okay MAJOR ya sake ruƙo hannunsa tare da cewa"Sorry Sir! Nasan Abun da ciwo, Amma mu gode ma Allah da muka ƙaraso akan Lokaci batare daya kai ga Cutar da ita ba" huci kawai yake yi yana kallonsa da idanuwansa waɗanda suka canza Launi bakomai yake tunawa ba fa ce yarda Baba alamu ya yayyaga ma Husana rigar jikinta, in ya tuna wannan abun zuciyarsa Tafarfasa take yi saboda 6acin rai, muryar major ce ta katse shi da cewa" Allah ya huci zuciyarka yakamata mu hanzarta barin gidan gonar nan domin muyi gaggawar kai su asibiti, Jin hakan yasa shi yin saurin zura hannu tare da curo wayarsa daga aljihun wandonsa, nan take ya shiga camera tare da saita gawar baba Alamu ya ɗauke ta hoto da kyau, bayan ya ammala ya mayar da wayar cikin aljihun sannan ya kalli Major yace "Duba min aljihun wandonsa kona rigarsa kaga ko za'a samu waya," Cikin hanzari Major ya zura hannunsa cikin aljihun baba alamu daker ya lalubo wata ƙaramar waya nokia, taji duniya don bala'e batteryn wayar saida aka sanya robali sannan aka ɗaure shi baya cikon da akayi masa,duk ta rakwakkwa6e wayar, "Sir ga wayar," ya faɗi tare da miƙa masa, bai kar6a ba bin wayr yayi da kallo kafin yace "Major cewa nayi ka ɗauko mun wayarsa ba wannan abun ba," ya faɗi yana nuna wayar hannun major ɗin Ƙiris ya rage major ya fashe da dariya saboda ya lura cewa Boss Man ɗin nasa baya cikin hankalinsa, "Sir wannan itace wayar, ka duba da kyau ta tsufa ne sosae shiya sanya ka ganta hakan," Ajiyar zuciya ya saki tare da cewa "Keep it in ur place, zan neme ta," yana faɗin hakan yakama hanyar fita daga ɗakin, Muryar Major ce ta dakatar dashi da cewa "yalla6ai rigar fa? zan iya ɗauko maka ita," ya tambaya yana jiran amsa , Bai amsa mashi ba ya fuce kawai cikin sauri major ya ɗauko Jacket ɗinsa da yayi wurgi da ita sannan ya fito daga ɗakin ruƙe da ita a hannunsa a lokacin har yakai wurin motarsu da suka zo da ita, kai kana ganin yarda sukayi parking ɗinta kasancewa a tsiyace suka shigo da ita, domin kuwa har katakon ƙopar gidan gonar duk sun tarwatsa shi, Cikin sauri Major ya rufa masa rigar abayansa shi kuma ya ƙara gyarata ajikinsa sannan ya zuge zeep ɗinta, buɗe motar yayi sannan ya shige back seat ɗin shikuma major ya shige driver seat sannan ya tayar da motar yayi baya² da ita kafin ya karya kwana ya fito daga gidan gonar da gudun gaske yake driving ɗinsu, Sam ya gaza ɗauke idonsa akan hosana dake langwa6e asume kusa dashi, duk gashin kanta ya gama tarwatsewa dama a hargitse yake sai kuma aka ƙara hargitsar dashi, duk ya rufe mata fuskarta, lumshe idonsa kawai yayi har lokacin yana mamakin yarda akai wannan Lamarin ya afku amma yana da tabbacin cewa major yana da masaniya akan hakan," adai dai hanyar da baba alamu yayi wurgi da jahad Major yayi parking ɗin motar, cikin sauri ya buɗe motar ya fito gabansa ne kawai ke faɗuwa tsoranshi kar ace ta mutu, wani saurayi ne zuƙunne a inda jahad take yashe, da alama ba ƙaramin taimako yayi mata ba, domin kuwa ya ciccire mata ƙayoyin da suka soki ƙafarta sannan kuma yayi amfani da Mayafinta wurin kekketa shi izuwa kashi uku, ya ɗaure mata goshinta sannan kuma ya naɗe mata ƙafafunta dake zubar da jini, Fitowa major yayi shima yana kallonsa, "Major karfa ace yarinyar nan ta mutu," ya faɗi a tsananin tsorace "Sir she's still alive, suma ce kawai," ya bashi amsa, saurayin yace"yalla6ai tana buƙatar taimakon gaggawa saboda jinin dake bleeding a goshinta da kuma tafin ƙafarta," Cikin tsananin tashin hankali ya ƙarasa tare dasa dukkan hannayensa ya tallabo JAHAD ya ɗaukota da sauri Major ya buɗe masa motar ya shigar da ita a kusa da Hossana ya zunar da ita a sume, sannan shima yashiga motar, zuge glass ɗin yayi tare da kallon saurayin yace"Ka shiga mu tafi tare," saurayin yace"yalla6ai machine ɗina fa"? tunkan ya bashi amsa major yayi saurin cewa"daraban kayima arziƙi ƙulli ana maganar arziƙi wake ta wani machine"? Jin haka yasa saurayin tasowa sai da ya bari major yashiga, sannan shima ya shiga kusa dashi ya zauna, rufe motar su kayi sannan da gudu suka bar dajin suka miƙi santalelen titin da zai sadasu da inda suka dosa Kallonsu kawai yake yi ransa na ƙara ƙuna ganin irin jigatar da yaran su kayi yaran daya kai Amana, sam kwalwarsa ta rikice yarasa gane ma wannan lamarin ba komai yake son ji ba face yarda akai har tsohon can ya ɗauko yaran izuwa cikin gidan gonarsa don ya lalata rayuwarsu! taya akai ya fito dasu daga gidan general Ishaq? taya akai Aunty laila tayi gangancin da har wani zaizo ya ɗauki twins ɗinsa? da sa hannun wa akayi wannan ƙulla-ƙullar, tabbas kowaye bazai ƙyale shi ba, muddin ya gano gaskiyar lamarin!!, ya ƙarasa zancen zucin nasa adai² lokacin da suka ƙetaro Abuja, kai tsaye suka wuce dasu izuwa katafaren asibitin SGR, ***************SEHRISH*************** Sam bata gane mai ake koyarwa acikin class ɗin saboda wata irin yunwa dake jibgarta ga wani irin bacci da take ji, sai faman hamma take yi tana lumshe ido, Wuraren ƙarfe tara da rabi, time ɗin break yayi gaba ɗaya ƴan class ɗin sai fita suke yi don suje cin abinci, Sehrish na kwance saman desk ɗin gabanta sai faman sharar bacci takeyi, juyowa Amrish tayi daga seat ɗinta tana kallonta, murmushi ta saki tare da sa hannunta taɗan bubbigi bayan sehrish tace "Get up baby ! time ɗin break yayi, yakamata mu fita," daker sehrish ta buɗe ido tare da ɗago kanta daga saman desk ɗin tana kallonta biji², miƙewa Amrish tayi ta fito daga seat ɗinta, sannan ta ruƙo hannun sehrish tana cewa"Get up mana Let's go,ko bakya jin yunwa ne"? ta tambaya tana kallonta, miƙewa sehrish tayi tare da biyota suka fito daga Class ɗin gabanta nata faɗuwa tsoranta kar ace siyen abincin zasuyi don ko sisi bata fito dasu ba, babu wanda ya bata kuɗi, saukowa sukayi daga saman benen duk inda suka bi sai an samu wanda zai yi ma Amrish magana, kuma yawanci akan Sehrish suke tambayarta ko ƴar uwarta ce, sai dae kawai tace musu eh, saboda tasan son jin gulma ne kawai, Hanya suka miƙa bada jimawa ba suka ƙaraso Lunch room ɗin makarantar wurin cin abincinsu, lokacin da suka shiga wurin mamaki ya kama sehrish ganin ɗalibai aciki kowa zazzaune saman dining tables masu mazaunin mutun 4, kowa wanne gabansa cike shaƙe da abinci sai ci suke yi, Ruƙo hannunta Amrish tayi adai² wani tebur da bakowa tace ma sehrish tazauna sai faman zare ido take yi gabanta na faɗuwa tsoranta kar ace tabada kuɗin abinci, "Me kike so na amso mana muci"? Amrish ta tambaya tana kallonta daga tsaye, zuru sehrish tayi tana tunanin yarda za tace ma Amrish bata da ko sisi,' "Kin yi shiru baki ce komai ba"? Amrish ta tambaya a ƙagare, murya na rawa Sehrish tace "Ni bana jin yunwa, a ƙoshe nake," Cikin mamaki amrish tace "but alamu fa sun nuna cewa kamar kina jin yunwa? Yakamata ko Coffee ne kisha taya zaki zauna da yunwa acikin ki"? sehrish tace"kada ki damu bana jin yunwa ne kawai," jinjina kai amrish tayi tare da cewa "its ok bazan takura maki ba, tunda kince bakya jin yunwa, ni bari naje na amso abunda zanci," tana faɗin hakan ta wuce wurin masu zuba masu abincin, ɗagowa sehrish tayi tana kallon students ɗin dake zazzaune suna faman cin abinci hankalinsu akwance, haɗiyar miyau tashiga yi ganin yarda suke Cusa pancakes da zuma abakinsu, sunnar da kai tayi gaba ɗaya tarasa yaya zatayi ga yunwa tana ji amma tana tsoran taci musu abinci ba kuɗin biya, tana cikin wannan tunanin sai ga Amrish tadawo hannunta ɗauke da plate guda biyu da murmushi afuskarta, ta ajiye su saman table ɗin sannan ta juya ta koma domin amso masu abunsha, Zuru sehrish tayi tana kallon plate ɗin mai ɗauke da banƙararriyar kaza ta gasu sosai hada ƙaramar knife wadda mutun zai yanka yaci, ɗayan plate ɗin kuma Snacks ne acikinsa shaƙe, runtse ido tayi tana ji tamkar takai ma plate ɗin hari, sai faman cixon la66a takeyi, dawowa Amrish tayi hannunta ruƙe da Laca sera mai sanyin gaske roba biyu, wuri tasamu tana fuskantar sehrish tazauna tana cewa "Wai haryanzu kina akan bakan ki na ba zaki ci komai ba"? tun yanzu zamu fara haka dake? ɗan murmushin yaƙe Sehrish ta saki tare da cewa "ba haka bane just bana jin yunwa ne shiyasa," ta faɗi tamkar zatayi kuka, Ido ya gani rai naso, Murmushi kawai Amrish tayi kafin tasa hannu ta ɗauki ƙaramar wuƙar dake ajiye saman kazar tashiga yankar naman tana ci, Ƙiris ya rage sehrish tasaki miyau saboda tsabagen kwaɗaituwa da tayi cikin sauri ta gyara natsuwarta gudun kar tayi abun kunya agaban sabuwar ƙawarta, Muryar amrish ce ta katse ta da cewa "Ko lemun ba zaki sha ba"? Cikin sauri tace"eh a ƙoshe nake," giɗa kai tayi sannan taci gaba da cin abunta, suna cikin zaman nan sai gasu Naja'at da parveena sun shigo, kai tsaye wurinsu suka nufa suka samu wuri suka zazzauna, Naja'at tace "Wlh da wata irin yunwa na fito Class ɗin can, sam bana gane ma karatun, dama can nifa ba gane math nake ba,' tayi maganar tare da sa hannu ta ɗauki robar lacasera tare da buɗeta ta kwafa abakinta tana kwankwaɗa, hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin tashanye mata lacasera ɗin da Amrish ta kawo masu, Ana cikin haka parveena ta tsoma hannu suka cigaba da cin roasted chicken ɗin da Amrish ta kawo masu, kafin kace mai tuni sun kwamushe komai, duk tana zaune tana faman haɗiyar yawu, sai da suka kammala sannan ma suka lura da ita, parveena tace "Au! Wai dama Yarinyar nan tana a wurin nan? Yo aini yunwa tasa nagaza gane ku nawa ne zaune a table ɗin muka tarar," ta faɗi da mamaki Naja'at ma tace"ko ni ban lura da ita ba, sai da kikayi magana Allah, sannu ko? Meyasa ke bakici komai ba ne," Tamke fuska sehrish tayi rai a6ace tace "bana jin yunwa," jinjina kai su kayi atare naja'at tace "halan kinyi breakfast dayawa ne a gida"? A ƙule sehrish tace "Bansani ba," acikin zuciyarta tayi maganar a fili kuma tace "eh," daganan suka ci gaba da firar su har Parveena ta ƙaro masu abincin duk tana zaune suka zauna suka lamushe suka bar rishi da tanɗar baki, da lokacin komawa Class yayi kowa ya wuce Ajinsu naja'at da parveena class ɗinsu ɗaya don haka suka wuce atare, ita kuma tabi Amrish izuwa nasu Class ɗin, Sehrish ba ƙaramin jiki taji ba, saboda azabar yunwa har wani jiri take gani, dishi² ta runƙa gani a idonta sam batasan me aka koya masu bama, Lokacin da suka taso daga school tunani ta soma yi wa zai zo ya ɗauke ta, ga school bus tashigo cikin makarantar amma tsoranta kar ace kuɗi za'a biya,tsayawa tayi hannunta ruƙe da school bag ɗinta sai faman lullumshe ido take yi, suna cikin tsayuwar nan sai ga drivern Amrish ya iso, sallama tayi ma sehrish sannan ta shige cikin motar suka tafi, Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin sai zuwa ake ana kwashe sudents ɗin ita gatanan tsaye zugudum babu alamar wani zaizo ya ɗauke ta, tana cikin wannan tunanin motar JUNAID tashigo cikin makarantar adai² inda take tsaye yayi parking ɗin motar tare da zuge glass ɗin motar yace "madam muje ko," ajiyar zuciya ta saki ba ƙaramin daɗin zuwan shi taji ba, buɗe motar tayi tashiga sannan yaja motar suka fita daga makarantar, Miƙar hanya yayi dasu yana cikin driving ɗin yaji sehrish ta faɗo masa a kafaɗarsa ta langwa6e, saboda shock ɗin daya ji har saida yaɗan ci burki a tsakiyar titin, aza idonsa yayi akanta, wani irin wahalallan bacci ne ya ɗauke ta batare da saninta ba, shine ta faɗo masa a shoulder ɗinsa, gaza janye idonsa yayi akanta yadda take ta faman sharar baccin ta ba ƙaramin kyau tayi masa ba, ya jima yana kallon kyakkwawar fuskarsa, sam.ya manta cewa a tsakiyar titi suke, sai go slow suke haɗawa batare da saninsa ba, har sai da wani babban mutun yayi masa magana ta waje, sannan ya tashi motar yaci gaba driving ɗinsa cikin kasala, har suka ƙaraso gidan adai² parking space ɗinsu ya ajiye motar, sannan yajuya ya kalli sehrish tare dasa hannunsa ya shafa gefen fuskarta tare da ambaton sunanta"Sehrish mun iso gida fa, wake up pls ," ya furta yana kallon yadda take motsi da idonta alamun zata tashi, daker ta iya buɗe idonta tana kallon shi sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa, junaid yace "reesh kamar baki lafiya fa? Look at ur eyes fa sun janza kala, A kasalance tace "yunwa nake ji sosai banci komai ba tunda naje school, ga wani wahalallan bacci da nake ji," ta ƙarasa maganar tana faman yin hamma, har time ɗin suna acikin motar, Tun da tasoma magana junaid ya saki baki yana kallonta har sai da takai ƙarshen maganarta sannan yace "Kina nufin wai baki ci komai ba a school to saboda me? Ya tambaya yana kallonta Yamutsa fuska tayi tare da cewa "junaid ban fa da ko sisi balle na sayi abinci, shiya sanya," Wani irin kallo junaid ke bin ta dashi kallon na tausaya maki, ga takaicin daya hanasa yin magana,jin yayi shiru yasa ta cewa "ka tashi mu shiga ciki, kuma naga kana kallonta," A ƙule yace "Haushi kika ban ne,shiyasa nagaza magana, reesh waya ce maki sai kin biya kuɗi zaki ci abinci? An fa riga anbiya kuɗin komai na school ɗinki, tun daga school fees har kuɗin abincin ki dana school bus da zaki dunga hawa har na tsawon 3 months fa," Jin haka yasa sehrish zaro ido waje baki asake tana mamakin ashe itace shashashar batasani ba ta hana kan ta cin haƙƙinta, ashe an biya kuɗin komai ita kanta takaicin ne yasa ta yin kasaƙai, Fitowa sukayi daga motar atare suka shige cikin gidan a babban falon suka rabu ta wuce bedroom ɗinta shi kuma ya wuce upstairs ɗakinsa, babu kowa acikin gidan abunda ya ɗaure mata kai, tana shiga ciki tayi wurgi da school bag ɗin sannan tashiga tu6e uniform ɗin suma duk nan tayi watsi dasu saman gadonta, bayan ta kammala ya rage daga ita sai half vest da gajeran wando, toilet tashige shaf shaf tayi wanka tare da ɗauro alwala tafito, cikin hanzari ta buɗe wardrobe ɗinta ta zumbula doguwar riga, sannan ta zura hijabi tare da shimfiɗa darduma ta kabbara sallar, tana kammala sallar ko addu'a bata tsaya yi ba, ta haye saman gadonta ta baje tashiga sharar bacci maganar yunwa kuma wata'kil saita tashi sannan tashiga neman abinci, Turo ƙopar Azmee tayi ta sameta tana ta jan minshari bin ko'ina tayi da kallo ganin yarda tayi wurgi da school bag ɗinta ga uniform ɗinta data watsar saman gadon, murmushi kawai tayi tare da girgiza kai tace "ƴan makaranta kenan, tun yau anfara wurgi da shool bag ga uniform a watse saman gadon maimakon ta ninke su," ta faɗi da murmushi a fuskarta sannan taja mata ƙopar ta fuce, ta jima tana bacci sai wuraren sallar la'asar sannan tafarka da wata irin matsiyaciyar yunwa ba arziƙi ta fito ta wuce kitchen, har time ɗin babu kowa, roƙon da take yi Allah yasa babban yaya ba us suka koma ba, Acikin tray ta haɗa abincinta sannan ta zauna a kitchen ɗin tana ci tana tunanin duniya,' **********Twins*************** Duk yinin ranar ba inda suka je saboda tashin hankali sam sun rasa inda zasu tsoma ransu, tun da sanyin safiya bayan sun dawo daga sallar asuba, haroon ya faɗo masu ɗaki domin ya ƙara jaddada masu akan buƙatun daya nema a wurinsa, Jahan ya tsawatar masa akan cewa ko nawa yake so zasu bashi amma kada ya sake yayi kuskuren cewa zai ƙara kusantar ɗaya daga cikinsu, da jin wannan maganar sai haroon yace ya amince amma bisa sharaɗin cewa zasu ƙara mashi miliyan 80 in har suna son ya daina bibiyarsu Kuma cikin sati guda kacal ya basu in ba haka ba zai tona masu asiri 😥😳 tun safe basu ci komai ba, ko fitowa ba suyi ba daga bedroom ɗinsh, kuma babu wanda ya lura da hakan illa junaid da yayi ta tambayarsu har ɗakinsu sai da yazo yayi ta faman knocking yana kiran sunan su, suna jin shi tamkar zasu yi kuka amma basu amsa mashi ba,ƙarshe yayi tunanin cewa basa nan yayi tafiyarsa, Ayaaan ya sha kuka aduk lokacin daya tuna abunda ya faru dasu daren jiya sai yayi yunƙurin amai, yanzu haka ma yana zaune gefen gadon idonsa jawur ya ɗago ya kalli jahan dake ta faman safa da marwa acikin ɗakin yace "Dan Allah jahan mu hanzarta mu sama mashi kuɗin daya buƙata, if not wlh so yake ya kashe mana rayuwa," ya faɗi yana faman matse hancinsa da yayi jawur saboda matsar daya sha da hannunsa, Jahan ya dubesa cikin damuwa tare da cewa "Ayaan bansan ya zanyi ba ! Wa zan fara tunkara game da kuɗin nan? duk wanda zamu tambaya acikin brothers ɗin mu ko Abban mu dole sai sunji me zamuyi dasu kafin su bamu, daga baya ma zasu tambaye mu ina abunda muka siya dasu, don haka Mommy ce kawai nake tunanin zata iya bamu kuɗin amma matsalar shine tana fushi da mu saboda bama kiranta a waya muna gaishe ta," Jahan ya ƙarasa maganar tare da samun wuri ya zauna kusa da Ayaan ɗin, "Jahan mom ita kaɗai ce solution, mu jaraba kiranta kawai mu sanar mata mu ji mai zata ce," "Video call zamu kira ta, may be tafi tausaya mana in taga yanayin mu" Acewar jahan, yayi maganar tare da miƙewa ya ɗauko laptop ɗinsu dake ajiye saman drawer ɗinsu, komawa yayi ya zauna dab da Ayaan sannan ya zaro wayarshi tare da buɗe laptop ɗin, duk ayaan na zaune zugudun yana jiransa ya kira, zama su kayi suka ƙurama screen na laptop ɗin ido suna jiran mommyn nasu ta ɗaga kiran cikin sa'a ta ɗaga masu kiran, har haɗa baki suke yi wurin cewa "Mommy," tana zaune cikin haɗaɗɗen garden saman gujera hannunta ɗauke da cup na coffee da alama sha takeyi, ta jima tana kallonsu sai daga bisani tace "sai yau kuka ga damar kira na"? "Sorry mom ba haka bane.....," suka faɗi atare, girgiza kai alexandra tayi tare da cewa "to menene? halan wani abu ku ke buƙata shiyasa kuka kira ni"? Shiru su kayi suna kallonta ba bakin magana, tsoki taja tare da cewa "if u can't talk to me, i will reject the call right now"! Cikin sauri jahan yace "pls mommy don't reject the call, zamu yi magana, pls Ayaan kayi mata bayani" ya faɗi yana kallon Ayaan shima murya tamkar zaiyi kuka yace "Jahan i don't know what to say, kai kayi mata bayani pls," mamaki ne ya kama Alexandra ganin yadda suke ta jayayya akan wanda zaiyi mata bayanin dangane da kiran da sukayi mata, tsawa ta daka masu tare da cewa "bana son shiriri James! kuyi mun bayanin kiran da kuka yi mun within 5 mins if not zan kashe kiran " Natsuwa su kayi gaba ɗayan su sannan jahan ya soma cewa "Mom dama.....um......kuɗine...muke....so...awurin ki, ki bamu," tana jin haka ta fashe da dariya hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda mommyn nasu ke 6a66aka dariya, Ayaan yace "mom why are u laughing pls, don Allah ki tausaya mana mommy muna cikin wani hali ni da Jahan....' dakatawa tayi sannan ta soma magana anatse "Har nawa ne kuɗin"? Jahan yace "80million," ɗan zaro ido tayi tare da cewa "har 80m? what are going to do with it? Ayaan yace "mom dan Allah kada ki tambaye mu me zamuyi dasu, saboda ba zamu iya yi maki ƙarya ba, kawai ki taimaka ki ba mu," Murmushi ta ɗan saki tana kallonsu na wani lokacin kafin tace "Ni a wuri na miliyan tamanin tamkar naira tamanin take, naji zan taimaka na baku amma bi sa sharaɗi ɗaya"! Har sun fara sakin fara'a amma jin maganarta ta ƙarshe yasa su dakatawa da murna, Jiki asanyaye Jahan yace "what mom"? alexandra tace "Inaso ku sa ROMEO ya kira ni a waya, sannan ya kira ni da sunan mommynsa Kuma ya bani haƙura na bijire mun da yake yi, kiran yakasance video call ne, in har ku ka sa romeo ya amince ya kira ni awaya,i promise to give each one of u 50 50millions,' tayi maganar tare da jaddada musu, Zaro ido suka yi gaba ɗayansu ga samu ga rashi, domin kuwa sunsan cewa Junaid bazai ta6a kiran mahaifiyarsu ba harya bata haƙuri kuma ya kirata da sunan mommynsu tabɗijancan, gaba ɗaya sun tafi zurfin tunani suka ji tace "i will be waiting to hear from u guys," tana faɗin hakan ta kashe video call ɗin, Hannu ayaan yasa ya rufe laptop din sannan ya kalli jahan wanda shima kallonsa yake yi yace "Yanzu ya zamuyi jahan? ga samu ga rashi ! duk da nasan junaid yana son mu sosai kuma yana yi mana biyayya zai iya yi mana komai amma banda wannan ALFARMAR, zugudum su kayi cikin tsananin tashin hankali da kuma tunanin yarda zasu tunkari junaid da maganar! 😥 ***********JAHAD***********"** a hankali ta soma buɗe idanunta biji² ta dunga gani a idonta, daker take motsa su zata buɗe su, sai faman ambaton sunan Allah take yi a hankali, lokacin da taƙarasa buɗe idanun nata mamaki ne ya kamata ganin ta kwance a wani ɗaki, komai na cikinsa fari ƙal a tsaftace, ga mutanen dake tsaye akanta farare fat hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, gaba ɗaya ranta ya bata cewa mutuwa tayi ne, saboda yanayin wurin da ta gani fari ga mutanen dake tsaye akanta farare, hawaye ne suka soma zubo mata a idanunta cikin kuka take cewa "Ya Allah kasa ba mutu nayi ba,nabar hussana aduniya wurin wancan fasiƙin mutumin, nashiga uku wa zai taimake ta acan, meyasa mutuwa bata ɗauke mu, mu biyu ba atare? Sai ta ɗauke ni nikaɗae tabar hussana a waccen duniyar mai cike da ruɗani," gaba ɗaya jahad ta fashe musu da kuka, Hankalin nurse ɗin dake tsaye da likitan ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin sauri su kayi kanta, ko da jahad tagansu sai ta ƙara sautin kukan tana cewa "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,! dan Allah su wanene ku farare haka, ina hussana take, zama nurse ɗin tayi daga gefenta sannan tace "Sannu da jiki ƴar uwata, ni ce nurse ɗin dake kula da ku, sunana Camila ke fa"? Jin tayi mata magana raɗau da hausa yasa jahad dawowa cikin hayyacinta sosai tana kallonta da mamaki, kana kallonta ka ga english woman, Cos majority na ma'aikatan asibin sgr daga u.s suke, wasu daga india, wasu kuma ƴan nan nigeria, akwai kwararrun likitoci da nurses acikin asibitin, ƴunƙurawa jahad tayi zata tashi cikin sauri Camila tasa hannu tare da mayar da jahad kwance tace "Ana miki ƙarin jini ne, ko baki lura ba ne"? ta faɗi tana kallonta da murmushi a fuskarta, ɗan juyawa jahad tayi ta kalli ledar ƙarin jinin da akeyi mata, sassauta muryarta tayi sannan tace "sister dan Allah ina ne nan? Kuma waya kawo ni nan? Murmushi Camila tayi sannan tace "nan asibiti ne, sannan yayanki ne ya kawo ki domin mu baki kyakkyawar kulawa!" Cikin mamaki jahad tace "Yayana kuma? ae ni bani da kowa aduniyar nan ƴar uwata ce kawai hussana nasani, dan Allah tana ina"? tayi maganar tana jiran amsa, duk tattaunawar da suke yi dr Emran na tsaye yana jin su , kafin Camila ta buɗe baki tace wani abu sai ga MARSHAL OMAR ya shigo ɗakin shida Major, gaisawa su kayi da dr emran, sannan ya matsa wurin da jahad ke kwance, tsayawa yayi yana kallonta fuskarshi asake saboda ganin yarda ta wartsake alamar tasamu kyakkwar kulawa awurin Nurse ɗin, Sam jahad bata lura da marshal omar ba dake atsaye har sai da ya ambaci sunanta "JAHAD," A razane ta wurga kwayar idonta akan shi, ganin Ya Omar ɗinsu yasa ta zabura zata tashi zaune da sauri Camila ta mayar da ita, duk tabi ta zazzare idonta tana nuna shi da hannu tana ambaton sunan shi cikin tsananin mamaki, tashi Camila tayi taba Omar wuri donya zauna kusa da jahad saboda ta lura yarinyar nason magana dashi, Zama Omar yayi saman chair ɗin dake facing medical bed ɗin da jahad ke kwance asama sannan yace "Ya jikin naki"? tana jin haka ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, hannunta tasa ta ruƙe hannunsa tana cewa "Ya Omar ina ka shiga tsawan kwanaki kabar mu, bakasan halin da muke ciki ba..........' tana magana muryarta na shasshaƙewa saboda kukan da take, sam Omar ya gaza cewa komai tuni idonsa sun cicciko da kwalla, Jahad taci gaba da cewa "Ya Omar har yanzu nagaza yarda cewa kaine! dan Allah kayi mun magana taya akai haka tafaru ya omar, kuma ina hossana take? mutumin nan ya gudu da ita ya omar..........." kasa ƙarasa maganar tayi saboda hannunsa daya sanya ya rufe mata bakinta........................................Bin idanunta yayi da kallo itama tana kallon nashi hawaye ne cike taf da idonta, bai janye hannunsa daga bakinta ba har sai da ya tabbatar cewa ta samu natsuwa sannan ya zame hannunsa yace "Jahad duk wani abu dake faruwa ni bansani ba,bani da masaniya akai,jiya ne aka turomin saƙo da privet number bansan ko wanene be,let me show the message, Hannu yasa ya curo wayarsa daga trouser pocket ɗinsa kunna wayar yayi sannan ya shiga wurin messages ya buɗe saƙon ya nuna ma jahad don ta gani, Zuba ma screen ɗin wayar tayi da ido tana karantawa kamar haka _"Omar ka yi ganganci daka bar rayuwar yaran nan a hannun Laila, ina baka shawarar ka hanzarta zuwa ka ɗauko su, saboda naji cewa gobe goben nan za'a fitar dasu daga gidan_" Janye wayar yayi sannan yace"lokacin da message ɗin ya shigo mun bana cikin natsuwa ta, saboda mun shiga tashin hankali,ƙanne na da aka tura aiki miyagu suka farmake su, mun samu nasarar ceto rayuwarsu kuma mun kama wasu daga cikin waɗanda suka farmake sun, yanzu haka da nake maki magana ɗaya daga cikinsu yana kwance a A&E ward, baisan inda kansa yake ba,saboda sai da suka banka mashi kayan miyagun ƙwayoyi sannan suka azabtar dashi, ba don Allah yasa an samu wani daga cikinsu ba yayi mana waya da shikenan ba'asan mai zai biyo baya ba, Shiru Omar ya ɗanyi na wani lokaci kafin yaci gaba da cewa "tun shekaran jiya da muka fita daga gida muna can wurin cetonsu,a asibitin nan aka kwantar da waɗanda suka raunata sosai daga cikinsu,gaba ɗayan mu babu wanda ya samu runtsawa adaren jiya saboda tashin hankalin kada mu rasa su,kuma a daren jiyan ne acikin asibitin nan saƙon ya shigo mun,duk nabi na rikice saboda narasa yarda zanyi, Major shine babban na hannun dama na, shi na kira na nuna mashi saƙon da aka turomin game daku, koda ya gani sai cewa yayi dama ya jima yana son ce mun wani abu, amma ba zai iya sanar dani ba saboda bayason shiga tsakanina da matar yayana, sai abun ya ɗaure mun kai jin abunda yace,a lokacin ban matsa masa ba akan son sanin wani abu ne yake son sanar dani ba,a time ɗin duk da halin da nake ciki burina kawai inzo in ganku, Major shine yace nabar masa komai a hannunsa kar na damu, sai a washe gari major ya sanar dani cewa mu shirya mu tafi, sannan kuma yaban wata number yace mu bi diddiginta, atare dashi muka fito mu biyu kawai muka miƙi hanya, da wayata nayi amfani wurin bindiddigin numbar daya bani har muka ƙaraso titin da dajin nan yake,mu ka shiga cikinsa kai tsaye, muna cikin tafiya naji an kwala mun kira ta waje "yalla6ai," cikin sauri na zuge glass ɗin motar don naga wanene, shine naga wani saurayi zuƙunne a ƙasa, ga ki kuma kwance a sume duk jini a goshin ki, hankali atashe na zabura zan fito daga cikin motar, kawai sai saurayin nan yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar acikin motarsa, gashi can ya miƙi hanyar da tayi dama don Allah ku ceto rayuwarta, " jin haka yasa gaba ɗaya na rikice, cikin sauri major yaja motar mu da gudun gaske muka bi motar wannan tsohon mutumin da gudun gaske har cikin gidan gonarsa, ina shiga najiyo kukan hossana hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, tuni na makance na afka ma ƙopar ɗakin gidan gonar na tarwatsa ta, ina shiga naga hossana a lokacin har yayi nasarar yage mata rigarta ya ruƙe ta a hannunsa, raina yayi mugun 6aci abunda ya hanani yin motsi a lokacin saboda bansan wane irin hukunci zan yanke masa ba,yanzu haka da nake baki labarin nan babu wannan tsohon a duniyar nan saboda na kashe shi,kuma na ɗauko hoton gawarsa don na nuna ma hossana," Wani irin murmushi jahad ta saki har ta gaza rufe bakinta don murna,shima Omar ɗin murmushi yakeyi yana kallonta, Nasan dayawa za suyi mamakin yarda akai hakan ta kasance,abun da ya faru shine cikin sojojin dake gadin gidan general ishaq akwai wani matashi Abokin major ne, a lokacin da suka kawo su hussana da jahad gidan Omar ya shiga tare da su ciki , A nan major suka haɗe da wannan saurayin abokinsa ne tun suna yara ,sunan Shi Osman bayan sun gaisa Osman ke cewa "Abokina waɗancan yaran fa? dana ga ka shiga ciki dasu ƴa'yan wanene? ko dai ogan naku ne yayi aure matar ta haihuwa, Dariya Major yayi tare da cewa "Wai dama Osman har yanzu kana nan da shegen sa idon nan naka? Haba no wonder shiyasa Allah yabarka a matsayin mai gadi, in banda abun ka ina ogan mu yakai shekarun da zai iya ajiye ƴa'ƴa kamar waɗancan? shima fa ba wani babba bane duka shekarunsa bazasu wuce 28 years, matsayi ne kawai Allah ya bashi," jin haka yasa osman ɗan zaro ido tare da cewa "ka ce ashe shima ɗan shila ne, amma dan Allah tun yaushe nake ta fama dakai ka taimaka ka sama mun aiki a ƙarƙashinsa amma ka ƙiya, kafi son kaita ganina a matsayin mai gadin gidan genar, kalli fa yarda na rame nayi baƙi, kai kuwa har wani tumbi kafara ajiyewa saboda jin daɗin rayuwa, wlh abota bata ce haka ba," ya faɗi yana tsuke fuska, dafa kafaɗarsa Major yayi tare da cewa "Ina sane da wannan Osman, kuma insha Allah zanyi ƙoƙari na sama maka gurbi a kusa dashi, mutumin kirki ne sosai yana da sauƙin kai kuma ina jin daɗin aikin dashi,yana kyautatamun domin kuwa kafin ƙarshen wata yayi ina samun ninkin ba ninkin abunda nake samu a albashina wurinsa," jinjina kai Osaman yayi zugudun yayi masa fuskar tausayi kafin yace "Kaji daɗi mutumina,ni dai zan jira naji daga wurinka don Allah karka manta kasa ma mun kusanci dashi, nima na dangwali arxiki," Major yace"baka da damuwa, yanzu ma haka ga wani aiki ka samu, waɗancan yaran da kake gani ogan mu yana sonsu sosai, bashi da alaƙar komai dasu hasalima a asibiti ya taimake su,ya kawo su nan ne domin su zauna tare da matar yayansa ishaq, to ni hakan bai kwanta mun araina ba, shi ne nakeso ka sanya mun ido akansu! ka zama tamkar ɗan leƙen asiri duk da nasan hakan ya sa6ama dokar aikin ku amma inaso kayimun wannan Osman,ka lura da duk wani motsinsu acikin gidan nan, so nake kayi aiki tamkar jami'in sirri! dalilin dayasa nayi hakan saboda bana son duk wani abu da zai cutar dasu don na lura da yadda ogan mu ke tsananin ƙaunar yaran,ni kuma bana son duk wani abu da zai 6ata masa rai, ta6a yaran nan tamkar ta6a masa zuciya ne," ya ƙarasa maganar yana kallon osaman da yayi kasaƙai, daga bisani yace "Na amince zanyi hakan, amma wlh ka sani duk ranar da asirina ya tonu, sunanka na ciki ! don ba zan shiga haɗari ni kaɗai ba," dariya major yayi sannan yace"Ai ni babu wanda ya isa ya ta6ani muddin ina tare da Marshal, don haka kaima ka kwantar da hankalinka, ba abunda zai same ka face alkhairi,tunda ka amince zaka yi ɗin, inaso duk wani hali da suke ciki ka tabbatar da ka kira wayata ka sanar mun," Osman ya amsa masa da "toh," daga nan su kayi sallama, a lokacin marshal Omar ya fito daga cikin gidan jikinsa asanyaye suka shiga cikin mota su ka tafi, tun daga wannan lokacin Osman ya zaman ɗan leƙen asiri duk wani hali da su hossana ke ciki yana sane dashi kaf, kuma duk rana yana kiran major ya sanar dashi halin da suke ciki, Major bai ta6a sanar da marshal Omar ba, saboda gudun karya shiga tsakanin shi da matar yayansa ishaq,kullum yana sanar da osman cewa yaci gaba da sa musu ido, Idan har masu karatu zasu iya tunawa akwai lokacin da Aunty babba tayima su hussana da jahad bugun mutuwar nan, har suka kaisu asibiti bayan sun dawo suka shige cikin gida ita da hafsat suka bar jahad tsaye gaban motar tana kuka saboda hossana na'a cikin motar kwance rai hannun Allah gashi bata iya ɗaukarta bare tashiga da ita cikin gidan, a lokacin idan zaku tuna akwai wani soja daya zo yana tambayarta meke faruwane, take ce masa ƴar uwartace acikin motar kwance bata lafiya kuma bazata iya ɗaukarta ba, sai sojan yace maza "Can i help," take ce masa eh, yasa hannu ya ɗauki hossana ya shigar mata da ita ciki, ya kwantar da ita saman doguwar kujera, yayin da jahad tabisu, to wannan sojan ba kowa bane face Osman abokin major ɗan leƙen asirinsa, ko lokacin da zai fita daga falon bayan ya kwantar da hossana sai da ya ɗan tsaya daga bakin ƙopar ya juyo yana kallon jahad dake zukunne saman guiwarta agaban hossana tana yi mata addu'a tana kuka, jinjina kansa yayi tare da fuce wa bayan yafita, ya ɗauko wayarsa tare da buga ma major kira, bayan ya ɗaga kiran yake sanar dashi abunda ke faruwa, nace wa shifa yana zargin cewa Matar ishaq tayima yaran mugun bugu har ma ɗaya daga cikinsu ta jigita sosai tamkar ba zata rayuwa,don haka ya hanzarta sanar da ogansu Omar yazo ya kwashi yaran tunkan ta kashe su, har lokacin major bai sanar da Omar ba game da wannan ma, saboda yana tunanin koya faɗi masa daker ya yarda kuma yasan makircin mata, abun zai iya dawowa kansa, tun fa lokacin da su jahad da hossana ke wanki abayan gidan ita da jahad, Osman yake ganinsu sai yazo ya gifta ta wurinsu tamkar yana yin waya alhalin su yake kallo, har video yake yi masu yana turawa major donya gani," Major ya tsorata da ganin irin uƙubar da yaran suke sha, Bayan wannan lokacin kuma sai salon ya canza, duk osman na zuba ido yana kallon ikon Allah yarda hafsat ke nuna ma yaran soyayya, aduk lokacin da hafsat ta fita dasu cikin motarta, sai osman ya bisu da machine ɗinsa dom yaga ina zata dasu, dashi suke yin yawo abayansu batare da sun sani ba, duk inda zasu osman na biye dasu a sirrince, daya kira Major ya sanar dashi abunda ke faru na cewa yaran fa yanzu suna samun kulawa sosai a wurin mutanen gidan, sai major yace mashi "Wannan salon da suka canza,alama ce dake nuni da cewa sun kusa salwantar da yaran,ina da tabbacin cewa so suke su zubar dasu kaci gaba dasa musu ido,daga yanzu banaso ko bacci ka dunga yi osman, saboda wannan lokacin ne mafi haɗari, aduk lokacin da maƙiyin ka ya canza maka salo na soyayya to kaji tsoransa halakar dakai zaiyi," Tun daga lokacin da Major ya sanar dashi haka, bawan Allah osman bai ƙara yin bacci ba, koda bashi ke akan duty ba, yana nan yana lura da shige da ficen da hafsat keyi dasu hossana, A ranar da baba alamu zai tafi dasu hossana, akan idon osman Aunty babba ta fito tare dasu jahad da hossana,ta buɗe masu motar hafsat suka shiga, duk yana kallonsu, daga bisani kuma sai yaga hafsat tafito hannunta ɗauke da trolley hakan na nufin wani ne zaiyi balaguro, bayan hafsat ta shiga cikin motar taja motar tafito dasu daga cikin gidan, cikin sauri osman ya hau mashine ɗinsa da yake ajiyesa acikin gidan yabi bayansu a hankali yake tuƙa mashin ɗin don kar su ganshi, da hafsat ta tsayar da motar abakin titi tana jiran ƙarasowar baba alamu, sai osman ya dakata da tukin mashin ɗinsa, cikin sauri ya sauka tare da samun wuri ya cire rigar jikinsa ta kakin sojoji ya 6oyeta a ƙarƙashin wani benci dake agaban wani shago dake rufe, sannan ya tu6e wandon jikinsa ma, ya ajiyesa a ƙarkashin bencin bakomai yasa shi yin hakan ba face don karsu ganshi da kakin sojoji yana binsu, Asirin shi zaiyi saurin tonuwa ne, Sai daya rage daga shi sai farar shirt da gajeran wando ajikinsa a lokacin motar baba alamu taƙaraso,cikin sauri Osman ya zuƙunna agaban mashin ɗin tamkar ya samu matsala yana gyaransa, alhalin nan duk salon dabaru ne na jami'ae, yana gyaran mashin ɗin yana satar kallonsu, akan idonshi hafsat ta buɗe ma jahad da hossana mota suka fito sannan ta ɗauko masu trolley ɗinsu da food basket ɗinsu ta basu,bayan hafsat ta tafi, baba alamu ya amshi akwatin Su hossana da jahad ya wurga cikin boot ɗin motarsa, daga nan jahad da hossana suka shiga cikin motar, shima ya shiga tare da tashin motar suka tafi, cikin sauri Osman ya haye mashin ɗinsa tare da tashinsa yabi bayan motar baba alamu da gudun gaske amma bai bari ya ƙurewa motarsa ba kasancewar Motar baba alamu glass ɗin jikinta duk ya fashe, muddin osaman ya ƙurewa motar tofa zasu iya hango shi, hakan yasa ya basu tazara sosai, yana cikin tuƙin mashin ɗin ya ɗan jinkirta tare da zura hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa tare da bugama major kira, bayan ya ɗaga yake sanar dashi duk abunda ke faruwa, Hankali tashe major yace "Osman kada ka bari ya kubce maka, kaci gaba da bin motarsa, sannan kabar wayarka a kunne zamu biyo diddigin layinka, mu zo inda kuke," bayan osman ya amsa masa, ya mayar da wayar, sannan ya ƙara ma mashin ɗinsa gudu, a lokacin da motar baba alamu tashiga dajin da gudun gaske, jahad na ƙoƙarin fitowa tana ihu bayan ta samu ta harba murfin motar ya buɗe, sai baba alamu ya girgiza motar da mugunta, ta faɗo ƙasa timmmm goshinta ya bugu, ta taso da gudu tana bin motar tana kiran sunan hossana daga bisani ta yanke jiki ta faɗi, adai-dai lokacin shi kuma osman ya ƙaraso ba komai yasa shi yin jinkiri ba fa ce wayar da yayi da major shiyasa bai ƙaraso akan lokaci ba har baba alamu ya kubce mashi, ganin jahad da yayi yashe a ƙasa ta sume ga jini, ba ƙaramin razana yayi ba, cikin hanzari yayi wurgi da mashin ɗinsa ya nufe ta hankali atashe, ya zuƙunna gabanta yana faɗin "ke!ke!! tashi ki tashi dan Allah, kada ki mutu," Adai-dai lokacin kuma motarsu Marshal Omar ta faso cikin dajin ta hanyar tracking layin osman da sukayi yasa har suka ci nasarar cimma inda yake, Osman na ganin motarsu Marshal yasan cewa sune aciki, a lokacin omar ya zuge glass ɗin motar a tsorace ganin jahad kwance duk jini a goshinta, harya harzuƙa zai fito daga cikin motar, cikin sauri Osman yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar, gashi can ya miƙi hanyar dama da ita, don Allah ku ceci rayuwarta," jin haka yasa Omar fasa fitowa daga cikin motar, cikin sauri major yaja motar da gudun gaske suka bi motar baba alamu a lokacin ya ɗanyi masu nisa, hayaƙin da bayan motar baba alamu ke fitarwa shine yasa suka gane hanyar da yabi, suna isa basu tsaya buɗe kopar katakon gidan gonar ba, kai tsaye major yabi ta ƙopar atsiyace ya tarwatsa katakon gidan gonar suka shige, Tamkar zaki haka omar ya fito daga cikin motar ya afkawa ɗakin da baba alamu ya shige da hossana, *Wannan shine abunda ya faru taƙaice kenan* "Ya omar ina hossana take ita'? Omar yace"hossana tana cikin ƙoshin lafiya, itama ƙarin jini akeyi mata, yanzu haka bacci take sha tana a kusa da ɗakin nan," ajiyar zuciya jahad ta saki kafin ta kuma cewa "ya omar kullum hossana saita ambaci sunanka, komai akayi sai tace "ya Omar fa," ita bata son rabuwa da yaya omar ɗinta," Murmushi Omar ya saki jin abunda jahad tace, "Amma ya Omar ba zaka ƙara rabuwa damu ba ko? dan Allah kada ka haɗamu da kowa kabarmu kawai a wurin ka, kai kaɗai ke son mu," tayi maganar idonta akansa tana jiran amsar shi, Omar yace "ko wancan time ɗin bada son raina nabar ku ba, jahad you're always in my mind ina jin ku araina,amma yanzu komai ya wuce just forget about the past, ku ƙaddara cewa wani abu bai ta6a faruwa da rayuwarku ba na ƙunci, saboda yaya omar ɗinku ya shirya maku kyakkyawar rayuwa ta jin daɗi da walwala, masarauta ce wadda ku kaɗai zaku mulketa sai yadda kuka ga dama zakuyi acikinta, hatta yaya omar ɗinku zai zama tamkar bawa agare ku," dariya kawai jahad ke faman tiƙa saboda murnar jin abunda omar ke cewa, hatta dr Emran da Camila dake tsaye murmushi kawai suke saki, shima major dake tsaye daga ƙopar ɗakin murmushi ne a fuskarsa, ƙarasa shigowa ciki yayi yana cewa "Sir idan ba damuwa inaso a bani muƙami acikin masarautar nan, zanso na zama sojan dake kula da princesss ɗin dake acikinta, bama ni kaɗai ba ga abokina osman nan shima yana roƙon gimbiya jahad da ta bashi damar zama ɗaya daga cikin masu kula dasu," Abun sai ya zama tamkar shirin wasan kwaikwayo gaba ɗayansu dariya ce a fuskarsu, hakan ba ƙaramin farantawa omar rai yayi ba ganin yadda jahad ke faman tiƙar dariya, sai yaji sanyi aransa sam ya gaza janye idonsa akanta, Muryar Camila (kameela) ce ta katse su da cewa "Yalla6ai nima idan ba damuwa ina neman alfarmar zama ɗaya daga cikin masu yi ma gimbiya jahad hidima, ko da a matsayin jakadiya ne mafi kusanci dasu," Fashewa da dariya jahad ta ƙara yi daga kwancen da take har omar na cewa "Bi a sannu my baby, kada ki shaƙe," gaba ɗayansu sun natsu sai raha akeyi, suka ji Muryar hosana kamar daga sama tace"YA OMAR," Atare suka juya suna kallonta, tsaye take a bakin ƙopar ɗakin daker take buɗe idanunta tana kallonsu, hannu tasa ta murza idonta sannan ta ƙara buɗe su da kyau donta tabbatar da abunda idonta ke gane mata, tabbas kuwa shine wato yaya Omar ɗinta, tsananin farin ciki ne yasa hossana ƙarasa shigewa ciki da gudun gaske tana isa inda Omar yake ta zube saman guiwowinta tare da kifa kanta asaman laps ɗinsa tana kuka, Shiru su kayi gaba ɗayansu na wani lokaci suna sauraren kukan da hossana ke yi, gaba ɗaya jikin omar ya gama mutuwa saboda yasan yarda yarinyar ke tsananin ƙaunarsa dole tayi kewarsa, hannu omar yasa tare da shafa gashin kan hossana cikin muryar lallashi yace "Am so sorry hossana,nasan nayi laifi ban ma san da wane baki zan iya baki haƙuri ba," Maimakon ta ɗago sai ta daddage ta gartsa mashi ciwo a laps ɗinsa, runtse ido omar yayi saboda yaji zafin cizon, babu wanda ya lura da abunda ke faruwa sai jahad, tun da taga omar ya runtse ido tasan cewa Hossana Cizon shi tayi, tayi mashi hakan ne don yasan irin raɗaɗin da suka ji acikin zuciyoyinsu na ƙin zuwan da yayi ya tafi dasu, buɗe idonsa yayi a hankali yana sauke ajiyar zuciya ya kalle ta, a lokacin itama ta ɗago tana faman huci ta ɗaure masa fuska tare da haɗe masa girar ƙasa da sama tana kallon shi, Cikin sanyin murya ya sake maimaita "Am sorry again," ya furta tare da kai hannunsa a fuskarta yana share mata hawayenta dake kwaranyowa daga idonta, Cikin kuka tace "Ya omar yanzu ka kyauta abunda kayi mana? ka tafi kabarmu cikin tashin hankali ko waiwayon mu, ba kayi ba yanzu da mun mutu shikenan bazan sake ganin Ka ba sai dai a lahira ko? ƴar dariya omar yayi tare da cewa "Amma ae yanzun baku mutu ba ko? Kuna raye kuma ga yaya Omar ɗinku atare daku, mai yayi saura yanzu"? ya tambaya yana kallonta Hossana tace "sai ka kaimu gidan ku inda kake rayuwa, don wlh duk inda zaka je, ƙafarka ƙafarmu, mu da kai mutu ka raba takalmin kaza," ta ƙare maganar tana zumbura baki, Gaba ɗayansu na cikin ɗakin dariya kawai suke yi, Kallon dr emran omar yayi kafin yace "yanzu mai ya rage dr?yaushe kake tunanin za'a sallame su, in yaso sai acigaba da basu kulawa acan gida? dr emran yace "zuwa night, ae jikinsu yayi ƙarfi yanzu saboda ƙarin jinin da akayi masu, idan ma ba damuwa Camila zata iya cigaba da kula da lafiyarsu, in har kana buƙatar hakan, tunda dama naji tace tana son zama hadimar princess ɗin naka," Murmushi suka saki gaba ɗayansu banda hossana don batasan zancen ba, tuni ta mayar da kanta akan laps dinsa tana faman sauke ajiyar zuciya, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, mahaƙurci kuma mawadaci ne wata rana, babu wani yanayi na rayuwa da yake kasance wa na dundundun, Innallaha ma'assabirin tabbas wannan haka yake, iya haƙuri dae su hossana sunyi kuma sun jurema duk wata jarabawa da suka fuskanta na ƙuncin rayuwa, basu fasa yin addu'a ba suna kai kukan su ga Allah ba kuma basu fidda rai da cewa Allah zai kawo masu ɗauki ba, idan muka sa haƙuri kowa zai cimma nasara, gashi yanzu zamu iya cewa Masha Allah 😍👑 **************Twins ******************* daker suka samu suka yi wanka suka canza kaya izuwa jeans da t-shirt suka fito wuraren ƙarfe 5 na yamma, tafiya suke yi gabansu na faduwa tsoransu kar suci karo da haroon don yanzu ya zamar masu tamkar dodo, suna cikin tafiya sai ga Junaid ya fito daga upstairs yana ganinsu ya ɗan zaro ido cike da murna yace "Yaya Jahan ina kuka shiga inata neman ku, naga da safe ko breakfast ba kuyi ba, duk na shiga damuwa," ya yi maganar tare da ƙarasa saukowa down ɗin yayi ya tunkaresu, suna tsaye baki asake suna kallon shi saboda neman shi suke yi ruwa a jallo, yana ƙarasawa yabi su ɗaya bayan ɗaya yayi hugging ɗinsu tare da manna musu kiss a gefen fuskarsu, irin gaisuwar da suka saba, Ganin sun zuba mashi ido batare da sunyi mashi magana ba yasa shi bubbuga ƙafarsa tare da cewa "Dan Allah wai menene haka duk kun Canzamin, ko magana ma ba zaku iya yi mun ba why pls? ya faɗi tamkar zaiyi kuka, gyaran murya jahan yayi tare da cewa "no ba haka bane junaid, ba mu jin daɗi ne, ni da Ayaan shiyasa ka ganmu a haka, yanzu haka ma kai muka fito nema akwai maganar da muke son yi dakai, amma ba'a nan ba, acikin ɗakin ka," junaid yace "magana kuma dani? Allah yasa ba laifi nayi ba" Murmushi Ayaan ya saki tare da cewa "ba laifi kayi mana ba junaid taimako ne ma zakayi mana," ruƙe ƙugunsa yayi sannan yace "Naji toh, amma kafin nan sai naga kun ci abinci tukunna, saboda baku ci komai ba tun safe ina sane da hakan, bayan na hana ku zama da yunwa," Yadda yayi maganar tamkar wani yayansu, alhalin sun girme shi, Murmushi suka saki atare sannan jahan a ruƙo hannunsa tare da cewa "Zamu ci abincin ne,amma kafin nan, mu shiga daga ciki muyi magana, tasa ƙeyarshi su kayi har cikin ɗakinsu, suka tsaya daga tsaye suna fuskantar shi, gaba ɗaya sun rasa ta inda zasu soma neman alfarmar nan a wurin junaid, Ganin sun tsayar dashi sun zuba mashi ido yasa shi hasala tare da cewa "Yaya Jahan nifa bansan menene ma'anar zuba mun idon nan da kuka yi kuna kallona ba," ya faɗi yana hura hanci, Ayaan ne ya soma magana "am...junaid ka gane, dama wata alfarma ce muke nema awurin ka, "Am listening to u," junaid ya faɗi yana kallonsu Jahan ya daura da cewa "junaid sabo da mu zakayi wannan abun, so muke ka kira Mommy a waya video call ka bata haƙuri sanna ka ambaci sunanta ka kirata da Mommy, dan Allah junaid.........' tunkan jahan ya ƙarasa maganar tasa junaid yabi ta gefensu zai fuce daga ɗakin yana cewa "da nasan wannan alfarmar zaku nema awurina, wlh da ban 6ata lokacina wurin sauraronta ba, Cikin sauri suka ruƙo rigar jikinsa har suna haɗa baki wurin cewa "Janaid dan Allah ka taimaka ma rayuwarmu, kai kaɗai ne a yanzu zaka iya fitar damu daga halin da muke ciki pls junaid do this favour for us" a fusace junaid ya fusge rigar shi daga hannunsu yace "Wlh bazanyi ba, ni bazan ta6a kiran wannan matar da sunan mommyna ba, saboda bata sona ta tsane ni, Yana faɗin hakan ya kama hanyar fita, Ayaan yayi sauri sake cafko rigarsa, aikuwa a fusace junaid ya sanya hannunsa tare da buge na Ayaan, rai a6ace jahan ya janyo shi tare da kwashe shi da mari, zaro ido junaid yayi yana kallonsu yayin da ya sanya hannunsa ya dafe kuncinsa saboda zafin marin da jahan yayi masa, tunda yake arayuwarsa zai iya cewa ba'a ta6a bugunsa ba, ko da wasa wani bai ta6a yin gigin ta6a fatar jikin junaid ba da sunan bugun, amma sai gashi yau an samu wasu daga cikin yayyansa da yake matuƙar ƙauna yasa hannu ya mare sa, tuni idonsa sun ciko da kwalla red lips ɗinsa har rawa suke yi wurin cewa "Yaya jahan ! Yau kai da kanka, kasa hannu ka mare ni? Saboda na bijire ma buƙatarku? akan abunda yake haƙkina nifa aka cuta, abun har yanzu yana yi mun ciwo azuciyata bana faɗi ne kawai..............' kuka ne yaci ƙarfinsa har ya gaza ƙarasa maganar tasa yaci gaba da sharar kwalla, tuni jikinsu yayi mugun sanyi musamman jahan daya mare sa, baisan lokacin da shima ya fashe da matsanancin kuka ba, hakan yasa junaid dakatawa da kukansa ganin yarda Yayansa jahan ke kuka agabansa tamkar ƙaramin yaro, nan take hankalinsa ya tashi cikin sauri yasanya hannayensa a fuskar jahan yana share masa hawayensa yana cewa "dan Allah yaya jahan ka daina kuka, bana son ganin hawayen nan naka, in dai ni ne na sanya ka, yin kuka wlh zan baka hakuri ka yafe mun bazan ƙara, Cikin shessheƙar kuka jahan yace "junaid naji na tsani kaina fiye da tunaninka, wai yau ni ne na kasance mutun na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ka, da wannan mummunan hannun nawa, ina danasanin wannan ranar kuma bazan ta6a yafe ma kaina ba..........' gaba ɗaya tausayin jahan ya gama kama junaid cikin sauri ya janyo shi ajikinsa tare da rungume shi sosai yana ɗan bubbuga bayansa, cikin muryar rarrashi yake cewa "Ba laifinka bane yaya jahan, Laifina ne nayi rashin kunya, na buge hannun ayaan duk da raina ne a6ace bansan nayi hakan ba, amma ku yafe mun abisa kuskuren da nayi maku bazan ƙara ba,' gaba ɗayansu sun shiga cikin wani kalar yanayi, Ayaan kam tuni jikinsa ya gama mutuwa saboda tausayin junaid da kuma kansu daya kama shi, Bayan sun tsagaita jahan ya janye jikinsa daga na junaid sannan yace "Junaid dan Allah kayi mana wannan alfarmar na roƙe ka kai kaɗae ne zaka iya fidda mu cikin halin da muke ciki, kuma nason kana tsananin son mu ba zaka so wani abu ya cutar damu ba,' ya ƙarasar maganar yana kallonsa da idanunsa da suka gama runewa, Jiki a mace Jahan ya kalli Ayaan cikin tsananin damuwa, ganin junaid yayi shiru baice komai ba yasa su yin saurin zubewa agabansa saman guiwowinsu suna roƙonsa, Cikin tsananin tashin hankali shima junaid ɗin ya zube saman guiwowinsa agabansu tare da fashewa da wani sabon kukan yana cewa "meyasa zakuyi mun haka?yaya Ayaan da ya jahan saboda me zaku duƙamin nifa ƙaninku ne, ku kuma yayyena ne dan Allah kudaina mun hakan banaso! banaso!!bana so!!" ya ƙarasa maganar tare da cewa "naji na amince zan kirata, Amma ba yanzu ba," ajiyar zuciya suka sauke gaba ɗayansu nan take suka ji wani irin sanyin ya ratsa zuciyoyinsu, Ayaan yace "yaushe zaka kirata"? Junaid yace "an jima kaɗan," ya faɗi a shagwa6e Murmushi suka saki gaba ɗayansu har haɗa hannu suke yi wurin goge masa hawayansa da suka wanke masa fuska, har lokacin suna a zuƙunne su duka ukun suna fuskantar juna, Jahan yace "Am Sorry junaid, ka yafe mun marin da nayi maka, nayi dana sani sosai," ya faɗi cikin sanyin murya, Junaid yace "gsky bazan yafe ba yaya Jahan har sai kunci abinci sannan nagani da idona tukunnan, Ayaan yace "shikenan junaid komai kake so zamu yi," Murmushi ya saki sannan ya ruƙo hannayen su suka miƙe tsaye atare, bayan sunyi wiping tears ɗinsu, Sannan suka fito daga ɗakin nasu, Ajere suka jera suna tafiya sun sanya shi tsakiyarsu a lokacin Sehrish da azmee suna a cikin kitchen suna aikace-aikacen girkin dinner ɗin gidan, Sai da junaid ya tabbatar Ayaan da jahan sun zauna saman dining chairs ɗin sannan yace "ku jira ni, yanzun nan zan kawo maku abinci ku ci," ya faɗi da murmushi a fuskarsa sannan ya wuce kitchen ɗin, har lokacin jahan dana sani yake yi akan marin da yayiwa junaid,ya gaza yarda cewa shi da kansa ya ɗaga tafin hannunsa ya zabga ma romeo ɗinsu mari, yana ganin abun tamkar a mafarki,😥Kitchen ya wuce yana ganin sehrish ya soma sakin murmushi, sallama yayi masu sannan ya shiga, amsa mashi su kayi gaba ɗayansu, sannan ya matsa wurin sehrish dake agaban chopping board tana yayyanka kayan lambu,   "Reesh idan akwai abun da kuka kammala inaso ki shiryamun a tray zan kai ma yaya Ayaan da Yaya jahan ne, yunwa suke ji ssae," ya faɗi yana yamutsa fuska tamkar shike jin yunwar, zuba mashi ido sehrish tayi tare da cewa "junaid ! meya faru dakaine? waya mare ka har haka"?    Cikin sauri junaid yasa tafin hannunsa ya rufe gefen fuskarsa yane cewa"ki daina ɗaga murya sehrish kada wani yaji, banaso wani yaji kiyi shiru kawai da bakin ki,"  Jikinta ne yayi wani irin sanyi aranta tana mamakin yarda akai har wani ya aza tafin hannunsa a fuskar junaid ga sahun yatsu nan sun bayyana raɗau a fatar fuskarsa yayi jawur wurin, Jinjina kanta kawai tayi tare da cewa "Shikenan bari na shirya maka abincin ka kai masu," ta faɗi tana kallonsa cikin jin tausayinsa, Ajiyar wuƙar hannunta tayi sannan ta wuce ciki donta haɗa masa, hannu yasa ya ɗauki knife ɗin da ta ajiye yaci gaba da yanka mata lettus ɗin data bari,  Azmee ce ta taya ta zuba masu acikin warmers duk tana jin magananun da suka yi ita da junaid, aranta tana mamakin marin da taji sehrish ta ambata anyiwa junaid, har satar kallonsa tayi taga yarda fuskarsa tayi jawur gefen da aka maresa ga alama nan tabbas in wani yaji acikin gidan sai an tada husuma,    Ruƙo tray ɗin tayi a hannunta zata wuce takai masu cikin sauri junaid ya ajiye wuƙar ya tare ta da cewa "kawo na kai masu,"miƙa mashi tayi yasa hannu ya kar6a yana kallon fuskarta da murmushi yace "thank u," itama murmushin ta sakar mashi duk tashiga damuwa akan yanayin fuskarshi,  Yana karba ya fuce yakai masu, yadda yabarsu haka ya same su, sunyi zugudun suna kallon junansu, Jahan na ganinsa ya saki fara'a tare da cewa "Yawwa heart beat mun gode sosai da irin kulawar daka ba mu, duk ka damu akan mu," murmushi junaid ya saki a lokacin ya ajiye masu tray ɗin kayan abincin asaman table ɗin,    Jikin Ayaan har kerma ya keyi wurin ɗaukar jug ya zuba lemu mai sanyi acikin cup yana kwankwaɗa, abun ya ɗaure ma junaid kai ashe dai da gaske yunwar suke ji,    Shima jahan jiki na rawa ya shiga zubama kansa abincin, cikin sauri junaid ya wuce wurin freezer ɗinsu ya buɗe tare da ɗuko masu cool drinks ya kawo masu agabansu,   Hannu jahan yasa ya ɗauki bottle water yana kwankwaɗa har yana kusa shaƙewa, agalabaice ya ajiye robar ruwan sannan ya kalli Junaid dake tsaye akansu yace "Allah yayi maka albarka junaid, kaje ka ci gaba da wasan ka,"    Juya junaid yayi ya koma kitchen wurinsu sehrish, tana ganinsa tace "Za'a a ƙara masu abincin ne"? Girgiza kai junaid yayi tare da cewa "zuwa nayi na taya ku aikin, bana jin daɗin zama ni kaɗai ne,"  Azmee tace"so kake kaja mana ko? taya za'a ganka acikin kitchen kana tayamu aiki, kaima kasan ba zaiyiyu ba,"   turo bakinsa yayi tare da cewa "Aunty azmee nifa ba wani abu zanyi mai yawa ba, kawai zan taya sehrish yanka kayan lambun ne,"    "Ban amince ba junaid, wai ni yau ba ka zuwa wurin buga ball ɗinka ne? ina laptop ɗinka ne? kaje ka kunna kallo kayi mana ko ka buga game,"    Ruƙe qugu yayi tare da cewa "Aunty azmee korata kawai kike son yi ne, to Allah ba inda zani ƙafata ƙafar sehrish, tazo mu tafi tare," ya faɗi da shagwa6a   Dariya su kayi gaba ɗayansu, sai lokacin sehrish tace "junaid ɗina shigo ciki ka samu wuri ka zauna, zan haɗa maka Cornflakes, kana sha kana kallon yarda muke girki,"    Murmushi ya saki sannan ya shige ciki tare da samun wuri saman dinning chairs na kitchen din ya zauna yana jiranta,   Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Shaƙuwarku fa da junaid ƙara gaba take yi, don na lura kema bakyaso yayi nisa dake,"   Sehrish tace "Aunty azmee yana ɗebe mun kewa sosai, ina jin shi tamkar ƙanina ne shiya sanya.... .  ' Muryar junaid ce ta katse ta da cewa "Wanene ƙanin naki"?   Cikin sauri sehrish tace "bafa maganarka muke yi ba" tayi maganar yayin da tasa hannu a cup board ta zaro kofin tare da wuce wa wurin dispenser saboda ta ɗebi ruwan zafin da zata haɗa masa dashi, "Koma meye dae zanji ne," ya faɗi yana ɗan hararar ta daga inda yake, Bayan ta haɗa masa takai masa nan ya zauna yana sha suna fira tare dashi, ________________________________ After magrib prayer motocinsu suka dunga shigowa cikin gidan da gudun gaske atare suka yi parking ɗinsu, Abbansu ne tare da SGR suka fito, motar dake bayansu kuma Su irfan ne tare da jabeer da khaleed, kana ganin su kasan sunji jiki, amma su da sauƙi babu alamar rauni ajikinsu sun dai jigata ne,   buɗe motar dake bayan tasu suka yi wadda fawan ne kwance acikinta, gaba ɗaya jikinsa sahun bulali ne ta ko'ina, saboda hasken fatarshi duk zanen bugun da miyagun su kayi mashi ya fito raɗau jawur wani wurin ma harya fashe, amma da yake ya samu emmergency treatment duk ansanya mashi magani awurin, babu riga ajikinsa gajeran wando ne kawai guntu suka barshi dashi, asaman ƙirjinsa hada ɗinki akayi masa, ba ƙaramin jiki ya ji ba yaji gata sosai, Amstrong ne babban na hannun daman SGR ya fiddo shi tare da Irfan suka tallabo shi sannan suka wuce dashi cikin gidan, har lokacin bai dawo cikin hayyacinsa ba saboda hodar da suka shaƙa mashi,    Suma sauran mutanen da suka halarta domin yi masu jaje duk suka harhaɗu nan suna tayi ma Abbansu Allah kyauta, daga bisani suka haɗu gaba ɗayansu izuwa cikin gidan,    Tun da Sehrish taji dirar motaci tarasa samun kwanciyar hankali burinta taga su wanene suka zo, a lokacin sun kammala aikace-aikacensu na kitchen fitowarta kenan daga wanka, ta buɗe closet dinta ta zura doguwar riga sannan ta matsa jikin window tana leƙensu bata samu damar ganinsu da kyau ba saboda mutanen dake zagaye ta ko'ina, Jiki asanyayae ta rufe window in gabanta na faduwa tsoranta kar ace wani ne ya rasu, hannu ta aza akanta tana ambaton "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un ya Allah kasa ba wani bane ya mutu,"  Cikin sauri ta bar wurin tare da  buɗe kopar ɗakin nata ta fito waje a lokacin itama Azmee tafito daga ɗakinta a ruɗe jikinta na sanye da zumbuleliyar hijabi alamar salla ta kammala yi, ko addu'a bata tsaya yi ba ta fito saboda jin jiniyar shigowar motocinsu,    tsayawa su kayi gaba ɗayansu suna son ganin abunda ke faruwa, gaba daya sun rikice ganin yarda Amstrong da irfan suka shigo da Fawan duk ciwuka ajikinsa saman 3 seater suka zaunar dashi saboda masu zuwa dubiya, Fitowa Ayaan da jahan sukayi daga ɗakinsu suma jin hayaniyar dake cikin gidan ganin fawan a wannan yanayin yasa su ƙarasawa da gudun gaske suka zube saman guiwowinsu agaban shi cikin tsananin tashin hankali suke cewa "fawan meya faru dakai haka? Waye yayi maka haka? Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,   Daker fawan ke iya kallonsu duk da baya iya tantance su wanene agabansa amma yaji muryarsu, juyawa su kayi suna kallon Irfam da jabeer don son jin ƙarin bayani,    Jabeer yace "Fawan bazai iya yi maku magana ba a halin yanzu baima san ko ku su wanene ba, addu'a kawai zakuyi masa,' jin haka yasa hawaye soma zuba daga idanunsu,   Shigowar da mutane suka soma yi ne yasa su samun wuri ƙasa suka zauna kowa ya zabga tagumi, kana kallon fuskar Abbansu kasan cewa acike take da tashin hankali saboda arayuwarsa ya tsani abunda zai ta6a masa jininsa,  Ganin SGR ya shigo yasa sehrish jin faɗuwar gaba, gaba ɗaya babu annuri a fuskarshi, white shirt ɗin dake ajikinsa duk shedar jini ne daya fallatsar masa hada hannunsa, ba jinin kowa bane face jinin waɗanda suka farmaki su fawan, mugun bugu sukayi masu na fitar shari'a gaba ɗayansu suna a headquater dinsu an killace su can domin horar dasu da kuma yin bincike akansu, Tuni jikin sehrish ya soma yin kerma saboda tashin hankalin da tagani ajikin SGR tunaninta ya gama bata cewa ko harbinsa akayine da bindiga shiyasa taga jini, hannu tasa ta rufe fuskarta tana kuka da gudun gaske ta juya ta koma ɗakinta saman gadonta ta faɗa tana cigaba da kukan,"   Abun ya ɗaure ma azmee kai ganin yarda sehrish ta gudu tana kuka kuma tasan ba don komai bane fa ce sai don ganin jini a jikin rigar sgr da hannunsa,    Ganin manyan mutane sun fara cika babban falon yasa azmee komawa cikin ɗakinta jiki asanyaye, zama tayi tana jiran mutane su ragu sai taje ta dubo shi,    Hannu Abbansu yasa ya ruƙo na Ayaan yace "taso ina son magana dakai,"  Tasowa ayaan yayi daga zaunen da suke yabi abbansu suka ɗanyi nisa da mutane sannan ya kallesa yace "Ina junaid yake"?   Ayaan yace "ina ji yana a ɗakinsa bana tunanin ya fita, Amma abba tayaya hakan tafaru da Fawan? Suwaye suka yi mashi haka? ya fadi idonsa cike tab da hawaye,   Dafa kafaɗarsa abbansu yayi shima fuskarshi tamkar zaiyi kuka yace "Ayaan bamu son ko su wanene ba, Babban yayan ku da Omar sune suka je wurin da suka farmake su, kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, yanzu haka akwai mutun 3 daga cikin miyagun suna a headquater ɗin mu,"    "Abba don Allah karku kyalesu akashe su kawai," ayaan ya faɗi cikin jin ɗaci aransa   "Ba zamu ƙyalesu ba ayaan, mutanene masu haɗarin gaske, babban tashin hankalin ɗaya daga cikinsu da muka aza shi saman kujerar lantarki muka bashi horo ya bamu wasu bayanai nacewa macace take basu Umarni duk wani kashe-kashen da suke yi a ƙasar nan,"!     waro ido Ayaan yayi cikin tsananin mamakin abunda Abban nasu ya faɗa masa, aruɗe yace "What! Mace kuma Abba? mace wannan dana sani?   "Of course Ayaan, ba kai kaɗae ba kowa daga cikin mu yayi mamakin jin hakan, yadda akasan mata da rauni amma har acikinsu asamu wata mai ƙarfin halin haɗa tawagar ƴan ta'adda masu farmakar mutane suna kakkashe su, Amma koma wacece insha Allah zamu ganota bi'iznillah zata ɗanɗani kuɗarta!"    Jinjina kai Ayaan yayi yana cewa "Insha Allah Abba, Allah ya tonu asirinsu aduk inda suke, abun yayi yawa wlh rashin imanin nan har ina? mutun baya tuna cewa shima wata rana zai mutu yabar duniyar ne?shin menene ribarka idan ka kashe wani bayan kai baka isa ka hana kanka mutuwa ba?    Kafin Abbansu yace wani abu muryar kanal yusif ta katse su da cewa "Abba ka matso kusa mutane suna son magana dakai,"   Amsa mashi yayi da "toh gani nan zuwa" sannan ya kalli ayaan yace "Abun dayasa na tambaye ke game da junaid kasan halin shi, muddin ya fito yaga halin da fawan ke ciki tofa zai iya sume wa ko ya zauce, dan Allah kusan yarda za'ae ku hana shi fitowa daga ɗakinsa indae yana ciki,"     Ayaan yace "Shikenan abba bari naje na duba shi," cikin sauri ayaan ya wuce upstairs ɗakin junaid, a hankali ya tura ƙopar ɗakin cikin sanɗa ya shiga, abun mamaki samun shi yayi saman gadon shi zaune ya toshe kunnan shi da headphone yana kallo acikin laptop ɗinsa baya jin duk wata hayaniya da akeyi acikin gidan,     Murmushi Ayaan ya saki sannan ya ƙara ja mashi ƙopar ɗakinsa dakyau ya rufe masa ita, sannan ya juya ya sauko down wurin su, Har wurin dare mutane suna ta zarya agidan sai wuraren ƙarfe 9:30 sannan suka fara raguwa, tuni Sgr ya wuce part ɗinsa saboda ya gyara jikinsa ga matuƙar gajiyar da yayi idonsa ma kansu daƙer yake buɗesu ga yunwa ga bacci, har lokacin zuciyar shi tafarfasa takeyi duk in ya tuna irin artabun da su kayi tare da miyagun nan, duk da sunci nasara akansu sosai, bakomai bane ya tsaya masa aran shi ba face wannan maganar nace wa macace take ɗaukar nauyin tawagar miyagun dake kashe-kashen, yaci alwashin cewa sai ya gano ko wacece ita,  yanayin salon nata ya nuna cewa hada ɗaukar fansa take yi,' 😳😳😳 A asibiti marshal omar ya barsu hussana a hannun Camila kafin zuwa da safe zaisa a sallame su, shi da major suka wuce izuwa gida saboda kiran wayarsa da ake ta faman yi ga kuma tsananin damuwar daya shiga game da halin dasu Fawan ke ciki, daker sehrish tasamu ta fito sam tagaza samun natsuwa ta ko ina, ta damu da yanayin da taga Sgr da kuma halin da fawan ke ciki, a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya sannan ta kwankwasa tare da jiran ta buɗe mata,    tana tsaye azmee ta bude ƙopan tana kallonta tace "kin gama kukan?  Shiru kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta,  "hmmmm me kike yi ma kuka ne ɗazu"? Cikin sanyin murya tace"babu komai Aunty azmee kawai nadamu ne da halin dana ga fawan,'   Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "gsky yaji jiki sosai, nima na tausaya masa bawan Allah, Yakamata muje mu duba shi, dama na jira ne mutane su ɗan rage sosai," Sehrish tace "ae nagama babu kowa a falon bansan inda suka kai shi ba," "Sun kwantar dashi ne, a ɗakin da suke kwantar da mara lafiya, bari nazo mu tafi tare, inyaso in mun dawo sai mu jera masu dinner ɗin duk da nasan abune mai wuya ma a samu wanda zai iya cin abincin, don duk suna cikin damuwa," tana fadin haka tashige cikin ɗakin bada jimawa ba ta fito sanye da mayafi, sannan suka jera da sehrish izuwa ɗakin dake anan downstairs, A buɗe suka same shi don haka su kayi sallama, muryar kanal yusif ce ta amsa masu tare da cewa "ku shigo ciki mana,"     shiga ciki sukayi sehrish har tsoran kallon jikin fawan takeyi, wanda ke kwance saman gadon idonshi arufe alamar ya samu bacci, Ayaan da jahad ne zaune daga gefen gadon sai kanal yusif dake atsaye, Azmee tace "Yusif ashe haka abu ya faru? Mu ba mu sani ba"!  Kanal yusif yace "Wlh kuwa aunty azmee abun babu daɗin ji, ƴan ta'adda ne su kayi masu kwanton 6auna, amma anci nasarar Cafke wasu daga cikinsu,"   Cikin nuna jimami aunty Azmee tace "Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin waɗannan mutanen, wlh duk jikina ya mutu dana ga fawan acikin wannan halin bawan Allah, Allah dae ya tashi kafaɗunsa,"   Suka amsa mata da ameen, sai lokacin sehrish tace "Yaya yusif ya mai jiki"?   Yace "Alhamdulillah da sauƙi sosai harma ya samu bacci,"    Tace "Allah ya bashi lafiya,"   "Ameen ," suka amsa mata  Kanal yusif yace "Aunty azmee ku matso kusa dashi kuyi mashi addu'a yana buƙatarta sosai," matsawa su kayi atare kusa da fawan suna yi masa addu'a tare da tattofa masa, daga bisani su kayi masu sallama suka fito waje   Kitchen suka wuce atare don sun shirya abincin dining azmee tace "bari na haɗa maki, ki kaima babban yayansu nasan zai buƙaci wani abun,"    "Toh," ta amsa mata, suna cikin kitchen ɗin haroon ya shigo cikin babban falon daga waje ya shigo ciki hango sehrish da yayi yasa shi wuce wa cikin kitchen ɗin, kamar yarda ya saba fado masu batare da sallama ba haka ya shiga,    ɗagowa su ka yi suna kallon shi hankalin shi kwance tamkar baisan meke faruwa ba, azmee tace "haroon me kake buƙata ne"?    tsoki ya ɗan ja tare da cewa "tun yaushe nake ta faman zarya ina jiran a jera mana abincin dare amma shiru babu, so ake akashe ni da yunwa ne"? yayi maganar fuska aɗaure yana kallon sehrish wadda tuni ta kawar da kanta,   Azmee tace "kayi haƙuri haroon, saboda halin da su fawan ke ciki ne ga kuma mutane shiyasa ba mu samu damar fitowa ba mun jera,"   Uban tsoki ya kuma bugawa wanda har sai da suka ɗan razana suka kallesa yace "And then so what? Mutuwa fawan ɗin yayi ne da zaku fake da cewa halin da yake ciki ya hana ku jerawa mutane abincinsu"? Ya tambaya a ƙule  Mamakine ya kamasu jin abunda yace yadda ya nuna ko ajikinsa halin da fawan ke ciki,     nuna sehrish yayi da hannu tare da cewa "Ke! ki kawo mun abinci na yanzun nan a bedroom ɗina ina jiran ki,   Cikin sauri sehrish tace "Ni babban yaya zan kai mawa yanzu, sai dai ko in aunty azmee ta jera a dining ka zauna ka ci,'    Zaro ido haroon yayi afusa ce yace "Ke! Ni kike fadama cewa wani wai babban yaya zaki kaima abinci"? Ke ga futsararra ko"? ya tambaya yana faman huci    da ido azmee tayi ma sehrish alamar tayi shiru da bakinta, tsit tayi bata kuma cewa komai ba,   cike da bada umarni yace "Ina jiran ki ki kawo mun idan kuma ba haka ba zaki ga mai zai biyo baya," yana faɗin hakan ya fuce daga kitchen ɗin,   Murya tamkar zatayi kuka tace "Aunty azmee nifa bazan kai masa ba Allah,"   Azmee tace "sehrish ki daure ki kai masa, nikaina na tsorata da yarda yake mana magana, ina tunanin kamar yayi shaye-shaye ne baya cikin hayyacinsa,"    "Aunty azmee nifa bazan kai masa ba,kema da kan ki kince baya cikin hayyacinsa yanzu in naje zai iya kai mun bugu,"    ganin ta dage akan cewa ba zata je ba yasa Azmee cewa "to shikenan bari ni nakai masa, ke kuma ki kaima Sgr nasa," ajiyar zuciya sehrish ta saki tare da cewa "to," bayan sehrish ta kammala shirya masa a tray ta wuce upstairs part ɗinsa, sallama tayi ba'a amsa ba don haka tashiga daga ciki, babu kowa acikin falon alamar yana a cikin bedroom ɗinsa,    takawa tayi izuwa ƙopar bedroom ɗin nasa tayi masa sallama kusan sau uku sannan ya amsa mata da cewa"Come in,"   Shiga ciki tayi zuciyarta na dar-dar lokacin da ta aza idonta akanshi yana zaune gaban dressing mirror saman chair din dake gaban madubin, ya sanya tafin hannayensa ya tallabo gefe da gefen fuskarsa ya zabga tagumi agaban mirror, sam babu riga ajikin shi daga shi sai short green colour, da alama ma daga wanka ya fito yagaza yin komai shine ya zabga tagumin, Sumar kanshi duk ta barbazo ta rufe masa gefen face dinsa, da wasu siraran gashi da suka sauko ta saman fuskarsa idonshi na arufe saboda gajiyar da ta lullu6e ga66ansa da kuma baccin da yake ji ga kuma yunwa duk shi kaɗai tsayawa sehrish tayi jiki asanyaye tana kallon shi tsananin tausayin shi ne yakamata ganin yarda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, alamar baya jin daɗi   Ta jima tana kallon shi kafin ta ɗanyi gyaran murya tace "dama abinci ne na kawo maka, bansan ko kana buƙata ba," ta fadi adan tsorace gudun kar tayi kuskure a maganarta,    daker ya buɗe bakinsa tare da cewa"keep it on the table, then i wanna see u," gabanta ne ya faɗi rass ! jin abunda yace na yana son ganinta ƙarasawa tayi ta ajiye masa dinner din saman table ɗinsa, sannan ta matsa kusa dashi ta tsaya sannan tace "gani,"   Hannu yasa ya ɗauko wata ƙaramar kwalba ta magani daya ajiye a saman mirror din sannan ya miƙa mata tare da cewa "rub it on my back," ya fadi tare da kifa kansa saman gaban mirror ɗin yadda zata samu damar murza masa maganin, tama rasa ta ina zata fara shafa masa shi, gaba daya duk tabi ta rikice wai yau itace sgr da kansa ya bata magani don ta shafa masa abayansa, jikinta har kerma yakeyi tsoranta kar ta fasa masa fatar bayansa saboda hasken fatar fes tamkar in kasa yatsa jini zai fito,   Matsawa ta ƙara yi dab dashi sosai sannan ta buɗe mufin kwalbar, tasa yatsa ta lakuto maganin tare da ɗan russinawa ta lakuta masa shi abayan, sannan tasanya hannunta a hankali tana shasshafa masa shi, tun da Allah ya halicce ta bata ta6a jin skin mai tsananin laushi da daɗin tabawa ba irin fatar bayan sgr,  Shi kuwa ajiyar zuciya kawai yake saukewa saboda relief daya fara samu sosai na ciwon da ga6o6insa suke masa, tun sehrish nayi masa da hannu ɗaya har takai ga ajiye kwalbar maganin ta sanya duka hands ɗinta a faffaɗan bayansa tana yi masa massage, a tunaninsa in ta kammala zata cire hannunta ne, amma sai yaga ta zarce gaba ɗaya babu alamar zata daina shafa masa gashi kuma yaji ko'ina na bayansa yaji maganin sosai, shiru kawai yayi bai ce komai ba, almost one hour kenan sehrish na shafa masa magani har sai da ya ɗan ɗago da kansa daga kwancen da yake tare da cewa "Har yanzu maganin bai shafu bane"? Cikin sauri ta janye hannunta tare da ɗagowa tana kallonsa suka haɗa ido ta cikin mirror,   gabanta ne taji ya ƙara faɗuwa rass ganin yarda kwayar idonsa ke shining sai taga tamkar tana canza launi ne daga blue zuwa green,.     sunnar da kanta tayi ƙasa tana faman haɗe yatsun hannunta dake dankare da maganin data shafa mashi, lumshe idonsa yayi tare da sake buɗe su yace "kin haɗo mun da coffee ne? ya tambaya a kasalance hakan ba ƙaramin kashe ma sehrish jiki yayi ba, tuni ta nemi natsuwarta tarasa sai ta kama en ena tana faman wurwurga ido  "Its ok, idan babu akawo mun shi," ya faɗi tare da mayar da idonshi ya lumshe su, Juyawa sehrish tayi cikin sauri ta fuce izuwa kitchen donta haɗo masa, a lokacin har azmee ta kammala shirya masu abincin dinner ɗin a dining amma babu kowa asaman shi alamar basu kaiga fitowa ba,  tayi mamakin hakan duk da tasan cewa duk suna cikin damuwa ne,bata ji daɗin hakan ba, tasa ba ganin mutanen gidan cikin raha suna nishaɗi suna cin abinci yau kuma wayaam babu kowa, Yau da gobe kenan,    tana acikin kitchen ɗin bayan ta kammala haɗa masa coffee din ta ruƙo cup ɗin a hannunta, sai ga haroon ya faɗo mata kamar daga sama cikin sauri taja da baya hankalinta atashe, daga shi sai vest da singlet, shu'umin murmushi ya saki yana kallonta yace "ke shine nasa ki kaimun abinci kika ƙi ko? Ke ga isassa mai walkin sa harni ɗan masu gida zan saki aiki, ki bijire mun," ya faɗi yana kallonta   Murya na rawa sehrish tace "kayi hakuri dama na fara kaima babban yaya ne, kafin na kawo maka nakan......'  Bata ƙarasa ba ya katse ta da cewa "Sorry for your self sehrish! wlh kin shiga uku ! kin jefa kanki cikin masifa, daga rana irin ta yau inaso kullum ki kasance cikin yin sallar dare kina rokan Allah akan ya kare ki daga Sharrina," zaro ido tayi tana kallonsa jin abunda yace cikin tsananin tashin hankali tace "saboda me zaka ce haka"? laifin me nayi maka, dan Allah kabarni inyi rayuwata cikin salama,"   Fashewa da dariya yayi kafin ya tsagaita da cewa "kinsan wani abu?kina da kyau sosai musamman idan kika tsorata idanunki ba ƙaramin fizgata sukeyi ba, idan kika amince a shirye nake dana aure ki, kuma zan shiryu nadaina duk wani abu da nake yi, amma idan kika bijire mun I pity u wlh," cikin sanyin murya yake yi mata magana,.   Tamkar zatayi kuka tace"Dan Allah na roƙe ka kayi hakuri nidai ka fita daga cikin rayuwata, kabarni dan Allah kaje can ka samu mace irinka ka aura, amma ni ina da wanda nake so," tayi maganar tare da bi ta gefensa gabanta na faduwa ta wuce cikin sauri,   murmushi kawai haroon yayi tare da jinjina kansa aransa yace "nasan ba kowa take hari ba face wancan mai zubin ifritan, ni kuma ba zan ta6a bari hakan ta faru ba, target ɗina na farko da zanyi zan fara 6ata sunanki ne a wurinsa," yana fadin hakan ya saki shu'umin murmushi tare da wuce wa room ɗinsa   Maganganun da haroon ya faɗa mata sun tsaya mata arai, tunaninta ya rayuwarta zata kasance nan gaba acikin gidan batasan me haroon zai yi mata ba, tana tunanin tana tattaka stairs ɗin jiki amace, adai² lokacin Marshal ya shigo gidan cikin sauri saboda yarda yake agajiye shima, har sai da ta juyo daga saman stairs din ta ɗan kalle sa, ta other side ɗin yabi ya wuce part ɗinsa da hanzari sam bai lura a ita ba,    bakomai bane ya faɗo mata arai face yaran da taji yace zasu zauna gidan Uncle Abusufyan ɗinsu, ko ya ɗauko su? ta tambayi kanta  cikin sauri ta wuce part ɗinsa bedroom ɗinsa ta shiga da sallama ya iznin shiga, a lokacin harya dawo gefen bed ɗinsa ya zauna yana cin abincinsa, yau ba sai ya jira anyi saving ɗinsa,   ƙarasawa tayi kusa dashi sannan ta samu wuri agefen plate ɗin abincinsa ta ajiye masa cup ɗin,"  A hankali ya furta "thanks,' a tunaninsa zata tafi amma sai yaga tayi masa tsaye akansa, sam bata son ta tafi tabarshi saboda a ganinta in ta tafi bazai ƙarasa cin abincin bacci zai iya ɗakarsa, Hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin data kawo masa sosae yasha, bayan ya kammala ya ajiye shi, sannan ya gyara kwanciyarshi ya kwanta luf abunsa, ya janyo blanket ɗinsa ya rufe har zuwa chest ɗinsa nan take bacci ya ɗauke sa,  bata bar bedroom ɗin nasa ba sai da ta tabbatar tayi masa addu'a tukunna tasa hannu ta kwashe kayan abincin acikin tray ta fuce dasu a hannunta,    Kitchen ta koma da hanzari ta haɗa ma Marshal Omar nasa shima acikin tray sannan ta wuce masa dashi part ɗinsa, tana shiga a lokacin ya fito sanye da jallabiya fara wuri ya samu asaman 3 seater ya zauna hannunsa ruƙe da wayarsa ganin sehrish yasa shi sakar mata murmushi tare da cewa "kamar kinsan a yunwace nake abunda nake jira kenan,"   Murmushi ta saki tare da ƙarawa ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗin dake a gabansa sannan tace "Ya mai jiki ya omar, naji abunda ya faru Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin su,"   "Ameen Ameen," ya amsa mata, hannu tasa ta buɗe warmer tare da ɗaukar plate da saving spoon zata zuba masa abinci taji yace "baki tambaye ni twins ɗina ba"? Murmushi ta ɗanyi tare da ɗagowa ta kalle shi tace "dama ƴan biyu ne"? Yace "eh kamannin su ɗaya sak, ke ma haka fuskarki irin tasu ce sak komai da komai,"    gabanta ne taji ya faɗi jin abunda omar yace dakatawa tayi da zuba mashi abincin tana son tunano wani abu arayuwarta amma sam takasa tunawa, tabbas tana jin cewa akwai wani abu da ta manta arayuwarta mai matuƙar muhimmanci agare ta, a duk lokacin da tayi ƙoƙarin tunawa sai taji zuciyarta tayi mata wani irin nauyi sosai, "Wata rana zan kawosu ku ga juna, saboda inaso ki ga abun al'ajabin da nake son nuna maki," Cikin sauri tace "Shikenan ya Omar Allah ya kaimu lokacin nima zanso nagansu," ta jima suna dan fira dashi kafin daga bisani ta bar part ɗin nasa ta koma ɗakinta,   Bayan Omar ya kammala cin dinner ɗinsa fitowa yayi tare da wuce wa ɗakin da suka kwantar da fawan   Yanayin daya samu Twis zaune zun zuba mashi ido ga kanal yusif shima zugudum duk cikin jimami, gyaran murya yayi duk suka ɗan ɗago kana yace "ku tashi ku je ku kwanta, tun da ya samu bacci"    Amsa mashi su kayi da "toh" sannan suka miƙe tare da fuce wa daga ɗakin shima yusif yayi yabi bayansu, zama Omar yayi daga gefen fawan dake ta faman sharar bacci, addu'o'i ya shiga karantowa yana tatto fa masa, ya jima yana yi masa addu'a sannan ya tashi yabar ɗakin tare da tufe masa ƙopa, **************** Wuraren ƙarfe sha biyu ya fito cikin sanɗa hannunsa ɗauke da pillow yana duddubawa yaga in ba kowa duk sunyi bacci lokacin murmushi ya saki tare da cewa "sheggu saboda wancan ɗan shilan shine duk suka susuce har suka gaza cin abinci, bari na ƙarasa shi lahira sai in ga ya zasu yi, zasu bi shi ne  Yana faɗin hakan ya wuce ɗakin da suka kwantar da fawan cikin sanɗa ya tura ƙopar tare da sa ƙafa yashiga cikin, bin shi yayi da kallo jinjina kansa yayi sannan ya lalla6a ya haye saman gadon tare da ɗaga pillow ɗin ya taushe ma fawan hancinsa dashi , nan take fawan yafarka tare da zazzare idanunshi yana mutsu-mutsu sam bashi da sauran ƙarfi ajikinsa da zai iya kwatar kansa........... ... ... sai faman kiciniya fawan yake yi saboda ya kwaci kansa daga hannun haroon wanda ya taushe masa fuska da pillow da mugunta ma yake kara danna masa shi, tun fawan yana wutsil wutsil da ƙafafunsa numfashinsa na kokarin daukewa gaba daya har jikinsa ya fara saki, suna cikin wannan halin aka kwankwaso kopar da karfin gaske,a wani irin tsorace haroon yayi wurgi da filon dake hannun shi, yayi wuff tamkar giftawar walkiya ya afka bayan labule ya boye yana faman zazzare idanun shi kamar na mujiya tsoran shi kar ace wani ne ya taso cikin daren nan, Hannu yasa a hankali yaɗan buɗe labulen don yaga kowanene, gabansa ne yayi bugun bugu ganin Abbansu ya shigo ciki jikinsa sanye da jallabiya fara, cikin sauri haroon ya mayar da labulen ya rufe ruff tuni zufa ta soma tsattsafo masa a jikinsa tamkar wanda aka tsamo daga kogin maliya,     ganin yarda fawan ya tashi zaune saman gadon yana faman hargowa yana fadin "zasu kashe ni ! bansan me nayi masu ba! Sun biyo ni don su kashe ni, ku ce musu su daina azabtar dani !!!! Gaba ɗaya ya zauce sai zuba sambatu yake yi yana zazzare ido,    A hanzarce Abban nasu ya ƙarasa tare da haye wa saman gadon dab dashi yana cewa"fawan sannu ya jikin? ka dawo cikin hayyacin ka ko? ka kwantar da hankalin ka, kana a gida yanzu babu wanda zai iya cutar da kai,'.      girgiza kai fawan yashiga yi yana sake maimaita cewa "Har yanzu suna nan, bibiyata suke yi so suke su kashe ni, ni bansan me nayi masu ba," yana magana daker daker yake sakin numfashi, hancinsa har ya fara bleeding kaɗan jinin ke ɗigowa,    tallabo fuskarsa Abban nasu yayi tare da ɗago da ita don ya kalle shi sosai yace "fawan Ni ne fa,Abban ku ina tare dakai, babu wani anan da zai cutar da kai,"   A hankali fawan ke kallon Abban nasu yayin da idon shi ke rurrufe wa yace "Abba ruwa zan sha," ya faɗi agalabaice,     Cikin sauri Abban nasu ya matsa tare da kai hannun shi saman bedside drawer ganin dakwai bottle water mai sanyi ajiye asama, ɗauko wa yayi tare da buɗe murfin ya kwafa masa abaki yana sha, jikin shi har wani kerma yake yi tamkar zai kwace roban ruwan daga hannun Abban nasu daya kwafa mashi, ganin yarda yake shan ruwan throat ɗinsa har wani sauti yake fitarwa kwattt!kwattt!! Saboda yarda yake kurbarsa a zafafe, ba ƙaramin tausayi yaba Abban nasu ba, tamkar ya zubar mashi da kwalla haka yake ji, daurewa kawai yake yi   Sai da ya shanye kusan rabin ruwan sannan ya janye mouth ɗinsa alamar ya ƙoshi, sannan Abban nasu ya rufe robar ruwan ya mayar da ita saman side drawer din ya ajiyeta,   Sannan ya mayar da idon shi kan fawan dake ta faman sauke ajiyar zuciya yana fidda sound na radaɗin ciwo abakinsa,   Haroon daka la6e acikin labule yace "shegen yaji dannar manya,an gaya ma jin ƙamshin mutuwa wasa ne,dole ka nemi ruwa yaro, ba don jatuminka ya faɗo cikin ɗakin nan ba, da yau saina aika ka barzahu wurinsu munkar, gskiya Abba ya kawo mun cikasss amma ba komai mu haɗe gaba,' ya faɗi yana cizon la66ansa,   Haroon kenan duk da yana cikin tashin hankali amma hakan bai hana shi sambatun nan nashi ba, mutuwa ce kawai zata iya zuge zeep ɗin bakinsa,  muryar shi na rawa yace "Abba ashe zan ƙara rayuwa? abba nasha wahala sosai tamkar bazan rayu ba,ashe da rabon na sake ganinku a idona"? Ya faɗi yayin da idonshi ke zubar da kwalla,    shima Abban nasu jiki asanyaye yace"Fawan nasani wlh,nashiga damuwa sosai game da halin da kake ciki har nagaza runtsawa saboda son nazo naga wani hali kake ciki,kayi haƙuri fawan iya cuta dae sun cuce ka sosai sun raunata dukkan ga66an jikinka, amma nayi maka alƙawarin cewa ɗaya daga cikinsu bazai sha ba, wlh muddin ina da raina da kuma lafiyata saina ƙuntata duk wani jin daɗinsu na duniyar nan,"   Lumshe ido fawan yayi tare da kwantar da kanshi a kafaɗar Abban nasu yana sauke ajiyar zuciya sannan yace "Abban sunce fansa suke ɗauka akan family ɗin mu,wannan harin da suka kai mana, ba don kowa su kayi shi ba face saboda mu kawai,"  Jin wannan maganar ta fawan tasa zuciyar Abban nasu yin wani irin bugu duk da yasan maganar revenge ɗin amma baisan cewa akan ƴa'ƴansa bane abun zai afka,   "Insha Allah, Allah bazai ta6a Basu nasara ba fawan,zamu tashi tsaye wurin ganin mun kawar da koma su wanene su,Kuma zamu dage da addu'a akan Allah ya tonu asirinsu ya Kuma Kare Mana zuri'ar mu da dukkan al'umar musulmi,"   "Ameen Abbana," ya amsa mashi daker,   Haroon dake a la6e bayan curtains duk yana sauraronsu gaba daya ya ƙagu abban nasu ya fuce daga dakin shima ko ya samu ya gudu,tuni kafafunsa suka soma daskare wa suna mashi raɗaɗi saboda tsayuwar da yayi, ga wani irin fitsari daya matse shi, sai uwar zufa ke wanko masa daga fuskarshi, runtse idanun shi yayi yana cewa "wayyyo Allah na, ko yaushe wannan tsohon zai ware nima in samu in gudu,lallaima mutumin nan wato saboda wannan ɗan shilan shine harya gaza yin bacci, ya wani kwaso kafafunshi yazo don ya gan shi,ina sane da komai wato ya daura son duniya ya aza masu,duk ranar dana hallaka ɗaya daga cikinsu zanga in haukacewa zaiyi ko kuma zaiyi suicide ne,'    Ya faɗi yana cizon lips dinsa yana wani irin huci, bude idonshi yayi tare da sa hannu ya sake bude labulen a hankali ya leƙa su, har time din abban nasu na zaune dirshan saman bedmattress din, fawan kuma ya kwantar da kanshi a kafaɗar shi,da alama ma bacci yayi awon gaba dashi gaba ɗaya ya lafe masa kwance luffff abunsa,    Tuni ran haroon ya ƙara 6aci saboda takaici da baƙin cikin dayake ji aduk lokacin daya ga Abbansu na nuna ma ƴa'ƴan alexandra soyayya,zuciyar shi tafarfasa take yi saboda jin haushi, mayar da idon shi yayi kan pillow dinshi da yayi wurgi dashi kasa, nan gabansa ya faɗi tsoranshi kada abban nasu yaga fillon don za'a iya samun matsala,   Bari dae in taƙaice maku zance,Abban su bai bar ɗakin ba anan bacci ya ɗaukesu su duka biyun azaune fawan kwance a shoulder ɗinshi,   Kamar yarda suka kwana a zaune suna bacci haka Sir Commender Haroon ya kwana a tsaye ba bacci duk yarda yayi motsi zai fito sai Abban nasu ya buɗe ido, hakan ne ya hana shi fitowa daga bayan labule,    ya kuke tunanin wanda  ya kwana atsaye idonshi buɗe fuskarshi zata kasance, koda yake fa soja ne 😂    (Wata dae tace commendern ƴan Iska dae, Bana sojoji ba)😹😹😹 ****************************Morning tun da sassafe sehrish tafarka daga guntun baccin daya ɗauketa bayan Sallar asuba anan saman sallayar ta kwashe da bacci, duk jikinta amace tafarka sai faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji, gashi yesterday night bata samu enough sleep ba saboda tayi nafilfilin dare,    tunawa da school yasa ta yin hanzarin tashi tashiga toilet shaf shaf tayi wankan ta, fitowa tayi jikinta ɗaure da towel fari, a bakin ƙopar toilet ɗin ta tsaya tana kallon uniform ɗinta da sukayi uban squeezing tun jiya da tadawo school ta cicciresu ta jefar saman gadonta bata ninke su ba kuma anan tabarsu,girgiza kai tayi sannan ta ƙarasa agaban mirrow ta tsaya tana shafa body oil ɗinta,bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗinta, hannu tasa ta ɗauko ɗayan uniform ɗinta mai pencil skirt ɗin nan sannan ta dawo ta ajiyesu gefen gadon tashiga zura su ajikinta, tana cikin sa kayan maganar haroon ta faɗo mata aranta nace wa ta fara sallar dare domin neman tsari daga sharrin shi, tabbas maganarsa ta girgiza ta saboda tun daga lokacin da ta dawo daki at midnight tafarka tayi nafilfili saboda neman tsari daga sharrin shaiɗanin mutun irin haroon, ta jima tana jin cewa wasu abubuwa zasu faru tabbas acikin gidan!!!!! duba da irin mafarkin da tayi a baccinta na jiya, kuma taci Alwashin cewa ashirye take data fuskanci duk wani abu da zai taso ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wani da zaizo don tarwatsa rayuwarta ko kuma family ɗin SALAHUDDEEN HUSSEIN, Hakan na nufin SEHRISH ta shirya zama AYYANA wato mai bama family ɗinsu kariyyya daga miyagu irinsu Haroon da kuma ire-irensa masu irin wannan mummunan kuɗirin,nace ba Allah ya ba mai rabo sa'a,     Tana cikin wannan tunanin azmee ta kwankwaso ƙopar ɗakin tana cewa "Allah sa dai kin tashi," Murmushi sehrish tayi a lokacin ta kammala sanya uniform ɗin, ba ƙaramin kyau sukayi mata ba tafito ɗass especially skirt ɗin da ya bi shape ɗin jikinta sosai,    ƙarasawa tayi ta buɗe mata ƙopar ɗakin tana cewa "ae tun ɗazu na tashi nama kammala shirya wa,"   Bin ta da kallo azmee tayi tana jinjina kai kafin tace "To fa yau wankan skirt aka ɗauka? masha Allah kinyi kyau ƙanwata, ya maganar breakfast fa? ta tambaya tana kallon ta,   Sehrish dake ta faman murmushi tace "aunty azmee yau a school zanci abinci na gaskiya,amma zansha koda tea ne,"   Azmee tace "okey, shikenan bari na kawo maki tea ɗin,' gefen gado ta Zauna tana jiran dawowarta, A 6angaren haroon kuwa bashi ya samu damar barin ɗakin da fawan ya ke ba har sai wuraren sallar asuba bayan abbansu ya kwantar da fawan dake ta faman sharar bacci a kafaɗarsa, sannan ya samu yabar ɗakin don zuwa yin sallah, sir commender haroon na ganin haka ya lalalla6a ya fito ya sungumi pillow ɗinsa daya shigo dashi, sai da ya jinkirta abakin ƙopar ɗakin ya tabbatar da cewa sun harhaɗu sun tafi gabatar da sallar asuba sannan ya koma ɗakin shi, agalabaice ya hankaɗa kopar bedroom ɗin nasa yayi wurgi da filon hannun shi,sannan ya afka toilet don tuni mararsa ta ɗaure saboda fitsarin dayayi ta ruƙo har na tsawon awannni, fitowa yayi daga toilet ɗin har wani biji biji yake gani saboda yarda idanun shi suka galabaita sun kumbura sunyi jawur saboda rashin baccin da baiyi ba, saman gadon shi ya afka batare da tunanin yin sallar asuba ba, sai ma addu'a daya shiga yi yana cewa "ya Allah ka yafe mun,zan ɗan rama baccin da banyi ba da safe in na tashi zanyi sallar anjima,'yana faɗin hakan ya shiga sharar baccin shi, Babu wanda ya tayar da junaid daga bacci saboda basu son kwata-kwata yaga fawan ko kafin su tafi yin sallar asuba sai da Abbansu ya buɗe door ɗin ɗakinsa ya same shi baje magashiyyan yana sharar bacci rungume da pillow, murmushi kawai yayi tare da rufa masa door ɗin suka wuce mosque, turo ƙopar azmee ta ƙara yi hannunta ɗauke da tea set ta miƙa ma sehrish cikin sauri sehrish tasa hannu ta kar6a tana cewa "Nagode aunty azmee," Azmee tace "ki hanzarta fa kada kiyi late dayawa,"   "Toh," ta amsa mata sannan ta shiga shan tea ɗin, . har azmee zata fita sehrish tayi saurin cewa "Aunty azmee dama inaso nakaiwa babban yaya nashi kafin natafi school,"    tsayawa azmee tayi hannunta ruƙe da door handle ta juyo ta kalle ta tana ɗan murmushi tace "i knew, raina sai da ya bani cewa sai kinyi magana akan RAFAYET, ,ɗan sunnar dakai sehrish tayi tana kallon tea ɗin dake hanunta yana faman tiririn zafi    "Ni nake maki magana ba tea ɗin dake hannunki ba, naga kin zuba mashi ido,' guntun murmushi sehrish ta saki kafin ta ɗago tana kallonta daƙer ta iya cewa "aunty azmee baya jin daɗi jiyan nan that's why nake so nakai masa breakfast ɗinsa,nasan zai buƙace shi,"   Sakin baki azmee tayi irin mamakin nan tace "to ko dai kece ALEXANDRA ban sani ba,'   shiru sehrish tayi tana sakin murmushi saboda tagane cewa wannan sunan mommynshi ne,shiyasa azmee ta kirata da sunanta,    fuce wa azmee tayi tana cewa "shikenan kiyi sauri kizo ki kai masa breakfast ɗin," tana jin haka tayi saurin ajiye tea ɗin hannunta asaman bedside drawer inda kayan tea ɗin suke,    hijab ɗinta ta ɗauko ta zura ajikinta yar dai² shoulders ɗonta, sannan ta wuce kitchen ɗin tayi mamakin ganin yarda azmee tayi uban aiki duk ita kaɗai, da alama ma tun bayan sallar asuba bata koma bacci ba,saboda tasan cewa dole manyan baƙi su hallara saboda zuwa duba fawan, ..shirya ma sehrish tayi breakfast ɗin SGR acikin ƙayataccen tray sannan ta miƙa mata, ruƙo wa tayi a hannunta sannan ta miƙi hanyar zuwa part dinsa, tana cikin tafiya taji anyi gyaran murya juyowa tayi da sauri don taga wanene junaid ne tsaye jikinsa sanye da shirt pulover tare jeans, ......har ya kammala shiryawar shi cike da ɗaukin kaita makaranta ya fito, sai faman zabga murmushi yake yi sam baida wata damuwa, ɗan dawowa baya tayi dai² saitinsa sannan tace "junaid ! Ya akai naga kana ta faman zabga murmushi, kai bakasan meke faruwa ba acikin gidan nan"? tayi maganar tana kallon shi, ..cikin mamaki junaid yace "kamarya kenan? meya faru ne ni bansan komai ba,"   Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"jiya wani abu ya faru mai matuƙar raxanar wa, zan faɗi maka amma bari nadawo," ta faɗi tare da saurin haye wa upstairs tana murmushi, taso ta faɗama junaid abunda ya faru amma azmee dake tsaye daga kitchen tayi mata alamar karta kuskura ta faɗa masa, shine dalilin dayasa tace mashi ya bari tadawo, . tuni jikinsa yayi sanyi a ƙagare yake daya ji mai reesh zata sanar dashi,   Kitchen ya wuce wurin azmee da sallama ya shiga sannan ya gaishe ta yana cewa "Aunty azmee a shirya mun breakfast a yunwace nake, gashi inaso nayi sauri nakai sehrish school,   Sakin baki azmee tayi tana kallon shi kanta ya gama ɗaure game da lamarinsu su duka biyun, ita tagaza samun natsuwa saboda son takaima babban yaya breakfast ɗinshi, shi kuma junaid damuwarsa yakaita school,kowa da wanda ya damu dashi kenan,   Zama yayi saman dining chairs yana jiran azmee dake shirya mashi bf ɗinsa ta kawo mashi yaci, Acan ciki kuwa bayan sehrish ta isa part ɗinsa da sallama ta shiga baya cikin falonsa don haka ta wuce bedroom ɗinsa tsayawa tayi daga bakin door ɗin sannan tayi masa sallama, da wannan sexy voice ɗin nashi ya amsa mata, tare da bata permission din shiga daga ciki, .a hankali tasa ƙafarta ta shiga ciki tsayawa tayi zuciyarta na faman bugawa ba ƙaramin kyau yayi mata ba, ya juya bayansa yana tsaye a agaban mirrow jikinsa na sanye da bathrobe white colour wadda ta tsaya mashi dai² guiwarsa,a buɗe rigar take bai ɗaure igiyarta ba, amma akwai shorts ajikinsa,sumar kan nan tashi ta zubo mashi tayi irin Curly ɗin nan dark brown very smooth ta rufar masa abayansa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba, ...gaba ɗaya jikin sehrish ya gama mutuwa murus cos aduk time ɗin da tayi arba da wannan kyakkyawar surar jikin tashi rasa hankalinta take yi gaba ɗaya duk ta bi ta susuce,tana hangen shi ta cikin mirror saboda madubin yana facing dinta,   tabbas yaji alamar shigowar mutun tun da harya bada iznin shigowa daga ciki amma har yanzu baiji an motsa ba, a hankali ya ɗago da blue eyes ɗinsa ta cikin mirror ɗin karaf suka sauka akan na rishi dake tsaye jikinta na rawa ɗan zaro idanun nata tayi tana kallon nashi dake kallon cikin nata ta cikin mirror, hankali atashe cikin tsananin tsoro tayi saurin sunnar da nata ƙasa gabanta na faɗuwa,   gyaran murya ya ɗanyi kafin yace"a ajiye mun shi a palor, sannan agyara mun bedroom dina,' amsa mashi tayi da "toh" sannan ta juya ta fuce tana faman sauke ajiyar zuciya, a saman table ta ajiye masa sannan ta ɗan tsaya tana jiran ya kammala kimtsawa,after some minutes ya fito jikin shi sanye da tunic shirt milk colour tare da trouser, sai ƙamshi yake fitarwa, shiga cikin falon yayi ya samu wuri ya zauna saman royal sofa ɗin sannan ya shiga yin breakfast ɗinsa anatse, Wuce wa sehrish tayi cikin bedroom ɗinsa ta shiga gyara masa shi komai agyare yake,bedsheet ɗinne kawai da yayi squeezing ya tattare inda ya kwanta, cire shi tayi sannan ta musanya masa wani sabo mai kyan gaske ta shimfiɗa masa, bayan ta kammala gyara ko'ina cikin sauri tafito saboda tunawa da school karta yi late, a lokacin da ta fito samun shi tayi yana yin waya da alama kan fawan suke magana da mutumin daya kira shi awaya,        Kama hanyar fita tayi har takai baƙin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi gudun kar ace yana buƙatar wani abu gashi zata tafi batare daya bata izni ba, ganin alamar mutun ta wutsiyar idonshi yasa shi ɗan juyawa karaf suka haɗa ido da sehrish dake tsaye tana kallon shi cikin sauri tace "Can i go"? tayi maganar aɗan tsorace,   Lumshe idonshi yayi tare da ɗan jinjina kai alamar eh,   Murmushi sehrish ta saki sannan ta fuce cikin sauri aranta tana cewa "Sannu bata hana zuwa,"😇   Saukowa down tayi cikin sauri adai dai lokacin ta ji saukar motoci cikin gidan alamar sunyi baƙi, kitchen ta wuce anan tasamu junaid zaune saman dinner table harya kammala cin breakfast ɗin shi, yana ganinta yace "dama yanzu nake shirin biyo ki, bansan meya tsayar dake ba gashi har time ya ƙure ma,da ace ana bugu a school ɗin wlh da kinsha bulala yau," dariya sehrish tayi jin abunda yace   "Bari na ɗauko school bag dita," ta faɗi tare da juyawa cikin sauri ta koma bedroom ɗinta,   Sallama junaid yayi wa aunty azmee sannan yabaro kitchen din, jin sallamar Cg Abbas yasa shi ɗagowa cikin tsananin farin ciki yace "Yaya Abbas kaine tare da Aunty Amani !!!"  murmushi suka saki gaba ɗayansu da yake tare suka zo shi da AMANI yana sanye cikin shigar shadda maroon color ita kuma tana sanye da Arab gown white colour mai kwalliya ajikinta na duwatsu tayi rolling veil a kanta, ba ƙaramin kyau tayi ba,   sam junaid ya gaza rufe bakinsa don murna, buɗe mashi hannu abbas yayi cikin sauri junaid ya ƙarasa tare da faɗawa ya rungume shi sosai ajikinsa yana cewa "i really missed u our last born, duk da ina fushi dakai saboda baka son zuwa kawo min ziyara,' yayi maganar a lokacin da ya raba jikin shi dana junaid,   ɗan turo mouth dinsa yayi cikin shagawa6a yace "Yaya Abbas saboda me zaka ce kana fushi dani dan Allah, bakasan yarda na damu dakai ba koda yaushe inason zuwa amma shaiɗan ya hanani zuwa,' dariya sukayi gaba ɗayansu jin abunda junaid yace,   ɗan gyaran murya amani tayi masa tare da cewa"Junaid ni baka ganni bane"?   matsawa yayi tare da kai hannu zai rungumeta ajikin shi, ae kuwa a razane Abbas ya finciko rigarshi tare da janyo shi baya baya yana cewa "Sannu mati na mata,!matar tawa zaka rungume agabana? salon mu koma gida ta juya mun baya ko?"   Fashewa da dariya Amani tayi shima junaid ɗin dariyar yake yi cikin jin kunya ya sunnar dakai, shi aganin shi ba wani abu bane don ya rungume matar yayan shi, duk cikin waye wa ne,   Abbas ya kuma cewa "Oh ni junaid? Yanzu fa in na ƙyale ka sai ka rungume ta ko"?    ɗaga mashi kai yayi alamar Eh, hannu abbas yasa tare da ɗan jan kunnan shi har yayi ƴar ƙara yana faɗin "wayyo yaya Abbas karka cire mun kunne na in rasa na jin magana,"    "Hanzarta ka cire masa kunnan, hukuma ce zata raba ni dakai," acewar Abbansu wanda bai jima da fitowa ba ganin su yasa shi tunkaro su,    Murmushi suka saki gaba ɗayansu, adai dai lokacin Sehrish tafito daga ɗakinta, harta sanya Sandals ɗinta taruƙo school bag ɗinta, ƙarasawa tayi inda suke,   tunkan taƙaraso Amani ke kallonta cikin jin bugun zuciya, shi kanshi Abbas kallon matashiyar yarinyar yake yi cike da mamakin ina aka samu yarinya mace acikin gidan, Ganin duk hankalinsu yadawo kanta yasa jikinta ya soma yin kerma, dakatawa tayi da tafiya sannan cikin en ina tace "umm....ina kwananan ku,"   atare abbas da abbansu suka amsa mata banda Amani dake tsaye ƙiƙam tana kallonta cikin tashin hankali, ita kanta sehrish atsorace take da kallon da Amani ke yi mata,    "Zonan My daughter nayi missing ɗin ganinki, gashi bakya zuwa kina gaishe da Abbanki ko"? Yayi maganar yana kallonta,   Ƙarasawa sehrish tayi gab da Abban nasu ta tsaya tana faman ƙaƙume hannun jakarta da ta sargafo a kafaɗarta, Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta yace"yaushe kika fara zuwa school ne ba'a sanar mun ba"? ....daker sehrish ta iya cewa "jiya ne nafara zuwa," Jinjina kansa yayi tare da cewa "okey,ki maida hankali sosai akaratun ki kinji ko? Banda biye ma ƙawaye    "Insha Allah Abba," ta amsa mashi, Baki asake Abbas yace "yakamata a wayar mun dakaina mana, ina aka samu yarinya kyakkyawa kodai daga cikin danginmu ne na damaturu ko zariyya"?   Ya tambaya aɗan ruɗe yana kallon Abban nasu, tunkafin Abban nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa "ƙanwata ce yaya Abbas, sunanta Sehrish kuma abbane yayi mun ƙanwa da ita, itama ƴar Abban mu ce, ba'a jima da haihuwarta ba, nasan zakayi mamakin yarda tayi saurin girma har haka, ka tambayi Abba zaiyi maka bayanin komai,'    yana faɗin haka yaja hannun sehrish suka bi ta gefensu suka fuce,   Dariya kawai Abbansu ke saki hada shi Abbas ɗin,   "Ji wata shiririta irinta junaid,hakanan kawai ya zabga mun ƙarya, ina na ajiye matar bare harna haifi ƴa kamar wannan,'  Ya fadi tare da yi masu alamar su shiga daga ciki, bin shi su kayi tare da samun wurin saman royal sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna, Amani na kusa da Abbas yayin da Abban ke fuskantar su yace "sannun ku da zuwa,nayi mamakin ganinku da wuri haka," Abbas yace "tun jiya muka so muzo,amma dare yayi sosai lokacin, wlh sam nagaza samun natsuwa ne game da halin da naga fawan a asibiti, shine nace mata tashirya muzo har gida mu duba shi,"    yayi maganar fuskarshi dauke da damuwa, Amani ma tace "Abba ya mai jiki? sai jiya da daddare yake faɗamun abunda ya faru dasu fawan hankali na ya tashi sosai, tun jiya nima naso ko wayane nakira na tambayi jikin shi amma duk layin dana kira ba'a ɗagawa," Abba yace "ae ba zaki same su ba, saboda duk muna cikin damuwa ne,bakowa ma yasan inda ya jefa wayarshi ba,abun ne ya tayar mana da hankali sosai, Cikin sanyin murya tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya,ya tashi kafaɗun shi, su kuma waɗanda sukayi mashi wannan aika aikan Allah ya toni asirin su,"   "Ameen Ameen," suka amsa mata  Daga bisani Abbas yace "bari mu shiga ciki mu dubo shi,"   Miƙewa su kayi hada Abban yayi masu jagowa izuwa ɗakin da aka kwantar da fawan,   Da sallama suka shiga ciki, har lokacin fawan na kwance sai faman sharar bacci yake yi, Abbas yace "masha Allah jikin nasa yafara sauƙi, tun da harya samu bacci,"   "Ae tunjiya dana shigo ɗakin na same shi yana ta faman fisge-fisge yana cewa sun biyo shi zasu kashe shi,saina zauna wurin shi anan zaune muka kwana ni dashi da asuba ne nabar ɗakin," Abban nasu ne yayi maganar ayayin da yake samun wuri gefen gadon tare da zama yana kallon fawan ɗin dake kwance magashiyyan yana kwasar bacci,   matsawa Abbas yayi shima tare da samun wurin kusa da Abban nasu ya zauna sannan yakai hannun shi ya dafa forehead din fawan yana cewa "Baƙaramin jiki yaji ba gaskiya,sun azabtar dashi sosai bawan Allah, amma asannu zai warware insha Allah,   Kafin Abban nasu ya kuma cewa wani abu wayar Amani dake acikin handbag ɗinta tashiga yin ringing da ƙarfin gaske,   Kallonta Abbas yayi tare da cewa "ki fita waje ki amsa wayar," cikin sauri ta amsa mashi da toh sannan ta fuce,  dama so take ta fita daga ɗakin saboda gulmar data ciyota kunsan mu mata abun ajinin mu yake,da zarar abun gulma ya samu nan take zaka ga jikin mutun har rawa yake yi don ya faɗama ɗan uwansa, (Amma fa ni bana gulma) 😒 Cikin sauri Amani ta sauko down stairs jikinta har rawa yake yi ganin Azmee na jera masu breakfast a dining table, yasa cikin sauri ta wuce wurinta    Azmee naganin ta ta soma sakin fara'a tana cewa "aaa yau kune agidan namu? saukar yaushe," Batare da Amani ta amsa mata ba tace "Yawwa Aunty azmee dama akwai abunda nakeso na tambaye ki,"!   Cikin mamaki azmee tace "meke nan"?   "Ga me da Yarinyar dana gani acikin gidan nan, wata ƴar matashiyya shin ita ɗin jinin su Abba ce?   murmushi azmee ta saki aranta tace "Gulma ajali, in ba'ayi ba a mutu," a fili kuma tace "abokiyar aikina ce a aka kawo don ta runƙa tayani aiki,"   yamutsa fuska amani tayi kan ta yagama ɗaurewa ta kuma cewa "ƴar aiki fa kika ce? But i was confused ya akai naganta cikin uniform kuma har junaid na kiranta da ƙanwarshi? Kuma naji Abba ma ya kirata da My daughter,duk kuma a matsayin mai aikin?   dariya azmee tayi ganin yarda amani ta ɗaga hankalinta akan sehrish   "tabbas mai aiki ce itama, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyarsa,bata da banbanci da sauran ƴa'ƴanshi a yanzu, saboda yana son Yarinyar sosai,"   Jin haka yasa Amani ɗan zaro ido waje bata ƙara cewa komai ba saboda wayarta da ta ƙara yin ringing, cikin sauri ta zura hannu tare da buɗe handbag din ta zaro wayarta, tare da duba screen din wayar don taga mai kiranta, sunan Aunty laila ne ya bayyana asama, kallon Azmee tayi tare da cewa "ina zuwa," tayi maganar tare da kama hanya ta danyi nesa da azmee sannan ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta tana cewa "barka da safiyya Auntyna fatan kin tashi lafiya," Murmushi Aunty babba tasa ki daga can 6angaren tace "Lapiya lou Alhmdllh my sister, nazo maki da labari mai daɗi ina fata kina da kunnan saurara,"   Amani tace "nima ae ina tafe da labari zazzafan gaske, amma bansan wa zai fara bada labarin shi ba acikin mu,"    Saurarawa tayi tana jiyo dariyar aunty babba ta cikin wayar sai da ta tsagaita da dariyar sannan tace "ina tunanin labarina yafi naki daɗi kuma zaifi ƙayatarwa, bari dae ni nafara baki,"   murmushi Amani tayi tamkar tana agabanta tace ina sauraronki auntyna,   gyaran murya Aunty babba tayi sannan tace "ina yaran nan da nake baki labari Omar ya kawo mun gidana?   Amani tace "eh nagane su," Aunty babba taci gaba da cewa "ae tuni nasa an kwashe su, an jefar mun dasu bayan gari,yanzu haka hankalina kwance na rabu da alaƙaƙai, yanzu banda wata sauran damuwa saura target ɗina nagaba nake jira...." tunkan taƙarasa maganar Amani ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya, Jin dariyar da amani keyi ne yasa aunty babba dakatawa da maganarta tana sauraronta ta cikin wayar, ganin cewa amani bata da alamar jinkirtawa da yin dariyar da takeyi ne yasata cewa "ke bana son iya shege, na ji kina mun dariya kodai daɗin labarina ne yasa ki jin daɗi har haka," ta tambaya tana jiran jin mai amani zata ce,   daƙyar Amani ta tsagaita da yin dariyar sannan tace "Aunty laila an fa yanka ta tashi,labari da ɗumi ɗuminsa idan ma kina atsaye to wlh ki zauna don kar in sanar dake ki yanke jiki ki faɗi,"   Jin maganar Amani yasa hankalin aunty babba ɗugunzuma,murya na rawa tace "ba atsaye nake ba,ina zaune saman 2 seater ne ina shan tea,dan Allah ki sanar mun wane irin labari ne wannan,"    wani irin shu'umin murmushi amani tayi kafin ta soma cewa"Yanzun nan muka zo gidansu Abbas saboda mu duba jikin fawan da miyagu suka kai masu hari, ina fata kinsan wannan labarin"? Ta tambaya tamkar tana agabanta, Aunty babba tace "eh nasani,ae muna nan muma zamu zo tare da ishaq don mu duba jikin shi,"   Jinjina kai Amani tayi sannan taci gaba da cewa "Shin ko kinsan cewa akwai wata matashiyyar yarinya kyakkyawar gaske da muka tarar acikin gidan !!!'   darammm !!!gaban aunty babba ya faɗi rasss a firgice ta saki cup ɗin dake hannunta ya tarwatse ƙasa, zumbur ta miƙe tsaye tana cewa "kamarya Amani ! Bangane abunda kike cewa ba anya ba kunne na bane suka jiyo mun hakan"?   dariya amani tayi kafin tace "ba kunnanki bane Aunty laila,zahiran ne wannan nake faɗa maki, wlh da ido na naga yarinyar,kyakkyawar gaske har na tambayi azmee nake cewa wacece ita yarinyar kodai cikin danginsu Abba take, sai azmee ke sanar dani cewa house maid ce itama amma Abba ya mayar da ita tamkar ƴarsa, har fa school sun sanya yarinyar babban abunda zai tayar maki da hankali sai kin ga yarda Abba ke kiranta da ɗiyarshi, yarinyar ba ƙaramin wuri ta samu ba....... Fuska a damuje aunty babba tace "nifa hanyanzu ban fahimta ba, shin yarinyar ƙarama ce sosai ko babba"?   Amani tace "ina fa, wlh balagagga ce nace maki fa matashiyar budurwa kyakkyawar gaske mai cikar sura,ni kaina dana kalle ta sai da gabana ya faɗi to ina ga matasan gidan da suka kasance maza ne dukansu,   Jin wannan maganar yasa aunty babba dake atsaye tana zarya a falon nata, aza hannunta na dama akanta, ɗayan kuma na ruƙe da wayar tashiga cewa "Ae shikenan wlh an yanka ta tashi, ni ina nan sake da baki ina murnar rabuwa da waɗancan tagwayen da Omar ya kawo min ashe abanza ga wata can ta riga ƙetare iyakar da bana so aje,amma an gama dani wlh ya akai har takai wannan lokacin gidan baki sanar dani ba,"? ta tambaya a kiɗime,   Amani tace "nafa ce maki ni kaina bansan da zamanta ba, yau ɗin nan muka ganta kwatsam tafito ɗas da ita cikin school uniform wlh abun ba'a magana yarinya haɗaɗɗiyar gaske,tasamu wuri fa sosai agidan, kuma yarda naga Abbansu na kiran sunanta da daughter dinshi kinga kuwa hakan na nufin nan gaba ma da sunan Surikata zai kirata,"    ƙasa ƙasa amani ke sakin dariya tana sauraron aunty babba dake faman Zabga salati, dama dagangan take tunzurata don ta rikitar da ita,  "Nashiga ukuna,wannan masifar har ina matashiyar budurwa kuma agidan surikina, wlh hakan bazai ta6ayiyu ba, wlh saina son yarda zanyi na rabata da gidan, badai zamu zo da ishaq ba hmmmm zanganta ne !! zanga KOWACECE ITA 😳😳😳   Sun jima suna waya da aunty laila kafin daga bisa ni sukayi sallama da juna amani ta koma daga ciki, ranta fess don tasan yau ko bacci aunty babba bazata iya yi ba har sai taganta a Abuja, gata ga yarinyar data bata labarinta, Fitowa hafsat tayi daga bedroom ɗinta jikinta sanye da sleeping dress ganin mommyn nata tsaye tana ta faman zarya a falon tana zazzaga bala'e ita kaɗai kamar zararriya, hakan yasa hafsat ƙarasawa kusa da ita tana cewa "wai mommy lafiya kuwa kike ta faman tada jijiyoyin wuya duk akan wanene? Uban tsoki Aunty babba ta saki sannan tace "wani mummunan labari amani ta sanar dani yanzun nan, wlh nagaza samun natsuwa, so nake kawai naganni a abuja wlh,"   Wuri hafsat ta samu tare da zama saman 2 seater sannan tace "mommy wannan wane irin labari ne haka daya tayar maki da hankali haryasa kika fasa cup ɗin da kike shan tea dashi," tayi maganar ayayin da take kallon kofin da aunty babba ta saki ƙasa ya fashe,   juyo tayi ta kalle ta rai a6ace tace "ba dole hankali na ya tashi ba, ina murnar rabuwa dasu hossana da jahad sai gashi yanzu Amani ta kirani awaya tana sanar dani cewa sunje gidan su Abba, sun tarar da wata matashiyar budurwa wai mai aikice fa, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyar cikinsa," tayi maganar tana huci,   Shiru hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin daga bisa ni ta saki ƙayataccen murmushi tace "Mommy kenan, dama kina tunanin haƙƙinsu hossana da jahad zai barki ne? to inaso ki sani haƙƙinsu ne yafara bibiyarki, kuma ba zaki ta6a cin nasara ba akan wannan yarinyar da aka baki labarinta yanzu, saboda mommy sam baki kyauta ma rayuwar yaran nan ba, basu miki laifin komai ba kinsa an kwashe su,ki kayi mun ƙaryar cewa gidan marayu za'a kaisu ashe zubar dasu kikasa ayi,yanzu wayasan wani hali suke ciki.........' hawaye ne suka soma zarya a fuskarta saboda raɗaɗin da take ji aduk lokacin da ta tuna dasu hossana da jahad,tun jiya da aunty babba ta sanar da ita cewa ba gidan marayu tasa akaisu ba, zubar dasu tasa ayi bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, abun namata ciwo azuciyarta . kallonta kawai aunty babba keyi ganin yarda take zubar da tears ɗinta akan tsintattun yaran da bata haɗa alaƙar komai dasu ba,   tsoki ta sake ja tare da cewa "kin dai ji haushin rayuwarki wlh, saboda waɗancan marasa galihun kike ta faman sharara kuka,har kina ikirarin haƙƙinsu ne ke bi na,to ki zuba ido ki gani saina sa anyi waje da waccen yarinyar da amani taban labarinta,"    afusace hafsat ta miƙe tana kallonta tace "mommy! Ina miki fatan nasara," tana fadin hakan ta juya tare da komawa bedroom ɗinta,   Jinjina kai aunty babba ta shiga yi tana faman sakin huci kamar zakayan, afili tace "Tabbas dole nasan kowacece wannan yarinyar dake ƙoƙarin tarwatsa mun plan ɗina, yakamata nasan abunyi dole na kira HAYAAM awaya in sanar da ita cewa ta tattaro kayanta itama ta koma gidan da zama, tunda har ƴar aiki ta samu irin wannan gatancin ina ga ita da take ƙanwata !!!!!!🤭   Sai faman balbali bala'e take yi ita kaɗae tana ci gaba da zarya a falon, ******************************* tun bayan da junaid ya sauke sehrish a school su kayi sallama ta shige ciki shi kuma yakama hanyar komawa gida yana driving yana tunanin fuskar rishi ɗinsa tsantsar sonta ne ke sanya shi jin wata irin kasala a jikinsa, lokacin da ya ƙaraso gida sai da gabanshi ya faɗi rass ganin dandazon motoci suna ta shiga gidan nasu,manya manyan mutane ne aminnan abbansu suke ta zuwa dubiyar fawan, wasu daga cikinsu manyan shuwagabannin sojoji ne da kuma mr president da kanshi ya tako yazo don duba jikin ɗan aminin nasa atare dashi hada mataimakinsa da kuma babban ɗansa Captain Shattima wanda ya kasance aboki ne ga Marshal Omar da SGR tun a U.s don acan shima yayi karatunsa na Airforce, halayyarsa da ɗabi'unsa sak irin nasu ne shiyasa tafiyar tasu tazo ɗaya, ƙwararre ne a6angaren aikin shi, sannan kuma shima mace sam bata gaban shi,tamkar dae su ɗin dae,   Gida fa ya ɗinke ɗuff da mutane tamkar rasuwa akayi, ta ko'ina jinsin bil'adama ne ke ta shigowa,   Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba tunkan yayi parking ɗin motarsa yake ta faman sharar hawaye tsoran shi kar ace wani abune ya faru dasu fawan saboda yasan sune basa a gida anturasu aiki,a hankali ya tsayar da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fito yana kallon mutanen dake shigowa, ...jingina bayansa yayi ajikin motar tashi sannan ya zura hannun shi cikin trouser pocket ɗinsa, wayar shi ya zaro tare da shiga contact ɗin wayarsa, lambar abbansu ya gano sannan ya buga masa waya,   ta jima tana ringing kusan sau uku kafin Abban nasu ya ɗaga kiran,   Kara wayar yayi a kunnansa tare da fashe mashi da kuka,   Shiru Abbansu yayi yana sauraran kukan da junaid ke yi masa acikin wayar,   Cikin shesshekar kuka yace "Abba......wanene ya mutu, naga dandazon mutane acikin gidan...'daker ya iya yin maganar zuciyar shi na faman bugawa,    "Kana ina ne"? abban nasu ya tambaya .."gani awaje abba, nakasa shigowa,ina jikin motata yanzu haka ban jima da shigowa gidan ba, saboda nakai sehrish school ne,"   Ajiyar zuciya abbansu ya saki kafin yace "sauraran ni kaji da kyau, babu wanda ya mutu, nasan halinka ne shiyasa tun jiya ban sanar maka ba, amma yanzu zan faɗa maka, but promise me first cewa zaka daina kuka,"    Ajiyar zuciya junaid ya shiga saukewa yana cewa "Okey, abba nadaina tell me pls,"    gyaran murya abban nasu yayi tamkar yana agaban shi sannan yace "abunda ya faru shine, su irfan da aka tura aiki,miyagu suka farmake su amma alhmdllh duk suna cikin ƙoshin lafiya, fawan ne kawai suka samu nasarar cutar dashi harya zauce ssae tun shekaran jiya suna asibiti ana duba su sai jiya ne muka dawo gida tare da su............'   tunkan abban nasu ya ƙarasa maganar tashi tuni Junaid ya saki wayar dake hannun shi sakamakon faduwar da yayi nan take ya sume...................dama abunda abbansu ke gudu kenan  hankali atashe yake cewa "junaid!junaid !!! Kana jina kuwa !! Meya faru ne,   yarda yake fidda sautin maganar yasa kowa dake a falon kallon shi, dama duk suna a falon sun hallara saboda sun fiddo da fawan yana kwance asaman 3 seater yana amsa ya jikin da mutane keyi masa, gaba ɗaya hankalin kowa ya tashi,suka shiga tambayar shi meke faruwa ne, zumbur ya miƙe yana cewa "wlh junaid ne daga faɗi mashi halin da fawan ke ciki shikenan ya yanke jiki ya fadi ina tunanin ya suma ne awaje,' "Subhanallahi," mutanen wurin suka haɗa baki wurin cewa haka, fawan dake kwance kuwa tuni ya shiga kiran sunan junaid yana fadin "Abba akawo mun junaid inason ganin shi," ya faɗi akasalance,tun jiya dama yake so yasa shi a idonshi amma bai samu dama ba,   atare abbansu da cg abbas suka fito domin ɗauko shi, tun kan su isa sai gashi ɗaya daga cikin soldiers din dake cikin gidan ya ɗauko shi sa6e a kafadarshi, cikin sauri Abbas ya kar6e shi tare da yima sojan godaiya, sannan su ka koma ciki dashi, ********************SGR hospital tun safe su hossana da jahad suke ta faman jiran yaya Omar ɗinsu saboda yazo ya ɗauke su amma shiru babu alamarshi, suna kwance a gado ɗaya saboda since yesterday night hossana ta maƙale ma jahad aɗaki ɗaya suka kwana tana agefenta,hankalinsu kwance saboda kyakkyawar kulawar da suka samu a wurin nurse Camila,tun da sukayi breakfast wanda anan asibitin suke rabawa marasa lafiya abinci kyauta kuma lafiyayyen gaske,sunci sunyi hani'an suna jiran omar yazo, duk in Camila tashigo duba su sai sun tambayeta yaya Omar dinsu yazo? Sai tace musu a'a su ƙara jira kaɗan tun suna tambayarta har suka gaji suka daina, Around 12 na rana, Motar Omar ta shigo cikin asibitin, bai samu damar zuwa ba saboda busy ɗin daya shiga hakanne yasa shi aiko major domin ya ɗauko su kamar yarda yayi musu alƙawarin cewa da safe zai sa asallame su, dalilin dayasa ya turo masu da major kenan amaimakon shi,   Bayan major yayi parking ɗin motar sannan ya fito ya shiga ciki, kai tsaye ɗakin dasu su hossana ke ciki ya nufa,   suna ganin shi suka fara murna don sunsan cewa yana tare da Ya omar,      "Ya jikin naku"? Cikin sauri suka amsa mashi da cewa "Alhmdllh jiki da sauƙi," Yace "masha Allah,kun ganni ni kaɗai ko? Hossana tace "eh, ina ya omar din, shi bai zo ba tun ɗazu muke jiran shi,"   Murmushi major yayi kafin yace "kuyi mashi Uziri yana busy sosai, amma ya aiko ne nazo don na duba ku,sannan nasa a sallame ku mu tafi gida,"   ba ƙaramin daɗi suka ji ba, don aƙagare suke da su ga inda zasu zauna wurin da zasu fara sabuwar rayuwa,   "bari naje naga dr, yanzu nan zan dawo," yayi maganar tare da fuce wa daga ɗakin,   Cike da murna hossana tace "Shikenan mun rabu da wahala, yanzu zamu fara kyakkyawar rayuwa, saboda nasan yaya omar har makaranta zai samu,har na hango ni yarda zan koma nan da 1 month,"  Kallonta jahad tayi da yake sun tashi daga zaune tace "jibgegiya zaki koma kamar buhun fulawa,nikaina naƙosa naga yarda rayuwarmu zata canza,abu biyu nake tunawa da suke sani kwanciyar hankali na farko shine bani da wata sauran damuwa dama hossana ke nafi ji, damuwata aduk lokacin da muka shiga hadari kece ina tsoran kar na rasaki,abu na biyu kuma shine ƴar Uwarmu SEHRISH,duk da bansan a ina take ba amma inaji araina cewa TANA TARE DAMU, INA NUFIN TANA A KUSA DAMU SABODA INAJI A ZUCIYATA!! With confidence tayi maganar in serious matter,   jinjina kai hossana tayi kafin tace "Jahad nima inaji araina cewa REESHI TANA A KUSA DAMU,komai ma zaizo mana cikin sauƙi yanzu tunda zamu samu kwanciyar hankalin nemanta,ga kuma YA OMAR,NASAN DAGA MUN FAƊA MASA CEWA ƳAR UWARMU TA 6ATA MUNA NEMANTA KUMA KAMANNIN MU ƊAYA SAK MU TRIPLET NE,SAI MU FAƊA MASHI SUNANTA NASAN ZAI TAIMAKA MANA WURIN GANO TA.................✍️💋 Shin mai zai faru idan Aunty babba tayi arba da fuskar Sehrish😳 yaya zata kasance tsakanin Haroon da twins? Baku tunanin cewa dole ALEXANDRA tazo nigeria domin duba jikin fawan😲? haka zalika AMMI ma muna hasashen zuwanta domin ganin fawan😲, ga kuma goggon katsina karfa ace itama zata zo domin ganin fawan shin ya zatayi a lokacin da tayi arba da fuskar sehrish wadda takasance kamanninta ɗaya da ƴa'ƴan abusufyan ɗinta?🤣, to kodai shima abusufyan dake zaune ƙasar turkey zaizo nigeria ne?😯, ni duk bama wannan ba🤨 abunda yafi damuna shine HAYAAM ƙanwar aunty babba wadda ke shirin dawowa gidan da zama 🥱 in har dagaske ne kenan sehrish itace a tsaka mai wuya tabɗijan can, ga haroon ga aunty babba ga wata wai hayaam🥴 wayyo har kaina yafara ciwo don tunanin yadda zatakasance, yakamata naje na kwanta fa, amma kafin nan akwai hasashe ɗaya daya rage mun shin ya zata kasance idan Hossana da jahad suka sanar da Omar game da ƴar uwarsu wadda takasance ita ɗin ƴar ukunsu ce kuma sunanta SEHRISH 🥺🥺🥺     💋Boss Bature💋_ dawowa major yayi shida dr Emran,a cikin ɗakin da aka kwantar dasu hossana,fuskar major ɗauke da murmushi yace. "An yi discharge ɗinku,kwanan asibiti ya ƙare yanzu zamu wace gida,"    Murmushi suka saki gaba ɗayansu,jiki na rawa hossana ta sauko daga saman gadon,itama jahad lalla6awa tayi a hankali ta sauko saboda ƙafarta,   Kallonsu dr emran yayi tare da cewa"zamu yi missing ɗinku sosai gsky,amma tun da a wurin omar ku ke, zamu dinga zuwa muna ganinku,"    Murmushi suka saki gaba ɗayansu,gaisawa major ya ƙara yi da dr emran sannan yayi mashi sallama,    shiga gaba yayi su hossana suka bi bayanshi, daker jahad ke taka ƙafarta da taimakon hossana take tafiya saboda ta dafa kafaɗarta gudun karta fama ciwon ƙafarta,     A haka har suka ƙaraso harabar asibitin wurin ajiye motocinsu, hannu major yasa tare da buɗe masu ƙopar back seat don su shiga su zauna,har jahad tasa kai zata shigo suka jiyo muryar nurse camila tana cewa "wait !! Wait !!,   Dakatawa su kayi gaba dayansu suna kallonta dama kuma sun so su tambaye ta,ɗan zaman da su kayi da ita ba ƙaramin shiga ransu tayi ba, ƙarasowa tayi kusa dasu tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta na ruƙe da jakar kaya, daga bisani ta ɗago fuskar nan ɗauke da murmushi tace"ba sallama twins?yanzu da banzo ba shikenan zaku tafi ko? Ku barni da kewarku,   murmushi sukayi gaba ɗayansu jahad tace "a'a bamu ganki bane shiyasa,"    kallon major tayi tare da cewa "tare dani zaku tafi, saboda already mun yi magana da marshal omar, ya dauke ni amatsayin wadda zata cigaba da kula da lafiyarsu,inaso naga gidan saboda in na tashi zuwa,   wani irin farin ciki ne ya rufe su hossana da jahad saboda sun lura da irin mutuncin dake gare ta, ba ƙaramin kula zasu samu a wurinta ba,   Murmushi major yayi tare da cewa "naji daɗin jin hakan sosai,saboda na lura da yadda kikeson yaran ina fata zaki kasance tare dasu,kuma zaki riƙe su amana,".     Jinjina kai Camila tayi tare da cewa "NA RIƘE AMANA,"   daganan suka shiga cikin motar jahad da hossana suna a back seat,major na a mazaunin driver yayin da Camila ke Zaune a other seat ɗin,"     a hankali yake driving dinsu harya fuce daga asibitin,ya miƙi shantalelen titi dasu, ajiyar zuciya kawai suke sauke wa ga wani farin ciki daya baibayesu, ba don komai ba sai don sanin cewa Ƙarshen wahalarsu yazo, yanzu lokacine da zasu huta ma rayuwarsu,suyi rayuwa ta ƴanci kamar kowane ɗan adam, batare da an ƙuntata masu ba ko an cutar 😇   Lokacin da suka ƙaraso gidan Uncle Abusufyan nan fa hossana ta zaro ido tare da buɗe baki alamar mamaki yarda kasan ƴar babyn roba haka ta koma sam bakinta yaƙi rufuwa don murna, ita kanta jahad bakinta a buɗe don murna fararen hakoran nan nata kamar gonar auduga, adai dai bakin gate ɗin major ya tsayar da motar sannan ya danna horn da ƙarfin gaske,   sai gashi an buɗe masu gate ɗin ta ciki, ba kowa bane face abokin Major ɗan leƙen asirin shi, acikin gidan ya kwana saboda omar ya dauke shi aiki, bayan alherin da yayi masa na kyautar mota sabuwa mai kyau da tsadar gaske, ga kuma uban salary daya yanka masa,😇    A hankali major ya shigar da motar cikin gate ɗin ɗan dagatawa yayi da driving ya zuge glass ɗin motar ya kalli osman yace "Shege mutumina, ka ga yarda ka canza jiya izuwa yau har wani haske ka fara? Cike da zolaya yayi maganar,   Dariya Osman yayi tare da cewa "ba dole kaga canji ba,an gaya ma yin karin kumallo da farfesun kaza wasa ne? mutun ya kwana a ac,sannan yayi wanka acikin kwami haba ae dole ma ne in canza,"    gaba ɗaya suka fashe da dariya jin abunda yace,    Major yace "nifa wasa nake maka malam, taya zaka canza kawai daga jiya zuwa yau don ka kwana a ac, kayi breakfast da farfesun kaza? Nace sannu ko uban son banza ae sai nan da irin one month haka,nan zamu ga canji,   Murmushi osman yayi tare da cewa " ka shiga ciki ka sauke su,in ka dawo zamuyi magana dakai, akwai labari mai daɗi,"     Major yace "okey bari nazo," yayi maganar tare da sauke glass din motar ya wuce dasu ciki, adai adai stairs ɗin da zai sadaka da main palour ɗin gidan ya sauke su,    Buɗe motar Camila tayi ta fito, sannan suma su jahad suka fito daga ciki suna ƙarewa katafaren gidan kallo ya haɗu iya haɗuwa abun ba'a magana, Omar yasa an canza mashi komai nashi an ƙara ƙawata gidan sosai,    gaba dayansu sun ƙame suna kallon haɗuwar gidan, ganin basu da niyyar shiga daga ciki yasa major cewa "let's go in pls,"    Cikin rashin sani jahad ta take ƙafarta ba don komai ba sai don hankalinta daya tafi wurin ƙarewa gidan kallo,ƙara tasaki tana yarfa hannu tana faɗin "wash Allah na," jin haka yasa camila tayi saurin dawowa ta inda suke, ta taimaka mata wurin yin tafiya don su shiga ciki, Major ne yayi masu jagora su kuma suna abayan shi, har suka shiga cikin haɗaɗɗen jigunannan falon,nan fa suka baza ido suna kallon haduwarshi, wasu irin matsiyatan royal sofa set ne acikin sa masu numfashi ɗunɗuma ɗunɗuma a jere launin su brown colour,ga wasu set na Cushions Jere asamansu difference colour,duk gasu nan ba ƙaramin ƙawata kujerun su kayi ba, daga tsakiya wani ƙayataccen table ne legs dinshi brown ne, while daga saman glass ne, an ajiye flower asaman shi, ga fruits basket mai dauke da kayan mar mari, ba komai yafi tafiya da hankalin hossana ba face tanƙameman kwan filitar dake bama ɗakin haske tamkar zai faɗo ma mutun akai haka yake, sai kuma tv stand din dakin faskekiyar plasma ma ce mai dauke da speakers na jin sauti, ga wani telephone table dage a gefe, bari dae in taƙaice maku zance komai wannan da kuka sani a palour an zuba masu shi,    Sai faman yarfa hannu hossana take yi, yarinya fa takusa zauce wa ganin irin gidan da yaya Omar dinsu ya gwangwaje su dashi, wani abun ma sai mun shiga bedroom,    Jahad kuwa murmushi kawai take saki tana bin ko'ina da kallo,ita kanta Camila gidan ba ƙaramin burgeta yayi ba komai tsaf a natse ba tarkacen hauka,    Can dae hossana tace "Allah yasa ba mafarki nake yi ba,dan Allah koma mafarki nake yi jahad kada ku tashe ni," ta fadi tana faman hadiyar yawu, Dariya su kayi gaba ɗayansu, Major yace "wannan zahiran ne ba mafarki ba ne, kaɗan daga cikin irin son da ya'ya omar dinku yake yi maku kenan,zai iya yin komai akanku more than u think, ni dae fatana agare ku shine ku kasance masu yi mashi biyayya, ku bishi sau da ƙafa kada kuyi amfani da son da yake yi maku wurin karya mashi zuciya,ko ku ce zaku canza halayyarku saboda wata dama da kuka samu, yanzu lokaci ne da zaku more rayuwarku bayan duk wahalar da kuka sha,"    Sosai major yashiga yi masu nasiha, duk sun kasa kunne suna sauraronshi,sannan kuma suna amsa mashi da insha Allah,   Bayan ya kammala daga ƙarshe yace "ku samu wuri ku zauna mana,nasan kuna jin yunwa yanzu zan sa ayi maku oder na abincin da zaku ci, sannan ga bedroom nan zaku iya shiga ciki ku huta,"   A natse suka ƙarasa tare da samun wuri suka zauna fuskar nan fa awashe,   Mayar da idonshi yayi kan Camila yace "zamu tafi tare ne? Na sauke ki a asibitin ko kuwa,"   cikin sauri tace "no i will stay here wit them,cos i ave done my work bani da sauran duty till tomorrow,"   Murmushi kawai major yayi sannan yace "okey," sannan yasa kai ya fuce, A jiyar zuciya ta sauke tare da samun wuri itama ta zauna, bayan ta ajiye jakan kayan data zo da ita,    kallon juna suka shiga yi suna murmushi,yanayin iskar falon badae daɗi ba yadda sanyin ac ke ratsa sassan jikin mutun,    Ganin sun zauna shiru yasa Camila cewa "ba ku buƙatar shiga daga ciki ne? ta tambaya tana kallonsu   Jahad ce tafara cewa "inason nayi wanka, hossana ma tace "nima,"    tashi camila tayi tare da cewa "mu shiga daga cikin ɗakin to, nima inason nayi wankan," tayi maganar tare da ɗaukar jakar kayanta,   gaba tayi suka bi bayanta ɗaya daga cikin bedrooms ɗin suka tunkara, ƙoparsa a rufe take amma bada key aka datse ta ba, hannu tasa ta tura nan take ƙopar ta buɗe, shiga ciki su kayi atare, haɗaɗden bedroom mai ɗauke da tafkeken gado fankacece, yaji lumbutsetsiyar katifa lallausar gaske ga wasu matassan kai masu laushi asama an jera su, irin gadon da kana hawa saman shi ko bakayi niyyar yin bacci ba nan take zai ɗauke ke saboda daɗinsa 🥱 an gyare komai an shimfiɗe shi da bedsheet,side by side na gadon akwai side drawers, masu ɗauke da lamps,  daga can ɗayan bangaren ɗakin kuwa wurin Closet dinsu ne, ga wani haɗaɗɗen Dressing mirror an cika masu front dinshi da kayan make up da tsadaddun mayuka na jiki, komai an sanya masu, jerin wurin takalmansu,hand bags da sauran abubuwa da dama ba abun da omar yabari komai ansa masu,    jahad ce tafara shiga toilet ɗin don a ƙagare take da tayi wanka,lokacin da ta shiga cikin toilet nan fa taga zallar haɗuwa ta jima tana bin ko'ina da kallo kafin daga bisa ni tayi wankar daker tare da yin alwala saboda in an kira sallah tayi, fitowa tayi a hankali waist dinta daure da towel mai ɗan tsayi wanda ta samu acikin toilet ɗin, hannunta na ruƙe da doguwar rigarta da ta cire, samun su tayi zazzaune daga gefen gadon suna fira da hossana da Camila,   Ganin ta fito yasa camila tashi ta shiga toilet ɗin, a cikin laundry basket ta turo rigar, sannan ta ɗan juya ta kalli hossana dake ta faman lumshe ido alamar bacci tace "karfa kiyi bacci don na son halinki, ki bari kiyi wanka ke ma,"    Murmushi tayi kafin tace"ae bazan iya bacci ba jahad, saboda gani nake kamar in na kwanta zan farka na ganni a gidan wannan matar da ta azabtar damu,nakasa yarda cewa wai mune acikin wannan katafaren gidan nan mu kaɗai abun mu,gsky yaya omar ba ƙaramin ƙaunarmu yake yi ba,"     Jahad tace"nikaina ina mamakin hakan hossana,ashe akwai wata rana da zato mana irin wannan,mun samu yaya mai son mu tamkar ƙannensa duk don saboda mu ya Omar yabar komai nasa don ya ceci rayuwarmu,har yanzu ina mamamkin hakan hossana, yaya omar ya sanar dani cewa ɗan uwanshi yana kwance rai hannun Allah babu tabbacin cewa zai rayu,amma a hakan ya tsallake shi yazo wurin mu wannan wane irin mutun ne?samun mai iri Kyakkyawar zuciyarshi zaiyi wuya a faɗin duniya. Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jikinmu  Karanta>>> Tsumin Matan Aure  Don Inganta Auratayya Karanta>>> Tasirin Da Tazargade Ke Yi Ga Lafiyar Mata (shiyasa Hafsat bature take kamu) 🙄    ta yi maganar ne a lokacin datakai wurin closet tana neman ta inda zata buɗe shi,tana aza hannunta a jikin closet din nan take doors din dake jiki suka zuge da kansu, har sai da jahad ta ɗan tsorata tayi baya,   tasowa hossana tayi itama tana kallon wurin kayan nasu, yadda suke tagwaye haka omar yasa aka jera masu komai kala biyu, jerin wurin pyjamas ɗinsu daban, jerin wurin dogayen riguna daban,jerin wurin jeans da t shirt daban, ga jerin under wears shima daban, komai nasawa ajiki an zuba masu shi,har sun wuce iyaka,   "jahad har naji inason nayi wanka wlh,saboda in canza kayan jikina," acewar hossana dake ta faman yarfa hannu tana kallon kayan,   Hannu jahad tasa tare da curo wasu pakistan masu kyan gaske,tana shafa jikinsu tunkan tasa har ta gano kyan da zasu mata,       a gefen gado ta ajiye su, sannan ta koma gaban mirror tana shafe jikinta da ɗaya daga cikin mayukan da tagani ajare, bayan ta kammala ta kuma feshe jikinta da turare mai ƙamshin gaske,    Sannan ta dawo ta tsaya a gefen gadon tana zura kayan ajikinta, duk hossana na can tsaye wurin closet ɗin tana ƴan ta6e ta6e,ji take tamkar tabi kowannansu ta gwada ajikinta,    Bayan jahad ta gama kimtsawa cikin pakistan din komawa tayi gaban mirror tana kallon jikinta,riga ce mai dogon hannu har guiwar ƙafarta sai wandon burgujeje irin nasu,ta yafa mayafin asaman kafaɗarta, sumar kanta kuma ta zubo a bayanta, murmushi kawai takeyi tana kallon kanta a cikin mirrow,   Muryar hossana ce ta katse ta da cewa"kinyi kyau sosai jahad saina ga kin koma mun tamkar ketrina kef,"      Jahad tace"sannu shugaban makaryata ni bada ketrina nake kama ba sai dae helen,oumma tace kamannin mu sak irin nata,' tayi maganar tana gyara gefen gashinta da hannunta,   Hossana tace"wacece helen kuma"?   "Ƴar film ce mana ta ƙasar ethiopia," Jahad ta bata amsa atakaice, kafin hossana ta ƙara cewa wani abu, sai ga Camila tafi to daga toilet din daga ita sai ɗan pant da bra, cikin sauri suka sanya tafukan hannayensu tare da rufe fuskokinsu cikin jin kunya,   tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki take cewa"why are u hidding ur face pls? Can i know   Jahad tace"mun ji kunya ne,"    Murmushi camilla tayi tare da girgiza kai tace"kuna da kunya sosai,in dae haka ne kam ba zaku iya rayuwa a ƙasar mu ba,"     "Wata ƙasa ce"? Hossana ta tambaya,   Camila tace "Mexico," Jinjina kai tayi tare da cewa"ni ko sunan ƙasar ma ban ta6a ji ba gsky...."jahad ce ta katse ta da cewa "hossana zoki wuce kije kiyi wankan kema,"  Amsa mata tayi da toh sannan ta wuce cikin toilet ɗin,   Ita kuma jahad ta kama hanyar fita daga ɗakin har lokacin fuskarta na rufe da tafin hannayenta, abun sai ya ba camilla dariya sosai,   Sai da ta fita daga bedroom ɗin sannan ta soma sauke ajiyar zuciya, shiga cikin falon tayi, tana ƙare masa kallo, zagaye shi ta shiga yi tana tatta6a dogayen curtains ɗin dake kewaye dashi,    Sallamar Osman ce ta dakatar da ita, cikin sauri ta amsa mashi da wa'alaikum salam,sai da ya fara tambayar iznin shiga daga ciki, ta amsa mashi sannan yasa kai cikin falon,    Hannun shi na ruƙe da manya ledoji na abincin da yayi masu oder a restaurant,yarda yaga jahad ta kimtsa tamkar ba ita bace ya gani  acikin daji ba sume cikin ciyayi,ba don akwai dressing na ciwo a forhead dinta ba, da bazai iya shaida taba,  .murmushi kawai yayi tare da miƙa mata ledojin hannun shi, cikin sauri tasa hannu ta kar6a tana yi masa godiya,   Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo ya kalle ta yace"pls game da abunda ya faru da ku a gidan yayan Omar,wurin matar yayan shi kada ku sanar dashi komai don nasan zai tambaye ku ne,   Murmushi jahad tayi tace"insha Allah ba zamu sanar mashi ba,"    "Yawwa" ya faɗi tare da juyawa yasa kai ya fuce,    Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye ledojin a saman table,tana jiran su kammala kimtsa wa su fito suci atare,    Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana faman sakin murmushi,bakowa ne ke faɗo mata aranta ba face yaya Omar dinsu,ta ƙosa ta sashi a idonta saboda tayi mashi godiya sosai,kuma tayi missing din wannan kyakkyawar fuskar tashi,    tana cikin wannan tsayuwar sai ga Camila ta fito fes abunta har ta canza kayan jikinta,v neck shirt ce ajikinta fara sai wando jeans, ta ɗaure sumar kanta da ribbom,fuskarta asake ta ƙaraso tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna tana kallon jahad tace"kina so ciwon naki ya dawo sabo mu koma asibiti gobe ko?   Girgiza kai jahad tayi tare da cewa"a'a bansan na take ta bane,ciwon bai mun zafi yanzu ina ji kamar naji sauƙi ma,"     Tace "duk da haka yakama ki kula just in case,"    Amsa mata tayi da toh sannan tace "ga abinci nan,an aiko mana shi," ta fadi tare da ƙarasawa wurin table ɗin ta matsar mata dashi kusa da kujerar da take zaune,    Sannan itama ta samu wuri ta zauna a kusa da ita,hannu camila tasa ta buɗe ledar ta farkon,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger, shawarma da sauran wasu tarkacen, ɗayar ledar kuma da ta bude masu fried meat ne (tsiren nama) mai yawan gaske yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,   Dole ne su buƙaci plate don haka jahad ta tashi tare da cewa "bari na ɗauko mana plate," camila tace "plate yayi kaɗan tray zaki samo mana,"  Amsa mata tayi sannan ta tunkari doors din dake a cikin falon tana neman kitchen babu alamar kitchen na a wurin,   "Ki duba down stairs baza arasa acan ba," acewar camila,   Cikin sauri jahad ta hau benen da zai sauke ta a dowm stairs tana sauka cikin sittingroom din ta hango kitchen ɗin, tasha mamakin ganin yarda aka ƙawata ɗakin,    Cikin hanzari ta wuce kitchen ɗin an tsara shi sosai,ƙarasawa tayi jikin kitchen shelves anan ta samu trays a jere ta ɗauki ɗaya,komai na cikinsa sabone wasu acikin kwalinsu wasu kuma a buɗe suke, tare da cokali ta haɗo masu da knife saboda taga tsiren naman basu zuge shi ba acikin tsinken shi yake,zasu buƙaci su yayyanka shi in zasu ci,   Fitowa tayi daga kitchen ɗin sannan ta koma upstairs ɗin, tunkan ta ƙarasawa ta samu hossana zaune agefen camila hannunta ɗauke da tsiren naman nan ta tura abaki sai ci take kamar kura,hankalinta kwance, bakomai bane ya burge jahad ba face ganin yarda hossana tayi wani irin kyau cikin gajeran skirt mini tare da riga ƴar t shirt tabi shape din jikinta, hada ƴar hoda ta shafa ma fuskarta da jan baki,    Ganin jahad ta soma washe mata baki, girgiza kai jahad tayi tare da cewa "dama nasan dole kiyi ƙara'e hossana irin wannan ɗaukar wanka haka,"    "Kaɗan kika fara gani ma,aunty camila ma tace in ta samu hutun aiki zata kaimu saloon a gyara mana gashi tare da ƙunshi ma duka za'a yi mana,"    murmushi jahad tayi a lokacin taƙarasa wurin table ɗin, aza tray ɗin tayi asaman shi sannan ta samu wuri ta zauna itama suka saka Camilla a tsakiyarsu,    ita ta baje masu tsiren acikin tray ɗin ta jera masu shi,sannan ta zuba masu chips ɗin daga gefe,    Nan fa suka gyara zama duka ukun suka tasar ma kayan lashe lashen, ba baka sai kunne, ba kaji komai sai sautin taunar shi da suke abakinsu, **********************SEHRISH tun da english teacher ɗinsu ta fita daga class ɗin, sehrish ta kifa kanta asaman desk din gabanta tana ta sharar bacci, har amrish ta gane mata daga jiya izuwa yau sam bata gajiya da yin bacci,alamu ma sun nuna cewa bata fahimtar komai kanta dashi da kwankwon ashana duk ɗaya suke,tashi amrish tayi tare da fitowa daga seat ɗinta ta ɗan sa hannunta tare da bubbuga bayan sehrish tace"ki tashi mu tafi time ɗin break yayi," kusan sau uku tana tashinta daƙer ta buɗe idonta da suka canza launi saboda bacci, miƙa tayi tare da yin hamma alamar yunwa take ji ga baccin ma bai isheta ba, fitowa tayi daga seat ɗin nata tana cewa"ashe har lokacin break yayi " Amrish tace"taya za'ae ki sani, bayan baccinki kawai kike tasha, anya kuwa ma kina yin bacci a gida ne? Ta tambaya tana kallonta a yayin da suke fita daga class ɗin,   "Ina yin bacci mana sosai,"_ "To meyasa kike yin bacci a class?ko karatu ma bakya saurara salon azo yin test ko exam kiyi ta baza idanu kina kallon question paper kina cizon biro ko? Ta fadi fuskarta ɗauke da dariya, itama sehrish din dariya tayi tana cewa "insha Allah hakan ma bazata faru ba,kafin lokacin zanyi karatu sosai,"   Suna tafiya suna fira har suka isa Lunch room ɗin nasu atare suka shiga ciki, students duk sun hallara suna ta having lunch dinsu,   ruƙo hannun sehrish tayi tare da kaita gaban table ɗin da zasu zauna,sai da rishi ta zauna saman table chairs din sannan amrish ta wuce ciki don ta amso masu abunda zasu ci,   Ajiyar zuciya sehrish ta saki tana kallon students din dake zaune a wurin suna cin abincinsu suna shan fira abunsu,zahiri su take kallo amma abaɗi ba komai take tunawa ba face fuskar SGR ɗinta,murmushi ta saki aranta tana cewa "koyana ina yanzu?me yake yi?ko yaci abincinsa?Allah yasa dae baibar cikin shi da yunwa ba, babu mai bata amsar tambayarta, cigaba da cewa tayi"bani da wani burin daya wuce naganshi cikin nishaɗi batare da wata damuwa ba,amma narasa dalilin dayasa kullum fuskarshi aɗaure baison yin fara'a,inaso na kawo sauyi a cikin zuciyar shi ya Allah ka bani wannan damar da zan zama ɗaya daga cikin farin cikin ran shi,"     Gaba ɗaya tayi nisa acikin tunaninta, batasan meke wakana ba kwatsam taji hannun mutun a ƙirjinta an shafa mata, a wani irin firgice ta buɗe idanunta gabanta na faɗuwa,    Bin su da kallo tayi atsananin tsorace, kai kana ganinsu kasan tantiran ƴan iska ne,su biyu ne mata jikinsu na sanye da uniform riga da wannan mini skirt ɗin,kai kace ba musulmai ba saboda ko head babu akansu, iya gashi ne kawai suka ɗaure abayansu shima ɗin na ƙari ne, ga uban bleaching sun sha abun dae kawai ba'a magana,.   Kallon juna su kayi suna dariya kafin ɗayar tace "wow gaskiya an mana nisa, Sofia tun yaushe aka kawo wannan zazzafar a school ɗinmu batare da sanin mu ba"? ta tambaya tana faman sakin murmushi gefen fuska, tuni jikin sehrish yayi mugun sanyi bakomai ta tuna ba face nasihar da kanal yusuf yayi mata kafin tafara zuwa school,   wadda ta kira da sofia tace"ni kaina bansani ba, amma yanzu tunda Allah ya haɗamu da ita, zatayi mana bayani ne, ta faɗi tana kallon sehrish tare da kashe mata ido ɗaya tace"ƴan mata,naga kin ɗaure fuska may be don na shafa chest ɗinki ne batare da izninki ba,ae mun afwa irin salon tamu gaisuwar kenan,ya sunanki ne"?    ƙara tamke fuska sehrish tayi jikinta na rawa Allah Allah take yi Amrish tadawo don tasan ita zata iya dasu,    ɗan ta6e baki zeenat tayi tare da cewa"Can't u talk to us? May be don baki son ko mu su wanene ba a school ɗin nan ba,zamu yi maki uziri ne," ta faɗi tana yarfa hannunta, yatsun nan zira zira tayi fixing nails dogaye a hannunta,    shiru sehrish tayi burinta amrish ta ƙaraso in ba haka ba tashi zatayi tabar musu table din gaba ɗaya ta koma Class, duk da yunwar da take ji acikinta,   Suna cikin zaman ne sai ga Amrish ta ƙaraso fuskar nan ɗauke da murmushi ta ruƙo tray a hannunta mai ɗauke da plate biyu na abincinsu tare da coke,   Sehrish na ganinta ta shiga sauke ajiyar zuciya,amma abunda ya daure mata kai time ɗin da amrish ta ƙaraso kai tsaye bayan ta ajiye masu tray ɗin asaman table din, sai ta miƙa ma Zeenat hannu suka gaisa tare da cewa"Am really glad to see u guys, nayi missing ɗinki sosai my zeenat," murmushi zeenat tayi tare da cewa"nayi missing ɗinki nima,bcox of u na matsa wa mommy sai mun dawo nigeria sbd a ƙagare nake da na haɗu dake ko fa isasshen bacci bana samu saboda rashinki,"     bin su da kallo kawai sehrish takeyi baki asake, yarda suke magana tamkar irin mace da namijin nan,   Muryar sofia ce ta katse su da cewa "oh ni ba'a ma ta tawa ko Amrish? Zeenat kaɗai kika gani shikenan bari na tafi," ta faɗi tana ƙoƙarin tashi cikin sauri Amrish tayi holding hands dinta tana cewa"am sorry kada ki tashi pls, in naga zeenat ina mantawa da komai ne,"   ɗaure fuska sofia tayi tace"i can't stay here,cos am getting jealous bazan iya jure yarda kike son Zeenat ba,   Dariya zeenat tayi tana cewa"in dai akan Soyayyata da amrish ne ke 6ata maki rai sai dae ki mutu,"     ta faɗi tana mayar da idonta akan sehrish da tayi zugudun tana kallon ikon Allah,   wuri Amrish tasamu ta zauna, kusa da sehrish suna facing ɗin su Sofia da zeenat,   ɗan kallonta amrish tayi tare da cewa"am sorry my friend nabarki da yunwa ko"? ta faɗi tana kallon Sehrish wadda jikinta ya gama mutuwa,   "A'a" ta bata amsa a takaice, Mayar da idonta tayi kansu zeenat tace"bansan zaku zo ba ae dana haɗo mana abincin tare,amma bari na tashi yanzu naje na ƙaro mana yadda zai ishe mu,"    cikin sauri zeenat tace"no ba sai kinje ba its ok ba mu jin yunwa a ƙoshe muke,"     murmushi amrish ta saki tare da kallon sehrish tace"bismillah mufara ci time ɗin komawa class ya kusa,"     Gaba daya hannunta kerma yakeyi a haka ta ɗauki spoon ɗin zata fara cin fried rice din da takawo masu shaqe da plate,tana ɗebowa shinkafar na zube wa saboda rashin natsuwar da take ciki ba don komai ba sai don zeenat data tsare ta da waɗannan manyan idanun nata zubin na karuwai a tsaitsaye suke ga eye lashes da tayi fixing sinsu kamar ɗiyar roba,   Ganin yarda hannun sehrish ke kerma ta kasa kai koda one spoon ne yasa Amrish ɗagowa ta kalli zeenat wadda ta zuba mata ido ko kyafta su bata yi,   ɗan gyaran murya Amrish tayi tare da cewa"Zeeta pls kidaina kallonta hakan na hana ta samun natsuwa,class mate ɗina ce jiya tafara zuwa school bata saba da kowa ba,"   ƙayataccen murmushi zeenat ta saki tare da cewa"its okey,ashe new comer ce, tayi mun kyau ne shiyasa nagaza janye idona akanta,ina fata kin sanar da ita komai game da zama cikin team ɗin mu?   Cikin sauri amrish tace"a'a pls mubar maganar nan,ita ba'a team ɗinmu take ba kawai class muka haɗa da ita,"    zeenat tace"that's impossible amrish tun da har kina yawo da ita a school dole ta zama ɗaya daga cikin mu,not only that yarinyar ta burgeni sosai........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda ƙarar cokalin amrish data bugi gefen plate dinta dashi tace"Zeeenat! Nace kidaina wannan maganar agabanta bana so," rai a6ace tayi maganar sannan ta mayar da idonta kan sehrish tace"pls ki ci abincin ki,"   gyaɗa kai sehrish tayi tare da mayar da hankalinta akan abincin dake gabanta,ci take amma batasan inda abincin ke zuwa ba,saboda tsoro da ruɗin da ta shiga,   yunƙurawa su kayi su biyun atare suka miƙe, cikin sanyin murya amrish tace"Am sorry zeenat i don't mean to hurts u,just bana son muna wannan maganar agabanta ne,saboda batasan komai ba ko mutane batason shiga cikinsu," hankali atashe take maganar tana kallon su,   atare suka yatsina fuska sannan zeenat tace,kinsan bana fushi dake amrish shiyasa kike mun duk abunda kika ga dama,amma ina so ki sani 6ata mun rai tamkar 6atawa mommynki raine, kuma kinsan mai zo biyu baya ya zama dole kibi umarnin duk abunda nace, don haka wannan yarinyar dole tashiga team ɗin mu !!!   tana gama faɗin hakan taja hannun sofiya suka fuce daga lunch room din   ita dae sehrish zuru tayi tana kallon ikon Allah bayan sun fuce ta mayar da idonta kan amrish wadda jikinta yayi mugun sanyi tuni kuma idonta sun cicciko da kwalla, amma bata bari sun zubo mata ba, sai ma kallon sehrish da tayi tare da ƙaƙaro murmushi tace"ki ci gaba da cin abincin ki mana,naga kin tsaya,"   jiki asanyaye sehrish ta mayar da hankalinta kan abincin tana ci amma zuciyarta ajagule saboda halin da taga Amrish ta shiga akan waɗannan ƴan matan da suka zo,ko su wanene oho, Ta tambayi kanta, ***************************Twins Fitowarsu kenan daga wanka atare kamar yarda suka saba kwatsam sai ga haroon ya turo ƙopar ɗakin nasu fuskarshi ɗauke da wannan shu'umin murmushin nashi, tsayawa yayi yana binsu da wani irin kallo jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da wata figaggar riga daya sanya, ya tada kwalar rigar tsaye,sam haroon baya kama da musulmai ko a fuska, balle ma daya kasance yana sanya chain a wuyan shi da kuma earrings irin yarda jigunannun ƴan iska ke sakawa,   Kallon juna su kayi atare kafin suka mayar da idanunsu akanshi,tuni ran Jahan ya 6aci ganin yarda yake bin jikinsu da kallo kamar wani tsohon maye, dama daga su sai short towels ajikinsu, farar surar ne mai jan hankali ta bayyana muraran,   ɗaure fuska jahan yayi tare da cewa "me ya kawo ka ɗakin mu? me kuma kake buƙata,indai kuɗi ne suna nan zamu baka,"    ta6e baki haroon yayi tare da yatsina fuska yace "yakamata kasan yarda zakayi magana dani with respect,ko don darajar wannan videon dake ajiye acikin wayata,'    tsuke fuska su kayi atare zuciyarsu na tafarfasa tamkar su rufe shi da bugu haka suke ji,    Cigaba da magana yayi "zuwa nayi don na ƙara tunasar daku, don na lura kamar kun manta da maganar dukiyata dake a wurinku, saboda waccan farin balbelen ɗan uwan naku da bai lfy na lura duk kun wani tashi hankali akanshi,'   Buga tsoki ayaan yayi yace "kada ka sake kiran shi da sunan balbela kadaina haɗa sunayen mu dana dabbobi domin kuwa mu bamuyin munayen ɗabi'un da za a haɗa sunan mu dana dabba, domin kuwa dabba yasan inda yake"    waro ido waje haroon yayi jin abunda ayaan yace a tsananin mamaki yace "Ayaan ni kake kira da sunan dabba"?! Ya tambaya a dan fusace   Cikin sauri jahan yace"kayi shiru ayaan kada kaja mana wani bala'en don na lura bai da Imani ko misƙala zarratin, tunda har bai damu da halin da ɗan uwansa ke ciki ba, burinsa kawai ya ƙuntata ma rayuwarmu," yayi maganar yana jefar haroon din da mugun kallo,   fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikinsa kafin yace "Waye kuma ɗan uwana? ae ni bana ɗaukarku jini na,ko ajinsi ku farare ne ni kuma baƙar fata ne, in fact ni bani da wata alaƙa daku, Uba fa kowa muka haɗa uwa kuma kowa da tashi, bayan shi kuma sai me?   shiru su kayi suna sauraron shi gaba ɗaya tsanarshi ƙara ninkuwa take yi acikin zuciyarsu,     juyawa yayi tare da cewa "Zan wuce ni ku huta lpy ƴan samari," yana faɗin hakan ya fuce yana sakin dariya kamar zautacce,   Mayar da ido ayaan yayi kan jahan yace "bro i ave an advise abt that bastard, why not mu kashe shi kawai kowa ya huta, cos i don't think ko mun bashi kuɗin zai goge videon,"    aɗan razane jahan ya kalle shi yace "ashe baka da hankali ayaan, kisa fa kace? Mu zamu kashe shi? In muka jefa kanmu cikin matsala fa? ya fadi yana kallon sa,    Ayaan yace "ba wata matsala jahan, just lettus kill him kowa ya huta !!!!!!!!!    "Mu bashi time in har muka bashi kuɗin bai goge videon ba, sai mu kashe shi kawai,don da abunda zai ta6a mutuncin family dinmu gwara abunda zai tada masu hankali na ɗan wani lokaci ya wuce" Acewar jahan,    Gaba daya sun amince da shawarar kashe haroon 😳   Duk mutanen da suka zo duba fawan duk sun ragu, har sun mai dashi daki sun kwantar dashi tun ɗazu,   Junaid kuwa lokacin da Abban su yashigo dashi ɗakin shi ya wuce dashi tare da kwantar dashi ya farfaɗo daga suman da yayi amma ya dasa da bacci,    Yanzu wanda suka rage a cikin gidan daga su matasan gidan sai abokin su sgr Shattima sun hallara a garden din gidan suna tattaunawa tare da marshal Omar dashi babban yayan,    Cg Abbas ya jima da tafiya amma yabar Amani a gidan saboda yace zai dawo da daddare ya ɗauke ta, duk ita ta taya azmee rarraba ma masu zuwa dubiya lemun a cups har suka lafa,    shigowa ɗakin Abbansu yayi yana kallon junaid dake baje asaman bed dinsa yana ta sharar bacci, ƙarasawa yayi wurin shi tare da zama daga gefen gadon nashi, sannan yaɗan sa hannun shi tare da bubbuga ƙafar junaid kamar mai jira aikuwa a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare kyawawan idanun shi da suka canza launi saboda bacci, yana jin muryar abbansu ya kira sunan shi nan take ya fashe da wani sabon kukan yana cewa "Abba yaya fawan ! Yana ina ! meya faru dashi.....'  Murmushi abbansu yayi yana kallon shi yarda yake kuka yana magana red lips din nan nashi na shagwa6a66u sun tatta6e,    Cikin natsuwa abban nasu ya soma cewa "Calm down ur mind junaid,ɗan uwanka yana cikin ƙoshin lpy yanzu haka yana can medical room dinmu mun kwantar dashi, shima sai kiran sunanka yake yi yana cewa Abba ina junaid akawo mun shi in ganshi, inaso in ganshi,"    jin wannan maganar ta abban nasu yasa junaid dakatawa da yin kukan nashi ya zuro da ƙafarsa zai sauko daga saman gadon, abbansu ya ruko hannun shi tare da cewa "pls junaid kada kaje mashi kana wannan kukan saika tayar mashi da hankali yaga kamar mutuwa zaiyi,   Cikin sauri junaid yasanya tafin hannayenshi tare da share hawayen dake zubo masa sannan abban nasu ya saki hannun shi, jikin shi har rawa yake yi wurin saukowa daga gadon, bin shi da kallo abban yayi har cikin ranshi yana mamakin yarda junaid ke tsananin son ƴan uwanshi don ji yake yi da wani abu ya same su kwara shi ya same shi koda mutuwa ce,akwai wani lokaci da abbansu bazai ta6a mantawa ba in ya tuna abunda ya faru har dariya yake yi wani sa'in kuma yaji saukar hawaye, wannan ba kowane lokaci bane face lokacin da junaid yana da kananun shekaru, idan suka je masallaci tare dashi suke zuwa saiya bari an kammala salla an natsu liman na kora addu'a, sai shi kuma ya ɗaga hannayen shi sama ya ɗaga murya yana cewa "Ya Allah ya Allah kasa na riga Abbana mutuwa da ƴan uwana,ya Allah kafara ɗaukar raina kafin nasu," a lokacin kowa mamaki ya kama shi jin abunda ƙaramin yaron kecewa, har wasu ke tambayarshi dalilin dayasa yake son ya riga abban nasu mutuwa da yan uwan shi sai cewa yayi "Saboda idan na riga su mutuwa bazan ga tasu mutuwar ba in tazo,zuciyata zata samu salama akan na rasa su da raina," gaba daya mutanen dake a masallacin abun ya basu mamaki sosai, kuma ka'ida ne duk in suka je masallaci tare dashi dole liman ya jira shi ya kammala addu'o'in shi mutane na amsa mashi da ameen, kafin shi liman yayi tashi addu'ar saboda rigimarshi,   Murmushi abbansu ya saki lokacin daya kammala tunanin nashi aranshi yace "Allah yabar mana kai junaid,ni kuma banaso naga mutuwarka nafiso nariga kowannan ku mutuwa don bazan juri ganin gawar ɗaya daga cikinku ba a kan idona," jikin shi a kasalance yake wannan zancen zucin,   Wayarsa ce ta soma ringing daga cikin aljihun rigarsa ta yadi, cikin sauri ya zura hannu ya ɗauko ta tare da duba sunan mai kiran nasa sunan AMMI ne ya bayyana akan screen din wayar hakan na nufin mahaifiyarshi ce Ammi ke kiransa    Nan da nan ya shiga natsuwarshi tare da ɗaga kiran ya kara a kunnan shi ya zabga sallama,    daga can bangaren Ammi ta amsa mashi sallamar sannan tace"yaro na ya kake ya kuma jikokin nawa? Naji abunda ya faru da fawan shiyasa ma na kira don na tambayi ya jikin nashi,    Tamkar yana agabanta cikin biyayya ya soma magana "lpy lou ammi suna cikin ƙoshin lpy,amma ba zaki zo gida ki duba jikin nashi ba?   "Hmmmm ni me zanzo inyi agidanka? Ae yafi ƙarfi na, daga nan ma zan iya yi masa ya jiki ba sai na kwaso jiki nazo ba balle inga abun tashin hankali abun kunya,'    nan da nan fuskar Abban nasu ta canza jin abunda tace,    "Ammi dan Allah kidaina faɗin hakan bana jin daɗi saboda me zaki ce gidana yafi ƙarfinki bayan nikaina a ƙarƙashin ikonki nake ke fa kika haife ni, kuma wane irin abun tashin hankali da abun kunya kike magana akai"? yayi maganar fuskarshi a yamutse,   tsoki taja tamkar zata fasa screen din wayar sannan tace "babu wani iko da nake dashi akanka hussein! Tunda har ban isa nasaka abuba kayi, wato son ƴa'ƴa ya rufe maka ido ko? ka daina ganin kowa da gashi? ba yarda banyi dakai ba akan ka tattara ƴa'ƴan nan duka ka haɗasu ka aurar kaƙi jin maganata, ka tara ƙattan maza,garada acikin gida sai sinturi suke yi acikin gidan ka,kaine jagoransu kai Gwauro su kuma tazurai gasu nan jibga jigba dasu kaƙi aurar dasu, daga anyi magana sai kace baka son ka takura masu ko kace ba su isa suyi aure ba don ka rainawa mutane hankali, dukansu kaf babu wanda in aka aura masa mace bazai iya yi mata ciki ba hatta wancan shagwa6a66en daka sangarta.......'   runtse ido abbansu yayi tare da saurin cewa "Ammi dan Allah kidaina fadin hakan, aure fa lokaci ne kuma in yayi duk zan aurar dasu ne.....'    wani tsokin ta sake buga mashi kafin ta kuma cewa "haka kullum kake faɗamin, narasa meyasa ƴa'ƴana duk basu jin maganata,daga kai har azeeman da wancan fitsararren da yayi hijra yabar ƙasar batare da sani na ba, ban ta6a tunain hussein zaka yi mun haka ba saboda duk kafi yi mun biyayya acikinsu amma yanxunn. .....' kukan da ta fashe dashi ne ya yasa ta kasa ƙarasa maganar nan take hankalin abbansu ya tashi, muryarsa har rawa take yi wurin cewa"Ammi dan Allah kidainamun kuka, ke fa mahaifiyata ce saboda me zakiyi mun kuka, hakan zai iya jefa rayuwata cikin matsala,dan Allah kidaina na roƙe ki mommyna indai akan wannan maganar ne yasa kike mun kuka wlh ashirye nake da nayi maki biyayya koba da son ransu ba, zan aurar dasu ne kawai saboda farin cikin ki !!!!!   jin abunda yace ne yasa ta sassauta kukan nata tace "yaushe kenan zaka aiwatar da hakan? kasan natsufa sosai kada na mutu ba'ayi auran nan ba, dan Allah hussein ka tattarasu duka ka aurar a lokaci ɗaya in har kayi mun hakan zan shaida cewa kai hussein ɗinane dana haifa,'    Ajiyar zuciya abban nasu ya sauke yana kara gyara wayar a kunnan shi yace "Insha Allah ammi nan bada jimawa ba,amma ki ban time saboda yanzu muna cikin fargaba game da waɗanda suka kaima su fawan hari,kin san sunce fansa suke ɗauka,kuma babban tashin hankalin ma maca ce AVENGER ɗin,'   shiru ammi ta ɗanyi kafin tace "Shikenan hussein,nima na shiga damuwa dana ji hakan,dama nasan dole hakan ya faru saboda mahaifinku kafin yabar duniya ya tara maƙiya sosai kasancewarshi kwararren jami'en Soja sun halaka dubban masu tada ƙayar baya a ƙasar nan, shiyasa nake tunanin ko daga 6angarensa ne maƙiyan suke son ɗaukar fansa,duk da nasan cewa wannan mai shuɗin idon baya rasa maƙiya don mutun ne mai haɗarin gaske shima baya gajiya da kame ƴa'ƴan mutane yana kaisu lahira, kaga kuwa dole su ɗauki fansa suma,yakamata kasanya tsaro sosai agidanka, kuma akwai shawarwarin da nakeso na baka,"    Abba yace "Ammi dan Allah kixo gida mana,ina ga zaifi in kika zo sai mu zauna mu tattauna akan matsalar tunda wannan abun ya shafi zuri'armu, kuma nama fi jin cewa akaina abin zai ƙare tunda ni ne na tara ƴa'ƴa,"     Ammi tace "shikenan zan fidda lokaci nazo insha Allah, amma inaso ka sani in zanzo saina tattara ƴan matan family ɗinmu gaba ɗaya na kwaso su don suzo ayiwa ƴa'ƴanka baiko dasu,"    dariya kawai abba yayi yana sauraronta sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi Sallama 😊   ya ajiye wayar gefen shi yana ɗan murmushi,    A can kuwa junaid na isa ɗakin da fawan yake kwance yana bacci, cike da tausayi yake kallon shi yadda yake jan numfashi da ƙarfi da ƙarfi,   ƙarasawa yayi tare da hayewa saman gadon yayi zaman cin tuwo tare da zabga uban tagumi yana kallon shi hawaye na zuba a fuskarshi,    Jin shessheƙar kukan junaid a kunnan shi yasa shi farkawa daga baccin da yake yi, ya buɗe idon shi a hankali yana kallon shi, yarda ya tallabe fuskarshi hannu bibbiyu ya tasa shi gaba yana sharar kwalla,a hankali fawan ya furta "junaid "   Kallon shi kawai junaid yake yana cigaba da matsar kwallo,hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda jikin fawan yayi ruɗu ruɗu da bulali wurin yayi jawur ya faffashe duk da anyi masa dressing na wurin an shafa masa magunguna,ga kuma ɗinkin da akayi masa a chest ɗinshi,   dakyar ya daddage ya tashi daga zaune yana fuskantar junaid ɗin daya tasa shi gaba,     "Junaid," fawan ya sake ambaton sunan shi a karo na biyu ganin yarda ya zabga tagumi yana kallon shi hawaye na zubowa gefe da gefen fuskarshi, zama su kayi suna fuskantar juna, kallon shi kawai junaid keyi batare da yace uffan ba,   daƙyar fawan ya ƙaƙaro murmushi yana kallon shi, hannun shi yakai tare da shafa gefen fuskar junaid yace "bari nabaka wani labari ƙanina,"  junaid ya zuba mashi ido yana sauraron shi,   fawan yace "lokacin da waɗannan miyagun suka ɗauke ni ko, suka shiga dani wani ƙogon dutse mai rikitarwa, suka ban za6i biyu, su kashe ni ko su azabtar dani wanne nakeso, kasan me nace masu? ya fadi yana kallon shi, girgiza kai junaid yayi alamar a'a,   Fawan yaci gaba da cewa "a lokacin kai kawai ka faɗo mun araina, aranar da zamu tafi kai ta zabga kuka kana cewa babu inda zamuje ƙafarka ƙafarmu dakyar abba ya shawo kanka, ka tuna abunda ka faɗamun lokacin?   shiru junaid yayi yana tuna lokacin daya cakumi rigar fawan yana ce "ya fawan kayimun alƙawarin cewa zaka dawo araye inaso na sake ganin ka,' a lokacin fawan yace mashi "junaid ae tafiya ba mutuwa bace, insha Allah zan dawo araye in Allah ya yarda," murmushi junaid yayi tuna wannan   shima fawan murmushin yayi sannan yaci gaba da cewa "saina ce masu ni bana tsoran mutuwa, ban isa na hana kaina mutuwa ba in lokacina yayi, kamar yarda kuma baku isa ku hana kan ku mutuwa ba idan tazo maku, sai ɗaya daga cikin su yace mun "Ka za6i ka mutu kenan? mu kashe ka kawai? Saina girgiza kai nace "a'a ku azabtar dani kuyi mun duk irin hukuncin da zakuyi mun amma kubar ni da raina saboda akwai ƙaramin ƙanina da nayi ma alƙawarin cewa zandawo da raina, inaso na cika mashi wannan alƙawarin nasa na gani na araye, bana so na karya mashi zuciya nafiso ko mutuwarce ma to na mutu agabanshi yadai ganni da raina...............' dakatawa fawan yayi da maganar saboda hawayen da suka zuzzubo mashi, junaid kuwa tuni ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai,  haɗe kansu su kayi wuri ɗaya suna faman shessheƙar kuka atare,   dakyar fawan yaci gaba da cewa "Shine suka bankamun kayan maye sannan suka ɗaure ni tamkar dabba, su ka dunga zuba mun bulali da kaca a jikina har saida suka ga jini na zuzzuba ajikina amma hakan bai ishe su ba, ba don su babban yayan mu sun zo ba to da tabbas kashe ni sukayi niyyar yi a lokacin, Amma alhamdlh naji daɗi sosai da Allah yacika mun burina na ganin na rayu don na cika maka alƙawarinka...... .. murmushi junaid ya saki tuni ya ji sanyi ya ratsa mashi zuciyarsa,   janye kansa yayi daga na fawan sannan yace "kana jin yunwa in kawo maka abinci"?    girgiza kai fawan yayi tare da cewa "junaid a ƙoshe nake,ɗazu azmee ta haɗamun kakkauran tea tare da fruits na sha,naji daɗin su sosai,"    "Bari nabarka ka huta sosai, na katse maka baccinka, amma ka sani zan dawo don atare zamu kwana," yayi maganar yana ƙara jaddada masa ayayin da yake sauka daga saman gadon,   Murmushi kawai fawan ke bin shi dashi harya fice daga ɗakin,komawa yayi a hankali ya kwantar da bayansa saman filonsa tare da lumshe idon shi,    Cikin sauri junaid ya fito tare da tunkarar hanyar fita saboda tunawa da sehrish wadda ke a school, lokacin tashin su yayi gashi time na salla na kokarin wuce shi, yana dab da fita daga ƙopar Amani ta kwada masa kira, dakatawa yayi tare da juyawa yana kallon ta da murmushi a fuskarsa, cikin sauri ta ƙaraso gab dashi tana cewa "ina zaka je ne? Junaid yace "inaso zance masallaci ne nayi sallah, daganan zan wuce na dauko sehrish daga school,"    ɗan jinjina kai tayi kafin tace "wannan yarinyar da muka gani ɗazu itace sehrish"? Ta tambaya tana kallon shi duk da tasan akanta yake magana   "Yeah itace," ya bata amsa atakaice tare da fucewa yana cewa "Sauri nake aunty amani time ɗin sallah zai wuce ni,"     Juyawa amani tayi tana jinjina kai, a ƙagare take da junaid ya dauko yarinyar daga school saboda tana son ta sake ganinta har ma ta yi magana da ita,  *wannan kenan*😍👍 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994    *Boss Bature* Who's the AVENGER❗‼️⁉️ ************************** Har suka koma Class jikin sehrish a sanyaye ita kuma amrish fuskarta ta nuna alamun damuwa sosai game da abun da zeenat tace mata, gaba ɗayansu dae babu daɗi har suka taso daga school ɗin,tsayawa su kayi daga wajen school din sai ga drivern Amrish ya ƙaraso, juyawa tayi ta kalli sehrish tace"Ni zan wuce,sai mun haɗu gobe in Allah yakaimu,"   Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"Allah yakaimu lpy,"   "Ameen" ta amsa mata sannan ta wuce cikin motar,   ta jima a tsaye tana jiran ƙarasowar motar junaid dalilin dayasa bata hau bus ba kenan saboda tasan dole yazo ɗaukarta,masu motoci saiyi mata tayi suke don tazo su rage mata hanya amma taƙi yarda tahau motar kowa saboda tasan cewa ba kowa bane zai ɗauke ta don Allah ba, tana cikin wannan tsayuwar ta hango motar junaid ya shawo kwana,murmushi ta soma saki tamkar tayi tsalle don murna tunkan ya ƙaraso ta tunkari motar da sauri,   yana tsayar da motar ta sanya hannu ta buɗe motar sannan tashiga ciki tare da rufe motar,   juyawa tayi ta kalle shi tare da cewa "ka manta dani ko"? Ina ta faman jiranka,"    ɗan murmushi yayi yace "am sorry ba da son raina ba reesh, kina araina ynx ma daga mosque na wuto nan,' ya ƙarasa maganar yana kallonta, bin fuskarshi tayi da kallo alamun damuwa ta gani sosai atattare dashi,tuni itama taji zuciyarta babu daɗi, cikin sanyin murya tace "junaid kayi kuka yau ko? kuma kana cikin damuwa"?    jinjina mata kai yayi alamar eh,   ɗan 6ata fuska tayi tare da cewa "dan Allah junaid kadaina sa damuwa aranka wlh bana so, natsani naga mutun mai cike da farin ciki irinka a Yanayi na damuwa,'    A kasalance yace "don't worry ur self,zan daina ne reesh da zarar nasamu abunda nakeso, ki sani acikin addu'arki da kuma sauran ƴan uwana,'   "Insha Allah junaid bana mantawa da kowannan ku acikin addu'a ta," ta fadi tana jaddada masa maganarta,    "Yanzu kayi mun dariya in gani magana kona samu kwanciyar hankali,"   tunkan takarasa maganarta, ya wage bakinsa yana dariya,bin fararen haƙoransa tayi da kallo a jere tsaf suke tamkar mai tallar maclean saboda kyal ɗinsu, ga 2 dimples dinsa da suka lotsa sosai,   Yatsanta takai acikin dimple ɗinsa ta zura shi saboda burgetan da yayi, sun jima suna shiririta acikin motar kafin ya tayar da motar suka miƙi hanya, cike da nishaɗi suke sauraron waƙar da junaid ya kunna masu ta lilin baba,natsuwa yayi a hankali yake driving yana sauraron muryar rishi dinsa dake bin waƙar   "Kaine zuciya take ta yabo🎶kaine nawa in da rai da rabo, amanar zuciya ka damkeee, da kaine zanyi Wuff, zanyi wuff zanyi wuff🎶🎶   Fashewa da dariya junaid yayi saboda daɗin waƙar da yaji, sai yaji tamkar dashi take, musamman da tadinga nuna shi da hannu tana cewa(dakaine zanyi wuff)    Tana kai baitin ƙarshe shima ya ɗauka,    "Ke ce zuciya take ta yabo kece tawa inda rai da rabo,amanar zuciya ki damkeee, da kece zanyi wuffff !🎶    Zuba mashi ido sehrish tayi tana kallon shi, yana driving yana raira wakar kuma yana ɗan waiwayon ta,   gaba ɗaya sun shagala basuyi aune ba, suka ji wata mota a bayanzu ta bugi motarsu da karfin gaske,ƙarar da sehrish ta saki ne yasa junaid sakin sitiyarin motar gaba ɗaya, aikuwa nan take motar ta karkace ta nufi wata tamkekiyar bishiya da gudun gaske,   Waro ido sehrish tayi tare da cewa "Junaiiiid !! Innalallahi wa'inna ilaigirraji'un,   Ƙanƙame shi tayi ajikinta saboda gaba ɗaya yagama rikice wa, gaba ɗaya sun ƙanƙame juna, maimakon Sehrish ta taimaka mashi ya rike sitiyarin motar yayi control dinta, Amma saita janyoshi jikinta ta kankame suka bar motar Tana control din kanta,    Cikin ikon Allah motar ta kashe kanta adai dai bakin bishiyar ƙiris ya rage su gabje ta da ba ƙaramin buguwa zasu yi ba,    Ajiyar zuciya suka shiga sauke wa tare da dagowa atare suna kallon bishiyar, Allah ya takaita wahala da motar ta kashe,    Sai faman zazzare Ido suke Yi su duka biyun, sun ji kamshin mutuwa, juyawa Sehrish yayi tare dasa hannu ta zuge glass din motar Don taga wanene ya bugi motarsu,   wata bakar motace Mai black tunted kirar range Rover, Kamar jiranta suke ta leƙo,suma na cikin motar suka zuge nasu glass din motar,   Gabanta ne yayi mugun bugawa daraaam !! Ganin mutanen dake cikin motar, giggan Yan iska ba Imani a fuskarsu bakeke ne wulik, kana ganinsu kasancewa turo su akayi, da gangan suka bugi motar Junaid din,"   duk Tasha jinin jikinta, ɗaya daga cikinsu ne ya ɗago mata hannu tare da cewa"hi We're sorry guys mun bugi motarku batare da mun sani ba,kuyi mana afwa,amma yakamata kija masa kunne ya dinga kulawa wurin yin driving yana yin tukin ganganci, hakan zai iya halakar daku wata rana,"   Suna faɗin hakan suka ja motar tasu da gudun gaske suka bar wurin,   Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyawa ta kalli junaid wanda yayi wuri wuri da ido, duk a tsorace yake da abunda ya faru dasu,    Murya asanyaye tace "junaid kayi sauri mubar wurin nan,"   daker ya iya tashin motar sannan yaja ta da baya baya suka baro jikin bishiyar, ya hau kan titi dasu sannan ya miƙi hanyar gidan,.     gaba ɗaya sehrish jikinta ya gama yin sanyi saboda ta hasko wani abu game da bugun motar junaid da sukayi,maganar da sukayi mata tamkar gargaɗi ne sukayi mata akan wani abu da zai faru dasu,tabbas tashiga ruɗani,   A hankai suka shiga babban entry din gidan, yayi parking motar sannan suka fito atare kowa na faman sauke ajiyar zuciya,atare suka jera suka nufi cikin gidan   ɗan kallon sehrish yayi ganin tamkar ranta ya 6aci don haka yace "am sorry rishi laifina ne,nayi ganganci dana kunna mana waka acikin mota har muka shagala sosai,"   fuskarta a yamutse tace "its not ur fault junaid, ba ka yi tuƙin ganganci ba,da gangan suka bugi motar mu,karka sama kanka damuwa ni bana ganin laifinka, Allah zai saka mana ma,"   tuni yaji sanyi ya ratsa ransa, bayan sun shiga babban falon ta wuce bedroom ɗinta, shima kuma ya wuce nasa ɗakin,    Shaf shaf ta tu6e uniform ɗinta,  asaman gadon tabarsu tare da school bag din duka, toilet ta fada tayi wanka tare da dauro alwala, tana fito wa ta bude wardrobe dinta tare da ciro wata gown mara nauyi ta zura, sannan ta shimfiɗa carpet ta zura hijab tare da kabbara sallah, anatse tayi sallarta, bayan ta kammala bata ko nemi abinci ba saboda taci tayi hani'an a school, gado kawai ta haye tare da baje wa tana bacci,   Shima junaid daya wuce nashi dakin nashi ya faɗa toilet ya yi wanka tare da canza kayan jikin shi izuwa riga da wando,    Yana kokarin fitowa daga ɗakin sai ga su twins sun faɗo ciki atare sun ɗau wankan jeans da t shirt,   Yana ganin su ya saki fara'a tunkan su fara magana yace "maganar kiran mommy ce ko"?   dariya su kayi atare, ayaan yace "ashe dae ka gane,Allah yasa bamu takura maka ba,"   girgiza kansa yayi tare da cewa"a'a yanzun nan zan kirata insha Allah,"   Jahan yace "yawwa masoyi junaid mai son farin cikin ƴan uwan shi,pls idan ka kirataa wayar,kayi mata biyayya kaji? kada kace zaka ƙi mata magana, ita mahaifiyarmu ce,idan bata son ɗaya daga cikin mu ae bazama ta ɗauki cikinmu ba balle har ta ruƙe sa na tsawon wata rana, kuma tayi naƙudar haihuwarsa,nasan kai mai ilmi ne junaid kasan hukuncin wanda ya sa6a ma iyayensa dan Allah ka manta da komai," yarda jahan ke yi masa nasiha cikin daɗin rai yasa shi jin sanyi aransa harma yaji cewa ya ƙosa ya kirata a wayar,    "Shikenan ya jahan da ya ayaan,zan kirata yanzun nan amma ba a gabanku zanyi wayar ba,idan nagama dae zan sanar daku duk yarda mukayi da ita,"   Cike da farin ciki suka ce "yawwa ɗan ƙanin mu, yanzun nan kuwa zamu fita daga ɗakin,sai mun ji ka," suna fadin hakan suka juya tare da fucewa daga ɗakin hada rufo masa ƙopar da kyau,   ɗan murmushi junaid yayi sannan ya koma gefen gadonsa ya zauna tare da kai hannu ya ɗauki wayarsa dake asaman side drawer,    Zuba ma screen ɗin ido yayi yana tunanin ta yarda zai fara kiran mommyn tasu, for the first time zaiji muryarta,a lokacin baya kusan kullum saita kirashi awaya bai ɗauka don ko saving na numbarta baiyi ba,saboda haushin ta da yake ji,    A hankali yashiga danna wayar, kai tsaye cikin messages yashiga saboda akwai last messages da ta tura mashi, buɗe sakon yayi ya ƙara karanta shi "Thanks 4 ignoring me, i won't call u again bye,"    tanan ya ɗauki number tare da danna mata kira, ta shiga ringing,   Almost 3 times tana ringing ba'a ɗauka ba,ana huɗunne yana ƙara kira tayi picking,shiru yayi baice komai ba,har sai da tashiga tambayar wanene jin anyi mata shiru, yanayin muryarta akasalance saboda bacci,     Cikin harshen spanish take tambayar wai wanene,   Sai a lokacin junaid ya ambaci sunan "Mommy," shiru tayi tana nazari don ta gano muryar wacece wannan acikin ƴa'ƴanta,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Romeo ɗinta duk da basa waya amma abbansu na turo mata voice ɗinshi da yake mata recording aduk lokacin da suke fira dashi ko kuma lokacin da yake tsaka da shagwa6a,   tuna wannan yasa Alexandra cewa "Romeo ɗina ne"? Ta tambaye shi donta tabbar cewa shiɗinne da take hasashe,    Ashagwa6e yace "junaid ɗin abbana ne," Jin hakan yasa alexandra tashi daga kwancen da take asaman shimfiɗeɗen gadonta, cikin sauri takai hannu ta kunna bedside lamp, bedroom ɗin nata ya ɗanyi haske tamkar zata iya gashinin zahiran agabanta, cikin tsananin farin ciki tace "allah yasa ba mafarki nake ba,romeo da kan shi yau ya kira ni a waya, harya kirani da sunan mommyn shi, cikin tsantsar farin ciki take maganar, Duk junaid na sauraronta sai da takai aya sannan yace. "Mom ki ƙaddara cewa mafarkine, saboda bashi da banbanci da mafarkin cos i called u by force ba don son raina ba, ya faɗi with angry face tamkar yana agabanta,   murmushin takaici tayi kafin tace"na sani dama saka akai ka kira ni,koma manene laifina ne nasan fushi kake yi dani,baka sona romeo ni kuma nadamu dakai sosai.....' ta faɗi cikin muryar kuka,   "Mom ba ki sona,da ace kina sona da baki tafi kinbarni ba a lokacin da bansan komai ba soyayyarki kawai nake buƙata da kulawarki, amma duk wannan bai dame ki ba,kin tafi kinbar ɗan jinjiri ya yi rai ko kar yayi duk bai dame ki ba,kashe ni kika so kiyi............' Fashe mata da kuka yayi mai cin rai, nan da nan hankalinta ya tashi duk yadda taso ta lallashe shi ya daina kukan amma yaƙiya,janye wayar tayi daga kunnanta tare da zuba ma screen ɗin wayar ido tana sauraron kukan shi, har cikin ranta ba ƙaramin ɗaci ta ji ba, tama rasa ta yarda zata fahimtar dashi, Sai da junaid yayi mai isar shi sannan ya tsagaita yana faman sauke ajiyar zuciya,    Jin haka yasa tace "pls can i turn it to video call,cos i wanna see u face to face," Rai a6ace junaid yace "ban amince ba mommy,if u really want to see my face then come to nigeria,"   Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa "ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba'a son raina nabar ƴa'ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne... '   Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce ƙarya take masa ba saboda shi kanshi ya jima yana tunanin dalilin dayasa mom ɗinsa tabarshi, saboda shi ya kasance yaron da kowa ke so mai farin jinin gaske, taya za'ace uwar da ta tsugunna ta haife shi, itace zata ƙisa ta guje shi just without any reason !? Idan ka samu kaɗan ka gode ma Allah gobe saiya baka mai yawa😁 Cikon page din ɗazu dama 3 page nace zan haɗe maku, sa'an nan ku gyara zama 😱😨 Ina guga ina editing gashi nan har na ƙona mata hijabi ynx jira nake tadawo inga mai zatayi mun😇🤣 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku🤩😍 It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.  The father Of Soldiers```   Story &  Written         By        Hafsat Bature           (Boss Lady) _💋Boss Bature💋_ Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa "ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba'a son raina nabar ƴa'ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne... '   Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce ƙarya take masa ba saboda shi kanshi ya jima yana tunanin dalilin dayasa mom ɗinsa tabarshi, saboda shi ya kasance yaron da kowa ke so mai farin jinin gaske, taya za'ace uwar da ta tsugunna ta haife shi, itace zata ƙisa ta guje shi just without any reason !?    gaba ɗaya ya tafi duniyar tunanin ya amince da zancen mahaifiyar shi ko kuwa, shessheƙar kukanta daya ji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa cikin sauri yace "its okey mom,ni banason nayi sanadin da zan zubar da hawayen wani,bare ke da kike mahaifiyata ma,"    Ajiyar zuciya alexandra tashiga saukewa jin kalamansa masu daɗin gaske, muryarshi ce tasake katse ta da cewa "pls wipe ur tears mom,"    Murmushi ta saki tamkar tana agabansa,hannu ɗaya tasa tana share hawayenta kamar yarda ya umarta tayi,  . bayan ta gogesu tace "baka son ganin hawaye ne? amma meyasa baka amsa kirana duk in na kira wayarka, ko na kira wani nace ya baka muyi waya,a duk lokacin da hakan ta faru ina zubar da hawaye na sosai,   Murya asanyaye take magana, har cikin zuciyarshi yake jin maganar mommyn nashi,   "Mommy inaso zan aje waya,i wll call u next time, Cikin sauri tace "ka haramta mun ganin fuskarka ko? Shikenan my romeo,ka faɗi kome kake so zan maka shi"   "Komai nace kiyi zaki yi ne"? Ya tambaya yana jiran amsa   "zan yi maka shi koma menene,"   murmushi junaid yayi sannan yace"yaya ayaan da jahan suna son wani abu wurin ki, kiyi masu shi, sannan ki dawo gida ki bani kulawar da baki bani ba tun ina yaro,"    Murmushi tayi sannan tace"shi kaɗai kake so"?  Yace "eh,"     Jinjina kai tayi tare da cewa"duk abunda kace zanyi saboda in tabbatar maka da cewa ina tsananin ƙaunarka my romeo,sannan koda daga bayane kaga wani abu kana so ka sanar mun, zanyi maka koma menene shi indae acikin duniyar Nan yake, sun jima suna yin wayar daga bisani su kayi sallama, bayan ya ajiye wayar ya dinga jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarshi ga wani irin kwanciyar hankali da yazo mashi yasan cewa duk saboda wayar da yayi da mom in shi ne yasamu wannan natsuwar, Sai wuraren ƙarfe 4'dai dai sehrish ta farka tana faman yin hamma, ba ƙaramin daɗin baccin taji ba,saukowa tayi daga saman gadon nata ta wuce toilet jim kaɗan tafito da alwalarta, hijab ta dauko ta zura a jikinta sannan ta kabbara sallah, tun tana cikin yin sallar taji ana knocing ƙopar ɗakin nata, don haka tana kammala shafa addu'a ta miƙe a hanzarce ta buɗe ƙopar,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin matar nan ta ɗazu,murya na rawa tace "ina yini," murmushi Amani tayi tare da cewa "lpy ya kike,"? "Ina lpy," ta bata amsa ataƙaice, dan ta6e baki amani tayi kafin tace"naso ɗazu dana ganki da safe muyi magana amma naga kina cikin sauri ne zaki school," ta fadi a wayance   Sehrish tace"eh hakane," duk tarasa natsuwarta, tsoranta me take son ce mata,    Amani taci gaba da cewa"Tun yaushe kika fara aiki a gidan nan ne"? Saboda ni ban ta6a ganinki ba gsky,"   Sehrish tace"banjima da farawa ba,"   "Amma nayi mamamkin yarda shaƙuwa ta shiga tsakanin ki da mutanen gidan har abbansu ya mayar dake ɗiyarshi,kuma naga kina da kusanci ssae da junaid har yana ruƙe maki hannunki kamar wata ƙanwarsa, bayan matsayinki bai wuce na ƴar aiki ba," ɗagowa sehrish tayi a ɗan rikice tana kallonta jin abunda tace,    Murmushi amani ta kuma saki kafin tasanya hannu ta dafa kafaɗar sehrish tace"idan ba damuwa inaso in baki wata shawara wadda zata amfane ki, domin na lura kinason jefe kanki cikin hatsari, karfa ki ruɗa kan ki,".   Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"ina sauraronki," amani taci gaba da cewa"ki nisanta kanki daga kowa na cikin gidan nan,ka da ki bari wani ya so ki acikin matasan gidan nan,kuma kada ki kuskura ki bari zuciyarki ta faɗa tarkon son wani,idan da hali ma ki tsaya a iya matsayinki na ƴar aiki,zaki fi samun kwanciyar hankali,"   Tun da tasoma magana sehrish ke bin ta da kallo fuskarta ta nuna alamun rikicewa don sam batasan inda zancen matar ya dosa ba,   "Kada kice na cika ki da surutu,its just an advise in kinyi amfani da ita ke zata amfana,but if u don't hmmmmm u can even lost ur life........'  Wani irin bugu zuciyar sehrish taji saboda abunda amani tace, na cewa zata iya rasa rayuwarta, tuni jikinta ya shiga yin kerma alamomin tsoro sun bayyana a fuskarta, hankali atashe take cewa"meyasa kika ce haka?saboda me zan rasa rayuwa ta?don kawai naso wani ko wani ya so ni acikin gidan nan"? Ta tambaya tana kallon Amanin,    Kafin Amani tace wani abu, muryar Azmee ta katse mata hanzarinta da cewa"tsayuwar me kuke yi ne, ke da nace ki kira mun ita don tazo mu haɗu mu fara girkin da wuri"? Ta tambaya tana kallon Amani, . cikin sauri Amani ta dan basar tare da sakin fara'a a fuskarta tace"dama muna ɗan tattaunawa ne,kinsan bata sanni ba nima kuma haka, so ina gabatar mata dakaina ne don musan juna,"   Zuba mata ido sehrish tayi kawai baki asake tana kallonta,   Azmee tace"Hakan na da kyau, sehrish wannan matar yayanku ce Abbas sunanta AMANI,ina fata zaki saki jiki sosai da ita domin kuwa tana da mutunci sosai,   daƙer sehrish ta ƙaƙalo murmushi tace"Insha Allah aunty azmee,"    tayi maganar tana kallon Amanin ita ma kallonta takeyi har lokacin, Azmee ta lura da kallon kallon da suke yi don haka tace"Amani mu wuce kitchen,ke ma sehrish ki ajiye hijabin jikinki ki zo mufara aiki,"    Juya ciki sehrish tayi su kuma suka wuce kitchen ɗin, kanta ya gama ɗaurewa da maganganun da Amani ta gaya mata,amma duk da hakan ba tajin zuciyarta zata karaya saboda wasu ƴan kalamanta,hannu tasa tare da tu6e hijabin ta ajiye ta nan saman gadon, sannan ta ɗauko ɗan mayafinta cikin wardrobe tayi rolling ɗinsa,   A dai dai lokacin da ta fito daga ɗakin ta tunkari hanyar kitchen ɗin sai ga haroon ya fito daga part ɗinsu,sai da taji gabanta ya faɗi don ita yanzu kallon shaiɗan take yi mashi saboda ƙahone kawai babu akanshi,    Ƙarasowa yayi inda take suna facing ɗin juna yace"mutuniyar ba hello ba hi,laifin me nayi maki ne"? Yayi maganar yana ɗaga mata gira tare da kashe mata ido,   Tsuke fuska tayi tare da bi zata wuce cikin sauri yasha gabanta tare da ware hannayensa yace"daga kin ƙara motsowa zan rungume.........' kasa ƙarasa maganar yayi gabansa na faduwa ba don komai ba sai don ido biyun da su kayi da SGR wanda ke shigowa cikin babban falon su biyu ne tare da shattima suka shigo,banda omar wanda tun a masallaci suka rabu,   Cikin sauri haroon ya canza kalamansa da cewa"kin gane dole kisa tsoran Allah acikin zuciyarki idan kinason rayuwarki tayi kyau,amma in kika ce zaki biye ma ƙawayen banza zasu kaiki ne su baro ki," ya dage sai zuba yake yi mata,juyawa tayi don taga wanene ya shigo saboda ganin yarda haroon yabi ya susuce ya sauya magana,    hada ido su kayi da shi adai dai lokacin yana ƙoƙarin kawar da nashi idon daga na haroon,har cikin zuciyarta taji wani irin sanyi aranta dama da kewarshi tadawo gidan,ganin shattima na kallonta yasa tayi saurin cewa"ina yinin ku"? "Lafiyalou Alhmdllh ƴan mata," ya amsa mata fuskarshi asake,sannan suka wuce upstairs part dinshi,sam takasa janye idonta daga kallon Bayan sgr da takeyi ko kyaftawa ba tayi har suka 6ace ma ganinta,hakan ba ƙaramin fusata haroon yayi ba rai a6ace tace"Ke!!kina a gabana kuma kike kallon wani"?    ƴar dariya sehrish tayi kafin tace"Namiji nake kallo," tana faɗin hakan tabi ta gefenshi ta wuce izuwa kitchen,baki asake haroon ya tsaya yana huci jin abunda tace,aransa yace"lallai ma ƴar shilan can harni zata ce ma Namiji take kallo,hakan na nufin ni kallon ɗan daudu takeyi mun,zan yi maganinta ne! Watan fara shan uƙubarki yayi acikin gidan nan !!zan 6ata maki suna a wurin shi dama kowa na gidan nan"!!! Yana gama faɗin hakan ya gyaɗa kanshi yana sakin shu'umin murmushi ya fuce daga falon. Shiga kitchen din tayi ta same su har sun fara aikin girkin,sallama tayi masu suka ɗago suna kallonta atare, azmee tace"sannu da zuwa za'a fara aikin ne,"   Ɗaga kai tayi tare da cewa"eh amma inaso nafara kaima su babban yaya abunsha naga sun shigo tare da wani ynx," zuru amani tayi tana kallon ikon Allah,   Azmee tace"toh bari na haɗa maki tare da snacks ki kai masu,"    ɗan murmushi sehrish ta saki tana jiranta duk in ta ɗago sai sun haɗa ido da Amani,sai tayi saurin kawar da idonta,   Bayan azmee ta kammala haɗa mata two cups na coffee a saman tray tare da plate mai ɗauke da snacks ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi ta rike da kyau a hannunta sannan ta juya ta fuce daga kitchen ɗin tana faman sauke ajiyar zuciya,     Wuce wa tayi upstairs tayi a bakin falon ta tsaya tare da yin sallama,muryar wannan abokin nan nasa taji ya amsa mata da cewa"wa'alaikum salam," sai da ta dai dai ta natsuwarta sannan tashiga ciki gaban ta na faɗuwa kamar kullum,    Shattima ne kawai ta samu zaune saman 3 seater yana danna wayarshi,  Ƙarasawa tayi tare da ajiye tray din saman table din gabansa,maimakon ta tafi saita tsaya tana faman wasa da yatsun hannunta burinta kawai taga sanyin idaniyarta tasan cewa zai fito shiyasa ta tsaya,   Hannu shattima yasa ya ɗauki cup of coffee din yakai bakinsa yana kurba da alama ba ƙaramin daɗi yayi masa ba,sam takasa tafiya saboda bata ga sgr ba,ganin tayi masa tsaye yasa shi jinkirtawa da shan coffee ɗin da yake yi yace"Ya sunanki ne"? firgit ta ɗanyi tare da kallon shi tace"Sehrish," jinjina kan shi yayi kafin ya ƙara cewa wani abu sai ga Sgr ya fito sanye da short ajikinshi tare da singlet,nan da nan sehrish ta shiga natsuwarta, wuri ya samu ya zaune gefen shattima, cikin sauri ta ɗauki cup ta miƙa masa hannu yasa tare da kar6a yana dan sipping dinshi a hankali,   Mayar da idon shi yayi kan sgr yace"wannan fa ban ta6a ganinta ba is she ur sister? Ya tambaya yana kallon shi,   "U can ask her," ya faɗi batare da ya dago ya kalle shi ba, murmushi shattima yayi tare da mayar da idon shi kan sehrish yace"kina da connection dasu ne,ko yar wurin Aunt dinsu ce ko uncle dinsu"?   ɗaga mashi kai tayi alamar"eh" sunnar da kai tayi cikin jin kunyar ƙaryar da tayi,   Shattima ya kuma cewa"amma Abba yayi maki miji kuwa"? ɗagowa tayi tare da dan zare ido saboda jin abun yace mata,mamakin ta yadda yake ta tambayarta bayan sam ko a fuska baiyi kama da mai son surutu ba shima,    girgixa kai ta kuma yi tare da cewa"a'a bai mun ba"  "Because of what?ko babu wanda kike so acikin matasan gidan nan"? maimakon ta bashi amsa sai ta ɗan saci kallon Sgr dake kur6ar coffee din hannun shi,   Wani irin murmushi shattima ya saki saboda yaga inda sehrish take kallo, acikinsa ransa yace"hmmmm dama nasani,"   A fili kuma yace"yana da kyau ko'? A firgice sehrish ta mayar da idonta kan shattima tace"Wa"? da ido yayi mata nuni da Sgr, sunnar da kai tayi tana murmushi tace"eh,"    "Shi bai yarda da mace ba,yace mata matsala ne arayuwar namiji,but i want to ask u something a misali mace ta samu righteous husband kamar wannan lu'u lu'un,wanda ya haɗa komai ga kyau ga ilmi ga dukiya, kina tunanin akwai macen da zata yi gangancin Mallakarsa har ta zama matsala arayuwarshi balle ta 6ata mashi rai"?    jikin sehrish tuni ya soma kerma saboda tsoran dogon sharhin da abokin sgr ɗin ke yi mata,babban tashin hankalin ma gashi a kusa duk da yayi tamkar baya jinsu,ammma ae kunnan shi a buɗe suke ba'a toshe ba dole ne yaji abunda suke cewa,muryarta na rawa ta buɗe baki zatayi magana kenan kwatsam taji wannan sanyayyiyar muryar tashi tace"ba kowace mace bace zata so ni dan Allah in fact duk macen da zata soni sai don waɗannan abubuwan daka lissafa," yayi mgnar again batare da ya kalle su ba, sai ma hannun shi daya zura cikin short pocket dinsa ya ciro wayarsa dake ringing tare da yin picking ya kara a kunnan shi yana magana cikin harshen turanci,   gaba ɗaya jikin sehrish yayi mugun sanyi kalamansa akwai ƙamshin gsky acikinsu,yanzu ta ƙara gane dalilin dayasa mace sam bata agabanshi,saboda yasan cewa duk wadda zata so shi,ba zata so shi dan Allah ba face sai don wani abu daya mallaka,kamar wannan kyakkyawar surar tashi mai matuƙar jan hankali,da dukiyarsa kuma,  ga kuma ilmi duka dai😇 Amma har ga Allah ita ba don dukkan waɗannan abubuwan ba take son shi ba,ataƙaice ma tunkan taga fuskarshi tunkan tasan koshi wanene ta afka ma tarkon son shi ta hanyar sunan shi kawai da taji suna faɗi BABBAN YAYA,   gaba ɗaya ta tafi zurfin tunani muryar shattima ta dawo da ita daga dogon tunanin nata da cewa"dagaske ne abunda ya faɗa"? ya tambaye ta yana jiran amsa,ba komai yasa shattima sakin jiki da sehrish ba face tun da yaga yarinyar da suka shigo ta gaishe shi da ya kalle ta ba fuskar kowa ya gani ba a fuskarta ba face fuskar SGR bi ma'ana sun dace sosai,saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a ganin yarinyar da ta dace da Sgr ba face wannan yar matashiyar duk da ya lura cewa kamar tayi masa ƙanƙanta,yarinya ce ssae amma kuma tana da duk wani abu da namiji zai buƙata ajikin ƴa mace,🥱   A hankali sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa"hakane gskya ya faɗi....." daƙer takai ƙarasa maganarta, cikin sauri tace"kuna buƙatar wani abu"? shiru shattima ya ɗanyi saboda ya lura da chanjin da yarinyar tayi,kuma yasan saboda kalaman sgr ne,may be tana son shi ne da alama, ya faɗi aranshi a fili kuma yace"just its okey zaki iya tafiya,mun gode da wannan,"    Murmushi ta ɗanyi sannan ta juya da sauri saboda kukan daya ciyo ta har takai bakin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi, anatse yake yin wayarshi ya jingina bayansa ajikin kujerar,sa kai tayi ta fuce wuri tasamu anan upstairs ɗin ta zuƙunna ta cigaba da shan kukanta jikinta har rawa yake yi,tuni eyes dinta sun canza launi, fuskarta ta tur6une saboda kuka sai faman murzar hancinta takeyi kamar zata 6alle shi,sam ta manta da aikin dake gare su a kitchen su azmee nacan da amani sun taƙarƙare suna ta aikace aikace ba sehrish, gashi Amani sai faman tambayar azmee take yi na cewa har yanzu yarinyar bata dawo ba daga kai ma Sgr coffee,ko mai ta tsaya yi? Ita dae azmee bata ce komai ba, da tacika ta da tambayar ne tace"may be shi ya tsare ta,kinsan ita ke kula da apartment dinsa, Jin hakan ba ƙaramin tayarwa Amani hankali yayi ba,daure wa kawai take yi tana aikin,    Hawansa kenan upstairs ɗin ya miƙi hanya yana cikin tafiya yaji shessheƙar kukan ƴar mace,mamaki ne ya kama abbansu ganin yarinyar zukunne ta takure kanta sai faman matse hanci take yi tana kuka,tuni hankalinshi ya tashi ƙarasawa yayi inda sehrish take zukunne,a firgice ta miƙe tsaye lokacin da tayi arba da Abban nasu sam bata lura dashi ba sai da taji takon takalminsa na tunkarota,    lokaci guda ta rikice duk ta susuce tsoranta mai zata sanar mashi in ya tambayeta dalilin yin kukan nata,   Ko da ya isa dab da ita sai ya tsaya yana ɗan nazarin fuskarta,tsananin tausayin yarinyar ne ya kama shi,dama ita mace abun tausayi ce musamman in ta kasance ba'a gaban iyayenta ba,babu kowa nata a kusa da ita da zai lallashe ta ya kuma janyo ta jikin shi don jin damuwarta,ya mayar da ita yar shi amma kuma bai da isasshen lokacin jin abunda takeso ko me ke damunta,    Sunnar da kai sehrish tayi ƙasa murya na rawa tace"ina yini abba,"   bai amsa mata gaisuwarta ba sai cewa yayi"meya faru ne naga kina kuka? cikin en ina tace"babu komai," hannun shi yakai gefen fuskarta yace"ko da zaki yi ma kowa ƙarya,kada kice zaki yi ma abbanki,ga hawaye nan nagani suna zuba a idonki,kawai dai bakya son faɗamun ne," shiru tayi bata ce komai ba tana faman wasa da yatsun hannunta,   Murmushi yayi ganin tana ɗan satar kallon shi kamar wata mara gaskiya,   Cikin zolaya yace"faɗa mun gaskiya kodai aure kikeso ne?kin rasa wa zaki faɗamawa shine kika la6e anan kina kuka ko"? ɗagowa sehrish tayi taɗan zare ido can kuma ta fashe da dariya gaba ɗaya, shima dariyar yayi dama yayi hakan ne don yasata farin ciki yasan mata daga anyi masu maganar aure sai jin kunya da dariya,   ganin haka yasa shi ƙara cewa"hmmmmm dama nasani,mu aje wannan maganar a gefe nasan cewa akwai wanda kike so acikin ƴa'ƴana don na iya haihuwa gasu nan tubarkalla masha Allah ƴan mata sai rububi sukeyi hada masu kirana awaya duk safiyar Allah suna gaishe ni wai nan suna yi ma kansu ko ƴa'ƴansu kamun ƙafa,ni kuma har yanzu basu kwanta mun araina ba,Amma ke ɗin nan ko ta dabance in har kinaso in baki ɗaya daga cikinsu dole kema ki fara kamun ƙafa daga yanxu,"  Magana yake a natse sehrish kuwa ta kasa kunne tana sauraron shi,mamaki ya gama kamata yarda Abban nasu sukutun da guda yake fira da ita lallai ba ƙaramin wayayyen mutun bane,   bayan yakai ƙarshen maganar tashi tace"amma Abba,ni bansan yarda ake yin kamun ƙafar ba," ta faɗi cikin jin kunya,   dariya yayi tabi shi da kallo sai taga ya koma mata junaid saboda tsananin kamanceceniyar dake a tsakaninsu don dai shi fuskarshi akwai manyantaka, Bayan ya tsagaita da dariyar yace"kina nufin baki san yarda ake kamun ƙafa ba in mutun nasan abu,to ki tambayi AZMEE ta faɗa maki zata koya maki,   Jinjina kai tayi tare da cewa"insha Allah zan tambayeta,"   Murmushi yayi kafin yace"daga ynx zan fara zuba ido in ga yadda zaki fara kamun ƙafar naki,idan kinyi abu mai kyau sai na duba na gani wanne ya dace acikinsu na baki,idan marks ɗinki yakai matakin A1 to zan aura maki ɗaya daga cikin manyan ne, idan kuma Credit kika samu zan haɗaki da ɗaya daga cikin youngers ɗinsu,amma fa ki sani idan marks ɗinki yazo da matsayin(f)to zan aura maki Haroon ne........... " dariyar da sehrish ta fashe da ita ne ya hana shi ƙarasa maganar, zuba mata ido yayi yana kallonta sai ya dinga ganin kamanceceniyar fuskarsu da ta yarinyar sam yarasa gane dawa take masa kama nan da nan kan shi ya ɗaure yashiga mamakin kamannin daya gani kodae idonshi ne ke nuna mashi hakan tabbas fuskarta tayi tamkar photocopy ɗin fuskar ƙanwarsa AZEEMA,   daker sehrish ta tsagaita da dariyar tace"Abba zan tafi kitchen nabarsu suna aiki,"    Murmushi yayi tare da cewa"hakan nada kyau,kwara tun ynx ki koyi girkin shima yana daya daga cikin jarabawar da zan maki don bazan aura ma ƴa'ƴana macen da bata iya girki ba,then idan nasamu free time zan wa junaid magana ya kira mun ke don mu ƙara tattaunawa,"   Amsa mashi tayi fuskarta cike da annashuwa tabi ta gefenshi tana faman sakin murmushi ba don komai ba sai don maganar Abban nasu dayace idan marking ta F9 ne zai aura mata haroon hakan na nufin shi kanshi yasan cewa haroon cikon bencin gidan ne 🤣😂😅   Har juyawa abban nasu yayi yana kallonta a lokacin tayi nisa wurin sauka daga stairs ɗin,ajiyar zuciya ya saki saboda ganin farin ciki a fuskar yarinyar, dama yayi hakan ne don ya mantar da ita damuwar da ta shiga har ta la6e tana kuka,kama hanya yayi ya wuce,dama bedroom ɗin junaid ya nufa, *************************** Tun ɗazu da suka kammala lunch ɗinsu after Azhar hossana da Camila suka koma bedroom din saman katafaren gadon suka baje suna bacci abun ba'a magana,ita kuwa jahad sam tagaza yin bacci tun  da tayi sallar la'asar tafito daga ɗakin ta tsaya a falon tana zagaye, bakomai take burin gani ba face Ya Omar dinsu ko zafin ciwon ƙafarta yanzu tadaina ji,har wurin ƙarfe biyar da wani abu tana wannan safa da marwar in betwn seater's ɗin dake a palourn,tana cikin wannan zagayen MARSHAL OMAR ya shigo falon da sallamar shi, sam bata ji shi ba saboda ta juya masa baya tamiƙi hanya tana tafiya,   Murmushi ya saki ya tsaya yana tunanin wacece acikinsu jahad ko hossana,koma dae wacece ba ƙaramin kyau tayi masa ba acikin kayan,yaji daɗin hakan saboda dama burinshi ya gansu cikin jin daɗi da walwala,ganin bata da alamar juyowa yasa shi yin gyaran murya da ɗan ƙarfi, cikin sauri jahad ta juyo tana faman zare ido don batayi tsammanin ganin mutun ba,nan da nan wani irin farin ciki ya mamaye fuskarta da karfi ta furta"Ya Omar," lumshe idonshi yayi tare da buɗe su yana murmushi,   Watsa wa tayi da gudu tamkar zata rungume shi,sai da taje dab dashi sannan taci burki tana dariya,yana ganin hakan ya gane cewa Jahad ce,don da ace hossana ce sai tayi hugging dinshi,   "Fatan na same ku lafiya"? Ya furta yana kallonta,fuskarta awashe tace"Alhmdllh ya omar,dama tun ɗazu nake jiran zuwan ka, ashe zaka zo da har na fidda rai,    Omar yace"naso nazo ɗazu to bansamu hali ba,shiyasa na aiko maku da major don ya ɗauko ku,ina fata gidan yayi maku?   "ya omar ni nama rasa da wasu kalmomi zanyi amfani dasu wurin yi maka godiya Allah.........."tuni idanunta sun cicciko da kwalla sun soma gangarowa daga cikin idanunta,   Cikin sauri yace"Why jahad?me yasa zakiyi mun kuka bayan kinsan bana son ganin hawayen ku,sannan bana son godiya kada na sake ji,duk wani abu da nayi maku nayi shi ne don Allah,kuma haƙƙin ku ne dake akaina har yanzu ma ni ji nake kamar akwai sauran abubuwan da banyi maku ba, ..kallon shi kawai take yi yana bayani har yanzu tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Marshal omar, Cikin shessheƙar kuka tace"ya omar kai wane irin mutun ne?narasa dame zan fasalta ka,kyawawan ɗabi'unka da halayenka da kyakkyawar zuciya irin taka bana tunanin a doran duniyar nan za'a samu mai irinsu,koda za'a samu sai anci baƙar wahala kuma cikin kashi 100 bai wuci asamu kashi biyu ba,kai na musamman Ne ya omar,ina taya iyayenka farin ciki sosai da samun ɗa kamarka,saboda kai abun alfahari ne........ni bansan da me zamu saka maka ba ya omar,ka bamu kyakkyawar rayuwa ka cire mu daga ƙangin rayuwar da muke ci,a lokacin da muke tunanin cewa kowa ya tsanemu bai son mu mutuwa ma kawai muke jira,sai gashi Allah ya haɗamu dakai,tun a lokacin nasan cewa kai kyauta ne daga Allah...........   tun da jahad ta soma kora jawabi ya goya hanneyen shi a faffaɗan kirjinshi ya natsuwa yana sauraronta fuskarshi ɗauke da murmushi,saboda kalamanta ba ƙaramin shigarshi su kayi ba yadda take magana a natse ga wata irin murya dake gareta mai sanyin gaske irin muryar da duk 6acin ran da kake ciki in. Ka ji ta sai ka manta dashi,ae jahad akwai natsuwa ga tawakkali nima na shaida hakan 😘 "Ya omar ka faɗamun dame zamu saka maka?nasan ma babu Ba mu da abunda zamu iya saka maka aduniyar nan face addu'a itace kawai ke gare mu,i will keep pryaing 4 u ya omar hada family ɗinka duka zan saku a addu'ata till the end of my life bazan manta ba aduk lokacin da nayi sallah ko nayi karatun alkur'ani har night prayers ma zan dinga tashi inayi just because u ya omar and ur family,   ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya har lokacin hawayen fuskarta basu tsaya da kwarara ba,   Hannu omar yasa tare da zaro handkerchief ɗinsa dake front pocket dinsa dake a t shirt din jikinshi,   Da hannun shi yasa yana wiping tears dinta a hankali,runtse idonta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa a tattare da ita,   Muryarshi ce ta tsinkaye ta da cewa"jahad ngde ssae kalamanki kawai da kikayi mun a yanzu ma sun wadatar dani,sannan idan kuna so ku saka mun abunda nakeso shine koda nan gaba kada ku juyamun baya bana son ku canzamin inaso ku tsaya a yarda nasan ku,ina tsananin ƙaunarku sosai bana son abunda zai raba ni daku,inason zumunci ya ɗaure a tsakanina daku daganan har can...... katse shi tayi da cewa"har ina kenan ya omar,"   Cikin zolaya yace"gidan Aljanna mana," dariya tayi sosai kafin ta tsagaita da dariyar tace"insha Allah ya omar ba zamu ta6a baka kunya ba,zamu kasance kamar yarda kakeso,"   Jinjina kansa yayi sannan yace"where's my hossana banganta ba,ko tana ciki ne? Ya yi nuni da hannun shi,   Jahad tace"hossana suna ciki tare da wannan nurse camila din sai sharar bacci suke yi tun ɗazu,"   Murmushi yayi tare da cewa"naso na ganta,"   Cikin sauri tace"ya omar ka shigo daga ciki mana ka zauna na kira maka ita don itama hossana a ƙagare take data ganka,"   Omar yace"sauri nake na koma gida yanxu,ki gaishe mun da ita dae,ko kuma zan kira wayane ae akwai telephone sai mu gaisa," jinjina kai tayi tare da cewa"shikenan zan sanar mata,amma nasan zatayi kuka in taji cewa kazo kuma ka tafi bata ganka ba,    juyawa yayi yana faman sakin murmushi har ya kusa fita daga falon tace "ya omar," juyowa ya kuma yi yana kallonta,    "Tun jiya inata so in kazo inyi maka ya mai jiki,abun yana araina ɗan uwanka daka sanar mun cewa bai lpy,"    Omar yace"oh fawan da sauƙi jikin shi sosai,kada ki damu zan bashi waya inyaji sauki ssae sai kiyi mashi ya jiki,"   Jinjina kanta tayi alamar toh daga nan sukayi sallama ya fuce daga falon,   Ajiyar zuciya ta saki tare da wuce wa ciki fuskarta asake 😇 ****AUNTY BABBA****** 💋Boss Bature💋_ ********AUNTY BABBA************ Zaune take agaban dressing mirror ranta a matuƙar 6ace fuskar nan tayi jawur saboda kukan da taci,ta zabga uban tagumi zuciyarta sai faman tafarfasa take yi,bakomai bane ya haddasa mata wannan 6acin ran ba face General ishaq daya hanata zuwa abuja,duk yarda ta kwallafa rai akan zuwa abujan ya hanata,sai da ya bari tasha wankanta ta kimtsa cikin leshi ta yafa mayafi ta ruƙo jakarta, tana fitowa ta same shi zaune a falo jikin shi sanye da gajeran wando baki,wani irin kallo yabi ta dashi tare da cewa"Ina zuwa," washe masa baki tayi tare da cewa"Abuja mana,kai fa kace zamuje duba jikin fawan," kai tsaye yace"ae nafasa wannan,ni kaɗai zanje inyaso ko a waya ne kun kira Abba kuyi masu Allah kyauta," Tur6une fuska tayi tare da cewa"dan Allah idan wasa kake mun ka daina,"    Shima ya tamke fuskarshi yace"ba wasa nake ba,ni kaɗai zanje inyaso saina wakilce ku,"   Hankali tashe tace"Haba Abban hafsat sai da na kammala shirina, tafiya kawai ta rage zaka ce wai an fasa gaskiya ni sai naje," ta faɗi tare da ruƙe qugunta tamkar zata buge shi,   Miƙewa ishaq yayi fuskarshi ba wasa yace"to ki sani muddin kikasa ƙafarki kika bar gidan nan without my permission hmmmmmm ke kinsan mai zai biyo baya,    Yana faɗin hakan ya fuce ma daga falon yabarta,   da gudu ta koma bedroom ɗinta a ƙasa ma tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado ta faɗa tadinga shan kukan baƙin ciki har bacci ya kwashe ta, Ta jima tana baccin kafin ta tashi cike da kunci ta koma gaban mirror ta zabga tagumi rai a6ace, Download>>> Dangin Rabi Complete Document Ta jima tana tunanin meyasa general ishaq ya hanata zuwa gidansu don ta duba jikin fawan,abun ya ɗaure mata kai saboda shi da kansa yace zasu je dubiya atare amma ya canza ra'ayinsa yanzu,    tsoki ta buga tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake agaban mirror ɗin,contact ɗinta ta shiga ta lalubo numbar wayar HAYAAM ta danna mata kira,ringing ta shiga yi kusan sau uku ba'a ɗaga ba, tana a cikin toilet kiran ya shigo a lokacin wayar na hannun wani matashin saurayi dake zaune saman wani haɗaɗɗen gado, daga shi sai shorts ajikin shi ya baje abun shi, ganin sunan Aunty Layla ya bayyana akan screen ɗin wayar yasa shi ɗaga murya tare da cewa"babe!babe!ur phone is ringing,   Daga cikin toilet ɗin tace"wanene ke kirana?in dae mommy ce ko Abi ka kashe wayar gaba ɗaya bana son takura,   "No basu bane,wannan auntyn naki ne Layla," Jin sunan Aunty laila yasa ta yin wuff ta fito daga cikin toilet ɗin, doguwa ce sosai fara sol babu ko tabo ajikinta kai kana ganin fatar nan zakasan cewa ba ƙaramin kuɗi take kashe mata ba saboda yarda take ɗaukar ido, ta ko'ina Allah ya bata ga dogon wuya, Bin ta da kallo saurayin yayi sam yagaza janye idonshi akanta sai kace batare suke rayuwa acikin gidan ba, Towel ne kawai ta ɗauro ajikinta cikin hanzari ta miƙa hannunta tare da kar6ar wayar tana cewa"nashiga ukuna Aunty laila kuma a awaya?yanzu zata rufe ni da faɗan ba gyara ba dalili mtswwwwww    Ta ƙarasa maganar tare da ɗaga kiran ta kara a kunnanta tana faman zazzare manyan idanunta, A ƙule aunty babba tace"ina kika je ne inata faman kira ba'a ɗagawa? Cikin en ina tace"Nashiga toilet ne yanzu na fito na sami wayar tana ringing asaman gado, aunty babba tace"hmmmm kina a gida ko kina awaurin yawon gantalin naki? Cikin sauri tace"am....ina a gida......" bata bari ta ƙarasa ba a tsawace tace"Karki kuskura kiyimun karya Hayaam ina sane da duk wani yawon gantali da kikeyi ana sanar mun da komai,saboda tsabagen iya shege da fitsara idonki ya buɗe wuyanki ya isa yanka hada tattara kaya da komawa gidan saurayi da zama koba haka akai ba? Ta tambaya azafafe tamkar tana a gabanta,tuni ran Hayaam ya 6aci juyawa ta ɗanyi ta kalli Sofwan dake kallonta bai sauraron me suke cewa amma ya lura da yanayin fuskarta daya canza saboda hayaam bata iya 6oye 6acin ranta duk mun ƙanƙantarsa,   sassauta muryarta tayi tare da cewa"Aunty layla mgnr da kika faɗa gaskiya ne,i can't hide it 4 u ni bazan iya rayuwa a cikin gidan nan ba saboda baida marar raba da kwango a wurina,fentin gidan duk ya ƙoƙe kamar munfi kowa talauci a layinmu,bama wannan ba ɗakinmu bai da banbanci da kwankon ashana katifa ce kawai duk ta gwaigwaye sai akwatin kayan mu, ko na fidda kuɗi na siyi furnitures mommy bata barin komai sai dae kawai nadawo na taras ta siyar da komai ta hanani jin daɗin rayuwa kuma kinsan ni macace mai son rayuwar hutu rayuwar ƴanci wannan shine dalilin dayasa nabar masu gidan don wlh ko abincin da suke ci ynx 6ata mun ciki yake yi saboda wannan yarinyar ƙanwar Amani ita suke ba girkin gidan,yarinyar da bata wuci 14years duk wani aiki na gidan ita take yin shi har yanzu mommy bata haƙura ba akan ɗaukar fansar abunda mommynsu tayi mata" yadda take magana kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ba ƙaramar ƴar duniya bace magana take tana faman wurga ido tana kora jawabi  Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa"ae ni tayimun dai dai,wato wayewa tasa kin manta da irin azabtarwar da matar nan tayi mana shine har kike ganin laifin mommynmu,kwara su kashe yarinyar ma kowa ya huta ae ni nafison su wulaƙantata," ta fadi tana faman huci kamar tana agabanta, Download>>> Yaro Ne Complete Document Ganin wayar tasu ba mai ƙarewa bace yasa Sofwan tasowa daga saman bed dinsa ya sauko, takawa yayi izuwa bayan Hayaam dake atsaye ya rumgumota tare da zagayo da hannayen shi ta waist ɗinta sannan ya kwantar da kanshi daga gefen wuyanta yana cewa"babe yaushe wayar zata ƙare?nifa a ƙagare nake, ƙasa ƙasa da murya tayi tare da cewa"pls karkaja min bala'e,"   Muryar aunty babba ce taci gaba cewa"Yanzu abunda nakeso dake kibar komai da kike yi ki tafi abuja gidan surukaina acan nakeso ki cigaba da zama,   Ƙiris ya rage hayaam ta saki wayar dake a hannunta saboda jin sa6on da auntyn nata ke faɗi, cikin ruɗu tace"haba dae Auntyna amma dae wasa kike yi ko?if not ni mai zai kaini gidan in-lows din mu da zama abun ma babu daɗin ji........, Tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa"ke dalla yi mun shiru!duk ƙoƙarin da nakeyi akanki bakya gani!kina nan sake da baki ga wata can a gidan matsayin yar aiki Abbansu ya mayar da ita ɗiyarshi sun gatanta yarinyar har makaranta take zuwa,idan har kikayi gangancin rasa wannan damar ta komawa gidan da zama ina mai tabbatar maki da cewa Kin rasa cikar burinki na har abada," shiru hayaaam ta ɗanyi gabanta na faɗuwa saboda ba abunda ta tsana fiye da ace zata Rasa SURGEON GENERAL RAFAYET saboda mutuwar son da take yi mashi ta kwallafa rai akanshi a lokacin baya tasa naci sosai akan shi sa'adda suke zuwa gidan sosai,amma tun da ta lura cewa kafin ya ma ɗaga idonshi ya kalli mace aiki ne don sai da ta share 2 weeks a gidan sau ɗaya suka ta6a hada ido shima ɗin by mistake ne ya ɗago a lokacin,abun ya tsaya mata arai, yadda take da kyawun surar nan babu namijin da zaiganta ya kawar da ido batare da ya neme ta ba sai akan SGR,tun a lokacin ta soma fidda rai akan shi amma yanzu aunty laila ta soma dawo da ita kan network, lumshe idonta tayi tana tuna kyakkyawar fuskarshi har lokacin sofwan na manne da jikinta ya lafe mata kamar wani maye,   ƙara kara wayar tayi akan kunnanta tace"Aunty laila komai zan iya yi akan na mallake shi,saboda shine namijin daya haɗa komai da nake kwaɗayi nake tsananin so a jikin ɗa namiji,amma abunda bansani ba aunty layla shin kina ganin zasu kar6e ni in naje gidan a matsayina na ƙanwar matar yayansu? Wani irin shu'umin murmushi Aunty babba ta saki wato anzo dai dai wurin da tafi so, miƙewa tayi daga zaunen da take agaban mirror tashiga zagaye bedroom ɗin nata tana cewa"Hayaaam baki da Matsala indae a gidan nan ne! Kinsan yarda Abbansu ke da son ƴa'ƴa hannu biyu zai kar6eki abu daya kawai nasani shine dole sai da iznin Abi sannan zai kar6eki don haka kibarmun wannan a hannuna ni zanyi magana da mommynmu tunda ita ke juya shi da zarar tayi mashi magana zai amince!abunda kawai nakeso dake hayaam shine kiyi gaggawar komawa gidan da zama acikin watan nan!Ke bama sai kin je da komai ba tsurarki zaki tafi batare da trolly na kayanki ba,saboda inaso ki fara fakewa da cewa kinje duba Fawan ne da bashi da lafiya daga nan kawai saikiyi zaman ki dirshan babu mai tanka maki saboda duk matasan gidan miskilai ne babu ruwansu,da ace dae yana da ƴa'ƴa mata shine za'a samu matsala kinsan mu mata da bakin ciki da hassada muke....'   Murmushi kawai hayaam ke saki tana faman lumshe ido tare da cizon pink lips dinta saboda shock ɗin da takeji na sofwan dake bin jikinta da hannun shi yana shafa ko'ina,Auntyna indae ni ce just karki samu damuwa,ki ƙaddara cewa gani can ma acikin gidan ina watayawa ta,ita kuma wannan yarinyar da kika sanar mun cewa tana zaune a gidan tuni zansa su yi mata checking out badai ni bace ba hmmmmmm,   Dariya aunty babba ta saki tare da cewa"har naji sanyi araina,burina na dab da cika," Download>>> Yar Harka Complete Document   Sun jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama da junansu,    Buge hannun sofwan tayi tare da cewa"duk kabi ka takuramin wai kai wani irin jarababben mutun ne mai nacin tsiya haba mtwww,"taja dogon tsoki   Baki asake yabi ta da kallo tare da cewa"ni kike ma tsoki wai?wato wannan haɗamammar auntyn taki takira duk ta tunzuraki akan abunda bazai ta6a faruwa ba,duk naji mai kuka tattauna da ita,   ya fadi yana faman sakin hucin 6acin rai,murmushi hayaam ta saki tare da cewa"Sofwan zamana dakai ya ƙare!!!!!!!    Zaro ido waje yayi yana kallonta hankali atashe yace"saboda me hayaam?kada kiyimun haka don Allah!amma dae nasan wasa kike mun ko?   ƴar dariya tayi kafin tace"na ta6a maka wasa irin wannan?zanje na nemi namijin duniya ne!cikakken namiji jarumin gaske wanda ya kasance burin kowace ƴa mace ne shi bazanyi gangancin rasa cikar burina ba sofwan....... Bata ƙarasa ba ya dauke ta da mari ji kake faaaauuuu!    Rai a 6ace yace"Wlh baki isa ba hayaam ki katse mun jin daɗina ba!!saboda ke dakikiya ce sam bakisan meke maki ciwo ba wannan wani irin abun kunyane zaki kwasa kawai ki koma gidan surukanku da zama?Anya kuwa yayarki ba mahaukaciya bace.....    bata bari ya ƙarasa maganar tashi ba ta zame hannunta data dafe kuncinta dashi ta daddage ta zabga mashi zafafan maruka har guda uku sannan tace"karka kuskura ka ƙara kiran auntyna da sunan mahaukaciya!!maganar tafiya kuma ba fashi sofwan inka ga ban tafi ba to wlh numfashi na ne ya tsaya don ko ba ƙafa saina je,😳   Tuni sofwan ya rikice ganin yarda hayaam ta zabga masa mari batare da jin komai ba,duk irin yarda yake tarairayarta don karya rasa ta amma lokacin guda auntynta ta canza mata tunaninta,   Kallonta ya shiga yi yana girgiza mata kai yayin da idonshi suka cicciko da kwalla muryarshi a kasalance yace"Hayaam kada kiyimun haka dan Allah!saboda ke na wulaƙanta iyayena na baro komai nawa don muyi irin rayuwar da kikeso,wannan gidan fa duk don saboda ke na gina shi hayaam,ki duba gidan da iyaye na suke ciki duk ya rakwakkwa6e amma saboda ke na gidan wannan katafaren gidan ko don saboda wannan pls hayamm kada kibarni komai kikeso zanyi maki shi," yayi maganar tare da zubewa saman guiwowin shi a gabanta yana faman sharara hawaye,amma maimakon yaga alamun tausayi a idonta saima ta fashe mashi da dariya tashiga tafa hannaye tana cewa"sofwan kaifa dakanka kace ka wulaƙanta iyayenka saboda Ni?shin ni wacece a wurinka?mutumin da bai daraja iyayensa ba musamman uwarsa data tsugunna ta haifeshi taci baƙar wahala kanshi!ga kuma mahaifinsa daya fitar da gumi wurin nema masa kyakkyawar rayuwa duk bai duba wannan ba,burinka kawai ka farantama wasu can waɗanda basu son ciwonka ba,waɗanda ko yau ka faɗi ka mutu wlh shewa zasu yi suce Allah raka taki gona,shine har kake mun kwatance da ka wulaƙanta iyayenka don saboda wata banza can Ni?hanyar Aljanna nake sanya ka kota wuta?ko zan taimake ka ne ranar lahira?sofwan haƙƙin iyayenka ma kawai ya isa ya tarwatsa dukkan wani farin ciki na rayuwarka!!idan ma naci gaba da ra6arka nima zan shiga matsala ne don haka kawai muyi break up kawai kowa yayi rayuwarshi,"   ta ƙarasa maganar tare da ruƙe waist dinta tana kallon shi a tsiyace,   Miƙewa yayi daga kneel down din da yayi ya kalleta da fuskar tausayi yace"kada kiyi mun haka hayaam indae alaƙata da iyayena ne zan gyara komai...'   girgiza mashi kai tayi tare da cewa"na yaushe sofwan?hmmm ba don Allah zama kayi masu ba sai don saboda ni abanza kam,shiyasa koda yaushe soyayyar SGR take ƙara ninkuwa araina duk da irin tarin dukiyar dake gare shi hakan baisa ya canza ma iyayenshi ba ko wani nashi,zokaga Namijin gaske mai tsananin biyayya ga iyayensa wanda yasan darajarsu yake binsu sau da ƙafa kaifa? Har yau mahaifinka bai daina siyar da kifi a gefen titi ba, ga Mahaifiyarka cen kullum safiyar Allah sai tafito da murhu kopar gida tana suyar ƙosar da kunu,taya ma zan cigaba da kasancewa dakai!!? Kana da arziƙin da zaka iya ciyar da karuwai ka gina ma iyayensu gida ka kuma gina masu su kansu Amma iyayenka fa!!!?   shiru Sofwan yayi yana kallonta idanun shi sunyi jawur dasu ga wani ƙululun baƙin ciki daya tsaya masa a maƙoshinsa,   Wuce wa hayaaam tayi wurin wardrobe dinshi saboda anan kayanta suke nasawa, hannu tasa ta buɗe wurin kayanta tana raira waƙar nan ta namej dayake cewa"ko babu mota ba abun hawa wlh saina jee,"    A wani irin fusace Sofwan ya cafki hannunta data ruko bra dinta dashi,dakatawa tayi da yin waƙarta ta tace"Malam sakarmin hannu na,"   Yana wani irin huci yace"Hayaam baki isa kibar gidan nan ba, batare da kin mayar mun da duk wani abu dana kashe maki ba!!wlh bazaki ci bulus ba,duk kin taƙaitani duk ƙarshen wata saina kawo maki kayan abinci kwalin indomie kwalin taliya da sauran kayan abinci, sannan duk ƙarshen sati muna zuwan shopping mall dake nayi maki siyayya kuma mu fita restaurant cin abinci,ga kuma kuɗin mayukan da nake siya maki su kansu kudinsu yakai na dubu dari biyar,in kin ga kin bar gidan nan to ki tabbata kin haɗa mun kuɗaɗe na kin mayar mun dasu," ya ƙarasa maganar yana jifanta da wani irin kallo,   ta6e baki tayi tare da cewa"Naji duk zan biyaka ni kuma da me zaka biyani jikina da kayi amfani dashi?donni ma bazaka Ci bulus ba tunda ba uwar mutun ta haife ni ba,ka biyani budurcina nima saina biyaka kudinka"A shagale take maganar tana faman sakin murmushi,   Shiru sofwan yayi yana faman mazurai aransa yana tunanin taya zai biyata virgin dinga da take magana akai?   tsoki taja tare da buge hannunshi tabar shi tsaye a wurin ta koma daga gefe tana zura brazier dinta,   Muryarshi ce ta kuma katse ta da cewa"naji wannan tabbas bazan iya biyanki budurcinki ba,amma inaso ki sani bazan bari ki ɗauki ɗaya daga cikin abunda nasiya maki ba da kudina,daga ciki kuma hada kayan sawa don dama a tsiyace kikazo gidan nan, Download>>> Babban Yaya Complete Document   harara ta wurga mashi tare da cewa"Matsalarka ce wannan!ae ni abun kunya gaba na bashi ba baya ba,in ka hanani sa sutura sai in tafi a zir abuna," ganin tana shirin ɗaura mashi hawan jini yasa shi buga jikin wardrobe din da hannunshi yana kallonta idonshi jawur rai a tsananin 6ace ya fuce yabar mata ɗakin gaba daya, Murmushi tasaki tana cizon la66anta aranta tace"ƙaramin ɗan duniya har ni zakayi wa barazana," ******************* Tsare ta da ido hafsat tayi wadda shigowarta kenan  bedroom din ta, Ta jima a la6e tana sauraron firar da mommyn nata keyi da Hayaam a waya, sai da tabari ta kammala sannan tashiga daga cikin ɗakin tana kallonta, tunkan tace wani abu aunty babba tayi saurin cewa"to ƴarsa ido uban me yakawo ki dakina? murmushin takaici hafsat tayi kafin tace"narasa meke damunki mommy!gaba daya naji wayar da kikayi da aunty hayaam,saboda me zaki ce ta tattara kaya ta koma gidansu Abbana da zama?wannan wane irin abun kunya ne ace ƙanwar matar yayansu tana rayuwa acikin gidansu? menene alaƙarta dasu?gsky wannan tsarin sam baiyi ba mommy yakama ki dakatar da hayaam daga zuwan gidansu........' tunkan taƙarasa aunty babba ta kwatsa mata tsawa tare da cewa"munafuka!!ashe la6e kikeyi mun ni narasa gane meke damunki hafsat!!tunda waɗancan yaran da omar yakawo mun suka zo gaba ɗaya duk sun canzamin ke, yanzu bakya goyon bayana......' Tana magana tana yin nuni da hannunta dake ruke da wayarta, ta6e baki hafsat tayi tare da cewa"Mommy kenan,mgnr da kika faɗa gaskiya ce,Jahad da hossana ba ƙaramin sauyani su kayi ba saboda akansu na fara tausayin wani dan adam a duniya,sun goga mun kyawawan ɗabi'unsu da halayansu waɗanda ke baki ta6a gwadamun ba,haƙiƙa nayi rashinsu sosai kuma ina fata Allah ya ƙara hadani dasu wata rana.....' murya asanyaye tayi maganar,   Sakin baki Aunty babba tayi tana kallonta kamar me son gano wani abu can dae tace"Hafsat kodae kece kika sa Abbanki ya hanani zuwa abuja ganin jikin fawan?ina zargin hakan!! kaitsaye tace"Nice mommy!ni nasame shi na roƙe shi akan cewa kada yabari ki tafi ke kaɗai sai tare dani saboda bana jin daɗi yanzu bazan iya zuwa ba,"   a fusace tace"Meyasa"! Murmushi hafsat tayi tare da cewa"Saboda ba don Allah zakije ba!bakuma don kije duba jikin fawan ba face donki je ganin yarinyar da Aunty Amani ta sanar dake, ni kuma gsky bana son ma ki ganta balle har kiyi yunƙurin cutar da ita, don kuwa bazan sake bari ki cutar da wani ba saboda wani buri can da kike dashi wanda bazai ta6a cika ba.......' Da gudu hafsat ta fuce daga dakin ganin yarda Aunty babba ta zabura zata cafkota takai mata bugu,'   bedroom ɗinta ta koma tana faman tiƙar dariya hadasu dafe ciki, Ita kuwa aunty babba tuni idonta sunyi jawur saboda 6acin rai,tama rasa me zatayi ta huce,ashe hafsat ce ta hana ishaq barinta taje abuja yau lallaikam zata ci ubanta ne dani take magana, Ta fadi tana faman huci, *********AFTER 2WEEKS************ *Bayan Sati uku* Tuni jikin fawan ya ɗan murmure yaji sauƙi sosai har yana iya miƙewa ya taka yaje inda yake so hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,a 6angaren su twins kuwa murna har ba'a magana saboda alert ɗin kuɗin da mommynsu ta turo ta wayar jahan a cikin dollar acct dinsa, a tsakar dare alert din yashigo a lokacin suna maƙale da juna kamar yadda aka saba,gaba ɗayansu suka buga shewa cikin jin daɗi ba don komai ba sai don zasu rabu da matsin Haroon su huta,a daren ranar har nafilar dare sukayi atare suka roƙi Allah akan ya yaye masu masifar dake damunsu, sun sha kuka kamar kamar me,sannan kuma sun shirya zuwa bank domin su kar6o masa kuɗinshi miliyan tamanin su damƙa mashi,😣 dama sai zarya yake yi masu kullum safiyar Allah yana musu barazana,ba don sun nuna mashi kuɗin ba dake cikin acct dinsu ba ya gani awayarsu, da bazai ƙyalesu ba, DOWNLOAD: "HARIJI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT" A 6angaren Hossana da Jahad kuwa hmmmmm just speechless,wata irin rayuwar hutu da jin daɗi suke gudanarwa acikin hamshaqin gidansu,babu ruwansu da kowa su biyu abunsu sai Camillah dake yawan zuwa dubasu wani lokacin takan tsaya ta kwana ma acikin gidan,ba ƙaramin gyarasu tayi ba,domin kuwa sun canza fiye da tunanin mai tunani,fatarsu kanta abun kallo ce, ga wasu irin surorin kyau da suka bayyana ajikinsu,sun koma rainon Madara rainon bonvita 😂 Ƴancin da su hossana suka samu ko mutanen nigeria a 1960 basu samu makamancin shi ba,hossana fa har wasu kumatun jin daɗi tafara ajiyewa🤣 dama bata wasa da abinci gashi Omar ya cika masu store da kayan abinci kala kala, ga freezer dinsu dake shaƙe da kayan sha,kullum in jahad tayi mata maganar tadinga ci ahankali sai tace"ina ruwanki!In suka ƙare yaya Omar zai siya mana wasu," 🥱 Marshal omar bai barsu hakanan ba, sai da ya ƙara masu security guards har mutun huɗu, Osman kuma shine a matsayin drivern da zai dunga kaisu School da wuraren shaƙatawa,tuni ya cike masu form na school koda akazo wurin sanya sunan uba ya tambayesu sunan mahaifinsu sai cewa suka yi "kasa mana sunanka kawai ya omar,mu bamu da uba," wani irin kallo yayi masu tare da cewa"ban shirya haramta ma kaina ɗaya daga cikin ku ba,don haka zan sanya maku sunan Uncle ɗina ne a matsayin Mahaifinku amma banawa ba,' Sam basu gane mai ya omar ɗinsu ke nufi ba da cewa bai shirya haramta ma kanshi ɗaya daga cikinsu ba,sun dai bar abun ne kawai azuciyarsu,   Alhamdulillah Omar ya kammala cike masu form da sunan Uncle dinshi,JAHAD ABUSUFYAN da kuma HOSSANA ABUSUFYAN,ba ƙaramin daɗi suka ji ba saboda jin ya saka masu sunan mutumin nan da goggon katsina ta ƙaƙaba masu amatsayin Ubansu, sunan makarantar da suka fara zuwa D.A International acadermy wato makarantar da Sehrish ke zuwa🤔 _💋Boss Bature💋_ *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 11:30 na dare Fitowarta kenan daga toilet jikinta ɗaure da towel,ba ƙaramin canzawa tayi ba gaba daya ta sauya saboda hutun da take samu ga kuma kwanciyar hankali,tun daga kan natural skin colour dinta zaka gane hakan,yanzu bata wasa da tsaftace jikinta kullum cikin ƙamshi take,   Ƙarasawa tayi gaban mirror tana cigaba da tsane jikinta da towel ɗin hannunta,bayan ta kammala tayi hanging dinsa daga gefen mirror din,sannan ta kai hannunta jikin drawer chest na mirror,janyowa tayi tare da zura hannunta ta ɗauko hand dryer,jona ta tayi ajikin socket nan take ta soma buso da iska, cikin sauri ta kanga ta saitin kanta taci gaba da busar da gashinta,cikin nishaɗi take yi saboda ta mayar da abun tamkar na wasan yara, natsuwa tayi tana tunano abunda suka tattauna da Azmee acikin kitchen bayan ta sanar da ita maganar da sukayi da abbansu nacewa tafara kamun ƙafa tun daga yanzu,   dariya sosai azmee tayi tare da cewa"Abba da zolaya wato in marks dinki yazo da F shine zai aura maki haroon gsky kwara ki dage,"   Murmushi sehrish tayi tare da cewa"Amma aunty azmee ya akeyin kamun ƙafa inaso na iya"?    ɗan gyaran murya azmee tayi kafin tace"Kyautatawa mana,kinsan ita zuciya nason mai kyautata mata,kamar abbansu atlease yakamata ace duk safiyar Allah kina zuwa har bedroom ɗinshi kina miƙa gaisuwa hakan zai ƙara maki daraja a idanunshi kuma zai tabbatar da cewa kina da tarbiyyya sosai,sannan 6angaren girki yakamata ace ma yanzu kinfi ni iya girki,tuntuni dama inaso nayi maki magana akan koyon girki,saboda maza nason macen da ta iya girki,kin ga mazan gidan nan basa wasa da abinci akwai son cin mai daɗi,shiyasa nake da kusanci dasu sosai saboda yarda nake masu girki,don haka kema daga yanzu ki fara trying bafa dole sai irin nawa ba a'a salo na daban yakamata ki koya,bari na baki satar amsa kamar abincin gargajiya haka namu na hausawa saboda a gidan nan sunfi sabawa da abincin turawa,yakamata ki fara jaraba yi masu shi,ki koyi sarrafa abinci kala kala hada abunsha da kuma irin kayan makwalashe haka da sauransu,sannan 6angaren tsafta domin kuwa itace gaba da komai,idan ma kina da tsafta to ki ƙara akan wadda kike da ita,saboda mazan gidan nan basa son ƙazanta ko miskala zarratin,tun daga kan tsaftar jiki yakamata ki fara kulawa,wurin yin shaving na armpit dana under,da kuma kula da teeth dinki wurin yin brush akai akai banda barin datti ajiki,da kuma kula da gashin kanki wurin gyare shi,hatta nails ɗinki ki runƙa kula wurin yankesu banda tara akaifa,ina fada maki wannan ne domin amfanin kanki,don ita mace da tsafta akasanta da son ado,inaso kema ki kasance haka.........   Sosai azmee ta koyar da ita abubuwa da dama na rayuwa waɗanda zasu amfane ta,kuma tun daga lokacin duk in suka shiga kitchen suna aiki tana ƙara ilmantar da ita,hakan yasa sehrish ta soma canzawa sosai, yanzu kullum cikin gyara kanta takeyi,sannan bata wasa wurin koyon girki dalilin hakan yasa tashiga whatsapp grp na koyon girki,kullum tana cikin ɗaukar videos ɗin girki tana kallo donta koya,a hankali a hankali yanzu harta fara jin zata iya jaraba yi masu abinci acikin gidan 😇 murmushi ta saki bayan ta kammala tunanin a fili tace"bansan da wasu kalmomi zan iya godema aunty azmeena ba,saboda tagama yi min komai a rayuwa ina jinta tamkar mahaifiyata ne,Ya Allah ka barni da aunty azmee na,"❤    jin alamar shigowar motocinsu yasa ta yin saurin cire hand dryer ɗin daga socket ta mayar da ita inda ta ɗaukota, sannan ta taka izuwa wurin wardrobe ta buɗe tana neman kayan da zata sanya,wurin jerin kayan baccinta ta duba,wasu riga da wando ta dauko ƴan qasar indonesia masu matuƙar kyan gaske ga laushi jikinsu,launinsu maroon colour ne masu ɗigon baƙi baƙi ajikinsu, cikin sauri ta zurasu ajikinta sannan ta ɗauki mayafi tayi rolling dinsa akanta, sai da ta tabbatar da cewa sun shigo ciki kusan 15 mins ta ƙara sannan ta buɗe ƙopa tare da fitowa daga ɗakin nata,ƙafarta na sanye da flat shoes,miƙo hanya tayi tana tafiya a hankali ta biyo ta main palour din babu kowa har sun wuce ciki,kitchen ta wuce don ta haɗa mashi tea tare da kayan marmarin dayake buƙata kamar kullum, Tare da Marshal Omar suka bar gidan,amma SGR ne kawai ya dawo saboda Omar ya wuce wurin su Hossana,tun akan hanya suka rabu dashi, a galabaice ya shiga part dinsa saboda rashin jin daɗin jikinshi dayake yi,tun safe bai da lafiya amma saboda juriya irin tashi da ƙarfin hali ba wanda ya lura da hakan,wani irin sever headache tare da zazza6i mai zafine ya rufe shi, Jikin shi na sanye da Army trouser tare da shirt light green colour,kai tsaye yana shiga bedroom dinsa ya faɗa saman bed dinsa batare da ya rage kayan jikinshi ba,saboda rashin ƙarfin jikin shi da yake ji,abun yazo mashi wani iri saboda kafin yayi ciwo da wuya mutun ne mai cikakkiyar lafiya,sam bai sanarwa kowa ba saboda baya son tayar masu da hankali kuma baison aga raunin shi, Sehrish Fitowa tayi daga kitchen ɗin hannunta ruƙe da tray mai ɗauke da ƙayataccen plate na fruits sai cup mai ɗauke da Hot tea sai faman tiririn Zafi yake yi,a natse take tafiya kai tsaye ta nufi stairs ɗin tana cikin tafiya kamar daga sama taji muryar haroon yana cewa"Wurin Namiji za'a ne"? A wani irin firgice ta juya tana neman ta inda zata ganshi,   Yana zaune saman 3 seater shi kaɗai abunshi jikin shi na sanye da night dress riga dai dai guiwa,ya aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana faman sakar mata murmushi,     Ba ƙaramin tsoro ya bata ba saboda bata tsammace shi a wannan lokacin ba,cikin sauri ta wuce upstairs gabanta na faɗuwa aranta tana cewa"Anya haroon Ba Aljani bane?in ba haka ba yaushe har ya shigo babban falon nan amma banga gifcin shi ba," tana tafiya tana sambatu aranta har ta ƙarasa part dinsa, sai da ta tsaya tare da dai daita natsuwarta sannan tashiga ciki, wayaam babu kowa a falon hakan na nufin yana a cikin bedroom dinsa, Takawa tayi a hankali har zuwa ƙopar bedroom din nashi sannan tayi sallama,kusan sau uku ba'a amsa mata ba sai a na huɗun ne taji muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mata "come in,"   a hankali tasa ƙafarta tashiga ciki,lokacin da ta ɗago da idanunta nan take taji faɗuwar gaba rasss!yanayin da taganshi yayi uban goho saman gadon yana fitar da numfashi daƙer daƙer ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tuni jikinta yayi mugun sanyi,ƙarasawa tayi ciki tare da ajiye mashi tray din saman table tace"Sannu da dawowa ga tea nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata"? shiru bai bata amsa ba sai numfashi kawai da yake fitarwa mai hucin zafi,bin shi tayi da kallo sumar kanshi ta rufe dukkan fuskarshi side by side,tana so ta tambaye shi ko lpy amma tana jin tsoro,   Kusan 15 mins tana a tsaye bai ce komai ba ƙoƙari yake ya tashi amma sam jikinshi ya hana shi,sai da yayi dagaske sannan ya samu ya miƙe tare da matsowa ya sauko da legs dinsa ƙasa idanunshi a rufe rufff,fuskarshi ba ƙaramin canzawa tayi ba,jikin shi sai kerma yake yi tamkar wanda yashiga snow hatta pink lips dinsa sun gaza tsayuwa,tsananin tausayin shi ne ya kama sehrish saboda ta tabbatar da cewa bai da ƙoshin lpy sbd alamomin da tagani atattare dashi,tuni taji hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idonta,   muryarshi ce ta tsinkayeta da cewa"ki duba a cikin side drawer ɗina thete's a jotter wit pen pls bring it 4 me," cikin sauri sehrish ta matsa tare da kai hannu jikin side drawer ɗin,ta janyo gida na farko ajikinta, anan ta samu Jotter ɗin tare da biro,ɗaukowa tayi tare da miƙa mashi,   daƙer ya cire hannunshi ya kar6a har lokacin eyes ɗinshi na'a rufe,aza jotter ɗin yayi daga gefen table ɗin gabanshi,buɗe papers din ciki yayi kafin ya aza biro din ya soma rubutu bayan ya kammala yayi tearing wurin da yayi rubutun ya ɗauko takardar ya miƙa ma Sehrish,cikin sauri tasa hannu ta kar6a tare da aza idonta kan rubutun wani irin handwritting gare shi domin koda ta kalla ko *A* bata iya ganewa ajiki ba hakan yasa ta kalle shi tare da cewa"Bangane menene ka rubuta ba,"ta faɗi a ɗan tsorace "Go nd bring it 4 me," shine kawai abunda ya iya furta mata, Cikin sauri sehrish ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin nashi tana waiwayonshi,   Saukowa down stairs tayi tana faman cizon yatsa saboda tarasa gane menene ya rubuta mata,tamkar zatayi kuka,tana cikin wannan halin muryar haroon ta katse ta da cewa"Can I help u"? ɗagowa tayi aɗan razane tana kallon shi,fuskarnan tashi nadauke da murmushi yasa hannu ya kar6i takardar yana duba rubutun jiki,daga bisa ni yace"Ki jira ni anan yanzu zan dawo," yana fadin hakan yajuya da sauri ya shige part ɗinsu na nan downstairs, ajiyar zuciya ta saki aranta tana Allah Allah saboda tsoron kada haroon ya tafka mata kuskure don tasan halin shi,bai da tabbas gajiya da tsayuwa tayi,don haka ta samu wuri saman last step na benen ta zauna tana jiran dawowarshi,. Ba da jimawa ba sai gashi ya fito daga part din nasu, sai faman sauri yake yi irin da himmar nan hannun shi na ruƙe da syringe da kwalbar injection,tunkan ya ƙaraso sehrish ta miƙe tare da sa hannu ta kar6a tana yi mashi godiya,,   da buɗar bakinsa sai cewa yayi"Ba sai kin gode mun ba,Aikin lada ne fa nidae burina ki kai mashi allurar ya hanzarta yi yanzu,in ma godiyar ce gobe da safe kinzo ki same ni kiyi mun ita," yana magana yana sakin wannan shu'umin murmushin nasa, jiki asanyaye tasa hannu ta kar6a tana kallon fuskarshi shima kuma ita yake kallo da wannan murmushin nashi, cikin sauri ta juya tare da hayewa upstairs cikin sauri take tattaka matattakalar benen har ta wuce part dinsa Ruƙe qugu haroon yayi tare da sakin wani irin bazawarin murmushi yace"Lokacin Bacci yayi bari naje na kwanta gobe da safe akwai labari zazzafa,ƴar shila zata zo miƙo mun godiya da kanta," ya fadi tare da sakin dariya ya wuce sashen shi   Lokacin da sehrish ta koma ɗakin nashi yarda tabarshi haka ta same shi zaune idonshi a rufe, cikin sauri ta ƙarasa tare da miƙa mashi allurar da sirinjin tace"Ga allurar," hannu Sgr yasa ya kar6a daƙer ya iya buɗe idonshi sam baya iya gane wace kalar allura ce yarinyar ta kawo mashi saboda idanunshi biji biji suke gani hakan bai bashi damar karanta abunda aka rubuta ajikin ƙaramar kwalbar allurar ba,    fasa bakin kwalbar yayi tare da curo sirinjin ya fiddo da kan allurar ya tsoma acikin kwalbar ya zuƙo ruwan allurar iya yadda yasan ya dace yayiwa kanshi, .Tuni jikin sehrish ya soma rawa saboda tsoron allura gareta,cikin sauri ta kama hanyar fita daga dakin saboda ta bashi damar yin allurar,   Muryarshi ce ta tsinkayeta da cewa"kada ki tafi," ya furta yana faman sakin huci daga bakin shi da hancinsa, A bakin ƙopar ta tsaya idonta a rufe jikinta na kerma,muryarshi ta kuma ji yace"ki zo," cikin sauri ta koma ajiyar zuciya tasaki ganin harya kammala yin allurar, miƙa mata kwalbar allurar yayi tare da syringe din duka yace"kisa a dustbin," amsa mashi tayi tare da kar6a ta wuce wurin bedroom dustbin dinshi ta saka tarkacen allurar, sannan ta dawo ta tsaya tana jiran jin ko zai buƙaci wani abu tunda ya nuna baison ta tafi,   Lokacin da allurar ta gama gauraye ko'ina na jikinshi da wani irin ƙarfi ya ware idanunshi azare,har sai da sehrish taɗan ja da baya saboda firgitar da tayi,bin yatsun hannunshi tayi da kallo ganin yarda yake wawwaresu suna miƙewa tsaye,tamkar dae yadda mutun ke komawa Zombie acikin film,gabanta ne yashiga faɗuwa saboda tsoran da taji murya na rawa tace"Zan iya tafiya"?   ɗagowa yayi da wannan sexy blue eyes din nashi da launinsu ya ƙara Cizawa gwanin ban tsoro kai kana ganinsu kasancewa akwai matsala,ido cikin ido yake kallonta batare da ya kawar da idonshi ba hakan yasa zuciyarta ƙara karaya ga wani irin fargaba daya zo mata,ganin irin kallon da yake yi mata ne yasa nan take tadinga jin bugun zuciya,ja da baya ta soma yi jikinta na kerma har lokacin bai janye idonshi daga kanta ba bin ta kawai yayi da kallo,sai da taga taɗanyi mashi nisa sannan ta nufi hanyar fita daga bedroom din nashi da saurin gaske sai dai ina, kafin ta Ankara tuni SGR yayi wani irin kwakkwaran motsi tare da miƙewa tamkar wani Zaki ya bi bayanta azafafe yakai ma Waist ɗinta wani irin ruƙo ya ɗaga ta sama gaba ɗaya ta saki wata irin razananniyar ƙara mai rikitarwa bata gama rufe bakinta ba yayi wani irin wurgi da ita kai tsaye ta faɗa tsakiyar gadon shi yaraaaff tuni mayafin da tayi rolling dashi ya jima da barin jikinta !!!! Ba ƙaramin buguwa sehrish tayi ba daƙer ta iya tayar da kanta daga jikin bedmattress ɗin ta ɗago hankali a matuƙar tashe take kallon shi ganin yasanya hannayenshi tare da ruƙo shirt ɗin dake ajikinshi ya cire ta gaba ɗaya tare da yin wurgi da ita ƙasa,    gabanta ne yasake yin wani irin mugun bugu tuni hawaye sun soma wanke mata fuskarta cikin tsananin tashin hankali take girgiza mashi kai tana cewa"innalalahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga uku !!!!"    Sam babu alamar sassauci a tattare dashi kai kana ganin yanayin action dinsa zakasan cewa ba a hayacinshi yake ba, Hatta ƙarfin jikinshi bana shi bane a matsayin shi na wanda bai da Cikakiyar lafiya, Ganin ya zame belt ɗin wandon jikinshi gaba daya yayi throwing dinsa, tare da sa hannu yana ƙoƙarin zame wandon dake jikinshi, hakan ya ƙara tsoratar da sehrish yunƙuri tayi da ƙarfi zata diro daga saman gadon ta gudu,aikuwa batayi wani aune ba taji saukarshi saman gadon gaba ɗaya ya afka mata tare da yi mata Rumfa da faffaɗan ƙirjinshi tsulundum taji ta ajikinshi,🙆🏽‍♀   nan fa ido ya raina fata,dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi gaba ɗaya tagama rikicewa muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa"Dan Allah kayi haƙuri kabarni na tafi,ni nasan cewa ba halinka ba....ba yin kanka bane.......' kasa ƙarasa maganar tayi saboda idonshi dake kallon cikin kwayar idon nata,SGR fa a halin yanzu zamu iya cewa baya ji baya gani,    Wani irin huci yake yi yana groaning just like a hungry lion,runtse idonta tayi saboda bazata juri kallon cikin nashi ba yayin da idonta ke cigaba da zubar da hawaye...........🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♂️😳 Zuwa ga masu share na littafina lokacin da mutun zai sayi littafin nan ba muyi yarjejeniya nacewa zai turama wasu ba, amma sai gashi grp ba iyaka ana tura littafin koma waye yaje don kanshi kuma yasani akwai haƙƙina akanshi👍ya Allah kashiga tsakanina da koma waye, ************* It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku😍u  💋Boss Bature💋 runtse idonta tayi saboda bazata juri kallon cikin nashi ba yayin da idonta ke cigaba da zubar da hawaye........... Jin shiru yasata ta sake buɗe idanunta don taga me ya dakatar dashi har lokacin blue eyes ɗinshi na akan fuskarta tamkar mai nazarin wani abu,Allah sarki duk da bai a hayyacinsa yana ƙoƙarin ya dakatar da kanshi yayi control na kansa,Amma ina allurar ƙara zaburar dashi takeyi,sai faman ciccije pinkish lips dinsa yake yi,gaba ɗaya sumar kanshi ta lullu6e fuskarsu su duka biyun,    wata irin Zufa tagani tana tsattasofa mashi daga fuskarshi hakan ba ƙaramin razanar da ita tayi ba,ɗigowa sweat din tadinga yi daga fuskarshi tana sauka a fuskar Sehrish,    tuni ta soma haɗiyar yawu ganin yaƙi moving daga rufe ta da yayi hakan yasa,ta tattara dukkan ƙarfinta gaba ɗaya don ta ingije shi kota samu yayi gefe ɗaya ita kuma ta gudu,amma abun mamaki koda tasa hannunta tayi attempting ingije shi,ko motsi wannan baiyi ba saboda wani irin ƙarfine yazo mashi bana wasa ba, ..zaro ido tayi tana kallonshi hankali atashe,abun mamaki for the first time saita samu fuskarshi ɗauke da wani irin ƙayataccen murmushi naban mamaki lokaci guda yagama kashe mata jiki gaba ɗaya taji wata irin kasala ta rufar mata,    kwakkwarar damka yakaima wuyan rigar jikinta ya yage ta biyu nan take big boobs dinta suka bayyana gashi bata saka brazier ba,kokawa suka shiga yi dashi domin kuwa ta damƙe rigarta da yake ƙoƙarin yin wurgi da ita,sai faman ƙoƙarin rufe ƙirjinta take yi da ita,a ƙarshe daya fi ƙarfinta sai ta fashe mashi da wani irin matsanancin kuka da ƙarfin gaske take cewa"...Ya Allah ka kawo min ɗauki......Ya Allah ka dawo dashi cikin hayyacinshi ni nasan cewa ba yin kan shi bane.....   tuni ya afka ma ƙirjinta ya tasar masu, hannu takai tana ƙoƙarin janyo bedside lamp ɗinshi amma koda ta ruƙo fitilar ji tayi bazata iya cutar da shi ba kokaɗan saboda tsananin son da take yi mashi,tana jin duk wani motsin shi ajikinta,    Har bakinta takai a damtsen hannunshi don ta gartsa mashi cizo amma ina koda ta aza teeth ɗinta a fatar jikinshi sai dae kawai tafashe da kuka saboda bazata iya ba😢    Suna cikin wannan yanayin Marshal Omar ya faɗo cikin falonsa dawowarshi kenan daga wurinsu hossana bakomai ne ya kawo shi ba face message ɗin da sgr ya turo mashi a wayarshi nacewa bashi da lafiya,bai sanar mashi ba a lokacin da suke atare sai da suka rabu yana acikin mota ya rubuta mashi message ɗin, ganin saƙon da yayi ne yasa shi yin hanzarin dawowa gidan don ya duba shi,    Yana shigowa falon yaji sautin kukan Sehrish acikin ɗakinsa ga wani irin gurnani da sgr keyi na irin kura taga naman nan, hankalin shi a matuƙar tashe ya afka bedroom ɗin nashi,ba ƙaramin razana Omar yayi ba ganin yarda Sgr ya rufar ma Yarinyar gaba ɗaya ya danneta a lokacin harya zame dogon wandon jikinshi,shorts ne kawai ya rage mashi shima ƙoƙarin zame shi yake yi daga jikin shi,    A tsawa ce Omar ya kwaɗa mashi kira da ƙarfin gaske ya furta "RAFAYET!!!!!!!!!!!!!!!!! Tamkar maƙoshin shi zai 6allo waje haka ya ambaci sunan har kunnan sehrish, amma shikuwa gogan sam ba alamar yaji balle ya ɗago,    Ganin hakan yasa Omar yin hanzarin ƙarasawa tare da kai hannunshi a matuƙar zafafe ya damƙi sumar kanshi da karfin gaske ya janyo shi yayi wurgi dashi gefe guda saman gadon,   Cikin sauri sehrish ta rufe ƙirjinta da rigar ta wadda sgr ya yage mata ita,tashi tayi zaune tana ta faman sessheƙar kuka ga jikinta dake ta faman kerma,    tamkar zaki haka Sgr ya kuma ɗagowa daga wurgin da Omar yayi dashi gaba ɗaya ya makance,wani irin ihu sehrish tasaki ganin yasake nufota yana wani irin gurnani,   Cikin hanzari Marshal Omar ya damƙo damtsen gannunshi yana cewa"Wai meyake damunka ne!!!me kake ƙoƙarin yi ne!!!    Juyowa sgr yayi yana wani irin huci ya kalleshi tamkar baisan omar ba haka ya zabura ya miƙe tsaye tare da dirowa daga saman gadon ya daddage ya dunkule hannunshi yakai mashi kwakkwaran naushi a saman ƙirjin shi,ba ƙaramin zafi Omar yaji ba,rai a6ace shima ya cakume shi tare da kai mashi naushi,nan fa suka kaca me gaba ɗayansu tamkar ƴan wrestling haka suka shiga bugun junansu,   ganin haka yasa sehrish saukowa daga saman gadon dama ta samu ta zura rigar ajikinta duk da ta yayyage daga gabanta sai dae ta sanya hannu ta ruƙo rigar ta tattare wurin daya yagen,cikin sauri ta kama hanyar fuce wa daga ɗakin,aikuwa karaf akan idon Sgr a wani irin zafafe yayi wurgi da Marshal Omar gefe guda, da gudun gaske yabi sehrish tare da cafkota jikinshi nan take ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka,     Da hanzarin gaske Omar ya yunƙura ya taso yabi bayanshi tare da rurruƙe hannunshi tabaya da ƙarfin gaske,sai da yayi da gaske sannan yayi wurgi da sgr gefe guda, hakan yaba sehrish damar watsawa a guje tabar ɗakin,   Kafin Sgr ya yunƙura ya taso tuni Omar ya janyo ƙopar ɗakin ya datse ta, ya rage daga shi sai shi acikin ɗakin suna kallon kallon,    Omar bai ta6a tsorata da sgr ba sai ranar ganin yadda yake zazzare mashi ido tamkar baisan shi ba, gaba ɗaya kanshi ya gama ɗaurewa saboda yasan cewa ba Halin shi bane,shi da sam mace bata agaban shi ko kallo wannan amma kuma ace yau shi da kanshi yake ƙoƙarin yiwa Mace fyaɗe,bayan shike hukunta masu aikatawa da hannunshi,lallaikam akwai matsala,    ganin yadda yake ta faman huci yana cizon la66a yana kallonshi yasa shi saurin dakatar dashi da hannu yana cewa"Look rafayet!!! Ni nasan ba yin kanka bane,nasan ɗan uwana bazai ta6a aikata hakan ba,dan Allah ka amsa mun don na tabbatar da cewa ba yin kanka bane.......'kafin Omar yakai ƙarshen maganar tashi tuni sgr ya kai mashi kwakkwaran ruƙo duk irin nauyin marshal Omar sai da sgr ya ɗaga shi ya ɗaɗɗagoshi tare da yin wurgi dashi,aikuwa ba ƙaramin buguwa Omar yayi don gaba ɗaya yatafi ya zube gaban drawer dinsa nan take forehead dinsa ya bugu ajikinta har wurin yaɗan fashe kaɗan dafe goshin sa yayi tare da ɗagowa da idonshi ya kalli sgr cikin sanyin murya yace"Ni fa ne Omar ɗinka yau da kanka kake buguna?so kake ka kashe ni,    tamkar tunzura shi yayi maganar da yayi aikuwa gadan gadan ya tunkare shi da wannan tafiyar ta basawa,   "In fa na biye mashi wlh naƙasa ni zaiyi da alama," ya fadi acikin ranshi, cikin sauri Omar ya tashi tare da yin hanzarin afkawa cikin toilet ɗinsa ya rufe ƙopar,yayi hakan ne saboda tsoran karsu raunata junansu don inya bugeshi ba ƙyaleshi zaiyi ba ƙarfine zai haɗu da ƙarfi daganan kuma abunda zai biyo baya su dukansu bazasu ji daɗin shi ba,   Tamkar zai 6a66ake ƙopar toilet din haka yadinga bugun ƙopan saboda Omar ya buɗe mashi yashiga,su cigaba da gashi don ba ƙaramin fusata shi yayi ba so yake ya karairaya ƙasusuwan jikinshi,    "Wlh ka yi mai isarka,bazan buɗe ƙoparba," yana magana dariya tana cin shi saboda lamarin ya gama ɗaure mashi kai,    tuni jiri ya soma ɗibar sgr ja da baya baya yadinga yi yana ambaton sunan Allah nan take ya yanke jiki ya faɗa saman gadonshi abaje ya sume,   jin shiru tsit yasa Omar sanya hannu tare da buɗe ƙopar toilet ɗin yaɗan leƙo,ganin shi kwance saman gadon ya sume ba ƙaramin sanyi yaji ba aranshi,   fitowa yayi daga cikin toilet ɗin yana faman sauke ajiyar zuciya,ƙarasawa yayi inda sgr ɗin yake,hannayen shi yasanya tare da tattaro dogayen ƙafafuwanshi ya azasu saman gadon gaba ɗaya, sannan ya gyara mashi kwanciyarshi tare da janyo blanket dinsa ya lullu6e mashi jikinshi,     Addu'o'i ya tattofa mashi sannan ya kama hanyar fuce wa daga ɗakin harya kai baƙin ƙopa karaf idonshi ya sauka kan Syringe din allurar da sehrish ta zuba acikin dustbin,cikin sauri yakai hannunshi cikin dustbin ɗin tare da ɗauko kwalbar allurar yana karanta rubutun dake ajikinta,nan da nan hankalin shi yayi wani irin mugun tashi tuni kanshi ya gama ɗaurewa tunaninsa taya akai SGR yayi ma kanshi wannan allurar!!!!?    "I can't believe it!!!" ya furta yana sake jujjuya kwalbar dake hannunshi,    Tare da ita ya fito daga ɗakin yaso yaje wurin Yarinyar saboda ya rarrashe ta ya fahimtar da ita amma dare yayi sosai baisan awane hali take ciki ba yanzu,wuce wa bedroom ɗinshi kawai yayi tare da kwalbar ruƙe a hannunshi saboda yin Investigation akanta,dole ya binciki yarda akai akasamu allurar acikin gidan saboda dama sun jima suna neman haramtaccen companyn miyagun kwayoyin dake sarrafa allurorin a 6oye masu cire imanin mutun lokaci guda, 😳😳😳   *** A 6angaren sehrish kuwa abun gwanin ban tausayi haka ta faɗa ɗakinta tana faman shan kuka,gefen gadonta tazauna domin ƙarashe kukan nata,ta jima batare da yin motsi ba,hannunta na ruƙe da rigarta sai ƙara matse wurin take yi tana kuka,duk wurin da sgr ya damƙa ajikinta ba ƙaramin raɗaɗi yake yi mata ba saboda baiyi mata ruƙon wasa ba,idanunta sun kumbura sosai saboda kukan da tasha.......'   Bakomai tafi ji ba face yarda taga Omar na bugunshi,tsoranta karya lahanta shi akan abunda take da tabbacin cewa ba yin kanshi bane,😢 Daƙer ta iya miƙewa ta wuce toilet saboda ta tsarkake jikinta,rufe ƙopar toilet ɗin tayi kusan 15 mins sai gata ta fito ɗaure da towel tana faman sauke ajiyar zuciya,har cikin ranta ba ƙaramin sanyi taji ba da Marshal Omar yazo don da baizo ba adai dai wannan lokkacin da SGR ya jima da yin raping dinta,kuma babu tabbacin cewa zata rayu saboda ba ɗigon Imani atattare dashi lokacin,      Wardrobe ɗinta ta buɗe tare da curo wata rigar baccin ta zura ajikinta, sannan ta koma tare da hayewa saman gadon,janyo bargonta tayi tare da lullu6e jikinta dashi, rufe idanunta tayi nan take brain ɗinta,ta tariyo mata fuskar sgr lokacin da yake kallon cikin idanunta sweat dinshi na zuba a fuskarta nan take wata irin kasala ta rufe mata jikinta,sam bacci yaƙi ɗaukarta saboda daga tazo runtse idonta sai taji kamar SGR zai faɗo mata cikin ɗakin,firgita ta dinga yi duk tabi ta tsoratar da kanta duk da ta rufe ɗakin ammma ji take kamar zai biyota ne,saboda yarda taga ya buge omar ya afko mata ɗazun,tana cikin wannan halin wayarta ta buga uban ringing aikuwa a gigice ta wuntsila ta faɗo ƙasa daga saman gadon tana ƙoƙarin shigewa ƙarƙashin gadon,yadda kasan wadda sanyi ya kama,haƙoranta sai kerma sukeyi kaf!kaf!!kaf, yatsun hannunta kuwa kamar waɗanda aka sanyawa battery sai rawa sukeyi ba ƙaƙƙautawa,ta jima a haka tana faman zazzare ido, sai daga bisani ta gane cewa wayarta ce ke ringing,lalla6awa tayi tataso tana tafiya cikin sanɗa har ta ƙarasa wurin side drawer ɗinta buɗewa tayi tare da ɗaukar wayarta ta dake ringing,tamkar wayar zata sul6e daga hannunta saboda kermar da fingers din nata keyi,Sunan AMRISH ne ya bayyana akan screen din wayar,lokaci ta duba kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare,katsewa kiran yayi saiga message ya shigo nata,cikin sauri ta buɗe tare da karantawa kamar haka   _Hi reesh,nayi missing ɗinki sosai shiyasa na kira don na tsoratar dake saboda nasan cewa zaki firgita in kirana yashigo a wannan lokacin,May be ma kina nan kina Jan minshari ne_    Murmushi sehrish tayi sosai bayan tagama karanta,reply ta mayar mata da cewa"i missed u too my lovely friend,kinci nasara akaina saboda kin tsoratar dani sosai,gobe ba school amma zamuyi video call ne,"    Bayan ta kammala tura mata saƙon ta mayar da wayar asaman drawer din ta ajiye,safa da marwa tashiga yi acikin bedroom dinta tana tunanin taya akai Sgr yyi attempt na raping ɗinta!!!? tsayawa tayi cak lokacin da zuciyarta ta ambaci sunan HAROON,gabanta ne taji ya faɗi bakomai ta tuna ba face maganar daya yi mata nacewa"Basai kin gode mun ba Aikin ladane,nidai burina ki kaima shi ya hanzarta yi gobe da safe kinzo kiyi mun godiyar,    Dafe ƙirjinta tayi cikin tsananin tashin hankali, hannu ta aza akai muryarta na rawa tace"innalallahi wa'inna ilahirraji'un nashiga ukuna!!haroon yaja mun bala'e...tabbas shine silar komai !! Shiya bani allurar dana kaima babban yaya, wayyo Allah na...yanzu dole su tuhume ni akanta!!Haroon ya gama dani.............   A daren ranar sehrish bata runtsa ba yarda taga rana haka taga dare,tasha kuka kamar kamar me ƙarshe ma tashiga toilet tayo alwala tafito ta shimfida carpet tashiga jera salloli har sai da ƙafafunta suka soma raɗaɗi sannan ta dakata tare da ɗaga hannayenta sama tana roƙon Allah ya tsareta daga sharrin Haroon,sai wuraren asuba bayan tayi salla sannan bacci yayi awon gaba da ita a saman sallayar,💔         Morning ❤❤❤ Wuraren ƙarfe takwas azmee tashiga bugun ƙopar bedroom dinta,har cikin tsakiyar kanta tadinga jin bugun,a gigice tafarka tare da miƙewa ta nufi kopar ta buɗe tana tambayar wanene,   Bin ta da kallo azmee tayi ganin yarda fuskarta ta kumbura suntum ga idanunta ma sun ƙankance saboda rashin isasshen bacci,hankali atashe tace"Lafiyarki kuwa sehrish?Anya ma kinyi bacci jiya? Fuskarki kamar ta wanda yasha kuka?     Maimakon ta bata amsa sai ta fashe da wani kukan saboda tunawa da halin da take ciki,ganin hakan yasa azmee shiga cikin ɗakin tare da rufo masu ƙofa,.     ruƙo hijabin sehrish tayi taja ta suka zauna daga gefen gadonta sannan ta kalle ta anatse tace"faɗamun meya faru ƙanwata?meyasa ki shiga cikin damuwa....."    cikin shessheƙar kuka sehrish ta Zayyana mata dukkan abunda ya faru adaren jiya ta ƙare da cewa"a....Aunty azmee wlh ba laifina bane Haroon ne ya bani allurar, banyi tunanin zai cutar dashi bane,yanzu ni bansan ya zanyi ba! Idan babban yaya ya tuna abunda ya faru jiya dole ya tuhume ni akan ni na kawo mashi allurar.........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,   Shiru azmee tayi kamar mai nazarin wani abun kafin daga bisani tasanya hannunta a kafaɗar sehrish din tace"Just Calm down ur mind!ki share hawayenki,ynx yakamata muyi tunanin samun solution before ya tuna din, amma nayi mamakin a ina haroon ya samu allurar daya baki ashe dama kuna ƴar tsama dashi baki ta6a sanar mun ba!?   cikin shessheƙar kuka sehrish tace"bansan me nayi mashi ba aunty azmee haroon ya tsaneni nima bana son ganinshi saboda ya jima yana ƙuntatamun bana son na tayar maki da hankaline shiyasa ban ta6a sanar dake ba......'    Jinjina kai azmee tayi kafin tace"Kinyi kuskure sehrish!!baki ɗaukeni kamar yarda na ɗauke ki ba,rashin gayan mun da kikeyi shine zai jefa ki cikin matsala....'rai aɗan 6ace azmee keyi mata magana,   "Aunty azmee kiyi hakuri nasan nayi kuskuren rashin sanar dake yanzu nagane hakan,"     ajiyar zuciya azmee ta saki kafin tace"shikenan ya wuce,naji daɗi sosai da yakasance Omar ne ya ƙwaceki a wannan lokacin da bansan mai zai biyo baya ba,ynz babban matsalar dole ne suyi zargin wani abu akanki,koda Omar ya tambayeki wanene ya baki allurar ki sanar mashi kawai that's the only solution!!!    girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"a'a aunty azmee bazan iya cewa haroon ne ya bani allurar ba,saboda bakowa ne zai yarda dani ba,kuma zai iya ƙullamun sharri ne,ina tsoran hakan,"    gyaɗa kai azmee tayi tare da cewa"hakane kuma kin faɗi gsky,abun zai iya juyewa ya dawo kanki,amma naso ki sanar dasu cewa shi ya baki allurar saboda ki samu ki tsira,amma bakomai nasan cewa Omar zai fahimce ki in kikayi mashi bayani,babban tashin hankalin shine idan shi Sgr din ya tuna abunda yafaru gsky akwai matsala!!!!    Sun jima suna tattaunawa kan yarda zasu shawo kan matsalar kafin daga bisani Azmee tace"ki kwanta ki huta don nasan jiya bakiyi bacci ba,ni bari na wuce kitchen,"   Amsa mata tayi da toh,sannan ta cire hijab ɗin jikinta ta kwanta saman lallusan katifan gadon,lamo tayi a hankali brain din tadinga tariyo mata abunda ya faru adaren jiya,musamman yarda yayi mata rumfa da wide chest dinshi yana faman gurnanin nan yana kallon cikin idonta,wani irin yanayi mara misaltuwa, ba ƙaramin shock taji ba alokacin duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hanata jin emotion dinshi ba,    Hannu tasa tare da janyo fillow ta rungume shi sosai ajikinta saboda yanayin daya zo mata tuni taji wata irin kewarshi ta lullu6eta kamar maijin zazza6i,runtse idonta tayi nan take wannan ƙayataccen murmushin daya sakar mata jiya yadawo mata a idonta,cikin sauri ta buɗe su tana faman sauke ajiyar zuciya,ban ta6a ganin kyakkyawan murmushi ba sai adaren jiya Ya Allah ka mallaka mun shi ❤💋    Ta furta fuskarta dauke da murmushi daga bisani wani baccin ya kuma yin awon gaba da ita, ****** fitowa Omar yayi daga bedroom dinshi jikin shi na sanye da jallabiya maroon colour,jiya da tunanin abunda ya faru tsakanin SGR da yarinyar nan ya kwana,burin shi kawai yaje yaga ya rabin ranshi ya kwana, shiga part dinsa yayi tare da wuce wa bedroom dinshi, abun mamaki samun shi yayi tsaye agaban mirror jikinshi na sanye da bathrobe ya ɗaure suman kanshi ta baya,da alama fitowarshi kenan daga bathroom,   shiga ciki omar yayi tare da yi mashi gyaran murya,juyawo sgr yayi ya kalle shi tare da 6ata fuska yace"Am angry wit u omar,bana son ganinka cos i even texted u about my sick amma shine ko kazo ka ganni ko? Ya fadi tare da tsuke mashi fuska,   Tsayawa Omar yayi yana kallon shi kamar mai nazarin wani abu,yayi wani fresh dashi sam babu alamun damuwa attare dashi,    Cikin mamaki yace"Oh kana nufin ka manta abunda ya faru jiya"?   "Meya faru"!? Ya tambayana yana kallonshi aɗan ruɗe,    matsawa kusa dashi Omar yayi tare da aza hannnayenshi akan shoulders ɗin Sgr yace"Wai dagaske kamanta komai?duk abunda ya faru jiya"?   girgiza mashi kai yayi tare da cewa"Omar ni fa i don't know what are u talking abt explain to me pls,   fashewa da dariya Omar yayi daker ya tsagaita yace"pls ka tuna mana ko kaɗanne,   Shiru sgr yayi yana bin shi da kallon bana son raini, can dae yace"Jiya ni bansan ina kaina yake ba,i Can't remember,    jinjina kai Omar yayi har lokacin fuskarshi ƙumshe da dariya yace"kaine kayiwa kanka allura jiya?   ɗan yatsina fuska yayi kafin yace"yeah its me meya faru ne?   girgiza kai omar yayi tare da cewa"babu komai kawai inaso inji kaine ka ɗauko allurar?kuma kasan wace allurace kayi ma kanka"?   ɗan shiru Sgr yayi yana kallon fuskar Omar na wani lokacin a ƙoƙarinshi na ya tuna meya faru,ajiyar zuciya yasaki tare da cewa"Bani bane,wannan yarinyar ne, itace ta ɗaukomin,"    ruƙo hannunshi Omar yayi yaja shi suka zauna daga gefen gadonshi sannan yace"da ka tashi yau da safe kana nufin kwata kwata baka ga wata alama ba ajikin ka ba"?    ɗaure mashi fuska yayi yace"Omar banason wannan tmbyar nifa ban gane me kake nufi ba,"    Hannu omar yasa yana shafa ƙirjinshi yace"kwantar da hankalin ka mana,just tell me da wani yanayi ka tashi yau ajikin ka,    Shiru sgr yaɗanyi na wani lokacin kafin yace"bro i can't explain it,yanayi mara misaltuwa jiya na kwanta da ciwo, but dana tashi naji ni'ima atattare dani ga wani ƙarfi da nake Ji not only that omar When I went to the toilet, I saw something that really confused me because I had never seen it before..................🙊 Weekend mu haɗu on monday insha Allah, don't forget to follow me on tiktok boss_bature❤️ 💋Boss Bature💋 Follow this link to join my tiktok acct 👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 "What's it"? Omar ya tambaya yana kallon shi, ganin yarda Omar ke kumshe dariya yasa shi fasa yin maganar ya ɗan ɗaure face ɗinshi yace"omar banason wasa fa pls tell me the truth, Did something happen last night? Naga bed sheet dina duk yayi wani squeezing kamar anyi dambe asaman shi,     dariya sosai Omar yayi kafin yace"no ba wani abu just forget about it, na same ka ne kawai a wani yayi na ciwo so na ɗan taimaka maka ne har nasamu bacci ya ɗauke ka," ta6e baki sgr yayi yana kallon shi don bai yarda da abunda ya faɗa mashi ba, hakanan omar bazai tasa shi gaba yana mashi dariya ba just without any reason,     miƙewa Omar yayi tare da kallon shi yace"bari na sauka down ko kana buƙatar wani abu ne nasa akawo maka"?   juyawa sgr yayi ya kalli tray din da ke ajiye saman table ɗinshi yace"wannan yarinyar tazo ta tattara wannan kayan,ga bedroom dina ma inaso a gyaramun,"    "Okey zan faɗa mata, ka huta my man,"    Juyawa omar yayi zai fuce har yakai bakin door din ya waiwayo  don ya kalli sgr karaf suka haɗa ido, cikin mamaki yace"Omar nifa wani kallo naga kana min irin kallon jarababben namijin nan......' ya faɗi yana tsuke mashi fuska,   Fucewa omar yayi yana ƴar dariya, yamutsa fuska sgr yayi tare da cewa"Omar nason haukata ni, bansan wannan dariyar nashi me yake nufi ba," yayi maganar tare da kwantar da bayanshi saman lallausar mattress ɗin, kwakkwaran juyi yayi asaman gadon, kai tsaye idonshi ya sauka akan siraran gashin dake zube saman bedsheet dinsa, cikin sauri ya ɗago da kanshi tare da zuba ma gashin ido, mamaki ne ya kamashi taya akai gashin kanshi ya zuba don kuwa yana da tabbacin cewa sumar kanshi bata kakka6a saboda gyaran da take sha, hannun shi yakai a hankali tare da ɗauko siraran gashin guda uku ya zuba masu ido yana kallonsu, dogon gashi ne mai tsayin gaske, sak irin launin sumar kanshi wato dark brown colour, natsuwa yayi yana nazarin gashin, kafin yasanya hannunshi tare da ɗaukar siraran gashin a hannunshi,yunƙuwa yayi tare da miƙewa daga saman gadon, ya nufi gaban dressing mirror dinshi, zama yayi asaman front chair din madubin, sannan ya ajiye siraran gashin asaman shi, hannu yasa tare da tsinko gashin kanshi siriri guda ɗaya, sannan ya ajiye shi a gefen waɗancan sauran guda ukun, within 5 mins ya gane difference ɗin dake tsakanin su,tabbas wannan ba hairs ɗinshi bane to na wanene, asaman bedsheet ɗinshi kuma?  hannu yasa ya ɗauki siraran gashinan guda uku, sannan ya tashi tsaye ya nufi bedside drawer ɗinshi, buɗewa yayi tare da buɗe jotter ɗinshi dake ajiye acikinta, a shafi na farko ya saka siraran gashin sannan ya rufe jotter ɗin, tare da mayar da drwer chest din ya rufe, wuce wa yayi wurin closet ɗinshi domin shirya kanshi, ***********💋  bayan fitar marshal omar daga part din  Sgr kaitsaye down stairs ya wuce wurin dining area dinsu ya nufa ganin aunty azmee nata faman jera masu breakfast dinsu, tunkan ya ƙaraso ta soma sakar mashi murmushi tana cewa"Omar barka da fitowa fatan ka tashi lafiya,"?     fuskarshi asake yace"lafiya lou Alhmdllh,"    shiru ya ɗanyi kafin yace"am ina wannan yarinyar take ne sehrish"? Har sai da gaban azmee ya fadi rass jin abunda yace,dama tasan saiya tambayeta akan maganar nan,    murya na rawa tace"bata jin daɗi ne tana a bedroom ɗinta,ni nace mata ta kwanta ta huta shiyasa bata fitowa. Ba.......'   "Ta sanar dake game da abunda ya faru jiya"? Ya katse ta da tambaya,    "Eh ta sanar dani komai," ta fadi adabarbace,    Omar yace"okey ina son magana da ita, ki ce tazo tasame ni a part ɗina ina jiranta,"   Cikin sauri ta amsa mashi da toh, sannan ta bar jera abincin da take yi ta wuce ɗakin sehrish,    A hankali ta tura ƙofar tashiga da sallama, kwance ta same ta sai faman sharar bacci take yi, har lokacin jikinta bai daina yin kerma ba,    matsawa tayi dab da ita tare da sanya hannu ta ɗan bubbugi kafadarta "Sehrish !!sehrish!!   Har cikin dodon kunnanta taji kiran a firgice tafarka tare da miƙewa tsaye tana cewa"La'ila ha'ilallah.........' rufe mata baki azmee tayi tare da cewa"ki natsu ni ce" a hankali tashiga sauke ajiyar zuciya tana kallon azmeen da idanunta da suka canza launi saboda bacci,  Janye hannu azmee tayi daga bakinta sannan tace"Omar ne ke son magana dake yace ki same shi a part ɗinshi yanzu,"    zare ido sehrish tayi murya na rawa tace"Aunty azmee ni kuma.....na shiga uku....me zai tambaye ni......'. Katse ta azmee tayi tare da cewa"kada ki damu nasan game da allurar nan ne zai tambaye ki, kawai ki fada mashi gaskiya a wuce wurin,"     fuskarta tamkar za tayi kuka tace"Aunty azmee ina tsoro fa kada naja ma kaina,"    girgiza kai azmee tayi tare da cewa"ba wani tsoro omar zai fahimce ki, kina 6ata lokaci fa ki tashi ki tafi,  Tana kai ƙarshen maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, jiki asanyaye sehrish ta sauko daga saman gadon, hannu tasa ta ɗauki hijab ɗinta wadda ta ajiye asaman gadon milk colour ta zura ajikinta,   Buɗe ƙopar ɗakin tayi ta fito tare da miƙar hanya ta wuce part dinsa, tsayawa tayi daga ƙopar shiga tana ƙoƙarin dai daita natsuwarta,sallama tayi mashi amma shiru ba'a amsa ba, ƙafa tasa tashiga daga ciki,babu kowa a falonsa komai anatse yake sai ƙamshi dake tashi,    Shiga ciki tayi tare da samun wuri ta tsaya a kusa da royal sofa din dake a kewaye, gabanta sai faɗuwa yake yi kamar mara gaskiya,     "Ya Allah ka bani ikon amsa tambayar da zaiyi mun,bana son nashiga matsala da kowa acikin gidan nan, nasan zasu iya zargina wayyo Allah na," ta furta tana faman yarfa hannunta, cike take da zullumin me zai biyo baya,   tana cikin wannan tsayuwar wayar shi ta shiga ringing a firgice taɗan ja da baya saboda bata tsammaci jin sautin wani abu ba, bin wayar tayi da kallo tana ajiye asaman 3 seater din don anan yabarta,     katsewa kiran yayi sai ga wani ya kuma shigowa, matsawa tayi a hankali saitin kujerar tana kallon wayar, ranta ne yabata ta ɗaga kiran taji wanene wata'kil kiran gaggawa ne,    Tamkar ana tunzurata haka taji, hannu takai tare da ɗaukar wayar tayi picking call din tare da karawa a kunannta, tun kafin tayi sallama taji ance"Ya Omar shi ne jiya kace in ka koma zaka kira ni awaya amma naji shiru ko? Muryar hossana ce ke magana,   Shiru sehrish tayi tana sauraron maganarta,.    Acan kuwa jin tsit Omar ɗin yayi mata shiru yasa ta cewa"kana ji na kayi mun shiru ko, Allah idan bakayi magana ba yau ko breakfast bazanyi ba....' ashagwa6e tayi maganar,    murmushi sehrish tayi jin yarda yarinyar ke magana, sai a lokacin tace"bashi bane, baya kusa ne,"     Jin muryar mace yasa hankali hossana tashi ruƙe qugu tayi dama tana atsaye jikinta nasanye da kayan bacci riga da wando red colour, ta ƙara kara telephone din a kunnanta, tace   "ƙanwarshi ko budurwarshi ko matarshi wacece ke aciki ? ta tambaya a ƙule,     "Matar shi ce," sehrish ta faɗi cike da zolaya, aikuwa nan take hankalin hossana ya tashi, muryarta tamkar zatayi kuka tashiga kwalama jahad kira tana cewa"Jahad!!Jahad!! ashe dama ya omar yana da aure shine bai fadamana ba,     Yadda hossana ke kwala mata kira yasa ta fitowa daga kitchen cikin sauri ta nufe ta tana cewa"Hossana lafiya meya faru ne kike kwalamun kira? Ke da waye a waya? Ta tambaya a yayin da take ƙarasawa wurinta,   duk sehrish ta kasa kunne tana jinsu,  Cikin shessheƙar kuka hossana tace"Ashe dama ya omar na da aure bai fadamun ba,"    Cike da mamaki jahad tace"kai haba wai dagaske?    "Eh mana gatanan muna magana awaya," ta faɗi rai a6ace tana miƙa ma jahad telephone ɗin,,   Hannu jahad tasanya ta kar6i wayar sannan anatse tace"Assalamu Alaikum," fuska dauke da murmushi sehrish tace"Wa'alaikum salam,"   Jahad tace"ina kwana aunty,"    "Lafiya lou," sehrish ta amsa,  Jahad ta kuma cewa"dagaske ne kece matar yaya Omar"? ta tambaya tamkar tana a gabanta, Sehrish tace "eh nice,"   jinjina kai jahad tayi tare da ɗan ta6e baki tace"Amma bai ta6a sanar mana ba, dan Allah sabon aure ne ko tsoho "   Ƙiriss ya rage sehrish ta fashe da dariya daƙyar ta basar da ita tare da cewa"tsoho ne, mun jima atare ynx haka ma ina ɗauke da juna biyu ina fata zaku zo suna in na haihuwa,"    Jiki asanyaye jahad tace"insha Allah idan ya barmu zamu zo, amma aunty baki faɗa mana sunanki ba"?    Ƙara kashe murya sehrish tayi tare da cewa"sunana Zainab amma mijina yana kira na da Hayaty," KARANTA ZAFAFA 2022 ✓Gurbin Ido... Na Huguma (Zafafa2022) ✓Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022) ✓Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022) ✓Babu So... By Billyn Abdul (Zafafa2022) ✓Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)   Jinjina kai jahad tayi tare da kallon hossana wadda ke tsaye cikin ƙunar rai,   Sun jima suna waya da sehrish kafin suyi sallama, mayar da wayar sehrish tayi ta ajiye saman seater ɗin, sannan ta koma tana faman tiƙar dariya,    ɗagowa jahad tayi ta kalli hossana gaba ɗayansu jikin su yayi mugun sanyi, duk basu ji daɗin cewa ya omar yana da mata ba, sam hossana ta gaza jurewa komawa tayi saman 2 seater ta faɗa tare da kifa kanta tana kuka, jahad kuwa kitchen ta wuce saboda tabaro dankalin da take soya masu, ita kanta jurewa kawai take yi amma ba ƙaramin ɗaci taji ba na jin cewa ya Omar dinsu yana da aure, tsayawa tayi agaban fan din dake asaman gass sam ta kasa juya dankalin saboda tashin hankali, cikin sanyin murya tace"koma wacece matar shi ina tayata murna sosai, domin kuwa tayi dacen miji nagari........' kwalla ce ta zubo daga idonta ɗas ta zuba ƙasa, 😖     Shigowa omar yayi cikin falon nashi, sehrish na ganin shi nan da nan ta shiga natsuwarta,    "Ina kwana ya omar"?   kallonta yayi tare da sakar mata murmushi yace"lfy lou Alhmdllh, ki zauna mana," ya faɗi tare da samun wuri ya zauna asaman 3 seater,  wuri tasamu itama ta zauna suna fuskantar juna,    sunnar dakai tayi ƙasa tana jiran jin mai zai ce mata,   Cikin natsuwa ya soma magana "Am really  sorry abt wht happend last night, banji daɗin abunda sgr yayi maki ba, nasan abun zai tsaya maki aranki,amma inaso ki sani ba yin kanshi bane! wannan allurar ce da kika kai mashi ya sanar dani cewa ke kika kai mashi ita...........' hankali tashe sehrish take kallon shi a tunaninta sgr ya tuna abunda ya faru ne,    Cigaba da magana omar yayi anatse yace"Calm down ur mind, sgr ba zai iya tuna abunda ya faru ba a yanzu amma fa dole ya tuna wata rana abun zai dawo mashi ne akan shi, so nake ki fadamun a ina kika samu allurar da kika kai mashi ? Da sanin ki kika kai mashi ita? Ya tambaya yana kallon fuskarta cike da tuhuma ,   Lokaci guda duk ta dabarbarce ta rasa natsuwarta,      " Tell me the truth who brought it to u? don nasan ba ke kika dauko ta ba, in fact bamu da irinta acikin gidan nan...'    shiru tayi tana kallon shi zuciyarta na raya mata ta fada mashi gaskiya kawai,     murya na rawa tace"Ya omar ni ba da sani na ba Allah, babban yaya yayi mun rubutu a paper ya bani, ko a lokacin sai da nace mashi ni bansan meya rubuta ajiki ba, amma yace mun naje na ɗauko mashi kawai saboda baya cikin hayyacin shi ne, lokacin dana fito da takardar a hannuna  ina zullumin meya rubuta ajiki shine kawai sai ga h.....h.....' wani irin ruƙo taji anyima maƙoshinta tamkar wani abu ya tokare wurin,nan take taji numfashinta na shirin ɗaukewa gaba ɗaya, kakari tashiga yi tana ƙoƙarin furta sunan haroon amma sound ɗin ya ƙi fidduwa daga bakinta, abun mamaki abun al'ajabi,    Ganin yarda zufa ke tsattsafo mata gefe da gefen fuskarta gashi sai faman numfarfashi take yi sama sama,   Hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba cikin sauri yace"Ke lafiya meke faruwa ne? Ko baki da lafiya ne?    cikin kuka tace"maƙoshina ne ke mun ciwo, nagaza furta sunan wanda yaban allurar raɗaɗi nake ji a wurin,     tashi marshal omar yayi tare da ƙarasawa wurin frigde din dake a falon shi, buɗe wa yayi tare da ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya dawo ya zauna dab da sehrish ya buɗe murfin robar ya miƙa mata, cikin sauri ta kar6a tana sha sai da tashanye kusan rabi sannan ta janye tana faman sauke ajiyar zuciya,   Hannu omar yasaka tare da kar6a robar daga hannunta yasanya murfin ya rufe sannan ya ajiye robar ruwan a ƙasa, mayar da idonshi yayi akan sehrish sannan cikin natsuwa yace"pls taimako nake so kiyi mana,bansan wacece ke ba amma har a raina naji, na yarda dake dan Allah karki sa na fara zarginki, ki fadamun gaskiya wanene ya baki allurar da kika kai mashi? allura ce mai haɗarin gaske a lokacin da Allah baisa na faɗo na ceceki a hannun shi ba tabbas ba zaki rayu ba....    Hankali atashe sehrish ta ɗago idanunta tana kallon shi, nan da nan taji wasu hawayen sun sake wanko mata fuskarta cikin shessheƙar kuka tace"ya omar wlh ni bansan komai akai ba bazan iya cutar dashi ba kuma nima bazan so na cutar da kaina ba..........'    jinjina kanshi yayi tare da cewa"to ki fadamun wanene ya baki allurar"?    buɗe baki tayi zata furta haroon nan take ta sake ji an damƙi maƙoshinta saboda zafin da taji kawai saita fashe mashi da kuka saboda ta rasa yarda zata yi ta sanar mashi........'    Zuba mata ido yayi yana kallonta tana ta faman shan kuka, tuni yaji tsananin tausayinta ya kamashi,musamman daya dinga ganin fuskarta kamar su jahad ne ke kuka,     Cikin sauri ya dakatar da ita da cewa"its okey, kiyi hakuri banyi hakan dan na 6ata maki rai ba, inaso kawai na gano wanda ya baki allurar ne don inyi investigation akan shi, amma tunda bakison faɗi, zaki iya tafiya,     tsagaitawa tayi da kukan tana kallon shi cikin sanyin murya tace"dan Allah  kada ka zargeni wlh bazan iya cutar da wani acikin gidan nan ba, saboda na ɗauke ku tamkar ƴan uwana na jini na.......'      murmushi Omar ya ɗanyi kafin yace"don't worry ur self nima kamar yarda kika ɗauke mu haka muka ɗauke ki, ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce insha Allah,amma aduk lokacin da kika tuna sunan wanda ya baki ita, ki hanzarta sanar mun pls......'    "Insha Allah zanyi hakan," tashi tayi tare da yi mashi sallama ta nufi hanyar fita daga falo dinsa, a hankali take tafiya hannunta dafe da saitin zuciyarta, muryar shi ce, ta sake katse ta da cewa"yana buƙatar a gyara mashi bedroom ɗinsa yakamata ki je, a firgice ta juyo tana kallon shi, ganin yarda ta razana ne yasa shi cewa"ki kwantar da hankalin ki, kada abunda ya faru jiya yasa ki dinga jin tsoranshi, nasan ko wanene ɗan uwana, am really proud of him, ki saki jikin ki in ba haka ba zai gane cewa wani abu ya faru adaren jiya,    jinjina mashi kai tayi tare da cewa"toh zanyi yarda kace," tana fadin hakan tasa kai ta fuce,    Murmushi Omar yayi saboda tunawa da babban aikin da sgr yaso yayi jiya, tabbas da yarinyar ta rasa ranta don ayadda yake jin wannan ƙarfin ba ƙaramin illatata zaiyi ba,    "godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yabani ikon zuwa adai dai wannan lokacin har na ceci rayuwarta, na kuma taimaki ɗan uwana daga aikata wannan aika aikan," ya furta yana faman sauke ajiyar zuciya, *************💋 Gaba ɗaya sun hallara a saman dining chairs suna yin breakfast dinsu, Abban su tare da junaid, sai Ayaan da jahan ga kuma su irfan khaleed da jabeer da kuma Fawan, har yanzu bai fara sanya riga a jikinshi ba sai dae gajeran wando kawai yake zurawa yayi ta yawon shi,   "Aunty azmee ina reesh take ne, banganta ba"? Junaid ya tambaya yana kallon azmee dake tsaye tana saving dinsu,     Abbansu ma yace"tun ɗazu nake so in tambaye ta nima, yau banga daughter ɗita ba ina tashiga ne?   Murmushi azmee tayi tare da cewa"tashiga sashen Omar ne,"    cike da mamaki jabeer yace"wacece kuma sehrish? ko dai wannan yarinyar dana gani tana yawo acikin gidan nan? Ya tambaya yana kallonsu,   irfan yace"nima ina taso na tambaya wlh, naga kyakkyawar yarinya tana ta yawo acikin gidan nan gwanin burgewa,"   da buɗar bakin fawan sai cewa yayi "Oh wai dama mutun ce? Ae ni nayi tunanin ko idona ne ke ganemun ita shiyasa ban ta6a tambaya ba," dariya suka fashe da ita gaba ɗayansu banda shi fawan din da yayi mgnr, saboda shi bada wasa yayi maganarshi ba, duk a tunanin shi ko ya samu ta6uwa ne shiyasa yake ganinta,       "Sunanta Sherish tare da azmee suke aiki, amma na mayar da ita ƙanwarku ina fata zaku ji daɗin hakan, tunda dama baku da ƙanwa mace," acewar abbansu,    kallon juna su kayi atare kafin fawan ya kuma cewa"ni duk ba wannan ba, wai ina tukur mai aikin mu ne? Nayi kewar shi sosai tunda muka dawo banga gifcin shi ba acikin gidan nan,"? ya tambaya yana kallon junaid dasu twins,   murmushi suka shiga saki gaba ɗayansu batare da sunce komai ba,     Khaleed yace"wannan sullu6iyon mai aikin namu, dama nasan bazai kai labari ba halan an kore shi daga aikine"?    Junaid ne yace"kai yaya fawan yanzu kuna nufin baku gane wanene tukur ba? Wannan yarinyar fa itace fa tayi shigar maza tana mana aiki........'    Saboda tsabar ruɗu har suna haɗa baki wurin cewa"Are u serious!? ɗaga kai yayi tare da jaddada masu maganar shi yace"of course ku tambayi abba kuji,"     Kallon abban nasu sukayi suna jiran jin bayani murmushi yayi tare da cewa"itace mai aikin da kuka bari a matsayin namiji,"     cikin mamaki suke kallon shi sam sun gaza cewa komai saboda abun yafi ƙarfinsu wai tukur mai aikinsu ne ya koma mace ? dama maca ce tayi shigar namiji kenan? Murmushi fawan yayi aranshi yace "lallaikam nama har gida," kamar abbansu yaji mai yace sai ɗagowa yayi ya kalli fuskokinsu yace"ko da gigin wasa bana son wani ya ta6a mun ɗiyata,ko kallon banza wannan ban amince wani yayi mata ba,"     har suna haɗa baki wurin cewa"Insha Allah hakan ma bazata faru ba, ae ƙanwarmu ce," dariya junaid yayi ƙasa ƙasa saboda yasan halinsu sarai musamman fawan,  Sehrish~   Koda ta fito daga part ɗin omar, wuri ta samu anan upstairs ɗin ta zuƙunnna tana shan kuka ba don komai ba sai don baƙin cikin kasa furta sunan haroon da tayi, taso ta sanar ma Omar kodan ta fita zargi amma hakan yaci turo saboda maƙoshinta da taji an shaƙe mata shi, babban abunda take fargaba shine kada su fara zarginta akan abunda ba laifinta bane, yanzu kuma duk ranar da sgr ya tuna da wannan abun daya faru a tsakaninsu dole ya tuhume ta, batasan wane irin kallo zaiyi mata ba,😖   "Ashe so yayi ya kashe ni !" ta furta cikin sanyin murya, "ni bansan me nayi mashi ba, ya Allah ka kare ni daga sharrin shi, ya Allah kada ka bashi nasara akaina,"    tana cikin wannan tunanin sam bata ji takon tafiyarshi ba, fitowarshi kenan daga part dinsa ya kimtsa cikin suits farare ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba,    tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yarinyar da yake ta faman jira ta gyara mashi bedroom dinshi itace zuƙunne tana shessheƙar kuka, cike da mamaki ya ƙarasa har inda sehrish take sam bata zaci ganin shi ba, sai dae taga ƙafafunshi masu sanye da haɗaɗɗun takalma, gabanta ne taji yayi wani irin bugu duk da bata san wanene ba amma tana da tabbacin cewa shi neeee saboda ƙamshin turaren nan nashi,    ƙara ƙanƙame jikinta tayi tana faman zazzare ido a tsorace, muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"ke tashi tsaye,"    cikin sauri sehrish ta miƙe tsaye jikinta na kerma kamar wadda taga wani horror sam taƙi yarda ta kalli fuskarshi saboda ta tsorata dashi,      shiru ya ɗanyi baice komai ba tamkar mai nazarin wani abu, hannunta yabi da kallo sai faman kerma yatsun hannun suke yi,    "Are u okey"? ya tambayeta,cikin sauri tace"eh"     "Okey agyaramin bedroom ɗina," yana faɗin hakan ya kama hanya  ya wuce,   Sam takasa janye idanunta daga kallon bayanshi  har sai da ya 6ace ma ganinta, sannan ta wuce part din nashi, lokacin data shiga bedroom dinshi ba komai ta tuna ba face abunda ya faru atsakaninsu daren jiya, bin shimfiɗeɗen gadon shi tayi da kallo har yanzu zanin gadon a cukuikuye yake, saboda damben da suka sha jiya, hannu takai tare da yaye bedsheets ɗin nashi ta rungumo shi a kirjinta tana shinshina ƙamshin turarensa, ita kaɗae tasan irin yanayin da tashiga a wannan lokacin duk da firgicin da take ci amma hakan bai hanata jin wannan yanayin ba.............💋😉 *💋Boss💖Bature❤*✍️ A galabaice take hura wutar murhun wani irin uban hayaƙi yake fitowa baƙiƙƙirin duk ya cika kitchen din, idanunta sunyi jawur kamar na mai shan taba, matashiyar yarinyace da bazata wuce shekara goma sha huɗu ba aduniya, a wani matsakaicin gida na masu rufin asiri, jikinta na sanye da koɗaɗɗen zani na atampha tayi ɗaurin gaba dashi, duk ya yayyage jikinshi yayi baƙiƙƙirin saboda dauɗa, gaba ɗaya ita kanta yarinyar abun ban tausayi ce, ta bushe ta rame ta ƙanjame yadda kasan skelaton haka take, saboda kasusuwan wuyanta da suka firfito mata waje kamar zasu fito daga fatar jikinta saboda tsabar rama, saboda koɗewar da fatar jikinta tayi baza ma a iya tantace launin fatarta ba, fara ce ko baƙa 😢 sai faman goho take yi agaban murfin tana hura wutar da bakinta amma wutar taƙi kama wa, zuƙunnawa tayi gaban murhun ta zabga uban tagumi hawaye na faman kwararowa daga idanunta, cikin murya kuka ta soma cewa"Ya Allah ka kawomin karshen wahalar da nake sha acikin gidan nan........'     Muryar mammynsu ce ta katse ta da cewa"AMAL!! wai uban wa kike so yayi wankin nan ne? zaki fito kiyi shi ko saina maki dukan tsiya ne? Hankali atashe tace"mammy iccen girkin ne ɗanye baya ci, tun ɗazu nake faman wahalar hura shi amma yaƙi ruruwa,"    Uban tsoki matar ta buga tare da cewa"wannan ba damuwa ta bace ba, ki tabbatar da kin hura wutar ta kama,sannan ki fito ki wanke mana kayan mu, bayan kin gama kuma ki share gidan,"     cikin ƙunar rai ta amsa mata da "toh," Sannan taci gaba da hura wutar don ta kama,     cigaba da magana matar tayi tana cewa"Yayarki nacen gidan huta, ta manta dake gaki nan a wulaƙance kin zama tamkar baiwa a wurin mu, da ace tana sonki ae bazata barki a hannun mu ba,"    Shiru Amal tayi hawaye na zuba daga idonta, har yau tagaza yarda cewa yayarta zata iya yi mata hakan, saboda me zata tafi tabarta hannun waɗannan mugayen? Ta tambayi kanta,    muryar mammyn tasu ce ta sake katse ta da cewa"hmmm dama tsiyar talaka kenan anyi mata hanyar arziƙi amma ta manta da mutane, baƙin halinku iri ɗaya dana uwarku, ae duk laifin laila ne ko uban waya faɗa mata ana yiwa ƴa'ƴan kishiya abun arziƙi," tana zaune saman gujera ƴar tsugunno sai faman sambatu takeyi kamar zautacciya, wata tsamurarriyar mata ce fara siririya ta fara tsufa don gashin kanta harya fara hurhura, jikinta na sanye da atampa riga da zane, ta tsoge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsire, hannunta na ruƙe da aswaki sae faman kwalkwalar haƙoranta takeyi wadanda sukayi jawur saboda tsabar cin goro, kai kana ganin ta zaka shaida cewa ba ƙaramar jarababbiya bace, irin tsaffin nan da basa gajiya da mita,    daƙer Amal tasamu wutar ta huru, sannan ta fito agalabaice, kai tsaye ta wuce inda uban kayan wankin suke dila guda,gaba ɗaya kayan sawarsu ne su duka dana uwar dana su abra da hayam, ga zannuwan gado da barguna duk sun tara mata su don ta wanke, abun babu imani acikin shi, babu irin wahalar rayuwar da yarinyar bata shaba,uƙuba iri iri suke yi mata, ko bacci bata samu, in ma tayi baccin da duka suke tashinta, ko kuma taji saukar ruwa bokiti guda ajikinta, fatar jikinta duk cizon sauro ne gashinan ruɗu ruɗu, saboda awaje take kwana, su kuma su shige ɗaki sai ita kaɗai ga tsora da Allah yayi mata, kullum cikin zullumin mai zai faru da ita take yi, duk yarda taso su haɗu da yayarta abun yaci tura, a halin da ake ciki ita kanta Amani batasan cewa yarinyar na raye ba, tun wani zuwa da tayi suka sanar da ita cewa yarinyar ta 6ace an neme ta an rasa, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, a lokacin tasha kuka sosai wurin neman yarinyar amma babu ita babu alamarta, tun tana sanyawa a nemo mata ita har tagaji ta daina saboda kullum babu labarin anga yarinyar shiyasa ta fidda rai da ita, ashe lokacin 6oye yarinyar sukayi a gidan makwabtansu acikin wani ɗaki aka rufe ta kamar akuya, duk in amani zataso maiduguri sai su kaita can gidan ajiya har tazo ta tafi bazata sani ba, hakan yasa basu ta6a haɗuwa da ita ba tun auranta da Abbas na wata takwas a lokacin abun ya faru, taso ta ɗauki yarinyar ta zauna a wurinta amma saboda baƙin hali irin nasu sun hanata ganin ƴar uwarta....😭     "Maza ki hanzarta ki wanke mana kayan," muryar mammynce ta katse ta,     Hannu tasa ta ɗauki bokitin dake ajiye awurin kayan, sannan ta wuce izuwa inda fanfonsu yake,ruwa ta tarbo acikin shi sannn ta ɗauke shi tadawo ta ajiye, ledar klin ta dauka tare da fasawa ta zazzaga aciki sannan tashiga tsoma kayan aciki tana wankewa idonta na zubar da kwalla,      suna cikin wannan zaman suka ji ƙarar dirar mota a ƙofar gidan, washe baki mammy tashiga yi tana cewa"ƴar albarka ta iso, nasan tadawo mana da abun arziƙi, ni dae naji daɗi ƴa'ƴana badae farin jini ba........' bata ƙarasa maganar ba Hayaam tashigo cikin gidan  ba ƙaramin wanka ta ɗauka ba, jikinta na sanye da swiss lace ash colour, doguwar riga akayi mata dashi, ta matse ta tsam tamkar in tayi motsi rigar zata yage saboda yarda tayi tighting ɗinta, ta  kashe ɗaurin kallabi nan, mayafin kuma ta aza shi a kafaɗa,    fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa wurin mammyn tasu, tashi tayi ta rungumeta tana cewa"ƴar albarka sai yau zan saki a idona"?   Murmushi hayamm tasaki tare da cewa"Ammi yau ɗin ma sa'a kika ci, ki gode ma Allah da kika ganni yau, domin kuwa gobe zan wuce abuja nazo ne nayi maki bankwana saboda zan koma can da zama ina fata Aunty laila ta sanar dake game da komawa ta can? Ta tambaya tana kallonta,    gaba ɗaya Amal ta kasa kunne tana sauraronsu,    Washe baki tayi tare da cewa"ta sanar dani mana, ae ba ƙaramin daɗi naji ba kwara ki tattara ki tafican kema ki shafo mana arziƙi,"     Fari da ido hayaam tayi tare da cewa"baki da damuwa in dae nice mommy, arziƙi mun gama yin shi, muddin burina ya cika tuni zan canza maku tamfatsetsen gida na kece raini, na siya maku manyan motoci na alfarma sannan na biya maki aikin hajji, mommy kuɗi fa har sai kin gaji dasu wlh," ta faɗi tana faman sakin murmushi,    Cike da farin ciki mammy tace"Allah?   "wlh kuwa mommy," hayamm ta bata amsa,     ganin amal na kallonsu yasa mammyn kwatsa mata tsawa tace"zaki mayar da hankalin ki kan kayan da kike wankewa ko saina zo nan na karya maki wuya, magulmaciyar banza ƴar sa ido," jiki na rawa amal ta mayar da hankalinta kan kayan da take wanke wa,      ruƙo hannun hayamm mammyn tayi sannan tajata suka shige cikin ɗakinsu, don kar taji me zasu ce,     a hankali take wanke kayan  tunani iri iri na zuwa mata aranta, tana yawan jin suna ambaton abuja abuja, kodai can aunty amani take zaune ne? Ta tambayi kanta, jinjina kai tayi tare da cewa"ina da tabbacin cewa auntyna tana zaune acan itama, dole na nemi mafita bazan zauna su kashe ni ba, zan gudu ne batare da saninsu ba," ta fadi tare da tsame rigar da ta sanya acikin ruwan wankin..........'😳   **************** A 6angaren su hossana kuwa saboda damuwar da suka shiga na jin cewa ya Omar ɗinsu na da aure gaba ɗayansu ba wanda yayi breakfast saboda damuwa, su kansu sun rasa gane dalilin dayasa suke jin kishin matar shi data kirasu a waya,  abincin da jahad ta shirya masu har yayi sanyi saboda tun safe yake ajiye saman dining table babu wanda ya ta6a shi, gashi har ƙarfe ɗaya yanzu yayi na rana,      A tare suke kabbara sallah bayan sun kammala suka zauna suna addu'o'i, shiru jahad tayi tana sauraron addu'ar hossana da take yi,    "Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba na cewa ya Omar yana da mata, in ma dagaske ne ya Allah kasa ya sake ta su rabu, zuciya ta tafarfasa takeyi mun bazan iya jurewa ba........'     katse ta Jahad tayi da cewa"hossana kina a hayyacinki kuwa? ya sake ta fa kika ce? Idan yana son matar shi fa?    harara hossana ta jefa mata tare da cewa"waya faɗa maki yana sonta? Auren dole ne akayi masu, da ace yana sonta ae da bai 6oye mana cewa yana da mata ba har da ciki...'        Itama jahad ɗin harar ta mayar mata tare da cewa"baki da hankali wlh,dagaske ɗin ke zararriya ce, yaya omar yana son matarshi, ke bakiji muryarta ba yarda take magana daga gani tana cikin kwanciyar hankali, kuma tana samun soyayyar mijinta tunda gashi har tana da ciki zata haifa mashi baby..........' jahad bata ƙarasa maganar ba, hossana takai ma wuyan hijabinta cakuma tana cewa"Ni ce zararriya? ɗaga kai jahad tayi alamar e,     Bugu hossana tashiga kai mata, ganin bazata iya jurewa ba yasa suka kacame da faɗa, abu kamar wasa sai da dukkansu suka sha kuka, dama ransu a6ace yake, duk don saboda matar Omar,    (Sehrish tayi tsiya) tsaf ta kammala gyara mashi bedroom dinshi da toilet dinshi da falonsa duka ko'ina a kimtse tabar mashi shi, fitowa tayi ta sauko down stairs a lokacin duk sun kammala yin breakfast ɗin nasu babu kowa a falon, kai tsaye ta wuce bedroom ɗin Haroon gabanta na faduwa rass rass, ƙopar a rufe take don haka saita sanya hannu tare da yin knocking ɗinta, daga cikin ɗakin tajiyo muryarshi yana cewa"Wanene"?    "Ni ce," ta bashi amsa cike da ƙarfin guiwa,    buɗe mata ƙopar yayi fuskar nan ɗauke da murmushi, jikinshi na sanye da singlet fara tare da shorts baƙi,    "shigo daga ciki mana," ya faɗi yana nuna mata hanya, kallon shi kawai takeyi , sa kai tayi ta shiga ciki  daga tsaye ta tsaya tana kallon shi, rufe ƙopar yayi sannan ya juyo ya kalle ta yace "wlh har naji sanyi araina dana ganki cikin ƙoshin lafiya,ae nayi tunanin  e warhaka kina asibitin kwance magashiyyan rai hannun Allah.....' bai ƙarasa maganar tashi ba tace"me nayi maka? Meyasa kake son kashe ni? saboda me ka bani wannan allurar?     tafi yayi da hannunshi yana dariya, wuce ta yayi tare da samun wuri daga gefen gadonshi ya zauna yana facing ɗinta yace"Ko da ace zan iya kashe kowa a duniyar nan, ni bazan iya kashe abunda raina ke so ba!!! nasan cewa ba zaki mutu ba, akwai wanda zaizo ya taimake ki shiyasa nayi hakan ! kinfiye taurin kai shiyasa na gwada maki kaɗan daga cikin shaiɗancina, kin manta maganar da kika faɗa mun nacewa NAMIJI kike kallo? Shiyasa na haɗaki da namijin...........' ƙarasa maganar yayi yana faman tiƙar dariya, sakin baki sehrish tayi tana kallon shi. Da ƙyar ya tsagaita da maganar tashi yana kashe mata ido yace"Yarinya taji maza,baki ban labari ba ya kuka ƙare jiya?     shiru tayi tana kallon shi kawai saboda abun yafi ƙarfinta haroon ba ƙaramin shaiɗani bane,      ta6e bakin shi yayi yana kallonta sannan yaci gaba da cewa"wannan allurar da na baki, miyagu irina suke amfani da ita, aduk lokacin da mutun yayiwa kanshi allurar nan, imanin shi gaba ɗaya take cire wa, zai iya yi ma mata sama da goma sha biyar raping a lokaci guda batare da ya gaji ba tamkar engine zai dinga aiki, sannan koda ace mahaifiyarshi ce akusa dashi itama hakan ce zata faru da ita ba zai iya tantance fari ba balle baƙi, saboda gaba ɗaya take tayarwa mutun da wata irin jarababbiyar shawa'a da kuma ƙarfi na ban mamaki, kuma muddin a lokacin bai samu ya kawar da sha'awarnan  ba, to fa zuciyarshi zata iya bugawa nan take,.......'    tunda ya soma bayani sehrish ke kallon shi cikin tsananin tashin hankali har sai da yakai ƙarshe sannan cikin sanyin murya tace"me yasa ka fita daban acikinsu ne? Saboda me kake son cutar da shi ne? idan ni nayi maka laifi saboda me laifin zai shafe shi?       shu'umin murmushi haroon ya saki  kafin yace"tun ina yaro nake da son yin mugunta, ni ko dariya ban cika yi ba sai in anyi abun mugunta sannan take zuwa mun, burina kawai naga kowa cikin masifa da tashin hankali,natsani inga ana ta rayuwar farin ciki mai ɗaurewa, wannan ne dalilin dayasa nakeson in kawo canji acikin gidan nan,". Hankali kwance haroon ke kora mata bayani batare da nuna alamun wasa ba,     tuni taji idonta sun ciko da kwalla cike da takaici tace "tausayinka nake ji ! kana bani tausayi saboda kai abun tausayi ne, ban ta6a tunanin cewa a jinin abba za'a samu mai irin waɗannan mugayen ɗabi'un da halayen irin naka ba, saboda me yasa kai ba zaka yi koyi da sauran ba? ka zama mutumin kirki tamkar sauran"?     tasowa haroon yayi daga zaunen da yake ya ƙarasa dab da inda take  a wannan karan fuskarshi babu wasa acikinta yace"kina so in shiryu ne? In zama mutumin kirki?    ɗaga mashi kai tayi alamar eh,   Murmushi haroon yayi kafin yace"kece mutun ta biyu, da kikayi mun fatan shiriya arayuwata, sai dae kash hakan bazai ta6a yiyuwa ba sehrish ni ba cikakken mutun bane kamar yarda kike tunanin....................' a wani irin firgice sehrish ta ɗago tana kallon cikin idanunshi fuskarta cike da tsoro tace"kana nufin kai ba mutun bane"?     dariya ya ɗanyi kafin yace"kona faɗa maki ba zaki yarda ba, amma bari na sanar dake wani abu da baki sani ba, ni da kaina na turo marshal Omar ɗakin sgr domin ya taimake ki ! kuma ni ne nan na hana ki furta sunana agaban Omar, na shaƙe maki maƙoshinki na hana sautin fita daga bakin ki, shin bakiyi mamakin taya akai duk nasan da wannan ba !!!!!!!!!!!    Zazzare ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa, tuni zufa ta soma tsattsafo mata, ja da baya da baya tadinga yi tana kallon shi.....   dariya sosai haroon yayi kafin yace"Shiyasa nace ki nemi tsari daga sharrina wlh ni shaiɗanin aljani ne ba mutun ba..........'   tunkan ya ƙarasa maganar tashi  Da gudun gaske sehrish ta  juya tare da buɗe ƙopar ɗakin nashi ta fuce ji kake garam !!!! Ƙopar ta datse,    Fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikin shi, daga bisani kuma ya ɗan tsagaita da dariya tare da cewa "Yarinyar tana da kyau, shiyasa na tsoratar da ita saboda inga kyawawan idanuwan nan nata masu kashe mun zuciya," ya furta tare da kai hannun shi saitin zuciyarshi yana faman sakin murmushi...............😳 tashin hankali anya kuwa haroon 👹😈      Ko kallon gabanta ba tayi saboda gudun da take yi gaba ɗaya ta gama firgita da haroon, bata yi wani aune ba ta faɗama junaid wanda ya nufo part din nasu, aikuwa gaba ɗaya suka faɗa ƙasa a manne da juna, atare zuciyoyinsu ke bugawa, musamman sehrish yana jin yarda zuciyarta ke faman bugawa da ƙarfi da ƙarfi, sun jima a haka kusan 8 mins sannan junaid ya ambaci sunanta "Sehrish,"     lamo tayi a jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya sai da ta samu natsuwa sosai sannan ta ɗago daga jikinshi,tayi gefe guda zaune dirshan tana kallon shi, tasowa yayi daga kwancen da yake yana faman sakar mata murmushi, tun safe yakeson ganin ta amma basu haɗu ba sai yanzu, shima zama yayi suna fuskantar juna da ita, wankan jeans da t shirt red colour ne ajikinshi, sai faman ƙamshi yake yi,       "Me ya faru ne naga kina ta tiƙar gudu kodai motsa jiki kike yi ne? ae muna da wurin gym acikin gidan nan,'    Ya faɗi yana kallonta, tayi mashi zuru da ido,    Ganin bata da niyar yin magana yasa shi cewa "Labari mai daɗi "! cike da zumuɗi tace "dagaske ? Wani irin labari ne wannan,  "Mafarki nayi jiya,"  "Me ya faru acikin mafarkin"? ta tambaye shi cike da son ji,     gyara murya yayi tare da cewa" mafarki nayi da wani narkeken zaki acikin wani ƙurmin daji ya biyo ki da gudun gaske, kamar zaki tashi sama haka kika dinga gudu kina ihu, kinsan waye ya cece ki a wannan lokacin"? Ya jefa mata tambaya, hankali tashe tace "A'a," ƴar hararar ta yayi tare da cewa"Ni ne nan, nazo da suffar jemage na ɗauke ki da fika fiki na mukayi sama can cikin gajimare...........' ganin yarda sehrish ta fashe da dariya yasa shi dakatawa da labarin yana kallonta, nuna shi tayi ta yatsa tana cewa"junaid kaji tsoran Allah, jemage fa kace? taya jemage zai iya ɗaukar mutun ? sannu malam fesal ka feso mun ƙarya,   gaba ɗaya suka sanya dariya, ba ƙaramin nishaɗi junaid ya sanyata ba duk da fargabar da take ciki, sun jima a zaune ƙasa suna fira, kafin daga bisa ni suka tashi, shi ya wuce mosque ita kuma  ta wuce bedroom ɗinta saboda tayi sallar itama,``The father Of Soldiers```   Story &  Written         By        Hafsat Bature ********** zaune take agaban mirror ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar material blue colour mai kyan gaske, rigar tabi shape ɗin jikinta daga can ƙasa yayi ƴar baza tamkar mermaid haka shape ɗin ya bada,hoda ta ɗauka tana shafa ma fuskarta, bayan tagama ta ɗauki jan baki red colour ta murza, ba ƙaramin kyau tayi ba, set na brushes ɗinta ta ɗauko ta gyara eye brows ɗinta,bayan ta kammala gyara gashin giran, ta ɗauki ribbom ɗinta data ajiye saman mirror ɗin, tattara sumar kanta tayi tana kiciniyar ɗaure gashin amma sam tagaza saboda yawan da yayi,ita kanta tayi mamamkin yarda gashinta yake toho,ba ƙaramin tsayi yayi ba ga yawan gaske dami guda dashi,bakomai ya jawo hakan ba face mayukan da take amfani dasu na gyaran gashi sun amshi kanta sosai,    Sakin gashin tayi ya tarwatse a bayanta,saboda gajiyar da tayi da ruƙon shi,hannu takai cikin jerin perfumes dinta ta dauki kwalbar turaren flower bomb wanda junaid ya ɗaukar mata a lokacin da suka je siyayya saboda shima yana da irin shi, shiyasa ya haɗa mata dashi don suyi anko, feshe jikinta tayi da turaren ko'ina ya ji, nan take daddaɗan ƙamshinsa ya gaure ko'ina na ɗakin gaba ɗaya,mayar da kawalbar turaren tayi bayan ta kammala fesa wa, sannan ta zuba ma madubin ido tana kallon fuskarta,fuskar sgr ta dinga gani acikin mirror ɗin,nan take ta tuna lokacin da ta watsa a guje zata bar ɗakin ya biyota da gudun gaske tare da ruƙota a jikinshi,tafin hannunta tasa tare da rufe fuskarta tana faman sakin murmushi,sake tunawa tayi da lokacin da ya yage rigar jikinta kai tsaye ya afka mata,nan take taji wani irin sanyi da kasala sun rufar mata,gaba ɗaya fa sehrish ta shiga yanayi cike da shauƙi take tariyo duk wani abu da ya faru da ita a daren jiyan ta shagala sosai, taji knocking daga waje, muryarta cike da kasala tace"Wanene"?  .muryar Azmee tajiyo tana cewa"Auntynki ce," jin hakan yasa sehrish tashi tare da ƙarasawa ta buɗe mata ƙopar,tana a tsaye jikinta sanye da jallabiya ta mata maroon colour, ta yafa mayafi akanta ba ƙaramin kyau tayi ba,   sakin baki tayi tana kallon Sehrish kafin tace"Masha Allah, irin wannan kyau haka? sai kace sabuwar amarya,kinyi kyau sosai,"murmushi kawai sehrish ke saki,    matsa mata hanya tayi tare da cewa"Aunty azmee ki shigo daga ciki mana,"    "A'a basai nashigo ba, dama nazo naji ya kuka ƙare da Omar?ina fata kin sanar dashi gaskiya?     shiru sehrish tayi tana tunanin amsar da zata bata,ranta ne ya bata cewa kawai ta amsa mata da eh,saboda tana da tabbacin cewa muddin ta faɗa mata cewa takasa furta sunan haroon agaban Omar to tabbas azmeen zata iya cewa zata sanar dashi ita da kanta,idan kuma hakan ya faru to tabbas itama azmeen zata fuskanci irin abunda sehrish ta fuskanta wurin Furta sunan Haroon,kuma bazata so hakan ya faru ba don ba ƙaramin raɗaɗi taji ba,.    Sam ta tafi duniyar tunani taji muryar azmee ta katsa ta da cewa"Lafiya kuwa naji kinyi shiru baki ban amsa ba"?.     cikin sauri sehrish tace"aunty azmee na sanar dashi gaskiya kuma yace zaiyi bincike akan haroon ɗin,"    "Kin tabbata"? ɗaga kai sehrish tari alamar eh,   Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"kayan sunyi maki kyau sosai Allah," murmushi sehrish tayi tana sunnar dakai,    Azmee ta kuma cewa"Munyi magana da junaid akan kayan nan naki da aka kai ɗinki,yace mun tailor din ya kammala ɗinki shi zaije ya amso maki kayan," cike da farin ciki sehrish tace"ngde sosoe aunty azmee na,"     Murmushi azmee tayi tare da kai hannu taja kumatunta tace"bani zaki godemawa ba, ko kin manta waɗanda suka bada kuɗi akayi maki siyayyar ne"?    girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"a'a ban manta ba,amma ina jin kunyar zuwa inyi masu godiya,"    "Gaskiya yakamata kije kam,zasu ji daɗi sosai su son cewa kinji daɗin abunda sukayi maki,ki same su kiyi masu godiya,"    "Insha Allah zanje," ta amsa mata, sakin kumatun nata tayi sannan ta juya zata futa, har ta ruƙe ƙopar zata buɗe ta jinkirta kamar mai tunanin wani abu, sake juyowa tayi tare da kallon Sehrish dake a tsaye tace"wai nikam akwai abunda nake taso in tambayeki tuntuni sai in ta mantawa,"    cike da kulawa sehrish take kallonta don jin me zata ce,   Cigaba da cewa tayi "a kwanakin baya kinyimun magana akan cewa kinason zuwa garinku domin ki duba ƴan uwanki da basa lafiya ko"? ta tambaya tana kallonta,    A ruɗe sehrish tace"ƴan uwana kuma aunty azmee? Su wa kenan ? ni ba muyi wannan maganar ba kodai kin manta ne"?    hararar wasa azmee tayi mata tare da cewa"banason wasa fa, kinsan me nake magana akai mana, nan kwanaki kikazomin kina kuka kina cewa in taimaka maki kije kiga ƴan uwanki shine kuma yanzu zaki ce mun har kin manta?    Hankali tashe sehrish tace"aunty azmee ni bani da wasu ƴan uwa, bani da kowa wlh, bansan akan me kike magana ba,"     mamaki ne ya kama azmee ganin yarda sehrish ta haƙiƙance akan cewa bata da wasu ƴan uwa kuma fuskarta babu alamun zolaya,bayan ita da kanta ta sanar da ita game dasu,    ɗaure mata fuska tayi tare da cewa"banason rainin hankali sehrish!kina nufin dama baki da wasu ƴan uwa!ƙarya ce kawai kika shirga mun?tun farkon zuwanki gidan nan aiki, kika sanar dani cewa ƴan uwanki ne basu da lafiya shiyasa kikazo neman kuɗin da za'ayi masu aiki, har na ranta maki kuɗi dubu ɗari tara domin ayi masu aiki a amatsayin kuɗin aikin ki na shekara ɗaya da rabi, shima wannan duk plan ne kika tsara mun !!!!?  Rai a6ace azmee ke magana hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, tuni idonta suka soma zubar da hawaye saboda tagaza gane kan me azmeen ke magana akai,.      "Aunty azmee wlh ni duk bansan anyi wannan ba! Bamu ta6a magana dake akan cewa ina da wasu ƴan uwa ba,kuma ni ban amshi wasu kuɗi ba saboda ayi ma wasu aiki ba.....'    tunkan ta ƙarasa maganar azmee ta kwatsa mata tsawa tare da cewa"Ya isa haka Sehrish!!ashe dama ke maƙaryaciya ce!! kin cuce ni kinyi mun karyar cewa kina da ƴan uwa,ashe duk tsara ni kikayi saboda ki samu kuɗi,danasan haka kike da tunfarko ban yarda dake ba, wlh sehrish kinban mamaki kuma na gama yarda dake.......' tana kai ƙarshen maganarta, a fusace ta juya zata bar ɗakin cikin sauri sehrish ta ruƙo jallabiyar jikinta,muryarta na rawa cikin kuka tashiga cewa"wlh aunty azmee bansan komai game da abunda kike faɗa ba,na rantse maki da Allah wlh bani da wasu ƴan uwa aduniyar......' Karanta>>> Taswirar Ƙaddara Complete Novel Document   girgiza kai azmee tashi ga yi tana cewa"wlh kin ban mamaki sehrish,bansan haka kike ba ae da tun farko ban bari kin fara aiki agidan nan ba!!kin cuce ni kin rushe duk wata yarda da nayi maki,sai faman rantse rantse kikeyi mun ko tsoran Allah bakiji," rai a6ace azmee tayi maganar tare da fusge rigarta daga riƙon da sehrish tayi mata, cikin sauri tasa kai ta fuce daga ɗakin,   A wani irin yanayi sehrish ta zube saman guiwowinta tana faman sharara kuka,mutun ɗaya da ta yarda da ita aduniyar nan ayau ta juya mata baya akan abunda batasan dashi ba,har ga Allah ita gaskiyarta take faɗi amma azmee taƙi fahimtarta,tuni zazza6i ya fara hawa jikinta,sam tagaza tashi daga kneel down din da tayi 😭 Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!       Tun da azmee ta fuce daga ɗakin sehrish, kai tsaye ta wuce nata bedroom ɗin, shiga ciki tayi tana faman safa da marwa,ranta ba ƙaramin sosuwa yayi ba,gaba ɗaya taji sehrish tafara fitar mata arai,saboda ƙaryar da ta shirga mata,cikin ƙunar rai take cewa"kin cuce ni sehrish,banta6a tunanin zakiyi mun haka ba,natsani makaryaci arayuwata, me yasa tunfarko bata fito fili ta faɗamun cewa kuɗi takeso ba,don me za tayi mun ƙarya?    tuni idon azmee sun cicciko da kwalla saboda ƙululun baƙin cikin daya tsaya mata arai,daƙyar ta iya samun wuri ta zauna daga gefen gadonta tana cigaba da tunani acikin ranta,   "ɗan adam kenan!yanzu duk yardkyautatama yarinyar can sai da ta butulce mun,saboda farin cikinta nakeyin wasu abubuwan don na faranta mata,amma hakan bai hana tayi mun ƙarya ba!!idan har dagaske ne sehrish ba ta da wasu ƴan uwa ƙarya  ne tayimun,TO WAYE TASA NA TURA MA KUƊIN!!!!!!? miƙewa azmee tayi lokaci guda gabanta yashiga faɗuwa tuni taji zufa tasoma tsattsafo mata,hankali tashe tace"nashiga uku!! tabbas na tafka kuskuren yarda da yarinyar can!! meyasa tunfarko najata ajikina?kada fa ace da wata manufa tazo cikin gidan nan!!!   abubuwa iri iri suka dinga zuwa mata acikin ranta game da SEHRISH,😥 Lamarin dae ba daɗin ji 💋BOSS BATURE💋 A 6angaren su hossana kuwa tun bayan da suka yi faɗan nan atsakaninsu,su kayi fushi da junansu,saman gado hossana ta haye tana baccin wahala bayan ta gama shan kukan nata,Jahad kuwa bayan sun gama faɗan toilet tashiga tayi wankanta,bayan ta fito ta shirya cikin riga fara off shoulder tare da dogon wando baƙi,ba ƙaramin kyau tayi ba,musamman gyaran gashin kanta wanda akayi masu a wurin saloon ya ƙara ƙawata ta sosai,   komawa tayi ta zauna daga gefen gadon kusa da hossana, bin ta da kallo tayi sai faman sharar bacci takeyi tana jan minshari,haryanzu kayan baccin nan ne ajikinta tun na daren jiya,     Hannu tasa tare da bubbuga bayanta a hankali tana cewa"hossana ki tashi!ko baki jin yunwa ne?     tsoki taja tare da juya mata ƙeya don karta takura mata, sake bugun bayanta jahad tayi tace"wai ba zaki tashi bane!?     buge hannunta hossana tayi tare da cewa"ki rabu dani, babu ruwanki dani,idan banyi wankan ba jikinki ne ko nawa?ko kin ta6a ganin zararre mara hankali yayi wanka ne? ni mahaukaciya ce kibarni inyi rayuwata.......'cikin kuka hossana ta ƙarasa maganar,da alama abun ya ta6a mata zuciya dama ta tsani akirata da zararriya,   Cike da lallashi jahad tace"am really sorry hossana nasan ban kyauta ba,raina ne ya 6aci shiyasa har na gaya maki hakan,bazan ƙara ba insha Allah,"     tayi maganar tare da ruko hannun hossana donta tashi,fisge hannunta tayi daga cikin nata tace"pls jahad leave me alone,zuciyata ba ta mun daɗi,yaya Omar kawai nake jira yazo,"    Murmushi jahad tayi tare da janyo gashin kan hossana tana wasa dashi a hannunta tace"faɗa mun gsky hossana kodae son yaya omar kike ne"?     juyowa hossana tayi tare da kallonta fuskarnan ɗauke da murmushi tace"eh ina son yaya omar sosai ke fa"?     jiki asanyaye jahad tace"Wani kalar so kike nufi? Na soyayya da aure? ta tambaya tana kallonta,   hossana tace"shi nake nufi,jahad inason ya omar sosai,"   shiru jahad tayi gabanta na faɗuwa tuni yanayin fuskarta ya canza izuwa matsananciyar damuwa,ganin hakan yasa hossana tashi zaune tana kallonta tace"jahad naga kamar fuskarki ta canza meya faru ne"?    cikin sauri ta basar tare da ƙaƙaro murmushi tace"bakomai hossana,ni zan wuce kitchen na shirya mana lunch," tana faɗin hakan ta miƙe da hanzari tabar bedroom ɗin nasu,saukowa daga saman gadon hossana tayi tare da wuce wa cikin toilet don tayi bath,    sam jahad tagaza jurewa tana fitowa daga bedroom ɗin ta wuce cikin falon tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna jiki amace,   "dagaske ne hossana ya Omar take so?amma hossana ba ta da cikakken hankali bana tunanin tasan menene *SO* ya Allah kasa hakane saboda bazan iya jurewa ba......' ta furta tare da kai hannunta saman goshinta,bakomai bane ya faɗo mata aranta ba face farkon haɗuwarsu dashi a asibiti,lokacin ba ƙaramin tafiya yayi da zuciyarta ba saboda yarda yake acting dinsa,kyawawan ɗabi'unsa da halayansa sune suka sa jahad faɗawa tarkon shi, ita kanta bata tashi tabbatar da hakan ba sai ranar daya sanya handkerchief dinsa yana goge mata hawayenta..........."    tayi nisa cikin tunanin nata  muryar hossana ta katse ta da cewa"jahad nayi tunanin zanzo na sameki a kitchen ne ashe kina nan zaune," firgit jahad tayi tana kallonta sai da ta dai²ta natsuwarta sannan tace"har kinyi wankan kenan," ta faɗi tana kallon hossana dake nufota jikinta na sanye da gown black colour, ta saki curly hairs ɗinta ya barbazo mata abayanta,     Amsa mata tayi da cewa"Eh baki ga har na canza kaya ba," ta faɗi tare da jujjuya mata donta gani,   Murmushi jahad tayi tare da cewa"kinyi kyau sosai," ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye tace"kizo muje kitchen ɗin atare saiki tayani aiki, muyi sauri mu kammala,"   Amsa mata tayi da toh, sannan suka wuce atare kitchen ɗin atare,   *************** Zaune yake acikin motarsu Ƙirar mercedes S450,ash colour,jikin shi na sanye da kakin sojoji,sai faman duba wrist watch ɗin dake hannun shi yake lokaci zuwa lokaci,gajiyar da yayi da jira ne yasa shi ɗauko wayarshi daga cikin trouser pocket dinsa ya buga ma Jahan kira nan take kiran ya shiga bada jimawa ba Ya ɗaga kiran, tsoki ayaan yaja tare da cewa"Wai kuɗin sunƙi fidduwa ne? Nifa nagaji da jira wlh," fuskarshi a yamutse yayi maganar,.     on the other hand jahan yace"Am sorry yanzu haka ma na fitowa daga bankin gani nan zuwa,"     katse kiran ayaan yayi tare da mayar da wayar inda ya ɗaukota ya ajiye,   Cikin ƴan mintuna saiga Jahan ya fito daga cikin bankin hannunshi ruƙe da jaka,   Yana ƙarasawa gaban motar ya buɗe back seat dinta tare da yin wurgi da jakar ciki, sannan ya rufe ya kuma buɗe front seat ɗin ya shiga ya zauna a gefen Ayaan dake zaune a driver seat,   "Yau dae zamu jefar da kwallon mangwaro mu huta da kuda," acewar Jahan,murmushi ayaan ya saki yana kallon shi yace"baka ji daɗin da nakeji ba wlh,saboda a ƙagare nake da mu bashi kuɗin nan mu huta da shegen nacin nan nashi,ya takurama rayuwarmu gaba ɗaya,Haroon bai da imani jahan," fuskarshi a yamutse yayi maganar.  Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!          "har yau in na tuna abunda yayi mana zuciyata tafarfasa takeyi mun saboda 6acin rai,haroon ya wulaƙanta arayuwarmu,Allah bazai ta6a barin shi ba, Insha Allah ƙarshen shi bazaiyi kyau ba," acewar jahan    Jinjina kai Ayaan yayi kafin yace"amma Jahan kana tunanin in muka bashi kuɗin nan zai goge video ɗin duka?am just doubting about it,don na lura ba ƙaramin shaiɗani bane,    jahan yace "ae ba zamu bashi kuɗin ba har sai mun tabbatar daya goge videon agabanmu mun gani,"     "Duk da haka nidae ina fargaba wlh," cike da damuwa ayaaan yayi maganar,   Sun jima suna magana kafin daga bisani Ayaan ya tashi motar suka miƙi hanyar gida,babu wanda ke ma wani magana acikin motar saboda duk sun tafi duniyar tunani, gaba ɗaya zulluminsu akan haroon,   Koda suka ƙarasa cikin gidan basu shiga da kuɗin ba,acikin motar suka barsu cikin jakar saboda tsaro, sun ajiyeta ne da nufin in dare yayi suzo su ɗauketa su kai mashi,    Bayan sun fito daga motar kaitsaye suka shiga cikin gidan tare da wucewa bedroom ɗinsu don rage gajiyar da suka kwaso, Sehrish Tasha kuka kamar kamar me,har sai da zazza6i da ciwon kai mai tsanani suka rufar mata sannan ta lalla6a ta haye saman gadonta ta kwanta,ta jima tana roƙon Allah akan yasa mafarki ne ba gaske ba,abunda ya faru tsakaninta da Aunty azmeenta,gaba ɗaya jikinta baya mata daɗi saboda dama can akwai fargar haroon dake damunta ga kuma wani ciwon kan ya taso mata na Azmee,duk ita kaɗae😢   ta jima tana juyi asaman gadon amma bacci yaƙi ɗaukarta sai ma ciwon nata dake ƙara gaba,fuskarta harta fara kumbura saboda kukan da tasha,dakyar ta lalla6a ta tashi jikinta na kerma ta wuce toilet jin an fara kiran sallar la'asar,bayan wasu ƴan mintina tafito daga ciki tana faman ƙanƙame jikinta saboda sanyin daya rufar mata gashi ta ta6a ruwa,    wurin wardrobe ɗinta ta wuce tare da buɗeta, ta zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta ta zurata ajikinta sannan ta ɗauko carpet ta shimfiɗa,sam babu natsuwa ajikinta haka ta kabbara sallar tana karanta fatiha hawaye na wanko mata a fuskarta a haka ta kammala sallar tare da zama saman dardumar ta ɗaga hannayenta sama cikin shessheƙar kuka tashiga cewa"Ya Allah kasa aunty azmee tadawo cikin hayyacinta ta gane cewa ni ba ƙarya nake mata ba,bansan ya zanyi ba in ta juyamin baya,Ya Allah ka yayemun damuwar da nake ciki,ka kawomin sauƙi acikin rayuwata.........' sosai sehrish tashiga jera addu'o'i tana roƙon Allah akan abubuwan dake damunta, Karanta>>> Kishi Da Aljan Complete Novel Document    ta jima zaune saman dardumar tana tunanin maganganun aunty azmee,har lokacin tana kokwantan cewa anya Aunty azmee tana a cikin hayyacinta kuwa,    Har kusan ƙarfe biyar sehrish bata motsa ba tana zaune zugudun,sai da biyar da rabi ta buga,sannan ta tashi jiki a mace ta cire hijabin tare da naɗe carpet ɗin duka ta haɗa ta jefa asaman gadonta,cikin toilet tashiga ta wanko fuskarta sannan ta fito ta ɗauki mayafi acikin wardrobe ɗinta ta yafa shi asaman kanta, sannan ta buɗe ƙopar ɗakin ta fito,    Kitchen ta wuce saboda sanin cewa suna da aikin dinner,lokacin da ta ƙarasa kitchen ɗin tuni Azmee har tayi nisa a aikin nata,shiga ciki sehrish tayi tare da tsayawa tana kallon azmee dake tsaye agaban kitchen sink tana wanke naman da ta ɗebo acikin roba, Gabanta na faɗuwa tace"Sannu da aiki aunty azmee," tamkar bata ji taba haka ta shareta, kusan sau uku sehrish na maimaita maganar amma taƙi amsawa,    Jiki asanyaye sehrish ta ƙarasa gaban chopping board ganin ta jera vegetables ɗin da zata yayyanka,  hannu takai zata ɗauki wuƙa,muryar azmee ce ta katse ta da cewa"kada ki ta6amun komai! Zanyi aikina ni kaɗai kamar yadda nasaba yi lokacin da baki nan,don haka ki fuce kibarmun kitchen ɗin....' fuska aɗaure tayi maganar batare da ta juyo ta kalli. sehrish ba, .  cikin tashin hankali sehrish tace"meyasa kika ce haka aunty azmee?tare muka saba yin aiki amma yau ke da kanki kike korata!?     rai a6ace azmee ta ɗago tare da nuna mata hanyar fita tace"dan Allah sehrish ki fuce kiban wuri!aikine nace bana so ni zanyi kayana,bana buƙatar taimakon ki,     ganin yarda azmee ke kwatsa mata tsawa yasata fashe wa da matsanancin kuka tana cewa"aunty azmee dan Allah kada kiyimun haka, nasaba dake na ɗauke ki tamkar mahaifiyata,wlh bazan iya yi maki ƙarya ba,ni bansan akan me kike magana ba,dan Allah kada kiyi fushi dani akan abunda banda masaniya akanshi,"!   tunda tasoma magana azmee ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah,tamarasa me zatayi ma Sehrish ta huce,ƙiri ƙiri tana neman raina mata wayau,    "Sehrish in har kinason na kuma yarda dake to ki faɗamun gaskiya waye  kika bani acct number dinsa na tura kuɗin dana baki naira dubu ɗari tara da kikayi mun ƙaryar cewa ƴan uwankine basa lafiya!!?    Jinkirtawa sehrish tayi daga kukan da takeyi tana tunanin wai ma ina takai kuɗin?bama wannan ba yaushe ta amshi kuɗin?     "Ina sauraronki"! Muryar azmee ce ta katse ta daga tunanin da ta tafi,     girgiza kai tashiga yi tana cewa"aunty azmee kiyi haƙuri amma ni bansan me kike magana akai ba,"    tabbas in taci gaba da sauraron Sehrish ranta zai cigaba da 6aci ne don haka tace"ki wuce kiban wuri banasan sake jin wata magana daga bakin ki," jiki asanyaye sehrish ta juya tare da barin kitchen ɗin,    a hankali take tafiya jikinta ba kwari,   "Sehrish"! Muryar junaid ce ta katse ta,a hankali ta ɗago ta kalli gefen hagunta ta inda yake tunkarota,shigowar shi kenann cikin babban falon,    tunkan ya ƙarasa ya lura da yanyinta,tsayawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta da tayi suntum saboda kukan data sha,    Cikin sanyin murya yace"reeeesh! Meya faru ne kike kuka?    ganin cewa bata da wanda zata faɗawa mawa face junaid tunda shine abokin shawararta, don haka ta sanar dashi dukkan abunda ya faru da ita, tsakaninta da aunty azmee    Cike da mamaki junaid ke kallonta tamkar mai nazarin wani abu can dae yace"sehrish saboda me za kiyima aunty azmee ƙarya?meyasa zaki ce mata baki da wasu ƴan uwa?     gaba ɗaya sehrish tagama ruɗewa cikin tashin hankali tace"junaid wlh bani da ƴan uwa,ni bani da kowa ba ƙarya nayi mata ba,'    harara yaɗan watsa mata kafin yace"idan har dagaske baki da ƴan uwa,to su wanene kike kira a wayata? Lokacin da kike ɗaukar mun phone ɗina batare da sani na ba?kin manta last time har na nuna maki message ɗin da ƴar uwarki ta turo a wayata?sannan har kika roƙeni akan na kaiki ki gansu? A lokacin nace maki ki bari sai babban yayanmu sun koma Us ni da kaina zan kaiki ki gansu ko shi ma duk kin manta? Ya ƙarasa maganar cike da tuhuma,    wani irin jiri sehrish tadinga gani a indonta,a hankali tashiga furta "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" ganin tana ƙoƙarin zubewa yasa shi yin saurin ruƙo shoulders ɗinta yana cewa"ko baki da lafiya ne"? Ya tambaya yana kallon eyes ɗinta dake a rufe, .....daƙyar ta iya furta cewa"junaid inaso nashiga bedroom ɗina,inaso na kwanta,"    gaba ɗaya sehrish tayi confusing ɗinshi lamarin ya ɗaure mashi kai,ruƙo hannunta yayi ya taimaka mata suka nufi bedroom ɗinta,buɗe mata yayi tashiga ciki, sai da yaga ta kwanta saman gadon sannan ya rufo mata ɗakin,   Cikin sauri ya wuce kitchen wurin Azmee,da sallama yashiga kitchen ɗin a lokacin tana tsaye agaban gass tana motsa farfesun data ɗaura,jin muryarshi yasa ta juyo wa fuskarta babu fara saboda ruɗin da sehrish ta jefa ta aciki, Amsa mashi sallamar tayi sannan tace"junaid kana buƙatar wani abune"?     girgiza kai yayi alamar a'a Sannan yace"dama kan maganar sehrish ne,ta faɗamun duk abunda ya faru,bansan meke damunta ba,ni kaina tayi confusing ɗina,"     "Junaid sehrish tayimun ƙarya,ban ta6a tunanin haka daga wurinta ba,meyasa za tayimun ƙaryar cewa tana da ƴan uwa,bayan ba haka bane saboda kawai ta cimma wani buri nata shine ta shiryamun plan,"!  Karanta>>> Shakuwa Ce Complete Novel Document    "Aunty azmee bana tunanin sehrish tana cikin hayyacinta ne!saboda nima nasan da maganar ƴan uwan nata,da wayata takeyin amfani wurin kiransu tun a lokacin baya,akwai ma last message da sister ɗinta ta turo mata a wayana,nacewa suna buƙatar taimakonta har a lokacin naso na tura masu kuɗi amma lokaci guda wayarsu tadaina shiga kwata kwata,sehrish da kanta ta nemi na kaita garinsu tagansu,nace mata Sai babban yayanmu ya koma Us sannan zan kaita amma yanzu kuma ace ta manta komai? Yyi tmbyar yana kallon azmee itama kallon nashi takeyi,   Cikin mamaki tace"junaid naji kace tana amfani da wayarka wurin kiransu,kuma har message sun tura maka dan Allah idan wayar na'a kusa inason gani,'    cikin sauri junaid ya zura hannu acikin aljihun wandon jeans ɗinshi ya curo wayar,dannata yashiga yi can cikin messages ɗin shi yashiga sai ga saƙon da Jahad ta tura mata,   Ƙarasawa yayi dab da azmee ya miƙa matar wayar yana cewa"kin ganshi nan,"   Hannu tasa ta kar6i wayar tashi ta zuba ma screen ɗin wayar ido tana karanta saƙon, Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"Tabbas ƴan uwanta ne,idan bazan mantaba ta ta6a ambaton sunan JAHAD da HOSSANA amatsayin ƴan uwanta na jini,amma meyasa sehrish take ƙoƙarin mantawa dasu?ko don saboda tana cikin wannan daular ne......'   Junaid ne yayi hanzarin katse ta da cewa"i don't think so!rishi bazata ta6a mantawa da ƴan uwanta ba saboda abun duniya,na yarda da sehrish sosai kuma nayi imanin cewa rishi bazata ta6a yi maki ƙaryaba!tabbas akwai wani abu dake faruwa ne!!amma rishi bata cikin hayyacinta!!, .. azmee ta gamsu da bayanin shi amma har lokacin tana mamakin yarda akai hakan ta faru,    jinjina kai kawai tayi tace"yanzu ya zamuyi da ita junaid?inaso ni nasan awane hali ƴan uwan nata suke ciki ne,saboda inaso na haɗata dasu tun a lokacin naci burin hakan,nayi alƙawarin zan haɗata da ƴan uwanta,saboda yarda naga tana shiga damuwa akansu,    "Aunty azmee,yanzu babu halin yin wannan,in ma muka ce zamu cigaba dayi mata magana akansu to fa za'a samu matsala saboda zata iya samun ta6in hankali,amma in muka bi komai a hankali insha Allah dakanta zata dawo cikin hayyacinta wata rana,addu'armu kawai take buƙata,    Ajiyar zuciya azmee tayi maganganun junaid sun sa ta fara saukowa daga fushin da tayi da ita,    amsar wayarshi yayi daga hannunta sannan ya kuma cewa"pls aunty azmee karki ce zaki juya mata,ko kice zaki canza mata hakan zai iya haifar mata da damuwa,saboda ta saba dake sosai ta ɗauke ki tamkar mahaifiyarta,"   murmushi azmee tayi tare da cewa"shikenan junaid romeo insha Allah hakan ma bazata ta6a faruwa ba,kana da hankali sosai junaid shiyasa kake shiga ran mutane,ni nagaza fahimtar rishi,amma kai gashinan ka fahimce ta,"    murmushi shima yayi tare dasa kai ya fuce daga kitchen ɗin, ************* Agalabaice Amal ta kammala wanke uban kayan da suka tula mata,kaf sai da ta wankesu,ba ita ta kammala wankin ba sai wuraren la'asar,da zazza6i taƙarasa shi,gaba ɗaya ga66an jikinta ciwo suke yi mata,    ɗakinsu tashiga ganin babu kowa aciki saboda duk suna can ɗakin mamynsu hayaam da abra wadda bata jima da dawowa ba,tana jiyosu acikin ɗakin suna ta faman ciye ciyen kayan daɗin da abra tadawo masu dashi,babu wanda ya tuna da ita duk wannan uban aikin da tayi masu,shiga ciki tayi jikinta na kerma ta faɗa saman lumbutsetsiyar katifarsu,bargo taja ta lullu6e jikinta dashi,dakyar take numfashi,da wani irin hucin masassara numfashin ke fita,rayuwarta gwanin ban tausayi tun safe ko wanka batayi ba,saboda babu lokacin yin wanka,koda tayi niyyar yin wankan,sun riga da sun hanata amfani da sosonsu ko sabulun wankansu,wani lokacin in jikinta ya soma yi mata tsami,ruwa kawai take ɗiba tashiga ta watsa,daga bayane tayi dabarar yankar buhu tayi amfani dashi amatsayin soso, ba sabulu haka take gurje jikinta dashi,😭   Cike take da tsoran karsu shigo su same ta acikin ɗakinsu,saboda sun hana ta shiga ko'ina na gidan in ba kitchen ba,shima ɗin in zatayi masu girki ne, tana acikin wannan yanayin tajiyo murya abra tana cewa"ke!uban mi ya kawo ki cikin ɗakin mu?ba mamynmu ta hanaki shigar mana ɗaki ba!! A fadace tayi maganar,tana a tsaye bakin ƙopar ɗakin,yarda kasan photocopy ɗin aunty babba haka kamanninta suke,   Shiru Amal tayi batace komai ba zuciyarta ce kawai ke ta faman bugawa,   Rai a6ace abra tace"ko ki tashi kona zonan inyi wurgi dake ƙazama kawai,"    har lokacin Amal tagaza motsawa saboda nauyin da jikinta yayi mata,jinjina kai abra tayi tare da shiga ciki azafafe don tayi wurgi da ita,har takai hannu zata fisgi bargon da ta lullu6e dashi,jin muryar hayaam yasa ta dakata daga ƙoƙarin cire mata bargon da take yi,   Shigowa cikin ɗakin tayi tare da cewa"meya haɗaki da ita ne,naji kina ta faɗa,"?    turo baki abra tayi tare da nuna Amal ɗin da hannu tana cewa"baki ga yarda ta haye mana katifarmu ba da wannan baƙin jikin nata duk dauda,"    Sai lokacin Amal tasamu damar buɗe bakinta daƙyar murya na rawa tace"dan Allah kuyi haƙuri bani da lafiya,banjin daɗin jikina,"😭 dakatar da abra hayaam tayi tare da cewa"ki rabu da ita,wahalar tayi yawa just for to day ta huta,tunda bata da lafiya," sam ba haka taso ba,bata ji daɗi da Hayaam ta hanata hukunta amal ba,a fusace ta fuce daga ɗakin tana huci Shiga ciki hayaam tayi tare da samun wuri daga gefen katifar ta zauna,jin muryar Amal tana sambatu  na raɗaɗin ciwo yasa ta kasa kunne tana sauraronta,     "Ina jin cewa bazan rayu ba,dan Allah ku kaini wurin auntyna,inaso naganta kafin na bar duniya,"    dariya Hayaam tayi tare da cewa"aikuwa dae ba zaki ta6a ganinta ba adae nan duniyar, ae kin ɗaura aure da wahala tunda kika bari aka haifoki acikin gidan nan," tayi maganar tana ƙarashe dariyarta,   Amal kuwa fashewa tayi da kuka mai cin rai,    tsawa hayaam ta daka mata tare da cewa"yi mun shiru, kuka baya maganin komai sai ma ya ƙara jaza maki wani ciwon," shiru Amal tayi tana shassheƙar kuka ƙasa ƙasa Shigowa abra ta sake yi hannun ta ɗauke da wayar amani iphone 13 sai faman ruri take yi,miƙa mata wayar tayi tare da cewa"Sofwan ne ke kiranki,"  "ɗan wahala," ta fadi tare da kai hannu ta amshi wayar,juyawa abra tayi ta kalli Amal dake ƙumshe cikin bargo,guntun tsoki taja tare da cewa"salon ki sakarwa mutane miyan bacci asaman katifarsu,sai kin shanye shi don ubanki," ta ƙarasa maganar tare da kama hanya ta fuce daga ɗakin, Kara wayar tayi a kunnanta bayan tayi picking call ɗin,magana suka shiga yi dashi akan tafiyarta,duk wulaƙancin da tayi mashi hakan baisa ya rabu da ita ba, sai ma kiranta da yayi akan cewa gobe yanaso su tafi tare yakaita abujan, Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama, tana ƙoƙarin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa,tsoki ta ɗanja tare da cewa"wani jarababben ne kuma yake kira na"!?    Duba screen ɗin wayar tayi Sunan AMANI ne ya bayyana,ɗan juyawa tayi ta saci kallon Amal dake ƙumshe cikin bargo alamu sun nuna cewa bacci yayi awon gaba da ita,hakan ne yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta tare da yin sallama,   On the other hand amani tace"wa'alaikum salam,hayam y kk ya gida yasu mammy"?    yatsina fuska tayi tare da cewa"duk suna lafiya,"    Amani tace"labarine ya same ni daga wurin aunty laila nacewa zaki koma gidansu Abbas da zama,sam abun bai dace ba wannan abun kunyar har ina?menene alaƙarmu dasu da har zaki koma gidan surukan mu da zama?amatsayin ƙanwar matar yayansu!  Jin wannan maganar ta Amani yasa ran hayaam 6aci,miƙewa tayi daga zaunen da take saboda tsiwa tamkar zata fasa screen ɗin wayar haka tashiga cewa"Ki tsaya iya matsayinki AMANI!!babu ruwanki dani, iya sa idone kawai naki  kada kice zakiyi mun shisshigi acikin lamarina! Ni ba kamar Aunty laila bace data saba jan ki ajiki har tayi maki sanadin auren Abbas,kina magana ne da HAYAAM!!!yakama ki iya bakin ki!!!!    jin yarda hayaam ke zazzaga mata rashin mutunci yasa tayi rejecting kiran,   tsoki hayaam ta saki tare da cewa"matsoraciyar banza!!ae banso kika kashe kiran ba,so nayi na sauke maki kwandon rashin mutunci shashasha kawai," rai a6ace ta ƙarasa yin maganar tare da yin wurgi da wayar saman katifar,kama hanyar fita ɗakin tayi domin taje ta sanarwa mamaynsu yarda su kayi da Amanin,  fitarta ke da wuya, Amal ta buɗe idanunta  waɗanda suka kumbura jawur saboda raɗaɗin ciwo, ta samu bacci amma tsiwar hayaam ce tafarkar da ita, gaba ɗaya duk wayar da su kayi da amani tana ji a kunnanta,saboda taji lokacin da hayaam ta ambaci sunan Amani, Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!     A hankali ta sanya hannunta tare da yaye bargon,a galabaice ta ɗan tashi zaune, hannu takai tare da ɗaukar wayar hayaam wadda tayi wurgi da ita asaman katifar kuma cikin sa'a wayar bata kai ga shiga security ba,    jiki na kerma ta shiga wurin kiran,sai ga sunan amani ya bayyana a list ɗin farko da tayi waya dasu,cikin sauri Amal ta buɗo numbarta, zuba ma numbar ido tayi tana tunanin yarda zata ɗauki numbar,babu wurin da zatayi copying dinta,tuni hawaye sun soma zarya a fuskanta, wannan shi ake ce ma ga ƙoshi ga kwannan yunwa,   runtse idonta tayi tare da buɗe su  akan screen ɗin wayar,nan take taji cewa zata iya haddace numbar akanta,muddin taci gaba da bitarta akanta, a hankali take ƙarewa numbers ɗin kallo tana naɗarsu akanta,motsin mutun taji alamar an tunkaro ɗakin cikin sauri  Amal ta fita daga wurin numbar amanin ta danna power ɗin wayar tayi duhu sannan ta ajiyeta,da hanzari tashige cikin bargon ta lullu6e dukkan jikinta, Hayaam ce tashigo  kai tsaye ta ƙarasa inda wayar take tasanya hannu ta ɗauka tare da fucewa daga ɗakin,   ajiyar zuciya Amal tashiga saukewa,har lokacin tana cigaba da bitar numbar amani akanta, ******************* Bacci sosai sehrish tasha, har wuraren ƙarfe biyar da wani abu babu alamun zata farka kamar matatta, kusan sau huɗu azmee na leƙowa don taga kota farka saboda ta lallashe ta akan abunda ya faru amma duk in tashigo sai ta same ta tana ta faman shan bacci,  Ƙarar jiniyar motocinsu ce tasa sehrish farkawa a gigice, fuskar nan tayi jaga-jaga da ita saboda kukan da tasha,ko da ta farka zuciyarta nata faman bugawa, a kasalance ta tashi zaune saman gadon tana faman sauke ajiyar zuciya, idonta takai kan agogon bangon dake manne, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin cewa har lokacin sallar magrib yayi, gashi ba tayi la'asar ba, cikin sauri ta sauko daga saman gadon ta wuce cikin toilet donta ɗaura alwala,  Yau da wuri suka dawo, Abbansu tare da marshal Omar da kuma Sgr sai kanal Yousouf, a nan main palour ɗin suka rarrabu, Abbansu tare da kanal yousouf suka wuce bedroom ɗinsu dake a nan down stairs, Omar da Rafayet atare suka haye upstairs,  Tuni azmee ta kammala jera masu dinner ɗinsu a dining, duk anan suka hallara suka ci abincin, banda sgr da bai fito ba, bayan sun kammala ita tashiga kwashe warmers din da sauran tarkacen da sukayi amfani dashi tana kaiwa kitchen, ganin tana ta faman ɗawainiya ita kaɗae ba sehrish yasa junaid kama mata kayan suna kaiwa kitchen atare ba ƙaramin daɗin hakan taji ba,barin shi tayi a cikin  kitchen ɗin ita kuma ta wuce don ta gyara masu  dining area ɗin, kafin ta dawo har junaid ya kammala yin wanke wanken kayan da sukayi amfani dashi, tare da gyara kitchen ɗin tsaf tamkar ba'ayi amfani dashi ba,    tsayawa tayi tana kallon shi yana ƙoƙarin haɗama sehrish cornflakes acikin  kofi,   Juyowa yayi ya kalle ta tare da cewa"aunty azmee irin wannan kallo haka"?  Murmushi tayi tare da cewa"junaid kai na musamman ne,kana bani mamaki yanzu kai da kanka kayi wanke wanken nan?kuma ka gyara kitchen ɗin nan?  Murmushi yayi tare da cewa "menene aciki aunty azmee?nifa ba aikin da bazan iya yi ba,kuma aiyukan mata suna burge ni sosai, naji ma ina shawa'ar inga ina wanke wanke girki da shara,"    dariya sosai azmee tayi tana girgiza kai tace"gsky baka da dama junaid, koda yake abune mai kyau ka koya,yana da amfani hakan saboda wata rana zaka taimaki matarka ne da wasu aiyukan cikin gidan,Ko ba haka ba?" ta tambaya tana kallon shi,.     ɗaga mata kai yayi alamar eh, sannan yace"aunty azmee ki tayani da addu'a Allah ya cikamin burina,inaso nayi aure very soon insha Allah end of this year.....' kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azmee ta saki baki galala tana kallon shi,   fashewa da dariya yayi a lokacin har ya kammala haɗa ma sehrish cornflakes ɗin,    "Joking aside pls faɗamun gaskiya amma dae wasa kake mun ko"?    girgiza mata kai yayi alamar a'a sannan yace"just keep praying for me, insha Allah soon i wll get marriage," yana faɗin hakan ya kama hanyar fucewa daga kitchen ɗin hannun  shi ɗauke da Cup sai faman tiriri yake, Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!    shiru azmee tayi tana kallon bayanshi har ya 6ace mata, lamarin ya ɗaure mata kai tabbas tasan halin junaid tunda harya iya furta mata aure yakeso to kuwa fa auren zaiyi dagaske, kuma duk abunda ya nuna yanaso sai abbansu ya mara mashi baya,  "Ashe zamu sha biki," ta faɗi da dariya a fuskarta,     Knocking kopar ɗakin sehrish ya shiga yi, a lokacin har wani baccin ya soma ƙoƙarin ɗaukarta asaman sallayar,tana jin bugun ƙopar a firgice ta tashi tana faɗin "Waye"!    daga waje junaid yace"Mijinki ne insha Allah," ita kanta batasan lokacin da tasaki murmushi ba,    "Ka shigo ciki," ta bashi amsa, tura kopar yayi tare da sa kai yashiga ciki yana faman zabga mata murmushin nan nashi, wuri yasamu kusa da ita anan ƙasa ya lankwashe ƙafarsa ya zauna tare da miƙa mata cup ɗin yace"nasan zaki buƙaci wannan,haɗine na musamman daga mijinki insha Allah,"  fashewa da dariya tayi tana kallon shi, kafin ta zuro hannayenta daga cikin hijabin jikinta ta kar6a, jikinta har rawa yake yi wurin ɗaukar spoon ɗin dake aciki tashiga ɗebowa tana kaiwa bakinta, ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,   Tun tana sha da cokali har ta tsame cokalin daga cikin kofin ta miƙa mashi tare da cewa"ruƙe mun," hannu yasa ya kar6a, kafa cup ɗin tayi abakinta tashiga kwankwaɗarshi harta shanye duka,  tausayi ta bashi saboda ya lura ba ƙaramar yunwa take ji ba, cikin sanyin murya yace"nasan kina jin yunwa sosai,bari naje na kawo maki dinner ɗinki," yayi maganar tare da yunkurawa zai miƙe cikin sauri tace"a'a nagode da wannan ma,ba yunwa bace damuwata ba, abunda ke damu na shine Har yanzu aunty azmee fushi take dani"? fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,    "Kada kisa damuwa aranki, nayi ma aunty azmee magana kuma ta fahimce ki,tun ɗazu ma take ta son tayi magana dake,"    Cike da farin ciki tace"dagaske Aunty azmee bata fushi dani kuma nema na take"?    jinjina mata kai yayi alamar eh, cikin sauri ta miƙe tana naɗe dardumar don taje ta ganta,     ɗaukar cup din da ta ajiye yayi sannan yayi mata sallama ya fuce daga ɗakin,     cire hajib ɗin tayi, sannan ta ɗauko mayafi mai girma ta rufe jikinta dashi, buɗe ƙopan tayi sannan ta fito tare da wuce wa ɗakin azmeen, kwankwasa mata ƙopa tayi, a lokacin azmee bata jima da kammala salla ba,    tasowa tayi tare da sanya hannu ta buɗe mata ƙopan, jikinta na sanye da dogon hijabi hannunta na ruƙe da cazbaha,    Zuba ma sehrish ido tayi tana kallonta, cikin en ina tace"Aunty azmee dama junaid ne yace kina son gani na," ta ƙarasa maganar tana sunnar dakai cike da fargabar amsar da Azmeen zata bata,   murmushi azmee tayi tare da cewa"hakane tun ɗazun nake ta son in yi maki magana amma duk in nazo saina same ki kina bacci," jinjina kai sehrish tayi sannan tace"nasan na 6ata maki rai aunty azmee, ki yafe mun,"    hannu azmee tasa tare da shafa gefen fuskarta tace"just forget about the past komai ya wuce ki manta kawai, yanzu ma nake shirin zuwa in shirya maki abinci don nasan kina jin yunwa sosai,   Murmushi sehrish tayi ba ƙaramin kwanciyar hankali tasamu ba,       Sannan tace"bari na barki  ki huta nasan kinyi aiki sosai kin gaji,banji daɗi ba ɗazun da kika hanani tayaki aiki," cikin sanyin murya ta ƙarasa maganar,    Azmee tace"ki manta da wannan, yanzu kije ki haɗa abincin ki ci," amsa mata tayi da toh,sannan ta juya zata fita, Muryar azmee ce ta sake katse ta da cewa"Au na manta ban sanar dake ba, babban yayan ku fa ya dawo, yau da wuri suka shigo, shi kaɗae ne ma ya rage bai ci abincin shi ba, ki fara kai mashi pls,"   Amsa mata tayi da toh sannan tasa kai ta fuce daga ɗakin nata,   *SGR* gaba ɗaya hankalin shi na akan Laptop dinsa da yake dannawa, yana a hakimce saman royal sofa mai mazaunin mutun biyu, jikin shi na sanye da kimono robe ta cotton,green colour jikinta akwai zane zane masu kyan gaske, rigar bata rufe faffaɗan ƙijinshi ba,hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mashi ba,ya ɗaure igiyar rigar adai dae saitin shafafen cikin sa, a natse yake danna laptop din da zira ziran yatsun hannun shi, ƙamshi ta ko'ina    da sallama sehrish  ta shiga falon nashi, batare da ya ɗago ba ya amsa mata sallamar,      Shiga ciki tayi hannunta na ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da fruits tare da coffee,    koda ta ƙarasa dab dashi murya na rawa tace"sannu  da aiki,fatan kana lafiya,"   "Alhmdllh," ya amsa mata har time ɗin bai ɗago ba, ajiye mashi tray ɗin tayi daga gefen laptop ɗinsa, sannan tace"kana buƙatar wani abu"? hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin yakai bakinsa ya ɗan kur6a, janye shi yayi daga bakin shi sannan anatse yace"na manta phone ɗina asaman pillow a ɗaukomin ita," juyawa sehrish tayi da sauri zata kama hanyar zuwa bedroom ɗin nashi kamar daga sama taji gaba ɗaya mayafin jikinta ya sulale ƙasa daga jikinta, cikin sauri ta juya tare da kai hannu zata ɗauki mayafin daya faɗi ƙasa, ganin ƙafar sgr tayi asaman mayafin ya take shi da farar ƙafarshi, kasa ɗaukar mayafin tayi saboda fargabar da tashi ga, ranta ne ya bata cewa ba dagangan yayi hakan ba, da alama baisan ya take mata mayafin ba,   A ɗan tsorace tace"mayafi na" batare da ya ɗago ya kalle ta ba yace "ina Sane," jiki asanyaye ta juya tare da nufar ɗakin nashi, tsoranta kar ace alluran nan ta jiya bata sake shi ba,    faɗawa cikin ɗakin nashi tayi tare da nufar saman pillow ɗinsa wayar na ajiye asama,hannu takai zata ɗauki wayar kwatsam taji motsin mutun abayanta hakan ya sanyata juyowa a firgice gaba ɗaya sumar kanta ta watso harta gaban fuskarta, tsananin tsoro ne yakamata ganin mutumin da tabaro yana shan coffee tsaye agabanta, a wani irin yanayi yake bin jikinta da kallo tundaga kan ƙafarta har izuwa saman ƙirjinta, ganin haka yasa sehrish ta soma ja da baya a tsananin tsorace saboda tunawa da abunda ya faru jiya atsakaninsu hakan na nufin cewa Allurar bata sake shi bane, har yanzu akwai saura ajikin shi,  Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!     tuni zufa tasoma tsatstsafo mata a fuskarta, takawa sgr yayi yana matsawa kusa da ita, ja da bayan da zata ƙara yi ke da wuya , gaba ɗaya ta faɗa asaman gadon shi, bin ta saman gadon yayi gadan gadan ya tunkareta, hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka atsorace ta dinga girgiza mashi kai tana cewa"wlh bani bace na ɗauko allurar ba ! Bani ita akayi....ba zan iya cutar dakai ba.......!!" sai faman sambatu takeyi ita kanta batasan me take cewa ba saboda ya ƙureta sosai ta runtse idanunta zuciyarta nata faman harbawa, sam batasan cewa sgr yana cikin hayyacin shi ba,da gangan yayi mata haka saboda akwai abunda yakeson ganowa game da daren jiya da kuma abubuwan da ya gani na canji a bedroom ɗinshi da kuma body ɗinshi, yasan cewa itace last person daya kasance tare da ita,       jin shiru baice komai ba yasa ta ɗan buɗe idonta, ba komai yake kallo ba face doguwar sumar kanta, sai yanzu ya gane inda ya samu siraran gashi guda uku masu tsayi, hakan na nufin gashin kan Yarinyar ne ya tsinta asaman gadon shi ɗazu da safe, acikin sambatun da tayi mashi ta ambaci cewa ba ita bace ta ɗauko allurar ba, ba ta ita akayi, nan ma ya gane cewa kwa6a tayi mashi jiya har ya ɗirka ma kanshi allura, that's why omar ya tambaye shi akan cewa shi ya dauko allurar, natsuwa yayi a hankali yana ƙare ma fuskar sehrish kallo, ita kuwa sai faman haɗiyar yawu take yi saboda tsoro ga zufa dake gangarowa ta cikin gashin kanta kamar mara gaskiya, duk da sanyin A.c dake gudana aciki,    rufe idanuwanta tayi tana faman karanta addu'oi' acikin bakinta,    for the first time daya ƙarewa wata ƴa mace kallo irin wannan aduniyar nan, yana kallon kyakkyawar fuskarta ne aƙoƙarin shi na ya tuna abunda ya faru jiya,amma yarda take motsi da siraran la66anta tana karanta addu'oi'n neman tsari hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai ya samu kan shi da shagala wurin kallon bakinta, tunanowa yayi da ranar daya turketa amatsayin mace yarda ta tsorata har ta sume mashi, shi kuma rayuwarshi mace mai shegen tsoro ba ƙaramin burgeshi takeyi ba,ba don komai ba sai don ya ruƙa tsorata ta don ya samu nishaɗi,     ɗan gyara muryarshi yayi tare da cewa"jiya kin ban allura nayi ma kaina har nayi ƙoƙarin yin raping ɗinki, ko ba haka akayi ba? ya tambaya fuskarshi a ɗaure,.     hankali tashe sehrish ta shiga furta"innalallahi wa'inna ilaihirraji'un. Nashiga uku, kasan Allah ni bani bace na ɗauko allurar ba  bansan komai akai ba,.     shiru sgr yayi yana kallonta har lokacin taƙi buɗe idanunta, abunda bata sani ba shi guessing yayi bai tuna komai ba, amma yayi mata rijiya ta faɗa,    cigaba da magana yayi anatse"then tell me who brought it to u"?     shiru tayi lamo saboda tasan ba zata iya furta sunan haroon ba, ganin taƙi magana yasa shi daka mata tsawa tare da cewa"ba magana nake maki ba!!," wannan tsawar da yayi mata ne yasa ta sume mashi, dama sai da ranshi ya bashi,   Saukowa daga saman gadon yayi tare da fucewa izuwa palour dinshi, kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsa tare da buɗewa ya ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya koma cikin bedroom ɗin nashi,zama yayi daga gefen gadon tare da sanya hannu ya buɗe roban rubar saida ya fara sha sannan ya ɗebo a hannun shi ya yayyafa mata a fuskarta, a gigice ta ware idanunta kai tsaye suka shiga cikin nashi a lokacin ya mayar da  bottle din abakin shi yana ƙara shan ruwan, tamkar a mafarki take ganin abun har lokacin jikinta bai daina kerma ba, cire roban ruwan yayi daga bakin shi sannan ya mayar da murfin ya rufeta tare da ajiyewa saman side drawer ɗinshi,     sannan yayi mata nuni da hanyar fita yace"zaki iya tafiya," cikin sauri ta sauko daga saman gadon nashi, hanyar fita ta nufa da sauri da sauri, jinkirtawa tayi tare da ɗan juyawa don ta saci kallon shi, samun shi tayi a kashingiɗe saman gadon ya aza head dinsa asaman pillow, eyes dinshi a lumshe tamkat zasu rufe amma hasken kwayar idonshi blue ya ɗan fito alamar bai runtse idanun duka ba,    Muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"akwai wani abu ne"? Cikin sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta fuce daga ɗakin, sai da tafara ɗaukar mayafinta dake zube a ƙasa, ta yafa shi akanta sannan ta fuce daga part ɗin nashi, tafiya take anatse fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tayi mamakin yarda akai Sgr bai tuhumeta ba,bayan ya tuna duk abunda ya faru atsakaninsu jiya, tayi tunanin zata sha mari ne a wurin shi amma sai gashi abun yazo mata da sauƙi, har yau tana mamakin sauƙin kai irin nashi da ba kowa zai fahimta ba, amma tabbas bai da girman kai ko kaɗan, jan ajine kawai dake gare shi ko jinin sarauta bazai nuna mashi wannan ba, Domin kuwa shi kanshi Sarki ne mai cike da ƙarfin iko👑   a hankali take taka steps ɗin down stairs zata sauko, jin alamar shigowar mutun cikin babban falon yasa ta tsagaitawa da tafiyar tana kallon shi, jahan ne ya shigo cikin falon hannun shi ruƙe da jakar kuɗin da zasu ba haroon, ganin yarda yake tafiya cikin sanɗa yasa ta gane cewa bai son wani ya ganshi cikin sauri ta ja da baya tare da samun wuri ta la6e,    sai faman ƴan waige waige yake yi yaga ko akwai mutun amma wayaam ba kowa hakan yasa cikin sauri ya wuce bedroom ɗinsu, ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da lalla6awa ta fito kai tsaye ta nufi kitchen tana zullumin ko menene Jahan ya ɗauko acikin jakar hannunshi, da alama dae wani mugun abunne tunda har yake sanɗa don kar aganshi, ta faɗi acikin ranta a lokacin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin don ta zuba ma kanta abincin da zata ci,    turo ƙopar yayi a hankali yashiga daga cikin ɗakin nasu, jin alamar shigowar mutun yasa ayaan dakatawa daga zirga zirgan da yake yi acikin ɗakin,   Cikin sauri ya nufe shi yana cewa"Jahan ka tabbata babu wanda ya ganka"? Amsa mashi yayi da cewa"eh babu da alama duk sunyi bacci, kazo yanzu mu hanzarta mu kai mashi kuɗin,"    Atare suka fito daga bedroom ɗin nasu,  duka suna sanye cikin jallabiya, ɗakin haroon suka nufa, koda suka ƙaraso ƙopar ɗakin a rufe take, kwankwasawa Jahan yashiga yi a hankali,   "Su waye ne"? Ya tambaya daga ciki, Har suna haɗa baki wurin cewa "twins ne ",    kwance yake daga saman gadonshi,daga shi sai shorts ajikinshi ba riga, tasowa yayi tare da nufar kofan yasa hannu ya buɗe masu tare da cewa"ku shigo daga ciki," kallon juna su kayi kafin daga bisani suka shiga daga ciki,   tunda haroon yayi arba da jakar kuɗin dake hannun jahan yashiga sakin murmushin nan na shu'umanci yana cewa"ince dae kuɗina ne acikin jakar nan ko"? yayi maganar tare da miƙa hannu zai kar6i jakar,janye ta jahan yayi tare da cewa"ka fara goge  video ɗin tukunna mu damƙa maka su,"    ta6e baki yayi yana kallon su,kafin ya juya ya nufi saman gadonshi inda wayar shi ke ajiye ya ɗaukota, yatsan shi yasa ta buɗe sannan ya shiga wurin videos ɗinshi ya lalubo nasu daya ɗauka sannan ya miƙa masu tare da cewa"Gashi nan ku goge da kan ku,ina ga hakan zai fi ko"?  Kallon juna suka sake yi duk jikinsu yayi sanyin, tsoransu karya cuce su,ayaan ne ya kar6i wayar tashi yayi deleting ɗinsa gaba ɗaya, sannan ya kalli haroon ɗin dake ta faman sakin murmushi yace"ka  tabbata babu wani videon namu dake gare ka bayan wannan!?   ɗaga mashi gira yayi alamar eh, jahan yace'laptop ɗinka fa babu wani aciki"? nan ma ya sake cewa"babu wannan ne kawai gare ni,"    ajiyar zuciya suka saki gaba ɗayansu,  Miƙa mashi wayar Ayaan yayi, sannan jahan ya damƙa mashi jakar kuɗin, kar6a yayi yana cewa"kun tabbatar  cewa miliyan 80 ɗinne"?   ayaan yace"ka ƙirga su mana sai kaga in sun cika,"  Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!  Zuƙunnawa haroon yayi tare da zuge zeep ɗin jakar, sai ga bandir bandir ɗin ƴan dubu dubu, dami dami shaƙe acikinta, hannu yasa tare da curo bandir guɗa ɗaya yakai a saitin hancin shi yana shinshinasu yace"Anya wannan ba kuɗin ganye bane?harara suka watsa mashi jahan yace"a'a na bishiya ne," dariya haroon yayi yana faman shaƙa kuɗin a hancin shi,   gaba ɗaya ransu ya gama 6aci burinsu ya ƙirga kuɗin yaga in sun cika, amma ya tsaya yi masu shegantaka,    tass ya fiddo da kuɗin ya ƙirga su, duk dami ɗaya na dubu ɗari ne, a haka yayi counting ɗinsu 80 millions ne bayan ya kammala ƙirgasu, ya shiga cusa su acikin jakar kaf ya kwashe su, sai da ya zuge zeep ɗin sannan ya ɗago ya kalle s u cike da shaƙiyanci yace"Au na manta ban baku la'ada ba,"    atare suka haɗa baki wurin cewa"mun fi ƙarfinsu,kai ke buƙatarsu kai daga ganin mu kasancewa ba matsiyata bane,"    "Wow," ya furta yana tafa hannunshi "abu yayi kyau ƴa'ƴan billionaire,karfa kuce zaku gayamin magana!ku fuce mun daga ɗaki cikin salama,"    Jahan yace"ba sai ka kore mu ba, mukan mu aƙagare muke da mu fita mubar maka wannan ƙazamin ɗakin naka wanda ko numfashi mutun daƙyar yake iya fitarwa!!kuma inaso ka sani Haroon baka ci bulus ba, zamu rama duk wani wulaƙancin da kayi mana!!   yana kai ƙarshen maganar tashi ya ruƙe hannun ayaan suka juya zasu fita daga ɗakin karaf idonsu ya sauka akan mutumin dake shigowa cikin ɗakin, A wani irin firgice suka ja da baya gaba ɗayansu, shi kanshi Haroon ya sha jinin jikin shi saboda basu son da mutun ba, gaba ɗaya duk abunda suka tattauna acikin kunnanshi kaf ya gama naɗar komai,    hankali tashe suke kallon shi,kamar yarda shima hankali atashe yake kallon su  Follow my tiktok acct 👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 Atare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da suka shaida cewa junaid ne,sai faman murza idanunshi yake yi da hannunshi,da alama magagin bacci ne ya shigo dashi,hakan ya basu tabbacin ba lallai in ya fahimci komae ba,     cikin sauri Jahan yace"junaid tun yaushe kake anan?me kake yi har yanzu baka yi bacci ba"?    Cikin shagwa6a yace"nima bansan ya akai na shigo ba,dan Allah kutaimaka mun ku kaini ɗakin abbanmu in kwanta,wurin shi nake son zuwa,"  Shu'umin Murmushi haroon yasaki yana kallon shi,   ganin yarda yake binshi da kallo yasa su twins saurin ruƙe hannun junaid suka fuce dashi daga ɗakin,     "Ayaan kaje kawai ka kwanta,ni bari nakai shi ɗakin Abban namu," Amsa mashi yayi da toh,sannan ya wuce bedroom ɗinsu,   Shi kuma jahan zuƙunnawa yayi tare da ce mashi"ka hau na goya ka karka faɗi,"    daddagewa junaid yayi ya haye bayanshi tare da ƙanƙame shi,sannan jahan ya miƙe ɗauke dashi abayansa ya wuce bedroom ɗin Abban nasu,    A hankali ya tura ƙopar bedroom ɗin Abban nasu,yana kwance sai faman sharar bacci yake yi asaman royal bed ɗinshi,shiga da junaid ciki yayi a hankali ya sauke junaid saman gadon daga gefen abban nasu,      gyara kwanciya junaid yayi tare da rungumo Abban nasu da hannunshi sannan yace ma Jahan"thank u,"   murmushi jahan yayi ba ƙaramin burge shi yayi ba,sam junaid bashi da wata damuwa,sai yaji dama shine ke irin rayuwar shi,    "Sleep well," ya furta tare da juyawa ya fuce daga bedroom ɗin yana sauke ajiyar zuciya,ɗakinsu ya koma lokacin daya shiga a kwance ya samu Ayaan har bacci yayi awon gaba da shi,shima wucewa yayi tare da haurawa saman gadon ya kwanta daga gefenshi, Yaushe rabon da suyi bacci irin na daren nan harsun manta,saboda fargabar haroon kullum da damuwarshi suke kwana,yau dae sun huta ma rayuwarsu tunda sun sallame shi, A 6angaren haroon kuwa tun bayan da suka fita ranshi ya raya mashi cewa tabbas akwai alamar tambaya game da zuwan junaid bedroom ɗinshi,saboda tun da yake junaid bai ta6a faɗowa ɗakinshi ba irin haka,duk irin magagin baccin da junaid yake yi bai ta6a zuwa ɗakin shi ba,amma sai yau kwatsam zai faɗo mashi ɗakin shi adai² lokacin da suke tattaunawa dasu twins kuma? Anya ba turo shi akayi ba❓    zama yayi daga gefen gadon nashi yana tunani,dakyar ya iya tashi yakai hannu ya kinkimi jibgegiyar jakar kuɗin,wuri yayi mata acan cikin ɗakin nashi ya 6oyeta,    Sannan ya koma tare da hayewa saman gadonshi ya kwanta,      ********************* Washe gari  A hankali ya buɗe idanunshi da su kayi mashi nauyi saboda bacci,hannu yasa tare da yaye blanket ɗin daya lullu6a dashi,miƙa hannu yayi tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye saman bedside drawer dinshi,missed calls ya gani nasu hossana da jahad,tashi yayi daga zaune yana kallon screen ɗin wayar tashi,jiya yaso yaje ya duba su amma bai samu time ba,    danna musu kira yayi tuni tashi ga ringing,   A lokacin Jahad ce acikin falon zaune saman 2 seater tana ta jiran kiranshi,hossana kuwa tana can tana sharar bacci,     har ta fidda ran cewa zai kirasu saiga kiran nashi ya shigo,cikin sauri ta miƙe ta nufi telephone ɗin tasa hannu ta dauka tare da karata a kunnanta,    Cikin sanyin murya tace"Assalamu Alaikum ya Omar an tashi lafiya,"   murmushi yasaki tamkar yana agabanta yace"lafiya lou Alhmdlh,nayi laifi ko?jiya banzo na duba ku ba,ayi mun afwa ina busy sosai,amma kuna araina,"    "Babu komai ya Omar,dama mun damune akan rashin zuwan naka,kuma mun kira wayarka jiya da safe,baka a kusa sai dai matarka Aunty zainab ta ɗaga kiran,"     "What!matata kuma? Wacece kuma aunty zainab?pls explain to me ni bangane me kike cewa ba,"    murmushi jahad tayi tare da cewa"Ya omar meyasa ba ka sanar damu cewa kana da aure ba?baka so mu sani ne?   Sam Omar baisan inda zanjen nata ya dosa ba,    "Jahad nifa bansan me kike cewa ba! Wacece kuma matata?   kafin jahad tace wani abu,sai ga hossana ta fito da saurin gaske jikinta sanye da kayan bacci,tana ƙarasowa tasa hannu ta kar6i telephone ɗin tare da karata a kunnanta cikin shagwa6a tace"eh mana ya omar ashe kana da aure,jiya da safe mun kira wayarka,mace ta ɗaga kiran tace mana kai mijinta ne kuma baka a kusa,sannan kuma tace mana tana ɗauke da juna biyu,kuma sunanta zainab amma kana kiranta da Hayaty,"    tunkan ta ƙarasa maganar Omar yashiga 6a66aka dariya,natsuwa su kayi gaba dayansu suna sauraron sautin dariyarshi,   "Ya omar kayi shiru baka ce komai ba," muryar hossana ce ta katse mashi dariyar tashi,daƙyar ya tsagaita tare da cewa"Am sorry na fahimci abunda kuke cewa,bazan iya yi maku bayani anan ba,insha Allah bayan na kammala breakfast dina zan shigo sai muyi magana ta fahimta ko?    Atare suka haɗa baki wurin cewa"Eh muna jiran zuwanka,sannan in ka tashi zuwa kazo mana tare da Hayati ɗinka muganta,"    murmushi kawai yayi tare da rejecting call ɗin,sai lokacin ya duba kiran nasu da sukayi mashi jiya acikin wayarshi,cike da mamaki yaga kiran da sukayi mashi jiyan da safen kuma already an ɗaga kiran,natsuwa yayi yana tunanin wanene ya daga mashi kira harya tsara wannan ƙaryar,tabbas junaid zai iya yi mashi wannan aikin,.     Miƙewa yayi tare da saukowa daga saman gadon nashi,ya wuce cikin toilet dinshi,within 15 mins ya fito ya wuce wurin closet ɗinshi,tsaf ya kammala shiryawa cikin shadda purple colour ba ƙaramin kyau tayi mashi ba yabi jikinshi duka ya feshe shi da turare,   Bayan ya ɗauki wayar shi ya fito tare da wuce wa part ɗin Rafayet,da sallama ya shiga ciki,baya acikin falon shi don haka ya wuce cikin bedroom ɗin shi,   Yayi mamakin ganin shi a kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi,jikin shi na'a sanye da bathrobe da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,    Shiga ciki omar yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna sannan ya ambaci sunan shi a hankali"Rafayet wai haryanzu bacci kake yi?    Yamutsa fuska yayi alamar idonshi biyu sannan yace"Omar,yau lalaci nake ji ajikina,duba fa ka gani tun ɗazu nayi wanka amma nagaza tashi in shirya kaina,"    sakin baki Omar yayi yana kallon shi tare da jinjina kai yace"nasan meye matsalarka,wato har yanzu abun nan bai bar jikinka ba ko? Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!     "Mekenan"? Sgr ya tambaya yana kallon shi daga kwancen da yake,    Murmushi Omar yasaki batare da yace komai ba,    Miƙewa Sgr yayi tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna shi da Omar yace"Na fa tuna duk abunda ya faru jiya a tsakanina da yarinyar nan,"!   "dagaske"? Omar ya faɗi da ɗan mamaki a fuskarshi,   "yeah,amma bakomai na tuna ba,so nake ka faɗamun gaskiyar abunda ya faru,time ɗin da ka tarar damu asaman gadon nan,shin na cire shorts ɗin jikina ko ban cire ba"?    tunkan ya ƙarasa maganar omar ya soma sakin dariya,   Ɗaure fuska sgr yayi tare da cewa"pls Omar banason wasa,just tell me the truth,cos banaso yarinya ta raina ni,"     tsagaitawa omar yayi sannan ya zayyana mashi dukkan abunda ya faru tsakanin shi da Sehrish,    hannu sgr yasa tare da dafe forehead ɗinshi yace"OMG!Omar ashe kaine ka katse mun jin daɗina a wannan lokacin!meyasa baka bari na ƙarasa aikina ba"? ya ƙarasa maganar yana jifar shi da harara,    dariya omar ya kuma yi kafin yace"nifa taimakonka nayi,kisan kai fa zakayi,"    tsuke fuska yayi tare da cewa"babu wani nan,ni narasa meyasa kake mun haka,"   Yayi maganar tare da kai hannu ya dauki pillow ya wurga mashi shi a fuskarshi,tarbe pillow ɗin Omar yayi a hannunshi tare da cewa"Am sorry bro,bansan abun yayi hurting ɗinka ba,amma ae ko yanzu bata 6aci ba,kasan inason farin cikin ka,bari natashi naje na kira maka yarinyar sai ka ƙarasa aikin naka,"   Yana kai ƙarshen maganar tashi ya mike tare da nufar  hanyar fita daga bedroom ɗin  yana  karashe dariyar shi,yana jiyo muryar sgr cike da zolaya yana cewa"Am waiting," Kai tsaye bayan Omar ya fito daga sashen sgr down stairs ya sauko tare da fuce wa daga main palour din,ko breakfast din bai tsaya yayi ba ya wuce wurinsu hossana, Wuraren ƙarfe tara kiran Amrish ya tashe ta daga dogon baccin daya ɗauke ta tun bayan sallar asuba,dakyar ta iya buɗe idanunta da sukayi nauyi saboda bacci,hannu takai tare da daukar wayar dake ajiye asaman side drawer ɗinta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta a kasalance tace"Assalamu alaikum Amrish irin wannan kira haka tunda sanyin safiya"?    daga can 6angaren Amrish tace"Sleeping sickness wai kina nufin har zuwa yanzu baki tashi daga bacci ba?duba time ki gani kusan 9 fa yanzu,"   Jin haka yasa sehrish sa hannu tare da janye blanket ɗin jikinta ta tashi daga zaune tana kallon clock, ɗan xaro ido tayi tare da cewa"subhanallahi wai har 9 tayi?meyasa aunty azmee bata tashe ni ba,ya ilahi,"    dariya amrish tayi tare da cewa"kin cika bacci reeshi yakama kije kiga psychiatric doctor ya duba brain ɗinki,"    ɗaure fuska sehrish tayi kamar tana agabanta tace"oh ashe dama kallon da kike mun kenan ko?      muryarta cike da dariya tace"no ba haka bane inason lafiyarki ne shiyasa na baki shawarar kije aduba ki,"    "Okey thanks for ur advise amma fa ni ba inda zanje,da raina da lafiyata bazan kwasa na tafi asibiti ba,salon su ja man bala'e,"  ƙarasa maganar tayi tare da cewa"pls inason zan shiga kitchen yanzu,i wll call u later bye,"     sallama su kayi da amrish sannan ta mayar da wayar saman side drawer ta ajiyeta, saukowa tayi daga saman gadon cikin sauri ta wuce cikin toilet, brush tayi tare da wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce wurin wardrobe ɗinta,buɗewa tayi tare da ɗauko mayafi ta daure shi akanta kamar ɗan kwali, Lokacin da fito har azmee ta kammala jera masu breakfast ɗin asaman dining,junaid ta samu tare da fawan zaune suna yin breakfast dinsu,kamar waɗanda yunwa ta koro sai faman turawa suke yi abakinsu suna ci,    dagowa junaid yayi tare da kallonta nan take ya sakar mata murmushi tare da kiran sunanta"sehrish,"    Juyowa fawan yayi tare da kallonta yace"ke zo nan,"    nan da nan taji gabanta ya faɗi dama basu ta6a magana dashi ba,   jiki asanyaye ta ƙarasa inda suke dai dai kusa dashi sannan ta tsaya tana faman ƴan kame kame,    cikin sanyin murya yace"jira kike na fara gaishe ki ne"?   cikin sauri sehrish tace"ina kwana,ka tashi lafiya,"   fashewa da dariya junaid yayi yana kallonsu,harara fawan ya watsa mashi tare da mayar da idonshi kan sehrish yace"lafiya lou,haka yadace daga yanxu basai nace ki gaishe ni ba,daga zarar kin ganni kiyi hanzarin gaidani amatsayina na yayanki,"   Murmushi sehrish tayi tare da amsa mashi da"toh,"     junaid yace"bismillah ki zauna muyi breakfast atare mana," girgiza kai tayi tare da cewa"a'a inaso zan shiga kitchen ne wurin aunty azmee,"   Amsa mata yayi da"okey,"   Sannan cikin sauri ta juya tare da nufar kitchen din,    time din da taƙarasa kitchen ɗin azmee ta kammala gyare kitchen din tsaf, dakyar ta iya cewa"ina kwana aunty azmee,"    sai lokacin ta lura da ita,murmushi tasakar mata tare da cewa"lafiya lou babyn junaid,sai yanzu kika tashi daga baccin naki?dazu nashiga ɗakin naki na sameki kina bacci,    ciki sehrish ta shiga tana cewa"Aunty azmee ae da kinsani kin tashe ni,nikaina banasan yawan baccin nan da nake yawan yi,"   Azmee tace"ai baida amfani atlease yakamata ace duk in kika kammala sallar asuba ki daure kina karanta al'qur'ani, sannan ki dinga yawaita yin azhkar,insha Allah duk wani abu dake damunki Allah zai yaye maki shi,"   "Insha Allah zan yawaita yinsu kamar yarda kikace,yanzu inaso in kaima babban yaya breakfast ɗinshi,bansani ba ko kin kai mashi,    Azmee tace"a'a ban kai mashi ba,bari na haɗa maki sai ki kai mashi,"    Tsayawa sehrish tayi tana jiranta,   Bayan azmee ta kammala shirya mata breakfast din nashi acikin tray ta miƙa mata,hannu biyu tasa ta kar6a tare da kama hanya ta fuce daga kitchen ɗin,   Da sallama abakinta tashiga part din nashi,     har time din bai fito ba,yana acikin bedroom ɗinshi,ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinshi daga bakin kopar ta tsaya tare da maimaita sallamar,    daga cikin bedroom ɗin tajiyo muryarshi yana cewa"wanene nan"   tuni tasha jinin jikinta,musamman data tuna abunda ya faru jiya ba ƙaramin tsoro ya bata ba,    murya na rawa tace"Ni ce,breakfast nakawo maka,"    "Okey,come in," a hankali tasa ƙafa tare da shiga ciki zuciyarta nata faman ɗar ɗar,   tsayawa tayi daga bakin ƙopan tana kallon shi,har lokacin yana kishingiɗe kamar yarda Omar ya barshi,    ganin ta tsaya abakin ƙopar yasa shi cewa"lafiya?    cikin sauri tace"bakomai," "Okey shigo ciki,ki fara gyara min toilet ɗina,"    ƙarasawa ciki tayi a hankali take tafiya tana satar kallon shi,eyes ɗinshi na'a rufe tamkar mai jin bacci,duk wani motsinta acikin kunnanshi yake jinshi,tura ƙopar toilet ɗin tayi tare da shigewa ciki,    Sai bayan da ta shiga ciki sannan ya buɗe idanun shi tare da bin ƙopar toilet ɗin da kallo,tunawa da abunda ya faru jiya tsakaninsu yayi,mayar da idonshi yayi tare da lumshe su,    ba da jimawa ba sehrish tafito daga cikin toilet tare da cewa"na kammala gyarawa,saura bedroom din,"    buɗe idanunshi yayi ba tare da ya kalleta ba yace "okey,ki duba cikin closet ɗina,ki ciro mun kayan da zan sanya,"   Cike da mamaki ido waje sehrish tace"dani kake"?    "Ni da waye" ya tambaya a ataƙaice,d'an murmushi tayi tare da wuce wa can ciki wurin wardrobe ɗinshi,mai girma da faɗin gaske gaba ɗaya glass ne ta gabanta,daga waje kana iya hango kayan sawarshi dake aciki gasunan abun kamar a company jeri jeri komai a tsare,tana ɗauke da sliding doors ajikinta,   Hannu sehrish takai ajikin wardrobe ɗin nan take ƙopar ta zuge da kanta,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,ruwan ido ta tsaya yi tama rasa wanne zata ɗauko mashi,saboda kowanne acikin kayan sawar nashi kyau suke yi mata,wata ƙopar ta zuge anan taga jerin kayan hausawa ta jima tana mamakin ashe yana dasu amma bai ta6a sanyawa ba,hannu tasa tare da ɗauko mashi haɗaɗɗiyar shadda gezna sky blue mai ɗaukar ido,    ruƙowa tayi a hannunta tare da dawowa wurin gadon Shi a lokacin harya gaji da jiranta ya sauko da ƙafafunshi ƙasa yana ƙoƙarin tashi,jin takon tafiyarta yasa shi ɗagowa yana kallon kayan data ruƙo a hannunta,   tsayawa tayi dab dashi sannan ta miƙa mashi,     ƙin kar6a yayi saima nuna mata hanya da yayi tare da cewa"basu nakeso ba,ki canza mun wasu bana sa kalar wannan,"       Jiki asanyaye sehrish ta koma ta maida shaddar sannan ta ɗauko mashi jeans da t shirt baƙa,       Komawa tayi tare da miƙa mashi,hannu yasa ya kar6a tare da furta"thanks" a gefen shi ya ajiye kayan sannan ya miƙe tare da kai hannu ya zame bathrobe ɗin jikin shi,cikin sauri sehrish tayi hanzarin barin bedroom ɗin takoma daga waje tana faman sauke ajiyar zuciya,ƙiris ya rage sgr ya saki murmushi don ba ƙaramin dariya ta bashi ba,ita duk atunaninta babu shorts ajikinshi shiyasa tayi saurin guduwa daga ɗakin nashi,   Tsaf ya kammala zura kayan ajikinshi bayan ya gama ya koma gaban dressing mirror ɗinshi tare da kai hannu ya ɗauki kwalbar turarennan nashi shumukh yabi ko'ina na jikinshi ya feshe shi da shi,sannan ya koma wurin shoe rack ɗin shi tare da zaro takalma ya zura a ƙafarshi,    tana atsaye tana jiran fitowarshi muryarshi ta ratsa kunnanta da cewa"ki shiga ciki ki gyara mun,"   Sannan ya wuce ta izuwa cikin falon nashi,    Shiga ciki sehrish tayi anatse ta soma gyara mashi bedroom ɗin nashi,     ************** A hankali motarsu tashiga cikin gidan abusufyan major ne ke driving ɗinshi yayin da yake zaune a back seat na motar,   Bayan yayi parking ɗin motar omar ya fito tare da wuce wa ciki,   Koda yashiga cikin falon samun su yayi azune saman 3seater sun haɗa kai sun kurawa plasma tv ɗin dake manne abango suna kallon tashar bollywood,    ba ƙaramin burgeshi su kayi ba,gyara muryar yayi tare da yi masu sallama,atare suka dago tare da kallon shi,hossana na ganin shi ta miƙe da gudun gaske ta tunkare shi,dakatar da ita yashiga yi da hannun shi amma ina sai da ta faɗa mashi,sosai ta rumgume shi tare da kwantar da kanta a saman wide chest ɗinshi,lokaci guda yaji wani irin yanayi atattare dashi,   Jahad kuwa a fusace tace"hossana menene haka wai?ba zaki bari ya ƙaraso ciki ba?    tamkar bata jita ba,haka ta ƙara ƙanƙame shi tana cewa"ya Omar nayi missing ɗinka sosai,jiya ko isasshen bacci bansamu ba saboda ban saka a idona ba,   hannu omar yasa tare da janyeta daga jikinshi suna kallon juna ido cikin ido yace"Am sorry pls,amma yanzu ae gashi nan nazo ko?   daga mashi kai tayi alamar eh,sannan tasanya hannunta cikin nashi suka ƙarasa ciki atare suka zauna kusa da Jahad saman 3 seater ɗin da take,   Cikin sanyin murya tace"sannu da zuwa ya omar,yasu abba da sauran mutanen gidan,   Fuskarshi dauke da murmushi yace"yawwa jahad,duk suna lafiya,ina fata kuma nasame ku cikin ƙoshin lafiya,"    Amsa mashi tayi da eh,sannan tace"namanta ban tambayeka ba,yasu Aunty zainab,"?    kafin yace wani abu hossana tace"ya Omar wai dagaske kana da aure"?a shagawa6e tayi maganar tamkar zatayi kuka,    cikin natsuwa ya soma kora masu jawabi"Ni banta6a aure ba,saurayi ne ni,ko budurwa ban ta6a ajiyewa ba,"   Jahad tace"amma ya Omar wacece ta ɗaga kiran wayarka da mukayi a lokacin?     shiru ya danyi kafin yace"ina tunanin younger brother ɗina ne Junaid,ya cika zolaya sosai," Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!    maimaita sunan Jahad tayi "JUNAID!ya omar ƙaninka ne shima?   kallonta yayi tare da cewa"eh ƙanina ne,yana da kyau sosai ga kyan hali sannan ya iya kyakkyawan murmushi kuma shagwa6a66e,"   Murmushi su kayi jin yadda Omar ke zayyana musu ƙanin nashi da alama dae ba ƙaramin sonshi yake ba,    "Ya omar ka nuna mana hotonshi mu gani mana," acewar hossana,   Batare da 6ata lokaci ba Omar ya zura hannu a ajihun wandonshi ya ciro wayarshi tare da shiga gallery ɗinshi,hoton junaid ya buɗo tare da miƙa ma Hossana,hannu tasa ta kar6a tana kallon hoton cike da mamaki tace"wow! yaya Omar wai dagaske ƙaninka ne?wlh yana da kyau sosai dan Allah ka kaimu gidanku wata rana mu ganshi,"   Jin yarda hossana keta santin hoton junaid yasa Jahad sa hannu tare da kar6ar wayar,   Lokaci guda taji gabanta yayi wani irin bugu,tunda ta aza idonta akan kyakkyawar fuskar junaid bata ƙara cewa uffan ba,sam tagaza janye idanunta akan fuskarshi,bakomai take furtawa acikin zuciyarta ba face"Tabarakallahu Ahsanul khaliqin,"    Muryar omar ce ta katse ta da cewa"jahad naji kinyi shiru"?   jiki asanyaye ta ɗago tare da kallon shi tace"ya omar pls zan iya tafiya da wayarka cikin ɗakinmu?yanzu zan dawo,"   murmushi ya saki tare da cewa"ba damuwa zaki iya zuwa,"   cikin sauri ta miƙe tare da nufar bedroom ɗin nasu ta shige ciki,      "Ya omar bari nakawo maka breakfast nasan baka ci komai ba," hossana ce tayi maganar yayin da take miƙewa daga saman kujerar,"  Ruƙo hannunta yayi tare da cewa"dawo ki zauna,idan kika tafi wa zai tayani fira,"    ƙayataccen murmushi tasaki tare da komawa ta zauna daga gefenshi sannan tace"Ya Omar yaushe zakayi aure ne?   "Ranar dana samu maisona," ya bata amsa yayin da idonshi ke akan agogon hannunshi,   cikin shagwa6a tace"ya omar ni nasan cewa kana da ƴan mata dayawa da suke sonka,kawai dae kaine baka shirya yin auren ba,"   "haryanzu bansamu kalar wadda nakeso ba hossana,"  ɗan turo baki tayi tare da cewa"ka faɗamun kalar matar da kakeso ka aura,zan tayaka da addu'a insha Allah,"   murmushi ya ɗanyi tare da kwantar da bayanshi ajikin sofa ɗin yadda zai samu damar kallonta sosai sannan yace"Inason mace natsastsiya kamila,miskila mai ilmin addini dana zamani,mai ladabi da biyayya,idan Allah ya bani mace mai irin wannan suffar tuni zanyi wuff da ita,"    tunkan ya ƙarasa maganar hossana ta ɗaure mashi fuska,sunnar dakai ƙasa tayi tamkar zata zubar da hawaye,   "Meya faru ne"? Ya tambaya yana kallon ta,   Cikin shessheƙar kuka tace"ya omar ba dole sai mace nutsastsiya ba,ko miskila,in dai tana sonka tsakani Allah kawai ka aureta,"    kawar da fuskarshi gefe guda yayi yana murmushi,   Sanya hannunta tayi acikin nashi tare da kwantar da kanta asaman kafaɗarshi, ...sun jima a haka batare da wani yace ƙala ba,kusan 30 mins sai ga jahad tafito hannunta ɗauke da wayarshi,tsayawa tayi tana kallonsu shi ya lumshe ido,hossana kuma har ta fara bacci,   murmushi ta saki tare da samun wuri ta zauna daga gefen shi sannan ta ambaci sunan shi "ya Omar,"   Buɗe donshi yayi a hankali yana kallonta,miƙa mashi wayar tayi tare da cewa"thanks,"hannu yasa ya kar6i Wayar sannan ya mayar da idonshi tare da rufe su,.     Ajiyar zuciya tasaki tare da miƙewa ta koma cikin bedroom ɗinsu,saman gadonsu ta haye a inda ta ajiye drawing book ɗinta,ashe lokacin da ta kar6i wayar omar ta shigo dashi bedroom ɗin nasu,zama tayi tare da ɗauko kayan zanen ta acikin school bag ɗinta,a natse ta zauna tare da zana fuskar,ba ƙaramin kyau zanen yayi ba,fuskar ta fito raɗau dauke da wannan murmushin nashi,zuba ma zanen ido tayi tana kallon shi,lokaci guda taji tana son taganshi face to face~~~~    ************************ Yau tunda ta farka da kewarsu jahad ta tashi saboda mafarkinsu da tayi,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗinta jikinta na sanye da riga bubu ta material,   tsayawa tayi daga tsaye tana sauraron wayar da Aunty babba keyi,da alama da hayaam suke magana saboda taji ta ambaci sunanta sai faman 6a66aka dariya take yi,    "wlh ba kiji irin farin cikin da nake ji ba,yau burina zai cika na ganin kin koma gidan da zama,hayaam bana so ki raga ma yarinyar nan!so nake acikin one week ki ƙuntata ma rayuwarta har taji ta tsani zama acikin gidan,maƙirci kawai zaki cigaba da haɗa mata ae nasan kin ƙware a wannan 6angaren shiyasa nake yin ki,"    girgiza kai hafsat tayi tare da ƙarasawa ciki ta samu wuri saman 2 seater ta zauna tana sauraronta,sun jima suna wayar kafin daga bisa ni su kayi sallamar,mayar da wayar tayi tare da ajiyewa agefenta,sannan ta ɗago tare da kallon hafsat tace"gulmawuya halan kin fito don kiji abunda muke tattaunawa ne?   Murmushi hafsat tayi tace"mommy kenan ashe haryanzu kina akan bakanki na ganin cewa hayaam ta koma gidansu Abbana da zama hmmmm whatever ni wannan ba damuwa ta bane,kawai akwai shawarar da nakeso na baki in ba damuwa,"   zuba mata ido aunty babba tayi tana sauraronta,.    Ci gaba da magana hafsat tayi"Mommy aunty hayam zata koma gidan da zama wannan ba laifi bane Amma zai iya zama abun kunya,amma maganar a ƙuntata ma rayuwar yarinyar dake acikin gidan sam wannan bai taso ba,in ba haka ba wlh zaku yi danasanin yin hakan,"   wata uwar harara aunty babba ta watsa mata kafin tace"ke tashi ki ban wuri!tun kafin ranki ya 6aci,"   Maƙe kafaɗa hafsat tayi tare da cewa"mommy dama ita gaskiya ɗaci gare ta,kullum ina faɗa maki kiji tsoran Allah,ki daina biye ma ruɗin duniya.....'   Katse ta aunty babba tayi tare da cewa"karfa kice zakiyi mun nasiha,ko iyayen da suka tsugunna suka haife ni ban ta6a sauraran nasiharsu ba balle ke ƴar cikina dana haifa,   tana kai ƙarshen maganarta,takai hannu tare da ɗaukar wayarta sannan ta miƙe tare da wuce wa ciki,   "Mommy ae da alama basu  yi maki nasihar ma,don da ace suna yi maki da duk ba haka ba,nibansan ma ya akai abba ya auroki ba anya ba rufa ido kukayi mashi ba,"    "Hafsat! Me kike cewa"? A ɗan firgice hafsat ta juya tana kallonta duk a tunaninta ta jima da barin falon ashe bata ƙarasa fita ba,   Cikin sauri tace "haka nace ni dae na gode ma Allah daya bani uwa tagari kamar ki,"    ba don ta yarda da maganarta ba ta juya tare da wuce wa upstairs,   Ajiyar zuciya hafsat ta saki tana faman tiƙar dariya,   _💋Boss Bature💋_ Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 Lokaci guda Amal ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya,ashe magen hayam ce ta faɗo ɗakin,sai faman kuka takeyi miyauu miyauu,da alama yunwa take ji ne,Batare da 6ata lokaci ba Amal ta zuƙunna ta shiga tattara kuɗin da sauri da sauri jikinta na kerma,don a matuƙar firgice take saboda magen nan data tsorata ta,   Miƙewa tayi hannunta ɗauke da kuɗin cikin sauri ta fice daga ɗakin,komawa tayi cikin ɗakinsu hayamm,jiki na rawa ta buɗe wardrobe ɗin kayansu,doguwar riga ta ɗauko ta Abra tare da mayafinta, A hanzarce ta shiga zura rigar ajikinta,ba ƙaramin yawa rigar tayi mata ba har ƙasa take ja,ga wuyar rigar da yayi mata yawa,yafa mayafin tayi,   Sannan cikin sauri ta fito daga cikin ɗakin,a nan waje ƙopar ɗakin ta ɗauki slippers tare da zura wa aƙafarta,    Jiki na kerma AMAL ta kama hanyar fucewa daga cikin gidan,sai da takai baƙin ƙopar fita sannan ta ɗan tsaya tare da juyawa tana kallon cikin gidan yayin da hawaye ke shararowa daga idonunta,bazata ta6a mantawa da irin uƙubar da tasha acikin gidan ba, ta dan jima a haka,daga bisani tasa kai cikin sauri tabar gidan,    Kamar walk'iya haka Amal tabar santar gidan gaba ɗaya,duk da bata jin kwarin jikinta,haka ta jure ta kama hanyar sauri sauri gudu gudu,ita kanta batasan ina zata dosa ba,amma tana da tabbacin cewa tasha zata nema domin ta hau motar zuwa Abuja, ...(Finally Amal taci nasarar barin gidan,saura fatan sauka lafiya) ***************** Sosai jahan ke ta faman sakin dariya cike da nishaɗi,bakomai yasa shi dariya ba face Ayaan dake zayyana mashi irin halin daya shiga na barazanar da haroon ke masu,hankalin su kwance basu da wani sauran damuwa,suna a kwance cikin hotel room ɗinsu,basu jima da fitowa daga wanka ba,kowannansu na sanye da white shorts ajikinshi,suna rungume da juna cikin lallausan bargo,   "Wlh jahan naji jiki sosai,wai ashe haka abun yake?sai gani a sume,gaskiya haroon ba ƙaramin shaiɗani bane,nasha Wahala a ranar nan,"      "dama kai rago ne Ayaaan,nafi ka juriya shiyasa abun yazo maka ahaka,ranar naji kishi da baƙin ciki sosai,har yanxu in na tuna abun ba ƙaramin ƙuna zuciyata ke yi mun ba,"acewar jahan,    "Pls ni banaso muna tuna abunda ya wuce,hakan zai iya sanya mana damuwa acikin zuciyoyin mu,mubar maganar kawai,"   Jahan yace"shikenan mu bar maganar amma inaso na tambayeka pls,yanzu kwatsam a lokacin nan da ace bamu ba haroon kuɗin nan ba,ya saki videon mu a social media har Abba da babban yayanmu suka gani,me kake tunanin zai biyo baya,"   Da wasa jahan yayi maganar amma har sai da zuciyar Ayaan ta ɗan buga,    "Abunda zai faru shine,zuciyar Abban mu zata buga anan take ya yanke jiki ya faɗi,babban yayan mu kuma zai yi mana bugun mutuwa,abunda ba'a fata kenan,"Ayaan ya ƙarasa maganar yana dariya,     Shima jahan dariyar yayi yana cigaba da sauraron shi kafin daga bisani suka ɗaura daga inda suka tsaya,"    **************Sehrish Tun bayan da tadawo cikin bedroom ɗinta,wanka tayi tare da ɗauro alwala,bayan ta kammala sallar,ta koma wurin wardrobe ɗinta,ta ciro kayan da zata sanya,dogon wando ne na roba,Army trouser tun lokacin da suka je siyayya,ta ɗauke shi saboda ba ƙaramin burgeta kayan sojoji suke yi ba,tare da farar shirt off shoulder ta zura ajikinta,ba ƙaramin kyau tayi ba,komawa tayi gaban dressing mirror ta ɗauki turarenta tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi,wuri ta samu saman chair ɗin da ke a front ɗin madubin,ribbom ɗinta ta ɗauko tare da zura shi a hannunta,yau taci alwashin saita ɗaure gashin kanta, da iya ƙarfinta na ƙarshe ta tattare gashin ta haɗo shi wuri guda,tare da zura ribbom ɗin ta ɗaure shi sosai,ya sauko a gadon bayanta,    Murmushi ta saki tana kallon kanta acikin mirror ɗin kafin daga bisani ta miƙe tare da wuce wa gaban gadonta,within 15 mins ta kammala gyara bedroom ɗinta,komawa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu ta ɗauko wayarta dake ajiye saman side drawer,    Wi-fi ta kunna nan take messages ɗin whatsapp dinta suka soma shigowa acikin wayarta,shiga whatsapp grp tayi na school ɗinsu,new student ne ke ta introducing ɗin kansu tare da pics ɗinsu,tunani ta soma yi bata da hoto ko ɗaya,gashi tana buƙatar pictures saboda ita ma tayi nata introduction din,    tana cikin wannan tunanin kiran junaid ya shigo wayarta,cikin sauri tayi picking tare da karawa a kunnanta,   Tun kafin tayi sallama yace"yunwa nake ji,"yana faɗin hakan ya katse kira,murmushi Sehrish tayi tare da cewa"shagwa6a66e kawai"   Ajiye wayar tayi saman pillow sannan ta miƙe tare da saukowa daga saman gadon,sam ta manta bata yafa mayafi ba,saboda saurin da take yi nata kai mashi tadawo don tayi pictures din,takalmi kawai ta zura a ƙafarta,sannan ta buɗe ƙopar ta fita,   A natse take tafiya hanyar kitchen ta nufa,wayam babu kowa a main palour ɗin da alama duk suna cikin bedroom ɗinsu wasu kuma sun fita,    Batare da 6ata lokaci ba ta haɗo mashi cornflakes tare da snacks acikin tray,kai tsaye ta wuce upstairs bedroom ɗinshi,   Tsayawa tayi tare da yin knocking ƙopar bedroom ɗin nashi,   daga ciki tajiyo muryarshi yana cewa"a buɗe take fa,just come in,"   a hankali ta tura door din tare da shiga cikin ɗakin nashi,   yana tsaye agaban mirror waist ɗinshi na ɗaure da farin towel da alama fitowarshi kenan daga wanka,    ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table din dake kusa da gadon shi,    Juyowa junaid yayi daga gaban mirror ɗin da yake,zuba mata ido yayi yana kallon bayanta,wandon jikinta ba ƙaramin fidda mata shape ɗin jikinta yayi ba,   takawa yayi a hankali ta bayanta ya tsaya sannan yakai hannunshi tare da ruƙo lallausan sumar kanta,a firgice Sehrish ta juya tana kallon shi,sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi yayi,   A hankali ta ambaci sunan shi"junaid"!   bai amsa mata kiran sunan shi da tayi ba,sai cewa yayi"reesh ina mayafin ki yake ne"?    Sai lokacin ta tuna cewa bata yafa komai ba ajikinta ta fito,    "Mantawa nayi ban sanya ba,"ta bashi amsa tana kallon fuskarshi,   "Kinyi kyau sosai,but pls kada ki ƙara fitowa haka batare da mayafinki atare da ke ba,"ya ƙarasa maganar cikin sanyin murya,   Har lokacin bai saki wutsiyar gashinta ba daga hannun shi,sai faman murza gashin yake acikin hannun shi,   Sakin gashin yayi tare da zagayawa da hannun shi ta bayanta,ya zame ribbom ɗin dake akanta,nan take sumar kan ta tarwatse abayanta,duk tana tsaye tana kallon shi batare da ta hana shi ba,    tura hannunshi yayi acikin lallausan gashin kan nata,wasa ya shiga yi mata dashi,ganin abun nashi ba mai ƙarewa bane yasa tace"junaid wai menene haka?kamar wata ƴar baby ka kama mun sumar kai sai murzawa kake yi,"    Murmushi yayi tare da cewa"kwarkwata nake son cire maki,don nasan baza a rasa su acikin kan nan naki ba,abunda baki sani ba su suke saki yawan mantuwa,"   Buge hannun shi tayi tana dariya tace"wlh ka 6aci da ƙarya junaid,bansan waya koya maka ƙarya ba,"   tayi maganar tare da wuce wa tana nufar hanyar fita daga ɗakin,cikin sauri yakai hannu tare da ruƙo nata acikin nashi yace"pls kada ki tafi,ki tsaya na kammala lunch ɗin mana,inyaso sai mu fita atare,     Batare da musu ba tace"bazan tafi ba amma zan fita daga waje,idan ka kammala sanya kayan saina shigo,"     ƙarasa maganar tayi tare da fucewa ta tsaya daga waje tana jiran shi, Shaf shaf ya kammala shirya wa cikin jeans da t shirt,sannan ya samu wuri daga gefen gadon ya zauna tare da kwala mata kira,    dawowa ciki tayi tare da takawa zuwa gefenshi ta zauna,    "Sehrish inason magana dake," Yanayin yarda junaid yayi mata maganar da wata irin kasalalliyar murya yasa ta jin faɗuwar gaba batare da sanin dalilin hakan ba,      Cikin sauri ta juyar da fuskarta tana kallon cikin idanunshi tace"menene junaid"   ƙara matsawa yayi kusa da ita,fuskarsu ta kasance a kusa data juna,numfashinsu har harhaɗewa yake dana juna don ƙiris ya rage tsinin hancin shi ya ta6a nata,hakan ba ƙaramin tsorata sehrish yayi ba,tun da take arayuwarta bata ta6a ganin fuskar junaid da irin wannan yanayin ba batare da Murmushi ba,sam babu murmushin nan a fuskarshi,   Cikin en ina sehrish tace"..junaid wai menene haka?me yake faruwa ne"?   Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu a hankali ya furta"I LOVE U REESH,I wanna be with u,for the rest of my life," in serious matter junaid yayi maganar,amma sai Sehrish ta fashe.da dariya kamar kamar me,    Mamakine ya kamashi ganin tana yi mashi dariya,   Miƙewa tayi daga saman gadon nashi tana ci gaba da yin dariyar,dakyar ta tsagaita tare da kallon shi tace"gaskiya junaid ka iya wasan kwaikwayo,wlh ni har gabana ya faɗi duk atunanina wani abun kirki ne ashe zolayar taka ce ta motsa,"   Hankali atashe junaid ya miƙe tsaye yana kallonta yace"reesh nifa ba wasa nake maki ba,inason bayyana maki irin tsananin son da nake maki ne,"    Muryarta ƙumshe da dariya tace"wlh junaid da ace kai actor ne acikin film ba ƙaramin ƙayatarwa zaka yi ba,saboda ka iya tsara wasan kwaikwayo,"    Tana kai ƙarshen maganarta,ta kama hanya da sauri ta fuce daga cikin ɗakin nashi tana ƙarashe dariyarta,   Jiki a mace junaid ya koma tare da zaunawa saman gadon,    jinjina kai yayi tare da cewa"tashin hankali!ashe irin kallon da sehrish keyi mun kenan!yanzu taya za'ae na bayyana mata irin yarda nake ji a game da ita?   Ya jima yana wannan tunnanin aranshi kafin daga bisani ya mayar da idanunshi akan cornflakes ɗin da ta haɗo mashi,.    A sanyaye yakai hannu tare da ɗaukar spoon ɗin dake acikin cup din,ya fara ɗebowa yana kaiwa bakin shi, adai dai lokacin da Sehrish ke gabda shiga Corridorn da ɗakinta yake Sgr ya fito waya kare a kunnan shi,da alama waya yake yi,karaf idonshi ya sauka akan bayanta wanda lallausar gashin kanta ke baje har wurin ƙugunta,don bata maida ribbom din da junaid ya cire mata ba dama dakyar ta ɗaure shi ɗaxu,ƙarasa fitowa yayi slowly ya dafa handrail da hannunsa guda har lokacin yana amsa wayan da yake yi, yayin da blue eyes dinsa ke bin bayanta da kallo, ba komae ne ya ja hankalin shi ba face Army trouser din dake jikinta don ba ƙaramin kyau yayi mata ba dama kuma favorite color dinsa ne...... _💋Boss Bature💋_ Wuraren biyu na rana hossana tafarka daga dogon baccin daya ɗauketa,miƙewa tayi daga kwancen da take asaman sofa,sai faman hamma takeyi tana murza idanunta, a hankali ta ware idanunta tana neman Omar da bacci yayi awon gaba dasu,wayam tagani babu shi alamar ya tafi bataso hakan ba, dakyar ta iya tashi daga saman sofa din,tana tafiya a hankali saboda jirin da take ji,ga wata irin Yunwa dake cin ta, Bedroom ɗinsu ta shiga,a nan ta samu jahad zaune saman darduma ta jima da kammala sallar Azhar,amma bata bar saman sallayar ba,tana zaune zugum tana tunanin duniya, Jin alamar tafiyar mutum yasa ta juyowa tana kallon hossana dake tunkarato, Ƙarasawa tayi wurin jahad tare da zuƙunnawa kusa da ita tace"jahad ashe ya omar ya tafi bai tashe ni ba,ko sallama ba muyi ba,"murya a kasalance ta ƙarasa maganar, murmushi jahad tayi tana kallon fuskarta tace"kada ki damu,in dae ya Omar ne zaki iya ganin shi da anjima ko da daddare ma," Ta ƙarasa maganar tare da cewa"ko kina jin yunwa ne?naga kina ta hamma" "E inaji sosai,'ta bata amsa, Jahad tace"Okey,yanzu nake shirin tashi na shiga kitchen in girka mana abunda zamu ci,amma kafin nan ki fara ɗaukar fresh milk a fridge sai ki haɗa da wani abu kisha,sannan in kin kammala kiyi sallah,gashi har time ma ya wuce,' amsa mata tayi da toh,sannan ta miƙe tare da fucewa daga bedroom ɗin, Murmushi jahad tayi tare da cewa"nan ba da jimawa ba zamu sha bikin Amarya hossana tare da bride ɗinta ya Omar," Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga saman sallayar, hannu takai zata cire hijabin jikinta, nan take ta tunano da maganar da mahaifiyarsu ta ta6a yi masu a lokacin da suke tare da ita, "Burin da nake dashi kafin nabar duniya Allah ya nuna mun ranar Aurenku,kamar yarda na haife ku arana ɗaya haka nakeso na aurar daku ku duka ukun arana ɗaya kuma a lokaci ɗaya,zan cigaba da yi maku addu'a Allah ya baku mazaje nagari," Cikin sauri jahad ta ƙarasa cire hijabin tare da ajiyeta nan saman gadonsu,sannan cikin sauri ta fito cikin falon anan tasamu hossana zaune saman 3 seater hannunta ɗauke da sinkin bread tare da fresh milk sai cusawa abaki takeyi tana haɗawa da madarar, jin alamar tafiyar mutum yasa ta ɗagowa tana kallon jahad dake tunkarota, Ganin yanayinta yasa hossana cewa"jahad meya faru naga kamar kina cikin damuwa"? jiki asanyaye jahad tace"hossana mun manta ba muyi ma Ya Omar maganar SEHRISH ba!banji daɗi da muka manta da batun nemanta ba,baiwar Allah bamusan wani hali take ciki ba," cike da damuwa Jahad ta ƙarasa maganar tare da samun wuri saman hannun kujera ta zauna, Nan take yanayin hossana ya canza,lokaci guda taji komai ya fita ranta, ba don komai ba sai don tunawa da Sehrish, murya na rawa ta soma cewa"inason ganin sehrish sosai jahad, zan sanarwa ya Omar ya nemo mana ita,bazan ƙara mantawa ba insha Allah," "Nima bazan manta ba, da zarar yazo zamu sanar dashi,". a cewar jahad, Daga haka ta miƙe tare da wucewa kitchen, ********************** Wuraren ƙarfe biyar na yamma,motar sofwan ta shigo layin gidan,tun a bakin Gate security guards suka tsayar da motar tasu,kamar wasu zakuna haka sojojin suka tunkari motar shi,hankali tashe ya juya tare da kallon hayaam dake manne ajikinshi tana bacci ta aza kanta asaman kafaɗarshi,jikinta na sanye da dogon hijabi har ƙasa ta sanya niƙab a fuskarta,kamar wata Malamar Addini,   da ƙarfi ya ambaci sunanta"Hayaam!!Hayaam!!"har cikin kanta ta dinga jin kiran nashi,daƙyar ta iya buɗe baki tare da cewa"wai menene"?    "Mun ƙaraso gidan fa,dan Allah ki tashi kiyi ma waɗannan dakarun bayani,nifa a tsorace nake dasu,".    guntun tsoki taja ta janye jikinta daga nashi,sannan tace"haba sofwan bafa yau ka fara zuwa gidan nan ba,menene abun tsoro aciki,sai kace ba namiji ba,"    wani irin kallo yayi mata tare da cewa"ba yau na fara zuwa gidan ba,amma ae ko lokacin da na ta6a zuwa ɗaukarki a iya bakin babban gate ɗin nan nake tsaya......' Bai ƙarasa maganar ba,saboda bugun glass ɗin motar daya ji anyi daga waje,muryar wani basamudan soja ce ta karaɗe kunnansu da cewa"Oya wind down ur glass,"   A hanzarce Sofwan ya sauke glass ɗin motar,yana ta faman mazurai kamar wani mara gaskiya,    tambayarsu yashiga yi"Su wanene ku!kuma wurin wa kuka zo,?    Murya na rawa sofwan yashiga nuna hayaam yana cewa"am..yalla6ai..itace zatayi jawabi,bani ba,"    girgiza kai hayaam tayi tare da kai hannu ta ɗauko purse ɗinta dake ajiye saman laps ɗinta,cikin sauri ta ciro wayarta tare da ruƙe ta a hannunta,nan fa tashiga tunanin wa zata kira acikinsu don yayi masu magana subarsu su shiga,   "Madam ke muke jira,bama son 6ata lokaci and remove dat thing u covered ur face with" muryar sojan ce ta sake katse ta,yana nuna nikab din da yatsansa.   Tuni taji zufa ta soma karto mata a fuskarta da sauri tasa hannu ta cire nikab din,contact ɗinta tashiga tare da dialing numbar Kanal Yousof,cikin rashin sa'a wayar tashiga ringing amma ba'a ɗaga ba almost 3 times,cikin sauri ta kuma lalubo numbar Junaid,har ta gama ringing junaid bai ɗaga kiran ba,da alama shima baya kusa da wayar tashi,   Hankalin Hayaam ba ƙaramin tashi yayi ba,dama su biyu kawai take da numbarsu a wayarta gashi duk sunƙi ɗaga kiran,     ganin zata 6ata masu lokaci yasa sojoji bashi umarnin yaja motar shi yabar wurin,      Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta,ba ƙaramin 6acin rai tashiga ba,amma babu yarda zatayi dolenta su koma,   Sofwan na ƙoƙarin tashin motar su bar wurin,sai ga motar Sgr ta kunno kai daga cikin babban gate ɗin gidan, Zuba ma motar ido sukayi gaba ɗayansu musamman hayaam da take jin cewa sauƙi yazo mata,don tasan kowanene zai bada Umarnin abarsu su shiga ciki ne, "Sir I think something is wrong here," Amstrong ne yayi mashi magana, Don haka sgr ya bashi command ɗin ya tsayar da motar tasu don jin meke wakana, A daidai saitin motarsu Hayaam Amstrong ya dakatar da tasu motar,sannan a hankali a wani irin slow glass ɗin motar suka soma saukewa atare, Waro ido waje hayaam tayi nan take zuciyarta tayi wani irin bugun bazata,ba don komai ba sai don ganin mutumin da tajima bata sashi a idonta ba,wato abun harinta, A hakimce yake zaune a back seat ɗin motar,ba ƙaramin kyau yayi ba yayi wani fresh dashi,musamman wankan daya ɗauka,Red shirt ce ajikinshi,tare da black trouser, launin rigar ya ƙara fito da wannan hasken fatar nashi sosai fari sol kamar ka ta6a jini ya zuba,sumar kan nan kuwa tana ɗaure abayanshi,yayin da idanunshi ke lumshe tamkar mai jin bacci, Cikin sauri sojan ya ƙarasa inda yake tare da buga ƙafa ya sara mashi sannan yace"Sir,wasu baƙin fuska ne ke son shiga cikin gidan,kuma basu da shaidar da zamu iya barinsu su shiga cikin gidan,shiyasa muka dakatar dasu, kusan 5 mins bai buɗe bakin shi ba,babu alamar cewa zaiyi magana ma,kowa yayi tsit yana jiran jin ta bakin shi,kai har sai da sojan ya fidda rai da zaiyi magana sannan Calmly yace"What about asking their details? Sojan yace"ban tambaye su wannan ba,amma bari naje na tambaye su," juyawa yayi tare da ɗan matsawa kusa da motar Sofwan yace"yana buƙatar bayani a wurinku,ku gabatar da kanku don yasan su wanene ku," jin shiru hayaam bata ce komai ba yasa sofwan juyawa zaiyi mata magana,sakin baki yayi yana kallon ikon Allah,gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan Sgr,ba ƙaramin tafiya da imaninta yayi ba, Nan take yaji wani irin kishi ya rufe shi,acikin ranshi yace"haba no wonder,sai yanzu na gane dalilin dayasa hayaam ta haukace mun akan wannan Namijin,mutum kullum ƙara kyau yake yi,kamar shi yayi kanshi don kyau,muddin irin wannan na yawo agari tofa bazamu ta6a yin kasuwa ba," "Don't waste our time"! muryar sojan ce ta katse mashi tunanin nashi, Cikin sauri yace"Hayaam!magana fa ake maki,kiyi masu bayanin alaƙarki da mutanen gidan," Ajiyar zuciya hayaam tasaki,sannan anatse ta soma magana"ka sanar dashi cewa ƙanwar matar yayansu ce hayaam," Juyawa sojan yayi tare da komawa wurin motarsu Sgr yace"yalla6ai tace ita ƙanwar matar yayanku ce kuma sunanta Hayaam," a hankali sgr ya ɗan buɗe idanun shi, Hakan yasa Hayaam dake hangen shi ta soma washe baki,ba don komai ba sai don ita atunainta sgr ya gane jawabin da Sojan yayi mashi, Cike da ƙasaita yace"sam wannan bayanin bai kwantamin araina ba!infact,I don't know any person wit dat name hayaam or what...,ban ta6a jin sunan ba,Sergeant!!a sallamesu su koma,nd add more security!!" Yana ƙarasa maganar tashi,glass ɗin motar ya ɗaga sama sannan a hankali Amstrong ya tashi motar,anatse yake driving ɗinshi har suka bar wurin gaba ɗaya, dariya ce ƙumshe abakin sofwan amma ya gaza fitar da ita saboda tsoran 6acin ran hayaam,sam yaƙi yarda su haɗa ido da ita,saboda tsoran karta huce akanshi, Kamar ta aza hannu akai ta fasa ihu haka taji,zuciyarta har wani boiling take tana burning saboda tsantsar 6acin rai da baƙin ciki,ashe duk haukan nata ma abanxa ne Sgr baisanta ba,baisan wacece ita ba duk zuwan da takeyi gidan a lokacin baya, daƙyar sofwan ya daure ya cije tare da ce mata"mu juya ko"? A tsiwace tace"bansani ba!!mtswww" ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki, Can kuma tace"babu inda zanje wlh,kota tsiya kota arziƙi wlh saina shiga cikin gidan koda kuwa zamu kwana anan ne,don bazanyi tafiyar banza ba," Cikin sanyin murya sofwan yace"Hayam ki bi komai a hankali!su fa waɗannan mutanen da kika gani ba kamar sofwan ɗin da kika raina bane,muddin kikace zakiyi masu rashin kunya wlh dukan tsiya zaki sha,kakkarya ƙasusuwan jikinki zasu yi,kuma kada kiyi tunanin cewa zakiyi masu kwarkwasa ko kija hankalinsu da kyanki,don wlh babu ruwansu da mace,su ba mayin mata bane irina,so u ave to be very careful," ya ƙarasa maganar fuskarshi ɗauke da dariya,don yau ba ƙaramin nishaɗi yasamu a wurin Sgr ba,ba ƙaramin burge shi yayi ba yanayin acting ɗinsa babu wasa aciki,Namijin ne dae na gaske, Tsuke fuska hayaam tayi,harara ta watsa mashi tare da jan dogon tsoki batare da tace komai ba, tunani tashiga yi akan yadda za'ae su shiga cikin gidan,nan take zuciyarta ta bata shawarar ta kira Aunty babba ta sanar mata,tana ƙoƙarin kiran nata sai ga Motar Haroon ta shararo da gudun gaske cikin layin, tunkan ya ƙaraso wurinsu ya rage gudun motar tashi,sai da yazo dai dai bakin gate ɗin gidan sannan yayi parking ɗin motar tare da sauke glass ɗinta,da alama yasha ya bugu har takai mashi karo,saboda yarda idanunshi ke ta faman rurrufewa sunyi luhu luhu dasu, dakyar ya iya tsayar da idanunshi akan Motar sofwan,nan take suka hango mashi kyakkyawar fuskar hayaam,ɗaga murya yayi tare da kwala ma sojojin kira,cikin sauri suka tunkari motar tashi tare da sara mashi, Yatsina fuska yayi ya kallesu a wulaƙance yace"Meke faruwa anan ne?su wanene acikin motar can"? ɗaya daga cikinsu ne yace "Yalla6ai,ba mu san ko su wanene ba,mun hana su shiga ciki ne saboda basu da shaidar da zamu iya barinsu shiga cikin......' Tunkan ya ƙarasa maganar haroon ya katse shi da cewa"Saboda gidan na ubanku ne!wai ma uban wanene ya kafa wannan dokar ta hana mutane shiga cikin gidan nan ne!"?ni banga amfanin takurawa mutane ba,idan tsaro ne ba Allah ke tsarewa ba mtswwww, Shiru sojojin sukayi suna sauraron faɗan nashi kamar ubansu,hayaam kuwa tunda taji yana zazzaga masifa yasata ɗagowa tana kallonsu,ganin yarda yake banbamin bala'e akan an hanasu shiga yasa ta soma sakin murmushin jin daɗi, Sofwan kuwa jinjina kai yayi tare da cewa"ikon Allah,kowanene wancan jarababben da yake ta faman tada jijiyoyin wuya,da alama ba ƙaramin hatsabibi bane,' Cikin lallashi sojojin suka haɗa baki wurin cewa"Sorry sir!Allah ya huci zuciyarka!" Hura hanci haroon ya shiga yi kafin daga bisani yace"Ban amince abarsu su shiga da motar da suka zo da ita ba!shi namijin yaja motar ya koma gidan ubansa,ita kuma budurwar kuce mata tashigo daga cikin motata na sauke ta cikin gidan,idan har bata amince ba to su tattara su koma inda suka fito,". "An gama yalla6ai,"atare suka amsa mashi,sannan suka juya tare da tunkarar motar sofwan,tun kafin su ƙaraso hayaam ta buɗe motar jiki na rawa ta fito saboda taji duk bayaninshi acikin kunnanta, Hankali tashe sofwan yace"Hayaam ni kuma awani matsayi kika ajiye ni ne"? Batare da ta waigo ta kalleshi ba tace"Zan kiraka a waya,in nasamu lokaci,ta bude back door ta dau jakanta" Jiki asanyaye Sofwan yaja motar,yayin da zuciyarshi ke cike da 6acin ran abunda tayi mashi,yasha wahalar kawota,amma ko godiya babu balle yayi tunanin sake samun wani abu awurinta,tuni yaji hawaye sun cika mashi idanunshi,tabbas hayam ta cuce shi sosai ba ƙaramar wahala yasha akanta ba,duk don ya mallake ta amma gashi nan ya tashi a tutar babu!dashi da Zero basu da bambanci ƙwara ma zero yana da amfani wurin yin lissafi, Shu'umin murmushi haroon ya saki lokacin da hayaam ta ƙaraso jikin motar tashi,hannu tasa tare da buɗe gaban motar tashiga ta zauna tare da rufe motar,sannan ta mayar da idonta akan haroon daya zuba mata ido ko kyaftawa baiyi, ita kanta saida tasha jinin jikinta da ganin irin zubin shi,cikin sanyin murya tace"Sannu ko," ɗan ta6e la66ansa yayi tare da cewa"Yawwa,amma naga baƙuwar fuska ina buƙatar ƙarin haske," Cike da kwarkwasa tace"Sunana Hayaaam,ni ƙanwar Aunty laila ce da kuma Aunty Amani," murmushin gefen fuska haroon yasaki kafin yace"Wow,no wonder that's why naga kamanceceniyar ki da Aunty laila,ashe ke ƙanwarsu ce,amma fa am really sorry game da abunda ya faru,securities ɗin gidan nan basu son ciwon kansu ba,in ba haka ba taya zasu ga mace kamila irinki sanye cikin dogon hijab kuma su hanaki shiga? Sunnar dakai Hayaam tayi tana faman sakin shu'umin murmushi,aranta tace"dalilin dayasa na sanya dogon hijabi kenan saboda nasan cewa kowa zaiyi tunanin ni mutuniyar kirki ce,hmmmmm basu san cewa da fuska biyu nazo masu ba," (Rashin sani yafi dare duhu!hayaam batasan da wa take magana ba," "Kada na cika ki da surutu,bari nashiga dake cikin gidan," Ya faɗi tare da jan motar da gudun gaske ya shige cikin babban gate din gidan (Finally hayaam ta samu nasarar shiga cikin gidan)  *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. Abban sojoji part 2 ❤ Bayan Haroon yayi parking ɗin motar,hayaam tayi mashi godiya tare da ɗaukar bag ɗinta,ta fito daga cikin motar sannan ta nufi cikin gidan,   Shu'umin murmushin nan nashi ya saki yabi ta da kallo tare da cewa"Nifa bana abu don Allah,kowani tsautsayin ne da ƙaddara suka kawo ta cikin gidan nan!Allah yasa ta kwanan mana biyu...." ya jinjina kai tare da cewa "tsuntsu daga sama gasasshee!"ya ƙarashe maganar tashi tare da zura hannun shi cikin aljihun jeans ɗin dake a jikinshi,wayar shi ya ciro tare da duba screen ɗin, missed calls aka mashi da wata hidden number,     shiru yayi yana tunanin taya zai bi kiran saboda kira ne mai mahimmanci a wurin shi gashi dole sai in shi mai 6oyayyiyar numbar ne ya kira ka,   Yana cikin wannan tunanin sai ga kiran ya sake shigowa,cikin sauri yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnan yana jiran jin me za'a sanar dashi   Wata irin muryace ta irin hamshaqan matan nan waɗanda suka ji duniya ta soma magana"Haroon!kana shirin jamin bala'e ko?meyasa ka fiye shiririta ne?ko kamanta plan ɗin mu ne"?    nan take haroon yashiga en ina murya na rawa yace"ban manta ba,inaso nabi komai a hankali......'bata bari ya ƙarasa maganar ba ta kwatsa mashi tsawa"Ya isa Haka! kasani wlh akanka bazan bari nayi gangancin rasa damar da nake da ita ba!haroon zaka iya rasa ranka muddin kace zaka kawomin wasa acikin lamarina!kai kasan wacece NI!bani da imani,"   Wata irin zufa ce ta soma gangaro mashi daga cikin sumar kanshi,lokaci guda duk yabi ya rikice yashiga zazzare idanu,    sautin dariyarta ce ta karaɗe kunnan shi,tsagaitawa tayi da yin dariyar sannan ta sassauto da muryarta wurin cewa"Am sorry fa,na tsorata ka ko? Nannauyar ajiyar zuciya haroon ya saki tare da cewa"Yanzu me kike so ayi ne,just command me zanyi maki koma menene,"!    "So nake ka kashe JUNAID!saboda shikaɗai ne hanyar da zanbi wurin ƙuntata masu,banaso junaid ya rayu,muddin yana araye toh farin cikin gidan zai cigaba da wanzuwa ne,ni kuma abunda bana so kenan!,"      girgiza kai haroon yashiga yi tare da cewa"Kiyi haƙuri wannan ne karo na farko da kika ban umarni na musa maki tunda na fara maki aiki!junaid is innocent  I can't kill him,zan iya kawar maki da duk wanda kikeso acikin gidan nan,Amma banda junaid!banda Abbana,Rafayet kuma yafi ƙarfina banda wata hanyar da zan iya cutar dashi,sai ma in jefa kaina cikin matsala!"    fashewa da dariya tayi tamkar zata fasa screen ɗin wayar,bayan ta tsagaita da yin dariyar taci gaba da magana"kasan koni wacece,kasan kuma abunda zan iya!idan har bazaka iya kawar mun dasu ba,to ni zan iya kawar dasu ta cikin ruwan sanyi,Haroon u must do what i command you!if not i wll expose ur secrets,kai kasan me zai biyo baya,ko ka kashe junaid ko kuma ni in kashe maka rayuwa gaba ɗaya...!!!!    Waro ido waje Haroon yayi yana sauraronta,   Cigaba da magana tayi"Maganar videon su Twins daka ɗauka,nasan ka goge na wurinka,amma akwai wani a hannuna,zanyi amfani dashi wurin tarwatsa zuciyar mahaifin nan nasu,da kuma masoyina Rafayet!inason ganin tashin hankalin shi sosai...."   A tsorace haroon yace"Kada ki kuskura ki saki bidiyon nan!in ba haka ba asirina zai tonu ne!kuma kina sane da cewa,muddin asirina ya tonu to ke ma kin gama yawo!!atare zamu fuskanci sakamakon mu,zasu kamo ki ne aduk inda kika 6uya!!"     ya ƙarasa maganar yana faman sakin huci yayin da idanun shi sukayi jawur saboda tsananin 6acin rai,    fashewa ta kuma yi da wata irin mahaukaciyar dariya kafin ta tsagaita da yin dariyar tace"Haroon!Iska bata ruƙuwa!domin ni tamkar iskar nake,kada kamanta ina amfani da baƙaƙen aljanu wurin gudanar da aiki na,kuma zanyi amfani dasu ne wurin ganin na tarwatsa dukkan zuri'ar Salahuddeen Hussein!wannan alwashi ne na ɗauka,rai uku masu mahimmanci suka kashe mun,ni kuma rayuka zan ɗauka!don bana yafiya arayuwata!"   Shiru yayi bai ce komai ba kusan minti biyar, sam baison wani abu ya samu abbanshi shi kaɗae yafi ji sannan yace"Maganar yaran nan fa?su kuma ya zakiyi dasu?    "Inaso saina fara sanya soyayyarsu acikin zukatan ƴan uwansu sosai,saboda inaso inyi amfani da wannan damar ne wurin ƙuntatawa dukkan wani jin daɗi na zuri'arsu,kamar yarda suka ƙuntata ma tawa zuri'ar,"     Jinjina kai haroon yayi kafin ya kuma cewa"Yanzu menene plan ɗinki"?    Wannan karan anatse ta soma magana"plan ɗina shine kawar da junaid,dalilin dayasa nakeson kawar da junaid shine!sihirina bazai ta6a tasiri akan Rafayet ba har sai an samu lagwanshi,kuma ba kowa bane lagwanshi ba fa ce Junaid,da zarar ya rasa junaid zaiyi sakaci da ibadarshi hakan zai bani damar yin aiki akanshi,kuma shi ya kasance Bugun zuciyar family ɗinsu inaso na ɗanɗana masu raɗaɗin rasa mutumin daka kwallafa rai akansa!sannan maganar bidiyon nan zan sake shi a social media kowa ya gani,daga zarar hakan ta faru nasan cewa Martabar family ɗinsu da kuma ƙimar da suke dashi a duniya gaba ɗaya zasu zube,kowa zai tsani zuriyarsu duk wata daraja da suke dashi a idon duniya zata tashi abanza ne!ni kuma hakan nakeso,kafin na saki bidiyon inaso kayi amfani da kuɗin da suka baka wurin barin ƙasar,ka koma malaysia da zama,na shirya maka komai najin daɗin rayuwa acan,giya da mata har saika gaji dasu,"    shu'umin murmushin nan nashi ya saki aranshi yana ayyana irin rayuwar da zaiyi acan cikin daular da aka shirya mashi,nan take yaji cewa zai iya aikata komai takeso,   Sam yama manta da waya yake yi saboda tsabar farincikin da ya ziyarce shi,mayar da bayanshi yayi a jikin seat na motar yana cigaba da sakin murmushi,    "Kana jina kuwa,"muryarta ce ta ratsa kunnan shi,hakan yasa ya dawo daga dogon tunanin daya tafi,    Sai da ya samu natsuwa sannan yace"Naji duk abunda kika ce,hakan yayi mun sosai,musamman da kika ambaci giya da mata,sai naji wani nishaɗi araina dama irin rayuwar da nakeson yi kenan,amma akwai wata shawara da nakeson baki,in ba damuwa,"   Tace"ina sauraronka haroon," "Ga me da bidiyon tsaraicinsu twins,kada ki sake shi a social media pls,sun riga sun biyani kuɗi kamar yarda na buƙata,shiyasa nakeso ayi masu sassauci,mutun biyu kawai nakeson suga bidiyon nan Abban su da kuma wannan ifiritun sarkin jin kan nan,sannan maganar kashe junaid nasan ban isa na hanaki aikata abunda kika yi niyya ba,amma abunda nakeso ki bar komai a hannuna,ni ko ke babu wanda zai kawar dashi!kiyi amfani da sihirin ki kawai ta cikin ruwan sanyi yarda babu wanda zai zarge ni!!"      Dariya sosai tayi da alama shawarar Haroon tayi mata,    Sannan tace"daga yau komai zai fara"!!! murmushi haroon ya saki tare da cewa"Allah yaba mai rabo sa'a"   daga haka su kayi sallama ya kashe kiran,kasa fitowa daga cikin motar yayi ba don komai ba sai don kasalar da yaji ta baibaye shi,fuskar junaid kawai yake gani acikin idanun shi,😢    ****************** Lokacin da Hayaam ta shiga cikin gidan da sallama abakinta tashiga main palour ɗin,tsayawa tayi da tafiya ganin babu kowa acikin babban falon,takun tafiyar da taji ne yasa ta juyawa ta gefen hagunta tana kallon mai tafiyar,bakowa bace face Sehrish sai faman sauri take yi don ta shiga kitchen,har yanzu shigar ɗazu ce a jikinta,amma ta yafa mayafi ajikinta tayi rolling ɗinshi,    ta wutsiyar idonta ta hangi mutum hakan yasa ta dakata da yin tafiyar ta ɗan juya don taga wanene,karaf idonta suka haɗu akan na Hayaam,cike da mamaki take kallonta,batasan ko wacece ita ba,amma ganin hasken fatarta yasa tayi tunanin ko ƴar uwarsu Junaid ce,    tunkararta sehrish tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa inda hayaam take,tunkan sehrish ta ƙaraso zuciyar Hayaam ta shiga bugu,don ta gane cewa itace Ƴar aikin da Aunty laila take bata labarin cewa tana rayuwa acikin gidan,yarinyar da Abbansu ya mayar da ita ɗiyar shi,    fuska ɗauke da murmushi sehrish tace"Sannu da zuwa,"    hayaam tace"yawwa,ina mutanen gidan nan?naji shiru ko ba kowa ne"?   sehrish tace"duk sun fita,amma junaid da Fawan suna acikin bedroom ɗinsu,sai Aunty azmee tana acan cikin kitchen,    Jinjina kai Hayaam tayi har ta buɗe baki zata kuma cewa wani abu,sai ga Azmee ta fito daga cikin kitchen ɗin,ganin Hayaam yasa ta soma Sakin fara'a kamar gonar auduga,cikin sauri ta tunkaro wurinsu tana cewa"Wata sabon gani!Anya ba idona ne ke nuna min badaidai ba?   dariya hayaam tayi tare da wuce sehrish ta tunkari wurin Azmeen suka rungume juna,   ɗago da ita azmee tayi daga jikinta tana cewa"Oh ni Hayaam!ashe dama zan sake ganinki a duniyar nan?gaskiya kun yada zumunci!ina ji tun bikin Amani yaushe rabon ki da gidan nan!    Sai faman washe baki Hayaam takeyi ba don komai ba sai don sanin cewa Azmee zata kar6eta hannu bibbiyu kuma zata goya mata bayan zama acikin gidan,      "Kai Aunty azmee,nafa zo bayan bikin Amani kin dai manta ne,gaskiya nayi missing ɗinku sosai,shiyasa ma nace dole nazo naganku,"   Magana takeyi amma hankalinta na akan Sehrish,dake tsaye tana sauraronsu,    Azmee tace"mu ma munyi kewarki sosai,amma dai bada wuri zaki koma ba ko?don bazan bari ki tafi batare da kin zauna mana ba,".     Anzo wajen da tafiso nan fa tashiga washe baki tana cewa"ae Aunty azmee har sai kun gaji dani,in dae ba ku kuka kore ni ba,amma ni ina nan ba inda zanje,"   murmushi Azmee tayi tare da cewa"Ae bama wanda zai kore ki hayaam,".   taƙarasa maganar tare da mayar da idonta kan sehrish tace"wannan Hayam kenan!ƙanwar matar yayansu ishaq,da kuma Amani wadda tazo ran nan harna gabatar maki da ita"?   wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata ba don komai ba,sai don tuna kalaman Amani da tayi in har wannan takasance ƙanwarta ce,lallaikam akwai matsala,   da ƙyar sehrish ta ƙaƙalo murmushin yaƙe sannan tace"Allah sarki,ashe kanwarsu ce,naga suna yanayi da Aunty amanin,"    ta6e baki hayaam tayi jin abunda sehrish tace,    ruƙo hannunta Azmee tayi tare da cewa"Kada na cika ki da surutu,mu shiga ciki ki huta don nasan ba ƙaramar gajiya kika kwaso ba,"   atare suka wuce ciki da Azmeee,zuru sehrish tayi ita dai tun da tayi arba da Hayaam taji sam bata kwanta mata arai ba,kama hanyar shiga kitchen ɗin tayi tana cikin tafiya taji muryar junaid ya ambaci sunanta,    dakatawa tayi da tafiyar sannan ta ɗan juya tana kallon shi,fuskar nan tashi a yamutse alamar daga bacci ya tashi,sai faman sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi yake,    acikin ranta tace"Shagwa6a66e halan yunwa yake ji ne,"    ƙarasa saukowa yayi daga saman stairs ɗin kai tsaye wurinta ya nufa,      Lokacin da ya ƙaraso inda take tsaye muryar shi cike da kasala yace"Reesh har yanzu Abbanmu bai dawo ba"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tamkar zaiyi kuka yace"dama nasani,tunda wannan abokin nashi yazo mai farin gemu,nasan cewa ba zai barshi ya shigo ciki ba,yana can yaja shi sun tafi yawo gidan abokanansu,"   maganar shi ba ƙaramin dariya taba Sehrish ba,    "Amma dae baka da mutunci junaid,abokin abban naku ne kake ce ma mai farin gemu"?    turo baki yayi cike da shagwa6a yace"eh mana,farin gemu gare shi,ae ba ƙarya nayi ba, Ya ƙarasa maganar da cewa"nidai yanzu ki taimakamin bana jin daɗin bakina farfesu nakeson sha,"    bin lips dinshi tayi da kallo yarda yake magana ashagwa6e,sunyi dark red dasu kamar wanda yashafa jan baki,       Tunanowa tayi da maganar shi ta ɗazu da ya furta mata kalmar so,acikin ranta tace"yanzu ace dagaske junaid sona yake yi,tabbas zan iya haƙura da wanda nakeso don na aure shi,saboda ba ƙaramin tausayi yake bani ba,komai nashi kuma yana burgeni,sai dai bansan ya rayuwar auren mu zata kasance ba,yarda yake shagwa6a66en nan ba ƙaramar wahalar shi mace zata ci ba,wannan rainon shi ma zanyi kenan?kullum sai ya tashi tsakar dare da kukan rigima,don haka sai in tanadi feeder da zan rinƙa haɗa mashi madara yana sha.......' Kasa ƙarasa zancen zucin nata tayi saboda dariyar data zo mata,tafin hannunta tasa tare da rufe bakinta,ta ƙumshe dariyar don karta fito da ita,junaid ya gani ranshi ba ƙaramin 6aci zaiyi ba,   Harara ya watsa mata tare da cewa"meyasa kike kallona ne?kuma kinsa hannu kin rufe mouth ɗinki da alama baki da gaskiya sehrish,"    kafin tace wani abu,sai ga haroon ya faɗo cikin main palour ɗin,jin takon tafiyar shine,yasa gaba daya suka juya suna kallon shi,adaidai lokacin shima ya ɗago da idanunshi kai tsaye suka sauka akansu, Nan take sehrish taji gabanta ya faɗi rass,saboda ta tsani ganin shi acikin idanunta,   da alama wurinsu yake tunkarowa,murmushi junaid ya shiga sakar mashi yana cewa"Ya haroon sannu da dawowa,"     "Yawwa baby junaid,me kuke yi anan ne"? .   yayi maganar yayin da yake ƙarasawa wurinsu,    sunnar dakai sehrish tayi batare da ta ɗago sun haɗa ido dashi ba,   Junaid yace"muna magana ne da sehrish,"   ɗan ta6e bakin shi yayi kafin yace"okey,ka wuce ciki inason magana da ita,"    batare da musu ba junaid ya wuce cikin palourn tare da samun wuri saman 3 seater ya zauna,     ja da baya sehrish tayi aɗan tsorace tana jiran jin mai zai ce,    "Kinyi kyau sosai,shigar jikin ki tayi mun,"ya fadi yana faman bin wandon jikinta da kallo,    Shiru tayi mashi batace komai ba,jira kawai take yayi ƙoƙarin ƙure mata ta watsa a guje,    "dama nasan ba zaki ce komai ba,hakan yayi mun sosai,bakomai ne yasa nace inason magana dake ba face don in baki wata shawara mai kyau,sai dai bansan ko zaki ɗauka ba   Sai lokacin ta ɗago da idanunta tare da kallon shi tace"wata irin shawara kenan?kada kayi tunanin cewa zan ɗauki shawarar ka,saboda kai ba abun yarda bane!nagama yarda da duk wani abu da zai fito daga wurinka,burinka kawai ka cutar dani!"    hannunshi ya zura acikin aljihun shi tare da ƙara matsawa dab da ita yace"shawarar ba akanki bane!akan junaid ce!    daram!!taji gabanta ya faɗi a ɗan rikice take kallon shi,    "Nasan tunda na ambaci sunan junaid,yanzu zaki so ki saurari me zance,don na lura ba ƙaramin jinshi kike yi ba,"   Murya na rawa sehrish tace"me...me..kake son cewa ne agame da junaid?me junaid yayi ne?     Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cewa yayi"ran nan nayi maki ƙarya na cewa ni shaiɗanin aljani ne,wannan maganar ba gaskiya bace,abunda ya faru shine akan idona Omar yashigo cikin falon nan kai tsaye naga ya wuce upstairs sai raina ya bani cewa dole zai ji sautin kukan ki,kasancewar part ɗinshi dana sgr basu da tazara sosai a tsakaninsu,maganar cewa ni na shaƙe maki maƙoshinki alokacin da kika zo ambaton sunana agaban Marshal Omar shima duk ƙaryace,bani nayi maki hakan ba,kawai nayi guessing ne kuma da alama na canka dai dai,nasan kin tsorata alokacin kuma kinyi tunanin cewa ni ba Mutum bane,don haka inaso kisa aranki cewa Ni haroon cikakken mutum ne kamar kowa,"yana ƙarasa maganar tashi yasa ƙafa zai wuce part ɗinsu, ..cikin sauri sehrish tace"ka manta baka ban shawarar da kace zaka bani ba,"    dakatawa yayi da tafiyar batare da ya juyo ba yace"ku dage da addu'a," yana fadin hakan yasa kai ya wuce ciki,    Tsayawa tayi cike da zullumin maganar haroon nacewa su dage da addu'a,tana cikin wannan yanayin muryar Azmee ta katse ta da cewa"Sehrish!tsayuwar me kikeyi anan ne?nayi tunanin zan zo na same ki a cikin kitchen,'   cikin sauri sehrish ta nufe ta,tana cewa"yanzu nake ƙoƙarin shiga kitchen ɗin,wani abune ya ɗauke mun hankalina,"    Atare suka shiga kitchen ɗin,batare da 6ata lokaci ba suka soma aikace aikacen girke girken nasu kamar yarda suka saba,       Tun bayan da azmee takai hayaam ɗaya daga cikin bedroom ɗin da suka saba ajiye baƙi insun zo,zame hijab ɗin jikinta tayi,wata ƴar short gown ce ajikinta daidai guiwarta,kai tsaye toilet ta faɗa,bayan wasu ƴan mintina sai gata ta fito waist ɗinta ɗaure da towel,sai lokacin ta tuna cewa ashe tabar trolley ɗin kayanta acikin boot ɗin motar Sofwan,yanzu dole ta neme shi ko don ya kawo mata abunta,    ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon ta zauna,sannan takai hannu tare da ɗauko purse ɗinta da ta ajiye asaman gadon tun shigowarta tare da Hand bag ɗinta,     wayarta ta ciro anan taga missed calls na Aunty babba har kusan uku,   Murmushi ta saki tare da bin kiran nata,wayar na fara ringing Aunty babba ta ɗaga,.    kara wayar a kunnanta tayi tare da cewa"Auntyna takaina!yanzun nan naga missed calls ɗinki,banji ma da fitowa daga toilet ba,   on the other hand aunty babba tace"kin isa gidan ne!"?   Hayaam tace"eh,yanzu hakama gani asaman gadona inaso nayi bacci don na rage gajiyar dake ajikina,amma fa aunty nasha wahala kafin nasamu shiga cikin gidan nan!"    Aunty babba tace"wahala?kamarya kenan?     Nan hayaam ta kwashe duk abunda ya faru a wurin shigowarsu cikin gidan ta sanar mata,    uban tsoki aunty babba ta saki tare da cewa"Ke kika ban haushe wlh!taya zaki tsaya yi masu kwatance cewa ke ƙanwa tace?to menene alaƙar dake tsakani na dasu ne da har zasu shaidaki!tun a lokacin yakamata ki kirani awaya sai inyi ma wani magana daga cikin gidan akan yayi masu magana su barki ki shiga,amma don kince hayaam ƙanwar matar yayansu,to koni nan da kike gani Sgr baisan sunana ba,bare har yasan naki sunan hayaam,wannan mutumin ma bana tunanin yasan kamannin fuska ta nikaina,"    yatsina fuska hayaam tayi tare da cewa"aunty inaso in kwanta bacci nake ji," .  Aunty babba tace"to shikenan!kardae ki manta da abunda yakai ki cikin gidan,so nake kafin sati mai zuwa naji ana zancen bikinki da Sgr,kafin shekara mai zuwa kuma inji kukan jariri,"   Fashewa da dariya hayaam tayi jin abunda Aunty babba ke cewa,    Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama,wurgi da wayar tayi gefe guda sannan ta kwanta asaman lallausan bedmattress ɗin,nan take bacci yayi awon gaba da ita, ********************** Abun da ya faru bayan barin Amal gidan,wuraren bayan sallar la'asar mammy da Abra suka shigo cikin gidan,jikinta na sanye da hijabi abra kuwa atampa ce ajikinta ta aza mayafin asaman kafaɗarta,sai faman fira suke yi atsakaninsu,    "Mammy yanzu me zakiyi da kuɗin nan da sofwan ya baki?naga kamar suna da yawa,dama akwai ankon bikin wata ƙawata da nakeson yi,kinga sai ki aramun dubu takwas aciki inyi amfani dasu," .   tsuke fuska mammyn tayi tare da cewa"matsalarki kenan!daga kinga wani ya bani kuɗi sai ki bijiro da maganar anko,tun wuri ma ki fidda rai don ko sisi bazan baki acikinsu ba,malam zan kaima cikon kuɗin shi sannan sauran ni zanyi amfani dasu,ko ɗan farfesu naman nan an samu ayi,dama na kwana biyu ban sha ba,   ta ƙarasa maganar a lokacin da suka ƙarasa tsakiyar filin gidan,.    Rai a6ace abra tace"mammy kalli kiga fa har yanzu yarinyar nan bata fito daga ɗakin ba,ko ubanwa takeso ya ɗaura mana girki?gidan ma ko share shi ba tayi ba!    cike da masifa mammy ta shiga kwaɗa mata kira"Amal!!Amall!!don ubanki kina ina ne?bazaki fito kiyi mana aikin cikin gida ba!   Jin shiru bata amsa masu ba,yasa mammy ce ma Abra"maza kije ki tashe ta,ta fito tayi mana aiki,ko tasha na jaki,"   Kama hanyar ɗakin nasu abra tayi har ta kusa shiga ɗakin,ta tuna wata mugunta,cikin sauri ta juya tare da nufar fanfon cikin gidan,ƙaramin bokiti ta ɗauka na plastic ta ciko shi da ruwa sannan ta wuce dashi ɗakin a hannunta,    Murmushi mammy tasaki tare da cewa"haka nakeso,ƴa'ƴana su dinga koyi dani,"ta faɗi hakan tare da sa ƙafa ta wuce cikin ɗakinta,    ae tana shiga cikin ɗakin ta aza idonta akan gadonta inda tabar kuɗin da sofwan ya bata nan taga wayaam babu komai a wurin,hannu tasa tare da murza idanunta don ta tabbatar da abunda idanunta ke nuna mata,again ta kuma ganin wayaam babu komai asaman gadon,   Cike da mamaki tace"wai ba nan na jiye kuɗin da sofwan ya bani ba?kodai na jefa su wani wuri ne bansani ba!   ta faɗi hakan tare da sanya hannu ta zame zanin gadon tana kakka6e shi wai koda zata ga kuɗin a ƙasan shi,nan ma babu,   Cikin sauri ta zuƙunna tare da zoƙa kanta tana leƙen ƙasan gadon koda sun faɗo sun shige ƙarƙashin gadon,nan ma wayaam babu su,    Hankali atashe ta miƙe tana tafa hannu ranta ajagule tace"To wai kodai kuɗin nan ƙafafu ke gare su ne?in ba haka ba taya akai suka bar saman gadon nan!nifa nan na ajiyesu ban canza masu wuri ba,"   Lokaci guda tabi ta rikice ta rasa natsuwarta,saboda mace ce mai shegen son kuɗin tsiya,har faɗi take da naira biyar ɗinta ta faɗi kwara haƙorinta guda ya cire,    Acan kuwa bayan Abra tashiga cikin ɗakin da Amal take,sam bata lura babu mutun asaman katifar ba,saboda yarda shape din bargon ya bada kamar akwai mutun acikin shi,   Ciza le6anta tayi tare da cewa"ƴar jakar uba,yau zaki gane kuranki,wato banza tasamu tun jiya kike ja mana na rago asaman katifarmu duk kin 6ata mana katifarmu da yawun bacci,yanzu zanyi maganinki,ƙazama kawai   ta ƙarasa maganar tare da ɗaga bokitin ta kwarara ruwan asaman bargon tana faman 6a66aka dariyar mugunta,abun mamaki shiru babu alamar Amal zata saki ihun jin saukar ruwa ajikinta,.    Hakan yasa dariyar abra ta soma komawa ciki,ganin yarda bargon ya lafe ajikin katifar,yasa ta gane cewa babu mutum asaman katifar,   Hankali atashe ta saki bokitin ƙasa tana faman kwala ma Amal kira, Shiru bata amsa ba,cikin sauri ta fito tana nemanta a tsakar gidan,babu inda bata duba ba daga kitchen har cikin toilet ɗinsu duk bata nan,   da gudun gaske ta koma ɗakin mamynsu a firgice mammyn ta ɗago tana kallonta ganin yarda ta faɗo mata yasa tace"Abra lafiya meke faruwa ne"!    Muryarta har wani shakewa takeyi wurin fadin"Mammy!babu Amal acikin gidan nan!Amal ta gudu!dama saida raina ya bani cewa zata iya guduwa,'    jin hakan yasa mammy cewa"hakan na nufin itace ta kwashe kuɗin da Sofwan ya bani?    "Mammy dagaske baki ga kuɗin ba!aiko indae hakane toh Amal itace ta kwashe kuɗin,innalallahi bansan ya akai wannan daƙiƙiyar yarinyar har tayi tunanin guduwa ba,ina mata kallon shashasha....'     Katse ta mammy tayi da cewa"amma shegiyar yarinyar nan ta gama dani wlh!naci buri akan kuɗin nan,maimakon ta gudu tabarmin kuɗin shine ta haɗa dasu ta gudu,insha Allah a wulaƙance rayuwarta zata ƙare,Allah ma yasa kidnappers su ɗauketa su kwace kuɗin,sannan su lalata rayuwarta....."    "Subhanallahi!!me nake ji haka!"   Muryar Abbansu Abra ce ta karaɗe kunnansu,shigowarshi kenan cikin gidan ya same su suna ta tsinar Amal,    wani koɗaɗɗen mutum ne,tamkar baya a cikin hayyacinshi haka zubin shi yake,tsohon yadi ne ajikinshi duk yayi uban squeezing,kamar kanshi farau talauci,    ƙarasawa bakin kofar dakin yayi yana tambayar lafiya menene ya faru,     Tsawa mammy ta daka mashi tamkar ba mijinta ba haka tashiga ɗura mashi zagi    "Munafukin banza,munafukin wofi kazo kaji abunda muke tattaunawa ne!Anya bakaine kayi ma Amal hanyar guduwa daga cikin gidan nan ba!wlh ban yarda dakai ba!ka faɗamin gaskiya taya akai Amal tabar cikin gidan nan!?don nasan hakanan banza Amal baza tayi tunanin barin gidan nan ba!dole da taimakon wani,    Tuni yasha jinin jikinshi,saboda mugun tsoranta yake ji,gaba daya ta gama asirce shi,shiyasa baida ikon yin komai sai da Umarnin ta,    tsawa ta daka mashi tare da cewa"ba zaka faɗamun gaskiya ba!taya akai amal tabar gidan nan!    Zuru yayi da ido sai faman kyafta ido yakeyi yana mazurai kamar mara gaskiya,    tsoki abra taja tare da cewa"mammy dama kin daina wahalar da kanki,Abba bai ma da cikakken hankalin da zai iya taimakon Amal wurin barin gidan nan!6ata mana lokaci kawai zaiyi,ni ina ganin ki fito kawai muje mu nemo ta acikin gari,    harara Mammy ta watsa mashi tare da fitowa daga ɗakin ita da Abra suka kama hanyar fita daga gidan,   Bayan sun fuce daga cikin gidan,matsawa abi yayi tare da kai hannu ya ɗauki kujera ƴar tsugunno ya zauna asamanta,    Muryar Amal ya tuna acikin kunnan shi,ashe sun haɗu da ita akan hanya sai faman sauri take yi tamkar zata tashi sama,kamar daga sama taji an ruƙo mata rigar jikinta a firgice ta juya tana kallon shi,ganin Abbansu ne yasa ta fashe da kuka don tasan cewa zai iya mayar da ita gida,cikin shessheƙar kuka tace"Abie nasan inda Aunty amani take,bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba,kana gani zasu kashe ni,amma ba ka iya tsawatar masu akan su daina cutar dani,dan Allah Abie kabarni in tafi,kada ka sanar ma mammy cewa ka ganni akan hanya,ka nuna cewa bakasan komai ba,"   tsananin tausayinta ne ya kama shi,nan take yaji cewa zai iya taimakonta gudun karta faɗa hannun mutanen banza,tun da ƙaramar yarinyace mai ƙananun shekaru tsaf za'a iya yi mata wayau,    "Kiyi haƙuri Amal akan dukkan abunda ke faruwa,nima bada son raina bane,bani da yarda zanyi ne gaba daya mammy ta addabi rayuwata,ta hanani dukkan wani farin ciki na rayuwata,tun bayan da Allah yayi ma mahaifiyarku rasuwa ban ƙarasamun kwanciyar hankali ba,komai na duniyar nan ya fita raina Amal,mammy ta jima tana cutar da rayuwata da kuma rayuwarki,yanzu ina da kwarin guiwar iya taimaka maki!dama abunda yasa tuntuni banyi hakan ba saboda bani da ikon yin magana dake acikin gidan,inaji ina gani an rabani da ƴata kuma ana cutar da ita akan idona,babu komai akwai ranar sakayya,"   Yana kai karshen maganar tashi ya ruƙo hannun Amal tare da janta suka tafi,da kanshi yakaita tasha sannan ya damƙa ma drivern amanarta,kasancewar drivern ɗaya daga cikin abokanshi ne ana mutunci sosai,agaban motar drivern yayi mata wuri ta zauna kusa dashi,   Sai lokacin drivern yake tambayarshi inda zasu sauke ta a abujan,shi kanshi abie baisan inda amani ke zaune ba acan,    Cikin sauri Amal tace"ina da numbar wayar Aunty amanin,idan mun isa sai ya kira mun ita awaya,nasan zata zo,"    Murmushi abie yasaki yana tsaye daga waje yashiga tofa mata addu'o'i tare da yi masu fatan sauka lafiya,    tuni Amal taji hawaye sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta fito daga cikin motar tabi mahaifinta,haƙiƙa ta tausaya mashi sosai,haka ta dinga jin raɗaɗi azuciyarta har motar tasu ta kusa barin tashar,ya jiyo muryar Amal tana kwala mashi kira,   "Abie!!Abie!!" da saurin gaske ya ƙarasa inda motar take,kowa na cikin motar tsayawa yayi yana sauraron muryar yarinyar,    murmushi ta sakar mashi,tare da zura hannu cikin aljihun rigar Abra dake ajikinta,zaro kuɗin nan tayi kusan dubu arba'en,sannan ta zura hannunta ta saman glass ɗin murfin motar ta miƙa mashi su,    ganin ya tsaya yana kallon kuɗin yasa tayi saurin cewa"Abie dan Allah kada ka tambaye ni ina nasamu kuɗin,in dai ka yarda dani to ka kar6a kawai nasan kana buƙatarsu,"     Murmushi yayi tare da sanya hannu ya kar6i kuɗin,sannan a hankali glass ɗin ya soma dagawa sama,    Tana jiyo muryarshi yana cewa"ki kula mun da kanki,sannan in Allah ya haɗaki da ƴar uwarki Amani,ki gaishe mun da ita,kice Abbanta yana gaishe da ita sosai,     har motar tabar tashar Amal bata daina leƙenshi ba ta glass ɗin motar,haka zalika shima yana atsaye yana kallon motar tasu,har sai da ta 6ace ma ganin shi,sannan ya haƙura ya juya tare da kama hanya ya soma tafiya yayin da idanunshi ke akan hannunshi yana kallon kuɗin da Amal ta bashi,   Ba ƙaramin daɗin kuɗin nan ya ji ba,yaushe rabon daya ruƙe naira dubu tashi ta kanshi harya manta,ba damar ya samu kuɗi yashiga gidan shi,da zarar mammy ta gani zata amshe kuɗin,ko sisi bata son taga ya ruƙe a hannun shi,tafi son taganshi a matsiyacin shi yana yawo,wannan ba damuwarta bace,    Sanin cewa zata iya ganin kuɗin a hannunshi ta kwace mashi su hakan yasa baiyi gangancin zuwa gidan dasu ba,kai tsaye ya wuce wurin wani abokin shi mai siyar da nama abakin hanya,wuri yasamu ya zauna bayan sun gaisa ya bashi ajiyar kuɗin duka,sannan yace ya zuba mashi naman na dubu uku yaci,bai bar wurin ba sai da yaci ya ƙoshi sannan sukayi sallama da mai naman ya wuce gaba,    Murmushi abie ya saki bayan ya kammala tunanin nashi yace"Allah sarki Amal!kin taimaki mahaifinki,ba don ta bani kuɗin nan ba,da yau haka zan kwana da yunwa,"      Mammy da abrah tamkar zasu yi hauka wurin neman Amal,gida gida haka suka dinga bi suna nemanta,saƙo da lungu ba inda basu duba ba,har bayan sallar magrib suna waje wurin nemanta,a ƙarshe dasuka gaji agalabaice suka koma gidan suna faman haki kamar waɗanda suka sha gudu,tun acikin zauren gidan mammy ta yanke jiki ta faɗi a sume,saboda tsabar baƙin cikin Amal data gudar mata da kuɗinta, . hankali atashe abra tashiga zabga ihu tana kuka tana ambaton sunan mammy,   Da alama dae mammy sai anyi jinya, **************************** Around 11pm, fitowa tayi daga cikin toilet jikinta na sanye da sleeping dress riga da wando,white colour,da alama tayi shirin kwanciya,tun acikin toilet take jin wayarta na ringing,hakan ne ma yasa tayi hanzarin fitowa,ƙarasawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauki wayar dake ajiye asaman mirror,duba sunan mai kiran tayi,ganin baƙuwar number yasa taƙi ɗaga kiran,sai tayi rejecting ɗin kiran,kafin ta ajiye wayar sai ga wani kiran ya ƙara shigowa na baƙuwar numbar, Cike da mamaki tace"Wai wanene ke kirana a irin wannan lokacin,kuma da bakuwar number,salon ajamun bala'e,bari dae in ɗaga inji,picking call ɗin tayi tare da karawa a kunnanta,muryar namiji ce taji ya zabga mata sallama,aikuwa cikin sauri ta katse kiran tana faman dafe saitin zuciyarta,ta tsorata da jin muryar me kiran nata,koma wanene ba ƙaramin mutum bane,   tsayawa tayi tana tunanin wa tasani da wannan muryar,bata ta6a jin mai irinta ba,    tana cikin wannan yanayin sai ga message ya shigo cikin wayarta,cikin sauri takai hannu tare da janyo saƙon daya shigo daga saman screen din wayar tashiga karantawa kamar haka    _baiwar Allah,ina ta kiran wayarki kin ƙi ɗagawa,dama ƙanwarki Amal ce ta ban numbarki don na kira na sanar dake cewa kizo ki ɗauke ta,ni ne drivern daya kawota abuja,idan ba damuwa ki kira kuyi magana da ita,don kiji muryarta_   Wani irin bugu zuciyarta tayi,cikin tsananin mamaki tashiga maimaita sunan Amal,muryarta na kerma tashiga cewa'Amal!wata Amal yake nufi!ko dai Amal ƙanwata!!!    Cikin sauri ta danna ma numbar kira,yatsun hannunta har kerma sukeyi don aƙagare take da taji bayanin mutumin daya turo mata saƙon........... Pls read this👇👇👇 *Assalamu Alaikum,barkanmu da juma'a fatan kowa na lpy,yauwa inaso indan yi wani karin haskene,aduk lokacin da bansamu yin update ba har ranar ta wuce ina kokarin ganin nayi long page don yayi covering da wanda bansamu yi ba,nasan wasu sun fahimci hakan,yayin da wasu kuma basu fahimci hakan ba sai suyi ta maganar page kaza yakamata inyi tunda banyi na rana kaza ba,duk page da nake saki yafi ƙarfin page guda a ƙa'idar page,ina haɗe 2 pages ne sometimes ma yana haura 2 pages, Shiyasa in na sanya short page wasu ke complain saboda sun saba ganin long page,sannan ban kin yin typing sai don uzurin da ba yadda zanyi,da fatan zaku fahimce ni,sannan akwai masu maganata abayan idona nacewa wai ina jan littafi? Allah sarki rashin sani yafi dare duhu,bani da wani burin daya wuce inga na kammala littafin nan ayanzu saboda abubuwa da sukayi mun yawa,bani ke jan littafin nan ba!bada son raina ba kuma hakana ke faruwa ba!yanayi ne dake nake ciki,yakamata mutane su dinga yi mun uziri bai kamata arinƙa yi mun irin waɗannan maganganun ba,duk wanda kuma yake yi Alhakina na akanshi, wai wasu ma har cewa suke yi don naga littafinna yasamu kar6uwa mutane naso. shiyasa nake jan labarin,wlh dana ji wannan maganar kamar na fasa ihu don takaici, hmmmm babu komai akwai Allah,to my real fans nagode kwarae da hadin kai da kaunar littafi na da kuke,godiya mara adadi kuci gaba da yi mun uziru kuma acigaba da yi mun addu'a,shine kawai insha Allah komai mai wuce wane,Littafin nan inaji araina cewa kammaluwarsu tazo zanyi ƙoƙarin tabbatar da hakan!insha Allah*❤ *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. 🤍❤💖 Kiran na shiga drivern ya ɗaga,cikin sauri ta kara wayar a kunnanta tare da yi mashi sallama tace"kayi haƙuri bawan Allah,ban fahimci zancen ka bane,dan Allah ka ƙara yi mun bayani yarda zan gane,"    drivern yace"ƙanwarki ce Amal na kawota Abuja,yanzu haka ita kaɗai ta rage acikin tashar nan,kiyi hanzari kizo ki ɗauke ta saboda dare yana yi kuma ni yanzu nakeson na juya,"   Cikin sauri tace"ka turomin da address ɗin wurin gani nan zuwa,"      Amsa mata yayi da toh,sannan ya kashe kiran,ba da jimawa ba sai ga message ya shigo wayarta na address ɗin inda suke,   Da sauri Amani ta ƙarasa wurin wardrobe ɗinta tare da buɗewa ta ɗauko mayafi tayi rolling ɗinshi akanta,sannan ta dawo ta dauki purse ɗinta dake ajiye asaman bedside drawer ɗinta,         gaba ɗaya duk tabi ta dabarbarce ko escort bata nema ba, da kanta ta shige motarta,ta fisgeta da gudun gaske ta fice daga cikin gidan,driving take tana ta faman sambatu"Ya Allah ka tabbatar mun da abunda nake tunani,Allah yasa Amal ce ƙanwata,Ya Allah kasa itace,wayyo Allah da naji daɗi,       ji take kamar motar bata sauri,tamkar tayi fiffike ta tashi sama don ta ƙarasa da wuri, tun bayan da Drivern ya turama Amani adireshin wurin inda suke shiru bata ƙaraso ba,gashi dare sai ƙarayi yake,kuma babu wani passenger daya rage acikin station ɗin sai ita kaɗai kwallin kwal,sai kuma wasu daga cikin mazauna station ɗin,tana zaune acikin motar baiwar Allah ba ƙaramin galabaita tayi ba,ga gajiyar tafiya ga kuma ciwo da take fama dashi,don har yanzu zazza6in nan bai bar jikinta ba,ganin cewa zasu 6ata mashi lokaci gashi yana da wani uzuri mai mahimmancin da yake so yaje yayi,hakan yasa yace ma Amal ta fito daga cikin motar,daƙyar ta iya miƙewa tare da saukowa daga cikin motar ta fito waje tare da tsayawa tana jiran jin me zaice, Ruƙo hannunta direban yayi sannan yajata izuwa wurin wani benci yace ta zauna anan ta jira ƴar uwarta tazo,kada taje ko'ina,shi zai wuce don yana da uzuri,   Hankalin Amal ba ƙaramin tashi yayi ba ganin direban zai tafi yabarta acikin station ɗin gashi babu wata ƴa mace aciki sai ita kaɗae,   Shi kanshi baiso hakan ba,saboda amanace aka bashi,amma ba yarda zaiyi,ya zamar mashi dole ya juya ya koma da motar,    tana ji tana gani direban nan ya shige motarshi tare da janta yabar cikin tashar da ita,   Lokaci guda wani irin sanyi ya lullu6eta,nan da nan jikinta ya shiga rawar ɗari,hatta haƙoranta sai faman kakarwa suke yi suna fidda sauti kaf kaf suna game wa da juna,ƙanƙame jikinta tayi tana ta faman ambaton sunan Allah abakinta,   Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutane daga gefen hagunta,cikin sauri ta juya don taga su wanene,gabanta ne yayi wani irin faɗuwa ganin wasu giggan tantirai su uku suna tunkaro wurin da take,sai faman nunata sukeyi da hannu da alama ma abuge suke,sun sha takai masu karo suna tafiya suna tangal tangal kamar zasu faɗi,    ganin hakan yasa Amal ta miƙe cikin sauri ta soma tafiya tana waiwayonsu,muryar wani daga cikinsu ne tajiyo yana cewa"kai karfa ta kufce mana,naga kamar tana so ta tsere mana," haba ina ae Amal na jin wannan maganar ta manta da yanayin da take ciki,takai hannu tare da tattare rigar jikinta ta watsa aguje kamar zata tashi sama,suma ganin ta fara gudu yasa suka bi ta aguje don su taddota,    Gaba ɗaya duk tabi ta rikice tana gudu tana waiwayonsu hakan yasa ta hau saman titi batare da saninta ba,kafin tayi wani aune tuni wata mota tayi awon gaba da ita,wata irin razananniyar ƙara Amal ta saki yayin da ta baje asaman titin idonta na kallan sama,jini na zuba ta saman goshinta da kuma hancinta,da la66anta duka sun raunata,    Waro ido waje tantiran nan sukayi ganin abunda ya faru,aikuwa a gaggauce suka zura da gudu don kar ace sune suka kashe ta,     Hankali tashe suka tsayar da motar,sannan atare suka fito daga cikinta da hanzari suka tunkari wurin da yarinyar take kwance,gaba ɗayansu suna sanye da kakin sojoji ajikinsu,     Zuƙunnawa daya daga cikinsu yayi yana kallon fuskar yarinyar dake ta faman faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"    "bata mutu ba,har yanzu tana numfashi amma tana bleeding ya kamata muyi saurin kaita asibiti,"    Na zuƙunnan ne yayi magana,sannan batare da 6ata lokaci ba,yasa hannunshi tare da sungumarta asaman kafaɗarshi cikin sauri suka wuce da ita cikin motarsu,a back seat ɗin motar ya zaunar da ita,sannan shima ya shiga daga gefenta ya zauna tare da ruƙota jikinshi,   Shi kuma ɗayan ya shiga gaban motar tare da yi mata key,yaja ta aguje suka juya domin zuwa kai yarinyar asibiti,    Adai dai lokacin da Motar tasu take ƙoƙarin shiga shantalelen titin dake a left hand dinsu,Motar Amani ta kunno kai ta titin dake a right-hand ɗinsu, a wani slow Amani ta zuge glass ɗin motarta tana bin tasu motar da kallo saboda kukan mutum da tajiyo acikin motar ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,aranta tana cewa"Allah yasa dae ba wani mummunan abunne ke faruwa acikin motarcan ba,"   Tana ƙarasa maganar taja motarta da gudun gaske ta ƙarasa cikin tashar motocin,wuri ta samu tare da yin parking ɗin motar,cikin sauri ta fito tana faman gyara mayafin dake ajikinta,hannu tasa tare da ciro wayarta dake acikin purse ɗinta,sannan ta dannawa direban kira,cikin rashin sa'a aka sanar da ita cewa numbar da take kira a kashe take,    hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,   A ruɗe ta soma cewa"kodai ƙarya mutumin nan yayi mani ne?amma meyasa zai kirani a waya ya sanar dani cewa ƙanwata Amal ya kawo Abuja,kuma sannan yanzu na kira wayar shi a switch off,Ya ilahi amma dae bai kyautamun ba wlh,"    tana cikin wannan zancen zucin sai ga waɗannan tantiran guda uku da suka biyo Amal,ganin su yasa Amani tayi tunanin ko ta tambayesu may be a dace,   da hanzari ta tunkare su tare da yi masu sallama,    a firgice ɗaya daga cikinsu ya shiga cewa"wlh ba mu muka kashe ta ba,kawai mun ganta ne acikin tashar nan zaune ita kaɗae,shine muka biyota don mu tambayeta ina iyayenta suke ne...."tun kafin yakai ƙarshen maganar tashi wani daga cikinsu ya buge mashi baki tare da cewa"Ƙarya Haramun!Aunty bari na faɗi maki gaskiyar lamari,mu ɗinnan da kika ganmu 6arayi ne masu yankar aljihu,mun biyota ne domin mu kwamushe ƴan kuɗaɗen dake hannunta tana ganin mu sai ta watsa aguje,tana ta faman gudu kamar zata tashi sama kawai sai ga wata mota tayi Wuff ta ɗauke ta sama........'   gaba daya basu acikin hayyacinsu da alama giyar ce takai masu karo,sai faman kora mata bayanin abunda bata tambayesu ba suke,   Murya na rawa Amani tace"dan...Allahh ban gane akan me kuke magana ba?wacece kuma kuka bi aguje har mota ta buge ta?wace yarinya ce,!kuyi mun bayani,ni ina neman ƙanwata ne Amal,ɗazu wani driver ya kirani a waya ya sanar dani cewa ya kawota inzo in ɗauke ta kuma shine ma yaban addreshin wurin nan,"   Har haɗa baki suke yi wurin cewa"ae itace yarinyar da muke yi maki magana akai Aunty,ae yanzu haka ma yarinyar tana acikin motar waɗanda suka banketa,yanzun nan suka bar wurin nan da ita,   Tun kafin ya ƙarasa maganar Amani ta juya da saurin gaske ta nufi motarta saboda tunawa da tayi da Motar da tagani ta gifta ɗazu da kukan yarinya acikinta,   buɗe motar tayi tare da shigewa ciki taja ta da gudun gaske,tana jiyo muryar waɗannan matasan suna cewa"Aunty Allah tsare hanya,"        *************************** SEHRISH Sam ta hana idanunta bacci saboda jiran dawowar babban yaya,yau harya haura lokacin daya saba dawowa hakan ba ƙaramar damuwa ya jefata ba,harta sauya kayan jikinta izuwa na bacci riga da wando masu laushin gaske orange colour,tun wuraren ƙarfe sha biyu daidai takai mashi fruit a ɗakinshi,Coffee ne kawai bata kai mashi ba saboda tasan cewa bazai shaba idan ya salafce,don ta lura cewa yafi buƙatar shi da zafi zafinshi,don wani sa'en har yana tururi yake shan shi,    sai faman safa da marwa takeyi acikin ɗakin har sai da ƙafafunta suka soma yi mata raɗaɗi sannan ta koma tare da samun wuri gefen gadonta ta zauna,lokaci guda kuma ta soma sakin hammar bacci,duk yarda sehrish taso ta hana kanta bacci amma abun yaci tura,sai gata kwance abaje tana ta faman sharar bacci asaman gadonta,   da yake ta sama ranta abun sai gashi ta farka wuraren ƙarfe daya na dare,daƙyar ta iya mikewa tsaye tana kallon clock ganin ɗaya ta buga yasa taji gabanta ya faɗi rasss,tsoranta kar ace ya dawo tana cikin sharar baccin nan,   Cikin sauri ta taka izuwa wurin window ɗinta,hannu tasa tare da janye curtains din sannan ta zuge glass ɗin tana hangen wajen harabar ajiye motocinsu,anan ta hangi motarshi ajiye alamar ya dawo kenan,     dafe saitin zuciyarta tayi gabanta na faduwa a fili tace"Nashiga uku ashe ya dawo,yanzu ya zanyi kenan nasan ranshi zai iya 6aci akan ban kai mashi coffee ɗin ba,"   cike da takaici taja guntun tsoki tare da cewa"duk wannan baccin ne daya ɗauke ni,da hakan bata faru ba,yanzu ya zanyi kenan gashi dare ma yayi sosai,in naƙi kai mashi matsala, in nakai mashi ma hakan zai iya jamin wani abun kuma,"   taƙarasa maganar tare da yanke shawarar takai mashi kawai,hannu takai tare da daukar mayafinta,ta rufe kanta dashi,sannan ta zura silifa aƙafarta,a hankali ta buɗe ƙopar ɗakin kamar mara gaskiya haka ta dinga tafiya har ta isa kitchen,shiga ciki tayi tare da wuce wa kai tsaye wurin cupboard,hannu tasa tare da curo cup ɗin data ware mashi nashan coffee ɗinshi,batare da 6ata lokaci ba ta zuba mashi coffee ɗin da zafin shi aciki cup,asaman plate ta aza mashi kofin sannan ta nufi hanyar fita,tana ƙoƙarin fita daga cikin kitchen ɗin sai ga Hayaam ta faɗo ciki,ba ƙaramin tsorata Sehrish tayi ba don har saida takusa zubar da coffeen dake hannunta,ido azare take kallonta don bata tsammaci mutum ba adai dai irin wannan lokacin,   tun da tazo gidan take ƙumshe aɗakinta tana baccin lalaci,koda ta farka bata fito waje ba,sai yanzu Allah yayi ta samu ta fito,short gown ɗin nan ce ta ɗazu ajikinta,kan nan nata ko arziƙin dankwali babu balle mayafi,sai dai gashin kanta data ɗaure abayanta,    Murya a sanyaye sehrish tace"Sannu da fitowa,ya gajiyar tafiya,"   Ƙayataccen murmushi hayaam ta saki tare da cewa"yawwa ƴan mata,gajiya tabi jiki yanzu ina jina normal,"   Ta ƙarasa maganar tare da kallon cup din dake ruke a hannun sehrish tace"Wannan fa?ke zaki sha ne"?   girgiza kai sehrish tayi tace"a'a banawa bane,babban yaya zan kaimawa ne,"   yamutsa fuska amani tayi tare da cewa"Oh ashe ya dawo cikin gidan kenan,"   Sehrish tace"eh,ya dawo," "ra'ayin kanki ne kai mashi coffeen ko kuma shi ya buƙata ne"?ta kuma jifarta da tambaya,     "Ai shi ba'a yi masa katsalandan,shi yace na rinƙa kai mashi a kullum wuraren ƙarfe sha biyu idan sun dawo daga aiki," ta bata amsa tare da kama hanya zata wuce,   Cikin sauri hayaam ta sake shan gabanta tare da cewa"gaskiya bai kamata ace ƙaramar yarinya kamarki tana kai mashi abunsha adai dai irin wannan lokacin ba,sam wannan tsarin baiyi ba,yakamata ace yanzu kina kwance kina bacci ko don saboda zuwa school yana da kyau ki rinƙa yin bacci da wuri," ..murmushin yaƙe sehrish tayi sannan tace"nagode da shawararki,amma wannan aikina ne kula dashi,kuma nasaba da yin hakan"    ganin hayaam zata 6ata mata lokaci yasa tayi saurin wuce wa batare da ta saurari sauran abunda zata ce mata ba,   jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"yarinya dani kike magana,wato har wani faɗamun take itace mai kula dashi,shisshigi kawai da kutsi," ta faɗi hakan tare da jan dogon tsoki ta wuce bedroom ɗinta,    lokacin data ƙarasa part ɗinshi baya acikin falon hakan yasa kai tsaye ta wuce bedroom ɗinshi,sallama tayi mashi amma shiru ba'a amsa mata ba,almost 4 times tana zabga mashi sallama amma tsit babu alamar za'a amsa mata,   saurarawa tayi don taji ko zata ji motsin shi aciki,nan ma shiru ranta ne ya bata cewa kawai tashiga cikin bedroom ɗin nashi,    ƙafa tasa tare da shigewa ciki,nan take ƙamshin turaren nan nashi ya daki hancinta har saida ta ɗan ja da baya saboda yarda ƙamshin ya shigeta kai tsaye,sauke ajiyar zuciya tayi tare da ware idanunta tana bin bedroom ɗin nashi da kallo,wayamm tagani babu shi acikin ɗakin,tsayawa tayi tana tunanin ko'ina ya shiga ne,kodai bai dawo bane?amma kuma ae ga motarsu can awaje alamar sun dawo,har ta yanke shawarar barin ɗakin,zata juya kenan eyes ɗinta suka sauka akan fruits ɗin da takai mashi,wanda ta ajiye mashi asaman table din dake kusa da gadonshi,a rufe takai mashi kayan marmarin amma sai taga an cire plate din data rufe su dashi,alamar ya fara shan fruits ɗin kuma ya dakata,ranta ne ya bata cewa may be yana acikin toilet ne,    murmushi ta ɗanyi sannan ta ƙarasa wurin table ɗin tare da ajiye mashi cup of coffee din  agefen kayan marmarin,   tsayawa tayi tana tunanin ko dae ta tsaya ya fito daga cikin toilet ɗin wata'ƙil zai buƙaci wani abun bayan wannan,wata zuciyar kuma ta bata shawarar cewa ta tafi kawai tabar dakin saboda dare yayi sosai,    tana cikin wannan tunanin,sgr ya fito daga cikin toilet,waist ɗinshi na ɗaure da short towel wanda bai kai guiwar ƙafafunshi ba da alama wanka yayi aciki, sam bai lura da mutum a cikin bedroom ɗin nashi ba,gadan gadan ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,cikin rashin sani tafin ƙafarshi ya hau saman 6awon ayabar daya ci ɗazu,ya maƙale masa a jikin shirt ɗinsa saida zai shiga wanka ne ya lura dashi yasa hannu ya ka6e shi ya faɗi anan ƙasa,aikuwa nan take wani irin mugun sul6i ya kwashe shi bazato ba tsammani gaba ɗaya ya tafi a burkice zai faɗi,a firgice sehrish ta juya tare da yin ƙoƙarin taimaka mashi cikin sauri ta ruƙo shi nan take ƙarfin shi ya rinjayi nata gaba daya suka faɗa saman shimfiɗeɗen gadonshi a manne da juna,tashin hankali da ba'a sama shi date,   wata irin nauyayyiyar azuciyar zuciya Sgr yashiga saukewa,tabbas ya ɗan firgita saboda bai tsammaci hakan ba,bai ta6a yin irin wannan gangancin ba,hada ƙarin sam ya manta da 6awon ayabar a wurin bai jefa shi dustbin ba,da ace sehrish bata ruƙo shi ba awannan lokacin da ba ƙaramin buguwa zaiyi ba yanda yake dogon nan,    atare zuciyoyinsu suka shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,gaba ɗaya sehrish ta gama tsorata abun tamkar a amafarki take ganin shi,ta gaza yarda cewa itace tare da Surgeon general Rafayet kwance asaman gado ɗaya kuma amanne da juna,    gaba ɗaya jikinshi ya rufe nata hatta face ɗinta tana a saitin wide chest ɗinshi,tana jin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya,da kuma yarda heart ɗinshi ke beating very fast,    tsit kake ji daga ita harshi an rasa mai wani kwakkwaran motsi,danshin ruwan dake ajikinshi ba ƙaramin sanyaya mata jikinta yayi ba,daƙyar take iya breathing saboda hancinta daya manne da fatar ƙirjinsa,haka la66anta ma suna manne da fatarshi,   Boss man ɗin fa ya gaza ɗago da jikinshi daga nata,ba don komai ba sai don yarda abun yazo mashi unexpected,ba ƙaramin jinjinawa lamarin yayi ba shi kanshi,    Jin yarda yarinyar keta kokawa wurin fitar da numfashinta,yasa ya daure tare da yunkurawa zai tashi daga jikinta,baiyi wani aune ba towel din dake ɗaure a qugunshi ya shiga warwarewa gaba daya dama daurin ya saki,   Shi kanshi baisan lokacin daya mayar da jikinshi asaman nata ba ya kwantar da kanshi a saman left shoulder dinta,bakomai ne yasa yayi hakan ba face gudun kar towel din jikinshi ya saki agabanta,don muddin hakan ta faru tofa wannan karon ba sume mashi zatayi ba,zuciyarta ce zata buga tabar duniyar saboda tsabar firgici don ya lura yarinyar ba ƙaramar matsoraciya ba ce,     wani irin yanayi mara misaltuwa taji atattare da ita,jikinta yayi wani irin sanyi sanyi kasala kasala haka,sam bata jin nauyin jikinshi akan nata sai ma yanayin da hakan ya jefa ta,     idanunta na'a rufe sam tagaza buɗesu ba don komai ba sai don tsoran abunda zai biyo baya,a matuƙar tsorace take hakan yasa ko kwakkwaran motsi tagaza yi,lumshe idanunshi yayi yayin da hancinshi ke gogar fatar wuyanta,fragrance ɗin turarenta ne yake kaimashi ziyara acikin hancinshi,ƙamshin ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,har lokacin tana jin yarda numfashinshi ke fita afatar jikinta,   almost 15mins suna cikin wannan yanayin,tajiyo hannunshi a hankali ya zura shi adai dai saitin waist ɗinshi don ya gyara ɗaurin towel dinshi,wannan moving ɗin da ya runka yi da hannunshi awurin yana gogar jikinta ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,amace ta mace gaba ɗaya tashiga wani irin yanayi na daban....,    sai da ya samu ya ɗaure towel ɗin sannan a ƙaro na biyu ya ɗago da kanshi don ya raba jikinshi daga nata,nan take sehrish ta saki wata irin razananniyar ƙara gaba ɗaya ta gigita shi,ashe raɗaɗin Earring ɗinta ne daya sargafo gashin kanshi ya harɗe acikin ɗan kunnan,wannan ɗagawar da zaiyi ajikinta shine sumar kanshi taja ɗan kunnan nata da ƙarfi wannan ne dalilin dayasa ta fasa ƙara,cikin sauri Sgr ya mayar da kanshi tare da kwantar dashi agafen fuskarta,fashewa da kuka sehrish tayi sosai saboda ba ƙaramin zafi taji ba,don wurin harya fara fidda ɗigon jini,a hankali ya buɗe blue eyes ɗinshi tare da bin kunnan nata da kallo yarda sumar kan nashi ta harɗe acikin earring ɗin shine yafi komai bashi mamaki,tunani ya soma yi taya za'ai ya cire gashin nashi acikin ɗan kunnan nata?dole akwai buƙatar yabi a hankali wurin zagayo da hannun na dama don ya cire shi,    A hankali ya ɗago da fuskarshi daga gefen fuskarta,ya kasance cewa suna facing ɗin juna sosai,hatta numfashinsu yana haɗewa dana juna,wannan shessheƙar kukan da takeyi ne yaja hankalinshi wurin kallon fuskarta,la66anta har kerma sukeyi yayin da idanunta ke arufe,   Muryar shi ce ta katseta da cewa"I don't wanna hear that sound again,"   Cikin sauri sehrish ta tsagaita dayin kukan gaba daya,ta koma tana faman sauke ajiyar zuciya,   buɗe idanunta tashiga yi waɗanda ke cike tab da ruwan hawaye,tun kafin ta ƙarasa ware idanun nata take hangen hasken blue ɗin kwayar idanun shi,a hankali ta ƙarasa buɗe idanun sosai akan kyakkyawar fuskarshi dake fuskantar tata,duk da irin bugun zuciyar da take ji amma hakan baisa ta mayar da idanunta ba ta rufe su,    A natse ta soma bin pink lips ɗinshi da kallo shape ɗinsu ba ƙaramin kyau ne dasu ba,tausasan gaske,mayar da eyes ɗinta tayi akan dogon hancin shi da tsinin ke dab da nata hancin,ta jima tana kallon hancin nashi daga bisani kuma a hankali ta aza idanunta acikin nashi nan take taji wani irin bugun zuciya,     sai faman lumshe idanunshi yake yana kuma opening ɗinsu saboda baccin da yake ji,dama agajiye ya dawo cikin gidan,a hankali yake ɗan waresu akan idanunta,anatse yake bin long eyes lashes din idonta da kallo,har yanzu akwai sauran tears dake dripping a cikin idonta,sun jiƙa eyes lashes ɗin nata sharkaf,    Eyes balls ɗinta yabi da kallo a lokacin itama nata na'a kan kwayar idon tashi tana ƙarewa launin idon nashi kallo,kasa janye idanunshi yayi acikin nata,kamar yarda itama tagaza janye nata acikin nashi duk da tsoran kwayar idon nashi da take ji,    Suna cikin wannan yanayin a hankali ya zagayo da right hand ɗinshi ta saman kanta,ya ƙaraso dashi wurin ɗan kunnan nata sannan ya haɗa da hannun shi na hagu ya shiga ƙoƙarin cire gashin nashi daga jikin earring ɗin nata,         runste ido sehrish tayi saboda zafin da take ɗan ji a wurin,ganin hakan yasa ya haɗe fuskokinsu awuri guda,jin yarda lips ɗinsa suka manne da nata tamkar zaiyi kissing ɗinta hakan ba ƙaramin rikitar da ita yayi ba,    duk yarda yaso ya cire gashin daga jikin ɗan kunnan abun ya gagara ganin hakan zai 6ata mashi lokaci yasa yayi deciding tsinka gashin kan nashi daya sargaho earring ɗinta,    Cikin sa'a ya katse gashin nashi yabar mata sauran siraran da suka ruƙo dan kunnan nata,    Sai da ya raba ɗan kunnan sannan yaji wata irin kasala ta baibaye shi,lokaci guda ya rasa karfin janye jikinshi daga nata,ya dai samu ya ɗan janye face ɗin shi daga nata,sai kan head ɗinshi ya koma asaman boobs ɗinta,lamo yayi yana jin wani irin yanayin da bai ta6a ji ba arayuwarshi har wani bacci sosai ya dinga fisgarshi,sehrish kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita don bazata iya jurewa wannan yanayin ba,hannunta na asaman waist ɗinshi ta ƙankame shi sosai ajikinta,hada ƙarin hakan ya ƙara kashe mashi nashi jikin,   Mamakine ya kama hayaam ganin cewa har yanzu Yarinyar bata fito daga part ɗin sgr ba,ashe tun bayan da sukayi magana da sehrish ta koma bedroom ɗinta sam tagaza samun natsuwa shine ta dinga leƙowa don taga ko yarinyar ta fito daga part ɗin nashi,amma shiru babu alamar cewa ma zata fito,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,nan tashiga zargi kala kala acikin zuciyarta tana cewa"ko uban mi ya tsayar da ita ɗakin shi a irin wannan lokacin,ni dama banyarda da yarinyar can ba,daga ganinta irin sumu-sumu kasau ɗinnan ne,wlh saina yi maganinta bazan bari taci gaba da shiga sashen shi ba,     tun tana sa ran fitowar sehrish harta haƙura ta koma bedroom ɗin data sauka,shiga ciki tayi tana ta faman sambatu kamar wata zararra duk akan sehrish ne take wannan 6acin ran,      ****************** *Junaid Romeo* Bacci yake yi amma gaba ɗaya jikin shi kerma yake yi sosai da sosai,sai faman mutsu mutsu yake yi da alama baijin daɗin jikin shi,wata irin Zufa ce take tsattsafowa daga jikin shi saƙo da lungu na jikinshi gaba ɗaya ya kasance ajiƙe yake sharkaf,a wani irin firgice Junaid ya farka arazane yana faman zazzare manyan idanunshi da suke cike tab da kwalla,   Yana ƙoƙarin kai hannu ya tashi Abbansu dake kwance a gefen shi,sai ga wani baƙin hayaƙi ya fito daga Cikin mirror ɗin ɗaƙin mai yawan gaske baƙi wulik,bin hayaƙin junaid yayi da idonshi yana kallon shi a matuƙar tsorace,tattarewa hayaƙin yayi wuri guda kai tsaye ya nufi wurin shi,gaba ɗaya ya tunkare shi,ganin hakan yasa junaid faɗawa jikin abban nasu tare da ƙanƙame shi gaba ɗaya duk yabi ya firgice,kafin Abban nasu ya farka tuni wannan baƙin hayaƙin ya mamaye jikin junaid ta ƙofar hancin shi yabi ya dinga kurɗaɗawa cikin jikinshi,fashewa da matsanancin kuka junaid yayi yana ambaton sunan abban nasu,"Abba ka tashi dan Allah,abba pls ka tashi,bansan meke shirin faruwa dani ba,Abba ka tashi kaga halin da baby junaid ɗinka yake ciki",   duk wannan koke koken da junaid keyi abun mamaki ko motsi Abban nasu baiyi ba,sosai junaid ya dinga jijjiga jikinshi yana ambaton sunan shi amma shuru bai farka ba,babu alamar cewa zai farkama,    Allah sarki,sun sangartar da junaid sosai wanda hakan yasa bai iya ambaton wata addu'a acikin bakin shi ba,sai ihu da yake yi yana koke koke,ko addu'ar bacci wannan junaid bai ta6a yi ma kanshi ba,saboda ya saba kullum in Abbansu na nan shike yi masu addu'ar su kwanta atare,in kuwa abbansu bai nan anyhow yake baccin shi batare da tunanin yin addu'a ba,tsantsar son da suke yi mashi ne yasa basu son ya wahala ko kaɗan,junaid bai ta6a zuwa islamiyya ba don koyon wani abu na addini,amma Abbansu da kuma ƴan uwanshi suna zaunar dashi su koyar dashi wasu abubuwan sosai,a kwanakin baya har malami abbansu ya samo wanda zai dinga koya mashi karatu,tun rana ta farko da malamin yazo zai koya mashi karatu basu ƙara ganinshi ba,6at aka neme shi aka rasa,kusan sau huɗu hakan na faru duk in Abbansu ya samo malamin da zai koyar dashi addini daga yazo sau ɗaya sai a neme shi arasa,hakan yasa daga baya ya haƙura da neman malaman da zasu koyar dashi,musamman da yaga ƴan uwanshi na koyar dashi acikin gidan sai hankalinshi ya kwanta da hakan,abun da baisani ba kosu da suke koya mashi agabansu yake nuna ya fahimta kuma ya gane karatun amma da zarar yabar wurin karatun tofa komai ya zube acikin kanshi,yadawo zero 0    Wani irin sanyine ya gauraye ko'ina na sassan jikinshi,lamo yayi abayan abban nasu yana faman sauke ajiyar zuciya,a wannan yanayin kuma bacci yayi awon gaba dashi,🥺    Meke shirin faruwa ne!? A hankali ta soma buɗe idanunta dake ɗauke da bacci biji biji ta soma gani kafin daga bisani suka washe ta dinga ganin komai normal,jin babu nauyin mutum akanta yasa ta gane cewa sgr ya bar jikinta,cikin sauri ta miƙe zaune tare da kai idanunta inda yake kwance yana bacci,zuba mashi ido tayi tana kallon shi,yanayin yarda yake baccin zai tabbatar maka da cewa yana cikin kwanciyar hankali da natsuwa,    A hankali takai hannu tare da jan blanket ɗinshi ta rufe mashi jikin shi har wurin wuyan shi sannan ta saki bargon,    tamkar karta tafi tabarshi haka ta dinga ji,hannu takai tare da ruƙo sumar kanshi mai laushin gaske,ta tattare mashi ita tare da yin gefe guda da Ita,hakan ne ya bata damar kallon kyakkyawar fuskarshi sosai,   Cikin sanyin murya tace"inason farin ciki ya cigaba da wanzuwa a wannan kyakkyawar fuskar taka,kuma insha Allah zan tabbatar da hakan,zan cigaba da addu'a akan Allah ya mallakamin kai amatsayin abokin rayuwata,duk da nasan cewa zaiyi wuya hakan tafaru saboda kafi ƙarfina sosai nesa ba kusa ba"    Jiki asanyaye taƙarasa maganar yayin da ta juya tare da saukowa daga saman gadon nashi,sai da tafara kashe mashi hasken ɗakin sannan ta fuce daga part ɗin nashi,   A 6angaren Amani kuwa tunda tabi bayan motarsu da gudun gaske,bata ci nasarar taddo tasu motar ba saboda suma gudun sukeyi tuni sun 6ace ma ganinta,jiki asanyaye tayi parking ɗin motarta agafen titi,tamkar zata fashe da kuka haka ta dinga ji,hannu takai tare da ɗaukar wayarta dake ajiye asaman laps dinta,missed calls ta gani na Abbas har kusan shida,duk bata ji ringing ɗin da wayar keyi ba,saboda bata cikin natsuwarta hankali atashe tace"nashiga uku!Ashe abbas ya kira ni bansani ba,yanzu mai zan faɗa mashi,gashi ban hadu da wadda akace Amal ce..."    fuskarta a yamutse tayi maganar,yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin dialing ɗin numbarshi tabi kiran da yayi mata,tana fara ringing ya ɗaga kiran,cikin sauri takara wayar a kunnanta,saurarawa tayi tana jiran jin me zaice,    "Ki dawo gida inason ganinki," Yana faɗin hakan yayi rejecting ɗin kiran nata,   Nan fa ido ya raina fata,a kasalance ta tashi motar tare da karya kwana ta miƙi hanyar komawa gida, ************************* Sosai Amal ke kuka tana ambaton sunan Allah abakinta duk tabi ta zauce,   Rai a6ace JAHAN yace"yarinyar nan tayi mun shiru!nagaji da jin tsiwarta,duk tabi tayi confusing ɗina,Ayaan kodai ka toshe mata baki ko kuma in dakatar da driving ɗin nan don ni bazan juri tsiwarta ba,"    cikin sanyin murya Ayaan yace"pls take it easy Jahan,yarinyar nan fa ba ƙaramin jiki take ji ba,ita kanta bazata iya control ɗin kanta ba saboda raɗaɗin ciwon da take ji,"   Uban tsoki jahan yaja yana faman hura hanci,adai dai lokacin suka ƙaraso da Amal katafaren asibitin sgr,shiga da motar ciki yayi tare da samun wuri yayi parking ɗinta,fitowa Ayaan yayi kafaɗar shi ɗauke da Amal kai tsaye ya wuce da ita cikin asibitin,   Jahan kuwa zaman shi yayi acikin motar yana jiran ƙarasowar ayaan ɗin,don yace bazai shiga cikin asibitin ba,ya miƙata kawai ya fito su juya,    Ayaan na shiga ciki da sauri reception nurses suka kar6e ta,tare da wuce wa da ita medical room don a kwantar da ita,    tsayawa yayi yana faman zarya a wurin,kiran jahan ne ya shigo wayarshi cikin sauri ya ɗaga kiran tare da karata a kunnan shi,    tunkafin yayi magana jahan yace "what are u waiting for Ayaan!tun da ka miƙa ta awurinsu ka fito kawai mu juya gida,"    amsa mashi yayi da okey,sannan ya kashe kiran,   harya juya zai fita daga corridor ɗin,yajiyo muryar wata nurse tana dakatar dashi,tsayawa yayi tare da juyawa yana kallonta,ƙarasowa tayi da sauri cikin harshen turanci ta soma yi mashi magana"sir yarinyar taƙi bari mu dubata,da alama tana da damuwa sosai,akwai wani suna da take ta ambato abakinta,in badamuwa muna so ka shigo daga ciki kayi mata magana,may be ta samu natsuwa,"    batare da musu ba,Ayaan yabi bayanta har cikin ɗakin da suka kwantar da Amal,sai faman kuka takeyi tana kiran Sunan Aunty amani,tana cewa dan Allah su kira mata ƴar uwarta karta mutu bata sata a idonta ba,    ganin shi yasa sauran nurses ɗin dake aciki suka ja da baya tare da bashi wuri don ya wuce,   Ƙarasawa ayaan yayi tare da samun wuri daga gefen gadon da take kwance,yama rasa ta yarda zai shawo kan yarinyar don tayi nisa bata jin kira sai faman sharara kuka takeyi ta cika ko'ina da kukan nata,    tsawa ya daka mata,aikuwa a firgice ta mayar da idanunta akanshi yayin da jikinta yashiga yin kerma saboda tsoran da taji,   Yarda ya zare mata idanunshi ba ƙaramin tsoro taji ba musamman launin kwayar idonshi da takasance ash colour,   Lokaci guda tayi tsit tana faman zazzare idanu,   dama yayi mata hakan ne don tayi shiru,sassauto da murya yayi tare da cewa"faɗamun menene damuwar?bakyaso ne ayi treating wounds ɗin dake ajikin ki?ko so kike ki mutu ne?   Cikin shesshekar kuka tace"banso na mutu,inason ganin Auntyna ne,dan Allah ku kira mun ita tazo naganta kafin na mutu,inason ganinta,"    tsananin tausayinta ne ya kama shi,bin idanunta yayi da kallo ganin yarda hawaye ke kwaranyo daga cikinsu,yarinyar dae ba ƙaramin jiki taji ba da alama,    ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa"yanzu baki da lafiya,ki bari su duba jikinki,in yaso zuwa gobe ni dakaina zan kira maki auntynki a waya,kin amince da hakan"?    amsa mashi tayi da eh,sannan ya miƙe tare da yi masu sallama,ya fuce daga asibitin,    shaf shaf suka bar Asibitin da motarsu, Koda Amani ta koma gida,abbas baiyi mata faɗan komai ba,ko tambayarta inda taje baiyi ba,hakan ba ƙaramin daɗin yayi mata ba,dama fargabarta kenan karya tuhumeta akan ina taje acikin daren nan, *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. _💋Boss Bature💋_ قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Amalil Islam Kwance take saman gadon asibitin hankalinta kwance sai faman sharar bacci take,tasamu kulawa sosai wurin nurses ɗin nan gaba daya duk wani rauni da taji anyi mata dressing ɗin wurin,a daren jiyan nan har ƙarin ruwa su kayi mata fiye da leda ɗaya don taji jiki,da safe kuwa kyakkyawan breakfast tasamu na kyauta da suke rabawa asibitin,sai da taci tayi hani'an sannan tafara wannan baccin,har farkawa tayi tana neman waɗanda suka kawota asibitin don su kira mata Auntynta kamar yarda ɗaya daga cikinsu yayi mata alƙawarin cewa zai kira mata ita, nurse ɗin dake kula da itace ta sanar da ita cewa basu zo ba,sam hankalinta bai tashi ba,don ita ji take koda basu zo ba,ba inda zataje ita fa tayi gida acikin asibitin don ba ƙaramin daɗinshi take ji ba, Wuraren ƙarfe 12,Motarsu Jahan ta shigo cikin katafaren asibitin,a hankali sukayi mata gurbi a parking space ɗinsu,ɗagowa jahan yayi tare da kallon ayaan dake a gefenshi yace"zan jiraka anan and don't keep me waiting"    Wurga mashi kallo Ayaan yayi tare da cewa"bro kai fa baka da imani na lura,jiya kaine kayi causing accident ɗin nan,yarinyar ta raunata amma ko zuwa ciki ka leƙata bakayi ba,atlease ya kamata kaje ka dubata yau,"    ɗaure fuska Jahan yayi yace"bani ne Sila ba!yarinyarce ta fado mana agaban moto dinmu all of a sudden,har nagaza cin burki,so am not guilty,'    Cikin lallashi ayaan yace"pls mu shiga atare mana,"yarda yayi maganar da ƴar shagwa6a afuskarshi yasa Jahan cewa"taci albarkacin wannan shagwa6ar da kayimun da ba don haka ba,ba inda zanje,"    Murmushi Ayaan yayi tare dasa hannu ya buɗe motar ya fito waje,shima Jahan ya fito daga cikin motar,atare suka jera tare da nufar interior din asibitin,    Ayaan ne ya fara shiga room ɗin da aka kwantar da Amal sannan jahan yabi bayansa suka shiga ciki atare,   Lokacin da jahan ya aza idonshi akan Amal dake baje saman gadon tana sharar bacci,a wani irin firgice yaja da baya yana faman zare ido,   Kallonshi ayaan yayi tare da cewa"meya faru ne bro?naga kamar ka tsorata da wani abu,   Nuna amal yayi da yatsan shi tare da cewa"Ayaan dama wannan halittar muka kwaso acikin motar mu jiya?shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu Ya ilahi da nasan hakane da ban sha wahalar ɗaukota ba Allah,dole ayi mana wankin mota yau,"    baki asake ayaan ke kallonshi,duk wani wulakanci da anzo kan Jahan to an ƙare,don shi kankat ne dama yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauko ɗabi'un mahaifiyarsu da halayyarta kaf bai bar komai ba,"    girgiza kai kawai Ayaan yayi tare da wucewa wurin gadon da Amal take,wuri yasamu asaman chair ɗin dake fuskantar gadon nata ya zauna yana kallonta gwanin ban tausayi,   Jahan kuwa koda ya matso wurin bed din nata,goya hannun shi yayi asaman ƙirjin shi yana binta da kallo a ƙyamace yace"Anya Ayaan yarinyar nan ma tana numfashi kuwa?karfa mu ƙarasa gawar da ba tamu ba"   Murmushi kawai Ayaan yayi tare da kai hannu ya dan bubbugi pillown da Amal ta kwantar da kanta sama,   Firgigit ta ware idanunta tana faman binsu da kallo ganin mutum biyu iri ɗaya,hannu tasa tare da ɗan murza idanunta tana ƙare masu kallo, lokaci guda ta gane cewa identical twins ne,    "Barka da safiya,ya jikin naki,"?ayaan ne ke tambayarta fuskarshi asake,hakan ne yasa ta gane cewa shine na jiyan nan da yayi mata alƙawarin kiran Auntynta,   Ƙoƙarin tashi Amal tashiga yi,cikin sauri Ayaan ya taimaka mata ta zauna tare da dan tada bayanta a jikin pillown,    Cikin sanyin murya tace"Alhmdllh,naji sauƙi sosai,"    "Kinyi breakfast"? Ya kuma tambayarta,ɗaga mashi kai tayi alamar eh,   Lumshe idonshi yayi tare da cewa"Masha Allah,so now tell me, how can i help u? Zuba mashi ido tayi tana kallonshi,hakan ya tabbatar mashi da cewa bata gane me yake nufi ba,don haka yace"ina nufin taya zan iya taimaka maki ne?wurin haɗuwa da Auntyn naki"?   Cikin sauri tace"ina da numbarta akaina," Amsa mata yayi da okey,sannan ya zura hannunshi acikin trouser pocket dinshi ya ciro wayarshi,karanto mashi numbar Amal tashiga yi shi kuma yana dialling numbers ɗin acikin wayarshi,bayan ya kammala rubuta numbar ya buga call ɗin nan take Sunan Matar yaya ya bayyana akan wayarshi,tsananin mamaki ne ya kama shi aranshi yace wannan ae numbar Amani ne matar Yaya Abbas,kanshi ya gama ɗaurewa a lamarin,har kiran ya katse amani bata ɗaga ba,almost 6 times yana kiran numbarta amma ba'a daga ba,hakan yasa ya ɗan dakata tare da kallon Amal yace"idan ba damuwa inason jin yaya kuke da Auntyn nan taki da kika ban numbarta....'tunkan ayaan ya ƙarasa maganar jahan ya buga tsoki tare da cewa"Ayaan am tired ka tashi kawai mu tafi,bansan menene amfanin tambayarta ba,    mayar da idonshi yayi akan na Jahan yace"pls ka bani time,zan faɗa ma dalilin dayasa nake tambayarta,"   tsuke fuska jahan yayi yana faman hura hanci,    "Ina sauraronki," muryar ayaan ce ta katse mata tunanin data tafi,   Murya asanyaye tace"ƴar uwatace ita,na jima ina nemanta bamu ta6a haɗuwa da ita ba,ita ma kuma nema na takeyi,tunda tayi aure na rabu da ita,shine yanzu nasamu sunan garin da take nazo,amma bansan a ina zan sameta ba,abu ɗaya kawai nake dashi numbar wayarta,drivern daya kawoni ya kirata a waya ya sanar da ita cewa tazo ta ɗauke ni,batazo ba shine wasu mutane suka biyoni acikin tashar,wannan ne dalilin dayasa nayi gudu harna faɗa saman titi Motarku ta buge ni.........'    jinjina kai Ayaan yayi tare da cewa"Yanzu idan na kaiki gidan Auntynki,Ni kuma wani tukuici zaki bani,"    cike da mamaki tace"kasan inda take ne"?   Lumshe idonshi yayi tare da cewa"a'a bansan inda take ba,amma inaso zan kaiki wani wuri in ba damuwa,bari nasa doctor ya sallame ki,sai mu tafi atare,Zaki bini?    shiru ta danyi tana tunanin karfa tayi gangancin binsu wani abu ya faru da ita,tunda ita dae batasan ko su wanene ba,amma ta wani 6angaren taji cewar zata iya binsu saboda ta yarda dashi sosai,ba don komai ba sai don yarda yake yi mata magana cikin lallami,"    amsa mashi tayi da eh,miƙewa ayaan yayi daga saman chair din,ruƙo hannun jahan yayi tare da janshi gefe guda yace"ko kasan cewa numbar da yarinyar can ta bani na kira mata auntynta,ta matar Ya Abbas ce Amani!"   Fuska ɗauke da mamaki Jahan yace"Really?kenan ƙanwarta ce ita,amma indai hakane ya akai ita yarinyar ta kasance haka?   Ayaan yace"abunda nake tunani kenan nima,"    jahan yace"Ba shakka,dama na jima ina tunanin taya akai Ya ishaq da Ya Abbas suka auri waɗannan matayan nasu,Nidae raina ya jima yana bani cewa matsiyatan talakawa ne,saboda koda mu kaje ɗaurin aure fa a maid,bakaga tsohonsu ba wani zararre dashi,yadin jikinshi duk ya koɗe,zariyar wandonshi fa har ƙasa take ja,abun kunya...'   Rufe mashi baki Ayaan yayi cikin sauri saboda yarda yake magana yana ɗaga Voice ɗinshi,yarinyar zata iya ji,    "Pls jahan its okey,mubar wannan zancen nidae yanzu so nake mu ɗauki yarinyar mukaita gidan Auntyn nata...'tunkan Ayaan ya ƙarasa maganar Jahan yace"Wai a motar wa kake nufin za'a kaita?ae wlh waccan sauran ramin bazata ƙara zauna mana a motar mu ba,sai dai ka tsaida taxi ta kai ku atare,ni kaga tafiyata"yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da fucewa daga cikin room ɗin,    girgiza kai kawai Ayaan yayi tare da cewa"sai yanzu nasan da wa nake tare,Jahan sam baka da mutunci,haihuwarmu kawai akai atare amma zuciyoyinmu ba iri ɗaya bane,ni ta 6angaren Abba nake kai kuma ta 6angaren Mommynmu kake da kuma Ammi dama sune masu zafi,' Batare da 6ata lokaci ba,Ayaan yasa aka sallami Amal ba don komai ba sai don yayi suprising ɗinta,kamar yarda jahan yace sai dai su hau taxi hakan ce tafaru,a bakin Hospital ya tsayar masu da taxi suka shiga ciki atare, **********************Reeshi Zaune suke acikin class sun natsu suna sauraron karatun da akeyi masu,malaminsu ne mai koyar dasu islamic studies,tun da ya fara karatun ya lura da yarinyar dake kwance tana yi mashi bacci acikin class,shiru kawai yayi baice komai ba,sai da ya kammala karatun sannan yace"wacece waccan yarinyar dake yi mun bacci acikin class"?ya tambaya yana nuna sehrish da maker ɗin hannunshi,   kamar jira ƴan class ɗin sukeyi ya tambayesu nan fa kowa yashiga bada bayani,    "Uncle ae wannan yarinyar da kake gani sleeping sickness gare ta,ba'a ta6a yin darasi ba idonta biyu,kullum cikin bacci take kamar mai tsohon ciki," fashewa da dariya ƴan class din sukayi,   Wani kuma yace"sir,da zarar tearcher ya shigo cikin class shikenan zaka ga ta fara hamma,daga nan sai bacci,"    Bayan ya gama sauraron bayanansu,ya taka ya ƙarasa inda seat din sehrish yake,hannu yasa tare da ɗan bugun desk din,a firgice sehrish tafarka tare da ɗago da kanta daga saman desk ɗin tana kallonshi,    jallabiya ce ajikinshi fara,ya tara dogon gemu,kana ganinshi zaka san cewa ba ƙaramin malamin addini bane,fuskarshi na manne da farin glass yayin da kanshi ke anaɗe da rawani,     hankali tashe sehrish ke kallonshi tayi wuƙi wuƙi da ido saboda tsoran karya hukunta ta akan baccin da take yi mashi a class,    Cikin harshen larabci yace mata ta miƙe tsaye,jiki na rawa sehrish ta miƙe tana faman zazzare ido,    "Kalli cikin idona,"ya bata umarni,sunnar dakai sehrish tayi tana faman jin wani irin bugun zuciya,maimaita mata ya sake yi da cewa"bakiji me nace ba!ki kalli cikin idona!"    ƙin ɗagowa tayi da idonta ta kalleshi,kuma nan take jikinta ya shiga yin kerma,   Ƴan class ɗin duk sun zuba ido suna kallonsu,musamman amrish da tashiga damuwa ganin kamar malamin nason takurawa ƙawarta,   Cikin sauri tace"pls uncle ayi mata afwa,bazata ƙara ba,'   Batare da ya kalleta ba yace"Amrish ba laifi tayi mun ba,in fact nikeson taimakonta,shin wannan yarinyar ƴar wani gida ce"?ya tambaya yana jiran amsarsu,har lokacin sehrish na tsaye kanta na kallon kasa a matuƙar tsorace take,    amsa mashi su kayi da cewa"bamu san a wani gida take ba,lokacin da aka kawota class ɗinnan tayi introducing ɗin kanta amman bata faɗa mana family status ɗinta ba,,'   Amrish tace"nima bansan taƙamaimai daga inda take ba,amma akwai wani elder bro dinta dana sani sunan Shi Junaid romeo,muna shiri sosai dashi,'   mayar da idonshi yayi kan fuskar sehrish yace"Ke!a wani gida kike?su wanene iyayenki?   murya na rawa tace"Ni....ni..daga family din SALAHUDDEEN HUSSEIN nake Abban sojoji....'tunkan ta ƙarasa maganar malamin ya waro ido waje yana kallonta,bama shi ba hatta sauran student ɗin cike da mamaki suke kallonta,sun jinjinawa gidan da tafito bakomai yafi ɗaure masu kai ba face yarda ta kasance ba ruwanta da kowa haka,bayan duniya tasan da zamansu,   "Kina nufin ke ƙanwar Surgeon genaral rafayet ce!da marshal Omar!"? Amsa mashi tayi da cewa"eh,"kuma har lokacin bata ɗago da ido ta kalleshi ba,   Jinjina kanshi yayi yana tuna wani abu daya ta6a faruwa dashi wanda ke da alaƙa da gidan,"     gajiya da tsayuwa sehrish tayi nan take idonta suka soma shararo da kwalla,don bata da juriyar wahala irin hakan,tun lokacin data fara rayuwar hutu da jin daɗi,    "Insha Allah bazan fasa ba,kamar yarda nayi kyakkyawar niyyar taimakawa tun a lokacin baya,don haka zan taimaka maki tunda Allah ya haɗani dake," malamin ne yayi wannan maganar,sannan ya mayar da idonshi kan amrish dake zaune a seat ɗinta tana kallonsu yace"Amrish idan na kammala yi maku karatu ki same ni a office ɗina zan baki ruwan addu'a kiba wannan yarinyar tayi amfani dashi," Amsa mashi tayi da toh sir,sannan yaja da baya tare da juyawa ya koma wurin board,    Jiki asanyaye sehrish ta koma tare da zaunawa tana faman sauke ajiyar zuciya,aranta tana mamakin ruwan addu'ar mi zai bama amrish ta bata,gaskiya ni bazanyi amfani dashi ba,lafiya ta lou,koya ban zubarwa zanyi.......'   Sai faman sambatu takeyi ƙasa ƙasa sam takasa samun natsuwa har sai da Malamin yabar Class ɗin,tashi amrish tayi tare da binshi don ta amso mata ruwan addu'ar dayace zai bata. bayan mai taxi ɗin ya sauke su,hannunshi ruke dana Amal suka shiga cikin gidan,gaba ɗaya duk tabi ta susuce tana kallon katafaren gidan duk a tunaninta kodai gidansu ne ya kawo ta? Lokacin da suka shiga katafaren palourn babu kowa acikin shi,tsayawa yayi tare da ita atsaye yana jiran ganin ko wani zai fito,ita kuwa Amal wuyanta kamar zai tsinke saboda kalle kalle muryar Ayaan ce ta katse ta da cewa"har yanzu ciwon na maki zafi?girgiza kai tayi tare da cewa"a'a babu zafi ina lafiya,"   "Okey,ki ɗan ƙara jira nasan matar gidan zata fito ne,bari na sake kiran layinta,"   Hannu yasa tare da ciro wayarsa yana ƙoƙarin danna ma Amani kira,kunnan shi suka jiyo mashi takun takalmanta kwas kwas,ɗagowa su kayi gaba ɗaya suna kallonta,hannunta na ɗauke da tray da alama kayan breakfast ɗinsu da suka ci na safen nan ta fito dashi daga bedroom ɗinta dake a upstairs,jallabiya ce fara ajikinta ta yafa mayafin akanta,   A hankali take saukowa down stairs sam bata lura da mutane ba,ƙura ido Amal tayi tana kallonta sam takasa gane wacece,juyawa ta danyi tare da kallon Ayaan tana neman ƙarin bayani,a lokacin shima idonshi na akanta yace"baki gane ta ba ko"?   ɗaga mashi kai tayi alamar eh,murmushi yayi tare da cewa"Bari ta matso kusa,"   Gyaran murya Ayaan yayi wanda hakan yasa Amani tayi firgit tana kallonsu,murmushi ta saki ganin Ayaan cikin sauri taƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin ta tunkaresu,zuba mata ido Amal tayi tana kallonta tabbas taso ta shaidata amma abunda yayi confusing ɗinta shine,taya zata kasance wadda take tunani tunda saurayin ya kawota gidan tafi tunanin ko Auntynshi ce,   Tunkan Amani ta ƙarasa inda suke,hankalinta yakai ga Amal binta da kallo ta dinga yi cike da mamakin ina Ayaan ya samo wannan yarinyar haka,duk taji jiki kodai ya fara taimakon marayu ne,   tsayawa tayi kusa dasu idonta na akan Amal ita ma kallonta takeyi,ji tayi gabanta na faɗuwa rasss rassss,cikin sauri ta mayar da idonta akan Ayaan murya na rawa tace"who...who is she pls?    Murmushi ayaan yayi yace"i don't even know,ni dai ta bani numbar auntynta ne tace na kira mata ita,shine dana sa numbar Auntyn nata sai sunanki ya bayyana akai,that's why nayi deciding kawota wurinki,maybe adace.........'tunkan ya ƙarasa maganar a firgice Amani ta saki tray ɗin hannunta ya tarwatse ƙasa,zube wa tayi saman guiwowinta kusa da Amal ɗin ta ruƙo hannunta tana cewa"Amal kece dagaske nake gani,ko idona ne Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"!!!   Tuni hawaye sun cicciko acikin idonta,   Itama Amal ɗin tuni ta fara shararo hawaye saboda ta ganeta yanzu musamman data ambaci sunanta,   Cikin shessheƙar kuka tace"Ni...Ni ce aunty Amani,ashe dama zan sake ganinki arayuwata.........'kukane yaci ƙarfinta hakan ne yasa takasa ƙarasa maganar,atare suka fashe da kuka suna yi kamar kamar me,    Muryar Ayaan ce ta katse su da cewa"pls Aunty amani,ki lallasheta akwai wounds ajikinta idan tana kuka hakan zai ƙara mata raɗaɗin ciwon,"dakyar Amani ta tsagaita da kukan nata kallon fuskarta har izuwa jikinta,tayi matuƙar tsorata da ganin yarda yarinyar ta tsotse ta rame ta ƙanjame kamar kwarangwal,ƙashin wuyanta kamar zai ballo waje,komai na yarinyar da zai nuna cewa ita macece babu shi,sai dai ta hanyar shigarta ta mata da kuma muryarta,    Janyota tayi ajikinta tare da rungumeta sosai tana ci gaba da ambaton sunanta"Amal amal ɗita ce ta koma haka?meya faru dake Amal ya akai kika 6ata,ki ka tafi kika barni inata nemanki Amal,"   Ganin halin da suka shiga yasa Ayaan yanke shawarar tafiya yabarsu,juyawa yayi kawai tare da kama hanya ya fuce daga falon dama jahan sai doko mashi calling yake,   Anan ƙasa Amani da Amal suka zauna atare suna fuskantar juna,   "Amal kina jin yunwa"? Jin wannan tambayar yasa hawaye suka ƙara cika mata ido,yaushe rabon da wani ya tambayeta tana jin yunwa harta manta Allah sarki ɗan uwa mai ɗaɗi,musamman in ya kasance shaƙiƙin kane kuma kuna son junanku,    Murya asanyaye tace"bana jin yunwa naci abinci a asibiti,"    Jinjina kai Amani tayi tare da cewa"inason jin Ya akai kika 6ata Amal kika barni?mammy ta sanar dani cewa bakyajin magana wai kina zuwa yawo sun hanaki kin ƙiya shine kika 6ace aka neme ki aka rasa....'    Girgiza kai tashiga yi yayin da hawaye ke cigaba da sharara a idonta tace"Aunty amani wannan duk ƙaryace suke yi maki!nagode ma Allah da ya haɗani dake,a yau inaso zan sanar dake komai game da irin cin zalin dasu Mammy sukayimun na raba ni dake,    Hankali tashe Amani ke kallonta murya na kerma tace"faɗamun meya faru dake!wani irin cin zalin su kayi maki,"   Batare da 6ata lokaci ba,Amal ta zayyana mata duk irin ƙarairayin da sukeyi mata akan cewa ta 6ace,da kuma irin wahalar da takesha a hannunsu da kuma kaita da sukeyi gidan makwabtansu ana kulleta,babu abunda Amal ta 6oye mata kaf takwashe ta sanar da ita,   A kiɗime Amani ta miƙe tsaye cikin tsananin 6acin rai,jikinta har kerma yake yi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga shararowa a idonta,    Sai faman cizon yatsa take yi tana danasani,kai aƙarshe data rasa abunyi sai ta sake fashewa da wani matsanancin kukan tana girgiza kai tana cewa"Wlh bazan ta6a raga masu ba!mugaye azzalumai kawai,banta6a ganin mutane masu zuciyar kafirai ba irin tasu,Sun cutar dake Amal kuma sun cutar dani sun yaudareni sunyi mun ƙarya suna samun kuɗi awurina na cewa za'a ba malamai suyi addu'ar neman sa'a akanki ashe duk ƙarya ne!!!!basu tsaya a iya kanmu ba sun cutar da mahaifiyarmu har saida tabar duniya ga mahaifinmu da suke ta gana ma azaba,nayi tunanin soyyaya suke nuna min ta ƴan uwantaka shiyasa na saki jiki dasu har nake ƙoƙarin taimaka musu wurin cimma wannan mummunan ƙudirin nasu,ashe cutata suke suna can suna gana ma ƙanwata azaba,na cuci kaina!tun yanzu Allah ya fara nunamin irin kuskuren da nake ƙoƙarin yi na taimakama waɗancan bijimayen.......'tsagaitawa tayi da maganar tana faman shessheƙar kuka,daga bisani ta ɗaura da cewa"wlh saina tarwatsa duk wani plan ɗinsu uban kowa ya rasa don bazan kyalesu ba,muddin ina numfashi hayaam ko abra ɗaya daga cikinsu bazai ta6a auran jinin salahuddeen hussein ba!!!!, abun ba ƙaramin ƙona ma Amani rai yayi ba,ta fusata ainin zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda 6acin rai, Hannu tasa tare da matse kwallarta sannan ta juya tare da takawa takai hannu ta ruƙo hannun Amal ta miƙar da ita tsaye,sannan ta wuce da ita cikin bedroom ɗinta gado ta nuna mata tare da cewa"Amal ki kwanta ki huta kin raunata sosai,amma karki samu damuwa tunda Allah ya haɗaki dani ƙarshen wahalar ki tazo insha Allah,zakiyi rayuwa tare da Auntynki zan baki kyakkyawar kulawa,kuma zan kira doctor domin ya ƙara dubamin lafiyarki da kyau har kiji sauƙi, Ba ƙaramin daɗi Amal taji ba farin ciki har bakinta ya gaza rufuwa,sai da amani ta tabbatar cewa Amal ta kwanta sosae saman gadon sannan ta zauna daga gefen gadon tana kallonta har bacci yayi awon gaba da ita,amani bata bar wurin ba,kallonta take hawaye na zuba a idonta haƙiƙa su Mammy da Aunty babba ba ƙaramin cutarta su kayi ba, Jinjina kai tayi tare da cewa"rama cuta ga macuci ibada ne,Aunty laila kin shiga uku dani,zanbi duk hanyar da zanbi don ganin na tarwatsa plan ɗinki,dama ke jani talau ce sai yarda akai dake sannan kike bi,zanyi amfani da wannan damar wurin lalata shirinki" Haka Amani ta dinga tufka da warwara a ƙarshe ta shirya nata plan ɗin. **************** Hayaam na zaune saman gadonta hannunta ruƙe da wayarta tana jiran shigowar kiran Sofwan,harta fidda rai da zai kawo mata trolley ɗin sai ga message ɗinshi ya shigo wayarta,cikin sauri ta buɗe tana karantawa, _hi beb ya kike ya kwanan gidan surukai ina fata kina lfy,nafa zo gidan ki turo wani ya amsar maki trolley ɗin kayan,don bazasu bar ni nashigo ba_ Jin hakan yasa tayi saurin saukowa daga saman gadon tare da ɗaukar dogon hijabinta dake ajiye saman gadon,zurawa tayi ajikinta sannan tafito daga cikin bedroom ɗin,kama hanya tayi ta fito main palour ɗin tana wurga ido don tasamu wanda zai kar6ar mata kayanta,tana cikin wannan tunanin sai ga Fawan ya fito daga part ɗinsu, kwala mashi kira tayi cike da kisisina tace"Fawan"! ɗagowa yayi yana kallonta da wannan kallon nashi na rainin wayau, cikin sauri hayaam ta nufe shi sai da tazo kusa dashi sannan tace"dan Allah taimako nakeso kayimun,wani brother ɗina ne ya kawo mun trolley ɗin kayana,an hanashi shigowa ciki shine nace ko zaka taimaka ka amso mun," Yatsina fuska fawan yayi tare da cewa"Am sorry ni bazan iya wannan wahalar ba,zan dai kira ɗaya daga cikin security guards ɗin na basu umarnin su barshi ya shigo abokina ne inyaso sai kije ki kar6o kayanki," washe baki hayaam tashiga yi tana cewa"thank u so much fawan,kana da mutunci sosai naji daɗin taimakonnan da kayimun,' ɗan ta6e baki fawan yayi tare da kai hannu ya ciro wayarshi a aljihun rigarshi,call ya buga tare da kara wayar a kunnanshi,ɗaga kiran akayi sannan ya sanar dasu cewa subarshi ya shigo abokinshi ne,amsa mashi sukayi sannan ya kashe kiran, batare da ya kalleta ba yace"kije ki amso kayanki," da hanzari Hayaam ta juya tare da kama hanyar fucewa daga falon sai faman sauri take yi kamar zata tashi sama, Ruƙe ƙugu fawan yayi tare da cewa"Ikon Allah,nifa bangane ma Yarinyar can ba,Naji tana cewa zata amshi trolley ɗin kayanta me hakan ke nufi"?ya jefa ma kanshi tambaya,cizon la66ansa yayi tare da cewa"zaki gane kuranki ne,"yana faɗin hakan ya kama gabansa *💋Boss Bature💋* Wuraren ƙarfe 1:30 junaid ya ɗauko sehrish daga school,tun acikin mota ya lura da yanayinta duk a yamutse babu natsuwa a tattare da ita,har tambayarta yayi ko bata jin daɗine,sai ta sanar dashi cewa bacci ne kawai take ji,jin haka yasa ya ƙara gudun motar har suka ƙaraso cikin gidan, Fitowa tayi daga cikin motar tare da komawa ta buɗe back seat ɗin ta curo school bag ɗinta sannan ta wuce cikin gidan da sauri, Abun ya ɗaure ma junaid kai,ganin ta tafi batare da ta jirashi ba kamar yarda suka saba shiga cikin gidan hannunsu ruƙe dana juna, hannu yakai tare da buɗe motar ya fito bayan ya rufeta,ya kama hanyar shiga interior ɗin gidan,koda ya shiga main palour ɗin kai tsaye ya wuce upstairs bedroom ɗinshi don shima a gajiye yake, wani irin zazza6ine ya rufar mata,dama tun lokacin da suka haɗa ido da wannan malamin taji gaba ɗaya yanayinta ya sauya,tana shiga bedroom ɗinta tayi wurgi da school bag ɗin ƙasa,sannan ta faɗa saman gadonta tare da kwantawa tana faman juyi asaman shi, A wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita, Turo ƙopar bedroom ɗin nata junaid yayi anan ya same ta tana ta faman sharar bacci ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai fuce daga ɗakin karaf idonshi suka sauka akan Bottle water ɗin da malamin nan yaba Amrish takai mata,ashe lokacin da ta shigo ɗakin tayi wurgi da jakar nan take robar ruwan ta gangaro daga cikin jakar,saboda ta manta bata rufe zeep ɗin wurin data sanyata ba, Murmushi junaid yayi yace"Oh ni reeshi kamar wata ƙaramar yarinya,wai yawo da robar ruwa acikin school bag hmmm,"yayi maganar tare da ƙarasawa yakai hannu ya sungumi robar ruwan, Jin salaf babu sanyi ajikin robar ruwan yasa shi cewa"bari naje na sanya mata shi a fridge,zai fi daɗin sha," Yana ƙarasa maganar ya juya tare da fucewa daga ɗakin nata,kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsu,hannu yakai tare da buɗewa ya sanya robar ruwan aciki,sannan ya mayar ya rufe ya kama hanya yabar wurin, After some minutes sai ga su twins sun faɗo cikin main palour ɗin dawowarsu kenan daga masallaci,raba hanya su kayi Jahan ya wuce bedroom ɗinsu,shi kuma Ayaan ya wuce wurin fridge saboda wani irin ƙishin ruwa da ta zo mashi,hannu yasa tare da buɗe fridge ɗin,ya ɗauko bottle water ɗin da Junaid ya ajiye, Buɗe murfin yayi tare da kafawa abakinshi ya shiga ɗaɗɗakar ruwan,sai da yayi rabin robar ruwan sannan ya mayar da ita cikin fridge ɗin ya ajiye, Shafa ƙirjinshi yayi tare da cewa"Alhamdulillalh yanzu naji wani sanyi ya ratsa maƙoshi na," Yana faɗin hakan ya nufi bedroom ɗinsu,lokacin daya shiga samun Jahan yayi kwance yana jiranshi ya ƙaraso, ɗaga kafar da zaiyi kenan yaji gaba ɗaya jikinshi ya shiga jijjiga ta ko'ina,ganin hakan yasa jahan tashi daga zaune yana cewa"lafiya Ayaan meke faruwa ne!! A wani irin galabaice Ayaan ya zube saman guiwowinshi yana ambaton sunan Allah abakinshi,kafin Jahan yayi wani yunƙurin durowa daga saman gadon tuni ayaan ya yanke jiki ya faɗi kasa abaje idonshi na kallon ceilling yayin da launin idanunshi suka 6ace 6aat sai farar kwayar idon, "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un," jahan ne ya ambaci hakan a lokacin da ya ƙarasa durowa daga saman gadon ya ƙaraso a hanzarce inda Ayaan yake, ya zube saman guiwowinsa agabanshi,hankali atashe yake ambaton sunan shi "Ayyaaan!!!Ayaan dan Allah ka tashi!meke faruwa dakai ne rabin raina!!.,....' ganin bai da wata mafita yasa ya miƙe da gudun gaske ya fuce daga ɗakin nasu don yaje ya sanar ma wani, Fitar Jahan ke da wuya,wani siririn hayaƙi baƙi wulik ya dinga fitowa daga ƙofofin hancinshi da kuma bakin shi,da yawan gaske hayaƙin ke kurɗaɗowa ya mamaye ko ina,kafin wani lokaci ya disashe tare da 6ace wa 😳😳😳 *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.     _💋Boss Bature💋_ قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Am really sorry 4 the late post👌 Wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi a jikinshi kamar wanda aka tsamo daga cikin ruwa,lokaci guda yashiga Sakin atishawa yafi talatin a jere suke fitowa daga bakinshi,daga bisani kuma a hankali launin kwayar idonshi ya bayyana,komai nashi ya dawo yarda yake,ganin shi kwance a ƙasa yasa shi yin hanzarin miƙewa tsaye yana tunanin wai menene yakai shi ƙasa kwance?me ya faru dashi ne?hannu yasa yana shafo zufar dake a gefen fuskarshi har lokacin bata daina zuba ba,hakan yasa ya nufi toilet tare da shigewa ciki don yayi wanka, Bai jima da shiga ba sai ga Jahan ya faɗo ɗakin yana atare da kanal yousouf,tsayawa su kayi abakin ƙopar ɗakin,Jahan na mamakin Ina ayyan daya bari cikin wani hali yashe a ƙasa Kallon shi kanal yousouf yayi tare da cewa"Kace mun Ayaan ya faɗi ƙasa jikinshi na kerma,gashi kuma ni banga Ayaan ba,"   Fuskarshi aruɗe yace"Ya yousouf nikaina abun ya ɗaure mun kai,nan fa nabarshi kwance cikin wani yanayi yanzu kuma babu shi a wurin," jin hakan yasa hankalinsu tashi su duka biyun,   tsayawa su kayi kowa da abunda ranshi ke bashi,suna cikin tsayuwar nan sai ga Ayaan ya buɗe ƙopar toilet tare da fitowa jikinshi ɗaure da towel,ga danshin ruwan dake ajikinshi alamar wanka yayi,abun ba ƙaramin ɗaurewa jahan kai yayi ba hatta kanal yousof ɗin,shi kuwa hankalinshi kwance har zai gifta ya hangesu tsaye ta wutsiyar idonshi,hakan yasa ya ɗan ja da baya tare da juyawo yana kallon su,cike da mamaki yace"Ya yousouf!Jahan!meya faru naganku a tsaitsaye kunyi curko curko?ko lafiya,"?    ajiyar zuciya jahan ya sauke tare da tunkarar shi kai tsaye ya rungumo shi ajikinshi yana ɗan bubbuga bayanshi yace"babu komai ayaan,nashiga damuwa ne ɗazu dana ga ka yanke jiki ka faɗi nayi tunanin kowani mummunan abune zai faru dakai that's why nayi deciding kiran ya yousouf don yazo ya duba min kai," ya ƙarasa maganar tare da raba jikinshi daga na Ayaan,    "Nifa lafiyata lou,babu abunda ya faru dani,kawai jiri ne ya ɗan ɗebe ni but now Alhamdulillah har wani ƙarfi nake ji ajiki na,ko in gwada maka ka gani," yarda yayi maganar tare da ɗaga masu damtsen hannunshi ba ƙaramin dariya ya basu ba,girgiza kai kawai kanal yousouf yayi tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,    wucewa Ayaan yayi ya nufi mirror,cikin sauri Jahan ya bishi tare da hugging ɗinshi ta baya ya kwantar da kanshi a saman kafaɗar Ayaan,    Shiru Ayaan yayi yana tunanin mai jahan ke ƙoƙarin yi mashi ne,menene dalilin rungumar da yayi mashi ne hada wani kwantar da kanshi a saman shoulder ɗinshi,bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,yaji hannun Jahan agabanshi yana ƙoƙarin zame towel ɗin jikinshi,aikuwa a wani irin firgice ya ka6e mashi hannunshi tare da yin wurgi dashi gefe guda,sannan ya juyo fuskarshi a ɗaure yace"Jahan bana son iskanci!menene haka?bakasan me ka kama mun bane?so kake ka ciremun towel ɗin jikina ne!"   Murmushi Jahan ya saki tare da cewa"Ayaan banason irin wannan wasan pls,ka riga da kasan abinda nake buƙata a wurinka,"    Fuska ayamutse Ayaan ke kallonshi,ganin hakan yasa jahan tunanin cewa kodai bai jin daɗine duba da abunda ya faru dashi ɗazu,bai ƙara yi mashi magana akan abun ba saboda yasan cewa jarabar tashi zata motsa ne kuma zaizo ya sameshi ne,komawa yayi saman gadon tare da kishingiɗawa yana kallon Ayaan daga kwancen da yake, Ganin yarda jahan ke zuba mashi ido ko kawar dakai baiyi,hakan yasa shi tsuke fuska tare da barin gaban mirrorn ya shige can cikin ɗakin don ya sanya sutura,sa6anin da basa jin kunyar wannan bawani abu bane awurinsu in ɗaya ya tu6e kaya agaban ɗayansu. ❤🤍💛 Around 3:30,sehrish ta farka tana faman murza idanu,ba ƙaramin bacci tasha ba,sai hamma take saboda wata irin yunwa dake cinta,dama ko a school bata wani ci abun kirki ba,hannu tasa tare da yakice hijabin dake jikinta tayi wurgi da ita gefe guda,sannan ta zuro ƙafafunta tare da saukowa daga saman gadon,tsayawa tayi tana kallon school bag ɗinta da tayi wurgi da ita ƙasa bakomai ya faɗo mata a rai ba face Ruwan addu'ar da Malamin nan mai farin glass ya bata,ƙarasawa tayi tare da zuƙunnawa ta janyo bag ɗin,tana dudduba cikinta sam babu roban ruwan aciki,abun ya ɗaure mata kai,hannu tasa tare da zazzage kayan cikin jakar duka amman babu robar ruwan,   Tunanowa tayi da abunda Amrish ta faɗa mata"Ga ruwan addu'ar da malaman yace na baki,kuma yace indai bakiyi amfani dashi ba,ƙusumbi zai fito maki abayanki,"waro ido waje sehrish tayi tuna wannan maganar ta amrish nan take yatsun hannunta suka shiga kerma hatta la66anta,gaba ɗaya duk tabi ta rikice ba don komai ba sai don tsoran ƙusumbin da akace zai fito mata,mugun tsoran ƙumbin take yi saboda taji ana cewa aljanune ke ajiya a cikin ƙusumbin,ƙyamar abun take ji,    Hawaye ne suka soma wanke mata fuskarta murya na rawa tashiga furta"innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, nashiga ukuna!wayyo Allah na,yanzu ya zanyi?nan fa na ajiye robar ruwan nan amma yanzu na duba babu ita.....yanzu shikenan ƙusumbi zai fito min ya suffata zata koma tare da ƙoƙo abayana............'fashewa tayi da matsanancin kuka,anan wurin ta tsugunna tana matse kwalla duk tabi ta rikita kanta,sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe tana faman shasshekar kuka takai hannu tare da tattara books ɗinta tana mayar dasu cikin school bag din,bayan ta kammala ta ɗauke jakar taje ta ajiyeta,    Rage kayan jikinta tayi,ya rage daga ita sai white short da half vest,sannan ta shige cikin toilet cike da kasala,   Ta jima acikin toilet din kafin ta fito jikinta ɗaure da towel,har lokacin idanunta na cike tab da hawaye,zulluminta ƙusumbin da akace zai fito mata,saboda tasan in hakan ta faru hatta Junaid sai ya guje ta,shi da yafi kusa da ita,da wannan yanayin ta kammala shirya kanta cikin wando palazzo maroon colour tare da halter shirt black colour,just imagine it ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,ta ɗame jikinta sam rigar bata da hannu amma ta rufe ƙirjinta har neck ɗinta ta zagaye shi,komawa tayi gaban mirror tana feshe jikinta da turaren nan nata mai ƙamshin gaske,kafin daga bisani ta ɗauko ribbom launin wandonta maroon colour,tattare gashin tashiga yi zata ɗaure shi amma ina duk yadda taso ta haɗe shi wuri guda ta ɗaure abun yaci tura,har wani huci takeyi saboda 6acin ran yaƙi ɗauruwa,tana cikin dambe da gashin,taji ana kwankwasa mata ƙopa,dakatawa tayi da ɗaure gashin tace"Wanene,"   "Auntynki ce,"muryar azmee ce ta bata amsa daga waje,    ƙarasowa Sehrish tayi tare dasa hannu ta buɗe mata kopan,sanye take cikin hijabi hannunta ruƙe da cazbaha fuskar nan ɗauke da murmushi tace"irin wannan kyau haka? . sunnar dakai sehrish tayi tare da cewa"Ina yini aunty azmee,"   "Lafiyalou,tun ɗazu naso nazo na dubaki amma bansamu hali ba,ya school ɗin"?   "Alhamdulillah Aunty azmee," "ina fata kina lafiya,naga kamar akwai damuwa a fuskarki"?   girgiza kai sehrish tayi tace"a'a lafiyata lou,dana dawo ne bana ɗan jin daɗin jikina shine na kwanta nayi bacci sosai banjima da tashi ba,shiyasa fuskata take a haka,"   Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"okey,nagane ina fata kinyi sallah,   "A'a yanzu nake shirin yi," Azmee tace"okey ya kamata ki hanzarta yi time har zai wuce,"   Ta ƙarasa maganar tare da juya zata fita,tsayawa ta ɗanyi tare da jiyowa tana cewa"Oh namanta ban faɗa maki ba,ɗazu da safe da kika tafi school,hayaam ce taje kaima Sgr breakfast ɗinshi,'   Jikin sehrish ne yayi sanyi tunkan ta ƙarasa jin abunda takeson faɗa mata tasoma jin jealous a zuciyarta,   "Yanzu kenan itace zata cigaba da kula da part ɗinshi tana kai mashi abinci"?yarda sehrish tayi maganar taba azmee dariya,saboda a wani irin yanayi na tashin hankali tayi tambayar,    "Kin tari numfashi na baki bari na ƙarasa maganar ba ai,Hayaam takai mashi abinci amma baici ba yace ta mayar dashi saboda shi ba'a sharing a aikinsa,yafison mutum ɗaya daya fara yi mashi aiki yaci gaba da yi batare da an canza mashi wani ba,ko kuma mutum biyu na mashi aiki at thesame time bayaso,"    Wani irin ƙayataccen murmushi sehrish ta saki,farin ciki kamar anyi mata albishir da gidan Aljanna,tama rasa bakin magana sai faman zabga murmushi take,    Azmee taci gaba da cewa"yanzu haka tun safe ba'a gyara mashi bedroom ɗinshi ba,na dai kai mashi breakfast ɗinsa,amma ban gyara ba saboda ba aikina bane,aikinki ne don haka da zarar kin kammala salla ki hanzarta zuwa ki gyara mashi part ɗinshi before ya dawo,"    Dakyar Sehrish ta iya amsa mata da toh,kamar jira take azmee tabar ɗakin tana fita tashiga daka uban tsalle tana rawa don murna,    Sam ta manta da maganar roban ruwanta da take nema,    Sai da tayi salla sannan ta koma gaban dressing mirror ta shafa jan baki launin wandonta maroon colour ba ƙaramin kyau yayi mata ba,bayan ta gama ta kara feshe jikinta da turare sannan ta koma wurin wardrobe ɗinta tare da ɗauko mayafinta,ta yafa shi ajikinta,ta ɗauko takalmi baƙi ta zura a ƙafarta Open toe mai ɗan tsini,sai gashi ta fito ɗass da ita,    hannu tasa tare da buɗe door din ɗakin ta fito tare da kama hanyar fita daga corridor din,   Adaidai lokacin Hayamm ta fito daga masaukinta,itama ta ɗauki wankan lace mai ɗan karan kyau,riga da skirt ash colour,kayan sun matseta sosai,daga saman rigar kamar boobs ɗinta zasu fito waje gaba ɗaga,skirt ɗin kuwa wata tsaga gare shi tun daga guiwar ƙafarta tafara har wurin ƙafarta kana hangen fatar ƙafafunta,high heels ne a ƙafarta tana tafiya sautin na fita kwas kwas,ta cuge ɗaurin ɗan kwali abunta yarda kasan wadda zata gasar miss world    jin takun tafiya yasa sehrish jiyuwa bayanta,har sai da gabanta ya faɗi da tayi arba da hayaam saboda wankan data ɗauka tayi uban makeup kamar wata aljana,bakin nan yasha jan janbaki ta wani cuno shi irin na masifaffu, Tuni sehrish tasha jinin jikinta ganin irin wankan da Hayaam ta ɗauka,ba ƙaramin kyau tayi ba kuma zata ja hankali sosai, kawar da kai sehrish tayi tare da juyawa zata tafi,muryar hayaam ce ta katse ta dacewa"Wait inason magana dake ƴan mata," tsayawa sehrish tayi tana jiran jin me zata ce mata, Koda Hayaam ta ƙaraso,bin sehrish tayi da wani irin matsiyacin kallo tun daga ƙasa har sama sannan tace"nasan gabanki ya faɗi kuma kin tsorata da ganin irin kyau da kuma kyawun sura da Allah yayi mun," ɗaure fuska sehrish tayi batace komai, Hayamm taci gaba da cewa"so nake ki fahimci cewa ni ba sa'ar yinki bace!bansan wani irin shisshigi kike ma Sg rafayet ba da har kika samu matsayi a wurinshi,inaso na gargaɗeki ne, kuma naja kunnanki akan ki fita daga sabgarshi saboda yafi ƙarfinki nesa ba kusa ba,don na lura abunda kike hari kenan,in ma banda haɗama irin taki ina zaki kai mutum kamarsa?dan Allah jibarki fa ƴar ƙarama dake amma sai kankanbar tsiya,wai ma menene connection ɗinki da mutanen gidan nan ne? tayi tambayar tana kallon sehrish yayin da fuskarta ke ɗauke da shu'umin murmushin nan nata, jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba don tuni idanunta sun cicciko da kwalla,daƙyar ta iya shanyesu sannan ta dake tare da cewa"Bansan meyasa kike gayamun waɗannan maganganun ba,da alama dae baƙin cikin ɗazu ne da sgr ya ƙumsa maki shine kikeson ki huce akaina,sannan kuma yaushe nace maki inason shi ne da har kike cewa yafi ƙarfi na?bama wannan ba,Naji kina magana akan cewa menene alaƙata da mutanen gidan to bari na baki amsa," matsawa sehrish tayi dab da Hayaam sannan tace"Ni yar aikinsu ce,biya na suke ina masu aiki kuma suna jin dadin aikina shiyasa nasamu kar6uwa a wurinsu,kuma ina alfahari da hakan,wannan shine alaƙata dasu,ke kuma fa?ƙanwar matar yayansu ce fa?ina alaƙa take anan? Lokacin da sehrish takai ƙarshen maganarta,waro ido waje Hayaam tayi tana kallonta,bata ta6a tunanin cewa yarinyar zata iya mayar mata da martani ba ashe itama ba kanwar lasa bace,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,tuni idonta sun canza launi saboda fusatar da tayi, Sehrish kuwa murmushi ta saki tare da juyawa ta kama hanyar tabar wurin, Wani irin tafarfasa zuciyarta keyi mata,tama rasa mai zatayi ma sehrish ta huce don tsabar takaicin maganar da ta yada mata, "Da ace ban mayar mata da martani ba,dani zan kwana da baƙin ciki," sehrish ce tayi maganar a lokacin da take ƙarasa shiga part ɗin sgr, Sai faman murmushi take saki abunta,wucewa tayi cikin bedroom ɗinshi,wannan daddaɗan ƙamshin turaren nasa ne yayi mata maraba da zuwa,duk da baya cikin ɗakin amma ƙamshinsa ya gauraye ko'ina, Lumshe idonta tayi tare da buɗesu a hankali suka sauka akan shimfiɗeɗen gadonshi,tunawa tayi da abunda ya faru jiya atsakaninsu nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,nan take tashiga tariyo dukkan abunda ya faru jiya a tsakaninsu,musamman lokacin daya kwantar da kanshi asaman chest ɗinta sai taji shi tamkar babynta,hmmmmmm shiga ciki sehrish tayi batare da 6ata lokaci ba,tashiga gyara mashi bedroom ɗin nashi,tamkar sabo haka ta Canza mashi kamanni,bayan ta kammala da bedroom ɗin,ta cire mayafinta tare da ajiye shi daga gefen gadon sannan ta koma cikin toilet ɗinsa don ta gyara mashi, Bata jima da shiga ciki ba,sgr ya dawo cikin gidan,har yanzu wankan ɗazu ne ajikinshi,na warp shirt da black trouser,da alama a ɗan gajiye yake,kai tsaye ya nufi upstairs part ɗinshi,hankalin Hayaam ba ƙaramin tashi yayi ba lokacin data ga gifcinshi yana ƙarasa hawa upstairs ɗin,taso ta tarbe shi tayi mashi sannu da zuwa kota samu yasan ya idonshi acikin nata,amma bata samu damar yin hakan ba,saboda fargabarshi da take ji, A wani irin gajiye ya shiga bedroom ɗinshi yana faman lumshe blue eyes dinshi saboda baccin da yake ji,yana ƙarasawa ciki yasanya hannayenshi tare da ɗebe rigar jikin shi gaba ɗaya,ya azata asaman laundry basket dinshi,zame belt ɗin wandonshi yayi sannan ya zame shi daga jikinshi ya ajiye shi asaman rigar,ya rage daga shi sai shorts ajikinshi, Komawa yayi tare da hayewa saman royal bed dinshi ya kwanta don ya ɗan runtsa,sosai ya miƙe saman gadon yana faman sauke ajiyar zuciya har bacci yayi awon gaba dashi,almost 6 mins sai ga sehrish ta fito daga cikin toilet ɗinshi,tunkarar gadon tayi saboda ta ɗauki mayafinta sai da ta kusa dab da gadon sannan idonta suka hango mata Boss Man ɗin nata kwance yana bacci,wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata har sai da taɗan ja da baya tana kallonshi,hannu tasa tare da ɗan murza idanunta donta tabbatarwa idonta abunda take gani wai ko gizau ne,amma zahiran taƙara shaida cewa sgr ne da kanshi ya dawo, Hankali kwance yake baccin shi,ya zagayo da left hand dinshi ta saman sumar kanshi,yayin da hannun damanshi ke asaman shafaffen cikinshi, Ji tayi bazata juri kallon surar jikinshi ahaka ba saboda gudun jefa kanta cikin matsala,don ba ƙaramin fisgarta yake yi ba,kamar irin magnet din nan, Har ta kama hanyar fita daga bedroom din nashi cikin sauri taji jelar gashinta na gogar hannunta,tsayawa tayi Cak tunawa da Mayafinta data ajiye asaman gadon nashi kafin tashiga gyara mashi toilet ɗinshi,a hanzarce ta juya tana kallon inda ta ajiye mayafin,waro ido waje tayi cike da fargaba ganin yarda sgr ya mamaye mayafin nata gaba ɗaya,ya kwanta asaman shi,tabɗijan can Tunani tashiga yi kodai ta tafi tabar mashi mayafin tunda ba iya ɗaga shi zatayi ba,wata zuciyar kuma tace,idan ya farka ya samu mayafin naki asaman gadonshi bakya tunanin cewa zai iya zargin wani abu akanki?dole ya tuhume ki akan miya kawo mayafinki saman shimfiɗarshi,haka in kika fita ba mayafin wani ya ganki kin fito daga part dinshi haka fa,kiyi tunani sehrish barin mayafin risky ne,haka zalika daukarshi ma zai iya zama risky, Runtse idanunta tayi tamkar ta fasa ihu saboda tsabar takaici,taji haushin cire mayafinta da tayi tun farko da bata jefa kanta cikin matsala ba, Nan fa tashiga tunanin yarda za'ae ta dauke mayafinta batare da Sgr ya farka daga baccin shi ba, cikin sanɗa sehrish ta soma tafiya a hankali tana tunkararshi a tsorace batare da sautin takon tafiyarta na fita ba, Sai da tazo dai dai kusa dashi sannan tashiga cizon yatsa tana tunanin wai ma taya zata janyo mayafin daga jikinshi,Sehrish da kasada, Hannu tasa tare da ɗan kamo mayafin daya leƙo daga bayanshi tana janshi a hankali don ya sulalo daga bayanshi,amma ko motsi wannan baiyi ba don ba ƙaramar danna sgr yayi mashi ba,gaba ɗaya nauyin jikinshi na akan mayafin taya zata iya janye shi!? tun tana jan mayafin a hankali yana turjewa har takai ga hasala tashiga janshi da ɗan ƙarfi har sai da sehrish tashiga fitar da wani irin gumi a fuskarta,sakin mayafin tayi tana faman huci,duk da haka bata daddaraba,sai tasa hannu tare da dafa mattress ɗin ta haye saman gadon kaɗan daga gefenshi,hannu takai zata ruƙo mayafin karaf idonta suka sauka akan farar fatar ƙirjinshi,mayar da idonta tayi akan damtsen hannunshi,haryanzu akwai sauran zanen nan nashi na tattoo bai ƙarasa gogewa ba gaba ɗaya,tun farkon zuwanshi 9ja tare da zanen ajikinshi ya dawo kamar tambari ne na mukaminshi ba ƙaramin kyau yayi mashi ba, Gaba daya sehrish ta shagala da kallon surar jikinshi,kafin tayi wani aune,Sgr yayi wani irin kwakkwaran juyi zai gyara kwanciyarshi,aikuwa gaba ɗaya ya haɗa da sehrish yayi juyin tare da sanya hannunshi yayi hugging ɗinta tighly a faffaɗan kirjinshi,duk a tunaninshi pillow ne ya rungumo hakanne yasa ya matseta sosai a ƙirjinshi kamar yarda ya saba rungume pillow in zaiyi bacci wani sa'in,tashin hankali da ba'a sama shi date, Tabɗijancan,ƙiris ya rage sehrish ta saki fitsari saboda tsabar tsoran da taji,hankalinta yayi matuƙar tashi,saboda tasan mai zai biyo ba in sgr ya farka yaganta manne ajikinshi,yasan na jiya taimakon shi tayi gudun karya faɗi,na yau kuma mai zai kira shi!?meya kawota saman gadonshi da har ta faɗa jikinshi!? yarda ya matseta a ƙirjinshi ko kwakkwaran motsi sehrish ba ta iya yi,ba ƙaramin ruƙo yayi mata ba,tunkan ya farka taga irin hukuncin da zai yi mata harta fara zubar da hawaye,kai tsaye kuma hawayen suke shafar fatar jikinshi, sai faman shessheƙar kuka takeyi ƙasa ƙasa yayin da la66anta ke gogar fatar breast dinshi,gaba ɗaya Wannan jan bakin data shafa ya koma a fatarshi,sosai zanen lips ɗin sehrish ya fito raɗau tare da kalar jan bakinta maroon colour,duk bata lura da hakan ba,saboda la66an nata amanne suke a wurin, Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutum a falonsa alamar ana tunkaro bedroom ɗinshi,hakan ba ƙaramin firgita sehrish yayi ba,nan take tashiga haɗiyar yawu a tsananin tsorace, Muryar Abbansu tajiyo yana cewa"Wai har yanzu rafayet bai dawo bane?inaso naji ko sunyi waya da Mommynshi ne game da zuwanta Nigeria,' "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"sehrish ce ta ambaci hakan acikin zuciyarta,"Shikenan na mutu wayyo Allah na,ya Allah ka kawomun ɗauki,daga wannan sai wannan......'bata ƙarasa zancen zucin nata ba tajiyo muryar Marshal Omar yana bashi amsa da cewa"Abba ashe muna da manyan baƙi cikin watan nan,don munyi waya da goggon katsina ma ta sanar dani cewa mu shirya ma zuwanta don in ta tashi zuwan bazata zata yi kuma ba zata tafi ba har sai taga An shafa fatihar kowannan mu.....' ya ƙarasa maganar da dariya a fuskarshi, Suna tafiya suna nufar bedroom ɗin sgr yayin da suke fira a tsakaninsu, Abban nasu yace"Albishirinka," Cike da zumuɗi Omar yace"Goro," "Fari ko ja"? Abban nasu ya tambaya fuskarshi ɗauke da murmushi, Omar yace"Fari," ƙayataccen murmushi Abban nasu ya saki kafin yace"Uncle ɗinku Abusufyan shima yana nan tafe insha Allah,sannan Auntynku azeema tana nan tafe,uwa uba kuma Ammynku itama tana nan tafe,don haka ku shirya don ta sanar dani cewa muddin tazo sai an ɗaura auran kowannanku,da alama zata zo tayi yaƙi da tazuranci ne acikin gidan nan.....'ƙarasa maganar yayi muryarshi ɗauke da dariya,shima Omar dariyar yayi yana girgiza kai yace"Abba Allah yaso ni,ina da wadda nakeso,don haka ni bani da matsalar komai wlh,Alhamdulillah Allah ya kawota Lafiya musha biki,' Cike da mamaki Abban nasu yace"wai dagaske Omar kana da wadda kakeso?hakan na nufin kayi budurwa baka sanar dani ba"? ɗaga kai Omar yayi alamar eh,wani irin farin cikine ya cika abban nasu har ya gaza magana sai faman sakin murmushi yake yi yana cewa"Ikon Allah," A ƙopar shiga bedroom ɗin sgr suka tsaya suna cigaba da tattaunawa cike da nishaɗi atsakaninsu, Saboda tsabar tashin hankali har wani zazza6i ya lullu6e sehrish tuni temperature ɗin jikinta yayi wani irin zafi,zuciyarta har wani bugu takeyi daram!daram!!fargabarta karsu shigo su same su a wannan yanayin ita da sgr, Hayaniyar da suke yi ce,ta fara disturbing ɗin baccin nashi,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,waro ido waje sehrish tayi cike da fargaba jin alamar zai farka, Hannunshi ya janye daga ruƙon da yayi ma sehrish,hakan ne ya bata damar kufcewa daga jikinshi,kamar walƙiya haka ta mirgina tare da faɗawa ƙasan gadon,sam bata ji zafin buguwar da tayi ba,tana faɗowar nan ta yunkura tare da miƙewa tayi wuff ta faɗa bayan labulan ɗakin shi, Shigarta ke da wuya,Abba da marshal suka shigo cikin ɗakin nashi atare bakunansu ɗauke da sallama, A hankali sgr ya soma buɗe idanunshi dake cike da bacci ga wata irin kasala data mamaye shi don baccin bai ishe saba,daƙyar ya iya sa hannunshi tare da dafa mattress ɗin ya tashi daga zaune tare da jingina back ɗinsa asaman pillow yana kallon Abban nasu tare da Omar sai faman lumshe ido yake yi, Zama Abban yayi daga gefen gadon nashi yana kallon fuskar kyakkywan yaron nashi yace"Rafayet bacci kuma a irin wannan lokacin?ko baka ga time bane? Sai lokacin sgr yakai idonshi akan diamond clock ɗin dake manne a bangon ɗakinshi ƙarfe 6:30 na yamma, lumshe idonshi yayi kafin ya waresu akan Abban nasu yace"Abba bansan time ɗin da baccin ya ɗauke ni ba" jinjina kai abban nasu yayi kafin yayi yunƙurin cewa wani abu karaf idonshi suka sauka akan jan bakin sehrish dake zane asaman breast ɗinshi, waro ido waje abban nasu yayi tare da cewa"Kai me nake gani haka kodai idona ne"?yarda yayi maganar a ruɗe yasa marshal Omar ɗan matsowa daga tsayen da yake ya russina yana ƙare ma Ƙirjinshi kallo,cike da mamaki Omar yace"ba shakka Abba,ba idonka bane wannan alamar sumbata ce,ga zanen la66an mace nan raɗau asaman fatar kirjinshi, Gaba daya sun gama confusing ɗin Sgr,sam bai gane inda zancen nasu ya dosa ba," Hankali atashe Abbansu yace"Rafayet tell me the truth!wa kayi feeding haka har ta goga maka jan baki asaman breast dinka!!!" Saboda tsabar kiɗima tuni jikin sehrish ya soma tsastsafo da wata irin zufa,duk da sanyin ac dake gauraye da ko'ina, Ganin yarda sgr ya dabarbarce kamar bai gane kan me suke magana ba,hakan yasa omar ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinshi,yasa hannu tare da ɗauko ƙaramin madubin dake ajiye asaman shi, Ƙarasowa yayi wurinshi tare da saita mashi madubin yarda zai gani da kyau, Ware manyan idanunshi yayi yana kallon zanen la66an dake asaman chest ɗinshi cike da tsananin mamakin a ina ya same shi....... *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.*💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Ansamu long page🥱 ________________________Zuba mashi ido su kayi suna jiran amsa,Omar yace"pls ka faɗa mana gaskiya kawai,wacece wani abu ya shiga tsakaninka da ita har akasha wannan Love haka?kaga dai daga ni sai Abba babu wanda zaiji abun da ya faru,"wani irin kallo sgr ya wurga yana mashi ƴar harara yace"Omar bana so, ka fara ko"?   Murmushi Abban nasu yayi kafin yace"abunda Omar ya faɗa gaskiya ne,Son bai kamata ka 6oye mana komai ba tunda Allah dai yasa yau asirikinka ya tonu munga komai,ashe kana kula mata har romance kake dasu asaman gado ko?faɗamun ƴarwa ka kwamushe acikin ɗakinka har akai abun arziƙin nan bansani ba,"cike da zolaya Abban nasu ke magana,   ɗaure fuska Sgr yayi tare da haɗe girarsa wuri guda ya tsuke small lips ɗinshi yana kallonsu,yarda suka tasa shi gaba suna tuhumarshi kamar wani ƙaramin yaro ba ƙaramin hasala shi yayi ba,gashi sam ya rasa amsar da zai basu tunda bai isa ya ƙaryata abunda suka gani ba asaman ƙirjinshi,don shi kanshi a ruɗe yake da lamarin abun ya ɗaure mashi kai,taya aka samu jan bakin mace raɗau haka asaman ƙirjinshi!?bai gama zancen zucin nashi ba muryar Omar ta katse mashi tunani,   "Abba zargi fa ya tabbata,kalli ka gani,"Omar ne yayi maganar yayin da yake ruƙo mayafin sehrish dake a ƙasan laps ɗin Sgr ya danne shi,    dafe kirji abban nasu yayi cike da razana yace"ƙalu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Rafayet!wannan fa?ya akai yazo wurinka"?ya tambaya hankali tashe yana kallonshi, Runtse ido sehrish tayi daga 6oyen da take bayan labulen ɗakin,hada ƴan matan hawayenta saboda tsoran hukuncin da zata kar6a,   Cikin sauri sgr ya aza eyes ɗinshi akan mayafin da Omar ya ruƙo a hannunshi just speechless,amace bakin shi ya mutu yama rasa bakin magana abun ya zarce tunaninshi,   Omar ne yace"Abba tunda kaga yayi tsit ya gaza magana,to ya aikata ɗinne kasan mara gaskiya,ni fatan da nakeyi ma Allah yasa iya mayafi ya cire mata bai........'kasa ƙarasa maganar yayi saboda saukar pillow daya ji a saman fuskarshi,hannu yakai zai ƙara rarumar wani pillow abban nasu ya dakatar dashi da cewa"Wannan fa alamar rashin gaskiya ce,tun ɗazu kaƙi buɗe baki ka ce uffan,sai faman ƴan kame kame kakeyi mana,kaji tsoran Allah ka faɗa mana gaskiya,Rafayet yin hakan kuskure ne bai kamata don kana ra'ayin mace ka runƙa kawota har bedroom ɗinka ba asaman gadonka don ka rage zafi da ita ba,in kaga yarinya kanaso Ni zakayi ma magana sai aje masallaci ashafa fatiha kaga shikenan sai a kawo maka ita ɗakinka babu mai jin kanku,taka ce halak malak.....'   Zare blue eyes ɗinshi yayi yana kallon Abban nashi,rai a6ace ya ciji la66ansa tare da ɗago pillown hannunshi ya ɗaga sama zai jefa ma Abban nasu a saman fuskarshi,sai kuma ya saki filon a saman katifar,    Ganin ya dakata yasa Abban nasu cewa"ae fa kai yanzu komai ma zaka iya,saurayin da zai iya kawo mace ɗakinshi har saman gadonshi acikin gidan ubansa meke bazai iya ba Omar? Ya ƙarasa maganar yana kallon Omar dake ƙumshe da dariya yace"of course Abba,ina goyon bayan maganar ka,yanzu sai dai mu bishi da addu'a don na lura yarinyar ba ƙaramin zautar dashi tayi ba tunda gashi har ya gaza buɗe bakinshi yayi mana magana,rashin gaskiya dai baiyi ba,"   gaba ɗaya sun gama hasala Sgr,yama rasa amsar da zai basu su dukansu,a ƙarshe ma daya rasa abunyi kawai sai ya fashe da dariya unexpected,tsananin mamaki ne ya kamasu ganin Sgr yana 6a66aka dariya yau shi da kanshi,yaushe rabon da suga sgr yayi dariya irin haka,white teeth ɗinsa sun fito rairasss,da wuya kaga yana dariya sai dai wannan murmushin nashi na gefen fuska shima kuma in kaga yayi wannan murmushin tofa zai bada horo ne,don ya iya murmushin mugunta,    Hannu sehrish tasa a hankali ta ɗan yaye labulen tana leƙensu,ba ƙaramin bugun zuciya taji ba,kasa janye idonta tayi daga kallon kyakkyawar fuskar sgr da yake ta faman dariya kamar zautacce,gaba ɗaya dimples ɗin fuskarshi sun lotsa sosai abun ba'a magana sai wanda ya gani,suman tsaye sehrish tayi amace ta mace wurin kallon fuskarshi,aranta tana maimaita kalmar nan"tabarakallahu ahsanun khaliqin,"    Har wani duƙar da kanshi yake yi ƙasa yana dariyar hakan yasa sumar kanshi ta ɗan yarfo ta gaban fuskarshi,   Atare Omar da Abbansu suka haɗa baki wurin cewa"ikon Allah,abun mamaki abun al'ajabi,"    Tsagaitawa yayi da dariyar lokaci guda ya ɗaure fuskarshi tamkar dariya bata ta6a wanzuwa a fuskarshi ba,takaici ne dama ya ishe shi shiyasa ya fashe da dariyar,   Cikin sanyin murya yace"joking aside pls,abba nikaina bansan ya akai nasamu zanen lips ɗin nan asaman chest ɗina ba,sannan bansan ya akai mayafin nan yazo bedroom ɗina ba,na rasa ta yarda zansa kuyi understanding ɗina,gaba ɗaya kunyi confusing ɗina,kun tsareni da tambaya kamar wasu lauyoyi,that's why nayi shiru bance komai ba,"ya ƙarasa maganar a kasalance,    Murmushi Abban su ya saki yana kallon face ɗinshi,bakomai ya faɗo mashi araiba face Mommynsu,komai na fuskarshi irin na mahaifiyarshi ne,yafi kama da ita amma akwai wasu abubuwan daya ɗauko na Abbansu,    "Zan shiga toilet,"ya faɗi tare da saukowa daga saman gadon ya kama hanyar shiga toilet ɗin,    Bin bayanshi su kayi da kallo har ya shige cikin toilet ɗin, Sannan Suka janye idanunsu,cikin sauri Omar ya samu wuri tare da zaunawa yana fuskantar abbansu ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Allah ka aurar damu tare, nida Rafayet,kayi mun wannan alfarmar"   Murmushi Abbansu ya ɗanyi kafin yace"Omar bangane me kake nufi ba,har yanzu ɗan uwanka bai janye ra'ayin shi akan mace ba,ni kuma banson na takura mashi,duk da banda burin daya wuce wannan nima,inaso naga auran kowanne daga cikinku,musamman auran shi saboda ina tunanin cewa in soyayya ta shiga zuciyarshi zai rage wannan zafin kan nashi,zai sassauto ya zama tamkar kowa,idan har rafayet baiyi aure ba ya tsaya akan bakanshi,tabbas za'ayi asarar namiji har namiji Omar,bansan ya zanyi dashi ba,"yanayin da abban nasu yayi maganar zai tabbatar maka da cewa abun ba ƙaramin ciwo yake masa ba,   "Abba kadaina cewa bakasan yarda zaka yi dashi ba,shifa ɗanka ne halak malak Allah ya mallaka maka,kuma kana da iko Akanshi,idan yau kaso Abba gaba ɗayanmu zaka iya yi mana aure batare da son ranmu ba ko batare da saninmu ba kuma dole muyi maka biyayya,"    zuba mashi ido Abban yayi yana sauraran bayanin shi, Ƙasa ƙasa da murya Omar yayi gudun kada Sgr yafito daga cikin toilet ɗin yaji abunda suke tattaunawa,   Yasa shi yin hakan sannan yaci gaba da cewa"Abba,namiji irin rafayet,aure akeyi masu batare da saninsu ba,sai dai kawai suji an ɗaura auran...  "   Katse shi abban nasu yayi da cewa"baka tunanin cewa zai iya sakin matar anan take,kasan shifa ba'ayi mashi dole,"?     Murmushi Omar yayi tare da cewa"Abba ka fahimta mana,kaifa kake iko dashi,ka sama mashi mace ta gari wadda kasan cewa bazaiyi dana sanin zama da ita ba,ko kuma ni kaban za6i zan sama mashi macen data dace da rayuwarshi,ka aura mashi ita batare da sanin shi ba,sai bayan an ɗaura auran ka ware rana ɗaya ka sanar dashi cewa Umarnine ka bashi amatsayinka na mahaifinshi,in ya kuskure kuma yasan sauran,"   dariya sosai Abbansu yayi yana sauraron omar dakyar ya tsagaita da dariyar yace"Omar ka iya zolaya Allah kamar mahaifiyarku,yanzu rafayet kakeso nayima auren dole?so kake ya tashi bomb acikin gidan nan"?   "Abba baka fahimce ni ba,tunda muka taso tare da ɗan uwana,komai namu iri ɗaya muke yinshi tamkar twins haka muke,duk abunda nayi rafayet sai yayi shi,haka shima duk abunda yayi nima saina yi shi,yanzu abba aure ne zai banbanta ni da ɗan uwana"?   In serious matter Omar ke magana,wannan yasa Abban nasu ya gane cewa ba zolaya bace yake mashi,har cikin ranshi yake maganar kuma ba ƙaramin jin abun yake ba acikin zuciyarshi,bai gama zancen zucin nashi ba omar yaci gaba da cewa"Abba tuntuni ban ta6a sanar dakai ba,amma yau zan sanar dakai komai,najima inason na cika maka burinka na ganin cewa munyi aure, ba don komai ba sai don saboda farin cikinka,bakomai ne yasa nayi jinkirin yin aure ba face Rafayet!inason aure bawai banaso ba,rafayet shine dalilin dayasa naƙi yin aure,saboda ina ganin cewa kamar banyi mashi adalci ba,inna riga shi yin aure,saboda mun saba komai atare duk wani cigaban da zamu samu atare muke samun shi abba,taya zanso na samu wannan babban cigaban batare da ɗan uwana ba"? Ya ƙarasa maganar muryarshi asanyaye yana kallon Abban nasu, Gaba ɗaya Omar ya gama kashe ma Abban nasu jiki,ba ƙaramin tausaya mashi yayi ba,lalle ba ƙaramar shaƙuwa bace a tsakanin shi da ɗan uwanshi ba,tun da har zai iya hana kanshi wani jin daɗi na rayuwarshi saboda ganin cewa tamkar baiyi mashi adalci bane,    "Abba,na jima ina jiran ganin cewa ɗan uwana ya fara soyayya koya fara maganar aure,amma har yanzu ba wani sauyi abun ba ƙaramin ta6amin zuciyata yake ba,bana faɗi ne kawai saboda nasan faɗin bashi da amfani zan 6ata bakina ne kawae,sau da yawa ina janshi da fira akan mace don na bugi cikinshi naji koya fara ra'ayin yin aure amma kullum babu wani cigaba game da haka,Abba rafayet shine yasa Omar ɗinka ƙin yin soyayya tun da jimawa kuma shine ya hana nayi aure,wanda bani da burin daya wuce wannan arayuwata....,.......'   Kasa ƙarasa maganar yayi saboda siririn hawayen daya zubo mashi a idonshi na hannun dama,   Cikin sauri abban nasu ya sanya hannunshi tare da yin saurin goge masu shi yace"Omar ban ta6a tunanin haka ba,meyasa tuntuni baka sanar dani wannan maganar ba?meyasa nagaza fahimtarku amatsayina na mahaifinku?ashe shaƙuwar dake tsakaninku har takai haka?nagode ma Allah sosai da kuka kasance masu son junanku,ina matuƙar alfahari daku ƴa'ƴana," magana yakeyi yayin da idanunshi suke cike tab da kwalla,   Sehrish kuwa dake la6e bayan labule sai faman shessheƙar kuka takeyi ta rufe bakinta da tafukan dukkan hannuwanta,tsananin tausayinsu ne ya kamata,tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin ƴan uwa masu matuƙar ƙaunar junansu ba irin ahalin salahuddeen hussein,akwai soyayya da shaƙuwa tsakaninsu,zumuncin dake tsakaninsu mai ƙarfi ne sosai,da ace kowane ahali zasu kasance haka da ba ƙaramin cigaba za'asamu ba,amma yanzu zamanin da muke ciki,babu wannan soyayyar atsakanin shaƙiƙai ma,sai kaga na waje ma wani can yafika kusanci da ɗan uwanka shaƙiƙinka,idan kuwa akazo kan shiga matsala ko damuwa tofa zaka ga mutum indai bashi ta shafa ba,babu ruwanshi da damuwa akan halin da ɗan uwanshi yake ciki,sai ma ya kasance ɗan uwanka yana cikin ƙunci da matsanancin damuwa,amma kai kuma hankalinka kwance sai ma ajika kana ta faman tiƙar dariya,mai makon arunƙa jajantawa juna,shiyasa dayawa zaka ga na waje ma wani yafika kusanci dashi saboda yafi damuwa da ɗan uwan naka,wanda dayawa hakan ke jefa rayuwar ɗan uwan cikin hatsari,ba'a janshi ajiki cikin gida tun daga iyayen har ƴan uwan,bakamar salahuddeen hussein ba, ya ɗauki ƴa'ƴanshi tamkar abokanan shi,ƙaramin ɗanshi ma tamkar amininshi ya mayar dashi,kuma hakan yasa basa jin shakkar sanar da mahaifinsu abu in ya same su,ko neman shawara awurinshi,wanda a yanzu zaka ga cewa wani a gidansu tsoro ma yake ji ya sanar cewa wani na cutar dashi awaje,saboda wasu iyaye basa tsayawa su fahimci ƴa'ƴansu daga sun ji abu sai afara hantarar mutum in ƙarami ne kaga an haɗa mashi da bugu ma,babu wannan shaƙuwar ta iyaye,da ƴan uwantaka da har mutum zai iya faɗin damuwarshi acikin gidansu,sai dae ya nemi abokinshi ya sanar dashi halin da yake ciki instead of wani nashi nakusa dashi,daga nan kuma awajen in Allah yasa abokin ba nagari bane shine zaka ga anzo ana danasani, don mafi akasarin mutane na fadawa mugun hali ne ta sanadiyyar abokai,ku yi koyi da wannan ahalin wurin nuna ma junanku soyayya,ku zama naku ku kaɗai babu mai jin kanku👌👍 Sehrish bata bar bedroom ɗin sgr ba,har sai da aka kira sallar magrib suka fita tare da abbansu domin zuwa yin sallar magrib sannan ta samu cikin sauri ta ɗage curtains ɗin,da hanzarin gaske ta sungumi mayafinta sannan da sauri hadda gudu ta haɗa wurin barin part ɗinsa, Saukowa downstairs tayi a lokacin duk sun tafi salla masallaci,kai tsaye kitchen ta nufa tunkan ta ƙarasa ta hangi Azmee da hayaam suna ta haramar kammala dinner ɗin ranar,duk sai taji babu daɗi taso ace tare da ita suka fara,jiki asanyaye ta shiga kitchen ɗin da sallama a bakinta, Juyowa sukayi suna kallonta atare,da alama ma sun kammala aikin nasu,Azmee ce ke haɗawa Hayaam warmers acikin tray tana kaiwa dining, "Kin kammala gyara mashi part ɗin nasa ne?azmee ce ta jefa mata tambaya, "Eh,nagama," "Ya akai kika daɗe acan ne"? Sunnar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta saboda ta rasa amsar da zata bata, Hayaam kuwa sai faman wurga mata harara take yi kamar kwayar idonta zata faɗo ƙasa, Murmushi azmee tayi tare da cewa"ki wuce kije kiyi sallah,kada ki samu damuwa,nasan cewa wani abunne ya tsayar dake," Ajiyar zuciya sehrish ta sauke kafin ta juya tasa kai tabar cikin kitchen ɗin,bedroom ɗinta ta nufa domin tayi sallah, A 6angaren su hossana kuwa,tun bayan da suka dawo daga school suke ta faman saran zuwan Omar amma baizo ba,burin jahad ta sanar dashi cewa taga ƙaninshi a school ɗinsu,gaba ɗaya yinin ranar sunyi shi ne cike da kewar Ya omar ɗinsu musamman hossana ko lunch bata ci ba tunda suka dawo gashi ko'a school ma bataci komai ba,saboda tayi alƙawarin cewa tare da ya omar zasu ci abinci zai bata abaki,hakan yasa taƙi cin komai,duk yarda jahad taso ta fahimtar da hossana akan ta zauna taci abinci sam taƙi,har dai tagaji ta ƙyaleta, sai faman zagaye takeyi acikin bedroom ɗinsu,fuskar nan ɗauke da murmushi ae tunda tayi arba da Romeo sam tagaza samun natsuwa wani irin tsantsar son shi da ƙaunarshi takeji kamar kamar me,fiye da yarda take jin ya omar ma lokacin da taso shi,saboda shi son da tayi mashi hada ƙarin don ta kyautata mashi ne akan irin ɗawainiyar da yake yi dasu,shi kuma kalar son da take yi ma junaid kallo ɗaya tayi ma kyakkyawar fuskarshi tabi ta rikice,kuma tunda Omar ya furta cewa ƙaninshi ne nan take taji ya kwanta mata aranta,sai dai abunda jahad bata sani ba shine,junaid ba babba bane kamar yarda take tunani, **********haroon Gaba ɗaya ya rikita ɗakin nashi wurin neman kuɗin da su Twins suka bashi,sam hankalin shi ya gaza kwanciya yama rasa inda zaisa kanshi,wata irin zufa ce ke gangaro mashi a fuskarshi saboda tsabar 6acin rai,yafi ƙarfin awa 2 yana neman jakar kuɗin amma babu ita ƙasa ko sama,an ɗauke ta daga ɗakinshi babu ita babu alamarta,yayi ma bedroom ɗin nashi kaca kaca wurin binciken inda jakar kuɗin take,kamar zaiyi hauka saboda yarda ya zauce,sun rigada sun gama tsara plan ɗinsu, shirin tafiya kawai ya rage mashi daga zuwa ya ɗauki jakar kuɗin an ɗauketa daga ɗakinshi,gashi ya rasa wanda ya shigo har cikin bedroom ɗinshi ya ɗaukar mashi ita,komawa yayi gefen gadonshi ya zauna yana faman huci kamar wani zaki,tunani ya shiga yi wanene zai iya shigowa ɗakinshi ya ɗaukar mashi jakar kuɗin shi?kodai su twins ne suka yi mashi wayau,don sunsan cewa ya goge videon shine suka ɗauke jakar kuɗin,tabbas kuwa sune saboda su kaɗai ne suka san da kuɗin acikin bedroom ɗinshi, Jinjina kanshi yayi yana huci yace"yara kenan harni zakuyiwa wayau,ƙananun ƴan iska kawai masu kwana da wando,saboda sun mayar dani shashasha shine suka zagayo ta bayan idona suka ɗauki jakar kuɗin,wlh sai kunyi danasani saina illata rayuwarku gaba ɗaya muddin baku maido mun da kuɗina ba,"ya faɗi a lokacin da ya miƙe tsaye zumbur yana faman naushin tafin hannunshi na dama da hannunshi na hagu,tashin hankali da ba'a sama shi date, **********************Amani Zaune take saman 3 seater,yayin da Amal ke zaune kusa da ita,ta fito fess abunta tayi wanka ta bata kaya ta canza duk da rigar tayi mata yawa saboda kayanta ne taba ma amal ɗin ta sanya kafin zuwa gobe zata je da ita shopping mall ta zabi abunda take so,ta kuma yi mata siyayyar kayan sawa da sauran abubuwa na rayuwa wanda zata buƙata, Hannunta na ruƙe da wayarta,shiga contact ɗinta tayi tare da nemo numbar Aunty babba ta buga mata call,nan take wayar tashiga ringing, Hafsat na faman zarya acikin parlourn nasu taji shigowar kira a wayar mommynta dake ajiye saman hannun kujera,cikin sauri takai hannu tare da ɗaukar wayar,ganin sunan Amani ya bayyana ne yasa ta juya tare da tunkarar kitchen ɗin,tunkan taƙarasa aunty babba tafito daga kitchen din jin ringing ɗin wayarta,miƙa mata wayarta tayi tare da cewa"Amani ce ke kira," Yatsina fuska tayi tare dasa hannu ta kar6i wayar bayan tayi picking ta kara wayar a kunnanta tana cewa"Sai yau kika tuna dani"?_ on the other hand Amani tace"Am really sorry auntyna takaina,kullum kina araina,kawai abubuwane sunyi mun yawa," tsoki aunty babba taja tare da cewa"Abubuwa su kayi maki yawa,ciki gare ki ko goyo"?_ Amani tace"ko ɗaya daga cikinsu babu,pls mubar zancen ae nabaki haƙuri,yanzu akwai maganar da nakeso nayi maki pls," Aunty babba tace"kunne ke ji," "dama maganar Amal ne!wai har yanzu ba labarinta?ba'asan inda take ba?nagaza samun kwanciyar hankaline saboda mafarkin da nayi jiya agame da ita," Shu'umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa"Yawwa dama inaso nayi maki magana game da Zancen neman Amal,munyi waya da mammy ta sanar dani cewa an samu wasu malaman da zasuyi mata sauka,manyan malamai ne na addini kuma da zarar sunyi saukar nan ake cin sa'a buƙata ta biya," Ƙiriss ya rage Amani ta saki dariya,don tsabar takaici da ban haushi,aranta tace wai sai yaushe matar nan,zata daina ƙarya ne? Juyawa tayi ta ɗan kalli Amal dake zaune hankalinta kwance idonta na kallon plasma tv ɗin dake facing dinsu,tana kallon tashar mbc 3, gyara murya Amani tayi tare da cewa"Masha Allah,gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba auntyna takaina,ashe ansamu wasu malaman ae ni indai akan Amal ne ko nawa ne zan iya badawa,ko bani dasu zan nemo ne,'_ Jin haka yasa aunty babba,janye wayar daga kunnanta tana faman 6a66aka dariyar mugunta,duk hafsat na tsaye tana kallonta baki asake saboda tasan da zancen neman Amal ɗin,kuma a gabanta Jiya abra ta kira mommyn nata tana sanar da ita cewa Amal ta gudu,sarai tasan cewa yarinyar ta gudu shine kuma takeson ƙara cutar da Amani saboda tsabar son abun duniya? "Yanzu nawa zan tura kenan"?acewar Amani, Aunty babba tace"ba wasu kuɗine masu yawa ba,dubu ɗari takwas ne,ae ni nayi mamakin ma yarda suka faɗi kuɗin da sauƙi har haka," murmushin takaici amani ta saki kafin tace"okey,zanyi maki magana indae na samu kuɗin,yanzu dae mu koma zancen Hayaam,shin har yanzu tana maid ne ko tazo Abujan nan"? "Tun jiya fa ta ƙaraso,yanzu ae ta jima da zama ƴar gida,"ta ƙarasa maganar tana washe baki,anzo inda tafi auki, ɗan ta6e baki amani tayi tace"Okey yayi kyau,yanzu komai zai fara tafiya dai dai,akwai wani albishir da zanyi maki," Natsuwa Aunty babba tayi tare da cewa"ina sauraronki ƙanwata,faɗamun albishir ɗin," Shu'umin murmushi Amani tasaki tare da miƙewa daga saman sofa ɗin tabar Amal zaune tana kallo,takawa tayi nesa da falon,sannan tace"Nasan inna faɗa maki albishirin nan ko bacci ba zaki iya yi ba saboda tsabar farin ciki," A ƙagare Aunty babba tace"dan Allah shaƙamun mana kanwata wane irin albishir ne wannan, Murmushi Amani ta kuma yi sannan tace"nasamo ma Hayaam maganin mallaka a wurin wani hamshaƙin boka,aikin shi tamkar yankan wuƙa yake,saboda Ni shaidace akan idona aka ta6a amfani da maganin kuma yaci," Cike da farin ciki Aunty babba tace"Wai dagaske"? dariya amani tayi tare da cewa"dagaske mana!,wata neigbour ɗinace keson ƙanwarta ta auri ƙanin mijinta,sun rasa yarda zasu jawo hankalinshi acikin gidannan saboda mutunne mai matuƙar ji dakai,kamar dai sgr,ina baki labari kwatsam sai ga wata ƙawarmu ta bamu labari akan wani shu'umin boka,agabana aka shirya zuwa wurin bokan suka amso maganin,a yanzu dai labarin da nake baki,yarinyar na nan ta aure shi hada ciki ma sai faman shan soyayya suke abun gwanin burgewa,"_ Saboda tsabar Murna Aunty babba ta gaza rufe bakinta dakyar ta iya cewa"Yanzu ya za'ae kenan asama ma Hayaam maganin?nawa zamu nema"? "Ko sisi basai kin bada ba Auntyna,fisabilillah na amso ma hayaam maganin da kuɗina ai nima kanwata ce ko,nidae burina shine inga ta auri sgr Abra kuma ta auri marshal Omar," washe baki Aunty babba tashiga yi tana cewa"Allah sarki Amani,ashe haka kika damu da ƙannen namu?gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba,yanzu kenan Hayaam zatazo ta kar6i maganin gidanki kenan"? Amani tace"eh,in ma batasamu zuwa ba ni zanje nakai mata shi,babu damuwa,"_ Sun jima suna waya kafin daga bisani firar tasu ta ƙare anan, Tuntsirewa da dariya Aunty babba tayi tana tafa hannu tashiga cewa"ban ta6a ganin ƴar wahala ba irin Amani,duk irin abunda nakeyi mata amma ita burinta ta taimakamun wurin ganin na cimma burina,gaskiya na tausaya mata,abun tausayi, girgiza kai kawai hafsat tayi tare da wucewa ciki tabar mommyn nata tana ta faman sambatu, A can 6angaren kuwa fashewa da dariya Amani tayi tare da cewa"Aunty laila kenan!ke atunaninki kinyi mun wayau bakisan cewa Amanin da kika sani ada ba ita bace ayanzu ba,ashirye nake dana kwance dukkan wasu notikan kanki,zan mayar dake kamar wata zararra,ita kuma hayaam zanyi amfani da wannan damar wurin ganin na canza mata halittar jikinta,kamar yarda kuka canzawa Amal kamanni ta tsotse ta rame ta ƙanjame haka itama nakeson ta koma,dama ance ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,that's my plan! Tana faɗin hakan ta juya tare da komawa wurin Amal ta zauna,kallonta Amal tayi tare da cewa"Aunty amani,dan Allah kiyi haƙuri da abunda zan faɗa maki,bansan ko zai 6ata maki rai ba,nasan cewa su mammy sun cutar damu sosai,amma kada kice zaki ɗauki fansa,mubarsu da Allah kawai shi zai saka mana,sannan in zamu iya mu taimaki mahaifinmu don yana cikin mawuyacin hali" Shuru kawai amani tayi batace mata komai ba,amma fa har yanzu tana akan bakanta,maganar mahaifinsu kuwa tasan matukar mammy na numfashi bazata barshi ya sarara ba,don ba karamar shedaniyar mata bace,ita kanta yanzu tana shakkun in don Allah aka hadata da Abbas. _💋Boss Bature💋_ ______________________tunda yadawo daga masallaci yake jin jikinshi wani irin yanayi mara daɗi,bedroom dinshi ya shiga tare da nufan saman gadonshi ya haye yana faman sauke ajiyar zuciya,pillow ya jawo tare da aza kanshi a saman shi yana faman lumshe ido,yana cikin wannan yanayin yaji fitar wani abu daga hancinshi mai ruwa ruwa,cikin sauri junaid ya tashi daga zaune yana kallon pillown nashi,zuba ido yayi yana kallon jinin daya ɗigo daga hancinsa,abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,kafin yayi wani yunƙuri sai ga wani ɗigon jinin ya sake fitowa daga ƙopan hancinshi,abu kamar wasa jinin ya dinga ɗiɗɗigowa saman bedsheet ɗinshi,   Hankali tashe junaid ya sauko daga saman gadon da saurin gaske ya faɗa cikin toilet ɗinsa,kai tsaye ya nufi wash basin,dafa shi yayi yana kallon fuskarshi acikin mirror ɗin,hancin shi yabi da kallo ganin yarda hancinshi ke cigaba da bleeding,sam bai damu ba saboda yasan cewa yana yawan yin nose bleeding,don haka tunaninshi ha6o ne kawai,   Hannu yakai tare da kunna tap ɗin,ruwa ya soma shararowa da gudun gaske,tarba hannunshi yayi tare da ɗebo ruwan ya watsa a fuskarshi yana wanke blood ɗin,murzar wurin ya shiga yi don jinin ya tsaya amma yaƙi daina zuba,ya kusan 15mins a haka sannan jinin ya dakata da ɗigowa,ajiyar zuciya ya saki tare da kai hannu ya kashe tap din,   Sannan ya fito daga cikin toilet ɗin,yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarshi ya nufi gadonshi,wani irin jiri ya kwashe shi,hannu ya aza asaman kanshi tare da ambaton sunan Allah,yayin da idanunshi ke ganin mashi biji biji,   Yana cikin wannan yanayin Sehrish ta faɗo cikin ɗakin ambaton sunanshi ta shiga yi "junaid, junaid.....,"   ganin shi atsaye abakin ƙopar toilet ya sata tsayawa tana kallonshi tare da cewa"baby junaid meya faru ne naganka haka?baka jin daɗine,"    Jin muryarta yadinga yi acikin kanshi tamkar ana buga ganga,hakan yasa ya yanke jiki zai faɗi gadan gadan,   A wani irin slow sehrish ta ƙarasa wurin da sauri ta ruƙo shi suka faɗi ƙasa atare,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda yake kokowar fitar da numfashinsa,hankali a matuƙar tashe take faɗin"Innalillahi_!junaid!meke faruwa dakaine!me yake damunka ne?ka faɗamun dan Allah,    Ko iya ɗaga la66ansa ba yayi bare ya iya furta mata wata kalma,hannunshi dake kerma yasa tare da ƙara ƙanƙameta sosai ya kwantar da kanshi asaman ƙirjinta yana cigaba da ƙoƙarin fitar da numfashinsa,hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye,yanke shawarar zuwa ta sanar ma wani tayi don a hanzarta zuwa aga halin da yake ciki,ƙoƙarin janye jikinta tayi daga nashi,tamkar zata rabashi da ranshi haka yaji,ƙanƙameta ya kuma yi sosai da sosai sai lokacin ya iya furta"rishi kada ki tafi ki barni a yanayin da nake ji zan iya mutuwa," Cikin shessheƙar kuka take cewa"junaid ka bari inje in sanar dasu,idan wani abu ya same ka fa"?    "A'a nidai kada ki tafi kibarni,"ya ambaci hakan da wata irin kasalalliyar murya,tsananin tausayinshi ne ya kamata,mayar da hannunta tayi abayanshi tare da ƙara rungumo shi ajikinta tana tofa masa addu'a,lamo yayi ajikinta yana faman sauke ajiyar zuciya,lokaci guda kuma numfashin ya daidaita kamar yarda yake ada,komai nashi yadawo normal,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,idonshi na arufe yake shaƙar ƙamshin turaren rishi ɗinsa,gaba ɗaya ya shiga yanayin da bai ta6a shigar irinsa ba, Muryarta ce ta katse shi da cewa"junaid kana lafiya kuwa?naji ka tsit"?    shiru yayi mata,saboda bayason tasan cewa ya dawo cikin hayyacinsa,baison ta raba jikinta da nashi,ɗumin jikinta ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,yaushe rabon da yaji ɗumin mace haka akusa dashi tun yana da kananun shekaru,tunda mommynshi tabarshi,Aunty azmee ta ɗaura da shayar dashi,shima ɗin da zarar ta kammala bashi nono ƴan uwanshi ke ɗauke shi daga wurinta,don basu son rabuwa dashi kona minti ɗaya,ya saba da jikin abban shi,dana ƴan uwanshi yayi missing wannan feeling ɗin,    Jin yarda junaid ya lafe mata ajikinta kamar jinjiri,yasa tayi tunanin cewa kodai ya cika ne,cikin sauri takai hannu tare da ɗago da kanshi tana kallon fuskarshi,waro ido waje tayi ganin yarda yake ta faman sakin murmushin nan nashi,ranta ne ya bata cewa Dama duk plan ne ya tsara mata don ya tsoratar da ita,ɗaure fuska tayi tare da cewa"janaid wannan duk shirinka ne ko? don ka tsoratar dani," Buɗe idanunshi yayi a hankali yana kallon fuskarta data zuba mashi ido,tana mashi kallon Tuhuma,   Murmushi ya kuma saki tare da cewa"dan Allah rishi ki mayar dani a jikinki na kwanta,ba kiji wani irin daɗi dana ji ba,daɗi kamar nayi bacci,"ya ƙarasa maganar yana lumshe mata ido,tsuke fuska sehrish tayi tare da cewa"amma ka rainamin wayau junaid!wai meyasa ka fiye shiririta ne,kalli fa, ka gani hada hawaye na soma zubarma saboda halin da na sameka aciki,ashe duk plan ne ko"?    girgiza mata kai yayi tare da cewa"ba haka bane reesh,kona faɗa maki gaskiya ba zaki yarda ba,"   A hankali ta kwantar mashi da kanshi ƙasa,sannan ta matsa tare da saita fuskarta akan tashi tana kallon shi,shima binta yayi da kallo yarda ta duƙo da fuskarta asaman tashi sumar kanta kuma tayi masu rumfa,tunda ta faɗo bedroom ɗin nashi tashigo da gudu don ta tarbe shi mayafinta ya sulale ƙasa daga jikinta,    "Junaid waye uncle Abusufyan?naji abbanku na cewa zaizo nigeria,kodai shima ɗin yayanku ne"?   girgiza mata kai yayi alamar a'a yace"uncle ɗinmu ne,ƙanin mahaifinmu dake zaune a ƙasar turkey"    jinjina kanta ta ɗanyi kafin ta kuma cewa"bayan shi kuma naji Abbanku yana cewa,Mommynku zata zo itama,tare da wata goggonku ta katsina da kuma Ammi da Aunty azeema,duk zasu zo,"    Sai da ya bari takai ƙarshen maganarta sannan ya ɗan harareta tare da cewa"Ashe dama jin gulma ne ya kawoki ɗakin"?    Murmushi tayi tace"no ba haka bane junaid,inason nasansu ne saboda na koyi zama da kowannansu,bana so na samu matsala da kowa acikin family ɗinku,"    "Zan faɗa maki halin kowannansu amma bisa sharaɗi ɗaya'?ya jefa mata tambaya,   Tace"ina sauraronka wane sharaɗine wannan"?_   murmushi ya saki tare da kai hannunshi ya nuna mata red lips ɗinsa yace"kiss on lips,if u agree then saina faɗa maki,"    hannu tasa tare da ɗan buge bakinshi tace"pls junaid banason wasa fa,in zaka faɗamun ka faɗamun kawai,in ba haka ba zan tashi inyi tafiyata,"   tayi maganar tare da yunƙurawa zata miƙe cikin sauri ya ruƙo hannunta tare da cewa"rishi mommyn mu bata da sauƙi,nima haka naji ana faɗa,amma in har zaki iya zama da babban yayanmu to wannan bazai maki wuya ba,bambancin ita mace ce kinsan ku mata da tsiwa kuke,   Dariya tayi tana sauraronshi "Uncle ɗinmu kuma Abusufyan,wayayyen mutun ne,idan yazo zakiji daɗin zama dashi,bafa wani babba bane autansu daddynmu ne,yana da sauƙin kai sosai amma idan mutun bai kwanta mashi araiba hmmmmm bazasu ta6a jituwa ba,Aunty azeema kuma kamar abbanmu take wurin faran faran da mutane ga son ƴa'ƴa,zakisha mamaki idan tazo ta ganki sosai zata jaki ajikinta,goggon katsina kuwa......"bai ƙarasa ba ya kama dariya,   Murmushi ta saki tare da cewa"me tayi ita?ko batasan mutane"?    Girgiza kai yayi tare da cewa"a'a tanason mutane sosai,matsalarta ɗaya tana da mental illness.......'   Tunda junaid ya ambaci mental illness taji gabanta ya ɗan faɗi kaɗan kamar maison tuna wani abu acikin brain ɗinta,   "tana da ban dariya sosai,tana fa iya ganinki tace ke ɗiyar wani ce acikin family ɗinmu kuma dole ki yarda da hakan in ba haka ba ta sanya rigima hada kuka ma,'   Sai faman zuba junaid yake yi yana korama sehrish jawabi,ita kuwa tuni tayi nisa cikin tunaninta,kalmar da ya faɗi na cutar ta6in hankali ta tsaya imata arai,so take ta tuna waye ta ta6a sani da irin wannan lallurar amma sam tagaza tuna hakan,   Ganin ta tafi duniyar tunani yasa junaid kai hannu ya janyo sumar kanta yana cewa"wai menene haka reeeshi,kin barni ina ta zuba kamar rediyon da bata da saiti,"   Firgita ta ɗanyi tare da kallon shi har lokacin yana daga kwance tace"junaid thanks for the information,zan koma bedroom ɗina naji ana kiran sallar isha,kaima ka tashi kaje kayi sallar,'    Ba musu ya amsa mata da cewa"bari nayi alwala sai mu fita atare,"   Amsa mashi tayi da toh sannan ta miƙe tare da juyawa ta ɗauko mayafinta daya faɗi kasa ta rufe kanta dashi,toilet junaid ya shiga shaf shaf yayi alwala,bayan ya fito atare da ita suka saukko downstairs,    Anan ya haɗu dasu Irfan zasu masallacin suma yabi bayansu suka tafi,    Komawa bedroom ɗinta tayi kai tsaye ta fada toilet ta ɗauro alwala,bayan ta fito ta ƙarasa wurin wardrobe dinta tare da ɗaukar hijabinta da sallaya ta shimfiɗa tare da kabbara salla,anatse ta kammala sallar,fitowa tayi daga dakin nata sannan ta wuce kitchen don ta shirya ma kanta abincin da zata ci saboda yunwar data taso mata, _💋Boss Bature💋_ A hankali Motarsu tashiga babban gate din gidan Abusufyan,major ne ke driving dinshi yayin da Omar ke hakimce a seat ɗin baya,sai faman zullumin haɗuwarshi da hossana yake saboda yasan cewa ba ƙaramin fushi take dashi ba,saboda ƙin zuwan da yayi, Parking ɗin motar major yayi sannan ya fito tare da buɗe mashi motar,a hankali Omar yasa ƙafa tare da fitowa daga ciki,sannan cikin sauri batare da 6ata lokaci ba ya wuce cikin gidan, Tunkan yasa ƙafarshi cikin parlourn nasu yajiyo shessheƙar kukan hossana,tsayawa ya ɗanyi yana sauraron abunda suke cewa,    "Hossana wai ba zaki daina kukannan ba?salon ki 6ata kwalliyarki ko"?   "Jahad ba zaki gane bane,bakisan yarda nake ji bane,saboda ya omar nayi kwalliyar nan,amma ta tashi a banza,yau ma bazaizo wurin mu ba...'cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar, ƙayataccen murmushi Omar ya saki a fuskarshi,kafin yasa kai tare da shiga cikin palourn,samunsu yayi zaune asaman 3 seater,hossana ta kwantar da kanta asaman hannun sofa ɗin,yayin da jahad ke gefenta tana rarrashinta,gaba daya duk sunyi wanka sun canza kayan jikinsu,riga da skirt ne ajikin jahad,hossana kuma gown ce mai kyan gaske,    jin alamar motsin mutum yasa jahad ɗagowa tana kallon shi,cike da mamaki ta buɗe baki zatayi mashi magana,da hanzarin gaske ya dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da hannunshi alamar ta tashi ta tafi,murmushi jahad tayi tare da miƙewa cikin sanɗa tabar saman sofa ɗin ta koma saman 1 seater ta zauna tana kallon dramar da ya Omar ɗinsu zai shirya,cikin sanɗa ya lalla6a tare da komawa wurin da jahad ta tashi ya zauna,sannan yakai hannunshi tare da ɗan janyo wutsiyar gashinta, A fusace tace"dan Allah jahad ki rabu dani inji da abunda ke damuna,ki tashi kiban wuri," Murmushi Omar yayi tare da cewa"zan tafi amma ki fara faɗamun meyasa kika damu da yaya Omar ɗinki har haka"? Sam hossana bata gane voice ɗinshi ba saboda ranta a6ace yake, "Saboda inason shi sosai,jahad nasan ni kawai nake haukana,yana can wurin hayatyn shi,suna shan soyayya.....' Katse ta Omar yayi da cewa"kina kishi ne"? A faɗace tace"saboda me bazanyi kishi ba,nima ae zuciyata ce a ƙirjina ba dutse ba," Wannan maganar ta hossana ba ƙaramin dariya taba marshal Omar ba,hatta jahad sai da ta murmusa daga inda take, Kwantar da kanshi ya ɗanyi abayanta yana cewa"am really sorry babyn Omar,nayi missing ɗinki sosai,nasan nayi laifi ayimun afwa bazan ƙara ba..."jin muryar Omar raɗau a kunnanta yasa tayi hanzarin ɗagowa tana kallonshi da idanunta da suka cicciko da kwalla, Waro ido Omar yayi yana kallonta ba ƙaramin tsorata yayi ba da ganin makeup ɗin da ke a fuskarta,ta dambara Uwar foundation kamar wata aljana,Jan bakin da ta shafa ya 6ata fuskarta har wurin cheeks ɗinta saboda uban kukan da tasha,ga maskara ta zazzago mata a ƙasan idonta, Hankali tashe Omar yace"subhanallahi,kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Babyn Omar wannan kwalliyar fa?dama itace kwalliyar da ake cewa anyimun don inzo in gani,"cike da zolaya yayi maganar,amma tamkar ya tunzura hossana nan take ta 6are baki itare da fashewa da wani sabon kukan, Dariya jahad ta dinga tiƙa kamar kamar me har tagaza dakatar da kanta, Yama rasa ta inda zai fara shawo kanta don ya lallashe ta,hakan ya ƙara hasalata,kamar wata ƙaramar yarinya,ba ƙaramin tausayi ta bashi ba yasan duk don saboda rashin zuwan shi ne,hannu yasa tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta sosai yana ɗan bubbuga bayanta,lokaci guda ta nemi kukan da takeyi ta rasa,sai gata tana faman sauke ajiyar zuciya, a hankali ya furta"am really sorry hossana,bazan ƙara 6ata maki rai ba,kullum zan dinga zuwa idan ma bansamu halin zuwa ba zan kira ku awaya mu gaisa," Ya ƙarasa maganar tare da cewa"kin yafe mun"? ƙasa ƙasa tace"na yafe maka,amma karka ƙara," murmushi yayi tare da ɗagota daga jikinshi yana kallon fuskarta,sai faman cin magani takeyi tana haɗe mashi fuska, "Kin ci abinci kuwa"? "A'a banci ba," "Why"? Ya tambaya yana kallon bakinta da take ta faman turowa irin na shagwa6a66u, "Kai nake jira kazo ka bani abaki," "Really"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh, Juyawa ya ɗanyi tare da kallon jahad dake zaune tana kallonsu gwanin burgewa yace"dagaske hossana bata ci komai ba"?_ Amsa mashi tayi da eh,jinjina kai yayi sannan yace"ki kawo mata dinner ɗinta anan,sai na tabbatar da taci ta ƙoshi sannan zan tafi," Murmushi jahad tayi tare da miƙewa ta wuce downstairs don pta shiryo masu dinner din," _💋Boss Bature💋_ Yau da wuri suka dawo cikin gidan wuraren karfe goma dai dai,wani irin tsoro da fargaba sehrish taji,musamman da azmee ta sanar da ita cewa ga dinner ɗin sgr can taje takai mashi,bakomai ya faɗo mata arai ba face abunda ya faru ɗazu tasan cewa dole ya tuhumeta saboda ita kaɗai ce macen da take shiga part ɗinsa,sai faman zarya takeyi acikin bedroom ɗinta,tana tunanin yarda zata tunkare shi ayau ɗinnan, Hayaaam Tafiya takeyi cikin sanɗa tana waige waigen ko akwai wani a main palour din cikin sa'a taga babu kowa,murmushin mugunta ta saki tare da nufar kitchen din,tana shiga tayi arba da tray na abincin da Azmee ta shirya ma Sgr,asaman dogon table na kitchen ɗin ta ajiye mata,jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"hmmmmm yarinya kenan yau zaki fara sanin koni wacece wurin iya makirci," Tana faɗin hakan ta shiga ciki kai tsaye ta tsaya wurin tray din,hannu tasa tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da chicken ppr soup,sai faman ƙamshi yake yi,murmushi hayaam tasaki tare da kai hannu cikin sumar kanta,ta cinko gashin kanta sannan ta jefa acikin chicken ɗin hadasa hannu ta motsashi aciki,sannan ta rufe murfin,duk hakan bai mata ba sai da tabi komai na abincin ta sanya gashi aciki,sannan cikin sanɗa tabar kitchen ɗin,tana faman sakin dariya don tasan cewa da zarar sgr yaga gashin nan yarda yake da tsaftar nan ba ƙaramin ƙyamatar yarinyar zaiyi ba,kuma tasan dole ya koreta daga yi mashi aiki,bama wannan ba dole ya hukuntata, tashin hankali da ba'a sama shi date, 💋💋💋 Fitowa sehrish tayi bayan ta gama zullumin nata,kitchen ɗin ta nufa batare da 6ata lokaci ba ta ɗauko tray ɗin a hannunta tare da wuce wa upstairs,hakanan tadinga jin gabanta na faɗuwa kamar wani mummunan abu zai faru da ita,tsayawa tayi abakin ƙopar shiga falon nashi,sai da ta dai²ta natsuwarta sannan ta zabga sallama,tana jiran jin amsawar shi, Jin shiru yasa ta ƙara maimaita sallamar,har kusan sau uku ana huɗun ne tajiyo muryarshi yace"Come in," Ae tunda taji Voice ɗinsa jikinta ya shiga yin kerma,addu'o'in neman tsari tashiga karantowa abakinta,ta jima atsaye tana faman zullumin abun da zaibiyo baya kafin daga bisani ta daure tare da shiga cikin falon nashi,ƙamshin turaren nan nasa ne ya wanko mata hancinta har saida ta lumshe idanunta,tunkan taƙarasa ta hango shi kwance ya miƙe kafafunshi asaman 3 seater,jikinshi na sanye da pyjamas yellow,ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,kunnanshi na kare da wayarshi alamar waya yake yi,    Gabanta na faɗuwa haka ta nufe shi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table dinsa,saboda tsabar rashin gaskiya,tana ajiye tray ɗin ta juya cikin sauri zata bar parlourn nashi,kamar daga sama taji anyi ma mayafinta kwakkwaran ruƙo ta baya,nan take mayafin ya sulale daga jikinta,zazzare ido waje sehrish tayi jikinta na kerma,nan take tashiga haɗiyar yawu,tsayawa tayi tana jiran maizo biya baya,    Jin alamun motsin shi abayanta ya tabbatar mata da cewa shine yaja mayafinta daga jikinta,tsayawa tayi tana ambaton sunan Allah abakinta,ganin kusan minti biyar bata ji ya ƙara motsawa ba yasa tayi hanzarin juyawa a wani irin firgice sam bata tsammaci yana tsaye abayanta ba sai dai kawai taji ta kai mashi karo,ja da baya ta ɗanyi tana faman zare ido,tunkan ya tambayeta ta shiga cewa"dan Allah kayi haƙuri,nasan na 6ata maka rai,wlh nima bada son raina hakan ya faru ba,nashiga na gyara maka bedroom ɗinka ne,bayan na kammala shine na ɗan cire mayafina na ajiye asaman gadonka don naji daɗin yin aikin,ashe kafin na fito daga cikin toilet ɗin ka dawo,shine na same ka akwance kana bacci saman mayafina,saboda ina tsoran ka farka ka ganshi yasa nayi ƙoƙarin janshi daga jikinka,shine...cikin bacci batare da saninka ba ka...........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda jin yatsun hannunshi da tayi asaman lips ɗinta,alamar tayi mashi shiru,sannan ya hankali ya ɗan ware eyes ɗin nashi akan fuskarta............ *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. 💋BOSS BATURE💋 Follow this link to join my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Father of soldiers (takun ƙarshe) A tsananin tsorace take kallon fuskarshi ganin ya ware idanunshi yana kallon fuskarta,a hankali ya zame finger ɗinshi daga saman tausasan la66anta dake ta faman kerma,sai faman haɗiyar yawu take yi tsoranta wane hukunci zaiyi mata,sau biyu yana ƙoƙarin buɗe mouth ɗinsa zaiyi magana amma ya kasa,saboda ya rasa me zaiyi ma yarinyar,tun da yake wata ƴa mace bata ta6a ƙetare iyakar da yarinyar ta ƙetare ba,a matsayinta na wadda ba muharramarsa ba kuma ƴar aikin gidansu,ƙara matsawa yayi kusa da ita,cikin sauri sehrish ta ƙara ja da baya,tana faman girgiza mashi kai Alamar yayi haƙuri karya hukunta ta,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye a idonta,ba komai take kallo ba face damtsen hannunshi da kuma wannan faffaɗan ƙirjin nashi,uwa uba yarda ya tsaya agabanta tamkar wani zaki, Hannunshi yakai tare da ruƙe waist ɗinshi yana kallon yatsun hannunta dake ta faman kerma,  A natse ya soma magana"I will punish you for the mistake you made in my bedroom on my bed,so that you know under whom you are working,cos u crossed your boundary," Gabanta ne taji yayi wani irin bugu jin abunda sgr yace,hankali tashe take kallonshi,muryarta har kerma take wurin cewa"bazan ƙara ba,"    girgiza kanshi yayi alamar bai amince ba sannan yace"You are going to start frog jumping around the chairs without stopping, if you do that I will let you go, but if you dare stop,I will punish you badly," yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da komawa saman sofa ɗin yana kallonta yace"Am watching u,"yayi maganar tare da nuna mata blue eyes ɗinshi da 2 fingers ɗinshi,alamar idonshi na akanta,     Tamkar ta fashe da kuka haka taji,ga matuƙar tsoranshi da take ji,ga punishment ɗin daya bata na tsallan kwaɗi abunda ta tsana arayuwarta saboda tasan wahalarshi,ba abune mai sauƙi ba bazata ta6a mantawa da lokacin da fawan ya sanyata frog jump ba har jini ya 6alle mata,saboda tsabar wuyar da tasha har suma tayi lokacin,    gyaran muryar da Sgr yayi mata ne yasa tayi saurin zuƙunnawa tare da kama kunnanta da hannayenta sannan a hankali ta soma yin tsallen kwaɗin,in da Allah yasota ma Wando ne ajikinta ba skirt ba da abun yafi muni,da sauri take yin tsallen har ta zagaya ta bayan sofas ɗin ta kuma dawowa ta gabansu duk yana kallonta,tun Sehrish tana yin tsallen kwaɗin cikin daɗin rai har ƙafafunta suka soma rurruƙewa,wani irin zogi suka shiga yi mata,nan take hawaye suka fara shararowa daga idanunta har da majina duka ta haɗa,   Yana jin shessheƙar kukanta amma ko ajikin shi,a ƙarshe ma sai ya ɗauki lemu mai sanyi ya tsiyaya acikin cup ya shiga kur6arshi a bakinsa yana sha,tun yana shan lemun daga zaune har ya ɗan kishingiɗa kafaɗarshi saman sofa hand ɗin,    A wani irin galabaice sehrish ke ɗaga kafafunta tana yin tsallen kwaɗin,a ƙalla ta zagaye kujerun kusan sau takwas amma sgr baice ta dakata ba,tun tana sa ran zai tsayar da ita harta fidda rai,saboda tsabar tsoro da firgicin da take ciki yasa ta gaza gane cewa sgr fa bacci ya kwashe shi asaman sofa ɗin,duk in ta zagayo ta wurinshi sai taga kamar idonshi biyu,batasan cewa tuni bacci yayi awon gaba dashi ba,har ya ajiye cup ɗin dayake shan lemun dashi, Wani irin matsanancin ciwon kaine ya far mata,ga raɗaɗin da kafafunta keyi mata,lokacin da ta ƙara zagayo wa ta wurin shi,cikin shessheƙar kuka tace"...Am really sorry babban yaya,i ave realized my mistake,bazan ƙara ba nayi maka alƙwarin hakan," tabbas yajiyo muryarta acikin ears ɗinshi amma sam bazai iya buɗe idanunshi ba,saboda nauyin baccin da yayi,   Ganin bai tanka mata ba,yasa sehrish cigaba da yin tsallen kwaɗayin da takeyi dakyar dakyar,tana cikin wannan yanayin wani irin stomach pain ya taso mata haikam,nan take ta yanke jiki ta faɗi saboda galabaitar da tayi,taji jiki sosai, Sai faman zagaye hayam takeyi a tsakanin upstairs da kuma down,ba don komai ba sai don taga a wani yanayi Sehrish zata fito daga sashen sgr,har wani murmushin mugunta take saki don tasan cewa muddin Sgr yaga siraran gashi a cikin abincinsa dole ya kikkifa Mata mari,sannan ya kore ta daga yi mashi aiki,daganan  ita kuma zata samu shiga a wurin shi,gajiya ta fara yi da zagayen ganin cewa har ƙarfe sha biyu na dare tayi Sehrish bata fito daga part ɗinshi ba,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,baƙin ciki kamar ya kashe ta,tsayawa tayi ruƙe da qugu tana cewa"Ko uban me yarinyar can takeyi a part ɗinsa har wannan lokacin bata fito ba!wlh na tsani yarinyar can,ko son ganinta bana yi,shisshiginta yayi yawa nasan yanzu haka tana can ta liƙe mashi tana kalle mun surar jikin mijina,Allah bazan ƙyaleta ba sai nayi maganinta mtssw,!"ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki sannan ta kama hanyar komawa bedroom ɗinta tana faman sambatu kamar wata zautacciya ," _💋Boss Bature💋_ Kwance yake asaman gadon Abbansu hannunshi rungume da pillow,yayin da idanunshi ke arufe tamkar mai bacci, Yana jin lokacin da abbansu ya fito daga cikin toilet jikin shi sanye da Jallabiya,ƙarasowa yayi wurin gadon tare da samun wuri daga ɗan gefe ya zauna,sannan ya ɗan juya tare da kallon fuskar junaid da yayi likimo kamar mai bacci,hannu yasa tare da shafa sumar kanshi yace"sarkin rigima yayi bacci,"ya faɗi da murmushi a fuskarshi,janye hannunshi yayi daga saman sumar kan junaid,sannan ya miƙa hannu tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye a saman bedside drawer,contact ɗinshi ya shiga ya lalubo numbar mommynsu junaid ya danna mata kira,nan take kiran ya shiga,cikin sa'a ta ɗaga kiran nashi,murmushi yayi tare da kara wayar a kunnanshi yace"Noorul ƙalbina"   On the other hand alexandra tace"yau kuma soyayyarce ta motsa?ni zaka yaudara da kalamanka saboda kaji cewa zanzo nigeria ko?to ae ba saboda kai zanzo ba,zanzo ne don naga Yarona kuma da zarar nazo zan ɗauke abuna na dawo Australlia dashi,don bazan barshi a hannunku ba don ban yarda da irin rainon da kake mashi ba,"    girgiza kai abbansu yayi tare da cewa"Yaushe zaki canza ne?ke ko tausayina bakya ji ne?baki damu da halin da nake ciki ba,na rashinki a kusa dani,ina fa sonki har yanzu kuma ban rabu dake ba,kece kika rabu dani kika kama hanya kika bar ƙasar nan batare da sani na ba,yanzu kinyi mun adalci"? Cikin sanyin murya ya ƙarasa maganar yana sauraron Amsarta Junaid daya kasa kunne yana sauraransu sai faman murmushi yake yi idonshi a rufe,    Shiru Alexandra tayi yayin da idanunta ke kallon sararin samaniya ta cikin windown katafaren bedroom ɗinta,kunnanta na kare da wayarta tana sauraron shi,muryarshi ta kuma ji yana cewa"kinyi shiru baki ce komai ba"?   Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan jinjina kai tace"me kake so yanzu"?     Runtse ido abbansu yayi saboda ya rasa yarda zai fahimtar da ita,wata irin bauɗaɗɗiyar mace ce,ko don tayi aikin soja ne yasa ta kasance haka,saboda a tsaye take ba irin raunin zuciyar nan na mata,    "Hossein in baka da abun cewa,Ni zan aje waya ne,"   Muryarta ce ta kuma katse shi,a lokacin ranshi ya gama 6aci a faɗace yace"Fatima na gaji da irin wulaƙancin da kikeyi mun,nayi danasanin haɗuwata dake tun farko,kuma nayi danasanin haɗa zuri'a dake,saboda kin cutar da rayuwata,sam baki respecting ɗina a matsayina na mijinki,kuma uban ya'yanki,idan kinsan zaki tafi kibarni meyasa tunfarko kika sanyamun soyayyarki acikin zuciyata?    Muryarshi araunace yayi maganar yanayin sautin kamar zai fashe mata da kuka,    Jin tayi shiru bata ce mashi uffan ba yasa shi cewa"banaso ki dawo ƙasar nan!ki cigaba da zama acan,saboda zuwan naki baida amfani awurina,kuma babu ruwanki da ƴa'ƴana  dama can baki damu dasu ba,tun da har zaki iya tafiya kibarsu,batare da tunanin yaya rayuwarsu zata kasance ba"!   Jin wannan maganar ta Abban nasu yasa hawaye suka soma gangarowa a idanun junaid,sam baiji daɗin yarda mommynsu ke 6ata ma Abbanshi rai ba,    Bai jira Alexandra ta bashi amsa ba ya katse kiran nata tare da yin wurgi da wayar gefe guda,jiki amace ya kifa kanshi asaman gadon,idanunshi sunyi jawur sun cicciko da kwalla,    a hankali hawayen suka soma gangarowa,kamar daga sama yaji tafin hannu a fuskarshi,cikin sauri yakai idonshi akan junaid dake share mashi hawayen fuskarshi,   Cikin shessheƙar kuka yace"Abba don Allah kadaina zubar da hawayenka akan mommynmu,ba dole sai da ita zaka samu farin ciki ba Abba,Ni na isheka duk wani farin cikin duniyar nan,Abba ka ta6a faɗamun cewa ko kallona kayi kanajin sanyi aranka,why zaka Sanya ma kanka damuwa akan mommynmu?ka rabu da ita kawai Abba,akwai mata da yawa agari waɗanda suka fi ta hankali.........'    Murmushi Abban nasu yayi jin abunda junaid yace,    Miƙewa yayi daga zaune suna fuskantar juna yace"junaid bazaka gane ba!mommynku ba kamar sauran mata take ba,idon har tana raye ni bazan iya kula wata ƴa' mace ba,"    ɗaure fuska junaid yayi tare da zum6ura baki yace"Saboda me Abba?me tafi sauran matan?duk yarda take 6ata maka rai?     "Junaid she's special saboda ta bani babbar kyautar da har yau in na kalleta nake jin farin ciki araina,"    Cike da mamaki junaid yace"Wata irin babbar kyautace wannan? Ya tambaya yana kallon Abban nasu,    Murmushi Abbanshi yayi tare da nuna shi da yatsanshi yace"Am talking about u junaid!Matar da ta haifamun lu'u lu'u kamarka taya zan iya rabuwa da ita junaid?ta bani farin cikin da har na bar duniyar nan bazan ta6a samun makamancinshi ba,kyakkyawan yaron da kowa ke alfahari dashi,kowa yake so kuma yake ƙauna,Junaid bani da burin da ya wuce in farka in ganka akusa dani da ranka da lafiyarka...........'   Tsagaitawa yayi da maganar yana kallon junaid da bakinsa yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna,ya ma rasa mai zaiyi don tsabar farin ciki,a ƙarshe ya faɗa jikin Abban nasu tare da rungumeshi ya ƙankame shi sosai ajikinshi yana faman dariya,     Zagayo da hannunshi yayi yana ɗan bubbuga Bayan junaid yaci gaba da cewa"I love u so much my baby boy,Allah ya nuna mun ranar auranka kafin nabar duniya,koda ace shine abu na ƙarshe da zan gani kafin na koma ga mahalicci na,Ina rokon Allah ya nuna min wannan ranar,da shagwa6a66an yarona zaiyi aure,zanso naga yaron da matarka zata haifa mana,wanda zamu dinga kira da Babyn baby,"   Fashewa sukayi da dariya, suka dinga yi atare,har lokacin basu raba jikinsu ba,    Ƙarar shigowar message a wayar Abban nasu ce,yasa junaid janye jikinshi daga na abban nasu sannan ya rarrafa tare da kai hannu ya ɗauko mashi wayar,ya miƙa mashi,   Kar6a Abba yayi tare da duba message ɗin da aka turo mashi yana karantawa kamar haka    "Forgive  me my love.......nasan na 6ata maka rai sosae,kayi haƙuri ka yafe mun kuma inaso kasan cewa nima ina sonka sosai har yanzu ba abunda ya sauya na sonka acikin zuciyata,zan dawo nigeria ne saboda na gyara alaƙata da uban ƴa'ƴana,da kuma ƴa'ƴan nawa,ka shirya tarbar amaryarka Alexandra...........'   gaba ɗaya ya rikice saboda tsabar farin cikin saƙon da ya shigo mashi,saboda ruɗu har hannu yasa yana goge idanunshi wai ko badaidai ya karanta bane,saboda tunda yake arayuwarshi alexandra bata ta6a bashi hakuri ba,bai ta6ajin kalmar sorry daga bakinta ba,koda ace tayi mashi laifi sai dai shiya bata haƙuri ya rarrashe ta amma badai ita ba ae tafi ƙarfin wannan,amma yau ita da kanta take bashi hakuri!?_   Ganin yarda Abban nasu ke ta sakin murmushi yasa junaid cewa"Abba menene naga kamar farin ciki a fuskarka,"   Miƙa mashi wayar abban nasu yayi dama tsakaninsu babu 6oye 6oye,   "Junaid dubamin ka gani,kodai idona ne ke nunamin ba daidai ba,wai mommynku ce ke ban haƙuri da kanta,"   hannu junaid yasa ya kar6i wayar daga hannun Abban nasu ya shiga karanta saƙon,nan take yaji wani irin sanyi aranshi,    "Junaid baka ji farin cikin dana ji ba wlh,naji daɗin saƙon nan na mommynku,da ace bataban haƙuri ba da bansan a wani yanayi zan kwana ba yau,"   Murmushi junaid yayi bayan ya kammala karanta saƙon cike da zolaya yace"Su Abba an kusa angwancewa,amarya mommyn junaid zata dawo,amma dai Abba idan tadawo nigeria ba zaka kore ni daga kwana bedroom ɗinka ba ko?    Wani irin kallo abban nasu ya jefa mashi tare da cewa"Ae aranar da tadawo,zaka tattara yanaka yanaka kabarmin ɗakina,dama nagaji da kwana tare da ƙato a ɗakina.....'kasa ƙarasa maganar yayi saboda dariyar daya kwashe da ita,junaid kuwa tsuke fuska yayi yace"Allah Abba ba inda zanje ko mommy ta dawo,sai dai mu rinka kwana tare daku,ku sanyani a tsakiyarku muyi bacci atare," ashagwa6e ya ƙarasa maganar tashi,    harara abba ya watsa mashi tare da cewa"Allah ya kiyaye mu kwana tare da kai,"    Da buɗar bakin junaid sai cewa yayi"Abba kaima ya haramta a musulunce ka kwana tare da mommynmu......'tunkan ya ƙarasa maganar tashi,Abban nasu ya wawuro pillow tare da buga mashi asaman kanshi yana cewa"gidan ubanwa ka ta6a jin haka junaid?waya koya maka wannan kalamin ƙabihin?    dariya junaid ya shiga yi yana tarbe pillown da yake bugun shi dashi,gaba daya suka shiga yin wasan bugu da pillow shi da abban nasu,yarda kasan wasu ƙananun yara,sun jima suna shiririta kafin daga bisani bacci ya kwashe su gaba ɗayansu kowa hannun shi ruke da pillow, _💋Boss Bature💋_ Tun bayan da Jahad ta haɗo mashi abincin a tray,ta kawo mashi anan ƙasa ya sauko tare da hossana suka zauna,da kanshi ya dinga ɗebo abincin yana bata abaki tana ci,sai da ya tabbatar da taci ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta,ya jima a wurinsu suna fira atare gwanin ban sha'awa kafin daga bisani wurin sallar isha'e yayi masu sallama da nufin zaije yayi sallah ya dawo kafin ya wuce gida, Lokacin da Omar ya dawo,bai same su a palourn ba babu kowa aciki,hakan ya tabbatar mashi da cewa sunyi bacci don yadan jima daya fita masallacin,tsayawa yayi yana tunanin ya tafi ko ya tsaya,harya juya yaji cewa bazai iya tafiya batare daya ƙara sanya Hossana a idanunshi ba,    juyawa yayi tare da nufar bedroom ɗinsu,a hankali ya tura door ɗin ɗakin,sannan yasa kai ya shiga da sallama abakin shi,    Sunyi nisa acikin baccinsu,hankalinsu kwance sai faman sharara bacci suke yi,kowaccen su na sanye cikin kayan baccinsu,jahad riga da wando farare,hossana kuma ƴar riga ce dai dai guiwa pink colour,sharara rigar take,saboda daɗin bacci ta hankaɗe rigar tayi sama hakan ya bayyana santala santalan cinyoyinta da suka ji hutu,dama bata iya kwanciyar bacci ba,    tsayawa Omar yayi yana kallonsu ta hanyar hasken Bedside lamps ɗin da suka kunna,sun haskaka wurin gadon nasu,yarda suke bacci cikin kwanciyar hankali ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,har ya yanke shawarar ya juya yabar bedroom din idonshi suka sauka akan laps ɗin hossana dake dan  kerma alamar sanyi ya kama kafafunta,kafin su kwanta sai da Jahad ta lullu6esu,cikin bacci hossana tayi wurgi da bargon gaba ɗaya,ya yi gefe guda can ƙasan ƙafafunsu,    ƙarasawa ciki omar yayi da nufin ya rufe su da bargon,amma tunda ya isa wurin gadon,ya gaza janye idanunshi daga kallon surar jikin hossana,abun da bai ta6a yi ba,tamkar ana ingiza shi zuwa gare ta haka ya dinga ji,nan take yaji wata irin ƙishirwar sha'awarta ta kama shi lokaci guda,gaba daya ya makance akanta har baisan lokacin da ya faɗa jikinta ba gaba ɗaya,ya shiga ƙoƙarin biyan buƙatarshi,tuni ya zame hannun rigar jikinta,ya sulale ta izuwa kasa har wurin stomach ɗinta,ba ƙaramin rikicewa yayi da gani booobs ɗinta ba,a cike fam suke tuni suka tsone mashi ido,gaba daya omar ya farmasu kyakkyawar damƙa yayi masu ya shiga murzasu a hannunshi,jikin shi har kerma yake yi,laushin su ba ƙaramin gigita shi su kayi ba hakan yasa yakai bakinsa gaba ɗaya,    A wani irin firgice hossana ta farka saboda raɗaɗin da taji kan nipples ɗinta,jin mutum asaman jikinta yasa ta fasa wata irin razananniyar ƙara mai sautin gaske tana faɗin"Jahad!!jahad!!nashiga uku!Abba zai cutar dani!dan Allah kadaina !ka bari!kada ka kashe ni mutuwa zanyi!dan Allah kabari Abba banso!!!!!gaba daya Omar baya a hayyacinsa ƙoƙarin zame belt ɗin wandonshi yake yi don ya cimma inda yake son zuwa,     Wannan ihun da hossana keyi ne ya farkar da jahad,a wani irin gigice ta yunƙura tare da miƙewa zaune tana kallon wannan tashin hankalin,kamar a mafarki haka take kallon Lamarin,saboda tsabar ruɗu bata gane fuskar waye ba,da hanzarin gaske ta dunƙule hannayenta tare da daddagewa ta ɗuma mashi dundu abayanshi,amma ko gizau Omar baiyi ba sai faman cigaba da abunda yake ƙoƙarin yi yake,    Fasa ihu jahad tayi tana faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"gaba daya ta rasa ta yarda zata iya ceton Hossana,ƙoƙarin ruƙo shi ta shiga yi,aikuwa gaba ɗaya Omar yayi wurgi da ita,gaba ɗaya jahad ta gangara ta faɗa ƙasan gadon,kanta ba ƙaramin buguwa yayi ba,kafin jahad ta yunkura ta taso daga faɗawar nan da tayi,hossana ta daddage ta gartsa mashi cizo asaman damtse hannunshi,kusan sau uku tana cizon shi amma ko gezau baiyi ba,gashi harta fasa mashi fatar jikinshi,shaidar jinin harya fara fitowa ajikin farar shirt ɗin dake ajikinshi,   Ganin yana ƙoƙarin zame pant ɗin jikinta daya rage mata,yasa Hossana fashewa da wani irin sabon kuka tana cewa"Jahad kizo ki taimakeni!zai kashe ni!Abba zai cutar da rayuwata!Ya Omar bazai barka ba sai ya kashe ka........"idanunta na arufe take ambaton hakan yayin da hawaye ke 6ulbulowa daga cikinsu kamar an kunna fanfo,    Lokaci guda tunaninshi yadawo cikin hayyacinshi ta dalilin sunan shi da hossana ta ambata,zaro ido Omar yayi hankalinshi a matukar tashe yake kallon hossana daya raba ta da kayan jikinta,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,A uzubillahi minasshaiɗanin rajim!!!shine abunda ya shiga ambata abakinshi,gaba ɗaya yabi ya gigice kanshi yashiga sara mashi da wani irin matsanancin ciwon kai,kunyar duniya tabi ta baibaiye shi,a hanzarce ya miƙe da saurin gaske ya fuce yabar bedroom ɗin,cikin sa'a batare da Hossana ta buɗe idanunta ba,kuma batare da jahad taganshi ba,dukansu babu wanda ya shaida shi,ƙaramin kuskure kan iya jefa mutum faɗawa tarkon shaiɗan,omar yayi danasanin dawowarshi cikin gidan,yayi danasanin shiga bedroom ɗinsu,in banda tsautsai da ƙaddara bai ta6a gigin shiga ɗakinsu ba sai yau,      Fucewarshi ke da wuya,jahad ta ɗago da kanta daga buguwar da tayi a ƙasa wurin harya ɗan fashe kaɗan,da saurin gaske ta haye saman gadon tana faman shessheƙar kuka,tsayawa tayi tana faman wurga ido cike da mamaki ganin babu mutumin nan dake ƙoƙarin keta haddin hossana,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,6aat babu shi babu alamar shi,   Cikin sauri ta ƙarasa wurin hossana dake a kwance babu kaya ajikinta,da alama suma tayi saboda tsabar firgicin data shiga,     Hannu jahad takai tare da janyo bargo ta lullu6e mata jikinta,sannan ta rungumota ajikinta tana faman ambaton sunanta"Hossana!!hossana!!!"ganin ko motsi taƙiyi yasa hankalin jahad tashi,jijjigata tashiga yi tana cewa"Hossana ki farka dan Allah!!ki tashi!Allah yasa bai kaiga cutar dake ba!nashiga ukuna ni yau!meyasa haka ke faruwa dake ne?burin kowa yaga ya lalata maki rayuwarki hossana!meyasa bazasu barki kiji da abunda ke damunki ba!meyasa bai tunkare ni ba sai ke........'kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,mai raɗaɗin gaske,gaba daya ta fashe da matsanancin kuka tana cewa"Ya Allah kasa mafarki nake ba gaske ba!!Allah karka nunamin wannan ranar da zan rasa ƴar uwata!!hossana dan Allah ki tashi kada ki mutu kibarni.......'   Ganin ko motsi hossana taƙiyi yasa jahad sakinta tare da yin saurin saukowa daga saman gadon,da gudun gaske ta fito cikin falon tare da nufar telephone don ta kira Ya omar ɗinsu ta sanar dashi abunda ke faruwa cewa wani ya shigo musu cikin gidansu,    Hannunta har kerma suke yi wurin daukar telephone ɗin tare da danna numbers ɗinsa ta buga mashi kira,Allah Allah take akan ya ɗaga kiran ta sanar mashi saboda tsoran Kada mutumin ya ƙara dawowa,ga kuma hossana dake kwance araye ko amace,    Lokacin da kiran Jahad ya shigo wayar Marshall Omar,yana acikin motar shi bawan Allah,duk yabi ya takure yaji ya tsani rayuwarshi gaba ɗaya,kamar ya binne kanshi haka yake ji,wasu irin zafafan hawaye ne ke gangarowa daga idanunshi sai faman cizon la66anshi yake yi,idanunshi sunyi jawur,    Jikin Major ba ƙaramin sanyi yayi ba,saboda ya gane halin da Ogan nashi yake ciki,ga wayarsa sai faman ringing takeyi amma yaƙi ɗaukota bare yayi picking call ɗin,   A hankali major yayi parking ɗin motar tasu agefen titi ba don komai ba sai don baijin zai iya cigaba da driving yayin da oganshi ke cikin wani yanayi,    Ganin ya tsayar da Motar yasa Omar cewa"major meyasa ka tsayar da motar"?    Cikin sanyin murya major yace"ka gafarce yalla6ai,bazan iya driving ɗin bane,saboda gaba daya jikina amace yake,guiwowina sun sage tamkar anzare lakar jikina haka nake ji,bansan me ya faru dakaiba amma ina da tabbacin cewa wani abu mara daɗi ne yasaka shiga wannan halin da kake ciki,"    Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"Major yau nayi abun kunya,naji kunya sosai kamar na binne kaine,ashe dama shaiɗan baida tabbas"?yayi tambayar yayin da zuciyarshi ke cigaba dayi mashi ƙuna,   Cigaba da magana yayi"major yau ni da kaina nayi attempting rape,kuma ba kowa nayi yunkurin aikata ma hakan ba face hossana.....' *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.      *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Abban sojoji paid book ne,ga duk mai buƙatar karanta cigaban shi yayi mun magana kai tsaye ta number ta 08103884440 Whatsapp only banda phone calls, 300 ne only 🤝 Cigaba da magana yayi"major yau ni da kaina nayi attempting rape,kuma ba kowa nayi yunkurin aikata ma hakan ba face hossana.....'    Jin abunda omar yace yasa major cikin tashin hankali yace"Subhanallahi!!yalla6ai garin yaya hakan ya faru!nidai nasan cewa bayin kanka bane,na yarda dakai sosai,Ni shaidane akanka yalla6ai,kai da kanka kake hukunta masu aikatawa,kana ɗaya daga cikin mutanan dake daraja ƴa mace,ba zaka ta6a yin hakan abisa son ranka ba,"    "Major naji haushi sosai,zuciyata batamun daɗi,duk nabi na tsani kaina,nayi abun kunyar da bazan ta6a mantawa ba,indama na godema Allah yaran basu shaidani ba,da idanunsu da ace sun gane ni ne da nasan cewa duk wani girma na da suke gani zai zube ne,kuma zasu fara tunanin cewa ba don Allah na taimaki rayuwarsu ba...."    tsananin tausayinshi ne ya kama major,da yana da halin da zai cire damuwar dake acikin zuciyar ogan nashi da tuni yayi exchanging heart ɗinsu,ba don komai ba sai don ya tsani yaga marshal acikin wani hali na ƙunci,    daƙyar major ya kwantar mashi da hankalinshi ta hanyar yi mashi tausasan kalamai masu daɗin gaske har sai daya ga ya shiga natsuwarshi sosai sannan ya tashi motar suka nufi gida,    kuka sosai jahad keyi ganin tana ta jaraba kiran layin Omar amma ba'a ɗagawa,a ƙarshe ma da ta ƙara kira sai ta samu wayar a switch off,jiki asanyaye ta mayar da telephone din ta ajiye asaman table ɗin,    dafe kanta tayi saboda wani irin raɗaɗi da taji yana yi mata,gaza tsayawa tayi da ƙafafunta nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume, Tashin hankalin da ba'a samashi date!a can 6angaren sehrish ta sume,anan 6angaren kuma hossana da jahad sun sume,ko mai zai biyo baya? Wuraren ƙarfe 1:30 na dare,Ayaan na kwance cikin kayan baccinsa,yaji hannun mutun acikin wandonshi,a firgice ya farka tare da ware idanunshi akan wanda ke lalubar jikin nashi,ganin jahan asaman jikinshi yasa yayi hanzarin yin wurgi dashi gefe guda ya tashi zaune rai a6ace yace"Jahan!banason wannan wasan!karka kuskura ka ƙara ta6a jikina in ba......'bai ƙarasa maganar ba saboda haɗe bakinsu da jahan yayi wuri guda yashiga ƙoƙarin zura harshen shi acikin bakinsa,    Hankali tashe Ayaan ya rurruƙe shi yana kiciniyar kwace kanshi daga hannun jahan amma abun yaci tura,kamar wani zombie haka ya koma mashi, Muryarshi har shaƙewa takeyi wurin cewa"Ja...ja..jahan!ka rabu dani!wai meyake damunka ne!baka da hankaline kasan me kake ƙoƙarin yi mun ne,yayi maganar tare da janye jahan daga jikinshi yana kallon shi,    Wata irin zuface ke gangarowa daga cikin sumar kanshi saboda tsabar jarabar da yake ji,   A kasalance yace"ayaan kadaina mun wasan nan,kasan fa abunda nake buƙata awurinka,ka bani haɗin kai kamar yarda muka saba,baka ji yadda nake ji ba ajikina....'Ya ƙarasa maganar yana faman lumshe idanunshi,   Ayaan kuwa kallonshi yake yi gwanin ban tsoro,lokaci guda kuma ya tuna komai yace"Jahan kayi haƙuri bazan iya ba,na ƙyamaci abun acikin zuciyata,ya fita raina gaba ɗaya,bazan iya cigaba da aikata wannan mummunan zunubin ba,bayan Allah ya yaye mun,idan harna biye maka muka aikata hakan,hukunci zai hau kaina,Allah bazai......'kafin Ayaan ya ƙarasa maganar tuni Jahan yayi kukan kura ya afka mashi,don bazai juri sauraron kalamanshi ba,saboda a ƙagare yake daya kawar da muguwar sha'awar data taso mashi mai tare da wani irin raɗaɗi,   Dambe suka shiga yi atsakaninsu,jahan na ƙoƙarin zame ma Ayaan kayan jikinshi,yayin da Ayaan ke ƙoƙarin kufcewa daga hannunshi ya gudu,wani irin ƙarfi jahan ke ji gaba daya ya zauce ya fara fita hayyacinshi burinshi ya biya mashi buƙatarshi,kafin wani lokaci jahan ya yayyaga ma Ayaan rigar jikinshi,yayi mata kaca kaca,ruƙo wandon jikinshi yayi tare da janshi ya zame gaba ɗaya,ya rage daga shi sai short ajinshi,a lokacin ya tattara dukkan wani ƙarfin shi yayi wurgi da jahan gefe guda saman gadon,sannan da gudun gaske ayaan ya sauko daga saman gadon ya faɗa cikin toilet ɗinsu tare da rufe ƙopar,yana faman sauke ajiyar zuciya,a bakin kopar ya tsaya tare da kasa kunne yana sauraran gurnanin da Jahan keyi,   tsigar jikinshi ce ta soma tashi tsaitsaiye,nan take idanunshi sukayi wani irin ja tamkar garwashin wuta,saukar bulali ya dinga ji ta ko'ina abayanshi nan take yabi ya gigice ya dinga sakin ihu yana kuka mai cin ran,   Runtse ido Ayaan yayi wani irin tausayin shi ne ya kama shi,saboda yasan irin halin da suke shiga aduk lokacin da basu kusanci junansu ba,tabbas Jahan bazai rayu ba muddin bai bashi haɗin kai ba,fashewa da kuka Ayaan yayi tare da sulalewa ya zukunna abakin ƙopar toilet ɗin yana faman shassheƙar kuka,   Yana jiyo yarda jahan ke ta faman ihu yana kuka,akan kunnanshi yaji sautin faɗowar jahan daga saman gadon,ta hanyar sautin da yaji timmmmmm!   rarrafowa jahan yayi daƙyar yake jan jikinshi har ya isa bakin ƙopar toilet din,muryarshi na kerma yace"Ayaan yau kai da kanka kake guduna!bayan kasan irin halin da muke shiga aduk lokacin da bamu aikata hakan atsakanin junan mu ba!so kake na mutu ko"? daƙyar sautin maganarshi ke fita,maƙoshin shi tuni ya jima da bushewa ƙamas,numfashinshi daƙyar yake fita, Cikin muryar kuka Ayaan yace "am really sorry jahan,ina mai matukar takaicin gaza taimakonka a wannan lokacin,zanyi kuka sosai in na rasa ka jahan,bani da tamkarka aduniyar nan,ina tsananin kaunarka sosai ɗan uwana,kayi haƙuri ka yafe mun........"kasa ƙarasar maganar yayi saboda kukan daya ciyoshi,    tamkar zaiyi hauka haka ya dinga ji,gaba daya rayuwarshi tashiga cikin ƙunci,idonshi ya makance,makoshin shi ya bushe,ya rasa duk wani kuzarin jikinshi,lokaci guda ya zama zautacce yabi ya burkice sai faman magiya yake yi ma Ayaan ya taimaka ma rayuwarshi amma ina Ayaan sam yaƙi buɗewa bama alamar zai buɗe, Wani irin sauti Jahan ya shiga fitarwa tamkar ranshi ne ke fita,hakan ba ƙaramin gigita Ayaan yayi ba,muryar jahan yaji ƙasa ƙasa yana cewa"Ayaan maƙoshina ya bushe!mutuwa zanyi ka taimakamin da ruwa insha,"agalabaice yake maganar,   Da hanzarin gaske Ayaan ya buɗe ƙopar ɗakin,anan yayi arba da Jahan baje ƙasa rai hannun Allah jikinshi sai karkarwa yake,wasu irin sahun bulali ne a jikinshi ta ko'ina ga shaidarsu nan asaman farar fatar jikinshi,dama babu kaya ajikinshi iya gajeran wando ne ya bari,    ɗaga ƙafa ayaan yayi zaije ya ɗauko mashi ruwan,kamar daga sama yaji jahan ya ruƙo kafarshi da ƙarfin gaske nan take ya kife ƙasa timmmm,jan jiki Jahan yayi tare da hayewa saman jikin Ayaan ya ƙankame shi ruƙo bana wasa ba,sannan ya shiga biyan buƙatar shi,wa'iyazubillah!wannan wata irin masifa ce!   Gaba ɗaya jahan ya gama kashe mashi jikinshi,ko hannunshi bai iya ɗagawa,babban abunda yake tsoro kada wani ya faɗo ya same su acikin wannan yanayin da suke,    kiciniyar kwace kanshi ya shiga yi da iya ƙarfinshi na karshe amma hakan ya gagara,a ƙarshe daya rasa yadda zaiyi saiya daddage ya garza ma jahan cizo asaman ƙirjinshi,ko gizau baiyi ba,    wani irin juyi Ayaan yayi anan ya samu nasarar hankaɗe jahan yayi gefe guda ƙasa,shi kuma ya tashi cikin sauri yana gyara short ɗin jikinshi,       Har yasa ƙafa zai bar ɗakin,yaji gabanshi yayi wani irin mugun bugu,cikin sauri ya juya tare da kallon jahan da idanunshi ke kallon sama,kwata kwata baya motsi komai nashi ya tsaya cak da yin aiki,waro ido waje yayi da hanzarin gaske ya koma wurinshi tare da zubewa saman guiwar ƙafafunshi yana ambaton sunanshi hankali a matukar tashe!   "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Jahan!jahan!don Allah kayi magana!ɗan uwana kada ka mutu ka barni!bana fata ace ni nayi silar barinka duniya!na cuce ka jahan nagaza cetonka!ka yafe mun ba laifina bane!"    Kuka sosai Ayaan keyi yana jijjiga jikin Jahan,bai da wata mafita a halin yanzu,ji yake tamkar ya watsa aguje yaje ya sanar ma su Abbansu halin da ake ciki,amma fargabar kada ace jahan ba mutuwa yayi ba,in har hakan ta faru to tabbas zai iya farkawa agabansu ya cakume shi ya shiga ƙoƙarin biyan bukatar shi agabansu,tunda baya acikin hayyacinshi,    Yasha kuka sosai kamar kamar me,a ƙarshe ya yanke shawarar zuwa ya ɗauko ruwa don ya yayyafa mashi ajikinshi ya ga ko zai farka,   A hanzarce ya miƙe tare da kama hanya ya fuce daga cikin bedroom din,   Sauri yake yi tamkar zai tashi sama aranshi sai addu'a yake yi Allah yasa jahan ba mutuwa yayi ba, Fitar shi ke da wuya daga cikin bedroom din nasu,Haroon ya faɗo cikin ɗakin afusace don yayi masu magana akan Money bag ɗinsa da yake zargin su suka ɗauke shi,koda yayi arba da jahan kwance aƙasa baya motsi,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,ta6e baki yayi tare da shigewa ciki,ya zukunna adaidai inda jahan ɗin yake kwance,yakai hannu tare da shafa ƙirjinshi,da yake shu'umine,nan take ya gane awane hali jahan yake,    sunnar da kanshi yayi tare da haɗe bakinshi wuri ɗaya dana jahan,zura tongue ɗinshi yayi acikin bakin jahan,aikuwa awani irin yanayi Jahan yayi motsi alamar yaji abunda yakeso,batare da 6ata lokaci ba Haroon ya shiga biya mashi buƙatar shi,      Ayaan na ƙarasawa wurin fridge ɗin yasa hannu tare da buɗewa cikin sauri,hannu yakai cikin jerin bottles water ɗin dake a jere cikin frigde ɗin,har zai ɗauki robar ruwan swan idon shi ya sauka akan Robar ruwan addu'ar nan da junaid ya ajiye ta sehrish,bakomai ne yaja hankalin shi akan robar ba,face rubutun Larabcin dake rubuce ajikinta,tunda akeyi masu order na abunsha,ba'a ta6a kawo masu kalar robar ruwan nan ba,mai rubutun labarabci ajikinta,zubama robar ido yayi yana kallonta nan take abunda ya faru ɗazu ya faɗo mashi aranshi,wasiwasi Ayaan yashiga yi acikin ranshi yana cewa"wannan roban ruwan kamar itace na ɗauka ɗazu nasha!kuma tunda nasha ta komai nawa ya canza,tabbas ina tunanin cewa tana tattare da wani abu ajikinta,amma kuma waye ya ajiyeta indai haka ne?don ina da tabbacin cewa ba'a kawo mana kalar wannan bottle water ɗin acikin gidan mu!bari na jaraba kaima Jahan ya sha,tanan zan gane abunda ke tattare da robar ruwan nan!"   Yana ƙarasa zancen zucin nashi batare da 6ata lokaci ba,ya sungumi robar ruwan a hannunshi,bayan ya rufe frigde ɗin,da saurin gaske ya wuce part ɗinsu,   Yana gab da shiga bedroom ɗin nasu,ya dinga jin wani irin gurnani mara daɗin ji,a wani irin tsorace ya afka cikin ɗakin,waro idonshi waje yayi saboda tsabar 6acin rai baisan sa'adda yayi wurgi da Robar ruwan dake a hannunshi ba,nan take ta faɗi ƙasa tana gangarawa murfinta ya cire,ruwan cikinta ya kwarare ƙasa gaba ɗaya,    A fusace ya ƙarasa tare da damƙar rigar haroon da iya ƙarfin shi na ƙarshe yayi wurgi dashi gefe guda,ɗagowa haroon yayi yana kallon Ayaan da idanunshi waɗanda suka canza launi izuwa jawur dasu,sai faman lashe bakinshi yake kamar wani tsohon maye,    Rai a6ace ayaan yace"wai kai wani irin daƙiƙin mutum ne dabba!kuma jahili wanda baisan ciwon kanshi ba!mugu azzalumi kawai,banta6a ganin fasiƙin mutum irinka ba!wanda baya tsoran Allah!"ran Ayaan ba ƙaramin 6aci yayi ba,yana magana hawaye na gangarowa daga idanunshi masu zafin gaske,    Duk a tunaninshi haroon zai ji haushin kalamanshi,amma abun mamaki fuskarshi ɗauke da wannan shu'umin murmushin nashi yace"Kwantar da hankalin ka mana!nifa ceton rai nike,duk irin son da kake ma Jahan ka gaza taimakon shi,kana ji kana gani zai mutu,ni kuma bazan so haka ba saboda inason ɗan uwana,shiyasa nayi hakan don na cetoshi daka halaka......'   Tunkan ya ƙarasa maganar Ayaan ya daka mashi tsawa tare da cewa"Karka kuskura ka ƙara ambaton sunan jahan a matsayin ɗan uwanka!kai ba jinin mu bane,mutun mai halin dabbobi irinka bazai ta6a zama jinin mu ba,yanzu bana doubting akan haka,Haruna kai ba ɗan uwanmu bane!ka wulaƙanta rayuwarmu,Allah ba zai ta6a barin ka ba,ƙarshen ka bazai yi kyau ba haroon!tun wuri ina baka shawarar ka tattara kayanka kabar gidan nan tun kafin lokaci ya ƙure maka!!!!"    fashewa da dariya haroon yayi,a yayin da yake miƙewa tsaye daga zaunen da yake a ƙasa,takawa yayi izuwa wurin da Ayaan yake sannan yace"naji duk bayananka akaina,kuma naji shawarar da ka bani,inaso ka sani cewa ko kaɗan banji tsoro akan kalaman da kayimun ba,ka ajiye wannan zamuyi magana akanshi,abun da ya kawoni ɗakinku shine Jakar kuɗin Da kuka kaimun ban ganta ba,an ɗauke ta daga ɗakina,kuma ba kowa nake zargi ba face ku,saboda ku kaɗae kukasan da zancen kuɗin,bayan ku babu wani da yasan da maganar!!ina jakar kuɗina take!!"     takaici ne yasa Ayaan kasa yin magana tabbas da ace yana da halin kawar da haroon da tuni yakai shi inda ya dace,    Cike da takaici Ayaan yace"maganar ɗauke jakar kuɗinka sam bata shafe mu ba,don haka tun wuri ka nemi wanda ya ɗauke maka kuɗinka!idan ma kanaso kayi amfani da wannan damar ne don kayi mana wayau ka ƙara samun wasu kuɗin awurinmu to inaso ka sani cewa ko sisi bazasu ƙara fitowa a wurin mu ba!bazamu baka ba!kaje kayi duk abunda kaga dama,'   Wani irin huci haroon ya runƙa fitarwa yana kallonshi yace"Kadaina yi mun magana A gadarance!taƙamarka kun goge videon dake a wurina to inaso ka sani cewa akwai wani videon a wurina!ni ba shashasha bane kamar yarda kukayi tunani!dama sai da raina ya bani cewa akwai wata ƙullalliyar da kuka shiryamun,don haka muddin baku dawomun da jakar kuɗina ba saina fallasa ku Uban kowa yaga abunda kuke aikata........'bai ƙarasa maganar ba saboda Ayaan daya kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya,nan take kan haroon ya ɗaure yashiga mamakin dalilin dariyar ta Ayaan,   Sosai Ayaan yake 6a66aka dariya kamar kamar me,hada dafe cikinshi,tashin hankalin da ba'a sama shi date,kwatsam yake zuwa,   duk wannan surutan da suke yi Jahan yana kwance a ƙasa sai faman juyi yakeyi saboda raɗaɗin da cikinshi ke yi mashi,sam baya acikin hayyacinshi,saboda he isn't satisfied,    "Me kake yi ma dariya"?haroon ya jefa mashi tambaya,   tsagaitawa da yin dariyar yayi yana Girgiza kai yace"Haroon ka gama yawo!wlh ka mutu!kai baka da tunani ne,bazan baka satar amsa ba,amma kaje kayi tunanin waye ya ɗauki jakar kuɗin nan!taya akai wani yasan da zancen jakar kuɗin nan har ya bi ɗakinka ya ɗauke ta!junaid kaɗae ne ya shigo cikin bedroom ɗinka a lokacin da muke tattaunawa,kuma kasan cewa junaid baya acikin sense dinshi ya shigo,koda ace yana cikin hayyacinshi bazai iya ɗaukar maka jakar kuɗin nan ba!to waye ya ɗauki jakar kuɗin?mu dai bamu bane!"?   shiru haroon yayi yana kallonshi gaba ɗaya ayaan ya burkita mashi tunaninshi,hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa,bai ƙara tanka ma Ayaan ba,cikin sauri ya kama hanya tare da fucewa daga ɗakin, Ajiyar zuciya Ayaan ya sauke,jin hannun mutum a ƙafarshi yasa yayi hanzarin kai idanunshi ƙasa yana kallon Jahan dake ta faman fitar da numfashi sama sama,hankali tashe ya shiga neman robar ruwan daya shigo da ita acikin ɗakin,can ya hangota ta gangara wurin shoe rack ɗinsu,murfinta ya cire ga ruwan ciki ya malale ƙasa,dafe kansa yayi da hannunshi na hagu cike da takaicin ruwan daya zube,    ƙokari jahan yake yayi mashi magana akan ya kira mashi Abbanshi karya mutu baisa shi a idanunshi ba,amma kwata kwata sounds ɗin bai fitowa abakinshi,ko idonshi bai iya budewa bare ya iya yin magana,gaba ɗaya Ayaan ya rasa yarda zaiyi,kanshi ya gama kwancewa,kamar yayi hauka haka yake ji,yana cikin wannan yanayin dubara tazo mashi,juyawa ya kuma yi yana kallon roban ruwan,Ruwan ya malale gaba ɗaya kasa ya tattaru a wuri guda,    Da saurin gaske ya ƙarasa wurin robar ruwan,tare da zubewa saman guiwowinshi,hannu yakai tare da ɗago da robar ruwan ya zaunar da ita ta tsaya tsaye,sannan cikin sauri ya sanya tafukan hannayenshi tare da kwalfo ruwan acikinsu,ya dinga zubasu acikin robar,yana ɗebowa wani na zubewa ahaka ya samu ya ɗan tara kaɗan wanda bai wuce ayi mashi kur6a uku ba ya ƙare,    ɗaukar robar ruwan yayi da sauri ya koma wurin jahan tare da zuƙunnawa agabansa,sannan yasa hannunshi na dama asaman lips ɗin jahan yana ƙoƙarin buɗe bakinshi,ya rufe bakin gam,hakan yasa Ayaan ya gaza samun damar buɗe mouth din nasa,   tsoranshi kar ace jahan ya mutu,saboda yayi delaying wurin kawo mashi taimakon gaggawa,   "Jahan pls,ka buɗe nasamo maka ruwan ka sha!banaso na rasaka ɗan uwana,"muryar shi tamkar zaiyi kuka haka ya dinga rokon shi akan ya buɗe bakin nashi ya sanya mashi ruwan,amma ko motsi wannan baiyi ba,   hannunshi har kerma yakeyi wurin ɗaga robar ruwan ya kaita saitin idanunshi yana duba rubutun dake ajikinta,larabci ne kuma shi baijin harshen larabci,balle ya gane me aka rubuta ajikinta,   Ganin zai rasa ɗan uwansa yasa ya ajiye robar ruwan ƙasa,sannan ya daddage da iya ƙarfinshi na ƙarshe ya sanya dukkan hannayenshi biyu ya shiga ƙoƙarin buɗe bakin Jahan,cikin sa'a bakin ya ɗan saki,da sauri Ayaan ya ɗauko robar ruwan tare da kafata a bakin Jahan nan take ruwan ya dinga shiga acikin bakinshi daƙyar daƙyar,wani na shiga wani na fita,ahaka yasamu ya bashi,bayan ya kammala yayi wurgi da robar ruwan gefe guda,sannan ya zauna tare da zabga tagumi yana jiran ganin sakamakon da zai biyo baya,hawaye sai shararo mashi suke a idanunshi,aranshi yana cewa"idan na rasa jahan bansan ya zanyi da rayuwata ba,nima zan bishi ne kawai,"    Yayi maganar tare da runtse idanunshi yana matse hawayen dake fita daga eyes ɗinshi,   Kafin Ayaan ya ankare,wannan baƙin hayakin ya soma kurɗaɗowa ta cikin ƙofofin hancin jahan,yarda kasan an koro shi daga cikinsa,haka ya dinga fitowa kafin kiftawar ido,hayaƙin yayi disappearing gaba ɗaya,tamkar bai ta6a existing ba,     Fitarsa ke da wuya,zufa ta soma tsastsafowa a jikin jahan,kamar an watsa mashi ruwa ajikinshi,haka zufar tashiga feso mashi,a hankali bakinsa ya buɗe ya shiga ambaton"La'ila ha'illallah!    A wani irin firgice Ayaan ya ware idanunshi sai lokacin ya kalli jahan dake kwance zufa ta gama wanke mashi jikinshi,wani irin farin ciki ne ya cika Ayaan la66ansa har rawa suke yi wurin ambaton sunan shi"ja..jahan"   Amsa mashi yayi da"Na'am," "Alhamdulillah!Alhamdulillah!Allah na gode maka!" Ayaan ne ke faɗin hakan yayin da yakai hannunshi yana tatta6a fuskar jahan dake ƙoƙarin buɗe idanunshi,     Tunani yazo ma Ayaan aranshi yace tabbas Ruwan cikin robar can ba normal ruwa bane da suka saba sha,akwai wani abu atattare dashi,tun da gashi Yaba jahan yasha kuma ya tashi da irin yanayin daya tashi dashi ɗazu da rana daya sha ruwan,ya tashi yana zufa kuma shima Jahan gashi zufar ce ke fita,hakan na nufin cewa shima Jahan ya warke kenan,   Ƙarasa tunanin nashi yayi tare da kai goshinsa ƙasa yayi sujjada yana ma Allah godiya,🥰    Bayan Jahan ya gama farfaɗowa,Ayaan ya taimaka mashi wurin kaishi toilet yayi wanka,nan take yaji wata irin natsuwa ajikin shi,basu 6ata lokaci ba wurin hayewa saman gadonsu,tare da lullu6ewa da bargo saboda baccin da kowannansu ke ji,yau gaba dayansu sunyi bacci cike da kwanciyar hankali,kuma Ayaan Yaci alwashin sai yayi investigation akan wannan robar ruwan da suka sha, (Banji daɗi da ruwan addu'ar nan ya zube ba,wlh nima ina buƙatar shi don nasha) Yanayi mara daɗi,a daren ranar Omar ya kwana yana kukan zuciya saboda abunda yayi ƙoƙarin aikata ma Hosana, ya kwana da tunanin wane hali suke aciki?sunyi bacci kuwa?baida amsar tambayoyin shi dole sai inya gansu,gashi baya jin zai iya takawa yaje dubasu saboda fargabar karsu gane cewa shine yayi masu wannan abun kunyar,matsananciyar damuwar daya sa ma ranshi ne da tunane-tunane ya haifar mashi da wani irin severe headache na 6arin kai,yaji jiki adaren nan har magani yasha amma bai sauka ba,a haka ya kwana yana juyi asaman gadonsa,   Adaren ranar nan dai abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa daɗin ji,dama haka rayuwa take ba kullum ake jin daɗin ta ba,idan yau anyi farin ciki,gobe zai iya kasancewa baƙin cikine,idan yau anyi dariya gobe zai iya kasancewa kuka ne,haka rayuwar ke tafiya babu wani yanayi da yake kasancewa permanently,Allah yasa mu dace,yasa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu,kuma ya kare mu daga aikata aikin danasani,wasu sun ɗauki rayuwar duniya wani abu,da har suka ɗauke ta da zafi suna aikata abunda suka ga dama,sun manta da cewa acikin seconds za'a iya zare ransu su bar duniyar gaba ɗaya suje su fuskanci abunda suka shuka,duka nawa ne jin daɗin duniyar?basa tuna donme aka halicce su,ta wace ƙopa suka faɗo duniyar nan,taya zasu koma ga mahaliccinsu?daga kai fa sai likkafaninka za'a binne ka cikin ƙabarinka,sai kuma halinka daka je dashi,na gari ne kona banza,😢Allah yasa mu cika da kyau da imani🙏 Wuraren sallar Asuba Sgr ya farka daga dogon baccin daya ɗauke shi,a hankali ya buɗe eyes ɗinshi,yayin da bakinsa ke ambaton addu'ar tashi daga bacci,a kasalance ya miƙe daga kwancen da yake saman doguwar kujerar,mamaki ne ya kama shi ganinshi kwance a palour ɗinsa yana bacci instead of saman gadon shi,ya jima yana mamakin yarda bacci yayi awon gaba da shi adaren jiyan nan,sauko da ƙafafunsa yayi ƙasa,idanunshi suka sauka akan tray ɗin da sehrish ta kawo mashi na dinner ɗinsa da baici ba jiya,tsayawa yayi yana ƙoƙarin tuna abunda ya faru adaren jiya,yunƙurawa yayi tare da tashi tsaye daga saman sofa din ya soma takawa walking slowly,jin sul6in wani abu a ƙasan tafin kafarshi yasa shi yin saurin kai idonshi wurin yana kallo,mamaki ne ya kama shi ganin Mayafin yarinyar nan yashe a kasa,yasan cewa shiya cire mata mayafin amma abunda ya ɗaure mashi kai zaman me gyalenta keyi acikin part ɗinsa?    russunawa yayi tare da kai hannunshi ya ruƙo gyalen tare da ɗagowa dashi yana kallon shi,sai lokacin ya tuna abunda ya faru jiya tsakanin shi da ita,na commanding ɗinta da yayi akan tayi tsallen kwaɗi,to ina yarinyar take,tambayar daya jefa ma kanshi kenan,    Cikin sauri ya zagayo ta bayan sofas ɗin tunkan ya ƙarasa ya hangi yarinyar kwance magashiyyan a sume bata motsi,tasha wahala sosai sam baiyi tunanin cewa zata cigaba da yin frog jump ɗin ba,yasan ba komai ne yaja hakan ba face tsananin tsoronshi da take ji,shiyasa bata yi tunanin ta tafi ba,tunda taga bacci yayi awon gaba da shi,      A hankali ya ƙarasa takawa inda take sannan yaɗan zuƙunna agabanta yana kallon sumar kanta data rufe mata fuskarta,hannu yasa tare da ruƙo gashin kan nata,ya janye mata shi daga saman fuskarta ixuwa gefe guda,    Zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallon yarda tayi jaga jaga da hawaye duk ta yamutse saboda kukan da tasha,idonta sun kumbura,haka la66anta ma sunyi suntum dasu,tsananin tausayinta ne ya kama shi,baiji daɗin baccin daya ɗauke shi ba,da baibari tasha wahalar nan ba,ba da nufin ya cutar da ita yayi hakan ba,kawai yaso ya ɗan hukuntata ne donta kiyaye shi sosai,     miƙewa yayi tare da nufar wurin fridge ɗinshi,ya buɗe ya ɗaukko bottle water daga ciki mai sanyi,sannan ya dawo inda sehrish take ya cire murfin tare da ɗebo ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi a fuskarta,ruwan na sauka asaman fuskarta,taja dogon numfashi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,a hankali tashiga mutsu mutsu zata buɗe idanunta,    "Get up" yace,jin muryarshi yasa sehrish ware idanunta akan sgr dake zuƙunne agabanta,jikinta har kerma yake yi wurin yunƙurawa tare da tashi daga kwancen da take ta zauna,tun kafin taji me zaice ta shiga bashi haƙuri tana cewa"dan Allah ka yafe mun babban yaya,bazan ƙara maimaita kuskuran da nayi....,.'    Kasa ƙarasa maganar tayi,a firgice ta shiga girgiza mashi kai ganin yadda ya ɗago da hannunshi,duk a tunaninta marinta zaiyi amma sai taga akasin hakan,a hankali ya aza tafin hannunshi a saman lallausar fatar gefen fuskarta,ɗan zaro ido sehrish tayi tana kallon fuskarshi,yayin da shi kuma yake kallon brownish lips ɗinta dake ta faman kerma,    Almost 5 mins sannan yace"Tashi ki tafi,"ya ambaci hakan tare da zame hannunshi daga gefen fuskarta sannan ya miƙe tsaye hannunshi ruƙe da bottle water ɗin yana maida murfin robar,daddagewa sehrish tayi tare da yunƙurawa daƙyar ta miƙe,aikuwa nan take ƙafafunta suka bada wani irin sauti ƙasss!,a gigice ta saki wata irin razananniyar ƙara nan take ƙafafun suka gaza ɗaukarta,gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa,sai dai ina kafin takaiga ƙasan tuni hannun sgr ya damƙi qugunta kwakkwaran ruƙo yayi mata da hannu ɗaya,gabanta ne taji yayi wani irin bugu daga bisani kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya ba ƙaramin tsorata tayi ba,har lokacin hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta,janyota Sgr yayi ta faɗo saman jikin shi gaba ɗaya,sannan ya ɗan russinar da kanshi tare da ɗago da ita,ya sanyata a saman kafaɗarshi,yadda kasan ya ɗauki wannan ɗiyar robar ƴar tsana,haka ya sa6i sehrish asaman shoulder ɗinshi,tafiya ya soma yi ɗauke da ita,ya ƙarasa wurin fridge ɗinshi tare da ajiye roban ruwan dake hannunshi,sannan ya juyo tare da kama hanya ya fito daga part dinshi kai tsaye ya nufi downstairs,ajiyar zuciya sehrish ke ta faman saukewa tayi lamo abunta,yadda take jin daɗin kafaɗar tashi tamkar ta hau Jirgin sama,    A natse yake taka matattakalar benen ɗauke da ita har ya ƙarasa saukowa da ita cikin Main palour ɗin nasu,bin ko'ina yayi da kallo babu kowa da alama basu kammala shirin zuwa yin sallar asubahin ba,duk da dama lokaci bai ƙarasa yi ba,a lokacin ake ta haramar fara kiran sallan, Tunani ya shiga yi a ina zai sauke yarinyar,don shi bai ta6a sanin ma a ina yarinyar take rayuwa acikin gidan ba,har wani lumshe ido sehrish take yi saboda yanayin da ta shiga wata irin kasala ga baccin da take ji,ta gaza yarda cewa sgr ne da kanshi ya sa6ota asaman kafaɗarshi,jin abun take kamar a mafarki,duk da halin da take ciki amma har addu'a take yi cikin ranta Allah yasa dagaske ne ba mafarki bane,    Yana cikin wannan tsayuwar ɗauke da sehrish a kafaɗarshi,kwatsam Abbansu ya fito daga bedroom ɗinshi ya tunkaro main palour din,sai faman sauri yake yi don yaje ya tashi sauran su tashi su kimtsa lokacin sallah yayi,tunɗazu yake trying numbers ɗinsu don ya tashe su amma mutum ɗaya ne kawai yayi picking call ɗin,wato kanal yousouf,amma sauran babu wanda ya ɗaga alamar basu tashi daga bacci ba,    Da wa Allah ya haɗa shi?ae yana fadowa babban falon karaf idanunshi suka sauka akan Sgr dake ɗauke da Sehrish a kafaɗarshi,har sai da gabanshi ya faɗi,cikin sauri Abba ya ɗan ja da baya saboda kar Sg rafayet ya ganshi,har wani murza idonshi yake yi da hannayenshi don ya ƙara tabbatarwa da kanshi abunda yake gani,wai ko idanunshi ne ke nuna mashi ba dai-dai ba,lamarin ya ɗaure mashi kai,tsananin mamaki ne matuƙa ya kama shi,har ƙara leƙawa yake yi don ya tabbatar ma kanshi wanene acikin matasan nashi ya ɗauko mace a kafaɗarshi,    Hasken fatar sgr,da kuma wannan doguwar ƙirar tashi ne suka tona mashi asiri,uwa uba doguwar sumar kanshi,   Doubting ya shiga yi yana cewa"Anya kuwa shine?kodai idona ne ke nuna min ba dai dai ba,kodai tsufa ne yazo mun gadan gadan harya sa nake ganin hakan!kai wannan fa Rafayet ne ba wani ba,yarinyar daya ɗauko a kafaɗarshi kuma wannan yarinyar ce sehrish!ita kaɗae ce ƴar matashiya acikin gidan!idan har zargina ya tabbata toh me ya haɗa shi da yarinyar ne harya ɗaukko ta saman kafaɗarshi?Hakan na nufin a bedroom ɗinshi ta kwana"? Ya jefa ma kanshi tambaya,gaba ɗaya ya kuma ruɗewa,   Can dai yace"Ina yi mashi kyakkyawan zato,amma tabbas akwai alamar tambaya anan!"   Shiru ya ɗanyi yana ƙara leƙensu,abunne ya daure mashi kai sosai tunda yake bai ta6a ganin sgr da mace haka ba,aranshi ya shiga cewa kodai Ya fara kula mata ne?wata'ƙil akwai wata alaƙa atsakanin shi da yarinyar,'   Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Biri yayi kama da mutum tabbas!sai yanzu na gane inda ya samu jan baki asaman ƙirjinshi,Oh ni hussein ina nan sake da baki ana mun aika aika acikin gidana!nagode ma Allah daya nunamin wannan abu akan idona,nasan me zanyi!"   Yana fadin hakan ya juya tare da komawa part ɗin nasu,don ya tashi sauran dama Upstairs ya nufa don ya tashi Omar,abunda yasa ya koma saboda baison sgr ya ganshi ya gane cewa ya ganshi ɗauke da Yarinyar a kafaɗarshi,    Jin takun tafiya yasa Sgr juyawa don yaga wanene,Azmee ce ta fito tana ta faman ƴan waige-waige,bakomai ne ya fito da ita ba face neman Sehrish, taje bedroom ɗinta donta tashe ta daga bacci taga babu kowa,hakan yasata fitowa don ta nemeta acikin gidan,    "Ke,zonan,"a ɗan firgice Azmee ta kallo inda yake,dama tunda taji an ambaci hakan tasan cewa Sgr ne,saboda shi kaɗai ke mata wannan kiran kai tsaye kamar wata ƙaramar yarinya,ko sunanta bai iya faɗi sai dae ke,don shi a yadda ya ɗauka duk wata mace ƙarama take awurinshi,   Fargaba ta shiga yi,ganin Sehrish kwance a kafaɗarshi,zullumi ta shiga yi acikin ranta,tsoranta kar ace wani abu ta aikata masa,    ƙarasawa tayi kusa dashi murya na rawa tace"Gani yalla6ai," Ko uffan baice mata ba,a hankali ya saukko da sehrish daga saman kafaɗarshi ya tsayar da ita akan ƙafafunta dake ta faman kerma,cikin sauri Azmee ta ruƙo hannunta,hankali tashe take kallonta ganin yadda ko'ina na jikinta ke kerma,cike take da son jin me ya faru da ita,Me ya haɗata da sgr da har ya ɗaukkota haka asaman kafaɗarshi,    Juyawa sgr yayi cikin sauri ya haye saman stairs da sauri da sauri yake taka steps ɗin sai da yakai step na ƙarshe sannan ya ɗan tsaya kamar mai nazarin wani abu, A lokacin azmee ta ruƙo sehrish tana taimaka mata wurin yin tafiya,a hankali a hankali suka nufi part dinsu,gaba ɗaya sehrish taji wani irin yanayi a tattare da ita,sam bataso sgr ya sauketa daga saman kafadarshi ba,don ba ƙaramin relief ta samu ba,ita kaɗae tasan yarda take ji aduk lokacin da takasance tare dashi,   Runtse idonta tayi yayin da hawaye ke cigaba da zubowa sun jiƙa mata fuskarta sharkaf,suna cikin tafiyar nan,ranta ya bata cewa ta ɗan jiyo ta kalle shi,taga yana nan ko ya tafi,   A hankali ta ɗan juyo da fuskarta, ta kalli upstairs din,adaidai lokacin shi ma Ya juyo da fuskarshi a wani slow,kai tsaye idanunshi suka sauka acikin nata dake kallon shi,gaza janye idanunshi yayi daga kallon hawayen dake shararowa a fuskarta,wani irin tausayinta ne yaji ya kama shi,saboda yasan cewa shine silar zuban hawayen nata,kamar yarda yake kallonta,itama haka take kallonshi duk da sunyi nisa da juna,a hankali ya lumshe idanunshi tare da ɗauke kanshi daga kallonta ya ƙarasa hawa upstairs ɗin da sauri ya wuce bedroom ɗin shi,    Sai bayan da ya 6ace ma ganinta sannan itama ta juyar da kanta tare da mayar da hankali wurin yin tafiyar,har cikin bedroom azmee takaita,ta taimaka mata wurin hayewa saman gadon,ta kwanta yayin da idonta ke kallon ceiling ba komai take tunawa ba,face yarda Sgr ya tarbo waist ɗinta a lokacin da tazo faɗuwa,da kuma lokacin da ya ɗaurota asaman kafaɗarshi,da kuma kallon nan daya juyo yana yi mata kafin ya tafi,   Zama azmee tayi daga gefen gadon tana kallonta tace"Me ya faru dake ne sehrish?meya haɗaki da sgr dana ga ya ɗaukko ki asaman kafadarshi"?    bata 6oye mata komai ba ta sanar da ita duk abunda ya faru a tsakaninta da sgr,   Jinjina kai Azmee tayi tare da cewa"u ave to be very careful rishi,tun farko saida na gargaɗeki akan shi,amma baki ji ba ko?    Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Aunty azmee ina kiyayewa,wannan ma matsala aka samu har na manta da gyalena asaman gadonshi,banyi tsammanin zai dawo ba a wannan lokacin......'   Shiru Azmee ta ɗanyi kafin tace"Shikenan amma duk da haka ki ƙara kiyayewa nan gaba,karki ƙara yin  gangancin maimaita kuskuren da kikayi yau,"    Sehrish tace"Insha Allah bazan ƙara ba,"    "Allah yasa,ni zan wuce,ki daure ki tashi kije kiyi sallah," Amsa mata tayi da"toh," sannan azmee ta miƙe tare da fucewa daga bedroom ɗin nata,ajiyar zuciya sehrish ta sauke,tunda ta kwanta ko kwakkwaran motsi wannan bata iya yi ba,jikinta duk yayi mata tsami,ta so ta tashi ta ɗan gasa jikin da ruwan zafi amma sam tagaza motsi,kamar an aza mata Bulo asaman jikinta haka ta dinga ji,yayi mata wani irin nauyi,a wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita.    _💋Boss Bature💋_ A washe gari Around 7:00am A firgice Jahad ta farka daga dogon suman da tayi,sakamakon jin saukar ruwan sanyi da tayi asaman fuskarta,a gigice ta tashi zaune,lokaci guda ta fara ambaton sunan Hosana!hosana!   "Jahad ki buɗe idonki Ni ce fa" Jin muryar mutum a kusa da ita yasa ta ware idanunta tana kallonta,bakowa bace face Nurse Camilla,zuwanta kenan ta shigo cikin falon taci karo da Jahad a sume ƙasa,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,da sauri ta ɗauko ruwa mai sanyi ta yayyafa mata,   A hankali jahad ke kallonta da idanunta waɗanda suka rune saboda kukan da tasha,   Sanye take cikin jeans da t- shirt tare ta ɗaure sumar kanta da ribbom,      a ɗan ruɗe tace"Jahad me ya faru ne?na shigo na same ki a sume menene ya faru dake ne"?   Cikin shessheƙar kuka tace"Hossana tana cikin ɗaki,bansan tana a raye ba ko ta mutu,jiya da daddare wani ya faɗo mana a cikin bedroom ɗin mu har yayi ƙoƙarin yin raping ɗinta........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya kufce mata,hankali a matuƙar tashe camilla ta miƙe tare da nufar hanyar zuwa ɗakin nasu,   Miƙewa jahad tayi tabi bayanta cikin sauri,zuciyarta nata faman bugawa saboda fargabar a wane hali hossana ke ciki, karfa ace wannan mutumin ya ƙara dawowa don ya cutar da ita,   Yadda jahad ta bar hosana haka suka sameta,naɗe cikin bargon a sume bata motsi,    Hawa saman gadon camila tayi ta ƙarasa kusa da Hosana tare da kai hannu ta shafa wuyanta,kallon jahad tayi dake atsaye cike da fargaba tace"dauko mun ruwan da na bari a falo," amsa mata tayi da toh sannan ta fuce daga cikin bedroom ɗin,within minutes sai ga Jahad ta dawo hannunta ɗauke da bottle water ta miƙa ma Camilla,hannu tasa ta kar6a sannan ta buɗe murfin ta debo ruwan tare da watsa ma hossana a fuskarta,nan take hossana tafarka daga suman da tayi,a wani irin razane ta zabura zata yaye bargon jikinta tana cewa"karka ta6ani Abba banso banso!ka ƙyale ni in tafi,inba haka ba Ya omar zai kashe ka...."  Cikin sauri Jahad ta haura saman gadon tare da rurruƙeta tana gyara mata bargon jikinta gudun kar tsiraicinta ya fito,ganin tana ta faman fisge fisge tana hargowa yasa Camilla tayi mata magana cikin sanyin murya tace   "Hosana!ki kwantar da hankalin ki,babu kowa anan da zai cutar dake,Ni ce Sister Camilla tare da ƴar uwarki jahad a kusa dake,dan Allah ki shiga natsuwarki,"cikin rarrashi takeyi mata magana, Jahad tace"Hossana gani a kusa dake ki buɗe ido ki kalle ni,"   Jin muryar jahad yasa hossana ta buɗe idanunta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,fuskar nan tayi sumtun saboda kukan da tasha,idanunta duk sun ƙankance,     "kiyi haƙuri hossana,koma waye Allah bazai barshi ba,nayi ƙoƙarin na kwace ki daga hannunshi amma Allah bai nufa ba,inda na gode ma Allah da bai ƙarasa nufinshi akanki ba,nayi ƙoƙarin na kira ƴa Omar,amma layinshi yaƙi shiga,amma zuwa anjima zan ƙara jaraba kiran shi,nasan zai ɗaga,"   Cikin shessheƙar kuka tace"Jahad ki kira mun shi,a kiramun ya Omar yazo,inason naganshi,shi nakeson gani,"    Jiki a sanyaye Jahad tace "Kada ki damu zan kira maki shi,insha Allah,"  gaba ɗaya lamarin ya girgiza Camilla,ta jima tana hasashen waye yayi ƙoƙarin cutar da yaran acikin gidan!duk irin tsaron dake gareshi,ba ita ba hatta jahad tashiga zargin waye yayi masu wannan zuwan da daddare don ya cutar da hossana,sun jima suna wannan tunanin, a ƙarshe dai bakowa suka fi zargi ba face ɗaya daga cikin security guards ɗin gidan,   Bayan sun gama jimamin nasu,Camilla ta tashi tare da fucewa daga bedroom din ta nufi kitchen don ta shirya masu breakfast,   yayin da ita kuma Jahad,ta taimaka ma hossana bayan ta sanya rigarta sannan ta kaita toilet ta taimaka mata wurin yin wanka da ruwa mai ɗumi yarda jikinta zai ɗan warware,sai da su kayi alwala sannan suka fito daga cikin toilet ɗin, doguwar riga ta ɗaukko mata acikin wardrobe ta bata ta sanya sannan suka zura hijabansu atare,jahad ta shimfiɗa masu darduma suka hau sama tare da daidaita natsuwarsu suka kabbara sallah,har lokacin jikin hosana sai faman kerma yake yi,a tsananin tsorace take da abunda ya faru da ita adaren jiyan nan,bayan sun kammala sallar jahad tace mata taje ta kwanta tayi bacci,ita zata wuce kitchen wurin Camila,ta taimaka mata suyi aikin breakfast ɗin atare,   Bayan jahad ta fuce daga bedroom ɗin,hossana ta miƙe daga saman dardumar jikinta nata faman kerma ga rawar ɗari da take yi,saboda sanyin da take ji,lalla6awa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu tare da janyo bargon ta ɗan kakka6e shi zata rufe Jikinta dashi,kwatsam taji sautin faɗuwar wani abu ƙasa,cikin sauri ta leƙa ƙasan gadon tana kallon abun nan daya fado daga saman gadon, Diamond ring ne ɗan ziriri dashi sai faman ƙyalli yake,gabanta taji ya faɗi rass!ganin zoben da tayi ya faɗo ƙasa,yunkurawa tayi tare da tashi daga zaune sannan takai hannu ƙasan gadon tare da ɗaukko zoban,ɗago shi tayi a daidai saitin idanunta tana ƙare mashi kallo, Zaro ido tayi hankalinta a matuƙar tashe ta furta"Ya Omar!!!!!!!!!" 😳 *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.    *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Abban sojoji paid book ne,ga duk mai buƙatar karanta cigaban shi yayi mun magana kai tsaye ta number ta 08103884440 Whatsapp only banda phone calls, 300 ne only 🤝 Zuba ma zoben ido tayi tana kallonshi hankalinta a matuƙar tashe,gabanta na faduwa,a hankali take jujjuya shi a hannunta,lokaci guda hawaye suka fara gangarowa daga idanunta cikin shessheƙar kuka take cewa"I can't believe it! Ya omar ɗina ne yayi ƙoƙarin raping dina? Shine yaso rabani da mutuncina?why ya Omar why!?innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah kasa mafarki nake ba gaske ba.......'kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta gaza ƙarasa maganar,nan fa tashiga shararar kwalla,abun ba ƙaramin ciwo yayi mata ba,bata ta6a tunanin haka daga wurin shi ba,wannan zoben nashi ne,shi ya tabbatar mata da cewa Ya omar ɗinsu ne yayi yunƙurin yi mata wannan aika-aikan,amma meyasa!? tsagaitawa tayi da kukan tashiga girgiza kanta tana cewa"A'a ya Omar ɗina bazai ta6a yi mun haka ba,na yarda dashi sosai,nasan cewa bada son ranshi yayi mun hakan ba,Ya Omar bazai ta6a cutar da hosanar shi ba,ina yi mashi kyakkyawan zato kuma bazan ta6a tona mashi asiri ba,bazan bari kowa yaga zoben shi ba ko jahad bazan nuna mawa ba,saboda nasan ba dole ta fahimce shi ba,kamar yarda ni na fahimce shi,"ƙarasa maganar tayi tare da ƙankame zoben asaman ƙirjinta ta ɗan runtse idanunta hawayen naci gaba da sauka asaman fuskarta, Dama ance so hana ganin laifi,hosana ta makance akan son ya Omar ɗinta,kuma ta yarda dashi 100%, tana cikin wannan yanayin taji motsin mutum cikin sauri takai hannu tare da janyo bargo ta ƙudundune acikin shi,6oye zoben tayi acikin aljihun rigar jikinta,sannan ta sanya tafin hannayenta tana goge hawayen fuskarta, Jahad ce ta shigo hannunta ɗauke da kakkauran tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,ƙarasawa tayi tare da samun wuri daga gefen gadon kusa da hosana ta zauna, a hankali tace"ƴar uwata rabin raina ga tea na kawo maki, ki tashi kisha shi da zafi zafinshi karya huce nasan zaki ji dadin shi,'cikin lallami take yi mata magana saboda tasan a halin da take na fargaba tana buƙatar kalamai masu daɗi da zasu sanyata farin ciki, lamo hosana tayi batare da ta motsa ba abunda yasa tayi hakan saboda tanason ta daidaita natsuwarta don kar jahad ta gano wani abu, jin shiru yasa jahad,kai hannunta na dama ta ɗan bubbugi kafaɗarta tace"tashi mana hosana ko kinyi bacci ne"?ta tambaya tana kallonta naɗe cikin bargo, Har jahad ta yunƙura zata tashi,hosana ta soma motsi alamar zata farka,komawa jahad tayi ta zauna tana jiranta ta tashin,a hankali ta yaye bargon tare da tashi daga zaune tana mutsistsika idanunta alamar yanzu ta tashi daga guntun baccin daya ɗauke ta,wartsakewa tayi ta buɗe ido tana kallon Jahad, Murmushi jahad ta sakar mata tare da cewa"babyn Omar ya jikin naki?nasan har yanxu kina fargaba akan abunda ya faru dake jiya,dan Allah hosana kada kisa damuwa kinji?insha Allah koma wanene asirinshi zai tonu,zamu faɗama ya Omar zai gano koma wane tsinan.........'a firgice Hosana ta toshe ma Jahad baki da tafin hannunta tana cewa"Jahad dan Allah kidaina maganar nan,kina tunamun abunda ya faru jiya,ni banason ma ana maganar nan,gabana faɗuwa yake yi,'ta ƙarasa maganar a sanyaye tare da zame hannunta daga bakin jahad, Ajiyar zuciya jahad ta sauke tare da cewa"Shikenan mubar maganar,yanzu dae ga tea ɗin kisha,kuma sister camilla tace na tambayeki in akwai abunda kike buƙata a girka maki kici," Hannu hosana tasa ta kar6i cup ɗin da jahad ta miƙo mata sannan tace"Bana buƙatar cin komai yanzu,ni dai akira mun ya Omar yazo inason ganin shi,' Murmushi jahad tayi tare da cewa"kada ki damu babyn Omar,nasan zaizo ne ina ta trying numbarshi amma taƙi shiga still switch off,amma nasan zuwa anjima zai kunna wayar ne," Jin haka yasa jikin hosana yin sanyi,don tasan dalilin dayasa Omar ya kashe wayarshi,bata ji daɗi ba saboda tasan zai sanya damuwa sosai aranshi,tausayinshi ne taji ya kama ta,babban abunda take fargaba shine kada ya hana kanshi zuwa wurinsu, tashi jahad tayi tare da fuce wa daga bedroom din ta koma kitchen,yayin da ya rage hosana ce kaɗai saman gadon tana kur6ar tea ɗin a hankali,duk jikinta yayi sanyi, After some days Abu kamar wasa yau almost 1 week kenan ba Omar ba alamar shi,hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,kwana huɗu ba Omar ko layin shi suka kira kullum a switch off suke samun shi,hakan ba ƙaramin tayar masu da hankali yayi ba,sun shiga damuwa sosai na rashin zuwan shi,musamman Hosana duk tabi ta takure kanta,ko abincin kirki bata iya ci,ko isasshen bacci bata samu,kullum cikin kuka take na rashin ganin ya Omar ɗinta,duk bayan ƴan mintina sai taje ta ɗauki telephone ta danna mashi kira,da zarar taji wayar akashe sai ta fashe da kuka,daƙyar jahad ke samu ta lallashe ta,akwai lokacin da jahad ta farka tsakar dare ta samu Hosana saman darduma tana yin sallar dare abunda bata ta6a ganin hosana tayi ba,kuma duk don saboda ya Omar ta tashi yin sallar daren,tana roƙon Allah yasa Ya omar yazo karya rabu dasu,batasan yaya rayuwa zata kasance mata ba,batare da ya Omar ɗinta ba,tana yin addu'ar tana matse kwalla,a wannan lokacin ba ƙaramin tausayi taba Jahad ba, A washe garin ranar jahad ta yanke shawarar zuwa tasamu Osman ta sanar dashi game da halin da suke ciki na damuwa da rashin ganin ya Omar ɗinsu,ko da Jahad taje ta samu Osman ta faɗa mashi,yayi mata alkwarin cewa zai bincika masu shi, Bayan tafiyar jahad,Osman ya nemi major a waya ya sanar mashi abunda ke faruwa,na halin da yaran suke ciki akan rashin ganin Marshal da basuyi ba na tsawon kwanaki ,jiki a sanyaye Major yace mashi yaci gaba da kwantar masu da hankali,insha Allah zaizo ne abubuwane sukayi mashi yawa. Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,lokacin da major ya sanar dashi halin da su jahad da hosana suke ciki,tsananin tausayinsu ne ya kamashi,musamman hosana da aka sanar dashi cewa ko isasshen bacci bata samu saboda damuwa akan shi,tamkar ya zubar masu da hawaye haka yaji,duk yarda yaso ya daure ya hana kanshi fargabar tunkararsu amma ya gaza yin hakan,ya nisanta kanshi dasu ne, saboda gudun karya ƙara jefa kanshi cikin matsala,shi kanshi daurewa kawai yake yi amma ba ƙaramin cutuwa yake yi ba,yana tsananin son ganinsu yanaso yaga wane hali suke ciki, amma ba yarda ya iya. A 6angaren Sehrish kuwa ba ƙaramin jiki taji ba,a washe garin ranar da Sgr ya sanyata tsallen kwaɗi,ko school bata je ba,saboda jinyar jikinta da ta tsaya yi,ƙafafunta sunyi suntum,tun da ta lafe saman gadon ko motsi bata son yi,ba ƙaramin jiki taji ba sai da azmee ta taimaka wurin gasa mata ƙafafun da ruwan zafi,tayi mata tausa sannan taji sauƙin jikinta sosai har ta samu ta warware taci gaba da ƙiriniyarta kamar yarda ta saba. Hayamm taji haushi sosai kamar ta binne kanta saboda tsabar baƙin ciki,tun washe garin ranar da azmee taje gyara part din Sgr,ta fito hannunta ɗauke da tray ɗin kayan abincin da baici ba,jiki na rawa hayaam ta ƙarasa tare da kar6ar tray ɗin tace tabar mata kayan takai kitchen, tana shiga kitchen dasu ta shiga buɗe kayan don taga idan sgr yaci abincin,sai dae abun takaici bai ta6a komai na abincin ba,yarda sehrish takai mashi shi haka aka dawo dasu bai ta6a komai ba,lemu kawai yasha,kuma ta manta bata zuba gashin acikin abun shan nashi ba,taji takaicin hakan kamar ta aza hannu abisa kanta tayi ihu saboda haushi,amma taci alwashin cewa saita shirya mata wani tuggun tunda ta tsallake wannan. A 6angaren su Twins kuwa sai dae muce Alhamdulillah,Yara sun zama mazajan gaske,rayuwarsu ta gyaru sosai,yanzu basa wasa wurin yin ibadarsu suna neman tsarin ubangiji,don wani lokacin atare suke tashi suyi ƙiyamun laili da sauran nafilfili,sannan basa komawa bacci bayan sallar asuba,zama suke yi suyi ta karatun alkur'ani mai girma har gari ya waye, Allah sarki rayuwa kenan ayayin da matsalar su jahan ta ƙare, shi kuma junaid wani mummunan al'amari ya soma faruwa dashi batare da sanin kowa ba,shi kaɗae yasan halin da yake ciki,kuma yaƙi sanar ma kowa saboda baison ya tashi hankalin Abbanshi da kuma na ƴan uwanshi,baka ta6a gane halin da yake ciki saboda babu abunda ya canza na daga ƙiriniyarshi, da kuma wannan kyakkyawan murmushin nashi,abun yana damunshi sosai, wannan ɗigon jinin dake fitowa ta ƙopar hancinshi, kullum ne saiya tashi tsakar dare batare da sanin Abbansu ba, ya shiga cikin toilet yana wanke hancinshi, abun sai ƙara gaba yake yi, ga yanayin da yake tsintar kanshi aciki,yanayi mara daɗi wata irin kasala da kuma yawan faɗuwar gaba,da kuma razanar da yake yawan yi,ko kiran sunan shi kayi da karfi sai ya firgita,ba kowa ya lura da hakan ba,tabbas rayuwar Junaid tana cikin hatsari sosai,a cikin jikinshi ciwon ke cin shi batare da sanin kowa ba, hmmmmmmm. A 6angaren Commandern ƴan iska kuwa wato haroon komai ya gama hargitse masa,kamar wani zautacce haka ya koma wurin neman jakar kuɗin shi,sam ya rasa samun kwanciyar hankali gaba daya plan ɗin da ya shirya na barin nigeria yana shirin rugujewa saboda rashin kuɗin nan,a ƙarshe ya yanke shawarar turo ɗayan videon nan nasu jahan don ya sake yi masu barazana dashi,su ƙara mashi wasu kuɗin da zai samu yabar ƙasar tunkan asirinshi ya tonu, Wannan kenan👌 Gaba daya an canzama gidan kamanni sai faman gyare-gyare akeyi mashi ta ko'ina,kwararrun ma'aikata aka ɗauko wurin tsara decoration ɗin da za'ayi ma gidan, yarda kasan za'ayi wani shagalin biki haka suka ƙawata gidan,duk wannan shirye shiryen da suke yi na tarbar manyan baƙinsu ne da zasu zo acikin kwanakin nan,a yau dae mutum biyu ne zasu fara zuwa,daga ciki akwai uncle Abusufyan da zaizo daga ƙasar turkey,sai kuma hajiya azeema da zata zo daga lagos, gaba ɗaya tunanin matasan gidan Abbansu yasa aƙawata gidanne kawai saboda zuwan su Ammin sa ne,abunda basu sani ba shi da wata manufa yasa a gyara gidan, Tofah, Wuraren ƙarfe 7:00am dai dai sehrish ta kammala shirinta na zuwa school,tana tsaye agaban mirror sai faman feshe jikinta takeyi da turare,bayan ta kammala ta koma wurin gadonta tare da kai hannu ta ɗauki hijab ɗinta data ajiye anan saman gadon ta zura ajikinta, bata ɗauki school bag ɗinta ba saboda tana so tafara zuwa kitchen wurin su Aunty azmee ta kar6a ma babban yaya breakfast ɗinshi takai mashi, fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin tana tafiya tana ƴan kalle kalle kamar zatayi tuntu6e,decoration ɗin da akayima gidan ba ƙaramin kyau yayi mata ba,don ba ƙaramin ɗaukar ido yake yi ba, Ƙarasawa kitchen ɗin tayi tare da tsayawa daga bakin kopar tayi masu sallama,Azmee ce kaɗae acikin kitchen ɗin,jin muryar sehrish yasa ta juyowa fuskarta ɗauke da murmushi tace"Ƴan makaranta har an kammala kimtsawa ne? murmushi sehrish tayi tare da cewa"ina kwana Aunty azmee,ya aiki"? Azmee tace"Alhamdulillah,shigo daga ciki mana in haɗa maki breakfast ɗinki ki ci kafin ki tafi,' "A'a Aunty azmee bana jin yunwa,idan naje school zanci acan,' har ta ɗanyi shuru, cike da son jin gulma ta kuma cewa"Aunty azmee wai wanene zaizo zo yau"? Murmushi azmee tayi tare da cewa"Masu kama dake ne zasu zo yau,' "Masu kama dani kuma Aunty azmee"?ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki, azmee tace"kwarai kuwa kuna kama da azeema kanwar Abbansu junaid dake lagos,amman kinfi kama sosai da Uncle ɗinsu, Abusufyan dake zaune a ƙasar turkey shima zaizo yau,' wani irin farin cikine taji ya lullu6eta,saboda ɗokin ganin wannan uncle ɗin nasu da take yawan jin suna ambatar sunanshi,a ƙagare take da ta sanya shi acikin idonta, "Aunty azmee dagaske muna kama dashi?ko wasa kike yi mun"? Azmee tace"dagaske nake mana,ban ta6a faɗa maki ba,amma maganar gaskiya kamanninki dashi har sun 6aci,kullum na kalli fuskarki sai ya faɗo mun araina,saboda komai na fuskarki irin nashi ne,tun daga kan idanuwanki,hancinki,da kuma bakinki duk irin nashi ne,ke hatta launin fatarki chocolate colour irin nashi ne,da ace Abusufyan ya ta6a yin aure,zan iya rantsewa cewa ke ƴarsa ce' tunda azmee ta soma magana sehrish ta saki baki tana sauraronta, "abun ya jima yana ɗaure mun kai,shiru kawai nayi,amma kamanceceniyarki da wasu daga cikin matasan gidan nan har taso tayi yawa," Cika da mamaki Sehrish tace"Aunty azmee wai dagaske"? murmushi azmee tayi kafin taci gaba da cewa"na ta6a yi maki wasa ne irin haka"? Girgiza kai sehrish tayi alamar a'a, Cigaba da magana azmee tayi"kina yanayi da Abbansu junaid sosai kuma kina kama da Auntynsu Azeema,hatta junaid akwai kamanceceniya atsakaninku abunda yasa baza a gane ba saboda hasken fatarshi,amma kina kama da shi,bayan shi kuma sai Marshal Omar,shima akwai kamanninshi atattare dake,da kuma kanal yousouf,na jima da lura da hakan," tunda sehrish taji wannan jawabin na azmee take ta faman sakin murmushi,daɗi kamar ya kashe ta saboda ance tana kama da uncle Abusufyan ɗinsu, "Aunty azmee naƙosa na ganshi,Allah yasa kafin nadawo daga school ya ƙaraso,da kaina zanje inyi mashi sannu da zuwa sannan in kai mashi abun sha," Dariya azmee tayi tana cewa"Allah yasa toh,amma kin manta baki ce insha Allah ba," cikin sauri sehrish tace"Insha Allah Aunty azmee," Suna cikin firar nan tasu,sai ga junaid ya faɗo cikin kitchen ɗin ko sallama babu a firgice suka ɗago suna kallonshi, daga shi sai gajeran wando fari ajikinshi,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna, "Junaid anya lafiyarka kuwa?kaine yau kake yawo da short ajikin ka?ko ka manta akwai sehrish dani acikin gidan"? Acewar Azmee, Murmushi ya saki tare da nuna sehrish da hannunshi yace"Wurinta nazo,inason magana dake reesh,in ba damuwa ki biyo ni muje bedroom ɗina,' Kallon azmee tayi don taji me zata ce, "kije mana,amma kada ki jima," Amsa mata tayi da toh sannan tabi bayan junaid suka fuce atare izuwa bedroom ɗinshi dake a upstairs, atare suka shiga cikin ɗakin nashi,har wurin gadonshi yakaita sannan ya tsaya tare da nuna mata shaddojin daya jera asaman gadon nashi yace"Pls reeshi ki za6amun ɗaya mai kyau,inaso yau nayi shigar mutunci don na burge uncle Abusufyan yasan cewa na girma yanzu,'ashagwa6e junaid ya ƙarasa maganar, Sehrish kuwa zuba ma tsadaddun shaddojin ido tayi tana kallonsu,kala biyar ne sun sha uban aiki ajikinsu,hannu tasa tana ɗaɗɗaga kayan tace"junaid ae ni nama rasa wadda zan za6a maka acikinsu,saboda kowacce kasa acikinsu kyau zatayi maka,bakasan cewa kaine keyi ma kayan kyau ba"? Tayi maganar tare da ɗan juyawa tana kallon junaid dake tsaye yana ta faman sakin murmushin jin daɗin yarda sehrish ke hura mashi kai, ta jima tana ruwan ido kafin ta cankar mashi wata haɗaɗɗiyar shadda gezner Ash colour sai faman salƙi take yi, mika mashi tayi tare da cewa"Wannan tayimun sosai kuma ina da tabbacin cewa in har ka sanyata ajikinka,sai uncle abusufyan ya razana da ganin irin kyan da zakai,' Kar6ar shaddar yayi daga hannunta yace"thank u so much reesh,amma fa ba yanzu zan sanyata ba,sai zuwa anjima in zanzo ɗaukarki daga school zaki ga kalar wankan da zan ɗauka," murmushi tayi tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom ɗin nashi tana cewa"Allah ya kaimu lafiya,yanzu dae zan jiraka,in ka kammala shirin ka fito mu tafi kar nayi late,' Amsa mata yayi da toh,bayan ta fita ya tattara shaddojin duka ya mayar acikin wardrobe ɗinshi, ya zaro wasu jeans da t-shirt ya shiga zura su ajikinshi _💋Boss Bature💋_ Lokacin da sehrish ta koma kitchen ɗin bata samu Azmee ba,sae dae Hayaam ta samu acikin kitchen ɗin,tana atsaye ta ruƙe qugunta kamar mai jiran wani abu, Ganin sehrish yasata cewa"Sannu ko" firgit Sehrish tayi tare da kai idonta inda hayaam ta ke atsaye tana sakin wannan shu'umin murmushin nata, "Yawwa"ta amsa mata atakaice tare da wucewa wurin trayn da azmee ta ajiye mata saman table wanda ta shirya ma sgr breakfast ɗin shi aciki,hannu biyu tasa ta ɗauki tray ɗin sannan ta kama hanya tare da fucewa daga kitchen din,hakanan ta dinga jin kamar bata yarda da hayaam ba,anya ba wani abu takeyi acikin kitchen ɗin ba?in ba haka ba meyasa ta tsaya atsaye ruƙe da qugu,kamar mai jiran wani abu, haka tayi ta wasiwasi acikin zuciyarta har ta ƙarasa part ɗin sgr, Sallama ta fara yi mashi,jin shiru ba'a amsa mata ba,yasa tayi tunanin ko yana acikin bedroom ɗinshi ne, A hankali tasanya kafarta tare da shigewa cikin palourn komai agyare tsaf ta same shi,asaman table ta aza mashi tray din sannan ta tsaya tana jiran fitowarshi ko zai bukaci wani abu, tana cikin tsayuwar nan tajiyo muryarshi daga cikin bedroom ɗinshi yana tambayar wanene anan!" Cikin sauri tace"Ni ce,dama breakfast ne na kawo maka," kusan minti biyar da yin maganarta sannan taji yace"A shigo min da coffee shi kawai nake buƙata," murmushi ta ɗanyi tare da mika hannu ta ɗauki cup of coffee ɗin dake acikin kayan breakfast ɗin nashi,ta nufi bedroom ɗin hannunta ɗauke da cup ɗin, sai da ta tsaya abakin ƙopar shiga Sgr ya bata izini sannan tasa kai tashiga,wani irin daddaɗan kamshin turarensa ne ya bugi hancinta,nan take taji wani irin yanayi atattare da ita, lumshe donta tayi tare da buɗesu a hankali ta kallo inda sgr yake, a hakimce ya ɗan kishingiɗa daga gefen katafaren gadon nashi, Gaza janye idanunta tayi daga kallon kyakkyawar surar jikinshi,wankan daya ɗauka ba ƙaramin fisgarta yayi ba,white trouser ne na suits amma bai sanya coat ɗin sama ba,iya vest ɗin ciki ya bari tabi shape ɗin jikinshi,daga ƙasan vest ɗin ta ɗan tattare hakan ya bayyana farar fatar shafaffen cikinshi, ya harɗe kafafunshi wuri guda yayin da idanunshi ke a lumshe, tafiya take tana tunkarar inda yake idonta akanshi har ta ƙarasa tare da ajiye mashi cup ɗin asaman bedside table ɗinshi tace"Gm sir,ga coffee nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata"? Bai amsa mata ba,a hankali ya dan buɗe idanunshi sannan ya yunƙara tare da miƙewa daga zaune ya sauko da ƙafafunshi ƙasa, Zaki iya tafiya,ya ambaci hakan ayayin da yakai hannu tare da ɗaukar kofin coffeen yakai bakinshi yana kur6ar shi anatse, Juyawa sehrish tayi ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin a hankali,ji take kamar karta tafi ta barshi,don bata gaji da kallon kyakkyawar fuskarshi ba, Yana cikin shan coffeen nan wani abu ya sarƙe mashi adaidai saitin throat ɗinshi,a hanzarce ya ajiye cup ɗin tare da zura fingers ɗinshi guda biyu cikin bakin cikin sa'a ya ruƙo siririn abun, Lokacin daya fiddo da abun daga bakin nashi yayi arba da dogon gashi,ware idanunshi yayi, hankali a matukar tashe yana kallon gashin yace"in my coffee...! Jin wannan maganar tashi yasa sehrish saurin juyawa don taga menene,a lokacin har tasa ƙafa zata fita daga ɗakin, Gabanta ne taji yayi wani irin mugun buga ganin siririn gashin da Sgr ya ruƙo a hannunshi, Yunkurin amai yashiga yi,nan take ya miƙe da saurin gaske ya faɗa toilet,kai tsaye ya ƙarasa gaban basin yana kwarara aman,tamkar ƴan hanjin cikinshi zasu fito,kasancewar shi mutum mai tsaftar gaske ga ƙyanƙyami ya tsani ƙazanta a rayuwarshi duk mun ƙankanta,ranshi ba ƙaramin 6aci yayi ba,gashi a abun shansa kuma har ya shiga bakinsa!!,a wannan lokacin komai zai iya aikatawa he can't even control him self, cos he has a very bad temper,kuma ta motsa. Tap ya kunna,ruwa yashiga zubowa yana kora vomitting ɗin da yayi,sannan ya tarba tafin hannayenshi biyu tare da ɗebo ruwan ya watsa su a fuskarshi yana faman sakin huci, Sehrish dake atsaye abakin kopan bedroom ɗin nashi,jikinta sai faman kerma yake yi,gaba daya tabi ta rikice kan ta ya gama ɗaurewa,taya akai aka samu gashi acikin abun shan Sgr?ita dae tasan cewa ba gashin kanta bane,saboda ta sanya hijab ajikinta,hasalima ba ita bace ta shirya mashi kayan breakfast ɗin nashi ba,tunkan taga hukuncin da zaiyi mata har tafara matsar kwalla,don tasan bazai ƙyale ta ba,dole ya hukunta ta, A fusace ya fito daga cikin toilet ɗin,sai faman huci yake yi,ɗagowa yayi da idanunshi yana kallon inda sehrish take atsaye jikinta sai kerma ya keyi,tunda taga zufa na gangarowa a gefen fuskarshi, ta ƙara tsorata sosai, tamkar wani zaki haka ya tunkaro ta,a tsananin tsorace sehrish ta shiga ja da baya tana girgiza kai cikin shessheƙar kuka take cewa"wlh bani da masaniya akan gashin nan,banawa bane bansan ya akai ya shiga cikin abun shanka ba,' wata irin tsawa da Sgr ya daka mata nan take sehrish ta firgita agigice take zazzare ido tana kallon fuskarshi, biting lips ɗinshi ya shiga yi,yama rasa wane irin punishment zaiyi mata, Nuna ta da dogon yatsan sa yayi tare da cewa"as from today!bana son na ƙara ganinki a part ɗina!' Cikin shessheƙar kuka sehrish tace"Am really sorry babban yaya........ba laifi na bane bada sani na gashin ya faɗa aciki ba..........'tun kafin ta ƙarasa maganar ya ɗaga hannunshi da nufin ya sharara mata mari,runtse ido sehrish tayi tana jiran jin saukar marin nashi a kuncinta, ji yayi bazai iya ba saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a gigin ta6a jikin wata ƴa mace ba da sunan bugu,tun suna yara Abbansu ya hane su da yin wannan,kullum yana tunasar dasu akan su dinga daraja ƴa mace, Dunkule hannunshi yayi tare da yarfar dashi gefe guda,sannan yace"Get out from my bedroom!since before I show u my true colour!, ya ƙarasa maganar tare da juyawa yabarta tsaye anan tana faman shessheƙar kuka, Ji tayi bazata iya jure hukuncin da Sgr yayi mata ba, na hanata aiki a ƙarkashin shi ba, gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi, a wani irin yanayi ta zube asaman guiwowinta,cikin sanyin murya,muryarta na rawa tace"nasan na 6ata maka rai sosai,na cancanci kowane irin hukunci daga gare ka,amma ina neman alfarma a wurin ka........'dakatawa tayi da maganar tana kallon bayan shi daya juya mata, ganin ya tsaya da yin tafiyar yasa ta gane cewa ita yake sauraro, anatse taci gaba da magana"ka yanke mun kowane irin hukuncin daya dace da laifin dana aikata,amma kada ka hanani yin aiki a ƙarkashinka,wannan horon yayi mun tsauri sosai,bazan iya jurewa ba,tun da nake maka aiki banta6a yin irin wannan gangancin ba,ina kiyaye wa sosai wurin ganin na tsaftace duk wani abu da zan kawo maka kaci ko ka sha,ba zanso wani abu da zai cutar dakai ba,wannan ma bansan ya akai hakan ta faru ba,don Allah kayi haƙuri ka yafe mun............'ƙarasa maganar tayi cikin shashsheka yayin da hawaye ke cigaba da zuba a idanunta, shiru Sgr ya ɗanyi na wani lokaci batare da ya motsa ba,hakan yasa ta fidda rai da cewar zai yafe mata, Hannu tasa tana sharar hawayenta tana kallon bayanshi,cigaba da tafiya sgr yayi kai tsaye ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,hannu yasa tare da janyo drawer chest din dake ajikinshi,sabon scissors ya ɗauko cikin ledarshi, ya fiddo dashi yana kallonshi, lokacin daya juyo hannunshi ɗauke da almakashin nan,hankali atashe sehrish ta zaro ido tare da miƙewa tsaye daga kneel down ɗin da tayi tana ja da baya tana girgiza mashi kai,alamar karyayi mata haka, Gadan gadan Sgr ya tunkare ta,hannunshi ɗauke da almakashin nan sai faman salƙi yake yi,hannu sehrish ta aza asaman kanta tana cewa"Nashiga uku!innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..........dan Allah kada ka datse mun gashin kaina ......'tana magana tana ja da baya yayin da shi kuma yake tunkararta,abu kamar wasa haka suka shiga zagaye ɗakin yana binta tana ja da baya,a ƙarshe daya fusata a zafafe ya damƙo hijabin dake jikinta tare da tun6uke ta daga jikinta yayi wurgi da ita gefe guda,yarda ya fusge hijabin daga jikinta gaba ɗaya ta tafi zata faɗi kasa,yakai hannu tare da janyo ta ta faɗo saman wide chest ɗinshi,kuka take kamar ranta zai fita saboda ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nan nata ba,ta kwallafa rai akanshi shiyasa kullum take ƙokari wurin gyara shi,har tasamu tatara shi da yawa bayan yanke shin da akai da zata fara aiki gidan,gashi yau akan kuskuren da ba ita ta aikata ba,za'ayi mata aski tana ji tana gani ba yarda zata yi, tunda sehrish ta faɗa jikinshi gaba ɗaya ya rasa duk wani kuzari na jikinshi,ƙamshin turaren jikinta ba ƙaramin kashe mashi jiki yayi ba,abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,a hankali yakai hannunshi tare da Cire ribbom ɗin da ta ɗaure gashin kanta dashi,ya warwaro shi duka tare da yin wurgi dashi gefe guda ya fadi kasa saman hijab ɗinta, Nan take lallausar suman kan nata mai laushin gaske ya tarwatse abayanta yayi mata tamkar hijabi, Ai ina baku labari tunda boss man ɗin nan ya zura hannunshi acikin sumar kanta nan fa yashiga murza gashin acikin hannunshi,laushin gashin kan nata ne yake fisgarshi har yayi hakan batare da saninshi ba, A hankali ya russinar da kanshi tare da kai tsinin hancinshi saman sumar kanta yana shaƙar daddaɗan kamshin dake fitowa daga cikin sumar kan nata,wani irin bugu zuciyarshi tashiga yi da sauri sauri take harbawa, ƙankame shi sosai sehrish tayi ta hanyar zagayo da hannayenta abayan waist ɗinshi ta ruƙo shi sosai kamar wani zai kwace mata shi,ba ƙaramin yanayi ta jefa Sgr ba ta kara sanya mashi kasala ajikinshi,kamar yarda itama ta shiga yanayin,tunda ta lafe mashi ajikinshi tayi lamo,wata irin natsuwa ta ji da bata ta6a ji ba atattare da ita,shessheƙar kukan nan da takeyi gaba daya ta neme ta ta rasa,tsit tayi tana sauraron heart beat ɗinshi, Suna cikin wannan yanayin na shauƙi sai ga Abbansu ya faɗo cikin part ɗin nasa yana neman shi,ganin baya acikin falon yasa ya wuce izuwa bedroom ɗin shi,tunkan ya ƙarasa ya hange su manne da juna kamar tip da tyre, adaidai ƙopar shiga bedroom din nashi,abban nasu ya tsaya cike da mamaki yana kallon wannan abun al'ajabin,ko motsi basa yi,bakomai yafi ɗaure mashi kai ba,face yarda sgr yake cakuɗa sumar kan yarinyar acikin hannunshi sai faman murzar gashin kan nata yake,ga kuma hancinshi daya cusa asaman kan nata yana shaƙar kamshin da sumar kan nata ke badawa mai daɗin gaske, Ita kuma ta ƙankame mashi qugunshi da hannunta,ta kwantar da kanta asaman chest ɗinshi, baki asake Abbansu ke kallon wannan tashin hankali,jinjina kai ya shiga yi cikin ranshi yana cewa"Oh ni hussein!tun yaushe wannan al'amarin ya soma faruwa acikin gidan nan batare da sani na ba!Hmmmm yanzu haka zare mata ido yakeyi yana tsoratar da ita don ya samu abunda yake so,nasan maganinka Rafayet,"ya faɗi hakan tare da kama hanya yabar part ɗin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi,don shi wannan abun farin ciki ne awurinshi,ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don tsabar farin cikin ganin rafayet tare da mace,baida burin daya wuce wannan arayuwarshi,shi dae yaga Sgr yafara kula mace da sunan soyayya,yau dae gashi Allah ya nuna mashi, Janye hancinshi yayi daga cikin sumar kan nata,sannan ya tattaro gashin nata tare da sanya almakashin ya datse mata shi,sosai ya yanke gashin,yabar mata guntu wanda ko kafaɗarta bai sauko ba,' hankali a matuƙar tashe sehrish ta raba jikinta da nashi, da sauri takai idonta akan hannunshi dake ruƙe da dogon gashin daya yanke mata,kamar a mafarki take kallon gashin nata daya yanke mata, A hanzarce takai hannu tare da shafo kan nata don taji sauran daya rage mata, Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita,dakyar takai hannu tare da ɗaukar hijab ɗinta, sannan ta juya tare da watsawa aguje tana kuka ta fuce daga cikin ɗakin nashi, ajiyar zuciya ya sauke tare da takawa izuwa gaban dressing mirror ɗin nashi ya mayar da scissors ɗin aciki tare da gashin kan sehrish daya datse,duka ya tura shi aciki ya ajiye,sannan ya maida drawer chest ɗin ya rufe, Komawa yayi tare da haye wa saman gadonshi ya kwanta,yanayin da bai ta6a ji ba atattare dashi ba yake ji,tsananin tausayinta ne ya kama shi,har ya dinga jin tamkar baiyi mata adalci ba daya datse mata gashin kanta,ya lura ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nata ba,lumshe idanunshi yayi a hankali yana tariyo abunda ya faru tsakaninta dashi,especially lokacin da ta watsa da gudu tana kuka,duk baiji daɗi ba saboda shi baiyi mata hakan da nufin ya 6ata mata rai ba.          *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Saboda masu complain, nacewa nace zan tura da safe ban turo ba,Allah ne bai nufa zan tura da safen ba, Ga half page nan,later zan tura sauran komawa cikin bedroom ɗinta tayi tana ta faman sharar hawaye ranta na kuna,wuri ta samu ta zauna daga gefen gadonta tana ƙarashe kukan nata,babban takaicinta guntun gashin da Sgr ya bar mata da kyar in zaiyi parking da ribbom,koma yayin ba lalle ribbom din ya tsaya ba,ta jima tana azaune tana matsar kwallar bakin ciki,kafin daga bisani ta miƙe tare da nufar wurin dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta acikin madubin,cikin shessheƙar kuka tace"Meyasa bai aske gashin duka ba yabarmun kwalkwali?me zanyi da guntun gashin nan daya barmun?ban son gashin!na tsani ganin shi,'ita kaɗae take ta faman sambatu rai atsananin 6ace, Kwankwasa ƙopar ɗakin nata akai,a tsiwace tace"Wanene"!   Muryar junaid taji daga waje yana cewa"It's me junaid,tun ɗazu fa nake jiranki,ki fito mu tafi na sauke ki,'a ƙagare yake maganar don ya gaji da jiranta, Ita gaba ɗaya ma ta manta da batun zuwa makarantar,sai da junaid ya tunasar da ita,     hannu tasa tana share hawayenta tace"junaid ka jira ni,acikin mota yanzun nan zan fito,"   Amsa mata yayi da"Okey," sannan ya juya tare da barin kopar dakin nata, Sai da tafara shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito tare da ɗaukar hijab ɗinta dake ajiye gefen gadon ta zura ajikinta Cikin sauri ta fito ɗauke da school bag ɗinta,ta fice waje wurin harabar ajiye motocinsu,hannu tasa tare da buɗe motar junaid ta shiga daga ciki ta zauna,   ɗan kallon fuskarta yayi tare da cewa"Reesh,na jima ina jiranki,bansan me ya tsayar dake ba,gashi ma har kinyi late,ina fata dae lafiya?" daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa"lafiya lou ba wani abu,mu tafi kawai ina ƙara makara,"    ajiyar zuciya ya sauke tare da jan motar suka bar gidan. Ita kuwa Hayaam dama tunda taga Sehrish ta nufi part din sgr da coffeen ta sulale ta shige dakinta don kar a gano abunda ta aikata. *HOSSANA* Zaune take saman gadonsu ta takure kanta sai faman shessheƙar kuka takeyi,ta sanya uniform ajikinta amma taƙi tashi ta zura hijabin,ta hana kanta duk wani jin daɗi, Fitowa jahad tayi daga cikin toilet tana kallonta gwanin ban tausayi tace"Hossana,dan Allah kidaina wannan kukan,duk kinbi kin takure kanki,ni nasan cewa ƴa omar ba hakanan ya daina zuwa wurin mu. Ba,Abubuwane suka yi mashi yawa shi ya sanya bai samu halin zuwa ba,' muryarta na rawa tace"jahad ba zaki gane bane,bazan ta6a samun kwanciyar hankali ba in har bansa ya omar a idona ba,Allah in har baizo ba yau,zanci shinkafar 6era ne na mutu kowa ya rasa,'   dariya jahad ta fashe da ita,hakan yasa hosana ɗaure fuskarta tana jifarta da harara tace"jahad dariya kike mun ko?   tsagaitawa tayi da dariyar tana girgiza kai tace"hosana dole nayi dariya,shinkafar 6era fa kika ce?   ɗaure fuska tayi tana murguɗa mata baki,   Murmushi kawai jahad tayi tare da komawa wurin closet ɗinsu,ta buɗe tare da ciro uniform ɗinta ta shiga zura su ajikinta,shaf shaf ta kammala shiryawa,ta ɗauko school bag ɗinta,sannan ta dawo wurin hosana tace"tashi mu tafi kada mu makara,"   Girgiza kai hosana tayi tace"Jahad ku tafi kawai,ni zan zauna a gida,saboda ko naje ba gane karatun zanyi ba,'   Zuƙunnawa jahad tayi agabanta tace"pls hosana ki daina sa damuwa aranki kinji?ni da kaina yau zan nemo maki ya Omar,'   jin abunda jahad tace yasa hosana sakin murmushi tace"dagaske Jahad"?   ɗaga mata kai tayi alamar eh tace"nayi maki alkwarin,duk inda yake indae yana acikin garin nan saina nemo maki shi,"   Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hosana,jiki na rawa ta tashi ta ɗauko hijabinta bayan ta zura safarta da takalmanta suka fuce atare,    A waje suka samu motar osman na jiransu,bayan sun shiga ya tashi motar ya fuce dasu daga cikin gidan,hosana sai murna take jahad tace zata nemo mata Omar,batasan cewa ita da wasa ta faɗa mata ba don ta sanyata farin ciki ne kawai, Wuraren ƙarfe 12 na rana,jirginsu hajiya azeema yayi landing daga lagos,kanal yousouf ne tare da su irfan suka je tarbosu,a lokacin hayaam suna a kitchen tare da azmee suna shirya lunch ɗin gidan da kuma na tarbar baki,daga kasa ƙafarka acikin main palour ɗin zaka ji daddaɗan ƙamshin abincin da suke girkawa ya gauraye ko'ina, Cike da son jin gulma hayaam tace"Aunty azmee,wai Uncle ɗin nan nasu da zaizo daga ƙasar turkey,yana da aure ne"?   Azmee tace"a'a bai ta6a aure ba,ina tunanin ma ko budurwa bai ta6a ajiyewa ba,"   jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"tabɗijancen amma da alama zaiyi ji da kai,"   murmushi azmee tayi tare da cewa"yarda kike tunani ba haka yake ba,Abusufyan wayayyan mutun ne,ta wani 6angaren ma bai ɗan jin magana amma dai nasan yanzu ya kimtsu tunda girma ya kama shi,amma lokacin baya da yake zuwa mana nan, yarda kikasan junaid haka ɗabi'unshi suke,da yake shi rainon goggonsu ne,'    murmushi hayaam tayi tana ɗan ta6e baki tace"Amma aunty azmee,ita wannan yarinyar sehrish,yakamata ace aikinta ya qare acikin gidan nan,tunda gani nazo kuma zan jima anan ne,ni a ganina bai kamata tana yawo acikin gidan nan ba,ita kaɗae ƴar matashiyya da ita,ya kamata ace tana gaban iyayenta yanzu,'ta ƙarasa maganar tana faman yatsina fuska,ta zuba ma azmee ido tana jiran jin me zatace, shiru azmee tayi saboda bata da amsar da zata bata, Cigaba da magana hayaam tayi"Yarinyar ta cika rawar kai sosai,yakamata ta tsaya a iya matsayinta na ƴar aiki mana,ni ina ganin akwai abunda take hari acikin gidan nan shiyasa ta liƙe har ta samu matsayi a wurin babban yaya," "Hayaam muyi sauri mu kammala aikin girkin nan,lokaci yana ƙure mana,"da gangan azmee tace mata haka,don ta dakatar da ita daga yi mata zancen Sehrish,don ita ta tsani gulma arayuwarta,   ta6e baki hayaam tayi,aranta kuma taji haushin yarda azmee ta katse mata hanzarinta batare da ta ƙarasa maganarta ba,daga bisani kuma ta saki shu'umin murmushin nan nata,tana tunanin ko ya Sehrish ta ƙare da sgr,don tasan cewa dole yaga gashin nan kuma zai hukuntata akan hakan,taso taje tayi masu la6e amma tsoro ya hanata gudun kar wani ya kamata asoma zarginta, Ƙasa ƙasa tayi da murya tare da cewa"Koda ace bai hukunta ta ba,nasan cewa zai fara tsanarta ne,kuma zai gane cewa ƙazama ce ita,zanci gaba da shirya mata makirci har nasamu na maye gurbinta a wurin sg......'bata ƙarasa maganar ba,saboda jin shigowar Hajiya Azeema tare dasu kanal yousouf da sauran da suka je ɗaukota,zuba ido hayaam tayi tana kallonta,ganin irin ruwan wankan gwala gwalan data ɗauka,   jikinta na sanye da material launin sararin samaniya,mai tsadar gaske sai faman ƙyalli yake yi,rigar takai mata har wurin guiwarta,sai zane data ɗaura,ta yafa gyale asaman kafaɗarta,yayin da ta kashe ɗaurin ɗan kwalin nan ture kaga tsiya,amma ita nata sunan shi ture kaga arziƙi,don akwai abun arziƙi,gaba daya earrings dinta da awarwaron hannunta da kuma sarƙar wuyanta duk gold ne,ta wanku iya wankuwa,Hajiya azeema kenan ɗaya daga cikin biloniyas din family nasu,idan aka cire shugaba kuma jagora wato Surgeon General Rafayet, Sai faman sakin murmushi take yi,tsantsar farin cikine ya lullu6eta yau gata agidan ɗan uwanta hussein,anjima ba'a haɗu ba,harkar kasuwanci ta 6oye ta,saboda bata cika zama a nigeria ba,kunsan business woman bata nan bata can kullum cikin hawa jirgi take wurin zuwa harkar kasuwancinta,   Atare suka ƙarasa cikin main palour ɗin,Kanal yousouf na ruƙe da Trolley ɗin da tazo dashi,    Anatse take bin ko'ina na gidan da kallo komai ya canza mata,ba kowa take muradin gani ba,face Junaid don har mafarkin shi tayi,shiyasa ta ƙagara tazo don tagan shi,juyawa tayi tare da kallon irfan tace"wai ina yaya hussein ne?naga kamar ba kowa gidan ko"?   "Abban mu ya ɗan fita garden tare da babban yayan mu da kuma ya Omar,amma ina da tabbacin cewa nan bada jimawa ba zasu shigo ciki,"ya ƙarasa maganar tare da nuna mata wuri yace"Aunty ki zauna mana,bari nayi ma Aunty azmee magana ta haɗa maki farfesun nan nata,nasan baki manta ɗanɗanon shi ba,"   dariya tayi tare da dan bugun kafadarshi tace"wato kallon acici kakeyi mun ko?daga zuwana ko hutawa banyi ba zan fara neman farfesu,kamar wata mayya,ni duk bama wannan ba,nifa hankalina bazai kwanta ba in har bansa junaid acikin idona ba,'    Kanal yousouf yace"Aunty gaskiya nafara kishi da junaid,haba kowa junaid junaid,ko hutawa ba kiyi ba amma kin fara ambaton sunanshi kamar shi kaɗae ne ɗa acikin gidan nan,"cikin zolaya yayi maganar tashi, Kafin Azeema ta kuma cewa wani abu,sai ga azmee ta fito daga cikin kitchen fuskar nan ɗauke da murmushi tana cewa"wata sabon gani, hajiya azeema,Sai yau zamu sake sanyaki acikin idanunmu"?tayi maganar a yayin da take ƙarasawa wurinta suka rungume juna,dama suna ɗasawa da ita,mutuniyarta ce kodan saboda iya girkin azmee yasa take shiri da ita sosai,don ita bata wasa da abinci,akwai son cin mai daɗi,kullum tazo Abuja wurinsu burinta tasha farfesun azmee,   Raba jikinsu sukayi dana juna,Azmee taci gaba da cewa"Hajiya azeema kece kika koma haka? Dariya azeema tayi tace"kinji ki da wata magana,kamarya na koma?nasan halinki fa azmee yanzu kince na ƙara ƙiba,'   Azmee tace"kin tsargu kenan,tunda gashi nan kin rigani faɗin abunda zance,'   Ta ƙarasa maganar tare da ruƙo hannunta tace"nasan kin kwaso gajiya sosai,shiyasa na gyara maki shinfiɗa inda zakije ki yada gajiyar da kika kwaso,sannan akwai special suya da kuma wannan farfesun da kika fiso na shirya maki shi,da zarar kin kammala hutawa zan shiryo maki shi,kici ki ƙoshi,nasan mutuniyar tawa bata wasa da cikinta,akwai bama ciki haƙƙinsa,"     Sai faman murmushi hajiya azeema ke saki,da alama taji daɗin karramawar da azmee tayi mata sosai,atare suka wuce ciki izuwa bedroom din da zata sauka,dama already azmee ta gyara mata ɗakin sai ƙamshi yake,    bayan sun shiga bedroom din,Sai da suka ƙara gaisawa sosai,kafin daga bisani Azmee tabar cikin ɗakin ta koma kitchen,    Ajiyar zuciya hajiya azeema ta sauke tare da cire mayafin cikinta ta ajiye shi saman gadon,sannan ta wuce cikin toilet,   Bayan shigarta kanal yousouf ya shigo cikin bedroom din hannunshi ruƙe da trolley dinta,jingine mata shi yayi ajikin wardrobe,sannan ya juya ya fuce,    fitowa azeema tayi daga cikin toilet din har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi a fili tace"oh ni,koya junaid ya koma yanzu?nasan cewa ya ƙara girma sosai,gaskiya nayi missing shagwa6ar shi,nasan cewa da zarar yaji cewa na ƙaraso,zaizo ya ishe da rigima yana cewa Ina tsarabar shi,'ta ƙarasa maganar tare da hayewa saman gadon ta ɗan kishingiɗa donta runtsa, Bata jima da kwanciya ba,Abbansu ya shigo cikin gidan tare da sgr da marshal atare suka ɗunguma zuwa masaukin nata,a hankali abba ya tura ƙopar ɗakin suka shiga da sallama,   Jin muryar ɗan uwanta,yasa ta yunkura tare da miƙewa daga zaune tana kallonsu fuskarta ɗauke da murmushi,    Ƙarasawa ciki su kayi,sgr da omar suka samu wuri saman doguwar sofa din dake dakin suka zauna suna fuskantarta,yayin da Abbansu kuma ya samu wuri gefen gadon kusa da ita ya zauna fuskar nan awashe sai faman farin ciki yake yi na ganin ƴar uwarsa daya jima basu haɗu ba,    gaisawa suka shiga yi da junansu,don ba ƙaramin kewar juna sukayi ba,   Abba yace"ina fata dae da shirin zama kika zo mana,dan wannan karan bazan bari ki koma ba,nagaji da kewarku da nake ta faman yi,'    "Yaya hussein,nasan ban kyauta ba,na rashin zuwana wurinku,abubuwane sunyi mun yawa shiyasanya na jima banzo ba,amma Insha Allah wannan karan har sai kun gaji dani,zan zauna ne har sai an ɗaura auren junaid,'   Fashewa sukayi da dariya gaba dayansu,banda Sgr wanda tun shigowarsu,ya jingina bayanshi ajikin sofa din tare da lumshe idanunshi,sarai azeema ta lura dashi dama sai da ranta ya bata cewar bazai tanka mata ba,    Omar yace"ae ni fushi nake da Auntyn tawa,haba aunty azeema yau kusan wata nawa kenan?yaushe rabon da mu sanyaki a idanunmu,baku son zuwa ganin ƴa'ƴanku,kuma babu damar mutum yace zaizo ganinku saboda kullum baku a ƙasar,'ya ƙarasa maganar tare da ɗaure fuskarshi,    dariya azeema tayi tana cewa"kwantar da hankalinka mutumina,ae wannan zuwan daka ga nayi,bazan koma ba har sai naga an shafa fatihar auranku,kai da wannan namijin zakin,'   tayi maganar cikin zolaya tana kallon Rafayet,aikuwa ya ƙara ɗaure fuskarshi alamar baiso,   Murmushi Abbansu yayi tare da cewa"kada ki samu damuwa,ae kuna anan ma zamusha biki,Abusufyan kawai nake jira ya ƙaraso,don nafison ya shaida wannan ɗaurin auren,ayi komai tare dashi don shine waliyyi"   Jin wannan maganar ta Abban nasu yasa shi buɗe idanunshi tare da miƙewa daga saman sofa ɗin ya nufi hanyar fita,duk suka zuba mashi ido, Sai da yakai bakin kopar fita sannan ya ɗan juyo tare da kallon inda Hajiya azeema take zaune yace"Allah ya huta gajiya,"yana faɗin hakan yasa kai ya fuce daga ɗakin,   Girgiza kai Abbansu yayi tare da cewa"Rafayet sai addu'a abun nashi ƙara gaba yake yi,"murmushi kawai azeema tayi aranta tace"Jinin Alexandra kenan,in har rafayet baiyi mun haka ba,bazan tabbatar da cewa nononta ya sha ba, Ganin rafayet ya fice yasa Omar miƙewa tare da yi masu sallama ya fuce yabarsu donsu samu damar tatttaunawa atsakaninsu yasan sunyi kewar juna sosai, Bayan fitar Omar,azeema ta kalli abban nasu tare da cewa"Yaya hossein,ya maganar zuwan Abusufyan din?dagaske ne yau ɗin shima zaizo?kasan fa ya jima yana samana ran cewa zaizo sai kuma yaƙi zuwa daga baya,abun na damuna sosai,"fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,   "ya tabbatar mun da zuwan nashi,kuma ina da tabbacin cewa wannan karan dagaske yake mana ba wasa ba,inaso yazo saboda akwai abubuwa da dama da nake son muyi magana akai,na damu dashi sosai,na damu da halin da yake ciki," Jinjina kai tayi tace"amma abba,akwai wata alfarma da nake nema awurinka,"    "Wace alfarma kenan"?acewar abban nasu,   Cigaba da magana tayi"idan Abusufyan yazo nigeria wannan karon banso ku bari ya koma turkey,dan Allah ka ruƙe shi anan,ya zauna akusa dakai,banason yanayin nesa dakai,har yanzu akwai sauran yarinta atattare dashi,shi ne ƙarami acikinmu akwai buƙatar mu janyo shi ajikinmu,don muji menene ke damunshi,meyasa baya son zama ƙasar nan,ni nasan akwai dalilin da yasa abusufyan yake gudun zama anan,tabbas akwai damuwa atattare dashi,"    Abba yace"dama ni bazan barshi ya koma can ba,bazan ƙara yin gangancin barinshi yayi nesa dani ba,koda can daya bar ƙasar batare da sanin mu ya tafi ba,narasa gane mashi ni kaina,ba yarda banyi dashi ba akan yadawo nan gida amma yaƙi saurare na,wannan karan dae mun ci sa'a ya amince zaizo,kuma insha Allah idan yazo bazan barshi ya koma ba,zan ruƙe shi awurina,'   Ajiyar zuciya azeema ta sauke,hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,dama ita burinta Abusufyan yadawo kusa da Yayansu hossein su zauna atare da ƴa'ƴanshi,tafi son taga sun haɗa kansu wuri ɗaya,ita kanta ba da son ranta take zaune a lagos ba,sabo ne kawai sai kuma harkokin kasuwancinta da suka fi yawa acan,    Sun jima suna fira tsakaninta da ɗan uwanta,kafin daga bisani yayi mata sallama tare da fucewa daga ɗakin,komawa azeema tayi tare da kwantawa saman gadon,nan take bacci yayi awon gaba da ita, A 6angaren sehrish kuwa tunda taje school,fuskarta babu annuri ko kaɗan duk tabi ta takure kanta asaman seat ɗinta,ko magana batasan yi,juyowa Amrish tayi ta kalli fuskarta tare da cewa"wai meyake damunki ne Sehrish?duk kin bi kin canza,ki faɗamun mana in akwai damuwa,may be ina da shawarar da zan iya baki,"    shiru tayi na wani lokaci kafin tace"Zan faɗa maki,but pls kada ki sanarwa kowa,"   "Insha allah,i will keep ur secret bazan bari kowa yaji ba,"amrish tayi maganar tare da mayar da hankalinta kan sehrish,    matsowa sehrish tayi kusa da amrish tayi ƙasa ƙasa da muryarta sannan tace"Amrish,babban yayanmu ne ya datse mun gashin kaina,dana kwallafa rai akanshi,na jima ina gyara gashin kaina,sai da yayi tsayi sosai yayi kyau,shi kuma ya datse mun shi da almakashi,baki ga wanda yabar mun ba,ɗan guntu ko parking ma bayayi,in nasa ribbom ma zamewa yakeyi,baya ruƙe gashin,'    Hankali tashe Amrish tace"Are u serious!shi da kanshi yayan naku ya yanke maki gashi?baisan cewa gashi tsada yake yi ba,?amma garin yaya hakan ya faru?ta tambaya tana jiran amsarta,   shiru ta ɗanyi kafin tace"ni kaina bansani ba Amrish,da safe ne naje kai mashi coffee,yana cikin sha wani abu ya sarƙe mashi a throat ɗinshi,ashe gashi ne ya faɗa ciki,kuma ni banawa bane,nayi ƙoƙarin nayi mashi bayani akan hakan,amma bai saurareni ba,kawai yasa almakashi ya datse mun gashin,'ƙarasa maganar tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka,   hannu amrish tasa tare da dafe goshinta tace"Ya salam,amma banji daɗi ba wlh,ni babban abunda nafi takaici shine,wazai aure ki a haka da guntun gashi,kinsan fa mazan yanzu sunfi son mace mai dogon gashi,"cike da zolaya amrish tayi maganar tana ƙumshe dariya abakinta,   Harara sehrish ta watsa mata tare da cewa"Oh abun ya zama na zolaya ko?ina faɗa maki damuwata maimakon ki tayani jimami shine kike mun dariya,'    "No,ba haka bane sehrish,nadamu nima sosai,rai na ya 6aci amma kada ki sa damuwa aranki,zan iya taimaka maki da hular gashi in kinaso,'    Cike da farin ciki sehrish tace"dagaske kike ko wasa"?   Amrish tace"am serious,ina dasu ajiye a gida zan ɗauko maki ɗaya daga cikinsu,amma bisa sharaɗin zaki kawo mun gashin kanki da babban yayanku ya yanke maki,inaso zanyi amfani dashi wurin haɗa wata hular gashin,ba ƙaramin kuɗi zamu samu ba,'    murmushi Sehrish ta saki tare da cewa"shikenan insha Allah,zan kawo maki gashin gobe in zanzo school,'    "Allah ya kaimu lafiya,"Amrish ta amsa mata,ci gaba da fira su kayi atsakaninsu har sae da malamarsu ta shigo sannan suka dakata da yin surutun nasu, _💋Boss Bature💋_ Ana gab da za'a tashe su daga school,ciwon ciki yazo mata mai tsananin gaske,gaza jurewa tayi hakan yasa ta miƙe tare da zuwa wurin Aunty ɗinsu ta nemi izinin fita a wurinta,bayan ta amince mata ta fito daga class ɗinsu,sai faman sauri takeyi,hannunta ɗauke da school bag dinta,wani corridor ta nufa inda toilets din makarantar suke a jere,ɗaya daga cikin toilet din ta buɗe tare da shigewa ciki ta rufo shi,juyawa tayi tana kallon cikin toilet din komai na cikinshi fari ƙyal atsaftace,hannu tasa tare da zuge zip ɗin jakarta,ta ciro pad din da tazo da ita guda ɗaya,dama tun last week take jin alamun zuwan al'darta amma baizo ba,sai dae stomach pain da take ta fama dashi,wannan dalilin ne yasa take yawo da pad a jakarta just in case,    ajikin towel hanger,ta rataya jakarta,sannan ta zame dogon wandon jikinta,pant ɗin ta curo tana dubawa taga ko ya fara zuba,babu ajikin pant ɗin,amma da taje wurin yin tsarki bayan tayi fitsari sai ga ɗigon jinin ya fito,cikin sauri ta sanya pad din ajikin pant dinta,sannan ta sanyashi ajikinta,ta ɗauko dogon wandon ta mayar ajikinta,sai da ta zura shi ajikinta,ta ɗauko jakarta tana ƙoƙarin fita daga cikin toilet din kenan,cikinta ya murɗa mata,wani irin raɗaɗi mara daɗin ji,nan take ta zukunna ƙasa hannunta dafe da cikinta,zufa ce ta shiga gangaro mata agefen fuskarta,daƙyar take fitar da numfashi,lokaci guda gaba daya ta galabaita ta fita hayyacinta,anan ta faɗi kwance saman tiles tana juyi ita kadae acikin toilet ɗin,babu wanda yasan abunda ke wakana. *Junaid* *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 *Na sadaukar da wannan zazzafan page din,ga dukkan masoyan littafin Abban sojoji,especially members na paid grp dina,Abban sojoji paid grp,Father of soldiers,Abban sojoji Vip grp,da kuma Junaid romeo Much luv Allah yabar zumunci anatare insha Allah (08103884440)*😍😘 *Bazan manta daku ba,waɗanda suka ƙarfafamun guiwa wurin rubuta littafin nan,har yau ina alfahari daku, Fadeela lamiɗo da kuma sadeeq abubakar CEO na Lafazi writer association,da kuma auntyna takaina,bazan fadi sunanta ba,sai na nemi ixninta saboda tsaro🤣😂😅 Da kuma sauran members dinda akayi fadi tashi dasu,suma duk zan fadi sunayensu nan gaba* *Abban sojoji paid book ne,duk maison siye zaiyi mun magana kai tsaye ta layina,but pls banda kiran waya,only message ta whatsapp,bana shariya muddin mutun ya turamun saƙo zan duba ne,indae ina free,in mutun yayi payment zan tura mashi duka na baya da aka wuce shi har inda muke so* ❤🤍❤ *Junaid* Tun bayan daya kai Sehrish school ya biya gidansu wani abokinshi,wanda tun suna secondry school suke tare,acan ya yini har bacci yayi awon gaba dashi asaman gadon mamarsu abokin nasu,saboda tsabar gatanci bama gadon abokin nashi ba,a ɗakin mamarsu yayi baccin,daga shiga su gaisa da ita,ya samu ta shiga cikin toilet,shi ne ya ɗan kishingida saman gadon ya shiga sharar bacci,wuraren ƙarfe daya ya farka ganin lokacin tashin su sehrish daga school ya kusa yi,nan yayi sallama da mutanen gidan,jiki na rawa ya shiga motarshi tare da barin gidan,   da gudu ya fisgi motar saboda ya ƙarasa gida da wuri,ba don komai ba sai don alkawarin da yayi ma sehrish na cewa in zaizo ɗaukarta daga school zai nuna mata wankan da zai ɗauka na shaddar shi,    yana ƙarasowa cikin gidan bayan yayi parking din motarshi,ya wuce cikin main palour ɗin,a lokacin duk sun fita yin sallar azhar da ake cikin kira,bedroom dinshi ya shige tare da rage kayan da ke jikinshi ya faɗa cikin toilet,shaf shaf yayi wanka cikin minti goma sha biyar,ya fito daga cikin toilet din,jikinshi sanye da bathrobe,     Gaban dressing mirror dinshi ya zauna,yadda kasan mace haka ya zauna yana gyara jikinshi,sai da yabi ko'ina na jikinshi ya shafe da mai,sannan ya shiga gyara sumar kanshi,bayan ya kammala ya miƙe tare da komawa wurin wardrobe,ya buɗe tare da ɗauko shaddar,a natse ya shiga zura kayan ajikinshi bayan yasa vest da short farare kal,rigar takai masa har guiwarshi,sai wandon,lokacin daya kammala sanya shaddar ajikinshi dawowa yayi tare da tsayawa gaban madubi yana kallon fuskarshi ta ciki ya Allah!shi kanshi sai da ya tsorata da irin kyan da yayi,kamar shiya zana kanshi don kyau,shaddar ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,sae faman salƙi take ajikinshi kamar wani sabon ango,kyakkyawan murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"junaid kenan yakamata ka zama namiji mana,ka cire duk wata fargaba yau ka tunkari sehrish gaba da gaba ka bayyana mata irin son da kake mata batare da jin shakkar komai ba,'    shiru ya danyi aranshi yana cewa"gaskiya ina jin fargaba fa,anya reesh zata amince da son da nake mata?in tace bata sona fa?tabbas zan iya rasa raina,amma zan jure yau dae na fahimtar da ita tsananin son da nike mata,'   Ƙarasa maganar yayi tare da ɗauko hula mahadin kayan wadda take tsadaddar gaske sai daukan ido take itama ash colour ya aza saman kanshi,hmmmm abun ba'a magana madarar kyau ba kaman da sumar kanshi ta dan fito daga baya.   Zura takalmanshi yayi masu kyau da tsadar gaske suma mahadin kayan,sannan ya koma gaban dressing mirror ɗin ya ɗauko turarenshi ya shiga feshe jikin shi dashi ko'ina saƙo da lungu,nan take ƙamshin ya gauraye ko'ina na ɗakin,   Key ɗin motar shi ya dauko sannan cikin sauri ya fito daga ɗakin nashi ya sauko downstairs,babu kowa a falon duk sun tafi salla, A hankali yake driving din motarshi fuskar nan dauke da annuri,sae da yafara tsayawa masallaci yayi sallah,sannan ya miƙi hanyar makarantarsu sehrish,shiga ciki yayi tare da yin parking ɗin motar sannan ya fito ya tsaya tare da jingina bayanshi a jikin motar,zuba ido yayi yana jiran fitowar sehrish amma babu ita babu alamarta,ga students sai fitowa sukeyi,wasu na hawa bus wasu kuma ana zuwa ɗaukarsu,    Gajiya ya fara yi da tsayuwar, "Wai ina reesh ta shige ne,ta barni tsaye ina ta faman jiranta,'rai aɗan 6ace yayi maganar,    Juyawa yayi tare da kifa kanshi ajikin motar ya ɗan lumshe idanunshi,    adai dai lokacin Jahad ta fito hannunta ruƙe da school bag ɗinta,tana neman hossana duk atunaninta zata same tane a wurin da suke jiran osman yazo ɗaukarsu amma babu ita,da alama ma Osman ɗin bai ƙaraso ba,   guntun tsoki taja tare da juyawa zata koma ciki,karaf idonta suka sauka akan Junaid,cike da mamaki take kallonshi,tana ɗan leƙen fuskarshi daga inda take, Bakomai ne ya faɗo mata aranta ba,face alƙawarin da tayi ma hosana nacewa zata nemo mata ya Omar,aranta tace"ya Omar yace ƙaninshi ne wannan,kodae naje na tambaye shi ina ya Omar yake,may be ya taimakamun wurin haɗa ni dashi,   ƙarasawa wurin motar junaid tayi ta ɗan tsaya daga bayanshi,tare da yi mashi gyaran murya don ya juyo,    jin shiru bai juyo ba yasa tayi mashi sallama"Assalamu Alaikum,"   Nan ma bai juyo ba,hannu tasa ta ɗan ta6a bayanshi a hankali,aikuwa a firgice ya juyo,ita kanta jahad sae da ta ɗan tsorata taja da baya ganin yarda ya juyo kamar ya tsorata,     Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"am sorry,naga kamar ka razana,tun ɗazu nayi maka sallama baka ji ba,'    harara junaid ya watsa mata,har sae da tasha jinin jikinta,rai a6ace yace"yanzu abunda kikayi mun kin kyauta!kinsan tun yaushe nike atsaye nan ina jiranki!"    Gaba ɗaya jahad ta gama ruɗewa jin abunda Junaid ke cewa, Cikin sauri tace"dama...am..inaso ne na tambayeka game da yayan.......'   Kafin ta ƙarasa maganar tuni junaid ya gama hasala,ruƙo hannunta yayi tare da buɗe motar,yace mata wuce ki shiga,    Murya na rawa jahad tace"bangane me kake nufi ba?   A tsiwace yace"Ni ki wuce mu tafi,'   duk yarda jahad taso ta fahimtar da junaid cewar ba ita bace wadda yake nema ba,amma yaƙi fahimta,shi duk atunanin shi sehrish ce,   Tursasa mata yayi har sae da tashiga cikin motar,sannan ya shiga yaja motar da gudu ya fisgeta suka fuce daga cikin makarantar, A natse yake driving lokacin daya hau saman shantalelen titin,zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi,ta wutsiyar idonshi yake kallonta,ganin yarda ta zuba mashi ido yasa shi ɗan juyowa tare da sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi,   mamaki ne ya kama jahad,gaba ɗaya abun ya gama ɗaure mata kai,aranta tace kodae yana da ta6in hankali ne?in ba haka ba, nida bamu ta6a haɗuwa dashi ba amma kuma ya nuna ya sanni har ya tursasa mun na shiga motar shi,yanzu ni bansan ya zanyi na fahimtar dashi ba,kada hosana ta fito tayi ta nemana acikin school,    "Reesh banji kin yabi wankan nawa ba?ko banyi kyau bane,"yayi maganar a yayin da yake kokarin parking ɗin motar a gefen titi,sannan ya juyo yana kallonta,   zuru jahad tayi tana kallonshi,hakan ba ƙaramin 6ata mashi rae yai ba,cikin shagwa6a yace"Wai menene haka reesh,duk kin bi kin wani sauya mun,saboda ke fa na ɗau wankan nan don nazo na nuna maki,amma kin zuba min ido kina kallona kamar yau kika fara gani na,'   A tsorace take da shi,don tagama yarda cewa yana da ta6in hankali,cikin en ina tace"amm...ni fa...ba..' kasa ƙarasa maganar tayi gabanta na faɗuwa,ganin yarda junaid ya matso dab da ita,ya ƙureta gaba ɗaya ƙamshin turaren shi ya gama kashe mata jikinta,   murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa"kallon ya isa haka reesh,let's talk about serious issue,akwai abunda na jima inason sanar dake,amma inajin fargabar amsar da zan samu a wurinki,'ya ƙarasa maganar yana kallon cikin kwayar idanun jahad amatsayin sehrish,    a hankali jahad ke bin kyakkyawar fuskarshi da kallo,tun daga kan eye brows ɗinshi,dogon hancinshi da kuma red lips ɗinshi,komai nashi mai kyau ne kuma mai jan hankali,    Anatse yaci gaba da magana,"reesh,nasan cewa baki ɗauke ni cikakken namiji ba kamar saura,saboda na cika wasa da shiririta da kuma shagwa6a,kuma bani da aikin yi sae zama acikin gida kamar mace, nasan ba kowace mace bace zata so ta aure ni a haka" ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,wannan karon babu alamar wasa a fuskarshi,   natsuwa jahad tayi tana sauraran shi,    Hannayenshi yakai tare da ruƙo nata cikin nashi,nan take jahad taji gabanta ya faɗi,   ɗagowa yayi awani irin yanayi yaci gaba da magana"duk wannan abun da nake reesh zan daina in baki so,idan har kika amince mu kayi aure,xan zama kamar yarda kikeso,nidae burina ki amsa mun cewa kina sona,kuma zaki aure ni,ni ban ta6a son wata ƴa mace ba in bake ba,na shaƙu dake sosai kuma ina da tabbacin cewa in mukayi aure zaki bani kyakkyawar kulawa,pls reesh tell me will u marry me"?    Tamkar zai yi kuka haka yayi mganar yana jiran amsarta,   Shiru jahad ta ɗanyi tana yanke shawara da zuciyarta,tunda dae bai da cikakken hankali bari na jaraba biye mashi kona samu mu rabu lafiya Ƙarasa zancen zucin nata tayi tare da mayar da idanunta akan nashi tace"bana tunanin cewa akwai macen da zata samu namiji kamarka ta nuna bataso,kai na daban ne,kana da komai da mace zata buƙata a wurin namiji,kayi mun sosai kuma ka kwantamun araina,tayin soyayyar da kayimun na kar6a hannu bibbiyu,kuma na amince zan aure ka.....'    Tsantsar mamaki ne ya kama junaid bai ta6a tunanin cewa rishi zata amince da soyayyarshi ba,cikin sauƙi haka batare da ta wahalar dashi ba,ajiyar zuciya ya shiga saukewa wani irin farin cikine ya lullu6e shi,mara misaltuwa a hankali ya shiga furta"Alhamdulillalh Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar,dama sae da raina ya bani cewa reeshi ɗina bazata gujeni ba...."   Fuskar jahad ɗauke da murmushi take kallonshi har lokacin hannunshi na ruƙe da nata,    farin cikin da tagani a fuskarshi yasa taji aranta dama dagaske ita yake so,da ta bashi kyakkyawar kulawa,amma da alama akwai wadda yake so,tunda taji ya ambaci sunan reesh wannan ne yasa jikinta yin sanyi, "Allah yasa ba mafarki nake ba,in ma mafarki nake kada ki tashe ni,'yayi maganar yana dariya tare da zame hannun shi daga nata,ya tallabo fuskarta da tafin hannayenshi,yana ƙare mata kallo,hakanan ya dinga jin kamar ta canza mashi,ƙura mata ido yayi kamar mai son gano wani abu,   "Reesh kin canzamin sosae,sai nike ganin kamar bake ba,'    Shiru jahad tayi tana cigaba da kallonshi,sakin fuskarta yayi tare da zura hannunshi cikin hijab ɗin jikinta,ae kuwa a firgice jahad ta ƙanƙame jikinta dake ta faman kerma cike da tsoran abunda zaiyi mata,    Cikin lallausar suman kanta yakai hannunshi yana shafa gashin kanta yace"meyasa baki ɗaure gashin kanki ba?bai takura maki ahaka?    atsorace jahad tace"ni na cire shi,yana acikin school bag ɗina,"    Zame hannunshi yayi daga cikin hijab ɗin nata,   "Zan ɗaure maki shi,ki ɗauko ribbom ɗin naki,"   Kamar karta ɗauko mashi amma tunawa da cewar yana da ta6in hankali in ranshi ya 6aci zai iya kai mata bugu,hakan yasa ta janyo school bag ɗin tare da zuge zip ɗin,ta curo mashi ribbom din ta miƙa mashi sannan ta mayar da jakar abayanta,   kar6a yayi tare da zura shi a cikin hannunshi,sannan ya ƙara matsawa kusa da ita sosai,cire hijabin jikinta yayi sannan ya janyota asaman chest ɗinshi,gaba ɗaya jahad ta gama rikicewa,ba ƙaramin yanayi junaid ya jefa ta ba,   lamo tayi ajikinshi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarenshi,   Xuba ma yalwataccen gashin nata ido yayi yana kallonshi,kafin daga bisa ni ya sanya hannunshi tare da tattaro shi wuri guda,ya ɗaure mata shi da ribbom ɗin,    muryarshi taji acikin kunnanta yana cewa"Reesh,ya akai naga launin gashin kanki ya canza?ba brown colour bane?yanzu kuma naga ya koma dark black,?kodai idona ne ke nuna min ba daedae ba'?shiru jahad tayi batace mashi komai ba,saboda bata da amsar da zata iya bashi,   jin tayi shiru yasa ya ƙyale maganar,hannu yasa tare da rabata da jikinshi,bin ta da kallo yayi ganin yarda take ta faman lumshe ido kamar mai jin bacci,   Cikin sanyin murya yace"Reesh,kina jin feelings ɗin da nake ji agame dake"?   buɗe ido jahad tayi sosai tana kallonshi da wata irin kasalalliyar murya tace"eh,'    jinjina kanshi yayi tare da cewa"nasani,dama nasan kema zakiji abunda nake ji,pls reesh just for today kawai,kiyimun kiss koda a gefen fuskata ne,inaso naji ya ake ji,'   Shiru jahad tayi tana tunanin ya zatayi da wannan ɗan tahalikin,gashi duk yabi ya kashe mata jikinta,ita tausayi ma yake bata saboda ta6in hankalin da yake fama dashi,tausayin shi ne taji ya kamata,mutun har mutun amma bai da cikakken hankali tunda inda yana da hankali ai ba yarda za'ai ya kasa gane ba itace wadda yake nufi ba,tunawa tayi da hosana dake fama da irin lalurarshi,amma nashi haukan yafi na hosana,don bata ta6a ganin wanda bata sani ba,ta liƙe mashi da sunan tasan shi,     bata ƙarasa zancen zucin nata ba,muryar shi ta kuma katseta da cewa"pls reesh,just for today,"    ajiyar zuciya jahad ta saki tare da kai bakinta zata manna mashi kiss acikin dimple ɗinshi,batayi wani aune ba taji bakinta acikin nashi tsulundum,sakamakon wata mota da ta bugi bayan motar shi,wannan girgizar da motar tashi tayi ne yasa bakinta komawa cikin nashi,gaba ɗaya junaid yabi ya rikice ya zauce ya haukace mata,sosai ya ƙankame ta ajikinshi,yana kissing ɗin bakinta ta hanyar zura tongue dinshi acikin bakin,ita kanta jahad a lokacin ta gaza control ɗin kanta,biye mashi tayi, Sosai junaid ya shiga romancing ɗinta kamar zai zauce,duk yarda jahad taso ta kwace kanta a hannunshi amma yaƙi barinta,sai da yayi mai isarshi sannan ya zame jikinshi daga nata,cikin sauri jahad ta kifa kanta asaman laps dinta,tana faman sauke ajiyar zuciya,sam tagaza yarda cewa itace da kanta ta ba wani namiji damar kissing lips ɗinta abunda bata 6ata yi ba,to dama dae duk inda mace da namiji suka ke6e irin haka na ukkun su shaidan ne,Allah ya kyauta.     jikinshi ne yayi sanyi,shi kanshi baisan cewa abun zai kaisu ga haka ba,daƙyar ya iya tashin motar da wata irin kasala ajikinshi yake driving din,ya hau saman titi sosae tare da wucewa dasu gida,    _💋Boss Bature💋_ tashin hankali!Lokacin da Hosana ta fito a nan ta samu osman yana jiransu tsaye a bakin motarshi,    ƙarasawa tayi wurinshi tana cewa"ya Osman Ina jahad ɗin?ina ta nemanta banganta ba,nayi tunanin ta rigani fitowa ne,"    "Wai kina nufin jahad bata acikin school ɗin naku"?ya tambaya hankali a tashe yana kallonta,. daga mashi kai tayi alamar eh tace"babu kowa acikin makarantar ya Osman,na duba ko'ina ban ganta ba,"   Gabansa ne ya faɗi rass,saboda kullum jahad ita ke riga hosana fitowa,yau kuma hosana ta rigata fitowa,tabbas akwai matsala,   cikin sauri yace"shiga ki zauna bari nashiga cikin classes din na duba ko zan same ta acan,Allah dae yasa ba wani mummunan abune ya faru da ita ba,'   Ya ƙarasa maganar tare da yin saurin shigewa cikin makarantar,buɗe motar hosana tayi tare da shigewa ciki ta zauna tana jiranshi,   lokacin da Osman ya shiga cikin classes din yana neman jahad,duk ajin daya duba babu kowa wayam duk sun tafi gida,ko'ina ya dinga bi na makarantar saƙo da lungu yana dubawa amma babu jahad babu alamarta,tun yana sa ran ganinta har ya fidda rae,yafi ƙarfin awa ɗaya da rabi acikin makarantar yana neman jahad amma bai ganta ba,   Cikin sauri ya fito jiki na rawa ya koma cikin motar,ya zauna a mazaunin driver,   Ganin ya dawo shi kadae yasa hosana cewa"Ya osman ina jahad din?baka ganta ba"?    "Na duba ko'ina banganta ba,bansan ina jahad taje ba,bari na fara kaiki gida nasan kin gaji sosai,"    jan motar yayi tare da fucewa daga cikin gate ɗin makarantar,duk yabi ya ruɗe saboda fargabar kada ace wani abune ya faru da jahad,yana jiyo hosana tana shessheƙar kuka tana cewa"Nashiga uku,Allah yasa jahad bata 6ace ba,bansan ya zanyi ba in na rasata ba,kamar yarda na rasa sehrish,"     "Kada ki damu jahad tana cikin ƙoshin lafiya,zan nemo maki ita,in ma ban sameta ba,zan kira major na sanar dashi halin da ake ciki,nasan zaiyi ma marshal Magana,"ya ƙarasa maganar a lokacin da yake shiga kwanar gidan Abusufyan, Yana shiga ciki ya sauke hosana,sannan ya fisgi motar da gudun gaske ya fuce daga gidan, Abunda ya faru bayan fitar motar osman daga cikin school din,Sai ga sehrish hannunta ɗauke da school bag ɗinta,daƙyar take iya tafiya saboda ciwon da tasha,ta jima acikin toilet din tana juyi kafin Allah ya kawo mata sauƙi harta samu ta fito, ganin babu kowa acikin makarantar yasa taji gabanta ya fadi,nan tashiga fargabar Allah yasa junaid bai tafi ba,tasan dole ya gaji da jiranta, Lokacin da taƙarasa wurin gate din taga babu kowa sai security guard din dake tsaron makarantar,tamkar ta aza hannu akai ta fashe da ihu haka taji, Ganin yarinya tsaye cikin damuwa yasa mai gadin ya ƙaraso wurinta yana tambayar ko lafiya, muryarta tamkar za tayi kuka tace"Mai ɗaukata nake nema,kuma naga babu kowa acikin makarantar,bansan ya zanyi ba," mai gadin yace"meyasa baki fito kin tsaya anan waje ba?me kikeyi acikin makarantar ne"? cikin shessheƙar kuka tace"bani da lafiya ne,bacci ne ya ɗauke ni kuma babu wanda ya tashe ni,shiyasa bansamu na fito ba akan lokaci," "Kuma baki da waya a hannunki"?acewar mai gadin, ɗaga mashi kai tayi alamar eh, "Ko numbar wani baki ruƙe a cikin kanki ba," "Bani da numbar kowa,ban ruke akaina ba," Cike da takaici mai gadin yace"kaji matsalar,ni yanzu bansan ya zanyi dake ba,amma me zai hana ki ɗan fita daga wajen gate ɗin,wata'ƙil shi drivern naki ya dawo daukarki,nasan ma zai dawo ne,da zarar sunji shiru baki ƙarasa ba", Amsa mashi tayi da toh,sannan ta fice daga cikin makarantar ta tsaya a bakin gate din,tana ta ƴan waige waige ko zata hango motar junaid, _💋Boss bature💋_ A hankali motar junaid ta ƙetare babban gate din gidan nasu,a lokacin jahad ta ɗago da kanta,ta cikin glass ɗin take hangen katafaren gidan,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,yau gata acikin gidansu ya Omar dinsu,koba komai zata hadu dashi harma ta sanar dashi halin da suke ciki na rashin ganin shi,addu'a tashiga yi acikin ranta Allah yasa Ya Omar na nan, tsayar da motar junaid yayi tare da buɗewa ya fito sannan ya zagaya ya buɗe ma Jahad motar,cikin sanyin murya yace"Reesh,am really sorry game da abunda ya faru a tsakanin mu,na fita hayyacina ne shiyasa,kinsan cewa ba halina bane.....kuma bazan ƙara ba insha Allah, Murmushi jahad ta sakar mashi ayayin da take fitowa daga cikin motar tace"just forget about it,komai ya wuce,na yarda dakai sosai nasan cewa bada son ranka hakan ta faru ba, ba ƙaramin daɗi junaid yaji ba,ya jima yana mamakin nasarar daya samu akan reeshi ɗinsa,farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha, Bayan ya rufe motar ya ruƙo hannunta suka shige cikin gidan atare,a ruɗe jahad ke kallon katafaren gidan,jinjina kai kawai takeyi acikin ranta tana cewa"wai dama a wannan daular ya Omar ke rayuwa!gidan yayi mun kyau ya haɗu sosai,Allah yasa yana ciki,inaso na cika ma hosana alƙawarinta na ganin na haɗata da ya Omar dinta, Babu kowa acikin main palour ɗin,sakin hannunta junaid yayi tare da cewa"bari na shiga ciki na huta,da anjima zan shigo muyi magana," amsa mashi tayi da toh,cikin sauri junaid ya wuce bedroom din Abbansu, tashin hankali,jahad fa batasan ina zata dosa ba,gata dae acikin gidansu Omar,batasan a ina zata ganshi ba, Tsayawa tayi ƙiƙam batare da ta motsa ba, Gyaran muryar da taji ne yasa ta yin saurin juyawa don taga wanene, Azmee ce ta fito sai faman sakar mata murmushi takeyi,jikinta sanye da jallabiya,ta ɗaure kanta da mayafi,ta fito fess abunta, Gaban jahad ne ya shiga faduwa aranta tashiga tunanin cewa kodae wannan ce mahaifiyarsu?Amma meyasa naga tana sakar mun murmushi kamar tasanni itama...? Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,azmee ta ƙaraso tare da janyota jikinta ta rungumeta tana cewa"Sannu da dawowa kyakkyawata,ya school din? Tayi maganar tare da raba jikinta daga na Jahad, Zuru jahad tayi duk tabi ta dabarbarce ta rasa ganema wannan abun al'ajabin,tamkar a mafarki haka take ganin wannan ikon Allah, "Rishi lafiya naga kina bina da kallo?kodae bakya jin daɗi ne?nayi magana baki amsa mun ba" Cikin en ina jahad tace"am...um...lafiya lou,makaranta Alhamdulillah,' Azmee tace"ko ke fa,shigo daga ciki na hada maki lunch ki ci,ko kya dawo daedae don na lura yau ba ƙaramar yunwa kika kwaso ba," Tayi maganar tare da ruƙo hannun jahad taja ta suka nufi dakin sehrish,da kanta ta buɗe mata kopa tare da shigar da ita ciki tace"ki zauna ki huta,yanzu zan haɗo maki lunch,"tana faɗin hakan ta rufe mata dakin, Abun ya gama ɗaure mata kai,juyawa tayi tana ƙarema bedroom ɗin kallo ba ƙaramin kyau yayi mata ba,daga bisani kuma ta shiga damuwa akan wane hali hosana ke ciki,tasan cewa zasu nemeta sosai,kuma in basu ganta ba hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba, komawa tayi daga gefen gadon sehrish ta ɗan zauna,ya zama dole in koma gida,kada hosana tayi ta kukan rashina akusa da ita,bansani ba ko zan samu ya omar acikin gidan nan ba,ni ba komai yafi ɗauremun kai ba face yarda suke nuna kamar sun sanni,bayan bamu ta6a haduwa da kowannansu ba,to kodae dukkansu suna da mental illness ne?ta jefa ma kanta tambaya, Turo kopar azmee tayi tare da shigowa hannunta ɗauke da tray wanda ta shirya mata lunch,ƙarasawa tayi tare da ajiye mata tray din asaman bedside drawer dinta tace"Wannan farfesun da kike gani,hajiya azeema na shirya mashi,ƙanwar abbanku da nake gaya maki,tana nan ta iso,nasan bakisanta ba,amma kin ta6a ganinta lokacin da Sgr da Omar suka dawo daga U.S kin tuna"? Fuskarta ɗauke da murmushi takeyi mata maganar, Jin ta ambaci sunan Omar yasa jahad cewa"Ya Omar na nan"? Azmee tace"eh,yana acikin part dinshi,amma meyasa kika tambaye shi?maimakon ki tambayeni mutumin ki Sgr"? "Babu komai,kawai inason ganin shi ne,"ta bata amsa, Azmee tace"ki bari idan kin kammala shan farfesun sae kije ki same shi adakin shi,' gyaɗa kai jahad tayi tare da cewa toh,nagode sosai,bari na fara sha, Juyawa azmee tayi tare dayi mata sallama ta fuce daga dakin,a ranta tana tunanin ko wani abu ke damun rishin ne taga duk tayi sukuku. Zama jahad tayi tare da dauko plate ɗin dake ɗauke da farfesun,sae uban ƙamshi ke tashi,duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hanata shan farfesun nan ba,sae da taci ta ƙoshi, sannan ta miƙe tare da shiga toilet ta wanko hannayenta, Bayan ta fito komawa tayi saman gadon ta zauna cike da zullumin mai zai biyo baya, _💋Boss Bature💋_ Marshal Omar na kwance saman gadonshi yayin da idanunshi suke kallon saman ceiling bakomai yake tunani ba face hosanar shi,kowane hali take ciki yanzu?taci abinci kuwa?tambayoyi iri iri ya shiga yi ma kanshi, yana cikin wannan tunanin wayarshi dake ajiye gefenshi ta shiga yin ringing,miƙa hannu yayi tare da daukar wayar,duba mai kiran nashi yayi ganin sunan Major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi saurin ɗaga wayar tare da karata akan kunnanshi, Ko sallama major baiyi mashi ba saboda tsabar tashin hankalin da yake ci, "Yalla6ai yarinyar nan fa ta 6ace,an neme ta an rasa ko'ina na makarantarsu,ɗazu osman ya kira ni awaya yake sanar dani cewa yaje ɗaukarsu a school,hosana kaɗae ya gani banda jahad,mun duba ko'ina babu ita," Waro ido waje Omar yayi ba arziƙi ya sauko daga saman gadon yana cewa"Major!ban fahimci me kakeson sanar dani ba!kayi mun da yaren da zangane," Major yace"yalla6ai,jahad ce ta 6ace a school,' Rai a6ace Omar yace"Garin yaya hakan ta faru!taya akai Osman yayi gangancin da har ya bari jahad ta 6ace bai ganta ba!'duk inda take ku nemo mun ita in ba haka ba,ran kowa zai 6ace don bazan lamunta ba," Yana ƙarasa maganar ya kashe kiran,gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji daɗi,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoronshi kar ace jahad ta gudu ne don taje nemanshi saboda halin da hosana ke ciki, Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin nashi,zuciyarshi nata tafarfasa saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,abubuwa sunyi mashi yawa,yana cikin damuwa sosai,ga kuma wata damuwar da major ya ƙara mashi,na 6atan jahad, ɗago da wayar ya sake yi a hannunshi ya shiga dialing wasu numbers, sannan ya dannama numbar kira,nan take kiran Ya shiga aka ɗaga wayar, tun kafin yayi magana wata murya kakkaura ta karaɗe kunnanshi da cewa"We are waiting for ur command sir," Cikin harshen turanci omar ya shiga basu bayani akan 6atan jahad, Ya ƙarasa maganar tare da cewa yanzun nan zan tura maku da hoton ta,banason ta ƙara 1 hour awaje,duk inda take ku nemota,adawo mun da ita gida," "Okey sir,'suka amsa mashi,sannan yayi rejecting kiran nasu, sai bayan daya kashe wayar sannan ya tuna cewa baida hotonsu,amma yasan baza arasa ba wurin osman, Batare da 6ata lokaci ba,ya kira osman awaya,bugu ɗaya osman ya ɗaga kiran cike da fargabar abunda omar zai sanar mashi, "Osman!" Murya na rawa osman yace"Na'am yalla6ai," "Inaso ka turomin hoton jahad yanzu in kana dashi awayarka,inma babu ka ɗauko mun hoton fuskar hosana,ina jiranka yanzu karka 6ata mun lokaci,' yana kai ƙarshen maganar tashi ya katse kiran,cigaba da zagaye ɗakin yayi yana jiran osman, within 15mins,sai ga kiran osman ya shigo, ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnanshi, On the other hand Osman yace"yalla6ai na turo da hoton,ta cikin Whatsapp dinka," "Okey," ya amsa tare da katse kiran,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin duba whatsapp dinshi,anan yaga hoton da Osman ya turo mashi,zuba ma hoton ido yayi yana kallonshi,nan take yaji kewarta ta kama shi sosai,hoton hosana ne Osman ya ɗauko mashi,da alama sabon hotone yayi mata da wayarshi,ko uniform dinta bata cire ba,fuskarta da alamun hawaye saboda kukan da tasha na 6atan Jahad, Lumshe idonshi yayi tare da buɗesu akan hoton yana ƙare mashi kallo,a hankali ya furta"I love u so much hosana,nayi missing ɗinki sosai,kamar nayi hauka,nashiga damuwa sosai akan rashin sanyaki a idona,bazan iya jurewa ba hosana,kina buƙata ta a kusa dake,zanzo don na lallashe ki nasan zaki shiga damuwa sosai akan rashina da kuma rashin jahad akusa dake, Tura masu hoton yayi sannan ya kira major awaya ya sanar dashi cewa ya jira shi a waje,gashi nan fitowa, Yana kammala yin wayar cikin sauri ya fito daga part ɗinshi,ya sauko downstairs,da sauri da sauri yake nufar hanyar fita daga main palour din, yana ɗaga ƙafarshi zai fita yaji an ambaci sunan shi"Ya Omar," gabansa ne yaji yayi wani irin bugu,aranshi yace"wannan ae muryar Jahad ce, da saurin gaske ya juya tare da kai idanunshi wurin da jahad take tsaye sanye cikin uniform tana kallonshi,fitowarta kenan daga bedroom din sehrish,cikin sanɗa take tafiya zata gudu daga gidan,kwatsam ta hango shi sai faman sauri yake yi zae bar gidan, Kanshi ya gama ɗaurewa binta yayi da kallo gaba ɗaya ya rikice aranshi ya shiga tunanin cewa anya ba kunnan shi bane suka jiyo mashi muryar jahad!wannan ae yarinyar gidansu ce sehrish,muryarta ce tayi mashi gizo yaji kamar ta jahad, Murmushi ya saki tare da nufarta yana cewa"Sister har kin dawo daga school ɗin?ya karatun naku,ina fata kina mayar da hankali ko? Kamar zatayi kuka tace"Ya Omar,Jahad fa ce! Nice jahad,ya Omar meyasa ka tafi kabarmu,"! Zaro ido waje Omar yayi cike da mamaki yake kallonta, muryar shi na rawa yace"Jahad!dagaske kece kodae kunnena ne ke jiyemun ba dae dae ba"? fashewa tayi da kuka tare da ƙarasawa wurinshi ta kwantar da kanta asaman ƙirjinshi tana cewa"Ya omar dama kana nan,da ranka da lafiyarka amma kadaina zuwa wurinmu?meyasa ya Omar?bakasan halin da muka shiga ba ni da hosana,na rashin ganin ka,' tashin hankalin da ba'a sama shi date, ruko hannunta Omar yayi tare da janta suka shiga cikin wani corridor inda ba kowa,sannan ya kalle ta cike da mamaki yace"Jahad!nagaza yarda cewa kece!taya akai kikasan gidan mu har kika zo? cikin shessheƙar kuka tace"bani na kawo kaina ba,kawo ni akayi,wannan ƙanin naka junaid,wanda ka ta6a nuna mana hotonshi nida hosana a gida,shi ya ɗaukko ni daga school ya kawo ni gidan nan,bansan meyasa ya ɗauko ni ba,ya nuna kamar yasanni bayan bamu ta6a haduwa dashi ba.....' Tun kan ta ƙarasa maganar Omar yace"subhanallahi!an samu matsala,junaid yayi kuskuren ɗauko ki jahad,Yarinyar gidan nan yaje daukowa a school,da yake kuna kama da ita sosai,komai na fuskarku iri ɗaya sak,shiyasa ya ɗaukko ki amaimakonta,' mamaki ne ya kama jahad jin abunda Omar yace,sae lokacin ta tuna da sunan da Junaid ya dinga kiranta wato Reesh,taya akai suke kama da yarinyar gidansu har kanin nashi ya gaza banbantasu!" ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, "Jahad,muje na sauke ki gida,in yaso sai mu ƙarasa tattaunawa acan," Ya ƙarasa maganar tare da fitowa ruke da hannunta suka fice daga cikin babban falon,anan waje ya samu Major tsaye jingine da mota yana jiranshi, Koda ya ganshi ruƙe da hannun jahad mamaki ne ya kamashi,dama shi bai ta6a ganin Sehrish ba,tunda ba shiga ciki yake yi ba,basu ta6a arba da ita ba, Fuskarshi dauke da murmushi yace"Sir!anganta kenan"? Omar yace"eh,ba rabon musha wahala,wai junaid ne ya ɗaukota daga school shi duk atunanin shi wannan yarinyarce ta cikin gidan nan,da yake kamanninsu iri daya sak,' major yace"ikon Allah,amma ni ban ta6a ganin yarinyar ba,' ya ƙarasa maganar a yayin da yake buɗe masu mota suka shige ciki,sannan ya tashi motar yabar gidan ɗauke dasu, _💋Boss Bature💋_ A 6angaren sehrish kuwa,tana cikin tsayuwar nan agefen titi tana jiran zuwan junaid,sai ga motocin waɗannan fusatattun sojojin da Omar ya turo don su nemo mashi jahad,ae koda sukayi arba da sehrish,suka duba hoton da Marshal Ya tura masu suka ga iri ɗaya fuskar,sae ransu ya basu cewa itace yarinyar da Omar yace su nemo mashi, Da sauri suka tsayar da motocin nasu tare da diddirowa daga saman motocin tamkar wasu zakuna haka suka tunkari sehrish, Kamar ance ta juya,idanunta sukayi arba da waɗannan sojojin dake tunkararta hannunsu ruke da bindigu,bakomai ne ya fado mata a ranta ba face Ƴan boko haram da ƴan bindiga daɗin dake ta sace mutane agari, ja da baya tashiga yi gabanta na faduwa maimakon suyi mata magana cikin daɗin rae sai suka daka mata tsawa tare da cewa"ke zonan"! Aikuwa a firgice sehrish ta watsa da gudun gaske ta saki jakar makarantarta ƙasa,bin ta sukayi da gudun gaske,tana gudu suna bin ta tamkar zata tashi sama, yarda kasan wadda taci ƙafar kare haka ta dinga gudu,ita kanta batasan inda ta dosa ba,gudu kawai takeyi, adaidai nan su Omar suka ƙaraso gidan uncle Abusufyan,Wayarshi ta shiga ruri,cikin sauri ya fiddota daga cikin aljihun wandonshi,yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanshi yayi sallama, Muryar ɗaya daga cikin sojojin ce yaji yana cewa"Sir,munga yarinyar da ake nema,amma taƙi bari mu kama ta,' Hankali tashe Omar yace"Kada ku bari ta kufce maku,kuyi ƙoƙari ku kamota,kuyi mata magana cikin sanyin murya,saboda yarinyar tana da tsoro sosai,kun firgitata ne shiyasa ta gudu, "Okey sir,ya amsa mashi tare da katse kiran, "Yalla6ai meya faru ne"! Cike da takaici Omar yace"Major,an samu matsala!sojojin dana tura don su nemo mun jahad,sunyi arba da yarinyar gidan mu,dama na faɗa maka cewa kamanninsu sak iri ɗaya,ɗazu nace ma Osman Ya ɗauko mun hoton fuskar hosana,saboda in tura masu suyi amfani dashi wurin nemo min jahad,to da wannan hoton su kayi amfani wurin nemanta shine Allah ya haɗasu da ita yarinyar da junaid yayi musanya da jahad,' Tunda yasoma magana jahad ke kallonshi cike da mamakin wannan wani irin kamanni ne,dayasa har ba'a gane banbancinsu!? Major yace"Amma nayi mamaki yalla6ai!wannan wata irin kamanceceniya ce atsakaninsu da har ba'a iya bambanta tsakaninsu"! Omar yace"nikaina major abun ya jima yana ɗaure mun kai wlh,da farko nayi tunanin cewa saboda ƙaunar da nakeyi ma su hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan fuskar yarinyar,amma yau da junaid ya dauko jahad a matsayin ita yarinyar,sai na tabbatar da cewar ba gizau bane,tabbas kamanninsu ne ɗaya! Major yace"abun mamaki abun al'ajabi!yalla6ai kada kace na cika ka da surutu,dan Allah yaya kuke da ita yarinyar?ko ƴar wurin uncle ɗinku ce,' ya ƙarasa maganar adaedae lokacin da yayi parking ɗin motar a cikin gidan Abusufyan, murmushi Omar yayi tare da cewa"ƴar aikin gidanmu ce,sunanta Sehrish! Yarinyar tana da kirki sosai shiyasa Abbanmu ya mayar da ita tamkar ɗiyarshi,yanzu amatsayin kanwarmu take............' Waro ido waje Jahad tayi cike da tsananin mamaki ta furta"SEHRISH!!!!!!!!!!!!!!!!" juyawa Omar yayi yana kallonta jin yarda ta ambaci sunan kamar tasanta,shima major juyowa ya danyi daga zaunen da yake a front seat din suna kallonta, "Jahad kin santa ne!"? Muryarta na kerma tace"Ya...Omar...Bansan ko ita bace ba,amma akwai ƴar uwarmu da muka jima muna nemanta,kamanninmu sak iri ɗaya,Mu ƴan ukune dani da hosana da kuma ita,Sunanta Sehrish atare aka haife mu,ciki ɗaya muka fito tare da ita,arana ɗaya kuma a lokaci ɗaya.......' Kallon juna Omar da major sukayi cike da mamaki suke sauraronta,sae da takai ƙarshen maganarta,sannan Omar yace"Dama ke da Hosana ba twins bane!!!"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tace"WE'RE TRIPLET". Wannan shirin da kuke karantawa ba ammasco bane suka ɗauki nauyin kawo maki shi ba,Boss bature ce da kanta,ta shirya kuma ta gabatar,😂 Idan har kinji daɗin wannan update ɗin,kiyi following din acct dina a tiktok😍😂ga link can na bada daga sama *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.   *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Abban sojoji paid book ne,ga duk maison karanta cigabanshi zai biya 300 ne za'a tura mashi nabaya har inda muka tsaya,ga mai buƙata direct zaiyi mun magana ta whatsapp ɗina 08103884440, pls banda phone calls,Mijina ya hana ana kira na awaya🤭🤫 ❤🤍❤ Gaba ɗaya farin ciki ya lullu6e Marshal Omar da kuma major,tunda su kaji bayanin Jahad suka tabbatar da cewar ba shakka Itace ƴar uwartasu da take magana akai, "Jahad,wannan maganar ba anan ya kamata muyi ta ba,mu shiga daga ciki" buɗe motar Omar yayi tun kafin major ya buɗe mashi,fitowa jahad tayi itama,sannan shima major ya fito,duka dae a tare suka ɗunguma izuwa cikin gidan,har lokacin jikin jahad rawa yake yi,saboda tsabar doki da kuma zumuɗin ganin cewa Sehrish ce yarinyar da Omar ke magana akai, Lokacin da suka shiga cikin palour ɗin atare,hosana na a kwance saman 3 seater,tasha kuka harta gaji shine ta ɗan kishingiɗa nan,bacci ya kwashe ta, ko uniform din bata cire ba,bin ta da kallo Omar yayi bakomai ya faɗo mashi a rai ba,face abunda yayi ƙoƙarin aikata mata,tausayinta ne ya kama shi sosae,tsayawa yayi atsaye ya zuba mata ido ko kyaftawa baiyi, "Ya Omar,ka zauna mana,"muryar jahad ce ta katse mashi kallon da yake ma hosana,   Wuri ya samu saman 2 seater ya zauna,jahad kuma ta zauna asaman 1 seater,mayar da idonshi yayi kan major ganin ya tsaya daga tsaye yace"bismilllah mana,ave seat," ya nuna mashi gefen shi,murmushi major yayi tare da ƙarasawa ya zauna daga gefen Marshal,   "Jahad,inaso kiyimun bayani sosai yarda zan fahimta game da ƴar uwarku,taya akai kuka rabu da ita har tsawon wannan lokacin'? Omar ne ya jefa mata tambayar,gaba ɗaya suka zuba mata ido suna sauraron jin abunda Jahad zata ce,    "Ya omar ba da son ran mu muka rabu da ita ba,ƙaddara ce ta rabamu da ita,amma muna son junan mu sosai.....'dakatawa tayi da maganar yayin da idanunta suka cicciko da kwalla,   Anatse taci gaba da magana"ƴar uwarmu tana son mu sosai,tasha wahala akanmu,a lokacin baya Dani da hosana an ta6a kwantar damu asibiti,za'ayi ma hossana aiki,ana neman kuɗi kusan dubu ɗari tara da za'ayi mata aikin,bamu da ko sisi,bamu da mai taimakon mu sae Allah,mu kaɗae muke rayuwarmu tare da wata tsohuwa wadda take ruƙon mu a wurinta,wannan dalilin ne yasa sehrish ta nemi aikatau,don ta biya kuɗin aikin hosana da kuma na maganin da za'a siyamun,babu yarda muka iya alokacin wannan kaɗae ce mafita,muna ji muna gani ƴar uwarmu ta tafi neman kuɗi saboda ta nema mana lafiyarmu,ya Omar Sehrish tayi duk wata gwagwarmaya akanmu,damu da ita duk kanmu ɗaya,amma ita tamkar uwa take a wurinmu,tamkar yaya take a wurinmu,bamu da tamkarta aduniyar nan,rishi har ranta zata iya sadaukarwa saboda mu,nayi kukan rashinta sosai,nayi baƙin cikin yin nesa da ita........tun muna yara muke tsananin son junan mu,rayuwarmu a wulaƙance mukayi ta sakamakon mugun uba da muke dashi wanda bai ta6a nuna mana soyayya ba........'fashewa tayi da matsanancin kuka,   Gaba daya jahad ta gama kashe masu jikinsu yayi sanyi,   dakyar ta tsagaita da yin kukan taci gaba da magana"bayan sehrish ta tafi aiki,cikin sa'a ta samu kuɗin aikin hosana ta biya,lokacin da aka sallame mu daga asibiti,muka koma gidan tsohuwar da take kula damu,anan muke rayuwarmu,kullum muna kiranta awaya mu gaisa da ita,ita ma kuma tana kiran mu awaya taji ya lafiyar mu take,akwai wani lokaci da maganin hosana ya ƙare,ciwonta ya soma dawowa ta dinga hauka tana ƴan buge buge,hankali na ya tashi,gashi bamu da kuɗin da za'a siya mata wasu magungunan,shine na yanke shawarar sanar ma rishi halin da ake ciki,don ta taimaka mana dana magani,na tura mata saƙo ta waya,sai gashi ta turo mun da amsar cewa mu tura mata da acct number,cike da zumuɗi na zura hijabi na shiga gidan makwabtanmu wurin ɗiyar matar,don ta rubutamin acct number ɗinta tun da mu bamu da ita,ashe lokacin da na fita daga gidan,hosana tafarka daga bacci tana son shiga toilet,shine ta ɗauki wayar dana bari saman jakar kayanmu ta shiga toilet da ita,kafin nadawo cikin gidan hosana ta jefar da wayar cikin masan,wannan shine silar da muka rasa sehrish gaba ɗaya,saboda ba mu da wata hanyar da zamu iya magana da ita,sae ta wannan wayar.......'ƙarasa maganar tayi tana faman share kwallar da ke kwaranyowa daga idanunta,   sunnar dakai omar ya ɗanyi,yayin da yake jin zuciyarshi wani kala ba daɗi,haka shima major duk tausayin yaran ya kamashi,musamman ƴar uwarnan tasu sehrish,yarinyar tayi bajinta sosai,   ɗagowa omar yayi tare da kallonta yace"Jahad,inaso ki faɗamu taya akai kuka shiga hannun ƴan sanda?wane laifi kuka aikata ne"?   Cikin shessheƙar kuka tace"bamu aikata laifin komai ba ya Omar,sharri ne akayi mana,abunda ya faru bayan hosana ta jefar da wayar acikin rami,sae ga tsohuwar nan da take rainon mu ta shigo cikin gidan,anan ta same mu ni da hosana muna faɗa akan wayar da ta jefar mana,sai take tambayar meya faru ne muke faɗa,shine na sanar da ita abunda ya faru,hankalinta ya tashi sosai akan wayarta da mukayi mata asararta,rai a6ace ta shige cikin ɗaki ta rufe ƙopa,duk bamuji daɗi ba lokacin saboda bata ta6a nuna mana 6acin ranta ba irin na ranar,atsaye muka kwana muna bata haƙuri akan ta buɗe mana ƙopa mu shiga ciki,saboda a gidan ɗaki biyu ne,amma ɗaya ya rushe saboda ruwan saman da aka ta6ayi mana mai ƙarfi,ya Omar aranar waje muka kwana har ciwon hosana ya tashi,kafin washe gari kuma taji sauƙi,koda muka farka munyi tsammanin zata buɗe mana ƙopar amma abun mamaki sae muka ga ƙopar adatse,tun muna sa ran zata buɗe mana kopar har muka fidda rae,a ƙarshe agidan makwabtan mu muka shiga yin sallar asuba,anan ma muka ci abinci,da mamansu yarinyar ta tambayemu meya faru,muka sanar da ita duk abunda ya faru,shine yarinyar gidan ta rakomu har gidan mu,muka haɗu tare da ita muna babbuga ƙopar,a ƙarshe hosana ce tayi ƙoƙarin 6alle ƙopar......anan muka samu gawarta,ashe tun daren jiyan ta mutu.......mutane kuma suka daura mana laifin kisan nata,saboda sun gano cewa guba aka bata taci,wannan ne dalilin da yasa ƴan sanda suka kaimu police station,bayan an gama tattara hujjojin da za'a miƙa mu kotu dasu,sae kuma ciwon hosana ya tashi acikin cell,wannan ne farkon fitarmu daga cikin cell aka kai hosana asibiti,Ya omar kaji yarda akai muka kasance a hannun ƴan sanda..... "Ƙarasa maganar tayi yayin da hawaye ke ta faman sintiri a fuskarta,   "Ina mahaifiyarku take ne"?omar ne ya kuma tambayarta,   Jahad tace"bamu san inda take ba,bani da tabbacin cewa tana a raye kota mutu,abu ɗaya nasani koma a wane hali take yanzu indae tana araye to bata acikin hankalinta,"   Jinjina kai Omar yayi kafin yace"Insha Allah zan bincika komai a sannu zan gano duk wanda yayi sanadiyar shigarku cikin wannan halin,bazan ƙyaleshi ba,koda uban da ya haifeku ne,zan yanke mashi hukunci daidai da zunubin da ya aikata,'    major yace"wannan gaskiya ne,yalla6ai Allah ya taimaka kuma yayi jagora,nidae yanzu babban burina shine ƴan ukun nan,su kasance a ƙarƙashin kulawar family ɗinku,"   Omar yace"abun ya ɗaure mun kai major,kaji wani iko na Allah nan,gaba ɗaya yaran su ukun suna a ƙarƙashin kulawar family dinmu,duka Allah ya haɗasu awurinmu batare da saninsu ba,kuma batare da sanin mu ba,ita ɗayar ƙaddarar aiki ce ta kawota gidan mu,yayin da su kuma su hosana da jahad,ƙaddarar zaman asibiti ce ta haɗani dasu a lokacin da hosana ke hauka hannunta ruƙe da bindiga,Major abun akwai wata sarƙaƙiya acikinshi,tabbas akwai abunda Allah yake nufi da waɗannan yaran!akwai wani abu da Allah ke son bayyana mana shiyasa ya haɗasu duka awurin mu!"   Zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi ita kanta abun ya ɗaure mata kai,   Shi kanshi major ya shiga kokonton cewa Anya yaran basu da alaƙa dasu Marshal Omar?juyawa yayi ya dan kalli fuskar marshal sannan ya mayar da idonshi akan hosana,sae lokacin ya dinga ganin wata irin kamanceceniya atsakaninsu sosae,tabbas akwai wata alaƙa ta jini a tsakaninsu,shiru kawai yayi baice komai ba,   Kowa ya tafi duniyar tunani hafsat bature ma,ta ɗan ajiye typing tana tunanin wannan abun daya ɗaure mata kai tamau...,   "Ya Omar,"gaba dayansu sukayi firgit suna kallon Hosana dake kwance tafarka tana faman mutsistsike idanunta,jin muryar Omar yasa ta ambaci sunan shi,   Murmushi ya dan saki tare da ambaton sunanta "Hosana",   miƙewa tayi zaune tana ƙare masu kallo gaba ɗayansu,tashi Omar yayi ya koma gefenta ya zauna yana kallonta,    lokacin da ta tabbatar cewa shine saita fashe mashi da kuka tana cewa"Ya omar fushi nake dakai,meyasa ka tafi kabarmu kadaina zuwa wurin mu?laifin me mukayi maka da har kayi mana wannan horon"? Lallashinta ya shiga yi yana cewa"Am really sorry hosana..pls stop crying and wipe ur tears,komai ya wuce yanzu muna tattaunawa ne game da ƴar uwarku Sehrish...... '   Tunda ya ambaci sunan sehrish hosana tayi tsit ta nemi kukan da takeyi ta rasa la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"Anganta ne ya omar?"   Murmushi Omar ya saki tare da cewa"An ganta hosana!ƴar uwarku da ku ka jima kuna nema,ashe itace yarinyar dake yi mana aiki agidan......"bai ƙarasa maganar ba hosana ta fashe da kukan murna tana cewa"Ya omar tana ina?ina rishi ɗinmu take?inaso naganta!tana ina,wayyo Allah na....'   Yarfa hannunta tashiga yi saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa hawaye na zuba fuskar kuma ɗauke da dariyar farin ciki,   Itama jahad farin cikin ne tsantsa afuskarta yau takasance babbar rana agaresu rana mafi girma arayuwarsu ranar da Allah yasa suka gano inda ƴar uwarsu sehrish take,dole suyi farin ciki,bama su kaɗai ba,hatta masu karanta labarin rayuwarsu da kuma marubuciyar data zauna ta tsara labarin ita da kanta tana taya su farinciki,Ya Allah ka ƙara danƙon ƙauna atsakaninmu da ƴan uwanmu masu son mu,Allah ka bamu ikon faranta ma juna da kuma taimakon junanmu,a gudu tare kuma atsira tare❤ Omar ya jima a wurinsu hosana kamar karya tafi ya barsu haka yaji,abunda yasa bai tafi dasu yau ba saboda Yarinyar gidan tasu da ba'a gani ba,yafi son sai sun ɗauko yarinyar sannan ya kaisu gidan nasu don suga ƴar uwarsu ido da ido,zai so yaga wannan farin cikin a fuskokinsu, Bayan tafiyar su Marshal Omar,jahad da hosana duk sun bi sun ruɗe saboda tsabar murna ko abincin rana basu ci ba,sai faman sintiri sukeyi acikin babban falon nasu,aƙagare suke dasu ga sehrish,zuciyarsu sae faman azalzalarsu take akan son ganinta kamar suyi hauka. 💋BOSS BATURE💋 Ga wani tashin hankalin kuma,duk yadda sojojin nan suka so su kama sehrish abun yaci tura domin kuwa sehrish ta kubce masu,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita 6at ta 6ace kamar al'jana,abu kamar wasa har bayan sallar La'asar basu ganta ba, Niko sehrish ina kika shiga ne!kai jama'a daga antaro nan sae kuma nan ya ruguje, tunda Abbansu ya sanar mashi game da zuwan Aunty azeema,jiki na rawa junaid ya fito daga dakin Abbansu da gudun gaske ya nufi ɗakin da aka saukar da ita,faɗawa cikin ɗakin yayi ko sallama babu saboda tsabar ɗoki,a lokacin tana daga zaune saman gadonta tana daddana wayarta,sam bata lura dashi ba,bata ji shigowarshi ba,sae dae kwatsam taji faɗowarshi jikinta,gaba ɗaya ya ƙanƙameta sosai,yana yi mata kukan shagwa6a wai yayi missing ɗinta sosai, Dariya sosai hajiya Azeema tashiga yi tana cewa"Oh ni junaid,tun ɗazu nake ta tambayar ina babynmu yake ina babyn mu yake,duk na ƙosa naganka naso ace ina shigowa cikin gidan nan kaine mutun na farko da zaka fara tarbata da wannan sumbatar taka,"   ta ƙarasa maganar tare da ɗago shi daga jikinta tana bin shi da kallo tace"Masha Allah,junaid kaine ka koma haka?ka ƙara girma sosai kyakkyawan yarona,nayi missing ɗinka sosai,"   murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa"mommy azeema ina tsarabata?me kika kawo mun"?   Dariya tayi tana girgiza kai tace"Tsarabarka na nan junaid,wannan karan nazo maka da abun ban mamaki,inaso inga farin cikin da zakayi idan nabaka tsarabar nan,"   cike da zumudi junaid yace"tana ina,"   Harara ta ɗan watsa mashi tare da cewa"Shine damuwarka?ka manta baka bani kiss dina ba,"   matsawa junaid yayi tare da kai bakinshi gefen fuskarta ya manna mata kiss sannan ya ɗago yana kallonta yace"yanzu sai aban tsarabata ko"?   Dariya tayi tace"ɗaukomin trolley ɗin kayana,"tayi maganar tana yi mashi nuni da trolleyn da Kanal yousouf ya jingine mata ajikin wardrobe,   jiki na rawa junaid ya saukko daga saman gadon ya taka izuwa wurin wardrobe din ya ruƙo trolleyn tare da janyoshi har wurin gadon ya miƙa mata shi,sannan ya zauna daga gefe ya zuba ido yana jiran ganin tsabar da tayi mashi,    hannu tasa ta buɗe trolley din ta curo wani ɗan kit ƙarami sai faman ƙyalƙyali yake yi yadda kasan da gold akayi jikinshi,tunkan ta buɗe shi junaid ke ta faman haɗiye yawu yarda kasan yaga abunci,     Murmushi ta danyi tare da kallon fuskarshi tace"close ur eyes,"   Rufe ido junaid yayi kamar yarda ta umarta,    Murmushi ta kuma yi tare da buɗe akwatin tace"Now Open ur eyes,"    A hankali junaid ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka akan danƙareran Zoben diamond ɗin da ta siya mashi tare da agogonshi,sae faman ƙyalli suke suna ɗaukar ido,diamond bana wasa ba,wanda aƙalla price ɗinsu yayi miliyan ɗari uku,   Waro ido waje junaid yayi yana bin su da kallo saboda tsabar farin ciki ya gaza rufe bakinshi,hannunshi na kerma ya kar6i akwatin yana ƙare masu kallo, Cikin tsantsar farin ciki yace"aun...aunty..wannan duk nawa ne"?    dariya Azeema tayi ganin yarda yabi ya rikice ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba,saboda bata da wani burin daya wuce taga ta faranta mashi,tana son ganin farin cikin junaid sosai,yaron tun yana ƙarami take tsananin son shi,   "Junaid duk naka ne wannan,Na musamman ne nasa akayi maka shi,duk duniya babu mai irin shi sae kai kaɗae,ni da kaine na bada sample ɗin yadda za'a haɗa maka shi,ka duba a jikin zoben ka gani,Harafin J ne ajiki wato farin sunanka," Wani irin farin ciki ne,ya cika junaid,a ƙarshe daya rasa abun cewa kawai sae ya fashe mata da kuka Yana cewa"mommy azeema,narasa da wasu kalmomi zan iya gode maki,babu su abakina,kin sanyani farin ciki sosai da wannan kyautar da kika bani.    Hannu tasa tare da shafo gefen fuskarshi izuwa cikin sumar kanshi tace"kasan dae babu godiya atsakaninmu ko?nayi maka wannan ne saboda inga farin cikin ka,kuma Alhamdulillah nagani kuma naji daɗi sosai,abu ɗaya zakayi mun yanzu shine ka share hawayenka,bana son ganinsu suna zuba,"   Cikin sauri junaid ya sanya hannunshi tare da goge hawayenshi duka,sannan ya mayar da hankali yana kallonta,   Cigaba da magana tayi a natse"junaid kana addu'a kuwa"?   gabanshi ne yaji yayi wani irin bugu jin tambayar da Aunty azeema tayi mashi,baisan dalilin dayasa tayi mashi wannan tambayar ba,   A ɗan ruɗe yace"Mommy meyasa kikayi mun wannan tambayar"?   shiru ta ɗanyi kamar mai nazarin wani abu kafin taci gaba da cewa"junaid bibiyar rayuwarka akeyi!" Hankali atashe junaid yace"Ni kuma mommy azeema,to meyasa ake bibiyar rayuwata?su wanene ke bibiyar rayuwata,me nayi masu?kuma me suke so atare dani?"gaba ɗaya ya gama ruɗewa, "Just calm down ur mind,ba wani abu bane na tashin hankali ba,banaso ka sanya damuwa a ranka junaid,amma ya zama dole na sanar dakai,akwai wata baiwa da Allah yayi mun,duk in nayi mafarki yana xama gaskiya,bawan da yasan da hakan sai ni,abubuwa da yawa kafin su faru acikin gidan nan,ni nake fara ganinsu acikin mafarki na,Allah yana nuna mun...'ajiyar zuciya ta dan sauke tana kallon junaid daya kasa kunne yana sauraronta,    kafin taci gaba da cewa"Nayi mafarki akan ka junaid,mafarkin ya tsoratar dani sosai,wannan dalilin ne ma yasa na nace akan saina zo,ba don komai ba sai don na ganka naga wani hali kake ciki......'    gaba daya hankalin junaid yayi mugun tashi muryar shi na rawa Yace"Mommy azeema,dan Allah ki fahimtar dani wani kalar mafarkine wannan?wani mummunan abune zai faru dani ne?mutuwa zanyi ko?dama najima ina ji araina cewa bazanyi tsawancin kwana ba.........'bata bari ya ƙarasa maganar ba,tasa tafin hannunta ta rufe mashi bakinshi,tsit junaid yayi jikinshi na rawa,zuciyarshi naci gaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,   Cikin sanyin murya tace"Junaid,babu wanda ya isa yayi maka abunda Allah baiyi maka ba!tabbas rayuwarka na cikin hatsari sosai saboda duk wani dake son ganin bayan zuri'armu ta wurinka zai biyo junaid,dole sae da kaine za'a iya cutar damu junaid saboda kaine lagwon kowannanmu,kaine farin cikin mu gaba ɗaya.....' ƙarasa maganar tayi tare da zame hannunta daga bakinshi,    Jikin junaid yayi mugun sanyi,bakomai ya faɗo mashi aranshi ba face wannan ɗigon jinin dake ɗigowa daga hancinshi,da kuma daren ranar nan daya farka tsakar dare yaga wani baƙin hayaki ya fito daga cikin madubin ɗakin Abbansu,ya tunkaroshi ya shiga ta ƙopar hancinshi,a lokacin bayan ya farka washe gari,duk tunaninshi mafarki ne yayi ba gaske ba,amma yanzu da Aunty azeema tayi mashi wannan maganar sae wani tunanin ya faɗo mashi aranshi,tun daga daren ranar da hayaƙin nan ya shiga ta ƙopar hancinshi,a washe garin ranar jinin nan ya soma ɗiɗdigowa daga hancinshi,tabbas akwai wani 6oyayyen abu dake shirin faruwa dashi,   Tuna wannan abun yasa junaid ɗagowa idanunshi awaje yana kallon mommy azeema yace"Nashiga uku!mommy ina cikin tashin hankali!mutuwa zanyi bazan rayu ba...kashe ni zasu yi....bazasu bar ni da raina ba ..zasu rabani da Abbana'    Ganin yarda junaid yabi ya gigice yasa ta ruƙo hannunshi sosai tace"Ka natsu junaid!ba kayi imani da Allah bane?   Cikin shessheƙar kuka yace"nayi Imani da Allah mommy azeema,amma ni bana so na mutu yanzu,inaso na rayu ko don nacika ma abbana burinshi da kuma burin da nake dashi...  '   Katse shi tayi da cewa"tunda kayi imani da Allah,to inaso kasa aranka cewa babu wani mahaluƙi daya isa ya cutar dakai a faɗin duniyar nan face da izinin sa,sannan inaso ka dage da addu'a na sanka junaid baka ba addu'a mahimmanci sosai,kuma ita addu'a da kake gani takobin mumini ce,ka tashi tsaye ka dage da addu'a ka yaƙi duk wani wanda ke son ganin bayanka,kayi mun alƙawarin hakan,nima kuma zan tayaka da addu'ar,sannan zanyi ma abbanku magana akan ya dinga tashin ka tsakar dare kunayin sallah atare koda ace shi bai tashi ba,in har ka farka to ka shiga toilet ka dauro alwala kayi sallarka,sannan kuma zan sanar ma sauran ƴan uwanka duk zanyi masu magana akan su tayaka da addu'a Allah ya tsare mana babynmu,'   Wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi,kalaman Aunty azeema ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,ya samu ƙwarin guiwa sosai awurinta,har ya daina jin damuwa a ranshi,   "Kana da budurwa"?cike da zolaya tayi mashi maganar,don ta kawar da damuwar dake aranshi,   Sunnar da kai junaid yayi tare da cewa"am...um....eh..'   Dariya Aunty azeema tayi tana cewa"wai kunya ta kake ji ne?dalla faɗamun ni inji,"   Hannu yasa yana ɗan sosa ƙeyarshi yace"mommy azeema,akwai wadda nakeso sosai,kuma itama tana sona sosai,acikin gidan nan take,tare da Aunty azmee suke aiki,yau ta sanyani farin ciki sosai mommy,ta kar6i soyayyata,aure kawai ya rage yanzu inyi ma Abbanmu magana.....'kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azeema ta saki baki galala tana kallonshi,    Cike da jin kunya junaid ya kifa kanshi asaman laps dinta yana faman tiƙar dariya,   Suna cikin wannan rahar,wayar Hajiya azeema ta shiga ruri,tsagaitawa tayi daga yin dariyar da take,sannan takai hannu tare da ɗaukar wayar dake ajiye gefenta,ta duba mai kiran nata,a fili tace"Abbanku ne ke kirana,bari na ɗaga naji me zaice mun,"ta ƙarasa maganar tare da kara wayar a kunnanta,   Lamo junaid yayi kwance saman laps ɗinta,ba komai yake tunawa ba face soyayyar da suka sha tare da rishi ɗinsa acikin mota,soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarshi,musamman da ta kar6i soyayyarshi hannu bibbiyu kuma ta amince zata aure shi,yanzu bai da sauran damuwa,dama itace damuwarshi kullum fargabarshi taya zai tunkareta da zancen soyayyar,zata amince ko bazata amince ba!?   Yana cikin wannan zancen zucin nashi yaji muryar azeema tana cewa"Alhamdullillah!Alhamdulillah mun gode ma Allah daya sauke su lafiya,ba don na tara gajiya ba,da ba abunda zai hana nima na biku Airport din mu tarboshi ..'    cike da farin ciki junaid ya ɗago yana cewa"Mommy,Uncle ɗinmu ne ya ƙaraso nigeria"?    Fuskarta dauke da murmushi tace"Eh,yanzu Abba ke sanar dani cewa sun shirya zasu tafi airport ɗauko shi,jirgin nasu bai kaiga ƙarasowa ba,amma kafin su isa airport din zai ƙaraso da yardar Allah,   Cikin sauri junaid ya sauko daga saman gadon jikinshi na rawa yace"Mommy azeema,ki ajiye mun gift ɗina a wurinki,zanzo na kar6a anjima,inaso zanje airport ɗin nima tare dasu Abbanah,'ko amsarta bai saurara ba,ya fuce da sauri da sauri, Murmushi Azeema tayi yayin da take bin bayanshi da kallo har ya fuce, Goggon katsina Da gudun gaske ta fito daga cikin ɗakinta,hannunta ruƙe da wayarta saboda tsabar farin cikin jin zuwan Abusufyan ɗinta da abbansu junaid ya sanar mata, Adai dai lokacin Saude da dr haris suna manne da juna saman 3 seater a falo suna shan soyayya,yana ƙoƙarin manna mata kiss asaman wuyanta,kwatsam sai ga goggon katsina ta faɗo cikin falon tana murna ganinsu yasa ta aza hannu akai tana cewa"La'haula masalli ila!acikin gidan nan ake wannan baɗalar? A firgice suka ɗago suna kallonta hankali tashe,kamar yarda itama take kallonsu hankalinta atashe,    sunnar dakai ƙasa sukayi suna ƴan kame kame,    Jinjina kai tayi tare da cewa"munafukan Allah,yau asirinku ya tonu,dama abunda kuke aikatawa kenan duk in nashige cikin ɗaki ko?cike da tuhuma tayi masu maganar,.     buɗe baki saude tayi da niyar tayi magana,goggo tayi mata dakuwa da hannunta tace"Ungo nan,ja'ira dama kar nake kallonki,munafuka ashe shiyasa kullum nace zan maidaki rugarku sae kiyi mun narai narai da ido kamar na mujiya kina cewa bakison ki koma kiwon shanu,ashe kina nan kin kama wani shanun kina ta tatsa,ina nan sake da baki,Allah kaɗae yasan me kuke aikatawa,ni ban yarda daku bama Allah,ka fadamun gaskiya Harisu iya shinshine-shinshinen kuka tsaya ko kun zarce nan? Tayi maganar tana wurga mashi harara,duk kunya ta gama rufe shi,   Cike da jin kunya suka sunnar dakai ƙasa atare suna sauraronta,sae da takai aya sannan Dr haris yace"Mommyna ni fa ba abunda ya shiga tsakanina da ita,wannan ma da Allah yasa kika gani sharrin shaiɗan ne, ba yin kanmu ba......'bai ƙarasa maganarba,goggo ta tsige kallabin dake kanta,ta wurga mashi shi kafin ya ƙarasa saman fuskarshi,cikin sauri saude ta tarbe kallabin goggon a hannunta,   Baki asake goggo tace"Saude! don tsabar iya rashin kunya da tsageranci akan idona kike kare mashi don na jefe shi da kallabina?wato ya saba baki kina sha shiyasa kika raina ni ko"?    Waro ido waje Saude tayi tana kallonta hankali atashe tace"nashiga uku goggo,me kike nufi daya saba bani ina sha"?   Harara goggon katsina ta watsa mata tana murguɗa mata baki tace"nima bansani ba,nasan dae kina bashi kuma shima yana baki,Allah ya shiryeku in masu shiryuwa ne,sae yanzu nagane kuskuren danayi na barin ki acikin gidan nan,batare da an shafa fatihar Auranku ba,gashi yanzu kuna ƙokarin haifo min ɗan gaba da fatiha.....'fashewa tayi da kuka,cikin shesshekar kuka taci gaba da cewa"Allah sai kin bar gidan nan saude...bazan cigaba da zama dake ba,kina lalatamin yarona,kafin zuwanki gidan nan harisu ko kalmar kiss baisani ba,amma sae gashi yau na same shi yana ƙoƙarin manna maki kiss kamar wani maye,yabi ya kanenayeki don tsabar jaraba irinta ƴaran zamani,acikin gidajen iyayensu ma bazasu iya kame mutuncinsu ba,ni bandamu ba duk abunda zakuyi kuyi,amma ba agaban idona ba.....'   Atare Dr da saude suka kalli juna cike da mamakin jin abunda goggo tace,wato komai zasuyi suyi amma ba'a gaban idonta ba,tashin sense,    Miƙewa haris yayi tare da takawa inda take ya ruƙo hannunta,cikin lallashi yace"Goggo pls komai ya wuce,kuskure ne mun riga da munyi,kuma bazamu ƙara ba,kiyi haƙuri kinji mommyna"    fisge hannunta tayi daga cikin nashi tace"kada ma Allah yasa ku daina,ni wannan ba damuwata bace,yanzu ni bani da sauran damuwa zan tattara nabar maku gidan,idan kunga dama kuyi aure,in baku ga dama ba ku cigaba da abunda kuka saba,Allah dae na kallon mutun,'   Tayi maganar tana wurga ma saude harara,haushinta takeji kamar ta rufeta da duka,    "Mommyna,ina zakije ne?naji kina cewa zaki bar mana gidan"?cike da damuwa yayi maganar   Murguɗa mashi baki tayi tare da cewa"gidan Abba mana,zanje inga Abusufyan ɗina ne,yanzun nan zan shirya in tafi,'    "Mommyna pls ki bari sae gobe zan kaiki da kaina har can ki ganshi,amma yanzu marece yayi fa,naji kamar ana kiran sallar magriba ma,dare zai yi mana a hanya,'cikin lallami yake yi mata magana,don yasan halinta bamai iya mata,   Turo bakinta tayi tana gunguni kamar wata ƙaramar yarinya tace"Allah bamai hanani zuwa,sai naje naga Abusufyan dina tare da ƴa'ƴanshi,'   ɗaure fuska babban likita yayi tare da cewa"Muddin kikasa ƙafa kika bar gidan nan,akwai karnukan layi na nan suna ran gadi acikin anguwar nan,da zarar sunyi arba dake hmmmmmm Allah kaɗae yasan mai zai biyo baya,    tunda taji ya ambaci sunan karnuka,nan take jikinta ya shiga kerma,saboda mugun tsoransu take ji,bata ƙara tanka masu ba,jiki na rawa ta wuce bedroom ɗinta,   Ajiyar zuciya Dr haris ya sauke tare da juyawa ya kalli saude dake ta faman sakin murmushi yace"wlh naji kunya sosai,mommyna bata da saiti,komai yazo bakinta faɗinshi takeyi,yadda kasan rakwa6a66iyar motar da burki ya kwace mata,'.    Fashewa da dariya sukayi,daga bisani Saude ta tsagaita da yin dariyar tace"babyna,addu'a yakamata muyi mata akan Allah ya bata lafiya,idan tadawo dai dai mu kanmu zamuji daɗi sosai,saboda goggo tana da kirki sosae,'   Murmushi Dr haris ya kuma yi tare da cewa"insha Allah zamu cigaba dayi mata addu'a Akan Allah ya bata lafiya,'   _💋Boss Bature💋_    Wuraren ƙarfe 6:30 jirginsu Abusufyan yayi landing a Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja, gaba ɗaya su Abba sun gama hallara a airport ɗin suna jiran saukowarsu daga cikin jirgin,kowannansu a ƙagare yake daya ga fuskar Abusufyan da suka jima basu sanyashi a idanunsu ba,nikaina wlh amatse nake dana ga wannan Abusufyan ɗin da kowa yake ta ɗokin ganinshi, Gaskiya namatsu,namatsu namtsu, inga wannan ɗan tahalikin, daga cikin waɗanda suka hallara domin tarbar shi akwai Abbansu tare da junaid,kanal yousouf da kuma Irfan,jabeer,khaleed da kuma fawan,bayansu kuma akwai Twins suma duk suna zazzaune asaman waiting seats na airport din suna jiran ƙarasowarshi,suna zaune suka ji ana annoucement din ƙarasowar jirgin daya zo daga ƙasar turkey, Tsantsar farin cikine ya bayyana a fuskokinsu,duk suka zuba ido suna jiran 6ullowarshi, Passengers ne suke ta fitowa daga cikin jirgin kowannansu fuskarshi asake,sae bullowa sukeyi ta ko'ina, Sannu a hankali ya aza kafarshi asaman matattakalar benen,masha Allah sae dae muce tabarakallahu ahsanul khaliqin,   giant ne yana da tsayi da kuma cikakkiyar sura mai jan hankali,ta ko'ina Allah ya hore mashi,a launin fata kuwa chocolate colour ne,kala mai tsada,fatar nan tashi taji hutu ko a ido ka kalleta sae kasan cewa ba ƙaramin hutu taji ba,jikinshi na sanye da Suit maroon colour launin glass ɗin dake manne a fuskarshi,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fesowa daga jikinshi,hannunshi na sanye da tsadaddan agogo na diamond,   A hankali ya ɗaga hannunshi tare da kai shi saman fuskarshi ya zame glass ɗin da ke manne a fuskar,lumshe idanunshi yayi tare da waresu a hankali yana kallon mutanen dake shawagi a wurin,   Yayi kewar ƙasar shi sosai,shekara kusan goma sha wani abu,bai taka ƙasar ba,sai yau Allah ya dawo dashi, "Ƙaddara ta sake dawo dani wannan ƙasar" ya furta hakan yayin da yake ƙara ruƙe trolley ɗin hannunshi,jan shi ya shiga yi yayin da yake ci gaba da saukowa daga saman matattakalar jirgin,   Dirar shi ke da wuya,yaji an ambaci sunan shi da wani irin sauti yaji ance"Uncle Abusufyan! "firgit yayi tare da kai idanunshi wurin da yaji an ambaci sunan,   Waro ido yayi waje fuskar nan dauke da farin ciki ya ambaci sunan Junaid,   Da gudun gaske junaid ya ƙarasa tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi,ya kankame shi sosai kamar zai shige jikinshi,   sosai Abusufyan ke sakin dariyar farin ciki yana ƙara bubbuga bayan junaid da hannunshi yana cewa"WOW MASHA ALLAH MY BABY BOY KAINE KA KOMA HAKA,GASKIYA NAYI MISSING ƊINKA SOSAI JUNAID,AM REALLY GLAD TO SEE U ........' ya ƙarasa maganar tare dasa hannunshi ya ɗago junaid daga saman kirjinshi yana kallon fuskarshi,yayi mamakin girman yaron lokacin da daya tafi yana ɗan ƙaraminsa ya barshi, ganin hawaye na sauka asaman fuskar junaid yasa shi cewa"meya faru junaid?kai da zan ga kana farin ciki sae kuma naga hawaye a idanun ka why?   Cike da shagwa6a junaid yace"uncle bakaine ka tafi kabarmu ba,shekara da shekaru ka manta damu,ba ka damu da kazo ka ganmu ba,"    ƙayataccen murmushi Abusufyan ya saki tare da cewa"Am really sorry my boy,nasan ni mai laifine ayimun afuwa pls,shiyasa nadawo nigeria don in goge laifina....'   Yana cikin maganar tashi sai ga su Abba sun ƙaraso wurinsu tare dasu kanal yousouf,   Gaba daya suka ƙarasa one by one suna rungume shi ajikinsu cike da nuna farin cikin ganinshi, Sae da ya kammala rungumarsu,sannan ya ɗago yana kallon ɗan uwan nashi daya tsaya gefe guda,yana kallon shi fuskarshi aɗaure alamar fushi yake dashi, Tunkarar shi yayi zai rungume shi,cikin sauri Abba ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu yace"karka kuskura ka ƙaraso nan,bana son ganinka,ni banma san ya akai nazo airport ɗin nan ba," Hannu uncle abusufyan yasa tare da kama kunnan shi yana cewa"Am sorry my bro,ayi mun aikin gafara nasan nayi laifi,amma zan gyara kuskure na,yanzu dae ka barni in rungumeka kona ji sanyi araina,' Buɗe mashi hannu Abba yayi alamar ya taho,faɗawa jikin shi abusufyan yayi sosai suka rungume junansu,tuni hawaye suka cicciko a idanuwan kowannansu muryar abbansu junaid tamkar zaiyi kuka yace"Hakanan ka tafi ka barni batare da sani na ba,me yasa kayi mun haka abusufyan?duk irin son da nake maka,ka tafi ka barni da raɗaɗin rashin ka acikin zuciyata,abun ba ƙaramin ciwo yake yi mun ba," ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga na Abusufyan, Jikin shi yayi mashi sanyi,duk sai yaji ba daɗi,kuma bai kyauta masu ba, daƙyar yace"Ka yafe mun ɗan uwana,na cutar dakaina,na raba kaina da ƴan uwana,bawai don bana son kasancewa atare da ku ba......' Kasa ƙarasa maganar yayi saboda wani abu daya tuna a rayuwarshi daya ta6a faruwa dashi..., Jinjina kai kawai Abbansu junaid yayi tare da ruƙo hannunshi yace"Komai ya wuce,tunda kadawo nigeria,kuma inaso ka sani bazan ƙara bari kabar ƙasar nan ba,komai kakeso ka faɗamun zanyi maka shi,in ma akwai wani abu dake damunka duk ka sanar mu,zanyi ƙoƙari wurin ganin na share maka hawayenka,dama ni sae da raina ya bani cewa bada son ranka kabar ƙasar nan ba,akwai wani abu dake faruwa wanda kaƙi sanarma kowa.....' "Abba,uncle fa ya gaji sosai,ya kamata muyi hanzarin wucewa gida tare dashi,idan ya kwanta ya huta sae mu ƙara gaggaisawa dashi," Kanal yousouf ne ya katse mashi hanzarinshi, murmushi abba yayi tare da janyo hannun abusufyan suka kama hanyar fitowa daga airport din,gaba dayansu suka ɗunguma izuwa wurin da suka ajiye motocinsu,murmushi kawai Abusufyan keta saki yana kallon ƴan uwan nashi kamar ya haɗiyesu haka yake ji,saboda tsabar son da yake yi masu. Finally Uncle Abusufyan ya ƙaraso nigeria,saura mommynsu junaid da kuma Ammi,su muke jira, Koda suka ƙaraso cikin gidan,anan main palour din suka zazzauna ana ƙara gaisawa da juna,a ƙarshe abba ya ruƙo hannun ɗan uwan nashi yakai shi izuwa cikin bedroom ɗin da aka tanadar mashi,katafaren ɗakinsa da zai zauna aciki,sae da abba ya tabbatar da cewa Abusufyan ya shige cikin ɗakin sannan yaja mashi ƙopar ya rufe, Gaskiya zanso kuga irin farin cikin da ahalin nan suke yi na zuwan Uncle dinsu Abusufyan, Wuraren ƙarfe 11 na dare lokacin komai ya lafa,junaid ya nufi bedroom ɗin sehrish yana nemanta ganin bata fito ba,lokacin daya je,ɗakin nata ya shiga wayam yaga babu kowa,jiki na rawa ya wuce ɗakin azmee yana tambayarta ina reesh take,azmee tace"tun ɗazu dana kai mata lunch ban ƙara sanyata a cikin idanuwana ba,"fitowa junaid yayi daga ɗakin azmee hankalinshi a matuƙar tashe,saƙo da lungu na gidan ya dinga bi yana dubawa bai ganta ba,lokacin daya tabbatar da cewa sehrish bata acikin gidan,jiki na rawa ya wuce ɗakin Abbansu anan ya same shi zaune shi da Uncle abusufyan suna ƙara tattaunawa a tsakaninsu, Ganin yarda junaid ya faɗo masu ba sallama yasa suka shiga tambayarshi ko lafiya,hankali tashe yace"Abba,sehrish nake nema,na duba ko'ina acikin gidan nan bata nan,' cike da mamaki abusufyan ya maimaita sunan Sehrish abakinshi, Abba kuma yace"tun yaushe tabar gidan?baka je ɗaukota daga school bane"? "Abba naje,dakaina na ɗaukota kuma na kawota acikin gidan nan,amma yanzu na duba ko'ina babu ita," Jin wannan maganar ta abba yasa shi miƙewa daga zaunen da yake gefen gadon ya nufi junaid yana cewa"muje wajen," Juyawa junaid yayi suka fuce atare,yayin da suka bar Abusufyan azaune cikin ɗakin, Hankalin kowa fa ya tashi,abun sai ya baka mamaki,ashe ba ƙaramin so sukeyi ma yarinyar ba,duk wanda akace mashi Sehrish ta 6ace ba'a ganta ba,sae kaga ya fito daga bedroom dinshi yadawo falo cike da damuwa,gaba daya sae da kowannansu ya hallara banda Sgr,saboda tun ɗazu yabar cikin gidan, Hankalin Marshal omar ba ƙaramin tashi yayi ba,jin ana neman Sehrish,sam ya manta da bata a cikin gidan,tunda junaid yayi musanyarta da jahad,ya tura sojojin nan don su nemo mashi jahad,su kayi arba da yarinyar saboda kamanceceniyar dake atsakaninsu yasa sukayi tsammanin Jahad ce,yayin da suka bi ta da nufin su kamata ita kuma ta watsa aguje,tabar masu school bag ɗinta a ƙasa,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita ba alamarta 6at ta 6ace masu.........Shin Ina sehrish ta shiga ina!? "Abba wai meke faruwa ne naga kunyi curko-curko anan,kamar kuna cikin damuwa,"hajiya azeema ce ke tambayarshi a lokacin da take ƙarasowa inda suke tsaitsaye,duk sun hallara gaba dayansu kowa yana cike da zullumin abunda zai biyo baya game da yarinyar da ta 6ata, "Yarinyar dake taya azmee aikice ta 6ace,an nemeta an rasa babu ita acikin gidan nan,"ya bata amsa fuskarshi cike da damuwa, Fawan yace"Abba ita yarinyar bata da waya ne"? junaid ne ya bashi amsa da cewa"akwai waya a hannunta,amma na kira layinta a kashe,tun ɗazu nake trying still switch off, Hajiya azeema tace"gaskiya akwai matsala,yakamata ayi hanzarin binciko inda yarinyar take," Gaba daya duk sun shiga damuwa,musamman junaid hada ƴan hawayenshi, Gyaran murya Marshal Omar yayi suka mayar da hankalinsu akanshi,sannan yace"kada ku damu,insha Allah za'a ganota,na zuba sojoji acikin garin nan suna nan suna bibiyarta,kuma insha Allah zasu gano mana ita," Abba yace"naji daɗi sosai Omar,Allah yasa su gano mana ita,hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har yarinyar nan bata dawo cikin gidan nan ba,' Ya ƙarasa maganar tare da kallon su fawan yace"kuje ku kwanta,insha Allah za'a gano ta," Har suna haɗa baki wurin cewa"Abba,ba zamu iya runtsawa ba,in har ba'a ganta ba,zamu zauna anan ne mu jira har Allah yasa ta bayyana,' Abun ba ƙaramin mamaki ya ba Abbansu ba bai ta6a tunanin cewa sun damu da yarinyar ba,sae yau,abunda ke faruwa ita mace ce,kuma matashiya dole kowa yayi zullumin ina ta shiga,waya dauketa,sace ta akayi ko kuma cutar da ita akayi,? *Sehrish* *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.     *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari, "Aunty azmee wai meke faruwa ne naga kowa ya hallara a falo fuskokinsu kuma da alamun damuwa atattare dasu,wani abu ya faru ne"?Hayamm ce tayi mata wannan tambayar,fitowarta kenan daga bedroom dinta,da alama tafara bacci,sae faman hamma takeyi, Azmee dake tsaye daga wurin corridor ɗin shiga bedrooms ɗinsu,ta juya tare da kallonta tace"Ba dole ki ganmu a haka ba?Sehrish ce ta 6ata an nemeta an rasa,shiyasa kika ga kowa hankalinshi atashe,   cike da mamaki hayaam tace"Wai don sehrish ta 6ata shine kowa ya tashi hankalinshi haka?suka hana idanunsu bacci saboda wannan yarinyar?sae kace dae wata ƙanwarsu ko ɗiyar Uncle ɗinsu?menene alaƙarsu da ita da har zasu sanya damuwa aransu don ta 6ace!ƴar aiki fa ce ba wata tsiya ba,"    "Hayaam!Anya kina cikin hayyacin ki kuwa?mutun fa akace maki ya 6ace ba dabba ba!don me ba zasu tashi hankalinsu ba?don tana ƴar aiki?kamar kece fa ace kin 6ata acikin gidan nan!kina nufin kada kowa ya damu kenan tunda ke ma baki da irin alaƙar da kika ce dasu kamar dae ita din yarinyar!in fact sun ma fi sabawa da ita yarinyar,saboda hidimar da takeyi masu kullum tana cikin yi masu ɗawainiya acikin gidan nan,ta wuce ƴar aiki a wurinsu,tamkar ƴar uwarsu ta Jini suka ɗauke ta......'   Tunda Azmee ta soma magana,Hayaam take kallonta Rai a matuƙar 6ace jin maganganun da take gaya mata,bata ta6a tunanin cewa azmee zata iya furta mata su ba,a tunaninta matsayinta yaci ace tayi respecting ɗinta amatsayin wadda yayyanta ke auran wasu daga cikin matasan gidan,   "Aunty azmee yanzu saboda waccen ƙasƙantacciyar yarinyar kike gayamun magana!kin manta matsayina acikin gidan nan ne!ya kamata ki iya bakinki,ina girmamaki ne kawai saboda girma da darajar da kike dasu awurina,"   Ƙarasa maganar tayi tana faman huci,saboda an 6ata mata rae,nace sannu ƴar masu gida,   girgiza kai kawai Azmee tayi,dama tasan halin hayaam ciki da bai,bata da kunya futsararriya ce ta gidan gaba,tuna wannan yasa ta fasa mayar mata da martanin maganganunta,   murmushi kawai tayi kafin tace"Hayaam ni ban faɗa maki hakan don na 6ata maki rai ba,kawai banji daɗin maganganun da kika faɗi bane agame da rishi,koba komai ita mutunce mai daraja,kuma yarinya ce dole mushiga damuwar rashin.....'.   Bata bari azmee takai ƙarshen maganarta ba,ta buga uban tsoki tare da cewa"Ni bangan abunda damuwa ba anan,Ita tasan inda takai kanta,wama ya sani ko tana ɗakin hotel Kwance tare da kwartonta,ku kuna nan kun tashi hankalinku a banza"   Waro ido waje Azmee tayi jin abunda hayaam tace,   Shu'umin murmushin nan nata ta saki tare da juyawa ta nufi hanyar bedroom dinta,tabar azmee atsaye baki a sake tana bin ta da kallo,   Lokacin da hayaam ta shige cikin ɗakinta,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ba don komai ba,sae don jin 6atar sehrish,addu'arta Allah yasa karsu ganta, A fili ta dinga cewa"Allah yasa mota ta take kanta ta mutu kowa ya huta,dama natsani ganin yarinyar nan acikin gidan nan,"ta ƙarasa maganar tare da faɗawa saman gadonta hankalinta kwance, Azmee kuwa lamarin ya fi ƙarfinta,ta jijjiga sosai da jin kalaman hayaam akan sehrish,tabbas ba ƙaramin tsanarta tayi ba,wannan ma in ta samu dama da alama zata iya halakar da ita gaba ɗaya,' *Boss Bature* Abun da ya faru lokacin da Sojojin nan suka bi sehrish a guje suna ƙoƙarin kamata ta kubce masu,ta hanyar faɗawa wata corner,kafin da gudun gaske sojojin suka bi ta cikin kwana din don su kamota sae dae kash,lokacin da suka ƙarasa cikin lungun tuni sehrish ta jima barin shi,da sauri suka bi lungun har ƙarshen shi,anan suka tarar da dogon titi,ko'ina sun duba babu ita,hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,basu ga ta zama ba haka suka karaɗe ko'ina na garin wurin neman Yarinyar, Yayin da suke ta yawan neman sehrish,ashe tana ƙarƙashin teburin mai siyar da kayan marmari a bakin hanya,lokacin da ta faɗo lungun ta futo aguje tarasa inda zata sanya kanta,kwatsam ta hango teburin nan na mai kayan marmari,babu wanda ya lura da ita lokacin da ta saɗaɗa cikin sanɗa,ta shige ƙarƙashin teburin jikinta nata faman kerma,gaba ɗaya duk tabi ta rikice ta ruɗe,ta razana kuma ta firgita sosai,sanadin wannan uban gudun da tayi ne,ya ƙara mata raɗaɗin ciwon cikinta ya dawo sabo,a can ƙasan mararta ta dinga jin wani irin zogin ciwo mara daɗin ji,kuka sosai takeyi ƙasa ƙasa duk tabi ta takure kanta a ƙarkashin teburin,ta ƙankame jikinta saboda wani irin Sanyi dake shigarta,ba ƙaramin kamu sanyin yayi mata ba,ko'ina na jikinta sae faman kakkarwa yakeyi,hatta teeth ɗinta gamewa sukeyi da juna,Sehrish taji jiki sosai fiye da tunaninku,baiwar Allah tama rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,don ta jigata sosae ga uwar yunwar dake cin ta don ma ciwo da fargaba sun hana ta fahimci tana jin yunwar,gaba daya ta fita hayyacinta,wuraren ƙarfe sha ɗaya lokacin kowa ya watse babu mutane a wurin mai kayan marmarin,A hankali ta fito daga ƙarkashin Teburin tare da miƙar hanya tana tafiya tana tangaɗi akan hanya kamar wadda tasha Giya,da ƙyar take takawarma don jan kafa kawae take,a lokacin ita kanta batasan inda ta dosa ba,saboda ta fita hayyacinta, Tana cikin wannan tafiyar agefen titi,wata mota baƙa ƙirar Rav 4,tayi parking adai dai inda sehrish take,wasu matasa ne kusan su Huɗu jigunannun ƴan iska,Zubin ibliss ne suka fito daga cikin motar,dukansu suna sanye cikin Riga da wando crazy jeans,Kallo guda zakayi masu kasan cewa ba Allah aransu,fitsararru ne na ƙarshe,wani ɗan iskan gyaran gashi ne akansu,na tantirae wanda suka haura matakin deegre a6angaren Tashanci,    Jin motsin mutane yasa Sehrish yin firgit agigice ta juya tana kallonsu hankali a matuƙar tashe,kafin tayi wani yunƙuri tuni suka ɗauketa tare da toshe mata baki da tafin hannu suka turata acikin motarsu,back seat suka wurgata ciki,sannan suka shige ciki,tare da jan motar da gudun gaske suka fisgi Motar,    kokowa sehrish ta shiga yi tana ihu tana hargowa tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!ku rabu dani!ku ƙyale ni!ku barni na tafi gida,nashiga uku,Wayyo Allahna,   daya daga cikinsu ne ya sanya hannunshi tare da toshe mata baki ya daka mata tsawa yace"Ke!yi mana shiru anan,kin cika mu da hayaniya,its better ki rufa mana baki,don babu mai taimakonki anan,"    Ba ƙaramin tsorata tayi ba,kankame jikinta tayi tana cigaba da ambaton sunan Allah acikin bakinta,    Da gudun gaske suka shigar da motar cikin wani ƙayataccen garden tare da yin parking dinta,   Buɗe motar sukayi gaba dayansu suka fito,na ƙarshen ne ya fito hannunshi ɗauke da sehrish yayi wurgi da ita,gaba daya ta gangara goshinta ya bugu jikin wata bishiya,dafe wurin tayi tana faman shesshekar kuka,ba ƙaramin buguwa tayi ba,dakyar tasamu ta ɗago daga kwancen da take aƙasa,    buɗe idanunta tayi waɗanda suka kumbura suka ƙankance saboda kukan da tasha,a firgice taja da baya ta ƙure ma bishiyar dake bayanta tana kallonsu,idanunta azazzare hankalinta yayi mugun tashi,   Su duka huɗun suna tsaye agabanta,kowannansu na kwance belt din wandonshi,girgiza masu kai tashiga yi tana cewa"dan Allah kuyi hakuri.. ..kada ku cutar dani....kada ku rabani da mutunci na....ku ƙyale ni na tafi gida ..bani da lafiya..."   Abun nasu babu imani kwata kwata,duk wannan magiyar da sehrish keyi masu hakan baisa sunji tausayinta ba,   A wulakance daya daga cikinsu yakai hannunshi tare da Fisge hijabin dake jikinta yayi wurgi dashi gefe guda ya faɗi ƙasa,   Cikin sauri sehrish ta ƙankame rigar jikinta,saboda ta matse ta kirjinta ya fito sosai,    gaba daya sun kwaɗaitu da ita,musamman da sukayi arba da kyakkyawar surar jikinta,mai matuƙar jan hankali,    tamkar zata shige ma bishiyar haka ta manne tana kara matse kanta ajikinta,hawaye sae faman sintiri sukeyi a fuskarta,cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ku ƙyale ni na tafi gida!bansanku ba bansan su wanene ku ba,bansan me yasa kuka ɗaukoni ba......'ƙasa karasa maganar tayi saboda jin daya daga cikinsu ya cafko gaban rigarta,da ƙarfi yajata nan take ta tashiga yagewa Allah yaso akwai farar half vest da tasanya daga ciki,daddagewa tayi ta gartsa mashi cizo asaman hannushi,a gigice ya saki rigarta,tattare wurin tayi da hannunta,jiki na rawa ta yunƙura zata tashi ta gudu,    Wani daga cikinsu yasanya kafarshi tare da taɗiyo kafarta,nan take sehrish ta kife ƙasa,ta bugu sosai saukin ma ciyayi ne awurin ba duwatsu ba,.    fashewa sukayi da dariyar sheƙiyanci suna kallonta,kafin daga bisani ɗaya daga cikinsu,ya afka mata yana ƙoƙarin keta mata haddinta,   fashewa da kuka sehrish tayi mai sautin gaske saboda tarasa yarda zatayi ta kwaci kanta ahannunshi,    Damƙa yakai ma wandon jikinta yana ƙokarin zame shi kenan, dai dai lokacin wata danƙareriyar mota jeep ta kunno kai cikin garden ɗin atsiyace mai motar ke driving ɗinta, motar na tsayawa yasa hannu tare da buɗewa ya fito daga cikinta,gaba ɗaya matasan nan guda ukun dake awurin zuba mashi ido sukayi atare suna tunanin wanene wannan ya faɗo masu acikin garden ɗin lokacin da suke tsaka da jin dadinsu,ya rufe fuskarshi da face mask,sannan ya manna baƙin glass a fuskarshi,wannan yasa ba zasu iya tantance ko wanene shi ba   Jin sautin kukan yarinyar a cikin kunnanshi yasa shi juyawa cikin sauri yakai idanunshi akan wanda ke ƙoƙarin rabata da kayan jikinta,a wani irin zafafe ya tunkare shi,kwakkwaran damƙa yakai ma wuyar rigar shi da hannu ɗaya,ya ɗago shi tare da yin wurgi dashi gefe guda,   Kallon juna sauran suka shiga yi,hankalinsu tashe ganin yarda ya ruƙo shi da hannu guda,duk girmanshi yayi wurgi dashi, Kafin yayi wani yunkurin tashi daga wurgin da yayi dashi,ya dunƙule hannunshi tare da kai mashi naushi agefen fuskarshi,Nan take haƙora guda biyu suka 6allo tare da fadowa daga cikin bakinshi ɗauke da jini,   Koda sauran matasan nan guda uku suka ga wannan tashin hankali,maimakon suyi ta kansu,rabon wahala sae suka tunkareshi suna naɗe hannun riga alamar zasu yi mashi rubdugu,    Kamar jira yake su ƙaraso wurinshi,dukkansu ya haɗa yayi masu shegen duka,gaba ɗayansu babu wanda bai raunata shi ba,sae faman juyi sukeyi a ƙasa suna fadin Wash!Ash!    Juyawa yayi tare da kallon Yarinyar dake kwance ƙasa sai faman burgima takeyi tana fadin kada ku rabani da mutuncina,ku ƙyale ni na tafi gida,banaso!banaso ku daina ta6amun jikina,gaba daya sehrish bata a cikin hayyacinta juyi kawai takeyi tana sambatu,   juyawa yayi batare da yaje wurinta ba,dama taimako ne ya kawo su cikin garden din,Hanya ce ta biyo dasu ta saman titin shine suka ji sautin kukan mace acikin baƙar motar dake a gabansu wannan ne dalilin dayasa suka biyo bayan motar har suka gano inda suka shiga,cikin sa'a kuma suka tarar da abunda suke zargi,   Karasawa yayi wurin motar tasu tare da buɗewa ya shiga ciki ya zauna yana faman sauke ajiyar zuciya,    "Sir,yarinyar fa"? Drivern dake driving ɗinshi ne yayi maganar,     Muryarshi a kasalance yace"Armstrong,muje gida kawai,am very tired,so i need some rest,'    Armstrong yace"Sir,ya kamata ka ƙarasa aikin ladar da ka fara a taimaki yarinyar asan daga ina take"   "Banyi niyya ba!,why ta fito wannan lokacin almost midnight,zata tashi ta koma inda ta fito ne"ya bashi amsa,   Sam baiji daɗi ba,bai so Sgr yaƙi amincewa dasu taimaki yarinyar ba,yana ji yana gani zasu bar yarinyar kwance acikin garden ɗin cikin wani hali na neman agaji,ba yarda zaiyi,   Tashin Motar armstrong yayi tare da janta baya baya sannan ya karya kwana suka fuce daga cikin garden din,    Lumshe idanunshi yayi yana faman sauke ajiyar zuciya wani irin bacci ne ke fisgarshi,kwanakin nan yana stressing kanshi sosae,matsaloli sunyi yawa a kasar daga wnn sai wnn,abunda ma yafi bashi haushi yadda aka bar yarinya mace kamar wannan ta fito a irin wnn lokacin.   Yana cikin wannan yanayin,ringing din wayarshi ya karaɗe kunnansu,cikin sauri yakai hannu cikin aljihun wandon jikinshi ya curo wayar tare da duba sunan mai kiran nashi,My Own Father,sunan da ya bayyana akan screen din wayar tashi kenan,    ganin Abbansu ne yasa shi yin saurin picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanshi yana sauraronshi,   On the other hand abban nasu yace"Rafayet!kana ina ne"?   Sgr yace"Abba yanzu muna kan hanyar dawowa gida ne,akwai wani abu ne"?ya tambaya yana jiran amsar da zai bashi,   Cikin tashin hankali Abban nasu yace"Rafayet!yarinyar nan fa,ta 6ace an nemeta ko'ina acikin garin nan ba'a ganta ba"    "Abba,I don't understand what u'r talking about,wace yarinya ce ta 6ace"?   Kora mashi bayani abban nasu ya shiga yi game da 6atan sehrish,"    Cikin sauri Sgr yayi rejecting kiran abban nasu tare da dakatar da Armstrong daga yin driving din da yake yi yace mashi"mu koma garden din nan,kayi sauri," "okey sir,"ya amsa mashi tare da karya kwana ya miki hanyar da zata maida su can wurin da suka baro,   Tunda Abbansu ya sanar dashi 6atan sehrish,yake ji aranshi cewa kamar itace yarinyar da waɗannan matasan suka kai cikin garden din nan suna ƙoƙarin lalata mata rayuwarta,tabbas yana ji aranshi cewa itace yarinyar,duk da bai kalli fuskarta ba,amma yana ji aranshi cewa itace, Bayan sun shigar da motar cikin garden ɗin,da sauri sgr ya fito daga cikin motar tare da nufar inda Sehrish take kwance bata iya ko motsi,sai numfashi da take fitarwa sama sama,Kuma har lokacin matasan nan guda huɗu da yayi masu bugun mutuwa suna nan baje ba wanda ya iya tashi,   Ƙarasawa sgr yayi tare da zuƙunnawa wurin da sehrish take kwance,ya sanya hannunshi tare da juyo da fuskarta da kyau yana kallonta,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,taya akai yarinyar takai wannan lokacin awaje bata koma gida ba?da alama daga school take tunda ga uniform nan ajikinta,runtse idanunshi yayi tare da cizon la66ansa, buɗe idanun yayi gwanin ban tsoro sun canza launi saboda tsananin 6acin rae,aranshi yace wai dama ita ce!?   Wurga idanunshi yayi yana kallon matasan nan dake baje ƙasa suna ta faman juyi,yunkurawa yayi a zafafe ya nufesu,naɗe hannun jacket din jikinshi yayi,One bye one ya bisu sae da ya canza masu kamanni yarda ko uwar da ta haifesu in ta gansu bazata ganesu ba,sae da ya tabbatar cewar bazasu ƙara amfanuwa ba,sannan ya haƙura ya ƙyalesu,    dawowa yayi wurinta ya sake zukunnawa tare da sanya hannayeshi biyu,ya ɗaukota tamkar yar baby ya nufi motar da ita,   Tun kan ya ƙaraso Armstrong ya buɗe masu mota,shiga ciki sgr yayi tare da ita,sannan armstrong ya koma ciki yaja motar suka bar cikin garden din,    asaman kafadarshi sehrish ta kwantar da kanta,tare da ƙankameshi sosai jikinta nata faman kerma,yayin da idanunta ke a rufe la66anta nata faman kerma,   gyaran murya ya ɗanyi tare da ce ma armstrong ya kashe na'urar A.C,'   "Okey sir,"ya amsa mashi,batare da 6ata lokaci ba,ya kashe sanyin ac na motar gaba ɗaya,ya kunna masu warmer,na'urar dake dumama yanayi tamkar room heater,nan take cikin motar yayi ɗumi mai daɗin gaske,   A hankali jikinta ya rage kermar da yake yi,zuba ma fuskarta ido yayi yana kallon yadda la66anta keta faman kakarwa,har lokacin bata daina wannan sambatun da takeyi ba,kawar da idanunshi yayi daga kan fuskarta ya mayar dasu saman wuyanta,kafin yayi ƙasa da idanun nashi izuwa saman ƙirjinta,cikin sauri ya kawar da idanunshi gefe guda,saboda wani irin bugu da zuciyarshi tayi,    Janyeta yayi daga jikinshi ya jinginata ajikin seat na motar,sannan ya sanya hannunshi tare da cire jacket ɗin jikinshi,janyo sehrish yayi ya zura mata rigar sanyin tashi ajikinta,bayan ya kammala sanya mata rigar,ya janyo ta ajikinshi sosai ya ruƙota,saboda kermar da jikinta keyi,a firgice take har lokacin,ƙara ƙanƙame shi tayi sosai tana mutsistsike rigar jikinshi da hannunta,bai yi wani aune ba yaji hannunta asaman mararshi,ba ƙaramin gigita yayi ba,wani irin shock yaji ajikinshi,lokaci guda ta jefa shi cikin yanayi,sam ya gaza janye hannunta daga wurin,duk wannan abun da sehrish takeyi mashi bada saninta ba,saboda bata acikin hayyacinta,batasan wanene shi ba,raɗaɗin ciwo ne kawai ke fisgarta,    Kafin Sgr yayi yunkurin zame hannunta daga saman mararshi tuni ta zarce da hannunta inda ba'ason zuwa,a gigice ya damƙo hannunta cikin nashi yana faman jan numfashi,runtse idanunshi yayi yana cizon pink lips ɗinsa,ware idanun nashi yayi a hankali sun canza launi izuwa dan ja,    ƙasa ƙasa yaji muryarta tana cigaba da cewa"kada ku cutar dani dan Allah,ku barni na tafi, karku raba ni da mutunci na.....'   lumshe idanunshi yayi a yayin da yake cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta,jacket ɗin da ya sanya mata ba ƙaramin kyau tayi mata ba,duk da tayi mata yawa sosai,    yarda take motsi da tausasan la66anta tana sambatu ba ƙaramin burgeshi tayi ba,gaba ɗaya ya tsinci kanshi da bin su da kallo ko ƙyaftawa baiyi,   Murmushi kawai armstrong ke saki yana driving ɗinsu anatse,ta cikin mirrow yake satar kallon Sgr daya kura ma sehrish ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi, Kasancewar akwai hasken fitilun motar daya haskaka ko'ina na cikinta, wannan ne ya bashi damar ganinsu sosai,sun burgeshi sosai,bai ta6a ganin Sgr nama wata ƴa mace irin  kallon daya kamashi yanayi ma ƴar tahalikar ba,tabbas kowacece wannan ba ƙaramar mai sa'a bace,ya fadi hakan acikin ranshi,   ƙoƙarin kwantar da kanshi yayi agefen wuyanta,gyaran muryar da yaji ne yasa shi ɗagowa,kumshe dariya armstrong yayi,bakomai yasa shi yi mashi gyaran murya ba fa ce don ya tunasar dashi cewa bafa su kaɗae ne acikin motar ba,yana a kusa kar Ogan nashi ya sa6a number a gabanshi,   Harara sgr ya wurga mashi tare da miƙa hannunshi ajikin motar,ya danna wani wuri,nan take Labule ya sauko daga sama,ya raba tsakaninsu da armstrong ya kasance bai iya hangensu,balle ya san meke wakana,   Dariya sosai armstrong ya shiga yi,abun ba ƙaramin ƙayatar dashi yayi ba,bai so sgr ya sanya labule atsakaninsu ba,yaso yabarshi yaci gaba da kallonsu don ba ƙaramin kyau sukayi mashi ba,   a hankali motar ta ƙetare babban gate din gidan nasu,bayan sun ƙarasa ciki wuring parking space,tsayar da Motar armstrong yayi sannan ya fito cikin sauri ya zagaya tare da buɗe mashi mota,   A lokacin Hayaam na a tsaye gaban window tana leƙen motar tasu,dama tun ɗazu ta tsaya ajikin windown tana jiran dawowarshi,don takai mashi abinci tunda sehrish ta 6ace,tasan cewa yanzu dole ya haƙura ita taci gaba da kai mashi,cike da zumuɗin ganinshi,hayaam ke washe baki tana leƙo motar tasu,fitowar shi kawai take jira daga cikin motar,ta baza idanuwanta kamar na mazuru tana jiran ganin shi,ganin ya zuro kafarshi daga cikin motar yasa Hayaam lumshe ido tana sakin murmushin nan nata,   Lokacin da ya ƙarasa fitowa daga cikin motar,hannu shi ya sanya tare da ɗauko sehrish gaba daya ya azata asaman kafadarshi,   Nan take murnar hayaam ta koma ciki,hankalinta a matukar tashe take kallonsu,har hannu take sanyawa tana murza idanunta wai ko idonta ne ke nuna mata ba dae dae ba,lokacin da ta tabbatar da abunda idanunta ke nuna mata,na ganin Sgr ɗauke da Sehrish a kafaɗarshi,nan take ta fashe da matsanancin kuka tana bubbuga ƙafa,bakin ciki kamar ya kasheta,wani rin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata a maƙoshinta,kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka ta dinga ji,   cikin shessheƙar kuka take cewa"Wlh na tsani yarinyar nan!bansan ganinta!ƙoƙari take ta rabani da abunda nake hari!ni bansan ma ya akai ya ganta ba,harya ɗaukota acikin motarshi!Allah bazan barta ba saina illata ta,tunda har ta sanya na zubar da hawayena akanta!saina ga bayanta kafin ita taga bayan nawa"!   Haka hayaam taci gaba da sambatu tana zagaye dakin nata kamar wata zararriya,   Atare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da Sgr ya shigo cikin main palour din,kafadarshi ɗauke da sehrish,gaba dayansu sunyi mamakin ganinshi tare da ita,yarda akai har ya hadu da yarinyar,   fuskar Abbansu dauke da farin ciki ya shiga furta"Alhamdulillah!Alhamdulillah Allah mungode maka,ba rabon asha wahala!"   Wani irin farin ciki ne ya lullu6e junaid ganin sehrish dinshi,duk da ya ɗan tsorata da ganin yarda sgr ya daukota kamar bata numfashi,suma sauran duk sunyi tsaitsaye suna jiran jin bayani daga wurinshi, Ƙarasawa ciki yayi tare da kwantar da ita saman 3 seater,   Muryar Abbansu yaji a bayanshi yana cewa"Meya same ta ne?a ina kuka ganta"?   Bai bashi amsa ba sae da ya fara juyawa ya kalli su fawan dake atsaye suna kallonsu yace"Tsayuwar me kuke anan,ba kuje kun kwanta ba,"? "Sun shiga damuwa ne na rashin ganinta da akayi,shiyasa suka gaza runtsawa suma,"abban nasu ne ya bashi amsa,   "Kowa yaje ya kwanta,"cike da bada umarni yayi maganar,nan da nan kowa ya kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi ba tare da sunji wani bayani ba,   Mutum uku ne suka rage atsaye suna sauraron jin bayani daga wurinshi,Abbansu da kuma marshal omar sae kanal yousouf,    Matsawa omar yayi kusa da sgr dake atsaye ya dafa kafadarshi tare da cewa"Bro,a ina kuka same ta ne? da kyar Sgr ya iya buɗe bakinshi ya kwashe dukkan abunda ya faru ya sanar masu,   ba ƙaramin tausayinta suka ji ba,jikinsu duk yayi sanyi sosai,bayan komai ya daidaita,Sgr ya wuce part dinshi a gajiye, Azmee ce tayi ƙoƙarin ɗaukar sehrish ta wuce da ita cikin bedroom ɗinta,asaman gado ta kwantar da ita,tare da jan bargo ta lullu6e mata jikinta,ta jima azaune cikin ɗakin nata tana kallonta a ranta tana tunanin ya akai ta fita daga gidan,a lokacin ta samu bacci,sae da dare ya raba sannan azmee ta koma ɗakinta, Koda sgr ya shiga bedroom din shi,gaba daya kasala ta gama mamaye mashi ko'ina na jikinshi,hakanan ya dinga jin kamar yaje ya ganota,wane hali take ciki,ta samu bacci kuwa,tunani ya soma yi anya ba dalilin datse mata gashin da yayi bane yasa tayi yunƙurin guduwa daga wurinsu ba?saboda ya lura ba ƙaramin so take ma gashin kannan nata ba, Ya ƙarasa zancen zucin nashi a yayin da yake ƙarasa cire kayan jikinshi,zame belt ɗin wandonshi yayi ya tube shi daga jikin trouser ɗinshi,abunda sehrish tayi mashi ɗazun ne ya faɗo mashi a ranshi,lokacin da takai hannunta asaman mararshi,tuna wannan yasa shi jin wani yanayi mara misaltuwa atattare dashi,ya rasa me yasa yarinyar take ƙoƙarin canza mashi alƙiblarshi,da alama in baiyi dagaske ba zata ci nasara akan shi ne, Sai da ya kammala cire kayan jikinshi ya rage daga shi sae white short ajikinshi,sannan ya wuce cikin toilet don yin wanka, Bayan ya kammala wankan ya fito jikinshi sanye da bathrobe fara,wata irin kasala ta mamayeshi,har ya gaza shirya kanshi acikin sleeping dress dinshi,a ƙarshe ya lalla6a tare da hayewa saman gadon shi,hannu ya miƙa tare da janyo pillow ya rungumo shi asaman faffaɗan kirjinshi,a hankali ya rufe idanunshi da niyyar yin bacci nan take brain dinshi,ta shiga tariyo mashi abunda ya faru tsakanin shi da sehrish,ranar da ya taka 6awon ayaba,ta tarboshi suka faɗa saman gadon shi atare,' Mamaki ne ya kama sgr,ya shiga tambayar kanshi Why yake tunaninta?me yasa yake tuna abubuwan da suka faru atsakaninshi da yarinyar?me yasa take ta faɗo mashi aranshi? juyi yayi asaman katafaren gadon nashi ya canza position din kwanciyar tashi,ya jima a wannan yanayin kafin ya samu bacci yayi awon gaba dashi, A tsakar dare junaid ya farka daga bacci,dama tun kafin ya kwanta baccin yake ta addu'ar Allah yasa ya farka tsakar dare yayi sallah,sae gashi kuma cikin sa'a ya farka,dama sama rai ne abun,saukowa yayi daga saman gadon ya wuce cikin toilet,jim kaɗan ya fito daga cikin toilet din,ruwan alwala na ɗiɗɗigowa daga fuskarshi,darduma ya dauko tare da shimfiɗata,ya kabbara salla tare da wannan kyakkyawanr niyyar tashi,anatse ya shiga jera sallolin batare da gajiyawa ba,tun yanayi cikin daɗin rae,har ƙafafunshi suka soma rurruƙewa sannan ya sallame sallar tare da lankwashe kafafunshi asaman sallar ya ɗaga hannayenshi yana addu'o'i yayin da hawaye ke 6ul6ulowa daga cikin idanunshi,gwanin ban tausayi, Bayan ya kammala addu'o'in nashi ya tattara dardumar ya ninketa,bayan ya ajiyeta,yana ƙokarin komawa saman gadon ya kwanta,wani abu ya faɗo daga cikin hancinshi,cikin sauri junaid yakai idanunshi a kasan inda abun ya fadi, Dunƙulen jini ya gani,nan take hankalinshi yayi mugun tashi,jikin shi ya shiga kerma,gaba ɗaya yabi ya rikice ya razana sosai,ganin yarda dunkulen jinin ke faɗowa daga hancinshi,da gudun gaske ya faɗa cikin toilet,agaban basin ya tsaya tare da dukar da kanshi,dunkulen jinin ya cigaba da fadowa,tashin hankalin da ba'a sama shi date,haƙika junaid yana cikin mawuyacin hali,gashi yaƙi sanarma kowa bare atari abun da wuri,kuma da alama koma meye ya gama yi mashi Illah, Daƙyar ya samu dunkulen jinin ya daina 6ul6ulowa daga hancinshi,ya wanke fuskarshi tare da kora jinin da ruwa ya wuce,. Sannan ya fito daga cikin toilet din hannunshi ruƙe da tissue din daya yago,zukunnawa yayi tare da kwashe dunkulen jinin daya fara fitowa daga hancinsa ya faɗi kasan tiles din dakin,acikin tissue din ya dauke shi sannan ya jefa acikin room dustbin dinsu, jikin shi yayi mugun sanyin da bai ta6a yi mashi ba,Wanda hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa da wuya ya rayu,in ba wani ikon na ubangiji ba, jiki asanyaye ya taka izuwa wurin bedside drawer,ya ɗauki wayarshi dake ajiye anan sama,lalubo numbar mommynsu yayi tare da danna mata kira, Ringing ta shiga yi,kusan sau uku ba'a ɗaga ba,ana hudunne ta ɗaga kiran tare da cewa"Hello,babyn Abbanshi,yau kaine da kanka ka kirani awaya?ae nayi tunanin ka manta dani" maimakon yayi mata magana,sae ji tayi ya fashe mata da kuka, A gigice Alexandra ta shiga ambaton sunan shi tana cewa"Ju..ju..junaid..meya faru ne!me yasa kake kuka?waya ta6a min kaine!? Cikin shessheƙar kuka ya soma magana"Mommy ba zaki zo ba ko"! Yanayin yarda taji muryarshi yasa jikinta yin sanyi, Cigaba da magana yayi"dama nasani baki sona mommy,da ace kina sona ba zaki kai wannan lokacin baki zo kin duba halin da nake ciki ba,Mommy so kike sae ranar dana mutu sannan zaki zo ki ga gawata!" gabanta ne taji yayi wani irin bugu,maganar shi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,muryarta na rawa tace"pls Romeo na,kadaina wannan maganar banason ji,dan Allah kadaina......'yana jin shessheƙar kukan mommyn nasu, cikin sanyin murya yace"Shikenan zan daina mommy,amma inaso na sanyaki acikin idanuna,inaso na ganki a matsayin mahaifiyata,don Allah kizo mommy kafin na mutu ....idan baki zo ba bazan yafe maki ba.....' Wannan maganar ta junaid ba ƙaramin firgita momyntasu yayi ba, Hankali tashe ta shiga cewa"its okey,zanzo zanzo kayi shiru kaji zanzo insha Allah,' "When"?yayi maganar ayayin da yake share hawayen fuskarshi da hannunshi guda,yayin da dayan ke maƙale da wayarshi, "Ko da yaushe kakeso junaid zanzo," Jinjina kanshi yayi tare da cewa"gobe mommy,idan ya wuce gobe ba zaki ganni ba," cikin sauri tace"zanzo kaji My baby boy,ina sonka sosai," Lumshe idanunshi yayi har cikin ranshi yaji wani irin sanyi ya ratsa shi,yanzu baida wani burin daya wuce ya sanya mahaifiyar shi acikin idanunshi,bai ta6a ganinta ba ido da ido,tsoranshi karya mutu bai sanyata acikin idanunshi ba, "Naji kayi shiru baka ce komai ba" Muryarshi a kasalance yace"Bacci nake ji mommy zanje na kwanta,dare yayi sosai,yanzu ma farkawa nayi daga bacci,shine na kiraki a waya," murmushi tayi tamkar tana a gabanshi tace"kafin ka aje wayar zan tambayeka wani abu," Junaid yace"ina sauraronki mommy," Cigaba da magana tayi "ranar daka fara gani na,ido cikin ido faɗamun wane kalar farin ciki za kayi,kuma wata irin tarba zakayi mun," Sae lokacin junaid ya ɗanyi murmushi tare da cewa"Bazan iya bayyana farin cikin da zanyi ba,a wannan lokacin,abu daya kawai nasan zanyi shine zan rungumeki sosai na kankameki na kwantar da kaina asaman ƙirjinki sannan na kira ki da sunan Mommyna," dariya sosai Alexandra tayi ba ƙaramin daɗin maganar shi taji ba, tsagaitawa tayi da yin dariyar da takeyi sannan tace"Ni kuma kasan me zanyi a wannan lokacin"?. "A'a sai kin faɗamun,"ashagwa6e yayi maganar, Alexandara tace"ni kuma a wannan lokacin da zan fara sanyaka acikin idanuna a matsayin yaron dana bari tun yana ɗan jinjirinsa na tafi nabarshi ban ƙarasa shayar dashi ba,zanji kunyar ka sosai junaid kuma zan zubar da hawayena a wannan lokacin,sannan in janyo ka ajikina nayi hugging naka very tight,zan shafa sumar kanka da hannuna.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda wani sabon kukan da taji yazo mata, cikin shassheƙar kukan taci gaba da cewa"Junaid ka yafe mun,na cutar dakai sosai,ban kyauta maka ba,nayi maka alƙawarin cewa muddin nazo nigeria zanyi maka duk wani abu da banyi maka ba,a lokacin da kake yaro,shayar dakai ne kawai bazan yi ba,shima ɗin don saboda ka wuce matakin da zan shayar dakaine,amma har goya ka sai nayi,komai zan maka junaid,koda yaushe zan kasance tare dakai,zan baka farin cikin da ban baka ba a lokacin da kake yaro... ' natsuwa junaid yayi yana sauraron kalaman mommyntasu,hankalinshi ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta faranta mashi rae sosai a daren ranar,sun jima suna waya,kafin daga bisani sukayi sallama ya ajiye wayar saman drawer din,sannan ya koma saman gadon ya kwanta,tare da aza kanshi asaman bayan Abban nasu dake ta sharar bacci, Allah sarki junaid,bazan ta6a mantawa da wannan lokacin ba arayuwata,na zubar da hawaye na sosae akan rashin shi da nayi............" A 6angaren su hosana kuwa,saboda sun kwallafa rai akan ganin sehrish daren ranar ko bacci ba suyi ba,a zaune suka kwana,su biyu tsakiyar gadon sun manne da Juna, "Jahad me kike tunani"?hosana ce ta tambayata tana kallon fuskarta ganin tana ta faman sakin murmushi, Jahad tace"Ina tunanin ko ya Sehrish ta koma yanzu?ta ƙara haske ne?ko ta ƙara kiba?Ya zata ji idan ta ganmu.!      *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari, "Nima jahad,inaso naga ya rishi ɗinmu ta koma,a qagare nake da naje naganta,Allah yasa gobe ya Omar yazo ya ɗauke mu da wuri  ya kaimu gidansu,"cike da farin ciki tayi maganar, "Da zarar mun ga rishi shikenan bamu da sauran damuwa,abu ɗaya ya rage mana shi ne ganin Mahaifiyarmu, Inason sake ganinta bansan a wane hali take ciki ba,"jiki asanyaye Jahad ta ƙarasa maganar,   haka suka zauna tsawon daren nan suna jiran safiya tayi. Wuraren sallar asuba,gaba daya matasan gidan suka hallara domin zuwa gabatar da sallah,daga ciki hada Uncle ɗinsu Abusufyan,a jere suka jera tare dashi,yadda kasan tsaran su Sgr haka ya koma acikin su, A 6angaren sehrish kuwa,raɗaɗin ciwon nan ne ya kuma tashinta daga dogon baccin daya ɗauke ta,wata irin zufa ce ta shiga gangaro mata a gefen fuskarta,jikinta na ta faman kerma,daƙyar ta iya yunƙurawa ta miƙe daga zaune tana faman ƙanƙame jikinta tana dan bin dakin da kallo,sam bata lura da jacket ɗin da Rafayet ya zura mata ba, Jin alamun ana kwankwasa ƙopar dakin yasa ta yin saurin cewa"wanene," Muryar azmee taji daga waje tana cewa"Ni ce sehrish," Bayan ta bata amsa ta turo ƙopar ta shigo,saboda a buɗe tabar mata ita daren jiya,   "Kin tashi kenan,"ta ambaci hakan yayin da take ƙarasawa daga gefen gadon nata ta zauna tana kallon fuskarta,    Muryarta na kerma tace"Aunty azmee bana jin daɗi,tun jiya nake fama da ciwon ciki sosai,bansan me yasa junaid baizo ya ɗaukeni daga school ba,ina fata dai lafiyarshi qalou ko"?tayi tambayar fuskarta ɗauke da damuwa,   Cike da mamaki Azmee tace"kamarya junaid baije ya ɗauke ki daga school ba!?nifa da kaina na ruƙe hannunki lokacin da kika dawo daga school na kawoki har cikin bedroom ɗinki sannan na shirya maki lunch ɗinki,"   Tunda azmee tasoma kora mata jawabin nan,gaba daya duk tabi ta rikice saboda bata gane inda ta dosa ba,   "Aunty azmee wlh bani bace,nifa bani da lafiya,ina can kwance cikin toilet ɗin makarantar mu,bana acikin hayyacina,har aka tashi daga skul bansani ba,sae bayan da kowa ya watse sannan naji sauƙin cikin nawa,shine har na samu na fito,lokacin da nazo bakin gate ɗin babu kowa acikin makarantar,mai gadi ne ma yace na koma daga waje na jira mai zuwa ɗaukar tawa..............'gaba ɗaya sehrish ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar ma Azmee har zuwa inda taji an ɗauketa an turata cikin mota,tun daga nan ne bata ƙara sanin meya faru ba, Hankalin Azmee fa ya tashi,abun ya ɗaure mata kai,musamman da taga Uniform ajikin sehrish wannan ya ƙara tabbatar mata da cewa daga school ɗin take,tunani ta shiga yi,shin wacece kuma Yarinyar da junaid ya ɗauko daga makaranta a maimakon ita sehrish din!kodae Aljana ce ya ɗauko!tabbas zai iya yiyuwa aljannar ce in ba haka ba,kamanninsu yayi yawa komai na fuskarsu iri ɗaya,   jin sehrish na sakin nishi yasa azmee dawowa daga duniyar tunanin data tafi,cikin sauri ta ruƙo hannunta tare da cewa"Tashi mu shiga toilet na taimaka maki kiyi wanka da ruwan zafi,kafin mu fito nasan cewa sun dawo daga masallacin,zanyi ma wani daga cikinsu magana yayi ma babban yayansu magana akan ya baki maganin da zaki sha ki samu sauki,   a hankali tasamu ta sauko daga saman gadon tabi azmee suka shige cikin toilet din,daga baya azmee ta fito ta barta acikin toilet din tana ƙarasa wankan,    Zagaye ɗakin nata Azmee ta shiga yi,yayin da take cigaba da tunanin Wacece wannan yarinyar da tazo gidan ɗazu mai irin fuskar sehrish komai da komai,tabbas mutunce ba aljana ba,abun yayi confusing dinta,    amma me yasa ta tambayeni ya Omar na nan amaimakon Sgr!    Azmee ce ta jefa ma kanta wannan tambayar,lokaci guda ta tuna da twins ɗin da Omar yace zai kawo gidan Abusufyan ɗinsu,tabbas ba shakka yarinyar tasan Marshal Omar shiyasa har ta tambayeta shi,   cike da mamaki azmee ta ɗan tsaya daga zagayen da take yi na wani lokaci ta ɗanyi shiru tana nazarin wani abu kafin daga bisani tace"in har dagaske ne abunda nake hasashe,wannan yaran da Omar yake Ruƙo a wurinshi,ƴan uwan sehrish ne!dama ta ta6a sanar dani cewa su ƴan ukune,kuma kamanninsu ɗaya sak!ina tunanin cewa Yaran suma a makarantarsu sehrish suke,wannan dalilin ne yasa junaid yayi kuskuren ɗauko yarinyar amaimakon sehrish !" Bata da tabbacin abunda take hasashe ko gaskiya ne,amma ranta na bata cewa tabbas haka ne!    fitowar sehrish daga cikin toilet,yasa azmee juyawa tana kallonta,daƙyar take iya ɗaga kafarta,jikinta na sanye da inners farare,half vest da kuma white short wanda bai kai guiwarta ba,   Ganin yadda take tafiya tana dafe saitin mararta yasa azmee,ƙarasawa wurinta da sauri ta janyo ta ajikinta,ta taimaka mata harta haye saman gadon,abu kamar wasa sehrish ta soma yarfa hannu tana ambaton sunan Allah abakinta,daga bisani kuma tashiga bubbuga ƙafafunta asaman gadon tana matse cikin nata,   Cikin fita hayyaci take cewa"Aunty zan mutu!cikina zafi yake mun,kamar ana ƙona ƴan hanjin cikina,ko'ina raɗaɗi yakeyi mun,"   Jin wannan maganar ta sehrish ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba, juyawa tayi da sauri ta fuce daga cikin ɗakin,kai tsaye ta nufi main palour din tana jiran ƙarasowar su,saboda taji dirar motocinsu alamar sun shigo cikin gidan,     Marshal Omar ne tare da Sgr suka fara shigowa cikin babban falon,yayin da Uncle abusufyan ke abayansu shi da Abbansu sae Junaid dake ruƙe da hannun Uncle din nasu acikin nashi,   ganin azmee atsaye cikin damuwa yasa Omar cewa"meya faru ne naganki atsaye nan? tsayawa da tafiyar suka yi gaba daya suna jiran jin amsarta,    hankali amatuƙar tashe azmee tace"Sehrish ce bata jin daɗi sosai,tana acan ɗaki na barota tana ta kuka tana cewa zata mutu..dan Allah a taimaka mata,"     Omar yace"subhanallahi!meya ke damunta ne?   "Ciwon ciki ne,"ta bashi amsa,matsowa Abbansu yayi kusa dasu Omar yace"Tasha magani ne"?   "Bata sha komai ba,"azmee ta amsa mashi,   Mayar da idanunshi yayi kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,    Yace"Ko zaka iya taimakawa ka duba mana ita ne?in yaso ko allura ce sae ayi mata,zata fi samun relief ɗin ciwon nata,"   sakin hannayenshi yayi daga saman chest dinshi,sannan ya kalli azmee tare da cewa"muje ɗakin nata,"   murmushi Abbansu ya ɗan saki ba ƙaramin daɗi yaji ba,daya amince zai duba ta,shi fa yanzu abbansu kallon mata da miji yake yi masu,tun ranar daya fara kamasu manne da juna,tun daga ranar ya daina yi masu kallon wai saurayi da budurwa,fatihar ce kawai ba'a kaiga shafawa ba,   "Yaya hussein wai wacece bata da lafiya ne"?Abusufyan ne yayi mashi tambayar a lokacin da suke wucewa daga cikin,   Fuskar abba ɗauke da murmushi yace"Yarinyar dake taya azmee aiki ce,itace ɗazu junaid yake magana akan ba'a ganta ba,hankalinmu duk ya tashi da 6atanta,cikin ikon Allah sae gata an samu rafayet ya dawo da ita cikin gidan nan," Abusufyan yace"Allah ya bata lafiya," Abba ya amsa mashi da ameen,   Daganan suka raba hanya dashi,kowa ya wuce bedroom ɗinshi, Acan kuwa,bayan Azmee tayi ma sgr jagora har izuwa ɗakin sehrish,ita tafara shiga sannan ya bi bayanta har izuwa wurin gadonta,karo na farko kenan da Sgr yafara shiga ɗakin Sehrish,lokacin ne yama san inda dakin yake,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,sae faman juyi takeyi atsakiyar gadon gaba ɗaya tagama fita hayyacinta saboda raɗaɗin ciwon cikinta,   Hannu azmee tasa tare da janyo bargo ta lullu6e mata jikinta,ganin yarda surar jikinta ta fito sosai,    "Wane kalar ciwon ciki ne takeyi"?yayi maganar ba tare daya kalli azmee ba,yana da tabbacin cewa menstruation ne,amma yafiso yaji daga bakinta,   "Na al'ada ne,"azmee ta bashi amsa,   "Okey,"ya ambaci hakan tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,   Komawa azmee tayi tare da zama daga gefen sehrish tana kallonta gwanin ban tausayi,Ba ƙaramar wahala tasha ba,ta jigata sosai,ta wani 6angaren kuma taji daɗi da Sgr ne zai dubata,don tasan cewa zata samu kyakkyawar kulawa awurinshi,zaiyi mata abunda ya dace ne,"   15mins da fitar shi,sae gashi ya dawo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da Allura har ya ɗura ruwan allurar acikin sirinjin,    Ganin shi yasa azmee mikewa daga zaunen da take gefen gadon ta bashi wuri don ya samu damar yi mata allurar,   Zama yayi daga gefen gadon tare da ruƙo hannun sehrish da ta fito dashi daga cikin bargon da azmee ta rufa mata ajikinta sae faman hargowa take tana ambaton cikinta,    Yana ƙokarin tsira mata allurar,ta ware idanunta sosai kai tsaye suka sauka akan Syringe ɗin dake hannunshi,duk da bata acikin hayyacinta amma ta gane cewa Allura ce fa za'ayi mata,   a firgice sehrish ta fusge hannunta tare da yin wurgi da bargon da azmee ta yafa mata,gefe guda ta jefar dashi,matse kanta tayi ajikin headboard na gadon tana faman shesshekar kuka tana cewa"banaso!dan Allah ku kyaleni kada kuyi mun allura,"gaba daya duk tabi ta firgice dama ta tsani allura arayuwarta mugun tsoranta take ji,     sanin cewa Sgr yana da bad temper bazai iya jure koke-koken da sehrish keyi mashi ba,muddin taƙi tsayawa zai iya kwashe ta da mari,don ta dawo dai dai,   Cikin sauri azmee tace"Zan iya ruƙe maka ita?   "E" ya bata amsa ataƙaice, Wucewa saman gadon azmee tayi tare da rurruke sehrish,aikuwa a gigice sehrish ta shiga kokawar kwace kwanta hada gartsa mata cizo a hannunta,     Cire hannunta tayi daga ruƙon da tayi ma sehrish,saboda taji zafin cizon da tayi mata,   Ganin haka yasa sgr bata Umarnin ta fita daga ɗakin,    Saukowa azmee tayi daga saman gadon,tare da kama hanya ta fuce daga cikin dakin,   A waje ta samu junaid atsaye sae faman zagaye yake yi a wurin ɗakunan nasu,bawan Allah duk ya rasa natsuwarshi tunda yaji cewar Sehrish bata da lafiya,   "Junaid," jin an ambaci sunanshi yasa shi yin firgit ya juya yana kallon azmee dake tsaye a kopar dakin,   Ƙarasawa yayi wurinta fuskarshi ɗauke da damuwa yace"Aunty azmee wai meya faru da sehrish ne?ina taje ne?duk nabi na ruɗe wlh,bansan ta yadda akai ta sanya ƙafa tabar gidan nan ba,nifa dakaina na ɗaukota daga school na kawota gida,"   ruƙo hannunshi azmee tayi taja shi daga dan gefe suna fuskantar juna tace"Junaid ka kwantar da hankalinka,ba abunda ya faru da sehrish,stomach pain ne kawai kuma insha Allah zata ji sauƙi ne,sannan maganar fitar sehrish daga cikin gidan nan,kada kayi confusing kanka,ka manta da wannan kawai,komai ya wuce,"   ajiyar zuciya ya shiga saukewa,har cikin ranshi yaji daɗin bayanin da azmee tayi mashi,   "Yanzu kaje ka kwanta mana,zuwa da safe in yaso sae kazo ka dubata ko"?   cike da shagwa6a yace"Aunty azmee kona koma ɗaki bazan iya bacci ba,in har ban sanyata acikin idanuna ba,'   Murmushi azmee tayi tace"ummm romeo kenan shugaban ƴan soyayya,dama tunda na ganka nan tsaye nasan cewa abunne ya motsa,"   Sunnar da kai ƙasa junaid yayi yana faman sakin murmushi,     A nan suka tsaya suna cigaba da yin fira atsakaninsu,janye mashi hankali azmee ta dinga yi saboda ta lura da yadda yake firgita duk in yaji sautin kukan sehrish,daƙyar tasamu junaid ya wuce bedroom dinshi itama ta wuce nata ɗakin,   suna barin wurin hayaam ta fito daga ɗakinta,cikin sanɗa take tafiya harta ƙaraso wurin kopar ɗakin sehrish,anan ta tsaya tare da jingina kanta ajikin ƙopar ta kasa kunnanta tana sauraran kukan da sehrish keyi,duk atunaninta ita kaɗaice acikin ɗakin take kuka,hakan yasa taji daɗi acikin ranta har tana cewa"Shegiyar Allah yasa ta mutu kowa ya huta,wlh bazan shiga in taimaketa ba,koda ciwon zai kashe ta, acan cikin ɗakin kuwa duk yadda sgr yaso sehrish ta tsaya yayi mata allurar abun ya faskara,taƙi bashi haɗin kai,sae faman yawo take mashi da hankali,wannan ne yasa shi fusata har ya daka mata tsawa,wannan tsawar da sgr ya daka ma sehrish yasa ta dawo cikin hayyacinta sosai,waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe take kallon sgr,abun kamar a mafarki take kallonshi,wai dama shine!taya akai ya shigo ɗakinta? a tsananin tsorace take binshi da kallo,jallabiya ce fara ajikinshi mai gajeran hannu,hakan ya bayyana damtsen hannun nan nashi,    zazzare ido tashiga yi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,   Matsawa sgr yayi kusa da ita,suna facing din juna face to face,a hankali yake bin fuskarta da kallo yayin da itama take ƙare ma tashi kallo,har lokacin kokwanto takeyi anya shine da kanshi ya shigo ɗakinta,Sgr sukutum da guda yau a bedroom ɗinta zaune gefen gadonta,a kusa da ita?   Hmmmmm ina labarin Hayaam dake la6e ajikin ƙopar ɗakin tana sauraron kukan Sehrish,ae tun lokacin da taji muryar sgr ya daka ma sehrish tsawa,jinjina kai ta shiga yi tana faman sakin huci kamar wata zakanya saboda tsabar 6acin rai da takaici,acikin ranta tashiga cewa"lallaima yarinyar nan,wato harta samu matsayin da sgr zai dinga takawa da ƙafafunshi yana shiga ɗakinta,'   ɗagowa tayi tare da aza hannunta asaman kanta tana cewa"nashiga uku ni yau hayaam bansan ya zanyi da yarinyar can ba,tana shigar min gonata!tabbas dole nayi wani abu akanta,bazan ƙyaleta ba tayi nasara akaina ba,   Tana cikin wannan zancen zucin nata ta jiyo muryar sgr yana magana daga cikin ɗakin,cikin sauri ta kasa kunne tana sauraron me yake ce ma sehrish ɗin,    "Bana son wannan koke koken da kikeyi mun,kamar zan rabaki da ranki ne,"!.    tsit Sehrish tayi tana sauraranshi,yayin da take bin pink lips ɗinshi da kallo,   Cigaba da magana yayi anatse yace"idan kika natsu,ba da zafi zan maki ba,a hankali zanyi maki,batare da kowa ya ji mu ba,"    tashin hankali tunda hayaam taji wannan zancen da Sgr yakeyi ma sehrish nan take taji gabanta ya faɗi rass,zullumi ta shiga yi gabanta na faduwa,duk atunaninta wani mummunan abunne sgr da sehrish ke aikatawa,gaba daya ta rasa natsuwarta,kamar ta fada cikin ɗakin  taga me suke aikatawa haka take ji aranta,zuciyarta sae faman azalzalarta takeyi tana tunzurata akan ta shiga taga me sukeyi,   Yanayin yarda sgr keyi mata magana cikin sanyin murya,yasa taji wani irin yanayi atare da ita,da kanta ta miƙa mashi hannunta don yayi mata allurar,   Hannunshi yasa tare da ruƙo wrist din hannunta,sannu a hankali ya zura allurar a cikin jijiyar hannun nata,lokacin da tsinin allurar ya ratsa cikin jijiyar,a ɗan razane sehrish ta saki ƴar ƙara tare da runtse idanunta tana faman cizon la66anta,   a hankali sgr ya ɗago da blue eyes ɗinshi yana kallon fuskar sehrish,zuba mata ido yayi yana kallon eye lashes ɗin idanunta masu tsayin gaske,kafin ya mayar da idanun nashi akan la66anta dake ta faman kerma,tana ɗan cizon gefensu da Teeth ɗinta,   gaba daya ya gaza control ɗin kanshi,har ya gaza janye idanunshi daga kallon la66anta da yake yi,ba ƙaramin yanayi ta jefa shi ba,cos she looks so sexy a wannan lokacin komai tayi bashi sha'awa yake yi,   siraran hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin idanunta,batare da saninshi ba yakai hannu zai share mata hawayen,buɗe idanuwan da tayi ne yasa shi dakatawa tare da janye hannunshi, ya kawar da kanshi gefe guda a lokacin ya kammala yi mata allurar,    tayi danasanin buɗe idanuwanta da tayi,taso ace ya sanya hannayen shi ya share mata hawayen,ko ba komai zata ajiye wannan ranar a matsayin ɗaya daga cikin ranakun da suka kafa tarihi a rayuwarta,    Ganin ya miƙe tsaye tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom ɗin nata yasa tayi saurin cewa"ngd da taimakon da kayi mun,"   Batare da ya juyo ya kalleta ba yace"get well soon" Yana ƙarasa maganar tashi yasa hannu ya ruƙe handle ɗin ƙopar zai buɗe door ɗin ɗakin,jin motsin shi yasa jiki na rawa hayaam ta watsa da gudu izuwa cikin bedroom ɗinta, Upstairs ya nufa ya wuce part ɗinshi a wani irin yanayi ya faɗa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke kallon saman ceiling ɗin ɗakin nashi,    Wani abu ne ya faɗo mashi aranshi,lokacin suna da shekaru goma sha wani abu a duniya,a katafaren gidansu dake a los angeles California,su shida suke rayuwa acikin gidan bayan masu aikin dake kula dasu,Uncle donald tare da matar shi wadda suke kira da Mommy,sae Ƴa'ƴansu mata guda biyu Eva da jessy,Sae shi tare da Omar,wata irin rayuwar farin ciki sukeyi acikin gidan,saboda tarairayar da suke samu a wurin matar uncle ɗinsu kamar ita ta haifesu,Allah ya jarabceta da son su,ko ƴa'ƴan data haifa batayi masu irin son da takeyi ma Sgr da Omar,A wannan lokacin Uncle Abusufyan ya ta6a yi masu zuwan bazata,sunyi murna kamar kamar me,suka manne mashi suna tambayarshi ina tsarabar da yazo masu da ita,   Hannu yasa tare da ciro wasu hotuna biyu daga cikin aljihunshi,ya aza hotunan asaman table ɗin gabanshi,ya kifa hotunan yarda bazasu iya tantance hotunan menene ba,    yana daga zaune saman 3 seater,su kuma suna atsaye ruƙe da qugu suna jiran ganin wannan tsarabar da yazo masu da ita,maimakon suga chocolate suga iyayen shan zaƙi sae suka ga Hotuna guda biyu,nan take suka ɗaure fuskokinsu,atare suka haɗa baki wurin tambayar shi menene wannan yake 6oye masu acikin hotunan   Abusufyan yace"so nake kowanne daga cikinku ya za6i ɗaya daga cikin hotunan,kuma duk abunda mutun ya za6a dole ya rungume shi hannu bibbiyu,kun amince da hakan"?   "Yeah,"suka amsa mashi,, "Waye zai fara canka acikin ku"? Shiru rafayet yayi tare da maƙe kafaɗarshi alamar bazai fara ɗauka ba,Kallon Omar Abusufyan yayi yana jiran jin shi mai zaice ko zai fara ɗauka ne,   da yake shi mai sauƙin kaine,baiyi gardama ba,ya sanya hannu tare da ɗaukar ɗaya daga cikin hotunan,juyo da hoton yayi ta gaba yana kallon shi,   Kyakkyawar yarinyace,ƴar ƙarama bazata wuce 5 years ba,tana tsaye akayi mata hoton,'   Murmushi Omar ya shiga saki yana kallon hoton,   "Saura kai Mr arrogant,pick d other one,"yayi maganar cike da zolaya yana kallon Sgr,   tsuke baki yayi tare da miƙa hannunshi ya ɗauki ɗayan hoton daya rage asaman table ɗin,ɗago dashi yayi tare da juyo da gaban hoton yana kallonshi, Koda yayi arba da hoton yarinyar daya dauka nan take ya ɗaure fuskarshi ya haɗe girar idanunshi alamar ranshi ya 6aci,     Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace uncle I don't like her, she's ugly, she doesn't have even shoes on her feet,ko gashin kanta ma bata iya gyarawa,ƙazama ce"   Fashewa da dariya Omar yayi hada dafe cikin shi,hakan ya ƙara fusata sgr,   Abusufyan kuwa,ruƙo hannunshi yayi cikin sanyin murya yace"Look rafayet,itama ba laifinta bane kuma bada son ranta ta kasance haka ba,kai kana da gata ne shiyasa kake ganin cewa ita da son ranta ta kasance hakan,Bata da wanda zai gyara mata gashin kan nata ne,babu wanda zai janyota ajikinshi yayi mata wanka ne,kuma kaga ƙarama ce bata da hankalin da zata iya gyara jikinta da kanta,dole sai an nuna mata ga yadda zatayi sannan tayi.....'   Shiru Sgr yayi yana faman hura hanci shi an haɗa shi da mahaukaciya,ɗago da hoton yayi yana ƙare mashi kallo kafin ya kuma kallon uncle ɗin nasu yace"Ita bata da Mommy ne?ina daddyn ta yake ne?ko basu raye ne"?ya jera mashi tambayoyin yana jiran amsar su,   Abusufyan yace"bata dasu, marainiya ce,amma yanzu ta samu,in har ka amince zaka aureta,kaga shi kenan zaka ruƙe ta amana,kuma zaka dinga gyara mata gashin kanta,kana sanya mata takalma,har ma wanka sai kayi mata....'tun kafin abusufyan ya ƙarasa maganar Sgr ya bubbuga ƙafafunshi rae a6ace yake cewa"Uncle I can't marry her,but since I hv a lot of money i will give her to buy whatever she wants" Murmushi Abusufyan yayi yana kallon shi,wato shi bazai aureta ba,amman tunda yana da kudi da yawa zai bata kuɗi ta sayi duk wani abu da take so,yaji daɗin jin maganarshi,koba komai yaron yana da tausayi ta wani 6angaren,dama ya jarabasu ne don yaga reaction ɗin kowannansu,kuma ya samu abunda yake so, Har kawo yanzu,wannan hoton da uncle abusufyan ya basu,yana nan a wurinsu kowannansu ya adana hoton kamar yarda uncle ɗin nasu ya roƙesu akan su ajiye hotunan a wurinsu,karsu yadda su,' "Har yau uncle abusufyan,bai faɗamun wace yarinya ce ajikin photon nan ba,inason nasan kowacece ita,saboda in taimaketa,kamar yarda nayi niyyar taimakonta," Sgr ya fadi hakan. Lumshe idanunshi yayi tare da gyara kwanciyarshi,nan take bacci ya ɗauke shi, *su wanene acikin hotunan da Uncle abusufyan ya basu*!        _Ayi mun uziri,in bansamu damar yin posting gobe ba,abubuwa sunyi mun yawa sosai,bansan ya zanyi ba,amma koda ace banyi a gobe ba zan yi ƙoƙarin biyan bashin wanda banyi ba,tunda ina ƙoƙarin ganin na Kammala littafinn ne insha Allah Zan yi kokarin sanya maku long pages,sannan kuma Labarinsu sehrish da nake tacewa za'ayi za'ayi lokacin shi yazo dama akwai abunda nake jira ne_ *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack A*💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖 *Ga duk mai buƙatar littafin abban sojoji,from book one zuwa book two har inda muka tsaya,300 ne idan yayi payment za'a tura mashi duka sannan za'a sanyashi a grp da zai cigaba da samun cigaban shi akai akai,ga mai buƙata yayi mun magana kai tsaye ta whatsapp ɗina 08103884440 pls banda phone call,ban san meyasa wasu suke kirana a waya ba,Only message nace,kuma insha Allah mutun yayi mun magana bazan share shi ba,zan bashi amsa ne akan lokaci indae ba busy nake ba,sannan masu cewa suna som Book 3,pls su daina abun yana 6ata mun raina,cos ni ban rubuta book 3 ba,wasu can sarakan iyayi ƴan shisshigi suka haɗamun document ɗinshi,to abunda nake so na sanar daku,Abban sojoji dae Iya book two zai ƙare insha Allah,babu wani book 3,🤗* *Kada ku manta muna acikin takon ƙarshe ne🔥🔥🔥* _Father Of soldiers❤story and written by Hafsat Bature Mohamed Boss Lady_ ❤🤍❤ Gagarumar Walima Abba ya shirya masu awashe garin ranar,na murnar dawowar Abusufyan Nigeria,tun da wuri aka soma shirye shiryen gudanar da ita,basu yi inviting ɗin kowa ba,anan cikin gidan kawai za'ayi ta,yasu yasu batare da wani bare ya shigo ba,don nasan halin sumayyer yanzu ta kwaso ƙafa tace zata, Gaba ɗaya ko'ina na gidan ya karaɗe da ƙamshin dadɗaɗan girkin dasu azmee ke yi acikin kitchen ita da Hayaam,tun da sanyin safiya suka fara aikin girke girken,tun bayan da  Abbansu junaid ya sanar da ita game da walimar,suka soma gunadar da aikin batare da 6ata lokaci ba, Matasan gidan kuwa wankan shadda zasu ɗauka gaba ɗayansu,kamar yarda Abbansu ya basu Umarnin su sanya shadda ajikinsu in kuma ba shadda ba kowane kalar kaya zasu iya sanyawa ajikinsu indai namu ne na hausawa,duk sun amince da hakan, "Azmee wai ita yarinyar can bazata fito ta tayamu aiki bane?tun safe muke ta faman aikace aikace ko leƙowa batayi ba,"Hayaam ce tayi maganar yayin da take ta faman kwa6a fulawa acikin roba,duk ta haɗa gumi a fuskarta,' Azmee tace"kema ae ban matsa maki ba,naga kamar kina son aikin ne shiyasa ma nayi maki magana,amma idan kin gaji ko yanzu ma zaki iya tafiya," Rae a6ace tace"yanzu me ya kawo wannan maganar Aunty azmee?nifa ina magana ne akan waccen yarinyar sehrish ya kamata ta fito ayi aikin da ita,na lura kamar bakiso inayi maki magana akanta,kin gatanta yarinyar sosai,shiyasa bata da aikin yi sai dae ta zauna tayi ta sharar bacci kamar matacciya,bata tsinana uban komai acikin gidan nan hakanan take sunan yar aiki...." juyowa azmee tayi daga tsayen da take agaban gas cooker,ta kalli hayaam dake ta faman hura hanci ga uban gumi ta haɗa,   "Hayaam!sehrish ba tada lafiya,shiyasa ban tashe ta daga bacci ba,tun jiya da daddare take fama da raɗaɗin ciwon ciki daƙyar ma aka samu tayi bacci,wannan dalilin ne yasa banyi yunƙurin tashinta daga baccin ba,"    ta6e baki hayaam tayi tare da cigaba da aikin da takeyi cikin ranta tana fadin"ta dai gama iskancinta tayi bacci, Marshal Omar Tun yana cikin toilet wayar shi ke ta faman ringing,cikin sauri ya fito daga cikin toilet ɗin,jikinshi ɗaure da towel,ƙarasawa yayi inda ya ajiye wayar asaman pillow,ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar yana duba mai kiran nashi,murmushi yayi aranshi yace"Allah yasa jiya sun samu bacci,don na lura da yadda suke ta faman ɗokin son ganin ƴar uwar nan tasu,nima kaina a ƙagare nake dana haɗasu wuri guda,don su cigaba da rayuwa atare,   Picking call ɗin yayi ya kara wayar a kunnanshi,   Tun kafin yayi sallama muryar hosana ta katse mashi hanzarinshi da cewa"Ya omar!yaushe zaka zo ne!kai muke ta jira,jiya fa ko bacci ba muyi ba,   Tana kai ƙarshen maganarta Jahad ta kar6e da cewa"ya Omar dan Allah ka tausaya mana,wlh ko breakfast ba muyi ba,kuma muna jin yunwa amma mun fi so muci abinci atare da ƴar uwarmu," Jin wannan maganar ta Jahad,yasa jikin shi yin sanyi,da alama ba ƙaramin so suke yi ma junansu ba,   "Ya omar kayi shiru,"muryar hosana ce tayi maganar a ƙagare,   cikin natsuwa ya soma magana"kuyi haƙuri kunji,insha Allah yau zaku ga ƴar uwarku,bazan samu zuwa ba,amma zan turo major ya ɗauko ku,abunda nake so daku yanzu,ku ci abinci ku ƙoshi,sannan kuyi wanka ku shirya ku sanya kaya masu kyau,a kowane lokaci zaku iya ganinshi yazo,"   Yana jiyo muryoyinsu ta cikin wayar suna ta faman fadin Wayyo daɗi yau zasu ga rishi ɗinsu,'   Sallama yayi masu bayan ya ajiye wayar,ya juya tare da wuce wa wurin closet ɗinshi,tsaf ya shiga shirya kanshi acikin rantsattsiyar shaddar shi. SEHRISH, Kwankwasa ƙopar ɗakin da akayi mata ne da ƙarfi,yasa ta tashi a firgice tana faman zazzare ido,ƙankame bargon jikinta tayi tana ƙara lullu6e jikinta dashi,fuskarta duk a yamutse saboda kukan da tasha jiya,amma yanzu Alhamdulillah tun da tafarka babu wannan ciwon cikin atare da ita,tamkar bata ta6a yin ciwo ba haka ta farka,taji sauƙi sosai,    "Reesh,baby junaid ne fa,in shigo daga ciki"? Muryar junaid ce taji yana magana daga waje,   akasalance tace"eh,ka shigo," . tura ƙopar yayi tare da sanya kafa ya shigo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da cup sae tiriri ke fitowa daga ciki,bakomai bane aciki face Corn flakes daya haɗo mata,yaji Uwar madara acikinshi,    Sae faman murmushi yake sakar mata,wuri ya samu daga gefen gadonta ya zauna,sannan yace"reesh ya jikin naki?jiya ko bacci banyi ba saboda damuwa da halin da kike ciki,'   "da sauƙi junaid,yanzu bana jin ciwo atare dani,na wartsake sosai,amma ina fata kaima kana cikin ƙoshin lafiya ko?naga fuskarka kamar ta canza kamanni,kayi haske sosai kuma fuskar ta ɗan sauya haka,Lips ɗinka sun ɗan kumbura kaɗan kalarsu ta ƙara cizawa sosai'tayi maganar yayin da take ƙare ma fuskar tashi kallo kamar wata malamar duba   Junaid yace"farin cikin da kika bani jiya shine ya canza mun kamannin fuskata,ko kin manta abunda mu kayi jiya acikin Mota tare da ke?fuskarshi ɗauke da murmushi yayi maganar,   Cike da mamaki sehrish tace"wane abu kenan?yaushe muka haɗu acikin mota?bayan bakazo ka ɗauke ni daga school ba,ni da ka manta dani junaid,nasha wahala jiya sosai,kamar bazan rayuwa ba,na neme ka na rasa.......'muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,   "Sehrish!me kike nufi da banzo na ɗauke ki ba?ko raɗaɗin ciwo yasa kin manta da abunda ya faru jiya atsakaninmu"?   girgiza kai tayi alamar a'a tace"Nifa bakazo ka ɗauke ni ba,jiya da aka tashi daga school ciwon ciki ya kamani,shine na shiga toilet anan na yanke jiki na faɗi saboda azabar ciwon da nasha,gaba daya nafita hayyaci na.......'gaba ɗaya sehrish ta bashi labarin abunda ya faru da ita tun daga A har zuwa Z,abu ɗaya ne bata sanar dashi ba,shine zuwan waɗan nan matasan guda huɗu da suka ɗauketa a mota, Tun da ta soma kora mashi bayani,hankalinshi yayi mugun tashi,jikin shi har kerma yakeyi wurin cewa"reesh dagaske ne duk abunda kika faɗamun"!.   ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan tace"ka faɗamun me ya hana ka zuwa ka ɗauke ni junaid?nayi tunanin zaka dawo ka ɗauke ni,in kaji shiru ban dawo gida ba,amma bakazo ba,'   Gaba daya ta gama rikitar dashi duk yabi ya ruɗe,muryarshi har rawa takeyi wurin cewa"wlh nazo jiya school ɗinku,kuma naɗauke ki dakaina acikin motata.......'gaba daya junaid ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin shi da jahad ya sanar ma Sehrish,   Zuba mashi ido tayi tana kallonshi ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba da jin labarin da junaid ya bata,   "Junaid!ban karyata ka ba!amma anya ba gamo kayi ba?zai iya yiyuwa fa aljana ce in ba haka ba,taya za'a ce tana kama dani komai da komai har ka gaza gane cewa ni ce ko bani bace,"?a ruɗe tayi maganar tana kallon junaid, Junaid sarkin tsoro tuni idanunshi sun cicciko da kwalla tsoranshi kar ace lokacin mutuwar tashi ne yayi shiyasa ya fara ƴan gane gane,zai iya yiyuwa ma mutuwarce tafara kawo mashi ziyara kafin tayi wuff dashi,   tuna wannan yasa shi fashe mata da kuka yana cewa"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shikenan lokacina yayi sehrish,dama nasan daƙyar zan wuce yau araye,....'   Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yarda junaid ya fashe mata da kuka,da alama ya tsorata sosai'   "Junaid ya isa haka,ka daina kuka kaji,insha Allah ba yanzu zaka mutu ba,har sai mun yi aure mun haifi ƴa'ƴa,in ma zamu mutu atare mutuwar zatazo ta ɗauke mu,'   Jin wannan zancen na sehrish yasa shi yin tsit yana faman sauke ajiyar zuciya,ga dariya na cinta amma tana tsoran karya kuma fashe mata da wani kukan,aranta tace"Tabɗijancan su junaid ansha soyayya da al'jana,da sauƙi ma tunda iya kiss suka tsaya," Miƙa mata cup ɗin hannunshi yayi tare da cewa"gashi kisha,corn flakes ne ni na haɗa maki da kai na,"wani irin tausayinshi ne taji ya kamata,musamman yarda ya nuna damuwarshi akanta,har ya haɗo mata cornflakes dakanshi don tasha,'   zuba mashi ido tayi tana kallonshi,fuskarshi duk a yamutse babu alamun natsuwa atattare dashi,duk ya firgice da jin cewa ba ita bace ya ɗauko a school ba,kuma hankalinshi bazai ta6a kwanciya ba har sae ya tabbatar da cewa ba aljanu bane suka fara kawo mashi ziyara,   Cikin sanyin murya tace"Junaid,dan Allah ka share hawayenka kaji?ko ka manta da alƙawarin da ka ta6a yi mun na cewa ba zaka ƙara yin kuka ba"?   Muryarshi akasalance yace"nadaina,kiyi haƙuri bazan ƙara ba," yayi maganar yayin da yake miƙe mata cup din,   "Ba zaka ban abaki nasha ba"? ɗagowa yayi yana kallonta jin abunda tace,tayi mashi hakan ne don ta kawar da damuwar dake a fuskarshi, Matsawa yayi kusa da ita sosai,sannan ya zura hannunshi tare da dauko cokalin ciki,ya ɗebo cornflakes ɗin ya miƙa mata abakinta,   Buɗe bakinta tayi ya zuba mata aciki,a hankali take murzar shi abakinta tana haɗiyar shi,yayi mata daɗi sosai saboda madarar daya zuba aciki, Haka yaci gaba da bata abakinta tana sha,tun fuskarshi na aɗaure harya fara sakin wannan murmushin nashi,ganin ya washe daga damuwar da yake ciki yasa sehrish cewa"junaid,Wai jiya Uncle ɗin nan naku ya ƙaraso ne"?   "Eh,yanzu haka yana acikin gidan nan ma,ya kamata kije ki gaishe su,hada aunty azeema kanwar Abbanmu itama tazo jiya,"   wani irin farin ciki ne ya lullu6eta cike da zumuɗi tace"inaso naje na gaishe shi,amma ina jin fargabar zuwa wurin shi,"   Junaid yace"meyasa toh?na gaya maki cewa basu da matsala,uncle dinmu mutun ne mai sauƙin kai fiye da tunaninki,haka Aunty azeemarmu ma tana da mutunci sosai,baki ga gift ɗin da takawo mun ba,zan nuna maki anjima,zaki sha mamaki,"   murmushi sehrish tayi a lokacin harya kammala bata corn flakes ɗin, "Bari nashiga toilet nayi wanka,idan na kammala shiryawa sai mu tafi tare da kai ka rakani wurinshi in gaishe dashi,' Amsa mata yayi da toh,sannan ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin daya ajiye asaman side drawer dinta,ya fuce dashi, Ajiyar zuciya ta sauke,bayan fitar shi ta sauko daga saman gadon tare da nufar dressing mirrow dinta ta tsaya tana kallon kanta ta cikin madubin,hannu tasa ta shafo sumar kanta da sgr ya datse mata shi,nan take ta tuna da abunda ya faru jiya lokacin daya shigo yi mata allura,wannan kallon da yayi mata ya tsaya mata aranta,da kuma kalaman da ya furta mata cikin sanyin murya,tabbas tana ji aranta cewa sgr ya fara jin abunda take ji agame dashi,duk da tasan cewa zaiyi wuya ya gane cewa akwai soyayya atattare dashi,kuma zaiyi wuya ya iya furta mata ita, ta cikin mirror ta hango jacket din da sgr ya sanya mata,tana ajiye saman gadon,juyawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauko rigar sanyin tana kallonta,   tunani tashiga yi rigar wanene wannan?taya akai tazo bedroom ɗinta kuma asaman gadon nata!?   ƙamshin Turaren jikin jacket dinne ya bata amsar tambayar da take nema, Matse rigar tayi a hancinta,anan ta dinga jin ƙamshin turaren Sgr sosai ajikin rigar wannan ya tabbatar mata da cewa tashi ce,a hankali tashiga tunanin ta yadda akai jacket dinshi tazo bedroom ɗinta,kodai jiya ne daya zo yi mata allura.....  ' kwankwasa kopar da akayi ne ya dawo da ita daga zurfin tunanin da tashiga,   "Wanene"?ta tambaya tana kallon kopar, Turo kopar azmee tayi tare da shigowa ciki tana cewa"ni ce sehrish,ya jikin naki fatan kin tashi lafiya,tun ɗazu nake ta zarya wurin leƙowa ɗakinki inga ko kin farka daga baccin,amma duk in nazo sai in same ki,kina ta sharar bacci,'   murmushi sehrish tayi tana kallonta tace"ina kwana Aunty azmee?fatan kun tashi lafiya,ya aiki"? "Alhamdulillah sehrish,jiya mun shiga damuwar rashinki,kuma sai gashi Allah yasa an gano ki,da ba'a ganki ba,da bansan inda zan sanya raina ba,"ta ƙarasa maganar yayin da take ƙarasa shigowa daga ciki,ta tsaya a kusa da sehrish suna fuskantar juna,   "Aunty azmee wai meya faru dani jiya?ya akai nadawo cikin gidan nan?waye ya ɗauko ni?kuma naga wannan jacket din asaman gadona,kamar ta babban yaya ce," Azmee tace"ae jiya,shi da kanshi ya dawo dake acikin gidan nan,gaba ɗayanmu munyi mamakin ganinshi ɗauke da ke a kafaɗarshi,duk da banji da kyau ba,amma naji yana ba Abbansu labarin cewa acan suka same ki cikin wani garden wasu matasa suna ƙoƙarin lalata maki rayuwarki ..........'tunkan azmee ta ƙarasa maganar sehrish ta tunano da abunda ya faru jiya,sai lokacin komai ya dawo cikin kanta,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta jin cewa Sgr ne da kanshi ya taimaki rayuwarta a hannun waɗannan miyagun da suka kai mata hari,kuma taji daɗin bugun da yayi masu,don akan idanunta ya naushi ɗaya daga cikinsu,har haƙoran shi guda biyu suka 6allo daga bakinshi,tun daga sannan ne bata ƙara sanin meya faru ba,amma tabbas taji lokacin daya ɗauke ta a hannunshi ya sanyata acikin motarshi,kuma tana da tabbacin cewa shine ya sanya mata rigar sanyinshi,kilan saboda yaga jikinta na kermar sanyi,   Cike da farin ciki tace"Aunty azmee lokacin da babban yaya ya shigo dani cikin gidan nan akwai wannan rigar ajiki ne ko"?   ɗaga mata kai tayi alamar eh, Washe baki ta shiga yi kamar wadda akayi ma albishir da gidan al'janna,   Murmushi azmee tayi ganin yarda sehrish ke ta faman murnar jin cewa sgr ne ya taimake ta,   hannu tasa tare da dafa shoulders dinta tace"Ki shirya yau akwai walima acikin gidan nan,zuwa anjima wuraren ƙarfe huɗu za'a soma gudanar da ita,inaso kiyi kwalliya sosai yau,yanzun nan zan sanya junaid ya kar6o maki kayanki,wlh mantawa nakeyi,'   "Aunty azmee baki ga abunda babban yaya yayi mun ba?taya zan iya yin gayu da wannan guntun gashi dake akaina"tayi maganar tana damƙo wutsiyar gashin kan nata,   Sae lokacin azmee ta lura da kan nata,hankali atashe tace"garin yaya hakan ya faru?waye ya yanke maki gashi har haka"?   "Babban yaya mana,saboda laifin da bani na aikata ba,ya sanya almakashi ya datse mun gashin kaina,banji daɗi ba,saboda nasha wahala wurin tara shi da yawa yanzu bansan ya za'ae nadawo dashi ba,"cike da damuwa tayi maganar,abun har yanzu yana yi mata ciwo, "Wani laifi kenan kika aikata"? Sehrish tace"a cikin coffee ɗin da nakai mashi jiya da safe,yana cikin sha,gashi ya sarke mashi a makoshi,ran shi ya 6aci sosai har ya yanke mun gashin kaina,wlh aunty azmee ba gashin kaina bane,ni banta6a yin kuskuren barin kaina abuɗe ba,lokacin da nake acikin kitchen,"   shiru Azmee tayi na dan wani lokaci kafin tace"bakomai kawai,kiyi haƙuri nasan kowanene ya aikata hakan,amma banaso ki sanya damuwa aranki,"   "Shikenan,yanzu bari naje nayi wankan,"ta ambaci hakan tare da ajiye jacket ɗin asaman gadon,   "Kinason ƙunshi ne?idan kina ra'ayi zan zana maki da kaina na iya sosai,"   "Inaso sosai Aunty azmee,yaushe rabon dana ga lalle a hannu na har na manta wlh," Azmee tace"yanzu kije kiyi wankan,kafin dai zuwa ƙarfe huɗun zamu kammala komai,'   ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta fuce daga cikin ɗakin,   Wuce wa cikin toilet sehrish tayi domin yin wanka 💋Boss Bature💋 Zaune suke acikin mota su biyu,Ayaan ne ke driving ɗinsu yayin da jahan ke zaune gefen shi sae faman buga tsoki yake yi yana cewa"Ayaan wai ina zaka kaimu ne!ni fa gida nace maka mu koma,banaso afara shagalin walimar nan,bana a kusa,'   Murmushi ayaan yayi tare da cewa"kai dai kawai ka zuba ido ka gani,wani abun mamaki ne nakeso na gwada maka,nasan cewa zai girgiza ka sosai,'ya ƙarasa maganar yayin da yake shigar da motar tasu gate din gidan Yayansu Abbas, Jahan yace"wai dama nan zaka kawo mu?muyi me kenan?Anya kuwa ayaan kasha maganinka na safe kuwa?   dariya Ayaan yayi tare da cewa"a'a ban kaiga sha ba,amma yanzun idan nakai ka cikin gidan nan,na nuna maka abunda nakeso ka gani,bayan mun fito zaka faɗamun ni dakai waye mai buƙatar shan magani acikin mu,"cike da zolaya Ayaan yayi maganar, shiru jahan yayi bai ƙara cewa komai ba ya zuba ma sarautar Allah ido,   Bayan Ayaan yayi parking ɗin motar,ya fito tare da zagayawa ya buɗe ma jahan motar tare da nuna mashi hanya da hannunshi yace"mun ƙaraso yalla6ai," harara jahan ya watsa mashi tare da zura ƙafafunshi ya fito daga cikin motar,yana faman ɗaure fuska ya wuce gaba ayaan yabi bayanshi suka shiga cikin gidan,   Da sallama abakunansu suka shiga cikin babban falon gidan,a lokacin Amani na a cikin kitchen tana aikin breakfast,jin sallamarsu twins yasa ta fitowa da sauri don taga su wanene,   Ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganin ayaan da jahan atsaye ruƙe da hannun juna, Ƙarasawa wurinsu tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Sannunku da zuwa,ashe kune sam banyi tsammanin ganinku ba,"   Kawar da kai gefe jahan yayi batare da yace komai ba,.   Ayaan yace"yawwa Aunty amani,kun tashi lafiya,fatan mun same ku lafiya?   Ta amsa mashi da cewa"Lafiya lou Alhamdulillah,nayi farin cikin ganinku,ku ƙaraso daga ciki mana," Jahan yace"sauri muke zamu wuce,Ayaan ka shiga daga ciki ku gaisa ni zan jiraka a mota,'yayi maganar tare da juyawa zai fuce,   Cikin sauri Ayaan ya ruƙo hannunshi tare da cewa"haba jahan wai menene haka?just 15 mins zamuyi fa kafin mu wuce gida,'   ɗaure fuska jahan yayi alamar an takura mashi,   Amani kuwa murmushi kawai tayi,tana mamakin yarda suka kasance twins komai nasu iri daya,amma hali ba iri ɗaya ba,Ayaan ta 6angaren Abbansu yake,shi kuma jahan sak mommynsu ce,   daƙyar Ayaan ya samu jahan ya bisu suka shiga cikin falon,atare suka zauna saman 3 seater,ita kuma ta zauna saman 2 seater tana fuskantar su,yarda jahan ke ta faman yatsina fuska,ba karamin dariya yaso ya bata ba,ji yake kamar ya ɗosana ass ɗinshi asaman ƙayoyi haka yake ji, Ayaan ne ya soma magana"Aunty amani kinji mu shiru ko?ba mu sake zuwa mun duba jikin Amal ba,ban ji daɗi ba wlh abubuwa ne sunyi mana yawa,amma tana aran mu,shiyasa ma muka yanke shawarar zuwa yau mu duba ta,' taji daɗin kalaman ayaan sosai,fuskarta ɗauke da murmushi tace"Amal taji sauƙi sosai,kullum sai ta tambayeni ina twins ɗin nan suke,musamman kai Ayaan tafi tambayarka saboda kaine ka kawota wurina,yanzu bari naje na kawo maku abun ta6awa,kafin na kira maku Amal ɗin ku gaisa," Ta ƙarasa maganar tare da mikewa ta wuce cikin kitchen, Tana barin wurin jahan ya buga tsoki tare da cewa"Wlh ayaan ka bani haushi!ka zauna ka gama tsara mata ƙaryar cewa mun zo duba jikin wannan ƙarmasasshiyar yarinyar ne,yarinyar da nama manta da zancen ta ni,mtswwww,'ya kawar da kanshi gefe yana hura hanci, Ayaan yace"Am sorry bro,nasan ban kyauta ba,amma kayi hakuri kasan banason 6acin ranka,ni aganina bamu kyauta ba,tun ranar da nakawo yarinyar nan,ba mu ƙara zuwa mun dubata ba,kuma abunda ya dace ace munyi ne," ta6e baki jahan yayi tare da kallonshi yace"sannu ko?sarkin tausayi," Jin takun tafiyar Amani ne yasa su kayi shiru,ƙarasowa ciki tayi hannunta ɗauke da tray,cups ne guda biyu,sae lemu masu sanyi acikin roba tare da plate na snacks,asaman table ta ajiye masu sannan ta juya tana cewa"bari na kira Amal din ku gaisa," ɗaukar lemun ayaaan yayi tare da buɗe shi ya tsiyaya masu acikin cup,ya dauki ɗaya ya miƙa ma Jahan,ya kar6a sannan shi kuma ya ɗauki ɗayan,yana sha, Saukowa amani tayi daga upstairs,ta dawo wurinsu ta zauna saman sofa din tana cewa"gata nan zuwa," Ayaan yace"Allah ya kawota lafiya," Gaba daya sun mayar da hankalinsu wurin shan Lemun dake hannunsu,su ka jiyo takon takalminta,kwas kwas, Ayaan ne ya fara ɗago da ido yana hangen yarinyar dake saukowa daga saman benen,juyawa yayi ya kalli amani tare da yin ƙasa da murya yace"ita ce ko"? .murmushi amani tayi tare da daga mashi kai alamar eh, Satar kallon jahan yayi wanda hankalinshi ba a kansu yake ba, A hankali Amal ta ƙarasa saukowa daga saman benen ta nufo inda suke,lokacin da ta ƙaraso wurinsu fuskarta ɗauke da murmushi tace"sannunku da zuwa," Kai tsaye muryarta ta daki dodon kunan Jahan,daɗin muryarta ne yasa Jahan juyowa cikin sauri don yaga wacece,ai yanayin arba da wannan kyakkyawar fuskar ta Amal nan take ya saki Cup ɗin dake hannunshi ƙasa,ya tarwatse lemun ciki ya zube, A gigice ya miƙe tsaye yana kallonta yayin da zuciyarshi ke bugawa da ƙarfi da karfi,yarda kasan hurool aini awurin kyau haka yarinyar ta koma mashi, fara ce tass,har ma tafi Amanin haske,fatar jikinta har wani ƙyalli takeyi saboda gyaran da tasha,tabarakallah masha Allah ta ko'ina amal ta haɗa,ga manyan idanun nan nata dara dara dasu,ga dogon hancin nan nata kamar zaiyi sujjada,la66anta kuwa sunyi red colour sosai tamkar ta shafa janbaki,idan tayi murmushi kamar gonar auduga saboda hasken haƙoranta,lallai ba ƙaramin gyara Amani tayi ma ƙanwarta ba,ta canza mata kamanni sosai,ta fito a balarabiyarta,sleeping dress ne ajikinta pink colour riga da wando,ta yafa gyale fari asaman kanta, dare ɗaya Allah kanyi bature,acewar ayaan, Ina labarin Jahan daya miƙe tsaye ya zuba mata ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi,abun tamkar a mafarki yake kallonshi,gaba daya ya gama ruɗewa,muryarshi na rawa yace"ke!kece!'cike da mamaki yayi maganar, Amal kuwa aɗan tsorace taja baya,tana faman zazzare mashi kyawawan idanunta,ganin yarda ya harzuƙo kamar zai rufe ta da bugu, murmushi kawai Amani ke saki ita da ayaan suna kallonshi,dama wannan duk shirin Ayaan ne, "Aunty amani!surgery akayi mata ne?if not taya akai tayi transforming haka"? A ruɗe jahan ke tambayarta, miƙewa tsaye amani tayi tare da takawa zuwa inda suke ta ruƙo hannun Amal tana cewa"ikon Allah ne jahan,babu wani surgery da akayi mata,gyarane kawai tasha,dama can Amal kyakkyawa ce,wannan asalin kamannin fuskarta ne ya dawo,' Jiki asanyaye Jahan ya koma tare da zaunawa saman sofa din,har lokacin bai janye idanunshi daga kallon fuskar Amal da yake yi ba,kamar ya haɗiyeta haka yake ji,ya jima yana mamakin wannan ikon Allahn, Miƙewa Ayaan yayi tare da cewa"mu zamu wuce gida,ana can anata shirye-shiryen haɗa walimar murnar dawowar uncle abusufyan,ina fata zaki zo mana tare da Amal,'yayi maganar yana kallon Amani, Tace"mai zai hana,ae muna nan zuwa anjima insha Allah,tare da mu za'a buɗe taron walimar," "Allah ya kawo ku lafiya,'yayi maganar tare da mayar da idanunshi kan JAHAN daya ƙurawa Amal ido kamar mazuru yace"bro,tashi mu tafi mana,kada time ya ƙure mana," jiki amace jahan ya miƙe tare da ruƙo hannun ayaan cikin nashi,su kayi mata sallama tare da kama hanyar fita daga falon, Suna tafiya Jahan na waiwayon Amal kamar zaiyi tuntu6e,hakan ba ƙaramin dariya yaba shi ba,saida suka fito daga cikin falon,bayan sun shiga cikin motarsu,Ayaan ya ɗan kallo shi cikin zolaya yace"Jahan ya kaga ƙarmasasshiyar ne?ko nace kingin rami ko?ya ma kace mun ran nan a asibiti daka ganta"? A tsiwace jahan yace"bansani ba!dallah ni ka tashi motar mu tafi gida," dariya sosae Ayaan yayi yayin da yake tashin motar,ya ja ta suka bar gidan,yana driving yana kumshe dariya abakinshi,jin yarda Jahan ke ta faman buga tsoki,duk yabi ya susuce tunda yayi arba da Amal acikin idanunshi,ya nemi natsuwarshi ya rasa,a haka har suka ƙaraso cikin gidan, wuraren ƙarfe sha biyu,sgr ya fito daga cikin toilet jikinshi sanye da bathrobe,yayin da hannunshi ke ruƙe da guntun towel wanda yake goge Sumar kanshi dashi,agaban dressing mirror ya tsaya yana ƙarasa goge sumar kan nashi,koda ya ɗago da idanunshi da niyyar ya kalli fuskarshi acikin madubin,sae ya dinga ganin fuskar sehrish acikin mirror ɗin amaimakon tashi,lokaci guda ya shiga tariyo duk abunda ya faru jiya atsakaninsu,tun daga lokacin daya je taimakonta,har izuwa lokacin da yaje yi mata allura,tana faman cizon la66anta,hakanan yaji yana marmarin son ganinta acikin idanunshi,tambayoyi ya shiga yi aranshi yana cewa meyasa batazo ta kawo min breakfast ba?ko har yanzu jikin nata ne? Jin takun tafiyar mutun abayanshi yasa shi kai idanunshi wurin ta cikin madubin ya hange ta tsaye duk a tunaninsa yarinyar ce tazo,koda yayi arba da fuskar hayaam sai ya kawar da fuskarshi cike da mamakin wacece wannan?meya kawota bedroom ɗinshi, ƙarasawa ciki hayaam tayi tana tafiya cike da kwarkwasa,wankan atampa ta ɗauka ajikinta,riga da skirt ne,kayan sun matse ta sosai,sun bayyana surar jikinta soaai,musamman saman rigarta boobs ɗinta sun fito waje kamar zasu ciro daga cikin rigar,akwai mayafi a jikinta lokacin da ta fito daga bedroom ɗinta,tana ƙarasowa ɗakin nashi ta cire mayafin tare da ruƙe shi a hannunta don taja hankalin shi,cike da ƙwarin guiwa tazo ɗakin nashi,saboda kwallin data shafa ma idanunta,wanda bokansu ya bata don tayi amfani dashi,ya tabbatar masu da cewa muddin sgr ya sanya idanunshi acikin nata,shikenan sun gama dashi,zai haukace akanta,ya rasa natsuwarshi, Tsayawa tayi daga bayanshi,tare da kashe murya tace"ya kake ranka shi daɗe,ka tashi lafiya," Shiru Sgr yayi bai amsa mata ba,gaba daya lamarin ya gama ɗaure mashi kai,ƙarfin halinta ya bashi mamaki, daƙyar ya iya buɗe baki yace"Ke!wacece ke!what are u doing in my room?yayi maganar batare daya sanya idanunshi acikin nata ba zagayowa hayaam tayi ta gabanshi tamkar zata manna ƙirjinta asaman nasa, Cike da rangwaɗa tace"Zuwa nayi don na gyara maka bedroom ɗinka,tunda ita yarinyar dake kula da part ɗin naka,bata jin ɗaɗi bazata iya yin aikin ba,idan ba damuwa inaso ka bani damar na ci gaba da kula dakai kanka,ina mai tabbatar maka da cewar zaka ji daɗin kasancewa tare dani,saboda ni ina da komai da komai,ba gyara ɗaki kaɗai ba,hatta ɗebe maka kewa zan dinga yi,nasan dole ka buƙaci mace akusa dakae especially da daddare haka. Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,yau hayaam tazo yi ma Sgr kwartanci acikin ɗakinshi,ita ga kwararriyar ƴar bariki,tana magana tana ƙara kusanta jikinta da nashi, Just speechless gaba daya ta gama rufe mashi bakinsa,ya rasa abun cewa,shiru kawai yayi yana jira yaga me take ƙokarin yi mashi,daga nan zai san wane irin hukunci ya dace da ita,don ya lura cewa giya tasha,tana bukatar adawo da ita cikin hayyacinta,kuma har lokacin bai kalli cikin idanunta ba,   Wannan shurun da yayi ne yasa hayaam ta fara tunanin cewa kodae ya amince mata ne?shu'umin murmushin nan nata ta shiga saki tana bin surar jikinshi da kallo sae faman haɗiyar yawu takeyi kamar zata lashe shi,aranta tana cewa"dama nasani,muddin yayi arba da sura ta,dole ya kwaɗaitu,yanzun nan zan canza mashi alƙibla,zanja hankalin shi sosai,har nasamu abunda nakeso,   Kafin Sgr yayi wani yunƙuri gaba daya hayaam ta afka mashi tai hugging nashi sosae,tashin hankali saboda tsabar mamakin daya shiga ne yasa bai janyeta Ba,kanshi ya gama ɗaure wa,domin kuwa tunda ya ke arayuwarshi wata ƴa' mace bata ta6a kuskuren ta6a wani sashe na jikinshi ba koda gigin wasa,sae wannan mai rabon shan dukan, ita kuwa hayaam jin bai yi yunkurin yi mata wani abu ba yasa ta fara kokarin tura hannunta cikin Bathrobe din dake a jikinshi don tasan takan yadda zata ida kashe mashi jikinshi,aikuwa a zafafe ya finciko ta,ya ware faffaɗan tafin hannunshi da ƙarfin gaske ya kifa mata mari zazzafan gaske gami da hankadata ta daki dressing mirrorn,agigice hayamm ta fasa wata irin razananniyar ƙara,wani irin jiri ne ya ɗebe ta,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa tana birgima,taji ƙamshin mutuwa wlh,ihu ta shiga saki tana fadin Wayyo Allanta,   Adai dai lokacin Sehrish ta shigo part dinshi hannunta ɗauke da tray,na breakfast dinshi data kawo mashi,ganin bashi a parlourn yasa ta nufi bedroom din bakinta dauke da sallama, tana sanya ƙafarta acikin bedroom ɗin,ta jiyo sautin wannan ƙarar da hayaam ta saki,a firgice ta saki tray ɗin hannunta ya faɗi ƙasa kayan abincin suka tarwatse ƙasa,hankali a matuƙar tashe take kallonsu,sautin faɗuwar tray ɗin hannunta ne yasa sgr juyowa karaf idanunshi suka shiga cikin na sehrish,zuba mashi ido tayi tana kallonshi yayin da shima yake kallonta sae faman huci yake yi yarda kasan mayunwacin zaki,da ace sehrish bata faɗo ɗakin nan ba,da ba ƙaramin illata Hayaam zaiyi ba,so yayi ya nakasata,yarda bazata ƙara yin gigin takowa tazo bedroom ɗinshi balle har tayi yunƙuri ta6a wani sashe na jikinshi ba,   atsorace sehrish ta mayar da idanunta kan Hayaam dake a baje ƙasa,magashiyyan sae faman Birgima takeyi har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,wato taji tafin hannun maza,dama zafin hannu gare shi,shiyasa bai cika son yakai bugu ba,saboda za'a iya samun matsala,da mari kaɗae zai iya sumar da mutun, A zafafe Sgr ya juya ya tunkari hayaam dake baje kasa,da alama yau fa hayaam sai dai buzun ta,ganin hakan yasa hayaam da kyar ta rinka jan jiki tana ja baya gami da yi masa magiyar yayi hkr kar ya kasheta hannunta guda dafe da kuncin,gaba daya sautin jin kunanta ya ɗauke ɗuff ta 6arin da daya mare ta,cikin husky voice yace"who the hell are u? da sauri cikin shesshekar kuka la66anta na kerma tace"ni...ni..ƙanwarku ce....au ƙanwar matar yayyen kuce ishaq da abbas" tsayawa Sgr yayi lokaci guda ya gane itace yarinyar da tazo rannan har aka faɗa masa"to waye ya shigo da ita gidan? Ya jefa ma kansa tambaya, Ganin abunda ke faruwa yasa Sehrish ja da baya zata watsa aguje saboda tsoran kar itama laifin da hayaam ta aikata ya shafe ta,   da wata irin murya taji yace"ke!zonan,"   Jiki na rawa sehrish ta shigo cikin ɗakin nashi,sae faman kerma take yi kamar yace zai buge ta,   ƙarasawa kusa dashi tayi tana faman zazzare idanu hankali atashe take kallonshi,tana jiran jin me zaice mata,   daidaita natsuwarshi yayi tare da sassauto da muryarshi calmly yace"ya jikin naki!'?   Tsananin mamaki ne ya kama sehrish,jin abunda yace mata,kuma da irin muryar da yayi mata maganar,hakan yasa taji hankalinta ya kwanta,   muryarta na rawa tace"naji sauƙi sosai,yanzu bana jin ciwo atare dani," Jinjina kanshi yayi kafin ya kuma cewa"Okey,Allah ya ƙara lfy,' "Ameen,"ta amsa mashi, shiru suka ɗanyi na wani lokaci,kafin ya mayar da idonshi kan hayaam dake ta faman yi mashi tsuwa acikin dakinshi duk ta cika masu kunnuwansu,   A fusace yace"get out from my bedroom!'   Jiki na rawa hayaam ta miƙe da gudu zata fuce a tsawace sgr ya tsaidata ta hanyar cewa" hey! juyowa tayi har lokacin hannunta na akan kumatunta ya cigaba da cewa "make sure u pack all ur shit and leave this house! A kausashe yayi maganar, idasa fucewa daga cikin ɗakin tayi tana cigaba da shar6ar kukan nata, Lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu akan fuskar sehrish da tai tsuru² jin ance hayaam ta tattara kayanta ta bar gidan, yace"yanzu ya za'ae da breakfast ɗina da kika zubar mun a ƙasa?   cikin sauri tace"bari naje na haɗo maka wani" juyawa tayi da niyyar ta tafi,kwatsam taji ya ruƙo hannunta acikin nashi,a ɗan tsorace ta juyo tana kallonshi,gabanta ne taji yana faɗuwa ganin yarda Sgr yake kallonta,nan fa ta shiga taitayinta,   "Meyasa jiya,baki dawo gida ba?ko saboda na datse maki gashin kanki ne"?    Girgiza kai sehrish tashiga yi tana cewa"a'a ba haka bane,bani da lafiya ne,bacci ya ɗauke ni a school bansamu wanda ya tashe ni ba lokacin da aka tashi har junaid yazo dauka na bai ganni ba,shiyasa bansamu nadawo gida ba,'   Kallon bakinta dake bayanin kawae yake har ta gama,a hankali ya furta Okey,sannan ya saki hannunta daga ruƙon da yayi mashi,   juyawa tayi da sauri ta ƙarasa bakin kopar dakin nashi,zukunnawa tayi ta kwashe kayan abincin data zubar mashi aƙasa,duka ta tattara su acikin tray din,sannan ta fuce daga ɗakin nashi, Gaba daya ta rasa natsuwarta,wani irin yanayi ta dinga ji atare da ita,kallon nan da yake yi mata ba ƙaramin kashe mata jiki yakeyi ba,kamar wadda aka cire ma lakar jikinta haka ta dinga jin kasala, A kitchen ta samu azmee tana wanke kayan abincin da sukayi amfani dashi na breakfast,   Ganin ta ɗauke da tray a hannunta yasa azmee cewa"Har ya kammala yin breakfast ɗinne"?   girgiza kai tayi alamar a'a tace"matsala aka samu,ni ce na 6arar da kayan abincin,shine yace na sake kawo mashi wani,'   Azmee tace"wasa wasa sehrish kema kin iya shiririta wlh,kina sake da baki har kika zubar mashi da kayan abincin ko?   "Ae bada sanina,hakan ya faru ba,"ta yi maganar yayin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin,   "Shikenan bari na sake haɗa maki wani breakfast din ki kai mashi,Amma kada ki jima a part din nashi fa,da zarar na kammala gyara kitchen din,zanyi maki ƙunshin,ko baki so ne'?   "Inaso mana,"tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,   Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata wani kayan abincin acikin tray,ta bata takai mashi,sae da ta ja mata kunne akan karta kuskura ta ƙara zubarwa,'   fitowa daga cikin kitchen din sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da annuri,wani irin daɗi takeji aranta,kamar anyi mata albishir da gidan aljana,   A hankali take taka stairs din,yayin da Zuciyarta ke tariyo mata abunda ya faru aɗakin sgr,batasan meya faru tsakaninshi da hayaam ba,da har ya kwashe ta da mari,amma koma meye dae tana da tabbacin cewa wani abu tayi mashi ba dae dae ba,   Ta6e baki tayi tana cewa"to ni ina ruwana?meye damuwata da ita?koma meye ita taja ma kanta,nasan cewa babban yaya bazai ta6a ɗaga hannu ya mari mace ba hakanan batare da wani dalilin ba,na yarda dashi sosai,kuma baiyi mun kama da irin mazan dake dukan mace ba,Yau dae hayaam take kowa ma,tasha mari wlh ko a ha6ar zani na,ba ƙaramin daɗi naji ba wlh,babban yaya ya burgeni sosai daya kwashe ta da mari,gobe ma in halinta ne ta ƙara yi mun shisshigi a aikina,angaya mata cewa sauƙi ne kula da babban yaya?nikaina kullum cikin fargabar kada nayi mashi kuskure nake,shiyasa nake lalla6ashi kamar kwai acikin cokali,Allah sarki yau hajia hayaam taji tafin hannun babban yaya koya raɗaɗin yake?tabb dole ma akwae mugun radadi tunda ta kasa cire hannu daga kan kuncinta, gwara ni Almakashi yasa ya datse mun gashin kaina,nan da wani lokaci gashin zai fito,ita kuwa marinta fa yayi? nasan har abada bazata manta da wannan ranar ba, ashema hakanan take ma mutane kankanba ko sanin wacece ita bai yi ba" Dariya sosai sehrish takeyi kamar wata zautacciya,sae faman sambatu takeyi,da alama taji daɗin Marin da Sgr yayi ma Hayaam,abun ko ajikinta,   Lokacin da ta shiga part ɗin Sgr,a kishingiɗe ta same shi saman doguwar kujera,ya miƙe kafafunshi,bai kaiga shiryawa ba,Vest ce kawai ajikinshi sae shorts farare,   Karasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan tace"ga wani breakfast ɗin na kawo maka,"   sauko da ƙafafunshi yayi ƙasa ya miƙe daga zaune,ya jingina bayanshi a jikin sofan yana jira tayi serving ɗinshi,   Sehrish ta jima awurin sgr tana mashi ɗawainiya har sai da ya kammala yin break fast din nashi,sannan ta koma ta gyara bedroom ɗinshi,bayan ta gama ta dawo ta gyara falon sannan ta ɗauko kayan abincin da yayi amfani dasu,ta wuce dasu kitchen,sae da ta wanke komai ta mayar dashi a ma'ajiyar shi,sannan ta wuce ɗakin azmee don suyi maganar zanen lallen da zatayi mata, Wuraren ƙarfe biyu na rana,Junaid ya kar6o mata kayanta,akwati guda ne na atampha da lace,da kuma shadda,hada materials,duk an ɗinka mata su, acikin bedroom ɗinta ya ajiye mata akwatin kayan, sae da suka kammala sallar azhar,tukunna suka zauna zaman yin ƙunshi,anan corridor din ɗakunan nasu azmee tayi masu shimfiɗa suka zauna sama,tunda suka fara ƙunshin junaid keta zarya awurin sae faman santin kunshin sehrish yake yi,tun kafin a wanke mata ƙunshin ma,cikin nishaɗi suke yin firar su,tana yi mata ƙunshin suna fira tare da junaid,don ya kasa ya tsare sae anyi tare dashi, A6angaren Hayaam kuwa tunda ta faɗa cikin bedroom ɗinta saman gado,take ta faman shessheƙar kuka,fuskarta tayi jawur saboda kukan da tasha,gefen fuskarta dauke da sahun yatsun sgr ruɗu ruɗu sun fito wurin ya kumbura sosai gashi kunnanta daya dumm take jin shi,tunda take arayuwarta wani ɗa namiji bai ta6a gigin ta6a lafiyar jikinta ba,sae akan Sgr ta fara shan mari,ta jima tana mamakin yarda ya ɗaga hannu ya kwasa mata mari,duk irin yarda ta ɗau wanka,ta bayyana surar jikinta don taja hankalinshi amma hakan baiyi tasiri akanshi ba,kwallin data shafa kuma ya tashi abanza saboda bai kalli cikin idonta ba bare asirin ya kamashi,   ɗagowa tayi daƙyar take iya buɗe idanunta,wayarta ta ɗauko dake ajiye saman side drawer na gadonta,layin Aunty babba ta kira,wayar ta shiga ringing, Cikin sa'a ta ɗaga kiran,Aunty babba nayin sallama,hayaam ta 6are baki ta fashe da wani sabon kukan,   Tunda Aunty laila taji kukan hayaam hankalinta yayi mugun tashi,daga zaune take saman kujera amma tana jin kukan hayaam ta miƙe tsaye tana tambayar lafiya!   Cikin shessheƙar kuka hayaam tace"Aunty lailai,yau Sgr ya gama dani,ya wulakantani kuma ya tozarta ni,yayi mun abunda wani ɗa namiji bai ta6a yi mun ba!'   Hankali tashe Aunty babba tace"Me yayi maki ne!kiyi mun bayani yarda zangane,kuma kidaina wannan kukan da kikeyi,"   dakatawa da yin kukan hayaam tayi sannan taci gaba da magana tana cewa"Mari na fa yayi,banyi mashi komai ba ya ɗaga hannu ya kwasa mun mari agaban waccen ƙaskantacciyar yarinyar ya mare ni....'   Tunkan ta ƙarasa maganar Aunty babba tace"Ƙarya kike hayaam!Sgr bazai ta6a marinki ba batare da kinyi mashi laifi ba!dole akwai dalilin dabyasa ya mare ki,don nasan halinki baki da hankali,kuma baki da kamun kai,halan ƙoƙarin kai mashi hari kikayi saboda gajen hkr!!"   Cikin en ena hayaam tace"nifa banyi mashi komai ba,kawai da safe ne nashiga ɗakin shi lokacin ya fito daga wanka,nayi ƙoƙarin jan hankalinshi ne da surar jikina,amma ko kallo ban ishe shi ba,shine nayi hugging nasa nayi ƙoƙarin ta6a short ɗin jikinshi don in tayar mashi da sha'awar shi,amma shine kawai ya kwashe ni da wani mahaukacin mari.....'   dafe kai Aunty babba tayi tana cewa"ka ji tsiyar!wlh kin ban kunya hayaam!bansan ke wata irin mace bace!sam baki da kamun kai,idan jarabarki ta motsa, me yasa bazaki iya control din kanki bane agabanshi!wannan mutumin fa da kaina nayi maki alƙwarin cewa mijinki ne shi,idan kikayi haƙuri nan da ɗan wani lokaci zaki mallake shi duka,sae kiyi yarda kika ga dama dashi,amma tun yanzu saboda gajan haƙuri irin naki kin gaza jurewa,kina ƙokarin lalata mun shiri na!bazaki ta6a burge Sgr ba,saboda shi irin mazan nan ne da basa ra'ayin mace mara kamun kai ballagaza,wadda bata iya 6oye zalamarta akansu......' Ɗaure fuska hayaam tayi jin yarda Aunty babba ke ta zaginta a fakaice, Rai a6ace tace"Aunty laila nifa ban kiraki don kici mun mutunci ba,sae faman gaya mun magana kikeyi ta inda kike shiga bata nan kike fita ba,ni da na kawo maki kukana maimakon ki share mun hawaye na,Amma shine kike ta zazzaga mun masifa!wannan abun fa ba laifina bane,ko kece kika ganshi a yanayin dana same shi dole ki kai mashi attack balle ni da nake budurwa........'   Waro ido waje Aunty babba tayi rae a6ace tace"Hayaam don ubanki ni kike gayama wannan maganar!ashe ke daƙiƙiyace baki da hankali!an gaya maki ko wace mace irin ki ce mara aji da zata dinga kai kanta wurin namiji har tana ƙokarin ta6a jikinshi!ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar mijin da banawa ba,duk irin mugun halin da nake dashi kuwa,a iya miji na natsaya ban zarce nan ba!amma ke fa?kullum kina yawon biɗiɗi wurin raba jikinki ga kowane ƙazamin namiji yayi amfani dake,don ki samu kuɗi,ki faɗamun wace riba kika ta6a samu a yawon barikancin naki!acikin mazan da kikayi mu'amala dasu akwai shegen daya ta6a cewa zai aure ki ne!!saboda baki da wani amfani awurinsu,tamkar totuwar masara kike da zarar sun cinye masarar jikinshi ya gama amfani sae su jefar dashi ƙasa,ni kuwa kinga ina da daraja tunda ina da aure kuma a ƙarkashin kulawar mijina nake,shiyake amfani dani kuma shi yake bani kuɗin da zanyi abunda nake so,riba biyu ga kuma lada ina samu......'   Wani irin huci hayaam ta shiga fitarwa saboda tsabar 6acin ran kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata, Muryarta har shaƙewa takeyi wurin cewa"Aunty Laila!!ni kike faɗama waɗannan munanan kalaman!yau da kanki kike yi mun gori?Ya salam!wlh bazan ƙyale ki ba,kamar yarda kikayi mun gorin aure,nima zan raba auran ki Da Ishaq,ki dawo bazawara," fashewa da dariya Aunty babba tayi tana girgiza kai kafin tace"ni zan aje waya,kada ki manta kisha maganinki na rana,don da alama kin manta jawabin da likitan mahaukatan nan yayi maki,akan kula da shan magungunan ki akai akai,"ta ƙarasa maganar tare da kashe wayar,   Wani irin ihu hayaam ta zabga tare da aza hannunta saman kanta,tana fadin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...." Zafi biyu,gana marin da Sgr yayi mata ga kuma na zafafan kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata,zuciyarta tamkar ana rura mata garwashin wuta haka ta dinga ji,wani irin zazza6i ne ya lullu6eta,nan ta baje saman gadon tana ta faman birgima a ranta tana cin alwashin ba zata bar gidan ba har sai taga bayan Sehrish don ita taja mata duk wadannan abubuwan da suka faru da ita.          warah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*, Wuraren ƙarfe 4:30 gaba ɗaya matasan gidan sun hallara a baban falon gidan wanda yasha decorations abun ba'a magana,yayi kyau over tamkar wani babban hall na taro,an ƙawata shi sosai hada wasu kujerun aka ƙaro,an tsara komai na wurin anyi table arrangements,kowane table yana zagaye da Kujeru guda uku uku wadanda ke dauke da seat cover haka ma tables din,a jere Ayaan da Jahan irfan da khaleed da kuma jabeer da fawan,suka shigo main palour ɗin kowannansu ya ɗau wankan tsadaddiyar shadda ajikinshi,bayansu sae kanal yousouf shima ya fito cikin nashi wankan,ba ƙaramin ƙyau sukayi ba,sai hotuna suke ɗauka da wayoyinsu,kafin camera man ɗinsu wato junaid ya kammala shirin nashi ya fito ya ɗauke su hotuna,dama shine maiyi masu hoto duk in suka shirya walima irin haka,acikin gida, Lokacin da Abbansu ya fito jikinshi sanye da shadda fara taji aiki ajikinta,koda sukayi arba dashi da sauri suka ƙaraso wurinshi suna yaba wankan daya ɗauka,   "Abba harka fi mu yin kyau wlh,gaskiya bamu yarda ba Abba,'   Dariya sosai Abban nasu yayi yana kallonsu one by one,wani irin farin cikine ya lullu6e shi ganin ƴa'ƴan nashi gaba ɗayansu agabanshi,duk da ba wasu acikinsu,amma yasan duk zasu hallara ne suna ciki suna shiryawa,   "Abba,bari mu fara ɗaukar hoton tare dakai kafin Baby junaid ya ƙaraso,"   fawan ne yayi maganar yana kanga wayarshi saitin fuskar Abban nasu, dakatar dasu Abba yayi yana tambayar ina Abusufyan yake ne?bai fito bane? Kanal yousouf yace"naje bedroom ɗinshi lokacin yana acikin toilet ɗinshi,amma ina da tabbacin zuwa yanzu ya kammala wankan ƙila ma harya shirya shima,"   Jinjina kai abban nasu yayi tare da cewa"Gaskiya sae dae kuyi haƙuri to,babu wanda zanyi hoto dashi har sae naga ɗan uwana akusa dani,dashi nake son na fara ɗaukar hoton nan,don haka ku jirani yanzun nan zamu fito tare,"   Bashi wuri sukayi ya wuce ɗakin Abusufyan,tura ƙopar yayi yasa kai ya shiga ciki,a lokacin Abusufyan yana tsaye gaban dressing mirror yana maƙala links ɗin hannun rigar shaddar daya sanya,madarar kyau,gezner ce ajikinshi green colour,sae faman salƙi takeyi,yayi kyau Over,ta cikin madubi ya hangi shigowar yayan nashi,   Ƙayataccen Murmushi ya saki tare da cewa"Yaya hossein,yanzu nake shirin fitowa nima,wlh bacci ne ya ɗan dauke ni bayan mun dawo daga sallar la'asar,shiyasa na makara ban kimtsa da wuri ba,"   Ƙarasawa ciki Abba yayi yana cewa"tun ɗazu nake ta baza idanu inga 6ullowarka,amma bangani ba,shine nace bari ni nazo da kaina na janyoka mu fita tare,don na sanar dasu cewar babu wanda zan ɗauki hoto dashi har sai naga ɗan uwana mun fara yi dashi ,'   juyowa Abusufyan yayi a lokacin ya kammala sanya links ɗin ya kalli abba yace"yaya hossein bansan da wasu kalmomi zan iya bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,wlh sai yanzu nake danasanin yin nesa da ƴan uwana,domin kuwa babu abunda yafi kasancewa tare da ahali daɗi aduniyar nan,' Abba yace"ae bazan ƙara yin gangancin barinka kabar ƙasar nan ba,wancen lokacin ma satar hanya kayi ka gudu batare da saninmu ba,amma wannan karon zan sanya tsaro sosai akanka,ko nan da bakin gate zaka je sai da izinina,zan sanya security guards ɗin da zasu dinga bibiyarka a 6oye," Dariya sosai Abusufyan yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace"Ya hossein nima bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba,na tafiya nabarku,nasan ban kyauta ba,wlh naji ba daɗi sosai lokacin da junaid ya ƙankame ni yana murnar zuwana hada hawayenshi,sae naji wani iri araina,na tafi na barshi yana ƙarami bai mallaki hankalinshi ba,amma yanzu dana dawo na same shi ya girma sosai,a waya ne kawai nake jin muryarshi,iya wannan shaƙuwar da mukayi ta waya itace tasa ya ruƙe ni sosai aranshi,insha Allah bazan ƙara tafiya nabarku ba,nayi alkawarin hakan," Ba ƙaramin farin ciki Abba yayi ba,da jin kalaman ɗan uwan nashi,ruƙo hannunshi yayi acikin nashi tare da janyo shi suka fito daga cikin bedroom din, Kamar jira suke Abban nasu ya fito tare da uncle Abusufyan da sauri suka nufesu fuskar kowannansu ɗauke da farin ciki mara misaltuwa,nan fa suka shiga ɗaukar hotuna, 💋Boss Bature💋 Tabarakallahu ahsanul khaliqin!Azmee ce ta ambaci hakan yayin da take kallon sehrish dake tsaye,sanye cikin tsadadden cord lace red colour yasha adon duwatsu ajikinshi,riga ce har guiwa sae zani,azmee da kanta ta ɗaura mata ɗankwalin golden colour tamkar gwargwaro haka ta ɗaure mata shi a kanta,fuskar nan tasha make-up ɗan light ba over ba,ta gyara jagirar idanunta duk da ta ƙara zana ta da eye pencil brown colour,ta ko'ina kwalliyar ta fiddo mata da zunzurutun kyawun fuskarta,hancin nan yayi tsayi,ga bakin nan nata yasha jan janbaki,yadda kasan wadda zata gasar sarauniyar duniya haka ta fito ɗass da ita,wasu matsiyatan takalma ƴan ubansu azmee ta ɗauko mata daga cikin shoe rack dinta,ankle strap masu tsinin gaske golden colour ne suma,launin head dinta,wayyo Allah bournvitar kyau just imagine it, Wuyanta na sanye da ziririyar sarka golden colour,haka earrings dinta,da kuma rings ɗin da ta zura a hannunta duk launi ɗaya ne, Kai jama'a!,ga zanen fulawar da azmee tayi mata a hannunta na jan lalle,yayi mata kyau sosai hannun nata kamar a lashe don kyau, "Juya a hankali ki kalli madubi,"Azmee ce tayi mata maganar tana faman sakar mata murmushi, Ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da juyawa awani slow ta kalli kanta acikin mirror ɗin, Gabanta ne taji yayi wani irin bugu lokaci guda,zuba ma kanta ido tayi tana kokwonton Anya itace kuwa!? Yarfa hannu tashiga yi aruɗe take cewa"Aunty azmee wai dagaske ni ce!dama haka nake da kyau kamar macen aljanna! Am just speechless oh my God!! 🤣😂 Maganar sehrish ba ƙaramin dariya taba Aunty azmee ba,kama hanyar fita tayi daga cikin ɗakin tana cewa"Bari naje na fara jera abincin a falo,pls kada ki fito yanzu sai nan da 15 mins nake son ki fito saboda inason inga reaction ɗin matansan gidan idan sukayi arba dake,"tana kai ƙarshen maganar ta fuce, Ƙayataccen murmushi sehrish ta sakar ma kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta acikin madubin,lokaci guda Sgr ya faɗo mata acikin ranta,lumshe idanunta tayi tare da buɗesu a hankali tana ƙara bin jikinta da kallo, Sae ta dinga jin kanta tamkar amarya a wannan lokacin,amaryar kuma ta Sgr, "Ya Allah ka nuna min wannan ranar da nake ta mafarkin zuwanta,ranar da zan kasance mallakinshi,shi ma kuma ya kasance mallakina,a wannan ranar nayi ma kaina alkawarin cewa ko bacci ba zanyi ba,zan kwana ina sallar dare,ina miƙa godiya ta ga Allah daya cikamin burina,a washe garin ranar kuma zan tashi da azumi,' ta ƙarasa zancen zucin nata tare da samun wuri saman kujerar gaban madubin ta zauna, Gaba daya duk sun zazzauna saman kujerun yayin da table din ke shaqe da kayan ciye ciye iri²,Abusufyan tare da Abban nasu sae junaid suna a zaune wuri daya,Ayaan da jahan da kuma fawan suna zaune suma a wuri daya suna cin abincinsu,Irfan da jabeer sae khaleed suma suna zaune a table daya, Kanal yousouf ne ya buɗe masu taron da addu'o'i,kafin su fara kulu washarabu hani'an,sunyi haje haje da naman kaji,farfesu iri iri da sauran kayan maƙwalashe, ,kowa ya mayar da hankalinshi akan abincin dake gabanshi,   "Wai ni ina Rafayet da Omar ne?naga kowa amma bandasu,"Abusufyan ne yayi ma Abba maganar a yayin da yake ɗaukar cup na lemu,yakai bakinshi yana kur6a,   "Ina tunanin suna ciki suna shiryawa,kasan su fa manya ne nasu wankan ba irin namu bane,nasan shiyasa suka jima aciki basu fito ba,"a cewar abbansu, "Naga alama,amma ni ko ina so na tambayeka yaya,wai har yanzu Sgr da Omar basu fara soyayya bane "?yayi tambayar yana kallonshi,   Murmushi Abba ya ɗanyi kafin yace"Omar dae ya sanar dani cewa akwai yarinyar da yake so,kuma ashirye yake daya aureta,amma shi rafayet har yanzu fa babu wani sauyi yana nan yadda kasan shi,amma kwanan nan na fuskanci kamar akwai wani abu atsakaninshi da yarinyar gidan nan,wadda na faɗa maka cewa tana taya Azmee aiki,kamar akwai soyayya atsakaninsu,duk da dae bani da tabbacin hakan,"   tunda suka soma magana junaid baisan me suke tattaunawa ba,saboda hankalinshi na can wurin tunanin abu biyu,rishi ɗinsa da kuma zuwan mommynsu a takure yake,gaba ɗaya ya gaza samun natsuwa saboda ya kwallafa rae akan zuwan nata, Abusufyan yace"yanzu me ka yanke shawara agame dasu ne?zaka tunkari Sgr da maganar yarinyar ne ko kuwa"? "A'a,bana tunanin cewa zai amince cewa yana sonta harma ya yarda ayi auren kasan halin shi,yanzu dai akwai wani shiri da nakeyi dama zuwanka kawai nake jira,nan da sati mai zuwa zan sanar dakai insha Allah," Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"Allah ya kaimu lafiya," Abba ya amsa mashi da Ameeen, Juyawa abbansu yayi tare da kallon junaid ya ambaci sunanshi,   Firgit junaid yayi tare da aza idanunshi kan abban nasu yace"Abbana," ..murmushi sukayi gaba ɗayansu,Uncle abusufyan yace"junaid kodae ka fara soyayya ne?tun ɗazu muke magana amma hankalinka na'a wani wuri,"   Murmushi ya ɗanyi tare da sunnar da kanshi ƙasa yana kallon plate dake ajiye gabanshi shaƙe da Chips,tun da Azmee ta zuba mashi bai ko ta6a shi ba,   "Junaid naji kayi shiru kodae dagaske ne abunda Uncle ɗinku yace ka fara soyayya"?Abbansu ne yayi maganar cike da zolaya yana kallonshi,   Duk kunya tabi ta kama junaid,ba wai abban nasu yake ji ma kunya ba,uncle ɗinsu yake ji ma kunya,don ta Abbansu har zancen aure suna yi dashi in wasan nasu ya motsa,   yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,wayar shi ta shiga ringing,jikinshi na rawa ya zura hannunshi a aljihu ya curo wayar yana duba sunan mai kiran nashi,private number ya gani wato anyi hidden ɗin numbar,kallon abbansu yayi tare da cewa"Abba zan amsa waya," amsa amshi yayi da cewa"okey,amma kada ka jima,muna jiranka,don bamu gama hotunan ba,"   Murmushi ya saki tare da miƙewa yabar wurin,sae da yayi nesa dasu sannan ya ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanshi yana jiran jin wanene ke kiran nashi,   Wata sanyayyar murya yaji ta karaɗe kunnan shi da cewa"babyn abbanshi kana ina ne"?   Tunani ya shiga yi kodae mommynshi ce don haka yace"ina a gida ne,"   Matar tace"Idan ba damuwa kazo Airport kadauke ni,na ƙaraso Nigeria amma banaso kowa yasan da maganar,kai kadae kawai nakeso kazo ɗaukana,Kada ka bari kowa ya biyo ka"   da ƙarfi junaid ya ambaci sunan mommy fuskar nan tashi cike da farin ciki yace"mommy am coming right away"   Matar tace"okey,idan ka fito daga cikin gidan ka sanar mun,"   Cike da zumuɗi ya amsa mata da toh,sannan jiki na rawa ya katse kiran tare da zura wayar a aljihun shi,   Gaba ɗaya ya gaza rufe bakinshi saboda tsabar farin ciki,juyawa yayi yana kallon ƴan uwanshi dake zazzaune kowannansu fuskarshi ɗauke da farin ciki,aranshi yace"kodai na sanar masu cewa mommy ta ƙaraso?kuma dae tace kar na faɗama kowa,gaskiya bazan faɗa masu ba,zan basu mamaki ne nasan in suka ga mommy zasu yi murna sosai,amma kuma inason na sanya rishi a idanuna kafin nabar gidan nan,bari nayi sauri naje naga wankanta na yau,   Yayi maganar tare da nufar corridorn ɗakinsu sehrish da sauri da sauri ya ƙarasa kopar bedroom ɗin nata,   A lokacin tana acikin bedroom din nata sae faman zagaye takeyi,tarasa ya zatayi ta fita,kunya take ji su ganta da kwalliyar jikinta, Jin kwankwasa ƙopar ɗakin nata yasa ta cewa"wanene," daga waje junaid ya amsa mata da cewa"Mijinki ne insha Allah,"   Murmushi ta saki tare da cewa"ka samu iznin shigowa ciki,daga matarka insha Allah,"   tura ƙopar yayi tare da sanya ƙafa ya shiga cikin ɗakin,koda yayi arba da sehrish nan take yaji gabanshi ya faɗi,kokwonto ya shiga yi yana tambayar kanshi Anya wannan sehrish ce kuwa?   matsawa kusa dashi tayi tace"meya faru junaid naga ka toge anan?   "Reesh,kinyi kyau Over,"cikin sanyin murya yayi maganar,don ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,   Ƙayataccen murmushi ta sakar mashi tare da cewa"saboda kai nayi wannan kwalliyar,launin lips dinka red colour ne,shiyasa nima na sanya jan lace don inyi anko da kai,to ya kaga wankan"? tayi maganar tare da jujjuya mashi bayanta don ya kalla da kyau,aikuwa ba ƙaramin ruɗashi tayi ba,gaba daya yabi ya susuce, Kamar yakai mata runguma haka yaje ji,amma ba halin yin hakan jikin shi sae faman kerma ya keyi, juyawa tayi tare da nufar bedside drawer dinta,ta ɗauko wayarta tare da dawowa saitinshi ta ɗaga wayar tare da cewa"ka shirya in ɗauka?'tayi maganar tana jiran jin amsarshi, Jin hannunshi ta gefen waist dinta yasa ta ɗan razana kaɗan,sosai ya ruƙo qugunta tare da kwantar da kanshi saman kafaɗarta yace"ki ɗauka," Zuba mashi ido tayi ta cikin camera ɗin tana kallon fuskarshi,hakanan ta dinga jin zuciyarta nayi mata wani irin bugu,muryarta akasalance tace"junaid ka buɗe idanunka,taya zan ɗauka dakai ido a rufe"? Murmushi yayi tare da buɗe idanunshi yana cewa"Reesh,ƙamshin turaran nan naki,kashe mun jiki na yake yi,ba kiji yarda nake ji ba,don Allah reesh,kada ki guje ni kinji"? Martanin murmushin ta mayar mashi sannan tace"junaid banda hankaline da zan guje ka?angaya maka kai irin mazan da ake gudu ne?kai fa na musamman ne junaid,tun farkon ranar dana fara zuwa aiki gidan nan,dakai nafara cin karo,a lokacin da nayi arba da wannan kyakkyawar fuskar taka mai ɗauke da wannan tsadadden murmushin,lokaci guda na rasa samun natsuwa,kasan Allah junaid da ace siyar da wannan murmushin naka kakeyi da ba ƙaramin ciniki zakayi ba Allah," Fashewa da dariya junaid yayi saboda jin kalaman sehrish akanshi,ba ƙaramin hura mashi kai tayi ba,kuma ta samar da farin ciki acikin zuciyarshi, ɗaukar hoton sehrish ta shiga yi,style iri iri suka shiga yi ita da junaid,hada wanda ya manna mata kiss a gefen fuskarta,da kuma wanda ta lotsa yatsanta acikin dimple dinshi,hotunan sunyi kyau sosai, Sae da suka kammala hoton sannan ta lura da zoben diamond ɗin dake hannunshi,sae faman ƙyalli yake yi, Waro ido waje tayi alamar mamaki tace"wow junaid wannan fa,waya siya maka shi!" "Mommy azeema ce ta bani shi,dama ɗazu na sanar dake cewa zan nuna maki gift din da takawo mun,to itace wannan,' Ya ƙarasa maganar yana nuna mata zoben da Wrist watch din, "Junaid sunyi kyau wlh,musamman daya kasance kaine ka sanyasu," "Thank u reesh,sunyi mun kyau amman idan ke kika sanyasu sae sun fi yi maki kyau,bari na ciro maki su ki sanya,nafison su kasance a hannunki," cikin sauri tace mashi"no junaid that's impossible,Auntynku azeema ce ta baka shi,muddin ta neme shi a hannunka bata ganshi ba zata nemi jin ba'asin inda ka kai su,kuma ma in banda abun ka junaid wannan ae irin naku ne!kamar diamond ne fa,nida ko zoben azurfa ban ta6a sanyawa a hannu ba,balle diamond! Kafin ya buɗe baki ya bata amsa wayarshi ta shiga ruri,nan take ya tuna da abunda mommynshi ta sanar mashi na cewa ta ƙaraso nigeria tana a Airport yaje ya ɗaukota, Jiki na rawa yayi ma sehrish sallama tare da fucewa daga cikin bedroom ɗin, Junaid bai sanar ma kowa ba,ya shige motarshi tare da janta yabar gidan gaba ɗaya,ya miƙi hanyar zuwa airport din cike da zumuɗin son ganin Mommyn tashi. 💋Boss Bature💋 A hankali sehrish ta sanya kafarta tare da fitowa daga cikin bedroom ɗin nata,a natse take tafiya yayin da takalman kafarta ke bada sauti kwas,kwas duk in ta takasu ƙasa,cike da fargaba ta tunkari babban falon gidan, Jin takun takalmanta ne yasa matasan dake zaune acikin falon dawo da hankalinsu akanta,koda su kayi arba da sehrish,lokaci guda sukayi tsit yarda kasan mutuwa ta gifta,babu mai magana acikinsu ba don komai ba,sae don kallon da suka bita dashi, Abbansu ne yayi ƙoƙarin cewa"Masha Allah my daughter,irin wannan kyau haka kamar sarauniyar kyawun duniya"?yayi maganar fuskarshi ɗauke da murmushi, Ita ma murmushin ta shiga sakar mashi tare da ƙarasawa wurin table dinsu don ta gaishe dashi,a lokacin Abusufyan yabar wurin saboda kiran wayar da akayi mashi,yaje ya amsa kiran ne, "Ina yini Abba," Lafiya lou daughter,tun ɗazu nake jiran fitowarki amma ban ganki ba,har azmee na tambaya ta sanar dani cewa kina nan zuwa, Ya ƙarasa maganar tare da cewa"kinyi kyau sosai,da ace ƴa'ƴana zasu bari dana yi ta biyu dake......'yayi maganar cike da zolaya yana satar kallonsu fawan da suka ƙure ta da ido suna kallonta,koda suka ji abunda Abban nasu yace nan take suka ɗaure mashi fuska alamar basu son zancen,hakan ba ƙaramin dariya ya bashi ba, Sehrish kuwa sunnar dakai ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta cike da jin kunyar Abban nasu, "Have a seat my daughter,"yayi maganar tare da nuna mata empty chair din da junaid ya bari, Janyo kujerar tayi ta zauna har lokacin ta gaza sakin jikinta, Muryar fawan ta jiyo yana cewa"Sister idan an kammala,zamu yi pic atare," Jahan yace"tunda tayi kwalliya ae dole ka nemi yin hoto da ita,mayen mata kawai,waccen dae tafi ƙarfinka Allah,ko kallonta ka cika yi sai Abban mu ya tuhume ka,don na lura da yadda yake ji da ita kamar mommynmu ce ta haife ta," . Dariya su kayi gaba dayansu, Fawan yace"wai ni ina wannan tsinken sigarin take? Atare suka haɗa baki wurin cewa"wa kenan"? Irfan dake zaune a next table ɗin da ke akusa da nasu yace"yana magana ne akan wannan ƴar moli-molin da ke yawo acikin gidan nan," Kamar zautattu haka suka fashe da dariya,har sae da Abbansu ya tambayesu ko lafiya,suka ce mashi babu komai,nishadi kawai sukeyi, adaidai wannan lokacin Abusufyan ya dawo wurin da suke,da alama ya kammala wayar da yake yi,wuri ya samu ya zauna yana fuskantar sehrish,daga ita har shi ba wanda ya lura da wani, Gyaran muryar da Abba yayi mashi ne yasa shi ɗagowa yana kallonshi yace"meya faru ne yaya"? Da ido yayi mashi nuni da sehrish yace"baka ganta bane," A hankali Abusufyan ya mayar da idanunshi kan sehrish dake zaune tana faman wasa da yatsun hannunta,gabansa ne yayi wani irin mugun bugu ji kake daram!!!a gigice ya miƙe tsaye hankali tashe yake kallonta, Miƙewa Abba yayi yana kallonshi ganin yarda ya tsorata da ganin yarinyar, Sehrish kuwa tuni ta firgita da ganin yarda Abusufyan ya razana da ganinta,hankali atashe itama ta miƙe tsaye tana kallonshi ido cikin ido, Gaba daya fa kowa na falon ya miƙe yana kallon ikon Allah,duk atunaninsu uncle din nasu ya kamu ne shiyasa ya firgita da ganinta, jikinshi har kerma yakeyi wurin nunata da hannunshi,ƙoƙari yake yi ya ambaci sunanta amma sam ya kasa faɗin sunan,saboda ya kakare mashi,wata irin zufa ce ta shiga gangarowa daga gafen fuskarshi,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba, Adai dai wannan lokacin Sgr da Marshal Omar suke saukowa down stairs atare,Omar ne agaba jikinshi sanye da shadda maroon colour,yayin da Sgr ke sanye cikin riga da wando na lallausan voile baƙi,wa'iya zubillah wato tsayawa bayyana irin yarda yadin yayi mashi kyau ma 6ata baki ne,don zan iya karashe littafin nan gaba ɗayanshi wurin kwatanta haɗuwar da sgr yayi acikin boyel ɗin wanda akai ma dinkin Senator style,irin style din da rigar bata karasa kaiwa gwiwa ba yayin da wuyan ke a matse sannan hannun rigan ya dan wuce gwiwar hannunshi kadan,yayin da takalman kafarshi da agogon hannunshi duk launi ɗaya ne da boyel ɗin jikinshi,bai sanya hula ba akanshi,sai dae ya ɗaure sumar kan tashi,a tsakiyar kanshi,hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mashi ba,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fitowa daga saƙo da lungu na jikin kowannan su,fuskar nan tashi kamar ya aza mata makeup saboda tsabar kyan da tayi,yadin ba ƙaramin fito da hasken fatar shi yayi ba,yayi fari sol dashi,kamar asace don kyau,yarda kasan diamond haka ya koma,tauraro mafi haske acikin taurari. cike da wannan tafiyar tasu ta majiya karfi suka ƙarasa saukowa daga saman benen, Adai dai lokacin wayar Omar ta shiga ruri,hannu ya zura tare da curota daga cikin aljihun wandon shaddarshi,ganin sunan major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi picking call ɗin ya kara wayar a kunnan shi tare da cewa"kun ƙaraso ciki ne? On the other hand major yace"Eh,yalla6ai yanzu haka mun ƙetaro babban gate din gidan tare dasu,yayi maganar yana kallon su hosana dake zaune a back seat ta cikin mirror din gaban motar,fuskokinsu dauke da farin ciki yau zasu ga Sehrish ɗinsu, Omar yace"Okey,ka shigo dasu kawai,"yana fadin hakan ya katse kiran sannan ya bi bayan Sgr suka ƙarasa cikin main palour din. *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*, "Meya faru Abba"? Marshal Omar ne yayi mashi tambayar yayin da yake kallonshi kafin ya mayar da idanunshi kan Abusufyan dake tsaye duk a rikice,tsayawa Sgr yayi tare da goya hannayenshi asaman wide chest ɗinshi,tunda ya ƙaraso wurin idonshi na akan Sehrish da abusufyan dake atsaye cikin wani yanayi ita Sehrish a tsorace shi kuma Uncle abusufyan duk a firgice, Fuskar Abbansu aruɗe yace"nikaina bansan meke faruwa ba,uncle ɗinku ne tun da yayi arba da yarinyar nan duk yabi ya rikice,ya rasa natsuwarshi,"ya ƙarasa maganar yana yi mashi nuni da Sehrish, Matsawa Omar yayi tare da dafa kafaɗar Abusufyan yace"Uncle meya faru ne?ko kasanta ne"?    Shiru Uncle sufyan yayi batare da yace komai ba amma duk yanayin shi ya canza sosai,idanunshi har lokacin suna akan Sehrish kamar yarda itama take kallonshi,   Suna cikin wannan yanayin kowa ya miƙe tsaye,   Major yayi sallama,Omar ya bashi iznin shigowa daga ciki,   6oyewa jahad da hosana su kayi a bayan major saboda fargabar haɗuwa da dangin ya Omar ɗinsu, ..murmushi Marshal ya saki yana hangen ƙafafuwansu, Zuba ido kowa yayi yana jira yaga su wanene waɗannan dake ta 6oyewa,kowa ya mayar da hankalinshi akan Major dake tunkaro su, Koda major ya ƙaraso wurinsu,sae yace"Jahad hosana ku fito ga ƴar uwarku nan,"   Jin haka yasa su yin hanzarin fitowa daga bayanshi,   Tashin hankalin da ba'a sama shi date,   Waro ido waje su fawan su kayi suna kallonsu,tun daga Ayaan jahan,irfan khaleed da jabeer da kuma kanal yousouf kowannansu ya gama kiɗima da wannan abun al'ajabin,kowa ya gaza buɗe baki yayi magana,kallonsu kawai sukeyi,idan suka kalli Jahad da hosana sae su mayar da idanunsu kan Sehrish,   Tsayawa sukayi daga bayan sehrish,basu da tabbacin cewa itace amma ransu na basu hakan,   Atare suka haɗa baki wurin ambaton Sunanta,   "SEHRISH" Gabanta ne taji ya faɗi rassss,a firgice ta juya bayanta don taga su wanene suka ambaci sunanta,zuba masu ido sehrish tayi tana kallonsu,lokacin da ta juyo suka tabbatar da cewar itace rishi ɗinsu,wani irin farin ciki ne ya cika su,jiki na rawa suka tunkareta zasu rungumeta,abun mamaki sae suka ga tana ja da baya baya fuskarta da alamun tsoro tace"su wanene ku!ni bansan ku ba,dan Allah kada ku matso kusa dani,"   gabansu ne suka ji ya faɗi rass,nan take kuma idanuwansu suka cika tab da kwalla,   Muryar jahad na rawa tace"sehrish,ashe zamu sake sanyaki acikin idanuwanmu?mun rasa ki a lokacin da muke tsananin buƙatarki,ba mu ta6a tunanin cewa zamu ƙara haɗuwa dake ba,sae gashi Allah ya ƙara haɗamu.., "Sehrish.......'hosana ce ta ambaci sunanta,   Zuba ido kowa yayi yana kallon Wannan ikon Allah,   Girgiza kai sehrish ta shiga yi jikinta na rawa tace"Ni...ban..sanku ba..dan Allah ku daina kiran sunana,banason ji,"   Fashewa da kuka sukayi su biyun jin abunda tace masu,   "Omar kun barmu acikin duhu,!dan Allah ku sanar damu ina aka samu waɗannan twins ɗin!"Abbansu ne yayi maganar yana kallon Marshal, Abusufyan kuwa tunda yayi arba da Jahad da hosana ga kuma sehrish,batare da sanin kowa ba,yabar wurin izuwa bedroom ɗin da ya sauka,wani irin matsanancin ciwon kaine ya taso mashi,ga wani zazza6i daya lullu6e shi lokaci guda ya rasa in da zai tsoma ranshi,abun ya gama gigita shi, Gyaran Murya Omar yayi kafin ya soma magana anatse yace"Abba waɗannan twins ɗin da kake gani,sune yaran da nake baka labari,mun haɗu dasu a asibiti cikin mawuyacin hali,na taimakesu a wannan lokacin har na kawosu gidan Uncle abusufyan don su cigaba da rayuwa acikinshi,tun da nake dasu ba mu ta6a tattaunawa agame da danginsu ba,saboda tun lokacin da na fara haduwa da su sun sanar dani su basu da kowa,bayan nakawo su gidan uncle abusufyan aranar dana fara ganin Yarinyar nan sehrish,abun ya ɗaure mun kai ganin kamanninsu iri ɗaya sak da yaran da nake ruƙo a wurina,nasha tambayar sehrish ko tana da ƴan uwa don in bugi cikinta inji ko tana da alaƙa da yaran dake wurina,amma sae tace mun ita bata da kowa,daga baya na dinga tunanin cewa kodai son da nake ma Jahad da hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan ta yarinyar,amma abun da ya faru jiya ne ya tabbatar mun da cewa Bani kaɗae ke ganin kamanninsu ba,junaid yaje ɗaukar sehrish lokacin da aka tashe su daga school,cikin rashin sani ya ɗauko Jahad!amaimakonta ya kawota cikin gidan nan....! Tunda Omar ya soma magana kowannansu ya kasa kunne yana sauraronshi,fuskokinsu da alamun mamaki sosai,   "Jahad hosana da kuma sehrish,uwarsu ɗaya ubansu ɗaya,su ƴan Uku ne!na jima ina mamakin Yarda Allah ya haɗasu dukkansu a ƙarƙashin kulawar family dinmu,ni na haɗu dasu hosana a wani hali na rayuwa na taimakesu na kawosu gidan Uncle abusufyan,yayin da Sehrish aiki ne ya kawota cikin gidan nan.....'   Yana kai ƙarshen maganar Abbansu yace"Amma Omar abun ya ɗaure mun kai wlh!taya akai duk hakan ya faru?   matsawa Omar yayi wurin da su hosana suke tsaye suna faman sharar kwalla saboda ganin yarda sehrish ɗinsu ta nuna batasan su ba,duk murnar da suke tayi ta koma ciki,   Ruƙo hannun Jahad yayi cikin sanyin murya yace"Jahad,ki faɗa masu yarda akai kuka rabu da ƴar uwarku,har tsawon wannan lokacin baku atare,"   Daƙyar jahad ta Iya bayyana masu dukkan abunda ya faru,tun kafin zuwan sehrish aiki,har abunda yayi silar rabuwarsu da ita,da kuma wahalar da suka sha kafin Allah ya haɗasu da Marshal Omar,   Wani irin tausayinsu ne ya kama matasan gidan,jikin kowa yayi mugun sanyi,hatta Sgr dake tsaye yana kallonsu ba ƙaramin tausayi suka bashi ba,yaran sun sha wahala sosai,   "Amma Omar meyasa tun farko baka faɗamun komai agame dasu ba?ae da tuni mun haɗasu da ƴar uwarsu wuri guda sunyi rayuwarsu,"acewar Abbansu muryarshi tamkar zaiyi kuka yayi maganar,dama shi akwai tausayi Omar yace"Abba,nima naso nayi hakan,kayi haƙuri da rashin sanar maka da banyi ba,amma yanzu gasu nan na kawo maku su,kuma ina fata zaku kar6esu hannu bibbiyu kamar yarda kuka kar6i ƴar uwarsu sehrish,!!!   Hankali tashe sehrish tace"Ni ba ƴan uwana bane ya Omar,wlh bansansu ba,bansan su wanene su ba,dan Allah kada ku haɗa ni dasu,bansan ganinsu,bazan iya rayuwa wuri ɗaya tare da su ba,' Wannan kalaman na sehrish yasa kowannansu kallonta cike da mamaki,ƙiri ƙiri ga abu ya fito zahiri amma ta nuna cewa ba ƴan uwanta bane!bayan sunji cewa saboda su ne tazo aiki agidan don ta samu kudi,"   "Rishi mune ba ƴan uwanki ba!sehrish yau da kanki kike faɗin hakan!dan Allah kidaina cewa haka,wlh zuciyata zata iya bugawa na mutu....'jahad ce tayi maganar yayin da idanunta ke fitar da wasu zafafan hawaye masu ɗumin gaske, ..hosana tace"sehrish kin manta ni nima?kin manta hosanarki da kika bari kwance gadon asibiti bata acikin hayyacinta"?muryarta asanyaye tayi maganar,   gaba ɗaya sun rikita sehrish,ko son kallonsu bata yi,in su kayi magana ƙara mata ciwon kai sukeyi,kamar yarda suke kuka haka itama ta fashe da kuka tana rantsuwar cewar batasan su ba, tashin hankali! Sai lokacin kanal yousouf yace"Ina azmee take ne?fawan kaje ka kira mana ita,ina da tabbacin cewa tasan wani abu game da yarinyar nan,tunda tafi kusanci da ita,zai iya yiyuwa akwai wani abu da ta ta6a sanar mata,'   Fawan ya amsa mashi da toh,sannan cikin sauri ya wuce sashen su azmee don ya kira ta,   Ganin yadda su Hosana da jahad ke ta kuka yasa Abbansu junaid cewa"Ku zo nan,"   Hannunsu cikin na juna suka ƙarasa wurinshi,   bin fuskokinsu yayi da kallo na wani lokaci,kafin ya sanya tafin hannayenshi yana goge ma hosana hawayenta,cikin lallashi yace"kudaina kuka ya isa haka,kada ku sa damuwa aranku,yanzu lokacin farin ciki ne,tunda ƴar uwarku tana atare daku yanzu kuma insha Allah,babu wanda zai ƙara rabaku da ita,"   Cikin shessheƙar kuka jahad tace"Amma ta nuna batasan mu ba ai,"   Abba yace"kada ku damu da wannan,wasa take yi maku,zuwa anjima zata dawo dai dai ne,' "Rishi ba wasa take mana ba,"acewar hosana,bayin Allah gaba ɗaya duk zazza6i ya lullu6esu,   Tunda fawan ya sami azmee aɗakinta,ya sanar da ita game da bayyanar ƴan uwan sehrish,farin ciki ya cikata ta shiga faɗin"Alhamdullillah,Alhamdulillah" Jiki na rawa ta biyo bayan fawan suka nufo falon,   Tunkan su ƙarasa ciki take hangensu Jahad da hosana dake tsaye agaban Abbansu junaid,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,yanzu ta ƙara tabbatar da cewar Dagaske ne!sehrish tana da ƴan uwa,kuma su ƴan ukune,hakan na nufin cewa Sehrish ba ƙarya tayi mata ba,   Tana ƙarasowa sehrish ta nufeta tare da faɗawa jikinta ta rungumeta tana kuka tana cewa"Aunty azmee ni bansan su wanene waɗannan ba masu kama dani,sunce wae sun san ni,bayan ba haka bane,ni bani da wasu ƴan uwa,'bubbuga bayanta azmee ta shiga yi tana lallashinta,   "Azmee muna sauraronki,ko akwai wani abu da kika sani game da ƴan ukun nan!kunfi kusanci da Sehrish nasan cewa dole akwai wani abu da ta ta6a sanar maki agame da rayuwarta,"   Marshal Omar ne yayi maganar, Azmee tace"Sehrish bata ta6a sanar dani wani abu game da rayuwarsu ba,amma ina da masaniya akan Ƴan uwannan nata........'gaba ɗaya azmee ta sanar dasu,yarda sukayi da sehrish tun farkon zuwanta,da kuɗin da ta nema awurinta na biyan kuɗin aikin hosana,duka kaf ta kwashe ta sanar dasu,   "A lokacin ni da kaina,na kar6i acct numbar likitan da yake kula da ƙanwar tasu,na tura mashi kuɗi dubu ɗari tara na aikin yarinyar,acikin kuɗaɗen dana jima ina tarasu na albashina da kuma wanda kuke bani don inyi hidimar kaina....'   Tunkan ta ƙarasa maganar Sgr ya dakatar da ita da hannunshi,   Sai lokacin ya samu damar buɗe bakinshi yace"Meyasa baki sanar da waninmu game da waɗannan yaran ba!bayan ta sanar dake halin da ƴan uwanta suke ciki?sannan waya baki iznin bata kuɗi har 90k batare da sanin kowa ba?kuma kika hana ta zuwa ganin ƴan uwanta saboda kunyi yarjejeniyar zatayi aiki acikin gidan nan harna tsawon shekara ɗaya da rabi,Why AZMEE!?   Hankalin azmee ba ƙaramin tashi yayi ba jin tuhumar da sgr yake yi mata, "Ba laifina bane Rafayet!duk wani abu daya faru nayi ne saboda sehrish!bakomai ne yajawo hakan ba face tsoron kar asirinta ya tonu ku gane cewa ita mace ce ba namiji ba,Abban ku ya nemi mai aiki namiji,amma sai ga sehrish tazo aiki amatsayin namiji,dagani harku babu wanda yasan cewa ita mace ce ba Namiji ba,Ni ce na fara gane cewa ita mace ce,akwai wata rana da naje kiranta don muyi aiki,anan na same ta akwance babu gashin bakin nan da take sanyawa ga kuma dogon gashi akanta hakan ya tabbatar mun da cewa ita mace ce ba namiji ba,koda na sanar mata cewa nagane ita mace ce,a lokacin ta dinga roƙona akan na rufa mata asiri batason kowa ya sani,saboda sanin halin matasan gidan nan da nayi na rashin son ganin mace acikinsu,kuma ga laifin ƙaryar da tayi na zuwa a matsayin namiji,wannan ne dalilin dayasa na rufa mata asiri ban sanar ma kowa ba,daga baya kuma bayan kowa ya gane cewa ita mace ce,naso nayi mata maganar ƴan uwanta amma sehrish sai ta nuna mun cewa ita bata da wasu ƴan uwa aduniyar nan ita kaɗaice........'tun daga farko har ƙarshe azmee ta sanar dasu dukkan wani abu daya faru tsakaninta da sehrish akan maganar ƴan uwanta,da kuma abunda junaid ya sanar da ita na wayarshi da sehrish take ɗauka a 6oye tana kiran ƴan uwanta,komai ta sanar dasu,   Gaba daya sun gamsu da bayananta,duk da basu ji daɗin halin da ƴaran suka kasance aciki ba,sun so ace tuntuni sunsan da zancen,da tuni sun jima da kasancewa a wurinsu,   Jin takun tafiya yasa suka ɗan juya don ganin wanene,Hajiya azeema ce ta fito daga masaukin da ta sauka,ta ca6a ado,wurinsu ta nufo tana tambayar lafiya? mai ya faru ta gansu atsaitsaye cirko-cirko?   Koda ta ƙaraso cikin babban falon karaf idanunta suka sauka akan Jahad hosana da kuma sehrish dake manne da azmee taƙi sakinta,saboda halin da take ciki,   Cike da mamaki tace"Ya hossein!su wanene waɗannan ƴan ukun masu masifar kama?ƴa'ƴan wanene?   Abba yace"wannan wani case ne da muke tattaunawa akanshi,shiyasa kika ganmu atsaitsaye,zan sanar dake komai bayan mun dawo daga sallar magrib naga lokaci ya ƙarato,"   Ya ƙarasa maganar tare da kallon azmee yace"Ki wuce da sehrish ɗakinta,sannan waɗannan ƴan uwan nata ki sama masu ɗakin da zasu zauna kafin mu dawo daga sallah,"   Omar yace"a'a Abba banaso arabasu,yaran nan sun kwallafa rai akan ƴar uwarsu,jiya saboda murnar jin cewa tana a gidan nan,ko bacci basuyi ba,kuma basu ci abinci ba,saboda sunyi alƙawarin cewa atare da ƴar uwarsu zasu ci abinci,don haka inaso a haɗasu ɗaki ɗaya da ita,kuma ashirya masu lafiyayyen abinci suci tare da ita,ko tana so ko bataso," Jinjina kai Abba yayi tare da cewa"Shikenan,hakan ma yayi Azmee ki tabbatar da kin haɗasu wuri ɗaya tare da ƴar uwarsu,"   "Insha Allah zanyi hakan,"ta amsa mashi,sannan ta kalli su jahad da hosana tace"ku biyoni mu tafi," tayi maganar tare da ruƙe hannun sehrish dake ta faman faɗin bataso bataso a haɗata ɗaki ɗaya dasu,ahaka suka wuce bedroom ɗinta,   Bayin Allah,duk sunji sun tsani kansu saboda juya masu bayan da sehrish tayi,duk irin ɗoki da murnar ganinta da sukeyi amma ta nuna batasan su ba,kamar wasu bare haka take kallonsu,haƙiƙa zuciyoyinsu ba ƙaramin karaya sukayi ba,    Bayan azmee ta tafi dasu Jahad,anan su abba suka tsaya suna ƙara tattaunawa atsakaninsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,lamarin ya rikirkitasu,bakomai yafi tsaya masu aransu ba,face yarda Sehrish ta nuna batasan ƴan uwanta ba,bayan ga shaidunan sun bayyana karara nacewar ƴan uwanta ne su,kome yasa haka!? "Wai ni ina Uncle abusufyan yake ne!ko kun lura da yanayin da ya shiga lokacin da yayi tozali da Sehrish!"Khaleed ne yayi maganar yana kallon fuskar Abban nasu,   Fawan yace"Nima nayi mamakin razanar da naga yayi lokacin daya ganta,"   Jahan yace"ku ka sani ko kwalliyar da tayi ne,yasa ya tsorata da ganin kyawun fuskar.....'bai ƙarasa maganar ba saboda kallon da Sgr yayi mashi,tsit yayi da bakinshi,   "Gaskiya bana tunanin haka jahan,!sae dae wani abun na daban ne yasa shi firgita,"acewar Ayaan,kowa dae da abunda yake tunani acikin ranshi,   Marshal Omar yace"Kowa ya wuce yayi shirin sallah,kafin a fara kira,"   Amsa mashi sukayi da toh,sannan suka kama gabansu kowa ya nufi room dinshi,jikinsu duk a mace,sun jima basuji tausayin wani ɗan adam ba kamar yarda sukaji tausayin su sehrish,sun tausaya masu sosai ganin irin halin rayuwar da yaran suka shiga,   Bayan tafiyarsu,falon ya rage daga Abbansu sai Omar da Sgr sai kuma kanal yousouf,    "Ni fa ina zargin Uncle Abusufyan abba!kamanninshi da yaran nan yayi yawa abun is over,komai na fuskarsu irin nashi ne!kuma tun daga kan yarda ya firgita da ganin sehrish yasa na tabbatar da cewa akwai wani abu aƙasa,bayan wannan kuma akan idona uncle abusufyan yabar wurin nan agigice jikinshi na rawa ganin ƴan uwan yarinyar nan,ya kamata muje muga a wane hali yake ciki,sannan kuma muji dalilin dayasa ya razana da ganin yaran,"!   Jinjina kai Abbansu yayi jin abunda kanal yousouf yace,Tabbas ya yarda da maganarshi,don shi kanshi ya lura da halin da ƙanin nashi ya shiga,yana son jin meyasa shi firgita da ganin yaran!   Batare da 6ata lokaci ba,Suka nufi ɗakin Abusufyan atare, Lokacin da suka tura ƙopar ɗakin nashi suka shiga ciki,samunshi sukayi zaune dirshen a ƙasa gefen gado yana ta faman sharar hawaye hannunshi dafe da kanshi,sae faman sambatu yakeyi shi kadae, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,musamman Abbansu,da sauri ya ƙarasa wurinshi,tare da zubewa kasa daga gefenshi yace"abusufyan meya same ka ne!meya faru!me yasaka zubar da hawayenka har haka ne?dan Allah ka faɗamun wlh hankalina ya tashi sosai........'gaba daya duk ya ruɗe ganin halin da abusufyan ke ciki,   Daga gefen gadon Sgr da Omar suka zauna suna kallonsu,yayin da kanal yousouf yake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,turo ƙopar aka kumayi,Hajiya azeema ce tabiyo bayansu, "Subhanallahi Meya faru ne!naga Abusufyan na kuka?wani abu ya sameshi ne"?fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar ayayin da take ƙarasawa ciki ta samu wuri saman stool na gaban dressing mirror ɗinshi ta zauna tana fuskantar su, gaba daya suka haɗu suna tambayarshi dalilin yin kukan nashi, Sai faman share hawaye yake yi,ya gaza buɗe baki yayi magana,   "Uncle dan Allah kadaina kukan nan,duk ka sanyamu acikin damuwa,idan akwai wani abu dake damunka dan Allah ka sanar damu,koda bamu da maganin damuwar taka,zamu taya ka da addu'a akan Allah ya yaye maka ita,"Marshal omar ne yayi maganar cikin tausasa murya, Hajiya azeema tace"Ƙanina dan Allah ka sanar damu mana,meyasa ka ware kanka anan kana kuka kai kaɗae kamar wani ƙaramin yaro?mu fa nan danginka ne wanda baka da kamarsu aduniyar nan,dan haka kada kaji komai ka faɗa mana damuwarka insha Allah,zamu nemi mafita atare,'   ɗagowa yayi da idanuwanshi wadanda sukayi jawur suka kumbura saboda kukan da yasha ya kalli yayan nashi la66ansa na kerma yace"ƴa'ƴana yaya,Su ne damuwata,saboda su ne nake zubar da hawayen nan,na cuci rayuwarsu akan idona rayuwarsu ta wulakanta batare da na ɗauki mataki ba.........'   Hankali atashe Abba da Azeema suka haɗa baki wurin cewa"Ƴa'ƴa kuma!wasu ƴa'ƴa kake magana akai kenan!"   ganin yarda suka razana da jin maganarshi yasa jikinshi yin sanyi dama yasan dole suyi mamakin jin cewa yana da ƴa'ƴa, Sgr da Omar kuwa shiru sukayi suna sauraran abunda Uncle ɗin nasu ke cewa,   Jin yayi masu shiru yasa ran Abban nasu 6aci a fadace yace"ba zaka buɗe baki kayimana magana ba! Sam ya rasa ta yarda zai fara sanar dashi game da ƴa'ƴan da yake magana akai,tsoranshi karya ƙi amincewa da zancen shi,yana fargabar abunda zai biyo baya in ya sanar dasu cewa yaran nan ƴa'ƴanshi ne,   "Kai nake sauraro abusufyan!ka sanar mun akan wasu ƴa'ƴa ne kake magana!'wannan karan a rikice abba keyi mashi magana,   cikin sanyin murya Abusufyan yace"Yaya hossein,ina magana akan ƴa'ƴana ne,waɗanda na haifa,na haifi ƴa'ƴa batare da saninku ba...........' A razane abbansu junaid ya miƙe tsaye yana kallonshi yace"What!!abusufyan kai da kanka kake faɗamun cewa kana da ƴa'ƴa naka na kanka!?Anya ba kunne na ne ke jiyomun ba dai dai ba,"yayi tambayar fuskarshi da alamun ruɗu acikinta, jiki na rawa abusufyan ya miƙe tare da ruƙo hannun abban acikin nashi yace"dan Allah ka zauna yaya,zanyi maka bayanin komai,tabbas dagaske ne ina da ƴa'ƴa abba,kuma suna nan araye,jini na ne su,'   dafe kai Abba yayi saboda wani irin jiri daya ji yana niyar kwasar shi,dakyar ya iya buɗe baki yana ambaton"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!abusufyan ka cuce mu Kuma ka yaudare mu ka zubda ƙimar family dinmu!ashe dama abunda ka aikata kenan shiyasa ka gudu kabar ƙasar nan!?saboda kayi ma wasu ciki kana tsoran asirinka ya tonu shine ka tattara kabar ƙasar nan!"ƙarasa maganar yayi yayin da hawaye ke gangarowa daga cikin idanunshi,abun ba ƙaramin gigita su yayi ba gaba dayansu,basu ta6a tunanin cewa abusufyan dinsu zai iya aikata wannan mummunan abun ba, A faɗace yaci gaba da magana"ka faɗamun gaskiyar lamarin tun kafin ranka ya 6aci!tun yaushe wannan abun ya faru baka sanar mun ba!wacece ko kuma suwa kayi ma ciki har aka haifa maka ƴa'ƴa!kuma ina ƴa'ƴan suke,   gaba ɗaya abusufyan yasha jinin jikinshi ƙoƙari yake yayi mashi bayani amma  ya kasa, Marshal Omar ne yace"Abba,pls mubi komai asannu har mu samu uncle  ya warware mana komai,Ni ina da tabbacin cewa Uncle abusufyan bazai ta6a aikata abunda muke zarginshi dashi ba,dole akwae wani dalilin.   Girgiza kai Abbansu ya shiga yi ranshi atsananin 6ace yace"Kabarni Kawai Omar,abusufyan ya gama da mu,bansan iya zunubin da ya aikata ba,da yasa harya gudu yabar ƙasar nan tsawon lokaci, Amman tunda ni bazai sanar dani gaskiyar Lamarin ba, bari na kira Ammi a waya na sanar da ita abunda ya aikata,may be ita zai iya yi mata bayani tunda ni bazaka faɗamun ba!"   Yana ƙarasa maganar ya zura hannu acikin aljihun wandon shi yana ƙoƙarin curo wayarshi don ya kira ammi,   Cikin sauri abusufyan ya ruƙo hannunshi muryar shi har kerma takeyi wurin cewa"ya..ya hossein ka saurareni dan Allah,ina ƙoƙarin na fahimtar dakai ne,muddin ka sanar ma ammi wannan maganar zan tattara kayana nabar gidan nan ne!saboda bazata ta6a fahimtata ba,kamar yarda kai zaka fahimceni.......'   jikin Abbane yayi sanyi ganin yarda Abusufyan ke ta faman zubar da hawayenshi,   Sassauta muryarshi yayi cikin lallami yace"ka sanar dani Abusufyan!taya akai ka samu ƴa'ƴa"?   Hannuwanshi duka biyun yasa ya rike kanshi da yake jin kamar zai fashe,ga wata uwar zufa da ke zubo mashi har ta jika wuyan shaddar jikinshi,sai faman girgiza kanshi yake ya rasa ta ina zai fara komae ya dagule masa,da ka kalle shi zaka fahimci bai cikin hayyacin shi,    Kanal yousouf ne ya dan yi gyaran murya kafin yace"Abba ni ina ganin muje muyi sallah kilan uncle zai samu natsuwa yayi cikakken bayani don na fahimci kaman bai acikin hayyacin shi ma" jinjina kai Abban yayi don shima ya fahimci hakan,ya mika masa hannu tare da cewa"taso muje muyi sallah amman in muka dawo dole kayi mana cikakken bayani" daga masa kai Uncle Abusufyan yayi alamar ya amince daga haka suka fito gaba dayansu suka nufi masallaci kowa da abunda yake sakawa a ransa. Zamu so muji yarda wannan al'amarin ya faru,taya akai abusufyan da bai ta6a aure ba ya samu ƴa'ƴa',taya akai yayi aure batare da sanin Danginshi ba?suwaye ƴa'ƴan nashi da yake magana akai,amsoshin duka wadannan tambayoyin na a bakin Abusufyan,batare da 6ata lokaci ba zamu nutsa cikin labarin da Abusufyan zai ba yayan nashi hossein da zarar sun dawo daga masallacin. A6angaren su Sehrish kuwa,tunda azmee ta shigar dasu hosana da jahad a ɗakinta,gaba ɗaya ta takure kanta saman gado,jikinta sae kerma yakeyi ko son ganinsu bata yi,hakan ba ƙaramin raunata zuciyoyinsu yayi ba,zuba mata ido kawai sukayi suna kallonta yayin da hawaye ke zuba a fuskokinsu,a gefen gadon nata suka zauna,   Jahad tace"banta6a tunanin cewa zakiyi mana haka ba sehrish,nayi tunanin zakiyi murnar ganinmu bayan tsawon lokaci da bamu haɗu ba,amman sae gashi kin juya mana baya,agaban mutane kika nuna cewa baki san mu b....!"   Tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta kwatsa mata tsawa tana cewa"Karki ƙara yi mun magana!ni ko muryoyinku bana son ji wlh,bansan su wanene ku ba,kawai kunzo don ku takura ma rayuwata ne..,...'   Cikin shessheƙar kuka hosana tace"dan Allah sehrish ki daina faɗin hakan!bana jin daɗi,meyasa zakiyi mana haka?Yanzu kin manta da hosanarki?ga kuma jahad?rishi dan Allah kidaina yi mana wannan wasan,' Hannu sehrish tasa tare da toshe kunnuwanta alamar bata jin ma abunda suke cewa........'     Duk wannan budurin da akeyi Hayaam na kumshe aɗakinta batasan meke wakana ba,tsoranta karta fito su haɗu da Babban yaya awaje,don tasan muddin yaganta acikin gidan sai yasa an wurgar mashi da ita waje,wannan dalilin ya hana ta fitowa, Amani kuwa har sun kammala kimtsawa ita da Amal zasu zo gidan,sai ga Abbas ya shigo gidan,a lokacin suna tsaye ita da Amal acikin falon gidan, tarar shi tayi tare da cewa"Kai fa muke ta jira tun ɗazu mun kammala shiryawa,"   Abbas yace"sai dai kuyi haƙuri,yanzun nan Abba ya kira ni awaya ya sanar dani cewa wani babban al'amari na faruwa agidan,inyi sauri inxo Suna jira na,bana tunanin cewa suna yin wannan walimar ma,"   Jiki asanyaye tace"Allah yasa dae ba wani abunne ya faru ba,bari mu hakura to in komai ya dai dai ta munje,"daga haka Abbas ya shige ciki yayi abunda zai yi ya fice.   Wannan ne abunda ya hana su Amani zuwa gidan, Bayan sun kammala Sallar magrib,atare suka dawo a nan babban falon suka Hallara gaba ɗayansu banda Azmee da Hayaam da kuma su Sehrish,a lokacin Shima C.g Abbas ya ƙaraso gidan,kowa ya samu wuri ya zauna,Su fawan jabeer da kuma Irfan suna zaune a 3 seater,Abbansu tare da Uncle abusufyan suna zaune asaman 2 seater,Omar kuma tare da Sgr da Kanal yousouf suna xaune ne aɗayar 3 seater ɗin,Abbas da khaleed suma suna zaune asaman 2 seater,sai Aunty azeema dasu jahan kowanne na akan one seater, Gyaran murya Abba yayi tare da kallon Abusufyan dake zaune zugudum agefenshi yace"kamar yarda ka buƙaci mu hallara gaba ɗayanmu a falo,gashi nan duk mun haɗu a wuri ɗaya kai muke sauraro," Nannauyar Ajiyar zuciya Abusufyan ya sauke kafin ya soma magana calmy yace"abunda yasa nace ku haɗu ku dukan ku wuri ɗaya,saboda inaso in bayyana maku cewa ina da ƴa'ƴa,kuma ƴa'ƴan nan na same su ne ta hanyar daya dace,Banaso wani ya zargeni ne da laifin aikata zina,wlh ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,ban ta6a kasancewa tare da matar da ba muharramata ba ina nufin ba matata ba.......'   Shiru yayi na ɗan wani lokaci alamar yana nazarin wani abu,duk suka kasa kunne suna sauraron shi,kowa burinshi yaji taya akai Abusufyan ɗinsu ya samu ƴa'ƴa,kuma suwaye ƴa'ƴan nashi!? "Shekara ashirin da ƴan kai da suka gabata,mun samu sa6ani da Ammi saboda rashin jin maganata,babu jituwa atsakanina da ita,bakomai yake haɗani da ita ba,face irin rayuwar dana taso inayi,abota da mata,na maidasu tamkar maza awurina yarda nake friendship da mata ko maza bana kulawa haka,wannan abunne ke 6ata mata rai,saboda ta tsani ta ganni tare da ƴan mata,ko in aka bata labarin cewa anganni tare da mace acikin mota,nan fa hankalinta zai tashi,a ƙarshe data rasa yarda za tayi dani shine,ta tattara mun kayana gaba ɗaya tace in koma Kano wurin ƙanwarta Hajiya Ameena inci gaba da zama acan,saboda nafi ƙarfinta ba zata iya dani ba don ta lura kaina rawa yakeyi,amma tana da tabbacin cewa in na koma wurin ƙanwarta zan shiryu in dawo dai dai, Wannan ne farkon abunda ya rabani da gidanmu na koma wurin goggon mu da zama gaba daya,don ta gyaramun tarbiyyata kamar yadda ku su yaya hossein kuka sani,maimakon hakan sai ta sangarta ni saboda tsananin son da takeyi mun wanda ko ɗanta a wannan lokacin bata nuna mashi irin son da takeyi mun,komai nakeso shi takeyi mun,wankane kawai ba tayi mun,idan nayi laifi kuwa ko na janyo faɗa awaje rufe ido takeyi taita zazzaga masifa kuma tana sane cewa ni ne mai laifin,in mun shiga gida tayi ta lallashina tana bani haƙuri, TUSHEN LABARIN, Alhaji nuraddeen mai dala,hamshaƙin mai kuɗi ne kuma attajirin gaske,na bugawa a jarida,babban ɗan kasuwa ne wanda yayi kaurin suna a harkar kasuwancin saye da siyarwa atsakanin ƙasashe daban daban,haifaffen garin zariya ne,kuma yana ɗaya daga cikin Aminnan Salahuddeen,aiki ne ya kawo shi katsina kafin daga baya lokacin daya fara kasuwanci ya yanke shawarar komawa garin kano da zama saboda kasuwancinshi yafi ƙarfi acan,wannan dalilin ne yasa shi tattarawa ya dawo gaba ɗaya da zama anan kano tare da iyalanshi a katafaren gidanshi dake a unguwar Nasarawa g.r.a anan jihar kano,farkon haɗuwarshi da hajiya Amina kanwar Ammi wato goggon katsina,tun lokacin da suka je ɗaurin auren Salahuddeen da Ammi a jihar yobe damaturu,acan ya ganota ya ƙyasa,basu baro wurin ɗaurin auren ba sae da aka shafa fatiharsu su duka biyun a lokaci guda, Yaronsu ɗaya wanda sai da sukayi aure da jimawa kafin Allah ya albarkace su dashi,ba kowa bane wannan face Dr haris babban likita,shine ɗa ɗaya tilo da suke dashi,kafin Ammi ta mallaka mata Abusufyan don tagyara mata tarbiyarshi,sae suka kasance su biyu ne ƴa'ƴan dake a wurinta,ɗanta da kuma ɗan yayarta abusufyan,tom da kuma jerry,don gaba ɗayansu basa jin magana a wannan lokacin,ƴan abi yarima asha kiɗane,atare suke fita yawon dare,sun iya zuwa club a haɗu da ƴan mata ayita rawa,zuwa wurin party kuwa koba a gayyace su ba sai sunje,wannan shine rashin jin da ammi ta tsana na abusufyan,shi dae haka rayuwarshi take baida burin daya wuce afita yawo tare da ƴan mata akashe masu kuɗi,kullum yana manne dasu,shi dai kawai yaji mace akusa dashi ba namiji ba,kuma bawai don yayi wani abu da ita ba,sam shi wannan bai agabansa, Ana haka su Abusufyan suka samu hutun makaranta,atare da dr haris suka je kai ziyara zariya wurin danginsu, Bayan tafiyarsu ne,Hajiya Amina da Mijinta alhaji nuraddeen suka tafi umra,dama tun kafin su tafi alhaji ya sallami mai gadin gidansu baba buzu don yaje ƙasarsu niger ya gano danginshi kafin su dawo, Ba ƙaramin daɗi yaji ba,saboda dama atakure yake na rashin ganin ƴar shi tilo da yake da ita,kullum yana cikin damuwar rashin yarinyar a kusa dashi,saboda halin da ya barota acan,basu da kowa danginsu duk sun tarwatse ba haɗin kai,ga talauci dake damun kowannansu,ita kanta yarinyar ya barta ne a hannun matar babanshi,tunda baida kowa iyayenshi duk sun rasu,matar nan ta tsani yarinyar ta takurama rayuwarta gata irin tsoffin nan ne masu mitar tsiya,duk wani aiki yarinyar take ɗauramawa,girki,sharar gida,wanki,ɗebo ruwa,kuma ƙarama ce alokacin bazata wuce 16 years ba, Koda baba buzu yazo niger ganin gida,zuwan bazata yayi masu bai sanar ma kowa da maganar zuwan nashi ba,saboda yana so yaba Abu mamaki kuma yaga irin farin cikin da zatayi idan ta ganshi,kwatsam yana shiga gidan ya samu matar baban nan tashi zaune saman abu ta danneta a tsakar gida,yarinyar sai ihu takeyi tana wutsil wutsil da ƙafafunta,ita kuma matar sae sambatu takeyi tana cewa"Babu abunda zai hana inƙi kasheki acikin gidan nan Abu,dan ubanki ni zakiyi ma asarar tsintsiya?kin barta a ƙasa har ruwan sama ya jiƙata baki ɗauketa ba!ko don kina taƙamar ubanki ne ke turo mana da kuɗi muna siyan kayan abinci....' Hankalin baba buzu ba ƙaramin tashi yayi ba a wannan lokacin,ganin zai rasa ƴarshi ɗaya tilo akan tsintsiyar shara da bata wuce naira hamsin ba,ba ƙaramin fusata yayi ba,a ranar ko zama gidan baiyi ba ya ɗauki ƴarshi ya tafi da ita gidan wani amininshi,tamkar ya zubar mata da hawaye haka yaji a wannan lokacin,yarinyar duk ta rame ta fige ta ƙanjame kamar ba mutun ba,yarinyar da duk garinsu babu wanda ya kama ƙafarta a wurin kyau,tun lokacin da mahaifiyarta ta haifa mashi ita,Allah yayi mata rasuwa tabar mashi ita ƴar jinjira da ita,shi yaci gaba da kula da yarinyar,mutane sunsha zuwa suna nuna mashi kuɗi don ya bar musu yarinyar su ruƙe awurinsu amma yaƙi amincewa da hakan,saboda son da yake yi mata, Bayan hajiya Amina sun dawo nigeria ita da mijinta,Baba buzu ya shirya tafiya tare da ƴarsa abu,babu yarda abokinshi baiyi dashi ba akan ya bar mashi Abu suci gaba da kular mashi da yarinyar a hannunsu,amma ina yace ae ƙafarshi kafar abu,bazai ƙara gangancin barinta a wurin wani ba,kwara ta kasance atare dashi,yana jin motsinta a kusa dashi,zaifi samun kwanciyar hankali, Da daddare suka ƙaraso nigeria bayan uwar tafiyar da suka sha agalabaice suka iso cikin gidan,ruƙe da hannun Abu ya shigo cikin falon gidan,lokacin hajiya ameena na zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku tana kallo a tv,tun da sukayi sallama ta dago ta kellesu ganin baba buzu yasa ta saki fara'a tana cewa"marhabun lale ƙaraso ciki mutumina,ashe kana kan hanya banyi tsammanin zuwan.....'bata ƙarasa maganar ba,saboda ganin yarinyar dake ruke da hannunshi, .mikewa tayi tare da zame farin glass ɗin dake a fuskarta tace"baba buzu wannan yarinyar fa?yar waye kazo da ita,"   bai bata amsa ba,sae da suka ƙarasa wurin kujerar da take tsaye,suka zauna kasa saman carpet,sannan ya soma magana"hajiya shannunku da dawowa,ya gajiyar tafiya,' "Lafiyalou Alhmdulillah," Taƙarasa maganar har lokacin idanunta na akan abu,komawa tayi tare da zama saman kujerar sannan tace"bakayi mun bayani game da yarinyar nan ba,"Tayi maganar tana nuna Abu dake ƙankame jikin abbanta   Fargabarsa kada ya sanar dasu cewa ƴarshi ce,suƙi kar6arta baisan inda zai kai yarinyar ba,ya kwaso yarinya ya kawo masu batare da ya sanar dasu ba, dakyar ya iya buɗe baki muryarshi kamar zaiyi kuka yace"yarinyar wurina ce hajiya sunanta Abu,ina neman alfarmar ku taimaka mun ta zauna awurina,saboda bata da kowa acan niger,dama a hannun kishiyar babata take zaune,matar bata da imani naje na shame ta tana gallazama yarinyar nan,ban ta6a sanin abunda ke faruwa ba,sai da nayi masu zuwan bazatan nan.......'komai ya kawashe ya sanar ma hajiya ameena,   Kamar jira takeyi ya kai ƙarshen maganar tashi,nan ta rufe shi da faɗa tana cewa"Amma baba buzu ka bani mamaki wlh,yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu dakai,duk irin yarda muka ɗaukeka tamkar ɗanuwanmu,hakan baisa ka sanar damu cewa kana da ƴa ba,meyasa tun lokacin daka fara aiki agidan nan baka ɗauko yarinyar ka kawota gidan nan ba!....'ta inda take shiga bata nan take fita ba, Jin waɗannan kalaman na Hajiya ameena yasa baba buzu fashewa da kuka yana cewa"na cuci kaina da ban sanar maku ba,ban ta6a tunanin cewa zaku kar6i yarinyar nan hannu bibbiyu ba hajia,da tuni na jima da kawo maku ita,kullum ina cikin takaicin rashinta a kusa dani,saboda itace kaɗai nake gani inji dadi aduniyar nan......'sosai baba buzu ke zubda hawayenshi,   Abu kuwa ganin mahaifinta na kuka yasa itama ta fashe da kukan,jikin hajiya ameena ne yayi sanyi,tausayinsu duk ya kamata, tausasa muryarta tayi tace"baba buzu kukan ya isa hakanan,naji daɗin dawowarka musamman daka kawo mana wannan ƴar kyakkyawar yarinyar taka,kuma insha Allahu zamu bata kyakkyawar kulawa,zata zama tamkar ƴar cikina,dama kuma banda ƴa' mace,gashi inason ƴa mace,Ashe da rabon zan samu......'   Share hawayen shi ya shiga yi yana yi mata godiya,   "Yanzu abunda nakeso dakai,ka wuce ɗakinka kayi wanka zansa akawo maka abinci,nasan kun kwaso gajiya sosai kuna bukatar hutu,ita abu kabarta awurina,zan gyara maka ita sosai da anjima zata zo ta gaishe ka,"   Cikin shesshekar kuka baba buzu yace"hajiya bansan da wani irin kalamai zan gode maku ba,kunyi mun abinda bazan iya saka maku ba,kun jima kuna ɗawainiya dani kuma yanzu gashi zaku ɗauki ɗawainiyar yarinyata,Allah yasa ka maku da mafifincin alkhairinsa.....'sosai baba buzu ya shiga yi masu addu'o'i hakan ba ƙaramin dadi yayi ma Hajiya ameena ba, Tun daga wannan lokacin Abu tazama tamkar ƴa awurin hajiya Ameena,baka ta6a gane cewa ba ƴar cikinta bace saboda yadda suke ruƙe ta hannu bibbiyu duk wata ɗawainiyarta tadawo kansu,hatta makarantar islamiyya dana boko babu wanda basu sakata ba,dama yarinyar akwai hazaƙa sosai,akwai son karatun addini,kullum zaka ganta rungume da kur'ani a hannunta tana karatu,ko aiki takeyi zaka ji tana ta rero karatun haddar da aka basu,bata ta6a zama bakinta shiru batare da tana karatu ba,wannan abun ba ƙaramin burge hajiya ameena yake ba,shiyasa batajin wuyar kashe mata kuɗi,saboda ita ta ɗauko malamin da zai dinga zuwa gida yanayi mata karatu,malamin makarantar islamiyyarsu wanda suke kira da Ya sayyadi,tun da zainab tafara zuwa makarantar islamiyyar asatin farko kullum sai yazo gaishe da hajiya ameenatu,idan yazo yayi ta zuzuta zainab awurinta yana yaba irin ƙoƙarin dake gare ta,hajiya Ameenatu najin daɗin hakan,Amma mahaifin Abu,baba buzu mai gadi mutumin bai kwanta mashi araiba,ya tsani yaga malamin nan yazo wurin Abu zai koya mata karatu,shisshigin da yake yi ma yarinyar yayi yawa,kullum sai yazo da ɗan rugwagwar mashin ɗinshi ƙopar gate din gidan wurinta,hakan ba ƙaramin ƙona ma Baba buzu rai yake ba,shiru kawai yake yi don bai da yadda zaiyi ya hana shi zuwa gidan,tunda hajiya ameenatu ta ɗauke shi amatsayin malamin da zai dinga koyama Abu karatu,tun Abu na da wata daya acikin gidan haris ya dawo batare da Abusufyan ba,saboda shi yace bazai dawo ba sai daddy mijin Aunty ameenatu ya bashi haƙuri,saboda yace shi yake 6ata tarbiyyar Haris,rashin jin maganar shi yayi yawa,koda haris ya hadu da Abu acikin gidan saiya mayar da ita tamkar ƙanwarshi,idan aka bata assignment na school shike zama ya fidda mata shi,harma ya koya mata karatu. *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*, Bayan wani lokaci Tafiya takeyi tamkar batason taka ƙasa,jikinta na sanye da uniform na islamiyya,dogon hijab Brown colour har wuce guiwarta,wandon kuma milk colour,ta rufe fuskarta da nikab,yayin da hannayenta ke ruƙe da jakar makarantarta,da gudun gaske wata danƙareriyar mota ash colour ta faɗo cikin layin da take tafiya,gadan gadan mai motar ya tunkari inda Abu taja ta tsaya,waro ido waje tayi tare da ja da baya jikinta na kerma,koda mai motar nan ya ƙaraso inda take,sai ya shiga zagaye ta da motar gaba ɗaya ya tada mata ƙura,   Ƙanƙame jikinta tayi gabanta ya faɗi rass,tsoronta kar ace sace ta aka zo yi,   Sai da ya tabbatar da cewa ta gama tsorata sannan ya tsayar da motar wuri guda ta tsaya cak,   A ɗan tsorace abu ta buɗe idanunta tana kallon motar cikin ranta tana tunanin wanene wannan bawan Allahn daya firgitar da ita haka,   Bata ƙarasa zancen zucin nata ba taga ya zuge glass ɗin motar,lokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarshi sae da gabanta ya faɗi rasss!matashi ne wanda bazai gaza shekara 20 ba zuwa ashirin da daya,kana kallonshi zaka ga ƙuruciya atare dashi,jikinshi na sanye da crazy jeans sae farar t shirt agaban rigar an rubuta Am crazy,'da alama bashi kaɗae bane acikin motar,akwai wani agefen shi, Muryar mace tajiyo daga cikin motar tashi tana cewa"Hey,ƴan mata,mun tsorata ki ko?ki yi haƙuri Babyn nawa ne sae a hankali,wai kin burge shi ne,shiyasa yayi maki wannan wasan,'.     rai atsananin 6ace take kallon fuskokinsu ta cikin niqab din fuskarta,bakowa yafi bata haushi ba face shi saurayin daya yi mata wannan ɗanyen aikin,arayuwarta ta tsani mutane masu wayewa irin tasu,kallo guda tayi masu ta gane cewa ba mata da miji bane,amma sun manne ma juna acikin motar kamar zasu haɗe su zama ɗaya,    jinjina kai kawai tayi tare da zuƙunnawa ta ɗauki jakar islamiyyarta da ta fadi,cikin sauri ta kama hanyar zuwa gida,biyo ta sukayi da motarsu,hakan yasa hankalinta ya tashi,saboda gudun kada Abbanta ya ga motar dake biye da ita,don kullum yana ja mata kunne akan karta kuskura wani ya tsaidata akan hanya ta tsaya,yanzu in ya ganta tare da wannan jibgegiyar motar dake bin bayanta batasan wane hukunci zaiyi mata ba,dole ya tuhume ta akan ina ta samo su,    "Baby,kana ganin zata faɗa mana address ɗinta kuwa?da alama yarinyar kamar za tayi ji da kai nake gani,kasan ƴan islamiyyan nan,ji su keyi kamar sunfi kowa tsoran Allah,suyi ta kame kansu acikin hijabi,suna yi ma mutane kallon shaiɗanu,'matashiyar dake acikin motar ce tayi wannan maganar,kuma duk akan kunnan Abu,   Saurayin yace"ae ko bata faɗa mana address ɗinta ba,zamuyi ta bin bayanta ne har mu gano gidansu,"   Jin wannan maganar yasa,yarinyar zuƙunnawa tare da kwale takalman ƙafafunta,kafin su ankara ta watsa da gudun gaske kamar zata tashi sama,ko waiwayensu batayi,har ta 6ace ma ganinsu,,   Tun daga nesa Baba buzu mai gadin dake a zaune saman benchi yana sauraron radiyo dake ruke a hannunshi,ya hango ta sai faman tsala gudu takeyi,hankali tashe ya miƙe tsaye yana jiran ƙarasowarta,koda ta ƙaraso a galabaice ta zube agabanshi,saman guiwowinta tana faman haki,   "Abu meya faru ne naga kina gudu haka?waye ya biyo ki"? Muryar mahaifin nata ne ta dawo da ita cikin hayyacinta,   daƙyar ta iya cewa"wasu ne a mota,bansan kosu wanene ba,sae faman bibiyata sukeyi,shine na watso da gudu don karsu gane gidan da nake,"   Jin wannan maganar yasa ran buzun mai gadin ya 6aci sosai nan fa yashiga zazzaga masifa yana cewa"da kin bari sun ƙaraso don ubansu dana koya masu hankali,shikenan ba dama yarinya ta ɗan fita ɗauko karatu sae an samu wanda ya takura rayuwarta!zan yi maganin koma wane ɗan ja'irin ne yake son cutar mun dake.....'ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a ƙarshe dae yace"tashi ki shiga ciki,kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta kafin akira sallar magariba,ki kwantar da hankalinki kinji Abunah,ina nan ina jiran Koma wane ɗan iskan ne,saina koya masu hankali,'   Ajiyar zuciya abu ta sauke tare da miƙewa tayi mashi sallama,sannan ta shiga cikin gidan ta ƙopar gate ɗinsa, Lokacin da ta shiga cikin main palour ɗin gidan babu kowa,alamar suna can upstairs bedrooms ɗinsu,don haka ta wuce nata ɗakin kai tsaye, Bayan ta ajiye jakar islamiyyarta,ta cire hijab ɗin jikinta,ta ninketa tare da turata cikin wardrobe na kayanta,shaf shaf ta kammala cire kayan islamiyan nata ta wuce cikin toilet don tayi wanka, After some minutes,ta fito daga cikin toilet ɗin jikinta ɗaure da farin towel,jikin nan nata har wani ƙalli yakeyi saboda hasken fatarta ga gyaran da take sha,agaban mirror ta tsaya tana ɗaure sumar kanta mai tsayi da yawan gaske,tana da yalwataccen gashin kai wanda yakai har qugunta,tana cikin ɗaure gashin kan nan nata kwatsam taji anyi mata gyaran murya abayanta,a firgice tajiyo don ta ga kowanene,lokacin da tayi arba da mutumin da yayi mata gyaran muryar acikin ɗakinta nan take ta zazzaro ido amatuƙar tsorace take kallonshi,   kwance yake asaman gadonta,ya miƙe ƙafafunshi yayin da hannunshi ke ruƙe da brazier ɗinta da ta cire kafin tashiga toilet,sae faman latsa breast curve ɗin yakeyi cike da tsokana,   Hankali a matukar tashe abu tace"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...Nashiga uku....!'gaba daya taba ma ranta cewa al'jani ne shi,ba kowa bane wannan face saurayin nan daya tsoratar da ita da motarshi akan hanyarta ta dawowa daga islamiyya,shi da budurwarshi, Muryarta na rawa tace"wa..wanene...kai dan Allah!me kakeso a wurina ne!taya akai kasan gidan mu har ka biyoni ɗakina"?   Ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa"bani da amsar tambayoyinki,ni dai kawai nagani inaso,in kika yi mun biyayya mu rabu lafiya,koda yake bazama mu ta6a rabuwa ba,saboda kinyi mun wlh," ya ƙarasa maganar tare da kai bakinsa ya manna ma bra ɗinta kiss   Runtse ido abu tayi agigice ta fasa ihu tana neman ɗauki,akan azo a fidda mata aljanin dake aɗakinta,   Da gudu ta watsa waje babban falon jikinta na kerma ta shiga cewa"Mommy!!mommy!!ya haris!daddy!!dan Allah kuzo ku taimake ni,Aljani aɗakina saman gadona....'   Jin sautin kukan Abu yasa hankalin Hajiya ameena tashi,da saurin gaske ta sauko downstairs ta nufi wurinta tana cewa"Abu meya faru ne kike ta kwaɗa ihu? Cikin shessheƙar kuka tace"Wani ne acikin ɗakina saman gadona,bansan ko wanene shi ba,a kan hanyar dawowata daga islamiyya ya tsoratar dani da motarshi,shine yanzu kuma bayan na fito daga wanka na ganshi kwance saman gadona,'   Cike da mamaki hajiya Ameena tace"Wani kuma!acikin gidan nan saman gadonki?taya akai har ya samu damar shigowa cikin gidan nan....'   Ba ta kaiga ƙarasa maganar ba,sae ga Abusufyan ya fito daga cikin ɗakin abun,fuskarshi ɗauke da murmushi,   Ganin shi yasa abu yin saurin nuna shi da hannu tace"Ga shi nan mommy....wlh shine ..Aljani ne," murmushi hajiya Ameenatu tayi tana kallon Abusufyan tace"Son sai yau kaga damar dawowa gidan?irin wannan zuwan bazata haka?ka tafi kabarmu da kewarka ko?ko tunanin makaranta bakayi ba,ka kama hanya ka tafi kan abunda bai kai ya kawo ba,'   Langwa6e kai abusufyan yayi yana tsuke bakinshi alamar an 6ata mashi rai, ...zuru abu tayi tana kallon ikon Allah,aranta tana cewa"Ashe ɗan masu gidan nan ne,ni duk atunanina aljani ne shi,amma dae da alama baijin magana sosai,'   "Pls mom just forget about it,komai ya wuce tunda dae nadawo," Jinjina kai hajiya ameenatu tayi,kafin ta mayar da idanunta kan Abu dake tsaye sototo tana kallonsu tace"Calm down ur mind Abuna,wannan da kike gani ɗan yayata ne,sunan shi Abusufyan,bai jin magana amma kada wannan ya hanaki sakewa dashi,shima ki ɗauke shi tamkar Yayanki Haris,'   Jiki asanyaye tace"insha Allah mommy,"kafin ta ɗan wurga ido ta kallo shi har lokacin kashe mata ido yakeyi,hakan ba ƙaramin haushi yake bata ba,har tafara jin tsanarshi, Tun daga ranar da Abusufyan ya dawo cikin gidan abu ta shiga uku dashi,ya hana rayuwarta sakat,duk inda ta sanya ƙafarta yana biye da ita,toilet ne kawai bai binta shi dai kawai burinshi ta sake dashi kamar yarda take shiri da haris,ita kuma tace bazata ta6a ɗaukarshi yayanta ba,saboda bai da kamun kai,bakomai yaja mashi hakan ba face Abubuwan da yake yi mata na rashin kunya,da kuma ƴan mata da take ganinshi tare dasu manne da juna,hakan ba ƙaramin ƙona mata rae yake yi ba,duk a tunaninta Abusufyan ɗan iska ne kamar yana bin mata,saboda ita tayi believing da abunda idanuwanta ke nuna mata, Ana haka wata rana malamin nan nasu Sayyadi ya ɗaukota daga islamiyya asaman machine dinsa super cub,tun suna akan hanya motar abusufyan ke bin bayansu saboda ya hangota abayan mashin ɗin malamin,ranshi yayi mugun 6aci wani irin kashi ne ya lullu6e shi,saboda ya lura akwai soyayya tsakaninta da malamin nan nasu,babu yarda abusufyan baiyi da ita ba akan ta bari ya dinga kaita school amma taƙiya,da yake tana da kafiya sosai,mace ce mai wuyar sha'ani, A bakin gate ɗin gidan sayyadi ya tsayar da mashine ɗinsa,abu ta sauko hannunta ruƙe da jakarta,tsayawa tayi suna ƙara gaisawa dashi, "Abu har yanzu baki bani amsa ta ba"? Sunnar da kai ta ɗanyi tana murmushi tace"amsar me kenan"?   sayyadi yace"oh har kin manta kenan?abu kinfa san ina sonki sosai,kuma kema kina sona,bana buƙatar mu 6ata lokaci atare da juna batare da munyi aure ba,banda burin daya wuce wannan, in ganki amatsayin matar aure na,'   Cike da jin kunyarshi abu tace"dan Allah ka ƙara mun lokaci,zanyi tunani akan hakan,'   Kafin sayyadi ya buɗe baki ya ƙara yin wata maganar,suka ji dirar motar Abusufyan agefensu,tun daga kan yarda yayi parking ɗin motar ya tabbatar masu da cewar ba'a hayyacinshi yake ba, .zuba ma motar ido sayyadi yayi kafin ya mayar da idonshi kan abu yace"wanene acikin motar nan"? Muryarta na rawa tace"yayana ne Abusufyan,' ɗan ta6e bakinshi yayi yana jinjina kai, Atsiyace abusufyan ya buɗe murfin motar ya fito,jikinshi sai faman rawa yake yi,kai tsaye wurinsu ya nufo sai faman huci yake yi,   Wani irin mugun kallo ya jefa mata tare da nuna mata hanyar gida yace"Ke wuce ciki!tun kafin ranki ya 6aci shashasha kawai wadda batasan ciwon kanta ba!ki rasa da wa zakiyi mu'amala sae wannan ƙarmasasshen mutumin,ko uban miye abun so ajikinshi!mutumin da ya kusa tsaran ubanki!"   Hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba jiki na rawa ta kama hanyar shiga gida, Muryar sayyadi ce ta dakatar da ita"Abu kada ki tafi!bangama magana dake ba,"   Zuba ido abusufyan yayi yana kallon ikon Allah,tsayawa abu tayi saboda umarnin da sayyadi ya bata akan karta tafi, Rai amatuƙar 6ace Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa"ke!har ni zan baki umarni kiƙiyi mun biyayya saboda wannan munafukin mutumin malamin ƙarya!"   Waro ido waje sayyadi yayi yana kallonshi, Abu kuwa jin an ta6a masoyinta yasa tace"Abusufyan ya isa haka!karka ƙara zagar mun malamina,wannan mutumin da kake gani yafi mun kai so dubu,saboda yana da ilimin addini kuma shi yake koyamun karatu,mutum ne shi mai kamun kai ba kamar kai ba....'jin kalaman abu akan shi yasa sayyadi ya shiga sakin murmushi yana kallon Abusufyan dake tsaye zuciyarshi na tafarfasa, Tuni idanunshi sun ciko tab da kwalla saboda bai iya jurar 6acin rai ba,Zainab ta bada shi awurin malaminsu,   daƙyar yake iya haɗiyar yawun bakinshi da ya gama ƙafewa,jinjina kanshi ya shiga yi kafin daga bisani ya soma magana cikin sanyin murya"Naji duk abunda kika ce abu,amma inaso ki sani bakowane malami bane yake zama mutumin kirki,don kawai ya ruɗe ki da karatun kur'ani yana jawo miki aya da hadisi yana fassara maki su,shine yasa kike tunanin cewa shi mutumin kirki ne?mutun nawa kika sani yana da haddar al'qur'ani akanshi amma hakan bai hana shi aikata zunubin daya ga dama ba....."?   ɗaure fuska sayyadi yayi yace"Kaga ɗan saurayi yarinyar nan ta nuna cewa bata sonka,dan Allah karabu da rayuwarta mana haba,ita malami takeso mahaddacin al'qur'ani ba ɗan tasha ba mai yawo da mata acikin gari,'   Wannan maganar ba ƙaramin fusata Abusufyan yayi ba,har baisan lokacin da ya ware tafin hannunshi ba ya kifa ma sayyadi mari asaman kuncinshi,kafin abusufyan ya zame hannunshi daga kan fuskar Sayyadi yaji saukar mari ɗauuuu a kan fuskarshi agigice ya juya yana kallonta hankalinshi amatuƙar tashe bai ta6a tunanin cewa abu zata iya ɗaga hannu ta mareshi ba,tunda yake arayuwarshi ko dunguri wannan wani bai ta6a gigin yi mashi ba,sai yau da Abu ta mare shi saboda ya mari sayyadinta, Hawaye ne suka soma gangarowa daga cikin idanuwanshi,muryarshi har kerma takeyi wurin cewa"A..ab..bu..ni kika mara saboda na mari wannan ƙasƙantaccen mutumin mai fuska biyu!?   ɗaga hannu tayi zata ƙara kwasa mashi mari,kamar daga sama taji an ruke hannunta kafin tayi wani aune kuma taji saukar mari zazzafan gaske akuncinta,   A firgice ta juya tana kallon shi,bakowa bane ya mare ta ba,face mahaifinta shi da kanshi baba buzu, Fashewa tayi da matsanancin kuka tana cewa"baba...yau kai da kanka ka mare ni?" A faɗace yace"idan kika sake buɗe baki kikayi magana saina kikkifa maki wasu marukan,sakarya kawai wadda batasan halacci ba,yanzu saboda wannan mutumin kika mari abusufyan ko?   wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi jin yarda mahaifinta ya goya mashi baya,sayyadi kuwa ranshi ba ƙaramin 6aci yayi ba,sae faman mazurai yake yi,   Kafin yace"haba baba buzu,ni kake kira da wannan mutumin?ka manta matsayin da nake dashi awurin ƴarka?nifa ne malamin dake koya mata karatun addini,ya kamata ka darajani,kuma abunda abu tayi ba kuskure bane,yaron nan rashin kunya yayi mani dole ranta ya 6aci,dan Allah kaja mashi kunne ya daina yi mana shisshigi saboda ni da abu son juna mukeyi kuma aure zamuyi......'   Tunkan ya ƙarasa maganar baba buzu ya daka mashi tsawa tare da cewa"ubanwa zai auraka maka ita!ko ita take da ikon aurar da kanta ne!Ni ne mahaifinta kuma ni nake da ikon na aurar da ita ga wanda naso,kuma naga ya dace da rayuwarta,don haka tun yau inaso ka cire ta aranka,abu nayi mata miji,kuma ba kowa bane mijin nata ba face ABUSUFYAN!muddin ina numfashi abu bazata ta6a auran wani ba in ba shi ba!!!   Hankali tashe abu ke kallon mahaifinta da idanuwanta da sukayi jawur saboda kukan da tasha,mayar da idonta tayi kan Abusufyan dake ta faman sakin murmushi,girgiza kai tashiga yi tana cewa"baba...ni banason abusufyan,bai dace da rayuwata ba,ba mutumin kirki bane shi,bai da kamun kai,kuma baida ilmin addini,boko kawai yasa agaba,wayewarshi tayi yawa baba.....'   Ganin yarda mahaifinta ya harzuƙo zai rufe ta da duka yasa ta watsa aguje cikin gidan tana kuka,   "Yanzu abunda kayi ya dace baba buzu?yarinyar nan ta nuna tana son malamin addini mahaddaccin al'qur'ani saboda ya tarbiyantar da ƴa'ƴanta,ta san cewa idan ta aure ni zan bata kyakkyawar kulawa kuma zan ilmantar da ita da kuma ƴa'ƴan mu saboda me zaka hana ta aure ni!?kafi son ta auri wannan sangartaccen da baisan komai ba sai yawo da ƴan mata acikin gari?ahaka kake tunanin zai bama ƴarka tarbiyya in ya aure ta? sayyadi nakai ƙarshen maganarshi baba buzu yace"Ka gama sambatun naka?to kama hanya kabar ƙopar gidan nan tun kafin raina ya 6aci,banason ganinka tare da abu,don ban yarda dakai ba,akwai wata mummunar manufa atare dakai na son cutar da ƴa ta,shiyasa naji baka kwanta mun araina ba,amma abusufyan ya kwantamin araina,duk da ya kasance yana da ƙananun shekaru amma ina da tabbacin cewa yafi ka hankali da tunani........'   Jin wannan maganar ta baba buzu yasa hawaye sauka a idon sayyadi muryarshi a kasalance yace"Wai me nayi maka ne ka tsane ni?me na tsare maka ne?dama tunda na fara zuwa gidan nan ina koya ma abu karatu na lura da irin kallon da kakeyi mun,meyasa baba buzu?ko don na kasance malamin makaranta banda arziƙin da zan iya siyen zuciyarka ne?saboda banda kuɗin da zan dinga baka cin hanci don ka auramun ƴarka zainab,sae shi daya taso gidan naira,kasan cewa idan ka aura mashi abu tattalin arziƙinka zai bunƙasa,baba buzu ka tabka babban kuskure arayuwarka muddin ka aura ma abu wannan sangartaccen yaron........' Yana kai ƙarshen maganar shi ya tada rugwagwar mashin dinshi yabar wurin,   matsawa baba buzu yayi tare da dafa kafadar Abusufyan cikin rarrashi yace"kayi haƙuri abusufyan,duk sai naji na tsani kaina da abu ta ɗaga hannu ta mare ka,ni ina da tabbacin cewa wannan malamin dake bibiyar rayuwarta ba mutumin kirki bane,ba don Allah yake son abu ba,tabbas akwai wani abu dayake son cimmawa atare da ita,' Abusufyan yace"baba kada ka damu komai ya wuce,kuma ina baka haƙuri game da kalaman da sayyadi yayi maka,banji daɗinsu ba,'   Baba buzu yace"babu komai yaje don kanshi,Allah na gani ba don komai yasa nakeson ka auri abu ba,sai don saboda in saka ma mahaifiyarku da irin ɗawainiyar da take damu ni da ƴa ta abu,wlh bani da burin daya wuce wani acikin ƴa'ƴanta ya nuna yana son abu ni kuma in aura mashi ita,wannan ce kawai hanyar da nake da ita da zan iya sakamata,'   Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"Baba yanzu in na nemi auran abu a wurinka zaka aura mun ita?a yadda nake da ƙananun shekarun nan"?   baba buzu yace"mai zai hana?ni lokacin da iyaye na sukayi mun aure ban kai shekarunka ba,kuma muka zauna da matata lafiya har Allah ya al'barkace mu da samun zainab,abusufyan in har dagaske kana son abu,kuma zaka ruƙe mun ita amana,na amince kayi ma Abbanku magana ya nema maka auranta awurina nikuma zan baka ita,kai tun ma yanzu inaso ka sama ranka cewa abu ta zama matarka,saboda na mallaka maka ita,sadaki kawai zaku biya a aura maka ita,'   wani iri farin cikine ya lullu6e abusufyan,saboda tsabar farin ciki baisan lokacin daya ɗauki baba buzu ba ya daga shi sama yana jujjuya shi,dariya sosai baba buzu yayi yana cewa"Abusufyan ka sauke ni mana!ko nauyi na baka ji!duk murnar na mallaka maka abu ne yasa ka ɗauke ni haka kamar diyar roba,   Sosai sukayi nishaɗi atsakaninsu, Lokacin da abu ta shiga falon gidan tana faman zabga kuka,hajiya Ameena na ganinta ta tashi daga zaunen da take saman kujera ta tunkareta tana tambayarta lafiya,   adai dai lokacin Mijinta Alhaji nuraddeen yana kan saukowa ƙasa daga saman bene,tun kan yaƙaraso yake tambayarsu me akayi ma abu take kuka,   cikin shessheƙar kuka tace"Baba ne yace zai auramun abusufyan kuma ni bashi nakeso ba sayyadi nakeso in aura......' Jin wannan maganar ta abu yasa hajiya ameena ta ɗaure fuskarta tace"Abu yanzu saboda mahaifinki ya za6a maki abusufyan amatsayin mijin da zaki aura shine kike kuka!meyasa bakya son shi ne?   Muryar daddy ce ta katse mata hanzarinta"Wannan abun bazai ta6a yiyuwa ba!babu yarda za'ae abu ta auri Abusufyan yaron da bai gama mallakar hankalinshi ba!ban goyi bayan wannan maganarba,zanje na samu mahaifin naki muyi magana dashi,indai aure yakeson yi maki sai dae ya aura maki sayyadi saboda shi ya mallaki hankalinshi zai iya kula dake amma ba abusufyan ba,' Wurga mashi wani kallo mai kama da harara hajiya Ameenatu tayi tare da cewa"Wannan abun bai shafeka ba alhaji!babu ruwanka da shiga shirgin Abusufyan,tunda ubanta da kanshi ya mallaka mashi ita,babu wanda ya isa ya dakatar dashi daga auranta!aure kamar anyi an gama ne'   murmushi kawai alhaji nuraddenn yayi yana girgiza kai yace"oh kema kin goyi bayan Abu ta auri abusufyan?bayan kinsan halin shi sarai bai jin magana,kuma yarinyar nan ta nuna cewa bata son shi,dan Allah karku takura rayuwarta,ku bari ta auri za6in ranta karku tilasta mata!kuma sannan ke kin manta da cewa Yayarki hajiya Aishat bazata bari abusufyan yayi aure da ƙuruciyarshi ba!kuma kin manta da tsarinta na ƙin auren bare"? ta6e baki hajiya ameenatu tayi kafin tace"ni wannan bai dame ni ba,ba'a auran bare ita ta auri amininka salahuddeen?ko tana da alaƙa dashi ne?ba haɗuwar barikin sojoji bace,'tayi tambayar tana kallonshi,   Cigaba da magana tayi,"idan kuma kuruciyarshi kake magana,kai kamanta kana da shekara nawa na aure ka?wasan ƴar 6urun 6urun muka dinga yi dakai adaren farkon mu ko ka manta da wannan"? Bakin Alhaji fa ya mutu shiru yayi bai tanka mata ba,don bai da amsar da zai bata,   guntun tsoki taja kasa² tare da mayar da idanunta kan abu dake tsaye hankali tashe tana kallon mommyn jin ta goyi bayan auranta da abusufyan,   "Abu,kiyi hakuri ki bi za6in da mahaifinki yayi maki,ni ina da tabbacin cewa bazaki ta6a dana sanin auran abusufyan ba!nasan kina yi mashi kallon mutumin banza ne saboda son mu'amalarshi da mata,amma inaso ki sani abusufyan ɗina ba ɗan iska bane,kuma shima yana da ilmin addini fiye da tunaninki,shigar ƙananun kaya da yake yi da kuma yawan manne ma matan da yakeyi hakan ba yana nufin cewa shi mutumin banza bane,zainab abunda nakeso ki sani,bata suttura kota kalaman baki ake gane mutumin kirki kona banza ba,wannan azuciya yake,zaki iya ganin mutum malamin addini mai haddar al'qur'ani kanshi kullum sanye cikin jallabiya yana wa'azi bainar nasi,alhalin zuciyarshi baƙa ce yana aikata wasu muna nan abubuwan a6oye batare da sanin kowa ba sai mahalincinshi ,haka zalika zaki iya samun mutumin da kullum yake ɗabi'u irin na turai,sanya ƙananun kaya,hulɗa da mata rashin jin magana da sauransu amma kuma zaki samu zuciyarshi kyakkyawa ce tsarkakakkiya bai sa6ama ubangijinshi,ki daina yarda da abunda idanuwanki suke nuna maki abu,tun farko kinyi ma abusufyan mummunan zato shiyasa kika tsane shi,amma ni nasan cewa kina sonshi kamar yarda yake sonki,bansan me malamin can ya faɗa maki agame dashi ba,dayasa har kika za6e shi akan jini na,to inaso ki sani muddin kinason ganin farin cikina,tun daga rana irin ta yau ki cire soyayyar wancan mutumin aranki,ki fara koyama kanki soyayyar Abusufyan,kafin aɗaura auranku.,.......'   Murya na rawa abu tace"..mo..mommy..ke ma kin amince in auri abusufyan in rabu da sayyadina? Jinjina mata kai hajiya Ameenatu tayi alamar Eh, Fashewa da kuka Abu tayi tare da watsa wa da gudu ta shige ɗakinta saman gado tana kuka tana faɗin"Ni bani sonshi bana son abusufyan bazan aure shi ba,sayyadi nakeso,'kamar zautacciya haka tashiga sambatu har bacci ya ɗauketa, Alhaji dae bai ƙara tanka masu ba saboda baisan 6acin ran matarshi,ya zuba ma sarautar Allah ido,yana kallon ikon Allah, Batare da 6ata lokaci ba,hajiya Ameenatu ta biya sadakin abu dubu ɗari ta damƙa ma mahaifinta,shi kuma ya damka ma zainab kuɗin a hannunta,daƙyar ta kar6i kuɗin,ko da ta koma ɗakinta dasu,wurgi tayi dasu asaman gadonta,ta koma tana sharar kwalla, Duk wannan budurin da akeyi,iyayen Abusufyan basu son da zancen auren abusufyan ba,tun lokacin da Hajiya ameenatu ta kira Ammi awaya take sanar da ita cewa Abusufyan yaga yarinyar mai gadin gidansu yana so,tun kafin ta rufe bakinta ammi ta katseta a fadace tace"Kar na sake jin wannan zancen,ki rabashi da yarinyar don karya sama ranshi ita,ni bazan ta6a aura mashi yar mai gadi ba mara asali,ƴa'ƴana bazasu auri bare ba,auran zumunci zanyi masu,"tun da hajiya Ameenatu taji wannan zancen na yayarta ta tabbatar da cewar bafa zata amince abusufyan ya auri abu ba,saboda ita kaifi ɗaya ce in ta furta abu babu wanda ya isa ya dakatar dashi! Koda Hajiya ameenatu ta sanar ma Abusufyan abunda mahaifiyarshi tace na ƙin amincewa da aurenshi da abu,ranar har zazza6i yayi yaƙi cin abinci kuma,duk yabi ya hargitse ya shiga damuwa sosai,hakan yasa hankalin hajiya yayi mugun tashi saboda ta mutu akan son Abusufyan,batason ganin damuwarshi,shiyasa ta yanke shawarar aura mashi abu batare da sanin iyayenshi ba,ko wani daga cikin danginsu don kar Ammi ta samu labari,a wata ranar juma'a ne bayan an kammala salla,aka ɗaura igiyoyin auransu dubban jama'a suka shaida,daga ciki hada ni hafsat bature muhammad,da kuma makaranta wannan littafin, Tun lokacin da labarin auren Abu da abusufyan yaje kunnan sayyadi,tun daga ranar bai ƙara takawa yaje gidan ba,abun ya ɗaure mashi kai,yarda suka shirya komai batare da saninshi ba,suka aurar da yarinyar da yake mutuwar so,har gadon asibiti sai da ya kwanta yayi jinya, Bayan aurensu da sati guda hajiya Ameenatu ta ware masu katafaren ɗakin da zasu zauna anan cikin gidansu,ta zuba masu duk wani abu na more rayuwa acikinshi,duk don ta faranta ma abusufyan dinta,hatta lefen kayan abu duk ita ta siya mata komai da kayan ɗakinsu, Duk yadda abusufyan yaso ya shawo kanta ta amince suyi rayuwar aurensu amma abu taƙi amincewa dashi,har yau ganinshi takeyi tamkar ba mijinta ba,saboda bata son shi ita sayyadi takeso,kullum Abusufyan yayi yunƙurin ta6a ta,hana shi takeyi tana cewa ba tayi tanadin kanta  saboda shi ba sai don sayyadinta,'wannan maganar ba ƙaramin ƙona mashi rai takeyi ba,gashi Allah ya jarabce shi da tsananin sonta,duk wulaƙancin da abu keyi mashi,bai ta6a sanarma kowa ba,jurewa kawai yake yi donnya rufa mata asiri,yasan muddin ya sanar ma mommyn shi aminatu ko mahaifinta baba buzu sae ranta yayi mugun 6aci don mahaifinta har bugunta zai iyayi,saboda ya tsani yaji tana maganar sayyadin nan, Wuraren ƙarfe sha biyu na dare,tana kwance saman gadonsu tana bacci,ta dinga jin shessheƙar kukan mutum akusa da ita,buɗe idanunta tayi masu ɗauke da bacci,tare da miƙewa daga zaune tana kallonshi,   Ya tasa ta gaba ya zabga uban tagumi yana ta faman zubda hawaye,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin abusufyan na kuka da idanunshi,zuba mashi ido tayi tana kallonshi batare da tace mashi komai ba,   Cikin shesshekar kuka yace"Abu dagaske baki sona?meyasa kika tsane ni ne?   buɗe baki tayi tare da cewa"ba kaine ke bana so ba,ɗabi'unka da halayanka ne ke bana so,na tsani naganka kana mu'amala da wasu matan da sunan abokantaka,kuma natsani naganka kana sanya irin waɗannan kayan ajikinka,kuma baka da kunya abusufyan agaban kowa kake faɗin duk abunda yazo bakin ka,ni nafison kamilin mutun natsastse mai ilimin addini,'     cikin sanyin murya yace"zan canza halaye na saboda son da nake yi maki ne kawai,'   "Kayi mun alƙawarin bazaka ƙara kula wata mace ba in ba ni ba?   ɗaga mata kai yayi alamar eh yace"Nayi maki alƙawari abu,zan daina,daga rana irin ta yau bazan ƙara hulɗa da mata ba,zan kame kaina kamar yarda kikeso,zan zama irin mutumin da kikeso,'ya ƙarasa maganar yana kallon cikin idanunta, Jinjina kai tayi tace"idan kuma ka sa6a fa?ka yadda na yanke duk hukuncin dana ga dama akanka"? "Na amince"ya bata amsa, Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa hannunta ta ɗauko al'qur'anin dake ajiye asaman side drawer dinta ta miƙa mashi,yasa hannu biyu ya kar6a cike da mamakin me zaiyi da al'qur'anin da ta bashi,gabanshi ne ya shiga faɗuwa tsoranshi kar tace ya rantse da al'qur'ani don bazai iya rantsuwa dashi ba,   "Me kike nufi da wannan qur'anin da kika bani,"   Murmushi ta saki kafin tace"so nake ka rantse dashi cewa ba zaka ƙara hulɗa da wata ƴa mace ba aduniyar nan in ba ni ba,babu ruwanka da mace indai ba ƴar uwarka bace sai kuma ni da nake matarka,in kuma harka sa6a hakan na kama ka tare da wata ƴa mace zaka sake ni saki ukku!ka amince da hakan!!"   Shiru abusufyan yayi gabanshi na faɗuwa,aranshi yana zullumin amincewa da maganarta,saboda baisan halin da zai tsinci kanshi ba anan gaba,tsautsayi zai iya afkawa dashi a lokacin da baiyi tsammani ba, "Dan Allah abu ki janye maganar rantsuwa da qur'ani,banaso kuma ma babu kyau yin rantsuwa dashi,kiyi haƙuri pls,wlh nayi maki alƙawarin bazan ƙara kula mata ba,komai zan daina,"cikin sanyin murya yayi maganar yana kallonta,   ɗaure mashi fuska tayi tare da cewa"Abusufyan dole fa sai ka rantse mun da qur_'anin nan sannan zan yarda dakai!ƙin amincewa da hakan zaici gaba da haddasa rashin zaman lafiya atsakaninmu!"   babu yarda ya iya da ita,saboda aƙagare yake da su fara kasancewa amatsayin ma'aurata tare da ita,baison 6acin ranta ko kadan,baida burin daya wuce yaga suna zaman lafiya da ita,wannan dalilin ne yasa shi yin rantsuwar da har yau yake danasaninta, Hannu tasa tare da kar6ar qur'anin ta maida shi saman drawer ta ajiye shi,   "Yanzu zaki bani haƙƙina kenan"?ya tambaya yana kallonta,   jinjina mashi kai tayi alamar eh,kafin ta sanya hannunta tare da cire rigar jikinta,ya rage daga ita sae bra,nan fa hankalin Abusufyan ya tashi haikam da ganin surar ƙirjinta,gaba daya ya afka mata,suka manne ma juna,gaba daya suka zautar da junansu,sosai Abusufyan ya biya bukatarshi da ita,sai lokacin ta gane ba ƙaramin cutar kanta takeyi ba,na ƙin amincewa dashi tun ranar farko da aka ɗaura masu aurensu,ba ƙaramin so ya nuna mata ba awannan daren,kuka sosai abusufyan yayi mata saboda tsantsar farin cikin da yaji na kasancewarshi mutun na farko daya fara kar6ar budurcinta, Tun daga wannan lokacin soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninta dashi,saboda irin tarairayar da yake yi mata,da kuma irin kulawar da yake nuna mata,kullum yana tare da ita yana faranta mata,da kanshi yake kaita school sannan ya wuce tashi makarantar,idan an tashe su shi yake zuwa yaje ya ɗaukota ya kaita gida,tamkar romeo da juliet haka suka koma,har acikin mota soyayya suke sha,idan tana aiki a kitchen haka zai bita yana tayata aiki,gyaran ɗakinsu duk shi ke yi in yana gida,hatta gugar kayan makarantarta shi ke zama ya goge mata su,duk wannan soyayyar da suke sha akan idon Hajiya Ameenatu,dama itace ta bama soyayyar tasu wurin zama,in taga sunyi kwana biyu basu fita yawon shakatawa ba,da kanta take ɗauko kudi tabasu tace su tafi shan ice cream,ko suje suyi siyayyar abunda suke so,shi dai Alhaji nuraddeen har lokacin zuba masu ido kawai yake yi,mahaifin abu kuwa baba buzu mai gadi,hankalinshi ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ganin yadda Abusufyan ke kular mashi da yarinyarshi,yanzu baida sauran damuwa sae fatan cikawa da kyau da IMANI, Bayan wata guda da sati uku da yin auransu.................. Suna zaune a cikin class ɗinsu na islamiyya,ƙawayenta na kewaye da ita,tana basu labarin irin soyayyar da suke sha ita da abusufyan ɗinta,dama bata da wata magana sai ta Abusufyan,suna cikin firar nan sai ga malamin nan nasu sayyadi ya faɗo cikin ajin a fujajen yana ta faman huci,suna haɗa ido da abu ya kwaɗa mata kira"Zo nan zainab," ƙin zuwa tayi sai da wata ƙawarta tace mata"Abu kije ya sayyadi na kira,"ba don taso ba ta miƙe tare da zuwa inda yake,waje suka fita daga gefen ajin nasu, "Yanzu abu kin kyauta abunda kikayi mun?kawai sae dai naji agari an ɗaura auranki da abusufyan"? Muryar shi tamkar zaiyi kuka yayi maganar, "Dama Allah ya ƙaddara cewa kai ba mijina bane Sayyad,Abusufyan shine mijina,don haka ina baka haƙuri kuma ina yi maka fatan Allah ya baka mace tagari wadda ta fini,"tana faɗin hakan ta juya zaka koma class cikin sauri yasha gabanta tamkar zai rungumeta,ɗan ja da baya tayi tana kallonshi a tsorace, Rai amatuƙar 6ace yace"Zainab!kada kiyi mun haka kin manta alƙawarin da mukayi ma juna,zamu yi aure mu haifi ƴa'ƴa mu tarbiyantar dasu atare?abu ni fa kikeso ba Abusufyan ba?me zakiyi da namiji mai bin mata?ke da kanki kika sanar dani cewa Abusufyan mutumin banza ne mai hulɗa da mata,kuma bai da tarbiyya sannan baida ilmin addini rayuwar turae yasa agaba bai damu da addinin shi ba....' Abu tace"hakane ni na faɗa maka haka da bakina,tabbas munyi alƙawari dakai sai gashi Allah bai nufa ba,tunda bani ke iko dakaina ba,mahaifina shiya za6amun Abusufyan kaga dole nayi masa biyayya,malam kaida kanka kake yi mana nasiha akan mubi iyayenmu muyi musu biyayya,don haka bai kamata kaga laifina ba,don nabi umarnin mahaifina ba,sannan zancen cewa abusufyan na bin mata,rashin sani ne yasa nayi mashi mummmunar fahimtar nan,amma ni mijina baya bin mata,abusufyan mutumin kirki ne,yana mu'amala da mata amma bai ta6a kusantar su da sunan aikata zina ba,iya friendship yake yi dasu,maganar ilmin addini kuwa abusufyan shima malami ne mai zaman kanshi,da farko na dauka boko ya sanya agaba,amma yanzu nagane cewa yana da ilmin addini sosai,bai cika bayyanawa bane agaban mutane,amma shi da kanshi yake ƙara mun karatun hadda in aka bani a makaranta,kuma yana tashi na muyi sallar dare dashi,kuma muyi karatun alƙur'ani atare.......' Tunda tasoma magana sayyadi ke ta faman huci kamar ya rufe ta da bugu haka ya dinga ji,sae da ta kai ƙarshen maganarta sannan yace"yanzu kin haƙura da duk wasu munanan dabi'u nasa kin amince zaki cigaba da zama dashi yana hulɗa da mata," ɗaga mashi kai tayi alamar eh tace"Abusufyan yayi mun rantsuwa da alƙur'ani cewa bazai ƙara mu'amala da wata ƴa mace ba in bani ba,in kuma har yayi hakan zai sake ni ne mu rabu," tun daga kan yarda abu ke magana zakasan cewa akwai ƙuruciya sosae atare da ita, Jin maganarta yasa sayyadi jinjina kai tare da matsa mata hanya yace"ki koma aji," sallama tayi mashi sannan ta wuce cikin class, Bayan shigarta aji,murmushi ya shiga saki yana cewa"ta kwana gidan sauƙi,"yana fadin hakan ya ƙara gaba. *Zuwa gobe insha allah zamu kammala labarinsu sehrish ataƙaice sannan mu ɗaura daga inda muka tsaya*   *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*, ❤🤍❤ Da wuri bayan an tashe su daga islamiyyar Abusufyan yazo ɗaukarta,ƙawayenta sae santin shi sukeyi,dama haka kullum suke zuzuta kyanshi da kuma gulmar wankan da yake ɗauka na tsadaddun kaya,ba ƙaramin tafiya yake yi dasu ba,   Shiga cikin motar abu tayi tare da rufe motar,sannan ta juya tana kallonshi,ya kifa kanshi asaman sitiyarin motar da alamun damuwa atattare dashi,   Hannu tasa tare da shafa sumar kanshi tace"Mijina,meya faru ne naganka kamar cikin damuwa," ɗagowa yayi daga kan sitiyarin ya kalli fuskarta tare da cewa"babu komai abuna,yau dai hakanan nake jin gabana na faduwa kamar wani mummunan abu zai faru dani,dan Allah ki tayani da addu'a ko zan samu zuciyata ta daina yi mun bugun da takeyi,   jin wannan maganar ta abusufyan yasa hankalinta tashi,matsawa tayi kusa dashi suna fuskantar juna tace"Insha Allah babu abunda zai faru mijina uban ƴa'ƴana,zan tayaka da addu'a kuma inaso kaci gaba da Ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'in,insha Allah komai zai tafi dai dai,'    Murmushi ya ɗan saki tare da haɗa fuskokinsu wuri guda suna shaƙar numfashin junansu,   Cikin wata irin kasalalliyar murya yace"Kiyimun alƙawarin ba zaki ta6a rabuwa dani ba abuna,wlh ina sonki sosai fiye da yadda nakeson kaina,banda burin daya wuce na ƙare rayuwata tare dake,daga ni har ke akwai ƙuruciya atattare damu,ina fatan mu girma tare,mu kara wayau atare sannan mu tsufa kuma atare,'   Kalamanshi ba ƙaramin kashe mata jiki sukayi ba,nan take taji soyayyarshi na ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, Cikin sanyin murya tace"bazan rabu dakai ba Abusufyan ɗina,i luv u so much,more than my life,bazan ta6a bijire maka ba,yanzu na gane cewa bani da masoyin da ya wuce kai aduniyar nan abusufyan,ina fatan Allah yabarmun kai,'ta ƙarasa maganar tare da hugging ɗinshi sosai ta kwantar da kanta asaman wide chest dinshi,dama tubarkallah duk da kananun shekarunsa yana da cikar kira ga hutu daya ratsa shi,hannunshi ya zura acikin hijabin jikinta yana shafa sumar kanta,sun jima a wannan yanayin kusan 30mins,kafin ya tashi motar ya miƙi hanyar komawa dasu gida,a kasalance yake yin driving ɗin,saboda sakonnin da abu ke aika mashi ajikinshi,duk ta jefa shi cikin wani irin yanayi,   koda suka koma gida atare Suka ci abincin da Hajiya Ameenatu ta girka masu abun gwanin burgewa,bayin Allah ashe duk na bankwana ne,sukeyi ma juna basu sani ba, lokacin kiran sallar magrib,abusufyan ya fito daga cikin toilet,jikinshi da danshin ruwa alamar alwala yayi,a lokacin abu na zaune gefen gadonsu tana jiran fitowarshi,jin alamar buɗe ƙopar shi yasa ta ɗan dago ta kalleshi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Sannu da fitowa hayatyna," Ƙarasawa yayi wurinta tare da zama daga gefenta yace"me kika tanadar mun yau idan nadawo gida da daddare? Abu tace"komai kakeso," "To ki tanadar mun kan ki,yau zan baki mamaki,awashe gari zaki haifa mun babies bama ɗaya ba....'   Dariya tayi sosai jin abunda yace kafin ya tashi yayi mata sallama tare da fucewa,' Lokacin da aka kira sallar isha'e bayan tayi wanka ta ɗauro da alwala,sai da ta kammala sallar sannan ta shiga shirya kanta,tun tana shafa mai ajikinta take tunano kalamam abusufyan nacewa zata haifa mashi babies awashe garin ranar,ta lura ba ƙaramin son ƴa'ƴa gare shi ba,kusan kullum ne sai yayi mata maganar yaushe zasu haihu,wani lokacin har cewa yakeyi wai ko dae basu isa haihuwa bane shiyasa bata samu ciki ba,duk irin ƙoƙarin da yakeyi, don ba ƙaramin jarababbe bane, Murmushi tayi tare da cewa"Nikaina aƙagare nake dana ga ƴa'ƴan da zamu haifa ni da abusufyan ɗina,nasan yaran zasu zama kyawawan gaske in dai suka ɗauko kyawun fuskar kowannanmu,amma ni dae nafi son su ɗauko fuskar shi,saboda koda wata rana in yayi tafiya mai nisa,zan dinga kallon fuskarsu a matsayin tashi,hakan zai ɗebe mun kewa, Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren da abu ta feshe jikinta dashi,bayan ta gama shafe shi da haɗaɗdun mayukan jikinta,komawa tayi gaban wardrobe ɗin kayansu ta buɗe tana tunanin wasu kaya zata sanya waɗanda zasu zautar da abusufyan,ta jima atsaye tana ruwan ido kafin ta hango wata rigar bacci Babby doll black color,net ne ajikin rigar shara shara ana kallon komai na jikin mutun,tamkar ma mutun bai sanya kaya bane saboda yadda take fitar da tsiraici,ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,zubo da gashin kanta tayi ya sauko har wurin waist ɗinta,komawa tayi gaban mirror ta shafa jan baki red abakinta, Bayan ta kammala shirin nata,ta shiga zagayen ɗakin tana jiran dawowar abusufyan,tana yi tana kallon wall clock dake manne a bango tana duba time,abu kamar wasa har ƙarfe 10 na dare babu abusufyan,shi da ya saba dawowa da zarar an kammala isha'e,baiwar Allah har ta fara gajiya da yawon,komawa tayi ta zauna gefen gadon tana sa ran dawowarshi,da zarar taji motsin mutun ya shigo cikin gidan sai ta miƙe jiki na rawa ta leƙa taga wanene  ashe Haris ne ya dawo,na biyu kuma data leƙa Abbansu ne ya dawo,ƙarshe dae bacci ya kwashe ta,wuraren goma sha biyu ta farka,ganin har lokacin bai dawo ba,yasa hankalinta yayi mugun tashi,saukowa tayi daga saman gadon ta ɗauko hijabi ta zura ajikinta,sannan ta fito daga ɗakin ta wuce bedroom ɗin haris,   A ƙofar ɗakin ta tsaya tana kwankwasawa,   Cikin bacci haris ya jiyo bugun ƙopar ɗakin nashi,muryarshi akasalance yace"Wanene,"   Abu tace"ni ce Zainab,' Saukowa yayi daga saman gadonshi yazo bakin ƙopar ya buɗe mata tare da cewa"lfy,meya faru ne abu?   Abu tace"ɗan uwanka abusufyan har yanzu fa bai dawo cikin gidan nan ba,hankalina ya tashi sosai,bansan ko kana da masaniya akan inda yaje ba,"   Cike da mamaki Haris yace"wai kina nufin bro ɗina bai dawo gida ba?tare dashi fa muka je masallaci,amma ba tare muka dawo ba,saboda yace mun yana sauri yazo wurinki ne,ni kuma na biya gidansu abokinmu ne,"   Jin wannan maganar yasa hankalin abu ya ƙara tashi haikam,tuni idanunta sun cicciko da kwalla,dama bata da wuyar yin kuka,fargabarta kar ace wani abu ne ya faru da mijinta,   Lallashinta haris yayi tare da cewa"just calm down ur mind,duk inda abusufyan yake yana atare damu,bana so ki tashi su mommy daga bacci game da maganar nan,hankalinsu zai tashi ne,bari na jaraba kiran numbar shi muga in zata shiga,"ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya shiga cikin ɗakin nashi,   Sai gashi ya dawo hannun shi ruƙe da wayarshi yana dannata,numbar shi ya kira,tana fara ringing abun mamaki akayi picking kiran,   Da sauri haris ya kara wayar a kunnan shi yace"bros kana ina ne wai?har 12 baka dawo gida ba?duk ka tayar mana da hankali,"   Gaban haris ne ya faɗi rass jin muryar mace tana cewa"mai wayar ya shiga wanka ne,'   rejecting kiran yayi cikin sauri gudun kar abu tajiyo muryar macen da yaji,don ya santa da kishi,   "Me ya ce maka"! Ta tambaya tana kallonshi,   Daƙyar ya iya cewa"Am..um...kin gane wani aiki ne ya tsayar dasu a company,sai zuwa gobe ko da asuba zai dawo,dan Allah ki ƙara hakuri....'   Tunkan yakai ƙarshen maganar tashi abu ta watsa da gudu ixuwa ɗakinsu ta faɗa saman gado tana kuka,tasha kuka sosai a ƙarshe bacci ya ɗauke ta, Koda ta farka sallar asuba,abusufyan bai dawo ba,bayan tayi salla ta zauna tana karatun al'qur'ani don kar bacci ya kuma ɗaukarta,wuraren ƙarfe 7:30 tayi shirin zuwa islamiyya,duk da halin da take ciki na damuwar rashinshi,    batare da sanin kowa ba ta fice ko breakfast ba tayi ba,a bakin gate suka haɗe da baba buzu,    Zuƙunnawa tayi tare da gaishe shi"ina kwana baba,kun tashi lafiya,"   Baba buzu yace"me ya faru abuna?naga fuskarki tayi jawur ta kumbura kamar kinsha kuka"?   cikin sauri tace"a'a babu komai baba,lafiya ta lou,'ta bashi amsa tare da miƙewa tsaye,   "Ina abusfyan ɗin yake ne yau bazai kai ki makarantar bane"?   Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,    Bai kawo komai aranshi ba,yace"kada ki makara ki wuce ki tafi," Amsa mashi tayi da toh sannan ta fito waje ta kama hanya tana tafiya ita kaɗae cike da damuwa,   Kwatsam!kamar ance ta waiga ta hango Motar abusufyan yayi parking ɗinta a gefen hanya,mamaki ne ya kamata, Jiki na rawa ta nufi wurin motar tare da sanya hannunta ta kwankwasa glass ɗin shi,   Zuge glass ɗin akayi a slow,a gigice Abu ta zaro ido waje tana kallonsu,abun tamkar a mafarki, sun manne da juna abusufyan ɗin da take ta haukan nema tare da wata matashiyar budurwa cikin motar,budurwar ko kayan kirki babu ajikinta,inners ne kawai ta bari,da alama ma basu acikin hayyacinsu sunyi nisa cikin harkar tasu,   Hankali amatuƙar tashe abu ta aza hannunta akai tana fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una....!' Tana ƙarasa faɗar hakan ta yanke jiki ta faɗi a sume ƙasa,zubewarta ƙasa ke da wuya,Motar nan tabar wurin tamkar bata ta6a bayyana ba,   Adai dai lokacin kuma Motar Abusufyan ta shigo layin da gudun gaske,tunkan ya ƙaraso ya hangi abu sume a ƙasa cikin uniform dinta,gabansa ne ya faɗi rass,da sauri ya tsayar da motar tare da buɗe ta ya fito yana faɗin"kai!me nake gani haka?kodai idanuna ne suke nuna mun ba dai dai ba!abuna ce kwance a ƙasa!taya akai hakan ya faru!"   ƙarasawa yayi tare da zuƙunnawa agabanta yana shafa fuskarta,ya jima yana mamakin yadda akai abu ta sume ƙasa,kuma tabbas itace,   Hannu yasa ya ɗaukota ya nufi mota da ita bayan ya kwantar da ita abayan motar ya shiga gaban motar ya tashe ta suka nufi gida, Lokacin da abusufyan ya shigo da abu a hannunshi,Hajiya Ameena suna xaune saman dining chairs ita da alhaji da kuma haris suna yin breakfast, Hankali atashe suka nufo shi suna tambayarshi lafiya!meya faru da ita! Hajiya tace"Yaushe kuka fita tare da ita batare da sanina ba!? Abusufyan yace"mommy ba atare muka fita ba,ni jiya ban kwana agida ba,bacci ya ɗauke ni acikin mota ban ƙara sanin inda kai na yake ba sai da safen nan,kuma wayata ma an sace ta banganta ba," Mamaki ne ya kamasu su duka,musamman Haris kanshi ya ɗaure jin cewa an sace wayar abusufyan hakan na nufin cewa jiya wayar bata a hannunshi wasu ne suka ɗauke wayar,to garin yaya hakan ya faru,   Hajiya tace"Haba abusufyan ɗina garin yaya har bacci ya ɗauke ka acikin mota,kuma aka sace maka waya,duk ta yaya hakan ya faru"?   Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"wlh mommy ni kaina bansani ba,wayata tun a masallaci aka sace ta,ban tashi ankara ba sai da na shiga cikin motata bayan mun rabu da haris,na kamo hanyar zuwa gida na dinga ganin biji biji acikin idanuna,dalilin dayasa na dakatar da driving ɗin nayi parking na motar,tun daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba,sai yanzu dana farka,na biyo hanyar gida kenan naga abu a kwance ƙasa,ina tunanin wani abune ya tsoratar da ita shiyasa ta sume' Alhaji yace"kaɗan daga cikin sakarcin kane sufyan!in ba shashasha ba taya zaka bar bacci ya ɗauke ka acikin mota har ka kwana awaje,ko tsoron wani abu ya faru dakai baka ji!salon kaja ma mutane bala'e ko!?   Ganin ya rufe shi da fada yasa mommy ta 6ata fuska tare da kallon Abusufyan tace"Ka shiga da ita ciki"   Amsa mata yayi kafin ya wuce da abu cikin ɗakinsu,   "Dama ae kin saba goya mashi baya!yaron nan yayi laifi me yasa ba zaki bari ayi mashi faɗa ba!ke kina da tabbacin cewar baccin ne ya kwashe shi akan hanya har ya kwana waje?ni ban yarda da zancen nan nashi bama,akwai dae inda yaje,".    Rai a6ace Hajiya Ameena tace"ya isa haka Alhaji!kasan irin kalaman da zaka dinga faɗi akan abusufyan ɗina,in ba haka ba,ranmu xai 6aci ne gaba daya, Tamkar zasuyi faɗa atsakaninsu,ganin haka yasa Haris cewa"pls mommy dan Allah kudaina mana,banaso inga kuna faɗa akan abusufyan,wai meyasa kuke haka ne?daddy kaima ka daina sanya baki akan lamarinshi mana tunda mommy bataso,ba shikenan ba,'.   Jinjina kai kawai Alhaji yayi tare da kama hanya ya wuce upstairs,haris ya ruƙo hannun mommynshi suka koma don su ƙarasa yin breakfast ɗinsu, A6angarensu abu da abusufyan kuwa,bayan ya kwantar da ita saman gadonsu,ruwa ya dauko a roba ya ɗebo ya yayyafa mata a saman fuskarta,a hankali ta shiga mutsu mutsun buɗe idanunta,zuba mata ido yayi yana kallon fuskarta cike da tausayinta don yaga alamar jirwayen hawaye a fuskarta kuma ta ɗan kumbura, Ware idanunta tayi akanshi koda taga shine a firgice ta miƙe zaune saman gadon tana ja da baya,ƙure ma head board ɗin gadon tayi tana faman zazzare mashi idanu,   Cikin sanyin murya yace"Abuna,am really sorry jiya nasan kinyi kewata sosai,na kwana awaje ban dawo gida ba,nima ba da son raina hakan ya faru ba,"   Yana kai ƙarshen maganar tashi abu ta fashe da matsanancin kuka tana cewa"ka cuce ni abusufyan,ka yaudare ni!kayi mun ƙaryar cewa zaka daina mu'amala da mata ashe ƙarya kakeyi,har yanzu kana tare dasu,da idona nagani kuma na shaida,hakan ya tabbatar mun da cewar a hotel ka kwana kai da karuwar daka ajiye tana biya maka buƙata,tunda ni ban isheka ba....'   Hankalin abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,a ruɗe yace"abu bangane akan me kike magana ba!dan Allah ki fahimtar dani!"   Cikin shesshekar kuka ta sake maimaita mashi abunda tace   Hannu ya aza akai yana fadin"innalillahi'wa inna ilaihirraji'un! Ya Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba,abu yau ke da kanki kike jifa na da waɗannan munanan kalaman!abu bani kika gani ba,wlh bani bane ni ban yi mu'amala da wata mace ba,ban haɗu da kowa ba,waɗanda kika gani acikin motar nan bani bane, wasu ne can daban,idanunki ne suka gwada maki ba dai dai ba....'   A tsiwace tace"Abusufyan!nagama yarda dakai,saboda kai maƙaryaci ne kuma fasiƙi mazinaci.......'   Bai bari taƙarasa maganarba afusace ya kwashe ta da mari,dafe kuncinta ta tayi ko gizau batayi ba taci gaba da cewa"Ni ka mara da hannunka saboda na faɗi gaskiya?koda yake yanzu har buguna ma zaka iyayi ai saboda ka samu wadda tafi ni,' Kallonta yake yi yayin da idanunshi sukayi jawur jikinshi har rawa yakeyi saboda tsananin 6acin ran da ta sanya shi,   Muryarshi akausashe yace"Abu kada ki sake kirana da mazina ci!ban ta6a aikata zina ba arayuwata,ko sunanta bana son inji an ambata balle har nayi yunƙurin aikatata,wlh kika ƙara kirana da sunanta saina sa6a maki......'   duk wannan budurin da akeyi Hajiya da haris basu sani ba,saboda akwai tazara tsakanin bedroom ɗinsu abusufyan da kuma inda suke, Harara ta wurga mashi har lokacin hawaye naci gaba da zuba a idanunta huci kawai takeyi saboda 6acin rai,   daƙyar ta iya furta"Ka sake ni!saboda bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba!kayi mun alƙawarin cewa zaka daina mu'amala da mata,kuma har rantsuwa kayi da al'qur'ani cewa in har ka sake kula mata,zaka sake ni saki uku!!!'   Tsananin 6acin rai da takaici yasa abusufyan ya fashe da matsanancin kuka yana cewa"Zainab baki a cikin hayyacinki!wlh ba ke bace,nasan cewa ba yin kanki bane,aljanune suka shiga jikinki,"   "Abusufyan ka sake ni!in ba haka ba zan illata kaina kowa ya rasa,"tayi maganar babu wasa a fuskarta,   "Wlh bazan sake ki ba abu,bazan iya ba,saboda ni banyi maki laifin komai ba,zargina kawai kikeyi amma baki da shaida akaina,dan Allah abu kidaina wannan maganar zuciyata zata iya bugawa in mutu,kiyi haƙuri mu sasanta tsakaninmu nasan zaki fahimce ni,'   Babu alamar sassauci a fuskarta,tamkar yana ƙara tunzurata haka taci gaba da faɗin ya sake ta,   Ganin yaƙi sakinta yasa ta mika hannu tare da janyo drawer chest,sabuwar reza ta ciro daga cikin drawer ɗinta,   Hankali tashe abusufyan yace"me zakiyi da ita abu?     Fuskarta aɗaure tace"zaka sake ni ko bazaka sake ni ba!" shi kanshi sai da ya tsorata da yanayin yadda take magana,ganin yadda hijabin jikinta ya jiƙe sharkaf da zufa,kuma babu zafi aɗakin nasu,ga idanuwanta sunyi jawur dasu luhu luhu,jikinta kuma sai kerma yakeyi,   Cikin sanyin murya yace"Abu pls ki saurare ni,zan fahimtar dake..kinsan ina sonki bazanso abunda zai cutar dake ba,bazan iya cin amanarki ba abu,   damƙar hijabin jikinta tayi tare da cireta tayi wurgi da ita gefe guda,a fusace ta Sanya rezar nan abakin tafin hannunta na dama,ta tsarga wurin nan take jini ya soma tsastsafowa daga wurin   Agigice abusufyan ya yunƙura zai kwace rezar hannunta,dakatar dashi tayi da cewa"Idan har ka kuskura ka matso zan kashe kaina ne!"   Cikin shessheƙar kuka Abusufyan yashiga yi mata magiya yana roƙonta akan ta daina tsaga jikinta amma kamar yana tunzurata ne,   Saboda taurin kai da kafiya irin nata ko zafin rezar bata ji ajikinta,kafin yayi wani yunƙurin abu ta sanya rezar asaman wuyanta ta shiga tsarga wurin jini ya shiga bulbulowa,   A wannan lokacin ne abusufyan ya furta mata saki har ukku batare da saninshi ba,saboda tsoran karta kashe kanta,a gigice yace"ABU NA SAKE KI!NA SAKE KI!NA SAKE KI," 😭 Adai dai lokacin Hajiya da haris suka faɗo dakin kamar an jefo su,sakamakon Sautin ƙarar da abu ta saki da kuma kukan da abusufyan ya saki na fitar hayyaci,zubewa tayi saman gadon asume tana billayi saboda radaɗin rezar daya shigeta, Gaba daya suka rufar mata suna ambaton Sunanta suna tambayar meya faru,a lokacin shima abusufyan ya yanke jiki asaman gadon ya sume, Bayan wannan lokacin sai da abu tayi jinya agadon asibiti,inda Allah yaso rezar bata shiga cikin wuyan sosai ba amma ta tsaga fatar wurin sosai, Bayan an sallameta sun dawo gida anan fa suka hadu su duka a falon gidan don jin abunda ya haddasa faɗan daya shiga tsakaninsu,Zainab bata 6oye komai ba ta basu labari hada sakin da abusufyan yayi mata,hankali atashe Abusufyan ya shiga rantsuwar cewar shi bai sake ta ba,saboda baya acikin hayyacinshi baisan ya furta mata ba,gaba dayansu babu wanda baiyi takaicin faruwan wannan al'amarin ba,musamman mahaifinta baba buzu,tun daga ranar da aka sallameta daga asibiti ko kallonta bai ƙara yi ba,in ma tagaishe dashi bai amsawa,ta 6ata mashi rai sosai,bai ta6a tunanin abu zata aikata abunda ta aikata ba saboda kishi daya rufe mata idanunta, Abusufyan kuwa har ciwon zuciya sai da ya kusa kama shi a wannan lokacin,ba arziƙi hajiya Ameena tasa aka fitar dashi ƙasar turkey,wurin wata aminiyarta kuma abokiyar kasuwancinta,hajiya maimunatu dake zaune acan instanbul,a wurinta yaci gaba da zama,ta nisanta shi da nigeria ne saboda ta gusar da damuwar dake ƙoƙarin haddasa mashi Ciwon zuciya, Bayan abusufyan ya koma ƙasar turkey da sati guda kacal,sai ga sayyadi yazo yi ma Abu jajen mutuwar aurenta,tun abakin gate ɗin gidan baba buzu yayi mashi korar kare,wannan abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yayi ba, Ana haka kuma abu ta koma yar gidan jiya,soyayyar sayyadi ta dawo sabuwa fal acikin ranta,ko bacci bata iyayi batare da tayi mafarkinshi ba,ko sallah takeyi sai ta dinga kawo zancenshi acikin zuciyarta,Tashin hankali,zuciyarta ta dinga azalzalarta akan son ta sanyashi acikin idanunta gashi an hanata fita ko nan da bakin gate bata iya zuwa saboda mahaifinta dake fushi da ita,da zarar ya ganta awaje zai nufeta afusace da nufin ya bugeta sai ta watsa da gudu ta koma ciki,hajiya da alhaji nuraddeen har haƙuri suka bashi akan komai ya wuce amma yaƙiyi,burinshi ya damƙeta a hannunshi yayi mata mugun bugu,don ya huce haushinta da yake ji,Abu ta ƙumsa mashi baƙin ciki sosai, Ana haka,wata rana ƙawar abu ta islamiyyarsu wadda suke kira da Maryam ta kawo mata ziyara acikin gidansu, A falo suka fara gaisawa dasu mommy kafin suka shiga cikin ɗakin abu,anan take sanar da ita cewa Sayyadine ya aiko ta a 6oye don ta kawo mata wayar da zasu dinga gaisawa dashi,'hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abu ba, Nokia ce ƙarama maryam ta ciro daga cikin handbag dinta ta miƙa ma Abu,cike da farin ciki ta kar6i wayar,   Tafiyar maryam ke da wuya,sai ga kiran sayyadi ya shigo cikin wayar,jiki na rawa ta ɗaga kiran tare da yi mashi sallama,   ko amsa sallamar baiyi ba yace"Hmmmm abu kenan!yanzu kin tabbatar da abunda nake faɗa maki akan Abusufyan ko?ae tun farko saida naja kunnanki akan ki rabu dashi ba mutumin kirki bane amma kika ƙi jin maganata,' Abu tace"dan Allah mubar wannan maganar,ni ko sunanshi ma bana son ji,yanzu kaine araina,banda burin daya wuce muyi aure yanzu,dan Allah sayyadina ka turo gidanmu asanya ranar auranmu,'   Dariya sayyadi yayi kafin yace"kin manta da cewa idda kikeyi yanzu," Cike da damuwa abu tace"Nasani,amma ni bansan ya zanyi ba,so nake kawai mu kasance atare amatsayin ma'aurata,"   Shu'umin murmushi sayyadi ya saki aranshi yace"yarinya kinzo hannu,"   A fili kuma yace"yanzu ya za muyi abu?nikaina aƙagare nake da naga wannan lokacin,na ƙosa naganki amatsayin matata uwar ƴa'ƴana kuma,"   Suna cikin wayar yunƙurin amai yazo mata,da gudu ta miƙe tare da faɗawa cikin toilet wayar na ahannunta,ta karasa gaban fanfo tana kwarara aman,   Hankalin sayyadi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abu na amai,wannan ya tabbatar mashi da cewa Akwai Cikin abusufyan ajikinta,kuma muddin ya bayyana kowa ya sani babu shi babu abu,kafin ya cimma burinshi za'a ɗauki tsawon lokaci ne,   Kunna fanfon tayi,ruwa ya zubo ta ɗebo tana kuskure bakinta da ɗayan hannun,   Bayan ta kammala aman tadawo ɗakin a gefen gadon ta zauna sannan ta mayar da wayar a kunnanta tace"kayi hakuri sayyadina,wlh bana jin daɗin jikina ne,"   Muryarshi har kerma takeyi wurin cewa"Faɗamun Abu!kamarya kike ji ajikin ki"?   Abu tace"zuciyata ce ke tashi,ga wata irin kasala da nake ji.....'   Tun kafin ta ƙarasa maganar sayyadi ya katse ta da cewa"Abu!banason ki fada ma kowa yanayin da kike ji ajikin ki!kinji ko"?   Amsa mashi tayi da toh bazan faɗa ba,   Yaci gaba da cewa"Ni zanyi maki maganin lalurarki,addu'a kike buƙata,insha Allah yanzu bada jimawa ba,zaki ji sauƙi ajikinki,"   'Nagode sosai,"ta fadi kafin ta kashe wayar ta koma ta kwanta, Kafin wani lokaci abu ta daina jin tashin zuciyar da take ji,kasalar nan duk babu ita komai ya dawo mata dai dai,har abu ta kammala iddarta babu ciki ajikinta,kuma aranar data kammala iddar aranar sayyadi yazo neman auranta wurin baba buzu,tun abakin gate baba buzu yace"meya kawoka gidan nan!" Sayyadi yace"Naji cewa abu ta kammala iddarta,shine nazo neman auranta a wurinka,dan Allah kada ka hanani,tunda dae yarinyar nan ta nuna tana sona,kabarni kawai muyi auranmu,nayi maka alƙawarin zan kula maka da ƴarka,'   Wani irin kallo baba buzu yayi mashi kafin yace"har abada bazaka ta6a auran abuba,indai har nine ubanta,muddin ina numfashi bazan ta6a aura maka ita ba,"   Shu'umin murmushi sayyadi ya saki tare da jinjina kanshi yace"Idan kuma baka araye fa?ka isa ka hanani auranta?   Shiru baba buzu yayi yana kallonshi,dariya sayyadi yayi yana girgiza kai yace"shiyasa tun farko naso ace ka bini ta lalama ka auramun ita,amma saboda taurin kai da kafiya irin taka,yasa ka hanani auran abu,har marin abu kayi saboda ta sanya hannu ta mari abusufyan,sannan kayimun korar wulaƙanci saboda nazo wurin ƴarka,dama tara ka nake yi,yau zaka mutu baba buzu,kuma a sati mai zuwa zan auri abu,'_   Gabanshi ne yayi mugun bugu jin abunda sayyadi yace,nan take jikinshi ya shiga kerma yana rawa,wata irin zufa ce ta shiga gangarowa daga cikin ƙofofin hudar gashin jikinshi,   Muryarshi na kerma yace"Wanene kai!ka faɗamun!meyasa kake son abu,saboda me ka shiga rayuwarta!"   murmushi sayyadi ya saki tare da takawa ya matsa dab da Baba buzu suna fuskantar juna yace"Ni ba rayuwar zainab na shiga ba!rayuwar abusufyan nashiga,bansan zainab ba,abusufyan nasani!shisshiginka da bin ƙwaƙƙwafinka yau sun ja maka zaka rasa ranka baba buzu!kana tunanin cewa bansan bibiyata da kakeyi ba?don kawai kasan wanene ni!da wata manufa nake son ƴarka!shiyasa ba'ason mutun ya tsananta bincike wala tajassasu,da alama bakasan da hadisin ba,koda yake kaifa babu ilmin addini akanka.......'    Tunda sayyadi ya soma magana,baba buzu ya dinga jin tsigar jikinshi na tashi,tamkar ana tsige gashin jikinshi,nan take ya zube saman guiwarshi,idanunshi sukayi jawur muryarshi na rawa yace"Kada ka kashe ni,ka barni da raina!inason nasake ganin abu a idanuna,"   Fashewa da dariya sayyadi yayi tare da cewa"zaka iya ganin abu amma a lokacin da dukkan wasu kalaman bakinka suka daina aiki,ko uffan ba zaka iya furta mata ba,sae dai ka bita da ido kafin azare ranka,sannan kuma inaso nayi maka wani albishir baba buzu,Abu tana ɗauke da cikin Abusufyan,amma na 6oye hakan,zata haife shi ne acikin gidana kuma amatsayin ɗana.....'cike da shaƙiyanci sayyadi ke maganar,   Jin cewa abu nada ciki yasa baba buzu jin hawaye na sauka a idanunshi,dama yaji ma yana mamakin yadda akai babu ciki ajikin abu,ashe sayyadine ya kwantar da cikin don karsu gani su hanashi auranta,"   "Kaji tsoran Allah!kada ka cutar mun da ƴata!don Allah ka fita daga rayuwarta,wai lafin me mukayi maka ne?menene haɗinka da rayuwarmu,Ni da abu bamu ta6a cutar da kowa ba,mun taso mu biyu muke rayuwa bamu da kowa,Na roƙe ka akan ka ƙyale mun ƴa ta,koda zaka kashe ni amma kada ka ta6a abu,'   Bakomai zai baka mamaki ba face yadda ɗai-ɗaikun mutane ke giftawa a wurin amma babu wanda hankalinshi ke kaiwa wurinsu,hatta haris sai da yazo ya wuce ta gate ɗin gidan amma bai kai idonshi wurinsu ba,kuma wannan duk aikin sayyadine,    Juyawa sayyadi yayi ya nufi rugwagwar mashin ɗinshi dake ajiye inda yayi parking dinshi hawa yayi sannan yana kallon baba buzu yace"Zanyi amfani da abu ne don in ƙuntata rayuwar abusufyan,zan kuma yi amfani da yaron da abu zata haifa don in tarwatsa farin cikin zuri'arsu kamar yadda suka tarwatsa farin cikin namu family ɗin,nabarka lafiya,"yana ƙarasa maganar tashi ya tashi mashin ɗin da gudu yabar anguwar,   Barin unguwar tashi ke da wuya baba buzu ya yanke jiki ya faɗi,yana mirgina mirgina a ƙasa,kumfa na fitowa daga bakinshi,sai lokacin mutane suka dawo hayyacinsu suka lura da baba buzu dake kwance yana ta harba ƙafafunshi,   Lokaci guda mutane suka taru a kopar gidan sukayi dandazo suna kallonshi wasu na tambayar lafiya,wasu kuma nayi mashi addu'a,kafin su yanke shawarar kiran wani acikin gidan,    Koda aka sanarma su hajiya ameena abunda ke faruwa jiki na rawa suka kwaso gaba dayansu suka zo wajen gate din gidan,   Lokacin da abu tayi arba da mahaifinta dake kwance ƙasa yana ta birgima,zukunnawa tayi agabanshi tana jijjiga jikinshi tana faɗin'baba baba...meya faru dakai!baba dan Allah ka tashi....wayyo Allah na,nashiga uku......'haka ta dinga sambatu tana jijjiga,bawan Allah sai ƙoƙarin buɗe baki yake yi don ya sanar mata da cewa sayyadi ba mutumin kirki bane,kuma tana ɗauke da cikin abusufyan amma hakan ya faskara,anan dae rai yayi halinshi,baba buzu ya riga mu gidan gaskiya.........'   A ranar abu kamar ta zauce saboda tsabar tashin hankalin rashin mahaifinta da tayi,haka hajiya Ameena da alhaji babu wanda baiji mutuwarshi ba,sun jima suna tunanin menene yayi silar mutuwarshi amma basu gano hakan ba,kowa ranshi na bashi cewa kamar guba ce saboda wannan kumfar da bakinshi ke fitar wa, One week da rasuwarshi ko zaman makoki ba'a kammala ba,abu ta bijiro da maganar auran sayyadi,babu wanda baiji haushinta ba,don hajiya kamar ta rufe ta da bugu,a ƙarshe dae Alhaji nuraddeen ne ya goya mata baya,dama shi ya yarda da sayyadi kallon mutumin kirki yake yi mashi, Batare da 6ata lokaci ba,aka ɗaura auren abu da sayyad'    Kunji yadda akai Abu ta shiga gidan sayyad da cikin abusufyan,aurensu ko One month bai cika ba sai ga ciki ya bayyana ajikinta kuma cikin ba ƙarami ba,yayi watanni,nan fa mutane suka soma tsegumi akan cikin nata,abun ya ɗaure masu kai,aure ko wata baiyi ba ciki ya bayyana,dama ƙarami ne cikin da sauƙi,amma wannan cikin da girmanshi fa,ya haura 4 months, Tun zuwan da tayi gida,wurin Hajiya ameenatu don ta gaishe da ita,kallo daya hajiya tayi ma cikin nata,ranta ya bata cewa cikin abusufyan ne!duk da lokacin da suka rabu da abusufyan babu ciki ajikinta babu alamarshi, "Abu wannan cikin na jikin ki,kamar na abusufyan ne!raina yana bani haka,dama mutane na kawomin tsegumin cewa cikin jikinki yayi saurin girma daga yin aure ko wata baiyi ba sai  ya bayyana kuma da girma har haka"?   Tur6une fuska abu tayi tare da cewa"Mommy dan Allah kidaina maganar nan,taya za'ace cikin abusufyan ne?idan cikinshi ne meyasa bai bayyana ba tun lokacin da muna tare dashi,sai bayan watanni kuma har nayi aure sannan zai fito"?   Hajiya ameena tace"abu kenan,kika san ikon Allah?koda yake ba zanyi maki gardama ba,amma ni raina na bani cewa cikinshi ne,Amma zamu zuba ido muga lokacin da zaki haife shi,in har cikin nan yayi wata tara toh na sayyadine,amma in har kika haifeshi nan da 5 months,to na Abusufyan ne,'   Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Mommy nifa ba cikin abusufyan bane!na sayyadine,dan Allah mudaina maganar nan,'   Hajiya tace"naji zan bar maganar amma ina nan ina zuba ido,kuma in aka haifi yaron zamu je ayi mashi gwajin jini don a tabbatar da yaron wanene shi............'   Bayan abu ta koma gida cike da damuwar abunda mommy ta sanar mata,sayyadi na dawowa ta kwashe duk abunda suka tattauna ita da hajiyarsu ta sanar mashi,   Aikuwa tun daga ranar bakin mutane ya mutu murus,babu wanda ya ƙara tanka mata game da cikin dake a jikinta,abun ya ɗaure mata kai,sa6anin da da mutane ke tsegumin ta amma yanzu ko maganar cikin babu maiyi,   Kuma tun daga ranar Hajiya Ameena,ta fara samun ta6in hankali,na yawan mantuwa,yawan sambatu ita kaɗae da dai sauransu,a ƙarshe ma taji ta tsani zama a kano gaba ɗaya tamkar korarta ake,haka ta tattara ta koma katsina da zama,dama suna da katafaren gidansu acan wanda suka bari amma duk in suka zo garin a gidan suke zama,ita kaɗae ta koma gidan tana rayuwa acikinshi,tare da mai aikinta,kafin daga baya haris ya dawo wurinta,mahaifinsu kuma yana zuwa akai akai don ya dubasu, After 5 months A tsakar dare naƙuda ta taso ma abu,gashi ita kaɗae ce a gidan babu kowa,sayyadi bai dawo ba,dama wani lokacin in ya fita sai tsakar dare yake dawowa kamar aljani, Tun daga saman gadon ta faɗo ƙasa tana faman dafe cikinta tana cizon la66anta tana kuma ambaton sunan Allah abakinta,sosai cikin ya shiga murɗa mata tare da matsanancin ciwo. Daga ƙarshe ta zube anan wurin,bata tashi farkawa ba sai asaman gadon asibiti,kukan jariran da ta haifa ne suka tashe ta daga dogon baccin daya ɗauketa sakamakon allurar baccin da Dr yayi mata,a hankali ta buɗe idanunta ta ware su akan fuskar sayyadi dake tsaye hannunshi ɗauke da jariri naɗe acikin towel,murmushi ya sakar mata tare da cewa"Barka da sauka my wife,ina tayaki murna kin haifa mana kyawawan ƴa'ƴa," yunkurawa abu tayi ta miƙe daga zaune tana kallon yaran dake jere a gefenta guda biyu nade cikin towel ga kuma ɗaya a hannun sayyadi,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,saboda tsabar murna bakinta yaƙi rufuwa,muryarta na kerma tace"Wannan duk nawa ne?ƴa'ƴana ne ni kaɗai"? sayyadi yace"namu dae,naji kina cewa duk ƴa'ƴanki ne,bayan duk ƙoƙarin nawa ne,nakudarsu ne kawai kikayi,"cikin zolaya yayi mata maganar, Hannu tasa tare da daukar ɗaya daga cikin jariran ta buɗe fuskarta tana kallonta,gabanta ne taji ya faɗi rasss! ganin jaririyar na kama da Abusufyan,maimakon taga kamanninta kona sayyadi a fuskar yarinyar sai taga fuskar abusufyan, bin fuskarta da kallo sayyadi yayi ganin kamar tana cikin damuwa yace"meya faru ne?yanzu fa naga kina farin cikin samun ƴan uku,lokaci guda kuma naga kin canza? "Babu komai,"ta bashi amsa muryarta a kasalance, Haihuwar tazo mata cikin sauƙi,a ranar aka sallame ta,suka koma gida,bakomai yafi damun abu ba face yadda mutane suka ƙi zuwa yi mata barkan samun ƴan uku,ko leƙo gidanta babu wanda yayi,tayi tsammanin danginshi zasu zo amma abun mamaki babu wanda ya leƙo da sunan ɗan uwanshi yazo duba yaranta,jikinta yayi mugun sanyi,duk taji ta tsani kanta,amma daga ta kalli ƴan ukunta sai taji farin ciki aranta,suka dae ne dangin da take dasu aduniyar nan,su take gani taji daɗi aranta,lokacin da yaran suka kai wata ɗaya aduniya,aranar wata ƴar uwarshi tazo kawo mata ziyara,ita ta taimaka wurin yi mata wankan jego,da kuma yi ma yaran wanka,duk yadda abu taso taja ta da fira don taji a ina suke da zama suna da dangi,amma matar nan da shegen wayau ko uffan bata ce mata ba,a haka har suka kammala wankan jegon matar ta koma garinsu, Abu ba ƙaramar wahala tasha ba,wurin rainon ƴan ukunta,babu mai taimakonta,itace yi masu wanka har sau biyu arana safe da kuma dare in zata kwantar dasu,wankin kayansu da suka 6ata,ɗawainiyarsu da kuma ɗawainiyar kanta,abun duk ya jagule mata,ga sayyadi ko tsinke bai ta6a sanya hannu ya kawar mata ba,bayan kafin suyi aure shi da kanshi yake sanar da ita cewa in sukayi aure duk ranar da yake hutu bai aiki har girki sai yayi mata ashe duk ƙaryace yake yi mata,Abusufyan kuwa muddin yana agida bai barinta tayi aiki,sai dai yayi shi kaɗae ko kuma suyi atare,da kanshi yake cewa"Abuna idan har kika haifa mana ƴa'ƴa ni da kaina zan dinga yi masu wanka,idan mata ne zan dinga sharce masu gashin kansu ina gyara masu shi,bazan bari kisha wahala ba,'in ta tuna waɗannan kalaman nashi sai ta fashe da kuka,dama ita dana sani bata da daɗi,Allah ka rabamu da aikin dana sani,Amin Kunji yadda akai Abusufyan ya auri abu,da kuma yadda akai yabar nigeria da kuma yadda akai ta haifi ƴa'ƴanshi agidan wani wanda ya taso amatsayin ubansu, 💋Boss Bature💋 Lokacin da Abusufyan yakai ƙarshen labarin nashi sai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro,cikin sauri Abba ya janyoshi jikinshi yana lallashin shi,bashi kaɗae ba hatta su fawan,jabeer,irfan,khaleed dasu twins sai da idanunsu suka cicciko da kwalla,Sgr da Omar kuwa jinjina kai kawai sukeyi,Abbas ne yace"Yanzu ina ƴa'ƴan suke?suna raye ko sun mutu ne"? "Nima abunda nakeso na tambaya kenan,"acewar hajiya azeema da jikinta ya gama mutuwa,kowa mamakinshi ta yadda akai waɗannan abubuwan suka faru batare da Abusufyan da kuma goggon katsina sun sanar ma kowa ba, cikin sanyin murya Abba yace"ka faɗa mana ina ƴa'ƴan suke yanzu"? ɗagowa abusufyan yayi da idanunshi waɗanda sukayi jawur yace"ni kaina bazan iya cewa ga inda suke ba,a lokacin can baya ina bibiyar rayuwarsu,ta hanyar haris shiya kira ni a waya yake sanar dani cewa abu ta haifi ƴa'ƴa kuma yaran dani suke kama sosai,tun daga lokacin na sanya shi akan ya dinga bibiyar rayuwar yaran yana sanar dani duk wani abu dake faruwa arayuwarsu,shine yake turo mun da hotunansu ina ganinsu a wulakance,yara ne mata guda ukku wani lokacin babu kallabi a kawunansu kuma babu takalma a ƙafafunsu,tun lokacin nake tsananin jin tausayinsu,kuma raina yake bani cewa tabbas ƴa'ƴana ne su.....saboda akwai wani lokaci da nazo nigeria zuwan bazata batare da sanin kowa ba............." Bai ƙarasa maganar ba suka jiyo muryar goggon katsina tana sambatu tana cewa"ƙarfen nasara ba tabbas,Allah ka tsine ma baturen daya ƙirƙiri motar harisu,shegiyar motar kamar da katako akayita,tun safe muke a hanya take ta bamu matsala mtsswwwwww haba ina dalili,tafiya daga katsina zuwa abuja sai kace mutun zashi saudia a ƙasa?ae dana san haka zata faru da a kafa na tako wlh,shegen maƙo irin nashi,maimakon ya biya mana kuɗin jirgi,ya nace sai mun hau waccen rugwagwar motar tashi..........'kasa ƙarasa maganar tayi ganin yadda matasan gidan suka taru a falon gidan,ga kuma Abusufyan ɗinta dake ta faman sharar kwalla, Don bala'e,a hannu ta ruƙo zaninta daga ita sae dogon undi fari ajikinta,ta cire zanin gaba ɗaya,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,da alama, Tsayawa tayi cak baki asake tace"Na shiga uku ni yau,abun dae ba sa'a,Allah yasa dae ba wani ya mutu ba,wlh yanzu inyi kwana in koma katsina don ni ban shirya ganin gawa ba,dan Allah ku faɗa mun maiya faru"? Miƙewa sukayi gaba dayansu suna kallonta cike da tuhuma,adaidai lokacin kuma Dr haris ya shigo tare da Saude,suma duk suka tsaya cirko-cirko ana kallon kallon, Koda Abusufyan yayi arba da goggon katsina,jiki na rawa ya tunkareta,tare da faɗawa jikinta ya rungumota sosai yana cigaba da kukan, Nan fa hankalin goggon katsina ya tashi,hannu bibbiyu tasa tare da ɗago da fuskarshi daga jikinta tana cewa"Abusufyan ɗina meya faru?meyasa kake kuka?kai da zanga kana farin ciki?ko Omar bai nuna maka ƴa'ƴanka bane.....? cike da mamaki kowa ya zuba ido yana kallonta,Abusufyan dake kuka nan take ya dakatar da kukan nashi yana cewa"Mommyna...ina abu take ne?ina yaran da ta haifa suke?suna ina? Bata bashi amsa ba,sae ta kalli Omar dake tsaye yana kallonsu tace"Omaru ina kakai mashi ƴa'ƴanshi ne?yaran nan fa da kazo dasu gidana ƴa'ƴan abusufyan dina ne dama saida na faɗa maka,dan Allah ku nuna mashi ƴa'ƴanshi ya gansu yaga yadda suka girma ko hankalinshi ya kwanta banson ganinshi yana kukan nan" Tashin hankali! Nan fa kowa ya ruɗe yana tunanin su wanene yaran da gwaggon katsina take magana akai, "Gwaggo kina nufin cewa hosana da jahad ƴa'ƴan abusufyan ne!"?Omar ne yayi mata tambayar fuskarshi ɗauke da mamaki, goggo tace"Eh mana,sune ƴa'ƴan abusufyan ɗina,suna ina ne.....' Kafin wani ya buɗe baki ya ƙara magana,sai ga Jahad da hosana sun fito da gudun gaske jin muryar gwaggon katsina data karade gidan,tana ganinsu ta washe baki tana cewa"Yawwwa ga ƴa'ƴan abusufyan ɗina nan sun ƙaraso,maza ku ƙaraso in rungume ku ajikina,' ƙarasawa sukayi tare da faɗawa jikinta,ta hada su duka ta rungume ajikinta,tana ta faman murmushi, Fawan ne yace"Anya gwaggo tasan me take cewa kuwa?taya waɗannan yaran zasu kasance Ƴa'ƴan uncle ɗinmu?hakan na nufin cewa Sehrish itama ƴar shi ce kuma,su jinin mu ne? Cikin sanyin murya abusufyan ya juya tare da kallon fawan da yayi maganar yace"Tabbas su ƴa'ƴana ne!nasan zakuyi kokwanton maganarta ne saboda tana da ta6in hankali,to inaso ku sani cewa mommyna tana acikin hayyacinta,tasan me takeyi duk da akwai ta6in hankalin atare da ita,amma ba kowane lokaci bane take kasancewa dashi ba,' Jin maganarshi yasa Hosana da jahad suka juyo suna kallonshi yayin da zuciyoyinsu ke cigaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi, Kowa fa ya shiga ruɗani,wasu ma saboda tsabar mamaki sun gaza magana,irin su Sgr da kuma su Jahan, "Yanzu duk ba wannan ba!dole muji ya akai kasan cewa su ɗin ƴa'ƴanka ne!kuma ya akai kuka bar rayuwarsu ta wulaƙanta batare da kun sanar mana ba!sannan dole muji ta bakin yaran game da irin ruƙon da wannan mutumin yayi masu!'acewar Abbansu junaid,ranshi a6ace yake maganar, Gwaggo dae bata gane inda zancen nasu ya dosa ba,amma tana da tabbacin cewar abusufyan ya fasa abunda suka jima suna 6oyewa,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,dama ta gaji da 6oyon al'amarin da sukeyi,saboda ganin irin wahalar da yaran suke sha a hannun mugun mutumin nan, Omar yace"Abunda ya kamata shine,yanzu naga anata kiran sallar isha'e yakamata muje muyi sallah,kafin mu dawo nasan gwaggo ta ɗan rage gajiya,sai mu zauna ayita taƙare kawai,in yaso sai jahad tayi mana bayanin komai tunda itace mai cikakken hankali acikinsu,Sehrish ita kanta bana tunanin tana acikin hayyacinta yanzu, Kowa ya amince da maganar omar,batare da 6ata lokaci ba,suka wuje bedrooms ɗinsu domin yin alwala,hajiya azeema ce ta shigar da Gwaggon katsina cikin ɗakinta tare da saude kafin agyara masu inda zasu zauna, Yau dae gidan Abban sojoji a hargitse yake,Wlh ni kaina a hargitse nake,sai addu'a kawai, Abbansu na fitowa daga cikin toilet,junaid ya faɗo mashi acikin ranshi,nan fa gaban shi ya faɗi rasss,sae lokacin ya tuna da cewar babu junaid fa acikin gidan tun ɗazu,duk wannan budurin da akeyi babu shi acikinsu, Hankalinshi amatuƙar tashe ya tunkari wayarshi dake ajiye saman side drawer ya dauketa,tare da lalubo numbar junaid ya danna mashi kira cikin sa'a wayar tashiga tana ringing amma ba'a ɗaga ba,kusan sau huɗu yana kira ba'a ɗagawa, Ana biyar ɗinne aka ɗaga wayar,kara wayar yayi kunnanshi yana cewa"Junaid ina ka shiga ne!!"shiru yaji ba'a tanka mashi na,nan fa yabi ya rikice, "Junaid wai baka jina ina magana ne?bazaka amsa mun ba?junaid kodae wani abu ya faru da kaine? Nan ma shiru ba'a bashi amsa ba, Muryarshi tamkar zaiyi kuka ya kuma cewa"don Allah babyn Abbanshi kayi mun magana mana! Muryar mace ce ta amsa mashi da cewar"ka duba whatsapp ɗinka,zaka ga video mun tura maka," Jikinshi har kerma yakeyi wurin katse kiran ya shiga whatsapp ɗinshi,new number ya gani tayi mashi message da video, Saboda tsabar fargaba,tun kafin ya buɗe video ɗin zufa tashiga gangarowa a fuskarshi,dukkan ilahirin jikinshi ya shiga yin kerma,idanunshi sukayi jawur tsoranshi kar a videon yaga junaid cikin wani yanayi,bazai iya jurar wannan ba, Runtse idanunshi yayi yana karanto addu'o'i abakinshi,kafin daga bisani ya daure ya cije ya buɗe videon, Zazzare idanunshi yayi waje tamkar kwayar idanunshi zata faɗo ƙasa, A ƙarshe kuma ya fashe da dariya,tare da zubewa saman guiwowinshi yana tikar dariya, Bakomai bane acikin video ɗin nan ba,face Mommynsu junaid Alexandra rungume da junaid asaman gado,suna kwance abunsu,da alama ma kamar bacci yake yi ajikinta.......   *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*, 😔 Abunda ya faru,lokacin da wata mata ta kira junaid da sunan mommynshi don yazo ya ɗauketa a airport,jiki na rawa junaid ya shige cikin motarshi ya kama hanyar zuwa airport bayan ya fita daga gidanne ya tuna da tace in ya fito ya sanar da ita,fiddo wayarsa yayi da niyyar kiranta,tunanin taya zai kirata ma ba number ya shiga yi,adaidai lokacin ta sake kira tambayarshi tayi ya fito ne,ya amsa mata da eh yana a akan hanyar zuwa,cigaba da tafiya yayi zuciyarshi cike fal da son ganin mommynshi,driving yake yi yana ayyana farkon haɗuwarshi da mommynsu baisan wani irin runguma zaiyi mata ba,yayi zurfi acikin tunaninshi kwatsam sae ga wasu jerin motoci sun kusa goma sha biyu,baƙaƙe kuma da black tinted,da gudun gaske suka nufo inda junaid yake,koda junaid ya lura da motocin nan fa hankalinshi yayi mugun tashi,ƙarasowarsu ke da wuya suka zagaye motar shi,yadda bazai iya kubce masu ba,nan fa hankalin junaid yayi mugun tashi,jikinshi ya shiga rawa,tsoranshi kar ace mutanen da mommy azeema ta sanar dashi cewa suna bibiyar rayuwarshi ne,zama yayi acikin motar hankali a matukar tashe, ɗaya daga cikin motocin aka buɗe,sae ga wani gabjejen mutun faffaɗan gaske sanye cikin suits,kai tsaye ya nufi motar junaid hannu yasa tare da knocking glass ɗin motar,zuge glass ɗin junaid yayi atsorace yana kallonsu sae faman haɗiyar yawu yake yi da kyar, kafin yayi wani yunƙuri Mutumin nan ya buɗe motar tashi,gaba ɗaya ya cakumi junaid ya toshe mashi baki,ya nufi cikin motarshi dashi,bayan ya sanyashi acikin motor,atare suka tashi motocin da gudun gaske suka bar wurin, junaid dake a back seat na motar tuni ido ya raina fata,hawaye suka shiga wanke mashi face ɗinshi,muryar shi tamkar zaiyi kuka yace"Su wanene ku?laifin me na aikata maku?dan Allah kada ku rabani da rai na,inason na sake ganin Abbana.....'bai kai ƙarshen maganar tashi ba,ɗaya daga cikinsu ya daka mashi tsawa tare da cewa"Shut up!ko tari ka ƙara yi saina fille maka kai," Jin haka yasa junaid yayi tsit zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi, Wani katafaren gida suka shiga tare da shi,bayan sunyi parking ɗin motocin,ɗaya daga cikinsu ya buɗe motar tare da ɗauko junaid asaman kafaɗar shi,ya wuce dashi cikin gidan,a babban falon gidan ya sauke shi,sannan ya juya ya fuce, To fa,tsayawa junaid yayi cikin tashin hankali yake kallon haɗaɗɗen falon komai a gyare tsaf,tunani ya shiga yi mai yasa suka kawo shi nan suka ajiye shi?ko dae kidnapping ɗinshi sukayi ne?hannu yasa yana share hawayen shi,bai kammala wiping ɗinsu ba,yajiyo takun takalmi kwas kwas, A firgice ya ɗago don yaga wanene,zuba mata ido yayi yana kallonta,daga saman stairs take saukowa down,jikinta na sanye da doguwar riga fara mai shegen kyau tabi shape ɗin jikinta,ƙafafunta kuma na sanye da takalma high hills farare duk da tsayin da take dashi don sam ba gajera bace,ba ƙaramin kyau shigan tayi mata ba,kasancewarta farar fata,wuyanta na sanye da ziririyar sarƙa fara ta diamond,hannunta kuma na sanye da Zobe ɗaya kacal a middle finger,shima na diamond ne,ta ɗaure gashin kanta abaya,mai tsayi wanda launinsa yake tamkar golden yellow, A hankali ta ƙarasa saukowa daga saman benen,sannan ta tsaya tana kallonshi daga inda yake tsaye,duk da akwai tazara atsakaninsu amma suna iya ganin juna sosai,ƙare mashi kallo tashiga yi,burinta junaid ya fara shaida ita wacece kafin ta sanar mashi, hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa rass rasss,batare da jin tsoro ba ya tunkareta sai da ya kusa kaiwa inda take sannan ya tsaya yana kallonta,ƙwayar idanunta yabi da kallo blue colour wanda hakan ya tabbatar mashi da cewar mommynsu ce, dama kuma yasan ta a hoto,komai na fuskarta irin na Babban yayansu ne,duk da ta kwana biyu aduniya amma hakan bai 6oye kyawun fuskarta ba,tamkar ƴar shekara 30 haka fuskarta take,hatta jikinta yana nan yadda yake da kyau da kuma diri, A hankali junaid ya furta"Mommy!is you? jinjina mashi kai tayi alamar eh,da gudun gaske ya ƙarasa tare da faɗawa jikinta,sosai ya ƙankameta saboda tsabar farin ciki ya fashe mata da kuka,nan take itama kukan yazo mata atare suka shiga yin kukan babu mai lallashin wani,tamkar zasu haɗe jikin junansu su koma ɗaya haka suka ƙanƙame kansu,daƙyar Alexandra ta iya dakatar da kukan nata,ta sanya hannayenta tare da ɗago da fuskar junaid tana kallonshi,hawaye sun wanke mashi fuskarshi tass, muryarta na rawa ta ambaci sunan shi"Ro..meo.ɗina,' Cikin shessheƙar kuka junaid yace"Mommy,ashe zan sanyaki acikin idanuna,bansan da wasu kalmomin zan bayyana maki irin farin cikin da nake ciki ba,i luv u so much mom....' Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,duk irin watsin da tayi dashi tabar Nigeria,hakan bai hana shi sonta ba, Kwantar dashi ta sake yi asaman ƙirjinta,ta sanya hannayenta tana ɗan bubbuga bayanshi,kafin ta mayar da hannunta ɗaya acikin sumar kanshi,ta jima tana mamakin girman shi,ta tafi ta barshi a lokacin da yake ɗan jinjiri dashi,amma yanzu tadawo ta same shi ya girma ya zama babba,ba ƙaramin farin ciki taji ba,mara misaltuwa, ɗago dashi ta kuma yi daga jikinta cikin sanyin murya tace"romeo ɗina,kayi haƙuri ka daina wannan kukan duk da nasan na farin cikin ganina ne,ni kaina bazan iya misalta farin cikin dana ji ba,wai yau ni ce tare da babyn dana bari yana jinjirinshi,ya girma ya zama babba,nayi danasanin tafiya nabarka romeo,nayi kewarka sosai,hakanan na raba kaina dakai,ba don bana sonka ba romeo,zan iya cewa nafi sonka fiye da kowa aduniyar nan.....na godema Allah daya nunamin wannan ranar....inaso na sake neman yafiya a wurinka saboda na cutar da rayuwarka sosai,ko wani yaro lokacin da yake jinjiri burinshi yaji dumin mahaifiyarshi,ya kasance atare da ita don samun kulawa daga gareta a koda yaushe,koda ace yana da uba,amma kai baka samu wannan gatancin ba,ka tashi hannun maza ba'a hannun mahaifiyarka ba,baka samu soyayyar nan ba,duk da mahaifinka yayi ƙoƙari sosai wurin gina rayuwarka tayi kyau,haka ƴan uwanka ma ba su bari ka zubar da hawayenka ba,amma duk da haka nasan abun ya jima yana maka Ciwo..." Tana ƙarasa maganar,ta zube saman guiwowinta agabanshi,tana roƙon yafiyarshi,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,cikin sauri shima ya zube saman guiwowinshi suna fuskantar juna ita dashi, "Mommy dan Allah ki tashi,banason kina duƙamin,komai ya wuce yanzu tun da kin dawo wurinmu da ranki kuma da lafiyarki,har yanzu kina da sauran damar da zaki gyara kuskuren da kikayi abaya mommy," ashagwa6e ya ƙarasa maganar,murmushi ta saki tana kallonshi,ji take yi da tana da ikon da zata mayar dashi cikin cikinta,taƙara haifo shi da tayi,don kawai ta bashi wannan kulawar daya rasa, Sun jima a wannan yanayin,kafin daga bisani suka miƙe tare,ta ruƙo hannunshi cikin nata,ta wuce dashi upstairs ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake a wurin suka shiga,ɗakin ya haɗu sosai, "Mommy me yasa ba kije gidaba?wurinsu Abba su ganki? Yayi tambaryar yana kallonta, "I just came because of u junaid,inaso mu samu lokaci sosai atare,ka ganni dakyau nima na ganka da kyau,tun yanzu in fara aikina na baka kyakkwayar kulawa kamar jariri,in yaso gobe zamu shiga gidan da safe ko? Murmushin jin dadi junaid yayi tare da cewa"Eh,mommy,dama ni yakamata in fara ganinki tunda dama nine ban sanki ba a zahiri" "Bansani ba ko kana jin yunwa,amma zansa akawo mana abinci,in baka abaki kaci ka ƙoshi,yau dae atare da babyna zamu kwana,' Dariya junaid yayi,ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai mommynshi ta shiga bashi kulawa a wannan lokacin, Kunji yadda akai junaid ya kasance tare da mommynshi,har ta ɗauko ma Abbansu video ɗinsu saman gado ta tura mashi,abunda yasa kuma Abban bai gane Voice ɗinta ba,shine da kanta tayi amfani da wayarta wurin canza muryarta don ta tsoratar da Abbansu. 💋Boss Bature💋 fitowa Abbansu yayi daga cikin ɗakin nashi fuskar nan tashi awashe saboda tsabar farin cikin dawowar Alexandra,bakomai yafi faranta mashi rae ba face Junaid daya gani rungume ajikinta,yaji daɗi sosai,ko ba komai Junaid dae ya haɗu da mommynshi,hankalinshi zai ƙara kwanciya, Bai sanar masu da zuwan nata ba,saboda sunyi waya da ita ta sanar dashi cewar till tomorrow zasu shigo gidan don tana bukatar kasancewa da junaid don su kara fuskantar juna sosae,hakan yasa ya bari kawai sae goben sannan su ganta unexpected,duk da a kagare idanunshi suke da suyi tozali da ita. Gaba daya suka haɗu atare suka wuce masallaci, Jin shiru hayaam bata fito ba tsawon lokaci,yasa Azmee leƙawa ɗakinta,anan ta same ta zaune dirshan gefen gadon ta zabga uban tagumi,jin motsin mutun yasa ta ɗagowa fuskarnan a yamutse ta kalli azmee, "Hayaam wai dama duk budurin nan da akeyi acikin gidan nan kina ɗaki ƙumshe"? Jin abunda azmee tace yasa tace"hmmmm,to ina zani Aunty azmee?babban yaya ya kore ni daga gidan nan,nasan muddin na leƙa waje ya ganni sai yasa an kora ni daga gidan nan,' Cike da mamaki azmee tace"Subhanallahi!taya akai hakan ya faru?laifin me kika aikata mashi da har ya koreki daga gidan nan?shi da ma bai damu da mutane ba" ta6e baki hayaam tayi kafin tace"Ni banyi mashi laifin komai ba,Sehrish ce ta shiryamun makircin da yasa har ya kore ni,batare da nayi mashi laifin komai ba," Tunda tasoma magana azmee ke kallonta,ga rashin gaskiya nan ya bayyana ƙarara a fuskarta,taya akai ma Sgr yasan da zamanta da har zai kore ta?dole sai in itace tayi mashi shisshigin da yasa har ya ganeta kuma ya kore ta, "Allah ya kyauta toh,!yanzu ya zakiyi kenan?kinfa san halin shi!dole fa ki tattara kibar gidan nan!in ba haka ba wlh zaki fuskanci mummunan hukunci daga wurinshi,' Hankali tashe hayaam ta miƙe tsaye tana kallon Azmee tamkar za tayi kuka tace"don Allah aunty azmee ki taimaka mun,wlh banso in bar gidan nan!na saba da zama acikinshi,anan nake samun duk wani jin daɗin da nakeso,acan gidanmu duk babu waɗannan kayayyakin more rayuwar,nasan zaki taimaka mun," Dariya azmee tayi tana kallonta ko yaushe tazo da har zata ce tayi sabo da mutanen gidan ta ayyana a ranta, "Aunty azmee dan Allah ki taimaka mun,in xauna acikin gidan nan,nasan yana jin maganarki,ki roƙa mun shi akan yabar ni in cigaba da zama,wlh bazan ƙara shiga shirgin kowa ba,zanyi rayuwata cikin salama," Azmee tace"Tabɗijancan!so kike kija mun bala'e ko?ina zaman lafiyata agidan nan,Wacece ni?da har kike tunanin Sgr zaiji maganata?kin manta matsayina ne acikin gidan nan?kefa kike da alaƙa dasu ko kin manta ne"? Da biyu azmee tayi mata maganar saboda wulaƙancin da hayaam tayi mata, Magiya hayaam ta shiga yi mata tana roƙonta akan ta nema mata mafita tamkar zata zuƙunna mata saman guiwarta,don ita sam bata shirya barin gidan yanzu ba,tabb yo mima akai kenan"ta fada cikin ranta. Sosai abun yaba azmee dariya, "Hanya ɗaya ce hayaam in zaki iya!idan har kinason cigaba da zama acikin gidan nan"! jiki na rawa hayaam tace"Ina sauraronki aunty azmee,wlh koma manene zan iya ni," Azmee taci gaba da cewa"daga yau zaki dinga yin shigar maza,kinasa gashin baki kamar yadda sehrish tayi a lokacin da tafara aiki acikin gidan nan kinga sai kizama kamar sabon mai tayani aiki" Waro ido waje Hayaam tayi tare da cewa"Haba Aunty azmee ni zanyi shigar maza?so kike na ƙasƙantar da kaina har yarinyar can ta raina ni" Azmee tace"that's the only solution,if not sai dae fa ki tattara kayanki ki bar gidan nan!"ta karasa maganar tana jiran jin ta bakin hayaam din don tasan da kyar zata amince dama shiyasa ta fadi mata hakan, gyaɗa kai hayaam tayi tace"shikenan zanyi tunani in ga in zan iya,kafin nan zanci gaba da 6oye ma ganinshi" Azmee tace"to shikenan kiyi yadda kika ga yafi maki,ni dai gaskiya ba ruwana,kuma fa dole ki rika futowa kina taya ni aiki,indai kina a cikin gidan nan, don bazai yiwu ba ki zaune a daki baki komae gaskia " Hannu hayaam ta aza akanta tana faɗin"Nashiga uku! dariya Azmee tayi kafin ta kuma cewa"hayaam zamanki fa bazaiyiyu acikin gidan nan ba,Sgr ya riga da ya kore ki!muddin ya sake ganin fuskarki dole ya hukuntaki,kuma kinga gwaggonsu ta katsina tazo,!matar nan bazata ta6a bari ki zauna acikin gidan nan ba,in har taji cewa ke ƙanwar matar yayyansu ce,nan zaki ga tashin hankali,sae ta kunyataki acikin jama'a,shiyasa nace kiyi shigar maza kawai,Ni zan taimaka maki muna yin aiki atare inyaso duk wanda ya tambayeni xance mashi abokin aiki ne na samo,nasan babu wanda zai zargi wani abu, Komawa hayaam tayi ta zauna gefen gadon cike da damuwa,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,da tana zaman lafiyarta acikin gidan,kwaɗayinta da zalamarta su suka ja mata,gashi ita gskia bata jin zata iya yin wani shigar maza wannan ai kaskanci ne, "Na manta ban sanar maki ba!" Rai a6ace hayaam tace"Menene!" Azmee tace"SEHRISH TAGA ƳAN UWANTA,ASHE ƳAN UKUNE SU,YANZU HAKA SUNA ACIKIN GIDAN NAN!BAKI GANSU BA,ABUN FARIN CIKI KAMANNINSU IRI ƊAYA SAK!BAKI TA6A BANBANTA SU," A razane Hayaam ta miƙe tsaye hannunta dafe da saitin zuciyarta tace"WAI DAGASKE AUNTY AZMEE? AZMEE TACE"Zan maki ƙarya ne?yaran suna nan,kyawawan gaske,HOSANA DA JAHAD!!!!!" Jiki amace hayaam ta koma ta zauna,gabanta na faɗuwa rasss rasss!tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi, Murmushi azmee ta saki tare da juyawa ta kama hanyar fita daga ɗakin,buɗe kopar tayi tare da sa kai ta fuce, Kamar jira take azmee ta fita,nan fa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita,saboda tsabar 6acin rai,wani irin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata maƙoshinta,komae ya jagule mata,tabbas tana bukatar tayi magana da Aunty laila,lokaci guda yadda sukai da yaya babbar ya shiga dawo mata, sambatu tashiga yi tana bugun bed mattress kamar wata zautacciya, Bayan kammala sallar isha'e,atare suka dawo cikin gidan,a babban falon suka kuma zama kamar ɗazu dae, Gyaran murya Abbansu yayi kafin yace"Ina yaran suke ne?wani yaje ya kira mana su,domin jin ta bakinsu" Miƙewa fawan yayi kamar dama jira yake yi,wucewa ɗakin sehrish yayi bayan ya isa ya kwankwasa masu ƙopa,jahad ce ta buɗe mashi kopar jikinta na sanye da hijabi da alama bata jima da kammala salla ba, Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Abba nason ganinku,idan ba damuwa ku fito mu tafi atare," Jahad tace"Toh,bari na kirasu,"ta fadi hakan tare da juyawa ciki ta kira hosana da sehrish wadda har lokacin bata motsaba,tana nan saman gadon ta ƙanƙame jikinta, "Hosana kuzo Abbansu na son ganinmu!hada sehrish kema ki taso," Maƙe kafaɗa sehrish tayi alamar bazata taso ba, "Sehrish dan Allah kidaina abunda kikeyi,nasan duk don saboda ganinmu ne,idan har baki so zuwanmu ba zamu bar gidan nan,"acewar jahad, ɗaure fuska Sehrish tayi tare da kawar da fuskarta gefe tana faman hura hanci, babu yadda basuyi ba akan sehrish tabiyo su amma taƙi binsu,har fawan sae da ya leko yayi mata magana amma ko kallo ma bai isheta ba, A ƙarshe suka ƙyaleta,suka bi bayan fawan ya shiga babban falon tare dasu, gaba daya hankalin kowa ya dawo kansu,musamman Abusufyan dake zaune agefen abbansu,ji yake kamar ya tashi ya rungumosu ajikinsa,su twins kuwa dasu irfan zuba masu ido kawai sukayi suna kallonsu,haka Omar da Abbas da kuma hajiya azeema,kowa burinshi yaran su tabbata ƴa'ƴan abusufyan ne,duk sun ƙagu suji cewa yaransa ne,tabbas da ba ƙaramin farin ciki zasu ji ba, Sgr dae tunda ya ɗago ya kallesu ya gane cewa babu sehrish acikinsu,bayan yaji cewar dukansu Abbansu yace a kira mashi, Abbansu ne yace"Ina ɗayar take ne?ni bana gane ma wacece babu acikin ku! Omar yace"waɗannan hosana da jahad ne!sehrish ce babu acikinsu," Abbas yace"Masha Allah,gaskiya banta6a ganin yara masu kamanni irin nasu ba,Allah dae yasa mu tabbatar da abunda muke hasashe akansu....' "Meya hanata zuwa"?muryar Sgr ce ta karaɗe kunnuwansu,har sae da su jahad suka ɗan tsorata dashi,dama tunda sukazo hankalinsu ke kanshi saboda launin kwayar idonshi ba ƙaramin ɗaukar hankali takeyi ba, Fawan yace"Ba yadda bamu yi da ita ba,amma tace bazata zo ba,kamar tana cikin damuwa sosai,ko kallona fa batayi ba,da naje kiransu,' A zafafe Sgr ya yunkura tare da miƙewa daga saman kujerar da yake ya nufi sashensu Azmee, "Kuzo ku xauna kusa dani,"hajiya azeema ce tayi masu magana yayin da takeyi masu nuni da hannunta, Hannunsu ruƙe cikin na juna,suka ƙarasa wurin sofa ɗin da hajiya azeema take,a gefenta suka zauna,duk jikinsu asanyaye saboda basu saba dasu ba,tunda suka zauna jahad ke kallon Abusufyan,saboda tunawa da maganar gwaggon katsina da tayi ɗazu na cewa shine mahaifinsu,kanta ya gama ɗaurewa,tashiga tambayar kanta taya akai hakan zata kasance?meke shirin faruwa da rayuwarsu ne?dama suna da dangi ne?wai su wanene su?ya akai rayuwarsu take a birkice ne? tambayoyi iri iri tashiga yi ma kanta waɗanda bata da amsar su, ƙasa ƙasa hosana tayi da muryarta tare da kai bakinta saitin kunnan jahad tace"Wancan mutumin sai kallonmu yake yi jahad,ni duk nabi na tsargu wlh,tsoranshi nake ji,shi da wannan kyakkyawan mai wasu kalar kwayar idanu kaman aljani....' "Dan Allah hosana ki daina mun magana a kunne na,wai ke bakya ganin mutanene kuma duk idanunsu na akanmu,ni kaina atsorace nake wlh,yaya Omar kaɗae nake kallo naji dan sauki,da ace baya a wurin nan da tuni na gudu...'jahad ce tayi wannan maganar,cikin raɗa tayi mata ita don kar aji su, A lokacin da Sgr ya ƙarasa bedroom dinta,tura ƙopar yayi tare da faɗawa ciki,tsayawa yayi yana kallonta,ta takure kanta,jikinta sae kerma yakeyi yayin da hawaye ke saukowa daga cikin idanunta,sam bata lura dashi ba har sae da yayi gyaran murya,a firgice ta wurga idanunta akan fuskarshi,gabanta ne taji ya faɗi rass,nan take kermar jikinta ya ƙaru sosai, "Taso muje"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,girgiza mashi kai tashiga yi tana cewa"bazan iya tafiya ba,ƙafafuna ciwo suke yi mun,dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni,inji da abunda ke damu na,' Abun ya ɗaure mashi kai,yadda take yi mashi jayayya,tabbas akwai matsala hakanan dae yarinyar bazata ƙi bin umarninshi ba, Bai tsaya wani 6ata lokaci ba,ya ƙarasa shiga cikin ɗakin har saman gadonta ya bita,sai faman ja da baya takeyi,gaba daya ya ɗaukota tare da azata asaman kafaɗarshi ya fito da ita,sai kuka takeyi mashi tana cewa ya sauketa ita bazata je ba,su rabu da rayuwarta,suna ƙuntata mata,har bugun bayanshi ta dinga yi da hannayenta don ya sauketa,duk yana jinta, tashin hankalin da ba'a sama shi date! "Ga babban yaya nan ɗauke da sehrish din daman nasan sai dae ya ɗaukota,"acewar fawan,jin sautin kukanta yasa kowa yakai hankalinshi wurinsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,ƙiri-ƙiri tana gudun ƴan uwanta,bayan duk alamu sun nuna cewa su ɗin fa ƴan ukune, Koda Sgr ya ƙaraso wurinsu, a tsakiyar inda kowannansu yake,sai ya sauko da ita,Kamar dama jira takeyi ya sauke ta ƙasa da gudu ta kama hanya zata bar wurin,aikuwa a zafafe ya damƙo waist ɗinta da ƙarfi ya maido ta jikinshi, Har Abbanshi na cewa"ka bi ta a hankali don Allah,ta tsorata sosai,bansan meke damunta bane, ko ƴan uwan nata ne ke batasan gani "abusufyan kuwa runtse idanunshi yayi,har cikin ranshi yake jin soyayyar yaran, Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Na bani,na shiga uku!Na lalace!dan Allah ku rabu dani!ku barni na tafi, banason ganinsu!ni ba ƴan uwana bane!ciwon kai suke sani idan ina kallonsu,raɗaɗi nake ji acikin zuciyata kamar ana ƙonata...." Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda sehrish ke cewa,yanayin yadda take maganar zai tabbatar maka da cewar da gaske take tana jin duk wani abu da ta faɗi,musamman Sgr daya ruƙota,yaji jikinta da wani irin Zafi,har shi kanshi zafin na shafar jikinshi, Abusufyan ne yace"kuyi mata addu'a don Allah,zai iya yiyuwa akwai sihiri ajikinta,wani zai iya shiga tsakaninta da ƴan uwanta saboda ni shaidane akan yadda suke son junansu!nagani da idona,basa rabuwa da junansu kullum suna manne da juna,banta6a ganin ƴan uwa masu son junansu ba irin yaran nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke tsananin son junansu.....' Cike da mamaki Abba yace"meyasa kake tunanin cewa akwai sihiri ajikinta? kowa ya kasa kunne yana sauraronshi, "In har da gaske sune ƴa'ƴana kamar yadda nake hasashe to tabbas an shiga tsakaninsu ne,saboda mutumin da suka taso awurinshi,nayi bincike akanshi,bama haka ba shi da kanshi ya rabani da bibiyar rayuwarsu da nake yi,kowa zaiyi mamakin taya nabar yaran rayuwarsu ta wulaƙanta batare dana taimaka ma rayuwarsu ba,ko kuma na sanar ma wani daga cikin dangina don a taimaki rayuwarsu,ba laifina bane tursasamun akayi........' Kasa ƙarasa maganar yayi saboda hawayen da suka shiga kwaranyowa daga cikin idanunshi, Abbas yace"Akwai sauran labari kenan, bari mu gyara zama don a idasa warware mana komai," ɗagowa yayi da idanunshi da suka yi jawur har sun dan fara kumbura ya kalli sgr tare da cewa"idan ba damuwa,inaso ka zauna tare da ita akusa dakai,saboda ka ruƙeta karta gudu,in yaso sai kayi mata addu'ar koda bata dawo hayyacinta ba,zataji sauƙin radaɗin ciwon kan da takeyi, "Okey,"ya amsa tare da samun wuri ya xauna,asaman laps ɗinshi ya zaunar da Sehrish,sosai ya ruƙota jikinshi,tunda ta kwantar da kanta asaman wide chest ɗinshi,numfashinta ya fara daidaita,a hankali kuma zafin jikinta ya soma raguwa,saitin kunnanta yakai ƙaramin bakinshi yana karanta mata addu'o'i,bugun zuciyarta ne ya soma raguwa,jikinta kuma ya rage kermar nan da yake yi, "Ina gwaggon take ne?naga bata fito ba inaso ayi komai agabanta tare da Dr haris kuma"abusufyan ne yayi maganar yana kallon Abban nasu Fawan ne ya kuma miƙewa tare da cewa"Bari naje na kirasu,' cike da zolaya jahan yace"Messenger,aikinka na kyau,"murmushi kawai yayi tare da wucewa ciki,ae yau ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don murna don kuwa ranshi ya gama bashi cewa su jahad din yan'uwansu ne. Ba da jimawa ba,sae ga Gwaggon katsina ta fito har yanzu undin nan ne ajikinta Allah ma yasa irin dogon nan ne mai kauri,tana biye da bayan fawan tana dungurin keyarshi tana cewa"Shegen bisa,da kanshi kamar na tamola,baccin ma baza abar mutun yayi ba,matsalar mutun yazo gidan jikoki kenan duk subi su addabi rayuwarshi.....' Muryar Abba ce ta katse ta da cewa"gwaggo ku samu wuri ku zauna,magana ce mai muhimmanci zamuyi," Har zata zauna idonta suka sauka karaf akan Sehrish dake zaune asaman laps ɗin Sgr,hankali tashe tace"mun shiga uku!yanzu agabanku ake wannan aika-aikar amma babu wanda ya tanka?hosana ce ko jahad?wacece acikinsu?wlh bazan bari a lalatamun ƴa'ƴan Abusufyan ɗina ba,dasu zamu koma katsina ayau.......' ..da sauri Haris ya katseta da cewa"Dan Allah gwaggo kidaina wannan sambatun naki,bakiji abunda abba yace ba!magana mai mahimmanci za'ayi,ki samu wuri ki zauna kuma kiyi shiru,' Wurga mashi harara tayi kafin ta wuce tare da samun wuri ta zauna,shima haris ya zauna agefenta,sai da suka xauna sannan ta lura da hosana da jahad dake zaune gefen hajiya azeema, Da sauri ta mayar da idonta kan sehrish don taga wacece ita,ko dae idanunta ne suka fara samun matsala don taga kamar kamanninsu iri ɗaya sak, "Harisu,kana ganin abunda nake gani kuwa,wai yaran nan har nawa ne masu fuska iri ɗaya"? A dan ƙule haris yace"Eh,su uku ne!ko kinmanta su nawa ne,na faɗa maku Abu ta haifa!wannan ae cikon ƴar ukun tasu ce,' "Oh to,yanzu nagane"ta fadi tana faman gyara zamanta, Sae da kowa ya natsu sannan abusufyan ya kalli su hosana da jahad yace"Ya sunan mahaifiyarku ne?kuma waye mahaifinku"? Yayi masu tambayar ne don ya fara tabbatar da cewar sune ɗin dai dagaske, Har suna haɗa baki wurin cewa"Sunanta Zainab,amma anace mata abu ƴar buzuwa,sannan mahaifinmu kuma sunanshi Sayyadi.......'tunkan taƙarasa maganar kowanne daga cikinsu ya shiga sakin murmushi,jin sun ambaci dai dai da sunayen da abusufyan ya gama bada labari akansu,tunkan aje ko ina suka tabbatar da cewar sune dae ƴa'ƴan abusufyan ɗinsu, "Ina mahaifiyarku take yanzu"?ya kuma tambayarsu, Jahad tace"bamu son inda take ba,amma koma a ina take bata acikin hayyacinta,lokacin da tabarmu tasamu ta6in hankali,' jiki asanyaye ta ƙarasa maganar, "Yanzu zaki iya bamu labarin abubuwan da suka faru arayuwarku gaba daya,har izuwa lokacin da kuka rabu da junanku"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh, Kafin abusufyan ya ƙara cewa wani abu,Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa"Yakamata,ka fara sanar dasu game da alaƙar da take tsakaninka da mahaifiyarsu" Jinjina kai abusufyan yayi kafin yace"zaku iya tunawa da mutumin daya ta6a zuwa wurinku lokacin kuna ƴan ƙanana,har ya ɗauke ku hoto a wayarshi?lokacin da zan tafi kuka dinga kuka kuna cewa na tafi daku baku son zama da mahaifinku"? A razane hosana da jahad suke kallonshi yayin da suke ƙoƙarin tunawa da wannan lokacin......' Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"nasan ba zaku iya tunawa da wannan lokacin ba!,amma mun sha haɗuwa daku wani lokacin kuna ku kadae,wani lokacin kuma tare da mahaifiyarku........' Batare da 6ata lokaci ba,abusufyan ya basu labarin rayuwarshi da abu a takaice yadda zasu fahimta,sai lokacin suka san asalin mahaifinsu da kuma kakansu baba buzu daya rasu,da kuma irin rayuwar da abu tayi tare da abusufyan kafin su rabu,ta auri ya sayyadi,sunsha kuka sosai,aransu suna jin ƙuncin abunda mahaifiyarsu tayi masu,ashe duk itace taja masu bala'en da suka fuskanta, Kowa yayi shiru na wani lokaci suna sauraron kukan dasu hosana da jahad sukeyi gwanin ban tausai,banda sehrish wanda tayi lamo ajikin Sgr,duk wani abu da suke faɗi acikin kunnanta,amma bata ɗago ta kallesu ba,har yanzu dae bata dawo dai dai ba, Daƙyar su Omar suka lallashe su,kafin daga bisani Abbansu yace"Jahad yanzu ke muke sauraro!munaso muji irin rayuwar da kukayi a hannun mutumin nan!" Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan Haroon,ya jima da shigowa batare da sanin kowa ba ya la6e yana jin labarin da abusufyan ke ba su jahad,na rayuwarshi da mahaifiyarsu,hankalin shi yayi mugun tashi,gaba ɗaya ya tsorata ya rikice,wata irin zufa ce tashiga gangarowa a fuskarshi,bakomai ya razanar dashi ba face ganin Ƴan ukun gaba ɗayansu sun haɗu acikin gidan kuma ga Ubansu da kanshi ya gane cewa ƴa'ƴanshi ne wannan alama ce dake nuna cewar asirinsu ya kusa tonuwa, Tuni zufa tasoma tsastsafo mashi acikin jikinshi,sharkaf ta jiƙa t shirt ɗin jikinshi duk kuwa da ba zafi,jan ƙafarshi yayi tare da lalla6awa cikin sanɗa ya wuce bedroom ɗinshi, Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin,gaba ɗaya jikinshi sae faman rawa yakeyi,yama rasa inda zai tsoma kanshi kamar wani zautacce haka ya koma,a fusace ya dunƙule hannunshi tare da kai ma madubin ɗakin naushi,nan take glass ɗin jikinshi ya tsastsage ya zube ƙasa, Hannunshi ya shiga fitar da jini,ko kaɗan baiji xafin hakan ba,raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mashi yafi raɗaɗin glass ɗin daya shige shi, Da ƙarfi ya furta"That's impossible!ƙaryane ba gaske bane!!wlh bazan rasa rayuwata ba!dole na rayu ko da kowa zai rasa ranshi,zanyi komai zan yi don ganin na kwaci kaina!! Yana magana yana sakin huci,idanuwan nan nashi sunyi jawur dasu luhu luhu, Cikin sauri ya zura hannunshi tare da ciro wayarshi daga cikin aljihun jeans dinshi ya danna ma wata number kira,cikin sa'a aka ɗaga kiran! Wata irin muryace ta karaɗe kunnanshi mai tsoratarwa"Ba saida nace maka karka sake kira na ba!Tun farko ya mukayi dakai? hankali atashe haroon yace"Ni ba wannan maganar tasa na kira ka ba!ka faɗamun taya akai kukayi gangancin barin yaran nan har suka haɗu da danginsu!!!!!!! "Wasu yara kenan!" Haroon yace"Ƴan ukun nan!na gansu da idona acikin gidan nan!yanzu haka gasu can a falon gidan nan sun taru suna jin labarin rayuwar yaran nan! Nan take muryar mutumin da suke waya dashi ta canza, "Wai kana nufin hosana!jahad!sehrish!duk sun haɗu anan cikin gidan naku ko mi"? A ƙule haroon yace"Eh mana!akansu nake magana,wlh kowa yayi ta kanshi!saboda yarinyar nan dole ta ambaci sunanka acikin labarin da zata bayar kuma kasan cewa muddin waɗannan namun dawan guda biyu sukaji mugayen abubuwan da kuka aikata dole su binciko ka duk inda ka shiga kuwa,kuma koda a ƙarƙashin ƙasa ka 6oye,! Fashewa da dariya mutumin yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace"Baza su ta6a iya gano ni ba!nafi ƙarfinsu nesa ba kusa ba!zanyi amfani da ƙarfin sihirina wurin dakatar da tunaninsu.......' Tun kan ya ƙarasa maganar haroon ya daka mashi tsawa tare da cewa"Ya Isa haka!!zancen ku iri ɗaya da ita!daga kai har ita daga anyi magana sai kuce ƙarfin sihiri,zakuyi amfani da sihiri ku asirce mutun!angaya maku cewa kowane lokaci sihiri ke yin tasiri ne!sam babu Allah aran kowannanku don haka babu wanda zai tsira acikinmu!ko ka manta da irin mutuwar da mahaifinku yayi ne?duk wani sihiri da kuke taƙama dashi ae a wurinshi kuka gado shi,akan idon kowannanku yayi mummunar mutuwa sakamakon farmakar shi da kakanmu salahuddeen sukayi,ku baku da tunani ne?me yasa shi a lokacin baiyi amfani da ƙarfin sihirin shi ba don ya hana kanshi mutuwa?ko don saboda ya tsufa ne yasa nashi sihirin baiyi aiki bane? Gaba daya haroon ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga batanan yake fita ba,ba don komai ba sai don saboda yasan cewa bazai kai labari ba,sun ja mashi bala'e da masifa, Wata irin gigitacciyar tsawa mutumin ya daka mashi wadda tayi silar dawowarshi cikin hayyacinshi,yayi tsit yana faman sauke ajiyar zuciya, "haroon!ya kamata ka iya bakinka!kasan dawa kake magana!duk wannan tada jijiyoyin wuyan da kakeyi bazai hana kaga mutuwarka ba!zaifi kyau ka mayar da hankali wurin ganin ka sama ma kanka abokan tafiya,kada ka yarda wannan abun ya tayar maka da hankalinka,babu wanda ya isa ya ta6a ka acikinsu,!abu ɗaya kawai mukeso awurinka!muddin ka aikata hakan komai yazo ƙarshe zaka tsira kuma muma zamu tsira,sannan farin cikin gidansu zai tarwatse na har abada,......................' Natsuwa haroon yayi yana sauraron bayanan da mutumin yake kora mashi,sae amsa mashi yake yi da to,toh Alamar ya amince da abunda suke so ya akaitan, Acan main palour ɗin kuwa,kowa ya kasa kunne yana sauraron Jahad, **** *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.      *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*, 2 pages ne hada na monday *CIGABAN LABARI* Abu ba ƙaramar wahala tasha ba a hannun Ya sayyadi,daga ita har yaran bai raga masu ba,tun yana 6oye mata mugayen halayenshi,har ya fara bayyana mata su,babban tashin hankalin da ta fara fuskanta a wurinshi shine shigo mata da Manyan Alhazan da yake yi acikin gidansu,in suka shiga ɗaki sai suyi fiye da 6hrs basu fito ba,wani sa'in har gurnani take ji ya cika gidan tamkar namun dawa na yaƙi,wannan abun ba ƙaramin razanar da ita yake yi ba,kuma duk in ta tambayeshi me suke zuwa yi a wurinshi sai yace mata *Wala tajassasu*kuma ta tsaya a iya matsayinta kar tace zatayi mashi shisshigi irin na mahaifinta,tarasa uban me sukeyi acikin ɗakin,abun ba ƙaramin damunta yake yi ba,tun tana iya jurewa har dae wata rana ta yi masu la6e a window ɗin ɗakin shi,a ranar abu taga tashin hankalin da bata ta6a gani ba da idonta tunda uwarta ta haife ta,wani irin yunƙurin amai ne yazo mata da gudun gaske tabar leƙen sun da takeyi ta koma bakin fanfo tana kwarara amai tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito,agaban fanfon ta zuƙunna tare da fashewa da kuka,ta dafe kanta da hannunta saboda raɗaɗin da yake yi mata,gaba ɗaya rayuwarta ta shiga ƙunci taji ta tsani kanta,kamar ta kashe kanta haka ta dinga ji a lokacin, ta jima abakin fanfon kafin ta koma cikin ɗakinta,a lokacin triplets ɗinta suna kwance sae sharar bacci sukeyi,komawa tayi daga gefen gadon ta zauna tare da ɗan russinawa dai dai saitin fuskokinsu tana kallonsu,yadda suke sharar baccin su zai tabbatar maka da cewar suna cikin kwanciyar hankali,tasa su gaba tayi tana faman shessheƙar kuka muryarta na rawa ta dinga cewa"Na cuci kaina!Kuma nacuci rayuwar ƴa'ƴana,Haƙƙin mahaifina kadae bazai ƙyale ni ba,na bijire mashi na ƙuntata mashi duk don saboda in auri sayyadi,haƙiƙa na tafka babban kuskuren da bazan ta6a gyarashi ba,Ni duk a zato na kowane mutun daya iya jan ayar kur'ani ya fassarata kuma yayi wa'azi abainar jama'a,mutumin kirki ne bai aikata zunubi tsarkakakke ne shi,ashe ba haka bane,ko acikin malaman akwai nagari akwai kuma na banza,wanda suke amfani da iliminsu na addini don su cutar da mutane,Mommy saida ta gargaɗe ni akan hakan amma na bijire mata saboda na makance akan soyayyar sayyadi,Ni ban tsaya nayi bincike akan rayuwarshi ba,kawai natashi na aure shi,kuma na ƙuntata ma mahaifina duk don saboda shi,na kuma ƙuntatama Mijina mai sona da gaskiya,wlh na cuci rayuwata....!kaicona.......' Sosai abu ke shassheƙar kukan,sautin kukan da takeyi ne ya farkar da Sehrish sai faman mutsustsuka idanunta takeyi da hannayenta,hannu abu takai tare da ɗauko ta,ta zaunar da ita asaman cinyoyinta,shafa fuskarta tayi tare da cewa"Rishina kin farka?kina jin yunwa ne"?   A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar mahaifiyarsu,koda taga hawaye na zuba a idanun oumman tasu,sae ta sanya tafin hannunta tana share mata su tana cewa"oum ki daina,banasho,nima inyi kuka,'tayi maganar da hausarta ta ƴan koyon magana,hada ta6e la66anta zatayi kuka, Hakan da tayi yasa abu ta fashe da dariyar karfin hali tana kallonta,kwantar da kanta tayi asaman ƙirjinta tana shafa sumar kanta tace"na tambayeki kina jin yunwa baki faɗa mun ba,' Cikin shagwa6a tace"inaji,amma tare dashu usana da johad anci.  '   Abu tace"shikenan,bari mu jira su farka daga baccin sai in dafa maku ko indomie ce kuci,bayan kun gama ci sai inyi maku wanka,in shafa maku mai in canza maku kaya sannan in kaiku gidan maman sadeeq ku tayata fira,kina son zuwa ko?   Inasho,ta bata amsa, Suna cikin yin fira da ita sai ga sayyadi ya faɗo cikin ɗakin nata,tana ganinshi gabanta ya faɗi rass don yanzu yafi yi mata kama da ibliss,   Yadda ya nufo ta a fusace yasa tayi saurin sauke sehrish daga jikinta ta miƙe tsaye tana kallonshi fuskarta da alamun tsoro, Nuna ta yayi da hannunshi yana huci yace"Abu!uban me ya kaiki yin la6e aɗakin can!angaya maki banganki bane?duk wani motsin ki acikin gidan nan,acikin kunne na nake jinshi,basai da na faɗa maki cewa kada ki tsananta bincike akaina ba!   duk da tsoranshi da take ji hakan bai hanata tanka mashi ba, "Saboda baka da gaskiya shiyasa ka hana inyi bincike akanka!yau naga komai da idanuna ashe kai ba sayyadi bane!baƙin shaiɗan ne wanda ke 6oye mugayen halayansa!wlh nayi danasanin auranka sayyadi yafi sau aƙirga,banta6a sanin cewa kai dabba bane sae yau!wlh sai ka sake ni don bazan iya cigaba da zama da fasiƙin mutun irinka ba......'   Tunkan ta ƙarasa maganar sayyad ya fashe da dariya hada dafe cikinshi,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,shiru tayi tana kallonshi,   Sai da ya gama tiƙar dariyarshi sannan ya sassauta muryarshi tamkar zai lallashe ta yace"My wife,yau da bakinki kike jifana da waɗannan munanan kalaman?nifa ne sayyadin nan naki da kika kwallafa rai akai,ban wani canza ba,'tundaga kan yadda yake yi mata magana ta gane cewa ba karamin gogaggen ɗan bariki ba ne,ya kware wurin iya sarrafa harshe dama da irin kalaman nan nashi ya yaudareta tun farko,in yazo zance ya tsareta da idanunshi yana yi mata nasiha,   daƙyar ta iya haɗiye miyan dake bakinta,cikin sanyin murya tace"Kaji tsoran Allah!meyasa kayi amfani da ilmin da kake dashi na addini wurin cutar da rayuwata?saboda kasan cewa inason malamin addini mahaddacin al'qur'ani shiyasa ka biyomin ta wannan sigar don ka yaudare ni,laifin me nayi maka da har na cancanci hakan a wurinka"?   shu'umin murmushin nan nashi ya saki kafin yace"Ae malaman ma suna muka tara!abu kinyi kuskuren yadda da cewar kowane malamin addini mutumin kirki ne,wasu malam ne nagaske wasu kuma suna yin amfani da maluntar tasu da wata manufa don su Cimma burinsu kamar ni kenan!saboda kawai kin ganni malami ina yin shigar mutunci in yi wa'azi in janyo aya in fassara gani kuma mahaddacin kur'ani sai akace maki ni mutumin kirki ne?An rubuta a goshi na ne?me yasa kuke yin believing da abunda idanuwanku suka gwada maku ne?duk wani ɗan adam da kika sani aduniyar nan bai da tabbas!duk yadda kikaso ki gane mutun na gari kona banza abun zaiyi matuƙar wuya agare ki,saboda akwai masu fuska biyu,zaki ga mutumin banza yana aikata abunda yaga dama agaban kowa baijin kunyar kowa zai aikata zina zaiyi sata,zai zalunci wani zai sha giya,zai yi kaza yayi kaza,kinga shi wannan ya bayyana asalin suffarshi,wani kuwa zaki ganshi babban malami ne mahaddacin al'qur'ani wanda ya saba wa'azi agaban dubban jama'a yana faɗakar dasu cewa suji tsoran Allah kar suyi kaza idan sukayi kaza zasu shiga wuta idan sukayi kaza kuma zasu shiga Aljanna,idan kika bincika kuma wannan malamin ɗabi'unsa da halayansa iri ɗaya ne dana wannan mutumin dana fara kwatanta maki!amma shi bai bayyana suffarshi ta asali ba,yazo da sigar maluntaka don ya cimma wata manufa tashi ta hanyar yin amfani da ilmin addinin da yake dashi,wani kuma zaki ga malamin ne nagaske akwai ilmin addinin Akanshi amma baki ta6a ganewa, kamar dae Abusufyan yaron kirki,abusufyan tun yana da shekara sha wani abu aduniya ya haddace al'qur'ani mai girma tare da manya manyan littattafai na addini,amma ya ɗabi'unsa da halayansa suke?babu mai iya gane cewa yana da ilmin addini akanshi indae ba anyi mu'amala dashi ba,saboda irin rayuwar daya taso yanayi,abota da mata da kuma rashin kunya baijin kunyar furta kalami abakinsa ko gaban wanene 6arota kawai yake yi,kowa zaiyi tunanin cewa shi jahilin addini ne ashe ba haka bane,yasan me yakeyi kuma yana da kyakkyawar zuciya ba kamar sayyadi ba, *dawa zamu yadda aduniyar nan?lalube kawai mukeyi acikin duhu,musamman zamanin nan da muke ciki,Zaiyi wuya ka gane mutun na gari dana banza,shiyasa da yawa mata muke shan wahala wurin neman miji na gari da zamuyi rayuwa dashi,tunda bamu da tabbas akansu Mazan!haka matan ma bamu da tabbas mu kanmu,da mazan da matan wahala kowa ke sha wurin neman righteous life partners,A ƙarshe nidae shawarar da zan ba mutun shine ya dage da addu'a kawai,sannan ya gyara rayuwarshi in ma akwai wani kuskuren da yake aikatawa ko min ƙankantarshi,saboda da yawa wasu abubuwan wlh mu muke ja ma kanmu batare da mun sani ba,muyi ta ganin ba dai dai ba arayuwarmu,dole sai mun gyara sannan zamu ga dai dai mu kanmu,Allah yasa mu dace,Amin. Haƙiƙa su Sehrish sunga rayuwa fiye da tunanin mai tunani,uƙuba babu irin wadda basu sha ba a hannun mutumin nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke jin wannan sautin abun da mahaifinsu ke aikata shi da manyan alhazawan nan dake kawo mashi ziyara,abun ba ƙaramin tsoratar dasu yake yi ba,duk subi su gigice,babu yadda abu batayi ba akan ya daina shigo mata dasu cikin gidan amma ko ajikinshi,in ma ta takura mashi sai ya kwatseta da cewa ae gidan bana Ubanta bane,da kuɗinshi ya siyi gidan, Abu har ya fara affecting ɗinsu sehrish daga sunji gurnanin nan sai subi su gigice su firgice suna yi mata kuka suna cewa Oumma dodo,dodo,ta rasa yadda zatayi dasu baiwar Allah,ƙarshe ta dinga kaisu gidan makwabciyarta suna yini acan wani sa'en ma har kwana suke yi agidanta, Lokacin da Sayyadi ya gane hakan,ba ƙaramin faɗa yayi mata ba akan tadaina kai mashi ƴa'ƴanshi gidan makwabtansu,dama basu shiri da Mijin maman sadeeq,shima malamine sosai amma malamin gaske ba irin sayyadi ba,shiyasa ya tsane shi,saboda ya sanya mashi ido sosai akan lamurran rayuwarshi duk da bai ta6a tarar shi da sunan zaiyi mashi magana ba,babu wanda ke tanka ma wani acikinsu,ƙaryace ta haɗu da gaskiya,kuma a makarantar islamiyya ɗaya suke koyarwa,tun lokacin da sayyadi ke tarayya da abu,sae da ya ta6a kiranta ya gargaɗeta akan ta daina kulashi,su kansu basu san asalinshi ba,kuma basu yadda dashi ba acikin malaman makarantar amma abu taƙi jin maganarshi saboda ta makance akan son shi,maganin marasa jin maganar malamansu kenan da kuma iyayensu kai harma da mazajansu,babu wanda acikinsu bai ja mata kunne ba amma tayi kunnan uwar shaggu dasu ita ga Juliet,yanzu dae ga romeo nan yana ta gasa mata aya a hannu,duk da dae akwai aikin sihiri,Allah ya kara karemu da kariyarsa,Amin A kwana a tashi babu wuya wurin Allah su Sehrish suka kai shekara 5 a duniya,daga lokacin ne fa sayyadi ya fara sanya masu ido saboda kyawunsu dake fusgarshi,nan fa ya fara saƙa wani abu aranshi, Wani sabon salo ya 6ullo mata dashi,na horon yunwa kwata kwata yadaina kawo masu abinci acikin gidan,yaran suyita fama da yunwa,wani lokacin kamar zasu rasa ransu in suka fara billayi suna kuka,hankalinta yabi ya tashi ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,gashi bata da kuɗi bata da hanyar da zata same su balle tace zata ɗauki nauyin ciyar dasu,kamar maroƙiya haka ta koma bi gida gida na makwabtansu akansu ƴan mata abinci taba yaranta,tun tana samu suna ɗan mata har aka fara tseguminta abayan idonta,tun suna gulmarta a6oye har aka farayi agabanta,ƙarshe ma da zarar su sehrish sun leƙa kopar gida za'a fara gulmarsu ana cewa ga ƴa'ƴan abu almajira nan sun fito,haka zasu koma sunayi mata kuka,saboda tsokanarsu da akeyi,har jan gashin kansu akeyi ayita dungurin goshinsu,gaba daya mutane suka ɗauki karan tsana suka ɗaurama yaran,duk irin kyan dake garesu,kowa ya daina taimakonsu,bakomai yafi ɗaga ma abu hankali ba face yadda mutane suka tsani ƴa'ƴanta,babu damar su fita waje da sunan zasuyi wasa cikin ƴan uwansu yara sai ta gansu sun watso da gudu cikin gidan suna kuka,haka zata haɗasu a ƙirjinta ta rungumesu tana kuka,duk wannan abun dake faruwa sayyadi yana sane saboda shine silar komai dake faruwa dasu, Gaba ɗaya kowa ya ɗauki karan tsana ya ɗaura masu,mutun biyu ne kaɗae suke tausayin rayuwarsu,Maman sadeeq da kuma Mijinta,kullum cikin tausaya masu sukeyi,a kullum su hosana suka shiga gidan yunwa ta koro su,ita ke zama ta girka masu abinci,har ta kaiga in zatayi girki tare dasu take auna abincin don tasan zasu zo nema ne,ita kaɗae ce take kwantar ma abu da hankali, A ƙarshe dae da abun ya fara yi mata yawa da kanta ta tunkari sayyadi a ɗakinshi lokacin yana a gida baije aiki ba,tunda ta shigo ɗakin ya ɗaure fuskarshi yana daga kishingiɗe saman gadonshi, Wuri tasamu daga gefe ta zauna ta gaishe shi daƙyar ya amsa mata ma,yadda kasan auren ƙiyayya sukayi dashi, "Meyasa kake barin mu da yunwa baka ajiye mana abinci acikin gidan nan yanzu? ta6e bakinshi yayi tare da cewa"Yaushe rabon da kiban haƙƙina na aure?hakanan zan zauna ina ciyar dake da ƴa'ƴanki ne saboda haihuwata kukayi? "Allah ya kiyaye in ƙara haɗa shimfiɗa dakai sayyad!rashin sani ne yasa ko lokacin baya nake baka haɗin kai,amma yanzu nagane ko kai wanene.... ' Murmushi ya saki yana kallonta batare da ya ƙara tanka mata ba, Cigaba da magana tayi"bai kamata laifina ya shafe su ba,su fa ƴa'ƴanka ne jininka ne!meyasa zakayi masu horon yunwa saboda laifin da nina maka?haba sayyad sai kace ba ƴa'ƴanka ba?akan idonka ake wulaƙantasu amma ko ajikinka,narasa gane wannan abun.........'takaici ne yasa ta kasa ƙarasa maganar ta fashe mashi da kuka,cikin shessheƙar kuka taci gaba da cewa"tun da na haifi yaran baka ta6a nuna masu soyayya irin ta mahaifi ba,tun satin farko da suka zo duniya,ko ɗaukarsu bakason yi,me yasa dan Allah?kayan sawar su ma duk sun tsufa sunyi masu kaɗan,amma baka ta6a ɗaukar ko fallan atampha ba wannan kace gashi a ɗinka masu,wai kai wani irin mutun ne!? Da buɗar bakinshi sai cewa yayi"Dabba!" Shiru abu tayi tana kallonshi kamar ta rufe shi da duka haka take ji,   "Ko kin manta munanan kalaman da kika jefe ni dasu ne?da bakinki fa kika kirani da sunan dabba,"   "Dan Allah to kayi hakuri komai ya wuce,ni so nake kawai ka daina yi mana horon yunwa ko dan saboda yaran nan,koda ace ni ba zaka bani ba,su yara ne basu san komai ba,ba zasu iya jurar yunwa ba,sannan kuma ya kamata ka sanyasu makaranta tunda bakinsu yafara buɗewa sosai suna magana,"ba don taso ba haka ta dinga lallashi akan ya taimaki yaran,   Sai da ya mula ya sha iska sannan yace"ni bazan iya ɗaukar nauyin karatunsu ba,saboda ni ban fito gidan arziƙi ba kamar Abusufyan,kinsan cewa Ni malamin makaranta ne,makarantar ma ta islamiyya,salary ɗina bai wuci 20k ba,idan har kinason kula da yaranki ki tashi tsaye ki nemi kuɗinki mana,'   Fuskarta ɗauke da damuwa tace"Meyasa zakayi mun haka sayyad!idan kasan cewa ba zaka iya ɗaukar nauyin su ba,meyasa ka bari na haifesu....   '   Yunƙurawa yayi tare da miƙewa yabar mata ɗakin yana faman buga tsoki,ta jima zaune jugum aɗakin nashi,kafin ta miƙe ta koma bedroom ɗinta,zirga zirga tashiga yi tana neman mafitar yadda zata samu kuɗi don ta tallafama rayuwarsu,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Ya haris,tana da tabbacin cewa in yaji halin da take ciki zasu iya taimaka mata duk da tana jin kunyar tunkararsu amman bata da wata mafitar data wuce wnn,addu'a ta shiga yi Allah yasa har yanzu da number shi data sani yake amfani, Da wayar makwabciyarta tayi amfani wurin kiran Haris,cikin sa'a ta shiga,lokacin daya ɗaga kiran taji muryarshi sai ta fashe mashi da kuka,nan fa hankalinshi ya tashi ya shiga tambayarta ko lpy,bata 6oye mashi komai ba,game da halin rayuwar da suke ciki ita da ya'yanta,haris yayi mata al'ƙawarin zai taimaka masu,su bashi lokaci, Bayan wasu ƴan kwanaki haris yayi mata aiken kuɗi masu yawa,dasu tayi amfani wurin nema masu makarantar boko da kuma islamiyya,wani lokacin har zama takeyi da kanta ta koya masu karatu,sun ɗan samu sauƙi a wannan lokacin kafin sayyadi ya sake ƙunsa masu wani baƙin cikin,ya kwashe mata Sehrish da jahad 6at aka neme su aka rasa,kamar abu zata yi hauka wurin nemansu,ashe zuwa yayi ya saida ma ƙungiyarsu yaran don suyi amfani dasu,shi kuma suka bashi makudan kuɗi,Mijin maman sadeeq ne ya tona mashi asiri a wurinta,saboda yaga lokacin daya gudu da yaran a 6oye ya tafi dasu,ranar kaca kaca sukayi dashi har bugunta sai da yayi saboda shaƙo kwalar rigarshi da tayi tana jifanshi da munanan kalamai,a ƙarshe tace zata haɗa shi da Allah in bai dawo mata da ƴa'ƴanta ba,tun daga ranar ta fara sallar dare tana kai kukanta wurin Allah,duk yadda sayyadi yaso ya juye mata tunani akan ta daina ibadar nan amma abun yaci tura,ko yayi nufin yi mata asiri babu abunda ke yin tasiri ajikinta, A ƙarshe dae sae gashi a tsakar dare aka dawo mata dasu sun fita hayyacinsu sunyi jaga-jaga dasu,kamar an jefosu haka ta gansu sun faɗo ɗakinta,sae kuka sukeyi ko sutura babu ajikinsu,ga miyau na zalala abakunansu,hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba,sai lokacin taƙara sanin wanene sayyadi,kuma ta fara kokwanton cewa Anya ƴa'ƴanshi ne,gaba ɗaya kuɗinta sae da suka ƙare wurin nema masu magani don tunda suka dawo ciwon kai,ciwon ido,ciwon ciki,ciwuka iri-iri haka suka dinga fama dasu,har gadon asibiti aka kwantar dasu sukayi jinya duk ita ke faman ɗawainiya dasu tare da Maman sadeeq,har mijin ta yana zuwa dubasu a asibitin sannan ya taimaka masu da wani abun hadi da addu'oi,amma Sayyadi kuwa ko leƙo asibitin baiyi ba,koda aka sallame su suka dawo gidama basu same shi ba,haka abu taci gaba da shan wahalar rayuwa,ko makarantarma acikin sati bai wuci sau biyu suke zuwa ba,saboda rashin lafiyar da suke ta fama da ita,kuma duk in sukaje makarantar da kuka suke dawowa,saboda yara dake tsokanarsu akan cewa mahaifinsu ɗan mafiya ne mai yankar kawunan mutane,wannan abun ba ƙaramin cutar da rayuwarsu yake yi ba,shiyasa duk suka tsani zuwa makarantar, Akwai wani lokaci da Sehrish ta fito waje cikin unguwarsu ta miƙi hanya tana tafiya tana kuka abun duniya yayi mata,kwata kwata basu jin daɗin rayuwarsu ta ko'ina a ƙuntace suke,a daidai wannan lokacin Wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta,cikin sauri matashin dake cikin motar ya buɗe ya fito ya tunkareta,sam bata lura da shi ba har sae da ya ruƙo hannunta,a firgice ta juyo tana kallonshi da idanunta waɗanda sukayi jawur saboda kukan da tasha,ga majina duk fuskarta ta 6aci,zuƙunnawa yayi agabanta yana kallonta,gwanin ban tausayi ƴar ƙaramar yarinya ko kallabi babu akanta balle takalma,ga kayan jikinta duk sun 6aci, Kamar yadda yake kallonta haka itama take kallonshi,ɗan gayu dashi yasha wankan suit ajikinshi, Cikin sanyin murya yace"Ya sunanki"? ..cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ni ka rabu dani,ka ƙyale ni in tafiyana,' Abun yaso ya bashi dariya,shafo fuskarta yayi tare da cewa"Faɗamun me yasa kike kuka?idan kika faɗa mun zan taimake ki,' A ƙule tace"Nidai ka ƙyale ni dan Allah,kawai ka rabu dani,kona faɗa maka babu abunda zaka iyayi mana saboda babu mai sonmu Allah ne kawai ke son mu,' Tuni yaji hawaye sun cicciko mashi acikin idanunshi,Haris dake zaune cikin mota yana hangensu ta glass ɗin motar ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bashi ba, lallashinta ya shiga yi yana cewa"kiyi haƙuri kinji?bakowa ne baisonku ba,Nima gani kuma ina sonku sosai,ashirye nake dana taimake ku indae kunaso,zan ɗauke ku mu gudu mu bar ƙasar nan,in tafi tare daku can wani wuri mai daɗi kuyi rayuwarku ko baki so? "dagaske kake"?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar, ɗaga mata kai yayi alamar eh,tare da cewa"yanzu ki biyoni mu tafi batare da kowa ya ganmu ba," Girgiza mashi kai tayi tare da cewa"Su hosana fa?su bazaka tafi tare dasu ba?Oummanmu fa?itama anan zaka barta, "Kada ki damu suma duk zanzo in ɗaukesu daga baya," Maƙe mashi kafaɗa tayi tace"a'a ni bazan bika ba,sae dae inje in kirasu Johad da hosana,mu tafi atare," "Shikenan zan jiraki ki kirasu,kada ki faɗa ma kowa babu wanda zai san mun tafi," Amsa mashi tayi da toh sannan jiki na rawa ta juya da gudu ta koma gidan, Sai lokacin haris ya fito daga cikin motar jikinshi a sanyaye ya ƙarasa inda abusufyan yake zuƙunne,hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarshi yace"Yanzu ka tabbatar da abunda nake faɗa maka ko? Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"Haris yaran nan fa ƴa'ƴana ne!ina ji ajikina,hatta kamannin fuskarsu ma irin nawa ne,bansan ya akai hakan ya faru ba,mutumin nan baida Imani dama na jima ina zarginshi,kuma zanyi bincike akanshi,bazan ƙyaleshi ba haris,ni babban abunda yafi damuna yadda yake tafiyar da rayuwar yaran,kamar sunfi kowa rashin gata aduniya,ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan har tasan cewa kowa baison su,tama rasa ina zata tsoma ranta saboda ƙuncin da take ji,so yake su kamu da ciwon zuciya tunda ƙuruciyarsu," ƙarasa maganar yayi tare da miƙewa tsaye yana share kwallar data zubo mashi, "Akwai matsala fa,muddin rayuwar yaran nan taci gaba da tafiya ahaka,yakamata muyi gaggawar sanar da Abbanku domin ashawo kan matsalar tun kafin ka rasa yaran nan!amma inaso yanzu idan suka zo mu fara biyawa asibiti domin ayi masu gwajin jini don mu tabbatar da cewar ƴa'ƴanka ne," Yana kai ƙarshen maganar tashi,sae ga Sehrish ruƙe da hannun Hosana da jahad,ta ruƙo hannun kowannansu sun fito daga gidan,ko abu batasan da fitar su ba,saboda ta shiga makwabtansu wurin maman sadeeq don ta samo masu abincin da zasu ci, Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar abusufyan lokacin da yayi arba dasu,ruƙe da hannun juna,kamar jira yake yi su ƙaraso wurinshi,ya zuƙunna tare da haɗasu duka ya rungumesu a ƙirjinshi,ya jima dasu a haka kafin ya raba jikinshi da nasu,anan ne yayi masu hoto da wayarshi,ya ɗaukesu a yadda suke kaca kaca dasu da niyyar ya nuna ma gwaggon katsina don taga halin da yaran suke,ko zasu nemi mafita, Akan idon mijin maman sadeeq mlm nura,abusufyan ya sanya su sehrish acikin motarshi,a back seat suka zauna,haris kuma shike driving ɗinsu, Shi kanshi yayi mamakin yadda yaran suka amince suka biyo shi,ko mahaifiyarsu basu nema ba,duk irin shaƙuwar dake tsakaninsu da ita wannan zai tabbatar maka da cewar ta kansu sukeyi,sun gaji da komai, A katafaren gidan nan nasu inda sukayi rayuwa shi da abu,tare dasu hajiya Ameena anan yakai yaran,cikin gidan ya shiga tare dasu,ya rage kayan jikinshi,sannan ya bisu ɗaya bayan ɗaya da kanshi yayi masu wanka acikin toilet,ya wankesu tass ya kuma wanke masu gashin kansu da shampoo,bayan ya kammala yi masu wankan,anan bedroom ɗinshi,ya shafe masu jikinsu da mai,ya gyara masu sumar kansu,sai da yabi kowaccensu yayi mata kalaba guda biyu akanta,ba ƙaramin kyau sukayi ba,bayan ya gama yi masu kitson ya hau saman gadon tare dasu ya kunna masu cartoon awayarshi na tom and jerry suna kallo, Shigowa haris yayi cikin ɗakin hannunshi ɗauke da manyan ledoji guda biyu,lokacin daya samu abusufyan kwance saman gadon tare da ƴan ukunnan duk sun manne mashi suna kallo,abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba,sae yaji aranshi dama a wurin abusufyan yaran suka taso,da sun ji daɗin rayuwarsu, Ƙarasawa yayi tare da miƙa mashi ledar kayan,ya taso ya kar6a,kayan sawa ne daya siyo masu,sai kuma ledar abincin da yayi masu take away a restaurant, Bayan haris ya fito daga ɗakin ya fito falo yana jiran Abusufyan ya kammala shirya yaran su tafi asibitin, Sanya masu kayan abusufyan yayi,sannan ya fiddo masu da take away ɗin abincin suka zauna suna ta turawa a bakunansu,zuba masu ido yayi yana kallonsu,ganin ya kura masu ido yasa Hosana ta ɗebo abincin a hannunta takai mashi abakinshi don yaci shima, Murmushi abusufyan yayi ya buɗe bakinshi ta sanya mashi abincin,a haka har suka kammala cin abincin, Yayin da suke nan,Abu nacan tana haukan neman ƴa'ƴanta,gida gida haka ta dinga bi tana neman su hosana,har sai da Allah ya haɗa ta da Mijin maman sadeeq shi ne yake sanar da ita cewa wani matashin saurayi ne mai kama da yaran yazo ya ɗaukesu,tunda taji hakan ranta ya bata cewar Abusufyan ne,jiki asanyaye ta koma cikin gidan,gefen gadonta ta zauna addu'a tashiga yi Allah yasa shine,in ma dagaske shinen Allah yasa karya dawo mata dasu hosana ya tafi dasu kawai duk inda zaije,tabar mashi su, Lokacin da sukaje asibitin akayi masu gwajin jini,result ɗin ya nuna cewa yaransa ne,nan fa suka shiga murna shi da haris,duk da sunyi mamakin taya akai yaran suka kasance nashi!hakan na nufin da cikinshi abu tayi aure, Haris ne ya bashi shawarar su ɗauke yaran kawai karsu maidasu gidan nan,Abusufyan shima ya amince da hakan,bai maida su sehrish ba ya koma dasu gidansu,kusan kwana uku su sehrish sukayi awurin Shi,acikin waɗannan kwanakin sun samu kyakkywar kulawa a wurinshi,kullum sai sunce mashi yaje ya ɗauko oummansu itama ta dawo gidan,sai yace masu su ƙara haƙuri zai kawo masu ita, Ana haka sayyadi yadawo tun bayan da aka sallami su sehrish da jahad daga asibiti bai ƙara leƙo gidan ba sae a wannan lokacin yayi ma abu zuwan bazata,tun aranar ya soma tambayarta ina ƴa'ƴanshi suke,banza takeyi mashi bata bashi amsa,jinjina kanshi yayi tare da cewa duk ma inda takai su zasu dawo ne da ƙafafunsu, Aranar da yayi maganar,tsakar dare suna kwance abusufyan ne tsakiyarsu,hosana da jahad suna gefe da gefenshi,Sehrish kuma na kwance saman jikinshi duka ya sanya hannunshi ya dafe su, Kwatsam yaji kukansu acikin kunnuwanshi,a firgice ya farka nan fa yaga tashin hankalin da bai ta6a gani ba,sai birgima sukeyi idanunsu sun canza launi,kowacce ta dafe kunnanta sae ihu takeyi,saboda sunansu da ake ambata da wani irin sauti mara daɗin ji,hankalin abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar yaran su mutu,wata irin zufa ce ke tsastsafowa daga jikinsu,sharkaf suka jiƙe, Faɗowa cikin ɗakin haris yayi jikinshi na kerma,abusufyan na ganinshi muryarshi na rawa yace"Haris kalli yaran nan ka gani wlh bansan me ya same su ba,ko zamu kai su asibiti ne"? Girgiza kai haris yayi tare da cewa"Ko mun kaisu asibiti babu abunda zasu iya yi masu!yanzun nan sayyadi ya kirani awaya ya sanar dani cewa mu dawo mashi da ƴa'ƴanshi in ba haka ba zasu mutu a hannun mu ne,kuma zaiyi shari'a damu akan laifin mun kashe mashi ƴa'ƴanshi,ina da tabbacin cewar duk shirinshi ne wannan," Jiki na rawa abusufyan ya sauko daga saman gadon ya ɗauko hosana da jahad a hannnunshi,haris kuma ya ɗauko sehrish, Cikin mota suka sanyasu,sannan haris yaja motar suka nufi gidan Ya sayyadi,wuraren ƙarfe sha biyu kenan na dare,tun kan su ƙarasa ƙopar gidan suka hango sayyadi atsaye jikinshi sanye da jallabiya,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi, Parking ɗin Motar sukayi,da sauri suka ɗauko mashi yaran suka kai mashi,abun mamaki suna ƙarasawa inda yake sai gashi sun dawo cikin hayyacinsu,tun daga nan kowa yasha jinin jikinshi, koda suka saukesu ƙasa,suna ta faman murza idanunsu,suna yin arba da sayyadi,jikinsu na kerma suka ƙanƙame abusufyan suka manne mashi tamkar zasu koma jikinshi, Hasken fitilar kwan dake a kopar gidajensu da kuma hasken motar su abusufyan dake ajiye,shi ya taimaka masu wurin ganin junansu da kyau, Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Sayyad da kuma Abusufyan,maƙiya sun haɗu, Haris ne yace"kaji tsoran Allah,laifin me abu tayi maka ita da yaranta da har kake son cutar da rayuwarta? Murmushi kawai sayyadi yayi yana kallonsu yace"nagode sosai,da irin kulawar da kuka ba ƴa'ƴana,naga an canza masu kaya,an kuma saya masu takalma,abu yayi kyau,kaga masu Ji da naira,ba kamar mu ba ƴa'ƴan malam shehu.......' . afusace abusufyan ya katse shi da cewa"Kai malam!ka faɗamun taya akai ka auri abu da ciki na!don bincike ya nuna cewa yaran nan ƴa'ƴana ne!ba naka ba!dama najima ina zarginka wlh!kai ba mutumin kirki bane!" shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"Oh kanaso kasan yadda akai na auri abu da cikin ka"? Har suna haɗa baki shi da haris wurin cewa Eh, Dariya sayyad yayi kafin ya matso dab da Abusufyan suna fuskantar juna ido cikin ido yace"tabbas Ƴan ukun nan ba ƴa'ƴana bane!naka ne halak malak,tun lokacin da kuka rabu da abu ta sanar dani cewa tana jin tashin zuciya,anan nagane cewa tana ɗauke da cikinka,shine na kwantar da cikin ta hanyar yin amfani da sihiri na,babu wanda yasan cewa tana da ciki har na aureta,sannan na bayyanar da cikin a jikinta,don su taso amatsayin ƴa'ƴana.......' Katse shi haris yayi da cewa"meyasa kayi hakan toh"? Sayyadi yace"bana faɗin dalili sai dae kawai in bada amsa,' Jiki asanyaye abusufyan yakai idanunshi kansu hosana dake manne ajikinshi sun ƙankameshi,alamar basu so yabarsu anan,tuni yaji hawaye sun cicciko mashi a idanunshi aranshi yace ashe dae dagaske jini na ne su, "Amma meyasa ka auri abu?yanzu nake kokwanton cewa anya don kana sonta ka aure ta"? sayyad yace"ina fa?ni sam mace bata gabana!namiji kawai,da maza nake mu'amalata,Na auri abu ne duk don saboda in samu hanyar da zan shiga rayuwarka,kuma na samu,'yayi maganar yana nuna su sehrish dake ƙankame da jikinshi, Rae a6ace haris ya cakumi wuyan rigar sayyadi yana cewa"wlh bazamu ƙyaleka ba,mugu azzalumi!zamuyi ƙararka kotu akan yaran nan,' Dariya yayi tare da cewa"nafi ƙarfin kotu haris!babu abunda zasu iyayi mun,' ""Idan ka fi ƙarfin kotu ae baka fi ƙarfin Allah ba,zamu kai ƙararka wurinshi,kuma insha Allahu sayyad ba zakayi kyakkywan ƙarshe ba,sae kayi mummunan mutuwa kamar yadda mahaifinku kakah yayi......' Buge hannun haris yayi daga cakumar wuyan rigarshi da yayi,cike da mamaki yace"Oh ashe ka gane ni!" jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"bangane kaba,amma tunda ka ambaci cewa kana son shiga rayuwata na gane cewa kai daga family ɗinsu kakah kake,Azzaluman mutane,mugaye waɗanda suka mayar da zalunci hanyar cin abincinsu,masu tada ƙayar baya a ƙasarmu,asannu asirinka zai tonu kamar yadda na ubanku ya tonu kuma insha Allah,Abbana da kuma yayana Hussein,kai bama su kaɗae ba nayi maka alƙawarin cewa a hannun ɗaya daga cikin jikokin Amminmu zaka Mutu,mummunar mutuwa kuma a wulaƙance kamar dabba haka zakayi ta,idan Allah ya nuna mun wannan ranar ni kuma zan tuna maka waɗannan kalaman da nayi maka, Hannu Abusufyan yasa tare da dafa kawunansu sehrish dake manne da jikinshi yace"idan Allah yasa su kayi tsawancin kwana basu mutu a hannunka ba,A gabansu za'ayi komai," Fashewa da dariya sayyadi yayi hada dafe cikinshi,lokaci guda kuma ya tamke fuskarshi tamkar bai ta6a yin dariya ba yace"kai fa ƙaramin ɗan iska ne mai kwana da wando,har yanzu bakasan wanene sayyadi ba,labarina kawai kake ji,nafi ƙarfin duk wanda kake tunanin zai iya ɗaukar fansa akaina!danginku gaba ɗaga babu wanda zai iya ɗaga mun yatsa,kuma inaso na sanar maka cewa muna nan muna shirin tarwatsa farin cikin zuri'arku,muna nan muna shirya maku maƙarƙashiya,bani kaɗae bane yawa gare mu kuma muna nan kewaye daku,' Kallon juna haris da Abusufyan sukayi kafin su mayar da idanunsu kan Sayyadi, "Daga rana irin ta yau!ina mai gargaɗinka da cewa kada ka kuskura ka ƙara yunƙurin zuwa ɗaukar yaran nan!wlh in har ka ƙara takowa kazo inda suke!ko kuma ka turo wani naka da niyyar ya taimakesu!koma wanene sai ya Mutu!!!!na sanya katanga a tsakaninku dasu,zaku iya tafiya," Ya ƙarasa maganar tare da nuna masu hanyar inda motarsu take da hannunshi,hannu abusufyan ya sanya yana ƙoƙarin raba su hosana da jikinshi kuka suka fashe dashi suna roƙonshi akan karya tafi yabarsu a hannun wannan mutumin basu son zama dashi........'wata irin tsawa ya sayyadi ya daka masu a gigice suka raba jikinsu dana abusufyan suka shige gida da gudu suna kuka,ashe Abu tana a la6e a zauren gidan tana sauraronsu,tun lokacin da abusufyan yazo da su hosana,tasha kuka kamar taje ta rungumoshi ajikinta haka ta dinga ji,kamar ta zauce tayi hauka,su hosana na shigowa ta haɗasu duka ta wuce dasu ɗakinta,anan suka zauna suna ta sharar kwalla, Jiki asanyaye abusufyan da haris suka shige cikin motarsu,tun daga wannan lokacin ne abusufyan yabar Nigeria ya koma Turkey gaba ɗaya,bai ƙara leƙo nigeria ba,ya nesanta kanshi da kowa ne saboda bazai juri zuwa nigeria ba,yayin da ƴa'ƴanshi suke rayuwa awulakance baida ikon taimakonsu ko ya sanya a taimakesu,sai dae Addu'a da yake binsu da ita. Haka su sehrish suka ci gaba da shan wahalar rayuwa a hannun mutumin nan,wani tashin hankalinma sayyadi  ya fara kwaɗaita dasu,ya dinga nemansu a 6oye abu bata sani ba,duk in tayi kuskuren fita ta barsu acikin gidan yazo ya same su haka zai ƙumshe su aɗakin yana tsoratar dasu akan susha mashi gabanshi,duk abu bata ankare ba,sae wata rana da ta ta6a dawowa ta same su suna ta kwarara amai wani irin abu mai yauƙi yauƙi yana fitowa abakinsu,tsare su tayi da tambaya akan me suka sha ne ya 6ata masu ciki,ƙin faɗa mata sukayi saboda tsoran kada Abbansu ya kasheta kamar yadda yayi masu barazana in suka faɗa mata,ganin sunƙi faɗa mata yasa ta ɗauko wuƙa a kitchen ta nuna su da ita tana cewa"Ko ku faɗa mun ko in kashe ku a wurin nan,"gaba daya suka tsorata,sehrish ce ta buɗe baki ta sanar da ita abunda mahaifinsu ke sanyasu suna yi mashi,saboda tashin hankali nan take ta yanke jiki ta faɗi asume, Kukan da suka fashe dashi ne yasa makwabciyarsu shigowa gidan don taga meke faruwa ne,anan ta samu abu a sume ruwa ta ɗebo ta yayyafa mata ta farka,miƙewa tayi zaune tare da sanya hannu ta dafe saitin zuciyarta tana ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!ya Allah ka ɗauki raina tun kafin baƙin cikin mutumin nan ya kashe ni,Sayyadi ka cuci rayuwata ka gama dani nashiga uku! Wayyo Allah na!   Tasha kuka kamar ta zauce,daƙyar maman sadeeq ta lallashe ta bayan ta tsagaita da yin kukan take tambayarta meya faru,bata 6oye mata komai ba ta kwashe ta sanar mata,a lokacin maman sadeeq har hawaye sai da ta zubar masu saboda tsabar tausayin yaran,ranar yini sukayi suna jimamin abunda ya faru atare kuma suka duba yaran don su tabbatar in bai lalata su ba,duk da sun tambayesu ko ya masu wani abu a wurin sunce a'a,bayan tafiyar maman sadeeq ta koma gida mijinta ta samu tayi mashi magana akan Yayi ma sayyadi magana akan abunda yake aikatawa saboda abun yayi yawa,yana cutar da rayuwar yaran, nan gaba zai iya lalata masu rayuwarsu gaba ɗaya har ma yayi silar Rasa ransu,   Jinjina kai Malam yayi tare da cewa"Hmmmm taya zan tunkari mutumin nan?me zan iya yi mashi?Mutumin da kana ja mashi aya yana fassarata!taya zai fahimci cewa badai dai yake aikatawa ba?bayan yasani kuma yake take sanin!Tabbas na tausaya ma rayuwarsu amma babu ta yadda zan iya taimakon rayuwarsu sae dae na bisu da addu'a kawai,Allah shine zaiyi maganinshi"shi kanshi Abban sadeeq sae da ya zubar masu da kwalla,ya tausaya ma rayuwar yaran,tabbas suna cikin masifa, Bari in taƙaice maku labarin,sayyadi shine yayi sanadiyar ta6in hankalin hosana,a tsakar dare suna bacci ya ɗauketa batare da sanin kowa ba,ya kaita gidan wani Babban ɗan siyasa kamar yadda suka tsara dashi akan cewa zai kai mashi ita yayi amfani da ita don cin nasarar za6en shi,sam batasan ya ɗaukota ba sae dae kawai ta ganta asaman gadon mutumin,fasa ihu tayi da sauri ta diro daga saman gadon tana ƙanƙame jikinta,mutumin nan babu kunya babu tsoran Allah ya shiga tu6e kayan jikinshi agabanta,a tsorace tace mashi fitsari take ji,ya nuna mata hanyar toilet taje tayi fitsarin yana jiranta, Jiki na rawa ta shige cikin toilet ɗin ta rufo ƙopar,Kunna fanfo tayi don kar yaji ƙarar abunda zatayi,zagaye tashiga yi acikin toilet din tana neman abunda zata fasa window ɗin kewayen,annan ƙasa ta samu wasu ƙarafuna masu ɗan tsayi kamar an ta6ayin gyaran wani abu a toilet ɗin aka ajesu nan,   Hannu tasa ta ɗauka jiki na rawa ta haye saman toilet seat ɗin dake a rufe,ta faffasa windown da sauri da sauri duk mutumin nan baijiyota ba,sai da ta fasa glass din ya tarwatse sannan ta biyo ta windown duk batayi tunanin cewa bayan yana da tsayi ba,kawai ta afka,gaba ɗaya ta bugi floor ɗin da ƙarfi kanta ya fashe,hancinta da bakinta duk suka bugu ga sauran kananun glass da suka yayyanketa ta,gigitacciyar ƙara ta saki saboda azabar da tasha,amma hakan bai hanata yunƙurawa ta miƙe da gudun gaske ta nufi hanyar fita daga gidan,mai gadin gidan na sallar dare ta samu ta fice da gudu ta karamar kopa tana kuka ta miƙi hanya gashi dare ne, Acan kuwa tsakar dare Oummansu na bacci ta jiyo muryar jahad tana cewa"oumma ki tashi,hosana bata a gida fa,banganta ba,har kewaye na duba amma babu ita bansan ina taje ba,hankali atashe abu ta farka,a lokacin itama sehrish ta tashi,gaba daya suka shiga nemanta,duk sayyadi na ɗakinshi yana jiyo hayaniyarsu bai tanka masu ba,da suka duba ko ina basu ganta ba,anan fa hankalinsu ya ƙara tashi,fitowa sukayi suna bi gidaje suna tambayarta wasu a amsa masu da bata nan,wasu gidajenma ba mai zuwa balle ya basu amsa,kai tsaye suka miƙi hanya suna duddubawa ko wani mummunan abu ya faru da ita ne,lokacin da suka hau gefen titi suna tafiya........    Adai dai time ɗin Hosana ta shigo kan hanyar da gudu tana kuka hannunta dafe da kanta dake ta zubar da jini,tana ambaton oumma, oumma,    a gigice suka kai idanunsu wurinta,da gudun gaske suka tunkareta,abu na ƙoƙarin dakatar da ita akan ta kauce daga saman titin amma sam bata a cikin hayyacinta,wata mota ce ta bugeta da ƙarfin gaske gaba ɗaya ta kife ƙasa,mai motar na bugeta yaja motar da gudu yabar wurin alamar cewa da gangan ya bugeta,ashe ɗan siyasan nan ne yabiyo ta,bayan ya jima yana jiranta ta fito daga toilet bata fito ba,kawai ya afka ciki anan ya samu ta fasa glass ta gudu,yana huci ya fito ya mayar da kayanshi,ya bi bayanta cikin motarshi,don karta tona mashi asiri yasa yayi mata haka don ta mutu,   Zubewa sukayi agabanta suna ta kuka suna ta faman jijjigata a ƙarshe Abu ta sanya hannu ta ɗauketa,a ƙafa suka taka da sauri da sauri saboda babu abun hawa,gashi sae bleeding takeyi,suna cikin tafiyar nan sai ga Mijin maman sadeeq cikin napep,ashe tun lokacin da suka je gidan neman Hosana,bayan tafiyarsu ya gaza samun natsuwa shine ya biyo bayansu,napep ɗin ma bata shi bace arota yayi,saboda mashin ɗinshi babu mai,   Adai dai inda suke ya tsayar da abun hawan nashi,tunda yaga halin da hosana ke ciki bai tsaya tambayar ba'asi ba yace su shiga ciki,   A daren ranar suka kaita asibiti,likitoci suka shiga duba ta,tun nan aka sanar dasu cewa Sai anyi mata aiki,ana buƙatar kuɗi miliyan ɗaya da rabi,nan fa hankalinsu ya tashi,saboda ko sisi basu da ita, Har washe garin ranar ana kan abu ɗaya,andai samu an fara treating ɗin raunukan jikin nata,aikin dai ne ya gagara,sun jima a asibitin nan ana neman taimakon kuɗin da za'ayi mata aiki amma ba'a samu ba,sayyadi ko leƙo asibitin baiyi ba,bayan shine silar komai don ubanshi, Sanadin haukacewar mahaifiyarsu kuwa,lokacin anata neman yarda za'a harhaɗa kuɗin aikin hosanan,duk wani abu mai dan amfani tasa an sayar dama ba wasu abun kirki suka rage mata ba,don duk ta siyar da kayayyakinta wurin kula dasu Sehrish,a lokacin abu duk ta gama fita hayyacinta ta kode ta rame,duk da dae kyawunta na nan,amman inka ganta zaka yi tunanin ta girmi shekarunta saboda wahalar rayuwa, ta yanke shawarar zuwa gidan ta duba taga idan sayyadi yana nan jin shiru bai neme su ba,ko labarin kwanciyar hosana asibiti baije mashi bane,   Tana sa ƙafarta tsakar gidan nanfa ta dinga jin wannan gurnanin abunda sukeyi mara daɗin ji,ranta yayi mugun 6aci,kitchen ta nufa ta ɗauko tukunya ta zubo ruwa a fanfo kusan rabin tukunyar mai fadi,bayan ta ɗaura ruwan sai da ta jira ruwan ya tafasa sosai yana huci sannan ta sauke shi,tsumma ta ɗauko ta ruƙo tukunyar dashi,ta nufi ɗakin nashi,cikin sa'a sun bar ƙopar a buɗe dama da yawan lokutta basa rufe ƙopa turo ta kawai sukeyi,   Faɗawa cikin ɗakin abu tayi,mutun shida ta samu kamar wasu mayu manne da juna,aikuwa tana ƙarasawa wurin gadon,ta ɗaga tukunyar gaba ɗaya ta maka masu ruwan zafin ajikinsu,wa'iyazubillah,agigice suka rabe da junasu,wata irin gigitacciyar ƙara suka shiga saki ta azabar radaɗin tafasasshen ruwan zafin nan da abu ta watsa musu,ihu suka dinga yi suna birgima,fatar jikinsu duk ta ɗame ta lalace,   Duk atunaninta hada sayyadi acikinsu ashe yana acikin toilet,razananniyar ƙarar daya jiyo daga cikin bedroom ɗinshi ne yasa shi fitowa daga cikin toilet din,Waro ido waje Sayyadi yayi tare da aza hannunshi akai yana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Abu baki da hankali ne!!kinsan ko me kika aikata?   Idanunta jawur ta kalleshi rai amatuƙar 6ace tace"Na sani,kuma ina cikin hayyacina,wlh naso ace hada kai acikinsu na haɗa na ƙona,uban kowa ya huta da wannan masifar.....' Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya kifa mata mari zazzafan gaske har sae da gefen bakinta ya fashe,   Ɗagowa tayi da idanunta dake zubar da hawaye tace"Banji zafin marin da kayi mun ba!ada inajin shakkarka amma yanzu bana jin tsoranka acikin zuciyata,Wlh saina tona maku asiri duniya tasan me kuke aikatawa,daga nan in na fita gidan radio zanje in yaɗa duk wani mugun abunda kuke aikatawa,'   Wani irin huci ya shiga yi zufa na gangarowa daga jikinshi sae tsuma yake yi,hannu yakai tare da shaƙo wuyanta ya bugata jikin wardrobe ɗin dakin,   Sannan ya soma magana da wata irin murya mara daɗin ji yace"Ke daƙiƙiyace har yanzu bakisan ciwon kanki ba!kina tunanin cewa zan bari ki tona mun asiri ne!!kafin na juya maki tunaninki,inaso nasanar dake cewa Hosana jahad da sehrish ba ƴa'ƴa na bane!Da cikin abusufyan na aure ki!kuma nine na kashe mahaifinki baba buzu,saboda yana ƙoƙarin hanani auranki!' Wasu irin hawaye ne masu zafin gaske suka shiga gangarowa a fuskarta,tsabar baƙin ciki da takaici yasa ta gaza magana,saboda wani irin ƙululun baƙin ciki daya tokare mata maƙoshinta,    ƴa'ƴan naki ma bazan barsu ba!ɗaya bayan ɗaya saina kashe su!'   Yana faɗin hakan ya saki wuyanta,da gudun gaske abu ta fito daga cikin ɗakin nashi tana kuka,a ƙopar gidan ta tsaya tana faman ambaton sunan baba buzu tana cewa babana ka kashe mun ka raba shi da ranshi,ka kashe mun babana ko,kuma zaka rabani da ƴa'ƴana suma ka kashe su ko......'haka ta dinga sambatu ita kaɗae,   Tun daga wannan lokacin abu ta haukace ta miƙi santa tana faman sambatu, Wannan shine silar rabuwarsu da mahaifiyarsu basu ƙara sanin inda take ba, Abunda kuma yayi silar komawarsu katsina,labarin neman da mahaifinsu yake yi masu don ya kashe su kamar yadda ya fada ma abu,ya isar masu maman sadeeq,ko aikin ba'ayi ma hosana ba,amma ta miƙe saidae babu hankali ko kaɗan,da taimakon Mijin maman sadeeq ya sanyasu a mota tare da damka ma direban amanarsu,bayan yasa anyi ma hosana allurar bacci ya bama Sehrish address ɗin gidan tsohuwar nan,wadda ta kasance kishiyar mahaifiyarshi ce anan suke zaune,tsohuwa mai kirki koda yayi mata bayanin halin da yaran suke ciki ta tausaya masu sosae ta kuma ce zata rike su da tsakani da Allah,shima kuma yayi alkawarin zai rinka turo da dan abunda Allah ya hore,   Da daddare suka isa unguwar ba tare da sanin kowa ba,sai da aka taimaka masu kafin aka samu suka shiga da hosana gidan,a ɗaki ake rufeta saboda haukan da takeyi,na bugun mutane da jefe jefe,tsaf zata iya kashe mutun,    Wannan shine silar komawarsu gidan tsohuwar nan,tayi masu halarci arayuwa,ita ta dinga nema masu tallafi don a maida hosana asibiti ayi mata aiki,haka sehrish ma bata zauna ba,har wankau suke yi suyi guga itada jahad suna tara kuɗin da za'a kai hosana aiki,kafin tsotsai ya ritsa da jahad,      Akwai wani lokaci da suka je gidan wani ɗan majalissa jin labarin cewa yana taimaka ma marasa lafiya waɗanda ake buƙatar kuɗin da za'ayi masu aiki,tsohuwa da sehrish suka je gidan mutumin,yayin da suka bar jahad a gida tana aikin wanki,   Tana cikin yin wankin nan ta dinga jin kukan hosana gwanin ban tausayi tana cewa dan Allah su buɗe mata ƙopa su taimaki rayuwarta mutuwa za tayi,tana son ganin ƴan uwanta,me yasa kullum suke ƙumsheta a ɗaki,zafi ya isheta,itafa tana da hankalinta,ba mahaukaciya ce ita ba,tana da hankalinta,   Natsuwa jahad tayi tana sauraranta,yanayin yadda hosana ke kalamanta yasa tayi tunanin cewa kodai ta samu lafiya ne,tun tana tsoran buɗe mata ƙopar har dae tausayinta ya kamata sosai,da sauri taje ta buɗe mata ƙopar,   Kamar jira take a buɗe da ƙarfi ta damƙi wuyan jahad da hannunta,ta janyota cikin ɗakin,tana cewa"dama kece kika sace ni ko?kika rufe ni acikin ɗakin nan kina cutar dani!yau Allah ya kamaki!wlh saina rama,   Duk yadda jahad taso ta kwaci kanta a hannun hosana abun yaci tura saboda wani irin mahaukacin ƙarfi ne ke gareta,buga kan jahad tashiga yi ajikin bango,jahad ta fasa ihu saboda azabar da taji,nan take jini ya shiga bulbulowa daga goshinta,kuma hakan baisa hosana ta daina bugunta ba,har saida taga jahad ta daina motsi sannan ta saketa, Adai dai lokacin tsohuwa da sehrish suka dawo cikin gidan,da gudu suka faɗo ɗakin da hosana take ganinshi a buɗe nan suka samu jahad wanwar ƙasa jini na zuba,itama hosanar tana baje ƙasa sai faman mirgina-mirgina takeyi numfashinta na fita sama sama, Wannan shine silar da aka kwantar da hosana da jahad asibiti,har akayi ma jahad ƙarin jini,ita za ayi mata aiki,   Inda Allah ya taimakesu asibitin suna da wata ƙungiya wadda manyan masu kuɗi ke tallafawa marasa lafiyan da za'ayi ma aiki da wani parcentage,sun samu kuɗin amma akwai cikon da zasu yi dubu ɗari tara likitocin suka buƙata a wurinsu,    Sehrish tasha wahala sosai wurin neman cikon kuɗin nan,duk inda taje neman taimako sae an nemi ta bada kanta sannan abata kuɗin,anan ne wata mata dake jinyar wata a ward din da aka kwantar dasu hosana take ba sehrish labarin hajjaju dake ɗaukar ƴan aiki tana samo masu aikatau suna yi kuma suna samun alheri dayawa,saboda gidajen manyan masu kuɗi take samo masu aiki,matar tace in taci sa'a ma,aranar da tafara zuwa aiki sai tace ma masu gidan su bata kuɗin aikinta na shekera ko biyu ne,in aka dace zasu bata kuɗin,bayan matar ta bata address din gidan,tun daga ranar sehrish kullum sai taje ƙopar gidan hajjaju nemanta,har Allah yasa ta samu ganinta, Atakaice tarihin su sehrish hosana da jahad kenan,duk da bakomai aka fayyace ba, amma mutun zai gane inda aka dosa, 💋Boss Bature💋 Jikin kowa yayi mugun sanyi,masu raunin zuciya acikinsu tuni sun soma zubar da hawaye,hatta jahan dake da taurin kai sai da ya matse kwalla,Abusufyan kuwa tuni ya fashe da kuka,haka gwaggon katsina kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga kuka tana fadin"Allah ka tsine ma Sayyadi da duk zuri'arshi!Allah ya wulaƙanta rayuwarshi kamar yadda ya wulakanta rayuwar ƴa'ƴan abusufyan ɗina, Hatta Abbansu sae da ya matse kwalla shi da Abbas da su fawan,kowa ya harzuƙa ransu yayi mugun 6aci,tsananin tausayin su Jahad hosana da sehrish ne ya kamasu,marshal Omar kuwa sunnar da kanshi ƙasa yayi idanunshi sunyi jawur jikinshi sai kerma yake yi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda tsabar 6acin rai,   Sehrish kuwa lokacin da Jahad ta kammala bada labarin tasa kuka ita da Hosana,   Nan take ta miƙe daga jikin Sgr,hankali a matuƙar tashe take kallonsu yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi,kowa zuba mata ido yayi yana kallonta ganin yadda jikinta ke rawa tana kallonsu hosana da jahad,   Muryarta na rawa ta ambaci sunansu"Hosana jahad kune.........'tana faɗin hakan ta yanke jiki ta faɗi asume,   Da sauri abusufyan da hajiya azeema sukayo kanta hada su jahad ɗin,   Sam Sgr bazai iya jurewa ba,yunƙurawa yayi azafafe ya juya tare da nufar upstairs ya koma bedroom ɗinshi,agaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi wadda take daure tamau,gaba daya jikinshi sae kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,wata irin zufa ce tashiga gangaro mashi daga gefe da gefen fuskarshi,tabbas idonshi Idon Sayyadi............................... *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃 *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$* *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.* *LOCATION KANO* 08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.   *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* Zagayeta su kayi gaba ɗayansu,su jahad na ambatar sunanta,fawan ne ya ɗauko masu ruwa a fridge ya dawo ya miƙa ma uncle ɗinsu,kar6a yayi tare da buɗe murfin ya ɗebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskarta,nan take ta farka tana faman yin atishawa,Alhamdulillah suka shiga faɗi suna kallonta,yunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido,    Muryarta na rawa tace"jaj..jahad hos...sana...ku ne?ko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba?   Ba ƙaramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane su,atare suka faɗa jikinta suka rungume juna suna kuka,   Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaɗae ba ma fuskar kowannansu na ɗauke da murmushi,musamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka hajiya azeemarsu har cewa take yi"yanzu nan waɗannan ƴan ukun duka namu ne?ƴa'ƴan mu ne?Allah abun godiya,yau dole in yi nafilar dare don miƙa godiyata ga Allah S.W.A daya nuna mun ƴa'ƴan abusufyan ɗinmu da ranmu kuma da lafiyarmu,Ashe dae da rabon yara suga danginsu,bayin Allah sun sha wahalar rayuwa,amma bakomai har yanzu lokaci bai ƙure mana ba,zamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarku,Zamu baku duk wani jin daɗi na duniya da kuka rasa,zamu gatanta ku,sai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani ƙunci da kuka ta6a fuskanta arayuwarku,waɗanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sunji dama ba'a halicce su cikin duniyar nan ba, Abbansu junaid ya kar6e da cewa"Ae daga rana irin ta yau su fara ƙirgen kwanakin mutuwarsu,saboda ƙarshen su yazo,sun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEIN!Wallahi thumma tallahi ɗaya daga cikinsu bazai sha ba!' ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar,    Abbas yace"Abba ina ganin yakamata yaran nan suje su kwanta dare yayi sosai,suna buƙatar hutu,in yaso koma menene gobe zamu ida tattauna akai,'    Jinjina kai Abbansu yayi tare da mayar da idanunshi kansu sehrish dake manne da juna suna kuka,    Gyaran murya ya ɗan yi masu,atare suka ɗago suna kallonshi da idanunsu dake zubar da hawaye,   "Kuyi kuka yara bazan hanaku ba,dole kuyi kuka domin kuwa an cuci rayuwarku,an zalunce ku,an ƙuntata maku,an rabaku da mahaifinku na asali kuma an rabaku da danginku,duk akan laifin da baku kuka aikata ba,saboda son zuciya irin na mutanan nan su rasa akan wa zasu ɗauki fansar su sae akan waɗannan bayin Allahn....  'Shiru ya ɗanyi yana faman sauke ajiyar zuciya,   abusufyan na zuƙunne akusa dasu ya sunnar da kanshi ƙasa,hakanan ya dinga jin kunyar yaran yana ji aranshi tamkar duk shi ne silar jefa su cikin halin da suka shiga,   Su fawan kuwa dasu twins irfan jabeer da sauransu duk suna atsaye kowannansu jikinshi asanyaye kamar waɗanda aka zare ma lakka,lokaci guda sukaji tsananin Son yaran ya kamasu,   duk wannan abun dake faruwa gwaggon katsina,na zaune saman kujera tana ta faman matsar kwalla,har lokacin bata daina tsinar dangin Sayyadi ba,haris sai faman lallashinta yake yi tana buge mashi hannu tana faɗin"ka rabu dani Harisu!abun da ciwo wlh,Zuciyata tafarfasa takeyi,ƴa'ƴan abusufyan ɗina aka wulaƙanta kamar dabbobi?wlh bazan ta6a daina tsinewa Sayyadi ba,munafuki algungumi ɗan wuta,Ya Allah ka tsine ma sayyadi da duk zuriyarshi harda unguwar zomar da ta yanke mashi cibinshi, Ya Allah kayi mana maganinsu,Sayyadi ko ɗan iska,uwarshi ta haifa mana masifa....munafuki lokacin da yake zuwa wurin abu har ƙasa yake zukunnawa ya gaishe Ni,da wata guntuwar jallabiyarshi ta gado,ƙafafun nan nashi kaman shebur sanye cikin silifar ɗan ta shegiya...Muna yi mashi kallon Biri yana yi mana kallon ayaba.....'   sai faman sambatu takeyi abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,can kuma tace"Allah sarki abu,nasan yanzu ta gane cewa Allah ɗaya ne,yarinyar nan akwai taurin kai kamar kwallon goruba ga kafiya,kunnuwan nan nata kamar na Zoman daji falo falo dasu,ba irin jan kunnan da banyi mata ba,amma taƙi ji na,Ae ga irinta nan yanzu majnun ya koya mata hankali yanzu tana can Saman bola tana sambatu baiwar Allah,wama yasan uwa duniyar data shiga.......'   "Sehrish ku tashi ku tafi ɗaki ku kwanta,gobe zamu ƙarasa magana daku," Abbansu ne yayi maganar,   Miƙewa sukayi tsaye tare da yi masu sallama sannan suka wuce ɗakin nata,gaba ɗaya sehrish ta ɗan shiga ruɗu,batasan meya faru ba,amma bakomai yafi ɗaure mata kai ba face ganinsu hosana da jahad,taya akai suka San inda take har suka zo wurinta?abun kamar a mafarki take ganinshi,   Atare suka shiga cikin ɗakin,anan fa suka tsaya suna kallon juna fuskar kowaccen su ɗauke da tsantsar farin ciki mara misaltuwa, "Sehrish Ashe da rabon zamu sake ganinki a duniyar nan"?jahad ce tayi maganar yayin da hawaye ke sauka a fuskarta, ta ɗaura da cewa "Sehrish munyi kewarki sosai,munyi kukan rashinki atare damu,munsha wahala sosai,abubuwa marasa daɗi sun faru damu bayan rabuwar mu dake,amma duk wani hali da muka shiga hakan baisa mun manta dake ba sehrish kullum kina aranmu,koda yaushe muna cikin zullumin a wane hali kike?kina raye kuwa?kina jin daɗin rayuwarki?kina da ƙoshin lpy ko akasin hakan ....'   jin wannan maganar ta Jahad yasa ta fashe da kuka mai cin rai,janyota jahad tayi jikinta sosai ta rungumeta,itama hosana ta matsa tare da sanya hannayenta ta bayansu,suka haɗe su ukun,sun jima a wannan yanayin kafin daga bisani suka haye saman gadon su duka ukun suka zagaye junansu suna fuskantar juna a zaune   Sai lokacin sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa"inaso ku faɗamun meya faru na daina samun wayar tsohuwa,sannan kuma inason jin yadda akai har ku ka san inda nake,nayi mamakin yadda na manta daku gaba ɗaya acikin rayuwata,nasan ban kyauta maku ba,Amma kuyi haƙuri ku yafe mun........'   ta ƙarasa maganar tare da kai hannunta ta shafo gefen fuskar hosana tana kallonta da idanunta waɗanda suka canza launi sosai,sai lokacin ta gane cewa ashe sune yaran da Marshal Omar ke ruƙo a wurinshi,rashin sani yafi dare duhu,har waya suka yi dasu jahad amma bata ganesu ba,saboda bata acikin hayyacinta,   Jahad ce ta kwashe dukkan abunda ya faru tun daga kan Jefa wayar tsohuwa da hosana tayi acikin Masai da kuma mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu acikin cell,haɗuwarsu da Marshal Omar,zamansu a wurin gwaggon katsina da kuma rayuwarsu agidan Aunty babba,komai ta sanar mata, Sosai sehrish tayi kuka tamkar ranta zai fita,har zazza6i saida ya lullu6eta nan take,bakomai yafi girgiza ta ba face mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu hosana a gidan Aunty babba,abun ba ƙaramin ta6a zuciyarta yayi ba,wani irin ciwon kai ne ya rufar mata mai raɗaɗin gaske,rarrafawa tayi ta koma gefe guda saman bed mattress ɗin ta kwanta tare da janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,Wurinta su jahad suka koma tare da kwantawa kusa da ita,kowanannsu na acikin yanayi,tabbas sunga rayuwa...... Daƙyar bacci 6arawo ya sace su,amma fa dukkansu babu wanda babu zazza6i ajikinshi, Kowa fa ya manta da cikinshi saboda lamarin su hosana,a gidan babu wanda yaci abincin daren shi,saboda ƙunci da takaicin yadda rayuwar ƴa'ƴan uncle ɗinsu ta kasance, Lokacin da Azmee ta turo ƙopar ɗakin nasu samun su tayi kwance suna bacci kowacce fuskarta ɗauke da hawaye,bacci sukeyi amma hawayen basu daina zuba daga idanunsu ba,ba ƙaramin tausayinsu taji ba,ta jima tana kallonsu kafin ta rufe masu ƙopar ta koma bedroom ɗinta, Kwance yake asaman katafaren gadonshi,tunda ya dawo bedroom ɗinshi,ya shiga toilet yayi wanka,ya dawo ya kwanta yana tunanin duniya,juyi kawai yake yi asaman gadon bacci yaƙi ɗaukarshi,har lokacin zuciyarshi bata sauka ba,abun ya dame shi sosae,ya tsani zalunci arayuwarshi,ya tsani mugun mutun mai hali irin na dabbobi,tabbas idan har sayyadi ya bari ya shigo hannunshi sai ya ɗanɗani kuɗarshi,daga baya kuma ya dawo yana tunanin wai yanzu ƴar yarinyar nan da take yi mashi aiki,ashe ƴar uwarshi ce?jinin shi?ɗiyar Uncle ɗinsu?hakan na nufin cewa ita ƙanwarshi ce...? "Wonders shall neva end'ya furta hakan tare da lumshe idanunshi,nan take kuma ya tuna da hoton da Uncle abusufyan ya basu lokacin da suke a U.s,hakan na nufin cewa Hoton yaran ne ya basu lokacin da suke ƙanana,zan tambayi uncle hoton wacece nai selecting acikinsu,as I promised then zan taimaketa da kuɗi ta sayi duk abunda takeso bazan fasa ba...... ' Wasu dae sunyi bacci a wannan daren yayin da wasu kuma Baccin ya ƙaurace ma idanunsu,a tsaye Abusufyan ya kwana idanunshi sun ƙanƙance saboda raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi,bawan Allah,wlh abunda ciwo,taya ma zai iya bacci?yasha kuka dae,ga wani irin Matsanancin ciwon kai da yake fama dashi,yawo yake ta yi acikin dakin yama rasa tunanin da zai yi yayin da tafin hannunshi na dama ke dafe da saitin zuciyarshi,wani irin bugawa takeyi mashi mara daɗi, Yana cikin tsayuwar ne har aka kira sallar asuba bai ankare ba,sae da Yaji ana mashi knocking ƙopa,muryarshi ashaƙe yace"Wanene," "Ni ne"muryar Abban su junaid ce, Hakan yasa shi cewa"ƙopar abuɗe take yaya ka shigo daga ciki,".  Tura ƙopar Abba yayi ya shiga ciki yana ganin Abusufyan atsaye yace"dama saida rai na ya bani cewar baka yi bacci ba abusufyan,'   Yayi maganar tare da ƙarasawa ya dafa kafaɗarshi yana kallon fuskarshi da hawaye suka wanke ta sharkaf, Cikin sanyin murya yace"duk wanda yace maka kayi haƙuri tamkar ya cuce kane!amma ya zakayi abusufyan?dole haƙurin nan shi zakayi,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi na iya zarce na ƙunar wuta,abusufyan bazan ce kayi laifi ba,amma kasan cewa dole ne dama kaga badai dai ba!kayi aure batare da sanin mahaifiyarka ba,baka sanar mata ba balle tasanya albarka acikin auren naku,kunyi komai a6oye kai da gwaggon katsina,sai gashi yau Allah ya bayyana mana komai,nasan kai kanka kayi mamakin ganin Ƴa'ƴanka su duka ukun a ƙarƙashin kulawar gidan mu,kaɗan daga cikin Ikon Allah kenan!kwata kwata yaran basu san suna da dangi ba,garari kawai sukeyi a wulaƙance cikin gari,mu ma haka bamu son cewa akwai wasu ƴa'ƴa waɗanda suka kasance jinin mu ne su ba,babu wanda yasan haka,amma cikin ikon Allah da yake shi hakimun ne,sai gashi silar aikatau ɗaya ta faɗo hannunmu,yayin da silar ciwon ɗaya daga cikinsu da aka kai asibiti Allah ya ƙaddara haɗuwarsu da Omar yayin da shi kuma yaje wurin ɗan uwanshi Dr haris,lamarin ubangiji girma gare shi!gaba ɗaya Allah ya haɗa yaran a wurinmu ta hanyar da bamu ta6a tsammani ba,kamar yadda kai da gwaggon katsina baku yi tsammanin abunda kuka aikata asirrance zai tonu ba,tunda baku sanar mana ba sae gashi Allah ya sanar damu,su kansu yaran basu yi tsammanin zasu haɗu da dangin ubansu na asali ba,su dama basu da masaniya akan wanine ubansu......' Dakatawa abba yayi da maganar yana kallon abusufyan dake ta faman shessheƙar kuka muryarshi na kerma ya shiga cewa"Ya Allah ka yafe mun kuskuren dana aikata na auren abu batare da sanin mahaifiyata ba da kuma dangina ba......tun farko nine silar jefa rayuwarsu Cikin halin da suka tsinci kansu,da ace ban 6oye ma kowa ba,duk da ammi bazata barni in auri abu ba amma ina da tabbacin cewar Abbanmu salahuddeen zai aura mun ita inna nasanar mashi,iyakaci dae Ammi zata zangwameta ne daga baya kuma nasan zata fara sonta,wlh ni sam tunanin hakan baizo mani ba a wannan lokacin,idona ya makance,kuma ba laifin gwaggon katsina bane,Son da takeyi mun ne yasa ta aikata hakan don ta faranta mun ganin halin da na shiga a lokacin jin cewar Mommynmu ba zata bari in auri abu ba,gashi na mutu akan sonta kaicona.......'fashewa yayi da wani sabon kukan,dana sani kenan irin wadda ba'ason yinta,abun yayi ta maka ciwo azuciyarka,shiyasa kullum muke cewa Allah ya tsare mu daga aikata aikin danasani,saboda bai da daɗi,ɗaci gare shi,     Ba ƙaramin tausayi yaba Abba ba,tuni shima hawaye suka fara sauka akan fuskarshi,janyo abusufyan yayi ajikinshi sosai ya rungume shi yana lallashinshi,   A ƙarshe yace"Abusufyan ka manta da duk wani abu daya faru dazun,yanzu lokacin farin cikine,yakamata ka nuna godiyarka ga Allah subhanahu wata ala daya nuna maka wannan ranar da ya haɗaka da triplet ɗinka dukkansu da ransu kuma da lafiyarsu!wlh abusufyan dana ga yaran nan amatsayin ƴa'ƴanka kaɗan ya hana in buga tsalle saboda murna.....'yayi maganar yayin da suka raba jikinsu dana juna,   tallabo fuskarshi abba yayi cike da zolaya yace"Kasan me?   Abusufyan ya girgiza mashi kai alamar a'a,   Abba yace"nifa ɗazu dana ga ka firgita da ganin yarinyar nan nayi tunanin cewa ko ka ƙyasa ne,har ina cewa shikenan lokacin barin gwaurantakar abusufyan yayi aduniya ashe ashe uban ne gaba ɗaya........'   Ya ƙarasa maganar yana dariya,murmushi abusufyan ya ɗanyi,   Abba ya kuma cewa"Wai yanzu nan duk aikinka ne waɗannan abusufyan?ashe dae ƙanin nawa bana wasa bane...'   fashewa da dariya abusufyan yayi tare da sunnar da kanshi ƙasa,   Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Abba ba,dama so yake ya sanyashi farin ciki don ya gusar mashi da damuwar da yake ciki,   dafa kaɗarshi abba ya kuma yi tare da cewa"duk haihuwata ya'ya goma sha takwas akan su jahan ne kawai na samu ƴan biyu,amma kai da yake mai sa'a ne,na ku ba irin namu bane sai gashi ka haifa mana ƴan uku reras!ko Ya ammi zata ji in taga ƴa'ƴan mara jin maganar nan nata abusufyan....nasan zata ce shegen bisa zai aika ae,   Wannan karan atare suka fashe da dariya, Daga bisani Abusufyan yace"yaya hussein inaso naga yaran nan sosai,na damu dasu wlh....'   Wani irin kallon rainin wayau Abba yayi mashi kafin yace"yau naga ikon Allah!ni kake fadama kana son ganin ƴa'ƴanka?Yaran nan fa naka ne halak malak,ae ni nama yi tunanin a wurinsu zaka kwana,saboda suna buƙatarka sosai atare dasu,yanzu basu da burin daya wuce suga mahaifinsu atare dasu,"   Wani irin daɗi ne ya lullu6e abusufyan yace   "Zan iya zuwa wurinsu yanzu"? Abba yace"Ka bari mu dawo daga masallaci inyaso kai tsaye kawai sai ka wuce wurinsu,"   Fuskar shi ɗauke da farin ciki yace"okey,bari naje nayi alwala,"   Abba yace"muna jiranka a main palour in ka kammala,ka same mu acan,"   Yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da nufar ƙopar ɗakin nashi ya fuce tare da tura masa ƙopar,   Toilet abusufyan ya shiga batare da 6ata lokaci ba,ya ɗauro alwalar, Lokacin daya fito babban falon anan ya same su kowannansu ka kalla zakaga alamun damuwa a fuskokinsu,wasu ma da alama basuyi bacci ba,musamman Marshal Omar babu alamar yayi bacci adaren jiya,hatta Sgr ma akwai alamun rashin isasshen bacci atattare dashi,taya zaiyi bacci sayyadi na yawo acikin gari,shi fa in ya ƙullaci mutun irin haka har sai yaga bayanshi sannan yake samun kwanciyar hankali,su twins kuwa fuskokinsu sunyi jawur su da fawan,kowa dae da damuwa aranshi, Bayan sun kammala haɗuwa suka wuce masallaci atare, Tura ƙopar ɗakin nasu azmee tayi don ta tashe su sallar asuba,ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganinsu ajere suna sallah,kowaccensu na sanye da dogon hijabi a jikinta hijjaban sehrish ne hosana da jahad suka sanya,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,dama indae suna tare su ukun,musamman in akace maka akwai jahad atare dasu tofa basa wasa da ibada,duk da itama Sehrish ɗin ba daga baya ba,amma jahad ɗin itace kan gaba,saboda ita ba'a tashinta sallar asuba da zarar anfara kiran sallar asuba duk nisan baccin da tayi zata farka ne da kanta,abun sama rai ne da kuma sabo da yi,da kuma imanin mutun, *Murmushi kawai azmee ke saki tana kallonsu gwanin ban sha'awa,ƴa'ƴan abusufyan,jikokin Ammi da salahuddeeen,ƴa'ƴan ƙanin Abban sojoji Abusufyan,ƙanne ga Marshal Da Sgr duk su kaɗae,abun farin ciki abun murna!yanzu su sun zama abunso wlh,yayyansu gaba ɗaya sojoji har goma sha takwas,ko sauro ne yayi gigin Cixon fatar jikinsu sae yaji saukar alburushin bindiga asaman goshin shi* 🤣 Azmee na tsaye tana kallonsu taji alamun motsin mutun a bayanta,jin an dafa ta yasa tayi firgit ta ɗan juya,Hajiya azeema ce jikinta sanye da hijabi blue,hannunta ruƙe da carbi,fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Nazo ganin ƴa'ƴanmu ne,idan ba damuwa ki bani hanya in wuce ciki,"   Murmushi azmee tayi tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,sai da ta shiga ciki sannan azmee tabi bayanta tana cewa"sallah nazo in tashe su suyi,shi ne na same su ashe har sun tashi ma,abun ba ƙaramin burgeni yayi ba dana gansu ajere su ukun suna sallah,'   Murmushi hajiya azeema tayi ayayin da take zama daga gefen gadon su tace"Albishirinki,"tayi maganar tana kallon azmee,   Azmee tace"Goro," "Fari ko ja,"cike da zolaya tayi maganar,   "Fari dae,shi ne ke tare da alkhairi,wannan launin jan alamace ta hatsari," Dariya hajiya azeema tayi kafin tace"Tab jiya anyi babu ke!Labari da ɗumi ɗuminsa!zazzafan gaske....'   A ƙagare azmee tace"Meya faru"! A lokacin su jahad sun sallame sallah,suna zaune saman dardumar suna sauraransu, Nuna su hajiya azeema tayi tare da cewa"Ke wai ashe yaran nan ƴa'ƴan abusufyan ne!!!"   Gaban azmee ne ya faɗi Rasss!saboda yadda maganar ta dirar mata kai tsaye acikin kunnuwanta,   "Wai dagaske"?tayi tambayar cike da mamaki,   Hajiya azeema tace"hmmmm ke dae bari,wani iko sai ubangiji,dagaske fa nake,babu wanda baiyi mamakin wannan abun al'ajabin ba,yara dae ƴa'ƴan ƙaninmu ne sufyan,'   Juyawa azmee tayi tana kallonsu sehrish da sukayi zuru suna kallonsu musamman Sehrish da batasan kan zancen ba,saboda bata a hayyacinta lokacin da akayi maganar,amma lokacin da jahad ke bada labarin rayuwarsu taji komai a kunnanta kuma daga nan ne Sihirin jikinta ya lalace saboda tunaninta daya rinjayi kwalwarta harta tariyo dukkan abunda ya faru arayuwarsu ga kuma addu'ar da Sgr keta yi mata acikin kunne, Cike da mamaki azmee tace"taya akai hakan ya faru?dama abusufyan ya ta6a aure ne kenan?    Ataƙaice azeema ta bata labarin yadda abusufyan ya auri abu batare da saninsu ba,har suka samu ƙaruwar ƴan uku,'   Wani irin farin cikine ya lullu6e azmee saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa,    "Jahad!dagaske ne abunda kunne na ke jiyo mun"?sehrish ce tayi maganar tana kallon jahad da tsananin mamaki,   Murmushi jahad tayi ta jinjina mata kai alamar eh,ta ƙara da cewar"jiya duk baki a hayyacinki,abun farin cikin nan ya faru,Mun jima muna wahalar rayuwa ashe muna da dangi mai girma irin wannan bamu sani ba,cikin ikon Allah kuma sai gashi Allah ya haɗa mu dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba,ina tunanin addu'ar da muka jima munayi ne Allah ya kar6a mana,Ashe oumman mu sai da ta fara auren uncle ɗin su abusufyan sannan ta auri wannan fasiƙin mutumin sayyadi,da cikinmu ta shiga gidan shi........'   Aruɗe sehrish tace"taya hakan zai yiwu?   Hajiya azeema ce ta katse ta da cewar tabbas zancenta gaskiya ne sehrish!ku ƴa'ƴan ƙaninmu ne Abusufyan,sai da ya fara auren mahaifiyarku sannan Mugun mutumin nan daya ƙuntata rayuwarku ya aureta.......'gaba ɗaya hajiya azeema ta kwashe labarin rayuwar mahaifiyarsu agidan gwaggon katsina da kuma haɗuwarsu da abusufyan har izuwa rabuwar aurensu ta auri sayyadi ta sanar ma Sehrish,'   tun kan takai ƙarshen labarin nata,Sehrish tayi sujjada,tana shessheƙar kuka,saboda tsabar farin ciki,Ashe ita ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan?hakan na nufin su Babban yaya ƴan uwanta ne na jini!haba no wonder ae shaƙuwar dake tsakaninta da junaid tayi yawa,kai kana ganin abun zakasan cewar akwai alaƙa ta jini ajikinsu,ta damu da mutanen gidan sosai,ashe danginta ne su ɗin,   Jikin azmee ba ƙaramin sanyi yayi ba bayan hajiya azeema ta sanar mata irin zaluncin da sayyadi yayi ma su Sehrish,har idanunta sai da suka cicciko da kwalla saboda tausayinsu da taji,ta jima tana tsinar sayyadi acikin zuciyarta, Muryarta tamkar zatayi kuka tace"dama ina ta son mu samu lokaci Sehrish ta bani tarihinta wllh,ashe haka suka sha ukubar rayuwa bayin Allah,kai koma wanene wannan mugun mutumin ya cika babban azzalumi,saboda tsabar zalunci ya raba yara da mahaifinsu ya kuma ƙuntata rayuwarsu,duniya ina zaki damu.......'azmee na cikin magana,Abusufyan ya turo ƙopar ɗakin bakinshi ɗauke da sallama,gaba ɗaya hankalin su sehrish ya dawo kanshi,shi ma kuma yana ɗago idanunshi suka sauka akan ƴan ukun nashi,kwata kwata ma bai lura da hajiya azeema da kuma azmee dake a ɗakin ba,Su sehrish kawai yake kallo cike da so da ƙauna,ko kyaftawa baiyi,kamar ya haɗiye su haka yake ji,kamar yadda yake jinsu haka suma suke jinsu,sae ƙare mashi kallo suke yi kamar su watsa a guje su rungumo shi haka suka dinga ji,ta wani 6angaren kuwa abun ba ƙaramin yawo yake yi masu akai ba,Wai nan mahaifinsu ne halak malak,ubansu wanda yayi silar zuwansu duniwa,dama suna da uba da dangi a duniya?tambayoyi iri iri suke shiga yiwa kansu,   Ganin sun zubama juna ido tsakanin Abusufyan da kuma su sehrish dake zaune saman darduma suna kallon shi,hakan yasa hajiya azeema tayi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanta sannan tace"Zaman me kuke yi ne?baku ga mahaifin naku bane?ba zaku zo ku rungume shi ba,kuji ɗumin mahaifinku a jikinku?   jin wannan maganar ta hajiya azeema yasa su miƙewa gaba dayansu jiki na rawa suka ƙarasa wurin shi, Tunkan su ƙaraso ya buɗe masu hannayenshi alamar su shiga ciki,haɗasu yayi dukansu ya rungume su sosai ajikinshi kamar zai maidasu cikin cikinshi,hawaye ne suka shiga gangarowa a idanuwanshi da kuma idanuwansu sehrish,bai ta6a tunanin zaiga wannan ranar ba,yau gashi ga ƴa'ƴanshi sun dawo wurinshi,tabbas Allah ne ya kar6i addu'ar daya jima yana yi,atare suka ɗago idonsu cike tab da hawaye suka haɗa baki wurin cewa"Abba," Har cikin zuciyarshi yaji wani irin sanyi ya ratsa shi,muryarshi akasalance yace"Ku sake maimaitawa banji ba," "Abba,"suka maimaita mashi kamar yadda ya umarta, "Wlh kunyarku nake ji!duk wani abu daya faru arayuwarku ni ne sila,Na cuci rayuwarku,Naji na tsani kaina ƴa'ƴana suna a wani hali na rayuwa amma nagaza taimakonsu,zan iya zuƙunnawa saman guiwaowina agabanku domin in nemi gafararku.....,'tunkan ya ƙara maganar gaba ɗaya ya tafi zai zuƙunna saman guiwowins,cikin sauri suka rurruƙe shi suna cewa"Abba dan Allah kada kayi mana haka bamu so,ka daina ɗaura laifin akanka,dama Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan,dan Allah kada ka zuƙunna agabanmu,mu fa ƴa'ƴanka ne, Ganin dagaske kneel down zaiyi agabansu yasa suka riga shi zube wa saman guiwowinsu,tsayawa daga tsaye yayi yana kallonsu,Azmee da hajiya azeema duk suna kallon abunda ke faruwa,ba ƙaramin tausayi suka basu ba,   "Abusufyan"! Hajiya azeema ce ta ambaci sunanshi,amsawa yayi yayin da ya mayar da idanunshi akanta,   Anatse ta soma magana"yanzu ba lokacin baƙin ciki bane ko lokacin tuna baya,Lokacin farin ciki ne wannan,dariya yakamata in dinga gani a fuskar kowannanku ba hawaye ba,ko ba haka ba azmee?tayi tambayar tare da mayar da idanunta kan azmee, Murmushi azmee tayi kafin tace"Wannan haka yake,Abusufyan ina tayaka Murna sosai,nayi farin ciki mara misaltuwa,naji daɗi da sehrish ta kasance ƴarka ce,ko ince suka kasance ƴa'ƴanka ne,lamarin ubangiji da girma yake,babu wanda ya ta6a tsammanin haka,naji ma ina ganin kamannin fuskarka a fuskar sehrish ashe ƴar kace.....'magana take hawayen farin ciki na gangarowa daga fuskarta,    Murmushi kawai abusufyan ke saki,a lokacin harsu Sehrish sun miƙe tsaye suna tsaye akusa dashi,hosana ta rurruƙe hanunshi kamar wani zai kwace mata shi, Hajiya azeema ce tace"Azmee yakamata mu basu wuri su gana da juna,don na lura da yadda Uban ƴan ukun nan ke zumuɗi akan ƴa'ƴanshi,"cike da zolaya ta ƙarasa maganar tare da miƙewa taja hannun azmee suka fuce suna dariya,   Ajiyar zuciya ya sauke tare da mayar da idanunshi kansu jahad yace"kun samu bacci kuwa jiya?ya tambayesu ne saboda fuskokinsu daya gani duk a yamutse,musamman idanunsu sun ƙanƙance, Haɗa baki sukayi wurin cewa"Eh,"   Hosana tace"abba,dagaske kaine Abban mu ko?   "Ga zahiri kin gani,"yayi maganar yana yi mata nuni da fuskarshi,murmushi suka saki gaba ɗayansu,   Sun jima atsaye tare dashi suna magana jefi jefi saboda basu saba da juna ba,duk jin abun suke wani iri haka,kamar mafarki ne suke yi ba gaske ba,    "Ku koma ku kwanta,kuyi bacci ku huta,idan har akwai inda keyi maku ciwo ku sanar mun zansa aduba ku yanzun nan....'wannan maganar tashi ba ƙaramin sanyaya masu jiki tayi ba,   "Abba,lafiyarmu qalau,babu abunda ke damun mu,'suka faɗi hakan atare, Gyaɗa kanshi yayi tare da kama hanya zai juya da nufi yabar ɗakin nasu, Cikin sauri jahad ta ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Alla kada ka tafi kabarmu,muna buƙatarka a kusa damu,muna so mu kasance tare da mahaifinmu,' Sehrish ta kar6e da cewa"hakane Abba,ka dawo mu zauna atare dakai,muna buƙatar kyakkyawar kulawa daga wurinka,' tana kai ƙarshen maganar hosana tace"Abba pls,ko don saboda Ni," Wani irin murmushin farin ciki abusufyan ya saki yana kallonta,batare da 6ata lokaci ba,suka wuce saman gadon nasu,a tsakiya suka sanya abusufyan,yayin da suka kwanta gefe da gefenshi,sosai ya rungume hosana ajikinshi,duk in ya tuna labarin yada ta samu ta6in hankalinta nan take sai yaji idonshi sun ciko da kwalla, "Idan Allah ya kaimu gobe,da kaina zan gyara maku gashin kanku inyi maku kalaba guda biyu,kamar yadda na ta6ayi maku Lokacin da kuna yara,nasan ba zaku iya tunawa ba,' Jikinsu ne yayi wani irin sanyi, wani irin yanayi suka shiga gaba ɗayansu,    *💋Boss Bature💋* "Allah ya kaimu lpy,Abba,'jahad da sehrish ne suka haɗa baki wurin bashi amsa, Abusufyan yace"ba abba zaku dinga kirana ba,saboda ana kiran Yaya hossein da Abba,abun zai dinga ruɗa mutane ne arasa gane wani abban kuke nufi,amma ku dinga kirana Daddy,saboda a bambanta sunan,ina fata haka yayi maku? "Eh daddy,"suka haɗa baki wurin bashi amsa,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,   "Abba ita Oumman mu fa?dagaske ne ta haukace kuma tana saman bola tana hauka kamar yadda gwaggon katsina tace?kuma wanene majnun ɗin da naji gwaggo tace shi ya koya ma oummanmu hankali,'hosana ce tayi maganar,jahad tace"Ke fa matsalarki kenan baki da kan gado,tunda kika ji ance Majnun ae kinsan wa ake nufi,'Murmushi Abusufyan yayi yana sauraronsu,   Sehrish tace"dan Allah ku daina magana,kuna takurama daddynmu bacci fa yake ji,baku ga idanunshi ba,    Mayar da idanunshi yayi kan sehrish data aza kanta asaman kafaɗarshi,kafin ya mayar da idanunshi kan jahad itama tana manne dashi,ga hosana kuma data manne mashi asaman chest ɗinshi,kamar zata koma ciki,Allah kaɗai yasan irin farin cikin da yake ji acikin ranshi,daɗi kamar ya kashe shi,babban burinshi Ammi tazo taga yaran daga zarar ta amince dasu,bai da wata sauran damu,zancen sayyadi kuma ya gama sama ranshi lokacin mutuwarshi yazo,Saboda Case ɗinshi na hannun Zaki da damusa,tabbas sai ya ɗandani kuɗarsa,   "Daddy,bakace komai ba!oumman mu fa muna so mu sake ganinta atare,"muryar hosana ce ta dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga,firgit ya danyi tare da sanya hannunshi ya shafa kanta yace"Kada ku damu,insha Allah komai yazo ƙarshe,Oumman ku duk inda take bi'iznillahi za'a ganota ne,inason komai ya lafa ne,daga ni har ku mu samu kwanciyar hankali sosai,sannan zan fara sanyawa a binciko mun makwabtan nan naku,ina da tabbacin cewa za'a samu wasu bayanai masu muhimmanci a wurinsu,"   Ba ƙaramin daɗi suka ji ba,burinsu oummansu itama tashigo cikin wannan daular suci gaba da rayuwa acikin family ɗin Abbansu,   "Daddy Allah ya taimaka,kuma ya baku sa'a akan duk wani yunƙuri da zakuyi na ganin kun kawo ƙarshen Mugun mutumin nan dashi da duk wani wanda yake da hannu akan cutar da zuri'armu,Allah ya tonu asirinsu,kuma Allah ya bayyanar da Oumman mu da ranta,Insha Allah daga rana irin ta yau zamu kasance kullum muna taya ku addu'a saboda asamu nasarar kama ya sayyadi,'murmushi abusufyan yayi yana sauraran maganar jahad,bayan ta kammala maganar Sehrish tace"insha Allah daddy zamu tayaku da addu'a kuma zamu jajirce wurin ganin mun bada gudummawa wurin binciken gano waɗanda ke da hannu akan cutar da zuri'armu,duk da mu mata ne muna da rauni,amma hakan bazai hanamu miƙewa tsaye ba wurin kawo ƙarshen Ya sayyadi da kuma ire irensa,shaiɗanun dake take masa baya,'   tana kai ƙarshen maganarta hosana tace"Abba don Allah Idan kun gano ya sayyadi,inaso abani damar da zan fasa mashi tsakiyar goshin shi da bindiga,ko in harbi saitin zuciyarshi ta daina bugawa,"   Dariya sosai abusufyan yayi yana sauraron kalaman hosana,   "Hosana,ae idan ya mutu ta hanyar harsashin bindiga sai inga kamar yayi mutuwar sauƙi ne,nafi so ya rayu tamkar matacce,gashi da rai amma baida wani sauran amfani,shi kanshi sai ya dinga roƙon Allah ya ɗauki ranshi ya mutu ya huta,a tunanina ba,amma abunda nake gani yakamata mu shirya mashi mummunan ƙarshe,wacece acikinku zata bamu idea?yayi tambayar yana jiran amsoshinsu,   Kowacce da irin shawarar da take bayarwa akan yadda za'a shiryama ya sayyadi mummunan ƙarshe,bad ending kenan,ba kamar hosana tafi kowa bada mummunar shawara,daga bisani kuma suka fara tsara ma kansu Happy life bayan an kashe ya sayyadi da tawagarsa,zasu fita ƙasashe daban daban yawon shaƙatawa tare da daddynsu,oummansu da kuma ƴan uwansu,araina nace hada mazajanku ko abun kamar zaifi bada citta harda kanunfari.......' Bacci ne ya ɗaukesu atare manne da juna saman gadon,abun gwanin burgewa uba da ƴa'ƴanshi masu kama guda. Har wuraren ƙarfe goma na safe basu farka ba,dama sun tara bacci sosai a idanunsu,har Abbansu junaid sai da ya leƙo ɗakin ya same su a baje suna sharar bacci murmushi ya saki,tare da curo wayar shi daga Aljihun rigar jikinshi,hoto ya ɗaukesu kusan guda uku,bayan ya kammala ya maida masu ƙopar ɗakin ya rufe, Bayan ya fita daga sashen su kitchen ya nufa a lokacin Azmee harta kusa kammala aikin breakfast,yayi mamakin ganinta ita kadae tana ta faman aiki,   Tana ganinshi ta ajiye aikin da takeyi ta ƙaraso gaban shi tare da gaishe shi cikin girmamawa tace"barka da safiya Abba,antashi lpy?jiya sai muka ji abun farin ciki,Hajiya azeema ke sanar dani wai ashe su sehrish ƴa'ƴan Abusufyan ne,Wlh nayi farin ciki sosai,dama na jima ina ganin kamanninta da Shi,'. Fukarshi asake yace"wllh Alhmdllh,mun Samu ƙaruwar ƴan uku,ni dai ince jiya banganki ba,ae naso ace agabanki akayi komai,kema kiji wannan abun al'ajabin da kuma tashin hankalin,labarin dae babu daɗin ji,Amma ta wani 6angaren kuma mun gode ma Allah da ya bayyana mana yaran nan amatsayin jinin mu,munyi farin ciki sosai,har Walima ma nake so asake shirya mana saboda yaran nan,' Murmushi azmee tayi tare da cewa"Yaushe kenan?ko yau zamu fara shiryawa ne"?   Girgiza kai Abba yayi alamar a'a sannan yace"Wannan walimar ta musammance,gagarumin shagali za'ayi,akwai buƙatar kwanciyar hankali kafin lokacin,amma zanyi shawara da Abusufyan,idan har muka tsara komai,zan sanar maki,don ku shirya tarbar baƙi,zamu sa aƙaro wadanda zasu tayaki aiki.....'   Tunkan yakai ƙarshen maganar azmee tace"a'a Abba,zan iya ni kaɗai,basai an ƙaro masu aiki ba'   "Okey,ba damuwa naga kina ta wahala ke kadae,wai nikam ina yarinyar nan take ne?wata ƴar fara kanwarsu laila?naga kamar atare kuke aikin girki da ita ko ta koma gida ne"?   Azmee tace"a'a bata koma ba,bata jin daɗin jikinta ne,shine nace mata ta huta kawai,in taji sauƙi taci gaba da tayani,saboda yarinyar akwai son aiki,' Jinjina kai Abba yayi tare da cewa"Allah ya bata lpy,bari zanyi ma Kanal yousouf magana ya dubata...'   Cikin sauri azmee tace"A'a....ae na bata magani dama ciwon ciki ne,insha Allah zata warke,'    "Okey,' ya ambaci hakan tare da fucewa ya wuce cikin main palour dinsu,   Zama yayi saman sofa yana murmushi,bakomai yake tunawa ba face yadda yaga abusufyan tare da ƴan ukunsa,aranshi yace"Allah sarki,rayuwa kenan komai mai wucewa ne in bawa yasa haƙuri aransa,junaid tun yana jinjiri rabonshi da mahaifiyarshi,sai gashi jiya rungume da ita yana bacci,ƴan ukun abusufyan tun suna ciki rabonsu da ubansu, tun kafin cikinsu ya bayyana ma,sun sha wahalar rayuwa amma sai gashi komai na rayuwarsu ya canza yanzu tamkar basu ta6a shiga wani ƙuncin rayuwa ba,sannu a hankali zasu manta da duk wata uƙuba da suka sha arayuwarsu,Yau dae gasu can rungume da mahaifinsu suna bacci,Allah sarki, A ƙarshe kuma yace"Oh,ni kuma gani nan babu mai rungumata,abusufyan nacen rungume da ƴa'ƴan shi,junaid ma na can manne da mommynsu,gaskiya nayi kewarsu sosai......' "Abba!" karaf kiran ya sauka a kunnanshi a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,bakowa bane face Junaid yana tsaye hannunshi ruƙe da waist ɗinshi,har yanzu shaddar jiya ce ajikinshi,fuskar nan tashi cike da annuri sai faman zabga murmushi yake yi yadda kasan wanda akayi mashi albishir da gidan Aljana,   Wani irin farin ciki ne ya lullu6e abbansu,yunkurawa yayi zai miƙe tunkan ya ƙarasa miƙewar junaid ya watsa da gudu kai tsaye ya faɗa jikinshi sosai ya rungume shi yana faɗin"I really miss u Abba,'   "Nima junaid nayi kewarka sosai,jiya da tunaninka na kwana araina,'yayi maganar yana ɗan bubbuga bayanshi,    raba jikinsu sukayi dana juna,ganin abbansu na kallon bayanshi yasa shi cewa"Abba mommy ko?   murmushi yayi tare da cewa"Ashe ka gane,ta ina ne?ko ba tare kuka zo ba?   ɗan ta6e baki junaid yayi nan fa hankalin abbansu ya tashi,. Jiki asanyaye yace"Junaid bazata zo ba ko?Allah yasa dae ba Australlia ta koma ba,dama tunda na ganka kai kadae gabana ya fadi,don nasan halinta,'   Fashewa da dariya junaid yayi ganin yadda Abban nasu ya tashi hankalinshi don baiga mommynsu ba,   ɗaure fuskarshi yayi"oh ka ɗauki abun wasa ko?ba zaka faɗamun ina take ba,' Yana cikin maganar ya jiyo takun takalminta,baisan lokacin daya janye junaid gefe ɗaya ba,Zuba mata ido yayi yana kallonta fuskarshi ɗauke da murmushi,tsayawa tayi tana ƙare mashi kallo,ba ƙaramin kyau tayi ba saboda kwalliyar da junaid yayi mata,da kanshi ya shafa mata janbaki ya gyara mata jagirar idonta,duk da haskenta sai da yashafa mata hoda,wai don Abbansu ya ganta da kyau,kuma shi da kanshi ya za6a mata rigar da zata sanya,jallabiya ce brown colour mai kyan gaske tayi rolling mayafi akanta,kamar wata balarabiya,tayi haske sosai kamar wata fatalwa,ga tsayi dake gareta kamar Sgr,    Komawa junaid yayi saman sofa yana kallonsu,jira yake yaga mai zasu yi,sun wani ƙura ma juna ido,sae murmushi yake saki, Cigaba da tafiya tayi harta ƙaraso kusa dashi suna fuskantar juna,   Waro ido waje junaid yayi tare da cewa"Anshiga uku,Abba kaga yadda ka koma agaban mommy,wai dama ahaka kukayi aure Wayyo Allahna'   maganar junaid tasa suka fashe da dariya gaba ɗayansu,shi abunda ya bashi mamaki tsawonta agaban abban nasu,sae yaga abban nasu ya koma mashi guntu,   Sun jima suna sakar ma juna murmushi kafin daga bisani suka rungume juna sosai,kamar zasu zama daya,ba ƙaramin kewar juna sukayi ba,duk da akwanakin can baya yana kai mata ziyara Australlia,daga bayane ya daina zuwa saboda abubuwa da sukayi mashi yawa,   Kasa rabuwa sukayi da junansu,junaid kuwa ya tasa su gaba yana kallonsu kamar wanda ya samu television,   Adai dai lokacin twins suka shigo cikin falon,sakamakon Yunwa data ciwo su,karaf idanunsu suka sauka akan Mommynsu dake rungume da Abbansu,har suna haɗa baki wurin Cewa"Mommy!" Cikin sauri suka raba jikinsu dana juna,wurga idanunta tayi akansu jahan da ayaan dake tsaye suna kallonta fuskar kowannansu ɗauke da farin ciki,   Da gudun gaske suka ƙarasa inda take gaba ɗaya suka faɗa jikinta,haɗasu tayi duka ta rungume ajikinta,tuni taji hawaye sun cicciko a idanunta,tayi kewar ƴa'ƴanta sosai,muryoyinsu tamkar zasu yi kuka suka haɗa baki wurin cewa"we really missed u mom!ashe zamu sake ganinki acikin gidanmu,'suka ƙarasa maganar ayayin da suke raba jikinsu da nata,   Hawaye tagani a idanunsu,cikin sauri ta sanya hannunta tana share masu hawayen muryarta na rawa saboda kukan daya zo mata daƙyar ta iya cewa"i missed u too my twins,nasan ban kyauta maku..... '   Jahan ya katseta"Mommy abubuwa da yawa sun faru,wanda da ace kina tare damu na tabbatar cewar bazasu faru ba,mun yi rashinki akusa damu mommy,munyi kewarki......'   "Mommy..amma dae ba zaki sake komawa ba ko"?acewar ayaan Jinjina mashi kai tayi alamar eh sannan tace"nadawo kenan bazan sake komawa ba,I will be with u,for the rest of my life....."   Murmushi kawai Abbansu ke saki yana kallon uwa da ƴa'ƴanta,abubuwan farin ciki dae sai faruwa sukeyi acikin gidan,   "Mommy,kinga junaid ko ya girma sosai,yayi kukan rashinki sosai lokacin da baki nan,amma yanzu nasan cewar zaki bashi kulawa,dan Allah mommy ki bashi kyakkyawar kulawa saboda yafi kowa buƙatarki,'ayaan ne yayi maganar yana kallon junaid dake zaune yana ta faman murmushi, Itama kallon nashi tayi tare da cewa"Insha Allah ayaan,daga yanzu junaid zai canza gaba ɗaya,zan bashi kyakkyawar kulawa,bama shi kadae ba hada ku gaba dayanku,Amma banga fawan ba dasu Irfan,and kanal yousouf ko duk suna ciki ne"?   Jahan yace"basu tashi daga bacci ba,bari naje na kira maki fawan ɗin,' Dakatar dashi tayi da cewa"A'a kada ka tashe shi daga bacci,nasan daga ya farka yaji labarin zuwa na zaizo ne,but where is Alexander?   Atare suka haɗa baki wurin cewa"Mommy wanene Alexander kuma"?   Dariya Abbansu yayi tare da cewa"tana nufin Babban yayanku,ae sunan data raɗa mashi kenan ko kun manta,'   "Ae mun saba da kiranshi da babban yaya,mun manta da wannan sunan,shima yana a bedroom ɗinshi,duk bacci sukeyi saboda jiya bamu samu isasshen bacci ba,   Abba ne yayi mata nuni da 3 seater din dake gefensu yace"bismillahi,ki zauna mana ko baki gaji da tsayuwa bane,ko da yake na tuna fa Soja ce matar tawa,'yayi maganar cikin zolaya,   Murmushi kawai tayi tare da samun wuri ta zauna,shima abban nasu ya zauna daga gefenta,wuri su ayaan suka samu saman 2 seater suka zauna, Cike da kulawa tace"Amma meya hanaku samun bacci da wuri ne?naji kunce baku samu isasshen bacci ba ko wani abu ya faru ne'?    Ayaan yace"abun farin cikine ya faru jiya agidan nan mommy,nasan kin kwaso gajiyar tafiya,idan kika huta nasan cewa Abba zai baki labari anjima,"   Da sauri junaid yace"meya faru ne?dan Allah ayaan ka faɗa mana yanzu kawai,Mommy fa tun jiya tazo ƙasar nan,muna acan tare da ita agidanta ma muka kwana,bata sanar ma kowa ba,sae abban mu,'   Baki sake jahan yace"Wai dagaske?mommy abun ƴar haka ce,wato shine mu ba'a sanar mana da zuwan naki ba,junaid kawai kika sanar mawa,no wonder shiyasa jiya ban ganka ba,abun ya tsayamun araina,ba don abunda ya faru ba na bayyanar ƴa'ƴan uncle ɗinmu daba abunda zai hana mu nemeka a wannan lokacin,duk wannan abun shiya ɗauke mana hankalinmu....."tunkan ya ƙarasa maganar Junaid yace"Ƴa'ƴan uncle?wani uncle ɗin kenan"?aɗan rude yayi maganar,   Miƙewa Ayaan yayi tare da ruƙo hannun junaid yabar wurin tare dashi,sai da suka samu wurin da bakowa sannan yace"kai kasan meya faru jiya"?   Cike da zumuɗi junaid yace"taya za'ae in sani,ni da bana agida,don Allah ka sanar dani har naƙosa naji,' Ayaan yace"hmmmmm,labari da ɗumi ɗuminsa,ko kasan cewa yarinyar nan Sehrish ɗiyar uncle ɗinmu ce Abusufyan?   Gaban junaid ne ya faɗi rasss!saboda yadda maganar ta dira a kunnanshi,can kuma ya ɗan ɗaure fuskarshi yace"pls Ya ayaan dan Allah ka daina jamun rai,ni dae ka faɗimun gaskiyar abunda ya faru,'   Ayaan yace"kai nifa bada wasa nake maka ba,na ta6a maka wasa irin wannan ne!Sehrish ɗiyar uncle ɗinmu ce abusufyan,   Tur6une fuska junaid yayi tare da ɗan bubbuga ƙafarshi rai a6ace yace"yaushe uncle ya ta6a aure da har zai haifi ƴa'ƴa,kuma ma ƴar tashi ka rasa wadda zaka ce sae sehrish,kaji tsoran Allah ya Ayaan,babu kyau ƙarya,'   Rai a6ace Ayaan ya dunguri goshin junaid tare da cewa"Shashasha,ana ƙoƙarin a fahimtar dakai amma kaƙi yadda,don ubanka kaje ɗakin nasu ka leƙa,zaka ga abun mamaki,'   Turo baki junaid yayi tare da juyawa ya nufi hanyar xuwa ɗakin sehrish yana cewa"mai ƙarya dae ɗan wuta,'   Murmushi ayaan yayi yana kallon bayanshi,yasan cewa muddin junaid yaga Sehrish da ƴan uwanta sai ya haukace masu,farat ɗaya bazaiyi tunanin ƴan uku bane,sae ranshi ya fara bashi cewar Aljanune, aikuwa,junaid na ƙarasawa kopar dakin,a hankali ya sanya hannunshi tare da tura ƙopar dama a buɗe take,zura ƙafarshi ya fara yi kafin ya ƙarasa shiga bedroom ɗin,koda baby junaid ya shiga ciki bai kai idanunshi kansu ba,sae da ya fara rufe ƙopar ɗakin sannan ya juyo fuskarshi a washe,Karaf idanunshi suka sauka akan abusufyan dake rungume da hosana suna bacci,gabanshi ne ya faɗi rass cike da mamaki yace"Kai uncle tare da rishi ɗina,kwance saman gado suna bacci,Anya kuwa bansamu matsalar idanu ba......'   "Junaid!" Jin an ambaci sunanshi yasa shi juyawa a firgice yaci karo da Sehrish dake zaune gaban mirror tana shafa powder a fuskarta,sae faman sakar mashi murmushi take yi,waro ido waje junaid yayi a tsananin tsorace ya mayar da idanunshi kan hosana dake rungume da abusufyan ya kalleta ya sake juyowa ya kalli wadda ke zaune agaban mirror,   Muryarshi na rawa yace"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Nashiga ukuna!wai meyake damuna ne!meyake shirin faruwa dani ne!kodai nafara gamo da aljanu ne......'bai kai ƙarshen maganar tashi ba yaji an buɗe ƙopar toilet ɗin dakin,da sauri ya wurga idanunshi wurin,   Jahad ce ta fito,jikinta sanye da bathrobe,alamar wanka tayi,   Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,   Hankali amatuƙar tashe junaid ya dinga kallonsu ɗaya bayan daya,idan ya kalli jahad sai ya kalli sehrish dake zaune gaban mirror,sae ya kuma juya ya kalli Hosana dake manne da uncle ɗinsu, Tunkarar shi jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi,sehrish kuma na cewa"Junaid nice fa,baka gane ni ba,"   Ae ina,a gigice junaid ya fasa wata uwar ƙara wadda tayi sanadiyar tashin Abusufyan da hosana daga dogon baccin daya ɗaukesu, Da gudun gaske junaid ya damƙi handle din ƙopar ɗakin tamkar zai balle ta,buɗewa yayi tare da watsa wa da gudu har yanayin tuntube,tun kan ya fito daga corridor din dakin,Abbansu da mommynsu dasu twins suka nufo wurin saboda jin sautin razananniyar ƙarar da junaid ya saki,   A sukwane ya faɗo wurinsu,hankalin Abbansu ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yadda junaid ke gudu duk tsigar jikinshi ta tashi,   Daƙyar suka samu suka damƙoshi saboda ƙokarin guduwa yake yi daga cikin gidan, Hatta Marshal Omar da Sgr sai da suka jiyo ƙarar junaid,duk wani mai bacci acikin gidan sai da ya farka,ɗaya bayan ɗaya suka shiga fitowa suna tambayar ko lafiya,   Jikinshi sae kerma yake yi duk yabi ya firgice,tambayarshi suka shiga yi ko lafiya,   Muryarshi na kerma yace"Abba rishi uku acikin ɗakinta,Abba na mutu wlh aljanune ke bibiyata......'yana faɗin hakan ya sume ajikin Abban nasu,   Tunda sukaji haka ransu ya basu Cewar yaje ɗakin Sehrish ne,Abbansu baiso hakan ba,dama yasan shi firgitacce ne,yaso ace tun farko saida ya fara yi mashi bayani anatse sannan yaje ɗakin nasu,   Ayaan kuwa tun lokacin da yaji junaid ya fasa ƙara,ya ƙumshe dariya abakinsa,saboda yasan tsiyar daya tsula mashi,zaiyi wuya junaid ya yarda cewar Sehrish ƴan uku ne,ba kasafai yake fahimtar irin waɗannan abubuwan ba,sai an zaunar dashi cikin lalama anyi mashi bayani dalla dalla,sannan ake samu ya yadda, "Junaid ne ko"?abusufyan ne yayi tambayar,yayin da yake daga zaune saman gadon,   Sehrish tace"Shine daddy,ya ruɗe ne saboda ya ganmu mu uku,ya tsorata sosai naso na fahimtar dashi amma sai naga ya watsa aguje,'jin haka yasa abusufyan yin hanzarin saukowa daga saman gadon ya fuce daga ɗakin,   Jikin jahad ba ƙaramin sanyi yayi ba,ganin halin da junaid ya shiga saboda ya gansu su uku,tsoronta kar wani abu ya same shi,ganin yadda ya watsa waje aguje,    "Inaso naje naga halin da yake ciki,bansan meyasa ya firgita ba har haka,"sehrish ce tayi maganar a yayin da take miƙewa daga saman stool,jikinta na sanye da farar riga da dogon wando fari,kanta kuma na sanye da hula fara ta roba,buɗe ƙopar dakin tayi ta fuce tare da nufar inda suke, Komawa jahad tayi ta zauna saman kujerar gaban mirror,hannu tasa tare da ɗaukar man shafawar sehrish ta buɗe shi tana lakuto shi a hannunta tana shafa ma jikinta, "Jahad wai meya faru ne?naji sautin ƙara a kunne na," hosana ce tayi maganar,tana zaune tsakiyar gadon sae faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji, "Ƙanin Ya Omar ne,junaid ya shigo ɗakin nan,ina tunanin ya tsorata ne da ganinmu shiyasa ya firgita,saboda yaga fuskokinmu iri ɗaya dana sehrish," sauko da ƙafafunta tayi ƙasa tana cewa"bari naje naga meke faruwa a wajen," Da sauri jahad tace"Kada ki fita hosana!sehrish ta fita muddin ya ƙara yin arba dake zai zauce ne,ki bari sehrish tadawo sai muji daga bakinta,idan an fahimtar dashi ya fahimta,sai mu fita atare, Hosana tace"amma fa Yunwa nake ji sosai aciki na,' "Bari daddy ya dawo zanyi mashi magana,nasan zai sa ashirya mana breakfast ɗinmu,'acewar jahad, Murmushi hosana tayi tare da cewa"jahad bakiji irin farin cikin da nayi ba jiyan nan!,wlh inason Daddynmu sosai,tun lokacin da gwaggon katsina tace mu ƴa'ƴan abusufyan ɗinta ne,ta kuma kirashi awaya tabamu mu gaisa dashi,tun daga lokacin nake jinshi araina,na dinga addu'ar Allah yasa ya zama mahaifinmun duk da alokacin nasan wanene mahaifin namu......' "Nikaina hosana a lokacin,da muka fara waya dashi sai da naji jikina yayi sanyi,naji wani irin yanayi atattare dani ashe dae dagaske mahaifin namu ne,gaskiya munyi dacen uba,yana da kirki sosai duk da ban zauna dashi na wani lokaci ba,amma tun daga kan Fuskarshi zakasan cewar mutumin kirki ne,ashe lokacin da muna yara har zuwa ya ta6ayi ya ɗauke mu yakaimu gidansu yayi mana wanka sannan yayi mana kitson kalaba,bawan Allah,Allah kaɗai yasan yadda yaji acikin zuciyarshi lokacin da wannan baƙin mugun ya rabashi damu,' Hosana ta ƙara da cewa"Mummuna kawai,fuskarshi kamar ɗuwawu saboda rashin kyau,har naqosa naga yadda Ya omar ɗina zai karairaya ƙasusuwan jikinshi,"ta ƙarasa maganar tana yin nuni da hannayenta,yadda takeso Omar yayi ma Ya sayyadi, Ta cikin mirror jahad ke kallonta tana dariya tace"ae ba ƴa'ƴa Omar kaɗae ba,baki lura da yadda wannan mai blue eyes ɗin nan yayi ba,wani fari kyakkyawa mai ƙirar nan,har ni sai da na tsorata dashi ganin yadda ya zabura yabar wurin yana huci......' Hosana tace"ae nagane shi,Ni wlh tsoran idanunshi nake ji, kaman aljani,wai shima yanzu ɗan uwanmu ne ko?duk ƴan gidansu ya Omar ne ko? "Yayanmu zaki ce,ae yanzu duk wanda kika gani acikin gidan nan,to yayan mu ne,jiya baki lura da wani matashi acikinsu ba wani fari,mai mutunci wanda yazo ya kira mu,lokacin da alAbbansu ke neman mu"? Murmushi hosana tayi alamar tagane shi tace"daga gani zaiyi sauƙin kai sosai,kuma da alama ba ƙaramin farin ciki yake damu ba,mun gode ma Allah jahad daya haɗamu da dangin mu,'  Lokacin da sehrish ta shiga main palour din nasu,anan ta samu matasan gidan duk tsaitsaye akan junaid,dake kwance saman doguwar sofa ɗin da Abbansu ya kwantar dashi,a lokacin har sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,bakinsa sai faman kerma yake yi kuma har lokacin bai daina faɗin "Rishi guda uku"ba,   Abusufyan yace"bawan Allah,nidai naji an saki ƙara ashe wai junaid ne,bansan time ɗin daya shigo ba,lokacin ina bacci ne,ae da ban bari hakan ya faru ba,da tun lokacin na fahimtar dashi,ashe har yanzu junaid na nan da wannan firgitar tashi,ae nayi tunanin ya daina,'   Shafa gefen fuskarshi abba yayi a yayin da yake zaune daga gefen daman kujerar yace"Ya tsorata ne sosai,ae ni kaina banyi tsammanin zaije ɗakin nata bane,naso ace saida na fara yi mashi albishir sannan yaje wurinsu,'   Jahan dake tsaye yace"Aikin ayaan ne,shine ya tura shi ɗakin nata,'ya ƙarasa maganar yana hararar ayaan dake tsaye yana dariya,   Duk Alexandra na tsaye tana sauraronsu,sam batasan inda zancen nasu ya dosa ba,   Koda sehrish ta ƙaraso,zuba mata ido Alexandra tayi tana kallonta,gaban sehrish ne ya faɗi lokacin da tayi arba da ita,har sai da ta ambaci Innalillahi acikin zuciyarta,ba komae ya firgitar da ita ba face ganin fuskar sgr a fuskar matar,kuma batasan da ita acikin gidan ba, sai dai lokaci guda taji aranta kaman ta ta6a ganin hoton matar,   Cike da mamaki Alexandra tace"wacece wannan kuma"?tayi maganar tare da yin nuni da sehrish wadda tuni ta koma bayan abusufyan ta tsaya,   Jahan ne ya bata amsa da cewa"Ƴan ukun uncle abusufyan ne,'.   "Abusufyan kuma?dama ya ta6a aure ne?   "Eh,ya ta6a aure batare da sanin kowa ba,sai daga baya abun ya bayyana cewar ƴa'ƴansa ne,kuma ƴan ukune kamanninsu iri ɗaya sak,abunda yasa kika ga junaid ya ruɗe kenan,baisan cewa su uku bane,ɗaya ya sani acikinsu,muma sai jiya Allah yasa mukasan da zamansu muka san cewa ƴa'ƴanshi ne,Nasan abba zai sanar dake komai,'   Jinjina kai Alexandra tayi tare da ɗan ta6e bakinta,yayin da ta janye idanunta daga kan sehrish ta mayar dasu kan junaid dake ta faman sambatu,   "Abba pls ku fahimtar dani mana!meyasa nake ganin Sehrish guda uku?ko na samu ta6in hankali ne,'   "Junaid u should calm down ur mind,in baka natsu ba taya zamu fahimtar dakai,"acewar abbansu,   Jin hannun mutun acikin nata yasata yin saurin juyawa,sai lokacin ta lura dashi sam bata ga fitowarshi ba,   "Mommy,"ya ambaci sunanta cikin sanyin murya,cike da farin ciki tace"Fawan!ka farka daga baccin kenan"?tayi maganar ayayin da take janyo shi jikinta,sosai ta rungume shi,   "Mommy tun yaushe kika zo ba'a sanar mun ba?sae dai na fito na ganki unexpected"   "Tun jiya nazo fawan,muna tare da junaid acan gidana muka kwana tare dashi sai yau da safe muka dawo atare,da fatan na sameka cikin ƙoshin lapiya,'   "Alhamdulillah mommy munyi missing ɗinki sosai da sosai,'   "Nima nayi missing ɗinku fawan,'magana suka cigaba dayi atsakaninsu,   Duk wannan abun dake faruwa alexandra bata tanka ma abusufyan ba,shima kuma bai tanka mata ba,tun lokacin daya shigo falon yayi arba da ita,yaga ta kawar da kanta gefe tun daga lokacin shima ya share ta,dama bata shiri dashi,tun lokacin da Abba ya aurota,ya ta6a zama agidan,yanayin yadda take wahalar da yayanshi ne yasa yayi mata rashin kunyar da ta haddasa gaba atsakaninsu,saboda shi bakinshi bai rufuwa muddin yaga tana gaya ma Yayanshi hossein magana saiya mayar mata da martani mai zafi,wannan dalilin ne yasa Abba yace ya tattara ya koma wurin ammi don bazai iya jurar zama dashi ba,kullum haɗa mashi Bomb yakeyi acikin gida,shiyasa abusufyan bai zauna agidan yayan nashi ba,kuma ammi bata kawo shi gidan ba lokacin daya addabeta da rashin jin maganarshi,kawai ta yanke shawarar kai shi gidan hajiya Ameenatu,    Kowa daya fito tun daga kan su irfan jabeer,khaleed da kanal yousouf babu wanda baiyi farin cikin zuwan mommynsu junaid ba,daya bayan ɗaya saida tayi hugging ɗinsu ajikinta,kanal yousouf ne kawai ta manna ma kiss a gefen fuskarshi,ji suke tamkar mahaifiyarsu ce Maryam ta dawo gidan,Allah sarki Allah ya jiƙan rai,tun daga yanayin yadda alexandra ta kar6esu hannu bibbiyu tana rungumarsu ransu ya basu cewar ta shiryu yanzu,da alama babu wannan girman kan nata da kuma Zafin ran nan,    Sehrish dae duk jikinta yayi sanyi tun daga kan irin kallon da taga Mommynsu junaid nayi mata,ranta ya bata cewar akwai matsala,sam fuskarta babu yabo babu fallasa lokacin da Jahan ke sanar da ita cewar ɗiyar uncle ɗinsu ce,   Abbansu na ƙoƙarin fahimtar da junaid,suka jiyo muryar sgr yana tambayar"Meya faru ne!"yayi maganar ne ayayin da yake saukowa daga saman stairs ɗin,jikinshi na sanye da shirt fara ta ɗame jikinshi sai kuma dogon wando jeans,ba ƙaramin kyau yayi ba, Gaba daya suka juyo suna kallonshi,Marshal Omar na biye dashi abayanshi,atare suka sauko,   Wani irin farin ciki ne ya lullu6e alexandra lokacin da tayi arba da first born dinta wato Surgeon General Rafayet,gaba ɗaya tagaza rufe bakinta saboda ba ƙaramin so take mashi ba,tana matuƙar alfahari dashi,   Sehrish kuwa tunda taji muryarshi taji gabanta ya faɗi rass,tabbas tayi kewarshi sosai,jiya abubuwan da suka faru ne suka hana takai mashi dinner ɗinshi,tasan cewa daƙyar ne idan yaci wani abu ajiyan nan,   Aranta tace"bansani ba ko yana farin ciki da kasancewata ƴar uwarshi,ɗiyar ƙanin Mahaifinshi,ko yaya yaji aranshi"?    Jahan ne ya sanar dasu abunda ya faru da junaid,   ƙarasawa Sgr yayi wurin Mommyn tasu,ita tafara manna mashi kiss a gefe da gefen fuskarshi sannan shima yayi mata kamar yadda tayi mashi,daga bisani kuma suka rungume junansu, Abun ba ƙaramin burge sehrish yayi ba,har sai da ta ɗan saki murmushi kaɗan a fuskarta,   "Am really glad to see u mom,"ya furta hakan ayayin da suka raba jikinsu daga na juna,   Shafa gefen fuskarshi tayi tare da cewa"Yanzu ka kyauta mun?tun yaushe rabon dana sanya ka a idanuna Alex?ka daina zuwa wurina,kusan 1 year kenan baka tako ƙafarka kazo ba,'   Ganin hawaye sun cicciko a idanunta yasashi yin saurin ruko hannayenta tare da cewa"pls mom just forget about the past,nasan ban kyauta ba,amma kullum kina araina,kuma ina kiranki awaya muna gaisawa....'   Abbansu ne ya katse firar tasu da cewa"Ashe ba daɗi,Rama mun yayi Nima,ƙiri ƙiri kin rabani da aurena kinsa anata yi mun kallon Tazuru,'   Dariya sukayi gaba ɗayansu,banda sehrish dake tsaye jugum tana sauraronsu,   Matsawa Omar yayi cike da zolaya yace"Oh Mommy abun ƴar wariyar launin fata ce ko?atare da bro ɗina muka fito,amma ko kulani bakiyi ba...'yayi maganar yana ɗan ɗaure fuskarshi,   murmushi alexandra tayi tare da komawa wurin marshal,ta manna mashi kiss agefen fuskarshi sannan ta dafa shoulders ɗinshi tare da cewa"Omar ni bazan iya cewa komai ba,so nake nafara huce haushina akanshi kafin nadawo kanka,dama kaine mai ɗan son zumuncin,duk lokacin da kuka samu hutun aiki kana janyo shi kuzo wurina,amma yanzu duk kun juya mun baya,ni nasan duk shirin Abbanku ne yasan cewa dole nayi kewarku....'   Omar yace"no ba haka bane mommy,rayuwarce sai a slow,bamu manta dake ba,kuma kamar yadda rafayet ya fadi,muna kiran ki fa awaya kullum mu tambayi lpyrki,da ace kin ƙara 1 week baki zo nigeria ba,da kin ganmu munzo,ba don ma aiyuka da sukayi mana yawa ba,ae da mun rigaki zuwa....'   Ba ƙaramin daɗin kalaman Omar taji ba,yasan duk wata hanya da zaibi don ya kare kansu a wurinta,ba kamar SGR ba,shi kai tsaye kawai yake maganarshi ba wata kwana kwana,'   Sai da suka samu natsuwa sosai,sannan suka tattara hankalinsu kan junaid,    "Ina sehrish take ne"?Abbansu ne ya ambaci sunanta,saboda yaga gifcinta a wurin,   Da sauri ta amsa mashi da cewa"Gani nan Abba,"tayi maganar tare da fitowa daga tsayen da take abayan daddynsu,    Haɗa ido sukayi da Sgr,da sauri ta kawar da idonta,zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi,daƙyar ta iya ƙarasawa wurin abban nasu ta gaishe shi,   Bayan ya amsa mata yace"ki fahimtar da junaid,ina tunanin in yaji daga bakinki zaifi yadda cewa ku ƴan uku ne,'    Murmushi sehrish ta ɗan yi tana kallon fuskar junaid wanda ke kwance saman kujerar duk yabi ya rikita kanshi,tunda tayi magana yasan cewa itace saboda yaji muryarta,    Cikin sanyin murya ta soma magana,   "Junaid ka manta kwanaki na ta6a sanar dakai cewa Ina da ƴan uwa?waɗanda nake kira da wayarka? "Amma ai kince mun baki da wasu ƴan uwa lokacin da muka yi maki magana akansu ni da aunty azmee,"yayi maganar yana faman hura hanci,   "Junaid a lokacin bana cikin hayyacina bansan ya akai na manta dasu ba,amma yanzu nadawo hayyacina kuma Zan iya tuna komai a game dasu,idan baka yadda dani ba,bari na tuna maka,ko ka tuna Yarinyar daka ɗauko a school cikin motarka?tun lokacin saida nayi ƙoƙarin fahimtar dakai cewar bani bace,ni ina a makaranta ka barni,shine dalilin da yasa nasha wahala aranar,'   Jin wannan maganar ta sehrish yasa junaid miƙewa daga zaune,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face,yadda jahad ta kasa sakewa dashi,kuma launin gashin kanta baƙi ne ba irin na sehrish ba,hatta muryarsu ma akwai ɗan bambanci,haba no wonder shi dae ya jima yana tunanin cewa al'jana ya ɗauko a motarshi ashe ashe mutunce,indae dagaske ne xancen sehrish hakan na nufin cewa ƴar uwartace ya ɗauko a motarshi?to kodai sune yaran da Ya Omar ɗinsu yasa su gyarama gidan uncle ɗinsu zai kawosu suyi rayuwa aciki......'bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,Muryar Omar ta katse Hanzarin shi"Junaid!maganar da take faɗa maka dagaske ne!they're triplet,kuma ƴa'ƴan uncle abusufyan ne,dukanmu bamu son da haka ba sai jiya Allah ya bayyana mana komai,'   Yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da kallon fawan yace"Kaje ka kira mun su hosana da jahad suzo ya gansu da idanunshi don ya shaida cewar mutane ne ba aljanu ba,'   Cike da zumuɗi fawan ya wuce bedroom ɗin sehrish a lokacin har jahad ta kammala shirya kanta cikin riga da skirt na sehrish,ba ƙaramin kyau tayi ba,   Kwankwasa ƙopar fawan yayi kafin ya turo tare da cewa"Ya omar nason ganinku yanzu,'jin haka yasa sukayi saurin kimtsawa,duk suka yafa gyala a kansu,   Atare da fawan suka shigo cikin main palour ɗin,    Jerawa sukayi kusa da sehrish duk sun sha jinin jikinsu tsoransu kar ace wani abun ne kuma ya taso,   zuba masu ido junaid yayi yana kallonsu,idan ya kalli jahad sai ya kalli hosana,   A ƙarshe ya tsaida idanunshi kan jahad,ta hanyar gashin girarta ya gane cewa itace ya ɗauko a motarshi,har suka sha Love,   Dafe kanshi yayi tare da cewa"OMG!Abba kenan reesh ƴar uwata ce,jini na,ɗiyar uncle ɗinmu abusufyan!taya hakan ya faru?kuma dama rishi ƴan uku ne su ba ita kaɗae bace!idan har dagaske ne meyasa basu taso atare damu ba!!!!!!!_ Karaf maganganun da junaid ke faɗi suka dira a kunnan Hayaam,wadda fitowarta kenan,yunwa ta korota daga bedroom ɗinta ta gaza jurewa shine ta lalla6a ta fito don ta shiga kitchen,   Gabanta ne yayi wani irin bugu ji kake rasss!rarasss!hankali amatuƙar tashe ta ɗago da idanunta ta sauke su akan Mutanen dake tsaitsaye acikin falon,waro ido waje tayi ganin Sehrish dasu jahad,anan ta tuna abunda azmee ta faɗa mata jiya na cewa ƴan uku ne su,kuma kamanninsu iri ɗaya sak,a fili ta ambaci"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya Allah ka rabani da mugun Ji da kuma mugun gani!nashiga uku Ni yau Hayaam,bari dae na ƙara kasa kunne naji uban da suke tattaunawa,ya Allah kasa korar shaggun za'ayi daga gidan, "Junaid sehrish ɗin daka sani da kuma waɗannan biyun masu kama da ita sak,ƴa'ƴana ne,ni ne mahaifinsu,Na auri mahaifiyarsu ne ba tare da sanin kowa ba........'ataƙaice Abusufyan ya fayyace ma Junaid komai, Saboda tsabar kiɗima hayaam ƙiris ya rage ta fasa ƙara a wurin,ta matukar firgita da jin abunda abusufyan ya sanar ma jahad,tashin hankalin da ba'a sama shi date,gudu gudu,sauri sauri hada tuntube wurin komawarta cikin bedroom ɗinta,jikinta sae faman kerma yake yi kamar wadda sanyi ya kama,hannu ta aza asaman kanta tana faɗin"nashiga uku!na bani na lalace!ƙarshe na yazo acikin gidan nan!taya akai haka ya faru duk ina nan sake da baki bansani ba,wai yanzu dagaske yarinyar nan mai aikin gidan dana raina,nake ganinta ƙaskantacciya yar wurin uncle ɗinsu ce Abusufyan,Tabɗijancan,Kallo ya koma sama!kai anya kuwa banyi kuskure wurin sauraran maganar shi ba? Turo ƙopar da akayi ne yasa ta yin firgit ta juya, Tana ganin azmee hannunta ɗauke da plate na breakfast ɗin da ta kawo mata, Jiki na rawa hayaam ta ƙarasa wurinta tare da cewa"Aunty Azmee wai dagaske ne Seh...seh..rish ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan!" Ƙayataccen murmushi azmee ta saki tare da cewa"Dagaske ne mana!Nima sai da asuba nakejin wannan labarin a wurin Hajiya azeemarsu....'tunda azmee ta soma magana hayaam ta fita hayyacinta, Har sai da azmee ta ambaci sunanta"Hayaam!naga kamar kin tafi duniyar tunani ne?lafiyarki kuwa? Murmushin yaƙe ta saki tana ƙoƙarin danne damuwarta tace"Azmee bana jin daɗi ne,zuciyata tafarfasa takeyi ne," .azmee tace"Allah sarki,dama saida raina ya bani cewa baki lafiya,To Allah ya sawake,yanzu dae ga wannan ki fara karyawa nasan kina jin yunwa.....' Wani irin bugu Hayaam takai ma plate ɗin dake hannun azmee nan take yayi gefe guda ya tarwatse ƙasa,snacks ɗin dake aciki suka 6are, Ita kanta hayaam sai da ta firgita saboda ba'a cikin hayyacinta tayi hakan ba,tsananin 6acin rai ne da ƙiɗimar da tayi, Hankali tashe azmee tace"Hayaam!!' Tunkan ta karasa maganar hayamm ta zukunna jiki na rawa tashiga kwashe snacks ɗin dake zube aƙasa tana mayarwa cikin plate din, Muryarta na rawa tace"dan Allah aunty azmee ki tafi kawai,nagode sosai zanci....' Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,ganin yadda la66an hayaam ke kerma kamar gandar nama,tasan cewa duk akansu sehrish ne, "Allah ya baki lafiya,"ta ambaci hakan tare da juyawa tabar mata ɗakin, Azmee na fita hayaam ta jefar da plate ɗin, . miƙewa tsaye tayi nan fa tashiga safa da marwa tana zagaye ɗakin,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba face Aunty laila,tabbas ya kamata tayi gaggawar sanar da ita halin da ake ciki, Jiki na rawa ta ɗauko wayarta dake ajiye saman mirror,tana danna wayar yatsun hannunta na kakarwa,daƙyar ta tsaida hankalinta wuri guda ta danna ma Aunty Babba kira.        *💋Boss Bature💋* Join this link to follow my tiktok acct👇 https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1 قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖* *Father of soldiers* *🔥TAKUN ƘARSHE🔥* _Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_ *Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃* *nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅 Bismillah Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,    Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,"   Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,   Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,"   on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,   Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,'      cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,'   Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?   "Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa   "kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne....'   Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,    "Wani abusufyan din kuke magana akai,"   Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin,   Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet,   gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,'   A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,    Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam,   "W