare su. A zahirin gaskiya rayuwar Prisoners a gurin iyayen su sai son barka, wata irin soyayya suke nuna masu, tsantsar gatanci, kulawa da tarairaya kamar jinjirai, sai abun da suke so iyayen su suke yi masu, gaba ɗaya sun sanya su a school ɗin cikin estate ɗin su bayan private teachers ɗin da ke zuwa yi masu lessons na boko dana islamiya a cikin home classroom din su. Yara fa sun zama ƴa'yan mommy da daddy, hutu ya zauna masu, babu tashin hankali babu damuwa, sai zallar farin ciki da jin daɗin rayuwa, in ka gansu ba zaka ta6a yarda sun yi rayuwar ƙunci a gidan kurkukun ƙaddara ba, su kan su mantawa suke yi da sun ta6a shan wahala a rayuwar su, Yanzu sun waye, ilimin boko da na addini ya shiga kan su, halayan su da ɗabi'un su sun sauya, lamarin Ubangiji kenan, gwanin hikima, mai yin yadda ya so, mai jujjuya al'amurra, godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki 👑🌹 Bayan da ƙura ta lafa, kwanciyar hankali da farin ciki suka wanzu a zukatansu, bayan shekara ɗaya da rabi Dr Shureim ya auri Aisha, yayin da Taj ya mayar da Benazir ɗakinta, Owais ya auri Nazli, A canada aka yi shagalin bikin su na gani na faɗa, ya so ya haɗa da Unaisah ya aure su a rana ɗaya amma ta nuna bata shirya ba, tafi so ta kammala karatunta, bai musa mata ba, shima ya goyi bayan ta yi karatu, da taimakonsa ya yi mata hanya ta zana jarabawar ssce batare da ta shiga ss one ba, dama a baya kafin ƙaddara ta kaita kurkukun ƙaddara ta kammala junior secondary, shiyasa karatun nata ya zo mata da sauƙi, tana a jami'ar da su Sajeed suke, anan take karantar Computer Science, Owais ya yi masu alƙawarin in har suka kammala karatunsu zasu ɗauke su aiki a hukumar su ta Isod saboda suna buƙatar irin su. Tun farko abun da ya sa Unaisah ta ƙi yarda ya aure su a rana ɗaya ita da Nazli saboda tana jin shakkar ta zama kishiyar Nazli wayayyar ƴar gayu, tafi son ta ƙara wayewa ta yi zurfi a ilimi sannan ta koyi abubuwan da bata iya ba don kada Nazli ta raina ta, a yanzu ta dage damtse gurin koyon girki a wurin mommynta, kuma ta bada himma sosai gurin karatunta, bata wasa da yake Allah ya yi ta da brain she's gifted, tana da baiwar haddace karatu da saurin koyo shiyasa bata jin wahalar komai. Bayan da ya auri Nazli sai da ya yi hutun wata biyu a gidansa na Canada tare da amaryarsa Nazli, gaba ɗaya suka sauke girman kai da izzar su suka nuna ma juna soyayya, tun a first night ɗinsu suka raya daren su, daga bisani suka tafi honeymoon. Owais bai tashi dawowa Nigeria ba, sai lokacin bikin Omar da Salsabeel, kuma shi ya haɗa Omar da matar da zai aura, bakowa bace face ƙanwarsa Hindu, yayin da Momma ta haɗa Auran Salsabeel da Yusra ƴar gidan his excellency Abdul razak, kuma cikin sa'a jinin su ya haɗu, duk da a lokacin da momma ta zo mashi da maganar Yusra, ya ji shakkar haɗa shi da ita saboda yasan tafi ƙarfin shi, gata dai ɗiyar gwamna, wayayya, kyakkyawar budurwa, jinin shuwa, a da kafin yanzu tana da girman kai da izza, amma tun bayan faruwar lamarin nan ta sauya hali, ta zama mutuniyar kirki, koda momma ta faɗa mata game da Salsabeel ta kuma nuna mata hoton shi a waya, nan take ta ce ta amince in har yana sonta, zata aure shi, amma tana son bayan sun yi aure ya koma makaranta ya nemi ilimi, itama zata taimaka mashi, Salsabeel ya yi farin ciki mara misaltuwa a lokacin da momma ta faɗa mashi yadda suka yi da Yusra, har sujjada ya yi don nuna godiyar sa ga Allah, Auran gata Momma ta yi ma Salsabeel, ko sisin shi bai kashe ba, tun daga lefensa har sadaki ita ta bayar, har kuka saida ya yi mata saboda farin ciki, A ranar bikin su anyi gagarumin shagali a Imam Estate, amare sun tare a gidajen mazajen su, abun sai son barka. Idan muka koma bangaren Faryat, reshe ne ya juye da mujiya, yanzu ita ke son Jazz shi kuma yana ja mata aji, ta sauya hali ta nutsu ta koma tagari, ta daina duk wani abu mara kyau da take yi, amma Jazz ya ƙi sauraron ta, wahalar da ita yake yi, kusan kullum sai ta yi kuka saboda azabtuwar da ta ke yi da son shi, idan ta kira wayarsa baya picking, ko saƙo ta tura mashi baya mata reply, a ƙarshe ma ya yi blocking duk wata hanya da zata haɗa su, har gidansu ta zo gaban mommynsa ta zuƙunna kan gwiwowinta tana kuka sha6e sha6e ta dinga roƙonta akan ta sasanta tsakaninta da Jazz in har bata aure sa ba mutuwa zata yi, shi kaɗai take so, ta yi danasanin komai da ta yi masa, ta tuba. Turai ta tausaya mata musamman da ta ga ta gyara rayuwarta, ko shigar banza ta dai na yi, kullum cikin hijabi da jan cazbaha take, ta ce mata ta yi haƙuri zata yi magana da shi, amma ta ɗan ɗaga ƙafa saboda a yanzu jazz fushi ya ke yi da ita, ta bari sai lokacin da ya huce in sha Allah zata ci gaba da lallashin shi, da ƙyar ta shawo kan Faryat har ta samu ta koma gida, sai da ta kai ga kullum da zazza6i take kwana duk don saboda Jazz, Hajiya Saratu tasan komai da ke faruwa tsakanin Jazz da Faryat, amma bata sanya baki ba, saboda tana jin kunyar Jazz da Mahaifiyarsa, tsakaninta da Faryat addu'a ne da ta ke yi mata da kuma lallashinta. Shi kan shi Jazz ɗin ba don ya daina sonta ba yake share ta, sai don yana son ta ji irin raɗaɗin da shima ya ji a lokacin da ta ke yi masa wulaƙanci saboda ta ga ya mutu akan ƙaunar ta, amma har lokacin bai daina sonta ba, yana da burin auranta.... 💔 A bangaren Zayn ya yi nadama tun bayan afkuwar lamarin, ya shiryu ya sauya halayensa daga munana zuwa kyawawa, ya zama mutumin kirki, ya daina biyewa matan banza daga shi har Zaid yanzu basu wasa da ibadar su ko a masallaci sune a sahun gaba, sa6anin da ko masallacin basu zuwa sai an tasa ƙeyar su suke zuwa yin sallah. Soyayyar Zahra kullum ƙara nunkuwa take yi a cikin zuciyarsa, sai dai ya kasa tunkararta da maganar saboda kunyar wulaƙancin da ya yi mata a baya, duk da itama yasan hada mahaifinta a cikin elders, ƙaddarar su iri ɗaya, amma yana jin shakkun ya je gareta, gudun kada ta juya masa baya ko ta kore shi, da damuwa ta ishe shi ya kasa dannewa ya faɗa ma Zaid halin da yake a ciki, Zaid ya shawarce shi da ya shirya su je gidan su Zahran ya nemi yafiyarta yasan zata yafe mashi saboda yasan Zahra tana son shi. A ranar da su ka je gidan su Zahra, bayan sun yi parking suka kasa fitowa su shiga ciki saboda zullumi, har sai da Abie ya fito daga gidan zai tafi Office ya hango baƙuwar mota a harabar gidan, suna ganin shi suka fito tare da nufar shi cikin girmamawa suka gaishe shi ya amsa masu da fara'a ya ce baigane su wanene ba kamar ƴan'uwan Owais, har suna haɗa baki gurin cewa eh ƴan uwansa ne su, ƴa'yan Hajiya Saratu sun zo ne suna son ganin Zahra, murmushi Abie ya yi ya ce su shiga daga ciki, godiya suka yi mashi tare da wucewa cikin gidan. Sallamar su ce ta katse karatun ƙur'anin da Mahboob ya ke yi, sai da ya kai ƙarshen ayar da ya janyo, tukunna ya dube su yayin da yake akan kujera ruƙe da kur'ani, da murmushi ya amsa masu sallamar, sun ji daɗin sakin fuskar da ya yi musu. Mahboob kenan bawan Allah tun bayan mutuwar Ana ya canza, yanzu gudun abun duniya ya ke yi, baya son kuɗi tun da ya ga yadda suke kai mutun ga halaka ya ji sun fita a ran shi. A yanzu daka bashi kyautar kuɗi tsurar su ƙwara ka siya masa wani abu ka bashi saboda baya kar6ar kuɗi, har kawo wannan lokacin bai daina yiwa Ana addu'a ba, tana a ran shi, a duk lokacin da ya tuna zaluncin da mahaifinsu ya yi mata sai ya ji ɗaci a ran shi. Bayan sun shiga cikin falon ya nuna masu sofas suka zauna, ya miƙa masu hannu suka yi musabaha, daga bisani Zaid Ya tambayesa ina mutanan gidan? ya ce su Umminsu basa nan sun tafi anguwa, amma Zahra tana a ɗaki tana bacci. Sun ji daɗin jin tana nan, Zaid ya ce ya kira masu ita in ba damuwa, miƙewa ya yi ya nufi ɗakin Zahra ya yi sallama daga ciki ta amsa mashi, farkawar ta kenan daga bacci, bayan da ya faɗa mata baƙin da ke neman ta, ta yi mamakin jin zuwan Zayn, mutumin da ta sani da girman kai, tana kokwanton in shine! Me ma ya kawo shi gidansu nemanta bayan baya son ta? A ranta ta faɗa, har tambayar Mahboob ta yi ta ce ya kuwa tabbatar shi ɗinne ya zo? Yana murmushi ya ce mata da gaske shine ya zo tare da twin brother ɗinsa Zaid. Cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet, kafin fitowarta Mahboob ya wuce bedroom ɗinsa don ya basu guri su zanta. Bayan ta fito daga toilet shaf shaf ta shirya kanta cikin abaya, ta fito ta nufi falon, tunkan ta ƙarasa ta hango su, har saida gabanta ya ɗan faɗi ganin abun da bata zata ba.. Zama ta yi kan sofa ɗin dake fuskantar su, ta yi masu barka da zuwa, bayan sun gaisa kowannansu ya yi shiru, sam Zayn ya kasa haɗa idanunshi da nata saboda nauyinta da yake ji amma ganinta da ya yi ya sanyaya zuciyar sa sosai, yana jin in har ya mallaketa zata sama masa farin cikin da ya rasa a rayuwarsa. Jin sunyi shiru sun kasa magana yasa Zaid yanke shawarar fara gabatar mata da abun da ya kawo su.. Cikin nutsuwa ya fayyace mata komai ya ce yasan ɗan uwansa bai kyauta mata ba, ya yi mata wulaƙanci a baya, amma a yanzu ya yi nadama tun bayan fallasuwar sirrin grandpa ɗinsu da daddyn su sun sauya halinsu, koda can Zayn yana sonta, shi shaida ne saboda baida hira da ta wuce tata, amma a lokacin girman kai ne yasa bai nuna mata so ba. Tun da ya fara yin maganar Zahra ta zare idanunta cike da mamaki take sauraron Zaid.. Bai ƙare maganar ba, Zayn ya kar6e da cewa, "Wallahi na shiryu Zahra, na gyara halayena, Ki tausaya ma rayuwana, nasan kin daina sona a yanzu amma ki yi haƙuri ki yafe min abun da na yi maki a baya, na yi danasani kuma wallahi ina son ki, in har kika bani dama zan nuna maki irin ƙaunar da na ke maki. Tsantsar farin ciki ne ya lullu6e zuciyarta tsabar murna kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha amma kwata kwata bata bari ya gane ba, baiwar Allah tun bayan abun kunyar da ubansu ya aikata bata ƙara samun farin ciki irin na yau ba. Da suka ga ta yi shiru babu fara'a akan fuskarta sai suka yi tunanin bata ji daɗin zuwan su bane, Zaid ya ce ta yi haƙuri idan kalamansu sun 6ata mata rai, za su tafi amma ta zauna tayi tunani idan ta yanke shawara ta sanar da su.. Ya ƙarashe maganar cikin sanyin murya tare da ruƙo hannun Zayn da ya tsareta da idanunshi, shi kaɗai yasan me yake ji a game da ita, baya jin zai iya haƙura su koma gida batare da Zahra ta faɗa masa ra'ayinta akan shi ba. Zame hannunsa ya yi daga na Zaid ya miƙe daga kan kujerar ya je gaban sofa din da take a zaune ya yi kneeling a gaban ta, wani yanayi ta ji mara misaltuwa, ta kasa haɗa idanunta da nashi, cikin karyayyar murya ya ce, "Bazan iya tafiya batare da kin yafe min ba, nasan har yanzu kina fushi da ni, amma ki yi haƙuri Zahra! ki taimaki rayuwana, ki rufa min asiri, a halin yanzu zan iya haƙura da komai amma banda ke! Wallahi ban zo don na 6ata maki lokaci ba, Auren ki nake so na yi.. " idanunsa cike tab da ƙwalla ya ƙarashe maganar, ji tayi kamar ta fashe da kuka saboda tausayin shi, cikin sauri ta ce ya tashi ya zauna, ya girgiza mata kai tare da cewa in har tana son ya miƙe toh ta faɗa masa me ta yanke akan shi. Shiru ta yi tana tunani, a ranta ta ayyana Allah ne ya kar6i addu'arta, ta daɗe tana roƙon Allah ya karkato da hankalin Zayn akanta in alkhairi ne shi a rayuwarta, saboda tana son shi tana son ya zama mijin ta, sai gashi ya zo mata a lokacin da take buƙatar wanda zai rufa mata asiri, saboda samarin da take da su duk sun juya mata baya saboda abun kunyar da ubansu ya aikata amma yanzu ta yi farin ciki da zuwan Zayn saboda tasan ƙaddararsu ɗaya ce idan suka yi aure zasu rufawa kansu asiri, babu wanda zai goranta ma wani.. Numfasawa ta yi da ɗan murmushi akan fuskarta ta ce, "Ni ban fara son ka don in daina ba, har yanzu ina son ka, zan iya cewa na fi kowa farin ciki da ka gyara halayen ka, kuma na yi murnar ganin ka, sannan shawarar da na yanke na amince zan aure ka Zayn.. " Bata ƙarashe maganar ba, ta ga ya yi sujjada yana kukan farin ciki, batasan sa'adda ta ji hawaye sun wanke fuskarta ba saboda daɗin da ta ji.. Hatta Zaid dake kallon su saida ya ji ƙwalla ta cika idanunshi, ya tausaya musu ya kuma ji daɗin nasarar da ɗan uwansa ya yi akan Zahra.. Tun a wannan lokacin shaƙuwa ta shiga tsakanin su, daga bisani da kanta ta kawo masu abinci da abun sha ta ce suyi haƙuri mamakin ganinsu ne ya mantar da ita bata kawo masu komai ba. Duk da ba abincin ya kawo su ba, amma saida suka ci saboda ta matsa lamba akan su ci girkinta, aikuwa Zaid ya yi ta santi yana faɗin Zayn ya yi dacen mata saboda ta iya girki zai dinga zuwa gidan su cin abinci, Zayn ya ce karma ya soma, don shi kawai zata dinga yin girki shima in yanaso to ya nemi mata ya aura, Zahra duk tana jin su, murmushin farin ciki ya ƙi barin fuskarta, Zaid ya ce gashi farin sunansu duk iri ɗaya, dama can Allah ya ƙaddara Zahra ta Zayn ce shima zai nemo mai irin farin sunan sa ya aura. Cikin nishaɗi da annushuwa suka yi firar su, da zasu tafi har bakin mota ta raka su suka yi sallama kamar kar su rabu da juna, su kansu sun ji daɗin karramawar da Zahra ta yi ma su. bayan tafiyar su ta watsa da gudu ta nufi ɗaki tana taka rawar murna. Benazir ce ta haɗa soyayyar Aneelerh da Zaki Mubarak Obinna, cikin sa'a jininsu ya haɗu, soyayya mai ƙarfi ta shiga a tsakanin su, da farko Benazir ta yi zaton zai ƙi amincewa da Aneelerh a lokacin ma baya a Nigeria yana a Canada, a waya ta kira shi ta yi mashi tayin aminiyarta, harta faɗa mashi abun da ya faru da mijinta, ya ce ya gode da tayin da ta yi mashi amma baya jin zai iya son wata ƴa mace a halin yanzu, ta ce ya jira ta tura mashi hotonta tana da tabbacin in ya ganta zai so ta, saboda Aneelerh tamkar madadinta ce, bayan da suka kammala wayar, ta tura mashi hoton Aneelerh da baby Junaid a wayarsa, ko minti biyar ba a yi ba, sai ga kiran shi tana yin picking ya ce ta tura mashi contact ɗinta, amma baya son ta faɗa mata ita ce ta haɗa su, yana son ya nemi soyayyarta da amincewarta, ba tare da ta yi tunanin haɗa su aka yi ba, zata iya amincewa don ta yi mata kara ba don tana son shi ba. Benazir ta ji daɗin maganarsa, nan take ta tura mashi contact din Aneelerh via chats din su.. Lokaci na farko da Aneelerh ta ga kira da baƙuwar number kuma daga ƙasar Canada sai da gabanta ya faɗi saboda ruɗewar da ta yi, kamar bazata ɗaga kiran ba, amma ta yi shahada ta ɗaga, tun daga kan muryarsa ta fahimci mutunne mai nutsuwa da kamala, bayan sun gaisa ta tambayesa wanene shi? Kuma a ina ya samu contact ɗin ta? Da zolaya ya ce a mafarki aka nuna masa ita tare da contact ɗinta, da ta ji hakan sai ta yi dariya ta ce ita dai ya faɗa mata wanene shi? Tana ji aranta ya santa shiyasa ya kirata. Ya ce haka ne ya santa, amma ta yi haƙuri ya kar6i contact dinta batare da saninta ba, kuma ya kira batare da izininta ba, amma kar ta ga laifin sa, sonta ne ya ja hakan tun da ya ga hotonta ya ruɗe.. Tambayarsa ta kuma yi wanene ya basa contact ɗinta? Kuma a ina ya ga hotonta?" Still bai sanar da ita ba, sai dai ya ce ta duba whatsApp ya tura mata saƙo.. Bayan sun gama wayar, ta shiga whatsapp ta duba saƙon da ya tura mata.. Hotonsa ne tare da bayaninsa. Farat ɗaya ta gane ɗan uwan Chief Owais ne saboda kamanninsu, da kuma sunan shi da ta gani Zaki Mubarak Obinna.. Zurfin tunani ta shiga tana ƙoƙarin gano wanene ya bashi contact ɗin ta! Don ta ji aranta wani ne yake son haɗa su.. Da ƙyar ta tuna da labarin da Benazir ta basu na abun da ya faru da ita bayan ta bar gidanta da kuma hannun mutumin da ta faɗa! Nan ta fahimci haɗin Benazir ne... A ranta ta ayyana in kuwa hasashen ta ya zamana gaskiya zata yi farin ciki sosai, a lokacin ta yi mamakin yadda har ya kira ta a waya, gani take ya fi ƙarfin ta, gashi babban mutum mai arziƙi ga kyawun sura, ita kuwa har aure ta ta6a yi ga ɗa tana da shi, har kokwanto ta yi anya Benazir ta faɗa masa komai game da ita? Tayaya yana saurayi zai nemi soyayya da bazawara mai ɗa! Bayan da ya sake kiran ta, ta ce mashi ta gano komai, Benazir ce ta bashi contact ɗinta, kuma shine mutumin da ya taimaki Benazir bayan da ta bar gidan mijin ta.. Baiyi mamakin jin ta gano ba, nan take ya fayyace mata abun da ke tafe da shi, ya ƙara da cewa yana sonta ba don Benazir ta haɗa shi da ita ba, a karo na farko da ya kalli hotonta ya ji ya kamu da ƙaunarta, kuma da aure ya ke sonta.. Zare idanu ta yi, cike da mamaki ta ce dagaske ya ke ko wasa? Kuma Benazir ta faɗa masa ta ta6a aure tana da ɗa?" sautin muryarsa da annuri ya ce ta faɗa masa komai, har hotonta dana ɗanta ta tura mashi ya gani, kuma yana son yaronta, zai kula da rayuwar su gaba ɗaya, kar ta ji komai. Bazan iya bayyana maku farin cikin da Aneelerh ta yi ba, a daren ranar da suka fara soyayya, kusan kwana su ka yi suna waya.. A washe garin ranar, tun da sassafe ta je gidan Benazir don ta yi mata godiya, Taj da ya ji labarin a gurin Benazir ya nuna farin cikinsa duk da ya so ya auri Aneelerh saboda akwai sonta a zuciyarshi kuma yana son ya ruƙe Junaid a gurinsa amma sai ya haƙura saboda ya ji labarin kyawawan halayan Zaki sai ya ji ya kwanta masa arai, ita ma Aneelerh ta so Taj a baya, amma saboda bazata iya auran mijin aminiyarta ba shiyasa ta haƙura da shi, dama can Allah bai ƙaddara za su auri juna ba. Duk a shekarar bayan dawowar Zaki daga Canada, ya turo magabantansa gidan su Aneeleerh, abun Allah! daga zuwa sanya biki suka ji daɗi nan take suka zarce da ɗaura aure bayan sallar azahar, duk da Abie ya faɗa masu yana buƙatar lokaci da zai yi ma Aneelerh kayan ɗaki, Sir Mubarak ya ce basu buƙatar komai daga gare su, Zaki yana da gida da komai na buƙata a estate ɗin su, ba su son a kawo ta da komai. Alhamdulillah, bayan shagalin bikin Aneelerh a ƙarshe ta tare a gidan mijin ta.. A gurin bikin Aneelerh, Allah ya haɗa wasu masoyan, Zaid da Sajeeda! Da kallo ɗaya Allah ya jarabce shi da sonta, kuma cikin sa'a ta amince da soyayyar shi. Yayin da Mahboob namu ya faɗa tarkon son Zeenatu dama ya santa tun lokacin baya da Benazir ta ta6a zuwa da ita gidan su, amma bai so ta a lokacin ba saboda yana tare da Ana, bayan haka ko babu Ana ba zai so ta ba a lokacin saboda yana jin tashen maƙon shi baison auren mace mai kyau wadda zai yi wahalar kashe mata kuɗin zuwa saloon balle ita da ta ke baturiya😂 To a ranar walimar bikin Aneelerh suka haɗu, yaita kallonta yana bibiyarta batare da sanin ta ba, duk wani motsin ta akan idanunshi, kwata kwata bata lura ba, har saida Sajeeda ta ankarar da ita tukunna ta lura da bawan Allan dake ta bibiyarta, tarko ta ɗana masa ta fuce daga event hall ɗin walimar ta la6e baya gurin furanni, yana fitowa ta sha gabanshi, ta haɗe rai ta ce ya faɗa mata meyasa ya ke ta kallonta yana bibiyar ta duk ya hanata sukuni.! Baisan sa'adda jarumta ta zo ma shi ba, ya gyara tsayuwar shi cikin nutsuwa ya faɗa mata abun da ke a ransa. Abun ka ga rainon turai, da ta ji ya kwanta mata arai nan take ta kar6i tayin soyayyar shi, tun kafin a tashi daga walimar suka ke6e a garden su biyu suka sha soyayyar su, har bayan da suka koma gidajen su basu rabu da juna ba, chatting suka ci gaba da yi, tun daga wannan ranar ne shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, sai da ta kai ga Mahboob ne ke zuwa gidansu ya ɗauke ta ya kaita school idan an tada su ya je ya ɗauko ta, Hajiya Sarah tasan da komai, kuma ta ji daɗin kulawar da yake ba Zeenatu, saboda shi yasa yanzu bata zama da damuwa a ranta. Daga bisani Zayn Ya auri Zahra bayan kammaluwar bikin su, Anan gidan sa na cikin Imam Estate suke da zama, yayin da Zaid ya ke jiran Sajeeda ta kammala karatu kamar yadda ta nemi alfarma a gurinsa na cewa ya bari ta gama karatu sai su yi aure, Shi ma Mahboob Zeenatu ya ke jira ta kammala karatu kafin su yi aure. ___________________________________💗🔥 Taj bai manta da alkawarin da yayi akan Zai raka Danejo takai ziyara gurin yan uwanta fulanin Daji, bayan da suka samu kwanciyar hankali, a rana ɗaya suka shirya da shi da Unaisah da mommyn ta, tare da Danejo da kuma rakiyar Isod Soldiers wanda Owais ne ya Umarce su da su basu kariya saboda yaji Daji ne in da zasu je, bayan sun isa Dajin danejo bata manta da inda rigarsu take ba, ita ta jagorance su can cikin dajin har inda rigar ta ke, Ba zato ba tsammani Yan uwanta suka ganta tare da mijin ta da iyalinsa, tsantsar Al'ajabi ne ya kama su, nan take suka fashe da kukan farin ciki, itama ta kama kukan murnar ganin yan uwanta, bayin Allah basu ta6a tsammanin za su sa ke haɗuwa da Danejo ba, tun bayan da suka ba Taj amanarta ya tafi da ita, damuwa da zullumin awani hali take a ciki ya cika zukatansu, basu ta6a mantawa da ita ba, a lokacin har sun fidda rai da ita, duk in su ka tuna da ita sai sun yi danasanin ɗaukar ƴar su marainiya su ka ba bare, amma zuwan da Taj ya yi da Danejo Ya faranta ran su, sunyi farin ciki mara misaltuwa, sun ƙara jin kaunarsa ganin yadda ya ruke amanar ƴar su, sun kuma yi mamakin ganin Angel, Ƴar yarinyar da suka sani tun tana da shekara sha ɗaya sai gata sun ganta ta girma ta zama budurwa, itama Unaisah tayi farin cikin ganin su, musamman Hasiya Yar uwar Danejo. Benazir ta yi masu godiya sosai akan taimakon da Sukayi ma Yar ta Unaisah, gaba daya sunji dadin karramawar da sukayi masu, sati Ɗaya sukayi A rugar, Lokacin da zasu dawo Taj Ya roƙi alfarmar da su biyo su su dawo birni cikin mutane da zama, har ya yi masu alƙawarin zai taimaka masu da muhallin da zasu zauna, da farko sun nuna ƙin amincewar su saboda sun saba da rayuwar daji tun kaka da kakanni, amma da Danejo ta lallashe su ta kuma basu labarin rayuwar birni da kuma ababen more rayuwa sai suka amince da zasu biyo su, dama kuma suna cikin matsin talauci tun bayan da su ka rasa shanayensu da 6arayi su ka sace. Taj da Benazir sunji dadin amincewar su saboda suna son su saka masu da halaccin da su ka yi wa Unaisah, bayan da suka baro rigar, kaitsaye suka nufi Jihar Joss, already Ya gyara gidansa na Joss da niyar duk in zasu kawo ziyara sai su sauka anan, Gaba daya Ya mallaka ma Dangin Danejo gidan, da ya ke basu da yawa ya ishe su har ya yi masu yawa, Unaisah ta basu kyautar Kaso mafi tsoka a cikin kudin da kotu ta raba masu na Elders, yayin da Benazir ta ƙara masu da kyautar Kuɗin da zasuja jarin sana'a, ga kuma kudin da Owais ya bada abasu kimanin miliyan goma. suka dinga yin kukan farin ciki suna yi masu godiya, kafin tafiyar Taj da iyalinsa sai da suka rakasu kasuwa suka yi siyayyar dabbobin da zasu kiwata, a bayan gidan suka hada garken Dabbobin su, inda zasu cigaba da kiwon su, ga kuma sana'ar siyar da fura da nono da za su farayi, Taj ne Ya haɗa su da abokinsa Muhsin bayan daya nemi taimakonsa Akan ya dinga taimaka masu har su samu wayewa tun da shi anan joss ya ke da zama tare da family dinsa, Muhsin yaji dadin alfarmar da Taj ya nema agurinsa saboda shima yana Neman hanyar da zai saka mashi alkhairin da yayi masa. bayan Taj da iyalinsa sun koma Abuja, Muhsin da danginsa ne suka cigaba da kula da dangin Danejo, suna taimaka masu ta fannin wayar masu da kai game da rayuwar birni da kuma mu'amala da jama'a, sun kuma taimaka masu gurin neman ilmin addini dana zamani. *FLASH BACK💗💔* bari mu koma baya muji shin wanene Mahaifin Prisoner Chinonso wanda muka fi sani da Majnoon, Unaisah ce ta gano wanda ya sadaukar da shi saboda ta ƙwallafa rai akan son sanin wani mugunne ya sadaukar da ƙaramin yaro mai ta6in hankali har yayi silar mutuwar shi? saboda bata manta da shi ba, yana aranta, har Yau har gobe bata daina yi masu addu'a ba shi da Unaizah, da sauran yan uwansu prisoners wadanda suka rigamu gidan gaskiya, tun kafin ayi shari'ar Elders, ta ta6a jin labarin kundin rijistar fursinoni a gurin Owais shi ne ya fada mata yadda suka samu kundin ya kuma fayyace mata abun daya ƙunsa, ko da taji haka nan ta roƙe shi daya taimaka Ya dubo mata wanene ya sadaukar da Majnoon dinsu a cikin littafin rijistar fursinoni, bai tambayeta dalili ba, bayan daya kawo mata littafin, a gaban ta Ya buɗe shafin prisoners din da aka sadaukar Na sashen su a kurkukun, suna tsaka da dubawa nan take suka gano sunan Chinonso, da wanda Ya sadaukar dashi, bakowa bane face aminin baba Obie, Jan kunne, Chinonso yana daya daga cikin ya'yan sa daya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, gaba daya ma ya'yan da yake sadaukarwa bata hanyar aure yake samun su ba, Majority dinsu tsohuwa zafreen ce ta ke haifa mashi su, a tare suke sadaukar da jinin su gidan kurkukun, Unaisah batayi mamakin jin sunan wadanda suka sadaukar da shi ba saboda tasan Tsohuwa Zafreen takuma san kafurar zuciyarta, daga bisani tayima Chief Owais godiya daya taimaka mata gurin gano abun da ta ke nema 💔 __________💖TURAI_____, Shin wacece Harriet (khadija) Mahifiyar Dr Jazz ? Menene asalin su? Me kuma yasa ta baro ƙasarta England da danta tazo Nigeria? Tayaya kuma akai ta samu aikatau a obie estate? Harriet Baturiya ce ta usili, Yar asalin London ce babban birnin kasar England , ta taso a hannun Mariƙinta, kawunta kanin mahaifin ta, wanda tun bayan rasuwar iyayenta ya ɗauke ta ya dawo da ita gidan shi, Yana da mata daya tare da ɗansa Abraham wanda ya haifa tare da mariganya matar shi ta farko, kawunta ne ya rike ta tun daga ƙuriciya har ta girma ta zama budurwa, bayan data mallaki hankalinta, ta kammala karatunta, ya haɗa ta aure da ɗan su, wanda sun daɗe suna son Juna tun da kuruciya, bayan data samu cikin shi wata tara cuf ta haifi danta mai suna Eric wanda muka fi sani da Jazz, daddynsa Yana mutuwar son shi kamar ranshi, arayuwar Turai bata da matsalar daya wuce Matar Uncle dinta wato step mother din mijin ta Beatrice, Beatrice bata da mutunci ko kaɗan, ta ɗaura mata karan tsana tun lokacin da Mijinta Ya kawota gidan, bata son ta, bata kula da ita, kullum cikin ƙyarar ta ta ke yi, idan ya kasance su biyu ne a gida har wankin bango take sanyata, ta dinga yi mata barazana akan zata kashe ta. haka lokacin da Uncle dinta ya hadata aure da dan uwanta, Beatrice ta nuna ƙin amincewarta, saboda bata son idan Abraham Ya mutu ta gaji dukiyar shi, shiyasa tun farko taso ta hada shi aure da diyar kanwarta, amma ya bijire akan baison ta turai yake so, bada son ranta ba Abraham Ya auri harriet sai don saboda Ubansa Ya matsa akan saiya hada Yar dan uwansa da dansa aure saboda baya son bare Ya aureta, kuma ya fahimci son juna su ke yi, bayan auransu Ta ƙara tsanar turai babban bakin cikinta, Arziƙin Abraham da yake yana da dukiyar daya gada agurin mommynsa, tasan muddin Ya mutu turai ce zata gaje shi tare da danta, ita kuma batason hakan ya faru, gani take kamar ma Turai badan Allah ta aure shi ba, sai don saboda dukiyar shi, gaba daya ta hana rayuwarta sukuni, gashi ta kasa faɗama kowa game da ƙuntatawar da ta ke yi mata da ya ke a gida daya suke rayuwa kowa da part din sa, ta hana ta sukuni agidan Mijinta, karshe ma ta fara shiga tsakaninta da mijinta, ta dinga kulla mata makirci duk don ta rabasu amma Allah bai nufa ba, saboda daddyn Jazz yana yi mata son da baya ganin laifinta akan komai, a wata rana Allah yayiwa Uncle dinta rasuwa sunji mutuwarshi, musamman ita daya zama gatanta, hankalinta Ya tashi saboda tasan Beatrice ba zata raga mata ba tun da mai goya mata baya baya araye yanzu zata samu damar rabata da mijinta, ko ta kashe ta kamar yadda ta saba fadin itace zatayi ajalin ta. Kamar kuwa ta sani, bayan rasuwar Uncle dinta, ta canza salon cuzguna mata, har maza take dauka haya ta biya su kuɗi don su farmaketa saboda kawai ta shiga tsakaninta da mijin ta, amma Allah bai nufa ba, kullum batayin nasara akanta, kuma takasa tankwara zuciyar Abraham akan ya rabu da turai saboda a lokacin ya kara sonta fiye da da saboda kafin mutuwar daddynsa lokacin dayake jinya agadon asibiti saida ya roke shi akan ya kula da rayuwar yar uwarsa, ya bar mashi amana, Yasan step mom din sa bata sonta, zata iyayin komai donta rabashi da ita, don haka ya kula da rayuwarta, duk runtsi duk wuya karya rabu da ita, wannan wasiyar da babansa yabar masa ce tasa baya sauraron maganar Beatrice, akan Turai sun sha samun sa6ani da ita, saboda ya bijire mata akan Umarninta. a lokacin da Jazz yakai shekaru Biyar, daddynsa ya rasa ranshi a wata tafiya da ya yi tare da abokan kasuwancin shi, daga London zuwa turkey, Jirgin su yayi Crashing, yana ɗaya daga cikin wadanda suka rasa ran su. Turai tayi bakin cikin mutuwar shi har saida ta yi rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da ta samu lafiya, ta fara tunanin menene mafita? Saboda tasan a yanzu bata da gata daya wuce Allah, Wadanda suke kare ta daga sharrin Beatrice sun mutu, ta kuma san bazata kyale ta ba, tunda yanzu ta samu damar da zata iya salwantar da ita, aikuwa awata rana kwatsam tajiyo firar da su ke yi tare da aminiyarta adaki akan yadda zasu kasheta su gaje dukiyar Abraham, har tana fadin ita babban bakin cikinta, gaba daya sunan Turai ne akan kadarorin sa, ga lauyansa dake kokarin tsaya ma turai da danta don su kar6i hakkinsu, sai kawar tace"abun daya kamata suyi kafin araba gadon dukiyar tashi, su bi ta bayan fage su kashe Turai, sai su bar danta su ruke shi a hannun su ta yadda ba za'a zarge su ba" Koda jin wannan firar tasu hankalin turai ya tashi matuƙa, tayi mamakin jin furucin matar Uncle din ta, ta rasa gane meyasa ta tsaneta har haka? Bata san cewa ita bata damu da dukiyar shi ba, burinta ta zauna lafiya da ita, amma da taga da gaske kasheta zasuyi sai tayi dabarar kiran lauyan mijinta ta fada mashi abun dake faruwa, ya nuna damuwarsa yace in ba damuwa su dawo gidansa da zama zai basu tsaro, sannan zai kai ƙarar Beatrice akan furucin kisa da ta furta mata, turai ta nuna kin amincewarta akan shawarar shi, tace ita kawai bata jin zata iya cigaba da zama a kasar, ta rasa gatanta, ta tsani zaman london tafi son tayi nesa da su ta tafi can wata kasa inda zata raini danta, kawai ya taimaka mata su siyar da kadarorin mijinta da komai nashi batare da sanin Beatrice ba, Lauyan baiso shawarar data yanke ba, amma da dayaji irin barazanar da Beatrice keyi mata sai ya go yi bayan ta bar ƙasar, kuma hada karin kalaman data furta na cewa ta tsani zaman kasar kuma shi mai biyayyane ga umarninta saboda amanar dake a tsakaninsa da Abraham. ta bayan fage suka siyar da kadarorin Mijinta, dama Black card dinsa Yana a hannunta, tun bayan rasuwarshi ta ke boyen shi, Beatrice tasha tayi mata barazana akan ta bata komai nashi, a lokacin harta ƙwace mata key din motar, nema take ta kore ta daga gidan, amma saboda gadon Abraham data ƙwallafa rai akai Yasa ta dakata tana jiran ta kwace komai kafin ta koreta. Batare da sanin Beatrice ba, Lauyan ya taimaka mata suka siyar da kadarorin Abraham gaba daya kudin ya zuba mata a account din sirri daya bude mata, shine ya bata shawarar ta dawo abuja ta zauna ta bar nahiyar su, saboda shi dan asalin nigeria ne mazaunin abuja anan family dinsa suke, karatune yakai shi england harya zama lauya acan. A takaice da taimakonsa Turai ta gudu daga england tare da danta jazz suka zo Nigeria, agidan daya kama masu haya suka zauna, komai da ta ke bukata da kudin gadon su ta ke yi masu, Lauyan nan shike kula da su, duk da ba anan yake da zamaba amma baya gajiya da kiranta awaya don yaji ya lafiyar su.. Turai bata yi aikatau saboda rashin kudi ba, ra'ayin kanta ne, aranar da data tsinci Domestic Staff Application daga Obie estate a social media yana yawo hakanan taji tana son ta jaraba neman aiki, ko ta samu family din da zata jingina da su, musamman da taji labarin Family din Obie, nan take ta cike form din da bayanan ta, cikin Ikon Allah bayan kwana uku sai ga sakon Interview invitation ya shigo ta email din ta. taji dadin da ba zai misaltuba, ko da ta tashi zuwa yin interview din sai ta sanya sutura mara tsada, ta tafi tare da Jazz, a lokacin ba hajjaty bace head maid ba, bata ma kaiga zuwa Nigeria ba a lokacin, bayan da taje head maid din lokacin ta yi masu interview ta tantance waɗanda suka kware gurin aikatau, Turai tana daya daga cikin su, taji dadi sosai musamman da suka ware mata dakin ta, gaba daya ta dawo da zama tare da Jazz dinta ta baro gidan da ta ke haya. a lokacin tana jin dadin zaman gidan saboda baba Obie yana mutunta ta, yana kuma son danta jazz, Kowa ya tambayeta ina daddynsa sai tace masu bazata iya tunawa da rayuwarta ta baya ba, ta dinga nuna kamar tayi loosing memory saboda kawai batason kwata kwata labarin inda take ya komama Beatrice, tasan ba kyaleta zatayi ba, ta dade tana boye ma kowa identity dinta, ga dukiya tana da ita amma bata nunawa, ko jazz baisan tana da arziƙi ba, sai bayan Shari'ar Elders Ta damka mashi gadon shi, bayan ta labarta mashi komai game da danginta da irin rayuwar da tayi agidan Uncle dinta, ta kuma bashi hakuri na kin fada mashi da batayi ba da kuma dalilinta nayin hakan. Turai ta musulunta ne saboda kyautatawar da musulmai yan uwanta masu aiki sukeyi mata, tana jin daɗin yadda suke yin mu'amalarsu wannan ne yaja hankalinta har ta musulunta, ta sauya sunan ta daga Harriet zuwa Khadija, shi kuma Jazz daga Eric zuwa Abubakar, sunan Jazz nickname ne da baba Obie ya ke kiran shi da shi saboda yadda ya ke son Music. Tsanar da hajiya saratu tayi mata ta samo asaline saboda auran ta da sir mubarak yayi bayan rasuwar matar shi ta farko, a lokacin Saratu ta tsani talaka bare mara asali, kuma tana zargin danta shege ne shiyasa batason asan labarin ta, wannan yasa ta ɗaura mata karan tsana a lokacin, taso ta shiga tsakaninta da sir mubarak lokacin da taji suna soyayya amma Allah bai nufa zataci galaba ba har saida Ya aureta Ya dauke ta daga gidan baban tare da danta ya mayar da su gidan shi karkashin kulawar shi 💔 *(Wannan shine taƙaitaccen labarin Turai da Jazz)* *BAYAN WASU SHEKARU DA RASUWAR ELDERS🔥* Katafariyar Jami'a ce da ke a cikin birnin Abuja, tana ɗaya daga cikin makarantun da suka shahara a faɗin ƙasar, kuma tana daya daga cikin makarantun da suka wadatu da ababen more rayuwa. Shin meke faruwa ne a cikin wannan Hamshakiyar makarantar, naga interior designers daga kamfanin Zahra World Of beauty sun dage damtse sunata ƙawata katafaren event hall din makarantar, da wajen Pool da kayan ado masu matuƙar ɗaukar ido da jan Hankali.. Ashe Yau babbar rana ce mai muhimmanci ga malaman makarantar, kasantuwar yau ce rana ta farko da za su fara yaye ɗaliban jami'ar da suka kammala karatu. Gaba ɗaya Glass windows din Makarantar, da saman gate din makarantar wani hadadden rubutune ke displaying ɗauke da sunan Jami'ar. Da abaka labari ƙwara ka gani da idonka, don haka ni ma bazan bari abarni abaya ba, dani za'ayi shagalin yaye daliban nan, saboda in bawa idanuna abinci... Around Ƙarfe 12 na safe daidai agogon Nigeria ta buga, a wannan lokacinne School buses suka fara shigowa ta main gate din makarantar, ɗauke da Students a cikin su, daga jikin buses din hada Tambarin makarantar da suke mai ɗauke da sunan Imam Educational Institute (IEI) Kaitsaye buses din suka nufi Parking space na jami'ar. Na ƙura idanuna ina jira inga su wanene ɗaliban dake a cikin Buses din. Lokacin da Bus divers din suka yi parking, kofofin motocin suka soma buɗewa Tabarakallahu Gaba ɗaya na ruɗe ganin Ex-prisoners na kurkukun ƙaddara suna fitowa daga cikin buses, sanye cikin uniform din su kyawawan gaske sun sauya daga ka gansu kaga ya'yan hutu wadanda suka gaji arziƙi. Yan Secondry School ɗin suna a sanye da kyawawan Uniform ɗin su, ƴan matan sun yi rolling head scarf, ya yin da mazan kowan nan su ka kalli kanshi haɗaɗɗen haircut ne na wayayyu. Admins din makarantar ne su ka yi inviting ɗaliban Makarantar Imam da iyayensu donsu taya yan uwan su murnar kammala karatu, dress code din da suka basu shine uniform din su shiyasa kowannan su ya sanya uniform din shi banda Yan jami'a su nasu kayan gidane as usual suna asanye da Casual dress na kece raini. Rayuwa kenan, waya taba tunanin bayin Allahn nan zasu samu yan'ci da canjin rayuwa? Shiyasa kada ka taba fidda rai da rahamar ubangiji, babu wani yanayi na dundundun a duniyar nan, in ma bakaji dadi anan ba in kayi kyawawan ayyuka zakaji daɗi aranar gobe ƙiyama, fada ce ta Allah buwayi, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma Allah yana tare da masu hakuri, ga misali nan mun gani arayuwar fursinonin kurkukun ƙaddara, rayuwarsu su ke yi cikin jin dadi da walwala babu takura, babu tashin hankali, babu fargaba, ba wahala sai zallar gatanci da jin dadin rayuwa. ko wanda ya taso cikin gatantawar iyayensa bai kai su jin dadi ba ayanzu saboda kulawar da suke samu, babu abunda suka nema suka rasa sabanin da, da kullum cikin uniform daya suke, kulle adaki daya, cikin kurkukun karkashin ƙasa, abinci sau daya arana, ba shige ba fuce, rayuwar ƙunci da takaici, rayuwa mai cike da fargaba, rayuwa mara yan'ci amma yanzu komai ya zama labari 🤩 Fuskokin su ɗauke da murmushi cikin raha suke fira a tsakanin su Yayin da su ke tafiya atsanake suka nufi event hall din da za'a gudanar da taron. Katafaren event hall din Ya Cika makil da mutane babu masaka tsinke, ya kawatu da colorful balloons and streamers, ga wata katuwar banner mai ɗauke da rubutun *Congratulations Graduates!* Daga gaban Hall din dogon table ne mai ɗauke da Katon Cake tare da refreshments, and a microphone for the speeches, gaba ɗaya admins din makarantar suna a zaune kan kujerun gaban table ɗin. da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar ilmin kasar duk sun hallara, kowan nan su ya kure kur'adakansa shiga ta mutunci ta alfarma. gaba ɗaya manyan bakin da aka gayyata tare da iyayen yaran suna a zaune kan kujeru na alfarma da aka kawata musamman saboda su. Daga tsakiyar Hall din ƙawatattun kujeru ne aka jera wanda asaman su Students suka zauna. Daga gefe ɗaya na Hall din wasu hadaddun Chairs din ne musamman saboda Graduates din aka tanade su. Graduates din suna asanye da graduation gown da suka ɗaura asaman outfit dinsu, launin navy blue with golden trim, sun sanya Mortarboards On their head. Yan Jarida da photographers sun hallara domin gudanar da aikin su. Iskar Hall din ta gauraya da fragrance din mutanan dake a cikin shi. Hayani ce ta cika ko'ina sai fira ake cikin raha da annushuwa... Wasu gungun students na hango sun ke6e gefe daya suna tattaunawa atsakanin su ƙasa ƙasa kamar basu son aji me suke cewa. "Unaisah bata picking call, bansan meyasa ba, tun kafin inzo hall din nan nake ta kiranta..." Sajeed ne ya faɗa yana duba agogon hannunsa, shima yana daya daga cikin graduates Haris Yace"nima inata kiranta bata ɗagawa, Na kira Batool itama batayi picking ba, ban san me ya tsayar da su ba"! ya fada fuskarsa a yamutse. "May be basu kammala shiryawa bane..." sajeeda ce ta faɗa matashiya mai jini ajika, itama Graduate ce. Zeenatu da ke a tare da su bata tanka ba, Saboda hankalin ta baya atare da su, yana akan wayar ta da take dannawa ga dukkan alamu da saurayin ta take chatting duba da yadda take sakin Murmushi, tayi kyau a cikin graduation gown din ta. "Hmm Ko kuma suna can suna bacci ba" acewar Javed.. Sajeed yace "Bana so afara basu gama hallara ba, musamman Unaisah nasan dole a neme ta idan za'a bada award" Kafin wani daga cikin su ya kuma yin magana, Sautin taken makarantar da aka kunna Ya katse hanzarin su, Kowa ya nutsu yana sauraron University Anthem din su.. Bayan da taken Ya ƙare, Kowa Ya koma gurin zamansa, School Dean ya soma yin magana babban mutunne yana magana gently hankalin kowa ya koma kansa. "Distinguished guests, esteemed faculty, proud parents, and most importantly, our graduating students, welcome to the graduation ceremony of the Freedom's Gate University"! "Today marks a significant milestone in the lives of our graduates, It is a day to celebrate their hard work, dedication, and perseverance I am honored to lead this institution, and I am proud of each and every one of our graduates.." Gaba ɗaya jama'ar dake a hall din suka soma yin clapping! Fuskarsa ɗauke da murmushi ya karasa Speech dinsa mai ma'ana.. Vice Dean of Academic Affairs ta ɗaura da cewa "Today is a big day for us, a day we will never forget, a day of remembrance. It marks the first day our first student graduated from this university. Coincidentally, today is also the anniversary of the day we opened this school." "Over the years, our school has gained fame and received awards from around the world, thanks to our talented students who have become symbols of our glory." ɗan dakatawa ta yi da yin bayanin idanunta akan mutanen dake sauraranta suna ta tafa hannayen su. Numfasawa tayi cikin nutsuwa ta ɗaura da cewa"Before I finish my speech, Ina farin cikin gabatar da wadannan lambobin yabon ga haziƙan daliban da suka kammala karatun su, haƙiƙa sun cancanci ayaba masu saboda ƙwazon su da jajircewar su dan ganin sun cimma wannan matakin"! da jin wannan maganar ta vice Dean nan fa hankalinsu su Sajeed Ya tashi jin shiru sauran ba su ƙaraso ba. "ko bamu faɗa ba, kun san su wanene waɗannan fitattun da zamu kira sunayen su.." Tunkan Ta karashe maganar students suka din ga ambaton sunan Unaisah da twins da Zeenatu saboda kowa yasan su da kaifin basira. "ina fata suna a kusa kuma suna sauraron mu.." Ta faɗa tana bin graduates din da kallo kafin ta soma kiran sunan ukun farko kamar haka Sajeed Ubaid wadata, da Sajeeda Ubaid wadata, da kuma Zeenatu Ubaid wadata. miƙewa su ka yi daga kan kujerarsu, gaba daya idanu suka dawo kan su, suka ruke hannayensu cikin na juna, walking gently suka nufi kan stage fuskokinsu dauke da murmushin farin ciki.. Department Chair of cybersecurity ce ta damƙa ma Sajeed kyautarsa wani hadadden wrapped box ne mai faɗi tare da certificates na shaidar kammala degree dinsa na farko. hannayensa na kerma cike da zumuɗi ya kar6a cikin girmamawa yayi godiya. Director Of the Human Rights Program Ya bawa Sajeeda da Zeeenatu awards da gifts din su, cike da tsantsar farin ciki kowan nansu ya sanya hannu cikin girmamawa suka kar6a. cikin harshen turanci su ka yi godiya tare da nuna irin farin cikin da su kayi, su ka kuma ba sauran yan uwansu dalibai shawarwari akan su dage da karatu su maida hankali ta yadda zasu zama wasu agobe. Jama'ar da ke a hall din sai tafa masu su ke yi, musamman yan uwansu ɗalibai tsabar zumuɗin su tayasu murna, suna ta daga masu hannu tare da ƙwala masu kira.. Komai da ke faruwa akan idanun Hajiya sarah da su Alhaji ubaid da sauran Yan uwan su da su ka hallara, sam sun kasa rufe bakunan su saboda farin ciki kamar waɗanda akayiwa albishir da gidan Aljanna. suna saukowa daga kan Stage cike da zumuɗi su Haris suka nufe su da fara su ka soma rungume su suna taya su murna, daga bisani suka nufi gurin iyayen su da ke tunkaro su, rungume su su ka yi sunata taya su murna. Taken makarantar da aka kunna ne yasa Kowa yayi shiru tare da komawa mazaunin su.. Bayan da taken Ya dauke, Dean of the School ya soma magana "And now, it is my pleasure to present the 'Excellence in Computer Practice' award to an outstanding graduate from the Computer Science (CS) Department." gaba ɗaya hankalin masu sauraro ya koma kan shi cike da zakuwa suke jira suji karashen zancen shi. "The recipient of this award is *UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN"!* gaba ɗaya students suka soma tafi suna shewa saboda farin cikin jin Unaisah ce kamar yadda suka zata. "I WILL REPEAT, UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN, PLEASE COME FORWARD AND RECEIVE YOUR GIFT" shiru Babu alamun mai sunan zata amsa. Yan uwanta ɗalibai sai neman ta su ke yi a cikin hall din, kowa ya baza idanu yana jira yaga ta ina zata 6ullo sun san mawuyacin abune ta yi fashin zuwa school. Rashin baiyanarta ya haifar masu da rashin jin daɗi, daga malaman nasu har daliban da bakin da suka hallara gaba daya sun ƙagu da su ganta kamar kamar me. "UNAISAH ZAHEER TAJUDEEN! TANA INA NE? KO BATA ZO BA NE"? Duk wani mai numbar wayarta saida ya jaraba kiranta amma kwata kwata bata picking daga ita har iyayenta ba wanda ba'a tuntuba ba. Gunagunin da mutane suke yi ne ya cika hall din. "Meya hanata zuwa"! "Bata da lafiya ne"? "In bata da lafiya meyasa ba'a faɗa mana ba"? Kowa da abun da ya ke faɗa. "Sir, Unaisah bata zo ba, bamu san dalili ba, saboda bata kira ta fada mana ba, kuma mun jaraba kiran layinta bata ɗagawa", Sajeed ne ya daga murya yana magana, Hankulan Kowa ya dawo kan shi. "amma idan ka bani izni zanje gida na dubo ta..." Vice Dean tace "mun baka izni sajeed ka yi sauri..." (sunyi mashi alfarma ne saboda muhimmanci Unaisah a gare su) amsa wa yayi da toh bayan daya mikawa Haris gifts dinsa ya ruke masa, ya juya cikin sauri Ya nufi kofar fita daga Hall din. Bai kaiga ƙarasawa ba, Unexpected ta shigo ta kofar hall din da gudunta gaba ɗa ya hankali ya dawo kanta.. Wow Tabarakallahu Ahsanul khalikin! Kamar ranar suka fara ganin ta, kowa ya ƙura idanun sa akanta. Tana gudu graduation gown dinta na tashi sama saboda iskar da ta yayo, hakan ya bayyana Outfit din ciki data sanya, fitted gown ce baƙa, tayi tighting din jikinta ba Dan laifi, kamar a jikinta aka dinkata, daga wuyan rigan ta matse ma sha Allah in ka ganta bazaka taba cewa ƙwailar nan bace ta kurkuku komai ya fito raɗau, gudun da ta ke yi ne yasa jikinta ya dinga girgiza, musamman wide curvy hips dinta sun cika 6ul6ul da su. Fatarta tayi haske sosai sai sheƙi ta ke yi tana walwali daga gani taji gyara da tsadaddun mayukan gyaran fata, ga wani shu'umin ƙamshin turaren dake fita daga sako da lungu na jikinta kamar wadda aka tsamo daga cikin kogon turare. Hutu da kwanciyar hankali sun zauna mata, saboda saurin da takeyi ne yasa ta manta bata saka Mortarboard dinta ba, hakan ya bayyana kyakkyawar sumar kanta da ta sha gyara, tayi dark brown sai Shining ta ke yi kamar ba Unaisar da muka sani ba siririya yanzu ta zama cikakkiyar budurwa mai jini a jika. Kowa Kallonta ya ke yi, manyan baki sun saki baki da hanci, sunata kallonta, surar jikinta tayi matukar jan hankalin su, kamar su kai mata hari sai faman hadiyar yawu su ke yi kamar wasu mayu.. Sautin highheels din kafarta Ya cika kunnuwansu kwas! kwas! kwas!! Saboda hall din yayi tsit ko tari ba kaji kowa ya nabba'a yana kallon Unaisah yayin da take tunkarar Stage still da ɗan gudun ta. "Sis, Kin manta da hularki! ..." Muryar Batool ce ta katse mata hanzarin ta, a rude taci burki, sumar kanta tayarfo ta gaban forehead dinta, sai haki takeyi tana zazzare gray eyes dinta dara dara.. Kunya ta hana ta dubi mutanan da ke kallonta, duk ta kame kanta kamar marar gaskiya.. Ƙarasa shigowa ciki Batool tayi jikinta sanye da black abaya, ta saka niqab akan fuskarta, cikin sauri ta nufi Unaisah ta daura mata mortarboard din asaman kanta. "Thank you sis.." ta faɗa a wahalce kafin ta dubi admins din su adabarbarce tace.. "Ina bada haƙurin makara da nayi.." murmushi kowan nan su yayi su kansu suna alfahari da ita komai nata na burgewa ne. Dean yace"kinyi laifi Unaisah, bakizo da wuri ba, kin bar mu munata kwala kiran sunanki, makoshinmu duk ya bushe, don haka dole mu hukunta ki" arude tace"am sorry sir na gane kuskure na bazan ƙara ba ." ta faɗa tana kama kunnanta.. Photographers din dake a gurin har sun fara daukarta hotuna da videos, sautin cameras din su ya cika hall din ƙyat! ƙyat!! hasken camera duk ya kashe mata idanun ta, tunkan abasu iznin su ɗauka, ga dukkan alamu ta tafi da imanin su.. Da hannu vice dean ta nuna mata inda zata tsaya murya na rawa ta furta"thank you ma'am" ta hau kan stage din daga gaban mic ta tsaya, all eyes on her. Dean da kanshi Ya mika mata ƙyautarta tare da certificate din ta, cikin girmamawa tayi masa godiya. Students sunata kiran sunanta, waving ta dinga yi masu tana yin tsadadden murmushin nan nata. Calmly ta soma yin speech cikin nutsastsiyar muryarta "Alhamdulillah, thanks be to Allah for showing me this day I've been waiting for I'm incredibly happy I'd like to thank those who supported me, including my parents, my mentor, and my teachers, thank you very much, May God reward you with the best of his blessings" kowa dake a gurin ya nutsu yana sauraran speech dinta, yanayin yadda take magana cikin harshen turanci ba karamin tafiya tayi da su ba, muryarta kamar ana busa sarewa don dadinta, wasu har lumshe idanunsu su ke yi saboda yadda take ratsa kunnuwansu, gashi tana magana dimples dinta na lotsawa, in ta yi murmushi ko ta yi dariya ba ƙaramin Jan hankalin su ta ke yi ba. Bayan data kammala jawabin ta. Commissioner of Education ta nemi ganawa da iyayen ta saboda ta jinjina masu bisa ga kokarinsu na tarbiyantar da yar su. "Iyayena basu halarta ba.." ta fada tare da sunnar da kanta kasa, kowa ya shiga damuwa da jin abun da ta faɗa, azaton su wani abunne ya faru daya hana su zuwa. "Meyasa? Ko wani uzirin ne Ya ruƙe su? Amma ya kamata ace sun zo ta ya ki murna" vice ce ta fada. "hidima ce ta hanasu zuwa.." bata ƙare maganar ba, Batool ta yi su6ul da baka gurin furta "hidimar auranta... " dafe kai tayi da tafin hannunta, tana aikawa Batool harara a fakaice, wato ta kwafsa mata, gaba daya hall din suka sanya shewa da tafi kamar zasu fasa bangon hall din.. Muryoyin students suka cuka kunnuwanta. "Unaisah wanene zaki aura? Wani me nasaran ne zai mallake ki"? "Yaushe ne bikin naki? Gaba daya sun cika ta da tambayoyi kamar yan jarida ta rasa wa zata fara amsamawa. "Listen pls.." Dean ne ya faɗa nan take kowa yayi shiru. Dubanta yayi"Unaisah meyasa baki fada mana kin kusa yin aure ba uhym? Wani mai sa'ar ne zaure ki? Meyasa mu ba'a gayyace mu ba"? ya fada da fara'arsa. ga dukkan alamu kamar sun manta abunda su ke yi, jin maganar auren ta yasa hankali ya koma kanta. Kunyace ta kamata, ta sanya tafukan hannayenta ta rufe fuskarta, hakan ba karamin dariya ya basu ba, cike da nishadi kowa ke kallonta kamar sun samu tashar bollywood.. "Ke muke sauraro Unaisah.." zolayarta suka dinga yi.. Dakyar ta samu kwarin gwiwar furta sunan shi. "Dg Owais... " cike da mamaki kowa ya zare idanu yana kallon ta, suka kama tafa mata.. Manyan Baƙin dake a gurin suka shiga jinjina kan su aransu suka ayyana shine daidai da ita, don mallakar hamshakiyar mace irinta sai babban goro magogin karfe 👑 "I invite you all to my wedding next week, after Friday prayer, at the Sheikh Imam Malik mosque here in Abuja" ("Ina gayyatar ku baki daya daurin aurena a mako mai zuwa, bayan sallar Juma'a, a masallacin Sheikh Imam Malik da ke nan Abuja) bata kare maganar ba ya katse ta da cewa "There's no invitation card?" Tana noƙe kai cike da jin kunya tace "Sorry Sir, I forgot to send the invitation to our school WhatsApp group" Vice dean tace "Okay idan kin koma gida, kada ki manta ki tura mana, don ba zamu bari ayi babu mu ba, duk da bikin na manya ne amma tun da ɗalibar mu za'a aurar toh damu za'ay komai sai munga abun daya turewa buzu nadi" cikin zolaya ta ƙarashe maganar, dariya suka sanya gaba ɗayan su. daga bisani aka kikkira sauran graduates din da suka tantanci ya bo aka karramasu Daga bisani photographers suka cigaba da ɗaukarsu hotuna, sunyi da malaman su, sunyi da bakinsu, sun ku ma yi da yan uwansu dalibai, kowa burinshi ya yi hoto da Unaisah musamman special guests din nan ta tsone masu ido, saukin ta ɗaya sunji wa zata aura, da ba abun da zai hana su addabeta, ita Batool da yake ta rufawa kanta asiri ta sanya abaya da niqab bata ja hankalin kowa ba, da itama sai sunyi rubibinta saboda kyawun surarta. ~________________________________🌹~ Students ne tsaitsaye agaban katafaren Pool din makarantar sun kewaye Graduates. photographers sunata daukarsu hotuna. Graduates Suna ta wurga hulunansu saman Iska cike da nishadi. Kwatsam sukaga Unaisah ta wurgar da gifts dinta Cikin pool ta juya cikin sauri ta nufi parking space, gabansu ne ya fadi ganin abun da tayi kuma kwata kwata bata waiwayo ta dubi kowa ba.. Sajeed ne ya daka suka ya fada cikin ruwan ya dauko gifts din da ta jefar. Batool da sauran yan uwansu suka bita da gudu suna ƙwala mata kira, Unaisah! Sis! Ukhty! ko waiwayon su batayi ba, A kan ground floor ta jefar da graduation gown dinta da sauri Batool ta ɗauke mata ita. Ta kuma jefar da hularta haris Ya dauke ta, gaba daya sun rude sun rasa gane meke damun ta kamar mai ta6in hankali.. "Unaisah ki tsaya pls! Ina zaki je ba'a kammala party ba! Meke damunki ne? Kina cikin hayyacinki kuwa? Baki ga abun da ki ka yi ba"? Ko sauraron su batayi ba, kuma tana jin su. "Pls Unaisah ki bi a hankali, kada ki fadi, takalmanki zasu iya kayar dake.." Babu alamun zata tsaya, bodyguard din da ya kawo su yana atsaye bakin motorsa Yana jiran su, tun lokacin da ta fara zuwa School Chief Owais ya bashi aikin kula da su, don ya runka kai su school ko in zasu fita outing ita da Batool kwata kwata basu hawan Bus. Yana hango ta yayi saurin buɗe mata cardoor ta shige ciki ta zauna ta kulle kofar, tare da kifa kanta saman laps dinta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya! daga gani akwai wata damuwa da ke cin zuciyarta.." "Ma'am, what's wrong? Why are you crying?" Bodyguard din ne ya tambaya yana lekenta ta saman gilashin tagar da ke a bude. Batare data dago ta dube shi ba, cikin shesshekar kuka tace"am ok, ba abun da ke damuna, ka kaini gida kawai, banaso na kara minti daya a cikin school din nan.." "Amma yan uwanki suna ta kiran sunanki"? "Kada ka sauraresu, ka shiga kawai ka kai ni gida.." duk baiji dadin halin da take a ciki ba, lafiyalou ya kawo su baisan meya bata mata rai ba. Shiga ciki yayi ya zauna a driver's seat, kafin su Batool su karaso tuni motar ta fuce daga gate din makarantar. akan idanun su, kwata kwata basu ji daɗi ba, ko celebration din ba'a kammala ba ta tafi tabarsu da kayayyakin ta, mutane sai tambayarsu su ke yi Ina Unaisah? sai dai su ka yi karyar anyi mata kiran gaggawane shiyasa ta tafi, gaba daya suka kasa zama makarantar, saboda hankalinsu yaki kwanciya da halin da Unaisah ta shiga farat ɗaya.. A hankali Motar ta kunno kai cikin harabar katafaren Gidan daddynta dake a cikin Imam Estate. Drivern nayin Parking, ta buɗe motar, cikin sauri ta nufi main falo, tana dira kafarta ciki, kunnuwanta su ka jiyo mata muryoyin su. "Ni wallahi tun farko banso aka sanya bikin nan sati uku ba, yayi kusa, yanzu gashi abubuwa suna nema su haɗe min" "Dan Allah ki daina damuwa, meye a ciki toh? mu fa namu gyara amarya ne kawai, Owais ya riga daya yi mata komai" "Hmmm ba zaku gane ba" "Da yaushe ne za'a kawo Invitation bags din"? "Yau ne fa, ɗazu nayi waya da daddynta ya faɗa mun sunyi magana da Owais, wai daga Companyn su zahra za'a kawo kayan" "Allah ya kawo su lafiya" "Bari na sake kiran Aneelerh naji Ya jikin nata! Nasan ma ba lallai yau ta samu damar zuwa ba kinsan me laulayin ciki" da zolaya ta yi maganar.. A hankali ta dan saci kallon su da idanunta wadanda suka kaɗa jawur.. Su uku ne zaune kan Sofas, Mommynta da Ummi tare da Aunty Danejo, basu daɗe da dawowa daga kasuwa yin siyayyar kayan abincin biki, a falo suka baje kan rug suna huce gajiyar su. A hankali ta ɗan zukunna tare da zame takalmanta daga kafafunta, ta ruƙe su a hannayenta don kada suji sautin tafiyarta, Cikin sanɗa ta dinga tafiya har ta samu ta haye upstairs ta nufi bedroom dinta ta shige, jefar da takalman tayi kan floor, Idanunta cike tab da kwalla ta nufi gaban gadonta, ta zukunna tare da janyo drewer chest din jikin gadon, bakomai ne a ciki ba face kyaututtukan da ya ke bata, anan take ajiye su, ramadan boxes, Eid gift boxes, Hajj gifts, umra gifts. Cikin shekarun nan ya bata gifts sun kai guda ɗari Uku. Runtse idanunta tayi gam, hawaye suka dinga sintiri kan kuncin ta, ta rasa ya zatayi da zuciyarta? Meyasa bazata daina azabtar da ita akan son abun da bazata taba samu ba? _Ka hanani bacci, ka hanani sukuni, ka hana wani ya maye gurbinka a cikin zuciyata, ka mutu ban huta ba, ka zamar mun ƙarfen ƙafa, tayaya zanyi aure da jarabar son kasancewa da matacce? Ya ilahi_ Zancen zuci ne takeyi. Ta rasa gane ya akai hannun agogo ke nema ya koma baya! Meyasa saida auranta ya rage saura kwanaki kaɗan zuciyarta ta ke matsa mata akan son matacce wanda babu shi araye? Why why why...!!! da ƙarfi ta furta, tare da rufe drawer din, ta kifa kanta jikin gadon, ta gaza yarda itace zatayi aure ba tare da shi ba! Farin cikinta ragagge ne, duk nasarar data samu batare da shi ba faɗuwace a gareta. Da tunaninsa take samun kwarin gwiwar gudanar da komai, kuma da tunaninsa take jin dadi.." duk don ta cire shi a zuciyarta yasa ta rabu da komai na shi da take da shi amma ina kamar tana kara rura wutar sonshi a zuciyarta, bata da hotunanshi amma idanunta sun gaza mantawa da suffarshi, kwakwalwarta ta haddace memories din su, wata irin kasalace ta baibaye ta, dakyar ta lalla6a ta haye kan gadonta, ta janyo pillow tayi hugging dinsa a kirjinta sosai, ta dan lumshe idanunta, eye lashes dinta sun jiƙe sharkaf da hawaye. _Kyakkyawan murmushin shi, Kallon shi, dariyar shi, tafiyar shi, sumar kan shi, hancin shi, la66ansa, kyawun surarsa gaba daya, komai nashi takeso ta sake gani, tayi mahaukacin kewarshi, tayaya zata iya ganinsa bayan ya mutu? Wallah ji take da ace ana iya dawo da wanda ya mutu araye da ba abun da zai hana ta ki dawowa da shi._ Numfasawa tayi tana mai kara ƙanƙame pillow din data matse a kirjinta, ji take kamar shi ne ta rungume. Farkon haduwarsu ta fara tariyowa. At first time datayi tozali da shi duk da tashin hankalin da take a ciki saida ta razana da ganin kyawun shi. Nutsuwa tayi tana cigaba da tariyo komai daya faru a tsakanin su tun a gidan kurkukun ƙaddara. Rana ta farko da jikinsu ya fara haduwa dana juna, ita kadai tasan me taji but,taji wani abu mara misaltuwa duk da ba wani hankali gareta sosai a lokacin ba Amma abun yana a ranta... _"Kai wani irin jaki ne? ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko"?_ _"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."_ Tunawa da waɗannan maganganun da suka ta6a yi ne yasa batasan sa'adda ta ƙyalƙyace da dariya ba... "My man, inama ace kana araye, da na nuna maka baby Angel dinka ta girma, itama tayi abun nan irin na yar gidan daddy da ka ke muradin ganin ta da su.." ta faɗa cikin karyayyar murya kafin ta ci gaba da tunano abubuwan da suka faru a tsakanin su. _the sounds is soothing me, I can't stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_ "Dame zaka biya ni idan na koya maka"? "I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want" "does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?" "yeah" Murmushi tayi tunawa da wannan firar ta su. _"My man na soka kamar raina, na so mu rayu a matsayin ma'aurata, dana nuna maka irin masifar son da nake maka, zan zama baiwarka, in dauki dukkan ɗawainiyarka, in mallaka maka kaina kamar bana sona, meyasa ka mutu ka barni? Meyasa burin mu bai cika ba? Har yau ina danasanin tursasa maka da nayi duk da nasan wayou na ko dabarana bai isa ya sauya abun da ya ke rubutacce a cikin littafin kaddarar ka.."_ ita kaɗai take ta sambatunta, in ta fara tunanin shi saita shafe awanni tanayi kamar mara aikin yi... 💔 ~__________________________________💫~ Suna tsaka da fira, sallamar Batool ta katse su, a tare suka dago suna kallon ta yayin da take shigowa hannunta ruke da Graduation gown din Unaisah, sajeed da Haris suna abiye da bayan ta, kowannan su Ya ruke kayan Unaisah data jefar, a rude Benazir da Ummi suka mike suna duban su. "Babe! Ina kuka baro Unaisah din? Wannan ba graduation gown din ta bace"? Ummi ce Ta faɗa tana nuna rigar hannun Batool. Sajeed ne ya labarta mata abun daya faru, hankalinsu Ya tashi.. Batool Tace"ummina bata dawo gida bane"? "Bata dawo ba Batool, bamu ganta ba, amma abun da daure kai? Kamar dai mai tabin hankali, babu abunda akai mata kuma? Ta fada da ruɗu akan fuskarta. Damuwa ce ƙarara akan fuskar Benazir"Ku fada min gaskiyar abun daya faru! Ko dai ta samu sa6ani da wanine a cikin ku"? "Wallahi Aunty Benazir babu abun da akayi mata.." "To ina ta tafi ne"? Ta kuma tambaya. Ummi tace"tun da ranta a6ace ya ke zai iya yiwuwa ta shigo tagan mu saita lallaba ta wuce ciki, muje mu duba dakin nata.." Cikin sauri suka nufi bedroom din ta. "Babyna Kina a ciki"? benazir ne ta fada tana bubbuga ƙofar dakin. Daga ciki suka jiyo voice din"mommy, am sorry na dawo ban fada maku ba, bana jin dadi ne amma da sauki yanzu. " "Haba Unaisah, wani irin rashin lafiyane zai sa ki watsar da kayan graduation dinki"? Shiru tayi saboda bata da amsar da zata ba.. "Zoki buɗe min ƙofa tunkafin ranki ya 6ace" saukowa tayi daga kan gadon ta buɗe ƙofar, gaba ɗaya suka bi ta da kallo.. Daga yanayin ta suka fahimci bata da lafiya. "Me ke damunki"? "Mommy, zazza6i ne amma na sha magani" shafa wuyanta Benazir tayi jin da zafi yasa ta yarda da maganarta"Allah ya baki lafiya" ameen ta masa, danejo ma tayi mata sannu da jiki.. Ummi tace"Allah ya baki lafiya, ki koma ki kwanta, ki samu kiyi bacci" Amsawa tayi da toh. Ummi ta dubi Batool "Babe, ki zauna tare da ita, ki kula mana da ita" amsawa tayi da toh. sauran su ka yi mata fatan samun lafiya. Sajeed da Haris suka mikama Batool kayan Unaisah, bayan ta kar6a suka nufi ciki ita da Unaisah Bayan ta ajiye mata kayan a cikin closet din ta, ta juyo ta dubi Unaisah dake a kwance kan gado. "Sis, badai har yanzu baki daina wannan tunanin ba"? Ta faɗa da damuwa ta zauna kusa da ita tana kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tasha. "Batool na rasa ya zanyi, kwanakin nan kamar ana sabunta min kaunar shi..." ta fada tana jan majina.. "ke kadai kika san da wannan maganar, pls amana kada ki fada ma kowa amma bana jin zan iya zaman aure, saboda tunaninsa da nakeyi zai iya jaza min matsala..." idanun Batool tuni sun cicciko da kwalla, tausayin yar uwartata ne ya kamata. "Ba irin addu'ar da banyi ba akan Allah ya cire min son shi amma babu abun daya sauya, Ina azabtuwa Batool" ta fada tare da cusa kanta cikin pillow. Girgiza kai Batool tayi hawaye har sun fara sauka kan kuncin ta"bani da maganin abunda ke damunki, al'amari ne mai girma Unaisah, nima yafi karfina, zaman aure bazaiyi yiwu da tunanin son kasancewa da wani wanda babu shi araye, amma menene mafita"? "Babu mafita Batool" "Baki tunanin idan muka faɗawa su mommy zasu nema mana mafita" a firgice ta dago tare da zare idanunta cikin na Batool "ukhty kinsan me kike fada kuwa? Wannan ba mafita bace, tayaya ma zan iya fada masu? Abun da kunya kuma ba zasu dauki maganata serious ba, zasu ce bani da hankali ne" Jinjina kai Batool tayi"kin faɗi gaskiya Ukhty, to ko in fadama daddyna" wani kallo mai kama da harara Unaisah tayi mata, Batool ta kwashe da dariya.. "In haka ne nima inje in faɗawa daddyna mana ..' dariya su ka yi.. "Kinsan wani abu, pls mu cigaba da addu'a, babu abunda ya gagari ubangijinmu, in sha Allah zai yaye maki damuwarki, ni yanzu burina ki maida hankali akan shirye shiryen dake tunkaro mu, daga yau hutu ya kare mana, babu zama har sai mun mika ki dakin mijinki..." yamutsa fuska tayi"dama ni ai ba hutu gare ni ba, gaba dayana a takure nake, tun da aka sanya bikin nan bani da hutu, wlh har nagaji da zuwa beauty spa din nan, kamar wata yar sarki zatayi aure, gaba daya an sauya min jikina da gyara" dariya Batool tayi"sis tsakaninki da Allah baki ji dadin yadda kika koma ba? Fatarki tayi smooth babu ƙwarzane ko tabo kamar ka taba jini ya digo, ga gashinki ya ciza launin shi yayi laushi sai kamshin ya ke yi, ƙin ƙara kyau sosai, masha Allah kamar hurul aini..." ta6e baki Unaisah tayi aranta taji dadin yabon kyanta da Batool ta yi. "Kema kin sauya sis, gyaran jikin nan ya kar6eki wlh, kamar kece amaryar ma" murmushi batool tayi"Albarkacinki nake ci Unaisah, shiyasa nima nake samu ana zuwa dani spa din, naso ace tare zamuyi aure arana daya, amma Allah bai nufa ba, daddy yace saina kammala karatu ko zai barni in kula masu zuwa neman aurena" "Nima nayi fatan haka batool, amma karki damu, kema in sha Allah zakiyi aure nan bada jimawa ba" "Na cika ki da surutu mrs owais, ki kwanta ki huta, Yau henne night ne, har nakosa time yayi wlh..." Ta faɗa tare da lullu6e mata jikin ta da bargo "Nan da wasu yan kwanaki a gadon mijin ki zaki dinga kwanciya" harara Unaisah tayi mata tana murmushi.. Tana jiyo motsin fitar Batool daga dakin sama sama kafin bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita.. Wuraren Ƙarfe 4 da rabi, Yan matan Amarya suka fara taruwa cikin gidan, idan kuka ji na ambaci yan matan amarya kunsan wa nake nufi, Abokananta na amana wato ex-prisoners. Ringing din wayarta ne ya farkar da ita, slowly ta buɗe idanunta da suka kada jawur, tayi shiru tana kallon ceilling. Har kiran ya katse batayi picking ba, wani kiran ne ya kara shigowa da sauri ta ɗauko wayar daga kan drawer ta yi picking tare da karawa a kunnanta. "Na kira ki ne, don na tuna maki saura kwanaki kaɗan ki zama matata" murmushi tayi"I can't wait to own you my man" Sautin kayataccen murmushinsa tajiyo mai haɗe da fitar numfashin sa. "I saw your graduation pictures on social media, and people were commenting on them, I felt indescribable jealousy why did you share your photos? why babe? Ba nace banda pics ba.." yamutsa fuska tayi kamar tana a gaban shi"Am sorry, kasan ba yadda za'ai in hana photographers ɗaukar hoto na banma san sunyi ba, kuma wallahi bani nayi sharing din su ba, friends dina ne, amma zan kiyaye nan gaba" "Okay, karki damu, na fahimce ki" Yana kokarin katse kiran tayi saurin furta"am na manta ban fada maka ba, Yau Henna night ne, wani kalar lalle kake so inyi"? "Unaisah, check your WhatsApp I'll send you a message, take care" "Okay ka kulamin da kanka" daga haka su kayi sallama. Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet ta shige don tayi wanka. Bayan mintuna, ta fito Jikinta sanye da bathrobe fara, Closet ta nufa don ta shirya kanta, jim kadan ta fito jikinta sanye da kimono Robe. Wayarta ta dauko ta shiga whatsapp chat dinsu don taga idan ya tura mata sakon Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta sa'ilin da idanunta suka sauka akan screen din wayar tana karanta message din shi. _I prefer maroon henna, zaifi dacewa da soft skin din hannun ki, When the henna is done, send me pictures so I can see" Batasan ya akai ta ke jin dadi a duk lokacin data ga sakon shi ta whatsapp. Reply ta yi masa "Okay Sir" ~______________________________~ Unexpected ta tsinkayi muryoyin su daga waje "Our bride-to-be! Sis! Mrs Owais! Unaisah! Where are you? It's time for the henna! Masu lallen sun zo, we're waiting for you" Kafin ta yi wani yunkuri suka turo kofar ɗakin nata, Ko sallama babu, zare eyes dinta tayi da mamakin ganinsu ta shiga furta sunayen su"Hibba! Hawwa! Rubina! Hannah! Saukar Yaushe? Shine baku kira kun fadamin za ku zo ba"? Ta faɗa tare da nufar su ta soma yin hugging din su. "Muna sane muka ki sanar dake saboda mu baki mamaki" hanna ce ta fada tana dariya. Hawwa tace"tun bayan sallar La'asar, muka iso, a gidan daddyn mu mu ka sauka.." "Amma dai kun shammace ni wlh, naji dadin ganin ku mutan kaduna da lagos, da har na fidda rai da zuwanku"! Haɗa baki su ka yi gurin furta "mun yi missing na ki, muna tayaki murnar kammala karatu, ay mana afwa bamu halarta ba, mun zo a makare, fatan mun same ki lafiya"? "Nima nayi missing naku, wlh karkuji komai zuwan da ku ka yi ya fanshe laifin ku.. " ta fada tana kallon su, kowaccensu hutu ya zauna mata, sun ƙara girma sun zama cikakkun yan mata, suturun jikinsu masu tsada. "Ya gajiyar tafiya? Ya kuma kuka baro mutanan gidan" har suna hada baki gurin furta"suna nan lafiyalou, sunce mu gaishe masu da amaryar su" "Wow Sis kinga yadda kika canza? Kinyi haske kin kara kyau, fatar ki sai ƙyalli take..." rubina ce ta fada tana taba skin dinta" buge hannunta Unaisah tayi tana dariya. Hibba Tace"wallahi nima abun da zance kenan, kin zama babbar mace, tubarkalla anya Unaisah baki shan maganin ƙara hips da breast" zare mata idanu Unaisah tayi, gaba daya suka tuntsire da dariya.. Kamar daga sama suka tsinkayi muryar Batool daga bayan su.. "Ƴan sa ido, Tubarkalla, komai na sis dina natural ne daga Allah, dama zuwa kukayi don ku sanya mata ido ko" ta fada da zolaya yayin da take karasa shigowa cikin dakin. Dariya suka sanya gaba dayansu.. "Ba zuwa nayi don muyi fira ba, nazo ne don in fada maku ku fito mu sauka down lokacin ƙunshi yayi" ta ƙarashe maganar tare da ruko hannun Unaisah a cikin nata su ka yi gaba sauran suka bi bayan su. Tunkan su ƙarasa saukowa down, suka hango sauran bridemaids din da ke shigowa. Parveen ce agaba ta dauki wankan abaya, idanunta sanye da shade baki, Yadda kasan hajiya saratu na tafiya, Cikin dattako take taku ɗaiɗai tana hura hanci, ta ruke hand bag a hannunta na hagu, ɗayan hannun ta ruƙe Cupcake din da take ci. Sai shan ƙamshi ta ke yi kamar iska nayi mata wari, tana ji da kanta ɗiyar minister. "Wa nake gani kamar foodie? Dagaske ke ce"? Hawwa ce ta faɗa. Muryar ta da taji ne yasa ta kai dubanta garesu tana ganin su ta washe baki tare da ɗaga masu hannu ta nufe su, bakomai ne ya basu dariya ba face ganin gefe da gefen bakinta da yayi dama dama da cake din da take ci. Tana karasawa gurinsu suka soma rungumarta. "Ni babu wanda zai rungume ni? Ko baku ganni bane"? A tare suka dago tare da duban ƙofar shigowa falo, waro idanu waje su ka yi ganin Jemimah a tsaye ta ruƙe qugunta, sanye take da lace ta coge daurin kallabi, Yarinya fa ta girma a yanzu takai kusan shekara goma sha biyar. Su biyu ne su ka zo, tana a tare da yayarta Azeeza da ke tsaye a bayanta, itama ta ƙara girma duk da har yanzu babu tsawo sai dai tana da dirin jiki, ayanzu ta wuce shekara ashirin da ɗauriya. "Jemimah? Wa ya gayyace ki? Ba mun ce bamu san ganin Yara ba? Ko akwai tsaranki anan ne.."? da zolaya Parveen tayi maganar tare da nuna mata hanyar fita"Get Out"! harara Jemimah ta watsa mata"ki bari idan bikin ki yazo sai ki hanani zuwa, kuma ai Sis Unaisah ne ta gayyace ni, ba ke ba" "Gaskiya jemimah ki nemi tsararrakin ki, tayaya zaki zo cikin mu, akwai tsaranki ne"? Ƙyalƙyacewa su ka yi da dariya.. Zura hannu tayi cikin purse dinta suka kura ido suna jira suga dame ta zo masu. Pistol ta zaro, ta saita su da ita. Gaba daya suka razana tare da duƙewa ƙasa suna rokonta karta harbesu, kwashewa tayi da dariya. Bushewa da dariya Azeeza tayi tare da girgiza kai tace "bafa bindigar gaske bace, ta wasan yaran ce.." ajiyar zuciya suka sauke tare da mikewa tsaye gaba daya sunyi zaton bindigar gaske ce, saboda sunsan zata iya dauko ta daddyn ta.. "Duk wanda ya kara gigin kora ni, sai na fasa kan shi da bindigar nan" ta fada tana nuna kawunan su da bindigar, daga ka ganta kaga sangartacciya dabi'un ta irin na yara, tuntsirewa su ka yi da dariya.. Batool tace"Like father Like daughter, Jemimah wannan bindigar ta wacece kika dauko ko ta daddy mubarak ce"? Azeeza tace"shiya siya mata hada kakin sojoji, saboda ta faɗa mashi idan ta gama karatu soja zata zama irin shi, don ta dinga zuwa yaƙi" ƙyalƙyalewa su ka yi da dariya cikin nishaɗi. Kafin suka fara huggin dinsu irin gaisuwar da suka saba yiwa junansu duk idan suka hadu.. "Assalamu alaikum, me ake tattaunawa ne ba a jira na karaso ba... " gaba daya suka jiyo tare da kallon su, kusan a tare suka shigo, Deeja ce tayi maganar, shigowarta kenan jikinta sanye da atampa, ta kashe daurin dankwalin ture kaga tsira, ga wani hadadden shade da tasaka ma idanun ta. A kafaɗa ta yafa veil din ta hannunta ruke da wayarta.. Cike da farin ciki suka hada baki gurin furta"DEEJA!" "Na'am ƴan amanana! Am sorry amaryar mu, banzo da wuri ba, yau natashi ba lafiya amma da sauƙi yanzu Alhamdulillah". ta faɗa tana nufar su, daya bayan daya ta yi hugging din su tare da manna masu peck a foreheads in su, duk su ka yi mata ya jiki? ta amsa da sauƙi. Badajimawa ba, Sajeeda da Zeenatu suka shigo tare da Sarah da yasmin da sauran kawayensu wadanda gaba dayansu Ex-prisoners ne gaba dayansu sun daukin wanka na mutunci, sun kai su Ashirin bayan sun gama gaggaisawa da junan su nan fa wata sabuwar firar ta 6arke a tsakanin su, haniyar firar da su ke yi ta cika Gidan gaba ɗa ya, bakajin komai sai sautin surutun su da dariyar su. Ƙarfe biyar daidai masu ƙunshi su ka ƙaraso gidan. A main Falo suka baje kolin su, sai da suka fara ƙawata seating area din falon da kayan decoration din su, daga daidai inda zasuyi zaman ƙunshin suka shimfiɗa Red Rug (jan kilishi) daga kewayen shi floor sofa set ne daga saman kilishin wasu ɗunɗuma ɗunɗuman floor cushions ne a jere, kamar shimfiɗar sarki, daga tsakiyar rug din farantai ne ɗauke da kayayyakin ƙunshi. Kafin su fara Aunty Danejo ta kawo masu soft drinks da snacks a cikin tray, sunji dadi har su ka yi mata godiya. Music ɗin da su ka kunna a speakers ya karaɗe ko'ina na gidan, hakan ba karamin armashi ya karawa daren na su ba. Daga tsakiya Amarya ta zauna kan cushion. Bridemaids suka zazzauna gefe da gafen ta, Batool tana a hannun damanta kamar yadda suka saba kasancewa, yayin da Hennah artists din su ka zauna akan floor Sofas, batare da bata lokaci ba suka fara harhada kayayyakin lallen kafin daga bisani suka fara yiwa yan matan amarya ƙunshi. Gaba ɗaya Jira suke wadda zatayiwa Amarya ƙunshi ta ƙaraso saboda ta ce ƙunshin ta kaɗai ta ke so. Bridemaids cikin nishadi da annashuwa suke, ana masu kunshi suna bin wakar da aka kunna ma su... Wadanda ba'a farawa kunshin ba, suka miƙe tare da jan layi suka fara taka rawar tambola.. Jemimah da Parveen sun zaƙe sai tikar rawa su ke yi har haɗa qugunsu su ke yi. "Da girman kujerar ki Yar ministern Lafiya, Takawarki lafiya toron giwa, Hajiya Parveen, rai ba buri saina abinci, an gaishe ki ƙaramar su babbarsu Naja'at bi ni ka lalace" har sun fara washe baki jin kirarin da Unaisah keyi masu amma da sukaji sharrin da tayi masu sai suka haɗe rai suna zumbura baki. Gaba ɗaya suka sanya dariya hada ma su yi masu ƙunshin sai da su ka dara.. *HAJJATY🌹* Gaba daya ta shiga damuwa ganin Lokaci na nema Ya kure mata, sai sauri ta ke yi ta kammala Girkin da ta ke yi, tasan in har ba zuwa tayi ba, Unaisah ba zata bari wani yayi mata kunshi ba, duba da yadda ta kwalla fa rai akan son tayi mata kunshi tun da ta ta6a ganin zanen kunshinta a hannunta ta rude da kyawun shi. wannan ne karo na farko da zata farayi mata kunshi bataso taji ba dadi, shiyasa take ta sauri ta gama girkin ko ta samu ta shirya ta tafi. Tana atsaye gaban Gass Cooker ta bude soup pot tana jujjuya miya da spoon din hannun ta. Kwatsam taji an fusge spoon din hannun ta, aikuwa a razane ta saki murfin tukunyar, tayi saurin juyawa don ganin wanene Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da idanunta suka shiga cikin na shi.. Cikin rawar murya ta furta"um..yay.. Yaya mubarak, am sorry, bansan ko kayi min sallama ban ji ba" Murmushi yayi yana jin dadin rudewar da takeyi idan ta gan shi, ba karamin kyau takeyi mashi ba idan tana magana a tsorace. "No karki damu banyi sallama ba, ni yakamata na baki hakuri na tsorata ki" murmushi ta ɗanyi sam hankalin ta ba akwance ya ke ba Mika mata spoon din yayi tasa hannu ta kar6a. Wani kallon so da ƙauna suke jefawa junan su, duk tabi tasha jinin jikin ta, zallumine ya cike ta, tana jin tsoron Turai ta gansu a tare cikin kitchen, tasan zataji kishi. "Kin bar babynki da yunwa, Baki bashi abinci ba" ya faɗa yana shafa cikin shi.. Cikin rawar murya tace"am.. Sorry yayana, na kusa kammala girkin, ka koma dining ka jira ni yanzun nan zan kawo maka.. " ta fadi hakanne don ta samu ta lalla6a shi ya fita.. Allah mai jujjuya al'amurra, bata taba zaton zata so wani ɗa namiji bayan Praveen ba, ada ji take babu wanda zai iya maye mata gurbin dan uwanta Praveen amma a yanzu da babu shi, Sir Mubarak Ya sace zuciyarta da soyayyar shi, kulawar shi, komai ma.. "Kora ta ki ke yi ko"? Girgiza mashi kai tayi a'a wallahi.. Murmushi yayi "nasan me kike jima tsoro, to meye na damuwa a ciki? Ta riga da tasan ina sonki, da amincewarta ko kin manta cewa itace ta fara bani shawarar in nemi soyayyarki saboda tana son ku rayu a karkashin inuwa ɗaya.. " Kamar zata sanya kuka tace"na sani ni ba wannan bane damuwana, kasan dai babu kyau mace da namiji su ke6e ko"? Har ya buɗe baki zai yi magana Unexpected muryar Naufal ta katse su. "Daddy! dama kana a kitchen? Da sauri Sir Mubarak ya ja da baya tare da shan mur yace "Tambai, kai zan tambaya yaushe ka dawo gidan"? Ƙumshe dariya Hajjaty ta yi tare da juyawa ta cigaba da duba girkin ta. yamutsa fuska yayi aransa ya furta"hmm a sannu zan gano menene a tsakanin ka da mommyna, kai ta daure min fuska kana shan mur" "Tun ɗazu na dawo.." ya fada tare da nufar mommynsa data basu baya. "Mommy, Unaisah ta kira ni awaya tace tana ta kiran ki bakya picking, ke suke jira kije ki mata ƙun shi" Cike da jin kunyar shi ta furta"na manta wayar a daki, pls, Idan sun sake kira ka fada masu aikine ya rukeni, amma dana gama zan taho.." amsawa yayi da toh, ya juya zai fita ya ɗan juyo ya saci kallon Sir mubarak karaf idanunsu suka shiga cikin na juna. Ɗage mashi gira yayi"ɗan sa ido kwanan nan zan sake aske maka sumar kanka" ƙasa ƙasa da murya yayi maganar don kada taji su. Cike da jin kunyar shi Naufal yayi saurin fucewa daga kitchen din cike da fargaban kada ya aske mashi sumar kanshi daya tara kamar mace. Girgiza kai sir mubarak yayi.. Yana son Yaron sosai kamar yadda ya ke son Jazz ba ka ta6a gane ba ƴa'ƴansa ba ne. fuskarsa da murmushi ya dubu Hajjaty. "Ki aje girkin ki tafi zanyiwa yar uwarki magana tazo ta karasa, kin sa masu rai, Jira bashi da dadi" Girgiza kai tayi"no, pls, kada kayi mata magana, zanyi kokari in gama" "tun da baki so in kira ta, to ni ki bari in karasa maki girkin" zare idanu tayi da mamakin maganarsa tace "ya mubarak, da kanka.." girgiza kai tayi"ban yarda ba, bazan bari kayi girki ba, bayan kana da masu girka maka" Sallamar Turai ce ta katse firar su, Aruɗe hajjaty taja baki tayi shiru, gaba daya idanun su akan ta. Fuskarta ɗauke da murmushi tace"love birds, zan iya sanin me kuke zantawa ne"? Murmushi su ka yi Sir mubarak yace"kin hana in ajiye masu aiki a gidana, gayanan yar uwarki aiki yayi mata yawa, ga gidan biki sunata jiranta zatayiwa amarya ƙun shi..." 6ata fuska Turai tayi"banji dadi ba, meyasa baki faɗa min ba? Kin bar bayin Allah sunata jiranki" "Banaso na takura maki ne, kuma nama kusa karasawa.." bata ƙare maganar ba, Turai ta katse ta"bana son jin wani abu, pls, kije ki shirya ki tafi in ba so kike raina ya 6aci ba" har cikin ranta taji dadi"nagode sosai" Ta fada tare da kama hanya ta fuce. Kallon Sir mubarak tayi"pls, yakamata kana dan jurewa, ka san inda zaka dinga tunkarar hajjaty, yaron nan har yanzu wani kallo ya ke maka..." dariya su kayi. "In sha Allah zan gyara uwargidana, ina fata ban 6ata baki rai ba.." Harararsa tayi"kishi nake ji, idan naganka da hajjaty..." ta fada da zolaya. "Amma kasan wani abu, silar zuwanta cikin rayuwar mu abubuwa da dama sun sauya, Hajjaty tana da kirki bata gajiya da kyautatawa ya'yana, kamar ita ta haife su tana son su, bata gajiya dayi masu kunshi da kitso da kwalliya, saida nace ta bari bana so tana wahala amma ta nuna rashin jin dadin ta.." tun da tafara yin magana murmushi ne akan fuskar sir mubarak, yana jin dadin yadda Turai ke yabon ta. "Babe, bana jin zan iya kishi da hajjaty, duk da nasan dole inji ba daɗi amma Kuma idan na tuna, Nina baka shawarar ka aureta dadi nake ji, saboda ba karamin taimako zamu yi ma rayuwarta ba, ina jin tausayin rayuwarta, bata da kowa in ba Allah da mu ba" idanunta ne suka cicciko da ƙwalla. "Am so proud of you, bani da tamkarki turai, kin cika mata tagari, kyawawan halayanki sunfi komai jan hankalina, baki da son kai, da wata ce ba zata taba bari kawarta da take a cikin wani hali na rashi, ta auri mijinta ba, ke ta dabance..." ya fada tare da rungumota, murmushin jin dadi ta saki"kaima ka cika miji nagari, Uban marayu, ina alfahari da kai" yaji dadin kalamanta. Peck ya manna mata a forehead dinta. "Nagode sosai Ummu Naja'at, Allah yayi maki albarka, Allah ya saka maki da aljanna silar kyautatawar da kike mani" "Ameen daddyn Azeezaty.." dariya suka sakarwa juna. ~________________________________🌹~ Lokacin da Hajjaty ta karaso murna ta cika su, batare da bata lokaci ba, ta kama hannayen Unaisah ta fara tsantsara mata ƙunshi, both side na hands dinta da tafin hannunta dana kafarta, da yatsunta duka ta kawata su da maroon henna, sai da kowa ya raina kunshin shi saboda haduwar kunshin Unaisah, abunka ga fatar amarya taji gyara, duk da suma bridemaids din nasu yayi kyau. Ko da Batool taga kunshin Unaisah nan fa ta haɗe rai tace itama Hajjaty take so tayi mata kunshi kuma irin na Unaisah ta ke so komai da komai.. Hajjaty tace bazai yiwu ba, anfi son kunshin amarya ya banbanta dana bridemaids. Kowa bai goyi bayan ayi mata irin kunshin Amarya ba, hakan yasa ranta ya 6aci, har tayi zuciya ta mike zata bar gurin Unaisa tayi saurin dakatar da ita, cikin sanyin murya ta lallashe ta tace ta dawo ta zauna ayi mata irin kunshinta, dakyar ta shawo kanta ta koma ta zauna har suna tsonakarta da cewa copycat din amarya, komai amarya tayi sai tayi itama, bata ko kula su ba. Abun daya ɗaurewa Unaisah kai, meyasa Batool ta ke son yin komai irin nata? Yanzu ta gane dalilin dayasa tun farko taki yarda ayi mata kunshi ashe jira takeyi ayi mata irin nata, ta rasa gane meyasa batool take kishi da ita? Meyasa take kwaikwayonta? tun bata fahimta har saida tafara ankara, daidai da spa idan sukaje komai akayi mata na gyaran jiki, batool sai tace ayi mata irin nata, komai da ake ma amarya itama sai anyi mata, ko kallonsu kayi ba zaka ga banbanci ba, kamar dukan sune amaren, kuma idan ta nuna tanaso ayi mata irin nata wani ya nuna rashin goyan bayanshi, ranta baci ya ke yi, har sai ta samu ta lallasheta, bawai bakin ciki take yi da hakan ba, ta yarda da Batool sai dai tarasa gane meyasa take yi mata haka? Lokacin da lallen nasu ya bushe Hennah artists dinne suka wanke masu shi, su ka shafe masu zanan kunshin da mayuka masu kara fito da kyawun kunshi. Bayan da suka kammala zaman kunshin, henna artists suka tafi bayan da aka hada masu sha tara na arziki, Hajjaty ce kadai bata kaiga tafiya ba. ta kira Unaisah gefe daya ta fada mata tana son suyi magana. Unaisah tace su shiga daga ciki. A bedroom din ta suka shiga. Ta daura Handbag dinta akan gadon Unaisah suka fuskanci juna.. "Unaisah ba sai da nace maki kyauta zanyi maki kunshin ba? ya akai naga alert na dubu dari uku kudin menene har haka"? arude Unaisah tace"bani na tura maki kudi ba, amma muga alert din" miƙa mata waya hajjaty tayi tasa hannu ta kar6a tare da duba reciept din. Murmushine ya bayyana akan fuskarta"Aunty hajjaty, wannan alert din daga Chief ne, ni na fada masa ke zakiyi min kunshi amma bansan cewa shi zai biya ba" Murmushi Hajjaty tayi"sunyi yawa Unaisah, sai kace ni nayiwa duka yan matan amarya kun shi? "Please karki damu, rabonki ne, yaji dadi kinyiwa amaryarsa lalle shiyasa shima ya baki tukuicinsa.." annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, Taji dadin yadda Unaisah take bata girma. "Saboda za6ana da kikayi a matsayin wadda zata yi maki lalle, nima ga nawa gudummuwar .." ta ƙarashe maganar tare da buɗe handbag dinta, Unaisah ta kura ido a kagare da son ganin menene ta kawo mata. Set ta curo na kayan gyaran jikin amarya.. Dayawan su, Sudanese dilka, kabbasa spray, Hair bakhhoor diffuser, sandal sukkariya, dilka soap, turaren tsugunno da sauran su, saida ta gama jerasu agaban Unaisah tukunna ta soma yi mata bayanin yadda zatayi amfani da su, ta nutsu tana sauraron ta hadi da dan jinjina kan ta.. daga bisani ta ɗaura da yi mata nasiha "sai fa an cire kunya da girman kai ake nunawa miji soyayya, ki zama karuwar mijinki, kullum ki kasance cikin gyara da tsafta, bana son tuna rayuwata ta baya amma zan fada maki sirrina saboda inaso kisan surrukan mallakar miji ba boka ba malam, wanda in har kika bisu nayi imanin mijinki ba zai ta6a gajiya da ke ba, zai kasance kullum cikin marmarin ki" daɗine ya lullu6e Unaisah ta kasa kunne tana sauraron sirrikan da Hajjaty ke faɗa mata, ta bayyana mata komai batare da jin kunyarta ba, sai dai ita idan taji abun daya fi karfinta ta ɗan sunnar da kanta ƙasa ko ta rufe fuskarta da tafinta ko ta sanya pillow. Amma fa taji dadin shawarwarin da hajjaty ta bata game da zamantakewar aure.. Unexpected ta dinga hango inuwar mutun jikin window din dakinta, ta wutsiyar idanun ta kamar akwai wanda ke yi masu la6e. "Bansan da wasu kalmomi zanyi maki godiya ba aunty Hajjatyna, Allah ne kadai zai iya biyanki, ke ta dabance, Kina da kirki, kinason yar nan taki sosai. Taji dadin maganar Unaisah"karki damu Unaisah, ni dai fatana ki zauna lafiya a gidan mijinki.. " Ta fada tare da mikewa, itama Unaisah ta mike. Wayar Unaisah ce tayi ringing da sauri ta juya ta dauko tayi picking tare da karawa a kunnanta. "Mommy, har mun gama zaman kunshin, Naji shiru baku dawo nan ba" On the other hand Muryar Benazir ta amsa da cewa"muna a part din Danejo, aikine ya ruƙe mu, ba lallai mu shigo nan ba, zamu kwana anan" "Am sorry mommy, mun barku da aiki" "Karki damu, Ya zaman kunshin naku? Ina fata anyi maki mai kyau"? "Eh mommy, Aunty hajjaty ce tayi min, yanzu haka muna a tare, baki ga alherin da tayi min ba, ta kuma bani shawarwarin da zasu amfaneni" "Kai Amma naji daɗi wallahi, idan tana a kusa ki bata wayar inyi mata godiya" "Toh" ta fada tare da mikawa hajjaty wayar da fara'arta ta kar6a, Benazir ta dingi yi mata godiya. A hankali Unaisah take dan satar kallon Window glass ta wutsiyar idanun ta, Tarasa gane wanene ke yi masu la6e, kuma yaki tafiya yana nan yana sauraronsu baisan tana ganin inuwar shi ba. Bayan da hajjaty ta yi sallama da Benazir, ta miƙa mata wayar ta kar6a ta kara a kunne. "Unaisah, Ki kula min da kanki" "Toh mommy, kema haka" Daga haka sukayi Sallama, bayan ta ajiye wayar, suka fito tare da hajjaty don tayi mata rakiya. Gaba ɗaya ƙawayen amarya agidan za su kwana saboda sunyi dare sosai, duk da babu nisa gidajen su amma akwai tazara kaɗan. Har bakin gate ta rakota, bayan sunyi sallama ta dawo gida. Har lokacin bridemaids basu je sun kwanta ba, sun cika falon da haniyarsu. Gyaran muryar da tayi masune yaja hankalin su ga kallonta. "Kuje ku kwanta, Gobe akwai aiki agaban mu" ba musu suka amsa mata da toh. Bayan ta nunnuna masu Bedrooms din da zasu kwana a ciki, duk mutun uku daki daya. A tare da Azeeza da Jemimah suka nufi Bedroom din ta. Bayan sun shiga, ta ɗauko masu rigunan baccinta taba su suka musanya dana jikin su, kafin su ka kwanta kan gado. Kamar ance ta kalli kayan da Hajjaty ta kawo mata nan take gabanta ya fadi ganin babu wasu daga Cikin su, dayake komai kala biyu ta kawo mata, an ɗebi kala ɗaiɗaya anbar mata sauran. To fa! Ta fada da rudu akan fuskarta aranta ta ayyana wanene ya shigo dakinta ya sace mata kaya? Da sauri ta dubi window tunawa da inuwar mutumin data gani dazu yana yi masu labe, zato zunubi amma tana ji a ranta dakyar in ba Batool bace ta sace su tun da itace ke gasa da ita, In ba ita ba waya damu da kayan amarya. Girgiza kai ta danyi tare da kallon su jemimah har sunyi nisa a baccin su. Wayarta ta ɗauko, Ta kira layin batool almost 3 times tana ringing batayi picking ba. harta fidda rai sai ga kiran Batool ya shigo wayar Da sauri ta yi picking"sis Ina kika shiga ne? Ba adakina zaki kwana ba"? On the other Hand Batool tace"ai ni gani nan harna kwanta.." "A wani daki ne Kuma ku nawa ne"? "Mu ukune ni da Sajeeda da Zeenatu" "Meyasa ba zaki dawo nan ba? Nafi son inji ki a kusa dani" ta fada kamar zata saka mata kuka. "Kiyi hakuri Ukhtyna, na riga na kwanta, Kuma muna a down stairs, kinga dare yayi bazan iya fitowa ni kadai in dawo nan ba.." kanta ne ya daure, Batool bata taba yi mata gaddama akan tayata kwana ba in ta bukata sai yau, nan take ta tabbatar da zargin da takeyi mata, wato tana jin tsoron tazo asirinta ya tonu ta gane itace ta daukar mata kayanta.." cikin sanyin murya tace"karki damu sis, ki kulamin da kanki, sai Allah yakaimu" "Kema haka.." bayan sunyi sallama, ta koma kan kujerar gaban study desk dinta ta zauna, table Lamp ta kunna nan take haske mai kyalkyali ya gauraye gurin. Lumshe idanunta tayi tana shakar kamshin dake fita daga jikin ta. Duk yadda taso ta hana zuciyarta kawo mata tunanin shi saida ta gagara.. Kalamansa ne suka soma dawo mata a cikin tunaninta.. _Unaisah my desire for you burns fiercely, taking your virginity has become my utmost dream, For what feels like an eternity, I've been tormented by my longing for you, I've concealed it for your sake, but my craving for you only intensifies_ _I'm patient, Unaisah, not wanting to rush or harm you, I yearn to make love to you with your trust, your consent, I don't mean to pressure you, I simply can't wait to be with you_ _When I return, grant me my heart's desire, Unaisah And let's create a memory that will last a lifetime..."_ siraran hawaye ne suka soma gangarowa ta cikin idanunta dake a rufe kaitsaye suke dira saman kuncin ta.. Cikin rawar murya ta furta"meyasa tun lokacin da kana araye bangane yadda kake azabtuwa da son kasancewa dani ba? bani da hankali Danish, ni sakarya ce"! "Abun da kake ji nima inajin shi Danish, inama ana iya dawo da wanda ya mutu? Da ba abunda zai hana in dawo dakai don in cika mana burin mu.." da sauri ta toshe bakinta, gudun kada shesshekar kukanta ya farkar da masu yin bacci a ɗakin.. "Allah ya jaddada rahamarsa a gare ka my Man" _ta saba yi mashi addu'a duk da bata da tabbacin koya musulunta before ya mutu_ "ina fata nima Allah ya dauki raina saboda na kosa ayi tashin alkiyama kona sa ke ganinka" Tana kuka ta fada. (Unaisah da wauta) kamar mai tabin hankali ta dinga sambatu ita kadai, taki tashi taje ta kwanta, duk daren Allah Haka take fama. Unexpected kira ya shigo wayar ta, duba sunan me kira tayi ganin Angon nata ne yasa tayi picking call din tare da kara wayar a kunne.. Sexy Voice dinsa ce ta ratsa kunnanta"me kike yi har yanzu baki yi bacci ba"? Lumshe idanunta tayi slowly tana ji kamar Danish ne ke yi mata magana.. "Tunaninka nakeyi..." "Nima na kasa runtsawa saboda tunaninki, saura kwanaki kadan suka rage, i can't wait to see you on my bed" kunya ce ta kamata har takasa furta kalma, ta rasa ya akai take jin muryarshi sak irin ta Danish ko dan ta sama ranta shi ? Mayar da kiran yayi Video call ga mamakinta sai taga duhu a screen din.. "Tabarakallahu Ahsanul khalikin, dagaske kece kika koma haka? kyawunki ya razana ni Unaisah" "Why i can't see you honey, duhu screen din"! "Dagangan na toshe camera din, baki tuna wani abu ba?..." ya tambaya. tuntsirewa tayi da dariya tunawa da wannan ranar da bazata taba mantawa ba.. "Oh kaima ka kira ne don ka gaisa da mutanan duniya, shekararka nawa? Ina mai wayar?.. Ta fada da zolaya.. Sautin dariyar shi tajiyo ta cikin wayar. Murmushi tayi tana jin wani irin nishadi da kwanciyar hankali na ratsa ta.. "Unaisah, Ina fata babu namijin da ke kalle min ke? In ba haka ba Kishi zai iya kashe ni" dariya tayi har fararen hakoranta suka bayyana kamar gonar auduka tar da su. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta soma jin yana saukewa mai haɗe da fitar numfashin sa.. aruɗe ta furta"hubby? Kana lafiya kuwa? Naji voice dinka ya sauya. "Ke kika jefani a halin da nake ciki Unaisah, kallonki da nakeyi a yanzu ba karamin fusgana kike ba.." gabanta ne ya faɗi ta manta rigar bacci ce a jikinta time din daya kira picking kawai tayi ba tare data rufe jikinta ba, a rude ta soma dudduba jikinta duk fa yana kallonta da alama ta manta. Mikewa tayi daga kan kujerar ta je ta dauko throw pillow da duvet, ta dauki wayar ta koma kan couch ta kwanta tare da rufe rabin jikinta da bargon, ta rungume pillown a kirjin ta. Saida ta daidaita nutsuwarta tukunna ta saita fuskarta akan screen din wayar.. "Hello! Husband to be kana ji na"? Shiru taji bai tanka mata ba.. Tayi zaton matsalar network ne, batasan duk wani motsinta akan idanunsa. Har ta fidda rai da sake jin muryar shi taji yace"Ina ma ace nine kika rungume kamar yadda kika rungume pillow din hannunki.." runtse idanunta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa, sometimes idan yana furta mata kalaman soyayya har tunani takeyi ina matarsa Nazli sarauniyar kyau? Ko itama yanayi mata irin haka? Ko da yake ita da take agida ai already tafi ta jin ire iren daɗaɗan kalamansa. "Am sorry idan baki ji dadin maganata ba, bazan iya jurewa bane Unaisah, ni kadai nasan halin da nake shiga idan ina sauraron muryarki, kona kalli fuskarki shiyasa na haramtawa kaina ganinki har sai bayan an shafa fatihar auranmu, a lokacin dana tabbatawar kaina kin zama mallakina halak malak..." nema ya ke ya kasheta da daɗaɗan kalamansa gashi yanzu baya kunyar gaya mata irin wadan nan kalaman, gaba daya ya haifar mata da jin kasala a jikin ta.. Cusa kanta tayi cikin pillow duk wani abu da ya ke ji itama tana jin shi sosai.. Cikin harshen turanci ya daura da cewa "A wannan lokacinne zan bayyana maki irin kaunar da nake maki kamar raina, zan gatantaki Unaisah, zan baki dukkan kulawata da soyayyata, zan mantar dake duk wani bakin ciki da kika taba dandana a cikin zuciyarki, zaki zama sarauniya a masarautar gidana, zan zama hadiminki me yi maki hidima, zan kuma zama sojanki mai baki kariya, in kuma zama likitan da zai dinga ceto rayuwarki a kowani hali na ciwo, na maki alkawari a dare ɗaya zan canza maki rayuwa.." bitting lower lip din ta tashiga yi tsigar jikinta na ɗan tashi Cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, bacci nake ji, sai Allah yakaimu, ka kulamin da kanka.." tana karashe maganar bata jira amsarshi ba tayi rejecting call din. Fashewa tayi da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, gaba daya ya tuna mata yanayin da su ke shiga ita da Danish idan suna a tare, daƙyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ita. 💥💫 Allah yayi dare gari ya waye, Da sassafe Amarya da ƙawayen suka farka daga bacci kowaccen su ta shiga toilet tayo wanka, suka shirya kan su cikin abaya, Already an tanadar masu abinci mai rai da lafiya na breakfast din su a dining area.. Bayan da suka zauna yin beakfast, kowa Ya ci ya koshi, In ka cire Unaisah data kasa ci dayawa, kalaman chief owais ne keta dawo mata a cikin tunaninta, duk ta rasa sukununta, da tunanin shi ta farka daga bacci, batason ganin komai in ba shi ba, gashi ya haramtawa kanshi zuwa zance har sai bayan an shafa fatihar auransu. Around Ƙarfe shabiyu na rana, Benazir ta kira Unaisah awaya ta ce tana son ganinta tare da ƙawayenta, su hadu a part din Danejo... Bayan ta sanar da su, gaba ɗaya suka dunguma izuwa Sashen Aunty Danejo, suna shiga main falo suka fara hango haɗaɗɗun Invitation bags a saman rug, daga jikin kowace jaka an rubuta will you be my Bridemaid? tare da sunan mamallakin jakar. Nan take suka gane nasu ne za'a basu, farin Ciki Ya cika su kamar su zuba ruwa kasa su sha. Anan suka taras da Benazir da Ummi tare da Danejo, with respect suka gaishe da su, Unaisah ta zagaya ta bangaren mommynta tayi hugging din ta bayan sun gaisa tayi hugging din Danejo dake ta sakar mata murmushi. Batool tuni ta yi gurin mommynta, su kayi hugging din juna. Bayan sun gama gaggaisawa da ƴan matan amarya.. Benazir tace"gaba daya munayi maku barka da zuwa, jiya bamu samu zama ba, shirye shiryen biki ya hana mu leko gurin ku, shiyasa bamu samu zuwa munyi maku barka da zuwa ba, amma kuna aranmu, munji dadin zuwan ku..." Ummi ta ɗaura da cewa"muna fata kunyi bacci lafiya kun tashi lafiya, Ya kuma gajiyar zaman ƙun shi" atare suka hada baki gurin furta"Alhamdulillah, Mun tashi lafiya, muma munyi farin ciki da kuka gayyace mu, kuma in sha Allah da mu za'a kare bikin nan" murmushi suka saki gaba dayansu sunji dadin maganar su. Danejo tace"wadannan invitation bags din da kuka gani, musamman saboda ku ango ya bada akayi maku daga Company, ba wai iya jakar bace, hada kyaututtuka na musamman a cikin su, Kun shirya gani?.." Ihun Farin Ciki suka sanya tare da shewa Yeehhhhhh.. Ummi tace"yawwa my ladies, ku jera layi, duk wadda muka kira sunanta sai tazo ta kar6i nata" cikin sauri suka shiga layi suka yi shiru cike da zakuwa suke jira abasu don su ga menene a ciki.. Ummi da Danejo ne ke daukar bags din idan suka duba sukaga sunan dake a jiki sai su kira su ba mai ita.. "Sadeeja, Zeenatu, kuzo ku kar6i naku" Benazir ce ta kira sunansu atare. Bayan da sukazo ta damka masu bags din a hannayensu kafin ta manna masu peck a forehead dinsu"yan matana, Allah ya nuna min naku da raina da lafiyata..." ta fada tana shafa kafadarsu cike da jin dadi suka amsa da ameen Aunty tare dayi mata godiya. "Deejatun harisu! Azeeza matsoraciya, naja'at Sojanya foodie Rai ba aburi, kuzo ku kar6i naku.." Unaisah ce ta kira sunayensu tana jin dadin tsokanar su, gaba daya mutanan dake falon suka tuntsire da dariya jin sunayen data kirasu, Benazir sai kallonta takeyi kamar zata hadiyar yar tata, wani irin alfahari ta ke yi da ita. Bayan ta mimmika masu bags din su, ta ɗaga murya ta furta"UKHTY will You be My babbar kawar amarya? Ta fada tare da daga jakar dake a hannunta sama mai dauke da sunan Batool. Farin cikine Ya lullu6e Batool da sauri ta nufeta suka rungume juna. kallon juna Ummi da Benazir su kayi wani dadine ya lullu6esu ganin yadda ya'yan nasu suka hada kansu, suma sun zama aminnan juna kamar dai su ɗin. Bayan Sun gama rarraba masu jakunkunan, tun anan wasu suka fara budewa suna duba kayan dake a ciki.. A hankali Batool ta zaro outfit din da ke a ciki, fitted gown ce dinkakkiya, ta code lace maroon da ashoke, asaman sofa ta daura kayan, ta fiddo invitation card mai ɗauke da event programmes, hada phone case with wedding logo harafin sunan amarya dana Ango ne a jiki O&U ga wani karamin kit, bayan data buɗe cikin shi, tissues ta gani tare da breath mints and pain relievers. Murtuke fuska tayi wani irin 6acin raine Ya turnuke zuciyarta, babu wanda ya lura da yanayinta sai Unaisah dake ta satar kallonta, aranta ta ayyana meke damun Batool? Kishi take dani? Ko bakin ciki takeyi! Ya Allah kasa zargina karya zamana gaskiya. Batool in wani abu kikeso ni me iya bar maki ce ta fada a ranta. Ƙawayen amarya sun rude da ganin zunzurutun kyaututtukan da aka basu, ango ya gama masu komai, sun fahimci Yana ji da su, sai santin kayayyakin sukeyi suna yabawa banda babbar kawar amarya. "Yeehh hohoho Wayyo Allahna Nima ga nawa kayan" Jemimah ce ta furta da karfi, gaba daya hankali ya dawo kanta, tana akan kujera ta zazzage kayan dake a cikin jakarta sai washe baki takeyi farin ciki Ya cika ta.. Ƙyalƙyacewa su ka yi da dariya suna kallon ta. "Amma ni abin daya ɗaure mun kai? Tayaya akai wadanda suka dinka mana kayan sukasan size din mu, ku dube ni ku gani? Nayi kyau"? Parveen ce tayi tambayar yayin da take nufo su daga wani daki ta fito, jikinta sanye da kayan data gwada. Sakin baki su ka yi suna kallon ta, Kayan sunyi mata kyau sunbi shape din jikin ta. Benazir tace"masha Allah, autar minister, you look gorgeous, nafi tunanin angone ya bada awonku may be yana da shi, Ko kar6a ya yi agurin parents din ku" har suna haɗa baki gurin yi masu godiya. Ummi tace"bamu yakamata ku godemawa ba, Unaisah da angonta.." sunnar da kai Kasa Unaisah tayi, gaba daya suka nufeta sunayi mata godiya"thank you sis, pls ki fadama hubbynki muna godiya, Allah ya kaimu lokacin da rai da Lafiya, Allah ya cika maku burinku" kasa kasa da murya take amsawa da ameen. Tana lura da Batool data haɗe rai, sai ci ka takeyi tana batsewa, kowa yana yi mata godiya ban da ita, ta rasa gane laifin me tayi mata ❓ "banga na yan uwanmu maza ba, Ko su banda su ne"? Deeja ce ta tambaya taji shiru ba abata na yayanta ba.. Benazir tace"hada su, amma nasu ba gurin mu aka kawo ba, ai su ta bangaren ango suke ko"? ta fada tare da ɗage mata gira.. Dariya Deeja tayi"nagode auntyn mu.." Cikin kwanakin da suka rage, bothside dangin ango da dangin amarya sun dage damtse suna ta shirye shiryen Bikin ya'yan na su, haka zalika Amarya da ango suma shiri su ke yi na musamman domin tarbar ranar auran su. *ANEELERH🌹🔥* Fitowa tayi daga Bedroom din ta dake a downstairs ta nufi main falo, sanye take da bubu gown ta material, tayi rolling mayafi akanta, Masha Allah ta zama babbar mace, fatarta tayi haske irin na wadanda hutu ya samu mazauni a jikin su, daga gani tana samun kulawa agidan mijin ta. A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar mijin nata "idan ina yi maka Assignment ka dinga maida hankali akan bayanin da nake yi maka, kana ji na ko"? Ɗagowa tayi a hankali ta ɗaura idanunta akan shi, Su biyu ne zaune kan rug, ya tasa baby junaid agaba yana yi masa Assignment da textbook dinsa, daga gefen sa Laptop dinsa ce da ya ke aiki da ita.. Baby Junaid an girma yanzu sai dai har yanzu bai daina shagwa6a ba saboda step father dinsa ya sangartashi da gatanci, idan kagansu a tare ba zaka ta6a cewa bashi ne ya haife shi ba, hatta kayan jikin su kala ɗaya ne. "Assalamu alaikum.. " sallamartace ta katse su, a tare suke dube ta, Murmushi ta sakar masu Junaid ya ambaci sunanta Mommy "Na'am daddys Boy..." ta fada tare da kallon Zaki dake bin ta da kallon kauna. "Sannu da kokori honey, Halan shine ya hana ka yin aiki, kullum baya gajiya da kawo maka assignment, har cewa nayi ya dinga bani inayi masa amma yafi son wahalar min da kai" ta karashe maganar tana zama daga gefen shi. murmushin gefen fuska yayi mata"ai ni nace ya dinga kawo min inayi masa, saboda banaso ya takura min ke" Taji dadin maganarsa "kana ji da mommyn babynka, yanzu dai ya maganar zuwa gidan biki, please ka barni inje, gaba daya satin nan ban leka ma su ba, nasan me kake mawa, wlh zan kula maka da kaina.." ta faɗa tana marairaice masa fuska. "Ki fahimce ni wifey, bawai banso ki motsa jikin ki bane No, fita ayanzu bazaiyiwu gare ki ba, tayaya zakije gidan biki kina fama da laulayin ciki"? zumbura masa baki tayi. Hankalin baby junaid ba akansu yake ba, ya mayar da idanunsa akan plasma tv yana kallon cartoon. "Ai na daina laulayin, Jikin da sauƙi yanzu... " bata kare magabar ba, taji tashin zuciya, nan take ta soma yunƙurin amai kafin tayi wani yunƙuri aman ya kubce mata kaitsaye ta kwarara shi asaman lap dinsa, zare idanu tayi tana faman jan numfashi, babu alamun yaji kyankyami ko haushin ta sai ma murmushin daya sakar mata"kinji sauƙi ko? Kuma kin daina laulayi"? Ya faɗa da zolaya, cike da jin kunyarshi ta sunnar da kanta ƙasa. "A haka zakije gidan biki, kina yi masu amai, su kansu zasuji ba dadi" idanunta ne suka ciko da kwalla"na hakura da zuwa, amma pls ranar biki, kabarni inje" Jinjina kai ya yi"In sha Allah zan barki kije, yanzu tashi muje toilet ki wanke min wandona da kika 6ata da amai" atare suka mike, tare da barin falon, kwata kwata Junaid bai lura sun fita ba, "Junaid... " muryar khadija mai aikin su ce ta katse shi, dagowa yayi tare da dubanta yayin da take nufo shi "Aunty Khady, yunwa nake ji, har yanzu baki gama mana girkin bane"? Ya fada yana yamutsa mata fuska. Murmushi tayi sai naga tayi min kamanceceniya da tsohuwar mai aikin Anila. "kwantar da hankalin ka, na kammala shirya mana Dinner, Ina aunty Aneelerh da daddyn naka ne"? adan rude ya juya yana duban gurin da suke ganin babu su yasa shi cewa"nan suke zaune fa, ƙila sun shiga ɗaki" "Okay, kaje ka faɗa masu dinner is ready amma ka fara knocking room door din kafin ka shiga kamar yadda na koya maka" Amsawa yayi da toh ya mike da sauri ya nufi bedroom din mommynsa.. Shin wacece Khadija mai aikin Anila? ko zaku iya tunawa da Yan uwan mariganya Aisha wadda kuka fi sani da (ANA) 🥺? _Janet da Esther, wadanda bayan da suka musulunta Ana ta sauya masu suna, Janet khadija, Esther (Zainab) tun lokacin da al'amarin Mutuwar Ana Ya fasu sunji tashin hankali da bakin cikin abin daya faru da yar uwarsu a lokacin da labarin ya risƙe su, wanda silar hakan yasa gaba dayansu suka kamu da depression har jinya sukayi gadon asibiti, sunji mutuwar Aisha, saboda suna son ta fiye da komai, tamkar uwa take a gare su, da ya ke Anila tasan basu da kowa a arewa kuma marayu ne tasan idan suka koma ƙauyensu na kudu a matsayin musulmai danginsu ba zasu kar6e su ba, wannan dalilinne yasa ta kai kukan ta gurin abie a lokacin da sukazo cikin mawuyacin hali, ta rokesa akan ya taimaka ya bar su su cigaba da zama tare da su, abie yace ko bata fada ba shima bazai bari su koma ba, zai ruke su a hannun shi, kuma zai dauki nauyin komai na rayuwarsu, tun daga lokacin zainab da Khadija suka kasance karkashin kulawar Abie da iyalin sa, a yanzu haka Zainab tana zaune agidan abie yayin da khadija ta ke aiki agidan Anila, Yanzu haka sun kusa yin aure har an sanya bikin auran su_ ~_______________________ 💓💞~ *THE DAY BEFORE WEDDING DAY🔥* Tana a kwance cikin bathtube wanda ke a cike da ruwan ɗumi daidai kirjinta ruwan ya tsaya ta kishingide kanta, idanunta suna a lumshe tayi zurfi a cikin tunanin ta. "burina zai cika na ganin nayi aure sai dai farin cikina ragagge ne..." Bata ƙare zancen zucin nata ba, tajiyo sautin ƙwanƙwasa kofa daga waje, Kwan! Kwan!! "Unaisah! My baby Girl! Kina ina! Daddynki Ya dawo, Yana son ganin ki" Benazir ce ke kwaɗa mata kira.. waro idanu tayi cike da farin ciki ta yi saurin ɗauraye jikinta da ruwa, ta fito daga kwamin ta warci towel dake rataye jikin hanger ta yi daurin gaba da shi. Sai rawar jiki ta ke yi jin daddynta ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa joss, shigowa bedroom dinta ta yi adaidai lokacin Benazir ta shigo dakin. Unfortunately, garin rawar jiki, sul6i ya kwashi kafar Unaisah gaba daya ta tafi zata kifa, a gigice Benazir ta nufeta kafin ta karasa tuni ta kife ƙasa nan take daurin towel din da tayi ya warware ya dawo kan qugunta sumar kanta ta baje kasa. "Subhanallah, daughter, tashi baki ji ciwo ba! " kasa amsa mata tayi saboda zafin dataji sakamakon dakar tiles da kirjinta yayi. Cikin sauri Benazir ta nufe ta, tana kokarin kai hannu don ta miƙar da ita, kwatsam ba zato ba tsammani ta yi arba da waist tattoo dinta ya zanu raɗau. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Ta faɗa da tashin hankali tsantsa akan fuskarta. sallallamin da tayine yasa Unaisah ta tattara sauran karfin daya rage mata a jikinta tayi saurin miƙewa tare da jan towel din ta daure kirjinta. Ta yi zaton faɗuwar da ta yi ne yasa Benazir ta ɗaga hankalinta hakan yasa tayi saurin furta"mommy, banji ciwo ba, lafiyana lou," daura hannu biyu Benazir tayi asaman kanta tana fadin"nashiga Uku! Unaisah Uban wa ya zana maki tattoo a waist din ki! Yaushe akai! A ina"? gabanta ne ya faɗi aruɗe ta zabura ta mike Tsaye jikinta ya kama kerma kamar mazari duk tabi tasha jinin jikinta.. "Bakiji ina magana bane? Uban wa ya zana maki tattoo? Da yaushe akayi maki shi ." ta faɗa rai a6ace ta fusgota ta juyar da ita tare da tum6uke towel din ta ƙura idanunta akan tattoo din, zanan giant snake ne nannaɗe da sunan Garkuwa da wani irin salo akayi tattoo din launin black and red ya yi bala'en yin kyau a fatarta. Unaisah duk tabi ta rude tsabar kaɗuwa cikin sauri ta mayar da towel din da benazir ta cire mata ta mayar kan kirjinta ta daure shi. "banza shashasha!, kina a cikin hayyacin ki kuwa? Ba zaki amsa min tambayana ba? Sunan uban waye garkuwan? Ta fada kamar zata rufeta da bugu, ta tsorata sosai, bata ta6a ganin mommynta cikin fushi irin na yau ba. Cikin rawar murya ta furta"nick..nick.. Nickname dinsa ne"_ "Shi ubanwa"! Ta katse ta da tsawa. "Dad.. danish..." zare idanu Benazir tayi"na shiga Uku Unaisah, baki da hankaline? tayaya zaki yi zanan tattoo da sunan wani kato a waist din ki, Kin manta gobe za'a daura maki aure? Wani irin abun kunyane kikeso kija mana Unaisah? Idan mijinki yaga wannan me kike tunanin zai biyo baya..." ta faɗa idanunta cike tab da kwalla, ji ta ke kamar ta kikkifa mata mari kota huce takaicin da ta ke ji. Cikin shakakkar murya ta furta"ki yi hakuri mommy, nayi kuskure.. " "Sorry for your self Unaisah, wlh ba zaki kwana da tattoo din nan a jikin ki ba ! Wai meke damunki ne? Bayan kinsan haramunne yin tattoo a jiki? Ina hankalinki ne? Girgiza kai tayi batare data iya furta kalma ba.. "dole ki goge shi a yau din nan kafin gobe, ki rasa sunan wa zakisa sai sunan matacce mutumin da babu shi araye, Ina laifin ma sunan wanda zaki aura"! Ta faɗa cikin bacin rai... Zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta masu dumi In a weak voice ta furta"bazai gogu ba, in har ba fatar jikina za'a gurje ba.." "Kina nufin permanent tattoo ne"? Girgiza kai tayi"temporary tottoo ne, amma zai dauki lokaci kafin ya goge" "Hmmm, nasan maganinki, Idan na faɗa ma dadynki, kin yi bayani kuma Allah ba zaki kwana da shi ba, lalle zansa in dame shi, wallahi kin ban kunya, har kika iya zuwa wani ƙato ya zana maki tattoo a waist ɗinki don hauka" tana fada ta juya zata fuce, da gudu tabi bayanta tayi saurin shan gabanta tana kuka tace'dan Allah ki rufa min asiri kada daddy yaji, wlh ransa zai baci, zai yi fushi dani, bana so na rabu daku kuna fushi dani, zan iya samun matsala agidan aurena.." ta fada tana jan magina, hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta. "nayi danasani mommy banyi zaton zai zamarmin matsala ba sai da kika ankarar dani, ki yarda dani wallahi ba namiji ya zana min shi ba, babu wanda yaga tsiraici na, tsautsayi ne yasa naje akayi min a tattoo studio kuma artist din da tayi min macace, wallahi bata ga jikina ba, iya fatar gurin da tayi zanan tagani kadai ban kware jikina ba, kuma wallahi a private room dinsu ne babu wanda ya gani"! cikin shesshekar kuka ta faɗa. "Mommy ki taimaka min mu nemi mafita kafin gobe..." kalaman Unaisah sun karya mata zuciya, wani irin tausayinta ne ya kamata. "Unaisah meyasa kika yi tattoo da sunan garkuwa"? Ta kuma tambayarta! "Zan fada maki amma kada ki fadamawa kowa, ki rufa min asiri, nasan zakiji haushina watakilma kiyi min kallon mara hankali amma wlh ba haka bane, soyayyarshi jarabtace daga Allah, in ba haka ba tayaya zuciyata zata dinga azabtar dani da son matacce? Ba irin addu'ar da banyi ba akan Allah ya yaye min son shi, ya mantar dani tunaninsa amma har yanzu babu abun daya sauya mommy..." kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata. Da sauri Benazir ta rungumota a jikinta, taja ta suka zauna kan couch, ta ƙanƙamate cike da tausayin ta, take jin kukanta a cikin kunnanta. "Meyasa baki fadamin ba tuntuni? tayaya zaki zauna da damuwa aranki baki sanar dani ba? Kina da tamkatane Unaisah"? Cikin shesshekar kuka tace"saboda inajin tsoron abun da zai biyo baya, kuma banaso daddy yaji, saboda tunkafin rabuwa na da Danish ya nuna baya sona da shi, yaya owais ne zabinshi, shiyasa nake kokarin inga na cika mashi burin shi amma abun yaci tura.. " "La'haula wala'quwata Illah billah" ta fada tana shafa sumar kanta, batasan ya zatayi da ita ba! ta razana da jin abun da ke damunta, al'amarine mai girman gaske son wanda baya araye. "akwai wanda ya san da maganar nan"? "Batool kaɗai na taba fadamawa" "Kashh,! baki kyautamun ba Unaisah, Idan matsala ta same ki irin wannan ni ya kama ta, ki fara sanarmawa, ni na haifeki, ni nasan ciwon kanki, duk duniya babu wanda zai fahimceki kamar yadda ni zan fahimce ki, zanfi kowa rufa maki asiri"! "Nagane kuskurena mommy, zan dinga fada maki..." hankalin Benazir ya tashi sosai jin yadda jikinta yaɗau zafi, ko a tarihi bata taba jin soyayya makamanciyar wannan ba, tayaya wanda ke araye zai dinga dakon soyayyar mamaci? Lamarin akwai ɗaure kai duk da ba abin mamaki bane tunawa da halin data ta6a shiga lokacin da taji abun da ya faru da taj kusan hauka ta yi ita. "Kina kallon hotunansa ne ko akwai wani abu dake tuna maki da shi"? "Babu, saboda azabtuwar da nakeyi yasa na goge komai nashi daga kan wayata, Amma na kasa goge momeries dinshi dake a cikin brain dina, mommy, in zai yiwu, ki kaini asibiti su goge min memory dinshi ta yadda zan manta da komai nashi, Idan ba haka ba bazan iya zaman aure da waninsa ba, zanjama kaina zunubi ne.." Ta razana da jin abun da tace, aruɗe take kallon fuskarta da ta 6aci da hawayen ta, cheeks dinta sunyi jawur.. Benazir ta rasa ya zatayi da ita? Da me zata iya taimaka mata?lamarin yafi karfin tunaninta, bata taba ganin hoton Danish ba amma daga labarin da Unaisah ta taba bata na irin rayuwar da sukayi a tare yasa taji inama ace har yanzu yana araye, saboda taji dadin kyautatawar da yayima Unaisah... " Numfasawa tayi a hankali ta ce "Unaisah, na tausaya maki, i feel your pain, wlh da inada halin da zan iya cire maki son shi daga cikin zuciyarki da nayi, sai dai bazan iya ba, sannan bazaiyiwu muje asibiti don acire maki tunaninsa ba, kinsan bame yiyuwa bane amma tun da har kin fahimce son shi jarabtarkice to kiyi hakuri Unaisah kiyi hakuri, ki cinye jarabawarnan da hakuri da addu'a." Nasiha mai ratsa zuciya Benazir tayi mata sosai har saida taji tayi shiru ta daina shesshekar kuka, tukunna ta samu kwanciyar hankali.. "Zan tayaki da addu'a Allah ya yaye maki abunda ke damunki Unaisah.." "Ameen mommy, nagode da kulawarki a gare ni.." bata kare maganarba, Muryar Taj ta katse su"Ummu Unaisah naji shiru bata fito ba? Ko bacci takeyi ne"? Daga murya tayi"a'a na iske ta ta shiga wanke ne, Yanzu zamu fito.." "Tashi ki shirya, pls kada ki bari ya gane akwai abunda ke damunki kafin nasan yadda zamuyi da tattoo din nan" in a cool voice ta amsa da toh, dakyar ta miƙe ta nufi wardrobe dinta, ta dauko kaya ta sanya. Lokacin da suka sauko down a saman Sofa suka iske taj yana kallo a plasma tv Ya daura kafarsa daya kan daya. Takun tafiyarsu ne yaja hankalin shi ga kallon su, murmushi yayi tare da mika mata hannu. Da sauri ta nufeshi ta kwantar da kanta saman kafadarshi"sannu da dawowa daddy, nayi missing dinka, ya gajiyar tafiya ya ka baro uncle Muhsin din? Ina fata ya samu lafiya"? "Alhamdulillah My Angel, nayi missing naki nima, Muhsin yana gaishe da ku, jikinshi da sauƙi fatan na same ku lafiya, Ya shirye shiryen biki" cike da jin kunyarshi tace"Alhamdulillah." Kallonta yayi da kyau"masha Allah daughter, umminta me kike batane naga ta sauya min tayi kyau kamar lu'u lu'u ..." Dariya Benazir tayi"Sirrin mune na mata, kaima lokacin da zaka aure ni ba haka ka rude ba duk ka susuce da ganin yadda nayi kyau..." bata ƙare maganar ba ya galla mata harara afakaice kasa kasa da murya yace"meye haka pls"? Yar dariya tayi"me kuma ya rage Tajo, ai daga gobe ta wuce Unaisah zatasan komai.." ta fada tana ɗage masa gira. throw pillow ya janyo Ya wurga mata tayi saurin cabe shi a hannun ta "babu wani boye boye Tajo, daga gobe ne" "Ummu unaisah ki daina! Aa wai meke damunki ne"! Bushewa tayi da dariya, Unaisah data langwa6e kanta saman kafadar shi tayi shiru tana sauraron su. "Wai ya maganar sadakinta ne? Ko yayi tunanin kyauta zamu bashi ita ne? Naji shiru tun satin da aka sanya bikin naketa jira inji ance ga sadakin Unaisah amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa" "Mun yafe masu sadaki, salatin annabi za'ayi don auren yayi albarka ko Unaisahna" ya faɗa tare da leken fuskarta. murmushi tayi tare da jinjina mashi kai. "Hmm Yanzu mutun yayi magana ace ya yi sa6o, ko ya kafurta amma taj meya kawo wannan maganar? In albarkar aure akeso nima in na saka mata ya wadatar ko" Ƙyalƙyacewa su ka yi da dariya gaba ɗayan su cike da nishadi su ke yin firar su.. *AGIDAN DR SHUREIM🔥* A hankali Motar shi ta kunna kai cikin harabar gidansa, a tsanake ya ke yin driving yana bin karatun alqur'anin da ya kunna.. Bayan yayi Parking din motar ya kasheta, A hankali ya fito as usual sanye da arab dress dinsa.. Fitowa Ummi tayi daga cikin gidan, ta nufe shi da sauri tana karasowa sukayi hugging din juna kamar sun shekara basu hadu ba.. Dagowa tayi ta sumbaci kuncin shi"Welcome back habibina, ya kake ya aiki? Ina fata kana lafiya? Ta faɗa tare da kar6e jakar hannunsa.. Fuskarsa dauke da murmushi yace"mar'atussaliha, Alhamdulillah Ina lafiya, fatan na same ki lafiya.." "Lafiyalou" Ruƙo hannunsa tayi a cikin nata"mu shiga daga ciki.." A bedroom dinsa suka tsaya ta taimaka mashi ya rage kayan jikin shi. "His excellency, wanka ko abinci wanne kafi bukata in taimaka maka da shi .." ta tambaya tana kallonsa yayin da ya ke a zaune gefen gadon sa. "Ke" ya bata amsa a takaice Kayataccen murmushi tasakar ma shi" ta matsa kusa da shi bai aune ba yaji ta fara kissing nashi sai da tabari ya fara hawa kan network tayi saurin raba jikinta daga na shi. "Nasan akwai gajiya a tare dakai da kuma yunwa, bari na kawo maka abinci..." wani marayan kallo ya bita da shi yana hadiyar yawu. Kashe mashi ido daya tayi ta juya yabi bayanta da kallo mai cike da shauki, har saida ta bace ma kallonshi tukunna ya jingine kansa jikin pillow, yana mai kara godewa Allah daya mallaka masa ummi amatsayin matarsa, dadinta yakeji fiye da komai na duniyar nan, idan yana atare da ita mantawa ya ke yi da komai. Har ta shigo bai dawo daga duniyar tunanin da yake yi ba, a saman table ta daura tray din hannunta mai dauke da lunch dinsa. "Mijin so, am back, ka tashi in ciyar dakai girkina" murmushi yayi tare da mikewa ta janyo table din agabansa. Yana niyar bude baki yayi magana tayi saurin daukar glass na juice ta kafa mashi abaki ya dan kur6a yana jinjina kanshi alamar yayi dadi. Abaki ta dinga bashi abincin yana ci. "Ina Batool ne? Batasan na dawo bane? Ko ta tafi gidan Bikin ne"? Girgiza kai tayi"a'a bataje ko'ina ba, may be tana a bedroom din ta" "Taci abinci? "Nayi nayi da ita tace min bata jin yunwa, dana matsa mata sai tace min da anjima idan ta shiga gurin Unaisah zasuci a atare" Shiru ya danyi jimm kafin yace"kira min ita" "Okay Sir" aje spoon din tayi ta juya tana tafiya da rangwaɗa dagangan take yi don ta rikita shi. Murmushi yayi tare da dan girgiza kan shi.. A cikin kunnanta ta tsinkayi shesshekar kukan Batool, wani irin faduwar gaba taji, da karfi ta shiga bubbuga kofar dakin ta"babe! Babe! Me kike ma kuka ne? Zo ki bude mun kofa! Shiru taji ta daina kukan kuma babu alamun zata bude kofar. "Babe! Kina jina kika shareni? Ba zaki bude min kofa ba"? ta fada da damuwa akan fuskarta. Dakyar ta samu batool ta buɗe mata kofar dakin, bin ta da kallo tayi, idanunta sunyi jawur sun kumbura, Cheeks dinta sunyi jajir alamar tasha kuka, sumar kanta duk ta hargitse Hankalin ummi idan yai dubu to ya tashi. Dafa kafadunta tayi"meke damunki? Baki da lafiya ne? Waya ta6a min ke? Meyasa ki kuka.."? Duk tabi ta rude.. Cikin sanyin murya batool tace"babu komai, bana jin dadi jikina ne" girgiza kai ummi tayi"ban yarda ba batool, dole akwai abunda ke damunki, Mu shiga ciki ki fada min.." ta fada tare da jan hannunta suka shiga ciki ta zaunar da ita gefen gadon itama ta zauna. "Kada ki boyemin Batool dina, ki fadamin abun da ke damunki zan taimaka maki mu nemi mafita"! Kasa sanar da ita tayi saboda tana fargaban yadda zata dauki abun idan taji. Amma ya zatayi bata da mafita.. lallashin ta ummi ta soma yi tana lalla6ata don ta faɗa mata. Har saida taji zata iya sanar da ita. "Ummina, bana son kayan da aka raba mana na yan matan amarya, ni bazan sanyasu ba, nafison kalar rigar da Unaisah zata sanya a ranar bikin ta.. " kasa karasa maganar tayi ganin yadda Ummi ta saki baki sototo alamar mamaki ya kamata.. "Nasan zaki fahimce ni shiyasa na fada maki, wallahi in har ban samu kalar rigar Unaisah ba, ba zanje gidan bikin ba ranar auran ta.." ruɗune tsantsa akan fuskar Ummi"batool kinsan me kike fada kuwa? Dagaske kike ko wasa kike min" fuskarta babu annuri tace"wallahi dagaske nake maki, dan Allah ki siyamin kalar rigarta komai da komai" "Batool zan iya yi maki komai a dunyar nan indai baifi karfina ba, amma in banda abunki tayaya zaki ce irin bridal gown din Unaisah ki ke so? Batool tafi karfin mu, bamu da kudin da zamu iya siya maki ita, har yau ni banma ga rigar ido da ido ba, a hoto Benazir ta nuna min ita, ba'a kaiga kawota gidan ba! Sai zuwa gobe" kwata kwata Batool bata fahimtar bayanin ta"ummina ba za ku iya siya min irin ta ba? Shikenan ni bazan iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba? Idanunta cike tab da kwalla ta karashe maganar, arude ummi ke dubanta cike da fargaban kada abunda take kokwanto ya tabbata akan ta. "Ki fahimce ni Batool, bamu da halin da zamu iya siya maki ita!tafi karfin arzikin mu, kuma babu yadda za'ai ki sanya kalar rigar Unaisah aranar auranta, zakija mana surutu tun da ba auranki akeyi ba" "amma ki canza wata rigar mai saukin kuɗi in sha Allah zamu siya maki, amma dan Allah kidaina fadin ba zaki iya mallakar komai da Unaisah ta samu ba, kema zaki iya samun fiye da shi amma kinga wannan bridal gown din da kike magana akai ba iyayen ta bane suka siya mata ba, Mijin da zata aurane ya siya mata..." bata kare maganar ba, taga ta zabura ta mike tsaye jikinta ya hau yin kerma cikin muryar fushi mai tattare da bacin rai tace"zanje na fadawa Abbana, nasan zai siya min irin ta.." fucewa tayi daga dakin. A rude Ummi tamike tabi bayanta gabanta naci gaba da faduwa ta rasa gane meke damun Batool ne? kamar ƙamar yarinya, Meyasa takeson irin rigar Unaisah? Maganganunta kamar suna nufin tana hassada da ita, wallah bata fata abun da take hasashe ya zamana gaskiya. Ko sallama ba tayi ba ta shigo dakin, abun da ba dabi'arta ba, motsinta yasa shureim dagowa ya dubeta, kwata kwata bai lura da moods din fuskarta ba. Zama tayi gefenshi ko gaishe da shi batayi ba cikin shesshekar kuka tace"Abbana dan Allah, dan sonka da annabi, ka siya min irin rigar Unaisah ta aure! Wallahi ita nakeso Abba" bai san sa'adda ya furzar da ruwan lemun daya kur6a abakinsa ba, da sauri Ya aje cup din kan table ya dubeta da idon basira. "Batool me ke damunki? Ba kiyi min sallama ba, ko gaishe ni bakiyi ba, ba sannu da dawowa kuma ki rasa da wani zance zaki tarbeni sai da wannan"? Ya fada fuskarsa a yamutse. Bata kaiga furta kalma ba, Ummu ta shigo dakin, anan ta fayyace masa komai.. "Haba Batool, wallah idan akan farin cikinki ne sai inda karfinmu ya kare, ba abunda ba zamu iyayi maki ba, amma ki gane rigar Unaisah tafi karfin mu, kuma in banda abunki ai babu me sanya irin rigar amarya ita nata dabanne, kuma ba an baku kyautar anko na kawayen amarya ba? kiyi hakuri ki sanya su mana.." bai kare maganarba, ta fashe masu da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta daga masu hankali, suka rasa shawo kanta, dr shureim daya rude yayi zaton iskane suka shigeta nan take ya fara yi mata rukiya Cikin shesshekar murya ta furta"abba da hankalina! Ni ce batool, babu wani aljani a jikina, Ku dainayi min ruƙiya kawai kuyi min abunda nakeso, ban taba tambayarku wani abu kun kasa yi min ba, meyasa ba zaku iya siya min kalar rigarta ba! Tayaya zan yarda kuna sona? Maganganunta sun daga hankulansu. Tsawa dr shureim Ya daka mata ganin taki ta saurare su "Ya isa haka Batool, na fahimci rashin wayau ke damunki, karki kuskura ki kara wata magana anan idan ba so kike ranki ya 6aci ba! Haba sai kace yarinyar goye? Kodan kinga muna lallashin ki shiyasa kike mana abunda kika ga dama? In banda rigima me zakiyi da rigar amarya? Ke za'ay ma aure ne? Ummi ce ta balbaleta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, Dr shureim sai kokarin dakatar da ita yakeyi saboda baisan 6acin ran batool dinsa. Miƙewa tayi fuskarta sharkaf da hawaye cikin fushi ta fuce daga dakin, suka biyota da sauri suna ambaton sunanta kafin su karaso tuni ta shige daki ta kulle kanta. Bubbuga kofar suka dinga yi suna lallashinta akan ta buɗe ma su ƙofa, tana ji tayi banza ta kyalesu, gaba daya tsoro sukeji kada ta lahanta kanta. Da suka gaji da buga kofar, a kan stairs suka zauna ransu duk ajagule. "Ina ma ace zan iya siya mata rigarnan wlh dana siya mata, saboda banason bacin ran batool, Idan tana kuka har cikin raina nake jin ɗaci, saboda tana tuna min lokacin da tana jinjira" hawayen da suka cika idanun shi suka soma kokarin saukowa kan kuncinsa da sauri ummi ta sharesu da yatsunta. "Pls, kada ka sanya damuwa aranka, ni kaina nayi fatan hakan amma ba zamu iyaba, dole sai mun danne son da muke mata mun koya mata hakuri da babu idan ba haka ba zamuci wahalarta agaba.." Gyaɗa kansa yayi"ni lamarin ma tsoro ya bani wlh, lokaci daya ta sauya dabi'unta irin na yara amma meyasa takeson dolin doliya sai irin rigar Unaisah"? Ya tambaya yana duban ummi. "Kasan wani abu, nifa ba tun yau ba, na lura da wani abu, Batool tana kwaikwayon komai na rayuwar Unaisah, na rasa gane gasa ta ke yi da itane? Kishi ne ko hassada.." bata kare maganarba ya katseta"bana tunanin haka, pls mu kyautata mata tazo" Ummi tace"dole fa sai munsan meke damunta tukunna zamu kamo bakin zaren, Batool fa saboda bedroom din Unaisah yana a upstairs yasa itama ta nace mana akan mu maida mata bedroom dinta up, sannan ta matsa mana akan mu maidata jami'a don tayi graduation tare da su Unaisah, ka lura da kyau yanzu haka zanan kunshin hannunsu iri ɗaya ne babu banbanci" Ta fada tana duban shi, abun duniya ya ishe shi. "Aisha, bansan ya zanyi ba! Wai menene dalilin dayasa take son komai irin na Unaisah ne? Ummi tace"nima abun da nakeso na sani kenan, dole akwai abunda take mawa.." gaba daya sun rasa mafita. Gashi ta kulla kanta adaki tun safe su ke ta kokarin shawo kanta amma abun yaci tura, ba ci ba sha, har marece ya yi Batool bata fito ba, ko magana batayi gaba daya ta daga hankulansu. Suna a zaune cikin falo kan sofas sun zagba tagumi, kwatsam sallamar Unaisah ta katse su cikin sauri suka dubi kofar falon, Shigowa tayi sanye da hijab ta ruke lunch box a hannunta. Tuni kamshinta ya cika hancinan su. "Unaisah.." "Na'am Aunty Ummi, Uncle shureim ya ku ke? Ina fata kun wuni lafiya.." murmushin yaƙe suka sakar mata"lafiyalou Unaisah, Ya shirye shiryen biki" "Alhamdulillah, munji shiru baku leko ba, Nima gurin yar uwata nazo duk yau banji duriyarta ba" walwalar fuskar su ce ta dauke duff, damuwar da suke boyewa ta bayyana akan fuskokinsu. "Ina Batool din? Ko tana daki"? Har suna hada baki gurin furta"tana aɗa.. Au bata nan ta tafi unguwa.." kallon juna su ka yi. Da ruɗu Unaisah take dubansu jin yadda suka bada amsa daban daban. "Aunty Ummi, meke faruwa ne? Ina Batool? Ko wani abu ya faru da itane"? Ƙwafa Ummi tayi"Unaisah, Batool tana a daki, amma bata jin dadi, bacci takeyi, ki bari zuwa anjima zamu leko gidan tare da ita.." girgiza kai tayi"i'm sorry Aunty Ummi bazan iya tafiya banganta ba, Inaji araina wani abu na faru badaidai ba, gaba dayanku da damuwa akan fuskokin ku, bayan haka tunda bikina ya matso Batool kullum tana a tare dani, amma yau ko kadan bata leko ni ba, tayaya hankalina zai kwanta? Dan Allah kubarni naga yar uwata.." ta fada tana kokarin wucewa ciki da sauri suka sha gabanta kamar mara sa gaskiya duk sunbi sun rude, kwata kwata basu san tasan meke faruwa saboda sunsan son da take ma yar uwata zata iyayi mata komai donta faranta mata rai su kuma basu san hakan ya faru zataja masu abun kunya ne. "Dan Allah Uncle shureim ku fada min meke faruwa? Kada ku boyemin abunda ke damun ku.. " idanunta cike tab da kwalla tayi maganar. Kallon juna su kayi, Ummi ta dinga girgiza mashi kai donta lura kamar so ya ke ya fada mata. "Unaisah, dan Allah kiyi hakuri ki koma gida, wallahi bamu son kiji abunda ke faruwa, ba zakiji dadi ba," Gyada kai tayi"tunda ba zaku fadamin ba, zanje na fadawa mommyna da daddyna, nasan su zaku iya fada musu..." juyawa tayi cikin sauri suka tarota. "Unaisah, abun kunyane, Mun rasa gane kan Batool, ta canza mana, rigima takeyi mana kamar karamar yarinya, saboda kawai tace mu siya mata irin gown din auranki munce mata bamu da halin da zamu siya mata shine ta kama fushi damu, taita kuka, tun safe ta kulle kanta adaki, baci ba sha, munyi munyi da ita akan ta bude mana kofar dakin ta ƙiya.." dr shureim ne yayi maganar. Ummi tace"dan Allah karki damu kanki Unaisah, in banda abun Batool ai abun amarya na dabanne babu mai yin irin shigarta.." Gabanta ne ya fadi, damuwa ta mamaye zuciyarta, dama sai da tayi fargaban hakan cos tun shekaran jiya da aka raba ma su Invitation bags ta lura Batool bata gode ba. "Dan Allah Unaisah kada ki fadama kowa, daga mu sai ke, yadda mukayi maganar anan mu binneta anan pls, wlh abun kunyane maganar nan ta fita, kema mun fada maki ne saboda ba mu da mafita" Cikin karyayyar murya tace"Batool bata kyautamin ba, kawai saboda tana son rigar aure na shine ta haramtawa kanta zuwa gurina, Ta kulle kanta adaki? ta tambaya cike da takaici. "Bana fata Allah ya nuna min ranar da Batool zata nemi wani abu agurina in gaza yi mata shi, tafi karfin komai wallahi, zan iya hakura da komai in bar mata" waro idanu waje sukayi cike da mamakin maganarta, juyawa tayi da sauri ta nufi up, suka bi bayanta da sauri. Knocking kofar tayi"Ukhty Batool Buɗe mun ƙofa, Nayi missing naki, Inason ganin ki" A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah daga waje, tana a zaune kan couch ta yi kuka har ta gaji, jikinta sai kerma ya ke yi saboda zazza6in daya kamata. taji dadin jin muryar Unaisah saboda tayi kewar ganinta, sai dai batajin zata iya hada ido da ita.. "Nasan kina jina Batool, Dan Allah ki bude min kofa kinji"? Magiya ta dinga yi mata, dakyar ta samu Batool ta buɗe mata kofa.. Kallo daya da Unaisah tayi mata sai da taji tausayinta ya kamata, daga gani ko wanka batayi ba, rigar jikinta ta yamitse kamar wadda aka kwato daga bakin kura. bataji dadin halin da batool ta jefa kanta ba saboda kawai tana son irin rigarta? Ruko hannunta tayi suka koma ciki, a saman gado suka zauna suna fuskantar Juna. Ummi da shureim suna daga waje suna sauraron su. "Meyasa bakizo gidanmu ba? Kin barni da tunanin wani hali kike a ciki ." ta faɗa tana dan jifarta da harara. Duk ta kame kanta, kamar wadda tayiwa sarki karya fadawa suka turketa. "Um.. Bana jin daɗine, amma kina araina.." "Meke damunkine Batool?Dubarki dan Allah, daga gani ko wanka bakiyi ba.." ta fada tana bude Lunch box din data kawo mata. "Ba abunda ke damuna.." "Okay Aunty Ummi ta fada min baki ci abinci ba, ga lunch na kawo maki, abincin da mommy tayi ma daddyne na debo maki" murmushi ta danyi fuskarta ba walwala. "Naji dadi ya dawo lafiya, da anjima zan shiga na gaida shi, bari na wanko bakina" "Kina nufin ko brush baki ba" daga mata kai tay, ta sauko ta shige toilet, ajiyar zuciya Unaisah ta sauke a ranta tana mai mamakin ta. Jim kaɗan ta fito ta dawo kan gadon ta zauna, Unaisah ta soma bata abaki tana ci.. Duk akan idon su Aisha, jikinsu yayi sanyi sosai.. Saida taci ta koshi tana ta santin abincin, daga bisani Unaisah ta karasa cinye sauran data rage.. Ta daura lunch box din gefe ɗaya. Ruko hannunta Unaisah tayi a cikin nata, idanunsu a cikin na juna.. "Bayan rigar aurena sai me kikeso nawa"? Gabantane Ya fadi wata irin kunya ce ta kamata adabarbarce ta furta"um..waw..waya fada maki? Ni bance ina son rigar auren ki ba, cewa kawai nayi kalarta nakeso ba taki ba. " murmushi Unaisah tayi"meye na daga hankali aciki? Tambayarki nayi kawai ki bani amsa, banaso gobe ki ga wani abu nawa a ƙurarren lokaci kice kinaso kwara ki fadamin tun yanzu in sani.." "Unaisah karki.." ummi data dauko maganar bata karasaba, Dr shureim Ya toshe mata baki"pls, kibarsu suyi magana atsakanin su"! Cike da takaici tayi shiru "Kada kiji komai Batool, tun da har kika nuna kina son gown dina, ni kuma na bar maki ita har abada, nama haramtawa kaina sanyata, koda zan rasa suturar da zan sanya ne aranar aurena.." "Wallahi bazai yiwuwa ba, Batool bazata sanya rigarki ba, sai dai ita kada taje bikin, kima daina wannan maganar bame yiwuwa bane.." cikin fushi ummi ta fada ranta ya baci "Shashasha Unaisah har tafiki hankali da wayou bayan ke yakamata kifita saboda kin girme ta da shekaru biyu amma saboda kawai ki kunyata mu a idon duniya shiyasa kika nace akan rigarta kikeso to wlh ba zaki sanyata ba..." balbaleta da fada tayi ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Dr shureim yace"ummu batool, ki bar su suyi magana atsakanin su please.." "Aunty Ummi, Uncle Shureim pls, ina neman alfarma agurinku, kada ku hanani kyautatama yar uwata, idan har ban bata rigar nan ba wani abu da ba'a fata ya faru zanyi danasani ne,.." bata ƙare maganar ba ummi ta katse ta"Unaisah, koda zata hadiyi zuciya ta mutune ba zata saka rigarki ba.." bata kare maganarba dr shureim yaja hannunta suka fuce daga dakin. Batool ta fashe da kuka tana fadin"unaisah banaso, bazan kar6a ba, ki tafi kawai ki bani guri, na tsani kaina, na bata ma iyayena rai, kowa haushina yake ji, bansan meke damuna ba, bansan meyasa nake jin haushin inga kin fini da wani abu ba.." tallabo fuskarta Unaisah tayi ta soma lallashinta dakyar ta samu ta shawo kanta. "Yanzu fada mun bayan rigar me kikeso? Karki wani damu da su ummu, ni nasan ta yadda zan shawo kansu... " ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kankance saboda kukan da ta sha. "Inasan komai da zaki sanya ranar auranki, Jewelry dinki, da takalmanki, da irin make up din da za'ayi maki" gaban Unaisah ne ya faɗi arude ta ɗan zare idanunta tana kallon Batool, cike da fargaban kada ta furta tana son mijinta a ƙarshen zancen ta. Cikin sauri ta katse ta"ki kwantar da hankalin ki, za'ayi maki komai irin nawa.." farin cikine ya cika zuciyar Batool. "Nagode sis, yanzu na kara yarda ina da yar uwa maison farin cikina, wadda zata iya sadaukar da komai saboda ni.." murmushin yaƙe Unaisah tayi zuciyarta cike fal da zullumin kada nan gaba tace tana son mijinta, ba zata iya bar mata shi ba saboda shi kadaine madadin danish a duniyar nan, kuma bazata iya bari Batool ta zama kishiyar ta ba, saboda tana jin tsoron kishin batool tun ayanzu tana gasa da ita inaga idan su ka auri miji ɗaya"? Sau uku Batool tana kiran sunanta bata amsa ba, ta lula duniyar tunani. "Unaisah! " ta fada tare da bugun kafadarta, aɗan firgice ta Ƙyafƙyafta idanunta tare da duban Batool. "Me kike tunani ne"? washe baki tayi"bakomai sis dina, Ina fata babu sauran abunda kikeso ko"? "Idan kin bani kayan auran naki, ke wanne zaki sanya" "Karki damu, zan za6i cikin kayan da nake da su in sanya" "Amma baki tunanin yaya Owais zaiyi magana idan yaga baki sanya kayan daya siya maki ba ni na sanya? Kuma mutane ma zasu tuhume ni.." "Karki damu Batool, ai babu wanda yasan kalar rigar, mu ma awaya muka ganta baza asan tawa bace.." murmushi Batool tayi"amma bana so ki sanya wasu kayan da suka fi nawa kyau, nafison komai namu iri daya.." daure fuska Unaisah tayi ganin ta fara wuce gona da iri. "Batool, tun da na baki rigar, ni naji bazan sanya wata bridal gown dinba, idan bakiso in fi ki kyau Ki bani ankon ki in sanya kinga sai in saje da yan matan amarya, ke kuma ki zama amarya! Ina fata hakan ya yi maki" ta tambaya babu fara'a akan fuskarta Shiru tayi da alamun rashin jin dadi akan fuskarta, sai tayi abu yazo yana damunta. "Kiyi hakuri idan na bata maki rai" Girgiza kai Unaisah tayi"baki bata min rai ba" yanzu ki tashi mu tafi gida, kinsan yau daren biki ne, yan matan amarya zasu haɗu saboda su yi final rehearsal na rawar dinner da za'ayi bayan biki" "Toh, zan yi wanka, Ki jira ni" amsawa tayi da toh, ta zauna shiru tana jiran ta.. Saukowa Batool tayi daga kan gadon ta nufi gaban dressing mirror nata, ta wutsiyar ido Unaisah ta hangota yayin da ta ke kokarin boye robobin kayan matan data satar mata a cikin drawer chest. Ta ɗauki roba daya wanda na wanka ne, tayi sauri ta shige toilet da shi. Murmushi tayi tare da dan girgiza kanta. Lamarin Batool na nema ya ɗaura mata hawan jini, yanzu ta daina tunanin hassada take da ita ko gasa, cos in har gasa ta ke yi da ita meyasa batason tafita da wani abu? Ita kawai burinta komai nasu ya zo ɗaya kada ɗaya yafi Ɗaya ❗❓ ~_____🌹______💗______💋_______💫_____🌹_______~ Da marecen Ranar bridemaids su ka haɗu gidan biki, abayan gidan suka yi Final dance rehearsal. kowa dai ya ci burin zuwan ranar auren Unaisah, ni kaina jiran ta nakeyi, dani da readers dina, kai hatta alkalamina a ƙagare ya ke daya rubuta. har sai wuraren ƙarfe goma tukunna kowaccen su ta nufi gidan su da ke a cikin Estate din. kasa runtsawa tayi saboda zullumi da fargaban ranar daurin auran nata, gani take data runtse idanunta, safiya zatayi, ita kuma bataso hakan ya faru, da tana da halin da zata ƙara kwanakin da tayi sai dai ita kanta ta ƙagu data ga ranar nan da ta dade tana jiran ta tunkan ta mallaki hankalin ta, tarasa meyasa take jin kamar batayiwa Danish Adalci ba idan ta auri wanin sa? Amma in ta tuna baya araye kuma dan uwansa zata aure sai taji sanyi aranta. Yayin da take wannan tunanin tana a kwance kan gadonta tayi rubda ciki, babu haske a dakin saina laptop screen dinta data kunna tana kallon wani shortdrama mai taken Let me taste your husband, ta daura chin dinta saman pillow. su biyu su ke yin kallo daga bisani Batool ta 6ingire da bacci, tana a gefenta ta rufe masu rabin jikinsu da duvet. Abun da yafi damunta, yadda zata fahimtar da iyayenta game da rigar auranta da zata ba Batool, duk da tasan ba lallai su nuna bacin ransu ba tunda Batool ce amma dole suji ba dadi. Mutun ɗaya da take ganin ya kamata ta sanarmawa shine Chief, tasan bazaiji dadi ba ya sayi abun da kudin shi don ta sanya ya ji dadi, fisabilillahi kuma sai yaga taje gidansa babu rigar? Me zata faɗa masa idan ya tambayeta, sai dai batajinma zata iya fada mashi saboda tasan a karshe zaice zai siya mata wata ne, ita kuma bataso ƙwara ta nemi wata mafitar. Bacci ne ya fara cin karfinta ta fara gyangyadi tana ganin biji biji a idanun ta, a hankali ta fara yin hammar bacci tana lumshe idanunta. Phone ringing dinta ne Ya katse mata kallon, agajiye ta rufe laptop din ta tureta gefe, ta janyo wayar tayi picking ta kara a kunne.. "Na kira ne don na tuna maki, daga yau ne, ina fata kin fara bankwana da kowa, cos daga yau kin gama kwana a ko'ina sai a gidana" duk da baccin dake nema yaci karfinta sai da taji dadin muryarsa. "farin ciki kake yi don zaka rabani da iyayena"? "Yeah, ina farin ciki zan daukaka darajarki, in aureki, mu raya sunnar manzon Allah SAW, mu kuma hayayyafa kamar yarda iyayenmu suka yi, ko bakison kiyi koyi da su ne"?.. Batasan sa'adda murmushi ya su6uce mata ba, tattausar lafazinsa, Yana kashe mata jiki "Inaso, burina ne tun ina ƙarama... " kasa kasa take magana gudun kada batool taji ta farka tasan halinta yanzu ta matsa number akan tana son itama ta yi aure rana ɗaya da ita. "Fadamin me za ki shirya a agobe? Me kika tanadarmin? Me kuma zaki fara yi idan kika ganni amatsayin angonki? Hamma tayi cikin muryar mai kama data rada ta furta"ka jira goben tayi zaka ga shirin da nayi maka, zan tanadar maka kaina da soyayyata, idan na fara ganin ka amatsayin angona zanyi sujjada don nuna godiyata ga Allah daya mallaka min kyakkyawan bawan nan nasa..." shiru taji baiyi magana ba. "Yaya Owais? Kana jina ko kayi bacci?.. Har saida tafara gajiya, ga bacci daya kanainayeta har ta fidda rai da zai yi magana taji yace"bana tunanin zan iya cin abinci gobe, har sai naganki agidana, a tare zamu ci dinner saboda inaso ki bani abaki" "Nima bazanci komai ba, zan jira har time da za'a kawo ni gidanka" Tsawon mintuna babu wanda ya kara furta kalma sunyi shiru sun nutsu suna sauraron sautin numfashin junan su.. Kowannansu da abun dayake saƙawa aran shi. A haka bacci yaci karfinta bata Ƙara sanin inda kanta ya ke ba. ~_____🌹_______🔥_____💋_____💘_______💞______🌹_______~ 💥💫RANA BATA ƘARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA! FRIDAY AFTERNOON, THE WEDDING DAY (RANAR DAURIN AURE) 🔥 A washe garin ranar ɗaurin aure, tun da asubahin farko, baki suke ta yin sammako suna zuwa gidan biki Kafin rana ta haska, tuni Gidan Biki Ya cika makil da Al'ummar annabi, babu masaka tsinke, Yan Uwa da Abokan Arziƙi sun cika gida, Abun sai son barka.. Tun da asubahi Hajiya Layla da Hajiya Sarah tare da Ummi da Mami su ka fara ɗaura girke girken abincin bikin. Auren Unaisah Ya zo da abun ɗaure kai, Har ranar biki babu wanda yasan menene sadakin ta, ko lefenta ba'a kawo gidan su ba, kuma ba'a san ina za'a kai ta ba, amma kowa yasan da katafaren sabon Duplex house din Owais da ke a cikin Estate. Gaba ɗaya Unaisah ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankalin ta, jiya sun kwana adaki daya da Batool, Yau da safe ta farka babu Batool, ta kira layinta batayi picking ba, sai text message da ta ga ta turo mata. _sis kiyi haƙuri da abun daya faru jiya, bazan iya sanya Bridal Gown din ki ba, saboda bada ni ta dace ba, kece amarya ke ya dace ki sanya, pls na rokeki don darajar manzon Allah SAW kada ki ki sanya rigarki, In har kina son farin cikina, kuma kada ki damu da rashin zuwana, bana jin dadin jikina ne, sai zuwa anjima zan shigo, ki kula min da kanki rabin raina_ Abun da takaranta a cikin sakon kenan, sai dai takasa yarda cewa Batool ta hakura da sanya gown dinta, tana kokwanton anya ita ce da kanta ta tura mata sakon? Kodai sanyata akayi dole ta rubuta mata? Saboda tasan mawuyacin abune Batool ta canza ra'ayi, kuma jiya taga halin da ta shiga akan son rigar, bata tunanin ta cikin sauƙi zata iya hakura, saidai idan wani abunne ke faruwa. Taso taje gidan nasu, sai dai ba halin ta fita, saboda shirye shiryen da ake yi mata na shiga ɗakin Mijin ta. A yanzu haka tana a tsaye cikin bedroom ɗin ta agaban Dressing Mirror, tana fuskantar madubin ta nutsu tana jin motsin hannuwan designer din da ke ta aikin gyaggyara mata Bridal Gown din da ke a jikin ta, designer din ce ta zo da ita daga Wedding store din su da ke a cikin garin, a wurin su Owais ya yi Order din ta, daga waje su ke shigo da kayan su, babbar macace bayerabiya. tuni makeup artist ta kammala yi mata kwalliya, idanun ta suna a rufe gam, ta nutsu tana shaƙar fragrance ɗin jikin ta, Yayin da ta yi zurfi a cikin tunanin ta.. _Kada ki yi kuka Unaisah, kada ki bari wani yasan abunda ke damunki! Nasan da wuya, amma Ki daure ki jure, ki rufa mana asiri, dan Allah Unaisah, kada ki bamu kunya a idon duniya, ki bari ayi auran nan Lafiya, Allah yana sane dake, yasan halin da kike a ciki, idan kika miƙa lamuranki gare shi zai kawo maki mafita ta inda ba mu zata_ Maganganun mommynta take tunanowa a cikin zuciyarta, a lokacin data sameta da safe adaki tana kuka kan darduma. A cikin Kunnan ta ta tsinkayi Muryar Designer din da ke ta ya ba kyawun ta. "Wow, Oh My God! Unaisah, you look absolutely stunning, just like a real queen, This bridal gown fits your curves perfectly, and I can't wait to see your husband's reaction when he sees you in this amazing gown I'm sure he'll be blown away" "Unaisah, now you can open your eyes, please I want you to see how this bridal gown transforms you." Gently ta soma buɗe idanunta kaitsaye ta fara hango kanta ta cikin madubin gabanta. Speechless, da sauri ta karasa buɗe idanunta ta zare su, bakin ta abuɗe take kallon ikon Allah.. Wata hadaddiyar mermaid silhouette bridal gown ce, strapless dandatsetsiya "Unaisah, this bridal gown is custom-made and a limited edition, designed by the renowned fashion designer, Your husband bought it especially for you, and it was expensive" Waro idanu waje tayi ta kara bude bakin ta da mamakin jin abun da designer din tace. Kyafƙyafta idanunta tayi kamar a mafarki take kallon kanta ta cikin madubi da tsantsar mamaki akan fuskarta. A hankali Designer din ta soma kokarin daura mata wani diamond-ecrusted veil asaman hadadden hair style din ta. Ga wani hadadden Bridal flower hair pin da akayi mata ado da shi asaman gashinta. Ƙafafunta suna asanye da wasu hadaddun High Heels, irin takalmin da in ka sanyasu kake jin tsoron taka ƙasa saboda fargabar kar su 6aci, dakyar aka sanya mata takalman saboda bata saba sanya takalmi mai tsini irin wannan ba.. Akan idanunta ta ɗauko hadaddiyar diamond necklace mai fasalin 5-carat diamond center stone, an kewayeta da adon smaller precious stones, daga cikin jewelry box din data buɗe agaban mirror ta fara sanya mata a wuyan ta. Gaba ɗaya ta ruɗe da ganin tsadaddun kayayyakin da take sanya mata a jikinta sai kace wata sarauniya"? Gaba daya ji take kayan sunyi mata nauyi, adon yayi mata yawa, bata kai matsayin da zata sanya su ba, gaba daya kanta ya daure tamau da al'ajabi, So take ta tambayi designer din farashin su sai dai takasa saboda tana jin tsoron taji abun dayafi karfin kunnanta, tarasa gane diamonds din gaske ne ko na ƙarauƙarau ne? Taga dai sai kyalli stones din sukeyi, Badan badan kar ace matar dg batasan diamond ba ko ace tayi ƙauyanci da ba abun da zai hana ta tambaye ta. "Something Is missing!" designer dinne Ta furta. Aruɗe Unaisah ke kallon ta ta cikin madubin gabanta, ta ɗan yamutsa fuska, adabarbarce tace "ma'am ban gane me ki ke nufi ba? Murmushi tayi"its something special daya kamata ace na gani a yatsanki, wanda shi kadaine zai kara tabbatar mana da cewa Ke din amarya ce.." confusingly, ta ɗago da yatsunta da suka zanu da lalle ta ƙura masu ido, nan take ta gane me ta ke nufi wato zobe da babu" "Meyasa Angon naki bai sanya maki ba har ranar auranku, Bansan ko mantawa yayi ba amma ko dai bakuyi dating din juna ba before, auran haɗi ne babu shiri?" (gulma ajali) Wani irin haushin ta ne Ya kamata, dama tagaji da tsayuwa.. "Karki damu, bai rage maki kyawun yatsunki ba, kawai muhimmancinsa nake dubawa" Shiru tayi cike da takaici batare data furta kalma ba. "bari na kira angon naki muji" tana kokarin zaro waya daga aljihun rigarta Unaisah tay saurin ruko wuyan hannun ta.. "Pls, babu bukatar ki kirasa! yanzu haka suna a masallaci gurin daurin aure, bana so mu takura masa, Indai zobene ba mantawa yayi ba, ya riga daya fadamin zai saka min bayan daurin auren mu.... " ajiyar zuciya ta sauke.. A gidan Dr Shureim Yana atsaye gaban Mirror Yana karasa shirya kan shi, tsadaddar shadda ce a jikin shi Launin Blue sky, A hankali Ya ke sanya agogo awuyan hannunsa sai sauri yakeyi ganin Lokacin sallar juma'a na dab da cika.. Mika hannu yayi da niyar ya dauki arab turban dinsa daya daura gaban mirror, Unexpected yaga ta zura hannu ta bayansa ta riga ɗauka, juyowa ya yi tare da duban ta, sleeping gown ce sanye a jikin ta, ta tufke gashin kanta da ribbom. "Sanyin idaniyata" ta karashe maganar tare da manna masa sumbata kan kuncinsa, ta shafo sajen shi ya lumshe idanun shi tare da furta"Masha Allah" Janye hannun ta yayi tare da kawar da shi ya lura nema take ta zautar da maluntakarsa. "please, Ustatha, kada ki karya min alwalata, baki ga time ba, nafa kusa makara.." ya fada yana nuna mata agogon bango. "I'm Sorry, mijin so, nima yanzu zan shirya in tafi gidan bikin, Benazir tana ta kira na, kasan mune manyan kawayen uwar amarya, Yar mu zatayi aure yau dole mu kure kur adakanmu" Murmushi dr shureim yayi"Zan yi missing ummu Batool, inaso na zama mutun na farko da zai fara ganin shigar da zakiyi yau, but please ki rufemin ko'ina na jikin ki, bana so wani ya gane min sirri na.." Yar dariya tayi"karka damu abban batool, zanyi yadda ka ke so" murmushi suka sakar wa juna. "Ina Batool sarkin rigima? Ko acan ta kwana ne"? "Eh, tana atare da yar uwarta" Numfasawa yayi"pls nasan abun daya faru jiya ya 6ata maki rai, mu yi hakuri da ita, tun da bata taba mana haka ba.." "Kada ka damu komai ya wuce, amma zanji kunya yau in har Unaisah taba batool bridal gown dinta, mutane zasuyi tsegumi, su kansu iyayen ta bazasu ji dadi ba, inaga mijinta da ya siya mata rigar? Ta fada da damuwa akan fuskarta.. Shima damuwarce karara akan fuskarsa"bamu da mafita, kuma bana son ganin Batool cikin damuwa, jiya naji zafin ganin yadda take kuka akan mun furta ba zamu iya siya mata kalar rigar Unaisah ba, amma da Unaisah tazo kinga ta sasanta komai, muyi hakuri da komai zai biyo baya, tun da ta riga da tace zata ba, karmu shiga tsakaninta da yar uwarta pls.." ta6e baki Ummi tayi"tom, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" ya amsa da ameen. "Muje na rakaka bakin mota" "But ki tsaya abayana" dariya tayi dan ta gane mi yake nufi. Ahaka suka tafi yana agaba tana abayan shi.. Bayan taga Tashin Motar dr shureim da sauri ta nufo upstairs tun tana tafiya akan matakalar ta soma jiyo sautin bugun kofar da Batool takeyi daga cikin dakin ta Bam! Bam!! Bam!!! Daga bisani tajiyo muryarta cikin kuka "Ummina ki budemun Kofar pls, ki taimaka ki buɗe min, na gane kuskure na, kuma na tuba bazan ƙara ba, dan Allah don sonki da manzon Allah SAW ki buɗe min ƙofar ɗakina! Inaso naje gurin Unaisah! Inaso na hadu da yan uwana gurin biki, wallahi na haƙura da bridal gown din zan sanya ankon amarya, bazan ƙaracewa inason wani abu kalar nata ba" tsantsar tausayinta ne Ya mamaye zuciyar ummin nata, sai dai bata jin zata Iya buɗe mota ƙofa, Batool nema take taja masu abun kunya. Idanunta ne suka cicciko tab da kwalla, ta jingina kanta jikin kofar tana jiyo kukan Batool dake karya mata zuciya.. "Laifinki ne Batool, ke kika ja na rufe ki, bada son raina ba, meyasa baki jin maganata? Meyasa kikeso kija mana abun kunya ne"? "Bazan kara ba Ummina, na daina ki yafe min, ni ma bansan meke damuna ba!, bansan meyasa nakeson komai irin na Unaisah ba, banaso naga tafi ni da wani abu, nafison komai namu iri ɗaya" Da rudu Ummi ta saki baki sototo tana sauraron ta.. "Batool why why? Ba fa ciki daya kuka fito ba, sister dinki ce but ki sani don kuna yan'uwa ba hakan yana nufin kaddararku iri ɗaya ba, kowa da yadda Allah ya tsara mashi rayuwarshi, ni na narasa gane Kishi kike da ita? Ko hassada kike mata? Ko kuwa kawai gasa ne"? ta fada idanunta na fitar da ƙwalla.. "Ko kinyi tunanin bansan komai bane? Kinyi henna irin nata, kinyi gyaran gashi irin nata, komai na gyaran jiki da akai mata kema saida akai maki sai kace ku biyu za'a aurar? Angaya maki komai akeso mutun yayi irin na amarya? Ta karashe maganar tare da bugun kofar cikin 6acin rai "Why Batool? Kin ɗaga min hankali, na tsani hassada arayuwana, mugun ciwo ce dake kashe rayuwar mutun Ya gur6ata masa tunani, bana so ki zama daya daga cikin wadanda zasu nakasa rayuwarsu da hassada..." "Ki fahimce ni ummina, Wallahi ba hassada nake ma Unaisah ba, kuma bana kishi da ita, sannan ba gasa nake da ita ba, nima bansan meke damuna ba, Ina jin haushin abun da nakeyi, na tsani kaina.." cikin shesshekar kuka ta ƙarashe maganar.. "Batool na fahimce ki, Ki daina kuka bana sonji" amsawa tayi da toh.. Zurfin tunani ta shiga, tabbas ta yarda da maganar Batool amma meyasa take mata haka? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa"ko dai son Owais ta ke yi shiyasa ta ke yin komai irin na Unaisah donta burge shi kamar yadda Unaisah zata burge shi .." gabanta ne Ya fadi daram. Arude ta furta"batool Kina jina! "Inaji ummina" "Ki ji tsoron Allah ki faɗamin gaskiya! Ko dai Dg kike so"? "Ni ba sonshi nake ba.."_ bata kare maganarba Ta katse ta"naji bakison shi, amma baki tunanin shi? Ko jin faduwar gaba idan kika gan shi"? Shiru tayi kamar bataji me tace ba. Knocking kofar tayi"baki bani amsa ba, nasan kina jina, pls ki faɗamin zan nema maki mafita ne" "Duk abun da kika tambaya inayi, sai nayi tunaninshi nake jin dadi araina, ko 6atamun rai akayi da zarar na tuna shi nake mantawa da komai, kuma bana jin dadi idan Unaisah ta fadamin ya siya mata abu, ni bai siya min ba, ko inji suna waya, wlh haushi nakeji kamar in haɗiyi zuciyata, amma inason unaisah, kawai ni banason kulawar da suke ba Juna ita da Chief, .." kasa ƙarasa maganar tayi jin Sallallamin da Ummi ke yi.. "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, abun da nake gudun ya faru ya faru! Batool son shi ki ke yi! Shiyasa kike kishi da Yar uwarki, ki faɗa min tun yaushe kike son shi"? "Ummi ba son shi nike ba, Ni bazan iya son mijin Unaisah ba, kuma na daɗe inajin shi araina, tun kafin nasan yana son Unaisah ..." wani irin sarawar ciwon kai Ummi taji, ji take inama zata Iya cika ma batool burinta, saboda batason ta nemi wani abu ta rasa amma wannan karan tazo da abun daya fi karfin su. "Batool, Kiyi hakuri, nasan da ciwo, amma ki daure, ki cire shi aranki, nasan kin sani, Unaisah itace Second wife din shi, ba lallai In yana da ra'ayin ƙara aure ba, kuma ni bana so ma kaddarar aure ta hadaki da Unaisah, saboda zaku yi ta samun sabani ne, in sha Allah zan tayaki da addu'a Allah ya za6a maki mafi alkhairi cikin samarin dake zuwa neman auren ki. .." bata karashe maganar ba, Batool Ta rushe da kuka kamar ranta zai fita.. Itama kukanne ke nema Ya kwace mata.. "Zan tafi Batool, ummu Unaisah tana jira na, kada su ji ni shiru, nasan zaki kuntata amma bazan iya bude ki ba, zamanki agida sai yafi mana kwanciyar hankali please, Kiyi hakuri ki daina kuka banaso, kici breakfast din dana ajiye maki akan table" tana karashe maganar ta juya da dan gudunta ta sauko down tana kuka ta nufi ɗaki don ta shirya. A bangaren Batool, tana ta bubbuga kofar, hawaye sun wanke fuskarta, ƙunci da bakin ciki suka mamaye zuciyarta, gaba daya ta haukace ta koma bubbuga kanta jikin kofar, nan take hancin ta ya soma bleeding, fatar goshinta tayi jawur tana barazanar fashewa saboda buguwar da ta yi, lokaci daya wani azababben ciwon 6arin kai Ya ziyarce ta, wani irin jiri ne ya kwasheta bata sa'adda ta yanke jiki ta kife kan floor ba, ga wani irin chest pain daya fara addabarta, gaba daya ta fita hayyacin ta, cikin karyayyar murya ta soma sambatu _mutuwa zanyi in ban same shi ba, na fita son shi, ita bashi take so ba, ni nake son shi.. " 💔 Alhamdulillah, Aure Ya ɗauru, bayan kammala Sallar Juma'a Dubban Jama'a Sun shaida ɗaurin auren Director General Owais Sharafudeen Obinna tare da Amaryarsa Unaisah Zaheer Tajudeen, Wanda aka gudanar A Masallacin Sheikh Imam malik, duniya ce ta shaida daurin Auran Unaisah, ba'a taba daurin auren daya yaɗu irin nata ba, in a short time Labarin auranta ya karaɗe duniya,Yan jarida suka dinga magana akan shi, Social media ko'ina zancen auran ta ake yi, abu biyune Yasa Aurensu Yayi shura, Na farko kowa yasan Dg da Unaisah tun lokacin da asirin kurkukun kaddara ya tonu su ka yi farin jini na fitar shari'a. Abu na biyu dayasa Auran Unaisah Ya shahara a fadin duniya, bakomai bane fa ce Expensive Downry dinta, yana ɗaya daga cikin sadaki mafi tsada a duniya, sadakin da kowa ya ke ta jira yaji menene, Taj Bai bayyana ba ko ita Unaisan da mommynta basu sani ba, ya boye ne saboda baison surutun mutane, baima so sadakin ya kai haka tsada ba, ba yadda zaiyi ne saboda mahaifiyar ango ce ta biya sadakin shalelenta, sai agurin ɗaurin auren, shiekh Imam Malik Ya zayyana sadakin Unaisah tiryan tiryan kowa yaji kuma ya shaida. Sadakin Unaisah dai an biya shine da 50-carat Heart-Shaped Diamond Pendant mai darajar gaske. su nan wannan sadakin burin kowace ƴa mace, dole mutane suyi tsegumi, Labarin sadakin Unaisah Ya zama ruwan dare ko'ina zancen shi akeyi, Mutane har sun fara tunanin yaya gidanta zai kasance! Don sun fahimci angonta ashirye yake da ya ƙarar da tattalin arzikinsa akanta, ganin yadda yake almubazzaranci da dukiya akan amaryarsa, kamar baison zafin neman ta ba, ya siyeta da darajarta tun da aka fara shagalin bai kashe abun da yayi kasa da dala dubu ba, al'umar duniya sun ruɗe. Gidajen Talabijin da radio sai taɗin auren su a ke yi.. Kwata kwata Unaisah batasan Auranta ya kammalu ba, sai dai faduwar gaba da take taji, a lokacin designer din ta gama shiryata, Unexpected wayarta da ke ajiye kan drawer ta soma ruri. da sauri madam ta mika mata wayar, ta kar6a tare da duban me kiran nata. "Murmushi tayi, cike da zullumin mai zai faɗa mata tayi picking call ɗin ta kara a kunnanta.. Sanyayyar muryarsa ce ta ratsa kunnanta"Alhamdulillah Unaisah my Angel, kin zama mallaki na, halak malak, ke tawa ce, burina ya cika na ganin ranar dana daɗe ina jiran ta..." nutsuwa tayi tana sauraron shi aranta ta ayyana wai dagaske auranta ya ɗauru? Yanzu ita matar yaya Owais ce? Kishiyar Nazli? Ya Allah Idanunta ne suka cuccuko da kwalla cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, ina tayamu murna, Alhamdulillah.... " cikin shesshekar kuka ta yi maganar, tana so ta zukunna tayi sujuddusshukur sai dai gown din jikinta ta matse ta.. Kamar daga sama ta tsinkayi miryoyinsu a cikin kunnuwanta.. Wata irin buɗa suke rangwaɗawa cikin zazzaƙar muryarsu, daga can cikin gidan ayyyiririiiiiiii.. "You're no longer Unaisah Zaheer Tajuddeen! You're now Mrs Owais, Come and take your crown, our bride queen! His princess, Yeeehhhhhhh" A lokacin kiran nasa har ya katse, godiya tayi mata designer din, sukayi sallama da juna ta tafi. A tsanake ta soma tafiya zata fuce daga ɗakin cikin sauri. Tana fitowa taci karo da bridemates suna tunkaro inda ta ke, gaba daya sun razana da ganin adon jikin ta, tayi masu kyau, fuskokin su ɗauke da fara'a sai murna su ke yi, gaba ɗayan su sun sanya anko din su, sun daura Red Aso ke headband akan su, sunyi kyau sosai. suna tafiya suna ta ka rawa yayin da su ke bin waƙar. _Ta zamo amarya Badan tayi daukaka ba Ta zamo amarya Ba domin tafi kyau ba Ta zamo amarya Ba domin itace ba Sai dan mijinta nasan ta Ashe kaunace_ Baby yau ko gobe (baby) Ya zamo angon ki (eh) Amarya ta zama taka (baby) Kar kayi mata wayo (eh) Baby yau ko gobe (baby) Ya zamo angon ki (eh) Amarya ta zama taka (baby) Kar kayi mata wayo.. Kunyace ta kama ta ta juya zata koma inda ta fito, da sauri su ka yi mata ƙawanya suka cigaba da Waƙe ta suna kewaye ta sai tiƙar rawa su ke yi. Farin ciki ne ya cika ta, har ta kasa rufe bakin ta, ta dinga sakin dariya tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya. Walwalar fuskarta ce ta ɗauke, lokacin da ta lura babu Aminiyarta a cikin su.. "Ina Batool? Batazo ba? Ko tana a cikin gida"? ta tambaya tana duban su, Parveen tace"ba tazo ba, tun ɗazu muke nemanta bamu ganta ba.. " "May be bata gama shiryawa bane" acewar Sajeeda. "Kun tambayi mommynta"? ta faɗa fuskarta a yamutse. "A'a bamu tambayeta ba" suka haɗa baki gurin furtawa.. Nan take ranta ya bata akwai wani abu daya faru wanda ya hana Batool zuwa, zaiyi wuya in ba maganar jiya bace.. Cikin sauri ta soma tafiya suka bi bayanta kaitsaye suka nufi main Falo na gidan, tun kan su shiga suka soma jiyo haniyar al'umma da ta cika gidan, ga sautin kiɗan Ƙwarya daya karaɗe kunnuwan su. Suna shiga ciki gaba ɗaya idanu su ka dawo kan Amarya Unaisah, kowa ya zare idanu haɗi da buɗe baki suna bin ta da kallo kamar zasu haɗiyeta saboda kyawun da ta yi. Jemimah da ke ruke da hannunta ta dinga rada mata ta dinga fadin Tubarkallah kar su cinye mata kurwarta, batasan sa'adda ta saki dariya ba. Aikuwa kowa yayi ta santin ta suna yaba kyanta, duk ta kasa saƙewa dakyar take iya kallon su cike da jin kunya, Ankon da iyaye mata suka sanya tsadaddar atampa ce chiganvy, kowacce ta kashe ɗaurin kallabin ta abun sai wanda ya gani, gida ya cika makil wasu suna ta taka rawa, yayin da wasu suke cin abinci, wasu fira su ke yi cikin nishaɗi. Hajiya adama ce ta nufosu tana karasowa ta rungume Unaisah tare da shafa bayanta tana fadin"Masha Allah Unaisah, My baby Angel, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, Allah Ya baku zuri'a ɗayyiba..." a hankali take amsawa da ameen ameen mommy. . "Kai Masha Allah, tubarakallahu Ahsanul khalikin, Ayyiriyiriiiii! Amarsu Ta Ango! amarya Bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida!, Dan Allah ku bani guri, In rungumi jiƙata, adinga hadawa da tubarkallah.." muryar Hajiya layla suka jiyo tana magana cikin raha, kowa dake agurin ya kama dariya, murmushi Unaisah tasaki tana kallon grandma ɗin ta dake tunkaro su hannun ta ruƙe da juice da take sha, tana karasowa ta rungumeta tana shi mata albarka tare da fatan Alkhairi tana amsawa da ameen ameen hadi da yi mata godiya. Unexpected suka tsinkayi Muryar Sister Zahra tana yi mata kirari "farin wata sha kallo, tauraruwar dake haskaka sararin samaniya, dawisu sarkin ado, the Dg's wife, nan gani nan bari, dukiyar dg ce... " gaba ɗaya suka sanya dariya, suna kallon ta yayin da take shigowa ta ƙofar falo, ankon yan matan amarya ne a jikin ta, kana kallon ta zaka gane akwai ciki a jikin ta, tayi ƙiba hutu ya zauna mata, Unaisah taji dadin kirarin da tayi mata, tana ƙarasowa ta rungume Unaisah kamar zata mayar da ita cikin ta. "Unaisah ina yi maki fatan Alkhairi, Allah yasa mutuwa kadai zata raba... " amsawa tayi da ameen nagode Aunty Zahrana, Allah ya sauke ki lafiya. "Ameen nagode Unaisahna" "Ina Aunty Aneelerh"? Zahra tace"suna acan dakin Uwar Amarya..." "Nagode Aunty Zahra, bari naje na same su... " ta faɗa tare da juyawa ta nufi dakin mommyn ta. A bangaren Benazir, bayan da Taj ya kira wayarta ya faɗa mata aure ya ɗauru.. bai ƙare maganar ba, tayi rejecting call din ta zauna gefen gado, batasan sa'adda ta fashe da kuka ba saboda bata shirya rabuwa da Unaisah ba, tana jin kewarta tunkafin zuwan wannan ranar, Aisha da Aneelerh sun taru akanta, suna ta lallashinta tare da bata ba ki. "Haba mana, Unaisah ba wata uwa duniya zataje ba, a cikin estate din nan gidan ta ya ke, ko ihu kikayi zata jiyo ki ne, sunna fa zata raya, ke ba abun farin cikin ki bane? Yar ki tayi aure, ta auri nagartaccen namiji ɗan babban gida, da kowa ke burin ya haɗa zuri'a da su... " Aisha ce ta fada cikin sanyin murya. Tana shesshekar kuka tace"hmm ba za ku gane ba, ni banyi wata rayuwa mai tsayi da Unaisah ba, duka fa baifi shekaru ƙalilan ba da mukayi atare, yanzu kuma tayi aure, zata koma gidan mijinta da zama, ita kadaice fa gareni, ina sonta a kusa dani, gani nake kamar in ta tafi ba lallai ta samu kulawar da muke bata agida ba, har yanzu yarince fa, ku duba kuka ga irin kishiyar da zata zauna da ita, ina jin duk ba daɗi, bansan ya zanyi ba..." Aneelerh tace"please ki daina wannan maganar, kin san yadda dg ke sonta, in sha Allah Unaisah zata samu kulawarsa, karki wani damu da kishiyarta, bata fi Unaisah da komai ba, kuma kowa da matsayinsa a wurin dg, ni nasan zaiyi adalci a tsakanin su in sha Allah" Cigaba da share kwalla tayi tana sauraron su "Hakuri zakiyi Benazir, kowa fa haka akayi masa auran nan, kin sani kema, ni banaso Unaisah tazo ta sameki kina kukan nan wallahi zaki daga mata hankali ne..." jinjina kai ta danyi ta soma share hawayen ta da hanky. "Yawwa ko kefa, bari na gyara maki daurin ɗan kwalin..." ta fada tana gyara mata head ɗin ta daya karkace. gaba dayansu sunyi kyau cikin ankonsu.. Aisha tace"farin ciki yakamata muyi Benazir, tun da aka fara bikin nan dg ke 6arin dollars akan Unaisah, kamar baisan zafin neman su ba, sai fa kana son abu kake siyansa da daraja, maganar kishiya mu aje ta gefe, Unaisah fa babu mai iya ja da ita wallahi, ita da take da mu? Babu wani lagwon namiji da ban sani ba, Allah idan dg ya shiga tafin hannun Unaisah mai ƙwatarsa sai ya shirya...." gaba ɗaya suka sanya dariya.. Anilah tace"godiya yakamata muyi wa Allah, Wallahi Unaisah tayi dacen miji, ga kyawawan halaye, komai Allah ya basa! kinji kuwa yadda al'umar duniya ke taɗin bikin Unaisah"? Murmushi Benazir tayi"mungode ma Allah, ɗiyar mu tayi goshi, Ina alfahari da dg, na yarda da son da ya ke yi mata, fatana Allah ya basu zaman lafiya da ita da mijinta da kishiyar ta... " Gaba ɗaya suka amsa mata da ameen. "Ummm Itama dai Unaisah zataje taji abun da mu ka ji A first night din mu.." waro ido su ka yi jin abun da Benazir tace, aikuwa suka tuntsire da dariya, Aisha tace"Allah ya shirya ki Benazir, me hali bazai ta6a canzawa ba, har yanzu kina nan da rashin kunyarki, yanzu nan fa kika gama kukan munafurcin za'a rabaki da ƴarƙi..." dariya Benazir tayi"to ya zanyi Aisha! Abun nan fa ya riga daya faru, dole Unaisah ta tafi gidan mijin ta shikenan ba zanyi raha ba.." Aneelerh tace"baiwar Allah, tun kafin ta mallaki hankalinta take da burin yin aure, tunkan tasan ma'anar auren, ba dan komai ba sai don saboda ganin irin rayuwar farin cikin da mu ke yi Nida Uzair a lokacin, ni dai fatana Allah yasa Unaisah ta more rayuwar auranta kamar yadda take saran zataji dadi idan tayi aure, Allah yasa kar tayi danasani, saboda inason ta cika burin ta" idanunta cike tab da kwalla tayi maganar tunawa da marigayi Uzair. gaba daya jikin su yayi sanyi.. In a broken Voice Benazir da Anila suka hada baki gurin furta"ubangiji Allah yajiƙan Uzair, Allah yakai rahama kabarinsa" "cikin sanyin murya ta amsa masu da Ameen" Shiru su ka yi na ɗan wani lokaci babu wanda ya ƙara furta kalma. "Yakamata mu fita kar aji uwar amarya shiru bata leƙo waje ba, kuma mun bar su mami da aikin tar6ar baki" Aneelerh tace ta faɗa tana mikewa Ummi tace"in da Allah ya rufa mana asiri sai bayan biki da sati ɗaya za'ayi dinner, kafin ranar zamu ƙara shiri" "Ni dai ba haka naso ba wallahi, banji dadi da Owais ya tsara dinner har sai bayan sati daya da yin auren ba, dama dai agida zata zauna kafin ranar dinner din da naji dadi, kuma wai ba gidanta za'a fara kaita ba, gidan iyayensa za'a wuce da ita, jiya Taj ya ke faɗa min, na rasa gane meyasa suka za6i su yi hakan? Bansan ko haka suke yin auren su ba, Ni dai a asanina amarya gidanta ake fara kaita bayan biki" Ummi tace"wannan duk ba abun tashin hankali bane, munsan mutanan nan, sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, komai suka yanke akan Unaisah muyi masu kyakkyawan zato" Ajiyar zuciya ta sauke"hakane kuma, nima na faɗa ne kawai ba dan ina nufin wani ba" Aneelerh tace"ni nafi tunanin Owais ne a bayan komai, may be akwai wani surprise da zaiyi ma Unaisah shiyasa bayason kowa nata ya rakata gidanta, saboda ita ya ke son ta fara zuwa, shiyasa ya tsara a fara kaita gidan su daga can sai ya ɗauke ta yakaita gidan sa... " ta kare maganar idanunta a cikin na Benazir dake kallonta.. Ummi tace"ni kuma abun da nake tunani game da dinner din da za'ayi after one week da yin auren, watakil yana son kafin ranar ta samu ciki.... " waro idanu waje su ka yi jin abunda Ummi tace ita kanta da tayi maganar sai taji abun bankwarakwai, gaba daya suka bushe da dariya cikin nishaɗi.. Knocking din ƙofa ne ya katse firar ta su. "Wanene"? "Mommy ni ce..." ajiyar zuciya ta sauke"shigo ciki" buɗe ƙofar tayi ta shiga, waro idanu waje su kayi tare da bude baki suna kallon ta, wata irin kunya taji ta kamata, tayi saurin sunnar da kanta ƙasa. "Wow, babe Unaisah irin wannan kyau haka? Kamar wadda zataje gasar miss world? aisha ce ta faɗa tare da rungumar ta, tana dan shafa bayanta"masha Allah Unaisah finally kin zama matar dg, Allah ya sanya Albarka a auranku..." amsa mata tayi da ameen Benazir ta nufo ta, da murmushi kan fuskarta, tana ganin mamanta ta yi saurin karasawa gareta ta rungumeta tightly a kirjinta, batare da sun iya furta kalma ba, kowa yana jin rashin dadin rabuwar da zasuyi da juna. "Unaisah.." Anila ce ta kirata a hankali ta raba jikinta daga na mommynta taje ta rungume Anila. Bayan data dago Ummi ta ruƙo hannunta ta zaunar da ita daga gefen gadon mommynta, suka zauna gefe da gefen ta, Benazir tana daga tsaye tana kallonta da rinannun idanun ta. Ummi ce ta fara yi mata nasiha game da zamantakewar Aure, mai matuƙar ratsa zuciya, ta bata shawarwarin da zasu amfane ta, ba Unaisah ba hatta Benazir da Aneelerh sunji dadin nasihar da Ummi tayi mata sosai, bayan da tagama Aneelerh ta ɗaura da yi mata huɗuba, gaba ɗaya suka sa taji ƙarfin gwiwa atare da ita. Bayan da Aneelerh ta gama, Benazir tace"Unisah, ni ba abun da zance, saboda duk wani abu da zan faɗa, mommies dinki sun faɗa, illa iyaka ince ki ɗauki shawarar su, in sha Allah ba zaki ta6a yin danasani ba ..." idanun ta ne su ka cuko da kwalla. "Please kada ki zubar da hawayenki Unaisah, Zaki 6ata kwalliyar..." Ummi ce ta fada jinjina kanta ta dan yi tana kokarin shanye hawayen ta. In a broken voice tace"gaba daya Kun kashe min bakina, na rasa tayaya zan iyayi maku godiya, kun gatantani, kun nuna min ƙauna, kun yi min abun da bazan iya biyanku da shi ba, kullum cikin bani shawarwari kukeyi, kun gyarani, kun ilmantar dani, Allah ne kadai zai iya biyanku, Ina alfahari da ku.." tun da ta fara yin magana suke kallonta da murmushi kan fuskar su. Wayar Ummi ce tayi ruri ta mike ta nufi kofar dakin tayi picking, Unaisah tabi bayanta, sai da tabari ta kammala wayar sannan tace"Aunty Ummi, Yar uwata bata zo bikina ba, meyasa ko bata da lafiya ne"? juyowa tayi ta dubi Unaisah "ba zata samu zuwa ba, cikin ta ke ciwo, amma karki damu tasha magani, lokacin dana baro gidan bacci ta ke yi, ko ba yau ba Batool zatazo gidan ki tun da nan kusa ne" girgiza kai Unaisah tayi kamar zata saka kuka tace"Aunty Ummi, kiyi haƙuri amma raina na bani wani abu ne ya faru! Ko sakon da ta turo min raina na bani ba ita ta rubuta shi ba, Ba dan ban yarda da maganar ki ba, dan Allah ki fada min meke damunta? Meyasa ta canza ra'ayinta na kar6ar rigata"? "Me kuma ya hanata zuwa bikina? Bayan itace babbar ƙawar Amarya, nafi bukatar ganinta akan kowa" yanayin yadda tayi maganar da damuwa ne yasa ummi taji jikinta ya yi sanyi laƙwas. In a cool voice tace"haka ne Unaisah, kin faɗi gaskiya, amma ba abun da kike tunani bane, bazan iya fada maki ba, amma zuwan Batool gidan bikinnan ba alkhairi bane! Kwara zamanta a gida, zaifi mana kwanciyar hankali, ni narasa gane meke damunta kamar mai iskokai..." ta fada cikin kunci da 6acin rai. "Batool ta bani kunya Unaisah, ta karya min zuciyana..." gaban Unaisah ne ya faɗi ganin hawayen dake sauka kan kuncin Ummi. Cikin rudu tace"Aunty Ummi! Meyasa kikace haka? Saboda abun daya faru jiya? Ko wani abun tayi maki"? numfashi taja tare da dan jinjina kanta tace"ba wannan ba Unaisah, ai ƙwara abun da tayi jiya, yau takarasa haukacewa, kawai abun da nakeso dake, pls ki manta da batun zuwan Batool, ba zan ta6a bari tazo ba, kuma kema ban yarda kije inda take ba, ki bata lokaci har sai ta canza tunanin ta..." kalaman Ummi sun ɗaga hankalinta, kamar tayi kuka take ji, magiya tadinga yi mata akan ta taimaka ta yafe ma Batool laifin da tayi mata, tabarta tazo in ba haka ba bazataji dadi ba. Amma ummi ta rufe ido tace wallahi Batool ba za tazo ba, tama cire rai da ganin ta har sai an kammala bikin ta, kuma karta kuskura taje inda take ko tace zata faɗa ma wani in ba haka ba zata sa6a mata, Unaisah ba yadda ta iya dole tabi umarnin Aunty Ummi. Babu wanda yasan meye faru a tsakanin su, gashi kowa ya damu da rashin ganin Batool, musamman bridemaids, duk wanda ya tambayi ummi ko Unaisah game da Batool sai dai su ce bata da lafiya. ~_____________________________________🌹🔥~ Around ƙarfe biyar na yammacin ranar, motocin su Taj suka karaso cikin gidan domin daukar Amarya, bayan ya kira Benazir ya fada mata su fito da Unaisah suna jiran su. A main Falo, Benazir tare da aminnanta suka shugo da Unaisah... A saman Carpet ta zauna, Hajiya layla da Hajiya adama ne suka fara yi mata nasiha bayan sun gama daga bisani suka sanya mata albarka tare da yi mata fatan Alkhairi dakyar take amsawa kamar zata sanya kuka, Mamie da Ummi ma su ka yi mata huɗu ba kan zamantakewar aure a karshe suka sanya mata albarka tare da fatan Alkhairi.. Daga bisani Hajiya sarah tayi mata nasiha itama. Kowa dake agidan saida ya yi mata addu'o'i da nasiha tare da fatan Alkhairi, kamar zata fashe da kuka saboda sun karya mata zuciya ji take kamar in ta tafi ba zata sake ganin su ba. Sallamar Ƴan Uwanta Maza ne ta katse hanzarin su, atare suka kai duban su gare su.. Su biyar ne suka shigo, sun ɗauki wankan Shadda getzna blue sky, hannayen su sanye da tsadaddun agoguna, ga wasu hadaddun takalma a kafafunsu, hair cut din su yafi komai jan hankali, Sajeed da Haris ne agaba, Naufal da javeed suna abiye da bayan su tare da Mubeen a gefen su. Bridesmaids na ganin su suka fara murna tare da nufar su kamar za su yi hugging din su, suna ta sakin wani ƙayataccen murmushin gefen fuska. "Daddy Taj ne Ya turo mu don mu fito masa da Unaisah muna jira" Sajeed ne ya faɗa "Tashi mu tafi Unaisah..." Hajiya adama ce ta faɗa, sai da suka taimaka mata gurin mikewa saboda raunin da ta yi, rungumeta Benazir tayi sosai, ta dinga zuba mata addu'o'i tare da sanya mata albarka, tace ta kwantar da hankalinta, a duk lokacin da take bukatar ganinta ta kirata awaya, cikin shesshekar murya ta amsa mata da toh, kowa dake agurin sun basu tausayi sosai, tsakanin uwa da ya sai Allah.. Yan Uwanta maza suka shiga gaba, Bridemaids suka take mata baya, yayin da sauran yan rakiya suke abiye da bayan su. Daga cikin waɗanda zasu rakata, bayan braidsmaids, sai hajiya adama da hajiya layla, da kuma Aneelerh, da Ummi da sauran su. Har suka fuce daga falon Benazir bata daina bin bayansu da kallo ba, kamar tabi su take ji, badan hajiya layla ta kwa6eta ba ai da ba abun da zai hana taje raka diyarta, a karshe zama tayi dirshan kan kujera ta zabga tagumi idanunta cike tab da ƙwalla, Mami da Ummi ne suka kewayeta suna lallashin ta. A Parking space suka hango iyaye maza, gaba dayansu ankon shadda getzner su ka yi suna atsaitsaye suna jiran fitowar su, tun daga kan Taj dake a ruƙe da hannun Baby junaid, ya shige cikin manya, shima ankon ne ajikin shi, Ya manna bakin glass sai shan kamshi ya ke yi kamar shine angon, Dr shureim yana atare da su, Uncle Abdallah, ga mijin dr yusra wato yaya Salsabeel namu ya sauya ya zama babban mutun, amaryar fa yar gata ce, gaba ɗayan su ne su ka zo tafiya da Unaisah gidan Iyayen mijinta. Fuskokin kowan nan su ɗauke da fara'a, ta cikin mayafinta take hangen su, kaitsaye ta nufi daddynta, tana karasowa yayi hugging din ta yana shafa bayan ta, ji ta yi kamar ta fashe da kuka. A kunne yayi mata raɗa"Unaisah, nima inajin abun da ki ke ji, please kada ki sanya damuwa aranki, ki kwantar da hankalin ki, kinsan wa kika aura, ni nayi imanin ba zaki taba danasanin auran za6ina da ki ka yi ba, yau ranar farin ciki ce a gare ki dani kaina, burin da kika daɗe da shi Allah ya cika maki shi Unaisah kin tuna? Ko in tuna maki"? Ya faɗa yana leken fuskarta, dariya ta saki har fararen hakoranta su ka bayyanta. Ɗagowa tayi da kanta daga kan kirjin daddynta, Uncle Abdallah Ya ruƙo hannunta tare da yin hugging dinta, yayi mata addu'o'i tare da fatan Alkhairi, kafin ta matsa gurin Uncle shureim shima ya sanya mata albarka tare da fatan Alkhairi, ta dinga amsawa da ameen hadi dayi masu godiya, Salsabeel ma ya yi mata addu'o tare da fatan Alkhairi. Zuƙunnawa tayi gaban baby junaid daya haɗe rai kamar bai ta6a yin dariya ba. Shafa kumatunsa tayi"my little bro, fadamin waya 6ata maka rai"? Yana cika yana batsewa yace"hmm fushi ni ke da ke, bani ki ka ce zaki aura ba! Shine kikayi auran ki" gaba daya suka sanya dariya, tunawa ta yi da Uncle Uzair da daddynta a lokacin baya, sunyi burin su haɗa ya'yan su Aure, Allah bai nufa ba. Saitin kunnanshi takai bakin ta cikin raɗa tace"na gane laifi na my little bro, ka yi haƙuri, amma nayi maka alƙawarin in sha Allah zan haifa maka kyakkyawar baby kaga kaima sai kayi auran.." 6a66akewa yayi da dariyar farin ciki. "Ki haifa min kyakkyawa mai irin idanunki, da komai naki" dariya tayi cike da nishaɗi. "Pls kada ka fada ma kowa, daga ni sai kai, alkawari" ta fada tare da miƙa masa yatsanta, Ya sargafo shi da yatsan shi, suka sakarwa juna murmushi. Kowa ya nutsu yana kallonsu sun burgesu sosai. Peck ta manna masa a forehead dinsa. Kafin ta miƙe tsaye, Suna haramar shiga cikin motocin. Unexpected suka tsinkayi muryar Batool a cikin kunnuwan su. "Sister ku jira ni... " gaban Ummi ne ya faɗi rass! aranta ta ayyana kamar muryar Batool? Anya itace? Tayaya akai ta buɗe ƙofa bayan na kulle ta, Ya salam in kuwa itace An yanka ta tashi.. kusan atare suka dubi inda take.. cikin sauri ta ke yin tafiya dakyar take taka kafarta saboda tsinin high heels din kafarta, tayi bala'en yin kyau a cikin ankon ta, ta saka Red Aso ke headband akanta, Sumar kanta da tasha gyara ta lullu6e bayanta, sai ka rantse da Allah itama amaryar ce saboda yadda ta yi kyau. hankalin Ummi fa ya tashi a sukwane ta daura hannu daya akanta. sam taƙi yarda ta haɗa idanunta da Ummi saboda gudun karta hanata sukuni, tunkan ta karaso Unaisah ta nufe ta suka rungume juna, sauran ƙawayen suka nufe su gaba ɗaya su ka kewaye Batool suna ta santin kyan da ankon yayi mata. Jiki asanyaye Ummi ta dubi dr. shureim harara ya watsa mata tare da yin ƙwafa, nan ta ke ranta ya bata shine ya buɗe ma Batool ƙofa, haɗe rai tayi tana dan murguɗa masa bakin ta a fakaice. Ruƙo hannun ta Unaisah tayi suka nufo su, with respect ta gaishe da iyayen nasu, suka amsa mata da fara'ar su. daga bisani, daddyn Unaisah ya buɗe mata backseat ta shiga ta zauna, Aneelerh da hajiya layla suka sanyata tsakiyarsu. Taj Ya shige mazaunin driver, tuni ummi ta ruƙo hanun Batool suka shige motar dr Shureim, hajiya adama a motar abdallah ta zauna tare da baby junaid. bayan kowan nan su Ya shiga a jere motocin su ka soma tafiya slowly saman titin estate din wanda zai sadasu da gidan su Ango. Acikin motar Taj Aneeleerh da Hajiya layla sai ƙara yi ma Unaisah Nasiha su ke yi duk don ta sake ta daina jin fargaba. A hankali dr shureim keyin driving yana satar kallon Ummi da ke zaune a gefen sa ta cikin madubi, kwata kwata bata lura ba, ta dage sai aikawa Batool harara ta ke yi ta mirror, duk tabi tasha jinin jikin ta da ganin irin kallon da mommyn nata keyi mata, tuni idanun ta sun cuko da ƙwalla. "Why Aisha? meya haɗa ki da Batool dayaja har kika kulleta adaki? Laifin me ta yi maki please? Ko dan saboda abun daya faru jiya ? Har saida ta ɗan ji gabanta ya faɗi, cike da ƙarfin hali tace"bata faɗa maka abun kunyar da ta gaya min ba ne... "? Walwalar fuskarsa ce ta ɗauke, cike da damuwa yace"koma me tayi maki bai kai laifin da zaki kulle ta aɗaki ba, ita ka ɗai agida, idan wani abu ya faru fa? Baki ga yadda na taras da ita ba, kwance kan floor, hancin ta yanata bleeding, kwata kwata bata a hayyacin ta, badan Allah yasa naje gurin dakin nata ba har na jiyo shesshekarta da ban san me zai biyo baya ba" Hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba jin abun da ya ce, duk tabi ta rude ta juyar dakai ta dubi Batool data sadda kanta kasa. "Am sorry babe, banyi don na bata maki rai ba, kodan na ƙuntata maki, sai dan ina gudun abun da zai biyo baya, kinsan ina sonki, bana son duk wani abun da zai bata maki rai, nasan in har kikazo gidan biki za'a iya samun matsala shiyasa naso ki zauna gidan, zaifi mana kwanciyar hankali, bansan haka abun ya faru ba... " Cikin sanyin murya tace"bakomai Ummina, ya wuce, ni yakamata in baki hakuri, ban kyauta ba, nayi rashin hankali amma bana so ki damu akaina, In sha Allah bazan kara maimaita kuskuren da nayi ba,.." ajiyar Zuciya Ummi ta sauke, taji dadin maganar Batool. "Bakiji yadda naji dadi ba, haba yanzu nasan batool dina ce.."_ murmushin karfin hali Batool ta yi wanda bai kai zuci ba, ~____________________________________🌹~ Idan muka koma bangaren Gidan su Ango, gaba ɗaya Dangin su sun hallara a main falo suna jiran ƙarasowar Amarya da dangin ta, wasu daga cikin matan family din suna a tsaye gaban entry Hall suna jiran zuwan su don su tarbe su. Lokacin da Motocin suka ƙaraso slowly su ka yi parking a gefen Entry hall a jere, cikin sauri Securities din dake sintiri agurin su ka yi hanzarin matsowa tare da bude cardoors din su. Gaba dayansu suka fito, Unaisah tana a tsakiyar Aunty Aneelerh da Hajiya layla, ta rufe fuskarta da veil. Yan Matan Family din dake jiran karasowarsu suna ganinsu suka nufesu suna rangwaɗa buɗa Ayyiriyiriiii, gaba ɗayan su sun ɗauki wankan swiss cord Lace riga da skirt, sun saka asoke akan su dana kafada, sun wanku abunka ga dirarrun mata. Suka kewaye su suna rangwaɗa buɗa. A haka suka nufi ciki da Unaisah gabanta nata faɗuwa rass rass ta rasa me ke mata daɗi.. Suna shiga cikin katafare falon wani daddaɗan ƙamshin turare ya cika hancinan su, ga sautin kiɗan waƙar larabawa da ke tashi.. Ta cikin net din gyalen take satar kallon al'umar dake a cikin falon.. Gaba ɗaya Iyayen ango da kawunnansa da iyalan su sun hallara a babban falon, kowan nan su yana a zaune kan Sofas karkuso kuga yadda manyan matan suka ca6a adon zinari a wuyansu da hannayen su, wasu diamond necklaces suka sanya, sunyi shiga ta alfarma, sunyi matuƙar yin kyau, Yayin da Uban Ango da Uncles dinsa suke a sanye da dandatsetsiyar shadda blue sky, wuyan hannayen su asanye ya ke da expensive watches. cike da aji da ƙasaita su ke sakin murmushin dattako suna kallon dangin Amarya da ke shigowa falo tare da amaryar su.. Hajiya saratu tana a zaune kan sofa tsakankanin Uwar Ango da sheikha mujeedat, tayi ƙiba dumurmur da ita kai kace bata taba shiga damuwa ba arayuwarta, a yanzun ma da ta ke a zaune plate ne ruke a hannunta mai ɗauke da chicken wings soyayyu hankalinta kwance ta ke cin abun ta, hali na nan Can na hango Hajjaty da mommy Turai zaune kan Sofa suna ta fira, yanzu fa sun zama dangi, babu mai goranta musu, shigowar dangin amarya ne Ya katse hanzarin su, kusan atare suka miƙe gaba dayan su don nuna girmamawa, hakan ba ƙaramin faranta ran dangin amarya ya yi ba, cikin fara'a da mutunta juna suka soma gaggaisawa, mazan suka soma yin musabaha, matan kuma sunayin gaisuwar larabawa a tsakaninsu, sunyi masu kyakkyawar tarba, daga bisani kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, Dangin amarya suna fuskantar dangin Ango, Unaisah da bridesmates da yan uwan ta maza suna zaune kan lallausan rug.. Unexpected idanunta suka hango mata Prime minister ta cikin gyalenta, yana a zaune kan sofa, daga gefen shi mai girma Sharafuddeen suna fira, wani irin faɗuwar gaba taji, wallahi sai taga kamar Danish ne, saboda sumar kan da Hateem ya tara ta kara fiddo da kamanninsa da Danish, nan take tafara tariyo kyakkyawar fuskarsa, ta dinga jin zuciyarta na bugawa da matsanancin ƙarfi, hawaye su ka ciccika idanun ta, ƙuncin ya mamaye zuciyarta har wani zazza6i take ji a jikin ta, a hankali ta dauke idanun ta daga kan Daddy minister ta mayar da su kan Sheikha Mujeedat, mahaifiyar Man dinta, bazata ta6a manta al,ajabin da tayi ba aranar da taji cewa Danish dan Hateem ne, dama ta daɗe tana ji aranta danish dan wani hamshakin mai kuɗi ne ko basarake ashe hasashenta ba karya bane, wallah taso Danish Ya rayu da iyayen sa, duk da tasan koda yana araye bama lallai ya kulata ba, saboda yafi karfinta nesa ba kusa ba, ba ma ajinta bane indai ta matsayin family za'abi, aranta ji take inama man dinta yana araye koda bazai kulata ba, zataso tagansa cikin rayuwar farin ciki. Batasan sa'adda hawaye suka fara zarya kan kuncin ta ba.. Kunnuwanta ne suka soma jiyo mata tattaunawar su. "Madallah, Munji dadin karramawar da ku ka yi mana, wannan ya kara tabbatar mana da cewa yarmu ta shigo gidan mutane masu daraja, da ƙima kuma gidan mutunci da karamci_________ " Hajiya adama ce tayi maganar cikin nutsuwa. Gaba ɗayan su murmushine akan fuskokinsu ga dukkan alamu sunji dadin maganarta. Ta ɗaura da cewa"babu shakku ko fargaba a tare damu, saboda munsan hannun da ƴar mu ta faɗo, toh ga ƴarkunan Mun kawo maku amana, Allah ya tayaku ruƙon ta.." ta faɗa tare da nuna Unaisah da hannun ta.. Gyaran murya malika sarauta tayi, hankali ya dawo kanta, gently ta soma magana cikin ƙasaita "Mun kar6i amanarku da hannu bibbiyu, Gaba ɗayan mu muna farin ciki da zuwan ku, kuma muna farin ciki da zuwan Unaisah cikin Family din mu, wannan abun alfahari ne agare mu, samun suruka irin Unaisah, wadda ta fito daga gida na mutunci da tarbiya zai yi wuya a duniyar nan, in sha Allah, alkawarine mukayi maku, Unaisah bazata ta6a maraicin barin gidan iyayenta ba, kuma bazata ta6a danasanin Auran ɗan mu ba... " Kalamanta sun faranta ran su, aneelarh har taji ƙwarin gwiwa atare da ita tasan in ta bama benazir labari ba qaramin dadi zataji ba.. Hajiya saratu tace"Ai in sha Allah yadda Unaisah ta shigo family din nan, mutu karaba mu da ita, zamu tsaya tsayin daka don ganin ta zauna lafiya agidan mijinta, ko yaji bazai dawo da ita gidan iyayen ta ba..." ta ƙarashe maganar tana cizgar fiffiken kaza.. Gaba ɗaya suka sanya dariya cikin raha.. Burin Unaisah gimbiya Mujeedat tayi magana, so take taji muryarta kota samu salama a cikin zuciyarta, saboda gaba daya muryarta irin ta Danish ce dan banbancin kadan ne shi yana namiji ita kuma mace.. Aikuwa Cikin sa'a ta tsinkayi muryar Mujeedat a cikin kunnanta, cikin harshen turanci ta ke yin maganar ta.. "yadda Unaisah ta nunama jinin mu ƙauna, ta amince zata rayu da shi tabar gidan iyayenta da danginta saboda shi, ta dawo namu don ta raya sunnar ma'aiki, in sha Allah ba zamu bari tayi danasani ba, ba zamu ba ku kunya ba, Unaisah ƴace agurin mu, kuma lu'u lu'u ce mai daraja mai wuyar samuwa, da kowa ke burin ya mallaka amatsayin surukar sa, amma mu Allah ya azurtamu da samunta, iyayenta sun mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, sun dauki yarsu sun bamu badan isarmu ba, badan matsayinmu ba, badan sun gaji da ita ba, kuma badan basu sonta ba sai don suna son yarsu ta raya sunnar ma'aiki, tayi aure itama ta hayayyafa kamar yadda suma su ka yi, in sha Allah zamu ruƙe Unaisah da hannu bibbiyu, zamu bata kulawarmu, soyayyarmu, goyon bayan mu, kamar yadda muke yiwa ya'yan mu, saboda itama Amana ce agare mu.. " yadda ta ke yin magana cikin nutsuwa da kasaita tana watsa yatsun hannayenta dake asanye da zobban diamond ba karamin burgesu tayi ba, ta tafi da imanin su. Baiwar Allah Unaisah kamar sakarya tuni ta shagala tana ta kallon tausasan la66an sheikha mujeedat, danish kawai take tunawa, ji take inama ace itace surukarta wayyo Allah.. Babu wanda yasan kallon ƙurullan da takeyi mata saboda mayafin daya lullu6e fuskarta, falon yayi tsit kowa ya nutsu yana sauraron daddaɗar muryar Sheikha mujeedat, basu taba zaton zata iya magana har haka ba, saboda izzarta.. Sarauta taji daɗin jawabin Sheikha mujeedat, ta taimaka mata data ari bakin ta.. Matar akwai wayewa da tsantsar ilmi akan ta.. Basu bar gidan ba, anan suka tsaya saboda walimar da suka faɗa masu za'ayi anan, da lokacin yin walimar ya yi, gagarumin shagali suka haɗa masu, babu wanda bai nishaɗantu ba, sun ji dadin karramawar da su ka yi ma su. Bayan kammala walimar, around ƙarfe shida, suka yi masu sallama zasu koma. Unaisah kamar tayi hauka saboda zullumi da fargaban karsu tafi su barta, Har bakin motocin su suka rakosu, daddynta ya rungumota yana lallashinta, shi kanshi daurewa kawai yakeyi har kwalla sai da yaji ta cika idanun sa, ta rungume Aunty Aneelerh da aunty Ummi sunata lallashinta, duk saida tabi bridemaids ta rungume su, cikin shesshekar murya take yi musu godiya. Kwata kwata babu wanda ya lura babu Batool a cikin su har suka kammala yin bankwana da Unaisah da zumar zasu sake haɗuwa gurin dinner din ta bayan kowan nan su Ya shige cikin mota, akan idanun Unaisah motocin su ka tafi. Kamar tayi hauka, kwata kwata ta manta da mutanan dake a bayanta ta fashe da kuka, batai aune ba, taji an rungumeta, har saida taji gabanta ya faɗi jin kamar sheikha Mujeedat ce. Shafa bayanta tayi"karki yi kuka, zaki 6ata makeup dinki, tun kan angon naki ya gani, kiyi hakuri kinji surukata, nasan ba daɗi ka rabu da kowa naka ka shigo cikin dangin da baka taba rayuwa da su ba, amma ki kwantar da hankalin ki, mu ma da haka muka fara, nayi maki alkawarin zan share maki hawayen ki..." ai tun da hancinta suka shakar mata turaren sheikha ta kuma tabbatarwa kanta itace ta rungumeta tuni ta nemi kukan da ta ke yi ta rasa, ita dai tana son maman danish din ta, duk da tana jin fargaban karta ta juya mata baya tun da mijin yar ta ta Aura, sai lokacin ma ta tuna da kishiyarta Nazli bata ganta agidan ba. Komawa su ka yi da ita cikin gidan, Sarauta ta ruƙe hannunta suka nufi dakinta, a kan gado tace ta zauna, jikinta asanyaye ta zauna tana ta jin faduwar gaba, har abinci tasa maids suka ka kawo mata, tace mata bata jin yunwa taci abinci agida. Allah Allah take su mika ta gidan ta, saboda takasa sakewa anan gaba daya a matse ta ke, ta ƙosa ta cire bridal gown din jikinta, ta matse ta sosai. Around ƙarfe shida na mare ce bayan anyi magrib, su ka fito da Unaisah daga cikin gidan, suka nufi jigunanniyar Motar sarauta da ita, gidan baya ta shiga ta zauna sanyin A.c ya daki fatarta, ta ruɗe da ganin haɗuwar motar, irin wadda sarakuna ke hawa, Sheikha mujeedat da hajiya malika ne a mazaunin gaba, tayi mamaki sosai, tayi zaton Owais ne zai zo ya tafi da ita, amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci su biyu zasu kaita gidan ta. Gimbiya mujeedat ce ke sarrafa motar.. "Unaisah, Akwai gift boxes da muka ajiye maki a ɗakin ki, Idan kin shiga zaki gani... " Sarauta ce ta faɗa, cikin sanyin murya ta amsa da toh tare dayi mata godiya, tace batason godiya, babu wannan atsakanin su, sun zama ɗaya, murmushi tayi. "Ko akwai abun da kike buƙata"? gimbiya Mujeedat ce ta tambayeta, a hankali ta sanya hannu ta yaye mayafin ta ta saci kallonta ta madubin motar dake fuskantar ta, kaitsaye idanun su suka shiga cikin na juna, wani irin faɗuwar gaba taji ganin ta kashe mata ido ɗaya tare dage mata gira, cike da jin kunyarta ta sunnar da kanta ƙasa adabarbarce ta furta"bana buƙatar komai, nagode da kulawar ku" murmushin gefen fuska sheikha mujeedat tayi tare da kallon Sarauta itama da murmushi akan fuskarta. "Kina ta farin ciki kamar ba ƴarki akayima Kishiya ba" Saurata ce ta faɗa da zolaya. bushewa tayi da dariya"ba zaki gane ba, wallahi Sonta na ke yi, yarinyar tana da Qualities da nakeson inga mace da shi, gaskiya munyi dacen suruka, Owais Ya more mata.." ta faɗa tana satar kallon Unaisah da ta sadda kanta ƙasa, duk tasha jinin jikin ta, tun da sheikha ta kashe mata ido. GIDAN AMARYA UNAISAH, wani kaya sai amale, Alƙalamina ya girgiza, an kashe min bakina, saboda bazan Iya misalta Haɗuwar Katafaren Gidan ba, har motar tayi parking a parking space Unaisah bata ɗago da idanun ta ba, saida taji alamun buɗewar Cardoors din sannan ta lura. Bata motsa ba, har saida suka rigata fitowa daga cikin motar, Sheikha mujeedat ta miƙa mata hannunta"mun ƙaraso gidan naki, my baby in-law, zaki iya tafiya kan ƙafafunki, ko kinaso in goyaki in shigar da ke ciki.."? murmushi tayi cikin sauri ta zura hannunta a cikin na sheikha, ta rukota ta fito waje, suka tsaya daga gaban ta, addu'o'i su ka soma yi mata tana amsawa da ameen daga bisani suka sanya mata albarka, tayi zaton zasu rakata cikin gidan ne amma sai taji akasin hakan. "Ki shiga daga ciki, ki jira mijin ki yana akan hanya..." Sarauta ce ta faɗa. Jiki asanyaye ta amsa da toh hadi dayi masu godiya, walking slowly ta nufi ƙofar shiga falo... A hankali ta ke satar kallon ginin kamar a mafarki saboda tagaza yarda gidan ta ne, ta razana da ganin haɗuwarsa, wai anan zatayi rayuwa, hasken electricity ta ko'ina tamkar da rana... Rantane ya bata basu tafi ba, slowly ta juya tare da kallon su, ile ko suna atsaye gaban motar su suna kallon ta. Tarasa gane meyesa ba'abari kowa nata ya rakota ba, sai ita kadai? Kamar mara dangi? Ita a yadda ta sani kawayen amarya suna kwana a gidan amarya, amma ita ko rakiya babu wanda yayi mata, sai dai Uwar ango da matar Kawunsa suka rakota, duk da haka taji dadin gatantata da sukayi.. Tana isa bakin kofar, ta ɗaura hannunta jikin glass din da niyar ta tura nan take kofar ta soma zamiyewa, Unexpected tana dira ƙafarta, ta tsinkayi muryar sa a cikin kunnanta. _My baby bride, I've been counting the minutes until you walked through that door, I'm so glad you're home, I've got a whole night of love planned for us_ arazane ta zare idanunta ganin bata ga kowa ba, ranta ne ya bata muryar na'ura ce sai dai tayi sak irin ta Owais. Numfasawa tayi tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya, tana ƙarasa shiga ciki, ƙofar tayi locking kanta, Kamar 6arauniya cikin sanɗa take tafiya sautin takunta na fita ƙwas!!ƙwass! Batasan Ina zata Nufa ba, ganin hanyoyi daban daban Cikin falon, na ƙasa dana stairs harda glass Lift.. again ta kuma tsinkayar muryar na'ura a cikin kunnanta tana yi mata kwatance inda zata ga bedroom ɗinta, a hankali ta nufi hannunta na dama, ta hau stairs ta 6ulo second floor, harta fara gajiya saboda matsewar da takalmanta su ka yi, rigar ma ta fitine ta, dakyar ta gano wata hadaddiyar ƙofa, nan take ranta ya bata shine bedroom ɗinta, ganin tana da security yasa ta ɗaura finger ɗinta, nan take ƙofar ta buɗe a hankali, wani spiral stairs tayi aran gama da shi, cikin 6acin rai ta bubbuga kafafunta, aranta ta ayyana babu abun da zai hana ta tu6e bridal gown din nan ko yazo ko bai zo ba, sai ta cire ta.. Hawa tayi kan staircase din tana cikin tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa akai.. A matuƙar ruɗe ta ɗan dakata dayin tafiyar tana kallon abun daya daure mata kai, wato ainihi stairs din da take akan shi kaitsaye zai kaita cikin Bedroom ɗin ta daga inda ta ke atsaye kan staircase din tana hangen katafaren Master Bedroom ɗin. Farawa da bismillah, a hankali take bin bedroom din da kallo tun daga kan katafaren Four poster bed din cikin sa irin na sarauniya, an ƙawata shi da 24 karat gold leaf, and precious gems, gaba dayansa wasu dogayen curtains ne kewaye da shi shara shara with a velvet canopy, gefe da gefen gadon wasu dankara dankaran bedside drawers ne ɗauke da crystal lamps, buɗe baki tayi kamar shashasha tabi ceilling din dakin da kallo wasu kawatattun Feather pendant lamp ne da ke haskaka tsakar dakin, tun daga gaban gadon har izuwa interior din dakin an shimfide shi da tattausan Ivory shag rug, very fury, daga saman shi Glass candles ne a cikin kwalba sai ci suke da wuta gwanin ban sha'awa, ga wasu floor Lamps na tsaye a tsakar ɗakin, daga can cikin kusurwar data kalli bangaren dama na bedroom ɗin seating area ne wata White corner couch ce zungureriya yar ubansu mai numfashi, an ƙawata saman ta da throw pillows, gabanta glass tables ne mai dauke da crystal vase, ga wasu bean bag chairs dake a gurin ɗumduma ɗunduma jefi jefi take ganin gift boxes akan rug masu kyan gaske nan take ta fahimci kyaututtukan da Surukarta tace zata gani a ɗakin ta ne, ko menene a cikin su? wani ni'imtaccen sanyin A.c mai haɗe da kamshin turaren ɗaki ne Ya ratsa kofofin hancin ta har saida ta lumshe idanun ta, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a ganin tsantsararren bedroom irin wannan ba! Har ta fara kokwanton anya mallakin ta ne? Saboda yafi karfinta, batajin zata iya kwana a cikin sa" Ni kaina da nake rubutawa na jinjinawa haduwarsa, A hakan ma bakomai zan iya fayyace maku ba, saboda ina jin tsoron ruwan alkamina ya kare gurin zayyana maku komai. A hankali ta ƙarasa saukowa cikin bedroom ɗin wanda gaba ɗaya furnitures ɗin cikinsa launin Bold pink and navy ne, aranta sai santin bedroom din ta ke yi, tana kara jinjinawa haduwarsa, har wani jinjina kanta takeyi irin ta ruɗen nan. Bata nufi ko'ina ba sai gaban gadon daya tsone mata ido, saman shi tabi da kallo lumbutsetsiyar mattress ce shimfide da bedsheet, rabinta a lullu6e ya ke da lallausan duvet, gaba ɗaya kewayen mattress din an jera throw pillows a sama, daga tsakiyar mattress din furanni ne launin pink and Red masu ƙamshin gaske.. Juyawa tayi baya tana karewa ko'ina kallo kamar wuyanta zai balle "Hmmmmm " ta furta sautin tana ruƙe qugun ta, gaba daya ta kasa furta kalma.. Wuce wa tayi ta nufi interior din dakin, daga cikinsa kana Iya hangen komai dake a cikin toilet ta cikin Glass wall, haka zalika data nufi ciki tayi arba da kofar dressing room wadda shima bangon glashinne tana hangen walk-in closet dinta, shaƙe da suturun sanyawa kamar a company, ga wani faskeken dressing mirror ɗan uban su... Babu ce kadai ke babu adakin Amarya Unaisah, amma fa an zuba mata tsadaddun furnitures na gani na faɗa. Daga ganin fasalin ɗakin zaka fahimci don masoya akayi shi.. A ƙalla ta shafe rabin awa tana bin ɗakin da kallon ƙurulla batare da gajiyawa ba, daga bisani ta fara tunanin Ina mijin nata ya ke? Taji shiru babu motsin sa, gashi taƙosa tagan shi saboda idanunta sunyi maraicin ganin shi, ta yi kewar shi, tun bayan da aka sanya bikin su bata ƙara ganin sa ba, kamar yadda yayi alƙawarin sai bayan auran su zai bayyana saboda ba zai iya jure kallon ta ba, still tana jin fargaban haɗuwa dashi a matsayin mijin ta. Tana tsaka da yin tufka da warwara, cikin ta ya fara kukan yunwa, ga wani irin baccin gajiya dake kokarin fisgarta har wani jiri jiri take gani a cikin idanun ta da ke lumshewa, a hankali ta dubi agogon bango, ƙiris ya rage afara kiran sallar isha'i, baiwar Allah tana ta sa ran ganin shi shiru baizo ba, tunawa tayi da wayarta da sauri ta shasshafa jikinta, yamutsa fuska tayi tunawa da babu wayar atare da ita, ta mantata a gida, taji takaici kamar tayi kuka.. Matsawa ta yi daga gaban tamfatsetsen dressing mirror din ɗakin, ta zauna kan kujerar gabansa, tana ta jiran ƙarasowar yaya Owais, don su ci dinner a tare kamar yadda suka ɗaukarwa juna alkawarin zasuyi a karo na farko da suka kasance ma'aurata 🌹 Batasan sa'adda ta fara yin gyangyadi ba, ga wata jarababbiyar hamma data cuka bakin ta, ta ɗan kishindiɗa bayanta jikin kujerar.. A lokacin data fidda rai da zuwan angon nata, bacci ya yi awon gaba da ita, ta saki baki da hanci tana ta yin minsharin gajiya. ~_________________________________🌹~ *DG OWAIS🔥* Around ƙarfe tara na dare daidai wata Hamshakiyar Mota ta biyo titin da zai sada ka da gidan Amarya. Idanunsa suna a lumshe yayin da ya ke a hakimce cikin backseat na hamshakiyar motar shi, ya ɗauki wankan dandatsetsiyar shadda Getzner wagambari Launin sky blue short sleeve shirt, da dogon wando, ya daura babbar riga ta alfarma daga sama, anyi mata aikin hannu har ƙyalli ta ke yi. ga wata haɗaɗɗiyar Hula daya daura a kansa, hakan bai boye lallausar sumar kan shi ba, ta lullu6e ilahirin ƙeyarsa har izuwa saman wuyansa. Wuyan hannunsa na dama na asanye da tsadaddiyar agogo ƙirar Rolex Daytona. gaba ɗaya Ƙamshin turarensa ya buɗe Motar, girma da kwanciyar hankali sun zauna masa, ta yadda ko fatarsa ka kalla zaka shaida hakan, sajen fuskarsa ya fi komai jan hankali, Yadda ya lumshe idanunsa sai ka yi zaton bacci ya ke yi alhalin kuwa idanunsa biyu tsabar qasaita ce ta angon Gimbiyar Izza. Babban Amininsa big guy Omar yana a zaune saman seat din gefensa, ya tattara hankalinsa akan iphone dinsa da ya ke daddanawa, kusan shigar su kala daya banbancin su shi bai sanya babbar riga ba. Wayarsa ce tayi ringing, picking yayi tare da kara wayar a kunnansa.. "Wifey, me ki ke yi har yanzu baki yi bacci ba"? On the other hand tace"yaya Owais nake nema, Ina kiransa baya shiga, pls idan kuna a tare ka ba shi wayar" kallon Owais ya yi tare da cewa"Hindu ce, tana son magana dakai" batare daya buɗe idanunsa ba ya mika masa hannu ya kar6i wayar ya kara a kunne.. Shiru yayi yana sauraron ta"big bro, ka yi hakuri ban shigo gida ba yau, bana jin dadine, inataso in tayaka Murna, Allah ya sanya alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba..." Ƙasa ƙasa da murya ya amsa da ameen My Lil' sis, nagode da addu'arki, karki damu, nasan halin da kike a ciki bai kamata kina fita ba, idan kinji sauƙi ranar Dinner sai ki shigo" "Okay yayana nakaina, nagode da kulawarka agareni, Ka gaishe min Amaryarmu" "Zataji, nima ki kula min da kanki," amsawa tayi da toh kafin su kayi sallama ya mika ma Omar Wayar. "Kamar kana da damuwa? nifa na lura da kai tun gurin ɗaurin aure babu annuri akan fuskarka" Bai iya furta kalma ba, yayi shiru yanayin fuskarsa ba walwala. "Owais, kar dai kace min har yanzu kana... " bai ƙare maganar ba ya yi saurin katse shi da cewa"pls ba sai ka faɗa ba, kamanta kawai, bana son ji" jinjina kai Omar yayi batare daya ƙara furta kalma ba. Officer din da ke driving dinsu kwata kwata bayajin abunda suke tattaunawa, Yana a driver's seat, a hankali Motar su ta ƙara so layin Gidan tana kokarin kunna kai ta main entrance, kamar ance ya dubi window glass din Motar, Unexpected idanunsa sukayi mashi Tozali da mutun ra6e jikin bangon gidansa kamar aljana. Da ruɗu akan fuskarsa ya furta"tsayar da motar anan.." nan take drivern ya tsaya.. Big guy yace"meya faru naji kace a tsaida motar bayan bamu kaiga shiga ciki ba"? Ya faɗa yana kallon fuskar Owais da hankalinsa ke akan abunda idanunsa ke nuna masa.. Bai iya bashi amsa ba, cikin sauri ya buɗe murfin motar ya fito ya nufi bangon dayake hango mutun a ra6e. kasantuwar akwai hasken electricity tamkar da rana shiyasa ya iya ganin ta dakyau. Fitowa Omar ya yi daga Motar ya bi bayan shi.. Daya kusa karasa kusa da ita sai ya ɗan rage saurin shi ya ƙura idanun shi akanta. babu kallabi akanta, kamar mahaukaciya, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, mayafinta da gyalen suna a ƙasa ta jefar da su. Babu alamun taji motsin mutum kamar wadda ta suma atsaye. Daga gabanta ya tsaya sa'ilin daya gane wacece yayi mamakin ganin ta da dadaren nan tsaye jikin bangon gidansa kamar aljana, cikin ruɗu ya furta"Batool....! Kece! Me kike yi anan"? Shiru bata motsa ba.. Ɗaga murya yayi"Batool... "! Kaitsaye kiran ya shiga kunnanta bata tsammaci shine ba, a firgice ta zabura zata arta wa na kare yayi saurin furta"ni ne Batool, yaya Owais, meke damunki ne.."? dakawa tayi a tsananin tsorace ta zare brown eyes dinsa akan fuskarsa, wani shock taji sa'ilin data saka idanunta a cikin nashi, ƙamshim turaren shi ya cika hancin ta. Omar daya karaso daga gefen shi ya tsaya yana dubanta cike da mamakin ganin ta. cikin rawar murya ta furta"yaya Owais.. Yaya Omar.. " "Batool me kike yi da daren nan a jikin bangon gidana? Keda wa ku ka zo ne"? Shiru ta yi batare data furta uffan ba. Big guy yace"ba ƴan matan amarya sun tafi gidajensu daga gidansu ango bayan walima ba? Ko tare da ke aka rakota nan ne"? Kunya ce ta kama ta daƙyar ta iya furta"inason ganin Unaisah saboda banyi bankwana da ita ba, shiyasa nazo" kallon juna su ka yi da alamun rashin yarda da maganarta. "Batool dare ya yi, nasan iyayenki sunata nemanki, Unaisah ta yi bacci yanzu, Muje na sauke ki gida" dg ne ya faɗa cikin sigar lallashi. "Mu tafi kinji"? Jinjina kai ta yi ba dan taso ba, da sauri Omar ya ɗauko mata veil dinta da dankwalin ta, ta kar6a ta ruƙe a hannunta, su ka yi gaba tabi bayan su, buɗe mata mota Omar yayi ta shiga ta zauna, Dg ya zagaya Other side din ta ya zauna. Omar ya shiga mazaunin gaba ya zauna. Kafin Drivern su ya tashi Motar Omar yace"ka fara sauke ni agidana" amsawa yayi da toh.. Tun da Motar ta soma tafiya babu wanda ya ƙara furta kalma, Batool ta yi shiru ta nutsu tana shaƙar kamshin turarensa. Idanunta sun ciko da ƙwalla, sai satar kallon shi take yi da rinannun idanun ta da suka kaɗa jawur, bakomai take ji ba face raɗaɗin rasa shi da tayi, kallon shi da takeyi ba karamin fama mata raunin son shi yakeyi ba, wata irin wutar son shi ce ke rura a cikin zuciyarta. Kwata kwata baisan halin da take a ciki ba, cos ya mayar da idanunsa a lumshe yana ta tunanin baby bride dinsa yasan tana can tana jiran ƙarasowar shi. Bayan sun sauke Omair agaban gidansa, yayi mashi sallama tare da fatan alkhairi kamar karsu rabu da juna bayan tafiyarsa, drivern ya karya kwana ya nufi gidan dr. shurem. Daga bakin ƙofar shiga yayi parking, jin shiru Batool bata da niyar fita yasa shi firta"mun ƙaraso gidan naku, ki sauka ki shiga" ko uffan batace ba, lamarin ya daure masa kai, a hankali ya dube ta, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, wani faɗuwar gaba yaji ganin yadda fuskarta ta 6aci da make up dinta sakamakon kukan data sha, jan baki har takan kumatunta, idanunta sunyi luhu luhu jawur da su. Aruɗe ya furta"me yake damunki ne? Kinyi kuka ne? Baki da lafiya.. " cikin shesshekar murya tace"kukan rabuwa da Unaisah ne" girgiza kai yayi"ban yarda ba Batool, ba gaskiya kika faɗamin ba! Saboda wannan yafi karfin kukan rabuwa da unaisah, sai kace mutuwa tayi? Bafa kasar ta bari ba, tana a cikin estate din nan aduk lokacin da kikaso ganinta zaki iya zuwa gidanta ko ita tazo gidan ku, babu wanda yayi maki iyaka da ita... " yanayin yadda ya ke yin magana cikin tauttausan lafazinsa ba karamin rikitata ya ke yi ba, jikinta sai tsuma ya ke yi ji take kamar ta rungume shi ko ta samu sassaucin abun da take ji game da shi. "Fadamin me yake damunki? Kada ki 6oye min Batool, Ni mai share maki hawaye ne, zan iya komai saboda farin cikin ki... " bai ƙare maganarba, ta rushe da kukan daya razana sa, ta gaza jure raɗaɗin, gaba daya ya rasa shawo kanta, Cikin shesshekar murya mai hade da haki ta shiga zayyana masa abun da ke damun ta. "Ya.. ya .. Owais, kak.. Ka auri Unaisah ni baka Aureni ba, bayan na fita sonka, Why don't you love me? ko ban cancanta kaso ni ba? Meyasa ni ba zaka soni ba! Ka san yadda nakeson ka kuwa, zan iya rasa komai in jure amma bazan iya jure rashin ka ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, babu mai fahimtana, mutuwa zanyi yaya Owais... " Hankalinsa Idan yayi dubu toh ya tashi, kalamanta sun razana shi, sam ya kasa katse ta kuma ya kasa furta kalma saboda ruɗanin daya shiga! Kyawawan idanunsa daya zare suna akan fuskarta data yi sha6a sha6a da hawayenta, soft brown lips dinta sun jiku da hawayen ta tana magana tana shesshekar kuka cikin kunci, Jikinta har kerma yakeyi kamar wacce sanyi ya kama. "Kai kaɗaine namijin dana so na rayu da shi, bazan iya yin rayuwa da waninka ba, kayi hakuri idan na 6ata maka rai, na kasa jurewa ne, ina da kunya ina da hakuri, amma wannan karon na rasa su gaba daya akanka, tun da nasan na rasaka na har abada... " daƙyar ta ƙarshe maganar saboda kukan daya sarketa, ga wani zafi da kirjinta ya yi mata. Dakyar ya iya tattara nutsuwar shi guri guda ya fahimci inda ta dosa. cikin sanyin murya yace"meyasa tuntuni baki faɗamin kina sona ba? Meyasa kika 6oye min Batool? kuma baki tashi faɗamin ba sai bayan dana auri Unaisah? What do you want me to do now? Ya kike so nayi yanzu? wani irin zurfin ciki ne kikayi um"? Kasa magana tayi sai kuka takeyi. "Fadamin tun yaushe kika fara sona"? Cikin shesshekar murya tace "tun ranar dana fara ganinka amma nima bansan ina sonka ba, bansan me nake ji agame dakai ba sai daga baya na gane a lokacin kuma na makaro saboda na gane Unaisah kakeso tun da daɗewa.. " bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"What made you fall in love with me"? batare data ɗago da idanunta ta dube shi ba tace"saboda ina sonka saboda kuma kyawawan halayanka da dabi'unka, amma wlh bayan wannan banso ka don wani abu ba" lumshe idanun shi yayi a hankali tare da sake buɗe su kan fuskarta"Allah bai haramtamin auranki ba, don haka ki faɗamin kina son in aureki ki zama ta uku a gidana"? a ruɗe ta girgiza kanta"ko da zan mutu bazan iya auren mijin Unaisah ba, ina kishi da ita akan ka, idan na aure ka zamu samu sa6ani da ita, ni kuma banason duk wani abu da zai haɗani da yar uwarta, wallahi na ƙwammace ciwon sonka yayi ajalina"! Jinjina kansa yayi ya dan numfasa kafin yace"Do you want me to divorce her and marry you?" afirgice ta dube shi, cikin sauri ta kawar da idanun ta daga nashi saboda kwarjinin da yayi mata. "Nasan zolayana ka ke yi, ba zaka ta6a sakin Unaisah saboda ni ba, ita kake so, itace za6inka, kada ka tausayamin don na fada maka halin da nake a ciki game da sonka... " katse ta yayi"dagaske nake Batool, zan iya sakin ta in aureki in har kin amince min"! Ya faɗa babu wasa akan fuskarsa Gabantane Ya faɗi a ruɗe tace"har abada bazan ta6a bari ka saki Unaisah ba, kwara ni na ƙare rayuwata batare da nayi aure ba akan dai ni in rabaka da ita don ka aureni, kuma tafi dacewa da kai, tafi ni cancanta da kai... " murmushin gefen fuska ya yi still idanunsa na akan fuskarta, yafi kowa sanin kunyarta da kamun kanta, Yasan yadda Batool take jin shakkar shi shiyasa yayi mata uziri saboda ya fahimci takasa jure wa ne.. Ɗaga murya yayi tare da furta"ka maidani gidana" Drivern Ya amsa mashi da Okay Sir.. Aruɗe tace"zan sauka, Yanzu zan sauka" Ta fada tana kokarin ture murfin motar don ta fita sai dai ta kasa buɗe ta, a lokacin har drivern ya tashi motar. "Ki kwantar da hankalinki, Zan kaiki gurin Unaisah ne, Ko baki son ganin ta"? Girgiza kai tayi"inason ganin ta, amma ai ka fadamin tayi bacci, na hakura zuwa ranar dinner mun haɗu, Gida nakeso na koma banjin dadi inajin bacci..." a tsorace tayi maganar kwata kwata babu nutsuwa a tare da ita, tayi zaton zai mayar da ita gidanne don ya faɗa ma Unaisah abin da ta gaya masa duk da tasan mutunne shi mai sirri bazai iya yin hakan ba. "Yaya Owais dan Allah ku aje ni anan, bansan zuwa gidanka, ni banaso Unaisah tasan me na fada maka zata ji ba dadi, nasan nayi kuskure amma bazan ƙara ba.. " cikin kuka ta faɗa. Bai saurare ta ba, ya yi shiru tare da kawar da idanunsa daga kan nata. Baiwar Allah duk tabi tasha jinin jikin ta. Bayan motar ta ƙaraso Cikin gidan, A parking space drivern ya tsayar da ita, cardoors din suka buɗe, a tare suka fito Yana a 6angaren hagu tana a dama. Cike da mamaki ta ke bin katafaren ginin da kallo. "Mu shiga ciki" ya fada tare da yin gaba, cikin sanyi jiki tabi bayan shi.. Tunda suka shigo Main falon Ta soma zazzare idanunta tana ƙarewa ko'ina kallo, ta razana da ganin haɗuwar Furnitures din falon daga gani an zuba dukiya ta fitar shari'a. Ganin ta toge a falo yasa shi juyowa tare da kallonta, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsunta "Ki shiga tana a ɗaki" ya faɗa tare da nuna mata ƙofar bedroom da yatsansa, amsawa tayi da toh tana jin wani irin faduwar gaba kamar anayi mata lugudan ta6are a kirjin ta, tarasa meyasa take jin kamar wani abu badaidai ba.. Da sallama abakinta ta shigo bedroom din, har saida gabanta ya fadi rass saboda razanar da ta yi na ganin ƙawatuwar kayan ɗakin, kamar na sarauniya, tayi zaton zataga Unaisah aciki sai dai bata ganta a ko'ina ba, bata kawo komai aranta ba, ta soma ƙwala mata kira "Ukhtyna! Unaisah! Kina ina ne? Batool ce, ki yi hakuri nazo da daddare inaso nagan ki ne yanzu zan tafi" shiru ba'a amsa mata ba, ranta ne ya bata kota shiga toilet ne hakan yasa tayi tunanin komawa falon don ta faɗawa Yaya Owais. Juyawa tayi da sauri tana ƙoƙarin fucewa daga dakin Ya kunna kai ciki, Kirjinta ya bangaji na shi, da sauri taja baya adabarbarce ta furta"am sorry bansan zaka shigo ba, na duba banga Unaisah ba, ko tana a cikin toilet ne"! Ta faɗa tana zare idanun ta. "Unaisah bata anan, tana a gidan ta"! "Yaya owais... Ban.. Bangane me kake nufi ba, nan ba gidan ta ba ne? " bai kula ta ba, Ya nufi Ciki, Kayan jikinsa Ya soma ragewa, Batool ta razana da ganin yana tu6e kayansa saida ya rage daga shi sai short. Jikinta na 6ari ta nufi kofar dakin, ta soma kokarin budeta ta kasa, duk tabi ta ruɗe.. "Yaya Owais, ƙofar ta kulle, ka buɗe min in tafi gida tun da Unaisah bata anan, daddy zai min faɗa" Takun tafiyar sa ta jiyo daga bayanta, tayi zaton bude mata kofar zaiyi.. Kwatsam ta tsinkayi voice dinsa a cikin kunnanta "Batool, there's something I've been wanting to tell you for a long time" (Batool akwai abun da na dade inaso na faɗa naki") Zare idanu tayi batare data juyo ta dube shi ba. "Na daɗe ina sha'awar son kasancewa da ke ban ta6a bayyana maki ba saboda bana son na zubda mutuncina a idanun ki..." bugun zuciyarta ne ya tsananta, jin furucin chief, rudu da al'ajabi ya hana ta furta kalma.. "tun da kina sona, Ki bani hadin kai, babu wanda zaisan munyi, daga ni sai ke, zai zama sirri a tsakanin mu" A firgice ta juyo tare da duban shi, tsabar rudu yasa ta fara ganin kamar ba Chief bane. Sexy abs dinsa ba ƙaramin rikitata yayi ba. Murya na rawa tace"yaya Owais, kasan me kake faɗa kuwa? Kai da kanka" girgiza kai tayi"ni nasan bayin kanka bane, baka acikin hayyacinka, saboda Ba halin ka bane, Sharrin shaiɗanne"! Kashe mata ido yayi tare da ɗage mata gira, ya dan lashe pink lip dinsa. "ina a cikin hayyacina Batool, ba ku ma shaiɗan bane ke tunzurani ba, ni ne da kai na..." zare idanu tayi tana girgiza kanta'yaya Owais meke damunka ne? kamar wanda yasha kayan maye! kana da aure, kuma yau ka ƙara aure, idan kana bukatar ka kawar da abun dake damunka, ka tafi gurin matayenka, sune muhararramanka da Allah ya halatta maka ka sadu da su, amma bazaiyiwu in baka hadin kai ba! Kasan babu kyau, ba zan bari mu sa6ama Allah ba, kai mutumin kirkine mai tsoron Allah da son taimakon, ba zan ta6a bari shaidan Yasa ka aikata abun da zaka sa6ama mahaliccinka ba..." tun da tafara magana Ya kafe kyawawan idanunsa akan tausasan lips dinta kamar tana ƙara tunzura shi, kwata kwata baya fahimtarta. Sauke idanunsa yayi kan dukiyar fulaninta da su ka cika kirjinta sun matse gaban rigar kamar zasu fasa ta, Allah yayi ta da sura kamar umminta.. Yawu Ya haɗiya Yana shaƙar ƙamshin Humran ta.. Ganin yadda yake bin surar jikinta da kallo yasa ta ƙara tsorata da shi ta rasa gane meke damun yaya Owais"? Ta kasa yarda dagaske ne maganar daya furta, Ranta ne Ya bata kodan sun ke6e da junane? Dama kuma babu kyau mace da namiji su ke6e, can kuma ta tuna meyasa ya kawota gidan nan bayan babu Unaisah a ciki hakan na nufin dama can da wata manufa yayi hakan, girgiza kai tayi, zuciyarta ta raya mata Watakil yasha ƙwayane ko kuma zai iya yiwuwa gyaran jikin da tayi irin na Unaisah ne yasa shi kamuwa da sha'awarta, amma meyasa ma zaiji hakan? Bayan matayensa sunfi ta da komai a tunaninta kenan.. "Batool, ba zaki iya biyamun buƙatana ba? Sau ɗaya kawai, ki taimaka min, Zan iya rasa raina, bakiji yadda nake jin kwaɗayin In kasance da ke ba..." ya faɗa yana marairaice mata fuskarshi yadda kasan ba Chief namu ba, Ikon Allah Ikon Gaske.. Yawu mai zafi ta hadiya "Yaya Owais, kayi hakuri, ni maiyi maka komai kakeso ce don in faranta maka rai, nasan har abada ba zamu iya biyanka ba, amma wallahi bazan ta6a bari mu sa6ama Allah ba, ina jin tsoron shi, kuma banaso mutuncinka ya zube, ka dubi girman Allah, dan Son da kake ma ma'aiki manzo SAW ka tausayamin, nazo duniya bata hanyar aure ba, idan na amince maka muka aikata alfasha rayuwata zata gur6ace ne, pls kada ka matsa min, ka barni in tafi gida..." tana karashe maganar jikinta na kerma cikin sauri ta juya da niyar ta buɗe ƙofar. Batai Aune ba, Kwatsam Taji Ya tallabe waist dinta da tafukansa, Ya cuccu6eta ya daga ta sama tare da juyawa da ita Ya nufi katafaren gadon dakin, tuni mayafinta ya fadi kan floor. Fashewa tayi da kuka tana fadin "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! yaya Owais ka da Ka cutar da ni, na roƙe ka, ka barni in tafi gida, ka da ka yi amfani da son da nake maka gurin lalata rayuwana.." bai dakata ba har saida Ya Jefar da ita kan gadon, Ta faɗa ta rubda ciki, silar hakan yasa yalwatacciyar sumar kanta ta baje har saman mattress, jikinta na 6ari tayi saurin miƙewa zaune, Ta dube shi Yayin da ya ke kokarin zamiye short dinsa. Fashewa tayi da kuka tana fadin "Ni bazan iya cin amanar Yar uwata ba, bazan sabawa mahaliccina ba, kada ka goga min kazantar zina a jikina, Idan kanason In kwanta dakai har kwara ka aureni, zanyi maka abunda kakeso tunda ina son ka, amma wallahi ban ta6a sonka da zina ba" Runtse idanunta tayi tare da daddafe kanta da tafukanta, ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata abun daya faru tsakanin iyayenta kafin suka same ta, tsigar jikinta ce ta soma tashi, shatun jijiyoyinta suka fito ruɗu ruɗu saman fatarta, Lokaci ɗaya ta buɗe idanunta da suka kaɗa jajir, Agigice Ta zabura zata dira daga kan gadon yayi saurin haurawa kan gadon ya damƙo kafafunta tare da janyo da ita, ya rungumeta akan faffadan kirjin shi, kuka ta ke yi kamar ranta zai fita. Cikin shesshekar kuka take fadin"dan Allah yaya Owais kada ka cutar dani, bazan iya jurewa ba, Mutuwa zanyi, ina son na tafi gida, Idan ka aikata min hakan Iyayena zasu yi bakin cikin da zaisa su rasa ran su, nima zan mutu da bakin cikin abun da kayi min... " a hankali ya soma shafa sumar kanta yana tattare ta guri guda yana jin wani irin yanayi na shauƙin ta. Yana Jin yadda Zuciyarta ke bugawa da karfi, Numfashinta na fita a hargitse. Unexpected taji Ya furta"ki daina kuka, bazan iya cutar da ke ba, zan mayar da ke gida, amma sai kin shiga toilet kin wanke fuskarki sannan zansa akawo maki abinci ki ci.." wata nannauyar ajiyar zuciya data sauke har saida yajita a kirjin shi. Dakyar ta haɗiye kukan, taji nutsuwa da kwanciyar hankali sun zo mata. raba jikinta tayi daga nashi idanunsu suka shiga cikin na juna, tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda kumatunta suka yi ja, labbanta da fatar idanunta sun kumbura, sun yi jawur, hakanan ya tsorata baiwar Allah bata ji ba, bata gani ba. "Hankalina ba akwance yake ba idan ina a tare dakai, ka maidani gida kawai" "Kiyi abunda nace idan kina son komawa gida" da sauri ta amsa da toh, ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet ta shige tare da jan ƙofar ta datse don karya farmaketa a ciki. Ƙayataccen murmushi yayi. Almost mins yana jiranta before Yaji motsin bude toilet door. fitowa tayi daga ciki ta toge a bakin kofar, saukowa yayi daga kan gadon, da hannu Ya nuna mata kofar closet Room"ki shiga, Ki sauya kaya, na jikinki sun yamutse, banaso suga abunda zai sa su zargi wani abu" cike da rashin yarda ta furta"basaina shiga ba, idan munje gidan zanyi musu bayani" Ɗaure mata fuska yayi"zakiyi abun da nace maki ko kuwa"? Cikin sauri ta nufi closet room ta shige. Jim Kaɗan ta fito Jikinta sanye da abaya fara, tayi rolling mayafi akanta, Yana a zaune bakin gadon yabi ta da kallo from head to toe, ta yi mashi kyau a cikin abayar, ta fito a balarabiyarta. Miƙewa yayi tare da nufar kofar dining room "ki biyoni" cike da jin shakkar shi tabi bayansa. Saman dining chairs suka zauna suna fuskantar Juna, ga kayan dinner shaƙe da table din gabansu, ya lura har yanzu a tsorace take da shi, duba da yadda Jikin ta ke kerma.. "Zaki iya ci da hannunki! Ko in baki abaki"! Da jin Hakan Yasa cikin sauri ta ɗauki glass of juice me sanyi ta kwafa abaki tana sha tana satar kallon shi yayin daya sadda kan shi ƙasa sai taga kamar murmushi ya ke yi amma bata gaskata hakan ba. Bai yi zaton yarinyar ta samu tarbiya har haka ba, da wuya ya jaraba mace da tayin kanshi taƙi amincewa sai akan Batool, tsoron Allahnta, da kamun kanta, da kuma yardar da tayi masa sunfi komai Jan hankalin shi a gare ta. Satar kallonta yayi, tana tsaka da cin meatloaf mai dan karan daɗi, Yatsun hannunta nata kerma kaf kaf kamar wacce sanyi ya kama, Allah Allah take ta gama ta tafi gida. Kaɗan taci ta dakata, tare da duban shi "yaya Owais, na koshi, dama dazu naci abinci gidan biki, zan tafi basai ka kaini a mota ba, Unaisah tana can tana jiran ka, kaga dare ya yi sosai" Yanayin yadda ta ke yin magana cikin sanyin murya ba ƙaramin jan hankalinsa ta ke yi ba. Bata ƙare maganar ba, Ya katse ta da cewa"ban yarda kin koshi ba, You're still hungry, Either eat more, or we'll stay here forever" arude ta soma cuccusawa abaki, taci samosa, taci spring rolls, ta hada da straw berry shortcake, Tana gamawa ta kai hannu ta dauki milk shake ta sha sosai duk yana kallonta, bakin ta yayi dama dama da cake. Tana haki ta furta"yaya Owais na ci da yawa yanzu, zan tafi" bata jira amsar shi ba ta mike tana zazzare idanun ta. "Muje nakai ki a mota ta, idan kikayi min gaddama zamu kwana anan ne" a firgice ta amsa da toh. "Ki jira ni a falo, zan shiga ciki in sanya suturana" amsawa tayi da toh. Akan idonta ya fuce daga falon ya nufi Cikin bedroom. Cike da zullumi take ta jiran shi, babban tashin hankalinta, ummin ta da daddynta tasan zasu nemeta, gashi ta manta ma inda ta jefa wayarta. Tasan idan ta koma gida zasu iya yi mata faɗan daren da tayi a waje, kuma zasu tuhumeta akan Kayan da ta canza a jikin ta, Ya ilahi ta furta tana dafe goshinta daya jike da gumi. Fitowa yayi jikin shi sanye da jallabiya ash, ya ruƙe car key dinsa a hannu. "Na manta kayan dana cire a closet room" ta faɗa batare da ta bari sun haɗa idanunsu ba. "Zaki iya zuwa ki dauka" cikin sauri taje ta ɗauko kayan ta ƙuɗundunesu a hannunta. Bata iske shi a falon ba, hakan yasa ta fito harabar part din, a parking space ta hango shi a tsaye Ya jingina bayan shi jikin motar shi, ba wadda sukazo gidan da ita ba. Kafin ta ƙaraso Ya buɗe mazaunin driver Ya shiga, tana ƙoƙarin buɗe back seat muryarsa ta katse ta"Am I your driver"? Cike da izza ya furta. Da sauri ta dawo mazaunin gaba Ta bude ta shiga ta zauna tana ta faman sauke a jiyar zuciya, ta ɗanyi mamakin ganin shi ne zai yi driving da kan shi bayan bata saba ganinsa yana driving ba. Bayan ya tashi motar, ya yi reverse ya fusgeta da matsakaicin gudu motar ta fuce daga gida. ~____💘_____💋______🌹______💕_______💗________🔥~ *🔥UNAISAH💗* tana tsaka da sharar baccin ta, Kwatsam hasken ɗakin Ya ɗauke ɗuff, sai na Candles da ke ci, ƙarar qira'ar alqur'anin daya karaɗe ɗakin ne Ya farkar da ita a firgice ta farka tana zare sleepy eyes ɗin ta, wata irin faɗuwar gaba taji sa'ad da ta lura babu hasken fitilun ɗakin sai na candle lights! Zuciyarta ta shiga harbawa da sauri da sauri kamar ana mata lugudan ta6are a ƙirjin ta. Bata ta6a tsintar kanta a cikin tsoro irin na wannan lokacin ba tun bayan rabuwarta da kurkukun ƙaddara! Abu biyu ne yazo aranta, watakil Yaya Owais ne Ya kashe hasken ɗakin sa'ilin da take bacci don ya bata mamaki, ko kuma Electricity din gidan ne Ya samu matsala, gaba daya ta manta menene yayi silar farkawarta daga bacci. A tsorace ta furta"Yaya Owais? Kai ne ka shigo? Kana ina? Nasan kaine ka kashe min hasken ɗaki, dan Allah kayi min magana, gaba daya na tsorata.." Ta faɗa tare da miƙewa daga kan kujerar, jikinta nata kerma kamar mazari. La66anta na kerma ta kuma cewa"hubby, pls kada ka wahalar dani, bazan iya jurewa ba, idan kaine ka yi min magana ko hankalina ya kwanta, tun ɗazu nake jiran zuwanka... " bata ƙarashe maganar ba, Unexpected ta tsinkayi sautin takun tafiya a cikin kunnanta daga bayanta, tuni tasha jinin jikin ta, jin yaƙi amsa mata yasa tayi tunanin ba ya ya Owais ba ne, wani ne ya shigo gidan, nan fa ta ƙara shiga tashin hankali, tsoro ya hana ta juya ta fuskance shi, sai faman zazzare idanunta ta ke yi, dakyar ta iya ƙyalla idanun ta ta cikin mirror ɗin gaban ta ta soma hango shi da taimakon Candle lights... Walking magestically ya ke nufo cikin bedroom ɗin kamar baison taka ƙasa, daga ƙasa ta soma ƙare ma shi kallon ƙurullah da tsantsar ruɗani da fargaba saboda bata tantance wanene ba, tsayin sa ya zarce na Chief Owais. Sanye ya ke cikin shiga ta larabawa, wata hadaddiyar dishdasha long tunic, launin ivory white ta bayyana tsantsar zazzafar surar sa mai matuƙar jan hankali, daga fadadan kafadunsa wata madaidaiciyar bisht cloak ce (alkyabba ) launin Golden-brown, daga gefenta da bakin ta gaba daya adon duwatsu masu daraja ne lullu6e da rigar, sai kyalli su ke yi suna sheƙi, wuyan hannunsa na dama yana asanye da Expensive rolex Watch irin wadda sai dan wane da wane su ke sanyata, both mid fingers dinsa suna a sanye da gemstone-encrusted rings, yayin da kafafunsa ke asanye da hand made Leather arabian shoes, mayar da idanunta tayi akan fuskarsa cike da fargaba take kokarin gano wanene sai dai kash rabin fuskar tasa yayi covering dinta da Gold leaf Mask, gaba ɗaya kansa a naɗe ya ke da turban, irin naɗin larabawa, daga kasan rawanin doguwar sumar kansa ce ta zubo, wutsiyoyin kitsonsa biyu suka hauro ta saman kafaɗarsa har izuwa kan broad chest dinsa, daga bayan sa wata sumarce har mid back dinsa mai kyan gaske tana ta sheƙi brown shar da ita.. Duk ƙamshim da bedroom din ta ke yi saida Ƙamshin turarensa ya disashe shi, wani irin sweet fragrance mai rikita shauƙin bawa, daga yanayin tafiyarsa ta fahimci yana da izza da qasaita daga gani mutum ne mai tsantsar ilmi da aji kuma wayayye mai cikar kamala da nutsuwa. Unaisah ta gama ruɗewa, Tsoro da fargaba suka cika Zuciyarta da ke tayi mata dakan sakwara, aranta tana ta tunanin wanene wannan Hamshaƙin saurayin? shin tayaya akai ya shigo gidan Auranta? Kwata kwata bata yarda Mutun ne ba, tafi alakanta shi da jinsin jinn saboda zubin sa! Anya kuwa Yaya Owais ya sanya malamai suyi safkar alkur'ani a gidan kafin ta tare? Tana kokwanto saboda gayanan tunkan aje ko'ina ta fara ganin ifritun Aljani.. Yawu ta haɗiya mai zafi makoshin ta ya bada sauti ƙutt, cikin rawar jiki ta fara tunanin mafita! Gashi tamanta waya agida balle ta kira wani ta fada masa Aljani Ya kawo mata farmaki, ita kadai baiwar Allah, tunanin guduwa tayi duk da tasan ba lallai takalman kafarta su bata hadin kai ba saboda tsinin su. Ganin Ya kusa karasowa cikin ɗakinne Yasa Ta fara neman gurin da zata 6uya cikin rawar jiki ta soma ja da baya cikin sanɗa don karya ji takun ta. zukunnawa tayi ƙasa da rarrafe ta dinga yin tafiya ta nufi karkashin gado ta shige ciki ta 6uya gabanta nata faɗuwa, aranta tana mai cigaba da ambaton La'Ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin" ~________________________________🌹~ A hankali ya ƙarasa shigowa tsakiyar dakin, cikin takun ƙasaita ya nufi gaban gadon, Unaisah dake a karkashinsa tana leƙen ƙafafunsa da ke tunkaro gadon, tashin hankali tuni gumi ya wanke fuskarta, runtse idanunta ta yi gam ta dinga karanto Ayatul kursiyo a cikin zuciyarta da sauran addu'o'in neman kariya daga sharrin jin. A hankali ya zauna daga gefen gadon ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya.. Zuciyarta ce ta tunzurata akan ta duba ƙafarsa taga idan irin na mutanene ko kofaton jaki irin na aljanu kamar yadda Aunty Danejo ta ta6a bata labarin cewa Idan aljanu suka yi suffar mutane zaka iya gane su ta kafarsu saboda ba irin na mutane bane, Kofaton Jaki gare su. Cikin sanɗa ta zuƙunno da kanta ta ƙurawa fatar ƙafarsa ido, Har saida gabanta ya faɗi ganin kafar tasa fara sol kamar ta jariri yadda kasan bai ta6a taka ƙasa ba, hasken fatar sa irin pure shining white ɗin da ba acika samun shi ba ne naturally. Ruɗewa tayi, duk da tana kokwanton kamar mutunne tun da bata hango kofaton jaki ba, zuciyarta ce ta raya mata idanunta ne suke nuna mata ba daidai ba, watakil owais ne girgiza kai tayi in har Owais ne bazai ta6a zama fari ba. Ganin Ya motsa kamar ya miƙe yasa ta katse zancen zucin nata, kanta harya fara ciwo, ga yunwa da bacci tana ji, ga zullumi da fargaba sun cika zuciyarta.. Shigewa toilet ya yi, tana lekensa taga glashin bangon toilet din ya disashe, aranta ta ayyana ya koma mazauninsa kenan, tunda ance toilet gurin zaman aljanu ne, cikin sauri da rawar jiki ta fito da niyar ta fece, kwatsam ta hango tamfatsetsiyar waya ajiye saman bedside drawer, fasa fita tayi Yatsun hannunta na kerma ta dauki wayar ta danna number din daddynta ta kira ta kara a kunne cike da fargaba.. Unexpected wayar Taj dake aje kan bedside drawer ta fara ringing, at same time suka farka. "Wanene Ke kira" ta tambaya tana duban Taj daya dauko wayar yana kallon screen dinta yace"ban sani ba amma bari na ɗaga maybe wani emergency call ne" Amsawa tayi da ''to'' Picking yayi ya kara a kunne ko sallama batayi ba ta fashe da kuka kamar ranta zai fita. Har Benazir saida taji yo kukanta, hankali atashe suka dubi Juna.. Har suna haɗa baki gurin furta"Unaisah! Meke damunki? Meyasa ki kuka um miya faru wayar waye kuma wannan"? Dakyar ta shanye kukan, Cikin shesshekar murya tace"yaya Owais baizo ba, Inata jiran shi ni kadai agidan tsoro nake ji, kuma yanzu wani ifritun aljani ƙaton maridi ya shigo dakina, baka ganshi ba daddy, dogo fari fat kamar fatalwa ya saka kayan larabawa, tun dazu nake boye a karkashin gado har saida Ya shiga toilet sannan na samu na fito har na dauki waya, wallahi daddy Mutuwa zanyi in baka zo ka ɗauke ni ba, kashe ni zai yi, dan Allah daddy ka zo tare da Baba Imam ya kora mana aljanun gidan da ayar Allah, in har ba so ku ke ku rasa ni ba.... " daƙyar ta ƙare maganar.. Hankalin Benazir idan yai dubu to Ya tashi, Taj ne kadai bai ɗaga hankalinsa ba, kallon juna su ka yi. Kafin wani ya furta kalma kiran ya katse. "Bazan iya jira ba, zanje kawai na tafo da ita, tayaya zai barmin ƴa a irin wannan lokacin tana ta jiran shi, wunin yau ko abinci bata ci ba saboda sunce zasu ci agidan su, gashi harta fara gane ganen aljanu" Cikin 6acin rai ta ƙarashe maganar tana ƙokarin saukowa daga kan gadon Taj yayi saurin ruƙo hannunta, cikin fushi kamar zatayi kuka tace"kana fa jin abun da tace! So ka ke mu rasa ta ne? Tun kan aje ko'ina har ya fara nuna rashin kulawa akanta! Ba fa dan na gaji da ita na bashi ita ba" Murmushin gefen fuska Taj yayi"Ummu Unaisah, Ki kwantar da hankalinki, ruɗewa tayi ne amma ba aljani bane tagani, Mijin ta ne" Aruɗe Benazir tace"ita fa da kanta tace aljani ne! Unaisah batasan fuskar Owais bane da zata rasa gane shi!? ina Owais yaga hasken fata? idan kai baka dauki maganarta serious ba nina ɗauka.." tana ƙarashe maganar ta fusge hannunta daga nashi ta nufi closet ta dauko veil ta yafa. "Karki Fita Benazir, ban baki izni ba, ki dawo zanyi maki bayani.." "Ai fa sai ka yi Tajo, kaima kasan ba sauraron ka zan yi ba... " ~____________________________________🥺💘~ _A 6angaren Unaisah, batasan ya akai kiran ya katse ba, ta dinga trying baya zuwa, kamar ta yi hauka, batai aune ba, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsinsa abayanta, Kamar numfashinta zai ɗauke tsabar razana, bugun Zuciyarta ya tsananta, gumi Ya cigaba da tsastsafo mata ta saman goshinta da hancin ta, wani irin tsoro ne ya ziyar ce ta, duk tabi tasha jinin jikin ta..._ Kafin tayi wani ƙwaƙƙwaran motsi sanyayyar Muryarsa ta ratsa kunnanta"My Phone.... " Ya Ilahi Wani irin ruɗanine Ya cika zuciyarta jin muryar ifritun Aljanin tayi mata shige da ta wani wanda ta daɗe da rasa shi arayuwar ta, muryarsa da ko a mafarki taji ta saita shaideta, ko da tana a cikin maye ne.. Kwata kwata batasan wayar wacece ta ɗauka ba, sai da taji maganarsa, tana zazzare idanu ta ɗan saci kallon wayar da ta ruke a hannun ta, ƙara zare idanunta tayi tamkar ƙwayar idon zata faɗo ƙasa a kiɗime take kallon hoton ta da ke akan Wallpaper ɗin wayar ganin abin ta ke kamar a mafarki kamar idanunta sun samu matsala....! Mutun ɗaya ta ta6a turama hoton ta whatsapp dinsa, kuma a time din data tura masa hoton view once ne ba a iya ɗaukarsa ko ayi sharing even screenshot amma tayaya ya samu hoton? Nan ta ke ta ƙara tabbatarwa kanta ba mutun bane, sakin wayar tayi ta faɗi kan floor Ƙarfin halin juyawa tayi slowly ta fuskance shi cike da fargaba ta ɗan saci kallon fuskarshi, bata iya ganin ta dakyau sai dai Kyawawan sleepy eyes din sa waɗanda ke a lumshe Ko a mafarki taga me irin tsayuwarsa sai ta gane shi, Amma tagaza yarda da abun da zuciyarta ke raya mata, a ganin ta bame yiwuwa ba ne, cike da fargaba ta ɗan matsa dab da shi ta ɗan tsaya jikin ta na kerma ta ke ƙare mashi kallon ƙurulla... A ranta tana ta ambaton La'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.. Cikin rawar Murya tace"Bab.. Bawan Allah kaji tsoron Allah kada ka cutar dani! Ka faɗamin Wanene Kai? Mutun ko aljan? Kasan ni ne? A ina ka sami hoto na? Me kuma ya kawo ka gidan aure na har cikin ɗaki na"? shiru babu alamun zai furta kalma, ko motsi bai yi ba bai kuma ɗaga idanunsa ya dube ta ba.. Almost minutes.. Batasan ya akai take jin wani abu a zuciyarta wanda bazata iya misalta shi ba, kuma duk duniya mutun ɗaya ne idan tana atare da shi a kusa da ita take jin wannan abun... Kafin ta ƙara furta kalma, taga Ya motsa ta ɗan zare ido tana duban shi, gently ya sanya hannu ɗaya akan fuskarsa ya soma ƙoƙarin cire mask ɗin sa.. Lokacin daya zame Mask din gaba ɗaya Ya sake shi Ya faɗi ƙasa wata irin zabura Unaisah tayi kamar zata watsa aguje saboda ruɗewar da ta yi, Ilahirin jikinta Ya kama kerma kamar mazari, gaba daya ta rikice tabi ta ruɗe ta razana da ganin fuskar mutumin data rasa tsawon shekaru akan fuskar Ifritun Aljanin nan, tsigar jikinta duk ta tashi, wani irin faduwar gaba take ji a kirjinta kamar ana buga ganguna. Kyakkyawar fuskarsa da bazata taba manta kamanninta ba saboda haddar da tayi mata. cikin ɗimuwa ta soma murza idanunta da yatsunta sosai don taji aranta gizau ya ke mata bashi bane, saida ta gama murje idanun ta buɗe su still babu abun daya sauya yana nan yadda ya ke. Kamar mahaukaciya Ta bushe da dariya lokacin ɗaya kuma takama kuka tana fadin"ba zaka ta6a bari in zauna lafiya ba, ka mutu ban huta ba, fatalwarka bazata bari in zauna gidan aurena lafiya ba, ka hana zuciyata sukuni a gidan iyayena nan ma ka biyoni don ka tarwatsa aurena! Meyasa zakayi min haka? ya ka ke so nayi da raina? ko so ka ke nima na mutu nabiyoka mu rayu a kabari ɗayane um"? tuni idanunta sun kaɗa jajir. "Idan so kake mu rayu a tare, ka kashe ni sai mu koma kabarin ka a tare, nima zanso hakan saboda bana jin dadin rayuwana batare da kai ba.." ta ƙarashe maganar tana matsawa kusa da shi, kamar ancire mata tsoronsa da fargabansa daga zuciyarta, tun da ta sama ranta cewa fatalwarsa ce. A hankali ta kwantar da kanta saman broad chest dinsa, ta zagayo da hannayenta ta saman bayansa, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin wani bakon al'amari atare da ita, bugun zuciyarta a cikin nashi, nutsuwa da kwanciyar hankalin da taji a jikin ta sa'ilin data haɗa jikinta da nashine yasa ta kara ruɗewa, ta dinga jin kamar shine ba fatalwarsa bace tunda in fatalwace bazata iya riqeta ba duk da haka ta kasa gaskata cewa Danish ne. Cikin kuka tace "Ka ɗauke ni, mu tafi ƙabarinka, mu rayu a tare, bazan ta6a gudun fatalwarka ba my Man, nasan nice na hanaka kwanciyar kabarinka" ta riga ta sallama masa kanta yayi duk abin da zai yi. Duk wani motsinta yana jinshi a jikin sa, bugun zuciyarta, shesshekar kukanta, fitar numfashinta, dumin jikin ta da ƙamshin ta. Tayaya zai iya fahimtar da ita cewa ba fatalwarsa bace! bai mutu ba yana araye? Tayaya zai iya kare kansa daga gare ta, yana jin fiye da abun da take ji aranta, banbancin ɗayane shi yasan tana araye kuma ya nisanta kanshi da ita saboda manufar sa.. Yana jin yadda take ƙara narƙe mashi a jiki kamar zasu koma mutun ɗaya... Numfasawa yayi a hankali cikin nutsatstsiyar muryarsa ya furta. *_"UNAISAH, I'M NOT A GHOST! I'M NOT A DEMON AS YOU THINK, I'M NOT DEAD, I'M ALIVE, I'M YOUR DANISH! YOUR SHIELD, I KNOW IT WILL BE HARD FOR YOU TO BELIEVE ME"!*_ (UNAISAH NI BA FATALWA BA NE! BA KUMA ALJANI BANE KAMAR YADDA KIKA ZATA, NI BAN MUTU BA, INA ARAYE, NI NE DANISH DINKI! GARKUWAR KI, NASAN ZAI YI WUYA KI YARDA DANI..... " ) bai kai ƙarshen maganar tashi ba ganin yadda ta fisge jikin ta daga nashi, ta sanya runannun idanunta a cikin kyawawan idanun shi farare tass kamar an ɗiga zaiba, Reddish iris dinsa Ya ciza launinsa kyau iya kyau, cikin ruɗu da razana ta ke girgiza kanta, yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri kan kuncin ta.. La66anta na kerma tace"Ba zai ta6a yiwuwa ba, sai dai idan mafarki na ke yi, amma wanda ya mutu baya dawowa, ka riga da ka mutu, fatalwarka ce" tana ƙarashe maganar, tabi ta gefen shi da gudun ceton rai ta nufi door room din tana ƙarasawa gaban ƙofar Unfortunately tayi locking kanta.. Bugun ƙofar ta din ga yi tana ture ta da dukkan ƙarfinta kamar zata 6alle ta, cikin shessheƙar murya take ambaton "Mommy! Daddy!! Hubby !! Aunty Danejo!! Batool ... " don su kawo mata ɗauƙi Dan ba karamar firgita tayi ba. Duk yana atsaye yana kallon ta, phone dinsa data jefar kan floor ya dauko, Walking slowly ya nufi ƙofar, kwata kwata bata ji motsin tafowarsa sa ba, har ya ƙaraso daga bayanta ya tsaya tare da yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa hannayenta da take bugun ƙofar da su Ya ruƙo a cikin nashi Ya manna su jikin ƙofar, gaba ɗaya ya kashe mata sauran kuzarin daya rage a jikin ta ya haifar mata da jin matsananciyar kasala, tuni ta nemi shesshekar kukan da takeyi ta rasa wata nutsuwa ta soma ratsa ta.. sosai yayi tighting dinta ta yadda zai samu damar fahimtar da ita, da ya ke yasan halin kayansa da wuyar sha'ani ga kafiya. "Ki bani dama In yi maki bayanin da zaki fahimta! Ko da ba zaki yarda da ni ba... " kasa buɗe baki tayi don tayi magana.. Hakan Ya bashi karfin gwiwar cigaba dayin maganarsa.. "Ba ki shaida mutuwa na ba Unaisah! Baki ga gawata ba ido da ido! tayaya ba zaki yarda cewa ni ne ban mutu ba"? Daƙyar ta iya furta"saboda Danish ba zai iya rayuwa batare dani ba, in har yana araye bazai iya rayuwa nesa dani ba, ko inda babu ni, amma Yau kusan shekaru da mutuwarsa, tayaya zan yarda cewa yana araye"? Kwata kwata bata iya ganinsa cos Ya manne jikinta da glass din ƙofar, amma shi yana iya hangen fuskarta, wallah shi kadai yasan me ya ke ji, almost years rabonsa da muradin ransa.. Bata ƙare maganar ba Ya katse ta"ki faɗa min me zanyi maki wanda zaisa ki yarda da magana ta? "Babu, abunda zaka faɗamin In yarda, Kawai kabarni in tafi, ko ka 6ace ka koma ƙabarin ka, in ba haka ba daddyna yana akan hanyar zuwa gidan nan, tare da sheikh imam malik zai zo, Zaiyi maka ruƙiya ya ƙonaka da ayar Allah..." maganarta taso bashi dariya, tausasan la66anta Yabi da kallo sun jiƙu da hawayen ta... "Okay, bari na kira daddyn naki, may be Idan shi yayi maki bayani ki yarda.." faduwar gaba taji A hankali Ya zame hannunsa daga kan nata, Ya zaro wayar daya saka a aljihu Ya daddannata Unexpected taji Muryar Taj yana yin sallama ta cikin wayarsa.. "Nayi kokarin na fahimtar da Unaisah cewa nine ban mutu ba taƙi yarda dani..." "Idan tana a kusa ka bata wayar" Kara mata wayar ya yi a kunnanta.. Arude tace "wallahi Ba daddy na bane, ɗan uwanka aljani ka kira don ka ruɗani" sautin dariyar Taj ce ta cika kunnanta, arude ta ke dan zazzare idanun ta akan glass din ƙofar.. "Unaisah, ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki saurareni! Daddyn ki ne, muna waya ɗazu ta katse, ban samu damar da zan fayyace maki komai ba, bawan Allahn dake a tare dake Ba aljani bane, ba kuma fatalwarsa ba ce, Danish ɗinki ne ya dawo araye kuma a matsayin mijin ki... " maganarsa ta kara rikirkita tunanin ta, kokarin fahimtarsa ta ke yi sai dai tarasa nutsuwar yin hakan.. Mayar da wayar yayi kan kunnansa"bansan ya zanyi da ita ba, taƙi ta saurareni" Taj yace"ta ruɗene amma ka yi kokarin fahimtar da ita ta yadda zata yarda..." "Okay shukran... " sallama su kayi, ya mayar da dubansa kan Unaisah data haɗa uban gumi kan fuskarta.. Kafin ya furta kalma ta katse masa hanzarin sa _"Idan har dagaske kaine tayaya akai ka rayu bayan ka faɗa cikin rijiya? A ina ka ke yin rayuwa tsawon shekaru batare da sanin mu ba? Kayi loosing memory ɗinka ne? ko kuwa doguwar suma ka yi ne"?_ "Zanyi maki bayani, mu koma mu zauna" make kafadarta tayi"ba zan matsa daga inda na ke ba! Har saika bani amsar tambayana"! Yadda tayi maganar ya tabbatar masa da cewa ta fara yarda shi ɗin ne. ~_______🔥______🌹______💋_______💫_______🫀_______~ ~_______🔥______🌹______💋_______💫_______🫀_______~ *_FLASH BACK, WAIWAYE ADON TAFIYA, BARI MU KOMA BAYA MUJI LABARIN TAYAYA AKAI DANISH YA RAYU? TAYAYA GABRIELLAH TA KU6UTA DAGA CIKIN TAFKIN JINI? KUMA TAYAYA AKAI KHALA TA KU6UTA DAGA TARKON MUTUWAR DA ELDER YA ƊANA MATA?_* "Ku fara kokarin ceto rayukan fursinonin dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa daƙunan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh. Ta ƙara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..." Bayan tafiyarsu zullumi da fargaba Ya cika Zuciyar Tsohuwa Khala, ta kasa tsaye ta kasa zaune saboda tsoron kada su kasa yin nasara akan Giant da Elders tasan muddin suka san dasa hannun ta, Na lahira sai ya fita Jin dadi, bayan tafiyar su da mintuna, Allah Allah take su fara kawo mata firsinonin da suka ku6utar donta taimaka masu su fita daga kurkukun kafin Elders su Ankara. A lokacin da batai tsammani ba taji motsin mutane a kofar dakin ta, cikin sauri taje gaban kofar, da faduwar gaba ta tambayi su wanene"? Daga waje tajiyo murya mutun "Isod Soldiers ne, Chief ne ya umarce mu da mu kawo maki Fursinonin da muka ku6utar..." ajiyar zuciya ta sauke, jikinta na kerma ta cire sakatar ƙofar, ta leƙa kanta, Sojoji biyar ne tare da matasan Fursinonin da suka fara ku6utarwa dukansu jikinsu kerma ya ke yi bayin Allah.. "ku tsaya a bakin kofar dakina, Ni zan tafi da wadannan furnonin, Idan wasu sojojin sun sake ku6utar da wasu fursinonin ku ce masu su kawo su gurin da ku ka shigo kurkukun" amsa mata sukayi da toh, a hanzarce ta dubi fursinonin ku biyo ni" Cikin sa'a suka karaso wurin a lokacin sauran sojojin da suka karaso suna ta durowa ta cikin tagogin ta ko'ina sune sun cika wurin. suna ganin khala suka gane itace tsohuwar da danish ya fada musu zata basu hadin kai idan suka karaso.. "Kun gama shigowa Ko akwai wasu sojojin" ta tambaya tana dubansu, sukace sun gama shigowa sauran sojojin da suka rage awaje, matukan jiragensu ne dana motocin su.. Jinjina kai tayi tare da kallon Sojojin da suka rage a bakin tagogin rufin suna ta kokarin ɗaure igiyoyi masu gwa6i da tsawo jikin tagogin saboda idan zasu koma da su za su yi amfani gurin haurawa sama su fuce. Hakan ba karamin dadi yayi mata ba, batare da bata lokaci ba, suna gama daure igiyoyin suka zuro da su kasa har kan ground floor din gurin tace ma fursinonin su kama igiyoyin su haura sama idan sun isa suyi rarrafe akwai kofar da zata 6ular da su, wani Soja yace mata daga sun fita zasu iske sauran sojojin da ke a waje, already sun shirya komai. Bayin Allah sun kasa bin igiyoyin saboda basu iyaba, sai da sojojin suka taimaka masu gurin kwatanta masu yadda zasu bi igiyar, cikin ikon Allah sai gashi sun kama igiyoyin a hankali har suka haura sama, tun suna hawa daya bayan daya har suka koma suna hawa uku uku.. Suna kammala hayewa, sai ga wasu fursinonin gungu guda sojoji sun tafo da su, a gaggauce suka koya masu yadda za su bi igiyoyin. Na karshe da sojoji suka kawo sune wadanda su Danish suka ku6utar a dakin Fiɗa, hada mata masu ciki, yawanci ba koshin lafiya gare su ba, dama da taimakon sihirin Danish suka miƙe akan kafafun su har suka iya tafiya, dakyar suke bin igiyar, wasu ma daga cikin masu juna biyun hada kukansu saboda radadin da suke ji, tsananin tausayinsu ya kama sojojin da khala, sai dai ba yadda zasu yi da su, a haka suka haura saman rufin gaba ɗayan su, masu juna biyun sunfi shan baƙar azaba, saboda kuntatar da cikin su yayi, suna nishi da haki ga yanar data cika rufin da kananun kwari masu harbi da suka addabesu da kyar da sidin goshi suka karasa bakin Kofar da sojoji ke gadin ta, sai da suka taimaka ma kowani prisoner gurin mikewa saboda sagewar da gwiwowin su sukayi yasa basu iya mikewa, kaitsaye sojojin suka dinga shigar da su cikin jiragensu da motocin su, nan ma saida suka koya masu yadda zasu shiga, saboda basu san komai ba, hasalima tsoron jiragen su ke yi da motocin, bayan sun shigar da su duka, matukan suka tada jiragen da motocin ba 6ata lokaci suka basu wuta, da gudun gaske kamar zasu tashi suka nufi hanyar barin dajin da su gudun kada akawo masu farmaki ta bayan fage, tun acikin motocin sojojin suka rarraba musu ruwan sha, masu rauni a cikinsu kuma suka fara basu taimakon gaggawa dama suna da emergency box din su mai dauke da kayan agaji saboda tsaro. Idan muka koma cikin kurkukun bayan sojojin da ke kawo yaran sun tabbatarwa khala da sun kammala kwashe fursinonin da ke a ciki. Hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ganin bata ga yarinyar data kwallafa rai akan son ta taimake ta ba, arude tace ma sojojin su sake dubawa dakyau saboda ita tasan adadin fursinonin da suka rage a cikin kurkukun akwai wadanda babu" sojojin suka ce"Danish da Salsabeel sun tabbatar masu da babu sauran fursinoni," da ta matsa lamba akan su sake dubawa suka ce mata akwai bakwainin da suka gani a wani daki cikin containers kuma ba zasu iya jigilar daukarsu ba, saboda suna a cikin hadari basu da isasshen lokaci.." jikinta ne yayi sanyi lakwas taso duka acece su saidai bazai yiwu ba kamar yadda suka fada, cikin sanyin murya tace"akwai Allah, yana atare da su, shiyasan yadda zaiyi da rayuwarsu, duk da haka bayan bakwainin da kuka ce kun bari, akwai yarinya daya da babu a cikin fursinonin Ni banganta ba, kuma nasan ta, na ta6a taimakon ta, ni zanje na nemota da kaina" tana faɗa ta 6ace ma ganinsu, bata dira a ko'ina ba sai cikin ɗakunan fursinoni ta dinga bi tana dubawa sako da lungu, batare data bari wani yaganta ba, sai dai ita tana ganin yadda Giant da sojoji suke faɗa Ko'ina ta duba ban da ground floor da Hall din da ake bada horon zama giant saboda tasan zuwanta zai iya haifar mata da matsala. Damuwa ce ta cika zuciyarta, Hankalinta Ya tashi matuka, aranta ta furta"ina kika shiga Gabriella? Ga taimako kun samu, bana so damar nan ta wuce ki, Inaso na cika maki alkawarin dana daukar maki! Ko dai sun kashe ki ne"? abun da take jima fargaba kada ace sun haɗu da tsohuwa inno don tasan kuwa muddin suka hadu sai Ta cutar da ita, ba karamar wahala tsohuwa khala tasha ba gurin neman Gabriella, saida ta haɗa uban gumi akan fuskar ta. A karshe ta buga sandar hannunta a ƙasa tayi shiri donta samu damar ganin abun daya faru da Gabriela bayan giants sun fito da ita daga dakin ta, sai dai kash bata ga komai ba a inda ta buga sandar sai dai taga kasan gurin yayi jajir kamar jini ya 6are.. Abun ka ga mai ilmin matsafa, zukunnawa tayi gaban gurin tayi dogon nazari akan ma'anar launin jan, nan take ta gano me hakan ke nufi. 6acewa tayi 6att daga gurin. Lokacin da ta shigo ke6a66en wurin da tafkin jinin nan yake, bata iya ganin komai ba saboda idanunta basu cika gani ba idan babu wadataccen haske. kware murya tayi da karfi ta shiga kwala mata kira Gabriel! Gabriel! Gabriel, Kina ina? Kina jin murya ta, ni ce khala! Idan kina jina kiyi min alamar da zan gane a ina kike"! Saboda yadda take kware murya tana magana makoshin ta har zafi ya ke mata. ranta ne ya bata ko bata anan ne? Watakil tayi kuskure a duban da tayi, juyawa tayi har ta daga kafa da niyar ta fuce Unexpected kunnuwanta suka soma jiyo mata sautin wani azababben nishi mai hade da gurnani daga ji koma wanene keyin nishin yana a cikin mawuyacin hali, kuma yana fama da karancin iska da zai shaƙa.." saboda tsabar zumudin taga wanene, ta juya tana lalube da sandarta harta cimma bakin tafkin. batai aune ba taji safkar hannun mutun akan kafarta kamar laluban hanya ya ke yi. cikin duhun nan ta damƙi hannun da iya karfinta na karshe ta janyo da ita aikuwa gaba daya suka kife ƙasa, lokacin da khala ta miƙe tana laluba jikin mutumin data tsamo daga cikin jinin, Hankalinta ya tashi saboda ta gane Gabriella ce, taji tausayin halin da take a ciki, ganin yadda jini ya wanke jikinta, baka iya ganin komai nata, kuma tayi mamakin yadda har ta kai wannan lokacin a cikin tafkin jinin batare data suma kota mutu ba, ta jure ƙarni da ɗoyin jinin data shaƙa, ko magana bata iya yi sai nishi ta ke yi, kofofin hancin ta da bakin ta sai malalar da jini su ke yi. Idan har ta ce zata tsaya ta bata taimakon gaggawa anan za'a iya riskarsu, hakan yasa batai wata wata ba, ta dafe bayan gabriella da ke a kwance ƙasa, tayi masu sihiri suka 6ace daga gurin gaba ɗaya. Basu dira a ko'ina ba, sai cikin dakin Khala, kamar an wurgo su daga sama, suka faɗo kasa. wannan jinin da su Chief owais suka gani malale a kasan dakin Khala, ba jinin kowa bane face jinin da Gabriellah ta amayar, da hannu khala ta dinga buga mata dunduna, ta dinga sakin aman jini har saida ta fitar da jinin da ta sha. miƙewa khala tayi da sauri ta nufi daya daga cikin tulunan dakinta mai dauke da ruwa mai sanyi, ta kinkimo tulun ruwan da hannunta daya, yayin da dayan hannun ke a ruke da sandarta, ta dawo gaban Gabriella ta ƙwarara mata ruwan a jikinta. sai lokacin ta fara dawowa hayyacin ta, aje tulun kasa khala tayi, ta zukunna tare da kwalfar ruwa a tafin hannunta ta wanke mata fuskarta, ta kwafa mata bakin tulun abaki ta shiga kuskure bakin ta, duk wannan abun da khala tayi mata bata san wacece akanta ba, saida tasha ruwa sanyi ya ratsa makoshinta, tana dagowa da rinannun idanunta suka shiga cikin na khala, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, cikin sauri khala ta rungumeta a kirjinta, ta shiga lallashinta, tasan ta da zuciya, cikin shesshekar kuka ta zayyana ma khala abun daya faru tsakanin ta da tsohuwa inno, tace mata tayi hakuri ta jure, ta manta da komai, yanzu ga taimako sun samu, sojoji sunzo har ma sun ku6utar da fursinonin kurkukun gaba daya, a lokacin wani ihun farin ciki ta saki, arude tace mata ina dan uwanta gabriel? Shima sun fita da shi"? Khala tace mata eh, sune ma na farko da aka tafi da su" ta faɗa mata hakanne don ta samu ta shawo kanta tabi su su tafi. Cikin sauri Khala ta nufi bookshelves din dakinta ta zaro kundi biyu ɗaya na tarihin kurkukun ƙaddara ɗayan kuma littafin rijistar fursinoni ne ta rungumesu a hannunta ta nufi wata tsohuwar jakar fata dake makale jikin bango ta curota ta zazzage kayan cikinta, ta zura kundaddakin a ciki, Gabriella duk tana kallon ta bayan data gama ta miƙa mata Jakar tace ta ruke ta da kyau, suna da mahimmanci, Idan ta fita daga kurkukun ta bama sojojin, tace mata toh. Batare da bata lokaci ba, Ta janyo hannunta, suka fito daga dakin, lokacin da suka karasa gaban sojojin dake tsaron tagogin rufin ta damka masu gabriela tace su tafi da ita, cike da tashin hankali tace ma khala tazo su tafi tare, khala tace a'a su fara tafiya zatazo daga baya, idan sojojin sun kammala yaƙin zata biyo su, fashewa da kuka Gabriella tayi, ta sanya musu rigima akan bazata tafi ba in har khala ba zatazo su tafi atare ba, bata son ta tafi tabarta, gani take kamar zata mutu ne.. ganin zata 6ata musu lokaci yasa sojojin suka tasa ƙeyarta, tana ji tana gani suka rabata da khala, har ta fara bin igiyar bata daina waiwayen Khala ba, tana atsaye tana kallonta, fuskarta dauke da murmushi tace karta damu, tayi mata alkawarin indai da rai da lafiya zata zo inda su ke, sannan idan ta hadu da dan uwanta Gabriel ta gaishe mata da shi. itama tana kuka tace ta kula mata da kanta, duk runtsi duk wuya karta bari ta mutu, tana son ta.." bayan Gabriela ta dura ta rufin, ta rarrafa ita kadai tana kuka tabi hanyar da zata 6ular da ita... Saida sojojin dake tsaron gurin su ka ce ma khala tabi ta su tafi tace masu a'a, bazata iya tafiya batare da ta ga karshen fadan ba, saboda akwai burin da take da shi, tana son taga nasarar su akan idanunta, in har ta tafi zullumi da fargaban a wani hali suke a ciki bazai bari ta zauna lafiya ba.." badan sun so ba suka ƙyale ta. Idanun ta cike tab da kwalla, ta juya ta nufi hanyar komawa dakinta, zuciyarta a cike fal da kewar Gabriella, tana son yarinyar ta shaku da ita, tana son su sake haduwa sai dai tana ji aranta da wuya ta rayu, bayan irin 6arnar da tayiwa Elder bayan ta shiga dakin kasa zama tayi saboda zullumin awani hali su Danish suke a ciki.. Ta yi zurfi a tunaninta kwatsam tajiyo takun tafiyar mutun abayanta, juyowar da za tayi keda wuya idanunta suka sauka akan Elder Obinna daya faɗo a fujajen jikinshi sai tsuma ya ke yi saboda tsantsar bacin rai, har wani gurnani yake fitarwa.. wani irin faduwar gaba taji, Hankalinta ya tashi matuƙa. kallon kallon su ke jefawa junansu sam ya kasa magana, tun da taga ya kawar da idanunsa daga kallonta ya mayar da su akan akwatinan karfen da ke a kasa da buhunbuhunan makaman da tabari, nan fa tasha jinin jikinta, zufar tashin hankali ta fara wanko mata fuska, adabarbarce ta furta"E..el..elder...." bata karasa maganar ba, Ya daka mata tsawa tamkar zai fasa dodon kunnanta, Yana huci cike da bakin Ciki Yace"kin bani mamaki! Dake za'a haɗa baki a ci amanata? nayi kuskure dana barki araye tun farko.." duk da tsoron shi da take ji hakan bai hanata yin karfin halin cewa"kamar yadda nima ka bani mamaki Obinna, kaine ka fara cin amanata tun farko.."! bata ƙarasa amayar da abunda ke aranta ba, taga ya nufota gadan gadan Jiki na bari ta soma ja da baya, zagaye dakin suka dinga yi, ta soma yin tsalle tana hayewa kan tukwanan kasan dake adakin cike da tsoron karya kamata, cikin tashin hankali ta dinga daddafe bangon bayanta da tafin hannunta wanda ya 6aci da jinin data goga a jikin Gabriella, wanda silar hakan Yasa sahun yatsunta suka fito radau a jikin bangon kamar an zana shi, gaba ɗaya saida ta faffashe tukwanan da kafafunta, da ta ga zai cimmata ta 6ace ta koma kan gadonta, ransa ne ya 6aci nan take yayi tsafi gaba daya gadon da take akai ya jirkice wanda silar hakan ta kundumo ƙasa har kanta Ya da ku ta suma. Bata kara sanin inda kanta yake ba, sai dai ta farka ta tsinci kanta a dakin da yake hukunta wadanda suka ci amanarsa nan take ta fahimci shine ya kawota nan.. (Kunji yadda akai Elder Ya rutsa da Khala🔥) Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ƙafarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana ɗaga ƙafarsa kafin Ya dire ta ƙasa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ƙarasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ƙarfin shi na ƙarshe ya ingizasu gaba ɗaya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kan shi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi... (Evil wall rijiya ce mai faɗi da tsawo, tsohuwar rijiya ce da tayi shekaru aru aru tun zamanin kakannin Elder tun kan Elder ya gurfanar da kurkukun ƙaddara rijiyar ta ke anan, gaba ɗaya rijiyar ginin dutse ne tana da hatsarin gaske mutun bazai iya rayuwa acikin ta ba idan har babu sihiri a jikin shi, saboda giggan shaidanun dake rayuwa a cikin ta, ko maƙiyi na banayiwa fatan ya tsinci kanshi a cikin rijiyar koda a mafarkinsa ne saboda izayar da zai taras, daga jikin kowace kusurwa ta rijiyar yanace dadda6e da Evil spiders da manyan kunamu jibga jibga, ga giant snakes din dake bin jikin bangwayen rijiyar, gaba dayansu evils ne suka rikida ba ainihin kwarin ba ne. ga wasu zanunnuka masu ban tsoro jikin bangwayen rijiyar, ga wasu halittu bakake munana, masu idanuwa barkatai a jikin su, wasu gashi gashine buzu buzu a jikin su, wasu halittun kuwa har kananun macijjai suke fitarwa ta bakin su, bala'i iri iri, daga kasan rijiyar wani irin fadi gare shi, hada koramar ruwan jini na sihiri da manyan duwatsu, ga wata gajeruwar bishiya mai rassa tare da manyan ganyayyin da sukayiwa kasanta inuwa, daga kasan ta akwai wata shimfiɗa ta alfarma da akayita da jan carpet mai fadi anan giant din da suke horaswa ya ke zama kamar gunki bazai taba motsawa ba, in ba evils sun tashi bashi horo ba, koda yaushe da bakar izayar da zasuyi mashi, kamar yadda na fada abaya, tun suna bashi wahala su tsoratar da shi har sai sun kaiga bugun shi da bulalai su dinga azabtar da shi da masifu iri iri tun yana kuka ya suma su farfado da shi, har sai ya koma yana yin komai daga kwance tun daga kan amai, fitsari, kashi, saboda azabar da su ke yi masu takansa su fita hayyacin su, da zarar Elders sun tura ka rijiyar kayi bankwana da farin ciki da duk wani jin dadi, kunnuwanka ba zasu ƙara jin sauti mai dadi ba, sai na tashin hankali, baka da abinci daya wuce ƙwari da kwan halittun dake a ciki, ruwan sha kuwa sai dai kasha jinin dake a cikin tulunan da suka aje maka, ko wanka baka isa kayi ba, cikin kazanta zaka zauna shiyasa dayawa matasan da suke diba idan zasu basu horon zama giant da wuya suke tsalle rijiyar shaida nu, mafi rinjayen su anan suke rasa rayukan su. Rijiyoyin suna da yawa kowani giant a rijiya daya zasu kulle shi, kamar kabari, babu shige babu fuce, rayuwar kunci da azabtarwar, daga lokacin da tsoro yabar idanunsu, suka jure wahalar har suka fara rama bugun da evils keyi masu idan suna gabza fada atsakaninsu to daga nan evils din zasu gane zai iya jurewa, anan ne zasu zana mashi tattoo abayanshi yana kuka da ihu kamar ana zare ranshi saboda azabar raɗaɗi, irin tattoo din da su ke yi masu, ba irin wanda muka saba gani anayi bane, da akaifu evils suke zana masu shi abayansu, a faɗan da suke gabzawa da giant, idan yayi nasarar jure azabtarwar su ya rayu bai mutu ba, daga nan ne zasu samu matsugunni a jikin shi, su gauraya da shi ta yadda zasu ba shi ƙarfin su. A Lokacin da Danish Ya damƙi jeremiah ya ingiza su cikin rijiyar, Tun kan su dira kasan rijiyar a saman iska, suka fara gabza faɗa a tsakanin su baka iya jin sautin komai saina buge buge da naushe naushe da nishinsu hadi da gurnanin su kamar zakuna, bugun mutuwa sukewa junan su, babu imani babu tausayi, kowa jininsa akan akaifa ya ke, zuciyar su a wuya take, musamman jeremiah daya kasance mugun mutun, Ya tsani Danish tuntuni, ba dan komai ba sai don saboda lokacin da suke ƙanana yafi Danish yiwa elders biyayya idan suka bashi Umarnin ya aikata rashin imani jiki na bari zaiyi, danish kuwa kafiya da taurin kai ya ke yi masu, gashi Allah ya jarabce su da son shi, sai da takaiga sai sun haɗa da yi mashi sihiri suke samun abunda suke so, saboda yadda suke gatanta shi yasa Jeremiah ya ke yi mashi hassada, ya kullaci abun aran shi, yasha kulla makirci don ya sanya tsanar danish a zuciyar elders sai dai bai ta6a nasara ba, shiyasa a yanzu dayaga sun fada rijiya su biyu ya ke ta kokarin kawar da shi don ya fanshe bakin cikin daya kunsa mashi. wani jahilin naushi ya kaiwa Danish a tsakar mararsa, har saida Ya firgice saboda azabar daya ji, bai kaiga dawowa dai dai ba, jeremiah ya tallabe kansa da faffaɗan tafukayensa Ya buga jikin bangon rijiyar, tuni kuzarin jikin shi Ya ragu dama ya fara galabaita sosai saboda yakushin da Evil giants sukayi mashi a filin daga, duk da haka bai sare ba, jini na fita ta bakinsa da hancinsa, da bayan kansa, a haka Ya damƙi kan jeremiah Ya daddage da dukkan karfinsa ya maka shi jikin bango, amma kamar ya hada dutse da dutse kwata kwata babu alamun jeremiah Yaji jiki kamar ana kara masa karfinsa abunka ga sabon garkuwa, don bala'e kusan sau uku suna rikida su canza halittar su, kamar zasu kashe junansu babu tausayi ko kadan burin kowan nan su yayi nasara, kafin kace me tuni Wata irin kura mai hade da hayaki tamkar guguwa ta bude su baka iya ganin su kwata kwata, cakumar Danish yayi ya nutsa da su cikin rijiyar burinshi ya kaishi ƙasanta don ya azabtar da shi kafin Ya karasa kashe shi, shi kuma baya son yakai kasan rijiyar saboda yana jin tsoron Evils din cikinta su fusata zasu iya tarar mashi yasan cikin dakika zasu iya shafe babin shi. Duk yadda yaso ya turje saida Ya kasa saboda raunin da yayi, ta karfi ta tsiya Jeremiah Ya ingizasu suka kundumo kasan rijiyar gaba dayansu saida kawunansu suka daku. Duk da mawuyacin halin da yake a ciki hakan bai hana zuciyar shi tunanin Angel dinsa ba, har lokacin idanunsa basu daina tariyo masa irin haukan da tayi na za'a rabata da shi ba, kalamanta sun tsaya mashi a kahon zuciya, Shagalar da yayi da tunaninta yaja har Jeremiah Ya yi nasarar azabtar da shi, saboda rashin imani da sihiri yayi amfani gurin zane shi da bulalai yayi mashi jina jina, har saida Ya suma kusan sau uku jeremiah Yana farfado da shi. A lokacin Gaba ɗaya ya fidda rai da rayuwa, kamar jaki haka Jeremiah ya mayar da shi jini da majina ya hada mashi akan fuskar shi, saida Ya raba shi da kakin jikin shi, Yayi mashi zir haihuwar uwarsa dayaga Ya kusa kashe shi gaba daya baya iya ta6uka komai sai ya fara kokarin yin homo da shi saboda ta hakane kadai zai iya ƙwace sihirin jikin shi ya dawo nashi jikin saboda ya ƙara ƙarfi na fitar shari'a, bai kaiga cimma manufar shi ba, kwatsam rijiyar ta fara jijjiga, Lokaci daya sautin dariyar Evils mai matukar tsoratarwa da razanarwa Ya cika rijiyar, alamar Evils sun fusata, A lokacin Danish baisan inda kanshi ya ke ba yana akwance cikin jini rai hannun Allah, soft skin dinshi duk ta 6aci da munanan raunuka ko yatsansa bai iya motsawa.. Jeremiah Yana akansa Yana kokarin cimma manufarsa, Kwatsam ba zato ba tsammani evils suka fara ƙewayesu da suffar halittun da suka sauya masu tsotarwa, kamar kyankyasai saboda yawansu, manyansu da kananan su, koda Jeremiah yaga haka sai ya fara sakin shu'umar dariya yayi zaton zasu goya masa bayane akan abunda yake kokarin yi saboda yanzu shine garkuwar kurkuku. bai yi aune ba, kwatsam Yaga bakin hayaki ya soma kurdadowa yana fita ta bakinsa da hancin shi, kaitsaye hayakin ya ke shiga ta kofofin hancin Danish da bakinsa da duk wata kofa da iska zata iya ratsa jikin shi. lokaci daya yabi ya ruɗe ya zazzare jajayen idanunsa kamar na kwartan mazuru, jikinshi ya kama 6ari kamar mazari, yayin da tsoro da fargaba hadi da tsantsar rudanin al'ajabi suka mamaye zuciyarshi, abin da bai ta6a zata ba, ya rasa gane tayaya akai evils suka bar jikinshi tare da sihirinshi suka koma jikin Danish, da alama reshe ne ya juye da mujiya. cikin rawar murya ya furta bazai yiwu ba, meyasa zakuyi min haka? Ni ne sabon garkuwarku, Danish maci amanane, baya atare da mu! Ku dawo min da sihirina, Ku dawo jikina, ni ne nafi cancanta in samu karfin sihirinsa ba shi ba, ko kun makance ne? Baku da hankali ne"? Kamar mahaukaci ya dinga sambatu tare da mikewa ya bi halittun dake kewaye da shi Ya dinga yi masu tsawa yana zaginsu kamar zai doke su. sai masifa ya ke zazzaga masu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, wata irin kururuwa ya fasa kamar zaiyi hauka ya tallabe kansa da tafukansa, Ya dinga sakin kara mai tattare da bakin ciki, Har tsalle yakeyi kamar kwaɗo dama ba sutura a jikin shi. Girgizawar da rijiyar tayi ne yasa shi dawowa hayyacin shi, tunkan ya juya idanunsa suka safka akan Inuwar Evil din dake abayan shi, yawu ya haɗiya mai daci, gabanshi ya shiga faɗuwa. juyawar da zaiyi keda wuya idanunsa suka sauka akan Danish Dake atsaye kan kafafunsa, gaba daya idanunsa sun juye sun koma fari fat babu launin su, wani abun ɗaure kai ko ƙwarzane babu akan fatarsa gaba daya raunukan da yaji sun 6ace 6att ko tabo babu in ka cire tattoo dinsa, bakin cikine Ya turnuke zuciyar Jeremiah, kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Cikin fushi yace"burinka Ya cika Danish, Ka yi nasarar rabani da sihiri na, ba zaka ta6a bari in fi ka ba, ko da na sakanni ne ko da yaushe kaine agaba, na tsane ka danish, bana son ganinka, mutuwarka nake kwaɗayin in gani, bazan kyale ka ba, sai na kwace sihirina sannan In kashe ka. tun daya fara maganar Danish bai motsa ba, saboda a ba ɗini ba shi bane, Evils ne suka tada shi shiyasa harya iya mikewa tsaye, tsautsayi ne Yaja jeremiah Ya durfafesa da gudu Ya daka tsalle Ya dura akanshi kafin yayi wani yunkuri Danish Ya damƙi wuyan shi duk girman jikinshi Ya daga shi sama, nan take ido Ya raina fata, Ya dinga gurnani yana kokarin kwace kansa sai dai Ya kasa, idanunsa suka zazzago waje, Da azaba ta ishe shi Ya fara yi masa magiya akan yayi hakuri Ya kyale shi, kada ya kashe shi, koya manta abokantakar da ke tsakanin su. Wata shu'umar dariya Danish Ya fasa hahahahaha da wata irin budaddiyar Murya ya furta"baka cancanta ka rayu ba, saboda baka da tausayi, mugunta da zalunci kadai kasa a gaba, burinka kaga bayana, saboda nafika a komai, yanzu zan saukaka maka kishin da kake akaina, Idan na kashe ka ba zaka ƙara ganina ba, balle har ka ƙulla ce ni aranka" ya karashe maganar tare da matse wuyansa, ta yadda ko numfashi bazai iya fitarwa ba gurnani ya dinga yi yana ta kokarin kwatar kansa, azaba tasa ya saki fitsari, majina ta dinga zalalowa ta hancinsa.. saida ya tabbatar bazai kara amfanuwa ba, tukunna Ya jefar da gangar jikin shi kasa. Kunaman dake a cikin rijiyar da macijjai suka daddabe shi, suka dinga kai mashi sara da ɗalli.. ya dinga sakin Ihun azaba, Danish yana atsaye yana kallonshi har saida ransa yabar gangar jikin shi tukunna Ya daka tsalle Yayi sama Ya nufi murfin rijiyar yana karasawa Ya sakar mashi naushi ɗaya nan take murfin Ya balle biyu ya duro akan kafafunsa kuma nan take ya dawo cikin hayyacinsa.. yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa tsantsar tashin hankali da damuwa ganin gawarwakin sojoji barbaje a kasa, wasu gawarwakin ma ginin daya ruguje Ya rufe su ba'a iya ganin su, babu wani mai rai, kuma kwatata babu gawar giants a gurin sun 6ace 6att.. bawan Allah, aruɗe ya shiga neman gawar Chief da ta daddyn Unaisah, da Salsabeel, ya dinga bin gawarwakin yana dudduba fuskokinsu, tuni ya hada gumi, zuciyar shi ta karaya ganin babu corpses din su kwata kwata, da karfi ya dinga kwala masu kira tamkar makoshinsa zai balle shiru babu mai amsa mashi, bakin cikine ya turnuke zuciyar shi, yaji takaici, ganin duk kokarin da yayi don su rayu ya tashi abanza, wata irin ƙara ya fasa mai kuwar gaske har saida ginin Ya girgiza. Bakomai ne Ya faɗo masa aransa ba face tsohuwa khala, cikin sauri Ya zuƙunna a gaban gawar wani soja, Ya tu6e kakin sa Ya zura a jikin shi.. Daga inda Ya ke yayi tsafi Ya 6ace 6att bai dira a ko'ina ba, sai a tsakiyar dakin tsohuwa khala ya bayyana.. ~__________🔥__________🌹_______💫________💔~ Nan ma ya ƙara shiga tashin hankali ganin daskararren jinin daya malale kasan dakin ta ga gadonta daya jirgice nan ta ke ranshi ya bashi sun kashe ta, shikenan ya rasa damar da ya ke da ita, babu wanda zai faɗa masa su wanene iyayen sa in ba ita ba, gashi kuma ya rasa ta yanzu! baima san tayaya zai iya komawa gurin yan uwansa ba, zu6ewa yayi kan gwiwowinsa tsabar bacin rai, idanunsa suka kaɗa jawur kamar garwashin wuta, tuni jikinsa ya dau zafi rau, yana a cikin wannan halin kamar ance ya wurga idanun shi jikin bangon dakin ta unexpected ya hango kamar zanan wani abu ja zumbur ya mike ya nufi zanan Ya ƙura idanun shi Yana kokarin gano menene! dakyar ya iya gane sahun yatsun mutunne da jini. rufe idanunsa yayi tare da zurfafa tunaninsa nan take cikin ikon Allah kwakwalwarsa ta tuna masa da inda keda zanunnukan yatsun hannayen mutane, wato dakin da Elder ya ke hukunta wanda yaci amanar shi, ka'ida ne idan ya gama azabtar da wanda yaci amanarshi saiya fasa tafin hannunsa Ya manna jikin bangon ɗakin, har sai sahun yatsun hannayen shi sun fito raɗau tukunna ya ke cire shi, nan take Danish Ya fahimci Khala ta bar sahunne don wani ya kai mata ɗauki tun da tasan zasu dawo dakin nata idan suka gama faɗan. lokaci ɗaya ya waro idanun shi waje tare da ja da baya, batare da bata lokaci ba, Ya 6ace daga dakin Khala.. Lokacin da Elder ya juya Giants suka take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta. Ta kasance ita kadaice a cikin dakin, ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle ta iya kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta. sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar ɗaukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke, wutar Tana gab da zata rufe jikinta, Danish Ya duro dakin, cike da tashin hankali ya yi sahirinsa nan take wutar ta mutu kurmus, ramin Ya hade kanshi tamkar ba'a ta6a tsaga ƙasan gurin ba, kafafuwanta da suke daure da igiyar kaca nan take igiyoyin suka warware kan su sakamakon tsafin da yayi, kafin ta fado ƙasa ya rigata karasawa kasan fankar, igiyar na karasa kwancewa ta fado kan hannayensa, tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda hancinta ke fitar da jini, fatar goshinta har ta fara konewa ta tattare tayi duhu alamar wuta ta daki gurin sosai. ga wani irin ƙauri da jikinta ke fitarta, gumi ya wanke ko'ina na jikin ta, rungumeta yayi sosai a jikin shi, kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, idanunshi suka cucciko tab da kwalla, duk da baisan meya faru ba, amma yaji aran shi Elders sun gano taci amanarsu shiyasa suka hukuntata, da ba dan Allah yasa tayi dabarar yin alamar da zai gani ba, da yanzu ta kone kurmus ta yadda ko 6ur6ushinta ba zasu iya gani ba balle susan meya faru da ita. Cikin shesshekar murya ya dinga kiran sunanta yana fadin kada ta mutu ta barshi, Yana bukatarta arayuwarshi... " babu alamun zata farka, Ya rasa gane suma tayi ne ko mutuwa ta yi ne.. Zuciyarsa ce ta ankarar da shi akan ya mike ya tafi da gawarta kafin Elders su ritsa da shi. Yunkurawa yayi tare da mikewa tsaye ya goyata akan bayansa ya tallabeta da hannayensa, daga inda yake ya 6ace bai dira a ko'ina ba, sai a wajen kurkukun ta inda suka bar jiragen su da motocin yaƙin su yayi zaton zai taras da wasu daga cikin sojojin sai dai baiga kowa ba, babu su babu alamar su. hawaye ne suka wanke fuskarshi, bai san ina zai sanya ranshi ba, Zuciyar shi ta ƙara karaya, kamar zai fashe da kuka. Watsawa yayi da gudu Ya bazama cikin dokar dajin goye da khala abayansa, kwata kwata baiji nauyin ta ba saboda jikin tsufa, babu nauyi, Hasken rana ne Ya fara ƙwalarsa, ga yunwa da kishin ruwa da suka addabesa, maƙoshin shi har ƙaiƙayi ya ke yi ma shi, rabon shi da abinci tun jiya da suka baro Sansanin sojoji. Tsawon awanni takwas Yana tafiya daya gaji ne kafafunsa suka rurruke don dole Ya yada zango a gaban wasu bishiyoyi ya kwantar da khala asaman ciyayi ya tasa ta gaba yana kallonta.. saida ya huta kana ya mike ya kutsa cikin dajin don ya samo abun da zai ci. Duk inda ya duba babu abun da zai ci, a karshe da yaji bazai iya jure yunwar ba, ganyayyaki ya tasa agaba kamar dabba, da dadi da ba dadi ya dinga cusawa abaki yana ciki, saida ya cika cikin shi ya fara jin kishin ruwa kamar zai zauce, a galabaice ya baza ma neman ruwan da zaisha, tunawa da gawar khala daya baro yasa shi hakura da neman ruwan gudun kada namun dawa su handame ta, Yana akan hanyar dawowarsa wani irin hadari Ya haɗu bakikkirin cikin kankanin lokaci ruwa Ya fara safka tamkar da bakin kwarya, da gudu Ya koma gaban bishiyar yana isa ya taras da abun da ya faranta ransa, Khala ya gani ta farfado silar ruwan daya daki fatarta ashe sumane tayi. cike da farin ciki ya rungumeta a kirjin shi, kafin ya fara tarfa ruwan saman a tafin hannunsa yana bata abaki tana sha, sai kokari ta ke yi tayi masa magana sai dai takasa saboda muryarta tayi rauni sai dai rungume shi tayi ta dinga sakin gunjun kuka, a lokacin Allah ne kadai yasan farin cikin da tayi na ganin ta rayu kuma Danish ne ya ceto ta, taji dadi mara misaltuwa, Allah ya amsa addu'arta, ba ta ta6a zaton zata rayu ba,.. Tana kuka yana kuka babu mai lallashin wani, Yace mata tayi hakuri baisan meya faru ba, da bazai bari Elders su cutar da ita ba, yama yi zaton ta mutu ashe tana araye, yaji dadin da bazai iya misalta shi ba..." bai faɗa mata abun daya faru da shi ba, bai kuma nemi ta fada masa meya faru da ita ba saboda ganin halin da take a ciki na jinya.. A daren ranar agaban bishiyar suka kwana, ruwa ya jibge su, saboda babu mafaka akusa da su, kafin safiya tayi gaba daya zazza6i ya yi masu mugun kamu, jikin su yaita kerma.. Daya fahimci yunwa take ji, yaje ya tsunko mata ganyayyakin dayasan ba zasu cutar da ita ba, Yabata don taci, bayan ta kammala ci, Ya zukunna agabanta ta hau bayanshi Ya goyata, tare da mikewa Ya cigaba da tafiya batare da tsayawa ba. Akan hanyar su Ya labarta mata komai daya faru da su Yace baisan meya faru ba bayan ya fada rijiya, baiga gawarwakinsu Chief Ba yana ji aransa kamar basu mutu ba, saboda a cikin gawarwakin daya gani babu na su duk da akwai wadanda gini ya rufe gangar jikin su, shi damuwar shi mahaifin Unaisah baison ta rasa daddynta..." yayin da yake wadannan maganganun Khala tana agoye bayansa tana sauraron shi, kwata kwata bata iya magana saboda babu koshin lafiya atare da ita, gaba daya ta raunata, har kwara shi da ɗan kwarin shi, duk da shima yaji jiki karfin hali kawai ya ke yi, kuma hada karin Evils din da ke a jikin shi shiyasa bai rasa kuzarin shi ba.. Hakika ta tausaya ma rayuwar shi, ta damu da halin da suke a ciki, tayi bakin cikin abun da kakansa ya aikata masa, tasan hada alkawarin da tayi masa na zata fada masa su wanene iyayensa shiyasa ya damu da ita sosai, duk da har i wannan lokacin baisan cewa ita din kakarsa ce ba.. A cikin yan kwanakin da su ka yi a dajin, Sun sha bakar wahala, basu da abincin daya wuce ganyayyaki, Ga miyagun namun dawan da suke kawo masu hari badan Danish Yana atare da Khala ba, da tuni sun jima da kashe ta, Ya bata kulawa, baya bari ko ƙwaro Ya ta6a fatarta, duk in zata farka tsakar dare zata taras da shi a zaune a gefen ta Yana gadin ta, sai ta tursasa masa sannan take samu ya runtsa shima, bai ta6a bari ta taka da kafafunta ba, duk in zasu cigaba da tafiya abayan shi yake goyata kamar karamar yarinya. saboda depression din dake damunta kullum da matsanancin ciwon kai take fama, Ga konuwar da kanta yayi tana azabtuwa, don ma Danish Yana kokarin yi mata treatment da yan dabarunsa na sihiri, shima jikin nashi ba lafiya, mararsa tana matsa masa da ciwo, ga gabobin jikinshi da suka raunata, ahaka wata shakuwace mai karfi ta shiga tsakanin su. A daren wata rana ne, khala ta ɗanji saukin jikinta, bakinta ya bude, yaji dadi da yaga ta fara magana, tunkan ya tambayeta wani abu ta fayyace masa abun daya faru da ita sannan tace tasan ya ƙaraga da yaji su wanene iyayensa cike da zumuɗi yace mata eh. Tayi murmushi tace zata yi mashi wata tambaya daya kacal yace yana jin ta, tace ya fada mata lokacin da Owais yaje da su inda ya ke rayuwa, bai ta6a ganin wani mutum mai kama da shi ba sosai.." baiyi wani dogon tunani ba yace"Chief yana kama dani amma daddy minister yafi kama dani" "Wanene shi"? Ta tambaya kamar bata sani ba. Yace"Uncle din Chief.." tana murmushi tace ya bata labarin farkon haduwarsu, nan ya labarta mata tun ranar farko daya farajin muryarshi a lokacin daya dawo suffarshi ta mutane ashe yaji komai da Prime minister ya ke fada, hatta labarin da yaba Taj na dansa daya rasa, a cikin labarin daya bata hada ranar dinner din hateem da komai daya faru da zuwansu garden tare da shi. Tunkan Ya karasa bata labarin yaga ta fashe da kuka, hankalinsa Ya tashi ya soma tambayarta meya faru? Meyasa take kuka? Ko Labarin daya bata ne"? Jinjina mashi kai tayi, cikin shesshekar kuka tace"tayaya baza tayi kuka ba? Ko a tarihi bata ta6a jin soyayyar uba da ɗa irin wadda uban shi keyi mashi ba, tunkafin ma yasan shi din dan shi ne"! lokacin da tayi wannan maganar, ruɗewa yayi, muryarsa na rawa yace ta fada masa wanene daddy minister? Tasan shi ne? Ko shi ne daddynsa"! Cike da zakuwa yayi tambayar kamar zai hadiyi zuciya saboda zumudin ta fada masa, cikin karyayyar murya tace" shine mahaifinka, Prime minister Hateem, jaririn da kaji yana ba da labari bakowa bane face kai, kaine Omair dinsa, ita kuma matar nan data cire maka mask a ranar dinner din da ku ka je, Itace mahaifiyarka, sheikha Mujeedat, aranar da ta haifeka aranar ne munafukai suka hada baki gurin raba ka da ita" bata kare labarta mashi ba, sakamakon kukan daya fashe da shi, har saida ta razana da ganin yadda yake kuka a lokaci daya kuma yake dariya, ta rasa gane kukan bakin cikine kona farin cikin sanin su wanene iyayensa? Lamarin Ya daure mata kai tamau, saboda bata ta6a ganin Danish yayi irin wannan kukan ba da dai idanun ta A ruɗe ta shiga tambayar shi meya faru da shi? Meke damun shi? Meyasa ya ke kuka? Na bakin ciki ne kona farin ciki"? A lokacin kasa buɗe baki yayi ya bata amsa, tsabar yadda yake kukan jikinshi har jijjiga yakeyi, shatun jiyoyin wuyansa dana goshinsa sun fito ruɗu ruɗu kan fatarsa. kifa kansa yayi saman ciyayi, hankalin khala atashe Ta dago da shi tare da rungumeshi a kirjin ta, ta ɗaura tafukan hannayenta akan bayanshi, Cikin sigar lallashi ta dinga bubbuga bayanshi tace bata san ya zatayi ba don ta kwantar masa da hankalinsa, tasan idan tace yayi hakuri kamar ta cuce shi ne, amma yayi hakuri tasan an cutar da rayuwarshi, an tauye mashi hakkin shi na rayuwa, an kuma raba shi da iyayen shi, wanda tayi imanin da ace a hannun iyayensa ya taso ko chief Owais bazai kai shi samun gatanci ba, saboda arzikin iyayensa bazai misaltu ba, mahaifinsa prime ministern canada ne, mahaifiyarsa kuma diyar Ruler din dubai ce, amma har yanzu bai makaro ba, taji dadi da Allah ya raya shi, in sha Allah zai hadu da iyayen shi, tana da tabbacin a cikin shekara daya zasu sauya mashi rayuwar shi in har ya koma gurinsu, zai manta da duk wani bakin ciki da azabtarwar da ya fuskanta agidan kurkukun ƙaddara, zai zamanto daya daga cikin matasan da suka fi samun gata agurin iyayen su.." maganganu masu dadi khala ta dinga fada masa har saida ta samu ya lafa da yin kukan, sai dai Jikin shi yayi zafi rau, da alama zazzabine ya lullube shi, lokacin daya dago da fuskar shi, ta 6aci da hawayensa, idanunsa sun kada jawur, tayi tsammanin zai tambayeta wanene ya sadaukar da shi, sai baiyi hakan ba, muryarshi tayi rauni ta disashe dakyar ta iya gane me ya ke son fada mata.. Cewa yayi yau ce rana ta farko da yayi farin cikin da bai ta6a yin makamancinsa ba arayuwar sa, a halin yanzu baida burin daya wuce yaga iyayensa ido da ido, yana matukar son yagansu koda da numfashin shi na ƙarshe ne..." tsananin tausayinshi ne ya kamata aranar kwana sukayi a zaune yanata yi mata sambatu akan yadda yake zumudin yagan su har tambayarta yayi zasu ji dadi idan suka san shi dan su ne tace mashi fiye da yadda yaji dadin jin cewa sune iyayen shi..." A washe garin ranar da sukayi firar, bayan ya sama masu abun da zasu ci, suka kama hanya, dayaga bata sauri yace ta hau ya goyata tace aa bata so ya wahala, tun da ta danji sauki zata iya tafiya da kafafunta, ko ta dafa shi tun da babu sanda atare da ita. Batasan yadda ya matsu su koma gari ba, batai aune ba taji ya sungumeta akan kafadarsa ya 6ace da su.. Cikin sa'a suka faɗo wani forest din, A gaban wata bishiya ya sauke khala agajiye suka baje kasa nan bacci yayi awon gaba da su. Har mafarkin prime minister ya yi acikin baccin sa. Suna tsaka da yin baccin kwatsam ƙarar Mota ta cika kunnuwansu, a firgice suka farka har sun zabura zasu mike saboda sunyi azan wani mugun abunne amma da sukaga ba abun da suka zata bane sai hankalinsu Ya ɗan kwanta. Wata katuwar motar daukar kayace kirar toyota mai budadden baya, ta kunno kai cikin dajin, dattijai ne guda biyu daga gani wani mahimmin aikine ya kawo su cikin dajin.. Kwata kwata basu lura da su ba, har saida sukayi parking din motar, fitowa su ka yi daga ciki. ɗaya daga cikin su yana aruƙe da bindiga irin ta mafarauta, yayin dayan qugunsa ke a soke da Sheath Knife, daga gani mafarauta ne ko wani abun suka zo nema a cikin dajin, suna ƙoƙarin wuce wa cikin dajin idanunsa sukayi masu tozali da su, kura masu idanu sukayi kamar sunga wani mugun abu, kamar yadda suke kallonsu haka suma suke kallon su, khala ce ta yi karfin halin yi masu magana tace su taimaka su fitar da su daga dajin, kallon juna sukayi jin tayi magana da yaren da basa jin shi, da ta fahimci basu jin hausa sai ta maimaita maganar cikin harshen turanci. An ci sa'a suna jin yaren daya daga cikin dattijan yace tayaya zasu taimake su bayan basu san su wanene su ba? Don shi kwata kwata basuyi mashi kama da mutane ba, musamman matashin dake a bayanta" ya fada yana nuna Danish da yatsan shi, dayan dattijon yace"su fada masu gaskiya mutanene su ko aljanu? Me kuma su ke yi a cikin daji"? Ta lura Danish su ke ji ma tsoro duba da yadda su ke kallon shi ga dukkan alamu kyan shine basu taba cin karo da mai irin shi ba, ga zanan tattoo dinsa dayasa suke zargin dan wata ƙungiya ne ta ƴan ta'adda. Khala tace ba abunda suke tunani bane, suma mutane ne kamar su, matashin da suke gani atare da ita jikanta ne kaddara ce ta ritsa da su suka tsinci kansu a dajin su taimaka su shigar da su cikin gari.." Karya ta shirga masu ta dinga rokonsu dakyar ta samu suka aminta da su, su ka ce su shiga motar, su jira su su gama abun daya kawo a cikin dajin, bayan sun buɗe masu motar suka shiga daga ciki, hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba ganin sun samu taimako, nutsawa dattijan su ka yi cikin dajin tsawon rabin awa, kafin suka dawo hannayensu ruƙe da damun ganyayyakin da suka tsinko, abayan motar suka tura ganyayyakin, kafin suka bude motar, suna shiga mazaunin gaba suka yi arba da abun daya daure masu kai, mutanan da suka bari a motar sai bacci su ke yi ga zufa da ta wanke fuskokin su daga yanayin yadda suke fitar da numfashi yasa suka fahimci basu da ƙoshin lafiya. Jan motar su ka yi tare da bata wuta suka kutsa cikin gari sun danyi tafiya mai nisa kafin suka ƙaraso cikin birnin abomey-calavi da ke a ƙasar Benin. Koda suka shigo cikin gari, sai suka faka motar suka soma kokarin tada su daga bacci don su faɗa masu sun karaso cikin gari su sauko su tafi.. Sai dai me? Babu alamun zasu farka, har bubbuga kafadarsu su ka yi amma shiru, hakan ba karamin daga hankalinsu yayi ba, abunda suke ma fargaba kada ace sun mutu a cikin motar su, daga taimako? Har sun yanke shawarar kaisu wani guri su jefar da gawarwakin su, kwatsam tarin tsohuwa Khala ya katse masu hanzarinsu, da sauri suka shiga tambayarta meke damun su ne?ba su da lafiya ne? Cikin disasshiyar murya tace su taimaka su tafi da su gidan su, idan suka sauke su basu san ina zasu dosa ba, saboda su ba yan nan bane, taji suna wani yare da ba irin na su ba, koda suka tambayeta wani gari take a benin? Tace masu ita ba yar benin bace, Yar nigeria ce,.." waro idanu waje sukayi, alamar mamaki. Basu kara tambayarta ba ganin halin da take a ciki, saboda basu yarda da su ba, shiyasa suka ki kaisu gidan da iyalinsu suke, don karsu cutar da su, sai su ka garzaya da su gidan gonar su, su ka basu ɗaki ɗaya mai toilet a cikin sa, Ko gado babu sai katifa. Allah yaso sun fada hannun nagarin, Har abinci suka basu, duk da yunwar da su ke ji sun kasa cin abincin saboda ba irin cimarsu bace, sai dai suka sha kayan marmarin da suka tsinko masu na lambun su. Bayan sun yi wanka, suka kwanta kan katifar dakin anan bacci yai awon gaba da su.. Dattijan suna leƙan duk wani motsinsu a dakin, saboda suna kokwanto akan su. Saida suka ga bacci yayi awon gaba da su, suka lallaba tare da shigewa cikin dakin suka soma laluba aljihun wandon danish don suji in akwai kudi su sace su, Yana jinsu yayi shiru kamar yana bacci, jira yake su wuce gona da iri su ci uban su. Da suka ga babu kudi cike da takaici suka bar ɗakin, tafiya su ka yi sai dare suka dawo a lokacin suna zaune kan katifar suka shigo masu bayan sun gaida khala tayi masu godiya, su kace su yanzu so suke su san komai game da su, tace suyi hakuri zata sanar da zasu amma kafin nan tana so su fara bata waya zata kira gida.. Dakyar ta samu suka ara mata waya, bayan sunyi deal zata biya su kudin katin da zata ci ma su saboda sunga international call ne tace karsu damu zata biya su konawa su ke so. Saida ta kar6i wayar, ta fara tunanin wa zata kira cos gaba ɗaya ta manta phone numbers din ya'yan ta, Danish ne Yace ta bashi wayar zai kira Chief owais ya haddace numbar sa. da sauri ta bashi wayar ya kar6a Ya soma danna number din Chief bayan ya gama ya danna mashi kira, har sun fara murna ganin kiran ya shiga amma chief bai ɗaga ba, almost 30 times suna kira baya picking. har dattijon ya kar6e wayarsa a washe garin ranar da safe, da suka zo kawo masu abinci, ta k Ƙara roƙonsu su ara mata wayar, dakyar suka bata, ta dinga kiran Chief baya picking, kamar za su yi hauka, gashi tayi tayi da su su kaisu asibiti don aduba lafiyar su, amma suka kiya saboda gudun kada a caje su kuɗi. A ƙarshe Text message ta tura ma Chief owais, tace owais ka taimaka idan ka ga kiran nan ka neme ni, tsohuwa Khala ce ta gidan kurkukun kaddara, Ina a tare da Danish... 🔥 Bayan Sati ɗaya da ƴan kwanaki da kai farmakin farko gidan Kurkukun ƙaddara __________CHIEF OWAIS💓 Around ƙarfe sha daya na safe, yana a office dinsa tare da COO Commender Haroon suna dan ta6a fira kan abun daya faru agidan kurkukun ƙaddara.. "Har yanzu na kasa mantawa da tsohuwar nan, ta tsaya min araina, kuma inaji araina har yanzu Danish Yana araye, amma tayaya zan iya gane hakan? Anya Ba zamu koma kurkukun nan ba"? Ya fada da damuwa akan fuskarsa, Yayin da idanunsa ke a cikin na Haroon. "Tunanin mu yazo ɗaya Sir, Yaron nan yana araina, bazan 6oye maka ba, wallahi ban ta6a jin kaunar shi kamar yadda naji aranar da muka je kai farmaki, yayi kokari sosai, duk da halin dayake a ciki damuwar shi akan mune baison kowa ya rasa ran shi,..." Dg yace "Kusan kullum sai Uncle Hateem ya kira ni ya tambayeni Ina baby boy dinsa, sai in rasa amsar da zan ba shi, kasan ya kwallafa rai akan Danish, pls Commender ka bani shawara, tayaya zan san idan yana araye koya mutu"? Ya tambaya yana kallon Haroon daya yayi shiru yana kallon shi. Numfasawa yayi kafin yace"me zai hana mu sake yin meeting, idan komawar ta kama muyi sai muje, saboda ko da ace Danish Ya ku6uta tayaya za'ae mu iya sani mu? Yaron da baisan komai ba? Bazai iya kawo kan shi gidanka ba Sir, zai ma Iya fadawa wani gurin"! Maganar Haroon Ta ɗaga hankalinsa, Harya bude baki zai kuma yin magana kwatsam Wayarsa dake akan table ta hau yin ruri, janyo ta yayi tare da duba screen din, ya mutsa fuskarsa yayi batare da yayi picking ba.. "Sir, tun da muka fara magana ake ta kiranka awaya, yakamata ka daga kaji wanene"? Girgiza kai yayi"haroon, kasan bana ɗaga bakuwar number, babu wanda yayi requesting yana son magana dani wannan layin special ne ba kowa yake dashi ba, kuma numbar daga kasar benin ne tayaya zan ɗaga? May be wrong number ne tun jiya suke kira" Commender Yace"Sir, kayi hakuri ka daga kiran nan, Ni inaji araina kira ne mai mahimmanci, kuma saboda kai akayi shi, kamar yadda kace Contact dinka special ne, babu wanda zai iya hasashen numbarka in ba wanda ya ta6a gani ba, bana so rashin dagawarka ya zama silar da zamuyi danasanin rasa abun da wanda ke kira zai faɗa maka"! har kiran ya katse baiyi picking ba, Commender haroon ne Ya matsa mashi akan ya daga kiran, yana kokarin bin kiran sai ga sakon da Khala ta turo mashi, wata irin zabura yayi tare da mikewa yana zare idanunsa yayin da ya ke karanta sakon. A sukwane commender Haroon Ya mike tsaye yana tambayar shi lafiya? Meya faru"? Muryar shi na rawa ya furta"Khala da Danish suna araye! Ina tunanin su ne suke kira na"! washe baki Haroon yayi, tsantsar farin Ciki da al'ajabi ne akan fuskokin su.. Jikin shi na kerma Ya kira layin, kiran na shiga aka ɗaga. Cike da zumudi Ya furta"wanene ke magana"? Muryar Danish ce ta ratsa kunnuwan shi. "Chief, it's me Danish.." tsantsar al'ajabi ne ya ruke shi tamau, idanunsa azare, baisan sa'adda Ya yi sujjada ba tare da furta"Alhamdulillah Alhamdulillah.." miƙewa yayi ya kanga wayar a kunnansa" Danish dama kana araye? Danish Kana Ina yanzu? Tayaya zan hadu da kai"? Shiru bai bashi amsa ba, yana ta kiran sunan shi har ya yi tsammanin kiran ne ya katse Unexpected yaji muryar dattijo na magana da turanci "Barka yalla6ai, kana magana da adamu ne, daga nan Abomey-calavi benin". gaba daya tsohon ya zayyana masa ta yadda suka taimakesu a daji.. wani irin farin ciki ne Ya cika Chief Owais Ya ce ma tsohon su kula da su, zai basu ko nawa su ke buƙata, bai son komai ya same su, yau zai shigo ƙasar.." Dattijon Yace mashi Toh, Allah ya kawo shi lafiya.." yana gama wayar, Ya fayyace ma Haroon komai da suka tattauna da dattijon, ɗaga hannayensa sama yayi Tare da yin hamdala Yace dama shi saida ranshi ya bashi kiran nan mai mahimmanci ne shiyasa ya matsa masa akan yayi picking, yanzu abun daya kama suyi shine su kira Pilot dinsu . Batare da bata lokaci ba, nan take Chief Owais Ya kira jet Pilot din su. Bugu ɗaya yayi picking, "Captain I need you to prepare the jet for immediate departure." "Destination, sir?" "Abomey calavi benin, to be precise." "Benin Republic, sir?" "Yes, I have urgent business to attend to, Ensure all necessary clearances are obtained." "Understood, sir, What's the estimated departure time?" "Two hours from now, Make sure we have sufficient fuel for a return trip." "Consider it done, sir Will there be any passengers accompanying you?" "Yeah, ni da Commender Haroon ne" "Okay sir" Daga haka sukayi sallama, Ya mayar da wayar a cikin aljihunsa, Ruke hannun Haroon yayi a hanzarce suka fito daga office din tsabar sauri lift suka hau ta sauke su down, Suna futowa suka nufi parking space tun kan su karasa SA ya buɗe masu mota, a back seat suka zauna, SA din Ya shiga Ciki, Chief yace Ya wuce da su NAI Aiport, da matsakaicin gudu motar su ta fuce daga Headquarter din.. Lokacin da jirginsu yayi landing a Airpot din dake a cikin birnin abomey calavi.. Bayan sun fito daga Airpot din, Ya kira layin Adamu Ya fada ma shi Location din da zasu same shi. Bada jimawa ba, Sai ga Motar dattijan ta karaso inda suke, basu sha wahalar gane su ba, saboda Chief ya kwatanta ma adamu kakin da ke a jikinsu. Bayan sun ɗaukosu a motar suka nufi Gidan Gonar da su, kowa da abun da yake saƙawa aran shi, su suna Allah Allah aransu su isa don suga Idan sune, yayin da su kuma dattijan suke ta ayyana kudaden da zasu samu agurinsu, tun da suka ga yanayin shigarsu suka fahimci akwai arziƙi atare da su. Lokacin da suka karaso gidan Gonar, bayan motar tayi parking, suka fito gaba dayansu cike da zumudi Chief ya tambayi suna Ina. Dattijan sukace ya fara biyan su tukunna su nuna masu inda suke! Commender Haroon yace"karsu raina masu hankali, basu ga kakin dake a jikin su ba? harara daya daga cikinsu Ya watsa masu Yace"Idan har ba zasu biya su ba, to su koma inda suka fito.." Chief yace su fadi ko nawa suke so, zai biya su da dollar. Commender Yace ba zasu basu ko sisi ba, ya ma daina maganar zai biya su, kamar fa sunyi kidnapping dinsu ne, wanda hakan Ya sa6a ma doka a matsayinsu na jami'ae su biya kudin garkuwa.." Chief yace"bazai iya jurewa bane, Yana son ya gan su" Commender Yace"har yanzu bai yarda da su ba, kada sai sun biya su kudin su ki nuna masu su.." da harshen hausa sukayi maganar hakan yasa dattijan basu iya gane me suke cewa ba.. Haroon Ya ce"sunji zasu biya su ko nawa suke so, amma su fara nuna masu koda hotunan su ne, don su gasgata ba karya suke masu ba" da sauri adamu ya zaro wayarsa daga aljihu Ya buɗo hoton Danish daya dauka batare da sanin shi ba a lokacin dayake bacci shida khala Ya nuna masu Farin ciki ne ya lullu6e Zuciyoyin su, nan take Chief ya kar6i account number dinsu saida ya fara canza masu kudin da wayarsa Ya maida kudin kasar su tukunna Ya tura masu kimanin miliyan biyar" koda suka ga kudin sun sauka a cikin account dinsu, tsabar murna yasa suka zube kan gwiwowinsu sunayi mashi godiya kamar zasu kai goshin su kasa, daga gani Shegen son kudi gare su, gashi daga taimako sun samu kudin da sai sunyi shekaru zasu iya tara su.. Rakiya sukayi masu har zuwa dakin da suke. Chief ne Ya fara shiga dakin, kaitsaye idanunsa suka sauka akan Danish dake a kwance kan katifa Yana bacci, shi kadai A hankali Ya zauna daga gefen katifar, Commender Haroon Ya zuƙunna gefe ɗaya, Yayin da dattijan suke atsaye bakin kofar dakin suna kallon su sai faman washe baki su ke yi. Harara Haroon ya watsa ma su yace "ku rasa a ina zaku aje mai rai sai a wannan kongon gidan" ya fada Yana jifar su da harara, hakuri suka hau ba shi dayake sun basu kuɗi. Hankalin Chief baya akansu, Zuciyarshi ta karaya da ganin halin da Danish Yake a ciki.. A hankali Ya shafa gefen fuskarshi, ya ɗan bubbuga kirjin shi, numfashi Yaja tare da kokarin bude idanun shi da suka disashe saboda bacci.. "Danish, Chief ne, ka tashi kaganni, Ina atare dakai" a cikin kunnansa ya tsinkayi muryar Chief, Firgigit ya karasa ware idanunsa da suka kada jawur, yana ganin Chief jikinshi na 6ari Ya miƙe zaune tare da janyo shi suka rungume juna kamar zasu koma mutum ɗaya, gaba daya hannayen chief na a saman bayan Danish, Cikin sigar lallashi ya ke shafa bayansa. "Ina tsohuwar take? Ko itama sai mun biya zaku nuna mana ita"? Haroon ne ya fada yana jifar su da harara. kafin su furta Kalma sai ga Khala ta fito daga Cikin toilet din dakin, dakyar take taka kafarta koda idanunta su ka yi mata tazoli da Chief dake a rungume Da danish sai taji wani irin farin ciki ya lullu6e ta kamar ta zuba ruwa kasa ta sha. Cikin rawar murya tace "Owais! Danish cousin dinka ne, shine babyn Hateem na karshe da Sheikha mujeeda ta haifa masa, na fada masa komai game da iyayensa" lokacin da yaji wannan maganar daga bakin Khala baisan sa'adda ya kara matse danish a kirjin shi ba, wani kuka ne ya balle masa, daga shi har danish din aka rasa mai lallashin wani a cikin su. murmushin farin ciki Haroon Ya saki bayan ya gaishe da khala, Ya juya ya kalli dattijan da suka kura masu ido Yace"pls tun da kun kawo mu mun gansu, ku dan bamu wuri zamuyi magana ta sirri" Har suna haɗa baki gurin cewa dama abun dayasa suka tsaya suna son suji idan nan zasu kwana, don su kawo masu wata katifar da kuma abunda zasu ci" cike da kyankyami Haroon Yace"kasan su wanene mu kuwa? Kana nufin a wannan kongon zamu zauna"? Look bamu bukatar komai daga gare ku, mungode da taimakon da ku ka yi mana, Allah yasaka maku da Alkhairi, ga kuma kudi kun samu, don haka ku tafi, Idan mu ka gama tattaunawa, zamu bar maku gidan gonar ku.." amsawa sukayi da toh sunata washe baki sufa yau ashar dinsu kakarsu ta yanke saka. Har suka bar dakin Chief bai raba jikinshi daga na Danish ba, sun ki sakin juna.. Da murmushi akan fuskar Haroon Yace"finally Chief ya haɗu da cousin brother dinsa da ya rasa, dan uwansa mai kama da shi, me jarumta irin tashi." Cike da farin Ciki khala tace"tana tayasu murnar sake haɗuwa da juna, suyi kuka son ran su, suji ɗumun junansu, babu abun da zai sake raba su in sha Allah" kalamai masu dadi da karfafa gwiwa ta shiga gaggaya masu. Lokacin da suka raba jikinsu daga na juna wata irin zuface ta wanke fuskokinsu da jikinsu, ga wani zafi da jikin nasu ya dau ka, Idanun su cikin na juna, yayin da hawaye ke cigaba da shararowa kan kuncin kowannansu. Cikin shesshekar murya Chief yace"am really sorry danish! Nayi zaton kun mutu, wallahi Bansan kune kuke kirana ba, da tun ranar farko nazo na tafi daku, bansan kana araye ba, Danish kana araina dakai nake kwana dakai nake tashi, saboda yadda na damu dakai har mafarkin ka nakeyi, Danish ashe da rabon zamu sake ganin Juna? ....." Nan take ya labarta masa komai daya faru, Hankalin Danish Ya kwanta da jin cewa Daddyn Unaisah da salsabeel dinsa suna araye sai dai baiji dadin nasarar da basuyi ba akan Elders.. "Ku faɗa mana tayaya akai kuka ku6uta daga Kurkukun kaddara..." Haroon ne ya tambaya. "Owais Ni baka ganni ba"? Khala ce ta fada mikewa yayi tare da duban ta.. "Ina sane dake, kema kina araina tun ranar dana fara ganinki da kuma maganar da kika fada akaina, kamar kin sanni! Pls ki fada min wacece ke? Kamar na sanki, Inaso na sani!" "Owais baka gane ni ba har yanzu? Ka dubeni dakyau, duk da nasan tsufa ya boye ainihin kamannina.." kura mata idanun shi yayi sosai"wadda kike min kama da ita, ta mutu yanzu bata araye," Murmushin takaici tayi"owais, zan fada maka abun da kake son ji akaina, ba yanzu ba, saboda a halin yanzu Daga ni har Danish muna bukatar kulawar likitoci saboda ba lafiya gare mu ba..." nan take ta fayyace masu komai daya faru bayan Elder Ya ritsa da ita. Hankalin su Ya tashi matuka sun kuma tausaya mata, sun jima suna fira a tsakanin su. A ranar suka bar gidan gonar, Commender Haroon ne yayi masu booking Hotel Rooms din da zasu zauna, da taimakon adamu da ya shige masu agaba shi da yasan takan Birnin nasu.. Saida khala ta yi jinya a asibiti, na tsawon kwana biyu docs suna yi mata treatment na konuwar da kanta ya yi, Chief bai miƙa danish Asibiti ba saboda baya son ma wani ya gan shi, yasan yadda yake da jan hankali mutane zasu iya daukar hoton shi a boye wanda yin hakan zai iya jaza mashi matsala, tun da idan har Elders suka san suna araye, zasu nemi hanyar da zasu salwantar da rayuwarsu ne, sai dai ya dauki hayar Likitan da zai duba shi a boye, Cikin kwana ki biyu ya dan ji saukin jikin shi. Ganin sun murmure Yasa Chief Ya fara tunanin Komawa da su Nigeria, koda ya tuntu6i Haroon da maganar komawar su bai goyi bayan su koma tare da su ba, saboda rayuwarsu tana a cikin haɗari, In har Elders suka san suna araye sai sun nemi hanyar da zasu kashe su saboda sune silar da aka kai musu farmaki, kuma yadda suka ci amanar su ba zasu ta6a ƙyale su ba, dole su dauki fansa akan shi ƙwara su nisanta su daga Nigeria har zuwa lokacin da zasu kawo ƙarshen Elders. Maganar Haroon ta ankarar da shi kuskuren da ya ke kokarin yi dama yana zargin akwai sa hannun nashi a ciki! In har ya koma da danish cikin yan uwansa Elders zasu iya sani tun da yasan suna da yan leƙen asiri. basu gama yanke shawarar inda zasu boye su ba, Chief Ya ce ma Haroon zai nemi shawarar khala ya ji ra'ayinta. Bayan daya samu Khala a dakin ta, ya fada mata abun da suka tattauna da Haroon cike da damuwa tace sunyi tunani mai kyau tabbas idan Elders suka san suna araye zasu kashe su ne! Amma tana neman alfarma agurinsa, Ya taimaka Ya haɗa Danish da Iyayen sa! Tana son ya cika burinsa, rayuwa ba tabbas batason ya mutu bai gan su ba"! Shi kanshi baida burin daya wuce danish Ya haɗu da iyayen sa, sai dai baya jin zai iya haɗa shi da mahaifinsa tun da har yanzu bai kai ga gano su wanene ke da sanya hannu a kurkukun kaddara cikin Uncles din sa ba, wannan dalilin ne yasa shi yanke shawarar zai hada shi da mommyn shi amma fa ba zai hada shi da daddynsa ba har sai zuwa lokacin da suka kammala bincike. kwata kwata Khala bata nuna mashi tasan wanene Elder ba, ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta faɗa masa wadanda ta sani a cikin Elders ! Kuma yana son yasan tayaya akai tasan Danish cousin dinsa ne dan uncle Hateem! amma taƙi ta sanar da shi, daya matsa lamba tace in har yana son yaji amsoshin tambayoyin shi toh ya koma da ita Nigeria ya kuma hada kowa na family dinsa a estate dinsu, ita kuma tayi masa alkawarin a wannan lokacin ne zata fayyace mashi wacece ita sannan kuma zata tona wani sirri na family din su agaban kowa"! maganarta ta ɗaure mashi kai, Ya rude ba kadan ba, amma bai musa mata ba, Abun daya sa khala taƙi ta sanar da shi ta za6i ya koma da ita Nigeria ya kuma tara kowa na family dinsa, badan komai ba sai don tana son ta cika burinta na ganin ta tonawa Elder asirin agaban Ahlin sa. Masu karatu kunji dalilin dayasa Owais Ya roki alfarmar yana son ayi family meeting a ranar birthday dinsa, saboda bazai iya jira har sai date din family meeting yazo ba, kuma yana son kowa na family dinsu ya halarta duk don ya cika sharuddan Khala! Hakan na nufin dama can Owais Ya san da zuwan Khala. ___________________________🔥 Bayan daya faɗa ma Haroon yadda su ka yi da Khala, shima ya goyi bayan ya hada Danish da mommynsa a boye, tun da ba'a Nigeria ta ke da zama ba, ita kuma khala ya bashi shawarar in sun koma Nigeria da ita su boye ta a guest house din sa kafin zuwan ranar da zai kaita estate din su, Chief yaji dadin shawarar Haroon. Su uku suka san da wannan maganar, batare da 6ata lokaci ba, Dg Ya kira Sheikha Mujeedat awaya bayan sun gaisa ya fada mata cewa game da binciken da ya ke yi akan Danish, Ya gano cewa dagaske babynta ne da ta haifa babu rai shekara ashirin da suka wuce, yana tunanin akwai wadanda suka kulla makirci gurin raba su da shi.." Bai ƙare maganar ba, ta katse shi da cewa dama ita tajima da ji aranta jininta ne, saboda kaunar da Hateem ke yi masa da kuma kamanninsa da Hateem! shiyasa ta yi dna test din nan, amma tana so tasan su wanene suka rabata da shi? Meyasa su ka yi hakan? Laifin me tayi masu da har yasa suka rabata da yaronta tsawon shekara ashirin, bata san yana araye ba, daga haihuwarsa ko ɗumin jikinta bai ji ba, ba'a bari ta gan shi ba aka rabata da shi, akayi mata ƙaryar ya mutu! ita kawai so take ta san su wanene su ka yi mata aika aikar nan"! cikin lallashi chief yace tayi hakuri, ta kwantar da hankalin ta, Sun kusa kammala bincike akan wadanda suke zargin sun raba ta da shi, Yanzu haka da ya ke yi mata magana yana a tare da Omair dinta, sun riga sun faɗa masa cewa itace mommynsa, kuma tun da yaji hakan ya matsa lamba akan su haɗa shi da mamansa, ta taimaka in zai yiwu yana son ta haɗu da shi, amma baya son kowa ya sani! saboda rayuwar yaron tana a cikin haɗari, miyagun da suka rabashi da su suna nan suna farautar rayuwarsa, ya zamana komai cikin sirri zasuyi shi. kusan ruɗewa tayi saboda farin cikin jin cewa zai hada ta da dan ta. Cike da zumudi tace karya damu, in sha Allah zata kula da komai, ba zata bari kowa ya sani ba, yanzu ya fada mata da yaushe zai turo shi canada"? Chief yace "ba a Canada ya ke son su haɗu ba, yafi son ta hadu da shi a dubai, zaifi sirri, Yanzu haka suna a abomey-calabi benin, Zuwa jibi, zai kammala yi masa travel arrangment, kafin ya karaso ta tanadi private docs din da zasu duba lafiyar shi" Bai kare maganar ba, tace"ba zata iya jiya har sai jibi ba, yanaso ta kasa rintsawa ne? Dariya yayi jin abun da ta fada ya fahimci ta matsu taga danta. "owais Zan yi magana da UAE ambassador din mu dake anan benin game da shi, zai taimaka mashi ya samu same-day trip, on non-stop flight" Ba karamin dadi Chief yaji ba, jin zatayi mashi hanya, saboda a halin yanzu sai sun sha wahalar yi mashi cuku cuku kafin su fitar da shi daga ƙasar tun da karo na farko ne da zai fara tafiya kasar waje ba akan Private jet ba. Bayan sun kammala yin wayar, batare da 6ata lokaci ba, tun aranar Chief ya shirya mashi kayan daya siya mashi a cikin suitcase. A time din Yana a kudundune kan gado cikin duvet dinsa tun da Chief ya taimaka masa yayi wanka daga shi sai short Ya baje kan gado bacci yayi awon gaba da shi. Dakyar Chief ya tada shi daga bacci, bawan Allah ya damu sosai da Jin zafin jikin shi shiyasa ya kagara ya hada shi da mahaifiyarshi watakil saiyafi samun kwanciyar hankali, baya son danish Ya rasa ranshi batare dayaga mommynsa ba.. Sai da ya taimaka masa Ya shirya cikin suit na mutunci, ya zaunar da shi gaban mirror cikin sauri Ya gyara mashi sumar kanshi ganin yadda ta hargitse.. Around ƙarfe 2 na rana, sai ga kira daga UAE Ambassador Ya shigo wayar Chief bayan ya daga cikin girmamawa suka gaisa dayake harkace ta arziƙi da kuma wa ka sani yace sunyi magana da Sheikha Mujeedat game da yaro da take so akai shi dubai yau din nan, Chief yace mashi Eh hakane, yace toh yana bukatar bayanan yaron ko da na bogi ne ya tura masa yanzun nan cos sheikha mujeedat tace bata bukatar a 6ata lokaci ya amsa mashi da toh after sun kammala wayar, chief ya tura masa bayanan Danish ta email din daya turo masa ta sako. Bada jimawa ba, sai ga kira daga travel agent, after yayi picking suka gaisa daga muryarsa Chief ya fahimci matashin saurayi ne, sunan Airport din da zasu haɗu ya fada mashi bayan ya gabatar mashi da kan shi a matsayin wanda zai jagoranci tafiyar Danish zuwa dubai. Suna kammala yin wayar yaje ya sanar da Khala komai da suka tattauna da Mujeedat tayi farin ciki sosai, kafin tafiyar shi har ɗaki Danish Ya sameta, sukayi bankwana kamar karsu rabu da juna. Chief da Haroon ne suka yi masa rakiya a cikin motar haya suka tafi. Bayan sun karaso Airport din, sai ga Agent din Ya nufo su da murmushi akan fuskar shi suka gaisa daga bisani Ya mika ma Chief travel documents din Danish daya hada da duk wani abu da za'a buƙata, budewa Chief yayi a tsanake ya dudduba document din, murmushi yayi ganin sun shirya mashi komai, inda ma zai zauna a cikin jirgin business Class ne, ba main seating ba na kowa da kowa, a lokacin Danish fuskarsa a rufe take da mask, Ya kankame Hannun Akhi Owais dinsa a cikin na shi, Dayan hannun shi yana aruke a cikin na Commender Haroon, Agent dinne ya shige masu gaba yayi escorting dinsu to the gate for departure, duk inda suka je da zarar sun nuna masu Id cards dinsu Jiki na 6ari securities ke darewa su basu hanya, basu wani sha wahala ba, suka ƙaraso gaban jirgin da zai hau, chief ji yake kamar zai rabu da ransa saboda mutuwar son dan uwan nasa da yakeyi, da Agent din Ya lura da hakan sai yace mashi karya damu, Brother din shi zai kasance cikin koshin lafiya, zaiyi tafiya mai dadi saboda sun tanadar mashi flight attendants din da zasu kula da shi, just for his security and Comfort, duk da haka hankalin Chief ba akwance yake ba, Yaki sakin hannun danish, dayaga dagaske fa rabuwa zasuyi sai ya rungumesa sosai, Ya manna masa sumbata akan forehead dinsa da neck dinsa har kan Cheek dinsa yace mashi ya kula mashi da kan shi, kada ya sanya damuwa aranshi, Yasan bai cika son mutane ba, Inda zai zauna shi kadaine ba hayaniya, idan yana jin yunwa ko yana bukatar wani abu kada yaji shakkar komai ya fada ma Flight Attendants din da zasu kula da shi ya ƙara da cewa zanyi kewarka danish amma idan na tuna da wa zaka hadu sai inji sanyi araina, lokacin da yake wannan maganar idanunsa sun cicciko da kwalla, Agent din bai taba ganin kauna ta yan uwantaka ba irin na wadannan bayin Allahn daya fara gani ayau ba, Commender haroon Kuwa tuni Yaji kwalla ta cika idonsa saboda tausayin su. Cikin sanyin murya Danish yace mashi shima ya kula mashi da kanshi, zaiyi kewar shi, badan yana son yagana da mahaifiyarsa ba, da ba abun da zai raba shi da shi, amma ya sani koda basu a tare yana aran shi, ba zai ta6a mantawa da halaccin da yayi masu arayuwa ba, baisan da wasu kalmomi zai iya gode masa ba, abu ɗaya da zai iya cewa shine yayi dacen ɗan uwa nagari, kuma yaya agare sa, Yana matuƙar alfahari da shi, Yana son shi..." bai bari ya karashe maganar ba, saboda dadin da yaji Ya kuma janyo shi suka ƙara rungume juna cike da so da kauna. Cikin karyayyar murya Chief yace"kamar yadda yake alfahari da kasancewarshi dan uwansa shima haka yake alfahari da samun dan uwa jarumi irinsa, Yana son shi, bai ta6a yima wani dan uwa shi son da ya ke yi mashi ba.." ganin abun nasu ba me ƙarewa bane ga lokacin tashin jirgin Yana ta tafiya, yasa Commender da agent suka shiga tsakanin su, dakyar suka banbaresu daga jikin juna, Commender najan Chief, Agent din Yana jan Danish ahaka suka raba su. har akan matattakalar jirgin bai daina waiwayen Chief Owais ba har saida suka shige ciki, kamar zai fashe da kuka saboda kaunar ɗan uwan nasa. A wannin da sukayi a cikin Jirgin ba irin gatancin da bai gani ba a gurin masu kula da shi. sai dai farin cikinsa ragagge ne, saboda yana da damuwa aransa, bai manta da Unaisah ba, sai dai a wannan gabar yafi bukatar Ganawa da iyayensa, Saboda Yana son Ya cika sharuddan da Zai iya rayuwa da ita cikin salama batare data goranta mashi ko ya cutar da ita ba, don har yanzu kalaman data gaggaya mashi sun tsaya mashi arai, bai manta da su ba, amma babu abun daya sauya na daga son da ya ke mata. ~______________________________________🔥~ Kafin jirgin su yayi landing, tuni Sheikha Mujeedat ta riga shi ƙarasowa dubai daga Canada, A cikin private jet din ta ta zo. Bayan flight dinsu yayi landing a dubai International Airport.. passengers sunata fitowa daga cikin jirgin kowa ka gani hannunsa ruke da suitcase dinsa sai fara'a suke saki, royal guards din da ta turo don su tafo da shi, sun kewaye bakin matakalar jirgin sunata jiran fitowar shi duk sun kagara da suga wanene mutumin da zasu dauka, lokacin daya dira kafarsa akan matakalar, Gaba daya idanu suka koma kan shi, daga bayan shi agent din daya rakosa ne, shi ya ruke masa suit case dinsa da dufel bag din kayansa.. Suna ganinsa suka gane shine sheikha ta turo su su dauko mata, Suna karasa saukowa, guards din su ka yi masa ƙawanya kamar wani sarki, suka take masa baya, Ko kafaɗarsa baka Isa ka goga ba, mutane kansu darewa sukeyi su basu hanya, ganin kakin dake a jikin guards din, bayan sun fito daga airport din suka nufi danƙareriyar Motar da suka zo da ita domin daukarsa, Kirar mercedes benz yar uban su. A hanzarce wani guard Ya bude masa cardoor na back seat Ya shiga daga Ciki Ya zauna akan seat, Guard din ya saka mashi belt ganin baida niyar sakawa, bayan agent din Ya damka masu suitcase dinsa da jakarsa, Ya leko ta tagar motar sukayi bankwana cos wa'adin aikinsa na rakiya ya kare aranar zai juya. Sai da yaga tashin motocin tukunna Ya bar pickup area din.. UAE DUBAI Palm Jumeirah🔥 Off Jumeirah Beach Road Kai tsaye suka nufi daya daga cikin Katafaren private estate din Sheikha Mujeedat wanda ya ke a palm jumera's exclusive sector, bazan Iya misalta Haduwar Katafaren Gidan ba, Aljannar Duniya ce, anyi almubazzarancin Dirham gurin Ƙera ginin, irin daular da idan ka shige ta saima ka manta cewa da tur6aya aka halicce ka saboda shagala da ababen more rayuwar dake a ciki Tamfatsetsan gida ne na masu arziƙi wadanda suka gaji mulki da izza, akwai masu tafiyar da gidan wanda ya hada da Staff and services, Personal assistants din ta, Private Chefs na bangaren kitchen, and dedicated House keeping staffs. Lokacin da Motocin guards din da suka dauko Danish Suka karaso katafaren main enterance na Gidan a jere suka dinga shiga Ciki slowly kamar wadanda suka dauko eggs containers saboda Sheikha ta gargardesu akan karsu yi abunda zai 6ata ransa bai cika son hayaniya ba, suyi driving a hankali. Bayan sun yi Parking motocin a gaban katafaren Entry hall, time da security guard Ya bude masa murfin motar, Bacci ya same shi yanayi, cikin girmamawa yace "Sir, mun ƙaraso..." bude idanunsa yayi a hankali sun yi ja sun dan disashe, Ruko hannun sa guard din yayi ya taimaka masa ya fito daga Cikin motar, suka ta ke masa baya domin yi mashi rakiya, A hankali Ya ke bin ginin da kallo, wohoho He had never experienced such opulence, Ya tafi da imaninsa, Hankalin sa ya fi karkata akan kosassun dawakan dake harbin iska a tsakar fili gidan duk da shagalar da yayi da kallon kawatuwar Gidan hakan bai kawar da tunaninsa na son ganin Mahaifiyarsa ba. Suna ƙarasowa gaban main door ta shiga falo, Escorts din suka juya tare da barin Bakin kofar, Ya kasance shi kadai ne a tsaye, walking slowly Ya nufi ciki ganin ƙofar ta buɗe, wow wani ni'imtaccen Sanyin A.c ne mai haɗe da kamshin bakhhoor burner Ya daki hancinsa mai dadin gaske.. bangon falon ya bi da kallo an yi mashi ado da artwork nasu na royal family with rare callighraphy, mai tsadar gaske na harshen larabci. Takun Tafiyar dayajiyo ne Yaja hankalinsa ga kallon su, hadiman ta ne Sanye cikin Uniform dinsu, cikin sauri suke saukowa daga kan tagwayen staircase din da ke fuskantar shi, wasu ta bangaren dama wasu ta bangaren Hagu, Arude ya ke kallon su, time din da suka karasa saukowa Kaitsaye suka nufo shi, tare da russinawa kamar zasu durkusa kasa Cikin harshen Larabci Sukayi mashi barka da zuwa, bai iya gane me suke cewa ba saboda baya jin arabic. Idanunsa sun makance Mahaifiyarsa kadai Yake son gani a lokacin. Unexpected ya soma tsinkayar muryarta a cikin kunnan shi, "I've been asking myself how this can be true! Am I dreaming, or is it real? The baby I carried in my womb for nine months, na haifesa ba'a raye ba, shine ya yau ya dawo gare ni da ran shi! bayan shekara ashirin, OMAIR" a hanzarce Ya wurga Eye Balls dinsa akan ta, tun daga kasa Ya fara Bin ta da kallo, Hadiman dake a kewaye da shi cikin gaggawa suka watse tare da barin falon. Royal gown ce a jikin ta, tayi rolling wani hadadden Head Scarf (Shayla)asaman kanta. Kasa motsawa yayi yayin da idanunsa suka shiga cikin nata a lokacin da take tunkaro down ta kan stairs, walking magestically ta nufe shi tare da ware hannayenta, bai iya ganin fuskarta ba saboda chain mask din daya 6oye ta, muryar shi da rauni ya furta"Are you really my mom?" "You want proof..."? Jinjina mata kai yayi, Mika mashi hannayenta tayi, Cikin sauri Ya nufe ta Yana isa ta janyoshi tare manna shi kan kirjinta, Ta lullu6e shi da rigarta, yadda tayi tighting dinsa kamar zasu koma mutun daya, bugun zuciyarta a cikin nashi, wani irin yanayi suka ji atare da su mara misaltuwa, For the first time daya fara Jin ɗumin jikin mahaifiyar shi, gaba daya sassan jikin shi sai da suka amsa, jikinsu ya hauyin kerma kamar wadanda sanyi ya kama, ga wani zafi rau da temperature dinsu Ya dauka, Ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, Yau ce rana mafi daraja da ta wanzar da farin ciki acikin zukatansu. da ta fara manna mashi sumbata kamar zata haɗiye shi kai sai taji ma kamar bata ta6a haihuwa ba sai akanshi saboda wani azababben Son shi da kaunar shi na farat daya da suka mamaye kowani sashi na zuciyar ta. A lokaci ɗaya suka fashe da kukan farin ciki, kamar ruwan hawayensu zasu ƙare, shashshekar kukansu ta cika kunnuwansu,ƙanƙame ta yayi sosai, a haukace ta fara shasshafa bayan shi tana dan bubbuga shi. kusan zaucewa tayi ta kasa yarda gudan jinin tane data haifa a mace, Yau gashi agabanta araye da ranshi, batasan da wani baki zatayiwa Allah godiya ba, Yaron ya tafi da imaninta, ture shi tayi gefe ɗaya, ya dago suka hada idanunsu cikin na juna, cheeks dinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, haka idanun nasu sun rune kamar an watsa barkono a cikin su, labbansa sai kerma su ke yi dakyar ya iya furta"mom..." Durƙushewa kasa tayi ta fuskanci alƙibla, a hankali ta dogana goshinta kasa tayi sujudusshukr domin nuna godiyar ta ga Allah, cikin shesshekar kuka cikin harshen turanci ta furta "Alhamdulillah, Ya Allah, nagode da kyautar da ka bani, Ina son shi Ya Allah, fiye da yadda nakeson ya'yan da nake da su, bansan meyasa suka raba ni da shi ba, bansan laifi me na aikata masu ba, amma Ya Allah ka sani, kasan komai ya Allah, Ban cutar da kowa ba, Ni an cutar dani an rabani da gudan jini na, Ya Allah ka saka mana, Ka bi mana hakkin mu, wata tara na dauki cikin shi yayi rayuwa acikin mahaifata na jure laulayin shi, nayi nakudarsa na haifi abuna amma saboda rashin imani na wasu mutanan basu barni naga koda fuskarsa ba suka rabani da shi, sai gashi yau Ka dawo min da shi Ya Allah, a lokacin da banyi zato ba...." kasa jurewa yayi, Zukunnawa yayi tare da dafa kafadunta da tafukansa dake ta kerma, ya dago da ita cikin sauri ta ƙara janyo shi ta rungume shi, Ji take kamar ta mayar da shi cikinta ta sake haifo shi don ta raine shi da hannun ta. "I know you wonder about me being your mother, just as I do we don't know each other we've never seen each other Maybe you never thought you had parents because you didn't grow up with us amma mu muna tunaninka saboda mun san da yaron mu wanda muka haifa babu rai, kaga yadda Allah ke ikonsa ko"? Ta ɗan numfasa tana sauke ajiyar zuciya, yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta. "Bansan da wata manufa suka rabani dakai ba, amma inaso su sani basu rage ka da komai ba tun da har suka barka araye ka dawo gare mu, nayi maka alƙawarin zan sauya maka rayuwarka cikin kankanin lokaci, zaka manta da duk wasu wahalhalun rayuwa da kayi abaya, zan gatantamaka in baka dukkan jin dadin duniyar nan, kulawarmu da baka samu ba, har yanzu bamu makaro ba Omair zamu ba ka ita..." ta faɗa tana shafa sumar kanshi, Yayi shiru yana sauraronta, da hannayenshi biyu ya tallabe bayan mommynsa, wani irin tsantsar so da kaunar junane ya kama su, kamar za su dawwama ahaka. "Kada na cikaka da surutu, farin cikine Ya cika ni, na kasa samun nutsuwa, kamar in haɗiye ka na ke ji, ɗan uwanka Ya fada min baka jin daɗi, yanzu kana bukatar hutu, Mu shiga daga Ciki.." ta faɗa tare da ruƙo hannunsa a cikin nata suka mike a tare suka nufi Upstairs, ƙamshin turaren Mommynsa Ya cika hancinsa, zai iya cewa shine kamshi mafi dadin shaka da yaji a duniyar nan, kaitsaye suka nufi katafaren Part din ta, a saman royal bed dinta ya kwanta, da kanta ta cire mashi takalmansa da socks dinsa, tanayi tana kallon fuskarsa, idanunsu a cikin na juna, duk wani motsinta akan idanun shi, ganin abun yake yi kamar a mafarki, wai yau gashi da wadda tayi silar zuwan shi duniya, ta lura kamar akwai damuwa atare da shi saboda yaki sakar mata fuska, har murmushi tayi mashi don ya mayar mata da martani amma saitaga akasin hakan, ta damu da hakan, fatanta Kada yayi fushi da su ko ya zarge su akan abun daya faru da shi na raba su da akayi. "Ba laifin mu bane Omair, bada saninmu ba, kada ka tuhumemu akan abun daya faru dakai, wallahi da ace munsan kana araye, koda zamu rasa ranmu ne sai mun kwato ka don ka dawo gare mu.." tayi maganar nan ne yayin da take cire mashi Suit jacket dinsa, hawayenta ya gani sun ɗiɗɗiga akan hannunsa, shi kanshi dayasan iyayensa suna araye, kuma batare da saninsu ba aka sace shi daga gare su, da ba abun da zai hana ya dawo gare su, bai tashin sanin Elders sun cuce shi ba, saida yagano su wanene iyayen sa. batayi aune ba tafi safkar yatsun hannunsa akan fuskarta, lumshe idanunta tayi kanta har sara mata yakeyi saboda kukan da tasha, A hankali Ya shiga share mata hawayen ta, baisan ita damuwarta rashin sakewarshi da rashin maganar da bayayi mata, gani take kamar baya farin ciki amma tayi masa uziri saboda ta lura kamar rashin sabone yasa shi yin hakan ita kanta badan tanayi mashi kallon gudan jininta ta ba, da bazata iya sakewa da shi ba. "Me kake bukata In kawo maka"? Ta tambaya tana kallon shi, har time din bai daina kallonta ba, har saida ta tsargu da kallon.. "Pls kayi min magana, ko zaginane kayi, watakil inji sanyi araina, idan naji muryarka.." Ƙoƙarin buɗe baki yayi sai dai labban nasa sunyi masa rauni, numfashi Yaja tare da furzar da shi. Cikin rawar murya mai rauni da sanyi kamar tame yin raɗa ya furta"Stay by my side, don't stay away from me, I need your care, and I want to feel your hug even more, I love you more than anything, Mommy I'm overwhelmed with happiness right now because I'm with you I want to spend the rest of my life with you." bai kare maganarba, tayi saurin kwantawa gefen shi, ta tallabo kanshi da tafin hannunta, suka ƙura wa junansu ido batare da kyaftawa ba, kamar zasu hadiye junansu, at same time hawaye suka cika idanunsu kafin suka fara zarya kan kuncinsu.. Unexpected yaga ta sanya red tongue dinta akan fuskarshi ta lashe hawayensa kamar yadda ta sabayiwa daddynsa a duk time da hawaye suka zuba daga idanunsa, wani sanyi yaji aransa kamar ta ƙafe ruwan hawayen nan take suka daina zuba, kwanto da kansa tayi kan kirjinta, taci gaba da yamutsa sumar kanshi kamar tanayi mashi susar kadangare.. "I love you more than i love my self, more than everything.." ta faɗa calmly Daɗi ne yayi masa yawa har bacci ya ɗauke shi bata sani ba, sai da taji shiru tana ta ambaton sunan shi bai amsa mata ba, a hankali ta soma ƙare masa kallo kamar zata lashe shi ita kanta santin ɗan nata takeyi, abun da take ma zullumi tayaya royal family dinta zasu kar6e shi? Zasuyi farin ciki ko kuwa? Tayaya zatayi ma iyayenta bayanin ɗanta ne kuma Jikansu"? akagare take da Owaisa ya kammala bincikensa don ta samu hujjar fallasa baiyanar Omair dinta ga yan uwa da abokanan arzkinta tasan zasu yi al'ajabin ganin kyakkyawan ɗan. kamar ta samu tv haka ta dinga kallonsa, har saida ta fara jin bacci, a hankali tayi tighting dinsa a kirjinta donji take kamar za'a ƙwace mata shi. Tamfatsetsiyar wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta fara ruri kamar ba zata yi picking ba saboda batason komai da zai rabata da jikin danta. Gudun kada ringing din wayar ya katse mashi baccin shi yasa ta miƙe a hankali kamar wadda ta kwantar da jinjiri ta sauko daga kan gadon ta ɗauki wayar ta duba sunan me kiran ta, My in-law ta gani. Almost 30 misscalled yayi bata batare data sani ba, saboda hankalin ta na akan baby boy ɗinta. Gently tayi picking tare da kara wayar a kunne. "Danish ya ƙaraso"? Daga yanayin muryarsa ta fahimci hankalinsa ba akwance ya ke ba. "Owais, calm down your mind, Omair Ya karaso, Yanzu haka Yana akwance kan gado yana bacci" wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauke tare da furta"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah na gode maka" cikin karyayyar murya tace"Owais, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maka godiya ba, Owais, I couldn't bear it, when I hugged him tightly, I felt an indescribable sense of unconditional love, Owais daga ni har shi munyi kuka tamkar ranmu zai bar gangar jikin mu, Owais na kasa jurewa, bazan matsa maka ba amma ka taimaka min, ku gano su wanene suka rabani da shi tsawon shekarun nan, wallahi bazan ƙyale su ba, ko da hukumarku zata hukuntasu sai nayi ƙarar su Owais, dole su fuskanci hukunci mai tsanani dai dai da abun da suka aikata mana" ta faɗa da tsantsar 6acin rai akan fuskarta. Bata jira taji me zaice ba taci gaba da cewa "Owais wani irin rashin imani da tausayi ne? Bansan yana araye ba, shima baisan yana da iyaye ba, bamu san irin rayuwar da ya yi ba... " tun da tafara magana yayi shiru yana sauraronta, saboda a halin yanzu tana bukatar wanda zata fada ma halin da take a ciki kota rage radadin dake a cikin zuciyarta.. bata kare maganarba ta fashe mashi da kuka mai tsuma zuciya.. Kasa magana Owais yayi saboda tashin hankalin da ya ke a ciki, bai ta6a jin kukan Sheikha Mujeedat ba sai yau, shi damuwar shi Idan taji labarin azabtarwar da Omair yasha agidan kurkukun kaddara baisan Ya za ta ji ba. "Mommy, bansan tayaya zan lallashe ki ba, amma ki tuna Allah yana atare da masu haƙuri, nayi maki alkawarin zamu gano ko su wanene sukai maku aika aikar nan, kuma zamu dauki mataki akan su, pls mommy, ki kwantar da hankali, ki lallashi zuciyarki, mu godewa Allah daya bayyana mana shi da ranshi ta hanyar da bamu ta6a zata ba, Allah kadai yasan dalilin da komai ya faru mommy, a halin yanzu damuwa bata ki bace, baby Omair Yana bukatar kularki da lallashin ki, saboda baya da koshin lafiya...." lumshe idanun ta tayi a hankali hawaye suke sauka kan kuncin ta masu ɗumi. nutsuwa tayi tana sauraron Owais dake lallashinta tare da bata baki. Kwatsam ta soma jin nishi da gurnani cike da fargaba ta zare dara dara idanunta akan shi wani faduwar gaba taji, Ganin yadda ya ke birgima akan gadon, tafukan hannayensa daddafe da mararsa, gaba daya ilahirin jikinshi rawa ya ke yi, fatar jikin shi ta jike sharkaf da zufa, Idanunsa sun juye sun koma fari fat gwanin nan tsoro. Da karfi ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Om.. Omair! Meke damun ka"? Chief owais dake sauraronta aruɗe ya shiga tambayar meke faruwa da shi? Bata kaiga bashi amsa ba ta saki wayar ta fadi kasa, ta haye kan gadon tare da janyo shi yana ta hauka hauka, idanunsa sun kakkafe, lokacin ɗaya ya fara sakin ƙara mai sautin gaske, fuskarsa tayi jawur, duk yabi ya ciccije labbansa Ya faffasa su, gaba daya tabi ta rude, ta shiga tashin hankali mara misatuwa, Tana kuka Yana kuka tare da sakin kara, duk yadda ta kai ga ƙokarin kwantar masa da hankali takasa, fargabanta kada ta rasa shi arana ta farko da ta fara ganinsa amatsayin gudan jinin ta, rungume shi tayi a kirjinta wani zafi da taji a skin dinsa saida ta nemi zaucewa, cikin harshen larabci ta dinga furta Omair Meke damunka? Me ke faruwa dakai! Ya Allah ka kawo masa sauƙi, Omair kada ka mutu ka barni, Omair, dan Allah ka saurareni, inason ka, Ina ƙaunarka Omair, bana so na rasa ka"! Addu'o'i ta soma karantowa tana tottafa mashi akan sumar shi, ta dinga shafe mashi ita da tafin hannun ta, maimakon taga sauki atare da shi sai taga kamar ana kara masa Ciwon. tunawa tayi da maganar Chief da yace bashi da koshin lafiya, ta tanadi likitocin da zasu kula da lafiyar shi, a hanzarce ta soma kokarin raba jikinta daga nashi, wani abu daya karya zuciyarta yadda ya ƙanƙame hannayenta yaki bari ta matsa daga jikin shi, Sosai ta fashe da kuka cikin shesshekar murya ta furta"omair ba tafiya zanyi na barka ba! bazan jure ganinka a mawuyacin hali ba, lafiyarka tafiye min komai arayuwata.." tana ƙarasa maganar ta 6an6are hannayenta daga nashi, ta sauko daga kan gado tana faman share kwalla ta dauki wayar da ta jefar kasa, yatsun hannunta na kerma ta dannawa likitanta kira..💔 After few mins.. Ambulace ta shararowa da matsakaicin gudu zuwa cikin Gidan bayan Sunyi Parking, Medical team tare da nurses suka fara fitowa cikin sauri kowan nansu sanye da Uniform dinsa, wasu sun ruko emergency box a hannayen su.. A Falon suka iske gimbiya Mujeedat, da hannu tayi masu alamar su biyo bayanta, kaitsaye suka nufi bedroom din da Omair Ya ke, a lokacin kiris Ya rage ya ƙundumo kasa daga kan Gadon sai jan numfashi ya ke yi kamar ransa zai fita, cikin zafin nama Gimbiya Mujeedat ta tallabo shi tare da taimakon Docs Suka mayar da shi kan gadon nata, kasa barin dakin tayi saboda zullumi da fargaban kada ta rasa shi, duk tabi ta ruɗe, sai fadi take su taimaka mata kada ta rasa ɗanta, bata so wani abu ya same shi, ji take kamar ta ɗauke masa ciwon ya dawo jikin ta. Su kansu Medical team din mamaki ne ya kamasu jin kalaman Sheikha Mujeedat akan Yaron da basu san wanene ba ko a zuri'arta basu san da zaman shi ba. gaba ɗaya suka kewaye shi tare da bada himma gurin fara duba lafiyar jikin shi, duk da halin da suke a ciki na duba lafiyarsa hakan bai hana su yaba ƙyanshi a cikin zuciyarsu ba. Rage kayan jikin shi sukayi, suka bar mashi short da singlet fara, zanan tattoo dinsa Yasa su jin fargaba. Komawa tayi daga kofar dakin ta tsaya tana kallon su, jininta akan akaifa takasa tsaye ta kasa zaune gani take kamar basa yin sauri. Muryar team led din su ta tsinkaya a cikin kunnanta "Oxygen mask, stat! We need to get his oxygen levels up, And someone get an IV started, saline drip, now!" cikin sauri nurses din suka buɗe akwatinan, wani nurse ya soma sanya masa oxygen mask over his face, while another inserted the IV needle into his vein. Daga bisani docs suka fara Examining din shi. "Pulse is 120, blood pressure's 90/60, Let's get a blood sample for lab tests." wani doc ne ya fada Da sauri Nurses ya kar6i blood samples din Omair ya tura shi zuwa Lab.. A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacinsa, baima san su wanene akan shi ba, sai kokarin buɗe idanunsa yakeyi ya kasa saboda nauyin da sukayi ma shi. Gimbiya mujeedat kasa zama dakin tayi saboda tausayin shi, fitowa tayi bakin kofar dakin, ta kifa kanta jikin kofar hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta. "Let's keep him under close observation, I want vital signs every 15 minutes." gaba daya maganganun Doc din a cikin kunnanta, baiwar Allah tasha kuka kamar ba gobe.. Da damuwa ta mamaye zuciyarta, duk in ta rufe idanunta fuskarshi take gani, Prayer room ta shiga, bayan tayi sallah ta dinga yi mashi addu'o'i tana kai kukan ta gurin Allah.. Babu gajiyawa, har sai da kiran Doc Ya riske ta, fitowa tayi daga dakin with respect dr din Ya soma buɗe mata hotuna a tab din sa masu dauke da bayanan ciwon Omair. Yana magana yana duban fuskar sheikha Mujeedat, Tashin hankaline Tsantsa da damuwa.. Bai karasa Maganar ba ta dakatar da shi, jikinta kerma ya ke yi saboda damuwa.. "Please, I want you to do everything medically possible to save my son.." ta fada idanunta cike tab da ƙwallah "Consider it done, Your Highness." ya amsa mata kafin ya koma bakin aikinsa. Tun dare suke duba lafiyar shi, Har asuba ta rutsa da su, da suka bukaci zasu ƙara mashi jini, ita ta bada jinin ta duk da sun nuna in akwai namiji zasu so ace shi ya bada, amma ta kafe kan nata zasu diba, Dan a yadda takeji ko shine kadai jinin daya rage mata zata iya mallakama omair dinta, babu yadda suka iya duba da ganin lafiyayyar mace CE kuma zasu samu enough yadda suke buqata, bayan sunyi gwaji suka sanya mashi. Kasa jurewa tayi ta nufi bedroom dinta ta dauko waya, anan ta ga miss calls na family din ta, Hada na Chief Owais, kira ta danna mashi after yayi picking yace"meke faru da shi ne? Meke damun shi? Inata kira baki daga ba, duk na damu" Kuka ne yake kokarin kubce mata amma saboda jarumtakarta ta jure tare da numfasawa ta zayyana mashi sakamakon abunda ke damun shi Omair ta kara da cewa"Owais, bazan misalta maka tashin hankalin da nake aciki ba, pls ka fadamin garin yaya ciwuwwuka sukayi mashi mugun kamu? Bazan tuhume ka ba nasan kana iyakar kokarin ka amma Owais, ciwo kusan biyar duk a jikin bawa? Su wanene suka azabtar da shi"? Tashin hankali da damuwa sun cika zuciyar Chief, Sai yaji duk ba dadi badan ƙwararan dalilan dayasa Ya damka mata Omair ba, da yasani bai tura mata shi a haka ba, har sai ya samu lafiya yasan zuciyar uwa musamman akan Danta. Hakuri Ya kara bata yace ta jure komai zata gani atare da shi, ya kuma tunasar da ita yace kada ta manta Allah yana kar6ar addu'ar uwa akan ya'yanta, don haka ta dage dayi masa addu'a in sha Allah Omair zai samu lafiya, sannan Amsar tambayoyin da tayi mashi zata same su a lokacin da suka kammala bincinken su, baiwar Allah bata musa ba tace mashi toh har ta yi mashi godiya. Bayan ta katse kiran ta kira layin daddynta Sheikh Khalid after yayi picking cikin harshen larabci yace meyasa yanata kiranta bata picking? yana fata tana lafiya" rasa amsar da zata bashi tayi. Jin tayi shiru bata bashi amsa ba yasa shi furta"amsarki nake jira," numfashi taja tare da daidaita nutsuwarta kafin cikin sanyin murya tace"Alhamdulillah, ina cikin koshin lafiya baba, ina fata kaima haka"! daga yanayin muryarta Ya fahimci babu kwanciyar hankali atare da Gimbiyar tashi. "Meke damunki? Naji muryarki da damuwa" da sauri tace"babu abun da ke damuna, mura nakeyi, amma nasha magani, da sauki" "Allah ya baki lafiya, ki kula min da kanki" ta amsa da ameen. sun daɗe suna yin waya kafin su ka yi sallama.. Miƙewar da zatayi keda wuya sai ga khadima ta yi knocking kofa. Fitowa tayi daga dakin Khadimar ta sanar da ita medical team zasu tafi suna jiranta, da sauri ta nufi Down, Khadimar ta take mata baya, tana karasa saukowa down ta iske medical team din, wannan karon da walwala akan fuskokin su ga dukkan alamu sunyi nasara. Har suna haɗa baki gurin sanar da ita cigaban da suka fara samu akan Lafiyarsa sannan sukace kullum zasu dinga zuwa duba shi har zuwa lokacin da zaiji sauki, godiya tayi masu tare da jinjina, bayan sunyi sallama har suka tafi basu daina santin kyan patient dinsu ba, sun kamu da kaunar shi, sun kosa ya samu lafiya don suyi magana da shi, ba dan suna jin nauyi da shakkar gimbiya mujeedat ba da sai sun tambayeta menene alakarta da shi saboda sunyi mamakin yadda ta rude akan shi, da kuma kamanninsa da Nazli asaninsu bata da ɗa namiji amma sai gashi yau sunga wani zankaɗeɗan saurayi kyakkyawa daya tafi da imanin su, gashi ta gargaɗesu akan bataso kowa ya san wani abu game da kiransu da tayi da kuma yaron, sirrine in har suka sa6a sharadin data gindaya masu zasu fuskanci hukunci, shiyasa ko gulmarsa suka kasa yi sai dai suka bar abun aran su. Lokacin da tashiga dakin akwance ta same shii Yana sharar bacci, bawan Allah ya sha alllurai. A hankali ta zauna daga gefen gadon, Ta ruko hannun shi a cikin nata, ta sumbace ce ta ɗago tana kallon fuskarsa dake asanye da oxygen mask. "Allah ya baka Lafiya Omair, Allah ya tashi kafadunka, ya Allah ka musanya lafiyarshi da tawa, ni kamayar mun da ciwon nashi a jiki na, saboda ba zan juri ganinsa a mawuyacin hali ba, na damu da kai bugun zuciyata..." duk wani motsinsa akan idanunta, Owais ya kirata yafi sau akirga duk bayan mintuna saiya kira ya tambayi ya jikin Danish saboda ya damu da shi. Tsantsar kulawa take bashi kamar jinjiri, Lokacin sallah kaɗai ke sa tabar ɗakin, ko motsi ya yi sai ta tambayi yana lafiya? Ba ci ba sha ko da chefs suka faɗa mata sun kammala shirya mata Lunch, tace masu bazata iya cin abinci ba, su tafi kawai, haka ta wuni har dare tana tare da shi. A gefen shi ta kwana, ruƙe da hannunsa a cikin nata.. A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Har Danish Yayi One Week Agurin Mommyn sa, jikinsa Ya murmure lafiya tafara samuwa a jikin shi, ta ko'ina kulawa yake samu daga bangarori biyu, docs din da ke zuwa duba lafiyarsa kullum da kuma Mommynsa dake tsaye akan sa, itace mutun ta farko da ya ke fara yin tozali da ita a duk lokacin daya farka daga bacci, saboda tsantsar kaunar da take masa da kulawa bata bari ya yi komai da kansa in ba shiga toilet ya kama sa ba, abinci abaki ta ke bashi ya ci, da kanta ta ke wanke mashi sumar kanshi ta gyara mashi ita, bata barin shi cikin kaɗaici. tun aranar daya samu sauƙi ta lura bayayin sallah, ta kasa yin shiru har dai ta tambayeshi meyasa baya yin sallah yace'' mata in zai iya tunawa shi ba musulmi ba ne, tayi baƙin ciki da jin cewa ba musulmi bane shi, amma data tambayesa yana son ya musulunta babu gaddama yace mata eh yana so, nan take ta biya mashi shahada ya kar6i musulunci, Kuma duk ita ta koya mashi yadda zaiyi alwala da sallah. Har fita ta ke yi da shi tana nuna mashi wuraren shaƙawata da ke a cikin gidan, duk don ta faranta masa rai saboda tana son ya saki jiki da ita sosai, sannu a hankali suka fara shaƙuwa kullum sai sun shiga Personal gym din gidan a tare suke motsa jikin su, sometimes su shiga Private lounge su shaƙata abunsu harma suyi fira cikin nishadi ta dinga janshi da fira tun yana jin nauyin yin magana da ita harya fara sakewa sosai, wani lokacin kuma takan shiga library da shi ta dauko masu story books tana karanta mashi, sometime su shiga private cinema dinta su kalli movies, ba karamin nishaɗi da ilmi ya ke samu ba, in ka gansu suna wasa da dariya ya yin da su ke yin fira sai ka yi zaton sun daɗe da sanin juna. in a short time ta mantar da shi trauma din daya fuskanta abaya, gatanta shi ta ke kamar ranta, tarairayarsa takeyi kamar ƙwai a cokali, bata son ko tari ya yi, idan dare yayi a kan bedroom counch ta ke kwana tana fuskantarsa yayin da ya ke yin bacci saman gadon ta, saboda bata iya barin shi a bedroom shi kaɗai. Saboda shi ta kira ma'aikatan gidan dukan su, ta tarasu a falo ta nuna masu shi ta gargaɗe su akan karsu kuskura suyi ganganci gurin kula da shi, su ɗauke shi tamkar ran su, batason bacin ran shi, cikin girmamawa suka amsa mata da toh. Ta kuma bawa Private chefs dinta Jotter da doc ya rubuta na diet din sa.. Saboda Omair ta dauƙi hutun aikin ta, ta dakatar da duk wani business nata, gaba daya ta sadaukar masa da lokacin ta. She becomes his role model, his mentor, and his influencer, Mommynsa ta siye zuciyar shi da kulawarta, soyayyarta, kyautatawarta agare sa, tayi brainwashing nashi, yanzu halayansa da ɗabi'unsa sun sauya, komai nasa natural ne, babu sihiri babu evils gaba daya sun bar jikin shi tun aranar farko da yayi rashin lafiyar nan, Allah ya yaye mashi su, zafin fitarsu ne yasa shi yin jinya. Halayansa da ɗabi'unsa sun sauya sun dawo ainihin yadda Allah ya halicce shi da su, a lokaci yayi loosing memory dinsa baya tuna komai daya faru a baya, ko ta tambaye sa game da rayuwarsa ta baya sai yace mata bazai iya tuna komai ba. Mommynsa kaɗai ya sani da hadiman dake yi masu hidima, sai kuma Chief Owais da kullum Ya ke kiransa awaya suyi video call ko suyi phone call duk da ya manta wanene shi? Wata rayuwa su ka yi atare? A lokacin Yana masa kallon Cousin brother dinsa da Mommynsa ta gabatar masa da shi. Har Lokacin da Prime minister Ya kira ta awaya ya buƙaci Ya na son ganin su a Nigeria, baisan tana a tare da Omair ba, bata faɗa ma kowa ba, iya abun daya sani ta faɗa masa suna da hidindimu a dubai na bikin Ya'yan Uncle din ta, kuma idan ta tafi zatayi sati uku acan, ita ta fara zuwa dubai daga bayane su Nazli suka biyo ta, shi kuma a lokacin ya tafi Nigeria domin ya halarci family Meeting, hakan na nufin ko su Nazli basu san komai game da Omair ba. A lokacin ta shiga damuwar tayaya zata tafi tabar danta dake bukatar kulawarta duk da akwai maids dake kula mata da shi. Badan taso ba, Ta damƙa musu amanar shi, taja kunnansu sosai akan su kula mata da shi! Ranar kamar kar su rabu, ya rurruƙeta har bakin motarta da kyar ta shawo kan shi Yabarta ta tafi.. Daga guest house dinta ta wuce Zabeel palace the ruler's resident, kwana biyu tayi kafin su ka shirya tafowa Nigeria ita da Yazrin da Nazli. Bayan da suka bar ƙasar, cikin ma'aikatan gidanta, aka samu wani munafuki Yaje har fadar Emir ya kai masa tsegumin Yaron da Mujeedat ta ke boyo agidan ta, ta bayan fage, Emir Khalid Ya turo Royal guards don su Binciko masa wanene yaron da ta ke boye"? Ranar da guards suka zo palm Jumeira cikin guest house ɗin mujeedat, guards dinta na ganin su suka basu iznin shiga saboda sunsan Emir ne ya turo su. A lokacin Omair Yana a zaune kan dining Chair, Chefs sun kewaye shi, ga abinci sun jera mashi akan table, sunata lallashin shi don yaci abinci yaƙi ci sun rasa gane meke damun shi, ko magana bai yi masu tun bayan da Shiekha ta tafi! basu san kewa bace ke damun shi.. Sa'ilin da Royal guards din suka shigo dining din Wata razana su ka yi da ganin Omair, su ka ruɗe saboda ganin kyakkyawan matashi mai kama da jiƙar Emir. Cikin sauri ɗaya daga cikin guard ɗin ya ɗauke shi hoto da wayarsa Ya tura ma Emir duk Fa Yana kallon su a lokacin baisan su wanene ba bai kuma san meya kawo su ba. Ba'ajima da tura masa hoton ba sai ga kiransa bayan guard din ya yi picking Emir Ya Umarce su da su tabbatar sun tafo mashi da lu'u lu'un nan, Yana son ganin shi a cikin fadar shi"! Bayan guard din Ya gama yin wayar da Emir, suka Umarci Omair daya taso su tafi fadar mai martaba Khalid Yana son ganin shi. Rashin sani Yafi dare duhu, Omair baisan wanene mai martaba ba balle yayi musu biyayya ya bisu, hasalima ko kallo ba su ishe shi ba. Tun suna bashi Umarni yana share su, har suka fara haɗa baki gurin yi masa tsawa akan Ya taso su tafi, kai a karshe da su ka ga yaƙiya sai suka kama lallashin shi.. da sukaga dagaske bazai bisu ba, sai suka fara ƙoƙarin ɗaukarsa ta tsiya, aikuwa Ya fara naɗe hannuwan rigarsa zai yi dambe da su, wayaga Iliya ɗan mai ƙarfi. Koda Chefs suka fahimci me Ya ke shirin yi cikin sauri ɗaya daga cikin su tayi masa magana cikin harshen turanci tace mashi royal guards ne daga ruler's resident na dubai, kuma mahaifin Sheikha Mujeedat ne sarkin su sannan shine Ya turo su, kada yayi faɗa da su yayi musu biyayya su tafi ba cutar da shi zasuyi ba. Kasa fahimtarta yayi har saida ta kira sheikha Mujeedat ta faɗa mata abun da ke faruwa, tayi mamakin jin baban ta ya turo guards har guest house dinta don su tafi da Omair, amma bata damu ba nan take Ta umarce ta da ta bashi wayar suyi magana, bayan hadimar ta bashi wayar ya kar6a ya kara a kunnansa ta fayyace masa alaƙarta da mahaifinta tace karyaji shakku aranshi, Yabisu su tafi zai fi samun kulawa agurin daddyn ta. Bayan da suka kammala wayar ne, ya bi Royal guards din suka buɗe mashi mota Ya shiga ya zauna, suka tada motocin suka fuce daga guest house din ta.. ~___________________________________💋🌹~ Zabeel Palace 🔥 Fadar Zabeel hadaddiyar daular arziƙi ce dake a cikin daular larabawa, kuma Babban mazaunin Sheikh Khalid, mai ɗumbin tarihi da ikon, tana a tsakiyar Dubai, katafariyar Palace din tana a kewaye da kyawawan lambuna, tafkuna, da maɓuɓɓugan ruwa, ga dogayen bishiyin dabino, ta haɗu karshen haɗuwa, Alkamina bazai Iya misalta maku ƙawatuwar Katafariyar daular ba, Aljannar duniya, abun sai wanda ya gani Tun daga katafariyar main entrance zaka fara cin karo da Royal security Guards karfafa masu kirar Zakuna.. Bayan da Motocin suka karaso, a harabar ajiye motoci suka yi parking, lokacin da Danish ya fito daga Motar, ya ruɗu da ganin haduwar ginin kamar a mafarki Ya ke jin kanshi.. Guards ɗin ne su ka yi escorting din sa zuwa ciki tun shigowarsu Royal Guards suke ta Zare ido suna kallon shi, duk inda ya gifta idanun su akan shi haka da suka shiga ciki Hadimai da sauran jama'ar Fadar suka dinga binshi da kallo mai cike da tsantsar Al'jabi.. Har cikin Katafariyar Fadar Emir Khalid suka shiga da shiga, Fadawansa na ganin sa Suka zare idanun su cike da al'ajabi suke bin shi da kallo, Abunka ga wanda baisan takan Fadar Emir ba, maimaiko Ya zauna saiya Tsaya a tsaye ƙiƙam kamar gunki ko fara'a babu akan fuskarsa babu ladabi babu biyayya, Emir Khalid Yana zaune kan throne dinsa Cikin shigar sarakunan labarawa Na alfarma, Ya nutsu Yana kallon sa. Cikin harshen larabci fadawan suka dinga umartar shi daya zuƙunna Ya miƙa gaisuwa gurin Emir. Ko kallo basu ishe shi ba, har saida Emir Ya miƙa masa hannu alamar Yazo gurinsa tukunna Ya nufesa ba tare da jin fargababa, da ya ke yaga kamanninsa da Gimbiya mujeedat kamar yayi kakin ta. Ruƙo hannunsa yayi a cikin nashi ya rungumosa Yana shafa bayansa.. Karo na farko daya fara ganin shi, duk da baisan wanene shi ba? Menene alaƙarsa da Yarsa Mujeedat? Amma kamanceceniyarsa da surukinsa Hateem da jikarsa Nazli Ya sa ji aransa zaiyi wuya in ba yaron jikansa ba ne duk da yasan Mujeedat bata da ɗa Namiji. Bai ta6a jin tsantsar ƙaunar bare farat ɗaya a kallo ɗaya makamancin yadda yaji akan Omair ba, Bashi ba Hatta fadawansa sun kamu da kaunarsa, Kyawunshi Ya ruɗe su su da suke larabawa jinsin kyawawa, duk yadda suka kai ga ɗokinsa da jan shi a jiki sai dai sun kasa yin magana da shi saboda Yaƙi basu hadin kai, da Emir kaɗai Ya yarda shima albarkacin mommynsa ya ci. Daga Palace Emir Ya shiga da shi Cikin gidan, Zo kuga Yadda Royal Family mutane masu ƙima da daraja su Ke kallon Omair kamar zasu haɗiyesa saboda ruɗewar da su ka yi da kyansa da kuma kamanninsa da Nazli. Kowa Saida Ya hallara Dangin su, tun daga kan Grandparents, parents, Uncles, aunts, elders, kowa da kowa, kyawawan labarawa wadanda suka gaji Sarauta da arziƙi na fitar shari'a.. Kowa Tambaya ya ke yi wanene kyakkyawan matashin saurayin nan? ɗan wanene? daga Ina Ya ke? Wasu ma daga cikin su tambaya su ke yi mijin sheikha Mujeedat yana da wata matar ne da ta haifa masa Yaron ko kuwa Nephew dinsa ne (dan dan uwansa). Emir ne ya fayyace masu abun daya sani game da Omair, Ya daura da cewa su yi hakuri zuwa lokacin da sheikha Mujeedat zata dawo daga Nigeria, zata fada musu wanene shi, amma Yanzu Yana so kowan nan su Ya ja shi ajiki, su bashi kulawa kamar yadda suke kula da sauran ya'yan sheikha Mujeedat saboda yana ji aranshi da akwai wani abu game da yaron tun da har take 6oyen shi a guest house din ta.! kunsan larabawa da girman kai musamman ga bare amma dayake Omair ya kwanta musu arai sun ganshi da abubuwan ban al'ajabi atare da shi shiyasa su ka yi saurin amince ma shi. Omair bai ta6a sanin Yana da babban Family na hamshaƙan masu kuɗi ba kuma kyawawan gaske sai da Ya tsinci kanshi a cikin ruler's resident na dubai, ashe shi din ɗan dangine, Ya fito daga tsatson mashahuran larabawa. Kowa ɗokinsa Ya ke yi, amma Rashin sabo ya hana shi sakin jiki da su. musamman Emir Ya ware masa katafaren Bedroom dinsa tare da Hadiman da zasu dinga yi ma sa hidima, in a short time Emir Ya siye zuciyar Omair, shine mutun na farko daya fara sakin jiki da shi, saboda kyautatawar da ya ke yi masa, Har takaiga dare kaɗai ke raba su, ya zama kamar ɗan Cikin sa, In zai shiga Palace a tare suke zuwa, su ci abinci atare da shi da iyalansa su fita yawon shaƙatawa, Hadiman Gidan sun sanya mashi ido sosai, kunsan ba'a raba hadimai da tsegumi burinsu kawai su ji wanene shi"? Daga bisani Lokacin da Asirin kurkukun ƙaddara Ya Tonu duniya Taji, sa'ilin da labarin Ya risƙi Familyn Mujeedat, sun razana sun kuma shiga tashin hankali da jin wanene surukin su Obinna, Ransu ya 6aci matuƙa, Baba Obie Ya Karya musu Zuciya, Ya ci amanar yardar da su ka yi ma shi, sun kuma fusata sosai, sai da su ka yi dana sanin ƙulla alaƙa da shi saboda basu son abun da zai ta6a mutuncin su duk min ƙanƙantar shi, suna girmama mutuncin su fiye da komai. dama tunfil azal basu so sheikha ta auri bare ba kuma baƙar fata ɗan Nigeria saboda su a ƙa'ida basu fiye auran bare wanda ba jinsin su ba, abaya lokacin da Mujeedat tazo da Hateem amatsayin wanda takeso ba karamin rikici akayi a family din ba, duk da matsayinsa da arziƙinsa Yasha wahala kafin su bashi auranta, saboda ta rantse ta maya bata da miji a duniyar nan daya wuce Hateem, mahaifinta ne mutun na farko daya fara goyon bayan ta auri za6inta saboda tsantsar son da yake mata fiye da sauran ya'yansa ita kaɗai ce mace kuma autar sa, mahaifiyarta ma ta goyi bayanta, daga bayane kuma bayan sunyi aure Dangin nata suka Fara son Hateem saboda yadda Al'umma su ke yabon kyawawan halayansa. saboda fallasuwar asirin Obie Har Family meeting su ka yi game da Yanke alaƙarsu da surukinsu, Mafi rinjayen su wadanda su ka fi fusata, sun goyi bayan a kira Hateem Ya saki sheikha Mujeedat, Kaɗanne basu goyi bayan yin hakan ba, daga ciki hada Mahaifinta da kawunta da kuma yayanta sun ce sai dai A kira Mujeedat tazo Nigeria suji ra'ayinta in har ta nuna tana son taci gaba da zama da mijinta babu abun da zaisa su raba su. Haka wasu daga cikin fadawan Emir Khalid sun shawarce shi da ya yanke alaƙarsa da obinna saboda gudun surutun mutane amma Ya tsawatar ma kowa akan shi bazai Raba Mujeedat da mijinta ba, In har ba itace ta nuna tana son rabuwa da shi ba Komai da ke faruwa a family dinsu gimbiya Mujeedat bata sani ba, Ta kashe wayarta saboda rashin kwanciyar hankali da damuwa. Daga baya ne Emir Ya tuntubi Prime minister awaya, Ya umarce shi dayazo Yana son ganinsa, Idan masu karatu ba su mantaba akwai wani kira da Emir yayiwa Hateem Har yaji shakkar zuwa saboda zullumin kada Su raba shi da matar shi, to abun daya faru bayan ya amsa kiran, suka yi tafiyar sirri zuwa dubai tare da Iyalinsa. Bayan sun isa Airport Royal Guards suka zo Daukarsu a motoci, kaitsaye suka garzaya da su zuwa Ruler's resident, a lokacin Hateem Bashi da nutsuwa, zullumi da fargaba sun cika zuciyarshi Ya damu da fargaban meyasa Surukinsa ke nemansa? yasan Sun riga da sun ji komai a news, kuma yana da tabbatacin kiran da ya yi masa yana da alaƙa da Abun da ke faruwa a family din su.. ~______________________________~ Kwata kwata Hateem baisan Danish Yana a tare da dangin mujeedat ba, saboda a lokacin baida kwanciyar hankalin da zai iya tunawa da shi, bai kuma san komai game da kasantuwar sa ɗan shi ba. Bayan da suka Ƙarasa hateem bai samu tarbar daya saba samu agurin wasu daga cikin danginta ba. hakan ya ƙara haifar masa da matsananciyar damuwa, ta inda ya ji sanyi aransa Emir da Kawun mujeedat da Yayanta da ma wasu daga cikin su sunyi mashi kyakkyawar tarba, a bangaren Sheikha Mujeedat da ke a cikin gidan suka fara huce gajiyarsu, bayan hadimai sunyi masu hidimar kawo abinci daga bisani bayan sun huta sosai, sai ga kiran Emir ya shigo wayar Mujeedat bayan ta ɗaga yace su shigo ciki yana son ganin su. Gaba ɗaya suka ɗunguma izuwa Private Living room, A nan suka Iske Kowa na familyn sun hallara suna jiran su. A lokacin ba Hateem kadai Ya shiga damuwa ba, hada Mujeedat da Su Nazli, saboda sun san mawuyacin abune su ƙyale Hateem batare da sun raba alaƙar su ba. Cikin zullumi da fargaba suka zazzauna suna fuskantar Emir khalid da sauran family members din. Falon yayi shiru babu mai magana, Hateem Ya sadda Kan shi ƙasa cike da jin kunyar hada idanu da su, gimbiya Mujeedat ce ke ɗan tausarshi Tana matsa yatsun hannunsa dake a cikin nata duk dan ta kwantar masa da hankali. Gyaran murya Emir yayi, Hankalin kowa Ya dawo kan shi, cikin nutsuwa ya ce sunji komai da mahaifinsa Ya aikata, basu ji dadi ba, Ya karya musu zuciya, ya kuma ja masu abun kunya a idon duniya, amma ba zasu alaƙanta shi da laifin da mahaifinsa Ya aikata ba, hakika sun tausaya masu sun kuma jajanta musu, sai dai ya sani bazasu lamunci abin da zai taba martabar family din su ba..." Lokacin da Hateem ke sauraronsa Hankalinsa Idan yayi dubu toh Ya tashi. Emir Yana ƙare maganarsa, Khal din Mujeedat Ya daura da cewa"don haka, yayi hakuri da hukuncin da zasu Yanke! Sakamakon Mafi rinjayen family dinsu sun fusata sun nuna rashin goyan bayan alakar sa da mujeedat..." khal bai ƙare maganar tasa ba, Mujeedat ta fashe da kuka Hankalinsu Ya tashi saboda sun daɗe basu ga zubar hawayenta ba, Cikin karyayyar murya tace kada su rabata da Hateem! Bazata iya rayuwa batare da shi ba, tayayama zata iya barin shi a mawuyacin halin da ya ke a ciki? Dame zaiji? Su dubi girman Allah kodan darajar ya'yan dake a tsakaninta da Hateem kar su rabata da shi, zata iya rasa ranta su tausaya mashi!" duk yadda Nazli takaiga izza saida ta sanya baki ita da Yazrin suka taya mommynsu rokon danginta akan kada su raba su da mahaifinsu, ba laifinsa bane, ko Allah baya kama mutun da laifin da bashi ya aikata ba, su tausaya masu! In kuma har suka raba mommynsu da daddynsu suma zasu yanke alaka da su, saboda bazasu taba rabuwa da daddyn su ba. maganar Su Nazli ta ɗaga hankulan su, saboda suna son su kamar ran su amma still basu canza ra'ayin su ba.. Khalar Mujeedat tace ba zasu taba canza ra'ayin su ba, dole Sheikha ta za6a, ko dai Ta rabu da Hateem ta rayu da danginta, ko kuma taja ma kanta itama su Yanke alaka da ita. Hateem baisan sa,adda hawayen bakin Ciki suka wanke fuskarsa ba, sam Ya kasa magana sai dai jinjina kansa da ya ke yi. Daƙyar ya iya buɗe baki, cikin girmama yace baiga laifinsu ba, bai kuma ji zafin hukuncin da su ke so su Yanke mashi ba, mahaifin shi ne yaja ma shi! amma bai ta6a zaton jin hakan daga gare su ba, a matsayinsu na musulmai masu ilmin musulunci, sun san komai ya faru da shi mukaddarine daga Allah, bai kamata su juya mashi baya don mummunar kaddara ta same shi abun da ya faru da shi zai iya faruwa da kowa haka Allah ke jarabtar bawansa ta inda bai zata ba! amma kafin su fara yanke hukuncin raba shi da matar shi, yana neman alfarmar su akan su ba mujeedat za6i tun da tana da Ƴan ci, ta faɗi ra'ayinta akan alaƙarsu, saboda bazai ta6a sakin ta ba, kuma bazai rabu da ita ba, In har ba ita da kanta ta nemi ya sake ta ba, idan kuma su ka ce zasu tilasta masu, zai sanya lauyoyinsa a ciki. lokacin da ya yi maganar zuciyarsa a wuya ta ke, yana jin zai iya komai akan Mujeedat.. Gaba ɗaya sun kunna masu wuta babu wani sassauci so su ke kawai su raba su. A Lokacin da Hateem Ya sare da rokonsu akan su janye maganar raba su, Cikin fushi da 6acin rai ya miƙe cike da rashin kuzari Ya juya da niyar yabar falon harya fara tafiya, Unexpected Ya tsinkayi Muryar mutum a kunnanshi Yana kiran shi da sunan daddy minister... A sukwane ya dakata da yin tafiyar, Ya kasa motsawa, cikin ruɗu ƙwaƙwalwarsa ke kokarin tariyo masa muryar wanene Yaji a cikin kunnansa? Wanene me irin muryarsa? Wa kuma ya ke kira..."? Bai ƙarashe zancen zucin nashi ba Ya kuma tsinkayar muryarsa a karo na biyu yace"daddy minister, it's me Danish.. " Gabansa ne Ya faɗi a ruɗe Ya juya ya fuskanci inda Yake jin muryarsa kaitsaye idanunsa suka sauka akan Danish dake a tsaye sanye cikin shigar larabawa, kasa yarda yayi da abun da idanunsa ke nuna masa, ganinsa ya ke kamar a mafarki, Ya soma murza idanunsa da yatsunsa don ya tabbatarwa kansa daidai yake gani. Nazli da Yazin Tun fitowarsa suka hango shi, A rude suka miƙe tsaye kan kafafunsu suna bin shi da kallo mai cike da al'ajabi, ganin matashin saurayin da suka ta6a gani a farewall dinner din daddynsu, ba zasu taba mantawa da fuskarsa ba, musamman Nazli, cos a farko data fara ganinsa Taji kishi sosai saboda arayuwarta batason mutum me kama da ita, batason ace wani nada wani abu irin nata, saboda tsabar izzar ta, a lokacin abun daya ɗaure masu kai tayaya akai Yaron da yake a Nigeria ya zo dubai? kuma har cikin gidan family din su? Tayaya hakan zai yiwu? Wama ya kawo sa? Menene alakarshi da su? Sheikha mujeedat ce kaɗai bata motsa daga inda take ba, saboda tasan komai game da zamansa a gidan su. _Gaba ɗaya babu wanda yasan da zaman shi a falon, amma tun farkon da suka fara tattaunawa ya fito daga dakinsa da niyar ya tafi fadar Emir yana shigowa falon idanunsa suka hango mashi Mommynsa da Prime minister wani iko na Allah kallo ɗaya da yayi masa nan take ya tuna da komai daya manta, hakan nufin memory dinsa daya rasa ya dawo, yayi farin cikin sake ganin Prime minister musamman dayasan cewa daddynsa ne, to anan yaji komai da suke tattaunawa hankalinsa Ya tashi da jin zasu raba mommynsa da daddynsa_ Cikin rawar Murya Prime minister Ya furta"Danish! Kaine dagaske nake gani? Ko dai idanuna ne suka nuna min badai dai ba"? bai ƙare maganar ba, Danish Ya nufe shi da sauri yana isa gabanshi ya rungume shi sosai cikin farin ciki da murnar ganinsa. Babbar magana! Kallo ya koma sama, sai da Kowa dake a falon ya miƙe a sukwane cikin rudu su ke kallon su. Cikin shesshekar murya ya furta daddy ni ne, Danish, nayi kewarka, naji dadin sake ganinka arayuwa ta... " ji yayi kamar ana wanke damuwar dake a cikin zuciyarsa wani sanyi ne ya ratsa zuciyarsa, Ya ƙara ƙanƙamesa a kirjin shi kamar zasu koma mutun ɗaya sun dauki lokacin kafin Omair ya raba jikin sa daga na daddynsa ya juya ya nufi Emir da mamaki Ya hana sa furta kalma. zubewa yayi kan gwiwowinsa Ya dafe ƙafafunsa cikin sanyin murya ya shiga rokonsa akan karsu raba mommynsa da daddyn sa, su kaɗai ne fatan da ya ke da shi a duniyar nan! Su taimaka ma rayuwar shi, baisan komai ba baisan kowa ba, baisan Yana da iyaye ko dangi ba arayuwarsa saida Allah ya bayyana masa komai.. " Sannu a hankali ya fayyace musu irin rayuwar da yayi a kurkukun kaddara cikin harshen turanci, waɗanda basa ji a cikin su Yazrin ce ke fassara musu da larabci saboda sun nuna,suna son suji me Ya ke cewa. Labarin Danish Ya ta6a zuciyarsu, jikinsu yayi sanyi laƙwas, idanun su suka cuccuka da ƙwalla, tausayinsa ya kama su, sun razana da jin zalunci da kakansa ya yi masa sun kuma sha ruwan mamakin jin cewa jinjirin Mujeedat ne da ta haifa a mace shekaru ashirin da suka gabata. kafin ya ƙarasa musu labarin tuni hawaye sun wanke fuskar sa. Bayan ya ƙare ya cigaba da cewa"su duba halin da yake a ciki, baisan ko yana da tsawaicin kwana ba, amma su taimaka masa su barshi Ya samu kulawar iyayensa, su kaɗaine zasu iya bashi abun daya rasa arayuwar sa! Yana son su! Yana son ya rayu da su har karshen rayuwarsa"! Cikin karyayyar Murya Khal Ya dubi Mujeedat Ya tambaye ta dagaske ne komai da Yaron ya faɗa? Kuma tayaya akai suka gano ɗan su ne"? Idanunta cike tab da kwalla ta jinjina kanta, cikin raunanniyar murya ta fara basu labarin Danish tun farkon lokacin da Prime minister ya haukace akan son shi da ranar da suka fara ganin shi a farewall dinner din hateem, har zuwa Dna test da ta yi, ta kuma fayyace musu komai da suka tattauna da Owais har ta yi masa hanyar zuwa dubai, anan prime minister yaji komai da suka 6oye masa, bazan iya misalta farin cikin dayaji ba na kasantuwar Danish ɗansa, bakinsa Yaƙi rufuwa dama tun a kallon farko daya fara ganin fuskarsa yaji a jikinsa jininsa ne shi, Ya ilahi, baisan sa'adda Ya durƙushe ƙasa yayi sujudusshukur agaban kowan nan su bai iya ɗagowa ba saima ya kamayin kukan farin ciki. Gaba ɗaya Al'ummar falon suka furta Allahu Akhbar!! Allahu Akhbar!!! ~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Cike da nadama Emir Ya ruƙo damtsen hannayen Omair ya miƙar da shi tsaye a hankali ya soma share masa hawayen sa da yatsunsa kafin ya rungumesa a kirjin shi.. Cikin karyayyar murya yace ya yafe masa, yayi danasanin furucin da yayi na raba mommynsa da daddynsa, hakika labarinsa ya karya zuciyarsa, ya tausaya ma rayuwar sa, amma ya yi haƙuri da jarabawowin daya fuskanta arayuwarsa, In sha Allah yayi bankwana da bakin ciki, zasu bashi goyan baya gurin taimaka masa na ganin ya samu abun da bai samu ba arayuwarsa, bayan haka ya soke maganar raba tsakanin Iyayen sa, kuma Ya gargaɗi kowa daya janye maganar baya son a ƙara tadata. Tun da sukaji maganar Emir Kowa Ya zubar da makaman Yaƙin sa dama tuni jikinsu yayi sanyi, Farin Ciki agurin sheikha Mujedat da Hateem baya misaltuwa, Tun ayanzu sun fara alfahari da ɗan nasu saboda kyautar Allah ne shi agare shi, gashi tunkan aje ko'ina ya fara kawo masu maslaha. Tsabar Farin Ciki Yasa Yazrin Ta nufe shi jikinta na 6ari cike da dokinsa Ta rungume shi ta fashe da kuka tana fada masa Yar uwarsa ce ita, iyayensu ɗaya, yayarsa ce ita, daga ita sai shi, tana son shi tana ƙaunarshi kamar ranta, tayi farin cikin kasantuwarsa dan uwan su, tana taya su murna, tun ranar da tagansa ta fara ji aranta jinin su ne shi.. Bawan Allah ruɗewa ya yi da Yazrin ta rungumesa sai yaji wani dadi mara misaltuwa ganin yar uwarsa, a hankali ya sanya hannu biyu ya tallabe ta.. A lokacin Nazli tasha jinin jikin ta, son shi da ƙaunarsa sun mamayi izzarta, girman kai na nema Ya cusa kishinshi amma zuciyarta taƙi aminta da hakan saima azalzalarta data dingayi akan ta je gurin shi ta rungume shi. Batasan ma sa'adda ta nufe shi ba, ta baya ta rungume shi sosai taji wani daɗi ya lullu6e zuciyar ta, kwata kwata Danish bai san ta ba, lokacin data rungume shi batayi magana ba, saida sheikha mujeedat ta janyo hannunta ta dawo da ita ta gaban shi ta gabatar mashi da ita a matsayin first born dinsu Nazli kuma yayar sa, Ya razana da ganin kamannin su yadda kasan an tsaga kara, hugging dinta yayi tighly su ka ji ɗumin junansu, batasan sa'adda ta saki kukan farin ciki ba, tadinga lallashin shi tana shafa sumar kanshi tana kara kankame shi a jikinta kamar wani yace zai ƙwace mata shi, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi. (🥺) Dangin Mujeedat sun Tayasu murnar Ganin ɗan su Omair, sun kuma sasanta tsakaninsu da surukin su Hateem. Tun aranar Mai martaba Ya sanya date din da zai yi ma jikansa Omair Party saboda farin cikin ganin shi, da kuma tayashi murnar haduwa da iyayen sa. A daren ranar, gaba daya Iyalin Hateem A bangarem mujeedat suka kwana tare da Omair dinsu, raba dare su ka yi suna faranta masa har dinner suka yi a tare da shi, A ƙarshe ma da zasu kwanta yin bacci a tsakiyarsu suka sanya shi kamar wani yace zai sace masu shi. Lokacin da ranar Partyn ta zo, Khal din Mujeedat ne Ya ba Omair Kyautar tsadaddun kayansu na larabawa da takalma na alfarma, su ya sanya aranar, abi dinsa da umminsa ne suka tayashi sanya kayan a jikin shi, yayi kyan da ba zai misaltu ba, A katafaren Hotel din da babu tamkarsa a fadin dubai aka shirya shi wato Burj Al-Arab cikin katafaren grand ballroom din da ke a cikin hotel ɗin. Celebrity guests ne suka halarta, mashahuran business leaders na kasar dubai da arabic scholars, uwa uba gaba daya Rulers na UAE Sun hallara, tun daga kan President of the UAE, ruler of abu dhabi, da Ruler of sharjah, da sauran su, ƙwansu da kwarkwatarsu, Emir ne ya gayyace su saboda suzo tayashi murnar bayyanar Jikansa kuma sun amsa gayyatarsa. Bugu da ƙari a ranar manyan Baki suka zo daga Canada, advisors din Hateem, Chief of staffs, Deputy prime minister tare da Senior cabinet ministers, tun daga canada sukazo a cikin private jet, badan komai ba sai don su yi bikon shugaban ƙasar su daya yi murabus, kwata kwata Hateem baisan da zuwansu ba, saboda basu tuntu6e shi ba, hasalima layukanshi a kashe su ke. ta yadda akai har sukasan yana a dubai ta hanyar Canadian Polices din da ke a tare da shi. Zuwan bazata su ka yi mashi, Unexpected ya gansu a Ballroom din da ake gudanar da partyn yayi mamaki cikin girmamawa da karramawa Ya tarbe su da hannu bibbiyu saboda an yi zama na amana, sunyi farin ciki da ganin shi saboda sunyi kewar shi. Dakin Taron Ya cika makil da al'ummar Annabi, abunka ga taro na hamshakan masu kudi kowa ka kalla kayan alfarma ne a jikin shi, hada manyan mawaƙan larabawa da aka gayyata sai raye-raye da kide-kide su ke yi masu ƙayatarwa, ga Arabian dinner buffet domin baki su cika cikunansu. Hateem da Mujeedat tare da Mahaifinta harma da kawunta da Her highness sune masu yiwa baki maraba da zuwa.. Saida Kowa Ya hallara, Baka jin komai sai sautin kide kide da raye raye, da firarrakinsu cikin harshen larabci da turanci. Lokacin da Yazrin da Nazli suka shigo tare da Omair cikin ɗakin taron, sun sanya shi tsakiyarsu, yayin da suka ruke hannayen shi, karkuso kuga Yadda idanu su ka dawo kan su, wadanda basu taba ganinsa ba, tsantsar al'ajabi da rudune Ya cika zukatan su, suka dinga tambayar wanene shi? Dan wanene wannan yaron mai bala'en kama da Prime minister? A lokacin rudewa yayi ganin yadda mutane ke kallon shi, musamman matasan yan matan da ke a gurin ya tafi da imanin su, Jikinsa Ya hauyin kerma yayi saurin la6ewa bayan Nazli, ba karamin nishadi Ya basu ba, ta dinga kwantar masa da hankali tana cewa karyaji komai ya saki jikin shi, kallon da sukeyi mashi na mamakin waye shi su ke amma da zarar sunji wanene shi zasu daina. Cikin harshen Larabci Gimbiya Mujeedat ta gabatar musu da Omair baby Boy dinta data haifa a mace ya dawo araye, da yake sunsan komai daya faru da dangin hateem nan take suka fahimci Yaron Yana daya daga cikin waɗanda baban Hateem Ya sadaukar, aikuwa sunyi farin ciki da ganinsa, suka soma tayasu murnar ganin Yaronsu tare da yi mashi fatan Alkhairi, Kowa son shi ya ke yi, ɗokinsa su ke yi, Wani irin farin jini yayi a dakin taron kowa zancen shi ya ke yi, manyan baki suka dinga hugging dinsa suna manna masa kiss on his cheeks irin gaisuwarsu ta larabawa, da masu ruke hannunsa suna yin musabaha da shi. duk yasha jinin jikin shi saboda bai saba mu'amala da mutane ba, idan suka tayashi murnar haɗuwa da iyayen shi, dakyar ya ke iya buɗe baki yayi masu godiya. Advisors din Hateem sai nan nan suke da shi, har sun naɗa mashi nickname Young president acewar su nan gaba shi ne zai gaji uban shi. Amma Yayi farin cikin da bazai misaltu ba, musamman lokacin da mutane suka kewayeshi suna raira mashi waƙa, Daddynsa Ya ruƙo hannunsa su ka yi rawa atare harma da mommynsa, mutane sunata ɗaukarsu videos da hotuna wasu ma live suke dauka. Haka lokacin da zasu ci abinci Yaji dadi sosai, musamman lokacin da mommynsa ta bashi dabino abaki yaci, sisters dinsa suka ciyar da shi abinci yaci ya koshi, bayan ya gama cin abincin, daddynsa ya shayar da shi ruwan zam zam, a bainar Jama'ar dake dakin taron, idanun kowa akan su gwanin burgewa, wasu ji suke dama ɗansu ne Omair. Gab da za'a tashi daga taron Celebrities suka fara gasar bashi tsadaddun kyaututtuka na fitar shari'a, Mutun na farko daya fara bashi kyauta kakansa Emir ne Ya damƙa masa kyautar Private jet wanda darajarsa takai $50 million tare da dawakai biyar, President Of UAE Ya bashi kyautar katafaren private villa in Dubai's Burj Khalifa, ruler of sharjah ya mallaka mashi Private yacht. Chief Of Staffs na canada Ya ce shima baza a bar shi abaya ba, ɗan Hateem kamar dansa ne saboda haka Ya bashi kyautar Luxury penthouse in Ottawa wanda darajarsa takai dala miliyan biyu, tare da gold-plated, luxury cars, Khal din mujeedat shima Ya bashi kyautar Luxury villa a cikin dubai, Elder brother din ta Sheikh Hameed Ya mallaka masa kyautar danƙara-danƙaran SUVs, tare da Rolex watch wadda darajarta ta kai dala ɗari. kunsan harka ta mashahuran masu arziƙi akwai son gwaninta basa ƙaramar harka, kowa burinsa Ya bashi kyautar da tafi ta kowa, sun maida abun gasa a tsakaninsu, daga wannan ya faɗi kyautar shi sai a samu wani gwanin ya ninka wadda tafi ta shi, kamar basu san zafin neman dukiyar ba, kuma ahaka babu abunda ya ragu na daga arzikinsu, wani ji yake kamar bai cire sisi a cikin dukiyarsa ba, saboda tsabagen arzikinsa. *hmmm Dare Ɗaya Allah kanyi bature, gashi Allah yayi baturen Danish ko ince Omair 😍 nima ya Allah gani da ɗan ƙoƙwan barata 😂 ni ma Allah ka maida ni danshinsa 😄 Ina ma ace ni suke gasar ba kyaututtukan nan, wallahi da tsiya taji kunya😄 just for fun* Lokacin da suke gasar bashi kyaututtukan kowa Yana faɗin tashi kyautar, Gimbiya mujeedat da prime minister Sun yi farin ciki mara adadi, Omair baisan meke faruwa ba, sai da Yazrin ta dinga yi masa bayanin kyaututtukan da suke bashi in bai gane sunan abu ba, a cikin waya ta ke nuna masa hotunan su, bawan Allah Ruɗewa yayi saboda Ya razana da jin abubuwan da suka mallaka mashi, shi da ba kowan kowa ba arana daya sun maida shi billionaire. Baisan sa'adda Hawaye suka Wanke fuskarsa ba saboda tsabar farin ciki, Yama kasa bude baki yayi musu godiya saboda farin ciki, hawayen shi da suka gani ya sa suka fahimci farin cikine Ya kashe mashi baki hakan ba ƙaramin faranta ransu ya yi ba dama sunyi ne saboda su faranta ransa kuma sun samu abun da suke so. Agaban Kowa dake adakin taron prime minister da sheikha suka tambayesa ya faɗa musu me ya ke son su bashi a matsayin kyautarsu na iyayensa? Suna son suji komenene Karyaji shakku Ya faɗa musu in sha Allah zasuyi ma shi. A lokacin bakomaine Ya faɗo masa aranshi ba face kalaman Unaisah, da su Ya ke kwana da su Ya ke tashi aran shi. Cikin sanyin murya yace kyautar da ya ke so daga gare su itace su taimaka mashi, su bashi kwarin gwiwa da goyan baya don ya samu ilmi, kawai su wayar masa da kansa yanason Yasan komai Yana son ya goge ya koyi abubuwan da bai iya ba.... " ya karashe maganar da hawaye akan kuncinsa, gaba daya iyayen sa da sisters nasa saida suka zubar masa da ƙwalla, Tausayin shi ya kama su. Anan take su ka yi mashi alkawarin za su yi iya kokarin su gurin cika mashi burin shi, kuma zasu canza mashi rayuwa su mantar da shi duk wata wahala daya ta6a sha abaya. Ranar Omair ya ga tarin masoyan sa, mutane suka dinga daukar hotuna da shi, wasu ma video su ke yi, a karshe taro Ya tashi lafiya, kowa ya tafi da farin cikin ganin Omair. Bayan kammaluwar Partyn, daga bisani Hateem ya tafi Da mutanansa Private resident dinsa na dubai, A Falo suka zauna cikin muryar lallashi suka fara zayyana masa dalilin daya kawosu Dubai, su ka ƙara da cewa Ya taimaka ya dawo kan mulkinsa, canada tana bukatar shi, su basu gaji da shi ba, suna son shi, suna son mulkin sa, ya janye maganar murabus dinsa, kar ya damu su ba zasu ta6a alaƙanta shi da laifin babansa ba, sun yarda da shi, sun san bashi da sa hannu, mutane suna ta ƙorafi akan murabus dinsa Ya taimaka kar ya karya zuciyar waɗanda suka aminta da shi. Kalaman su sun so suyi tasiri a cikin zuciyarshi sai dai bayajin zai iya komawa ga mulkinsa. Yace yaji dadin nuna damuwa akan shi da su ka yi, shima Yana son su Yana jin inama zai iya cigaba da ruƙe canada sai dai kash zuciyarsa ta yi raunin da ba zai iya ba, ayanzu yafison Ya koma kasarsa cikin Yan uwansa don ya ci gaba da rayuwa da su. Kamar zasu sanya mashi kuka, ba irin magiyar da basuyi mashi ba amma ya kafe akan bakansa, a karshe sukace zasu tafi masaukinsu amma ba zasu bar dubai ba, har sai sun yi nasarar shawo kan shi tukunna. Bayan sunyi sallama da shi, Ya koma Ruler's resident Ya kira Mujeedat awaya, bayan ta same shi a part din ta, Suka zauna cike da damuwa ya fayyace mata komai da suka tattauna da bakinsa na canada. Ta numfasa tace ita kanta bazata goyi bayan murabus dinsa ba, tuntuni taso tayi masa magana bata samu damar yi ba amma bataji dadin murabus din da yayi ba a live video din daya saki, meyasa zai sare saboda laifin da bashi ya aikata ba? mutanan canada suna son shi, kada Ya karya musu zuciya, tun da har su basu nemi Ya sauka daga kan mulkinsa ba why shi zai aje"? Yace mata ta fahimce shi, ba zai iya ba, yayi rauni, mulkin ya fita aransa, dama siyasa ba ra'ayinsa bace, baban su ne Ya cusa masu ita, Yanzu kuma yaji ta fita aranshi, bayason komai daya shafi siyasa yafison Ya rayu tare da yan uwansa a Nigeria, tun da babu abun daya nema ya rasa, kuma abun da yafi damunshi lokacin da zai ba Omair, Idan har ya koma kan mulkinsa tayaya Omair zai samu kulawar sa? Yana son ko da yaushe ya kasance a tare da shi. Kalaman sa sun karya mata zuciya, ta fahimce shi sosai, ta kuma fahimci dalilin dayasa mulkin ya ƙara fita ran shi, amma tace yayi hakuri ya koma inyaso nan gaba kaɗan Sai Ya aje mulkin amma yanzu idan yayi murabus babu gaira ba dalili ga abun daya faru da mahaifinsa mutane zasu zargi wani abu. Dakyar ta samu ta shawo kan shi har ya ce zaiyi shawara da Yan uwansa yaji ta bakin su. Wata ɗaya su ka yi A Dubai ƙarƙashin kulawar dangin Mujeedat, daga bisani bayan daya gama yin shawara da yan uwansa gaba daya suka goyi bayan ya janye murabus din da ya yi har suka faɗa masa game da abun daya faru bayan zuwan dangin iyayensu mata, yayi farin ciki mara misaltuwa, ya kuma ƙara jin karfin gwiwa a tare da shi, su ka ce koda zaiyi murabus din kada yayi saurin yanke hukunci Ya bari sai nan gaba zuwa lokacin da ƙura ta lafa idan yaji baida ra'ayin ya cigaba sai ya yi murabus ɗin, suma sun nuna basu son mukamansu amma danginsu iyayensu mata sun nuna rashin goyan bayan su su yi hakan sun kuma ƙarfafa masu gwiwar su cigaba. haka kuwa akayi bayan ya gama yanke shawara da su, batare da 6ata lokaci ba su ka koma babban birnin Canada. ~________________________________Ottawa, Ontario, Canada~ A ranar da suka isa, Bayan da jirginsu yayi landing A airport, Yan jarida da Yan kasa suka cika makil domin tarbo sa sai farin ciki sukeyi da murnar dawowar Hateem da dansa Omair, dakyar Secuty details nasa suka yi masu ƙawanya har suka shiga cikin motocin escorts din da su ka zo ɗaukar su. A washe garin ranar da suka koma Canada, har party governor general Yasa aka shiryama Hateem da Iyalinsa saboda murnar dawowarsa da kuma tayasa murnar ganin ɗansa Omair. manyan ƙusoshin gwamnati da shahararrun ƴan jarida ne suka hallara domin tayasu murna. Danish dai Yasha ruwan mamakin Ganin yadda Al'umma suke Girmama iyayen sa, shi kanshi dayake baƙo a family din nasa girmamasa su ke yi.. Anan ma Ya samu wasu ƙarin kyaututtukan na ban mamaki har baisan ma inda zai sanya kanshi ba saboda ruɗewar da ya yi duk da azahirin gaskiya Omair bai damu da abun duniya ba, hasalima ba kowani kyale kyale ke burgesa ba, amma idan aka basa kyauta yana jin dadi sosai saboda akwai wadanda ya ke da burin ya bama kyaututtukan. Cikin ƙanƙanin lokaci rayuwar Omair ta sauya, musamman saboda ya samu gogewa ta bangaren ilmin addinin musulunci dana boko yasa Prime minister Ya ɗauki hayar private teachers din da zasu dinga zuwa har gida suna ilmantar da shi, bayan teachers din da Hateem Yasa suna koya masa karatu saida Gimbiya mujeedat ta dauki hayar therapist da Mentor saboda shi kawai, Albashi mai tsoka suke biyan su burinsu Omair Ya cika burinsa na samun ilmi, ya kuma manta da trauma din da ke damun shi. Bayan haka sisters dinsa duk idan suka samu free time suna ilimantar da shi ta hanyar bashi lokacin su, su fita yawon shaƙatawa da shi, haka mom dinsa da daddynsa basu gajiya da 6ata lokaci gurin faranta masa rai, gata yayi masa yawa, jin dadi ta ko'ina, Ya rasa gane waya fi son shi tsakanin iyayensa da sisters dinsa? Kowa burinsa ya faranta masa rai, basu san 6acin ranshi, Ko jinjiri bai kaishi samun kulawa ba, ko sautin tarinsa ya sauya sai sun kira doc dinsa ya duba lafiyar sa. Baida lokacin komai saina karatu, su kansu suna mamakin yadda yaba karatu muhimmanci fiye da komai in ka cire ibadarsa. Baya gajiya da yin karatu, idan kana nemansa, Ka duba cikin bedroom dinsa a saman kujerar study table dinsa, idan baka same shi anan ba, to ka duba a home library, In nan ma baka gan shi ba ka duba garden, ko Classroom dinsa Inda teachers dinsa ke koya masa karatu. Bawan Allah, kullum Yana a rungume da books yana karatu, sometimes da su ya ke kwana rungume a kirjin sa, yasa naci da dagiya, Ya sadaukar da ƙwaƙwalwarsa ga karatu, ko bacci ya ke yi ya dinga sambatun karatun da akayi masa. Abun dayafi basu al'ajabi game da shi kaifin basirar da ke gashi da saurin hadda ce karatu, he was gifted and a genus, masu wuyar samu a duniya, su kansu malamansa Yabon shi su ke yi suna al'ajabin irin hazaƙar sa. Malamansa har fita sukeyi da shi Yawon buɗe ido badan komaiba sai don su wayar mashi da kan shi ya kuma ƙara ilmi. Iyayensa sun ɗaura burin duniya akan shi, son shi su ke yi da zuciya ɗaya, Komai nasa mai tsada ne, suturarsa, takalmansa, turarensa, abincin sa, basu wasa da komai na shi, musamman su ka ware masa bodyguards masu kula da shi. Cikin shekara ɗaya kacal su ka yi nasarar goge masa trauma din Suka wanke masa ƙwaƙwalwar sa da jin dadin rayuwa, Ya sauya gaba ɗaya, Ya zama wayayye mai tsantsar ilmi, ya goge ta fannin rubutu da karatu, haddar al'qur'ani dayafi bada himma akanta, Har yayi izuf talatin a cikin shekara ɗaya da watanni, tsabar wayewarsa ko magana yayi sai yaja hankalin mutun saboda komai nasa cikin qasaita da aji yakeyin sa, hatta salon tafiyarsa ta sauya, idan yayi dressing Ya fito outing gaba daya idanun mutane ke dawowa kansa. Yan matan dake hauka kan soyayyar shi basu ƙirguwa. shafukansa na social media miliyoyin mutanene ke following dinsa. A cikin shekara ta biyu ne da iyayensa suka tabbatar Ya samu wayewa da gogewa ta fannin ilmi sanan suka fara tunanin sanya shi school, dama abun daya hana su sanya shi tun farko abu biyu ne! Saboda basu san ya fara zuwa makaranta a matsayin jahili wanda baisan komai ba, saboda gudun kada students su dinga tsokanarsa, dama ga baƙin tabon da kakansa Yabar masa dole asamu wadanda zasuyi bullying din shi akan abun da kakansa ya yi, shiyasa sukaji shakkar su sanya shi amma yanzu sun samu ƙwarin gwiwar kaisa school da zumar zasu baza guards dinsa har cikin Class din da zai zauna saboda tsaro. malaman sa na gida ma sun goyi bayan su kaishi school saboda zaifi samun ilmin zamantakewa da mutane idan yana mu'amala da su, dama dole sai kana tare da mutane ka ke iya koyan zama da su. Ko da suka tambaye shi me ya ke da burin ya zama nan gaba? yace baida burin daya wuce ya zama jami'in Isod saboda yana son aikin da zai taimaki rayukan Al'umma da kuma kawar da mugun iri a cikin su. Sun yi farin ciki da jin hakan sosai, duk da za6in nasa bai kwanta aran su ba, saboda basu san yayi aikin da zai iya jefa rayuwarsa a haɗari amma saboda jin kyakkyawar manufarsa yasa basu nuna ƙin amincewar su ba, bayan haka suna son abun daya ke so, dan kuma saboda Owais. Bayan Prime minister ya kira Owais awaya ya faɗa masa abun da suka tattauna da Omair, Owais yayi farin ciki sosai da jin burin da ya ke da shi na zama jami'in isod, dama ya dade yana yi masa sha'awar ya zama Jami'in Isod, tun lokacin daya ga irin ƙarfin da Allah yayi masa Yasan cewa zai iya! Nan ta ke ya shawarci prime minister da su sanya shi jami'a ya karanci cybersecurity, prime minister yace ya gode da shawarar da ya ba shi. Batare da 6ata Lokaci ba suka aiwatar da hakan. a wani zuwa da Owais yayi nan Canada, har bugun cikin shi yayi kamar yadda ya sabayi duk inyazo don yaji idan Yana tunawa da su Unaisah saboda iyayensa sun faɗa masa baya maganar kowa nasa, suna tunanin yayi loosing wani bangare na memory dinsa. yace masa ba zai iya tuna su wanene su ba, baisan su ba, lamarinsa ba ƙaramin ɗaurewa Owais kai ya ke yi ba, zai iya tunawa da wani bangare na rayuwarsa a kurkukun ƙaddara amma kwata kwata bai iya tunawa da yan uwansa fursinoni ba, bai matsa masa akan ya tuna ba. daga bisani suka tattauna fira kamar yadda suka saba duk idan yazo, kuma yana jin dadin Sauyin rayuwar daya samu ya zama cikakken mutum mai hankali da nutsuwa. Gaba ɗaya komai dake faruwa yan uwansa ex-prisoners basu san Yana araye ba, an 6oye masu komai game da shi, saboda abu uku, na farko saboda rayuwarsa tana a cikin haɗari yasa suka 6oye kasantuwarsa araye! Bayan da shari'ar Elders ta ƙare babu sauran tashin hankali, still basu baiyana ba, saboda yayi loosing memory dinsa, ko da sun fada mashi game da yan uwansa ba lallai ya kula su ba, za su ji ba dadi, kuma zuciyar su zata karaya, ace ga garkuwansu amma bazai iya tuna ko su wanene su ba. duk da unforgettable life din da sukayi a prison, duk da irin farin jinin da yayi a media basu taba cin karo dashi ba dan da yawansu ba ma'abota social media bane, tun bayan shari'ar su baba obie, amfani da social media ya gagare su, saboda wasu jahilan mutane da ke yi masu comment na cin zarafi ahlin su, a kan laifin da basu suka aikata ba yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa wasu suka daina hawa kwata kwata, kuma sunayin life dinsu a wuri guda ne daga gida sai school sai kuwa in za suje shopping ko yawon buɗe idanu shima din tare da rakiyar bodyguards din su, saboda su ba su kariya. Abu na biyu dayasa basu san su matsa masa akan ya tuna da yan uwansa saboda idan memory dinsa ya dawo a tunanin Owais zai iya katse karatunsa ya tafo Nigeria saboda su, Wanda shi a yadda ya shirya sai ya gama zama cikakken mutum ya samu ilimin rayuwa yadda ya kamata sannan ya gabatar da Danish ga yan uwansa, waɗannan ƙwararan dalilan ne yasa bai faɗa ma su ba, ya bari har zuwa lokacin da ya tuna su da kan shi, kuma hada ƙarin yaga yan uwansa a lokacin sun jure rashin shi azaton su ya mutu shiyasa suka fidda rai da shi, suna ta yin rayuwarsu cikin jin daɗi. daga cikin waɗanda suka san yana araye bayan yan uwan daddynsa sai kuma Taj da Salsabeel da big guy, da kuma Sheikh imam malik, Owais ne ya faɗa masu tuntuni, a ranar da sukaji yana araye sunyi farin ciki mara misaltuwa. Yan uwan daddynsa suna zuwa kawo mashi ziyara nan Canada, musamman Chief Owais baya gajiya da zuwa Canada saboda yaga beloved cousin dinsa, ko ba su a tare Yafi kowa kiran sa video Call, Taj kuma yana samun labarinsa a wurin owais kuma bai taba nunama Angel Danish yana a raye ba, ya barshi a matsayin sirri kamar yadda suka tsara. Abun da basu sani ba, Omair Yana sane ya ke yin pretending kamar yayi loosing memory din sa, idan Chief Ya tambayesa game da yan uwansa, ba dan Komai ba sai don bayason su san Yana araye, saboda Alwashi ne Ya ɗaukarwa kansa bazai ta6a komawa gurin Unaisah ba har sai Ya samu ilmi da wayewa ba dan Ya dauki fansar kalaman da tayi masa ba duk da Yaji zafin su kamar ta goranta masa ne amma shi a wurinshi ta taimaka masane gurin farfado masa da tunaninsa, ta sanya mashi buri a rayuwar sa, kuma komai da yayi yayi ne saboda ita, saboda yana son su rayu cikin jin dadin rayuwa batare da jahilcinsa ko evils dinsa sun cutar da ita ba, yana son tayi alfahari da shi aranar daya koma mata a matsayin mai ilmi da wayewa me kuma cikakken Asali dan babban gida, kuma Alhamdulillah Allah Ya cika masa burinsa duk da Yasha baƙar wahala na rashin Unaisah a tare da shi, ba ƙaramin azabtuwa ya ke yi da sonta ba, idan jarabar sonta ta motsa mashi kulle kanshi ya ke yi a daki ya dinga zuba karatun al'kur'ani, sometimes Shower Ya ke sakarwa kansa ko Ya sha sedative har sai ya samu sassauci tukunna ya ke lafawa. har rokon Allah ya ke yi daya rage mashi sonta saboda ya samu Ya ci ka burin shi, baya son duk wani abu da zai kawo masa cikas a karatun sa. A cikin shekara ta huɗu ne, wata rana Sheikha Mujeedat ta shiga bedroom dinsa don tayi masa sannu da dawowa daga school, ta iske ya shiga bathroom, taji bazata Iya fita batare data sanya shi a idanunta ba. Ta nufi Study desk dinsa inda Laptop dinsa da kayan karatun sa suke, Anan taci karo da Diary dinsa daya manta bai kulle shi ba, hakanan taji tana son ta buɗe taga menene a ciki. Tun a shafin farko ta fara cin karo da Destinyshield da ya rubuta tare da zanan Love. Aranta ta ayyana Omair ya fara soyayya ne? Da fara'a akan fuskarta ta buɗe shafi na gaba ta soma karantawa, nan take ta fahimci bai yi loosing memory dinsa ba, tun da gayanan Ya rubuta gaba ɗaya labarin soyayyar sa da Destiny ɗinsa, labarin rayuwarsu a prison yayi mata dadi sosai taji dadin karanta shi, sai dai akwai kalaman da tagani wadanda suka ɗan ta6a mata zuciya har ta fahimci cewa ya ta6a samun sa6ani da destiny ɗinsa, a cikin zuciyarta ta shiga maimaita maganganun daya rubuta. _"Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai kuɗi mai asali ɗan babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?_ _"Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"_ _"Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaƙi? Ko arne mara addini? Ko kuwa jahili da baisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"!_ Nan take ta fahimci destiny din nan itace silar da yayi pretending yayi loosing memory din yan uwansa, kuma kalamantane suka zaburar da shi harya sa dagiya da naci don ya samu ilmi, lallai ba ƙaramin so ya ke yi mata ba. Wani shafin ta buɗo ta shiga karantawa kamar haka.. _"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_ Ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta a sa'ilin da ta kare karantawa. Rufe diary din tayi, cikin sanɗa ta fuce daga dakin, bayan ta koma part dinta ta fara safa da marwa tana tunanin tayaya zata san wacece destiny dinsa"? saboda tana son taci ka mashi burin shi na ganin ya mallake ta, saboda yarinyar ta kwanta mata aranta tun da ta karanta irin kyautatawar da tayi masa ta fahimci tana son ɗanta kamar ranta. Layin Owais ta kira after yayi picking ta tambayesa wacece destiny? Taga sunan a diary din Omair harma da Takaitaccen tarihin alaƙar su. Owais yasha ruwan mamakin yadda Danish ya ke masa pretending ya manta da yan uwansa ashe yana sane da su, kuma a labarin da mujeedat ta fada masa ta karanta a diary dinsa, yasa shima ya fahimci saboda kalaman Unaisah ya nisanta kan shi da su amma yana da burin ya dawo gare su wata rana. nan ta ke Ya labarta mata komai daya sani game da alaƙar Danish da Unaisah harma da halin da ta shiga bayan da taji ya rasu. Ta tausaya mata sosai, Tace tana son hotunan Yarinyar Ya tura mata a whatsapp, sannan tana son Ya taimaka mata su nema masa auranta, saboda batason Ya rasa ta, zata iyayin komai don ta cika mashi burin shi. A lokacin da tayi maganar Owais baiji komai ba, saboda ya riga daya hakura da soyayyar Unaisah dama alkawarine Ya daukarwa kansa in har Danish yana araye shi kuma ya haramtawa kansa auran Unaisah, saboda yafi shi cancanta ya aureta, kuma bazai iya raba soyayyar su ba, tun lokacin daya gano akwai soyayya mai karfi a tsakanin su tun a Prison irin soyayyar da zasu iya rasa rayukansu akan Juna, ba zai ta6a mantawa da ranar da ya riske shi a cikin toilet yana bubbuga kanshi jikin sink saboda sun samu sabani da Unaisah, tun anan Jikin shi yayi sanyi. Nan ta ke ya goyi bayanta, Yace shima zai bada gudummuwa ta hanyar yi masu jagora gurin nema mashi auran ta, taji daɗi sosai ta dinga masa godiya. Bayan da suka gama yin wayar, ya tura mata hotunan Unaisah ta whatsapp hada videos dinta nan take ta gane fuskarta cikin yaran da yazo da su aranar farewall dinner na hateem, dama ta daɗe da siye zuciyarta, tayi farin ciki da kasantuwarta yarinyar da Omair dinta ya ke so. Kwata kwata bata nuna ma Omair tasan sirrin soyayyarsa ba, saboda batason Yaga kamar tayi masa leƙen asiri, tafi son ta bashi mamaki. daga baya Owais ya kira shi awaya, bayan sun gaisa cikin mutunta juna, yace mashi yadaina boye mashi, ya riga da yasan baiyi loosing memory nasa ba, kuma har yanzu yana son Unaisah!. A lokacin ya za6i daya bayyana masa gaskiya tun da ya riga daya gano sa, bayan daya faɗa masa dalilan dayasa bayason ya koma gare su. Owais ya fahimce shi, yace tun da yanzu ya cika burin shi, Yana da asali, Yana da dukiya, yana da ilmi da wayewa me zai hana Ya fara soyayya da Unaisah"? cikin sauri yace bayason Tasan Yana araye yanzu har sai ranar da ya ƙarasa haddace alqur'ani mai girma da kuma degree dinsa tukunna. Owais yace duk da haka zai taimaka masa yayi soyayya da ita batare da ta Iya gane shine ba. daƙyar ya samu ya shawo kanshi har ya amince. Unaisah batasan komai ba, babu wanda Ya fada mata, wata rana Owais Ya kirata awaya bayan da suka gaisa Ya fada mata ya canza sim din da zasu dinga yin waya saboda su kawai. Bayan daya tura mata new number dinsa tayi saving, ashe tsawon lokacin da ta ke yin chatting da Chief Owais a whatsapp ba shi bane Danish ne ya ke kiranta video call yayi hidding front camera don karta gan shi, sometimes tasha taji muryarsa tanayi mata kama data Danish amma saboda sanin baya araye yasa bata gaskata hakan ba saita barshi amatsayi gizau da muryar take mata a lokuta da dama. Sometimes Raba dare sukeyi suna yin video call, taita fama da shi akan Ya daina boye kansa tana son ta dinga ganinshi amma sai yaƙiya. Saida takaiga Wallpaper din wayarsa Hotonta ne, Haka gallery dinsa hotunan Unaisah ne da videos dinta da ya ke sanyawa ta tura masa. baya gajiya da kallon ta, a ranar data fara tura masa hotonta Ya razana da ganin kyawun da tayi, kamar ba Unaisa ba, mamaki ne ya kamashi sosai ganin Abin da ya ke tsokanar ta akan bata dashi yanzu sun girma irin yadda ya ke so, wata irin kewarta ya ke ji da kuma San kasancewa tare da ita, baya gajiya da kallon pictures dinta ko dan ɗebe ma kanshi kewa. Gimbiya Mujeedat ce ta fada ma abie dinsa da Sisters dinsa game da soyayyar Omair, ta kuma nuna masu hoton Unaisah, Prime minister yayi murna sosai saboda shima Ya shaida soyayyarsu musamman daya tuna ranar da suka kamata a ɗakinsa ta la6e cikin labule. Nazli data ga hoton Unaisah nan take ta tuna ta wato yarinyar da faryat ta kulle a cikin restroom saboda ita. tayi mamakin jin hakan, azaton ta soyayya ta ke yi da Owais sai kuma taji labarin soyayyarta da Kaninta, batare da sanin Kowa ba, Ta kira Owais awaya ta tambayesa tayaya akai yarinyar da ya ke so ta koma soyayya da kanin ta? Ko dama ba son ta ya ke yi ba"? Yace mata ya ta6a sonta abaya amma ya hakura da ita tun lokacin daya gano alakar dake a tsakaninta da Omair, amma ba hakan na nufin ita kaɗai zai aura ba, a yanzu haka Ya samu wadda zata maye masa gurbin Unaisah daya rasa. Daya faɗa mata hakan taji kishi har tayi danasanin kiran shi cikin 6acin rai tace meyasa bazai aureta ita kaɗai ba? me Allah ya rage ta da shi? ya fada mata ko tana da makusa ne"? Cikin lallashi yace tayi haƙuri daga zuciyar shi ne, bazai iya hana kanshi son wata ƴa mace ba, amma ta sani har abada itace mace ta farko daya fara yi ma son da bai ta6a yi ma wata ƴa mace ba, kuma har a wannan lokacin babu abun daya sauya na daga son da ya ke yi mata, shiyasa ma zai fara auranta, ita kuma Yarinyar da ya ke so ya aura Allah ne ya jarabce shi da sonta bayan daya rasa yar uwarta Unaisah. kalamansa sun tausasa zuciyarta, cikin sanyin murya ta tambayesa wacece yarinyar? tana so ta san ta. A takaice Ya bata labarin Batool, nan take Taji tausayinta ya kamata, har taji zata iya amincewa Ya aure ta, duk izzar Nazli tana da zuciyar imani. Nan take tace mashi ta amince saboda ta yarda da shi, ta yarda da son da ya ke yi mata kuma tasan shi din adaline zai kula da su. ya yi farin ciki da jin hakan daga gare ta cikin ruwan sanyi ba tare da yasha wahala ba. Bayan auran Owais da Nazli, a lokacin da suka dawo daga honey moon, da zai dawo Nigeria Prime minister Hateem ya biyo shi donsu zo nema ma Omair auran Unaisah, bayan da suka zo nigeria, Chief Owais Ya fada ma Iyayensa game da fasa auran Unaisah da yayi da kuma wanda ya bama ita, sun dan nuna rashin jin dadinsu saboda sunsan irin kaunar da yakeyi mata tun da daɗewa tunkan Yasan wacece ita, amma daya fada masu dalilansa da kuma alakar dake atsakanin Unaisah da Danish sai sukaji dadi aransu, suka kuma goyi bayan bar mashi ita din tun da har yaji zai iya jurewa kuma su ba zasu hana shi yin aikin alheri ba kuma kamar yayi ma zumunci ne. Ranar da suka shirya zuwa Neman auran Unaisah, kafin zuwan su saida Chief ya saisaici lokacin da Benazir da Unaisah basa agidan, Unaisah ta tafi School, Benazir ta tafi gurin aikin ta, sannan ya kira Taj ya faɗa masa game da batun zuwan magabatansa, yayi farin ciki sosai yace Allah ya kawo su lafiya. Kafin su ƙaraso gidan, Taj ya kira Danejo ya fada mata game da zuwan magabatan Owais, yace ta shirya masu abun da zasu ci, cike da farin ciki ta amsa mashi da toh, ya kuma kira dr shureim da Uncle abdallah, Hada Alhaji Ubaid duk ya sanar da su za'a zo neman auran Yar su Unaisah, kafin su ƙaraso gaba ɗayansu su ka hallara agidan. Hateem da ƴan uwansa ne su ka zo neman auranta tare da Owais da Omar, a main falo suka zazzauna kan sofas, gaba dayan su, sunyi masu kyakkyawar tarba cikin girmamawa suka gaggaysa da su. Danejo ta kawo masu abincin da ta girka masu tare da soft drinks, bayan ta gaishesu daga bisani ta fuce ta basu wuri, kafin suka fara tattauna batun daya kawo su. daga bisani bayan sun gama gaisawa, Owais ya soma magana cikin nutsuwa yace ma Taj ya yi hakuri da abinda zai ji daga gare shi, yasan burinshi ne Ya kyautata masa shiyasa ya bashi auran Unaisah, amma Allah bai kaddara shine zai zama mijin Unaisah ba, shima Yaso Ya auri Unaisah amma bazai Iya raba soyayyar Unaisah da Danish ba, In yayi hakan baiyi masu adalci ba, sannan Idan harya ba Omair auran Unaisah to kamar ya bashi ne, zai yi farin ciki fiye da shi ne zai aureta, still zai zama surukin su, don haka yana rokon alfarma agurinsa ya maida auran shi da Unaisah akan Omair, kar ya ji komai, tun da shi yaba ita shi kuma ya hakura yabarwa dan uwansa kar yaji ba daɗi, da shi da Omair abu ɗaya ne.." zuciyar Taj ta karaya da jin maganar Owais, Hawaye suka cika idanun shi, kwata kwata baiji baƙin cikin abun da ya faɗa ba saboda shima yana son Omair yana kuma son abun da yar sa take so, duk da ba haka yaso ba, yaso Ya cika burinsa na ganin Owais Ya auri Unaisah saboda halaccin da yayi musu arayuwa, Yana son Owais Yana son ya auri Yarsa amma Allah bai nufa shine zai zama mijinta ba, dama can rubutacciyar kaddarace! Wadda babu wanda Ya isa Ya sauyata! In har mutun ba kaddararka bane bazai taba zama kaddararka ba, Owais shiya fara sanin Unaisah, Amma Allah bai kaddara Unaisah zata san da zamanshi ba har saida ta fada kurkukun ƙaddara ta haɗu da Omair, gaba daya dai rayuwarmu abisa mizanin ƙaddara take, kana naka Allah na nashi, duk abun da kaga baka samu ba dama can ba rabon ka bane 💔 Ubangiji Allah Ya zaba mana mafi alkhairi arayuwar mu. Kowa da ke agurin saida ya lura da halin daya shiga, cikin sanyin murya yace tun da har shi da kan shi ya nemi alfarmar ya bar masa, shima ya amince ma auran su. Sunyi murnar da bazata misaltu ba, suka dinga yi masa godiya yace su daina sunfi karfin komai agurin sa, sune sukayi masa halacci da har suka nuna suna son yarsa ta auri dan su. daga bisani su ka ce basu san bikin ya ɗauki lokaci, Sati uku kacal Ya ishe su, Uncle Abdallah Yace su ɗan ƙara lokaci saboda suna son su shirya ma bikin. Su ka ce karya damu, sun san me su ke jimawa, Su kawai Unaisah suke so Abasu, basu bukatar komai daga gare su, ko tsinke basu son akawo ta da shi gidan ɗan su. Gaba ɗaya sunyi murna da jin hakan daga gare su. Duk a zaman Chief Ya bayyana masu game da son da ya ke yi ma Batool, harya nemi da su nema masa auranta tun da ga Mahaifinta akusa, kowa dake a gurin yayi mamaki, Musamman Dr shureim tsantsar rudu da farin ciki ne ya cika zuciyar shi, sai yaji ma kamar kunnansa ne suke jiye masa ba dai dai ba, Alhaji Ubaid yace shikenan faɗuwa tazo daidai da zama, wannan ai yar gida ce, sai ayi tuwo na maina, gaba ɗaya suka sanya dariya. Omar yace dama yana son Batool bai ta6a fada masu ba, yana murmushi yace ''itama batool din batasan yana son ta ba, amma shi yasan tana son shi, tsabar farin ciki yasa Dr shureim jin kwalla ta cika idanun shi, gani yake kamar Owais yafi karfin Batool, bayan yasan ta hanyar da suka same ta, amma ya za6i daya aure ta saboda Yana son ta, Allah abun godiya, kowa dake agurin saida ya fahimci farin cikin da ya ke a ciki, bawan Allah, dama yana ta zullumin wanene zai auri Batool ya zauna da ita lafiya batare daya goranta mata ba? Kullum in yayi sallah sai yayi addu'a akan Allah ya bata miji na gari wanda zai so ta, batare daya goranta mata ba, sai gashi Allah ya kar6i addu'arsa a lokacin da bai zata ba. Sa'ilin da hawayen da ya ke dannewa suka soma kokarin gangarowa daga cikin idanunsa, taj daya lura cikin sauri ya zaro hanky daga aljihu Ya mika masa ya kar6a tare da rufe idanunsa da shi, gaba ɗaya sun fahimci dalilin shigar shi halin da ya ke a ciki, haɗuwa su ka yi gurin lallashin shi don ya daina zubar da hawayen sa, Chief yafi kowa farin ciki da ganin yadda Dr. Shureim ya nuna jin dadin sa. Bayan da suka shawo kan dr shurem, Prime minister yace"yana neman alfarma agurin su da su bar komai a sirrin ce, baya son Unaisah tasan Omair yana araye koshi zata aura, kuma baya san kowa ya sani har sai ranar ɗaurin auran saboda mommynsa tana son ta bata mamaki" basu musa ba suka amince masa.. Chief Owais yace"shima yana neman alfarmar kada abari Batool tasan zatayi aure har sai bayan ɗaurin auren nasu, saboda yana son ya bata mamaki" Gaba ɗaya sun goyi bayan maganar sa saboda suma suna son su faranta masu. ~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~ Bayan komawar prime minister Canada, Ya labarta ma sheikha game da sanya auran Omair, taji dadi sosai, aranar da zasu faɗa masa bazata sukayi masa saida suka saisaici ranar daya gama degree dinsa na farko kuma duk aranar ya gama haddar alqur'ani mai girma. A gurin walimar safkar alqur'anin sa, suka bashi gift box daya buɗe akwatin Unexpected Ya tsinci Invitation card na auransa da Unaisah a ciki, tsabar farin ciki bakinsa kasa rufuwa ya yi. yadinga yi masu godiya kamar zai yi musu kuka, farin cikin da suka gani akan fuskarsa ba ƙaramin biyansu yayi ba sunji daɗin faranta masa da su kayi. Cikin shesshakar kuka yace ashe haka iyaye suke da daɗi? burin su su farantawa dansu rai da iyakar iyawarsu koda su zasu rasa jin daɗin su ne, ba abun da zai ce sai dai yayi godiya ga Allah da irin ni'imomin da yayi masa arayuwa, daga jahili zuwa mai ilmi daga mara asali zuwa mai cikakken asali, daga talaka zuwa hamshakin mai kudi, Allah Ya dawo masa da dukkan Hakkinsa da Elders suka tauye masa, a lokacin fa kwata kwata baya son tunawa da kurkukun kaddara, tun daya hadu da mommynsa Ya shafe babin su a memory din sa, a ranar da Yaji labarin farmaki na biyu da su Owais sukai da kuma nasarar da sukayi harma da shari'ar da akayi Ya ji komai abakin Owais ya kuma gani a labarai, Ya yi farin cikin kawo ƙarshen Gidan Kurkukun ƙaddara da Elders. A ranar ɗaurin aurenshi, sukazo Nigeria a privet jet din daddyn sa, a gidan su na estate din suka sauka, Yana ta zumudin ganin yan uwansa da yayi kewa tsawon shekaru, musamman babban amininsa Haris na amana. Bai tashi haɗuwa da su ba, sai a wurin ɗaurin aure, a masallacin imam malik, kwatsam ba zato ba tsammani sukaga Danish kamar a mafarki Ya zo, suka kasa tunkararshi saboda ruɗun da suka shiga, zullumin su kar ace bashi bane wanine mai bala'en kama da shi sai suka dinga satar kallon shi, Dayaga kamar suna kokwanto akansa Saiya nufe su da fara'a ya fada musu cewa shine Danish dinsu bai mutu ba, suka ki yarda har saida Ya labarta musu tukunna suka fashe da kukan farin ciki, Haris Ya rufe shi da fada akan don me ya nisanta kanshi dasu? Meyasa ya tafi yabarsu? Meyasa zai boye musu yana araye? Yasan kuwa halin da suka shiga lokacin da sukaji baya araye"? Murmushi yadinga sakar musu yana lallashin su dakyar ya shawo kan su suka daina kuka. Kafin ya soma bin su daya bayan daya ya rungume su sunata santin shi badan anyi rayuwar wahala atare ba da ba abunda zai hana su ji shakkar sake mashi saboda da kallo daya suka fahimci Danish din yanzu yafi ƙarfin su, yana magana zaka fahimci ilmi ya shige shi ga hutu daya zauna a fatar sa, kamar yadda suke mamakin sauyawar da yayi shima haka yake mamakin sauyawarsu, yaji daɗin canjin da kowan nansu ya samu, har yanzu yana son yan uwansa, musamman da suka kara samun kusanci na yan uwantaka ta jini da wasu daga cikin su. Abun da yafi faranta ran su jin cewa shi ne zai auri Unaisah, yaya Owais kuma zai auri Batool sunyi murna kamar kamar me amma yace masu bayason ta sani su yi shiru karsu fada mata har sai bayan an kaita gidan shi sannan zai bayyana mata kan shi, suma sun goyi bayan ya ba ta mamaki saboda suna son farin cikin ta. zan iya cewa Salsabeel yafi kowa murnar ganin Danish a lokacin da su ka haɗu a masallaci, yaji daɗin sauyin rayuwar daya samu, ya kuma ji dadin jin cewa shine zai auri Unaisah, burin sa ya cika, bakinsa ya ƙi rufuwa saboda farin ciki, daya rungume shi har saida ƙwalla ta cika idanun shi, shima Danish din duk sai yaji ba daɗi daya nisanta kan shi da su, sun yi kewar juna, hakuri ya dinga bashi yana lallashin shi har saida ya shawo kan shi. Sheikh imam already yasan shine zai Auri Unaisah tun a ranar da Taj ya kirasa ya sanar da shi komai, amma bai samu halartar gidan ba saboda baya agari, gaba daga a masallaci suka haɗu da shi kafin daurin auren. Bayan kammala ɗaurin auren, al'ummar Annabi suka dinga taya angwaye murna tare da yi masu fatan Alkhairi. Daga masallacin gaba daya suka wuce Reception, cikin farin ciki da ɗokinsa su ke ta bashi labarin abubuwan da suka faru bayan da babu shi, Yaji dadi sosai harya taya Sajeed murnar ganin yar uwarsa Sajeeda, daya tambayi haris Ya labarin deejan sa? Har yanzu suna son juna? Zai aureta? dariya yayi tare da girgiza kai yace hmmm ai zance Ya 6aci, aurensa da Deeja haramun, saboda uwar su ɗaya ubansu ɗaya". Danish ya yi mamakin jin cewa shaƙiƙai ne, duk agurinsu Yaji labarin Unaizah yar gidan daddy da Unaisah yan uwane da kuma alakar su, haka sajeed ma ya'yan kawunta ne jan wuya, ga kuma Cousin dinsa, Yaji daɗin kasantuwarsu Ya'yan wa da ƙani,dayake duk bai bibiyi wadannan labaran ba yasan dai kowa an mikashi ga iyayensa, a yadda ya samu labari but baisan su waye iyayensu ba,sai Yan zu ya gane dalilin dayasa su ke bala'en son juna ashe soyayyar su ta jini ce. Bayan da suka gama shagalin su Tare da Yan uwansa daga Reception suka tafi gidan daddynsa na estate din sunki rabuwa da juna, an dade ba'a haɗu ba, wuni yayi tare da su har saida lokacin daukar amarya yayi tukunna sukayi masa sallama kamar karsu rabu suka tafi dauko masa amaryarsa kamar yadda suka tsara. Kamar Yadda Iyayen Unaisah sukayi mata nasiha akan zamantakewar aure shima haka Iyayen sa su ka yi masa, a ƙarshe suka sanya mashi albarka tare da fatan alkhairi arayuwar auran sa. Daga baya ne Sheikha mujeedat ta shiga gidansu Owais donsu tarbi amarya idan danginta sun kawo ta, dama anan suka nemi alfarmar suna son su fara kawo ta, in yaso daga bisani sai ta kaita gidan angonta da kanta, sunyi hakanne saboda sunfi son Unaisah ta fara ganin sa a matsayin angon ta don su bata mamaki, kafin sauran su san yana araye kuma shi ta aura, haka Batool ma sun boye duk wani abu da zaisa tasan cewa anyi auranta da Owais. Daddynta bai sanar da su ba, saboda Sun tsara sai daga baya zasu sanar da ita. Shiyasa suka ɗage date din Dinnern Auran su zuwa bayan biki da sati. *Gaba ɗaya komai daya faru a cikin shekarun da suka gabata ne zuwa yanzu* ~__________________________________🌹✍️~ Safa da marya ta ke yi a tsakar falo, cikin fushi da bacin rai take doka tsoki, dr shureim Yana a zaune kan sofa, gaba daya babu annuri akan fuskokin su. damuwa da zullumin Ina Batool Ta shiga Ya hanasu sukuni, fin awa suna neman ta shiru babu ita babu alamarta, kowa suka kira wayarsa sai yace masu baya a tare da ita ko bai ganta ba. "Pls ummu batool, ki dawo ki zauna mana, In sha Allah ba abun da zai same ta, Ni nasan duk inda taje bazai wuce cikin Houses din da ke a kewaye da mu ba" Tana huci Tace"ai wallahi idan kaga na zauna to Batool ta dawo gidan nan ne! Zatasan da wa take, kawai don taga ana ji da ita kamar jinjira shine take nema ta manna min hauka! Tare da ita fa mukaje gidansu Owais amma saboda ta raina mana wayou sai ta zame jiki batare da saninmu ba ta kara gaba, awa daya da rabi bata dawo gida ba!da daren nan yarinya budurwa tana garari awaje, Na rasa gane me Batool take so ta zama ne! Ta sauya gaba daya, Ni bazan iya daukar rashin wayon ta ba wlh, dole in dauki mataki akan ta" akan Batool ta ke yin faɗa amma sai yaga kamar da shi take magana saboda yadda take zare mashi idanu tana watsa hannayenta, Tsabar yadda take zazzaga masifa jikinta na girgiza har saida daurin kallabin ta ya karkace. "Allah Ya huci zuciyarki Ummu Batool, kiyi hakuri, muyi mata uziri bamusan meya tsayar da ita ba tunda ba halin ta bane fita yawon dare ba.. " bata tanka mashi ba, ta ruke qugu tana huci kamar zakanya.. Mikewa yayi"ki shiga ciki ki kwanta, zan koma in ƙara neman ta watakil adace" "Sai dai kai ka shiga ka kwanta, amma ni banga ta zama ba, Allah ba wanda ya isa ya hanani in bugi batool Yau, da wayar wuta zan zane mata jikin ta.. " zare ido dr shureim yayi kamar zaiyi dariya yace"amma dai wasa kikeyi ko, Ina ma laifin kiyi mata nasiha, amma Batool ta wuce shekarun bugu, bafa yarinya bace, ta mallakin hankalin ta" bata kula shi ba, ta juya da niyar ta bar falon, Unexpected su ka jiyo sallamar Batool da ke ƙoƙarin shigowa falon cikin tafiyar sanɗa, ta rungume kayan data cire a kirjinta. jikinta sai kerma yakeyi saboda zullumin hukuncin da zasu yanke mata, yadda suka dubeta a lokaci daya yasa tasha jinin jikinta, musamman da taga kallon hadarin kajin da Ummi ke watsa mata. "Daga gidan ubanwa kike"? Kasa yin magana tayi, wata tsawa ta ta daka mata"ba zaki bani amsar tambayana ba? Ina kikaje tsawon lokacin nan?.." bata ƙare maganarba ta lura da kayan jikinta da wadanda ta rungume a hannunta"na shiga ukuna, Batool meya faru da har kika sauya kayanki? Ina kika samu jallabiyar jikinki"? Ta fada cikin fushi ta nufeta kamar damusa. Dr shureim yabi bayanta yana kokarin dakatar da ita, Batool data rikice arazane Ta juya zata fuce bata kaiga karasawa ba, Ummi tayi saurin shaƙo kwalarta kamar zata doke ta ta janyota. Cikin rawar murya tace"zan yi maki bayani ummi wlh zan fada maki komai, ina atare da Unaisah, Ni na rakata dakinta tare da yan uwan mijinta, abin dayasa na musanya kayana, 6acewa sukayi da Miyar abincin da mukaci a gidan ta.. " Dakyar ta ƙare maganar, Da yake bata saba yi mata karya ba, daga yanayin yadda take magana tana ƙyafƙyafta idanunta yasa ta gane ba gaskiya ta fada mata ba. "Hmmm me ya kai ki gidan Unaisah? Ko kinfi sauran yan uwan nakine da kika kwashi kafa kika bita? Ko kuwa kinje ne donki gano furniture dinta kice kema irin su kikeso ayi maki"? Girgiza kai tayi a tsorace take kallon daddynta don ya taimaka mata saboda tasan shi zai fi fahimtarta, babu alamun zaiyi magana saboda Ummi taki sauraron shi. "Ba haka bane ummi, ni banje da niyar hakan ba, kawai ina son in kara ganinta ne"! "Wallahi ban yarda dake ba, karya kika fadamin, kuma na rantse zan kira Unaisah ayanzu in har naji akasin abun da kika fada saina zane ki" ta ƙarashe maganar tare da sakin Wuyan rigarta, har ta daga ƙafa zata juya don ta dauko waya ta kira Unaisah batool tayi saurin furta"am sorry Ummina, nayi maki karya, ba gaskiya na fada maki ba, amma ki fahince ni, bana so na fada maki inda naje.. " juyowa tayi a sukwane ta dube ta"Batool yaushe kika fara yin karya? wai meke damun ki ne meyasa kika sauya halayenki"? Sunnar da kanta kasa tayi, hawayen da suka cuccuko idanunta suka soma dira kan kuncin ta, taso ace zata iya fada mata gaskiya sai dai bata son mutuncin ya Owais ya zube a idanunsu, tana son ta kare mashi martabarshi koda iyayenta zasu ƙi yarda da ita ne. "Batool, zoki wuce kije daki ki kwanta dare yayi, Gobe zamuyi magana," shurem ne ya faɗa, amsawa tayi da toh abba, cikin sanyin jiki ta ra6a ta gefen ummin data saki baki sototo tana kallon ta, har saida taga tabar falon. tukunna ta kawar da idanunta tare da duban shureim"kada son Batool ya rufe maka ido ka kasa bata tarbiyar data dace, saboda na fahimci baka son kaga inayi mata faɗa, tayaya ba zamu tuhumeta akan ina taje ba? Kana ji tayi min karya bayan ba halinta bane, kuma ta sauya kaya awaje, hakan bai dame ka bane"? Ta faɗa idanunta cike tab da kwalla ciki karyayyar murya tace "ina jin tsoron batool ta fuskanci irin rayuwar dana fuskanta abaya.." ta ƙare maganar tare da kifa kanta saman kafadarshi, tuni zuciyarshi ta karaya, tsantsar tausayinta ya kama shi"ummu Batool, mu zauna zanyi maki bayani" bata musa mashi ba, ta dago da kanta ta zauna kan Sofa, shima ya zauna daga gefenta. "Abun daya sa ban damu ba, ban kuma tsawatar mata akan ina taje ba, Saboda Na san inda taje.." aruɗe ta dube shi cike da son jin karin bayani tace"bangane me kake nufi ba! Kasan inda taje shine baka fadamin ba kabarni ina ta 6a6atu"? Tattausan murmushi ya sakar mata"saboda kinƙi ki saurareni shiyasa nakasa yi maki bayani, amma Batool tana a tare da mijinta, shiya ɗauke ta ya kaita gidan ta, Nima sai daga baya ya kirani awaya ya faɗa min" rudanine tsantsa akan fuskarta"har yanzu bangane me kake nufi ba! Dan Allah kadaina yi min wasa da hankali! wani irin miji? Yaushe batool tayi aure har da gidan miji ni da nake uwarta bansani ba"!? gyaɗa kansa ya ɗanyi. "A yau baba Imam ya ɗaura auran Batool bayan ya kammala daurin auren Unaisah.." bai ƙare maganar ba, ganin yadda ta zabura ta miƙa tana kallon shi. "ki yi hakuri na boye maki ne saboda mijinta ya bukaci da aboye mata har zuwa ranar da zata tare a gidansa, abun da kike burine ya tabbata, Batool ta samu miji nagari nagartacce, mai tsoron Allah, mai tsantsar ilmin addini da sanin yakamata, wanda nayi imanin Allah ne Ya rufa mana asiri ya kaddara son ta a zuciyar shi..." bai ƙare maganar ba ta katse shi "dagaske kake ko wasa? Wanene kuma mijin nata"? "Wanda take so, za6inta shine mijinta... " Kamar taji abun tashin hankali Ta furta Inna lillahi tare da dafe kai da hannu daya tana fadin"shikenan, Batool ta gama dani, taja min abun kunya, wato saida ta fada mishi tana son shi, shine Ya hada da ita ya aura, hankalinta ya kwanta, ta auri miji ɗaya da Unaisah, don taci gaba da yin gasa da ita.." kamar zata fashe da kuka ta ƙarashe maganar cikin baƙin ciki. Yar dariya dr shureim yayi"ba haka bane, Ki zauna zan yi maki bayanin da zaki gamsu" cike da damuwa ta zauna gefen shi, a tsanake ya soma fayyace mata komai tiryan tiryan. Yayin da take sauraron shi, tsantsar al'ajabine Ya kamata, batasan sa'adda ta fashe da dariyar farin ciki ba kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, hawayen farin ciki suka cuccuko idanunta, ta ɗaga hannayenta sama tana fadin"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah na gode maka daka cika mana burin mu, batool ta samu miji nagari, ta auri za6in ranta, mutumin da take ta hauka akanshi ashe shima yana sonta.." dr shureim da ke kallon ta murmushine akan fuskarsa. Saukowa tayi daga kan sofa, ta durƙusa kasa tare da yin sujudushshukur, Sa'ilin da ta dago hawaye ne sha6a sha6a kan fuskarta cikin harshen larabci ta dinga yiwa Allah kirari tana gode masa da ni'imomin da yayi masu arayuwa. Daga bisani ta mike tare da duban dr shureim"na kar6i uzirinka da ka ki fadamin ƴata zatayi aure amma ai da ka fadamin kodan in shiryata ko"? "Karki damu, ya bamu two weeks kafin ranar Dinner dinsu, don muyi shirinmu kafin amaryarsa ta tare a gidanta" ihun farin ciki Ummi ta fasa wanda yayi silar razanar da Batool daga bedroom dinta ta jiyo ta, jikinta na kerma ta fito ta nufi down tana fadin ummina meke faruwa? Meke damunki"! Kusan atare suka juya suna kallonta, har ta musanya kayan jikinta dana bacci"ki koma daki ki kwanta, babu abunda ke faruwa, fira mukeyi mai dadi" ummi ce ta fada tana dariya, Batool ta rude da ganin fara'a akan fuskar mommynta sa6anin dazu data rufe ta da fada ko annuri babu akan ta. Bata musa ba, tace"toh, ku kulamun da kanku, sai Allah yakaimu" har suna hada baki gurin furta"muma ki kula mana da kanki, Allah yakaimu lafiya," da murmushi akan fuskarta ta juya ta nufi bedroom dinta, taji dadin ganin su cikin farin ciki, da tana ta zullumin fadan da ummi zatayi mata don tasan ba ƙyaleta za tayi ba, amma yanzu taji hankalinta ya kwanta sosai. Faɗawa tayi saman gado tare da janyo pillow ta rungume shi a kirjin ta tana jin kamar shine ta rungume, a hankali ta lumshe idanunta tana tariyo abun da suka tattauna da shi bayan ya kawota agida a cikin motar shi. _"Nasan yanzu kin daina ganin girmana, may be kin daina sona tun da na neme ki ko"?_ _"Har abada bazan daina ganin girmanka ba, mutuncinka bazai ta6a zu6ewa a wurina ba, saboda nasan wanene kai kuma na yarda dakai.. "_ _"zaki iya rufa min asiri ba zaki fada ma kowa abun da na nema a gurin ki ba"_ _"Babu abunda zaisa in tona maka asiri, koda za'a azabtar danine don in faɗa"_ Da tunanin abun daya faru a tsakanin su ta kwana. ~___________________________________💋💗🌹~ *DESTINYSHIELD💘* bayan daya ƙarasa labarta mata, cikin fushi ta buga kanta jikin ƙofa ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita, wani irin ƙunci da bakin ciki ne ya ziyar ci zuciyarta, badan batayi farin cikin dawowarsa araye ba sai don takaicin tsawon shekarun da take ta dakon soyayyar mamaci ashe yana araye shiyasa soyayyarsa taƙi mutuwa a cikin zuciyarta, Hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba duk yabi ya ruɗe duk da yasan halin kayan sa dama sai da yaji shakkar bayyana mata kan shi. Cikin sanyin murya yace "Nasan ban kyauta maki ba, amma ki sani daidai da second ban ta6a mantawa dake ba, zuciyata da sonki take bugawa, babu abun daya sauya na daga kaunar da nake maki! kina araina Unaisah, kuma komai da nayi nayi ne saboda ke ! in har ban nisanta kaina dake ba bazan ta6a samun abun da na samu a yanzu ba" Ya ƙarashe maganar yana kallon gefen fuskarta da ta 6aci da hawayen ta sha6a sha6a. Wai Yana araye bata sani ba, bai ta6a nemanta ba, babu wanda ya faɗa mata. Fashewa ta kuma yi da wani kukan mai tsuma Zuciya, cikin fushi da tsantsar 6aci rai ta juya ta fuskance shi batare data dubi fuskarsa ba, ta cakumi gaban rigarshi da hannayenta, ta bubbuga kirjin shi, idanunta da ke tsiyayar da hawaye ta runtse su gam.. Cikin shesshekar kuka tace"I will never forgive you! You hurt me! You left me with the pain of your love, causing me heartache and anxiety that put me unconscious for four days! Why did you do this to me? What did I do to deserve that from you"? Dakyar ta karashe maganar tana jan numfashi. Kafin ta ɗaura da cewa "Ka ce saboda ni ka yi komai, Idan da na mutu fa? Ko kai ka mutu a cikin wadannan shekarun da bamu a tare"? ta faɗa tana cigaba da zubar da hawaye. Ko uffan bai ce ba, Yayi shiru yana sauraron ta. can ƙasan makoshin ta furta "Man so kayi ka kasheni wallahi" Numfasawa yayi a hankali cikin sanyin murya ya furta "i know everything that happened to you after I left, Akhi Owais yana faɗa min komai game da ke, and I'm not happy about it, I made a mistake by leaving you, duk da banyi hakan don na cutar dake ba, and I never stopped loving you Unaisah" ya fada yana kokarin fahimtar da ita. "amma inaso ki sani komai nayi kece sila Unaisah, You caused it all, you're the reason I distanced myself from you" Cikin ruɗu ta buɗe jajayen idanunta a cikin na shi wani irin ƙwarjini yayi mata da saurin ta kawar da su gefe ɗaya "Da farko na tafi kai farmaki na kuma sadaukar da kaina saboda ke, saboda inason in zama jarumi mara tsoron zuwa yaƙi don kuma in wanke kaina daga zargin da kike min na goyan bayan matsafa, ki san cewa ni ba matsafi bane, bana goyon bayan zalunci, ban kuma ta6a taimaka ma azzalumi ko ni nayi zalunci...." kalamansa sun ɗaga hankalin ta. "I chose to distance myself from you, even if the pain of loving you would kill me, alkawarine na daukarwa kaina Unaisah, bazan ta6a dawowa gare ki ba, har saina musulunta na kuma samu Ilmi don inyi yaki da jahilcina, saboda inaso kiyi alfahari dani Unaisah, And, Alhamdulillah, I now have everything I wanted, I've accepted Islam, gained knowledge, and overcome my ignorance, I'm proud to say that I've become a better person for you, ina da komai Harma da asali bawai iya kyau gare ni ba... " Gaba ɗaya ya kashe mata baki, wutarta ta ɗauke ɗuff, ko hada idanu da shi ta gaza yi saboda wata irin shakkar shi da ta ke ji, yanzu ta gane dalilin dayasa ya yi komai, babu ƙarya a maganarsa, itace sila itace kuma taja ma kan ta, duk da bata furta kalaman da nufin ta goranta masa ba. "There's no evils in me now, Allah has freed me from them, I have no magic, and I have peace of mind to live with you without hurting you, since I've become a complete person. (A yanzu babu Evils a jikina, Allah ya rabani da su, bani da tsafi, ina da kwanciyar hankalin da zan rayu dake batare dana cutar da ke ba, tun da na zama cikakken mutun) ya ƙarashe maganar tare da sauke ajiyar zuciya. Ya lura da yadda tabi ta ruɗe ta kame kanta ta shiga taitayinta kamar wadda tayiwa sarki ƙarya. "Ban faɗa maki da wata manufa ba, ban kuma yi hakan donna goranta maki ba, face sai don inason nasa ma mana mafita, nima inaso na zama mutum mai daraja da kima, mai kuma mutunci a idanunki dana kowa ma" ya faɗa yana bin fuskarta da kallo, Taƙi yarda su haɗa idanunsu cikin da juna saboda nauyinsa da ta ke ji. "a zaman da nayi da iyayena na dauki darussa sosai, idan har kanaso mutane su mutuntaka dole sai ka mutunta kanka, jahilci duhu ne arayuwar mu, ilmine kadai hasken daya ke kore su, haka rashin asali baida dadi ko kadan saboda sai da asalin nan mutun zai yi tunkaho, kuma rufin asirin bawane, duk da komai ya faru da ni ba laifina bane ja mun akayi amma yanzu komai ya wuce bani da sauran damuwa... " a tsanake ya kare maganar. Bai faɗa mata da wata manufa ba, amma duk sai taji ta muzanta agaban shi, gani take ma kamar ba Danish dinta bane saboda wannan yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, babban gorone magogin karfe, ba haka tasan danish din ta ba, tayaya ma zata iya rayuwa da shi bayan ya sanya mata tsoron shi a zuciyarta. Cikin disasshiyar murya ta furta"My Danish is dead, he's not alive You're not him and you'll never be him, because I don't feel that you're him! Your name is Omair, ɗan Prime ministern Canada da sheikha mujeedat, grandson of Emir Khalid of Dubai, knowledgeable, rich, purely beautiful, with royal blood and a noble origin" ("Dannish dina ya mutu, ba ya raye, Kai ba shi ba ne! kuma ba za ka taba zama shi ba, saboda bana jin kai ne! Sunanka Omair dan Prime Ministern Canada, da Sheikha Mujeedat, jikan sarki Khalid na Dubai, masani, mai kudi, kyakkyawa zalla, mai jinin sarauta da asali mai daraja") dakatawa ta ɗanyi tana share ƙwallarta da yatsun ta dake kerma, ta haɗi yawu mai ɗaci dakyar ta iya saka marayun idanunta a cikin na shi"meyasa ka aureni? Bayan kafi karfina? Ni ba ajinka bace! Ban kai ka ilmi ba, ban kai ka waye wa da asali ba, ni ba yar kowa bace, mahaifina bawani bane, mahaifiyata ba yar kowa ba ce, ba mu dace da juna ba Omair, ina kallon kaina a matsayin ƙasƙantacciya agaban ka, ba zan iya zaman aure da kai ba.. ta faɗa cikin shesshekar kuka tana girgiza kanta.. _"I love my Danish! I can only live with him because he loves me for who I am I also love him for who he is, we lived through difficulties and sadness, and we never changed for each other_" (Inason Danish ɗi na! Da shi kadai zan iya rayuwa, saboda yana sona a yadda nake nima ina son shi a yadda ya ke, mun rayu cikin wahalhalu da bakin ciki, kuma bamu ta6a canzama juna ba)" daƙyar sautin muryarta ke fita. "inason shi da jahilcin shi, Inason shi da rashin asalin shi, kuma Inason shi da talaucin shi, and I love him for being nobody's son, Ina kuma son shi da kasantuwar shi ba dan kowa ba, da burin zan aure shi in rayu da shi in kuma taimaka mashi ya nemi ilmi don ya inganta rayuwarsa" daƙyar ta ƙarashe maganar saboda shaƙewar da muryarta tayi sakamakon kukan da ta ke yi. Gaba ɗaya babu annuri akan fuskarsa, tamkar bai ta6a yin dariya ba, ba haka ya zata daga gare ta ba, ta 6ata masa rai ta kuma karya masa zuciya, kwata kwata baiga alamun tayi farin ciki da dawowarshi araye ba, batayi murnar sauyawar shi ba! Bayan saboda ita yayi komai? Anya Unaisah tana son shi har yanzu? Tana kuwa son cigaban shi"? Sam ya kasa furta kalma, ta kashe mashi baki, sai yaji dama bai dawo ba gaba ɗaya!. Jinjina kan shi ya ɗanyi cikin fushi yace "Tell me, how can I make you understand? What's wrong with you? kin sauya min! that's not what I expected from you, You weren't happy about my return at all, ba ki taya ni farin cikin samu asalina da kuma cigaban dana samu ba arayuwana ba"! wani irin faɗuwar gaba da sarewar gwiwa taji a lokaci ɗaya! "Ina kokwanton in har yanzu kina sona! may be kin samu wanda ya maye maki gurbinane! kamar bakison cigabana! bayan ke da kanki kika furta bani da komai da zakiyi alfahari da ni ban da kyan da Allah yayi mini, Unaisah you're the one who inspired me to achieve those goals! I followed your orders and did everything for you! Why can't you see"? Daƙyar ya ke yin maganar saboda bai saba yin surutu mai tsayi ba, wahala ya ke sha. "kin sauya magana Unaisah! Bakisan cigabana Unaisa! If not, why aren't you happy for me as Omair? You know I can never go back to being the Danish you knew, I regret coming back to you, I won't force you to stay with me If you can't live with me as Omair, you can choose to break up with me" yadda yayi maganar da tsawa yasa ta gigice, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya sara mata nan ta ke jiri ya kwasheta agalabaice ta yi taga taga zata faɗi batasan sa'adda ta durƙushe ƙasa ba, duk akan idanunsa ko gizau baiyi ba, balle tasa ran zai taimaka mata. Bai aune ba yaji ta rungume kafafun sa da hannayenta, jikinta na kerma ta rasa me ke mata daɗi duniyar nan! cikin shaƙaƙƙar murya ta furta Ina son Danish ɗina ya dawo gare ni, ka koma Danish dan Allah! shi kawai nakeson gani, Danish dina ba haka ya ke min ba, baya fushi dani, baya son 6acin raina, yana fahimtana, baya min magana da tsawa, bamu iya rayu nesa da juna, amma kai ba kamar shi ka ke ba, tayaya zan ji ka a matsayin shi? Bayan ka sauya gaba ɗaya.." zuciyarsa ta karaya da jin kalamanta, jikinshi yayi sanyi laƙwas kamar babu laka, baisan meyasa yayi mata haka ba? Meke damun shi ne, duk da itama da laifinta ta kasa fahimtarshi duk kokarin dayake Dan ta fahimce shi Abu yaci tura. Tsantsar tausayinta ne ya mamaye zuciyarshi har yaji kamar bai kyauta mata ba, bai san ya zaiyi da ita bane! Baisan me ta ke so ya yi mata wanda zaisa taji shi a matsayin Danish! _Tayaya zasu samu fahimtar juna a daren farko na ranar auran su? Bayan sa6ani ya shiga tsakanin su? Bayin Allah har alkawarin ciyar da juna su ka yi💔_ kwatsam Yaga ta kife kan floor babu numfashi, Tashin hankali, gabansa Ya faɗi rass! arazane Ya zube kan gwiwowinsa Ya tallabo kanta da tafukan sa. kyawawan idanunsa a kan fuskarta data jike sharkaf da hawaye kamar ba A.c a dakin gumi duk ya wanke ta, cikin karyayyar murya ya furta "Ya rouhi! My Angel! Habib albi! Wake up pls, Ni ban dawo don na 6ata maki rai ba, har yanzu ni danish ɗinki ne ban sauya ba, Ina sonki, bazan ta6a canza maki ba..." Cak ya tsaya da yin maganar sa'ilin daya fahimce suma tayi. Cuccu6arta yayi saman kafaɗarshi ya miƙe da ita Ya nufi katafaren Gadon su. A hankali Ya kwantar da ita, ya juya jikinshi na bari ya nufi minibar din ɗakin Ya dauko bottle water, ya dawo daga gefen gadon ya zauna tare da buɗe robar ruwan ya tarfa a tafun sa ya soma yayyafa mata ruwan saman fuskarta. Nan take taja dogon numfashi har saida kirjinta yayi sama tukunna a hankali ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sam takasa buɗe idanunta sai jan numfashi ta ke yi daƙyar daƙyar, ga dukkan alamu bata a hayyacin ta. Damuwa ce tsantsa kan fuskarsa ganin yadda ya jefa ta a mawuyacin hali. a hankali ya ɗaura yatsunsa saman wuyanta har saida gabanshi ya fadi jin yadda jikin ta yayi zafi rau da alamun zazza6i a tare da ita. "Rouhi! Are you Okay? meke damunki? Ko baki da lafiya"? ya faɗa yana kallon fuskarta kwata kwata bata fahimtar komai. Sumar data yarfo saman fuskarta Ya shiga kawar mata da ita da hannunsa don ya samu damar da zai ƙare mata kallo tun a karo na farko daya fara yin tozali da ita face to face saida ya razana da sauyawarta, tama fiyi masa kyau azahiri akan hoton ta da ya ke kallo, ta zama dirarran mace mai kyawu abar tunkaho ga Wanda ya mallaketa. "malak albi na! kina jina? faɗamin meke damunki? Ni ne na 6ata maki rai... " shiru babu alamun zata furta kalma, ko idanunta ta kasa buɗewa. Ganin yadda take zubar da zufa yasa ya fahimci zafin jikinta ne ya jawo hakan. Tunanin rage mata kayan jikin ta ya yi, A hankali cikin nutsuwa ya ruƙo hannayenta ya nutsu Yana kallon zanen lallen da akayi mata akan glowing skin ɗinta, lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su akan kyawawan hannunta ji yake kamar ya haɗiye su tsabar kyan da sukai masa. awarwaron ta ya zamiye daga hands din ta, a hankali ya ɗaurasu kan mattress. Baisan sa'adda ya tsinci kan shi da shafa lallausar fatar hannun ta yayin da ya ke tariyo rayuwarsu ta baya a prison. Sakin hannunta yayi ya ɗan matsa Ya ruƙo kafafunta ya daura su akan Laps dinsa cikin nutsuwa ya soma cire mata takalman dakyar ya zame su, bai ji daɗin ganin yadda suka raunata kafafunta ba, sun yi jawur kamar na jarirai a tsaftacen su, baisan sa'adda Ya sumbaci foots din ta ba, a ƙasa Ya ɗaura takalman, bayan ya cire leg chain ɗin ta, Ya matso daidai saitin kanta, gently ya tallabe shoulders dinta da hannun shi, Ya ɗago da ita tare da kwantar mata da kanta saman kafaɗarsa, shu'umin kamshin turarenta ne Ya daki hancin shi wani irin kamshi mai rikita shauƙin bawa. Zare sarkar wuyanta yayi cikin nutsuwa Ya cillar da ita ta faɗa kan mattress, kafin ya cire mata earrings dinta Ya watsar da su. Numfashi yaja Tare da furzar da shi saman fatar wuyanta, a hankali ya dinga goga tsinin hancin shi saman skin din ta. Ƙara haɗe jikinsa ya yi da nata a matse sa'ilin daya fara jin wani irin yanayi daya haifar masa da jarababbiyar kasala a jikin shi. Tun da ya cusa hancinsa a tsakankanin wuyanta da kafaɗarta ya nemi nutsuwarsa ya rasa, bugun zuciyarsa ya tsananta, bakomai ne ke fusgarsa ba face shu'umin ƙamshin jikin ta da laushin fatarta. tsawon mintuna bai motsa ba ya yi shiru yana jin yadda jikin shi ke tsuma. dakyar ya iya tattara sauran kuzarin daya rage masa a jikinsa, ya sanya hannu ya Cire mata head pies din da ke a kan sumarta baisan lokacin da ya soma shafa sumar Yana liliyata a hankali a hankali almost mins, Yana jin fitar numfashinta a jikin shi, ta narke masa a kirjinsa babu alamun tana a hayyacin ta. ya daɗe yana kwaɗayin Unaisah kamar zai rasa ransa bai ta6a nuna mata ba bai kuma ta6a neman ta bashi haɗin kai suyi ba. _saboda yasan bazaiyi mata da kyau ba, baya son ya cutar da ita, a lokacin da suke a prison ko harararsa tayi ko ta murguɗa masa baki nan ta ke ya ke jin tsananin sha'awarta, yaji kamar Ya afka mata, tun bai gane me ya ke ji agame da ita ba, amma ko time da take ganinsa a toilet da biyu ya ke shiga saboda ya samu sassaucin azabtuwar da ya ke ji agame da ita, amma yayi hakuri ya jure saboda bayason ya cutar da ita, kuma baya son ya yi batare da amincewarta ba,sonta da kaunarta da yakeyi da zuciya daya bazai bari ya iya aikata mata hakan ba._ Ya ja numfashi da karfi yana jin zafin jikin ta a fatar sa Dakyar ya iya motsa fingers dinsa gently cike da lalaci ya soma warware straps din rigarta, before he slid the straps off her shoulders.. Cikin muryar raɗa mai cike da shauƙi Ya furta"malak albi na! Are you awake? Kina ji na? Can I remove your gown? It's tight and causing you pain" shiru bata furta kalma ba, kuma bata buɗe idanunta ba, ya rasa gane meyasa ta fita hayyacin ta, amma yana ji aransa kalamansa ne suka jefa ta a halin da ta ke a ciki, bazai iya bar mata rigarba saboda yadda tayi tighly dinta, ga zufar da ta ke fitarwa, yasan tsiwar Unaisah kan tsiraicinta amma dole ya cire mata kuma ko ba komai muharramarsa. Gently ya zamiye wuyan rigar yayi ƙasa da shi har izuwa tudun mazaunanta adaidai nan ya bar rigar, Ya Salam sandarewa yayi saboda rudewar da yayi na ganin sexy curve din Unaisah, wata fitinanniyar Sexy under Corset ce tayi fitting dinta tighly ta bayyana zazzafar surar kirjinta da hips din ta, Jikinsa na kerma Ya daura tafukansa akan bubble butt dinta yadinga fitar da numfashi mai huci kamar zai zauce, yadda kasan mayunwacin zaki. A hankali Ya zamiye hannunsa daga kan butt dinta ya shiga shafa lallausar fatarta, Kasala Tahana ya tsayar da idanunsa a buɗe kamar mai jin bacci. Sulale hannunsa yayi zuwa kan Gold Thigh chin din da aka sanya mata mai jan hankali Ya murzata da hannunsa kafin ya warwareta tare da jefar da ita kan mattress din, gogon naka fa ya fara hawa kan network, linzaminsa nema ya ke ya rasa masarrafin sa. Kasa jurewa yayi cikin shauƙi ya sumbaci lallausar fatar boobs dinta, almost 15 times Yana sumbartarsu Wani irin fusgarshi sukeyi kamar ya zarosu daga ciki sai ƙwalele suke masa. Mayar da tafukansa yayi asaman wide Thighs dinta farare sol da su ya shiga murza su a hankali. Ɗumin Jikinta ba ƙaramin kaimi Ya ke ƙara masa ba, yaji dadi da Allah ya cika masa burinsa na ganin wannan ranar daya daɗe yana jiran ta duk da tazo mashi ba ayadda ya tsammace ta ba. Jin daɗinsa ragaggene saboda Ya haramtawa kansa kusantarta har saida izninta da amincewarta gashi sun samu sa6ani har ya yi silar data fita hayyacinta, dakyar ya iya raba jikin shi daga nata yadda kasan maganaɗisu da ƙarfe, yayi hakanne gudun kada ya farmaketa, don yadda yake jin yunwarta komai zai iya faruwa. Saukowa ya yi daga kan gadon shanyayyun idanunsa akan surar ta, yana jin yadda gumi ya ke wanke jikin shi, yadda kasan A.c din dakin bata aiki, kayan jikinsa ya rage ya bar short, ya mayar da kayan a closet, Bathroom ya nufa don Ya tsarka ke Jikin shi ko ya samu nutsuwa... ~________________________________________Final Episode🥺🔥~ Around ƙarfe shabiyu daidai na dare ta farka daga guntun baccin da yayi awon gaba da ita, a hankali ta soma kokarin buɗe idanunta da su ka yi mata nauyi ta ware su akan Canopy din gadon. tana faman sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa ta soma ƙoƙarin tariyo mai ya faru da ita a ƙarshe kafin bacci ya ɗauke ta? A ina take? Ruɗune tsantsa akan fuskar ta, kamar tayi loosing memory din ta. kwata kwata ba ciwon kan da takeji dazu sai dan zazzabi kadan, ga yunwar da tayi mata ƙatutu, ga wata matsananciyar kasala data haifar mata da jin lalaci a jikin ta. Yunƙurawa tayi a hankali ta mike zaune tare da ɗaura idanunta akan cinyoyinta, gabanta ne ya fadi ta shiga shasshafa jikinta ganin babu bridal gown dinta, daga ita sai corset, mamaki ne akan fuskarta ta kasa tuna tayaya akai ta rasa gown din jikinta? Wanene ya cire mata ita? Wuyanta ta shafa taji wayam babu necklace sai lokacin ta lura gaba ɗaya an cire mata jewelry din ta, tallabe kanta tayi da hannu ɗaya tana ƙoƙarin tuna meya faru da ita Last? wani irin faɗuwar gaba taji rass sa'ilin data tuna abin daya faru tsakanin ta da shi? Wani irin tsantsar rudani da tashin hankaline Ya sake bayyana kan fuskarta ƙarara, cike da firgici ta ke zare idanunta gaba daya ta rude ta rasa gane mafarki ne ko gaske? In dagaske ne yana ina? Meyasa bata ganshi a kusa da ita ba! Ya ilahi muryarta na rawa ta shiga furta"na shiga ukuna! Inna lillahi! mym.. Man! Danish! Kana ina? Mafarki ne abun daya faru tsakanin mu ko gaske! Ka amsa min! Kana ina"? Ta faɗa jikinta na kerma ta shiga shasshafa mattresa din don ta tabbatar babu shi akai, saukkowa tayi daga kan gadon ta shiga yan waige waige tana cigaba da kwala mashi kira"My man! My man!! My Man!! Danish!! omeeir!! Ya Allah kasa ba mafarkin nayi ba, Ya Allah ko a fatalwane ina son shi a haka!, ko a zombie ne Inason Ya dawo gare ni, Zan kar6e shi da hannu bibbiyu ko da a matsayin Omair ne! Wayyo Allahna Na shiga Uku na bani! naja ma kaina, yanzu Idan maganganun dana gaya mashine sukasa yayi fushi ya tafi ya zanyi da rayuwata... " fashewa tayi da kuka cikin tashin hankali ta watsa da gudu ta nufi tsakar dakin tana neman shi, duk tabi ta haukace kwata kwata bata da nutsuwa, kamar mai fama da ta6in hankali, juyawa tayi da gudu ta nufi closet door ta shiga bata ga kowa ba, ta fito jikinta na 6ari ta nufi laundry room ta duba ciki bata ganshi ba, fitowa tayi tana ku ka ta shiga prayer room wanda ƙofarsa a cikin bedroom din ta ke tana shiga taga babu aikuwa ta ƙara sautin kukan nata, kamar tayi hauka. batasan ina zata sanya ranta ba ji ta ke idan har mafarkinsa ne tayi ba gaske ba, babu abun da zai hana ta haɗiyi zuciya saboda ƙululun baƙin cikin da ta ke ji na rashin ganin shi! Meyasa zaizo mata a mafarki ya tafi? Kenan duk labarin daya bata a cikin mafarki ne"? Batare da gajiyawa ba ta cigaba da neman shi sako da lungu na gidan, sam ta manta da yadda ta ke, da ta galabaita awahalce ta nufo bedroom din donta sanya sutura da niyar ta koma gidan daddynta don bazata iya cigaba da zaman gidan ba. Shigowa ta yi bedroom din, A lokacin ta cire rai da ganin shi, ta sare gaba ɗaya ta sanya ma ranta mafarki ne tayi.. Har ta nufi closet don ta ɗauko sutura ta sanya sai kuma ta tsaya tana tunanin in har mafarki ne to wanene Ya cire mata gown dinta da jewelry din ta? Kodai yaya Owais ne yazo batare da sanin ta ba"? Durƙushewa ta yi kan gwiwowinta ta kife kanta kasa tana kuka tare da ambaton My man cikin disasshiyar muryarta.. Kwatsam ba zato ba tsammani ta tsinkayi motsin Mutun a cikin kunnanta daga bayanta. Cak ta tsaya dayin kukan, a razane ta ɗagowa tare da yin saurin juyowa don taga wanene cike da saran shi ne.. Juyowar da zatayi keda suya, Kaitsaye idanunta suka shiga cikin nashi yana atsaye gaban bathroom door, ya ɗaure waist dinsa da short towel da bai wuci gwiwarsa ba, sexy abs dinsa ya ƙara fito da kyawun kirjin shi, Har yanzu da sauran tattoo dinsa na tambarin kurkukun ƙaddara duk da ya ɗan disashe alamar an ta6a kokarin goge shi. ashe tun lokacin data farka tana ta kuka tana sambatu yana a cikin bathroom yana jiyota, bai daɗe da shiga ciki ta farka ba, ko wankan bai kaiga yi ba, ya tsaya yana sauraron ta, yanzu ya ƙara tabbatarwa kansa babu wanda ya maye gurbinsa a zuciyarta, babu abun daya sauya na daga ƙaunar da ta ke yi mashi, shi ɗin daine na har abada, garkuwar ƙaddara💗 Tsinkayar muryar sa ta yi "Kin yarda zaki rayu dani a matsayin Omair ko kuwa har yanzu kina akan bakan ki..." ya faɗa fuskarsa a ɗaure ba annuri. Yunƙurawa tayi tare da miƙewa tayi da dan gudun ta nufeshi tana isa gabanshi ta afka mashi gaba daya ta ƙanƙame shi da dukkan hannayenta biyu ta tallabe bayansa, ta cusa kanta cikin faffaɗan ƙirjinsa batasan sa'ad da ta fashe da kukan farin ciki ba, lumshe idanu yai a hankali yana jin wani sanyi da ya lullu6e zuciyar sa, ya nutsu yana sauraron kukan ta. Daƙyar cikin kuka ta furta"ko fatalwarka ce zan iya rayuwa da ita, kasan inason ka fiye da yadda nake son raina, i'm really sorry, banyi zaton kalamaina sun 6ata maka rai har haka ba, ka yafe min komai da nayi maka abaya mara daɗi, na kar6i laifina, na tuba my Man zan gyara kuskurena, Don't leave me again please, stay with me until my last breath! zanyi maka biyayya, amma kadaina fadin in bazan iya rayuwa da kai ba, mu rabu, It feels like you're telling me to give up on life, kai kadaine madadinka a zuciyana, nafi kowa son cigabanka My man, naji dadin ilmin da kayi, Allah shine shaidata, kuma Ina tayaka murnar haɗuwa da family din ka.. " Kwata kwata bai katse ta ba, ya nutsu yana sauraron daddaɗar muryar ta, yayin da idanunsa ke akan yalwatacciyar sumar ta, yadda ta manne masa kamar za su koma mutun ɗaya, kukan da ta ke yi yana karya masa zuciya, baya son jin kukan Unaisah arayuwarsa shi ne abun dayafi tsana, a baɗini bai faɗa mata da wata manufa ba, yayi amfani da hakan don ya kare kansa daga gare ta ko ya samu su sasanta cikin sauƙi, kuma plan dinsa yana aiki yadda ya kamata!. cikin nutsuwa ya shiga shafa Gashin ta da hannayen sa, cikin sigar lallashin ya furta"ya isa haka Malak albi, bana son jin kukan ki yana ƙona min rai, ki yi shiru, komai ya wuce, ni ban fada maki da wata manufa ba, sai don inason na shawo kanki Unaisah don ki kar6i uzurin daya hanani dawowa gare ki.. " bai ƙare maganar ba ta katse shi cikin shesshekar kuka mai haɗe da haki ta furta"cec.. Cewa ka yi in ba zan iya zama dakai a matsayin Omair ba, muyi break up! kasan yadda naji zafin kalmar nan a cikin zuciyana"? Dakyar ta ƙarashe maganar tana ƙara matse jikin ta da nashi. Baisan tayaya zai lallasheta ba, zuciyarta awuya ta ke, Ya fahimci taji zafin furucinsa sosai. Bazai juri cigaba da sauraron kukan ta ba, batai aune ba, taji ya tallabe bubble butt dinta da tafukansa ya janyo jikinshi sosai, ya shiga tsakanin cinyoyinta ya matse jikin su duk da taji faɗuwar gaba da zullumi amma bata iya raba jikinta daga nashi ba, saboda malalaciyar kasalar daya haifar mata tuni bugun zuciyarta ya tsananta, Kwantar da kanta tayi saman kafaɗarshi tuni ta nemi shesshekar da takeyi ta tarasa saboda nutsuwar da ta ziyarce ta, neman duk wani abu da zai sanyaya mata zuciyarta takeyi ko ta samu sassaucin raɗadin da ta ke ji. Tun da ya yi hakan ya nemi nutsuwarsa ya rasa,Yana ta k'ok'arin kame horny dinsa but he couldn't bear it, cos He still feeling her intense desire, nothing changed, just like she feels that too. Da niyar ya lallashe ta ta daina kukan da ta ke yi ya ɗauke ta, sai dai lamarin ya juye fiye da zaton shi, tamkar ya tsokano yunwar Sha'awarta, ji ya ke in har ya ɗaga kafarsa faɗuwa zaiyi saboda matsananciyar kasalar data haifar masa shiyasa ya ƙame atsaye. lokaci daya makoshinsu Ya bushe kamas wani irin kishi Ya ziyarce su. yana jin yadda iskar numfashinta ke buso fatar wuyan shi, jin baida alamun motsawa ne yasa ta tattara sauran ƙarfin daya rage mata ta ɗago da kanta a hankali ta saisaici saitin fuskarshi wani faduwar gaba taji sa'ilin da idanunsu suka shiga cikin na juna wani marayen kallo irin na mabuƙaci ya ke bin ta da shi dakyar ya ke iya buɗe sleepy eyes dinsa akan ta, duk tabi tasha jinin jikin ta ganin yadda ya sauya mata kamar ba Man ɗin ta ba sai yanzu da su ke gab da juna ta lura da girman daya ƙara. Muyarta na rawa ta furta"ƙishi nake ji, Ruwa zan sha" ta faɗa tana kokarin 6an6are jikin ta daga nashi cikin sauri saidai takasayin hakan, unexpected ta tsinkayi muryasa a cikin kunnanta "Let me quench your thirst with my saliva.." aruɗe ta ɗan zare idanunta akan nashi, tana kokarin bude baki ta furta kalma unexpected taji ya zura tongue dinsa a cikin karamin bakinta, ba shiri ta kar6e shi dukanshi cikin fitar hayyaci suka shiga kissing din juna azafafe, kamar zasu cinye harshen juna. cikin wani irin salo ta tallabe wuyansa da tafukan ta da ke kerma gudun kada ya kubce mata donji take zata iya rasa ranta, while she's kissing him passionately, like the way he's giving her French kissing, gaba ɗaya suka fita hayyacin su, sai da takai ga hatta numfashin su dakyar yake fita, sai huci su ke yi suna haki, Jikinsu kerma yake sosai ya ɗauki zafi rau cos this is their first time.. Jirine ke niyar dibarshi sosai Ya ƙara tallabe butt din ta, dakyar dakyar ya nufi bathroom da ita ahaka yadda suke manne da juna suna cigaba da kissing din juna. Kaitsaye ya nufi Walk-in Shower ɗauke da ita, wani katafaren Bathtub ne girke kan floor, gaba daya kewayen shi glass ne, daga sama, Ceilling shower din take tana fuskantar kwamin wankan a hankali ya kai hannunsa jikin Button din ta ya kunna ta. nan ta ke Ruwa Ya soma yayyafowa yana zuba cikin kwamin kamar ana ruwan sama, kwata kwata Unaisah batasan in da suka shigo ba, ta lula duniyar mayen shi. dakyar ya banbareta daga cikinshi kamar maganaɗisu Ya Kwantar da ita cikin ruwan batare daya rabata da corset din jikinta ba, ɗumin ruwan ne ya ratsa fatarta ta lumshe idanunta da suka kaɗa jawur kamar na yar ƙwaya. yana ta jan numfashi ya soma warware towel dinsa don shima ya shiga ciki,a lokacin dik da bata a cikin hayyacinta saida ta razana da ganin abun da ya ke kokarin yi. batasan sa'ad da ƙarfi yazo mata a jikin ta ba, tayi saurin durowa daga cikin kwamin a gigice ta watsa aguje zata fice, bata kaiga isa ga ƙofar ba, sil6i ya kwasheta tayi baya zata kife, a hanzarce ya tarota ta dawo kan hannun shi, Sa6arta yayi ya juya zai koma gurin kwamin da ita, ta bangaje shi, ta duro a makance ta shiga neman hanyar da zata fuce daga bathroom din tama rikice ta kasa ganowa, a lokacin ji yake kamar ransa yana a jikin ta kan abinda ya ƙwallafama rai, ta riga ta gama rikitashi da ganin wannan sura tata,cikin rashin sa'a ta ƙume kanta jikin glass wall din gurin. radadin da taji ne ya hana ta iya dagowa har ya cimmata, kamar mayunwacin zaki ya yi mata rumfa da broad chest dinshi, ya manneta da bangon ta yadda bazata iya kubce ma shi ba. Yana fitar da huci ya furta "Why are you running from me?".. runtse idanunta tayi sosai tana ji yadda jikinta ke tsuma. Adabarbarce ta furta "ba gudun ka na ke yi ba, nima ina jin abun da ka ke ji, I want to fulfill our dream of becoming one, but I'm scared, I'm hungry, sleepy, and I need to pray..." dakyar ya ke iya buɗe lumsassun idanunsa akan gefen fuskarta da ke ta zubar da gumi. Bai tsaya sauraronta ba, A hankali Ya soma warware corset din jikinta, gabanta ne ya shiga faduwa gashi ya matseta da jikin shi, Bata iya ta6uka komai ba har saida Ya rabata da rigar, Ya tum6uke ta ya jefar, Pant da bra ne kadai suka rage a jikin ta, rinannun idanunsa ya ɗaura akan bayanta, he gently Caressing her smooth butt, nutsiwa tayi tana jin duk wani motsinsa a jikinta, A hankali Ya soma tattare sumar kanta cikin tafin hanunsa bai iya hadeta duka ba saboda yawan da tayi, yayi niyar ya ƙarasa amma sai ya kasa saboda tunawa da halin da zasu iya shiga a first night din su, Ya fahimci tana jin tsoro bata saba da shi a matsayin Omair ba shiyasa ta gigice,shi kanshi yana mamakin yadda sarrafa kanshi ke neman zamar mashi aiki. A hankali ya saki sumar kanta, ya kwantar da kanshi saman sumar data yarfo kafaɗarta yana faman sakin numfashi kokari ya ke ya iya sarrafa kanshi ko ya samu nutsuwa. Ta yi shiru tana sauraron shi abayanta, ita kadai tasan me take ji a game da shi amma bazata iya jurewa ba a wannan lokacin. Raunanniyar muryarsa ta tsinkaya a cikin kunnanta "Let me help you bathe, I promise I won't harm you" Shiru tayi jim tana tuna time da ya ke tambayarta suyi wanka atare ko yayi mata wanka tun a prison tasan Danish da burin wannan. Cikin sanyin murya tace "I'm sorry if I upset you, but It's not right for us to be intimate in the bathroom.. " bata ƙare maganarba ya katse ta"karki damu, na fahimci ki, amma ki bari nayi maki wanka" Jinjina mashi kai ta yi alamar ta Amince, batare da bata lokaci ba, ya cuccu6eta da hannayen shi biyu, kamar jinjira Ya nufi shower ta jigin bango, ya lura ko hada idanu batason yi da shi, jikinta sai kerma ya ke yi kamar wadda kidnapper ya sace, hannu yakai da niyar ya tu6e mata bra, cikin sauri ta dafe kirjinta da ke bugawa da karfi da karfi, Juyawa mashi baya tayi, yayi shiru yana bin bayanta da kallo, yatsun hannun na kerma ta soma tu6e inners din da kanta. tun daga kan laps dinta yake binta da wani mayataccen kallo, sa'ilin data gama komai matsawa tayi batare data jiyo ta dubi halin da man ya ke a ciki ba, taje ta sargefe inners din jikin hanger, da hannayenta biyu ta rufe kirjinta don kar ya gani, ta dawo daga gaban shi ta tsaya tare da juya mashi baya Dan bazata iya kallonshi ba, tana ci gaba da jin faɗuwar gaba, ji take kamar a mafarki komai ke faruwa, saboda al'ajabin kasantuwarta da Man dinta a matsayin mijinta, kunyarsa ce ta kama ta har ta kasa jurar haɗa idanun ta da nashi. hannun shi ya kai jikin Automatic soap dispenser ya matso sabulun a tafin hannun shi, ta zare idanu tana kallon abun da ya ke kokarin yi, bata dakatar da shi ba, tayi saurin runtse idanunta, a hankali ya soma shafa mata liquid soap a saman lallaursa fatarta, tun daga kan bayanta ya fara har izuwa saman butt dinta, yadda ya ke murza fatarta ba karamin kashe mata jiki ya ke yi ba. Unexpected idanunsa suka sauka akan waist tattoo din ta, ya dan sunkuyar da kan shi tare da ƙura idanunshi yana kokarin gano zanan menene, duk tana kallon shi, lokaci daya taji ya furta"Garkuwa.. " da wani irin sauti, ya dan ɗago da idanun sa ya dube ta, murmushi ta sakar mashi tare da kawar da idanun ta gefe ɗaya, tsantsar farin ciki ne ya cika zuciyar shi, yaji dadin ganin tattoo din sunansa a jikin fatarta, hakan ya kara tabbatar masa da cewa Unaisah tana tuna shi a ko da yaushe, zanan ya tafi da imaninsa, Kissing din tattoo din ya soma yi da wani salo na jan hankali, tana jin kamar yana yi mata susar kadangare ta dinga fitar da numfashi cikin sauri wani irin yanayi take ji mara misaltuwa. bayan daya gama ya juyo da ita, da sauri ta fada kan kirjinshi ta kankame shi jikinta na kerma, hakan da tayi ba ƙaramin ƙayatar da shi yayi ba, tsadaddan murmushinsa ya saki. "Kin tuna"? Ya faɗa yana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Lumshe idanunta tayi tana tuna ranar da yayi mata wanka agaban ƙorama cikin dajin Evil forest, Yau kuma agidansu na aure, daɗin yayi mata yawa ji ta ke kamar ta fasa ihu saboda farin cikin Allah Ya dawo mata da farin cikinta, burinta Ya cika. Yana jiyo yadda take safke ajiyar zuciya, A lokaci ɗaya zuciyar su take bugawa cikin nutsuwa, tuni jikinsu Ya jiƙe da ruwan dumi dake saukowa daga cikin shower da ya kunna, sunyi sharkaf, sumar kansu ta manne ma fatar su, tana a manne da jikin shi ta narke mashi, a hankali yacigaba da cuɗa mata jikinta, tanajin yadda ya ke shafa fatarta da yatsunsa. Gajiya ta yi da tsayuwa duk da aruƙe take da shi, cikin sanyin murya ta furta"My Man, I'm tired of standing.. " bata ƙarashe maganarba, Ya tallabe booty dinta Ya daurata kan flat stomach dinshi,wani mayen yawu ya haɗiya ƙutt, Idaninsu na shiga cikin na juna, kunyarsa ta ji, batasan sa'adda tayi saurin lumshe idanunta tana sakar mashi wani ƙayataccen murmushin da ya rikitashi, ta riga da tasan ta gama zautar da shi, shi kanshi ya shaida ba Unaisar da ya sani bace ada. In har yabiyewa halin da ya ke a ciki ba abin da zai hana Ya farmaketa a daidai nan. Fuskarta yabi da kallon mai cike da shauƙinta, tun daga kan kwantaccen gashin forehead dinta, har izuwa zira ziran Eyelashes dinta, sauko da idanunsa yayi kan karan hancinta kafin ya dire su saman full lips dinta da suka dan kumbura sun ciza launin su. Unexpected Taji Ya direta kan kafafunta, ya kashe shower din Ya kunna masu Body dryer mai ɗumama jiki ta busar da shi, kunyarsa ta hana ta saki jiki amma ta ruɗe da ganin abubuwan da babu agidan father din ta wannan gayu har ina, tun da take bata ta6a ganin Opulent bathroom irin wannan ba. towel Ya dauko a hanger Ya yafa mata shi abayanta da sauri ta kar6e tare da daure waist din ta da shi, kafin su fito daga toilet din saida suka dauro alwala agaban sink. daga Bisani, Ya cuccu6ota kamar yar tsana, Ya fito Ya nufi closet room da ita, Anan Ya sauke ta gaban Faskeken Closet din kayansu wanda ya mamaye ilahirin bangwayen dakin, Da kanshi Ya zabo masu kayan da zasu sanya, satin pajamas set ya dauko biyu Na shi da nata launin hot pink riga da wando Ya mika mata ta sanya hannu ta kar6a ganin yana kokarin warware towel dinsa agabanta yasa tayi saurin juya baya,ta lura kwata kwata bayajin kunyarta, batasan duk yana kallonta ta cikin mirror din gabansa baisan me take jima tsoro ba a tare da shi? Yana ta satar kallon ta, yaga ta soma sanya kayan baccin ta, lura da rubutun da ke a gaban rigar yasa takai idanunta akai, My Shield taga an rubuta da wani irin salon rubutu mai jan hankali. murmushi ne ya su6uce mata, juyawar da zatayi keda wuya idanunta suka sauka cikin nashi, da yatsan shi ya nuna mata rubutun dake agaban rigarsa, waro idanu waje tayi yayin da ta ke karanta rubutun a fili ta furta My Destiny, Gaba ɗayansu suna da tambayoyin da su ke so suyi ma junan su musamman ita, tana son taji komai da komai game da Omair don bata gamsu da labarin daya bata ba, tana bukatar kari. Bayan ta ɗauko hijab ta zura a jikinta, Yace tabiyo bayanshi, suka fito daga dressing room suka shiga Prayer room, a tare su ka yi sallah, yayi masu addu'o'i suka shafa, basu wani jima ba saboda yunwar da suke ji ga bacci cike da idanun su, ya riga ta fita daga dakin bayan sun gama yin sallar. Daga bisani ta miƙe tare da cire hijab din, ta maida ta cikin closet, Ta dan tsaya tare da ruke qugunta tana tariyo komai daya faruwa a tsakanin su, fatanta Allah Yasa ba mafarki takeyi ba, don har yanzu ta gaza yarda mafarkin da ta dade tanayi ne Ya zamana gaskiya, can kuma ta kama tunanin wani irin arziki Danish yayi? Komai na shi ya sauya ya koma na hamshakan masu kudi, duk da dama ta dade tana ji aranta Danish jinin arziƙi ne amma gaba daya yafi karfin hasashenta musamman data lura katafaren gidan nan da suke a ciki mallakinsa ne. Abun dayafi daure mata kai yadda Allah ya juye al'amarin tun tana karama tana da burin ta auri attajirin mai kudi, amma lokacin da tafara ganin danish sai ta kamu da sonshi a yadda yake har taji zata rayu da shi har karshen rayuwar ta sai gashi Allah ya juye al'amarin shima ya zama Hamshakin Mai kudi kuma ya aureta. ~_____________DESTINYSHIELD💎💞💘~ Fitowa tayi daga dressing room din, A hankali take tafiya tana yan waige waige kamar mara gaskiya, ganin babu shi a bedroom din yasa ta tunanin Ina ya shige ne? Ita fa bata son kona minti daya yayi nesa da ita gudun kada Ya zamana mafarki ne komai daya faru.. Ɗaga murya tayi da karfi ta furta My Man, kana Ina"? Neman shi ta farayi saida tagama zagaye bedroom din babu shi, Ta fuce daga ɗakin tana tsaka da neman shi. Unexpected Ta hango shi A dining room ta cikin glass Yana a zaune kan dining mat ya tattara hankalinsa akan wayarsa da ya ke pressing, Nannauyar zuciyar ta sauke, Ta nufi Dining room din, ta tsaya daga bakin kofar tana ƙare mashi kallo mai cike da shaukin shi, pyjamas din jikinshi sunyi mashi kyau sosai sun kara fito da hasken fatarshi fara sol. Ya nutsu abunsa, bai lura da zuwanta ba, dadin kallonshi ta ke ji cike da ɗokinsa kamar ta haɗiye shi ta ke ji, Aranta ta ayyana wai yanzu nan mijinta ne Uban ya'yanta nan gaba? Wonders shall neva end, Allah ya za6e ta a cikin dubunnan mata ita ɗaya Ya mallaka mata shi! Ya Allah, kamshin Jikintane Ya ziyarci hancinsa, nan take ransa Ya bashi tana a tare da shi, a hankali Ya ɗago da sleepy eyes dinsa Ya dube ta da su, gaba ɗayansu akwai gajiya da bacci acikin idanun su ga yunwar da suke fama da ita wuni guda baci ba sha. "Ke nake jira, Kizo muyi dinner nasan kina jin yunwa" ya faɗa yana nuna mata kayan abincin dake shake akan mat din, nufo shi tayi kamar wadda aka zarewa Laka, daga bayan shi ta tsaya tana kallon dinner din, arabian dishes ne a cikin Silver platters and Coffer, aroma dinsu ne Ya fara dakar hancinta ta fara hadiyar yawu, tana leken abincin, Ganin bata da niyar zama ta tsaya bayan shi, yasa shi yi mata gyaran murya, dakyar ta motsa ta zagaya zata zauna daga karshen Dinner mat din, Tana satar kallonshi suka hada idanunsu cikin na Juna, girgiza mata kai yayi"kinyi min nisa, ba haka nakeso mu dinga cin abinci ba.. " dan zare ido tayi, tare da jinjina kai, ta dawo zata zauna tana facing nasa, still ya girgiza mata kai, Ta rasa gane me yake nufi, ganin ta toge yasa shi mika mata hannu"zonan"! Yadda ya kirata kamar ƙaramar yarinya, ya zatayi tun da karkashinshi take, Wuka da nama suna a hannunsa, sai yadda ya ga dama.. Matsawa tayi daga gaban shi, harta yunkura zata zauna agefen shi, Ya janyo hannunta gaba ɗaya ta rubzo saman laps dinsa,daidaita zamansa yayi yadda zataji dadin zama, kuma yana kallon face dinta. Wani shock taji kamar electric current Ya ta6ata. Saboda kunyar shi yasa ta rufe idanunta. Kallon fuskarta yayi kamar zaiyi murmushi, har cikin ranshi daɗi ya ke ji na kasantuwar su ma'aurata, yana mai mamakin kunyarsa da ta ke ji bai dauka angel dinshi zataji kunyarshi irin haka ba. "Haka nakeso mu dinga zama idan zamuci abinci" can kasan makoshi ta furta"toh" "Tayaya zamu iya ciyar da junan mu bayan kin rufe idanunki"? dakyar ta ɗan bude su batare data dube shi ba. A hankali ya dauko tea put me dauke da gahwa (Arabic coffee) Ya tsiyaya masu a cikin Silver cups, Ya ruko cup daya ya miƙa mata, hannunta na kerma ta kar6a ta kanga abaki, kamshin tea din ne Ya ratsa hancinta har batasan sa'adda ta kur6e shi duka ba, tana so ta dan ja aji kar yaga hadamarta amma takasa, sau uku yana ƙara mata coffee tana shanyewa, yayin da shi ko rabin cup dinsa baiyi ba, ta ƙosa su fara cin abinci yunwa ta ke ji kamar kamar me. Silver platter ya buɗe mai ɗauke da Chicken machboos (Abincin gulf ne, wanda aka yi da shinkafa da nama,) tuni taji miyanta yatsinke, sam ta shafa'a ta tsoma hannu batare data sanya spoon ba, ta fara duma loma abaki tana ci, kasa ci yayi ya nutsu yana kallon ta gwanin ban sha'awa, tana tsaka da cizgar cinyar kaza ta ƙware, da sauri Ya dauko glass of zamzam Ya miƙa mata, arazane ta dube shi bakinta dama dama da maiko, ɗaga mata gira yayi da sauri ta sunkuyar da kanta kasa cike da jin kunyarshi, ta bude baki ya kwafa mata bakin cup din tasha ruwan mai sanyi da dadi. "Kin tuna ranar da yunwa ta farkar damu tsakar dare agidan kurkukun ƙaddara, muna laluban kwandon abinci muka hada hannu atare muke ruke kwandon.." batasan sa'adda ta fashe da dariya ba, Murmushi yayi idanunsa akan white teeth dinta, dimple dinta yafi komai tafiya da shi. Ta shagala tana ta dariya har ta dan kwantar da kanta saman kirjin shi. Dama da biyu ya tuna mata ranar, saboda yana son ta daina jin kunyar cin abinci agaban shi, yafi son ta saki jiki da shi suyi rayuwar farin ciki. Tsagaitawa tayi da yin dariyar tana fadin"na Tuna ranar, idan bazan manta ba, dana hana ka har kayi zuciya ka ki ci ko"? Ta faɗa tare da kallon shi kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, dage mata gira yai alamar eh, da sauri ta kawar da idanunta gefe ɗaya, cikin nishaɗi suka cigaba da cin abincin, tun tuna jin kunyar shi harya fara bata abaki itama ta soma bashi, saida sukaci suka ƙoshi, a lokacin dare ya ritsa sosai, Suna kammala Cin abincin ya dauko mata pain reliever ya bata tasha saboda ta kara jin sauƙin jikin ta. Daga bisani ya sa6eta da hannayensa biyu Ya nufi Bedroom da ita, Asaman gado Ya shimfiɗar da ita kamar new born baby, tayi lamo tana bin shi da kallo,Addu'a yace suyi sannan, ya kashe hasken dakin, Ya Hau kan gadon daga bayanta, Ya Janyo duvet din Ya lullu6e masu rabin jikin su, kwata kwata bai matsa kusa da ita ba da akwai tazara a tsakanin su. Ji tayi bazata iya jirewa ba gudun kada ta juya taga babu shi yasa tayi tunanin ta ɗan juya ta saci kallon shi, A hankali Ta dan juya ta dube shi, ya lumshe idanun shi kamar maiyin bacci. Nutsuwa tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa yayin da take tuna komai daya faru a tsakanin su yau, kafin ta sauya a kalar tunanin nata zuwa kalmomin daya furta mata kafin tafiyarsu kai farmaki, taso ayau dinnan ta cika mashi burin shi amma tsoro ya hana ta, da dabara ta mirgina kamar irin cikin magagin bacci ta matsa kusa da shi, ta haɗe jikinta da nashi, da sauri ya tallabe bayanta da hannayen shi tare da cusa hancinshi tsakankanin wuyanta har wani sautin shakar kamshin ta yake fitarwa, a hankali itama ta cusa hannayenta a cikin sumar shi tana shafawa kamar tanayi mashi susa, tun sunayi cikin hankalinsu har bacci ya fara fisgar su cikin shauƙin juna, in a short time bacci mai nauyi yayi awon gaba da su, yadda suka ƙanƙame juna kamar zasu dawwama a haka. Tun ƙarfe 2 da rabi na dare suka fara sharar bacci, Har wuraren ƙarfe goma na safe ba su farka ba, Tsawon Awanni takwas Cuff. Lokacin daya farka daga bacci, Unaisah ko motsawa batayi ba, tayi nisan kiwo a cikin baccin ta kamar matatta, ta haura kafarta daya asaman waist dinsa. Abu na farko daya farayin tozali da shi sa'ilin daya buɗe idanun shi itace kyakkyawar fuskarta, Akan ta ya sauke eyes dinshi, yadda take fitar da numfashi kamar wata jinjira cikin natsuwa da kwanciyar hankali,murmushi ne ya subuce mashi Dan kadan kafin a hankali yayi kasa da idonshi ajikinta,yadda take numfashi a hankali haka kirjinta ke hawa da sauka ba karamin jan hankalin shi su ka yi ba, bakomai ya ke tunawa ba face time din da babu albarkatu a kirjinta, kamar na namiji saboda shafewar su, bai ta6a tunanin wannan ranar zatazo ba, kamar zaiyi murmushi ya dan ta6e red lips dinta. Fuskarta Yabi da kallo tana bacci kamar jinjira. Ya gaza yarda Ya mallaki Unaisah, Yanzu tashi ce ita, matar shi, uwar ya'yanshi masu zuwa, ta zama a karkashin ikon shi, Nauyin komai nata na akan shi, Allah ne kadai Yasan farin cikin da ya ke ji. a cikin zuciyarshi ya karanta addu'ar tashi daga bacci, A tsanake Yake sake bin eye lashes dinta da kallo, a hankali Ya Daura yatsunsa asaman sumar kanta Yana dan shafa mata ita kamar jinjira, kwata kwata bai lura da lokaci ba, saboda shagalar da yayi gurin kallonta. Kamar ance Ya dubi agogo, arude Ya zare eyes dinsa ganin karfe goma na safe, Bacci Ya shagalar da su har asuba ta wuce ba su yi Ibada ba. Tunani ya somayi tayaya zai tayar da ita daga bacci batare daya takura mata ba! Badan sallah ba da ba abun da zaisa ya farkar da ita. Saitin kunnanta ya kai labbansa cikin muryar raɗa ya furta "ya rouhi, Tashi muje muyi sallah, mun makara" shiru bata farka ba. Sau uku yanayi mata raɗa kamar wanda zai tayar da jinjira. Yasan ta da nauyin bacci wani lokaci,balle jiya data jigata. Qira'ar Alqur'ani ya soma yi mata cikin nutsatstsiyar muryarsa, Unexpected cikin bacci ta tsinkayi ƙira'arsa mai dadin sauraro irin ta Larabawa. Tana buɗe idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi, ta ƙura mashi idanu tana kallon yadda ya ke motsa labbansa yana qira'a tayi mamaki sosai, jin surar da yake Karanta mata da kai batare daya duba al'qur'ani ba, Saida ya kai aya tukunna ya dakata yana lumshe idanun shi yace"barka da safiya ya malak albi, kin tashi lafiya" lumshe idanunta tayi tana jin ta awata duniyar nishaɗi. Saida ta fara karanta addu'ar tashi daga bacci duk yana kallon ta daga bisani tace "My man In har zaka dinga tada ni daga bacci irin haka zanfi kowa more tashi daga bacci, zanji dadi idan ka zama mutun na farko da zan fara yin tozali da shi a duk lokacin dana farka daga bacci. Murmushi yayi wanda bai wuci fatar labbansa ba. "Mun makara bamuyi sallah ba" da sauri ta dubi agogo, zare idanu tayi, tare da yin saurin miƙewa, Batai aune ba, Taji Ya cuccu6eta ya sauko da ita daga kan gadon, A saman kafadarshi Ya sa6e ta, Babu alamun Yana jin nauyinta, Ji ya ke kamar ya ɗauki jinjira, Toilet Ya shige da ita. Bayan sunyi alwala, suka fito Coset room suka shige don su shirya kan su, jim kaɗan suka fito cikin shigar larabawa hannunsu ruke cikin na juna suka nufi prayer room wanda komai na cikinsa na yin ibada ne. Asaman wata dankareriyar prayer mat, suka tsaya tana gaba Yana abayanta, Shi yaja su sallar, dakyar ta samu nutsuwar daina kallon bayan shi ta maida natsuwarta kan sallar da suke.. A tsanake suka yi sallar, Bayan da suka kammala, suka zauna ya mika hannu Ya janyo prayer beads Biyu Ya mika mata daya ta kar6i, ya ruƙe ɗaya a hannun sa, suka soma yin tasbihi, tsawon mintina, ganin yayi mata nisa yasa ta ja jiki ta dawo gefen shi don taji dadin kallon shi. Tana jan Cazbaha tana satar kallon red lips dinsa, Dadi takeji Man dinta ya Musulunta Ya iya karatun al'qur'ani da komai ma,komai sabo yake zo mata a tare dashi tabbas wannan omair ne ba danish din da ba sauyin rayuwa ta ko ina,ransa ne ya bashi tana kallon shi, da zarar yayi kamar zai juyo sai tayi saurin sadda kanta kasa taci gaba da jan casbaha. Murmushin gefen fuska ya saki, shi kanshi yasan dole Unaisah ta susuce akan shi. Qur'ani ya buɗe masu akan wooden qur'anic stand. Muraja'a suka yi atare idan ta karanta aya sai ya karanta ayar gaba, Sura Uku suka karanta kafin Ya rufe al'qur'anin. A lokacin da bata zata ba, Taji Ya janyo hannayenta a cikin nashi ya shiga murza ziraran yatsunta yana kallon zanan kunshin ta. ta ɗago da farare idanunta ta dube shi. Yayin da ya saka idanunsa a cikin nata. "Jiya bayan ɗaurin aurenmu, daddynki Ya kira ni gefe daya ya faɗa mun wasu maganganu da suka karya zuciyata... " gabanta ne ya fadi aruɗe take duban shi. Numfasawa yadanyi before ya daura da cewa"ya yarda dani dari bisa dari, kuma yasan cewa babu namijin da zai iya sarrafaki bayan shi sai kuma Ni saboda ya shaida tsantsar son da kike min, Ya bani amanarki, rukon ki ya dawo gurina, da dukkan dawainiyarki, ya bani ke badan ya gaji dake ba, sai don yana son kema ki raya sunnar Manzon Allah SAW kamar Yarda kowani uba nagari yake fatan yayanshi sukasance sunyi koyi da wannan sunna, ya kuma rokeni akan na kula masa dake kamar yadda ya kula dake tun kina jinjira har ya labarta min zaman da kukayi ya kara da cewa yasan wani lokaci baki jin magana kina da saurin fushi amma inyi hakuri da ke, idan kikai min badaidai ba, kada in ƙwaurace maki, in zaunar dake inyi maki nasiha, zaki gyara, saboda ni kadaine kusa dake, ayanzu zanfisu sanin me kike a ciki, idan na juya maki baya zaki kuntata, kuma bai yarda son da muke wa juna ya rufe mana ido mu kasa ganin laifin junan mu ba, mu ji tsoron Allah mu tafiyar da rayuwar aurenmu bisa tafarkin addininmu, mu kuma yi koyi da rayuwar manzon Allah da matayensa, lokacin daya ke fada min maganganun nan abun dayafi karya min zuciyata, dayace yasan bazai hana ki fuskanci jarabawar rayuwar aure ba da kowace mace take fuskanta agidan ta, amma koda nan gaba naji kin fita araina kada in tsangwameki, In dawo mashi da ke bazai taba gajiya da yar sa ba kuma bazai ji haushi na ba, Unaisah yana magana hada kwalla ya zubar min wai ni... " ya faɗa tamkar zai fashe da kuka saboda abun ya ta6a zuciyar shi. tunkan ya karashe labarta ma, Idanunta suka cuccuko tab da ƙwalla, a hankali zafafan hawaye suka soma gangarowa saman kuncin ta, ta ƙarajin kaunar daddynta da tausayin shi yana sonta fiye da komai na duniyar nan tun tana kankanuwarta take azabtar da shi daidai da rana daya bawan Allahn nan bai ta6a tsanarta ba, hasalima sai dai Yaja ta a jiki in ta yi badaidai ba.. Batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba kamar jinjira, da sauri Ya janyota jikin shi Ya rungumeta a kirjinshi, Ya daura hannayensa bayanta Yana lallashin ta dakyar ya samu ta dakata tana shessheka. "Ni ban fada maki don na sanya ki kuka ba, sai dan Inaso ki taimaka min Unaisah ki bani hadin kai, mu zauna lafiya da juna, inajin tsoron na gaza ruke amanarki yadda ya kamata, amma nasan son da nake maki bazai bari ni in cutar da ke ba ko da ni zan cutu, a shirye nake dana baki dukkan kulawata da soyayyata, da lokacina"! Ya ɗan dakata da yin maganar kafin ya daura da cewa.. "jiya bayan daurin aurenmu naji dadin da bazan iya misalta shi ba, saboda farin cikin kin zama tawa, zaki rayu agidana a karkashin ikona da kulawata, gaba daya dawainiyarki ta dawo kaina, komai ni zanyi maki Unaisah, Ina da halin da zan tafiyar da rayuwarmu harma data ya'yan mu batare dana gaza ba.. " yayin da ta ke sauraron daɗaɗan kalamansa wani sanyi da daɗi ne ke ratsa zuciyarta.. "Nasan dole wata rana mu samu sa6ani a rayuwar auran mu, amma in har muka yarda da junanmu, muka zama masu hakuri da juriya, mu ka kuma ruƙe addu'a, batare da sonkai ko son zuciya ba, In sha Allah zamu zauna lafiya, Aure yana bukatar fahimtar juna da soyayya, uwa uba hakuri shine jigon zaman aure gaba daya ma, kuma ni nayi imanin akwai fahimta a tsakanin mu... " ya faɗa yana duban fuskarta, kanta na akan kafadardarsa bata motsa ba, hawayen dake tsiyayowa ta cikin idanunta ya bi da kallon ji yayi bazai juri kallon su ba, tana kokarin buɗe idanunta Batai auneba taji ya sanya red tongue dinsa akan fuskarta a hankali ya shiga lashe hawayen ta. A lokaci ɗaya ta dinga jin wutar kaunar shi na ruruwa a cikin zuciyarta, fiye dana kowani lokaci. Ɗaura idanunsa yayi acikin nata suka ƙurawa juna ido kamar yau ne rana ta farko da suka fara ganin juna, tun fil azal Allah ya jarabce su da kaunar juna, yadda kasan tushen soyayyar su a jikin ransu take saboda yadda su ke mutuwar son kansu. sunkuyar da kanta ƙasa tayi cikin sanyin murya ta soma magana yayi shiru yana sauraron ta. "In sha Allah zanyi iya kokarina gurin taimaka maka na ganin ka sauke nauyin dake akanka, zan dage da tayamu addu'a Allah ya tayaka ruƙona My man, Nima ka tayani da addu'a Allah Ya bani ikon sauke hakkinka da ke akaina, Allah ya bani ikon yi maka biyayya sau da kafa... " har cikin ranshi yaji dadin maganarta, a hankali yake amsawa da ameen yana kallon lips din ta still kanta na kallon kasa. "Allah ya bamu hakuri da juriyar da zamu rayu cikin farin cike da jin dadi batare da mun samu sa6ani ba, kuma koda zamu samu sa6anin in dai mun kasance munayi wa juna addu'a in sha Allahu shaidan ko zuciya ba zasu rinjaye mu ba balle wani, sai dai mu mu rinjaye su,sai kaga cikin kankanin lokaci mun shirya kanmu..." dakatawa ta danyi tana kallon Yatsunsu dake harɗe cikin na juna.. "My man, ji nake kamar nafi kowace mace a duniya, bazan iya godewa ni'imar da Allah yayi min ba, daya za6eni cikin matayen duniya ya mallaka min kai a matsayin mijina, kai din burin kowace ya mace ne, son kowa kin wadda ta rasa, namiji mai tsada da wuyar samu afadin duniya, Allah ya kar6i koken da nake masa Ya dawo min dakai, Tun da na mallake ka ji nake babu abun daya rage ban mallaka aduniya ba, Allah ya gama min komai atanan saura fatan cikawa da kyau da imani..." baisan sa'a murmushi ya subuce masa ba Yabon Unaisah agaresa kamar an masa albishir da gidan Aljanna ne. "Ina matuƙar alfahari da ke! Nima bazan iya godewa ni'imar da yayi minba Daya mallakamin mace mai tsada mai wuyar samu a duniyar nan ni daya ya zabeni ciki mazan duniya, Kinfiye min komai Unaisah, in babu ke babu ni, kece ni Unaisah, Inason ki, Ina son mu rayu har karshen nunfashinmu.. daɗaɗan kalamai suke ta gayawa junan su. Daga bisani Suka ɗaga hannayen su sama suna yiwa kan su addu'oi cikin harshen larabci. Atakaice Cikin kwanakin nan shaƙuwa mai karfi da zazzafar soyayyace a tsakanin ma'auratan nan, zan iya cewa ban ta6a ganin masoyan da suke masifar son juna da zuciya ɗaya irin su ba, tsantsar kulawa suke bawa junansu, tattalin juna sukeyi da tarairaya, sallah kadai ke fitar da shi daga gidansa kasantuwar bai fara zuwa Office ba,dayake a nan Nigeria ya zabi zaiyi aiki, hutunsa Yake sha agidansa tare da hurul aininsa, Basa gajiya da faranta ran junansu, kullum suna a manne da juna, Wanka atare suke yin shi, sanya sutura a tare, Cin abincin a tare, bacci a rungume da juna, su yi gym a tare, su yi karatun al'qur'ani a tare, ranar da zata fara yin girki a tare su ka yi shi, Musamman saboda ita Ya ko yi girki agurin mommynsa, shi ya ke zama Ya gyara mata sumar kanta idan Ya hargitsa mata ita gurin kwanciya, idan ya gama itama ta gyara mashi tashi sumar, a tare suke zagaye bangarorin shaƙatawar dake a cikin gidan, duk idan zasuyi fira saita tambaye shi ya bata labarin rayuwarsa agidan iyayensa baya gajiya da labarta mata, dadi takeji idan yana faɗa mata irin rayuwar da yayi tare da iyayensa da yayyansa, itama takan bashi labarin rayuwar da tayi bayan babu shi, abu mafi kayatarwa a tare da su yadda suke kokarin sauke hakkin junan su. Duk in ya rigata tashi daga bacci da karatun alqur'ani ya ke farkar da ita, sometimes da kissing yake tashin ta har saita farka, saboda dadin da takeji Yasa itama ta dinga tashin shi ta yadda shima ya ke tashin ta cikin salon soyayya.. rayuwar farin ciki da jin daɗi su ke yi, sun sangarta junan su, gatanta kansu su ke yi kamar ran su, One week sun kulle kansu a cikin kurkukun masoya ba shige ba fuce, abun da ba zata ta6a mantawa da shi ba arayuwar arayuwarsu shine daren daya kar6i budurcin ta, da kuma kyautar bazatan da yayi mata a washe garin ranar, saboda yaji dadin faranta masa rai da ta yi ne yasa ya bata kyautar Black card with A brand new Mercedes-Benz S-Class and A brand new BMW X5, ita kadai, Aranar kukan farin ciki ta dinga yi masa, sai da takai ga shi ya koma yana lallashin ta. Tun ranar da Taj Ya hana Benazir zuwa gidan Unaisah lokacin da ta kira su a daren auren ta, Ya fayyace mata komai game da wanda Unaisah ta aura, tsantsar al'ajabi ya kamata, tayi murna Har kukan farin ciki sai da tayi saboda murnar Unaisah ta auri za6inta, mutumin da take ta hauka akanshi ya rayu, da tana ta jin fargaban Kada Owais Yaga zanan tattoo dinta amma da taji cewar mamallakin sunan ne ta aura sai taji hankalinta ya kwanta bata da sauran damuwa. A bangaren Batool, Sai da ya rage saura Kwana biyu dinner din auran su, aranar abi dinta da mommynta suka kirata a falo suka zauna tare da fayyace mata game da bayyanar dan uwansu Danish da kuma auran shi da Unaisah harma da Auranta da aka daura tare da Owais, Tsabar rudani da al'ajabine yasa ta kasa furta kalma, ta razana da jin Danish yana araye tsawon lokacin nan yana tare da Iyayen sa, kuma ta ruɗe da jin cewa Yaya Owais mijinta ne, farin ciki biyu a lokaci ɗaya, jin abun tayi kamar a mafarki wai ta zama matar dg Owais, nan Ta ke ta fashe da kukan farin ciki, ta durƙushe kan floor ta yi sujudusshukur. Sam bakinta kasa rufuwa yayi saboda zunzurutun farin cikin daya cika zuciyarta, kamar wadda akayima albishir da gidan Aljanna, Ummi da Shureim sun ji dadi da ganin yadda ta nuna farin cikin ta, dama burinsu ne su faranta mata rai, sai da takaiga su ne suka dinga lallashinta don tayi shiru ta daina kukan, Ummi ta soma zolayarta da cewa yanzu sai hankali ya kwanta, tun da ta auri muradin ranta, qiyamul laili tayi aiki, yanzu sai ta daina kishi da yar uwarta, tun da bata aurar mata miji ba kowa da nasa. ko da jin wannan maganar ta Umminta tana kuka ta zarce da dariya, suma suka kama yin dariya, sham ta shafa'a ta daka tsallan farin ciki, da taga sun saki baki sototo suna kallon ta da murmushi akan fuskokinsu saita watsa da gudu ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta faɗa kan gado cike da farin ciki take tariyo abin daya faru a tsakanin da chief, dama saida tayi mamakin nemanta da tayi saboda tasan shi din mutunne mai tsoran Allah ba zai iya aikata abin da zai sa6ama mahaliccinsa ba, yanzu tagane jarabata yayi saboda yasan matarsa ce ita, cikin sanyin murya ta furta Am sorry My husband duk da ko a lokacin banyi maka mummunan zato ba, bansan kana sona ba Ya Owais, meyasa ka boye mi ni, ka barni da ciwon sonka! ka hanani bacci ka hana zuciyana sukuni, amma tun da ka aure ni bani da sauran damuwa, naji dadi da Allah ya amsa addu'ar dana daɗe inayi akan ka, In sha Allah zan zama mata tagari a gare ka, zan yi maka biyayya sau da ƙafa... " ita ka ɗai ta dinga sambatu cikin nishaɗi da annushuwa. A yammacin ranar da ana saura kwana ɗaya ayi dinner.. Batool tana saman darduma ta kudundune kanta a cikin hijab ɗinta, daga sallame sallar La'asar bacci mai ɗan karan daɗi yayi awon gaba da ita,tun dazu take ta sharar bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sautin ringing din wayartane yayi silar farkawarta ba dan tagaji da baccin ba, mikewa tayi zaune tana miƙa da hamma cike da kasala ta tashi Tsaye ta dauko wayar idanunta biji biji take kallon screen ɗin ko da ganin sunan Heartbeat nan take ta wartsake, jikinta na 6ari tayi picking call din ta kara a kunne kamar tana agabasan, ta nutsu ta zauna daga gefen gadon ta.. "Assalamu alaikum, yaya Owais barka da marece, ya kake? Ina wuni? Ya Aunty Nazli" On the Other hand taji ya furta"wa'alaikissalam my baby girl,Alhamdulillah, muna lafiya, ina fata kema haka" "Eh," ta bashi amsa a takaice.. "Inason ganin ki, zanzo after magrib.. " zare idanu tayi cike da zumudi tace"toh, shikenan sai kazo" bayan ya katse kiran, ta miƙe tana rawar murna ta tube hijab din jikinta ta jefar kan gado,jallabiyane a jikinta da sauri ta shige toilet, mintuna ƙalilan ta fito ta nufi dressing mirror, ta shafe jikinta da lotion din ta, saida ta gama shafe shafenta sannan ta dauko Atampa riga da skirt ta saka a jikinta tana gama sawa ana Kiran sallah magrib, hijab dinta ta mayar tare da kabbara sallah bayan ta gama taci gaba da shiryawa,tana cikin daura kallabi ya kira yace gayanan a waje ya iso da sauri ta qarasa daure kanta da dankwalin, gyalen ma a kafada ta yarfa shi, bayan ta saka high heels a kafarta, ta koma gaban mirror ta shafe jikinta da humra mai ƙamshin gaske.. Cike da rawar jiki ta fito daga dakin, ganin babu kowa a falon yasa ta nufi bedroom din abie dinta don ta fada masu game da zuwan yaya Owais, har takusa isa ta dakata tunawa da basu nan, abi dinta tun da ya fita office bai dawo ba, Ummi kuma ta tafi gidan Aneelerh, kuma shi zai biya su dawo tare.. Tunawa da cewa mijintane Yazo ba wani ba, yasa ta yanke shawarar fita tasan ko su ba zasu hana ta je gurinsa ba, duk da hakan saida ta turama ummi sako ta waya.. DG OWAIS Yana a zaune a driver seat na motarsa, ya jinginga kansa jikin headrest, sanye yake da riga da wando na voile launin dayafi so, Blue sky, ya lumshe idanunsa sam baiga tafowarta ba, sai dai yaji motsin buɗe Cardoor ɗin.. A hankali ya buɗe idanunsa akanta, yayin da take shigowa ciki, zama tayi saman seat tare da sunnar da kanta kasa cike da jin kunyarshi batare data furta kalma ba.. Tayi mashi kyau a cikin atampa ya danyi mamakin yadda ta amsa kiranshi cikin sauri batare da jin shakkar zai iya maimaita abun da yayi mata rannan.. Jin yayi shiru bai motsa ba, yasa ta dago da idanunta da niyar ta dube shi, kaitsaye suka shiga cikin nata, har saida taji gabanta ya faɗi saboda kyawun da yayi mata.. "Kin san meyesa na kira ki"? Girgiza kai tayi"a'a" "Okay, Unguwa nakeso ki rakani, zakije"? da sauri ta jinjina ma shi kai.. Da mamaki ya danyi shiru yana tunanin meyasa ta sake da shi? Kwata kwata bai kawo ma ransa tasan komai game da kasantuwarsa mijinta.. key yayi ma Motar, yayi reverse ya fuce daga gidan, yana driving tana satar kallon shi, komai nashi burgeta ya ke yi, kyawawan idanunsa, dogon hancinsa, karamin bakinsa, uwa uba yalwatacciyar sumar kan shi maikyau da santsi kamar ta jinjiri.. Sarai yana lura da irin kallon da ta ke yi mashi, ya yi kamar baisani ba, don ya bata damar da zata ƙarewa mijin nata kallo.. Wani katafaren Bridal boutique su ka je, bayan yayi parking din Motar, suka fito tana ta kallon katafaren store din, duk da batasa dalilin zuwansu ba, amma tanaji aranta siyayyar kayan amarya zaiyi, daga sunan Store din ta fahimci kayan amare suke siyarwa.. Tana tsaka da kalle kalle, batai aune ba, taji ya ruƙe hannunta a cikin nashi, wani shock taji, a rude ta saka idanunta cikin nashi har ya sanya mask akan fuskarsa saboda bayason a shaida shi yanzu mutane sun fara taruwa domin kallon shi.. Bayan sun shiga cikin Shop din, Bridal Consultants din dake agurin suka tarbe su tare da yi masu barka da zuwa, Dg ya faɗa masu Bridal gown ya ke son gani, daya daga cikin ma'aikatan ce ta kaisu sashen bridal gowns, kala kala masu kyau da tsada gasunan birjik jikin hangers, yana lura da yadda Batool ta ruɗe cike da mamaki take kallon rigunan tana ɗan zazzare brown eyes ɗin ta.. "Ki za6i wadda kikeso" ta ji ya furta, aruɗe ta nuna kanta da yatsa"Ni"? Jinjina mata kai yayi batasan sa'adda ta saki murmushin farin ciki ba, "Ki taimaka mata ta za6i wadda zatayi mata daidai" ya fada yana duban ma'aikaciyar wadda keta kallonsu tana ji aranta kamar tasan muryar hamshakin mutumin.. Ruƙo hannun Batool tayi a cikin nata, takai ta gaban wasu tsadaddun Bridal gown Limited edition, tana tsaka da kallon su Unexpected ta hango irin Bridal gown din Unaisah banbancinsu kaɗanne Hannunta na kerma ta soma shafa rigar. Ganin kamar tayi matane yasa matar tace"kina sonta"? Jinjina kai tayi"Eh" "Kin iya za6en riga, tana da kyau da tsada, kuma zata dace da ke.." ta faɗa da fara'a akan fuskarta ta curo rigar daga jikin hanger"muje na taimaka maki ki gwada rigar a jikin ki" ta faɗa tana nuna mata ke6ataccen gurin dake a kewaye da dogayen labulaye Amsawa tayi da toh, ta dan juya tana neman yaya Owais, can ta hango shi a zaune kan Arm Chair, ya kara waya a kunnansa.. Bayan sun shiga bayan labulayen, agaban wani katafaren madubi, suka tsaya, ɗayan wurin da ake shiga ta nuna mata ciki ta Shiga ta sanyo rigar saidai ko zip ta kasa zugewa, sai sunne kanta qasa takeyi matar ta fahimci kunya gare ta, ita kanta saida ta jinjinama kyawun surarta, da taimakonta ta qarasa gyara mata gown din, Tabarakallahu ahsanul khalikin yadda kasan saboda ita aka ƙera rigar, tayi mata daidai, ta ƙara fito da kyawun surarta, tun da ta tsaya gaban madubin bata motsa ba, bakinta yaki rufuwa saboda farin ciki, Matar sai yabo kyanta takeyi tana santin ta. Har tambayarta tayi wanene mijin da zata aura? Ko mutumin da suka zo a tare ne"? Tace mata Eh. Ta kuma tambayarta wanene shi? Tana ji kamar tasan shi tun da taji muryarshi, amma dai yana da arziƙi sosai shiru batool tayi batare data tanka mata ba, tun da ta fahimci irin matan nan ne da basu gani su ƙyale masu ɗan banzan ɗumi da son tsegumi.. Duk da ta shareta bata daina yi mata surutu ba, taci gaba da cewa"ai daga gani yana son ta sosai, dama mata irinsu masu kyau maza basa gajiya da kashe masu kuɗi, can kuma tace amma dai ita ba jinsin bakar fata bace ko"? ta fada tana jiran amsarta, fashewa da dariya Batool tayi hakan ba karamin mamaki yaba matar ba, juyawa tayi ta nufi curtains din da niyar ta fuce don ta gwado ma yaya Owais rigarta, tana kokarin dage labulen Unexpected ta gan shi yayin da ya ke kokarin shigowa ciki, ya gaji da jiranta yaji shiru basu fito ba. From head to toe yabita da kallo a hankali sai yaga gaba daya ta sauya mashi, tayi matuƙar yi mashi kyau a cikin bridal gown.. "Masha Allah" taji ya furta, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, Unexpected taji ya daura tafinsa asaman waist dinta ya janyota ta fado kan jikin shi, duk tabi ta dabarbarce, sam sun shafa'a sun manta da staff din dake a gurin, sai kallonsu takeyi gwanin ban sha'awa.. Hugging dinta yayi tighly,suka nutsu suna shakar kamshin juna cikin shauƙi.. Hannunsa ya daura saman sumar kanta ya soma shafata a hankali, batare da ya iya furta kalma ba, ba karamin kyau tayi mashi ba, Dakyar suka raba jikinsu daga na juna, bayan ya biya kudin rigar da bank card dinsa, Batool ta cire taba staff din ta sanya masu a cikin shopping bag, ita kuma ta maida atamfarta, ruko hannunta yayi a cikin nashi suka fito, bayan sun shigo mota, yaja suka nufi Estate dinsu.. Bayan motarsu ta karaso cikin estate din, yayi niyar ya mayar da ita gida, amma sai ya tsinci kanshi da juya sitiyarin mota, Ya nufi gidansa, kwata kwata bata tanka masa ba, da taga ya canza hanya, yanzu bata jin fargaban koma ina zai kaita tun da tasan mijinta ne halak malak, A ɗayan duplex din Gidan inda ya kawota a daren auren su, nan ya shigo da ita, ya ruke hannunta a cikin na shi suka nufi ciki still tana jin shakkar shi da fargaba amma ba kamar na ranar ba. Lokacin da suka shiga falon, yana a gaba tana abiye da bayan shi, zama suka yi saman Sofa daya, ta ajiye shopping bag din akan C-table. Ta yi shiru tana jira taji me zaice, batare data dube shi ba. Tsawon mintuna yana daddana wayar sa kamar ya manta da zamanta a falon.. Bacci ta fara ji, ta soma gyangyaɗi a karshe ta langwa6e kanta jikin Sofa, tuni bacci yayi awon gaba da ita.. "Batool ina fata sun faɗa maki.." bai ƙare maganarba, ganin tana bacci, shiru yayi yana kallon ta, yadda take fitar da numfashi cikin nutsuwa ba karamin jan hankalinsa ya yi ba, lura da takurar da tayine yasa shi yanke shawarar maidata kan gado, mikewa yayi a hankali ya sungumeta kamar jinjira Ya nufi Bedroom ɗinta, bayan daya shiga Ya kwantar da ita gadon,harya miƙe zai fita yaji wata irin kasala ta baibaye jikin shi, ya dingajin kamar bacci, baisan sa'adda Ya haura kan gadon Ya kwanta daga gefen ta ba,janyota yayi tare da rungumeta a kirjin shi, yana jin tsantsar son kasancewa da ita, sa'ilin data farka taganta a jikin shi a lokacin harya nutsa cikin baccinsa,kasa mikewa tayi, idanunta akan shi, ta nutsu tana kallon kyakkyawar fuskar shi, a hankali ta shafa sajen shi, kafin ta daura hannunta saman sumar kan shi da take marmarin ta6ata, da yake taga yana bacci shiyasa ta saki jiki ta dinga shafa sumar kanshi mai santsin gaske, a hankali ta sauke idanunta akan soft full lips dinsa, sun ciza launin su pink, sun dan bushe, ta kasa yarda Mijin tane yaya Owais! Har yanzu jin abun takeyi kamar a mafarki saboda al'ajabin ta yadda Allah ya juye al'amari ya mallaka mata muradin ranta.. Kallonsa da takeyi ne ya haifar mata da jin matsanancin sha'awar shi, zufa ta soma jike jikin ta, zuciyarta ta dinga azalzalarta akan ta sumbace shi tun da bacci ya ke yi, tsautsayine yakai bakinta saman nashi, ta haɗe lips dinta da nashi, ta fara licking dinsu da harshen ta kamar ta samu zuma, tun tanayi a hankali harta koma tana sucking din su sosai, Numfashinsane ya soma sauyawa alamar yanajin dadin abunda takeyi masa, tana kokarin raba bakin ta daga nashi, Unexpected taji Ya damƙi waist dinta da hannunshi, a firgice ta zare idanunta, tayi zaton cikin magagin baccine yayi mata hakan, tana kokarin raba jikinta da naga nashi Unexpected taga ya buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur cike da kasala ya ke kallon ta, cikin rawar Murya ta furta"ya Owais dama idonka biyu? Ko bacci ka ke yi"? Lumshe idanun shi yayi a hankali ya sake buɗe su kan fuskarta, da wata irin kasalalliyar murya taji ya furta"ki cigaba da yi min abun da kikeyi min, inajin daɗi sosai" gabantane Ya faɗi tana zare ido tace"am sorry.. bansan meke damuna ba, na ruɗe.." bata kare maganarba ya katse ta da cewa"karki ji kunyar nuna min soyayya, ni mijin ki ne, muharraminki.." lumshe idanunta tayi taji dadin furucin da yayi, yanzu ta fahimci shima yana jin abun da ta ke ji a game da shi.. Da kanshi ya soma yin undressing ɗinta, bayan daya kammala Ya tu6e kayan jikin shi, Ya janyo duvet Ya lullu6e su a ciki, gaba daya ta nemi kunyarsa da ta ke ji ta rasa, gaba ɗaya suka tsunduma cikin faranta ran junan su, almost Hour basu rabu da juna ba. ~______________________________~ A ranar Dinner din auran su anyi gagarumin Shagalin da ba'a ta6a yin makamancin shi a ƙasar ba, dangin Amare da dangin angwaye gaba daya suka hallara kwansu da kwarkwatarta su a cikin Event hall din domin tayasu murnar auransu, a dakin Taron Omair yayi abun daya ba kowa mamaki, gaba ɗaya Ya bi yan uwansa Ex-prisoners Ya basu kyautar key din mota, tare da Gift cards na Hajjin bana, sunyi murnar da bazata misaltu ba, surukan sa ya gwangwaje su da kyautar Motoci tare da Gift cards na hajj, Ummi da Aneelerh da dr shureim harma da Danejo duk saida Ya basu kyautar motoci tare da Albishir din Hajjin bana, saboda Yasan Alkhairin Da Aunty Aneelerh tayiwa Angel dinsa tun da tana ƙarama, itama Danejo tun a prison Yasan da ita, lokacin da Unaisah take basu labarin taimakon da tayi mata, ita kuma Ummi mahaifiyar aminiyarsa ta kuruciya ce wato Batool, bazai ta6a manta kyautatawar da tayi masa musamman a lokacin da ya ke fama da lalurarsa ta rashin son haniya. aikuwa gaba ɗaya suka dinga yi mashi godiya tare da addu'o'in fatan Alkhairi shida amaryarsa, Sun yi Murnar da bazata misaltu ba, musamman yan uwansa prisoners sun yi mamakin arziƙin Omair din su, ba komai yafi masu dadi ba kamar kasantuwarshi a raye especially matan da sai a lokacin suka ganshi sunji dadi mara misaltuwa, lokacin da yake basu car keys din, fashe wa sukayi da kukan farin ciki saboda ba su zata ba, duk wanda ya ta6a taimakon Unaisah saida Omair Ya bashi kyautar Mota da hajj, kuma babu abun daya ragu na daga arzikin da Allah yayi ma shi, gaba daya kyauttukan daya basu cikin wadanda ya samu ne agurin Partyn da Emir Ya shirya mashi, bayan tarin kyaututtukan daya ba su, saida ya ƙara ma Taj da kyautar Private Villa anan cikin Abuja tare da Diamond cufflinks, na lu'u lu'un gaske, Gaba daya Ya kashe surukin nasa da farin Ciki, Taj har kusan Zubar da ƙwalla ya yi saboda dadin da yaji na yadda Danish Ya girmama shi fiye da kowa, Unaisah Taji dadin kyautatawar da yayi wa Family dinta, sai taji ta ƙara ƙaunarsa fiye da komai a duniyar nan. Bayan dinner din auransu da sati ɗaya, su ka fara shirye shiryen tafiya Honeymoon, su biyar suka tafi, Omair da amaryarsa Unaisah, Chief da amaryarsa Batool tare da Uwar gidansa Nazli, tun da suka tafi sai da suka shafe Watanni uku suna zagaye kasashe, daga cikin kasashen da suke je yawon buɗe ido ya haɗa da Canada, Korea, China, UK, daga bisani suka ziyarci saudi arab, sunyi rayuwar farin ciki da jin daɗi, sun more lokacin su, abubuwa da dama sun faru wanda ba zasu ta6a mantawa ba. kafin dawowar su Nigeria, wasu masoyan sun yi Aure, Arana ɗaya aka ɗaura auran, Sajeeda da zaid, dr Jazz da Faryat, Zeenatu da Mahboob, a inda sheikh imam Malik ya auri Hajiya sarah Kowa yayi mamakin yadda har suka fada tarkon son Juna, ikon Allah kenan Musa Ya saka masa da sharri yayin da shi kuma ya saka mashi da alkhairi, Ya aure matar sa, bayan haka Abie Ya auri Ummi mahaifiyar su Zahra, da amincewar Mamie, itace ma ta bashi shawarar ya aureta in dai yana son ta saboda su rufawa juna asiri, ba iya nan ba ma'auratan suka tsaya ba, shima sir mubarak ya auri Hajjaty, a inda Hajiya saratu ta amince da auran dan Uwanta kanin Sarauta dan sarkin Yarbawa wanda yasota tun da daɗewa tunma kafin ta auri Praven amma saboda batason shi a lokacin shiyasa bata amince masa ba amma bayan shari'ar Elders ya bayyana mata cewa har yanzu yana son ta, kuma ashirye yake daya aureta, in har ta bashi dama, da farko ta nuna kin amincewarta saboda aure ya fita aranta, tana da ciwon abin da praveen yayi mata, amma daga bisani da yayyanta suka shawarce ta akan ta aure shi tunda yana son, kuma bafa lallai ta samu wanda zai so ta tsakani da Allah ya rufa mata asiri kamar shi ba, dama tunfil azal shine za6in su, shi sukaso ta aura amma ta bijire masu a lokacin ta kawo nata za6in, A yanzu da suka nuna suna son ta auri dan uwan ta bata musa masu ba, ta daina kin bin umarnin su, bayan data amince akayi auren su, ta zama second wife dinsa. duk a cikin shekarar Ahlin Elders Suka aurar da mafi rinjayen matasan family ɗin, Kuma auren zumunci su ke yi a tsakanin su, saboda su rufawa kansu asiri don kuma su ƙarfafa zumuncin su, Alhamdulillah Allah ya azurta wasu ma'auratan da samun ƙaruwa, ta bangaren Chief Owais Uwargidansa Nazli ta haifa masa kyawawan Twins mace da namiji masu bala'in kama da shi, kamar yayi kakin Su, ya yin da Batool ta ke ɗauke da cikin sa. Zaki Ya samu ƙaruwa tare da Aneelerh ta Haifa masa kyakkyawar Jinjirarta mace, a inda Zahra Ta haifi kyawawan Twins maza, Zayn da Yan uwansa sunyi farin ciki sosai, Salsabeel da Matar shi Dr Yusrah suma sun ƙara samun ƙaruwar Ƴa mace, Cikin Ikon Allah Danejo da bata ta6a haihuwa ba tsawon shekaru abun na damunta, a lokacin baya har asibiti Taj ya ke kaita in ta matsa mashi akan tana son ta haihu, amma ko sunje likita ya bincika ta kamar kullum sakamakon ɗayane bata da matsalar Haihuwa, Taj yasha ya kwantar mata da hankali yace tayi hakuri suci gaba da yin addu'a in Allah ya nufa tana da rabon samun ya'ya, zata haihu ne in da rai da lafiya, a lokacin kwata kwata baya nuna damuwa akan rashin haihuwarta, saboda damuwar rashin ƴar shi Unaisah, Danejo tun tana damuwa har ta cire rai, sai da ga Bisani a ranar da Imam Ya kawo masu ziyara gidan, suna tsaka da yin fira a falon Danejo su biyu Shi da Taj, lokacin da Danejo ta shigo kawo mashi Abinci, Bayan ta gaishe da shi ta ajiye masu kayan abincin, cikin jin kunyar Imam ta nemi daya taya ta da addu'a tana fama da matsalar haihuwa, Kallon ɗaya sheikh Imam yayi mata ya fahimci tana da evil jins a jikin ta, wanda ita kanta bata sani ba, Taj ma bai ta6a sani ba saboda basu ta6a tashi a jikin ta, Bayan da yayi mata tambayoyi a amsoshin da ta bashi ya fahimci Aljanun sun daɗe a jikin ta, tun tana a rigarsu ta daji, kuma sune suka haddasa mata rashin haihuwa, nan take ya yi mata alƙawarin in sha Allah zai tayata da addu'a, sannan zai aiko mata da ruwan addu'a da magunguna, ya kuma rubuta mata addu'o'in da zata dinga yi, sannan ya gargaɗeta akan ta daina sakaci gurin neman tsarin Allah. bayan da Sheikh imam malik Ya kawo mata magungunan ta fara amfani da su ta kuma dage da yin addu'o'in daya rubuta mata, Cikin Ikon Allah ta samu warakar lalurarta, salin alin Iskar suka fita daga jikin ta, sai gashi ta samu ciki, har kukan farin ciki sai da ta yi, tsawon wata tara cuff Ta haifi Twins ɗinta mata masu kyan gaske kamar indiyawa, kamannin su sak da ita kamar tayi kakin su, Taj ya yi farin cikin da bazai misaltu ba, haka Benazir da Unaisah sunfi kowa ɗokin ya'yan Danejo, Suna son su sosai. qarin abin farin ciki! Benazir da ummi suma daga baya ba zato ba tsammani suka samu ƙaruwa kusan a lokaci daya Dan har sun fidda rai da qara haihuwa musamman Ummi saboda ita da kanta ta dinga shan kwayoyin da zasu hana ta daukar ciki tun lokacin da take karuwanci, sune suka jaza mata matsalar rashin haihuwa, amma daga bisani sai gashi cikin ikon Allah sun sake samun qaruwa, gaba dayansu ya'ya maza suka haifa, murna a wurin Unaisah da Batool kamar su zuba ruwa qasa susha suma sun samu ƙanne shaƙiƙai, Cikin yan shekaru albarkar ƴa'ƴa ta yaɗu a zuri'ar Elders sun ƙara yawa sun bunƙasa, ga arziki ta ko ina. ~__________________________🔥~ *EVIL FOREST🔥🥺* Wata irin ni'imtacciyar iskace ke kaɗawa acikin dajin mai dadin gaske. baka jin sautin komai saina kukan tsintsaye dana namun dawa dake hargowa daga can cikin dokar dajin. mata da maza na hango sanye da shiga ta fararen kaya a jikin su, cikin Dajin Evil forest, Suna a zazzaune saman korayen ciyayi, sun kewaye ƙabari da ke agaban bishiya, yayin da suka ɗaga tafukan hannayen su Sama suna yiwa mamacin da ke a cikin ƙabarin addu'a, idanun su cike tab da ƙwalla. daga bayansu, Isod Soldiers ne sanye cikin Combat Uniform dinsu, Hannayen su ruke da bindigu, sun kewaye masu yiwa mamacin addu'a domin basu kariya. Bakowa bane wadannan bayin Allahn face ex-prisoners da kuka sani, gaba dayansune suka ziyarci kabarin tsohuwa tamira wadda duniya ta naɗa mata suna( Mother of the prisoners) Salsabeel ne Ya jagoran ce su zuwa kabarin nata, bazai taba mantawa da inda ya binne mahaifiyarsa ba, da taimakon shaidar da yayi ma kabarin ya ci sa'ar gano shi, bayan da suka kammala yi mata addu'o'in, suka yanke shawarar shiga cikin dajin don su yi yawon buɗe ido, babu tsoro ko fargaba atare da su, saboda akwai sojojin dake tsaron su, su kansu suna da bindigunsu na kansu da suka mallaka bayan sun zama jami'an Isod, cikin nishadi suke kutsawa cikin dajin suna tafiya sunayin fira yayin da su ke tuna rayuwar da su ka ta6a yi a cikin shi saida su ka yi nisa a tafiyar tasu suka lura babu Mutun biyu a cikin su, aruɗe suka ci burki hankulan su atashe suka soma ƙwala masu kira da karfi"Sister Unaisah! Big bro! Garkuwa! Kuna ina ne! ina ku ka shiga ne"? Yadda suke ƙwala masu kira kamar maƙoshinsu zai 6alle, raba kansu sukayi gida uku wasu suka miƙi hannun dama wasu sukayi hagu yayin da wasu suka miki hanya, Gaba ɗaya suka bazama neman su a cikin dajin.. Duk Kiran da suke ƙwala masu kwata kwata ba su ji ba, suna acan saman Wata gabjejiyar Bishiya mai girma da faɗi, tana da yalwar rassa da Ganyayyakin da su ka yi mata rumfa, ba zaka taba gane akwai mutane asamanta ba, saboda rassan bishiyar da ganyayyakinta sun lullu6e su hasken rana ne kadai ya ke hasko su, wata irin ni'imtacciyar iskace ke ratsa fatarsu mai dadin gaske. yana a kishingiɗe saman wani ƙaton reshe na bishiyar mai faɗi, yayin da ta ke akwance saman jikin shi, ta ɗaura kanta a kirjin shi. Gaba daya tafukan hannayensa suna a daddafe da matashin cikin ta, wanda baifi wata biyar ba, sunyi kyau a cikin fararen kayan su fiye da ko da yaushe ga dukkan alamu bacci ne ya yi awon gaba da su, sunyi nisan kiwon da basa jin kira a cikin kunnan su. kwatsam wani giant snake Ya biyo jikin reshen da suke a kai, Ya durfafe su gadan gadan, Yana gab da zai hau kafar Unaisah, Omair ya farka daga bacci, nan take idanunsa suka gane mashi macijin, wani irin faduwar gaba Yaji, Yasan muddin Ya hau jikin Unaisah zata iya firgitar da zaisa ta fado daga kan reshen. Yana tsaka da tunanin yadda zaiyi da macijin, Yaji ta ambaci sunan shi "My Man.." hankali atashe ya dubeta a lokacin da take kokarin buɗe idanunta, kaitsaye suka shiga cikin nashi, murmushi tasakar mashi, kwata kwata bata lura da halin da yake a ciki ba, abun dayake ma zullumi kartayi motsin da zaisa macijin Ya sareta, Hamma tayi kafin ta rufe bakin yayi saurin hade bakinta da nashi, gaba daya ya kashe mata jiki ta kasa motsawa, kissing dinta ya shiga yi yayin da yake zare pistol daga waist dinsa a hankali, idanunsa akan macijin Ya saita kanshi, Ya daddage Ya sakar mashi alburushi a tsakiyar kan shi, ji ka ke daramm!!! Tsabar firgitar da ƙarar harbin da kunnuwana suka jiyo min ne yasa na gigice har bansan sa'adda Na saki alƙalamin da nake rubutu da shi ba. Alhamdulillah 🤩 🥳🥳subhanallah🤩, Masha'Allah🤩 La'ilaha Ilallah🤲, Allahu Akhbar 💖 THIS IS THE END OF KURKUKUN ƘADDARA 😭😭😭 All praise is due to Allah, the Most Merciful and Benevolent, for granting me the strength and perseverance to complete my novel, "THE PRISON OF DESTINY" Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai rahama mai jin kai, Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) Ina Godiya ga Ubangijinmu Allah subhanahu wata'ala, da ya bani tsawaicin kwana da lafiya da karfin gwiwa da juriyar kammala rubuta littafina na biyu mai suna 'KURKUKUN ƘADDARA" wanda na shafe tsawon shekara ɗaya da watanni ina rubuta shi, da daɗi da ba daɗi amma Alhamdulillah yanzu komai ya wuce, na ƙara shaidawa cewa sannu bata hana zuwa, kuma komai mai wuce wa ne arayuwar mu indai mu ka yi hakuri, Tabbas Ina Alfahari da baiwar da Allah ya bani ta rubuta littafin kurkukun kaddara fiye da littafina na farko kuma fiye da sauran littattafan da zanyi agaba saboda ya fita daban babu tamkar shi ko dan darussan dake a cikin labarin wanda ni kaina dana rubuta shi, na ilmantu, na fadakantu, na kuma nishadantu, nayi kuka tamkar raina zai bar gangar jikina saboda yadda labarin ya ta6a zuciyata inajin shi kamar True life story, bani ba hatta makarantar littafin sun shaida hakan. Ina fata littafin Kurkukun ƙaddara Ya zama Alkhairi a gare ni, Allah Yasa kowa ya amfana da littafin Kurkukun ƙaddara burina ne, 😍Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da yan'uwana da dukkan masoyana a duk inda suke a faɗin duniya🥰 kura kuren ciki Allah ubangiji ya yafe man🙏_ _*Gaisuwar ban girma da karramawa ga mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya, she is my first luv and my everything, kin gama min komai arayuwa, Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana, bazan iya misalta kyautatawar da kikayi min ba, Allah ne kaɗai zai iya biyanki, kin gama min komai, Allah yasa Aljanna ta zama makoma agare ki💘, 🤲✍️*_ _*Jinjina Ta Musamman Da Ban Girma Ga Uwar Masu Uba Hadda Marayu, HAJIYA KUBRAH, kada Ku manta gaba ɗaya Littafin Kurkukun Ƙaddara tun daga farko har ƙarshen shi sadaukarwa ne ga Mommy Kubra, Jarumar mace, mai daraja da ƙima, saboda Ita yasa na jajirce na tsara labarin ya yi daɗi yayi ma'ana saboda inaso ya zama abun tunawa da ni da alfahari a gare ta, kin gama min komai arayuwa Mommy, goyan bayanki, tallafawarki, shawarwarin ki, da ƙwarin gwiwar da kike bani sun kasance ƙarfin kuzari na, Ina alfahari dake a koda yaushe kuma bazan ta6a mantawa da halaccin da kika yi mana arayuwa ba, Allah ya Kara Daukaka Darajarki Fiye Da Tunanin Mai Tunani da ke da Ahlin ku, Allah Ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada, Allah ya shirya maki zuri'a, Allah yasa ku gama da duniya lafiya Allahumma Amin 🤲*_ _*YABON GWANAYE YA ZAMA DOLE🤩JINJINA TA MUSAMMAN DA BAN GIRMA A GAREKU YAYYE NA NA KAINA DA BABU KAMARKU, ABUN ALFAHARI NA 🥺🥳🤩*_ AUNTY ZEE DA MUNAH BATURE MY P.E. haƙiƙa kunyi namijin ƙoƙari gurin gyaramin rubutuna tun daga farko har ƙarshe baku ta6a gajiyawa ba, kun nuna min kauna, kun bani goyan bayanku da karfafamin gwiwa aduk lokacin dana nuna na sare, kun bani shawarwari masu muhimmanci da suka amfane ni agurin rubuta littafina, Kun tsaya min tsayin daka don ganin rubutuna ya yi kyau, wallahi ni bazan iya biyanku kokarin da ku ka yi min ba, sai dai in cigaba da yi ma ku addu'a Ina son ku ina kaunar ku 🥺🤲 _*JINJINA DA BAN GIRMA 🤩🥳😍 ga masoyana na asali masu sayan book dina, Dumbin gaisuwa da fatan Alkhairi zuwa gareku a duk inda kuke a fadin duniya, members Na Paid grps ɗina*_ _*Kurkukun Ƙaddara paid Takun Karshe Posting section Prison Of Destiny kurkukun Kaddara Facebook Prisoners Posting section*_ _*bayin Allahn nan kunyi hakuri dani, kun jure bibiyana har zuwa karshen littafina, kun jure kar6ar uzururrukana, nasan kun wahaltu gurin bibiyar littafina musamman wadanda na fara da su tun farko, don haka ina mai ƙara baku hakuri ga duk wanda na 6ata ma rai yayi haƙuri ya dubi girman Allah da manzonsa ya ya fe mun, badan komai ba sai don mu rabu lafiya, ba lallai mu sa ke haɗuwa a wani littafin ba, tun da rayuwar mu a hannun Allah ta ke, bansan ko zan kai lokacin da zan ƙara rubuta wani littafin ba, ina sonku ina kaunarku, ina jin dadin Comments dinku, ina rokon Allah daya saka maku da mafificin Alkhairinsa, Allah Ya sada fuskokin mu gaba daya agidan Aljanna, Alfarmar Annabi Muhammad SAW🤲✍️*_ Special Thanks To My Teammates Aunty Zee Lalu, the Writer Of Asanadin Makwabtaka Oum Arwan, Writer Of Auren Katin ƙasa and Matar Taj Hafsat Amjad writer of Captain Janan da sauran su _*Karku bari abaku labari, ga wadanda basu karanta books dinsu ba, Ina baku shawarar ku hanzarta mallakar naku, saboda Labaraine da babu kamar su, kunsan Team dinmu akwai baiwar tsara labari, kuma salon mu na daban ne, we're new writers but da ƙwarewar mu muka fara rubutu, Readers sun shida hakan 🤩🔥✍️*_ _*DAGA ALƘALAMIN HAFSAT BATURE MUHAMMAD (BOSS BATURE) WRITER OF ABBAN SOJOJI AND KURKUKUN ƘADDARA🔥✍️*_ *SINCE 2023 TO MON, JAN 20, 2025*