*RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 1 FILIN SAUKAR JIRAGE NA ABUJA. BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Yanayin iskar dake busowa, suka haɗu da yanayin farincikin da take ciki, suka saukar da matsanacin farinciki mara misaltuwa a gareta. Rintse idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗar iskan da ke busowa wace ke saukar da ni'ima mai daɗi da kashe jiki. Kyakyawar matashiyar wacce ba zata wuce shekaru sha tara a duniya ba. Ta miƙe da sauri tana duba agogon hannunta cikin yanayi na ƙosawa. "He has to arrived by this time, ban san dalilin da ya sanya jirgin bai ƙaraso ba, kamar yadda aka faɗi ba." Raurau ta yi da idanunta tana, kallon kyawawan fararen yaran da suke gefen ta fuskarsu ɗauke da damuwar rashin saukar ɗan'uwan na su da wuri. "Haba, kun cika ƙosawa! Ummu, cewa ta yi zai sauka sha ɗaya kuma yanzu sha ɗaya saura minti minti biyar. Oh are you blind, ko duk ƙosawar da kuka yi ku ganshi ya sa kuka kasa bambance lokaci?" Cewar Fu'ad cikin fushin wasa yana kallon su. "Ƙyale su Ya Abidin yarannan, na lura duk sun fi son Ya Huwais, ka na ganin Anty Hilah, ku san a weeks nake ta roƙonta ta yi mini wainar indomie, amma ta ƙi sai ga shi tun jiya bata zauna ba tana wa Ya Huwais girki." Ya ce cikin ɓacin rai abin da ta yi mishi. Dukan wasa ta kai masa tana dariya daidai lokacin da Abidin ya ce, "Ai bambanci suke nunawa kamar yadda shi kansa yake nun bambanci ya fi sonta." Kama bakinta ta yi cikin mamaki tana faɗin,"Kar dai kuce you guys are really jealous about how I do care about him?" "Absolutely we are." Su ukun suka haɗa baki gurin faɗin haka Anty Hilah, har yanzu jirgin su Ya Huwais bai ƙaraso." Ƙaramar yarinyar da ke kwance tana bacci, da tafarki, furta hakan wacce ba za ta wuce shekaru goma ba ta faɗi tana kallonta. "I really don't know what happen, kuma Ummu ta gaya mini saura lokacin saukar har ya wuce." Ta ce ba tare da ta damu da ƙorafin da suke musu na sun ƙosa ba. "Allah ya sa ba wata matsala bane ya sa bai ƙaraso ba, cus na zaƙu na ga Ya Huwais, it been two years kenan yana abroad." "And so do I." Ta ce wa Umnah tana kallonta." A hankali jirgin yake saukowa har ya sauka ƙasa mutane suka fara sakkowa daga sama. Huwais dake sauka daga matakalar benen, cikin ƙasaita da isa yayin da idanunsa na kan mutanen da suka zo ɗaukar 'yan uwansu. Shekaru biyu ya yi hijira saboda ita kuma, amma a tsawon shekarun babu wacce yake son gani sai ita, domin cike yake da son ganinta da begenta. Idanuwansa ya rintse, yana jin wani abu na tasowa tun daga ƙafafunsa, har tsakiyar ƙwaƙwalwarsa wanda ya sa shi ajiyar zuciya mai ƙarfi, bayan ya aminta da waɗannan abubuwa da yake ji game da ita, ba za su taɓa dainawa sai dai in ya mutu. "Anty Hilaah, Ya Huwais."Amnah ta furta tana nuna shi da ɗan yatsa wanda ya sanya suka kwasa da gudu har da ita. Gabakiɗaya sika faɗa jikin shi har da ita suna ihun murna. "You are welcome Ya Huwais, we really miss you." Suka faɗi a tare da ƙara rungume shi. Wani irin abu mai kama da shokin suka fara tartsatsi a kansa, suna jansa wanda ta sanya ya janye ta daga jikin shi da sauri, yana kallonta yana jin yadda bugun zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi tamkar za ta fito waje. "Ya kamata ki san kin girma Hilaah, dubi yadda kika ƙara girma, amma har yanzu ba ki daina yi mini oyoyo kamar su Umnah." Ya faɗa yana murmushi tare da lakuce mata hanci. Idanunta da suke dara-dara ta zuba masa a cikin nasa wanda ya sa shi kusan mutuwar tsaye. "Tun ranar da ka ce mini you would be back to Nigeria na shiga cikin murna da ɗoki, and now ka dawo Ya Huwais is that what za ka saka mini da shi. All I do is caring, kar fa ka manta kai ɗan'uwana ne wanda muka fito ciki ɗaya, Ya in ban rungume ka don farinciki ba what do you want me to do." Ta ƙarashe maganar cikin sigar tambaya tare da hawaye a fuskarta. "To don Allah mene ne na kuka, da za ki yi mana asarar hawayenki?" Ya ce yana kallon su Abidin. "That is how Anty Hilah, is always crying ita fa ko abin murna ne kuka ne. Ranar da Abu, ya canza mata mota sai ta kama kuka." Kwashewa da dariya suka yi suna kallonta tare da faɗin,"Me bakin kuka." Wanda ya sanya ta yi fushi ta kalle su tare da kaɗa key ɗin motarta ta juya zuwa gurin motarta, wanda ganin haka ya sanya suka rugo da gudu su shidda ɗin suna faɗin, "Sorry Anty Hilah," Har da su Abidin da Fu'ad don su sanyata dariya. Rungumar ta kai masa a maimakon ta yi musu dariya."Farincikina ba zai iya ɓoyuwa ba akan dawowarka Ya Huwais." Ta ce tare da ƙanƙame shi wanda ya sanya ya ji tamkar zai fita daga hankalin shi, domin ji ya yi jikinsa ko ina ya ɗauki rawa. Wasu hawaye suka gangaro zuwa fuskarsa wanda ya yi sauri ya goge don kar su gani, yana ji a cikin zuciyarsa ƙaddararsa ta yi masa girma. Girman da yake jin tamkar girmar duniya akansa, domin bai san yadda zai kalli duniya ya bayyana musu ya kamu da son ƙanwarsa wacce suka fito ciki ɗaya, kuma ya raine ta tun daga ranar da aka haife ta. Ji ya yi tamkar ya haɗiye ransa ya mutu, domin yana jin samunsa a cikin family ɗin da suke rayuwa cikin farinciki da kwanciyar, hankali tamkar tsinuwa ne a garesu, domin matuƙar bai daina jin waɗanannan euphoric feelings ɗin ba akwai matsala, matsalar da yake ganin zai iya zama bala'i da musifa ga ahalinsu bakiɗaya. Duniya ta la'ance shi ya zamo abin tsinuwa da tur a rayuwarsa, kasancewar babu macen da yake a matsayin matarsa sai ƙanwansa wanda suka fito ciki ɗaya. A duk lokacin da suka haɗa ido, sai ya ji tamkar ya rungume ko ya samu sausaucin matsanancin sha'awarta dake ɗawainiya da shi, tun lokacin da ya fara mallakar hankalinsa, wanda bai taɓa jin haka ga waya 'ya mace ba." Ya rintse idanunsa yana faɗin,"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un." Daidai lokacin da suka haɗa ido da ita tana kallon shi cikin tsanannin so na 'yan'uwan ta ka. Ummu da Abu tsaye a farfajiyar gidan suna jiran isowarsu, wanda jin ƙarar hon ɗin motar ya sanya suka zaƙu cikin farincikin son ganinsa. Idanunsu na kan kataferen get ɗin gidan daidai lokacin da Inusa mai-gadi ya taso a hanzarce, ya wangame get ɗin dake ƙoƙarin fin ƙarfinsa. Cikin zaƙuwa Huwais ya buɗe motar ya fito tare da ƙarasowa gurin iyayensa ya zube yana gaishe su. Abu ya miƙar da shi, tare da shafa bayansa yana murmushi sai kuma ya rungume shi, wanda ya ba shi damar shiga jikinsa sosai yana jin ɗuminsa da ke ƙara masa sonsa. "Barka da dawowa son." Abu ya ce daidai lokacin da ya koma gurin Ummu tana shafa kansa. "Haƙiƙa zuciyata ta yi kewarku matuƙar gaske." "Ai ka san Allah son? Daga wannan babu inda zan ƙara barinka ka tafi. Saboda gida bai ƙoshi ba, ban ga dalilin da za a bawa waje ba. Ka tsaya ka kular mini da company nina da kasuwancina, don haka ko da miliyan za a baka duk wata ba zan lamunta ba, saboda na fara tsufa ina buƙatar wanda zai kula da dukiyata. Na kuma samu lokacin da zamu sha soyayya da Ummunku." Ya ƙarashe maganar cikin sigar barkwanci, wanda ya sa suka kwashe da dariya gabakiɗayansu . "Barka da dawowa ƙaramin maigida." Inusa ya ce lokacin da ya ƙaraso gurinsa ya durƙusa cikin girmamawa bayan ya kulle get ɗin gidan tare da ɗaukar jakarshi. "Barka, Inusa mun same ku lafiya?" Ya amsa yana faɗin haka. Gabakiɗaya suka rankaya zuwa haɗaɗɗen falon su mai matuƙar kyau da tsafta. Tun kafin su tafi ɗauko sa Hilah ta shirya masa lafiyayan abinci mai daɗi sosai. "Ya Huwais, wanka ko abinci?"Ta ce tana kallon shi bayan ta ƙarasa kan kujerar da yake ta zauna, har suna gogar jikinsu tare da jin numfashin junansu. Murmushi ya yi yana kallonta sosai ganin yadda ta ƙara kyau da cikar haiba. Abin sai ya ƙara ba shi mamaki ƙwarai, domin har yanzu kallon yarinya yake mata. Wacce ya yi rainonta da kanshi, tun tana ƙarama ya ci kashinta da fitsarinta, amma shi ne ta girma ta zama babbar mace da zata iya sace ko wane zuciyar ɗa namiji. Hannunsa ya zare daga nata, sakamaon jin wani abu mai kama da shokin yana zagaye ilahirin jikinsa. Haɗi da maganaɗisun ƙaunarta na bin duk wani bargo na jikinsa. Bugawar da zuciyarsa ke yi ba a bisa ƙa'ida ba, ya sanya shi ya matsawa tare da zare hannunsa yana kallonta. "Sis, bari na yi wankan kamar zan fi jin daɗi kuma abincin ya shiga. Ɓata fuska ta yi ganin ya janye hannunsa sai kuma ta miƙe tana faɗin, "Ok, bari na haɗa maka ruwan." Tana jin wani daɗin dawowarsa. "Karki damu je ki huta tun da na dawo kike ɗawainiya da ni, ma za je ki huta zan yi da kaina." Ya ce tare da miƙewa. "Akan me Yaya, na ga ko da can ni nake haɗa maka?" Ta ƙarashe maganar cikin damuwa. "Allah ya ƙara Anty Hilah dama sai wani murna kike na dawowarsa, sai ka ce ke kaɗai kike ɗoki. Ga shi nan..." "Ke ni sa'arki ne?" Ta nufe ta tare da ɗaga hannu za ta kai mata duka, wanda ganin hakan ya sa ta ruga ta ɓoye a bayansa. "Ke da ma baki da kunya sam! Shi ya sa na fi shiri da Umnaah ai." "Duk ku bar maganar bari na je na yi wankan, Abincin ma kisa Abidin ya kawo mini" Ya faɗi tare da kama hanya zuwa ɗakinsa. "No Yaya, gaskiya ya kamata ayi lunch a tare. Ka daɗe outside country, ya kamata ace ko ɗan ƙwarya-ƙwaryar liyafa mun haɗa." Ta ce mishi cikin damuwa. "Ke!" Ta ji muryar Ummu ta daka mata tsawa da take saman bene wanda sai da ta ji cikinta ya murɗa. "Kin san na tsani shegen kaɗifirin ki da iya surutu marasa kan gado. Ya dawo ba za ki barshi ya huta ba? Ke ce za ki gaya masa abin da zai yi?" Ta ce cikin tsananin zafi tana huci Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta sai ta fara ruwan hawaye tana jin babu daɗi a ranta. Huwais sai ya ji babu daɗi duk da hakan ba sabon abu bane, amma yayi tunanin Ummu ta daina ashe ba ta sake zani ba. "Wuce ka tafi ka yi wanka, zan sanya a kawo abincin sai ka ci ka yi baccin gajiya." Ta ba shi umurnin haka wanda ba shi da zaɓin da ya wuce ya bi. Kallon Ummi ya yi ba tare da ya amsa ba sai kuma ya juya ya kalleta har yanzu hawaye ta ke yi ya fice yana jin babu daɗi a ransa. Yana fita ta sakko ƙasan tare da ƙarasowa gurinda take tsaye kamar icce. "Ki kiyaye ni Hilah na gaya miki bana son wannan kusancin tsakaninku, duk da cewar nina haife ku, amma cases nawa ka samu na aikata ba daidai ba tsakanin 'yan'uwa. Ina kiyaye haƙƙin tarbiyarku da Ubangijina ya bani ne, don haka na gaya miki ki daina shishshige masa." Ɗaga mata kai ta yi alamun ta ji, a ranta take tunanin Ummu ta kasa fahimtar 'ya'yanta, ba su daga cikin irin waɗannan 'ya'yan. Ta yadda ta amince sun shaƙu da shi fiye da ƙanninta da suke mata, amma karta manta shi ɗin ta fara sani a lokacin da ta girma domin ya ci kashinta da fitsari. Shi ya fara ba ta abinci da shi ta yi wayo har ta girma." "Ma za ki wuce ki bani guri." Ta daka mata tsawar da ta fi wancan. Shiga ɗakinsa ya yi wanda yasha gyara yana ƙamshi turare mai daɗi. Ɗakin ya bi da kallo ya san cewa ita ta gyara ba masu aiki ba, domin gyaranta daban yake da na kowa. Ta san tsarin da yake so a ɗakinsa da yadda yake son a ije masa takalminsa da kayansa. Kai hatta hulunansa da dressing mirrow Hilah duk ta haddace yadda yake son su kasance. Ɗakin ya ƙara bi da kallo takaddun ne da bulunbulun masu kyau ta yi kwalliya da su, haɗe da sunansa tana masa murnar dawowarsa. Ɗaya daga cikin bulun-bulun ya ɗauko tare da rungume shi a ƙirjinsa yana jin tamkar ita ya rungume. Ya daɗe yana ƙarewa ɗakin kallo sannan ya miƙe zuwa bayi tare da shiga bayi. Wanka ya yi ya fito dga shi sai tawul ɗaure a ƙirjinsa. Tsayawa ya yi yana shafa mai daidai lokacin da Abidin ya yi sallama da tiren abinci ya ije tare da fita. Bayan ya gama gyara jikinsa ya feshe jikinsa da turare mai ƙamshi. Yana cikin riga da wando jeans da tishet ruwan bula domin shi ma'abocin ƙananan kaya ne, kuma suna mishi matuƙar ƙyau sosai tare da karɓar fatar jikinsa, da take ruwan tarwaɗa. Gashin da yake kwance a jikinsa ya ƙara ƙawata jikinsa, domin hatta yatsunsa ga shi ne kwance a jikinsu. Haƙiƙa yana da kyau mai ɗaukar hankali da rikita zuciyar 'yan mata. Yana da idanu amma ba manya sosai ba. Sai dai, duk macen da ya kalla sai ta ji tamkar ta yi tsuntsuwa ta ɓace daga gurin, domin wani irin ƙwarjini da haiba da ke cikinsu. uwa uba maganaɗinsu da suke da shi tamkar an zuba zaiba. Bashi da hasken fata, amma kuma yana mafani da mayuka masu kyau da tsada, waɗanda suke ƙara fito da ainihin kalar fatarsa da kyansa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 2 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Ba shi da hasken fata, amma kuma yana mafani da mayuka masu kyau da tsada, waɗanda suke ƙara fito da ainihin kalar fatarsa da kyansa. Sajensa da ya zagaye duniyar fuskarsa, da ɗan gemunsa mai kyawu. Shi yake ƙara rikitar da duk macen da ta yi tozali da shi, har ta ji ba ta wata addu'a face samun miji ko saurayi kamarsa. Dogo ne sosai yana da ɗan jiki kaɗan, wanda ya ƙara kyautata kyawun surarsa da halittunsa. Ƙirjinsa mai faɗi irin wanda mata suke kira da gadon bacci. Abin da zai fi ɗaukar hankali a halittunsa; idanunsa. Tabbas yana da wata irin idanu irin wanda turawa suke laƙabi da golden eyes, domin in yana kallon, sai ka rasa natsuwarka. Hakika kyawun idanunsa baiwan ne da Allah ke bawa wanda ya ga dama. Kasancewarsa mai rahma mai yin kyauta na baiwa ga wanda ya so, ba tare da ya duba cancantar hakan ba. Mutun ne mai yanga. Eh tabbas yana da yanga sam bai cika shiga rayuwar wasu ba, amma kuma yana da sauƙin mu'amala domin ba shi da zafi sosai, ko 'yan'uwansa shedane, saboda tun suna ƙanana har suka girma bai taɓa ɗaga hannu ya doki wani ba, sai dai faɗa wanda shi ma ba kasafai ba. Ballantana Hilah da take rayuwarsa gabakiɗaya, domin tun a ranar da aka haifeta Allah ya sanya masa sonta na mutuwa, wanda ada yana tunanin saboda ƙanninsa uku duk maza ne, sai ita ta zo a na mace shi yasa yake mutuwar sonta. Amma da tafiya ta yi tafiya girma ya kamasa sai ya fahimci soyayar aure yake mata, wanda yake kallonsa mahaukaci wanda bashi da cikakken hankali. Zama ya yi yana buɗe kular abincin. Wani irin ƙamshi ya ziyarce sa, wanda ya sa ya lumshe idanunsa da ake kira sexy eyes. "Anya yana ganin kwai macen da tafi Hilah ɗinsa iya abinci? Kai da wuya domin in har akwai to bayanta take, domin Hilah ɗinsa gwanace gurin iya girki sam ba ta da ƙiwa, a gurin haɗa abincin da mutum zai ci ya samu natsuwa. Tabbas duk namijin da ya same ta ya more rayuwarsa domin an gama ba shi rabonsa na duniya sai na lahira. Take ya ji wani irin tsananin kishi mai zafi, ya taso masa tun daga kan ƙafafunsa har i zuwa kansa, ya mamaye shi har baya iya ganin abincin sai dai dishi-dishi. Sai ya miƙe yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, tamkar ruwan xafin da aka ɗora na mai jegen da ta yi haihuwan fari ake shirin sauke mata don ta yi wanka. Idanunsa suka kaɗa har ya ji abincin da yake sha'awarsa da muradinsa sun gimsheshi ba tare da ya ɗanɗana ba. Zuciyarsa na tururi tamkar ya haɗiye kansa ya mutu. "Ni dai na shiga uku! Allah ka jarabce ni da abu mafi girma soyayya kuma ƙanwata wacce muka fita ciki ɗaya. Tabbas wannan girman jarrabawar ta zarce tunanina." Wani irin sha'awarta da ƙaunarta suka taso masa, har suna ƙoƙarin kawar da hankalinsa. Musamman yadda ya ga ta canza ta girma ta zama babbar mace. Duk wata halitta da zai sa a kira mace da cikakkiyar budurwa ta kai, domin in har memerinsa will served him well, ranar Juma'a 20/02/25. Za ta shiga shekara sha tara a duniya. Wato birthday ɗinta wanda ya shirya wa ranar domin ya tana ji kyauta ta musamman a ranar. "Allahumma gafirli, warahamni, waj burni, wahdini warazuqni." Ya fara faɗi a zuciyarsa yana maimaita domin tabbas Allah ya jarabce shi. Miƙewa ya yi, domin a halin yanzu babu abin da idanuwansa suke kwaɗaita masa son gani face ita, don samun natsuwar zuciyarsa. Ba tare da ya ci abincin duk da yunwar dake ƙwaƙularsa ya mai da abincin ya rufe. Ko da ya shiga falon sauran yaran ne a falo, amma ban da ita wanda ya san tana kicin domin ɗora girkin dare. Yana mamakin yadda Ummu ta hana rayuwarta saƙat ta mai da ita kukun gidan, duk da tarin masu aikin da suke cikin gidan. A cewarta abincin ta yafi daɗi kuma gata take mata, amma abin da yake ɗaure masa kai sam ba ta barin Azerh, Umnaah da Amnaah su shiga ko kaɗan. Don ance mutum tara yake bai cika goma, ba da sai ya ce takai. Ta fannin addini malama ce wacce ta samu tropy da yawa na gasar karatun alqur'ni har waje ta je. Sannan a makarantar boko ita ce best student a fannin computer Jami'ar Abuja birnin tarayya. "Laa Ya Huwais ka dawo mu yi hira?" Umnaah ta miƙe da sauri ta isa gare shi tare da kama hannun shi tana murna. "Taɓ! Ta ya ya zai iya cin abinci Ummu ta taɓa 'yar gidansa? " Azerh ta yi maganar tana kallonsa da ya ƙarashe shigowa falon. "Ya Huwais, tana kicin tana dinner." Cewar Umnah da ta kama hannunsa, ganin yana ta waige-waige. "Eh, yana da gaskiya domin a gaskiya abin da Ummu take yi sam ba ta kyautawa. Anty Hilah 'yar'uwammu ce biogically, amma sam ba ta barin ta huta kullum cikin aiki, kuma ta hana mu taimakon ta. Ta manta karatunta yana buƙatar lokaci." "You are right sis Umnaah, kuma ba ta duba ɗaukakarta da nasararta. Abin na ci mini tuwo a ƙwarya, ya kamata muje har ofis ɗin Abu mu yi mishi complaining, saboda a gida muna fara magana za ta hana mu." Naufal ya faɗa yana gyara zamansa. "Eh, mu je gaskiya don abin na ci mini tuwo a ƙwarya." Cewar Abidin da yake danne-danne a wayarsa. Wani irin tsananin ƙaunar 'yan'uwansa ya ƙara kama shi, ganin ba sa son abin da take mata ya kalle su zai ce daidai lokacin da Fu'ad. ya tari numfashinsa. "Mu ma yana ci mana tuwo a ƙwarya kuma na sha ganin su Umnaah sun je za su taimake ta, amma sai ta hana su. Ni kaina mun taɓa zuwa a tare taki. Kuma ban san dalilin da kullum take maganar ya kamata ayi mata aure da wuri ba, domin ta so ace kafin ka dawo an yi aurenta da Hammad." Idanunsa ne suka kaɗa bayan shi sheda ne kan Hilah 'yar'uwarsa ce na jini, domin a gabansa aka samu cikinta aka kuma haifeta ta girma sai ya ce a kwai lauje cikin naɗi, amma shi sheda kan hakan." "Bari gobe zamu same shi a ofis mu yi mishi magana karku damu kun ji 'yan ƙannina." "To." Suka haɗa baki gurin faɗi tare da bin sa da kallo lokacin da ya miƙe ya nufi hanyar kicin. A hankali ya tura ƙofar kicin ɗin tana tsaye a gaban gas tana juya damen tuwon semonvita da ta yi. Ba tare da ta san ya shigo ba tana aikinta tana rero karatun qur'ani suratul Maryam kasancewar tana matuƙar son surar. Bagan ta juya sai kuma ta koma ta zauna ta leƙa duniyar tunani wanda kusan 'yan mintina ta yi nisar kiwo. Kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurin talgen da har ya fara zuba. Buɗewa ta yi tana juyawa sai kuma ta mayar da murfin ta ije muciya ta ɗauki garin za ta tuƙa. Tana tuƙin yana kallonta, kamar wanda ya kunna fim har ta kusa gamawa, sai cikin rashin sa'a tuwon ya fallatsar mata a hannu, wanda ta yi ɗan ƙara ta yarda muciyar tana tsallen azabar zafi. Da sauri ya ƙarasa gurinta tare da kama hannu ta yana hura mata wanda ta kalle shi idanunta tab da hawaye. "Ya Huwais, ashe ka shigo." "Ki rinƙa aiki a hankali kar kije ki rinka cutar da kanki. Kinga ga shi nan har kina ƙona kanki." Ya faɗi cikin ɗan ɗaga murya ganin yadda gurin ya yi ja. "It pains me." Ta ce tare da saka kuka wanda hakan ya ƙara tana da hankalinsa. Janta ya yi zuwa tap, ya buɗe tare da tara kyawawan hannuta da suka sha jan lalli, waɗanda suke fisgar zuciyarsa zuwa ƙara ninka sonta. "Am sorry sis. Bari na ci gaba da tuƙa tuwon." Ya ce tare da ƙarasawa gurin gas ɗin ya ɗauki muciyar bayan ya wanke ya sanya a cikin tuwon. "No ka barshi zan iya Ummu za ta yi faɗa in ta gani." Ta ce yayin da hawayen da suke maƙale a fuskarta suka gangaro mata. Mayar da muciyar ya yi, tare da kamata ya zaunar ya kai bakinsa yana hura gurin, kamar sakwan talatin sai ya koma gurin tuƙin yana faɗin, "Let her do, ciwo kika ji saina kasa taimakon ki." Kallon da ya yi mata sai ta ji a karon farko ta ji wani abu game da kallon wanda ta kasa tantance ko mene ne shi. Idanunta ta sunkuyar ƙasa ba tare da ta ce komai ba, sai dai ƙarƙashin zuciyarta tana addu'ar Allah ya sa kar Ummu ta shigo, wanda ta san faruwar hakan ba ƙaramin faɗa za ta sha ba. "Zan yi wa Ummu magana, ba zai yiwu ace duk kuɗin mahaifinmu ba kina girki ba dare ba rana, kina buƙatar time Hilah, kar ta manta watanni ya rage ku yi musabaƙa, duk da na san you gonna rock it, amma kina buƙatar hutu sosai don kina da 'yancin hakan. I don ma don kar kije gidan aure ba ki kowa ba, zuwa yanzu sai dai ki kowa ya wasu" "Ummu, uwa ce a gareni wanda ko wane ɗa zai yi alfaharin samunta, domin ta gina rayuwata da gishirin duniya wato ilmi. Ba zan yi baƙinciki don ta sani aiki ba Ya Huwais, don Allah karka ka yi mata magana ko Abu. Ina son mahaifiyata ba na son na ɓata mata rai. Bayan haka ma gani za ta yi kamar ƙararta na kai maka." Sosai ta ba shi tausayi musamman da mood ɗin da ta yi maganar. Bai amsa mata da zai yi mata magana ba ko a'a ba, ya fara zuba garin tuwon a cikin tuƙunya yana tuƙawa, wanda ganin hakan ya sa ta saki dariya. "Kai ya Huwais! Dama ka iya girki ne?" Dariya ya yi jin yadda ta yi masa tambayar cikin zallar mamaki ganin yana tuƙin da ƙwarewa. Rufe tuwon ta yi bayan ya gama ya rage gas ɗin wanda take kallon shi har yanzu mamaki ɗauke a fuskarta. Sai ya matsa gab da ita zai ɗauko kular da zai kwashe tuwon wanda ta riƙe hannunsa tana faɗin, "A ka barshi zan iya kwashe na gode." Matsowa ya yi kusa da ita har tana jin kusancin ya yi yawa domin a tare suke saukar da numfashi kuma suna jin hushin juna. Dubara ta yi ta matsa ƙarshen sink ɗin tana mamakin hakan da ya yi mata. "Mamaki kike yi ko? Ai da na je London na kasa cin abinci na kowa sai tunanin na ki, shine na gwammace gara na yi girki da kaina ya ɗan fi kama da naki, tun da ina lura da yadda kike yin na ki." "Ikon Allah!." Ta ce da ƙarin mamakin a fuskarta. "Abincin kowa baya mini daɗi sai nawa. What if ka yi aure ya za ka yi da na matarka?" Tambayar ta ƙona masa rai domin ya so ya ji tace in suka yi aure ya huta da cin abincin kowa sai na ta, amma to in ta faɗi haka ta ya ya kenan? "Sai na ɗauke ki na kaiki gidan har sai ta koyi girkinnki." Jinjina kanta tayi tana mamakin menene a abincin ta da har ya bambanta daɗinsa da sauran na mutane. "Ai da yake da sauƙi tun da Anty Wajnaah ce duk da cewar tana da girman kai ba lallai bane ta koya, amma ina da yaƙinin ba za ta iya rasa ƙwarewa kan dafa abinci ...." "Sai kuma aka ce miki ita zan aura?" Ya jeho mata tambayar cikin ɓacin rai, yana miƙa mata tuwon da ya saka a leda tana nannaɗawa tana sakawa a kula. "Eh, na ga tun kafin ka tafi aka yi emgagement ɗinku, dalilin tafiyarka ya sa aka ɗaga auren sai ka dawo. Ga shi yanzu har ta gama servise kamar ta samu aiki na ji Ummi na faɗi." Ta yi maganar cikin ɗan shakku da rashin gasganta maganar sai kuma ta ɗora da cewa, "Eh haka ne, Uncle Nauhis na ji yana mata murna a lokacin da muka je bikin 'yar gidan Mummy Binta." "To ba ita zan aura ba domin bana sonta." "Haba Yaya! This isn't right. A kan me za ka sa ta ɓata lokacinta for almost two years, kuma yanzu ka ce ba ka sonta? Gaskiya in ka yi mata haka sam ba ka yi mata adalci ba." Tabbas ya san gaskiya ta faɗa, to amma kuma da ya aureta ya kasa bata haƙƙinta ya cutar da ita, wanda in ba mai iya riƙe kanta bane sai ta faɗa harkar banza ai gara ya ƙi aurenta, domin duk matar da zai aura ba ƙanwarsa ba matar shige take a gurinsa. "Kin san mene ne soyayya?" Ya tambayeta cikin sanyi tare da barin kwashe tuwon. "Ban sani ba Ya Huwais saboda har yau ban wani ji ina son Hamad ba, sai don mahaifiyata ta yaba da shi, kuma besides ya cancanci ko wace 'ya mace ta so shi." "Wannan dalilin ya sa kike ganin baike na, kuma duk abin da zan gaya miki ba za ki fahimata." "To Yaya, wata ka kamu da sonta?" Ta yi masa tambayar cikin mamaki har zuwa lokacin tana jin bai kamata ya yi mata haka ba. "Eh, ita ce zuciyata kuma rayuwata. Ita ce nake jin zan iya rayuwar aure da ita, ma kuma zauna da ita ko da ta kasance musaka. Ita ce mace ta farko da zuciyata ta kasa bacci take tunaninta babu dare babu rana har ya taɓa sashi na rayuwata." Mamakin abin da yake cewa ya kamata duk da cewa ba sa ɓoyewa junansu komai, amma sai take ganin bai kamata ya gaya mata waɗananan kalaman ba. Ita mamakinsa ma take yi da yake bai cika shiga rayuwar mutane ba har ya iya soyayya haka. A she ɗan soyayya ne. "Hilah ina jin in ban aureta mutuwa zan yi domin ta zamo rai da numfashi a gareni. Kin ga kuwa babu rayuwa in har babu ita, domin rasa yarinyar daidai yake da rasa rain.." "Wace ce ita, wace ce wacce take son ta yi mana sanadin ɗan'uwanmu? A ina kuka haɗu? In har kuɗi na iya komai ba su Abu ba ni kaina da kuɗin da na mallaka zan nemar maka aurenta ko 'yar shugaban ƙasa ne." Ta ƙarasa maganar cikin hawaye ganin yadda idaunsa suka cika da ƙwalla domin ɓata taɓa ganin abin da ya sa shi cikin wannan yanayin ba. "Wanne kike so na amsa miki Hilah? Tarin tambayoyin sun yi mini yawa? "Duka Ya Huwais. Duka nake so domin kawo ƙarshen matsalarka, saboda ba zan iya ganinka cikin wannan hali ba." 'Ba 'yar kowa bace kuma ba ta wuce matsayinmu ba, amma ta yi mini nisa da tazara;tazaran da yake kamar kwatankwacin sama da ƙasa. Ba zan same ta ba har abada. "To mene ne amfanin tunanin abin da ba za ka samu ba? Saboda abu physical wanda kake da tabbacin samunsa shine za ka yi tunani akai, amma abin da muka san yafi ƙarfinmu ko mallakin wani ne, tunaninsa babu abin da zai sa mana sai damuwa da ƙunci. Ka cire yarinyar a ranka hasashena yana bani ƙila ita ɗin matar aure ce ko kuma budurwar abokinka. Kaga waɗanɗan Allah ya hana neman aure cikin aure." "Haka ne kina da gaskiyarki na ga wauta na da na kamu da soyayyarta duk da cewa mutum ba shi yake sawa kansa so ba Ubangiji ne, amma soyayya Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 3 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Haka ne Hilah, kina da gaskiyarki na ga wauta na da na kamu da soyayyarta, duk da cewa mutum ba shi yake sawa kansa so ba Ubangiji ne, amma soyayya wata aba ce da take shiga zuƙata ba tare da umurni ba ko neman izini. Soyayya wata abace da take girmama a zuciyar mutum. Ta canza maka muƙaminka ko da ace Sarkin da yake kan karagar mulkinsa ne, sai ta sanya ga zama bawa ga abocin begenta." "Na fahimta amma..." "Wai Hilah abincin duniya kike girka ma wa da kika daɗe a kicin ɗin?" Muryar Ummu ta katse mata maganar da take yi, wanda ya sa ta yi saurin fara ƙoƙarin karɓar tukunyar da yake wankewa suka fara kokawar sai ya gama har ta shigo ta same su. Tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta domin ba ta yi tunanin yana kicin ɗin ba. Ƙarasowa ta yi cikin tsanannin fushi ta kwashe ta da mari da idanunta da suka firfito tun kafin ta ƙarasa. Kallonta ya yi zuciyarsa a harzuƙe tare da dafe ƙuncinsa domin ya gwammace ace shi ta mara ƙila marin zai fi masa sauƙi. 'Haba Ummu! Kan me za ki mare ta bayan ni nake da laifin na zo har inda take?" Ko za ka rama mata ne eh? Saboda na ga yadda kake cika kamar za ka iya rama mata?" Ta ce masa cikin tsananin fushi. "Allah karya nuna mini wannan ranar." Ya ce muryarsa a sanyaye. Sai ta ɗora da cewa ganin bai ƙara cewa komai ba, sai ƙasa da idanunsa da ya yi zuciyarsa na suya. "Na ga 'yata ce ni na haife ta kuma nake da iko da ita." "A gaskiya abi da kike yi Ummu bai dace ba kin nuna bambanci a tsakaninmu kuma bayan duk ɗaya muke a gurinki. Bayan kina da sani Hadisi ne ingantacce kan bambanta 'ya'ya." "Ok, ka je waje ka koyo rashin kunya za ka fara yi mini a gaban ƙanninka ko?" Ta tambaye shi tana kallon ƙanninsa da suka yi cirko-cirko Azerh, Umnaah, da Amnaah hawayen tausayin 'yar'uwarsu suke yi. "Ki yi haƙuri Ummu. Ya Huwais, don Allah ka daina ƙalubantarta ita uwace agare ni." Ta ce cikin muryar kuka tare da durƙusawa sai ta fashe da gigitaccen kuka. "A'a ki barshi ya yi mini rashin kunya, kin ga sai na san wuyansa ya isa yanka ya kai munzalin da zan kafa doka ya ƙi bi. Tarbiyarku nake dubawa domin boko ba zai sanya na bari ku aikata abin da ba daidai ba. Idan da ƙuruciya a yanzu kun girma ko su Amnaah da Fu'ad ba na barin su cika shaƙuwa sosai ballantana ku da kuka girma kuka mallaki hankalin kanku. Ku ɗin haƙƙi ne a kaina na kula daku, don haka kar ku ga kamar ina takurawa rayuwarku ne" Ta ce musu haka don su daina mata kallon da sam ba ta jin daɗinsa, yayin da fuskarsu take ɗauke da tarin tambayoyin da ba ta da masarsu. "Ummu, ina da hankali kuma kin bamu tarbiya kar ki bari temptations ya sanya ki zargin 'ya'yanki. Ko da kika ga na fi shaƙuwa da ita ina yi ne saboda ita ce mace ta farko da aka fara haihuwa a gidan, amma bayan wannan babu wani abu saɓanin hakan." "Munafuki duk mai hankali daga kallonka zai fahimci ƙaunarta kake. Ballantana ni mahaifiyarka da na raine ka na san abin da kake so da wanda ba ka so." Ta ce a ranta a fili kuwa cewa ta yi. "Na dai gaya maka sai ka kiyaye." Ta ce tare da ficewa. Ransa ne ya ɓace idanusa suka yi ja sai ya juya ya fice ba tare da ya kalli kowa ba. Yana fita Ummu da ke ƙoƙarin haye sama ta saki ajiyar zuciya tana jin wani irin tashin hankalin da yana saukar mata da ciwon kai ta nufi ɗakin Abu. Duƙawa ta yi ta saki kuka sosai wanda 'yan'uwanta suka yo kanta suna rarrashinta Kuka ta saka masa tare da faɗawa jikinsa wanda hankalinsa ya yi matuƙar ta shi ya fara rarrashinta. "Yaron nan daga dawowarsa yana son ya cigaba da sani cikin damuwa. Na yi tunanin shekarun da ya ɗauka zai sa ya daina haka, amma abin ci gaba ya yi. "Lafiya mai kuma ya yi?" Ya tambayeta cikin mamaki wanda ya sa ta share hawayenta ta ce, "Shaƙuwar da bana son yan nuna mata dai yake nunawa. Wallahi bani da kaffara mahaukacin yaron nan sonta yake. Ko a ina ya taɓa ganin an so wacce babu aure a tsakani? I don sonta da ƙyawunta yake ruɗarshi har yake jin ƙyashin wani ya aureta, ai akwai mata waɗanda suka fita kyawu sai ya je ya nema, amma ba wai ya tsaya yana nuna wa 'yar'uwarsa wacce suka fito ciki ɗaya soyayya ba." "Haba Laila, har yanzu hasashe kike baki tabbatar ba, kuma bai taɓa gaya miki ba. Yana da hankali ba zai aikata hakan ba. Duk kyawun da take da shi ai dole wani ya aureta tun da babu aure a tsakaninku. Ku dai mata kuna da sauran camfar abu don babu komai a tsakaninsu sai shaƙuwa. Tun suna yara ya kamata ki raba shaƙuwar ba wai sai da suka girma ba don hakan zai yi miki wuya." "Shiyasa na ce ayi musu aure kawai! Tun da ya dawo a haɗa aurensu tare ga Wajnaah har ta gama karatu aiki take yi. Ta yi haƙurin jiransa." "Eh, zan yi mishi magana amma ita Hilah gaskiya ba yanzu ba sai ta gama makaranta." Ya ce tare da ɗaukar agogonsa zai ɗaura wanda ta taso ta ƙarɓa tana ɗaura masa. "Ina kashedi da jawo hankalinka da ka da yaron nan ya kasa controlling emotion ɗinsa ya aikata ba.." "Haba ke fa uwace don Allah ki daina faɗin haka domin in sha Allahu hakan ba zai taɓa faruwa ba." Ya katseta cikin tsawa wanda ya sa ta yi shiru amma a ranta ita tasan abin da take tunani. Sai kuma ta ce"Haka ne Allah ya shige mana gaba." Tare da ɗaukar wayarta da ba ta san me za ta yi daita ba sai juya ta take yi. Huwais, zaune a kan kujera cikin ofis ɗin abokinsa kuma amininsa Doctor Khair. Kallonsa yake yana jin bayanin da yake masa wanda ya ɗora da cewa, "Sam bana shawartarka da ka cigabada shan irin waɗannan maganin it been for a while kana sha wanda a shawarce bai kamata ba ace kana sha ba. Duba ga illolinsa da abin da zai haifar nan gaba, saboda za ka kai mizanin da za su zamo maka illa.. Shiru ya yi cikin tunani ganin bai ce komai ba ya ɗora da cewa. "Please, ka daina shan maganin ɗauke sha'awa ka yi aure. Wata ƙila perception ne kawai na ka kan babu macen da za ka ji feelings a kan ta sai ita. Ta iya yiwuwa negatives ne ba gaskiya bane. Kai namiji ne cikkake mai ba dutse bane, bana tunanin za ka iya kaɗaicewa da mace ba tare da ka ji wani ba. Ka ga ƙila albarkacin auren ya ɗauke maka sha'awarta da ƙaunarta, don ƙila sheɗan ne yake saƙa maka hakan don ya yi nasara a kanka ka aikata ba daidai ba, saboda tun da nake ban taɓa jin wanda ya kamu da son yar'uwarsa biologically. "Ya zan yi, ya kake son na yi Khair? Ba ka san abin da nake ji game da ita ba shi ya sa kake cewa haka. A irin yadda na ke jin sonta sai zuciyata take kitsa mini akwai lauje cikin naɗi, amma na kan kore hakan ina tuna da rayuwarmu bakiɗaya. A gabama aka haife ta na raine ta ta girma. Ni na san soyyayarta ita ce ƙaddarata wace za ta kai ni kushewata lokacin abai yi ba." Ya ƙarashe maganar cikin murya mai rauni tare da saukar hawaye masu zafi kan ƙuncinsa. "Yanzu me kake son yi?" Ya tambayesa cikin tsananin tausayinsa na jararabawar da Allah ya yi masa. ""Ban sani ba! Ni ma ban sani ba." Ya faɗa yana watsa hannunsa cikin damuwa sai ya ɗora da cewa, "Amma sai dai ina jin zuciyata tana bani shawarar da zai iya zama mini ƙadangaren bakin tulu a rayuwata, domin zabbi shawarar da take bani, wataƙila bayan lalacewar lamarin sai na samu mafita a cikinsa. Zanbi makauniyar zuciyata domin samun mafita, duk da ance son zuciya, ɓacinta." "Karka je ka aikata abin da za ka yi dana sani. Ka amince da aure kawai shine mafita." Kallonsa ya yi ba tare da maganarsa ta shigesa ba. "I understand, I know that you are trying to help, amma ka sani kurmar zuciyata ta riga ta yi nisa ba ta jin kira, domin a shirye take ta yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada! Matuƙar za ta samu muradinta ko da na wucin gadi ne." Tabbas ya yarda so mahaukaci ne domin ga shi ya mai da amininnasa mahaukaci yana tunani ba tare da ya hangi abin da zai je ya dawo ba, ganin yadda zuciyarsa take masa ingiza mai kantu ya aikata lamarin da ya tabbatar xai yi dana-sani mara amfani. "Na fahimce ka duk da cewar ba na amince da ka ci gaba da sha bane, amma babu yadda zan yi da kai, don haka ga maganin ka ci gaba da sha Allahu ya kawo maka ƙarshen matsalarka." "Thanks." Ya ce tare da karɓar maganin ya fice yayin da zuciyarsa ke gasganta masa hakan shine kawai mafita a gare shi. Hilah ta shiga cikin tsananin damuwa na maganar da suka yi da shi. Tunaninta wa yake so, kuma mai ya sa yake faɗin ta yi masa nisa? Kan me zai ɗauki son mace ya ɗora ma kansa har yana tunanin in ba ita ba ba zai iya rayuwa ba. Bayan namiji ne wanda ko bai samu soyayyar mace ba zai samu wacce ta fita. A ɗan tunaninta sai take ganin duk ba matsala bace wanda zai tashi hankalinsa har ya saka shi cikin ƙunci domin shi ɗin namiji ne da Allah ya ba shi damarmarki da dama. Kwanciya ta yi tana tunanin halin da yake ciki. Tana wannan tunanin har bacci ɓarawo na yi nasarar sace ta. Zaune yake kan sofa daga shi sai gajeren wando. Duk da sanyin A.C da ya cika ɗakin sai yake jin zufa na kama shi ta cikin jikinshi, sakamakon abin da yake son aikatawa. Miƙewa ya yi, ya ɗauko ƙaton hotonta da ya zana ya rungume a ƙirjinsa cike da begenta. Ya ɗan ɓata lokacin yana rungume da hoton sai kuma ya miƙe ya ɗauko maganinsa ya ɓalla tare da haɗiya bisa ƙa'ida wanda a hankali ya fara aiki ya daina jin sha'awarta. Sabuwar wayar da ya siya da da sabon layi ya sanya hannunsa ya ɗauko. Bayan ya gama deciding da yanke hukunci zartacce akan lamarin ya aminta da komai ya faru in the future zai ɗauka, domin tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan duka. Sa layin ya siya wanda ba shi ya yi rigister ba ya ɗauko sai ya kunna wayar yana kallon wayar da ta gama serching ta kunnu. A hankali ya danna numbarta a cikin wayar da nufin ya yi mata magana ta whatsapp sai kuma ya fasa ya kashe wayar ya koma ya xauna yana tunani. A ƙalla sai da ya yi haka sau biyar da ga ƙarshe ya yi nasarar tura mata tsaƙo kamar haka: "Na kasa natsuwa na kasa sukuni kullum zuciya cikin begenki. Kar kinyi mamakin hakan, domin na riga na gama a concluding son ki da ya mai dani mahaukaci shi zai yi ajalina, amma kafin na mutu, akwai buƙatar ki san wani yana can yana begenki da fatan ki zamo ta sa na har abada. Na ki mahaukacin masoyi." Ya tura mata da hakan tare da kashe wagarsa gabakiɗaya yana jin yadda zuciyarsa ke bugu tamkar za ta fito waje! Ko wanda ya yi gudun kilometer 1000. Bayan ya tura mata alert na naira miliyan ɗaya. Hilah na zaune cikin hall ɗinsu tsaƙon ya shigo wanda ba ta duba ba, saboda lectured ɗin da ake musu hankalinta na kan malamin, domin sam ba ta wasa da sauraren lecturer in yana lecturing. Bayan ta fito sai ta nufi cafateria don ta ci abinci saboda yau a makare ta haɗa karin kummallon ba ta samu damar da za ta yi breakfast ba. Tana zaune ita da ƙawarta Nihal suna cin abincin sai ta tuna da tsaƙo ya shigo cikin wayarta, wanda ta ɗauko wayar da ke cikin jakarta don ta duba. Da sauri ta miƙe tana kallon alert na one miliyan da ya shiga cikin wayarta tun lokacin. "What!" Ta ce cikin mamaki tana kallon alert ɗin. "Miliyan ɗaya a ka turo mini! waye ya turo?" Ta yi tambayar cikin mamaki tana nuna wa Affrin wayarta da ta tsaya tana kallonta cikin mamakin abin da ya sanya ta razana. "Waye shi Hilah?" "Ban sani ba domin kamar ba da account ɗinsa aka tura ba ta banki ne." "Ok, kuma babu tsaƙon da ya turo? Ki duba wataƙila ya tura miki baki gani ba." Ba tare da musu ba ta shiga cikin inbox ɗinta jikinta na rawa. Ganin saƙon ya ɗan sanyaya zuciyarta amma ganin an rubuta anonymous sai ta ɗan ji faɗuwar gaba. "Ga message na gani sai dai da alamar wanda ya yi turo tsaƙon, ba ya son bayyana kansa domin anonymous ne." Ta ce tare da buɗe tsakon wanda ta fara karantawa sai dai ba ta ƙarasa ba ta tsaya cikin tsa Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 4 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Ganin saƙon ya ɗan sanyaya zuciyarta, amma ganin an rubuta anonymous sai ta ɗan ji faɗuwar gaba. "Ga message na gani, sai dai da alama wanda ya yi baya son bayyana kansa domin anonymous ne." Ta ce tare da buɗe tsakon, wanda ta fara karantawa sai dai ba ta ƙarasa ba ta tsaya cikin tsananin mamaki. "Waye wannan mahaukacin masoyi da ya tura miki tsako haka?" Afrin ta tambaya cikin tsananin mamaki. "Tabbas ya cika mahaukacin masoyi! Domin babu mai hankalin da zai bayyana soyayyarsa a ɓoye da alamar matsoraci ne." Ta ce cikin tsananin mamaki. Sai kuma ta ɗora da cewa kafin Afrin ta yi magana. "Kin ga shi ma da kansa ya sawa sunansa mahaukaci masoyi." Ta kashe wayar tare da maida ta cikin jaka tana jinjina lamarin lokaci guda kanta ya kulle ta shiga cikin duniyar tunanin. "Ni fa ina tunanin wani ne da yake can yana fama da sonki, amma ya kasa zuwa gareki kin san ke ɗin ba kowane namiji, zai iya tunkarar ki da maganar so ba; saboda baiwarki da da ilminki uwa uba kyau tamkar ke kika yi kanki." Shiru ta yi ba tare da kalamanta sun yi tasiri a ranta ba, domin hasashenta ne wannan. Besides, dukanninsu mutane ne kuma babu wanda ya fi wani a gurin Allah sai wanda yafi tsoron shi, don haka ba ta ganin wannan a matsayin hujja da zai sanya ya kasa bayyana kansa gareta. "Wannan ba hujja bace, amma ko ma mene kyautar kuɗi da ya yi haka dole ya bayyana kansa, bari na je gida na sanar wa Ya Huwais, na san shine kawai zai bani shawara da mafita." Sai ta miƙe tana saɓa jakarta tare da cigaba da cewa, "To amma ta ya ya akai ya samu account ɗina? Tunani nake ya san ni duk wanda ya turo wannan tsaƙon." "Eh, ai ba abin mamaki bane saboda kamar yadda duniya ta sanki haka account ɗinki. Mutane nawa suke turo miki da kyauta su ce sun karɓa a musabaƙa da kika cinye." "Haka ne." Ta ba ta masa sai suka fara tafiya tana cewa, "Bari na wuce da wuya na dawo tun da surmiting assigment za mu yi, in ban dawo ba ga shi kawai ki ba da." Sai kuma ta canza shawara ta ce, "Kai bari ma zan dawo kawai." "Ok." Ta masa tare da miƙa mata assignment ɗin, wanda ta karɓa ta mayar cikin jakarta tare da ciro makullin motarta ganin sun iso gurin. Da ta isa gida sai ta yi farking a ƙofar gida ta shiga cikin gidan wanda cikin sa'a Ummu na bacci. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa da yake kwance wayarsa a hannunsa ya rungume yayin da ya tafi duniyar begenta. Ƙamshin turarenta ya dawo da shi da duniyar da ya lula. Da sauri ya jawo laptop ɗinsa ya zauna ya buɗe tare buɗewa ya fara daddanawa fuskarsa a ɗan ɗaure. Kallonta ya yi da ta yi sallama tare da ƙarasawa inda yake ta zauna. "Lafiya sis, ba kin ce sai 4 pm za ki dawo ba?" Ya yi mata tambayar cikin tsannin mamaki duk da ya san dole ta dawo saboda shawarar shi kawai take nema, don baya manta ko a lokacin da ta fara menstration ɗin shi ta fara nuna wa mawa. "Haka ne Ya Huwais, amma ba zan iya zama har lokacin ba domin tsakon da aka tura mini." Sai ta ciro wayarta ta nuna masa tsakon ta ɗora da cewa, "Abin da yafi bani mamaki shine har da kuɗi ya tura mini miliyan ɗaya." Zare idanunsa ya yi cikin tsananin mamaki tamkar bai san abin da ke faruwa. "Miliyan ɗaya! Waye shi kuma mai yake so daga gare shi, ko kin san shi kike ɓoye mini?" Ya yi mata tambayar cilkin ɗan ɗaga murya har lokacin idanunsa a xare. Rau-rau ta yi da idanunta lokaci guda hawaye suka fara sintiri kan kyakykyawar fuskarta. "Kaicona! Sai na yi tur da ni in har zan fara ɓoye maka sirrina." Ta faɗa tana kallonsa. "To mene ne abin kuka?" Ya ce tare da jawo tissue yana ɗauke mata hawayen Hannunsa ta kama ta riƙe gam wanda sai da ya ji ɗumin jikinta, har cikin bargon jikinsa, ya rintse idanunsa yana jin yadda yake jin ɗumin na ratsa ko ina na jikin shi yana saukar masa da natsuwa, wanda ya sanya shi zare hannun da sauri yana istigifari da ta'awizi kan Allah ya kawo masa ɗauki tunkafin sheɗanin da ke ƙoƙarin galaba a jikinsa ya yi. Ba tare da ta fahimci halin da ya shiga ba ta ƙara kama hannun a karo na biyu ta riƙe sosai. "Ya kafahimce ni wallahi bani da masaniya kan lamarin nan." "Ok." Ya ce cikin basarwa ya cigaba da aikin shi yana tunanin mai zai ce mata. Ganin shirun da ya yi ya sa ta fara magana da cewa, "Ko ma waye wannna tabbas ya cika mahaukacin masoyi, domin ina ya taɓa ganin an yi soyayya a ɓoye? Wataƙila kuma mahaukaciyar zuciyarsa ta gaya masa zai iya siyen soyayyata da kuɗi ne, ba tare da ya san bani cikin makwaɗaitan matan da suke sayar da rayuwarsu saboda kuɗi ba. Namiji mai ilmin addini da boko nake nema, wanda zai amfani da ilminsa duka a cikin rayuwar aurenmu. Kuma ai ina da wanda zai aura don haka ya kama kansa." Wani kallo ya juyo ya watsa mata, take zuciyarsa ta fara zafi na kishinta, sai kuma ya juya zai ci gaba da aikin wanda ya sanya ta kama hannunsa. "Yaya, ka yi shiru ba ka ce komai ba." "Me kike so na ce domin na ga lokacin da Hammad ya ce yana sonki ba ki gaya mini ba." Ya jefo mata maganar cikin bazata. "Bani da zaɓi ne, bisa umurnin Ummu da ta ce kar na sake na gaya maka, ganin yadda kake tada hankalinka kake nuna kai xaka saɓa mini miji da kanka. Cewarta shi na gida ne, kuma ya cika criteria da kake son mijin da zan aura ya cika." Ta ba shi masa. Shiru ya yi dama ya san tursasawar Ummi ne har ta fara kula wani ba ta gaya masa ba. Karɓar wayar ya yi daga hannunta ya ɗan tsaya yana karanta tsaƙon tare da dogon nazari game da abin da zai ce mata. Bayan ya gama nazarin sai ya ije wayar saman cinyarsa yana ƙare mata kallo ganin yadda ta wani firgice. Tattara dukkan hankalinsa ya yi gareta ya ce,"Wa ki ka gaya ma wa?" "Babu kowa sai Afrin ƙawata, bayan ita babu wanda ya sani." "Good! To kiyi shiru karki gaya wa kowa har muka mai zai yi nan gaba. Ki bar wannna kuɗin a account ɗinki." "No Yaya, sai dai na yi maka transfer ba zan iya ije maƙudan kuɗi haka ba." Ta ba shi amsa cikin sauri. "Ki barshi dai gurin ki kafin na gama tunani sai na san yadda za mu yi da kuɗi." "Tom, amma kana tunanin ɓoyewar ba zai kawo matsala tsakaninmu da iyayena ba? Musamman Ummu don Abu ba zan samu sausauci ba." "Duk da hakan mu jira muga abin da zai yi kafin mu sanar musu ba. Sannan ki kwantar da hankalinki kar ya taɓa karatunki kin ji sis? Kin san kina da musabaƙa. Kwana uku ne ko?" Ya ce mata cikin tsigar rarrashi. "A,a biyar ne sun tura mana tsaƙo sun ƙara kwana biyu." "Masha Allah! Kin ga kin samu ƙarin kwana biyu za ki yi karatu sosai." "Na ma gama kawai dai ƙarin kwanar zai bani lokacin na ƙara bita." "Yauwa ma za tashi ki tafi makaranta ko na kai ki?" "Karka damu zan koma da kaina." Ta ce tare da miƙewa. Murmushi ta yi tana kallonsa wanda shima ya miƙe yana miƙa mata wayarta. "Mahaukacin masoyi!" Ta ce tare da jan tsaki da ƙarfi. "Mutumin nan ya raina mini wayo sosai Ya Huwais. Ga shi gabakiɗaya ya ɓata mini mood ɗina zai sanya na raba tunani gida biyu." "No kar mu yi haka dake, ki kauda lamarin kin san dole sai kin ciyo mana tropy ɗin nan." Ya faɗa yayin da yake jin babu daɗin kalaman da ta furta amma sai ya daure bai nuna koma ba ya ce. Ajiya zuciya ta saki mai ƙarfi tana ƙoƙarin comforting ɗin kanta domin gabakiɗaya ta ruɗe. "In sha Allahu, bari na tafi na yi wanka na koma school." "To shikenan, 'yar ƙanwata." Fita ta yi wanda tana yin nisa ya durƙushe a gurin yana jin yadda zuciyarsa ke masa zafi. Ji ya yi idanunsa sun cika da ƙwallah shi kan ya san yana cikin jarrawa, domin ya sanya a ransa ita ce jarrabawarsa. "Tabbas na cika mahaukacin masoyi! Domin soyayyarki gab yake da fallasuwa cikin raina, wanda zai sanya mutane sun tabbatar da na haukace game da sonki, amma kuma a shirye nake da na amshi duk wani ƙalubalen da zan fuskanta, domin ba zan yi sakaci ba ina ji ina gani wani ya aure ki. Kece farincikina kuma zuciyata." Kamar yadda ya gaya mata kar ta sanar da kowa. Ba ta gaya wa kowa ba, amma wunin ranar ta yi shi suku-suku, domin ta kasa samun natsuwa. Burinta kawai ta san wanda ya tura mata tsakon, amma iya hatsashenta ta yi ta yi hakarta ba ta cima ruwa ba. Don haka ta ga ji ta haƙura da tunanin sakamakon wani irin ciwo da kanta yake yi. Wuni ta yi tana duba tsaƙon da ta ji muryar Ummu ko 'yan uwanta sai ta yi maza ta kife wayar. Da ta zo bacci kasa bacci ta yi ta rinƙa juye-juye a kan makeken gadon da ke barazanar cinye ɗakin, wanda da ƙyar da siɗin goshi baccin ya yi nasarar ɗaukarta wanda sai da ta riƙe carbi tana ta Sayyidil istigafari. Ya rage gasar su saura kwana biyu, ta yi ƙoƙarin watsar da komai ganin tunanin na son zubar da haddar da ta yi. Ga shi ta burin amso wa Ƙasarta tropy da zai zamo abin alfahari ga al'ummar Musulmai. A ranar da ta kasance ranar tafiyarsu suka shirya da misalin ƙarfe goma suka ɗauki hanya. Hilah tana tsaye a gurin da za su fara musabaƙar. Idanunta ta runtse tana yin addu'a samun nasara. Da ta tuna irin yadda iyayenta da yan'uwanta suka ƙarfafa mata guiwa, sai ta ji wani irin ƙwarin gwuiwa ya zo mata. Wayarta ce ta yi ƙara wanda ta duba da sauri. Ganin numbar anonymous ya sanya ta ƙi dubawa, domin ganin tsaƙon na neman rikita tunaninta da matsuwarta. Sai dai, duk iya ƙoƙarinta na kar ta duba sai ta tsinci kanta da son duba tsaƙon, wanda har ta kasa jurewa ta buɗe cikin ƙarfin hali. "Ina miki fatan alkhairi ma'abociyar ilmi da baiwa. I know that you gonna rock it. Eh tabbas za ki ci. Ina kallon ki domin ina daga cikin mutanen da suka zo, domin sauraron daddaɗar muryarki da fatan ki cinye wannan gasar. Jikina yana bani za ki ci, domin ba bu faɗuwa a rayuwarki. gani a cikin dubban mutane ina murmushi zuciyata cike da miki fatan nasara." Da sauri ta shiga duba mutanen dake gurin jin gaya mata yana wurin "Wane ne wannan! Wane ne wannan yake son wasa da hankalina?" Ta furta tana waige-waige. Iya hangenta ba ta kowa ba sai Ya Huwais da yake sakin mata murmushi tare da ƙarfafa mata gwiwa da idanunsa. Da ta kalli sauran 'yan'uwanta sai ta ga kusan irin murmushi da yake kan fuskarsa iri ɗaya ne, musamman Abu da ta ga ya duƙufa yana ta kwaroro addu'a. Ta shiga ruɗani sosai tana ta tunanin sa. Zuciyarsa ta kwaɗaitu da ta gan shi. Haka kawai ta ji tana son ganin ko wane ne, amma iya tunaninta da son ganinsa ba ta gan shi. Da ta tuna dubban mutanen da suke gurin sai ta daina wahalar da kanta, domin ta san ya faɗa mata ne don kawai ya wahalar da ita, ko ya sa ta faɗi. Sai ta saka wa kanta anya mahaukacin masoyi sonta yake? Ko an yi amfani da shi ne don ta faɗi gasar. Ganin yadda ta rikice lokaci guda! A lokacin da ka aka kira ta sai ta ji ta rasa natsuwarta da karatun da ta yi bakiɗaya. Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta har ya sa ta dafe ƙirjinta tana jin gadda yake bugawa cikin rashin ƙa'ida. Da ta tsaya a gurin ta buɗe baki da nufin ta fara karatun sai ta ji ta kasa. Idanunta suka cika fal da hawaye. Tana jin yadda komai yake neman fin ƙarfinta. Huwais da yake kallonta cikin tsananin ƙauna da bege. A lokacin da ya tura mata tsaƙon, ta buɗe tana karantawa sai ya ji tamkar ya isa gareta ya kamata ya rungume ya ƙarfafa mata gwuiwa. Ganin ta tsaya tana duba tsaƙon ya sashi ɗan sakin murmushi yana kallonta. Burinsa bai wuce ace ta zamo ta ɗaya ba. Tabbas hakan zai ƙara masa sonta da begenta, kuma hakan abin alfahari ne ga zuriyarsu baki ɗaya. Ya fara shiga cikin tashin hankali lokacin da ya ga tana ta wilƙita idanunta wanda ya tabbatar da gaya mata cewar yana gurin ne ya sa take duba shi. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya ga layi na gab da zuwa kanta amma har lokacin nemansa take yi. Wani irin juya ya ji yana kama shi a zaunen har ya ji kanshi ya sara. Miyau bakinsa na neman ƙafewa. "Mai ya sa ta damu da ta ganshi, kuma mai ya sa na tura mata da tsaƙon?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamakin yadda ta rikice har yana jin in har ba ta ci gara ba ba zai yafe wa kansa ba. A lokacin da ta tsaya za ta yi karatun sai ya ga ta kasa idanunta cike da ƙwallah. Miƙewa ya yi cikin dana-sani zai fita daga gurin, domin yana ji ba zai iya ganin ta kasa cin gasar ba. Rintse idanunsa ya yi ya tsaya jin ta fara karatun cikin rawar murya. Tsaya wa ya yi tare da kafe ta da idanu wanda cikin ikon Allah sai ta kalle shi. Da hannu ya yi mata maganar kurame na ƙarfafa gwiya. Ga mamakinsa sai ya ji muryata ta dake ta fara karatun wanda tun da ta fara ba ta tsaya ba sai da ta dire. Gurin ya yi sit! Ba ka jin komai sai ƙarar A.C da numfashin mutane. Har ta ƙare karatun cikin murya mai tsananin daɗi. Huwais da ya koma ya zauna, hankalinsa ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana jin yadda take zubo karatun cikin murya mai daɗi, da fitar da tajweed tsantsa. Duk inda aka yanko mata sai ta ɗauka tana karantawa cikin gwanancewa. Ya tabbatar wa kansa a karo na biyu in har ya bari ta kubce masa a matsayin matarsa ya yi asarar da bai zai taɓa mayar da ita ba. To amma ta yaya? Don shi dai ko a garin gaɓa-gaɓa bai taɓa ganin Ya ya auri ƙanwa ba. To amma ya akai zuciyarsa da tunaninsa suke ƙarfafa masa watarana za ta zamo matarsa kuma uwar 'yayansa domin perspective ɗinsa kullum kuma mafarkinsa. Kabbarar mutanen gurin ya dawo da shi daga tunanin da yake yi wanda shi ma ya ɗauki nasa kabbarar. Kuka sosai take yi tana ganin yadda mutane suka ƙoƙarin ɗaukar ta hoto. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 5 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Kabbarar mutanen gurin ya dawo da shi daga tunanin da yake yi wanda shi ma ya ɗauki nasa kabbarar. Kuka sosai take yi tana ganin yadda mutane suka dabaibayeta suna son ɗaukar hoto da ita. Tun daga kan larabawa da jajayen fata. Da ƙyar iyayenta suka samu damar ɗaukar hoto da ita, wanda ana gamawa ta ja Huwais gefe. "Ya ya sanar da ni yana nan tabbas kuma naji a jikina yana nan, wasa da hankalina yake yi! Anya masoyi ne ko maƙiyi? Domin ba zai tura mini tsaƙon da ya rikita ni a daidai lokacin da zan fara musabaƙar ba." Ta ce tare da kama hannunshi tana kuka. Jikinsa ya yi sanyi sosai duk da ya san cewa bai kyauta ba, amma sai ya ji kalamanta tamkar dafi na maciji, musamman da kunnuwansa suka ƙara ji masa lokacin da take cewa. "Na tsane shi bana sonsa! Idan ya yi hakan ne don ya samu soyayyata, haƙiƙa ya yaudari kansa, domin a halin yanzu ba ni da maƙiyi sama da shi, kuma wallahi da ya sanya na faɗi a gasar nan, burina ya tashi a tutan ma'aho da bazan taɓa yafe masa ba, kamar yadda ba zan yafe ma kaina ba, domin lokacin da na fara shiga gasa na sawa burin karɓo wa Ƙasata kabbu!" "Bai kyauta ba shima ya yi kuskure! Tabbas ya zama cikkaken mahaukacin da baya iya gane komai sai cimma soyayarsa." Ya ce mata domin shi ma ya ga wautarsa. "Yana nan gurin ta ya ya zan iya gane sa na kikkifa masa mari ko zuciyata za ta yi sanyi." Ta ce tana kallon sa sai kuma ta fara dube-dube. "Ba za ki iya ganinsa ba duba ga dubban mutanen da suke gurin nan." "Zan iya Yaya, na yarda mahaukaci ne don haka dole ya fita daga siffar masu hankali." Ta ce cikin ɗan ɗaga murya. "Anya hanyar da na ɗauko mai ɓullewa ne, domin na gane a maimakon ta soni sai dai na ta tsane ni, tunkafin ta san ko ni wane ne." Ya ce tare da rintse idanunsa. Ba tare da ya hana ta ba ya koma kujerarsa ya zauna, yana ganinta tana dube-dube, amma bai ce mata komai ba, domin haushin maganarta sun sanya shi jin haushinta. Ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana dube-dube ya sanya shi miƙewa. Cikin rashin ƙarfin jiki ya isa gareta, tare da kama hannunta zuwa mota. Faɗawa ƙirshijin shi ta yi tare da sakin kuka mai ƙargi ta ce,"I hate him." Ji ya yi tamkar ta coka masa mashi a zuciyarsa har sai da ya rintse idanunsa, jin abin da ta furta. Bayanta ya shiga shafawa domin ya kasa janyeta daga jikinsa har tsawon lokaci. Suna a haka ya ga Ummu ta nufo motar da sauri wa da ya sanya shi zare ta daga jikinsa ya nuna mata Ummu. Da sauri ta fita daga motar tana zare idanunta. Ummu na isowa ta aika mata da mugun kallo cikin ɓacin rai ta juya ba tare da ta ce mata komai ba. Ganin ta yi tsaye ta kasa bin bayanta ya sanya shi fitowa daga cikin motar. Hannunta ya kama suka fara tafiya zuwa gurin mutane. Cikin nasara ta samu nasarar lashe gasar domin ta zamo zakaran gwajin dafi a tsakanin rawuna. Ta samu kyautittika da dama ita kanta ba za ta manta da wannan ranar ba, domin rana ce na musamman gareta. A ranar da ta kasance zinariya ga mutane ta amso wa ƙasarta kimarta da darajarta. Iyaye da dama sun mafarkin ace ita 'yarsu ce, wanda har da waɗanda suka tako suka nuna hakan. Bayan sun dawo sun yi hutun gajiya. Suna zaune a falo suna cin abincin da aka shirya mata. Gabakiɗaya abincin oder ɗin shi aka yi. Hira suke cikin nishaɗi da fara'a wanda rabin hirar duk kan gasar da ta ciyo ne. Ummu ne kawai ba ta cika soma baki ba sai dai ta yi murmushi, amma fuskarta cike take da farinciki matuƙa. Hamsiya mai aiki ce ta yi sallama ta shigo tare da duƙawa cikin girmamawa ta ce, "Inusa, direba ya ce na kawo wannnan wani ne ya turo tsaƙon a bawa Hilah har da mota a waje." Gabkiɗaya suka kalleta cikin tsananin mamaki. Hilah kuwa Huwais ta kalla, yayin da idanunta suka firfito saboda ta zargi tsaƙon daga mahaukacin masoyi ne. Amma sai ta ga ko a jikin shi domin ba ita yake kallo ba, wayarsa ya maida hankali kanta yana dandannawa. A daidai lokacin tsaƙo ya shigo cikin wayarta, wanda har sai da ta miƙe a zabure ta kasa kallon wayar, ballanatana ta ga wanda ya turo mata. Sai da ta ɗan ɗauki sakanni sannan ta duba. Hasashenta ya zama gaskiya domin shi ne. Mahaukacin masoyi ne ya ƙara turo mata tsaƙo kamar haka: "Amincin Allah ya tabbata ga wannan abociyar haske! Na san na yi miki laifi, don Allah ki yafe mini ga tsaƙo nan. Ina miki murnan lashe gasar da kika yi." Tsanananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta. "Waye shi wanda ya kawo tsaƙon irin wanna tsadaddiyar wayar da mota ya siya mata haka? Kai Huwais, ma za ka je ka gani." Ummu ta furta fuskarta bayyane da mamaki. "No, bari na je tun da ina nan." Abu ya ce tare da dakatar da shi da ya miƙe fuskarsa babu yabo ba fallasa sai ya koma ya zauna yayin da Ummu ta bi shi da kallo. "Inusa, ina wanda ya kawo tsaƙon?" Abu ya ce masa yana waige-waige tare da kallon tsadadiyar motar cikin tsananin mamaki. "Ranka ya daɗe, bayan ya gaya mini sai na je na gaya wa Hamsiya, kafin na dawo na neme shi na rasa kamar aljani." Mamaki ya ƙara kamasa sosai yana mamakin ace wanda ya kawo irin wannan tsaƙon ya ƙi bayyana kansa. "Ikon Allah!" Ya ce cikin mamaki tare da juyawa ya koma ciki wanda ya same su cirko-cirko ban da shi da yake ta cin abinsa hankalinsa kwance. Zama ya yi kan kujera domin ya ji abincin ya gimshe shi. "Ɗan tsaƙon ya tafi." Ajiyar zuciya ya saki domin ya ɗan ji fargabar kar su kama wanda ya turo, amma jin hakan sai hankalin shi ya kwanta tamkar ya yi baƙo ya mutu. "Waye wannan ya yi mata wannan kyautar! Ke Hilah kin san shi ne?" Ummu ta jeho mata tambayar da ya sanya ta ɗago a razane tana girgiza kanta. "Magana za ki yi mini ba girgiza kai ba, ko kin zama kurma ne? Ai na lura tun da aka gaya tsaƙon kika ruɗe. Uban me kike ɓoyewa." "Um ni wallahi babu! Dama an um!" Ta shiga faɗin haka sai kuma ta fara in-ina sai ta saka kuka, wanda hakan ya sa ta zargeta ranta ya ɓace. "Za ki rufe mini baki daga magana sai kuka ke ga ki mai fuskar kuka ko!" Ta daka mata tsawa tana faɗin hakan, wanda ya sanya ta haɗiyar kukanta cikin tsoro, don tsawar harta sauran 'yan'uwanta sai da suka razana. "Haba Laila, ki yi mata a hankali."Abu ya ce tare da kamo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi. "Kin san shi ne?" Ya tambayeta cikin tautausar murya. "Eh! A'a." Ta ba shi duka amsar cikin rawar murya sai kuma ta ɗora da cewa, "Da ma ya turo mini da tsaƙo kwanakin baya da kyautar miliyan ɗaya sai kuma ranar da musabaƙa ya tura mini tsako, amma wallahi ban taɓa ganin shi ba." Ta ce cikin kuka. Mamaki ya kamasu ƙwarai Ummu har da salati tana tafa hannu. Ganin yadda suka ruɗe sai ta ci gaba da gaba da magana cikin inda-inda,"Na gaya wa Huwais, shi ne ya ce kar na sanar muku." Ta ce tana kallonsa cikin jin haushin komin kula da ya nuna kan lamarin ga shi an tsareta an tambayarta ko a jikin shi. "Innalillahi! Yaushe kuka girma har kuke yanke shawara iya kanku? Huwais, shi ya haife ki, na ga dukkaninku ikonmu ne, amma ba ku sanar mana ba?" Ta ce cikin zafi zata mare ta wanda ta ɓoye cikin sauri bayan Abu tare da dafe ƙuncinta tana kuka. "Karki taɓata ga babban kwabo nan, duk da cewar shin a yaro bane, wataƙila yana da dalillinsa." "Dalilin me Abu? Wanda zai kasa sanar mana ai duk ƙarƙashinmu suke hakan da suka yi koyi suke yi wa na bayansu." Ta ce tana harararsa cikin zargi. Shiru ya yi kamar babu ruwan shi, ko bai san da zancen ba." Ya ce yana hararsa wanda sai a lokacin ya ije. "Ni fa ba da wani nufi na yi ba kawai na gaya mata ne, saboda ganin yadda ta tada hankalinta, kuma a lokacin gab da musabaƙarsu ne. Ba na son ta tada hankalinta ya sa na gaya mata hakan, dama na san in har da gaske ya ke yi zai ƙara tura tsaƙon." "Wannan ba hujja bace Huwais, ya kamata komai na ku mu sani, domin mun cancanci mu sani." "Ku yi haƙuri mun yi kuskure." Ya ce yana kallon Ummu da take masa wani kallo don gabakiɗaya ba ta yadda da shi ba. "To yanzu mene ne abin yi?"Abu ya tambaye sa cikin rashin dubara. "Ban sani ba mu jira lokaci, in dai ba aljani bane, dole ya bayyana kansa tun da babu wani identity na sa, da zamu mayar masa da kuɗin." Ya ce musu yana kallonsu. "Ai ya makaro ko ma waye, domin Hilah na da masoyi kuma na yi na'am da shi, sam ba ta da wani miji sai shi." Ummu ta ce cikin ɓacin rai! "Hilah tawa ce don in ina raye babu wanda ya isa ya mallaketa sai ni, domin kanta zan iya zama makashi ko ɗan dan daba Ummu. Ki jira lokacin da zan bayyana kaina na yi yaƙi da duk wanda zai hana ni mallakarta." Ya ce a ransa amma a fili bai ce komai ba sai ya fice daga falon wanda Ummu ta raka shi da idanu hankalinta a tashe. Ganin ya fita sai haushinsa ya kamata domin bai taɓa ɓata mata rai ba irin yau. Ɗakinta ta shige ta kulle ƙofa tare da faɗawa kan gado ta sakin kuka. "Wane ne wannan mahaukacin masoyin da yake so ya kawo mini rashin zaman lafiya da iyayena? Domin irin kallon da Ummu take mini ya girgiza ni." Ta ce cikin damuwa. "Anya mutumin nan ya san ciwon kuɗi ji motar da ya kawo mini da waya? Zuciyata ta fara zargin ɗan shan jini ne ko mai safarar mutane." Ta ce cikin ruɗani. Tana kwance kiran Hammad ya shigo wanda har sai da ya yi ringing uku sannan ta fahimci ana kiranta ta ɗaga. Jin yadda take amsa masa ya fahimci ba ta cikin hankalinta ya yi mata sallama ya kashe wayar, wanda ita ma jifa ta yi da wayar ta kifa kanta kan filo tana mai da numfashi. A haka ta wuni sukuku lokaci guda ta ji ta ƙara zaƙuwa da ta ga wannan mahaukacin da ya kamata a kaisa Dawanau. Ko da ta zo bacci duk iya satar bacci a wannan lokacin sai dai ya ganta ya haƙura, domin idanunta sun soye tamkar an soya gyaɗa mai gishiri Ta yi juyin har kan kujera ta dawo ta kwanta amma gwanin satar ya kasa sace ta. Duk da cewarta ba mai son rayuwar social media ba ce, don sai ta haɗa sati ba ta hau whatsapp ko facebook ba in dai ba relevant abu za ta duba ba. Don ita ba ta ɗauki wannan platform amatsayin wanda zai ɗauke mata kewa ba, sai dai amfani da shi da wasu gwara gurbin mutane suke yi suna watsa alfasha da ƙarerayi. Duk da cewar ko wane abu akwai merits ɗin sa da demerits ɗinsa. A wannan lokacin ta tsinci kanta da son hawa whatsapp musamman da ta tuna Muktar classrep ɗinsu ya gaya mata ya tura houndout that is meaningfull. Sai ta tsinci kanta da kunna datar wanda a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi daidai. Tana buɗewa ta fara duba tsaƙon Huwais dake zaune idanunsa babu bacci ko kaɗan. Bayan ya kammala ayyukansa ya tura musu sannan ya kashe lap ɗin ya koma kan gado ya kwanta tare da jan bargo. Tunanin halin da ta shiga lokacin da scene ɗin ya faru yake yi. Mamakin iya basarwa na sa ya nuna tamkar bai damu da lamarin ba ya kama shi, wanda a wannan lokacin Allah kaɗai ya san halin da yake ciki, domin da ace Abu ya ɗan matso kusa da shi sai ya fahimci halin da yake ciki. Sai dai Allah ya taimake shi Ummu ne kawai ya ɗan zargi wani abu domin ta san shi fiye da kowa. Sai ya ƙara tasbihi ga Allah, da ya rufa masa asirin domin da sun gane wata maganara ake ba wannan ba. Ya san an riga an yi disowning ɗinsa agidan duba ga wutar da yake so ya kunna a gidan. Ɗaukar wayarsa ya yi ya kunna data wanda yake son ko bacci ya kama shi. Da yake gb whatsapp yake amfani fa shi. Yana hawa ya ga an rubuta; little sis online. Wanda matuƙar mamaki ya kama shi domin a iya tarihin rayuwarsa sam ba ta hawa online da daddare ko assignment za ta yi tana ɗauko wa ne tun kafin dare, ballanatana wannan lokacin da yake ƙarfe biyu vai wuce awa ɗaya ta tashi ta fara haddarta ba. Ɗayan wayar da yake tura mata tsaƙo ya ɗauko can ƙarƙashin gadonsa tare da kunnawa ya kunna data. Sallama ya yi mata wanda ya matuƙar razanata, a lokacin da ta ga tsaƙon ganin an ɓoye lambar ya sa ta gane ko wane. "Matar mahaukacin masoyi! Ba ki yi bacci ba, mai kike yi a wannan lokacin? Wataƙila kuma soyayyata ce ta fara kama ki, kamar yadda ta hana ni bacci sai tunaninki nake yi." Ya turo dogon tsaƙo kamar haka. Tsoro ne ya fara kamata domin tana tunanin anya ba aljani bane? Dama ance suna soyyaya da mutane ko ita ma hakan zai faru da ita? Saurin kawar da tunanin nan ta yi, domin a yadda take addu'a ta san in sha Allahu babu Aljanin da zai iya wasa da rayuwarta. "Waye kai kuma mai ya sa kake ɓata lokacina?" Ta yi masa tambayar cikin haushi. "Da sannu za ki sanni ki kwantar da hankalinki. Domin watarana zamu yi aure na kwantar dake a ƙirjina ina miki fifita. Wannan pinky libs ɗin ki zai zama sweet ɗina." Kunyar abin da ya faɗa ya sa ta rintse idanunta tare da kawar da wayar tana mamakin lailai bayan zama mahaukaci tantiri ne shi. "Aiko ka yi kuskure domin zuciyarka yaudarar ka take. Ina da wanda zan aura don haka maza ka zo ka karɓi tsiyarka don ka san ko ni ina da kuɗin da zan siya duk abin da kake tunanin za ka iya siyata da shi." "Ina! Ke ɗin tawa ce ni kaɗai duk wanda ya yi gigin shiga gonata. Ina miki albishirin zan kashe shi na kuma kashe kaina." Miƙewa ta yi da sauri sai ta kashe datar ta tura wayar can tsaƙon filo domin wani irin tsoro ne ya kamata. Ta fara karanta addu'a tana son ta yi bacci don ta fara jin tsoron shi, amma idanunta sun bushe tamkar tekun da ya ƙafe da bazara. Huwais kuwa ganin ta sauka sai ya tabbatar da maganar da ya gaya mata ne ya ruɗata wanda ya san yanzu tana nan cikin tashin hanakali saninta muguwar matsoraciya ce. Dariya ya yi sosai har yana buga filo, ya sannan ya rungume wayar yana kallon hotonta yana murmushi. Mamakin jawo wayarta da ta yi ta kuma kunna datar ta yi. Ganin bai yi mata magana ba sai ta tsinci kanta da tura masa stiker na gargaɗi. Yana ganin lokacin da ta hau online ɗin shareta ya yi, ya ƙyaleta domin ta sauka ta yi karatu ganin uku daidai, amma da ta tura masa da hakan sai ya turo mata da ma soyayya. "Ki kular mini da kanki kuma ki tashi kiyi sallah ki yi istikhara kan lamarin." Ya kashe wayar. Ba tare da tunanin dare bane ta lalubi numbar Huwais ta kira domin ta tabbata zuwa wannan lokacin ya tashi yin sallah. Yana ganin kiran ya saki dariya tare da ɗaukar wayar ya yi shiru na ɗan lokaci. Jin shirun ya sa ta fara magana. "Ya Huwais ya yi mini magana ta whatsapp, amma ya ɓoye numbarsa still. Mutumin nan ya raina mini wayo sosai. Ya yi magana da ni sanda ya ga dama ya turo mini da presents ɗinsa alokacin da yake so. "To shine za ki tashe mi ina tsaka da baccina kan wani mahaukaci can masoyinki! Kar fa ki manta mahaukaci ne shi." Ya ce mata cikin fusji da kuma muryar da ya yi kamar daga baccin yake. Jin abin da yace ya ɗan sa ta tsorota domin bai cika bayyana fushinsa ba, musamman a kanta. "Am sorry. Na kasa haƙuri safiya ta yi." Ta ce kamar yana ganinta sai kuma ta tsinci kanta da jin haushin cewa mahaukacin da ya yi, wato itama mahaukaciya ce tun da ta biye masa. Tsaki ya ce, "Me kike yi a wannan lokacin ma za ki tashi kiyi sallah ki yi hadda, kina jina da safe za mu yi maganar, kuma ina son ki cire wannan maganar a ranki." "Ai ban sa a zuciyata ba. Hammad nake so kuma shi zan aura mai zan yi da mahaukaci." Ta ba shi amsa domin tunaninta kar ya ɗauka ko ta fara sonsa. Ya ji babu daɗi tun da shi ya jawa kansa sai ya ɓoye kishinsa ta hanyar cewa,"Ok, shikenan. Wataƙila a gida ba zamu samu damar yin magana sosa ba, ki shirya in sai na kaiki school." "Ummi ba za ta barni na hau motar haya ba, ko na ce mata motata ta lalace za ta ce na ɗauki nata ko na Ya Naufal. The worse part ɗin ma za ta iya saka direba ya kai ni. Zan fita da motata sai na jira ka gaba da gidanmu." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 6 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Ummu, ba za ta barni na hau motar haya ba, ko na ce mata motata ta lalace za ta ce na ɗauki nata ko na Ya Naufal. The worse part ɗin ma za ta iya saka direba ya kai ni. Zan fita da motata sai na jira ka gaba da gidanmu." "Yauwa haka ma yafi kai waye, kin ga sai na dawo a ta haya, kuma zamu fi samun natsuwa domin akwai shawarar da nake son na baki. In a gida ne ba zamu samu damar zantawa sosai ba. Ni kam na rasa mai ya sa Ummu ke son sanya shamaki a tsakaninmu!" Ya yi maganar cikin tsananin fushi da damuwa. "Wataƙila tana da haujjar hakan, kuma ita uwace dole ta kula da amanar da Allah ya bata." Ta gaya masa hakan. "Wataƙila ta gano soyayyar da nake miki tana tsoron abin da zai je ya dawo ne." Ya faɗa a ransa wanda har ya fara tunanin ko a fili ya faɗi hankalinsa ya tashi, amma sai ya ji ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Tom Allah ya kaimu bari na tashi na yi karatu ga shi har past three." Ta miƙe da nufin shiga bayi ta ɗaura alawala. "Ok, bye." Ya ce tare da kashe wayar. Bayan ta yi karatun ta yi sallar asuba ta zauna ta ci gaba da karatu. Tana ƙoƙarin miƙewa sai Ummu ta tura ƙofar ta shigo hannu ta riƙe da carbi. "Ina kwana Ummu." Ta ce tana mamakin zuwanta duk da ta sa baya wuce ta yi mata ƙorafin kalacin safe, amma ai ta shi da wuri. "Lafiya kau." Ta amsa a daƙile sai ta ɗora da cewa, "Na zo kiji tsoron Allah ki gaya mini wane ne mahaukacin masoyi? Domin zuciyata ba yarda da ku biyun ba, kamar a kwai abin da kuke ɓoyewa." Zare ido ta yi tana mamakin kalamanta da abin da za su iya ɓoyewa don ba ta fahimci komai ba. "Ummu wallahi babu komai da muke ɓoye wa kuma kamar yadda ma gaya muku initially, bayan kyautar da tsaƙon da ya turo mini na farko babu komai tsakaninmu." Ta ƙarashe maganar za tai kuka. "Idan hawayenki ya zuba saina tsintsinka miki mari! Shashashar banza, da an yi miki magana sai ki ce za ki yi kuka kamar ke kika fi kowa hawaye. Allah Ubangiji ya sa na ji wata maganar bayan wallahi dake da shi sai ranku ya ɓace. Kuma ba ki da miji sai Hammad. Ni uwa ce ina da ikon zaɓa miki wanda za ki zauna da shi. Allah ya sa mahaukacin masoyi duniya zai baki ko ya bayyana na haramta miki aurensa matuƙar ina raye." "To Ummu, ai dama ina son Hammad ɗin ba zan iya rabuwa da shi ba." Ta ce da sauri don ta kwantar mata da hankali ganin yadda ta fusata da lamarin "Gargaɗi nake miki ai." Ummu ta faɗa a ranta ta ji daɗin abin da ta faɗa. Bayan ta kammala ta shirya ta sanar masa da ta gama shiryawa. Ummu dake falo ta fito ta same ta tana karwa .. "Ummu zan wuce school sai na dawo." "Ki dawo lafiya." Ta ce fuska a ɗaure. Tana ƙoƙarin fita Huwais ya yi sallama ya shigo, gaishe shi ta wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba ya shiga cikin falon ita kuma ta wuce. Ummu ta amsa gaisuwarsa, tana kallon yadda ya yi kyau sosai ya ƙara zama wani handsome da shi. Kallonsa take cikin tsananin ƙaunar ɗan nata ganin yadda girma da kamala ya kama shi. "Ummu zan fita ni da abokina doctor Khair, ba zan daɗe ba." "Ok, ba komai sai kun dawo amma ga su Umnaah sun shirya ka wuce dasu school." Da sauri ya kalle ta jin abin da ta ce ganin tana son ɓata masa shiri. "Ba da mota zan fita ba don Allah Abidin ya yi mafani da motata ya kai su fita ce ta gaggawa, in tashi babu mai." Kallonsa ta yi cikin rashin yarda da maganarsa. "Anya kai ɗinne za ka fita ba da mota ba? Ko dai da inda za ka kake ɓoye mini?Domin ma san in dai ba lalura ba ba ka ko iya fita in ba a abin hawa ba." "Ummu a ƙofar gida zan jira shi yanzu haka ya ce miniti biyar zai ƙaraso." "Ai sai ku wuce da su Khair baƙo ne ƙanninsa ne." Ta ce mishi. "Don Allah Ummu ki sa Naufal ko Abidin ya kai su bari na je kinga har ya ƙaraso yana kirana." Ya ce tare da saurin ficewa ba ya ji abin da za ta ce ba. Yana fita sai ta ji ba ta yi na'am da maganarsa ba. Hamsiya ta ƙwala wa kira wanda ta fito ta durƙushe a ƙasa tana jiran umurni. "Ma za ki bi Huwais ya fita ki ga wa zai ɗauke shi a mota. In kika bari ya ganki sai na ɓata miki rai." "To." Ta ce tare da fita da sauri. Sai da ya yi nisa sosai ya hangeta a lokacin tana ƙoƙarin kiransa ganin ya buɗe motar ya shigo ya sa ta yi murmushinta ja motar. Hamsiya da take bin bayansa tana raɓewa a jikin gini, sai da ta ga ya hau motar da ta tabbatar na Hilah ce ta koma gida tana mamakin dalilin da ya sanya ta ce ta bishi, kamar wani ƙaramin yaro da dalilin da ya sa bai shiga motar ba, sai da suka fito waje. Taga ita ɗin 'yar'uwarsa ce ta jini. Tunanin kuma irin ɗan takurawa mata da take yi ya ɗan faɗo mata, amma kuma da ta tuna ƙaton enlergment na hotonsu da suke tun yarinta wanda ita Hilah, a lokacin har da na jarintaka, sai ta cire komai kamar yadda dama ba ta wani zargi komai ba. "Motar Hilah ya shiga wacce take ta jiransa tun da ta fita." Ta bata amsa wacce jin hakan sai da ta yi suman wucin gadi. "Amma yarannan sun yi masifar raina mini wayo.Huwais, za ka ja wannan karon ka yi tafiyar da harbabada ba za ka dawo ba, domin inta yi ƙamari zan yi maka aure na turaka Ƙasar waje tare da yi maka baki matuƙar ka dawo Ƙasar. Domin abin da kake shirin yi tamkar so kake ka ruguza farincikin iyalina. Ban taɓa ji ko a mafarki an taɓa soyyaya da ƙanwa ba." Ta faɗa tana wani irin zafafan hawaye yana bin ƙuncinta a ranta ita kaɗai ta san abin za ta yi musu in suka dawo. Hilah ta juyo tana lallonsa da yake kallon waje ganin ya ƙi magana kuma har ta kusa kai get ɗin da za ta shiga makarantar su. "Ya Huwais, ka yi shiru na zaƙu na ji shawarar da ka yanke." Ta ce mishi tare da shan kwana. "Jiya na yi mafarkin mahaukacin masoyi kuma har an nuna mini shi a mafarki." Ta ce tana kallonsa ta gefen ido. "Kim gane shi?" Ya jeho mata tambayar cikin mamaki. "A'a na gane wasa da hankalina kawai yake son ya yi, saboda na yi ta mafarkin shi ina ɓata lokacina. "Yauwa kin jina?". Ɗaga masa kai ta yi ba tare da ta kalle shi ba. "Na ce mu yi wani abu mana shi mahaukacin masoyi ki nuna masa kin amince da soyayyar shi, domin ta haka ne kawai zamu iya gano wane ne." Da sauri ta kalle shi jin abin da ya ce sai ta ci gaba da tuƙi ba ta ce komai ba. "Akan me zan fara soyayya da wanda ban sani ba ko aljani ne, musaki ne duka ba ni da matsaniyar hakan?" "Ni ma ai ba wai son gaskiya nake nufin ki yi masa ba. So nake ya yarda kina sonsa har ya bayyana kansa." Ya ce mata yana kallonta. "A'a, wannan ba mafita bace." Ta ce tare da kallonsa sai ta mai da hankalinta kan tuƙi ta ci gaba da cewa, "Hakan ba mafita bane ina tsoron kar na ƙara amincewa, abu ya kwaɓe ka zo ka barni a ciki irin wancan. Kuma Ummu yau ta yi mini kashedi mai ƙarfi kan ko waye kar na kuskura na amince masa. Don haka mu bar maganar in ya gaji da haukarsa zai daina. Da zarar na kammala karatuna na yi aure ai dole ya haƙura ya zo ya karɓi kayansa ko?" Ta ƙarashe maganar tana tambayarsa. "Over my dead body! Ke tawa ce kuma an halicce ki saboda ni." Ya faɗa a ransa ganin kallon da ta tsaresa ya ba ta amsa da cewa, "Mu gwada hakan wataƙila ma dace. Kuma na yi miki alƙawarin a duk lokacin da lamarin ya kwaɓe zan karɓi hukuncin duka." "Promised?" Ta tabbaye shi. Ɗaga mata kansa ya yi wanda ya sa ta ce, "To shikenan zan gwada. I will do as you said." Ta ce daidai lokacin da ta ƙaraso ta yi paking tare da kashe motar tana kallon shi. "Yauwa ƙanwata. Ma za ki shiga aji bari na koma gida." "A motar haya? Na san fa ba ka son hawa. Kawai ka je da motata sai ka sanya direba ya kawo mini amma a waje za ka ije karka shiga ciki da ita saboda Ummu." "Mai zai kai ni bayan na san ƙaryar da na shara mata." Ya ce yana dariya. Tsayawa ta yi har ya tada motar ya fara tafiya, sai ta ɗaga masa hannu tana kallonsa cikin tsananin ƙauna. Tana son yayan nata don ya damu da lamarinta. Rungume laptop ɗinta ta yi ta shige departmen ɗinsu. A lokacin da ya dawo, Ummu ba ta ce masa komai ba har ya ci abinci ya fita. Don ma ƙin fitowa ta yi ko da ya tambayeta tana bacci. Bayan Hilah ta gama lectured ta tuƙa motarta ta dawo gida. Ta shigo da sallama tana kallon su Umnaah dake zaune suna kallo. Gefen su ta zauna bayan sun yi mata sannu da zuwa. "Ke Azerh ba kin ce Malamin kunya gaya miki in har ba ki kai masa haddarki ba zai zane ki, shi ne kika tsaya kallo?" "Ƙyale shi Anty Hilah, ya cika takura haka jiya na ƙi ƙallah don na yi haddar, amma da na kai masa cewa ya yi ba ta zauna ba. Duka ne ya saba mini, don maimaici ne in ban kalla ba ya wuce." "Lailai haka kika ce? Ai ko kya ta shan duka kamar jaka." Amnaah ta ce. "Allah ya shiryeki, wasa kike yi wa haddar shi ya sa, randa kika yi ninya ai tana zama." Ta ce tare da miƙewa za ta shige ɗakinta daidai lokacin Ummu ta fara saukowa ƙasa wanda ya sa ta fasa. Huwais da ya ji dawowarta ya taho da sauri don y ganta yana shigowa Ummu ta ji daɗin hakan. "Sannu da fitowa Ummu." Ta furta cikin girmamawa. Ummi da take a fusace ba ta yi wata-wata ba ta ɗuke ta da mari. "Haba Ummu mai ta yi miki?" Ya yi tambayar cikin tashin hankali wanda kafin ya gama ta ɗaura masa na shi, sai ya riƙe kumatunsa cikin tsananin ɓacin rai. "Haihuwarku na yi! A tunaninku za ku yi mini wayo ne? Kar nake ganin ku marasa tunani kawai. Na tambayeka inda za ka ka yi mini ƙarya she tare kuka fita? In har ba rashin gaskiya kuke ƙullawa ba uban mene ne na ƙin gaya mini gaskiya. Har da ke munafuka kin kwashi littafai za ki makaranta gidan uban wa kuka je?" Ta yi musu tambayar cikinn tsare ido. Mamaki ya kama su duka musamman shi da yake tunanin wa ya gaya mata. "Ummu kar ki yi zargi babu inda muka je kuma ni ba ƙarya na yi miki ba, da gaske tare muka fita da shi." "Ok Hamsiya ƙarya ta yi maka da ta ganta ta yi parking ka shiga cikin motarta ko?" Zare ido ya yi don ba shi da bakin magana, amma da ya tuna umurnin da ya ɓata, kar faruwar hakan ya sa ta ƙi bin umurninsa domin so yake ta saki da shi ya koya mata sonshi yadda babu wanda ya isa ya raba su. "Eh, dama ita za ta rage mini hanya kuma abin da ya sa ban gaya miki ba, sam ba kya son kusantarmu da ita, wanda ban san dalili ba." "Dalili kake nema na ga ko cewa na yi ba za ka fita ba, dole ka yadda tun da ni na haife ku?" Ta ce cikin zafi. Abu da ya ji hayaniya daga sama ya saukkowa da sauri tare da ƙarasawa gurinta ya kama hannunta. "Kai Huwais, tafi inda za ka. Hilah je ki yi wanka kici abinci." Ya basu umurni wanda ya sa suka juya suka fita. "Ke kuma muje ciki ina son magana dake." "Ni ma maganar nake son mu yi." Ta ce tare da juya babu musu ta haye sama ranta na tuƙiƙi. Da ya shigo ya same ta a tsaye sai safa da marwa take yi. Hannunta ya kama tare da ƙarasawa da ita gaban frij ya ɗauko ruwa mai sanyi ya zuba a cup, ya miƙa mata wanda babu musu ta karɓa ta shanye. "Kina zafafa wa yarannan! Ki tsani tun ka ba sa tunanin wani abu sai su yi zargi bayan babu komai a ransu illa shaƙuwa ta jini." "Kai ne idanunka ya rufe kake ganin haka, amma ni na san mai nake ganin yaronnan a zuciyarsa. Ba ka san wane ne Huwais, ba ne shi ya sa kace haka, amma ni na haife shi na san abin da yake so da wanda baya so." Ta yi shiru ko zai ce wani abu, amma sai ta ga bai ce komai ba wanda ya bata damar ɗorawa da ce, "A lokacin da ya ji Hammad na sonta kamar zai yi hauka, wai ta fi ƙarfin shi kuma shi yake so ya zaɓa mata miji, amma a wannan ka ji ya yi ƙorafi? Ka na dai sane da irin haukan da yake nuna wa duk wanda ya bayyana soyayyarsa gareta, amma wannan ƙorafin me ya yi? Babu hankalinsa kwance har shawara yake bata. Na tabbata da ace babu sa hannunsa da yanzu ya tada hankalinsa. ko da ace ita babu komai kuma ba ta gane ba shi sonta yake." "Don Allah ki daina wannnn haukar tunanin ta yaya za a yi ya so yar uwarsa wacce suka fito ciki ɗaya? Kawai shaƙuwar jini ne, amma babu wani soyayya tunanin ku ne na manta na rashin hankali." Ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallonta. "Humh ba za ka gane ba kamar yadda ba na fatan lokacin da zai ganar da kai hakan, amma mafita ita ce kawai ayi musu aure. Hankalina zai fi kwanciya tun dama shi Wajnaah tana nan tana jiransa har ta gama servise don kamar ta samu aiki ba ta fara zuwa bane.." "Ni ma tunanina hakan, amma shi kawai ita sai ta gama karatun don ba zan yi mata aure tana karatu ba, duka guda nawa take." "Ko shi ɗin ne a fara masa hankalina zai fi kwanciya." Ta ce tana yarfar da hannunta cikin rashin dubara, yayin da zufa ke keto mata. "Kwanta ki huta zan yi mishi magana na ji ra'ayinsa sannan zan yi wa mahaifinta magana." "Kan me za a ji ra'ayinsa uzurin da ya bayar ai ya je kuma ya dawo. Yarinyar ma ta yi haƙuri, duk da tarin masoyanta ta zauna ta jira shi har na tsawon shekaru biyu, ai ta yi masa halacci in ba butulci xai yi mata ba." Ta ce tare da kwantawa kamar yadda ya bata umurni. Kamar yadda ya bata shawara sai ta ƙi yi har aka yi kwana uku duk da tarin tsaƙon da mahaukacin masoyi ke tura mata, amma da ta tuna ko don ta fita da ga zargin Ummu da take ganin kamar ta san mutumin ɓoyewa ta ke yi, sai ta saka a ranta gara ta yadda ta yaudare shi don ya bayyana kansa. Ta fara kula shi da kalamai mai daɗi har ta sanar mishi da tana son shi wanda ya yi dariya da stikers tare da nuna farincikin sa ya ce, "Jikina na bani kamar bakya sona kin amince ne don na bayyana kaina, amma ki sani ina da hankali da wayau, domin a iya sonki kawai na haukace don haka zan gwada soyayyarki na ga mizaninta." Tun daga ranar bai ƙara yi mata magana wanda har aka kwashe sawon sati biyu. Tun ba ta damuwa har ta fara shiga, sai ya zamana kullum cikin tunanin yaushe zai kira to ko ya daina sonta ne, in kuma haka ne kan wane dalili zai sanya ta fara tunaninsa sannan ya fita daga rayuwarta. Ire-ire waɗanɗan tarin tambayoyin suke damunta kullum wanda ta rasa amsarsu. Zaune take ta rafka uban tagumi hannu biyu-biyu. Idanunta cike fal da hawaye. Kamar dai kullum tunanin mahaukacin masoyi take yi. Bayan haukarsa ta lura mutum ne mai izza da girman kai. Domin a tarihin rayuwarta ba ta taɓa yi wa wani magana ba ya gani, amma babu reply. Sai ga shi yau ta yi duk kimarta da ji take ita ma wata ce. Ya ga messeges ɗinta amma bai duba ba. "Anya ma yana sona?" Ta yi wa kanta tambayar tare da miƙewa ta fara taku a ɗakin. Tabbas a ranar musabaƙarsu ta yi tunanin ya shigo rayuwarta ne don kar ya barta ta yi nasara, amma bayan ta dawo ya kawo mata kyauta sai wannan tunanin na ta ya kau. "Ƙanwata!"Ta ji muryar Ya Huwais da ya ƙaraso har cikin ɗakinta tare da rufe mata fuska. Ɗan murmushi ta yi wanda iya kansa saman leɓenta. Da hannunta tasa ta kamo hannunsa ta jawo shi gabanta. "Ya Huwais ka yi kyau matuƙa! Ina zuwa haka?" Ta ce masa tare da tambayarsa. Ba tare da ya amsa mata tambayar ba ya zauna a gabanta tare da kama hannunta ya rungume a kirjinsa yana jin kamar ita ya rungume, wanda ya sanya ta maza ta janye hannun. "Ina tsoron Ummu domin mundin muka ƙara shiga hannunta ba za ta yi mana da sausauci, don a wancan ranar Abu ya ce ce mu. Kuma ina zargin ta saka Hamsiya ta rinƙa spying ɗinmu" Kallonta ya yi cikin tausayawa. Ummu ta fita dubiya ita da Abidin dalilin da ya sa nazo kenan." Jin abin da ya ce ya sa ta saki ranta ta na yaƙe masa baki. "Meke damunki? Na lura kwana biyu ba kya magana, duk da cewar ba ki da yawan magana, amma shuru-shurun ya yi yawa." "Babu komai." Ta ba shi amsa tare da raurau da idanunta sai hawaye. "Wai ke baki da hanyar da za ki sanar ma mutum kina cilin damuwa sai kuka?" Ya yi mata tambayar cikin takaici ganin hawayen sun ci gaba da zuba. TUNATARWA Shin kina daga cikin matan da karatun Novels yake ɗauke musu hankali suke barin sallah ta wuce su? Ko kina daga cikin masu daina karanta Kur'ani ko azkar duk saboda karatun Novels? Don Allah yar'uwata musulma ki daina barin sallolinki na wuce ki saboda karatun litattafai Hausa, saboda ko mu MARUBUTA da muke yin typing da zarar lokacin sallah ya yi muke tashi mu yi sallah. A kiyaye da ibadu musamman sallah saboda ita ce farko da za a fara dubawa a cikin ayyukan mu. Da fatan za ki ji kuma ki hankalta. Fatanmu mu gudu kuma mu tsira tare. Allah ya bamu ikon aikatawa Amin. Taku Jamila lawal Zango. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 7 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Wai ke baki da hanyar da za ki sanar ma mutum kina cikin damuwa sai kuka?" Ya yi mata tambayar cikin takaici ganin hawayen sun ci gabaa da zuba. Ƙoƙarin sharewa ta yi tare da kallonsa da yake tsaye shi ma ita yake kallo. "Kin san fa ba kya ƙarya wannan dalilin ya sa da kin yi nake gano ki, ko a yarinyatarki." Ya ce mata wanda ya sa buɗe baki za ta gaya masa haskiyar damuwarta. "Mahaukacin masoyi ya daina kir..." Maganar ta maƙale mata sakamakon wani birkitaccen kallo da ya yi mata. "To kuma kan me za ki damu kanki don ya daina saboda dama neman hanyar rabuwa muke yi da shi, cikin sauƙi kuma ya kori kansa? Ni banga dalilin damuwar hakan ba." Ya faɗa ransa a ɓace. "Ni ma haka nake gani, amma ban san dalilin da ya sa zuciyata ta damu da hakan ba, domin sati biyun sa bamu waya sai na ke jin na kasa sukuni. Duniyar ta yi mini zafi." Ta ba shi amsa cikin wauta wanda hakan ya sa ya yi sororo yana kallonta. "To kan me za ki yi tunaninsa na ga kina da wanda kike so? Ke da bakinki kin gaya mini ba ki da ra'ayi akansa?" "Eh, haka nace. Ni ma haushin zuciyata na ke ji a bisa abin da ta bijiro mini da shi." "To wannan ba damuwa bane, kuma da yau kar na ƙara ganin kin saka kanki damuwa, domin kamar kin tsose ƙwallon mangwaro ne kin huta da ƙuda." "Har yanzu ka kasa fahimta ta Yaya, na gaya maka zuciyata ta aminta da shi." Kallonta ya yi kamar na baki da hankali tare da zare idonsa. "What! Mai kika ce? Kin ko san girman abin da kika saka kanki a ciki? Ni fa cewa na yi ki nuna masa soyayyar ƙarya, don mu gane wanda yake wasa da hankalinki amma ban ce ki aminta da shi ba, domin in har bai bayyana kansa ba bani da hanyar nemo miki shi." Ya faɗa yana kallonta da mamaki tare da kishi sosai a ransa ganin haka take da sauƙi da yawa, don ya ɗauka zai sha wuya sosai. To in da kuma ba shi bane shi ke nan ya rasa ta kenan. "Ba laifina bane laifin zuciyata ce. Kuma in har za ka iya ganin laifina tabbas za ka iya ganin laifin jaririn da ya faɗo duniya a mace." "Humh." Ya ce don ya rasa bakin magana sai kallonta yake yi. "Yanzu to mene ne abin yi?" Ya tambayeta cikin rashin dubura. "Ni ma ban sani ba kuma na ga kai ka ga kawo sharawar." Ta ce tana watsa hannunta. "Mu bar maganar yanzu ma za ta shi ki haɗa mini abincina ki bawa wannan munafukar ta kai mini ɗaki." Duk halin da take ciki sai da ta murmusa."Ba ita ta kashe zomonn ba, rataya aka ba ta. Tun tana yarinya Ummu ta ɗauko ta. Cinta da shanta duka kanta yake, idan ba ta yi mata biyayya ba ta butulce." "Duk da haka zan yi maganinta."Ya ce yana danna wayarsa. Da ta fita sai ya bita da kallon mamaki yana jin sam bai kyauta mata ba. Ko da ta dawo zama ya yi, ya rinƙa kwantar mata da hankali da ƙarfafa mata gwuiwar mahaukacin masoyi zai dawo. "Damuwata ya hana ni numbar da xan kira na ji ko da wani abu ne ke damunsa, sannan na yi masa magana ba zai kula ni ba kuma alamun ya gani." Da ƙyar ya samu ya rararsheta har ta daina kukan. Da fari ta jure amma daga baya sai ta ji ta kasa ta koma ruwa. Abin duniya ya haɗu ya yi mata yawa. Ga exam da zata fara saura kwana biyu. Lokaci guda ta rame ta fice hayyacinta ko abincin kirki ba ta ci. Ta zama tamkar amarya, don ko fitowar da take yi su yi hira da daddare ta daina. Ganin halin da ta tsira sai suka fara ƙorafi musamman Umnaah wanda hakan ba ƙaramin takurara ya yi ba, domon suna matuƙar son junansu. Amnaah ƙaracin shekaru bai saka ta gane ba, sai dai ƙorafi da take mata ta daina mata wasa. Dama ita Azerh cele ce ba ta damu da rayuwar kowa ba daga kallo dai chatting. Ganin hakan su Abidin suka tuntuɓi Yayan na su tare da tsare shi da tambayoyi. Take ya ji babu daɗi ganin a dalilin biyewa muradin zuciyarsa ya ɓata farincikin kowa. "Ni fa ina zargin patiality da Ummu ke nuna wane ya fara damunta. Which isn't good at all, domin ina agains ita dukanninmu ita ta haife mu." Cewar Naufal. "Don Allah Ya Huwais, ka yi mata magana domin duk mun yi mata, amma fa ce babu komai. Muna damuwa da yanayinta ko abinci kirki ba ta ci, domin breakfast sai ta kai har 11 ba ta yi ba." Sosai ya ji babu daɗi yayin da zuciyarsa take gasgata masa ya tabbata azzalumi mai son zuciyarsa. "Ku yi haƙuri in sha Allahu, za ta daina I will talk to her. I think distressed na karatun exam ne." "You have to, kuma bana tunanin haka domin exam baya bata tsoro saboda kafin lokacin ma ta gama karatun shi, ina ga dai kamar yadda Ya Naufal ya faɗa haka ne." Cewar Abidin Binsu da kallo ya yi har suka fice daga ɗakin. Daga ɗakin na sa kai tsaye gurinta suka nufa, tana kwace da waya a hannuta tana kallon tsaƙon da ya yi mata kafin ya daina mata magana. Kuka take sosai tana jin matuƙar kewarsa da ƙaunarsa na mamaye zuciyarta. "Anty Hilah kuka? Ummu ne ta dake ki?" Amnaah ta furta wanda ya sa suka yi saurin hawa gadon suna tallafo ta. Share hawayenta ta yi tana girgiza musu kai sai kuma ta tsinci kanta da ƙara sakin kukan wanda dukansu suka rungumeta suna taya ta. Bayan fitarsu ya miƙe tsawonsa a kan gadon yana dana-sanin biyewa zuciyarsa, na ba shi shawarar ya fara mata magana, domin ga shi yanzu ya afka kogin nadama. Miƙewa ya yi ya ɗauko wayar duk da gargaɗin da zuciyarsa take masa amma ba shi da zaɓin da ya wuce ya yi mata maganar. Tun da suka shigo suka gama kukan, sai ba su fita ba suna ta hira da ƙoƙarin ɗauke mata damuwa. Kiran sallar magariba ce ta fitar da su wanda Huwais ya ja su a Masallacin gidan su. Ko da suka dawo ɗakinta suka koma, ba su bar ta ba har sai da Ummu ta kora kowa ya je ya kwanta. Bayan sun fita ta yi shirin kwanciya, ta janyo wayarta tare da jero addu'in da ta saba zubawa kan ya kirata. Buɗe datar da fara shigowar tsaƙon sai na sa ya shi go kamar haka: "Barka da Juma'a kyakyawa mai farar aniya. Ina mai baki haƙuri bisa ƙin kiran da na yi, wanda na yi ne don ki fahimci soyayyar gaskiya kike mini ko ta ƙarya." Babu jan aji kamar ba ita mai daraja da kima ba. Ta tura masa stiskers na kuka sau ba adadi. Sai kuma ta ƙara da rubuta "Eh na faɗa soyayarka saboda iya kalamanka da adinin ka , don Allah kar ka ƙara guje mini." Tun daga wannan lokacin suka manne da juna a waya. Hilah da ba ma'abociyar waya ba, amma a yanzu datarta a kunne take barin shi, saboda dakon jiran tsaƙon mahaukacin masoyi. Wani lokacin sai dai ta danna waya tana murmushi. Gabakiɗaya ya sanya ta canza ɗabi'unta. Don Allah ya yi ta da kwanya da ta samu matsala a karatunta da haddarta. Tsananin mamaki wani lokacin take yi, tare da ganin wautarta na faɗawa son mutumin da ba ta taɓa ko jin muryarsa ba. Ballantana haɗuwa na zahiri, amma tana jin a ranta ta kamu da ƙaunarsa damu-dumu. A da duk maganar da suka yi sai ta gaya wa masa, amma da ta ga yana mata faɗa ta daina biye masa haka, sai ta daina sanar masa da komi, wanda hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai. Ganin ƙaramar magana na nema zama babba sai ya yi tunanin dainawa, saboda ranar yasha mamakin kukan da ta sanya masa, tare da yi masa magiyar ya tura mata hotonsa ko ya kirata ta ji muryarsa. Da sauri ya kashe gabakiɗaya tare da jifa da wayar yana gumi. Safa da marwa ya shiga yi a cikin ɗakinsa. Lokaci guda ya birkice saboda ya yarda cewar ta kamu da sonshi. "In har ta buƙaci mu haɗu ya zan yi?" Ya yi ma kansa tambayar cikin tsananin tashin hankali tare da kaiwa bango naushi har sai da ya ji zafi a hannunsa. Saboda tsananin zafin da yake ji rage kayan jikinshi ya yi. Ya rage da ga shi sai singileti da gajeren wando. A ransa ya yi ninyar daina kiranta gabakiɗaya a yau, amma kuma ya san da kamar wuya,gurguwa da auren nesa. Don yadda soyayyarta ta yi masa kamun kazar kuku, ba ya tunanin akwai a bin da zai iya dakatar da shi soyayyarta. "Ta ya ya zan bayyana kaina a gareta, shin in har ta san nine mai zai faru? Na san babu aure a tsakaninmu, amma to ya zan yi da soyayyarta da yake ƙara ninkuwa a cikin zuciyata? Kuma wane mataki iyayena za su ɗauka?" Irin tarin tambayoyin da suka cunkushe ƙwaƙwalwarsa kenan, wanda ke aiki bisa rashin ƙa'ida. Sai dai, kuma a ra sanya ya ɗauki ninyar duk wuya duk rintsi ko ana ha maza ha mata! Ba zai taɓa barin ta kuɓuce masa ba. Ko da Ummu za ta yi gunduwa-gunduwa da naman jikinsa ne. Kuma duk wani ɗa namiji da zai yi gigin kula ta shi e ajalinsa. Ga mamakinsa sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka. Yayin da zuciyarsa ke harbawa tamkar za ta fito waje. Ya san cewa kukan nan zai ta yi har ƙarshen rayuwarsa matuƙar bai mallaketa. Hilah kuwa ganin ya sauka ta shiga cikin matsananin tashin hankali har sai da ta ji zafafen hawaye sun gangaro mata. Da sauri ta fara tura masa da tsaƙo, amma ganin ya sauka gabakiɗaya ya sanya ta fasa tare da riƙe wayar tana ji kamar ta kwaɗa wayar da ƙasa. Jikinta a sanyaye tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki, ta fara gwada kiran numbar duk da ta san cewa ba ɗauka zai yi ba. Ganin wayar ta ƙi shiga, ya sanya ta kashe wayar tare da jifa da ita kan kujera. Hannu ta sanya ta tallabe kanta da take jin yana sara mata tamkar zai rabu gida biyu. "Ina jin son mahaukacin masoyi shi zai xamo ajalina." Ta furta cikin tsananin damuwa tare da kwaranyowar zafafen hawaye daga kwarmin idanunta. Zubbur ta miƙe tare da leƙawa falo ta duba ko Ummu na nan. Ganin babu kowa sai tangamemen tibin bangon da ke barazanar mamaye bangon falon, ya sanya ta ruga da sauri ta nufi sashinsa. Da sauri ta fara ƙwanƙwasawa a hankali tamkar wata mara gaskiya. Knoking ɗaya ya gane wacce take buga ƙofar. Hannu ya sanya tare da share hawayen da suke zubo masa ya miƙe. Har zai buɗe ƙofar sai ya kasa ganin kansa a madubi da ya yi. Idanunsa sun nuna alamun ya yi kuka. "Yaya ka buɗe ni ce." Ta yi maganar tamkar wata mai raɗa. "Ki je zan shigo."Iya abin da ya furta kenan tare da komawa cikin ɗakinsa. Mamakin kalar muryar da ya yi magana ya kamata, har ta fara tunanin ko ya fara shaye-shaye ne. Juyawa ta yi cikin takaici ta koma ɗakinta ta kwanta. Filo ta ɗauko tare da rungume shi a ƙirjinta tana ganin wauta da wawancin da ta yi har ta fara son shi. Washegari da safe bayan ta haɗa break ta karya ta wuce school. Suna zaune sun gama lectured suna jiran lokaci ya yi, don za su yi sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya. Ta kalleta wacce ta ke riƙe da drink na exotic tana sha. "Lafiya Hilah?" Ta yi mata tambayar tare da dafata ganin yadda ta shiga kogin tunani. Firgigit ta yi kamar wata mai bacci ta yi tana kallonta. Sai kuma hawaye shar! Suka fara zuba a ƙuncinta. "Ya zan yi? Son mahaukacin masoyi yana neman ya yi ajalina." Zaro idanunta ta yi cikin mamaki jin abin da ta faɗa. Miƙewa ta yi cikin damuwa tare da kallonta sai kuma ta zauna ta kama hannunta. "Kamar na san mai zai je ya dawo Hilah! Wannan dalilin ya sanya na ƙi aminta da shawarar ya da baki." "Ki fahimce ni sam bai yi da wata manufa ba, domin ya yi ne don mu gano wane n..." "To yanzu wa gari ya waya? Kuma mai hakan ya jawo? Kin faɗa son mutumin da ba ki sam wane ne ba. Musaki ne ko mummuna duk ba ki sani ba." "Ko ya ya yake ina son shi. Ji nake kamar zuciyata za ta kasa daurewa, akan shi zan yi fito na fito da iyayena su nemo mini mahaukacin masoyi." "Innalillahi! Hilah, kin san abin da kike faɗi kuwa? Bijirewa iyayenki za ki yi kan wani banza wanda ba ki san waye shi..." "Kar ki ƙara zagin mini masoyi domin zan iya ɗaukar mummunar mataki a kanki duk da alaƙar dake tsakaninmu." Tsananin mamaki ya kamata matuƙa gamin ta ɗaga hannu xa ta mareta. Saukar da hannun ta yi daidai lokacin da ta riƙe kumatunta tana faɗin,"Marina za ki yi?" "Zan iya miki abin da ya fi haka. Wataƙila ba ki san yadda nake son shi bane. Gab nake da na yi fito na fito da kowa." "Hmmmm!' Ta furta cikin tsananin mamaki tare da jan ajiyar zuciya mai ƙarfi. "In har za ki iya ɓatawa da kowa sai na ce kin ɗauko wa kanki dala babu gammo. Sanin kanki wace ce Ummu da kuma irin zafin da take da shi. Tana gani ba za ta yarda ki ƙi auren Hamad ba, saboda wani da ba ta san shi, kuma bayan hakan ba ki yi wa Hamad adalci ba, domin masoyi ne shi na haƙiƙa." "Allah ya sanya duniya da sama zan ɗauka. Sannan duk abin da zai faru a shirye nake." Lamarin sai ya yi matuƙar ba ta mamaki da ɗaure mata kai. Ta san wace ce Hilah, domin tana da haƙuri da matuƙar biyayya ga iyayenta. Za ta iya cewa wannan shi ne karo na farko da saɓani ya shiga tsakaninsu. Da sauri ta sha gabanta ganin ta miƙe zata wuce."Haba sahibata! Kar mu yi haka dake. Na fahimci yadda kike son shi." Jin abin da ta ce ya sanya ta jata suka koma suka zauna suna fuskantar juna. "Yauwa dama na san za ki fahimce ni. Soyayyaarsa ce ta sanya na yi miki haka, don ina jin duk wanda ya nemi ya raba ni da shi zan iya jan layi a tsakaninmu." "Na yarda tun da ga zahiri kin nuna."Ta furta cikin mamaki tare da jinjina soyayya. "Yanzu mene ne abin yi? Na kasa tunain komai. Kawai ji na ke yi sonsa zai kashe ni." "Mu yi addu'a, amma ki duba lamarin don Allah. Musammam yadda Hamad zai ji. Kin ga Abu ya hana shi kula ki sai dai ya kira bai fi sau ɗaya a sati a. Cewar sai kin gama karatu, kuma haka ya ji ya amince. Tsawon shekaru nawa yana jiran.." "Don Allah! Mu bar maganar nan, matuƙar ba shawarar yadda zai sanya ya bayyana kansa gareni ba." "Addu'a ita ce kawai zan ba ki shawarar ki ci gaba da yi." Da ta dawo makaranta kai tsaye sashinsa ta nufa domin ta san Ummu ba ta nan. Tun safe ta tafi ta'aziyar rasuwar da aka yi a family su. Yana zaune da remote a hannunsa yana kallo. Mamakin ƙofarsa da ta gani a buɗe ta yi. Da ta shiga falon tsayawa ta yi tare da ƙura masa ido cikin mamaki. Ƙurawa junansu idanu suka yi, yayin da take kallonsa cikin tsananin soyayya irin ta 'yan'uwanta, shi kuma kallon so yake mata. Wani irin abu yake fisgarshi daga cikin idanunta yana aika masa da maganaɗisu a cikin ƙwanyarsa. A hankali ta tako ta ƙaraso zuwa kan kujerar da yake har suna gogon juna "Ya faɗa min zan ce za ka je na ganka ka sha ado haka?" Dariya ya yi jin abin da tace tare da sanya hannu sa ya karɓi wayarta da take ƙoƙarin ɗaukarsa hoto. "Na yi miki kyau ne?" "Sosai kuwa! Ka ganka ne? Tamkar wata a cikin taurari." Murmushi ya yi sosai har kumatunsa suka lotsa wanda ya ƙara masa kyau. "Zan ce zani ba ki ba na buɗe ƙofata ba. Najib ya sanar dani yana hanya zai raka ni zance." Sosai ta bayyana farincikinta wanda ya ba shi haushi ganin ba ta kishinsa. "Wow! Wace mai sa'ar ce Yaya? Ko da yake bai kamata na yi maka wannan tambayar ba, tun da na san akwai wacce ta tsaya ta kashe kuma ta tsare tsawon shekaru." Kafin ta kai aya ta ga yanayinsa ya canza wanda ya sanya gabanta ya faɗi. "To ba zan ce za ni ba. Najib xan raka mahaifin Samahatu ya ce ya zo." Ya yi mata maganar cikin ɗaure fuska. Ganin yadda ransa ya ɓace ya sanya ta ji babu daɗi. "Am sorry ina ɓata maka rai! Ka yi haƙuri ni fa adalci na ke son ka yi wa Anty Wajnah."Sai kuma ta yi shiru ganin ita kanta soyayya ya sanya za ta yi butulci. Da sauri ta kama hannu sa da ya yi banza da ita yana canza tasha domin ta gama ba shi haushi. "Na fahimci yadda kake ji Yaya, domin ni kaina ina cikin halin da kake ciki, wanda in zan auna da yadda nake ji zan iya maka adalci." "Yauwa 'yar ƙanwata na manta ta faɗa son mahaukacin masoyinta." Ya ce mata cikin murmushi tare da jan hancinta. "A soyayya ta ne ya hauka ce, amma shi mutum ne mai hankali, musamman yadda iya furta kalamai cikin baiwa da da hikima. Sannan duk ilmina sai da na sara masa gurin amafani da ayar Allah da hadisan manzon Allah." "Au dama akwai namijin da za ki iya yabo kamar haka? Bayan kin sha gaya mini babu namijin da kika taɓa gani irin.." "Come on, Yayana. Kai fa na daban ne, kuma ɗan'uwana na jini, shi kuma soyayyace a tsakaninmu. Har yanzu kana nan a matsayinka na musamman ne kai. Special and extraordinary." "Hmmmmh!" Ya ce mata kawai amma ya ji babu daɗi yabonsa da ta yi." "Da gaske na ke yi, kuma magana na ke son mu yi." Ta furta mishi tana kallonsa tare da kama hannunsa duka ta riƙe. "Fita zan yi ki bari sai na dawo, don na san kan mahaukacin masoyinki za ki yi maganar." Ya ce domin har ga Allah kishi yake yi sosai, ganin ba ta san shi bane, amma ta faɗa son wani can. Ta buɗe baki za ta yi magana sallamar Najib ta katse ta. "In ka ga wata dole ka ga zarah. Ni dai har yau ban taɓa ganin ƴan'uwa masu tsananin ƙaunar junansu ba." Ya furta tare da ƙarasowa yana tafa hannunsa yana dariya. Dariya suka yi tare da miƙewa."Barka da zuwa Ya Najib." Ta furta yayin da ta nufi frij ɗin sa ta ɗauko ruwa mai sanyi da drink ta ine, sannan ta nufi kicin don ta ɗauko cup. Bayan ya amsa sai ya bita da ido kamar yadda ya ga ya raka ta da ido har ta ɓule. Naunauyar ajiyar zuciya ya saki tare da shafa sumar kansa yana murmushi ya juyo yana kallonsa. Hira suka fara yi har ta ɗauko kofin ta ɗaurayo ta ije masa. "Ni bari na tafi, Yayana, sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya dawo da kai cikin aminci." Da larabci ta furta tare da tsayawa tana kallonsa. "Yauwa, ƴar ƙanwata. Allah ya yi miki albarka." Ya furta cikin jin daɗin addu'ar da ta yi masa. "Amin." Ta amsa tare da ɗaukar jakarta tana yi wa Najib sallama. A hanya Najib yake driving babu wanda ya fara magana sai ya waiwayo ya kalle shi ya maida hankalinsa kan hanya. "Ina mamakin shaƙuwarku da ƙudirinka kan ƙanwarka, wanda na tabbatar da tsoron Allah da kake da shi ne yake rinjayar zuciyarka, amma da tuni ka yi abin da ba'a so." "Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba." TUNATARWA Shin kina daga cikin matan da karatun Novels yake ɗauke musu hankali suke barin sallah ta wuce su? Ko kina daga cikin masu daina karanta Kur'ani ko azkar duk saboda karatun Novels? Don Allah yar'uwata musulma ki daina barin sallolinki na wuce ki saboda karatun litattafai Hausa, saboda ko mu MARUBUTA da muke yin typing da zarar lokacin sallah ya yi muke tashi mu yi sallah. A kiyaye da ibadu musamman sallah saboda ita ce farko da za a fara dubawa a cikin ayyukan mu. Da fatan za ki ji kuma ki hankalta. Fatanmu mu gudu kuma mu tsira tare. Allah ya bamu ikon aikatawa Amin. Taku Jamila lawal Zango. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 8 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba." "To ta ya ya, za ka mallake ta? Kar ka manta ciki ɗaya kuka fito. Na sha gaya maka sheɗan ne kawai ke son wasa da zuciyarka, da yi mata ingixa mai kantun da xai sanya ka aikata abin da duniya za ta la'ance ka." "Shiru ya ƙara yi kawai ba tare da ya ce komai ba, domin tuntuni shi ma yana tunanin haka. "Gujewa haka don Allah ka tausaya Wajnah, ka aureta ka daina jiran gawon shanu, domin ko jiya sai da ta kira ni tana kuka, sam bai kamata ka yi mata haka ba." Shiru ya yi bai furta kalami ba wanda ganin hakan ya sanya ya kunna ƙira'ar Sulaiman Ahmad Suratul Isra'i. Bayan ya dawo ya yi wanka yana cin abinci ta shigo domin so take ta nemi shawarar shi. "Am sorry, na dame ka ko Yaya? Kan dai maganar mahaukacin masoyi ne." "Wannan dalilin ya sanya na ke kishi da shi, domin tun daga lokacin da ya ɓullo cikin rayuwarki, kika daina mini wata hira da magana sai na shi." Ya yi maganar yana tauna abincin a kasale. "Ka yi haƙuri bani da zaɓi ne." Ta ba shi amsa tare da zama a gefensa. "Ina son ya bayyana mini kansa kuma na buƙaci haka ya ƙi." Ta ce tare da ƙura masa ido tana kallon shi. "To ni mai zai ce miki Hilah?." "Saboda me? Karka manta kai ka bani shawarar na yi soyayya da shi." "Soyayyar wasa ko?" "Ya zuciya ba ta da zaɓi, ka san soyayya gaskiya ne. Kamar yadda ka kamu da son wannan budurwar kake ganin za ka iya mutuwa, matuƙar ba ka same ta ba, haka ni ma zan iya rasa raina in har ban auri mahaukacin masoyi ba..." A zabure ya miƙe daga ƙwanciyar da ya yi cikin tsananin mamaki. "Kin san me kike cewa? Anya ƙanwata ce? Wacce na santa da tausasa lafazinta a gare ni?" "Ka yi haƙuri bani da zaɓi ne, domin kan son shi na kurumce kuma na makance zuciyata ba ta ji, ba ta gani. Burina na rayu da shi, saboda yana da addini da iya kalamai." "Wane tabbaci kike da shi? Bayan baku taɓa haɗuwa na zahiri ba, kuma ba ki san ko musaki bane, wanda ƙila hakan ya sanya ya kasa bayyana miki kansa?" "Ni fa ko ya yake zan rayu da shi." Ta ba shi amsa kai tsaye wanda hajan ya sanya ya cika da mamaki da tashin hankali. "Ki dai sake tunani domin ko bayan wannan Ummu ba za ta taɓa yarda ki yaudari Hamad ba?" "Kai da kullum kake kushe sa, shi ne yau za ka faɗi haka. Na yarda da kaina Yaya. Yadda na ke tsananin roƙon Allah da ya ba ni miji na gari, ba zai haɗa ni da mutumin banza ba, domin Allah ma ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki. Shiru ya yi ya kasa cewa komai domin ko zai yi maganar bai san me zai furta ba. Ganin yadda ta tsare shi da idanu sai tsoro ya kama shi, tunaninsa ko ta gane shi ne. Ya tattaro hankalinsa da natsuwarsa ne, sakamakon tuna in har da ta gane shi ne, sam ba za ta yi masa magana cikin natsuwa ba, kasancewar yadda za ta ɗauki abin daban. Tsoro ne da damuwa suka bayyana a fuskarsa har ya firgita sosai. Gudun kar ta gane shi ya ɗaga mata hannu yana ce wa,"Please, ki je zan yi tunani na ba ki shawarar da ya makata, amma don Allah kar ki tambaye ni abin da na yanke har sai na neme ki." Ya furta cikin gundurar magana da ita. "Ok, ba zan tambaye ka ba, sai dai ina roƙonka da ka yi mini adalci, gurin yanke shawarar, domin matuƙar ka ce za ka bani shawarar na rabu da shi, zan fallasawa su Ummu ina son shi, tare da sanar musu da kai ka bani shawarar na fara ƙaunarsa." Mamaki ya sanya shi zaro idanunsa musamman yadda take maganar babu tsoro ko firgici. "Hilah!" Ya furta cikin razana ganin za ta fice, amma bai gama shanye ruwan mamakin da ta ba shi daga farko ba, ya ga ta rufe ƙofar ta fice ba tare da ta juyo ba. Dafe kansa ya yi tare da dunƙule hannunsa ya kai wa bango nushi. Naushin da yake jin dama ita ya kaiwa, saboda tsabar rainin da ya hango a idanunta. Fara tafiya ya yi zai bita sai ya ga kuma babu amfanin hakan ya dawo ya zauna. "Lallai na ibo ruwan dafa kaina!" Ya ce tare da sakon ajiyar zuciya mai ƙarfi. Da sauri ya miƙe ya ɗauki gorar ruwa ya buɗe murfin tare da saka murfin a dusbing ya fara sha. Sai da ya shanye tas ya saka robar a cikin mazubin sharar ya shige ɗakinsa cikin tunani. Hilah kuwa tana fita ɗakin ta saki dariya sosai, ganin yadda ya ruɗe sosai. Godiya ta yi wa zuciyarta na ba ta shawarar ta yi masa wannan barazanar, wanda gashi tana son ta yi tasiri ganin yadda ya ruɗe, saboda ya san ba ƙaramin hauka Ummu za ta yi masa ba. Saboda abin da ta gaya masa da daddare kasa hawa online ya yi, har sai lokacin da ta tura masa da tsaƙon karta kwana na cewar tana jirar sa. Ƙarar shigowar saƙon suƙa ƙara rikita duk wani tunaninsa kuma ya gaza sukuni. Ya kasa komai har sai da ya kunna data suka fara hira. Ba su daina hirar ba sai ƙarfe ɗaya, wanda shi ya umurce ta da ta kashe datar ta yi hadda. Ganin ba ta sanar da kowa ba ya sanya hankalinsa ya kwanta. Tamkar ya yi baƙo ya mutu. Don haka ya shareta suka ci gaba da soyayya. A cikin kwanakin ya ji yana buƙatar ya rinƙa jin muryarta, wanda ya san faruwar hakan kamar da wuya. Dubara ta faɗo masa wanda take ya ɗauki wayarsa ya shiga cikin Ai. Ba tare da ɓata lokaci ba ta canza masa muryarsa kamar yadda ya buƙata. Bayan ya gwada kiran Najib ya tabbatar masa da babu wanda zai gane muryarsa sannan ya bari zuwa dare ya yi surprizing ɗinta. Da daddaren misalin ƙarfe sha ɗaya saura tana tsaye a gaban madubi ta fito daga wanka tana ɗaure da tawul. Kiran wayar da Hamad ya yi ya sanya ta fasa sanya kayan baccin da ta fito da su ta ɗora kan gado. Amsa wayar ta yi kamar yada ta saba. Ba su wani jima ba ya kashe, don babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Shi kansa ya san ba ta son shi, amma sam bai damu ba, domin irin su mutum zai yi burin aurensu ya xauna da su, ko da ba sa ƙaunarka. Ballantana ya san yana cikin jadawalin mazajen da Allah ya yi musu tagomashi da kyawu da iya sace zuciyar mace da kalamai. Wannan ba matsala bane a gurinsa, domin yana sanya rai watarana za ta so shi ta shayar da yaransa. Bayan ta gama wayar ta ije tana tausayin halin da zai shiga. Kayan baccin ta sanya tare da ɗaukar wayarta ta kunna data. Mamakin ganinsa da ta yi yana online domin wani lokaci sai ta jira shi ya hau. Ba ta gama shaanye ruwan mamakin ba kawai ta ga kiransa, wanda saboda tsananin farinciki da mamakin kiran ya sanya ta kasa ɗauka. Miƙewa a zabure ta yi, har tana bugewa da gefen gado, amma ba ta kula ba, ta dawo falo don kar ta tashe su. "Mahaukacin masoyi ya kira ni? Ko dai mafarki na ke, ko kuma mantuwa ya yi?" Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki, tare da ci gaba da kallon wayar har sai da kiran ya tsinke. Ganin ya yanke bai sake kiran b,a takaici da jin haushi da kuma wautan rashin ɗaga kiran ya kamata, wanda ba tare da sani ba ta ji hawaye na sintiri a ƙuncinta. Da sauri ta lalabu layinta da har ta fara bacci.Kiran ya farkar da ita ta miƙe tama mutstsuka idanunta. Ɗaukar wayar ta yi tana mamakin dalilin kiran da addu'ar Allah ya sa lafiya. "Hello." Ta furta cikin muryar bacci tare da sakin hamma. "Sahiba! Mahaukacin masoyi ya kira ni." Jin abin da ta faɗa da kuma muryar da ta yi amfani da ita, ya sanya ta watstsaƙe cikin tsananin mamaki. "Haba! Da yaushe kuma mene ya ce?" Ta yi mata tambayar a jere. "Yanzu, amma abin takaici na kasa ɗauka har ta katse." Ta furta tamkar za ta yi kuka. Wani irin baƙincikin da takaici ya mamaye ta jin abin da ta ce, musamman da ba su yi magana. "To yanzu mene ne amfanin gaya mini, kuma ke da kike jiran wannan ranar, ban ga dalilin da zai sanya ki kasa ɗauka ba." "Tsoro ne da fargaba." "Bai kamata ki ji ko ɗaya daga ciki ba, tun da kin ji kin gani xa ki iya. Ni wallahi na ɗauka ma kin ganshi a zahiri ne. Ƙila ya ga ɓoye-ɓoyensa ya ga babu amfani zai bayyana kansa. Allah ya sanya ba tsoho bane wanda ya takwarƙwashe." Takacin abin da ta ce ya sanya ta saki tsaki za ta kashe wayar, daidai lokacin da kiransa ya ƙara shigowa cikin wayar. "Kashe yana kirana don Allah." Ta furta wanda ya sanya ta daƙile wayar tana mata dariya. Wani irin kyarma hannunta yake yi wanda ta rasa dalili. Garin ta danna inda ake masa kiran ta kashe, saboda takaici kawai sai ta sanya kuka, tare da jifa da wayar. Ba a ɗauki lokaci ba kawai ya sake kira.Cikin rawar hannu ta yi nasarar danna gurin amsawa. "Ni mutum ne mai tsananin kishi! Sam ba zan lamunta wacce Allah ya halicce ta don ni kaɗai tana waya da wasu ƙarti suna ji mini muryarta ba." Ta ji muryar ta yi magana cikin wani jrin zaƙi da daɗin saurara a zuciya, wanda ya sanya ta nemi natsuwarta ta rasa. "Eh a'a ba.... Ka yi haƙuri ba za ka sake kiran wayata ka ji ina waya ba." Ta furta cikin wani salo da muryar da bai taɓa tunanin tana da shi ba, don ko ita ba ta tunanin ta taɓa magana da muryar. "Ya kamata ki kiyaye domin a kanki zan iya kashe duk mazan duniyar nan, matuƙar za su raɓe ki." Nauyauyar ajiyar zuciya ta saki tana son inda ta taɓa jin muryar nan, ko za ta gane wane ne mahaukacin masoyinta, amma iya tunaninta ba ta taɓa jin muryar ba. "Am sorry gimbiyata! Kamata ya yi na yi miki sallama kamar yadda addinimu ya sharanɗa, amma sonki da ya yi mimi dabaibayi ya hana ni sukuni da kishinki ya sanya na manta hakan." "Ok, na fahimta kuma.." "Ki kwanta ki yi bacci zan kira ki gobe." Ɗif ya kashe wayar yana riƙe da ita tare da sakin tsadadden murmushi. Sororo ta yi na ƴan sakanni ganin ya kashe wayar. Halinsa ɗaya da ta tsana kenan, nuna isa da yanke shawara ba tare da ya ji ra'ayinta ba, domin ta so ace sun kwana suna waya. Cikin sanyin jiki ta kwanta a kan gadon ruf fa ciki tana kallon wayar tamkar zai fito a cikin. "Oh, Allah ka jarrabace ni da soyayyar wanda ban san asalinsa ba." Ta furta cikin hawaye. Ta yi iya ƙoƙarinta don ta yi bacci, amma ta kasa domin muryarsa, ke yi mata amsa kuwwa a kunenta. Tunani take yi kamar ta taɓa jin muryar, amma duk iya tunaninta ta gagara tuno inda ta ji ta. Wajnah zaune a ƙaton falonsu da ya sha kayan alatu. Wayarta a hannunta tana dannawa, wanda gabakiɗaya rabin hankalinta na kan wayar, tana duba wasu kaya da ƙawarta ta saro daga Dubai za ta siya. Kayan dogayen riga abayas da gyaluluwa sai kuma takalma. Bayan ta gama zaɓen kayan ta ije wayarta kan stool ɗin da ke gefenta, tana kallon mahaifiyarta da take zaune da aminiyarta Hajiya Fatiha suna hira. "Mom, na kammala abincin kuma is ready. Na kawo miki nan ke da Momy Fatiha ko a dinning?" "No, ki kawo nan sai ko kira Binta ta haɗa mini salat ta kuma kawo mini yajin da na siyo jiya." "Mom, ai na shirya duka har salat ɗin." "Masha Allah! Yarinyar kirki ma za ki kawo mana nan." Mom ta furta tana kallonta cikin so da ƙauna. "Wai ni Hajiya Fati, ya maganar haɗin auren da za a yi da ɗan ƴar'uwarki? Na ji shiru tun lokacin da za a yi Engagement aka ce biki sai ya dawo daga Turai?" "Eh, wallahi haka ne. Ai ta nan ɓangaren duk mun shirya, amma shi yaron ne yake wasa da hankalin iyayensa." "Anya haka ne, ko dai ba sa son haɗin ne?" Ta yi mata tambayar tana kallonta. "Kai bana tunanin Lailah, za ta ƙi auren, saboda duk wani ƙoƙari ita take yi." "To ai abin ne da mamaki domin ya kamata ace an yi tuntuni." "Haka ne wallahi kin san komai lokaci ne." "Eh, amma da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe! Saboda samun irin namiji kamarsa sai an tona." "Haka ne, in sha Allahu za a yi auren." "Allah ya tabbatar da alkhairi." Wajnah bayan ta kammala jera musu abincin ta haye sama. Kan gado ta hau tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Tana matuƙar sonsa amma sam hankalinsa ba ya gareta. Wayarta ta jawo ta danna nambobinsa da tuni ta riga ta haddace. Sai dai har ta gama ringing ba'a ɗauka ba. "Da ma na san ba zai ɗauka ba, Ubangiji ka karkato mini da hankalin bawanka." Ta furta cikin hawaye tare da shiga Whatsapp ta shirya mishi kalaman soyayya ta tura mishi. A lokacin da tsaƙon ya shigo yana zaune a cikin bedroom ɗinsa yana aiki a cikin laptop ɗinsa. Tsaki ya yi ganin saboda rashin zuciyarta bayan ƙin ɗaga kiran sai da ta tura masa da tsako. Ba tare da ya karanta ba ya goge tsaƙon tare da riƙe wayar ya faɗa kogin tunani. Abu ne zaune a gaban mota suna tafiya. Huwais ne ya ke jan motar cikin natsuwa. Abu da ya ke karanta magazine na daily trust ya ije jaridar, tare da juyowa ya kalle shi, da hankalinsa yake kan tuƙi. "Huwais," Ya kira sunan shi tare da gyaran murya. "Na am Abu,"Ya waiwawo yana faɗin hakan. "Maganar yarinyar nan ƴar gidan Alhaji Tukur. Shiru muna ta jiran bayan dawowarka za ka yi maganar bikin ku, amma shiru?" Jin abin da ya faɗa ya ɗaga hankalinsa ainun. Da sauri ya waiwaya ya kalle sa cikin tashin hankali. Ya buɗe baki xai yi magana sai ya rasa abin da xai faɗa, domin a wannan karon bai san uzurin da zai bayar ba. "Umh! Eh..." "Dakata." Abu ya ce masa yayin da lokaci guda fuskarsa ta canza. "Ka san cewa a wannan karon ba zan lamunci duk wani uzuri da za ka bayar ba ko? Domin in har da na ɗauki maganar mahaifiyarka, ba za ka yi tafiyar nan ba sai da matarka?" "Eh, Abu. Don Allah a wannan karon ina son a ƙara bani uzuri, domin sam Wajnah ba na jin ƙaunarta a cikin zuciyata." "Kana da zaɓinka kenan?" Ya yi masa tambayar kai tsaye. "Eh, amma akwai abin da na ke son na tabbatar. Don Allah Abu ka ƙara mini lokaci." Ya faɗa tamkar zai yi kuka. "Ba ka da wani mafita wanda ya wuce ka amince, domin ba za ka mayar dani ƙaramin yaro ba. Haba, Huwais, ka yi wa yarinyar adalci mana. Tsawon shekaru na wa ta ɗauka tana jiranka." Ransa ne ya ɓace ya rasa mai zai furta domin shi kasa ya san ba shi da hanyar da zai ce mafita ce a gare shi. Kawai zuciyarsa ce take ƙarfafa masa da kuma tabbatar masa da Hilah ta shi ce kuma watarana zai aurenta. Ganin ya yi shiru ba tare da ya furta kalami ba ya sanya shi gyaran murya a karo na biyu ya ce, "Mun gama magana da mahaifiyarku in sha Allah gobe zan tura su Kawunka Sulaiman su je su ji magana. Wani irin tsau ya ji a kansa wansa ya sanya shi juyowa cikin sauri yana kallonsa. "Don Allah Abu, kar a yi gaggawan yin lamarin nan, saboda na gaya muku bani da ra'ayin zama da ita." "Mun riga mun gama yanke shawara sai ka jira lokaci ya yi. Ka sani a wannan karo. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 9 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Mun riga mun gama yanke shawara sai ka jira lokaci ya yi. Ka sani a wannan karon sam ba zan lamunta ka watsa mini ƙasa a idanuna, don haka ba za a sanya lokacin bikin da tsawo ba, saboda in har muka biye maka, ban san lokacin da za ka yi aure ba, kuma kullum ƙara girma kake." Ajiyar zuciya kawai ya saki ba tare da ya furta komai ba, sai kaɗa kansa da yake kamar ƙadangaren kutu. "Maganar aikin da za ka fara a companyna ya kamata ka fara shirye-shiyen duk da kai za ka zama c.e.o na wurin. Cikin rashin ƙarfin jiki ya amsa masa wanda ganin yadda ya yi, sai ya ba shi tausayi, amma yi masa auren shi ne kawai mafita a gare shi da su duka, musamman Ummu da kullum take ta da hankalinta. Shiru suka yi babu wanda yake magana har suka shawo kwanan gidan. Huwais hankalinsa a tashe yana ta tsaƙawa da kwancewa. Idanunsa suka kaɗa sosao ji yake kamar ya ɗora hannu a sama ya rinƙa ƙwala ihu. Tunaninsa yadda zai yi rayuwa da wata ƴa mace a matsayin matarsa ba Hilah ba, domin ba ya jin zai iya mallakawa wata gangar jikinsa da zuciyarsa, don an halicce su saboda ita ne, domin matuƙar ta aminta da aurensa aka yi. To tamkar ta siyar da farincikin rayuwarta ne, don gangar jikinsa kawai ta aura, amma zuciya da ruhi suna gurin ƙanwarsa abin begensa, wacce da ita kawai yake jin zai iya rayuwa har ya shayar da ita madarar ƙauna. Abu kuwa bayan ya sanar masa bai ɓata lokaci ba, ya kira Kawu Sule kamar yadda ya gaya masa aka tura don a tsayar da rana. Wannan lamari ya yi wa Wajnah daɗi, domin da fari ta ƙi aminta sai take gani kamar mafarki ne. Lokaci guda kuma murnarta ta koma ciki tuna, wancan lokacin da har an sanya rana ya bar ƙasar, saboda haka sai ta rage murna ta bari sai ranar da ta wayi gari ta ganta a cikin gidansa. Tabbas ranar babu macen da ta kai ta sa'a a duniyar nan. Sai ya rinƙa jin kasa kamar zai rabu gida biyu. Yana isa cikin ɗaki ya faɗa kansa. Wani irin ƙunci yake mamaye zuciyarsa, ganin duk guje-gujen da ya yi wa auren bai hana yi ba. Kwanciya ya yi yana jin ransa babu daɗi don ƙirjinsa har wani fat!Fat! ya ke yi tamkar za ta fito waje. Kawu Sule a ranar ya shirya aka je suka ji magana wanda nan take aka tsaida biki wata ɗaya. Gabakiɗaya kowa murna yake yi in ka ɗauke uban gayyar. Zaune suke a dining ana cin abinci inka ɗauke Huwais da yanzu ya yi sallama ya shigo. Sallamarsa ya sanya Hilah da take bawa Umnah abinci a baki ta ije spoon ɗin tana kallonta da ya shigo fuskarsa tamkar ta shanu. Ummu kuwa murmushin jin daɗi ta ji, tuna cewar yanzu hankalinta zai kwanta domin da ya bar gidan shi kenan ba ta da wata matsala da shaƙuwarsu. In kuma sha'awa ke damunsa har yake ɗora ƙwaɗayinsa kan ƙanwarsa auren zai kawo ƙarshen matsala. Don haka hankalinta kwance take cin abincinta don har wani murmushi fuskarta ke ɗauke da shi. A hankali ya jawo kujerar da ke kusa da Abu ya zauna yana faɗin,"Barka da hutawa Abu, Ummu sannu da hutawa." Ya ce tare da ije wayarsa kan dining. A tare suka amsa sannan ƙanninsa suka haɗa baki gurin gaishe shi. Ba tare da ya amsa ba, ya ɗauki wayarsa jin alamun tsaƙo ya shigo. Tun da ya zauna gabakiɗaya hankalinta ya tashi, musamman da ko kallon inda take bai yi ba. Miƙewa ta yi za ta sanya mishi abinci, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar karɓar serving spoon ɗin ya ce," Thanks." Ya yi maganar ne ba tare da ya yi dubi gareta ba. Komawa ta yi ta zauna tana kallon yadda yake cin magani, bayan ya saka cokali ɗaya na dafadukar shinkafa da ta ji bushashshen kifi. Wani irin tauna yake mata tamkar yana cin magani, tare da juya abincin filet ɗin yana jin kamar guba yake ci, duk da irin daɗin da ta yi. Abu da Ummu duk abin da yake yi suna kallonsa, amma sam ba ta ji wani iri ba, ji take kamar da ma yanzu aka yi auren don ya tattara ya bar mata gidanta. "Kyakykywar albishir! Duk wanda ya canka zan canza masa waya." Ummu ta ce cikin tsananin murna tana dariya. "Ummu, ni zan faɗa." Cewar Azerhl tare ɗaga hannnunta. "No Ummu, ni zan faɗa." ya saukar da hannunta yana faɗin haka. Umnah ce ta miƙe ta isa ga Ummu tana dariya ta ce,"Ni ce Ummu, ni zan cinka." Sai ta kwashe da dariya ganin yadda suka cika falon da ihu. "Ke Hilah, ba za ki cinka ba?" Abu ya ce yana dariya. "Abu, ai na ga duk suna son su cinka ne, shi ya sa na bar musu." Kowa ya faɗa duk wanda ya canka mota zan ba shi kyau, in kuma Abidin, Naufal da Hilah ne canzawa zan yi. Jin abin da ya faɗa ya sanya su ƙara saka ihu kowa yana faɗin shi ne har da Hilah. "To shikenan, bari a fara kan ƙanana sai kowa ya faɗa." "Ok, bari a fara ta kan ƙanana, Umnah ki fara." "Abu, zai koma Ummara." "Ba ki ci ba." Ummi ta ce tana dariya. "Amnah, ina jin ki." "Ya Huwais, zai koma abroad." "Ke ma kin faɗi." Ta furta cikin dariya. "Abu ya canza mana gida." Dariya Abu ya yi. "Kai ma ka faɗi, saura Abidin." Ya faɗa yana kallon Huwais da ya wani ƙara cin magani, saboda ya san me za su faɗa. "Za mu yi relocating zuwa abroad." Ya faɗa da fatan ya ci. "No, kai ma ka faɗi. Saura Hilah." Kallon Huwais ta yi ganin yadda baya ko kallonsu, hakan ya sanya mata zargin ko maganar aurensa ne ya tashi, aanda ta san abin da zai sanya shi a cikin mood ɗin kenan. Ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, tana tsoron kar ta faɗi, amma sai ta daure ta ce,"An sanya ranar bikin Ya Ayaan." "Yes, ta ci." Ummu ta furta tana tafa hannunta wanda jin haka ya sa gabakiɗaya suka miƙe suna ihun murna tare da nufar gurinsa za su rungume shi, har da Hilah da ta manta gargaɗin Ummu saboda tsabar murna da ya cikata. Da sauri ya miƙe tare da daka musu tsawa."Wannan wane irin sakarci ne? Sai ka ce gidan biki. Ku yi mana shiru."Tsit suka yi suna zare idanu. Ummu bakinta ta taɓe ba ta ce komai ba ta ci gaba da cin abincinta. "Ƙyale su Huwais, murna ce su yi, saboda mahimmancin wannan ranar anjima ku shirya zamu fita." "Yeeeee! Suka haɗa baki suna faɗi cikin murna. "Our Ya Huwais, is gonna be married. We can wait to see!" Umnah ta furta tana ihun murna. "We need to celebrate Anty Wajnah will be part of us! Ya Huwais happy for the engagement." Hilah ta furta tare da miƙa mata hannu. Saboda tsabar takaici na rashin kishinsa da ba ta yi, bai san lokacin da ya ɗaga hannu ya wanka mata mari ba. Gabakiɗaya falon suka miƙe cikin razana. "Are you mad! Kanka ɗaya kuwa? Saboda me za ka mare ta?" Abu ya furta cikin tsananin ɓacin rai yana kallonsa da ya haɗa girar sama da ƙasa. Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba sai kuma ya juya ya fice ba tare da ya damu da kiran da Abu ya ke masa ba. "Ƙyale shi aure babu fashi." Ummu ta ce tana hararar inda ya wuce. Abu ya kama hannunta ya zaunar kusa da ita yana rarrashinsa. A hankali ta miƙe tare da share hawayenta ta kama hannun ƙanninta da suke jin kamar su yi kuka ganin marin da ya yi mata. Abu ya bi bayanta da kallo tare da farin zargin abin da Ummu ke faɗa masa gaskiya ne. Yana shiga ɗaki ya shige bayi tare da sakar ma kansa ruwa. Haushn marin da ya yi masa da ihun murnar da suke yi ya dame sa. Wani irin haushi ta ya ƙara mamaye shi ganin yadda take murna, sai kuma ya fara jin haushin kansa, saboda tunawa da ba ta san yana sonta ba, kuma dole ta yi murna saboda a matsayin ɗan'uwa ta ɗauke shi. Ya ɗauki tsawon lokaci yana watsa ma kansa ruwa har sai da yaji sanyin ruwan ya fara damunsa. Tawul ya janyo ya ɗaura iya ƙugunsa sannan ya ɗauki ƙarami yana tsane kansa. Bayan ya gama tsane kansa, ya shirya kansa cikin doguwar farar jallabiya da gajeren wando, ya zauna a falo yana tunanin yadda zamansu zai yuwu da Wajnah a matsayi matarsa. Yarinyar da sam tsarin rayuwarsa ba ta yi mishi ba, domin ko a cikin ƴan'uwansa ba ya shiri da ita, saboda yadda take nuna tsantsar wayewarta. Hannu ya sa ya tallabe goshinsa yana jin yadda tempareco na shi ke hawa. Hilah kuwa bayan ta shiga ɗaki gefen gado ta samu tana zubar hawaye. Mamakin marin da ya yi mata take yi, don kawai ta taya shi murnar samun iyali da zai yi. Maganar da ya gaya mata ya faɗo mata da ya ce mata yana son wata. Zubbur ta miƙe tare da ɗaukar hijabinta. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa. Yana zaune ta tura ƙofar ta shigo. Da idanu ya raka ta har ta ƙaraso gefensa ta zauna. "Yayana!"Haƙiƙa ban kyauta maka ba, kuma na cancanki fiye da mari." Ta yi shiru ko zai ce wani abu sai kuma ta ga ya ƙara cin magani, bai ce mata komai ba, sai juya kansa da ya yi zuwa wani gefen. Tashi ta yi ta koma gefen da ya juya kansa. "Yayana." Ta furta cikin sanyin murtasai kuma ta ɗora da cewa," Don Allah ka yi haƙuri." Ƙaramin tsuka ya ja saboda muryarta ta rikita shi tare da gusar da fushinsa. Wani irin kallo ya yi mata yana faɗin,"Dole ba za ki damu da auren dole da za a yi mini ba, tun da kina tare da mahaukacin masoyinki." Dariya ya ba ta da yadda ya yi maganar da kuma abin da ya faɗa. "Ka yi haƙuri, sam na manta ka gaya mini akwai macen da kake so." Maganar ta ƙara bashi haushi ganin ba ta damu da abin da ke damunsa ba. Sai kawai ya ƙi tankawa yana kallon sama. "Haba Yayana, ka zama mai rangwame gare ni don Allah." Ta ce tare da kama hannunsa. Hannunta ya ja ya ɗora daidai saman ƙirjinsa."Ki ji yadda zuciyata take tafasa da begen abar ƙaunata. Gashi kuma iyayena suna son su tilasta mini auren Wajnah. Sam ba ta a cikin tsarin macen da na ke so." "Ka yi haƙuri ka yi wa iyayenka biyayya sam ba za ka taɓe ba, kuma za ka ga alfanun hakan." Ta ce masa cikin taushin murya. "Yanzu duk yadda kike son mahaukacin masoyinki za ki iya rabuwa da shi?" "Bana jin zan iya haƙura da mahaukacin masoyi. Hakazalika, ba zan bijirewa iyayena ba." "Kenan, wane mataki za ki ɗauka?" Ya yi mata tambayar cikin zaƙuwa domin amsar da ta ba shi ba ta gamshe sa ba. "Zan yi addu'a ne in har mijina ne zai zo gare ni, domin babu abin da ya gagari Ubangiji." Cikin tsananin ƙauna ya ci gaba da kallonta jin abin da ta ce. Yana dafa cikin halayenta da suke ƙara zurfafashi zuwa ƙasan tafkin ƙaunarta "Yanzu nufinki na yi haƙuri na aminta da aurar Wajnah?" "Eh, kuma ina tabbata maka da in sha Allah, za ku yi zaman lafiya har ku ƙaunaci juna. Sannan kuma in wancan da kake so rabon ka ne za ka samu." "Wane tabbaci kike da shi zan so ta?" Zare hannunta ta yi da ya riƙe a saman ƙirjinsa jin yadda yake shafa hannun. "Za ku so juna Ya Huwais, saboda kullum Ya Hamad, cewa yake in muka yi aure zan so shi." Ƙaramin tsaki ya ja jin ta sako shi a cikin maganarsu. Mai da kansa ya yi ya kwanta tare da rufe idanunsa. Kaman yana ganinta lokacin da ta buɗe baki xa ta yi magana ya tari numfashinta yana faɗin,Ki je zan mu yi magana."Jim ta tsaya sai kuma ta juya ta fita. Bayan fitarta ya juyo yana kallon ƙofar da ta wuce. Ko babu komai magana da ita da ya yi ya samu sauƙi a zuciyarsa. Don ta tuna masa da darajar da Allah ya ba shi na ɗa namiji zai iya auren mace fiye da huɗu. Zuciyarsa ta fara lallaɓasa da ya amince da auren. Ta yadda idanun Ummu zai ɗauke daga kansu, wanda hakan zai ba shi damar mallakar abin ƙaunarsa hankali kwance. Miƙewa ya yi cikin ƙwarin gwiya ya fice daga falon zuwa gidan amininsa Najib da yake ta kiransa. Ba ƙaramin bajinta Ummu take a lokacin da watan bikin ya tsaya Ummu da kanta ta shirya tafiya London don ta haɗo kayan lefe. Su Hilah ma ba a bar su a baya ba gurin shirya yadda bikin zai kasance da events ɗin da za a yi, domin tafi kowa farincikin auran ɗan'uwanta. Gani take kamar auren zai kawo masa kwanciyar hankalin da ya rasa, duba ga yadda ya lalace duk ya fita hayyacinsa, sai ka ce amaryar da za a yi mata auren dole. Kullum cikin kwantar masa da hankali take yi, tare da bashi shawarar ya yi ƙoƙarin manta soyayyarsa, tun da shi kansa ya tabbatar da ta yi masa nisa. Suna zaune a falo suna zaban kayan da Ummu ta kawo musu. Kayan ne masu tsananin tsada da kyau! Bayan sun gama zabar wanda za su sanya ranar Kamu, dinner, lunchean da wedding day ɗin. Ummu ta umurce su da su kwashi kayan zuwa ɗaki, kafin tela ya zo ya karɓa. Hila na ƙoƙarin kwasar kayan ya yi sallama ya shigo. Yana sanye cikin doguwar jallabiya ruwan madara. A hankali yake shigowa cikin falon tamkar ba ya son ya shigo. Tun da shigo ya ga kayan jibge a gabansu ya sanya ransa ɓaci matuƙa, domin ya tsani ya ga abin da zai tuna masa da bikin. Yana ƙoƙarin juya wa Ummu ta lura da shi, domin bai yi sallama da ƙarfi ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 10 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Yana ƙoƙarin juya wa, Ummu ta lura da shi, domin bai yi sallama da ƙarfi ba. "A'a, ango ka shigo mana." Ta yi masa maganar cikin raha da tsokana. Haɗe ransa ya yi, tamkar an aiko masa da mala'ikan mutuwa. Kaman ba zai fasa juyawa ba, sai kuma ya tsaya yana ƙarewa falon kallo. Ba tare da ya so ba ya ƙarasa shigowa cikin falon yana yi wa Hilah wani irin kallo, wacce ganinsa ya sa ta tsaya tana kallonsa cikin damuwa. Wani iri ta ji game da kallon domin ba ta taɓa tunanin yana da sexy eyes ba. Ƙasa ta yi da kanta tana ta ya Wajnah murnar samun ingarman namiji kamarsa, domin ita kanta ta tabbatar Yayan na ta ya kai maƙura gurin haɗuwa, saboda samun irinsa a cikin maza sai an tona. Damuwar dake ɗauke a fuskarsa suka tayar da hankalinta har ta ji ta kasa jurewa, amma tun da Ummu a gurin ya sa ta yi ƙasa da kanta, don ta kaucewa mayataccen kallon da ta rasa dalilin yinsa. Gyaran muryar da Ummu ta yi, ya sanya ya dawo cikin hankalinsa tare da sakin ajiyar zuciya yana shafa kansa cikin kunya. Sam ya manta a gaban Ummu yake, domin zuciyarsa da idanunsa ba su hango masa komai sai ita. Ƙasa ya yi da kansa daidai lokacin da Ummu ta kalle ta cikin ɓacin rai ta ce,"Kwashi kayan nan ki kai ɗaki, kuma ki wuce kicin ki ɗora girki." "To," Ta amsa tare da saurin wucewa har ta kusa tuntuɓe tana kallonsa. "Sam na tsani na ga Yayana, a cikin damuwa. Allah ka kawo masa mafita ka sanya masa soyayyar Anty Wajnah, ka zaunar da su lafiya."Ta furta tare da zuba kayan a kan gado ta zauna tana mai da numfashi. Bayan ta shige Ummu ta dawo da kallonta garesa cikiin tashin hankali. Ji take kamar za ta yi hauka, duk a lokacin da ta hango ƙaunarta a cikin idanunsa. Gashi har an kai mizanin da ba ya iya ɓoyewa, domin idanunsa kawai zai tabbatar masa da tsaƙon da ke zuciyarsa. Ta tabbata dalilin da ya sanya Hilah ba ta fahimci abin da ke cikin zuciyarsa ba, domin ko a duniyar mafarki ba za ta taɓa sanya tunanin zai so ta ba, wanda ya sa sam ta gaxa fahimtar halin da ya ke ciki. "Ka daina kula kowa a gidan nan, sannan ba ka son cin abinci, kuma ba ka dariya ka canza ba kamar yadda na san ka ɗana mai ladabi da biyayya ba?" Ta yi masa maganar cikin raunanniyar murya tana jin tamkar ta fashe masa da kuka, domin ta wannan hanyar ne wataƙila zai gane abin da zuciyarsa ke tsaƙa masa ya kaucewa tsari na addinsa da kuma al'adarsa. "Ummu, ke ma kin daina sona. Korata kike yi, ba kya son rayuwa da na ke yi daku. So kike ki yi mini aure na bar miki gidanki." Ya bata amsa cikin murya mai sanyi. Kuka yake son ya yi mata wataƙila ta fahimci girman jarrabawar da yake fuskanta ya wuce mizanin hankalinsa. "Saboda ka kai mumzalin aure ne Huwais. Ka girma kana da buƙatar ka ije iyali, kuma mun ga ba ka da ninyar hakan shi ya sa muka yi maka zabi na gari." "Amma Ummu na gaya miki Wajnah she isn't my type. sam yarinyar nan tsari ta bai yi ba, domin ta cika rawar kai. Ni kuma mace mai aji da hankali da natsuwa nake son na aura kamar dai Hilah." Maganarsa ta duki ƙirjinta daram! Domin har sai da ya ga razana a fuskarta. A razane ta ɗago tana kallonsa, wanda ya sanya ya firgita ainun domin ya ɗauka ya yi suɓutar baki ne ya sanar mata da yana sonta. "Ummu, na ga kin ruɗe mai irin halinta na ce." Ya faɗa da sauri cikim rawar murya. Ga mamakinsa sai ya ga tana hawaye." Dole ne sai ka auri mace mai irin halinta? Mata nawa ne suka fita hali da natsuwa da kyawu? Huwais, ka da kyawun 'yar uwarka ya kai ka duniyar dana sani, domin abin da kake tunani ba zai taɓa faruwa ba. In har ba ka son Wajnah, ba zan yi maka dole ba, amma zan dawo maka da maganar da mahaifinka ya yi maka cewar ka tabbatar da wacce kake so kuma zaɓinka.'" Rintse idanunsa ya yi cikin hawaye."Shin Ummu ta gane yana sonta ne, ko kuma tana masa kallon mugun nufi a zuciyarsa? Zarginsa take da zai iya ɓata rayuwarta. Ko tana tunanin sha'awarta da kyawun surarta suke ruɗansa? Ina son Hilah, daga Allah ne domin a yadda na ke addu'a da sadaka da kuma saukar qur'ani Ubangijina ba xai sanya sheɗan ya yi galaba haka a cikin rayuwata ba." "Ummu, in har auren Wajnah, shi ne farincikin ki na aminta." Ya ce tare da miƙewa zai fice. Har cikin zuciyarsa yake jin zai haƙura ko da a ce son na ta zai zamo ajalinsa, da ace ya zama sanadiyar ɓacin ran mahaifiyarsa gara ya haƙura. In ya yi ajalinsa ya huta da baƙincikin da yake ƙurba a dalilin sonta.Ya miƙe yana layi tamkar zai faɗi. Bin shi da kallo ta yi cikin tsananin tausayawa. Tana matuƙar son ɗan na ta, saboda yaro ne mai matuƙar biyayya. "Huwais," Ta furta cikin sanyin murya. "Na siyo maka kayan da za ka ci biki da su set biyar. Na bawa Telanmu gayu. Ka duba kayan na tura maka a wayarka, in ba su isa ba sai na ƙara. Sannan ya kamata ku shirya kai da ƙannenka ku je ku gaida Hajiya, domin tana mini mitar baka son zuwa gurinta." "In sha Allah, za mu je. Bari na gaya wa Hilah su shirya bayan sallar la'asar sai mu je." "Kar ka damu je ka zan gaya mata, kuma ga kamata ka samu lokaci ka je zance, saboda Mommyn Wajnah ta gaya mini ba ka taɓa zuwa ba, don yarinyar na son ka ne ba ta ƙorafi." Maganar ƙarshe ya baƙanta ransa, domin ya kasa cewa komai sai kansa da ya kaɗa, tare da watsa mata kallon na rashin yadda da har yanzu ta kasa yi da shi. Wataƙila tunaninta zai iya cutar da Hilah ne, ko kuma wani abin take hasashowa a ranta. Sai dai kuma har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin matuƙar ta yi masa aure shi kuma sai ya san yadda zai yi ya ƙirƙiro abin da zai sanya Hilah ta koma rayuwa a gidansa, kafin ya samu hanyar da za ta zamo mallakinsa. Ɗaki ya shige tare da zama bayan ya ƙara ƙarfin A.C ya zauna kan kujera. Remote ya ɗauka ya kunna labarai. Wayarsa ya janyo ya kunna data. So yake ya yi hira da ita, tun da suke magana bai taɓa kiran ta da rana ba, amma yau a yadda ya a ganta cikin abaya baƙa sai ya ji ba zai iya haƙurin har dare su yi waya ba. A lokacin tana kicin tana yanka salat kiran ya shigo. Ba tare da ta kalli wayar ba, sai ta ci gaba da aikinta domin ba ta ƙaunar abin da zai katse mata girkin, musamman da ta yi ranar yin girkin. Ƙara kiran zuciyarta ta raya mata ko mahaukacin masoyi ya kirata.Da sauri ta kalli fuskar a zuciyarta tana addu'ar shi ne. Ga mamakinta sai kawai ta ga numbarsa da sitikar soyayya da ta yi saving da su. Ɗauraye hannunta ta yi tare da danna amsa kira ta kanga wayar a kunnenta. "Ina cikin damuwa masoyiyata rayuwata matuƙar babu ke! Haƙiƙa ba zam iya numfashi ba." Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta, domin in har ba gizo kunnenta suke yi mata ba, muryar Ya Huwais ta ji. "Ya Huwais?" Ta kira sunan shi cikin ƙara da raji. Saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga bai san lokacin da ya yi wurgi da wayar ba, domin ya rasa yadda aka yi ta gane muryarsa. Jikinsa na rawa ya ɗauki wayar cikin tsananin firgici da tsoro yana duba ko ya fita daga tsarin ne. Salati kawai ya yi tare da dafe kansa yana jin shikenan ruwa ya ƙarewa ɗankada! Domin bai san wane irin kallo za ta yi masa ba, matuƙar ta gane shi yake kiranta. Idanunsa suka firfito tashin hankali ya ƙara ninkuwa a fuskarsa. Jikinsa har wani mazari yake na tsananin tashin hankali. Dafe kansa ya yi a lokacin da ya shiga gurin tsarin ya ga ashe saitin ya fita. Tsananin mamaki ya kamasa domin shi bai son lokacin da ya cire tsarin ba. Dama masu iya magana sun ce kwana ɗari ba ɗaya na ɓarawo, kwana ɗaya na mai kaya. Yau asirinsa ya tonu. Wani irin kallo za ta yi masa? Yana wannan tunanin ya ƙara mai da tsarin, sannan ya danna numbarta don ya kira. A lokacin da ya fita Ummu ta bi shi da kallo har ya ƙarasa fita. Dafe ƙuncinta ta yi cikin takaicin, ganin yadda ya takurawa rayuwarsa game da abinnda ya tabbatar wa kansa haramcin hakan. Ko wani lokacin ta ji haushinsa sai kuma tausayinsa ya dabaibayeta, wanda ba ta san dalilin yin sa ba. Ɗaukar wayarta ta yi tare da nufar kicin don ta ga ko Hilah ta kammala abincin. Ƙarar da ta ji na ta tare da sakin wayarta ta faɗi ƙasa, bayan ta kira sunan sa da ƙarfi. A razane ta faɗa kicin tana tana salati. "Lafiya, kike ihu da kiran Huwais?" Tsananin razana ya bayyana a fuskarta, domin ko kasheta Ummu za ta yi, ba za ta gaya mata dalili ba, saboda gargaɗin da ta yi mata kan kar ta sake ta kula shi. Hawaye sosai suka wanke mata ƙuncinta, cikin rawar murya ta kalleta, da ta yi tsaye cikin ɓacin rai tana kallonta. "L.a.f.i.ya l.au! Ƙawata ce ƴar ajinmu aka sanar da rasuwarta, s.h.i.ne na firgita." Ta tsinci kanta da shirga mata wannan ƙaryar wanda ta faɗa cikin in'ina da rawar murya. "Sai ki rasa wanda za ki kira sai sunan Huwais?" "Eh, da yi ke ya santa." "Munafuka! Kin ji na gaya miki matuƙar na ji da abin da kuke ƙullawa. Wallahi sai na zama ajalinki, domin ba zan bari ku ja mini abin kunya ba." Maganar da ta yi, da abin da ya yi mata suka rikita kwanyarta da take aiki bisa rashin ƙa'ida. "Ko dai Ummu na tunanin ni da Ya Huwais, muna aikata masha'a?" Ta yi kanta tambayar cikin tsananin razana jin abin da ta ce. Ta"awizi ta fara tare da jin wasu zafafan hawaye suna sauka da ga ƙuncinta, ganin rashin yaddar da mahaifiyarta ta yi mata, amma kuma da ta duba abin da ya yi mata, sai kuma duk ta ɗora masa laifin in har abin da ta gani a idanunsa, wanda ya sa take nesanta ta da shi. "Ummu, wallahi babu abin da ya shiga tsananina da Yaya. Shaƙuwarmu soyyaya ce ta jini." Da sauri ta danna wayarta ta kasheta gabakiɗaya ganin kiransa na shigowa. Ƙirjinta ne ya ƙara dukan tara-tara. "Rufe mini baki." Ta ce tare da sakin tsaki ta buga ƙofar da ƙarfi ta wuce. "Sha'anin yarannan kullum cikin damuwa suke sanya ni. Gara ayi auren su hankalina ya huta." Ta ce cikin tsananin damuwa. Tana fita ta kashe gas ɗin tare da rugawa zuwa harabar gidan. Can cikin shuke-shuken gidan ta ɓoye sannan ta kunna wayarta. Kafin ta yi ƙoƙarin kira kiransa ya shigo. "Ya Huwais!" Ta kira sunan cikin tsananin tashin hankali da ɓacin rai. A ranta ji ta ke in har shi ne yake kiranta sai ta cire kunyarsa ta yi masa rashin mutunci, domin ya cuci rayuwarta. Idan ya yi da wasa ne haƙiƙa ya sanya mata tabon da ba za ta taɓa mantawa ba. Tana matuƙar son mahaukacin masoyi da take jin a yanzu son shi ya zama tamkar maganaɗisu a rayuwarta, domin in har babu shi rayuwarta kamar gangar jiki ne da babu numfashi. "Kin san ni mutum ne mai tsananin kishi! Duk da cewar na san shi yayanki ne, kan me za ki danganta muryarta da ta sa. Shi yana da kishiyoyi, saboda kina da wasu ƴan'uwan, amma ni kuwa Allah ya halicce ki ne don ni kaɗai, ko mutuwa na yi ba za ki taɓa aure ba!" Tsananin mamaki ya sa ta kasa cewa komai, jin muryarsa ta rikiɗa ta koma muryar mahaukacin masoyi. Cire wayar ta yi daga kunnenta ta duba ko Huwais ya kira ta ba ta lura ba ta ɗauka shi ne, amma sai ta ga da numbarsa dai ya kira ta. "Kenan muryar Ya Huwais ne take mini gizo ta koma kamar na mahaukacin masoyi?" Ta yi ma kanta tambayar cikin ruɗani! Ta ɗan ɗauki mintina tana auna hakan a mizanin hankalinta. Har zuciyarta ta amintar da ita gizo muryarsa ta yi mata. "Wataƙila don na damu da halin da yake ciki ne." Ta furta hakan a cikin ranta a fili kuwa buɗe baki ta yi ta ce, "Ka yi ha..." Ƙit ya kashe wayar, yana hamdala tare da saituwar zuciyarsa da ke dukan tara-tara. Dama so yake ta yarda. Hankalinsa ya kwanta yana ajiyar zuciya ganin ruwa bai ƙarewa ɗankada ba. "Hmmmmmh! In har da ta gane yau na shiga uku! Domin girmana da ƙimata zai zube a gurinta, wanda ba zan iya lamuntar hakan ba." Ƙwanciya ya yi, yana mai da numfashi saɓanin da yake ta safa da marwa, yana ta share zufa duk da A.C dake cikin falon. Bin layin ta yi, amma a kashe wanda ya ƙara tada hankalinta matuƙa, domin a yau ya yi mata alƙawarin sanar da ita sunansa. Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska. Hannu ta sanya ta share. Da sauri ta ruga zuwa ciki tuna rage gas ɗin kawai ta yi ba ta kashe ba. Sororo ta yi ganin Ummu a kicin ɗin dama tum kafin ta shigo ƙaurin kuskus ya cika gidan. Wani irin kallo ta watsa mata tare da kai mata mari. Da sauri ta matsa cikin muryar kuka. "Ummu, ki yi haƙuri ba..." "Fita ki bani guri! Sakaryar yarinya kawai." Ta furta cikin ɓacin rai wanda ya aanya ta ruga zuwa falo tana hawaye. Yana kwance a kan kujera yana ta tunani har yanzu zuciyarsa ba ta gama bugu ba. Su Tashi ya yi jikinsa babu ƙwari ya shiga bayi don ya watsa ruwa su tafi gidan Hajiya. Bayan ya yi wankan ya shafa mai sannan ya sanya dakakkiyar shadda ruwan sky blue. Shaddar ta yi matuƙar ɗaukarsa domin ya yi kyau sosai duk da damuwar da yake ciki, bai hana fito da zallar kyawunsa ba. Turarensa mai daɗin ƙamshi ya fesa sannan ya kulle ɗakinsa. Ya shigo falon da sallama zuciyarda na dukan tara-tara. A ransa yana fatan Allah ya sanya ta yarda ba shi ya ke kiranta ba. Ita kaɗai ce a falo tana tsaye a gaban dining da tsumma a hannunta tana goge kan dining ɗin da ta gama ba Umnah abinci. Sallamar da ya yi ta ji zuciyarta ta buga wanda ba ta san a tare suka buga da na sa ba. Kallonsa ta yi cikin ido tana son ta ga rashin gaskiya a tare da dashi, domin har yanzu zuciyarta na ƙara tanbatar mata da muryarsa ne. "Ya Huwais!" Ta kira sunan daidai lokacin da ya ƙaraso gurin dining ɗin cikin daurewa. Basar da kallon da yake mata take yi."Ina su Umnah? Ummu, ya gaya muku zamu fita." "Eh, amma ta ce ban da ni." Kallonta ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sai kuma ya zauna yana kallonta. "Je ki gaya musu su fito kuma ke ma ki shirya." Jim ta yi kamar za ta yi masa magana sai kuma ta jiya ta sanar musu tare da dawowa da sauri. Ganin da magana a bakinta ya sanya shi miƙewa da sauri tare da ije remote ɗin da ke hannunsa. "Ki ɗauko mayafinki bari na ɗauko abu na yi mantuwa."Tsaya ya yi ganin Ummu ta fito da carbi a hannunta. "Ka shirya ne Huwais? "Eh, Ummu. Su yi sauri domin ina son na je gidansu Najib." "Amma daga nan za ku je gidan su Wajnah ko?" "No Ummu, ba yau ba." Ya furta cikin ɗaure fuska. "Ma za ki kira su Amnah." Ta ce. "Na sanar musu Yaya ya fito." Kafin ta gama maganar suka fito dukannninsu a shirye. "Bro you look gorgeous!"Naufal ya ce cikin murmushi yana kallonsa. Ba tare da ya amsa ba, ya fara ƙoƙarin tafiya ganin sun kama hanyar fita, sai kuma ya juyo ya ce,"Ummu, Hilah ba za ta je ba ne? Ko ranar da muka je Hajiya ta yi maganar tana son ganinta." Ya yi maganar cikin basarwa. "Eh, ku barta kawai jibi in zani sai mu tafi tare." Ta ce wanda ya sa ya ƙara ɗaure fuska ba tare da ya kalle ta ba. "Ok,." Ya ce amma a ransa a jagule ji yake kaman shi ma ya fasa zuwa. "Please Ummu, don Allah mu je da Anty Hilah." Umnah ta ce wanda jin haka ya sanya Amnah ta ce, "Please Ummu," "Hilah, ki ɗauko mayafinki ku je." Ta ce tare da juyawa cikin ɗakinta wanda ya sa yaran suka saka ihun murna. Ɗaki ta koma cikin tsallen murna ta sanya abaya ja tare da rolling ɗin ɗankwalinta. Ta yi kyau sosai kamar ka sace ta gudu. Wayarta ta ɗauka sai ƙaramar pos ɗinta ta fito. Bayan sun shiga cikin motar har ya tada mai-gadi ya buɗe Umnah ta ce, "Ya Huwais, Ummu ta bar Anty Hilah ta bi mu. Shiryawa ta ke yi." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 11 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Ya Huwais, Ummu ta bar Anty Hilah ta bi mu. Shiryawa ta ke yi." Ransa ne ya yi fari kamar farar takadda, ba tare da ya ce musu komai ba. Ya kashe motar yana shafa sajensa. Ba ta ɓata musu lokaci ba ta fito tana tafiyarta cikin sanyi. Ta madubin motar ya hangota yayin da ya ƙura mata idanu ganin yadda ta yi kyau kamar ka sace ka gudu. "Ya Allah!" Ya furta da ƙarfi tare da dafe zuciyarsa daidai inda ta buga. A hankali ta ƙaraso, ta shiga bayan motar wanda sai da ya ɗan ɗauke numfashinsa, jin yadda ƙamshin turarenta ya cika masa hanci yake rikitar da kwanyarsa. Ba tare da ya kalleta ba ya ja motar yana sauke gwauron numfashi. A hanya tafe suke shi da ita babu wanda ya yi wa juna magana. Kowa da abin da yake tsaƙawa a ransa musamman ita. Da take son sanar masa da incident ɗin da ya faru da ɗazu. Shi kuwa hankalinsa na kan hanya, amma tunaninta yake yi, satan kallonta yake yi wanda ba ya son su haɗa idanu, domin za ta iya fahimtar wani abu, musamman yadda idanunsa suka canza. Su Naufal ne kawai suke ta hirar su, wanda yawanci suna sako su a ciki. Hilah ce kawai take sanya musu baki, amma shi da ga um sai a'a. Kafin su isa ya tsaya ya siyawa Hajiya Fruits sannnan suka wuce. A ƙofar gidan ya tsaya tare da yin hon, wanda Ilu maigadi ya taso da sauri ya buɗe masa, ya shiga da motar cikin ƙaton harabar gidan. Bayan ya yi parkinng sun fito ban da Hilah da ta tsaya nawa tana ƙoƙarin sanya takalminta. Saboda murna suka ruga cikin gidan ba tare da sun jira ta ba. Ta ɗauki takalmin tare da buɗe murfin ƙofar za ta fita, ba tare da ta ce masa komai ba, da hannunsa dafe da sitiyarin mota yana kallon gefe. Ganin za ta fita ya sanya shi juyowa da dara-daran idanunsa ya watsa mata. Wani irin faɗuwar gaba ta tsinci kanta da shi. Sai kuma ta rikice domin ba taɓa ganin ya yi mata kallon ba. "Yaya," Ta ce sai hawaye suka wanke mata fuska. Ƙaramin tsuka yaja don jin haushinta, domin shi ya kamata ya yi kuka ba ita ba. "Ba na hana ki sanya turare ba?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai. Ganin ba ta ce masa komai ba, domin ita ba wannan maganar take son su yi ba ya ɗora da cewa," Ke malama ce kina da sanin ki, kuma kin san hukuncin sanya turare wani namijin da ba muharraminki ya shaƙa ba." Ya Huwais, mahaukacin masoyi ya kita ni da rana." Ta yi masa maganar tana kallonsa ko zai ce wani abu, amma sai ta ga ya tsuke fuska hankalinsa na kan wayarsa da yake shafa bayanta. Gyaran murya ta yi, wanda ya ɗan juyo da idanunsa ya yi mata wani jirgitaccen kallo. "Damuwarki mahaukacin masoyinki, sam ba ki damu da rayuwar ɗan'uwanki da ake shirin yi masa auren dole ba." Yadda ya yi maganar da abin da ya faɗa suka sanya ta sakin dariya babu shiri. A hargitse ya juyo yana kallonta ganin dariya take. Ransa ne ya ƙara ɓaci ya buɗe furfin motar zai fita. Ganin haka ya sanya ta gimtse dariyar tare da kama hannunsa ta riƙe. "Please, Ya Huwais, don get me wrong." Ta fura tare da riƙe hannunsa duka biyu. "Ina cikin damuwa, amma ba kya tausayina. Tun da kika samu mahaukacin masoyinki kin daina kula da ni." Rau ta yi da idanunta."Kai ma ka san babu wanda na damu da rayuwarsa kamar kai. Bayan ƴan'uwanta ka ta jini har da shaƙuwa da soyayyar jini, wanda ta kai da har muryar mahaukacin masoyi tana rikiɗa tana zama irin taka." Gwauron ajiyar zuciya ya saki jin abin fa ta ce. Zuciyarsa ta yi fari ƙal tare da hamdala ganin ba ta gane ba. Da mamaki ya kalle ta ya ce,"So kike ki yi mini wayo na ɗauka kin damu da ni, amma na tabbata da ace babu son mahaukacin masoyi a rayuwarki, sai ki tausaya mini halin da na ke ciki." "I do care you! Wallahi kana raina ko da yaushe, amma ka sani Ummu, gata take yi maka, domin duk wanda ya auri mace kamar Anty Wajnah ya yi dace." Ƙara ɓata rai ya yi tare da buɗe murfin motar ya fito."Please, akwai buƙatar mu tautauna sis, ina tsananin buƙatar shawarki." "Haɗuwarmu xai yi wuya Yaya, Ummu sam ba ta son ganinmu a tare." "In mun gaishe da Hajiya ki same ni a waje ki raka ni gidan Najib." Kallon sa ta yi da nufin ta musa, amma kallon da ya yi mata ya sanya ta kasa tare da sauke kanta ƙasa. Ganin ya fita ya sanya ita ma ta fito tare da rufe ƙofar suka jera suna hira. Hajiya na zaune a falon, su Umnah sun sanyata a tsakiya sai hira suke mata. Sallamar su ya katse dariyar da suke yi mata. Ganin su ya sanya ta washe bakinta da ke cike da goro tana tafa hannunta. "Lale marhaba da zuwan jikokina!" Ta furta cikin tsananin farinciki domin tana matuƙar son jikokinnata. Huwais da fara'a ya isa gareta, tare da zaunawa a gefenta ya ciro wayarsa da ke gana aljihun rigarsa zai ɗauke su hoto. "Bari na yi hoto da gimbiya autar mata." Ya ce cikin tsigar tsokana. Hannnunta ta sanya ta ka masa duka da carbin da take ja, ta ture shi tare da kai hannu kamar za ta buge shi, wanda hakan ya sanya ya miƙe yana dariya. "Bari na gudu domin hannunki kamar icce yake." "Eh, ai gara ka gudu in ba haka ba, sai na karyaka saboda kishi. Don za ka yi aure sam ka daina zuwa inda na ke. To daɗin abin ba a canzawa tuwo suna, kuma tsohuwar zuma da ita ake magani" Fara'arsa ta ragu jin abin da ta ce, amma sai ya share ba tare da ya ce komai ba. Hilah kuwa rungume ta yi cikin tsananin ƙauna ta ce,"I miss you ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe." Murmushi ta ƙara saki tana cewa,"Sannu malama tun da kika ci gaza kika yi kuɗi kin guje mu." "Kai tsohuwar nan kin iya rigima. Kana jin abin da take cewa Ya Huwais, bayan ko da na dawo sai da na kawo mata nata kason." Murmushi kawai ya yi,ba tare da ya ce komai ba, ya zauna gefen da Hilah ta zauna hankalinsa na wayarsa da Najib ya turo masa da tsaƙo. "Ai kya faɗi haka saboda ba ki da gaskiya. Bari mutuminki na nan zuwa, tun da ya ji muna maganar zuwarki ni da Fatima ya ce ba zai koma Kaduna gurin aiki ba sainya ganki, yanzu haka yana hanya. Ni duk na ƙosa ayi auren nan duk mu huta." Da sauri ya ɗago kansa jin abin da ya ce. Zuciyarsa ta yi baƙinƙirin tare da jin wani irin ɓacin rai. Wani irin ɓacin rai ya ziyarce shi har baya gani sosai. "Ai ko ya zo wahala zai yi domin zamu bar su Umnah fita za mu yi." "Ku je ina? Lailai ba wuni ta ce mini za ku yi ba?" Ta yi masa tambayar da sauri. Miƙewa ya yi tare da ɗaukar makullin motarsa ya kalli Hilah da shi take kallo ganin yadda ya yi fuskar shanu. "Eh, wuni za mu yi, amma sai ta raka ni anguwa. In zai iya sai ya yi ta jira ɗan wahala kawai. Ni wallahi haushi yake bani, saboda yadda yake wani nuna son mace da nace mata kamar maye." Cikin tsananin xafi ya furta cikin ɓacin rai tare da yi mata nuni da su tafi. "An gaya maka kowa irin ka ne? Mata ai dole a kula da su, domin sune tushen kowa. Don kai ba ka damu da matar da za ka aura ba, sai aka ce maka kowa haka yake? Ka ji tsoron Allah Huwais, yarinyar nan tana sonka, kuma masoyiyarka ce ta haƙiƙa. Ka tuna iya tsawon lokacin da ta rinƙa jiranka, amma tun da aka sanya ranar ka kasa zuwa ko sau ɗaya ne." "Saboda bana sonta kun na ce sai na aureta. Ana soyayya dole ne? Na ga ko ke kin sha bani labarin ke da Alhaji auren soyayya kuka yi da mijinki. Sai ni a ayi mini cushenta? Don tana sona sai a tilasta mini, bayan na gaya muku ina da wacce na ke so."Ya ce cikin zafi. "Sau nawa ake baka damar ka kawo ta amma ka kasa Huwaisu? In dai ba aljana kake so ba, ko kuma aurenta kake son ka yi cikin haramci, ai ya kamata ka nuna mana ita iya tsawon lokacin da aka ba ka." Haɗiye miyau ya yi da ƙyar, tare da kallon Hilah da ta yi zuru tana kallonsa, a ranta tana son ya aminta da zai nuna musu ita, domin ita kanta tana son sanin wace ce ta sace zuciyarsa har yake fargabar tunkararta? Hannunta ya kamo yana faɗin,"Zo mu je Hilah, ƴar tsohuwar nan lokacina kawai za ta ɓata." "Ba dai ka son gaskiya kawai, amma ka sani ko ba ka so Wajnah don kai ba, ka sota saboda ita ɗin ƴar'uwarka ne, saboda karka manta da mahaifiyarka da mahaifiyarta ciki ɗaya suka fito." "Wannan dalilin zai sanya na aminta a kashe ni kenan?" Kafin ta ba shi amsa muryar Hamad ta daki kunnuwansu ya shigo da sallama. Gabakiɗaya suka ɗaga idanu suna kallonsa. Namiji ingarma da shi kuma mai cikar haiba da kyawu. Yana sanye cikin kaftani mai kalar maroon. Kayan sun yi masa kyau kuma sun dace da jikinsa. "Yauwa ga shi nan ma ya iso da kake shirin ɗauke masa mata." Hajiya ta furta tare da ƙara fafaɗa fara'arta bayan ta amsa sallamarsa. Cikin kamala ya ƙaraso cikin falo, tare da zama gefen Hajiya idanunsa, na kan Hilah da ta yi mutuwar tsaye tana kallon Huwais. A ranta ta sanya cewar matuƙar da ta san zai zo sam ba za ta yarda ta biyo su ba, domin ta san in har suka haɗu ba su kwashewa ta daidai, wanda hakan mamaki yake bata, saboda ta duba tare da mahangarta ta rasa dalilin da ya sanya ya tsane shi, saboda kaf Family nasu an shede shi yana da natsuwa da hankali, amma ba shi da maƙiyi da kamarsa. Huwais ya watsa masa mugun kallo ta ƙasan ido. A ransa haushinsa matuƙa yake ji, saboda da za a iya ba shi takubba tsaf zai sare kanshi, don ya tsane shi baya jin ɗigon ƙaunarsa, duk da ya kasance ɗan'uwansa, kuma dangantaka na jini mai ƙarfi. Ƙaramin tsuka ya ja tare da ji kamar ya kifa masa mari. Tuna karanbantar da suka sha ana gobe zai bar Ƙasar ya dawo masa. Haushi da takaici suka ƙara kama shi ya ji kamar ya shaƙeshi. Bayan Hamad ya gama gaisawa da Hajiya da ta cika da farincikin ganinsa, sai ya miƙa wa Huwais hannu da ya sha kunu kamar ba zai bayar ba. Hannunsa ya noƙe ko mai ya tuna oho ya miƙa masa kamar yana gudun kar ya shafa masa ciwo. "Ranki ya daɗe gimbiyar mata." Hamad ya furta hakan cikin tautausar murya, wanda ya ji kamar ya soke shi ne. Ɗan gyaran murya ta yi can ƙasan maƙoshinta tare da tattaro natsuwarta ta ce,"Ina wuni?" Ta furta ba tare da ta iya ɗago idanunta ta kalle su da suke kallonta kamar za su cinyeta. A maimakon ya amsa sai ya ɗan sakin mata murmushi tare da ƙara masawa kusa da ita." "Gimbiya da fatan kina lafiya?" "Hajiya, mu zamu wuce ba xamu jima ba, zamu dawo." Ya ce tare da kama hannunta za su fita. "Kai Huwaisu, ba na son rashin mutunci. Ɗan'uwan na ka za ka barshi ne a nan, bayan saboda ita ya zo." "Bai sanar da zuwansa ba, kuma ni na riga na tsara fitarmu." "Karya damu zan jira shi." Cewar Hamad tare da zama a kujera hankalinsa kwance, saboda tun ranar da suka yi faɗa mahaifiyarsa ta gargaɗesa da karya ƙara kula sa, Hilah dole za ta kasance na sa, domin ko da ace sonta yake yi, ya san cewa babu aure a tsakaninsu ko da sun kasance su kaɗai. Don haka, duk son da yake mata dole ya haƙura ya ɗauke idanunsa a kan zinariyar ƙanwarsa ya bar masa ita, saboda shi Allah ya yi wa wannan tagomashin da samun mace kamarta. "Huwaisu, ina gaya muku ku sasanta kanku ku rage tsanar da kukewa junanku, musamman kune manya in har ƙanninku suka taso suka ga abin da kuke yi ba za su yi zumunci." "Hajiya, sai mun dawo." Ya ce tare da kama hannunta suka fara tafiya. Suna fita ya saki hannunta ya buɗe motar ya shiga. Hilah kuwa kallonsa take yi cikin mamaki. Ta san yana sonta fiye da kowa duk a cikin ƙanninsa, amma dalilin sa na ƙin yarda da auren Hamad yake ba ta mamaki. Yana da hankali da addini uwa uba ga ƴaƴan banki. A tunanin ƙarfafata zai yi ta amince musamman da yake ɗan'uwa, kuma wanda suka tashi tare suka shaƙu fiye da kowa a cikin family ɗin su. Har suka fita gidan babu wanda ya tanka ko da tari ne. Sun yi nisa sosai har sun hau kan titi, kasancewar unguwar da ɗan tazara, ya waiwayo ya kalleta da hankalinta yake kan titi. "Yaya, ba ya son ko wane namiji ya raɓe ni, amma mai ya sa sam baya nuna hakan ga mahaukacin masoyi?" Kafin ta masa tambayar ta ji muryarsa yana cewa," Na tsani wannan gayen, wallahi sam ba ki dace da shi ba!" Ya ƙarashe maganar tare da buga sitiyarin mitar yana huci. A tunaninka mahaukacin masoyi ya fi dacewa da ni?" Ta yi masa tambayar da ya sanya ya ja burki babu shiri yana kallonta. Tsoro ne ya bayyana a fuskarta, wanda ya sanya ya tuna a kan titi suke. Cigaba da tuƙin ya yi yana mamakin abin da ta ce. "A kan me zan faɗi haka? Karki manta mahaukacin masoyinki ke kaɗai ce kika yarda da duniyarsa, domin har yanzu ba mu san mutum bane ko aljani." "Mutum ne kuma na gari in sha Allahu. Wani lokacin ina mamakin yadda ba ka nuna haushinsa da mu'alamarmu." "Wataƙila don ban ganshi a zahiri bane, amma sauran karki manya yadda suke nuna tsantsan soyayyarsu yake sawa na ji haushi da tunanin watarana za su raba ni da ke." "Har abada muna tare kai fa ɗan'uwana ne na jini tamkar jini da hanta muke." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 12 BISMILLLAHI RAHMANINR RAHIM "Har abada muna tare kai fa ɗan'uwana ne na jini tamkar jini da hanta muke." Kaɗa kansa kawai ya yi jin abin da ta ce. "Ya Huwais, ba ka tunanin lokaci ya yi da mahaukacin masoyi zai bayyana kansa ya daina ɓoye kansa?" Ta yi masa tambayar idanunta a kansa. Ganin bai tanka mata ba, sai gabansa da ya faɗi ya sa ta ɗora da cewa,"Zan gayyace shi bikinka, in har ya ƙi zuwa zuciyata na bani shawarar na haƙura da shi, ko da kuwa son shi xai kashe ni, domin babu soyayyar da na taɓa ganin an yi aure ba tare da haɗuwa." Wani rin faɗuwar gaba ya ƙara ji dum! Sai ya jikinsa na rawa. Ƙoƙarin daidaita na tsuwarsa ya fara yi, don kar ta fahimci halin da ya ke ciki. Kaɗa kansa yake kamar ƙadangaren kutu!"Ya kamata gaskiya ki gayyace shi, amma kar ki ce za ki rabu da shi, don ya ƙi zuwa bikina in har kina sonshi, domin jikina yana bani mahaukacin masoyi shi ya fi dacewa ya aure ki. Wani ne can wanda ba ki taɓa tunanin yana sonki ba, ya ke fama da dakon soyayyarki tsawon lokaci. Da ya ke ƙanwata mai zafi ne kuma kyakykyawa dalilin da ya sanya ya kasa bayyana kansa gareki." "Ni ma haka nake ji musamman a duk lokacin da na yi istikhara." "Da kyau malamar ƙanwata. Daɗina dake komai sai kin nemi zaɓin Allah. Ki ba shi lokaci matuƙar bai bayyyana kansa ba, ni da kaina zan gaya miki ki haƙura da shi." "Amma kai ma Yaya kana da kyau, domin ban taɓa ganin namijin da yake da kyau kuma ya iya tsara rayuwarsa da kula da addini kamar kai ba. Jin abin da ta faɗa kansa ya fasu har ya ji kamar zai cika duniya. "Duk kyawuna, bai kai ƙanwata sarauniyar kyawu da kula da addini ba." "Wannan dalilin ya sa na ke jin matuƙar haushin mahaukacin masoyi da kike sonsa." Ta buɗe baki xa ta yi magana, ya rigata daidai lokacin da suka isa ƙofar gidan, ya tsaya a get ɗin ba tare da ya yi hon ba. Kashe motar ya yi ya kalle."Please, na gaji da maganarsa as usual. Ke kullum damuwarsa kike kawo mini, da kuma na yi ƙorafi kice ba haka ba." Dariya ta yi tare da ce wa,"Kai Yaya," "Ki bani shawarar yadda zan zauna da Wajnah a matsayin mata." Kallonsa ta yi kamar ba ta gane mai yake cewa. "Yes, ina nufin wane irin zama za mu yi, domin kin san ba ta a cikin zuciyata. Tsoro na karna cutar da ita Allah ya kamani." "Ta ci albarkacin Mommy mahafiyarta. Ka yi adalci a zamanku." Kwantar da kansa ya yi kawai a saman kujerar motar domin ba haka ya so ta ce mishi ba. Gani suka yi an wangame get ɗin gidan. Najib ne da matarsa tsaye cikin mamaki suna kallonsu. "Kai! Wallahi kana da abin mamaki Huwais, na ɗauka amarya ka kawo mini kuka tsaya kana soyewa tun ɗazu a waje ashe ƙanwarmu ce." Ta faɗa daidai lokacin da ya shigo da motar cikin yana ƙoƙarin buɗewa. Hilah da ke dariya ya watsawa kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya ɗauko pos ɗinta da ta barshi a motar ya miƙa mata. Najib da ya san dawar garin bai yi ƙorafi ba. Ya yi musu jagora suka shiga ciki. Hilah ta zauna a gefen kujerar da ya zauna bayan ta gaida matar Najib mai suna Samahatu. Cikin sakin fuska ta amsa mata, daidai lokacin da ta ije musu gorar ruwa da drinks a gabansu. Huwais ya sanya hannunsa ya ɗauki ruwan ya buɗe, tare da ɗaukar kofi ya zuba mata. Miƙa mata ya yi yana murmushi. Ita ma murmushin ta mayar masa tare da karɓa ta ce masa,"Thanks, Ya Huwais." Da idanu ya amsa mata tare da ije gorar yana mata wani irin kallo. Samahatu ne ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallonsa. Ta juya ta kalli Hilah da take kurɓan ruwan cikin yanga kamar ba ta son sha, yayin da hankalinta yake kan wayarta. Idanunta ta mayar kan Huwais da har yanzu ita yake kallo, duk da maganar da Najib ya ke mishi, amma hankalinsa ba shi a kansa. Ƙara kallonsu ta yi tana son ƙara ganin kamar su. Ta san cewa Najib ya taɓa nuna mata hotonta har ya sanar da ita ciki ɗaya suka fito. To amma wane irin kallo yake mata kamar na soyayya? Ƙwaƙwalwarta ta rikice sai kuma ta fara tunanin ko dai ba ita ba ce. Gyaran muryar da ta yi ya sanya dukanninsu hankalinsu ya dawo kanta. "Baby, bari na haɗo abinci." Ta ce tana sakar masa murmushi. "Ok, honey, please ki kawo wa Huwais juice ɗin goribar da na haɗa ya ji na iya abinci." Dariya ya yi jin abin da ya ce ba tare da ya ce komai ba. Zubbur Hilah ta miƙe tare da kallonsa."Yayana, let me help her." Ta furta cikin taushin murya. "Haba, ƙanwarmu karki wahalar da kanki ai na kusa gamawa." "No, kar ki damu in ba ki gama ba, ki ba ta ta yi girkin domin she is the best cooker in the world" Ya furta hakan cikin tabbatar wa. Murmushi ta yi." No, kar ki damu yanzu xan gama." Ta ce za ta juya. Hannunta Hilah ta kama tare da cewa,"Mu je Anty Samah, kar ki damu. Amarya ce ke bai kamata ki yi aiki ba." "Good girl, na gaya miki ƙanaata akwai hankali da son taimako, domin zan iya cewa tafi ko wace mace hankali da natsuwa da iya komi." Sororo ta yi sai kuma ta yi yaƙe kawai ta kalleta da take murmushin jin kunya ganin yadda yake kurantata. Harararsa ta yi cikin wasa shi kuma ya aika mata da kallo suka shiga kicin. "Huwais, kana cika zaƙewa fa! Ba ka tunanin abin da kake yi kowa zai iya gane sonta kake yi? Kuma yabon ta da kake yi ba ƙaramin matsala zai jawo maka da iyalinka ba, domin babu macen da za ta zauna ta ji kana yabon ko da ƴarka ce haka, ba tare da ta ji kishi ba." "Let her be. Ai dama ta shiga gonar da mallakinta ba ta shiga." No, absolutely you need to change. Wallahi za ka iya jawo ma kanka rashin zaman lafiya da iyalinka, kuma irin kallon da kake mata duk yana wuce gona da iri." "Hmmmmmh," Kawai ya ce tare da mai da hankalinsa kan tibi. "Don't be delusional Huwais." Ƙin tanka masa ya yi, wanda ya sa shi mai da hankalinsa kan tibin suka ci gaba da kallo. A kicin suna aiki Samahatu na satan kallonta, musamman da ta cire gyalen da ta yi rolling ɗin kanta da shi. Da ta ga gashinta sai da ta yi wa Allah tasbihi. Satan kallonta take yi ba tare da ta kula ba, da ta maida hankalinta gurin haɗa salat. "Ance mutum tara yake bai cika goma ba, haƙiƙa wannan halittar ta cika." Ta furta a zuciyarta ganin yadda take da tsatsan kyau. Babu abin da ya ƙara ɗaukan hankalinta irin yadda gashi ko ina ya kwanta a jikinta, kamar wata balarabiya. Ƙara kallonta ta yi daidai lokacin da take goga karot. Murmushi ta sakar mata tare da cewa,"Sannu da aiki." "Yauwa Anty Samahatu, kin ga Yaya Huwais, yana mugun son salat. In har na yi masa santi yake yi, don yau sai kin yi haƙuri domin sai na yi masa waigi." Dariya ta ba ta musamman yadda take maganar cikin tsigar tsokana. "Yauwa ba ni lemun tsamin na saka, domin ya ce ina ɗiga kaɗan kunninsa har zut!Zut! Suke masa, kar kuma na cika ban san ko kuna so ba?" Dariya sosai ta yi, jin abin da ta ce,"Ki sa shi ma ya sanar dani tun kafin mu yi aure yana ci, kuma Yayanki ya koya masa." "Eh, ai ban taɓa ganin aminan da suke ƙaunar junansu kamar su ba, don ban taɓa ganin sun samu saɓani ba." "Saboda sun haɗa ilmi da hankali ne." "Haka ne Anty Samah." Ta ba ta amsa tana juya salat ɗin. "Gaskiya kina ji da Yayan na ki, ko na ce kuna ji da juna, amma sai dai na shiga kokwanto ko ƙanwarsa ce wacce suke ciki ɗaya, ko matar da zai aura?" Dariya ta yi, ta tsaya da abin da take yi,"Saboda me kika tambaya?" "Kulawar ta yi yawa." "Eh, yana ji da ni sosai. A cewar shi ni ce mace ta farko, da ya fara samu bayan ƙanninsa maza uku. Yayana yana ji dani sosai, wanda hakan ya samu asali ne da shi ya yi ɗawainiya da ni tun ina ƙarama, kuma ya kamata ki ga kama, musamman diple ɗin mu, duk da shi ba shi da hasken fata sosai kamata." "Na shiga kokwanto ne irin kulawar da kuka ba wa junanku, kamar na ma'aurata, amma kuma jin yadda kuka taso, gaskiya kin cancanci fiye da haka." "Sosai kamar yadda ni ma nake ji da shi." Kaɗa mata kanta ta yi tare da ɗaukar tiren abincin suka fito falo, yayin da Hilah ta ɗauki tiren juice ɗin. Tashi ya yi ya karɓi tiren yana faɗin,"Ina fatan ba ki wahalar mini da ƙanwata ba?" "Ni na isa a kore ni a garin Abuja?" Ta ce cikin dariya. Zama suka yi a dinning suka fara cin abincin. Yana kai abincin bakinsa ya tauna ya lumshe idanunsa yana kallonta. "Ƙanwata, ke kika haɗa salat ɗin nan ko?" "Please, Anty Samah, ki bani waigi na yi masa kar ya faɗi." Dariya suka kwashe da shi, ban da shi da yake harararta cikin wasa. Suna cin abincin kiran Hajiya ya shigo wanda ya tabbata Hamad ne ya gaji da jira. Dama tun da suka shigo ya fakaici idanunta ya ɗauki wayarta ya kashe. Kiran Hajiya bai daɗe da tsinkewa ba, na Ummu ya shigo. Zuciyarsa ne ya buga ya kalleta da sai wasa fa cokali take yi, domin ba ta jin yunwa. "Ki yi sauri ki gama za mu tafi."Ya ce zuciyarsa na bugawa, don tun da ta kira hankalinsa ya tashi abincin ya fita a ransa. Kasa ɗauka ya yi, don ba shi da abin da zai ce mata, kuma in ya kashe wayar hukuncin da za ta yi musu, sai ya fi muni sosai, musamman Hilah laifin duk a kanta zai ƙare wanda ba zai so hakan ba, don gara ta hukunta shi. Bayan sun kammala suka miƙe za su tafi. Samahatu ta shiga cikin ɗaki ta ibo mata kayan kwalliya da yawa ta miƙa mata a leda. Hannu ya sanya ya amsa yana faɗin," Kawo kar ki wahalar mini da ƙanwata."Miƙa masa ta yi tana dariya ba ba ta ce komai ba. "Ina fatan za ki dawo sis ɗinmu za ki dawo kin burge ni." "Zan dawo Anty Samah."Ta ce tana ɗaga mata hannu har suka fita. "Baby, na shiga cikin ruɗu! Wannan soyayyar da abokinka yake nuna ma ƙanwarsa na aure ne ko jinintaka?" Ta yi masa tambayar daidai lokacin da majgadi ya rufe get ɗin gidan. Kallonta ya yi ganin yadda ta ɗauki maganar serious, dama yadda ta ke musu kallo ya san sai ta tambaya. "Mu shiga ciki mai kika gani?" "Abin ne da mamaki suna rayuwarsu, kamar masoya ko dai akwai aure a tsakaninsu ne." "Ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya. Karki manta na gaya miki bikin shi ya rage kwanaki, ita kuma da zarar ta kammala karatunta akwai wanda za ta aura a family ɗinsu yake." "Ikon Allah! Gaskiya wannan soyayyar tasu akwai lauje cikin naɗi!" "Please, kar ki sanya kokwato a zuciyarki shaƙuwar jini ce." "Hmmmmmmh!" Kawai ta ce tare da fara tafiya sai kuma ta tsaya ta kalle shi ta ce,"Karka manta psychology na karanta so zan iya fahimtar komi. Kamata ya zo mana da wacce zai aura ba ƙanwarsa ba, amma har ya tashi ban ji ya ambaci sunanta ba." Shiru kawai ya yi, don ba shi da amsar da zai ba ta don haka shirun yafi, domin masana iya magana sun ce shiru ma magana ce. A mota ya miƙa mata wayarta da Ummu ta ƙara kira."Ummu ce take ta kirana shi ya sa na taho, amma bacin haka sai na tabbata wancan mai kama da mayen ya tafi." "Zai iya kwana tun da ɗan gida ne." Ta furta masa hakan. Harara ya wurga mata ba tare da ya ce komai ba ya ci gaba da tuƙi. "Innalillhi! Ka ce Ummu ta kira?" "Eh, sai ki san yadda za ki kare kanki, ai duk ke kika ja, wa sani ko ke kika sanar masa da zuwanki ya wani kwaso jiki ya taho?" "Wallahi bani ba ce Ya Huwais." Banza ya yi da ita ya ci gaba da tuƙunsa, wanda ganin hakan ya sanya ta kama bakinta, tana tunanin darun da Ummu za ta yi. Ba su ƙara magana ba har suka isa gidan. Hajiya da ta yi kici-kicin da ranta yana ƙarasowa ta buga masa dundu a baya. Dariya ya kwashe da shi,"Wayyo yar tsohuwar nan ashe akwai sauranki! Kin ji hannu kaman guduma." "Amma sam ba ka da kirki Huwaisu, sai ka ɗauke ta ku tafi, bayan ka san yana jiranta?" Satan kallonsa ya yi da ya ɓata fuska zuciyarsa a tuƙe, domin da ace bai yi wa mahaifiyarsa alƙawarin ba zai ƙara kula shi ba, babu abin da zai hana bai kai masa mari ba. Miƙewa ya yi ya kalleta da ta yi tsuru-tsuru tausayinsa ya kamata, domin abin da suka yi ta san cewa ba ta kyauta ba, amma ya za ta yi? Ɗan'uwa ta yana gaba da komai kuma takan hana kanta farincikinta ta ba shi na sa. "Gimbiya, muje waje ina son magana da ke!" Ya furta da murya mai sanyi da kuma ɓacin rai. "Babu inda za ta je domin gida zamu je, Ummu na ta kiranmu." Ya ba shi amsa yana kallon agogo fuskarsa a haɗe. "In ina magana ka daina sa mini baki da iyalina, domin ba zan duba tazarar da ka bani ba, wallahi yanzu za a yi ɓatacciya." Ya furta cikin zafin rai. "Mara kunya dukana za ka yi? Karka manta ƴar'uwata ce na jini, na fi ka iko da ita, domin ina da isan da zan hana aurenku." "Inda kuma ka yi kaɗan kenan, domin Hilah tawa ce, duk son da kake mata da nuna kishinka sai dai ka yi a banza, saboda kana ji jana gani zan ɗauketa a matsayin iyalina ta haifa..." Marin da ya kai masa ya hana shi ƙarashe maganar, amma sai bai same shi ba saboda ya kauce. Huwais jin ya kirata da matarsa ya sanya shi yin marin babu shiri. "Au, tarihi ne zai maimaita kansa? Har yanzu ba za ku daina wannan haukan ba? Duk fa ƙaunar da kake mata gidan wani za ta Huwaisu. Anya kana da hankali kuwa?" Ransa ne ya ɓace jin shika kaɗai ta bawa laifin. "Please, Ya Huwais ku daina. Don Allah Ya Hamad, ka je za mu yi waya." Ta furta cikin muryar kuka bayan ta shiga tsakaninsu. "Ki barshi rashin kunya zai yi mini." Ya furta yana huci. "In ba za su daina ba kai Affan, kira mini Babansu Hamisu ya zo ya yi wa abin tufka." Wani wulaƙantaccen kallo ya watsa masa har zai yi magana sai ya fasa, domin ya san abin da ya shirya yi masa sai ya ƙuntata masa fiye da maganar da zai yi masa. "Zan wuce Hilah. Ki kular mini da kanki ina sonki, na tura miki kuɗi a account ɗinki sai mun yi waya. I love you." Ya furta mata a kusa da kunninta ya watsa masa harara da zuciya ta kai masa wuya ya wuce. Ilai kuwa, kamar yadda ya yi tunanin sai ya fi baƙanta masa haka ya faru. Har ya fara taku zai bishi ta kama hannunsa tana kuka. Fita ya yi daga falon zuwa motarshi ba tare da ya yi ma Hajiya sallama. "Umma ta gaida ashsha! Ja'irin yaro kawai. Wannan kishin da kake nunawa da a kan matar da za ka aura kake yi sai armashi zafi fiye da ƙanwarka." Hon ɗin da yake yi musu babu ƙauƙautawa, ya sanya suka kwashi kayan su suka fito da sauri. Figar motar ya yi a guje suka bar harabar gidan. A gida kuwa Ummu ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ta kira wayarsa ya fi a ƙirga, amma ya ƙi ɗagawa, wanda hakan ya ƙara baƙanta ra ta ainun. Numbar Abu ta kira ta fara yi masa ƙorafi. "Ina kan hanya na kusa gida ki jira ni." Ya kashe wayar bayan ya ce mata haka. Yana mamakin yadda take zafafa lamarin. Shi a tunaninsa duk abin da take hange bai kai nan ba, domin yana da hankali da addini ba zai aikata wa ƙanwarsa mummunan abu ba, amma sai ta ɗaga hankalinta ta gadda za ta kasa sukuni. Yana shigowa ta fara hawaye tare da buɗe baki za ta ce. Dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu. "Duk ke kike rikita lamarin nan Lailah har yaran nan suka fara zargin wani abu, tun da an kusa bikinsa don Allah ki ƙyale shi har ayi bikin nan ya koma gidansa mu huta." "Laifi ne don na sanya idanu a kan tarbiyar Ƴaƴana? Karka manta yarannan amana ce Allah ya bamu domin ya ce dukkannnin mu masu kiwo ne, kuma rabar gobe kiyana sai a an tambaye mu. Kuma kula da kaya, ai yafi ban cigiya. Musamman yadda shi yake nuna soyayyanta ɓalo-ɓalo." "Duk ban ga laifin ki ba, amma kina zafafa lamarin ne, kuma hakan zai iya haifar da wata matsalar. Don Allah na roƙe ki in suka zo dawo kar ki hausu da faɗa ki yi musu kyakyawar fahimta." "Hmmmh!" Kawai ta ce tare da komawa ta zauna, tana jin haushinsa na ƙin ganin abi da da take hangowa, wanda tun a wancan lokacin take nuna masa, amma ya kasa hangowa ga shi hakan ya haifar da ɗa mara ido, kuma har yanzu bai fahimta ba. "To ai shike nan, tun da laifina kake gani, sai na daina sanya idanuna a ka su, kuma duk abin da ya faru kar ka yi kuka da ni." "Babu abin da zai faru sai alkhairi.Na yarda da tarbiyar da na bawa yarana, ba za su aikata abin da duniya za ta la'ance su ba, duk da shaƙuwar dake tsakaninsu." Suna isa ƙofar gidan gabansu ya buga a tare, domin sun san ba za su ji da daɗi a gurin Ummu ba. Ajiyar zuciya ta saki da sauri, ta buɗe motar ta bi bayan su Umnaah, da suka ruga da gudu suna murnar tsarabar da suka dawo da ita. Yana zaune a cikin motar yana hangen ta har ta shige cikin gidan. Kamar ba zai fito ba sai kuma ya buɗe motar ya bita ciki. A falo suka samu Ummu, da ke riƙe da waya a hannunta tana magana da Hajiya. "Yanzu dama abin da yaronnan ya aikata kenan? Shi ya sanya ya na ce sai sun tafi tare? Ki bar ni zai dawo ni da shi ne." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 13 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Yanzu dama abin da yarannan ya aikata kenan? Shi ya sanya ya na ce sai sun tafi tare? Ki bar ni zai dawo ni da shi ne, domin ina ji ina gani ba zai ɓata mana zumunci ba." Hilah ta tsaya cikin tsoro tana zare idanu jin abin da take faɗa. Ta yi sallama a cikin falon, daidai lokacin ta gama wayar, tare da kashewa ta ije a kan kujerar da take kai. "Sannu da hutawa Ummu." Wani mugun kallo ta watsa mata daidai lokacin da Abu yake saukowa daga saman bene. "Ina kuka je?" "Ta raka ni gidan Najib." Ta ji muryar Huwais ya amsa, a maimakon ita da aka yi wa tambayar. Idanunta ta mayar kansa, da yake shigowa hannunsa riƙe da ledar costimetics da matar Najib ta ba ta. "Sai yaushe za ka daina sa ni damuwa Huwais? Yanzu abin da ka aikata ka kyauta kenan? A tunanin shekarun da ka ɗauka a waje zai sanya ka daina sanya ni cikin damuwa." Ta furta cikin ɓacin rai tana kallonsa. Kafin ya amsa ta ɗora da cewa,"Kam me za ka tafi da ita, ba tare da ka sanar mini ba?" "Huwais, zauna magana za mu yi." Abu ya furta bayan ya samu guri ya zauna kan kujera. Yadda ya yi maganar, ya baƙanta mata duk da cewar ta san ba zai ɗauki lamarin da girma ba, amma ya kamata ya tsawata masa. "Ya kamata ka yi masa faɗa, saboda wallahi kan wani banzar tunaninsa ba zan lamunta ya raba mana zumunci ba." Ummu ta faɗa tana kallon Abu da Huwais yake kallo, sai kuma ya juya yana kallon Hilah wacce take tsaye tana mazurai. "Kai ba yaro bane. Sam bai kamata ace mun tsaya, muna gaya maka abin da ya kamata ba. Da ga yau kar na ƙara jin ka yi faɗa da Hamad. Karka manta ɗan'uwanka ne na jini. Ku wuce ciki ku bani guri." Ya ƙarashe maganar cikin ɓacin rai. Jin abin da ya ce masa ya ƙular da Ummu cikin fushi ta miƙe fuuu! Ta yi cikin ɗakinta. "Ka tabbatar da ka je gurin amaryarka tsakanin yau da gobe, kuma ka bata duk abin da take buƙata." Abu ya ce masa daidai lokacin da ya miƙe zai fice. Kaɗa masa kansa kawai ya yi cikin takaici ya fice yana jin zuciyarsa na yi masa tuƙuƙi. Bayan sun tafi dariya ya yi ya girgiza kansa ya bita zuaa ɗakin. Hilah ta ji daɗi da Abu yake gida, domin ta san cewa wataƙila da sai ta sha mari. Tana shiga cikin ɗakin ta rage kayanta, daga ita sai silet da vest. Kan doguwar kujera ta kwanta tare da ɗaukar wayarta ta kunna data. Da ga kunna datar tsaƙon mahaukacin masoyi suka rinƙa shigowa. Da sauri ta mayar masa da tsaƙon, wanda duk yawanci kalaman soyayya ne. Yayana, wanda na ke masifar so fiye da komai a rayuwata zai yi aure, kuma ina gayyatarka bikin, domin saboda mahimmancin wannan ranar nake son ka bayyana mini kanka a ranar. Matuƙar ka ƙi bayyana mini kanka ba zan ƙara kula ba, kuma zan yi ƙoƙari na haƙura da kai ko da ace soyayyarka ita ce ajalina. Huwais da ke riƙe da wayarsa, yana ta dariyar a bin da ta tura masa, sai kuma zuciyarsa ta buga da tsoron da gaske za ta iya rabuwa da shi. Rubuta masa ta yi ta tura, sai kuma ta kasa jurewa har ya turo mata da amsa, ganin ya kara ta bai turo amsar ba. Kiran layinsa ta Whatsapp ta yi har ta katse bai ɗauka ba. Tana ƙoƙarin ƙara kira sai ga kira sa ya shigo. Da sauri ta ɗauka tare da doka masa sallama cikin sanyin murya. "Ina fatan ka ga tsaƙona?" "Eh, na gani amma kuma kalamanki na ƙarshe da hukuncin da kika yanke sun yi tsauri a gareni." "Kuma na riga na ya ke shawara. In har kan sona da aure ka bayyana kanka a ranar bikin Yayana, in kuma ka ƙi bayyana kanka na haƙura da kai, domin babu inda na taɓa jin anyi aure ba tare da anga juna ba." Ajiyar zuciya ya saki, wanda bugun da ya sanya zuciyarta har sai da ta kauda wayar a kunninta ta rintse ido. "Kin shirya ganina?" "Eh, kuma na yi maka alƙawarin aurenka ko da ace kai musaƙi ne." "Shikenan, zan yi tunani in har ya kamata na bayyana miki kaina zan bayyana." Yana faɗin hakan ya kashe wayarsa cikin tsananin tashin hankali. Safa da marwa ya fara yi a ɗakin, saboda yana jin ko aure ya yi ba zai iya daina jin muryarta da take kwantar masa da hankali ba. To amma kuma ta ya ya zai bayyana kansa kamar yadda ta buƙata? Shin inta gan shi wane hali za ta shiga, wanda ya san lamarin da ƙarshe ba xai yi daɗi ba, saboda yadda ta riga ta mutu a kansa. "Zuciyarsa ta ba shi shawarar ya tura wani da bata taɓa sani ba, amma sai dai kuma ta gargaɗe sa da aikata hakan, saboda in har ta ɗauka shi ne mahaukacin masoyi ta kamu da son wancan, sai ya ce an yi ba ayi ba. A ransa ya ji ba zai iya bayyana kansa ba, domin a wannan lokacin yake son ya ɗauko rigimar da zata wargaza farincikin zuriyarsu ba, don haka a kwai sauran lokaci. Wayarsa ce ta yi ƙara alamun an turo masa da tsaƙo. Da sauri ya ƙarasa gurin wayar don ya duba tsaƙon "Yayana, na gaya masa cewar ya bayyana kansa gareni ranar bikinka, kuma na yi masa barazanar rabuwa da shi matuƙar ya kasa yin hakan, amma bai ce mini komai ba, sai ma ya kashe waya. Na san zai kira ni kuma ya amince, saboda na san yana sona. Wayarsa ya ije cikin damuwa ganin abin da ta rubuta. "Anya Hilah za ta yafe mini matuƙar ta san ni nake wasa da hankalinta?" Ya yi ma kansa tambayar cikin damuwa. Ga mamakinsa sai ya ji hawaye na bin ƙuncinsa. Kansa ya dafe da ke matuƙar yi masa barazana. Ta bangaren amarya gyara kawai ake yi babu kama hannun yaro. Tun a ranar da aka sanya bikin ta kama shan kayan mata ba tare da ta bi ƙa'idansu ba, saboda so take bayan biki, ya raina kansa. Wannan ji da kai da sham ƙanshi da yake mata ya gane kuransa. Wajnah na cikin jadawalin mata da ba su tausayawa namiji a bangaren soyayya da aure, domin a tsarin rayuwarta. Ta auri namiji da zai zamo bawanta wanda za ta rinƙa juyashi yadda take so. Wato ta samu miji janitalau, wanda ta ci alƙawarin ko da ba ta samu ba, sai ta maida shi hakan ta hanyar shaye-shayen maganin mata. A burinta ta so auren namiji wanda yake masifar sonta, don ta yi amfani da soyayyarsa ta juya shi yadda take so, amma cikin rashin sa'a sai Allah ya jarrabce ta da son Huwais, wanda shi ko a cikin family ta san basa shiri, saboda yadda take nuna wayewa da yawa. A rayuwarsa ya tsani mace wacce feminism ɗinta ya yi yawa. Tun kafin ta fara nuna tana son shi, ya gane ita mace ce wacce take ganin mata sun samu daraja ne ta hanyar buƙatar da namiji yake da shi a garesu, wanda hakan ya sa take ganin kamar namiji bawa yake a garesu, kuma suna da damar da za su juya su yadda suke so. Tun lokacin ya ɗaura mata karan tsana sam baya shiga sabgarta. Yana ganin ta a mara hankali da ƙarancin ilmin addini, domin duk wani gata da daraja mace Allah ya bawa mace, saboda ita ma halitta ce wcce ya halitta don su bauta masa. Zaune take a cikin falon ƙawarta mai suna Fahima, da waya a hannunta tana zaɓan kayan mata da Hajiya zamzam; wacce take saida kayan mata a online ta tura mata. Bayan ta zaɓi kayan da yawa wanda zaɓen yawanci Fahima ce ta taya ta, kasancewar ita matar aure ce har da yarinya ɗaya. "Kin ga wannan sha ka ga aikin wallahi ki ɗauka yana da kyau, domin Hajiya Zamzam in har kika ga ta kawo kayan mata na gargajiya yana da kyau, saboda kayanta kin san duk na bature take siyarwa. Kuma da bikina na sha irinsa, shi ne na gaya miki Baban Amrah ya bani kyautar hajji, saboda duk lokacin da na sha ni kaina da ƙyar nake iya riƙe kaina." Dariya ta kwashe da shi suka tafa. Aikuwa ya zama dalo na siye shi. Don so na ke Ya Huwais ya raina kansa. Ni fa so na ke ko kara na ije ya kasa tsallakawa, domin ya san in bai yi mini abin da na ke so ba, ba zan faranta masa rai ba." "Eh, gaskiya. Ke ai magani sosai ya kamata ki siya saboda wannan miskilin da za ki aura. Kin ga in ba tsaye kika yi masa ba, wallahi wulaƙanci za ki sha sosai. Musamman da ba ya sonki." Ƙuta ta yi cikin ɓacin rai." Ki barshi zai raina kansa sosai. Ba ni yake cika yake sharewa ba, saboda kawai na ce ina son shi. Wallahi sai na maida shi namijin ta ce babu boka babu malam. Don kawai Ummu ƴar'uwar mom ce, amma da ko ita sai na shiga tsakaninsu babu boka babu malam." Dariya ta saki." Ai gara ki je da shirin ki maza yanzu babu tausayi a tsakaninmu da su, saboda kina musu sakwa-sakwa sai wulaƙanci da rashin mutunci. Sam bana son na kasance daga cikin irin matan da suke hide my identity a sirrin ƴa mace groups, kin ga kuwa dole na dage na kashe kuɗina na gyara jikina, don na siyawa kaina daraja da mutunci." Dariya suka kwashe dashi suka tafa, ban da Habiba ta take kallonsu cikin mamaki tana murmushi. "Ke dai sha'anin rijalu sai su. Ƙiri-ƙiri sun mayar da mata mahaukata sun sanya musu depression." "Ai wallahi su suka so. Ke ni fa duk macen da ta zauna namiji na wulaƙanta ta ta ji za ta iya ne, don haka in har kuɗi na aiki zan siya maganin mata na gyara jikina, wanda kafin na ba shi haɗin kai sai ya yi kuka." "Lallai ba ki da imani wallahi." Habiba ta kalle su da suke ta magana ba ta sanya baki sai a lokaci ta yi murmushi ta ce," A tunaninku shan kayan matan shi zai gyara rayuwar auren ku? Ba zan fasa gaya muku ba a matsayina na ƙawarku aminiya. Wallahi ku guji shaye-shayen kayan nan da kuke yi, saboda ba ku san da me aka haɗa su ba musamman da bature, domin zai iya kai ku tashar dana sani. Kuna cusawa kanku abin da ba ku da tabbaci a kansa, don kawai ku juya mazajenku. To daga ranar da kuka daina shan kayan matan, ko kuma ya daina muku aiki shi kenan kun rasa damarku? Ni a ganina wannan kuskure ne, domin in har za ku riƙe biyayya da haƙuri za ku juya mazajenku yadda kuke so." "Hmmm!Ta fara ni wallahi ban san dalilin da ya sanya kika na ce za ki zo yau ba." Wajnah ta ce tana aika wa Habiba da mugun kallo. "Ki barta ta ci gaba bakinta ne ai. Gajiya da maganar ne ba ta yi ba, kuma kema in ban da abinki har akwai abin da za ta faɗa ya dame ki. Ita da take yi wa mijinta biyayya ai kin ga sakamakon da yake mata. Ƙiri-ƙiri ya muzanta ki a gabanmu, amma kike wannan maganar. Habiba ki zauna ustazanci ya kashe ki, kar ki nuna wayewa kina abu kamar ba graduate mai digiri da masters ba." "Sai ilmina ya sa na kar na yi wa mijina biyayya? Faɗa ya yi mini kan na yi dare ban dawo ba, kuma in har da bai yi mini faɗa ba, sai na yi tunanin baya sona, saboda duk namiji mai hankali da kishin matarsa ba zai ƙi yi mata faɗa ba a lokacin da muka dawo." "Eh, ai kin san ni mijina baya kishina, baya ƙaunata shi ya sa bai ce mini komai ba. Ki yi ta zama yana kashe rayuwarki kina fakewa da sunan biyayya." "Ki ƙyaleta Fahima ta yi ta yi dama ta saba. Cewar Wajnah da take harararta. "Ni har mamakin yadda muka kasa daina ƙawance dake na ke yi, domin Hausawa sun ce sai hali ɗaya ya zo ake ƙawance, amma sam ke ba ki wayewa kina abu kamar ba cikakkiyar wayyaya ba." "Ni dai ba zan fasa daina gaya muku haskiya ba. Don haka shawara ya rage ma mai shiga rijiya. In kun ga dama ku daina shaye-shayen kayan mata. In kuma ƙun ƙi ina jiye muku ranar da za ku yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada don za ku tsinci Talatarku a Laraba." "Ke ce dai za ki tsinci Talatarki a Laraba, saboda yadda kike nuna kina tsoron Abban Iklas, watarana sai ya sanya ki kuka, don sai dai ki ji a shanun tashi ya yi auresa." "Wannan tsakaninsa da Allah ne. Ƙin gaya mini shi ne kawai laifin, amma ni ba zan iya hana shi abin da Ubangiji ya ba shi dama ba." "Allahu Akbar! Sannu mai sani. Allah ya sa da gaske kike kar kizo mana kina kuka. Ni da kika ganni mijina da kishiya sai dai na ƙiyama da ba ni da ikon hanawa, amma bai isa ya ce zai yi aure ba." "Lailai ko kina da aiki in har mazan zamanin nan ne." "A'a Habiba, kar ki yi mata baki. Ko ni da Ya Huwais baya sona ba zan taɓa bari ya yi mini kishiya ba, saboda ko ƙanwarsa da yake ji da ita wallahi ina shiga sai na raba shi da ita. Ballantana wata kishiya can." "To Allah ya ba ku sa'a. Ni tafiya zan yi kar habibi ya dawo don zan yi masa tuwon shinkafa." "Hmmmh! Kina wahalar da kanki ga masu aiki, amma ki je aiki ki dawo ki yi girki." Cewar Fahima. "Ai ni kuma in dai abinci ne bani da matsala, saboda ni a shegen kishina ko abincin Ummu ya ci ba nawa ba, za a samu matsala." "Ni dai ba zan iya girki ba, haka kawai da girkin zanji ko da rainon yarsa da ɗaukar ɗawainiyarsa?" "Duka ai bautar Allah kike yi." Habiba ta ba su amsa tana riƙe da ɗan makullinta. "Bar ni na ji da ɗaya haka kawai na ɗaura wa kaina wahala. Yawancin full house wife duk a ƙanjame suke, saboda ba sa samun lokacin da za su huta ga ɗawainiyar gida ga miji da yara." "Allah dai ya bamu lada kawai." Cewar Habiba don ta guddura da maganar. Wayarta ta yi ƙara, wanda ta kalla ganin numbar mijinta ne, ya sa ta ruga da gudu zuwa gurin motarta tana ɗaga musu hannu. Bayan fitarta suka dawo cikin falon suka zauna. "Ni fa Habiba mamaki take ba ni, yadda ta yi sakaci mijinta na ba ta lokaci in xa ta fita, domin duk yadda nake son Ya Huwais ba zan aminta da wannan dokar ba." "Ita ta ga za ta iya, ai sai ta yi." Fahima ta ce tare da zaunawa a gefenta suka ci gaba da zaɓen kayan matan. Huwais ransa a ɓace yake, tun lokacin da Abu ya tursasa shi zance zuwa gurinta. A ransa yana jin bai san abin da zai ce mata ba, domin shi ko kallon kirki baya tunanin zai iya mata. Tsaki ya ja tare da ɗauko wayarsa da ke maƙale a soket yana caji. Numbar Najib ya kira wanda ringing ɗaya ya ɗauka da sallama. "Abu ya tursasa ni zuwa gurin Wajnah, please gobe da yamma zaka raka ni." Ya na faɗin haka, ya kashe wayar don baya son ya ce masa komai. Da ƙyar Abu ya shawo hankalin Ummu, har ta bar maganar don ta yi ninyar hukunta Hilah, amma maganganun da ya gaya mata, ya sanya ko a fuska ba ta canza mata ba. A mota suna tafiya shi da Najib babu wanda ke magana. Najib ne yake tuƙi da motarsa, shi kuma hankalinsa na kan wayarsa da yake chatting da Hilah. Duk da cewar da ɓacin rai a fuskarsa, amma duk tsaƙon da ya tura mata ta turo mishi da reply sai ya murmusa. "Ya kamata ka sanar mata da zuwan mu fa." Najib da ya waiwayo ya kallesa yana faɗin haka. Ganin bai tanka masa ba, wanda hakan ya tabbatar masa sai bai ji shi ba. Hannunsa ya kai ya fisge wayarsa tare da duba abin da yake yi. "Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 14 "Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya." "Please, bana son wulaƙanci ka bani wayata. Tun da ka ga Allah ya jarabce ni da sonta babu makawa sai na auret.." "Ta ya ya Huwais? Tun da kake ka taɓa ganin an yi irin wannan auren? Sheɗan ne kawai ke ruɗarka kaɗa maka gangar sheɗan." "Mu bar maganar kana ɓata mini raina." Ya furta cikin ɗaga murya. "Zan yi shiru ne don kar ka ɗora laifin a kan Wajnah, da ba ta ji bata gani ba, amma ba zan fasa gaya maka gaskiya ba, a matsayina na amininka, amma ka sani auren ka da Hilah sai dai in ana mutuwa a dawo, sai ku dawo ba a matsayin ƴan'uwa ba." "In kuma Allah ya ƙaddara sai ka mutu." "Ta ya ya?" "Ni ma ban sani ba amma jikina yana ba ni matata ce!" "Hammh!" Kawai ya ce cikin takaici ya ci gaba da tuƙi ba tare da ya ce masa komai ba. Da suka isa ƙofar gidan maigadi ya buɗe musu sula shiga. Wajnah na zaune a cikin ɗakinta mai dillah na dirzanta. Ƙanwarta Batula ta ƙwanƙwasa ƙofar. "Waye?" Ta yi tambayar cikin ɗaga murya. "Anty Wajnah, Batula ce. Mommy ta ce in gaya maka Ya Huwais na falon Daddy." Da sauri ta ture hannunta jin abin da ta faɗa. "Ok, ki ce gani nan zuwa." Ta bata amsa yayin da fuskarta ya cika da farinciki. "Ana dilkan za ki fita? Ki gaya mishi ya jira ki." "Mijin nawa zan shanya ya jira ni? Kin san da yadda na samu ya zo?" "To asarar dilkan za ki yi?" Ta yi mata tambayar a maimakon ta ba ta masa. "Eh, wankewa zan yi in ya tafi na dawo." Ta ba ta amsa tare da shigewa bayi. Saboda tsabar murna ɗauraye jikinta kawai ta yi. Cikin ƴan mintina da bai fi goma ba, ta shirya kanta cikin riga da siket masu kyau ta sanya mayafi ta fice zuwa falon. Da sallama ta shiga, idanunta na kan Huwais, da yake riƙe da waya har yanzu chatting yake yi yana murmushi. Murmushin da yake yi ya sa ta yi tunanin ko ita yake yi wa. "My baby, na yi tunanin ba za ka zo ba, sai an kawo maka ni a matsayin mallakinka." Ta furta cikin kissa tare da samun gefensa ta zauna har suna gogan juna. Ba tare da ya jinkirta ba, ya matsa can ƙarshen kujera bayan ya haɗe rai, ya ɗan tsaki ƙaramin tsuka, wanda ya sanya jikinta ya yi sanyi. Wataƙila da ta shigo ba ta yi tunanin da wani yake ba, domin ba ta lura da Najib da yake kujera one seater, sai da ya yi gyaran murya. Kasancewarta wayayyar mace sai ta basar da abin da ya yi mata. "Laah, ka ce da abokinmu kake tafe?" Ta yi masa tambayar tana kallonsa, sai kuma ta mai da hankalinta kan wayarsa da yake kallo. Datar ya kashe ba tare da ya tanka mata ba yana kallon gefe. Najib ne ya ce,"Amarya bakya laifi ko da kin kashe ɗan masu gida." Dariya ta yi tare da jin farinciki na kirarin da ya yi mata, wannan kirarin ya sanya kika shanya mu ko? Ko da yake laifinmu ne da bamu sanar miki ba." "Ku yi haƙuri ana mini dilka ne sai dai na wanke." "Mun haƙura dama ba mu yi fushi ba." Murmushi ta yi jin abin da ya ce tana satar kallonsa da ya ƙara kici-kici da fuska. "Ina wuni?" Kamar ya amsa kamar kuma motsi kawai da bakinsa ya yi. Ganin haka ya sanya Najib ya miƙe,"Ni bari na baku guri da fatan za ki kula mini da shi?" Yaƙe kawai ta yi ganin yadda yake cisgata, amma a zuciyarta ta ji daɗin fitan nasa, musamman da tun da ta shigo ta nemi natsuwarta ta rasa, yayin da kayan matan da take sha suka fara aikinsu. Ji ta yi kamar ta rungume shi ko ta faɗa jikinsa. Tana mishi wani irin so musamman yanzu da take jin baba so akwai buƙatar ta ji ta a jikinsa. "Ya Huwais don..." "Please, ba na zo bane don ki ɓata mini rai. Bisa tursasawar iyayena nazo. Na sha gaya miki bana ƙyaunarki. Sam ba ki a cikin jadawalin matan da na ke so, amma kin na ce dole sai kin aure ni, don haka ki shiryar kurɓar ruwan guban da yafi na maciji dafi a cikin gidana, saboda ba za ki taɓa samun farinciki a cikin gidana ba." "Eh na ji kuma na amince, matuƙar zan rayu a ƙarƙashin inuwar aurenka, a shirye na ke da ko wane irin zama a cikin gidanka." "Shikenan, sai ki je gidan ga shi nan ki zauna, amma ni ba za ki taɓa mallakata ba, kuma na gaya miki ina da wacce nake so, nake burin ta zamo uwar ƴaƴana." "Don Allah Ya Huwais, ka taimaka mini wallahi a shirye na ke na ba ka farinciki, domin ina matuƙar sonka."Ta ce bayan ta duƙa ta kama rigarsa. Fisge rigar ya yi cikin ɓacin rai," Ba za ki taɓa mallakar zuciyata ba, domin ba ki da matsuguni a cikinta." Kukanta ya ƙaru jin abin da ya ce. Fara tafiya ya yi. Tsaye ta yi cikin damuwa tana kallonsa. Lokaci guda ta ji ranta ya ƙara ɓaci, wanda har ta gwammace da bai zo ba. Yana ƙoƙarin fita Najib ya murɗa ƙofar ya shigo. Kallonsa ya yi da ya fice ba tare da ya tanka masa ba, sai kuma ya kalli Wajnah da har yanzu hawaye take sharewa. Kunya da takaici suka lulluɓe shi, ya kasa ce mata komai sai dai ya juya ya fice. Wajnah ji ta yi kamar ta kashe kanta. Wani tangaras da aka yi kwalliyar fulawa da shi, ta ƙwada shi da ƙasa tare da fashewa da kuka ta yi sashin Mommy. "Ya Huwais ba ya ƙaunata mommy." "Ki daina ɓata hawayenki mai wuyar ki shiga cikin gidan, domin kina da kyau da babu namijin da zai wulaƙnata ki." Abin da ta faɗa ya ɗan sanyaya zuciyarta, amma har yanzu tana jin tana mata ƙuna. Rintse idanunta ta yi tana kin kamar ta mare shi lokacin da yake gaya mata yana da wacce yake so, wani irin mugun tsanarta ya shiga cikin ranta har take jin za ta iya ajalinta. "Yanzu abin da ka yi ka kyauta? Don Allah ka tausayawa yarinyar nan, masoyinka ba ya taɓa zama maƙiyinka." Najib ya furta cikin ɓacin rai ya ɓna kallonta. "Yanzu mu da muka zo yin maganar abin da za mu ba su da biki ga shi nan ka ɓata komai, wallahi kunyar yarinyar na ji ya sanya na kasa magana." "Duk abin da na yi mata laifinta ne ai ba a aure dole." Tsaki kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba cikin takaici. Haƙiƙa Ummu ta shirya wa bikin nan domin kayan lefen da aka haɗa kaya ne na gani na faɗa. A falo aka baza kayan suna ta gani cikin sha'awa. Hilah ita kanta kayan sun yi mata ƙwarai! Don Ummu ta yi ƙoƙari sosai. Gidan da Huwais zai zauna gida ne mai tsananin kyau da tsari. Gidan part biyu ya kuma haɗu sosai. Daga sashin Wajnah sai na shi mai ɗauke da ɗaki biyu da dining kamar dai Wajnah. Abu ya gina masa gidan mai kyau da tsari. Iyayen Wajnah sun yi matuƙar ƙoƙari, domin hatta sashinsa sai da suka cika da kaya, duk da cewar Abu ya hana domin Huwais zai gyara bangarensa, amma suka buƙaci su sanya masa kayan.Kaya ne na gani na alfarka aka yi. Kasancewar mahaifin Wajnah shahararren ɗan kasuwa ne, da yake da shoping mall da yawa a garin Abuja. Ya yi bajinta sosai gurin yin mata kayan, musamman da take ita ce ƴa ta farko da zai fara aurarwa. Mahaifiyarta ma ba a barta a baya ba, saboda ita ma tana business na atamfa less sa sauran kayan amfanin mata. Haƙiƙa gidan ya tsaru matuƙar gaske. Ya rage saura sati ɗaya biki hankalinsa ya tashi matuƙar gaske! Domin abu biyu suka haɗe masa tare da rikita ƙwaƙwalwarsa. Cikin dare sam baya bacci, yana tunanin rayuwar da zai yi da Wajnah da kullum ƙara tsanarta yake a cikin zuciyarsa. Sannan ga shi Hilah ta takura masa kan yazo bikin. Abin duniya sun haɗu sun yi masa yawa. Gabakiɗaya ya rame ya fita hayyacinsa, wanda ya tsorata iyayensa, amma kuma hakan shi ne kawai zai kawo maslaha. Wata shawara ta bijiro masa take ya amince da zai zo. In ya so ranar ɗaurin auren sai ya yi mata wani ƙaryar. Duk da ya san cewa za ta yi fushi dashi mai tsanani, amma ba za ta iya rabuwa da shi ba, saboda kamar yadda yake jin sonta a cikin zuciyarsa, ya tabbata tana jin kwatankwashinsa duba ga yadda take gaya masa yadda ta damu da shi, kuma ya san Hilah ba za ta taɓa gaya masa ƙarya ba. Hilah tsaye a kicin tana dama kunun gyaɗa da ta ke son ta kai masa. Har cikin zuciyarta tana matuƙar tausaya masa domin rashin masoyi babu daɗi. Tana ji a ranta yadda take son mahaukacin masoyinta, matuƙar aka raba ta da shi za ta iya shiga kwatankwacin halin da yake ciki. Bayan ta dama masa kunun ta ɗauka ta nufi sashinsa. Yana kwance da waya a hannunsa. Hotonta yake kallo yayin da hawaye suka taru a gefen idanunsa. Ƙwaƙwansa ƙofar ta yi tare da kiran sunansa wanda ya yi maza ya aje wayar. Yana buɗewa suka zura wa junansu idanu.Tausayinsa da damuwa da halin da yake ciki suka ƙara kamata Tsayawa ta yi cikin yanayi na jimamai, sai kuma ta ɗauke idanunta ganin ya ƙi cire nasa. "A haka za ka yi angwancin?" Ta yi masa tambayar cikin tausayi. Ƙaramin tsuka ya ja jin tambayar da ta yi masa. "Ya Huwais, ka ga yadda ka koma? Dubi gashin ƙasumba da ka tara. Don Allah ka cire komai a ranka ka yi addu'a kar ka janyo wa kanka cuta mu shiga uku." "Ina jin zuciyata tana zafi! Ummu ba za ta gane ɗacin da na ke ji ba, saboda auren soyayya ta yi da Abu. Hilah, Ummu ta gama kashe mini farincikin rayuwata tun da ta hana ni da wacce zuciyata ba ta muradinta." "Please, ka daina faɗin haka. Aurenku sai family ɗinmu sun yi alfahari da shi. Anty Wajnah na da kirki ba za ka yi dana sanin zama da ita, kuma Ya Huwais, Allah ya ba ka damar ƙarin aure, in har ka samu damar auren wacce kake so za ka iya ƙara aure." "Ta yi mini nisa ba za ta aure ni ba, amma na san sonta shi ne ajalina." "Ka so abin da ka san za ka samu ba wanda ba za ka samu ba. Na ce ka gaya mini inda take zan je na gaya mata yadda kake son ta na kuma roƙe ta ta aureka." A ransa ya ce,"Ke ce Hilah! Kece wacce zuciyata take mafarkin samu a matsayin mata, amma kuma ba zan taba mallakarki ba." A fili kuwa zura mata idanu ya yi, wanda ya sanya ta ɗauko kunun gyaɗar ta iba ta miƙa masa a baki. Kauda kansa ya yi, yana faɗin,"Ba na jin ɗanɗanon abinci na rasa ɗandanon bakina." "Ka ci kar ka yi wa kanka horar yunwa." Babu musu ya karɓa jin abin da ta ce. Yana cikin sha su Abidin suka shigo. "Yauwa Hilah, dama neman ki muke a cikin gida. Tun ɗazu muka kawo masa break amma ya ƙi ci. Yaya yana son ya yi mana asarar kansa, bayan ya san in har babu shi ba zamu iya rayuwa." Affan ya ce tare da zaunawa a gefensa Tausayin ƙannin na sa ya kamashi ganin yadda suka nuna tsantsar damuwarsu. Hankalinsu bai kwanta ba, har sai da ya shanye tas! Hilah ce ta miƙe don ta gyara ɗakinsa. "Bari muje zamu karɓo ɗinki mu a gurin tela. Hilah ki kula da shi." Murmushi ta yi tare da ɗaga kanta ta ci gaba da gyara falon. Tana aikin duk ta ɗago idanunta sai ta ga yana kallonta. "Gaya mini Hilah in har mahaukacin masoyi ya bayyana yana da mata zaki aure shi?" "Mai yasa ka tambaya Yaya?" "Saboda ni ma na gane, in har wacce nake so ta ji ina da mata za ta iya aurena." Ya ba ta amsa jin tambayar da ta yi masa a maimakon amsar wace ya yi mata. "Eh, zan iya aurensa saboda ina matuƙar sonsa, in har zan auresa matuƙar ya cika duk sharuɗan da ya kamata na aure shi a addini ban damu ba." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 15 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Gaya mini Hilah in har mahaukacin masoyi ya bayyana yana da mata zaki aure shi?" "Mai yasa ka tambaya Yaya?" "Saboda ni ma na gane, in har wacce nake so ta ji ina da mata za ta iya aurena." Ya ba ta amsa jin tambayar da ta yi masa a maimakon amsar wace ya yi mata. "Eh, zan iya aurensa saboda ina matuƙar sonsa, zan auresa matuƙar ya cika duk sharuɗan, da ya kamata na aure shi a addini ban damu ba." Da fari murmushin jin daɗi ya yi, amma da ya ji ta ce sharuɗa, sai ya tuna da matsayinsa a gurinta, wanda ya faɗar masa da gaba. Ba tare da ya ce komai ba, ya kwanta a kan kujera bayan ya ɗora filo a samar ƙirjinsa. Bayan ta gama gyaran ɗakin ta ja masa ƙofa ta fice ganin bacci yake yi. Ya rage saura kwana biyu biki, Hilah ta cika da matuƙar murna. Shirye-shiryen haɗuwa fa mahaukacin masoyi take ta yi. Ta je ta gyara kanta, ta yi ƙunshi mai matuƙar kyau. Sannan har dilka ta sanya aka yi mata. Duk lokacin da ta shigo masa tana murnar zasu haɗu da mahaukacin masoyi sai hankalinsa ya ƙara tashi. "Yaya, zan ɗauko maka hotonsa, na san zai kasance kyakykyawa kamar kai." Ta furta mishi lokacin da take bashi indomie da ta dafa masa. Murmushin yaƙe kawai ya yi masa, amma yama jin babu daɗi sosai. "Ya ce zai gaya mini sunan shi, kuma na san cewa sunan yana da daɗi. Ni fa ina jin kamar na sanshi, domin na tana zuwa gasar musabaƙa ƙawata ta ce wani matashi ya tambaye ta sunana da inda nake. Jikina yana ba ni shi ne." "Huhm!" Ya ce cikin damuwa yana mata kallon tausayi. Miƙewa ta yi ta ce,"Yaya, bari na je na yi wanka. Za muje walima gidan su Anty Wajnah." Ɗaga mata kai ya yi ta fice tana ɗaga masa hannu. Siraran hawaye masu tsananin zafi suka wanke masa fuska." Haƙiƙa na zama mayaudari, kuma na biyewa zuciyata na sanya ƙanwata cikin wani yanayi. Ban san ya ya za ta ji ba, in har na ƙi zuwa." Ya furta maganar cikin nadama da damuwa. "Ka yi kuskure Huwais, tun farko sai da na gargaɗe ka da hakan, babu abin da zai haifar sai ɗa mara ido." Amin ya furta cikin wayar ransa a ɓace. "Ban san ya zan yi ba Najib, ko na yi ninyar daina kiranta, sai na ji ba zan iya rayuwa ba in ban ji muryarta ba." Ya furta jin abin da ya ce. "Ka daure ka karya layin, sannan ka daina kiranta ka rungumi matarka da za a aura maka. Wajnah na da kyau za ka sota. Sheɗan ne ke yi wa rayuwarka ingiza mai kantu don ya kai ka duniyar nadama." "Kana da gaskiya Najib! Kuma in sha Allah zan bi shawarar ka." Ya ce tare da rintse idanunsa da suka yi masa nauyi. Rana ba ta ƙara, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. A yau ranar Juma'a ya kasance family ɗin gidan Alhaji Nadabo suke cikin matsanancin farinciki. Ganin dubban mutanen da suka fara zuwa don halarta bikin Huwais da Wajnah.Kowa fuskarsa ɗauke da farinciki. Gurin ya cika maƙil da manyan mutane. A masallacin Juma'a za a ɗaura auren, daga nan sai a wuce gurin cin abinci. Abu zuciyarsa fara ƙal tamkar gonar auduga. Sai haba-haba yake da mutane yana tarbarsu cikin karamci. Ummu kuwa tafi kowa murna, domin ji take babu wanda ya kaita farinciki. Tun safiyar sai dai kawai ta ji hawaye sun zubo mata na farinciki. In ta tuna dargar da ya sanya ta da tashin hankalin da ta fuskata kafin bikin, da ƙalubalen da ya rinƙa faruwa sai kawai ta zube ta yi sujjada shukuriya. Shikenan daga yau ta huta Huwais ba xai ƙara sata damuwa ba, don ta gama yadda sha'awace take damunsa wanda kuma ya ɗora kan ƴar'uwarsa. A ranta duk ta ƙosa a ɗaura auren ya tattara ya bar mata gidanta. Najib ne zaune a cikin ɗakin Huwais, da sauran abokanansa suna ta fama da shi ya shirya, za su inda suka kama don masaukin baƙinsu bayan ɗaurin auren amma ya ƙi. Cikin ɓacin rai Taufiƙ ya kalle shi,"Wannan abin da kake yi sam ba ka kyautawa Huwais, ni wallahi zan iya yarda da aljana da aureka, saboda babu yadda za a yi ka kai har wannan lokacin baka yi aure ba." Ya tsagaita ko zai ce wani abu, amma sai ya ga ko kallon arziki bai samu ba. "Please, ka tashi." "Ka barni domin babu inda zan je." Caa suka yi masa ganin ya ƙi tashi ya yi wankan ballanatana su sanya ran za shi. Banza ya yi dasu, yana ta tunanin halin da Hilah za ta shiga, in har ta kira wayarsa ta ji a kashe, domin saura minti talatin lokacin da suka sanya za su haɗu ya cika. Ganin sun kaɗa sun raya, amma ya ƙi tashi sai Najib ya kalle su ya ce,"Ku ƙyale shi na san wanda za ta sashi ya yi wankan." Wayarsa ya ɗauko tare da fara neman numbar ta. Huwais ya ɗauka Ummu ce har zuciyarsa ta fara bugu. "Yauwa, ƴar halak ƙin ƙi ambato." Ya furta lokacin da ya ji muryar Hilah na yin sallama. Jin an bata damar shigowa ya sa ta shigo cikin natsuwa. Gabakiɗaya idanunsu suka hau kanta. Wani irin tsau ta ji tare da kunya ta lulluɓe ta. Kanta ta duƙar ƙasa cikin sanyaruar murya ta gaishe su. "Wow! Huwais ƙiri-ƙiri ka hana ni auren ƙanwar nan na ka." Ya furta yana mata kallo tamkar zai cinyeta. Zumbur ya miƙe cikin ɓacin rai ya ce,"Ba na hanaki shigowa ba in na yi baƙi?" "Ka yi haƙuri Yaya, zan tafi ne kuma ina ta kiran wayarka ba ka ɗaga ba." Muryarta ba shi kaɗai ba, duka mutanen ɗakin sai da ta ɗauki hankalinsu. Sai a lokacin ya tuna wayarsa, na cikin bedroom ɗinsa, tun safe da Wajnah ta kira ya yi wurgi da wayar. Hannunta ya ja cikin tsananin jin haushin yadda suke kallonta. Bedroom suka shiga. "Kai anya na taɓa ganin mace mai kyau irin ƙanaar Huwais?" Adnan ya faɗa shakku. "Dole ya rinƙa kishinta sosai. Wannan fulawar tun da babu aure a tsakaninsu, dole ya kula da wanda zai ba shi ya amanarta." Sudais ya ce. "Yayana, zan tafi saura minti ishirin mu haɗu da mahaukacin masoyi." Idanu ya zura mata na tsawon lokaci ya kasa cewa komai. Kwalliyar da ta yi da kyaunta, suka tafi da imaninsa. Ji yake kamar ya rungumeta ta rarrashe shi. "Har kin yadda da shi, da ya ce zai zo? Gani nake kamar yaudararki yake yi. Kuma in har da gaske yake yi gida ya kamata ya zo. Ki haƙura da shi ki manta shi a cikin rayuwarki." Raurau ta yi za ta yi kuka, sam ba ta son ya hana ta tafiyar."Don Allah ka barni na je, ni da Afrin zamu. Kasan Ummu ta hana ni kula sa, matuƙar ta ji ina tare da shi ranta zai ɓace."Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa. "Ok, ni ban ce kiyi mini kuka ba." Ya ce yana xare hannunsa. "Yauwa Yayana, sai na dawo. A ɗaura aure lafiya." Tsaya ya yi, tare da zura hannunsa a cikin aljihun wandon, kayan baccin da yake sanye da su ba tare da ya ce mata komai ba. Har ta buɗe ƙofar za ta fita, sai kuma ta tsaya tare da ƙare masa kallo. "Yayana, ango sukutum guda bai yi wanka ba?" Ɓata fuska ya yi, jin abin da ta ce tare da gyara tsayuwarsa. "Yauwa, gara ki san ya shi ya yi wankan, domin tun ɗazu muke fama da shi, ga kayan shi can wanda Affan ya kawo ya ƙi sakawa." Cewar Najib da ya shigo. Ɓata fuska ta yi tare da kama hannunsa."Don Allah ka yi wanka..." "Je ki kar ki ɓata masa lokaci kinga lokaci ya kusa." "Pleas.." "Hilah, ki je na yi miki alƙawarin zan yi." "Promise?" "Sure," Ya ce mata to sai ka shiga bari na haɗa maka ruwan wankan. Da sauri ta nufi bayinsa, wanda ko minti uku ba ta yi ba ta fito. "Yayana, na haɗa maka. Ka yi mini addu'a zuciyata na bugu." "Fatan alkhairi sis." Ya furta cikin wani irin yanayi. Ba tare da ta kula ba ta fice da gudu. Kallon ƙofar da ta fice suka yi." Ka cutar da yarinyar nan Huwais! Shin me kake tunanin za ta ji in har ba ta gan shi ba?" "Za ta ji babu daɗi na yi kuskure, amma yanzu zan tura mata da tsaƙon haƙuri, kuma ba zan ƙara kiranta ba." "Hakan shi yafi," Da ya shiga cikin bayin sai ya tura mata da tsaƙo kamar haka; Ina ba ki haƙuri bisa laifin da na yi miki. Haƙiƙa na cutar dake, amma soyayyarmu ba za ta yiwu ba.In a roƙon ki yafiya don a yau zan bar Ƙasar nan ki yafe mini na ɓata miki lokacin da na yi. Sai dai ina son ki sani ina matuƙar ƙaunarki daga Muhammad na ki. Sai ya tura hoto wanda daga baya ya goge. Wayar ya ije cikin ƙunci sai kawai yaji hawaye na zubar masa a ƙunci. "Da gaske ba zan auri Hilah ba za ta zamo mallakin wani? Innnalillahi wa inna ilaihir raju'un!" Ya furta a cikinn zuciyarsa. Wankan ya yi, sannan ya shirya cikin tsadaddiyar shadda. Haƙiƙa ya yi kyau duk da ramar da ya yi bai hana shi kyawu ba. Yana shiga cikin gidan, abokan wasa suka yo kanshi wanda ko murmushi ya kasa yi musu. A mota Hilah da take tuƙi cikin rashin natsuwa ta waiwayo ta kalli Afrin ta ce,"Har yanzu gabana faɗuwa yake yi, ji na ke kamar a mafarki zamu haɗu, da mahaukacin masoyina. Ko ya ya haɗuwarmu zai kasance? Ina fatan wannan haɗuwar ya zama sanadin da zai jagoranci zamanmu a inuwa ɗaya." "Amin," Afrin ta ce cikin zaƙuwa, domin ta ƙosa ta ganshi wanda ya sanya ta fara samun saɓani da ƙawarta. Parking suka yi ta tsaya tare da fitowa. Ganin babu motarsa a inda suka yi za su haɗu ya sa ta jingina da motar ta ɗan bashi lokaci ƙila yana hanya. Minti goma sha biyar bai iso ba, sai ta ɗaga waya don ta kira shi. Gabanta ya faɗi jin wayar a kashe, saboda ko da safe sun yi waya. Datar wayarta ta kunna, tare da shiga Whatsapp don ta yi masa magana. A nan ta tsinci tsakonsa da sai da ta yi taga-taga za ta faɗi Afnan ta riƙe ta. Hawaye shar! Suka wanke mata ƙuncinta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta tare da dafe kanta da take jin juya na ibanta. "Lafiya Hilah?" "Don Allah ki riƙe ni kar in faɗi." Da sauri ta kamata, ta buɗe murfin motar ta shigar da ita, ganin yadda take haƙi kamar wace ta yi gudun famfalaƙe. "Wayyo Allahna!" Ta furta tare da rushewa da kuka. "Lafiya, don Allah ki yi mini bayani." "Mayaudari ne mahaukacin masoyi! Ya turo mini da tsaƙon, na manta da shi a rayuwata zai bar ƙasar." Jikin Afrin ya yi sanyi, har ta kasa cewa komai, musamman yadda ta ga ta ruɗe matuƙa ta fita hayyacinta. "Don Allah ki natsu, ni dama tuntuni zuciyata ba ta aminta da shi ba, saboda bai kamata ki mallaka masa zuciyarki ba tare da haɗuwa ta zahiri ba.!" "Ya cuce ni ya sanya mini soyayyarshi ya guje ni ya zan yi?" Ta yi mata tambayar tare da kama hannunta. Wayarta ta zaro ta danna numbar Huwais, da yake cikin taro, zuciyarsa a cinkushe tunanin halin da za ta shiga yake yi. Ganin kiranta gabansa ya faɗi matuƙa. Ya kasa ɗaukar kiran har sai da ta yi masa yafi goma. Ganin ba za ta daina ba, ya kai hannu zai kashe sai ya ga rashin adalcin yin hakan. "Ya Huwais, mahaukacin masoyi mayaudari ne, ya tura mini da tsaƙo na manta da shi ya bar ƙasar." Ta furta cikin tsananin kuka. Rintse idanunsa ya yi, cikin wani yanayi yana jin babu daɗin yaudararta da ya yi, saboda shi da zaɓin da ya wuce haka. "Ni ma na zama mahaukaciya kamarsa, tun da na aminta da soyayyarsa." Ta ƙarasa faɗin hakan cikin kuka ganin ya ƙi cewa komai. "Ki natsu Hilah, ki bawa Afrin motar ta tuƙa ki ku da... Ko kuma ki faɗa mini inda kuka na zo." Wayar ta miƙa wa Afrin." Ki yi masa kwatance ba zan iya ba." Afrin ta yi masa kwatance tare da kashe wayar, tana rarrashinta da take kuka kamar ranta zai fita. Wani irin ƙaunarsa take bijiro mata ganin ta rasa shi. Duƙawa a gurin ta yi, ta saki kuka duk irin rarrashinta da take yi ta tashi taƙi. Huwais kuwa cikin tashin hankali ya miƙe xai fice. "Ina za ka ga baki kana da su?" "Ka kula da su, ina zuwa Najib." Ya furta hakan ba tare da ya amsa kiran ya juya ba. Yana isa guri ya buɗe motar ya fito. Tana ganinsa, ta fashe da kuka tare da miƙe wa ta isa gareshi ta faɗa jikinsa. "Ba zan yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata ya yaudare ni." Kama hannunta ya yi suka shiga motar bayan ya bawa Afrin umurnin ta tuƙa motar ta dawo gida. Ganin irin kukan da take yi, ya yi matuƙar daga hankalinsa matuƙa. Yana tuƙi amma shi kansa ba shi da natsuwar da zai mayar da hankalinsa ga titi. Kukan na ƙara mishi ƙunci a zuciyarshi sosai, musamman in ya tuna shi ne sanadin zubar hawayenta. Gangarawa ya yi ƙasan titi ya sauka, tare da paking ɗin motar ya kifa kansa a sitiyarin "Ya Huwais, ba zan taɓa yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata. In har ya san ba ya ƙaunata mai xai sanya ya shigo cikin rayuwata?" Kukanta ya ƙara tsananta bayan ta furta hakan. Jiyowa ya yi yana kallonta, yadda ta ci uban kuka, abin ka da farin mutum fuskarta har ta canza ta ƙara haske. "Hilah," Ya kira sunanta can ƙasar murya, wanda ya sa ta ɗago kanta da sauri tana kallonsa. Girman idanunta da suka canza kala, ya sanya ya kasa rarrashinta da ya yi ninyar yi, wanda ganin hakan ya sanya ta ci gaba da kukan har da ƙara sauti. "Please, don Allah ki daina kuka domin zuciyata na zafi." Ya furta cikin sanyin murya. Jin ta rage sautin kukan, ya sanya shi buɗe motar ya fito. Ta inda take zaune ya zagaya ya buɗe motar. A gabanta ya tsuguna yayin da ya yi narai-narai da fuskarsa. "Kina son damuwa ya sanya na mutu kuma ki ga hawayena ko?" Ya yi mata tambayar cikin wata irin murya tare da saukowar tagwayen hawaye a fuskarsa. Hankalinta ya tashi sosai! Da sauri ta share hawayenta tana kallonsa. "Don Allaah kar ka yi kuka na daina." Ajiyar zuciya ya yi lokacin da ya ji muryarta na faɗin haka. "Ina jin rayuwata wani iri Hilah. Yau ake mini auren dole, kuma ƙanwata wacce na fi ƙauna tana cikin wani yanayi. Ban san da wani irin kalamai zan rarrashe ki ba, amma na yi miki alƙawarin nemo mahaukacin masoyi duk inda ya ke, tun da na fahimci ya riga ya sace zuciyarki." A yadda ya yi maganar, ta kasa gane ko bai ji daɗin irin yadda ta nuna tashin hankalinta ba ne, ko kuma tsananin tausayin halin da take ciki, ya sanya shi shiga cikin yanayin. "Ka yi haƙuri ka gafarce ni, na sanya mahaukacin masoyi a raina, amma halayensa da iya kalamansa suka sanya na mallaka masa zuciyata ba tare da dogon nazari ba, kuma Yayana, duk wanda zai shiga rayuwata, ba zan taɓa ba shi matsayinka ba." "Na fahimta yadda kike ji, da kuma yadda soyayya take tasiri a zuƙatan masoya, ba tare da tsimi ko dubara ta masoya ba. Sam ban yi miki mummunan fahimta ba, saboda ni ma ina jin kwatankwacin ɗacin da kike ji." Miƙewa ya yi, tare da sanya hannu sa ya riƙe murfin motar, sai kuma ya saki ya kama gefen hijabinta. "Share hawayenki ƴar ƙanwata kin manta na gaya miki matuƙar ina raye ba za ki taba yin kuka ba?" Ɗaga masa kanta ta yi tana murmushi tare da saukowar hawaye a fuskarta. Gefen hijabinta da ya ɗauke hawayen da suke zuba, ya ƙara sanyawa ya ɗauke mata wasu da suka ƙara zubowa. Rufe motar ya yi, bayan ya sakar mata murmushi, ya zagaya ya koma ta bangaren mai tuƙi ya shiga. Bayan ya tada motar sai ya tsaya yana kallonta yadda ta ƙurawa titi idanu. "Yayana, ina sonka." Ta furta daidai lokacin da ta juyo ta kalle shi. Rintse idanunsa ya yi tare da jin wani irin tsau a ransa. "Ba irin wannan soyayyar na ke so ba Hilah;wace za ki zamo murfin asirina kuma farincikin rayuwata uwar ƴaƴana." Murmushin ya mayar mata sannan ya fara jan motar. "Ni ma ina sonki ƙanwata." A hanya suna tafe Hilah ranta a ɓace. A ranta tana jin in har ya ƙara kiranta, sai ta yi masa rashin mutunci, duk da cewar ba halinta ba ne. "Mai ya sa zai guje ni bayan ya yi mini alƙawarin kasancewa a tare da shi? Shi kenan ya guje ni na rasa shi har." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 16 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Mai ya sa zai guje ni bayan ya yi mini alƙawarin kasancewa a tare da shi? Shi kenan ya guje ni na rasa shi har abada?" Ya zan yi da soyayyarsa da ta shige mini zuciyata. Wayyo Allah ka dawo mini da shi a cikin rayuwata, domin shi ne irin mijin da nake masifar so." Haka ta rinƙa addu'a har ta fara jin sauki a cikin zuciyarta. A maimakon ya kai ta gida, sai ta ga ya ɗauke hanya. Gurin shaƙatawa ya kai ta mai kyau, ya kashe motar ya fito tare da zagayowa inda take. Hannu ya miƙa mata bayan ya buɗe motar. "Ya Huwais, mai za mu yi nan, kar ka manta yau ne fa auren ka? Mutane na can na jiranka." "Karki damu, farincikin ƙanwata kawai na ke so." Ya ce mata tare da kama hannunta da ta miƙa masa. Cikin gurin suka isa, wanda wurin ya yi kyau matuƙar haduwa iya gaya! Hilah ta sha zuwa gurin, domin yana ɗaya daga cikin guraren shaƙatawa da take so, kuma ya ke yawan kawo su. Siyayya ya fara yi mata har sai da ta riƙe masa hannu. "Don Allah ka bar kashe kuɗinka Yayana, hidima ce a kanka. Ko ka manta yanzu kai mai iyali? Ba zan so Anty Wajnah ta sha wahala a gidan ɗan'uwana ba." Ta faɗa cikin sanyin murya tare da riƙe hannunsa. Harararta ya yi, sai kuma ya ƙwace hannun ya ɗauki ƙaton biskit, wanda yasha cakulate ya saka a kwandon. "Kar ki damu farincikin ƙanwata kawai na ke so. Sam ban damu da kuɗina su ƙare ba, matuƙar hakan zai sanya ki farinciki." Murmushi ta yi tare da jan hannunsa suka fara tafiya. "Haƙiƙa ka zamo ɗan'uwa mai kau da damuwar ƙanwansa. Fatana na samu miji mai irin kyawawan halinka da nagarta, wanda hakan yana da nasa ba da fara soyayyata da mahaukacin masoyi, saboda yana da kyawawaan ɗabi'u irin naka." Ba tare da ya ce mata komai ba, ya fara tafiya, saboda in har bai bar gurin ba, zuciyarsa za ta iya fallasa abin da ke cikin zuciyarsa, saboda yabansa da ta yi. Ganin haka ta fara tafiya da sauri har ta kamo shi. Daga gurin da ake sayar da kayan maƙulashe gurin shaƙatawa ya kai ta. Tana son ta yi masa maganar su koma gida, amma in ta buɗe bakinta sai ya tsareta da idanunsa, masu kama da an zuba zaiba sai ta kasa cewa komai. Ganin an ɗauki lokaci suna gurin, kuma ga Najib sai kiran sa a waya yake yi, wanda daga ƙarshe ya kashe wayar ya yi gabakiɗaya. Wayar Hilah ce ta yi ƙara alamun ana kira. Da sauri ta duba mai kiran. Kamar yadda ta ayyana Ummu ce. Ilai kuwa ita ce. Da sauri ta kanga wayar a kunnenta."Kina ina tun rana ban ganki ba, kacaniyar biki ya ɗauke mini hankali, ban lura ba ki cikin gidan ba, sai yanzu da na zo ɗakinki?" "Na raka ƙawayena ne Ummu." Ta shirga mata ƙaryar hakan, tana kallonsa da hankalinsa ya ɗauku gurin tuƙi kuma yana sauraren mai za ta ce. "Ok, to ki yi sauri ki zo ina nemanki." "To Ummu." Ta faɗa tare da ije wayar. Waiwawo ta ya yi yana kallonta, daidai lokacin da take share sauran hawayen da yake maƙale a fuskarta. "Ya kamata ki wanke fuskarki in da hali ki yi make up kar Ummu ta gane halin da ki ke ciki." Babu musu ta buɗe jakarta, ta ɗauko kayan kwalliyar wanda ganin haka ya yi parkin tare da kashe motar. Fita ta yi zuwa waje ta wanke fuskarta ta fito A ƙofar gida ya ije motarsa ta shiga ciki shi kuma ya yi bangarensa. Najib da yake zaune cikin tsananin ɓacin rai, da waya a hannunsa. Layinsa yake ta gwadawa amma a kashe. "Ba ka da hankali ko Huwais? Shin ka san abin da ka aikata yau kuwa? Wannan wulaƙancin da ka yi mana, ko ni kaɗai ka yi wa da na san halin da kake ciki ba zan ji daɗi ba." Najib ke magana cikin tsananin ɓacin rai yana kallonsa da ya buɗe ƙofa ya shigo. Shiru ya yi masa, ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa kan kujera ya zauna jaɓar tare da sakin ajiyar zuciya ya dafe kansa. "Ina magana ka yi shiru? Wallahi ji na ke kamar na rufe ka da duka, saboda takaicin abin da ka aikata. Just see the time, this isn't good." Jajayen idanunsa ya watsa masa, tare da miƙewa bai ce masa komai ba zai wuce. "Sam bana jin daɗin abin da kake mini da halin da ka sanya kanka. Ya kamata ka farka da ga mafarkin da kake yi. Toxarcin da kake yi wa yarinyar nan ya isa haka. Ta bani tausayi da ta kira ni tana kuka. Don Allah ka tausaya mata ka amshe ta a matsayin mata, domin aurenku an riga an ɗaura yanzu tana da haƙƙi mai girma a kanka." '"Please, I need my space." Ya ce tare da yin hanyar ɗakinsa yana tangaɗi kamar wanda ya sha giya. Najib takaici da ya ibe shi gabansa ya sha. "I will inform Ummu, Huwais. Bana son ka kai ni iya wuya, domin zan sanar mata da duk abin da ke faruwa. Haka kawai ka sanya wa kanka damuwa da Hilah, don Allah kaɗai ya san halin da take ciki.". "Then go ahead." Ya ba shi amsa tare da kaucewa, zai shige ɗakin duk da cewa ya ji tsoron abin da ya faɗi. Tsaki ya yi, tare da kaucewa ya ba shi hanya ya shige ɗakin ya rufo ƙofar garam Sharaf! Ya faɗa gado yana mai da numfashi, yayin da cikin zuciyarsa Allah kawai ya san halin da yake ciki. "Ya kamata ka miƙe ka shirya ka san dinner ɗin nan ya kamata a fara da wuri." Tsaki ya yi tare da janyo wayarsa yana kiran numbar Hilah ba tare da ya tanka masa ba. "Hello, ƙanwata." Ya furta cikin sanyin murya. "Na'am Yayana," Ta bashi amsa tare da saukar da zafafen hawaye a ƙuncinta. "Har yanzu kuka kike yi ko?" Ya yi mata tambayar kamar yana ganin hawayen. "A'a, kawai ina jin zuciyata kamar za ta fashe in har na tuna da cutar da zuciyata da ya yi." "Ba na yi miki alƙawarin nemo miki shi ba, ko kina tunanin ba zan iya share miki hawayenki ba?" "Ina jin babu daɗi ne, amma na san kai Yaya ne da ya cike ko wane gurbi." "To shikenan, ki daina kuka ki ci abinci ki kwanta." "To, amma sai dai bana jin zan iya cin komai. Yaya Huwais, yau rana ce mafi daraja. Ranar da kake yin aure ya kamata ace na fi kowa farinciki, amma sai na tsinci kaina akasin haka. Ina maka murnan samun abokiyar rayuwa, Allah ya ba ku...." "Ina fatan Ummu, ba ta yi miki faɗa ba?" Ya katse ta yana faɗin haka don ba ya son maganar. "Eh, saboda yau tana cikin farinciki matuƙa, saboda kallonta ka yi kawai za ka tabbatar da hakan." "To ki ci abinci kisha magani ki kwanta, ko na zo na baki? Na san ba kya son magani." Dariya ta yi." Kai haba! Gidan a cike yake Yaya, zan sha da kaina." "Ok, to ki kular mini da kanki. Ni ma wanka zan yi na samu na kwanta." "Yaya, dinner ɗin fa..." Katse wayar ya yi jin tambayar da za ta yi masa. "Wallahi inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan." Cewar Najib cikin tsananin ɓacin rai. "Tun da aka fara shirye-shiryen bikin ka ban huta ba Huwais! Wannan ko ni zan ƙara aure iyakan wahalar da zan yi kenan. In ba ka tausaya mini ba, ka tausaya wa matata da ke fama da laulayi. Ƴan matan amaryar kamar za su yaga ni, suna tambayata inda na ɓoye ango. Yanzu kuma sai ka ce ba za ka je dinner ba?" Jin ya yi shiru yana kallon wayarsa wanda ya tabbatar hoton Hilah yake kallo, ya sanya shi fara duba contacts a wayarsa yana ƙoƙarin nemo numbar Ummu. "Ba zan ɗora wa kaina wahala ba. Kai da aure ni da shiga damuwa. Ummu zan kira na sanar mata da wulaƙancin da kake yi a wataƙila ta sanya ka kaje." "Bana son wulaƙanci Ummun za ka kaiwa ƙarata?" "To ya kake son na yi Huwais? Kai ma ka san iya rufa maka asiri ai na yi." "Bana jin zan iya halatar dinner ɗin. Xuciyata xafi take yi na yaudararta da na yi. Halin da ta shiga yau na ji babu daɗi da tsanar kaina." "I warned you! Na gargaɗe ka several times, amma ka ƙi saurare. Don haka yanzu kai za ka ji da lamarin ai dama duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan duka. " "Bari na yi wanka na shirya na je, amma duk abin da ya faru ka yi kuka da kanka." Ya ƙarashe maganar tare da shigewa bayi. Najib ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, domin ya ƙosa a kammala bikin ya huta da kiran Wajnah. Bayan ya fito ya shirya cikin shadda mai kyau. Kayan sun amshi jikinsa sai ƙyalli yake yi.. Wayarsa da ke kan dressing mirrow ya ɗauka. Numbarta ya kira tare da kanka wayar a kunnensa. "Yayana, kuma angon Anty Wajnah." Ta furta da dariyarta ƙasa-ƙasa wanda ya san ta yi ne don ya ɗauka babu abin da le damunta. "Kina ina?" Ya yi mata tambayar yana sanya handsfree a wayar ya ije ta kan gado yana ɗaura agogo. "Ina harabar gida ni da su Umnah da Yaya Naufal za mu tafi." "Ki jira ni yanzu zan fito mu tafi a motata." Jin abin da ya ce ya sanya ta zare ido da sauri. "Ka rufa mini asiri! Ango kake yau. Kamata ya yi ka je ka ɗauki Anty Wajnah ba ni ba." "Na damu da halin da kike ciki ne kina buƙatar na..." "Am ok Yaya, karka damu ka je ka ɗauko ta, kuma in har Ummu ta ji a motarka na tafi za ta yi..." "Kin..." "Please Ya Huwais, I insist!" Ta furta cikin muryar shagwaɓa. "Kashe wayar ya yi da jan tsuka mai ƙarfi. "Ƙanwarka ta fi ka hankali da sanin abin da ya kamata, ko da yake kai kasan kana cikin haukar soyayya shi ya sa." Najib ya ce tare da ɗaukar wayarsa ya yi masa tsaye aka don ya miƙe su tafi. Bisa dole ya miƙe suka tafi. A motar Najib ne suka tafi. Tsananin ɓacin rai ya ninku kan kyakykywar fuskarsa. "Na gaya maka ba zan je a ɗauko ta da ni ba, amma shi ne za ka kawo ni gidansu?" "Don Allah karka kunyata yarinyar nan a gaban ƙawayenta." Najib ya ce ba tare da ya amsa tambayarsa ba. Ƙara tsuke fuskarsa ya yi yana danne-danne a wayarsa, ganin ta fito ita da ƙawayenta. "Amarya ba kya laifi." Cewar Najib bayan ya fito ya buɗe mata bayan mota. Murmushin yaƙe ta yi, yayin da burinta ta yi tozali da angonta wanda tun da aka fara hidimar bikin ba ta ga ƙewarshi ba. Wani wawan ajiyar zuciya ta saki, lokacin da ta hango shi a hakimce yana danna wayarsa tamkar basarake. "Ni ban san wane irin mutum bane angon nan, sai rowarshi ake magana. Bari dai na ganshi sai na gane ko kina ɓoye shi ne don kar ayi miki ƙwace." Ƙawarta Hindatu ta furta tare da duƙawa cikin motar. Da sauri ta ɗago kanta, don ya firgitata musamman yadda ya haɗe girar sama da ƙasa babu fara'a. "Wai wannan miji na ki ai dole ki yi rowarshi.Kyawu kamar shi ya yi kansa." Ta ce tana mamakin inda ta samo shi duk da ita ma Wajnah ba baya ba, domin har ta fishi hasken fata. Sai dai na shi zallar kalar fatar ce, ita kuma tana haɗawa da shafe-shafe. A hankali ta shiga cikin motar, tamkar ba ta son ta shiga. Kallonsa ta ƙara yi tana jin kamar ta ji ta a ƙirjin shi yadda ya yi kyau. Wani irin wawan ajiyar zuciya ta furta ganinsa domin Allah ya jarabce ta da ƙaunarsa. Najib ya rufe motar yana faɗin,"Ku shiga ga motoci nan birjik sai mun haɗu a gurin dinner." "No, bamu buƙatar mota saboda ina da tawa." Cewar Hindatu tana wani yauƙi. Shiga cikin motar ya yi jin abin da ta ce. Ya kunna motar ya fara tafiya a hankali. Wajnah shiru tana sanya ran zai yi mata magana, musamman turaren da ta yi amfani dashi na sace zuciyar miji, amma sai ta ga ko arziki kallo ba ta samu ba, yayin da hankalinsa ke kan waya. "Habibina," Ta furta can ƙasa-ƙasa da wata irin murya kuma cikin salo da ƙissa, amma yadda kasan da gunki ta yi. Cikin tsoro ta sanya hannu za ta kama hannunsa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 17 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Cikin tsoro ta sanya hannu za ta kama hannunsa. Tamkar za ta ɗora masa wuta, ya janye hannun tare da watsa mata mugun kallo, wanda ya sanya ta yi saurin ɗauke hannunta zuciyarta a jagule. A haka suke tafiyar, babu wanda ya ƙara magana sai Najib da ya ga shirun ya yi yawa, ya kunna waƙar Umar M Sharrif ya sanya sauti. Huwais rintse idonsa ya yi cikin wani yanayi. Yana jin yadda kiɗan da waƙar suke sanya shi cikin shauki mai wuyar fassarawa. Surarta yake ayyanowa yana fatan ina ma a ce da ita ce a cikin motar nan. Ƙamshin turaren Wajnah da ya ƙara sanya masa ciwon kai, da ƙarar sautin waƙar suka ƙara birkita tunaninsa. "Please Najib, ka kashe waƙar nan tana sanya ni ciwon kai." "Na rage dai saboda na san kanka ya ɗau hayaniyar mutane. Karka manta yau ranar farinciki ne a gareka." "Sosai Najib! Allah kaɗai ya san farincikin da na ke yi na samun sa a matsayin miji, domin na san na yi dace." Wajnah ta furta tana masa mayataccen kallo wanda ko kallonta bai yi ba, ballantana ya san abin da take yi. A lokacin da suka ƙaraso gurin, Wajnah ta yi tunanin zai kama hannunta ko don ya cireta kunyar ƙawayenta da suke damunta da tambayar angon, amma sai ta ga saɓanin haka. Ya nufi ciki yana takun isa tamkar an aiko masa da mala'ikan mutuwa. Da ido Najib ya rinƙa masa nuni da ya kama hannunta, amma sai ya basar ya nufi hanyar shiga. ganin haka ya sanya ta ƙarasa da sauri gurinsa za ta kama hannunsa. Da sauri ya janye hannu tare da ƙarawa da sauri. Ranta ya ɓace har ƙwallah suka taru a gefen idanunta. Da sauri ta yi ma za ta mayar da hawayen ta bi shi suka jera. Suna isa gurin ya ɗauki tafi ina ihu yayin da aka saki waƙar Umar M Sharrif. Hilah yana shigowa duk yanayin da take ciki sai da ta ji wani irin farinciki ya kamata. Wayarta da ke hannunta tana ta turawa mahaukacin masoyi kalamai ta ije kan teburin. Murmushi ta sakar masa, tana kallonsa har lokacin da suka shigo ciki xa su zauna. Ganinta Huwais ya ji wani irin tsau a ransa. Duk da babu wani kwalliya a fuskarta, kuma in har ka yi mata kallon ƙurullah za ka fahimci tana ɗauke da damuwa, amma ta yi kyau kamar a sace ta a gudu. Wani tsadadden murmushi ya sakin mata daidai lokacin da suka zauna. "Anty Hilah, Ya Huwais ya yi kyau sosai. Ki bani wayarki na yi masa vedio recording." Amnah ta faɗi tana miƙa mata hannu. "Ungo ƙaramar wayar ki yi masa saboda ni ma ya yi mini kyau har a tashi zan rinƙa ɗaukarsa hoto. Yayanmu mai kyau ne ko ne, haka matar da ya aura ko?" Ta ƙarashe maganar tare da kama mata kumatu tana murmushi. "Eh kuma sun yi kyau kema kina da kyau sosai." Dariya ta yi bayan ta miƙa mata wayar ita kuma ta tafi. Kallonta yake yi kamar zai cinye ta gani yake duk babu wanda ya kaita kyau. A lokacin da M.C ya fara bayani tare da sanarwa abokin ango zaji ba da tarihin ango. Huwais, ya yi wa Najib nuni da ya zo. "Please, Hilah na ke son ta bada tarihina, domin babu wanda ya sanni sama da ita." Ya furta wa Najib cikin muryar roƙo. "Kana ganin hakan babu matsala?" "Bana tunanin akwai don Allah?" "Ok, shikenan." Ya ce tare da zuwa gurin M.C ya yi masa bayani. Bayan ya gana jawabinsa ya gyara muryar sannan ya ce, "A yanzu za mu kira ƙanwar ango wanda ita ce za ta bayar da tarihin Yayanta." Kowa ya ji wani iri har da ita kanta Hilah. Ummu kuwa sam ba ta ji daɗin haka ba, domin ta san duk shirinsa ne. Ɓata ranta ta yi daidai lokacin da Hilah ta kalle ta. Jikinta a sanyaye ta miƙe, tana kallonsa da yake ɗaga mata hannu don ƙarfafawa. "Gaskiya Wajnah, sai kin tashi tsaye, saboda yadda na ga mijinki na son ƙanwarsa zai iya sakinki saboda da ita." "Ba ki san yadda na tsane ta ba, duk da cewar ƴar'uwata ce, amma wallahi ko kallonta bana son yi, domin da zan samu ko rabin son da yake mata da na ji daɗi." "A to ki dai tashi tsaye dangin miji ba a iya musu, musammman yadda yake ta kallonta yana mata murmushi xai nuna yana sonta sosai." "Ki barni da shi za ki ga yadda zan juya shi. Mai wuyar na mallaka masa kaina." Ta ce cikin ƙuna tana kallon Hilah da take jin kamar ta shaƙeta. A hankalinda natsuwa ta fara bada labarinsa, wanda ya tsura mata idanu yana kallonta. Gurin ya yi tsit ba ka jin komai sai zazzaƙar muryarta da yake tashi a cikin speaker. Zuru ya yi mata da idanu yana jin yadda take maganar cikin harshen turanci. Kallonta yake yi da sha'awa yana mamakin yadda ta san kanshi fiye da shi. A ransa ji yake kamar ya tashi ya rungumeta ko ya sace ta su je can wata duniya daga shi sai ita su yi rayuwarsu. Bayan ta gama bada tarihin, rayuwarsa gurin ya ɗauki tafi da waƙa ban da Ummu da ta ci magani. Aminiyar amarya ta ba da tarihin amarya, sannan aka saki waƙa. An ci an sha an kuma na ta cashewa sai fatan ba da zaman lafiya. Hilah miƙewa ta yi tana rangaji ta fita daga cikin hall ɗin, saboda ƙarar waƙar yana hawa mata kai. Kallo ya bita da shi har fice daga hall ɗin. Tun daga lokacin ya rasa natsuwarsa sai kallon agogo yake yi yana kallon ƙofa. Wani guri wanda ba a jiyo sautin ta samu ta zauna. Gorar ruwan dake hannunta take watsa ma fuskarta. Zama ta yi tare da buɗe bakinta tana shan ruwan. Bayan ta gama ta ije gorar tana kallon ciyayin da suke luf a gurin, kuma suka ƙara ƙawata gurin. Rintse idanunta ta yi cikin damuwa har yanzu in ta tuna da yaudarar da mahaukacin masoyi ya yi mata, sai ta ji ƙwallah na zubar mata. Gefen hannunta ta sanya ta share hawaye tare da sunkuyar da kanta ta cusa a tsakanin cinyoyinta. "Hilah, har yanzu ba za ki cire damuwa a ranki ba?" Ta ji muryarsa da ta yi matuƙar tsoratata. Da sauri ta miƙe tare da waigawa don ta ga inda yake, amma sai ta ganshi a gefen ta yana zaune. "Innalillahi Yaya, yaushe ka fito?" "Hankalina ya kasa kwanciya bayan kin bar gurin kamar yadda na zargi tunani kika fito ki yi." "Don Allah ka koma ciki ƙarar kiɗan ne ya sanya kaina ciwo." Hannu ya sanya ya kama kan yana faɗin," Ayya, sorry bari na yi miki addu'a." "No ka barshi xan je mota na ɗauko magani a jakata." Ta ce tare da sauke hannunsa da ya ɗora saman kanta. "Ok, to mu je na raka ki." "Please, don Allah ka koma" Ta ce cikin wata irin murya kamar za ta yi kuka. "To sarkin kuka bari na koma kar ki yi kuka." Ya ce da sauri tare da juyawa yana waigenta. Har ya bule tana kallonsa. Haƙiƙa ta san yana mugun sonta. Kullum godiya take yi da Allah ya ba ta ɗan'uwa mai tsananin ƙaunarta, wanda ta san ko bayan babu ran iyayensu ba zai bari su wulaƙanta ba. Komawa ta yi ta zauna. Kiran wayarsa ya rinƙa shigowa. Da sauri ta miƙe ganin ya turo mata tsaƙo. Tana komawa gurinta ta zauna, ya saki ajiyar zuciya hankalinsa na kanta duk motsi ta yi sai ya kalleta. Kafin a tashi taron ran Wajnah ya ɓaci matuƙar gaske. Tun da suka je gurin ko kallon kirki ba ta samu ba. Ko da aka kira su yi rawa. Ransa a jagule ya miƙe shi ma don kallon da Ummu ta yi masa ne. Da ma shi rawa ba ɗabi'arsa bane don haka ya yi ƙiƙam kamar soja. Yana ganin yadda Wajnah take rawa kamar za ta karye. Bayan sun gama rawar, aka buƙaci iyayen ango su zo. Ummu ta yi ƙoƙarin manna musu ruwan kuɗi haka Abu. Daga ƙarshe aka kira ƴan'uwan ango. Tun da Hilah ta shigo hankalinsa ya koma kanta.Kuɗi ya ciro ya rinƙa manna mata. Ganin kuɗin da yake manna mata, ya sanya ta fice da sauri daga filin rawar. Ran Wajnah ya ƙara ɓaci har ta kasa jurewa tana harararsa. Bayan an gama dinner suka tattaro suka dawo gida. Daga gurin dinner aka wuto da Wajnah ɗakinta. Cikin tsananin farinciki take kallon gidan da kyawunsa ya yi matuƙar tafiya da hankalinta. Haƙiƙa tsarinsa da yanayin gidan ya burgeta, kuma iyayenta sun yi bajinta ƙwarai! Zama ta yi kan one seater tana kallon Wahida da take shayar da ƴarta mama. "Gaskiya gidanki ya yi kyau sosai! Abin da ya rage miki sai ki kama maigidan da kyau, yadda babu wata ƴar iska da za ta shigo miki gida, domin irin mijinki shi ne mace ke hauka in zai ƙara mata kishiya." "Lallia ma Wahida, har yanzu kamar kallon ƙaramar yarinya kike mini. Kin san yadda na samu har aka yi auren nan? Sau biyu ana sanya ranarmu ana fasawa. Ai yadda na sha fama kafin na shigo cikin gidansa ku ƴan'uwansa sai na ga dama zai rinƙa kula su, ballantana wata kishiya. Ni Allah ya tsare ai gaba da baya zan tsare don no kishiya in my house." Dariya suka kwashe da shi tare da tafawa. "Ai ban ga laifin ki ba Wajnah, don ko ni mijina shi da wata sai dai matan aljannah da ban isa na hana shi ba, amma a duniya babu macen da ta isa na yi sharing mijina da ita, in kuwa ta kuskura ta aurar mini miji sai na nuna mata mijin wata ta aura. Don ba zan yi shukar ƴaƴan itatuwa ba mu ci da wata." Mardiya ta ce. "Yadda mijin ki yake jarumin namiji, dole sai kin zama jaruma in ba haka ba kina ji kina gani za a yi miki sakiyar da babu ruwa." "Duk wacce ta kuskura ta shigo mini gida nice ajalinta, don sai na canza mata kammanni ta yadda ko iyayenta suka ganta ba za su gane ta ba ballantana shi." "Ato ai gara ki kula saboda kula da kaya yafi ban cigiya." "Shi ya sa maganin da Hajiya Zauzau ta bani ta ce na sha ƙwara ɗaya tall! Kin san Allah? Guda uku na shanye." "Kan uban nan! Wallahi babu ruwana in kika kashe kanki, kin san ƙarfin maganin mata na bature?" Cewar Wahida tare da zare idanunta. "Ai in za ka sha giya ka sha ta dubu." Ta furta tana dariya. "Wallahi babu ruwana kar ki kira ni." Dariyar ya yi ita ba ta ce komai ba. Huwais da Najib a gaban Abu suna zaune yana mishi nasiha. "Ƴar'uwarka ce Wajnah, kuma yau ta koma matsayin matarka. Tana da haƙƙi da dama a kanka, wanda in har ba ka sauke mata ba Ubangiji xai tambaye ka. Kana da sani kuma kai ba yaro bane, kasan haƙƙin da Allah ya rataya maka, don haka kar na ji na ga abin ƙi a rayuwar aurenku. Ka riƙeta tsakani da Allah Ubangiji zai jiɓanci lamarinka, sannan ka sani zaman aure bauta ne na Ubangiji ba zaman jin daɗi ko san rai ba. Duk abin da ka yi mata na cutarwa Allah sai ya tamabaye ka, kamar yadda in har ta saɓa maka ita ma Ubangiji zai hukunta ta. Don haka a matsayina na mahaifinka ina mai jawo hankalinka da ka riƙe amanar Allah sai Allah ya jiɓanci lamuranka." Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi, har yana jin hawaye na son zubo masa, jin nasihar da Abu ya ke masa. "Shin ko zuciyata za ta aminta na xauna da ita, bayan bana sonta kuma ban taɓa jin ta burge ni ba?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa. "Na gama za ka iya tafiya, sai dai in mahaifiyarka na da abin cewa." Ya ƙarashe maganar yana kallonta. "Ai ka gama cewa komai, sai dai na ƙara masa da cewar ya kula da ita, ya san cewa ita ƴar ƴaƴata ce, wacce muka fito ciki ɗaya, sam ba zan lamunci ya cutar da ita ba, kamar yadda ita ma ba zan barta ta cutar da shi ba. Ya riƙe ta tsakani da Allah don ɗorewar zumuncinmu " "To ka ji abin da mahaifiyarka ta gaya maka. Ka tashi ka tafi gidanka Allah ya yi maka albarka." Abu ya ce yama kallonsa. Har ya miƙe, sai kuma ya kasa tafiya ya ɗago idanu suka haɗa ido da Ummu, da tun da ya miƙe take kallonsa. Jikinsa ya ƙara sanyi da ya tuna nasihan da suka yi masa, wanda ba ya tunanim zuciyarsa xa ta iya amincewa ya aikata hakan. Ji ya yi kamar ya xauna ya gaya musu wacce yake so, amma ya san a matsayin mahaukaci za su ɗauke shi. "Zan wuce Abu, Ummu ku yafe mini." Ya furta yana share hawayen da ya fara zubo masa. Ummu ce ta zura masa idanu tana ji ita ma tamkar xa ta yi kuka. "Na san abin da ke ranka Huwais, ina matuƙar sonka da damuwa da halin da kake ciki. Sai dai abin da kake so da muradi sam ba mai yiwu ba bane!" Ta furta tana kallon sa cikin tausayawa. "Ma za ka tafi ga iyalinka Allah ya yi maka albarka." "Amin," Ya amsa jin abin da Abu ya faɗa da shi ma ya miƙe yana gayra zamansa. A kasalance yake tafiya Najib na bayansa. Yana fita Ummu ta sauke ajiyar zuciya. Tun lokacin da yaran nan suka mallaki hankalinsu na daina bacci mai daɗi. Haƙiƙa yau zan rama baccin da na daɗe tsawon shekaru ban yi ba." Ta furta tana kallonn Abu da ya ƙura mata idanu sai ta ɗora da ce wa," Ko da yake an sare kan maciji ne ba a yarda gangar jiki ba, domin matuƙar Hilah ba ta yi aure ba hankalina ba zai kwanta ba gabakiɗaya." "Kar ki damu ita ma aure zan yi mata, karatun na ta saura shekara ɗaya ne." Huwais kuwa yana fita ya shiga mota sai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar. Kuka yake son ya yi kuka sai mai ƙarfi. Wataƙila ya samu sauƙin tafarfasar da zuciyarsa take yi, tamkar kwatamin da aka cika shi da ruwan zafin da ya fara tafarfasa za a kaiwa mai jego. Idanunsa sum kaɗa sun yi ja kamar jan gauta. Ji yake wani irin miyau mara daɗi ya taru a bakinsa, wanda ya kasa haɗiyawa kuma ya kasa tofarwa. Ga mamakinsa, sai ya ji hawaye masu tsananin xafi waɗanda suka fi garwashin wuta ƙuna sun wanke masa fuska. "Be a man Huwais! Ka yi addu'a karka karaya." "Na rasata har abada! Ashe dama ba zan aureta ba kullum zuciyata take mini ƙawazucinta!" "Sheɗanne yake ƙawata maka don kawai ya ci galaba a kanka." "No Najib, na yadda da kaina. Soyayar da nake mata ba ta sha'a ba ce. Jikina yana bani kamar a kwai ɓoyayyen sirri ko kuma lamarin da zai iya halasta aurenmu." "Wane hujja kake da shi Huwais? Yarinyar da ita ce ƙanwarka ta uku. A gabanka aka yi rainon cikinta kuma aka haife ta, sannan kai ka yi rainon ta har ta girma. Wace hujja kake da shi wanda zai iya halasta mka ita a matsayin mata?" "Ban sani ba, amma ima sonta ita ce zaɓin raina. Don Allah ka yi mini addu'a zuciyata za ta buga, sam ba zan iya adalci ga matata ba." "Ka ƙoƙarta Allah zai shiga lamarinka."Ya ce masa cikin tausaya. "Ina son na yi sallama da ita. Ina son na ganta kafin na yi bacci. Na san cewa Ummu ta yi mini aure ne, don ta rana ni da ita. Sai dai ta yi kuskure saboda mutuwa ce kawai za ta zamo katanga a tsakaninmu." "Huwais, karka kunna wutar da ba za ka iya kashewa ba, kuma ba ya zama ba ka da mafita a lamarin, bayan ka ɓata sunan ahalinka." Girgiza kansa ya yi, ya kasa ce masa komai domin duk abin da ya faɗa gaskiya ne. Ƙoƙarin buɗe motar ya fara ganin Najib na ƙoƙarin tada motar. "Ba zan iya tafiya ba tare da na ganta ba." Hannunsa ya kama yana kallonsa."Ka kira wayarta karka sanya Ummu ta yi mata faɗa." Kamar umurni ya ba shi, sai ya koma ya yi cikin motar ya zauna tare da ɗaukar wayarsa don ya kiranta. Tana zaune a ɗakinta kan gado ta haɗe kai da gwiya tana hawaye. Abin da mahaukacin masoyi ya yi mata yake ƙara ɓata ranta. Hawaye masu zafi suke ƙara shatato mata a saman ƙuncinta. Wayarta da ke kusa da ita ya sanya ta kai hannu xa ta kashe wayar. Ƙaramin tsaki ta yi domin a tunaninta Hamad ne, amma dai dai ganin mai kiran, ya sanya ta ɗauka tare da yin sallama cikin siririyar murya. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 18 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Wayarta da ke kusa da ita ya sanya ta kai hannu xa ta kashe wayar. Ƙaramin tsaki ta yi domin a tunaninta Hamad ne, amma ganin mai kiran ya sanya ta ɗauka tare da yin sallama cikin siririyar murya. "Ki zo waje ina jiranki muyi sallama." Karo na farko ta ji wani iri a rayuwarta.Ganin Yayanta wanda yake ji da ita da ƙaunarta yau xai bar gidan. Haƙiƙa a rana ta yau ba za ta taɓa mantawa da ita ba, domin ta rasa abubuwa da dama. Ta san cewa duk soyayyar da yake nuna mata zai rage tun da ya yi aure, musamman in ya haihu soyayyar za ta koma kan yaransa. Wataƙila ya manta da ita ba zai damu da lamarinta ba. Tunanin hakan ya ƙara sanya mata damuwa fiye da ta ɗazu, wanda sai da ta ji dama bai kirata don su yi sallama ba. Da sauri ta miƙe, tare da zura dogon hijabinta ƙasa kasancewar kayan bacci ne a jikinta. Ba ta yi fargabar fita ba, saboda Ummu tana can da ƴan bikin da ba su gama watsewa ba. Hannu ta sanya ta murɗa ƙofar get ɗin gidan, daidai lokacin da ya gaji da jira ya ƙara kira. Ganin ta fito ya sanya ya kashe wayar yana kallonta dusu-dusu da hasken watan da bai gama girma ba ya haska gurin Da sauri Najib ya fita daga motar ya koma can baya, wanda hakan ya yi masa daɗi sosai, ta yadda zai samu damar magana da ita sosai. Kallon juna suka yi na ƴan sakanni. Ita ce ta fara cire idanunta ta buɗe motar ta zauna a kujerar gefensa. "Na kasa tafiya har sai na ganki. Ina jin wani iri yau zan bar ƴan gidanmu da gidanmu na koma rayuwa da wata can." "Anty Wajnah ƴar'uwa ce ba bare ba, ka daina kiranta da wata can." Ta furta tana kallonsa. "Haka ne, amma ba kamar jinina waɗanda muka fito ciki ɗaya ba." "Za ka saba da ita kuma ina gaya maka za ka ji daɗin zama da ita." "Hmmmmh!" Ya ce wanda ya sanya ita ma ta yi shiru ta kasa cewa komai. "Zan tafi gidana, amma ki sani duk da Ummu ta yi hakan ne don ta nesanta ni da ku, ba za ta yi galaba ba." "Ummu, fa gata ta yi maka kar ka yi mata mummunar fahimta." "Zan wuce ki yi mini fata na gari. Ina sonki ƙanwata." Hannunta ta zare da ya riƙe cikin nasa."Allah ya xaunar da ku lafiya ya baku ingantacciyar zuriya." Addu'ar da ta yi masa sam ba daɗaɗa masa ba, har ya ji da ya san abin da za ta roƙa masa kenan, da bai roƙi addu'ar ba." "Shikenan, ki kula da kanki, kuma ki cire tunanin mahaukacin masoyinki za mu yi maganar." "To Yaya, Allah ya tsare ka gaida Anty Wajnah sai mun zo." Ba tare da ya amsa ba, ta fito motar wanda ganin haka Najib ya shigo motar suka kama hanya. Sai da suka biya suya spot, sannan suka siya tare da siyan drinks masu yawa suka kama hanya. Bayan sun shiga cikin gidan sauran abokannasu da suke jiransa a ɓangarensa suka fito. Yana ƙoƙarin shiga cikin falon, ya ji darararrakun ƙawayenta wanda ya sanya shi dawowa da sauri ya kalli Najib "Ba na son shiriritar nan ka gaya ma ƙawayenta su tattara su bar mini gida so na ke na kwanta." "Kar ka yi mini haka don Allah. Yau rana ɗaya ka daure mu sayi baki, sanin kanka al'adace ta Bahaushe don haka kar ka wulakanta matarka." Jan numfashi ya yi tare da jan ƙaramin tsaki.Tafiya yake yi tamkar ba shi ba har ya shiga cikin falon. Sallamar su ya sanya suka natsu, yayin da masu gyara zaman gyale su na yi masu ajusting zaman su na yi. Wajnah kuwa jin siririyar sallamar da ya yi, ya sanya ta ɗago idanunta da saurinta zuba masa. Wani iri ta ji a cikin ranta yayin da kwalliyar da ta yi ya tafi da imaninta. Abokannasa suka xauna a sauran kujerar, sai wanda Wajnah take ita kaɗai, wanda hakan ya sanya ba tare da zaɓi ba, ya zauna a kujera. Zamansa ga sanya ta ji ta rasa natsuwarta gabakiɗaya. Ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa suka sanya ta shiga cikin wani irin yanayi. Lumshe idanunta ta yi, tana jin kamar ta kwanta a jikinsa. Cikin dubara ta matso kusa dashi ta yadda jikinsu yana gogon juna, wanda yanayin da ta tsinci kanta ta rasa kasa bayyana shi. Huwais yana jinta, amma bai kula ba sai dabara ya yi ya matsa. Ƙara matsowa ta yi sosai. Ganin ya ƙure kujerar ya sanya shi haƙura a zuciyarsa yana alla-allah a kammala siyan bakin ya kwanta. Yayin da yake wannan tunanin Wajnah tunaninta ya tafi ga yadda first night ɗinsu zai kasance. Tunanin yadda za ta rama wulaƙancin da ya yi mata za ta yi, domin sai ta bari ya shiga hannu za ta nuna masa ita ma mace ce da ranarta. Gabakiɗaya ta rasa natsuwarta. Buƙatar mijinta da magungunar da ta rinƙa sha ba tare da ka'ida ba suke ɗawainiya da ita. Najib ne ya yi gyaran murya tare da buɗe taronnda addu'a. Bayan nan sai kuma aka fara tsokanar juna. Duk maganganun da suke yi bai tanka musu ba, duk da cewar a kanshi da Wajnah suke yi. Wajnar ce kawai ta buɗe baki tana kare shi, da ita wanda hakan ya ƙara ɓata mood ɗinsa, domin ya tabbata da Hilah ce a matsayin amaryarsa, kunya da natsuwarta ba zai sanya ta rinƙa magana haka ba. Tunaninsa ya yi nisan kiwo gurin tunaninta ya ji muryar Najib na faɗin,"To ango, zamu wuce da ƴan matan, sai na ce asuba ta gari. Ubangiji ya ba ku zaman lafiya da zuriya ɗayyiba. " Ba tare da ya amsa addu'ar ba, ya miƙe sai ita ta masa da sauri tana faɗin,"Amin," Ɗago manyan idanunsa ya yi, ya kalle ta jin rashin kunyar da ta yi na amsawa, amma bai ce komai ba ya fara tafiya don ya raka su. Ganin haka ta bi bayansa suna magana da ƙawayenta. Maryam ta kama hannunta tana faɗin,"Don Allah karki manta asubar fari ki kiramu ki gaya mana yadda daren zai kasance, domin bana jin zan iya bacci, saboda ƙosawa na ji yadda ya kasance. Wallahi kin yi sa'ar miji da za ki more rayuwarki, kuma ki ci duniyar aurenku da tsinke." "Karku damu da zarar komai ya wakana zan sanar muku conference calls zamu haɗa duka na gaya muku, ai sam ba zan yi wasa da wannan ranar ba. Wannan gayen sai na nuna masa iyakansa, domin sai ya zamo tamkar bawa a gareni." Dariya suka kwashe dashi tare da tafawa. Najib ya kama hannunsa tare da raɗa masa. "Please, kar ka ɓata muku first night ɗinku. Kana ganin amarya ta shirya duba ga irin yadda take yi kamar ta haɗiye ka. Ka ba ta haɗin kai ku samar mana takwarar Hilah." Ƙara ɓata ransa ya yi jin abin da ya ce."Zuciyata da gangar jikina na Hilah ce." Da sauri ya shige motar jin yadda ya yi maganar da ƙarfi domin a tunaninsa wasu sun ji abin da yake faɗi. Bayan sun fita maigadi ya rufe get, Huwais ya ɗan tsaya a farfajiyar gidan yana ƙarewa gidan kallo. Tun lokacin da Abu ya fara ginin gidan ya sanar masa da mallakinsa ne. Ya yi buri da addu'ar shi da Hilah xa su yi rayuwa cikinfarinciki a cikin gidan, amma sai dai ya san da wuya gurguwa da auren nesa. Yau ga shi da macen da ya tsana a rayuwarsa fiye da komai a matsayin wacce za su yi rayuaar aure a cikin gidan. Ko ya ya rayuwarsu xai kasance, domin ya san gangar jikinsa ta aura, amma zuciya da ruhi na gurin ƙanwarsa abin begensa Hilah Rintse idanunsa ya yi ji yake ina ma ace yau ita ce daga shi sai ita a cikin wannan gidan. Da hannunsu na maƙale da juna za su taho. Bayan sun tafi shi zai ɗauke ta har zuwa cikin gidansu. A wannan ranar sam ba xai barta ta rintsa ba, domin zai kasheta da zazzafar soyayyarsa wanda ba zai sa ta manta da wannan rana ba.. Yana cikin wannan tunanin, Wajnah da ta gaji da jiransa ta fara kiran sunansa, amma ta ji ya yi shiru babu amsa. Hannunsa ta kamo tare da kwantawa a kafaɗansa. "Babyna, ina ta..." Maganar ta maƙale sakamakon tureta da fara tafiya da ya yi. Sororo ta tsaya cikin tsananin mamaki. Abin da yake mata yana mugun ci mata tuwo a ƙwarya, musamnan inta duba ta ga babu inda Allah ya rage ta. Duk da cewar ta san namiji ne ingarma a cikin mazaje. Ita ma babu wata makusa a jikinta da xai sanya ya rinƙa wulaƙanta ta, domin duk da cewar ita ba fara sosai bace, amma ta haɗa da na kanti wanda ya ƙara mata haske mai kyau sosai, don ba ta siyan kashama marasa kyau, kuma dama siyen na gari mai da kuɗi gida. Tana da zubin aje bota kalar jikinta kamar fanta. Don da ka ganta kaga jiki duk madara😄😄😄 Idan kuma magana ake ta ƙira, ta kuma ya haɗa duk wani sura da xai jawo hankalin ɗa namiji gareta. Mace ce wacce ta yi amanna da supplements na gyaran jiki masu kyau da in ka sha magani take take siye. Musamman da bikinta ba ƙaramin siye magungunan ta yi ba. Ƙuta ta yi ganin yadda ya kusa shigewa ya barta. Da sauri ta fara binsa a ranta tana faɗin,"Za ka sani in ka shigo hannu, da xarar ka ɗanɗani zumar jikina za ka manta da ƴar'iskar da take ɗauke mata hankali, domin hatta shegiyar ƴar'uwark da kake so da Ummu sai ta gane ɗanta ya canza." Da sauri ta buɗe ƙofar falon da ya buga da ƙarfi. Huwais kuwa cikin ɓacin rai ya buga ƙofar falon ya shige. Yana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinsa ta ya ƙaraso inda yake. "Haba mijina, ina ta yi maka magana ka yi banxa da ni. Karka manta yau rana ce ta musamman a garemu." Ta faɗa cikin wani irin murya da zai ɗauki hankalin duk wani ɗa namiji tana ƙoƙarin haɗa jikinsa da nata. "Ke!" Ya daka mata tsawa tare da kaucewa ya ɗauki wayarsa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 19 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Haba mijina, ina ta yi maka magana ka yi banxa da ni. Karka manta yau rana ce ta musamman a garemu." Ta faɗa cikin wani irin murya da zai ɗauki ha kalin duk wani ɗa namiji tana ƙoƙarin haɗa jikinsa da nata. "Ke!" Ya daka mata tsawa tare da kaucewa ya ɗauki wayarsa. Ƙarar da ya yi mata, ya santa matsa tana xare idanu. Wayarsa ya ɗauka tare da fara tafiya xai shiga cikin bedroom ɗinsa. Ganin zai shige ya santa ta ƙara sauri ta tsaya a gurin ƙofar. "Wallahi ba xan yarda first night ɗina ya tafi a banxa ba, domin ban san yadda xan yi da maganin da na ɗirka wa kaina ba." Ta furta a cikin zuciyarta tare da kashe masa ido. "Haba Ya Huwais, karka manta ni ƴar'uwarka ne. Ko babu aure bai kamata ka wulaƙanta ni ba. Matarka ce ina da haƙƙi a kanka. Karka ruguza ranar farkon mu domin na yi wa wannan rana tanaji na musamman da ba zamu manta da shi ita." "Ni sa'an ki ne? Kauce ki bani guri." Ya ce tare da sanya hannunsa ya tureta ya shige cikin ɗakinsa. Takaicin abin da ya yi mata ya sanya ta fara hawaye. Ganin kamar haƙarta ba xa ta cimma ruwa ba, bayan cika baki da kuranta wa ƙawayenta yadda daren zai kasance fa ta yi. Tana tsaye sororo tamkar gunki, ya murɗa ƙofarsa ya shiga tare da bugata da ƙarfi. Da sauri ta juya don ta shirya kanta ta shiga cikin ɗakin, domin ta rantse ba za ta bar wannan rana ta wuce a tutan ma"aho ba. Ɗaki ta shiga ta faɗa kan gado tare da sakin kuka. Sai kuma ta miƙe ta tuɓe kayanta ta shige bayi. Wanka ta sheƙa wanda ta ɓata lokacinta tana dirzar jikinta da mayuka masu ƙamshi da kyau. Bayan ta gama wankan, ta zauna zaman shafa. Inda ta ɓata lokacinta gurin ƙyalƙyale jikinta da mayuka da turare masu ƙamshi da daɗin shaƙa. Wata doguwar rigar bacci ta sa mai kyau fari. Rigar har ƙasa take, amma kuma ta na bayyana surar mutum. Ƙara ɗauko turaren da Hajiya Zamzam ta ba ta yi tare da ƙara shafe ko ina na jikinta. Sannan ta sanya a rigar baccin. Wayarta ta ɗauka ta duba kanta a madubi sannan ta rufe ƙofar. A lokacin da ta murɗa ɗakin yana kwance a kan gadonsa, hannunsa riƙe da wayarsa. Bayan ya yi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa kayan bacci. Riga ya sanya da ƙaramin gajeren wando. Kyawawan dogayen cinyoyinsa masu ɗauke da zararan gashi ya kwantar a saman filo, sannan ya kwantar da kansa a ɗayan filon. Kallon hotonta yake yi, yayin da hawaye suke zuba a ƙuncinsa. Hannunsa ya kai ya shafa fuskarta, tare da sanya yatsarsa a saman idanunta, yana shafa idanunta da suke ɗaukar hankalinsa ƙwarai. Ya faɗa cikin kogin tunaninta, ba tare da ya san Wajnah na tsaye tana ƙarewa halitarsa kallo ba. Wajnah kuwa ji ta yi kamar xa ta sume. Haƙiƙa Allah ya yi mata tagomashi da samun miji mai kyawu kuma ɗan gayu, musamman da ta kalli yatsun ƙafarsa sai ta ji kamar ta duƙa ta lashe. "Huwais," Ta ce tare da ƙara matsowa kusa da shi. Da sauri ya miƙe tare da kifa wayarsa domin ya ɗauka ta ga abin da yake kallo. "Ke! Uban me ya kawo ki cikin ɗakina?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai yana zare mata idanu. Wal ta yi da idanunta tare da yi mata fari."Ni da ɗakin mijina sai na tambayi izinin shigowa? Karka manta da kai da duk gidan nan mallakina nane." Tsaki ya yi, tare da da ɗaukar wayarsa ya fita a cikin galary sannan ya ije wayar. Ganin tana matsowa tana son haɗa jikinsa da nata, ya sanya shi matsawa tare da ƙara daka mata tsawa. Yana ganin zallar rashin kunyarta na shigo masa a haka. Ransa ya ƙara ɓaci sosai, ganin rashin kunyarta da tarbiya, domin ya tabbata da Hilah ce mai kunya ba za ta taɓa bayyana surarta ba. "Ya Huwais, don Allah ka bari mu more rayuwar aurenmu. Wallahi na yi maka alƙawarin yin maka biyayya da zama tamkar baiwa a gareka. Ina sonka duk abin da kake son xan yi maka Yayana." "Ba za ki taɓa samun zuciyata ba, domin na gaya miki tun farko baki cikin jadawalin matan da nake so. Sam ba ki yi mini ba, amm kika na ce sai kin aure ni. Ga gidan nan sai ki zauna a ƙarƙashin aurena, amma ni da jikina ba xa ki taɓa mallakarsu ba." Duƙawa ta yi jin abin da ya ce. Jawaye ta fara tare da kai hannu za ta kama ƙafarsa wanda ya janye da sauri ya yana harararta. "Don Allah mijina, ka soni mu zauna lafiya. Ka dubi tsarina da surata babu wacce mace da za ta tsere ni." "Akwai ta ita ce wacce take zaɓin raina kuma na ke sonta. Ko da ace ba ta kaiki sura ba, amma ta fi ki komai a gurina." Ya faɗa tare da toshe hancinsa saboda ƙamshin turarenta dake hawa masa kai. Ganin ya toshe hancin ya ƙara baƙanta ranta matuƙa. Ita da take tunanim ƙamshin zai karkato da hankalinsa, sai ga shi yana nuna baya son ƙamshin. "Wallahi baka isa ba, matuƙar ina cikin gidan nan babu wata ƴar iskar da xa ta shigo gidan nan, in ba so kake mu yi mutuwar kasko dukanninmu ba." "Karki ƙara zaginta domin a kanta xan yi mummunar saɓa miki." "Ka kashe ni in ka so, ai xanfi jin daɗi ranar aurenmu ka yi mini shegen duka, kan babu abin da ya shiga tsakaninmu." Hannu ya ɗaga, sai kuma ya fasa don ya san za ta iya gaya wa a gida. "Dama na san ba ki da kunya, amma wallahi ba xan ɗauki rashin kunya ba." "Matuƙar za ka rinƙa kiran wata banza a gidan nan, ni kuma abin da ya fi banxa zan kirata da shi." "So kike na canza miki halitta." Ya ce tare da komawa ya kwanta. "Ya Huwais, don Allah ka tausaya mini ka karɓe ni a matsayin mata." Ta ce cikin rawar murya jin mararta ya ƙara murɗawa. Tsaki ya yi mata tare da komawa ya kwanta. Ganin haka ya ta bin bayansa ta kwanata tare da rungumeshi ta bayansa. Wani irin wawan ajiyar zuciya ta saki jin yadda gabakiɗaya tsigar jikinta ya tashi. Da sauri ya miƙe yana mata mugun kallo da mamakin zallar rashin kunyarta. "Tashi ki fita ko na saɓa miki." Abin da ya faɗa, ya sanya ta ɗago idanunta, da ƙyar da suka rine suka canza kala. "Don Allah ka taimaka mini ina cikin wani hali." Hannunta ya kama, ya janyota har ƙofar ɗakin ya watsar da ita, tare da mai da ƙofarsa ya rufe. Kallonta kawai ya yi, ya fahimci halin da take ciki. Sai dai inhar jikinsa zai mallaka mata ba zai taɓa ba, domin komai na sa mallakin Hilah ce. Komawa ya yi ya kwanta, yana mamakin yadda ta nuna zalamarta da shan kayan matan da ta yi wanda ya san su suke ɗawainiya da ita. Takaici da baƙinciki suka cika mata rai. Duba ga maza masu kyau da suka nuna suna son aurenta, amma ta nace sai shi. Ga shi ta aure shi yana wulaƙanta ta. Ƙara ta saki jin mararta ya murɗa sai kuma ta fara ciwo. Da kyar ta miƙe tana faɗin,"Na shiga uku! Ya Huwais, don Allah ka taimaka mini xan mutu cikina, marata." "Ya Huwais," Ta kira sunan a gigice jin yadda mararta ta ƙara murɗawa. Huwais kuwa yadda ya ji muryarta ya rikice sam bai damu ba. Kwanciyarsa ya yi tare da kunna karatun qur'ani, ta yadda xai daina jin buga ƙofa da sunansa da take kira. Wayarsa ya jawo ya kunna data ya hau online. Zuciyarsa ke kwaɗaita masa, ya tura mata da tsaƙo, amma wani bangare na zuciyarsa na yi masa gargaɗi. Sauka ya yi dafa kan gado tare da buɗe labulen windon ɗakin. Tsakar gidan yake kallo, wanda hasken wutan lantarki ya haskaka farfajiyar gidan tankar rana. "Anya zan iya daina waya da ke? Kai ina ba zan iya ba, domin ta hakanne kawai na ke samun natsuwa a cikin raina." Ya tambayi kansa tare da furta hakan cikin ransa. "Hilah, ina sonki." Ya ce yana kallon fuskarta a wayarsa, sai kuma ya sanya bakinsa kan nata, ya yi mata kis yana murmushi. Har ya fara yi mata typing, sai kuma ya kashe wayar duka ya ja bargo ya kwanta. "Ya kamata na ba ki lokaci." Wayar kuma ya kunna tare da tura mata tsaƙo. A lokacin da tsaƙon ya shigo, tana zaune a kan sallaya bayan ta idar da sallah tana kuka. Sosai take jin zafin yaudarar da ya yi mata, domin ta ɗauka yadda yake kalamansa da natsuwarsa, da kuma kyautar ban girma da yake mata mutum ne mai nagarta. Ashe mayaudari ne. "Wayyo Allahna! Haƙiƙa ka cutar da zuciyata." Ta furta cikin muryar kuka tana jin zuciyarta kamar za ta yi bindiga ta fito. Wayarta ta ɗauka tana duba duk chatts ɗin da suka yi. Wasu ta yi dariya wasu kuma ta yi murmushi mai haɗe da kuka. "Ina sonka, why za ka yaudare no?" Ta rubuta mishi hakan sai kuma ta ƙara da "Don Allah ka bayyana mini kanka, wallahi na yi maka alƙawarin zan aureka matuƙar kana sona." Ji fa ta yi da wayar, ganin duk tsaƙonnin da take tura masa babu amsa, domin tun jiya lokacin da suka yi alƙawarin xa su haɗu, ya kashe waya bai ƙara hawa ba. Tana ije wayar tsaƙo ya shigo, wanda da sauri ta ɗauka a ranta tana addu'ar Allah ya sa shi ne. Ƙaramin tsaki ta ja, tare da canzawar fuskarta ganin tsaƙon Yayanta ne. "Ya Huwais, ya ke yi? Shi da ya kamata ya kasance da matarsa." Ta yi ma kanta tambayar hakan. Tsaƙon ta duba inda ta ga ya rubuta jamar kamar haka; Ƙanwata, na kasa bacci tunanin halin da kike ciki da kewar gida sun dame ni. Murmushi ta yi sosai tana mamakin ƙarfin zuciyarsa, domin ta yi tunanin duk borin da yake yi da xarar sun keɓe a tare zai ba da kai bori ya hau, kasancewar babu namiji da zai kasance da Wajnah ba tare da ya kware mata ba. Yayana, don Allah ka yi bacci. Ina hadda ne kuma ni ma yanzu zan kwanta.Ta rubuta tare da tura masa tsaƙon sai ta kashe wayarta ta kwanta. A lokacin da tsaƙon ya shigo, hankalinsa ya tashi sosai don bai yi tunanin idanunta biyu ba. Da sauri ya janyo wayar, ya karanta murmushi ɗauke a fuskarsa. Iska ya ja tare da fesarwa. Juyawa ya yi ɗaya ɓangaren ya danna numbobinta don ya kira. "Ba ta yi bacci ba, tana cikin damuwar da na sanya ta. Ki yafe mini Hilah sonki da ƙaunarki suka janyo mini haka. Ransa ne ya ɓace, matuƙa jin wayarta a kashe. Ya san ta kashe ne don karya kirata. Ƙaramin tsaki ya ja, tare da jan bargo daidai lokacin da ya ji Wajnah ta ci gaba da buga ƙofa. Duk yadda ya so ya yi bacci ya kasa.Ji yake gidan kamar ba mallakinsa ba. Miƙewa ya yi ya shiga cikin bayin ya ɗauro alwala tare da shinfiɗa dadduma ya tayar da sallah. Kamar kullum istikhara kan lamarin ya fara. Tun ranar da ya fara sonta yake istikhara kamar yadda ma'aiki ya umurce mu da mu yi in muna son aikata wani abu. Istikhara * Neman zabin Allah, wata sallah ce mai raka'o'ibiyu, wacce yinta sunnah ce mu'akkada (sunnahce mai karfi), wacce manzon Allah ya koyar dasahabbansa ita har tazo garemu kamar yadda al-qur'ani ya iso gare mu, sallace da akeyi yayin neman zabin Allah akan wani al-amari kamar;aure, sayan gida/mota aikin gwabnati da daisauransu, sai dai ita wannan sallar ba'ayin ta a kan abin da ya ke wajibi ko mustahabbi akan ka; kamar neman zabin Allah akan yin azumin ramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitar da zakka, azumin alhamis da litimin da dai sauransu. * Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan sun ci karo, misali: mutum ne yake son yaje umra karo na biyu a lokaci guda kuma yana so ya je wata kasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allah akan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su. * Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikin lamarin sa, to ba zai yi nadama ba In sha Allah. Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159]. * Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce: "Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkumta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibatiamrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaanathumma raddini bihi." "Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari] * Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannan karantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafan koyarwa don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace * Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi. * Wannan Addu'a ta istikhara ana yin tane bayan ka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970]. * Babu wani hadisi daya inganta da yazo dasurorin da ake karantawa, a cikin sallar nemanzabin Allah. * Haka kuma babu wani hadisi da yazo daga Annabi cewa idan mutum yayi istakhara zaiyimafarki ko zaiga wani mutum yana yi masa bayani al-amarinsa. * Babu shakka duk wanda ya yi zai samu natsawa cikin abin da Allah madaukakin sarki ya zaba masa. * Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutane dayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai kaji zuciyar kata qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka farasai kaji zuciyar ka tanutsu da sana'ar. * Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana,ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita ne daga lokaci zuwalokaci har sai ka sami biyan buqata, sannan Ana yin tane ko da lokacin da aka hana yin sallah ne,idan bukatar hakan ta taso, domin ita tana daga cikin "Nawafilul Asbab" - "Nafiloli masu dalili". * Wannan kenan don gane da abunda ya shafi Sallar neman zabin Allah madau kakin Sarki,Muna fatan Allah ya bamu damar Aiki Abin da muke rubutawa da karantawa. Still yanzu ma natsuwa fiye da ta, da ya samu wanda ya ƙara ninka masa ƙaunarsa. Ajiyar zuciya ya saki tare da janyo filo ya kwanta a sallayar. Wajnah kuwa tun tana buga ƙofa, tana kuka tana kiran sunansa, har ta kasa sakamakon mararta da ya riƙe ya murɗe ko numfashi ta kasa. Kallonsa kawai xai sanya ta rikice ballantana da ta haɗa jikinsa da nata. Rintse idanunta ta yi cikin azaba tana kiran sunan Allah. Ta haƙura ne saboda duba agogo da ta yi ƙarfe ɗaya har da kwata. A lokacin ta gane ko kwana ta yi tana buga wa sam ba zai buɗe mata ba. Jikinta ya yi sanyi matuƙar gaske! Domin bata taɓa tunanin bayan auren ba zai iya ɗauke kansa daga jikinta har ya wulaƙanta ta ta. "Wace ce wannan da ta sace zuciyar mijina?" Ta yi wa kanta tambayar tare da jifa da filon da ta danne mararta. Kuka sosai take yi yayin da wani sashe na ɓangaren zuciyarta yana gaya mata Huwais ba zai so ta ba. Hawaye masu zafi suka ƙara kwaranya a idanunta, daidai lokacin da mararta ta ƙara murɗawa. Gurmususu a ƙasa ta shiga yi, tana kiran sunan Allah har ta samu sauƙi. A hankali ta miƙe tana jan ƙafa ta shiga cikin ɗakinta. Kan gado ta kwanta tana nishin wahala da ƙyar. Ta daɗe a haka har zuwa ƙarfe uku. Wayar Wahida kuwa ta kira yafi cikin kwandon masaki. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 20 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Ta daɗe a haka, har zuwa ƙarfe uku. Wayar Wahida kuwa ta kira yafi cikin kwandon masaki. Tun da take ba ta taɓa kwanar wahala ba, domin yadda ta ga dare haka ta ga rana. Har zuwa kiran sallar farko ba ta rintsa ba Kiran sallah na biyu ta ɗauki wayarta, tana dafe da mararta ta kira numbar Wahida, tana adduar Allah ya sa ta ɗauka. Ta cika da farinciki jin wayar na ringing. "Wash! Fahima ki taimaka mini mutuwa zan yi." Ta furta tana nishin wahala. "Innalillahi lafiya?Ai sai da na gaya miki kar ko sha maganin nan da yawa, saboda shegen kafiyarki kika kai kanki kika baro. Allah ya sa bai illata ki ba." Ta faɗa tana mata dariyar mugunta. "Ni in da ma ace wannan ne ya sanya ni wahala sai na ji daɗi, saboda na tabbata kwana zan yi mala'iku suna rubuta mini lada. Wahida ban san wane irin kalar miji na aura ba, domin wallahi jiya kallon kirki ban samu ba, daga ƙarshe ya tura ni waje ya rufe ƙofarsa." Ta ƙarashe maganar tana share hawaye sai kuma ta ɗora da cewa jin ta yi shiru. "Na rantse sai Hajiya Zamzam ta biya ni kuɗina, saboda da na shafa turaren kin san Allah, toshe hancinsa ya yi, baya ta gaya mini haka zai rinƙa bina sai yadda na yi dashi." Matuƙar mamaki ya kama ta matuƙa jin abin da ta ce. "Anya mijin ki ba aljana ta aure shi ba? Domin na ga ko ni da na ke har na haihu, wallahi ina shafa turaren haka oga yake bina ina shan ƙamshi." "Babu wata aljana tsabar ƙiyayya ce da taurin kai. Ba ki ji yadda ya rinƙa kushe ni yana yabon wacce yake so ba. Ni da ya kamata jiya ya zamar mini rama memorable sai ga shi na yi kwanar wahala." Ta ƙarashe maganar tana cije baki. "Ikon Allah, ni kam ban san wane irin miji kika aura ba, amma duk ƙawayenmu da suka yi amfani da shi sun ce ya yi musu." "Wash! Ki taimaka ki gaya mini abin da zan sha na samu na rintse. Jiya sam ban rintsa ba." "Kai amma wannan gayen ya ɓata mana show. Ni da na kasa bacci sai zumuɗi na ke yi Allah ya kaimu gobe musha labari. Kuma wallahi ya ja miki abin kunya, saboda duk ƙawayenmu kowa sai ya ba da labarin first night ɗinsa a group sai ke? Kin san yau daren farkon ki shine topic of discussion ɗinmu." Tsuka taja tare da jin wasu zafafen hawaye sun wanke mata fuska, saboda yau ta yi ninyar babu abin da za ta rage wanda ya faru a tsakaninsu." Wa'iyazubillahi "Ya zan yi? Haka nan zan shirga musu ƙaryar period ɗina ya zo kafin na gama na san yadda zan yi seducing ɗinsa." "Gaskiya ya kamata domin hakan kamar wani abin kunya yake son ya ja miki." "Ya ma isa ina babban yarinya kamata ya ce zai toxarta ni gurin ƙawayena." "Allah ya kyau abu dai yi daɗi ba." Cewar Wahida cikin takaici. "Ko gaya mini abin da zan sha." "Ki sha kanwa za ki samu sauƙi." Ta ce tare da yi mata sallama ta kashe wayar. Sororo ta yi cikin takaici da damuwa. Sai yanzu ta fara dana-sanin gaya mata da ta yi. Ta so ace ƙarya ta shirga musu sai dai kuma hakan ba zai yiwu ba, kasancewarsu ta san su da shegen bin ƙididdifi har sai sun gano gaskiya. Miƙewa ta yi tana tunanin inda za ta samu kanwa amma ba ta gani a kicin ɗinta ba. Wayarta ta ciro tare da sanar mata ta aiko direba da kanwar. Huwais kiran sallar farko ya tashi farka daga baccin da ya ɗauke shi. Miƙewa ya yi bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, sai kuma ya yi salati yana miƙa. Bayi ya shige ya yi wanka sannan ya fito masallacin gidansa. Shi ya ja musu sallah suka yi sannan ya ɗan zauna a masallacin har gari ya yi sha. A lokacin da gari ya waye ya fito daga masallacin ya shiga gida, daidai lokacin da Wajnah ta fito direba ya kawo mata kanwar. Cikin rashin sa'a ya kalle ta wanda ya sanya shi ɗauke kansa da sauri. Dariya ƙeta yake mata a zuciya ganin yadda ta yi wujuju da ita, alamun sam ba ta rintsa ba. Wucewa ɗakinsa ya yi, yayin da ta bishi da kallo tana ji kamar ta jawo shi ta rufe shi da duka. Da idanu ta raka shi har ya shige ɗaki ya rufe ƙofar. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta wuce kicin ta kaɗa kanwar a kofi tasha. Sai a wannan lokacin ta ɗan fara sanun natsuwa ta shiga bayi ta yi wanka da alwala ta fito. Bayan ta yi sallar tana idarwa ta ɗauki waya ta kira Mommy. Tana ɗauka ta fashe da kuka. "Mommy, ban san cewar ƙiyayyar da Ya Huwais, ya ke mini ba ta kai haka! In kika ga yadda ya wulaƙanta ni sai kin tausaya mini. Momy kulle ɗakinsa ya ya bar ni a falo." Tausayin ƴar tata ya kamata da ma ta san xa a rina, wai an saci xanin mahaukaciya. Sam ba ya ƙaunarta su ne suka nace auren. "Kina jina ko Wajnah? Dole sai kin yi haƙuri kin zama jaruma, domin kin san babu so a tsakaninku. A hankali cikin kissa da kisisina irin ta ƴa mace za ki karkato da hankalinsa." "Hmmmm! Ba ki san shi bane, jiya na tsorata da lamarinsa." "Sam karki tsorota ki ci gaba da yi masa duk abin da kika san zai faranta ransa, kuma karki nuna masa kin ji haushi. In muka ga yaƙi canxawa sai mu sanar da mahaifiyarsa ayi wa abin tufka hanci, amma bai kamata daga aurenku afara kai mata ƙorafi ba." "To Mommy, yaushe za ki zo? Har na fara kewarki." Dariya ta yi jin abin da ta ce. "Ina nan zuwa ni da Anty ki Hibba, za ta kawo sauran kayan turaren wutan da ba gaba ma." "Sai kun zo na gode Mommy." Tana gama wayar bacci mai ƙarfi ya kwasheta. Huwais kuwa alla-alla yake gari ya waye ya bar gidan. Tun da ya farka idanunsa suke masa gizagonta, musamman da ya kwana mafarkinta. Yana dawowa daga masallaci, ya shirya cikin shiga mai kyau ya shiga motarsa ya fice daga gidan. Ƙarar buɗe get ɗin, ya tashe ta wanda ya sa ta miƙe a zabure tare da jaye labulen ɗakin tana hangen harabar wajen "Kan uba! Ina wannan ɗan rainin wayon xai je da safiyar nan?" Ta yi wa kanta tambayar cikin mamaki a zuciyarta tana ji kamar ta danna masa ashar. Sakin labulen ta yi, daidai lokacin da ya fice maigadi ya rufe get ɗin yana ɗaga masa hannu. Zama ta yi tana huci kamar mesa, sai kuma ta shige ɗaki fuuu! Ta jawo waya. Har ta fara neman numbar Wahida za ta gaya mata, sai ta fasa tuna yadda take ta cika musu baki, wanda sanin zaman doya da manjar da suke yi, zai iya sanya wa su yi mata dariya, da gulmanta ko da a bayan idanunta ne. Fasa kiran ta yi ta fara neman numbar Ummu sai kuma ita ma wata zuciya ta hana ta musamman da ta tuna maganar da Mommy ta gaya mata. Wayarta ta yi jifa da ita, tare da kwanciya a kan gadon tana birgima! Huwais kuwa, a hanya yana tafe yana tunanin yadda za su kwashe da Ummu, in ta ga ya yi sammakon zuwa gidan, amma duk abin da xai faru sai dai ya faru, domin idanuwansa babu wanda suke son gani sai ita. Saboda tsoron kar ya tashi mutanen gidan a waje ya yi parking ɗin motarsa ya shiga ciki. Kai tsaye falo ya shiga, amma babu wanda ya gani sai ɓuruntu da ya ji a kicin. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya nufi kicin ɗin domin ya san ita ce a ciki. Hilah bayan ta tashi ta shiga bayi sai ta ga ta fara fashin sallah. Gyara kanta ta yi, ta fito daga bayin ta shiga ɗakin su Umnah ta tashe su, sannan ta wuce kicin don shirya abin karyawa. Ita da autar su Ummu, Sauwama suka fara haɗa abincin karyawar suna yi suna hira. Bayan sun gama kammala abincin, suka sanya a cikin fulas sannan suka sanya wanda za su kai gidan Huwais a basket. Hilah na gyara zaman abincin yayin da bakinta ɗauke da tasbihi tana faɗin Subuhanallahi wa bihamdihi wa subuhanallahil azeem. Hadisi ne inagacce wanda ya yi maganar cewa, Kalomi masu sauƙin faɗi a harshe, kuma mafi soyuwa a gurin Allah masu kuma nauyaya mixani. Da wannan hadisi take amfani yawanci bakinta ɗauke da shi. Tana ƙoƙarin ɗaukar basket ɗin ta kai mota ta ɗago idanunta. Turus! Ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallon agogon da ke manne a saman bangon kicin ɗin. Mamaki ya sanya ta kasa magana sai kallonsa take yi. "Yauwa ma za ki je ki kai mota. Ni ma bari na gama dama wa Fitha custard sai na ɗauko mayafina muje, saboda yau nake son na koma Gobbe. Jin ta yi shiru ba ta amsa mata ba, ya sanya ta ɗago idanunta, tana kallon inda take kallo. "A'a ango da sassafe haka, lafiya ko dai Wajnah ce babu lafiya?" Shafa kansa ya yi cikin jin kunya yana kallonta da har yanzu ta kasa magana. "Lafiyarta lau, kewar gida ne kawai ya dame ni. Dariya ta kubce mata jin abinnda ya ce." Daɗi ne ya yi maka yawa kawai Huwais. Kuma in ban da abin ka namiji ne da kewar gida? Ai kamata ya yi a ce Wajnah ta faɗi haka." "Please Anty Sauwama yunwa na ke ji, ni fa tun jiya rabona da abinci." Ya faɗa yana shafa cikinsa. Daga ita har Hilah suka zaro idanu."Ace jiya bikinka amma ka zaina da yunwa? Ita Wajnah aikin mai take yi da ba ta tabbatar ka ci abinci ba kafin ka kwanta?" Taɓe bakinsa ya yi yana ƙoƙarin ɗaukar filet. Hilah kuwa karɓar filet ɗin ta yi cikin damuwa tana faɗin,"Yayana, don Allah karka ƙara horar da kanka da yunwa." Watsa mata kallo ya yi bai ce komai ba. "Kamata ya yi ya tafi da abincin sai su je can su ci, wataƙila Wajnah ba lafiya ba za ta iya musu abin kari ba" "No bari na ci nawa anan."Ya ce yana kallon Hilah wacce ta daina ƙoƙarin zuba masa, jin abin da ya ce ta fara zuba masa. Miƙa masa ta yi sai kuma ta fasa ba shi."Bari na kai maka dinning." Ba tare da ya ce komai ba ya bi bayanta. "Thanks," Ya furta yana kallonta da ta miƙa masa ta tsaya a gabansa tana kallonsa. Bayan Sauwama fa gama haɗa wa ƴarta custard ɗin, sai ta ɗauki kofin ta yi cikin ɗakin Ummu wanda anan suka kwana. Ummu na zaune da carbi a hannunta, tana wa Allah godiya da ya nuna mata auren ta samu guri ta zauna. Lamarin Huwais sai a hankali." Ta ce tana dariya wanda ya sanya ta juyo da sauri yayin da gabanta ya faɗi. "Wai shi da yake da amarya, amma har ya baro ta yazo gidan nan yana ihun yunwa." Gabanta ne ya ƙara faɗi, wanda ya sa ta miƙe cikin ɓacin rai, tana jin kamar ta kifa masa mari. "Huwais ɗin ya baro gidan matarsa yana nan?" "Ki je yana falo yana cin abinci kika sheda, don har mun haɗa abin lari za mu je a kai mas..." Ba tare da ta ƙarasa jin abin da take faɗi ba ta wuce falo da sauri. Turus ta tsaya cikin tsananin ɓacin rai, tana kallonsa da ya kashe Hilah da ke xaune gabansa tana murmushi. Tsananin ɓacin rai ya ƙara kamata. Ji ta yi kamar ta rufe su da duka. "Huwais," Ta kira sunasa da ƙarfi tana huci. Gabansa ne ya faɗi, amma sai bai ce komai ba ya amsa yana kallonta. "Mai ya kawo ka cikin gidan nan da sassafe bayan matarka na gida?" "Ummu, kewarku na yi kuma yunwa na ke ji." "Huwais, zan yi maka rashin mutunci matuƙar ka ce za ka wulaƙanta ƴar yayata." Ta furta cikin tsananin ɓacin rai wanda ya sanya Hilah ta yi maza ta shige kicin. "Ummu, laifi ne don na zo gidan nan?" "Lai fi ne babba, domin yanzu kai magidancinne kuma matarka na buƙatar lokacinka." Shiru kawai ya yi, cikin takaici domin ya san dalilin da ya sa take faɗa. Ummu ta buɗe baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa ta koma ta ɗauki wayarta da take kan gado. Numbar Wajnah ta fara kira. Ringing ɗaya biyu ta ɗauka dama tana kwance a saman gado tana hawaye. "Sakacin na ki har ya kai, ki bari mijinki ya yi sammakon barin gida a washegarin aurenku? Ka da wayewa ta sanya ki kasa kula da mijinki, saboda ga shi ya zo gida yana cin abinci wai yunwa yake ji." Takaici ya sanya ta rushe da kuka."Ummu, Ya Huwais ya toxarta ni jiya, saboda in kika ga yadda na ke buga ƙofarsa ina kuka ya buɗe mini, amma ya ƙi bayan ya yi mini zagin ƙare dangi ya sanar mini da wacce yake so a zuciyarsa." Maganarta suka ƙara ninka tashin hankalinta har ta fara ganin jiri-jiri. "Anya yaron nan na da hankali?" Ta yi wa kanta tambayar sai kuma ta kashe wayar fuuu!Ta yi sama tana huci. "Abu, yaron nan na lura ba zai taɓa nari na na samu sukuni a zuciyata ba. Ina murna na auren da shi hankalina xai kwanta, amma ga shi can a falo yana karyawa Hilah na gefensa." Wani gumi ya tsatso masa kallonta ya yi da sauri tamkar yana son sanin ko ƙarya ta yi masa. Gabansa ne ya faɗi da ƙarfi, saɓanin da tun da Ummu take zafafa lamarin sai yake ganin duk da sauƙi matuƙar aka yi masa aure, don shi a ganinsa sha'awace kawai take damunsa ya ɗora kan ƙanwarsa, amma yanzu da yake da matar da zai sauke buƙatunsa sai hankalinsa ya tashi kwatankwacin kayan masarufi. "Nufinki yanxu yana gidan nan?" "Ka je ka ganin ma idannunka, wallahi in har ba mu yi wa Hilah aure ba, sai ya janyo mana abin da xai wargaza farincikinmu." Miƙewa ya yi, ba tare da ya ce mata komai ba, ya zura jallabiyarsa fara ƙal, ya fita wanda ganin haka ta bishi. Huwais ganin ta yi hanyar ɗakinta gabansa ya faɗi. Shi kansa mamakin ƙarfin halinsa yake yi, domin duk abin da yake aikawatawa yana jin tsoron iyayen na sa. Gyaran muryar da Abu ya yi, ya sanya shi tashi da sauri gabansa na faɗi ya ce,"Ina kwana Abu?" "Kana da hankali Huwais? Kan me za ka baro ƴar mutane da sassafen nan ka zo gida?" "Umm..." "Bana son sakarci." Ya katse shi yana faɗin haka sannan ya ɗora da ce wa,"Ma za ka tashi ka tafi gida." Miƙewa ya yi ba don ransa ya so ba zai fice. "Da kun barshi ya karya, sai in ya so idan ya gama ya kaimu ni da Hilah da ma za ku kai abinci." "Sai dai ke da su Umnah, amma Hilah za ta yi mini aiki." "Ai ba daɗewa za mu yi ba ki barta ta je, saboda tun da muka tashi take murna za ta je ganin gidan Yayanta." Ummu ta buɗe baki xa ta yi magana Abu ya ce,"Ki barta ta je amma kar ku daɗe." "Ba zan daɗe ba saboda yau na ke son na koma Gobbe." "Ok, Allah ya kaiki lafiya." Abu ya furta wanda ta amsa da amin sannan ya juya zuwa ciki. Harararsa Ummu ta yi sai ta juya ta bi Abu. Sauwama Hilah ta ƙwala wa kira, tare da sanar da ita ta ɗauko mayafinta. Cikin murna ta juya ta shige ciki. Yana jin da Hilah za su je abincin ya fita a ransa. Ture abincin ya yi tare da faɗin,"Anty Sauwama mu je." "A,a ka gama cin abincin mana." "Karki damu na ƙoshi." Bin sa da kallon mamaki ta yi ganin bai ci abincin da yawa ba. Azerh da ta ke saukowa daga sama, tana hamnar sauran baccin da bai saketa ba, ta ƙara so da sauri. "Ni ma Anty Sauwama zan biku, amma sai yamma zan dawo." Ta furta daidai lokacin da ta ƙara so. "Ok, yi sauri ki ɗauko mayafinki sai ki same mu a mota." "To," Ta amsa tare da komawa sama da sauri. Hannu ya sanya ya karbi yarta, sai da suka je gurin mota ya miƙa mata bayan ta buɗe motar ta shiga. Lakuce mata hanci ya yi, yana dariya ganin yadda take wangale masa bakin da babu haƙora. Kafin ya tada motar, Hilah ta karɓe ta tana ta yi mata wasa tana dariya. A mota Anty Sauwama ce a gaba, sai ita da su Umnah suna baya. Tana riƙe da ƴar Sauwama tana mata wasa. Sai satan kallonta yake yi ganin yadda take ɗaga yarinyar sama tana dariya. Zuciyarsa ta raya masa ina ma ace ƴarsa ce. Yana ta satan kallonta ta madubi, in aka yi rashin sa'a suka haɗa idanu sai ta sakin masa murmushi, shi kuma ya ɗaure fuska yana harararta cikin wasa. Suna isa cikin gidan, ya yi parking tare da buɗe wa Sauwama murfin mota. "Yauwa ɗana ashe kana son albarka." Ta faɗa tana fariya. Harararta ya yi domin kusan sa'oin juna ne, kuma a hannun Ummu ta tashi. "Kuma fa haka ne bai kamata na rinƙa girmama ki ba, saboda na san lokacin da kike yawo ba wando." Wani irin dundu ta sakin masa a baya har sai da ya duƙa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 21 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Kuma fa haka ne, bai kamata na rinƙa girmama ki, ba saboda na san lokacin da kike yawo ba wando." Wani irin dundu ta sakin masa a baya, har sai da ya duƙa. "Kai Anty Sauwama, wallahi tsaf zan iya rama dundun nan, saboda ba ki ji yadda na ji zafi ba." "Ashe kuwa zan ƙara maka wani, ka san dai ko lokacin da muke yara kuka nake saka ka." "Ni kuma na saki birgima ba." Dariya suka kwashe dashi suna tuna yarintarsu. Wajnah da take laɓe a windo tana kallonsa, suna wasa sai matuƙar baƙinciki ya kamata. A ranta take mamakin dariyar da yake yi. Ganin Hilah ranta ya ɓace sosai, domin har ga Allah ta tsane ta, musamman jiya da ya sanya ta ba da tarihin rayuwarsa. Sakin labulen ta yi, ta xauna a kan kujera tana gyara xaman guntun hijabinta. Da sallama suka tura ƙofar suka shigo. Turus Sauwama ta yi tana ƙare mata kallo. "Lafiya kike Wajnah? Kin ga yadda kika dawo kamar wacce ta yi ciwon shekara?" Kuka ta fashe da shi, tare da faɗawa kan jikinta. Shi kuwa tsaki ya yi, zai wuce ciki sai ya fasa yana kallon Hilah da take kallon Wajnah. "Anty Ya Huwais ba ya ƙaunata! Duk yadda na so na faranta masa, amma kulle ɗakinsa ya yi ya bar ni na kwana a falo." "Falo?" Ta faɗa da ƙarfi tana kallonsa da ya yi halin ko in kula da su yana kunna tibi. "Kai Huwais, kana da sukuni kuwa? Amarya sukutun da guda xa ka bari ta kwana a falo?" Ɗago idanunsa ya yi, ya kalle su sai kuma ya mayar gurin Hilah, da ta yi jugum tana kallon ƙasa. "Fitina ta sanya wa ranta ai na gaya mata bana son..." "Kul kar na ƙara ji ka faɗi haka musamman a gaban ƙanninka. Ke Wajnah mu shiga bangarensa." Ta ce wanda babu musu ta riga su murɗa ƙofar. Harara ya bita da shi sannan ya miƙe. Zama ya yi a kusa da Sauwama, yana sauraren Wajnah da take gaya mata ƙarya da gaskiya. "Ya gaya mini ya tsane ni ba ya ƙaunata, yana da wacce yake so. Jiya Anty na yi burin da ma mutuwa na yi, kan baƙar rana da na gani." "Kar ki ƙara faɗin haka, kuma ki kasance mai biyayya da haƙuri za ki ci ribar hakan. Kai kuma Huwais abin da ka yi sam ba ka kyauta ba.." "Laifin me na yi? Gaya mata na yi bana buƙatarta a rayuwata, kamar yadda tuntini na sanar mata, amma ta yi kunnen uwar shegum Ta shafa ma idanunta toka a dole sai ta aure ni." "Mene ne laifina don na ce ina sonka? Ko ba ka soni don soyayya ba, ai ka soni saboda dangantakar da ke tsakaninmu. Ni na sam wannan tsinannanniyar da kake so ne take sanyawa kana mini wulaƙanci, kuma wallahi idona idanunta sai na yi ajalinta in ya so ka kashe ni nima, don matuƙar ina raye babu kai ba wata ƴa mace..." "Anty kina jin abin da take cewa ko? In har za ta rinƙa zagin xaɓin raina, wallahi watarana sai dai ku zo ku ɗauki gawarta." "Eh ka kashe ni zan fi buƙatar hakan da na yadda wata ta ƙwace mini kai. Na san wacce kake so ba wata bace face kilayar karuwa, saboda in ta gari ce ai ya kamata ka nuna ta." Miƙewa ya yi cikin zafi zai ɗaura mata mari, wanda ganin hakan ya sanya Sauwama shiga tsakiyarsu. "Kuna da hankali kuwa? A washegarin aurenku kuke wannan sa'insar? Kai Huwais, biye mata za ka rinƙa yi kuna cece kuce a gidanku?" "Amma ki na jin abin da take cewa ko? Ba marinta ya kamata na yi ba farfasa mata jiki zan yi, don wallahi matuƙar ta ƙara xagin abar ƙaunata sai na zama ajalinta." "Ka kashe ni ai ba kanka farau ba namiji ya kashe matarsa, amma ba zan fasa zaginta ba." "Wawiya mara tunani! In har da zan kawo miki zaɓina wallahi sai kin raina kanki, domin ita ɗin mai tarbiya ce, na san duk abin da na yi mata ba za ta yi sa'insa da ni ba, saboda ta fiki hankali da natsuwa." "To ka nuna ta mana in har mutuniyar kirmi ce." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ni kam na yi matuƙar dana sanin zuwa gidanku, domin da na san abin da zan tarar gara na tafi ban zo." Ta furta tare da fashewa da kuka. "Ki yi haƙuri raina ne ya ɓace." Ya ce tare da zama kusa da ita yana huci. Wajnah ita ma zama ta yi tana harararsa ta gefen ido. Matuƙar haushinsa take ji, saboda da ace ya yarda ya kwana da ita da yanzu yana nan yana rawar jiki a kanta, amma saboda wulaƙanci ya toxartata a ranar daren amarcinsu. Ga shi ko da ta faɗa a group, cewa ta fara al'ada sun ƙi yadda haka kawai ya zubar mata da mutunci. "Ke Wajnah fita ina gama magana da shi xan kira ki." Ta faɗa mata haka domin ta lura ta tara su babu abin da zai ƙara sai rigima. "Kai Huwais, irin tsarin da xa ka ɗauka a zaman gidanka kenan?" "To ya kike so na yi Anty Sauwama? Kin san sam bana son raini. Tun daren jiya mara kunyar yarinyar nan take ta gaya mini maganganu marasa daɗi, kuma wallahi ba zan ɗauka ba don ƙasa-ƙasa zan yi da ita." "Ai ko ina ba ka shawara ka canza, in ba haka ba maƙota za su jiyo ku kuma sa'insa.". "Jikinta ne zai gaya mata sam ba zan ɗauki raini ba." "Amma ka san ba daidai bane ka ƙi kwana da ita ko? saboda Allah ya ɗora maka haƙƙi a kanta dole ka sauke." "Ni fa bana sonta ina da wacce nake so. Ba zan iya ɓoye miki komai ba, ba zan iya haɗa jiki da ita ba, kuma bayan haka na tsani mata masu shan kayen mata, saboda jiya abin da tasha kenan ta wahalar da kanta ta koma kamar mahaukaciya." Kasancewar babu kunya a tsakaninsu ya sanya ta kalle shi ta ce. Tun da muka mallaki hankalin kanmu kake gaya mini kana sonta, amma kaƙi sanar dani wace ce. Huwais a tunanina babu abin da xa ka iya ɓoye mini." "Ba zan iya gaya miki ita ba." "Don haka babu amfani wulaƙanta matarka kan wacce na za ka iya bayyana ta ba, in kuma aljana ta aureka sai na sanar wa Ummu ta yi maka ruƙiya." Dariya ya saki tare da kai mata duka yana faɗin,"Eh ina ga hakan ki sanar mata, amma har da wannan ƙyamushshshen mijinki xa a haɗa ayi mana ruƙiya." "Ba na son iskanci Huwais ni fa a matsayin mahaifiyarka na ke kake dukana." "Kin manta sanda na ke zane ki a makaranta kenan? Ai ƙaramar uwa abokiyar wasa." Dukan ta rama, sai kuma ta kalle shi tare da mai da hankalinta gare shi. "Don Allah ka canxa tsarin gidanka ku, xauna lafiya karka barinta raina ka." "Hmmmmh!" Ya ce tare da miƙewa ganin ta miƙe. "Bari na je na yi mata magana." "To," Ya ce sai ya miƙe, ya biyo bayanta don ya yi kiran su Hilah su shigo sashinsa. Hilah wacce tun da ta shigo suka fara sa'insa ta tsure da lamarin Wajnah. Mamakin ƙarfin halinta take gani na rashin kunyar da take yi masa. Ta san cewa yana wasa da ita, kuma duk ya fi sakin mata, amma ba ta taɓa ko da gigin masa rashin kunya ba, domin ba halinta bane, kuma shi ma ba ya ba da fuskar da za a raina sa. Tana cikin wannan tunanin, Wajnah ta buɗe ƙofar ta fito cikin ɓacin rai tana share hawaye ta yi ɗakinta. Sororo ta yi tana tunanin irin zaman doyan da za su yi, domin matuƙar ta ce raina shi za ta yi, ba za ta ji daɗi a gurinsa ba. Anty Sauwama ta tura ƙofar ta fito yana biye da ita. Bangaren Wajnah ta yi sh,i kuma ya kama hannun Umnah da Amnah yana faɗin, "Ku zo muje sashina." Miƙewa suka yi zuwa ciki. "Wow! Gaskiya gidanka ya yi matuƙar kyau Yaya." Hilah ta ce tana zama a gefensa. Azerh tana kallon falon admiringly. "Allah ko?" Ya yi mata tambayar idanunsa cikin nata. Yes Ya Huwais the house is fine." Hilah ta bashi amsa tana zama a gefen kujerar da yake. "How about mace mai irin ki tsafta da iya decorating ɗin gida take a ciki. Na san the house would be finer than this?" "Anty Wajnah ma za ta yi koƙarinta. Yar gayu ce itama." Taɓe bakinsa ya yi, yana shafa kansa tare da kallonta har ta zauna. "Hilah, akwai maganar da na ke son mu yi kan maganar mahaukacin masoyinki, amma ba anan ba ya kamata na zo makarantarku." Jikinta ya kama ɓari jin abin da ya ce." Kallon Azerh ta yi wacce sam hankalinta ba ya kansu. "Yaya..." "Ba yanzu za mu yi maganar ba. In kin samu lokaci ki kira ni." "To," Ta ce amma ba don haka taso ba. "Please Yaya tsakaninka da Anty Wajnah..." "Ke yarinya ce ba ki san komai ba don haka kar ki interfering." Kama bakinta ta yi, ba ta ƙara cewa komai ba kan lamarin, suka ci gaba da hira, amma hankalinta na can tana tunanin abin da xai gaya mata. Anty Sauwama kuwa, ɗakin Wajnah ta tura ta sameta ta yi wanka tana shafa mai. "Ashe ba ki da hankali? A haka za ki gina rayuwar auren na ki, kuna sa insa? Wallahi matuƙar ba ki canza ba zai iya illata ki, kin san shi da baƙin xuciya. Kin kwana da sanin baya sonki dole aka yi masa, amma kike gaya masa magana son ranki." "Anty to ya kike son na yi? Inda kin ga rashin mutuncin da ya yi mini, sai kin tausaya mini. Ƙiri-ƙiri ya barni cikin mawuyacin hali jiya." "Eh, ai gara ma da ya yi miki haka, saboda ki daina biyewa waɗannan sheɗanin ƙawayen na kina ɗirka wa kanki maganin matan da xai cutar dake. Kina sane da shan maganin da yawa babu alfanu kuma daga ƙarshe xaki yi nadama mara amfani. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 22 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Anty to ya kike son na yi? Inda kin ga rashin mutuncin da ya yi mini, sai kin tausaya mini. Ƙiri-ƙiri ya barni cikin mawuyaci hali jiya." "Eh, ai gara ma da ya yi miki haka, saboda ki daina biyewa waɗannan sheɗanin ƙawayen na kina ɗirka wa kanki maganin matan da xai cutar dake, saboda shan shi da yawa babu alfanu, kuma daga ƙarshe xaki yi nadama. Ina Gobbe aka kira ni, aka sanar da ni cewar tun da aka sanya ranar kike bankan maganin bature. Kin kuwa san illar da kike yi wa kanki? In maganin matan za ki sha, ga ba ƴaƴan itatuwa nan ba da kuma na gargajiya wanda baya cutarwa." Tura bakinta ta yi, ta ci gaba da kwalliya tana faɗin,"Ni na san Anty Hibba za ta gaya miki munafuka kawai." Duka ta kai mata tana faɗin,"Don ubanki ƴaƴar ki kike zagi? Ai ita tafi ki hankali, ko da yake laifin Anty Fati ne, da ta barki kike abin da kika ga dama." "Yanzu laifina duka za ki gani Anty?" "Eh mana tun da kin zubar da mutuncin kanki kike roƙonsa ya taimaka miki." "Ni ban ga abin kunya ba domin mijina ne." "Shikenan, ki ci gaba da zubar ma kanki da mutunci." Ƙara tura bakinta ta ƙara yi, ta ba ce komai ba ta ci gaba da kwalliayrta. "In ɗauki shawarar da na ba ki, sai ki canza taku ta hanyar yi masa biyayya, in kuma ƙin ƙi sai ki xauna fitsara da rashin kunya ya ƙwatar miki darajar ki. Miji dai yana da babban matsayi da kima a gurin matarsa, kuma dole sai ta ƙarƙashin ƙafarsa za ki samu ya ɗaga ki shiga aljanna. A yanzu da aure ya zama a lallaɓa auren zamani, waɗanda suka yi auren soyayya ya suka ƙare? Ballantana ke da kin san yadda aka yi aure. In zawarci kike son yi Allah ya taimaka, kin san dai namiji na da dama sosai a rayuwarsa. In yau ya rabu dake xai iya auran mata huɗu duka ƴan mata. Don haka in kunni ya ji, gangar jiki ya tsira. Miƙewa ta yi yayin da jikinta ya yi sanyi jin abin da ta ce. Sashinsa suka shiga, inda suka same Hilah da su Azerh suna ta kallon hotunan biki. Shi kuma hankalinsa na kan wayarsa, yana duba chatts ɗin da suka yi a matsayin mahaukacin masoyi, yana murmushi sai kuma ya ɗago ya kalleta ya girgiza kansa. "To ni zan wuce, don Allah ku rinƙa haƙuri kar ku ɓata zumunci." Ta ce tana kallonsu duka. "In sha Allahu Anty Sauwama, Allah ya kiyaye hanya." Ta ce mata cikin sakin fuska kamar babu abin da ya faru. "Hilah ku tashi muje." "Ki barsu mana na kai ki, zuwa anjima sai su koma." "Ƙafata kafarsu tun da ka ga Ummu ba ta so zuwan ba." "Ni ma zan biku." Cewar Wajnah tana kallonsa da tun da ta shigo bai kalle ta ba. "To ka ji Huwais ta raka ka sai ku dawo tare?" "Ina da inda za ni." Ya faɗa fuska a ɗaure tare da hanyar waje. "Ki yi haƙuri da kanshi zai kaiki kin ga duka jiya aka kawo ki, kuma mutane ma ba su gama watsewa ba, sannan ki xama mai biyyaya kin ji?" "To,"Ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa ta bisu zuwa waje. Abu da ya koma ɗakinsa wayarsa ya ɗauka ya yi kiran Ummu. Shi kansa lamarin ya rikirkita shi tare da tabbatar da zargin Ummu, wanda yake ƙoƙarin ƙawar da zargin da yake yi. Ummu ce ta shigo fuskarta a ɗaure ta zauna a gefensa. "Ni kaina na fara tunanin abin da kike zargi." "Tun tuntuni na ke gaya maka a ɗauki mataki tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada." "Amma yaron nan ba shinda hankali. Wane hauka zai sa ya rinƙa kallon ƴar'uwarsa da kallon soyayya. Tuntuni na ke ganiin haka daga gare shi, amma sai na watsar da batun." "Wataƙila dalilinsa na ban shayar da Hilah ba..." "Kan me zai ɗauki wannan a matsayin hujja har ya fara sonta? Yana gani ko Umnah ciwon mama bai bari an shayar da ita ba. A gaban idanunsa aka yi cikinta kuma aka haife ta. Yaron nan ba shi da hankali. Tun kafin ya ja mana abin kunya, ayi mata aure kawai xan sanar da Hamad ya turo ayi auren in ya so ya kama mata haya in ta gama karatun su koma Kaduna." "Hakan shi ya fi. Tuntini na ke gaya maka ka ɗauki mataki. In aka yi musu aure hankalinmu zai kwanta." "In sha Allahu, zan kira mahaifinsa na yi masa magana, amma kafin nan ya kamata mu kira shi Huwais ɗin, sai mu sanar mishi da za a sanya mata rana, in ya so sai muga yadda zai yi." "Wane hujja kake son ka tabbatar? Karka manta haukar da ya yi lokacin da Hamad ya nuna yana sonta kuma aka bashi damar ya rinƙa kiranta sau ɗaya suna gaisawa." "Duk da haka mu ƙara kwatanta sa mu gani." Bayan ya dawo da su gidan Najib ya wuce. Yana ganinsa ya kwashe da dariya suka tafa. "Ango kasha ƙamshi." Tsaki ya yi jin abin da ya ce sai ya zauna yana kallonsa. "Ina madam? Ta kawo mini abinci yunwa na ke ji." "Ikon Allah! Ango kamarka yana ɗauke da yunwa." "Hmmmh! Ba za ka gane bane. Yau korar kare Ummu ta yi mini ni da gidammu." "Dama ta haɗa maka da duka, saboda na tabbata ba yunwa ya kai ka ba." "Kamar ka sani, amma ai a banxa nama na jan kare. Saboda ita wacce na je gani tare muka koma gidana." "Hmmmmh! Iska na wahalar da mao kayan kara." Ya ce yana ƙoƙarin kunna tibi. Banza ya yi da shi daidai lokacin da Samahatu ta fito daga kicin. "Baby, kamar ango na ke gani." "Shi ne ba gizo idanunki suke miki ba. Ki taimaka masa da abinci karya mutu." "Haba! Mai amarya guda yake neman abinci. Ko da amarya na hutun girki, ai ya kamata a restourant za su yi oder. "Ki taimaka masa, ƙila kuma amaryar ce ya yi mata laifi ta yi masa horar yunwa." Harararsa ya yi, ba tare da ya ce komai shi kuma yana dariya. Abincin ta kawo masa sannan ta shiga cikin ɗakinta. "Ina fatan jiya ka bai da kai bori ya hau? Saboda yadda na ga amaryarka jiya, na san cewa ba za ta yi wasa da wannan ranar ba." Ƙaramin tsaki ya ƙara ja."Ni kuma da yake shashasha ne sai na biye mata ko? Kana ganin irin iskancin da ta fara yi mini. Kulle ƙofata na yi, domin mace mai arha ba ta birgeni." Takaicin abin da ya faɗa ya kama shi."Arha fa ka ce Huwais? In kai ba ka kai kanka ba sai ta kawo matarka ce fa." "Please, don Allah ni ban zo gidanka ba don ka dame ni da surutu. In kuma abincin ne ba ka son na ci sai ka gaya mini." "Gaskiya ce dai ba ka so, amma kuma dole a matsayina na abokinka, na tuna mala da haƙƙin da ke kanka." Ture abincin ya yi yana harararsa."Ga abincin ka nan sai ka cinye, ai na lura dama ba ka so a kawo mini ba." Ya faɗa tare da miƙewa zai fice. Dariya ya yi tare da kama hannunsa bayan ya miƙe."Ka dai ƙoshi amma ai na san ba za ka yi fushi ba, saboda ba ka wasa da abinci." Tare suka fito yana ta bashi baki kan ya yi haƙuri su zauna lafiya. Bayan ya fita daga gidan sai ya ji baya son komawa gida. Sam ba ya ƙaunar ya ganta a cikin gidan. Gidan abokinsa Isma'il ya wuce. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya kwanta. Da yake ba shi da mata. Bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi. Wajnah bayan fiyarsa, tun tana sanya ran xai dawo da wuri har ta cire. Tana kwance a falo da wayarta a hannunta cikin ɓacin rai. Baƙin da ta ke yi suka ɗan rage mata damuwar da take ciki. Sallamar su Wahida ya sa ta miƙe da sauri ta tare su. "Amarya ba kya laifi." Suka haɗa baki gurin faɗin haka. Taɓe bakinta ta yi, sannan ta shiga kicin ta kawo musu snaks da drinks Hira da ta yi daɗi daga falo suka koma cikin ɗaki suka yi ɗare-ɗare kan gado. "Wai ina angon ne? Tun da muka shigo bamu gansa ba, irin maganin da kika sha, ai kamata ya yi yanzu yana maƙale dake." Ta faɗa tana kallonta Ƙaramin tsaki ta ja sannan ta yi ƙuta ta ce,"Ya fita tun ɗazu nake jiransa amma shiru. Ni fa ina cikin damuwa, saboda gabakiɗaya hankalinsa ba shi a gareni." "To tsayawa xa ki yi kina gani ya wulaƙanta ki? Zagewa xa ki yi ki nuna masa ke wayyayace ƴar boko. Sai ka ce ba mace ba, wallahi in ni ne duk yadda zan yi ya faɗa tarkona sai na yi, saboda yadda kika shirya kanki da zarar ya ɗanɗani zumarki shi ke nan." "Ba za ku gane ba! Ya ƙi yadda ya kusanta kansa da ni. Jiya fa kulle ɗakinsa ya yi." Ta faɗa tana kallon Maryam da ta gama magana. "Yau da daddare ki ɗauki safaya na makullin ɗakinsa, kar ki shiga ki bari sai dare can bacci ya fara ɗaukarsa. Ki cire kunya mijinki ne kar ki ji shakkar yi masa komai. In kuma hakan ba ki ci nasara ba, zan siyo miki maganin tada sha'awa ki sanya nasa a cikin abinci, wanda dole shi zai kawo kansa gareki. "Ba na tunanin zai iya cin abincin da zan girka ba ku san shi bane." "Shi ke nan zana za ki yi kina kallonsa yana miki ƙwalele?" "Hmmmmmh!" Kawai ta ce musu. Ƙara zugata suka yi tare da gaya mata yadda xa ta jawo hankalinsa. Sun daɗe a gidan suna jiran ya dawo, har suka gaji suka shirya gab da magariba suka tafi. Wajnah ganin bai dawo ba ta rinƙa kirabsa amma ya ƙi ɗauka. Miƙewa ta yi bayan tafiyarsu ta shiga kicin ta ɗora abinci. Girki ta yi mai daɗi ta jera a dining sannan ta shjga wanka. Bayan ta yi wankan, ta shirya cikin wata doguwar rigar da ta matseta kuma ta yi mata kyau. Falo ta dawo ta zauna ta kunna kallo, amma hankalinta ba shi a kallon. Ganin ya ƙi ɗaukar wayarta ya santa yi masa text message. Huwais bai tashi dawowa gida ba sai gab da magariba. A wajen gidansa ya yi parking ɗin motarsa ya yi alwala ya shiga massalaci. Ko da aka idar sai ya yi zamansa yana karanta qur'ani har aka yi isha. Bayan an idar da sallar ya tuƙa motarsa zuwa ciki. Tana jin dirin motarsa ta saki ajiyar zuciya tare da leƙa shi ta windo. Tana kallonsa ya kashe motar ya fito daga motar ya nufo cikin gida. Sakin labulen ta yi, tana gyara zaman rigarta sai kuma ta ruga da sauri ta ɗauko turarenta ta fesa. Ta fito daga ɗakin daidai da ya buɗe ƙofar. "Sannu da dawowa baby." Ta furta cikin salon jan hankali tana kallonsa. Ba tare da ya amsa ba ya ƙarasa shigowa ciki. "Ya Huwai.." Ta daina kiran sunan ganin ya shige ɗakinsa. Fara diddira ƙafafunta ta y,i cikin takaici tana zaginsa a zuciya. Haƙuri ta bawa kanta ta jera abincin a faranti ta ɗauka ta nufi ɗakinsa. Da sallama ta shiga cikin falon tana riƙe da farantin abincin. Ganin ba shi a falo ya sanya ta ije abincin ta nufi ɗakinsa. Murɗa ƙofar ta yi da sallama."Ya Huwais, ga abinci na kawo maka." Ta faɗi tana kallon ƙirjinsa da ya cire rigarsa zai shiga wanka.... "Ke! Ba na hana ki shigo mini ɗaki ba? Ma za fita." "Don Allah ka tausaya mini ni fa matarka ce." Ta furta cikin muryar kuka sai kuma hawaye suka wanke mata fuska. Ƙaramin tsaki ya ja ya wuce bayi ba tare da ya ce mata komai ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 23 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Murɗa ƙofar ta yi da sallama."Ya Huwais, ga abinci na kawo maka." Ta faɗi tana kallon ƙirjinsa da ya cire rigarsa zai shiga wanka.... "Ke! Ba na hana ki shigo mini ɗaki ba? Ma za fita." "Don Allah ka tausaya mini ni fa matarka ce." Ta furta cikin muryar kuka sai kuma hawaye suka wanke mata fuska. Ƙaramin tsaki ya ja ya wuce bayi ba tare da ya ce mata komai ba, wanda gabin haka ya sanya ta zauna a gefen gadonsa. Bayan ya fito kai tsaye ya wuce wandrop ɗinsa, ya ɗauki kaya ya wuce bayi ya sanya sannan ya fito zuwa falo Ranta ya ƙara ɓaci, amma sai ta danne ta ɗauki abincin zuwa falon. Yana zaune da remote a hannunsa ta ije abincin ta xauna gefen shi. "Ya Huwais," Ransa ya ɓace ya juyo yana kallonta."Sau nawa xan gaya miki bana buƙatarki cikin rayuwata?" Duƙawa ta yi a ƙasa tare da ɗaga hannunta cikin muryar kuka ta ce"Don Allah ka tausaya mini ka soni, wallahi ina matuƙar sonka, kuma zan yinduk abin da zai faranta ranka." Shiru ya yi ba tare da ya tanka mata ba. Ganin haka ya sanya ta miƙe tare da ɗaukar filet ta zuba masa abinci. Duƙawa ƙasa ta yi ta miƙa masa. "Mijina ga abinci." Juyowa ya yi yana kallonta. A rayuwarsa baya ƙaunar wulaƙanta mutum, musamman mace da suke da daraja, wannan dalilin ya gargaɗeta da kar ta yarda ta shigo rayuwarsa. Miƙewa ya yi zuwa ɗakinsa saboda zuciyarsa ta fara karyewa. Ɗaki ya koma ya sanya ɗan makulli ya kwanta cikin damuwa. "Ya zan yi na manta da ke Hilah na karɓi Wajnah a matsayin matata?" Ya yi wa kansa tambayar yana sosa fuskarsa. Damuwa ta ƙara kama shi, yana jin yadda take buga ƙofar cikin muryar kuka, tana kiran sunansa. Ganin ba zai buɗe ba, ya sanya ta shiga ɗakinta ta ɗauko ɗan makullin za ta sanya, amma sai ta ji ya ƙi shiga saboda akwai ɗan makulli a ciki. Tana ta buga ƙofar da kiran sunasa amma ya ƙi buɗewa. Da ta gaji a gurin ta xauna har zuwa ɗayan dare, sannan ta tashi ta koma ɗakinta. Kuka ta fashe da shi a zuciyarta tana jin ba za ta iya jure wulaƙanci ba.Kwanciya ta yi cikin damuwa, ta kasa bacci har zuwa ƙarfe huɗu. Huwais kuwa yana jin tana buga ƙofa amma ya yi biris da ita. Jin ta daina bugawa ya miƙe ya shiga cikin bayi ya ɗauro alwala. Sallah ya fara yi yana roƙon Allah ya kawo masa ɗauki a rayuwarsa. A karo na biyu ya sake janyo wayarsa tare da yanke shawarar tura mata da texts na ban haƙuri. "Ina son ki Hilah ba zan iya haƙuri da ke ba." Ya ce tare da rubuta mata tsaƙo kamar haka. "Haƙuri da rarrashi ba za su ta ɓa wanke laifin da na aikata ba. A shirye na ke da na karɓi duk wani hukuncin da za ki yi mini tauraruwar zuciyata. Ki gafarce ni rashin haɗuwarmu, maihaifiyata ce ba ta da lafiya aka kira ni wanda ya sanya dole na je. Amma in sha Allahu zan bayyana kaina gareki. Tura tsaƙon ya yi zuciyarsa na zillo. Ya san cewa abin da yake yi bai kyauta ba, amma ya xai yi kece kaɗai wacce ya ke son ya yi rayuwa da ita. Ya furta hakan cikin damuwa. Hilah na kwance da waya a hannunta ta na yin assigment tsaƙon ya shigo. Da sauri ta miƙe tana zare ido. Jikinta na kyarma ta fara karantawa. Ta karanta ya fi sau uku sannan ta ije wayar cikin damuwa. Tura tsaƙon na sa sai ta rasa gane farinciki za ta yi ko baƙinciki. Wataƙila in ta ƙara aminta da shi ya yi mata abin da ya fi haka. "Wannan mutumin ya raina mini wayo." Ta furta cikin ɓacin rai tana ƙara karanta tsaƙon sau ba adadi. Tsaki ta yi, sai ta yi wurgi da wayar, amma kuma hankalinta na kan wayar. Tura tsaƙon da ya yi, sai ta kasa samun natsuwa a zuciyarta. Sonsa ne da take ƙoƙarin ɓoyewa ya fara bijiro mata. Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska. Tana cikin wannan halin kiransa ya shigo. Jikinta ya ɗauki rawa tana kallon wayar har ta tsinke, amma ta kasa ɗauka. Wayar na tsinkewa ta ɗauki wayar. layin Huwais ta kira. Ganin kiran wayar ya sanya shi sakin murmushi domin dama ya xargi za ta kira. Ƙin ɗaukar wayar ya yi har sai da ta kira sau biyu. Tana gabda tsinkewa ya ɗauka. Cikin muryar bacci ta fara magana."Hello Hilah," Jin yanayin muryarsa ya sanya ta yi dana sanin kiransa. Ta manta shaf yanzu yana da mata. "Ya Huwais, mahaukacin masoyi ya kira ni." "Kin manta ina da mata shi ne xa ki kira ni da tsakar dare?" "Yi haƙuri halin da na ke ciki ya sanya na manta." Ta faɗa tare da kashe wayar ba tare da ta jira ya ce komai ba. Dariya ya yi ganin ta datse kiran. Layinta ya kira, amma har ta katse bata ɗauka ba. Ƙara kira ya yi. Tana gabda katsewa ta ɗauka. "Am sorry Yaya, ka kwanta za mu yi maganar gobe." "Ok, ki ɗauki wayar ki ji mai zaice." "Ba zan ɗauka ba zuciyata cike take da ɓacin rai na wulaƙancin da ya yi mini. Sai da safe." Ta ce tare da kashe wayar. Murmushi ya saki yana kallon wayar. Zan shigo makarantarku mu yi magana. Ya tura mata da tsaƙon ya kashe wayarsa ya kwanta. Tunani fal a zuciyarsa. Bacci ne mai ƙarfi ya kwashe shi. Hilah kuwa kasa bacci ta yi. Gani take kamar mahaukacin masoyi ya mai da zuciyarta abin wasa. "Anya da gaske yake xai aure ni?" Ta yi wa kanta tambayar haka. Kiran sallar farko ya miƙe ya shiga bayi. Wanka ya yi sannan ya canza kayansa ya wuce masallaci. Bayan ya yi sallah, ya zauna a masallacin yana karatun qur'ani har gari ya yi sha, sannan ya miƙe ya shigo ciki. Falo ya sanya karatun qur'ani ya wuce ɗakinsa. Kan gadon ya hau ya ja bargo. Bai farka ba sai ƙarfe tara, ya yi wanka ya shirya. Falo ya fito daidai lokacin da Wajnah ta ƙara shigowa. "Ina kwana Ya Huwais?" Ba tare da ya amsa ba ya nufi hanyar fita yana gyara hularsa. "Don Allah ka tsaya ka ci abinc..." Maganar ta tsaya ganin ya fice.Maigadi ya wangale masa get ya fice. "Ka gama guje-gujenka dole ka shiga hannu tun da aka ɗaura ai an yi mai wuyar. Ba ka da matar da ta wuce ni. In sha Allahu ni ce uwar ƴaƴanka." Ta furta tare da sakin labule ta shiga kicin. Karyawa ta yi sannan ta ɗan gyara gidan ta yi kwanciyarta. Wayarta ta ɗauka ta hau online suka fara hira a group ɗinsu. Nan kowacce ta fara kawo rayuwar gidanta da abin da mijinta ya yi mata suna dariya suna shewa da tsinewa rijalu. Maigadi yana buɗe masa get ya shiga cikin gidan. Ganin Abu da jaka a hannunsa da alama gurin aiki xa shi ya sanya shi fitowa da sauri. "Ina kwana Abu." Ya ce yana kallon Ummu da ta fito daga ciki hannunta riƙe da ƙaramar wayar Abu da alama ya manta da wayar ne ta ɗauko masa. "Ina kwana Ummu?" "Lafiya lau, ya kwanan Wajnah?" Ta yi masa tambayar cikin sakin fuska. "Tana lafiya." Ya ce yana kallonta. "Abu, fita aiki za ka yi?" "Eh, amma da ma ina son magana da kai. Tun da ka zo mu koma ciki mu yi maganar." Gabansa ne ya faɗi a tunaninsa ƙararsa Ummu ta kai na zaman gidansa. "Ok," Ya ce tare da bin bayansu ganin sun juya za su shiga ciki. Abu ya yi gyaran murya ya ce,"Game da ƴar'uwarka Hilah." Gabansa ne ya ƙara faɗi tun bai san mai ya faru da ita ba. "Tun da ka yi aure, sai muke ganin ita ma ya kamata mu ɗaura mata aure da Hamad, in ya so sai ya kama mata gida a Kaduna har ta ƙarasa karatu..! Zubbur ya miƙe yana xare idanu cikin tashin hankali. "Aure Hilah?" Ya furta cikin ɗaga murya wanda ya tabbatar nusu da zarginsu. Ummu ne ta kalli Abu, sannan ta kalle shi da yake share zufa da ke keto masa. Jijiyoyinsa suka miƙe yana jin wani tashin hankali na ziyartarsa. "Abu, kan me xa a yi mata aure bayan ba ta kammala karatun ba?" "Saboda gaka ya kamata. Kuma ya kamata mu tausayawa yaron nan, tuntuni yake jiran ta kammala ba tare da ƙorafi ba. Yanzu semester biyu ya rage, ai karatu ya zo ƙarshe." "Gaskiya bai kamata ayi mata aure ba, saboda za dakusar da karatunta. Kuma Hilah ɗin ba ta da ra'ayin haɗa aure da karatu. Don Allah ku yi haƙuri har ta kammala karatunta." Ya furta kamar xai yi kuka. "Ita ta gaya maka haka? Ka san irin son da Hilah ke yi wa Hamad. Ko bakinta za ka ara ka ci mata albasa?" "Hilah ba ta son Hamad, ni na sani sam ba ta ƙaunarsa." "Ko ba ta sonsa, dole ta aure shi mun sanar maka ne a matsayinka na ɗan'uwanta." Tashin hankali ya ninku a fuskarsa idanunsa suka firfito ji yake kamar zai yi hauka. "Kai ina!Hilah tawa ce ba za ya taɓa auren wani ba ni ba." Ya ce aransa yana firfita da hannunsa. Abu ne ya miƙe ganin yadda ya riƙice ya kasa cewa komai. "Ni zan wuce ofis kar na yi latti. In sha Allahu yau zan yi wa mahaifin yaron magana." "Abu, ka bari ka ji bakinta.." "Babu wani bakinta da za mu ji ai ta san da maganar aurensu." Ummu ta faɗa. Miƙewa ya yi, yana jin kamar ƙasa ba zata iya ɗaukarsa ba. Siraren hawayen da suƙe ƙoƙarin saukommasa yake son mayarwa. Gfen hannunsa ya sanya ya share hawayen Ba tare da ya ce musu komai ba ya miƙe xai fita, saboda in har ya yi magana za su fahimci halin da yake ciki. Binsa da kallo suka yi ganin yadda yake tangaɗi kamar zai daɗi. "Na gaya maka wallahi wannan mahaukacin yaron sonta yake yi. Gara mu yi mata auren shi ne kawai sanun kwanciyar hankalinmu.". "Ummh! Biri ya yi kama da mutum." Abu ya ce cikin tsananin mamakin halin da ya shiga. Huwais na fitowa ya shiga cikin motarsa. Kifa kansa ya yi kan sitiyarin motar. Wasu irin zafafen hawaye suka sauka a ƙuncinsa. Ba tare da ya share ba ya kunna motar ganin maigadi ya buɗe masa ƙofa. Sai da ya yi nisa da gidan sannan ya faka motar ya tsaya. Hawaye ke bin ƙuncinsa yana jin tashin hankalin na ƙara ninkuwa.. "Ba zan taɓa barin ki auri wani ba matuƙar ina raye. " Ya furta tare da duka sitiyarin motar. "In har ba zan aure ki ba mai ya sa ba ke son ki?" Ya yi wa kansa tambayar cikin tashin hankali. "No, Hilah tawa ce an halicce ta don ni. Matuƙar ban aure ta ba sai na kashe duk wanda ya aureta." Ya furta hakan tare da figan motarsa aguje. Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida. Hon yake yi babu ƙauƙautawa. Da sauri maigadi ya buɗe masa get yan kallonsa. Gaisuwar da ya yi masa bai amsa ba ya buɗe motar ya shiga cikin gidan. Ko motar bai kulle ba ya shiga gidan. Wajnah da ke zaune tana kallo da saurinta miƙe. "Ya Huwais, lafiya?" Ta yi masa tambayar ba tare da ya kula ba ya wuce ciki. kai tsaye bayi ya shiga ya kunna shower. Ga mamakinsa sai ya ji wasu irin zafafen hawaye suna sauka daga ƙuncinsa. Ya daɗe yana sakarwa kansa ruwa, har sai da ya ji ɗan dama-dama a zuciyarsa sannan ya fito ya sanya kaya. Key ɗin motarsa ya ɗauka ya fito falo. Wajnah da ke tsaye hankalinta a tashi tana jiran ya fito ta sha gabansa. "Matsa ki ba ni guri!" Ya furta cikin kakkausar murya. Da sauri ta kalle shi jin muryar da ya yi amfani da ita. Tsoro ya bayyana a fuskarta, amma sai ta dake. "Don Allah ka sanar da ni abin da ke faruwa. Ni fa matarka ce dole na damu da lamarinka." Jin abin da ya ce ya sanya yaja tsaki tare da tureta xai wuce. Gefen rigarsa ta ja cikin ɗaga murya ta ce,"Dole sai ka gaya mini abin da ke damunka, ai ni matarka ce ina da haƙƙi .." Maganar ta maƙale mata, sakamakon marin da ta ji ya wanke ta da shi, wanda ya sanya ta sake shi da sauri tare da dafe ƙuncinta. "Marina fa ka yi?" Ta furta cikin muryar kuka. "Abin da yafi mari xan yi miki matuƙar kika ƙara yunƙurin dakatar da ni." Ya furta cikin ɓacin rai xai fice. Wani irin ƙara ta saki saki ta ruga da gudu cikin ɗakinta. Tsaki ya ja yana kallonta."Wawiya kawai!" Ya furta sannan ya murɗa ƙofa ya fice. A hanya tafe yake yana tsaƙa da warwara. Gani yake sam iyayensa ba su yi masa adalci ba, amma kuma in ya tuna lamarin da yake shirin ibo ma kasa sai ya ji damuwa sosai. Shi kansa ya sani ihu yake bayan hari. Ko da ace ba a yi wa Hilah aure ba, ba shi da damar da xai bayyana yana sonta. Wayarsa ya ɗauka da ya sanya a caji. Numbar Hilah ya nemo sannan ya danna kira. Hilah da ta fito daga lectured kenan suna tafiya da Affrin za su je Cafateria. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 '*RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 24 Jin wayarta na ringing, ya sanya ta buɗe jakarta ta ɗauko. Ganin Huwais ne, sai ta tsaya tare da danna gurin kiran, ta kanga ta a kunni. "Hello Yayana." Ta furta da muryarta da ya bayyana, tsantsar gajiyar da take ciki. Jin muryarta ya sanya shi rintse idanunsa, yana jin wani abu yana yawo a kwanyarsa. "Hilaaah, kina ina?" Ya yi mata tambayar tare da jan sunanta. "Ina school mun gama lectured zan nemi abinci." "Ok, ki yi ma za ki ci abincin zan jira ki a bakin get ina kan hanyar makarantarku." Daɗi ta ji a ranta sosai, dama tuntuni take son ya sanar mata da ranar da za su huɗu. "Ok, sai ka zo amma Yaya lafiya kake?" "Lafiya lau." Ya ce mata tare da kashe wayar yana sauke numfashi. Bin wayar ta yi da idanu, tamkar za ta ga abin da ke damunsa a wayar. "Ya Huwais, ne ya kira ni yana kan hanyar zuwa makarantarmu. Mu yi sauri na mu ci abincin kafin yazo." "Yayanki yana matuƙar ji dake. Ina ma ace ni ce na samu wannan gatar. Na ɗauka zai canza in ya yi aure, amma abin gaba ya ci." Dariya ta yi jin abin da ta ce."Wannan dalilin ya sa na ke son shi sosai." Suna gama cin abincin kenan, ya kira wayarta tare da sanar mata da ya iso. "Tashi mu je kar na barshi jira." "Ki dai je in har kuna tare mantawa muke da kowa." "To shikenan, tun da ba za ki je ba." Ta ce tana dariya. A hankali take takunta cikin natsuwa kanta a ƙasa. Yana tsaye ya hangonta. Gyara tsayuwarsa ya yi, tare da zuba mata idanu, tamkar zai cinyeta har ta ƙaraso tana masa murmushi. "Yayana," Ta ce tana kallonsa. Yanayin fuskarta ya canza hannunsa ta kamo. "Lafiya Ya Huwais?" Ta yi masa tambayar cikin damuwa. "Mu samu guri za mu yi magana." Ya ce mata tare sakin hannunta. Babu musu ta shiga gaban motar ya ja suka fara tafiya. Sun yi nisa sosai, babu wanda ya yi magana, sai ita da take satan kallonshi cikin damuwa. Ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi wanda ya sanya ta kalle shi. "Yayana, mai ke faruwa? Na damu da halin da kake ciki." Bai ce mata komai ba, sai da ya yi parking sannan ya fito. Ganin haka ya sanya ta buɗe ƙofar ta fito. Gurin wasu fararen kujeru suka samu suka zauna. Kimanin ƴan sakanni sun zauna babu mai cewa komai. "Hilah Abu ya gaya mini xai sanar da iyayen Hamad su kawo kuɗin aurenki." Ras! Ta ji gabanta ya yi matuƙar faɗi. Miƙewa ta yi, yayin da hawaye ya wanke mata fuska. Ganin razanar da ta yi ya sanya shi jin sanyi. Hannunta ya kamo ya xaunar da ita. "Kina son Hamad?" Ya yi mata tambayar yana kallon ƙwayar idanunta. Kallon da yake mata ya sa ta ji wani irin nauyi. Domin kalar idanun da ya canza ba ta taɓa hango hakan a ƙwayar idanunsa ba. "Bana sonsa, amma kuma matuƙar xan samu saɓani da Ummu kan auren ba ni da xaɓi." Ta faɗi haka cikin rawar murya. Ransa ya ɓace jin abin da ta ce."Kenan za ki sadaukar da kanki saboda farincikin Ummu? Karki manta rayuwar aure ana samun natsuwa ne, in har mutum ya auri xaɓin rayuwarsa. Ki duba halin da nake ciki tun da aka ɗaura mini aure ban samu kwanciyar hankali ba." "Ya zan yi Ya Huwais? Ka san halin Ummu, ko soyayyarsa ita ta sanya na amince har na yarda da zan aure shi." "Shikenan kin haƙura da mahaukacin masoyinki?" Ɗago idanunta ta yi da sauri jin sunan da ya kira. "Zan iya haƙura da shi tun da bai damu da ni ba. Zan yi wa Ummu biyayya na san cewa ba zan taɓa taɓewa. Mahaukacin masoyi ya cuce ni ya yaudare ni. Auren da zan yi shine kawai zan baƙanta masa rai. Ya san cewa ban rasa masoya ba. Hamad yana da nagarta kum...." "Ya ishe ni! Ban zo nan don ki gaya mini nagartar sa ba." Ya katseta cikin fushi yana huci. Shiru ta yi tana kallonsa tare da share hawaye. Miƙewa ya yi, ya fara taku sai kuma ya tsaya ya juya mata baya. "Na san wane ne mahaukacin masoy..." "What!" Ta furta cikin tsananin razana tana kallonsa. Yadda ta ruɗe ya firgita shi. Kama hannunta ya yi ganin ta fara kuka. "Please, ki zauna mu yi magana na fahimta." Zama ta yi hawayen na bin ƙuncinta."Haba Yaya, da kai xa a haɗa baki a ruguza farincikina. Dama ka san mahaukacin masoyi ya rinƙa wasa da rayuwata? Haba Yaya! Sam ban yi taɓa tunanin zaka yi mini haka ba why?" Ta ƙarashe maganar tana gurzar kuka. Huwais ya yi shiru cikin tashin hankali yana kallonta. Irin tashin hankalin da ta nuna ya sanya shi ƙara shiga cikin damuwa sosai. A koda yaushe gani yake tana ƙara son mahaukacin masoyi. Shin idan ta ji shine za ta so shi kamar haka?" Tambayar ya sanya cikin shi murɗawa. "Mai ya sa aka haɗa baki aka cutar da ni?" Ta ƙara cewa ganin ya yi shiru. "Waye shi? Waye wannan mugun azzalimi wanda ya yaudare ni? Na zaƙu da na san ko waye na ɗauki hukunci mai zafi a kansa.". Miyau ya haɗiye da ƙyar, yana jin yadda maƙoshinsa ya bushe, babu ɗigon miyau. "Yaya Huwais ka gaya mini wane ne?" Ta ce tana girgiza shi. "Zan gaya miki, amma ki natsu mu yi magana ta fahimta." Ya ce bayan ya mayar da ita inda ta xauna. Zama ta yi tana share hawayen da yake xubo mata. "Tabbas Hilah na san shi. Abokina ne kuma yana matuƙar sonki. Saboda kyawunki da matsalar da yake hango ya kasa bayyana miki soyayyarsa. Saboda yana da hankali kuma ya dace dake shi ya sa na ƙyale shi, ya fito miki a matsayin mahuakacin masoyi don ya samu soyayyarki ya sanya ki bijire auren Hamad." "Amma mai ya sa ya kasa bayyana kansa a gareni? Mai ya sa ya yi mini alƙawarin xamu haɗu ya ƙi zuwa?" "Kamar yadda ya gaya miki, mahaifiyarsa babu lafiya za a yi mata aiki a ranar kuma zai sanya hannu." "Saboda me ya kasa bayyana mini domin zan fahimce shi. Wannan ba hujja bace mai ƙarfi. In har zan iya yafe masa saboda kai ne, da kai ne don na san ba za ka taɓa yadda a haɗa baki a cuce ni ba." Rintse idanunsa ya yi yana jin babu daɗi jin abin da ta ce. "Ki yafe mini Hilah ba ni da zaɓin da ya wuce na samu soyayyarki ta haka." "Na san duk abokananka don Allah ka gaya mini wanne ne daga ciki." "Ba ki san shi ba Hilah, kamar sau ɗaya ya ganki a taron da kuka yi na musabaƙa tun daga ranar ya nuna yana sonki. Na ba shi shawarar ya fito miki ta wannan tsigar, saboda na san yana bayyana kansa za a dakatar da shi." "Don Allah ka nuna mini hoton shi." Ta ce cikin zaƙuwa. "Ba zai yiwu ba saboda ya roƙe ni kar na nuna miki." Ɓata ranta ta yi jin abin da ya ce." To ya kamanninsa yake?" "Shin idan kika samu miji mai irin surata da halina ya za ki ji?" "Zan yi farinciki saboda samun miji kamarka, sai macen da Allah ya yi mata tagomashi. Shi yasa kullum na ke ganin Anty Wajnah a mace mafi sa'a da ta same ka." Jin abin da ta faɗa kansa ya fasu. Ji ya yi kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukarsa ba. "To ki ayyana surarsa da haliinsa kamar ni, amma kuma ni na fi shi sonki." Ya ce cikin murmushi. Dariya ta yi cikin farinciki."Aiko na samu mijin aure in har kamanka yake." "Ba ki da kunya Hilah a gabana kike wannan murnar ko?" Rufe fuskarta ta yi tana dariya."Amma abokin nan na ka ya cutar da xuciyata." 'Ki yi haƙuri xai bayyana kansa ba da jimawa ba. Yanzu wane shawara kika yanke game da auren Hamad." "Zan fito fili na gaya wa su Ummu akwai wanda na ke so." Gabansa ne ya faɗi tuna in har aka ce ta kawo shi ya xai yi. "Yauwa ƙanwata, karki bari Ummu su yi miki auren dole kamar yadda aka yi mini." Yadda ya yi maganar ya ba ta dariya."Ya Huwais, ka amshi Anty Wajnah a matsayin mata ku zauna lafiya. In Allah ya sa wacce kake so matarka ne sai ka aureta." "Ba za ki gane yadda zuciya take ƙuntata ba, yayin da mutum ke zama da abin da ba ka so." "Na fahimta, amma ka yi mata adalci ko don zumuncin da ke tsakaninku." Shiru kawai ya yi, bai ce mata komai ba sai ya nisa ya ce,"Ki rinƙa ɗaukar kiransa, kuma ku koma kamar da in sha Allah zai bayyana kansa a lokacin da ya kamata." "To Yaya." Ta faɗa tare da miƙewa ta maƙala jakarta, ganin shi ma ya ɗauki wayarsa ya miƙe. Tafiya suka fara yi har suka isa mota suna hira. Daga nan makaranta ya ije ta hankalinsa ya ɗan kwanta, ganin yadda take matuƙar ƙaunarsa, ya san ba za ta yadda ayi mata auren dole ba. Wajnah kuwa bayan ta shiga cikin ɗaki tana kuka, wayarta ta ɗauka tare da danna kiran numbar Mommy, ta zayyane mata ƙarya har da gaskiya. Ranta ne ya ɓaci sosai ta shiga rarrashinta. "Ki kwantar da hankalinki yanzu zan kira mahaifiyarshi, don ba xan lamunta ya rinƙa dukanki ba, daga yin aure ai ba jaka na auro masa ba." Bayan ta kashe wayar cikin fushi ta danna layin Ummu ta zayyane mata. Matuƙar mamakin marin da ya yi mta ya kamata. "Ki yi haƙuri kin barni da shi xai gane ba shi da wayo." Tana gama waya da mommy ta kashe wayar tare da neman layinsa. A lokacin da ta kira, yana kan hanyar dawowa da ga makarantar su Hila. Ganin kiran gabansa ya faɗi amma ya daure ya ɗauka. "Huwais, ashe ba ka da hankali? Amaryar da ko sati ba ta rufa a gidanka ba za ka dake ta." Ransa ya ɓaci jin abin da ta ce."Umm.." "Ma za ka zo gida ina nemanka." Ta furta cikin ɓacin rai tare da daƙile wayar. Wayar ya bi da kallo cikin ɓacin rai, yana tunanin abin da zai yi mata don ba zai lamunta, ta rinƙa haɗa shi da Ummu ba. Juya motar ya yi zuwa gida. A falo ya same ta, zaune ta haɗe girar sama da ƙasa tun da ta ji shigowar motarsa. Ganin yadda ta sha kunu, ta amsa sallamar ba tare da ta kalle shi ba, ya sanya gabansa ya faɗi. Zama ya yi cikin sanyi jiki tare da gyaran murya ya ce,"Ummu ga..." "Ashe ba ka da hankali? Kan me za ka daki Wajnah?" Ta katse shi cikin ɓacin rai tana faɗin haka. "Ummu, k..." "Ba ka da hujjar da za ka kare kanka da shi. Kuma ka ji na rantse maka wannan ya xama na farko na ƙarshe da za ka kai hannunka jikinta. Sannan a matsayina na mahaifiyarka, ina umurtarka da ka karɓe ta a matsayin mata ka sauke duk haƙƙinda ke kanka, matuƙar ka ƙi yin hakan za ka fuskanci fushi mai tsanani. Kan auren nan matuƙar ba ka cire banzar tunanin da kake yi ba, kun zauna lafiya zan iya maka mummunar lafazi, domin ba zan bari a cikin dangina ana yamaɗiɗi da ni, cewar ban isa da ɗan cikina da na haifa ba" Kansa ya ɗago da sauri cikin tashin hankali jin hukuncin da ta yanke. "Amma Ummu sam ba a yi mini adalci ba na gaya miki bana..." "Ai bakin alƙalami ya bushe, tun da aka ɗaura aurenku, ba ka da wani xaɓi da ya wuce ka zauna da ita." Miƙewa ya yi, cikin damuwa xai fice sai ya ji ta kira sunanshi. "Huwais, wannan ya xama magana ta ƙarshe kan aurenka. Kar na ji kuma kar ta ƙara kawo mini ƙararka." Ƙarashe ficewa ya yi cikin ɓacin rai zuciyarsa na tafasa. A hanya tafe yake, yana tunanin abin da Hilah ta gaya masa. Tabbas Allah ya ba shi damar da xai iya auren mata har huɗu, amma ba ya jin zai iya karɓar Wajnah a matsayin mata. Kalaman da Ummu ta gaya masa, suka ƙara rikita ƙwaƙwalwarsa har ya gaza tunanin mafita. A lokacin da ya isa gida. Ƙarasa shiga cikin dakin yana huci tamkar mesa."Da ma kin aure ni ne don ki haɗa ni da iyayena?" Ya yi mata tambayar cikin fushi yana tsaye a kanta. Raurau ta yi da idanunta tana kallonsa."Don Allah kar ka yi mini mummunar fahimta, wallahi ina sonka Ya Huwais." "Ki ji daɗi kin haɗa ni da mahaifiyata. Ki sani ko zan zauna da ke bisa umurnin mahaifiyata ce, amma bana sonki kuma babu soyayyarki a zuciyata." Miƙewa ta yi, cikin sanyin jiki tana jin ɗacin kalmar bana sonki, da yake gaya mata. "In har na ci albarkacin Ummu, zan yi farinciki na sam watarana za ka so ni." "Kin yaudari kanki domin ba zan taɓa ƙaunarki ba." Ya ce tare da wucewa fuu zuwa ɗakinsa. Jaɓar ta xauna kan kujera, tana jin babu daɗi yadda yake gaya mata ya tsaneta. Hawayen da ke zuba a ƙuncinta, ta share tare da miƙewa zuwa ɗakinta. Wayarta ta fara ƙara alamun ana kira. Ganin kirar Ummu ce ya sanya ta ɗauka da sauri ta shige cikin ɗakinta. Bayan ta ɗauki wayar ta yi sallama ta gaishe ta. "Ki na jina Wajnah? Dole sai kin yi haƙuri tun da kin san dole aka yi masa. Ki daina rashin kunyar da kike masa sannan ki zama mai biyayya, cikin sauƙi za ki mallake shi a hannunki. Ita wacce yake son hauka yake yi, saboda ko mutuwa zau yi don sonta ba zai aureta ba." Mamaki ya kamata, domin ba ta taɓa sanin Ummu ta san wacce yake so ba. Ajiyar zuciya ta yi jin abin da ta ce take hankalinta ya kwanta. "Ba ya cin abincina kulle ɗakinsa yake yi da na shiga yake koro ni." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. "Kar ki damu ki yi masa girkin, kuma ki shirya kinje ɗakinsa, na yi masa mummunar lafazi matuƙar ya ƙi kula ki." Zuciyarta fes ta rinƙa murna tana gode wa Ummu. "Duk abin da xai yi miki karki kula shi ki yi masa biyayya kin ji?" "To Ummu," Ta ce tare da kashe wayar tana tsallen murna. Miƙewa ta yi cikin farinciki, ta shiga kicin ɗin, tana kallon ƙaton kicin da aka cika shinda kaya. Tunanin abin da za ta girka masa ta yi. Buɗe frij ta yi ta ɗauko naman kaza ta kunna famfo don ta saki. Cikin farinciki take yi masa tuwon shinkafa da miyar taushe. Bayan ta kammala ta koma ta dafa masa farfesun kan rago. Ɗaki ta koma ta yi wanka ta sanya kaya masu kyau. A lokacin da ta fito falo shi kuma ya fito don ya je sallar isha'i. Kallonsa ta yi cikin shauƙin ƙauna tana wani tafiya tana yauƙi. Ko inda take bai kalla ba ya wuce zuwa massalaci. Ganin haka ita ta miƙe cikin gaggawa ta yi nata sallar sannan ta fito tana jiran dawowarsa. Bayan an idar da sallar zama ya yi, yana tunanin umurnin da Ummu ta yi masa, domin bai san ta yadda xai ɗauke ta a matsayin matarsa ba. Mace ɗaya kawai yake so kuma yake burin ya yi rayuwar aure da ita. Ita ce wacce yake ganin duk ji da kansa da yake yi, zai xama bawa matuƙar xai mallaki zuciyarta, amma kuma ba zai iya bijirewa umurnin Ummu ba. Miƙewa ya yi, ya kulle masallacin sannan ya shigo cikin gidan. Zuciyarsa na yi masa nasihar ya bi umurnin mahaifiyarsa. Jin alamun buɗe ƙofa, ya sa ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurin ƙofar don ta buɗe masa, dama ta kulle ƙofar saboda ta san lokacin da xai shigo. Buɗe ƙofar ta yi da murmushi a fuskarta."Barka da dawowa farincikin rayuwata." Ta faɗa cikin wani irin murya yayin da ta matsa kusa dashi kamar xa ta rungume shi. Karo na farko ya yi mata kallon tsanaki, domin tun lokacin da ta fara nuna maitarta a fili ya ji babu wacce ya tsana fiye da ita, kuma tun daga lokacin bai ƙara yi mata kallon da xai gane yadda take ba. Ganin ya kalleta ya sanya ta ƙara matsowa kamar xa ta shiga jikinsa. Ya buɗe baki da nufin ya magana, amma sai ya ji ya gaza furta kalami. Wucewa ciki ya yi, ba tare da ya ce mata komai ba, wanda ganin haka ya sa ta bishi zuwa ɗakinsa. "Ya Huwais, na kawo maka abincin ka ɗaki?" Ta yi masa tambayar tana ƙarasowa inda yake xaune. Ƙara ɓata fuska ya yi tare da kauda kai. Kusa da shi ta isa ta rage tsawo."Don Allah Ya Huwais ka ji abincin nan, horas da kanka da yunwa babu abin da zai jawo maka sai cuta." "Bana buƙata." Ya furta a gajarce yana kauda kansa. Shiru ta yi take ranta ya ɓace, ganin duk wahalar da ta sha ya tashi a banxa. Idanunta suka ciko amma sai ta jure ta fita daga cikin ɗalkin "Haƙiƙa duk macen da take son wanda ba ya ƙaunarta, tana cikin jarrabawa." Ta furta hakan tare da warware ɗaurin ɗankwalinta cikin takaici. Har ta ɗauki waya xa ta kira Ummu, sai ta fasa ta wanke fuskarta, da ruwan hawaye ya gama jiƙata ta gyara kwalliyarta. Numbar Wahida ta lalubo tare da danna gurin kira,"Hello," Sai kuma ta fashe da kuka." Cikin takaici Saboda ta zabga tsaki daga cikin wayar ta ce,"Na gaya miki zuba mishi maganin yaci shi kawo zai karkato da hankalinsa gareki. Ki cire tsoro da tunanin komai. Mijinki ne kuma in ba ta haka kika yi masa ba, wannan mutumin ba zai lalle ki ba." "Ba ya sona ya tsane ni. Ban san ya zan yi ba." Ta ƙarshe maganar cikin kuka tana wurgi da filo. "Na gaya miki abin da za ki yi kenan, wanda zai jawo hankalin sa gareki, amma kika tsaya kallon ruwa har kwaɗo zai yi miki ƙafa. Maganin yana da ƙarfi, don sai ya raina kan sa." "Ok, na gode." Ta furta tare da ije wayarta kan dressig mirror.Kayan bacci ta sanya ta koma ɗakinsa. Bayan fitarta ya bi ta da kallo yana son ganin inda ta gaza, amma ya san Wajnah tana da duk abin da ɗa namiji yake so a jikin mace. Shi kawai babu soyayyarta a cikin zuciyarsa. Yana wannan tunanin ta murɗa ɗakin sai ta ji a kulle. Fara bugawa ta yi tana kiran sunansa. Har ya yi banxa da ita sai ya tuna umurnin Ummu. Da sauri ya miƙe tare da buɗe ɗakin ya tsaya a bakin ƙofar ta yadda ba za ta iya shigowa ba. "Lafiya?" Ya yi mata tambayar fuska a ɗaure. "Ummu, ce ta ce na shigo na kwanta in kaƙi buɗe ƙofar na kira ta." "Ke zan yi mugun ɓata miki rai, matuƙar za ki rinƙa haɗa ni da iyayena." Ya faɗa cikin ɗaga murya. "Ni fa bani na kirata ba ita ta kira ni yanxu, kuma ta ce za ta ƙara kira." Matsawa ya yi ta wuce yana faɗin,"Ga ɗakin nan sai ki cinye." TO MASU KARATU.. AN CE LAIFIN DAƊI ƘAREWA.LITTAFIN RANAR WANKA... BOOK ONE YA ƘARE SAI MU HAƊU A BOOK TWO. Mai ke faruwa ko na ce mai ya ke shirin faruwa?🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄 Wajnah na yin nasarar sace zuciyarsa har ya maida ita cikakkiyar mace? Ya kuma manta da HIlah a rayuwarsa? Mai ya sa Huwais ya ke jin kamar Hilah za ta iya zama matarsa? Wai ku tsaya masu karatu. Hilah dai ƴar Ummu ce ta uku, saboda me Huwais zai rinƙa tunanin ba yar uwarsa bace? In har ta gane shi ne mahaukacin masoyi ya za ta yi, kuma wane mataki za ta ɗauka? Shin in Wajnah ta gane Hilah ce wacce ya ke so kuma yake wulaƙanta ta saboda ita. Wane mataki za ta ɗauka? Soyayyar da suke yi wa junansu zai ɗaure bayan ya bayyano sirrin da zai canza rayuwarta? Duk da cewa ranar wanka, ba a ɓoyen cibi. To ita ɗin wace ce kuma su waye iyayenta? Sannan mai ya faru ta shigo cikin rayuwarsu? Shin zai yi nasarar mallakarta a matsayin mata, kuma ya rayuwar aurebsu xai kasance? Hilah za ta zauna da shi a matsayin miji, ko kuma a matsayin ƴaƴanta za ta ɗauke shi? Huwais zai ɗauke idanunsa a kanta ya zauna da ita ba tare da ya amshi sadakinsa ba? Ko.kuma girma ne zai fadi ya yi rayuwar aure da ita? Ina Wajnah mai kishin mijinta da sha maganin mata? Za ta iya barin mata Huwais ko kuma za ta zauna a fafata zaman kishinda ita? Sannan burinta zai cika na fatan ya mallaka mata kansa su zamo abu ɗaya? Ya rayuwarta xai kasance in har ta cigaba da shan maganin mata? Shin za ta daina sanar da ƙawayenta rayuwar aurensu ko kuma za ta ci gaba? To ku sha kuruminku domin duk amsar tambayarku. Yana cikin littafin book two wanda yake paid kan Naira 500 kacal, in kuma aka gama ya zama complete 600 wanda Jamsy ƴar baiwar mai son faranta muku ba ta bar amsar tambayoyinku ko ɗaya ba, domin ta wasa ƙwaƙwalwarta ta bayyana muku har abi n da ba kubsani ba. labarin cike yake da rikita-rikitar soyayya da tausayi haɗe da jimami da shakwakiya. Ma za ku garzayo ku biya don ku karanta. Kar ku bari a baku labari, domin ya tsari kuma akwai soyayya mai tsuma zuciya. Ƙayataccen littafin naira 500 ne kacal, amma in aka gama rubuta shi 600 ma za ku garzayo ku biya don ya ɗebe muku kewa. Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun 8144072423 Jamila lawal opay Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423 FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423 Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp. Shin kin karanta littafin "SAKACINA KO HALIN MAZA" ko kuma "KURA DA FATAR AKUYA"? In har ba ki karanta ba ma za garzayo ki siya kan naira 600 kacal dob ki more karantunki. Labarine masu daɗi da darasi a cikin su, wanda shararriyar marubuciyar na . Jamila Lawal Zango Jamsy